¤¤¤TARKON MUTUWA¤¤¤
Littafi Na Biyu
Part A
A ranar kwana na ashirin din ne suka hango kofar wani babban gari daga can nesa.
A wannan lokaci safiya ce ,cikin farin ciki Hatayan ya tsaya da gudu ya kira sunan Sadirat amma sai ya ji shiru ba ta amsa ba ,
Ko da ya dan waigo ya dubeta sai ya ga ashe barci take yi,
Nan take ya kwanceta daga bayansa sannan ya shimfideta a kasa .
A sannanne ya ji wata irin muguwar gajiyar gudun da ya sha gami da matsananciyar yunwa don haka bai san sa'adda ya sulale kasa ba.
Karar faduwar da yy tasa Sadirat ta farka, Tana bude idanu taga Hatyan kwance a kasa jiknsa na karkarwa tmkar mai cutar farfadiya,
Cikin rudewa ta kamoshi ta dora kansa a kan cinyar ta ta yayyafa masa ruwa a fuska, Nan take ya yi dogon ajiyar numfashi ya budi baki dakyar ya ce da ita bani abnc.
Cikin rawar jiki ta bude jakar guzirin sa ta fidda abncin wanda bai wuce loma biyar ba, ta rinka bashi a baki da hannunta .
Abncin na karewa ta kora masa da ruwa , A sannan ne Hatyan ya dan dawo cikin haiyacinsa ya dubeta ya yi mata guntun murmushi ya ce, na gode da kika cece ni daga yunwar kwana saba'in da tara.
Cikin tsananin mamaki ta dubeshi ta ce ban gane yunwar kwana saba'in da tara ba ,
Caaa nake cewa kayi gudun kwana ashirin za muyi??"
Hatyan ya ce 'Ai guduna na kwana ashirin dai dai yake da tafiyar kwanan casa'in da tara akan doki, kinga kenan tafiyar da mukayi yanzu ta kusan wata uku ce, wannan dalili ne yasa komai saurin dakarun da sarki Shamsal ya turo su kamamu ba zasu iya riskar mu ba.
Yanzu dai ga wani Babban gari nan a gaban mu kuma dole ne mu gaggauta shiga cikin sa domin har yanzu jikina rawa ya ke yi saboda yunwa.
Inason na sami abnc isashe naci na koshi amma fa ba zamu iya shiga cikin grn ba kai tsaye dole ne mu yi 'yar dabara saboda tsaro.
Gama fadin hakan ke da wuya sai ya daga kafadarta ya karanta wadan su dalasimai na tsafi.
Faruwar hakan keda wuya sai nan take shi ya rikide ya zama tsoho tukuf rikr da san da ita kuma ta zama yaro karami dan kimanin shekara goma,
Kawai sai dubeata ya ce,"Sunanki Sahalu maza ki yi mini jagora mu shiga grn nan muna bara,
Ba tare da wt grdama ba kuwa sai Sadirat ta kama sandar dake hannunsa ta jashi suka nufi kofar babban birni kai tsaye bada wata fargaba ba,
<<<<< Khaleed >>>>>
Da isar su bakin kofar Birnin suka kamu da tsananin mamaki kuma tsoro ya shige su amma sai suka bsar suka ci gaba da bara don kada a ganesu, Bakomai ne ya basu tsoro da mamaki ba face,
ganin taswiwar fuskokin su bisa takardu a lika a ko i'na a jikin bango bj-bj , kuma ajikin taswairar an rubuta cewa wadan nan manyan masu laifine na sarki Shamsal don haka ana nemansu ruwa a jallo,.
Duk wanda ya kamasu ko ya fadi inda suke to za a bashi ladan dinare dubu dari.
Hatyan da Sadirat na cikin karanta wannan bayani ne a bakin kofar birnin sai shugaban dakaru da tsaitsaye a wajen wani narkeken kato sai ya dubeshi ya daka masa tsawa ya ce kai wannan almajirai,
suwa ye ku kuma taya kuka iso nan birnin alhalin kai makaho ne ski kuma jagoran ka yaro ne karami ??
Ko da jin wannan tambaya sai Hatyan ya rikirkice irin yadda tsofaffi ke yi ya ce Yaro har kasa hantar ciki na ta kada saboda wannan tsawa taka , Mu baki ne daga kasar Misra kuma tare muke da wani ayari na fatake a cikin jirgin ruwa jirgin namu ya yi hatsari a kusa da gabar wannan gari naku ya nutse karkashin ruwa ,
Kadan ne daga cikin mu suka ragu muka rarrabu a cikin daji saboda firgita, Da kyar muka gani hanya har muka iso nan,
Ko da jin wannan batu sai wani can daga cikin dakaru ya ce, "Hakika wannan makaho ya yi gskya domin kuwa tun shekaran jiya ire iren wadanan fatake suke shugowa garn nan suke bayar da labari irin wanda ya bayar yanzu,
Ko da jin haka sai shugaban dakarun ya sa aka budewa su Hatayan kofa suka kunna kai ciki suka dur fafi cikin gari kai tsaye ba tare da wata Fargaba ba..
Download Complete Book Here
0 Comments
Thank you for this comment