SARKIN SARAKAI
Littafi Na Biyar (5)
Part A.
.
Marubucin littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa..
LOKACIN DA AKA RUGUNTSUME DA AZABABBAN YAKI TSAKANIN wadannan Halittu da sarki Sahibul Hairi, sai gurin gaba daya yaruguntsume yazama babu Kyan gani, banda ihun Halittun da karar karafuna babu abinda make iya ji. kura kuwa ta turnuke dajin gaba daya.
Nan sarki Sahibul Hairi, da Bawa Haluf da yarinya Alfila suka zame musu alakakai, domin duk Inda suka durfafa sai kaga Halittun suna zubewa kasa.
A duk lokacin da sarki Sahibul Hairi ya sari Halittun sai kaga suna rabewa biyu yana tsargesu idan wiyansu ya Sara sai dai kaga Wiyan ya fita fit yayi same sannan ya fado kasa.
Shima wanan gwaggwan birin haka ya rinka ragargazar Halittun da wadannan dogayan itatuwa guda biyu da ke hannunsa.
Ita kuwa yarinya Alfita kan wata doguwar bishiya mai tsawon gaske ta hau harta isa izuwa karshanta sannan ta ci gaba da harbin Halittun da bakanta tana sakar musu kibiyoyi, sai dai kaga kibiyoyi na cakewa a cikin idanun Halittun, ko a wiya ta samesu sai kaga sun fadi kasa matattu.
Duke wannan Abu da ke faruwa sarki Barusa da jaruma Humaira na tsaye a can gefe da gefe suna kallon juna kuma suna kallon abida ke faruwa.
Koda sarki barusa yaga irin gagarumar barnar da akai masa, wato yaga wannan Dakar nasa suna zubewa kasa ya zamana cewa a kaso uku babu kaso biyu sai ya harzuka ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa sanna ya rugo inda jaruma Humaira ke tsaye domin ayi ta ta kare.
Ya yin da Humaira taga sarki Barusa ya dirfafo a guje rike da takobinsa sai itama ta ruga gareshi tana mai kwala kabbara Kuma ta zare takubbinta guda biyu.
Suna haduwa suka kacame da azababban yaki suna masu kaiwa juna sara da suka cikin zafin nama, juriya da bajinta.
Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda suke da mutukar zafin name tankar jikinsu bana jini da tsoka bane, kai kace na karfe ne.
Sai da suka shafe awa uku cur suna dauki back dadi dayansu bai sami nasarar koda kwarzanar daya ba. A dai-dai lokacin ne Sarki Sahibul Hairi, Bawa Haluf, Gwaggwan birin da Alfila suka gama kashe gaba dayan halittun.
Koda suka hango mugun artabu da akeyi tsakanin Humaira da Sarki Barusa sai hankalinsu ya dugunzuma ainun.
Nan take sai Sarki Sahibul Hairi ya ce "ya kamata mukaiwa Humaira dauki domin Ina ganin cewa bazata iya hallaka Sarki Barusa back".
Koda jin haka sai Bawa Haluf ya dubi sarki Sahibul Hairi cikin damuwa ya ce, "ya shugabana shin kamanta Humaira ta gargademu da cewar Kada mukuskura mutari sarki Barusa idan ana wannan gagarunin yaki? Ai kawai muci gaba da zuba ido domin muga abin da zai faru".
Koda jin haka sai sarki Sahibul Hairi ya zauna kasa durshan ya city gaba da ganin artabun Humaira da sarki Barusa. Alfila kuwa sai ta ci gaba da zamanta akan wannan doguwar bishiya.
Ya yin da sarki Barusa da Humaira suka ga sun shafe wannan lokaci suna kaiwa juna sara da suka ba tare da samun nasarar komai ba sai suka ja da baya suka yi carko-carko kamar zakaru sun haki da kallon juna.
Tsawon 'yan dakika suna tsaye a haka sai sarki Barusa ya fara amfani da karfin tsafi ya watsowa Humaira garwashin wuta mai yawa. Kafin garwashin wutar ya zuba a jikinta tuni ta kama karanta wadansu addu'o'i na musamman na neman tsari.
Duo garwashin da ya ta6a jikinta sai ka ga Kamar a cikin ruwa ya fada.
Nan take garwashin wutar zai mutu ya fado kasa a jike.
koda ganin haka sai ya sake yin wani tsafin ya watsa ma ta 6angorin kankara mai tsananin sanyi.
Duka kankarar da ta ta6a jikinta sai ta narke ta zama ruwa mai dumi.
Haka dai sarki Barusa ya yi ta jefawa Humaira mugayan abubuwa iri-iri har kala Dari ba daya amma bai sami nasar komai ba.
Al'amarin da ya mutukar fusatashi Kenyan ya kara kwarara uban ihu a karo na uku sannan ya yi jifa da takobin hannunsa ya gyara tsayuwarsa gami da dunkule hannayansa yana mai nuni da su.
Koda ganin haka sai itama Humaira ta gyara tsayuwarta Kumar ta dunkule hannayanta.
Sarki Barusa ya dubi Humaira ya yi murmushi ya ce, "idan ina son na tabbatar da ce wa za ki yi wan an gumurzu ne zallan karfin dantsenki said dai ki cire wannan damara da me kugunki saboda na San cewa darajarta ne kika iya samun Laguna".
Koda jin haka sai Humaira ta sa hannu zata kwance damarar da ke kugunta.
Cikin tsawa sarki Sahibul Hairi yace da ita, "kada kiyi hakan.
Lallai sarki Barusa yana son ya yaudareki ne ya sami nasara akanki.
Idan har yana ganin damarar ce abin dogaranki me yasa shima bai mallaki damarar ba? ai kar6ar wannan damara a hannun mai ita sai cikakken jarumi mai sadaukantaka ta ban al'ajabi".
Humaira ta kalli Sarki Barusa cikin murmushi ta ce, "kaji abin da sarki Sahibul Hairi ya fadi, me zaka iya cawa?"
Sarki Barusa ya bushe da dariya sannan ya ce, "ai bada tsagwaran karfin damtsanki kika kar6i damarar ba a hannun Shamzabul Azwas face kin yi amfani da Marfin sihiri irin naku na ma'abota addinin musulinci.
Humaira ta ce, "ai mu bama da wani sihiri face taimakon Ubangijimmu."
Barusa ya ce, "haka dai kika ce, amma ban yarda ba. idan Ubangijin naki ne yake baki sa'a ki cire damarar mana na gain".
Kafin sarki Barusa ya gama rufe bakinsa tuni Humaira ta kwance damarar daga kugunta ta ajiyeta gefe daya.
Nan take ta shiga kiran sunayan Allah tsarkaka a cikin zuciyarta tana mai Neman taimakon Ubangiji".
Koda sarki Barusa ya ga Humaira ta kwance wannan damarar ta ajiye a gefe daya sai ya bushe da dariyar farin ciki, sannan ya ruga gareta da dukkan karfinsa cikin mugun nufi. Ita Kuwa ta tsaya cak tana jiran karasowarsa harya iso kusa da ita ko gezau ba ta yi ba.
Sarki Barusa ya kawo mata wawan naushi a fuska da dukkan karfinsa. Ko kaucewa bata yi ba, Hannun nasa na naushin fuskarta sai yaji kamar dutse ya nausa, kuma yaji kamar 'yan yatsun hannunsa sun karye.
Basan sa'adda yayi kara ba gami da yarfar da hannu ya ja da baya cikin tsananin mamaki da firgici.
Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf , Alfiya da ke can gefe daya suma kallo suma sai da suka cika da tsananin mamaki bisa ganin abin da ya faru.
Jaruma Humaira ta kalli Sarki Barusa cikin murmushi ta ce, "yanzu gashi na ajiye damarar da kake tunanin da ita nake dogaro kuma na sami sama da karfin da nake da shi. Sirrin shi ne, na karanta addu'ar da keep jikin wannan damara ne na naimi taimakon Ubangijina.
Ita kuwa wannan addu'a ba komai bace face wadansu ke6antattun sunaye tsarkaka na Ubangiji wadan da bakowa ne ya san su ba.
Idan kayi imani da abin da name fada yanzu ka tuba ka daina shirka da tsafi ka kar6i addinina kuma mukoma kasarka ka kaddamar da addinin nawa ga jama'arka Idan kuwa ka ki ni da kai babu sauran sulhu sai dai mu ci gaba da yaki har dayammu ya ga bayan daya.
Koda jaruma Humaira tazo nan a zancenta sai sarki Barusa ya bushe da mahaukaciyar dariya sannan ya tur6ne fuska ya ce, "Ai ni tsakanina da ma'abota addinin musulunci sai yaki.
Ina son kisani cewa iyaye na da kakannina duk sun shude bisa tafarkin tsafi don haka babu wani dan zamani da ya isa ya gusar dani daga kanwannan tafarki na iyayena wanda nai imani da shi dari bisa dari.
Dan haka ga maza nan bisa kanki yarinya komai shaidancinki sai naga bayanki".
Koda gama fadin haka sai sarki Barusa ya durkusa ya dauki takobinsa ya tafi izuwa kan jaruma Humaira yana wani irin ihuda ruri mai firgitarwa.
Hatta kasar wajan sai da ta kama motsi kamar zata rufta.
Tsuntsaye da ke sama kan bishiyoyin kuwa suka kama yin hijira.
Wannan abu kuwa ya daurewa such sarki Sahibul Hairi kai shi ne, Jaruma Humaira dai ko motsi ma batayiba bare ma ta Naomi takobinta ta dauka amma bakinta na ta motsi alamar cewa tana karanta addu'ointa.
Ai kuwa sarki Barusa na isowa daf da ita sai ya kai mata wawan sara a weya da nufin ya tsage mata kai, cikin zafin nama ta kare saran da hannunta.
Take takobin ta 6alle gida biyu, al'amarin da ya mutukar razana sarki Barbuda ke nan ya juya da baya da sauri domin ya ruga da gudu, amma sai Jaruma Humaira ta shako wiyansa ta baya da hannu biyu tayi hajijiya da shi sannan ta dagashi sama tayi filfilwa da shi ta kwala da kasa.
Sarki Barusa ya baje a kasa a lokacin da yaga taurarin wuya a idanunsa kuma jiri ya kwashe shi ya yunkura da nufin ya mike tsaye amma sai ya Ji ya kasa. Humaira ta kafarta guda ta take wuyan sarki Barusa.
Nan take ya fara kakarin mutuwa, wani irin jini ya fara fitowa ta cikin kofofin hancinsa.
Koda ganin halin da sarki Barusa ya shiga sai Humaira ta fara jin tausayinsa ya dan darsu a zuciyarta, dan haka sai ta dan durkusar da kanta kasa dai-dai fuskarsa ta ce, "ya kai wannan sarki, idan har za ka yi imani da Ubangijina a yanzu zan Dauke kafata data kan wuyanka domin ka ray.
Koda jin wannan batu sai sarki Barusa ya tofawa Humaira jinin bakinsa ya dubeta cikin tsananin kiyayya da fushi ya ce, "Had abada ba zan kaunaci addininki ba domin na tsaneshi fiye da yarda na tsani mutuwata.
Kawai ki kashe ni shi ne abin da zai fiye miki alheri domin ba zan ta6a daina adawa da Ku ba har na mutu zan kasance a cikin tunanin kawar da addininku".
Koda jin wannan batu sai zuciyar Humaira ta kama tafarfasa kamar zata kone ta dubi sarki Barusa taga ya yi mata muni tamkar dodo, kawai sai ta kama kansa da hannayanta biyu ta murde masa wuya.
Sai da karar karyawar ta cika dajin gaba daya.
Nan take sarki Barusa ya zama gawa ko motsi bai kara yi ba.
Humaira ta mike ta nufi inda sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suke tsaye a lokacin da suka kura mata idanu suna yi mata jinjina bisa ganin gagarumar bajinta da tayi ta ban al'ajabi.
A dai-dai wannan lokacine yarinya Alfila ta sakko daga kan wannan doguwar bishiyar da ta hau. Humaira na isowa daf da su sai ta tsaya ta dubi sarki Sahibul Hairi ta ce, "yanzu mun rage daya daga cikin manyan abokan gabarmu saura guda daya wanda yafi kowanne hadari"
Cikin mutukar mamaki sarki Sahibul Haiti ya dubi Jaruma Humaira ya ce, "wanene Kuwa wanda ya fi sarki Barusa a garemu?"
Humaira tayi murmushi ta ce, " ba wani bane face matarsa Gimbiya Shukura.
Ka sani cewa ita mace ce Kuma bata da burin da ya fi a yanzu ta illa ta mallaki yarinya Alfila domin ta hada sihirin da za ta iya mallakar duniya.
Tabbas sai munyi da gaske wajan kula da Alfila domin nasan cewa a ko yaushe Gimbiya Shukura zata iya shammatarmu, ta zo ta saceta.
yanzu dai babu abin da ya kamacemu face mu hanzarta kai Alfila wajen mahaifinta domain na kawo karshen tafiyata da ku.
Koda gama jin haka sai Jaruma Humaira taji sarki Sahibul Hairi ya kirawo sunanta.
Cikin mamaki itama ta juyo ta dubeshi, sarki Sahibul Hairi ya ce, "kin manta da waccan Damarar".
Koda jin haka sai Humaira ta dubi can inda Damarar take sannan ta dubi Alfila ta ce, "ya ke 'year uwata maza ki ruga inda Damarar take ki daukota muci gaba da tafiya".
Cikin hanzari kuwa Alfila ta ruga da gudu taje ta dauko wannan Damara ta kawowa Humaira tana mai mika mata.
Humaira bata kar6i damarar ba sai ta dubi Alfila ta ce, "daura a kugunki tunda kema yanzu kina da ikon daurawata tun da kema musulmace".
Ba tare da gardamar komai ba kuwa Alfila ta daura Damarar a jikinta.
Faruwar haka ke da wuya sai Alfila taji wani irin gagarumin karfi ya shigeta kamar zata iya daga gammo tayi dakon duniyar gaba daya amma sai tayi shiru da bakinta bata fadawa kowa sauyin yanayin da taji ba.
Nan fa aka ci gaba da tafiya ba sassauci, domin tun kafin a fara tafiyar Humaira ta gayawa sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf cewa su tabbatar da cewa sun bita sahu da sahu, duk inda ta dauke kafarta to su sa ta su.
Ai kuwa ba su yi sanya ba said suka dinga binta sau da Kafa. Humaira ta ci gaba da tafiya tana mai karanta wadansu addu'o'i na musamman, nan da nan su sarki Sahibul Hairi suka ga tafiyar ta su tana mutukar sauri tamkar a sama suke yinta bisa aljani saboda gani suke suna ta gifta dazuzzuka Tamar walkiya.
Nan da nan suka sun shafe tafiyar sa'a bakyai a rabin sa'a.
Tun safe suka fara tafiya, amma basa tsayawa face idan lokacin sallah ya yi.
Sannan Humaira da Alfila suka yi Alwala suka gabatar da sallah sai suka ci gaba da tafiya.
Bisa mamaki sai suka ga har sun gifta ta manyan garuruwa guda biyu.
Daf sallar magariba suka isa birnin su Alfila.
Koda Alfila ta fara hango gine-ginen garunsu sai farin ciki mara misaltuwa kuma ta cika da mamaki yadda aka yi suka shafe wannan doguwar tafiya.
Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf kuwa dama tun sa'adda suka ga yadda Humaira ta sami nasara akan sarki Barusa sai suka tsinke da al'amarinta kuma suka Jim zuciyoyinsu sun fara gamsuwa da gaskiyar addininta gamma saboda burin da ke zuciyarsu bass son su yi saurin nuna yardarsu don Kara burin nasu ya tarwatse.
Da isowar su Humaira kofar garin sai suka iske kofar a kulle, masu gadi kimanin dakaru arba'in na tsaitsaye a bakin kofar birnin sun yi shirin yaki kowannansu na rike da makami sai muzurai suke kamar za su ci babu.
Da yake Humaira ce a kangaba sai ta dubi masu gadin ta ce, da su "ku bude mana kofa mu shiga birnin ku, mu bakine na salama kuma mun zo muku da alheri".
Koda jin haka sai shugaban dakarun wani narkeken kato mai kirar mutanan farko ya dubi Humaira ya ce, "Sarkin mu bamamu umarni kada mubudewa bako kofa ya shigo.
Wannan karamar yarinya da Luke tare da ita kadai zamu iya budewa ta shiga domin itace 'yar gari".
Sa'adda Humaira taji wannan batu sai ranta ya 6aci, kawai sai ta juya ta kalli Alfila ta ce, "ya ke 'yar uwata jeki ciki ki sadu da mahaifinki, ki bashi labarinmu in ya so shi yazo ya shigar damu cikin birnin naku idan sarkin naku ya bashi izini".
Alfila ta yi murmushi ta ce, "angama ya 'yer uwata".
Koda fadin haka said masu gadin kofar suka bude kofar, Alfila ta shiga ciki tana ta waigen Humaira kamar zata yi kuka, kai da gani kasan ba a son ranta aka yi haka ba, taso a ce anbar such Humaira sun shigo cikin
garin gaba daya. Alfila na shiga cikin birnin sai masu gadi suka mai da kofa suka rude.
A lokacin Humaira da sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka raka6e a gefe daya suka zauna domin su huta a lokacin ne hira ta fara wakana tsakanin sarki Sahibul Hairi da Humaira inda ta dubeshi ta ce, "Amma fa nayi mamakin irin wannan doka. Akan wana dalili sarkin wannan gari zai kafa dokar cewar baki baza su shiga garinsa ba.
sarki Sahibul Hairi ya yi ajiyar zuciya ya ce, "ni kaina na yi mamakin wannan al'amari, amma babu mamaki akwai mugun abu da wani bakon ya zo ya yi, kin san ance wake daya 6ata gari, babu mamaki wani bakon ne ya shafa mana kashin kaji."
.
Zan dakata a nan saikuma Allah yakaimu gobe zamu cigaba
Admin
AA Misau Ke Magana
SARKIN SARAKAI
Littafi Na Biyar (5)
Part B.
.
Marubucin littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa..
HUMAIRA TA YI AJIYAR ZUCIYA SANNAN TAYI SHIRU NA DAN WASU DAKIKOKI KADAN SANNAN TA CE, " YA KAI WANNAN SARKI SHIN HARYANZU BAKA YANKE SHAWARA BANE a zuciyarka bisa kar6ar addinina?
Ka sani cewa nifa na gaji yin wannan tafiya tare da ku, in da back don ina kwadayin in ga ka kar6i musulinci ba da tuni mun rabu.
Ba komai ne yasa kaga ina so ka sami wannan babban rabo ba face saboda naga cewa kai adalin mutunne mai tausayi da jin kan talakawa Kuma kasar ka ta kunshi muliyoyin al'umma. Idan ka kar6i addinin musulinci tamkar muliyoyin jama'a sun kar6i addinin ne.
Sa'adda Humaira ta zo nan a zancenta sai sarki Sahibul Hairi yai ajiyar zuciya gami da Sunkui da kansa kai sannan ya dago ya dubeta cikin alamun tsananin dimuwa ya ce, "ya ke wannan jaruma mai karamci da ban al'ajabi kiyi sani cewa na sha bakar wahala tun daga lokacin da na baro kasata har name gamu da ke kawo i yanzu kuma gashi har yanzu abin da na fito dominsa ban samu ba
Zuciyata ta kwadaitu da son ganin 'yammata ukun da aka ce sai na auresu sannan burina zai cika.
Yanzu gashi har nazo garin su sadauki Awaisu wanda shine kadai mutumin da zai iya kai ni inda wadannan 'yan mata uku suke.
Yanzu fa idan na kar6i addininki shi ke nan ba zan ta6a ganin wadannan 'yan mata ba har abada.
Saboda me zan bar wannan dama ta wuceni alhali aski ya zo gaban goshi saura kiris ya kammalu".
Sa'adda jaruma Humaira taji wannan batu sai takaici ya kamata, zuciyarta ta yi bakikkirin nan take taji tayi nadamar biyo sarki Sahibul Hairi tun daga kasarta domin Jan hankalinsa izuwa addinin musulinci tun da gashi har yanzu ya ki kar6ar addinin duk da cewar ya ga abubuwan al'ajabi na gas gata Allah".
Cikin tsananin fushi Humaira ta kalli sarki Sahibul Hairi ta ce, "Ai shi ke nan ni dai na gama cika nawa aikin kuma lallai a yau ne zan rabu da Ku.
Abin da ya tsai dani kawai a nan shi ne, na tabbatar cewa Alfila ta sadu da mahaifinta kuma ina kwadayin na ga mahaifin Alfila shima ya kar6i addinin musulinci kamar yadda 'yar sa ta kar6a.
Lallai zan so na gana da shi domain naga inda ra'ayinsa ya karkata.
Idan har sadauki Awaisu ya kar6i addinin musulinci, sarki garin nan ma zai iya kar6a, idan kuwa sarki ya kar6a tamkar mutanan birnin ne gaba daya ne suka kar6a. Wannan shi ne iyakar Burina".
Koda jin wannan batu sai hankalin sarki Sahibul Hairi ya dugunzuma yai shiru ya rasa abinda zai ce da Humaira, ya sunkwi da kansa kasa yana tunani.
Babban abin da yasa hankalinsa ya tashi shi ne, jin cewar a yau ne Humaira zata rabu da shi.
Nan take sarki Sahibul Hairi ya ji kamar ya fashe da kuka domin kauna da bergen Humaira ne ya taso masa ya cika masa zuciya, kuma ya rasa abin da ke masa dadi.
Shima Bawa Haluf sai ya ji ya kamu da tsananin damuwa kamar roki Humaira akan ta ci gaba da zama tare da su har izuwa lokacin da maigidansa zai cika burinsa, amma sai ya kura ma ta idanu kawai ya kasa cewa komai.
Ya yin da Humaira taga Bawa Haluf ya kura mata idanu sai ta daka masa harara ta ce, "kai kuma fa lafiya ka kura mini ido haka? ko kuwa baka ta6a ganina bane sai yau".
Koda jin wannan tambaya sai Bawa Haluf ya yi murmushi ya ce, "ki gafarcene ya shugabata wani Abu na tuno wanda me da sarkina kuka manta da shi."
Cikin mutukar mamaki Humaira ta ce, "wana abu ke nan"?
Bawa Haluf ya ce, batun goggon birin da ya taimaka mana a yakin da mukayi da sarki Barusa.
Tun sa'adda muka gama yakin bamu sake ganinsa ba, kuma dayanmu baiyi zancensa ba. shin an kasheshine a wajan yakin ko kuwa sulalewa ya yi yayi tafiyarsa bamu sani ba ko ya ya?"
Koda jin wannan batu sai Humaira da sarki Sahibil Hairi suka kalli junansu cikin tsananin mamaki sannan sarki Sahibul Hairi ya ce, "Hakika Haluf maganarka gaskiyace, domin duk mun sha'afa mun manta da batun wannan biri, amma ni a tunanina wannan birin ya mutu domin kuwa inda yana raye bazai daina biyomu ba, said dai idan ya koma wajan 'yan uwan sa inda ya fito".
Humaira tayi ajiyar zuciya ta ce, "ai wannan biri bazai koma inda ya fito ba, domin idan ya koma wajansu kasheshi zasuyi tunda sun san cewa ya za6imu a Kansu.
Ni dai abinda nake zargi shine, lallai an kasheshi a lokacin da Mike wannan yaki amma Kuma abin mamakin shi ne bamu ga gawarsa ba a wajan".
Koda gama fadin haka sai Humaira ta kashingida saboda gajiya tayi shiru bata kara cewa komai ba.
Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka yi shiru basu kara cewa uffan ba.
WANNAN SHI NE ABIN DA YA FARU GA SU SARKI SAHIBUL HAIRI BAYAN DA JARUMA HUMAIRA TA KAWOSU GARIN SU ALFILA A CIKIN KANKANIN LOKACI BISA TAIMAKON ALLAH.
Al'amarin yarinya Alfila kuwa, lokacin da aka bude mata kofar garinsu ta shiga sai ta nufi izuwa hanyar gidan mahaifinta sadauki Awaisu cikin farin ciki tana dokin ta isa ta sadu da shi.
A sanin Alfila daga bakin kofar garin zuwa gidansu tafiyace ta a kalla sa'a uku, amma bisa mamaki sai taga ta share tafiyar a cikin abin da wuce wadansu 'yan dakiku ba. Al'amarin da ya matukar ba ta mamaki ke nan.
Abin da ta manta shine, wannan damara ta Shamzabul Azwas tana nan a daure a kugunta.
Sa'adda Alfila ta isa kofar gidan mahaifinta sai ta iske gidan a kulle kuma dakarun sarki sama da mutum dubu sun kewaye gidan sai muzurai Duke.
Al'amarin da ya mutukar bata mamaki ke nan, jikinta ya yi sanyi, kuma hankalinta ya duguzuma ainun.
Alfila ta karasa da sauri zawa ga dakarun ta Dubi daya daga cikinsu ta ce, "mene ne yake faruwa ne, ina mahaifina?"
Koda jin wannan tambaya sai badakaren nan ya dubeta cikin tsananin tausayi ya ce, "ya ke Alfila ai tunda aka saceki mahaifinki ya kamu da rashin lafiya saboda bakin cikin rabuwa da me da sanin cewa bazai iya zuwa inda kike ba ya Kar6oki.
Bisa wannan dalili ne ya kwanta rashin lafiya kullum sai dai a kwantar a tayar. Babu irin kokarin da 'yan uwansa basu yi ba na nema masa magani amma abun sai ya ci tura.
Kinsan cewa mahaifinki shine sarkin ya ki a garin nan kuma sarki na mutukar kaunarsa bisa hakanne sarki yasa aka daukeshi aka kaishi can gidan sarauta domin ya yi jinyarsa da kansa kuma ya umarcemu da muyi gadin gidan naku saboda kin san cewa akwai tarin sirrikan tsafinsa a cikin gidan Wanda duk duniya babu kamarsu. an ce ke kadai kike da irin sirrikan tsafin a jikinki"
Lokacin wannan badakare ya so nan a zancansa sai hankalin hankalin alfila ya dugunzuma fiye da ko yaushe, nan take hawaye ya zubo mata, tai shiru tana tunani.
Babban abinda ya tayar mata da hankali shi ne, a iya saninta da mahaifinta bai ta6a zuwa gidan sarki ba.
Koda yaki za'a fita sai dai a tura a gaya masa ya shirya ya taho a hadu da shi a filin daga.
Asalin sadauki Awaisu shima dan gidan sarauta ne kuma ubansu daya da sarkin garin, amma ko kadan shi baya sha'awar harkokin sarauta.
A rayuwar sadauki Awaisu shi ba shi da wani buri wanda yafi ya gawurta a harkokin tsafi da jarumta a duniya, amma ko kadan dukiya da mulki basa gabansa.
Sarkin garin da sadauki Awaisu su kadai ne 'ya 'ya a wajan mahaifinsu, amma awaisu ne babba tun mahaifinsu yana da rai Awaisu ta ce shi bazaiyi sarauta ba ya barwa dan uwansa kuma tun daga sannan ya hada nasa i nasa ya bar gidan sarautar ya gina nasa a can bayan gari ya tare.
A wannan lokaci mahaifiyar Alfila na dauke da cikin Alfila. A ranar da ta haifi Alfila ne ta mutu.
Alfila ta taso bata San kowa ba sai mahaifinta da kuma hadimansa.
Sa'adda ta fara girma ne ya bata labarin mahaifiyarta da kuma labarin dangantakarsa da gidan sarauta.
Koda sau daya bai ta6a daukarta ya kaita gidan sarautar kuma shi sarki ba a garin bai ta6a zuwa gadansu ba a matsayin ya kawo ziyara ga dan uwansa
Wata rana Alfila ta dubi mahaifinta Sadauki Awaisu ta ce, "ya abbana ka gaya mini cewa sarkin garin nan dan uwanka ne to me yasa baka zuwa wajansa shi ma baya zuwa wajanka?"
Lokacin da yaji wannan tambaya sai ya sunkwi da kansa kasa ya yi shiru kamar banzai ce komai ba, sannan ya yi ajiyar zuciya ya dago ya dubi Alfila ya ce, "ya ke 'yata abar soyuwa a cikin raina kiyi sani duk ranar da naje gidan sarki ko kuma shi yazo gidana to daga wannan rana sai daya data cikinmu ya rasa matsayinsa. ko dai ni na rasa dukkan sihirin tsafina ko kuma shi sarki ya rasa mulkinsa.
Sa'adda Alfil ta zo dai-dai nan a tunaninta said zuciyarta ta buga da karfi, domin tasan dolane cikin biyu dolene ayi daya.
Ko dai mahaifinta ya rasa dukkani. sihirin tsafinsa ko Kuma sarki ya rasa karagarasa.
Nan take taji bata gamsu da bayanin da wannan badarakare ya yi ma ta ba sabo da haka sai ta juya da gudu ta nufi hanyar da za ta kai ta gidan sarautar garin.
Nan da nan kuwa Alfila ta isa kofar gidan sarautar.
Da zuwa sai ta iske mahaifin ta tsaye a kofar gidan idanun sa sharkaf da hawaye ya kura mata idanu.
Al'amarin da ya mutukar girgizata Ke nan ta cika da tsananin mamaki ta tsaya cak! daga nesa suna kallan juna tace a ranta, "ya ya mutunin da aka ce da ita yana kwance magashiyan bashi da lafiya kuma gashi yanzu a tsaye a gabanta bisa duga-dugansa. Kuma ina dalilin zubar da wannan hawayen a idanunsa ko kuwa name farin cikin ganinta ne?
Alfila ta tambayi kanta a cikin zuciyarta kuma ta kasa baiwa kanta amsa.
Koda Sadauki Awaisu yaga Alfila ta tsaya a nesa ta ki karasowa gareshi sai ya durkusa bisa gwiwoyinsa ya bude hanyansa ya ce, "Rugo gareni ya ke 'yata na ji ki a kirjina ashe zamu sake saduwa a wannan duniya?.
Rugo gareni ya ke rabin jikina, rabin ruhina Kuma cikamakin Burkina".
Koda jin haka sai Alfila ta ruga da gudu saboda ta San cewa mahaifinta ne kadai yake mata irin wannan furuci.
Sai da ya rage saura kiris ta isa gareshi sai taga ya 6ace daga inda yake durkushe ya bayyana a bayanta yana mai kyalkyala dariya.
Al'amarin da ya mutukar firgita Alfila ke nan ta juya a tsorace ta dubi Awaisu ta ce, "wanene kai ina mahaifina take?"
Koda jin wannan tambaya sai Awaisu ya rikide koma gimbiya Shukura matar sarki Barusa tana kyalkyala dariya.
Daga can kuma sai ta murtuke fuska ta dakawa Alfila tsawa ta ce, "ke yarinya kiyi sani cewa rayuwar mahaifinki da ta dan uwnsa duk suna hannuna
Idan kina so su tsira da rayuwarsu to ki big dukkanin umarnina.
Ki sani cewa a halin yanzu mulkin wannan gari a hannuna yake domin nazo na yaki garin nan gaba daya ni kadai na ci su da yaki".
koda jin wannan batu sai Alfila ta tsandara ihu ta ce, "ya ke wannan hatsabibiya ki sani cewa karyarki ta sha karya domin baki isa kiya yaki da mahaifina ba har ki cishi da yaki domain duk abinda kike takama da shi ya Fiji."
Shukura ta bushe da dariya sannan ta hade fuska ta ce, "Ai ba fito na fito mukayi da shi ba, kamar yadda na yaudareki a yanzu haka na yaudari Kowa a garin nan na ci su da yaki.
Yanzun nan zan nuna miki halin da mahaifinki yake ciki.
Idan kika bi umarnina ya ku6uta, Idan kuwa kika bijire mini ya hallaka.
Koda gama fadin haka sai sukura wuce izuwa cikin gidan sarautar, Dakaru suka rinka ratsewa suna bata hanya cikin dari-dari.
Alfila ta bita a baya har suka shiga cikin turakar sarki.
Babu abinda ya daurewa Alfila kai face yadda daya Dakarun gidan hadimai ki ta ratsewa shukura cikin girmamawa tamkar itace sarkin birnin.
Alfila ta tambayi kanta cikin zuciyarta ta ce, "wai shin gimbiya shukura da karfin tsiya ta kar6i birnin ne ko kuwa da karfin sihiri?"
Amsar da ta kasa baiwa kanta ke nan.
Da shigarsu cikin turakar sai Alfiya tayi arba da mahaifinta sadauki Awaisu kwance akan gado an daureshi tamau da wata irin sarkar tsafi wacce ta kanannade jikin gaba daya tana ta zagayeshi.
A 6angaren kudancin dagon da yake wani gadon ne daban sarkin garin na kwance shima an daureshi tamau da irin wannan sarka.
Koda shukura tayi nuni da hannunta izuwa kan sadauki Awaisu sai sarkar tsafin ta daureshi tamau ya kwalla ihu sakamakon zafin da yaji tamkar kasusuwan jikinsa za su kakkarye.
Gimbiya shukura ta bushe da dariyar mugunta ita kuwa Alfila ta ruga da gudu izuwa kan mahaifinta ta rungumeshi kuma ta fashe da kuka tana mai duban shukura ta ce, "ya ke wannan matsafiya ki gayamin abin da ki ke so na yi domin ki kyale mahaifina kada ki salwantar da rayuwarsa".
Koda jin haka sai sadauki Awaisu ya yi farat ya ce,"ya ke 'yata kada kibi uamarnin wannan azzaluma domin ko kinyi abin da take so ba zata fasa hallakamu ba.
ki sani cewa ta cika mayaudariya kuma maci amana, kuma a halin yanzu tafi kowa karfin sihiri a duniya. sihiri daya ne ya rage mata wato wanda ke cikin jikinki".
Alfila ta kalli Awaisu cikin mamaki ta ce, "ya kai abbana yaya akayi wannan mata ta samu nasara a kanka alhalin kafi karfin dantse da na sihiri?"
Awaisu ya kwada kai cikin takaici ya ce, "Ai kamar yadda na gaya miki ta zo garinnan a siffar 'yar uwar mahaifiyarki wacce ke zaune a birnin kisra wadda rabona da ita tun da aka yi rashin mahaifiyarki tun da ta tafi bata sake dawowa garin nan ba. kwatsam sai na ganta ta zo.
Bayan na sauketa a gidana sai ta gaya mini cewa anyi yakine a birnin kisra an kashe mijinta da 'ya 'yanta biyu don haka yanzu bata da kowa a duniya shi yasa ta dawo garemu.
A lokacin ne ta tambayi labarinki na gaya ma ta cewa ai boka shamzabul Azwas ya sace ki tsawan shekaru.
Koda jin haka sai ta fashe da matsanaicin kuka na bakin ciki.
Da kyar da sidin goshi na shawo kanta ta daina kukan.
Ina mai rarrashinta ta na cewa shi ke nan yanzu babu wanda za ta kalla ta gani a matsayi. tsatson jininta.
Daga wannan rana ta ci gaba da zama a gidana ya zamana cewa tanayin ayyukan gida kamar yadda mahaifiyarki ke yi mini sa'adda tana raye. Hatta abinci itace take girkawa tana bani ina ci.
Kin sani cewa da ma ita 'yar uwar mahaifiyar taki kamrsu daya da mahaifiyar taki don haka sai soyayya ta shiga tsakaninmu.
Cikin kankanin lokaci magaar aure ta wakana.
A daren da na shiga dakin Amarya ne na tsinci kaina a cikin wani irin mugun hali domin nan take na daina Jin kwarin jikina na yan ke jiki na fado kasa daga kan gado kuma naji ko danyatsan hannuna bazan iya dagawa ba.
Haka kuma sai na ji gaba daya sirrikan tsafina sun daina aiki.
A wannan lokacin Amaryata tana zaune a gefan gado kawai ta Kura mini ido tana murmushin mugunta.
Da kyar na juyar da kaina na kalleta kuma na bude baki na ce, "ya ke matata ina dalilin faruwar wannan al'amari a gareni?.
Koda jin wannan tambaya sai ta bushe da mahaukaciyar dariya sannan tayi girgiza ta rikide izuwa kamannin Shukura matar sarki Barusa.
Nan take ta gabatar da kanta a gareni sannan ta ce,"ya kai wannan Sadauki kayi Sani cewa 'yar uwar matarka tana can birnin kisra tare da mijinta da 'ya 'yanta lafiya kalau, Kawai na juya izuwa kwmannin ta ne na zo nan kasar domin na Kama garin naku Karin su sarki Sahibul Hairi su iso tare da 'yarka Alfila".
Koda jin haka sai na cika da farin ciki duk da cewa ina cikin wannan hali name ce yanzu kina nufin cewa su sarki Sahibul Hairi sun sami nasarar dauko Alfila daga fadar sarki Shamzabul Azwas?"
Shukura tayi murmushi ta ce, "kwarai kuwa kuma suna nan akan hanyarsu ta zuwa nan domin su mika Alfila a gareka.
Bukatar Sarki Sahibul Hairi itace ka daukeshi ka kaishi gurin 'yam mata uku wadanda idan ya sure su sai yafi kowa na sarki daukaka, mulki da karfin arzuki.
Ni kuwa bazan ta6a bari ya samu wannan matsayin ba, idan ya sameshi burina na son mulkar duniyar nan gaba daya ba zai cika back. Lallai nice nake son na hau wannan matsayi wanda sarki Sahibul Hairi ke bukata.
Abu na farko da zanyi shi ne, na sake rabaka da 'yarka Alfila na tafi da ita izuwa can birninmu na cire sirrikan tsafin jikinta wanda ka sa Mata na Mai da shi jikina domin na samu irin karfi da boka Shamzabul Azwas ya Samu.
Kai kanka ka sani cewa Alfila ce kawai mai
irin wannan karfin.
Bayin na cire sirrin daga jikinta na sa shi a
jikina sannan sai ka rakani inda wadannan
mata uku suke domin na kamasu suma na
cire sihirin da ke jikinsu ya zamana cewa
nafi kowa arziki da daukaka a duniya tunda
na fi kowa karfin sihiri".
Koda gama wannan jawabi sai Shukura ta
bushe da dariyar mugunta.
Tana cikin dariyane ta dafani, nan take
muka 6ace tare ni da ita.
Bamu bayyana a ko ina ba sai a tsakiyar
turakar nan inda muka iske a kwance kan
gadonsa yana ta shara barci.
Nan take tayi nuni da hannunta sarkar tsafi
ta daureshi.
Nima sai ta nunoni da hannu na tsinci kaina a kan gadon daure da sarkar sihiri kamar yadda sarki ya kasance.
Tun daga wannan rana Shukura ta rinka wanzuwa a cikin siffar sarkinmu shi yasa kika ga kowa yana biyayya a gareta sai abin da ta ce shi ake yi.
Yanzu ke kadai ce kika ganinta a cikin ainihin siffarta.... Hatta ni da sarki a cikin siffar sarkin muke ganinta".
Koda jin wannan batu sai Alfila ta juya ta kalli Shukura ta ce, "yanzu me kike son na yi miki ki kyale mahaifina baza ki kashe shi ba?".
Sa'adda gimbiya Shukura ta ji wannan batu daga bakin Alfila sai ta tuntsure da dariyar farin ciki sannan ta murtuke fuska tamkar wadda aka aikowa mata da sakon mutuwa ta ce, " abu na farko da nake so ki yi shi ne, ina so ki cire damarar da ke jikinki ki ajiyeta a gefe daya sannan na baki wuta ki kona damarar da hannunki
Abu na biyu da za kiyi shi ne, zaki koma can kofar garin tare da ni, kuma zan je ne a siffar mahaifinki domin mutarbu su sarki Sahibul Hairi mu shigo da su har nan cikin fadar domin na hallakasu cikin salim alim sannan na dauke ki na tafi da ke".
Koda jin wannan batu sai Alfila ta mike tsaye daga kan mahaifinta ta dubi shukura ta ce, "yanzu mene ne tabbaci idan na aikata duk abin da ki ka umarceni baza ki ta6a lafiyar mahaifina ba.?"
Da jin wannan tambaya sai shukura ta yi murmushi ta ce, zaki sameni mai cika alkawari idan har ki ka aikata abin da na umarceki".
Alfila ta ce, "ai ke ba mai cika alkawari bace. Idan da mai cika alkawari ce baza ki ta6a cin amanar mijinki ba sarki Barusa tunda bai rageki da komai ba a rayuwarsa, sannan ya nuna miki tsananin kauna kamar yadda uwa ko uba yake son dan da suka Haifa".
Kada jin wannan batu sai Shukura ta fusata ta sake nuni da hannunta izuwa kan sadauki Awaisu kawai sai wannan sarka ta sihiri ta kara matse sadauki Awaisu tamau fiye da karon farko.
Awaisu ya kurma uban ihu, wannan karon har sai da kashin kafarsa ya karye yai kara kal!
Alfila ta rusa ihu Kuma ta zare takobinta tai kan Shukura da nufin ta sareta, sai Shikura ta daka mata tsawa ta ce, "idan ki ka karaso inda nake zan karasa mahaifinki.
Kawai ki yi abin da na umarceki baki da wani za6i".
Cikin karfin hali Awaisu ya dubi Alfila a lokacin da gaba dayan fuskarsa ta cika da gumin wahala ya ce, "Na gaya miki kada ki bi umarninta.
Da dai ta umarceki ki ci amanar su sarki Sahibul Hairi wadanda suka sha wahala suka daukoki daga cikin fadar Shamzabul Azwas kuma suka kawoki har nan domain ki sadu da ni ai gwara ki bari ta kasheni
Fatana shi ne burina kada ya cika tunda ta kasance azzaluma wadda zata haddasa zalunci da bakin mulki a doran kasa.
ya ke 'yata na gani a cikin madubin tsafina cewa kin kar6i addinin musulinci a gurin gimbiya Humaira tun kafin Shukura tazo garin nan, kuma ko kadan bana bakin ciki da hakan.
Dama shirina shi ne, da zarar kin dawo gareni ni ma na kar6i wannan addinin kuma nasa sarkin mu shi ma ya kar6a domin gaba daya al'umar kasan nan su ma su kar6eshi.
ya ke 'yata in kika ka bi umarnin shukura duk wannan shirin ya wargatse ke nan. Ina tabbatar miki da cewa ni da sarki duk mutuwa zamu yi".
Lokacin da sadauki Awaisu ya zo nan a zancensa sai hankalin Alfila ya dugunzuma ta rasa abinda zata yankewa kanta hukunci. kawai sai ta Kama kallon fuskar sarki da ta sadauki Awisu a sannan kuma sai ta dubi shikura wacceke tsaye tana ta murmushi mugunta.
Alfila ta kama duru-duru da sake-saken zuciya. Bayan ta danyi nazari a cikin zuciyarta sai kawai ta kwance wannan damara dake jikinta ta ajiye a gefe daya.
Koda ganin haka sai shukura ta bushe da dariyar mugunta da farin ciki.
Nan take shukura tai tsafi sai ga wutar ice ta bayyana a hannunta.
Kawai sai ta mikawa Alfila wutar sai ta kar6a sannan tace da ita, "maza ki kona wannan damara".
Alfila ta nufi inda ta jefar da damarar tana waigen shukura da su sadauki Awaisu hawaye na zuba daga cikin idanuwanta, kai da gani kasan ba a san ranta zata kona damarar ba sai bisa dole tunda ba yadda za ta yi.
Shi kuwa sadauki Awaisu sai takaici ya rufeshi bai san sa'adda ya matso kwallar bakin ciki ba.
Shi kuwa sarki dama ya dade yanata kukan zuci da zahiri bisa halin da ya tsinci kansa karkashin ikon gimbiya shukura a matsayinsa na sarkin guda mai cikakken iko amma sai yadda aka sarrafashi tun da gashi an kwace masa karagasa da jama'arsa.
Tun daga ranar da ya bude ido daga bacci yaga shukura tsaye a kansa bai kara mikewa zaune ba yana kwance kan gado a daure, shukurace ta ci gaba da zartar da komai na sarautar Kasar.
Haka Alfila ta dosana wannan wuta a kan wannan damara tana ji tana gani. Nan take damarar ta kama cin wuta, cikin dakika kadan ta kone kurmus ta zama toka.
Koda ganin haka sai gimbiya shukura ta bushe da dariyar farin ciki, ta ce, ‘’yanzu kin bi umarnina na daya da na biyu saura na uku kawai. Sai ki biyoni a baya muje can kofar gari inda kika baro su sarki Sahibul Hairi.
Kafin mu tafi ina mai gargadinki da kada ki kuskura ki ce za wani abu ba dai-dai ba a gareni domin kina yin dan kuskureko kika ce zaki tona min asiri a wajan su gimbiya Humaira a bakin ran mahaifinki.’’
Gama fadin haka ki da wuya sa gimbiya Shukura ta juya ta fice daga cikin turakar, Alfila ta bita da sauri a lokacin da sadauki Awaisu ya bisu da kallo kawai cikin tsananin takaici da bakin ciki hawaye na kwarara bisa kumatunsa.
Gimbiya Shukura da Alfila suka jera suna tafiya a cikin harabar gidan sarautar tamkar babu wata damuwa a tsakaninsu.
Abin da idanun jama’ar gidan ke gani shi ne, Sarkinsu tare da Alfila ‘yar sarkin yaki don haka duk inda suka wuce sai ayi ta kallonsu cikin mutukar mamaki domin an san cewa Alfila ta 6ace tsawon shekaru amma yanzu gashi ta dawo, alhalin an ce sarkin bokayan aljanun duniya ne ya saceta kuma babu mahalukin da zai iya shiga fadarsa ya kar6ota.
.
Zan dakata a nan saikuma Allah yakaimu gobe zamu cigaba
Admin
AA Misau Ke Magana
SARKIN SARAKAI
Littafi Na Biyar (5)
Part C.
.
Marubucin littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Admin
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa..
.
ALHALIN ANCE SARKIN BOKAYEN ALJANUN DUNIYA NE
YA SACETA KUMA BABU MAHALUKIN DA ZAI IYA ZUWA
FADARSA YA KARBOTA
To wai shin yanzu yaya aka yi ta dawo gida ?
Amsar da babu wanda ya san ta ke nan, sarki sahibul hairi,
bawa haluf, da gimbiya humaira suna zaune a kofar
birnin
sun gaji ainun da jiran dawowar yarinya alfila,
sun kagu sosai, har humaira ta fara zargin anya
kuwa lafiya? Bai kamata suci gaba da jiran gawar shanu
ba
cikin matukar damuwa sarki sahibul hairi ya dubi
humaira yace yake wannan jaruma mai abin mamaki, yanzu me ya kamata muyi?
Humaira tace ai tun da dai yarinyar nan ta dade bata
dawo ba lallai akwai abin da ya faru ba dai dai ba
saboda haka ina ganin cewa kawai mu shiga cikin
garin nan ta kowanne hali koda salama ko da tsiya tsiya
nan take humaira ta mike tsaye ta zare takobinta ta nufi
bakin kofar cikin sauri sarki sauri sarki sahibul hairi da
bawa haluf ma suka zare nasu takubban suka take mata baya
koda masu tsaron kofar suka hangosu sai suma suka zazzare nasu
makaman suka tsaya suna jiran isowarsu a ruguntsume
ba zato ba tsammani sai masu tsaron kofar sukaji an daka musu tsawa daga bayansu
cikin sauri suka waiga sai suka ga ashe sarkinsu ne tare da yarinya alfila
cikin gaggawa suka dare suka basu hanya suka
wuce ta tsakiyarsu suka nufi inda su humaira suke
humaira sarki sahibul hairi da bawa haluf sai suka
cika da tsanannin mamaki lokacin da suka hango yarinya alfila tare da mahaifinta sadauki awaisu a tafe cikin
nishadi
awaisu rike da hannun alfila, da isowarsu sai awaisu
ya dubi sarki sahibul hairi cikin tsananin farin ciki ya ruguntsumeshi yana mai cewa, lale marhaban da sarki mai daraja wanda ya share mini hawayen bakin ciki na tsawon shekaru
lallai zan kasance mai taimakonka har izuwa lokacin
da bukatarka zata biya koda kuwa zan rasa rayuwata
koda jin haka sai sarki sahibul hairi ya cika da matukar
farin ciki ya janye jikinsa daga cikin nasa awaisu, sannan ya bashi hannu suka gaisa
koda gaisuwar tasu sai jikin sarki sahibul hairi yayi
sanyi, ba komai ne ya janyo hakan ba face irin yanayin da
yaji hannun awaisu mai tsananin taushi tamkar na mata
awaisu ya dubi sarki sahibul hairi ya ce yanaga jikinka ya yi sanyi
ne sarki sahibul hairi yayi murmushi yace, babu komai, kawai na tuno da irin halin da kake ciki ne a yanzu na
farin ciki bisa sake saduwa da yarka alfila
tabbas na san cewa a yanzu babu wanda ya fika murna da kwanciyar hankali a wannan birni
koda jin wannan batu sai awaisu ya bushe da
dariya yace tabbas abinda ka fadi gaskiya ne kuma babu
wanda ya fini bakin ciki a lokacin da aka rabani da alfila
inda baku je kun daukota kun dawo mini da ita ba, tabbas zan iya kamuwa da cutar
ajali a ko yaushe
koda gama fadin haka sai awaisu ya dubi gimbiya humaira da bawa haluf da kyau
sannan yayi murmushi yace an gaisheku manyan jarumai
hakika kun sha gwagwarmaya tsakaninku da sarki
shamzubulu azwas da sarki barusa, na gamsu cewar kun cika manyan sadaukai a duniya
wadanda har abada ba za a manta da tarihin sadaukantakar suba
cikin matukar mamaki humaira ta dubi awaisu tace
yaya akayi ka san irin gwagwarmayar da muka yi dasu shamzubul azwas alhalin tsafinsu yafi naka
tasiri ba za ka iya ganin al amarinsu ba a cikin tsafinka
koda jin wannan tambaya sai sadauki awaisu ya dan rikice ya kasa bada amsa da wuri
amma sai ya dan wayance yace ai alfila ce ta bani labarin duk abinda ya faru a gareku
koda jin haka sai sarki sahibul hairi da bawa haluf suka yi dan murmushi
ita kuwa sai ta tsuke fuska domin ko kadan bata ji ta aminta da awaisu ba
awaisu ya dubesu gaba daya cikin fara a yace yanzu saiku
zo mu shiga cikin gari domin muje gidana ku zauna ku huta kuci abinci
ba tare da gardamar komai ba kuwa su humaira suka bi
sadauki awaisu da alfila izuwa cikin garin
sai da suka yi yar tafiya mai dan tsawo sannan suka iso gidan sadauki awaisu
da zuwa masu gadi suka bude musu kofa suka shiga ciki
shigarsu keda wuya sai ga kuyangi maza da mata sun tarbesu da lale marhaban, sukayi musu rakiya har izuwa
babbar turakar gidan
daga nan kuma sai awaisu ya umarci wani hadimi
da yaje ya nunawa humaira nata dakin daban
sarki sahibul hairi da bawa haluf ma sai aka kaisu nasu
dakin daban kuma aka umarci kuyangi da su shirya abinci
na musamman ga baki
lokacin da aka kai humaira dakinta aka tafi aka barta ita kadai sai ta rufe kofar dakin sannan ta shiga kewaye
taje taayi alwala ta gabatar da sallah, a lokacinne ta tuno da alfila da tace a ranta
'Allah ya sa dai alfila bata shagala ba ga barin yin sallah
bisa farin cikin saduwa da mahaifinta
koda aiyana hakan sai humaira taji zuciyarta ta buga da
karfi nan take hankalinta ya dugunzuma ta tuno da tambayar da ta yiwa
awaisu dazu ya dabarbarce ya kasa bata amsa da wuri
nan take taji bata amince da awaisu ba a cikin
ranta ta fara wasi wasi a zuciyarta tana mai cewa
'Anya kuwa wannan awaisun ne ainihin mahaifin
alfila? Nikam ba zan saki jiki dashi ba har izuwa lokacin
rabuwarmu
AA Misau Nake Magana,
Gama aiyana hakan keda wuya sai humaira taji an kwankwasa
mata kofa
Al amarin da ya fusata ta kenan tace a ranta, Me za ayi
da irin wannan al adar banza ta kafirai, sai dai a kwankwasa
maka kofa ba za ayi maka sallama irin ta addinin musulunci ba ?
Kawai sai ta bude baki tace shigo koda kofar ta bude tayi
arba da wani kyakkyawan saurayi mai tsananin kyau
tun da humaira tazo duniya bata taba ganin da namiji mai
kyansa ba
saurayin yaci ado na gaban kwatance cikin sutura mai tsadar gaske wacce tafi karfin
karamin sarki
hakika babu wata ya mace lafiyayyiya da zataga wannan saurayi bataji sha
awarsa ba
saurayin na dauke da farantin abinci na kasaita
iri iri gami da ababan sha danginsu ruwan inibi da ruwan hadaddan tataccen sauran yayan itatuwa
kamshinsu ya cika dakin gaba daya, koda humaira tayi arba da wannan saurayi sai zuciyarta ta buga da karfi a karo na biyu
nan take tayi hailala a cikin zuciyarta ta nemi tsarin Allah daga shaidan, nan take kuwa
taji ta tsani saurayin kuma ta tsani abincin da ya kawo
yayin da saurayin ya ajiyea farantin abincin bisa wani tebur dake daf da humaira
sai ya tsugunna ya dauki tambulan na ruwan inibi zai zuba a kofi da nufin ya mika
mata domin ya birgeta
ko kallonsa batayi ba ta daka masa tsawa tace bana bukatar kayi mini komai
kuma kayi sauri ka bace mini da gani, cikin rawar jiki
saurayin ya mike zumbur ya fice daga cikin dakin
bai zame ko ina ba sai wannan babbar turaka ta gidan inda ya iske alfila da
awaisu zaune sunyi jugun jugun babu mai cewa uffan
cikin girmamawa saurayin ya durkusa a gaban awaisu sai ya rikide ya zama wani
bakin aljani mai matukar muni da ban tsoro
awaisu ya dubi aljanin yace menene labari yakai zarmalu?
Aljani zarmulu ya dukar da kansa cikin alamun tsoro da fargaba yace ya shugabana aiko
kadan humaira bata saurareni ba, koroni ma tayi
kuma sa adda na matsa daf da ita sai naji kamar an tsamoni a cikin tafasashshen ruwa ba shiri na fito daga cikin dakin
koda jin haka sai bakin ciki ya lullube awaisu ita kuwa alfila sai ta cika da farin ciki , awaisu ya sake duban aljani zarmalu yace ya ya batun sarki sahibul
hairi da bawansa haluf kuma?
Koda jin wannan tambaya sai zarmalu yayi murmushi
yace ai wadannan tuni mun fara samun nasara akansu
domin tuni sunci abincin da muka basu har sun bingire da barci
awaisu yayi murmushi yace da kyau zarmalu, aikinka na
kyau
AA Misau Ke Magana, Lallai a daren yau zan hallaka
sarki sahibul hairi da bawansa haluf ita kuwa humaira
kafin daren yayi lallai zamu sake jarraba wani tuggun akanta domin mu sami
lagonta
Ka sani cewa ita musulma ce tana da karfin tsari irin nasu
a jikinta sai munyi da gaske, zarmalu yayi ajiyar zuciya yace ai ni dai kam tafi
karfina ya shugabana ba zan iya sake tunkararta ba sai dai
ke da kanki ki san hanyar da zaki bullo mata
Dajin haka sai awaisu ya bushe da dariya yace ai babu mai
tarar zaki sai dan uwansa zaki ka barni da ita, lallai a
daren yau zanga karshenta kafin wayewar gari
tashi ka tafi na sallameka, koda gama fadin haka sai aljani
zarmalu ya daidaice tamkar yayan kwayar zarra sannan
ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa a wajen ba
bacewarsa keda wuya sai awaisu ya dubi alfila ya tuntsire da dariya sannan ya
hade fuska yace na gama da abokan tafiyarki biyu
saura guda daya jal
ina mai dada yi miki tuni da cewar idan kika kuskura kikayi
wani abu ba dai dai ba lallai zakiyi arba da gawar mahaifinki
a ko yaushe
koda jin wannan batu sai idanun alfila suka ciko da
kwalla ta fara zubar da hawaye hawayen takaici da bakin ciki
AL AMARIN gimbiya humaira kuwa bayan ta kori
wannan kyakkyawan saurayi daga cikin dakinta sai taki cin
wannan abinci da ya kawo mata na alfarma
duk da cewa kuwa tana jin yunwa da kishirwa
kawai sai ta bude jakarta ta dauko ragowar wani gasashshen
nama daga cikin guzurinta na tafiyar taci kuma ta daga battar ruwanta ta sha sannan tayi
godiya ga Allah
kammala cin abincin keda wuya sai taji babu abin da take so
sama da ganin abokan tafiyarta, gashi bata san dakin
da aka kaisu ba
kawai sai ta mike tsaye ta fara tafiya ba tare da fargabar komai ba ta bude kofar dakinta ta fita ta janyo kofar
ta rufe sannan taci gaba da tafiya a cikin gidan tana shiga
wannan lungu, ta fada wancan sako tana leka kowanne daki
bisa mamaki sai humaira taga Allah ya makantar da dukkanin barorin gidan da hadimai sam basa ganinta kuma gashi ta gabansu take wucewa, wani lokacin ma ta tsakiyarsu take ratsewa har tana bangazar kafadunsu amma ko alamun ta basa ji bare su
ganta
AA Misau Sunana haka dai humaira taci gaba da leka cikin dakuna daban daban har ta shiga dakin dasu sarki sahibul hairi suke
da shigarta cikin dakin sai ta iskesu a kwance tamkar gawarwaki ko numfashin kirki basa yi
cikim rudewa da tashin hankali ta ruga kansu ta tsugunna kawai
sai ta fara karanta addu oi na musamman tana tofa musu, cikin dakiku kadan suka farka a tare suna masu jan
dogon numfashi a lokaci guda kuma a firgice suka mike zaune
zumbur suna zare idanu
Al amarin da ya baiwa humaira dariya kenan
Bata san sa adda ta dan dara
Ba
cikin rudewa sarki sahibul hairi ya dubeta yace, yake ma abociyar
kyau da jarumta menene ya faru garemu nida bawana
haluf?
Sa adda humaira taji wannan tambaya sai tayi ajiyar
zuciya sannan tace nidai ina zaune a can dakina ni
kadai sai ga wani saurayi mai tsananin kyau irin wanda ban taba gani ba ko a mafarki da labarai ya shigo mini dauke da abinci na alfarma
ina ganinsa sai tsigar jikina ta tashi naji ban aminta
dashi ba don haka sai na daka masa tsawa na koreshi
daga cikin dakin
yana fita sai naji bani da sauran sukuni face na ganku domin nasan halin da kuke ciki
saboda haka sai na kama karanta wadansu adduo i a cikin zuciyata sannan na fito daga cikin
dakina nayi ta dube dube da leke leke har na shigo nan ubangijina bai baiwa kowa
ikon ganina ba
ina shigowa ana iskeku a kwance tamkar gawarwaki ko
numfashin kirki bakwa yi, cikin hanzari na karanta
wata addu ar daban na tofa muku, faruwar hakan keda
wuya sai naga kun farka firgigit a cikin dimauce tamkar
wadanda sukayi dogon suma, lallai abincin da aka
baku kuka ci an sa banju mai karfi, a cikinsa saboda haka
ni dai ko kadan ban aminta da wannan awaisun ba a matsayin mahaifin alfila
AA Misau Ke Magana, Sa adda humaira tazo nan a zancenta sai sarki sahibul hairi da bawa haluf suka yi ajiyar
zuciya a tare suka jinjina al amarin, sannan sarki
sahibul hairi ya dubi humaira cikin alamun karayar zuciya
yace
yake ma abociyar kyawu da jarumta hakika kin ceci rayuwata har sau uku
kenan, lallai kina bina bashin da ba na zaton zan iya biya
amma ina fatan na samu damar biyanki wannan
bashi koda sau daya ne kafin mu rabu, yanzu dai
menene abin da ya kamacemu dayi? Humaira taja numfashi tace ya zama dole
muyi bincike mu tabbatar da cewa wannan awaisun shine
ainihin mahaifin Alfila? Idan kuwa muka gane cewa bashi
bane, to fa dole ne ya bamu alfila mu nemi mahaifin na
gaskiya mu dankata a hannunsa, nifa abin da ya zaunar dani
kenan, kawai a garin nan saboda haka yanzu yanzun
nan nake son mu tura a kirawo alfila da mahaifin
nata domin mu tantance komai, kafin humaira ta
gama rufe bakinta sai sukaji an kwankwasa kofar dakin
cikin hadin baki sukace shigo, nan take aka turo kofar
saiga bakin bawa ya shigo fuskarsa cike da annuri
bawan ya risina a garesu gaba daya yace, yaku wadannan manyan baki masu
daraja kuyi sani cewa mai girma sarkin yakine ya turoni
nayi muku jagora izuwa can filin shakatawa domin yayi
ganawa ta musamman daku
koda jin wannan batu sai humaira tayi farat ta fara mikewa
tsaye tana mai gyara takobinta dake daure a kugunta
tace mu je zuwa ya babban hadimi, koda ganin haka sai sarki sahibul hairi da bawa haluf
suma suka mike tsaye da hanzari nan take kuwa bakin
bawan ya juya ya fita daga cikin dakin ya nufi wani bangare
daban na gidan su humaira na biye dashi
haka dai suka ci gaba da tafiya cikin harabar gidan su
kutsa nan su fita can kamar tafiyar ba zata kare ba
babu abin da ya daurewa su humaira kai face ganin yadda suke ta shiga sako sako,
lungu lungu, tafiyar nata kara tsawo kamar ba zasuje inda suka nufa ba, kwatsam ba zato ba tsammani sai suka tsinci kansu a cikin ainihin gidan
sarautar birnin kuma a tsakiyar fada, zaune akan karagar
mulki sarkin yaki awaisu ne yayi gagarumar shigar yaki
mai matukar kwarjini da bam sha awa
da isowar su humaira cikin fadar suka ga dakarun yaki
na aljanu da na bil adama masu yawan tsiya ba adadi
sunyi musu kawanya
tun da sarki sahibul hairi yake gumurzu da gwagwarmaya bai taba ganin dakaru
masu matukar ban tsoro ba irin wadannan, domin girmansu ya wuce misali, makaman yakin da suke rike dasu kuwa wani kalarma ko a tunani
kwakwalwa bazata taba kawoshi ba, koda su humaira
sukaga wadannan dakaru sunyi musu kawanya sai duk su ukun suka zare takubbansu
suka hada bayansu a tsakiya, ma ana kowannansu ya dubi
fuska guda ya zamana cewa sun hade jikinsu a tsakiya suna
nazari ta bangaren da za a fara kawo musu farmaki
kawai sai humaira taji jikin sarki sahibul hairi dana bawa
haluf ya kama karkarwa kai da gani ka san cewa a tsorace
suke ainun
koda fahimtar hakan sai humaira ta daka musu tsawa
tace yaku abokan tafiya ku saki jikinku, ku daina shakkar komai, da izinin ubangijina babu abinda zai sami dayanku
tabbas mun fado cikin tarkon abokan gaba kuma ta kowanne hali sai mun fita
yakai sarki sahibul hairi ka mantane da duk irin hadarurrukan da aka shiga a baya
ka sha bakar wahala tamkar ranka zai salwanta, amma sai
gashi duka ka tsira?
Ai mai rabon ganin badi ko ana dakawa a turmi sai ya
gani
kafin humaira ta gama rufe bakinta sai sukaji sarkin yaki awaisu ya kece da dariyar mugunta, kawai sai ya
mike tsaye daga kan karagar mulkin yana mai sauya kamanninsa izuwa ainihin siffar gimbiya shukura matar
sarki barusa
koda ganin haka sai humaira dasu sarki sahibul hairu
suka cika da tsananin mamaki, sahibul hairi yai ajiyar zuciya yace, haba ni fa naji ajikina
sa adda na gaisa dake na kama hannunki, tabbas ba hannun namiji na kama ba
hannun mace ne, ashe kece kika yaudaremu yaya aka yi kika
rigamu zuwa wannan
gari harkika yi mana wannan mugun tanadi, kuma yanzu ina alfila da mahaifinta ?
Koda jin wannan tambaya sai shukura ta bushe da
dariyar mugunta sannan tace ai a halin yanzu tuni yarinya
alfila anyi tafiyar kwana arba in da ita a sararin samaniya an tafi da ita can inda baku isa ku
jeba har abada
naso na sami damar hallakaku cikin ruwan sanyi ba tare da kun ankara ba, amma sai wannan hatsabibiyar humaira
ta gano dukkan makircina
to idan kun san wata baku san wata ba, lallai idan hagu taki sai a koma dama
a yau dai, kuma a yanzu, banga ta yadda zaku iya tsira
ba daga sharrina ban ga wanda daga cikinku ya isa ya hanani na zama sarkin
sarakunan duniya ba
tap ! Babbar Magana Jin wannan kalami yasa Nima AA Misau na dakata a wannan gaba
kuma nake cewa Sai allah Ya kaimu gobe zan cigaba
Admin
AA Misau Ke Magana
Daga Zauran Labarai
nake
SARKIN SARAKAI
Littafi Na Biyar (5)
Part D.
.
Marubucin Littafin
ABDUL’AZIZ Sani M/Gini
Typimg
AA Misau Ke Magana
Admin
.
BANGA WANDA DAGA CIKINKU YA ISA YA HANANI NA ZAMA
SARKIN SARAKUNAN DUNIYA BA, Sai nafi dukkanin sarakunan duniya matsayi, mulki
da arziki, mutane da aljanu duk sai sun zamo a karkashin
ikona ya zamana cewa ina sarrafa duniyar nan gabaki dayanta
akan tafin hannuna, batun awaisu da sarkin wannan gari
kuwa duk suna cikin mugun hali na tsakanin RAI DA MUTUWA, sai hukuncin da na yanke
musu
idan naso su rayu , idan naso kuma su hallaka a cikin yan dakiku zan kashesu
kafin gimbiya shukura ta rufe bakinta sai humaira ta daka masa tsawa tace ke tsohuwar munafukar Allah, algunguma, maci amanar mijinta
kiyi sani cewa ba ayi duniyar nan domin ku kadai ba
batattu ma abota shirka da izinin ubangijina ba zaki cika wannan
mugun buri naki ba
cikin tsananin fushi shukura ta tari numfashin humaira tace
aishikenan ga mai fili gamai doki, sainaga wanda ya isa ya
hanani ida abin dana soma, nan take shukura ta dakawa
wadannan samudawan dakaru nata tsawa tana mai umartarsu dasu afkawa su humaira
ai kuwa sai dakarun suka zare makamansu
sukayi caa a kansu aka ruguntsume da azababben yaki a tsakiyar fadar
shukura ta koma kan karagar mulki ta zauna tana mai harde kafa cikin nishadi ta zuba ido kawai taga yadda karshen
wannan yaki zai kasance
haka dai wuri ya gama yamutsewa karar karafa da cika dodon kunne gami da ihun
mazaje, dakarun suka lullube su humaira suka yanyamesu tamkar an ajiye kwayar hatsi guda daya a tsakiyar miliyoyin tururuwa
duk inda humaira da sarki sahibul hairi suka durfafa saidai
kaga suna tarwatsa dakarun suna ragargazarsu suna
zubewa kasa, amma abin haushi shine dakarun basa
mutuwa duk wana ya fadi kasa koda kuwa an daddatsa shi yayi filla fill saikaga komai na jikinsa ya koma ya hade
tamkar ba a taba gididdibashi ba, sannan ya mike zumbur ya
cigaba da fafatawa
al amarin da ya matukar dugunzuma hankalin su sarki sahibul hairi kenan domin sun fahimci cewa wadannan dakaru basa gajiya, kuma muddin aka sami tsawon lokaci ana wannan fafatawa a haka tabbas zasu iya gajiya har dakarun
su sami lagonsu
Al amarin bawa haluf kuwa tuni a wannan lokaci ya fara gajiya in ba don ma humaira da
sarki sahibul hairi na kareshi ba da tuni dakarun sun
hallakashi
ana cikin wannan artabu ne wani daga cikin dakarun ya
sababa ta bayan bawa haluf ya dankara masa sara a gadon baya da takobi nan take bayan nasa ya dare, jini yai
tsartuwa haluf ya kurma uban ihu ya sulale kasa sumamme
koda ganin abinda ya faru ga bawa haluf sai sarki sahibul hairi ya fusata ainun yayi kururuwa mai firgita maza wacce tasa dakarun suka jajja da baya a tsorace
cikin zafin nama sarki sahibul hairi ya sunkuyo kasa ya dauki takobin bawa haluf ya hada guda biyu kenan a hannunsa
ya sake rugawa kan dakarun yaci gaba da saransu tako
ina
AA Misau Ke magana gabas da yamma kudu da arewa
suna zubewa kasa tamkar yana ta adi a gonar kabewa amma duk a banza domin ba sa mutuwa sai dai kaga suna mikewa kamar a sannan aka haliccesu
koda aka sake samun gushewar lokaci sai dakarun suka
shammaci sahibul hairi suka yankeshi har a waje biyu a lokaci guda
yanka na farko a tsakiyar kafarsa ta hagu, daya yankan kuma akan cinyarsa ta dama, duk da
juriya irin ta sarki sahibul hairi sai da ya kwala ihu ya
durkusa kasa bisa guiwoyinsa, a lokacinne yaji wani irin
jiri ya debeshim idanunsa suka kama lumshewa suna gani dishi dishi kwai sai ya tafi kasa luuu ! Zai kife Ba zato ba tsammani sai yaji an rukoshi da hannu
Daya anyi cilli dashi izuwa can saman tudu kusa
da karagar mulki inda gimbiya shukura ke zaune
Ba wani ne yayi wannan bajinta ba face humaira,
cikin zafin nama humaira ta sake daukar bawa
haluf wanda ke kwance a kas sumamme tamkar
gawa shima ta cillashi inda ta cilla sahibul hairi
ya zamana cewa saura ita kadai a tsakiyar
wadannan dakaru
Kawai sai ta fara jaranta wata addu a ta
musamman kuma ta kutsa cikin tsakiyar
dakarun taci gaba da gididdibasu
Wannan karon kuwa sai labara ya sha
banban domin duk wanda ta sara ya fadi
kasa baua tashi sai dai kaga ya kama da
wuta ya ruburbushe ta zama toka
Koda gimbiya shukura ta hango abinda
ke faruwa ga dakarunta sai ta fusata
ainun ta mike zumbur daga kan karagar
da take zaune ta zare takobinta ta daka
tsalle daga inta take tamkar an janyeta
da majajjawa ta dira a inda bawa haluf
yake takaimasa suka da takobinta a
cikinsa da nufin ta maidashi gawa
Cikin matukar zafin nama sahibul hairi
ya daka tsalleya kai masa dauki da nufin
ya kade takobin shukura
Maimakon takobin tata ta soki bawa haluf
sai ta soki sahibul hairi a gefen kirjinsa
tabullo ta gadon bayansa
Sahibul hairi ya kwala ihu a karo na biyu ihu
mai karfin gaske wanda yasa humaira ta juyo
a dimauce ta kalli abin da ke faruwa kawai
sai tag a sa adda shukura ta zare takobinta
dafa cikin kirjin sahibul hairi sannan ta sake
daga takobin tata sama zata fille kan
sahibul hairi tamkar an harbor kibiya daga
cikin baka humaira ra dako wawan tsalle
sama ta baro cikin wadannan dakaru
Kafin takobin shukura ta kai wuyan sarki
sahibuk hairi tuni humaira ta doki kirjin
shukura da kafafunta biyu saboda karfin
dukan said a shukura tayi tsalle sama ta
gwaru da bango ta fado kasa a galabaice
jinni na yoyo a hancinta
Koda shukura ta shafa hancinta taga jinni
sai ta kwarara wani irin uban ihu tankar
saukar aradu
Take wata irin tsawa ta sauka akan wadannan
ragowar dakaru yaki na ta kawai sai duk
suka fadi kasa matattu dayansu bai tsira ba
Shukura ta mike tsaye a fusace ta tnkari
inda humaira take tsaye koda ta kusa zuwa
kusa da ita sai ta tsaya suka fara kallon kallo
irin wanda ke nuna KAR TA SAN KAR
a wannan lokaci sarki sahibuk hairi na
kwance a kas magashiyan yana nu,fashi sama
sama kai da gani ka san cewa abu ne mawuyaci
ya rayu domin har a sannan jinni ne ke
bulbulowa ta cikin gefen kirjinsa inda shukura
ta sokeshi da takobi
Da kyar da makyarkyatar hannu ya cisgi suturar
jikinsa ya dora akan raunin kirjin nasa ya danne
raunin don tsaida jinni AA Misau Ke Magana
Bayan anyi kallon kallo na yan dakiku tsakanin
humaira da shukura sai shukura ta bushe da
dariya sannan tace yake wannan jaruma mai
taurin rai a hatsabibanci kiyi sani cewayau kin
gamu da dai dai dake domin niba sarki Barusa
bane kuma ni ba shamzubul azwas bane
Yadda duk kike tsammani na na wuce nan yau
shekarata goma sha uku kenan ina tanadin wannan
rana ta haduwa da ke domin tun-tuni nayi
bincike a cikin tsafina na gano cewa ke kadai
ce zaki iya kawo mini matsala a cikin kokarin
cika burina na son zama SARKIN SARAKAN
DUNIYA. Hm AA Misau Ke Magana,
Ina tabbatar miki da cewa duk abin da kike
takama da shi baki fini ba idan karifin damtse
ne da jarumtaka kike takama da shi ai yanzu
zamu fitar da raini, idan kuwa takamarki ki nemi
taimakon ubangijin musulunci to ki sani cewa
baki fini sanin ubangijin musulunci ba
Ki sani cewa ni asalina na fito ne daga
zuri’ar sheik abul nasir na birnin misra,
mahaifiyata ce babbar ‘yarsa, don haka
an haifeni a cikin musulunci, kuma na girma
a cikinsa na sami karatu da ilimi mai yawa
a wajen kakana
Tun a wannan lokaci bani da burin da ya fi na
sami matsayi da daukaka irin wanda babu
wani mahaluki daya sameshi a duniya
A lokacin da kakana Abdul nasir ya rasu
ina da shekara goma sha hudu a duniya
kawai sai aka wayi gari aka nemeni aka
rasa domin sulalewa nayi na gudu na bar
birnin misra a cikin dare
Daga wannan rana ba a sake jin duriyata
ba sai na bazama a duniya na rinka farautar
abubuwa uku
Abu na farko shine, ilimin addinin musulunci
, duk da cewa na sami mai yawa a wajan
kakana, amma sai na ci gaba da neman kari
Abu na biyu sai na dinga ziyartar bokaye ina
yi musu bauta suna bani iliminsu
Abu na uku na dinga koyon fada da yaki
a wajan sarkin yaki na kasashe daban daban
Sai da na shekara shida ina wannan yawo a
duniya ina koyon abubuwa ukun har said a na
tabbatar da cewa na sami kowanne isashshe
kamar yadda ya kamata sannan na fara bincike
a hallarar tsafina akan yadda zan sami nasarar
cika babban burina na duniya
A cikin binciken nawa ne aka nuna mini cewa
bazan taba samun nasara ba face na fara
auaran daya daga cikin manyan sarakunan
duniya
Bisa wannan daliline naje birnin sarki barusa
na zamo daya daga cikin dakarunsa na yaki
har jarumtakata da kyawuna suka burgeshi ya
aureni
A wajan sane na sami labarin boka shamzubul
azwas da batun yarinya alfila a sannan ne na
gano cewa ashe iyakar amfaninsa kenan a
wajena wato na san mataki na karshe da zan
cika burina
Koda na sake yin bincike a tsafi sai aka nuna
mini zuwan sarki sahibul hairi domin ya dauki
gatarin sihiri na mijina sarki barusa
Koda ganin hakan saina cika da farin ciki domin
nasan cewa lokaci yayi d azan rabu da sarki
barusa na bi sarki sahibul hairi domin na
mallaki yariny alafila wacce a jikinta ne zan
sami sirrin tsafin da babu kamarsa a duniya
Abinda dukkan matsafan duniya basu gano
ba shine, yarinya alfila ta taba shan wani
tsumin tsafi na sarkin aljanu wanda ya yi
zamaninsa kimanin shekaru dubu dari biyu
da arba’in baya
Shi dai tsumin tsafin a hannun wata jikarsa
yake wacce wara rana ta fita yawon shan
iska sai ta shiga gonar wani azzalumin bakin
aljani ta tsinka amfanin cikinta, ashe yasa
guba a jikin duk amfanin gonar saboda
maganin masu yi masa sata
Ai kuwa sai wannan aljana ta kama aman
jinni da kyar ma ta bude fukafukabta tayi
sama ta bar cikin gonar ta fada daji tna
shure-shure AA Misau Ke Magana
A wannan lokaci tsumin tsafin na cikin wata
batta dake rayaye a wuyanta, amma saboda
dafin day a shigeta yaci karfinta sai ta kasa
cire battar tsumin daga wuyanta tasa a bakinta
tasha
Tana nan kwance a kas tana shure shuren
mutuwa sai ga mahaifiyar alfila tazo giftawa
ta wajan ta dawo daga daji samo itace
A wannan lokaci alfila bata fi shekara biyu
bad a haihuwa mahaifiyar na goye da ita a
bayanta kuma a sannan rana ta take matuka
duk su biyun suna jin kishirwa
Mahaifiyar alfila sauri take ta isa cikin agri domin
ta nemi ruwa ra shayar da kanta da yarta koda
mahaifiyar alfila taga wannan aljana a kwance
tana kakarin mutuwa sai ta firgita ainun ta
yunkura zata gudu cikin karfin hali aljanar
tace kada ki gujeni yake wannan bil’adama a
wannan lokaci da nake neman ceto
Na rokeki daki zoki cire battar dake wuyana ki
budeta ki tsiyaya mini rowan cikinta a bakina
Idan kika yi min haka nima zanyi miki sakayya
da abinda duk duniyar nan babu mai irinsa
Koda jin wannan batu sai mahaifiyar yarinya
alfila ta tsaya cak a waje daya
Jikinta na karkarwa saboda tsananin tsoro
tana tunanin tabi umarnin wannan aljana
ko kuma ta gudu
Daga can sai ta yanke hukuncin ta taimaki
aljanar koda kuwa tarkone tayi mata domin
ta cutar da ita
Hunnunta na karkarwa taje ta durkusa akan
aljanar sannan ta cire nattar daga wuyanta
ta budeta tasa mata a baki tasha rowan
Faruwar hakan keda wuta sai aljanar tayi
kumallo na wannan dafi da taci a jikin amfanin
gonar
Nan take ta sami lafiya ta mike zaune daram
kamar wani abu bai taba samunta ba
Aljanar ta dubi mahaifiyar alfila tayi mata godiya
sannan sai ta karbi battar daga hannun mahaifiyar
alfila ta girgiza taji rowan dake ciki dan kadanne bai
wuce makarwa uku ba
Aljanar ta girgiza kai gami da ajiyar zuciya tace
kinga wannan ruwan dake cikin wannan battar
maganin kowacce irin cutace kuma sinadarine
na sihirin tsafi wanda babu kamarsa a duniya
Wanda duk ya sha wannan tsumi babu wani
makami da zaiyi tasiri a jikinsa kuma duk irin
matsayin da mutum ke son kaiwa a duniya sai
yah au
Na gaji da wannan tsumi ne a wajen kakana
kuma duk duniya babu mai irinsa sai ni kadai
bincike ya nuna cewa nan gaba bazan kara
shekara goma ba a duniya zan mutu kinga kenan
idan na mutu babu mai sauran wannan sihiri
face wanda na baiwa ragowar wannan tsumi yasha
saboda haka ni yanzu zan baki ragowar tsumin ki
sha albarkacin taimakon da kika yi mini kika ceci
rayuwata dama kuma gashi na fuskanci kina
fama da kishirwa lallai wannan tsumin zaiyi miki
maganin kishirwar
Sa adda a;jamar yazo nan a zancenta sai mahaifiyar
alfila tce ai duk yadda nake son kaina bai kai yadda
nake son wannan yar tawa ba wadda na goya a
bayana saboda haka indai kin bani wannan tsumin
ita zan baiwa tasha AA Misau Ke Magana
Aljanar ta jinjina kai tace ai zabi na gareki amma ki
sani cewa duk wanda ya sha wannan tsumin
tsakanin keda ita sai ya fuskanci wata matsala
guda daya idan kece kika sha tsumin ba zaki
yi nisan kwana ba a duniya idan kuwa itace
tasha zatayi nisan kwana a duniya amma zata
rabu da ke tun tana karama kuma idan ta fara
girma matsafan duniya zasu saceta daga wajan
ubanta saboda su cire sihirin tsafin dake
jikinta amma a karshe sai ta daukaka a duniya
Lokacin da aljanar tazo dai dai nan a zancenta
sai mahaifiyar alfila tace ai kuwa indai hakane
na zabi yata ta sha wannan rowan tsumin
Koda jin haka sai aljanar ta bude bakin alfila ta
dura mata wannan ragowar rowan tsumin ta
shanye, sannan aljanar ta gargadi mahaifiyar
alfila akan cewar kada ta kuskura ta gayawa
kowa wannan al amari day a faru a tsakaninsu
Koda gama fadin haka sai aljanar tab ace bat
Daga wannan rana mahaifiyar alfila tayi shiru
da bakinta bata taba gayawa kowa ba sai a
ranar da ta kwanta cutar ajali
Koda ta fahimci cewa ciwonta bana tashi
bane sai ta sanar da mijinta sadauki awaisu
duk abninda ya faru tsakaninta da wannan
aljana a daji
Aikuwa wannan shine babban kuskuren da
tayi domin inda bata fada masa ba babu yadda
za a yi sauran matsafan duniya su san da batun
tsumin tsafin dake jikinta har suyi kokarin cireshi
daga jikinta
Ina son ki sani cewa boka shamzubul azwas
shine matsafi na tara wanda yayi kokarin cire
sihirin tsafin dake jikin alfila amma sai kuka je
kuka tarwatsa masa shiri
Yanzu nice matsafiya ta goma wacce zata
cire wannan sihirin tsafi daga kikin wannan
yarinya kuma ba makawa saina sami nasara
domin ku baku isa ku hanani ba…………………..
.
Kai nima dai AA Misau zanje domin na yi fafa
wajan ganin na zama wanda zai cire sihirin
tsafin dake jikin yarinya alfila domin na zama
sarkin sarakan duniya, saboda ai ba jarumta
aka fini ba
Bari dai naje na shirya kayan yakina naje na
samesu a can hahahahahaahahahah
Kafinnan Nine
AA Misau Admin Na Zauran Labarai
Ke Magana
Ku Huta Lafiya
SARKIN SARAKAI
Littafi Na Biyar (5)
Part E.
.
Marubucin Littafin
Abdul aziz Sani M/Gini
Typing
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau Cewa....
.
YANZU NICE MATSAFIYA TA GOMA WACCE ZATA CIRE
WANNAN SIHIRIN TSAFI DAGA JIKIN ALFILA KUMA BA MAKAWA
SAI NA SAMI NASARA DOMIN KU BAKU ISA KU HANANI BA
yake humaira ki dubi abokan tafiyarki Sarki sahibul hairi da bawansa haluf
ga su nan duk a kwance magashiyan sun kasance ragowar mutuwa
ke kadaice kika rage
kuma kike nema ki zame mini matsala, tabbas ba zaki zame mini matsalar ba domin
yanzun nan zan hallakaki sannan na tafi can fadata
in da aka kai alfila aka ajiye mini na cika burina a kanta
koda shikura ta zo nan a zancenta sai humaira ta tari numfashinta
ta daka mata tsawa tace
yake wannan munafukar Allah hakika ire irenku annobace a doron kasa domin kun san gaskiya kun taketa, kyma irin azabar da Allah zai yi muku idan kuka koma gareshi ta musamman ce
lallai ba zan bari ki je ki ida wannan nufi naki ba idan kika ga kin fita daga cikin
fadar nan sai dai idan bana numfashi
koda jin haka sai shukura ta bushe da dariya tace ai ga fili ga mai doki kuma inda babu kasa nan ake gardamar kokawa
nima ba zan yarda na fita daga nan ba face na tabbatar keda abokan tafiyarki
babu mai numfashi domin idan na tafi na barku a raye tamkar na kashe maciji ne
ban sare kansa ba domin na san sai kun bini har can
fadata kun tarwatsa mini shirina kamar yadda kuka tarwatsawa
boka shamzubul azwas nasa
Yanzu zaki san cewa shirina ba irin na shamzubul azwas bane
takadarancina da hatsabibanci na ya ninka nasa sau goma
koda gama fadin haka sai shukura ta daga takobinta
sama tayi kukan kura ta ruga kan humaira, da ganin
haka sai itama humaira ta daga tata takobin ta tareta
suka ruguntsume da azababben yaki
nan fa shukura ta rinka kaiwa humaira sara da suka
cikin tsananin zafin naman da bata taba haduwa da sadaiki mai irinsa ba kuma
saboda karfin saran duk sa adda humaira ta kare
sai taji kamar katon dutse mai nauyi aka buga mata har sai ta durkushe kasa
wani lokacin ma har faduwa kasa take, in ba don itama
tana da zafin nama ba da tuni shukura ta hallakata
al amarin da ya dugunzuma hankalin humaira kenan ta tabbatar da cewa lallai yau dai kam ta gamu da gamonta
babu abinda ya sa humaira takaici face ganin yadda
shukura ke ta karanta addu o'i irin na addinin
musulunci a lokacin da take karanto nata addu o'in domin samun nasara a tsakaninsu
sahibul hairi dake kwance a can gefe daya yana ganin abindake faruwa sai hankalinsa
ya fi na humaira tashi domin zuciyarsa ta karaya bisa
ganin yadda wannan gumurzu ke wakana domin fadan ya
nuna cewa shukura ce zata sami nasara saboda juma ar
da zatai kyau tun daga laraba ake ganeta
kuma da zarar shukura ta gama hallaka humaira ya san cewa kansu shukura zata
dawo wato shida bawa haluf tasu tazo kusa, haka dai
humaira da shukura suka ci gaba da fafatawa babu sassauci
har tsawon sa a uku
shukura bata sami nasarar koda kwarzanar jikin
humaira ba
saboda tsananin naci da juriya irin na humaira, duk da
cewa an fita zafin nama da karfin damtse, a wannan lokaci
ne shukura ta fahimci cewa indai fada da makami zasu ci gaba
dayi ba zata taba samun nasara akan humaira ba domin ga dukkan alamu ba karamin horo
humaira ta samu ba akan sarrafa makaman yaki
koda gama aiyana hakan sai shukura ta shammaci humaira ta doki hannunta da kafarta
takobin ta subuce kasa
itama shukura sai ta yarda tata takobin ta dunkule
hannayanta biyu kuma ta gyara tsayuwa ta ce yauwa
yanzu ne zamu banbance tsakanin aya da tsakuwa
kuma yanzune zakisan cewa ruwa ba sa an kwando bane
koda jin haka sai itama humaira ta gyara tsayuwarta
kuma ta dunkule hannunta tayi kabbara ta ruga kan shukura
ai kuwa itama shukura sai tayi kabbarar ta tareta
suka ruguntsume da sabon masifaffen fada ya zamana cewa suna kaiwa juna naushi
da bugu hannu da kafa, fara hakan keda wuya sai humaira ta gane cewa shayi ba ruwa bane
domin shukura tafita karfin damtse nesa ba kusa ba
nan fa shukura ta rinka gabzawa humaira naushi a fuska da cikinta AA Misau Ke Magana
tun humaira na kokarin kare naushin har ta kasa ya
zamana cewa tana layi a tsaye tana yin baya
taga taga kamar zata fadi, amma sai kaga ta cije
ana cikin haka ne shukura ta gabzawa humaira wani
katon naushi a fuska har wani gudan jini yayi fitar
burgu daga cikin bakin humaira kawai sai ta sulale kasa
magashiyan ta kasa koda motsawa bare ta mike tsaye, koda ganin haka sai shukura ta bushe da dariyar
farin ciki sannan ta hau kan gadon bayan humaira ta zauna
ta kai hannayanta biyu izuwa kanta da nufin ta
murde mata wuya, ba zato ba tsammani sai shukura taji an daki bayanta da kafa
saboda karfin dukan sai da taji kamar bayan nata ya burme kuma sai tayi
tsalle can gefe daya ta fado kasa da fuska ta fasa hanci
da baki jini ya kama zuba, a fusace shukura ta waigo
don taga wanda yayi mata wannan dukan shammace, ai kuwa sai ta ga ba wani bane face sarki sahibul hairi,
yana tsaye amma yana tangadi kamar wanda ya sha
giya ya bugu sakamakon jinin dake zuba a
Raunin kirjinsa
bisa mamaki sai shukura taga sahibul hairi ya durkusa a gaban humaira yana duba lafiyarta
jar hawaye na zuba a idanunsa domin a zatonsa ta mutu
koda ganin haka sai shukura tayi murmushin mugunta
sannan ta mike tsaye zumbur ta dubi sahibul hairi
ta bushe da dariyar mugunta tace
yau fa ga masoya biyu
duk a cikin mugun hali babu wanda zai iya ceton rayuwar wani, lallai daya bayan
daya zan kasheku domin ku dandana takaicin kisan gillar da zanyi muku, koda gama
fadin haka sai shukura ta daka tsalle daga inda take ta dira a gaban sahibul hairi
ta rinka tumurmusashi tamkar ta sami tamola harma tana fyadashi a kasa
kaico yaufa ga maza a hannun mata sun kasa tabuka komai
a dai dai wannan lokaci ne humaira ta farfado ta dawo haiyacinta
koda ta bude idanunta taga yadda shukura ke tumurmusa
sahibul hairi harma tana naushinsa akan raunin nan na kirjinsa yana
jini yana ihu da kara sar hankalinta ya dugunzuma
nan take humaira ta fara kiran sunayen Allah tsarkaka tana yi masa kirari tana cewa
ya ubangin da bashi da kishiya kaine kayi alkawari cewar zaka
kare addininka da kanka ya allah kada ka bari wannan batacciyar ta sami nasara
akanmu
domin addininka take son ta dakusar ya allah ka
karfafani da karfi irin naka na sami nasara akanta
ai kuwa humaira na cikin yin wannan addu a ne sai taji wani irin gagarumin karfi ya shiga jikinta irin wanda bata
taba ji ba kawai sai ta mike zumbur itama ta daka tsalle daga daya ta dira a kan shukura
ta cakumo gashin kanta ta baya ta rukeshi tamau tayi hajijiya da ita sannan ta fydata a kasa
shukura ta baje a kasa cikin wani irin hali mai kama da
rabi suma rabi mutuwa
domin kanta ma ya fashe jini na zuba
a tsammanin humaira shukura ta mutu don haka sai ta
ruga kan sahibul hairi a dimauce ta dora kansa akan cinyarta
yayinda yake numfashi sama sama kamar zai mutu
cikin hanzari humaira ta dauko jakar guzurinta ta foddo wani garin magani
ta zuba akan raunin da sarki sahibul hairi ke dashi ya kwalla ihu sakamakon zogi da radadin da yaji
humaira ta yagi rigar jikinta ta daure raunin sahibul hairi tamau sannan ta shiga
karanta addu o'i tana tofawa akan raunin nasa a lokacin da hawaye ke zuba daga idanunta yana diga bisa fuskarsa
cikin matukar karfin hali sahibul hairi ya bude idanunsa
suka dubi juna sai yace yake ma abociyar kyau da jarumta
kiyi sani cewa tsananin
ciwon da nake ji a jikina yayi yawa don haka ba zan rayu ba
mutuwa zanyi
koda jin haka sai humaira ta rube bakin sahibul hairi
da tafin hannunta tace
yakai abin kauna ba zaka mutu ba har sai ka karbi addinin
gaskiya
ka sani cewa tun a ranar farko da na ganka naji zuciyata
ta kamu da kaunarka don haka ba zanso ka mutu ka barni ba
idan har ka karbi tayin soyayyata hannu biyu to ka karbi
addinin gaskiya
dajin haka sai sahibul hairi ya sake bude baki da kyau ya
karanta kalmar shahada kamar yadda yaji humaira ta
biyawa yarinya alfila a lokacin da ta musuluntar da ita
koda humaira taji sahibul hairi yayi wannan kalma
sai ta cika da tsananin farin ciki bata san sa adda ta rungumeshi ba ta fashe da
kukan farin ciki
AA Misau Ke Magana. A daidai wannan lokaci ne shima
bawa haluf ya dawo cikin haiyacinsa koda ya ga shukura a kwance gefe daya cikin jini kuma yaga humaira
rungume da maigidansa tana rusa kuksa sai shima ya kama kukan domin a zatonsa maiginda ya mutu
dajin sautin kukan bawa haluf sai sahibul hairi ya
janye jikinsa daga cikin na humaira ya dubi bawa haluf yace kukan me kakeyi yakai amintaccen bawana ai ban mutu ba domin masoyiyata ta ceto
rayuwata
koda bawa haluf yaga maigidan sa a raye har yana magana sai ya rarrafo da guiwoyinsa izuwa gareshi suka rungume juna
cikin tsananin farin ciki
kwatsam ba zato ba tsammani sai suka ji an bushe da dariya koda suka dubi inda shukura ke kwance sai sukaga wajen ya zama wayam babu ita sai jinin kanta da
ya zuba a kasa amma sun ga wata guguwa tayi sama
ta fice ta cikin rufin dakin, cikin matukar damuwa humaira ta dubi sahibul hairi tace
akwai sabon aiki a gabanmu kuma gashi kai da bawa
haluf kuna cikin wani irin hali dolene mu zauna a nan har tsawon wadansu kwanaki domin kyi jinyar raunikan
jikinku
sannan mu tafi neman gimbiya shukura domin mu tarwatsa shirinta mu karbo Alfila
yanzu ku jirani anan domin na shiga cikin gidan sarautar nan na nemi inda shukura
ta boye mahaifin alfila da sarkinsu, koda gama fadin hakan sai humaira ta mike tsaye ta goge
jinin dake bakinta da hancinta sannan ta nausa cikin gidan sarautar, sannu a hankali humaira ta isa har cikin turakar
sarki inda ta iske sarki da awaisu a kwance akan gado kuma a daure da sarkokin sihiri
nan take humaira ta karanta wata addu a ta tofa musu sai
sarkokin
sihirin suka bace bata sannan suka dawo cikin haiyacinsu
suka mike zumbur a dimauce zasu ruga waje da
gudu sai humaira ta daaka musu tsawa
nan take ta sanar dasu du abinda ya faru garesu bisa shirin gimbiya shukura kuma
ta basu labarin yadda suka zo gurin tare da alfila har shukura ta so ta yaudaresu ta hallakasu da bata sami nasara ba
tayi fito na fito daasu aka
Kafsa gagarumin yaki bayan tuni tasa aljanu sun dauke
alfila sun gudu da ita kuma karkashin yakin sai aljanu ska sake zuwa suka dauke shukura
suka tafi da ita bayan ta suma a tsammaninmu ma mutuwa
tayi ashe bata mutu ba
sa adda su sadauki awaisu suka gama jin wannan labari sai suka cika da tsananin
al ajabi kuma hankalin sadauki awaisu ya kara dugunzuma
fiye dako yaushe ya ce nikam tun bayan dana ga yaata alfila
sa adda ta kwanta a kaina tana kuka sai hankalina ya
gushe sakamakon azabar da shukura tayi mini ta matse mini jiki da sarkar sihiri
har kafata ta karye
koda fadin haka sai duk suka dubi kafar awaisu sukaga har ta kumbura nan take
sarki ya kwallawa wani hadiminsa kira ya shigo cikin
turakar
da shigowar hadimin sai sarki ya daaka masa tsawa yace
duk ina dakarun gidan nan suke har wata matsafiya ta shigo ta kamani ta daureni
basu sabi ba
hadimin ya risina yace ya shugabana ai mu bamu ga kowa ya shigo gidan nan
ba kuma kullum kai muke gani kana harkokinka kamar yadda ka saba
koda jin haka sai sarki ya sake cika da mamaki ya tsinke da al amarin hatsabibancin gimbiya
shukura
ba tare da bata lokaci ba aka tura aka kirawo likita yazo ya gyara karayar sadauki awaisu sannan likitan yaje ya duba
sahibul hairi da bawa haluf suma yayi musu magani
aka kaisu masauki mai kyau, sai da su sahibul hairi
suka kwana goma sha tara suna jinya sannan suka sami
lafiyar jikinsu sosai
A wannan rana ne sarki yasa aka yi shela gaba daya jama ar
garin suka taru a fada
nan take sarki ya baiwa jama alabarin sarki sahibul hairi tun daga lokacinda ya baro
kasarsa domin neman matsayi da daukaka har izuwa lokacin
da ya hadu da gimbiya humaira a can garinsu suka dunguma suka tafi fadar shamzubul azwas da duk irin fafatawar da sukayi har suka iso
wannan gari suka yi bakin gumurzu da gimbiya shukura har ta sake guduwa tare da
Alfila
lokacin da sarki ya gama bayar da wannan labari sai gaba dayan
mutanen garin jikinsu yayi sanyi nan take kowa yayi imani da addinin musulunci
sarki sahibul hairi ne ya karanta kalmar shahada
sannan gaba dayan jama ar garin suka maimaita
farin ciki a wajen gimbiya humaira a wannan rana ba zai
misaltuba
bayan an kaddamar da addinin musulunci ne a kasar
humaira ta shiga koyar da jama a yadda zasu
bautawa allah sai da ta shafe kwana bakwai tana
wannan hidima sannan aka sami masu basira suka
lakanci abin da ta koya musu suma suka dinga koyar
da wasu
A wannan lokacine sadauki awaisu, sahibul hairi da bawa haluf suka yi zama na musamman suka shiga tattaunawa akan yadda zasu tafi neman yarinya alfila domin suyi gumurzu na karshe da gimbiya
shukura
suga bayanta a sannan ne sarki sahibul hairi zai sami damar
komawa kasarsa ya jaddada addinin musulunci ga jama arsa daga nan kuma sai su tafi izuwa garinsu gimbiya
humaira domin ya nemi auranta a wajan iyayanta
sahibul hairi ya dubi humaira cikin alamun damuwa yace
yake abar kaunata yanzu tayaya kike ganin zamu iya
zuwa inda shukura takai alfila harmu yaketa mu karbo alfila?
Sa adda humaira taji wannan tambaya sai tayi ajiyar zuciya tace babu wanda zai iya yi mana jagora izuwa wannan tafiya face Allah
domin don haka zamu rokeshi akan ya taimakemu kuma ya bamu sa'a bisa abindake gabanmu , bawa haluf yai ajiyar zuciya yace a gaskiya ni dai na tsorata
da al amarin gimbiya shukura kuma ina tsoron karonmu da ita na biyu domin
na tabbatar dacewa shirin da zatayi yanzu kanmu sai ya ninka na baya sau dari
AA Misau Kenan Sunana, Sa adda humaira taji wannan batu
sai tayi murmushi tace ai duk shirin da shukura zaatayi ba zata sami nasara akanmu
ba
tunda dai mu akan tafarkin gaskiya muke ita kuwa akan tafarkin karya take
duk abinda take takama dashi kafin ita anyi manyan
kafirai a duniya wadanda sukafita komai da komai, amma a karshe sai da suka wulakanta suka zama mushe
ina tabbatar maka da cewa babu wani abu madawwami face
Allah
Sarki guda daya wanda bashi da abokin tarayya
shine wanda ya halicci sammai da kassai da duk abubuwan
dake cikinsu
kunga kenan shine mai ikon Tafiyar da mutane da aljanu a doron kasa da izininsa ne kowa ke yin abinda ya ga dama
idan Allah ya so ya kawar da mutum ko aljan take yake kawar dashi sai dai kawai ayi masa jinkiri izuwa iyakar wa adin da aka diba masa zaiyi a
duniya
lokacin da humaira tazo nan a zancenta sai taga sarki sahibul hairi da sadauki awaisu sun fara hanmma
alamar cewa suna jin barci Don haka sai tayi shiru
ga barin zance tace ya kamata mu tsaya a nan sai wani
lokaci kuma idan mun sami dama saimu cigaba da wannan labari
Kuma ku sani cewa a daren yau zanyi Addu a da rokon Allah Akan yayi mana jagora bisa tafiyar da zamuyi
gobe don neman inda fadar gimbiya shukura take domin mu yaketa mu kawar da ita sannan
mu karbi Alfila daga Hannunta
Koda jin haka sai murna ta kama sadauki Awaisu yace da izinin ubangin musulunci saimun sami nasara kuma lallai dani za ayi wannan tafiya
Sarki yace Ai nima dani za ayi wannan tafiya domin na sami irin ladan da ake samu na JAHADI...
kainima AA Misau Dani Za ayi wannan Tafiya
Kafinnan Sai Gobenku......
Zakuji karshen wannan littafin
AA misau ke magana
SARKIN SARAKAI
Littafi Na Biyar (5)
Part F.
.
Takun Karshe The End....
Marubucin Littafin
Abdul aziz sani m/gini
Typing
AA Misau
Ke Magana
.
.
SARKI YACE AI NIMA DANI ZA AYI WANNAN TAFIYA
DOMIN NA SAMI IRIN LADAN DA AKE SAMU A JAHADI
humaira ta dubi sarki tace to yanzu idan ka bimu izuwa wannan tafiya wane ne kuma zaici gaba da mulkin jama arka
kayi hakuri ka zauna ka jagoranci jama arka har Allah ya dawo da sadauki awaisu
lafiya mu kuwa a can zamu rabu dasu awaisu mu tafi
birnin Misra domin sarki sahibul hairi ya jaddada
addinin musulunci a can, da wannan furuci aka tashi daga taron kowa ya je ya kwanta
Kashe gari da sassafe kuwa humaira , sahibul hairi da bawa haluf da sadauki
awasiu sukayi gagarumar shigar yaki sannan suka yi bankwana da sarki da sauran jama ar gari kuma suka bukaci jama a da su tayasu da addu a bisa wannan JAHADI da zasu tafi
koda jama ar gari suka ga su humaira zasu tafi su barsu sai suka kama kuka saboda sabon da sukayi dasu
al amarinda ya karya zuciyar su humaira kenan suma suka kama kuka
nI kaina AA Misau Saida na Tausaya Musu, Nan dai suka yi musu sallama sarki ya sa aka kawo dawakai ingarmu guda hudu gami da isashshen guzuri yace ga nawa gudumawar
humaira ta dubi sarki tayi murmushi sannan tace mun gode da wannan kyauta taka
amma bama bukatar wadannan dawakai kamar yadda Allah ya kawomu birninka a kafafunmu muka shafe tafiyar watanni a cikin kwanaki kadan haka Allah zai kaimu inda Gimbiya shukura take
wannan guzuri dai daka bamu na abinci shi muke da bukata
koda gama fadin haka sai kowannansu ya karbi jakar guzurin ya rataya a bayansa sannan suka kama hanya suka fice daga cikin garin tun jama a na hangensu har suka kule
su humaira suka wanzu suna masu tafiya dare
da rana cikin karanta addu l'i na daurin kasa da neman taimakon Allah akan ya kaisu inda fadar Gimbiya shukura take
da yake Allah maji rokon bawansa ne nan da nan kuwa su
humaira suka shafe tafiyar watanni da dama a cikin kwanaki kadan
su shiga nan su fita can wani lokacin ma sai su kera kwale kwale sun shiga sun ratsa ta cikin koguna da koramai
wani iko na Allah tunda suka fara tafiyar sai wani kankanin tsuntsu ya zamo tamkar jagoransu
duk inda tsuntsun yabi nan suke bi dalili kuwa shine
humaira tayi mafarki da wannan tsuntsun tun kafin ya baiyana garesu kuma a cikin
mafarkin tsuntsun yayi magana da ita yace
duk inda kukaga nabi kuma kubi insha Allahu zan kaiku fadar Shukura
Wata rana kwatam sai suka hango wani katon gida akan wani dogon tsauni a tsakiyar dokar daji
Girman gidan ya wuce misali domin ya ninka gidan boka shamzubul azwas sau goma
tunda ga nesa su humaira suka tsaya suka yi cirko cirko suna kallon gidan suka sha jinin jikinsu akan cewa lallai wannan shine
fadar gimbiya shukura
bayan sun gama nazarin gidan sai humaira ta dubi sahibul hairi, bawa haluf da
sadauki awaisu tace ku bini a baya duk inda na dauke sawuna ku sa naku da
izinin Allah harmu shige cikin gidan can babu wanda zai ganmu, da zarar mun tsinci kanmu a ciki kowa yayi iya kokarinsa wajan kwatar kansa gami da neman tsari daga Allah akan makiya
koda gama fadin haka sai humaira ta wuce gaba tana karanta
wata addu'a ta musamman, sahibul hairi bawa halu da awaisu, kuwa suka rinka bin sawunta kamar yadda ta umarcesu
AA Misau Nake, haka dai suka ci gaba da tafiya har suka hau kan tsaunin
da zuwansu gaban katon gidan sai suka ga dakarun Aljanu sama da guda miliyan dubu daya sun yiwa gidan kawanya
wasu a sama wasu a kasa
kuma gaba dayansu muninsu da kwarjininsu ya ninka na wadancan aljanu da suka fafata dasu a garin su Awaisu
bisa mamaki sai su sahibul hairi sukaga sam aljanun basa ganinsu
abinda ya basu matsala shine, kwata kwata babu kofa ko taga a jikin gidan gaba daya bare su bude su shiga
koda ganin haka sai humaira ta dafa bangon gidan ta karanta wata addu ar daban
take bangon ya tsage suka shiga ciki wohoho ! Da shigarsu ciki suka tsinci kansu cikin Aljannar duniya domin irin kayan
alatun da suka gani da kuma dukiya iri iri ko a tarihi basu taba jin kamarsu ba domin sai dai a kwatanta yawanta da karuna
sai da suka shafe sa a tara suna tafiya a cikin gidan suna wuce
fadoji kala kala suka iso fadar karshe inda suka yi arba da yarinya Alfila a cikin wata katuwar kwalba cike da ruwa ko motsi batayi a ciki kamar gawa
dakarun aljanu da suka kewaye kwalbar suna tsaronta sun kai su dubu saba'in
kuma girmansu da kwarjininsu ma ya ninka na aljanun dake wajan gidan sau goma
sannan sai ga karagar mulki a gefe daya wacce aka kerata da zallar lu'u 'u'u
babu kowa a kanta
koda humaira tayi arba da wannan kwalba wacce alfila ke ciki sai ta zare takobinta karar
zare takobince tasa wadannan dakarun aljanu suka juyo sukayi arba dasu
ai kuwa sai aljanun suka taso musu gaba daya suna wani
irin gurnani da ihu wanda ka iya sa mutum ya zautu ko ya mutu nan take
ai kuwa suma su humaira sai suka kwala kabbara suka tari Aljanun aka ruguntsume da azababben yaki
sai da aka kwana aka yini ana wannan yaki sannan humaira ta sami nasarar saran wannan kwalbar sihiri cikin kiran
Sunan Allah
take kwalbar ta fashe ruwan cikin kwalbar ya cika fadar gaba daya
tamkar tekuce ta balle
koda ruwan ya lullube wadannan dakarun Aljanu sai dukkaninsu suka zagwanye a cikinsu dabansu bai rayu ba
humaira ta tsamo Alfila daga cikin ruwan ta tofa mata Addu'a
ta farfado daaga dogon suman da tayi sannan ta goyata a bayanta
A sanna ne suka ji ihu da kururuwar gimbiya
shukura
tsulum sai gata ta baiyana a cikin ruwan tana sanye da kayan yaki na bakin sulke kuma ta rike takubba guda biyu
humaira da shukura suka kurawa juna ido
sannan shukura tace yaune za ayita ta kare koni koke
kafin humaira ta budi baki ta maida raddi tunu shukura ta afka musu su ukun da azababben yaki
nan fa ta zame musu alakakai suka rasa yadda zasuyi da ita sai da suka sake shafe sa a bakwai ana wannan bakin gumurzu
ya zamana cewa shukura ta yiwa dukkaninsu mugayen raunika a jikinsu duk ta bazar dasu a kasa harda ita kanta humairan babu mai iya mikewa tsaye
Amma banda Jarumi AA Misau hahaha A sannan ne humaira ta sake yiwa Allah kirari irin wanda tayi masa a wancan karon ai kuwa nan take ta sami wannan gagarumin karfi ta dinga ragargazar shukura
har sai da ta daddatsa sassan jikinta filla filla A karshe humaira ta yanke jiki ta fadi kasa
sai da suka kwana ashirin a cikin wannan gida suna jinyar jikinsu sannan suka warware suka fita
cikin tsananin farin ciki sadauki awaisu ya karbi
yarsa Alfila ya koma garinsu
Sahibul hairi, bawa haluf da Humaira kuwa sai suka je birnin misa aka kaddamar
da addinin musulunci sannan suka tafi garin su humaira aka
daura auransu suka sake komawa birnin misra suka ci
gaba da rayuwa mai cike da farin ciki, bisa mamaki a wannan lokaci sai arziki mai tarin yawa
ya samu ga sarki sahibul hairi da tarin daukaka a tsakanin
sarakunan dake nahiyar, ya zamo shine babban Sarki kuma yaci gaba da yake yake na
jaddada addinin Islama har zuwa karshen Rayuwarsa !!!
ALHAMDULILLAH !!!
Bayan nan kuma sai Sadauki AA Misau ma aka daura Auransa Da yarinya Alfila inda suka ci gaba da rayuwarsu cikin jin dadi da kwanciyar hankali hahahahaha
-------------------------------------------------
Alhamdulillah Anan ne muka zo karshen Littafin sarkin sarakai 1-5
dafatan littafin ya kayatar daku wanda AA Misau Ya jagoranci typing dinshi,
sannankuma nake cewa ku huta lafiya
marubucin littafin
Abdul aziz sani madakin gini kado
typing AA Misau ke Magana
Download Sarkin Sarakai Complete Littafi Na Biyar
0 Comments
Thank you for this comment