[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B'??R??UNIY??R
??M??RY??
????♀
N??
SADNAF????
??
ʍʀs ʄaաաaʐ ??
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
_Dedicated to All members of pure moment of life writers P.M.L we love you oll Allah yakara hada kanmu yabarmu tare_❤????
Page 1-5
GIDAN K'UNSHI
'Yan mata ne a zaune a wani k'aton tsakar gida, sun sha k'unshi hannu da k'afa a k'alla za suyi goma sha, wata tsalleliya ce a tsakiyar su kyakyyawan gaske ko ba a fad'a ba da alama itace Amaryar, sakamakon k'unshinta ya fita daban da sauran 'yan matan sai tsokanar ta, suke tana murmushi, wasu dake zaune a can gefe da suma suke jiran layi yazo kansu ne suka fara gulma "Binta gaskia Amarya nan kyakyawa ce da alama bafullatana ce" cewar Amina "kijiki, ni kuma kallon 'yar shuwa Arab nake mata, baki ga gashin ta bane har gadon baya ba?" "uhum kuma fa haka ne, dama su gayyace mu bikin ni ko photo ne muyi da ita"
"rufa mana asiri a ina zasu gayyacemu kina ganinsu ma kin san hatimin nassara ya zauna," sallama da suka jiyo daga bakin k'ofa ne ya katse musu hirar da suke suka maida kallonsu bakin k'ofa, ciki kuwa harda Amarya da k'awayenta,wasu yanmata biyu ne suka shigo su biyu sanye suke da wani arnen less da kud'in su zai yi dubu sittin, kunensu sanye da tapka-tapkan d'an kunnen gold, haka ma hannunsu.
Taku suke d'ai-d'ai har suka k'araso wajensu,tunda suka shigo Amarya kausar ta saki baki tana kallonsu, bawai kyaunsu ne ya tafi da imanin ta ba a'a k'iyasta irin dukiyar dake sanye a jikinsu takeyi, zama da d'aya daga cikinsu tayi a kusa da ita da daddad'an k'amshin daya ziyarci hancinta ne ya dawo da ita daga tunanin data tafi,yan matan hannun suka mimmik'awa k'awayen kausar sukayi musabiha suka mik'awa kausar hannu suka gaisa Inda suma suka kasa d'auke idansu daga kan kausar sabida ba k'aramin kyaunta suka gani ba,Hanne mai k'unshi kuwa cikin rawar jiki ta fara gaishe su Dan tasan indai suka zo ko iya hannu tayi musu k'unshi dubu ashirin suke bata, da rawar murya tace "hajiya fareeda da fadeela gani nan zuwa bari nayi sauri na k'arasa mata gani nan zuwa"
Murmushi wacce aka cewa fareeda tayi tace "karki damu Hanne ki gama yi musu a hannu kawai zaki mana"
"To ranki ya Dad'e bari nayi sauri nagama"
Juya wa tayi ta kalli Amina da Binta dake zaune a gefe da suka saki baki suna kallonsu fareeda tace musu "kuyi hak'uri gobe ku dawo sai na muku Dan yanzu Idan na gama yiwa wanan su hajiya zanyiwa kuma daga kansu nagama ta fad'i haka ne Dan tasan ba kud'in kirki suke biya ba Dan sai ta gama musu k'unshi su had'a ta da D'ari biyar,tsaki Binta tayi tace
"kya ce haka mana tunda kinga masu kud'i sunzo"
Amina da sauri ta tashi taja hannun Binta suka bar wajen,fadeela kuwa wayarta ta Ciro a jakarta k'irar iPhone 7 ta ringa dannawa ko d'agowa ba tayi ba ballantana tasan mai ke faruwa,Amarya kausar kuwa tunda suka zauna ta fara raya abubuwa a ranta, hankalinta bai tashi ba sai data ga wayar da fadeela ta ciro a jakarta, a ranta tace turk'ashi mutanen da gani ba k'aramin masu kud'i bane "Allah ka bani sa'a" tace tana mai kallon jakar fareeda dake gefenta a ajiye, maganar Hanne ne yadawo da ita daga tunanin da take
"Hajiya Ku matso na muku nagama" Hanne tace tana gyara inda zasu zauna.
fadeela ce ta fara mik'ewa taje ta zauna Hanne ta fara mata minti goma da fara mata ta d'ago ta kalli k'awayen kausar tace dukan su zasu iya wankewa tunda ya bushe,mik'ewa suka fara yi d'aya bayan d'aya suna nufar bakin pampo dake tsakar gidan suna wankewa, hakan ne yabawa fareeda dama ta matsa kusa da yar uwarta Dan taga k'unshin da ake mata,hakan da kausar tagani ne yasa ta matsa kusa da jakar fareeda ta bud'e ba tare da kowa ya ganta ba ta zura hannu ta dauko rafar kud'i bata tsaya ganin kalarsu ba ta cusa a skirt d'inta tayi sauri ta matsa daga wajen duk abinda tayi a idon k'awarta Aminiyar ta Jameela tayi,girgiza kai Jameela tayi cikin takaici tana mai k'yamatar halin k'awarta,kausar kuwa mik'ewa tayi tace fitsari take ji ta nufi band'akin gidan da buta a hannu tana shiga band'akin tayi sauri ta zaro kud'in, waro ido tayi cikin mamaki data ga bandir d'in D'ari biyar-biyar ne tace "Alhamdulillah na samu kud'in dazan rage bashi" d'aga vest d'in jikin ta tayi tasa kud'in da yake vest d'in mai roba ne. tana fitowa daga band'akin wayar fareeda ya fara ringing, mik'ewa tayi ta d'auko Jakarta ta zura hannu Dan ta d'auki waya taga wayam dubu hamsin d'in data sa a jaka babu, salati tayi da k'arfi hankalin kowa ya koma kanta,k'arasawa tayi wajen fadeela tace "our money is missing"
waro ido fadeela tayi tace "how?" anan tace "an sace mana kud'i," "what" Fadeela tace tana mik'ewa,salati Hanne tayi tace "tabd'ijan anan d'in aka yi sata? wlh sai na chaje kowace yar iska" da gudu ta nufi k'ofa taje ta sa sakata.
turk'ashi Readers yanxu
Aka fara
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B'??R??UNIY??R
??M??RY??
????♀
N??
SADNAF????
??
ʍʀs ʄaաաaʐ ??
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Page 5-10
Hankalin amarya kausar bak'aramin tashi yayi ba data ga hanne ta cire dankwalinta tasha damara gata gwabjejiya, sai zare ido take cewa take"hajiya Fareeda da Fadeela Ku kwantar da hankalinku wlh kudinku zai fito ba wacce bazan chaje ba inta kama ma a cire pant induba Allah sai kowace ta cire dan nasan B'??R??UNIY??R tana cikinmu dan wayacan biyun dasuka tafi yanzu ba su matso kusa damu ba awancan bencin suka zauna tace tana nuna bencin," wani irin shu'umin murmushi Fadeela tayi tace ki kwantar da hankalinki Hanne munfi karfin dubu hamsin ko fatar jikinmu kika kalla kinsan shegun sun zauna,amma abinda yabani haushi wacce ta d'auki k'udin nan meyesa batace a taimaka mata ba zata sace mu masu bata ne kyauta ko a jikinmu dan kingamu nan k'udin da ta sace kad'an yake mana arana amma tunda yar iska ce zanyi maganinta yan sanda zan kira azo atafi dasu acimun uban B'??R??UNIY??R gobe idan taga k'udin wani bazata kara marmarin d'auka ba,hayaniya ,k'awayen kausar suka kaure dashi kowace taringa zazzaga kayanta suna b'ub'ud'e poss dinsu suna nunawa Su Fareeda,inda Kausar ta jike da gumi kirjinta kamar yafad'o sabida fargaba, jameela aminiyarta kuma ta zuba mata ido tana kallonta cikin takaici muryar Hanne ne yadawo dasu hankalinsu" hajiya wlh basai kin wahalar da kanki wajen kiran yan sanda ba wlh dakaina zan chajesu,"daga mata hannu Fadeela tayi tace ki kyalleni yan sanda zan kira,d'aukar wayarta tayi tafara k'ok'arin kira,Fareeda da tunda aka fara hayaniya ta dafe kai dan mace CE dabata San hayaniya kwace wayar tayi daga hanun Fadeela tace you don't need to do all these,nawa 50k yake dazaki tada jijjiyoyin wuya zauna acigaba da miki k'unshinki Wanda ya d'auka Allah ya shiryeshi,afusace Fadeela ta fusge wayarta zatayi magana,fareeda tace shhhhhhh bana so nakara jin wani magana k'udinki ko nawa,"cikin tak'aici takoma ta zauna tana jijjiga k'afa hanne kuma takasa hakuri sai datayi magana "yanzu hajiya kina nufin Wanda ya saci dubu hamsin dinan yaci bulus kenan dubu hamsin fa" murmushi Fareeda tayi tace bakomai Hanne cigaba da aikinki Allah ya shiryi Wanda ya d'auka bayin Allah zaku iya tafiya Allah ya shiryi wacce ta d'auka fareeda tace tana kallon kawayen kausar da kausar da sukayi jingum jingum suna zare ido da sauri suka fara zura takalmansu suna ficewa Kausar ce akan gaba,Hanne kuwa kamar ta hadiyi zuciya dan bak'inciki atsawace tace shegu barayi kawai,suna fita waje k'awayen kausar suka ringa mata sallama suna cemata sai sun had'u akamu anjima ahaka suka watse suka bar Kausar' da jameela sai da sukayi nisa jameela ta cakumi wuyan Kausar tace" Wai meyesa bakyajin kunyar yin data ne, da bikinki ma bazaki bar sata ba wanan masifa dame yayi kama,sabida wanan halin b'eran naki aka sha korarki a makaranta,yanzu da asirinki ya tonu yau yazakiyi, kinga da kin bar abun fad'e dan kowa da B'??R??UNIY??R ??M??RY?? zai na kiranki,kisan Allah kika kara d
Sata ina wajen sai na tona miki asiri,Wai ma tsaya mai zakiyi da k'udine,? Rau rau Kausar tayi da ido tace jameela nasan banida sama dak'e duk da halina na sata baki tab'a k'yamatata ba, jameela kinsan ni marainiyace kuma bamuda hali mahaifiyata yan dabaru takeyi,sai nayi yan d'auke d'auke nake samun abinda nakeso yanzu wlh bashin danaci zaiyi dubu d'ari biyar banida mai taimakamin sai nayi yan d'auke d'auke,aikuwa wanan ba d'ab'iar arziki bace dan baki d'auko hanya mai billewa ba kidaina d'orawa kanki wahala ki ajiye kanki a inda Allah ya ajiyeki wlh wataran asirinki zai Tonu ,ya khaleed zai ji inyasamu labarin kina sata", insha Allahu ma baxai tab'a sani ba",uhmm jameela tace Allah ya shirya ni kinga tafiyata zanje wajen mai dinki,""au bazaki rakani saloon din ba,"? "Bazan rakaki ba haka kawai kije ki janyomin abun kunya,gaba tayi tabar Kausar a tsaye,kausar zaro k'udin tayi daga vest dinta tayi musu kiss direct gidan wata mai siyar da zanuwan gado taje tabata k'udin tayi mata alkawari zata ciko mata sauran dubu talatin din.
Tana Barin gidan wani katafaren saloon tanufa dake tarauni
OKE BEAUTY SALOON
Saloon ne k'aton gaske babu nauy'in mai da babu na gyaran gashi dan harda kayan siyarwa akwai, saloon din Aunty oke kenan wata inyamura mai San k'udin gaske.
tofa readers ko dai kausar ma an an zata kara gwada halin Nata muje zuwa wasa farin girki.
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B??R??UNIY??R
??M??RY??
????♀
N??
*SADNAF*????
*&*
*ʍʀs ʄaաաaʐ*??
®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Page 15-20
Tirtirjewa Kausar taringayi,Aunty Oke taringa marinta tana janta tana surutai " dan bura uba shege Amarya barawon amarya zanci ubanka yau we must go to police station"Aunty Oke tace da gurgurarran hausarta,shan gabanta wanan hajiyar tayi tace" haba Aunty Oke tunda kinga k'udinki pls let her go,"tureta Aunty Oke tayi daga gabanta tace"kina kallo barawo kice bazan kaita police station ba,all this suffer we are they suffer zanfito 7 o'clock ina neman k'udi dan nakula dayarana mijina yagudu yabarmu,am the one taking care of them,amma dayake wanan dan iskan barawon bashida imani shine zai zo yamin sata I swear I must take her to police station if not next time if she see somebody money she go still carryam look at how beautiful you are but na thief you be tufiyakwa"tace tana tofawa Kausar din data sunkuyar dakai tana kuka yawu,kara komawa hajiyar tayi gabanta tace" Aunty Oke pls let her go she has made a mistake,"tsaki taja tace da gurgurran hausarta,"hajiya ina ganin mutuncinka saboda yarenku d'aya bahaushe shi yasa kana so karna kai shi police station, sai na kaishi fa, am telling you, Abu kamar wasa fa yazama gaske,dan Aunty Oke bilhaki take Jan Kausar zata kaita wajen yan sanda, Inda yan mata nan da akewa kitso hankalinsu ya tashi suka je sunata r'okon Aunty Oke amma fir taki, Kausar kuwa ganin har Aunty Oke tafitar da ita waje tafara cewa Ole ne yasa ta zube akasa ta kankame k'afar hajiyar nan tana cewa su rufa mata asiri,tausayin Kausar ne yarufe hajiyar,tajawo Aunty Oke,Aunty Oke kuwa tafusge tace" since una no want make I carry her go police station, make I shout oley make people disgrace her wangala baki tayi zatayi ihun barawo,Hajiyar nan tayi Sauri tafito da k'udi daga Jakarta ta cusa mata a baki,ai kuwa nan da nan Aunty Oke tahau murmurshi tana "ehe is now you are talking dey for say you no bribe I swear I for disgrace am,hararar Kausar tayi data buya abayan hajiyar ta rankwasheta tace idiot ole buruku,dan iska barawo Amarya," ta kara dungure mata kai tashige,girgiza kai hajiyar tayi tace Allah ya shiryeki da San k'udi Aunty oke, yan Matan nan ne suka karaso wajensu suna kallon Kausar d'ayar CE tafara cewa ke kuwa baiwar Allah mai yakaiki sata Allah ya rufa miki asiri,gaki kyakyawa tabarkallah masha Allah",rufe fuska Kausar tayi tacigaba da kuka,da add'uar shirya suka bita,suka tafi suna gulmar B??R??UNIY??R ??M??RY??, hajiyan nan kuwa gefe taja Kausar tayi mata nasiha sosai Inda take nuna mata dayanzu bata gurin Allah ne yasan irin kunyar dazata sha,Kausar zubewa tayi akasa tana mata godiya,hajiyar ta tambayeta Ina zatayi ta rage mata hanya tace mata hotoro tayi,cewa tayi tahau motar ta rage mata hanya,godiya Kausar tamata tahau motar suka tafi,suna tafiya Hajiyar namata nasiha tana nuna mata illar sata ga ya mace,gyada kai kawai Kausar take tana kallon zobunan gold guda uku dake ajiye agefen hajiyar da Alama cirewa tayi,tari Kausar tafarayi sosai tana gaba tana baya hakan ne yasa hajiyar tace "subhanallahi bari nabaki ruwa,bayan mota tajuya dan ta d'auko mata ruwa Kausar kuwa tana ganin haka tayi sauri ta dau d'aya tacigaba da tarinta,mik'a mata ruwan tayi taringa mata sannu,karbar ruwan tayi tasha ta mata godiya suna dan yi gaba Kausar tace ta sauketa anan zata karbi dinkinta,nasiha hajiyar takara mata na ta ajiye kanta a inda Allah ya ajiyeta talauci ba hauka bane dayake Kausar karyar data mata kenan wai talakawa ne su zaa mata aure basuda komai shiyasa take sata, dubu biyar takirga tabata,Kausar taringa mata godiya tasauka daga motar tana daga mata hannu tana ganin hajiyar taja mortar ta ta tafi tayi Sauri tayanki wani kwanar tafara zuba sauri, adaidaita sahu ta Tara,tahau tace ya kaita bakin asibiti inda make siyar da gold,sai dasuka fara tafiya tafito da zoben tagani zobe ne K'aton gaske,murmushi tayi tace ahankali " haba yau ace nafito ba SAA,yauwa yanzu nasamu na biyan mai zannuwan gado saura mai turare,kai Amma Aunty Oke nan sai Allah ya tsine mata tsinaniya,"suna isa wajen masu siyarda da gold,taje tabasu zoben,sunka auna sukace mata k'udin zoben dubu sabain da takwas da Dari biyu da ashirin,murmushi tayi tace subata k'udin k'irga kudin sukayi suka bata, anan ma taso tayi dan halin Dan bata sa hijabi bane,tana Barin Kasuwar wajen mai zanin Gadon ta wuce ta bata cikon k'udin ta wuce wajen mai turare tabata sauran k'udin tayi mata alkawari zata ciko mata sauran tafito daga gidan tanufi gidansu Dan tundazu k'awayenta ke mata waya.
Hajiya mai saloon wanda aka fisani da hajiya zulaihat,sai datayi gaba ta kai hannunta zata kwashi zobunan ta taga babu babban ciki,sallati tasaki tajuya dasauri tanufi wajen data sauke Kausar tambayar mutane tayi da ko sunga wata fara yanzunan data sauke mai sanye da doguwar rigar atamfa,wani ni yace yaganta tabi nan ya nuna mata hanyar da Kausar tabi dasauri tabi tagurin bata ga alamarta ba,girgiza kai hajiyar tayi tace" mai hali baya Fasa halinsa insha Allahu zamu hadu dake ai nagane fuskarki nayi miki hallaci kiyimin butulci,"juyawa tayi tahau motarta tana Allah wadai da halin Kausar.
KAMU
yan mata acike suke dam awani k'aton gida farfajiyar gidan yasha decoration, Kausar tasha ado ta gaji anrufe mata fuska da wani net mai k'yaun gaske,daga dangin amarya har na ango sun samu halarta kamun acan gefe kuwa Hajiya Zulaihat nahango atsakiyar wasu manyan mata tana rik'e da faranti mai k'yaun gaske acikin farantin rafar yan Dari biyu ne guda d'aya sai turarruka masu kamshin da wani kwab'ebb'en lele,mik'ewa hajiya Zulaihat tayi dawasu suka nufi wajen amarya Dan su kamata.
Turkashii readers ba hajiya Zulaihat amarya Kausar tayiwa halin beta ba dazu tab kubiyomu kusha labari.
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B??R??UNIY??R
??M??RY??
????♀
N??
*SADNAF*????
*&*
*ʍʀs ʄaաաaʐ*??
®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Page 20-25
Kausar data sunkuyar dakai jin DJ na cewa ga dangin ango nan zasu zo su kama amarya, d'agowa tayi dan ta taga suwaye a dangin ango,gabanta ne yayi wani irin fad'uwa datayi tozali da fuskar Hajiya Zulaihat,ta nufota wani irin gumi Kausar tafarayi jikinta yadau k'yarma janyo net din tayi ta rufe fuskarta sosai tareda rik'e net din gam ajikinta,tafara zancen zuci,"shikenan yau asirina ya tonu ni Kausar na bani na lalace matar danayiwa sata dazu ashe Yar uwarsu Khalid CE bansani ba,Ya Allah ka dubeni da idon Rahama ka rufamin asiri"jin gurin ya k'aure da gud'a ne yasa ta dawo hankalinta adai dai lokacin da hajiya Zulaihat takaraso ta sunkuya tana so ta daga net din da ta rufe fuskarta dashi,gam ta rik'e net din ta sunkuyar dakai k'irjinta na dukan Tara Tara,murmushi hajiya Zulaihat tayi takara rik'e net din taji Kausar ta rik'eshi gam,jameela dake gefen Kausar matsawa tayi kusa da Kausar tamata rad'a a kunne "ke mai haka ki cika net din mana a fesa miki turarren," girgiza kai Kausar tayi ta kara rik'e net din gam,hawaye na zubo mata Dan tasan yau asirinta zai tonu a bainar jamma'a agaban danginta Dana mijinta,ita kuwa Hajiya Zulaihat ganin ta rik'e net taki cikawa ne yasa tayi murmushi ta kalli hajiya rufaida dake gefenta,tace"lailai amaryar Khaleed bak'aramin kunya ne da ita ba,d'aukar turaren tayi ta feffesa mata aka saki gud'a ta dauki kwab'ebb'en lalle nan ta lakuta mata a k'afafu ta d'auko rafar dubu ashirin din ta d'ora mata a cinya,aka k'aure da gud'a sunkuyawa tayi tacewa jameela "kicewa kawartaki ta bud'e fuskarta muyi hoto,matsawa jameela tayi kusa da Kausar ta rad'a mata,Kausar ta kara kankame net din tana girgiza kai,murmushi hajiya Zulaihat tayi tace gobe ai dinner zata ga fuskar amarya ta juya suka tafi anan hankalin Kausar yadan kwanta kad'an jameela ta lekata tace " Kausar anya kinada gaskia kuwa ko dai kintab'awa yiwa matar nan halin naki ne, dubi yanda kike gumi jikinki yake rawa, aikuwa in haka ne kin tapka babban asara,Dan yar uwarsu Khaleed ce",Kausar bata Ce komai ba illa ma kara kallon direction din dasu hajiya Zulaihat suke tayi takara rufe fuskarta da net,a takaice ahaka Kausar ta rufe fuskarta taki bud'ewa sai data ga su hajiya Zulaihat sun tafi sanan ta bud'e fuskarta, anan jameela takara gasgata zarginta,ta girgiza kai tana mai nemawa Kausar shirya Dan tasan Kausar tayi nisa.
ASALIN LABARIN
Kausar 'ya ce ga margayi mallam garba su biyar ne agidansu uku maza biyu mata Adamu shine nafari sai bello da kamal,matan kuma Kausar sai auta jidda, usulinsu Fulani ne gaba da baya, mahaifinsu ya rasu ne a lokacin autar Jidda Nada shekara biyu a duniya,dukiyar daya bari gona biyu da shannu,a lokacin suna yola,sanadiyar rasuwar Mallam Garba ne yasa suka dawo kano da zama,tun lokacin da mahaifinsu ya rasu,Hajjo take iya bakin k'ok'arinta Dan taga yaranta basu rasa komai ba, Adamu dinki ya koya tun yana da shekara goma sha biyu har ya girma yakuma iya dinkin sosai dahaka yake tallafawa kanensa,haka ma su bello suna buga buga duk mazan babu Wanda ya zauna haka asanadin hakan ne yasa su Kausar basu wani nemi Abu sun rasa ba koma dai yaya ne suna samun biyan bukatunsu,hajjo ma tana daga gida tana yan sana'ointa. Kausar kyakyawa CE ta ajin karshe Dan komai na mahaifiyarta ta d'auko hajjo,tun Kausar Na yarinya ta koyi d'auke d'auke Dan hajjo zata ajiye yan chanjin ta Kausar sai ta d'auke sai dai hajjo tagaji da nema ta hakura,ahaka har Kausar ta isa sawa a makaranta,yayanta Adamu ya sama mata wani makarantar gwamnati take zuwa,daga fara makarantar ta takara dagewa wajen Dan yan ajinsu insukayi break, suka fita dawowa take ta chaje jakarsu intaga biyar ta d'auka goma ashirin,ba iya k'udi ba har abin ci d'auka take,inta Tara k'
Kud'in data sata ko ta siyi kayan k'wadayi ko tasiyi tasiyi kayan wasan yara,kuskuren da Hajjo tayi inta ga k'udi ko abun wasa a hanun Kausar bata damuwa ta tambayeta a ina tasamu,ranar da asirin Kausar ya tonu a lokacin yan ajinsu sun gaji da kana na kanan satar da ake musu,ranar wasu a ajin bayan a fita break suka lab'e ta window aikuwa minti goma da fita break sai ga Kausar ta dawo aji tafara bincike jakar yan ajinsu,wayanda suka lab'en tuni suka fito suna ga B'??R??UNIY?? mun kamata tuni Kausar ta w'ular da jakar tana Neman hanyar guduwa,yan ajinsu suka rufar mata suna mata ihun B'??UR??UNIY??, aranar headmaster dinsu ya zaneta agaban Assembly, ya tura aka kira yayanta adamu aka fad'a mishi abunda Kausar keyi,duka kam aranar Kausar tasha a gurin y'ay'enta Dan takaicinsu ba abinda Kausar ta nema ta rasa,atakaice ahaka Kausar taringa yan d'auke d'auke har taje secondary school anan tahad'u da Jameela suka zama k'awaye,fara secondary dinta ne yasa idonta yakara bud'ewa da kud'i, duk satar da akeyiwa yan ajin basu tab'a kawowa Kausar bace,amma suna dai Adduar Allah ya tonawa b'arawo asiri,akwai wata bilkisu dake kawo alewar madara su aya kantu da sauransu,kullum inta kawo tagama siyarwa inzata K'irga kud'in baya cika abun na mutukar damunta, nan kuwa Kausar CE ke d'aukar mata,wani Sain ma ba kud'i kawai take d'auka ba alewar madara take diba tasa ajakarta injake gida tayi ta sha,Jameela CE tafara kama Kausar ranar bataje break ba ta batada lafiya ta kwanta kamar mai bacci amma ba bacci take ba,Kausar data shigo zata yi Dan halin,sai data leka fuskar Jameela taga alamar bacci Take sanan tafara chaje jakar yan ajinsu,batasamu komai ba Dan yan ajin ganin irin satar da ake musu akai akai ne yasa suka daina ajiye k'udi ajaka, ganin batasmu komai ba yasa ta dibi alewar madara da kantu da bilkisu ta ajiye Jakarta ta d'auko Dan ta zuba,taji ance ajiye,dagowa tayi cikin fad'uwar gaba ta kalli Jameela data zauna tana kallonta,Jameela fusge jakar hanunta tayi ta wular tace mata ta "mayar mata da kayanta, anan Jameela kecewa Ashe itace B??R??UNIY??R ajinsu Kausar rok'on ta tayi data rufa mata asiri ta daina sharrin shaidan ne, atakaice ahaka Kausar taringa yan D'auke d'auke jameela tana rufa mata asiri sai ranar da dubunta ya cika.
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B??R??UNIY??R
??M??RY??
????♀
N??
*SADNAF*????
*&*
*ʍʀs ʄaաաaʐ*??
®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Wanan page d'in sadaukarwa ne ga duk fans *B'ARAUNIYAR AMARYA* Muna jin sak'onni Ku kuma mun gode d'umbin k'aunar ku.
We love u??
Page 25-30
Tun lokacin da su Kausar sukaje SS 1 aka kapa doka a makarantar akan duk ajin da akayi sata,sai yan ajin sun hada kud'i anbawa Wanda akayiwa Satan koda nawa ne, sabida yawan complain d'in da principal ke samu na Satan da akeyi a ajinsu Kausar,bayan sun had'a kud'i akwai punishment d'in da za a yiwa yan ajin gaba d'aya ko kaine kayi Satan ko ba kai bane,idan kasha wuya zakayi k'ok'ari kaga kanemo b'arawon,tunda yan ajinsu Kausar sukaji irin matakin da hukumar makaranta ta kapa,hankalinsu ya tashi,suna komawa aji, monitor ajinsu tace su had'a kai su samo Wanda yake musu sata,kuma kowa ya kiyayi ajiye kud'insa a ajaka,kuma sunyi alk'awari duk lokacin da asirin B'??R??UNIY?? ya tonu sai sun mata zigidir,tunda Kausar taji haka tashiga hankalinta dan sai da Jameela tak'ara bata shawara akan ta daina idan ba haka ba tana tausaya mata ranar da dubunta ta cika,aikuwa Kausar ta d'au shawarar Jameela Dan taga alamar inbatayi wasa ba asirinta tsaf zai tonu,dan ta lura yan ajin burinsu kawai su gane B'??R??UNIY??R Ajinsu, tunda aka kapa dokar yan ajinsu Kausar suka samu sauk'in satan da ake musu,Wanda hakan yasa Kausar cikin tashin hankali dan yanzu bata samun kud'i,a gida hamsin ake bata, ko break baya isarta takuma saba da kud'i, hakan data gani ne yasa tafara tunanin hanyar da zata bi tasamu kud'i dan akwai ankon da takeso tayi na wata kawarta dazatayi aure,wani dabara ne yafad'o mata tahau murna,gidansu wata makociyarsu taje Rahama sa'anin juna ne kuma k'awaye akwai wani agogo mai k'yau da yayan Rahaman ya kawo mata tsaraba da yaje aikin Hajji, shi Kausar taje ta ara agurin Rahaman tace mata zata nunawa yayanta ne Dan yasiyo mata irinshi,Rahama data bata agogon makala shi tayi ahanunta ta tafi dashi makaranta,da isarta kuwa ajinsu ta cire agogon taringa nunawa yan ajin tana cewa yayanta ya kawo mata tsaraba,babu Wanda bata nunawa agogon ba,aka ta ta yata murna wasu harda karb'a su d'ana, ana dab da fita break Kausar ta tafi gaban aji Dan tanaso kowa yaganta, cire agogon tayi tasa ajakarta, ta ajiye jakar a Inda ake ajiyewa,takoma ta zauna,bayan anfita break,dawowa tayi ta d'auke agogon ta cusa a gashinta dayake tanada gashi ta d'aure kanta sosai yanda agogon bazai fad'o ba,bayan andawo daga break,Kausar Jakarta ta d'auko tafara dube dube,can ta juye littattafanta akasa ta saki sallati,yan ajin gabad'aya hankalinsu ne ya tashi Dan sun San dak'yar in b'arawo baiyi halinsa ba,Kausar kuka ta fashe dashi tace an sace mata agogo tashiga uku ta lalace,yan ajinsu gurinta suka nufa suna tak'ara dubawa,monitor Jakarta ta k'arba taK'ara dubawa taga babu,yan ajin tuni suka ringa zaro jakankunansu suna dubawa ,monitor kuwa ganin ba aga agogon ba ta tafi wajen displine master ta gaya masa anyiwa Kausar Satan agogo,sai dayasa takira labour prefect da wasu prefect d'in suka nufi ajinsu,kowane da bulala hannu,tuni yan ajin wasu suka fara kuka Dan sun San yau sai sunci duka dan displine Master bashida mutunci,cewa yayi wacce akayiwa satar tafito yaganta,fitowa Kausar tayi gaban aji tana kuka,tambayarta yayi ya agogon ta yake,ce mishi tayi sabo ne yayanta ya siyo Mata shine yau tazo dashi makaranta dan ta nunawa k'awayenta shine aka sace,tambayarta yayi ko tasan nawa ake siyo mata agogo,cewa tayi dubu uku da d'ari biyar yayanta yace yasiyo mata,g'yada kai displine master yayi yace dole "su biyaki agogonki,amma kafinan zan zaneki sabida kinzo dashi makaranta,kallon yan ajin yayi yace ba kun iya sata ba yau zan koya muku hankali,kowace acikinku takawo sabain sabain gobe idan bahaka ba kunsan sauran,b'arayin banza b'arayin hofi ba kun iya sata ba yau zan koya muku hankali,kowace sai na mata bulala goma,sanan kunje kunyi wanki b'andaki gobe inkuka ga abun mutum bazakuyi marmarin d'auka ba,inku zuciya yau kuhad'a kai fito da wacce take sata a ajinan, tuni yan ajin suka hau kuka suna rantse rantse,Kausar kuwa said yanzu tayi da ta sanin abinda tayi Dan ta d'auka cewa zaayi kawai ahad'a mata kud'in gashi yanzu harda ita za'a Zane,jin datayi displine master nacewa labour prefect sufara chaje kowace a cikinsu tunda mata ne su chaje ko INA har ita kanta Kausar d'in a chaje ta,duk wacce taki tsayawa a chajeta su mishi reporting,zai fita waje ina an gama zai dawo,ficewa yayi waje prefects d'in suka kulo k'ofar ajin,sukasa sukayi layi aka zagayesu,suka fara zuwa d'aya bayan d'aya ana chajesu dai-dai da d'ankwalin sai kin cire,Kausar tuni ta jik'e da gumi dataga haka yan ajin kuwa dayake sun san sunada gaskiya cire komai suka ringayi ana chajesu,in aka gama chajeka sai kayi waje kayi kneel down,Kausar kuwa kuka taringayi a b'oye dan tasan yau asirinta ya tonu, saura layi biyu azo kanta tacewa wata prefect tanaso taje tayi fitsari harta barta tafi,labour prefect ta dawo da ita tace ta cire hijabinta da dankwalinta achajeta ido awarwaje Kausar tafara tari,ganin tana bata musu lokacine yasa ta tsinka mata mari Dan bata wasa ta fuzgo hijabin Kausar tare da cire dankwallin kanta aikuwa sai ga agogo ya fad'o kuka Kausar ta fashe dashi,prefect d'in tabita da kallon mamak'i dagudu d'aya daga prefect d'in takira displine master tafad'a mishi Kausar ce ta saci agogonta,tuni wata a ajinsu Kausar mai zuciyar ta shak'e Kausar, dak'yar aka rabata da wuyan Kausar,prefect sukayi waje da Kausar data rufe fuska tana ta kuka,yan ajinsu dagudu suka bisu suna kaiwa Kausar duka suna janyo rigarta,a tak'aice Kausar sai da a ka koreta daga makaranta,Hajjo sabida bak'inciki sai da suka bar unguwar dan yan makarantarsu Kausar sun hana Kausar sakat,ya'yenta ma Dan takaici fita sukayi daga harkarta Dan basu San me Kausar ta nema ta tarasa ba, Hajjo ce ma tasa ayiwa Kausar addua a fad'arta Kausar aljanu ne da ita na sata,Kausar kuwa tunda yan ajinsu suka tozartata,tayi sanyi tarage sata,indai tak'arasa secondary awani makarantar,kawancen su na nan da Jameela bata gujeta ba ,tana gama secondary tahad'u da Khalid,inda soyayya yayi k'arfi a tsakaninsu har takai ga manya sun Shiga maganar, gabatowar bikinsu ne ya d'aga hankalin Kausar dan ta raina abinda ya'yenta suka mata anan tahau Neman kud'i k'arfi da yaji bashin dataci ba a magana,kud'i take nema Wanda zata biya basukan da ake binta.
CIGABAN LABARIN
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B??R??UNIY??R
??M??RY??
????♀
N??
*SADNAF*????
*&*
*ʍʀs ʄaաաaʐ*??
®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
*UP UP PURE MOMENT OF LIFE WRIT ERS YOU GUYS ARE DOING A GREAT JOB,MAY ALLAH's BLESSING AND LOVE BE WITH US LOVE YOU GUYS SO VERY MUCH THIS PAGE IS FOR EACH AND EVERYONE OF YOU*❤??❤????
Page 30 -35
Tunda aka gama kamu Kausar ta fara tunanin hanyar da zata bi tak'i zuwa dinner da Khaleed ya had'a dan tasan intaje dole Hajiya Zulaihat taganta,dan d'azu taji tana cewa Jameela zata ganta gobe,da wanan tunanin jikin Kausar yayi sanyi zazzab'i k'arfi dayaji ya nemi ya rufeta dan tasan asirinta yagama tonuwa indai Hajiya Zulaihat ta ganta gobe,ga Khaleed yanaji da dinner daya had'a gobe dan komai nasu iri d'aya yamusu,gashi rabin 'yan uwansa da basu Santa ba musamman zasuje dinner gobe dan suganta, kasancewar Khaleed d'an dangi ne gaba da baya. a wanan halin Jameela tazo ta sameta, ba yanda Jameela batayi ta gaya mata abinda ke damunta ba Kausar tak'i. kiran Khaleed ne ya shigo wayarta ta d'aga, yace mata yazo yana waje. doguwar Riga kawai ta zura tafita waje ta sameshi akan mota a zaune,murmushi ya sakar mata dan shi kullum cikin godewa Allah yake dazai mallaka mishi sarauniyar kyau, sunan dayake kiranta dashi kenan,tsokanarta ya hau yi da Amarya kinsha k'amshi,daurewa kawai tayi tana murmushi,hira suka d'an tab'a sama sama inda Rabin hira Khaleed keyi,hirar yanda dinner gobe zata kasance, D'an murmusawa tayi tace mishi tana so ta tambayeshi,yace yana sauraranta "akwai wata Hajiya d'azu da ita ta kamani, ya kuke da ita bansanta ba?"
"Wai Aunty Zulaihat kike nufi,k'anwar Babanmu ce ai ita nake baki labarin bata K'asar zanso ace tana nan za ayi bikin mu dan tana bala'in Son taga matar dazan aura,lucky enough kuwa ta dawo, kuma kinsan wlh sabida bikina ta dawo? ai d'azu take cemin "ko Amaryar tawa mummuna ce shiyasa tak'i bari naga fuskarta?", nace mata "ta kwantar da hankalinta gobe idonta zai gane mata inke mummuna CE ko kyakyawa,".
Tunda ya fara magana Kausar jikinta ya hau rawa dan tasan babu gudu babu ja da baya asirinta ya tonu,zancen zuci tafarayi
"yanzu Ashe Hajiyar dana yiwa sata K'anwar Baban su Khaleed ce? nashiga uku na lalace ina zan kai wanan abun kunyar?"
K'arya tayiwa Khaleed da kanta ciwo yake zata je ta kwanta,nan kuwa gudawa takeji. Khaleed jin Amarya na ciwon kai ne yasa hankalinsa ya tashi, dagewa yayi sai ya kaita chemist yasiya mata magani amma fur tak'iya, da k'yar dai ta samu ya tafi.
Tana komawa cikin gida band'aki ta wuce tana sukurkuta gudawa,hankalin ta a tashe.
Ita da kanta tayi Allah wadai da wannan hali nata,gashi yanzu tayi inda abin ya sha mata kai,to amma ya ta iya? Buk'atar kud'in ne ya ja mata shiga wannan halin don bashin da ta ci idan ba satar tayi ba babu yanda za ayi ta iya biyan kud'in.
Da dare bacci ya k'aurace a idon Kausar, sai tufka da warwara take yi na yanda zata samu ta kaucewa zuwa dinner d'in gobe,don ta San idan har ta je asirin ta ya gama tonuwa kuma in khalid ya San tana sata Ai kashinta ya bushe,. A haka tana ta tunani ta kasa samun mafita har aka yi sallar asuba.
Da safe haka ta tashi idonta sun kumbura ga kuma headache na rashin bacci da damuwa. Ganin haka ya sa ta k'ara langabewa wai ita a dole bata da lafiya,ko don wannan Ai ta San dole dai Khalid ya k'yale ta da batun zuwa wannan dinner d'in.
Ita kanta ba k'aramin buri ta ciwa dinner d'in ba, amma kuma dole ta hak'ura don ta tsira da mutuncin ta,tunda ma ya ce Anty Zulaihat ba a k'asar take ba don haka zata yi ta b'oye mata har sai ta koma inda ta fito.
Wuraren 5:00pm Khalid ya kira a phone ya sanar mata gashi nan mai makeup zata zo gida ta mata makeup.
"Ai my pretty na San dole ne ki yi kyau ki fito sosai, don na biya makeup artist d'in sosai,so nake kowa ya ganki yasan babu raini"
Mak'ale voice ta k'ara yi cikin shagwab'a tace "hubby ni fa bani da lafiya tun jiya d'in nan".
"Haba my pretty me ya same ki? Ya salam sannu pretty na am on my way sai muje in kai ki asibiti a duba ki",Kausar sad'akarwa kawai tayi da zata je dinner dan tasan duk abinda zatayi Khaleed bazai barta ba sai taje,har yanmata sunfara cika gidansu Kausar kowace inka ganta sai kasan batada matsala dan su burinsu suga ma lokaci yayi suntafi Wanda ita kuma duk motsin da agogon bangon d'akinsu yayi sai k'irjinta ya buga,Jameela ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi," Kausar wai mai yake damunki ne tun jiya awajen Kamu kika susuce yau ma dakikafi ciwa buri sai gashi kin langab'e dan Allah kifadamin damuwarki kinsan nasan sirrinki, kifad'amin damuwarki nikuma insha Allahu zan baki shawara"dagowa Kausar tayi haka kawai taji aranta gwara ta gayawa Jameela halin datake ciki, tunda tariga tasan halinta, watak'ila ma Jameela tasamo mata mafita, gyaran murya tayi ta labartawa Jameela komai har satar datayiwa Aunty Oke, da irin taimakon da Hajiya Zulaihat tayi mata anan takarasa zancenta da "Jameela babu yanda zanyi sai nayi satar zan iya biyan bashin dake kaina kuma insha Allahu inagama biyan bashin nadaina sata dan naga alamar Khaleed nada rufin asiri babu abinda zan nema narasa", tunda tafara magana Jameela tasaki baki tana kallonta cikin tsananin mamak'i dan bata tab'a tunanin satar da Kausar keyi yayi tsamari haka ba, sallati Jameela kawai take tana girgiza kai"Kausar wanan halin naki bazaki taba iya dainawa ba koda kuwa kinada naki kud'in dan kinriga kin saba, d'auke d'auke gashi kin janyo wa kanki abun kunya kinje kinyiwa kanwar sirikinki sata, " katseta Kausar tayi tace " zandaina insha Allahu dan Allah kibani shawara yazanyi inkaucewa had'uwa da hajiyanan" shiru Jameela tayi tana tunanin tace "ki kwantar da hankalinki ba kince mai makeup ta taho ba, indai tazo wani irin makeup zakice ta miki tacanja miki kamani kinsan in akayi makeup din kamanin ma canjawa yake, dabaru zamu sata tayi ki canza kamani yanda Hajiyar bazata ganeki ba", wani irin ajiyar zuciya Kausar tayi tace kai amma naji dad'in shawararki, katseta Jameela tayi taringa mata fad'a data gyara halinta, zuwan Khalid da mai makeup ne ya katse mata shawarar da take bata, Kausar data fita Khalid dagewa yayi sai yakaita chemist tace mishi tasha magani, cemata yayi kud'i yabiya da tsad'a ayi mata makeup yanaso anjima inya ganta kar ya ganeta dahaka sukayi sallama, suka shiga cikin gida ita da
Mai makeup din.
Cikin awa d'aya da rabi Kausar ta canja kamani SADNAF TA KALLI MRS FAWAZZ tace "makeup shegen abune kinga yanda Kausar ta canja kamani" "ni muni ma naga tayi" Mrs Fawazz tace tana daga wuya dan taga Kausar sosai, "tashi murigasu zuwa wajen dinner muga ko Hajiya Zulaihat tazo, intaga Kausar B'??R??UNIY??R ??M??RY?? zata ganeta kuwa, Sadnaf tace tana yin gaba, mrs Fawazz da gudu tabi Sadnaf tana "kijirani mana sai zuba sauri" kike.
DINNER
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B'??RUNIY??R
??M??RY??
????♀
Na
S??DN??F
*&*
ʍʀs ʄaաաaʐ??
*®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
P.M.L
35-40
Mai makeup ta tak'ark'are sosai ta yi ma Kausar makeup Wanda idan ba farin sani kayi mata ba ba zaka tab'a gane ta ba,tayi kyau iya kyau,Jamila sai yaba kyau da tayi take yi.
Kausar ta ce mai makeup ta D'an basu waje zasu gana da jamilan
Bayan fitar ta Kausar ta dubi jamila ta ce "ya kika gani?" Murmushi Jamila tayi tace "wallahi ba k'aramin kyau kika yi ba Amaryar khaleed".
"Ke nifa tambayar ki nake ba za dai a gane ni ba ko?" Jamila ta ce "gaskiya ko ni ba Dan a gaba na aka yi ba da wallahi ba zan yi saurin gane ki ba ,ballantana ita da ta ganki sau d'aya".
Murmushi Kausar tayi had'e da wata ajiyar zuciya mai nuna alamun ta samu relief , suna cikin Wannan maganar sai ga call d'in ango ya shigo yake cewa sun iso fa,ta ce to suna zuwa.
Kausar ta dubi jamila ta ce "angwaye fa sun k'araso", jamila ta ce "Tou bara a yiwa k'awayen mu magana sai su fara fita".
Sai da kowa ya gama fita tukunna mai makeup ta D'an k'ara gyara ma Kausar face d'in ta sannan jamila ta rik'o tail d'in gown d'in Amarya suka fito, "subhanallah" shine abinda khaleed ke fad'i domin kyaun da ya ga Kausar tayi ba'a magana,
wedding gown ce a jikin ta,sai ta saka net d'in kanta ta rufe face d'in ta,da yake net rub'i biyu ne sai ba a ganin fuskar sosai. Khaleed fitowa yayi daga mota ya zo inda take, kama hannun ta yayi suka k'araso ya bud'e mata mota ta shiga ita kuma Jamila ta shiga gaba suka d'au hanya.
Khaleed yasa hannu ya bude net din ya ga yanda face din ta sha ado kamar doll baby, kasa d'auke idon shi daga kanta yayi, kallonta kawai yake yana k'ara godewa Allah da ya bashi wannan zankad'ed'iyar matar.
( kyaun D'an maciji)
Ya ce "my preety gaskiya ba k'aramin kyau kika yi ba, kin ci sunan sarauniya kyau, ke ni idan ma akwai abinda ya fi sarauniya kece, yau dai family na zasu ga matar khaleed, dama kowa ya samun ido ana son aga wadda zan aura",
Ita dai Kausar murmushin yak'e kawai take yi,amma har yanzu hankalin ta ya kasa kwanciya, a haka har suka isa wajen dinner d'in.
Jamila ce ta fita ta sanar cewa ga Amarya da Ango nan sun k'araso, don haka aka tattaro yaran da zasuyi flower girls, suka zo,sun D'an jima a wajen kafin aka jera yaran a gaba biyu kuma a baya suna rik'e da tail d'in rigar Amarya, gaskiya abin ya burge kowa a wajen suna tafe ana watsa ma Kausar da Ango flowers ,taku suke d'as- d'as dasu gwanin ban sha'awa, ai kuwa masu camera suka hau aikin su.
A haka har suka isa inda aka tanadar musu, zaman su da 10 minutes jigajigan iyayen ango Wanda suke ji dashi shima yake ji dazu suka taho wajen, a lokacin. E khaleed yake rada ma Kausar " ga Anty zulaihat din nan da nake gaya miki ta taho" ji tayi zuciyata fa fara lugude kamar zata fara k'irjinta ta fito waje.
Su Hajiya zulaihat suna karasiwa wajen ta ce yau dai zanga Amaryar khaleed dama jiya ta boye fuska ta hana ni ganinta amma yau duk abin ta siya na ganta". Jin haka ya sa Kausar jikin ta ya fara rawa kamar ana kada mata mazari, Anty Zulaihat ta sa hannu ta yaye net d'in da ya rufe ma Kausar fuska, suna hada ido Hajiya zulaihat ta ja da baya tana kallon Kausar din
Ganin haka yasa khaleed fara washe baki yace "Anty na ya kika ga Amaryar,ko duk kyaun ta ne ya sa kika rud'e haka?" Ta ce " hahh aa ba wai haka bane kawai dai ta min kama ne da wata shegiyar yarinya da tayi min sata, matsoraciya, Amarya ce fa amma ta ke sata,Amma ba ita bace wannan, Ai gaskiya Amarya tayi ka iya zab'e"
A nan Anty Zulaiha take Labartawa khaleed yanda suka yi da B'??RUNIY??R ??M??RY??
Jikin Kausar ya dinga rawa gumi ya dinga keto mata,khaleed kula yayi da yanda jikin Kausar ke rawa ya matsa yamata magana yace beauty me ya faru dake naga jikin ki narawa?
Tace ba komai kawai ni ban saba da shiga jama'a haka ba duk a takura nake
Yace Mata calm down my preety Ai ba wani Abu bane
Jamila ta lura da yanda gaba d'aya Kausar ta rikice don haka sai ta zo take mata magana a kunne tace ta nutsu mana kada a gano ki mana.
Lokacin da Hajiya zulaihat zata tafi ta zo sai ta sake zuwa ta kalli Kausar ta ce "Amarya baki da k'anwa ko wata 'Yar uwa mai suna Fatima?"
Kausar mak'e muryarta tayi don kart a gane ta tace "a'a"
Khaleed ya ce "kai Antyna lallai ba k'aramin haushin satar nan kika ji ba"
Ta ce "Ai kai kam Dole ne inji haushi mana zoben gold d'ina da mijina ya siya min tsinanniyar yarinyar nan ta sace ,Ai wallahi duk inda na had'u da yarinyar nan sai na tozarta ta na wulak'anta ta".
Khaleed ya ce "gaskiya bata kyauta ba dole kiji haushi".
Bayan an tashi ne a mota khaleed ke bawa Kausar labarin B'??R??u??NIY??R ??M??RY??, sai yake ce mata "Ai wallahi preety na na tsani sata bana shiri Sam da mai sata, don duk Wanda yake sata babu abinda ba zai iya aikatawa ba,ita kam waccan Amarya mijinta ya shiga uku, Ace matarka taje saloon tayi sata Ai wallahi abin kunya ne, yanzu da an kaita station d'in da wane ido zata kalli Angon ta gaya masa sata tayi ana shagalin bikinsu? Kai Allah ya sawwak'e,ba gwarama ta tambaye shi ba idan bata da kudi nE? Amma ace mace da sata? Ai gaskiya girma ta fad'i"
Kausar dai shuru tayi ta kasa cewa komai,don gani take kamar ya gane itace shi yasa yake mata hannun ka mai sanda.
Can dai khaleed yaji sai zuba yake amma Kausar tayi shiru ya dube ta yace my pretty ya dai? Ko jikin ne? Kai kawai ta d'aga mishi alamar "E" Amma bata yi magana ba don ita kadai ta San halin da take ciki.
Shi kuwa jin tace jikin ne yasa shi ya tausaya mata, sai sannu yake faman jera mata tana amshewa.
Sai da suka biya suya spot ya siya musu Chips da kaza sai exotic manya guda biyu sannan suka wuce gida.
Jamila kuwa tunda khaleed ya fara labarin b'arauniyar Amarya take dariya a ciki din ta San mutuniyar tata tana cikin wani hali,bata sake shan dariya ba sai da Kausar tace bata da lafiya da sannun da khaleed yake ta jera mata.
Lokacin da suka shiga gida Kausar gown d'inta ta cire ta shige toilet ta sauke gudawar da ta ke matsinta, Ai kuwa jameela ta sake kwashewa da wata dariyar tace "gobe ma kya kuma"
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B??R??UNIY??R
??M??RY??
????♀
N??
*SADNAF*????
*&*
*ʍʀs ʄaաաaʐ*??
®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Page 40-45
Kausar tana fitowa daga band'aki ta zube akan gado tana hamdala,tab'e baki Jameela tayi tace "dan Allah mai amfanin haka kinji dai abinda mijinki yace ya tsani mace mai sata, dan Allah Kausar ki gyara halinki da yau wanan matar ta ganeki dawane ido zaka kalli Khalid da danginsa,sata bashida amfani,yanzu kinga ma idan asirinki bai tonu yanzu ba zai Tonu nan gaba dan hajiya Zulaihat d'inan dole wataran ta ganki ba makeup ki kuma dubi alwashin data sha na tozartaki dan Satan da kikayi mata ya mata ciwo," ajiyar zuciya Kausar tayi tace Jameela ki tayani da addua bansan ya akayi na tsinci kaina acikin irin wanan mumunar d'abiar ba,amma insha Allahu na daina,yanzu basukan mutane danaci nake tunanin yanda zan biya kinga yanzu bashin wajen dubu dari uku da sittin ake bina,bansan ya zanyi ba,hajiya SA'A Dana karbi kuloli agurinta kawai dubu Dari da ashirin kud'inta agurina gashi bata wasa da kud'i gobe na mata alkawari bansan daga ina zan fara ba," tsaki Jameela tayi tace "tun farko Kausar ke kika janyo wa kanki ki ajiye kanki a inda Allah ya ajiyeki mana gashi kinzo kin d'orawa kanki bashin mutane,nidai shawarar dazan baki Allah cikin mutunci da mutunta wa duk wayanda kika k'arbi kayansa ki mayar mishi kice bakida kud'i da dai ki kara sata Kausar kinga nabaki shawara tin wuri ki tsira da mutuncinki karkiyi abinda mutuncinki zai zube a idon mijinki da mutane," kiran daya shigo wayar Kausar ne ya katse musu maganar dasuke,d'aukar wayar tayi ta gwallo ido tana kallon Jameela "ki d'aga mana kika tsaya kina kallona," "hajiya SA'A danake miki zancenta yanzu ita ke kirana wlh batada hakuri akan kud'i" Kausar tace tana daga wayar,bayan mintina uku ta kashe wayar tace " kinji ba wai bazata k'arbi kulolin ba sun d'ade awajena kud'inta kawai takeso goben nan yanzu jameela ya zanyi" ajiyar Zuciya Jameela tayi tace "ki tambayi Al ameen yabaki da dai kiyi sata Kausar ko rabine inya baki sai ki r'oketa ta daga miki k'afa ahankali zaki cika mata sauran" "to shikenan Jameela zan gwada tambayarsa Allah yasa nasamu" Ameen Jameela tace tana cire rigar jikinta.
Kausar tunanin yanda zata samu kud'i taringayi,Wanda kuma take ganin bai kamata ta tambayi Khalid kud'i ba sabida intana da tausayi yakamata ta tausaya mishi sabida bak'aramin kud'i ya kashe a bikinan ba,dan lura ma dayayi basuda karfi sosai shiyasa ya saki bakin aljihu dai dai da abincin da zasuyi a gidansu shi ya siya musu,ahaka ta kwana tana tunanin mafita har bacci b'arawo ya saceta.
Washegari k'arfe 11:30 duban mutane suka shaida d'aurin auren Kausar da Khalid akan sadaki dubu hamsin, Khalid sai washe baki yake cikin gidan yashiga da abokanansa suka sha hotuna da amarya Kausar data gaji da k'yau dan wanan Karin ba make up aka mata ba simple make up tayi ,takuma yi masifar k'yau Khalid kasa d'auke idonsa yayi akanta ji yake kamar ya rungumeta a cikin taron mutane,Allah Allah yaringayi yamma tayi akai mishi amaryarsa,bayan sunsha hotuna sitting room d'in gidan suka nufa da abokanansa dan anan aka ajiye musu abinci, amarya Kausar kuwa d'aurewa take tana dariya dan Hajiya SA'A tun da sassafe take damunta da waya akan kud'inta hakan shi ya jefata acikin zullumi da tunani,yakumbo kanwar hajjo ita tazo taja hanunta daga tsakiyar k'awayenta tace mata yayan mahaifinta na kiranta kasancewar shine walliyinta,suna isa wajensa ta durkusa akasa duka y'ayy'enta na wajen da Hajjon ita kanta,rafar dubu dari biyar biyar ya danka mata yace mata ga sadakinta ahannunta hakkinta ne tayi yanda taga dama dashi, yayi mata nasiha da add'uar zaman lafiya tskaninta da Khalid ya tashi dan yatafi,godiya tayi mishi,zuciyarta fall murna dan tasan yanzu ta samu kud'in dazata rage bashin Hajiya SA'A tasan indai tabata wanan dubu hamsin d'in zata d'aga mata K'afa,kawun nata nabarin d'akin da y'ayy'enta Hajjo ta d'auke kud'in daga cinyarta tace mata ataru rufawa juna asiri tasan cewar taci bashin mutane agarin yimata kayan d'aki sabida haka dashi zata rage bashin dake kanta,k'irga dubu goma tayi tabata tace ga shi ta rik'e ahanunta tunda kud'in hakkinta ne, Kausar gabad'aya ji tayi tarasa mai ke mata d'adi dan abinda tasa rai dashi gashi hajjo ta k'wace tahadata da dubu goma,a zuciye ta mik'awa hajjo dubu goman tace suhada su biya bashin dashi,tuni kuwa hajjo ta amshe ta sa mata albarka,mik'ewa Kausar tayi tabar d'akin rai a bace ta nufi d'akinsu Jameela ce ta tambayeta da mai yafaru taga ranta abace, labarta mata tayi,takuma d'auki wayarta ta nunawa Jameela taga yawan miss call d'in da hajiya SA'A tayi mata,akarshe ta fashe da kuka wai batasan yazatayi ba,rarrashinta Jameela tayi tace ta kwatanta mata gidan Hajiya SA'A taje ta bata hakuri ta d'aga musu k'afa,da wanan maganar hankalin Kausar ya kwanta,haka kuwa akayi Jameela taje tasamu Hajiya SA'A tabata hakurin ta d'agawa Kausar k'afa fir tak'iya tace tabasu nan da gobe Idan ba akawo mata kud'inta ba hukuma ce zata rabasu da Kausar dan wata d'aya kenan data kwasar mata kaya,babu irin ban baki da Jameela batayi mata ba tak'i ahaka suka rabu,tadawo ta gayawa Kausar yanda sukeyi da ita,atakaice abinda ya ragewa Kausar walwala kenan aranar har aka kaita gidanta tana tunanin yanda zata samu kud'i.
Khalid kuwa bayan abokanansa sun rakoshi sun siyi baki,sun musu addu'oi tashi yayi dan ya rakasu,wani abokinshi banbangida yaja shi gefe ya d'auko wani Leda yabashi yace masa kud'ine dubu dari uku da hamsin ya ajiye mishi jibi zai k'arba, dan yau babu banki ne da a banki yayi niyyar sawa bayaso kuma ya tafi da kud'in gida,karba Khalid yayi sukayi sallama yanufi cikin gida,da murmushi ya shiga d'akin yana "amaryata takaina ya zauna agefenta ya ajiye ledar akan gadon, yabud'e mayafin data rufe fuska dashi, tayi sauri ta runtse idanta Dan haka kawai takejin kunyar Khalid, wani irin runguma yamata kamar zai maidata ciki,sai daya jagwalgwalata ya cikata,yace ta tashi suje suyi alwala suyiwa Allah godiya mik'ewa yayi yad'auki ledar yabude ya fito da kud'in ciki ya duba Dan K'arba kawai yayi bai duba ba,Kausar ware idonta tayi sosai tana kallon rafar dubu dubu guda uku da rafar dari Biyar guda d'aya dake hanun Khalid, a drawer ya ajiye kud'in ya juyo tayi sauri ta kau da kanta hanunta ya rik'e suka nufi band'aki,Kausar kuwa tuni zuciyarta yafara raya mata abubuwa,ahaka sukayi sallah zuciyarta da hankalinta na wajen kud'in da Khalid ya ajiye acikin drawern,ahaka suka rayya daren tana tunanin kud'in.
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B??R??UNIY??R
??M??RY??
????♀
N??
*SADNAF*????
*&*
*ʍʀs ʄaաաaʐ*??
®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Page 45-50
Khalid dasafe shi yataya Kausar yan gyare gyare,aka kawo musu breakfast daga gidan Hajiya Zulaihat,Kausar kuwa tun asuba da Khalid yashiga wanka taringa attempting din d'aukar dubu hamsin nakai sai wata zuciyar ta hanata haka ta hakura tana tunanin yanda zatayi,bayan sun gama breakfast suna zaune a Palo suna hira,kiran Hajiya SA'A yashigo wayar Kausar gabanta ne yayi wani irin fad'uwa atake murmushin datakeyi ya kau,Khalid kuwa dayayi noticing changes d' inta once,wayar hanunta ya k'arba dan yaga wake kiranta,ganin Hajiya SA'A a rubuce ne yasa ya kalli Kausar yace " wacece Hajiya SA'A"? Kausar da take da saurin kuka tuni hawaye ya ciko a idonta,hankalin Khalid ya tashi,Kausar da tayi niyyar boye mishi amma ganin batada mafita ne yasa tace bari ta gwada fad'a masa da dai ta d'aukar masa kud'i tunda su biyu ne agidan inta d'auke mishi dole zai San itace,cikin sanyin murya tace mishi bashin Hajiya SA'A taci dubu hamsin shine take damunta,shiru Khalid yayi yana tunanin can sai yace "dan haka kike damuwa" hanunta ya ruk'o yace "beauty wlh yanzu haka banida kud'i, kud'ina duk sun kare awajen bikin nan,kinga kud'in Dana shigo dashi jiya wlh ba Nawa bane nawani abokina ne Banbangida kuma gobe yacemin zai k'arba Dana ranta nabaki amma ina zuwa bari natabo Aunty zulaihat naji ko zan samu agurinta,sai da gaban Kausar yafad'i dataji ya ambaci Hajiya Zulaihat ,wayarsa ya d'aukar yakirata yasa a handsfree sai da yakusa katsewa ta d'aga bayan sun gaigaisa ta tsokaneshi yake cemata yana bukatar kud'ine Dan Allah zai samu a gurinta,murmurshi tayi tace kar yadamu zai samu Dama tayi wanka shiryawa take tana so tazo taga amarya su gaisa Dan jibi zata bar kasar watak'ila ita da dawowa sai amarya ta haihu dan haka gata nan zuwa intazo ta kawo mishi kud'in murmushi Khalid yayi cikin Murna yace sai tak'araso,Kausar kuwa dataji mai tace tuni cikinta ya murda hanjin cikinta ya Kad'a gumi sai keto mata yake, Khalid cikin farinciki yakalleta yace sai ki kwantar da hankalinki yanzu Aunty Zulaihat zata taho mana dashi,ganin yanda ta Kausar ta canja gabad'aya hankalinta a tashe ne yasa ya ruk'ota yana " lafiya kuwa my Angel yanaga kin d'aga hankalinki bakiji abinda Aunty Zulaihat tace bane zata taho mana da kud'in ki k'wantar da hankalinki" "d'aurewa tayi tace Honey pls ka kirata kace tabarshi basai tazo ba pls anjima zankira Hajjo ta kai mata kud'in" kallon mamaki yabita dashi yace" saboda me zance kartazo ai ko badan kud'in ba tanada niyyar zuwa bakiji mai tace bane ki kwantar da hankalinki ita ta raineni babu wani Abu dan tazo" Kausar wani yawu ta hadiya kut tace "to shikenan sai tazo" mik'ewa tayi dagudu tayi band'aki dan gudawan daya matsota ,Khalid bin bayanta yayi da kallo yana mamakin yanda tabi ta firgice lokaci guda,Kausar kuwa tana band'aki rufe bakinta tayi tana kuka dan tasan yau babu makawa asirinta ya tonu dama Jameela tafad'a mata,jitayi gabad'aya ta tsani kanta wanan abun kunya ina zata kai tayiwa Kanwar sirikinta sata,indai yau hajiya Zulaihat taganta yau babu abinda zai hana ta ganeta, wani kukan takara fashewa dashi yau kwana d'aya da tarewarta Khalid zai San halinta na sata sai yau take mut'ukar nadamar abinda ta aikata watak'ila yau ne ma karshen zamanta agidan Khalid dan lura datayi da yanda yace ya tsani B'??R??UNIY?? arayuwarsa take wani zazzabi yarufeta tsaftace jikinta tayi tafito ta nufi d'akinta tana rawar d'ari Khalid jin shiru shiru bata dawo bane yasa yabi bayanta hangota dayayi akan gado tana ta rawar d'ari ne yasa yak'arasa kan gadon dasauri yana "subhanallah princess mai yasameki" kasa magana tayi hakoranta sai kar kar suke, cewa tayi ya lullub'eta da bargo sanyi takeji har fuskarta rufeta yayi,yana mata sannu ya mik'e dan ya d'auko mata magani horn ya jiyo abakin gate,yace " ga Aunty Zulaihat dinma ta k'araso inazuwa bari nashigo da ita"waje yayi dasauri,Kausar kuwa a lokacin kiris yarage tasaki fitsari sai adduoi takeyi tana karatu sadak'arwa tayi kawai yau asirinta ya tonu,zumbur ta mik'e ta zauna tana Neman hanyar guduwa dan ta gwammace ta gudu da hajiya Zulaihat ta tozarta ta agaban Khalid,jin sun doso k'ofar d'akin ne yasa tayi Saudi takoma ta kwanta k'irjinta kamar ya fito dan fargaba,sallama sukayi ,Khalid ya amsa yana Aunty Zulaihat inaga fa asibiti zan kaita jikinta yayi tsanani"hajiya Zulaihat cewa tayi ba dole ka kaita ba ka wahalar da yaya mutane,Sosa kai Khalid yayi yace kai Aunty ba abinda namata fa,zama tayi a gefen gadon tana "Amarya sannu kinji tashi muje asibiti,wani irin zazzafan hawaye ne yazubowa Kausar tana shikenan mun had'u,jitayi tana " Khalid 'd'agata mukaita asibiti"yaye bargon Khalid yayi Kausar ta runtse idonta dak'arfi,wani irin mik'ewa Hajiya Zulaihat tayi taja da baya tana kallon Kausar cewa tayi Khalid wanan B'??R??UNIY??R CE matarka,kallonta Khalid yayi cikin mamaki yace kamarya Aunty Kausar cefa naga kuma kinganta jiya,wani irin shu'umin murmushi tayi tace Alhamdulillah in k'ere na yawo zabo na yawo wataran zasu had'u ke dan ubanki bani zobena kafin naci ubanki tace tana shak'o Kausar.
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B??R??UNIY??R
??M??RY??
????♀
N??
*SADNAF*????
*&*
*ʍʀs ʄaաաaʐ*??
®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
***
In dedication to:
Eshat aysm
Aysha ali garkuwa
Momyn sultan
Maryam s bello
Janart
Husnah
Fhareeda
Dija waziri
Kausar luv
Momyn Jana
Sadnas
Mmn ihsan
Page 50-55
Kausar kallo tabi khalid dashi dan taga matakin dazai d'auka akanta.
Khalid dasauri yace "Aunty you must be mistaken wannan kausar ce ba fateema ba, dan Allah ki cikata". Yace yana k'ok'arin rik'o hannunta.
"Dalla matsa kabani waje! wannan itace wacce nake fad'a ma tayi sata a saloon d'in Aunty Oke ana shirin kaita police station na taimaketa amma dayake butulu ce sai tarasa da mai zata saka min sai tamin satar Gold d'in da mijina yabani. Ai ko a mafarki ne sai naganeta, nice har da mata nasiha nad'auko kyautar kud'i na bata, ta musa min dan ubanta tace min ba ita bace wlh da sai munje shagon Aunty Oke munje ka tambayeta kaji".
Wani irin kuka kausar tafashe dashi tace
"Hajiya wlh bani bace sai dai in kama muke da wacce ta miki sata dan ni bansan wata Aunty Oke ba, bana sata. Mai na nema na rasa hajiya akan me zanyi sata, ni bantab'a ganinki ba ma inba ranar kamuna ba".
Kausar ta fad'a tana kara fashewa da kuka
Khalid magana yafarayi cikin 6acin rai dan ya yarda da maganar kausar
"Haba Aunty? ya zaayi kausar tayi sata wlh mai kama da ita ne tamiki sata, amma badai kausar ba wlh".
Hajiya zulaihat sakin baki tayi tana kallon ikon Allah tana kuma mamakin k'arfin halin kausar. Wani tunani tayi tace "eee gaskiya ne khalid sai yanzu naga kamane suke kamar waccan tafi haske kuyi hakuri"
Kausar kallon mamaki tabi hajiya zulaihat dashi, ita kuma ta zuba mata ido. Khalid tsaki yayi yace
"Allah Aunty abinda kika min banji dad'insa ba sai kace wacce tafara tsufa yanzu wacce ta miki satar ma kin kasa ganeta bansan ma mai yasa kika damu da zoben nan haka ba dan nasan kinfi karfinshi, in kikayi niyya zaki siyi dubunshi". Murmushin tak'aici hajiya zulaihat tayi tace
" Hakane Khalid nafi k'arfin zoben da B'??R??UNIY??R ??m??RY?? ta sace min, abinda yamin ciwo shine ace nidana taimaketa ba a tozarta ta ba, ni tadawo tayiwa sata tana 'ya mace tana sata"
Duk maganar datake tanayi tana kallon kausar dan da biyu take magana, kausar kuwa k'irjinta inbanda dukan uku uku babu abinda yake dan tasan rufa mata asiri hajiya zulaihat tayi amma tasan itace.
Khalid zama yayi a gefen gadon yace "Kiyi hakuri kausar, aunty satar da aka mata ne yamata ciwo shiyasa take neman shegiyar B'ARAUNIYAR data mata sata ido rufe banji d'adi ba da aunty tace kamarku d'aya da ita yanzu sai dai muyi a hankali wajen shiga cikin mutane dan Allah kad'ai ne yasan adadin mutanen datayiwa sata kar aganki a d'auka itace kiyi hakuri kinji"
Gyad'a kai kausar tayi tana satar kallon hajiya zulaihat data k'afeta da ido.
Zama Hajiya zulaihat tayi itama tace "Khalid yafita yabasu guri zasuyi magana da Kausar"
Hankalin kausar ba k'aramin tashi yayi ba data ji abinda tace ba. Khalid kuwa dayaga fuskar Hajiya zulaihat babu wasa mik'ewa yayi yabar d'akin yana fita kausar ta sauko daga kan gadon ta durkusa agabanta, ta fara yi mata magiya.
"Hajiya dan Allah dan Annabi kiyi min rai. Wlh sharrin shaidan ne, dan Allah ki rufa min asiri kar khalid yasan nice na d'auke miki zobe dan Allah hajiya ki taimaka ki rufamin asiri"
Tunda kausar tafara yiwa hajiya zulaihat magiya, taringa mata wani wulak'antaccen kallo.
"Ke yanzu dan Allah baki ji kunya ba? Tunda nake bantab'a ganin mace mai k'arfin halin sata irinki ba, har ni dana taimaka miki. Ni zakiyiwa sata. Kash! Banji dad'in kasancewarki matar khalid ba mai zaayi da kyakyawa mara hali wlh daraja d'aya kikaci ban tozartaki ba narufa miki asiri sabida khalid bazai ji d'adi ace B'??R??UNIY?? ya aura ba naga alamar kuma yana sonki badan haka ba wlh daga kaina bazaki k'ara marmarin sata ba akarshe ina mai k'ara baki shawara wlh ki guji sata wataran dubunki zai cika a bainar jamaa karshen abun kunya dai ace kinyi sata dangin mijinki sun sani kinga kuwa kunyar dazaki ji nan gaba idan baki gyara halinki ba sai yafi yawa duk da nasan mai hali baya fasa halinsa duk ranar da kika bari khalid yasan Ke B'??R??UNIY?? CE babu abinda zai hana yasakeki kuma sai kowa yasan abunda kika aikata
Allah ubangiji ya shiryeki shirin addinin musulunci ya rabaki da san zuciya"
Mik'ewa tayi kausar tayi sauri ta rik'e mata k'afa tahau yimata godiya ko saurarenta batayi ba tayi waje.
A Palo ta tarar da khalid a zaune yana kallo, tace mishi zata tafi. Allah ya sauwake "Ameen" yace yana ta hakura da neman wacce ta mata sata tace bakomai ta hakura Allah yashiryeta hannu tasa ajaka ta d'auko dubu hamsin tabashi ta kuma d'aukar wani dubu ashirin d'in tabashi ya bawa kausar godia yaringa mata tace "Bakomai"
Har bakin motar ya rakata yadawo da murna yanufi d'akin.
A kwance yasamu kausar ta lumshe ido, ajiye kud'in yayi a gefenta yaruk'o hannunta yace
"Princess kiyi hakuri da abinda Aunty zulaihat ta miki dan Allah nasan ranki ya 6aci data dangantaki da B??R??UNIY?? tace nakara baki hakuri ga wannan tace nabaki ga kuma dubu hamsin d'in da kika tambayeni"
Yak'arasa zancen yana d'ora mata kud'in a cinyarta wani irin farinciki ne ya lullub'eta batasan lokacin data rungumeshi ba dan tana ta tunanin inda zata samu kud'i dan nasihar da hajia zulaihat ta bata ya shigeta takuma yi alk'awarin daina sata dan badan Allah ya rufa mata asiri ba da khalid yasan ita B'ARAUNIYA CE.
KAUSAR ZAKI IYA KUWA? MUJE ZUWA
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B??R??UNIY??R
??M??RY??
????♀
N??
*SADNAF*????
*&*
*ʍʀs ʄaաաaʐ*??
®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Page 55-60
Da Kud'in da Khaleed yabawa Kausar ta rage bashin wajen Hajiya SA'A, takuma ringa tunanin inda zata samu sauran kud'in dan tayi alkawari ta daina sata koda kuwa bashi zai kasheta ahaka tayi sati biyu da tarewa tana tunanin samun kud'i.
MAI HALI
Abokanan Khalid ziyara suka cewa Khalid zasu kawo musu daga nan sai matayensu su San juna,cikin murna da farinciki Khalid yasamu Kausar yafad'a mata yace mata ta tanadesu,aikuwa ran lahadi abokanan Khalid suka zo da matayensu,a d'akinta ta saukesu abokanan Khalid su kuma suka zauna apalo kayan saukar baki irin danginsu snacks tafara kaiwa abokanan Khalid kafin takai musu abinci haka ma takaiwa matayensu ta zauna suka gaigaisa tana Satan kallonsu dan kowace sanye take da sarka da dan kunne na gold ga manyan zobuna da alamu dai Khalid shine bashida hali sosai kamar mazajensu,tuni halin nata ya motsa,tafara tunanin yanda zata sace wani abun daga gurinsu dan kwana hud'u kenan wacce tahad'a mata turaren wuta ta matsa mata da ta bata kud'inta kuma bata da inda zata samu kud'i, inda su kuma suke yaba kyaun Kausar suna dama sune.
Matar Babangida ce tafara mik'ewa tace zatayi alwala Badariyya,Kausar taje ta zuba mata ruwa a buta ta nufi band'akin,bayan tafito Fatima matar Aminu tashiga,itama data fito Habiba ta mike sai data fara cire k'aton zoben hanunta tasa ajaka sanan ta nufi band'akin,Kausar kuwa tana ganin tashiga band'akin sauran kuma sallah suke,dasauri ta matsa kusa da jakar ta d'auke zoben dayake jakar bata wani rufeshi ba,barin d'akin tayi tanufi kitchen dan ta duba abincin tana shiga kitchen ta b'oye zoben a breziyarta, tana cikin juye abincin Khalid yashigo kitchen d'in dan ya duba ko tagama abincin murmushi suka sakarwa juna yace,
"Amarya ba agama bane duk kin cika mu da kamshi" murmushi tayi tace"nagama wlh bari nazuba ka tafar muku dashi,"dariya yayi yace "Amaryata ta kaina yanda kike da kyau haka kika iya girki mai dadi kai ita kanta ma Amaryar dadi gareta" rufe fuska tayi tace kai dan Allah wlh ni kana bani kunya" lakuce mata kumatu yayi adai dai lokacin dayake d'aukar farantin data jera kulollin abincin yace mata,
" dan Allah ki tabbata su Badariyya sunci abinci kinji kinsan mazajensu abokanai na ne sosai wlh ina je gidansu zakiyi mamakin irin tarb'ar dasuke min,"murmushi tayi tace ,
babu matsala ranka ya dade,kiss yamata a kumatu ya fice itama ta d'auki daya farantin tanufi d'akinta,azaune ta tarar dasu akan sallaya sunata hira Habibar data d'aukewa zobe sai zuba take suna ganin ta shigo suka hau murmushi suna mata sannu itama a kunyace tace musu yauwa dan dukansu sun girmeta farantin ta ajiye agabansu ta zuba musu abincin takoma gefe suka,suka hau ci dan su basa wani jin kunya,sai da suka kai bayan laasar agidan suka fara shirye shiryen tafiya inda Kausar ita kuma gabanta yahau fad'uwa tana adduar Allah yasa kar Habiba ta duba zobenta har sai sun tafi sai,sai da suka gama shafe shafe da pante pante,Habiba ta d'auko Jakarta ta zura hanunta dan ta d'auko zobe, zobe yace d'aukeni ahankali,gaban Kausar dukan Tara Tara yafarayi dataga yanda fuskar Habiba ya koma Habiba zazzage kayan jakarta tayi tana dube dube hankalinsu Badariyya ne yakoma kanta,Fatima tace,
"Habiba lafiya mai kike nema"? Amsa ta bata da zobenta data cire tasa ajaka take nema,Badariyya d'aurinta tacigaba da yi tace mata " ki maida hankali ki duba sosai Ai bazai bata ba,"Abu kamar wasa Habiba ba Inda bata duba ba bata ga zoben ba,Kausar kuwa cikin K'arfin hali tace"anya kuwa ajakarki kika sa zoben ko zaki duba band'aki ko fad'uwa yayi,"rai ab'ace Habiba tace " wane irin fad'uwa kuma ba agabanki na cire nasa ajakata ba ni bana alwala da zobe ahanuna" Habiba ganin fa dagaske bata ga zobenta ba yasa ta dura ashar tafara "yau zaayi ta agidanan zobena yayi layar zanna banganshi ba,ko sati baayi ba da fahad yasiyo min daga Dubai had'e da sarka da dankunne" su badariyga ma sallati suke suna duduba jakankunansu ,Kausar kuwa cikin tashin hankali tafara dube dube tana ikon Allah abinka da Mara gaskiya tuni tafara gumi,Khalid ne yashigo d'akin yana "madams mai kuke jira ne mazajenku na jiranku fa" ganin suna dube dube ne yasa yace "lafiya kuwa mai kuke nema" Kausar ce tafara magana cikin rawar murya tana masa bayanin abinda ke faruwa, sallati Khalid yayi ya kalli Habiban dake girgiza tana harare harare dan tana zargin Kausar ce ta d'auke mata zobe dan su Badariyya bazasu tab'a d'auke mata zobe ba,Khalid kallan Habiba yayi yace "garin yaya wai kika cire zoben",
Dayake Habiba bata fiye kunya ba bud'ar bakinta sai cewa tayi " Khalid agidanka zobena ya b'ata fa inaga dakazo shekaranjiya nake gaya ma katayani yiwa abokinka godiya na kyautar gold d'in dayamin sai kawai daga zuwa gidan ka na nemi zobe narasa ina bazai yiwu ba afito min da zobena kawai" tak'arasa zancen tana hararar Kausar,Kausar kuwa tuni tafara nadamar d'auke mata zobenta,Khalid kasa magana yayi yana mamakin ya akayi zoben Habiba ya bata,kwalla masa kira su babangida sukayi da mai suke jirana suna bata musu lokaci,jiki asanyaye ya nufi Palo yaje yagaya musu abinda ke faruwa,Fahad mijin Habiba mamaki ne yarufeshi ya k'wallawa Habiba kira tafito ya tambayeta abinda yafaru takara kora masa jawabi,Khalid hakuri yabata yace bari su kara dubawa ko zasu gani,yana shiga d'akin yaga Kausar sai dube dube take tana had'a gumi shima tuni yaji yafara zarginta dan yanayinta yanuna bata da gaskiya,fita yayi daga d'akin Yakoma palo yana cewa Habiba anya kuwa tazo da zoben gidanan"a "fusace Habiba tafara magana " wlh Nazi dashi gidanan agaban amaryarka ma nacire zoben nasa ajaka lokacin su badariyya suna sallah,kaga Khalid babu wani batun boye boye Amaryarka ce ta d'auke min zobe kace mata tabani zobena kawai" Khalid kasa magana yayi yana kallon Habiba dan yarasa tacewa Fahad kuwa yana ganin haka yacewa Habiba ta wuce sutafi careless ness d'inta ne yasa tarasa zobenta,Kausar kuwa data tsaya daga bakin k'ofa dafe k'irji tayi tace yazata ce ita ta d'aukar mata zobe, wani mugun ashar Habiba ta dura mata tace wlh itace ta d'auke mata tafito mata da zobenta kawai "ganin da Fahad yayi inya bar Habiba haka zata yi ta rashin mutunci ga Khalid yakasa magana kuma yanajin kunyar Khalid, tsawa ya dakawa Habiba yace ta wuce su tafi,Habiba tak'i sai daya nuna mata zai sassab'a mata tayi waje tana Allah ya isa taringa cewa Kausar B??R??UNIY??R ??M??RY??,
Fahad hakuri yabawa Khalid yace yashareta ta yar da zoben ne awani wajen batasani ba yabawa Kausar hak'uri,su babangida ma hakuri suka bawa Khalid da Kausar dake ta kuka sukayi waje,Khalid rakasu yayi har bakin mota,Kausar tana ganin sun fita tayi sauri taciro zoben daga breziyarta ta bude drawern mudubinta ta jefa shi aciki,Khalid kuwa rai abace ya dawo ya wuce Kausar dake zaune apalo tayi tagumi tana goge hawayen munafirci,d'akinta ya wuce direct yafara hargitso da kayan ta Kausar kuwa ta tsaya tana kallonsa cikin tashin hankali,tambayarsa tayi ya yard a kenan ta dau zoben,ko kallonta baiyi ba ya cigaba da birkita kayanta,ba Inda bai duba ba har akwatunanta ya sauko dashi, gaban Kausar inbanda fad'uwa babu abinda yake jikinta sai rawa yake, duk karatun dayazo bakinta sai ta karanta,ganin ya nufi gaban mudubi cikinta yayi wani irin murdawa dasauri tasha gabansa tace yanzu ya yarda zata iya sata, tureta yayi daga gabansa dan ransa ya masifar back,haka kawai ya yarda Kausar ce ta d'au zoben,drawern janyo yafara hargitsawa aikuwa sai ga zoben,d'auko zoben yayi ya juya yana kallon Kausar.
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B??R??UNIY??R
??M??RY??
????♀
N??
*SADNAF*????
*&*
*ʍʀs ʄaաաaʐ*??
®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Dedicated to all Readers of B'??R??UNIY??R ??M??RY??
Page 60-70
??
"Zoben waye wanan Kausar " ?
Khalid yace ransa a mutukar b'ace yana nufarta,
Kausar d'ora hannu tayi aka tana ja da baya dan da akwai yanda zata iya hak'a rami ta binne kanta da ta binne kanta wanan abun kunya da mai yayi kama,
"Tambayarki nake kibani amsa kafin na k'wada miki mari" Khalid yace a tsawace,
Kausar durkusawa tayi agabansa tace,
"Khalid kayi hak'uri wlh ba halina bane sharrin shaidan ne narasa yanda zanyi nasamu kud'i na biya basukan dake kaina dan Allah ka rufa min asiri" wani wulak'antacen kallo ya ringa mata can yafara magana,
"Kausar dama Ashe ke B'??R??UNIY?? ce bansani ba?,Kausar kinsan yanda na tsani mai halin b'era kuwa? namiji ma ya yak'are ballantana mace, mai kika nema kika rasa Kausar in badan rashin godiyar Allah irin naki ba,wane irin bashi kika ci da bazaki gayamin inbaki kud'i ki biya koda banida shi ko ranta ne Kausar sai nayi da ki kunyatani agaban abokaina yanzu dawane ido kike san suringa kallona,sun San kece kika d'au zoben,gaskiyar Aunty zulaihat datace ke kika d'auke mata zobe Ashe shiyasa kika bi kika rud'e dakikaji zata zo, , kafin ki mata kikayi a saloon Kausar wanan wane irin masifa ne ahaka in aka ganki kamar bazaki aikata ba,nagode wa Allah daya nuna min halinki tun wuri dan nasan kunyar da zaki sani naji nan gaba sai yafi Wanda naji yau dan haka Kausar wlh duk San da nake miki hak'ura zanyi dake dan wlh bazan iya zama da B'??R??UNIY?? ba, dan haka ki tafi gidanku idan kin gyara halinki na dawo dake," Kausar kuka ta fashe dashi tana
"Khalid karka yimin haka wlh Sharrin shaidan ne bansan ya akayi nake sata ba yanzu inkace natafi gida Khalid ka tona min asiri sati biyu da aure aga nakoma gida,tsaki yayi yabarta awajen yace kar yadawo ya sameta bazai iya zama da b'arauniya ba,kuka Kausar taringayi sosai tana nadamar d'aukewa Habiba zobe yanzu wane riba taci daya wuce shan kunya ga aurenta na rawa, Khalid k'ara dawowa yayi da mukullin mota ahannu yace tazo ta fita zai kulle gida dan zai mayarwa da Habiba zobenta,ba irin rok'on da Kausar bata masa ba yak'i sai daya ga ta d'auko hijabinta yayi waje ,itama tafito tana kallonsa kamar ba Khalid mai k'aunarta ba dan yanzu ita k'iyayyarta ta hango k'arara a idonsa,motarsa yaja yabarta a tsaye.
Kausar data isa gida kuka take sosai inda hankalin Hajjo ya tashi ba irin tambayar da bata mata ba akan ta gaya mata mai yafaru tak'i akarshe yayanta ta k'ira Murtala yazo shima yana tambayarta fir tak'i tagaya masa,Hajjo sa Murtala tayi ya kira Khalid awaya suji lafiya,Murtala yabi shawararta ya kira Khalid bayan sun gaisa yake cemasa sun ga Kausar ta dawo gida ko lafiya,ce masa yayi maganar bata waya bace zai zo gida ya samesu ya katse wayar,bayani yayiwa Hajjo abinda Khalid yace taringa sallati tana mai yafaru haka sati biyu da aure Allah yasa dai Kausar ba wani gagarumin Abu tayi ba.
Khalid kuwa dayaje gidan Fahad bai sameshi ba, Habiba yasamu a zaune a Palo sai cika take tana batsewa dan fad'a sukayi sosai da Fahad dan dagewa tayi ita fa Kausar ta biyata zobenta ko Khalid ya biyata sai da Fahad ya mata kaca kaca tukuna yabar mata gidan,tana ganin Khalid taja tsaki,hakan datayi kuwa ya masifar k'ona mishi rai,matar datake masifar girmama shi sai gashi Kausar ta janyo mishi raini agurinta,mik'a mata zoben yayi yace mata bayan sun tafi suka d'aga karkashin gado suka gani,dasauri ta amshe tana murna shikuma yajuya dan yatafi bud'ar bakin Habiba sai cewa tayi,
"Danji naji amma ban yarda akarkashin gado aka gani ba kai dai bakayi dace mata ba,ga k'yau amma ba hali", bai ce mata komai ba yafice zuciyarsa na tafasa da bacin ran abinda Habiba tayi masa yanufi gidansu Kausar tana can a kunshe a d'aki tana ta kuka,sallamarsa dataji ne yasa ta Mik'e ta zauna ta dafe k'irjinta dan tasan yau Hajjo sai ta kusa kasheta da duka intaji abinda tayi,Hajjo tabarma ta shimfid'a masa ya zauna bayan sun gaisa ya gaya mata abunda Kausar tayi masa, sallati Hajjo taringayi tana tafa hannu tana tunanin anya kausar ita kad'ai ce batada aljanu masu sata, sata hak'uri tabawa Khalid tace dan Allah kar dan haka yafaru yace zai saketa tana tunanin Kausar Aljannu ne ajikinta dasuke sata sata zata sa mallami yamata ruk'iya jikin Khalid ne yayi sanyi daya tuna fa kad'an da aikin aljannu,cemata yayi babu komai zai dawo yaji mai mallamin yace,sallama ya mata ya tafi,Kausar dake d'aki sai kuka take data ga yatafi baice akirata ba,Hajjo zuwa tayi ta sameta tace mai yakai ta sata Ashe har yanzu bata daina sata ba,fad'a sosai Hajjo taringayi uwa ta ari baki Kausar ita dai sai kukanta take tana nadamar abinda ta aikata.
Washegari wajen wani babban mallami Hajjo takai Kausar tace ya dubata ko tana da Aljannu,Mallamin kuwa dayayi yan adduoinsa yace Kausar bata da wani aljannu San zuciya ne kawai da tariga tasaba tun tana karama sai andage mata da adduar Allah ya shiryata,itama a matsayinta na mahaifiyata ta Dage da addua,ahaka suka koma gida Hajjo ta dage da adduar Allah Ya shurya Kausar taku ma sa ana tayata yiwa Kausar addua,kullum sai anyo mata rubutu tasha.
Khalid kuwa tunda yabar gidansu Kausar ya kira Hajiya zulaihat yaga mata abinda Kausar tayi masa, amadadin Hajiya zulaihat taji haushin Kausar tausayinta ne yarufeta dan tana tunanin Kausar ba ita kad'ai bace,hak'uri tabawa Khalid akan ya maida Kausar tana tunanin ba yin kanta bane Aljanu ne da ita,yadage ya ringa taya Kausar addua,da wanan shawarar da hajiya zulaihat tabawa Khalid zuciyarsa tayi sanyi,amma dayake Khalid yanada zuciya da ruk'o yakasa manta abinda Kausar tayi masa, sai da Kausar tayi wata d'aya a gida yaje gidansu ya d'aukota Kausar tabi tayi baki ta rame kullum cikin kuka take da nadamar abinda tayi.
Tunda ta koma Khalid yake k'afa k'afa da ita indai zai kwanta bacci sai yayi pillo da kud'insa Wanda hakan kesa Kausar kuka sosai dan yanzu Khalid baya baya yakeyi da ita baya sakin jiki da ita,ko waje zasuje sai yaja mata kunne akan karfa tayi d'an halin.
ALLAH MAJI ROK'O
shekara d'aya kenan da Auren Kausar bata k'ara sata ba tun zoben Habiba data sata, dan Khalid babu irin gwajin da bai mata ba dan yaga ko har yanzu inta ga Abu zata d'auke da gangan zai ajiye kud'i yanda ya ajiye haka yake zuwa yasamu abunsa,gwaji iri iri yamata amma Ina ba Kausar d'in data sani bace a da,dan ALLAH SAMIU DUA NE MAJI ROK'ON BAWANSA MAI KUMA SHIRYA BAWANSA A DUK LOKACIN DAYASO.
Khalid kuwa bak'aramin murna yayi da canzawarta ba ahaka zamansu Yakoma normal,Kausar duk lokacin data tuna irin b'arnar datayi kunya kan kamata dan kwanaki ta had'u da Aunty Oke a hanya bud'ar bakinta sai cewa tayi B'??R??UNIY??R ??M??RY?? dafatan ka daina sata dan sata ba cyau,aranar bak'aramin kunya kausar tasha ba da kuka ta dawo gida tana ta data sanin abinda tayi abaya.
Whuuuuuuuh Readers Allah yarabamu da San zuciya irin na Kausar masu hali irin nata Allah ya shiryesu Allah ya shiryemu gabaki d'aya bisa tafarkin addinin musulunci kuskuren da mukayi a wanan novel d'in Allah ya yafe mana anan muka kawo karshen wanan novel mai tak'en B'??R??UNIY??R ??M??RY??.
Download Barauniya Amarya Littafi Na Daya Complete
0 Comments
Thank you for this comment