Ga ubangijin talikai daya bani ikon rubuta
wannan ta'kaitacan rubutu kan MATSALAR
JINNI. Ubangiji yadda kabani ikon farawa kabani
ikon kamalawa.Sa'kon godiya ga daukacin member na group d'ina MATA MASU AJI. Ubangiji ya 'kara had'a kawunanmu amin.



SADAUKARWA.
Gareku bazan manta karamcinku ba.
Teemah Cool
Safdeeq Cool
Maryam Idris Katsina.
Jamila Umar Katsina.
Aina'u Jega.
YABAWA.
Taurari cikin NAGARTA (NWA).
Ummu Fadila.
Miss Hafcy
Meesha Luv
Aunty YBK.
Aunty Chuchu.
Addah Jabo.
Beneziratu Ammar Saje.


JINJINA GA 'DAUKACIN MASOYANA.
Kaduna.
Katsina.
Narasawa.
Gashuwa
Kebbi
Kano
Da sauran jahohi ubangiji ya kara mana 'kaunar juna.Sadaukarwata gaba d'aya ga
TAURARUWATA ita ce MAHAIFIYATA ubangiji ya bani ikon kyautatta maki.


************
GAMUNAN DAI.
Hassana Muhammad Kano.
Hassana Zakariyya Shahada Kano
Hussaina Garba 'Danlami Kano.
Hussaina Zamfara.
Hussaina Kaduna Shantaly.
Hussaina Gashuwa Munayshat.
************


1-3
Cikin matsanancin gudu take wuce tsaunika tare
da tarin bishiyu, taka 'kayoyi take amma hakan
baya d'aya daga cikin abinda ya dameta, burinta
kawai ta tseremasa daga mummunan nufinsa a
kanta, cikin rashin tsamani ta taka wata
'katuwar 'kaya mai tsanani kaifi. Take ta 'kwala
giggitaciyar 'kara hakan yai dai-dai da
farkawarta. Cikin hanzari tabi 'kafarta da kallo
abinda yai matu'jar tsorata ta. 'Kayar data taka
a mafarki gata a tafin 'kafarta ga jini na bin
'kafafunta cikin tashin hankali ta soma waige-
waige. Shiru garin babu motsin bil'adama sai
kukan karnuka da tsuntsaye. A hankali takai
kallonta kan 'kofar d'akinsu cikin sakan guda
cikinta ya bada wani sauti. 'Kuuuuuuuuuu.
Cikin tsoro ta dinga ja da baya tare da karanto
duk adu'ar data zo bakinta. Ta runtse idonta ta
jiran 'karasowar 'KADDARARTA saidai ga
mamakinta sai ta tsinkayi muryar Mahaifiyarta
tana fad'in "Najwa me kikeyi baki kwanta ba?
Cikin sauri ta bud'e idonta. Sai ta saki ajiyar
zuciya. Cikin azama takaiwa 'kafarta bahagon
kallo dansan nunawa mahaifiyarta. Abin mamaki
da tsoro babu ciwo babu alamunsa. Nan da nan
ta nemi nutsuwarta cikin kaucewa kwataragin
daya dumfarota tace "Innarmu farkawa nai".
Cikin d'aurewar fuska tace " ina d'ankwalinki?".
Nanfa ta kama kame-kame sabida bama dashi
ta kwanta ba. Cikin fad'a mara sauti tace " wato
Najwa bakya jin magana ko ke kullum baza
agaya maki kijiba, kwanciya kai a bud'e ke ba
gwanar adu'aba sai anyi magana kice antakura
miki ko?". Cikin gunguni tace "Mantawa fa nayi".
Cike da mamaki tabita da kallo tana jinjina
taurin rai irin nata.Cikin nutsuwa take tafiya tamkar mai tausayi 'kasa, saidai zuciyarta cike da rud'anin mafarkinta na jiya tana jin kodai tagayawa Husnah kotai shiru. Can wata zuciyar tace " Ke Najwa yanzufa zamani ya sauya mutum ba'abun yadda bane, wani zaimiki kwance- kwance yaji matsalarki kawai dan yaji dad'in falasawa. Wani kuwa dan yaji dad'in yimiki gorine. Ki ri'ke matsalarki a ',kar'kashin zuciyarki da sannu ubangiji zai miki maganinta. Saidai ki ri'ki adu'a. Cikin farin ciki tai na'am da abinda zuciyarta ta fad'a.Kamar daga sama akaimata salama" Assalamu alaiki Gimbiyar mata". Shaidar mai muryar ne yasa ta d'ago cike da murmushi tana kallinsa cike da so da kuma 'kauna. Sai taji kaf damuwarta ta wuce. Amma miskilar saita maze. Mustapha yai murmushi yana dubanta yace,
"Najwa ina zaki cikin ranar nan?, ta ya mutsa
fuska alamun gajiya tace "gidan yaya Maryam
zani mijinta baya nan zan tayata kwana zuwa
jibi". Cikin jin dad'i yace "kice kwana biyu muna
tare"?. Ta gintse fuska "ba lallai bane tunda
kasan ra'ayin Innarmu shine nata". Yai ajiyar
zuciya " shikenan Najwa sai munyi waya". Yana
fad'ar hakan ya juya idonsa jajjir cike da
sassarfa. Duk sai ya bata tausayi, to amma ya
yakeso tayi ? Yasani sarai mudun ta sami labari
rayukane zasu 'baci a haka ta 'karasa 'kofar
ruwa cike da kasala. Tun daga soro Walid yake
oyoyo. Tilas ta aro juriya ta tari fara'arsa suka
shiga gidan. Da fara'a yayarta ta amsheta suka hau wasa da dariya. Cikin zolaya tace 'ina kuwa MUS'AB?". Take fara'ar data aro ta gushe. Kai tsaye d'akin da take sauka ta wuce ta barta anan shanye da baki. Tanata bambamin fad'a. Tana shiga kiranwayarta na shigowa jaka kawai ta ajiye ta wuce kan kujera. Tana karar wayar a kunnanta suka saki ajiyar zuciya lokaci guda.
Cikin tausasawa yace "menene?" Kai tsaye ta
amsa masa "babu komai hubbynah hope (fat an)
ka'isa gida lafiya"?. "Ba wannan ke gabana ba
Najwa dalilin ajiyar zuciyarki nake san ji, tai gum
tana juya lamarinsa a ranta tasani kad'ai ko
muryarta yaji yana gane yanayin damuwarta,
bale kuma ga rabuwar da sukai. Jin shiru yayi
yawa ya kira sunanta. "Najwah!!!!!!" Yar cigar
jikinta ta tashi cikin kasala ta amsa. "Na'am
hubbynah". " please menene damuwarki?".
"Mustapha kaine damuwata, kaine abinda ke
sani damuwa, ina duba yanayin da muka rabu
inajin araina ban kyautaba. Kobaka cancanci
SADAUKARWA ........"Ya'isa Najwa kinci abinci".
Duk saitaji haushin kanta wato shi 'ko'karinsama
cikinta, gaskiya inta auri Mustapha zata ga
tarairaya. Shigowar Yaya Maryam yasa tai masa salama. Bai matsa da sanjin daliliba ya katse. Zuciyarsa cike da tausayin rayuwarsu cikin azanci yace,
"KADDARARMU CE a hakan.
Haka ta 'karasa kwanakinta gidan cike da takura
sabida rashin samun jin muryar abin 'kaunarta.
Ranar da Abdul zai dawo tafi kowa murna da
zumud'i tun safe taimata aiki ta had'a kayanta.
'Karfe hud'u ya dawo gida, 'karfe biyar Najwa
taiwa unguwarsu tsinke. Tana shiga layinsu ta
saki sassanyar ajiyar zuciya sabida hango
'kawarta da tayi cikin sauri ta tarbeta suka shiga
gida tana fad'ar ",bestyna miss u more" ( ma'ana nayi kewarki da yawa). Cikin murmushi wanda ya zama al'adarta suka shiga gida.Inna na ganinta ta ta'be baki "wuuuu! Najwa 'yar nema wato har kin gudo ko"?. Ta turo baki " dole in gudo Innarmu aita saka aiki ba godi bare na gode, kuma kanayi ana hantararka". Duk sukai dariya Husnah ta jata d'akinta suna shiga tace "Mus'ab yazo sau biyu bakya nan, ya nemi numbarki Inna ta aiko na bashi, hope ya kiraki?.
Next Mustapha ya bani sa'ko anjima in munje
makarantar dare zan baki". Tunda ta soma
magana sai yanzu Najwa tai murmushi jin an
ambaci Mustapha . Cikin zolaya Husna ta d'aka
mata duka tai waje, aikuwa a guje ta biyota
kafin ta kamata ta kyalle. Cikin dariya Inna tace
"sababbu kun dawo zaku adabeni".
Cike da haushi ta cire d'ankwalinta ta suri buta
zuwa kewaye (band'aki), Inna kawai ta tsaya
taga gudun ruwanta, saidai bata da alamun
tsayawa ta daura. Cikin hargagi ta daka mata
tsawa." Keee! Najwa ina kalabinki? ('Dan kwali)
cikin basarwa tace "zan d'aura bari in fito". Bata
jira cewartaba ta shiga abinta. Mamaki ya kashe
Inna kwata-kwata Najwa bata jin tsoran fad'anta
mudin akan saka kalabine ko batun Mustapha
tun bata damuwa da lamarin harta soma
damuwa. Tana fitowa ta tareta da balbalin fad'a "wato ke Najwa bakyajin magana ko? Nahanaki zama babu kalabi kin'ki ji ko' uwa uba shiga bayi
babushi, waikin manta band'akine matattarar jinu amma kike 'kuga (saka) kanki ciki babu hijabi, wanda na tabbatar ko adu'arma da 'kyar idan kinayi". Inkin taka biron hanuna ya tanka haka Inna taita bambaminta Najwa tai biris.

Najwah Usmar Salis wadda abokanta suka fi kira
da Nus, d'iya ce ga Malam Usman marigayi tare
da Inna Hafsatu. Su shida iyayansu suka haifa
duk mata. Suna zaune a unguwar dandinshe
cikin 'karamar hukumar dala. Babbar yayarsu
Zainab na auran wani prof a gadon 'kaya
yaranta hud'u. Auwal da Sani da kuma Mahfuz
da Mahfuzaht. Sai mai bimata Saudat. Tana
zaune a unguwar tudun yola yaranta biyu,
Muhseen da Muhseenaht. Sai ta tsakiyar itama
yaranta biyu mai suma Fiddausi. Sai Ayshat ita
kuma tana 'kurfi tana aure bata ta'ba haihuwa
ba. Sai Maryam mai yaro guda tana 'kofar ruwa
sai autarsu Najwa. Mahaifinsu ya jima da rasuwa, tun suna yara. Rainansu da kulawarsu duk 'kar'kashin kulawar Inna Hafsatu. Innarsu macece mafad'aciya sossai. Bata san wargi (raini). Haifafiyar Kano ce unguwar 'kwali wajan gidan sarki hakan mahaifinsu haifafan 'kofar nasarawa ne. Tun bayan rasuwarsa danginsa basa basu wata cikakkiyar kulawa kasancewar shine bare cikinsu. Mahaifiyarsa ta rasu, tun tana kai yaran harta daina. Haka nan duk auran yaranta ita tai fadi tashinta babu taimakonsu. Macece mai zuciyar nema babu sanar da bataiba don rufawa kanta da yaranta asiri. Tana tsaya musu sui karatu kafin aure iyakarsu secondary inyaso inkinje mijinki na muradi kya cigaba. Itace yin surfe, wanki da sauransu. Harta gama auransu yaranta sai autarta Najwa.
Asalin iyayan Inna Hafsatu 'yan 'kasar Niger ne,
kyawawan fararren buzaye masu gashi da kyan
fasai. Doguwar mace sam'bal zubin Karas ba
d'ata ba. Cikin bayin da ake kawowa gidan sarki
aka had'o da mahaifiyarta anan ta had'u da
mahaifinta shima mutumin can ne kasan
cewarsu 'KABILA d'aya ba jinkiri sukai aure.
Inna Hafsat kad'ai suka haifa kyakkyawar mace,
shekarunta sha biyu akai wata annobar kwalara
suka rasa rayukansu. Hakan ya sa Usman yake
tausayinta har ya juye zuwa so ansha fama
kafin auransu saidai ikon Allah. MATAR
MUTUM....hausawa sukace wai 'kabarinsa. Duk
cikin yaranta Najwace ta d'auko komai nata.
Dan haka ina keji da d'iyarta.
Tunda ta gama aurar da yayyanta sai hankalinta
ya kwanta, Najwahce kad'ai gabanta. A da
yaranta makarantar gwamnati suke, amma ganin wadata da bud'i daga ubangiji tare da taimakon surukanta. Najwah na gama primaryn makara huta ta sama mata gurbin karatu a gora
academic. Najwa ta tashi cikin so da kulawar
yayye uwa da mazajan yayyanta. Kullum cikin
samun gata da kulawa take. Saidai duk cikin
yayyunta tafi shiri da Maryam dan haka tafi
zuwa gidanta. Sui tsiya sui dad'i sabida Maryam
akwai tsokana. Duk cikin yaran Innarsu Maryam ita ta kwashe halin Inna, akwaita da fad'a ammafa kan gaskiya batasan raini. Najwa bata da 'kawa ko daya sai ma'kwafciyarsu mai suna Husnah, 'kiriniyarsu iri d'ayace saidai akwai kwanyar nacin karatu. Ga masifaffiyar tsokana akwai wata al'adah guda d'aya da Najwa keda ita wadda kullum takesa su sami sa'bani da Inna.............

'Dabi'ar Najwa itace yawo a tsakar gida babu
d'ankwali, ko banda'ki zata bata damu ta
d'aurashi ba. Ga yawan shigar kaya masu shara-
shara ko matsatsu. Duk lokacin da tai hakan
sukan haura sama ita da Innarta. Hakan kan
'kona ran Najwa ganinta yadda take da gashi har
tsakiyar bayanta bai kamaci tasa kalabiba. Uwa
uba 'yan ajinsu na fasa mata kai idan akazo
exfection.
Najwa irin matan nan ne dogaye masu fad'in
',kugu da cikar 'kirji hakan yasa duk suturar data
saka take mata das gata chaculate colour mai
haske. Kalar da ba a siyanta komai kud'inka.
Tun tana 'karama take fama da'ita tayi dukan
duk a banza har zuwa girmanta. Hallayarta na
ba'kanta ran mahaifiyarta sossai,tun tana
'karama har yanzu da takai matakin shekaru sha
biyar, komai nata ya kara kyau da girma, kullum
cikin nuna mata kuskurenta take amma abu yaci
tura. Mus'ab matashin saurayine dan bayan layinsu tun Najwa na jss one yake 'kwa'kwar santa, saidai Innarta tace saitayi karatu. Yace yaji ya amince zai jira. Najwa ta tsani Mus'ab kullum ta ganshi wani mugun abu takeji ya taremata 'kirji. Zagi kuwa yana shansa lodi-lodi. Tasha saka yara su sace masa tayar kekensa d'an tsura ta basu lada. Wata ranma ita da shakiyiyyar 'kawarta suke zuwa. Tun bai saniba harya ganosu. Najwa na jss 3 wani ba'kon al'amari yasoma giftawa cikin rayuwarta mai cike da mamaki da ban tsoro.
Wasu irin mafarkai take masu tsananin ban
tsoro, wasuma ta kanjisu ajikinta suna matu' kar
wahalar da'ita tare da rikita tunaninta. Da fari
taso sanarwa Innarta saidai tana tsoron tayar
mata da hankali. Gashi mafarkin yana sata
kokwanto ta kanji anya a kantane koko a kasin
hakan. Tsanar Mus'abu ta cigaba da yad'uwa a
zuciyarta harzuwa lokacin data had'u da
Mustspha.
Najwa ta tsinci kanta cikin yawan mafarkai
barkatai. Lokuta da dama ta kanyi mafarkin gata
a harabar wani babban gida yara 'kanana suna
zagaye da ita. Kota ganta rungume da jarirai a
hannu. Kota ganta tana tana feeding (shayarwa)
d'in jarirai. Lokacin tana jss three, sai ta maida
abun tamkar wasa. Tana matakin Sss one ne,
ubangiji ya had'ata da Mustapha a hanyar
makarantarsu wato 'kofar ruwa. Mustapha
nitsattsan saurayine mai tsantseni da Ibadan.
Tunda ubangiji yasa ya d'ora idannunsa kan
Najwa ubangiji ya jarabceshi da 'kaunarta. Tun
yana kkakaucewa har yai shahadar ',kuda ya
isar da sa'kon zuciyarsa. Najwa macece mai san
soyyaya da kulawa hakan yasa cikin 'kan'kanin
lokaci Mustapha yai nasarar samun soyayyarta.
Cikin 'kan'kanin lokaci sukai wata irin sha'kuwa
mai wuyar fassaruwa. Kullum tafito zuwa
makaranta ta 'kofar gidansu take wucewa, yana
zaune ya dakkonta (jiranta) in kuwa ta wuce
zaimata fatan alkhairi ya shiga gida. Wasu
lokutan ya rakata sch yana tsokanarta yanai
mata wa'ka.
Najwa fara kyayyawa, matata abar sona.
Babyna ina sanki Kuma kema nasan kina sona.
Inmunyi aure musha 'kauna ke zan miki wanki
duk dan 'kauna.
Zanmiki wanke- wanke harma da goyo sabida
'kauna.
Ira-iran kalaman Mustapha kenan, ya iya salon
sace zuciyar mutum. Najwa najin dad'in al'ka
dashi gashi mudun zasu zauna hira saita 'karu
dashi fanin addininta da all',amuran rayuwa. Irin
mazan da ake buri kenan arayuwa. Ubangiji
kabamu mazaje nagari.
Mus'ab hankalinsa ya tashi ganin kwata-kwata
hankalin Najwa baya Kansa. Hakan yasa yasoma
yiwa Inna Hafsatu 'barin kud'I a fakaice batare
da sanin Najwa ba. Inna Hafsatu hankalinta ya
tashi ganin yadda diyarta ta karkata kai ga
Mustapha, batare da laifin komaiba. Mugun
tsanarsa takeji a ranta. Abinda bata saniba
matsalar Najwa ce ta haddasa hakan, saidai
rashin kula ya hanata fuskanta.
Zagin yau daban na gobe daban, Mustapha yana
da hakuri da juriya, bai taba d'aga kai ya kalli
Inna da batunba. Sau tari zaizo gida amma Inna
ta hanata fita. Yaya Maryam tafi kowa assasa
lamarin sabida basa shiri da gidansu Mustapha
kan mijinta Abdul nasan 'kanwarsa Farida.
Kasancewarsu akwai ma'kotaka saitai amfani da
damar dan 'kuntattama danginsu.
Mahaifin Mustapha ya jima da rasuwa, daga shi
sai 'kanwarsa da mahaifiyarsa. Yana kyautatta
musu sossai ya kamala karatunsa na NCE
da'kyar. Yanzu koyarwa yake a wata nursery
dake kusa dasu mai suna HASMAH
INTERNATIONAL SCHOOL PRI- NURSERY AND
NURSERY AND PRIMARY. Balaifi yana samun
albarka. Bai zauna hakaba yana koyarwa a
makarantun dare guda biyu magarba da isha
mai suna UMMU SAMHAT TAHAFIZUL QUR'AN
da kuma MADINATUL AHBAB.




Kwanci tashi babu wuya gurin ubangiji al'amura
sunka cigaba da faruwa masu dad'i da akasinsu.
Ana hakan kwatsam Mus'abu ya aikowa Najwa
kyautar waya sabuwa dal. Wadda mahaifiyarsa
ce da kanta ta kawo kyautar kasancewarta
aminiyar Inna. Wannan yasa Inna ta 'kara san
Mus'ab sossai. Da farko Najwa ta'ki amsar
wayar amma data gayawa Husnah tuni ta shirts
mata hanya mai 'bilewa. Da sassafe ta tashi
cikin shirin zuwa makaranta taima Inna salama
ta wuce zuwa gidansu aminiyarta suka rankaya.
Tafe suke suna tad'i (hira) su biyu cikin
nutsuwa da sanyin rai Najwa tace" aminiyansi
jiyafa 'kolo ya kawomani waya 'kirar gione
amma ban kar'bata tana gun Innah". Cikin
masifa Husnah tace " gaki dai kamar wayyayiya
kina neman yin kwa'ba, banda ke ai wayar wata
hanyace ta 'karfaffa ala'karki da Mustapha". Tai
jim alamun tunani, can ta saki murmushi
'kayatace wanda yasa dimple d'inta motsawa
tace "gaskiya Husnaty ke mission ce, aikuwa
hakan zanyi walahi, in'kulle a d'aka ina waya da
hobby a Inna nayin magana nace 'kolone". Gaba
d'aya sukasa dariya dai-dai lokacin suka 'karaso
bakin geta d'insu suka shiga makaranta.
Najwa alla alla take a tashi makaranta taje ta
amshi waya. Ana kuwa tashi kai tsaye tayo gida
ko Husnah bata tsaya jiraba. Kasancewar rana
ta take haka ta taho tana zumud'i tazo gab da
layinsu akwai wata 'katuwar kuka mai koguna da
yaw a a kan layin anan idonta yai katari da wani
kyakkyawan farin mutum yanai mata murmushi,
da farko taji ya birgeta dan yaimata yanayi da
hubbynta amma daga bisani saita lura jikinsa
duk gashine kuma kasansa maimakon 'kafaffu
aaaa jikin micijine. Cikin sassarfa ta bar gurin
tana waiwaye yana d'aga mata hannu. Wajan
shiga gida tai karo jikake 'kumm ta 'kwala 'kara
nan da nan Innarta ta fito tana tambayar ba'asi.
Tuni goshinta yayi lukuni abinka da farar fata.
Cikin sauri tasoma mulmula mata, suna shiga
gida tana zumud'in fadar abunda ta gani. Saita
samu kanta da tsanani tsoro domin mutumin
kemata barazana yana tsiratatta da wata
sharbebbiyar wuka. Luf tai ajikin Inna tana ajiyar
zuciya. Uniforma ta cire ta d'aura zani still babu
dankwali ta shiga bandaki ta watso ruwa
abunta.
Tana nan zaune Husnah ta shigo, tana
bambamin anbarota saitai turus ganin lukuni a
fuskarta, ga wani uban tagumi data rafka, cikin
tsoro ta girgizata ajiyar zuciya tai lokacin data
dawo daga tunani. " bestyna meya sameki" "
bigewa nai tafada cikin bagararwa" " wannan
tunaninfa?". Take abinda ya faru ya dawo mata
ta bud'e baki zatai magana sai bakinta ya'ki
magana tashin hankali kawai saitasa kuka "
Besty nima bansaniba walahi bansan abinda ke
damuna ba". Husnah tai musmushi duk zatanta
Innace ta hana wayar ko garin zumudinta ta
fasa musu kwai kawai saita shiga ciki taiwa
Inna dad'in baki ta am sonata wayar ta
hadamata komi tadangamata tajata d'akinta.

Suna shiga ta dubeta da yanayin kulawa. "
bestyna menene damuwarki? Zatona
Mustaphane kuma kinsamu hanyar jinsa what
next"?. Cikin jimami ta bud'e baki zata bata
labari amma hakan ya gaggara. Kawai sai
Husna ta Samara number Mustapha dake
wayarta ta dana kira. Lokacin da kiran ya shiga
yana niyyar shiga masallaci saiya share kiran.
Ganin shiru bai d'agaba yasa Husnah taimata
salama tare da lallashinta ta wuce gida.
Najwa tai ajiyar zuciya ta kwanta kan katifarta
ya illahi wazata tunkara da batun. Mustapha
yana fitowa masallaci yai karo da wani ba'kin
'kadangare ya kawowa babban yatsansa cafka
cikin nutsuwa ya furta" hasbunallah". ' Bat ya
'bace babushi babu lamarinsa. Cikin rashin
kuzari ya 'karasa kan benci ya zauna. Wayarsa
ya zaro ',karama mai sau'kin kud'i mai suna G-
best ya kira numbar d'azu. 'Karar wayar ita ta
dawo da Najwa daga dogon tunaninta cikin
nutsuwa ta d'aga tana murmushi, tana jan jelar
gashinta. Jin muryar juna ya haifarmusu da
nutsuwa domin rabansu da juna tun had'uwarsu
a zuwanta gidan yayarta. Cike da kulawa yace "
Najwa yanajiki wani sanyi- sanyi?". Hawaye
yabiyo kuncinta tace " bakomai Hubbyna hope
kana lafiya ya jikin Mama"?. Cikin sar'kewar
murya yace "aa'a Najwah ban aminta ba".
"Hmmmm! Kafi 'karfin komai a gurina ka yarda
banda damuwar data wuce ka". "
To nagode Allah yabar 'kauna inajin dad'in
hakan sai dai zuciyata zafi Najwa inajin kamar
kin 'boyemun ne. Inasan inji nasamu sanyi inajin
kamar idona zasu zubar da hawaye
hmmmmmm! Kicema Inna ina gaisheta, ki dinga
yi mana adu'a".
Sunyi shiru na mintina, ya kauda shirun" ina kika
sami waya naga ba layin bestynmu bane?". Dum
' kirjinta ya buga bazata iyayi masa 'karya ba
kawai saita gaya masa gaskiya. Jikinsa yai
sanyi duk yaji babu dad'i amma yasani
sarewarsa na nufin sarewarta. Sarewarta na
nufin bijirewa mahaifanta, bazaiso hakan ba
baimata adalciba inyai hakan ba santa yake ba
cikin murmushi yace .
" Najwa You make me smile for no reason
whatsoever, you make me laugh at the unfunny
things, but most of all, you make me love you
when I shouldn't be loving you". Bai jira cewarta
ba ya katse kiran. Cikin nutsuwa tabi wayar da
kallo tanajin dad'i mara misaltuwa. A fili ta furta
"Mustapha ina 'kaunarka". Bazaki aureshiba inko
kin sureshi kina tare da bala'i da masifa.


Cikin yanayin damuwa Mustapha ya ajiye wayar
hannunsa. Zuciyarsa nasan gargad'insa abisa
matakin daya ke shirin d'auka. Saidai yana ganin
hakan shine dai-dai. Yana tashi gida ya nufa da
salama. Farida dake wanki ta amsa masa da
kulawa tanai masa kirarin dake sashi murmushi.
"Angon Aunty Najwa sai dubu ta taru"
mahaifiyarsu ta kallesu cike da murmushi
tanaiwa ubangiji godiyar samun nutsattsun
'ya'ya.
Cikin ladabi ya zauna ya gaisheta, kansa a
sunkuye tace " mai sunan manya ya akai?
Bakinka akwai magana". Yai murmushi ya sosa
kai "mama dama maganar yarinyar can ne".
Sarai ta fahimceshi amma saita bagarar da
zancan" ban fahimtaba Mustapha wacce
Kenyan?". "Mamanmu Najwah nake nufi". Cikin
murmushi tace "to ya akayi ko sunce mu
mutsane?". "A'a mamanmu nine dai nake ganin
dacewar hakan sabida takai matakin aji biyar".
"Hmmmmm! Ban'ki ta takaba amma baka ganin
zamui musu riga Malam masallaciba,
kasancewar basu but',kaci hakan ba?". "Insha
Allah ba matsala". Da haka suka rufe zancan.
Da yamma mama ta shiga gidan liman
ma'kocinsu ta shaida masa bu'katarta tasan
nemawa Mustapha aure tare da wasu cikin
abokan mahaifinsa. Sun amshi batun hannu biy-
biyu ana sallahr isha'i suka d'auki hanya bisa
rakiyar mustapha. Saidai kash sunyi takaicin
abinda suka riska, domin Inna taci mutuncinsu
tas, tare da shaida musu sati mezuwa zata
Karl'bi kud'in auran 'yarta.
Sun dawo jiki a sanyaye basu 'boyewa
mahaifiyarsa komai ba, tai musu godiya sossai
tare da yiwa Mustspha nasiha. Najwa tayi kuka
kamar ranta zai fita, washegari taiwa gidan Yaya
Zainab tsinke tun daga soro to soma gunjin
kuka, da 'kyar ta lallasheta tai shiru tare da
yimata bayanin lamarin. Zainab tai jigum tana
jinjina batun kaf yaran mamansu babu wanda
taiwa auran dole to miyasa zata soma a kan
Najwa?. Cikin jimami tace "anya ba laifi kukai
mata ba koke ko Mustaphan?". "Walahi Aunty
baimata komai ba kawai na rasa shin 'KIYYAYA
CE KO SON ZUCIYA Innarmu keyiwa
Mustapha?". Ha'kuri ta bata ta nuna mata
d'akinta "shiga ki wanka duk wani hargitse". Ba
musu ta shiga tai wanka ta kwanta. Sallahr
azahar tai kasancewar d'aya ta gota, tana
idarwa batai adu'aba ta cire abayar gashinta ya
bazo tabi lafiyar katifa ta kwanta.

MAFARKI.
A hankali ta riski kanta a wani daji mai tsananin
duhuwa da koguna, babu abinda takeji sai wani
irin 'kugi da gurnani, a hankali wasu halitu suka
fara bayyana masu launin ban tsoro, kawunansu
manya kamar me, saidai jikinsu na majizai. Can
taji ana 'kwalamata kira Najwa! Najwa!! Najwa!!!
A rikice ta juya tana waige-waige. Karaf ta
had'a ido da fuskar da baza ta mantattaba,
saidai wannan karan sa'banin wancan ne,
maimakon murmushi fuskarta a d'aure take
tamau cikin 'karaji yace " kali nan" a d'imauce
ta juya Mustapha da Mus'ab ta gani wasu
manyan hallitu sun d'add'auresu hannu, cikin
tsananin rud'ewa tai nufin zuwa gur in amma
wasu sar'ko'ki sun mata mugun d'auri ta bud'e
baki tana kuka tana magiya kan ya sakesu. Cikin
murya mara dad'in sauti yace " Najwa waya
gayamiki anayiwa ASHIQ kishiya? Kina neman
cutar dani na'ki JINSINA sabida ke, amma ke
kina neman gujemun, nasanya hijabi tsakaninki
da duk wani JINSI inba nawa ba. Da bana
samun matsala dake shiyasa bana bayyana
kaina a gareki, amma zuwan wan an
BIL'ADAMAN kinsoma yimun taurin kai ko
shimfid'ata nai 'kokarin kiranki saiki kauce
yarana sundaina samun kulawarki. Cikin masifa
Mustapha yace "kai la'anan Allah" cikin jin
haushi ASHIQ yakai masa duka da takobinsa
amma sai wani haske yai sama da mustapha
take takobin ya sauka kan wuyan MUS'AB. A
firgice ta farka tana fad'ar MUSTAPHA!!!!!!!!!!!.A
tsorace takaiwa jikinta bahagon kallo wani
mugun bugawa yai das-das-das sakammakon
abinda ta gani ku biyoni danjin wai me Najwa ta
gani?.
Cikin tsananin razani ta soma duban kusan
da'ita zahiri jinine a jikin rigarta da gefan gadon.
Kanta yai muguwar sarawa ga wata muguwar
fad'uwar gaba. Da sauri Zainab ta shigo tana
tambayar "lafiya Najwa kike 'kara haka kina
kiran Mustapha?". Saita 'kan'kameta tana fad'in
"Aunty kingani" tana nunamata jikinta. Take
Zainab ta tureta tana nuna tsananin jin haushi
"gaskiya Najwa kinfiya abin haushi, period d'in
kikewa wannan wula'kancin?". Cikin rudani ta
furta " Aunty ba period nai ba, kiduba fa sossai".
"To gayamin mekikayi?". Bud'a baki tai da niyyar
bata amsa gam baki ya kulle cikin bagararwa
Zainab tace." Hmmm! Shiga ciki ki gyara jikinki
banasan shirme, koni d'in ba'kuwarki ce?". Take
ta fice ta bar d'akin. Jikinta yai sanyi, tana fita
d'akin ya gauraye da wata irin hargowa
hhhhhhhhhhhhhhh "Najwa kinyi kuskure tunda
kikesan BIL'ADAM zakija na dasawa kowa
tsanarki, zan tozartaki a duniya, ki kasance dani
ni kad'ai zai fimaki kwanciyar hankali". Cikin
kuka Najwa ta bud'e baki zatai magana
fuuuuuuu iskar tabar d'akin. Cikin hanzari ta
d'auki wayarta ta kira Mustapha kira d'aya ya
amsa muryarta na rawa tace "Mustapha! Take
tsigar jikinsa ta zuba ya amsa "ya akai Najwa?
"Lafiya 'kalau kake"? Ta fad'a murya na rawa jin
a yanayin da take yasashi cewa. " Cool Najwa
menene duk kin rikice ne?". Cikin jimami ya
saita kanta "dama........dama" saita kama kame-
kame. Murmushi yai yace " Najwah ki kwantar
da hankalinki kiyimun bayani". Kasacewa komai
tayi.
***********
Kawai saita samu kanta da yimasa 'karya" dama
kiranka nai inbaka ha'kurin abinda Inna tayiwa
wakilanka" "dakata Najwa Innafa mahaifiyatace
menene abin bada ha'kuri a ciki? Kar insake ji
kinji ko". Kawai saita fashe da kuka "yanzu
Mustapha kanji kana gani zata rabamu? Kasanfa
munasan juna, gaskiya kai wani abu". Cikin
dauriya yace "me zanyi Najwa?". "Mustapha
kawai mugudu". " subhanallah haba Najwa idan
rai ya 'baci hankali baya gushewa, Inna ta isa
damu ta isa komai a kanmu bazanso ki gujewa
mahaifiyarki sabida niba, kisani idan ubangiji ya
nufa muna da raban kasancewa babu wani
mahalukin dazai hana idan kuma 'KADDARARMU
CE a haka bamu isa hanawa ba. Abinda fa
ha'kuri baibamuba rashinsa bazai bamu ba".
Jikinta yai sanyi cikin shagwa'ba tace to ani
banasan auran dole kuma ba kyau ko a addinan
ce kodai ka daina sonane?".
Cikin sautin jan hankali yace "Najwaty! Ajiyar
zuciya tai ya cigaba Najwa True lovers
are like upper & lower eyelids!.They often meet
because they miss each other
and
when they meet, they don't see the world
around". Najwa tai shiru kalamansa nai mata
dad'i cikin jan hankali yace "Najwah say me
something please"( Najwa kice mun wani abu
can Allah).
Cikin so shau'ki 'kauna tace " Mustapha!! MY
HEART IS LOCKED KEYS ARE WITH U OPEN
AND SEE HOW MUCH I LOVE YOU".
Kawai saita katse layin tana tsananin jin nauyi
tamkar yana kallonta.
Cikin hanzari ta shiga band'aki ta gyara jikinta
tayo alwala lokacin har biyar tayi.
Kubiyoni
A daran Zainab ta kira sauran 'yan'uwanta
Fiddausi Maryam Saudaht tace su had'u gida da
safe sabida tattauna matsalar Najwa. Ta kira
Husnah tace ta gayawa Inna Najwa na gunta kar
hankali ya tashi. Haka Najwa ta kwana sukuku
da'ita, washegari drivern Zainab ya d'aukosu
zuwa gida. Tun a hanya gaban Najwa ya dinga
mugun fad'uwa tana jin kururruwa a
kunnuwanta kamar ana kiranta wasu lokutan har
rufe idonta takeyi. Suna shiga layinsu taga taron
mutane, abin ya tsoratata ya kuma bata mamaki
gabanta ya cigaba da fad'uwa har suka wuce
taran mutanan da makara zasu ma'kabarta. Ta
dinga biybiyarsu da kallo har sukai parking suka
fito. Gab da zasu shiga gida taji ankira sunanta,
sai taji kamar muryar Mustapha cikin azama ta
juya amma ga mamakinta ASHIQ ne cikin
murmushi yake nuna mata takobinsa duk jini
jikinta a hankali yaimata nuni da hannunsa
saitaga MUS'AB kwance cikin jini. Wata
giggitaciyar 'kara ta saki daga nan bata sake
motsiba cikin sauri Zainab ta shiga gida da'ita.
Abin mamaki tana shiga duk 'yan'uwanta na
zaune cikin damuwa Inna har sharce hawaye
takeyi, ganin sun shigo da Najwa ranga- ranga
yasa sukai kanta suna tambayar lafiya. Cikin
jimami tace " nidai muntaho lafiya 'kalau kawai
sai ganin nai ta zube". Ruwa mai sanyi aka zuba
mata ta saki ajiyar zuciya a hankali ta soma
motsi can cikin 'karaji ta furta MUS'AB. Gaba
d'aya wajan suka bita da kallon tausayawa
banda Zainab data bita da kalon mamaki. Inna
ta share hawaye "Najwa Mus'ab kuma saidai
wani bashi ba ya tafi ya barmiki duniyar saiki
zuba ruwa kisha". Cikin rud'ewa tace "Inna ya
mutu? Dama mafarki na zama gaskiya? Allah
kasa in farka daga wannan mummunan
mafarki". Cikin jin haushi Maryam takai mata
duka dama cike take da haushin anbawa Abdul
auran Farida. Da sauri Zainab ta tare tana
tambayar abinda yake faruwa.
Inna ta share hawaye tace" Zainab tunda na
kori mayen yaron nan da danginsa Najwa ta
gudo gidanki jiya, a daran na aikawa iyayan
Mus'ab sukace yau zasu aiko ai maganar
auransu, yau muka wayi gari da mummunan
labari wai Mus'ab ya mutu". Cikin tashin hankali
Zainab tace "ya mutu?". Maryam tace "tabbas
ya mutu ni walahi badan ance ya shiga dakinsa
ya rufeba akajiyo ihunsaba kuma yasa sakata
walahi tsaf zance Mustaphs ne ya kasheshi don
gadon marasa imanine". Cikin sauri Saudaht ta
doke mata baki " garin shegen kishinki saikin
d'aukowa kanki masifa".
Inna ce tai musu tsawa suka bari. Najwa kuwa
jin ana neman la'kabawa Mustapha yasa ta
had'e fuska tanasan furtawa amma tsoro ya
hanata. Take idonunta suka sauya launi daga
fararre tas zuwa jajjaye tamkar gauta. Wata
muguwar sha'ka taiwa Maryam ta soma
dukkanta tun sunaiwa lamarin kallon wasa saiya
zama babba. Sunyi sunyi su 'kwaceta sun kasa
bata saketaba saida ta 'bala mata hannu 'baras.
Sunyi jigum suna kallonta zuciyoyinsu fal tashin
hankali Maryam sai 'burarri takeyi Zainab ta
dinga kallon Najwa cike da zargin wani al'amari
amma tana tsoran furtawa.
Bata tankawa kowa ba ta shiga dakinta tai
kwanciyarta dukkansu suka kasa yimata
magana tamkar an d'aure musu bakuna. Suka
d'auki Maryam suka kaita wajan me gyara.
Bayan sun dawo sukaje sukaiwa iyayan Mus'ab
gaisuw.
Najwa sai laasar ta farka lokacin duk yayyenta
sun tafi gidajansu, bata ko kali inda Inna take ba
ta shige bayi tayi wanka ta fito ta tada sallah
azahar da la'alar ta had'a tana idarwa idonta
yakai kan wata leda a d'akinta sai 'kyali take da
sauri ta d'auka abin mamaki take a way ne ciki.
Batai tunanin waye ya ajiyeba kawai ta bud',a ta
hau ci. Husnah ta shigo kamar anjehota cikin
masifa tace " Besty baki da imani Mus'ab ya
mutu ko ajikinki ko?". "To dan ya mutu sai me?
Nina kasheshi?". Yake jikin Husnah yai sanyi ta
dinga yiwa Najwa kallon mamaki takai idonta
kan abincin gabatanta "waya baki?" "Hmmmm!
Sabida kinmaidani matsiyaciya banda kudin siya
ko?". Husnah sai taji wani bambarakwai duk
Najwa ta sauya mata. Jiki a sanyaye tai mata
gaisuwa ta wuce.Tun daga ranar babu jituwa tsakanin Najwa da
Inna, hakama Husnah ta kasa gano kanta.
Najwa duk ta rame tayi ba'ki ga wasu 'kuraje a
fuskarta da suka haddasa mata muni na bagaira
babu dalili, hakan yasa duk ta tsangwami kanta
ko fita batayi. Chat ta bud'e a wayarta wanda
hakan ya taka muhimmiyar rawa wajan
d'aukemata hankali ga yin adu'a ko sallah tayi
tana idarwa zata d'auki waya babu batun adu'a
hakama bacci da ita take kwana a hannu.
Mutuwar Mus'ab tana nu'kur'kusarta a zuciya
hakan yasa mata yawan fargaba mai tsanani.
Gani babu sarki sai Allah Inna ta soma janta a
jiki tanai mata nasiha zatanta tunanin Mus'ab
ne, cikin 'kan'kanin lokaci suka koma dai-dai.
Maryam tasha jinya sossai hannu ya warke,
saidai bikin Abdul da Farida babu abinda aka
fasa. Tayi mitar tayi masifar a banza.
A hankali fuskar Najwa ta washe ta dawo
normal, suna waya da Mustapha lokaci lokaci
yaso ya zo yaiwa Inna gaisuwa saidai tsoro ya
hanashi. Yana shakar Inna matu'ka.
Bacci yake jinsa yake kamar a farke a hankali
'kadangaran ya mi'ke a tsaye tamkar mutum
yana murmushi yace "Mustapha ka cika taurin
rai, nace kafita gonata kana neman yimun wasa
da hankali sau biyu ina kawoma farmaki kana
kufcemin, tabbas zaka tafi ma'kabarta tamkar
yadda d'an'uwanka ya tafi cikin rashin tsoro
yace " kai ma'kiyin Allah inshaa Allahu nafi
'karfinka, bazakai nasara a kainaba, wai kai
waye? Kana neman takuramun fa".
Take ya zabga masa wata bulala take Mustapha
ya saki 'kara ya farka daga mafarkin abin
mamaki da tsoro shatin bulallar rad'au a
hannayansa harda kwailewa. Kansa ya d'aure
yanasan sanin ainihin abinda ke bibiyarsa amma
bayasan sanya kansa cikin hallaka.
Adu'a yayi ya mi'ke yai wanka ya fita duk jikinsa
a sanyaye. Mahaifiyarsa taitai masa nasiha daya
shiga gaisheta zatanta ko batunsa da Najwa ne.
Kai tsaye gurin Malamin Islamiyyarsu ya nufa
Ustaz Yusuf, bayan sun gaisa yai masa bayyani,
yai jim daga 'karshe yace ya bashi gobe zaiyi
istihara. Washegari cike da azama ya koma
saidai kalaman Malaminsu ya bashi tsoro da
mamaki, bayan sun gaisa yace "gaskiyar magana
Mustapha lamarinka 'boyyayan sirrine, domin
nayi istihara jiya amma bana ganin komai sai
wani wani duhu da 'bur'bushin wani 'karamin
haske wanda ya rufeka, inaga mubarwa Allah
komai mu durfafi adu'a domin ubangiji baya
bacci".
Haka suka rabu jiki a sanyayye.
Ku dakace ni........
Cikin kwanciyar hankali soyyayarsu ta cigaba da
bun'kasa a 'boye batare da sanin Inna ba, sukan
had'u a gidansu Husnah ko inzata makaranta ko
intaje weak end gidan Zainab.
Ina na kula da takunta kwata - kwata ta daina
maganar Mustapha ammafa kowaye zaizo
nemanta bata fita, tayi hancinin tayi dukan harta
gaji.
Zama ba d'ankwali kuwa sai abunda ya cigaba,
musamman yanzu da ake turomata style
(samfir) na gyaran gashi da kitso a chat, wani
abun birgewa har gashi ake d'auka bayan anyi
parking ai disple picture dashi wato (Dp) ba tare
da la'akari da wa kake chat ba. In tunaninki
kinsan bakya bada numberki ga maza akwai
masu had'a number haka kawai. Wata kuma duk
sanda takai caji budewa suke su kwashi
numbobi kawai dan san zuciya.
A duk lokacin da Najwa tai Dpy na parking zakiji
freind d'inta na yabawa itoko tanajin dadin haka.
Har so take azo exfection a sch dan kawai a
yaba gashinta. Kwanci tashi suka zana
jarrabawar shiga aji shida ita da Husnah duk
sunyi nasara.
A hankali Mustapha ya soma zuwa gidansu
Najwa, sabida bayasan ke'bewarsu wani waje
daban gudun fad'awa TARKON SHAI'DAN gara a
gidansu komai zai faru ya faru. Tun yana zuwa
ana hanata fitowa harta soma satar jiki tana
fitowa.
Hankalin Inna ya tashi matu'ka ganinta
Mustapha asiri yaiwa Najwa taki kowa saishi. Ta
tara yaranta kaf tana kuka kan itafa tagaji susan
matakin d'auka. Aunty Zainab cikin lallashi tace
"Inna kidaina zubarwa Najwa hawaye, hawayan
mahaifa masifane ga yaransu, musamman
Najwa da take mace, kamata yai mui mata
adu'a. Kuma idan mun duba ai Mustapha baida
wani hali da za'a gujewa auransa. Nagartacan
mutum ne da kowa yake yabansa". Cikin masifa
Maryam tace " inji ubanwa? 'Dan iskane". A
zafaffe Zainab ta wanka mata mari " Maryam na
fahimci kece jagorar wargaza tafiyar nan sabida
mijinki zai auri 'kanwarsa, shi aure ai nufin Allah
ne kuma MATAR MUTUM kabarinsa ke baki isa
hana abinda ubangiji ya tsaraba. Harkike neman
zagina kan rashin gaskiya. To ainayi bincike kan
lamarinsa 'karshema yanzu shiyakewa yarana
lesson kuma nayiwa Abban yara magana yace
yayi bincike Mustapha ko abokin fad'a bashi
dashi".
Cikin borin kunya Maryam tace " Inna kinji ko
wallahi Najwa 'KADDARARMU CE kina kallo
yadda Yaya ta mareni akanta kuma ai bashari
duk wanda zaifadi halinsu baya nane tunda ni
munfi kusa dasu......kallon da Najwa taimata
yasata gum dan yanzu mugun tsoranta takeji
tunda tasha duka. Cikin tausassawa Saudaht
tace "shiyasa yayan 'kurfi take birgeni da tana
kusa da tuni ta sasanta mtssss! Auran nesama
baiyiba". Fiddausi tai murmushi tace "Inna
gaskiya ubangiji ya haramta auran dole miyasa
zakiyiwa Najwa bayan mu bakiyi mana ba?
Kuma ma yanzu aibata da saurayi inba
Mustapha ba mafi a'ala kibarta ta aureshi karta
jawo mana magana. Ma'aikifa ya hara ta hakan
da kansa ya raba auren dole har sau biyu.
Ma'aiki (S A W) yana cewa:- Zuciyoyi rundunane
daban- daban, idan wad'anda suka dace da juna
suka had'u sai suyi 'kawance. Idan basu dace
da juna ba sai suyi baram-baram.
Wata rana wata mata mai suna Asmah'u Bint
Khidam taje wajan Manzon Allah (s.a.w). Tana
mai cewa. 'Babanta ya aura mata wani d'an
'kaninsa dan ya kare matsayinsa a wajansa sai
ma'aiki (s.a.w)yace mata:" idan kinso na raba
tsakaninku idan kin ha'kura shikenan ki zauna da
mijinki".
Haka Ma'aiki (s.a.w) ya raba aura tsakanin
Usman bin Muz'um da iyalanka. Kamar yadda ya
raba na Abdullahi d'an Umar da matarsa".
Zamani ya sauya Inna yanzu yara a tsaye suke
ko kana tarbiyarsu sai kana adu'a domin duk
tsarewarka sai ubangiji ya tsare maka". Jikin
Inna yai sanyi nan da nan ta sako. Sun daidaita
magana akan Najwa zata kira Mustapha ya turo
magabatansa. Aunty Zainab ce ta hana tace
zatai masa magana. Da haka taro ya watse
saidai tunda aka ajiye magana Najwa ta kasa
walwala da farin ciki gaba d'aya ta sauya daga
Najwarta zuwa

Yaya Zainab hargida tai kiran Mustapha kan
maganar inda gaske yake ya fito, yaimata
al'kawarin zai sanarwa mahaifiyarsa. Da farko
Mama taso tirjewa sabida abinda Inna tai musu,
amma yaitai mata nasiha yana bata ha'kuri.
Mama tai musu fatan alkhairi akasoma shirye-
shiryen kai kud'i naira dubu talatin yakai sai
dubu ashirin nasa rana. Mijin Yaya Zainab shiya
amshi kud'in anyi komai a mutunce.
Gaba d'aya Najwa ta sauya, miskilancinta ya
'karu fiye dana da. Al'amarin mafarkinta ya
cigaba da faruwa saima abunda yai gaba.
***********
Mustapha kansa ya kasa gane kanta a haka
suka cigaba da tafiya. Ko hira yazo ta dinga
d'aure fuska tana 'kun'kune daga uhmm sai
uhmmm tun baya damuwa har yakai ga nunawa
Husnah. Saidai itama bata samun sakin fuska
daga gareta. Ko makarantar boko ta daina
tsayata saidai abinda ya d'aure mata kai kullum
inta dawo makaranta a wajan kukar nan ta
layinsu take samunta sannan su jera kamar
basuba su tafi makaranta.
Inkuwa akaje makaranta itace tsokani wancan
yima wancan ba'a. Ga wani 'karfin masifa da
take dashi ko malamai sai sunyi da gaske suke
tan'kwarata, dukan makara kuwa tuni aka daina
yimata sabida duk Malamin daya daketa to
kuwa zaikwana yana jinyar hanunsa.
Kwanci yashi har suka zana jarrabawar gama
makaranta, lokacin Najwa ta 'kara wani kyau na
fizgar hankali, abinda basu saniba duk daran
duniya ASHIQ ke zuwa ya d'auketa a mafarki ya
kaita aimata gyaran jiki irin nasu. Nan da nan ta
soma had'uwa da manyan alhazawa saidai bubu
wanda taken a fuska, Mustapha kad'aine
taurarranta. Saidai zuciyarta najin haushinsa
idan bata 'bata masa raiba bata jin dad'i. Gaba
d'aya Mustapha damuwa da fargaba ta sashi
gaba duk ya zabge yayi ba'ki adu'ace kawai
take ri'ke dashi.
Kullum ASHIQ cikin tsora tashi yake tare da
barazanar d'aukar ransa. A haka har aka tsaida
lokacin biki.
Najwa zaune a dokin 'kofa Inna tana d'akin girki
cikin fad'a tace " waike Najwa wace irin
hallitace da bakya jin magana?". Cikin so'baro
baki tace "menayi kuma Innarmu?". Cikin takaici
tace " Najwa duba fa jikinki kali shigar da kikai
kida acikin gida kike kinsan wazaya shigo? Kai
babu kalabi ga kuma kin zauna dokin 'kofa
mattatarar shaid'anu, anya Najwa wannan
rayuwa ce?".
"Kefa Inna kinsoma matsa mana , haka ake
rayuwa? Kawai ki barmu muji dad'i haba". A
zafaffe tace "kee! Najwa saurara ni zaki gayawa
maganar banza?". Itama cikin zafi ta waigo take
muryarta ta bud'e ta koma muryar babban
mutum idonta yai shud'i da ja ta nuna Inna da
yatsa take ta soma lan'kwashewa bakinta da
hannunta suka soma juyewa cikin minti uku
kacal ta koma tamkar mai cutar shan Inna. Ba
kowa yai hakanba face ASHIQ, domin lokacin ita
Najwa ma tana gefene tana chat jira take Inna
ta gama fad'anta ta tambayeta wace Najwar?
Najwa tana kallonsa sai hawaye babu bakin
magana. Takuma kasa tunanin yin adu'a sai
bayan fitarsa ta samu damar mi'kewa tai waje
tana kururuwa.
Ku biyoni.......
'KADDARMU CE!
SANAH S MATAZU
16-17
Da taimakon Maman Husnah Najwa ta fito da
Innah daga dakin girki saidai babu hannu babu
'kafa. Hankalin yaranta ya tashi sossai. Aka
dirfafi neman magani amma ina, wani ikon Allah
da sukayi suka gaza saisuka watsar da lamarin
tamkar ankauda tunaninsu da hankalinsu a kanta
kullum cikin zaryar kulawa da'ita suke amma
basa yun'kurin nema mata magani. Mustapha
inya takura Najwa da batun har rigima sukeyi
dan haka kowa ya tattarasu ya zuba musu na
mujiya.
Jikin Inna yasa aka 'kara bikin su Najwa zuwa
wata guda, saidai babu wani cigaba tilas aka
ha'kura Yaya Zainab ta d'aukowa Inna mai kula
da'ita aka soma shirye- shirye. Hankalin Najwa
yai mugun tashi zuwa lokacin duk tafita
hayyacinta, ko gidansu Husna ta daina zuwa,
lokuta da dama kasancewar layinsu shirune in
muguntar ASHIQ ta motsa saiya tunkud'ota
wajan kukar nan ya kawo yara ya zube yana
gefe yana kula da'ita suita shirme. Husna kad'ai
ke kula da zamanta a gun amma ta kasa
fad'awa kowa.
Kullum ASHIQ cikin wasa da hankulan
makusanta Najwa yake babu wanda ya ke lura
da lamuranta, dana cutar Inna dama-dama
Fiddausi tafisu tsayuwa wajan du'a'i.
Biki ya 'karato ankawo lefe an tsaida lokacin
biki, sati biyu duk wani shige da fice Husnah
keyi, dan wayarsma yanzu saita gadama take
d'agawa, Mustapha ya gyara 'bangare guda a
gidansu babban parlour yayi cikinsa da toilet da
kitchen da stor sai bed room da 'bangaran ba'ki
d'aki guda. Anyi fenti anyi siminti da komai .
Ansoma hidimar biki Inna na kwance, sai gani
da'ito duk wanda ta kalla saidai aga tana zubda
hawaye hankula sun tashi sossai gidan biki sai
koke-koke. Amarya dai gata nan sukukku kawai
sha'ani ake amma bata da nutsuwa duk ta
zabure. Tunanin kowa cutar Innarta ke damunta.
Babban tashin hankalin Najwa matsawar da
ASHIQ yai mata kan ta kori Mustapha ta'ki
sabida ya kasa nasara a kansa. Babban tashin
Najwa duk lokacin datai yun'kurin yimasa rashin
mutunci wuyarta su had'a ido ko taji sautin
muryarsa take yanke jikinta yakeyin sanyi. A
haka aka d'aura aure ka soma shirin kai amarya.
Yaya Zainab da sauran 'yan'uwanta sunyi rawar
gani sossai. Sun 'kawata dakin Najwa ko mai
uba sai haka. Najwa dai gata a gidan masoyinta
datafi 'kauna, saidai tsantsar tsanarsa da takeji
kamar ta kashe kanta. Amma da zarar taji
muryarsa angama tsiya. Da farko zaman nasu ya
soma dad'i amma daga bisani sai Najwa ta
koma zam Najwan ASHIQ sabida tasoma nasarar
hana Mustapha gudanar da wasu ibadunsa,
kamar azumin littinin da alhamis. Tsayuwar dare
kau daya soma ASHIQ zai soma tsoratata ta
dnga iface- iface tilas zai katse ya saurareta.
Mijin yayarsu ta 'kurfi tunda yazo yaga jikin Inna
yace zai turo mai magani daga can a dan yana
komawa ASHIQ ya gama dashi bai kwanaba.
Tilas washegari ta koma 'kurfi domin yin takaba.
Saidai zuciyarta cike da zargi sabida yadda aka
bada labarin mutuwarsa domin kwatankwacin
rasuwar Mus'ab ne.



Da taimakon Maman Husnah Najwa ta fito da
Innah daga dakin girki saidai babu hannu babu
'kafa. Hankalin yaranta ya tashi sossai. Aka
dirfafi neman magani amma ina, wani ikon Allah
da sukayi suka gaza saisuka watsar da lamarin
tamkar ankauda tunaninsu da hankalinsu a kanta
kullum cikin zaryar kulawa da'ita suke amma
basa yun'kurin nema mata magani. Mustapha
inya takura Najwa da batun har rigima sukeyi
dan haka kowa ya tattarasu ya zuba musu na
mujiya.
Jikin Inna yasa aka 'kara bikin su Najwa zuwa
wata guda, saidai babu wani cigaba tilas aka
ha'kura Yaya Zainab ta d'aukowa Inna mai kula
da'ita aka soma shirye- shirye. Hankalin Najwa
yai mugun tashi zuwa lokacin duk tafita
hayyacinta, ko gidansu Husna ta daina zuwa,
lokuta da dama kasancewar layinsu shirune in
muguntar ASHIQ ta motsa saiya tunkud'ota
wajan kukar nan ya kawo yara ya zube yana
gefe yana kula da'ita suita shirme. Husna kad'ai
ke kula da zamanta a gun amma ta kasa
fad'awa kowa.
Kullum ASHIQ cikin wasa da hankulan
makusanta Najwa yake babu wanda ya ke lura
da lamuranta, dana cutar Inna dama-dama
Fiddausi tafisu tsayuwa wajan du'a'i.
Biki ya 'karato ankawo lefe an tsaida lokacin
biki, sati biyu duk wani shige da fice Husnah
keyi, dan wayarsma yanzu saita gadama take
d'agawa, Mustapha ya gyara 'bangare guda a
gidansu babban parlour yayi cikinsa da toilet da
kitchen da stor sai bed room da 'bangaran ba'ki
d'aki guda. Anyi fenti anyi siminti da komai .
Ansoma hidimar biki Inna na kwance, sai gani
da'ito duk wanda ta kalla saidai aga tana zubda
hawaye hankula sun tashi sossai gidan biki sai
koke-koke. Amarya dai gata nan sukukku kawai
sha'ani ake amma bata da nutsuwa duk ta
zabure. Tunanin kowa cutar Innarta ke damunta.
Babban tashin hankalin Najwa matsawar da
ASHIQ yai mata kan ta kori Mustapha ta'ki
sabida ya kasa nasara a kansa. Babban tashin
Najwa duk lokacin datai yun'kurin yimasa rashin
mutunci wuyarta su had'a ido ko taji sautin
muryarsa take yanke jikinta yakeyin sanyi. A
haka aka d'aura aure ka soma shirin kai amarya.
Yaya Zainab da sauran 'yan'uwanta sunyi rawar
gani sossai. Sun 'kawata dakin Najwa ko mai
uba sai haka. Najwa dai gata a gidan masoyinta
datafi 'kauna, saidai tsantsar tsanarsa da takeji
kamar ta kashe kanta. Amma da zarar taji
muryarsa angama tsiya. Da farko zaman nasu ya
soma dad'i amma daga bisani sai Najwa ta
koma zam Najwan ASHIQ sabida tasoma nasarar
hana Mustapha gudanar da wasu ibadunsa,
kamar azumin littinin da alhamis. Tsayuwar dare
kau daya soma ASHIQ zai soma tsoratata ta
dnga iface- iface tilas zai katse ya saurareta.
Mijin yayarsu ta 'kurfi tunda yazo yaga jikin Inna
yace zai turo mai magani daga can a dan yana
komawa ASHIQ ya gama dashi bai kwanaba.
Tilas washegari ta koma 'kurfi domin yin takaba.
Saidai zuciyarta cike da zargi sabida yadda aka
bada labarin mutuwarsa domin kwatankwacin
rasuwar Mus'ab ne.
'KADDARARMU CE!.
SANAH S MATAZU.
17-18.
Tunda yayarsu ta gama takaba ta dawo gida
d'ungurun gum ta soma kulawa da mahaifiyarsu.
Kullum takan tofa Ayyatul kursiyu da fala'ki da
nasi ta shafa mata cikin sati guda 'kaffafunta
da bakinta suka dawo dai-dai saidai bata
magana sai nuni da hannu.
Tunda ta soma yiwa Inna adu'o'i sai ASHIQ
yasoma tsoratata, saitaji ana kiran sunanta ko
kuma ana dariya mai 'karfi. Ko taga Najwa na
binta da wu'ka. Kanta ya kulle ta tab star
matsalar Innarsu daga Najwa ne. Dan haka taje
gurin limamin unguwarsu saidai amsar da ustaz
Usman ya bawa Mustapha itama haka abata.
Saidai ya bata adu'o'i sossai tare da yimata
bayani kan kodai Najwa ba jinsusu bace ko
kuma ala'ka ta tsakanin MUTUM DA ALJAN.
*************
Husnah ta soma ja tanai mata tambayoyi akan
Najwa saidai babu wata satar amsa, abu d'aya
ta tsinta game da Najwar zuwa biyu 'kiyyayar
Mus'ab da zaman bakin kuka. Hankalinta ya
karkata da batun kukar dan dama takan yawaita
jin tsigar jikinta na harbawa intazo wucewa.
Koma menene zata cigaba da adu'a.
*******
'Ya'yanta sunji dad'i sossai saidai sunyi
mamakin sauyin da aka samu. Musamman
Najwa da tun a gun fuskarta ta sauya idonta yai
jajir. Bata wani tsaya dogon bayani ba. Tai
murmushi tace "kudai kudinga adu'ar nemawa
kanku da yaranku tsari a koda yaushe" duk sai
jikinsu yai sanyi. Nan da nan Najwa ta azalzali
Mustapha kan sai sun tafi gida basu wani jimaba
suka wuce. A hanya yake mata 'korafi kan
meyasa tace su taho?. Cikin 'kun'kuni tace "
yayar nan zanyi maganinta tana yimana
shisshigi" da sauri ya dubeta saita wayance tace
" nufina tafimu kusa da Inna sossai". Dariya yai
amma 'Kazan zuciyarsa yana auna kalamant.
Haka zaman nasu ya kasance, matsalar yau
daban ta gobe daban, yanzu abinda ta tsira
shine xuwa taiwa Mama rashin kunya wanda
hakan kan tunzura Farida su hau dambe.
'Karshe kuma Faridan ake cuta. Dama wazai
had'a 'karfin MUTUM DA ALJAN (Munayshst).
Kullum cikin kawo 'kararta suke ya rasa yadda
zai 'bulowa lamarin. Matsalar da tafi damunsa
tun auransu 'barinta uku kenan, yana lura da
sakacinta wajan yin sallah kan lokaci inyai
magana sai ta hau fushi da 'kun'kuni. Sai ya
ha'kura ya 'kyaleta amma da zarar da kwanta ya
kan lalla'ba yai mata adu'a.
**********
Mustapha na zaune a 'kofar makarantarsu bayan
antashi yara 'yan tahafiz sun soma zuwa. Kamar
daga sama wata sumammiyar mota ba'ka tai
parking a bakin TEEMAH COOL SHOPPING,
katafaran kanti saida kayan 'kwalam da
ma'kulashe. Bai damu da lura da irin wannanba
amma haka nan ya samu zuciyarsa da san ganin
na cikin motar. Gabansa ya tsananta fad'uwa
yana jin wani irin abu mai nauyi a 'kirjinsa. Cikin
dog on wando jeans ta fito yai matu'kar kamata
sai wata half best fara tas kanta yasha 'karin
gashi. Cikin jin tsanarta yake Allah wadarai
da'it. Saidai me ? Hantar cikinsa tai mugun
kad'awa lokacin da ya had'a ido da'ita. Ya
murza idanuwansa sossai, tabbas itace meya
kawota nan? Kayan jikintama zahiri dasu ya
barota gida. Karaf idonsa yakai kan na kusa
da'ita fuskar tamkar ya santa amma tunani yake
ina ya santa?.kafin ya gama d'ibar tashin
hankalin daya kwasa har sungama sun fito
sunzo giftashi ta sakar masa murmushi ta d'aga
masa hannu.
Cikin tsananin tashin hankali ya nufi gidan da
yake tazararsu babu yawa nan da nan ya isa
gida. Gab da zai shiga gida wani yaro yai masa
salama ya basji takarda kan yai magana yaron
ya gudu. Da sauri zuciyarsa ke azalzalarsa ya
bude takardar yana bud'ewa gabansa yai mugun
fad'uwa.
"MATARKA TA ZUBDA CIKINTA" wasu 'kwalan
tashin hankaline suka zobo masa.
Yana shiga Farida ya samu cikin rad'a yace
mata "yau Auntynki ta fita?" Kai ta girgiza ,"a'a
tunsafe tana kwance wai cikinta ke ciwo". Da
azama ya 'karasa turus yai lokacin dayai arba da
manyan ledojin TEEMAH COOL SHOP. Cikin
masifa ya 'kwalawa Farida kira jiki na rawa ta
taho cikin hargowa yace "kikace bata fita ba
wannan fa?". A tsorace takaiwa kayan kallo
tabbas kayan shopping ne to waya kawo cikin
tsoro tace " walahi bata fitaba yaya "A zafaffe
yace "jeki". Jikinta na rawa ta koma ta cigaba
da aikinta.
Dai-dai lokacin Najwa ta farka cikin wata
giggitaciyar 'kara tana dafe kanta. Ga
mamakinsa jini ke bin 'kafaffunta cikin kallon
tsana Mustapha ya soma kallonta yana zagaye
zagaye d'akin Najwa a tsorace ta soma ja da
baya tana mamakin sauyawar Mustapha.
Ku dakaceni ya tabbata Najwa ce a mota?
Shin menene makomar auransu? Shin cikin ya
zubene? Ya batun Inna? Shin ina Auran Farida
da Abdul? Mustapha na sakin Najwa?.
'KADDARARMU CE!
SANAH S MATAZU.
18-19.
Cikin tsananin zafin rai ya soma nunata da
yatsa" Najwa kin cutar dani kin zalunceni, bazan
yafe miki ba". Kuka ya ci 'karfinsu su duka cikin
rauni murya tace "Mustapha menai maka? Meye
laifina? Kaimun bayani yadda zangane ka
sanyani cikin duhu". Takaici ya kashe Mustapha
abu guda ya fad'o masa bayan yawace-yawace
tana kora 'kwayoyi banda haka kanmi zata raina
mashi wayau. Kawai sakai yai ya bargidan
bayan ya gargadi Farida karta fadawa Mama.
Cikin sanyin jiki Najwa ta tashi ta gyara jikinta.
Shayi me kauri taso had'awa idonta yakai kan
TEEMAH COOL SHOP cikin hanzari ta bud'esu
ta d'auki kaza guda da nono ta hau ci duk
zatanta Mustapha ya ajiyesu.
Haka zamansu ya sauya salo kwata - kwata
babu jituwa makwancin kowa daban amma basu
bari a fuskanta ko a magana bale a fuska sai
isu-isu.
**********
Jikin Inna saisan barka,kullum samun cigaba
akeyi. Cikin 'kan'kanin lokaci Mustapha ya rame
yayi duhu, kullum yanayin da zaiga Najwa
daban. Najwa zamansu baya damunta koda
wasa tamafi sakewa a ganinta takurata yake.
Koda Husnah tazo ta kawo mata ankon bikinta
bata wani fuskanci akwai matsalaba hakama
Yaya Zainab da su Saudaht da sukazo. Ganin
babu sarki sai Allah Mustapha ya nemi shiri
suka dawo normal. Saidai kuma me? A duk
lokacin da yau Yuan',kurin kusantar Najwa wani
zafi ke fitowa ajikinta kamar tururin oven na
bread. Hankalinsa yai matu'kar tashi sossai
yanaji yana gani saidai yaita fama da ciwan ciki.
Yauma kamar kullum kwaliya tai cikin dogon
wando three quarter jeans yai mata kyau blue.
Rigarta pink kanta yasha gyara sai kamshi
takeyi abin sha'awa. Cike da kulawa suke hira
harya fita taimasa rakiya. Tana dawowa ta
ma'kala eirpiece tanaji a haka tai bacci kai
abud'e. Tana kwanciya ASHIQ yai muguwar
dariya ya soma zagayata.
**********
Mustapha yana isa makaranta principle ta bashi
takarda shaidar neman aiki da wata makaranta
ta nemi yaiwa d'alibanta horo na wata uku. Can
zoo road zaije yakai sa'kon, dan haka yad'auki
machine d'in abokinsa ya tafi. 'Karfe d'aya da
rabi dai-dai yazo kan hanyar titin gyad'i gyad'i
zai biya wajan wani abokinsa kamar ance kali
can gabasan yai mugun fad'uwa. Najwa ya
hango tana tuka mota sabuwa dal 'kirar korolla.
Gefanta wani kyakkyawan saurayine suna had'a
ido ta kashe masa ido ta 'kara wuta.
Mustapha a million ya rufa mata baya amma bai
risketa ba 'karshema fad'uwa yai har yai
targad'e. Ko gurin mai gyara baijeba ya nufo
gida a zafaffe ya shigo gida abin mamaki tana
kwance tana bacci. Ko kayan karinsu bata
kwasheba ga eirpiace a kunnuwanta. Take
jikinsa ya mutu mut. Cikin kasala ya zauna
gefanta.
Kansa ya d'auki zafi shin kodai gamo yai ake
neman rikitashi. Mi'ka tai ta farka tana fad'in
"wash" da sauri ta ware ido tana masa kallon
mamaki "hubbyna lafiya kadawo?". "Lafiyarki
nazo gani Najwa amma miyasa bakyasan adu'a
inkin farka?". Cikin shagwa'ba tace "hmmmmm
hubbyna mantawa nayi amma zan kiyaye, hope
kamun afuwa?". Ta fad'a tan langa'be kai cikin
murmushi ya ri'ko hannunta tai saurin zamewa
sabida jitai kamar antsikara mata alura. Da sauri
ya dubeta sai taimasa nuni da kumburin
hannunsa. Sai lokacin ya tuna da ciwan " miya
sameka" ta fada tana 'ko'karin barin kusa dashi.
"Oh! Najwa faduwa nai bari inje a gyaramun, a
gurguje yai mata bayanin samun aikinsa taimasa
fatan alkhairi. Yana fita tai tsaki ta yamutsa
fuska ta soma gyara dakin.
Muje dai.......
'KADDARARMU CE!.
SANAH S MATAZU.
19-20.
Satin hannun Mustapha d'aya ya warke zuwa
lokacin ya shiga duhu sossai abisa lamarin
Najwa. Yau da wuri ya dawo aiki sabida gajiya
sossai a tare dashi yana shigowa Najwa tana
zaune kusa da saurayin daya gansu a mota baiyi
wata-wata ba ya rufeta da fad'a kamar yaci
babu da haka ASHIQ ya shammaceshi ya 'bace
'bat. Najwa cikin masifa tace " kagafa nagaji
Mustapha walahi nagaji da takurawarka idan
kadaina sonane ka sauwa'kemani inhuta basai
kayiman shariba. Ina zaune ni kad'ai a d'aki
zakace nida wani". Cikin zubar hawaye yace
"shikenan Najwa kije na sakeki saki d'aya" Cikin
fashion hankali ta d'ora hannu akai "Mustapha
karkaimun haka, ina zan dosa ina nakama wazai
fuskanceni bayan na'ki kowa sabida kai, dan
Allah ka tausayamun".Cikin hawaye yace "Najwa
kisa a ranki 'KADDARARMU CE a haka bazan iya
cigaba da zama dake ba". Cikin kuka tace
"Walahi walahi Mustapha sai kayi nadama sai
kayi dana sani da Lanka sai kazo kana nemana".
Daga haka ya bar gidan Najwa jikinta yai sanyi
saita sami kanta da fad'uwar gaba. Tunaninta
ina ta nufa haka ta zari kayanta kala biyu ba
wanda ta kula ta nufi gida. Tana shiga yayarsu
ta dubeta da alamun tambaya duk ta hargitse a
ta'kaice tace mata "sakeni saki d'aya".
"Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un Najwa mekikai
masa haka yadda yake sanki harya sakeki?".
"Oho masa shiya rasa ko yanzu nai kwalliya na
fita miji zan samu". Ta wuce tana kad'a jiki ta
wurgawa Inna harara tuni ta sunkuyar da kai
'kasa.
Tunda Najwa ta tafi Mustapha ya tsinci kansa
cikin damuwa yanasan yaje gidan biko sabida
fad'an Mamarsa. Amma daya tunkari hanyar
gidan saiya rasa gane gidan yai d'imuwa. Mama
tayi tayi ya fad'amata abinda ya had'asu ya'ki
ta tattarashi ta watsar. Nan da nan ya sussuce
ya koma 'kazami kullum cikin damuwa.
Najwa tunda ta dawo bata zama yawan yau
daban na jibi da daban, tun Husnah nai mata
magana har takaisu ga gaggarumin fad'a babu
wanda ke kula kowa cikinsu.Aikuwa ko cangal
batayi ga tara samari matar dako iddah batai
ba.'Yan'uwanta sunyi fad'an sun gaji sun
ha'kura. Har gida Yaya Zainab tasa aka kiramata
Mustapha amma babu batun amsar komawa
'karshe yace mata zaiyi shawara bai sake
dawowa ko kiransa tai baya zuwa hakama
lesson ya daina zuwa kwata-kwata.Saidai kullum
tinanin Najwa na hanashi sukuni saidai ya zauna
yaita shinshina kayanta yana kuka.
Yauma Najwa tun safe tafita sai magarba ta
dawo. Kuma wani ikon Allah indai tafita sai
ASHIQ yai dabarar had'uwarsu waje d'aya da
Mustapha. Cikin sassarfa ta shiga gida jarkar
faro ta gani ajiye zatanta ruwane ta ganshi
garai-garai ashe ruwan tofine yayarsu ta
kar'bowa Inna wajan Leman cikin hanzari ta
d'auka ta soma sha ba tsayawa.
Tsawa biyu ta ratsa kunnuwan Najwa lokaci
guda, tsawar yayarsu data ASHIQ cikin fad'a
take tambayarta miyasa take shamata zatan
Najwa siya tai shiyasa ta kara kafa kai da
mugunta. Shikuwa ASHIQ takaici ya kasheshi
ganin za a wargaza masa shiri sabida tofin
ayoyin tsarine wata muguwar sha'ka yakaimata
take ta saki jarkar tana kakkari amma ina. Tuni
ruwan ya shiga cikinta. Da sauri yayarsu ta
tareta tana tambayarta men ene? Dai-dai lokacin
ya soma nuna Najwa yana fad'ar kinyi kuskure
saidai duk yun'kurinsa ya kasa aiwatar da komai
a kanta. Cikin rawar murya tai niyyar gaya mata
waye ASHIQ ga mamakinta a wannan karon
bakinta yana magana sa'banin shud'ad'din
lokutan da suka wuce" Yaya ASHIQ shine shine
shine yaiwa Innarmu haka........." Take bakinta
ya karkace hallitarta ta sauya daga Najwa zuwa
mummunar hallita.

KUNEMESHI A KASUWA KATANGAR KARFE ZAI KOMA


Download Complete Book Here