[3/1, 12:34 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜

      *'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱
.                      👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 




©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼

Dedicated to
 *AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*

📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com


GARGADI 
BAN YARDA A SARRAFA WANNAN LABARIN TA KOWACCE HANYA BA, YIN HAKAN ZAI SANYA MUTUM YA FUSKANCI HUKUNCI DAGA SHUWAGABANNIN KUNGIYA A KIYAYE. 

TUNATARWA 
WANNAN LABARIN BANYI SHI DOMIN CIN ZARAFI BA FA CE DOMIN NEMAN MAFITA GA YANAYIN ZAMANTAKEWAR MU A IRIN WA'INNAN GIDAJEN. IDAN HAR YAZO DAI-DAI DA RAYUWAR WASU AYI HAKURI KIRKIRA NE. 

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

            *1~5*
_SHIMFIDA_


*'YAN GIDAN HAYA* 
Gida ne mai dauke da dakuna goma sha biyu sai bandaki *guda hudu, wato kowanne biyu.* Suna da rijiya a hanyar kicin dinsu wanda ke manne da famfo guda daya, sai igiyar shanya guda biyar. Gida ne mai dauke da mutane masu bambamcin ra'ayi da harshe. Suna zaune tare yayin da wasu suke da sana'ar yi a unguwar.  Suna da mai unguwa sunanshi Malam Tanko yana da mata biyu Jummai da Hannatu sai yara biyar Lado shine babba, Buba, Sani, Saratu da laraba. Duk manoma  ne mazan, matan kuma sun yi aure. Malam Tanko ya kasance mutum mai saka idanu kan wannan gida na yan haya wanda su kuma basa kaunar hakan. Maman Ladi ita ce kusa da rijiya tana sana'ar waina da daddare, Maman David tana saida akamu da safe, Ladidi bata saida komai sai gulma, matar malam tana sana'ar kayan miya, Iya beji mai kosai, Mama akintola mai kankara, Mama Dare mai icce, Abule bata sana'a sai Maman Usman itace babba a gidan ma'aikaciyar gwamnati ce, sai Inna Talatu tana da injin nika. Kusa da hanyar bayi Mairon Ado mai sana'ar kuli da man gyada, Inno dillaliya itace hanyar kofar gida.

    *BARI MU LEKA CIKIN WANNAN GIDA NA YAN HAYA*

Zaune Maman Ladi take a kofar dak'inta tana tsintar shinkafar da zata yi waina da ita yau. Da gudu ta hango dillaliya ta shigo cikin gidan tana fadin "Taimako Maman Ladi ga yara can na fada, na raba sun ki rabuwa kwarankwatsi". 
Ajiye shinkafar ta yi tare da bin bayan dillaliya. 
"Kai! Butar ruwan iyayen ku idan baku daina fada ba" cewar Maman Ladi. Caraf ta ji an riko hijabinta ana janta, da sauri ta waiga tana sababi.
"Wanne mai ido a tsakar ka ne ke jana don uwatai?"
"Nine nan ka ji ko Mama Ladi, ni ne waye ya ce ka zagi yaro nawa yanzu?" Maman David kenan ta dauka butar iyayen ku da Maman Ladi tace zaginsu ta yi, tana hargowa tare da rike kugu. 

"Jar uban nan yanzu dan nazo rabon fada shi ne za ki min rashin kunya? To alkur'an sai na sabautaki yau" tana gama fadi ta kai ma Maman David wani irin mangari a baki, take saiga jini na zuba. Ihu Maman David tasa tana kiran "Mama Ladi ya kesheni Iya beji kazo fa" Da gudu sauran matan gidan suka fito don jin kururuwar Maman David. 

Gyara tsayuwa Maman Ladi ta yi tace " sai na sauke ma ko wacce shegiya abun dake kanta a gidan nan ai dama ina sane da gulmata da akeyi idan na fita, kullum sai Ladi ta fadamin. to yau..." gum taji an rafka mata abu akai wanda ya hanata karasa maganar da ta keyi. Tsaye ta yi gaban Maman Ladi tana huci cikin tsananin fushi tace" to wata shegiyar ce ke gulmar ki? Kinzo kina zagin mutane a tsakiyar titi waye sa'an ki? Ko dan.." tass taji saukar mari a fuskarta, Matar Malam kenan wacce ba ayi tai shiru. Juyawa ta yi dan ganin waya mareta? Maman David ce "da kaine anayi fadan da kazo ka hana na rama dukeni da Maman Ladi ya yi?"  "Kan butar duma, ni kika mara? To wallahi zakisan kin tabo Matar malam yau a gidan nan" kafin Maman David ta ankara kawai jinta ta yi a kasa matar Malam ta turmushe tana duka. Tim tim ka keji Iya beji ta hau kan matar malam tana duka ita ma. Jitai an buga mata abu a baya, ba shiri ta tsagaita da dukan matar malam domin mai dukan ya shammaceta taji dukan sosai. Abule ce tsaye rike da icce tana hararar Iya beji tace "yo hidi miki ankai matar malam batta da gata? Na rantse ina fasa kanki da wanga icce kinka kuma dukanta" tashin hankali ashe gefe ma fadan ne tsakanin Ladidi da Mairon Ado. Gida fa ya rikice da fada, dama kowa na da cikin kowa. Ganin haka yasa dillaliya ficewa da gudu don kiran mai unguwa.

    *********

Zaune yake kofar Jummai tana dama musu kunun da zasuyi karin safe dashi, Hannatu na tsifar kai. Jummai tace "Malam kaga ragowar kullin kunun nan kadai ya rage mana cikin gidan nan ka taimaka a bude rumbu mu debe abinci". 


"tabdijam! Rumbun da na kidaya sai karshen wata shine zan bude yanzu? To wallahi ku sake shawara bazan bayar da ko kwayar hatsi ba ai nasan siyarmin da hatsi akeyi, mugaye kawai". Shigowar dillaliya da gudu tana kiran "mai unguwa kazo yau unguwar ka babu lafiya kwarankwatsi za ai kisan kai a gidan haya" da hanzari ya mike ya yi facali da robar kunun mai dak'insa. Rawani na warware wa yana daurawa ya fice ko waige. 



*Mezai faru da mai unguwa kenan?*

Muje zuwa 


*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:34 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
       *'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱

.                      👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 




©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to 
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

         *6~10*

Fada sosai sukeyi kaman zasu kashe junansu, ga mazajen su basa nan. Sai makwafta ne keta kokarin raba wannan rigima. 
Mai unguwa ya iso da sauri yana gyara babbar rigarsa. 
"Yanzu saboda Allah bazasu bar wannan fadan ba? Yaran ku na kallon ku fa wannan ai abun kunya ne gareku." 
"Abun kunya ya wuce sa'ido irin naka" cewar Ladidi. 

Gyada kai ya yi lokaci daya kuma ya daga salularsa yana fadin "Ranka-ya-dade mai unguwa Tanko ne, yauwa sai kunzo" cak suka tsaya da fadan jin mai unguwa ya kira yan sanda. 

Dillaliya dake tsaye kusa da mai unguwa ne ta saka dariya hade da mika wa mai unguwa batirin wayarsa tana fadin. "Mai unguwa ga batirin sanda ka ciro wayar naga ya fadi kasa, ashe dama ana magana ko ba batirin?" 
"Ke kam anyi matsiyaciya basai kiyi shiru ba tunda sun daina fada da barazanar da nayi ba? Ai dama nasan ko kwandala banda ita a wayar" ya fadi yana muzurai. 

Saukar katako dillaliya taji tsakiyar kanta wanda ya haddasa mata zubewa kasa ba shiri,ga jini na zuba. 
"munafuka bayan kin sani na ajiye shinkafar sana'ata shine kika zagaya kiran wannan kidahumin ko?" 
"Haba Maman Ladi da girmanki kike irin wannan abun?" 
"Dalla rufemin baki munafiki mata maza, in banda gulma baka ajiye komai ba uban me kazo yi nan inba gulma ba". 
"Yanzu Maman Ladi da girmana kike zagina?"
"Anzage ka din, talakan banza kawai" tass ya dauke ta da mari. 

Aikuwa saijin saukar katako ya yi tsakiyar goshin sa, shima sai jini. Nan fa fada ya kara kaurewa tsakanin matan gidan aka bar dillaliya da mai unguwa zube a kasa da jini. 
Jiniyar motar yan sanda ya dakatar dasu kowa ya yi tsaye cirko-cirko. Yan sanda suka fito bisa jagorancin wani makocin gidan hayan, aka tasa su gaba zuwa station shi kuma mai unguwa aka kaisu kemist da dillaliya.

Zaman sulhu akayi kasancewa DPO mai kirki ne, ya sanya yace ayi sulhu. 

Bin ba'asi akayi inda aka baiwa Maman David da Maman Ladi rashin gaskiya kan cewa sune suka haddasa rigima, sai matar Malam data siya fada a sama. Mai unguwa kuma aka tuhume shi kan bai kyauta ba bisa marin Maman Ladi da ya yi, ita kuma an tuhumeta da amfani da makami sannan dole ta biya kudin maganin su. Nasiha sosai DPO Muhammad Abubakar ya yi musu kan muhimmancin zaman lafiya, sannan ya sallame su suka dawo gida. 

           **********

A gidan mai unguwa kuwa bayan ya barar da kunun ya fita ya barsu, sukai shiru suna tunanin yanzu me zasu sha gashi basu da ko kwayar gero. 

Jummai tace "Hannatu idan kina da gero ki bani na sirfa nayi kunu wallahi yunwa nakeji."
"Maman Sani kenan, nima nan yunwa nakeji gashi ya barar da kudin, ya tafi neman suna. kawai mu balle rumbu mu debo hatsi mu dafa" 
"uhm tsoran jarabar shi nake yi Hannatu"
"to mu zauna da yunwa tunda kina tsoro"
"A,a to bari mu debo idan yazo sai mu nemi abun cewa."
"Yauwa Maman Sani gara haka ai."

Suka debo shinkafa suka daura suna zaune tare da addu'ar Allah yasa ta dahu kafin ya dawo. Aikuwa suna saukewa mai unguwa ya shigo da bandeji manne a goshi. 




*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:34 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
       *'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱

.                      👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 




©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to 
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

           *10~15*

Da mamaki suka bishi da kallo ganin shi manne da bandeji ga leda a hannu da alamun magungunane a ciki. 
"Malam sannu da zuwa"cewar Jummai. 
"Yauwa Jummala"
"Malam hatsari kayi ne na ganka haka?"
"Tirela ce tabi ta kaina." ya bata amsa cikin tsawa tare da zama bakin kofa. 
"ke Hannatu baki iya sannu da zuwa ba ko?"
"Allahu Malam gajen hakuri ka yi, ina jiran Maman Sani ta gama ne sai nayi nawa"
"Ja'ira mai ladabin munafukai."

Girgiza kai kawai sukayi domin sun saba da halin mai gidan nasu, irin mazajen nanne masu zagin matan su. 

"Malam dan Allah meyafaru kaji ciwo?"
"Bari kedai Jummala wadannan shegun mutanen ne suka kusan sabautani."
"Wasu mutane kuma mai gida?"ta tambayeshi da mamaki. 

"Yan gidan haya mana matsiyata daga rabon fada saijin saukar icce nayi a fuskata."

Dariya dukkansu suka saka suna farin ciki dama gashi ya barsu da yunwa dalilin zuwa neman suna. Aikuwa a fusace ya mike yana fadin. 
"Duk shegiyar data kara yi mani dariya saita bakunci gidan uban ta yau wallahi, shegu marasa tausayi kawai na fada muku madadin kumin jaje shine ko wacce zata bude baki kamar kofar gari tana dariya, to wallahi na karaji ku gani."

Shiru sukayi suna kallon shi, jin ya kuke yana sababi hade da tallafe kanshi dake tsananin bugawa ya shige dak'i.

"Maman Sani abinci ya sauka" 
"to Hannatu zuba mana muci"
"Nima a zuba min zanci insha magani."
Suka ji mai unguwa na fadi. 

Zuba mai sukayi aka kai mai, nan suka zauna sunaci, sai da ya cinye yasa ruwa ya kalle su. 
"Amma kuwa abincin nan da dadi yake, ina kuka samu shinkafa?"
"Malam kenan, ai rumbu muka bude muka debo."
"Rumbu Jummala?"
"Eh Malam ko so kake mu zauna da yunwa bayan ka zubar mana da kumallon safe" ta bashi amsa cikin zafi itama.

Da yake yasan halinta idan ranta ya baci bata mai da sauki, dan haka yace, "To shikenan an debo Allah ya isa, kuma anci Allah ya isa."


         ********
Zaune ko wacce take a bakin kofarta tana gyaran kayan sana'arta. Maman Usman tana ta yi musu nasiha kan abun da suka yi yau basu kyauta ba. 
" Yanzu ba kuji kunyar kanku ba don Allah, ace matan aure a ofishin yan sanda?"
"wallahi Maman Usman duk laifin wa'innan munafukanne" cewar Ladidi tana nuna su Iya beji. 

Aikuwa Maman David ta mike tana fadin, "Ledidi kace nine munafuki? ehen baban kane munafuki." 
"Babana fa ki kace, don uwarki na kira sunan ubanki ne?"
"Ladidi amma magana nake yi daku ko?"Maman Usman ta fadi cikin tsawa. 

"Haba Maman Usman kina ji fa wai ubana take cewa munafuki" kawai ta saka kuka tana cigaba da fadin, "Malam mai carbi har ya bar duniya bai taba zagina ba, amma yau ga wata tsinanniya ta zage shi dalilina." 
"Wallahi ki zagi uban babanta Ladidi karki  yarda taci bulus" cewar matar Malam dake zaune tana gyaran kayan miya. 
"Au Matar Malam ina magana kina kara iza wuta ko?"
"A,a ayi hakuri Maman Usman na tuba."

Nan dai Maman Usman ta sasanta tare da kara basu hakuri, da nusar dasu illar abun da sukeyi. Da yake suna ganin girmanta yasa suka aminta da abun da tace musu kamar gaske. 

Da daddare Maman Ladi ta kafa kaskon wainarta ta fara sana'arta a kicin din gidan. Bata kula kowa ba da yake tana ciki dasu kan kudin maganin data kashe, ta fara sana'arta masu siye nata zuwa. 

Mama akintola ce ta fito da niyyar daura girki, bayan ta dawo daga wurin sana'arta. 
"Iya Ladi kenan ya kasuwa fa"
"lafiya, kuma sunana Maman Ladi ba iya Ladi ba."
"oh I'm sorry Maman Ladi"
"Allah ka tsine ma duk matar data zageni da yare."

Inna Talatu dake zaune bisa rijiya ta kwashe da dariya, "Kai jahilci dai baiyi ba wallahi, su oo a taimaka a je makaranta" 
"Malam Dauda dai baida kudin zuwa makaranta nasani" Maman Ladi ta bata amsa. 
"Aifa shiyasa a kace sorry mutum ya zata zagin shi akayi, gara ubana zamanin su babu makaranta"
"Wai cin danko harda su kaza"cewar Ladidi. 
"Ganemim hanya Ladidi wai makaho yaso tsegumi"
"a,a ba dani ba gada a hurumi Maman Ladi" 


A fusace Inna Talatu tai kan Maman Ladi dake zuba waina, aikuwa kaya-kaya aka hau dambe kan tandar waina. 
"Maman Usman taimaka ki fito kafin ayi aika-aika cikin gidan nan"

Baiwar Allah da sauri ta fito jin maganar Ladidi, wanda yasa sauran matan gidan fitowa. 

Tana shiga kicin din lokacin Inna Talatu ta daga bokitin kullun waina sai a jikin Maman Usman. 




*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:34 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
       *'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱

.                      👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 




©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to 
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com

*Ummyn Yusrah nida sweet mum Rano muna godiya da dedicating Allah ya kara basira, muna Jin dadin Rayuwar Aseeya.*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

            *15~20*

Wani irin zabura Maman Ladi ta yi ganin an shekar da kullin waina kasa. Ita kuwa Maman Usman mamaki ya hana ta motsi ganin wannan almubazzaranci irin na Inna Talatu. 

Bakin wuta Maman Ladi ta dauka ta yi kan inna Talatu tana duka inda Maman Usman ke kokarin raba su, ganin ta kasa yasanya ta fara kiran sauran matan gidan dasu kawo mata dauki. 

Dai-dai shigowar malam Isah mijin Inna Talatu, yana hango wannan fada ya afka kicin din da niyar ceto matarsa. Rufe su da duka Maman Ladi ta yi ta ko'ina tana fadin, "Dama haushin ku nake ji, kuma wallahi a biyani kullin wainata ko na daki kudina yau." ganin da gaske ba zata bar dukan su ba, yasa Maman Usman shiga tsakani. Maman Ladi ta sauke bakin wutan tana haki gata dama jibgegiya. 

"Zo ki fita daga kicin dinnan inna Talatu" cewar Maman Usman tana nuna mata hanyar waje. 
"Ba inda zani wallahi sai na rama dukana da ta yi harda hadawa da mijina."
"A,a Talatu mu fita kawai ina ganin aljanu gareta."
Cikin takaici ta kalle shi "kaidai wallahi anyi matsaoracin namiji, to yau kodai ka rama min dukana wallahi ko kuma ayi tashin hankali a gidan nan". Shiru ya yi yana kallon Maman Usman wacce ke tsaye cikin takaicin fadan su ga shi anyi mata wanka da kullin waina. 

"baki daku bane wallahi shiyasa kike tunanin ramawa, saura kudin wainata wallahi kodai a bani ko kuma mutum yaji a jikinsa." Fadin Maman Ladi kenan dake tsaye rike da robar wainarta. 

"Maman Ladi nawane kudin wainar?" malam Isah ya tambaya domin bai kyaunar a sake wani tashin hankali tunda yasha jibga. 
"hadin dubu uku da dari tara nayi, na saida ta dari tara" ta bashi amsa. 

Lalibo aljihu ya fara yi yaji an riko shi da karfi. Gaban shi ya fadi ya zata wani fadan ne dan haka a tamanin ya waiga, Inna Talatu ya gani, ya saki ajiyar zuciya. "lafiya kuwa Talatu?"  "Na rantse da Allah ba zaka biya kudin nan ba, bata isa ba ubanta ya yi kadan bayan dukan da tai mana, sai kuma a kara da kudi to wallahi bazaka biya ba." kau! Taji an dauketa da mari.

Maman Ladi kuwa kallon matan dake leke ta yi tace "Angama ai sai ko wacce shegiya ta bar lekena" 

"A, a Maman Ladi karki sake ki zage mu wallahi" cewar matar Malam dake tsaye gefen rijiya. 
"Na zaga nace ko wacce shegiya naji duka, yan iska maglmata" 
"Ko wacce ta tafi dak'in ta don Allah na roke ku" Maman Usman ta fadi lokacin da take fitowa daga wanka. 

Sumi-sumi suka wuce ba wacce ta kara magana. 

    Washegari Lahadi 

Kasancewar yau lahadi, yasa da yawansu wanki su keyi da kwalemar dakunansu. 

"Matan gida zanje sunan kanwata sai na dawo, don Allah mu zauna lafiya" cewar Maman Usman sanda ta fito daga dak'inta. 

Sukai mata a dawo lafiya ta fice. 

Mairon Ado zaune kofar Abule suna wanki tare, ta dubi Abule tace. 
"Ban baki labari ba kawata."
"Menana ankayi hwadi mun". 
"Wata mata ce a tsohuwar unguwar da muka taso, kullum saita tsine ma mijinta, gata da masifa amma bata da karfi."

"Kai Mairo taya kinka sani?" Abule ta tambaye ta tana cigaba da wankinta. 

Mtsw... Mairon Ado ta yi tsaki "kefa dadina dake wulakanci, to ai a kusa da gidanta nake". 

Girgiza kai Abule ta yi tana dariya domin ta gane dawa Mairon Ado ta keyi, tace "Alkur'ani Mairo wanga batu nake haka yiki, kin hwadi gaskiya" ta mika mata hannu suka tafa hardasa shewa. 

Ba tare da sun lura ba, saijin saukar  ruwa sukayi a jikinsu. Cikin masifa suka mike tsaye suna kallonta, Maman Dare ce mai icce ta wanke su da ruwa. 
"Me mukai miki ke kuma?"Mairon Ado ta tambaye ta cikin bacin rai. 

Kasancewar tana jin hausa sosai yasa ta fahimci abun da suke nufi tace. "Mairo muna zaune lafiya shine zaki janyo mana masifa ko, ina ruwanki da ita?" 
"Tabdijam! Shine zaki watsa mana ruwa, to kanwar tsohuwar kice kenan?" 
"Mairo kenan, kinsan dai bani da lokacin batawa don haka ki shiga hankalinki dani."

Tass! Abule ta dauketa da mari tana huci take fadin,"Kekam anyi bagidaja walla, yo mi naki da zaki wanke muna jikki da wanga ruwan wanki?to walla ki yi abun da yadda meki ba ruwana ta dake". 

"Yauwa Abule tawa haka nake so kicimin kaniyar duk wacce ta yi damu a gidan nan." 
"Barsu ta dani ina ma mace dukan tsiya walla ni bani daukar reni". 

"Ni kika mara Abule?" Maman Dare ta tambaya tana dafe da kuncinta. 
"Yo me zaki yi?"
"Ina zuwa zakiga abun da zanyi yanzu kuwa" ta wuce dak'inta da sauri.

Ita dama Mairo bata da karfin yin fada, dan haka tana ganin Maman Dare rike da wuka tai daki da gudu tare da danna sakata a kofarta. 


Abule ta ruga kicin ta dauko bakin wuta gashi sai ci yake wanda matar Malam ta hada ta dora girki. 




*Badeeyerh Beauty Queen*
[3/1, 12:35 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
       *'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱

.                      👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 




©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to 
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com

When I Am Glad,
 You Are In My Smile,
 When I Am Sad,
 You Are In My Tears,
 When I Am Walking
 you Are In My Steps,
 When I Am Sleeping,
 you Are In My Dreams.
 I Love You! Abu Uthaemin.

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

         *20~25*

InnaTalatu dake wanke injin nikarta  ta kalle su ta yi dariya, domin duk zancen da suke yi tasan da ita suke, gashi yanzu ta kwabe musu. 

Maman Akintola ce ta fito daga dak'inta dauke da buhun kankara a kanta zata kasuwa, taga wannan aika-aika dake shirin faruwa, ta ajiye  buhun tare da riko Maman Dare. 
"A'a Mama Dare menene yana faruwa aka, da wanini zakiyi fad'a da wuka?"

Tana haki ta kalli Maman Akintola tace "waccan shegiyar zan koya ma hankali naga alama bata da shi". 
"kece shegiya wallahi ba Abule ba"cewar Mairon Ado dake makale jikin tagar dakin ta. 

Abule dake tsaye rike da bakin wuta ta yi dariya tana kallon Mairon Ado tace "walla ke kau kin rako mata matsoraciya na kawai" 

"A'a Mama Dare idan kayi fad'a da wuka kasen dai mai anguwa zata kai karan ka station ko? So please be patient". 
Hararar Abule ta yi kafin ta juya da nufin komawa daki, rabon ayi saiji ta yi Abule na fadin "Banza da kin hwadi mun wanda bai da hankali yau walla". 

Aikuwa jefar da wukar ta yi ta nufe Abule tare da cakumar rigarta ta yaga tun daga sama har kasa kasancewar doguwar riga ta sanya, sannan ta hau jibgarta kamar an aikota. Kokari take ta rama amma ba hali domin ba karamin riko Maman Dare ta yi mata ba. 

Ganin ana dukan Abule yasa matar malam fitowa tana fadin "Bari na rama wa kura aniyarta"  ita ma ta hau jibgar Maman Dare. 

Maman Akintola ta dubesu sannan ta dubi yanda buhun kankararta ya fara ruwa, kawai ta karasa ta dauka tana cewa "Bana da kudi berinje kasuwa nawa kawai"  ta fice. 

Maman David ce ta shigo daga wurin saida akamunta a waje, ganin wannan fad'a na wanda ka sani, ita ma kawai ta shigar ma Maman Dare. 

"wallahi ba za'ayi babu ni ba gara nima  na rama abun da ya faru jiya" cewar Inna Talatu. 

Itama ta shiga cikin fad'an, sai dai nata kowa duka ta keyi sabanin matar Malam dake ramawa Abule, aikuwa da karfin tsiya itama Abule ta yaga t-shirt din dake jikin Maman Dare, hade da kai mata wawan duka a hanci da ya yi sanadiyar fitar jini. Ganin wannan jini ya harzuka Maman Dare ta gabza ma Abule duka a baki, sai ga hakori ya fado daga bakin Abule. Ihu ta sanya tare da rarumo iccen data yarda ta cire rigar da aka yaga tai kan Maman Dare. 

Matar Malam kuwa  Maman David ta samu ta kwantar kasa tana duka kamar kayan wanki. Hargowa da hayaniyar su ta fito da sauran matan gidan, ganin irin fad'an da a keyi na wanda na sani ya sanya itama Maman Ladi shiga ta hau jibgar Maman David dake kwance kasa suka rufan mata ita da matar Malam. Iya beji na ganin haka tace "Abun nayi ne dole na shiga"  ta rufan ma Abule da duka. 

Gida ya rikice, ba wanda ke kokarin bada hakuri sai dai ya shiga ya rama ma wanda ya sani koya fanshe haushin shi kan wanda yake tsumayi. 

Ganin ba mai rabo ya sanya Mairon Ado bude sakata, ta fice da gudu sai gidan mai unguwa.


           *GIDAN MAI UNGUWA KUWA*
 


Zaune yake a zauren gidan sa tare da yaran shi Sani da Lado. Ya dubi Lado yace, "Ya kamata kayi aure badi Lado, ka girma da yawa ga kannen ka nasan kai suke jira" 

Sosai kai ya yi yace "Insha Allah Baba a tayani da addu'a"  "To Ubangiji ya yi maka zabi na gari" 
"Ameen Baban mu" Sani ya amsa. Mai unguwa ya kalle shi "to mara kunya dama nasan saikai ai, tashi ka bani wuri" tashi ya yi yana dariya ya shiga cikin gidan. 

Mahaifiyarsa ce zaune bakin madafi tana gyaran shinkafa. "sannu da aiki Mama kawo na tayaki"  ya fadi yana niyar amsar tiren shinkafar. 
"A'a Sani barshi na gode, jeka ga Hanne can a wurin dabbobi tana shara ka amsa ita sai tazo muyi girki" "to Mama" ya wuce. 

Kasancewar suna zaman lafiya kamar ba kishiyoyi ba, yasa komai nasu tare suke yi. Ta taho tana fadin "Maman Sani shine zaki sanya shi aikin wahala maimakon ki bashi shinkafa ya tsince?" 
"A'a Hanne gara ya amsa ai, kizo nan muyi aikin abinci"
"To shikenan na gode" ta zauna suna hira suna aiki. 

Mai unguwa ya shigo yana hade fuska ya kalli Hanne "Sai a kaimin ruwan wanka bandaki" 
"Malam tun dazu fa na sirka ruwan, da naga baka shigo ba shine na juye nai wanka"
"Hanne! Hanne! Hanne! Sau nawa na kira ki?" 
"Uku malam" ta bashi amsa. 
"To wallahi tun da girma da arziki ki nemo min ruwan wanka na, in ba haka ba billahillazi karar ki zan kai gurin ubanki."

Cikin takaici Jummala ta kalle shi tace "Malam wulakancin ka ya fara isar mu cikin gidan nan,meye na saka uba cikin wannan maganar? To wallahi na gaji da wannan halin naka" 
"Yo ba sai a dakeni ba idan za'a iya, ko kuma a rama zagin"
"Ba wanda zai deke ka balle ya rama zagi, saboda munsan darajar aure, amma wallahi halin ka ya isheni"
"Aikin banza ruwan wanka nake bukata yanzu ba sai anjima ba"

Ta kalle Hannatu wacce ko dago kai ba ta yi ba dan takaici tace "Hanne juye mai ruwan sanwar can, gara ya fita ko zamu sha iska mai dadi" 
"Ba inda zani ina cikin gidan nan naga mai fitar dani." ya fadi lokacin da yake shiga dak'i. 


Ba wacce ta kula shi cikin su, Hannatu ta juye mai ruwan ta aje bakin kofar bandak'in. 
"Malam ga ruwan nan na ajiye"
"gani nan zuwa ai 'yar magoriya, zaki fadawa makawafta zanyi wanka ko?"

Bata amsa mai ba, taci gaba da gyaran shinkafarta. 

Yana fitowa ya dauki bokitin da niyar shiga bayi, sai ga Mairon Ado ko mayafi babu ta shigo a guje tana kiran "Taimako! Taimako mai unguwa uban al'umma, gidan 'yan haya zasu janyo a daure ka shekara dari a kurkuku idan sukai kisa a unguwar ka."

Sakin bokitin ruwan ya yi ya tuntsire kasa ya bita da gudu, Hannatu na fadin" Malam baka warke ba zaka koma?" Ina tuni ya fice daga gidan. 



*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:36 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
       *'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱

.                      👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 




©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to 
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

          *25~30*

Tallafe kumatu ta yi tare da duban Jummala tace "Maman Sani kina kallo ko?"  "Kema ce da neman magana wallahi, yaje shiyasa ni."

Nan suka cigaba da girkinsu suna hirar halin mai gidan nasu. 


        *A  GIDAN 'YAN HAYA*

Shigowar mai unguwa ya yi dai-dai da bugawa Maman Dare icce akai wanda Abule ta yi wannan aiki. 

"Kai! Kai! Kubari nace don iyayen ku" cewar mai unguwa. 

Ina! kamar basu ji ba domin Iya beji ce ta rafka ma Abule icce itama ganin Maman Dare zube a kasa tana kuka. Shake wuyan Iya beji Abule ta yi tana jijjigata, wanda ya sa juwa dibar Iya beji ta zube a kasa, Abule ta hau kanta tana duka. Ganin haka Maman Dare dake dafe da kai ta dau iccen da Iya beji ta yarda da nufin dukan Abule dashi, ganin haka mai unguwa ya yi tunanin shiga tsakani aikuwa sai a gefen kafadarshi yaji saukar iccen wanda ya haddasa mishi yin taga-taga kamar zai fadi, kafin ya samu ya tsaya a gefe dafe da kafadarsa da yake ji kamar zai cire don tsananin zafin da yake ji. 

Mairon Ado dake labe tana leke, ganin an rafka ma mai unguwa icce yasa ta kurma ihu sanin cewa yanzu ba mai rabon wannan fada. Ganin ihun nata bazai yi maganin komai ba, yasa ta shiga dak'i ta dauko bokitin ruwanta tare da sheka masu Maman Ladi dake dambe a kasa. Saukar ruwan yasa suka mike a firgice suna kallon mai wannan aiki, yayin da mai unguwa ke duk'e a kasa ya dafe kafadarsa kamar ya yi kuka. 

Maman Dare ta samu gefen kumatun Abule ta gantsara mata cizo wanda ya sanya ta saki Iya beji ba shiri ta kurma ihu domin taji zafin cizon. Sanadin da ko wacce ta mike tsaye kenan ana kallon-kallo. Shigowar Malam Isah da Baban Dare kenan gidan domin makwafta suna jin wannan fad'a amma suna tsoran shiga gidan. Shigar mai unguwa ma duk akan idanunsu, jin ihun ya cigaba suka san mai unguwa baiyi nasarar rabawa ba, shine suka kira mazajen a waya. Kasancewa suna kusa domin kanikawane su biyun a bakin titin kan layin. 


Baban Dare nufi mai unguwa dake tsugunne ko numfashin arziki ya kasa yi, yace "Mai unguwa kina lafiya, menene ya same ki?" 

Cikin zafin mai dashi jinsin mace ga kuma azabar ciwon hannu yace "Dalla daukeni ka kaini gidan Usaini mai dori kafin hanuna ya lalace, kuma wallahi sai nayi shari'a da matar ka". 

Duk da Baban Dare bai fahimci abun da mai unguwa ke nufi ba, amma yasan wurin Usaini mai dori, don haka ya mike yana kiran "Esa kizo ki rike mai unguwa akaita wurin Huseni ya yi gyara annu nata". Da sauri malam Isah ya karaso don dama yana tsaye ne wurin su Inna Talatu dake zage-zage. 

Suka rike mai unguwa zasu fita da shi, ya juyo yace "ke matsiyaciya! Wallahi ki jira na dawo billahillazi sai nayi karar ki wurin hukuma".


Ba wanda ya tanka shi har suka fita, malam isa cike da zullumin mai zai faru idan suka bar gidan? Sanin cewa zasu iya yin wani abun ya sanya ya kalli baban Dare sanda suka isa waje yace "Ka rike mai unguwa ku tafi nasan matan nan zasu iya yin wani aika-aikar, bari na koma gidan" ya fadi cikin harshe turanci yanda baban Dare zai fahimta. 

Ya gyada mishi kai kawai tare da kara riko mai unguwa domin su tafi, fir mai unguwa ya dage lallai sai malam Isah yazo an tafe tare dashi duk da bayanin da ya yi mai, amma mai unguwa ya dage. Haushi ya kama Baban Dare yace "ke mai unguwa kina so mata namu ya yi kisa ne? Kina gani fa mun bershi shi kadai ya na fada ba meza a gida fa." 
"Yo ina ruwana dasu? su kashe kansu mana, amma billahillazi sai kun kaini gidan Usaini dukkan ku."
"Haba mai unguwa taya kake tunanin dukkanmu mubar gidan? Kiran mu aka yi domin tsawatar musu, amma ganin halin da kake ciki muka zabi taimaka maka, shine kuma kake cewa su kashe kansu?" cewar Malam Isah. 
"Esa berta ki shiga gida, nine kadai ze kaita gidana huseni tefi kawai" Baban Dare ya fadi. 


Malam Isah ya wuce ba tare da sauraron abun da mai unguwa ke fadi ba. 


Baban Dare ya kalli mai unguwa dake ta aikin sababi, ya nade hannun riga tare da daukar mai unguwa da nufin goyawa a bayan shi. 

Ganin wannan aiki yasa mai unguwa daga hannun mai ciwo ya kaimai duka a baya, wanda yasa hannun kara amsawa sai kuma ya dafe tare da matsar kwalla don ciwo .Baban Dare ya kalli mai unguwa yace "ok asema hannun ki yana lafiya shine kince aje gidan huseni ko? To walah ba zen kaiki ko ina ba" ya juya ya yi shigewarshi cikin gida ya bar mai unguwa tsugunne ga hawaye nabin fuskar shi. 

Makocin 'yan gidan haya ne ya tausaya ma mai unguwa tare da daukar shi a mashin suka nufi gidan mai dori. 

       
         *A CIKIN GIDAN' YAN HAYA*

Zage-zage akeyi tsakanin su, ko wacce na zagin wanda sukai fad'a tare. Ganin mazan sun dawo ya sanya sukai shiru aka koma hararar juna. 

Baban Dare ya dubi Maman Dare cikin yarensu yace "Na gode da kika zubarmin da mutunci, kullum ina fada miki ki daina shiga abun da babu ruwanki kinki, to wallahi duk abun da ya faru babu ruwana" ya shige dak'i. 

Tasan halin mijinta da zuciya, jikanta ya yi sanyi ta rufa masa baya ita ma. 

Malam Isah ya kalle su yanda sukai tsaye suna jifan juna da mummunan kallo yace "Talatu kuna da masaniyar kun kar ya mai unguwa ko?" 
"Kar ya shi kuma, ta ina?" ta tambaya a rikice. 
"A'a wallahi Maman Dare ce ta buga mai icce" cewar Mairon Ado dake tsaye gefe. 
"To wata shegiyar ce ma ta kira shi gidan nan?" Maman Ladi ta tambaya tana hararar Mairon Ado. 

Takaici ya kama Malam Isah ganin mai makon su jajanta, amma suna kokarin mai da zuwan nashi ma abun fad'a, dan haka yace, 
"Ko wacce ta kira mijinta kafin zuwan 'yan sanda gidan nan,kun san halin mai unguwa" ya shige dak'i. 

Suna tsoran batun' yan sanda don haka ko wacce ta shige dakin ta, tare da neman mazajen su. 


An hallarra a tsakiyar gidan. 

*Kome zai faru???*

*Ina labarin mai unguwa???*



*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:36 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
       *'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱

.                      👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 




©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to 
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


*WANNAN SHAFIN KYAUTA NE GARE KI ZUWAIRA MADARA. AUNTY ZETTY NAYIN KI IRIN SOSAI DINNAN, TANA YI MIKI FATAN ALKAHAIRI, ALLAH YA RAYA HANEEFAH, KEDIN TA MUSAMMAN CE.*

📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

           *30~35*

 Mai Unguwa zaune gaban Hussaini mai gyara, yana jiran ayi gyaran hannunshi saboda azabar ciwon da yake ji. Hussaini ya kalle shi bayan ya taba hannun yace "Mai unguwa ka samu tsagewar k'ashi a kafadar ka, garin ya hakan ya faru?" 
"kayi aikin ka ba tambaya ba malam "cewar mai unguwa a fusace.

Gyada kai Hussaini ya yi yana murmushi, ya dauko wani mai ya diba sannan ya kama hannun mai unguwa da karfin tsiya. Wani ihu mai unguwa ya saki wanda ya janyo hankalin yaran gidan, suka dinga leke suna dariya. 

Cikin azaba mai unguwa yace "Allah ya isa Hussaini, billahillazi ban yafe maka ba duniya da lahira azzalumi kawai". 

Kara shafa man Hussaini ya yi ba tare da ya kula mai unguwa ba, ya sake riko hannun ya matsa ya shafe da wannan mai. Mai unguwa ya kwalla kara yana hawaye yana zagin Hussaini, shi kuma Hussaini saiya kama kafadar mai unguwa sai ya fanshe zagin da yake yi mishi. Ganin azabar ta yi yawa ya sanya ya warce hannun shi tare da mikewa ya share kwallar idonsa yace "Zakasan ni mai unguwa Tanko ka yi ma wannan mugunta wallahi, har da kai 'yan sanda zasu hada yau." ya juya zai fita. 

"Mai unguwa kudin aiki na fa?" cewar Hussaini. 
"Na karfine kazo ka k'wata azzalumi kawai"
"Haba mai unguwa, wannan fa hakkina ne."
"Naci hakkin naka, kayi abun da zaka yi." ya juya ya fice. Yana isa tsakiyar gidan ya ga dandazon yara sai dariya suke ganin ya fito. Tsawa ya daka musu, amma ina sai fadi suke "Mai unguwa ya yi kukan gyara yeeee ra go, matsoraci mai unguwa Tanko" suna shewa.

Da gudu ya bisu ga hannu a rike, aikuwa suka k'wasa da gudu suna dariya. Ganin bazai ka masu ba ya sanya ya wuce yana aikin sababi yana fadin "Yau hatta iyayen ku suma sai sun kwana ofishin 'yan sanda, billahillazi tare da 'yan gidan haya. Yanzu ma can zani na kira su." jin hannun nashi namai ciwo idan yana tafiya, yasa ya k'wance rawaninsa ya daure hannun dashi yana cije baki. Sannan ya mike hanya sai station. 

          *********

     *A TSAKAR GIDAN 'YAN HAYA*

Kowa dake gidan ya hallara wurin wannan taro, bayan an zauna ne malam Isah ya mike da bayani kamar haka. 
"Ina fatan zaku mai da hankali ku fahimci ainahin abun da ya taramu anan? Dalilin wannan taro kuwa bazai rasa nasaba da fadace-fadacen dake yawan faruwa ba a gidan nan. Misali na yau wanda ya kai mizanin babu mai hankali a cikin matan mu, ko wacce kokari take na ganin ta yi fad'a badai ta raba fadan ba yau, mai unguwa da ya kasance uban al'umma kuma matsayin mai kula da wannan gida yau shima sun ji masa ciwo a hannu. Kuyi sani cewa mai unguwa bazai taba barin wannan magana ba face ya danganta ta da hukuma, shiyasa nace ko wacce ta kira mijinta domin sanin abun yi"

Cikin takaici Baban Dare yace " sunayi fad'a kaman kaji wada beci abinci ba".Dariya wasu suka yi dajin hausar shi. Mijin Maman Ladi ya mike yace" Tabbas abun da matan mu keyi kwata-kwata basu tsare mana mutunci, sai kace mu kadaine 'yan haya cikin wannan gari, kullum sai sun ja mana jaraba wurin mai unguwa. Ranar cewa ya yi wurin sarki zai kai karar mu a koremu domin ya gaji da masifar matan mu" ya karasa cikin bakin ciki. 


Haka aka dinga mai da bayani kan halayyar matan gidan, inda aka hana matan magana. Kowa ya yi ma matarsa kashedi kan wannan halayyar tasu. Ana cikin wannan magana ne suka ji jiniyar motar 'yan sanda, cikin takaici mazan suka mike da niyar fita waje, amma sai ganin 'yan sanda suka yi tare da jagorancin mai unguwa dake sak'ale da hannu a wuya kai babu rawani. 


Mazan ne suka yi musu tayin zaman sulhu, amma mai unguwa yace sam babu sulhu sai dai a tafi da Maman Dare ofishi tunda itace taji mai ciwo. 
"Kwarankwatsi sai an tafi da ita, matsiyaciya ita ta bugamin icce kawai don nazo rabon fad'a, shi kuma shegen mijinta ya barni a waje harda cewa wai na mutu ai basu suka kirani ba."
"Haba me unguwa kiyi hakuri mana ki fadi gaskiya" cewar Baban Dare jin bayanin mai unguwa. 
"Yauwa Usmanu kaji ba? Mace yake kirana shegen kwanon" Mai unguwa ya fadi yana nuna Baban Dare. 

Dariya dan sandan da ya kira da sunan Usmanu ya yi yace "afuwan mai unguwa bai iya hausa bane shiyasa"
" Yo dama an fadi mai hausar kayan banza ce? Ai dole ya kasa tunda ba muhallinsa bace" Mai Unguwa kenan. 

Sauran mazan ne suka shiga maganar don ganin ba a tafi da Maman Dare ba albarkacin mijinta, sunyi ma mai Unguwa Alkawarin biyan kudin jinyar hannun shi har ya warke. Jin haka dama gashi da masifaffen son kudi, take ya amince da wannan tayin. 

Nasiha sosai 'yan sanda sukai musu, tare da basu hakuri ganin an zauna tare, sannan mai unguwa ma yace "Na daina zuwa gidan nan koda zaku kashe kanku." Dariya sosai suka yi, sannan kowa ya kama kansa. 


       *SHIGAR MAI UNGUWA GIDANSA*

Matan na zaune tare da Lado, Sani da Buba suna hira. suka ganshi kai babu rawani, da sauri yaran suka mike cike da mamaki suna yi mishi sannu da zuwa. Ko kallon su baiyi ba ya zauna cikin zafin ciwo yana fadin "Hanne kawo min ruwa" 
"Malam meyasa meka a hannu?"
"Jummala! Jummala! Kar wata banza ta kuma tambayata abun da ya faru muddin nine mai gidan nan"
"To babu mai kara tambaya Malam, kayi hakuri." taja bakinta ta yi shiru tana binshi da ido. 

Ruwa yasha sannan yace "wato Jummala mata matsiyata da ban suke". Banza ta yi da shi. 

Cikin hassala yace" magana fa nake kuka shareni"
"Baba kayi hakuri"cewar Lado. 
"Don uwar ka na saka bakinka ne a wannan maganar?"
"Yi hakuri Malam bazai kara ba" Hannatu ta fadi tana mikewa. 
"Zauna ma za anan munahika kawai, za aje dak'in don ga bala'i ya dawo ko?"
"Abince zan kawo maka Malam " ta fadi ta yi hanyar dak'inta. 

Abincin ta kawo mai, amma ko kallon kayan bai yi ba sai ma cewa da ya yi ta kwashe bazai ci ba. Ta kuwa kwashe a ranta tana fadin"Mun samu na karyawa da safe". 

"Baba ga wannan ka sai magani, ni zan wuce sai da safe." cewar Sani ya mika mai dari biyu. 
Amsa ya yi yana dariya yace "Sani dan albarka, yaro mai halin dattijai na gode sosai magaji na" 
"Yauwa Baba had'ari kayi ne?" Sani ya tambaya. 

"Hmm! Sani in fad'a maka matan 'yan gidan haya ne suka kassarani yau wallahi"

Kunshe dariya suka yi dukkansu, sannan yaran sukai mai sallama suka tafi. Su kuwa matan dak'i suka shige suna dariya jin mai unguwa na fadin,"wallahi ban kara zuwa gidan 'yan hawa billahillazi kuwa". 


          *ANYA KUWA MAI UNGUWA? MADARA KIN YARDA DA HAKAN KUWA??*

             *********

     *' YAN GIDAN HAYA*

Kwana biyu an samu kwanciyar hankali babu fad'a, amma ko wacce na nan da cikin yar'uwarta. 

"Ke Inno jibi ranar cika ciki fa" cewar Ladidi dake wanke-wanke. 

"Ayererere" Inno tasa guda, sannan ta dora da fadin"Za muga k'wanjin mazaje masu zuciyar siyan akuya, da masu cin bashi irin na waccan shekarar. 

Mairon Ado ta yi tsalle ta ja gefe tana fadin "Uban mata zanci wallahi muddin ta kasa dani cikin zancenta."
"Uba fa kinka ce Mairo kawata? Ai wanga uban Baban ta shi ad dai-dai walle" suka tafa suna dariya. 

Ladidi ta yi murmushi ta kama waka"_ayye nanaye wacce mijinta bai da sulalla, wazai taimaka yaji tausai, ya aiko da gashin kaza ran dadi"

Kau! aka dauketa da mari, da sauri ta dafe kuncinta tana waigen mai marin. Inna Talatu ce tsaye gabanta. 

*Hmm yanzu aka soma*



*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
       *'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱

.                      👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 




©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to 
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
     
              *35~40*

Ba tare da tambayar ba'asi ba ita ma ta kwashe Inna Talatu da mari. Jin zafin marin yasa Inna Talatu durkusawa kasa dafe da kuncinta. 

"Ahayye gidan haya gidan dadi, gidan da ba uwar ka ba uban ka sai kallo." cewar Mairon Ado. 

Gaurewa Ladidi da Inna Talatu suka yi da fad'a, yayin da Abule da Mairon Ado ke kara iza wutar ta hanyar yi musu waka. 

Hayaniya ta yi yawa yasa Maman Usman wacce ke bacci a dak'i fitowa ganin maike faruwa, aikuwa taga wannan fad'a da ake. Da sauri ta karasa wurin tana janye Inna Talatu tare da kokarin shiga tsakani, amma ina bata yi nasara ba. Riko Ladidi ta yi da nufin janta, ganin yasa Ladidi kai ma Inna Talatu wani wawan duka wanda ya sauka a fuskar Maman Usman ta kuwa durkushe kasa. Ganin Maman Usman kasa ya sanya duk sukai kanta suna tambayar lafiya. 

Dago da fuska ta yi, ganin jini da alamu habo ta yi, yasa Abule rugawa ta kawo ruwa, Maman Usman ta wanke fuska. Kallon su ta yi tace "Na gode sosai da abun da kuke yi, ina fatan watarana ku gane illar da hakan zai haifar muku a gaba, domin yaran ku na kallo kuma duk abun da kukayi shi zasu koya." daga haka ta shige dak'inta. 

Shiru suka yi dukkansu suna jinjina fushin Maman Usman, daga bisani ko wacce ta koma kan aikinta ba tare data kula kowa ba.

Yau ranar cika ciki. 


Matar Malam dake kiwon kaji ce ta debo su cike da isa ganin tun safiyar yau babu wacce aka aiko mawa ko fiffiken kaza. Don haka ta debo kajinta guda biyar kosassu ta mika ma wani yaron makwotansu ya yanka mata. 

Ko wacce na zaune kofar dak'inta suna hira kamar ba mafadata ba. 

"Mairo zoki taya ni fikar kaji" cewar matar Malam. 
"Yo ni kuma ina da tumatiri zan gyara na kai nika."
"Haba mairo kardai bakin ciki kike don kinga zanci kaji?"

Murmushi Mairo ta yi tana fadin "Matar Malam aikuwa ko saniya zaki yanka alkur'an bazan taya ki ba, nima ina da nawa aikin."
"Kai jama'a wai anai maka hassada har kan abun da za kaci."
"Kedai kika sani" Mairo ta bata amsa sannan ta shiga ta dauko tumatirinta ta hau wanke wa. 

"Bari na taya ki matar Malam."
"Yauwa Ladidi na kuwa gode miki wallahi" Nan suka zauna suna gyara wa suna hira, wanda rabin hirar duk gulma ce kan babu wacce aka kawo ma nama. 

Yaro ya yi sallama suka amsa ya shigo yana tambaya ina Abule. I fito ya mika mata bakko cike da nama inji mijinta daga kasuwa. Ta amsa ta ajiye kofarta ta dauko roba babba ta juye, nama ne mai yawa wanda ya dau hankalin su matar Malam. 


"Wallahi Ladidi na tsane makaryacin namiji mai cin bashi, dube naman can, bashi ya amso fa kila, amma shine ya kimo shi da yawa." 
Dariya Ladidi ta yi tace "ga kuma su makwadaita a kusa ba". Ta fadi ganin Mairon Ado taje taya Abule gyaran nama. 

Basu tanka su ba suka cigaba da aikin su suna hira. 

Maman Ladi ta shigo janye da akuya wani saurayi na biye da ita. Bayan ta ajiye kayan Hannunta ne the dubi saurayin tana fadin "Yanka acan wurin" ta nuna mai wurin wanke-wankensu, ya kuwa tafi wurin ya hau aiki. 


"Matar Malam wasu fa miji bashi da ko sisi amma sai anyi karya harda siyo dabba." cewar Ladidi cikin bakin cikin har yanzu ba a kawo mata komai ba tunda mijinta y fita. 
"Na banza ne wallahi gara mu mazajen mu na kaunar farin cikin mu shiyasa zasu siya da guminsu." suka sanya shewa. Maman Ladi na jinsu ta yi bakan dasu ba tare data tanka musu ba. 

Inno zaune tare da yaranta suna gyaran kaji guda biyu tace "Maman Ladi yanzu nawa akuyar nan?" 
"Dubu hudu da dari shidda na siya Inno."
"Gaskiya ta yi arha sosai."

Dariya Maman Ladi ta yi tace "Inno kina burgeni baki da gadara irin nasu oo masu kiwon kaji."

Dariya suka sanya suna kallon matar Malam da Ladidi. 

Mijin Ladidi ne ya shigo, don haka tabar taya matar Malam ta bishi dak'i. Can ya fito ya tafi, ita kuma the fito tana yatsina fuska rike da leda a hannu. Ta zauna bakin kokarta tare da dungurar da ledar. Aikuwa Maman Ladi dake zaune ta mike tare dauko ledar the bude. 


"Aeyerere yau zamu ci ganda."

Warce ledar ta yi hannun Maman Ladi cikin fushi take fadin "zanci uban mata wallahi muddin ta shiga sabgata."


Shewa su Abule suka sanya, wanda yasa Ladidi da Maman Ladi juyawa don ganin menene. 

Mairon Ado ce aka aiko mata da nama da yawa kamar na Abule. Takaici ya kuma kama Ladidi ganin daga ita sai Inno ce masu nama kadan, don haka ta dau ledarta hadi da shigewa dak'i. 

Mario, Ladidi,Inno dillaliya da Abule suna zaune kofar kicin sun dora girki.Matar malam da Maman Ladi sun dora tafashen nama duk a cikin kicin suke aiki suna hira sabanin Maman Usman da ko lekowa bata yi ba. 




*To fah gasu a kicin daya duk suna girki, ko mai zai faru??*


*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
       *'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱

.                      👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 




©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to 
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

             *40~45*


Suna ta kai kawo cikin kicin ko wacce na duba girkin ta na tafashen nama dana kayan miya. 

Matar Malam ta dora tafashen kaji, Maman Ladi ta dora ruwan shinkafa duk a cikin kicin din. Maman Akintola ce ta shigo tana fadin "Yau zamu ci dadi fa a gida namu kowa ya nayi kirgi nama."
"Eh wallahi yau mai kallon gabas zaici dadi" cewar matar Malam. 

Da yake bata san mai hakan ke nufi ba dariya ta yi tana fadin "mata malam menene kina dafawa ne?" 
"Ina dafa kaji masu motsi ba ganda ba" cewar matar Malam. 
Cikin huci Ladidi data fuskanci da ita ake ta mike tana fadin "Don uban mata idan ta isa ta fadi sunana ta gani."
"Uban wa kike zagi mara kunya?" matar Malam ke fadi lokacin data mike tsaye. 
"Idan ana saida kunya ki siyo ki kawomin banza 'yar sa ido kawai."

"A'a Ledidi babu fad'a yau fa kayi hakuri please" Maman Akintola kenan sannan ta wuce ta barsu. 

Robar da Ladidi ta jika ganda ciki matar Malam ta yi kwallo da ita tana fadin"Ga rashin kunyar nan na siyo miki, banza mai kirar samudawan farko."
"Jar uban nan, zaku wa kisan kin zubar min da nama wallahi."

Maman Ladi ta mike tace "Ku dakata don Allah, meyasa baku da hakuri ne, ace kullum sai kunyi abun fade cikin unguwa?" 
"Maman Ladi ba ruwanki cikin wannan magana, kina gani ta zubar min da ganda."

Shewa su Abule suka sa ita da Mairo jin Ladidi tace ganda. Wanda hakan ya kara tunzura Ladidi ta daga kafa ta sauke kan tafashen kajin matar Malam, sai ga kaji zube a kasa. Ruwan ya zuba kan kafar Inna Talatu, ai kuwa ta mike ta dauke Ladidi da mari, zafin marin yasa Ladidi cakumar Inna Talatu da fad'a. Matar Malam ta kalli kajinta dake zube a kasa, ta yi kan Ladidi da duka ita ma. Su kuwa sauran matan ba wacce ta yi yunkurin raba wannan fad'a sai ma kara ingizawa suke. 

Kiff! Aka watsar da tukunyar tumatir din Abule na tafashe. Tashin hankali ganin wannan aiki ya harzuka Abule ita ma ta kifar da tukunyar tafashen naman Inna Talatu. Ganin haka Maman Ladi ta sunkuci tukunyar namanta ta yi hanyar barin kicin din, tana kawowa kofa matar Malam ta kwashe mata kafa, sai ga Maman Ladi a kasa nama ya watse har tsakar gida. 

Yaran gidan suka shigo, ganin nama zube ga Maman Ladi ta kasa tashi, suka sanya wa-wa suna rugawa waje da gudu.

Mikewa Maman Ladi ta yi ta koma cikin kicin din. Shakar matar Malam ta yi suka hau dambe. Naman Mairon Ado Ladidi ta juye ma Inna Talatu gaba daya a jiki. Zafin da taji yasa ta kwalla kara wanda yasa Mairon Ado k'wasa da gudu ta yi daki ta danna sakata tana haki. 

Gaba daya sukai kaca-kaca da kicin din, ga duk sun watsar da wuta. Maman Dare ta shigo, ganin ana fad'a yasa ta koma waje da gudu ta yi hanyar gidan mai unguwa ko takalmi babu. 

       *GIDAN MAI UNGUWA*

"Malam gaskiya ka kyauta da wa'innan kaji, amma da akuya ka yanka mana kasan dai kaji hudu baza su ishe mu ba."inji Jummai. 

"Uhm wallahi a kiyayi fushi na a gidan nan, domin babu wacce tsohon ta ya taba cewa Tanko ga ciyawa ka ba dabbobi." 
"Kenan Iyayen mu kake zagi Malam?"
"Oho ban sani ba, nidai a kular min da nama ko kafar kaza bance a ciba idan an gama ni zan raba abuna da kai na."

Hannatu dake zaune ta yi tagumi ta doka tsaki. Jin tsakin ya sa mai unguwa juyowa yana fadin "Yar matsiyata kinyi ma mai alewa."
"Matsiyaci shine wanda bai san ya wadata iyalinsa ba."

Aikuwa mai unguwa ya mike ya nufota, ganin haka Jummai ta shiga tsakani tana aikamai da mugun kallo. Sanin idan ya tanka bazai ji dadi ba yasa ya juya yana fadin" Shegu mayu kawai, kuma ni zan dafa kajina da kaina yau billahillazi." ya karasa bakin murhu ya dau mafici yana fifita wuta. 

Babu wacce ta kuma kula shi duk mikewa suka yi suka kama sauran ayyukansu na gida. 

Shi kuwa mai unguwa cire malun-malun dinshi ya yi yana fifita wuta. Nama ba ruwa sai kamu yake amma bai masan yana yi ba. Matan najin yanda naman ke konewa sukai banza dashi. 

Maman Dare ta shigo da gudu wanda hakan y tsorata mai unguwa ya mike zai gudu, ta dakatar dashi ta hanyar fad'owa gabanshi tana haki hade da fadin"Sun kashe sun kashe."
"Ke wa suka kashe?" ya daka mata tsawa. 

"Don Allah mai unguwa kazo sun kashe kansu a gidan mu."

Jin haka ya fahimci mai take nufi don haka yaja tsaki "Babu inda zani su kara nakasa ni alkur'an."
"Don Allah kazo wallahi sunyi barin nama yara nata diba fa."
Jin ta ambaci nama yasa ya saba babbar riga yace" Muje na gani." suka fice bayan y babbaka m tukunyar naman shi wuta. 


*Mezai faru kenan ga mai unguwa ya kuma komawa gidan 'yan haya, bayan yace bazai kara zuwa ba.*



*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
       *'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱

.                      👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 




©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to 
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com


_K'awas Ummu basher nd Anty Maimounath. Ina kuke 'yan'uwa rabin jiki, wannan shafin na kune kyauta domin soyayyar ku daban ce kuna raina kodayaushe. Ina godiya gareku sosai ana tare Allah ya kara basira._


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
     
            *45~50*

Matan shi na dak'i suna ji har ya fita, babu wacce ta kalli tukunyar naman. 

Lado ya yi sallama hannunshi rike da bakar leda. Suka amsa mishi ya zauna bayan ya gaidasu, ya ajiye ledar yana fadin "Gashi nama ne na siyo muku na cika ciki."

Murna sosai suka yi suna fada mishi 'yanda suka yi da mai unguwa kan nama. Dariya ya yi sosai ya mike" Na wuce ba nasan yazo ta sameni gidan nan." Nan ya tafi abun shi. 

"Maman Sani mu dafa mu boye kafin ya dawo." cewar Hannnatu. 
"Basai kin fadi ba yanzu zamu dora mu raba, idan ya dawo ya dau nashi naman."

Suna hira suna aiki ko kallon naman mai unguwa basu yi ba. 


       *CIKIN GIDAN 'YAN HAYA*

Dambe ake na kin karewa, gashi duk sun tattake naman da tumatirin da suka zubar. 

Maman Usman na dak'i tana girki, duk abun da suke tana jinsu ta yi banza dasu, domin tasan halinsu. 

Inno ce tsaye gefen rijiya tana kwashe sauran naman Maman Ladi da ya zube. Jin saukar duka ta yi bayanta wanda ya haddasa zubewar naman hannunta. 

Maman Ladi ce ta kai mata wannan duka bayan ta baro matar Malam cikin kicin ko motsi ta kasa yi. Cikin bala'i Inno tace "Maman Ladi ashe ke matsiyaciya ce ban sani ba, taya ina kwashe miki zakiyi min wannan duka?" 
"Na zata ai cikin namanki zaki zuba yi hakuri."maman Ladi ta fadi tana haki. 

Watsar da naman Inno ta yi tace "To don kaza-kazan mata na fasa kwashe wa."
Kau! Maman Ladi ta kwashe ta da mari, cikin huci take fadin" Ba a haifi matar da zata zageni ba wallahi don ubanta, nice nan Maman Ladi murucin kan dutse an buga an barni."

Nan sabon dambe ya kaure dai-dai shigowar mai unguwa. Aikuwa yana zuwa ya hau rabo yana rokon don Allah su bari, amma ina kamar basu ganshi ba. Gashi sai take nama suke yi, can ya leko kai cikin kicin da niyar ganin mai na ciki keyi. Saukar ruwa yaji a fuskar shi wanda ya haddasa daukewar ganinsa na wani lokaci.

Jin ba ruwan zafi bane ya sanya mai unguwa bude ido tare da goge ruwan fuskar shi da rigarsa. Inna Talatu ce ta watso ruwan da nufin ya sauka kan Ladidi, ganin bai zuba inda ta watsa ba yasa ta kuma daukar tukunyar ta nufi Ladidi ta k'wada mata. Mai unguwa na tsaye yana kallon wannan rikice ya rasa yanda zai yi ganin da gaske fad'a suke ba kakkautawa. 

Matsawa ya yi kusa da dak'in Maman Usman yana sallama. Tana ji ta yi shiru domin ta gaji da rabon fad'a. Jin mai unguwa nata doka sallama yasa ta leko tace "Kayi hakuri mai unguwa, bansan ya zanyi su daina ba ni kaina takaicin fad'an nake wallahi."
"A'a Maman Usmanu baza mu barsu su kashe kansu ba, ki taimaka ki fito don Allah."

Jin magiyar mai unguwa yasa ta amince ta fito. Matar Malam na kwance ta kasa motsi sai taka ta suke yi. Maman Usman ta shigo ta daga ta da taimakon Abule suka fitar da ita suka aje ta kan dandamalin kofarta. 

Maman Usman ta shiga tsakanin Ladidi da Inna Talatu ta rabasu suka fito waje, ta kalli yanda kicin din ya yi kaca-kaca da nama da kuma tumatiri. Girgiza kai ta yi tana takaicin halayyar matan gidan. 


Duk suna tsaye ga mai unguwa dake yi musu fad'a da sunan nasiha. Maman Ladi ta kalle shi cike da takaicin fad'an da yake musu tace "Dalla malam rufe mana baki."
"Walle wanga mai unguwa gulma ta dashi, sai kace shi na da wanga gida." cewar Abule tana aikamai da harara. 

"Billahillazi zanyi karar duk shegiyar data kuma zagina, kaji mahaukata ana yi..."
"Kaine mahaukaci wallahi ba dai mu ba, banza mai bakar fuska." Ladidi ta katse shi. 
"Uban ki ne banza ba Tanko ba matsiyaciya mai zubin munafukai."
"Kai kuma mai zubin 'yan wuta ba." cewar Inna Talatu. 

Takaici ya cika Maman Usman dake tsaye tana kallon duk abun da suke yi. Ganin abun nasu zai yi kamari ga mai unguwa kamar zai yi duka yasa ta daka musu tsawa. Duk sukai shiru suna kallon ta. 
"Sai yaushe za kuyi hankali, ku gane abun da kuke bai dace da ku ba?, yara gare ku fa kuma tarbiyyar ku shi zasu dauka na roke ku don Allah ku yi ma kanku karatun ta natsu, ku gane zaman lafiya yafi komai dadi."
"Kiyi hakuri Maman Usman zamu gyara." cewar Mairon Ado dake tsaye jikin kofarta. 

Sauran shiru suka yi suna hararar mai unguwa jin yana fadin " hankali ne bai ishesu ba shiyasa suke wannan haukan."
"A'a mai unguwa kai babba ne bai kamata kana fadin haka ba" 
"To Maman Usmanu ayi hakuri, amma dubi yanda suka wulakanta nama kamar ba kudi aka sanya aka siya ba, dubi kiga matar Malam zube ko motsi ta kasa."
"Dadin abun mazajen mune suka siya mana, ita kuma matar Malam gulma ya kawo ta." Maman Ladi ta fadi tana jefa mai mugun kallo. 

"To nidai na fada muku kuyi hankali domin watarana duk bama nan." cewar Maman Usman ta shige dak'i. 

Ganin Maman Usman ta wuce yasa mai unguwa shima ficewa yana sababin anci mutuncin nama. 

Sanin cewa sunyi ma juna ta'asa ya sanya babu wacce ta nemi a biyata namanta ku tumatir. Mai saura ta deba ta cigaba da girka wa. 


        *GIDAN MAI UNGUWA*

Matanshi sun gama nasu girkin tsaf sun raba, inda suka bar mishi nashi bisa wuta ko dubawa basu yi ba. Suna zaune suna hira ya shigo da sallama. 

"Barka da dawowa Malam." cewar Hannatu tana dariya kasa-kasa ganin jikin shi duk ruwa. 

Banza ya mata ya wuce tukunyar naman yana duba wa. 
"Jakar uban nan, yanzu dama duk bakin ciki kuke dani ko, arzikin da tsohon ku bai dashi kuke wulakanta wa ko?, kaji tun dazu dana fita babu shegiyar data duba min."

"Haba Malam! Haba Malam! kai fa kace kar mu taba amma yanzu ka zo kana zagin iyayen mu?"
"Na zaga Jummala, nace na zaga akwai 'yar kwal uban da zata rama ne?, shegu masu zubin ifiritai."

Sanin idan suka biye shi makota na iya ji, yasa Jummai ta yi ma Hannatu alamun ta yi shiru. 

"Kuma wallahi Allah ya isa tsinannu kawai, zanga uban da zai baku abinci yau a gidan nan. Kuma wallahi sai na kai karar ku gun ubannin ku, ko wacce sai ubanta ya biyani kazata data kone." ya fadi yana facali da tukunyar ya yi waje. 



         *GIDAN 'YAN HAYA RANAR LARABA*




*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
       *'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱

.                      👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 




©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to 
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com


*'Yan uwana abokan aiki wannan shafin ya zamu naku kyauta wato Zamanawa masu karamci, mutane masu halin dattako, ina gaisuwa the musamman gareku. Allah ya daukaka Zamani ya kara hade kanmu.Ina son ku sosai domin kodayaushe Kuna fadakar da al'umma da dunbin basirar ku, Allah ya kara basira ya kare mu daga sharrin mahassada ameen. One Love ZAMANI WRITERS*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

           *50~55*

*GIDAN 'YAN HAYA RANAR LABARA*

Suna ta aikin su, duk sun shirya da juna a nata raha ana dariya. Inno ta fito zata je unguwa tace "Mutan gida da alheri zan tafi sai na dawo."
"Adawo lafiya dillaliya."duk suka fadi. 

Tana fita Ladidi tace" Tabdijam! Kunga atamfar da Inno ta saka kuwa?"
"Uhm Ladidi aini mamaki ya hanani magana, yaushe Inno ta yi kudin siyan wannan atamfa?" cewar Inna Talatu tana tafa hannu. 

Shewa Mairon Ado tasa suka tafa da k'awarta Abule da suke zaune kullum tare. Tace "Mijinta ya siya mata ai tun wancan watan ta nuna min."
"Kwarankwatsi bari yallabai dawo dole nima ya siyamin."Ladidi ce ke wannan magana. 

" Ayerere ina mijin ki yaga kudin siyan wannan atamfa?"
"Haba Maman Ladi wallahi kinsan dai yafi mijin Inno samun kudi."
"Amma bai fi shi zuciya ba ko?"Mairon Ado ta tambaya. 

A hasale Ladidi ta juyo tana kumfar baki "Ke Mairo idan ina magana ki daina saka min baki kwarankwatsi kona miki shegen duka."
"Da shike an hwadi miki ina barin ki ki taba Mairo kawata ko?" Abule ta fadi tana hararar Ladidi. 

Maman Ladi ta yi dariya tace "A'a fa dama kwana biyu mai unguwa bai shigo ba, da alama yau zai shigo."

Dariya suka sanya dukkansu sanin cewa ko wacce da tanadin dake ranta game da mai unguwa. 
" Inno ta saka atamfa mai tsada, idan kuna da zuciya gobe kuma ku siya."cewar matar Malam dake fitowa daga dak'inta. 
"Fadi ma mai zuciya zuwa biki ba mai abun kai wa ba matar Malam, domin ina da kudin da zan siya sofa waz wallahi."cewar Maman Ladi don tasan da ita matar Malam take. 

Dariya ta kama Inna Talatu ta dinga yi, suna ta kallon ta har ta tsagaita tace "wallahi Maman Ladi kina burgeni super wax ake cewa fa ba sofa waz ba" 
"Yo sai me dan ban iya fadi ba, na dai san nafi wasu kidahuman."

Nan ko wacce ta daure fuska, ita kuma Inna Talatu ta dinga dariya tana tsugunne kusa da injinta. 

"Mairon Ado hala ke baki taba yin boko bane?" 
"Babana ya hanani matar Malam, da yanzu na wuce wulakanci."
"Ke Mairo walle ni kuwa nayi boko har aji biyu walle kafun ankayi mun amre da Haladu."
"Iyye ashe Abule anyi boko har aji biyu?" Inna Talatu na dariya. 

"Talatu zanci ubanki idan baki daina ma mutane dariya ba, matsiyaciya kawai kin tasa mu gaba kina dariya kamar wacce hau ya hau kanta." cewar Maman Ladi. 
"Banda zagin iyayena Maman Ladi bana san wulakanci."
"Na zage ki din, ko za ki rama ne Talatu?"

"Ku dakata haka, abun raha ne ba fad'a ba sababbu."cewar Ladidi. 
"Ina raha anan Ladidi ana zagin iyayen ka?"
"Abar maganar haka don Allah ya wuce babu fad'a."

Haka kuwa ko wacce ta kama aikin ta.


*GIDAN MAI UNGUWA*

Yana zaune kofar gida ya yi tagumi. Abokin shi malam Kallah yazo ya zauna kusa dashi yana fadin "Ranka-ya-dade fatan dai lafiya kayi tagumi haka?" 
"Ina fa lafiya Kallah?"
"Ashsha Allah ya sauwaka, mai ya faru?"
"Wato Kallah idan Allah ya baka mata irin nawa, na tabbata mutuwa zaka yi."
"To babbar magana kenan dai mata ne suka tasa ka gaba Ranka-ya-dade?"
"Kwarai kuwa matan gidana Jummala da Hannatu duk munafukai ne, don yanzu zakai fad'a da wannan idan kaje wurin dayar to billahillazi ita ma fad'a zaku yi."
"toh na gane, kenan sun hade kai?"
"Kamar kashin awaki kuwa."
"wannan ai abune mai sauki, kawai aure zaka kara."

Da sauri mai unguwa ya dubi shi yana zare idanu "Aure fa kace Kallamu?" 
"Kwarai kuwa aure zaka kara, kuma yarinya zaka auro."

Shiru mai unguwa ya yi can kuma yace "To ina zan samu matar auren Kallamu idon gari?" 
"Don wannan ai mai sauki ne, Ladi kawai zaka samu ka aure ta."
"Wacece Ladi kuma?"
"Diyar Maman Ladi ta gidan 'yan haya."

Zabura mai unguwa ya yi yace "Kallamu baka kaunar farin ciki na billahillazi, ban da haka ta ina zaka hadani da wannan matar mai kirar samudawa kace na aure diyarta?, matar da ko mutuncina bata gani?"

Kallah ya dubi mai unguwa yana dariya" Ranka-ya-dade ai uban yarinyar yana iya komai kan kudi"
"Kenan zai bada diyarsa don kudi?"
"Na rantse maka zai bayar, amma ga wata shawara." ya matsa sosai kusa da mai unguwa sukai kus-kus, dariya suka sanya. Mai unguwa na fadin "Haka za a yi Kallah shawara mai kyau, nagode sosai Kallamu idon gari zan same ka gobe."
"To Allah ya kaimu."


Sukai sallama ya wuce, shi kuma mai unguwa ya shiga gida cike da farin ciki. 



*Tabdijam! Wata sabuwa kenan, muje zuwa..*



*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
       *'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱

.                      👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 




©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to 
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com


Dedicated to 
*GSS Dr. Ahmad makarki hayin Banki kawo. Ina mutukar alfahari daku sosai duk inda kuke, Allah ya kara ilmi. One love 2013*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

        *55~60*

Mai unguwa na shiga gida ya nemi wuri kan turmi ya zauna, yana cika yana batsewa shi ga mai gida sai zare ido yake. Ya dubi matan ba wacce ta kalle shi ya yi kwafa yace "Na kusa kawo karshen wulakanci a gidan nan."

Babu wacce ta kalle shi sai aikin su suke ta yi. 

" Jummala zan kara aure kwananan nan billahillazi."

Duk suka kalle shi cike da farin ciki kwance kan fuskar su, Hannatu tace "Kai amma naji dadi wallahi, yaushe ne bikin Malam?"

Harara ya daka mata" Munafuka mai bakin hali kawai, harda murna ko?, to billahillazi ba da wasa nake ba."
"Malam ai murna muke yi zaka kara aure shiyasa muke tambaya." cewar Jummai. 
"Lallai matan nan iyayen ku sun koya muku mugun hali, inace idan za ayi ma mace kishiya haushi take jin, amma ku don tsabar algungumai ne wai murna kuke ko?"
"Malam kenan mai hali bai canzawa."
"Ke Jummala alqur'an ki fita idona, bazan canza halin ba inga uban da zai can zani."
"Allah ya baka hakuri." ta shige dak'i, ganin haka Hannatu ma ta shige dak'i tana hararar shi. 

"Duk zaku gane kuranku billahillazi bari na auro yarinya danya sharkaf ku gani." ya kakkabe rigarsa ya fice daga gidan yana sababi. 



       *CIKIN GIDAN 'YAN HAYA*

Kwana biyu anyi sauki da fad'a, ana zaman lafiya gidan yasha iska. Ko wacce na sana'arta cikin lumana, mazan su na cikin kwanciyar hankali. 

Gashi an fara wahalar ruwa kuma babu na fanfo, da kyar ake samu a rijiya. Da asubar fari suke rige-rigen fitowa dibar ruwa a rijiyar, kowa na kokarin ya ri ga wani diba, idan ka ri ga tashi ka diba sai a dinga hararar ka ana yada habaici. 

Yau duk suna dak'i basu fito ba, sai matar Malam tana zaune tana wanke-wanke hanyar fanfo ita kadai, kawai taga an kawo ruwan fanfo. Da sauri ta karasa ta kashe fanfo tana waige kar wani ya ganta, ta ruga dak'i ta kwaso robobinta masu yawa ta nufi fanfo. Ta dinga tarawa tana cikawa. Jin karar zuban ruwa yasa Maman Dare lekowa, aikuwa tana ganin ruwan fanfo ne ta koma dak'i da sauri ita ma ta debo kayanta harda tukwane ta nufi fanfo, daga ita sai matar Malam ke jidar ruwa suna kai wa dak'i. 

Abule ta fito zata bandaki ita ma taga wannan al'amari, amma maimakon ta yi yanda sauran suka yi na yin shiru, it kurma guda ta yi tana sanar da mutan gidan an kawo ruwan fanfo. Da sauri suka dinga fitowa da manyan robobi suna rige-rigen bin layi. Haushi ya kama Maman Dare ganin gayyar da Abule ta yi musu tace "Shegiya mai hankali a hannun riga." matar Malam ta fashe da dariya "Banza ce ai bata da nutsuwa."

Ba wacce ta kula su, kowa so yake ya samu ruwa. Maman Ladi ta ga alamun za a raina mata hankali ganin harda tukunya ake diban ruwa, gashi bata da ruwan ko kadan dan haka tace "Yakama ta kusan me kuke yi, kubari muma mu diba gaskiya."
"Maman Ladi a dai bi layi sannu a hankali zamu samu." cewar Inno. 
"A'a Inno duba fa ki gani harda tukwane dan bakin ciki ake dibar ruwa."
"An saka ayi yanda za ayi damu." cewar matar Malam. 

Shiru Maman Ladi da Inno suka yi basu kara magana ba, ganin Iya beji na hararar matar Malam. Can dai da suka ga zasu iya rasa ruwan, Iya beji ta kutsa ta warce tukunyar hannun Maman Dare ta yi jifa dashi ta aza nata robar. Maman Dare ta kalle ta ta kalli tukunyarta dake yashe a kasa tace " iya beji nawane fa bana matar Malam ba kika yadda."



*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
       *'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱

.                      👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 




©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to 
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com


*Wannan shafin na kune hazikan masana, jagororin adabi, _MARUBUTA GROUP_ gaskiya bani da group a whatsapp dake ilmantar da al'umma da kuma koyar da zallar adabi irin ku, ina alfahari daku a kodayaushe fatan alheri ga ilahirin al'ummar wannan gida, Allah ya kara daukaka ya bar zumunci mun gode.*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

        *60~65*

Harara Iya beji ta zabga nata, "Ai nasan na kine shiyasa na yarda shi." 

"Lallai ma Iya beji, mun ri ga ki zuwa layi ai." cewar Inno. 
"Baku damu ku samu ruwa ba, ai wuri kuka samu ku ka tsaya."
"Dalla can matsa min." Maman Ladi ta bige robar hannun Iya beji ruwan y zube, ta sanya nata robar. 

Haushi ya kama Iya beji ita ma ta kifar da ruwan Maman Ladi. Nan fa fad'a ya kaure tsakanin su, Abule ganin yawanci hankalin su na wurin rabon fad'a yasa ta dinga jidar ruwan tana kaiwa dak'i. Maman Dare ta yi dariya ita ma rabi sahun Abule, lura da hakan da Inna Talatu ta yi ne yasa ita ma ta tara robarta bakin fanfo, aikuwa Matar Malam ta kifar da shi tana fadin"Algungumai kun wani zo kuna jidar ruwa kamar.." Mari aka sauke mata wanda ya tilasta mata yin shiru. Inna Talatu ce rike da robarta tsaye tana hararar matar Malam, "Kece dai algunguma bani ba, banza kawai mai halin matsiyata."
"Talatu ni kika mara?" 
"Kina da abun yi ne?"

Haba sai fada kuma ya tsarke, suna yi suna jifar juna da robobin ruwa. Maman Ladi ta yarda Iya beji kasa gashi wurin duk ruwa ne, aikuwa ta bugu sosai ta kasa tashi. Maman Dare nasan shiga kuma tana tsoro don haka ta je taimakon daga Iya beji wanda ya yi dai-dai da Matar Malam ta jeho bokitin karfe ya sauka kuwa kan Maman Dare ta zube kasa jikin Iya beji. Kuka Iya beji tasa tana tsine masu Maman Ladi, da kyar Maman Dare to mike tana dafe da kanta ta taimaka ma Iya beji ta mike. 


Hayaniya da fad'a sosai suke yi a bakin fanfo. Shigowar Malam Lawal mijin Maman Ladi ne ya sanya Maman Ladi barin wurin da sauri ganin shi da manyan ledoji a hannu, ta amsa tana mai sannu da zuwa. Washe baki ya yi yace " ke kam kin iya haihuwa wallahi, wannan arzikin duk dalilin haihuwa ne."ya fadi tare da shigewa dak'i. 


Gudar da Maman Ladi tasa ce ta dakatar da fad'an da matan gidan ke yi, suka juyo suna kallonta. Yara suka dinga shigowa da kayan abinci suna zubewa kofar Maman Ladi. 

Ladidi ta karaso tana fadin " Maman Ladi wannan kayan fa?" 
"Ahayye duniya Ladidi gulma, to bari naje dak'i na tambayi wanda ya kawo sai nazo na baki satonri (story)" ta shiga dak'i ta same shi. 

"Baban Ladi ina ka samu kaya haka?"
"Kedai bari uwargida kayan toshen Ladi ne, wani attajiri ya ganta shine dazu y kirani ya ban wa'innan kayan."ya fadi yana kirgo kudi a aljihun 'yan dari biyu. Maman Ladi t warce kudin tana cewa"Wannan rabo na ne kenan ko?, nasan dai an baka naka."
"Kayya Maman Ladi kina da gajen hakuri baki zanyi dama wallahi, yanzu yaushe zamu sanya bikin?"
"Sati biyu kawai za a saka saboda mahassada malam."cewar Maman Ladi. 
Gyada kai ya yi yana gyara aljihun shi wanda ke damke da kudi. 

Galala matan gidan ke bin kayan da kallo kamar makafi sun warke makanta, nan suka fara kus-kus aka manta da batun fad'an ruwa. Fitowar Maman Ladi daga dak'i tana washe jajayen hakoranta yasa suka marmatso kusa da ita domin jin kanun labarai. 

"Ladi ce zata auri wani attajiri shine aka kawo wa'innan kayan, ku duba harda su buhun shinkafar waina wallahi na samu karin jari."

"Yanzu Ladi nawa take da zaki aurar da ita?"
"A'a Talatu kardai kina bakin ciki kan wannan abun arzikin dana samu ne?"
"To wani mai arziki kenan zata aura?" matar Malam ta yi tambayar. 
"Sai ranar auren zaku sani, nan da kwana goma sha hudi zaa yi bikin."

Nan aka dinga cafta ana duba kayan arziki, Inno da Inna Talatu muraran suke nuna bakin ciki kan kayan, yayin da Maman Dare wacce har gefen goshinta ya kumbura sanadin wannan bokiti ke nuna ma Maman Ladi illar auran. Iya beji dama data samu ta tashi dak'i ta wuce da alwashin sai ta rama. 

Maman Ladi kuwa sai rawar kai take tana nuna isa da takama diyarta zata aure mai arziki. 

       *MAI UNGUWA*

Matan mai unguwa sai murna suke ganin ana gyara dak'in amarya, suna fatan zasu huta da wannan masifar tashi. Sun tambayeshi wacece amaryar yaki fadi musu wai kada suje suyi mai munafuncin da suka saba, shiyasa suka saka mai idanu suna kallon duk abun da yake yi. 

Mai unguwa zaune a cikin zaure tare da Baban Ladi. 

"Kai Lawal nawa ne sadakin?, sannan ka tabbata wannan shegiyar matar taka bata san ni zan auri diyarta ba." cewar mai unguwa. 
"Ka bada jaka goma Ranka-ya-dade, kuma na rantse maka bata sani ba ce mata nayi wani attajiri ne."

Haka ya kirga ya mika yana washe baki ya kusa zama ango.


 Shikuma Malam Lawal gida y nufa ya damka ma Maman Ladi kudin sadakin, ita kuma ta mika ma Inno dillaliya data kawo mata kayan gado da dorowa. Ana ta shirye-shiryen aure sai gyara amarya Maman Ladi take, yayin da matan gidan wasu ke bakin ciki wasu kuma suna taya ta murna. 

Sosai Maman Ladi ta shirya ma wannan aure ganin kudin sadaki jaka goma wanda a tarihin unguwar ba wanda aka taba ba irin wannan kudin matsayin sadaki. Hidima sosai matan gidan ke ta yata kama daga kan alkaki, dubulan, nakiya, da sauransu. 
     *RANAR AURE*

Ranar gidan 'yan haya ya cika sosai, domin gayyata Maman Ladi ta yi na auren tilon diyarta. A nata hidimar girki, amarya ansha atamfar batik cikin kayan auren da mai unguwa ya aiko. 

Karfe biyu aka daura auren Zainab wato Ladi da ango Nasiru Tanko mai unguwa. 

Maman Ladi anci kwalliya ana tsakiyar jama'a wannan sakon the isketa, a hargitse take tambayar "wani mai unguwa aka ba auren Ladi?" 
"Wanne kuwa bayan mai unguwa Tanko."cewar Inna Talatu dake tsaye bakin kofa. 

Ai a tamanin Maman Ladi ta fito tana kwallo da duk abun da tagani a hanya, tamkar zararra tana kwalla kiran sunan Baban Ladi. Mutane da aka gayyata suka dinga kallonta domin basu san komai ba, matan gidan kuwa sai yamadidi suke da ita suna dariya. 

Shigowar su kenan daga wurin daurin mazan gidan, Baban Ladi na gaba suna biye dashi a baya. 
Yana sako kai yaji an shake shi sosai ba da wasa ba, kokari yake ya ya kece daga rikon amma ya kasa. Maman Ladi data yi shakar ta wanke shi da mari tana fadin " munafuki macuci kace min wani attajiri zai auri Ladi, ashe wancan shegen ne to wallahi sai an warware auren nan muddin kana bidar zaman lafiya dani."

Juya kai kawai yake yana kokarin kwace wa daga rikonta, mazan nata aikin bada hakuri inda matan dake wurin suka maidata tamkar talabijin suna ganin ikon Allah. 

Da kyar ta sake shi, aikuwa yana jin yasha ya sa kafa sai hanyar waje yana fadin "Na rantse da Allah aure ya auru naga uban da zai kwance shi mahaukaciya kawai."
" Zaka dawo ai wallahi zaka san da Hajara uwar Ladi ka yi a gidan nan". 



*INA LABARIN ANGO MAI UNGUWA TANKO??*





*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
       *'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱

.                      👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 




©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to 
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com


No matter the Distance between
 Us.. I am as Close To U today
 As I was Yesterday.. For as
 Long As U are In my Heart..
 We are Never Truely Far Apart.! I love you fan's of 'YAN GIDAN HAYA. One love to you.


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
 
             *65~70*

*GIDAN MAI UNGUWA*

Suna zaune suna hira da yaran su da makota da suka zo biki. Lado ya shigo yana sharce zufa ranshi a hade yace "Mama zo kiji wai diyar gidan haya baba ya aura."

Salati Hannatu ta sanya tana dafe kirji" Diyar gidan haya fa kace Lado?"
"Wallahi ita ce ya aura wannan yarinya karama da ita, wacce wallahi ko ni ta yimin kankanta da aure wai ita baba ya aura."

Zugum suka yi suna jimamin wannan masifa da mai unguwa ya kwaso musu. Sai gashi ya shigo yana saba babbar riga, yasha fararen kaya yana ta bude hakora. Makota sukai mishi fatan alheri suka fita. Ya kalle su yanda duk sukai shiru kamar masu zaman makoki yace "Lafiya kuwa kuke zaune da tagumi kamar ance iyayen ku sun mutu?" 

Cikin takaici Hannatu tace " cewa akayi mai unguwa Tanko ya mutu shine muke jimami."
"Ubankine ya mutu billahillazi bani ba, munafukai kawai duk kishi ne na sani."

Jummai ta kalli yanda yaran ke zaune rai a hade tace" Ko wacce ta wuce gidanta, kuma ku tafi wurin sana'ar ku an gama taro."

"Allah sarki Jummala ayi hakuri dai aure ne nariga nayi ko da taro ko babu taro sai amarya tazo." ya fice daga gidan. 


Haka kuwa yaran jiki a sabule suka yi musu sallama duk suka fita. Suka bar iyayen cikin jimamin wacce mai unguwa ya debo musu matsayin kishiya. 

Yana fita ya hadu da da baban Ladi yana haki kamar dan tsere. 

"Kai Lawal meye haka kake ta haki, lafiya dai ko?"
"Ina lafiya Ranka-ya-dade Maman Ladi ta gane kai ne mijin, tace wallahi ba zata bada amarya ba."

Shekeke mai unguwa ya bishi da kallo "Yo ita shegiyar matar taka an gaya mata tana da ikon kan matar dana biya sadaki ne?, to billahillazi ka koma ka fada mata anjima a bani amaryata ko wallahi taga kalar nawa haukan, banzaye bayan na biya kudi na sai ace za'ayi min iko."
"Ranka-ya-dade wallahi shakeni ta yi bazan iya komawa ba."
"Aikuwa zata san waye Tanko billahillazi a garin nan." ya shige gida a fusace. 


        *CIKIN GIDAN HAYA*

Maman Ladi da 'yan korenta zaune kofar dak'inta, suna kara zugata kan kada t yarda akai diyarta gidan mai unguwa. 
"Nifa da hankali na wallahi bazan ba Tanko Ladi ba, kuma yazo ya gani."
"Wallahi Maman Ladi gidan shi babu abinci, babu suturar arziki."cewar Ladidi. 
"Nifa nasan waye Tanko, domin munyi artabu da shi watarana ana fad'a gidan mu yazo rabo y dinga tsine mana" cewar wata kawar Maman Ladi mai suna Atuwa. 

"Ayererre a dade anayi, aure dai the auro dole a ba Tanko matarsa."
"Ke Talatu wallahi ko Ubankine bazan bayar ba, kuma ki daina shiga sabgata Maman Ladi nake."
"Aifa yau ko uwata zaki zaga bazan damu ba ai dama duk wanda y shiga motar kwadayi yasan inda zata kaishi."

Cikin fusata Maman Ladi ta nufo Inna Talatu ta hauta da duka, sai dambe. Kaya-kaya ana kokarin rabawa sunki rabuwa domin a zuciye Maman Ladi take sai jibgar Inna Talatu take yi, ganin haka yasa Inno shigarwa Inna Talatu dama tare suke adawa da wannan aure. Aikuwa hadasu Maman Ladi ta yi t dinga jibga tana gwara kawunansu.

Ladidi dake tsaye gefe ta kalli Mairon Ado tace"Ke Mairo zo ki tayani dibar abinci idan kina so." 

Abule dake zaune tana kallon fad'a ta dubi su Mairo "Walle Mairo ta karkije wanga cin amana ta zata yi."
"Wani shegen yace miki cin amana zanyi?" 
"Ke na shegiya." cewar Abule. 


Mari Ladidi ta kawo ma Abule, Mairon Ado ta tare tana hararar Ladidi"Kika tabata sai na sabautaki wallahi matsiyaciya kawai mai..." bugun bakinta da Ladidi ta yi yasa ta yi shiru ba tare data shirya ba. 

Abule na ganin haka ta hau Ladidi da duka baji ba gani. Suma suka hau fad'an su uku, gefe kuma gasu Maman Ladi. Gudar masu daukar amarya ne y dakatar da wannan rikice, aka shiga kallon-kallo. 

"Munzo daukar amaryar mai unguwa."Cewar Maimounath makociyar mai unguwa da ya roka suzo dauko amarya tunda yan'uwan shi sunki zuwa. Ita kuma Maimounath dama da biyu tazo saboda basa ga maciji da 'yan gidan haya. 


Shewa Inno data gama dokuwa gurin Maman Ladi tasa tana fadin"Gaya musu su fito muku da amarya ku cika umarnin mai unguwa." 
"Aikuwa dai yar'uwa abamu amarya a mutunce mu kaita dak'in ango a mutum.." wani duka taji ya sauka a kanta wanda yasa ganinta ya dauke na 'yan sakanni. 


"Bari naji' yar iskar data kara cewa na bada diyata akai gidan mai unguwa." cewar Maman Ladi dake tsaye rike da muciya. 

Nan fa 'yan koren Maman Ladi ko wacce t dauko abun duka.'Yan daukar amarya na ganin haka ga Maimounath durkushe a kasa, ai sai suka sanya gudu suka barta. Ladidi ta kalle ta ta tuntsire da dariya tana fadin "Su yan daukar amarya ansha wahala, ina bakin fadin amarya yake?" 

Cikin karfin hali Maimounath ta mike ta shake wuyan Ladidi ta fara jibga, ganin haka Maman Ladi da sauran suka rufeta da duka, sukai mata lilis suka barta kwance. 

        *WURIN MAI UNGUWA*


Sauran da suka koma suka fadi ma mai unguwa abun dake faruwa, aikuwa ya mike ya saba riga shida abokin shi Kallah da baban Ladi suka nufi gidan.


Yana fadin " Wallahi yau Lawal matar ka zata san Tanko take raina wa."
" Ayi hakuri don Allah Ranka-ya-dade."

Matan naji Hannatu t dinga dariya "Maman Sani yau zaki ga angon da daukar amarya, Allah yasa Maman Ladi ta mai dukan tsiya."
" Uhm Uhm Hannatu mijin kine fa."
"Maman Sani ayi sha'ani kawai wallahi."


Nan suka dinga tattaunawa suna kara jajantawa kansu aikin da ya dauko musu. 


     *CIKIN GIDAN 'YAN HAYA KUWA*


_MEZAI FARU DA ZUWAN MAI UNGUWA_



*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
       *'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱

.                      👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 




©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to 
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com

*WANNAN SHAFIN NA MUSAMMAN NE GAREKU DOMIN KU DIN NA MUSAMMAN NE, KODAYAUSHE INA YI MUKU FATAN ALHERI*
_BRO HUSSAIN ATK_
-BRO HASSAN ATK_
_AUNTY HASSANA ATK_


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

              *70~75*

Maimounath kwance ko motsi bata yi saboda ta daku, su mai unguwa suka doka sallama suka shigo. Ganin ta kwance yasa sauran matan suka nufeta da sauri suna tambayar lafiya. Inna Talatu dake tsaye kofar dak'inta ta bude baki da karfi tace"Su Maman Ladi ne suka jibgeta wallahi."

Mai unguwa ya kalle su fuskannan a daure yace " ku dauketa ko kaita kemis ina zuwa."
Suka dauketa su uku suka fice. 

Ya kalli Maman Ladi dake tsaye bakin kofarta, inda ta rufe Ladi dake aikin kuka ita batasan mai unguwa. Yace" Nazo daukar matata da kai na."
"Sai dai idan uwar matar ka zaka dauka."ta bashi amsa. 

Ya kalli Baban Ladi, ai kuwa da sauri ya matso jiki na kakkarwa yace"Haba Maman Ladi don Allah ki bari a tafi da ita wallahi yanzu bamu da iko da ita."
"Algungumi ba inda zata indai nina haifeta, kuma wallahi naga uban da zai dauketa."


"Nine kuwa uban da zai dauketa billahillazi."cewar mai unguwa. 
"To kana iya zuwa ka dauketa ai matsiyaci."
"Kece dai matsiyaciya shegiya me bakin hali."

Da sauri Kallah yace" Ranka-ya-dade surukar kace fa yanzu a tauna kalamai."
Wani kallo ya buga ma Kallah wanda yasa Kallah tsugunnawa yana fadin "Tuba nake Yallabai."

"Wallahi yau zaa bani matata ko kuma na yi bala'i billahillazi,kuma wannan mai kama da buhun fulawar ta yi kadan na kira ta da suruka."
"Kana iya zuwa ka dauketa ai idan kai ka haifa min yarinyar, mai kama da sauro."

Karasawa kofar dak'in ya yi yana kokarin shiga, aikuwa Maman Ladi da mutanen ta suka rufe shi da duka ga makota nata shigowa kallo. Dukan shi suke suna karawa shikuma kokarin ceton kansa ya ke don kuwa baisan tsiyar da suka shirya mai ba kenan. 

Kallah da Baban Ladi nata rokon su dai na amma sunki don haka Kallah ya ranta ana kare yana fadin"Naji bayanin yanda aka kare idan mun hadu, domin wa'innan matan babu alamun tausayi tare dasu."

Makota na leke suna bada hakuri wasu kuma suna kara zuga wa. 


Jiniyar motan 'yan sanda suka jiyo, aikuwa suka sake mai unguwa da sauri suka shige dakunan su.'Yan sanda suka shigo su biyar uku mata biyu maza cikin gidan. Mai unguwa na ganin su ya sanya ya mike da kyar yana goge jinin bakin shi yace"Kuci uban su sosai ku tafi dasu setation don Allah, billahillazi bazan yafe musu ba kuma a fito min da matata."
"Kayi hakuri mai unguwa zamu dauki mataki insha Allah."

Nan aka sanya 'yan sanda matan suka shiga dakunan duk aka tarkato su waje. 

Maman Usman ce kadai bata nan, domin ta yi tafiya bata gari duk wannan bidirin da ake yi. Gaba daya matan gidan aka tasa su gaba zuwa ofishi, mai unguwa yace a taho masa da mata, aka kuwa fito da ita sai kuka take.
Aka tasa keyarsu hada 'yan biki sai setation. 


*Ofishin' yan sanda*

Suna zaune Dpo ya shigo, ganin mai unguwa manne da bandeji a Hannunsa da gefen kunne yasa ya karaso da sauri. 
"Mai unguwa maiya same ka haka ne, ba dai hatsari kayi ba?"
"Bari Ddo waccan tsinanniyar matar ce ta jimin ciwo wallahi."

Sai lokacin Dpo Muhammad Abubakar ya lura da matan dake tsaye gefe guda. Da mamaki ya kira sajan yana tambayar meyafaru, nan suka fada mishi tun daga kiran da akayi musu da kuma yanda suka tadda mai unguwa ga Maimounath ma sun daketa. 

"Dankari! Kenan menene matsalar?"
"Ranka-ya-dade sai dai a kira mai unguwa ya yi bayani."
"Kirashi su."
"Yes sir." ya fita ya kira mai unguwa suka shigo tare. 

Nan ya zaiyane komai da ya sani dangane da fad'an da kuma dukan da suka yi mishi da Maimounath. Nan Dpo ya fito ya tara su wuri daya ya fara tambayar ba'asi. Wasu su fadi gaskiya wasu akasin haka, dukka ya tattara ya hada ya yi tagumi yana kallon su. Duk sukai shiru suna kallon shi yace "Aba mai unguwa matarsa su tafi."

Kuka Maman Ladi ta sa tana fadin" Wallahi bazan yarda diyata taje gidan shi ba, domin da farko ai basu fadamin gaskiya duk munafukai ne."

Tsawa ya daka mata ta yi shiru tana kallon shi. Ya yi musu dogon sharhi kan boye mata da suka yi sannan ya yi umarnin Maman Ladi da sauran duk zasu bada dari biyar-biyar na dukan mai unguwa da Maimounath kudin magani. Haka suka bayar suna Allah ya isa a zuci. Haka ya dinga musu nasiha yana ankarar dasu illar abun da suke yi, daga bisani ya sallame su suka fito. Maman Ladi na kuka Ladi nayi suka rabo ta hau mashin din mai unguwa suka tafi. Su kuma matan gidan da 'yan biki ko wacce ta yi hanyar gidan ta.

Maman Ladi na koma wa ta dinga rabawa 'yan gidan duk kayan bikin data hada tana cewa "Wallahi dana kai gidan mai unguwa gara na zubar dashi."  Ta kira almajirai ta dinga rabo. 


       *GIDAN MAI UNGUWA*

Yana tsayar da mashin ta sauka ta tirje taki shiga, juyin duniya Ladi taki shiga gidan. Mai unguwa ya fusata ya dinga zaginta. Hayaniyarshi ta sanya matan lekowa jin yana surfa zagi, aikuwa ganin Ladi tsaye kikam kamar gunki yasa Jummai dauko mayafi ta fito,tana zuwa ta riko hannun Ladi, aikuwa bata yi gardama ba ta bita suka shiga gidan. 

Takaicin hakan yasa mai unguwa gunduma musu ashar yana cewa"Ban aurota don ku zauna da ita ba, billahillazi kar wacce ta koya mata bakin hali." basu kula shi ba suka shige dak'in Jummai dukkansu. 

Zaunar da Ladi ta yi tana rarrashi Hannatu ta debo mata abinci suka saka ta gaba suna ta bata hakuri. Da kyar ta yi shiru yana ajiyar zuciya taci abincin tasha ruwa ta haye gadon Jummai ta kwanta. Kallon juna suka yi Hannatu tace "To yanzu ya zaki yi taje dak'inta?, kuma fa dak'in ba komai basu kawo kaya ba."
"Barni dashi Hannatu zai gane kuranshi ya sake ya shigo da sunan tafiya da yarinyar nan dak'inta."

Duk suka zauna suna dakon zuwan mai unguwa, kamar ya sani kuwa yaki zuwa ya shige dak'i ya kwanta yana jinyar jikin shi. 


      *WASHEGARI GIDAN HAYA*

Maman Ladi ta tashi zuciya tunkushe da bakin ciki, ta kira Inno tace "Inno ki kwashe kayan gadon nan ki siyar dasu ki ban kudina ko nawane gara nayi asara dana kai ma mai unguwa."
"Haba Maman Ladi kiyi domin diyar ki mana, kinsan dai mai unguwa bazai kula da ita yanda ya dace ba, kiyi hakuri ki kai mata." 

Shiru Maman Ladi ta yi tana tunani, can tace "Shikenan ku shirya kukai kayan to." ta shige dak'i. Gyada kai Inno ta yi domin ta tausaya wa Ladi da auren mai unguwa dama dan basu san waye angon ba yasa suke bakin ciki. 


Haka kuwa rana na yi aka kwashe kaya sai gidan mai unguwa. 


      *LADI GIDAN MAI UNGUWA*

Da safe suka tashi suka fara ayyukansu, Ladi nata baccin gajiya har suka gama hadin karin safe. Hannatu t taso ta, aikuwa t sanya kuka ita gida zata je, da kyar suka samu ta yi shiru t zauna suka kar ya. Mai unguwa na jinsu yana kwance dak'i duk jikin shi ciwo yake domin yaci duka ba kadan ba. 

Suka zauna suna da janta da hira har ta sake dasu. Mai kura ya yi sallama suka shigo tare dasu Inno da Ladidi, Abule, Maman Dare, Maman Akintola, Inna Talatu, matar Malam da sauran matan gidan d makota. 

Nan su Jummai suka yi musu tarba ta mutunci, mai kura ya jide musu kayan suka hau shiryawa. Ladi t dinga yi musu kuka tana cewa su tafi da ita. Hakuri suka dinga bata Maman Akintola tace " Ladi kana da iyaye fa a gida na me anguwa kayi hakuri kawai ka zona kaji ko." ta gyada mata kai tana kuka har suka gama jere suka tafi. Mai unguwa na dak'i yaki fitowa yana kunyar ya yi ido biyu dasu saboda dukan da ya sha jiya, sai da suka tafi sannan y fito yana hura hanci.
Yace"Jummala ruwan wanka"
"Babu." ta fadi a takaice. 
"Allah ya hana ki muguwa kawai." ya fice yana hararar Ladi. 

Nan Jummai ta dinga rarrashe tana nuna mata ta yi biyayya zata ji dadin zama tare dasu, ta gyada mata kai tana kuka suka shigar da ita dak'inta. 


     *'YAN GIDAN HAYA*

Suka koma suna bata labarin matan mai unguwa sun rike Ladi kamar yarsu, wannan yasa Maman Ladi ta saki ranta domin tasan matan nada mutunci ba kamar shi ba. Hankalinta ya dan kwanta ta rage fargabar diyarta zata cutu gidan mai unguwa. Mijin kuwa tun ranar bai dawo ba sai yau, ko kallon shi bata yi ba. 



*Ya ya zaman Ladi zai kasance da mai unguwa kenan??*


*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
       *'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱

.                      👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. 




©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to 
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com

_ALHAMDULILLAH SADAUKARWA GA DAUKACIN AHALIN ALHAJI ABUBAKAR SA'EED ARDO BORO, UBANGIJI YA TSARE MU YA KARE MU GA SHARRIN MAKIYA, ALLAH YA SHIRYA MANA ZURI'A DAYYIBA AMEEN._

🌹 *BAMU DACE DA JUNA BA*🌹

_UMMU BASHER_

       *Allah sarki wasu iyayen basu san cewa kwanciyar hankali yafi kudi ba, shiyasa suke ganin 'ya'yansu sunfi karfin talaka. Amma ga Ummu basher ta fada mana cewa zaman lafiya, kwanciyar hankali, soyayya da sauransu duk ana samu koda babu kudi, zaa dace da juna. ina taya ki murna na kammala wannan littafi k'awas, Allah ya kara basira da zakin hannu hade da kwarin idanu. Ina yinki sosai dinnan. Muna biye a DANA SANI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_Ma cherie ta mai unguwa Tanko ina kika kai mana SAADAT angon BUSHRA, kina kamshi muna miki feshin humra tawan more grease._


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

          *80~End*


Sosai gidan 'yan haya fad'a ya yi sauki, ko wacce na kokarin kare martabar sana'arta tun bayan dawowar Maman Usman taji duk abun da ya faru, nan ta nuna musu cewa muddin suna da sana'ar yi to ba zasu kasance suna ganin bakin juna ba. Hakan yasa suka dage kowa ya kama sana'a suna kuma kokarin ganin an zauna lafiya. Bata taba kai ma diyarta ziyara ba, sai dai tana samun labarinta wurin kawayenta. 


        *GIDAN MAI UNGUWA*

Sosai suka rike amanar Ladi, kasancewar yarinyar tana yi musu biyayya ta shammace su basu yi tsammanin zata yi hakuri ba duba da halayya ta gidan data fito. Suna kare ta sosai don ganin mai unguwa baici zarafinta ba, sun yarda duk abun da zai ma ta ya yi musu gudun magana cikin gari. 


Sun hada kai suna ganinta kamar yaran su mata dake gidan aure.mai unguwa ya yi jarabar ya yi masifar hadin kansu yaga basu da niyar canzawa, gashi duk abun da suka ce shi Ladi keyi don haka yasa musu ido kawai yana kallon su. 


Lokaci yaja kwanaki sun shude haka satittika haka watanni yau Ladi watan ta biyar gidan mai unguwa ba tare da taje gida ba. don haka yau take ta zumudin zuwa gidan su. Ta gama shiryawa ta fito da mayafinta a hannu tace"Maman Sani zan tafi."
"Lallai Ladi da safiyar nan zaki tafi?"

Rau-rau ta yi da ido kamar zata yi kuka tace"Maman Sani ina son ganin Mamana fa." 

Dariya suka yi suna tsokanar ta ganin zata yi kuka. Da sauri mai unguwa ya fito yana gyara mashin dinshi yace " ke zo mu tafi ki bar wa'innan matan."
"To a dawo lafiya Ladi a gaida gida."
"Insha Allah za suji." ta fita suka tafi. 


       *GIDAN 'YAN HAYA*


Maman Usman na zaune cikin su suna hira, sai nishadi suke kamar basu ba. Maman Akintola tace " wallahi gida namu ya yi dadi fa kowa ya yi shiru ya yi hakuri kome ya wuce."

Suka sa dariya dukkan su, sai jin sallamar Ladi suka yi. Da gudu ta shigo ta rungume uwar sai kuma tasa kuka. Maman Ladi murna Sosai ta yi na ganin Ladi tace" To rigimatu kukan na menene?"
"Mama baki taba zuwa gidana ba."

Duk matan gidan sukai dariya, Maman Usman tace " Ladi sai kuma aga Maman ki gidan ki ba kunya ko?, kamar ba diyar fari ba."
"Kai mama kema sau daya kika je ai."
"To zan dinga zuwa kullum." ta fadi tana dariya. 


Ladi ta rufe ido da hannayenta tace "Yana waje fa tare muke dashi."

Rankwashi matar Malam ta sakar mata akai" Ja'ira shine tun dazu baki fadi ba kika zauna shagwaba?"

Da sauri Maman Usman ta dauko tabarma ta shimfida tace "Maza jeki shigo dashi."

Tare suka dawo sai sunkuyar da kai yake yi alamun kunya, domin ya tuna abubuwa da yawa da ya faru cikin wannan gida, gashi kuma yau ya shigo matsayin sirikin su. Ya nemi wuri ya zauna, Ladidi ta kawo mai ruwa, matar Malam ta kawo mai fura. Suka zauna suna gaisawa a kunya ce.


Bayan sun gama gaisawa suka zauna. 


Maman Usman tace "Alhamdulillah nayi farin ciki ganin wannan rana, domin ada can ba muyi tsammanin abu makamancin wannan ba, mai unguwa matsayin suriki cikin gidan haya. Lallai abun mamaki ne sosai da hakan ya faru amma sai gashi sanadin haka zaman lafiya da fahimtar juna ya dore tsakanin mu, ina fatan zamu kasance masu hakuri mu jure neman na kanmu mu guje ma rigima da tashin-tashina."


"Kwarai hakane Maman Usman domin kin dade kina nusar damu illar fad'a cikin gidan nan, amma bamu dai na ba sai gashi tun bayan auren Ladi da mai unguwa zaman lafiya yazo ya daure sosai, Allah yasa mu kasance koyaushe haka." cewar Inna Talatu. 

Maman Ladi ta yi ajiyar zuciya tace "Gaskiya munyi zaman rashin hakuri da junan mu, mun kasance masu biye ma zuciya da rashin sanin meke mana ciwo muna fad'a da junan mu alhali Allah ya ri ga ya kaddara zaman mu tare, musamman ni na kasance mai daukar duk abun da diyata ta fadamin game da mutanen gidan nan koda bana nan, sai dai abun farin ciki shine bata dauki wannan hali taje gidan miji dashi ba, ina kira ga iyaye dasu dinga kwabar ya'yansu kan maganganu, su daina yarda da maganar yara koda suna tunanin gaskiya ce. ina fatan zamu yi hakuri mu kasance masu yafiya mu zauna lafiya."



"Gaskiya ne Maman Ladi mun kasance masu kyashi da hassada, mun dauki mugun hali na fad'a da juna mun yafa, mun tsane junan mu kan bambamcin ra'ayi, ina fatan zamu cire kyashi a ranmu mu rungume zaman lafiya." cewar Ladidi. 

Maman Dare ta yi dariya tace "To a madadin yan'uwana da basa jin hausa sosai, muna mika namu hakurin gare ku da fatan zamu cigaba da kasance wa cikin farin ciki da zama lafiya gaba dayan mu duk kuwa da bambanci yare da addini da muke dashi."

" Tabbas auratayya na daya daga cikin abun da ke haddasa zaman lafiya, domin sanadin auratayya ne zaman lafiya da farin ciki suka wanzu cikin gidan nan, ina fatan kowa zai maida hankali wurin bada aure tsakanin al'umma domin hakan na bada gudunmawar zaman lafiya." cewar Inna Talatu.

Mai unguwa ya kalle su yace " Lallai haka ne maganar ku gaskiya ce, domin dukkan mu masu laifi ne, mun kasance mutane marasa hakuri a rayuwa, komai muna sanya ido kanshi, mun kasance mutane masu addini da ban da kuma harshe wanda mu kammu muka kasa hade kai mu zauna lafiya, amma ina fatan yanzu zamu yi hakuri mu duba akasin da muka fuskanta a baya mu hadu mu gyara da kanmu. Mu gudu tare mu tsira tare domin zaman lafiya yafi zama dan sarki."


Kowa ya yi na'am da zancen su aka hadu aka nemi yafiyar juna aka yi addua aka tashi. Mai unguwa ya yi musu sallama ya dau matarsa suka wuce gida cikin farin ciki da annashuwa. 


       *GIDAN MAI UNGUWA*

Bayan sun dawo aka zauna hira bayan magriba. Mai unguwa yace " Ina fatan zaku yi hakuri da halina muci gaba da zaman lafiya daku, kuyi hakuri ku yafe min duk abun da nayi muku."

Cikin farin ciki suka dinga murna suna jin dadin canjin da aka samu daga mai gidan nasu. 

Rayuwa kenan yau mai unguwa ne ya bada ijiyar mabudin rumbu a hannun matanshi saboda tsananin zaman lafiya. 


Yau gashi duk sun fahimci juna sun yanke duk wani abu da zai haddasa masu rashin fahimta, sai fatan daurewar zaman lafiya. 


Ina fatan madaukakin sarki Allah ya cigaba da zaunar damu lafiya, da kasar mu lafiya. Allah ya bamu ikon fahimtar amfanin zaman lafiya, mu rungume zaman lafiya fiye da tashin hankali mu hade kanmu cikin aminci da salama ameen. 


Alhamdulillah tammat bihamdi, nan na kawo karshen wannan littafi na 'YAN GIDAN HAYA, ina fatan Kuskuren dake ciki ubangiji ya yafe mun, wanda nayi dai-dai Allah ya karbi niyyata na fadakar d al'umma muhimmancin zaman lafiya ya sanya muyi tarayya cikin ladan da dukkan masoya. 


*Ina yi muku fatan alheri masoya duk inda kuke, Allah ya sada mu da alheri, na gode ma kowa da kowa duk masu jumurin bibiyar littafi na tunda ga kan BADDEEYERH, GIDAN MARAYU, SANADIN K'AWATA, SAI KUMA 'YAN GIDAN HAYA.*


*Ku kasance dani cikin TUSHE MAFARI domin yanzu wasan ya fara, tare da daukacin members dake rubutu kan _TUSHE MAFARI_ . Ga Fauziyya Lawal Ammany muna tafe muku da wani sabon littafi mai suna _BAHAGON TUNANI_ nan ba da dadewa ba insha Allah fans fatan alheri.*

_Allah ya daukaka zamani writers ya kara mana zumunci tsakanin mu ameen_


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك 🙏🏼🙏🏼👏🏻👏🏻👏🏻


Download Ýan Gidan Haya Littafi Na Daya Complete