By
HAYATU BABA ZUBAIRU
        (admin
   Arewa hausa novels
       Novels villa
     Duniyan novels
   Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
          And
Cool novel, makeup and cooking)

      WHATSAPP NO:
    +2347039625239

☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠


Page 1-2
     By
Gentle Lady💃🏽


Dasunan Allah mai rahma maijinkai"" dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki maikowa mai komai ina kara godiya ga Allah subhanahu wata ala "" Wanda yabani ikon fara wannan labarin Allah yasa jama a zasu amfana da fadakar wardake cikinsa

Hakika komai kaga yasamu bawa mukaddarine daga Allah Amman kuma akwai sanadi wannan labarin kirkirarren labarine nayishi domin tsokaci dawadansu abubuwa dasuke faruwa acikin al umma""

Wacce wannan labarin yaxo daidai darayuwarta saita tuba tadaina domin ganin makomar Wanda yake kwatankwacin irin halintaa Allah yasa mudace Ameen

Wannan labarin narubutashine ra ayin kaina danhaka Wanda yaji zai iyah karantawa banhanashiba saidai kuma akiyaye karwani ya sarrafamun shitawata hanyaa idan kunne yaji gangar jiki tatsirah


*BISMILLAH*


***********************
 Gabadaya unguwar cinkushe take da manyan motoci sai kaikawo sukeyi alamu sun nuna wani mihimnin buki akeyi na wani kasurgumin maikudii Dan la akari da yawan motocin dasuketa karakaina hakazalika masu tsadar gaske kaima kasan ba bikin"" fukara"u bane

Bakin kofar gidan tacika makill da maroka dakuma masu kidaa"" ahakan nasamu tattakawa zuwa kofar gidan duk da dakyar nasamu nakai wajen asheni banga jama a ba dankuwa cikin gidan tamkar anabikin nadin sarautane""

Sai rarraba ido nakeyi domin samun hanyar shiga wannan katafaren gidan ginane namusamman maihawa hudu anyimasa fentiii da farin fentiii maishegen kyau da shekiii wannan gidan kusan yafi kowanne gida kyau dakuma tsari gabadaya ya haskaka unguwar anayiwa gidan nan lakabida farin gidaa!! Tofa Allah yasa abunda yakecikinsafarine🠽򢠊
Kutsa kaina nayi Cikin gidan kofar shigama abar adubace""nagama zagayena nikam banga alamar  matar gidan ba"" dankuwa irin wannan gidan yakamata ace matar gidan ta banbantaa dayanbukiii ajikinta kadai za agane""

Nayi zugum inabinsu dakallo nace tomezaihana insaurari firarsu watakil nagane matar  gidan  aciki🤔 wannna shawarar nayarda da itah nafarabi lungu dasako ina saurare abun takaici abun bakinciki duk inda nawulga zancensu kusan dayane kishiyaaa!!!!

Waimenene illar kishiyane??? Kumata kunada abun mamaki idan mijinku ya aureku yace zaikara aure kuyita fitinaa toyakenan idankuma keza a aura??? Itakuma matarsa taceme??? Yakamata zuwa yanxu mata sugane Susan kalar kishinda zasuyi kuyi koyi da matan Manzon Allah (S A W) suma sunada kishi saidai nasu sunayinsane abisa tsari kowacce tanarigengen wajen kyautata masa domin tasamu matsayi fiye Dana dayar

Amman wasufa saboda tsabar bala.i da masifa daga ranarda yasoma maganar kara aure tofa ya ballowa kansa likii zatadaina wanka tabar dafamasa abincii wata hatta gadonta baxata barshi yakwantaba dazaran yace yimun kaza tace bazanyiba kajecen wajen amaryarka taimaka tabar yayanta acikin wahala waifa a irintata wautar waita naso tazubawa mijin haushine shikuwa dayafita iyawa saiyabuge iskanta yayima dadai duniya kamarma baisan da zamantaba sai idan tayi masifar  tagababuci kuma biki yanata karatowa sai afara yangyare gyare waidaga bayakenan sadaka da bajawara bayan kinzubarda girmanki kimarki darajarki

Bari nabaku wani sirri wlh idan mijinki zaiyi aure kika kwantarda hankalinki zakici arziki komai kikeso zaiyimaki domin yataushi zuciyarki kuma zai rika tambayarki menene kikeso haka zalika komai zaiyiwa amaryar zairika neman sha wararki"" sabanin idan kikasoma fitina zaiyibanza dake duk wuyartadai kece akasa bazaki hanashi auren ba

Saikiyi ba1 ba 2. Darajarki dayake gani kinbata bazaisake yarda dakeba kuma koda amaryar tashigo gidan akatada fitina kodakuwa kece mai gaskiya bazai yardaba zaice aiyaga take takenki tunkamin yayi aure kiketa fitina tosaidai kiyi abunda zakiyi matadai matar sace matsayinku daya awajesa uwargida kinga mutuncinki yaragu

Idan kikacigaba da fitina karshenta yasakeki yazauna da amaryarsa wagari yawaya???? Hakan yana faruwa sosai acikin al.umma

Iyayena mata iyayen gobe mukula mukiyaye kishii ba haukabane!!!

Nafara biyar lungu dasako cen saman hawa na uku nayi katari da matar gidan "" sosai nafirgita daganinta sam bazaka taba cewa matar gidan bace"" irin matan nan ne wadan da mazajensu suke dakudi amman idan kagansu bazaka siyesu kwandalaba duk kayanda suke siyamasu basa sakawa idan kagansu mai aikinsuma tafisu daraja amman fa idan zasuje gidan bukii kokuwa zasuje unguwa zakadauka basason taka kasa saboda tsabar tsafta""

Abokananta dasuke gefenta dayar tace wai lubabatu mezaihana kitashi kiyi wanka gidan nanfa yanbiki sunfara cikashi kosokike araina class nakii
           Wacce take gefenta nadama tace hajiya larai kibarta hakan mana"" dame zataji dakishiyarda akai mata kokuma da kwachakwaimar kwalliya?? Kinsan Allah danice kotaron biki bazanyiba

Wata tace habadai hajiya larai aiyanzu andaina wannan yayin idan za akawomaka kishiya kahana kanka jindadin rayuwa yanxu kissa akeyi kikwantarda kai tamkar mumina ni wlh mijina yayi aure saina gasawa amaryar gyada ahannunta

Suka kwashe da dariya haryanzu uwargidan uwar iko batayi  maganaba"""
       Larai tace hajiya sadiya  kenan ashe wacce tsautsayi yasaka tashigo gonarki zatafi gwammacewa kwana akabarintaa" suka sake shekewa da dariya"" amman banda itah""

Haba kukuwa banda abinku ai kishiya abokiyar  zamace menene abunkishin??? Abunda akasaba bakifa badainawa za ayiba nisam banajin kodar akan auren nan
Hajia lubabatu ce mai wannan maganar""

Hajia larai tarike haba lallai hajiya kodayake wannan bashine nafarkoba bakyada jinkomai nikam wlh bazan sakewa mijina fuskaba dahar zaiyi sha awar karawani auren"" tirkashi ranarkuwa dahakan tafaru wlh sai yayi zaton aturu aka kwantoni dan zankoma masa  mahaukaciyar karfi dayajii

Wannan karon harda hajiya lubabatu wajen dariya wata matashiyar budurwace tabude kofarda sallama""" sukabita dakallo babu  wanda ya amsa tafara kallon mutanen dasuke cikin dakin daga bisani tadauke kanta kamar taga kashi
       Hajiya lubabatu ce ta daka mata tsawa ke wacce irin shashashar yarinyace labila???? Zakishigo wamutane daki haka bakiganin bakine dani??? Baki tatabe nagansu mana mom kuma ainayi sallama "" takai karshen maganar tanasake wurgamasu mugun kallo ta murguda bakiii
           Kinyi sallama gidanwa mu kuramene dabamujiba"" ta kwabe fuska to tayazakuji bayan kuna tazuba shegen surutu wanda bazai kareku  dakomai ba""
        Ido lubabatu tazaro sukam su hajia larai inda sabo yaci acesun saba dahalin  labeela"" tace labila waiyaushe kikazama tsagera nifa mahaifiyarkice kinamun magana tarashin da a

Tasake mere baki"" tacee  malamai niku gyara zanduba jakata "" tayi maganar tana rike kunkumi afusace hajia lubabatu tasauko daniyar dukanta su hajiya sadiya sukariiketa haba hajia baidace kidaketaba ai labila karamar yarinyace kuruciya ce take damunta

Kotakansu batabiba tahauduba  jakarta"" tadauko sannan takallesu daibayan daya tace naji kuruciya tana damuna amman karani saudubu daku sakarkarun  mataa mstw tsaki taja tafita tabar dakin

        Gabadaya  dakin yayi tsit bakajin motsin komai saina saukewar ajiyar zuciyarasu" labila karamar yarinya amman kullum tasamesu agidan saita soka masu miyagun maganganu

Dasauri tasauko kasan tana rike dajakarta"" sai kutsawa takeyi cikin taron mutane ranta yayi matukar kuna bataso mahaifiyarta tana hulda da wadan nan matan saboda dukansu babu Allah azuciyarsu amman mahaifiyarta batada wasu shakikan abokai bayansu
          Wayarta tajawo takamo wata nomber tadanna kirah babu jimawa akadauka"" tayi sallama ya amsa dad dan Allah katuro driver yamiyar dani bazan iyah zama anandinba!!

Ajiyar zuciya yasaukar yace saboda menene labila bazakijirah akawo antyn takiba cikin sauri tagirgiza kai no dady"" dagabaya zandawo inganta yanzu akwai muhimmancin tafiyar tawa gobe munada harda a islamiyya""  amman inshaa Allah idan komai ya daidaita zandawo naga mom din kafin lokacin tazama yargida da murmushi afuskarta tafurta hakan shima murmushi  yayi badamuwa labelaa yanzun bari nakirashi yazo amman nayi kewarki yata gashi zaki tafii amman bamudan zantaba"'

Tashafo gefen fuskarta bakomai dady zansake zuwa saimuyi firanko?? Yace yauwa yata kikasance cikin amincin Allah

Tasaki sassanyan murmushi tace kaima haka"" inasonka babana  yace nima inasonkii tace bye yace ok bye taciro wayar akunnenta takuramata ido Allah sarki babana"" Allah. Yasa kayi dacen mata Allah yasa daka wannan auren  kasamu kwanciyar hankali wasu sirarun hawayene suka sauko mata tasa gefen mayafinta tashare sake matsawa tayi saboda cinkoson mutane ga shi ankusa la asar"" batawani jimaba driver yazo bayan sungaisa tashige motar suka kama hanyar kano

Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Page 3-4
     By
Gentle lady💃🏽





Sai bayan fitar" labila sannan hajiya lubabatu tasamu tashiga wanka ganin duk jikin kawayen nata yayi sanyi da maganganun da labilar tafadamasu yarinya tamkar banice nahaifeta ba sam bataganin mutuncina
Tayi kwabaa

Batajima dashiga wankaba tafito tasheka kwalliya tamkar wacce zataje gasar sarauniyar kyau" ta chanchade cikin wani tsadadden bugaggen less dan ubansu akalla kudinsa zasukai dubu dari da hamsin""
              Tasaka sarkar diamond hannunta yasha awarwaraye na gwal"" nantake tasoma shekii tashi sukayi dukansu suka fara zaga gidan duk indasuka wurga sai anjinjinawa kwalliyarta nikuwa araina nace wato yangulma kikewa kwalliya illai kuwa kwalliya tabiya kudin sabulu dankuwa tayankesu kowacce takoma gidansu tana Allahummar zukuni""

Wani abun saigidan manya bakuga yanda akasoma fitowa dakayan ciye ciyeba bikin gidan masu kudi ko ba agayyacekaba kaje kodakuwa ba asakarmaka fuskaba kakwaso gara""
           Dankuwa yanda akacika gidan kaima dagani kasan wadansu abincin kawaine yakaisu "" babujimawa akafara fitoda dakwalen kajiii dakuma babba kakkun raguna masu maiko"" anyimasu gashi Na musamman sunsha shafen barkono saizubarda mai sukeyi saikuma lemuna namanyan mutane wanidinma bantaba ganin irinshiba

Kowa kaganshi rabonsa yake yaga"" masu DJ ne sukafara sakin kidaa bayan suncika tunbinsu""" hajiya lubabatu ce tafara takarawa cikin murna kaikace ba itah za ayiwa kishiyaba babuwanda bata burgeba  wasuma sunata rokon Allah yabasu uwargida maihalinta Sam batadauki kishi abakin komaiba

Kai ranarfa tasha rawa  nikam nace jikinki zaiyi ciwo kuwa""duk wannan bidirinda akeyi banga ma mallakin gidanba""

Yinin ranarfa sunchashe son ransu DJ yakwashi kudii wadanda akaita masu likidasu kasan biki na kusoshin yan duniya wadanda sukarika

Shigar hajiya lubabu goma kowacce shigarkuma saiwanda yaganie komai kuma kalar kayan" anzuba hotona"" magrib tana kawojiki kowa yafara haramar barin gidan"" daki suka sake kowama"" suna nan kowadai saifadin albarkacin bakinsa yakeyi

Karfe takwas mukafarajin dirar motocin amaryaa"" sunata rangada gudaa"" akashigo da itah"" zuwa bangaren uwargida sukashiga da sallama ta amsa dasakin fuska marabanku lale marhabin kuzazzauna mana""
       Daga kawayenta harmasu kawo Amarya bakisake suke kallonta sambatada  bakinciki taja hannun amaryar tace zo Kanwata kizauna nan"" cikin jinkunya"" tazauna kanta yanakasa ayanda akebata labarin matarsa babu ruwanta ashema tafiyanda akabata labari""
       Take tamike tafara jidomasu kayan makulashe dakuma kayan sha"" da gasassun naman kajie"" bayan sungaisa sukace ga amanar kanwarkinan munkawo maki
      Duk dakowa yana shaidunki bakida wata illah Dan Allah kiyi hakuri dahalin kuruciyarta  dan kingirmeta nesa bakusaba idan tayi badaidaiba kiyimata fada""
     Tayi murmushi aibakomai abokin zama dadine dashi tadafa kafadarta"" Kanwata nandin kidauka gidane komai yashigemaki duhu karkiji shakkar komai kisanardani nikuma zanwayarmaki dakai

Allah yasa nandin gidan zamankine Allah kuma yasa ace karada akayi Allah yabamu zaman lafiya"" gabadaya aka amsa da amin""
     Mikewa sukayi tace yabazaku taba koda ruwabane ai anzama daya nibazanji dadi idankuka kicin komaiba nima idan nazowajenku tareda Kanwata aibazakuji dadiba idan nakishan koda ruwane

Sukace tayi hakuri akoshe suke ganin tamatsa yasaka sukadan kurba lemun"" tareda itah akafita zuwa bangaren Amarya """  harkuryar dakin tazaunarda itah yanganin daki Duk suncika dakin"" sunfara tabe tabe"" hajiya lubu tasoma miyarmata"" dakayanda akasoma turewa tadade taredasu sannan tayimasu sallama takoma wajen kawayenta indasuma sunsoma haramar komawa gidan mazajensu"""

Tahadamasu shatara Na arziki tarakasu kowacce takama hanyar gidanta"" bangarenta takoma"" hawa na uku shine Nata nabiyu na Amarya maigidan shine hawana karshe""

Idanzakije bangarensa Mahayar Na ura zakishiga kidanna zuwa sama bàsàikin wahalda kanki wajen taka matakalaba

Tanashiga bangarenta tarage kayan jikinta tahaye saman makeken gadonta tasoma sharar barciii hardà minsharii hankalinta kwancee saijuyi takeyi sànyin Ac yanashigarta tako ina"""


Gabadaya gidan anwatse kowayatafi yana yabon lubabatu da kyawawan halayenta"" karfe shadaya motarsa tashigo gidan"" bayan driver yayi fkng yayi saurin fitowa yabudemàsaa kofaa

Yafito"" yacewa driver n ina" habu driver dubamun   kagani nayita kiran"" wayarsa batashiga labila kuma bata dauki wayarba

Yadan gurfana dasaurii yayi hanyar dakinsu yanakwala masa kirah haryasoma barcii yaji anakiransa firgigit yamike yafito dasaurii taresuka  koma  wajen alhajin""





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA*☠



Chapter 5
       By
Gentle Lady💃🏽



Dukawa yayi yace yallabai andawo lafiya??
Qalau habu tundazu nake neman layinka Amman inajinsa akashe""
    Ah yallabai wayarne batada chaji wlh" haba habu yanzu duk wadatacciyar wutar nan da ake sakowa kuma ga gen Amman asamu wayarka babu chaji??? Duk kacinye chajin wajen shiriritaccen cheating dakukeyi kaidai koyaushe  maganata dakai akan rashin wayane
    Yasosa kansa yallabai ayi hakuri kuskurene baza asakeba"" murmushi yayi yace hakan kake fada dai kullum"" ya labilar kun isah gidan lafiya ko????

Kai yagyada ah yallabai kafin magrib nihar najuyo tabada sakoma akawo maka"" yana murmushi yace to daukomun""
Dasauri yakoma cikin dakin yadauko key yabude motarda yaje da itah wata katuwar kulace dakuma leda"" yakarba ""
            Sukai masa saida safe yawuce cikin gidan kaitsaye hawa nahudu yadosa nikuwa ina biye dashi huhuhu ashe banga komaiba saboda wannan yafi sauran kyau nesa bakusaba

Komai gashinan gwanin sha awa" tundaga flowers da kujerun dakin da center Capet"  green color  ne mai haske" sai makeken TV n bango" saikuma babban agogon bango""
Sai fream da ke dauke da ayatul kursiyyu dayan amanarrasulu gudan lakadja akum"" sai wadansu masu addu.o

Sosai tsarin yaburgeni"" kularda take hannunsa ya aje yakarasa kuryar dakin"" kayan jikinsa yarage yashiga yawatsa ruwa yafito jallabiya yazura yafeshe jikinsa da turare yafito kular yabuda danbun kaxane"" sai babbar ledar gasassun kajine gashin gida harda diminsu kansa yadafe shisam yama manta bairikowa Amarya kazaba shikullum cikin mantawa yake"" yayi murmushi labilaa kenan"" mikewa yayi yabude fridge yadauko madarar yoghurt     yasauko zuwa bangaren hajia lubabatu  da sallama yashiga tayi daidai sai kwasar barcinta takeyi""  ledar hannunsa ya aje yakarasa saman gadon yakura mata ido murmushi yayi yashafo fuskarta shikawai yasan abunda yace azuciyarsa ahankali yasoma tashinta ta ture hannunsa cikin alamun mai barcii kuma yanamata dadi yace  maman laby kitashi kokinyi sallah??? Cikin barci tace ah nayifa alhaji harkadawo???

Yace gashi kinyi barci bazaki rakani gun kanwar takiba murmushi tayi wlh nagaji alhaji baxan iyah zuwa ko inaba saida safe tasake juya kwanciya
Murmushi yasakeyi

Yaja bargo yarufemata jikinta  yafito zuwa bangaren Amarya Yanashiga  daddadan kamshi yadaki hancinsa yalumshe ido sannan yabude ahankali yafurta Alhamdulillahi ala ni imati"
Yataka harcikin dakinta tana zaune tsakiyar gado yadine sanye ajikinta "" dashikuma akarufe mata kanta dashi""

Ahankali yataka yazauna saman gadon yayimata sallama ta amsa ahankali""  hannunsa yasaka yadage mayafinda akaimata rufadashi

 Murmushi tasakarmasa takanne ido daya"" wani dadi yaji yamamayeshi yana tunanin zaihuta sosai ajikin habiba dantunkafin ya aureta yagano macece mai yawan sha awa shine dalilinda yasaka hartarabu damijinta Wanda tafara aura""

Mayafin yasaukar yace Amarya bakya laifi"" koda kinkashe Dan masu gida"   tayimasa fari"" da ido""   yasaki fara a tashi muyi sallah mugodewa Allah""  mikewa" tayi daga kan gadon tashiga tayi alwala tafito tasamu yashimpida abar sallah yanagaba yajasu sallah bayan sun idar yagabatar masu da kajin da labiba ta aikomasa dasu kitchen dinta yaje yadauko plate yajuye masu naman yakalleta yace bisimillah cikin jinkunya tace nakoshi

Yace wasa kikeyi nasan bakici komaiba hidimar buki nima kaina yunwa nakeji kodai nabaki abakine?? Yayi maganar yana jawota tanarke ajikinsa tashagwabe murya nakoshi my love

Yace nifa banyardaba kokadanne saikinci  ahakan yadibo yanufo bakinta cikin kissa take karba harsaida yatabbatar takoshi shima yaci yasha madarar""
 sannan sukafara wasanni

Ganin kasan bazaimasuba sukakoma saman gado yatashi zaikashe masu wutar dakin koda yadawo yasameta sai munsharii takeyi abunyabashi mamaki matuka dagazuwa kashe wuta wane irin barcine zaidaukeka kuma ayanda takeyin barcin kamar tadade dafarashi"" baikawo komai aransaba duk da amatseyake yauyaso more Daren amarcinsa da Habiba jiki asanyaye yaja bargo yarufemata jikinta yamiyarda kayansa"" yakwanta gefenta ido yakuràmatà

Kamar maison tunawani Abu"" munshariii takeyi tamkar gurnanin zakii yayita juyi Sam barci yaki daukansa"" haryasoma jantsaki   karshedai mikewa yayi yakullemata kofar dakin yakoma bangarensa

Aisha✍🏼
☠  *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 6
     By
Gentle Lady💃🏽


Dashigarsa dakinsa bai tsaya ko inaba sai akan makeken gadonsa "" yazube tamkar gajiyayyen mutum wanda yayi tafiyar yini guda cur batareda ya hadiye kwayar  hatsi acikin saba" gabadaya damuwa ta mamaye zuciyarsa

Take yafara sake sake acikin ransa" wai me wannan takenufine??? Kowacce matar dazan aurah salonta daban yake itakuma wannan natasalon yaudarar abarci zata fake?? Yayi kwaba bakomai komai daren dadewa aizankaigaci inhar tasan wata aibatasan wataba lallai inkere nayawo zabo nayawo babu shakka saisun hade

Inma makircine irin nasu namata zanganota idan yanzu tayi makircin barci saina gani idan darana zatayi hakan"" yayi tsaki maganar banzama  yau Allah kadai yasan bururrukan dasuke cikin raina awannan Daren Amman komai yarushe nakoma tamkar wandama baitaba aureba "" ina amfanin dukiyata??? Kansa yadafe Wanda yaji yanayimasa barazana tamkar zairabe gida biyu saigashi yana kuka da idanuwansa hawaye wadansu sunabin wadansu""

Waini saiyaushe zansamu kwanciyar hankali??? Wacce irin rayuwace nakeyi?? Duk irin tarin dukiyarda nakeda itah nakasa samun abunda nakeso saboda duka matan bakin halinsu dayane kowacce zan aura sainaga salon cin amanarta yafigaban kwatance

      Yashafe dakiku arba in yanata kuka shikadai batareda mai rarrashinshiba  daga bisani mararsa tasoma ciwo wanda wannan ciwon kusan yazame masa tamkar ibada  yadade agun yana mirgina tareda addua sannu ahankali ciwon yasoma sauka tamkar yanda ruwa suke sauko wadaga sararin samaniya ""  yana nan agun bai motsaba saida sanyin alfijir yasoma bugomasa yatashi""alokacin yaji jikinsa yakoma daidai tamkar wani Abu baisameshiba

Kaitsaye bandakinsa yashiga  yawatsa ruwa sannan yadauro alwala yashinfida  abar sallah yafara sallah""
Saida akayi kiran asalatu sannan yasauko da charbinsa  ahannu yanufi bangaren lubabatu hawana uku kamar yanda yabarta da dadaren hakan yasameta saidai wannan karon zaninda yakejekinta tuni yakoma gefe tamkarma tunfarko batareda  shidin takwantaba"""

Bayan under dayake saye ajikinta da tinbir zatakasance gashi tatara taiba sai kirjinta dasuke manya manya kowanne daya yayi girman kofin roba

Gefe da gefe nacikinta amurde yake alamar jindadi dakuma Hutu sunkwanta akan lafiyayyar fatar jikinta tamkar irin dika dikan matan yarbawa hakan take

Yaduka ahankali yadauki zanen yarufamata ajikinta daga bisani yasoma tashinsa ahankali"" yadade yana tashinsa sannan tabude idonta"" yace tashi kiyi sallah"" murmushi tayi tasake juya kwanciya tace hutunake "" batareda yace komaiba yawuce zuwa bangaren habiba cikin yanmintuna kalilan Na urar tasadashi da bangarenta  dakin yashiga tanakwance takama filo tarungume kamar wacce tasamu jariri""  haryanzu lullube take ciikin zanen gadon"" yataka kusa da itah yasoma bubbugarta ahankali yanakiraan sunanta"" tasoma juyi cikin barcinta maidadi tasoma bude idonta  ahankali tadorasu akan mijinta tasakarmasa  murmushi maikamada tusar jaki"" tabude bakinta daniyar magana tuni yakawarka fuskarsa sakamakon wani mugun doyi dayafito acikin bakinta tamkar gawar mushe ya tunkari kofofin hancinsa" cikin sauri yajuya yayi taku biyu tareda toshe hanchin nasa sakamakon yankayan cikinsa dayaji suna hautsinawa  cikin sauri yace  sauri nake kitashi kiyi sallah"" baijirah Jin amsarda zatabashiba yayi waje haryacin tuntube

Sam habiba batakawo komai arantaba saitadauki hakan amatsayin yanasaurine karyarasa jam i saboda falalarda kecikin sallar asubah acikin jam"i


Shiru tayi nawani lokacin tana tunanin daren jiya"" Sam tamanta abunda yafaru tayi iya kokarinta kozata iya  tuna abunda yafaru bayan hawansu akan gado damijinta Amman takasa tunawa datamatsà datunani saitaji kanta yasoma ciwo take tayi saurin fatattakar tunanin daga zuciyarta tamike tadaura zani takarasa bayin domintayi wanka

Shikuwa dafitarsa yasoma saurii haryana waigen dakinta haryanzu dayan hannunsa yanakan hancinsa yadadeshi kyam  yace aransa waiii wannan wane irin warine naji tamkar rubabben mushe"" wannan warin daidai yake da aturmuya kanka acikin shadda wacce taikwana shida arufe itakuwa wannan dawanne kalar mangoge hakorah take amfani dashi kodai rashin wanke bakine??? Idankuwà hakane akwai matsala dankuwa bazan iyah kusan tartaba muddin inajin wannan doyin

Dawannan tunanin yasauka kasa yasoma tashin ma aikatan gidan domin wucewa masallaci dama al adarsa kenan bayazuwa masallaci sallar asuba batareda yatada dukan ma aikatan gidanbà wannan dabiar tashi tanamatukàr burge yaran gidan asanadin hakan drivernsa  Sunday yakarbi addinin  musulunci Wanda yanzu akekiransa da Abdullahi

Sosai halin maigidàn nasu yana burgesu basu kadaiba hatta makotansa Dan mutunne Wanda yasan hakkin makotàka sautari idansukàje masallaci inyaga ankusà tàda sallah wani makocinsa baishigoba dakansà yake zuwa ya bugamasa duk da shidinfa maikudine Amman Sam dukiiyarsà batasakashi yazama maigirman kaiba




Aisha✍🏼
☠  *HATSABIBIN BOKA!!*☠


Chapter 7
    By
Gentle Lady💃🏽



Sautari talakawan anguwar suna matukar mamakinsa saidai shi Sam baidauki wai girmankai yadorawa kansaba girmankai Wanda mafiyawan masu kudi suka sakawa ransu"  dazaran sunyi kudi zasufara daukar kai Sam sumanta da lokacinda suke fakiransu  gabadaya  abokanansu nabaya saidai idansuka wulgo cikin mota sudagamasu hannu wanikoma dagahannu bazaiyiba yama manta dayataba zama wata majalisa"" dazaran yaga Wanda yasani talaka saiya saki gilashin motarsa yakauda kai gefe tamkarma baiga mutumen ba

Wannan girman Kaine kuma duk Wanda yakedashi yasani yakama hanyar halakarsane saboda abunda kesauran halakarda bawa girman Kaine dagahakan zakafara hassada kanadaukar kanka wata tsiya bakaso wani yayi kudii kamarka kasani ko shaidan abunda yasakashi hassada girman Kaine haryakaishi ga fadawa halaka
.              Allah yaciremana girman kai dakuma hassada acikin rayuwar mu Ameen"" saida yajirasu dukansu sukayi alwala sannan yawuce suma suka Mara masa baya "" zuwa masallacin unguwar

Babu nisa Dan gabangidansa kadan akagina masallacin Ku San babu kwadagar kowa wajen ginin shine yadauki nauyin komai masallacinda aka kawatashi ko acikin manyan unguwanni saikayi dakyar kafin kasamu mai kyansa"" Dan asalin wajen wata tsohuwar ginace akazagaye korufin kwano babu akarosheta akagina wannan masallacin  Wanda fankoki da ac kamar suyi magana idan kashiga kamar karka fito sannan gatarin littafai nan idan kanason karantawa"" bayan an idarda sallah"" yakoma gefe yasoma karatu inda sauran ma aikatan wajen sukasoma karatun zuwa adanjima sukafita zuwa wajen aikinsu""

Dai daikun jama ar wajen suka soma fita ahankali haske yanagama wartsakewa shima yatashi yakarasa wajen liman sukai musabaha sannan yafita zuwa gidansa tun a hanya suketa gaisawa da  makotansa haryakai gidan dashigarsa yasamu ma aikatan gidan sungama aiki shikawai suke jirah bayan sungaisa yawuce cikin gida sukuma sukawuce

Dayake yauranar lahadine babu aiki duk da yakeshidin dankasuwane  yanada campani masu yawan gaske Amman yanayin tsarinsa tamkar aikin gomnaty dashi da ma aikatansa
 Basazuwa aiki asabar da lahadi acewarsa takasance ranar Hutu gakowa saboda idan sukaje takwas nasafe basa tashi sai karfe takwas darabi

Ranar lahadi da asabar taxama ranar Hutu kowanne magidanci yafuskanci iyalansa yaji damuwarsu""  idankuma marar aurene yaje wajen budurwarsa idankuma yanada wata lalurah yayi koyayi ziyara"" musamman jumua dan ranar juma.a karfe hudu aketashi

Shikuma ranar asabar inhar yashiga gidansa bayafitowa bayan zuwa masallaci yanatare da matansa yakasance lokacinsune komai sukeso kosunada damuwa saisufadamasa duk da kafinsu kwanta kowanne darema suna ganinsa

Kaitsaye bangarensa yanufa yasakeyin wanka  yakwanta kasancewar barcin jiya Yana nan a idonsa take barci yayi awon gaba dashi
         
Hajiya lubabatu ce tashigo dakin cikin takun kasaita balaifi yautayi kwalliya dass da itah fuskarta saifitarda sihirtaccen murmushi takeyi ahankali tataka zuwa saman gadon taxauna hannu tasaka tanashafo lallausar sumar kansa Wanda takwanta luf gwanin sha awa hakika tana matukar son mijinta dakuma kishinsa fiye da tunanin mai karatu hakaxalika tana mutuwar kaunarsa da begensa fiye da tunanin duk wani mai tunani taja gauron numfashi" atake talulaya wata duniyar daban

Sai farkawa yayi yasamu hajia lubabatu tasakashi gaba hannunta yanakan gashin kansa  idanuwanta suna kallon saitin drawer yayi kuru yana kallonta daga bisani yasaka hannu yashafo fuskarta tadan zabura sannan tasaki murmushi hannu tasaka tajawo hannunsa daga kan fuskarta tace harkatashi ???

Murmushi yasakeyi akaro nabiyu yace ah tunanin mekikeyi??? Taware ido waini batunani nakeba
Yace bayan Wanda nagani"" tayi murmushi ah ah alhaji wai shin inakabar Kanwata??? Tayi saurin kawarda zancen dawannan tambayar"" yace tanadaki tanabarci mana""

Cikin zolaya tace barcin gajiyako nasan halinka basauki jiya bakabarta tahutaba duk da take yarinya batasaba sosaiba
Yayi murmushi yace kinfara ko lubabatu yayi kyau inhar nakama ki akoma zakiyi bayani

Aransa kuma yace hmm inakikasani saida ta talemun kaza tacinye sannan tasoma barci kamar kasa yayi maganar yana mikewa daga kan gadon yashiga toilet domin watsaruwa




Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 9
      By
Gentle Lady💃🏽


Bazato kawai saiyafara jin amai"" dasauri yasauko zuwa bayin dakin dagudunsa yasoma kela amai tamkar zai amayarda kayan cikinsa yayi matukar galabaita"" take yazube acikin toilet din yana hakii tamkar wanda yayi gudun tsere da kartii goma""

Tsayin mintuna talatin yana wajen sannu ahankali yasoma samun natsuwa mikewa yayi yasakarwa wajen ruwa yawanke bakinsa sannan yafito kallo daya yamata yadauke kansa wasu hawayene suka sauko akan fuskarsa harzai wuce saikuma yadawo tareda saka hannu ya dade hancinsa zuwa saman gadon" yaja abun rufa yarufe mata jikinta sannan yawuce dasauri

       Dayake akwai yalwatattun dakuna abangarensa tamkar wani babban gidane ahawan wani bangaren yashiga"" jiki sanyaye yakarasa bayin yayi wanka yadauro alwala domin koda yakwanta bazai iyah barciba


Washe garin ranar Sam fuskarsa batada wani walwala dankuwa alal hakika wannan lamarin yasoma kaishi bango yanaji yanagani zai halaka kansa"" ko lunch dasukayi sama sama yaci daga bisani yamasu sallama yawuce ko rakiyar bainemaba dama dai yau rakiyar habibace Dan haryanzu hannunta yake

Saida akayi kwanaki uku cur kamar yarda addini yasimfida budurwa sati daya bajawara kwana uku Amman harzuwa wannan lokacin baisamu kwantawa da itah ba"" gashi hargirki yadawo akan hajiya lubabatu""
                Dadare suna zaune akan kujerah sunashan kayan itatuwa habiba tana barin gefensa nadama hajiya lubabatu tana barin hagu kokadan ayanzu bayajin warinta koda tabude bakinta"" aransa kuwa yana ayyana damacen muguntane bataso yakusanceta akwai abunda take sakawa ajikinta duk lokacinda tasan zaizo mata""" ahankade yake kallonta

Bayan sungama Shane yayi gyaran murya yasoma yimasu nasiha akan zamantakewar aure daga bisani yace  kamardai yanda kukasani yaudai kwanana uku dakin Amarya danhaka yau za araba kwana kwana biyu kukeso ayi ko daya daya???

Hajiya lubabatu ce tayi saurin tarar numfashinsa tace maigida nidai kasan banda wata matsala amatsayina na antynta nidai nayafe nawa kwanakin nabaku watadaya kumore amarcinku

Jiyayi tamkar yafasa ihu
Dasauri yabude baki daniyar yin magana ta dakatàr dashi tahanyar rufe masa baki dahannunta tana girgiza kai cikin murmushi tace karkadamu basaika godemun ba nimaisonkace

Inason duk wani farincikin ka ninasan amarcin nan bai ishekaba"" bazan cutuba harcikin raina nabar maku zuwa watadayan saika rabamana kwana

Gabadaya jikin habiba yayi sanyi son hajia lubabatu yashiga ranta lalai kowa da irin halinsa bata taba ganin macenda batadau kishiya abakin komaiba kamarta Allah yabarmu tare hajia

Al amarin alhaji kuwa sandarewa yayi awajen saboda kaduwa dajin furucin lubabatu anyakuwa tasan masifarda nake fuskanta???

Yanisa aransa batasaniba nasan datasani dabazataso incutuba"" yanda takesona fiye darayuwarta "" kuma haramun ne kasanarda matarka sirrin abunda ketsakaninka da dayar matarka dasaina fadamata"" yaja dogon nunfashi yace shikenan mungode hajiya yanayin yanda yayi maganar kaida ganinta kasan ba cikin dadin rai yayiba"""

Basuwani jimaba hajiya lubabatu tayimasu saida safe tawuce bangarenta"" shima hakan yasaka yamike zuwa dakinsa hakama habiba"" sosai yau taraya aranta zatafaranta ran maigidanta domin samun abunda yakeso

Bayan tayi wanka tashirya cikin shigar kayan barci farare masu sharara tafeshe jikinta da kalolin turarukka"" kaitsaye bangarensa tanufa

Tasameshi yayi shirin kwanciya yana ganinta gabansa yafadiii yaukuma meyakawota alhalin bankirataba ????

Batareda tanemi iso daga gareshiba tayi saurin fadawa jikinsa""" ’’kafin yayi kokarin tureta daga jikinsa hartafara aikamasa dasakonni tako ina"""

Takesuka zube akan gadon tunbaya maida martani haryasoma maida mata da martani""" abukamar zaitafi ahakan sannu ahankali yasoma jin doyin tunyana daurewa tareda toshe hancinsa saiyaji abun kamarma karoshi akeyi  kusamma doyin yafi nakoyaushe

Bashiri yahankadata gefe yamatsa baya dasaurii""" itakuwa alokacin hartayi barci abunta saitasake gyara kwanciya

Gefenda take yakuramata ido tamkar maison tunowani abun dagakarshe wanka yashiga koda yadawo baisametà dakinba tafita

Tsaki yayi damashi yasan komai takeyi dagangan takeyi kawai danyanason hakkinsa tana nema takasheshi indai Dan wannan ne bazansake nemantaba

Darenkuwa daciwon ciki yakwana"" tundaga ranar kullum idan sukatashi don su kwanta"" saikawai yarufe dakinsa kuma koda tabugàmà  bazai budeba Amman Sam bayanuna komai idansuna tareda lubabatu ahakan har akacinye watadayan da hajiya tabasu






Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*



Chapter 8
     By
Gentle Lady💃🏽


Tabishi da kallo dawani boyayyen murmushi Wanda itah kadaice tasan ma anarsa"" tana nan akan gadon haryafito yana daure da towel

Yadauki comb yana   taje sumar kansa""  saida tayi luf sannan yadauko turarukka yasoma fesawa ajikinsa"" yafesa akalla turare kala biyar sukahadu sukabada wani kalar kamshi na daban kaisaikace ma aiikatar turarece tayi ambaliya

Wata bugaggar shadda ja wacce taji aikin hannu da zare jinin kare maiduhu dinkin tazarcene daidai wandonsa bataja kasaba kamaryanda wandonsa baiwuce idon kafarsaba"

Yadauko hukarsa kube maikalar kayansa hatta Zanen hular tamkar tarema aka kerasu"" yadaidaita tsayin hularsa sannan yajuyo wajen hajia lubabatu yasakar mata murmushi yace mujeko dannafarajin yunwa yayi maganar yanashafo cikinsa

Batareda tayi maganaba tamike sukajerah zuwa kasa kowannensu  fara a kwance akan fuskarsa"" aka idar sa falon kasa yakeyin break saboda masu aikine sukeyin komai shiikuma  bayason masu aiki suhau saman sa inhar ba matarsaba babu Wanda yataba shiga saman""

Kaitsaye saman dinner suka nufa yaja kujerah yazauna tadubeshi tace bari nakirah Kanwata ko batareda yakalletaba yace ok"

Kaitsaye tasake hawa mahayar zuwa bangaren Habiba""  bakin kofar dakin tatsaya tana kwankwasawa cikin dakin akace waye shigo" taturah kofa habiba tana ganinta tasaki faraa danta shaidata tace Anty kece inakwana

Tamayar mata da martanin murmushinta tace lafiya qalau Amarya yakwanan amarci ya kuma bakunta?? Murmushi tayi kawai tadone kanta kasa""

Hajia lubabatu tace hmm kunyata kikeji Amarya nifa antynkice kinga taso muje mukarya nasankema kinajin yunwa""

Batareda tace komaiba tamike hajia lubabatu tanagaba tanabayanta itakuwa saikada mazaunai takeyi kamkar randar ruwansha

Harsukakai kan dinner din itah ta gabatar masu da abincin sukaci sukai hamdala sannan suka koma cikin falon suka zauna sukasoma firah

Dama ankusa azahar bayan yayo sallah yasake dawowa falon alokacin duk basanan"" baijima daxamaba hajia lubabatu tafito tanaganinsa tawashe baki harkadawo yace ah wlh kusadashi tazauna

Yace inakuma habiba??? Tasake murmusawa tace banda abunka alhaji kasan kunya takeji bata sababa nidai nayafe hirar kakoma bangarenta zakufi sakewa kudarji amarcinku

Murmushin yake yayi yace hakane kuma kinkawo shawara mai kyau yamike yana gyara tsayuwar rigarsa yayi hanyar mahaya itakuma takoma bangarenta

Kofar dakinta yatsaya yana sake sake aransa karshedai kawai yayi kundun bala yaturah kofar tareda sallama tana zaune cikin katon falon tana kallo tadago cikin fara.a ta amsa masa" dannesa da itah yaxauna yana Dari Dari yace kallo kike???

Tace ah kanta yanakasa yace dakyau"" dagahakan baicekomaiba"" saidai yanata satar kallonta takasan ido haryana hadiyar yawu kafin cikar mintuna ashirin yaji baxai iyah dakatarda kansaba cikin kasalarlar murya yakirah sunanta ahankali ta amsa yayimata nuni akan tazo babu musu kuwa tataso

Al amaridai anan yasauya yafara aikamata da sakonni dayake yanayi yana kauce hancinsa dankarya shakomasa abunda yafi karfin Tunaninsa tsayin mintuna goma yasunkuceta zuwa kuryar dakin

Abun mamaki yana ajeta akan gadon yajitafara wani minshari arazane ya kwalalo ido cikin kaduwa yace barcin kuma???? Waimeke faruwane kodai yarinyar nan aljanun barcine da itah?? Kuma dantsabar shakiyanci ace barcin bayazuwa sai idan nazoda bukatata"??? tsaki yaja yamike akan dagon yafita abunshi zuwa bangarensa

Saida akayi la asar yafito da mamaki yasameta cikin falon kasa da itah da wata kawarta"" kallo daya yamasu yadauke Kansa yawuce fuuuu tamkar kububuwa dansosai amaryar  nan tasa tasoma batamasa rai jiyajiya dakawota jifa dazun barcitake haikam Amman gashi kawarta tazo tawartsake tamkar batayi barciba
 Anjima nasan mezanyi
Dawannan yakawarda tunanin yakarasa masallaci""

Habiba kam tacika da mamaki duk da bata nunawa kawarta dakwai wani abuba Amman tanacikin damuwa tarasa meke faruwa aduk lokacinda zaitara da itah batakoma sanin meke wakana saidai tafarka taganta itah kadai idan kuma tamatsawa kanta da tuna abunda yafaru saitaji kanta yasoma ciwo

Har da dare taresukai dinner sukadan taba firah tayi masu saida" safe tayi bangarenta" batajima datafiyaba hajia lubabatu tamike tayi hamma"" tace nizan kwanta" alhaji saida safe"
             Shima yamike yace kenan duk kunwatse kunbarni""anan kamar tsinkàkken silifas"" bakomai muje inrakaki" tayi murmushi tayigaba""   yana bayanta saida yarakatà har bangarenta"  saida takwanta sannan yarufemata kofa Yakoma bangarensa yayiwanka

 Yayi shirin kwanciya wannan karon kiranta yayi awaya tasameshi bangarensa""cikin shigar kayan barci masu sharara dukkan halittar jikinta ta bayyana" take Yakama zumudi jikinsa yasoma karkarwà tamkar zakinda yakwana biyar yanajin yunwa aganinku mezaifaru idanyayi arba da abinci

Ahankali ta takazuwa wajensa"" babuwani   bata lokaci sukafara faranta ranjunansu"" kafin wani lokaci sunkai saman gado kamar almara saigashi tasoma barci

Ganin hakan yasa yaji haushi aransa yace kobarcin mutuwane bazai hakurabà saiya Kore kishinsà yanata"" kokarin biyan bukatarsa tasoma gurnani tanabude bakinta wani"" mugun doyi yana fitowa babu shiri yasa hannu daniyar rufemata bakiii yajikamar yataba wasu hakorah zagan zagan"" take Kuma zuciyarsa tasoma tashi
"
Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*



Chapter 10
      By
Gentle Lady💃🏽



Alokacinne akaraba girki" yakoma hannun lubabatu""
Habiba Sam takasa gane wanne irin aurene tayi gatadai batadawata makusa wacce zatasa namiji yaji baya sonta"  batada matsala tabangaren kishiya saidai tabangaren miji"" sosai yakesonta kafin auren ammankuma gashi tunda tashigo gidan komai yadargwaje tarasa gane kuma dalilin yinhakan gashi tanada tsananin bukata zuwa yanzu tarame tafige tafita hayyacinta"""

Kwance take cikin falonta kasancewar yauma ranar hutuce yanagida Amman takasa fita domin ganinsa kawai zaisake tasomasa da bukatarta wacce tasan bazata samu maganintaba "" lallai tayarda akwai abunda yajefaruwa da itah cikinta taji yasoma juyawa tafara murkususu""

Tun tana kankujerah hartafado kasaa wata irin kara ta kwallah daidai shigowar hajiya lubabatu tazo kiranta suci abinci dasauri takarasa arude tadagota tana tambayar lafiya kafin tarufe bakinta jinine yasoma zubowa dakarfiii ta gabantaa""

Cikin tashin hankali lubabatu tace habiba dama bakida lafiyane???ina habiba tamatukar galabaita bata iyah kodaga kanta dasauri hajiya lubabatu ta kwantarda itah tafito dasauriii zuwa kasan

A firgice tana kuka yana ganinta yamike yana tambayarta lafiya hajia??? Cikin kaduwa yaji meyafaru tace munshiga uku habibace ba lafiya

Kafin tarufe bakinta tuni yahaurah saman baimabi takan na urarba tasaman benen yataka tuni hajiya lubabatu tabi bayansa koda suka karasa hartasuma ga jininan yanata malala"" gakuma wata karamar halitta wacce batawuce girma Dan kadan gareba""  take jikinsa  yahau rawa duk da abunda yagani Amman hakan baisa yadamuba ya ciccibeta  duk dajinin dasauri yasauko kasa hajiya lubabatu tana bayansu sai kuka takeyi

Tunkafin yafita yasoma kwalawa driver Kira"" dasauri yafito jinkiran jikinsa yanarawa Dan dagajin kiran yasan ba lafiyaba"" ganinshi damaidakinsa ahannu yasaka yabude masu Mota dama ashirye take"" akasakata taresuka dunguma  har hajiya lubabatu zuwa hospital""  emergency akawuce da itah kaitsaye bakin kofa aka dakatar dasu aka hanasu shiga"""

Dagashi  har hajiya kaikawo sukeyi awajen kowanne kagani kasan yanacikin tashin hankali tsayin awanni biyu likitan yafito dasaurii alhji yatareshi "" saidai yadagamasa hannu yawuce haryana hadawa dagudu""

Zuwacen yadawo yashiga dakin"" ansake shude wasu awannin saigashi yafito
Alhaji yatareshi tareda hajiya lubabatu harsuna hadabaki wajen tambayar yamaijikin???

Zufan kansa yashare yace kukwantarda hankalinku insha Allah zatasamu lafiya"" yanzudai muna bukatar jini cikin gaggawa"" kafinma yarufe bakinsa yace muje a auna idan nawa zaiyi"" hakan kuwa akayi saidai jininshi baiyiba

Adole akakirah yan uwanta mahaifiyarta "" dakuma yayyunta""" su ukune kowanne akadibi gorah biyu ajikinsa"" take akajonamata anasaka jini jinin yanafita"""

Harzuwa dare babuwani haske hakazalika  sunkasa tsayarda zubar jinin"" yanda yakezuba zuba banawasaba hakan yasaka sukanemi Karin wani jinin"" duk dayana fita idan ansakamata""

Yan uwanta basuda wadataccen jinin gashi har andibi gorah biyu dagahakan baza sake dibaba"" gashi duka jininta ya tsiyaye"" hajiya lubabatu sai kuka take tace aduba konata zaiyi itakam bataso tarasa kanwarta

Likitan yatausaya mata sosai yace saidai hakuri hajiya ba adiban jinin mace"" cikin karaji ta chakumo wuyansa tace inaruwanka jininka konawa

Tasakeshi cikin kuka tahada hannuwanta gida biyu Dan Allah doctor kataimaka mana wlh koda zanrasa raina tasanadin dibar jinin nawa"" wlh nayarda Amman banaso kanwata tamutu

Jiki asanyaye yagyada kai ganin kowanawajen yazubamasa ido"" take aka auna jininta baidakomai"" akasoma diba  anasakawa Habiba"""likitàn yafita mahaifinta dawani kaninsa sukabishi abaya"" zuwa office dinshi"" mahaifintane yasoma tambayarsà meyakedamuñ yarsa???
Yayishiru dagabisani yace  barine tayi" cikin kaduwa mahaifinta yace barin lafiya watadaya da aurentafa??? Yajinjinà kai tareda turomasa takarda gabansa yace sakamàko yanuna tanashañ kwayoyin zubarda cikine babisa ka idaba shine yajawomàtà wannan matsalar

Kafin yarufe bakinsà alhaji yashigo dasauri yace doctor kataso jinin ya facce kusan taresukà mike dasauri zuwa dakin harsunà hadawa dagudu

Sannu ahankali tabude idonta takurawa gadonda hajiya lubabatu take kwance ido sirarun hawaye suka saukomata

Take tasoma Kalmar shahada"" idanuwanta sukai sama take Na urah tasoma kara"" daidai shigowar su doctor yakarasa wajentà yayi yan aune aunendà zaiyi yagirgizà kai

Yacire abun Karin jinin tareda Na hajiya lubabatu yarufe mata idonta yaja kallen yarufeta"" gabadaya dakin shisuke kallo Dan haryanzu basu fuskanci meyafaruba

Yajuyo dakallonsa wajen alhaji yace saidaifa kuyi hakuri Allah yakarbi abarshi""

Daga haka yajuya yafita hajiya lubabatu tasoma kururuwa tana wayyo itah tabani mahaifiyar habiba saman gadon lubabatu takoma tanabata hakuri suka rungume juna sunata kuka""" akarasa Wanda zai rarrashi waniii

Tsayin mintuna talatin mahaifin habiba dasauran yan uwa da sukazo dakyar akasamu su hajiya lubabatu sukai shiru

 Kanin Mahaifiyarta yakalli alhaji yace waimenene musabbabin ciwon nata""??? Kodama tadade batada lafiya???

Ciikin sanyin murya yace shima baisaniba yadaifàdamasu iyah abunda yasani  ahakan"" mahaifinta yace sai asamo mota suwuce gida babu wani bata lokaci akadauki gawar zuwa gidan iyayenta""





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 11
      By
Gentle Lady💃🏽



Gabadaya gidan iyayen nata akanufa harda Alhji"" saidai dare yayi Dan lokacin andade dayin sallar isha I"" hakan yasa akaimata wanka aka suturtata" zatayi kwanan keso washe gari sai akaita gidanta na gaskiya
         Cikin Daren su labila sukasamu labari anasanarda itah tarabka salatiii kukane yakwace mata taruga cikin daki waisaiyaushe mom zatadaina kashewa dad matane???

Meyasa haryanzu nakasa sanardakowa abunda take aikatawa??? Ninasan koda nafadadin babu Wanda zaiyarda dani ganin irin yanda take nunarashin kishi akan matanda yake aurah

Ya Allah ka gaggauta tona mata asiri"" wasu hawayene suka sauko akan fuskarta tashare""" tundaga bangaren lubabatu har alhaji babu Wanda ya runtsa acikin Daren sai rarrashinta yakeyi washe gari labila  abdulmajed da hajiya da kannen alhaji hafis da kubra suka kamo hanyar kaduna

Koda sukashigo kaduna bakwai darabi"" alokacin har anyimata sallah antafi Kaita makwancinta"" su hajiya gidan su habiba aka kaisu sukayiwa iyayenta gaisuwa""
 Harda hajiya lubabatu sukaje idanuwanta sunyi suntul saboda kuka kowayaganta saiya tausaya mata"" iyayenta Kansu basuyi kuka kamar yanda tayiba"" labila Kuwa dage take kallonta dankuwa tasan aikintane""
                Ahakan akayi zaman makoki akawatse "" Dan babanta yace bayason wani zama saidai kowa yabita da addua"" aranar kowa yawatse anayiwa habiba Neman gafarar Allah
        Kowa yazo gaisuwar dole yakoma dason lubabatu acikin ransa ba alfahariba ko mijinta baikaita nuna bakincikiba""
Ahakan akayita lallashin juna"" aranar sukadawo gidansu

Hajiya lubabatu harda karamar jinya tayi tarashin kanwarta adole alhaji yabar aikinsa yatsaya jinyarta"" su hajiya kwanansu hudu sukajuya suka koma""

Bayan satii daya darasuwarta yan uwanta sukazo gidan suka kwashe kayansu"" ranarma Ku San kukanda sukayi dasu da lubabatu tankar yafi naranar rasuwarta wata kanwar Innar habiba harcewa tayi da alhaji yanason yarta ai wlh databashi Dan sosai sunason lubabatu kamar yanda takesonsu""

Bayan sungama yan koke kokensu tarakasu sukawuce takoma cikin gida""tasheke dawata mahaukaciyar dariya""" tasoma tafawa lallai kimabashi yarki??? Aikuwa dakin yankarwa yarki ticket din zuwa lahira barganina ahakan  bakar kunamaçeni🦂 "nidin damoce Amman nafi maciji hadarii

Babu wata wacce ta isah nayi kishi da itah ba ahaifetaba""" idankuwa tsautsayi ya saka wata tashigo gidan nan tabbas tasoma kididdigar ranar mutuwarta tasake shekewa da dariya tawuce saman

*WADANSU SHEKARU BAYA*


 Alhaji adamu yunusa"" wani gawurtaccen maikudine kudikuma bana wasaba"" attajiri wanda yakrtashen kudi yanada mata biyu hajiya binta itace uwargida yayanta uku Usman hafis da kubrah"" sai Amarya hajiya hannatu yayanta biyu duk maza kabeer Ahmad"" Alhaji adamu irin mutanen nan ne wadanda sukeda kudi kamar hauka Amman ba agane hakan ajikinsu kokuma asuturansu domin bayaci kuma baya bawa iyalansa komai nagidan kwab kwab akedashi acewarsa aidukiya tattali take so" idan bahakaba tawargaje😂

Sam yan uwansa abun yanabasu haushi barinma hajiya hannatu dankuwa itah macece maison karya danuna isah

Abudayane bayawasa karatun yaransa danyafison kowanne yayi karatu yanemi nakansa dankar zuciyarsa  tamace akan na mahaifinsa""

Usman tunda yatashi Sam dukiyar mahaifinsa bata burgeshi tunda yasoma karatu yamaida hankalinsa wajen karatu"" harya kammala degree dinsa fannin kasuwancii""

Alokacin babansu yabasu jari Usman da kabeer dankusan taresuka kammala karatu""
Usman yanada farinjini hakazalika akwaishi  dason mutane babu ruwansa dashiga harkar dabata shafeshiba   yanada wani aboki akaduna sunansa abdullahi shine kawai abokinsa baban abdullahi dankasuwane shima yakarfafamasu guiwa akan suyi karatunsu bangaren kasuwanci

  Alokacin da mahaifinsu yabasu kudi yanunawa mahaifiyarsa tasanya masa albarka ranar yakirah Abdul yasanardashi""

 Yace gobe zaizo kaduna hakan kuwa akayi mahaifin Abdul yahadashi damanyan yankasuwa yafara sana a

Cikin yan shekaru Allah yasakawa dukiyarsa albarka"" alokacinne hajiya binta tafara masa maganar aure"" damakuwa yadade yanason wata ameena wacce take tuyar awara alayin gidansu Abdul
       Ameena marainiyaçe mahaifiyarta tarasu tuntana yarshekara hudu aduniya"" babu kalar wuyarda bataciba wajen matar ubanta huwaileDuka kuwa dayunwa dasuna kashi datuni sunkashe ameena

Mahaifinta yanasonta sosai Amman dagabaya da akaci karfinsa yakoma da itah dababu itah duk daya gashikuma itace kawai yarsa

Huwaile tasoma dauramata talle kuma baburuwanta nairah inhar tayi ciwon kai ajikinta Zata debe tashayi mata tsarki da attarugu tawanke mata daruwan zafiii

Azaba iri iri babuwaççe ameena batashaba"" tunlokacinda taga tasoma kirgan dangi saitafàra yimata awara tana toyawa alayinsu

Dayake unguwar kowayasan mahaifiyàrtà babu Wanda yatabajinta tayi sa insa da makota bakamar huwaile ba harfada takeyi da kartii idansunçi bashinta basu biyaba babu ruwanta dawai itah matar aurece!!!




Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠


Chapter 12
       By
Gentle Lady💃🏽



Malam garba kuwa dashi da babushi duk daya kobanza yana bala in tsoronta tunda ba banza tabarshiba""
Duk saurayinda yace yanason ameena har gigi yakaishi kofar gidansu huwaile ce zatafito tazageshi ta uwa ta uba"" hakan bazai ishetaba saita samu iyayensa tayi masu Tass kuma tace sujawa dansu kunne kartasake ganinshi kofar gidanta dayawa samari sunason ameena Amman balain huwaile suke gudu""
       Tunranarda Usman yaganta yaji takwanta masa arai barinma lokacinda Abdul yasanardashi ainahin tarihinta saiyaji babu matarda yakeso aduniya sama da itah"""

Lokacinda mahaifiyarsa tayimasa maganar aure saida yafara neman shawarar abdul akan yasanarda itah"" dariya yasoma yimasa yace zakafara wautar taku ta yayanfari tomenene dankafada mata kokunyarta kakeji""

Dariya yayi yace wacce irin kunya Abdul tunani nayi yarinyar nan bataSanniba kawai dai saninda tamun inazuwa cin awararta lokacinda nake karatu" atunaninka itah zatasoni??? Nifa banaso nacutarda itah

Abdul yasake kwashewa da dariya yace kwantarda hankalinka mutumina indai ameena ce wlh bakada damuwa kasan sarai itama kamar akan kayatake agidansu yanda aka azabeta nikam hakan yayima kaga huwaile Batasan da soyayyar kuba ballantana ta fatattakeka

Tare suka kwashe da dariya yace fatattakadai abokina aitasan wadanda zatayiwa hakan sudinma rainasu tayi kodayake hakan datayi alhairi ne agareni dayanxu banine zansamu wannan kyakkyawarba"" sosai Usman yarude akan sonta cikinwai ma bata kwalliya Dan huwaile batabari waidan kartasamu samari

Ranarda yasanarda mahaifiyarsa tafadawa alhaji adamu yayi murna sosai Amman kafin yanema masa auren saida ya tabbatarda kasuwancinsa dayanda yasamu riba sosai fiye dakudinda yabashi

Bawani batalokaci yasanarda limamin unguwarsu dawasu abokansa sukaje kaduna sukanema masa auren ameena awajen mai unguwa

Saboda Usman yafadamasu komai akan matarsa""mai unguwa yaji dadi sosai yasa akakirah malam garba" agabansa akayi komai sunbada harda kayan nagani inaso dakuma kudin saka rana ahakan alhaji   adamu yace asaka biki kusa kusa kumashi yaron yace basaitayi komaiba shizaimata kayan daki dakomai malam garba kam yayi murna duk dakasan zuciyarsa halbawa yakeyi shikawai yasan fitinarda zaihadu da itah agida"" mai unguwa yace totunda har hakane mezaihana adaurah auren ayanzuma idan ashirye kuke"" hakan bakaramin dadi yayiwa alhaji adamu ba babu bata lokaci yakirgo kudi dubu hamsin amatsayin sadakii

Goron saka rana shi akayita   mikawa mutane mai unguwa shiyazama waliyin Amarya"" take akadaurah aure jama a suka shaida bayan yan gaishe gaishe"" alhaji adamu da tawagarsa suka kama hanyar kano cikin farinciki

Malam garba yanarike da sadakin ameena dagoro yatunkari kofar gidansa gabansa yanafaduwa"" yadade bakin kofar gidan dagabisani yashiga da sallama
          Ameena tana tsakar gidan tana darzar wankin huwaile da fa Iza " ita kuma uwar ikon tana inuwa zaune tanayiwa fa Iza tsifar kaiii"" fa iza yartace Amman batareda  malam tahaifetaba bayan tahaifetane tarabuda mahaifinta saita auri malam

Bagidan take zamaba saidai tanazuwa akai akai duk sanda tazokuwa kafin takoma komai ameena takemata duk dakuwa ameena tagirmeta""

malam yakalleta yadauke kansa aransa yace kinkusa hutawa da wahala ameena "" tunkafin yazauna huwaile tamike tanakallonsa yanda yake fara"a

Kujerah yaja yazauna yana mai fuskantar huwaile sannan yakwalowa ameenar Kira""
Huwaile tace haba malam yaxaka kirata bayankuma kana ganin wanki takeyi???

Cikin in inna yace ainaga ba wani abubane dannakirata badadewa zatayiba"" tace kaikasan wannan nidanakeso tagama dawuri tafita tuyar awara
            Cikin malam yahau hautsinawa jin furucinta lallaikuwa akwai aiki jajir"" takatsemasa tunaninsa tahanyar karbe kudin hannunsa tana jujjuyasu tanakallonsa

Sunahada ido yaji zawo tamkar zaizubomasa"" tajefomasa tambaya kudin waye wannan??? Yace eyin eyin"" takatsamasa tsawa batambayarka nakeba""
           Cikin kaduwa yace dama yarkice kinsan kwanaki kinacemun gashinan tagirma"" Amman"batada mabidi "" kinsan komai lokacine da"" katseshi tayi cikin karaji kamar mai magana da danta tace sai akayime??? Kafito kayimagana kadaina wani yan zagaye zagaye""

Saida yahade wasu yawu yace sadakin ameenà ne"" gakuma goro "" kafinma ya ajegoron tamike tafara liliyo ashar"" tawatsa masa kudin afuskarsa

Tace  kayi gaggawar daukar sadakin nan kamiyar dasu inda suka fito nibantashi aurar da itah ba"" malam garba yashafo zufar goshinsa yace saidai kiyi hakurii Dan maigama tagama har andaurah auren

Wohoho inawuta tasakashi "" jitayi tamkar tarufeshi da Duka"" tace tabdijam wato Dan anunamun iyakata shine akaje waje aka kimtse magana tsofaffun munafukai dama ninadade dasanin duk yan unguwar nan munafukaine

Wato ana bakincikin yar tallarda nake doramata saida sukai kutunguilar samomata miji"" tonikuma sainaga wanne shafaffen damaine ya isah yashigo gidan nan yadauketa

Tallekuma yanzu akafara hartuwo tuwo zanfarà yimata tanazuwa kasuwa yan bakinçiki saidai su mutu kuma ko anki ko a anso ko anasonmu ko anakinmu dole aganmu akyale

Cikin sanyin murya yace kiyi hakuri nikainà badason raina akayi abunba aikin mai unguwane

Rufemun baki tsohon munafuki aikaine babban mailaifin kafadamun tareda mai unguwa kukayi cikinta dazaiñuñà maka iko akanta???





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 13
        By
Gentle Lady💃🏽


Yanisa bahaka bane kiyi hakuri abun duk baikai na tashin hankaliba"" tayi saurin gwatseshi tace awajen kaba ?? Wato malam dakai za ahada kai acimun mutunci a unguwar nan

Saboda  banice nahaifi ameena ba?? Amman inda kara aitamkar nidince na haifeta tunda nake auren ubanta kuma bauta wacce hawalane banshaba tunyar nan tana tatsitsiya saiyanzu data girma za anunamun halin karfi bakomai aure ko aje ayi "" inazaune zatadawo tasameni taja hannun fa iza sukashige daki

Ameena kuwa tun lokacinda suke maganar tanaduke banda kuka babu abunda takeyi Sam abunda akemata agidan bayadamunta

Sama da abunda akeyiwa mahaifinta !"tana tsaka da tunani taji yadafata"" tadago dahanzari takalleshi saita done kanta tacigaba da sharar kwallah""

Yanisa kiyi hakuri ameena ninasan amatsayina na uba bankare maki hakkin kiba dayake akaina"" inajin tsoron tambayar ubangijina agobe kiyama abisa amanarki datake hannuna nakasa riketa

Nikaina bansan yazanyiba alal Hakika inason ganin farincikin ki"" yasake jan ajiyar zuciya kiyi hakuri kuma kisa Allah aranki insha Allah zakiga sakamakon hakuri

Tagyada kanta nagode Abba inshaa Allah zancigaba da hakuri har lokacinda zanbar duniya Amman Abba auren nan idanhar inna bataso kawai abarshi kwanciyar hankalinka shine nawa banason abunda zai rika sakawa kanasamun sabani da itah""

Ya murmusa karkidamu ameena magana anriga da angama kizama cikin shiri aduk lokacinda mijinki yazo zakibishi"" Allah yabaku zaman lafiya"" inarokonki akan kizauna da mijinki lafiya da yan uwansa ""
Tanisa nagode Abba"" kudin yamiko mata"" yace gakudinki"" kanta tasanne kasa alamar kunya"" tace Abba kadauka nabaka Kayi wata lalurar dasu"""

Yace haba ameena ina kikataba ganin anyi haka sadakin kinefa?? Tace bakomai wlh Abba""" yace shikenan Amman ninasan mezansiya maki dasu idan bukatar kudi tasameki saiki tambayeni"" tagyadamasa kai kawai"""anan yabarta yashige dakinsa itah kuma tacigaba dawankin datakeyi"""

Alhji adamu yakoma gida murna fal ransa"" alokacin Usman yanagida sosai yakagara mahaifinsa yadawo yaji ko ambashi ameena"" saiyasamu labarin harma andaurah aure wani dadine yakamashi tamkar yayi ihu""" dukawa yayi yayi sujjada yanamai godiya ga Allah dayabashi ameena""

Take yakirah Abdul yasanar dashi"" yatayashi murna""  nesa kadan"" dagidansu Abdul Usman yasiye gida Dan madaidaici mai dakuna biyu ajere"" kowanne daki daya dabayi sai falo daya dayake farkon shigowà saikuma bayin tsakar gida""sai kichin komai yasaka acikin gidan daidai gwargwado""

Yakuma tanadi kayan abincinda zasu bukata"" alokacinne yasanarda mahaifin Abdul yasamu mai unguwar yafadamasa Usman yanason abashi matar sa"" domin haryanzu huwaile batadaina doramata talleba""

Mai unguwa yaturah maidakinsa taje gidan tahado mata kayanta"" tatasota gaba ammanfa ansha rigima saida taji alamar za ahadata dayan sanda sannan tabarta"" matar mai unguwa babu laifi"" tagyara ameena daidai karfinta satinta daya agidan mai unguwa akace Usman yazo yadauki matarsa

Alokacin ameena tayi Dan kyau tayi yar kibarta daidai gwargwado""" ranar kuwa Usman sukaje tareda Abdul sukadaukota""

Alhamdulillah sunazamansu lafiya babu wata fitina"" saidai huwaile datake zuwa gidan takwashe mata kaya har abinci"" Amman Sam bata taba fadamasaba "" kodakuma abincin yakare dasauri tafadamasa bayacewa komai zaisiyo wani

Wataranane huwaile taje gidan harda mai baro Wanda za alodo kaya saboda tamiyardasu hajarta"" dankuwa har suturah takedauka"" barta ameena harta Usman dauka take"" aranar tayi rashin sa a kubrah kanwar Usman tanagidan"""

Dashigarta"" ameena tanazaune kotakanta batayiba kallon banza"" kawai tawa tsamata tawuce kuryar"" dakin""

Tasoma jido kaya"" tana ajiyewa bakin kofa"" daidai fitowar kubrah tace La Anty wanki zakiyine shine kokimun magana intaso intayaki bayankinsan kwance kawai n"" batakarasa rufe bakintaba saiga huwaile dazannuwan gado""

Sabbine hull maman Usman tasiyomata su jiya kubrah takawomata""" aikuwa kubrah damamaki takalleta tace wannan kuma wacce mahaukaciyarce?????

Sai alokacin huwaile tadago kai afusace tace uwarkice mahaukaciya yar iskar yarinyà"" aikuwa batama rufebakintaba kubrah tadauketa damari jikake tasss

Batagama mamakiba"" tasake dauketa dawani"" Marin tareda nunata dayatsa karki kuskurah wlh mahaifiyàtà  bakalar zagi bace ki kiyaye harshenki

Sannan kisan kalar furucinda zakiyi agidan nan"" daganinki nasanke kowacece"" taduka tadauki kayan tawuce tagefenta hartana tureta sainagani idan ubankine yakesiyo kayan

Huwaile tanatsaye rike dakumàtu baki bude takasa cewa kala"" har kubrah tagama miyarda kayan"" itakuma ameena tamkar gunki takoma sai rarraba ido takeyi"""

Tadawo gabanta tareda kyasta yatsunta biyu"" daidai saitin fuskarta"" tace oya mekike jirah kama hanya kibar gidan nan tunkafin inrasa natsuwàta wlh inlakadamaki shegen dukanda yausaikin kwana agadon asiviti""

Hannunta dafe dakunci tawuce sumui sumui"" kubrah tadakamatà Tsawa Keee!!!  saida tazaburah harsaida guntun zawo yazubo awandonta"""

Kubrah tace sauran idan bananan kisake wanko wannan jemammar kafartaki maikamada kashin shanuu kidawo gidan nan hmm  wannan gargadine nakemaki Dan muddin nasamu labari hargidanki zansameki inlakadi banzaa tsohuwar banza wacce batasan Allah ba ke kokunya bakijiba kisamu marainiyà kina zalunta" kebaki kawomataba kidauki nata""
      Bàrima nahadaki dahukumà suje hargidàñki sudibomatà kayanta"" dannasan bawannan nezuwanki nafarkobà!!





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 14
       By
Gentle Lady💃🏽


Cikin fushi kubrah tajuya dakin domin dauko waya"" aidasauri huwaile tafita ko takalmanta batajirah tadaukaba yau Allah yahadata da hatsabibiyar yarinya kuma take taji tsoronta harcikin ranta

Tana rayawa aranta lallai kubrah ba itah kadai takeba kokuma tanada tabin hankali"" dasauri takoma gida tareda danbaro tasoma jido kayanda suke gidan wadanda bata salwan tarba tadorawa danbaro tace yakawo gidan dataje dashi yanzu yadawo tabashi kudinsa"""

Tashige dakinta takulle"" jikinta sai kyarma yakeyi"" bayan fitarta gidan kubrah tafito daki tana kallon ameena tasheke da dariya tace Anty yanaga duk kintsurene????

Tanisa badoleba bakisan halin inna huwaile ba wlh masifaffiyace babana ma tsoronta yakeyi nayi mamakin daharkika mareta batace komaiba""

Kubrah tasake shekewa da dariya tace aiyauta gamuda daidai itah kudinne kuke kyaleta na tabbata yau saitakwana gudawa"" sallama sukaji akofar gidan""

Ameena tace shikenan wlh tadaukoman yan sanda"" kubra tsaki tayi tace kwantarda hankalinki Anty indai inagidan nan wlh ba dansanda zatadaukoba tadauko alkwali ni daidai nakedashi danni walkice daidai kugun uban kowa"" tayi maganar tana Jan mayafii tafitaa fuuu

Tana bude kofa taga maibaro dakaya"" akatunan da Usman yayiwa ameena duka tadibe"" kubrah cike da mamaki haka tayita daukar kayan tanakaiwa cikin gidan saida takwashe duka sannan tacewa danbaron kafadamata nace ta saurari sammacii akotu sainasa andaureta""

Takoma cikin gidan"" tasamu ameena tanabuda kayan""" tace waiyanzu Anty fisabilillah duk kayanki matar nan takwashe kallifa harda abinci kuma kizubamata ido???.

Matar nanfa ba itah tahaifekiba??? Tanisa toyazanyi kubrah ni fitinane banaso kawai Dan azauna lafiya itah abun duniya yadama "" nakyaleta aiba anan za atabbata ba"" kubrah tace hakane Amman hakurinki yayi yawa Anty aiwannan wlh tacutardake sosai tunfarko danasani aida sainasakata tsallen kwado wlh agidan nan""tare suka kwashe da dariya""

Ameena tace koyanzu aitatsure nibanyi tsammanin tanada tsoroba wlh"" kubra tamiyar mata"" da  kayanta duka dakinta

Danbaro yana komawa yashaidawa huwaile sakon kubrah saiga huwaile tabarke dazawo"" yinin ranar daki tawuni kulle dataji motsi anshigo gidan tashige karkashin gado"" saida aka kwashe sati biyu sannan huwaile tasoma fita"" Amman batasake gigin zuwa gidan ameena ba""

Ko ameena tazogidan nan babu ruwanta da itah"" tsayin shekaru uku da aurensu Amman batasamu cikiba"" kokadan Usman baidamuba alokacin Abdul yayi aure matarsa"" Hauwa"u

Watan bikin Abdul ameena tasamu ciki"" alokacin kuma Allah yabudewa Usman kofofin arziki kasuwancinsa yafara habaka saigashi ansoma damawa dashi cikin masu kudin garin

Tuni yasiye babban fili kusa da gidansa""" akasoma gini"" hawa hudune akayi gini Wanda yakeshine"" bayan cikinta yashiga wata Tara"" tahaifi danta kyakkyawa kinkowa Wanda yarasa sati yana zagayowa akaradamasa suna khaleed

Sosai Usman yakeson yaronsa"" suna kuladashi bama kamar kubrah"" kaleed yanada shekara daya mahaifin Usman alhaji adamu yarasu bayan doguwar jinya dayayi sosai mutuwarsa tagirgiza su Usman

Sunagidan har akai sadakar uku sannan sukadawo gidà"" su hajiya sunagama takaba hajiya hannatu tace araba gado abata na yayanta damakuwa tanajin haushin Usman saboda kudinda yayi lokacinda akabasu kudi suja jari da danta kabeer duk ya halakarda nashi wajen Neman mata"" dakuma shaye shaye""

Babu wani bata lokaci akaraba akabawa kowa hakkinsa"" take ta tattara yayanta da dukiyarta suka koma bauchi damacenne tushenta"" mahaifiyar Usman tahademasa  dukiyartà data kannensa yafarayimasu kasuwanci dasu shikuma nashi yahade danasa"""

Cikin shekaru uku Alhaji Usman yazama dai dagacikin masu kudin Nigeria"" idan za akirga masu kudi a Nigeria inhar baizo nadayaba babu shakka zaizo nabiyu"" tuni angama ginin gidansa yatare tareda matarsa dakuma dansu kaleed Sam alhaji Usman baida sha awar yin aure"" saboda ameena tanayin bakin kokarinta wajen biyamasa bukatarsa batagajiya da yawan bukatarsa kuma azamansu basutaba yin fadaba kowannensu hakurii gareshi"""

Kaleed yanada shekara biyar kubrah tayi aure"" mijinta yana karatu maleshia"" aurensu dasatiii daya sukadaga cikin jirgi zuwa maleshia


Dajine mai matukar duhuwar gaske"" bakajin motsin komai awajen hartakukàn tsuntsaye""" zaune take saman wata shimfida"" tana fuskantar kogon"" wata karaaa najiii wacce tayi sanadin zaburata hardawacce takezaune

Bishiyar kukarda takecikin kogon tasoma amsa kuwwwa wacce tasakani rufe kunnuwaña"" wata wutace tayi tartso tareda walkiya haske yafaltsu sama saiga bishiyar tarabe gida biyu"""

Wacce takezauñe awajen tasaki murmushi""" lubabatu kenan wacce akafisani da lubcy!!




Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 15
      By
Gentle Lady💃🏽


Lubcy yar  kasar bauchi ce Amman iyayenta  duka aikin gwamnati sukeyi zamane yadawo dasu"" legos

Su biyarne awajen iyayenta hudu maza itah ce kawai mace"" iyayenta rikakkun yan boko ne shiyasa sukeson yayansu suyi zurfi wajen karatun boko baburuwansu dawai susaka  yayansu islamiyya"".

Sudai burinsu yayansu suyi karatu inhar anaganin karshen biro da takarda babu shakka yaransu zasugani saikuma akayi rashin sa a lubcy dakikiya ce yanda kukasan dusa haka kanta yake bata iyah rike komai harta sunanta bata iyah rubutashi daidai

Tunsanda take primary batada wani kokari duk akayi jarabawa ita take kulle ajinsu"" babu yanda babanta baiyiba komai takeso zaisiyamata Amman abanza dayake babanta maikudine sai akarika badakudi anazauna mata jarabawa hartasamu ta kammala primary da secondary sai yaturata America

Acen tahadu da wasu mugayen kawaye sadiya"" da rabi atu  sajida  da anisa"" dukkanninsu hausawane"" tare suke tsula tsiyarsu saboda duka basada kokari kodasunje ajima babu abunda suke iyah ganewa

Zaune take cikin skull dinsu wata bayeraba tana kusa da itah tanawaya department dinsu daya da itah kusan duk akai jarabawa itah take lashewa"""

Aranta tace wannan dai babu alamar kokari gareta kodayake baridai nasamu nakullah abota da itah konasamu inji metakesha takeyin wannan kokarin

Tashi tayi tataka zuwa inda take tace hye"" sannunkida hutawa"" tadago takalleta tace yewwa sennude""

Lubcy tace zan iyah zama"" anan??? Tasaki fara a bademuwa zauna"" lubcy tazauna tabata hannu sunana lubabatu Amman zaki iyah kirana da lubcy
.tajinjina kai tace am heelin"" by name

Lubcy tamurmusa tace suna maidadi"" heelin tawaro ido tace dagaske kinayi?? Lubcy tagyada kai heelin tace tnx dea

Duk da lubcy batagane Hausar heelin Amman haka ta manne mata harsuka sabu"" ansoma shirye shiryen fara jarabawa suna zaune dakin heelin lubcy tanata duba littafi dukda batagane komai dankar heelin tacewani Abu saitaga itah heelin din Sam bata karatu saima danne danne takeyi awaya""

Takirah sunanta tadago takalleta tace yadai friend?? Lubcy tanisa tace waike banganki kina karatuba kinsanfa ankusa fara jarabawa "" heelin tabushe da dariya tace ai wahala saiku nibana karatu ai"""

Tace kamarya??? Toyakuma akeyi kina cinye jarabawa??? "" tayi tambayar tana kallonta murmushi tayi sannan tatashi zaune tana kallonta taciro wani biro tanuna mata tace kinga wannan??

Lubabatu tagyada kai"" tacigaba dazeran nadorashi akan takarda nawa dekansa zairubutamun amsa"" lubabatu tazaburah tace biron???

Heelin tamurmusa tace shifa"" wannan nasamoshine awajen wani boka" sunansa *HATSABIBIN BOKA*  duk wani bukata nawa wajenshi nakezuwa take zaibiyamun dabukata

Nitunda nake baburuwana de karatu" kuma danagama wajensa zanje yasamamun aiki mechau"""

Tuni lubcy tadawo kusa da heelin tace Dan Allah Kawata nima kikaini wajensa yabani""  heelin tace anya zaki iyah kawayenki ma sunyimun magana Amman nace bazasu iyaba saboda kinga addinina de naku badayaba"" bazaku iyah bin dokokin siba

Murya narawa tace wlh komenene zamu iyah indai zaibiyamana bukatarmu heelin tace inde wannan ne atake kuwa"" saiki fadawa kawayenki kushirya sainakaiku

Lubcy tayi ihun murna tarungume heelin"" aranar tasanarda su anisa ranar weekend sukashirya sai taraba acenne garinsu heelin Amman basuje gidansu heelin ba suka samu hotel sukahuta anan"" anasoma kiran magrib sukafita zuwa dajinda yake

Cikin kauyen taraba yake"" ka idar zuwa wajensa"" inrana tayi tsaka harzuwa dare"" tundasukashiga jejin jikinsu lubcy yasoma rawa fitiluni gasunan cikin jejin suna reto kuma ba daure sukeba basu sama basu kasa"""

Gabadaya ajikin heelin suka labe bakin wani katon iccen kuka suka iso"" kasansa anzagayeshi da karaa saman karan lullube sukeda fatuu Na namun jeji"" babu alamar kofa awajen heelince tasoma wadansu suruttai na gwalamniya"" tana kiran sunansa *hatsabibin boka*  take dajin ya amsa kuwa"" takesu lubcy sukasaki fitsariii ganin wutaa Yakama bakin wajen balbal kaitsaye heelin taja hannun lubcy tatuñkàri kofar"""

Aikuwa lubcy tadaddage zatafasa ihu saidaime jitayi muryanta yadisashe"" heelin tasake jawo hannunta tana tirjewa sukashigà tacikin wutar"" saigasu cikin daki maigirman gaske"" su anisa sunawaje jikinsu na kyarma kowacce tacika wandonta da fitsari

Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 16
      By
Gentle Lady💃🏽



Jira suke kawai ace kat su yanki nakare""wata tsawa aka dakamasu wacce tayi sanadin faduwarsu su uku duka asome""

Heelin da lubcy suna samun kansa cikin babban dakin"" saiga wata shimfida kamar tabarmar kaba"" tataso zuwa indasuke tashimfida kanta"" batareda wani tsoroba heelin taja hannun lubcy zuwa saman shimfidar cikin tsoro tazauna gefe zaunawarsu yayi daidai dazubesu aneesa saman shinfidar take kuma suka farfado tamkar wadanda aka watsawa ruwa""
Nanfa suka soma kallon kallon aneesa tasoma kuka"" Dan tarigada ta sadakar mutuwarsuce tazo

Dukansu arikice suke inka debe heelin wacce ko ajikinta da alamu Sam batadamu dakomaiba dantasaba "" wata rikitacciyar tsawa akasaki"" tayi tartso"" bakin bishiyar yasoma cidawutaa tareda wani kugiii

Yan hanjinsu lubcy har motsi sukeyi""" tsawar tacigaba da hauhawa tareda darewar katuwar bishiyar kukar zuwa gida biyu"" wata kujerace tafito zuwa daidai kusa dasu lubcy tatsaya chak"""

Kafin kiftawar ido wata guguwace mai karfii tataso wacce tasaka gabadaya wajen yahautsine baka iyah ganin komai wannan karon ba su lubcy ba hatta heelin saida ta kare fuskarta datafin hannuwanta"""

Su lubcy kuwa gabadaya suka kankame  junansu jikinsu yana kyarma  tamkar mazari"""tsayin mintuna biyar komai nawajen yakoma kamar yanda yake kurar wajen talafa saiga *hatsabibin boka* ya bayyana asaman kujerar""

Heelin ce tafara zungurarsu lubcy dukansu suka"" bude idonsu""  wani gabjejen mutum sukayi arba dashi Wanda basutaba ganin koda maikamadashi ba acikin duniya wannan zaifikyau akirashi da dodo

Kaiyamafi dodo muni saboda katone majiyi karfii yanada damatsa manya manya tamkar irin namasu danbe""" kowanne damtse nashi daure yake dalayu nafata dakuma wani kambum karfee

Kafarsama haka""" baya sanye dariga"" cikinsa dame yake Amman kanaganin gurayenda yatara ajikinsa""" yanada tsayi sosai dantsayinsa zaiyi kamu ashirin"" kirarsa tamkar Wanda yayi alaka da samudawa""

Bakine wuluk tamkar bakin kwalta bakaganin komai afuskarsa sai jajayen idanuwansa"" kowanne mutum tsakiyar idonsa bakine ammanshi kuma zaibarda take zakiyar idonsa"" farace tass saikuma ja azagaye da itah"""

Idan yadaga ido gabadaya"" farin facewa yakeyi "" saidai ja yamamaye gurbin ido"" sumar kansa tanada yawa Wanda yawanta yasa tazubo har akan faffadan kirjinsa tayiwa mummunar fuskarsa inuwa wannan mutum dazaifito waje babu shakka dayawa mutane zasurasa rayuwarsu sanadin yin Arba da mummunar fuskarsa mai kamada ta dodanni""

Tsayawar guyuwar keda wuya yakece dawata mahaukaciyar dariya wacce tasaka dajin gabadaya ya amsa kuwa"" yadauki tsayin mintuna biyar yana wannan dariyar dagabisani yamurtuke fuska tamkar Wanda baitaba dariyaba"" heelin tabuda baki tasoma jero masa kirari"" Saikai takadiri kuma gagare kigudu sagudu sa abokan gaba sugudu"""

Turmin karfe kake shakwaramniya""" Saikai *hatsabibin boka* sugaban duk wani tantirin ajani"" komai Tsagerancin   aljani idan yazo gabanka dole yaduka nasaramaka uban maza uban hatsabibai maidakawa maza gumbaa"""  take yasake kecewa dawata mahaukaciyar dariyaaa

Heelen tasake buda baki  daniyar magana yadaga mata hannu

Yace kafin kice wani Abu inaso insan kokin sanardasu dukokinmu dakuma sharadin mu??? Cikin saurii tace nafadamasu yasarkin bokayen duniyaa

Yagyada kansaa duk dahaka zansake sanardasu dangudun kuskure dakuma fadawa hafushinmu""" kusanii akwai sharadiii guda biyar wadanda zanfadamaku

Inhar kuka kiyaye kuntsira sharadi nafarko"" ma abota sallah basa shigowa fadataa""" duk ranarda zakuzo inda nake karwacce takuskurah tadorah goshinta akasa""

Sharadi nabiyu"" karwacce takuskurah tabada sadaka!! Domin yanadaya dagacikin abunda zaibata aikina"""

Doka ta uku muddin kika fara aikidani babuke basake zuwa wajen wani bokan "" yinhakan kuwaa zaijanyomaki masifa da bala.i dagake harbokan nakii

Sharadi nahudu duk abunda akace kikawo karkitsaya musu ko gardamà idankuwa  kikatsaya watamagana take bakaken aljanu zasu zuke jininki

Doka tabiyar wajibine idan akabaki Abu dole ki aikata idankuma kinki to zaijuye zuwa kankiii""" sannan kuma duk abunda kukagani anan karkutaba idankun kiyaye kuzauna lafiyaa

Tunsa inda yasoma wannan jawabin jikinsu sadiya yasoma kyarma dama yalafiyar kurah kowaccensu tayi danasanin zuwa wajen
yanagama rattafo sharadansa saisuka fara kallon kallo atsakaninsu gabadaya idonsu yaraina fata""

Lubcy tanason yin magana babu halii "" saida yabata izinin magana cikin sauri tace"" dama dama munasone mudanyi shawara

Batagama rufe bakintabà yadakamata wata razanan nar tsawaa wacce tasaka lubcy tayi danasanin maganar

Hatta dakin saida ya amsa kuwaar yace bakuda wannan damar kusani kafin azonan akeyin shawaraa basai anzobaa danhàka Ku kiyaye!!!




Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 17
      By
Gentle Lady💃🏽


Cikin kyarma lubcy ta gyada kantaa heelin ce tace tuba suke"" uban hatsabibai"" sunji kuma  sunyarda da sharuddanka idan muka fitaa zamu turoda kayan aikiii
   yajinjina kai" saiki sanardasu zasuga abunda sukeso""" tadan dukarda kai tace godiya muke""" tasake dukawa tace munbarku lafiyaa"" sannan tamike aitana tashi su aneesa sukai zumbur suka Mike dama Kuwa kamar akan kayasuke"""
 Kamar yanda sukashigo wajen yarufe kansa babu alamar"" kofa"" suna fuskantar wajen"" heelin tasake kiran sunansa saigashi wajen yasake kamawa dawutaa suka ratsa tacikin wutar  saigasu waje""
            Gabadaya dajin yayi tsit saiwani gurnani sukeji kamar na kuraye da zakuna suna nane da heelin harsuka kai karshen"" dajin"" tace duka surufe idonsu

Rufe idonsu sukayi kafin mintuna talatin sukaji tace kubude suna budewa sukagansu cikin masaukinsu"" aneesa cikin tsoro tabuga uban ihuuu tashige cikin zanen gado"""

Heelin takwashe da dariya tace Amman kumanyan matsoratane nibantaba ganin masu tsoro kamar kuba"" jiyanda kuka tsure kamar kusaki zawo awando
 Lubcy tace heelin ai ba kamabane""   ni bana raba dayan biyu wlh fitsarina sau biyar awando idan ancema harda zawo bana musawa sainashiga toilet in tabbatar,"""

Sadiya datake sharce zufa tace wlh nima fitsarina shida awando kai nadaukafa mutuwa zanyi niko amafarki bantaba tunanin zantaba ganina a irin wannan wajenba"""

Wannan anyakuwa mutum ne??? Idankuwa har mutum ne anyi mumm bata karasa rufe bakintaba heelin ta dademata baki tace wlh karkisake duk abunda kikeyi tamkar agaban *hatsabobin boka* kike!!jin wannan furucin yasaka sadiyaa saurin hadiye wasu miyagun yawu masu dacin gaske idanuwanta suka firfito kulu kulu tamkar wacce taiwa sarki karya"" tace nashiga uku kardai yakasheni tayi maganar tana dafe kirjinta"""

Heelin tace bazai kashekiba saidai zaisa akaiki kurkukunsa Wanda yake ganawa bokaye azaba dakuma wadanda suka bijirewa umurninsa cikinsu kuwa harda aljanu"" zamanki acikin kurkukun saikin gwammacewa mutuwarki akan haka domin zakisha azaba iri iri wacce bakitaba tunanin irintaba"""

Zaiyafemaki sabodake sabuwar zuwace bakisan komaiba Amman daga wannan ki kiyaye kisan abunda bakinki zairika furtawa""!!

Duk yanda kike tunaninsa yawuce saninki"" nikaina awajen mahaifiyata nasamu damar ganinsa"" babuwani boka dazaishige gabansa inhar zaku kiyaye sharudansa har abada bazaku nemi Abu kurasaba kudenajin sorofa"" anisa"" nasan kinfisu jin soro"" dukanku kuyanke shawara gobe zamuje musiye kayan aiki"" saimu aikamasu

Aneesa wacce haryanzu batafito acikin zanenda tarufe kantaba tace badai wajen zamusake komawaba??? Heelin tayi murmushi tace ah ah gobedai zakuga yanda zamuyi yanxu kutashi mushi abunshi"" saimu kwanta nagajii woo

Tayi maganar tana mikewa tayi hamma"" sannan tawuce "" dukansu ido zuru zuru suma sukamike lubcy kam dayake tanada dakakkar zuciya hartadainajin tsoro

Sukai wanka suka shirya"" bayan sunci abinci kowaccensu tasamu wuri takwanta dukansu sukayi lamo tamkar masu barci Amman azahirin gaskiya ba barcin sukeyiba zuciyoyinsu sunyi nisa wajen tunanin inda tsautsayi yajefasu kokuma ince sukajefa Kansu

Inkadebe heelin wacce takeyin chat hankalinta kwance"" sai dariya takeyi da alama tanayin fira mai dadi wacce take sakata nishadi""

Intakaice maku labari darendai kam basu samu barciba kowaccensu saiganin abunda sukajeyi take tamkar anayimata video nashi heelin kuwa tashaki barcinta

Indasuma saida asuba barcin yadaukesu"" basu suka farkaba sai shadaya narana"" bayan sunkimtsa"" sunci abinci suka shirya heelin tace suje suyi"" abundayake gabansu"" suyiharamar komawa"skull"taresuka fita zuwa kasuwa dama sunzo dakudii heelin cemaidubawa""" duk inda sukaga bunsuru baki Wanda bashida sulkin farii dakuma maifari akai"" uku kawai sukasamu sukai ciniki"sukabiya""   heelin tariko su sukafito kasuwan""koda sukafito basugakomai  hannun heelin ba"""
Lubcy ce tace ke heelin ina suke??? Tayi maganar tareda soma waigen bayansu takesuma su aneesa sukasoma dube2  kowai tabarsu abaya""

Heelin dariya tasoma yimasu tace waiku kundauka nasakesune??? Ai hadiman aljanunsa sundaukesu yanzun haka akwai sauran su sunajirah mukarasa siyen sudauka tace yanzu wajen da akesiyarda kaji zamuje"

Sudaikam binta kawai sukeda kallo haka sukaje sukasiye kaza maiwake Wake sai jajayen zakaru tareda farar kazaa""

Kamar yanda wadancen sukabace hakama kajin"" daganan sukadawo gidansu sukayi haramar komawa skull

Ranar sukadawo america kowaccensu tasamu Biro acikin kayanta"" zokuga murna tunkafin suzana jarabawar"" hankalinsu kwance basayin wani karatun har akasoma jarabawa

Dazaran sun kalli Question sukadorah biron takezasuga sunata rubuta amsa sukansu basusan tayama amsar take fitowaba

Bayan ankare jarabawa dukansu sukalashe"" wannan shine ainahin yakininsu akan wannan *hatsabibin bokan*tundaga lokacin inhar bukatar waninsu tatashi cenyake zuwa hartakaima suna iyah zuwa mutum daya badole saida Dan uwansaba
Harsuka kammala makarantar sunkomagida kowacce dasakamako maikyau ranar mahaifin lubcy saboda jindadi yayimata kyautar dankareriyar mota tareda babbar waya""

Tun lokacin batasake waiwayar *hatsabibin boka*ba saiyau kome ketafe Da itah oho!!




Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 18
       By
Gentle Lady💃🏽


Lubcy tasake sakin murmushi ganin  wata katuwar darduma  irinta sarakai tafito acikin katon kogon kukar tayiwa kanta mazauni akasa"" nantake iska mai karfiii tatashi tamkar ana hada hadari tsawa tareda hargowa sukacika dakin kogon"" saiga *hatsabibin boka* ya bayyana asaman dardumar nantake komai dayake wajen yatsaya chak iskar sannu ahankali tanatse""

Lubcy tadago cikin girmamawa tafara mika gaisuwa tareda somayimasa kirari"" saikai hatsabibi uban hatsabibai"" abuga adaka sai kalwa""saikai namijin gaske uban duka bokayen duniya""

Shugaban shaidanu uban hatsabibai kai kanka tsoron kanka kakeyi"" anbuga dakai anbarka"" kowa yatabaka yanemawa kansa bala i

Saikai uban dawa uban kangararru"" takawarka lafiya kaci zamaninka kaci nadangi bakada tsoro bakasan tsoroba " komai gaba kabashi ba nayaba""

Sosai *hatsabibin boka* yake jin dadin kirarin nan tace gaisuwa nake shugaban bokaye kaiyajinjina""
TaCe ayimun afuwa tsawon lokaci bandawo nanba kasancewar daga garinmu zuwa nan akwai tafiya yanzun mawata bukatace dani maigirma"" ina

Hannu yadaga mata yace bakomai munsan komai agamedake domin munatare dake"" dangane dabukatarki kuwa tuni nasanda itah wanne irin miji kikeso???

Take lubcy tawashe hakorah jin *hatsabibin boka* yasan da bukatarta"" tace inason mijine na nunawa sa a kyakkyawa maikudi kuma maitashin kuruciya tunbayan gama karatuna zuwa yanzu duk wadanda sukezuwa wajena basuyimun ba

Indai kudi sunadakudi saidai suntsufa sannankuma basuda kyanda yadace ace kamata nazama mallakinsu"" wannan dalilin yasaka nazo wajenka domin nasan Kaine zakasharemun hawayena kabani mijinda yatara dukkan abunda nalissafo ayanzu

Tanarufe bakinta *hatsabibin boka* yakece da dariya yace kinkawo kuka inda za asharemaki hawayenki yadaga hannunsa sama saigawani madubi maigirma ya bayyana ahannunsa""

Take yashafa gilashin yanawadansu suruttai""" saiga hotunan mutane sun bayyana acikin gilashin su goma sha biyar""

Yanuna mata yace kiduba saiki zabi daya dagacikinsu"" jikin lubcy har rawayake sai kallonsu takeyi tarasa wanne zata zaba" saboda kowanne yanada nashi kyan babu makusa"""

Idonta yatsaya akan wani matashin saurayi Wanda yafisu kuruciya daganinsa ko aure dakyar idan yayi"" takafeshi da ido batako kyaftawa"""

Ganin hakan yasaka madubin yajuya wajen *hatsabibin boka* take yakece dawata mahaukaciyar dariya yace wannan shikika zabà??? Cikin sauriii tace ah

Yagyada kai sannan yaja layi daidai saitin photon"" zuwa yan mintuna kadan yadago yakalleta yace wannan saurayin sunansa Usman sunan mahaifinsa adamu mahaifiyarsa binta yanada kanne biyu wadanda suke daki daya Hafiz da kubra

Akwai yan uwansa kabeer da ahmad 'abokinsa daya Abdul"" yanada mata sunanta ameena sunada yarodaya kaleed yanzun shekarar yaron biyar aurensu shekara Tara"" asalinsu yan kano ne Amman yanazaune akaduna anan yake kasuwancinsa

yanafità kashashe""" yanzun haka yana maleshia"" kwanansa biyu acen gobe zaikoma gida"" mahaifinsa yamutu yabarmasu dukiya maitarin yawa wacce basusan adadintabà

Dukiyardà hatta tattabakunnen su bazaitaba talauciba"" yakai karshen maganar yana kallonta
Tayi shiru Sam batayi tunanin yanada aureba"" tadago murya cikin damuwa tace yanzu yaza ayi Sam wlh banasoñ kishiya banyi tunanin yanada aureba""

Yace kwantardà hàñkàlinki komai awajenmu maisauki ne ammanfà kisañi muddin tàñaràye bazaitaba aurenkiba
Lubcy tadafe kirjinta tace  nashiga uku to akasheta kawaiii

Yasake kecewa dawata mahaukaciyar dariya yace wannan daidaine"" kisa aranki yazama mijinki"" tace toyanzu taya zanganshi alhalin yana kaduna ina legos ????

Yasake kwashewa da dariya yace ko birnin sin yake kina sokoto kisani dazaran munturashi dole yaje inda kike"" abudaya zakikoma gida kafin mugama aikinmu akan matarsa daganan zamu sanardake  inda zakuhadu

Amman akwai sharadinda zangindayamaki karki kuskurah tsautsayi yakaiki fadar sunansa inhar bashine yafadamakiba hakazalika danginsa kinuna tamkar bakisan komai gamedashiba sai idanshine yasanardake

Sannan aranar kiyi shigar mutuncii"" komai dazaifaru tsarinane saiki kalli abunda zaifaru""

Yasake daga hannunsa sama saigawañi madubi karami ya bayyana ahannunsa"" yamikamatà
Bayan takarba yace kasancewar tafiya mainisaçe tsakaninmu
Na mallàkà miki dai daga cikin madubin taskar *hatsabibin boka* aljanin da yakegadiñ wannañ madubin sunansa dukursusu""" kisani wannan aljanin hatsabibin aljanine kuma azzalumi inharkikai wasa da madubin nan dakansa zai halakaki babuwanda zaitaba tunaki aduniya

Kirikeshi tamkàr rayuwarki karkibari wani yaga inda kike ajeshi"" bacewarsà  daidai yakeda tonuwar asirinki

Dazarañ kinada wata bukata tokishàfi fuskar madubin kikirah sunana sau uku zanbayyana acikinsa sàiki sanardani bukatarki




Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 19
      By
Gentle Lady💃🏽



Duk maganarda zamuyi saimuyita atake tamkar kina nandin wannan saukine agareki bake kadaiba akalla akwai su wajen mutane sama da milion daya wadanda basa iyah zuwa nan saidai muyi magana cikinsu akwai yan kasuwa dakuma manyan attajirai dakuma shuwaga banni"" danhaka saiki kula Kuma ki kiyaye idan kinfita saiki kirah aljaninda ke kulada wannan madubin domin yakaiki gida"" dankiyaye lafiyar madubin

Yana gama fadar hakan wata guguwa mai karfiii tazo"" take wajen yakaure da iska"" guguwar tayi sama saida tagama shawagi  kasar wajeñ tadare gida biyu tashige karkashin kasa bat tabace komai nawajen yakoma daidai

Lunby mikewa tayi madubin yana hannunta takaraso bakin kofar bayan takirah sunan *hatsabibin boka* kofar takama dawuta takutsa tacikin wutar tafito"""

Tsaye tayi tana tunanin sunanda yafadamata na aljaninda ke gadin madubin Sam tamanta"" lallai dole taje hotel takwana washe gari takoma gida"" jakar hannunta tazuge daniyar saka Dan karamin madubin wata tsawa aka dakamata wacce takusan sakawa lubcy tasakii madubin

Cikin daga murya akace"" wannan shine kulawar dazaki bashiii kisani duk kika kuskure abudaya rayuwarki zatashiga hadariiii yanda maganar taketa amsa kuwwa acikin jejen tuni lubcy tasaki fitsari duk darashin tsoronta Dan abuguda takijini aduniya taji anyimata maganar mutuwa kokuma ace zatarasa ranta

Natsuwarta batagama dawowaba wata iska maikurah tataso wajen tayi sama""" wacce dazata daga kanta bazataga karshen guguwarba""" tuni lubcy ta kankame jikinta kafin tayi wani motsi kawaitaji an sunkuceta anyi sama"" take yalulaya da itah cikin gajimare

Al amarinda yasa lubcy tasome danta sadakar kasheta zaiyi"" batakara sanin meke faruwaba saidai ta far fado taganta kwance akan gadonta"" Jakarta tana gefenta . gakuma madubin ajiye akusa da itah dasauri tamike tasoma yandube dube babushakka dakinta take"" idanuwanta suka sauka akan agogon dakin Wanda yabuga karfe hudu na dare"""tashafo fuskarta yaukam tasake tsorata da lamarin wannan bokan

dolema akirashi *hatsabibin boka* domin yaci sunansa"" mikewa tayi daga kan dagon"" tasoma neman inda yadace taboye wannan madubin""" wani karamin akwati tadauko tasakashi aciki tarufe takaishi cikin lokar karamin gado"" take akwatin yafito yadawo kasa""

Tayi shiru aranta tace watakil mazaunin baiyiba tayita tunanin inakuma zatasaka "" karshen lokar kayanta takasa tabude tasakashi

Tana ajeshii""  taga yazauna daram tasaki murmushi"" sannan tarufe lokar tacire kayanta tawatsa ruwa takoma takwanta"""

Batasake farkawaba sai washe garii""" mamanta Sam batasan lokacindà tadawoba tasan kodasuka kwanta batagidan"" Amman sambata damu data tambayeta inda tajeba aganinta ai itah ba yarinya bace daza atuke da tambaya danyanzu tarigada ta mallaki hankalin  kanta

Wautarda dayawa mafiyawan iyaye sukeyi ayanzu"" waisunaganin yayansu sungirma sun mallaki hankalinsu bazasutaba kaikansu indasukasañ zasu cutuba

Shinmezai hana idan yayanku zasufita kutambayesu inazasuje???" Idankuma sundawo kutambayesu indasukaje harsukai dare

Sautari yammata da samari sukan lalaceñe"" asanadin rashin kulawar iyaye mafiyawan lalacewar tarbiyar yayanmu"" munada hannu aciki iyaye sunataka muhimmiyar rawa wajen lalacewar yayansu

Kowa yasan akwai kaddara Amman Kuma akwai sakaci"" Allah yashirya mana zuri armu ameeen
Lubcy kam hankalinta kwàñce tacigaba da harkokinta

       *KADUNA*
Ameena  ce cikin kitchen din gidanta tareda masu aiki tanahadawa Usman abinci domin sunyi waya lokaciñda yake shirin shiga jirgi

Tana saran kara sowàrsà biyar na yamma"" gefenta kaleed ne tsaye yana kallonta duk inda tayi yanabiye da itah kamar jela"""

Harsuka kammala hadamasà hadadden girki Wanda tasan yanaso gabaya tajeresu akan dinner"" anan tazaunarda kaleed tàzubamasà soyayyen nama tace yazauna tana zuwa
.
Ta umurci mai aiki tagyara wajen"" akashare akagoge tàjona turaren wutaa"" tuni gidan yarude da kamshi ganin harhudu tagota dasauri  tahaye sama dantayi wankaa

Tana turah kofar dakintà tàyi tozalii dawasu manya manyañ beraye kowanne daya yakai girman Dan akuya sunada kunba zaro zaro hakorañsu kowanñe yafitodaga bakiñsa zuwa saman labbansa idanuwansu manyane tamkàr kwayayin fitila saidaisu jajir suke kamàr gautaa ihu tafasa dakarfi tarufe idonta ganinsuna tunkarota tàkejikinta yasoma kyarmà

Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 20
      By
Gentle Lady💃🏽



Jikinta sairawa yakeyi tanatsaye takasayin komai jira kawai takeyi taji yakushin berayen domin tunda take aduniya bata taba ganin beranda yayi girman koda Dan kaza ba banlantana kuma akuya

Shiru taji tsayin mintuna ahankali tasoma bude idonta bataga komaiba tawaiga ko ina bakomai ahankali tasaukarda karamar ajiyar zuciya"" tayiyu bakomai bane kawai kallonda tayi dazune kaset din horo shine takejin tsoro"""

Batareda wani kokonton tunanin taba takarasa dakin kawaidai saitaji jikinta yayimata ba dadi"" fitowa  tayi takoma bangaren Usman tayi wanka tayi sallah""" sannan tayi kwalliya duk da bawata kwalliyace tayiba Dan jikinta jitakeyi tamkar anlikidamata shegen duka""  

Bayan tagama shiryawa cikin kananun kaya Riga da sket""" masu karamin hannu"" tadauko Karamin hijab fari tasaka"" yar karamar fuskarta  tafito tayimata kyau"" saukowa tayi kasa wajenda tabar"" kaleed""
Yana zaune kasa kusa dashi wadansu kadan karune manya"" masu katon kai  kowanne daya girmansa yakai girman  tsarii idanuwansa jajir tamkardai nawadan cen berayen""" cikin daga murya tace kaleed bar wajen nan""" tanarufe baki wadan nan manyan kadangarun suka soma keta wata muguwar dariyaa "" wacce ta karade dukan falon"" shikuwa kaleed sam baijitaba saiwasa yakeyi dasu yana dariya""" jikin ameena yasoma bariii tasoma ja baya ganin suna nufo inda take "" daidai shigowar Usman"" aidagudu taruga tafada jikinsa taboye fuskarta"" 

Cikin firgici yayarda jakar hannunsa yana tambayarta lafiya meenal?? Menene yafaru"" dahannunta ta nunamasa wajen kaleed shikuwa kaleed maganar babansa ce tasaka yadago kansa dasauri yadauko Dan kadan garensa  naroba mai batir yarugo yana oyoyo papa"" jikin mahaifinsa yashige Usman yashafo kansa da hannu guda

Sannan yamaida kallonsa wajen ameena yace please meenal kidago kikalleni nigabadaya  kintayarmun da hankali"" 

Shiru yaji batace komaiba yasake girgizata saiyaga ta langwabe dasauri yature kaleed gefe yadagota illaikuwa AMEENA tadade dasomewa"""  Cikin sauri yakarasa jikin kujerah ya kwantarda itah"" dasauri yadebo ruwa yazo yaballe murfin robar yasoma yayyafamata"" 

Tasaukarda ajiyar zuciya ahankali tabude idonta zunbur tamike tasake kankameshi tafashe dakuka """ jikinsa yajawota murya araunane yace waimenene meenal Dan Allah kisanardani kinsan halinda zanshiga idan inaganin kukanki???

Har abada bazanso kizubarda hawayeba muddin inaraye Dan Allah kidaure kisanarsani menene dalilin kukanki ???
Cikin muryar kuka tace Yaya kadangaru naketa gani masu magana"" akusa da kaleed

Usman yakalli kaleed shima kaleed din shiyake kallo Wanda tunda mamarsa tafadi yakuramasu ido yana makale da kadan garensa  naroba

Usman yayi murmushi  yace meenal kadangaren robar kikewa kuka?? Inakin saba ganinshi dashi sai alokacin tadago daga jikin Usman cikin tsoro tsoro takalli kadangaren

Tsayin mintuna tamaida kallonta wajen Usman tace wadanda naganifa manyane kuma suna dariya"" kaleed yayi charab yace mom nan ake karamasu gilma"" yamatsa wata yar kunama saigashi yayi tsayi yanadaga kansa tamkar kadangaren  gaske"""

Usman yace tokingani dama bakisan haka yakeba"" idan tsoronsa kikeji kibari na konashi damacen kece kikasiyomasa danni banason ire iren wadan nan 

Dakinsa duka kincikashi da Teddy waiduk kayan wasane bakisan gunki bane kike ajewa badole saida wadan nan zaiyi wasaba kwanaki inaganifa harda macijin roba kika siyomasa"""

Ameena tasaukarda gajeruwar ajiyar zuciya tace wlh natsorata Yayana"" tashi muje kayi wanka kakwaso gajiya"" karan hancinta yalakuta yace bayan kintayarmun da hankali

Ninadaukama nine na aikatamaki wani gungumen laifii harna tanadi kalar hukuncinda zanyiwa kaina"""

Murmushi tasake taboye fuskarta cikin jikinshi tace rufamun asiri wanne laifi zakamun nikuwa aduniya Wanda zaisakani kuka"?? Nayi kuka lokacinda nake marainiya tunranarda na aureka  bakinciki baisake tunkaroniba Wanda zaisa kabatamun rai hartakaini gayinkuka

Inaji araina nagamayin kukan bakinciki aduniya Allah yasharemun  hawayena yahadani da nagartaccen namiji Wanda kowacce mace zatayi gurin samun abokin rayuwa kamarka

Ina mai addua kowacce mace tasamu miji mai kwatankwacin halayenka""" ido yakwalo yace daina zigani hakamana

Kinsa nafarajina asama ina shawagiii karkisa kaina yafasu dayawa"" 
Tayi dariya gaskiya nafada baban kaleed Dari bisa daribakada makusa duka dabi unka irinna nagartattun mutanene

Yaja hancinta yace kamaryanda kike nagartacciya ba kisani nayarda dakefiye dayandà nayarda dakaina kyawawan halayenki sune sukesakani karasonki

Babu shakka ke yar ajannace"" cikin zolaya tace idan kadagamuñ kafarkaba""" yayi dariya yace aituni nadage kafar wlh meenal da aljanna ahannuna take dakuwa kullum sainabaki itah sama dasau goma

Murmushi tayi tamike dagajikinsa yadago yana kallonta  zaiyimagana tadorah Dan yatsanta saman labbansà tace ka Adana kalamanka. Harsaimun kwanta yanzu katashi muje kayi wanka kaci abinci kafin nan lokacin sallah yayi saikaje masallaci
.
Yamike yana murmushi yace tomuje Amarya dariya tasaki tajindàdin sunanda yakirata dashi sosai tanajin dadin yakiratà dasuñan

Tayigaba yanabayanta zuwa bangarensa tahadamasà ruwan wanka wadanda sukasha turareñ wanka masu kamshi

Tataimaka masa  yarage kayan jikinsa yashiga toilet din"" tarufemasa kofa yana zolayarta waibazata tayashi wankanba saboda yadebo gajiya





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 21
      By
Gentle Lady💃🏽


Dariya tayi tace hannuna ciwon kai yakeyi kaidai kagama kafito tayi maganar tana karasa rufemasa kofar toilet din

Wajenda yake ajiye kayansa tanufa tabude tafitomasa da jallabiya"" tafesheta da turare"" wayarsace tasoma ringing

Tadauko ganin sunan little sister akan wayar yasaka tadauka cikin fara a tareda sallama dayan bangaren aka Amsa"" tace la Anty kicehar yasauka

Tayi dariya tace ah wlh yagidan yamaigida"" kodayake aibakibada sakon gaisuwa akawomun ba"" tace la anty yaya baifadamakiba???

Tace baifadamun meba ??? nasan dakince agaidani aidabai mantaba dasaukansa zaisanar dani"" kubrah tace afuwan matar Yayana takaina kema kinsan bazan rasa turo sakon gaisuwata agunkiba inajindai gajiyar jirgi tasaukarwa Yaya yamanta da babban sakona

Tayi murmushi to ankarbi uzurinki dukansu sukasa dariya kubrah tace Anty ina my son dina"" tace hmm sarkin rigima aini sonake babansa yakwasheshi dakayansa yaturah makishi cen konahuta da rigimarsa"" 

Kubrah tace la Anty wlh kaleed baida wata kiriniya  kamar sauran yara"" tace aidole kice hakan tunda shine naki""" ya amarci yakuma kasar""

Tanisa Alhamdulillah wlh Anty nayi kewar gida sosai "" Ameena tace yaushe akai aure dukafa wata biyar yanzu kice kinyi kewar gida bayankuma kinatareda rabin ranki """
Kubrah tace hmm Anty kedai ayita sha ani waidama haka aure yake kullum inason intambayeki Amman saiyakureni da kallo idan inawaya bahalin inyidan sirri 

Dariya tayi tace wannan ma sirrine zaman aure ba komai kikagani azaman"" aure hakuri zakiyi wannan itace ibadar""" tace hmm Anty bazaki ganebane wlh nihar gajiya nakeyi saikace agogo kullum babu Hutu

Ameena tanisa tace nagane mana Amman azancenki bazan ganeba kubrah shilamarin aure akwai sirri acikinsa barganin ina mace yar uwarki kiyi tunanin sanardani abunda kike fuskanta tareda mijinki 

Kisani kowanne dan Adam dakalar tashi sirrinki ki adanashi kizama maikunya nisam irin wadan nan maganganun wlh kunyarsu nakeji menene amfanin kazauna kana fadar mijina kaza mijina kaza "" duk yanda mijinki yake kibarwa zuciyarki saikiyita hakuri watarana sai labari kodai kinason yasake aurene???

Cikin sauri tace la ah ah Anty Sam bahakan nake nufiba kawaidai inadauka kowama hakan yakeyi kamar nawa"" Ameena tasakeyin murmushi tace ah ah
Aiyanda kikasan halitta akwai banbance banbance atsakaninsu hakayake ako ina akwai banbanci

Tanisa nagamsu Anty kuma insha Allah bazansake maganar ba""tace yauwa Kanwata "tace Anty wai ina Yayana??? "daidai fitowarsa wanka"" tace ga shinan yanzun yafito wanka"" yanadaure da towel daya hannunsa yanarike da karamin towel yana goge ruwan jikinsa yace naji ana gulmata

Dariya tayi tace bafa gulma mukeyiba"" yace tayazangane bayan inajinku kunata kus kus kus"" dariya takeyi harda kubrah 

Tace sister ce takira taji kasauka lafiya"" yanataje sumarsa yace ainasan itace Dan idan ba itaba babuwanda zaikirah wayana kidaga"""

Aisaiki fadamata nasauka lafiya """ tace ainafadamata tace Allah yahutarda gajiya""" yace Ameen sai ayi sallama ayidaniko"" yayi maganar yanarike kunkuminsa dariya ameena tasoma tace kinga sister zamuyi waya anjima"" 

Usman yace anjimadai meenal saikace wasu yammata"" tokaratunfa wazai karani tuni ameena takatse kiran tunda tagano abunda zaifada

Tace kai baban kaleed wannan saikasani jinkunya agaban yar Kanwata""" baki yatabe yace wayajiyo kitaso kishiryani yunwafa nakeji"""

Wayar ta aje tana murmushi ganin yanda yayi maganar kamarwani yàro dangoye""" saida tashiryashi suka sauka kasa"" kaleed yanasaman kujerah yana gem da TV

Saman dinner suka karasa tagabatar masa da abincin ita tarikabashi abaki saida tatabbatar yakoshi alokacin magrib takawo jiki yawuce masallaci itakuma taka she TV taja hannun kaleed zuwa sama sukai sallah"""

Usman baidawoba sai bayan isha"" falo sukatsaya suna kallo saikusan shadaya sukahau sama lokacin kaleed yadade dayin barcii

Bayan sunyi wanka suka kwantaa""tunda suka kwanta ameena taketa mugayen mafarkai"" har asuba""" batasamu barci maidadiba saida sukasake kwanciya bayan haske yafito

Sai wajajen karfe Tara tafarka""" koda tatashi har angama shiryamasu break"" bayan sunyiwanka suka karya"" tashirya kaleed cikin kayan makaranta"""

Zasu wuce yasheka dakinsa saigashi yafitoda kadangaren  roba"" dagudu ameena takarbe tayi wurgi dashi tace mezakayi dawannan a skull kuma???

Yace mom anty dinmu dukana takeyi idan nayi sulutu"" gobene wani kadangale yashigemata ajiki tanata ihu taluga munata dariya shine danje danawa databugeni inli amatashi"""" yakai karshen maganar yana dariyaa

Ameena da Usman masaida sukadàara tace aimaganinkà kenan"" inba shashancibà mezaisaka surutu amakaranta anacikin aji ana karatu

 Yace mom banikadai nake sulutuba" tace kodakai dawanefa kadaina sannan bakyau tsoratarda musulmi kasani

Yace to ai itah ba musulma bace sai wannan karon Usman yayi magana yace kaiwaye yafadamaka???

 To aibata saka kaya ilinna mom kuma idan tashigo aji bata sallama"" ameena tace umm kaga kuwuce zaku makara idan kabiyewa  surutun wannan

Tariko hannun kaleed din sukafità Usman yabi bayansu"" harwajen mota tarakasu""" saida taga tashiñsu tanadaga masu hannu sannan takoma cikin gidan 

tana turah kofar shiga tayi Arba da katon kadangaren yanaganinta yanufota"" cikin saurii saboda tsabar firgita maimakon tayi waje saitakoma cikin falon"""
Kadangaren kuwa yatasomata  haikan tuni sukafara tsere acikin falon!





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 22
    By
Gentle Lady💃🏽


Zagaye takeyi tanaganin kamar zaikamota kuma haryanzu bakinta yakasa furta addua Sam tama manta dawata addua

Tana tsaka dagudun siket din jikinta yatadeta tafadiii'' take tayuyo  tafashe da kuka mai karfiii ganin kadan garen yana dosota idanuwanta ta tamke waje daya""

Muryar maitayata aiki taji tana sallama"" Amman batayi gigin buda idontaba""" mai aikin tamatsa inda take tace uwar dakina meyasameki

Cikin tsoro tace kadangare bakiganshi ba gashinan gabana ! Tawaiga bataga komaiba saicen nesa dasu tahango kadangaren kaleed naroba yanata yawo"""

Tayi murmushi tace uwardakina babuwani kadangarefa narobane kawai na kaleed shikuma zai tsorataki??? Cikin tsoro tsoro tabude idonta taduba bataga komaiba saicen tahangoshi

Takurah masa ido"" tasaukarda ajiyar zuciya tace wlh tabawa biyana yaketayi cikin falon nan munata zagaye dashi""" tabawa tace  kawaidai dankinsaka tsoronsa arankine kike ganin haka"" barikiga" tabawa takoma saitin kadangaren tana  kallonsa "" tawuce aikuwa saiyabita"" tasaka hannu tadaukeshi tace kinganiko bawai yanabinki bane kawai haka na urarsa take tana aikine da inuwar mutum

Ameena tasaukarda gajeruwar ajiyar zuciya tace Amman ya akai kikasan haka tabawa??? Murmushi tayi tace uwardakina kinmanta nataba fadamaki nayi aiki gidan gomnan garin nan""????

Babu kalar kayan wasanda banagani awajen yayan matansa shiyasa nisam basa bani tsoro duk da wadan nan kayan basuda amfani"" dama wadan nanne wadanda alhji yake siyowa kaleed rakumi maiyin labbaikallahumma labbai"" ko wadan nan Na urorin masu addua duk Wanda"  kadanna dakalar addua rda zaiyi tashiga bandakine kota fita gida dakuma ta fitowa bandaki

Haka wacce take da complete Qur'an kowace surah dakin danna tasoma karatu irin wannan ne yadace da yayanku  tanan ne yaranku zasu iyah addu o.in neman tsari kuma su iya karatu idan sunabi ahankali Amman nagake Sam bakitaba kunnasuba saidai kullum  kibarsa  da macizai dakunamu"""" ameena tanisa hakika abunda tabawa tafada gaskiyane 

Tunfarko data nunawa kaleed son wadancen abun dabazaiso wadan nanba"" gashi yanzu yasaba dasu abune bai wahala yayarda akarbesu daga gareshi"" tabawa takatsemata tunani tace me za adorah uwar dakina????

Tace kiferah doya yau sakwara za ayi"" Ina ladidi batazoba yau"" ??? Tabawa tace wlh nabiyamata jikanta  bashida lafiya saisama nayo saurii idan masu girkin safe basu tafiba juwaira saita tayani idan aikin yanada yawa

Ameena tace ina tunanin sunwuce Amman jeki kigani"" tace to sannan tawuce anan tabar ameena zaune takurawa kadangaren 
 Ido tana tunani duk da tanatsoronsa  tanagani tamkar yana biyarta

Aikuwa kamar jirayake tabawa tabar wajen yayo wajenta "" cikin zafin nama tamike"" ta cakumeshi tayi waje""" sai kalle kalle takeyi"" wani katon dutse tadauko tayarda kadangaren tahau dukansa saida tayimasa"" raga raga batir da injinin sa duka sukafita dagajikinsa gefe takoma tana maida numfashi tamkar wacce taidanbe""" tayi tsayin mintuna biyar awajen sannan tatashi takoma cikin gida

Saiyanzu hankalinta yadan kwanta"" sama takoma tadauko wayarta tashige kitchen wajen tabawa

Karfe shabiyu akadauko kaleed daga skull tun abakin kofa yacikaro da gawar kadan garensa tuni yayi wurgi da jakarsa yasoma tattare kadangaren yana kuka

Yanda yake kukan harcikin gidan anajinsa cikin falon yashiga yanata kuka dakarfi tamkar Wanda akedukansa

Tabawa da Ameena kusan taresuka fito suna tambayar lafiya??? Ganinsa dauke da tarkacen gawar kadangare yasaka ameena taja tsakii cikin fada tace karufewa mutane baki""

Yace mom waye yakashemun adangalena??? Tace uwarkace akan wannan zakadameni dakuka maza kazubasu ashara ko inzaneka

Tsayinsa yayi tace bazaje kazubasuba saina hadaka kaida kadangaren nawatsaku Shara tayi maganar tanayowa wajensà

Yakwatsa ihu yayi waje dagudu yana nabani nabaniii gudu yake yana waigenta yaga kotakusa kamashi yanafita da itah da tabawa saida sukayi dariya

Danyanda yake kiran yabani kuma yanakuka yana waige sai abun yabaka dariya""tabawa ta tsagaita da dariyarta tace waiwaya kashemasa kaya??/

Tace nice wlh tabawa haka kurum Abu saitsoratani yakeyi idan baiyi hankaliba gabadaya kayan wasar wlh saina cinnamasu wuta

Kamar yasan inatsoron wannan shegen kadan garen"" kullum yana nan makale ajikinsa ainayi maganin abun tayi maganar tana shigewa kitchen tabawa Tamara mata baya""""

Kaleed kuwa wajen yakoma yayi zaune akasa yarungume kadan garensa yanata kuka""" yanasharar majina


Karfe biyu Alhji Usman yakunno hancin motarsa gidan " idanuwansa suka sauka akan kaleed dayake kwance akasa yana barcii

Baikaiga inda ake aje motociba yatsaya  yàfito dasaurii yatunkari indayake barciyake sai Jan ajiyar zuciya yakeyi alamar yasha kukaa





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠


chapter 23
       By
Gentle Lady💃🏽



dukawa yayi yadaukeshi"" aikuwa yanajin antabashi ya zaburah yakwallah kara mom kiyi hankuli wlh inason adangalena""" idanuwansa arufe yake magana"" Usman yasharemasa hawaye yace bude idonka nine jin muryar dadyn sa yasaka yabude idonsa 

Yace yi shiru kadaina kuka wayadakeka"" ??? Yanajan ajiyar zuciya yana kuka ahankali"" yace mom ce takashemun adangale"" yayi maganar yana nuna masa""" yakalla yace toyi shiru bari kuka zansiya maka wani yaduka yadauki jakar makarantar da kaleed yayar yanufi cikin gida

Ameena tana cikin falo" taci kwalliya""cikin wani tsadadden less tahakimce saman kujerah tanajiyo maganarsa da kaleed suna shigowa tasha toka tadauke kanta gefe "" kaleed yanaganin haka yasake makalewa jikin dadyn sa""" Usman yalurah dahakan murmushi yayi sannan yayi sallama "" ta amsa kawai batasake cewa komaiba

Yace yaukuma mom hardani fushin akeyi dani ??? Yanda yayi magana batasan sanda tayi dariyaba saikuma tadaure fuska ta harari kaleed tace bance karkasake dawoda wannan shegen kadangaren gidan  nanba??? 

Aikuwa yasake bare baki saida usman yarufe bakin yace yishiru sannan yakalleta yace waimeyasa mom yanzu kikacika fadane??? Dabahaka kikeba""

Tace hmm nidai kadaina cemun mom wlh dolensa yazubardashi ko inhado sauran kayan wasansa in cinnamasu wuta"" wannan kadangaren tsoratani kawai yakeyi wlh nayi danasanin siyensa""" 

Shiru yayi yana nazarinta  sannan yamaida kallonsa wajen kaleed yace kaleed kaga mamanka tanajin tsoron wannan kadan garen kazubardashi shara kokanason mom tayi fushi dakai??/

Yayi sauri girgiza kai yace yauwa my son kaga itah tasiyomaka tunda yana bata tsoro aisaimu bashi kashi muyardashiko???/

Dariya yayi yace ah dady shima murmushi yayi sannan yasaukarda shi yace oya sheka kazubardashi shara"" yace to sannan yaruga dagudu Usman yakalleta  yayi murmushi yazauna kusa da itah yace madam adan Samman murmushin mana"" wannan tamke fuskar yayi yawa kodai bakisan yanda kikai kyauba tamkar Amarya wacce za akaita gidan mijinta

Dariya ameena tasomayi tana jefansa dakallo mai tattarreda soda kauna"" 

Waje yakaishi saida yakarasa dandakesa sannan yawurga cikin kwandon Shara

 Dasauri yadawo cikin falon wajen Usman yakarasa yace dady nayardashi saida nasake masa bulala tunda yana olatamun mom

Usman yashafa kansa yana murmushi yace kabawa mom hakuri to yajuya wajenta yace mom kiyi hakuli ""ko kallonsa batayiba Usman yace  kace Dan Allah bazansakeba yasake maimaita  abunda Usman yace haryana kuka" yarike kunnensa kansa tashafa tace nahakurah Amman karkasake kansa yagyada to yajuya yace dad mom tahakurah""" 

Yadafa kansa  Allah yamaka albarka"" yamike muje maza kacire kayan nan Tare suka Mike zuwa sama saida suka shirya sukasauko kasa sukaci abinci

Daren ranar mugayen mafarkai da ameena takeyi duk akan wannan kadangaren ne tanaganinsa yatashi yahade kansa" ranarma batasamu wani ishasshen barciba saida tayi sallar asuba

Bayan fitar Usman wajen aiki da tsoro tazauna cikin falon dazaran taji motsi takalla wajen dasauri"" idanuwanta sunasauka akan katon hotonsu dayake manne abangon falon saigani tayi suna motsi takesuka fara kyalkyatar dariya ba kakkautawa gabadaya suka cikamata kunne 

Hannuwa tasaka tarufe kunnenta tareda fashewa da kuka"" suma kamar hadin baki sukafara kuka aikuwa saigabaya hotunan dasuke falon kowanne yafashe dakuka

Kukan yacigaba daratsa dodon kunnenta kowanne cikin murya daban daban""" take tahada gumi awajen sallamar tabawace tasaka ameena tadago kantaa ganin halinda takeciki yasaka tabawa saurin karasawa wajenta tana tambayarta lafiya???

Cikin tsoro tace bakiji dariyaba ??? Wadancen hotunan suketa dariya saikuma sukafara kuka

Tabawa takalli hoton bataga komaiba  tamaida hankalinta wajen TV dayake kunne tace to ai uwardakina cikin  TV ake kukan

Inajin kinsaka tsorono aranki shiyasa kike ganin hakan dama babu amfani saka wadan nan hotunan bakisaniba mugayen aljanu sunasamun wajen zamane agida idan sukasamu hotuna agidan koda rukiya za ayi sukan labe ajikin photon tayanda bazasu fitaba 

Mizai hana kisaka na ayatul kursiyu aiyafi wadan nan""" hawaye ta share tace taimakamun incire hakan kuwa akayi duka tacire hotunan harna dakinta""

Wasa wasa ameena tasoma ramewà tana lalacewà dagatsaye abunyasomà damun Usman"" yayi tambayar duniya tafadamashi meke damunta tace bakomai 

Tanemi yakaita wajen dangin mahaifiyartà"" baikawo komai araiba yakaita bayan yayimatà tsaraba maiyawan gaske"" kwananta hudu acen yaturah driver yadaukota yan uwa sunata kewarta 

Gidansu akawuce da itah ranar tashafirah da malam haryake tambayarta meyake damuntaa""" duk tarame saidai tace masa bakomai"""

Sai dadare Usman yajedaukarta bayan isha I"" sunatafiya amota tanagefensa kaleed yajima dabarci"" takuramasa ido tana murmushi

Ya murmusa yana kallonta yace wannan kallofa Amarya kamardai bakisanniba??? 

Murmushi tayi tasanne kanta kasa tanawasa dayan yatsuntà""" Usman saijanta yakeyi dafirah harsuka kaigida""""
.bayan sunshirya sukaci abinci sukai shirin kwanciya sunraya wannan Daren fiyeda Daren amarciñsu

Sosai Usman yasamu yanda yakeso saikusan biyu sukai wanka suka kwantaa"""" karfe hudu darabii Usman yafarka agigice jin kiran sunansa DA ameena takeyi dasaurii yatashi yakunna wutar dakin abunda yagani yamatukar tayarmasa da hankali jinine yakefita tabaki da hancinta sare sare duk yabata zanen gadon"""

Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 24
      By
Gentle Lady💃🏽


Cikin kidima yayi kan gadon yana girgizata yana kiran sunanta dakarfiii Amman ina ko motsi batayi""" 

Daukarta yayi kamar jaririya yafito gidan tacikin na urah yashigo zuwa kasa saboda yayi sauri tunkafin yasauka yasoma kwalawa driver kirah 

Cikin barcinsa yaji ana kiransa"" firgigita yafarka yafito dasauri yana ganin halinda alhaji  yakeciki Yakoma dasauri yadauko key din mota riga ahannu yafito 

Haryanzu usman jijjiga ameena yakeyi idanuwansa sunyi jajir tamkar gauta kadan yarage yasoma darzar kuka saidai kawai danyana namijine yanada juriya"" tuni driver yabude masa bayan motar yashiga da itah shikuma yazagaya yafita dasauriii zuwa hospital"" 

Tunkafin sukai yakirah family doctor dinsu yasanar dashi  yace yana asivitin dan yana dutyn dare ne"" sunakaiwa yanabakin asivitin tareda wadansu nurse tareda gado""" yanayin pkng yadaukota akaturahta saman gado zuwa emergency

Abakin kofa akabarshi Saikai kawo yakeyi  tamkar yayi kuka"" tunda suka shiga da itah sukahau dubata saidai Ashe raiyayi halinsa"" zuciyarta ce tabuga!! 

Sosai yayi mamakin ciwon zuciya dahar yacita haka haryayi mata wannan illar Amman Sam shi baisan ciwon nata yakai hakanba"""

Jiki asanyaye yafito dakin tareda sauran nurse "" Usman yana ganinsa yasoma tambayar lafiyar meenal"" 

Doctor yajikinta ???? Tasamu saukiko???? Dan Allah zan iyah ganinta?? Banaso narasata doctor haka yayita jeromasa tambayoyi tamkar maitabin hankali

Gabadaya yabawa likitocin tausayi"" yace doctor bakace komaiba yajikin meenal din?? Yanisa yace tasamu  sauki yadafashi saidai kayi hakuri Usman

Koda kukashigo asivitin nan tuni Allah yakarbi abarshi""" cikin razana yadago manyan idanuwansa yadorasu akan doctor din

Hannunsa yasaka yature hannun doctor dayake kan kafadarsa yayi cikin dakin dagudu doctor yabishi yana kiran sunansa

Yanaashiga yajaye kyallenda aka rufeta dashi fuskarta tayi fayau tamkar tana murmushi  tayi haske dukawa yayi akan guiwarsa yariko hannunta cikin nashi

Cikin rawar murya yace yanzu dama tafiya zakiyi kibarni meenal duk wannan abun dakikemun na bankwanane take yafashe dakuka """

Doctor ne yadafashi yace hakuri zakayi Usman lokacintane yayi babu magani saimuyi mata fatar Allah yajikanta yasa tahuta"" ayanzu adduarka kawai takebukata

Mikewa yayi yayi hanyar fita""" saidai yaji yarabke yafadiii dasauri yakarasa wajensa yanakiran nurse "" dagudu sukazo akadauki Usman akadorah akan gado take aka bashi taimakon gaggawa

Ganin yafarfado yasaka akajona mashi Karin ruwa tareda allurar barcii "" driver"" yana waje baisan halinda uban gidansa yake cikiba"" saida doctor yasanar dashi""" 

alokacin ansoma kiraye kirayen asuba" wayarsa doctor yadauko aka Kira hajiya akasanarda itah""" 

Karfe bakwai darabi yamata acikin kaduna tuni labari yakai gidansu ameena"" mahaifin Abdul da Abdul suna asivitin 
Tuni akadau gawar ameena zuwagida dangin ameena saidai sukaji mutuwar kamar dagasama

Koda yafarfado hajiya da Hafiz sunakusa dashi hawayene yasoma sauka gefen idanunshi hajiya tace sannu babangida"" 

Runtse idonsa yayi yace mom tatafi tabarniko??? Tashafo kansa tace addua zakaimata babangida lokacintane yayi"""

Yanisa inason ganinta kicewa Hafiz yakirah doctor"" takalli Hafiz tace yakirashi yace to tareda juyawa Abdul yadawo kusadashi yadafa kansa Amman yakasa cewa komai"" yana tausayin abokinsa  danyasan yanason ameena sosai

Doctor yanazuwa yace badamuwa yana iyah zuwa"" taresuka fito suka dunguma"" saigidansu Ameena sunsamu har anyimata wanka""" Usman yamatsakusa da itah yayi mata addua tare akai mata sallah 

Tatara mutane sosai akakaita makwancinta""" Sam babu Wanda yatuna da kaleed saibayan da hajiya takoma gidan tasameshi yanata kuka sosai ta tausaya masa""" 

Saida akai sadakar uku kubra tazo tareda mijinta"" itakanta tasha kuka datasamu labarin"" Usman yakoma shiru shiru dagashi har kaleed sunrame danbasacin  abinci sai hajiya tayi dagaske

Bayan wata biyu darasuwar Ameena zuwa yanzu Usman yafauwalawa Allah lamarinsà"" Yakoma wajen harkokinsa Amman haryanzu baikoma daidaiba

Hajiya takoma tareda kaleed hannunta saboda haryanzu yaki kwantarda hankalinsa"""

Kwance take tanajuyi cikin barcinta"" zunbur tatashi "" tasoma dube dube mafarkinda tayi kamar almara"""ihun murna tayi tamike yauzataga handsome dinta  towadanne irin kayama zatasaka tarasa inda zatasaka ranta danjin dadi

Mikewa tayi tafada wanka"" agurguje tayi wanka tashirya cikin atamfa takawo hijabinta tasaka harkasa""" 

Wayarta kawai tadauka tafita unguwar kowa yayi mamakin ganinta da hijabi akafa take tafiya tayi nisa da unguwarsu sosai wata motace tayo cikinta sauran kadan tabugeta tayi gefe dasaurii Amman dukda haka saida yasameta  aikuwa tafadiii kiiii yatsaida motarsa yafito dasauriii dasauriii yana furta innalillahi tadago takalleshi tuni tawashe hakorah tunawa dazancen *hatsabibin boka* yasa tayisaurin dukadda kanta gabanta nafaduwa

Muryansa maisanyice taratsa dodon kunnenta sannuko inafatardài bakiji rauniba??? Kaitagyada masa tamike tana karkabe hijabinta"" yakuramata ido takeyaji Sonta yashiga ransa talurah da irin kallondà yakematà dadi kamar tafasa ihu arantakuwa tana aiyanawa ashema yafi kyau afili





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 25
      By
Gentle Lady💃🏽


Muryansa tasake katsemata tunani yace inazakije yanzu??? Cikin sanyin murya tace mamana ta aikeni inyomata cefane"" yayi murmushi yace to idan bazaki damuba muje mana kisiyo daganan sainakaiki gida nabada hakuri 

Tadan waro ido tace hakurin mezaka bayar nifa banji ciwoba"" yasake gyara tsayuwarsa yace duk dahaka sainakaiki gida daganan sainaga waje aiko ??kobakyaso zumuncin mu yadorene?? nalurah kinaso kidatseshi iyah nan""

Munmushine ya subuce akan fuskarta tace waceni aiban isah ba Amman naga kaima kanada uzuri kawai kabarshi nagode zanhau Dan adaidaita"" harararta yayi cikin wasa yace tozanga yanda zakihau Dan adaidaita gani kusa ashekuwa yau akwai rigima

Tace la abunfa duk baikai hakaba"" nayarda muje Amman idan mukaje unguwarmu nesa dagida zaka ajeni"" yace najidai muje 

Dakansa yabude mata gaban mota sukashiga yaja yasoma tafiya kifa nunamun wajenda akesiyarda kayan miyan"" batareda takalleshiba tace kana cikin legos kace bakasan inda ake siyarda kayan miyaba"""

Murmushi yasaki yace ashekuwa yauzamuyi tayayo agari idan harsaini zan kaimu wajen"nida nake bako saiyanzu takalleshi tace wai dagaske kake???? Yace todakumafa nayimaki kamada yan Lagos???? 
Tace ausu yan legos harwata kamane dasu???? 

Yace sosai aidakingansu zakiganesu kullum suna sanye da dangakallun kaya"" sannan Kuma basada Faraa gadukkan alamu kema ba yarnan dinbace""tace ya akai kasanhaka??? Yace dabi unki mana"" ke komainakima so nice

Murmushi tayi maidan sautiii tace kaidai wlh kafaye zolaya!" Sunakawowa daidai wata kwana tace nan zakabi""" tayita nunamasa hanya harsuka kawo 

Karyafa tasheramasa dankuwa bata tabazuwa siyen kayan miyaba"" toyanzu idanma tafita batafitoda ko asiba"" karfa asirinta yatonu yagano karya tashekamasa jitayi yabude mota""" zatafita yayi saurin dakatarda itah yace dame dame za asiyo??? Cikin rawar murya tace komaima

Kaitsaye yawuce wajen maikayan miyan dayake inyamurine yace yahadamasa kayan miya"" na dubu biyar komai ahada""" 

Nankuwa akahada komai harda cucumber da kabeji dasu carrot" saida yanuna mata yace dubakiga ko akwai abunda babu asiyo"" tace komai akwai sannan akazuba bayan but sukakoma 

Tace kayan miyanfa sunyi yawa"" yace to kibawa wani idan sunyimaki yawa"" kidai nunamana hanya karmu bace""

Dariya tasoma kai malam akwaika daban dariya wlh""  takasan  ido yake kallonta tana matukar burgeshi sosai"" yace basunana malam ba sunana Usman"

Ido tawaro tace sunan uncle dina"" yace dagaske kenan nima nazama uncle" dinki""" tace sosaima
Yanda sukeyin firah hankali kwance idan kagansu saika dauka sundade dasanin juna"""

Suna kawowa unguwarsu tace ajeni nan zankarasa"dakafa
Batareda yakalletaba yace babu amfanin zuwan nawa kenan tunda banga gidaba""" 

Ahakan tanuna masa gidansu""" yayi hon maigadi yahangame masa kofa yakutsa kan motarsa kamar wani dangida""" bayan yatsaya da motar"" yajuyo yana fuskan tarta yace gashi harmunkawo Amman bakifadamun sunankiba"""

Naga abun yar rowar sunace""murmushi tayi taboye fuskarta cikin hijabi tace sorry aiban isah nayiwa uncle rowar sunanaba"""

Yamurmusa yace nifa banyarda da uncle din nanba''' tarausayarda kai tace saime???? Yace aboki daganan kuma saiyayi shiru yana kallonta yanadariya kasa kasa

Murmushi tasakeyi tace bari nashiga gida kar mom taga nadade""" yaduba agogon hannunsa yace shikenan ataimaka abani phone no"""
Wayarsa yamika mata afuskar wayar PIC dinsane da Ameena kaleed yana tsakiya""" talurah da pic din saikawai tawuceshi tasaka masa Tamika masa 
Tace katsaya koruwa kasha""" ah ah inasaurine wlh akwai abunda nazoyi gobema zankoma Amman zansake zuwa gobe saimu gaisa"" 

Tabude motar tafita"" kayan miyar yafitomata dasu tabawa maigyaran fulawa tace yashiga dasu cikin gidan

Sukai sallama tasake masa godiya tawuce yace amm jimana"" tajuyo ciikin wani salo Wanda yakusa sumarda Usman da ido tamasa akamar menene??? Yace sunan???/

Tadan dafe kai sorry namanta lubabatu tanafadàr maganar tayicikin gidan Usman yabita da murmushi wani sanyi""yaji yanaratsa dukkan sassan jikinsa rabonsa dayaji farinciki haka tunranarda meenal tabar duniya 

Murmushi yayi yashiga motarsa akabude masa get yafita Sam baiso zuwa legos dinba Ashe arzikine yake kiransa aransa yake ayyana hakan

Tanashiga tasamu mom dinta tanadubà kayan miya""" tanaganinta tace lubcy wadan nan kayanfa??? Batareda takalletaba tace kiyi amfani dasu wanine yasiyamun tawuce bangarenta

Mom dinta tajidàdi aranta tana adduar Allah yasa saurayintañe dantamatsu lubcy tayi aure

Tanashiga daki tacire hijab tawurga akan gado tasoma tikar rawa tana murna harda ihu wayartace tasoma ringing tadauko dasaurii ganin sabuwar nomber tasan shine takidagàwa hartayanke akasake kirah batadaukàba saida yasake kirah tadauka cikin yanga kamar yanaganinta ta amsa sallamarsa sannan tace waye





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠


chapter 26
       By
Gentle Lady💃🏽


Murmushi yasaki maidan sautiii yace nashiga tara yanzun har ammanta dani ba aje ko inaba anya kinason zumuncin nan yadaure kuwa"""

Gabantane yafadi karfa garin jan ajinta ta lalata komai""" tayi saurin taran numfashinsa tace bahaka bane uncle kaga aibansan nomber nakaba kuma kasan waya yana sauyawa mutane murya dat way banganekaba!! Amman kayi hakuri

Ajiyar zuciya yasaukar wacce har lubcy tajiyota  yace najisanyi araina"" itama murmushin tayi"" sukataba firah daganan sukai sallama 

Lubcy tamkar tazuba ruwa akasa tasha Dan Murna"dole"yau taturàwa *hatsabibin  boka* kayan aiki nagodiyà!"""
 daren da itah dashi kasa barci sukayi kowa yana tunanin dayansa Usman jiyake tamkar kirjinsa yafaso zuciyarsa tafito saboda tsabarso nda yakeji nata yanahudashi"""

Kwance take cikin dakinta tana danne danne dawaya saiga kiran Usman yashigo"" da murmushi tadaga tareda sallama daya bangaren ya amsa"" 

Yace gani akofar gida"" tawaro ido harkazo??? Harararta yayi kamar tana ganinsa yace dolekice harnazo danke bakidamu da niba nida nadamu dake darenjiya kasa barci nayi"""

Tarike baki yihakuri uncle bawai haka nake nufiba ganinan fitowa"" takashe wayar akahau safe safe da feshe feshe saigata tafito das da itah tasaka hijabinta tafita""" mom dinta tanacikin falo zaune tace mom nayi bako kibawa kande kayansha takaemasa muna falon bakiii

Tawuce abunta" yanajingije jikin motarsa yakurawa kofar gidan ido yanaso kawai yaga bullowarta""  kirjinsa sai harbawa yakeyi dasauri dasauri yakuramata ido yanda take tafiya    tamkar hawainiya komai nata tsaf

Kamar yanda yaraja.a akallonta itama haka shigarta yau Tayimasa kyau yau kananun kayane ajikinsa sabanin jiya dayasa manyan kaya idan kaganshi wlh koda anrantsemaka bazaka yarda yatabayin aureba   sai idan kaganshi da matar kakuma tabbatar lallai itace 

Damurmushi takaraso inda yake tagaidashi"" tace karaso ciki sukajerah harcikin falon bakin"" tazauna nesa dashi suka gaisa""" yace badadewa zanyiba zuwanayi kawai mugaisa zanwuce

Sam bataji dadiba Dan fuskar tama. Tanuna hakan cikin sanyin murya tace sai yaushe kenan?? Nasan dakyarne idan zakasake dawowa legos tunda bawajen zuwanka bane

Yayi murmushi yanawasa da key din motarsa yace zancen baya kikeyi aiyanzu zuwa legos yazama dole dankuwa nayi babbar mantuwa acikinta

Tace mantuwa?? togashi baka fitaba kakoma  kadauko mana"" murmushi yasaki maidan sautiii yace kinaso ayimun ihu ace nasaci abunda banawaba!! zandauka Amman bayanzu zanjirah  har abun yaxama mallakina

Tace inamaka fatan alkhairi""yace nagode daidai mai aikinsu tashigo dauke datire cike dakayan motsabaki na marmari dakuma danbun nama"" saida ta aje taduka tagaisheshi """ 

Ya amsa cikin skin fuska"" zatafita yakirata kudii yaxaro cikin aljihunsa zasukai dubu goma yabata"" taki karba saida yamatsa mata sannan takarba tayi godiya""

Bayan tafita bajimawa yaduba agogo yace yakamata intashi haka"" karnayi dare ahanya"" gashikuma ban gabatar maki dakainaba"" 

Nasandai bakimanta sunanaba"" inaxaune a kaduna yanzu haka anan nake tafiyarda harkokina Amman iyayena akano sukeda zama 

Mahaifina Allah yamasa rasuwa inada kanne biyu kubra tayi aure sai Hafiz nataba aure karkiyi tunanin ni saurayine fuskarsa cikin murmushi yafurta hakan""

Yanisa Amman Allah yadauki abarsa tatafi tabarni dayarona daya kaleed tuni idanuwansa suka koma jajaye yace inasonsa sosai fiye dakomai arayuwa banajin zanso wani Abu samadashi 

Idan naganshi yana debemun kewar meenal azuciyata"" banason abunda zaitabashi komai kankantar abun" wlh lubcy yaron tausayi yakebani 

Yanzun yana hannun mahaifiyata "" inason narikajiñ dimin jikinsa akusa dani nasan mom bazata banishiba tunda bansan yanda zanrika kuladashiba aganinta zanraba hankalina gida biyu

Shine nakeson nayi aure" kozansamu wacce zatakula damu dannikaina inabukatar kulawar""" yadago yakalleta yace kinji takai taccen tarihina aranta tace duk nasan wannan"""

Afilikuwa tace Allah sarki Allah yajikanta""" yace Ameen toyanzu mekikace??? Tadanyi yake tace nikuma mezance???? Yasake gyara zamansa yace tomenene amfanin sanardake tarihina???

Takada kafada maybe kasanar danine as ur friend""" """ yace ya inatubka kina warwarewa"" dariya takwacemata ganin yanda yayi maganar

Yace dolekimuñ dariya danbakyajin abunda nakeji gamedake""basaina tsaya kwanakwanaba agaskiya lubabatu tunda naganki naji nakamu dasonki 

Sobana wasaba""" kuma aurenki zanyi bansaniba kozaki iyah aurena amatsayina nawanda yataba yin aure yakai karshen maganar yana kallon fuskarta

Tadanyi Jim yace please lubcy"" tarausayarda kai tace tokabani lokaci inyi shawara"" yayi saurin tarar numfashinta yace  yanada kyau hakan amman nanda gobeko????

Tawaro ido gobe kuma??? Nanda satidaya dai"" bakiyabude cikin mamaki yace um lallai dasaurana bansamu shigàba""bari nasamu wajen zama a legos

Dariya tasoma tanarufe bakinta tace lala nina isah nafurta hakan ayihakuri to abani nanda kwana uku"" yace biyudai koshidai sainakai zuciyatà nesa danzata iya bugawa!!  tace to abarshi biyun
.
Yace yauwa amman please karkice baxaki aurenibà"!! Danzan iyah shigawani halin"" tayi murmushi saidai kajini kasha lemun mana tayimagana tareda nunamasa tirenda kedauke dakayan marmari""" 

Yace banajin zan iyah cin wani Abu harsainaji matsayina yayi maganar yanamikewa"" tace Amman kasandai banji dadiba acekayi bako koruwan gidanku baishaba

Ahakan nasan iyah matsayinà"" yace yihakuri kinsan bansan yanda akeyin zancenba Ashe idan kazo dole kasharuwa

Zansha Amman bayanzuba sainasañ matsayiña

Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 27
      By
Gentle Lady💃🏽


Tace shikenan"" saimunyi wayako"" yace ah Amman aizakimun rakiyaba ko anan zakibarni kamar saniyar ware??? 

Dariya tayi kai wlh kacika sa mutum dariya mujeto"" yace tofa dagayanzu kuka zanrika sa mutane.

Nidai banceba baban kaleed""" sosai yaji dadin sunanda takirashi dashi har farincikinsa yakasa boyuwa  yace nagodefa" daidaii get din gidansu tamasa sallama  takoma gida"" 

Yabawa maigadi kayanda yasiyo mata yace yakaimata cikin gida sannan shima akabashi dubu goma"" zokuga bakinsa harkunne saikirari yakewa Usman shikam saidai yace kara da akayi

Cikin gidan yashiga dasauri yana sallama  niki niki dakaya"" ya aje gaban mom yace uwar dakina gashi inji alhaji"" takai bakin kofar dakinta tace barsu wajen mom tayi shigewarta

Mom tabita dakallo aranta tace anya lubabatu batada aljanu??? Koda tafita gidan nan tana fara a Amman tadawo fuska yakunai  yakunai kamar lawashin albasa"" idan yakwana

Maigadine yakatsemata tunaninta yace yaunashiga uku uwardakina tana nema tamun bakinciki yanzun wannan Dan zinariyar tana nufin baiyimataba???.

Hajiyarce tace wayafada maka ado?? Kaidai bakagani saika maganta tashi katafiii"" yace toya za ayi hajiya wayaki alhairi"" dubu gomafa tashi daya wlh hajiya kingansu a aljihuna yayi maganar yana bubbuga aljihunsa yacigaba tunda nake samartakata kawowa yanzu babu Wanda yataba mun kyautar dubu goma

Keko dubu biyu ma duka alhazan dasuke zuwa wajenta shegiyar rowa tayimasu kanta aduwawu babuwanda yajeso yacire naira yabawani""" 

Amman wannan tunda naganshi nasan Dan albarkane""🤓 Dan Allah hajiya kirarrasheta  kartace batasonshi 

Dama inada kwadayin dakwalen kajii kafin ayi auren na murmure"tace ado fisabilillahi  kakoma wajen aikinka waikai meyasane kafaye shegen surutune uwa aku"""

Yace saihakuri hajiya sai hakurii"" matsalarda akasamu kenan"" ranarda aka haifeni gidanmu anataron biki wannan hayaniyar tayan bukiii haya haya sanadinta tatakulo nakuda nayowaje

Ashe surutun yanbikin yataba kakwalwata tun ina jariri idan nasoma dariya ina witsil witsil sai abun yabaki tsoro"" 

Yanbarka kowayazo saboda dariya sai yayi hawaye babana yakaini wajen likita yana tsammanin haukace takamani koda likita ya aunani yagano inada dauke da ciwon surutu kuma babu maganinsa harsaina cinye kaza Dari

Tunda aka haifeni zuwa yanxu inakan lissafi naci kaxa ashirin dabiyar hargamida  ta amarcina kinga koyanzu akwai sauran 75 tukuna inwarke

Hajiya tace aikuwa baburanar dazaka warke dawannan surutun"" yace dainamun wannan fatar hajia kina raina surutuna kinsanfa magana jarice inaji ajikina dawannan surutun nawa zanyi arziki

Tace ahakan? Aiwannan surutun bayan duka babu abunda zaijamaka"" aisaidai yajamaka tsiya"" um um hajiya raina kamafa kaga gayya"" inamai tabbatar maki sainayi govno agarin nan

Hajiya batasan sanda takwashe da dariya "" auwal ne yadawo yayan lubcy yanata faman hon yaji shiru afusace yafito zuwa cikin gidan 

Yace haba ado waikai saiyaushe  zaka daina wannan surutun Mara amfani nayi minti goma inabuga hon Amman kananan kanazuba

Yace haba maigida toyazanyi banjikabane kasan bakyau akunkume baki saiyayi duyi""😆

Hajiya tanadariya tace waifa cewa yayi saiyayi governor agarin nan akan surutunsa"" auwal yaharareshi yace Na mahaukataba

Ai wannan nangaba gadinma saiyarasashi "" yawuce fuuu kazokuma kabudemun kofa"" ado yawuce yana ta zuba ganinan zuwa karka gididdibani gida gida

Lubcy tanashiga dakinta tayi wurgi dahijab tacije danyatsa tanakasa tanadabo kenan """ asheni banyi komaiba

Dasake wlh kenan yafison dansa akaina???zai aurenine dannakula dayaronsa"!! Babbar magana nasan muddin yaron yanaraye lallai bazansàmu wata soyayya awajensaba

Zairaba soyayyarsa gida biyune"" ina bazaitaba yiyuwaba dole naga *hatsabibin boka* yaudin nan Saikai kawotake acikin dakinta tanajiyo hirar ado da hajiya taja tsakii mstw surutun ado  haushi yakebata idanyana magana bakinsa harkunfa yakeyi

Tana zaune saman kujerah tana tunanin maganar Usman saigakiràñsa yashigo"" tadauka sukagaisa yakesanarda itah yakai  

Tayimasa sannu Allah yahutarda gajiya"basujima suna firaba yamata sallama yace ansoma kiran magrib zaiwuce masallaci sukai sallama yakashe wayar sake mikewa tayi akan kujerah  batajima dakwanciyaba barci yadauketà

Momdinta tashigo tasameta tanabarci saitafita karfe daya tafarkà taje tawanko idontà tadawo lokar kayantà tabuda tadauko karamin akwatin tabude tadauko madubin yana nan"" yanda ta ajeshi

Saman gado tazauna tasahanñu tashafiii madubin tareda kiran sunan *hatsabibiñ boka* sau uku saigawani haske yashiga tacikin madubin saigashi yawashe *hatsabibin boka* yabayyana samañ kujeràrsa

Cikin damuwa tace akwai Matsala sarkin bokayen duniya haryanzu tanakasa tanadabo""" yace yakikeso ayimasa??? Bataredà fargabar komaiba tace aturashi wajen mamarsa aganina zaifisàmun kwanciyar hankali darayuwa ataredani
.inaso gabadaya danginsa sumanta dashi sukuma mantada mahaifiyarsa

Inaso Usman yaji aransa baitaba haduwa dawata diyamaceba saini aciremasa son kowa adasa nawa"""

*hatsabibin boka* yakeceda wata hatsabibiyàr dariya yace angama lubcy jeki kikwanta  abunki kafin nandakwana 2 angama komai

Bakaken aljanu sunagaisheki sunyaba dajininda kika aikomasu kamar walkiya hasken yafita daga madubin boka yabace tamkar walkiya.

Lubcy tamaida madubin cikin jindadin bukatàrta tabiya takoma saman gado tayidaidai tañabarçiñta cikin kwanciyàr hankali.





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 28
       By
Gentle Lady💃🏽



Bayan kwana biyu kamar yanda sukai da Usman saigashi yakirata"" cikin zumudi tadauka cikin rausaya"

Tace aminci yatabbata agareka annurin zuciyata"" wani sanyine   yaràtsa sassan jikinsa yalumshe idonsa sannan yabude

Yace taredake ma abociya sassanyar murya

Dafatar kina lafiya??? Tasake rausayarda kai qalau nake tareda tarin dinbin soyayyarka

Yace wow Amman najidadin hakan sosai abisa dukkan alamu tarkona yakama tsuntsu

kanta tagyada tace aitunima "" yace Amman shine baki sanar daniba kikabarni inata shawagi duniyarda bakowa acikinta saitarin furanni da ababen more rayuwa. Tace to aikuwa hankali kwance tunda kasamu jindadi aduniyar 

Yace kisani bazasu burgeniba matukar babu tauraruwa acikinta"" 

Zuciyata tayita jiran bakuwar soyayya wacce zata tallafeta zuciyata tazama fanko bakomai acikinta tana bukatar abokin zamanee

Cikin zolaya tace to ai akwai kaleed"" gakuma marganyiya mamarsa"" shiru yayi kamar maison tunawani Abu daga bisani yace makotanku suke??? Cikin rashin fahimta tace suwaye??? 

Yace kaleed danaji kin ambata mana"" takyalkyale da dariya tace kainifa danka nake magana akai""

Yace danakuma??? Wanda zakihaifamun inmunyi aure??? Tace dankadai nayanzu yace Wayafadamaki inada da??? Yaushe harnayi auren dazan haifi da??? Wani sanyine yaratsa zuciyarta lallai boka yagama aiki saitace bakaine kasanardaniba kanada yaro mamansa tamutu

Dariya yayi haryana rike ciki yace badainiba abunda nafadamaki kawai nacemaki nataba aure Amman fa ba azahiriba cikin mafarki mukai auren kuma munyi soyayya doguwa da itah Amman bata haihuba saitarasu  tanarasuwa nafarka abarci wlh yanzu ko kamanninta bazan iyah kawomakiba kingakuwa shirmene

Tasake shekewa da dariya tace hakane" yace yanzu idan kin amince zansanarda mamana anemamun aurenki 

Dannagaji dazama gauro abokina yayi aure nibanyiba nasan rashin auren ne yasaka naketa mafarkin nataba aure tace shikenan zan sanarda dad komai yace zakaji bayani yace yauwa tawan

Sunkwashe tsayin wata daya sunabuga soyayya usman yamaida legos tamkar dakin kwanansa bayawuce kwana biyu baijeba

Yasaba da ado maigadi sosai lubcy tagabatardashi ga mahaifinta a matsayin wanda zata aurah tasanardasu saurayine baitaba aureba

Baban lubcy yace yaturo magabatansa"" ranarda lubcy tasanar dashi ranar yayiwa kano tsinke"" tunda mom taganshi sai fara a yakeyi sunazaune cikin falo yatankashe kafarsa kasa yanashan kankana

Hafiz yana saman kujerah yanabuga game hajiya tace wainikuwa babangida wanne irin farinciki kakeciki nagatundazu saiwasar hakorah kakeyi???

Yasaka kankana cikin bakinsa yace hmmm mom albishirinki"" tace goro fari tasss tana gyara zamanta"" Allah yasa alkhairine

Yasake murmusawa yasosa kansa yace sosaima "" tace tofadamun inji"" yace nasamo maki suruka mom Allah yakarbi adduarki nasamu wacce nakeso

Aikuwa hajiya tarangada guda kai Amman najidadin wannan labari haba kokaifa duka abokanka sunyi aure Amman kai katsaya ganin garii inason nima insamu jika 

Yasunan surukar tawa??? Yana murmushi maikunshe dajindadi yace lubabatu saiyanzu Hafiz yayi magana  yace Allah yasanya alkhairi

Suka amsa da Ameen"" aikuwa hajiya tasanarda abokan mahaifinsa kasancewar yan uwan babansa bakusa sukeba"" Dan asalinsu buzayen Niger ne""

Cikin satii daya akagama komai anbiya sadaki dakudin angani anaso"" akasa bikin nanda wata daya""" ranar lubcy tasiye dabbobi guda goma ta aikawa *hatsabibin boka*

Usman dakansa yaje Dubai yahadomata lefe Wanda ya amsa sunan lefe akwati talatin kowanne akwatin shake yakeda kaya sannan dasabuwar mota hul duk acikin lefen

Lubcy saida tahada gagarumin farty gabadaya kawayenta sadiya.aneesa.rabiatu.larai.sajida"" suma saida kowaccensu  tazo datata tawagar kawayen awani babban hotel sukayi fartyn kowannensu  saida yagirgiza daganin kayanda akadirkowa lubcy amatsayin lefe

Ranar sun gwangwaje sosai  saikusan magrib suka watse""

Cikin watadaya lubcy da Usman tamkar suhadiye Kansu Abdul ma saubiyu Usman yana zuwa dashi wajenta

Biki yakarato kowanne bangare sai shirye shirye ake kubra matazo da dankaramin cikinta ansoma hidimomi Usman yagyare gidansa an sake komai kuma anyisabon fenti

Bangaren lubcy kusan sati biyu sukayi suna program event itakanta tasan takere sa a ta auri mijin nunawa sa a

Bikinsu Na gogaggun yan boko ko ince yankarya Dan yanboko akwai karya kankanba danuna sudin wata tsiyane 

Ranar lahadi dubban jama a suka shaida daurin auren lubabatu da Usman akan sadaki million 1 
Karfe uku motochin Amarya sukadauki Amarya zuwa kano wajen mahaifiyar
Usman yankai Amarya censukà kwana tareda kawayenta

Washe garii akawuce da itah dakinta ai kawayenta basu tsureba saida sukayi arbada aljannar duniya acewarsu 

Dan babuce kawai babu acikiñ wannan katafareñ gidan kowa sai santin gidan yakeyi saidare akawatse akabar amarya

Daren Usman ya angonce zokuga ririta tamkar zaimiyarda itah ciki sosai takemasa ladabi hartakan mantar dàshi kowa muddin yanatare da itah

Bayan wadansu watanni lubcy tafara gajiya dabukatarsà saitatsiri ciwon karya kofashin sallah"" lokacinne kubra tahaihu mace akasamata suna bilkisu hidimar kwana biyu tasaka  lubcy tadan sarara





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 29
        By
Gentle Lady💃🏽



Bayan wata uku lubcy tafara laulayin ciki ranarda doctor yasanardashi tanadauke daciki zokuga murna daga hajiya har Usman tamkar suhadiyeta tuni labari yakai wajen kubra

Takirata tatayata murna taimata fatan sauka lafiya cikin sosai yake wahalda ita gakuma yawan kwadayi kamar manya"" 

Aikin komai tadainayi acikin gidan saidai taci takwanta saikuma Usman yasake manne mata da lakuwa kamar danyaye"" 

Cikin yana shiga wata Tara kafafuwanta suka kunburah komai bata iya yikobanza gatada sonjiki sai akagamu akadace 

Ranarda nakuda takamata akadauketa sai hospital tasha wuya Amman haihuwa tayi tsayinta gashikuma tagalabaita

Likita yace dole Usman yasaka hannu aimata aiki aciro yaron domin dan cikin yawahala   tareda mahaifiyarsa ""  Usman hankalinsa yayi matukar tashi

Saida doctor ya rarrasheshi yasaka hannu akashiga da itah dakin tiyata akaciro kyakkyawar beby maikamada Usman sak tamkar yayi kaki yatofar

Bayan anyimata dinki aka kaita dakin Hutu"" sosai Usman yakejin son jaririyar harcikin ransa take yadauki waya yasanarda hajiya da Abdul da kubrah yakirah gidansu lubcy yasanar

Ranar duka sukazo saigashi ancika asiviti makil damasu dubiya har makotanta saboda tanada mutane sosai"" satinta daya sannan aka sallameta kaitsaye Lagos akawuce da itah"" aikuwa Usman yamaida Lagos garinsu kullum yana zaryar hanya

Anasaurah kwana biyu biki kubra tazo""" sosai sukejida yarinyar ranar suna akaradamata suna  labila

Usman gida biyu yakasa kansa"" bayawajen aiki baya Lagos aikuwa tanayin arba in akahadota tadawo

Sosai tadan huta da jarabar Usman kwana biyu Amman ranar taraina kanta dankuwa saida yafanshi nakwana arba in datayi basatare danyagaji iyakar makurah

Labila tayi wayonta sosai ko ina tanazuwa tanada shekara daya dawata bakwai aka yayeta"" lubcy batasake samun cikiba saida labila tacika shekara uku

Shima wajen haihuwa saida aka fasata saboda wahalarda tasha yaron yamutu cikin ciki"" tunlokacin batasake samun cikiba

Saida labila tacika shekara goma"" sannan tasamu ciki shima hallau tiyatarsa akai mata tace ajuye mata mahaifa dantagaji Amman badasanin Usman ba""

Katon danda akaciro mata shima kyakkyawa Amman labila tafishi kyau Dan ita ta fidebo kamannin mahaifinta""ranar suna akasa masa suna abdul-majeed sunakiransa majeed

Yana isah yaye tayayeshi domain sun shirya wata tafiya tareda kawayenta "" tatambayi Usman duk da badason ransaba Amman bazai iyah musamataba ita tadauki nauyin tafiyar har aje adawo

Sukayi shirye shiryensu ranar talata jirginsu yadaga zuwa charo satinsu biyu acen usman yadameta da azarbabi yace wlh tadawo hakanan badan tasoba dandama gudun hijirane taimasa tadan huta

Ranarda sukadawo tsautsayi ya afkamasu akan hanya dukkansu sunji ciwo sosai bakamar lubcy dangaba gareta yaji chiwo sai alokacin akalurah dakarinda kejikinta yagirma tamkar bishiyar kuka haryazubarda Yaya

Shiyasa batason Usman yakusanceta likitoci suka tabbatar sai anyimata aiki kuma Karin babbane danhaka zatafara dashan magani

Usman kamar yayi kuka danyasan tashi takare dankuwa likita yace karya kusanceta saida suka kwashe watadaya hardasati sannan suka murmure Tass alokacin Duk hankurin Usman yakare

Kawai yafada Neman auren wata suwaiba acikin kaduna take sosai sukeson junansu yasanarda hajiya bata tambayeshi daliliba tunda tasan yanada halin yin auren

 Tadaimasa nasiha akan yakwatanta adalci cikin sati biyu akagama komai harlefe Amman yakasa sanarda lubcy

Dankunya yakeji yazata dauki maganar kenan baigodeba duk da hakurin datakeyi dashi danyanzu matsala tasameta zaigujeta kumashi Sam baida burin hakan

Zaune yakecikin falonsa yana tunani wayar sa tasoma ringing kamar bazai dagaba saikuma yadauko cikin sauri yadauka danharta katse an sake Kira hajiya ce yadauka tareeda sallama ta amsa"" yagaida itah cikin ladabi ta amsa tace ina yaransuke

Yagyara zamansa yace suna islamiyya tace hakane Sam na sha afa yaune asabar mamansufa????

Yace inatunanin barci takeyi"" tace toyajikinta??? Yace todasauki za ace"" Hafiz yana gida?? Tace yanzun nan Na aikeshi wlh

Dama kiranka nai insanarmaka kamar yanda kabukata  ansaka bikin sati biyu "" yasaki fara a kai alhamdulillahi Amman najidadi

Tanisa Allah yasanya alkhairi yace Ameen tace babangida"" yace Na am tareda saita natsuwarsa tace inafatardai kasanarda lubabatu batun aurenka???

Shiru yayi yanasosa kai kamar munafuki yayi karya""" tace shirunka yanuna kenan baka fadamataba

Cikin kunya yace ah hajiya wlh nakasa tunkararta da maganar kayanda nazodasuma suna falon baki na aje dazaran naso sanarda itah sainaji tabani tausayi

Hajiya tace totunda tausayi takebaka kafasa auren mana"" idanuwansa ya kwalalo aransa yace kice inmutu kenan""

Cikin zuciya yayi maganar baisan tafito filiba hajiya tace wacce irin mutuwa duk wadanda suke zaune damata daya kaga sun mutune??

Yayi shirudai aransa yace hajiya bakisan halinda nake cikiba""" tace totunda har kaidin bazaka iyah hakuraba yazamar maka dole kasanarda matarka

Amman muddin karufemata harsai randaurin aure kokuma taji ashanun tallah tokuwa liki za atono





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠


chapter 30
      By
Gentle Lady💃🏽


Yanisa shikenan hajia zansanar da itah "" tace yauwa kokaifa ai boye boye bashida wani alfanu ansan kowa yanada kishi Amman hakuri zatayi ai tunda mijinta yanada bukatar kari

Yace zanfadamata insha Allah tace hakan yayi sunjima suna firah  sannan sukai sallama yayi shiru yana kallon wayarsa shikam gabansa sai faduwa yakeyi 

Mikewa yayi yasauko dakinsa"" hawayayi zuwa bangarenta cikin falo yasameta kwance remote ahannunta tana cenza tasha tana ganinsa tamike da fara a

Alhaji Kaine dakanka bayan kakirani inzo"" yayi murmushi bakomai aigani nazo yayi maganar yanasamun wajen zama kusa da itah

Yace hutawa akeyi"" tace ah wlh kafin majeed yadawo kasanshi akwai Rigima jiya da dare damuna yayi dakuka kamar karamin yaro

Yace todakumafa haryanzu  bakimasa kaniba  aidole yayi sakuwa dar taji agabanta Sam tama manta da anjuyemata mahaifa Kuma bazatayarda wani tsautsayi yasaka tasanarda Usman hakaba 

Dantalurah sosai yana mutuwar son yara gashi biyune kawai da itah" yakatsemata shirun tahanyar kiran sunanta

Datago ta amsa cikin fara a"" yanisa dama akwai maganarda nakeson yidake"" tadanyi shiru sannan tagyara zamanta dandama kishingide take gahannun kujera

Takalleshi inajinka alhaji"" yadanyi jim sannan yace kafin nacekomai inamai baki hakuri akan abunda zanfurta maki nasan bazakiji dadiba Amman kiyi hakuri wlh nadade ina kumuiniyar maganar dantayi nauyi akan harshena

Yasake nisawa karkiyi zargin naraina kokarin da kikeyi akaina kodaya wlh najinjina maki hakaxalika  ina alfahari dake

Karki zargeni dawani Abu Dan Allah wlh haryanzu inasonki sonda bantaba yiwa wata mace makamancinsaba aduniya

Lubcy dai tayi shiru tana saurarenshi haryakai karshe murmushi kawai takeyi yadago yakalleta murya araunane yace aure nakeson karawa kuma maganarda nakemaki harnasamu wacce zan aurah

Nakasa sanardake ne tuntunii"" nasan kinsanni kuma kinsan lalurarda nake dauke da itah bazan iyah rike kainaba nasoyin hakuri Amman nakasa doctor yasanar dani akallah zakifi shekara komafi kafin ayimaki aiki Dan likitocin dasuke wannan aikin sunakan wani aikine tayiyu sugama kafin nan kuma ka idar aikin saikinsha magani akallah nawata biyar sannan

Yasake kallonta idanuwansa sunkada jajir banaso na aikata zina abarda nakyamata tun ina saurayina yanxu dagirmana da Yayana bazanyiba dankuwa zansiyawa Yayana halaka dahannuna dankuwa duk abunda nayi nima sai anyimun

Nayi kokarin  fara azumie amman duk dahaka nakasa Amman kiyi hakuri kinji matata yayi maganar yanariko hannunta ga mamakinsa saiyaga tatintsire da dariya

Bakisake yake kallonta tace wlh baban labila kasakani dariya yanzu akan wannan maganarne kakasa sanardani?? 

Tundazu kakeson fadar abudaya Amman kakama kwana kwana kawai kacemun aure zakayi zanhanakane??? Nasan mata sunada kishi Amman nisam banadashi kuma bawai Dan banasonka bane kodaya 

Amman kasani dole inhar soyayya tacika soyayya kaso abunda masoyinka yaso kome kakeso aduniya komai muninsa gareni inhar kafurta kanaso tonima dole naso abun

Kaddarama abun bakine aguna inhar yazama fari awajenka nima yazama tuntuni nasobaka wannan shawarar tunda nidai banada jimirin dauke lalurarka kuma sainaga 

Kamar zanyi shishshigi sainakama bakina Amman bakomai awajena kasaki ranka Allah yasanya Alkhairi tsuru yayi yanakallonta

Baisan sanda yarungumetaba yafara sunbatarta ganin yasoma fita hayyacinsa yasa tatureshi tace kamantane

Karamin Tsaki yaja yace wlh kamar namutu nakeji tanisa cikin alamar tausayi tace tomezaihana asabikin kusa kusa kozaka samu abunda kakeso

Yace ah sati biyu akasaka bakomai zancigaba dahakuri zuwa lokacin""" tatausaya masa matuka yace nagode sosai lubcy hakika ke Yar aljannace  inama sauran mata zasuyi amfani da shawarata surika hakuri idan mijinsu zaikara aure

Dazasukoyi irin halayenki nakwarai da duniya tahaska"" murmushi tayi nidai kadaina zugani wannan zuzutawa haka

Dariya yayi aikin chan chantane"" yasake riko hannunta nagode sosai tace bakomai yasunan kanwar tawa??? Cikin nunajin nauyi yace suwaiba""😌 tace wow suna maidadi yakamata kafin akawota anunamun photo n kanwar tawa yadan Sosa kai yace bari nadauko wayata kigani Yar duma dumace kamarke

Yayi maganar yana mikewa  tace bansaka wahalaba??? Yace kodaya daganan kobirnin sin kikaturani dakafa zanje saidai indade bandawoba tasa dariya ko maigidana ashedai kanaji dani ??? Yace kamar kwai kuwa yawuce 

Tabi bayanshi damugun kallo yanafita taja wani dogon tsaki aranta tace wai aure???🙄 To ayi auren mugani ai wlh danabarka kakusanci wata matar amatsayin matarka nafiso kamutu

Inaruwana da lalurarka saidaifa kaje kayi zina komata Dari zakanema ni lubabatu bandamuba kazantarda bakaganiba tsabtace😏

Amman bazan taba yarda kakawo wata acikin gidan nanba Dan nawane danida Yayana"" bazantaba bari Yayana susamu yan ubaba

Karuwai ka ajedari awaje aidama akan abun zakayi aure nikuwa inamai tabbatàr maka bazaka samuba hmm namiji munafukiñe jiyanda yakewani lallaf yadauka salihar mace yakawo agidansa baisan kububuwa takeba cinnaka bakasan nagidaba  zumanake maizaki ammankuma gaharbi harbinama yazarta Karin maciji dafii
Afili nake mumina Amman azuciyata nafikowa sharri jin motsin dawowarsa yasaka lubcy tadaidaita natsuwartà

Yashigo da sallama ta amsa"" kusa da itah yazauna yajawota jikinshi yakamo mata pic din tana kallo

Tace kai ammanfa kanwar nan tawa bakaramin kyaune da itaba"" yadan hararetà yaçe batakai kiba lubcy aranta tace kunji munafuki waya sàñima koharzagina kukeyi 

Amman afili saitace ko??? Yace sosaima yanda kikasan kyawawan fure haka nakeganinki wai anyama wani yataba fadamàki kinada masifàr kyau?? Dariya tayi cikin nuna alamun jindadi tace ah ah Amman gashi aikai kana sanardañi





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠


chapter 32
       By
Gentle Lady💃🏽




Dasauri tamike zuwa bandaki yabita da kallo tunda suke tare bata tabayin wanka aLookacinda suka taraba

Koda yace tatashi tayi wanka cewa takeyi bayanzu zatayiba saida safe idan suntashi sallah Amman yanzu dabama Kusan tarta yayiba tajeyin wanka yanatsaka da tunaninsa tafito daure da towel

Yasake binta dakallo yana hadiye yawu shikam baisan yawan bukatarda yakeda itah ba baitabajin ya gamsuba komenene dalili

Ruwan jikinta tadan watsamasa yadago yana kallonta gira tadaga masa tace tunanin me kakeyi??? 

Yace kekanki kinsan tunanina bayawuce matsalarki wlh kokadan banji nasamu natsuwaba hartausayin kaina nakeyi

Kusa dashi tazauna tana goge kanta tace hakuri zakayi basaura kwana sha huduba aikamar gobene zaka angwance ni idan kayi auren nayafemaku kayi wata daya dakinta kasamu kamore amarcinka

Cikin alamun nunajin dadi yace dagaske kikeyi??? Talunshe ido tabude kadaina shakka ko kokwanto akan maganata babu abunda bazan iyaba indai akankane"" fatana shine kasamu abunda kakeso

Inason ganinka cikin kwanciyar hankali yalumshe  ido yabude yace nagode matata farincikina 

Tace karka damu kaje kayi wanka ko yace hakane yamike yadaura towel yashiga toilet dasauri tadauki wandonsa tareda abunda kecikin kwalba lakame da towel dinta tafita zuwa dakinta

Tanazuwa ta ajesu waje daya tasaka kayan barci tafito zuwa dakinsa koda yafito yasameta hartakwanta wasu kayan barci yasaka shima yahau gadon

Yajawota jikinsa tareda saukarda ajiyar zuciya sosai yanason jin duminta Amman tunsanda batada lafiya batasake hada shinfida dashiba kullum dakinta take kwana sake jawota yayi cikin jikinsa barci maidadi yadaukeshi tareda mafarkai masu dadi washe gari saida yasake wanka kafin yaje masallaci

Bayan kwana biyu yashigar mata da kayanda yasiyomata tanata murna tanayaba kayan"" yadaukesu sukaje kasuwa yace kowa yazabi kalar abunda yakeso 

Sunkawo kaya sosai duka yabiya kudin Dan sainan nan yakeda itah" tuni tasanarda kawayenta suzo ranar asabar maizuwa akwai fatynda tashirya Na musamman"" agidanta Sam bata sanardasu aure Usman zaiyiba

Ankai lefe gidan Amarya kuma duk wadansu kudi da ake bukata ankai dagashi sai Abdul sukeyin hidimominsu saboda"" bashida wasu abokai""

Ranadai bata karya saida"" uwar diya taji kunya""yaune dubban jama a suka shaida daurin auren Usman da suwaiba akan sadaki dubu Dari biyar"

Daurin auren yasamu halarta mutane sosai dayake Usman mutumen mutanene"" ango yasha farar shadda sai wasar hakorah yakeyi shikadai yasan abunda yatanada adaren yau

Lubabatu ce cikin dakinta tareda kawayenta sadiya larai sajida aneesa rabi atu""  sadiya tace waini kince muzo gidanki Amman bakisanardamu komaiba kuma munga gida cike da alamun biki akeyi"" 

Tamurmusa tace  biki akeyi kuwa"" larai tace bikin mene??? Tace aure dadyn majeed zaikara kusan tare suka hadabaki aure???? 

Tagyada kai tana shan lemu "" sajida tace tirkashi kuma kike zaune anan??? Takalleta tace tome kikeso inyi kinasone intada hankalina bayankuma mijina yanasona???

Rabi atu tace soyayyar banza ai wlh duk sonda danamiji yakemaki dazaran yakara aure zakizama photo"" aiyanzu yadaina yinki tunda yasamu yarinya bayankuma shine yamaidaki hakan

Ta aje kopin hannunta tace  ninasan mijina yanasona sosai"" kuma babu tayanda wata zatafini matsayi acikin zuciyarsa

Sajida tasheke da dariya tace naga alama giyar soyayya batagama sakinkiba tokibude kunne kiji namiji dakike ganinsa tsohon munafukine bazaki gane hakanba sai ankawo matar

Barinma ya tas tata yagano tafiki sweet hmmm sunanki sorry kinaji kinagani zakikoma borah agidan nan
.takarewa gidan kallo kinga wannan gidan wlh kinagani zai gagareki zama

Dake dayayanki gidan nan zaikoma maku tamkar kurkuku bari kiji yanda mukayi da dadyn ihsan lokacinda yakeson yin aure Sam bainunamun komaiba kamar yahadiyeni dama gayanda muke kullum sai riritani yakeyi da dadin baki

Nikuwa ahaukana sainaga aisonda yakemun kamar baxaiso wata bayan idona ba"" saiban dauki matakin komaiba nayita rawar kafa har aka kawo Amarya

Nikam sai lokacin nasan natabka babban kuskure na aminta da danamiji dansaboda kawai yamun dadin bakin soyayya

Idan yanadakinta wlh ko motsinsa bakyaji saidai inshige daki inyita kuka saboda takaici sairawar kafa yakeyi inhar girkinta yazagayo Amman ranar girkina sainaga baya walwala bayanuna zakuwarsa 

Lubcy tace toyakikayi??? Tace hmm aisaboda naga wankin hula yanashirin kaini dare" kawai nakai sunanta wajen *hatsabibin boka* aka kadamun Yar banza hatta cikin datafita dashi aka narkardashi yabi mazubar ruwa

Sukasa shewa suka taba rabi.atu tace wlh kinmun daidai"" aikishiya ba abokiyar zamabace mekike jirah kinsandai yanda kikashigo rayuwarsa danhaka idan kikatsaya wasa wata tashigo takarbemakishi

Lubcy hmm kawai tace sajida tace kaikudaina wahalda kanku tasan abunda tataka"" lubcy takwashe da dariya tace kudai akeji mahaukaci yafada rijiya 

Kamar ance sudaga Kansu sukayi arba da labila tanarike dakugu takallesu dai bayan daya tace hmm wannan muguwar hudubar kukazauna kuna koyawa mamana duk danasan batada mugun hali  Amman bazan shedetaba danzata iyah sauyawa 

Danzama damugayen kawaye irinku hatsarine garayuwar iyali "" lubcy tadago afusace takunduma mata zagii abunda bata tabayiba tace asheke shasha shace??? Anandin kinunamun abokin wasanki

Wlh karnasake ganin kin shigomun daki waima tsaya labe kikemana ko??? Idanuwanta sunakawo kwallah tace komadai menayi wlh muddin matar dady wani Abu yasameta saina sanardashi gun boka kikezuwa lubcy tataso daniyar dukanta taruga dagudu tace kukuma kuji tsoron Allah inkuwa bahakaba kuyi mummunan karshe takafro kofa ganin tana niyar dankotaa

Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 33
       By
Gentle Lady💃🏽




Lubcy tadawo"" tanata sababi saida su sajida sukaita bata hakuri sukace ai kuruciyace zatadaina nan gaba"" 

Aranta kuwa tanatsoron shegen surutun labila tunda hartace hakan bamakawa zata sanarda Usman

 kuma zaiyarda da maganarta danbataimasa karya sosai tasan yana yarda da maganar labila 

Lallai kuwa yazama dole tayiwa tubkar hanci zata sanarda *hatsabibin boka* dawan nan tunanin sukacigaba da harkokin gabansu

Yanbiki sukafara cika gida alokacin taiwanka tafita cikin mutane akafara jidoda kayan ciye ciye"" 

Karfe hudu nayamma akatafi wajen faty Wanda uwargida tashirya awani babban hotel namaza damata inda Amarya dakuma ango tareda uwargidansu  agefe aka zauna saman dandamali

Bayan anbude taro da addua akafara gabatarda shirye shirye inda maikida yayita  wasa uwargidan Alhaji usman akan wannan katafaren biki data gayyacesu

Aka umurci Amarya da ango sufito tsakiyar taro sutaka rawa haka sukafita anatakemasu baya

Nan take akasaki kida tareda sowa""" lubcy tayi ruwan kudi tamkar dagasama suke zubowa sailiki takewa Amarya inda Usman shikuwa yakeyimata 

Kawayenta suma sukafara  yimata likiii"" sosai masu kida suka kwashi kudiii"" tarokam yayi taro duk inda lubcy tawurga maganarta akeyi anayaba halinta

Lubcy macece wacce ta iyah zamada mutane sosai tasan yanda take tafiyarda rayuwarta macece wacce tasan takan kissa dakuma kisisina

Shiyasa har makotanta""suna sonta sosai" dakuma yaba halayenta"" basu suka tashi wajen Fatyn ba saida akasoma kiran margin sannan akatashi bayan anci ansha anyi katt

Amarya anazuwa akasoma shiryata domin Kaita gidanta"" karfe takwas motocin daukar Amarya suka faka kofar gidansu

Bayan iyayenta sungama yimata huduba akadauketa sai katafaren gidanta bangaren uwargida aka Kaita akabata amanarta taredayi masu nasiha

Tacee bakomai ai kanwace niban dauketa kishiyaba aikuwa dazasu tafi har bangaren Amarya tarakasu kowayatafi dayabon halayenta

Karfe goma kowa yawatse akabar Amarya agidanta tareda uwargida gidan yayi tsit

Tasake wanka tadawo cikin falon tana zaman jiranshi zamanta babu jimawa Usman yashigo 

Yana yin arba da itah yasaki fara a yace haryanzu kinafalo bakyajin tsoro ina labila??? 

Tamike cikin fara a tace sunyi barci nimadai shinakeji natsayane inrakaka wajen Amarya karkashiga kaidaya

Yace kamar kinsani bazan iyah shigaba" tace tomuje karage kayan jikinka kawatsa ruwa sainarakaka Amman yabanganka da kazaba

Kansa yadan Sosa yace tana mota wlh namanta"" tace tokadauko bari nahada maka ruwan wankaa yace yauwa nagode yajuya cikin zumudi tabishida murmushin mugunta dakinsa taashiga tahadamashi ruwan wanka yadawo yashiga yawatsa tadauko masa kayan barci masu kyau

Tafeshesu da turare yana fitowa yasaka kayan suka fita tanarike da plate da madarar shanu bakin kofar dakin tatsaya Tamika masa

Yace yahaka bazaki shigo bane??? Ido tagwalalo ah ah kaikam damadai rakiya naimaka kagaisheta dai 

Tamika masa kajin yace tokebaki dauki takiba tace ainima nacitawa lokacinda aka kawoni wannan  ta amaryace tasunbaceshi akumatu asha amarci lafiya tawuce abunta tana murmushi yabita dakallo cikin soyyya yana fatar Allah yabarshi da matarsa 

Baisan wanne irin so takemasaba dahartake iyason abunda yakeso duk abunda akeyi bisa kunnen suwaiba tagodewa Allah dayabata kishiya tagari 
Yashiga bangaren da sallama ya aje kayan hannunsa saman gadon yahau yaciremata mayafi yana murmushi Amarya ta ango murmushi tasaki cikin jinkunya

Yace yaudai Allah yacikamana burinmu kitashi muyi alwala mugodewa Allah"" bamusu tamike domin dauro alwala saiga jinin al ada jiki asanyaye tafito

Ganinta dayayi sai ahankali yatambayeta tafadamasa tanafashin sallah baice komaiba yagabatar masu dakajin sukaci saida yayi nafila yakwanta 

Yadade yanajuyi kafin barcin yadaukeshi saikusan asuba washe gari sukuku yawuni Sam baida walwala

Bayan sunyi break dazasuci abincin rana yahau samanta saiyasamu tana sallah bayan jiya yatambayeta kwana  nawa takeyi tace biyar kenan karya takemasa???

Baicekomaiba yace tafito suci abinci"" itakanta jikinta yayi sanyi daganin yanayinsa""

Dadare bayan sunyi saida safe da lubcy sukayi dakinsu wannan karon saida komai yakusa kankama tasomajin amai"" dasauri tasauko tashiga toilet

Tanashiga taji batajin komai""" Usman tunyana saran fitowarta haryagaji yaje bakin kofar yana bubbuga mata shiru kuma tasa sakata karshe dole yahakurah yakoma bangarenshi

Tundaga ranar dazaran yashigo dakin saitaruga toilet karshedai centake kwana har akakusa kwashe watadaya karshema  saiya samata ido

Duk halinda sukeciki baisanardà lubcy ba itakuma bata nunawani abuba suna zamansu lfy  zaman gaskiya da mutunta juna tadauki yayan Usman kamar nata

Zaune suke da marece lubcy tamike zuwa kitchen tazubo lemu a cup biyu tadawo falon tazauna tayiwa suwaiba bisimillah tadauka tasha sukaciga dafirah

 Dadare bayan Usman yadawo dayake anraba girki yau hannun lubcy yake bayan sunci abinci  suntaba firah sukaiwa juna saida safe





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 34
       By
Gentle Lady💃🏽


Bangarenshi suka nufa tayo wanka shima yayi"" suna kwantawa yakuramata ido"" tasaki murmushi tace akwai matsalane??? 

Ido yalumashe sannan yabude yace sosai ma tace mekake bukata inyimaka yanzu?? Yace ke kawai nake bukata"" tayi masa kallon rashin fahimta tace haba  jiyafa kabaro bangaren kanwata kana nufin haryanzu baka koshiba??? Tonayafe kwanan nawa wlh kakoma cen wajenta

Yakalleta da tausayawa aransa yace mace tagari kenan kekina tausayamun bakisan waccen bata tausayinaba "" tadan tabashi tace injidai bawata matsala naga kayi shiru??

Yace hmm bakomai nidai kitaimakamun zatayi magana yadorah lallansa akan bakinta daganan yacigaba da aikamata sakonni jikinsa yanda kukasan Mazari saidai babu yanda zaiyi saidai kawai yayi wasa da itah yadan samu natsuwa kadan

Bangaren suwaiba kuwa tunda tashiga daki takasa barci wata muguwar sha awace tataso mata tarasa yanda zatayi takwanta Amman Sam barcin ya gagara daukarta

Mikewa  tayi cikin sanda tafito waje tafito daga bangarenta tasauka kasa tafita waje"" dakin driver gidan tawuce kaitsaye babu wani tsoro ko shakka acikin zuciyarta

Taturah kofar saitajita rufe ahankali tasoma bubbugawa cikin barci yaji anabuga masa kofa yace waye cikin muryan rada tace nice kabude ba lafiya dasauri yazo yabude kofar yana budewa tayi kududuf tashige

Dagashi sai gajeren wando takalleshi tundaga sama harkasa tahadiye yawu wani irin shu umin kallo take jifanshi dashi

Yana kallon kofa cikin tsoro yace suwaiba meyakawoki dakina??? Murya takaryar tace haba kb yazakace meyakawoni dakinka 

Harkamanta soyayyarda mukayi dakai??? Tsaki yaja yace soyayyar banza aikinsan inasonki kina sona Amman danbanida kudi akahanani aurenki

Kituna shekararmu biyar tare"" sake matsowa tayi kusa dashi tace kayi hakuri masoyina wlh nikaina badason raina akayi auren nanba kaikasan inasonka babanane dayaga kudi yace bazan aurekaba

Yace kinga malama banason dadin baki kifita kibarmun daki banaso alhaji yasan wata alaka tataba hadani dake danzan iyah rasa aikina kuma dashi na dogara

Tamarairaice fuska haba KB baidace kajuyamun bayaba kayarda dani wlh ina mutuwar sonka Allah yarigada yakaddaro saina auri wannan alhajin Amman wlh banasonsa
Yawatsamata wani mugun kallo yace kifita kibarmun daki wlh konaimaki ihu

Ninarigada nafiddaki araina tunranarda nasan maigidana kika aurah""" abunda suwaiba takeji bazaisa ta iyah hakurah takomaba"" zanenda yake jikinta tacire tadawo daga itah sai wasu arnayen kayan barciii 

KB yasoma kallonta tundaga kasa harsama tuni jikinsa yasoma kyarma yadimauce daganin surar jikinta sha awarta ta tasomasa shedan yanata haskomasa ni imarda zaikwasa ajikinta
Ganin natsuwa takauce daga gareshi yasa tatako cikin takun Jan hankali tafada jikinsa tasoma kaimasa Sumba tako ina take yasoma maidamata da martani

lubcy ce tamike tanarike da kirji tashinta yasaka Usman mikewa yace lafiya??? Tagirgiza kai cikin damuwa tace ba lafiyaba gabana nakejin yana tsananta faduwa 

Anya antynsu lafiya take! Dayake hakan take kiranta yace kikwanta bakomai bane bakiyi addua ba dazaki kwanta tace nayi Amman haryanzu baidaina faduwaba

Tamike nidai barnadubata ganin tamike shima saiyatashi yabiyota harbangaren suwaiba saisuka kofar abude

Dasauri taturah tashiga da sallama harkurya basugantaba gabaya suka bade dakunan danema batanan  hankalin Usman yatashi dasauri yasauko kasa

lubcy tanabiye dashi sukadubà kaf bata gidan yanaturah kofar fita yajita bude kaitsaye yafita dayake dakin kabeer shine farko yayi hanyar dakinsa arude

Damamaki yajikofar abude dayaje domin kwankwasawa"" yaturah kofar yanacewa kabeer taso gida ba bakinsa yasankame ganin abunda idanuwansa sukai arba dashi

Kalu innalillahi wa inna ilaihir rajiun"" shine abunda kawai yake furtawa take hawaye sukafara sintiri akan fuskarsa

Ganin baifitoba lubcy tace alhaji nataada maigadi yace bata fitaba tayi maganar tanashiga dakin ganin abunda yake faruwa lubcy tabuga salati dakarfi salatinta yafargarda KB yadago kansa dasauri

Lokacin yana kokarin shigar suwaiba dayake budurwaçe baisamu hanyaba yanashiriñ shigarta dakarfi lubcy tayi salati Wanda yadawodashi duniyar gaskiya aidasauri yasauko yaja zanin gadon yarufe jikinsa saizare ido yake gawani zawo dayaji nantake

Muryar suwaiba yaji tanacewa haba masoyina yakadaina abunda zakayi karkaji komai dama jikina nakane kasan kaikawai nakeso" tamiko masa hannu kazo mufaranta ranjunanmu nadade inajiran wannan ranar dazan mallakamakà Kaina

Ido rufe take maganar dukda turarta da KB yakeyi dantarufe bakinta ganin bazaitasoba tadago tafada jikinsa tasoma lalaubàr bakinsa

Usman daya sandare waje daya tamkar gunkii wani bakincikine yatokareshi gakahon zucii baisan sanda yararumi wayar TV ba yatuzgeta dakarfiii yasoma aunamata itah saukar bulalar dataji ajikintà yasaka takwallah kara

Ko kakkautàawa bayayi idonsa yarufe tuni yazulawa KB shima Wanda yasoma kuka ganin abunda yake faruwa ga suwaiba

Da itah dashi sukarude gidan tuni ma aikatan gidan sukafito kowayaga abunda kefaruwa saidai yajuya yana tsinemàsu

Ganin zai iyah kashesu yasa KB yadauki kayansà ahannu yafita dagudu"" tuni suwaiba tasuma Amman Usman baidaina dukantàba saida lubcy tarike bulalar cikin kuka tace sokake ka kashetañe hàbà tundazu naketa bakahakurii

Wani mugun kallo yawatsomàta idanuwañsa sunyi jajir itah kañta tàfirgita dàyana yinda taganshi danbatà taba ganiñsa cikin irin yanayinbà bulalar hannunsa ta rike kam dole yasakarmàtà yàfità dakin dasauri ko kallon masu aikinda suke tsaitsàye baiyiba yayicikiñ gidaa

Labila tanafalo saikuka take tana rungume da majeed Dan hayaniyar gidance tatasheta takasa fita saizagàyen falon takeyi gànin dadynta yashigo taruga tafada jikinsà tanakuka tureta yayi yahau sàmañsa Dasauri





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 35
       By
Gentle Lady💃🏽



Mamaki matuka yacika labila tana tambayar kanta meyasamu dadynta yau"" majeed  tuni yakoma barci daman"" 
Bangaren lubcy kuwa" tana ganin yafita tadauko ruwa dasauri tawatsawa suwaiba take tafarfado tachandara ihu 

Lubcy tarufe mata baki tace Dan Allah kidaina ihun nan makota sunajinmu fa"" sai alokacin hankalinta yadan dawo jikinta  takallijikinta taga batada kaya dasauri tajawo zanen gadon tarufe  jikinta dashi tafashe dakuka tana girgiza kanta nashiga uku

Yazanyi Anty"" lubcy ce tadafata tace kiyi shiru kinji kanwata tashi mukoma cikin gida "" idanuwanta tadago zuna zubarda kwalla tace Anty na aikata babban kuskure arayuwata wlh aikin shaidanne ninasan idan mahaifina yaji wlh saiya kasheni

Lubcy tanisa tace bama zaijiba insha Allah kitashi muje kigasa jikinki gobe zanbashi hakuri"" tasake kallonta akaro nabiyu tace wlh nasan bazaitaba hakura ba kakama matarka da yaronka suna aikata zina ai hankalima nazai daukaba ballantana tunani

Lubcy tace hakane Amman meyakaiki aikata hakan da iliminki??? Tashare hawaye tace Anty wlh banason baban majeed wannan shine saurayina atadalilin kudin sa dayace yanasona sai mahaifina yadage saina aureshi nima sainaji inasonsa narabu da kb saboda baida kudin aurena

Tunranarda nazo gidan nan sainaji Sam banasonsa soyayyar kb tasake linki acikin zuciyata hardai ranarda naganshi gidan nan amatsayin driver duk hanyarda zanbi dannaga nakadaita dashi bansamuba saiyau da shedan yakadamun gangarsa batareda  kokonton komaiba naziyarceshi domin yakawarmun da muguwar sha awarda tatasomun tasake fashewa da kuka tace wlh Anty niba yar iska bace bantaba yin iskanci dakowaba yanzun ma ina mamakin kaina da abunda yakawoni dakinsa nayi takaicin wannan ranar

Lubcy tajawota jikinta cikin alamun tausayawa tace na fahimceki Amman mahaifinki baikyauta makiba aiyanzu andaina auren dole kinga saka kayanki mukoma cikin gida

Tadago dasauri tana girgiza kai tace wlh zai iyah kasheni tatoshe bakinta saboda kukanda yakwacemata

Tace taya zaikasheki kitashi muje kinga masu aikin gidan nan suna waje mujeciki Dan Allah tamike tajuya tace kisa kayan

Bakin kofa tafita tasamesu tsaitsaye bata fuska tayi tace tomekuke jirah kowa yakoma yakwanta sumui sumui sukawuce tana tsaye saida takwatanci  tasa kayan sannan tashiga taja hannunta suka wuce cikin gidan

Cikin falon suka samu labila zaune rungume da majeed tana ganinsu ta ajeshi tace mom lafiya??? Meyasamu Anty??? Me akaiwa babana???? Wadan nan tambayoyin tajefowa  lubcy tace bakomai kidaukeshi kukoma daki dagahaka batace komaiba tawuceda suwaiba zuwa dakinta

Harkuryar daki takaita ta zaunarda itah fita tayi zuwa kitchen tasamu ruwan zafii tagasamata jikinta tabata magani tace tasamu takwanta

Ta share hawaye wadanda suketa zubowa akan idonta tace Anty konakwanta wlh bazan iyah barciba

Tace kiyi hakuri kidaina kukan nan saiya haifarmaki daciwon kai kikwanta kinji kaitagyada mata itakuma tamike taimata  saida safe hartakai kofa takirata Anty

Ta amsa tareda juyowa tace nagode da soyayyarki agareni agaskiya kinchanchanci duk wata soyayya dankuwa samun mai irin halinki sai antona nagode

Tasaki lallausan murmushi tace karkidamu yiwa Kaine tawuce tana sakin shu umin murmushi  aranta tace kadan kenan yarinya wannan aikin *hatsabibin boka* ne kaitsaye bangarensa tanufa

Taturah kofa tajita kulle tayita bugu yayi banza da itah karshe takoma bangarenta takwanta

Daga labila har Usman suwaiba babuwanda yaruntsa nasan bangaren KB ma hakanne Amman lubcy barci harda minshari 

Bata farkaba sai bakwai agurguje tasauya kaya"" koda tafito  masu aiki harsungama komai saidai tazuba akula tadaura saman dinner

Bangarenshi tanufa taturah kofar saitajita bude da sallama tawuce ciki tsaye tasameshi yanadaura agogon hannunsa tace ina kwana

Batareda yakalletaba yace lafiya yadauki takardunsa da key din motar sa yafita"" dasauri tabishi tana kiransa kowaigenta baiyiba harsuka sauko kasa

Labila tsaye da itah da majeed sunyi shirin skull cikin uniform
Lubcy tasauko kamar tafadi tace abban majeed Dan Allah katsaya 

Afusace yajuyo yace wai lafiya??? Idan natsayà mezanyimaki"" gabanta saida yafadi tadan dake tace bakomai naga zakafita bakayi break ba

Yace nakoshi yasakai yawuce labila""tabishi dasauri zuwa waje tanakiràn sunansa kamar karya tsaya bayaso labila tafuskanci hàlinda yakeciki ya juyo tareda kirkiro da fara a 

Takaràso tace dady morning"" yace morning my doter kintashi lafiya tace kalau idanuwanta sunakawo kwallah

Yace menene nakuka labila" yayi maganar yana dago habarta tace dad nagakamar kanacikin damuwa

Dariyar yake yayi yace bakomai banada damuwa maza Kira majeed insaukeku makaranta

Tace dad kabeer fa??? Yadanyi Jim sannan yadago yace bayajin dadi yatafi gida maxa kirashi karku makara

Tace to sannan tajuya cikin gidan yabita dakallo yacije kasan lebonsa"" 

Lubcy kuwa tunda yafita tayi tsaye sakeda bakiii suwaiba wacce tasauko duk akan kunnentà komai yafaru dasauri takoma saman tanakuka





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




chapter 36
        By
Gentle Lady💃🏽


Tana shiga batako kalli wajenda mom dinta takeba tadauko jakarsu tariko hannun majeed sukawuce

Murya asanyaye tace inakuma zakuje baku karyaba"" batareda tajuyoba tace munkoshi tafita abunta driver n dady ne yatukasu yafara kaisa company sanan yabiya yakai labila yakai majeed shima

Lubcy guiwa a sake tahau saman ta takasa tsaye takasa zaune karfa wannan abun yashafeta ranarda aka kawo Amarya aranar tasanarda *hatsabibin boka*  bayanin labila da abunda tafada

Yace kwantarda hankalinki nasan mezanyi mata"" cikin saurii tace karfa aimata wani abun nacutarwa yatace

Yamurmusa yace nasanda haka bakomai zanyimata ba zankullemata bakine koda tayi niyar sanarda wani abunda kikeyi zatakasa magana

Kodakuwa akan idonta kikai kisan kai bazata iyah sanarda kowaba tamurmusa yauwa hakan yayi saikuma maganar wannan shegiyar matar wlh boka banason tadade gidan nan

Inatsoron karwani Abu yashiga tsakaninsu kasanshifa dashegiyar lakuwa"" yakece da dariya yace abunda naimasu wlh koda dagashi sai itah ne acikin duniyarsu  bazaitaba kusan tartaba

Yace gobe kiduba cikin drower dakike aje madubinki Zanbada wani magani akawomaki dazaran kinji kina ra ayin tabar gidan kizubamata a lemu abunshadai tasha 

Toranar zatanemi namiji mukuma zamu turata wajen driver ngidanku Dan tsohon saurayintane idan bakimantaba nafadamaki
.
Tagyada kai dazaran kinji gabanki yafadi to sunacen tare saikiyi yanda zakiyi kifitardashi harkuje dakinsa

Inda za akawo maki maganin zakiga wani Abu cikin kwalba saiki daure bakin kwalbar bayan kin tabbatar tasha maganin daganan komai zaifaru zakigani

Godiya tahauyimasa sannan tamaida madubinta"" watan suwaiba biyu yanzu agidan saitazuba mata maganin kuma takulle bakin kwalbar

Shine dalilin abunda yafaru tadan nisa akwai matsala watakil nayi kurene gashi laifinta yana nema Nina yashafeni gashi dasafe bahalin kiran *hatsabibin boka*

Ranar babuwanda yakarya agidan tana ganin ranatayi takulle bangarenta tadauko akwatin tadauko madubin bayan tagama kiransa saigashi yabayyana tazayyana masa komai

Saida yayi dariyarsa wacce yasaba sannan yace laifinkine keda nacewa kidaure bakin kwalba shine kikadaure tamau kisani zuciyarsace kika kulle babu inda iska zaishiga danhaka kuncine yaketa mamayar zuciyarsa

Bayajin sanyi kokadan wannan dalilinne bazakiji dadinsaba idanma kika matsa hukuncinda zai yankemata yashafeki

Ido tawaro tace nashiga uku to yazanyi yanzu??? Yace abune maisauki kisassauta kamunda kikaimasa shikenan zai sauko 

Tasaukarda nannauyan ajiyar zuciya nagode boka ahuta lafiya tana miyarda nadubin tadauko abun ta sassauta daurin tamiyar ta aje saiyanzu taji hankalinta yadan kwanta


Baidawo da ranaba koda dare baidawo dawuriba"" yanashigowa dakinsa yanufa bangarensa yayi wanka yasaka kayan barci yafeshe jikinsa da turare yasauko zuwa dakin lubcy

Kwance takesaman gado abun duniya yashamata kai tunaninta daya karfa reshe yajuyeda mujiya?? Duk da tayarda da boka tasan bazaiyi abunda zai cuyarda itaba

Da sallama yashigo dakin Amman batajishiba saman gadon yahau tabayanta yarungumota yasunbaci wuyanta

Kamshin turarensa tareda sunbatardà yamata sukadawo da itàh duniyar gaske ahankali yaradamata akunne juyo kikalleni

Shiru tayi komotsi batayiba hànñu yasaka yajuyoda itah dakansa
Tasanne kanta kasaa hannu yasaka  yatallafo fuskarta yace meyasamu gimbiyata????

shiru taimasa haryanzun take yasoma aikamata dayan sako tuntana share shi hartasoma maidamasa martani

Sundade suna wasa dajunansu saida yasamu yar natsuwa yasake jawota jikinshi

Tadago tana kallonsa idonsà yanarufe kamar maibarci tace baban majeed murya atausashe yace inajinki akwai matsalane???

Tace akan kanwat batagama rufe bakiba yàsà hannu yarufematà bàki yace barci nakeji night 

Baisake dago kai yakalletaba yajata jikinsa yacigaba dà barcinsa itama ahakan barcii yadauketà 
.
Tundaga ranar baisake haduwa da suwaiba ba itakuma batada aiki saikuka  duk tarame saboda tunanin makomarta
.
Girki yanadawo wà hannuñta lubcy tace tashirya susameshi dàkinsa tabashi hakuri dadare lubabatu dakanta tashirya suwaibà

Cikinwàni bugaggen less tanajin dawowarsa tariko hannuntà sukai bangareñshi kirjin suwaiba sàifaduwa yake

Lubabatu cegaba taturah kofar da sallama yàña xaune saman kujeràh yana danna laptop lemune ahannunsa yanasha

.yadago yakallesu  kallodàya yamiyada hankalinsà wajen abunda yakegabansa






Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN  BOKA!!*☠


Chapter 37
       By
Gentle Lady💃🏽



Lubabatu tace barka da hutawa yace yauwa barka batareda ya dagoba"" tadanyi jim sannan tace dama dama wajenka mukazo

Yace inajinki to"" tasake gyara zama tace akan kanwata ne Dan Allah kayi hakuri akan abunda yafaru

Tayi shiru tanajiran taji mezaice yace yakiikeso ayi yanzu??? Saida gabanta yafadi karfa yace ya yafemata saikuma tadake tace kayi hakuri karkayanke mata hukunci mai tsaurii

Sai wannan karon yadago  yakallesu suwaiba tunda suka shigo  kanta yanakasa saikuka takeyi wani mugun kallo yawatsamata yace munafuka kawai aransa 

Yamaida kallonsa wajen lubcy yace wane hukunci  zanyimata bayan tazabi abunda yazama daidai arayuwarta

Saiyanzu taimagana cikin kuka tace Dan Allah Alhaji kayi hkuri wlh bahalina bane wannan shairin shaidanne

Baki yatabe yace  ban iyah ganewa yace waima menene dalilinda yasaka kika shigomun da itah dakina??? Wlh banason ko kallon fuskarta dazaran naganta  raina baci yake

Lubabatu tace nasan ranka zaibaci Amman hakuri zakayi tunda babu abunda yafaru tsakaninsu kadaure kahakurah Dan Allah badan halinmuba

Yace waikina nufin incigaba da zama da itah??? Hmm abunda bazaitaba yiyuwa bane tunda aka kawo yarinyar nan agidan nan ko hannunta bantaba rikawaba 

Amman hartayi wayonda zaraje wajen yarona waitabashi kanta tatube agaban wani katon banza suna aikata masha a kuma batsoro aranta batajin tsoron Allah ballantana na mutane tace Dan Allah kayi hakuriii alhaji cikin kuka take maganar 

Yamike afusace tashi  kibarmun dakina banason sake sakaki  acikin adanuwana nayi bakincikin aurenki wlh danasan haka halinki yake tunfarko bazan kai kainaba

Bata tashiba yasake daka mata tsawa wacce tasakata mikewa dasaurii tajuya lubabatu tace meyasa kakehakan nifa nasanka da hakuri

Yajuya mata baya yace banda irin wannan sannan  kema ina gargadarki karki sake zuwada itah gurinda nake

Tace wannan bahujja bace to akanme"" yace nasaketa itace kalmarda suwaiba taji aidasauri takara wucewa tana kuka

Jikin lubabatu yayi sanyi batasake cewa komaiba tajuya tafita abunta farinciki fal ranta amman idan kakalleta zakadauka tanada damuwane sosai

 kaitsaye bangaren suwaiba tanufa tasamu tanakuka tana hada kayanta "" lubabatu takarasa dasauri tace inakuma zakije suwaiba???

Inazanje bayan inshiga duniya kinsan sarai bazankoma gidan mahaifinaba Dan muddin yaji ansakeni kuma yaji labarin dalilin sakin nawa kashina yabushe

Dan wlh zai iyah kasheni"" lubabatu cikin alamun tausayawa tace toki zauna anan mana"" harkisamu miji saikiyi aurenki

Tagirgiza kai tace Anty duk yarda kikesona dole kibarni natafi saboda gidan nan"" bawajen zamana bane

Lubabatu tace nasani Amman aidarene kibari mana hargari yawaye"" tace bazan kwana agidan nan ba wlh Anty tafiya zanyi

Jakarta tadauka tayi gaba lubabatu tabita dasauri tana kiran sunanta Amman takasa tsayawa hartakai  bakin kofa sukaji muryansa

Yace ina zakije??? Tsaye tayi chak! Batareda tajuyowa  tace zanshiga duniyane amsarta saima tabashi dariya

Aikuwa yasoma dariya harsuka juyo suna kallonshi cikin mamaki yatsagaita dariyar yace idanma shizakiyi kece kika zabarwa kanki hakan

Amman kafin nan dole kizauna kiyi idda adakinki idan kingama idda daganan komai kika yankewa kanki daidaine dagahaka baice komaiba yajuya dakinsa"" 

Tsaye tayi  itah bata fitaba kuma bata komaba saida lubabatu takarbi Jakarta tamiyarda itah

Tundaga lokacin suwaiba takoma rayuwar daki saidai idan bayanan lubabatu taje suyita firah yawancin abincima taresukeci

Hartayi idda yabata takardar sakinta tareda motarda zatakwashe mata kayanta lubabatu ce tarakata hargida 

Tabawa babanta hakurii akan karya daketa dantuni dama yasamu labarii makudan kudii tabaiwa suwaiba sukarabu kowa yana kukan rabuwà saidakuma Innar suwaiba takoma rarrashinsu

Tace aibasu rabuba tunda mutuncine yahadasu saikusan magrib lubabatu taimasu sallama tawuce Dan gidanma taci abincin dare

 bayan kwana uku dafaruwan hakan sunayin break dasafe labila tace dady magana nakeso muyi takai karshen maganar tanakallon lubabatu""
Itakuwa saida gabanta yafadi

Yamurmusa to yarlele kyabaridai nagama cin abinci tundayau  bafita zanyiba kaitagyada masa"" bayan sunkammalà

Sukadawo cikin falon sannan yacemata inajinki maganar mezakiyi tanisa tace inaso kasa a kaimu gidan hajiya murmushi yayi yace saboda wannan kawai?? tokushirya zanyiwa Sunday magana yakaiku

Tace dady idanfà mukaje badawowa zamuyiba yagyara zamacikin rashin fahimta yace wani Abu mom dinku takemaki Wanda bakyaso???

Tadanyi Jim sannan tagirgiza kanta bakomai dady nidai nafison zama agidan hajiya kabarmu mukomacen islamiyar nan basucika karatu sosaiba cendin zamufi jindadi kuma uncle Hafiz zaikoyamana karatu

Yajinjina maganarta sannan yakalli lubcy yace kinji abunda tace menene ra ayinki???

Tace mefa tunda ita tazabarwa kanta kabarta tatafi duk inda zataje mana Amman tabarmun Dana"" tagallàwa labila  harara aikuwa majeed yafasheda  kuka yace 
  wlh dady nidai wujin Anty nakeso "" yace daina kuka zakabita jikin labilà yalake tasoma bubbugar bayansa cikin lallashi

yace tozuwa yaushe zakuje tayi karaf tace harnashirya kayanmu gobe  zamutafi  yayi murmushi to Allah yakaimu"" hajiya zatayi manyan bakii labila tayi murmushi yace Amman zanyi kewarku tace mumahaka

Washegari sukawuce wannan shine   mafarin zaman labila kano





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 38
       By
Gentle Lady💃🏽



Acen aka sakata islamiyya dakuma boko rayuwarsu sukeyi cikin jindadi dakwanciyar hankali tabbas tasan mamanta ce tayi sanadin mutuwar auren mahaifinta 

Amman batada halin sanarda wani koda tasofadawa dadynta saita kasa fada"" lubabatu tacigaba da zamanta sai yanda taso gida yakoma nata

Saikuma tatsiri yawace yawace kasashe wajen kasuwanci Sam tadaina zama gida babu yanda Usman baiyiba dantadaina taki yace mena rageki dashi mekika nema kikarasa tace bannemi komai narasaba Amman kasuwancin nakeso saboda kawayena duka mazansu sunbarsu suna kasuwancinsu

Dayake babanza akabarshiba duk da yanadan cijewa karshe dole yasaka mata ido wasu lokutan tanagida Amman kawai wasa zaiyi da itah 

Aibashiri yasoma azumie domin gojewa fadawa zina watarana dadare bayan sungama abunda yasaba akullum tajuya daniyar yinbarci

Yakira sunanta tadanjuyo tanakallonsa tace yadai??? Nisawa yayi yace waimezaihana muje kasar waje adubaki ni wlh nagaji hakurina   yakare ina gudun infada ga hakala

Tace toyazamuyi hakurindai xakacigaba dayi" cikin daga murya yace kullum maganarki kenan hakuridai hakuridai shin hakurin haryanzu yabani abunda nakesone??? 

Sokike garinyin hakuri infada ga aikata zina??? Wlh ninasan Allah yanakareni dayanzu nadade na afkawa ga aikata alfasha

Dakudina dakomai "" Amman abunda baifi karfinaba yana nema ya gagareni haba
Tace toya kakeso inyimaka  inda lafiyata qalau zaka furta hakan to banda lafiya ai

Yayi saurin gwaceta yace naji bakida lafiya Amman Allah dayasaukarda cuta saida yasaukarda maganinta 

Koda banida kudi wlh zan iyah yinrance domin samun lafiyarki Amman inadakudin nan bawai banidasuba Amman kinnace dole sai anan kikeso aimaki aiki

Dafarko nayi tunanin kobakyason zuwa wata kasane toyanzu gashi kinazuwa kasuwanci Amman Neman lafiyarkine bazakiba to wlh nagaji kara infadamaki gaskiya nadaina cutarda kaina

Tamarairaice fuska tace abban majeed kayi hakuri tomezai hana kayi aure kodan samun abunda kakeso

Yace wanne irin aure zanyi agaban idonki komai yafaru nayi auren Amman baikareni dakomaiba saitashin hankali""haba wannan wace irin rayuwace

Komawa yayi ya marairaice fuska please lubcy kitaimakeni  badan niba dangirman Allah kiyarda aimaki aikin nan

Baki tatabe tace nifakoda anyimun aikin Nan bazandauki lakuwarkaba kullum acebawa yanakanyin abudaya kamar abinci haba

Wani mugun kallo yawatsamata yace nafuskanceki kenan duk abunda kikemun dagayya kikemunshi ko??? Anya lubabatu kinatsoron Allah?? Mijinki yanason abu amman dantsabar mugunta kihanashi abunda kuma yazama halalinsa ranar gobe kiyama mezaki fadawa mahaliccinki

Hannu tadagamasa tace dakata usman shiruna bashine zaibaka lasisin gayamun magana son rankaba "" nihaka Allah yayoni banada jimirin daukar lalurarka danme zakaga laifina tunda banice nayokaina hakanba 

Zan iya juran komai amman banadaukar bakar magana"" da mamaki yake kallonta 
Baki budee yace umm lallai yaukinfito mun da ainahin halinki dakika  koya wajen kawayenki danni bahakan nasankiiba 
Kuma
Nagode inhar kudi suna biyawa rai bukata kibani sati daya zanbaki mamaki nidakaina bazansake cewa kije ayimaki aikiba 
Kiyita kumuiniya da kayanki indai jikinkine nadaina rabarsa ballantana abunda kike takama dashii

Yatashi daga kan gadon yadaukii kayansa yawuce fuuuu yabarmata dakin"" kallo tabishi dashii ta daura hannu aka tace nashiga ukuna🙆🏿 menene yakeshirin faruwa dani haka""???

Dasauri tadirko daga saman gado tadauki zani tadaura tafito""dakunan dasuke bangarenshi tahau bidaya bayan daya"" kowanne tabuda saitajishi bude 

Aranta tace kenan bayanan dasauri tasauko zuwa kasa falon kasa tahango haske ta matakala tasauko kasan

Chak tatsaya sakamakon abunda kunnuwantà sukajiyo  mata"" tasake saurarawa kodai karya kunnuwanta sukejiyomata

Yana kwance saman kujerah yadaura kafadaya akan daya alamu sun nuna yanajin dadin firarda yakeyi yalumshe idonsa yace ninedai bawaniba

Daya bangaren akace haba ammandai batan hanya kayi nikuma awa daza a kirani cikin wannan lokacin 

Dariya yayi yace aikinwuce komai awajena kingakuwa kinada mukami azuciyata dannakiraki bawani abubane

Tace hakane Amman inakabar uwargidan taka"" bakiyadan mere yace inajin tayi barci nikuma banajin barcii

Tasaukarda ajiyar zuciya tace  bakaji yanda najiba lokacinda nagakirankà dannituni nafiddarai dasamunka

Dariya yasakeyi yace togani nasake dawowa tamurmusa najidadi sosai inasu labila??? Yadan shafo kansa yace suna kano

Tace kana nufinwai haryanzu basu dawoba??yace eh yanzu aisunyi shekara acen sukandanzo suganemu tareda hajiya

Tajinjina kai Allah yataimaka yace Ameen




  
Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 39
       By
Gentle Lady💃🏽




Shirune yabiyo baya nayan dakiku sannan yakirah sunanta samrat tace na am"" yanisa maganafa nakeso muyidake bata wasaba

Tadan gyara kwanciyarta tace inajinka yace inaso gobe naturo gidanku maganar aure 
Baki tarike tace dagaske tareda kalalo ido

Yalumshe ido yabude tamkar tana ganinsa wani nishadine yakeji aransa cen kasan makoshi yace dagaske kuma banaso auren nan yawuce sati daya inafatar dai ashirye kike
.tarausayarda kai sosaima kuwa"" indai katashi " yace wlh sosai natashi inamatukar bukatarki atare  dani

Wani mugun dadi taji aranta  tace maganina yayi aiki kenan"" dasannu zan mamaye zuciyarka"" yace yanaji kinyi shiru kodai barci kikeji???

Tace barcin lafiya inatare dakai kawai inaganin kamar mafarki nakeyi wainice zaka aurah"" yagyara kwanciyarsa yana fuskantar kasa yace kwarai dama kinsan kamai lokacine yanzun kokacin auren namu yayi bakiji yanda nakejinki arainaba

Lubcy wacce saboda tsabar tsurewa batasan sanda fitsarii yasoma bin kafartaba tunda Usman yasoma soyayya da suwaiba baitaba kiranta awayaba 

Haka zakila baitaba furtamata wata Kalmar soyayya ba waisaigashi yautaji da kunnenta yana fadawa wata kalamai masu sanyaya zuciya Wanda rabon dayazauna yana koramata kalamai masu sanyi tun tana amarya

Nikuwa  nace kece kiKajawo bakibashi abunda yakesoba taya zaibata lokacinsa wajen fadamaki kalamai bayankuma babu abunda kalaman zasu kareshi dashi

Shin mezaihana ke idan bakyada juriyar daukar lalurarsa kibarsa  yayi aure mana yasamu wacce zata daukemasa lalurarsa 

Amman kinhanashi kanki sannan kinhanashi aure kenan sokike yaje ya aikata zina bakyajin tsoron cutar zamanine??? 

Idan ma baikwaso maki cutaba wlh kincutardashi kinkuma zalunceshi saikisan amsarda zaki kare kanki ranar gobe kiyama agàbàñ mahaliççinmu

Dayawa akwai mata masu irin wannan halin musamman matanmu nayanzu inhar bazan baka farincikiba bazan hanaka aureba 

Watafa tahanashi hakkinsa idankuma yace zaikara aure tace ba aimata adalciba"" aikoda yayi auren bazaiyi adalciba dan Allah jama a kunga laifinsa??? Wlh konine shi inda nakesamun kulawa nan zanmaida shekata kuma komai tanema zanyimata tunda nima tanabani abunda nakeso

Daga hakan saikuma tafara surutu tace anmaganceshi gashinan yanabin ta kamar bantee

Kullum yana manneda itah kamar jela dasafe bayafita aiki dawuri dadare kuma saiyadawo dawuri Amman bayahaka ranar girkina "" shinwai intambayeki wayajawo hakan??? Kome kikagani kece kikajawo kuma wlh dole kiga banbanciii
Kedakanki kinsan dole asamu banbanciii
Inakirah ga iyayena yayuna abokaina kannena mata muji tsoron Allah musan yanda zamutafida lalurar mazajenmu mukuma ji tsoron Allah musani komai mukayi sai antambayemu yazamanmu na aure gobe kiyama karmu manta da kwancin kabari tsallakar siradii sannan kuma karmu manta gida biyune alahirah akwai wuta akwai aljanna dole kasamu kanka adaya Allah yasamuna cikin tawagar yan aljanna Ameen Allah yasamufi karfin zukatanmu

Gabadaya hankalin lubcy yagama tashi jinyanda Usman yake furtawa wata Kalmar soba itaba wani wawan zagi tafurzar Wanda nikaina bansan ta iyashiba

Dasaurii tayunkura domin komawa aranta tana ayyana bamazata bari wannan tashigo gidan ba"" santsin tayes dakuma sanyin fitsarinda tasaki suka kwasheta tafadii jikake kuuuu

Tasaki wata kara wacce taisanadin dawoda hankalin Usman saman aikuwa dama bakin bene take hakan akafara gangaroda itah kamar kwallon magwaro sai ihu take tana kawowa kasa tabuga kanta dakarfe take tasuma kantaa yasoma fitarda jini daidai kawowar usman wajen

Sam baijiwani damuwa Aransaba kodan tabata masa raine oho"" atsanake yafita yakirah driver dakyar ya iya Kaita mota akawuce da itah hospital

Taji mugun rauni akai akayimatà gyara takuma goce akafa"akasamata Karin ruwa"" washe gari akagyara mata kafar 

Usman yasanardà doctor idan dahali suwuce ayimata aiki kasar waje"" yace aikin mene ai matarka batada wata matsala
.
Yadubeshi darashin fahimta yace bakagane menake nufiba kwanaki sunsamu hatsarine akan hanya towajen gyaranne doctor yace tanada kari agabanta shine dalilindà yasaka takasa haihuwa dakanta

Yabata wadansu magani yace tayi amfani dasu kafin aimata aiki" doctor yayi murmushi yace tanada kari agabanta kuma harka kusanceta tasamu ciki???
.
Inhar agabanta yake bazaka iyah kusan tartaba Usman shiru yayi dankansa yadaure"" doctor yalura dahakan yace barinasa akoremaka kokonto

Nanyakirah wata nurse yace takiramasà doctor Asma.u tace to tafità babu jimawa sukadawo tare yayimata bayaniñ komai itama yanda doctor yafada hakan tafada

Yajuya wajen Usman yace kadaijiko"" yasake kallonta yace kije rum 11 kiduba mana saikizo kimana bayani tace okay tareda fita

Doctor yacigaba da rubuce rubucen shi Usman kuwa saisake sake yakeyi aransa yanata jinjina maganar doctor





Aisha✍🏼
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
        (admin
   Arewa hausa novels 
       Novels villa
     Duniyan novels 
   Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
          And 
Cool novel, makeup and cooking) 

      WHATSAPP NO:
    +2347039625239
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠


Chapter 40
       By
Gentle Lady💃🏽


Bayan kamar mintuna talatin tadawo taturo kofar tareda sallama"" Usman yana ganinta yadago kansa"" kujerar kusa dashi taja tazauna

Tanafuskantar doctor Wanda shima ya aje alkalamin hannunsa yana saurarenta tace nadubata batada wata matsala""

Doctor yace shikenan kina iyah tafiya"" tace to tareda mikewa tafita" doctor yanisa yana kallonsa yace dama ninasan babu wannan ajikinta kamanta a hospital din nan tayi haihuwa biyu inda munga wannan matsalar aidatuni mun maganceta

Kodama tanada wannan karin ai a take zamucireshi basai andau wani dogon lokaciba haihuwa dabata iyah yidakanta yadanganta dayanayin jikinta sannan kuma yaranta sunada matukar girma kofar jikinta bazata ishesu fitaba

Idan munga kamar za arasa wani acikinsu shiyasa  harmuke mata aiki"" yakai karshen maganar yana kallonsa

Usman yanisa yace nagamsu da bayaninka Amman meyasa doctor yasanardani hakan???

Yace wacce asiviti kenan??? Usman yace abuja"" doctor yanisa yace baxaicemaka hakanba  inhar ba ita tace yasanarda kaiba ai itah tanajin yanayi ajikinta koda yafurta zata iyah karyatawa

Usman yadago da alamun damuwa afuskarsa yace meyasato zatamun haka???  Doctor yace to wannan amsar  abakinta zakajita kabari idan tasamu sauki kuka koma gida saikaji abakinta akwaidai manufaryin hakan

Yanisa shikenan doctor nagode bari Nayi waya yabashi hannu suka gaisa sannan yafito hajiya yafara Kira yasanarda itah sannan gidansu lubcy din

Ranar hospital din yawuni sai marece su hajiya sukazo labila kinzuwa tayi waisunada harda islamiyya washe gari yangidansu lubabatu sukazo harda kanwar mamanta anan suka barta suka koma

Hajiya kwananta daya takoma washe gari aka kai kudin auren Usman gidansu samira  mahaifin abdul tareda abokansa sune suka  nema masa auren ko hajiya baisanar mawaba danyasan zatace yabari sai matarsa taji sauki shikuma yanason bata mamakine

Ranar litinin aka kai sadaki akasa bikin sati daya duk da bahakan Usman yasoba Amman sunce sunason yin shirye shiryene

Sai anasaura kwana biyu daurin auren yasanarda hajiya itadai fatan alkhairi kawai tayimasa"" labila dataji labari murna tahauyi harsaida hajiya tabuge ta tace waikinji abunda akafada kiketa faman tikar rawa??

Tace najimana hajiya ba dad ne zaiyi aureba??? To idan banji dadiba mekikeso nayi??? Sainafadawa sahiba muhada faty na musamman
.hajiya takaimata duka taruga tana dariya tace banda shashanci mahaifiyarki tana gadon asiviti harta faty kikeyi??

To naga yanda zakihada Fatyn labila tayi cikin daki tana dariya tace aikuwa zakigani"" tunda lubcy tafarfado tamatsa akaita gida batason zaman asiviti

Doctor yakibata sallama yace takara hakuri hartaji sauki"" saida kanwar mamanta ta rarrasheta akan takara hakuri Usman yanazuwa Amman bainuna mata yasan komaiba saiyayima kamar babu abunda yashiga tsakaninsu
.
Wata zuciya tana rayamata kodai yafasa aurenne watakuma tana karyata hakan dole tanason taga *hatsabibin boka* totaya gata agadon asiviti wazatace yadaukomata madubin

Takaicii yabi yadameta nan take jininta yahau saida akaimata allurar barci dantasamu natsuwa
Washe gari kuwa da azahar akadaura auren samira da Usman akan sadaki dubu Dari hudu lakadan

Ranar samira tamkar tazuba ruwa akasa tasha saboda murna"" wai itace matar Usman" mutumenda yace bazai auretaba hmm gaskiya dolene tagodewa aminiyarta datakaita gun bokanta

Gashi tasamu soyayyarsa acikin ruwan sanyi yanzu dazaran tashiga gidan saikuma tayi yakin fitarda kidahumar matarsa wani murmushin mugunta tasakii

Saina rabaka da itah yazamana bakowacce mace agabanka faceni tasakeyin murmushin jindadi

Da marece motocin kai Amarya suka dauko samrat zuwa gidan Usman ranar ko asibiti baikomaba tunda yaje dasafe
Ranar Usman kam yahuce takaici dankuwa samrat batahanashi kantaba saida yabarshi Dan kanshi koshima yatausaya matane ganin tawahala sosai

Bayan yayi wanka yayi sallah yanamai godiya ga Allah daya sharemasa hawayensa yabashi samrat

Lubabatu  tana asiviti batasan wainarda ake toyawaba"" yakanje dasafe kuma yajemata da abinci sambata kawo yayi aurenba Amman tagayanzu kullum cikin fara a yake kamar tatambaya saidaikuma takama bakinta

Kachar tabari takara sati tamatsa dole aka sallameta ta tattara takoma gida ranar kanwar mamanta tatafi

Tunda Usman yafita baidawoba saidare"" lubabatu  tana bangarenta kaitsaye bangarensa yanufa yayi wanka sannan yatafi bangaren samrat

Cikin falonta yasameta tachanchade cikin adonta tayi kyau tana ganinshi tamike tatarboshi kiss yamata akumatu yace Amarya Kinsha kamshi

Tayi farida ido tace andawo lafiya"" yace qalau dauko mayafinki muje bangaren maman majeed kidubata tace to tareda wucewa tadauko sannan tafito suka jerah sunayar firarsu ta ma aurata

Tunda lubabatu taji muryan mace gabanta yayanke yafadiii" shine gaba tanabayansa yaturah kofa da sallama lubabatu ta amsa fuskanta tanakan matar da sukashigo tare

Usman ne yanuna mata waje yace tazauna kusa dashi tazauna tareda gaidata Anty inawuni yajiki

Duk daharyanzu lubabatu takasa yarda dagaske usman aure yayi tanakan gadon asiviti  tace qalau naji saukii yagidan

Tace Alhamdulillah "" usman ne yace maman majeed ga zainab  amaryatace yajuya wajenda zainab take yace zainab ga matata kuma farincikina itace ni nine itah inasonta fiye dakomai banason abunda zaibata mata rai inafatar zakitayani wajen faranta mata rayuwaa

Baki tatabe cikin ranta tace basaika fadamun yanda kakeson matarkàba jinhakan bazaihana inrabakuba

Amman afili murmushi tasaki tace karkadamu zanyima fiyedakai murmushi yayi yace nagode yajuya wajen lubabatu yace ga kanwakinan dan Allah inhar tayi badaidaiba kitsawatarmata kiyita hakuri kuma dukda nibanida  matsala ta bangarenki

Tasaki murmushin yake tace karkadamu bazantaba sauyawa ayanda kasanniba fatanadai Kanwata tarikeka amana""" takai karshen maganar tanajifartà dawani kallo nikam nace dàbiyu kenan

Kusa dàkunnenta yaradamatà magana kigodewa kanwarnan taki tanaji dani sosai nasamu abunda nakeso gaban lubcy yabada rass tace nashiga uku😳 ya akài hakan tafaru????gabadaya tashiga tashin hankali Amman dayake  yarduniyace saita wayance





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 41
       By
Gentle Lady💃🏽



Tace kai Amman naji dadi sosai hakan nakeson ji """ Allah yabarmun Kanwata"" yace ameeen itakuma samrat kunya duk takamata tamkar tanutse agurin

Fuskarta yashafo yace to yamaganar raba kwana tunda yanzu hartayi sati daya"" rausayarda kai tayi tace kaga banada lafiya   haryanzu dasaura

Kawai kabari  sai nanda satiii biyu kafin nan nawarke kaikuma kaci amarcinka sosai"" wani dadine yakamshi baisan sanda ya makaletaba yasakar mata kyakkyawar sunba abakinta

Wani mugun  kishi yaturnuke samrat kamar tasaki kuka"" lubcy talurah dahakan"" cikin ranta tace ke kenan dakika tsinceshi darana tsaka inakuma gani da nayi shekara  shabiyar tare dashi"" mekiike tunanin zanjiii

Afili kuwa saita dantureshi " murya kasa kasa yace please kibarni naji dimin jikinki Sam shiya manta yana tareda samrat lubcy ce tace baban majeed Kanwata kaifa takejirah naga alama kamar barci takeji

Sai alokacin hankalinshi yadawo jikinsa wata uwar kunyace  takamashi yadan Sosa kai sannan yamike yace mujeko samrat"" mikewa tayi tadan kirkiro murmushi tace Anty saida safe Allah yasauwake

Tace ameeen Amarya  nagode saida safe gaba tayi abunta yana bayanta harsuka bude kofa tafita shikuma yadawo dasaurii yasunbaci lubcy abakinta nadan tsayin lokaci sannan yadago yalunshe idonsa yabude fuskarta yashafo yana kallon cikin kwayar idonta  kamar mai karantar wani Abu
.
Tace kabarta tsayefa"" murmushi yasaki sannan yace saida safe yawuce koda yafita samrat bata wajen dasauri yabi bayanta"" bangarenta yasameta

Kuka take Amman tanajin motsinsa tagoge hawayenta tasake gyara fuskarta saman gado tahau dasauri tarufe jikinta"  da bargo

Yanashigo wa yayi sallama  ciki ciki ta amsa masa sallama saman gadon yahaye yadaga bargon yashige ciki"" idanuwanta arufe suke fuskarta bayabo ba fallasa

Ido yakuramata daga bisani yace yahaka kuma samrat??/ tace damefa??? Batareda tabuda idontaba yace hmm yau bazamuyi firabane??? Tadan muskuta  nibarci nakeji""

Yace tofa wannan shan kanshin wai duk Na menene?? Baki tatabe tace barci nakeji kawai"" yace kuma nibazan barki kiyi barcin ba chakulkuli yasoma yimata

Tasoma kyalkyatar dariya tanacewa bataso yabari"" yace shikenan barikawai inkoma wajen antynki dama dantanason kibani kulawane tabarmana kwananta

Yayi maganar yana yunkurawa  daniyar tashi hannutasa tajawoshi yafada jikinta take sukasaka dariya subiyun yace af ashedai anasona ba ason nadaga

Taharareshi cikin sigar wasa tace zanrama wlh dariya yasoma yimata takaimasa dukan wasa hannun yarike suka soma kokawa daganan suka zarce wasa yasauya

Bangaren lubcy kuwa sunafita tatashi da dingishi tarufe bangarenta tawuce kuryan dakinta tadauko madubin tashafa tareda kiran sunan *hatsabibin boka*

Cikin second daya yabayyana acikin madubin yanayinda  lubcy takeciki kallodaya zakaimata kagano tanacikin Matsala
.
Kafimma yayi magana tafashemasa dakuka""" kukanda yasaka shikuma yasoma sheka wata irin dariya saida tagaji dakukan tatsaya sannan yace mata menene dalilin kukanki

Tadago raunannun idanuwanta tace inaso akashe wannan matar mutuwa mafi muni waitayama taci nasaran shigowa gidan nan harta rushemun duk shirina

Yace tayanda kikazo masa kisani wannan matar tabanbanta dawadancen"" cikin tsoro murya na karkarwa tace kamarya boka???

Yace saboda itama tanada wani masha hurin boka agunsa tasamu damar ketawa zuciyar mijinki tadusashe haskenki agunshi wannan yasamo sanadi nahanashi kanki dakikai

Dama anan akeso kusamu sabani daganan komai zaifara lokacinda kikafadi aljanine yatureki harkikaita gangara zuwa kasa

Bokan yayi hakane domin karkisamu damar sanardani indau matakiii"" tace tomeyasa baka dakatar dashiba""" kaiyagirgiza yace niban isah inhana wani abunda sukaimaki yasameki ba yanzu haka Suna shirye shiryen yanda za afitardake kokuma ahaukataki

Baki tadafe tace nashiga uku toyanzu yazanyi???boka??? Yakece dawata dariya yace karkidamu aikogaba da gabanta zannuna masu babu maijadani yakwana lafiya

Sannan kisani mijinki yagano lafiya qalau kike saikisan yanda zaki kare kanki idan yatambayeki""  domin ta nanne sukasamu damar karya shihirindà mukai makiii

Dabaki hanashi kankiba dahakan baifaruba"" tashare hawaye tace nibansan abun yakai hakaba nibanason atausayà Mata tundahar tsautsayi yakaita takwanta damijina totajawa kanta mutuwa

Banaso abarta darayuwa"" *hatsabibin boka* yasake barkewa da dariya yace angama kisake yimun magana zuwajibi komenene zakiji bayanie  yanzuñ inatsakà  dayinwàni aikine nabarkiii lafiyàa

Yanakaiwa nan hasken yafito takeyabace  lubabatu tamiyardà madubiñ tasoma zagayen falon hankalinta atashe yaukam tasan koda kwanciya tayi barciii bazai dauketaba





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!!*☠



chapter 42
      By
Gentle Lady💃🏽



Taciji dan yatsanta yanzu kenan tashigo gidana tasameni da mijina Amman kuma takeso takoreni?? Hauka kuma to wlh nibazanyi haukaba saidai uwarta tayi

Yanda nakeganinta shiru shiru ashedai munafukace"" tanawani cemun Anty Ashe tasan tuggunda tahadamun nimadai nace taya Usman zaiyi soyayya aisaidai yayi aure domin kore sha awa Amman bazaisake sonwata halitta aduniya sama daniba

Kema kijirah nakusan fatattakarki daga harabar zuciyarsa bazanyi wasaba ko auren ma bazan barshi yasake yiba ballantana yasamu yanda yakeso
Lallai zancen duniya gaskiya duk abunka akwai irinka dubu aduniya

Yanda lubabatu tagadare haka taga safiya ko gyangyadi batayiba dasafe bayan yagama break yayi shirin zuwa aiki harsaida suka kawo kofar fita yatuna da lubcy yace wash tareda dafe kansa yajuya dasauri tatari gabansa tace mekamanta kabari indaukomaka

Yace wlh namanta bandubo maman majeed ba kinsan batada lafiya" tadan marairaice fuska tace to aiyanzu ka makara kabari saikadawo Mana.

Murmushi yasakar mata yace nagode dakulawa Amman kinmanta company nane kuma nine shugaba koda kinzuwa nayi hakan bazai samarda hayaniyaba

Tace hakane Amman"" shiru tayi tanajin faduwar gaba Amman dole tadake dantagwada ko maganin jiya yafara aiki tace nidai katafi muje"" sake kallonta yayi cikin murmushi yace nipa bance kirakaniba naga alama kamar hawanne bakyasonyi

Kizauna nan nizanje indawo tace bazakaba Allah da mamaki yakalleta yace waike mekike nufine??? Barifa ganin ina lallabaki kidauka banason matata karfa kimanta inada Yaya biyu da itah

Kodama banasonta albarkacin yayanda suke tsakaninmu zankula da itah ballana  inason matata
Idan ma dawasa kike banason irin wannan wasar inkuwa da gaskene kiyi saurin fatattakar wannan tunanin azuciyarki yawuce abunshi

Jiki sanyaye tabi bayanshi gabanta  yana dukan uku uku tabbas boka yace inhar tasaka abunnan agabanta harya kusanceta to duk abunda takeso dazaran tafurtashi Usman zaizama maibi yayya agareshi

Shima zaiso abun ufiyeda itah Amman jiya jiya Abu haryaso fara aiki yanzun kuma yaki anya banyi kuskure wajen saka abunba???

Kai ina daidai nayishi tanadai iyah yiyuwa ko akwai wata matsalane dole na gaggauta kiran raliya tunkafin wankin hula yakaiga kaini dare

Dawannan tunanin takarasa bangaren lubabatu kusanma tare sukashiga lubabatu tanafalo kwance saman kujerah tadafe kanta sakamakon ciwonda yakemata narashin barcinda batasamu tayiba adaren jiya

Dasauri yakarasa saman kujerar yadagota yana tambayar lafiya""??? Karamin tsaki taja tace wlh kainaciwo yakemun kamar  yarabe gida biyu

Samrat tadan harareta aranta tace munafukar banza yataba goshinta zafiii rau yayi saurin dauke hannunsa yace haba meyasa zakimun haka bakida lafiya Amman kikasa sanardani

Tayi yake tace karkadamu basosai nakejinsaba banaso nadamekune shiyasa fuskarsa duk tasaukarda alamun rashin jindadi

Samrat tamere baki saikuma tace inakwana Anty lubabatu ta amsa dasakin fuska tace ya amarci

Cikin yanga tace munakancinsa amsar tabaiwa Usman haushi ganin yanda take magana cikin gadara

Guntun tsaki yaja yace samomun ruwa kamar bazata amsaba saikuma tawuce kandai kandai kamar yartsana""

Hartafita dakin yasakejan dogon tsaki"" alamu sunnuna ambashi haushi kenan""" yamaida kallonsa wajen lubabatu yashafi fuskarta da murmushi yace kiyi hakuri kinjii

Talumshe idonta tabude saboda zafinda zuciyarta takeyi tace bakomai nifa ba aimun komaiba karma kadamu dawannan

Janta yayi jikinsa yana saukarda ajiyar zuciya"" tayi lamo ajikinsa ahankali tace dadyn majeed dan Allah kayi hakuri akan abunda naimaka

Saitafasheda kuka dasauri yadago kanta yace mekikamun kuma???? Tace ninasan mailaifice awajenka tadanyi Jim abunda naimaka ranar

Nafitone daniyar inbaka hakurii sainazame nafadi ranarnaso sanardakai lafiyata qalau dama nayihakane waidan karnasake samun ciki ganin yanda nake wahala waini anawa wautar hakan dabarace

Saigashi najawa kaina nasan yanzu bakasona ma" tunda kasamu wacce takebaka abunda kakeso "" ninajima natsani kaina Allah yasama inmut saurin rufemata baki yayi yace yakike wannan maganar

Nibanrikeki dakomaiba kuma nayarda da maganarki Amman dakinfadamuñ aisai murika shan magani duk da inason kihaifamun yara dayawa

Tace Kayi hakurii bankyauta makaba"" yace bakomai indai tabangarena babu abunda zansamu agurin wata dazaisa nadaina sonkii

Tasaki murmushi nagode Allah yabarmuñ  kai yace ameeen yasunbaceta saitin bakintaa daidai shigowar samrat wacce takelabe tanajiñ duk abunda sukefadà


 Shigowarta baihanashi cigaba da sunbatar lubcy ba"" hartakawo wajensu tadauke kantaa gefedaya Tamika mashi ruwan Sam hankalinshi bayagun""

Saida taga yanashirin wuce gonada iri tajaye bakinta hakan baimashi dadiba danyasamu natsuwa

Duk indayaje bayajin natsuwa matukar batareda lubcy ba"" saiyanzu yaga samràt yace au ashekin kawo ruwan??? Yayi maganar yanakarbà sorry nabarki tsayeko

Ko alamar jinkunyar abunda yayi baiyiba takaicine yakama samrat dayake macece wacce bata iyah siyasaba  sannan kuma tanada kishi sosai sambata iyah boye kishinta kokadan

Tsaki taja tawuce fuuuu tanakàiwa bakin kofa kuka yakwacematà tabude kofa tafita dagudu

Usman yatabe bakinsa tareda daga kafadà alamar baidamuba
 Karamin towel yadauko yanatsomà ruwan yanadanna mata jikinta tace kanagani tafita tanakukafa!!!

Cikin nunarashiñ damuwa yace tomezanyimata tunda badukantà nayiba"" zatayi magana yadorah yatsanshi akan labbantà yace bakida lafiya kidaina yawan magana yacigaba da abunda yàkeyi ahankali zàfiñkan yaraguuu

Idanuwañta suna lumshe tace katashi kabita dan Allah yayi murmushi yace waike meyasà kikacika damuwa  dawanda baidamu dakeba????

Tabude idonta tace saboda matarkace kumani komai kakeso nima inasoñsa"""  cikin tausayawa dakuma soyayya yashafo fuskartà yace wai anya za asamu irinki aduniya???

Kallifa kigani tsakitamun saboda inakulàda matata tanagani kuma bakida lafiya kefa harkwananki kika barmataa Amman waihartake kishiñki kebakiji haushintàba datari kemaki miji tsayin satii biyu

Aràntà tace nikuwa naji haushi bana nunawane kawai afili murmushi tayi tace aini natsufa nabarma yara aikishi bashine so ba abunda akekiràh so kasoduk abunda masoyiñkà yakeso






Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 44
        By
Gentle Lady💃🏽


bayau nasaba fadamaki hakanba kamar inakara cewa kicigaba tashare hawaye tace toyakikeso inyi.
.
Nikaina bansan sanda raina yakebaciba bana iyah juran ganin wani tareda abunda nakeso musamman Usman danban hadashi dakowaba

Raliya tace hu um abunnaki babbane tonidai yanzun mama ta aikeni idan nadawo zanbiya saina sanarda ummar hakan yayimaki???

Tayisaurin gyada kai tace yayi Amman Dan Allah kicemata taje yauyau din nan danni banaso narasa mijina tace karkidamu zansanarda itah idankuma yakasa sainasake karbomaki inda mukaje

Tace shikenan sukai sallama tana aje wayar taji tashin motarsa ta window taleka tana kallonshi watakan saiyanzu yaga damar fita takai kallonta kan agogo shabiyu saurah tayi kyacci aisaina rabaku bazan dauki wannan ba

Cendinma da akafitardani tafi karfina Amman wannan daganinta sokuwace cikin sauki zanfitarda itah dawan nan tunanin takoma takwanta

Bayan kwana biyu dafaruwar hakan lubcy tasake kiran *hatsabibin boka* bayan yabayyana tace maganarmu taranar wlh boka nakasa samun sukuni kokadan inaganin kamar takusa rabani damijina""

Dariya yafashe da itah wacce taisanadin girgizawar madubin saida yadade yana dariyar sannan yagintse fuska yace"wayafadamaki akwai bokanda ya isah yayi jayayya dani

Yasake shekewa da dariya sannan yadauko wani madubin yashafa yayi yansurutunsa saigawata wuta tayi tartso saiga bokan ya bayyana acikin madubin daure cikin sarkaa

Yanacikin mawuyacin hali yanuna mata"" yace kinganshinan yana ajiye acikin kurkukuna nakarkashin kasa""  babu wani mahalukinda yataba shiga ciki faceni

Sannan kuma duk Wanda nasaka aciki bazai fitoda raiba saida najamasa kunne akan kodatazo karyasake yamata aiki

Amman saiyayi jayayya nikuma Na aika dakarun aljanuna suka daukomun shi"" yanakaiwa nan yashafa madubin bokan yabace

""  yamaida kallonsa"" wajenta yace naturah daya dagacikin aljanuna yayi shigar bokan domin nasamu labarin sunakan zuwa wajensa yabasu magani akan mijinki yadaina kulaki karshema saiya koreki

Yanisa dalilinda yasa mukai hakan zanturah aljani hayyanul zairi domin ya magance matsalar

Tagyara zamanta tace kamarya boka??? Hannunsa yadaga yasoma kiran hayyanul zairii saigawani haske yabayyana kafin kyaftawar ido saigawani kyakkyawan aljani

Yabayyana ciikin shigar bil Adama kamarshi sak Usman lubcy tazaburah bakinta yanarawa tace wannan ai mijinane

*hatsabibin boka* yasake kecewa da dariya yace wannan dakikegani bamutum bane aljanine shine Wanda zaigama maki aikinki cikin saukiii

Lubcy tayi tsuru kamar tasaki fitsariii yacigaba zanturashi wajen kishiyarki azuwan mijinkune"" cikin rashin fahimta tace to ainikuma bazan banbance tsakaninsuba karfa asamu sabani

Yasake shekewa da dariya yace awajenki fuskar bokanta zakigani cikin kyakkyawar shiga mijinkima haka sauran mutanema haka

Amman awajenta zataganshi mijinki kullum zairika zuwa yanadaukarta sunafita unguwa kowasaiyasan dahakan ranarda mijinki zaiganta aranar aljanin zaikasheta yashanye jininta tareda bokanta saiya sawa motar wuta

Kowa zaidauka hadarine sukasamu sannan kowabazai zargekiba itakuma zatadauka aikintane yaci yayi shiru yana kallonta

Sannan yace dangane damijinki kuwa tunda dakinta yake kwana zamuhada maki wani maganie gobe gobe kibabbatar tashashi

Dazaran sunkebe adaki zatarika sakin wata irintusa maishegen doyi"" idankumà takwanta kafinsafe zatayita fitsariii
.nasan mijinki babu abunda yatsana kamar kazantaa cikin kwana biyar zamumaidatà kàzama

Mijinki bazaisake shiga dakinba daganan hayyanul zairi zaifara aikinsaa Amman kafin nan sunce kituromàsu kayan aikii

Zakiga abunda kikeso"" tawashe hakorah tace gobe gobe zakagansu godiya nake daganan yabace tamiyarda madubinta

Washe garikuwa tacewa Usman tanason zuwa gidansu sajida tadubata batada lafiya "" sosai yasotabari yakaita tace ah ah aitasamu saukii zataje dakanta

Yabata kudiii masuyawa tàyiwa sajida sayyyar kayàn jinya kaitsaye kasuwa tanufa tasiye dabbobin Shannan tabiya gidan sajida sukasha firah

ice cream tasiyo tazo dashi gidan ta ajeshi yahuce saida taga maganin tabarbada tabarbada aciki tayamutse tasaka cikin fridge yayi kankarà

Dama sunadàn tabafirah akasa kafin yadawo tasaukomasu dashi"tabata daya tasoma shannata""" itama tafara shaa

Tace kaigaskiya akwài dadi Anty idandawañi kikaromàn"" tace ashedai kinasonsa sosai bari nàdàukomaki





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




chapter 43
       By
Gentle Lady💃🏽



Yace Amman bakowacce mace tasan wannan ba ko??? Dankuwa dakowa yasani aida samrat kwata kwata bazatayi kishinkiba

Kodayake hali badayaba"" tamurmusa tace lokacintane taci yarintarta "" murmushi yayi yace yarinta da kishi aibazaiyiba yamike yadauko mata maganin ciwon kai yasauka kasa yahadamata tea tasha sannan yace sukoma cikin daki

Tace aikifa zakaje"" murmushi yasakar mata yace karkidamu dakinsamu barci zantafii yayi maganar yanajan hannunta suka shiga dakinta
.
Yakwantarda itah yanashafa bayanta ahankali"" cikin yan mintuna kalilan barci yashureta damakuwa barcin takeji

Bangaren samrat kuwa tanafita tayi bangarenta tanata darzar kuka"" abunda yake kasa gareta takwakwaloshi tayar tana hara rarsa tamkar shine yayimata laifi

Lallai tsuguno baikareba tana takamar tashigo gidan Usman asaukake ashebatayi komaiba yanda take tunanin yanason matarsa abunhar yazarta tunaninta

Wayarta tadauko takamo lanbar raliya tasoma kirah"" saida takatse tasake Kira sannan tadaga tafashemata da kuka

Cikin tashin hankali tace raliya inacikin matsala Dan Allah kije kifadawa mamana wlh aikin nan data bani baiyiba

Raliya tace bangane baiyiba wajenwa ta karbomaki maganin??? Tashare hawayenta tace wajen bokanta nima dai bansanshiba kuma wlh nayi duk yanda tace

Raliya tanisa tace tomenene nakuka kuma?? Kodai kinyi halin nakine nasanki dashegen kishin tsiya

Tashare majina  tace haba raliya kinsan meyamun kuwa???? Tace inakuwa zansani basaikin fadamunba "" anan takwashe komai tasanarda itah

Tace haba aiko zuciyar dutsece dani dole inji haushi agabanafa yahau tsutsar bakinta kamar yasamu mintiii

Raliya tafashe da dariya hartana  rike ciki abun yatunzurah samrat saitasake fashewa dakuka tace yanzun sakayyar dazakimun kenan duk irin abunda naimaki nikuma infadi bukatata kihauni da dariyar mahaukata bakomai nagode  sai anjima

Tace please karki katse wlh badariyar mugunta nakemakiba ina mamakine kisamu mace damijinta harda yaranta Amman kifita kishi

Tace to aikishi halittace kikasani ko itah ba ahalicceta dakishinba""" tayi maganar tana harare harare kamar raliyar tanakusa da itah

Raliya tace kowacce mace dakikagani  tanada kishi akan abunda take so damadai batasonshine zakifadi hakan
.
Amman kinsan tanasonsa tundahar tahaihu dashi kawaidai kishin watane yafinawata kuma bawai finshi yayibaa kawaidai akwai masu boyenasune

Wannan shine babbar matsalata dake rashin boye kishinki menene yakashe maki aure dafari bawannan mahaukacin kishin nakiba

Kisani komai maganinda kikeyi"" muddin kinada kishi sosai maganinki bazaiciba"" kishi yanarage karfin soyayya azuciyar miji

Bawaikuma kinuna bakya kishinba yasan kinayi Amman saikidanne kiga yanda matarsa tayi kincefa tana asiviti akayi aurenku Amman datadawo maimakon tatada fitina saimatace tayafemaku kwananta

Tabaku harsati biyu kusha amarci atunaninki tagaji damijinne??? Kodaya kawaidai tasan komai narayuwar tafiyada danamiji

Anan zandanyi magana akan mata masu shegen kishin tsiya watakishin nata kamar badiyar musulmaiba

Kisani kishi mafarin sakine domin duk macenda tafaye kishi dawuya kaga aurenta yarane ba asaketaba "" nikaina matanda nasan ansaka gameda mugun kishi bansan iyakarsuba

To kintada bakin kishinki adole kekawai zakizauna damiji kuma anfisamun haka awajen uwargida tunkinayi mijin yana lallabaki karshema yabuge iskanki
 Ninasan wata wlh tanatare damijinta baida arxiki sunatare haryayi kudii lookacinda yadace tazauna taci arziki akan yakara aure kishi yaturata tahau bala I taki kwantarda hankalinta

Tundayayi aure baida kwanciyar hankali kullum cikin fadatake da amaryar tunyana lallashiñtà haryagaji yagano itace batason za man lafiya

Zancenda nakemaku yanzu wlh yasaketa saki daidai har uku dadaya daya akafara koda yasaketan takoma gida idan aka sulhunta tadawo maimakon tagyara hali saitadorah daga inda akatsaya

Abunda saki yakenuni jankunne ne idan anyimaki daya saikiyi hankali Amman ayimaki harbiyu sai ancike sannan kidora hannu aka🙆🏿 kice nabani Na lalace

 Shin mezaisa kafin hakan tafaru kiyiwa kanki karatun tanatsu??? Ni mata kunabani mamaki dayawa sunsanifà Amman basa aiki dasanin saisuyi aiki dazuciya kusani duk wacce take aikida zuciya lallai zatakaita gahalaka imma mata imma mazà domin zuciya abokiyar shaidance bayada wajen zama facekusa da itah domin abukadan zairayamata yikaxa yikaxa

Kuma kunsan shaidan baya sanyawa ayi alkhairi saidai akasin hakan idankuwà haryasakà kayi toyanada manufaryin hakan zai darsamaka abun azuciyarka dukdanfa kakauce hanya

Ya Allah kakaremu damuda zuriarmu dagafadawa tarkon shaidàn kahana kunnuwanmu jinsautin kidansa Allah kakaremanà zukatanmu da imaniñmu Ameen


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 45
       By
Gentle Lady💃🏽



Mikewa tayi tahausaman tana kallonta ganin tahaye tamaza tawarware wani Dan kulli na magani tazuba daidai inda lubabatu tatashi tamiyarda kullin saitin zanenta takulle

Tagyara zamanta tacigaba da shan ice cream dinta"" lubabatu tasauko tareda ice cream ahannunta taxauna tamika mata sanan tasamu guri tazauna suka cigaba da labari

Ba ajima sosaiba lubcy tace barci takeji zataje takwanta" tayimata saida safe tahaura sama takwanta abunta

Ita ma kaitsaye bangarenta tanufa tasake sheka wanka tadauko ragowar maganinda aka karbomata wajen boka tashaa babu jimawa dashansha taji kaman cikinta yasoma mirdawa

Tadan dafe cikin zuwa cen saitaji tusa tadan karkace kafarta tusar tafito suutttt suuttt tasa hannu tana kore warin tusarr

Ba afimintuna gomaba tasake dage kafaa tusar tafito buuuut buttt tayanzu tadara ta dazu wari sau hamsin

Wanna karon saida ta Dade hancintaa"" motar Usman taji tashigo gidan dasauri tatashi tadage labule tareda fesa turaren daki

Aranta tace danasani banci waken nan yaudayawaba gashi duk yabatamun ciki"" sannu sannu warin yafita koda usman yashigo kaitsaye bangarenshi yanufa

Saida yayi wanka yashirya yayi bangaren lubcy yasamu tayi barcii saiyawuce bangaren samrat

Yana saka kafarsa bangaren yaji wani bakon al amari wani shegen doyi kamar Yakoma saikuma yayi tamaza yashiga dakin tareda  sallama

Tanasaman gado tanata mutsuiniya domin wata tusar takeji
Saman gadon yazauna yace  nashigo yau bansameku a faloba"


Tace ah wlh cewa tayi barciii takejii nikuma nagaji dazama nidaya shiyasa nadawo daki""" tamike dasauriii yace inazaki kuma???

Hartakai bakin kofa tace inazuwa Dan Allah harda dangudunta tasauko kasa tasaki tusarta tanata matsar ciki wai idan daragowar tusar tafito 😂nikuwa nace tusa bakashi bace samrat

Tadanjima wajen sannan takoma dakin tareda  ragowar warin"" bayan tazauna yasoma jinwani chanjii yadan bata fuska yace samrat wannan kuma warin menene??? Tunsanda nashigo nakejinsaa sama sama

Tace eyem umm umm inajin berane yamutu adakin nan nima inajin warin sa sosai"" shiyasa naketa fesa turare tayi maganar tareda daukar tirare tasoma fesawa

Yayimata kallon rashin yarda yace berah kuma samrat agidan nan ??? Tunda nake gidan nan bantaba ganin berah yashigoba

Tayi saurin gwatseshi tace aishine dalilin dayashigo yasaka yamutu wlh berane maganarta tayi daidai dasurbuno wata  tusar wacce batasan dazuwantaba
Babu shiri Usman yadade hancinsa

Yana kallonta yanda itama tarufe hancin yace umm lallai dole kirufe hanciii wannan shine beran dayamutu????

Tsuru tamasa da ido uwar kunya takamata"! Yace mekika cihaka samrat yabatamaki ciki??? Cikin jin nauyi tace wlh rabon ayi nadafa wake jiya nacikuma nasan bayashafamun lafiya batamun ciki yakeyi

Yanisa tareda cire hannunsa daga kan hancinsa yace Amman dakin kirani kinfadamun aisai insiyomaki magan" kafin yakarasa furta magani tasake sakin wata

Aibaisan sanda yazama natsayeba saigashi bakin kofa yacemata night baiko juyoba yawuce""  tayi tsuru yau Wake yatonamun asiri ina zaman zamana""

Turare tadauko takwanta dazaran barcii yasoma figartaa tasaki tusa tsabar warin tusar saiya farkarda itah

Usman kuwa yanafita dasauri saida yakai bangarensa  yasaki hannunsa dagakan hancinsa yaja iskaa yasaukarda ajiyar zuciya aransa yace wai ashedai tusar mata doyine da itah wannan abun aisaiya kashe mutum"""

Yasake nisawa nikam bazankomaba dannima idan nayi wasa cikina zai lalacene gabanza"" dawan nan tunanin  yakwanta yaukotakan abinci baibiba danyasan kodayacishi saiya amayardashi

Bangaren samrat Kuwa tarasa dalilin bacin cikinta duk datasan wake taci amman warin tusar yayi yawa ahakan taketa fesa turere duk sa inda tayi tusar

Kafin safe tiraren sanyaya dakin yakusan karewa""" washe gari tamakara koda tafarka takoma qalau fita tayi tayi break dantasan Usman yajima dafita

Duk lokacinda yatunkari kofar dakinta warin tusar yakemasa maraba hakan yasaka yamadaina shiga tsayin kwana hudu batasakashi a idontaba

Zaune take cikin falo damuwar rashin ganinsa tayimata yawa tana tunanin anya aikin boka yayi kuwa

Kofar dakinta akaturo Usman ne cikin shigar kananun kaya sunyi masifar karbarsa"" yayikyau kuruciyarsa tadada fitowa

Fuskarsa  tana kumshe dawani sihirtaccen murmushi tsaye yayi bakin kofa yarungume hannuwansa yajingina dakofar yana jefanta dawani salon kallo nasoyayya maimatukar kashe jikin Wanda akayiwa

Itakanta tayi mamakin ganinsa alokacin""" cikin sanyin murya tacemasa sannu dazuwa"" yace yauwa sammmratt yanda yaja sunanta harkarkashin zuciyarta tajiii talumshe idonta tabude tace ka karaso mana"""

Kafada yamake yace bayan kinki kitaso kiyimun welcome bayankuma kinsan wajenki nazo"" tadan zaro ido tace nikuma???

Kaiyagyada ahankali yace sosaima inawajen aiki gabadaya narasa natsuwata jinake kamar zanhaukace idan bansakaki a idonaba

Saiyanzu danaganki nasamu natsuwaa "" aranta tace wow maganina yafara aikii tayi Farida ido tace kaidai kodai wajen Antyna kazo

Tsakiii yaja yace nibata gabana wlh nitunfarko danasan akwai irinki mezaikaini aurenta atsarina nibanason mace maikiba  sannan banason macenda tafaye fari sosai nafison Dan daidai kamardai ke

Yakai karshen maganar yanajifanta dawani kallo maisaukarda kasalaa"" itakuwa dadi duk yakumeta ganin tayi shiruuu yasaka yatako zuwa inda take yazauna juyoda itah yayi tana fuskarntarsa yace Yanaga kinyi shiru

Tarausayarda kai bakomai yace so bawan nanba yanzu mekikeso ayi"" cikin shagwaba tace yawotakeso akaita yace bakida matsala tashimuje damakuwa ashirye take mayafinta kawai tadauka sukafito

Falon kasa sukasamu lubcy tanaganinshi tace anzo gurin """ juyawa yayi kamar baigantaba saida samrat tace bakaga antyba???

Yace idanma nagantà mezanyi mata nibata gabana muje please" cikin murmushi tace Anty zamudanje yawo"" itama murmushin tamiyar mata tace tosaikundawo azomun dayan

Usman yaja dogon tsakii yawuce fuuuu samrat tawuce kandai kandaii  ita aladole gamai miji saimundawo antyy

Tace to adawo lafiyaa sunafita lubabatu tatintsire da dariya hartana tafa hannuwa saida tasoma hawaye

Sunafita yan aiki sukafara kallonta da mamaki dama sunga lokacinda yashigo kuma yacemasu wajenta yazo Amman sundauka yayantane saigashi sungansu cikin yanayinda zainuna soyayya sukeyii





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 46
      By
Gentle Lady💃🏽



Hannunta tasagalo cikin nashi harsuka kai bakin motar""" yabude mata tashiga shima yazagaya yashiga sannan yatada motar" yayi hon maikulada get din yabude masu yafitaa"""

Suna hawan titi tasukarda nannauyar ajiyar zuciya  "" yakalleta yace yadai?? Talumshe ido tace wlh wani farinciki nakeji danasameka

Yanakallon titi yace dagaske???? Tace sosaima kuwa"kaifa????  yacenima fiye dahaka wani dadine yakara kumeta

Yace ina kikeso mufara zuwa???? Tace zoo yace angama""" gidan zoo sukafara zuwa ko ina tana makale dashii sunhadu damutane da dama harwadanda tasani tana gabatardashi amatsayin masoyinta abun alfaharinta

Kamar suce to mijinkifa??? Saikuma sukyale yinin ranar sunyi yawo harsun gaji saigoshin magrib yadawo da irah gida yana saukarda itah yace zaije sallah nansuka rabu tayi cikin gida cikin yanga shikuma yakoma motarsa

Yaja yafita yanahawan titi yabace batt dashi da motar"" dayake ranar baranar gurkinta bane wasa wasa kullum aljani usman saiyaxo  suntafi yawon gari

Tuni samrat takara kyau  tayi haske abunta" abudaya yake damunta duk yanda tamatsu  dason Usman yakusanceta  yakii abun yasoma damunta

Yaukam takuduri aniyar duk yazo sukafita saitasan yanda zatayi yabiyamata bukatar ta dawannan tunanin tawuni

Yanazuwa kuwa tace yajirata  tayi wanka tafito daga ita sai dangalallen towel saiwani kwarkwasa takeyi agabansa"" ido yakura mata shikansa tadimautar dashi Amman bazai safa alqawarinda yadaukarwa sugabansaba koda zaiyi hakan sai mijinta yagansu tare

Duk yanda taso tadauki hankalinsa Sam baidamuba hartagama yau   shigar kana nan kaya tayi sun bala in matseta komai najikinta anagani tadauko wani fitsitsin gyale tayafa tafesa turare wasu takalma masu matsakaicin  tsayi tasaka"tajuyo takalleshi shimadin ita yake kallo tayi fardayan idanuwanta tace yakaganni????

Wow So beautiful"" kinganki kuwa tamkar wata tauraruwa gaskiya nayi dace dasamunkiii" tasake sakin murmushi tace tomuje sukafito tana makale da kafadarsa yanzu ko lubcy bataiwa magana suketafiya

Bangaren Usman kuwa yauyakasa zaman office wata matsananciyar sha awa take damunsa saboda yakwana biyu baijegun samrat ba saboda doyinda yakeji

Itakuma lubcy duk dayagano kalau take yashareta  danyakudira aransa inhar ba itah tanuna tana ra ayiba bazaisake nemantaba abunda baisaniba lubcy ko ajikinta bataki suyita zama ahakanba

Yaso daurewa Amman yaji ina Dan maararsa tamatsamasa key din motarsa yadauko tarreda turare domin yakare kansa da warin yasanarda ma aikatan wajen zaije yadawo

Kaitsaye gida yanufa yayi hon maigadi yaduba yaga kowaye gabansa yafadi ganin Usman sannan yadawo dakallonsa ciki wajen samrat dataketa zubawa wani shagwaba

Muryar Usman yaji yanacewa sani waime kakejirah??? Kabarni anan?? Cikin rudewa yabude masa kofar yanatunanin mekuma zaifaru yau

Yanakunna hancin motarsa yagansu ido yazaro waje"" yanakallonsu da mamaki"" ahasale yataka burkii yafito kamar walkiya daidai zaibude mata mota sushiga Usman yadafe murfin motar yace malam wayekai??? Kuma mekakeyi anan ???

Mutumen yajuya wajen samrat yace wannan kuma waye??? Inakika kwasoshi??? Tashagwabe murya tace haba sweetyna ni inazansanshi yanda kaganshii nima hakan naganshi wlh bansanshiba

Usman yayi kururuwa yachakumo wuyanta"" yashakee yace nikikecewa baki saniba to wlh yaukoni koke saina kasheshi mutumen yaturreshi dakarfii yace matar tawa zaka kashe???

Wlh dakuwa ka aikata babban kuskure barganin nakyaleka da itah tsawon lokacii inason matata"" Usman baki bude yake kallonsa yajuya wajen samrat wacce tamakale jikinsa yace kifadamun samira waye wannan???

Cikin daga murya tace mijina nemana maisona kuma maison farincikina"" saunawa zanfadamaka banasonka natsanekaa waimenene yakawoka gidan nan yanzu????/

Tsaki taja takalli mutumen tace mujeko sweety nagayana nema yabata mana lokacii wai ma inazamuje yau""" kaitsaye yacemata hotel tayi ihun murna yauwaa masoyina takaimasà sumbata akumatu sannan taballawa Usman harara shikuma yabudemata kofa tashiga yazagaya mazauninsa sai murmushi yakeyi yauyagama aikinsa yatada motar ganin basu bude get ba yasoma hon kafin yayunkura hartafito tace kai sani Dan iskanci baxaka budemana kofaba tsofaffun munafukai saura kukara gaba kuce kunga wani yazo gurinà tajatsaki takoma cikin motar

sani jikinarawa yabudemasu yaharba motar kantiti tundaga Usman masu aiki dakuma lubabatu wacce hayaniyarsu tafito da itah tareda kawarta sajidaa tsaye suke kowa yana al ajabin wannan abun Usman kasa magana yayi raibace yawuce cikin gidan ko sannu dazuwan da lubcy takemasa bai tsaya amsawaba

Shikam yaga jarabta duk macenda zai aurah saiyasamu sabani da itah haryau baiyi daceba

Bangaren samrat kuwa sunafita Usman dinta yace wai waye wannan mutumen??? Baki tatabe tace barshi wani tsohon saurayinane wlh bansanma waye yanuna masa gidanaba murmushin gefen bakii yayi

Kaitsaye wani babban hotel suka zarce Yakama masu dakii tundasuka shiga tamakalemasa damashi irin wannan ranar yakejirah yamorewa jikinta kafin yashanyemata jini

Kaitsaye yasoma sunbatarta harsukakai kangado wani yanayi tasamu kanta acikinsa Wanda batasan konameyeba dagahaka batasake sanin komaiba

Hayyanul zairi yakoma ainahin suffarsa ta jinnu sannan yakusanceta samrat batasan mekefaruwaba saida yagama abunda zaiyi sannan yadafata suduka sukabace

Samrat sanyitaji yana ratsata ahankali tabude idonta cikin wani dajii tagansuu ga bokan akusa da itah zabura tayi tanajada baya tace kaiwaye??? Ina mijina??? Kodai Usman Dan yankan Kaine????

Bokan yakalleta ahasale yace wazai amsamaki wadan nan tambayoyin naki??? Kuka tafashe dashii tace Dan Allah karka cutardani banmaka komaiba kamiyardani inda kadaukoni

Dariya yafashe da itah maitsoratàrwà dagabisani kuma saiyafasheda kuka maitsuma zuciyaa samrat abun yatsoratata tuntana jadabawa hartadake tamatso kusa dashii tace kaiwaye???mekakeyi anan Kuma meye dalilin kukanka da dariya alokaci daya???

Bokan    baicemata komaiba  saidayayi kukan mai isarsa sannan yadago yakalleta yace yake wannan yarinyar kisani bansan inane nanba dangane dani kowaye sanin hakan bazai amfaneki dakomaiba dalilin dariyata shine kekanki nalurah bakisan halinda kike cikiba dalilin kukana kuwa inatsoron namutu bansan mezan tarar acikin kabarinaba

Tayi saurin tarar numfashinsa tace mezaisa bazaka sanardani kaiwayeba??? Yace saboda bazaki fita ananba kingakuwa babu amfanin kisanii

Zaburah tayi tace mezakamun??? Kasheni zakayi??? Menaimaka tana maganar tana kuka kaiyagirgizà mata yace nikaina mutuwar zanyi mezan kàrudashi idan nakasheki????






Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 47
      By
Gentle Lady💃🏽



Tatsagaita kukanta tace wayene zaikasheka??? Batareda fargabar komaiba yace Wanda zaikasheki"" idanuwa tazaro waje tace laifin me kaimasu????

Yadanyi jim sannan yace sunana uwaisu nakasance nidayane awajen iyayena suna matukar sona sundauki son duniya sundora akaina bakamar mahaifiyata batason tagakomai yatabani

Mahaifina baida hali sosai saidai yanada danrufin asirinsa kwatsam sai Allah yayiwa mahaifiyata rasuwa mahaifina ya auro wata azzalumar mace batada imani kokadan bata tausayina nikuma gani sangartacce bansan komaiba na ilimin boko ko arabiya

Matar babana  duk abunda takemun sainarama domin ni mugune Na iyah mugunta bana yarda kowa yacutardani dataga takasa komai dani harbokanta baiyi nasara akainaba saitasa mahaifina yaturani almajiranci

Muna zaune asokoto sai akadaukeni akaturani Maiduguri nikuma tunda aka kaini sainafara biyar yara munazuwa yawo nasake hinjirewa inasake yinwayo mukaballe dawani  yaro jabir zuwa tarabà

Dagacen mukawuce jos yawomukaitayi harmuka samu wani boka yasoma koyamana bokanci"" abokina Wanda muke tare mundade muna harkar bokanci harmuka kware sosai saimukadawo zariya dazama

Acikin wani jeji kusan duk dare mukan hadu muyi tadi dani dashi kusan abunda yarabani dagida nafada bokanci matar ubace shima haka

Munakan haka saiyayiwa wata mata aiki itakuma kafin tayi aikin sai mijinta yakamata shine yatutseta saita sanardashi Wanda yayimata shine takaishi wajen abokina

Dayaje yayimasa  wa azi sai abokina yadaina wannan harkar kuma yasameni akogon danakeda zama yayimun nasiha dayake shiyafini ilimin addini danshi yanada sani sosai

Nikuwa sainace nikam bazandaina harkar bokanciba saboda anan abincina yake sainayi amfani da maganar mutane dasuke cewa duk sana arda kasamu kanka acikinta to itah Allah yazaba maka

Babuyanda abokina baiyiba domin ganardani harkarnan batada amfani kuma tanada hadari Amman nayi burus nasa auduga natoshe kunnuwana

Daya nace yana fadamun Allah yace kaza yace kaza natashi afusace na soma tsibbona domin in halakashi saiyafara wadansu Abu yana daga hannuwa sama

Sambansan meyake fadaba saidai nagane addua yakeyi domin natabajin malamin da aka kaimu makarantarsa yanayi take sainaga wata guguwa maikarfii tataso tarufemun ido

Dani dakayan tsibbona aka watsamu gefe anan nasuma saidai nafarfado naganni yashe agefen kukar banga abokina jabirr ba"" yanisa daganan natattara nakoma ilori saboda nasamu labarin wani boka acen

Acen nasake shahara da aikin bokancii lokacin natura aljani yadaukomun matar babana nadaureta akogon kuka nayita amfani da itah hartamutu nayihakanne domin narama cin mutuncinda tayimun

Nadade INA aiki dabokan saiyazo yamutu dalilin mutuwarsa kuwa yajadawani bokane Wanda ake kirah *hatsabibin boka* shine yakasheshi yakwashe komai na sihirinsa nikaina nasamu labarin hakanne awajen wani aljanina kabusaa

Daga lokacin saina tattara nadawo kaduna inamai bakinciki kuma naraya araina sainaga bayan wanann *hatsabibin bokan* nayiduk bincikenda zanyi domin nagane ainahin inama yakeda zama Amman nakaa duk bokancina bantaba ganin wani hatsabibi irinshiba yabatarda komai na sirrinsa babuwanda yasan takamaiman indayake saifa masuyimasa hidima cikin rawar murya tace tonikuma menaimashi???😨

Yace kishiyarki lubabatu itatace akasheki kirjinta tabuga tace matar Usman???? 😳Yace kwaraikuwa yacigaba

Kwatsam watarana saiga mahaifiyarki tazonamaki aiki"" yanisa bansan kishiyarki tana daidagacikiñ masuzuwa wajen *hatsabibin boka*ba naimata aikii nafarko tabaki kekuma dake dakawarki kukaje wajen wani bokan

Bayan bikinki dashi *hatsabibin boka* yaturo asanardani karnasake nasakeyimaki aiki kuma nawarware Wanda nayi danagane shine yakashemuñ ubangidana sainace aje afadamàsa bai isaba bazan bariba shikuma dayan bokan kawarkii yace yadainà yimàki aiki

Nikuma danaso jayayya dashii aka daukeni zuwa kurkukunsa"" anata ganamun azaba damayausuke jirah suhadamu sukashee dani dake

Yakai karshen maganar yana kallontà hannutadora akaitace nashiga uku lubabatu yazakimun haka"""🙆🏿 uwaisu yace kidaina kiran sunanta domin bazai amfaneki dakomaiba sai bakinciki""

Cikin kukatace kakirah aljanunka sufitardamu mana"" murmushin yake yayi yace dazan iyayin hakan danayi tun lokacindà nake kurkukunsa amman kisàni tunranarda abunyàfaru dukà aljanuna suka tsere yanzun haka sunkoma karkashiñsa

Abokina jabirr yayi aure ya hayayyafa hayayyafa Yakoma wajen iyayensa yanzun nasan yama mantadani tundani nabijirewa umurnin ubangijina aidole inga badaidaiba😞

Samrat tace waikana nufin zaunawa zàkayi sukasheka??? Bayankuma munadà damar guduwa?? Kaga katashi mugudu danñibazan zauna akasheni abanzaba

Yace karki wahaldà kanki wajen gudu danbazaki tsiraba abunda yafikawai muzauna mujirah mutuwarmu muguwar hààrara tasakar masaa tace ammankai bàhone wayafadamaka zañmutu ayanzu idanzakàje kataso

Yace ah ah jeki abunkii ammankisani zakidawo"" tace saidaiwatà banibaa dama wandone ajikintà tatankwasheshi tàyañkii saitinda takejiyo wilgin motocii





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!!*☠



Chapter 48
        By
Gentle Lady💃🏽


Gudu takeyi kamar ranta zaifita Amman kokadan bataga alamun takusa kaiga titinba""" takara kadan kenan tacikaro  dawadansu manyan namun jeji masu matukar girma dakuma tsoratarwa tunda take ko atarihi bata tabajin wadanda sukace sunga wannan namun jejinba

Manyane tamkar giwa Amman kuma bagiwa bace sunada hakorah zagan zagan tamkar hakoran Damisaa harsundara  nata dagirma dan tsayinsu zaiyi kamu hudu yawansu akalla sunkai su hamsin naman mutane suketa yagalgala kowa yanajan rabonsa sunayin arba da itah sukayo wajentaa

Wani wawan burkii taci tajuya dagudu maimakon takoma inda tafito saitayanki gefen hagu da dajin tanagudu tana waige ganitake kamar baifi taku uku sukamotaba

Gudu take tanakuka kamar ranta zaifitaa saikuma taji wata mahaukaciyar dariya gabadaya ta karade ilahirin dajin samrat bata daina guduba takusan shafe sa a daya tanagudu sannan tacikaro  dawadansu manyan kunamai bakake kirin sukuwa wadan nan kunamai sunada wadansu faratai manya manya kamar fartanya  "" da yatsunsu  suke yagalgala naman mutum bawai dansuciba ga gawarwakin mutane nan bila adadin

Tunkafin samrat takai gurin tajuyo dagudu tana mai danasanin barowarta wajen uwaisu gashi tawahala gabadaya Kuma hanya tabacemata tayama zatamaida kanta gunda yake


Tanagudu tana kuka kamar ranta zaifitaa chak tatsaya sakamakon abunda tagani agabanta Wanda yafi dagamata hankali daduk abunda tagani abaya..

Wadansu manyan dodanni tagani masu matukar munin gaske kowanne daya girmansa  yakai girman karamin daki dazaibude bakinsa bashakka mota zatasamu titi maikyau awajen ""
.
Idanuwansu manya manya kamar kwan fitila jajir dasu sunada farata irinna damisaa saitin bakinsu akwai wani tsinke mai matukar tsini

Shisuke chakawa daidai saitin kwanyar mutum suzuke kwanyar kansaa saikaga yafadii ragab
Daga gefensu akwai wasu tarin dodannin basukai wadancen girmaba dazaran wadan nan sunshanye kwanya sukuma zasu tsotse jinin jikinka daganan sujefawa wadansu dasuke bayansu gangar jiki

Sukuma dasun jefomasu zasufara wawason naman jikinka wadansu sucire Kafa wadansu hannuwa wadansu kai kafin kafarga anyi gunsuwa gunduwa dakai tamkar sauroo wadan nan halittun  sunada matukar munin gaske

Dankuwa ganinsu kawai zai iyah haifarmaka da hawanjini sunayin arba da samrat sukayo cikinta dasaurii tajuya inda tafito tafi gwammacewa kunamu sukasheta da wadan nan dodannin sukamata

Gudu taketayi tanahaki kwatsam saitaganta tadawo inda uwaisu yake yana zaune yanda tabarshii kusa dashi tafada tanahaki kamar wacce aka jefo

Kuka tafashe dashi maiban tausayi"" uwaisu mezaiyi inba dariyaba yayi ta kyakyata dariya haryana hawaye yana buga hannu akasa tasharbe majina tana kallonsa Tace

Yanzu  uwaisu kana cikin wannan halin harkasamu damar yin dariya??? Hannuwa yayarbar yana kallonta yace to samrat mezanyi??? Konayi dariya konayi kuka nasandai sai ankasheni

Tobagwanda indaraba inmore kafin namutu"" yanunata dayatsa yanacigaba da dariyarsa yace Amman meyadawo dake bayankuma  kince bazaki dawoba??

Hawaye tashare tace wani bala in aiyadara wani nagwammace namutu anan din dakalar mutuwarda nagano acen kasan duk abunda kaga yakoro bera yafada wuta katabbar yafi wutar zafi

Yatsagaita da dariyar sa yace kingano abundayafi nandin tashin hankaline?? Tace sosaima kuwa anan tasanardashi abunda tagano takarasa dacewa dan Allah kasamo mana Mafita mana domin mukubuta daga wajen nan

Wlh koda banganiba nasan batasauki zasu kashemuba danbasuda imani tasake fashewa dakuka

Uwaisu yace hanya dayace zata fitardamu idanhar mun iyah abunda malaman makarantar allo sukeyi addua kenan

Tonikuma wlh ko alif bansaniba acikin adduar Amman tayiyu ke kin iyah maizaihana kiyimana kozamu tsira daga hannun wadan nan azzaluman

Ido tazaro tana muzurai yace yadai samrat?? Tahadiye  wadansu yawu masu daci tace wlh kilanta kwara  kai kataba zuwa islamiyya nikam danake yargata agidan mu

Iyayena masu kudine sosai danhaka basu damu dazuwana islamiyyaba saidai babana yadauko mana wani malami yana koyamana agida

Dana kwatanci malamin zaizo sainashige bandaki bazansake fitowaba saina kwatanci yatafi babana baisan hakanba

Mahaifiyata kuma babu ruwanta saboda itakanta  batasan komaiba waccema takezuwa wajen boka atsammaninka tasan addini???

Saidai Duk abunda yashigemata duhu taje wajen boka tasanar dashi idan narantsemaka banyi karyaba ko alwala ban iyaba inadai wankawa inda naga mutane sunayi idankuma zanyi sallah bana karanta komai

Saidai nakama dungura goshina sallar ma taganin damace danbanayi sai idan inaganin mutane kowajen buki dankar ace banasallah

Amman yanzu rabona dasallah tunda nayi aure gashi lubabatu batayi itama dako awajenta zan iyah koya "" takai karshen maganar tana kallonsa

Yace tokawai kigyara zaman jiran mutuwarki domin kuwa hanya dayace zata fitardamu yaukinga ranar zuwa islamiyya ..

Yaune karatun islamiyya zaiyimana rana sanin dokokin ubangijinmu shine zai taimakemu adduar Neman tsari daga azzalumai bamu iyah komaiba Hakika mutuwace tadace damu domin kuwa rayuwarmu batada wani amfani nayi danasanin barowata makarantar allo a yau

Samrat  tace kadaina cewa mutuwarmu tafi amfani idan mukakoma gida aisaimushiga islamiyya

Yayi murmushin yake dagabaya kenan aibakida wata dama niyanzu kallon gawarwaki nakemana kisani Allah yabamu damarda zamuyi aiki da itah domin neman ilimi Amman mukai watsi dawaccen damar

Hausawa sunacewa idan kasamu rana tokashanya garinka niyanzu bansan iya adadin mutanenda Na haukatarba wadanda sukamutu tasanadina

Bazan iyah kirgasuba"" nasan kema hakanne ta share hawaye yanzu kenan mutuwar zamuyii??? Yace bamakawa Kuwa""  tace yanxu lubabatuce tasakani cikin wannan halin laifin menaimata???wlh saina fadawa duniya abunda take aikatawa

Uwaisu yatari numfashinta yace idan kinrayuko??? Karfa kimanta rayuwa guda dayace dazaran kinrasata shikenan duk Wanda yamutu bayadawowa

Tasake fashewa dakuka tace idankuwa namutuuu anan wlh sainazama fatalwa nakasheta!!!!





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 49
      By
Gentle Lady💃🏽


Dariya yafashe da itah yace fatalwa ko?? Basai ruhin naki yatsira daga dukan da zakisha akabariba bari kiji kafin kedin kifadi hakan matar babana kafin tamutu saida tafurta hakan yafi sau ashirin

Kisani wannan abunda yasamemu sakayyace tun aduniya munga sakamakon abunda muka dade muna aikatawa""

Wlh samrat alokacin bansan zanyi nadamaba bantaba kawo akwai wata rana dawani zaiganamun azaba makamanciyar wacce naganawa matar baba naba

Arana daya nakan sadu da itah fiye dasau goma"" duk lokacinda naji bukata ta tasomun haka zanbiya bukata bayankuma nagama inyimata shegen duka

Abinci kansa akasa nake ajiyemata saidai tarika cinta tanaci kamar dabba"" duk da itace silar lalacewata nasan nacutarda itah

Saitayi kwana biyu banbata abinciba  kuma baburuwana datana jini ahakan zanbiya bukatata da itah hartamutu nasa aljanu sukadauki gawarta suka kaiwa namun jeji

Samrat tace Amman gaskiya  kai bakada imani"" yakada kai yace bazan musamakiba dankuwa bansan ma menene imaniba"" dani dake aikuma duk daya tunda kema gashi son zuciya yakaiki ga halaka kema wayasan iya adadin wadanda kika kashe

Shiru tayi tana kallonsa dankuwa maganarsa gaskiyace mijinda tafara aurah matansa biyu tazubawa guba sukaci suka mutu

Tahaukatarda mata uku ciki harda Yar uwar mijinta dataga tasamata ido saigashi ya auro wacce tafita iyah hatsabibanci

Itakuma duk datana magani kishinta yafiye yawa saigashi waccen tarinjayeta mijin yasaketa Allah mayasota bata kashetaba Tanisa hakane uwaisu nikaina nasan na aikata abubuwa

Zaiyi magana tace mubar zancen hankalina bakwance yakeba inatunanin ta ina mutuwarmu zata riskemu agaskiya dazanfita anan akwai abubuwa dayawa dazanyiii

Uwaisu yace duk cikin abunda zakiyi babu Na alkhairi "" takalleshi sabodame yasa kafadi hakan??? Yace saboda halin Dan Adam idan yashiga tashin hankali zaizubarda makamansa yayita Neman tsirah Amman dayatsira zakiga yawatsarda alkawullan dayadauka zaiyi

Samrat batace komaiba"" shima uwaisu baisake maganaba duk abun nan dasuke aljani hayyanul zairi yanakusa dasu yanajinsu ammansu basa ganinsaa

Wani kalloo  yakebin samrat dashi yana lasar labba daganan yamike"" yatunkareta uwaisu kawai gani yayi samrat tafadii Tanata mutsuniya""

Gabansa  yahau dukan uku uku dasaurii yamatsa bayaa"" tuntana motsi hartasuma"" take uwaisu yasaki fitsarii awando danyasan wajenshi  zatazo yanzu""

Anyi akalla dakika hamsin dafaruwar hakan saiyaga tayi zumbur tamike tanaduban jikinta saikuma tafashe dakuka domin abunda taji kamar Wanda taji lokacinda Usman yake saduwa da itah a hotel

Batagama tunaniba sukaji dariyaa takarade dajin takesuka hau waige waige""  dajin yasoma amsa kuwaa wata murya sukajii maikarfi dakuma kururuwa tasoma fadin "" kumore rayuwarku takwana uku kafin kumutu ayaudin nan nasokasheku. Kamar yanda shugabana ya umurceni amman ni imarda kejikinki wacce nadandana adaxu itace tahanani kasheku zanbarku zuwa kwana uku idan nagama morewa jikinki saina zukemaku jiniiii yasake haukacewa dawata dariyar

Kuma zaku iyah gwada guduwa hanya abudeee take saidai kushirya  ganin mugayen namun jejinda zakuhadu dasu  karkuyi tsammanin zaku tsira danyanxu haka kuna karkashin wata duniyarne


Yasake shekeewa da dariya saigawata iska maikarfin gaske tatashi tamamaye ilahirin dajinnn kukanta kawai zai iyah kurmantarda mutum

Tsayin mintuna biyar guguwar talafa saigawani akushi shake da abinciii taredawani koko maidauke daruwaa yace ga abincinan idankuna bukata kokuciii kokuma kumutu dayunwaaa yanagama fadar hakan dajinnn yayi shiruuu

Samrat taduke inda take tasoma darzar kuka itakam yanzu tagammace mutuwarta da rayuwarta

Uwaisu ne yakaraso inda take yaduka yana kallonta yace dama kindaina bannar hawayenki dankuwa babu abunda kukanki zaijawo maki saiwani bakincikin

Yajawo akushin gabansa yace kitaso muci abinciii idanuwanta tadago takalleshi tace abinci uwaisu??? Kaihar kasamu damar cinwani Abu???

Yaushe harzan iyah cinwani Abu"" uwaisu yakalleta da mamaki yace samrat kici kokarkici kasheki zaiyi kwarama kici kirage hasahi idankuma bazakiciba  nizanci Dan bazanbari yunwa takasheniba

Maganarsa tabawa samrat dariya tace karfa kamanta mutuwa zakayi ni danamutu hannun wannan marar"" imani wlh kara yunwa takasheniii

Uwaisu shikam yasa abinci gabansa yaci mai isarsa"" ya turah sauran gefensa""  sannu kan hankali duhu yafarayi saihantar cikin samrat tasake duran ruwa tasan tabbas yau anan zatakwana""

Gefe daya tamakure gawani mugun sanyi gashi kayanta kananun kayane saiyanzu tayi takaici inama kayan kwarai tasaka sannu kanhankali akafara yayyafo masu kankara"" tuni hakoransu suka fara bugar najuna"""

Usman tunsanda abun nan yafaru baisake lekowa  wajeba"" dakinsa yashige kuma yarufe babu bugunda lubabatu batayiba danyabude Amman yayi banza da itah""

tagaji dankanta takyaleshi takoma wajen kawarta sukaciga ta maganarsu anan take sanarda itah ai aikin *hatsabibin boka* ne sajida tace haba dama naraya hakan araina sukataba sunamasu dariya

Ranar Usman baiciko abinciba lubabatu dakinta takwana aranar"" washe gari takimtsa tajera abinci a dinner sannan tanufi dakin Usman"""

Bangarensu samrat kuwa kwance nahangosu kamar gawarwaki saboda kankara tagama lullubesu""" ruwa aka kwaramasu masu zafiii wadanda sukai sanadin tashinsu gasanyi gazafiii

Bayan kankarar tasauka dagajikinsu wannan karon ba samrat ba hatta uwaisu saida yafashe dakuka takekuma aljani hayyanul zairi yasoma bushewa da dariyar muguntaa


Lubabatu tanashiga dakinsa tasameshi yagama shirinsa Amman yayi zaune yabuga tagumi shigowarta yasaka yadawo hayyacinsa

Kusa dashi tazauna jiki asanyaye tagaidashi"" yasakar mata murmushi tareda amsa gaisuwarta"" yace kintashi lafiya tace qalau

Sukai shiru sannan tace katashi ga abincinka yana jiranka"" danguntun tsaki yaja sannan yace wai zan iyah cin abinci wlh damuwa tayimun yawa

Cikin alamar tausayawa tace kayi hakuri"" yanisa toyazanyi idan banyi hakurinba tunda banada naganin damuwata

Rabona da farinciki tunsanda matata Dana aurah acikin mafarki tatafi tabarni wlh inajin kamar tatafi daruhina duk da mafarki ba gaskiya bane Amman nawa nakeganinsa kamar gaske inajikamar natabayin rayuwa da itah azahiri

Haryanzu takanzomun amafarkina tanamun magana Amman dazaran nafarka zanmanta komai abudayane bana mantawa tanayawan cemun indage da addua rayuwata tanacikin hadari

Ashe wannan abunne dazaisameni taketa nunamun"" lubcy wacce tasaki baki😮 cikin tsoro dafargaba aranta taçe kardai sotake tatonamun asiri!!

Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 50
      By
Gentle Lady💃🏽



Tsuru tayi tana saurarenshi ammanfa tashiga rudani dajin maganarsa dole tasanarda *hatsabibin boka* domin adakatarda itah Dan muddin tanazuwa masa watarana zata iyah fadamashi komai.

Kuma duk ranarda hakan tafaru aikashina yabushe dannasan bazaikara zamadaniba"" Usman yace yadainaga kinshiga damuwa??

Tayi yake bakomai wlh damuwar kace  tahaifarmun dahaka"" yasaki fara a yace gaskiya kinasona sosai tashi Muje indan tsakurah inwuce aiki yanajirana""

Tace to tareda mikewa sukajerah zuwa saman dinner din yadanci abincin balaifi, tarakashi yashiga mota saigakiran labila"" cikin fara a yadauka

Yace yarleleta  kina lafiya"" tace qalau dad ya kake tunjiya inata jiran naga kiranka Amman shiru banganiba harnakwanta"""

Yadanyi shiru nadakiku uku tace yadai dad ko akwai wata matsalane??? Yace bakomai labila kidai tayani da addua inacikin damuwa wlh

Shiru tayi aranta tace ga babbar damuwar nan ataredakai afilikuma tace dad kodai muzone??? Yalaso busassun labbansa yace ah ah dakinyi zamanki bafa wani abubane

Tanisa shikenan dady"" hajiya suna gaisheka"" yace ina amsawa zankiraki anjima yanzun zantafi aikine inada meeting yau dakarfe shadaya

Tace to Allah yabada sa a yace ameeen nagode tace love u dad"" yace mee2 takashe wayar tareda saukarda ajiyar zuciya

Usman yabi wayarsa dakallo bayan yacirowayar daga kunnensa"" yamaida kallonsa wajen lubcy wacce take kallonsa yace natafi sainadawoko tace to adawo lafiya

Tajuya cikin gida tana zancen zuci waiyanzu shikenan labila tayafeta tamkar ba itace tahaifetaba""

Yarinya saikace mai shafuwar aljanu hmm yanzu wamazaice nice mahaifiyarta""" tayi saman dakinta tanata surutu

Bangaren su samrat kuwa tunlokacinda aka watsamasu ruwan zafi sukatashi idanuwa zuru zuru sai sukahau kallon kallo""
Take sukaji dariyar tacigaba da karade ilahirin dajin

Uwaisu saiganin samrat yayi tafadi kamar jiya shidai jikinsa sairawa yakeyi gefe yakoma yanata makyarkyatar tsoro

Saida yagama abunda zaiyi sannan tafarfado tanashan matukar wahala duk lokacinda yatara da itah saitagammace yamakasheta  tahuta bayan ta farfadone yakawo masu abinci kamar jiya tace bazataciba uwaisu shikam yalakadi abunshi

Zuwa rana dayasake  Ku Santarta wannan karon kam dayakawo masu abinci saida taci danyunwarda taji saibayan tagama citadawo tanajin haushin kanta

Dadare suna kwance akan gado lubabatu takalleshi tanasonyin magana tayi shiru yakurah dahakan yakalleta yace akwai maganane???

Tace ah yace tokifadamana inajinki"" tanisa dama zancemaka ne haryanzufa samira batadawo gidan nan ba""

Tagefen ido yakalleta sannan yatabe bakinsa yace to shine me??? Kokuma sokikeyi infita nemanta??? Danina aiketa??

Tace bahakan nake nufiba Amman ainaga matarkace tanada hakki akanka"" yasake mere baki yace aini tunjiya nagama da matsalarta takardar sakinta tana nan asaman gadonta dazaran tadawo zataganta""

Tanisa tanakallonsa tace nidai wlh inaji ajikina ba lafiyaba ina samirah zatashiga agarin nan kuma nakirah wayarta akashe take""

Guntun tsaki yaja yace aisaikiyi nidai karkidameni barci zanyi" idan abun yadameki saikitashi kije nemanta nidai kibarni inyi barci domin banida wata Alaka da itah""

Yanakai karshen maganar yajuya mata baya"" yaja mayafi yarufe jikinsa lubcy dariya tayi ahankali tayanda bazaijitaba sannan tajuya tayi barcinta

Washe gari bayan yafita aiki "" saiga raliya tazo gidan saboda kwana biyu sunata Neman layin samrat basa samu"" tana shigowa suka gaisa da lubabatu tace tanaciki kuwa???

shiru  tayi saida tasake tambaya sannan lubabatu tafada mata komai aikuwa tahau zage zage yanzu danrashin mutunci Kawata tabata agarin nan Amman kukasa zuwa cigiyarta???

Duk arzikin gidan nan saikacedai bamutum yabataba atunanina koda dabbace tabata aje nemanta ballantana mutum

Lubabatu tace nikaina saida nayimasa magana tokinsan Abu bakaine kakeda ikon kankaba yace bazashiba ai itah bayarinya bace dazata bata

Kuma bashine ya aiketaba"" raliya tarike kugu tace kicedai baida mutunci to wlh munfishi rashin mutunci kuma bari Kawata tadawo tadaina zama agidan sa dolene yabata takardarta kokuma hukuma tarabamu

Lubabatu tace kwantarda hankalinki basaikunkai wajen hukumaba takardarta tana nan ya ajemata adakinta

Bakisake raliya takalleta tace yasaketafa kikace??? Damuyake zancen tajuya fuuuu tafita tana sababi kaitsaye Dan adaidaita Tatara zuwa unguwarsu samrat

Dama mamartane ta aikota tajiya maganar aikin yayikome dantun ranarda ta aikamata dashi tadainajin duriyarta

Shine takirah raliya tadubomata itah saigashi tasamu wannan labarin gyalenta kawai tarida tadau jaka sukafita taja motarta zuwa dajinda boka uwaisu yake
.
Koda Suka karasa dajin saidai sukaganshi share babu ko alamar wani halitta yataba zama wajen sukayita tambaya a kauyukan dasuke makotaka da dajin

Saidai akaimasu kwatancen wani bokan bayan sunfadamasa komai yayi yandubansa yace wannan aikin yanada hadari bazai iyaba"" dasuka matsa da magiya yace zaibada jininsu ga aljanu dole suka mike jiki bakwari wajen bokanda raliya tacezuwa wajensa sukaje shima yace wannan aikin yafi karfinsa"" sukaita yawo gidajen bokaye dayan bori karshe sukaje wajen wani boka nabakin rafiii bayan sunfadamasa bukatarsu  yayimasu yandube dube yace tana raye Amman batacikin wannan duniyar"" hajiya tace kataimaka konawa kakeso zanbaka indai yata zatadawo"" yace karkidamu za ataimaka yasanarda itah turarenda zatakawo dakuma kaji dansai anyi yanka aikine mai wahalar gaske dakuma hadari tace

Itah konawane zatakashe inhar yarta zatadawo yace takwantarda hankalinta takoma gida takwanta yarta' zatadawo hargida tace tozata bada kudin aikin saiyasaka asiyomasa komai yace badamuwa haka tazube masa bakin aljihunta sannan sukadawo gida hankalinta kwance

Bayan kwana hudu dabatan su"" darana suna zaune duk sun rame sun lalace fargaba dakuma tashin hankali saboda tunranarda aka kaisu dajin kullum kafin safe kankara saita daskaresu saida safe atayardasu daruwan zafiii yaunekuma adadin kwanakinda yadibarmasu""  suncika""  saiyan dube dube suke suga ta inda mutuwar zatabullomasu wata iska sukaga tataso maikarfiii tayiiii samaa wani duhu ya mamaye ilahirin saman dajin take hadari yahadu yayi baki kirin anata tsawa mai firgitarwaa!!!


Kuyi hakuri wlh bansamu damar yin typn dinba kuyi hakuri da wannan



Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 51
      By
Gentle Lady💃🏽


Tuni uwaisu yasoma sakin zawo" sabanin samrat datasoma kuka tanakiran wayyo yanzun mutuwa zanyi

Sunacikin wannan yanayi akasoma huromasu iska tamkar ruwa tafashasshi suna suraci take. Fatar jikinsu tasoma dayewa dakanta""

Dasauri uwaisu yaruga domin yadimauce dayanayinda yakeji ajikinsa"" ganin hakan yasa samrat tabishi sukaita gudu

Guguwarce tatari gabansu take tadauke uwaisu saigashi yana shillo acikin iska tamkar guguwa tadauko karmami"" samrat tasake kwalla karaaa Amman takasa guduwa uwaisu kam sai witsil witsil yakeyi da kafaa

Zuwa mintuna biyar akasauko dashi yafadi ragajab babu rai ajikinsaa idanuwansa sun kakkafe harshensa yafito waje

Wannan yanayin yasake firgita samrat dagudu tajuya tanamai kuka tanawaige waikar itama azo gurinta"" tayi gudu mai nisa daga inda gawar uwaisu take cikibis tayi da usman yashigo jejin

Dasauri tayi wajensa tafada jikinsa tanakuka tace Usman kafitardamu wajen nan wlh mugayene  kashemu zasuyi""

Hannunsa yasaka yasoma bubbuga bayanta ahankali cikin rarrashi"" tasake shigewa jikinsa tana saukarda ajiyar zuciyaa

Hannuwansa dasuke cike da kumba "" yasoka mata tacikin bayanta take tagantsaraa idanuwanta suka ganomata  usman bakinsa duk yabaci dajini

Kafin tayi wani yunkurii yashanye jininta duka saidai kawai gawarta yayar yakoma guguwa zuwa inda ya aje gawar uwaisu yadaukota sannan yadawo yasauki dawar samrat yatashi sama yabace cikin gajimare

Yau tsayin sati daya maman samrat hankalinta yaki kwanciya kullum takwanta barci saitayi mafarkin samrat tanakuka tanacewa mom yanzu harkinada lokacin kwanciya ??? Nikuma ganinan inashan azaba akan abunda Na aikata aduniya

Duk abunda yafaru dani mom kece sila tunda kika kasa tarbiyartar dani akan addinin Allah ban iya sallah ba bansan yazan bautawa ubangijinaba

Kisani duk bala inda zanshiga kema kinada linkin nakii yana nan yanajiranki"" hannunta tasaka tace mom shigo ciji zafinda nakeciki tayi maganar tanariko hannunta

Aituni takwallah wata mahaukaciyar Kara tatashi firgigit tasoma bin hannunta da kallo Wanda yayi jajir saboda zafindake jikin samrat datarikata"""

Sai zazzare ido takeyi kamar wacce tai karya jikinta yahaubari dasauri tasauko dagakan gadon tayi waje

Falo takoma tazauna tanata fiffita jikinta wannan wace irin masiface kai anya mafarkin nan bagaske bane???? tarike baki komadai watace takeson korana gidan nan shine tabiyomun tahanyar yata dantaga bayana

Kai aizama baiganniba tamike dasaurii takoma daki tawanko fuskarta tasake shiga tadauki kudi da key din motar ta tayi hanyar dajinda bokanda aka kaisu da itah da raliya

Kodataje tasameshi yana ganawa dawata hajiyar bakin Yar bukkarsa tatsaya""dantasamu bukkar andan sakayata kuma taga mota bakin bukkar hakan yasa tatsaya domin tajirah

Tayi tsayin awa uku awajen sannan taga anbude bukkar saiga matar tafito tana gyara daurin zanenta da mayafi tanacewa saiyaushe kuma boka???

Shikuwa yana lasar baki yace kidawo zuwa jibi yamaki ko??? Tace haba boka ai wlh koda kullum kace indawo indai hakan zaihana mijina kwasomun wannan tsinanniyar wlh zanyii

Yawashe hakorah karkidamu hajiya aitunda akai wannan aikin mijinki bashi bakoma saduwa dakowace mace matukardai yakusanceki aduk lokacinda akaimaki wannan aikin

Yanzu anyi sau uku sauran bakwai Dan aka idar aikin sau goma akeyinsa daga lokacin da aka kammala aikin shikenan kisamu waje kibarje guminki dankuwa babuke bakishiya saidai kiji sunanta awani gurin badai agidankiba!!

Tawashe baki godiya nakeboka sainadawo jibin ta bude kyauren tafito sukaiwa juna kallon kallo da itah da maman samrat tawuce abunta itakuma tarakata da ido  ganin babbar mace maijidakanta ta iyah kwanciya dawannan kazamin baki duk goro Wanda bayawanka bakinsa baitaba samun wankiba""

Matar babbar motarta tashiga tajata tawuce ko kallon indatake batayiba"" sai alokacin tasaukarda ajiyar zuciya taturah  kyauren kofar tashiga

Yanazaune yamike kafarsa saiyanxuma yake gyara daurin zariyarsa yana sharce zufa"" tayimasa gafaradai yace takaraso nesadashi tazauna danwani mugun kyankyaminsa takeji

Yayi yanzane zanensa sannan yadago yacemata meke tafedake??? Cikin muryar damuwa tace akan maganar yata wlh nayi mummunan mafarki akanta yaudin nan"" tasanardashi mafarkinda tayi

Tanagama fadamasa yasheke dawata irin dariya wacce tasaka hanjin cikinta murdawa"" saida yagama dariyarsa sannan yace bahakan mafarkinki  yake nufiba kisani mijinki yanason karo aurene!! Gabanta yayanke yafadii

Yacigaba yarki tana nan raye Amman tanacikin wani halii yauyau nakeson tura aljani yadaukota kudin aikinkine sukai kadan aidatuni tadawo

Tace haba boka aiyakamata kafadamun konawane nizan iyah bayarwa "" tanisa toyamaganar kuma yarinyarda maigidana yake nema????

Yayi kaki yatofar yace tana nan amman kuma zamuyima tufkar hancii yanzu zakibada dubu Dari uku danaki danata saboda aikin akwai wuyaa

Tayi shiru sannan tace to gaskiya dari biyune nazodasu saidai idan zakabini gobe gobe zankawomaka yace shikenan Amman kitabbatar kinkawo dankonairah idan babu aikin nan baxai yiyuba tace zankawosu gobe gobe

Yace shikenan tazube kudin tatafi tazubeduka kudin Jakarta sannan tawuce zuwa gida tanaxancen zuci wato baban samrat aure zaikara Amman shine kullum yake lullubeta da dadin bakii humm hartakai gida tana tunanin""

Dadare dukkansu sunacikin falo suna sauraren tashar labarai"" tanagefe zaune danhaushin baban samrat takeji""

Salatinda taji yanayi yasaka itama takai dubanta akan TV gawarwakin wasune subiyu akan mota sunkunburah kuda saibiyarsu sukeyi

Daidai akanuno fuskar samrat gabadayansu sukamike suna rabka salati banda mamanta datadorah hannu akatarabka ihu nashiga ukuna asheda gaskene kinmutu??? Baban samrat yabita dakallo cikin mamaki yajuya wajen yayunta yace sutashi yanzun suje asivitin

Babu bata lokaci yaso sosai sufara biyawa tagidan Usman"" saiyayyunta sukace sufara daizuwa su tabbatar inhar itane

Dasukaje kafinma abarsu suga gawarta saida suka wahala"" sungani kuma suntabbatar itace tomeya hadata dawannan mutumen gashikuma bamijinta bane???

Yayanta ayuba yace subari saigobe dankuwa baza abasu gawarba zuwagoben da sassafe suje gidan Usman din hakan akayi ammanfa Daren babuwanda yarumtsa musamman mamanta dataketa kuka

Washe gari ayubanne yajegidan Usman maigadi yafadamasa ana masa sallama yayi mamaki wazaizo nemansa irin wannan lokacin tunda yatunkaro yagane kowaye saiyasha toka

Yakaraso yabashi hannu suka gaisaa ayuba yace yagidan?? Usman yace lfy"""

Ayuba yanisa yace dama nazone akan maganar Kanwata tunkafin yarufe baki Usman yace Toni inaruwaana duk abunda yasameta karku nemeni"" bakisake ayuba yakalleshi saida yakai karshe yanisa yace Amman Usman banji dadin abunda kafadabà yarinyar nan matarkacefa???

Yayi saurin tarar numfashiñsà yace adaba aini nadade dasakintaa yanzunhaka jiranake kawai tadawo wajen kwartancinta taxo takwashemun kaxaman kayanta daga gidana

Ayuba yace kasaketafa kace??? Yace kwaraikuwa kumabata gidana danrabontà dagidannan sati daya hardakwàna biyu
Ayuba yace ammandai kàibakàsan mutunciba





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 52
       By
Gentle Lady💃🏽



Yanzun ace samirah batagidan nan tsayin sati dakwana biyu Amman kakasa Neman mu kasanardamu...

Wani mugun kallo yawatsa masa yace dayake Nina aiketa ko anfadamaka ni Dan aiken kune dazanje insanardaku inda take

Duk gidan ubanda taje nibandamuba idan kunganta kufadamata tazo takwashemun kayanta daga gidana tunkafin nasaka yara suyimun waje dasu

Maganar Usman tatunzura ayuba Duk dayana ganin Usman babban mutum ne baihanashi kaimasa dukaba saboda bacin rai

Usman yayi saurin tare dukan"" dadaya hannunsa yarike hannun daya yawanka masa mari"" yace kaiharka isah kazo gidana kace zakadakeni??

Aikuwa fadane yakarke tsakaninsu sukasoma jefar juna damasifa kamar zasubuga maigadine da driver sukayo wajensu sunajaye ayuba

Yatuge hannunsa daga rikonda yamasa yace badai nikamaraba wlh kabar takamar ganin kanada kudi sainadaureka komai dukiyarka bakin azzalumi

Anaganinka da suffar babban mutum ashekai bakasan mutunciba"" Sunday yarikeshi yace karfa kaga lefin alhaji saboda balaifinsa bane agabanmu akai komai""

Usman yacewa Sunday kubarni dashi nizanyi maganinsa wlh bari nafito yayi cikin gida dasaurii Sunday yaja hannun ayuba yace kazo kafita tunda har kaga ran Alhaji yabaci komai zai iya yi

Shikuma yace babu inda zaije saidai idan kasheshi zaiyi yakasheshi danshi baya tsoronsa
Dakyar sunday da sauran ma aikatan gidan sukafita da ayuba lokacin Usman yafito da bindigarsa kamar wani mahaukacii

Hayaniyar suce tafargarda lubabatu aitana jin masu aiki suna fadar bindiga dagudunta tahau saman tadauko kwalbar tasassautoda kullinda taimasaa

Dasaurinsa yatunkari kofar fita ana rirrikeshi dankuwa jiyakeyi zuciyarsa tanata tafasa masu aikin suna rirrikeshi yana turesu""

Lubabatuce tafito dasauri tarike bindigar yajuyo afusace yakalleta cikin sanyin murya tace kayi hakuri Dan Allah alhajii

Saiya sakarmata bindigar yajuya fuuuu cikin gida tajuya tabi bayanshi Sunday kuwa sunafita yasanarda ayuba duk abunda yafaru gabadaya jiyayi kunya tarufeshi

Dangabadaya masu aikin kowayace hakan akayi harma sukafadi Wanda sukasani Wanda akai ba agaban Sunday ba"" sunday yace babban tashin hankalin yanzu ba asan inda takeba dantunda tabar gidan alhaji batadawoba"" jiki asanyaye yace aitarasu gabadaya sukace tamutu??? Yagyada kansa yanzun abunda yasaka nazoma sanardashi gawarta tana mutuware "" gabadaya sukai zugum yace damuna mamakin waye take taredashi Ashe dama samira tana Neman mazane da aurenta??? Yashare sirarun hawayenda suka saukomasa  yabar kofar gidan zuwa asiviti""gabadaya sukabishi da kallon tausayawa suna jinjina Kansu

Dayaje asivitin suka tambayeshi  Usman yafadamasu komai kowannensu jikinsa yamutu saikusan azahar akabasu gawar bayan sunzube masu kudi dubu talatin

Aranar akaimata sallah aka kaita makwancinta"" Usman Sam baiji labariba saida aka sake kwana biyu Sunday yake sanardashi

Dayafadawa lubabatu tayita kuka hartabashi haushi"" saida taje tayimasu gaisuwa Amman Usman kinzuwa yayi"" saboda kunyar abunda yayiwa ayuba saida gabaya yajibai kyautaba

Tundaga lokacin Mamar samrat takoma saliha kullum kasameta rike da charbii tasaka akanemo mata wani malami yana karantarda itah

Su hajiya sunsamu labarin sukaimasa gaisuwa dakuma fatan Allah yabashiwata tagari labila kam wata tsanar mamanta tasakeji tundaga lokacin Usman yacire sha awar aure aransa saidai yaje asiviti yasiye magungunan da zaisha domin yarage yawan sha awa

Idankuma tatasomasa saiyasha maganin "" tsayin shekara daya"" dafaruwar hakan watarana dayaziyarci family doctor dinsu akano akan ciwonda yake damunsa
A mararsa yanzu takaima idan yasha maganin baya masa amfani"" saboda yanada tsananin bukata kuma lubabatu babu abunda yasauya awajenta domin sukan kwashe sati biyu bata yarda yakwanta da itah ba

Kuma idan tace bataso dolensa yakyaleta"" suna office din doctor din bayan yagama yimasa bayanin  komai yana kallonsa saida yakai karshe  yanisa

Yace wannan laifinkane alhaji batunyauba nake sanarda kai shan wannan maganin bazaiyiba kawai Kayi aure shine kawai Mafita

Tunda kanada kudinka ballantana kace bakada kudin auren"" Usman yace doctor bakagane abunda nake guduba wlh niyanzu tsoron aurema nakeji saboda halin matan bawai banada kudin auren ba Alhamdulillah Amman matanne nayanzu kafin kasamu takwarai sai kahawala

Doctor yayi murmushi yace hakane Amman kasan ba ataruwa azama daya dole akwai nakirki nidai shawararda zanbaka kagaggauta yin aure

Dan maniyyi yatararmaka amara"" yanason fita kuma saika guji cinkayan dadi masu saka maniyyinka kara yawa"" idan bakai wasaba wannan abundakake dauka bawani abuba zaijawomaka kwanciya asiviti

Usman yayi shiru nawadansu dakiku sannan yanisa yace shikenan zanyi inshaa Allah katayani da addua"" yace karkadamu sukai sallama yawuce gidan hajiya

Labila Batasan dazuwan saba dantana gidan sahiba"" damadai bajimawa zaiyiba yabarwa hajiya sakonta yawuce

Wannan shawarar Usman yayi aiki da itah Amman abun mamaki dazaran yasamu wacce yayaba da hankalinta sai magana ta kankama yarinya tace bataso tasamu  wani said ayanemi yarinya hudu kowacce hakanne tahudu saima da akabiya sadaki tace bataso da iyayenta suka matsamata ganin alhajine maikudi ta nanewa wani talaka sanadin hakan yasaka tashiga duniya

Su awajensu tabijirewa umurninsu basu saniba aljanine ake turomasu basune suke furta hakanba"" Usman kullum zakasameshi masallaçi  gayawan azumie alokacinne Sunday ya musulunta"""  sannu sanñu abunyasoma damun Usman saiya sanarda dahiru abokinsa""

Dahiru ne yahadashi da habiba"" wacce ya aurah daga karshe yargidan mutunci saigashi batadibo da yawaba tarigamu gidan gaskiyaa

      *CIGABAN LABARI*

Lubabatu saman gadonta tahaye tadauko madubintaa tashafo tareda kiran sunan hatsabibin bokaa shafawarta keda wuyaa saigashi yabayyana kamar kullum

Kirari tasomayimasa tanafasa masa kai yasaki wata shu umar dariya""" itakanta saida tatayashi tace boka aiki yayi kyau saidaikuma maganar yata labila take takenta yasoma isata nifa inagudun watarana tatonamun asiri yarinya kamardai banice nahaifotaba kodaya batabiyo halinaba

*hatsabibin boka* yatsagaita da dariyarsa yace waimeyasa kike shakkune akan aikina" narantse dagirman tsafina babu wani mahakulinda zai iyah fallasa asirinki tundahar kikahada damu bakida sauran bakinciki yarki kuma kimanta da itah komai kikaga tanayi kisamata ido zata iyah fadamaki magana Amman bakinta bazaibata iyah furtawa waniba kodataso fadadin

Tasaki murmushi godiya nake boka toyanzu mezanbayar amatsayin kyautar murna??? Yace abunda kikasaba bayarwa"" tace to gobe zakagansu takehasken yafito tajikin glass din boka yabace tamiyarda madubin cikin jindadi

Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 53
         By
Gentle Lady💃🏽



Yanzukam Usman yafitarda rayuwar kara aure yabarwa Allah zabinsa yasan wannan jarabtace Allah yabashi ikon cinye wannan jarabawar

Zaicigaba da azumie yakumaci gaba dashan magani idankuma harciwon yacijikinsa inkwanansane yakare to Allah yajikansa

Tuni yakauda kai gadukkan abunda yasan zaitadomasa da sha awarsa gabadaya company nsa yasallami ma aikatansa mata baibar kodayaba bayan yabasu makudan kudi yace sunemi wani aikin daban sosai sunji bakinciki dankuwa babu inda ake biyan su albashi mai gwabigwabi sama da wannan company sosai maishi yasan darajar aiki dakuma biyan ma aikata kudinsu  akan kari kuma amutunce


Baibar mace kodayaba yasaka duka maza"" duk satii saiyayi sadaka yana Neman Allah ya bashi lafiya" Yakuma yayemasa damuwàsa


Zaune yake cikin falonsa sama lubabatu tana gefensa suna kallo wayarsace tahau ringing"" tana gefensa yanadubawa yaga labila cikin fara a yadauka

Tareda sallama ta amsa adaya bangaren""   tace dad
Barka dadare??? Yace yauwa kina lafiya?? Tace qalau nake dad fatan kaima hakan??

Yanisa insha Allah "" yakaratun??? Shekaranjiya ainakirah akacemun kina makaranta wajen harda" tace wlh kuwa dad abunda yasakama nakiraka kenan

Yagyara zama wani abunne??? Tace ah maganar walimarda za ayi makarantarmu tawadanda suka hardace AlQur'ani dakuma wadanda suka sauke


Hardar mataki matakine akwai masu hizifi sittin akwai arba in akwai talatin akwai masu a shirin goma dakuma biyar

Daga kowanne aji ni inacikin masu arba in" yace masha Allah godiya tatabbata ga Allah madaukakin sarki

Allah yataimaka tace Ameen""  wlh naji dadi sosai  labila yaushene walimar??? Tace saurah satii uku Amman Dan Allah dad wannan karon kazo yace karkidamu zanzo "" tamarairaice fuska kamar zatayi kuka race  sanda nasauka bakazoba ai""

Yace sha kuruminki wannan karon koda tafiya takamani zansoke tafiyar indai zuwan nawa zaisa amanta dawancen laifinda nayi

Dariya tayi tace bakayi laifiba ai kawaidai naga kowacce mahaifinta yanazuwa mata"" yace aikema haka baga uncle Hafiz nanba

Taturo  baki nidai dad ah ah kainafison kazo inaso naganka"" yamurmusa tokarki damu zanzo dame dame kike bukata zan aikomaki dakudi saiki siya""

Tace la dad damakabari wlh uncle yasiyamun komai harnakai ankon wijin dinkii"" yace duk dahaka ni ai yakamata nabada tawa kyautar

Tace hakane to dad kabani duk abunda Allah yahoremaka komenene zanji dadi"" yace dagaske??? Kaita gyada sosai

Yace shikenan ga mom dinki"" saida tadan yakuna fuska kamar wacce taji anfadi abun kazanta tace bata mugaisa yace to tareda mikawa lubabatu wayar

Damamaki take kallon wayar tamaida kallonta wajenshi tace wayene?? tasan labilace Amman kuma tundatake labila bata tabacewa abata wayaba shine takeson gazgata abunda taji

Usman yace kinajifa sanda nakirah sunanta to labilace zakugaisa"" Tamika hannu takarbi wayar takara akunnenta batareda tace komaiba

Labila takatsemata tunani tace mom kinyi mamakin jinnace abanike mugaisako??? Hmm bawani abubane kawaidai inason insanardake yarki tahardace hizifi arba in acikin littafi mai tsarkii za ayimasu walima

Yanadakyau kema kisamu kizo walimar kozaki tuba kidaina abunda kikeyi kumakinemi gafaran dad dankuwa kina cutardashi nabarki lafiya

Tanakaiwa nan takashe kiran"" lubabatu tayi murmushi tamikawa Usman wayarsa batace komaiba

Amman aranta tana jinjiina maganar labila

Usman yanisa yanamai  kallonta yace waiku meyasa haryanzu bakwa barin wannan al adar taku waishikenan idan kanada darfari bazaka sakemasa fuskaba??

Saikanuna  tamkarma bakasonsa alhalinkuma kanason sa wayezaihaifi dayace bayasonsa Amman abunda kuke nunawa yayan fari baidaceba hartakai sukansu basa sakinjiki daku"" lubabatu tasaukarda  ajiyar zuciya tace to aihakan mukatashi mukaga anayi ai kunyace bawai rashin soyayyaba"" baki kawai yamere yacigaba da kallonsa

Itama batakoma kansaba tundadai basurutun takeson yiba"" washe gari kuwa ya  mata siyayya kaya masu kyau ya aiki driver yakaimata tareda kudi takara wajen hidima


Tun anasauran  sati daya walimar akasoma sanarwa kafafen yada labarai su labila ansha kyau anyi gyaran gashi da itah da sahiba anko sukayi komai nasu iri dayane"" hatta kunshi da akaimasu zanen iridayane

Anagobe walimar labila agidansu sahiba takwana saboda batakarisa hardartaba"" sahiba sai dariya take mata waitafaye son wasane takaimata dukan wasa tagoce tana dariya "" labila tace wlh bawasa bane kinsan baiwa kowa da irin tasa tace hakane"" yauwa sahiba banfadamaki ba gobedai babana zaizo inaso zannuna makishi kugaisa tunda baizoba sannan

Tace shikenan sahiba Amman kinsan wani abu??? Labila tace ah ah saikinfada"" tayi shiru daga bisani tace wlh tunsanda akacemaki saurah kwana biyu walimar nan gabana yaketa faduwa narasa dalilin faduwar gaban""

Labila takalleta saikuma takyalkyale da dariya tace Allah yasadai alkhairine"" mukam musha biki "" takalleta da harara tace dagafaduwar gaba kuma saikusha biki ?? Tobikin mene???

Labila tana linke kayansu tace kikasani ko wani kyakkyawa zakiyi gamodashi"" tace waini??? Haba sahiba ainayi kankanta dayin aure yanzu sainan gaba aikoke bazakiso nayi aure yanzuba


Labila tace saboda me?? aini tuni nazaba miki miji kawaidai inajiran hukuncin Allah ne yazabamun abunda yafi akhairi nasankuwa kowaye nazabawa sahibata bazataki amincewaba
Murmushi kawai tayi batasake cewa komaiba!!

Harabar islamiyyar cike take makil damutane bakako hangen karshensu gabas dayamma hangu da dama dandazon dalibaine wadanda suka sauke dakuma masu harda

Cen saman dandamali malaman makarantane""gefensu kuma wata babbar rumface shake take damanyan mutane yankasuwa suwagabanni harda sarkin kano yana cikin shigarsa ta alfarma""  gefensa fadawansane sukemasa fiffita gamnoni daga kasashe daban daban duka sun ziyarci wannan walimar domin taya daliban dakuma iyayensu Murnar wannan babban abudasu kasamu nahardace littafi mai tsarkii

Bayan annatsu aka kirah amirar makarantar wato khadija Muhammad domin tabude taro da addua""

Wata karamar yarinya naga tataso cikin shigarta ta alfarma tanasanye dahijab harkasa fuskarta lullube take cikin likab kafarta tanasanye da safa shekarunta bazasu haurah goma sha shida ba" tana tafiyarta cikin natsuwa idanuwanta suna kasaa

Takarasa inda malamin yake tadan gurfana takarbi lasifikar tasoma addua Cikin harshen larabcii  gabadaya wajen kaji yayi tsitt bayan tagama bude taro da addua takoma mazauninta

Usman gabadaya yarasa natsuwarsa saibinta yakeda kallo tunsanda aka kirah sunanta yaketa nanata sunan aransa

Shikanshi tunsanda anasaura kwana hudu walimar yakejin matsanancin faduwar gaba"" saiyanzu dayaji muryanta yasakejin faduwar gaban tayawaitaa idanunsa suna kanta duk da akwai tazara maiyawa atsakaninsu

Kusada itah watace zaune itama cikin shigar kamar ta khadija tsayinsu zaizo kusan dayasam hankalin Usman bayawajenda ake gabatarda dalibai tundaga matakin sauka har aka kai matakin harda





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




Chapter 54
     By
Gentle Lady💃🏽



Akasoma kiran masu harda" tundaga mataki nafarko masu hizifi biyar har akakai kan masu hizifii arba in labila Usman itace wacce akasoma kirah

Usman saiyanzu hankalinsa yadawo jikinsa jin ankirah gudan jininsa yasoma dube dube yaga ta inda zata bullo

Idanuwansa sundauke daga gunda labilar take tacewa sahiba kitayani addua please tana dariya tace kije kawai zakiyi nasara insha Allah"" labila tawuce cikin takunta ahankali saidai yaji tasoma kira a

Sosai yanatsu yana sauraren yarsa harta kammala akasomayi mata tambayoyi akan fikihu da kawa idi wasu hawayen dadine suka sauko akan idanuwansa yakaikaice yashafe yanamai sake godewa Allah daya nuna masa wannan ranar""

Bayan tagama akacigaba dakiran sauran har aka kai matakin hardar hizifi sittin akasoma kiransu dai bayan daya" karshe akakirah amerah wato khadija Muhammad tanacikin masu hardar hizifi sittin tunkafin tasoma karatu gabadaya wajen yakaure da kabbara!!

tasoma karatun fatiha acikin daddan sautiii maimatukar sanyi dakuma kashe jiki""tana kammalawa tasoma karanto suratul bakarah gabadaya wajen yayi tsit Usman sai lunshe idonsa yakeyi saboda dadin karatun kowanne harafi tanabasa hakkinsa wajen gunna tafitarda gunna kowanne harafi tana fadinsa daidai""  harwata kasala tasaukar masa""

Yayi nisa wajen tunani hartagama akasoma yimata tambayoyi tana bada amsa daidai  bayan takammala takoma mazauninta""

Gabadaya wajen akasake kaurewa da kabbara kowayasaurari karatun khadija dole yayi kwadayin inama ace yarsace wannan kokuma yayi kwadayin yasamu mata kamarta

Usman yanadai dagacikin wadanda suka furta hakan azuciyarsu"" bayan ankammala akasoma rarraba kyauta  dagukkan dalibai"" inda abangaren masu hardar hizifi sittin khadijace tazo tadaya tasamu kyauta maitarin yawa ciki kuwa harda kujerar makka"" sosai taburge kowa tayanda akabata kyautarta "" saitasoma kuka domin tunawa da mahaifiyarta inama tana raye taga yanda abunda tabari aduniya tazama

Labilace tafito tajata zuwa wani aji tasoma rarrashinta tace haba sahiba wannan fa ranar farincikice menene abun kuka kuma keda zakinuna farincikinki cikin kuka tace sahiba mamana!!

Labila tace Dan Allah kidaina kuka abun alfarine  awajen mama ayaudin nan idan akanuna mata yanda kikazama bakuka zakiyiba sukarungume juna suna kuka saikuma akarasa  Wanda zai rarrashi wani sunyi akalla mintuna ashirin awajen Amman basudako alamar daina kukan

Yana tsaye yana kallonsu yarungume hannuwa saidai sukaji muryarsa yace kukan ya isah haka shima yana goge guntun hawayenda suka saukomasa

kusan tare suka juya suna kallon kofa labila cikin muryar kuka tace kaiwaye???
Khadija takalleta cikin fara a tace sahiba Yayana nefa" ya muktar

Bakitarike tareda murmushi""tace afuwan yayanmu tamaida kallonta wajen khadija tace Amman bakifadamun yazoba ai"""

Takalleta tace nikaina bansan yazoba danmunyi waya jiya dashi dayakirah kawu cewa yayi baxaisamu zuwaba""

Takarasa wajensa cikin jindadi tafada jikinsa saikuma tasake fashewa dakuka""daya hannunsa yasaka yana  bubbugar bayanta cikin tausayawa yana rarrashinta yace menene nakukan bagashi nazoba ???

Idankuma bazaki dainaba zantafi abuna baxansake zuwaba kinkuwa San aikinda yake gabana Amman nabarshi saboda kawai inga farincikinki"" tace nadaina Yayana karkatafi kabarni

Labila tayi tsuru tana kallonsu cikin soda Kauna murmushine kwance akan fuskarta sunbala in matukar burgeta
Sunanta taji anakirah aharabar waje  khadija muhammad labila usman Hafsat m shareef "" yayi saurin jayeta daga jikinsa yace kije anakirah"" hawayenta takarasa sharewa tajuya wajen labila tareda murmushi tace mujeko sahiba

Murmushi itama tamiyar mata tariko hannunta sukafita muktar yabisu da kallo sosai yanason kanwarsa dama wannan itace sahibar tata tanayawan bashi labarinta duk da baiga fuskartaba yanaji ajikinsa kyakkyawace

Sunafita wajen yasake kaurewa da kabbara"" tare suka karasa wajenda aka kiraasu khadija takarbi lasifika tasoma yin addua sannan tasoma jawabin muhimmancin ilimin Islam cikin harshen larabci inda labila take fassarawa cikin harshen Hausa"" hafsat takeyi cikin harshen turanci daki daki sukebin komai

Hakika nayarda
Ilimi wani abune maidadi hakazalika maisanya nishadi azuciya"ilimi gishirine narayuwa"dukkan Wanda yakeda ilimin Islam bazaitaba tabewaba duniya da lahirah Allah yabamu ilimi mai amfani

Bayan sunkammala khadija tayi Yar takaitacciyar nasiha gameda muhimmancin bin iyaye cikin harshen Hausa wadansu sunyi mamakin jinyanda take magana dahausa Dan Sam basuyi tsammanin tanajin hausaba

Birrul walidaini"" wato biyayya ga iyaye "" Yakamata yan uwa musan mahimmancin iyaye arayuwarmu musaman uwa!! uwa!! uwa!!!

Kasani komai kazama aduniya karkasake kawulakanta iyayenka babban abunda yake damun al ummarmu ayanzu dayawa mutane basusan darajar iyayensuba

Baka daraja iyayenkaba toballantana kuma iyayen wani"" shinkokasan dukkan cigaba yana samuwane idan harkabi Allah da manzonsa sannan kuma kabi iyayenka""

wasu yayan babu ruwansu sudai kawai suyi abunda yake gabansu karkumanta wahalarda uwa takesha tunsanda kake cikinta ranarda zata haifeka wahala cikin wahala harkazo duniya tayi dawainiyar shayardakai sukabaka ilimi Amman dagakarshe saikayi tamkar bakasan dawainiyarda sukai dakaiba"" shinkayiwa kanka adalci kuwa??? Kokadauka basuda hakki akankane??? Kamar yanda akace matarka aljannarta tana karkashin kafarka haka kaima taka tana karkashin ta iyayenka inhar kasaba musu bazaka shiga aljannaba.

Sukuma iyaye Susan tarbiyarda zasu baiwa yayansu domin suyi alfahari dasu"" abun alfaharinkane kaji ance wannan Wanda yacinye gasar musabaka aidan wanene bazakaso kaji ance ankama danka yana kanta daureba kokaji ance aidanka babban danfashine
 Ku kyautata atsakanin Yaya yenku

Manzon Allah yanacewa awani hadisi""
 وقال صلی الله ءليه وسلم ساووا بين أولادكم  kusasanta  "atsakanin   yayanku a

Awani hadisi manzon Allah yabacewa وقال صلى الله ءليه وسلم إن من حق الولد ءلى والده أن يعلمه الكتا به و أن يحسن اسمه و أن يزوجه إذا بلغ رواه النجار

Yanadaga    hakkinda yarataya akan iyaye bisaga yayansu  ya karantardashi littafinshi  ma ana alqur ani maigirma ""   kokai zaka karantardashi kokuma kakaishi islamiyaya la ba asan"" '' ka kyautata sunansa""  sannan ka aurardashi idan yabalaga""





 Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




chapter 55
      By
Gentle Lady💃🏽


وقال صلى الله ءليه وسلم من بلي من ه‍ذه البنات بشيء فاحسن اليه‍ن کن له ستر من النار    Wanda yakeda Yaya biyu mata ya kyautata agaresu ma ana ya tarbiyantardasu harsuka girma ya    aurardasu zasu zame masa sutrah daga daga  wuta"""
Inakirah ga iyayena maza da mata dasu tsayu akan Yaya yensu kusan kalar tarbiyarda zakubaiwa yayanku  domin duniya tayi alfahari dasu

Kukasance kuna ciyarda matayenku abinci na halat domin samun Yaya nagari masu biyayya agareku sannan kusa ido akan yayanku abokansu makotanku yanda suke mu amala

Musamman wannan zamanin  damuke ciki wai uba zaiyi zina dayarsa Yaya. Yayi zina dakanwarsa makoci yayi zina da matar makocinsa  da yayi zina da mahaifiyarsa wa iyazubillah  waihartakai anayiwa kananun yara fyade kayiwa yarshekara biyar ko uku ko hudu fyade bisabillahi mezakaji??? Banda zalunci kuma dakai za ayiwa yarka ko kanwarka yazakaji??? wai wane irin lokacine mukeciki ayanzu babu shakka manzon Allah yayi gaskiya

Duk ilimi ya bace acikin alumma barna tayawaita adoron kasa tobala ine zaiyita  shigowa gashinan kuwa munagani

Duk wannan tsadar rayuwar damuka samu kanmu aciki mune mukajawa kanmu"" kashe mutane sai yawaita yakeyi anmaida rayuwar  mutane tamkar takiyashi kiyashima yafita daraja

Lalacewar Yaya iyaye sunada hannu dumu dumu yaro tunyana karami ake koyardashi yanda zaibi Allah Amman wasu iyayen koda sunga yaro yanayin badaidaiba wani yayi magana saisuce kukyaleshi kuruciyace

Wai kuruciya bayankuma ayanzune yadace kuginamasa komai tayanda zai zauna akansa

Manzon Allah yanacewa  awani hadisi""  هفزل غلم سغرن كنكسن بلهحر .وهفزل رحل بااد ميغبر كل كتبت ألل ماء  kiyayewar yaro karami kamar rubutune bisa dutse kiyayewar babban mutum bayan yagirma kamar rubutune bisaga ruwa

Idankukai rubutu akan dutse zai zaunane daram bazaitaba gogewaba sai idan zakusaka nakiya ne kufasa dutsen kodakuwa kunyi hakan za asamu wani gefen darubutun Amman bazaitaba goguwaba

Amman kugwadayin rubutu akan ruwa kugani shinzai tsayakuwa???? Tokamar hakane idan yaro yagirma babu abunda zai iyah tsayawa akansa

Hausawa sukance icce tunyana danyensa ake tankwasashi idankuwa yabushe bazai tankwasuba inharkuwa kamatsa saidai yakarye

Tokamar hakane idankukaga yayanku sunayin abunda baidaceba kutsawatar masu kuma kuzaunardasu kununa masu illar yin hakan kusanardasu irin azabarda akeyiwa mai aikata hakan tozasuji tsoron aikatawa

Kundarsa masu tsoron aransu dashikuma zasutashi""misali kamar yanda akecewa yara Karya haramunne maikarya Dan wutane

Zakaji yara harsunayi dawaka idansukaji wani yayi karyaa"" ya Allah kashiryar mana da zuriyarmu Kaine maishiryarda Wanda kaso idan kashiryarda mutum babu mai iya batardashi idankuma mutum yabace babu mai iyah ganardashi gaskiya sai idan kaso

Allah kakaremana yayanmu da jikokinmu yan uwanmu musulmai duka kabamu ilimi mai amfaninmu duniya da lahirah kadoramu akan tafarkin gaskiya"" kasadamu da rahamarka"" رب اغفرلي وتب ءلي إنك أنت التواب الغفور.  سبحا نك الله‍م وبحمدك أشه‍د ان لاإله إلاأنت أستغرك وأتوب إليك

Tamikawa malamin lasifikar"" gabadaya akakaure wajen da kabbara
Cikin natsuwa  suka karasacikin taron wajen muktar tatafi"" inda akarufe taro da addua"" akasoma  watsewa saiyanzu labila taga dad inta"" yana nufosu"" da fara a afusarka""

Hajiya tace yan kaduna saukar yaushe???  Yace kafin afara nakaraso labila tagaidashi ya amsa yana tayata murna" Dukawa yayi yagaida hajiya ta amsa cikin sakin fuska yabawa Hafiz hannu suka gaisa yace kaga yarka ko banyi tsammanin haka takeda kokariba

Hafiz yace hakane Yaya ai ina shirye shiryen turata saudiya tayi karatu acen inshaa Allah sai anyi alfari da itah

Majeed yace uncle nikumafa??? Kansa yashafo yace sha kuruminka aihardakai za aje inajirane kaima kasauka kamar yanda tasauka saika miyarda hankali sosai idan kanaso katafiii

Hajiya tace tomuwuce gida ko"" labila tace nidai hajiya kukarasa nizan jirah sahibane mutafi tare"" Usman yace wainikuwa wacece sahibar nan???

Kullum maganarki sahibadai sahibadai yaudaikam inaso naga wannan sahibar
Tace zakaganta kuwa dad"" yace lallaikam inason ganinta dankam nalurah bakaramin so kike mataba

Hajiya tace inama kasan haka kayanda kasiyomata cewa tai bazata sakasuba saboda bakasiyo biyuba da itah da sahiba saboda Hafiz yasaba komai zaisiyo dolensa yasiyo biyu idankuma  bahakaba bazatayi amfani dashiba""

Yace um lallai naga alama tokutafi muje gidan gabadayansu suka karasa wajen motarda Hafiz yazoda itah""

Labila kam wajen sahiba takoma tacemata suwuce gida"" dayake bawani nisa dasubane tsakanin gidansu da islamiyya Amman akwai yartafiya

Motar abokin muktar suka shiga zuwa gida"" anakaiwa gidan taja hannunta tace muje kigaisa da babana""

Juyawa tayi tace Yaya inazuwa yanzun zandawo yace to ba Matsala sukawuce cikin gidan gaban khadija sai yatsananta bugawa

Zaune yake shikadai acikin falon wayace ahannunsa yana latsawa tunda sukayi ido biyu da ita tasanne kwayar idonta kasa wani abune takeji yanamata yawo ajiki tareda harbawar kirjinta

Taresuka  duka tace inawuni daddy wani sanyine yaji yaratsashi aransa yace ya salam badai khadija itace Kawar labilaba???

Labila takatsemasa tunani tahanyar cewa dad ga kawata sunanta khadija Amman yangidansu sunakiranta da safna saboda sunan mahaifiyartane

Nikuma inakiranta sahiba dad inasonta fiye dayanda nakeson kaina itah marainiyace mamanta tarasu tana zaunene ahannun kawunta tareda yayanta

Sannan takalli khadija tace sahiba ga babana""" abun alfaharina kuma maisharemun kukana"" yaudai kinga babana ko

Khadija tasake dago kai karaf sukasakeyin ido hudu dasauri tamike jikinta yana karkarwa"" tace sahiba bari naduba wani Abu

Tayi gaba Usman yabita dakallo hartashige dakin labila yasaukarda gajeruwar ajiyar zuciya labila tana kallonsa Da kuma yanayinda yashiga

Yadawo dakallonsa wajen labila saiyaga shiitake kallo nantake yaji wata irin kunya takamashi"" murmushi labila tayi tace dad barinaje gurintaa





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 56
       By
Gentle Lady💃🏽



Kasace mata komai yayi saboda kunyarda yaji"" mikewa tayi kawai tana murmushi tawuce abunta""

Bangaren khadija kuwa tanashiga daki tafada akan gado tadafe saitin zuciyarta inda yake harbawa tamkar kirjinta ne zaifaso zuciyar tafito

Tanacewa لاهولاولاقوت الابل لله   kasa samun natsuwa tayi duk da jero adduarda takeyi bataji wani sauyiba azuciyarta "" tagumi tayi yayinda tashiga wata duniyar daban murmushi tasaki afili batasan sanda bakinta yafurta gaskiya kyakkyawane

Daidai shigowar labila tace baban nawa?? Kunyace takama khadija tace nifa badawata manufa nafadaba ina nufin yanada kyau Ashe shikika biyo ba ummaba"""

Nantake annurin fuskar labila yagushe"" khadija talurah dahakan tace meyafaru sahiba??? Kodai bakiji dadin abunda nafadabane???

Labila tace bakomai kawaidai naji raina yabacine!!! Tatari nunfashinta dakikaji na ambaci umma ko???

 Waime yasaka kullum naketa jankunnenki akan muhimmancin umma agareki?? Tanisa kodayake tunda kinada itah araye bazaki gane mahimmancinta ba saikin rasata

Labila tace sahiba kenan wlh dama nice ke dama tun wajen haihuwana tamutu"" khadija tayi saurin rufemata baki tace a uzubillahi Allahumma izna min hazal kalamiki"" kinkuwasan mekike fada???

Kinaso yayanki sucemaki  hakan"" wasu hawayen takaici tashare tace inhar banzama nagartacciyar uwaba bazanga laifinsuba koda jifana sukai da dutse

Khadija tadafata tace kome kikeji agameda ummah hakuri zakiyi itace dai mahaifiyarki kuma kinsan babu Wanda zai karkare hakan

Labila tanisa tace babban takaicina kenan danashigo cikin tsatsonta inama ace babana ba itah ya auraba har aka haifeni

Khadija tabata fuska tace sahiba waime yasakike hakane kin isah kisauya hukuncin Allah ne"" kisani kowa dakikagani aduniya bai isah yagoge kaddarar saba

Ballanata ummah batada wata makusa kawaidai dankina yarfarine yasa batajanki ajikinta tokuma bakece kawai akayiwa hakanba kigaggauta Neman tuba awajen Allah

Tashare hawayenta tana maineman yafiya awajen Allah astagfirullah wa atubu ilaihi"" aranta kuwa tana mamaki yanda take kasa sanarda wani damuwarta

Khadija ce tajawo hannunta tafada saman gadon"" tace kiyi hakuri kinji sahibata wlh banason inaganin damuwa atare dake kwata kwata kasa samun sukuni nakeyi

Labila tayi murmushi nadaina sahiba kinga ya muktar fa yana jiranki muje narakaki indawo wajen dad

Tace to tareda mikewa "" aranta tanata addua Allah yasa bayacikin falon labila tanagaba tana binta baya

Yana nan kamardai yanda sukabarshi Amman yadorah kafarsa daya akan dayaa sabanin dazun dayake danna waya yanzu idanuwansa kyam sunakan kofardasu  labila suka shiga

Suna fitowa yatada kansa zuwa fuskarta take idanuwansu suka sarke cikin najuna dasauri khadija tasaki likaf yakarasa rufemata yan idanuwanta  dama sune kawai abude

Wani iri yaji aransa kardai yarinyar nan tagano itah nake kallo??

Muryanta yaji tanacewa dady sai anjima""" yadago ahankali yakuramata ido saikuma yasaki murmushi yace to Khady kigaida gida" taresuka fita da labila yarakasu da ido

Khadija kafarta har sassarfa takeyi"" sunafita Usman yadafe kansa yace ya salam meyake shirin faruwa dani wannan wane irin abun kunyane zuciyata takeson kaini gareshi kawar yata!! Yayi saurin kawarda tunanin aransa tunkafin yasamu matsuguni

Wayarsa yadauko yakunna kira a yadorah akan kunnensa yadan kishingida saman kujerar babu jimawa barci yadaukeshi awajen

Hajiya yaji tana tashinsa yatashi yayi sallar la asar gashicen anyi kirah mikewa yayi tareda mika yawuce zuwa dakinsa dayake gidan

Yana nan tsaf dashi tamkar akwai mutum aciki toilet yashiga yawatsa ruwa sannan yadauro  alwala yawuce masallaci acen yahadu da Hafiz

Bayan sundawo ahanya yake masa maganar yaushe zaikoma america  yace wani sati ainakusa gamawa inhuta yawon nan basonsa nakeyiba

Usman yace Allah yataimaka aini namatsu kagama in hannan tamaku dukiyarku"" Hafiz yace habadai Yaya niba fa kasuwanci zanyiba aikin gamnati zanyi
Kawaidai kacigaba dakula dasu

Yana dariya yayi maganar Usman yace naki wayon nauyi yayimun yawa akaina bazaku ragemunba"" Hafiz yace aigirman Kane""Kaine fa babanmu dole kakarbi girman""  Usman yace naji waikai yamaganar auren inata zuba ido naji tsit karfa yarka tarigaka aure???

Kakuwasan dakaji kunya'' Hafiz yasosa kai yace aini karamin ubane bazanji kunyaba tunda Ban isah aureba"" Usman yaharareshi yace ahakan???

Tokodai kafitarda mata ko inhadaka da Abu mai kuli kuli da awara"" baki Hafiz yarike yace abun haryakai cen tokwantarda hankalinka dazaran nadawo zakaji komai

Usman yace sauran watanawa??? Hafiz yace bakwai koyanzu walimar labila tadawo dani danbanaso ayi bana nan"

Usman yace shikenan munadai zuba ido daidai sunkai kofar gidansu sukashiga tare sunafira suna raha hajiya bakaramin  dadi takejiba idan taga yayanta cikin farinciki

Saman kujerah suka zube labila tadauko masu abinci sukaci sukahau firah sai shida saurah Usman yayi haramar tafiya harbakin mota suka rakashi yawuce yana daga masu hannu

Labila batakoma gidan sahiba ba saboda hankalinta yanakan yayanta shima washe gari tunda safe zaikoma""


Agogon Nigeria yabuga karfe biyu nadare alokacinda nasan kowa yayi nisa cikin barcinsa saikuma masu ibadar dare. Bakajin motsin komai saikukan karnuka dasuke cikin layin

Inkadauke Usman dayake tsaye yakai gwauro yakai mari tunsanda yabaro kano yakasa samun sukuni cikin ransa"" komai yakeyi fuskarta yakegani sanye cikin nikaf haryana ayyana suffarta yanda zata kasance

Gabadaya ta dabai bayemasa zuciya dakuma tunaninsa hatta abinci idan zaici fuskarta yake hangowa akan plate wanan wace irin makauniyar soyayya ce????  Kawar labila yafurta ahankali komawa yayi saman gadon yazauna yadafe kansa wanda yayimasa nauyi

Kai bazaitaba yuyuwaba wlh tunwuri dama kindaina son abunda bazakitaba samun saba dawanne ido zan kalli labila ince inason kawarta ???

Taya zata kalli maganata?? Yakamata inhana zuciyata afkawa inda baichanchanci yazama muhallinaba "" wata zuciya tace masa taya hakan zai yiyu kokamanta soyayya batayin shawara dakowa

Yayinda zatashigeka batadubà matsayi kochanchantar Abu"" yace idankuwa hakane gaskiya bataimun adalciba saboda abun nan bazaitaba yiyuwaba""


Wata zuciya tacemasa yiyuwa kai saidai inhar bakace kanasontaba koda kaki fada Dole sai zuciyarka ta tilas taka
Yace wlh karyane wannan abun kunyar badanibà ganin abun yanason haifarmasa da damuwa yayisaurin kawarda tunanin abun yafaskara tashi yayi yadauro alwala yasoma nafila yanarokoñ Allah yaciremasa sonta tunkafin yayinisa

Saikusan asuba yakwanta Amman abun mamaki maimakon yaga sauyi aransa saiyaji kamar ansake linka sonnata sau ashirin acikin zuciyarsa

Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 57
       By
Gentle Lady💃🏽




Har akayi kiran asalatu idonsa biyu bairuntsaba"" tashi yayi yasake dauro alwala yafita yatada lubabatu sannan yakarasa sauka kasa yasoma tashin yan aikin gidan kamardai yanda yasaba

Saida sukai alwala sukawuce masallaci baidawo ba saida haske yagama mamaye gari cikin masallacin ma zaune kawai yake tamkar mutum mutumi tundayake baitabajin soyayya irin hakaba

Waidama Ashe haka soyake??? Lallai Wanda baisan soba shine zai karyatashi baitaba tunanin hakan akejiba gameda abunda zuciya takeso tomeyasa banajin hakan lokacinda nahadu da lubabatu???

Kodai itakanta soyyyar matsayi matsayine da itah nasan Na auretane Dan inasonta towacce irin soyayya??? Kawaidai inajinta cikin raina yanda baxan iyah rabuwa da itah ba

Sauran matanda na aurah fa??? Sume yasa banajin haka atattare dasu??? Suma tasu kalar soyayyar dabantake

Khadija ce kawai lokaci daya soyyyarta tashiga harcikin barko dakuma jinin jikina"" tomeyasa hakan??? Saboda kanasonta"" !! Tomeyasa nakesonta alhalin kofuskarta banganiba ??? Saboda tarbiyarta to ai itama lubabatu tanada tarbiya meyasa banajin sonta kamar wannan ??? Wannan kuma daga Allah ne

Haka yayita yiwakansa tambayoyi kuma yanabawa kansa amsar tambayarsa haryabaro masallacin kwana biyu tsakani yakasa gane kansa abinci kansa yarage ci


Zaune yake office dinsa yana tunani yakamata insanarda labila halinda nakeciki nasan bazata zargeniba saboda tasan banine nasakawa kainaba"" kai anya zan iyah kuwa???

Tomezaihana kadai tsaya kallon ruwa kwado yayimaka kafa kawai kasanarda itah zata fuskanceka dawannan shawarar yayarda yadauko wayar yakamo lanbar Sannan yasoma jujjuya wayar

Yayi tsayin mintuna ashirin sannan yakirah"" tanafara ringing yaji gabansa yafadii rasss"" tayita ringing harta katse ba adaukaba yasake kirah hartakatse bata dagaba

Khadija tana kwance adakin wayar tasoma ruri harzata daga taga sunan wanda yakirah dadyna gabantane yabada rasss tadafe kirjinta tanamairufe idonta

Waimenene hakan kikeyi babananefa"" taja tsakii hartakai hannu tadauka kuma takasa saida yayi kiran saubiyu gana uku tadauka

Jikinta yanadan rawa cikin siririyar muryanta tace Assalamu  Alaikum daya bangaren wani irin sanyine yaratsa zuciyar usman haryasaukarda gajeruwar ajiyar zuciya


Yace Amin wa Alaikumus salam" Wani yanayi khadija tasamu kanta aciki jin muryarsa yasaukar mata da kasala cikin sassarfar murya tace dady ina kwana"" yace lafiya qalau kina lafiya tace umm sannan tace batanan taje gida tadawo batajirah mezaiceba taka she kiran
Tace wai tareda murmushi tanadafe da kirjinta dayake harbawa""


Yanajin taka she yajiwani iri cikin ransa Sam baijidadin hakanba"" yaso koda muryantane yaji yanatsaka da tunani saigakirah yashigo

Dasauri yadauka atsammaninsa itace tasake kirah yanadauka yaji muryan labila bahakan yasoba cikin sanyin murya ya amsa gaisuwarta tace dad tundakazo bakasake kiranaba

Yadan shafo kansa yace tubanake aikine yayimun yawa wlh "" tace shikenan yace yasu hajiyafa??? Tace qalau munga sako dani dasahiba mungode

Yadan murmusa bakomai tayidanjin dad akwai matsalane??? Yace ah yayi saurin cewa sorry ah ah babuwata damuwa kinga wani abune???

Tace dad aibahakan nasabajin muryankaba indai akwai damuwa kasanardani please"" yace bakomai dama nakirakiine naji idan kina lafiya

Tanisa qalau nake dad yace tosai anjima"" tace inasonka dad cikin sanyin murya yace nimahaka yakashe kiran yanamai runtse idanuwansa why why meyasa nakasa sanarda itah???

Bayankuma tatambayeni damuwata yayi wulgi dawayar yadafe kansa wani irin suracine yake fitowa tajikin zuciyarsa yanafita ta hancinsa tamkar suracin tafashasshen ruwan zafii


Labila tsuru tayi tana kallon wayar"" khadija tace yadai sahiba???? Ajiyar zuciya tasaukar tace bakomai tareda zaunawa saman gadon"""

Abu wasa wasa kullum saiyakirata kamar yasanarda itah saikuma yafasa itah tagano manufarsa Dantun ranarda yazo walima taga kallonda yakeyiwa khadija kawaidai yana jinjina sanarda itane amatsayinta nayarsa itakuma taraya aranta inhar bashine yafurtaba bazata taba nuna taganoshiba sai idan yatunkareta da maganar

Yau yakasance weekend ne karfe takwas nasafe Usman yakama hanyar kano yaukam zaisanarda labila abunda ke zuciyarshi saidai koma kunyar ne yajita danyagaji da ajiyar abunda yafi karfin zuciyarshi

Bangaredaya  kuma yanason ganin khadija koda muryantane yaji zaiji sanyi "" koda yakarasa gidan hajiya bata nan"" dama kuma Hafiz Yakoma"" bayan yayi pkng suka gaisa damaigadi yake sanardashi yace bakowa gidan kenan???


Yace ah ah yar dady tana nan"" kamar yacemasa tareda kawarta saikuma yashare yawuce cikin gidan tanajiyo sallamarsa tafito dagudu tanamasa oyoyo

Yace labila waiyaushe zaki girmane aiyanzu kinwuce wannan saidai majeed "" baki taturo tace ah ah banwuceba sai anhaifamun Kanwa sannan

Murmushi yayi yanasamun waje yaxauna yacire hularsa yana fiffita kaiyaufa akwai zafi babu wutane???

Tace ah yanzun nan tadauke bari inkawo maka ruwa tayi maganar tana wucewa ruwa tadauko masa tareda cup tadauro akan wani karamin faranti maikyau taduka ta ajemasa tanayimasa ya hanya

Yace alhamdulillah ruwan tazuba masa Tamika masa yakarba yanasha wani sanyine yake ratsashi saida yashanye duka tace akarane dad??? Yace kara Amman kadan

Tasake Karamasa yashanye sannan yasaukarda ajiyar zuciya yace Alhamdulillah nagode"" inakuma hajiya taje baba maigadi yacemun tafita???

Tace ah wlh gidan wata kawarta akayi rasuwa shine tatafi gaisuwa"" yace ayya wayarasu mace ko namiji"" tace wlh bansaniba nima

Yace to Allah yajikan Wanda yarasu tace Ameen" Amman meyasa bakibita kuntafi tareba""??? Tace dad kusa da islamiyar munefa kuma zasuga banzoba saitace induba gida sahiba ma tatafi tundaxu

Shiru yayi baisake cewa komaiba gashi yanason magana Amman yakasa.......





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 59
      By
Gentle Lady💃🏽



Yace nidai hajiya natafi"" sukayimasa Allah yakiyaye yawuce cikin farinciki gabadaya jiyake tamkar anyaye masa wani katon dutse daya taushe zuciyarsa fatansa kawai Allah yasa khadija zata ameence

Dawan nan tunanin yakarasa gida"" lubabatu tana zaune cikin falon kasa tana kallo yanashigowa tabishi dakallon mamaki

Kusa da itah yazauna yace yakina kallona bazakimun kosannu dazuwaba"" baki tatabe tace aibansan inda katafiba kaida bakafita koda kofar gidane idanhar ranar weekend ne Amman yaunaga bakon al amari

Yanisa yanashafar kansa yace kano natafi"" takalleshi dahanzari tace incekodai lafiya???  Yace qalau natafi ganinsune kawai yaunatashi dason ganin Ya'yana

Har abada baida niyar boyemata Amman yasamu kansa dakin sanarda itah dalilinsa nazuwa kano tundasafe dankoda yabarta bata tashi barciba shima saman hanya yasha lemu

Tace wlh harkasa gabana yafadi nadauka wani abune yafaru"" yace bakomai wlh hamma yayi yana Shafa cikinsa yace akwai ragowar abinci yunwa nakeji

Tace babu iyah cikina kawai nace agirka kuma nacinye  inda kafito bakaci abinci bane??? Shiru yayi baice komaiba "" tace sai idan kanaso nasake sakawa adafa maka wani"' yace shikenan barshi kawai nahakurah inci dadare""

Baijirah jin mezatace ba yamike yahaura sama tabishi damugun kallo"" sosai tanason tarika juya Usman tamkar dancikinta Amman tarasa gane dalilinda  yasaka duk aikinda akaimasa baicika tasiri akansaba

Wanda akayi cikin kwalbane kawai yakeyin aiki akansa kumashi zafin zuciya kawai yake sakashi idankuma takulle barta mutane har itah kanta bata tsirah da fushinsa

                Abokanta duka suna juya mazajensu son ransu duk da batanemi komai tarasaba Amman tanason harta wanki shine zaiyi mata dagyaran daki

Tanajin tsoron sakashi tunda tasan yanada zuciya zata iyah sakashi yace bazaiyiba girmantama dayake gani yadaina gani kuma batason kowa yarika zargin wani Abu

Usman tunda yahau saman baisaukoba saida yaji kiran sallar la asar yasake watsa ruwa yadauro alwala yasauko tana nan inda yabarta yawuce abunshi batareda yacemata komaiba
Itama batadamuba Dan hankalinta yanakan TV datake kallo""

Kwance take dakin khadija itakuma tanazaune tana yankan kumba"" labila tace sahiba dama magana nakeso muyi dake""..

Tana yankan kumbar ta daina inajinki"" labila tanisa tace gameda alkawarinda mukaiwa juna yaudai inason nafurta maki sunan mijinda nazaba maki

Khadija tayi kasake tana kallonta sannan tanisa tace sahiba atsarina inasone muyi aure tare kinaganin baiyi sauriba idan kika zabamun miji ayanzu

Labila tatashi zaune tace nidai awajena baiyiba kuma nafison ayikomai dawuri"" Saidai idan zakiki zabinane

Khadija tace habadai Nina isah naki abunda kikazabamun nasan har abada bazaki zabamun abunda zaicutardaniba""

Nayarda kowaye zansoshi sahiba idan harkedai yayi maki bamasai kintsaya Neman yardataba kawai kicemasa Na amince

Labila tasaki fara a tace bahaka zamuyi dakeba inasone kifadi ra ayinki"" khadija tace inhar yayi maki wlh yayimun"" karkidamu


Labila tace shikenan Amman akwai bukatar kusamu lokaci domin kugana  kafin nan zansanardashi yaturo iyayensa atsaida magana domin cikin kankanin lokaci za ayi bikin"" khadija tace haba sahiba karatunfa!??

Karkidamu da karatu zakicigaba agidanki"" tace shikenan Allah yatabbatar mana da alkhairi labila tace Ameen tarungumeta cikin jindadi
Bayan kwana uku kamardai yanda sukayi dashi saigashi yakirata tana falo tanayiwa hajiya tausa tamike dasauri tayi hanyar dakinta

Hajiya tabita da kallo tana girgiza kai labila waisai yaushene zatayi hankali"" Allah yakyauta

Tanashiga dakin tadauka tareda sallama ya amsa sallamar taredacewa lafiyadai naji shiru kodai kinmantane???

Nayita jiran kiranki gashi har dare yayi"" tace sorry dad wlh mantawa nayine""" idanuwa yakwalo aransa yace umm lallai bakisan abunda dadynki yakeji gameda itaba aida bazaki mantaba

Takatsemasa tunaninsa tahanyar cewa ta amince""" baki yawashe yace dagaske??? Tace sosai ma yace  Amman tasan nine tayarda dawuri haka??? Tanisa ah ah batasaniba

Sai murnarsa takoma ciki yace mekikayi haka??? Taya zan aureta alhalin  bakisanarda itah gaskiyar kowaye niba

Tace naso fadamata saitace koma waye inhar niyayimun tobasaina nemi yardar taba"" tayarda""  tasan bazantaba zabamata abunda zaicutarda itaba

Yayi shiru daga bisani yace ninasan bazata yardaba"" labila tace maisaukine dad yanzudai inaso kazo kasamu kawunta""  idan kungama magana"" saikazo danka ganta idan kaganta taganka komenene ninasan yanda zanyi

Amman fa akwai sharadi bayan amincewarta"" yanisa wanne irin sharadi kuma labila??? Tace awajena maisaukine bansaniba kodai awajenka dakuma matarka!!

Dif yayi shine illarfa kaso karamar yarinya kuma abokiyar yarsa yanisa shikenan kifadamun sharadin" tace bayanzu ba dad sai idan maganar ta tabbata yace shikenan

Sukai sallama yadade yana nazarin kalaman labila daga bisani yadaga kafadarsa alamar baidamuba kowanne sharadine zai yarda dashi matukar zaisamu hadinkan Khadija dawan nan tunanin yawuni


Bayan kwana biyu dazancen yaje kano hajiya yasamu yalabarta mata komai"" shiru tayi nawadansu lokutta sannan takalleshi tace anya khadija zatayarda idanhar tasan labila Kaine zabinda taimata???

Yanisa nikaina bansan yazata kayaba Amman banada mafita hajiya tunda kikaga harnayiwa labila magana kinsan abun nan ba karami bane

Kece mahaifiyata nasan bazakiso abunda zaitaba lafiyataba wlh inacikin damuwa sosai abun yana Neman taba lafiyar jikina likita yacemun nadaina shan maganie nayi aure

bansanarda ke bane kawai tunsanda kikaga inata aure Amman matanne duka kinga irin yanda suke kasancewa hardanacire son aure araina nabarwa Allah komai idan yazama shine ajalina Allah yagafartamun saigashi kwatsam naga wannan khadijar gabadaya narasa natsuwata"!!!

Tanisa shikenan bari zanyi maka kwatancen shagonsa danbaicika zama agidaba kafara tuntubarsa dazancen kanemi izinin ganinta idan hartaganka kuma tayarda zata aureka komai zaizo cikin saukiii yace shikenan

Tayi masa kwatance shagonsa akasuwa Yakuma sameshi yabashi hannu suka gaisa Ashe shima yasanshi"" Usman nekawai baiwayeshiba""






Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




Chapter 58
       By
Gentle Lady💃🏽



Saiya kalleta kamar yayi magana saikuma yakasa itakuwa tana kallace dashi ganin yayi shiru tamike tace dad nikam bari nadan kwanta"" tayi maganar hartasoma tafiya

Yace amm dawo labila magana zamuyi""" tace to tareda juyowa tazauna kasa tana fuskantarshi saikuma yayi shiru

Yacije lebonsa nakasa yanasake jinjina nauyin maganar"" tace yadai daddy??? Yadan nisa yace bakomai tashi kije kikwanta

Murmushi tayi maidan sauti tace dad kadaina boye abunda yake zuciyarka hakan babbar illace atareda zuciyar

Komai nene kasanardani mana zanfuskanceka amatsayina nayarka banason damuwarka kokadan Kaine kawai kasan damuwana yanda zanfadamaka Abu bana iyah sanarda mahaifiyata

Kadaure kasanardani wlh batunyauba nalurah kanacikin damuwa kullum kakirah ni dankasanardani saikuma kafasa

Nifa yarkace menene bazaka fadamunba kaima kasani zanbaka goyon baya Dari bisa Dari idankuma abunda zanbada shawarane saina baka daidai sanina""

Yanisa yana kallonta yace hakane labila Amman gaskiya inajin nauyin fadamaki bukatata dankuwa tanada matukar nauyi.


Tayimun nauyi abakina hakazalika zuciyata takasa daukarta inaganin kamar bankyautaba kuma abun kunyane

Nayi nayi incire abun azuciyata Amman yagagara fita"" tanisa bakomai dad inhar fadinsa shine zaisaka zuciyarka nishadi kasanardani please


Shiru yasakeyi nawadansu dakiku sannan yace labila akan kawarkine khadija tunranarda naji tana karatu amakaran tarku wajen walima haka kurum naji taburgeni

Banyi tunanin kawarki bace saida kika nunamun itah sainayita kokarin incireta araina amman abun yafaskara Amman karki zargeni da wani Abu please

Nasan abune maiwahalama tayarda ta aureni dannayimata tsufa"" dariyace takwacewa labila wacce tasaka Usman darawa tunfuskarsa nanuna alamar damuwa sanda yake maganar


Saida tayi mai isarta tace haba dai dad akan yar wanann maganar dakake cewa kayimata tsufa ai wlh dad babu Wanda zaiganka yace kahaifi kamata""

Saidai kuma hanzari baguduba"" cikin sauri yace menene??? Tace sahibata tuni tayi mijin aure!! Wani kululu yaji yatokaremasa akahon zuci yayita maza yace shikenan dama haka Allah yakaddara

Amman kibar maganar nan dagani saike saikuma Allah dayake kallonmu banaso tasan wannan batun kartadaina ganin girmana

Labila tace harkasaki dawuri haka dady bayan kashiga kaima agwabza dakai"" yayi murmushin yake yace aikinsan bakyau Neman aure cikin aure

Tace hakane tobaka tambayeni sunan Wanda zata auraba??? Yakishingida saman kujerah zuciyarsa nayimasa zugi yace menene amfanin jinsunan labila kawai kibar maganar kamar adole yake maganar Dan idanuwansa harsun sauya kala""

Marairaice murya tayi tace dad sahibar tawa??? Yace yihakuri towaye??? Tamurmusa sunanku daya ai

Yace masha Allah inatayashi murna"" tace mungode kumafa akaduna yake zama unguwarku dayama

Yalurah abunnata na ba ane yace kinsan Allah banason shashanci dariya tayi tace dagaskefa dad yanzun hakama munataredashi afalon nan

Dasauri Usman yadago yanakarewa falon kallo baiga komaiba yamaida kallonsa wajenta yace waikina nufin ni??? Murmushine akan fuskarta tagyada kanta  alamar ah


Wani farinciki marar misaltuwa yamamaye masa zuciya bakinsa yaki rufuwa saboda tsananin murna tace nasan kayi mamaki danacekaine mijinta

Tunbayauba nakeyimaka kwadayin samunta inada yakinin zakasamu abunda kakeso awajenta komenene dad tunda nahadu da sahiba wlh bantabajin tayi koda musayar yawu dawaniba

Tanada hakuri gakuma addini bashakka zata tarbiyantarda yayanka kowanne uba anaso yasamarwa yayansa uwa tagari banada kokonto akan sahiba

Nikaina dakaganni Allah yahadani da itah domin sanin halinda nakeciki Wanda babuwandà yasanshi sai Allah

Munyi alkawari atsakaniñmu kowacce acikinmu daya zata zabamata miji tun alokacin nazabarwa sahiba kai kamar yanda nasanka haka itama

Nasan zatayi alfahari dakai anan gaba kamar yanda kaima zakayi kumanasan baxata tabakin zabinda naimataba dukda sainayi dakyar kafin ta aminta idanhartaji nace zabinda naimata Kaine


Tanisa tana kallonsa kabani kwana uku komainene zankiraka insanardàkai yanisa bakomai Amman idan batayardaba karki tilas tata akan abunda bataso dannima bazanji dadiba

Tace in Allah yayarda zata amince"" yace to Allah yayardà labila yanaduba agogo yace bari nadanfità kafin hajiya tadawo
Ammanfa karki manta da maganar please"" tace bazan  mantaba dad tanarufe bakinta hajiya nayin sallama damamaki tace kai wanga saukar y aushe???

Labila tace bakijima dafitaba yashigo"" tace aidanasani danayi zamana tunanin nayi nakatsemaki makaranta shiyasama nadawo dawuri

Usman yagaida itah ta amsa tana tambayarsa lubabatu"" yace qalau take hajiiya "" tace madallah saikitashi kishirya kiwuce makaranta Dan nakai majeed dagacen

Taturo baki wlh hajiya nayi lattifa kafinma nakai antashi" Usman yace kishirya nakaiki daganan sai inwuce inda zanje

Tace dad ankusa tashifa wlh danaje rikeni malam zaiyi sai azahar"" hajiya tace tosaiki zauna abokan karatunki saizu tsere maki ""

Tace ai sahiba zata fadamun idan tadawo damakuma nawucesu dasura uku tunda inayi agida tayi maganar tana dariya murmushi Usman yayi yace nidai hajiya barinaje nadawo sainawuce

Tace kaikuwa mekazoyi kano kanacikin aiki??? Murmushi yayi yadan Sosa kansa yace kawaidai nazo ingaishekune

Tace kakyauta kuwa Allah yabada ladar zumunci yace Ameen tareda mikewa yadauki key dinsa yafita""

Saikusan azahar yadawo yaci abinci yawuce bayan yasake jaddadawa labila kartamanta"" tace bazata mantaba

Hajiya tace waimenene aketa kumuiniya ba aso inji??? Usman yana dariya yace bakomai hajiya

Baki tatabe tace komadai menene inazaune za afadamun indai wannan ce maishegen surutun tsiya"" kamar suda""  majeed ya kyalkyace  da dariya yace Anty tazama suda hajiya dama aku kikacemata

Labila tamaka masa harara"" tace zanbugeka majeed wasa nakeyi dakai??? Jikin hajiya yashige yace aihajiya bazata bari adakeniba""

Usman yana dariya yace saidai idan bakayi laifinba"" hajiya tace kodayayi laifi babu maidakarmun maigida inakallo"" majeed yacee yeee hajiya tanasona gabadaya sukasa dariya






Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!!*☠




Chapter 60
       By
Gentle Lady💃🏽



Yace yanzun kazone??? Usman yace ah wlh .to ansamesu lfy ko???..

Yace cikin godiyar Allah""" to masha Allah ""Allah yakara mana lafiya Usman yace Ameen"" saikuma shiru yabiyo baya yalura akwai magana abakinsa yace Alhaji Usman mukarasa ciki ko babu musu yamike shikuma yashige gaba yanabiye dashi

Dayake shagon babbane akwai kujeru biyu aciki yanuna masa bisimillah zauna taresuka zauna yasake bashi hannu suka gaisa"""

Yace banyi mamakin ganinkaba nadauka wani kaya kazokasiya saikuma nalurah akwai magana abakinka""

Usman yasanne kansa yace hakane malam"" dama akan yarwajenkane "" tunranarda nazo walimar su labila naganta amakaranta naji takwantamun araina

Banyi tunanin Kawar labila bace saida nagansu gida tare"" tun alokacin naso cireta araina"" saikuma abun yafaskara

Kuma inajin nauyin nasanarda itah shine danasanarda labila tasanarda itah tace ta amince Amman kuma bata fadamata ainahin waye yakesontaba

Shine Nazo wajenka Neman izini inaso inda hali ingana da itah banaso intilas tamata idanhar batasona karsai magana tayi nisa yazama nacutarda itah

Danasanarda hajiya shine taturoni nan nayi tambaya har akanunamun shagonka"" inafatar ba aimata mijiba daga wurinku dagaske nake bawai wasa nazoyiba auren ta zanyi inda halima banaso adau tsawon lokaci yakai karshen maganar yana kallonsa

Malam garba yanisa yace to Alhamdulillah naji dadin jin wannan maganar Amman wani hanzari  baguduba gaskiya banine mahaifin yarinyar nanba"" asali uba muka hada da mahaifiyarta


Mahaifinta Dan yolane sunrabu da mahaifiyarta tuntana ciki wata uku"" tazo tareda yayanta muktar anan garin dama nan ne tushenta"" ranar da tahaifeta aranar tarasu ko waigowa batayi taga yarba yayanta shiyayi rainonta hartagirma duk damaidakina tana kulada itah sosai bayason yayi nesa da itah

Yanzun yana america wajen karatu ni awajena babu damuwa kafara ganawa dayarinyar idanhar ta aminta zankirah yayanta insanardashi saikasamu kashirya muje yola tare dakai duk daharyanzu babanta baitaba waiwayarmuba kodai yanedai muzamu nemishi

Usman yace hakan yanada kyau Allah yajikanta"" yace Ameen daganan sukadan taba firah yayimasa sallama yakoma gidan yasanarda hajiya yace tafadawa labila zaidawo jibi yayimata sallama yatafi

Ranarda takama zaizo takai khadija akayimata lalli akagyara mata kai tashirya masa abinci mairai dalafiya"" gidansu khadija suka karbi mabudin dakin ya muktar suka gyarashi suka kunna turaren wuta""

Dakinsai fitarda sihir taccen kamshi yakeyi"" da khadija taiwanka labilace tayimata kwalliya Dan itah bamaiyawan kwalliya bace

Bayan tagama kimtsawa labila takalleta tundaga sama harkasa aranta tace dady hakika kayi dacen mata wacce zata share maka hawayenka

Dakuma tatunoda gidanda zataturah kawarta saikuma tarungumeta tafashe dakuka"" bataso tarasa kawarta haka zalika tanason ganin karshen bokan mamarta kuma tasan babu wacce zata iyah tunkararsu sai khadija domin itace ta chanchanta

Khadija tace lafiya sahiba idan bakyason abun nan karfa afara hankalina bazai kwantaba idan inaganinki cikin damuwa

Labila tayi saurin share hawayenta tace karkidamu sahiba bawani abubane yasakani kuka ganin wannan kyanda kikayine kamarwata sarauniya

Harara tayimata cikin wasa tace aikinfini kyau sahiba kawaidai bakyaganin nakine kina hango nawa"" zatayi magana kirah yashigo wayar labila

Tadauka cikin fara a tayi sallama daya ban garen aka amsa tace harka iso??? Yace ah tace ok ganinan zuwa takashe kiran tana kaidubanta wajen khadija wacce takuramata ido bugun kirjinta harwaje kanajinsa

Murmushi tasakarmata tace yadai sahiba??? Tasanne kanta kasa tanawasa dayan yatsunta tace wlh gabana faduwa yakeyi

Kamar kirjina zaiballe"" labila tace please kisaki ranki nasan zaiyimaki kyakkyawane sosaifa barinakaishi dakin nadawo

Tayi maganar tanaridar mayafinta tayafa tafita"" innah tana tsakar gida tacemata innah bakon ya iso"" tace to gashi bangama dama furarba barinayi sauri tace to tawuce

Yanacikin motarsa yanaganin tafito yafito yana tunkarota da murmushi akan fuskarsa""

Tace dad inawuni"" yace lafiya qalau yagidan

Tace qalau mukarasa ciki sainakirata ko"" yace to bisimillah"" tana gaba yanabinta abaya tabude masa dakin yashiga yazauna sannan tafita tayita jidomasa kayanda suka hadamasa takaimasa

Shidai yakagara yayi ido biyu da khadija kamaryayi magana saikuma yadake kartace yafaye zumudi tazuba masa ruwa sannan tafita khadija takoma tamkar mutum mutumi duk jikinta yamutu labila tadauko hijab tasakamata""

Tariko hannunta sukafita haryanzu kirjinta harbawa yakeyi bakin dakin labila  tatsaya tace kishiga inazuwa""

Khadija tamake kafada tace saidai mushiga tare"" labila ta kwalalo ido tace gaskiya bazai yiyuba haba""

Khadija tace tosaidai mukoma Amman kinsan bazan kebe dawani namijiba alhalin ba muharramina bane

Tace kinyi gaskiya tokishiga dazaran kungaisa wlh zanshigo tace kintabbata??? Tace ah saiki tangale kofar idan kikashiga tace shikenan

Labila tawuce tadade tsaye bakin kofar kafin tadaure tareda addu oi abakinta tasamu damar shiga dakin tareda sallama

Wani sansanyar kamshin turarensa yadaki hancinta idonta yana kallon kasa cen nesa dashi taduka muryansa maisanyi taji taratsa dodon kunnenta wa alaikumus salam""

Gabantane yasake fadii talumshe idonta tabude aranta tace sak muryan dad"" murya kasa kasa tacemasa inawuni


Idanuwansa suna kanta yace lafiya qalau Khady yagidan yakaratu"" wannan karon kam tunaninta yafara gagararta ahankali tadago kanta saicikin idonsa

Zumbur tamike tadafe kirjinta tace dady dama Kaine??? Yanda take magana kasan tanacikin matsanancin tashin hankali gakuma bugun kirjinta ya tsananta

Lallausan murmushi yasakar mata yace nine kinji mamakine khadija"" hawayenda suke akan fuskarta suka karasa gangarowa tace dad menene hakan?? labila dasaninta ta aikata hakan???

Yasakeyin murmushi yace balaifin labila bane nine nafara samunta da maganar"" cikin muryar kuka tace nashiga uku  ni khadija menene sahiba ta aikata haka bazai yiyuba

Kafin Usman yayi magana tuni khadija taruga tafita dakin tana kuka kamar ranta zaifita usman yatashi tsaye yana kiranta ina kojuyowa batayiba yadunkule hannunsa yanaushi iska

Lebonsa nakasa yacije adayanaji kamar zai iyah hakurah da khadija Amman ganinda yamata ayanzu babu nikab yasake haukatoda soyayyarta ya Allah kasa kartace bazata aureniba

Dagudu tashiga gidan labila tana tareda innah kawaiganinta sukai dagudu tafada daki tana kuka"" suka kalleta suduka sannan suka dubi juna innah tace dama nafadawa malam tayarda da maganar kine dan batasan kowaye kika zaba mata ba

Ainidama nasan za ayihaka"" saikishiga kilallaso abarki"" labila kamar tayi kuka takama hanyar dakin innah tabita dakallo tace Allah yasa zatayarda tunda intakafe akan Abu bamaijuyata saidai nasan yanda kuke watakil tasaurareki







Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 61
      By
Gentle Lady💃🏽



Taturah kofar tashiga da sallama khadija tana saman gado saidarzar kuka takeyi"" labila takarasa saman gadon tazauna

Tadade tana kallonta daga bisani tadafata tareda kiran sunanta sahiba"" juyowa tayi tarungumeta tasake fashewa dawani kukan tace menene kikayi haka sahiba??

Dama dady ne kikecewa kinzabamun??? Meyasa zakiyi abunda kinsan bazaitaba yiyuwaba meyasa kikamun haka meyasa  tasake fashewa dawani kukan

Labila ahankali tasoma bubbuga bayanta tace sahiba saboda shine yachanchanci zama mijinki

Duk da araina nayimasa kwadayin aurenki dabaisameni yace yanasonkiba wlh bazantaba cewa ya aurekiba please sahiba karkice bazaki aureshiba

Dasauri tadago dagajikinta tana girgiza kai tace bazan iyah ba sahiba wlh tamkar mahaifina nake ganinsa bazan iyah auren babankiba"""

Labila akufule tace kawai kifito fili kicemun bakyason babana kawai  basaikincemun bazaki aure shiba

Tanakai karshen maganar tamike daniyar fita dasauri khadija tasha gabanta tahade hannu waje daya alamar roko tace kigagarceni sahiba niba haka nake nufiba

Amman kisamarmun wani wlh kowaye zan aureshi""" labila tacije lebenta nakasa tace shi mahaifin nawa baiyi makibane????

Hannunta khadija taja tace kizauna muyi magana" tafige hannunta komai zakifada kifadamun inajinki basai nazaunaba

Tace haba sahiba Dan girman Allah kisaurareni"" tace ahakan kinamun kuka?? Dasauri tagoge hawayenta tace nadaina please kizauna

Tanisa sannan takoma tazauna tajuya mata baya"" khadija tagirgiza kanta tace yanzu sahiba akan Dan wannan abun zakiyi fushidani???  labila tace awajenki yakedan nikam awajeba babban al a marine haba abudebaki ace ba ason ubana wlh kinbani mamaki danice wlh kowaye kikabani narantse saina aureshi tundahar kece kikafurta banice nace inasonshiba

Khadija tace bazan iyaba sahiba haba dady dawanne ido zankalli mom??? Labila taja tsaki tace dayake kinsantane bakisantaba bakitaba ganintaba amatsayin matar mijinta zakishiga gidan tomenene

Indai nizakiyiwa kara wlh banaso karkiji waidan tana mahaifiyata wlh nafison babana saudubu da itah farincikinsa shine nawa

Kodawata yace yanaso zanyi ruwa inyi tsaki danganin yasameta ballantana kuma gudan sahibata"" tariko hannunta please sahiba babu musu atsakaninmu karki ki babana wlh yanasonki"" kirane yashigo wayar labila dama tundazu taketa ringing tasan dadyn tane tanadauka yace labila idan batayardaba kibarta""" nibari inwuce Tanisa tana kallonta tace kajiramu gamunan fitowa takashe kiran tanakallonta tace please sahiba""

Khadija ta sake share hawayenda suka saukomata tace bazan iyaba sahiba""

Labila tamike tunkafin khadija takarasa rufe bakinta"" tace magana takare tajuya dasauri tasake jawo hannunta labila tabuge dakata karkisake rikemun hannu tundakince bakyason babana"

Wlh khadija kokiso kokarkiso nasan kinasonsa dasauri khadija takalleta tana girgiza kai tacigaba wlh kinasonsa tunranarda kikaganshi nasanda kinasonsa dan nakula dake sosai

Yawan faduwar gabanda kikeji itace alamar harcikin jininki yakeyawo kuma ninasan bazaki iyah rayuwa bataredashiba kawaidai kinason hanawa kanki abunda kikeso"" tarufe bakinta tace bazakigane menake hangowaba

Labila tadaga hannu tace ki amsamun zaki aureshi ah ko ah ah??? Tace kiyi hakuri please tayi maganar tanasake riko hannunta tajaye hannunta tawuce dasauri

Khadija tabita dagudu tanafita tarufe kofar tayi hanyar gidan tana kuka hartana hadawa dagudu bawai komaitakeyiwa kukaba tanajin tausayin babantane""

Usman yanaganinta shima yafito yabi bayanta yana kiran sunanta"" kowaigensa batayibà saima tasake rugawa

Khadija kofar gidan taduke tanata kuka kamar ranta zaifita gaskiya labila tafada idantace batasonshi tayi karya Amman abunda kunya mahaifin kawarta

Inna ce tadafata"" tamike tafada jikinta tace inna yazanyi labila tayi fushidani" kinajifa abunda tayi"" innah tace nidai aganina ki amince kawai tunda kinasonshi

Tace innah dangan takarmufa?? Tace
Khadija meyasa kikeson haramtawa kanki abunda yake halal nee agareki"" ???

Kisani wani baya auren mijin wani hakazalika wani baya auren matar wani kidaina cutarda kanki nikaina nalurah dake tunranarda akayi walima kikashiga damuwa

Saikiyi zugum kedaya kuma wani sa in sainaganki kina murmushi harnakanji kina magana da zuciyarki kinacewa tadaina babanki""

Adazaki iyah kauda kai Amman yanzu bawan Allah nan yataso tundaga  kaduna yazo wajenki Kuma yasamu kawunki yamasa magana

Kitunafa yarsa yayiwa magana batadauki komai arantaba tonamenene zakice baki yardaba

Ta share hawaye tace toyazanyi inna kinagani tayi fushi""" innah tadafata tace dauko takalmanki kibita gidan kibata hakuri shima kibashi hakuri kice kin amince shikenan aiko

Tagyada kai tanakara share hawayenta innah tace saikidaina wannan kukan karyace tilas taki akayi kuma tace to saida tasake gyara fuskarta  tafita duk dahaka idanuwanta jajir suke kamar gauta"" ahankali take tafiya hartakai gidan gabanta kuma saidukan uku uku yakeyi

Tanayin sallama cikin falon yana zaune saman  kujerah yajingina kansa idanuwansa suna kallon silin da alamu tunani yakeyi kuma yayi nisa cikin tunanin

Yanda hartayi sallama baijitaba kodan muryanta ta dusashe tagefen ido take satar kallonsa saitaga yakara kyau yanda yayi Sam fuskarsa ba walwala

Dakin labila tashiga takosameshi abude harkuryar tawuce dan bata same ta falonba"" tana kwance saman gado tahau saman tajuyo dafuskarta wajenta

Labila tasha toka "" khadija tace kiyi hakuri sahiba nibawai naki dad bane inaganin kamar cinfuskane na auri mahaifinki" "labila tace toshine me bashine yace yana sonkiba kuma ninayarda""

Tanisa shikenan sahiba indai hakan shine muradinki Na amince  kiyi hakuri"""sannan kibawa dad hakuri naga kamar ranshi yabaci""  labila tace anki ahakura din 😏  tamurguda mata baki yanda tayi saiyabawa""khadija dariya tatintsire da dariya

Labila takaimata dukan wasa tagoce tana dariya itama dariyar tasaka"" suka rungume juna"" suna dariya

Khadija tace kije kibashi hakuri please"" labila tace kitashi mujedai inrakaki aibani nayilaifinba""😕

Tace kunya nakeji wlh""🙈 labila tace ke yanzu andaina jinkunya gaskiya dole nafara koyamaki darashi tayanda zaki yimasa kwarkwasa kiyimasa Farida ido

Yanda idan yanatare dake bazaisake tuna kowaba"" khadija mayafinta taja tarufe fuskarta tanadariya

Labila tace ashedai inada aiki agabana kunyar nan zanfara ciremaki tukun tamike mujeko
Bayanta khadija talabe harsuka fita yana nan kamar yanda taganshi dazu

Saidai yanzu murmushine kwance akan fuskarsa danyaji duk abunda sukefada"" bayajin muryan khadija saita labila Dan khadija kamar rada takeyi

Kusa dashi taduka khadija talabe bayanta tasunne kanta haryanzu baidago ba kamarma baisan da zuwan suba labilace takirah sunansa daddy

Batareda yadagoba ya amsa saikuma tayi shiru dantarasa mezatace masa"" saikuma tahau zungurar khadija
Murya kasa kasa khadija tace dad kayi hakuriii cen kasar zuciyarsa yatsinkayi muryanta wacce tasaukarmasa da wata mugunyar kasala!!!





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 62
       By
Gentle Lady💃🏽


Yadago fuskarsa wacce take kumshe da murmushi idanuwansa yadorah akanta duk da tadukarda kanta"" yace laifin me akamun daza abani hakuri???

Aini yadace inbada hakuri gashi tasanadina nasa kinyi hasarar hawayenki masu tsada"" khadija  kara sanne kanta tayi

Labila ce tamintsileta"" itama tarama mikewa labila tayi tace inazuwa kafin khadija tayunkurah tuni labila taruga tashige daki tarufe kofa

Dolece tazaunarda khadija Amman sai mutsuiniya take kamar wacce take akan kaya"" Usman haryanzu baidauke idonsa akantaba"

Ahankali yakira sunanta khaaadeeeja hardawani Jan haruffan sunanta yanayin yanda yakirah sunanta yasaukar mata da kasala kasa amsawa tayi""

Saida yasake kiranta akaro nabiyu sannan ta amsa cen kasan makoshi""" yanisa inafatardai ba labilace ta tilas taki kibani hakuriba
..... Kai tagirgiza"" yace tomenene ra ayinki akaina nayimaki konayimaki tsufa ??? Bakinta tarufe tana dariya kasa kasa shima yadan saki dariya maidan sauti yace kifadamun gaskiya idan banyi makiba tayiyu nayi furfura dayawa bansaniba

Wannan karon saida khadija tadago takalleshi ta sake sanne kanta kasa"" aranta tace anya kasan yanda kake kuwa??? Kamar matashi Dan shekara ashirin dabiyar""

Yace bakice komaiba??? Cikin jinkunya tace ah ah dad"" yamurmusa tokinyarda yanzu  zaki aureni??? Tagyada kai

Yace to Alhamdulillah insanarda malam kenan kin amince"" tace ah amman dady karatunafa""" yace hakane ainasan kunkusa gamawa koba ajinku daya da labila ba???

Tace ah ah ba skull dinmu dayaba"" suna riganmu zana jarabawa"yace shikenan badamuwa aikunkusa gamawa zan iyah jirah kikammala""

Shirune yabiyo baya kuma Usman yamaida kansa saman kujerah wani dadine yaketa ratsashi tako ina"" jiyakema tamkar gobene za adaurah masa aure da itah

Farinciki yakeji marar misaltuwa Wanda baitabajin irinshiba"" shi run yayi yawa hakan yasaka khadija tasaci kallonsa saitaci sa a ba itah yake kalloba

Takuramasa ido tana murmushi"" tanaganin yadan motsa tayi zumut ta mike dad nizantafi gida"" yace au harkingama firar??? Cikin zolaya yayi maganar batace komaiba

Yace shikenan kigaida innah tace to dasauri tawuce hartanadan hadawa dagudu yabita da kallo cikin soda kauna saida tafita yasaukarda ajiyar xuciya mai nauyi yace Alhamdulillah

Yalunshe idonsa yasake budewa yakwalawa labila kirah"" tana kwance tana game tace na am tareda mikewa tafito kusa dashi tazauna akasa tace waihar tatafi???

Yace ah tatafi"" murmushi labila tayi tace Allah yatabbatar da alkhairi yace Ameen"" sannan yagyara zamansa yace wanne irin sharadine kikace zakisanardani inhar tayarda zata aureni???

Labila tagyara zama tace  inafatar ranka bazai sosuba??? Yace bakomai inajinki"" Tanisa kanta yanakasa tace  banaso katambayi dalili akan komai dazanfada ""

 yace shikenan inajinki tanisa banaso kasanarda mom zakayi aure kabari sai ana sauran sati daya bukin

Kamar yacemata menene dalilinta Saikuma yatuna tace karya tambaya shima anashi bangaren baidaniyar sanarda itah dansai kumuiniya yakeda maganar shiyasa yanzun ma dagawajen aiki yawuce kanon

  yace uhum inajinki saime kuma""tace inhar bikin yatashi karkabari mom tayi taron biki sannan koda tatambayeka zataje unguwa karkabarta

Waifa awautar labila sai lubabatu tasamu fitane harzataje wajen bokanta abunda batasaniba lubabatu batazuwa ko ina bokanta madubinta danmuddiñ ba madubin tarasaba babu abunda zaikaita wajen bokan

Yayishiru aransa yace kodai labila zargin mahaifiyarta takeyi??? Allah sarki batasan baburuwan lubabatuba harmatafini son inyi auren kawaidai halin matanne

labila tacigaba Kawata bazata zauna bene Na biyuba kodai kabarmata naka kokuma mom takoma naka sahiba tazauna na mom din  kaisaika zauna nabiyun


Idan harkayimun wannan kagama mun komai saidai nayimaku fatan Allah yabaku zaman lafiya""

Yasaki murmushi taredacewa Ameen indai Dan wannan ne aibakomai"" maisaukine awajena"" yakalli agogon hannunsa yace wai ina abdulmajeed yashigane??

Tanadariya tace ainaturah shi gidan abokinsa tunda nasan zakazo yana iyah kwabsamana"" hajiya ma danasanarda itah zakazo shinefa itama tafita unguwa""

Yamike tokuwa bazan jirasuba aiki yanacen wlh nabaro muje nabaki sako sainawuce tace to tajuya daki tadauko mayafinta tafita"" yanagaba tanabiye dashi kofar gidansu khadija suka nufa labila takarasa tarufe kofar

Tace dad koyanruwa bakashaba??? Yace taruwa nakeyi wacce nazo wajen ta tagudu tabarni dariya labila takamayi tace ayimana afuwa dad

Motarsa yabude yadauko wani karamin kwali guda biyu yace gashi saikiduba kotayi biyu nasiyo saikidauki daya"" tace la dad nifa daya nafadamaka nitawa uncle baijima dasiyamun itaba waccema kasiyomana lokacin walima ya muktar yakarbeta ahannunta waibaiyarda tarika wayaba

Yace toyanzu kikaimata aizanyi magana dashi yabarta da wayarta inaso zandinga kiranta munagaisawa tunda bakullum sai nakirah awayarkiba idankuma bakwatarefa

Kije saiki saka mata chaji nibari nawuce tace tomungode Allah yakiyaye hanya yace Ameen yashiga motar yawuce tanadaga masa hannu

Labila takunna wayar tadauki dayar tasaka number din dad tayi serving hubbyna daya number sa tasaka my everything""


Tayi murmushi taka she wayar tamiyar cikin kwalinta tawuce gidan tsakar gidan tasamu khadija suna labari da innah tanaganin labila tahau dariya

Labila taharareta cikin wasa tace haka akefirah waidaga shigana daki kodanafito bangankiba tayi maganar tanazama tace wlh sainatashi tsaye naga alama sahiba batasan yanda ake tarairayar saurayiba

Bacinma kiyita janshi dafirah harsaiyamanta inda zaije dareyamasa agarin nan"" inna banda dariya babu abunda takemasu itakuma duk labila tasata jinkunya""

Tamikawa innah tace gawayar sahiba dad yace abarta da wayarta zairika kirah suna gaisawa saurankuma idan yakirah kiki dauka dannalurah bakisan love ba""

Innah tace nadaiganoki labila kamfen kikewa dad"" tace bahaka bane innah sonake tutarmu tayi sama aikingane tayi maganar tanakashe ma khadija ido daya

Takaimata duka tagoce tana dariya bari nawuce gida kitashi kisaka chaji kikunna bamamaki idan yakai office zaikirah yaji muryar maisanyinsa

Idan yakirah kilankwashe murya kice helo my love tayi maganar tanayin Farida ido khadija tamike tabita dagudu tafita gidan tana dariya

Inna ma dariya takeyi tace kecedai labila ce maishiga tsakaninku zaiji kunya"" kidauki wayar kisaka chajin tace to

Wayar tadauka zuwa dakinta takunna wayar sannan tajonata chajii takurawa wayar ido fuskar Usman takegani ajikin glass din wayar sai murmushi takesaki

*WACECE KHADEEJA!*

Kubiyo yargidan Ibraheem domin kuji cikakken tarihin rayuwarta
""

Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



Chapter 63
       By
Gentle Lady💃🏽


Fateema shine sunan mahaifiyar khadija innar fateema Yar nigar ce "" sunanta hauwa"u  mahaifin malam garba"" Dan kasuwane yanazuwa kasuwanni kasashe daban daban

Matarsa daya"" sadiya dansu nafari Abubakar Amman amfikiranshi da garba"" saikuma  tagwaye datahaifa duka mata hasana da Husaina daga garesu batasake haihuwaba

Mahaifin malam garba acen wajen kasuwancinsa yabullah Niger yahadu da Hauwa" u kunsan bozayen Niger basucika bada yayansu ga hausawaba

Acewarsu basada rikon Aure itah kuma Hauwa"u ta tsunduma wajen son buhari"". Babu yanda iyayenta basuyiba akan tafita harkansa tabuga kaidakasa tace batason kowa saishi

Duka kuwa babu kalar Wanda batashaba Amman takekashe kasa tace shitakeso iyayenta sukace tosaidai tazaba koshi kosu awautarta saitace tazabi buhari
Wannan shine babban kuskureñda tatabka

Rashin bin maganar iyaye
Sukuma sukace toduk abunda yabiyo bayan auren karta kuskurah tanemesu koda auren yakwabe saidai tanemi wasu iyayen basuba tace ta amince""

Yayan mahaifinta shine sarkin Niger baiso suyanke mata wannan hukuncinba Amman tunda tanace ita shitakeso saisuka cire hannunsu daga sha aninta sukace tacemasa yaturo

Takuwa sanardashi ya turo iyayensa yabiya sadaki atake akadaurah masu aure sukace yadauki matarsa babu wani biki da akayi

Taci kuka hartagode Allah gashi itace kawai awajen mahaifiyarta"" ranar sukataso daga Niger sukazo kano acikin danginta ko kuda babu Wanda yarakota

Sadiya tariketa hannu bibbiyu duk da halayensu  badayaba saboda Hauwa u tanada hakuri sosai itakuwa sadiya akwai fada dakuma mita Amman baruwanta daharkar kowa saifa idan antabata Amman Hauwa u koda dukanta kayi zata tambayeka Allah yasadai bakaji ciwoba😉

Shekaranta uku taredashi sannan tasamu ciki cikin yanabata wahala sosai haka tayita fama harta sauka tahaifi yarta mace sak kamanninta  ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar buhari fateema suna kara anacemata yarbaba kamar yanda buhari yake kiranta  tuni sunan fateema yabace sai yarbaba  buhari yadauki son duniya yadorah mata

Kamar babuwata ya agabanshi face itah yanda yakerawar kafa akanta kaikace baitaba haihuwaba hakan saiyasoma damun sadiya tanarayawa aranta bayason yayanta

Watakilma magani Hauwa u taimata dantasan yan Niger matsafane yanda takejin labari saitasoma sauyawa Hauwa u idan yarbaba tamatso inda take saita tureta tanacewa matsanan dangin mayu aniyarku tabiku

Kowani Abu Hauwa u tadafa bataci saitace ina nasani ko saida aka barbadeshi za aban Toni ba kwadayayya bace bataci kuma batabarin yaranta suci

Saikuma takoma tanayiwa hauwau gorin danamiji tanacewa komaidai tsafin mutum dole yabarta kuma itace dagida bamai Yar maceba

Tun abun nan bayadamun Hauwa"u haryakai yanadamunta gashidai batada wani Dan uwa dazata kaimasa kukanta yasharemata hawaye

Mijinsu kuma bayazama kuma idan yana nan Sam sadiya batanuna komai agabansa sannu kan hankali   tasoma ramewa tanafita hayyacinta"" tatsakure kullum sai buhari yasata gaba datambaya meke damunta tacemasa bakomai idan yamatsa saita fada masa saita azamasa kuka haryagaji yakyaleta bayan ta yaye fateema dawata hudu

Kawai tahada kayanta tacewa buhari gida zataje shikuma yace bazataba tace saitaje yace totabashi yarsa yakarbe fateema tanata kuka tatafi tabarta sadiya tanagefe kokallonta batayiba

Tundaga lokacin batasake waiwayarshiba shidinma bai waiwayetaba Fateema babu kalar ukubarda batashaba agun
sadiya batajin tausayinta kokadan

Tuntana karama hartagirma cikin wahala take"" lokacinda tagirma saitahadu dawani Muhammad shikuma dan yola ne bafulatani

Suka Kama soyayya sunatsaka da soyayya ne sadiya tasoma rashin lafiya

Hawan jinine yakamata gakuma mutuwar Rabin jiki damuwa tamata yawa hasana aurenta hudu abokiyar zama tahanata sakat duk inda tai aure sai abokiyar zama takoreta

Itakuma Husaina tahadu dawata arniyar kishiya tamaida itah boyarta  komai aikin gidan itah takeyinsa kuma miji baida halin shiga dakinda take hasalima dakin awakai take kwana

Wannan damuwar ita tahaifarwa sadiya daciyo datagadai ciwon saigaba gaba yakeyi saita tara kowa fateema hassana Husaina garba dakuma buhari

Tanemi sufaye mata"" laifinda taimasu"" kowayace batayimasa komaiba tana kuka takalli fateema tace Dan Allah yarbaba kiyafemun abunda naimaki son zuciya dakuma zugar makociyata itah takaini ga halaka nacutardake fateema narabaki da mahaifiyarki

Ta sake fashewa dakuka buhari yace haba yazaki daurawa kanki laifi ai ba aimata komaiba tatafi danhaka idan kawai mailifi tonine"" tasake share hawayenta tace wlh bakada laifi malam nice naimaku asiri na farraku gabadaya wajen sukahada baki asiri!!😳 Tace kwarai kuwa lokacinda aka kawo hauwau wlh dazuciya daya nariketa tamkar Kanwata hartazo tahaifi yarbaba bantaba cutarda itaba

Lokacinda naga malam yasoma fifita fateema akan Yayana sai nasoma jin haushi tawannan hanyarne shaidan yasamu yashiga zuciyata yadinga yimun huduba sainafara kyararta ina tsangamarta

Danazauna inyita zaginta inacemata  mayya"  Amman bata taba fadawa kowaba saidai tabarwa zuciyarta watarana ina zaune saiga makociyar mu matar kabiru tashigo tasameni nayi tagumi tayita sallama banjiba alokacin Hauwa tana barci

Saida tatabani sannan nazaburah nanisa hannuna taja zuwadaki tace menene yasameki kika buga tagumi kamar wacce tarasa mijinta

Nadanyi tsaki nace dama shinarasa dasauki kinjikinji meyake damuna nalabarta mata komai shine tace nakwantarda hankalina akwai wani boka komai nakeso zaiyimun indai dakudi

Duk danasan zuwa wajen boka baidakyau Amman shaidan yarufemun ido nace sonake kawai arabasu tabar gidan

Shine nace Amman bazaniba saidai nabata kudin takarba tatafi waini wayone nayi saboda naji ance duk Wanda yatafi wajen boka kowani Dan tsibbo Allah bazai karbi ibadarsaba hartakwana arba in idankuma yamutu akan hanyarsa tagidan bokan yamutu kafiri waini nakizuwa domin natsirah

Bayan kwana biyu takwawomun laya tace inkama bakin layar indaure dawani kyalle na kayan hauwau injefa amasai sannan tabani wani garin magani tace inbarbada kofar dakinta nakarba nayimata godiya

Washe garikuwa tanabarci nalababa dakinta nayanko gefen zaninta nadaure layar naje najefata amasai nakuma barbada maganin kofar dakinta "" inatsakar gidan zaune nakwallomata kirah

Yautaji nakirata rabonda nakirata hartamanta cikin fara a dazumudi tafito batasan ni damugun nufi nakirataba tana tsilga maganin sainaga tajuya daki tahau hada kayantaa!!!





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!!*☠




chapter 65
       By
Gentle Lady💃🏽




Amman saikuga adinga kyararta abunma yawuce gida har yan unguwa todakuma aikomai daga gida yake tashi sunga kunayi mezaihana suma suyi

Rukayya tayita hakuri dasu hartakai sunazuwa sunacewa fateema in rukayya tabata Abu kartaci dantana bakincikin cikinda kejikinta

Dayake fateema tanada hankali Sam bata daukar maganarsu Amman kunsan dawatace ahakan saikuga wata fitinar ta auku kaimiji kanacen kana nema masu abinci


Bakasan ta inda fitina zatakunno kai agidankaba koda zaka farga wuta hartaci tacinye alokacin koda kaso ka sasantasu abun yafikarfin tunaninka

Cikin fateema yacigaba dagirma haryanzu tanabaiwa rukayya girmanta" bata daukan zugar dangin miji sukuwa abunsu saigaba gaba yakeyi cikin fateema yanashiga wata Tara tasuntulo kyakkyawan danta kinkowa Wanda yarasa babansa sak

Waiyo zokuga murna wajen rukayya musamman tahada walima saboda murnar saukar fateema lafiya kayanda tasiyawa yaron kuwa kowadanda mahaifinsa yasiyamasa basukai yawan nataba

Ko maijego kala goma tadinka mata tayi gayyar abokananta sukansu kallonta kawai sukeyi da mamaki dangikuwa tunda sukaga fateema tahaifi namiji saikuma gori yadawo sabo

Ranar suna akasawa yaro suna muktar harsu hassana saida sukaje biki"" taro yawatse su hassana dakin rukayya suka kwana sunsha firah washe garin suna suka koma

Wata tsohuwace takekulada fateema hartayi arba in"" sukacigaba dazamansu lafiya"" saifa dangin miji idan sunzo gidan basakiran muktar dasunansa saidai sucemasa magajin gida!!

Sam abun baidami rukayyaba harma abun yasoma bata dariya watarana tanazaune alokacin muktar watanshi goma dayake bayada kiuya hannuntama yake kwana nono kanshi baidameshi ba saidai idan yana kuka da anbashi ruwa shikenan

Fateema tatafi wajen kitso da lalli tunsafe tabarmata shi sallama tajiyo anayi tata so tana am sawa tadage labulen kofa tace la la la Asma.u kece agidan nan???

Maraba maraba shigomana tadorah muktar akafadarta wacce akakirah dasunan asma u tawuce saman kujerah tazauna rukayya tace daga inakike haka cikin tsakiyar rana

Asma"u  taharareta tace zakice haka tundake bakyason zumunci aini karanima inazuwa tunda bakyason zumunci sainadauke kafata

Rukayya tace habadai Yar uwa wlh aikine bayabarina fita ko kitso rabona danaje amun harnamanta saidai maman muktar takeyimun danzanen yawo

Asma" u tamere baki"" rukayya tace rikamun shi nakawomaki ruwa tayi maganar tana mikamata shi tajaye jikinta dasauri tace wa ?? Ninadauki Dan kishiya Allah yasauwake

Rukayya tayi dariya tace kice haryanzu halin yana nan???🤔 Tace hargobema indai akan kishiyane sai abunda yacigaba!!😕
.
Rukayya tayi dariya tace Allah yashiryeki Kawata nidai bansan lokacinda zaki saki makamankiba kiyarda kishiya abokiyar zamace

Asma"u tasheke da dariya tace inakika taba ganin anzubarda makamai afilin daga??? Shifa abokin gaba dakike gani duk wani kwantardakai dayakeyi na munafurcine soyake yashammaceki

Dazaran yasamu sa arki kasheki zaiyi"" ance kakashe makashinka tunkafin yakasheka"" rukayya tace kedai kikasan wannan hadisin"" tawuce baridai inbaki ruwa yana akafadarta takawomata ruwa tasha

Tazauna kusa da itah saiga muktar yasaki fitsari tace kai yaudai kasharuwa dayawa saifitsari kaketayi batagama rufe bakintaba yasaki zawo tuni yabata mata kaya

Asma" u tayi saurin rufe hancinta wai itah doyi rukayya tana rungume dashi tanabuga bayansa ahankali haryagama taje tawanke masa tasauya wani zani tasakamasa wando

Tadawo tazauna yihakurifa Kawata nabarki kedaya"" tajatsaki ahakadai zaki kare dabautar danwani rukayya tabata fuska tace menene haka Asma"u Dan mijin nawa shine danwani dakikecewa zankare abautarsa aidama bauta nazoyi

Idan inason mijina yazama dole naso jininsa Asma"u tace tosannu daddawa dadi amre najinjina maki tobari kiji kokiso kokiki yaron nan dayagirma uwarsa yasani

Dakike ikirarin bauta kikazo kefa yanzu hotoce kawai awajen mijinki" tayisaurin kallonta tace ahmana kehotoce saboda mijinki yanason Yaya sosai kingakuwa wacce zatayita haifamasa Yaya saitafiki fada keyanzu amatsayin Yar raino suka ajeki tanahaihuwa anabaki kinacinkashinsu dafitsari dazaran sungirma lokacinda dadi yazo maimakon kucidadin tare saitanunamaki kefa bakisan yanda dayake kwanciya amahaifaba

Alokacin zata nunamaki itace tahaifi danta""  aini tunranar suna kikabani mamaki nasona kyaleki saikumà naga idan naihakan bankyautaba amatsayina na kawarki.

Tagyara zama ninazomaki damafita idan kinaso??? Rukayya tayi shiru tace nidai mubar maganar nan nima indarabo zanga nawa

Tayi saurin gwatseta tace yaushe??? Inda kinada rabon haihuwar aidakin haihu tunkafin yakaro aure gashi yayi Amarya daga zuwanta tasamu ciki zauna nan wlh saitacika gidan nan dayaya kekuwa kizama Yar kallo

Shekararki takwas da aure tunyana talakansa futuk kika aureshi gashi yazama maikudi tamurmusa kibar ganin wannan daular wlh dazaran yamutu bazaki tsirah dakomaiba sai bakinciki

Bazakiyarda da maganataba saiyafadi yamutu sukuma Yaya sukoma wajen uwarsu kinga bakiga yantusa yanzawo suntsere yanzu kikeda dama idankuma kikabari damarki tawucemaki tokece zakiyi kuka baniba nidai amatsayina na kawarki naga abunda zaicutar dakene nazo nafadamaki inkindauka ruwanki idanbaki daukaba ruwanki sainangaba zakiyi danasani alokacinda danasaninki bashida wata rana

Ta mike nidai kinga tafiyata idan kin sake shawara kije gida kisameni ashirye nake da intaimaka maki sai anjima idan uwargidan Muhammad tadawo kimika gaisuwata tawuce abunta

Kotadakai rukayya batayiba har fateema tadawo tasameta cikin wannan halin tatambayeta meyake damunta saidai tacemata kartadamu bakomai""

Kunsan shaidan shifa danwaje yakeso yasamu ya lababa yaitayi mana busa akunne hakanne yasamu rukayya maganganun Asma" u sukaita mata yawo azuciya taso takawarda tunanin takasa

Sati daya dafaruwar hakan fateema tafara rashin lafiya anazuwa asibiti akace tanada ciki wata uku abunda yayi matukar tayarda hankalin rukayya sai aka yaye muktar akabarshi hannunta

Kullum Muhammad yana nane da fateema mekikeso mene bakyaso rawar kafarda yakeyi yanzu saitasoma baiwa rukayya haushi hartasomajin haushin fateema

Gashikuma cikin fateema yazoda laulayi komai taci saita amayar dashi "" sai Muhammad yatarkata aiki yadawo jinyarta watarana yana zaune yanabata abinci abaki saida tagama cinyewa tasoma kwara amai

Saida ta amayardashi duka"" Muhammad duk yarude sai sannu yakemata rukayya tanazaune tana kallonsu yacemata taimakamun da Abu ingoge

Kamar tace bazaniba saikuma ta mike tafita yacema fateema sannu kaitagyada yace yanzu mekikeso kici??? Kaitagirgiza yace haba uwar Yayana yazaki zauna dayunwa kisamu koda tea ne kisha
.
Kuka tafashe dashi tace banaso banajin dadin komai yakoma rarrashinta najito uwar Yayana Amman kinsan likita yace kirika cin abinci saboda Karin kafiyarki dakuma Dana dayake jikinki shiru tayi batace komaiba

Rukayya kuwa sanda yakecewa uwar Yayana Kalmar tafada akunnenta tafara nanata sunan aranta lallai zancen Asma" u gaskiyane inhar fateema tacigaba da haihuwa agidan zatacika gidan da Yaya

Idankuma hakan tafaru itakuma menene matsayinta wata zuciya tace Yar raino mana dasauri tace wlh karyane bazan yardaba

Ganin tajima bata dawoba Muhammad yasake kwalamata kirah tazaburah tashigo dasauri tace yihakuri jinayi kamar kukan muktar nadauka yatashine sainaje naduba shiyasa nadade

Yace bakomai yakarbi ruwan da abun gogewa yagogemata bakinta rukayya tanayimata sannu tanakuma harararta😣😂😂





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




Chapter 64
        By
Gentle Lady💃🏽




Tana fitowa kana shigowa. Tace maka gidansu zataje kaikuwa kacemata bazataba takafe akan saita tafi shine kace totabaka yarka Tabaka tatafi dama shine rabuwarku ance bazaku sake Neman junaba

Nikuwa tundaga lokacin nayita ganawa fateema azaba naso tamutu harguba makociyata tabani tace nasakamata acikin abinci Amman dayake batada rabon hawala kwananta basu kareba saigashi akuyata uwar gargen da yayanta takunce daga daurinda naimata tafada madafa dayayanta sukacinye abincin alokacin tana wajen dibar ruwa

Koda tadawo saidai naji tanasalati tana kiran sunana koda nafito damasifa sainaga abunda yafaru ga dabbobina wannan shine asalin abunda yafaro ciwona domin dasu nadogara akuya bakwai duka sukai musai

Takaici yasakani nakilmawa fateema kashi nace itah tazubamasu guba dantana bakinciki da arzikina kaikuma saika yarda kasake dukanta taja majina kaji abunda yafaru tun alokacin naketa ganin i shara gashi Ya.yana sunyi aure abunda naiwa Hauwa suma anaimasu

Ninasan abunda nashukane nakegirba wlh nayi nadama Dan Allah kiyafemun fateema yarbaba tana kuka tashare hawayenta tace bakomai innah ninayafe maki duniya da lahirah

Buhari kam shiru yayi danyakasa magana saida tasake neman gafararsa yace nayafe naki sadiya bakece dalaifiba nine mailaifin tunfarko daban fifita son yarbaba akan sauran yayanaba dahakan batafaruba

Hakika nikaina na aikata babban laifi duka yayanane kowanne amanace agareni baidace kafifita danka akan wani danba koda kafisonsa aranka kadinga yin kawaici musamman idanma yaran ba uwarsu dayaba hakan zai iyah janyo rabuwar kan iyalinka kekuma dakinkirani kinyimun  nasiha aibawani abubane

Amman kin aikata babban laifi wacce kika zalunta Hauwa inazakiganta kiroketa gafara kokinsan Allah baya yafe hakkin wani hakika hakkintane ke bibiyarki kamar yanda itama hakkin iyayenta yake binta

Mun aikata son zuciya munbiyewa soyayya hakan yasaka batayi rabuwar dadi da iyayentaba sunce tazaba kosu koni tazabeni rashin bin maganar iyaye shine yajawo mata haka harkuma yashafi yarta

Allah ya yafemana  kura kuranmu suka amsa da amin tace malam taimako daya zakamun kaje Niger wajen danginta tayiyu takoma gidane idan kaganta kanemamun gafararta sannan kamaida matarka nasan haryanzu kanasonta ninasan ciwon nan nawa banatashi bane """

Yace nayimaki alkawari zantafi duk danasan abune mai wahala su saurareni dansuna ganin kamar nine silar rabasu dayarsu  kidaina maganar mutuwa aicuta bamutuwa bace insha Allah zakisamu lafiya dakanki kinemi gafararta tace hmm kawai dan itah kawai tasan metakeji

ranar jikin kowa yayi sanyi sukuku suka wuni washe gari kodasuka farka saidai sukaga gawarta  tacika cikin dare tashin hankali sunganshi bakamar garba yanaganin mahaifiyarshi  tashuka abunda bazai barta kwanciyar kabariba

Sati biyu darasuwarta garba yamatsa aje Niger buhari yashirya suka dunguma hardasu hasana da Fateema"" Amman dasukaje gidansu Hauwa mahaifinta ko saurarenshi baiyiba yayimasa korar kare

Dayaki tafiya fateema kuma tahau kuka bindiga yadauko yace kosubarmasa gida koya dirkesu da bindiga dole suka futa fateema tanata waigen kakarta wacce taketa kuka" dankuwa babu abunda yaraba Hauwa da fateema

Agarin suka kwana buhari yayita tambaya koda tadawo garin akacemasa batadawoba tunda ta auri wani bahaushe tayafe gida aikowa yabargida gida yabarshi

Washe gari sukadawo Nigeria saikuma buhari yakwanta jinta danyanzu soyayyar Hauwa tadawomasa sabuwa watanshi daya shima yace ga garinku

Fateema takoma marainiya garba shike tallafe dagidan haryayi aure alokacinne Muhammad yafito daniyar auren fateema

Muhammad yanada mata daya sunanta rukayya sunyi auren saurayi da budurwa amman haryanzu bata tabayin koda batan wataba
Aurensu kuma wajen shekara takwas kuma shi yana masifar son Yaya Amman yanason matarsa hakan yasaka yakiya kara aure saigashi yakawowa wani abokinsa ziyara kano haryayi sati daya akasuwa yahaduda fateema an aiketa siyo kayan miya yabiyota haryaga gidansu kunji sanadin haduwarsu

Garba dayaji yanada mata kuma gashi zatayi nisa dasu saiyace  tahakurah dashi tasamu wani itakuma tace shiitake so tarihidai yasake maimaita Kansa domin fateema takafe kaida fata saishi

Garba yanajin tausayinta dakuma halin kuncin rayuwa datashiga bayaso yatakurah mata sanin yanda soyayya take saiya amince Muhammad yaturo magabatansa akasarana suka biya sadaki suka kawo lefe akasa biki wata uku

Wata uku sunacika aka dauramasu aure matar garba balkisu macece wacce baruwanta itace komai na fateema su hassana ma suntaka rawargani sun nuna bajintarsu amatsayinsu Na antys dinta garba yahada kudinda za asiyamata kayan daki acen yola akasiya akajerah mata babu laifi sunyimata kaya kamar diyar maikudi

Ranarda za akaita har yola saida suka rakata sukaga gidan  sun yaba sosai dahalin rakayya sai nan nan takedasu sunsan kanwarsu tayi dacen abokiyar zama

Saida suka kwana washe gari kuwa dazasu taso sunsha kukan rabuwa haka suka rabu suna kewar juna saidai rukayya tayita basu hakuri

Watan fateema uku saigaciki yabullu nawata uku danbata cilge wataba"" zokuga murna wajen rukayyya harma taso tafi Muhammad murna""batabarin fateema koda chokali taka war komai itah takemata hatta wankin kayanta

Saikuma dangi sukafara jefan rukayya da habaici dama anacemata juya  toyanzu zance yatabbata itace juyar gashi Amarya tasamu ciki itakuma batada aiki saidai taci takasayar

Hasbinallahu wa ni imal wakil kalu innalillahi wa inna ilaihir rajiun waimenene amfanin yiwa wani gorin haihuwa???

Shinkeda kika haihu wani Abu kikayi yasaka kika haihu??? Wayonkine kokuma dabararkice??? Anasiyenta dakudi kokuma mulki zaibaki???

Itah dabata haihuba laifi tayiwa Allah ko anfada maki Allah bayasontane??? Waimeyasa mutane basuda tunani kisani duk wacce kikaiwa gorin haihuwa wlh hartamutu bazata manta dakeba kuma kema bakiwuce Allah yakarbe yayanda yabakiba sannan kidaina haihuwar aganina inhar wata acikin danginku matar yayanki ko matar babanki ko kanwarki kishiyarki inhar hakan yasameta saiki kwantarmata da hankali kice tacigaba dayin addua Allah maji rokon bawansane







Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




Chapter 66
       By
Gentle Lady💃🏽


Daga fateema har Muhammad basu lura dawani chanji tattare da itah ba saidaifa tadaina sakewa da fateema kamar da

Saisuka danganta hakan da damuwarda tashiga narashin lafiyar fateema idan fateema talangaye wa Muhammad tana kuka sai rukayya taraya aranta duk kissace da kisisina babu abunda yake damunta

Shedan yadinga yimata huduba tawanke kafarta tatafi gidansu Asma" koda tashiga da sallama tasamu mijin Asma u yanawankin kayanta yashanya wasu gakuma wasu tulin kayan sannan kuma gashi yana girki

Yatara uban zufa sai sharcewa yakeyi rukayya tagaidashi sannan tawuce dakin rukayya saman kujerah tasameta tahakimtse tanacin naman kaji abun nan yamatukar bawa rukayya mamaki tana ganinta tatashi daga kishingidarda tayi tace yaukece agidan nan kodai batan hanya kikayi???

Rukayya Tanisa tace kusan haka"" ta sake kallon kofa tace anya Asma"u kinatsoron mutuwa??? Tace danayime???

Rukayya tace hmm abunda nagani mijinki kike sakawa wanki??? Tamere baki waisaboda dan ""wannan wayasa ya auroni idan bazai iyah daukar dawainiyataba

Rukayya tace lallai haryanzu dasauranki karfa kimanta aljannarki tana karkashin kafarsa"" idan baidagaba bazaki shigaba

Kunkumi tarike tace abudole tsufa da duwai aiyazama dole yadagamun inshiga""abunsaiya bawa rukayya dariya tace  Allah yashiryaki

Tace  ameen bamaki addua ba"" 😕rukayya tace bawan nan banidai zuwanayi akan maganarmu taranar Asma "u tasheke da dariya tace bake bace idan kaga kigudu sagudune baizoba inazuwa tayi maganar tanamikewa

Rukayya tabita dakallo yanda Asma u tagoge kamar wata hajiya miji duk yakanjame bakin kofa tatsaya tace isihu korufe bakinta batayiba saigashi dagudu yazo haryanacin tuntube yace mekikeda bukata rankiyadade

Tayatsina fuska bakomai kafita waje kasha iska zuwa anjima karka dawofa saina kiraka"" yace shikenan godiya nake yajuya yafita dasauri

Tasaki murmushi sannan takoma wajen rukayya wacce tasaki baki tanakallon abunda yafikarfin tunaninta

Asma u tace Kawata inajinki " rukayya tanisa tace maganarda mukai ranar yanzu maganarda nakemaki cikine da itah

Asma"u tace kadanma kikagani bake tsoron Allah ba"" rukayya tace yanzudai duk abar maganar menene mafitarda kika samamun???

Asma" u tagyara zama tace duk mafita tawuce irin tawa Rukayya tace kamarya banganeba Asma"u tace akwai wani boka sunansa *hatsabibin boka* aikinsa kuwa nantakene inhar kinyarda zakije wajensa tokeda kuka har abada

Kunyi bankwana da bakinciki jinta ambaci sunan boka yasaka rukayya tazama tatsaye tace Asma u yanda nake ganinki ashema kinwuce nan boka dai! gaskiya danasan wannan itace mafitarda kikasamamun dabanzo gidankiba Allah yakareni da hatsabibancinsa

Asma"u ta sake darawa tace aini gatanaimaki tundahar nakeson hadaki da babban boka Wanda babu kamarsaa aduk fadin duniyarnan

Rukayya tace gatafa kikace ahakan??? Aibashima yadace akirah hatsabibiba faceke sunan yafi dacewa dake

Asma"u tace kinga nidai bansakaki doleba ra ayine idankinji bazaki iyaba""kitafii haka kurum kefa kika kawo kanki banice" natilas takiba idan abun yadameki dakanki zaki dawo

Rukayya tamike tace badai wajen *hatsabibin kuba* wlh bazaniba haka kurum ina zaman zamana kinzo kintayarmun da hankali duk tunani yadameni

Tace kinga tafiyata Allah yashiryeku tawuce abunta Asma u tace tokigaida uwar yayan Muhammad wannan kalmar tana matukar tsayawa azuciyar rukayya

Koda takoma gidan tasamu Muhammad gida sai lailayar fateema yakeyi taci abinci tanatayi masa kuka abun yasake kularda rukayya tanashiga da sallama tadage kanta tawuce fuuu kamar kubu buwa

Fateema tace me akayiwa Anty kuma"" Muhammad yace tobadai mune mukabata mata raiba"" idan tahuce aizata fito dayake fateema batason magana saita kama bakinta

Itakuma rukayya tayi tunanin zaibiyota taji tsit saita fashe da kuka tayi mai isarta dole ta share hawayenta ahakadai akayita gurgurawa da dadi ba dadi harcikin Fateema yakara girma tadaina laulayi ""cikin ta yana shiga wata Tara takama  nakuda

Cikin tashin hankali Muhammad yasakata amota zuwa hospital batawani jimaba ta sake haiho santalelen danta kinkowa Wanda yarasa kyakkyawa sak kamar muktar

Zokuga murna awajen yan uwan Muhammad kamar suhadiye fateema""kayakuwa tashasu kamar hauka kokayanda Muhammad yatirka mata saiwanda yagani
Sati yana zagayowa akayi suna wannan karon su hasana kawai sukazo Dan matar garba tana fama da laulayi

Yaro yaci sunan Umar faruq"" anakiransa faruk yanbiki sukaci sukasha sukai kat kowa yawatse akabar maijego da yaronta

Muktar kullum yana makale da fateema danyana mutuwar son yaron duk da ko anbashi baya iya daukarsa danyanzu shekaransa daya dawata takwas

Fateema tanaganin yan sauye sauye atattare da rukayya Amman batakawo komai aranta tacigaba darainon danta" tuni rukayya tadaina sakewa muktar fuska

Faruq yanada wata shida saigashi fateema tasoma laulayi tunda akace cikine da itah tahau kuka ita wlh bazata yardaba saidai azubarda cikin

Shikuma Muhammad yace wlh baza a zubar dashiba shiyanason abunshi takaicima yasakaa tabaroshi asivitin

Yanata kiran sunanta kowaigensa batayiba tanafita tatari Dan adaidaita tasanardashi inda zaikaita Muhammad raibace yabaro asivitin

Anakaita gida tabiyashi kudinsa tafada gidan tana kuka"" rukayya tataso dasauri tace lafiyarki fateema ina abban faruq din??? Meyasameki kiketa kuka

Batagama rufe bakintaba yana shigowa yace fateema Ashe haka kikeda  taurin kai"" taballamasa harara tace dankawai kaibakasan wahalarda akeshaba da ajikinka yake aidabazakace hakanba""

Rukayya tace waimeyake faruwa niduk kuntayarmun dahankali tayi maganar tana kallon Muhammad

Yace tambayeta gatanan"" tajuya wajen Fateema tace meyafaru cikin kuka tace wai Anty cikine dani

Rukayya tace ciki nashiga uku harkin kuma samun wani cikin itah batasan inda maganar rukayya tadosaba tace ah wai Anty shinefa nace azubar waibaza a zubarba

Haba kwata kwata shekarana nawa da aure ace inada yara har uku kumama ba wannan ba umar fa watanshi shida aikodan sabodashi zaiji tausayinsa

Rukayya dai daka tahana wuri magana dangaba daya hankalinta yagama tashi lallai idan tayi sake maganar Asma u gaskiyace fateema zatacika gidan da yaya haihuwa kamar akuya😾 dama matane dadan sauki koyanzu watakil namijine zata sake haihowa

Muhammad yakatsemata tunani wajen magana yace wlh fateema baza a zubarba ai wannan rashin godiyane kitunafa aurena shekara takwas Amman bansamu magajiba saiyanzu danake ganin gudan jinina kinaso azubar Yayana Na halak ne kuma inason kayana nibanki wlh kihaihu duk bayan wata taraba

Rukayya Tananata Kalmar aranta *magaji* babbar magana dolene nadau mataki idankuma bahakaba inaji inagani gidan nan zai gagareni soyayya taci ubanta🙄

Koda tafarga har fateema tashige dakinta saidai taji Muhammad yana bubbuga kofar yana hadata da Allah tabude itakuma sairusar kuka takeyi

Dasauri yafita idonshi jawur kaman Wanda akadaka yaja motarsa yayanki titi tsaye nahango rukayya kamar mutum mutumi tarasa inda zata saka kanta

Tana nan tsaye tajiyo sallamarsa bayansa kuma"" gwaggo rabiee ce kanwar mamarsa tashigo dasauri rukayya tana gaida itah kokallonta batayiba tayi hanyar dakin  fateema tasoma bubbugar kofar bude Fateema nice haba Yar kwarai irin albarka kibude kinji fateema

Fateema CE tabude takoma tazauna tacigaba da kukanta"" gwaggo rabie takarasa saman kujerar tazauna Muhammad shikuma yanatsaye yakuramata ido

Gwaggo tace haba mai babban suna yazakiyi haka kitausayawa babangida mana dayake haka suke kiransa sunan babansune

Tace ai wanann abun farincikine abun alfarinkine ace kinada ciki menene amfanin azauna saidai aciyarda mutum yana tula kashi

Indai faruq ne karkisamu damuwa babu abunda zaisameshi dazaran anyi wata uku zanzo inkarbeshi saina yayeshi kekuma saikiyi rainon danku

Kinji fateema kiyi hakuri tunda kinga babangida yanason yaran nan"" kinji mai babban suna"" fateema tashare hawayenta tace tahakurah wani dadine yalullube Muhammad

Bayan tagama bata baki sannan tafita suka gaisa da rukayya tace kiyi hakurifa wlh hankalinane atashe shiyasa bangankiba""

Tace bakomai ai nikam nasan taciki naciki dankuwa ranar rukayya kasa barci tayi saidai takai gwauro takai mari

Mafita  dayace dolene inkoma wajen Asma" u muje wajen bokan dankuwa banada wata mafita wacce tawuce wannan ai Allah maiyawan gafarane idan nadawo saina nemi ya yafemun

Shikenan ai Allah yaga zuciyata wannan abun zaicutardani kuma Allah yace tashi in taimakeka Dan nanemarwa kaina mafita bazai kamani da laifiba

Dawan nan shawarar hankalinta yakwanta takoma takwanta tanamai murmushin jindadi "" wai hauka shaidan yazo yalailayomata wadansu banzayen maganganu wai Allah yace tashi in taimakeka aibata wannan hanyar yace abiba

Koyace acutarda wani dansamun farincikin wani waifa tace idan tadawo tanemi gafarar Allah kwarai Allah gafurur raheem ne

Amman Allah baya yafe hakin wani shinbatayi tunanin tanakan hanyar kobayan tadawo tahadu da ajalinta kafin tatuba ??shin idan taje gaban Allah tanada hujjar dazata kare kanta ??indai abunda tafada shine hujjarta lallai hujjar banzace dankuwa batariki hujjaba

Rukayya abunda batasaniba duk Wanda yaje wajen boka to Allah zai zaremasa imaninsa tamkar yanda akezare lakka ajikin kashi

Aganinku duk wacce taje wajen boka tanada sauran imani kije kawai dankisa acutarda Yar uwarki ke kodama badaniyar cuta kikajeba baikamata kijeba

Dawan nan bakin kudirin takwana washe gari lomar fari tunda take bata taba fitah gidanba batareda izinin Muhammad ba saigashi tayi satar hanya

Koda taje gidan tasamu Asma u zaune mijin yanayi mata tausa akafafunta tanaganinta tasheke da dariya tace bakebace

Tamaida kallonta wajensa tace sai abamu wuriko kanata kallonmu wiki wiki da she gun idanuwanka tuni yasanne kansa kasa

Yamike yafita tamaida kallonta wajen rukayya cikin fara a tace zauna Kawata tazauna tana kallonta"" tace koyauma zuwa kikai kicimun mutunci dani da *hatsabibin boka???*

Rukayya tashare hawaye tace bar maganar wasa Kawata zuwanayi kitaimakamun yanzufa waikuma tasake kunsar wani cikin

Tasake fashewa da kuka"" tace wlh komenene zanyi indai zatabarmun gidana banason buda ido naganta  cikin gidan dashegun yayanta

Asma "u tasheke da dariya"" tace bakebace dai ainafada maki"" rukayya tace toyazamuyi
Asma u tagyara zama tashinfida mata dukkan dokokin shiga dajinda *hatsabibin boka* yake dakuma saradansa idan zata iyah
Tace komenene wlh zan iyah Asma" u nidai banaso naganta agidan

To Rabie da Aisha saiku shirya Dan tare zakuje kudibo mana labarai😂😂 karnaji kunce bazakubà dankodà igiyane sainajaku  inda Wanda zàshi kàllo yamun magana naga kamar motar takusa cika🚌


Download Book Here