[4/2, 10:05 PM] nabilalady5: 🏡🏡 A WANI GIDA🏡🏡
          😭😭😭

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

        Part 50  ⏩ 55

JINJINA GA DUKKANIN MASOYA LITTAFIN A WANI GIDA, HAKIKA INA MATUKAR JIN DADIN YANDA NAKE SAMUN SAKON NIN GODIYARKU DA KUMA GAISUWA ZUWA GARENI. NAGODE DA ADDU'ARKU AGARENI, ALLAH YABAR ZUMUNCI.


INA MIKA JIN JINA GA 'YAN GROUP DIN NABEELERT LADY 1&2, HAKIKA INA JIN DADIN ADDU'ARKU DA KUMA GWARIN GUIWAR DA KUKE BANI, TARE DA COMMENTS DINKU AGARE NI. ALLAH YABAR ZUMNUCI AMIN🙏🏻😘.



Zaune suke gaba dayansu a falo, Fahad da Farouk se bata rai sukeyi saboda an dawo Faskari, ba kamar Farouk saboda shi agarin yake karatu. Bayan sun gama cin abinci kowa yayi wanka Malan yace kowa ya kawo result dinshi.

Faisal da Fatima ne suka fara shigowa falon, amma sauran seda suka dade kafin su dawo, sosai Malan yaji dadin yanda result din Fatima yakasance, gaba daya Excellent sun fi yawa, Good dinta biyu.

Hakama result din Faisal, na wannan karon yafi na koyaushe, domin yasamu grade me kyau, hannu ya mika ya karbi result din Farida, kallonta yayi yana fadin wannan ai ba rubutun malaminku bane.

Kuma duk wanda ya kalli score dinki ko be yi total ba yasan be isa ace kin samu wannan mark din da average din ba. Mama tace kamar ya? Kasande Farida ai tana da kokari. Murmushi Malan yayi yace to ai koni ba Malamin makaranta bane ya isa ingane abinda kikayi.

Kuma da alama ga wani bakin lalle nan daya zuba adede kan ai nihin total dinki da average dinki, ya akayi hakan tafaru? Ciccira ido Farida ta fara tana fadin muna kunshi ne yazuba akai.

Dariya Malan yasa yace lallai wannan lalle akwaishi da lura, wato daya tashi zuba seya zuba adede inda rubutun yake, kuma daga nan be kara matsawa ba ya tsaya adede wajen. Hmmm Farida kada ki bata mani rai.

Wannan rubutun ba na malami bane. Farida tace wallahi Malan bani ce na rubuta ba, haka Malamin mu yabani shine ya rubuta. Malan yace to inajin shine yayi kuskure wajen total din.

Amma zan sake total in fidda mark din kuma da average din. Kinga idan zaku koma se inje insameshi, ya kamata anuna mashi kuskurenshi. Saurin dago kai Farida tayi kamar zatayi kuka tace dan Allah Malan ka kyaleshi.

Hannu Malan yasa ya dauketa da mari wanda gaba daya falon seda suka firgita, Mama kuwa saurin tashi tayi tana kallon Malan cike da mamaki. Sosai ranta yabaci, wani irin ihu Farida tasa tana birgima akasa.

Cike da bacin rai Malan ya jawo dorinarshi yafara dukanta, duk yanda Mama taso ta kwaceta kasawa tayi, tun Farida tana kuka da karfi har ta dena. Seda yayi mata dukan dabe taba mata shiba ya saketa.

Hankalin  Fahad ne yatashi, domin ya gane dalilin da yasa Malan ya doki Farida, saboda tayi mashi karya. Hannu Malan yadora abaki yana fadin rufe mani baki, idan na kara jin kukanki sena kara maki.

Komawa Mama tayi tazauna ranta abace, sede sam babu wanda ze iya gane hakan. Farouk ne yayi saurin mika nashi result din, sosai yakara jan baya, kallonshi Malan yayi fuska a daure yace kana JSS3 amma kana kawo mani wannan result din.

Babu abinda zan ce maka, domin yanzu ka girma, duk abinda kayi dede da kai ne, idan kuma akayi maka repeating banida matsala, kuma wallahi seka maimaita ajinka. Kallon Fahad yayi yana fadin ina naka? Ja da baya Fahad yafarayi yana fadin nawa faduwa yayi.

Saurin cafkoshi Malan yayi, haka ya zaneshi yana tambayarshi inda ya kai nashi, ihu kawai Fahad yake yana kiran Mama, seda Malan yayi mashi dukan tsiya ya fasa mashi jiki sannan yace yaje yadauko mashi result din.

Da gudu yafita se gashi yadawo dashi duk ya dukun kune, karba Malan yayi yana dubawa, gaba daya result din beyi kyau ba, gashi wajen teachers comment malamin yakawo karar Fahad na rashin jin da yakeyi.

Kuma baya zama a class, sosai ran Malan yabaci, kallonshi yayi yace ka kyauta, ai dama tunda naji ka fadi haka nasan bakayi abin kirki ba, kuma gashi Malaminku yace ba ka zama aji, gidan Uban wa kake zuwa? Cikin Kuka Fahad yace wallahi ina zama.

Malan yace irin wannan halin ka dorama kanka ko? To kasani wallahi duk wanda yaja aka koreshi daga makaranta ni babu ruwa na, sede yadawo yazauna agida, bazan kara bata lokacina da kudina wajen nemar maka makaranta ba.

Mutanan banza, gashi de daga farko kamar kune mutanan arziki amma daga karshe kune mutanan banza, wadan da nake ganin kamar sune zasuyi irin halinku gashi sun bani kunya, dan Allah kalli result din su Faisal.

Ke kuma babbar munafuka, kina karamarki har kin iya yin munafurci, JSS 1 kike amma kinsan ki canza rubutun da malaminku yayi, wai ni zaki fadama lallae ne ya zubar maki. To kisani sena kaima malaminku result din, idan yaso seya nunaki agaban 'yan ajinku kuma shima ya zaneki dan hakan yazama darasi ga sauran yaran.

Kutashi kubani waje. Saurin tashi Farida tayi tana kuka, tasan idan Malan yakai ma malaminsu result dinta dariya za'ayi mata, kuma zatasha kunya. Tashi su Faisal sukayi, Fatima se kunshe dariya takeyi, shiko Faisal se murmushi yakeyi.

Mama se binsu take ta wani irin kallo, tsanarsu ta kara shiga ranta, haka suka fita, shima Fahad se hararar Faisal da  Fatima yakeyi, haka ma Farida, Farouk kuwa se dariya yake masu.


Suna fita Mama ta matso kusa da Malan tana fadin kayi hakuri, kasan halin yarinta kowa da irin tashi, wata rana se labari. Malan yace labari marar dadi ba. Murmushi Mama tayi tana fadin haba Malan ya zakace haka? Kada kamanta fa maganarka me dadi da marar dadi zasu iya yin tasiri akan yaranka.

Addu'a ita kadaice abinda yafi kamata kayi masu, amma ni nasan akwai abinda yake faruwa da yarana. Kukan munafunci tasa tana fadin kaima sheda ne akan yarana, duk unguwarmu babu wanda yafisu kokari, amma lokaci guda ace yarana sunja baya.

Wallahi na dade ina zargin wani abu, ai koda zasu ja baya be kamata ace su duka sunja baya ba, kalli Farouk, yaron da sam karatu baya mashi wahala, kalli irin kyaututtukan dayake amsa, amma tunda yashiga wannan makarantar shikenan komai ya lalace.

Uhm, ninasan dama Inne bazaki barni haka ba, waye besan halin 'yan gidanku ba, saboda tsabar asiri uwarta harta tsufa bata bar mijinta yayi aure ba, so nawa yana zuwa neman aure se maganar ta yi karfi kawai ta lalace.

Yanzu kuma gashi nima Allah yahadani kishi da jinin asiri ni wallahi dama nice tayimawa na bar gidan, inbar mata yaran tarike matukar zata barsu da kokarinsu. Kana kallon yanda Faisal yake wani irin murmushin mugunta. Yaron da ko dariyar kirki baya yi agabanka.

Ai ni tun da Farouk yashiga makaranta Inne take bashi wani abu aboye kuma tace kada yafada maka nasan ba abun arziki bane, duk idan ze tafi seta daka mashi yaji da kuli tabashi se kace yaron mayu, haka ma Fahad da zasu tafi shima abinda tabashi kenan, ashe dama akwai abinda ta kulla. Na dauka kawai tanayi ne dan Allah, shiyasa tace base anfada maka ba, ni kuma ganin abun arziki ne yasa bana fada maka, dan ba'aso dan mutum yayi abu se an fada.

Kuma ka kira Farida ka tambayeta, tunda kuka dawo tace zata fada mani wata magana akan Inne wai taje makarantarsu, sede bata gama fada mani ba ka kirawo mu nan, idan gaskiya ne me Inne zataje yi makarantarsu Farida.

Jikin Malan ne yayi sanyi kuma lokaci guda fuskarshi ta canza, kalon Mama yayi yana fadin kin tabbata Jamila taje makarantarsu Fatima? Mama tace ni ban gama jin labarin ba, amma ka kirawo Farida da Fatimar zakaji komai.

Jinjina kai yayi yace biri yayi kama da mutum, ai nasan irin bakin halin Jamila zata iya yima yaran nan wani mugun abun, gashi nan yanzu yaranta ne kadai suke kokari a gidan nan, yanzu kuma ta koma zata bata mani yara.

To wallahi duk da inajin kunyar Alhaji Mansur zanja mashi layi tsakaninshi da yarana. Tashi ki kira mani su. Saurin tashi Mama tayi cike da farin ciki tafita. Kafin suzo seda tace ma Farida ta fadi duk abinda tasani harma dana kari duk ta fada.


Ai ko suna zuwa Malan ya tambayi Farida akan zuwan Inne, tsaf Farida ta kwashe duk abinda ya faru harma da kari tafada masu. Daga karshe tace kuma da naje wajensu Inne koro ni tayi, bata bari naga abubuwan data kawoma Fatima ba, sede kawai Fatima takawo mani wasu kaya.

Lokacin da naci wani abu da tayo mana seda nayita amai, har clinic seda aka kaini, kuma tun daga lokacin idan ana koya mana karatu se inji nagaji da class din kuma bana gane komai, amma farkon zuwanmu har kyautar kudi malamin mu yana bani idan na bada amsa.

Salati Mama ta farayi tana tafa hannu, jawo Farida tayi tana duba idonta, tana fadin nide tunda kuka dawo nake kallonki, gaba daya naga kin canza, kuma Fatima tayi wata irin kiba ashe da abinda kikaci.

Kallon Fatima Malan yayi wadda tayi kasa da kanta yana fadin ke da gaske Uwarku tazo makarantarku? Cikin Kuka Fatima tace e tazo amma wallahi duk abinda takawo mani shine na dibar ma Farida, kuma mu da mukaci babu abinda ya samemu.

Tsawa Malan ya daka mata yana fadin rufe mani baki, yarinyarki karama amma kin iya hali irin na Uwarki. Kallon Faisal yayi wadda gaba daya ya hade rai, kai Faisal Mamanku taje makarantarku? Kanshi yana kasa yace e taje ta duba ni.

Zufa ce kawai take zubo ma Malan, jinjina kai yayi yace ku tashi kubani waje. Bayan sun tafi Mama tace kaji da kunnanka ko? Ai nafada maka, wallahi Inne ba ta sonka da yaran nan, kaga yanzu tunda suna boarding zata rika zuwa tana hure masu kunne, tunda mijinta me kudi ne zata rika saya masu abubuwan da baka siya masu.

Idan suka ga haka dole sufara tunanin komawa wajenta, kuma kaga yarana sune abaya, domin iyakar abinda kasiya masu dashi kadai zasuyi amfani, su kuma sunacin kashi 2. To wallahi seka dauki mataki, idan kuma baka dauka ba, nizan dauka saboda kare yarana.

Bazan zauna ta nakasa mani yara ba, yanzu gaba daya Fahad ya kangare, yaro me nutsuwa me kunya amma yanzu beda ita, ga rashin kokari, haba ai abun yayi yawa. Malan yace kiyi hakuri, seyanzu na fahimci komai.

Kuma nayi dana sanin dukansu, kuma zan basu hakuri, tabbas ba laifinsu bane, daga yanzu bazan kara dukansu ba, ita kuma ita da mijinta zan dauki mataki akansu, idan sukayi wasa wallahi daga Fatimar har Faisal din zan maidosu Day anan garin.

Kinga bazata kara ganinsu ba. Kiyi hakuri zan dauki mataki sosai, bazan bari wannan karon Jamila taci nasara akai na ba. Sosai Mama taji dadin abinda Malan yace, aranta tana fadin yanzu naji batu, amma kawai ka kama yarana kana jibgarsu, kuma wallahi sena saka ka doki Fatima Da Faisal kamar yanda ka doki yarana.

**** ****

Bayan kwana biyu da faruwar haka, malan yakira Farida da Fahad ya basu hakuri kuma yace surika yawan addu'a saboda sharrin makiya. Haka Mama ta sasu daki tana tambayarsu dalilin da yasa basa kokari? Fahad ne cikin gungunai yace kawai Mama yanayi ne.

Mama tace to inaso ku kara dagewa, nasamu nayima Malan dabara daga yanzu baze kara ganin laifinku idan bakuyi kokari ba. Fahad yace Allah Mama sena rama dukan da Malan yayi mani akan Faisal, kinga yanda yake mani dariya shida wannan munafukar.

Mana tace kabarni dasu, kasan de Faisal yafi karfinka, yanda Malan ya dokeku haka zansa ya dokesu. Farida tace wallahi Mama bakiga mijin Inne ba, kudi gareshi, kinga acikin motar da sukazo, kamar wani gwamna.

Yanzu Fatima ta samu wata kawa 'yar gidan 'yan gayu ko kallona batayi amakaranta.  Bakiga uban naman da Inne takawo mata ba, amma seda ta bani, niko ban bata nawa ba, kema Mama kirika zuba mata idan kin dafa mani.

Mama tace Farida kenan, ke yarinya ce, Fatima tafiki wayau, kada kiyarda da duk abinda zata maki, so take ta fiki kokari idan tazo wajenki kidena kulata, banaso ta koya maki mugun hali. Murmushi Farouk yayi yace kema de Mama kin cika wata magana.

Taya Fatima zata koyama Farida mugun hali? Duka nawa suke su duka, kede kawai baki son su ne. Hannu Mama takai ta bige mashi baki tana fadin wallahi kashiga hankalinka dani, wai meyasa kakeso ka rai nani ne? Dama fa nasan kai baka bin bayana.

Fahad da Farida su kadai sukeson suga farin ciki na, bakasan irin bakar wahalar dana sha awajen Inne bane shiyasa, lokacin da aka aurota kai kana yaro bakasan komai ba.

Shine yanzu kake goyama yaranta baya. Farouk yace koma menene ai yanzu bata gidan, be kamata kirika nuna masu haka ba, kinga ita Farida bata ba ta abincinta ba,  amma ita Fatimar ta bata.

Kuma kinga yanzu Innensu zata rika je mata visiting da kaya masu yawa wanda sukafi na Malan, ai ba zakiji dadi ba idan Fatima ta hana Farida ko? Mama tace tashi kabani waje, kuma daga yanzu kada ka kara zama akusa dani matukar zaka rika kawo mani irin wannan maganganun. Banza wanda be kishin Uwarshi.

Tashi Farouk yayi yana murmushi yafita. Fahad yace ai dama wannan Yayan yafi goyon bayan Faisal, ko muna kwance adaki sekiji yana bashi labari amma banda ni. Mama tace ka kyaleshi, kaide kada ka biye mashi, banaso ka sakarma Faisal fuska. Kutashi muje kitchen.

****  ****

Amira ce take ta kuka wai se an kaita wajen Yaya Faisal, su Munnir, Abba da Saddik se dariya suke mata, Maman Saddik har ta gaji da lallashi. Da sallama Baban Saddik yashigo yana fadin wai me akayima Mamana ne? Saddik ne yace wai wajen Yaya Faisal take. son zuwa.

Kuma munje gidansu a kulle. Zama yayi yana fadin zo muji abinda kikeso. Bade wajen Yaya Faisal zakije ba? Kai ta daga tana goge idonta. Baba yace karki damu zamuje ki ganshi kinji.

Murmushi tayi, tana fadin to yaushe zamuje? Baba yace se ranar da babu islamiya se muje, ai tunda yanzu kina kokari amakaranta duk abinda kikeso zanyi maki. Kinga yanzu ke kadai ce a Primary, Saddik yatafi ya barki.

Amira tace nima to akaini Secondary Baba. Dariya suka sa Mama tace to ai yanzu ajinki 4 damma sunga kina kokari yanzu shiyasa suka maidaki can, ki bari idan kika shiga aji 5 se akai ki JSS 1.

Baba yace ai nayi matukar mamakin kokarin Mamana, ban taba tunanin Mamana zatayi kakori a makaranta ba, amma kuma kome akace Allah angama magana, shiyasa na fada maki bana dana sanin kashe mata kudi.

Saboda haka zan nema mata Secondary din makarantarsu, duk da sunyi first term kawai su dauketa haka, ai Mamana ta zaunu a Primary, ki duba fa Saddik kaninta ne, amma yanzu yana JSS 1.

Idan mukace seta gama Primary lokacin fa Saddik yashiga JSS 3, dama me akeso, ta gane abinda ake koya mata, kuma alhamdulillah, yanzu babu abinda Mamana bata sani ba, matsalarta daya har yanzu akwai yarinta ajikinta.

Wannan kuma bawani abu bane, duk ranar da tayi aure hankali zezo mata. Dariya Mama tasa tana fadin kaji Baban Saddik da wata magana, wai aure? Baba yace emana, kinsan yawancin masu irin wanna matsalar silar aure tana kawo masu sauki.

Shiyasa nake rokon Allah yabata miji nagari. Mama tace yanzu de maganar makaranta akeyi, yarinyar da ko Primary bata gama ba kake maganar miji. Baba yace ai dole inyi. To naji, yanzu de kinji abinda nace.

Allah gara ta tafi secondary haka nan, amma bazan kaita boarding ba, gara tazauna a private dinsu, ta saba da malaman  su, kuma sun san matsalarta duk da yanzu wasu malaman zata samu amma yafi ace inda tasani ne.

Mama tace hakan ma yana da kyau. Allah yasa su amince. Baba  yace zasu amince ma, private ce kudi kawai sukeso, kuma sun san yanda ta dade amakarantar ba zan sha wahalar amincewarsu ba.

Kuma kinga karin dadin amakarantarsu zan barta. Kallon Amira yayi yace Mamana kema wannan term din zaki shiga JSS 1. Tsalle Amira tayi tana murna hada rawarta tana ma Saddik gwalo. Su Abba se dariya suke mata.

Turo baki Saddik yayi yana fadin gaskiya Baba ba zamu zauna aji daya da ita ba. Dariya Baba yayi yace ai kai boarding kakeyi, ita kuma Day zatayi, kaga ba makaranta daya ma zaku zauna ba. Murmushi yayi yana fadin ai de baza arika maki provision ba.

Amira tace wai haka Baba? Baba yace rabu dashi, kullum se an saka maki biscuit acikin kwandon makarantarki, gwalo tayi mashi, ze kara magana Mama tajawoshi tayi mashi rada. Murmushi yayi yana fadin iye, Amira 'yan JSS 1.



Zulai ce tashigo tana ta sallama, da sauri Mama tafito  tana amsawa, dariya tayi tana fadin ashe kece, ina ciki ina fama da yara na sasu aiki. Zulai tace aifa yara sun dawo hutu se hayaniya.

Mama tace kishigo mana, zaune suke afalo suna fira Fatima ta fito da kayan miyan data gyara tana fadin Mama nagama akawo kudin markadan. Harararta Mama tayi tana fadin atsaye zaki mun magana, kuma bakiga bakuwa ba? Dukawa Fatima tayi tana fadin ina kwana. 

Zulai tace lafiya lau, ke kam baki dago kai kike sunne kai kamar wata munafuka? Mama tace ai itace, kema kenan da baki santa ba, gashi daga zuwanki har kin ganota. Zulai tace kadde itace Fatimar? Mama tace itace fa me hali irin na Uwarta.

Tabe baki Zulai tayi tana fadin sannu da kokari Maman Farida. Naaira 20 Mama ta wurga ma Fatima tana fadin kuma kimun sauri kizo kidora girkin kada Malan yadawo yasamu ba'a gama ba.

Bayan ta fita Zulai tace ita ce take maki girki? Mama tace to mezatayi? Ai duk aikin gidan nan itace takeyi ita da Yayanta, domin Uwarsu ta sangartasu, komai itace take masu shiyasa yanzu nake horar dasu.

Zulai tace wallahi kinyi dabara, ai dama rikon Dan daba naka ba, sekayi da gaske, domin idan ya lalace kai za'a zarga, gara aga kana matsa mashi ayi gulmarka da kyau, duk ranar daya zama mutum za'a gane abinda kake nufi.

Mama tace kema de kya fada, damma ina taka ma Malan burki akansu, ai da yanzu yarana sun koma baya, kinsan duk yaran da aka ce Uwarsu bata gida Uba yafi sonsu, gani nayi yana so ya maida mani yara Saniyar ware yasa nima na bullo da nawa makircin.

Shewa Zulai tasa tana fadin shiyasa nake sonki, baki barin seta kwana, wallahi ina bayanki, me ake da Dan kishiya, wallahi duk yanda ka rikeshi banza kake awajenshi, ke koda tun yana jariri kika rikeshi ida ya girma yagane ba kece kika haifeshi ba, wata rana seya yi maki butulci.

Bare su da aka barsu da wayonsu. Ai se kinyi da gaske sannan ki kwaci kanki. Mama tace ke damma na iya allo na awajen Malan ai da tuni nazama abin tausayi, yana bala'in daukar maganata, domin nidin bakin ganga ce. 

Zulai tace duk inda aka buga zakin daya ne. Dariya suka sa, Faisal ne yafito fuskarshi a daure, dan duk abinda suke fada yaji, ko kallon inda suke beyi ba ya nufi hanyar waje. Mama ce ta daka mashi tsawa tana fadin gidan Uban wa zakaje? Tsayawa yayi amma be jiyo ba.

Mama tace ba magana nake maka ba? Kuma bakaga bakuwa ba zaka wuce ta babu gaisuwa ko haka Uwarku ta koya maku? Kwalla ce tacika idon Faisal bece komai ba ya nufi waje. Da sauri Mama ta tashi ta fisgoshi ta baya harseda rigarshi ta yage.

Zulai tace lallai Maman Farida kin sake ma yaran nan, kamar wannan abun har ya isa kiyi magana ya kyaleki? Hannu Faisal yasa yana fadin ki sakar mani riga. Farouk ne da Fahad da Farida suka fito jin hayaniya.

Suna fitowa Mama tafara fadin dani zakayi fada Faisal? Faisal yace ni yaza'ayi nayi fada dake, kawaide nace ki sakar mani riga. Hannu yasa yakara kama hannunta. Kukan munafurci Mama tasa tana fadin yau naga ikon Allah.

Ni kake zagi Faisal? Kokarin kwace jikinshi yakeyi, ita kuma Mama tana kara matsowa jikinshi kamar masu shirin dambe. Fahad da zuciya ta gama ciyoshi yace kai Faisal bakada hankali da Mamar zakayi fada? Faisal yace ina ruwanka.

Ko nasa da kai? Sosai wannan maganar ta batama Farouk rai, matsowa yayi ya wanke Faisal da mari, Mama ma ta kara wankeshi da mari. Dun kule hannu Faisal yayi ya kaima Farouk naushi, tsautsayi yasa  hannunshi ya sauka a idon Mama.

Wani irin ihu tasa tare da dukewa kasa. Ganin haka da Farouk da Fahad suka rufarma Faisal da duka, shima haka yarika dukansu ta ko ina, amma dayake Farouk yafishi karfi kuma gasu su biyu hakan yasa sukafi karfinshi.

Zulai da taga abin yaki karewa tayi saurin fita takira wani namiji yazo ya rabasu da kyar, duk an fasama Faisal baki, shima kuma yaji masu ciwo. Mama kuwa tana gefe ta dafe idonta da yayi Ja lokaci guda.

Fita Zulai tayi tana fadin se anjima Maman Farida zuwa gobe zan dawo. Wucewa daki Faisal yayi yashiga bandaki yana wanke jikinshi, Fatima ce tashigo, ganin kowa yayi shiru yasa ta wuce kitchen, bayan ta aje nikan ta nufu dakinsu Faisal.

Zaune ta sameshi yana ta kuka, saurin karasawa tayi tana fadin Yaya waya dukeka? Hannunta yakamo yabata labarin abinda yafaru, cikin kuka Fatima tace wallahi nima haka tayi mani, kayi hakuri Yaya Allah ze saka maka.

Faisal yace wallahi ba dan ke ba da yau katsina zan tafi, Fatima tace a'a Yaya kayi hakuri, kasan Inne tace muyi hakuri da duk abinda za'ayi mana. Kaga nima yanzu girki Mama tasani, Faisal yace zauna bazakiyi ba.

Bugo kofar dakin akayi, suna daga kansu sukaga Mama ce, wajen da Faisal ya bigeta har yayi baki gaba daya zagayen idon. Kallon Fatima tayi tana fadin bazaki tashi kidora girkin ba sena sa kema an zaneki? Ai ni wallahi naji dadi.

Daga yanzu bazan kara bata bakina akanku ba, tunda Allah yasa yarana sun kawo karfi sune zasu cigaba da rike gidan nan, kuma dani kuke magana, kujira dawowar Malan. Ke kuma kada kije kidafa abincin.

Fita tayi tana masifa, tashi Fatima tayi tana kuka, rikota Faisal yayi yana fadin wallahi ba zakije ba, ko kinje kinyi aikin seta hadamu da Malan, gara ki kiyi tafada da hujja. Fatima tace nide Yaya ina tsoron Malan, kuma kaji tace zatasa adukeni. Kwace hannunta tayi ta nufi kitchen. Kara fashewa Faisal yayi da kuka, yana matukar tausayin Fatima.


Zaune suke gaba dayansu afalo, Mama se kuka takeyi tunda Malan yashigo, gashi yaga idonta yayi ja kuma gefen yayi baki, tambayar abinda akayi mata yayi, Farida ce tace Yaya Faisal ne ya nausheta a ido dan tace ina zeje.

Saurin kallon Faisal Malan yayi, shima ga bakinshi nan afashe. Cikin kuka Mama tace tunda nake da kai ban taba bata maka rai ba, narike maka yara tsakani da Allah, amma yau nice yaranka zasu hade ma kai, shi Faisal ma hada naushi na.


Ita kuma Fatima na sata aiki tace bazatayi ba. Allah yasani nayi iyakar yina, bazan iya zama ana cimani mutuncina da girmana ba, domin nima na haifa, kuma babu wani Dan da zega ana dukar Uwarshi ya kyale.

Badan ina zaune da yaranka lafiya ba, Allah kadai yasan abinda zaka dawo ka iske a gidan nan, domin nice na raba fadan da akai tsakanin Fahad da Faisal, domin Fahad baze iya ganin ana dukana ya kyale ba, shima Farouk dan na hanashi ne.

Amma wai har Fatima tasan tashigar ma dan uwanta, wannan wace irin rayuwa ce haka, gaskiya idan har baka dauki mataki ba wallahi sena bar maka gidanka, idan yaso seka zauna da yaranka ni kuma in koma gidanmu.

Malan yace haba Hauwa meyayi zafi haka? Ai ko dabba inde ta gidan nan ce zata iya bada shedar yanda kike zaune da yaran nan, kuma ni ba sakaran Uba bane, bazan lamunci irin wannan rashin tarbiyar agida na ba.

Kallon Faisal yayi yace kaji abinda tace, anyi haka ko ba'ayi ba? Mama tace karyata ni kake ma? Malan yace niba karyataki nakeyi ba, inso ya amsa da bakinshi ne. Ina tambayarka? Shiru Faisal yayi hawaye ne kawai suke zuba a idonshi.

Cike da bacin rai Malan ya wanke shi da mari, tashi yayi yadauki dorinarshi, haka yakama Faisal da Fatima ya zanesu, Fatima se kuka takeyi tana boyewa bayan Faisal, shiko se kara kareta yakeyi.

Malan kuwa dukansu yake yana fadin yara kanana daku har kun isa ku raina matata, wato Uwarku taje wajenku tayi maku mummunar hudu ba, shiyasa da kuka dawo kukazo da sabon rashin kirki.

Ada ai ba haka kuke ba, se yanzu da taje wajenku, to wallahi zan iya maido ku Day ba damuwata bace, bazan zura ido ina gani abata mani yara ba. Ganin dukan da yake masu yasa mama tace kabarsu haka nan ai sun daku.

Wurgar da bulalar yayi yana fadin gobe ma ku kara. Sosai suka bama Farouk tausayi, domin yasan ba gaskiya Mama ta fada ba, kawai de baze iya karyata ta bane. Sosai jikinsu ya fashe, Fatima se shashsheka takeyi.

Mama tace kayi hakuri nasa ranka yabaci, abun ne naga kada yayi yawa shiyasa na fada maka, amma ba wannna bane karo na farko da suke mani rashin kunya, kawai banason yawan kawo karar sune, domin suma yarana ne.

Amma na yau yayi yawa shiyasa na fada maka, gashi nan ranka ya baci abanza. Malan yace ke zan bama hakuri, kuma daga yau bance ki kara boye mani duk abinda sukayi maki ba, shi icce tun yana danye ake lankwasa shi.

Nan gaba bamusan abinda zasuyi ba, nagode da irin kaunar da kike nuna mani. Kuma zan kira Alhaji Mansur ince yajama matarshi kunne, idan kuma taki zan maidosu Day. Kutashi kubani waje, yaran Banza kawai.

 Ruwa Mama takawo mashi tana fadin dan Allah kasaki fuskarka, banaso ina ganin bacin ranka, da na san haka ne ma daban fada maka ba. Murmushi Malan yayi yace shikenan yawuce, amma zamuje chemist aduba mani idonki, dan banzan yaro ze bata mani fuskar mata. Murmushi Mama tayi tana fadin ai yarinta ce, aranta tana fadin burina yacika tunda ka dokesu.


Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[4/3, 5:38 PM] nabilalady5: 🏡🏡 A WANI GIDA🏡🏡
          😭😭😭

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

        Part 55 ⏩ 60

Malan kasa kiran Alhaji Mansur yayi, domin yana matukar jin nauyinshi, zama yayi ya tsara mashi message ta yanda ze fahimci abinda yake nufi cikin ruwan sanyi, dan yana tsoron yayi mashi rashin mutunci kuma aikinshi ya samu matsala.

       Assalamu Alaikum.

Ya gida kuma ya aiki, nasan zakayi mamakin wannan sako dana rubuto maka. Bawani dalili bane se dan inaso in toshe wata matsala da take shirin fitowa daga gidanka.

Kamar yanda kasani ni tsohon mijin matarka ne, kuma akwai yara guda biyu atsakanin mu, matarka tayi matukar kokari wajen raba tsakanina da yarana.

Kwata kwata yarana basa sona saboda mahaifiyarsu, bayan mun rabu da ita daga lokacin nafara samun soyayyar yarana. Amma yanzu sena samu labarin tafara bibiyarsu tana so takara raba tsakaninmu.

Kuma zuwan datayi wajensu tabbas naga sauyi daga wajensu, domin sabuwar hudubar datayi masu tashiga zuciyarsu, kuma tayi matukar tasiri, yanzu dariyar da suke mani ma sun dena, basa zama kusa dani.

Basa son sauran 'yan uwansu, babban abinda yafi daga mani hankali shine abinda Faisal yayi. Kamar Faisal har yasan yayi fada da mata ta, wallahi da za kazo da kaga yanda ya nausheta a ido.

Nasan yanda Hauwa take matukar sona shine ya hanata kai Faisal wajen 'yan sanda, bakaga yanda idonta yayi ja ba. Ita kanta Fatima da take karama idan ta sata aiki batayi.

Wannan abu yayi matukar tada mani hankali, shiyasa nace zan maka magana domin kajama matarka kunne. Wallahi Alhaji ina matukar ganin girmanka shiyasa nakasa kiranka.

Da ace wani ne ba kai ba Allah kadai yasan matakin dazan dauka, da zaka tambayi mutanan unguwar mu na Mani zasu fada maka halina. Amma kai kana da girma a idona bazan iya maka rashin kirki ba.

Kuma matarka taci darajarka,kuma bata isa inkirata muyi maganar ba, kawai na fada maka dan kaja mata kunne. Kada takara zuwa wajen yarana, abinda nake siya masu ya ishe su.

Kuma ina matukar kokari akan yarana, babu abinda suka nema suka rasa. Idan kuma taki daukar maganata, to zan iya cire duka yaran daga makarantar in maidosu nan kusa dani suyi Day, idan nayi hakan nasan bazata iya tasowa tazo gidana wajensu ba.

Ina fatan zaka fahimci abinda nake nufi? Nagode.

                    Principal, 
             Science Faskari.
           Malan, Bature Mani.


Malan ya karanta message din da yayi yafi so 5 kafin ya tura, domin bayaso ya rubuta wata kalma marar dadi wadda zata batama Alhaji rai, domin shide aikinshi yakeji.

***** *****

Lokacin da message din yashigo Alhaji yana kwance kusa da Inne suna fira, Inne ce ta miko mashi wayar tana fadin gashi anyo maka message. Alhaji yace nifa bana son duba message, yanzu haka campany ne.

Amsar wayar yayi ya bude, saurin tashi zaune yayi ganin wanda ya turo mashi sakon. Murmushi yayi yace Innen yara ga mutuminki yayo mani sako.

Inne tace to akaranta mana muji. Alhaji yafara karanta mata tana sauraro, seda yagama sannan ya juyo yana kallon Inne. Hawaye ne suke zuba daga idonta. Murmushi yayi yace wannan kukan kuma na meye? Kara fashe tayi da kuka.

Lallashinta ya farayi yana fadin haba Innen Yara, meye abin kuka anan? Daga ganin yanda ya rubuto wannan sakon kema kinsan yana jin tsoro.

Kuma tunda baze iya kirana ko yazo yasameni muyi magana baki da baki dashi ba ai yayi abanza. Kuma babu wata shari'a data raba tsakanin Uwa da 'ya'yanta, koda kuwa basa tare da Ubansu.

Kuma wannan maganar banza ce yake fadi, sede kamar yanda yabani girmana, kuma ya nuna yanajin nauyi na, nima bazan bada kai naba. Kiyi hakuri da hukuncin dazan yanke yanzu.

Kamar yanda ya bukaci kidena kula mashi yara dole zamu samo wata mafita, domin ya gane baki zuwa wajensu, sede kuma ba kamar yanda yafada abun ze kasance ba.

Zan tura mashi message na ban hakuri, kuma zance inde nine mijinki bazaki kara zuwa wajensu ba. Sede zamu sake salon kai masu ziyara, haka kuma zamu jama su kunne akan kada su sake su fadama kowa kina zuwa.

Idan zakije ganin Fatima gidan Principal zamuje kamar munje wajenta, kinga zata sa akira Fatima tazo gidanta batare da Farida ta sani ba. Na Faisal kuma me sauki ne, domin babu wanda ze fada mashi kinje.

Kiyi hakuri, duk wannan abun da yakeyi na lokaci kadan ne, da yaran nan sun girma komai zezo karshe, domin ayanzu ne kawai yakeda iko dasu. Ina me tabbatar maki akwai ranar da se yazo wajenki yana rokon kisaka baki domin surika zuwa wajenshi.

Kuma banaso wannan maganar tashi ta dameki, tunda ni yayi ma magana ki bar mani komai a hannuna, domin da dan gari akanci gari. Murmushi Inne tayi tace nagode Alhaji, bansan da wane baki zan gode maka ba.

Alhaji yace kin gama mani komai, domin kin rike mani marayuna tsakani da Allah. Lokacin da mamansu ta rasu kukan da nayi hada na tunanin matar dazan aura, wane irin riko zatayi masu.

Ga sude yara nasan idan ban samu mace tagari ba shikenan rayuwarsu zata shiga matsala, kina ganin se yanzu Ansar zeje secondary, ita kuma Khairat tana primary 4, kinga ko ai za'a kwaresu idan basu hadu da marikiyar kirki ba.

Inne tace ai bakomai, kowa yarike dan wani ze samu lada me tarin yawa, bare kuma marayu, wadan da ko kansu ka shafa kana da lada. Wallahi banajin bakin ciki dan ina rike yaranka da kyau ni kuma nawa ana wulakantansu. Allah yabani ikon cigaba da kula dasu. Alhaji yace amin, kema ai kin kusa sauka. Murmushi Inne tayi.


Faisal gaba daya ya canza agidansu, idan kaga yana magana shida Fatima ne, haka idan yana dariya da ita duk wanda yazo yake denawa, tsakaninshi da Malan gaisauwa ce kawai.

Haka ma Mama gaisuwa kawai take hadasu. Fatima ma sam tadena kula kowa, duk aikin da tasan tanayi bata bari ayi mata magana, tana tashi take yin abunta. Haka idan rana tayi zataje ta tambayi Mama abinda zata dafa.

Sosai Fatima ta iya aiki da girki, domin Mama abincin safe kawai takeyi, amma komai Fatima ce keyi, tun tana nuna mata yanda zatayi har ta dena. Farida kuwa sede adafa taci, bata aikin komai se zama cikin manya.

Ko wankin da Faisal yake ma Farouk yanzu ya dena, shima Farouk din yadena bashi, kuma shikadai ne yake kula su Faisal, kasancewarshi bame son magana ba yasa ba koda yaushe yake masu magana ba.

Fahad kuwa yafi kowa rashin mutunci agidan, Malan kadai yake tsoro, amma baya daga ma kowa kafa hatta da Mama, kuma duk tafi sonshi shida Farida, kuma sunfi kowa rashin kunya.

Bayan kwana biyu Alhaji ya maido ma Malan amsar sakonshi. Sosai Malan yaji dadin abinda Alhaji yace, kuma yaji dadi daya fahimceshi, dama tunda yatura sakon yake cikin zullumi, musamman da yaga anyi kwana biyu be maido mashi da amsa ba.

Mama yakira yace dama nafada maki zan dauki mataki akan zuwan Jamila wajen su Fatima, dazu Alhaji ya maido mani da amsar sakona, kuma yabani hakuri sosai, yace besan haka abun yake ba da be barta taje ba.

Kuma yace baze kara barinta taje wajensu ba matukar shi take aure. Dariya Mama tasa tana fadin yanzu haka shima yafara gano bakin halinta, ina nan da kai ya kusa korota daga gidanshi.

Malan yace ai shima yana da yara, kuma awajenta suke, yanzu haka tafara kokarin rabasu dashi kuma wannan message din danayi mashi shine ze kara haska mashi asalin boyayyen halinta.

Mama tace ai naji dadi, kaga yanzu yaranka zasu dawo kamar da. Malan yace na manta ma ban fada maki ba, kifadama yara nan su shirya gobe zamuje Mani tunda saura sati biyu su koma, Hajiya tana maganar ban kaisu sun gaisheta ba.

Mama tace ai nima abinda naga yafi tunda de ka kusa aje aiki, kuma lokacin da zaka aje aiki Mazan ne kawai suka gama karatu, kawai da anyi hutu murika tafiya Mani, tunda kaima idan akayi hutu ba aiki kake zuwa ba.

Kaga fa tunda suka dawo basuje islamiya ba, kuma ni nafison islmiyarsu ta Mani, gara murika tafiya can, suna komawa hutu semu dawo nan, suma kansu sunfi sabawa da unguwarmu ta can.

Gashi akwai yaran da zasuyi wasa acan, kuma ni nafi yarda da tarbiyar yaran can. Malan yace ba naki taki bane, inajin tsoron su Faisal surika zuwa Mashi wajen Kakanninsu, tunda de yanzu Uwarsu ta bar garin amma akwai iyayenta ai.

Mama tace matukar kaja masu kunne nasan bazasuje ba, kuma yaushe rabonsu da garin, bama zasu iya gane gidan ba. Malan yace yanda kikace haka za'ayi, kawai ki sasu kowa ya hada kayanshi se amaidasu can, idan yaso se mubar namu tunda zamu dawo.

Cike da farin ciki Mama tace nagode. Zuwa tayi ta fadama Yaran suje su hada duka kayansu gobe zasu koma Mani. Wani murmushin farin ciki Faisal yasaki, har seda hakoranshi suka fito.

Ita kanta Fatima seda tasaki dariya, sauran yaran kuwa ihu sukasa hada tsalle. Ido kawai Mama ta zuba ma Faisal, wato yana son akoma can shima, tsaki taja aranta tana fadin kunci sa'a nima inaso murika zuwa saboda ina son garin.

***** ******

Washe gari tunda safe Mama taje yima Zulai sallama ta fada mata nan da sati 2 zasu dawo. Zulai tace kawaide kinyi mana wayau, Mama tace haba ba haka bane, kawai ina kewar gida ne. Zulai tace to Allah ya tsare, ayo mana tsarabar Mani.

Haka suka kulle gidan suka tafi, acikin mota Farida da Fahad se wasa sukeyi suna dariya, Fatima kuwa tana kusa da Faisal yana bata labarin Saleem. Se dariya takeyi, tace ai da mun koma zan fadama Lubna kuna tare da Yayanta, dama ta fada mani Yayanta yana makarantarku. Duk haushi ya gama cika Mama ganin yanda suke labari suna dariya.

Lokacin da suka isa Abba da Saddik suna kofar gida suna wasa, da gudu Abba yashiga gida yana fadin Amira fito gasu Fatima Da Yayanki Faisal. Abinci Amira takeci alokacin, ai da gudu ta tashi tayi waje, duk kiran da Mama take mata tadawo tasaka hijab amma bataji taba.

Su Faisal suna fidda kaya yaji an rungumeshi ta baya ana dariya. Fatima ce tace lah, Yaya Amira ce, saurin juyowa su Malan sukayi suna kallonsu, juyowa Faisal yayi yana dariya ya kama kafadarta yana fadin Amirata ashe kinji nazo.

Sakin baki Malan yayi shida Mama yana kallon yanda Faisal yake wata irin dariya cike da farin ciki, shi betaba ganin farin ciki akan fuskar Faisal irin na yanzu ba. Saddik ne yace Fatima angirma.

Dan kwalinta ta buga mashi suna dariya, acikinsu babu wanda ya kula su Fahad, se murnar ganinsu Faisal sukeyi. Amira tace dan Allah Yaya kada ka kara tafiya ka barni, Faisal yace bazan karaba kinji? Kai ta daga tana murmushi.

 Mama ce ta buga masu tsawa tana fadin dalla sakar masu yarinya, ko an fada maka Fatima ce da kuke ciki daya zaka rika taba ta.

Saurin sakin Amira Faisal yayi tare da hade fuska, turo baki Amira tayi tana fadin aide shima Yaya nane. Malan yace haba Hauwa meye haka? Ke bakisan yara ba, kuma bakisan yanayin da Amira take ciki ba.

Mama tace idan ita bata da hankali aishi da hankalinshi, meye amfanin riketa da yakeyi, kai dalla kuwuce yanzu mukazo zakuzo kudame mu. Hannun Amira Abba ya kama tana ta hararar Mama suka wuce, idonta har ya cika da kwalla.

Haka suka shiga da kayan ciki ran Faisal a abace. Fita Malan yayi yana fadin zanje wajen Hajiya nasan yanzu gyaran gidan zakuyi. Mama tace gaskiya kam, saboda yayi kura. Yana tafiya tasa su Faisal da Fatima su share gidan, wani kuma ya goge.

Farouk yace kai Fahad kaje ka gyara mana dakin mu ni kuma in gyara dakin Malan. Mama tace bazeyi ba, ai kanajin wadan da nace suyi aikin shine kai kuma uban iyayi zakace yaje ya maku shara. Farouk yace gaskiya Mama abinda kikeyi baki kyautawa.

Allah fa yana kallonki, yanzu kanar Fahad da Farida ba zasuyi aiki ba, kuma ai Malan yace arika sa kowa aiki. Kuma wallahi idan basuyi ba sena fada ma Malan, juyawa yayi yashige falon Malan ya fara sharewa.

Sakin baki Mama tayi tana kallonshi, yaushe yaron nan yafara rai nata? Wato yanzu bayansu Faisal yakebi kenan? Idan ko haka ne zata dauki mataki. Kallon Fahad tayi tace yi hakuri kaje ka share maku dakin.

Kaji de yace ze fadama Malan, kuma Malan zaneka zeyi, kabari zan kamashi, Fahad yace kaji Mama, to tsoronshi kikeji, nide bazan share ba, sede kishare mana. Mama tace haba Fahad, nima zan gyara mana kayan mu ne, kayi hakuri zan baka naira 100 ka kashe.

Da kyar ta shawo kanshi yatafi yaje yafara sharewa. Haka suka gyara gidan yayi fes, sannan kowa yaje yayi wanka, Malan ya aiko da cefane, haka Mama tasa Fatima ta dafa masu taliya.

Zaune Faisal da Fatima suke agidansu Amira, se wasa sukeyi, Faisal da Amira kuma suna gefe ta dauko mashi littattafanta yana dubawa, sosai yaji dadi ganin yanda Amira ta iya rubutu, kuma tana karanta duk abinda ya rubuta mata.

Maman Saddik da Baba sunji dadin dawowar su Faisal, dan kullum Faisal yana gidansu suna wasa da Amira, kuma yana koya mata karatu, da Maman Saddik ta fada mashi za'a kai Amira Secondary sosai yaji dadi.


Mama sosai takejin haushin zuwan su gidansu Amira, tana so ta fada ma Malan kuma tana tsoron kada yagane tana jin haushinsu ne, hakan yasa ta kyalesu, sede Fatima bata cika zuwa ba, sede idan Mama ta fita, dan ko taje se Mama tasa ankirata tasa ta wani aiki.

Sosai su Momyn Teemah sukayi mamakin girman Faisal da Fatima, domin sunje har gida sun gaishe su, har seda Momyn Teemah ta kira Inne ta hadasu suka gaisa. Ana bama Fatima wayar ta sama Inne kuka.

Duk abinda akayi masu seda tafada mata, hada dukan da Mama tasa Malan yayibl masu seda tafada mata, kuka sosai takeyi tana fadin dan Allah Inne kizo kidauke ni. Itama Innen kuka takeyi.

Haka tarika lallashin Fatima kuma ta fada mata yanda Abbansu yace, kuma tace kada takara bama Farida komai, kuma kada tabari tasan tana zuwa. Fatima tace bazan fada mata ba. 

Faisal ne ya karbi wayar, shima seda yayi kuka, Inne tace kanaji ko, kada ka kara fada da Mama, itama Mamanka ce tunda tana kula daku, kaga Farouk da yake maka kirki bazeji dadi ba idan kana ma Mamanshi rashin kunya.

Duk abinda tasaka karikayi, kuma kadena rai nata, wata rana komai ze wuce, kayi hakuri kaji? Faisal yace to. Nan shima tafada mashi abinda Abbansu yace, haka suka yita fira, domin itace ta bugo.

Bayan sun gama gaisawa sukayi sallama dasu, godiya tayima Momyn Teemah. Abinci tasa masu sukaci sannan suka tafi. Suna komawa suka iske su Farouk zasuje gaishe da Hajiya.

Haka Malan yace sutafi gaba daya su gaisheta. Sosai Hajiya taji dadin zuwansu, Mama tace ai Hajiya daga yanzu nan zamu rika hutu. Hajiya tace ai haka yafi, amma ace ya daukeku gaba daya wai se dogon hutu sannan zakuzo.

To ya gidan, kuma ya hakuri da yara? Tabe baki Mama tayi tana fadin Hajiya kinsan ai yanda zama da Dan da ba naka ba yake, sede hakuri kawai, amma inashan wahalarsu Faisal. Kwanakin baya har naushi na yayi a ido.

Kalli wajen har yanzu be gama washewa ba. Hajiya tace shi Faisal din? Mama tace wallahi kuwa, ai da gashi har Fatima sun rai nani, ko aiki na sasu basayi. Hajiya tace ja'irai masu hali irin na Uwarsu.

Kunnan Faisal dana Fatima takama ta murde tana fadin, idan kuka kara mata rashin kunya se nasa Malan ya maidoku wajena, se inga koni zakuyi mani rashin kunyar. Mutanan banza, ko kunyar Diyanta bakwaji kuke mata rashin kunya.

Seda Fatima ta fara kwalla sannan ta sakar masu kunnan. Haka Mama tayita fada mata karya da gaskiya tana kara batasu awajenta. Sosai ran Hajiya yabaci, haka ta yita bama Mama hakuri, kuma tace idan suka kara ta kirata ta fada mata.

Zatasa Malan ya maidosu wajenta. Haka suka wuni aranar, su Farida se wasa sukeyi, shiko Farouk yama tafi wajen abokanshi, Faisal da Fatima jisukayi kamar sutafi, dande Malan yace zezo ya daukesu, ko abincin da aka basu beda wani yawa.

Lokacin da Malan yazo daukarsu haka Hajiya tayi mashi fada akan yarika tsawatar ma su Faisal akan rashin kunyar da suke ma Mama, kuma tace idan suka kara ya maidosu wajenta. Malan yace ayi hakuri Hajiya, nima na nadauki mataki, kuma bazasu kara ba. Haka sukayi mata sallama ta bama yaran Mama kudi tana fadin bazan ba marassa kunya ba, seda Malan yaji ba dadi abinda Hajiya tayi, haka suka tafi.

****** *****

 Lokacin da hutu yakare haka Malan yayima kowa provision, har Faisal seda ya siyama wasu abubuwan kasancewar shi basa zuwa da komai na abinci amma seda ya siya mashi sabulun wanka dana wanki da omo, mai hada turare da maclean.

Sosai Fatima da Faisal suke cikin farin cikin komawa warsu, dan Fatima duk ta rame, shima Faisal duk ya yi baki ya rame. Amira kuwa tasha kukan tafiyar Faisal, shima seda yayi hawaye, dan yanda Amira take kuka.

Faisal ya rigasu tafiya  dan tare suka tafi da Nura, Baban shine yakaisu Katsina,  seda Fatima tayi kuka daze tafi. Su Fahad se dariya suke mashi dansu se ranar lahadi suke komawa, su kuma asabar shida su Fatima.

Kafin Malan yaje yadawo haka Mama ta kwashe kusan rabin kayan Fatima ta karama Farida, kuma ta sama Farida sauran abubuwan data siya mata, babu wanda yasan ta kwashe dan Fatima tana dakinsu kuma sun gama hada kayansu sun kulle komai.

A cikin jakar Farida Mama tasa mata dubu daya tace kada tabari Malan yasan ta bata idan ba haka ba baze kara mata ba. Haka Malan yazo suka saka kaya amota, seda Mama ta rakosu sannan ta bama Fatima dari 200 tace gashi ku kara ko, kema Farida ga taki Dari biyun, se ku kara da wanda Malan ze baku, adage ayi karatu kunji.

Sosai Malan yaji dadi kuma yayi mata godiya, haka suka tafi Farida tana kuka. Lokacin da suka isa malan ya basu dubu dai dai kuma yayi masu nasiha akan su kara dagewa. Kallon Farida yayi yace kada kimanta da addu'ar dana baki, kullum kirikayi duk abibda kikeji zaki dena, kuma kokarinki ze dawo.

Kallonshi Fatima tayi, wato Farida kadai ze bama addu'a banda ita, kwallace ta cika mata ido, shi kuma Malan anufinshi saboda yana tunanin anyi mata asiri. Ita ko Fatima se ta karajin haushin Malan.

Haka yayi masu sallama yatafi, da gudu Lubna tazo ta rungume Fatima tana dariya, itama Fatimar dariya tayi tana fadin ashe kin dawo? Lubna tace tun dazu. Tsaki Farida tayi ta dauki kayanta tana fadin aikin banza.

Zinatu ce tazo tana fadin ga kawata, rungume juna sukayi suna dariya, haka suka nufi hostel. Lubna ce tace Fatima amma rashin lafiya kikayi ko? Kwallar da Fatima take boye wace ta zubo.

Kamata Lubna tayi tana fadin mutafi kada aganki kina kuka, haka suka dauki kayan suka tafi........... Duk abinda Mama tayi masu seda Fatima ta fadama Lubna, sosai Lubna taji tausayin Fatima, har seda tayi mata kwalla.

Hakuri tayita bata, haka suka fara fiddo kaya dansu jera a loka. Tsayawa Fatima tayi tana kallon kayanta, fashewa tayi da kuka tana fadin wallahi ba haka Malan yasiyo mana ba. Mama ce ta kwashe mani kaya, ai dama tunda tace intafi daki nasan kayana zata kwashe.

Lubna tace kiyi hakuri, taje tayi ta kwashewa, kinga wannan jakar, Inne ce jiya tazo takawo mani tace inkawo maki, shima Yaya Saleem ta bashi ya kaima Yaya Faisal. Dariya Fatima tasa tana fadin dagaske? Lubna tace wallahi kuwa, kuma tace kada kibari Farida tasan ankawo maki.

Fatima tace kai nagode ma Inne na, jinake kamar in watsar da wadan nan kayan ma. Dariya Lubna tayi tace ai seki watsar. Zama Fatima tayi tace ashe Yaya Saleem da Yaya Faisal abokai ne? Lubna tace emana nima shine yake fada mani.

Kullum seya dameni wai inbashi labarin shagwabarki. Dariya Fatima tasa tace lallai ma nice me shagwabar, Lubna tace sosai ma, kawai bakisan kinayi bane. Ga jakar sweet ma yace inkawo maki.

Fatima tace haka fa yabama Yaya Faisal yakawo mani da akayi hutu, nima idan zaki tafi zan siya mashi wani abu. Lubna tace to tashi mu hada kayan.

***** *****

Haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya, sosai Fatima da Lubna suke maida hankali a makaranta, lokaci guda Fatima ta maida jikinta, kuma yanzu babu ruwanta da Farida.

Koda akayi visiting Fatima bata damu da abinda Mama takawo mata ba, bayan kwana biyu kuma Inne da Alhaji suka zo gidan Principal, haka ta aika aka kira Fatima Da Luban, sosai Fatima tayi murnar ganin Inne.

Haka suka sha fira kuma takawo mata kaya masu yawa hadasu Inner wears, haka tabata kudi, Fatima takara bata wasu tace tasa mata a asusu, haka suka dauki kayan sukayi masu sallama suka tafi daki.

Tun daga wannan rana Inne take zoma Fatima Visiting a boye, kuma Farida bata gane ba, hankalin Inne yanzu ya kwanta dan tana ganin yaranta, kuma tanajin dadi ganin Fatima se girma takeyi tana kiba.

Fatima tafi jin dadin rayuwar makaranta, har bataso ace an kusa hutu, domin tanajin dadi sosai. Farida kuwa bata karatu, sede wasa da maza, gata da son aikama wani tana sonshi, yan ajinsu duk sun ganeta, idan suna zaune da kawayenta komai tayi masu labarin aure. Zinatu ce kawai take biye mata sunayi.

**** ****


A yaune Inne ta haihu, inda tasamu diya mace me kyan gaske, sosai Alhaji yayi farin cikin samun diya mace, dan yanason yara mata, su Ansar ma se murna sukeyi, ba kamar Khairat, dan tasamu abokiyar wasa. Haka Inne ta buga ta fadama su Salamatu.

Ranar suna yarinya taci sunan Amatullah, dan Alhaji yace yanason sunan, sosai Inne tayi mutane, su Momyn Lubna sune akan gaba, dan zumuncinsu yakaru sosai. Su Momyn Teemah da Salamatu ma duk sunzo.

Taro yayi kyau, Inne takara zama babbar Hajiya, tayi kyau takara gogewa tazama 'yar birn, idan ka ganta ba zakace Innen daka sani bace ada, dan yanzu ta waye sosai.

Kamar yanda Alhaji yace idan ta haihu ze biya masu makka kuma ze koya mata mota, haka yasa aka fara koya mata mota lokacin da tayi arba'in,  kuma yace zasuje Makka tunda saura wata bakwai atafi, kafin lokacin Amatu takara girma, seta ajeta idan ta dawo tacigaba da shayar da ita.

***** *****

Abubuwa da dama sun faru, yara sun kara girma, Fatima tazama yan mata, tagama horuwa da aiki yanzu sam bata bari Mama tayi mata fada, sede idan Mamar taso yin fadan ne, Farida ta zama kwarkwar, gashi abun bakin cikin anyi mata repeating yanzu Fatima tana gabanta.

Duk tayi sanyi bata da sauran rawar kai a cikin kawaye, hatta da Zinatu yanzu ta wuceta. Lokacin dasu Faisal sukayi JSCE da za'azo ma Lubna visiting seda Saleem yazo, hakama Faisal seda Malan yace su shirya shida Fahad atafi dasu.

Sosai sukayi murnar ganin junansu Saleem da Faisal, Fahad kuwa sakin baki yayi yana kallonsu dan ko magana basayi da hausa, lokacin dasu Fatima sukazo sosai tayi murnar ganin Faisal.

Saleem kuwa ido ya kura mata, itama shi take kallo, Lubna tace Yaya Saleem wato baka ganni ba ko? Dariya yayi yana fadin am sorry Lil sis, ya makaranta? Faisal yace bata amsawa, kyaleshi Lubna zo kifada mani labarin makarantar ku.

Duk maganar da sukeyi da turanci sukeyi, Mama da Farida da Fahad sun zama yan kallo, sosai haushi ya gama kama Mama, dan tunda Fatima ta gaisheta suka ware dasu Faisal.

Farida kuwa kuka tayi ta mama tana fadin acanza mata makaranta, Mama hakuri tabata tana fadin kinsan de halin Malan, baze taba canza maki ba, gara ki kara dagewa, yanzu kina ganin se Fatima ta rigaki gamawa. Narasa meke damunki keda Fahad, so kuke ayi mani dariya.

Haka ta yita bata hakuri, lokacin da zasu tafi seda Fatima tayi kuka, shima Saleem seda idonshi yayi ja, wani zobe dake hannunshi yabama Fatima, su Faisal da Lubna se tsokanarsu sukeyi. Momynsu kuwa se dariya take masu, haka suka rabu cike da kewa.

Bayan koma warsu SS1 ne Fahad yafara biyema abokan banza, kuma anan ne suka fara koya mashi shan taba, tun yana sha yana kwarewa har yasaba, daga taba se kuma abun yaci gaba, kullum da dare se sunje bayan makaranta sunyi shaye shayensu kafin su dawo.

Lokaci guda ya kware, kuma ya kara zama dan iska, lokacin da akayi hutu Mama tace wai Fahad me yake damunka, duk kayi baki karame? Kallonta yayi yace mefa, kawai wahalar makaranta ce, haka ta dage tana bashi abun dadi dan yasamu yaciko.

Gashi yanzubsam yama dena kokari, kuma Malan yadena masu fada akan rashin kokari tunda Mama tace asiri akayi masu, hakan yasa ya zuba masu ido, duk zasu koma seya kawo ruwan addu'a yace surika sha, sede baya ba su Faisal, saboda suna kokari, besan kuma hakan da yake ba kara hura wutar kiyayya yake azuciyarsu, dan sun dauka bayaso suyi kokari ne shiyasa yake bama sauran.

Kullum idan Fahad yafita baya dawowa da wuri, kuma da dare ma seyayi shaye shayenshi sannan yake shigowa gida, gashi hada dauke dauke yakeyi, duk abinda yakeyi babu abinda Faisal be sani ba.

Shiyasa yanzu yake lallabashi, dan abu kadan yake harzuka Fahad, har da Farouk dambe sukeyi, Mama tarasa inda Fahad yasamu wannan zuciyar. Faisal yaso ya fadama Farouk dan yanzu suna mutunci sosai, se kuma yaji tsoron kada Mama tace sharri yake mashi.

Dan shi yanzu Farouk babu abinda yasa agaba kamar dinkin hularshi, sosai yazama gwani a dinkin hula, kuma da yayi saidawa yakeyi, sosai yake samun riba, kuma ba laifi yanzu yana maida hankali dan tun wani lokaci da Faisal yabashi shawara akan yarika maida hankali idan yasamu yagama karatun se yayi dinkishi sosai.

Tun daga lokacin Farouk yake maida hankali, kuma yana zuwa masallaci dan inde suka zauna suna fira da Faisal to seya yimashi wa'azi cikin dabara, dayake Farouk beda girman kai haka yake daukar duk abinda Faisal yake fada mashi. Amma tsakaninshi da Fahad fada ne kawai, dan yanzu Fahad sosai yakejin haushinsu.

Shakuwar Amira da Faisal ta wuce wasa, domin yanzu Amira takara girma, yanzu tana JSS3 itama, kuma takara dagewa wajen karatu, sede har yanzu akwai yarinta atare da ita saboda yanayin datake ciki.

Amma ita da Faisal abun ba'a magana, sosai yake sonta, duk abinda yasamu ita da Fatima yake bamawa, kuma ga Lubna itama sun shaku da ita, Baban Saddik har cemata yake Matar Faisal, itako tayita dariya.


Inne kuwa yanzu ta zama Hajiya Inne, motar datake tukawa kanta abun kallo ce, duk da mijinta ya aje aiki amma yana da hanyar samu sosai, ita kanta shagon saida kaya ya bude mata yazuba mata kaya kuma ya mallaka matashi, haka tasamo wani dan Uwanta a Mashi yake tsare mata, sosai tayi arziki, 

Kuma ba ta manta da kawayenta su Salamatu ba, ita da Momyn Lubna sun zama tamkar yan gida daya, Ansar da khairat ma anzama manya duk sunje secondary, Amatu kuma tana nursery, sede daga ita Inne bata kara haihuwa ba.

Wata rana da Momyn Teemah ta haihu lokacin ana hutu, haka Inne ta sako yaranta amota sukazo suna, ba karamin kyau sukayi ba, lokacin da tashigo cikin unguwar kowa seda yabita da kallo. 

Maman Sultan da Mama sun taho zasuje wajen sunan su kaga tsayuwar mota.Tsayawa sukayi suna kallon wanda ze fito. Inne tana fitowa Salamatu ma tafito daga gidanta.

Cike da farin ciki tace ga Hajiya Inne oyo oyo, saurin kallon Inne su Mama sukayi, tabbas itace, ido Mama ta tsura ma Inne, tanajin zuciyarta kamar zata fashe, Fatima da Amira suna zaune suka hango Inne, ai da gudu suka rugo suna murna.

Fatima tana zuwa Inne ta rungumeta, Amatu tana rike da hannun Khairat se dariya takema Fatima, dan sun saba, da ita. Daukar Amatu Fatima tayi tana mata wasa, Khairat ma ta rungume Fatima.

Su Faisal ne da Abba suka karaso yana ta dariya, Ansar ne ya rungumeshi yana fadin Yaya ina wuni? Faisal yace lafiya lau Ansar ina Abba? Yace yana gida.

Takawa Inne tayi har wajen su Mama tana murmushi, Salamatu tana binta abaya, kallonsu tayi tana fadin Maman Farida ina yininku? Maman Sultan ce ta amsa da kyar, Mama kuwa mamaki da haushi sun hanata, magana.

Murmushi Inne tayi ta juya tana fadin Salamatu muje wajen sunan ko, haka ta juya tana takawa cike da takama. Mama kuwa kasa shiga gidan sunan tayi, haka ta juya takoma gida kamar zatayi kuka saboda bakin ciki.

Kalli yanda Inne ta koma, itako gata nan yanzu kaya masu tsada ma bata dasu, tashin hankalin Farida da Fahad ya hanata yin kiba. Haka ta koma gida tana me cike da bakin ciki.




**** ****

BAYAN WANI LOKACI

Farouk yagama makaranta inda su Fahad suka zana jarabawar shiga aji shidda, dansu makarantarsu se wanda yaci jarabawa yake shiga aji shidda. Kuma akaci sa'a Fahad baci ba, hakan yasa aka mashi repeating.

Ya dawo mate din  Fatima, dan itama Farida tun suna aji 2 akayi mata repeating, yanzu Fatima tana gabanta, duk da lokacin Mama taji haushi haka nan ta hakura tunda de tasamu ta rufe bakin malan da cewar Inne ce tayima yaranta asiri, kuma shima ya yarda da hakan.

Lokacin da suka gano jarabawar Fahad kuka yayi tayi yana fadin baze koma makarantar ba.Malan yace aiko be isa ba seya koma, dama ai nafada maka. Kallonshi Malan ya karayi yana fadin wai ni tsaya ma, baka da lafiya ne? Fahad ya dago jajayan idonshi yace lafiya kalau.

Malan yace amma kalli bakinka, duk yayi baki, kaima kanka kayi baki kuma ka rame.. Fahad yace kawai nadanyi zazzabi,ne. Malan yace ni kake fadama kawai? Mama tace haba Malan kayi hakuri mana, kaima daga gani ai kasan  bayada lafiya, kallifa yanda yarame.

Malan yace to ai seku shirya mukaishi asibiti. Mama tace, tashi kaje Fahad, haka yatashi yana wata 'yar iskar tafiya yafita. Malan yace nifa ina zargin yaron nan. Tashi Mama tayi tana fadin a'a Malan kada kafara fadar irin wannan maganar akan yarana.

Me kake nufi da kana zarginshi? Nifa banaso kana ma Fahad haka, na lura da dadewa kafara tsanarshi acikin yaranka, to wallahi zamu fara batawa matukar kana mani haka, fita tayi tare da bugo kofar.

 Murmushi Malan yayi yace Hauwa kenan, kowa yaga Fahad yasan halin dayake ciki, amma tunda bakiso infadi gaskiya nabarki dasu, na dade da sanin kina goyon bayan yaranki, amma tunda haka kikeso zan sa maki ido. Allah ya shirya.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[4/4, 2:30 PM] nabilalady5: 🏡🏡 A WANI GIDA🏡🏡
          😭😭😭

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

        Part 60 ⏩ 65


Kwance Mama take a dakinta tun bayan fitowar ta daga wajen Malan, zuciyarta se zafi take mata. Wannan wane irin bala'i ne haka? Yanzu Malan yadena kula da yarana kamar yanda yakeyi ada.

Tunda Inne tabar gidan nan soyayyar da Malan yake ma yarana ta fita daga zuciyarshi. Kenan saboda zaman Inne agidan yake son yarana? Meyasa ma nasa yasaki Inne? Gashi yanzu ita ta cigaba ni kuma ina nan kullum se kara tsotsewa nakeyi.

Gaba daya tafiyar Inne daga gidan nan haske ne akan yaranta, ni kuma duhu ne ya mamaye ni da yarana. Shi kanshi Malan yanzu arzikinshi ba kamar da ba. Amma kalli irin motar da Inne take hawa.

Kalli kayan jikinta, gashi ta rike 'ya'yan mijinta tamkar itace ta haifesu. Yaranta sun zamo abin so ga kowa, kansu ya bude yayin da kan nawa yaran ya toshe gaba daya. Duk kokari irin na Farida da Fahad be hana anyi masu repeating ba.

Nida naso ace yaran Inne ne ja baya akaratu, lokacin da  zasu fara karatun jami'a yarana sunyi nisa alokacin kuma gashi Malan ya aje aiki. Se gashi  kuma anyima yarana repeating, gashi Faisal gwamnati ce take daukar nauyin karatunshi.

Ita kuma Fatima zata riga Farida gamawa, nasan duk sauran kudin Malan akansu ze kashe, tunda zasu rigasu shiga jami'a. Allah na rokeka kasa Farouk shi yaci jami'a, koshi kadai nasamu yayi karatu nasan seya riga Faisal gamawa.

Idan yasamu aiki nasan ze kula da sauran. Hawaye ne suka zubo mata, tabbas maganar Malan gaskiya ce, yanayin Fahad ya dade da canzawa, narasa meke damunshi, gashi yanzu duk abinda na aje se inga andauke, wanda ada ba haka ake mani ba.

Kadde ace Fahad yafara sata? Saurin girgiza kai tayi tana fadin, ina, acikin yarana babu barawo, domin duk dangin mu babu barawo. To kode yafara shaye shaye ne? Kara girgiza kai tayi tana fadin hakan ma baze yuwu ba.

Domin Fahad tun yana karami baya son warin koda sigari ce. To meya samu Fahad? Tabbas nasan akwai sa hannu acikin rayuwarshi, kuma koma wanene senayi maganinshi, kuma daga yau duk abinda za'a kawo na kayan dadi nashi seyafi yawa.

Bazan zauna ina kollo yarona ya lalace ba, duk yayi baki yarame, tabbas kafin ya koma sena ginashi. Hannu tasa ta goge idonta ta tashi tana kwalama Farida kira.


Shigowa tayi tana fadin kai Mama, wannan kira kamar kin makance. Mama tace wato nice ma na makance ko? Dariya Farida tayi tana fadin ai naji kina ta kwala mani kira ne. Mama tace nasan Fatima tana can gidan su Amira.

Jeki dora farar shinkafa idan ta dawo setayi miya. Farida ta turo baki tana fadin lallai ma, ai kin sande itace take aiki taya zakice inje in dora abinci? Mama tace Farida kinga yanzu kin girma, inaso kifara koyon aiki domin wata rana aure zakiyi.

Farida tayi murmushi tana fadin ai kamar kin sani, muna gama makaranta aure zanyi nida kawata. Zaro ido Mama tayi tana kallonta, Farida tace kinsan yanzu samarina nawa? Su 2 ne, damma suna tsoron Malan shiyasa basu taba zuwa gidan nan ba.

Mama tace rufa mani baki, ke yanzu har kinsan maganar aure? To bari kiji in fada maki, yanda kowa zeyi karatu a gidan nan kema sekinyi karatu. Haba Farida, so kike bakin cikinku ya kashe ni? Kina ganin yanzu shima Fahad yadawo baya.

Kema kin koma baya, Farouk ne kawai acikin yarana yagama Secondary, so kuke wadan can yaran su zama wasu manya agidan nan, ga uwarsu ta zama babbar Hajiya, suma suzo suyi kudi, shikenan ni kuma na zama baya kenan.

To kima cire tunanin aure aranki, matukar ina raye se kinyi karatu kamar kowa. Kuma daga yau zan raba maku aiki keda Fatima, idan ma bazaki iya shara da wankin bandaki ba, wannan ba matsala bane.

Nide fatana ki iya girki, sauran ko baki iya ba badamuwa domin akwai masu aiki, amma shi girki kyan mace ta iyashi, idan na dare kikeso to, idan kuma na rana zakiyi duk daya seki zaba.

Farida tace Allah Mama bazanyi ko daya ba, tunda de Fatima takeyi kawai ki barta ta cigaba, Mama tace haba Farida, meyasa bakison farin cikina? Kuka Farida tasa tana fadin ai dama yanzu naga kindena son mu.

Gashi Malan kullum seyayi mana fada, se wadan can kawai yakeso. Kuka sosai Farida tasa tana dire dire. Jawota Mama tayi tana fadin yi hakuri, ni na isa ince bana sonku? Kawai inaso in koya maki girki ne, tunda bakiso shikenan.


Je ki kira mani Fatimar tazo ta dora, share hawayenki, bakida mesonki sama dani. Murmushi Farida tayi tace anjima zanje gidan 'yar makarantarmu daga can zanje ingaishe da Hajiya. Mama tace to jeki kira mani Fatima an jiman seki tafi.


Abinda Mama bata sani ba shine, inde Farida ta tafi wajen 'yar makarantarsu da gidan Hajiya to haduwa takeyi da wani saurayinta Salisu, yana da shagon provison, kuma hade yake da dakin da yake kwana.

Tun wata rana da Farida taje siyen sukari ashagon suka hadu, tun daga nan suke soyayya, kuma Farida tana bala'in son shi, saboda yace ze aureta, ita kuma babu abinda takeso kamar maganar aure.

Sanin halin Malan yasa be taba zuwa gidansu ba, sede tayi dabara taje shagonshi, wani lokacin ma dakinshi suke shigewa suyi fira, sosai Farida ta sake dashi, duk lokacin da taje haka yake gama tabeta ya kawo kudi da kayan zaki ya bata.

Haka take boye kudin tace ma Mama sauran kayan agidan kawarta aka bata. Ta saba da abubuwan da yake mata sosai, hakan yasa duk bayan kwana 2 setaje wajenshi, daga can seta wuce wajen Hajiya dan kada tace bata zuwa.

Kuma sosai Hajiya take jin dadin zuwan da Farida takeyi, har cewa take ita da Fahad sune yan gidanta, domin shima da gidanta yake fakewa yatafi yawon shaye shayenshi.

***** *****

Bayan sun koma makaranta first term, Faisal na SS 3, Fatima da Fahad kuma SS 2, yayinda Farida take SS 1, ba laifi Fahad ya ciko, yayi kiba kuma lokacin da zasu tafi seda Malan ya kara mashi fada sosai akan rashin maida hankalin da bayayi, kuma yace idan har aka kara mashi repeating to ze maidoshi Day.


Haka suka tafi Fahad kamar ze fashe, Mama duk bataji dadin abinda Malan yayi mashi ba, haka ta dauki fushi da Malan dan yanzu haushin shi takeji sosai, duk wata kissar da takeyi ada yanzu babu, abu kadan se fada.

Shi Malan ma dariya take bashi, shiyasa baya biye mata, idan kuma ta kureshi haka zeyi mata tass, dan shima Malan akwai fada, sanin halinshi ne yasa take jin tsoron yi mashi wani abun, koya bata mata rai ma sede ta dauki fushi dashi, idan ta gaji kuma ta sauko.

Yanzu gaba daya Malan ya canza, baya ma yaranshi fada, babu abinda yake fata kamar ya dedeta tsakaninshi dasu Faisal, dan ya dade da gano tsantsar tsanarshi a idanuwansu, sede har yanzu be yarda cewa ba Inne bace ta rabashi da su ba. 

Haka sam yadena ma yaran Mama fada, ya kyalesu kamar yanda bataso yana masu. Kuma har yanzu yaki barin su Faisal suje wajen Inne, suma kuma sun dena mashi maganar, domin basu da damuwa tunda suna ganinta, shi kuma Malan ya dauka sun fiddata daga ransu.

Jarabawar su Farouk ta fito, ba laifi yaci, sede be samu English ba, gashi mark dinshi na JAMB be kai ya tafi jami'a ba, kuma duka subject 5 yaci, Math, Biology, Geography, Hausa se islamic.

Sosai Mama taji haushin rashin samun mark din daze tafi jami'a, samun Malan tayi tace abarshi zuwa shekara me zuwa se ya kara sake JAMB din kuma ya nemi English idan yaso seya tafi jami'ar.

Murmushi Malan yayi yace kina da tabbacin shekara mezuwa zeci duka abinda kikace? Mama tace amma de kasan ai Farouk ba jaki bane, duk da banso ya gama karatu tare da kannanshi ba, amma dole inyi hakuri ya sake jarabawa tare da Faisal.

Malan yace to kimayi addu'ar yasamu direct a makarantar dazan samar mashi, domin tunda naga beci JAMB sosai ba na siya mashi form din Isa Kaita Collage Dutsinma yaje yayi N.C.E, kinga yanzu beci English ba.

Kinga kuwa basa bama mutum direct N.C.E se yana da Maths and English, zanje inji idan zasu daukeshi, idan kuma bazasu daukeshi ba sede yayi PRE N.C.E.

Mama kamar zatayi kuka tace kasan Allah, Farouk bazeje wanan makaranta ba, makaranta kamar gidan biki, duk wanda yataso se kaji yace can zeje, gaskiya gara ya hakura yayi zaman shekara guda, zuwa wata shekarar se yasake jarabawa yatafi jami'a.

Tashi Malan yayi yana fadin, idan ke kike da iko dashi zaki iya hanashi tafiya, kuma wallahi iname tabbatar maki matukar Farouk betafi wannan makarantar ba, wallahi bazan kara nema mashi wata ba.

Fita yayi yana masifa. Kwallace ta cika idon Mama, Farouk kuwa da yake tsugunne yayi shiru yana sauraronsu. Mama tace Farouk kana jina ko? Duk yanda Malan zeyi kada ka amince da wannan makarantar.

Idan ka nuna kanajin tsoronshi shikenan an maidaka baya, kai ne babba agidan nan kai yakamata ace anfi daukakawa amma yanzu ace wai waccan banzar makarantar zaka tafi. Ai ko Fahad da kafi kokari bazanso yaje can ba.

Dago kai Farouk yayi yace gaskiya Mama nide zan tafi kawai, koma menene nine na jama kaina, Allah yabani kokari amma na tsaya biyema abokai muna shiririta. Da ace na dage nasan zanci duka jarabawata.

Babu amfanin inzauna jiran wata shekara, domin banida tabbacin zanci jarabawar dazan sake,nide kiyi hakuri kawai zantafi. Hannu tasa ta daukeshi da mari tana huci, hannu Farouk yasa ya dafe kuncinshi.

Mama tace tunda haka kace se kaje katafi, kuma naira 1 tawa bazata kara ciwo akanka ba, tunda yanzu kaima ka koma bayan Malan da wadan can banzayen yaran sekaje kayi tayi,wata rana kai ne zakayi kuka da idon ka.

A lokacin da Fahad da Farida zasu tafi jami'a kai kuma sede ka kare da alli kaga kayo gadon ubanka. Tashi kabani waje. Mikewa Farouk yayi yafita yana kuka. Duk abinda sukeyi Malan yana jiyosu.

Har Farouk yakai kofar gida Malan ya kirashi, sosai yaji tausayinshi, hannunshi yakama suka bar gidan. A cikin mota Malan yace Farouk duk naji yanda kukayi da Mamarku.

Kada kalamanta su tsorata ka, kuma tunda yanzu ka gane kuskurenka inaso kasani lokacin gyara baya kurema mutum har se mutuwa ta riskeshi, kuma kai namiji ne, kayi hakuri da duk abinda ze zo maka arayuwa.

Kada ka dauki wannan karatun da zakayi da wasa, kuma kada ka rai nashi, idan ka dage kayi karatun kana cikinyi ma zaka iya sake jarabawa ka nemi English din, kaga duk lokacin daka gama karatunka ko kana aiki ne zaka iya tafiya ka karo karatunka.

Shi karatu da kake ganinshi ba'a rai nashi komin kan kantarshi, kuma inaso kadage idan kashiga makarantar domin ka gyara kuskurenka, inaso kadawo da kokarinka na da. Farouk yace insha Allah. Malan yace Allah yayi maka albarka. Yace amin.

**** *****

Cikin sa'a Farouk yatafi makaranta inda suka bashi Pre N.C.E ze karanci Biology/Geography, haka Malan ya shiryashi babu abinda be sai mashi ba, Mama kuwa ko sisi bata bashi, da kyar ma tace Allah ya bada sa'a, haka yatafi yafara karatunshi.

Sosai yake maida hankali wajen karatu, kuma yana dinkin hularshi, idan yagama ya kaima Malamai, cikin lokaci guda Malamai suka sanshi dan Farouk ya iya dinka hula, sosai yake ciniki a cikin makaranta har ma da wajen makaranta.

Kuma acikin aji sosai yake dagewa, duk abinda akayi masu baya bacci seya karantashi, gashi yanzu yana son addini sosai, sam baya wasa da sallah.

Wata rana sunje cikin gari shida wani abokinshi Hamza da yamma, yaje siyo kayan dikin hularshi, haka suka taho akasa se sauri sukeyi dan ankusa magriba, da yake ranar asabar ne babu class.

Ta wajen makarantar su Fahad suka biyo dan babu nisa daga makarantarsu zuwa tasu. A gefen katangar makarantar sukaga wasu 'yan makaranta kusan su biyar a jikin katangar makarantar, hayaki ne kawai yake tashi daga inda suke.

Hamza ne yace dan Allah Farouk kalli wadan can kamar ba 'yan makaranta ba, ace wai yaro tun yana secondary ya bude hun hunshi da hayaki, zuwa gaba kuma me kake tunanin zasu zama.

Juyawa Farouk yayi danshi bema kallesu ba. Karaf idonshi ya sauka akan Fahad ya daga wata farar takarda daya kunna yana zuka yana fesar da hayakin sama se daruya suke mashi.

Murtsike ido Farouk yayi domin ya tabbatar da abinda idonshi ya gane mashi. Tabbas ko a amafarki yaga Fahad ze iya ganeshi, wasu hawaye ne yaji sun zubo mashi, Hamza yace Farouk lafiya de? Hannun Hamza Farouk ya kama suka nufi inda su Fahad suke.

Daga sama Fahad yaji muryar Farouk, dede lokacin ya zuki wiwi dinshi, ido yazaro lokacin da sukayi ido biyu da Farouk, zumbur ya mike tsaye, kwarewa yayi hakan yasa hayakin yarika fitowa daga bakinshi.

Saurin wurgar da sauran wiwin yayi yana kara kallon Farouk, sauran abokanshi ma duk suka mike.  Kwalla ce kawai take fita daga idon Farouk, Hamza ne yace wai Farouk ka sanshi ne?  Share idonshi yayi yace Fahad din gidammu ne.

Cike da mamaki Hamza yakara kallon Fahad din. Fahad cikin sanyin jiki yace Yaya? Girgiza kai kawai Farouk yayi ya juya baya yana fadin ashe halin da kasa kanka kenan Fahad? Dama na dade ina zarginka ashe zargina gaskiya ne.

Ka cuci kanka, kuma kanka zaka lalata ma rayuwa, tun kana yaronka zaka bata hun hunka da hayaki. Cikin kuka Fahad yace dan Allah Yaya kada ka fada ma Malan. Murmushi Farouk yayi yace Malan kadai kake tsoro ko? Baka tsoron Allah.

Kuma baka tsoron lafiyarka. Shikenan, bazan fadama kowa ba, duk abinda kayi dan kanka. Hamza muje anfara kiran sallah. Fahad yace Yaya dama anan kake? Farouk yace E, kuma ka tabbatar ka koma makaranta.

Juyawa sukayi suka nufi makaranta, zuciyar Farouk kamar zata fashe wai Fahad ne yake shaye shaye? Dama yasha zarginshi akan hakan, dan wani lokacin idan yadawo da dare se yarika jin warin sigari ajikinshi.


Hamza ne yace dan Allah Farouk kada kabari wannan abun ya dameka, tabbas nasan akwai ciwo,amma hakuri shine zefi, kuma kamar yanda kace ba zaka fadama Malan ba, wannan ba shawara bace.

Domin ba'ayin shiru a irin wannan yanayin, Fahad yaro ne, idan har ba a dauki matakin hanashi wannan shaye shayen ba to tabbas idan ya girma abun zefi haka. Gara kabata dashi akan kace zaka rufa mashi asiri dan yaji dadi.

Farouk yace ina tsoron yanda Malan ze dauki maganar ne, Malan yana da zafi, kawai zan fadama Mama nasan zata iya shawo kan matsalar. Hamza yace amma Malan zefi yimashi ta zafi akan Mama.

Farouk yace baka san halin Malan bane, kawai kabari zan fadama Mama. Hamza yace to Allah yasa ya gane, kuma Allah ya shiryeshi. Farouk yace amin. Haka suka nufi makaranta.

Fahad kuwa gaba daya hankalinshi yatashi, tsoro yake kada Farouk yafadama Malan, wani abokinshi ne yace haba abokina, meye na wani damuwa? Ai tunda kaga be dauki wani mataki sosai ba shima be rasa afawa.

Koda ya fada agida kawai kace masu ka dade da denawa, amma taya zasu hanaka jin dadinka, kai bakaji yanda kakeji ba idan kana sha? Nima lokacin da aka kamani agidan mu inasha kawai dan fada ne akamun.

Kuma na nuna masu nabari, shikenan kuma se aka koma ana jidani. Haka suka yita yima Fahad hudubar banza, kafin subar wajen seda wani yakara kunna mashi yabashi yasha sannan suka koma makaranta hankalinshi kwance.

****** *****

Lokacin da akayi hutu malamin su Farida ya bama Fatima takarda ta kawo ma Malan, saboda an kama Farida da wani yaro da dare acikin class suna 'yan tabe tabe, alokacin malamin shi kadai ya kamasu, haka ya zanesu kuma yace seya kaisu wajen Principal.

Kuka suka rikayi suna bashi hakuri, seda ya farfasa masu jiki sannan yace suyi mashi alkawarin bazasu kara ba, haka sukayi alkawari suna kuka. Lokacin da akayi hutu shine ya rubuta takarda ya bama dan uwan kowa yace su kaima iyayensu.

Yasan idan yaran yaba bazasu kai ba, duk da be fadama kowa ba seyai tunanin ai kama iyayensu domin sukara ja masu kunne, kuma yafada masu idan suka sake korarsu za'ayi.

Bayan Malan ya dauko su sam Fatima ta manta da takardar, haka su Fahad da Faisal suka dawo, gidan kowa se murnar ganin dan uwanshi yakeyi. Farida tace shikenan yanzu batare zamu rika dawowa da Yaya Farouk ba? Mama tace Yaya ai yana gidan biki.

Farida tace ina ne gidan biki kuma? Mama tace Isa Kaita mana. Farida tasa dariya tana fadin N.C.E zeyi shi kuma? Mama tace shida Malan sukace sun amince, base yaje yayi tayi ba.

Kude ku dage kutafi jami'a. Fahad ne yashigo yana fadin Mama ina abinci na? Mama tace Oh! Ni, yanzu ya akayi cikinka ya bude haka? Da de baka da cin abinci, ko kun dawo makaranta se kowa yaci kake cin naka.

Fahad yace yo Mama mutum ya kwaso yunwar makaranta ba dole ya nemi abinci ba. Mama tace to kaje kacire kayanka kayi wanka sekaci, dan Allah kalleka kamar ba senior ba, duk kazama kazami wallahi.

Dariya Farida tasa, kafa Fahad ya kai mata yana fadin zanci Uwarki wallahi. Dukewa Farida tayi tana kuka dan taji zafin harbin da yayi mata a cinya. Mama tace bana son sakarci fa, ya daga dawo warku zaku fara fada abinda bakuyi ada.

Tun dazu take son kadawo kuma shikenan kana dawowa zaka hauta da duka, wai meyasa yanzu kake da saurin zuciya ne Fahad? Kuma ko kunyata ba kaji zaka zagi Uwarta, to bayan ni akwai wata Uwar da kuke da ita ne? Juyawa Fahad yayi yana fadin wallahi Mama duk kece kike bata yarinyar nan.

Wallahi idan kikace zakimun wannan rashin kunyar taki Uwarki zanci, fita yayi yana zaginta. Rike baki Mam tayi tana mamakin canjin halayen Fahad, ada yafi Farouk son Farida, amma yanzu shine yake dukanta hada zagi.

Fatima ce da Faisal suka shigo tana rike da hannunshi suna ta dariya tana fadin Allah Yaya seka bani alawata, ai Yaya Saleem ni yace akawo mawa. Faisal yace ai nafada maki sekin biyani zan baki. Kwace hannunshi yayi ya ruga dakinsu itama ta bishi da gudu suna dariya.

Wani bakin ciki ne ya kama Mama, kallon Farida tayi tana fadin yi hakuri kitashi kiyi wanka kici abinci. Farida tace ni da nayi wanka ma gidan Hajiya zanje. Mama tace a'a kibari se gobe, yanzu kizauna ki huta. 

Farida tace kai Mama, nide kibarni intafi. Mama tace kinsan de yanzu Malan ze dawo kuma nemanku zeyi, ki bari kawai se gobe. Farouk ne yashigo da sallama hannunshi dauke da jaka.

Farida ce tasa ihu tana fadin ga Yaya oyo oyo. Murmushi yayi yana fadin Farida yan mata, ashe har kundawo? Amsar jakar tayi tana fadin tun dazu ma. Murmushi Mama tayi tana fadin ashe kaima kana hanya? Farouk yace wallahi kuwa.

Gani nayi duk an tafi week end shine nace nima bara inzo nasan 'yan makaranta sun dawo semu gaisa. Mama tace sannu da zuwa, yace yauwa na sameku lafiya? Tace lafiya lau. Shiga ciki inzubo maka abinci.

Yana shiga Faisal yace la! Yaya yaushe kadawo? Farouk yace yanzu nashigo, ai nasan zaku dawo hutu shiyasa nace bara indawo mugaisa. Fatima tace Yaya sannu da zuwa, yace yauwa Fatima ya karatu? Tace Alhamdulillah.


Zaune Farouk yake a dakin Mama bayan yagama cin abinci tana ta tambayarshi yanda makarantar take,Farouk yace lafiya lau Mama, tace to wa yake maka girki kuma? Farouk yace ai na iya tun ina Faskari, Mama tace da kyau.

Dukar da kai kasa Farouk yayi yana wasa da hannunshi. Mama tace wai ni tun dazu nake ganinka kamar baka da lafiya, ko wani abun ne yake faruwa? Kwallace ta cika idon Farouk. Kara matsowa Mama tayi tana fadin kafada mani mana.

Fatima ce tayi sallama, amsawa Mama tayi tana fadin lafiya? Shigowa Fatima tayi tana fadin dama Malaminsu Farida ne yabani takarta yace inkawo ma Malan, shine na manta dazu a mota ban bashi ba.

Mama tace kinji gulma kai, ba anjima Malan din ze taraku gaba dayanku kowa yakawo takardunshi ba, bazaki iya ajewa anjima ki bashi ba? Fatima tace ai batawa bace ta Farida ce. Mama tace ita meyasa be bata ba? Se ke uwar rawar kai? Dukar da kai Fatima tayi kasa. Domin ta karanta abinda yake cikin takardar, kuma ta nuna ma Faisal.

Shine ma yace kada tabama Malan ta kaima Mama dan yasan Malan ze iya dukan Farida, sosai sukayi mamakin abinda Farida tayi, Faisal yake tambayar Fatima yace dama kinsan tanayin haka ne? Fatima tace nide naji ana maganar tana yawan cewa tana son maza.

Amma gaskiya bansan lokacin da tayi wannan abun ba, kuma ma kaji malamin yace be fadama kowa ba. Faisal yace Allah ya kyauta, ina fatan kede ba ruwanki? Fatima tace wallahi ni ba ruwana da kowa.

Cikin tsawa Mama tace to Uwar me kika tsaya kinayi, kitafi kibani waje, idan Malan din yadawo seki bashi. Farouk ne yadago kanshi yace kawo nan mugani, mika mashi tayi ta fita. Mama tace ai da baka amsa ba.

Bude takardar yayi Mama tana fadin karanta mani inji abinda yace, lokacin da Farouk ya fara karantawa seda hawaye suka zubo mashi, kasancewar da turanci malamin ya rubuta yasa Mama bata fahimci duk abinda ya karanta ba.

Sede ganin yana karantawa yana kuka yasa tagane akwai matsala. Mama tace bade korarta sukayi ba ko? Girgiza kai yayi yace wai meyasa komai yake zuwa mana a haka ne? Mama tace wai me yake faruwa? Farouk yace malamin su Farida ne yakawo karar ta.

Mama tace kamar ya? Nan Farouk ya fada mata abinda yace, sosai hankalin Mama yatashi, amsar takardar tayi ta yaga tana fadin baza'a fadama Malan din ba, nida kaina zan ja mata kunne.

Wannan bala'i dame yayi kama? Farouk yace shikenan kowa da tashi kaddarar, shi Fahad ga halin daya jefa kanshi, ita kuma ga abinda take aikatawa. Mama tace bangane ba? Cikin kuka Farouk ya fada mata halin da Fahad yake ciki.

Sosai hankalin Mama yakara tashi, kuka kawai takeyi, wannan wace irin jaraba ce tashigo mata gida? A fili tace Allah ya isa tsakanina dake Inne, burinki ya cika kin lalata mani yara. Farouk yace haba Mama, me kuma Inne tayi maki? Inne bata da laifi laifinsu ne.

Mama tace wallahi banyarda ba. Kuma inaso kaja bakinka kayi shiru, wallahi idan kabari naji wannan maganar a wajen wani sena bata maka rai, kasan de yanda Malan yakejin haushinsu Fahad, idan yasamu wannan labarin shikenan sun zama abun kyama awajenshi.

Ka barni nasan matakin dazan dauka, bazan bari Malan yaji wannan maganar ba bare ya maida mani yara saniyar ware. Nasan halinshi sarai, shi kullum wanda yakeyin abun kirki shine mutum awajenshi, dan haka bazan bari yasan komai ba.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[4/5, 4:22 PM] nabilalady5: 🏡🏡 A WANI GIDA🏡🏡
          😭😭😭

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

        Part 65 ⏩ 70

Zaune su Farida da Fahad suke adakin Mama, da ka kalli fuskar Mama kasan ranta abace yake. Dago ido tayi ta kalli Farida, gyaran murya tayi tace Farida tashi kije gidan Maman Sultan kice ta bani kayana da na bari jiya agidan ta.

Bayan Farida ta fita Mama ta kalli Fahad, dama bata son tayi mashi magana agaban Farida ne shiyasa ta aiketa. Fahad! Dago jajayen idonshi yayi ya kalleta, ganin fuskarta babu alamun wasa yasa yakara nutsuwa.

Meya sami idonka yayi ja haka bayan kuma baka da ciwon ido? Dukar da kai kasa yayi yace wani abu ne ya fada mani a ido. Mama tace bana son karya, kafada mani abinda kake sha? Fahad yace yoni me zansha.

Mama tace kwanaki kuna makaranta kun hadu da Farouk? Saurin dago kai yayi yana kallonta. Tambayarka nakeyi kun hadu? Fahad yace E, awane waje kuka hadu? Mama makarantar mu yaje fa.

Amma ba cikin makaranta ya ganka ba. Shiru Fahad yayi yana zare ido. Fahad irin rayuwar daka daukar ma kanka kenan ko? Yanzu ba kajin kunya su Faisal su san halin da kake ciki? Bakasan zasuyi mana dariya ba.

Me kake tunani idan Malan yaji wannan magana? Kuma kasan yana jin haushinka saboda yanzu baka maida hankali akan karatunka ko? Yanzu Fahad duka shekararka nawa da zaka fara shaye shaye? Kuma ba sigari kadai kake sha ba.

Bakasan kwakwalwarka zata iya samun matsala ba? Kuka Mama tasa tana fadin so kuke bakin cikin ku ya kashe ni? Kai ka fada shaye shaye, ita kuma Farida ta fara bin maza. Haba Fahad, kai ne wanda kafi kowa sona duk cikin yara na.

Meyasa yanzu kuma zaka zamo wanda zesani cikin damuwa? Dan Allah Fahad ka rufa mani asiri kadena wannan halin banzan, idan baka sani ba nasan kana mani dauke dauke. Fahad yace ni gaskiya Mama bana sata.

Mama tace bana son gardama, idan ma ba kayi to kasani shaye shaye babu abinda baya sawa, kuma se yanzu na gano dalilin da yasa kake da zafin zuciya yanzu, halinka ya canza Fahad, ka daure ka canza wannan halin.

Kuka Mama takeyi sosai. Fahad yace Mama kiyi hakuri daga yau na dena duk abinda nakeyi. Mama tace Allah yasa Fahad. Tashi kaje kuma bazan fada ma Malan ba, banaso ya kara jin haushinka. Dadi Fahad yaji jin tace bazata fada ma Malan ba, aranshi yana fadin da sauki ma.

Bayan Fahad ya tafi Farida ta dawo daga aiken da akayi mata. Haka Mama ta sata gaba tana tambayarta metayi amakaranta, Farida Kamar zatayi kuka tace Allah Mama babu abinda nayi. Mama tace amma ya akayi Malaminku ya aiko da takarda abama Malan? Farida tace wallahi ba wata takardar daya bani.

Mama tace ai Fatima yaba, kuma Farouk ya karanta mani duk naji abinda kikayi. Farida tace wai fa Mama daga yazo same mu nida kawata a class munje wajen wani dan ajinmu bayan antashi daga pref muka tsaya ya nuna mana aikin da aka bamu shine fa Malamin yazo yace wai iskanci mukeyi.

Mama tace kenan bake daya bace? Farida tace mu 3 ne fa. Kuka Farida tasa tana fadin kin gani ko za'a jamani sharri, dama Malamin ya tsaneni yafison Fatima saboda wai ni bana mashi magana.

Tsaki Mama tayi tana fadin ai dama nasan karya ne, na sanki bazaki iya aikata abinda akace ba, dama Fatima akace zan yarda domin ba tada abokan wasa se yan gidansu Amira.

Kuma ba tajin kunyar taba namiji. Farida tace damma bakiga yanda sukeyi da mazan ajinsu ba, wai se su zauna suce karatu sukeyi basa komawa daki da wuri. Mama tace ki rabu da ita, in Allah ya yarda seta debo ma Malan da Inne abin kunya.

Bade ita yakeso yanzu ba, kibarshi ai duniya zata koya mashi hankali. Abinda nakeso dake ki kara dagewa kada kibari wannan karon akara maidoki baya. Farida tace zan dage sosai, itama Fatimar ai kawarta ce take bata satar amsa. Mama tace kirabu da ita ai duk nasan komai, ba kokarin ta bane.


Zaune Faisal da Farouk suke a kofar gidansu saman benci suna fira, Farouk yana ta bama Faisal labarin makarantarsu. Faisal yace ai nima idan nagama makaranta duk makarantar dana samu tafiya zanyi.

Kaga yanzu ka huta, nasan akwai abokanka da yawa da suke zaune basu tafi makaranta ba saboda basu sami wadda suke so ba. Farouk yace da yawa ma. Shide Mannir yaci sa'a ya samu Federal University Dutsinma, muna haduwa dashi wani lokacin.

Faisal yace haka Abba yake fada mani, bakomai kowa da rabonshi, kuma kasan kowa yana tafiya da sa'arshi, se kaga wani yafika da wani abun kaima kuma seka fishi da wani abun. Farouk yace hakane. Amma gaskiya ko na gama makaranta zanyi kokarin neman aiki a katsina.

Faisal yace meyasa? Farouk yace kawai ni banajin dadin zaman gidan nan yanzu. Jinjina kai Faisal yayi yace amma kana ganin Malan ze barka? Kuma ma a Katsina wajen wa zaka zauna? Farouk yace kaide Allah ya kaimu in gama, amma gaskiya bazan zauna garin nan ba.

Kaga wannan dinkin hular da nakeyi ba karamun samu nake ba, kuma tun yanzu nafara tara kudi, kafin ingama insha Allah nasan zan tara kudade masu yawa. Faisal yace Allah yasa, amma ko ni bazan zauna garin nan ba.

Fahad ne yataho yana wani cika yana batsewa, domin tunda Mama tace Farouk ne yafada mata abinda yake aikatawa yake jin haushinshi, kuma ko da yafita daga gidan seda yaje yayo shaye shayenshi sannan, yanzu haka daga can yake.

Ko kallonsu beyi ba yashige cikin gida. Girgiza kai Farouk yayi bece komai ba. Faisal ne yace Yaya nikam akwai abinda na dade inaso in fada maka, sede bansan yanda zaka dauki maganar ba. Farouk yace maganar Fahad ce ko? Faisal yace E.

Murmushi Farouk yayi yace nima nasani, domin agaban idona nagashi yana shan wiwi, Faisal yace bayan sigari yanzu har wiwi yakesha? Farouk yace to wama yasan iyakar abinda yakesha, nide abinda nasani kenan.

Faisal yace amma Yaya ai be kamata ace anyi shiru ba. Farouk yace nayi mashi magana, kuma na fadama Mama kuma tace zatayi mashi fada. Faisal yace amma baka ganin yakamata Malan yasani? Farouk yace Mama tace kada afada mashi.

Kuma kasan halin Malan ze iya zaneshi kuma yace babu ruwanshi dashi. Faisal yace haka ne, Allah ya kyauta. Farouk yace amin. Faisal yace yaushe zaka koma Yaya? Farouk yace gobe. Tashi Faisal yayi yana fadin bara inje gidansu Amira kafin akira sallah. Farouk yace kai da Amira kode? Murmushi Faisal yayi yace kawai de mun saba da ita ne. Farouk yace to Allah yatemaka.


***** *****

Haka hutunsu yakare sam Fahad be dena abinda yakeyi ba, sema karuwa da abun yayi, dan da an bata mashi rai to seya sha, kwata kwata yadena zama gidan sosai, komai yace yatafi gidan Hajiya, itako inde yaje seta bashi kudi.

Gashi yanzu son kudinshi yayi yawa, ga roko duk inda abokan Malan suke seyaje ya gaishe su, sata kuwa sede idan ba'a aje ba. Malan tun yana mashi fadan kai dare awaje har yadena, domin duk lokacin da yayi mashi fada to aranar se sunyi fada da Mama.

Farida ma babu abinda ya canza sema abinda yayi gaba, haka suka shirya suka koma makaranta, danshi Faisal daga wannan dawowar sede yazo sallah amma se sun gama zasu dawo gaba daya.


Lokacin daya koma makaranta shida Nura haka Saleem ya sashi gaba yana ta tambayarshi Fatima, Faisal se yanga yake mashi yana fadin seka bani cin hanci zan fada maka.

Seda Saleem yayi kamar zeyi kuka sannan Faisal ya bashi wani zobe da Fatima ta bada akawo mashi Saleem yace dan rainin wayau, Faisal yace wallahi zan anshe. Faisal yace ina Lubna fa? Saleem yace nima bansani ba.

Faisal yace kada kasani, Nura yace Saleem Amira zaka tambayeshi, dariya Saleem yayi yace ka kyaleshi, mun rasa ma wane fanni yake, maganarshi dama bata wuce Fatima, Amira se Lubna.

Faisal yace ai dole in fadesu domin su 3 suna da matukar muhimmanci agareni. Fatima de kanwata ce wadda duk duniya babu wanda nakeso sama da ita, kai kanka saboda yanda kake nuna kulawarka akanta yasa na amince maka.

Amira kuwa jini na da nata ne a hade, bansan irin shakuwar da mukayi da ita ba. Lubna kuwa itace wadda ta debema Fatima kewa kuma ta nuna mata yanda rayuwa take. Wannan dalilin ne yasa nake son  su gaba daya.

Nura yace kila de Mata biyu zak aura. Dariya sukasa Faisal yace kutashi mutafi masallaci an kusa kiran sallah. Saleem yace tunda anyi maganar aure ai dole kace atafi masallaci, bayan saura minti 15 akira sallar. Faisal yace E naji koma me zakuce.



Zulai ce ta kira Mama tana tambayarta ina ne gidansu gata tazo Mani, cike da Farin ciki Mama tace da gaske? Zulai tace wallahi da gaske nakeyi, biki mukazo katsina ni kuma na tambaya akace mani babu nisa shine na taho.

Mama tace yanzu kina ina? Zulai tace gani nan an sauke ni atasha, Mama tace samu me mashin ki bani shi. Bayan Zulai ta samu me mashin ta bashi wayar. Kwatancen gidan Mama tayi mashi yace yasan gidan, dan babu wanda besan Malan ba.

Da sallama Zulai ita da wadda suke tare suka shiga gidan Mama, fitowa Mama tayi tana fadin sannunku da zuwa, ashe ma ku biyu ne? Zulai tace wallahi kuwa nida kanwata ne. Mama tace kushigo.

Bayan takawo masu ruwa da abinci sunci nan suka fara gaisawa. Mama tace amma naji dadin zuwanki Zulai. Ban dauka zaki zoba. Zulai tace ai nafada maki sena rigaki zuwa, ke kam tunda kuka dawo nan ai nasan bazaki kara zuwa Faskari ba.

Dama kuma baki taba zuwa ba. Mama tace wallahi inda wani abu babba ya faru da ke da kin ganni, Zulai tace sede haihuwa ko biki, kuma babu wanda zanyi. Mama tace kai Zulai bazaki kira mu zuwa suna ba.

Zulai tace rufa mani asiri, dama ni ba wasu yara gareni da yawa ba. Mama tace ai kin huta, ya sunan kanwar taki? Zulai tace Suwaiba, itace autar mu. Mama tace Allah sarki ba tayi aure ba kenan? Zulai tace kinsan itace auta seda tayi karatu sannan.

Mama tace ai taji dadinta, yanzu se aiki ko? Zulai tace tana aikin ma, ai agidan Yayanmu take zaune  anan Katsina, to anan tasamu aikin koyarwa. Mama tace Allah yakawo miji nagari to. Zulai tace amin.

Wai ya naji gidan shiru ina yaran suke? Mama tace ai duk suna makaranta. Zulai tace haka fa, amma ai Farouk ya gama ko? Mama tace yagama har yatafi wata makarantar. Zulai tace lallai Maman Farida kin kusa hutawa, ace babban danki har yashiga jami'a.

Wane gare yake? Mama tace na'am, E, a jami'ar Ummaru Musa yake. Zulai tace lallai ya more, kinga nan da wani lokaci kema zaki fara cin albarkacin 'ya'ya. Murmushin yake Mama tayi tace ai kuwa.

Sam ba taso Zulai tasan Farouk ba Jami'a yake ba, dan bataso a rai nata. Zulai tace ina kuma su Fatima? Mama tace munafuka tana makaranta, Zulai tace amma yanzu takara girma ko? Mama tace sosai ma, baki gantaba, yarinya tun bata gama secondary ba amma ta koma kamar wata uwar mata.

Sam bata da kirar mata, ni tsoro ma nakeji kada afara tanka mana gida, kuma gashi Malan yace se sunyi karatu zasuyi aure. Zulai tace kada taje tajawo maku abun kunya fa.

Mama tace wallahi kamar kin sani, yanda take ganin ta girma tazama budurwa se shige ma maza takeyi, shiyasa yanzu na hana Farida taje kusa da ita dan yanzu zata iya canza mata hali.

Zulai tace kede ki kula da diyarki, idan ta kwaso abun kunya ki korama uwarta ita. Mama tace dama waze zauna a juye mashi abun kunya agida. Mama tace amma de Zulai nan zaku kwana ko? Zulai tace dama cewa nayi kwana zamuyi musha fira.

Mama tace amma naji dadi, sallamar Malan ce ta katse masu firar da sukeyi. Tashi Mama tayi tana fadin sannu da zuwa Malan, murmushi yayi yace yauwa baki mukayi ne? Mama tace wallahi Zulai ce da kanwarta suka kawo mana ziyara.

Tazo biki Katsina shine tazo, nan ma zasu kwana dan sun gama bikin. Malan yace lallai ta kyauta, muje mugaisa ko. Malan yana shiga suka hada ido da Suwaiba, seda gabanshi ya fadi, lokaci guda yaji ta burgeshi.

Zulai ce tace Malan sannu da zuwa, zama yayi yana fadin yauwa Zulai sannunku da zuwa, tace yauwa ina wuni? Yace lafiya lau, ya megidan naki? Tace lafiya lau yana gaisheka.

Ai suna cewa sunyi kewarka. Suwaiba ce ta dago kai tace ina wuni? Murmushi Malan yasaki yana fadin lafiya lau, kunzo lafiya? Tace lafiya lau. Mama tace autar su Zulai ce, itama malamar makaranta ce.

Malan yace da kyau, Allah yatemaka, a Faskarin take itama? Zulai tace a'a a Katsina take, Malan yace Allah sarki, acan take aure ko? Mama tace ai batayi aure ba karatu tagama.

Murmushi Malan yayi yace yayi kyau, tun da angama karatu har ana aiki ai se ayi aure ko, Zulai tace kaima de ka fada, har yanzu Suwaiba taki tsayawa ta fitar da miji. Washe baki Malan yayi yace to ai aure ba'ayi mashi gaggawa, gara ta tsaya tafitar da wanda ranta ya kwanta dashi.


Mama tace wannan haka yake, domin abunda yake kawo yawan mutuwar aure hada rashin tsayawa a gama fuskantar juna. Tashi Malan yayi yace bara inje indawo, yau muna da manyan baki ai dole mu karramasu.

Ai mijinki Zulai mutumin kirki ne. Mama tace ai dagashi har ita haka suke, shiyasa duk a unguwar munfi shiri da ita. Zulai tace mungode. Mama tace baza kaci abinci ba sannan? Malan yace bara indawo. Tashi Suwaiba tayi tana fadin zanyi sallah.

Mama tace to kishiga ciki dauki kayan akwai bandaki aciki. Tana tafiya suka cigaba da firarsu, sam babu wanda yatashi domin yin sallah.

*** ****

Washe gari tunda safe Malan yace ma Mama zeje katsina, Mama tace lafiya de? Malan yace inaso inje induba wani abokina da aka kwantar a asibiti. Mama tace to ko su Zulai su shirya kawuce dasu, kaga nima se inje mu duboshi kada kutafi ku kadai nasan bazakaji dadi ba tun da baku saba ba.

Malan ya daure fuska ganin zata rushe mashi plan, danshi saboda Suwaiba ya shirya wannan tafiyar. Mama tace dan Allah Malan katafi dasu kaga zasu rage kudin mota. Malan yace sede inbasu kudin mota.

Mama tace toshikenan hakan ma yayi. Saurin kallonta yayi danshi latsa ta kawai yayi dan kada taga yayi saurin amincewa. Harta juya yace naga kamar kin bata rai? Mama tace wallahi ni ban bata rai ba. Malan yace wallahi kin bata rai, Mama tace a'a.

Ai nasan halinka ba kason tafiya da matan da baka saba dasu ba, shiyasa nace inshirya mutafi tare. Malan yace a'a kiyi zamanki, zan tafi dasu kawai dan kawarkice, kuma sunzo har sun kwana.

Murmushi Mama tayi tace amma nagode. Malan yace kice su shirya. Tana fita ya saki ajiyar zuciya, aranshi yana fadin zan jama kaina, an mun tayi ina wani sharewa.

Haka Mama ta bama Suwaiba turare Zulai kuma ta bata barkono da kuka. Godiya sukayi mata suka tafi, sede Malan cema Mama yayi su shiga baya dan bayaso adauka wasu ya dauko, seda Mama taji dadi daya fadi haka.

Shiyasa suna fita ta bude masu baya tace su shiga, sosai Zulai tayi mata godiya, haka suka tafi zuciyar Malan cike da farin ciki.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[4/9, 1:34 PM] nabilalady5: 🏡🏡 A WANI GIDA🏡🏡
          😭😭😭

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

        Part 70  ⏩ 75

A cikin mota Malan se kame kamen labari yakeyi Zulai kadai take biye mashi. Sun kusa shiga Katsina Malan yace Zulai nide akwai maganar da nakeso inyi, sede bansan yanda zaki dauke ta ba.

Zulai da tun dazu ta dade da harbo jirginshi tayi murmushi tace haba Malan, ai babu wata magana daza ka fada mani in kasa fahimtar ta, kai fa namiji ne, kawai kafadi maganarka. Murmushi Malan yayi yace to shikenan bara mu isa.


Zulai ce tayi mashi kwatance har suka isa kofar gidan Yayansu. Malan yace Malama Suwaiba kishiga ciki zan danyi magana da Yayarmu. Murmushi Suwaiba tayi tace to bakomai mungode ka gaida gida.

Bayan ta tafi Malan yace Zulai dama ba wani abu bane, inaso in hada iri dake. Murmushi Zulai tayi tace to Malan Allah yasa alkhairi ne. Malan yace dama akan maganar Suwaiba ne, nide ina rokon abani dama inshigo cikin mane ma.

Amma ke nakeso kishige mani gaba dan naji kince bata son kula samari, bare kuma ni da nake tsoho. Dariya Zulai tayi tace haba Malan, ina wani tsufa anan? Kawai dan de kana zaune da mace ba 'yar zamani ba.

Duka yaranka biyar fa, wallahi kabari Suwaiba ta amince da kai nasan zata canzaka, domin Suwaiba akwai son gayu. Malan ya washe baki yace Allah ko? Zulai tace sosai mana. Malan yace amma ya kike gani ta wajen Hauwa gashi ke kawarta ce.

Zulai tace haba Malan, ai Hauwa cutar da kai kawai takeyi, na tabbata itace take kara tsufar da kai, domin Hauwa shu'umace, se mutum me zurfin tunani yake iya gane kai dinta. Amma shawarar da zan baka kafara sa mata ido musamman idan tayi baki.

Ko kuma lokacin da yara suka dawo gida hutu. Kuma ni badamuwata bace dan ka auri Suwaiba, domin ni ba garin nake ba. Kome zatace banida damuwa, idan kuma duniyanci takeji dashi na fita.

Kuma tabbas nayi maka sha'awar auren Suwaiba, kuma nasan itace zata maye maka gurbin Inne, domin kayi asarar mace ta gari, kuma ba kowa bane yayi silar rabuwarka da ita se matarka.

Idan kabi komai a sannu zaka fahimta da kanka. Kada kadamu zan samu Suwaiba, kuma nasan zata amince da kai. Malan yace amma nagode Zulai, samun Number dinki domin inji abinda ake ciki.

Bayan ta samashi number ya ciro dubu 5 yabata yace ta bama Suwaiba, dubu 2 yabata yace tayi kudin mota. Sosai Zulai taji dadi, godiya tayi mashi tana fadin aduba mejikin. Malan yace ai dama nine me jikin, kuma yanzu naga likitan gakinan azaune, maganin kuma yana ciki, idan kika amso mani maganin seki aika mani dashi. Ni yanzu gida zan koma. Dariya Zulai tasa ta bude kofa tana mashi asauka lafiya.


Bayan Mama ta gama gyaran gida tayi bakuwa wata 'yar uwarta da take aure a Shargalle, sosai Mama taji dadin zuwanta, bayan sun gama gaisawa Mama tace bara tashiga kitchen ta dora masu abinci, Matar me suna Amba tace muje mana nima ai banason zama ni kadai.

Haka suka shiga suka dora girki, bayan sun gama suka zauna suna fira. Har Malan yadawo Mama bataji karar motarshi ba, domin a waje ya ajeta, kai tsaye falonta ya nufa yana kiranta, yazo shiga yaji ana magana alamun mutum biyu ne.

A lokacin kuwa Mama tana bama Amba labarin irin abubuwan da tayi ta jawo hankalin Malan, da kuma yanda tasa ya saki Inne, da yanda takema su Faisal, har zuwansu Fatima Makaranta da abubuwan da take mata. Komai de seda Mama ta fadama Amba.

Sosai suke dariya, Amba tace amma Hauwa ke ta da bance, babu boka ba Malan kin kwace komai na gidan, kuma kin kama Malan a hannunki, Mama tace wallahi kuwa, ai yanzu ne nake iya daga mashi murya.

Shima gani nayi ze maida mani yara Saniyar ware, niko duk abinda mutum zemun zan iya jurewa, amma idan mutum yafara tabo mani yara wallahi anan zega bacin rai na. Damma de waccan munfukar matar ta shiga ta fita ta saka ma yarana rashin kokari, ai da har yanzu yarana su ke haskawa agidan nan.

To shi kuma Malan yanda halinshi yake, sam baya tunani da kwakwalwarshi, shi akullum duk yaron daya kasance me kokari agida to shine abun so awajenshi, haka kuma duk wanda yaga yana mashi aiki ko kuma yana wani abu da yakeso agaban idonshi to shine tauraro a wajenshi.

 Irin wannan halin nashi nayi amfani dashi wajen saka kaunar yarana azuciyarshi, domin inde yana gida yarana komai sune sukeyi, kuma basa tafiya masallaci seda shi. Haka kuma na saka kiyayyar yaranshi a zuciyarshi, kinga ko ai nayi mashi babban aiki.

Nasan har yaran nan su mutu bazasu dena ganin bakin Malan ba, domin basu taso da soyayyarshi ba, ko yanzu da yake kokarin jawosu ajiki da kinga yanda suke mashi kinsan basu saba ba.

Ganin yanzu yafison yaranta da nawa yasa nake mashi masifa, domin naga idan na tsaya wannan kissar to nice zan kwana ciki, dama saboda wa nakeyi, saboda kishiya ne, kuma tunda na koreta ai se in kwatar ma yarana 'yancinsu.

Kinga yanzu na zamar mashi kargen kafa, domin yanzu Malan baze iya kallon wata mace yace ze aura ba, nidin de nice abokiyar zaman tashi. Amba tace gaskiya agaisheki, ai ban taba jin labari me abun al'ajabi ba kamar naki.

Idan zaki shiga gidaje goma masu kishiyoyi to da wuya ki samu masu irin halinki, domin abinda kowa ce mace ta yarda dashi na hanyar da zata mallake mijinta ko kuma ta kori kishiyarta to hanya daya ce, wato Boka.

Segashi ke cimin ruwan sanyi kin gama da komai. Mama tace aini dama can a rayuwata banyarda da wani abu waishi boka ba, ai duk macen data isa to wallahi base taje wajen boka ba zata kwaci kanta, aini abun da na dauki boka marar aikinyi.

Kuma idan kura tana maganin zawo tayima kanta mana. Kullum yanda kika sanshi ahaka zaki sameshi, sekiji yayi aikin miliyoyi amma idan kika kalleshi kome aikinki bazaki hada dashi ba.

In banda cutar da mata babu abinda sukeyi, su kwanta dasu, kuma su kwace masu kudi, daga karshe su kafa masu sharadin daze halakasu, domin duk wani boka idan yabama mace magani daga karshe sekinji yace idan ta kuskure kaza aikin ze dawo kanta.

Kuma abun haushin se yace mata ciwon daze sameta beda magani, kinga kenan suna sane suke aikata masu haka. Sede har yanzu su Matan basu gane ba, domin zuciyarsu ta mace akan bokansu.

Amba tace wallahi da gaskiyarki, gara mutum yayi amfani da kwakwalwarshi ya kwatoma kanshi 'yanci. Mama tace gani nan de ina zaune agidana lafiya. Amba tace kinga kada dare yayi mani gara intashi in tafi. Mama tace haba ki bari kiyi la'asar mana.

Amba tace ai zan tsaya Mashi. Tashi Mama tayi ta hado mata wasu kayanta dazata bayar da sabulun wanka ta bata da dari biyu tace ta kara tayi kudin mota. Malan da jikinshi ya gama mutuwa haka yaja kafa yashige dakinshi.

Har bakin kofa Mama ta rakata Amba tana ta mata godiya, ganin motar Malan yasa Mama tace ashe Malan din ma yadawo, bara in mashi magana ku gaisa. Amba tace dakin barshi ma. Mama tace kede kibari in mashi magana kila ma ki kara samun na mota.

Yanajin Mama ta taho yayi saurin shigewa bandaki, koda tazo taga yana bandaki seta fita tace tashigo yana bandaki. Amba tace Allah kibarshi wucewa zanyi. Mama tace toshikenan ki gaida gida da yaran.

Malan kuwa wanka yayi yafito, adaki ya iske Mama tana jiranshi, kallo daya yayi mata ya dauke ido, gaba daya tsanarta ce tashigar mashi zuciya, fuska a daure ya zauna. Murmushi Mama tayi tana fadin Malan har kadawo? Amma kayi sauri.

Be kalleta ba yace E, tashi tayi ta kawo mashi ruwa da abinci, alokacin yana kwance ya rufe idonshi. Mama tace Malan tashi ga abincinka, be bude idon ba yace kibarshi idan natashi zanci bacci nakeji.

Mama tace ko inzo in tayaka baccin? Bude ido yayi yace dan Allah kifita banason surutu. Tashi Mama tayi tana tsaki tace dan ma nace zan ta yaka shine zaka kore ni, anjima zaka gani idan ka nemeni ko zanzo, fita tayi tana masifa.

Runtse ido yayi lokaci guda wasu zafafan hawaye suka zubo mashi. A ranshi yana fadin Hauwa kin cuceni, Allah ya isa tsakanina dake, kin gama tarwatsa mani gida, amma kisani wallahi kema sekin dandani irin bakin cikin da kika sani. Kuma yanzu ne zan kara dagewa wajen karo aure.


***** ******

Tun daga wannan ranar Malan ya canza ma Mama, ita kanta shakkarshi takeyi, domin yanzu ko zama gidan bayayi sosai, daya dawo yaci abinci ze kwanta, ana la'asar kuma ze fita, kusan kullum ya kwanta seyayi kuka.

Babu abinda yake damunshi irin rashin mutuncin da yayi ma Inne, yanzu gashi Inne tayi mashi nisa da babu abinda ze hana yaje ya maidota, gashi kwata kwata su Faisal basa sonshi, basa son zama dashi.

Sauran yaran daya saba dasu yanzu sun canza hali, Farouk ne kadai yake ganin hankali yana shigarshi, ya ma rasa ta inda ze fara. Gashi ya aje aiki, tunani yayi akan ya ciro kudinshi da yake tarawa a banki ya gina babban shago a wani karamin filinshi da yake cikin gari, idan yaso se ya zuba provision da kayan masarufi.

Se ya rika zama da kanshi dama yana gajiya da zaman rashin aikin yi, danshi ba ma'abocin zama majalissa bane, saboda yanayin shi yasa beda wasu abokai da yawa.

Wayarshi ce tayi kara, har ta kusa katsewa ya dauka, sunan Zulai yagani hakan yasa ya katse kiran ya kirata.  Bayan sun gama gaisawa Zulai tace albishir na bugo in maka. Murmushi Malan yayi yace ai na kosa inga kiranki, daurewa kawai nayi yasa bankira ki ba.

Zulai tace kasan halin Suwaiba, da kyar ta amince, sede tace ya za'ayi da aikinta? Washe baki Malan yayi yace haba wannan ai bawani abu bane, inada hanyar da zansa ayi mata transfer.

Zulai tace to babu damuwa, kuma nayima Yayanmu magana shima yaji dadi kuma ya amince da maganar sede yana son ya ganka. Malan yace wannan badamuwa bane, zan shirya zuwa gobe inje, amma kituro mani number Suwaiba bazan jira se zuwa gobe inganta ba.

Zulai tace toshikenan, godiya Malan yayi mata ya kashe, tana turo mashi number yakira Suwaiba.



Washe gari haka Malan ya caba ado kamar me shirin zuwa hawan sallah, sallama yayi ma Mama yanufi hanyar fita. Binshi Mama tayi tana fadin ina kuma zaka Malan? Kallonta yayi fuska adaure yace haifata kikayi ne? Cike da mamaki Mama tace bangane ba.

Tsaki Malan yayi yace dole duk inda zanje sena fada maki? Tunda nayi maki sallama aikin ki kice mani Allah ya kiyaye, in ba kuma yanzu kin dena Kissar ba. Juyawa yayi yafita.

Sakin baki Mama tayi tana kallonshi. To me yake nufi da wanna kalmar? Komawa falo tayi ta buga uban tagumi. To wai meyake samun Malan? Tunda yadawo daga Katsina gaba daya ya canza, sam yanzu baya mata fara'a.

Kuma baya son zama agida, gashi yanzu abu kadan se masifa. Gyara zama tayi tace to kode Inne tashiga tsakanina dashi ne? Mikewa tsaye tayi tana fadin wallahi bazan barta ba wannan karon, idan har Malan yaci gaba da yimani haka sena yimata babban tabon da bazata manta shi ba, kuma. Ba akan kowa zan dau fansa ba se akan Fatima.

**** *****

A cikin kwana biyu Malan da Suwaiba suka kulle, sosai suke zuba soyayya, gaba daya Suwaiba ta fara canza Malan, yanzu sam baya damuwa dan Mama batazo dakinshi kwana ba, haka suke kusan kwana suna waya.

Idan kuma yaga ranar tana jin kirki to baya dawowa gida da wuri seya gama wayarshi da Suwaiba sannan, gashi duk bayan kwana biyu seyaje Katsina, sam Mama takasa gane kanshi.

Gefe guda kuma ya fara gininshi na shago. Haka yaje ya samu Hajiyarshi da maganar aure, Hajiya ta rufe ido tana ta masifa tana fadin me ka nema karasa a wajen Hauwa? Mace me kirki, ai kaga yanda ka kare da kayi wancan auren, kuma yanzu zaka zo mani da maganar aure.

Malan yace Hajiya bakisan ko wacece Hauwa ba, nima se kwanan nan nasan asalin halinta................. Labarin duk abinda yaji tana fadama Amba ya bama Hajiya, sosai hankalin Hajiya yatashi.

Babu bata lokaci tace ta amince, kuma kada yafada mata  zeyi aure yabari ta gani daga sama, domin ta cuceshi, kuma zata samu Kawunshi suje domin suyi magana da Yayan yarinyar. Sosai ran Hajiya ya baci, haka tayi ta masifa, haka Malan ya yi ta bata hakuri yayi mata godiya ya tafi.


Haka Kawun shi da wani abokinshi suka je Katsina wajen Yayan Suwaiba bayan sun gaisa suka ba da kudin neman aure, sosai sukaji dadin yanda Yayanta ya amshe su, kuma yace idan sukayi shawara suka tsaida rana zasu aiko masu, godiya sukayi masu sukace zasu aiko da kayan sa ranar. 

Sosai Malan yaji dadin labarin da suka fada mashi, haka ya cigaba da shirye shiryen aurenshi ba tare da Mama ta sani ba.

A ranar visiting kuwa da Mama tayi mashi magana cewa yayi ta shirya masu kayan zeje masu shi kadai, sosai tayi mamaki, data taso mashi da masifa yace idan ita takeda iko da kanta se taje.

Haka yakawo mata kayan miya da nama yace tayi masu miya, kuma ta sama kowa tashi a cooler da abinci da ban. Haka yayo masu provision kowa da kwalinshi, dakinshi ya wuce dasu ko gani batayi ba.


Lokacin data gama hada masu komai ya dauka yasa mota, dakinshi yake ya dauko kayansu ya saka mota se kallonshi takeyi, haka yashiga mota yana fadin bakida sakon da za'a kaima Farida? Saboda mamaki kasa magana tayi haka ya tafi.

Kasa tsayuwa tayi, haka ta jingina tana tunanin kode Malan yasan wani abu daga cikin abun da take yima Fatima ne? Jin jina kai tayi tace tabbas Fatima itace ta fada ma Malan, wannan dalilin ne yasa ya canza mata lokaci guda.

Idan ko hakane wallahi zata dauki mataki, komawa tayi ta dauko hijabinta  ta wuce gidan Maman Sultan.


Lokacin da Fatima taji ana ne manta tasha mamaki da akace babanta ne yazo masu visinting, Farida ta rigata zuwa itama tayi mamakin ganinshi, har take tambayarshi Mama, yace tana gida baki tayi shiyasa.

Haka suka gaisa yabama kowa kayanshi ya basu kudi, haka sukayi mashi sallama, har sun tafi ya kira Fatima, juyowa Farida tayi tana kallonsu duk bakin ciki yagama kamata, meyasa ita ba'a kirata ba? Tsayawa tayi tana kallonsu.

Malan yace Fatima nasan kinajin haushi na ko? Girgiza kai tayi tana dukar da kai kasa, Malan yace kiyi hakuri nasan Hauwa tana rage maki kayan abinci, shiyasa ma yau nazo da kaina, kuma daga yau bazata kara zuwa maku visiting ba.

Fatima tace to, murmushi yayi yace zan tafi kidage da karatu, juyawa Fatima tayi aranta tana fadin kaji malan, da can besan ana mata haka ba seyanzu da yaga takusa gamawa sannan zece haka, kuma gashi Innenta tana gidan me kudi shi kuma ya aje aiki shiyasa yanzu zece yana son mu.

Gaba daya ma ranta baci yayi haka ta wuce wajen Lubna, tana zuwa ta bata labarin abinda yafaru. Lubna tace kiyi hakuri Fatima, tunda ya fadi haka kila da gaske yakeyi be sani ba. Tashi Fatima tayi tana fadin Lubna bakisan ko waye Malan ba. Wallahi zan iya cika littafi da labarin gidanmu. Dariya Lubna tayi tace ai seki fara.

***** ****

Haka Malan ya dage da gyaran bangaren Inne, kuma ya tada wani gini me dakuna biyu daga bayan dakunan gidan, kasancewar daga can baya dama yabar fili saboda yanaso ya gina ma yaranshi maza dakuna hakan yasa yanzu yake gina dakuna biyu.

Ita de Mama kallonshi kawai takeyi, dan lokacin da tayi mashi magana cewa yayi ina ruwanta, ba gidanshi bane, tace to ai naga bangare daya kake gyarawa, yace kisa ido kiyi kallo idan zaki iya.

Bayan angama gyaran dayen part din yace itama ta kwashe kayanta da maida dakinshi za'ayi gyara, haka ta kira Maman Sultan ta ta yata suka kwashe. Maman Sultan tace anya Malan ba aure zeyi ba? Mama tace haba de aure.

Ai wallahi babu matar data isa takara shigowa gidan nan, kuma Malan sam beda son mata, ko bayan rabuwarshi da Inne cewa yayi dama rabo ne kawai yasa ya aureta amma shi beda ra'ayin mata biyu.

Kawai de yanaso yayi gyara ne saboda kinga su Farida sun zama 'yan mata kila bangaren su Fahad ze maidasu su kuma ga dakunansu can ana masu abaya. Maman Sultan tayi murmushi tace Allah ya temaka.


Bayan angama mata gyara ta maida kayanta shima aka gyara mashi nashi part din, cikin lokaci kan kani aka gama ginin dakinsu Fahad, kowane daki da banda kinshi, daya Fahad da Faisal, dayan kuma na Farouk ne. Haka ya maida masu gadonsu da kayansu ya kulle part din Inne.


Daga Katsina kuma suka aiko masu da sa rana nan da wata 2, amma idan sunaso akara to, babu bata lokaci sukace yayi. Kudi Malan ya bama Suwaiba yace ta hada lefenta da kanta dan bayaso ya bama wasu su siya mata kayan da bataso.


**** ****


Lokacin da biki yarage saura sati 3, a na saura kwana biyu hutu.  A ranar laraba aka kama su Fahad shida abokanshi sun dira gidan wani malami da sukayi tafiya shida iyalanshi, lokacin da dare ne, Vice Principal shida wani malami sun dawo da school area bayan kowa ya tafi daki wajen karfe 10 na dare.

Vice Principal ne yafara ganin yaro na karshe daya dira katangar gidan, nuna ma malamin dasuke tare yayi, cikin sauri yace yaje yakira masu gadi guda biyu, haka ya nufi kofar gidan.

Masu gadin suna zuwa Vice Principal yace kawai su shiga, haka suka dira, da Fahad suka fara cin karo ya dauko wata bakar jaka hannunshi daya kuma ya kunna wiwi yana zuka.

Sauran ma kowa da abinda ya dauko sunata shan wiwinsu wasu kuma suna shan sigari, Fahad yana fadin kuyi sauri mufita, lokacin da suka fito su kuma masu gadin sun boye, suna zuwa zasu haura katangar Vice ya dallesu da fitila.

A kidime suka zubar da kayan suka fara neman hanyar guduwa, masu gadin ne sukayi saurin cafkesu. Gaba dayansu hankalinsu yatashi, saurin yadda abinda suke sha sukayi.

Vice yace kowa yadauki abunshi, haka suka dauka jikinsu yana rawa, sawa yayi dayan malamin ya haska mashi su, haka ya matso da kayan da suka yarda akusa dasu ya daukesu hoto.

Kuka sukasa suna rokonshi yayi hakuri, yace bade kune 'yan iskan makaranta ba, daga kanku wasu bazasu kara marmarin aikata irin wannan laifin ba, kushigo har cikin gidan malami ku rika sha mashi wiwi da sigari saboda ku 'yan iska ne.

Megadi, kutafi dasu su kwana a wajenku, domin gobe za'a yanke masu hukunci. Haka suka tafi dasu se kuka sukeyi, ba kamar Fahad, dan yasan ya shiga 3 awajen Malan.


Washe gari ranar alhamis bayan malamai sun gama meeting aka kada assembly, gaba daya makarantar kowa ya taru, kowa da abinda yake tunani, wasu ma suna fadin ko hutu za'a bada. Principal ne da Vice suka hau saman step din, sauran malaman kuma suna gefe.

Haka masu gadi suka fito dasu Fahad gaba dayansu sunyi zuru zuru, agaban mutane aka ajesu daga sama, kowa se dukar da kai ya keyi. Gaba daya 'yan makarantar kowa da abinda yake fadi, domin da yawa mutane sun san halinsu.

Hannu Vice ya daga hakan yasa kowa yayi shiru, bayan sun gaishesu yasa akayi addu'a, bayani yafara kamar haka:

Ina fatan kowa yaga wadan nan yara da suke agabanku, kuma kowa yasan suna daya daga cikin daliban makarantar nan, wasu daga cikinsu suna SS 2, wasu kuma SS 3, ajiya da dare nida Malan Shu'aibu muka kamasu sun haura gidan Malan Bala, kasancewar basa nan sunyi tafiya.

Bayan nakira masu gadi muka shiga gidan, ace bayan sata hada shaye shaye sukeyi, kuma ba sigari kadai ba, wiwi muka kamasu suna sha acikin gidanshi saboda rashin tarbiya.

Wayarshi ya daga sama yana fadin hotunansu suna nan ciki kuma zamu nuna ma Uban kowane yaro, bayan nan kuma daga yau su ba daliban wannan makarantar bane, mun yanke wannan hukunci ne saboda hakan yazamo jan kunne ga sauran Dalibai.

Kuma daga yanzu duk wanda aka kama yana mana shaye shaye acikin makaranta, ko a waje, tabbas shima ze fuskanci irin wannan hukunci. Me kuka sani arayuwa da zaku jefa kanku cikin irin wannan rayuwar? Me zaku iya zama nan gaba idan har baku dena wannan banzan halin ba.

Iyayenku sun kashe kudi abanza sun kawoku makaranta amma da abinda zaku saka masu kenan, to wallahi ko suwaye iyayenku daga yau kun bar makarantar nan, sede kowa ya koma gida iyayenshi su sake mashi wata makarantar.

Kuma kowannansu ze karbi bulala 20, kuma daga nan kayanku kawai zakuje kudauko Principal ya bada School bus domin akai kowa gida, badan komai ba saboda mu damka ku a hannun iyayenku kamar yanda suka kawoku suka damka mana ku.

Kuma mu nuna masu irin ta'asar da kukayi. Alhamdulilahi anyi sa'a acikin ku biyar mutum 3 a Katsina suke, suran biyun kuma daya dan Mani ne, dayan kuma dan Kaita ne, dan haka bayan kun amshi bulalarku masu gadi zasu raka ku kudauko kayanku kuzo mutafi.

Ina fatan wannan ze zama darasi agareku. Masinja aka kira wanda dama shine yake ma duk wani me laifi bulala, wata katuwar dorinace a hannunshi, haka Vice yasa masugadi suka rika turosu daya bayan daya ana zanesu.

Ihu kawai sukeyi, wasu daga cikin 'yan makaranta sunji tausayinsu ganin yanda suke kuka, jikinsu duk ya fashe, haka aka gama zanesu sannan aka sallami yara masugadi suka tasa su zuwa daki domin su dauko kayansu.

Da kyar suke tafiya haka kowa ya dauko kayanshi suka saka a mota, Vice da wasu malamai guda biyu ne suka shiga motar suka tafi dasu. Acikin mota se kuka sukeyi, anan ma Vice fada yayita masu.

Haka suka fara kai 'Yan Katsina su 3, kowa seda suka ga mahaifinshi, kuma suka nuna mashi hotonsu sannan suka damka mashi takardar kora, duk mahaifin da aka mikama danshi da takarda se yayi kuka.

Bayan sun gama da Katsina suka wuce Kaita, daga karshe suka dauki hanyar Mani, Fahad in banda kuka babu abinda yakeyi, Vice kuwa se fada yake kara mashi, domin yasan Malan, haka suka shiga cikin garin Mani nan suka tambayi Fahad ya nuna masu hanyar unguwar, yana kuka yana nuna masu.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[4/10, 12:19 PM] nabilalady5: ,🏡🏡 A WANI GIDA🏡🏡
          😭😭😭

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

        Part 75  ⏩ 80

Malan ne ya fito daga gida yana shirin tafiya sabon shagonshi da aka gama ginawa domin ya duba aikin da akayi, Mama tana biye dashi abaya tana ta masifar seya fada mata dalilin da yasa yanzu baya kulata, kuma baya sakar mata fuska.

Shikam yayi banza da ita bayan ya fitar da motarshi ya koma domin rufe gate din. Mama tace Malan da fa kai nake magana. Malan yace ina ganin kin fara samun tabin hankali, domin babu wata mace me hankali da mijinta zefita ta biyoshi da irin wannan haukan da kike yi.

Ina a gidan nan na kwana? Me ya hana tun jiya da dare idan kina son magana da ni bakizo dakina kikamun ba? Saboda kina tashen iskanci shiyasa kikayi kwanciyar adakinki dan kina tunanin idan na damu dake dole in biyoki.

Se kuma yanzu dan rashin hankali zan fita ki biyoni har bakin gate kina daga mun murya. Idan kece kike iko dani dan Allah kicigaba da yimani irin wannan iskancin wallahi zakiga matakin dazan dauka.

Mutuniyar banza wadda duk kissar da take takama da ita irin ta jahilan mata ne. Gate din yarufe yabar Mama da sakin baki. Har zeshiga mota yaga School Bus ta Dutsinma tana karasowa.

Maida murfin motar yayi ya kulle, tsaye yake har suka karaso, haka nan yaji gabanshi se faduwa yakeyi. Vice yafara ganin yafito hakan yasa yasaki murmushi, shima Vice din murmushi yayi se kuma duk yaji babu dadi.

Sanin abinda yakawosu. Malan yace ikon Allah kaga mutanan Dutsinma, yau kaine da safen nan. Sauran malaman ne suka fito se kuma ga Fahad yafito yana dauke da jakarshi se katifarshi a kulle.

Fuskarshi duk a kumbure take, jikinshi duk datti sannan ga sahun bulala awuyanshi da hannunashi. Kurama Fahad ido Malan yayi jikishi duk yayi sanyi, bayan sun karaso Vice ya kalli Fahad yace shiga daga ciki.

Hannu yabasu suka gaisa Malan yana fadin kushigo daga ciki mana. Vice yace kai bama se mun shiga ba, Malan yace haba ai bazamu tsaya anan ba, dan Allah kushigo. Zaune suke afalo Malan yasa Mama takawo masu ruwa dan ita bama tasan Fahad yashigo ba, dan yana shiga yayi part dinsu yana Kuka.

Bayan ta gaishesu ta tashi zata fita Vice yace ai Hajiya da kin zauna wajenku mukazo gaba daya. Malan yace to Vice Allah de yasa lafiya, dan ban gamsu da ganin da nayima Fahad ba, gashi kuma se gobe ne hutu yan Fedaral ne kawai zasuyi hutu yau.

Yanzu ma fitar da nayi zanje shago ne daga can inwuce in daukosu kuma se gaku? Gyara zama Vice yayi gaba daya kunyar sanar da Malan abinda danshi yayi yake, amma babu yanda ya iya haka ya zayyane mashi duk abinda yafaru har zuwa hukuncin da makaranta ta dauka, kuma ya nuna masu hoton daya dauka.

Kuka Mama tasa tana fadin wallahi bazan taba yafe maki ba, muguwa azzaluma me bakin hali, gaba daya kin gama lalata mani yarana. Malan da zufa ce kawai take zubo mashi ya daka mata tsawa yana fadin tashi kibar wajen nan.

Saurin tashi Mama tayi tana kuka ta nufi bangaren su Fahad. Malan ya dade beyi magana ba, da kyar ya iya bude baki yace Innalillahi wa inna ilaihirraji'un. Sosai yabama sauran mutanan da suke falon tausayi.

Vice ne yace Malan kayi hakuri, nasan kai babban Malami ne, asalima karike mukamin Principal, nasan kasha haduwa da irin wadannan laifukan har ma da wadan da suka fisu, na tabbata ko kai ne iyakar abinda zakayi kenan.

Kayi hakuri dama haka duk wasu iyaye suke fuskanta musamman idan akace sun tara zuri'a, dole se sunyi hakuri da duk wata kaddara tazata fado masu. Inde mutum yana da yara dole seya hada da addu'a musamman yaran zamanin nan.

Tunda har Allah yasa yana SS 2 abinda zefi ka maidashi Day, koba komai kullum agabanka ze tashi kuma ya kwana agida, zakafi samashi ido fiye da idan baya gabanka, kuma kada kace zaka dauki mummunan mataki akanshi.

Domin irin wadan nan ba'a juya masu baya alokacin da suka kauce hanya, alokacin ma yakamata afi jawosu ajiki, idan Allah yaso sekaga sun shiryu, amma idan aka watsar dasu wallahi abinda zasuyi se yafi na baya.

Yawanci manyan barayin da muke dasu da yara masu shaye shaye idan kaduba karuwar lalacewarsu hada sakacin iyayensu, domin wani Uban daga inda akace ya kama danshi da wani mugun hali shikenan se ya dora mashi karan tsana.

Wasu korar yaran suke daga gidansu, wasu kuma shikenan daga ranar yaran sun zama abun kyama da kyara agaresu, gaba daya se su fara nuna masu banbanci tsakaninsu da sauran yaran gidan, ko shawara za'ayi basa kiran su.

Gaba daya se kaga sun zare hannunsu daga kansu, idan karatu ne bazasu tsaya su kula da sunje ko basu je ba, yawanci Iyaye mata sune kadai zaka samu suna janyo masu irin wannan hali ajiki, domin Uwa tafi Uba tausayi.

Daga irin haka kuma se asaka ma yaron wani tunani na daban, idan be shan wani abun ma dalilin banzatar dashi da akayi se yaje yakara haduwa da wasu mugayen abokan sukara koya mashi wani abun.

Kuma shima daga lokacin daya fahimci an cireshi daga layin sauran yara shikenan shima baze kara shiga cikin sauran 'yan uwanshi yazauna ba, daga lokacin ze fara kebe kanshi, se kuma tunani kala kala yarika shigarshi.

Kadaici se yafara damunshi, idan ba'ayi sa'a ba yafara shan kwaya shikenan kuma ya gama kashe kanshi, ga damuwar abinda aka mashi, ga kuma aikin kwaya, shikenan se kaga yaro ya kangare, daga karshe idan be koma babban barwo ba, to kwakwalwarshi zata tabu.

Kaga duk abinda yaje ya aikata dan gidan wa za'ace? Dole akira sunan mahaifinshi ko mahaifiyarshi, kuma har ya mutu baza 'a cireshi daga cikin gidansu ba. Haka zalika duk iyayen daka ga wai yaransu yana cikin irin wanna halin sun ce sun manta dashi wallahi karya ne.

Kai koda tafiya yayi yabar gidan har abada bazasu taba iya cireshi daga zuciyarsu ba. Kaga kuwa babban rigakafin da yakamata iyaye suyi shine surika kokarin jawo yaransu masu irin wannan hali ajiki.

Hakan zesa yaro yarika jin kunyar aikata wani abu marar kyau. Kasan Allah, akwai wani abokina dana sani Allah ya hada yaronshi da wasu mugayen abokai, haka suka koya mashi shaye shaye na fitar hankali.

Kasan matakin daya fara dauka daga lokacin daya kama yaron yana shaye shaye? Makarantar da yakeyi yafara cireshi, dama makarantar kwanace, Day ya maidoshi, kuma duk inda zeje tare yake zuwa dashi matukar baya makaranta.

Wani lokacin ma shi yake aike zuwa wani wajen, kuma koda yaushe suna tare agida, haka idan dare yayi baya barinshi yafita yawo idan ma shima Uban baze zauna gida ba, haka yake jan yaron sufita waje.

A hankali se yaron yadena shan abubuwan dayake sha, domin koda yaushe suna tare da uban, kuma gatan da yake nuna mashi ada seya linkashi, idan wata shawara zeyi to seya sakoshi aciki.

Koda sauran yaran kowa yafadi ra'aryinshi sekaji Uban yace ajira wane yazo. Irin wannan abubuwan da ake mashi sune suka kara sashi farin ciki, kuma yaga babu wanda yake tsangwamarshi saboda yana shaye shaye.

 Wallahi Malan cikin ikon Allah wannan mutumin yana addu'a kuma shima yana kokari wajen temakon yaron Allah yasa yaron yashiryu.

Yanzu haka maganar da nake maka yaron ya gama karatun degree dinshi a fannin likitanci, idan ba an fada maka ba bazaka taba cewa ko goro yasha ba. Kaga me yajawo haka? Saboda iyayenshi basu banzatar dashi ba.


To bare kuma kai, duka Fahad shekararshi nawa? Kasan wani lokacin kowa da irin yarintarshi, wasu manyan mutanan idan da za'a tono yarintarsu wallahi abun baze fadu ba, dan haka ina rokon ka kada kabari zuciya ta debeka kayanke danyan hukunci wanda ze saka danasani nan gaba.

Yana da kyau ka nuna mashi fushinka, amma dan Allah kada kazamo kamar sauran wasu iyayen. Ka kokarta kayi da jikinka, kamika ma Allah sauran, Allah yana karbar addu'ar bawansa aduk lokacin da yarokeshi.

Allah yashirya mana zuri'a baki daya, kuma yabamu ikon tarbiyantar dasu. Se alokacin hawaye suka zubo ma Malan, sosai yake kuka kamar karamin yaro, haka suka yita bashi hakuri. Wayarshi ce tayi kara, yana dubawa yaga wani malaminsu Fatima ne yakirashi.

Hannu yasa ya goge idonshi sannan ya daga wayar, bayan sun gama gaisawa Malamin yace dama yarane sukaga haryanzu ba'azo daukarsu ba, kuma sauran yaran duk sun tafi. Malan yace dan Allah Malan kamun wani temako, bansani ba ko suna da kudin mota a hannunsu.

Nima har nashirya zan taho wata matsala ta tsaidani, amma idan suna da kudi ka temakeni kadorasu a motar Mashi, nasan idan sukazo zasu iya kowa kansu Mani. Malamin yace badamuwa, idan ma basu da kudin za'a basu. Malan yace to nagode.

Kallon Vice yayi yace nagode da irin bayanin da kayi mani. Kuma tabbas koda nine nasamu irin wanna case din to irin matakin da kuka dauka zan dauka, babu abinda zance sede ince Alah yasaka da alkhairi, kuma Allah yashirya mana yaranmu.

Kuma insha Allah zanyi amfani da shawarar daka bani. Tashi sukayi suna fadin Allah ya tsare gaba, godiya Malan yayi masu suka tafi. Kasa fita yayi haka ya koma ya kwanta yanajin wani bakin ciki yana shigarshi.

Dama shi yadade da zargin Fahad yana shan wani abu, sede yanda Mamarshi ta dage akan babu abinda yakesha hakan yasa ya kyaleta. Tashi yayi ya nufi dakin Mama domin yaga Fahad din.

Yana saka kafarshi afalo yaji Mama tana kuka tana fadin, haba Fahad, yanzu seda kajawo mani abun kunya ko? Duk irin gargadin danayi maka baka jiba ko? Ai na dauka tunda Farouk ya kamaka kana shaye shaye yazo yafada mani nayi maka fada kuma nace bazan fada ma Malan ba nasan yana iya tsanarka zaka dena.


Ashe daka koma makaranta ma se abun yafi na da, yanzu ya kakeso inkasance acikin unguwar nan? Kasande ba kai kadai bane dan garin nan a makarantarku, karewa ma hada dan unguwarku a makarantar.

Kuma dole gobe wannan maganar ta fasu a garin nan har ma da unguwar nan, shikenan kasani jin kunya,ko wata sabga akeyi bazanji dadin shiga cikin mutane ba, duk inda nashiga haka za'a rika nuna ni.

Dama kowa yasanni da iya yada magana idan aka samu yaron wata yayi wani abun, se gashi yau Dana ne aka kama wai yaje sata, kuma yana shaye shaye, daga karshe kuma an koreshi daga makaranta.

Haba Fahad baka kyauta mani ba, meyasa duk yanda nake kokari wajen kareku daga fadan Malan baka gani? Bani da wani buri agidan nan kamar inga cewa kune asaman kowa, kuma kune nagaban goshin Malan, amma kai baka gani.

Dama yanzu Malan baya sona, kaga yanzu ka kara debo wata mganar shikenan komai akai na ze kare, duk yanda naso ace yaran Inne sune suke cikin irin halin da kuke amma abun ya gagara.

Ka duba lokacin daka jima Faisal ciwo, saboda in kareka daga fadan Malan nasa shi yace faduwa yayi, ko lokacin da Malan yace mun yana zarginka tabbas nima alokacin naga alamun shaye asheya a wajenka, amma saboda banason laifin ka haka na rufe ido nace banyar da ba.

Kalli yanda aka maida maka jikinka kamar wani jaki. Cikin kuka Fahad yace dan Allah Mama kada kibari Malan yakara dukana, wallahi jikina ciwo yakeyi, bulala 20 akayi mana, kuma da katuwar dorina.

Mama tace niyanzu banida bakin magana, amma insha Allah baze duke ka ba, sede nasan tabbas daga yanzu kai ne ja baya acikin yaranshi, yanzu Faisal ze amshe ragamar gidan shida Fatima.

Fahad yace shikenan yanzu Malan baze kara sona ba? Mama tace bazan taba bari hakan yakasance ba, kamar yanda Inne ta lalata mani kai, nima sena saka tsanar Faisal da Fatima a zuciyar Malan.

Idan yana tunanin kai kadai ne wanda yake shaye shaye, to shima Faisal din zamu san yanda zamuyi Malan yasamu wani abun ajakarshi, kaga koya rantse mashi baya sha baze yarda ba. Ita kuma Fatima nasan sharrin da zan ja mata.

Ka kwantar da hankalinka babu abinda ze faru da kai, idan ma tsanar ce to sede ya tsaneku ku 3. Tashi kaje kayi wanka kazo kaci abinci kasha magani se in shafa maka magani ajikinka.

Murmushin takaici Malan yayi seya fasa shiga dakin kawai ya juya ya koma falonshi, aranshi yana tunanin wane irin hali Hauwa take dashi haka? Mace kamar wadda bata da tunani, ashe dama tasan Fahad yana shaye shaye amma ta boye mashi.

Shima Farouk ya sani amma yayi shiru. Ko dayake ba laifinshi bane, dama dole ita ze fara fada mawa, kuma duk umarnin da tabashi dole yabi. Amma tunda haka ne ze kyaleta dashi.

Kuma baze taba yimata maganar Fahad ba, idan kunya ne se ta fishi jin kunya tunda itace take shiga cikin mutane, shikam yasan babu wanda ze tareshi da maganar, idan ma za'ayi maganar sede bayan idonshi.

Kuma shi dama bame shiga cikin jama'a bane. Murmushi yayi daya tuna sharrin da takeso tajama Faisal da Fatima, aranshi yace wannan kuma tsakininki da Allah ne, domin kin cutarsu dasu da yawa, kuma Allah baze barki ba.

Idan kuma kina tunanin Malan din da kika sani ne ada wanda baya bincike to kin makaro, Allah ya kaimu lokacin da zaki ja masu sharrin, dadin abun ma Faisal baze dawo hutu ba, Fatima kuwa da nayi aure tabar dakin ki.


Se wajen azahar su Fatima suka iso, Farida da gudu tashiga gida tana kwala ma Mama kira, fitowa tayi da fara'a tana fadin ga yan makaranta, rungumeta Farida tayi tana fadin wai meyasa Malan beje ya dauko mu ba? Mama tace kede muje kicire kayanki.

Baki yayi shiyasa. Fatima ce tashigo tana goye da jaka, sosai takara kyau, kamar ba makaranta takeyi ba, tayi haske tayi kiba, kyanta seya kara fitowa, lokacin data shigo Mama harta juya tajiyo sallamarta.

Juyowa tayi tare da amsawa, sakin baki Mama tayi tana kallonta, gani tayi tazama cikakkar budurwa, gashi tazama me kyau, kamar ba a kauye take ba, jikinta kanshi yayi kyau se sheki yakeyi.

Risnawa Fatima tayi tana fadin Mama ina wuni? Seda ta maimata so biyu sannan Mama ta farga da maganar da take mata, daure fuska tayi tace lafiya. Juyawa tayi tashige ciki gaba daya bakin ciki ya gama kamata.

Saboda ba zaka hada Fatima da Farida ba awajen kyau, ita Faridar ma duk seta rame takara duhu. Wucewa Fatima tayi dakinsu domin ta cire kayanta tayi wanka, Farida kuwa tana dakin Mama, sosai Fatima tayi bakin cikin rashin dawowar Faisal, tasan wannan hutun zata yishi ne kawai amma bazataji dadin komai ba.

Amira ce da Saddik suka shigo da gudu, kai tsaye dakinsu Fatima suka shiga, suna shiga Amira ta rungume Fatima tana dariya, Fatimar ma dariyar take tana fadin Amira, Saddik yace Fatima an girma, hararshi tayi tace wallahi ka rai na ni.

Dariya yayi yace to sannu da zuwa, ai de mun rigaku dawowa. Fatima tace muma de ai gashi mun dawo. Amira tace ina Yaya na? Fatima tace ai Yaya baze dawo ba se hutun sallah. Turo baki Amira tayi ta saki Fatima ta juya tana kuka.

Dariya suka sa mata,Saddik yace yau akwai rigima, kinsan Mama tace tun jiya duk abinda aka bata seta ragema Yaya, yanzu haka bataci abinci ba wai shitake jira, ganin ba taji karar mota ba yasa tace inzo in rakata wai tsoron Mamar su Farida takeyi.

Fatima tace nima wallahi duk banajin dadin rashin dawowarshi. Saddik yace ai se hakuri bara inje inji dramar da takeyi, har yanzu yarinya tana SS 2 amma batasan ta girma ba. Fatima tace Amirar ce yarinya? Kasan de ai ta girmeka. Saddik yace ada ba. Dariya suka sa yafita.

A can gida kuwa rigima sosai Amira takema Mama wai Yaya bedawo ba, se kuka takeyi, da Mama tagaji da lallashinta ta dauko bulala tace wallahi ko kimun shiru ko inzaneki, wai ke se yaushe ne zakisan kin girma? To Yayan baze zauna yayi karatu ba? Tashi ki bani waje.

Baban Saddik ne yashigo yana fadin haba Maman Saddik, ya zaki hada mata zafi biyu, amma de kinsan tun jiya take dokin dawowarshi ko? Mama tace tun jiyan inda kafada mata gaskiya ai da yanzu bata ji ciwo sosai ba, amma ka biye mata kana fadin yau ze dawo, ai gashi nan bedawo ba. 

Baba yace taso Mamana Yaya zedawo daya gama karatu, kuma ai zedawo hutun Sallah kinji? Haka yayita lallashinta da kyar ta hakura.


Zaune suke gaba dayansu a Falon Malan, bayan sunci abinci sunyi sallah suka shigo gaishe shi dan tunda sukazo basu ganshi ba. Fahad kuwa kasa fitowa yayi dan ko abincinshi sede Mama ta ai ka mashi dakinsu na can baya, datace yafito yace baze fito ba.

Bayan sun gama gaisawa,  Malan ya tambayesu ya makaranta, sukace lafiya lau. Tambayarsu result dinsu yayi, Fatima ce ta fara mika mashi nata, gaba daya ta cinye subject dinta, duka excellent.

Farida kuwa da kyar ta mika result dinta, murmushi Malan yayi ganin irin result din data kawo mashi, kallonta yayi yace tabbas idan kika cigaba da kawo mani irin wannan result din, to bazaki wuce wannan ajin ba.

Kinsan de halin makarantarku, basa barin mutum yawuce haka zasuyi ta mashi repeating, to kisani hukunci daya zan yanke maki, matukar wannan karon baki wuce SS 1 ba, to kinbar makarantar kenan, zan maidoki Day, idan kina fita kinashan rana da tafiya zaki fi maida hankali. Kutashi Allah yayi maku albarka.


Lokacin da dare yayi haka Malan ya nufi dakin Fahad, lokacin Fahad yana zaune ya gama cin abinci ya kunna sigari yana sha, tunda Malan ya doshi dakin yafara jin wari, yana isa kofar dakin ya daga labulen, ido biyu sukayi da Fahad.

Da sauri Fahad ya wurgar da guntuwar sigarin ya mike tsaye, hannu Malan yasa ya kamo hannunshi tare da take sigarin suka fito waje. Kai tsaye falonshi suka nufa Fahad se zare ido yakeyi, dan tunda yadawo basu hadu da Malan ba.

Zaune Malan yake asaman kujera yayin da Fahad yake duke agabanshi. Kallon shi kawai Malan yakeyi, duk ya rame yayi yayi baki, bakinshi ya dafe kamar wanda ya dade yana shaye shaye.

Fahad! Malan yakira sunanshi, kasa dago kai Fahad yayi, Malan yace irin rayuwar daka daukarma kanka kenan ko? Yanzu wace riba kaci da aka koreka daga makaranta? Shikenan sauran yaran da kuka shiga makaranta tare sun wuceka.

Haka zasu gama karatunsu su zama wasu manya kai kuma ka lalata rayuwarka. Kana karaminka amma kasan kasha abinda ze bugar da kai. Shin kana sallah kuwa? Kara dukar da kai Fahad yayi, Malan yace gaba daya ka zanca.

Kuma ni bazan duke ka ba kamar yanda kake tunani, sede zan baka shawara kayi kokari kabar wannan halayyar da kakeyi, kada ka biye ta Mamanka, domin bata baka shawara me kyau.

Idan aka koma hutu zan maidaka Day kuma zanyi kokari su daukeka a SS 3, nasan ba'a gama registration na WAEC da NECO ba, idan suka yarda se inyi maka kazauna kasamu kayi jarabawarka kaga seka gama tare da sauran 'yan ajinku.

Idan kadena duk abubuwan da kakeyi zakaji dadin rayuwarka nan gaba. Kuma inaso ka koma islamiyar da kukeyi ada, dan nasan tunda kuka shiga makaranta kadena zuwa, amma Mamar ku tana fada mani kullum kuna zuwa. Tashi kaje, amma duk ranar dana kara ganinka kana sha mani sigari ko wani abu agida to aranar zakaga fushina. 

Tashi Fahad yayi rai abace yafita,  danshi maganganun Malan ma bata mashi rai sukayi, taya zece yadena biye maganar Mama, bayan yanzu ita kadai take son shi. Daki ya koma ya dauki wani abu kawai yazo ya fice. Yazo fita ya hadu da Farida, dariya tayi tana fadin Yaya yaushe ka dawo? Harara ya buga mata, dariya takara sawa tana fadin Yaya kalli wuyanka sahun duka waya dokeka? Kafa yasa ya harbeta yana fadin zanci uwarki wallahi. Ihu Farida tasa yafice yabarta.


Tun daga wannan rana Fahad yade zaman gida, kafin kace me labarinsu ya baza gari, mutanan unguwa se gulma sukeyi, duk yaron da yayi ma Fahad maganar korarshi seya dokeshi, haka yarika fasama yara baki.

Ganin irin illar da yake masu yasa suka fara tsoranshi, sede suyi maganar bayan idonshi, amma idan yafito babu me mashi magana. Sam baya zama gida, haka kuma baya dawowa da wuri. Maganar shaye shayenshi kuwa se abinda yaci gaba, domin inda suke haduwa da sauran abokanshi idan yadawo hutu can yake zuwa.

Gaba daya Mama tshiga damuwa, lokaci kadan duk ta rame, ta rasa abinda yake mata dadi, gashi Malan beyi mata maganar Fahad ba bare tasan yanda za'a bulloma abun, gashi Fahad baya zama gida, idan yadawo to abinci zeci.

Gashi yanzu seyaci abincin mutum 3, saboda shi yanzu takara yawan abincin gidan, dan idan be koshi ba seta sa Fatima ta dafa mashi wani abun, ita ko Fatima ba ruwanta dashi, dama can bata shiga harkarshi.

Farida ce kawai take shiga harkarshi, itama tunda yayi mata wani bugu tadena mashi magana. Gashi yanzu iskancinta ya kara yawa, kusan kullum tana dakin me shago, yanzu abubuwan da sukeyi ma yafi na da. Fatima so biyu tana kamata tafito daga dakinshi, amma sanin halin Farida dana Mama yasa taja bakinta tayi shiru, tunda taga Mama bata fadama Malan laifin da Farida tayi amakaranta ba wancan karin.

Malan kuwa ya saka ma Fahad ido, ganin Malan yaki ma Mama magana yasa ta yanke shawarar ta samehi da maganar, shiko Malan hidimar bikinshi kawai yakeyi. 


Bayan su Fatima sun dawo hutu da kwana 4 yakirata yace tashirya ze kaita wajen Inne tayi hutu. Saboda mamaki kasa magana tayi, wani farin ciki ne ya kamata.

Haka taje ta hada kayanta taje ta fadama Mama, wani kulu kulun bakin ciki ne ya taso ma Mama, wato yanzu Malan ya canza, har ma hutu ze kai Fatima. Tana murnar aiki zemata sauki shine dan bakin ciki ze dauketa.

Farida ma sosai taji haushi, yanzu Fatima birni zata tafi gidan 'yan gayu amma banda ita, jitayi kamar tace itama zataje, amma saboda bakin ciki yasa tayi shiru. Ganin Mama batayi magana ba yasa Fatima ta tashi ta fita.

 Mama kuwa jin Malan yashigo yasa ta tashi domin tana so tayi mashi maganar Fahad. A bincinshi ta kai mashi bayan ta zuba mashi ta zauna, kallonta yayi dan yasan akwai magana tunda tazauna, dan data kawo mashi abinci take fita.

Shiru yayi yana cin abincinshi, ganin bazeyi magana ba yasa tace Malan wai naji shiru tunda Fahad yadawo bakayi mani magana ba. Murmushi Malan yayi yace maganar me zanyi maki Hauwa? Ke da kika rigani sanin halin da Fahad yake ciki ai kece yakamata ki fara mani maganar.

Uhmm, Hauwa kenan, a tunaninki duk abubuwan da kikeyi agidan nan bansa ni ba? Wato kece kika hana Farouk ya fada mani halin da Fahad yake ciki, saboda bakiso nayi mashi fada.

Yayi kyau, ai ko yanzun da aka koreshi banyi mashi fadan ba, na barki dashi tunda zaki iya kula dashi, nide amatsayina na Uba zanyi kokarin sauke duk wani nauyi da yake kai na, kuma zan kara sama mashi wata makarantar yaje ya zana jarabawa kawai.

Sede a Day zan sakashi, kuma zanyi kokari wajen nema mashi duk abinda yakamata, idan ya tsaya yayi karatu yatemaki kanshi, sauran kuma nabar maki, tunda kina tunanin kece kikafi iya kula da yara ba se kinyi masu fada ba.

Mama tce ai shikenan, dama na dauka bazaka nema mashi wata makarantar bane, amma kasani wallahi irin wannan ban bancin da kake nunawa Allah seya tambayeka, yanzu gaba daya baka son yarana.

Gashi dan munafurci ma wai Fatima zaka kai hutu Katsina, wannan ai salon kwadai ne, dan kaga Uwarta tana gidan masu kudi shiyasa zaka kaita. Da can meyasa baka taba kaisu ba tsawon shekaru da dama? To yaran nawa daka tsana insha Allah sune zasu daukaka.

Malan yace dan Allah tashi ki bani waje tun kafin rai na ya baci, ba zakisan kin shiga damuwa ba senan gaba, kin tsani wasu kina nunama yaranki soyayya, kuma zakisan cewar kin dorasu akan turba marar kyau.

Tashi Mama tayi tana fadin kai zaka ga abun kunya agidanka, amma wallahi yarana sunyi gaba. Mugu kawai, murmushi Malan yayi aranshi yana fadin duk tsiyarki wallahi bazan sake ki ba, domin sakaran namiji ne yake sakin matar data cuceshi.

Kina nan tare dani, bazan sake ki kibarni da bakin ciki ba, yanda kika jawoshi gidan nan haka zaki zauna kishashi.🤣


***** *****

Washe gari da safe haka Malan ya tafi da Fatima su Farida kamar suyi hauka saboda bakin ciki, Fatima kuwa ko sallama batayi masu ba, dan taga Mama tun jiya take masifa. Haka suka tafi zuciyarta tana me cike da farin ciki.

A mota Malan yace insha Allah shima Faisal zanyi kokarin zuwa makarantarsu lokacin da za'ayi bikin yayesu, domin ban taba zuwa mashi visiting ba,duk da ba laifina bane, idan naso zuwa se Hauwa ta hanani. Fatima nasan akwai abubuwan da Hauwa tayi maki kiyi hakuri, kuma daga yanzu zan rika barinku kuna zuwa wajen Inne.

Kafin ki dawo ma zaki samu sabuwar Inne, kuma dakinta zaki koma da zama. Kallonshi Fatima tayi, yace E aure zanyi, bakiga na gyara dakinsu Faisal ba? Dukar da kai tayi batace komai ba. Dan ita har yanzu jitake kamar de Malan ba gaskiya yake fada mata ba, duk lokacin da ta tuno irin dukan da yayi masu se tsanarshi takara shiga zuciyarta, shiyasa kome zeyi mata bata farin ciki, yaune kawai tasan tayi farin ciki.

Wai sabuwar Inne, ai yanzu babu wata mace da zata kara yarda da ita amatsayin matar Malan, domin tasha wahalar Mama, dan haka bazata kara yarda da duk matar da Malan ze kawo ba, idan ada tana yarinya anyi mata abubuwa yanzu babu macen da zata kara dukanta. Allah yakawota lafiya,wai zeje ma Yaya visiting, dama can rashin sone yasa baya zuwa amma kaji zeje wai laifin Mama, kawide dan yaga yanzu mun girma shiyasa yakeso yajawo mu ajiki,  ganin Malan ze dameta da surutu yasa ta kwanta.



A kofar gidan Malan ya ajeta, domin yasan gidan Alhaji, kuma yace ta gaishe mashi da Inne, sannan tace mata tayefe mashi. Ita de Fatima ta amsa ne kawai, haka tafita tabarshi dan har yanzu bata saba dashi ba.


Ihun su Khairat da Ansar ne yasa Inne tayi saurin fitowa. Tsayawa tayi tana kallonsu yanda suka rungume Fatima, kara murza idonta tayi dan ta tabbatar da abinda take gani. Da gaske itace. Ya akayi Malan yabarta tazo? Kuma ai Fatima batasan gidan nan ba.

Matsawa tayi ta kamota tana murmushi tace da gaske kece Fatima? Fatima tace nice Inne, kuma tare mukazo da Malan, amma yatafi. Inne da ta cika da mamaki tace mushiga ciki.


Bayan Fatima taci abinci ta bama Inne labarin abubuwan dasuke faruwa agidansu, hada labarin abinda Farida tayi amakaranta, kuma ta bata labarin abunda su Fahad sukayi har aka koreshi, kuma ta fada mata auren da Malan zeyi. Sosai Inne tayi mamakin Fahad.

Dama kuma duk cikin yaran Mama shine yakeda wata zuciya, kuma shine tafi sangartawa. Inne tace Allah ya kyauta kuma ya shiryasu, ashe su Hauwa za'a samu wata kishirya kuma. Fatima tace yanzu Inne kozaman gida Fahad bayayi, gashi da anyi mashi abu yayita zagin mutum, bakiga irin dukan da yayima Farida ba.

Inne tace kede ba ruwanki dashi, Fatima tace ni dama bana shiga harkarshi, Inne tace ina Farouk fa? Fatima tace Allah sarki Yaya me kirki ba, yana makaranta wannan karon bezo week end ba. Inne tace ai zan samu numbershi ince yazo mugaisa, haka sukayi tafira, abubuwa kala kala Inne takawo ma Fatima, da yamma kuma suka shiga kitchen tare.

 Lokacin da Alhaji ya dawo shima yayi mamakin zuwanta, anan Inne tabashi labarin da Fatima ta bata, hada maganar auren Malan, sosai shima yayi mamaki, addu'a yayi shima yace Allah yashiryasu. Allah yasa kuma su Fatima suji dadin matar daze aura.


**** ****

A na gobe daurin auren Malan Farouk yazo gida sunyi hutun mid semister, dan yanzu suna a second semister ne, sosai yakara girma, gashi yakara hankali, bayan sun gaisa da Mama yaci abinci take fada mashi halin da ake ciki.

Sosai yayi bakin cikin abinda yafaru, yace kin gani ko Mama, shiyasa tun wancan lokacin naso kibari afadama Malan, domin Fahad yana jin tsoron Malan yanzu ga irin abinda yajawo ma kanshi.

Mama tace dan Allah kada ka bata mani rai, shege me hali irin na Ubanshi, abun bakin ciki yasamu Dan uwanka amma ka tsaya kana fadar maganar banza, to de abun kunya ba akan Fahad aka farashi ba.

Kuma ni nasan wadda tayi mashi haka, kasa ido kayi kallo wata rana akan yaranta asirin ze koma. Farida tace Yaya yanzu kana dinkin hular? Hararar ta yayi yana fadin bansani ba, sakarai ya kawai, inda Fatima ta fiki kenan.

Kina kallon mutun bazaki iya mashi sannu da zuwa ba bare ki gaisheshi, seyanzu zaki tambayeni abinda be shafeki ba. Mama tace tashi kabani waje, Fatimar taje tayi ta finta seme? Ai de har abada bazaka canza Farida ba.

Kuma Fatima bazata taba zamowa jikinka sosai ba, domin rabin jininka ce, Farida itace take cikakkar jininka. Fatimar da kake fadi yanzu ma tana ajen Uwarta, kaga kuwa dole ka rungumi Farida tunda a inuwa daya kuke zaune.

Sakarai wanda baya kishin yan uwanshi da ni kai na, wallahi idan kace irin wannan halin zaka kawo mani zakasha wuyata, domin bazan lamunci karika tsanar yarana kana fifita wasu banzaye can ba.


Tashi Farouk yayi rai abace, saboda halin Mama yasa ko week end bayason zuwa, mutum yadawo daga makaranta yana farin ciki amma daga zuwanshi ko hutawa beyi ba an fara zaginshi, ya kamata ace yanzu tadena zaginshi agaban Farida.

Shiyasa da akayi hutun waccan semister yayi zamanshi makaranta, dan dinkin hularshi yafiye mashi yazo gida, seda ana saura kwana 3 adawo sannan yazo gida. Dakinshi ya wuce yaje yayi wanka lokacin Malan yadawo yashiga suka gaisa.


Sosai Malan yaji dadin ganin Farouk dan duk wanda yaganshi seyaga nutsuwa atare dashi, komai cikin nutsuwa yakeyi, anan Malan ya mashi maganar Fahad kuma yace meyasa be fada mashi ba. Farouk yace kayi hakuri Malan.

Naso infara fada maka se Mama ta hana, Malan yace ai shikenan, amma daga yanzu duk abinda yake faruwa banaso karika boye mani, nafiso kome zaka fada kataho wajena muyi magana, kaga kaine babba idan ba ka sakin jiki dani kana fada mun komai  ai sauran yan uwanka bazasuyi koyi da kai ba.

Farouk yace haka ne, kuma insha Allah zan gyara. Malan naga anyi mana dakuna, Allah yasaka da  alkhairi mungode. Malan yace bakomai, wancan dakin ma gobe za'a kawo amaryata. Farouk yayi murmushi yace Malan aure zakayi? Malan yace ko na tsufa? Farouk yace a'a, amma Mama bata sani ba ko? Malan yace zata sani amma se an kawota. Farouk yace Allah yasa alkhairi.

Malan yace amin, kaima Allah yayi maka albarka, nan Malan yafada amshi ya bude shago, haka suka yita fira, daga karshe yajashi suka fita dan yaga shagon.

***** ****

Washe gari wajen karfe 12 Malan yashirya cikin babbar riga se kamshi yakeyi ko sallama beyima Mama ba haka yatafi dauri aure, Mama bata san wainar da ake toyawa ba, hatta da mazajen unguwar sunje daurin auren amma babu wadda ta fada mata.


Salamatu da Momyn Teema sosai wannan aure yayi masu dadi, Maman Sultan ma batasan zeyi aure ba dan mijinta baya gari.


Bayan angama daurin aure kowa ya nufi wajen da za'a ci abinci, domin suna gamawa zasu dauki amarya su taho da ita, dan yanzu andena daukar amarya da dare. Kowa yaga Malan yasan yana cikin farin ciki. Bayan sun gama reception sukayi la'asar sannan aka basu amarya.


Farouk ne yashigo dakin Fahad domin tun da yadawo basu zauna dashi ba, dan har yanzu Fahad yana jin haushin Farouk, ko magana baya mashi, har Mama seda Farouk ya fada mawa, amma babu abinda tace se cewa tayi tunda kaima ka tsaneshi ba dole ze kyaleka ba, jin abinda Mama tace yasa Farouk ya kyaleta.

Warin wiwi yaji daga bandakinsu, fita waje yayi yana jiranshi yafito. Fahad yana fitowa ya jawo dakinsu dan fita zeyi. Koda yaga Farouk be kalli inda yake ba haka ya nufi hanyar fita.

Farouk ne yace wai kai Fahad meyasa bakada hankali ne? Yanzu dan rashin mutunci acikin gida zaka rika mana shaye shaye? Duk irin abinda yafaru da kai be zamar maka darasi ba? Yakamata ace kaji kunyar abinda ka aikata har yasa aka koreka daga makaranta.

Wallahi inda nine kai daga ranar da aka koreni daga ranar nabar shaye shaye, domin shine silar jefani cikin halin da nashiga. Amma dayake kai ba kada tunani shikenan seka dawo kabude sabon iskanci agida.

Fahad yace na bude dan Ubanka, ai gidan banaka bane, nima ina da gado aciki, kuma naje nasha wiwin, idan dakinka nashiga nasha se kayi mani mgana. Da aka koreni kuma ai ba kai aka kora ba zakazo kana zagina banza kawai, wallahi yanzu na tsaneka.

Daukeshi da Mari Farouk yayi yana fadin ni kake zagi? Dun kule hannu Fahad yayi ya kaimashi naushi a hanci seda jini ya fita.

Haka suka fara kokowa suna ta dukan junansu. Farida ce ta taho kiran Farouk, ai tana ganin an danne Fahad a akasa ana duka ta ruga da gudu tana kiran Mama. Da kyar Fahad ya ture Farouk lokacin daya watsa mashi kasa a ido.

Yana tashi ya hangi wani karfe babu bata lokaci yadaukoshi ya caka ma Farouk aciki, dede lokacin da Mama da Farida suka zagayo, hannu Mama ta dora akai ta fasa ihu tana fadin Fahad bakada hankali.

Farouk kuwa tuni ya sume awajen. Kuka kawai Farida takeyi, haka Fahad ya fice yana huci, yana fita yaga motoci suna parking akofar gidansu, ko kallonsu beyi ba yayi gaba, Malan da yake fitowa daga mota yabishi da kallo.

Mutanan unguwa se lekowa suke suna kallon masu kawo amarya, da gudu Mama tayi waje domin ta nemo wani yazo akai Farouk asibiti. Tana zuwa bakin gate ana shigowa da amarya se guda akeyi.

Tsayawa tayi tana binsu da ido, da Zulai suka fara hada ido, ko kallonta Zulai batayi ba haka suka wuce wasu mata suna fadin Suwaiba kin samu gida dankari. Daskarewa Mama tayi a wajen tana maimaita sunan Suwaiba abakinta.

Farida ce tafito da gudu tana fadin Mama wallahi jini se zuba yake a cikin Yaya, zubewa Mama tayi awajen a sume dan batama san abinda Farida take fadi ba. 


Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263

😘😘💋💋 Ina mika godiyata agareku, kucigaba da kasancewa dani. Love u all


Download Wani Gida Complete Book Here