IDAN RANA TA FITO
NA
Halima m/mashi
PAGE 1.....! Na karama motar idanu kai bani ba ma duk mutanan da ke kauyan kallon motar suke domin ni dai a sanina wannan shi ne karo na uku daga na mota kuma duk gidan hakimi take zuwa wato gidan maigari dai su ne suke da yan uwa a birni,na bi motar don in ga gidan da zata na ma manta da batun aike na a kayi kaikuwa kofar gidan maigari ta tsaya,na kuma ci gaba don ina matukar so in ga cikin motar ina son sanin ko kamar daki take? Zare idanu na yi lokacin da naga wanda ya fito daga cikin motar wani saurayi ne dan birni me kyau yana sanye da wasu irin kaya,ga kuma wani kamshi yana tashi.Sam ban san na saki baki ina kallonshi ba,ya nufi cikin gidan maigari ashe nima na bishi ban sani ba sai kurum na ji ni cikin kwata,lokacinne fa hankalina ya dawo na gane me nake yi,na kuma tuna zan je siyan kanwar miye ne.Lallai yau zan ci duka gurin Baba Gaje,babu rana ta banza da ba za a dake ni sau uku ko sau hudu ba na sani wani lokacin da laifina domin bana ganin abin kallo na wuce kuma abin mamaki ba ya wuya a gurina.Lokacin da na....! Lokacin da na dawo siyan kanwa sai da na kuma yin zagaye ta gidan maigari ko zan sake katarin ganin motar tare da wannan dan gayun dan birnin.Abinda na gani yanzu shine ya fi bani mamaki tare da daure min kai.Wata yar karamar a ba ce na gani a hannunshi ya kara ta a kunnanshi yana ta magana shi kadai ba ni ba har samarin kauyan kalloshi suke ringa yi.Ya shiga motar ya tashe ta,na so in matsa kusa da motar in taba ta ko dan in karasa amma in tsoro,haka ya tasheta ya tafi ban nufi gida ba sai da motar ta kule.Ina isa na hau rabe-rabe saboda hangowar da nayi Baba Gaje tana kwashe tuwonta,miyar kuma tana aje gefen murhu,da alama an sauke ta tuni.Ta banko min harara "sai yanzu ki ka ga damar dawowa? Yar iska shegiya matsiyaciya babu,abinda zai hana ni kirbarki yau yar asara". Na soma kuka ina cewa "Don Allah Baba kiyi hakuri". Lanto ta dube ni ke ina ki ka tsaya ne?cikin kuka na ce um....um kofar gidan maigari ne a ke kallon mota shi ne fa na dan tsaya..." Ta katse ni kallo koh? Na yi shiru,ta ci gaba da shararta.Jummala da ke can gefe ta ce "ai kallon Haka matan gidanmu suka yi ta surutu.Baba Gaje tana ci gaba da sine min, dama haka fadan gidanmu yake musamman a kaina babu wanda ke bada hakuri domin kowa yasan masifar Baba Gaje kuma tsoronta suke yi, domin ta fi su samun kudi sana'o'i babu wanda Baba Gaje bata yi, kuli, goro, man gyada, shinkafa da wake ga kuma koko, sannan duk kauyen mu ita ce uwar adashe. Ina labe bayan rumbu ina ji Babana na nemana, na fito in shashsheka,
2...Ina la6e bayan rumbu ina ji
Babana na nemana, na fito ina
shashsheka, ya ce "Jidda wai me
yasa kullum sai kin nemi laifin da za
a ta6a lafiyarki ne?" Cikin
shashshekar kuka na ce,"Baba siyan kanwa aka aike ni." Ya kama
hannuna shine ki ja samu kallanki
na tsiya ki ka dade ko? Na ce mota
ce kofar gidan Maigari shi ne na dan
tsaya ya ce, na ce ki daina tsayawa
kalle-kalle kin. Gaje dai dukanki zata yi, eh dakunta zan yi Muka ji muryar Baba Gaje dama kun saba
ku dunga la6ewa kuna zagina duk
wahalar da nake da ita ba a ganoma
ba zan yarda ba, ehe." Baba ya ce,
Saurara Gaje ni ba na hana ki dake ta ba ne ina dai yimata nasiha ne ta daina tsayawa kalle-kalle, amma
yanzun ki mata hakuri in yaso nan
gaba in ta kara sai ki dake ta. "Ai
wlh sai na dake ta, kuma ba za ta ci
tuwon gidannan ba. In aike ta don ita 'yar tsinanniya ce sai ta je ta yi zamanta, tasan zata fita da goro ta
dan zaga don mugunta ta ki
dawowa. "Na ce kiyi hkr
don......"Kafin na karasa na ji saukar mari. Baba yasa kai ya fita
don na sani ba zaya iya ganin halin
da zan shiga ba ne dama nata tsarin
in tana dukana duk wanda ya ce
tayi hkr to zata ce yana goyon
bayana ne. Daga nan sun kulla gaba ita dashi, in kuma tana gaba da ke to doke ne duk matan gidan su
daina shiga harkarki, in kuwa wata
ta kula ki to itama ta shiga. Bisa ga
wannan dalilin sai dai su sa idanu, in
ma za su yi magana sai dai su ce maganina kenan duka, haka ta jibge
ni son ranta ta sake ni tare da
shurina da kafa tayi tafiyarta, na ci
kukana na gaji na koma gefe na
ra6e. Su Indo da Shafa suka biyo
mana gada Hinde ta fiti 'yar gabn gishin Baba Gaje kenan, ta kira Salame da Laminde suka fita, na
tashi zan bi su duk da na san Hinde
zata iya koro ni sai Baba Gaje ta ce,
"Ke Kuluwa zo nan yau in ake ba
zuwa dandali sai dai kai goron nan na dawo nta nuna min tiren gashi can kin san kudinshi saura kallon ki
na tsiya ya ja ki bar goron yau ki
sha wuya, ni dai na fita." Muryar
Baba na ji ya ce,"Jidda ya ki nan." Na
je na tsugunna "Gani Baba. "Ya ce,"Ungo, nasan ba ki ci abnci ba
ko?" Na ce, "Eh." Bakar leda ya bani
ban san ko me ciki ba, ya ce," kici
kin ji? Tashi ki tafi. Ina za ki ne da
tire?" Na ce "Dandali zan kai goro."
Ya jinjina kai "kada ki damu ki zama mai hkr, Allah yaba tare da masu hakuei, tashi kije ki kula da kanku
da kuma sana'arki kin ji ko?" Na ce
"To Baba....
[18/09 9:00 am] Inna👬👫: Idan rana tafito
3... Sai da na tafi na duba naga rogo
ne da kuli, a fiki na ce Allah Sarki
Baba, Ina tafe ina ci sam ban ankara
ba sai ji na yi na ci karo da mu2m,
tuni tiren goron ya yi baya ya fadu
na fara kallon da wa na ci karo gabana ya fadi ganin Ado. Yana
tsaye yana kallona. na duka na
soma tsince goron ina fadin nashiga
3 na yau zan sha jibga in ban gansu
duka ba... Ado ya tsugunna tare da
hasko cocila 'yar karama duk da cewa akwai hasken farin wata
musamman yau watan yana 14 ya
ce duba a hankali na kalli cocilar 'yar
mai kyau ba kalar ta Babana ba da
ya ta6a sautu birni a ka siyo mishi,
sai na ji muryarshi yaba cewa ki duba mana me ki ke kallo haka? Ban
ce komai ba na ci gaba da
duddubawa banga wani ba ya ce
kirga ki gani ki ya cika, na ce ban
san ko na nawa ta zuba ba, ita ce ta
kirga da kanta, ya ciro naira 10 nawa nawa ne goron? Na ce"Da na ficika ne da na kwandala." Ya mika
min 10n "To rike wannan ki cika." Ya
yi tafiyarshi na bishi da kallo, ko
cikin mafarki bn ta6a zaton Ado
zaya iya yi min magana ba, saboda Ado Saurayi ne mai girman kai
game da jan aji, in ji 'yanmatan
kauyenmu sannan shi kadai ne ya yi
boki duk wata wasika in za a rubuta
ko za a karanta sai annemi Ado, duk
cikin kauyan shi ne babban yaron Maigari kuma duk kauyan babu
wanda ya kai Magari dukiya,
dabbobi da gonaki sannan su kadai
ne ke zuwa birni. Jin an dauke tiren
goron daga kaina sai na dawo cikin
hayyacina yare da yin firgigit don ganin ko waye.......Bint o ce kanwar Ado, ta ce Kuluwa garin kallo wata rana sai an sace ki, nayi
'yar dariya na ce "Binto ina za ki?"
Ta ce, "Dandali can za ki kai goron?
Na ce, "Eh." Ta ce "hu'um, ke dai
gaskiya ba kya hutawa gashi kin daina zuwa Mkrnt, na ce kema Binto
kin sani in ban ke ba duka zan ci
Mkrnt kuwa saboda kudin Laraba, ta
ce in daina zuwa da Baba ya bani
kuma ta kwace ta ce bani ba Mkrnta.
Binto ta ce, shi yasa na daina zuwa gidanku ce min take yi in daina kula ki kai ke kula Maza ne da ke su
Hinde sune dai-dai ni ni ko kin san
ko a dandali rana daidai ce ba ma
kwasar ta da su akanki....ko kin zo
ko ba ki ba, a haka muka isa dandali na zauna kusa da mai gyada don ta kunna aci balbal, wato fitlar
gwangwani
Mar 6, 2015
Aisha Ummu Shureim Sa'eed
4..Binto ma gurina ta zauna muna ta
hira ina bata labarin karon damu ka
yi da Yayanta, lokacin da muka
dawo gida ba wanda ya sai
goron,don haka sai na mika mata
naira goman a zuwan cinikin da nayi, ta zauna ta kirga goronta
sannan ta dube ni "Siyan goron aka
yi?" Na ce "Wani ne ya zubar min
bai sani ba shi ne ya bani."Ta daga
zaninta ta saka cikin lalitar ta tare
da cewa "Irinsu ake so, shi ko wannan wanene? Na ce "Ado ne na
gidan Maigaro."Hinde ta mike tab
karya ki ke yi, Adi ne zai saurare ki?
Sai dai in Mazan ki ki ka kula kalmar
na bakanta min rai suna nufin ni
'yar isla ce. Cikin Muryar kuka na ce kai Hinde da yaushe na kula Maza? Baba Gaje ta ce to sarkin ruwan ido
ke da ba kya raina abn kuka, in ma
Mazan ki ke kulawa ina ruwana ni
dai kudi na sani. Mikewa na hi naje
nayo alwala don yin sallah dama kullum ba a barina yin sallah sai dai in na zo kwanciya in hada gashi an
ce hada sallah babu kyau, su Baba
Gaje ma sallar ba damun su ta yi ba,
koda zata yin ma sai dai ta yi ta
dokota ba tare da tasan hukunce- hukunce nta ba. Na dawo a gajiye ga yunwa, murnata daya shinkafa da waken sun kare, na shigo da
kwarin gwiwata. Baba Gaje tana
suyar kuli ba mika mata kudin ta
kirga sannan ta kalmashe ta zuba
cikin lalita ga sauran tuwi can dauki kici ki zo ki fita da wancan kunun, na dube ta Baba bana Hinde ba ne? Cike
da masifa ta hayyako min, eh nata
ne ta gaji don haka maza ki fita da
shi kuma kada ki dawo min da ko
kwano daya ne hakan na fita da kunun tsamiyar, ina Hawaye
tsautsayi na fito ta lungun gidan
Liman zan bi layin gidan Maigari
domin in kai ma wasu masu faskare
icen gidan Maigari kawai sai ga wani
yaro ya shigo da gudu ya bangaje ni kafin na yi wani kokari tuni tiren ya fado, kunun ya zube........... Jikina yana rawa na shiga kuka ina cewa sai naje gidanku an biya ni n
[18/09 9:00 am] Inna👬👫: IDAN RANA TA FITO
( 7)..! Na ce ta rasu, nan na soma kuka domin tunowa da na yi da mahaifiyata, ya ce daina kuka kada wani ya zo wucewa ya ji ya zargi wani abu daban, Allah ya jikanta. Cikin kuka na ce Ameen. Na dube shi. Mahaifiyata yar kauyen Rimi ce a can sumaila, shi ko Babana dan asalin nan kauyanne, wato farau ta nan Garko. An ce ya auro ta ne sanadin wani abokinshi, wanda ya kasance dan Rimin mahaifanta sun rasu sai wanta gurin shi take zaune kuma shi ne ya aurar da ita ga mahaifinmu, kamar yanda ka sani gidanmu gida ne da ya tara yan uwa wato gidan gado. Babanmu shi ne babba yana da kanne hudu kowanne da matarshi sai ko autarsu Baba Dije tana aure a sekahu, mahaifiyata ladidi ta samu Gaje uwargida da ya yanta shida. Sani da Awwalu da Musa, isa da kuma Hamisu sai cikin Hinde masifaffiya ce sosai, kaf gidan kowa tsoronta yake ji haka nan shima Babanmu yana shakkarta yanda Babana yake bani labari tun da aka kawo mahaifiyata gidan sam bata huta ba duk ayyuka da na gidan da na saidawa mahaifiyata ce ke yinsu, ko lokacin da take da cikina ba sauki rai da take mata,ya ce min ....! Wasu ma suna zargin cewa ita ce ajalin mahaifiyata domin ita ce a kanta lokacin da zata haihu, ta hana kowa shiga har ta haihu sannan ta fito ta sanar da haihuwar tare da rasuwa, a nan ne kowa ya zarge ta sai dai babu mai hujjar fadin hakan. Da wuya tana kisa kila da na mutu tun ina jaririya, madarar shanu nasha na girma ko yaushe ina gurin babana saboda Baba Gaje bata da lokacina kuma ta hana wasu su dauke ni in nayi kashi kuwa zagi da tsinawa haka take min uma sai dai mahaifinah ya wanke min, lokacin da na soma zama zuwa rarrafe idan nayi mata yarban nata yara dukana take yi iyaka karfinta hakanata so, babanah ya ce ba zai manta lokacin da na yi kyanda ba ya cire rai da ni danta yi min mugun ka mu gashi babu kulawa shi ne ya ke jinyata, ya ce a duk sanda ya fita neman dan na cefane ko yaje masallaci ko a ka kira shi yin aski baya sa ran cewa zai dawo ya same ni da rai in ma kashi nayi ko amai ko dai wani abu haka sai sanda ya dawn zaya gyara ni shi ne ya koya min sallah da kuma karatu, kai duk wata tarbiya da ya dace uwata ko ya ma yarta shi ne ya koya min sai da na soma zuwa makarantar allo sannan Baba Gaje ta maido dani dakinta ashe da! Ashe da manufa tayi hakan, nan ta kara sana'o'i talla kuwa tun daga lokacin na duka yinta ina siyar na tsira in ban saida ba duka, sannan Hinde in ta dawo da nata ni ce zan hada duka. Ado ya yi ajiyar zuciya cikin tausayi ya ce toh sauran mazan gidan dukh babu wanda zaya iya daukan wani mataki kanta??? Na ce babu saboda gurinta suke rancan kudi randa basu samu ba ka gako ba za su so su bata da ita bai ni fa gidan bani da wani gata sai mahaifina haka kuma ya yansu su hadu ne kanmu daya dasu amma ban isa ko magana in suna yi in saka baki ba, sai su shiga zagina ya ce yau fa wane laifin ki ka yi?? Na sanar dashi komai, ya mike ya nufi gurin akwatin shi ya bude ya ciro kudi. Kunun na nawa ne?? Na ce na talatin ne ya bani sannan ya ce ina zuwa. Cikin gida ya shiga kai tsaye dakin mahaifiyarshi ya ce Baba bani tuwan ta ce shigo ka dauka mana, ka kuma canza shawara ne za ka ci?? Abokiyar zamanta da ke zaune a kofar dakin tana gyaran waken kosan safe na karyawa ta ce Ado yau kaine za ka ci tuwon dawa? Ya ce Baba ya ya zan yi na nemi wani abun ban samu ba. Kakarshi da ke can kwance ta ce gara Ta ce gara dai ka ci ko kayi karfi kana dan karkara ka ce ba za ka ci dawa ba? Haja za ki sa in fasa. Ta ce toh fasa mana, yau ka kwana da yunwa. Ya fita yana dariya. Ya dire min abincin a gaba tare da cewa kici sai in raka ki gida. Na ce zata iya kala maka sharri fa, ya ce gurin mahaifinki zan kai ki na ce, toh ya shiga ya kawo min ruwa kallon mamaki ya bini dashi nasan mamakin ganin yanda nake cin tuwon tamkar nama yake yi ban taba cin tuwon ma dadinshi ba kuma har da rama, na side kwanukan tas na sha ruwa sannan na jingina da bango ina ajiyar zuciya ya kalle ni cike da tausayi kila na jima banci abinci ba, ya ce ina zuwa dubawa ya yi ko har yanxu masu neman din suna nan? Ganin sun tafi ya shige ya ce min taso muje. Babana yana tsaye kofar gidanmu yana ta leken hanyar da zan bullo sai gamu, ina gaba Ado yana biye dani har kasa ya tsugunna ya gaida Babana, ni kuma ina tsaye kusa da Baban, ya ce Ado gidanku taje? Nan Ado ya koro mishi bayanin yanda ya ganni Baba ya ce na gode Ado ni kuma na nuna ma Baba kudin tare da cewa gashi ma ya ce in kai mata kudin kunun. Nan baba ya sake yin godiya ga Ado, shi kuwa Ado cewa ya yi Baba don Allah .. ..! Baba don Allah kasa ido sosai akanta in za a ci gaba da matsa mata irin na wata rana za a yi da na sani, ko dai ta bar garin ko kuma ta hadu da bata gari wadanda zasu bata kudi su cutar da ita, ba a fata. Baba ya ce, toh zan kokarta lamarin ne wato sai dai Allah. Ado ya ce toh ni zan tafi, ga kudin nan don Allah kada su dake ta. Baba ya ce toh na gode na gode. Shi ne ya kai ni har dakin Baba Gaje, dama tun kafin mu iso ya ce in mun shiga in bata hakuri muna shiga ta kalle mu dama kai ne ka boye ta ko?? Ya ce haba Gaje ya ya zan boye ta bayan nasan duk tsiya dole ta dawo nan ta kwana,ni kuwa sai na mika mata kudin tare da cewa Baba ga kudin. Cikin sauri ta amsa tare da cewa Baba ga kudin. Cikin sauri ta amsa tare da kirgawa sannan ta ce in sha. Gobe ma in halinki ne ki kara. Baba ya ce Amma Gaje ai kya tambayi in da ta samo kudin nan ko? Ta kalle shi ta watsar, sannan ta ce kana yi kamar baka san wacece ni ba, to ina ruwana da inda ta samo kudi? Nasan dai ba zai wuce mazanta ta kula suka bata ba.
8----Baba ya ce gaskia Gaje ya dace ki dinga yiwa yarinyar nan adalci ita da Hinde dukansu ya yanki ne ta mike tsaye gara ka dake ni ko ka huce, ya ce batun duk bai kai nan Ba, kiyi hakuri ta ce ka ishe ni da batun wani adalci, adalci ban san shi ba,kuma kuluwa da Hinde suna da bambanci don ko kai ma ka nuna, ko ba kuluwanka zaba ba??? Ya ce ba zabenta na yi ba, ina dai tausaya mata ne, ni duk daya na dauke su, tunda ni na haife su. Ta ce ni na bambanta, me ake yi da kuluwa watsattsiya ya dube ta da dai na kowa ne kuma fa ta nagari lamiri ne ya sa kai ya fice ya barta tana cewa, toh ba sai ka sake ni ka zauna da kuluwan ba ta juyo ta zubamin don kwashi a tsakiyar kai koma daddiyar banza tashi mun a kai ni har cikin ya tsana naji rankwashin tamkar in saki fitsari, ...OHHH NI HAANAT NAGA MASIFEFFIYAR MATA. Na koma can gurin kwanciyata na rabe kan yan tsummokaran kayana. Shi ko Ado dakin haja ya koma wato kakarshi mahaifiyar babanshi Dattijuwa mai shekaru taga jiya tana ganin yau, gobe sai Allah haja ta haifi yaya da dama suna rasuwa da mijinta marigayi malam shehu maigari na yanzu Alhaji sallau, sai kanin shi maigari kawo kenan Alhaji sidi sai ko kanwarsu kuma yar auta mai suna Mairo ta yi aure an kai ta Garko mijinta Alhaji Dahiru dagabisani suka koma! Cikin kano,dan shi ma'aikaci ne na gwamnati domin yana daya daga cikin wadanda suka ya boko zamanin ana gudun bokon, gwammaja suka zauna daga bisani ya samu matsayin sakataran gwamnati suka koma nasarawa cikin jerin gidajan masu kudi. Mairo ta rasu gurin haihuwar ta ta biyu, bayan gama zaman makoki haja ta koma kauye tare da jikanta Muhammadu Bello, gurinta ya zauna har shekaru shida sannan mahaifinshi yazo ya dauke shi don saka shi a makaranta. Duki hutu ana kawo shi kauye gurin haja kafin a kai shi kasar waje. Ado ya zauna bakin gadonta ya ce tsohuwa mai dan koko, Allah kashe ki musha gunba. Ta ce raggon namiji daga ina kuma?? Ko gurin budurwarka ka je?? Ya ce Ai kin san dai ni bani da wata budurwa a kauyannan. Ta ce, ka zauna karatun shirme har ka tsufa. Ya ce haja don bakya zuwa birni ne shi yasa da kin ga maza manya ba su yi aure ba suna karatu. Ai ni insha Allah zan kafa tarihi a kauyannan. Haja ta ce burinka kenan kullum tadinka kenan. Ya ce ki taya ni da addu'a. Ta ce, ina yi amma na fita
[18/09 9:00 am] Inna👬👫: IDAN RANA TA FITO 5.. Jikina yana rawa na shiga kuka ina cewa sai naje gidanku an biya ni na kwashe kwanukan na nufi gida, koda na shaida ma Baba Gaje ta ce ita fa ba sunanta sarai ba, don haka in je gidan su yaron in amso mata kudin ta ai dama ta kula ba da son Raina na dauki kunun ba, in ko ba haka ba tasha alwashin yau sai ta sumar dani. Cikin kuka na nufi gidan malam bawa da yake nasan yaron,Lanto ta ce bata maganin sisi bare naira talatin, in je in yi hakuri na ce za a dake ni ne ta ce ai shima din zata dake shi. Tun daga nan ban koma gida ba in bi wannan layin in bi wannan soron har dare. Lokacin da na hango yaya Auwalu da musa nasan ni za su kama, don haka da na killa da god sai zauran gidan Maigari. (soro) zaure biyar ne a gidan kafin ka shiga ainihin cikin gidan, zauran farko da dakin baki ciki zaure na biyu har zuwa na karshe duk na samarin gidan ne wato dakunan su na cikin zaurukan, zauran da ke tsakiya wato na uku kenan shine ake cewa zauran duhu. Ko da rana ne dindim yake nan na labe. Tun dana ga yau har da cocilar ta taba su musa don su nemo ni hakika tana nufin aikata abinda ta furta. Ina nan tsugunne sai kawai na ji an yi karo dani sannan aka ce wanene? Ban yi magana ba na kuma lafewa. Ya dallaro ni da yar cocilarshi tare da zuba min idanu, ke daga ina? 6...."Na yi shuru tashi mana, ya doka min tsawa jikinah na bari na mike. Me ya kawo ki nan? Cikin dashasshiyar murya
Da ta disashe da kuka na ce za'a dake ni ne ya ce wa zai da ke ki? Na ce Baba Gaje ta ce sai ta sumar dani kuma wallahy zata iya. Ya tuno kwanaki ita ce yarinyar da suka yi karo tayi bari, ya tuna kalaman da take furtawa tana kuka. Ya ji muryar wasu a zauran farko sai ya kashe cocilar ni kuma sai na lafe jikin bango su musa ne ya tare sua zaure na biyu yana tambayar su, wasu ke nema? Suka ce wata yarinya ce kanwarsu ta yi laifi ta gudu ya ce to an ce muka tana nan ne? Suka ce a'a za dai su duba ne ya ce musu to babu kowa su fita, nan suka yi waje ya dawo gurina zo nan,na bishi zuwa wani daki nan cikin zauran duhu, yar katifa ce da filo tasha shinfida kasan kuwa wata leda ce mai santsi sannan bangon dakin yasha ado da farin fenti an yarfa baki a jiki sai wata adaka wato akwati tana dore kan wani dan tebur gaskiya dakin ya tsaru ya zauna kan kujerar katako ita kadai ce cikin dakin sannan ya yi min umarni da in zauna gefen katifar. Ado ya ce min ya sunanki? Na ce sunana kuluwa, amma babana yana kirana jidda, ya ce wanene baban naki? Malam kasim ya dan yi jim, sannan ya ce nan gidan wanzamai? Na ce eh, to ina mahaifiyarki?
[18/09 9:00 am] Inna👬👫: Idan rana tafito
9.... Ado Ya ce, ya dace su Baba su taka
mata birki. Haja ta kama baki ina
aka ta6a jin anyi haka?" Ya ce, To ba
shi ne Maigari ba?" ta ce, don kawai
yana Maigari sai ya kama shiga
harkar gidan wani? Ina ce sai an kawo kara sannan zai yi hukunci?
Ado ya ce don dai kauye ne, amma
can birni har kungiya akwai me kare
hakkin kananan yara." Haja ta ce, to
ai su kansu waye yake." Ya mike
tare da cewa bari in je in duba wani littafi, ta ce aikinka dai kenan krt, a
tsurama littafi ido shi ba kur'ani ba
ba Ahalari ba." Ya fita yana dry tare
da cewa shima Kur'anin mukan duba
shi ta kwanta tare da fadin "karyar
banza.... Muna zaune ni da Binto muna hira ina bata lbrn taimakon
da wanta Ado ya yi min,
kasancewar yau Lahadi domin duk
lahadi nakan samu sassauci don
Baba Gaje tana zuwa cin kasuwar
Lahadin-Makoli, wani sa'in ma har da Hinde take zuwa. Yau kam bata
je da Hinde ba, suna zaune can
gindin bishiya suna hirarsu ita da su
Salame. Ashe zancanmu suke yi.
Hinde tana son yin kawance da
Binto amma ita Binto a gabn kowa tana nuna cewa ni ce kawai kawarta
kuma dalilina take zuwa gidanmu,
to ashe suna jinmu lkcn da na ke
cewa, Binto Adonko yana da
mutunci don ranar ya taimake ni, to
bayan tafiyar Binto na dawo daga rakiyarta sai su Hinde suka zo suka
sani a tsakiya. "Mun ji kina cewa
Adon su Binto yana da mutunci, mu
za ki yiwa salo? Me ya hada ku da
shi?" Na ce To ni ai da Binto muke
hirarmu ba da ku ba."Laminde ta ce, "Dalla can ku kyaleta Ado ne ma zai
kula ki ga kyawawan 'yammata
cikin kauyannan bai kula su ba sai
ke kucaka, kazama, mummuna,
baka 'ya matsiyata da ke Na ce "To ni na ce muku da wani
abu ne tsakaninmu, in ina ruwana
ma da samari. Amina ta ce, "Ina dai
ruwan su da ke ai ke bandaro za ki
yi, Hinde ta ce, "To wane mahaukaci
ne zai aure ki ma dubatta da Allah su Jummala wato mahaifiyar Salame
sai sheke dry suke dama suma
manyan da kansu ba'ar da suke min
kenan. Na bar musu gurin na koma
can gefe daya na zauna ina
tunani.........10 ...Na sani ni baka ce kuma ba na daga cikin kyawawa,
gaskiya ne su Hinde ba karya suka
yi ba, sun fini kyau, don haka ban
ta6a tunanin cewa za a wayi gari
wani namiji zai zo ya ce yana sona
ba, bare irn su Ado dangin Maigari, ga kyau ga krtn boko gashi yana
zuwa birni yana ganin masu kyau,
yanda Binto ke bani lbrn matan
birni ina so kafin Allah ya dauki
raina ya kawo sanadin zuwana
birni,, insha kallo in ga irin hanyar da Binto ke bani lbr wai ko min dare
zaka samu titi da haske wai na
lantarki da ruwan da ta ce ana
matso shi wai na ko famfo! Muryar
Baba naji yana cewa. Jidda lafiya ki
ka yi tagumi? Na mike tare da amsar jakarshi ta wanzanci na ce
"Sannu da zuwa Baba, ina tunanin
birni ne, wai Baba kai baka da dangi
a birni ne?" Ya yi murmushi bani da
kowa a cikin birni sai dai a da
mukan je rani ya nufi dakin shi na bishi ina cewa ni dai ina so in je birni
ko dan na yi kallon abubuwan da
Binto take bani labari ya yi dariya
dai-dai lkcn ya zauna gefen 'yar
katifarshi ta rimi (wato ta auduga).
Ke jidda in ki ka je birni ai sai ki 6ace saboda shegen kallon tsiya na yi
murmushi in Binto tana bani labrin
birni Baba sai in ji tamkar gani a
garin ina son zuwa koda nan
kasuwar GARKO, amma Baba kaje ta
ki Baba ya dube ni cikin tausayawa, kada ki da mu wata rana za ki je har
birnin ma na yi dry bari na dibo
maka ruwan sha. *************** Ranar kasuwar Garko ina zuba abinci siyarwa cikin kwanuka ina
kallon su Hinde suna ta kwalliya don
zuwa kasuwa su da kawayanzu
dama duk ran kasuwa Hinde bata
zuwa talla. Sha'awarsu nake sunci
ado gashi sun jan baki, Hinde har da turaran dan duwala da Baba Gaje ta
siyo mata daga kasuwar Makoli ga
sabuwar atamfarta gami da
gyalanta. A raina ina cewa Allah ka
kaini in ga na shafa janbaki koda ba
zai min kyau ba in dai ji yanda ake yi saukar dundun na ji a gadon
bayana.........
[18/09 3:32 pm] Inna👬👫: Idan rana tafito
11...Husna ta ce, " yes nima na
manta ne wai ka jirata in ka dawo.
Ya mike tare da cewa "Allah yasa ta
yi sauri don wanka kawai zan yi na
fita. "Ya nufi gefenshi, dauke da
goran ruwan FARO. Ya fito cikin wando Jeans baki da T-shirt mai
kalar sararin samaniya. Yana da
kyau namiji mai sufar karfi dogo
mai kwarjini da haiba. Sai dai miskili
ne wai kafi mahaukaci bn haushi, shi
ne dan farko gurin mahaifinshi Alhj Tahir, kuma da namiji kacal, wanda kuma yafi soyuwa a zuciyar
mahaifin saboda biayayyarsa da
kuma kwazon sa. Ya yi karatun sa
na primary a S.S.B. Nursery and
primary da ke Nasarawa sannan ya yi secondary dinsa a kasan England har zuwa Jami'a din shi. A son
mahaifin nasa ya so ya zama Likita
ne amma sai dan nasa ya rikede
zuwa Dan Sanda ya halarci-kwasa-k wasai tare da dabru na binciko masu laifuka daban-daban kuma yana durowa gida Nigerai bai sha
wahala ba hukumar "yan Sandan
ciki ta kasa ta dauke shi aiki,
dubuwar farko samun matsayi
babba. M.B. Tahir dan Sandan ciki ne yana da kimanin shekaru 28. Hjy Shuwa matar mahaifinsa tana da
yara 2 Hunsa 'yar shekara sha 18 da
kuma Safina 'yar 14, kyakkyawar
mace ce mai ji da kanta 'yar boko ce
ma'ikaciya a (NNPC). Alhj Tahir na sonta sosai ya aure ta ne bayan mutuwar mai dakinshi Hjy Maryam
mahaifiyar M.B din shi ne Silar da
Alhj Tahir din ya kai shi kasan Turai
don ya yi krtn shi na gaba da
primary, lkcn da ya dawo a matsayin dan sandan ciki kwararre,
sai Hjy Shuwa ta 6oye akidarta ta
kin nashi nunuwa ta ke yi tana
sonsa, tamkar dan da ta haifa nan
ko me zata yi ta kan yi shawara da
shi nufin ta dole sai ya yarda kaunarshi ta ke tamkar daga cikinta haife shi, shi ko ya jima da harbo
jirginta yana dai binta ne sau da
kafa da kuma addu'ar Allah yasa
nan gaba ta canza hali ita kam cikin
zuciyarta matukar kin shi take yi, taso a ce 'ya'yanta maza ne gashi tuni haihuwar ta tsaya cak, nata
ra'ayin 'ya'yanta su zama su kadai
ne gurin mijin nata su gaji dibn
dukiyar da mahaifin nasu dashi ne,
mahaifin ta Alhj Shu'aibu Turaki Dan Majalisa ne na Tarayya mutumin Maiduguri ne asali, mahaifyarta
Shuwa Arab ce ta rasu duk a fi
shekara 3 ba. Su 4 ne gurin mahaifin
nata kuma ita ce babba, kannanta
guda 2 Nasir da Nazir, sai ko 'yar Autarsu Basma.
12..Kwance yake ruf da ciki a
tsakiyar gadonsa, kafafunshi suna
zube a kasa, yayinda ya doro
cikinshi da hannunwanshi da kuma
kanshi a filo. Ya mikar da filon ne
tsaye maimakon ya gicciye shi kamar yanda a ka fi yi, bacci yake yi domin duk kwanakin nan wani aiki
ya hana shi bacci. kowanne lkc ya fi
maida hankalinshi ga yanda zaya
binciko wadanda ke yiwa Familyn
A.D Biliya tsohon Ministan Abuja kisan mummuke, sai a jiya ne aikin
ya kammalu, don haka ya samu
wannan baccin. Sama-sama yake jin
wayarshi tana rigin, kusan sau 4
kenan cike da bacci ya kalli fuskar
wayar, tsaki yaja sannan ya daga wayar Husna ya ya? Hjy ta ce kazo zamu fita ne har da Dady." "Ina
zamu?" ya tambaya. Ta ce, "Sai ka
zo za ta fada maka." Ya kashe
sannan ya yi mika sosai, ya shiga
toilet, ruwa ya watsa ya fito, ya yi fes cikin blue Jeans da farar riga, M.B yana son kananan kaya in ka gan
shi da shadda ko yadi to Dady ne ya
dinka mishi su, kuma ya tilasta
mishi sa su in za su je daurin aure
ko ziyarar dangi ya same su cikin falon shi da mahaifinshi kawai a ke jira. Cikin girmamawa ya kalle ta,
Sannu Hjy cikin murmushi ta ce
yawwa MUHAMMAD ka koyi kyau
sosai, Safina ta ce, Hjy Bros ya san
kaya fa, duk kayan da yasa suna yi mishi kyau sosai, Husna da Hjy suka hada baki gurin cewa tabbas, Guntu
murmushi ya yi, na gode. Ya dan
yamutsa fuska ina za mu? Za ka gani
bari Dady ya fito. Itama haka take
kiran Maigidan nata. Muryar Dady suka ji ya ce, "Gani na fito." Ga zaton M.B gidan abokan Dady za su kila
ana yin wani abinne, to kuma biki
ranar Sunday? Haka dai ya yi ta
sakawa yayinda suke tafe cikin jin
dadi. Direba ke jan su gefen shi M.B ne baya su Dady da Hjy tsakiya kuwa su Husna. Shahararren gurin
shakatawar suka nufa bayan
[18/09 3:52 pm] Inna👬👫: Idan rana tafito
13.....Cikin mamaki gami da sha'awa
Shuwa ta ce, "Kin birge ni, kai Allah
ya ba ki 'ya'ya masu zuciya, ni su
Husna ba su da kishin kai da kyar in
za su bani hadin kai. Yanzun kuma
kudin ku na nan dankare?" Kilishi ta dube ta sosai matar ta zo nima haujaciya ce zan bari ya auro matar
ta same ni da yara guda 3 ba dadi
sannan ta baje wannan ta yi
zazzaga haihuwa mata da maza
haihuwarta fa 7, Shuwa ta ce tabdi gaskiya bn da wannan dabarar da tuni kudi sai dai a samanku, nima
yanzun dabara hada shi nayi da
Autarmu BASMA kuma tuni ya shige
ciki ma'ana ya soma ruftawa cikin
gadar zaren da na hada, domin zuciyarshi ta shagaltu da sonta.
Kilishi ta nisa da cewa, "Menene
dabarar?" Shuwa ta ce "zan gyara
wani kuskure ne da na yi can baya
lkcn yaron yana karami, na nuna
mishi tsabar kiyayya karara inda na ringa hada shi da shokin in kona shi da wuta cikin tafin hannu ko kuma
in zuba mishi barkono a idanu. Tilas
ce tasa mahaifinsa ya fita dashi waje
ba don yaso ba. Kilishi bai tashi
dawo min ba sai a matsayin Dan sandan ciki, shi da ya tafi karatun Likita, kin san dole ne sai da dabaru
kafin in cimma burina?" ta dan
dakata kafin ta ci gaba "Ina so ne da
zarar an daura auransu kafin shi da
BASMA, sai in bata guba ta zuba mishi cikin ruwan sanyi ma'ana ba
tare da kowa ya zarge mu ba. Yana
mutuwa shi kenan daga ni sai
'ya'yana sannan tasu dukiyar ta
gada domin yana amsar makudan
kudi albashin sa bn da hayar da wasu kasashen suke yi. Hjy Kilishi ta ce, "Kina nufin har wasi kasashen
suna hayar shi? Shuwa ta ce,"sosai
kuwa, ya kware matuka kan aikinshi
kasar da ya yi krt sun so rike shi da
kyar suka bar shi ya dawo gida. Kilshi ta yi ajiyar zuciya tare da girgiza kai. Shawarata a nan ki bi
sannu ki hana da hikimomi nasan
wannan partyn da ki ka hada yana
daga cikin dabarunki na son ki nuna
kina son shi, sannan ya manta cewa kin ta6a mishi azaba. Shuwa ta ce, "Kin gane kawata, kuma a duk lkcn
da na fahimce kwa6ata zaya yi ruwa
zan kira ki in nemi shawararki don
kina da basira. Suka yi dariya irin ta
kawaye, sannan Kilishi ta sure Jakarta Bari in tafi sai na ji daga gare ki. Har gurin mota ta yi mata
tattaki inda direba ya ja suka yi
sallama ta dawo ciki.*********
.14....Ina tafiya na dawo talla na
hango BINTO, kira na kwala mata ta
juyo sannan ta nufo ni da fara'arta,
ta ce gida za ki? Na ce, eh, Yaya ADO
yana gida? Binto ta ce, Eh, na barshi
gida, na ce, mu dan je ya kara min mana domin na haddace na jiya. BINTO ta ce haba?" Na ce, Allah
kuwa, ai zan ma biya za ki ji. ADO na zaune kofar gida yana
dauke da wani littafi yana nazari, na
durkusa na gaishe shi, cikin fara'a ya
amsa tare da cewa, kin zo ne? Na ce,
eh, ya ce shiga ina zuwa, ban jima
ba ya shigo don ya sani lkcn nawa kilalanne, ya ce biya in don ya ji na jiyan. Na yi Bismillah sannan na
karanta, ya kara min wani da haka
na iya addu'o'i da dama Cikin Haka ne batun auren su BINTO,
ya tashi domi kaka ta matso su
HINDE ma duk an kawo kudinsu ni
kadai ce babu manemi to wa zai so
ni, ni ba kyau ba ga kazanta, bugu
da kari ga ni baka, su ko na lura samarin kauyanmu in dai kina fara komai muninki za ki samu miji, na
lura abn yana damun Babana, ni ko
bn damu ba don zancan da ni ke
lkcn fa shekaruna 12 an ce ma wai
sai watan Mauladi ya kama. ADO yana kwance a shimfidarsa,
zuciyarsa tana nazari, ne a kan Jidda
yana son taimakon yarinyar sai dai
ya rasa me zai yi don ganin ta fita
cikin halin da ta ke, gata da kwazo
shi dai ya shaku da JIDDA, har ma yana cewa da ya tashi aure ne babu abn da zai hana shi aurenta, Bai
damu da so ba ba ya sani suna tare
wataran zai so ta. Sama'ila ne ya katse mishi tunanshi
da sallama, ya amsa ya tashi zaune
dai-dai lkcn da shima ya zauna kan
kujerar katakon dakin....
Mar 7, 2015
Aisha Ummu Shureim Sa'eed
24...Ya kalli Ado ya ce, "ya naganka
kwance ina fatan dai lafiya?" ADO ya
yi ajiyar zuciya, "Wlh lafiya ta lau,
wani abu ne ke damuna.'" SAMA'ILA,
ya ce "Me ke nan?" ADO ya ce,"kan
zancen KULUWA ne, Ina matukar tausayin yarinyar gashi d
[18/09 4:50 pm] Inna👬👫: Idan rana tafito
15.....Sama'ila ya ce, "To Allah ya za6a mana abinda ya fi zama
alkairi."Ado ya ce,"Amin. Wata rana da daddare an aike ni
kar6o kudin dashi ina tafe da 'yar
sandata ina wakar "wayyo Allah na
wayya Allah na kalalla6a tashi ga
idona kalalla6a, wanda ya cire min
kalalla6a, shi ne mijina, sai na ji murayar ADO ya ce Kalalla6a, ya iso
gurina. Bayan na tsaya ya dube ni
gani zan cire miki, na sunkuyar da
kai sannan na ce, "Yaya Ado ai kai
Malamina ne." Ya ce, daga ina haka? Na ce amso kudin dashi naje,
Ya ce, zo nan dama ina son in yi
wata magana da ke. Jingina ya yi
daga jikin wata, bishiya da ke nesa
dama kadan, hasken farin wata ya
haske gurin. Ya zuba min idanunshi, ni ko kaina na kasa ina wasa da
kudin hannuna, ya ce, "JIDDA kina
jina?" Na ce ina jin ka, sai na ji
kalmar saukar aradu,
za ki aure ni?"
Sai da na yi tamkar zan fadi don firgici, sannan na gyara tsayuwata
na ce, "Uhum, Yaya AdO kenan. Yaushe muka sona 'yar tsokana?"
Ya ce, "Gaske ni ke magana." Na yi
murmushi a zotana ko da wani zaya
tsokane ni ban da kai, duk
kyawawan 'yanmatan kauyan nan
suna burin ko magana ka dinga musy ciki har da yata Hinde duk ba
ka ce zaka aure su ba sai ni KAZAMA,
MUMMUNA,BAKA, MARAINIYA,
MARAR GATA?" Tausayinta ya kuma cika shi, ya uba
hannunwanshi cikin aljihu, JIDDA ni
ko kin ga wadannan abubuwan da
ki ka lissafa sune suka kwadaita min
auran ki.
Na kalle shi cikin mamaki, sannan na girgiza kai. "Yaya Ado na sani kana dai tausaya
min ne amma ba sona ka ke yi ba.
Shi aure zama ne ba na kare ba, in
ka aure ni zaka yi na dama a gaba."
ya ce,"JIDDA kina da hangen nesa,
sai dai bana jin hakan ata faru insha Allah, abn da kawai nake so ki
amince dani kuma daga yau zan
soma zuwa zance gidanku. Edited · Like · 3 · Report · Sep 6, 2014 Aishat Yusuf sannu mmy ashe an maido miki da
16...Na yi 'yar dariya zaka sa Baba
Gaje ta kara tsanata kenan, don tana
maida ni baya ne saboda kada wani
ya nuna yana sona.
Ado ya ce, "To ai "IDAN RANA TA
FITO TAFIN HANNU BA YA KARE TA, ki je gida sai na zo, ."Na tafi ina waigen
shi, anya kuwa ma Ado ne?" Ko dai
wani Aljanin ne? Abin da na saka wa
a zuciyata kenan. Washe gari muna zaune a tsakar
gida, Hinde suna ta cin abincin su da
su Jummala ba sa ci da ni ni ko ina
can gefe ina cin nawa murfin kwano,
hirar samarin suke yi suna min
haibaici tare da wakar zanbo wai Allah min tsarin da auran kazama
na tashi naje nayo Sallar Isha'i na
dawo na zauna, sai ga sallamar
Baffa kanin Ado,
ya ce, sannunku,
suka amsa ya ce wai ana sallama da JIDDA,
Hinde ta ce, Jidda kuwa a ka ce,
maka?"
"Ya ce, "Eh in ji Yaya Ado."
Baba Gaje ta ce "Yana ina?"
Baffa ya ce gashi nan a waje ta ce to ka ce tana zuwa. Ta kwala wa Hinde
kira zo ki je kin ji Ado, yana kiranki,
dan nasan ke yake kira ba waccan
ba, ina jin su ban ce komai ba. Har da turare Baba Gaje ta ce Hinde
ta fesa bayan ta can za kaya. Babana yana kofar dakinshi na je na
zauna kusa dashi zuciyata cike da
damuwa, domin jiya ne kawai ADO
ya gabatar da kanshi gare ni amma
ji nake tamkar mun yi shekaru
dashi, waton sonsa ne ya shige ni ba na wasa ba, na ce "Baba gurina Ado
ya zo, amma Baba Gaje ta ce, Hinde
taje.'" Baba ya kama hannuna "Kada
ki damu nasan Ado ba zaya can za
miki ba, tunda yasan da Hinde ya ce
a kira ki." Edited · Like · 4 · Report · Sep 6, 2014 Saleesu Nasarauniya Funtua Munata gdy.
17...Ita kuwa Hinde lkcn data fita sai
ta canza tafiya ta nufi Ado, shi kam
lkcn ya shagaltu da tunanin anya za
ma abar JIDDA ta fito kuwa?
Sai ya ji takun sawu, kanshi yana
kasa sai ya ji kamshin turare dan goma ko bai dago ba yasan ba
JIDDA ba ce, domin ita in ta kusanto
ka sai dai ka ji kaurin hayaki ko
warin datti. Ya dube ta lkcn da ta zo
ta tsaya gantsartsar a gabn shi, tare
da cewa, gani, ya girgiza kai bn kira ba JIDDA nake nema, ta turo baki
kai ko ga dan ziza da kai me zaka yi
da kucakar mata? Ya yi mata wani
duba je ki turo min ita, ta rike kugu
t
[18/09 6:00 pm] Inna👬👫: Idan rana tafito
18..Ya kashe laptop din ya maida shi
gidan shi sannan ya sako ta a ma
adaninta, ya koma kan gado ya
kwanta yana nazarin duk
maganganun nasu. Ya jima da
zargin cewa haka zata faru shi yasa bai 6ata lkc ba gurin manna wata 'yar mitsitsiyar na'urar daukar
magana a duk kan dakunan gidan
domin samun rahotannin abnda ke
faruwa ko zai faru. Damuwa daya ya shiga dama Basma
turo ta aka yi don ta yaudare shi?
Lallai ta yi kokari domin yana son ta
so mai tsanani duk da ranshi ya
sosu da jin batun bai sa sonta ya yi
rauni daga zuciyarshi ba, amma zaya cigaba da bin su yaga iyaka
gudun ruwansu. Dady ya kalle shi bayan ya kur6i
shayi.
"Muhammad ya kamata zuwa yanzu
a ce wani abu game da aurenka da
Basma."
M.B ya ce, "Dady ai magana tana gurin ku, ko Hjy?" ta aje cokalin hannunta tare da cewa "Wannan
gaskiya ne Muhammad, Dady sai a
yunkuro a shiga maganar." Dady ya
ce, "Shi kenan, Insha Allah week end
zamu shigo Abujan kafin sannan zan yi waya gida sai mu tafi da Sani." Hjy Shuwa ta ta6a baki "kana da son saka 'yan kauye cikin komai naka."
Ya dube ta "Ni din dan ina ne?" M.B
ya ce, "Kauye Husma ta ce yaya
kuma zaya guji kauye Hjy. Dady
yana da gaskiya ina son yanda Dady ke son asalinsa."
M.B ya jinjina mata hannu, Tsaki
Hjyn taja ai nima ban ce ya ki
asalinsa ba, amma ka duba zuwa
Abuja ba sai ya samu wasu daga
abokansa su tafi tare ba? M.B ya ce, "bar shi kawai, Hju gara yaje da danginsa ba don ranta ya so ba ta
ce shi kenan Dady ya yi dan
murmushi sannan ya ce kamar
yanda ni ke daura auren 'ya'yan
Sani haka nan shi ne zai auradda nawa." Husna ta ce zamu sha biki fa Bros, Hjy ta ce kai Husna akwai ki da
zumud'i, ta ce dole ne nayi zumudi
Hjy ba mu fa ta6a yin wani biki
namu na kashin kanmu ba cikin
gidannan, sai dai in za k yi wani abu na dangan ki." M.B ya ce kina da gaskiya Husna.
19...Cikin lkc kankani manya suka
cikin zancan aka yi sa rana ko in ce
baiko, biki sosai aka yi tamkar
lkcnnne bikin tare da rabe-raben
kyautuka. Hjy kuwa Dubai suka tafi
don hado lefe tare tare da kayan da za su ci biki dashi ita kuma Auta ta za6o kayan dakinta irin wadanda
take so. Shi kuwa M.B ya yi sallama
da su kan cewa za ya tafi kauye don
sanar da su Haja.
*************** Kimanin kwanaki 4 ne suka shude
Ado da Kuluwa ba muga juna ba, sai
ranar Lahadi ina dawowa daga talla
na biyo ta gefen gonarsu shi ga su
shi da Sama'ila, na tsaya turus ina
kallonsu, har suka karaso inda nake, waige-waige na shiga yi domin ina tsoron koda akwai wanda zai kaiwa
Baba Gaje labarin.
"Ado ya ce kwantar da hankalinki
JIDDA, babu kowa." Na yi ajiyar zuciya, amma na kasa
kallonsu, ya ce kin saida ne? Na ce
saura kwano 2, ya ce muje na bi su
zuwa cikin gonar, ya kira daya daga
cikin mutanan da suke aiki ya ce su
dauki abinci karkashin wata bishiya muka zauna, ya ce nasan an dake ki ranar ko? Na ce eh, ta dake ni.
Ya ce shi yasa ki ke ta 6oye min har
kwanaki 4 ko? Nayi shiru,
ya ce kin fasa auran nawa kenan? Na
kalle shi sannan na kalli Sama'ila na
sunkuyar da kai, na za ci kayi fushi ne game da abinda ta yi maka ka fasa.
Sama'ila ya ce, "Allah Sarki, Abokina
samun kansa ya yi da kara muradin
auranki, kuma insha Allahu ba fashi,
sai dai wani iko na Allah, Ado ya ce matsalar daya ce, Jidda na kalle shi gabana na faduwa zuciyata cike da
son jin wace matsala ce wannan?" Ya ci gaba zan tafi birni karatu, kuma zan dauki kimanin shekara 3
ya ya ki ke ga za ayi? Nayi shiru ina
nazari sannan cikin karaya wato
cikin amincewa raina na rasa Ado na
ce Allah ya bada sa'a Sama'ila ya ce abinda za ki iya cewa kenan? Na ce to me zan ce? Ado ya ce Jidda
shawararki nake son ji game da
mokamar auranmu?
Na ce Yaya Ado haka kurum na ji a
jikina auranmu ba zaya yiwu ba, saboda zai iya kasancewa in ka tafi birni ka manta dani, sannan ga
matsalar Baba Gaje in ta gan mu ta
ji labari kamar yanda ta ce kai kara
gurin mahaifin ka ba ka jin akwai
matsala? Ya ce don Allah bar zancan wannan
Babar taki, zan fa ci gaba da zuwa
zancena tunda Babanki ya yarje min
kuma kada ki damu kinji na ce to.
[18/09 6:15 pm] Inna👬👫: Idan rana tafito
20
Ban damu da su ba na ci gaba da
aikina, sai da zan fita muka ci karo
da Babana ya dawo zai yi shirin
Masallaci, cikin murna ya ce,a'a wa
nake gani haka? Kulun majadan, kai amma fa kinyi kyau cancadi." Dadi ya rufe ne, kun san mu2m yana son
ya yi gayu a kuranta shi, kuma ban
ta6a sa rai wata rana za ta zo da zan
ji irin wannan kalmar ba. Na ce "Baba ba ta nan shi ne na saka wannan." Babana ya ce,"Ai ko kin yi
kyau, na jima ina son in sai miki
kaya in ganki haka tamkar sauran
yara, amma hakan ya faskara. Allah
ya sakawa Ado da alkhairi, na fita cikin farin ciki, duk wanda ya sanni in ya kalle ni sai ya sake kallona,
saboda mamakin kwalliyar da na yi,
wasu kuma su ce iyen ba, an ci gayu
cikin zuciyata kuwa ba wanda nake
so daga ni irin Ado, yau dai ya ganni cikin gayu. Wasu Dattijai suna cikin siyan goro sai na ji muryar Sama'ila yana cewa,
"Yammata muna son goro." Na kalle
su cikin kunya, bayan an gama
sayan goron na rusuna na gaishe su
cikin ladabi. Ado ya ce a"a Sama'ila kaga mutuniyar taka ko?
Yau kam duk kauyannan kin cinye
'yammata a kyawun kwalliya."
Sama'ila ya ce,"Na yarda da kai.'
Dadi ne ya rufe ni, na ce "ko dai
kuna tsokana ta ne?" Ado ya ce, tunda ki ka fito tsakanin ki da Allah mu kadai ne muka yaba adon naki?
Na yi dan murmushi sannan na ce,
a'a Baba ma..........21......."S auran kalmar ta ki fitowa lokacin da na hango Baba Gaje ita da kawarta Dija suna
dawowa daga biki, tuni su Ado suka
gano ina cike da fargaba, sannan
suka kalli inda nake kallo, ba su san
Baba Gaje ba, amma duk sun yanke hukunci cewa ita ce, musamman
Ado wanda ya ganta da dare, tana
furta kalmar Kuluwa ina ki ka samo
wadannan kayan? Cikin mamaki
take magana, Ado ya shaidata a
muryarta, don haka sai ya ce "Sannu Baba."
Ya tsugunna shima Sama'ila sai ya
tsugunna bata kalle su ba ni krum ta
zuba wa idanu cike da masifa, tana
karkada kai. Dija kuma tana fadin
"Tabdijam, lallai yarinya ta rika." Ni
kuwa tuni tsoro ya cika ni na soma
kuka domin ban ta6a ganin fushinta
irin na yau ba, don jikinta har 6ari
yake, ta ce shin kai Ado ka ke ko wa? Ban ce ka fita hanyar ta ba?" Sama'ila ya ce, "Baba da aure muke
sonta don Allah kiyi hakuri." Ta
zaburo baki na kumfa "Ban hakura
ba, na ce ban hakura ba iskanciin
banza da wofi, na ce da ku aure zan mata? Tsinannu kun gama lalata 'yar uban wa zai aure ta?" Ado ya fusata ya kalle ta ya ce, Ni ne
zan aureta." Ta kara kusanto shi"kai
mara kunya ka fita daga inadunan
in rufe ka kiyaye ni bar ganin
ubanka ke da gari. Ado ya ce,"Baba
insha Allahu sai na aure ta, ki rubuta ki ajiye sai na tsame ta daga wahalar da ki ke bata."
Dija ma ta matso "kai dan sara
sa'arka ce! ku ji mu da tsagera,"
Suka mike tsaye, Ado na cewa, "Yi
hakuri Jidda, ki daina kuka kukanki yana soya raina." Baba Gaje wani tukuki ta ji cikin zuciyarta , ta cije
yatsa sannan ta yi gaba fuu.
Dija ma ta bita tana cewa, "Gaje
gidan su zamu ke kai kashedi." Gaban Maigari suka zube, Baba Gaje
ta saki kuka tana fadi "Maigari kun
ne masu hukunci ya ya zaka yi da
danka Ado wanda ke lalata min
yarinya?"
Dija ta yi zaraf ta ce, "Har batun cikin da ya yi mata kwanakin baya ki sanar da shi." Nan da na kuwa ta
dad rushewa da kuka. Dija dama
baki tuno min da wannan ba, Ranka
ya dadw kwanaki har ciki ya yi mata
cikin zuaran nan naku mai duhu, sai da kyar asibitin Garko suka cire shi, na ji tsoron kawo kara ne don naga
ku ne masu garin amma sai naga an
ci gaba ni dai ranka ya dade a shiga
tsakanin su." Wakilin Maigari ya nuna ta "Ke ba
mu son zancan wofi, Ado za ki ma
sharri?" Maigari ya daga mishi hannu tare da
cewa,"Dakata Wakili." Ya kalle ta
"To baiwar Allah, kiyi hakuri zamu
yi bincike kuma zan dau mataki.
Ta ce,
"Na gode, na gode." Ta mike suka tafi. Cikin dakin Baba Gajen suka yada zango sai sheka dariya suke yi,
Gaje tana ta zugawa Dija godiya da
dabarar da ta kawo mata.
Shi ko Maigari Sai ya dubi Wakili da
Liman ya ce, Dan yau zaya iya aikata abin da ya fi haka, shi yasa na ce ba zai je karatun nan birni ba,
Liman ya ce ni kuma sam ban yarda
Ado za ya aikata haka
[18/09 6:50 pm] Inna👬👫: Idan rana tafito
22.......Su kam karkashin wata bishiya suka
zauna suna hangen ruwan daga in
da suke. M.B yana jefa 'yan kananan
dutsuna cikin ruwa, ya kalli Ado ya
ce Adamu yarinyar can da ta wuce kamar itama 'yar gidan ku ce. Ado
ya ce da ba ka santa ba? M.B ya ce
ba duka kannanka na sani ba,
'yanmata da Bintu da Asma'u na
sani." Ado ya ce, to ai sune
'yammatan, ita wannan da ka gani da ita zan aura, sai wasu matsaloli suka shigo, kuma ni na yi niyyar
auranta ne don na taimaka mata
bawai don so ba. Cikin ikon Allah da
na sama zuciyata auranta a 'yan
kwanakin da muka yi sai na samu kaina da soma sonta nan ya kwashe komai har da tarihin Jidda ya ba wa
M.B
Nan ya ji ya kara tausayin yarinyar
sosai, ya kuma bawa Ado labarin
turetan da ya yi dazun na. Bayan sun dawo cikin gari suka sake
hangen ta dauke da tiren goro.
M.B ya ce wai shin Ado yarinyar can
bata da aikin da ya wuce talla ne?"
"Kwarai kuwa. "In ji Ado,"Tana talla
ne sau 4 a kowacce rana, safe, rana, yamma da kuma dare."
Tausayinta ya kuma cika zuciyar M.B
kazalika sai gata da daren dauke da
tire. Ado ya ce, "In na jin takaicin
halin da yarinyar take ciki, lokacin
da na yi nufin taimaka mata sai na kara mata damuwa." Ya dubi M.B Muhammad tana zaman zamanta na
jawo ta, na kimsa mata sona cikin
zuciya, a karshe a ka raba mu don
Allah ban zalince ta ba?"
M.B ya ce "Ba ka zalince ta ba, kayi nufin taimakonta ne. Zan yi nazari nima na gani wane irin taimako zan
mata?"
*************23.....
Komai na bikin M.B suna tafiya dai-
dai, yanda Hjy ke rawar kai da ji da Ango tare da fidda kudi daga cikin jakarta take kashe su yana ba wa
M.B mamaki, ban da yasan komai
game da makarkashiyar da suke
kulla mishi, to da zai karyata duk
wanda ya zo mishi da batun cewa da wata manufa suke son auran shi
da Basma. Don haka ya bi ya lika
security a guraran da bai saka ba,
domin kara samun cikakken
rahoyan sirrin duk wata
makakarkashiya. Akwai fatitiikan da za a yi kafin
daurin auren, da kuma bayan
daurin auran tun saura kwana 2 biki
dangin mahaifiyar M.B da Kakarsa
Haja suka bayyana birni cikin su har
da Binto da kuma Ado, haka nan dangin Mahaifinshi daga Garko,
Binyo kam ta tsinke da lamarin
bikin 'yan birni, fadi take ina ma da
Kulawa muka zo bikin nan ta sha
kallon duniya,
, Allah Sarki Haja ta ce wa zai barta? Binto ta ce ai zan kai mata wadannan hotunna ta gani ki ko kai
mata in ji Haja, Allah yasa ina son
yarinyar na so kwarai Ado ya aure
ta, domin yanda yarinyar ke sha
wuya nasan Ado zaya rike ta da amana zai kula da rayuwarta, Binto
ta ce Baba ya yi saurin yanke
hukunci koda yake ya ce shekaru da
dama da suka gabata suka kulla
alkawarin auran Yaya Ado da Aina,
haka ne in ji Haja, amma ban gushe ba ina mata addu'a Allah ya bata wanda ya fini, amin in ji Binto. Hjy ta jawo aminiyarta cikin dai
wato Kilishi ta maida kofa ta rufe
tare da cewa kin san sirri dukkansu
suka zauna bakin gado. Hjy Shuwa
ta kalli Kilshi ta ce, "Kawata kinga
dai yanda komai ke tafiya min daidai ko?",
Kilishi dafa ta tare da cewa "Kawata
na ta6a ki da alheri na kula sai dai
menene shirinki na gaba?"
Shuwa ta ce, "Shirina na gaba kuma
na karshe shi ne kashe Bello, ta hanyar sa mishi gabu cikin abinci." Kilishi ta zuba mata idanu. "ZUWA yaushe za ki aikata haka?"
Kilishi ta tambaye ta.
"Da zaran anyi biki." In ji Shuwa.
"Ba ki tsoron a zarge ta in abin ya yi
wuri? Sannan Likitoci za su gano cewa ya
ci guba wacce amsa a ki bada
lokacin da kanwarki ta ji tuhuma ta
yi yawa? Ta ce ke ce ki ka bata?"
In ji Kilishi.
Shuwa ta yi dan jim sannan ta ce,"Haka ne.
Na so in yi wauta, zan bari sai sun
dan kwana 2.
Kilishi ta girgiza kai tare da yin
murmushi.
"Ya ya za ki yi da cikin da kanwar taki zata samu, musamman in an
samu irin natattun cikin nan an yi
an yi ya fita ya ki fita? Ina nufin
dadewarsu za su kusanci juna kuma
ciki zai iya shiga, kinga dan in ya zo
duniya in bai gaji Kakanshi ba dole ne ya gaji dinbin dukiyar da ubansa ke da ita wadda ki ke burin
kanwarki ta gada daga b.aya ki
mallake." Shuwa baya"Haka ne kuma fa, lallai
Kilshi kina da baiwa. To yazamuyi
[19/09 9:15 am] Inna👬👫: Idan rana tafito
24.....
Nan da nan Jami'an tsaro suka nufi
gurin da mutumin ya fado, shi kuwa
Ango tuni dangi suka zagaye shi
don jin me ke faruwa? Lokacin da su
Hjy Shuwa suka fahimci M.B ne ya yi harbin ba shi aka harba ba, sai suka cika da mamaki gami da tsoron me
zai biyo baya?
Lokacin da suka isa guri inda
mutane suka yi cincirndo don ganin
kowane ne Hjy Shuwa ta riko hannu M.B tana cewa
me yake faru ne Bello? Ya ce,"
An turo shi ne don ya kashe ni?"
Ta ce,"Su waye za su mana wannan
dayan hukunci?",
Ya ce "Sai Allah, shi ne kawai ya sani.
Sai dai kada ki damu ko su wanene
burinsu bai cika ba, kuma na sani
zamu hadu dasu karo na 2.
Jikinta na rawa "To bari in kira Dady
in sanar dashi. "M.B ya ce "Hjy ki bar shi kawai, wannan Jami'an tsaro za su yi gaba dashi in yana da sauran
rai ne ya musu bayanin dalilin sa na
son kashe ni, in kuma ya mutu shi
kenan sai in mun tsaya a gabn
Ubangiji." Hjy Kilishi ta matso,"To ai dama
karsa shi kayi domin barin irin
wadannan a bayan kasa fitina ne."
M.B ya yi murmushi ya kalli
mutumin lkcn da Jami'an suke saka
shi a mota, sannan ya dubi Hjy Kilishi"Da ina da wata dabara da zan iya yi lkcn da na hango shi wacce
zan kama shi kon kare kaina bayan
harbin to da ban harbe shi ba. Tilas ke sa mu harbi don mun fi son
mu ji bayani daga bakin me laifi,
kila ba shi kadai ba ne ta yiwu wasu
suka sa shi da makamancin haka kin
ga duk zamu ji'."
Ya zuba hannuwanshi cikin aljihu "Hjy ku koma ciki lkcn tashi ya kusa, kada wannan ya dame ku, domin
IDAN RANA TA FITO TAFIN HANNU BA
YA KARE TA.
HAKAN NAN ZAKARAN DA ALLAH YA
NUFA DA CARA KO ANA RUWA MUZURAI SAI FA YA YI."
Mar 7, 2015
Aisha Ummu Shureim Sa'eed
45..
Cikin sanyi jiki tare da tunaninko ya
gano sune? Suka ce "Haka ne."
25.....Amarya dai tana can gurin kawaye
suna lallashi ta don ita kuka ta kama
riris, sannan ta kasa zuwa gurin suna dawowa gurin ta rugo ta
rungume mijinta shi ko ya shiga
lallashinta.
Hjy Suwa ta kira mai abun magana
ta ce ya sanar da kowa an gode za a
tashi haka saboda wannan farmaki da aka kawo. Maimakon gidansu za
su wuce kamar yanda a ka tsara
daga gurin party ango da Amarya
za a yi musu rakiya zuwa gidansu
sai kawai a ka koma gida gaba daya
in da suka iske mutanan gidan cirko-criko. Haja sai kuka take lkcn da su Ado suka zo mata da labarin dukkan su
suna falo ne suna jiran zuwan su M.B
bayan an gama jajantawa yana
rungume da kafadun Haja yana
lallashinta ya dubi Hjyr "Ina su Basma su zo mu tafi dare na kara
yi." Nan take Hjy Tasa kuka,"
Gaskiya ba za kuje ba, ka sani ko ba
shi kadai ba ne me nemn ran naka? Haka kawai kuma sai ku je can ku kadai su kashe mana kai a banza."
Husna da Safina suka gurin Mahaifin
su da ke tsaye yana saurarn kowa,
Dady kada ka bar Bros ya tafi fa." Ya
dubi Hjy." Kada wannan farmakin ya dame ku,
don ba zai zama barazana ko
tsoratarwa a gurin dan Sanda
kamar ni ba, zamana ni kadai ko
zamana cikin mutane ba shi ne zai
kare ni daga mutuwa ba, ku fahimci wanna ni ba zan canza da komai ba kuma ba zan kasa walwa ba don
wannan.
Haja ta ce "A'a ka dai zauna tukunna
Muhammadu kada su kashe min kai
Marayan Allah, me ka tare musu?"
Ta sake sushewa da kuka tare da
cewa "Ni shi yasa birni bata ban sha'awa, yanzu ka ji an kashe mutum."Su Ado suka ce "Da ka dan
saura tukunna."
26... Husna da Safina
suka kyale mahaifinsu suka je suka
rungume Yayan nasu suna jijjiga
shi"Don Allah Bros kada ka tafi ka ji Dady ka ce wani abu mana." Dadyn ya yi gyaran murya sannan ya ce "Hakika Bello ya fiku gaskiya,
domin kuwa duk wata kariya da
wani dan Adam zai baka tana bayan
ta Ubangiji, ku lura mana duk cikar
gurin da ku ke da yawunku bai sa kun ga mai harin nashi ba sai shi kansa, Allah ya kare shi kuma ya
kare kansa." Dady ya kalli M.B "Bello
kai kuma sai ka hakura na kwana 2
saboda an ce masu rinjaye sune
sama, kai da ni ne muke tare amma duk falon nan basu amince ka je gidanka yau ba." M.B yana dariya ya
daga hannuwa sama na bi, suka
kwashe da dariya shima yana
murmushi don da wuya kaga M.B
yana kyalkyata dariya. Ya kal
[19/09 6:51 pm] Inna👬👫: Idan rana tafito
27...Tana shiga gurin Hajiya Shuwa nan
take ta hau ta da zagi"Yar iska me ki
ka je yi gurinsa?
Ban gargade ki ba ne?"
Basma ta ce, "Na je fa gaishe shi ne." Ta ce "To ban ce ki dinga zuwa gurinsa ba, don na gaya miki kada
ma ki yarda da shi ko gidan ki ka ji."
"To" kawai Basma ta ce amma cikin
zuciyarta cewa take yi ai mijina ne
kuma ba zaki haramta min abnda Allah ya halasta min ba. Basma zata juya Hjy ta ce
"Ina za ki?" Zan je dakin su Husna
ne, a'a cewar Hjyn shigo nan ki
zauna. Duk da wannan gadin da Hjy
ke yi wa Basma ta saka ta a dakinta sun zauna tamkar kurame, bai hana Basma ciro wayarta ba shi ta turawa
text tana me shaida mishi irin
tsantar son da take mishi tare kuma
da shaida mishi cewa ta yi mafarkin
tana kwance bisa kirjinsa, le6unnanshi yasa kan nata yana
mata sunba ta bn mamaki, ina son
ganina haka a gaske zan samu?
Lokacin da sakon ya same shi
murmushi ya yi duk da ya ji dadi bai
hana shi ji a cikin zuciyarshi banbarakwai ba, a son zuciyarshi shi
ne zaya fara kai kokon bararshi
gare ta matsayinshi na miji duk da
addini ba ya hana ba ne matsayinshi
na mijinta. Sai ya rubuta cewa, Ni na ki ne
Basma yanda na tabbatar da cewa
ke tawa ce, daina mafarkina zamu yi
zama na har abada insha Allah. Zamu kasance cikin yanayin da yafi mafarkinki. Ya tura mata tana gama
karantawa ta yi murmushi tare da
cewa, my D kenan, haka nan suka ci
gaba da yiwa juna musayar
kalaman so da kauna har zuwa lkcn yin Sallah, inda M.B ya fita.
28....
Inda M.B ya fiya. Ranar da suka cika
sati daya, ranar Dady ya rike wuta
sai sun tare kuma ranar ne suka
tare. Kafin a kaita sai da Hjy da
kawarta Kilishi suka saka Basma a gaba kan cewa kada ta kuskura ta
ba da kanta ga angon nata, wai ta
bijire mishi ta wannan fanni. Basma
ta dubi Yarta ta ce "Anty har
yanzun kin kasa sanar dani dalilinki
na hada wannan lamarin?" Kilishi ta ce, "Kin kusan gama aikinki,
kuma nan za ki ji komai." Basma ta
ce "Shi kenan." Ko kayan gyaran
Amarya da ake hadawa ita dai da
kudinta ta siya kuma a 6oye.
Amarya ta gama sakin jiki yau za su 6arji Soyayya ita da mijinta, amma ga mamakinta 12:30 bata ji
shigowar Maigidan nata ba, gashi
tuni take neman layinshi amma ya
ki shiga, fitowa cikin falon tayi don
duba dakinshi kofar na kulle don haka ta daga labulan window shi ta hango kwance rigingine filo manne
a kirjinshi yana bacci. Sai kawai ta
juya ta koma dakinta cikin
sanyin jiki.
Washegari bayan ya dawo daga Masallaci dakinta ya nufo ta yi dai-
dai bisa gadonta me shegen kyau,
ya maida wani abu da ya yi
yunkurin taso masa sannan ya yi
karfin halin karasawa ya saka
hannunshi ya girgiza kafadarta a hankali. Mika ta yi wadda dole tasa shi kau da kan shi gefe, domin ganin yanda
surarta ta matantaka ta firgita shi,
ta bude idanunta a hankali ta zuba
su kan fuskar M.B tare da furta
"My D." ya dube ta "Amarya tashi kiyi sallah
ko?" Ta tashi zaune cikin yanayi na
shagwa6a ta ce, shi ne jiya ka bar ni
ni kadai ina ta jin tsoro.
Ya dan ware idanu cikin murmushi,
sorry my dear, jiyan nan na gaji sosai ban san lkcn da bacci ya
kwashe ni ba, yanzun dai tashi ki je
ki yi sallah kafin gari ya yi haske,
kin ji ko? Ta yunkura ta nufi bayinta
da kallo ya bita yana son fantama
amarci da abar son tasa amma zuciyarsa ta kasa amincewa da
hakikanin son da take masa, ma'ana
ya sani tana sonshi amma me yasa
ta kasa sanar dashi game da shirin
da Yayarta ke yi kansa? Koda yake
ya sani bata san rayuwarshi ake nema ba, sannan bai san me zayo
biyo baya ba cikin zaman nasu, sam
bai ji dawowarta ba sai dai ya ji
muryata tana cewa "My D, baka
zauna ba." Ya ce dama zan je kicin
ne don shirya mana breakfast, ya nufi fita ta ce my D ba mu da masu aiki ne? ya girgiza kai tare da cewa
bana son masu aiki masu yi mana
gadi kawai sun isa, amma duk aikin
cikin gida zamu yi kayanmu ta
marairaice fuska ban fa iya aiki ba musamman girki ka kuma sani ya ce ni zan yi mana kada ki damu
maimakon mu dauki masu aiki
tunda ba dadewa za a yi ba yana
fadin haka ya fita
[19/09 7:52 pm] Inna👬👫: Idan rana tafito
29...
Sai dai su ba kamar mutan birni ba
wai har da kungiyar da suke
kwatarwa yara 'yancin kai kamar
yanda Ado ya sha bani lbr.
Ina cikin wannan halin ne sai na ji muryarshi tana fadin subahanallah, 'yammaya me ya yi zafi.....
Na dube shi da jayayan idanuna
babu komai ya shiga waige-waige
can ya dube ni zo muje karkashin
bishiyar can in ji damuwar ki.
Wala Allah ko zan iya taimaka miki. Na girgiza kai zai yi wuya ka iya taimaka min sai dai ka taya ni da
addu'a ya ce kada ki zama mai
gardama a gare ni kila ni ne sanadin
fitarji cikin matsalar. Jin haka sai bn
kuma magana ba, ya yi gaba na bishi.
Komai na karanto mishi har zuwa
yau dinnan shiru ya yi cikin
tausayawa tare da tunanin ita ina
zai fara?" Can ya yi wani tunani
kuma ya gamsu da cewa za ya gwada hakan. Sai ya ce Kuluwa zan
taimake ki hanya ta farko shi ne zan
nemi Baba Gaje in bata kudi masu
yawa ta bani ke in tafi dake can
birni ki dinga taya matata aiki, zan
saki Makaranta Islamiyya da boko kiyi ilimi shi kenan kin zama yar birni sam bn san sanda na shiga
sheka dariya ba, na dube shi Allah
da gaske ka ke yi kuma?" Shima
cikin murmushu ya ce sosai ma na
ce wai wa ka ganni a birn?" Ya ce balle kin shiga Makaranta, na
yi ajiyar zuciya na yi shiru ina
tunanin yanda zan zama 'yar birnu,
can kuma na tuna Baba Gaje fa zata
iya hana ni zuwa, nan take sai raina
ya yi duhu cikin sanyin jiki ya ce menene kuma?" Na dube shi in ta ki yarda fa?" Ya ce sai mu canza dabara.
Na ce to Allah ya dora ni a kanta,
domin duk kudin da za a bata in ta
tuna cewa zan iya jin dadin rayuwa
ta zata ki amincewa ya ce kada ki damu Allah yana tare da mu na ce
to Allah ya shige mana gaba. Ya
tashi tare da cewa ki koma gida
kada ki yarda ki daga hankalinki kan
wannan insha Allah tare zamu bar
garin nan. Ina tsaye ina kallon dan birni ya tafi
har ya 6ace wa ganina kai ko
wannan ya ishe
30.
Ya ce kada ki damu Allah yana tare
da mu na ce to Allah ya shige mana
gaba. Ya tashi tare da cewa ki koma
gida kada ki yarda ki daga
hankalinki kan wanna insha Allah tare zamu bar garin nan.,
Ina tsaye ina kallon dan birni ya tafi
har ya 6ace wa ganina kai ko
wannan ya ishe ni alfahari duk cikin
kauyannan akwai wadda dan
birninan ya ta6a kallo ma balle magana kazalika babu wadda Ado
ya ta6a cewa yana so sai dai ni, don
ko Aina'u bashi aka yi. Daga nan bn
nufi gida ba na koma gurin su Binto
ina tare da su har muka kai Amarya
muka fito waje muna ta gada, duk sanda na tuno gida sai na ji tamkar kada na koma, sannan na samu
kaina da taurarewa cikin zuciyata
ina fadin ai dama yau kawaye gidan
amarya suke kwana sai gobe in anyi
rufi da budar kai bayan an gama jere sannan kowa zai watse don
haka a sai na yi kwanciyata.
Da safe muna cikin karyawa Laure
ta shigo tana cewa "Kuluwa ga
Babanki nan a waje ya zo neman ki
na fito da sauri na rusuna ina kwana Baba?"
Ya ce lafiya Jidda nan ki ka kwana?"
Na ce I ya ce to shi ne ba ki zo kin
shaida min ba?
Sanin kanki ne zan damu na rike
hannunsa to i hakuri Baba jiyan na neme ka bn ganka ba nan na koro masa labarin duk yanda muka yi
dasu Baba Gaje har zuwa batun dan
birni Baba ya ce anya zan bari kiyi
nesa da ni Jdda? Ke ce kurum ki ke
kwantar min da hankali, na ce in ba dama ko Baba Gaje ta bari ni sai na fasa, muka nufi hanyar gida yana
cewa aure ne ya zama dole Jidda shi
ne kurum zai raba mu. Sallamar dan
birni ce ta dira a kunnunwanmu,
Baba ya amsa masa dan birni ya tsugunna ya gaida shi sannan ya
dube Jidda Baba ne wannan ko na ce
i shi ne Baba kaga wannan shi ne
dan birni da nake fada maka.
Baba ya ce af towo yanzu nan take
yi min zancanka, dan birni ya shiga sanar da Abbana, nufinshi na son taimaka mini. Baba dai ya yi shiru
na sani yana jinjina rabuwa da ni ne
can ya ce to bari dai muji ta bakin
Babar tata dan birni ya ce to gobe
ya zo zaya wuce ya ce shi ba bako ba ne a garin dan gari ne dan Maigari wan mahaifiyarsa ne. Baba
ya ce haba yaro ai ni nasan ka kai
ne dai baka saniba. .....
Don Allah yan uwa kuyi hakuri wlh book 1 din anyi sallakel dayawa wlh dasani da sallakel da yawa haka da ban faraba
Banida karshen bk 1 amma 2&3 akai infara 2 din ko inbari? Ko akai wanda yake karshe ya cigaba pss
Download Idan Rana Ta Fito Littafi Na Daya
0 Comments
Thank you for this comment