Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
        (admin
   Arewa hausa novels
       Novels villa
     Duniyan novels
   Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
          And
Cool novel, makeup and cooking)

      WHATSAPP NO:
    +2347039625239


*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

1_Nishi take iya karfinta rike da baya a tsugunne a band'akin dake a cikin d'akinta cikin zufa.
Nishin da ta sake yi ne mai karfi shi yai sanadin fadowar jaririyar,da saurin taro ta cikin karfin hali daga tsugunnen.

Murmushi ta saka har hakwaranta suka bayyana ganin abinda take da muradin samu ne a kullum wato 'd'iya mace'.
A hankali ta ware zaninta da ke gefe tare da shinfid'e ta a gefe jin mibiya na kokarin tahowa ta jijjiga cikinta ta fito.

Reza sabuwa ta sa yatsanta domin daidaito ta yanke cibin.
Ita kanta tasan yau kam haihuwar tazo mata da zafi ganin ta kasa mike wa.
Kofar band'akin ta tura a hankali ta fara jan jiki rike da jaririya har ta iso d'aki.
Cikin cije le6e ta kwantarta tare da kok'arin kwata tashi tsaye dan taimaka wa kanta kamar kullum amma ta kasa.

Kusan min 10 tana a haka har ta soma jiyo hargowar yaran.
"Maman Saifu!... Maman Saifu!!.
Ido ta rintse,dan bata so har yaran su kai da dawo wa tana a halin da take ba.
Babban cikin ne ya ja ya tsaya tare da bin inda taja har band'aki da kallo ganin jini ya dire kan jaririyar da ta sau kuka.

Da baya ya koma yana kwada kiran Abban shi,
"Abba jini a d'akin Mama da jaririya,kuma...
Bai jira ya karasa ba ya karasa da gudu-gudu,sauri-sauri d'akin yana fad'in
"Haba Halima,ya zaki min haka bayan kinyi alkawarin bana a asibiti za ai komai.

"Sam bana kaunar haihuwar gidan nan taki a kullum gudun matsa..
Shiru ya yi shima ganinta a durkushe hannu d'aya a ciki d'aya a kan babyn wacce ke kuka tana jijjigata.

"Innalillahi.. Maman Saifu..
Da sauri ya karasa tare da kok'arin tallafota yaji hayaniyar yaran cikin murna Mama ta haihu zasu shigo ya tsayar su.
"Maza ku je ku kira Aunty Rabi ku ce tazo yanzu.
Da gudu kuwa suka fuce banda babban da ya makale ganin halin da Maman shi ke ciki.

Taimaka mata ya yi ta sauya kaya tare da sanya pad ya rirrikota yana mata sannu.
Juyar da kai tayi da halamar ya zasuyi da babyn?
"Muje zan d'akkota.
Kan su kai ga fita har yaran sun dawo tare da makociyarsu Aunty Rabi.

"Dan Allah ki taimaka min da jaririyar kan na sata a mota.
Kai ta kad'a tana ma Halima sannu.
Maigidanta ta fad'owa tare da sanya yarinyarta babba tazo ta gyara band'akin kan suka wuce asibiti.

Duk yadda zasuyi jini ya tsayawa Halima abin yaci tura.
Tun mai gidan yana fad'a har ya dawo ya rissina ganin ba sauki,irin abinda a kullum yake gudu kenan.

"Kai ne mai gidan Halima?
Da sauri ya tashi tare da kad'a kai,
"Eh ni ne, jinin ya tsaya?
Kai nurse din ta girgiza tare da fad'in
"Likita na neman ka aciki ne.
Jiki a sanyaye ya bi bayanta har office din likita.

Tsam ya yi jin bayanin likitan,
"Y'ar uwata ce,wanchan karan ma jinin mu yazo d'aya, zaku iya diban nawa ba matsala.
Kai likitan ya kad'a,
"Ba damuwa,amma dole za'a kara auna wa,gaba ne dai ta guji haihuwar gida ita kad'ai dan gudun matsala.

Kai ya kad'a.
"InshaAllah doctor, wannan ma tsautsayi ne,ba kuma za'a kuma ba.
Da taimakon Allah aka samu jini ya tsaya washegari da taimakon likita aka kara mata jinin ta farfado.

Kan washegari har ta ware,dake ba garinsu suke ba,sai washegarin aka samu mai zuwa mata daga kano bazawarar kanwarta dake a gida.
****

Kallonsu take daga shi har yaran gwanin ban sha'awa tamkar wani sa'an su in suna wasa.
Sosai take jin nishad'i a duk lokacin da ta gansu a haka cikin kaunar juna da kulawa.
Ajiyar zuciya tayi tare da dan yatsine fuska jin wani irin zafi da cikinta ya yi.

Dagowa ya yi lokacin da suke ma jaririya wasa shi da yaran duk sun dirirritseshi shi kam koh a jikinshi.
"Ya akai ne Maman Saifu,koh jikin ne?..
Murmushi tayi tare da gyara kwanciya cikin dauriya ta girgiza mishi kai.

"A'a.
Gunta karamin ya yi,wanda babban yake da shekara 6,mai binshi 4,karamin biyu.
Cikin gwaranci ya ce
"Maman Saifu baby na chan hannu.
Yake tai mishi cikin dauriya tare da shafo fuskarshi.
Al'adar su ce in sun so har yaran da Abbansu su kira ta Maman Saifu.

Baban ne shima ya matso tare da fad'in
"Mama Saifu yaushe zamu koma gida,ni nafi son kina min wanka da bani abinci...
Murmushi tai mishi tare da miko mishi hannu tana kallon maigidan.

Ido Baban ya zuba musu cikin murmushi had'i sakar mata wani dan kallo a takaice.
Kai ta dauke tare da rungumo yaran bisa gadon da take a kai.

"Yanzu kam Saifu ai ka girma,kannen ka uku fa,yanzu daga yau kai zaka rika bawa Amjad da Nass da baby abinci da hannunka koh?
Kai ya girgiza mata cikin murmushi.
"Nima na girma koh Mama?
Murmushi tayi tare da jijjiga mishi kai.

"Uhmmm...
Gyaran murya Abban nasu ya yi duk suka kalloshi.
"An mantamu fa..
Yaran ta saki tare shima da miko mishi hannu halamun yazo gareta,ba musu kuwa ya tashi rike da baby ya isa gadon yaran suka matsa shima ya tutsu cikinsu ya zauna.

"Kin shagwa6a mu fa Maman Saifu, da gaske gida ba dad'i in baki a cikinshi,mun saba da tarairayarki.
Murmushi tayi tare da maida hawayenta ciki.
"Shi yasa nake son ko fara koyan komai da kanku,dan komai zai iya kasance wa.

Ido yasa mata da halamun tambaya, kan ta kai da bashi amsa likita yazo.
"Kai,kai..
Juya wa sukai gaba d'aya jin maganar doctor.
Da hannu ya fara lissafa su
"D'aya, biyu,uku har shida a gado d'aya?
Ai sai ku bangare mana.

Tashi Abban nasu ya yi yana ma likita dariya.
"Bari tunda madam ta samu lafiya zamu sallameta dan naga ita ta 6ata ku da yawa.
Kai tayi kasa dashi cikin murmushi jin tsiyar likita har ya gama ya fita.
Kamar mai jira duk suka sake komawa saman gadon tamkar zata gudu,karan nan sai ya basu babyn shi yabi likita.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

2_Kwana uku suka sake yi aka sallame su,duk da a zahiri dauriya kawai take yi dan ta kosa da zaman asibitin.
Y'an barka sun lafa zuwa dare ta tasa babynta a gaba,yayinda lokaci-lokaci tana duba agogo jin y'an gidan shiru basu dawo ba har Fatima kanwarta.

Ruwan zafi ta zuba tare da d'auka tana sha koh zata samu saukin zafin ciwan da cikinta ke yi.
Ido ta daga tare da kallon katon hotonsu nasu duka da tsohon cikin da suka dauka kwanan nan.

Kwalla ce ta tarar mata a ido,a hankali ta kau da kai tare da fashewa da kuka tana girgiza kai.
Jin dirin motar su halamun sun dawo yasa da sauri ta hau goge ido ta maye kukan da murmushi dan tarar su.

Kayan da suka jido na sawarsu ranar suna suke nuna mata cikin murna ganan na baby shima da yawa.
Kai ta kautar ganin yadda mai gidan ya zuba mata ido da halamun yana son karantar ta.

Yasan Halima ciki da bai,yasani tana da matukar hakuri,amma yafi kuma kowa sanin wacece ita..
Dan haka ko ya ta sauya yana saurin gano ta.
Sa Fatima ya had'a yaran tare da fad'in ta basu abinci suka fara make kafad'a wai su dashi zasu ci.

"Toh shikenan, anji.

Kanta ya dawo,tare da fad'in
"Meye matsalar?.
Ido tasa mishi,sai ganan wani hawayen ya sake cika.
"Ok,ok,na gane,mun jima koh?
Dan ta kwantar mishi da hankali ta daga kai.
Murmushi ya yi tare da fad'in
"Ai mana afuwa.
Murmushi tayi tare da mika mishi baby da yai mata huduba da sunan Ummanshi Rukayya.

Tare har ita suka ci abinci tana bawa yaran a baki da cokalinta kamar kullum,sai dai a yau takan zuba musu ido a takaice cike da sauraron labarin shagon da suka je har aka gama cin abinci.

''Ba dai anan zasu kwana ba?..
Kai ta kad'a mishi tana cigaba da shirya su,jin ta ce eh ne yasa suka hau murnar yau zasu kwana da baby.
Kallonsu kawai yake yi,har ta gama shinfid'e su itama ta haye.

"Ni fa?
Cikin marairaita yai maganar yana mata wani kallo,sai ta nuna mishi da ido halamun yara fa na kallonsu tana kunshe dariya.
"Abba zo kusa dani ga waje dayawa...
Da dan gudu ya karasa tare da d'aukar filo yana fad'in
"Yauwa Abban..

Kallonsu take yadda ya zamo sun saka yaran a tsakiyarsu,hakan yasa ta zuba musu ido ba koh kiftawa har uban.
Kai ya dago tare da kallonta,sai ta wayence tare da k'au da kai gefe tana mishi murmushi..
Shi tau ya rasa wacce kunya take ji haka.

"Mama..
Amjad ne ya kira ta.
Juya wa tayi gaba d'aya garesu.
"Na'am Habebee.
 "Yi mana tatsuniya toh...
Kanshi ta shafo tana mai jinsu har bayan ranta.

Cikin nutsuwa ta fara basu labari irin na littafin yara suna kallonta,da sannu har suka fara bacci d'aya bayan d'aya.
Bargo taja musu lokacin da hawayen da take rike wa suka zubo mata.

Tashi ya yi tare da zama yana kallon yadda take sunke kai dan kar ya gani.
"Halima...
"Uhmm"..
"Muga"
Kautar da kai tayi gefe dan jin zai mata wayo,sai dai kan ta farga har ya taso ya dawo bangarenta.

Daga kwancen tai saurin rungumoshi tare da sakar kuka mai tsuma rai a hankali.
Ya sani da tun dazun ya ga halamun kuka take son yi,yasan kuma ko ma meye toh babban al'amari ne,dan haka kawai sai ya dagota ya hau lallashi.

"Ina tsoron ne Kabir..
Ina tsoron ranar da mutuwa zatai mana yankan kauna yarana su tagaiyyara in bani ne..
Shiru tayi hawaye na zuba sakamakon hannu da yasa ya rufe mata baki yana girgiza mata kai halamun tayi shiru.
 
Yaran ya matsar har jaririyar,a hankali ya kwanta tare da kwantar da kanta a kafad'arshi cikin lallashi.
"Sshhhh..It's ok...
A hankali har ta nutsu.
"Wa ya fad'a miki zamu rabu?..
Kai ya kad'a mata,kan ya cigaba.

"Muna a tare InshaAllah har girmansu.
Kai ta kad'a,tare da fad'in
"Zanso haka,dan duniyar ce yanzun..
"Ba abinda zai faru fa,believe me.
Shiru kawai tayi tana kallonshi.

A hankali yana dauke hankalinta har ta fara gyangyad'i.
"Rufe ni sanyi nake ji..
Murmushi ya yi,
"Sanyi?.. Zafi fa ake.
Kai ta kad'a mishi tare da sakar ajiyar zuciya.

"Gobe fa y'an Kano zasu zo,bana sun makara har jibi suna.
Murmushi tayi kawai.
A hankali yana mata fira har yaji tai shiru halamun tai bacci.
Tsam ya yi yana kallonta cikin tunanin kalamanta,kawai dai sai ya kawar yaja mata bargon kad'an ya rufesu har ita.

Asubar farko ya farka,baccinta take,duk da baby Sultana na motsi kad'an amma bata tashi ba.
Bargon ya kara ja mata tare da sauka yana gyaran sauran yaran.

Sako kanshi a gidan kenan ya fara jiyo ihun kukan Sultana da sauran yaran suna fad'in Mama.
Ja yai ya tsaya ganin Fatima bata ma san anayi ba d'akinta a rufe,dan haka da sauri ya karasa d'akin.

Amjad da Saifu rike da jaririya ya samu suna jijjiga kafad'un Maman tasu da fad'in
"Mama baby na kuka.
Amma shiru ba koh motsi, da sauri ya karasa tare da tallafota ganin duk ta sake.

"Halima!..Halima!!..
Girgiza ta yake iya karfinshi yana mai sa hannu a hancinta amma Halima kam ba sauran numfashi.
Kukan da yai yawa ne ya fito da Fatima a d'aki tana tsaki,lalle daf take da ta bar gidan nan,haka kawai,yara sai shegen 6acin tsiy...

"Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un...Halima!!!.
Jin kalmar nan ne yasa ta yin shiru tare da nufar d'akin da sauri.
Daga uban har yaran kuka suke,wanda da halama yaran suna taya baban nasu ne ba wai dan sun san mey yake wa kukan ba.

Da sauri ta karasa tare da fad'in
"Mey ya samu Haliman Ya Kabir kuke kuka?
Da sauri ya dago tare da fad'in
"Lafiya fa na batta Fatima duba min ita dan Allah bata numfashi..
Kan ya karasa har ta hau jijjiga itama amma Halima shiru.

A kai ta d'aura hannu tare da runtuma ihun
"Wayyo yayata,wallahi ta mutu Ya Kabir.
Kai ya hau girgiza mata yana mai sake girgiza Haliman hawaye na zubar mishi.

"Subhanallah.. Ihun nan na lafiya kuwa a gidan nan Rabi?
Kallo maigidan nata tayi tare da girgiza mishi kai.
"Gaskiya kukan ya yi yawa,ka leka ka jiyo shin lafiya?

Zaga wa ya yi yana sallama,jin shiru ga ihun kukan Fati da yara yasa ya karasa bakin kofar yana fad'in
"Malam Kabiru lafiya kuwa?
Da azama Kabir ya tashi tare da fitowa ido fal hawaye yana mishi bayani.

"A'a, bari dai muje asibiti a gani,kar mu zauna a gida.
Kai ya kad'a da sauri,sai yanzu ma ya tuna da wani asibiti.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

3_Ido kawai ya zuba mata a asibitin hawaye na zuba,kafad'arshi likitan ya dafa tare da fad'in
"Kai hakuri,tabbas rai ya yi halinshi,a iya binciken da mukai yanzun na gano 'internal bleeding' take a hankali ta ciki har yai illah..

Kanshi ya d'aura a gawar tare da rungumota,
"Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un..
Ita ce kalmar da yake ta nanatawa yana hawaye.
Sabo tirken wawa,koh ba aure yasan Halima jininshi ce halak-malak,wacce suka shaku tun zamanin yarintar ta.

Hak'uri makocin yake bashi,kan a d'au lokaci har zancen rasuwar Halima ya iske masu tahowa suna a yau.
Halima mutum ce,har da guda,dan haka kowa yaji mutuwar nan barin in anji yadda Kabir ke sururun fad'in yadda suka rabu yana hawaye.

Ga kukan da Sultana take tare da yayyenta suna kiran su Maman Saifu,abin sai ya kara rikitarwa barin Saifu mai wayo.
Rayuwa kenan.
****

Yau kimanin sati uku kenan da rasuwar Halima,zaune yake a d'akin Haliman ya jingina kai da bango,yayin da yaran duk sukai matashi da cinyarshi Amjad da Nass suna wasa.

Ido Saifu ya zuba ma Abban nasu,chan ya ce
"Abba yaushe Maman zata dawo?
Kai ya kautar jin zancen Saifu,ya gaji da zula mishi karyar zata dawo kullum.
"Kai hakuri Saifu,ta kusa dawo wa..
Kuka yasa mishi yana fad'in shi fa Mamanshi kawai zaije.

Ganin haka yasa sauran kannen ma suka hau tayashi shima yana yi.
Umma dake a d'akin waje ta tashi tare da ajiye madarar da take bawa Sultana ta nufi d'akin da ita dan lallashin d'an da jikokinta.

"Fisabilillahi Kabiru rayuwa zata yu a haka?
"Kai ne fa zaka sa yaran nan su manta mahaifiyarsu ta yadda zasu ji basuyi maraici ba,amma a kullum sai dai ka tasa su gaba kai kuka su kuka,toh wa zai lallashi wani?.. Halima ta rasu,kasan kuma ba wai zata dawo bane...

Kallonta suke har yaran,sai dai sun daina kukan sai na Sultana.
"Daf nake da tafiya kuma har yaran muddin bazaka sawa ranka salama ba.
Hawaye ya goge tare da girgiza kai.
"Kiyi hakuri Umma,na daina.
"Yauwa,koh kaifa.

A sannu yau da gobe har sun ware sai abinda baza'a rasa ba har ya koma aiki.
Ido jajir ya dawo ma Umma yau halamun yaci kuka yana mai mika mata takarda.
"MashaAllah, Allah sanya alkairi, mashaAllah.

Tashi ya yi tare da shiga d'aki, a kullum adu'ar Halima ita ce Allah d'auka ka shi,gashi yau ya samu promotion amma ba Halima,a lokacin da dad'i yazo bayan wuya Halimanshi ta k'au.

BAYAN WATA BIYAR.

"Na fad'a maka dole kasan abinyi,koh dai ka kara aure,koh na tattare inawa-inawa na bar maka gidanka,mutum sai taurin kai,karan nan kam zan matukar baka mamaki.

Kasa ya yi da kai tare da fara bata hakuri kamar kullum.
"Hakuri d'aya ne shine kai aure,in ba haka ba a goben nan zan bar garin nan.

"Dan Allah Umma kiyi hakuri,toh ni ina ma naga matar aure,wallahi bani da ita sai dai ki nema min na yarda.
Baki ta washe tare da gyara zama.
"Ko kai fa,yanzu naji batu.
"Ganan Jamila y'ar wajen kanwata, nasani kaima ka sani dan kai taki aure har yanzu,a da ban goya maka baya ba dan sam bazan so kai wa Halima haka ba yarinyar kirki.

"Amma yanzu tunda babu ita sai ai tuwona mai na kawai,nasan Jamila nada hankali, zata rike yaran nan tunda tana kaunarka.

Shiru ya yi,amma shi kam in ta shi ne a barshi aure ba yanzu ba sai ya huce,amma tunda Umma ta ce zance ya kare,kawai sai yai na'am

Kan wani lokaci zance har ya kankama, Jamila tai murna, cikin nasara akai aure amarya ta taro garin Kaduna,sati guda Umma ta tafi ganin Sultana tayi kwari.

Kallon Sultana take tana maka tsaki ganin yadda take tsala kuka ta tashi bacci.
"Mtsww,wace rayuwa ce wannan, mutum yai aure dan ya huta amma jarabar ya'yan nan ta hanaka hutu.
Bargo ta yaye tana kara naka tsaki tare da kallon agogo.

Kai ta girgiza tare da yin kwafa,
"daga fita siyan alewa har kwalliyar da nayi ta tuje har yanzun bai dawo ba.
Kukan da Sultana ta kara yi ne yasa a tunzure ta maka mata tsawa.
"Dalla kimin shiru kema,jarababbu kawai.

Shiru kuwa Sultanan tayi tare da sanya hannu a baki tana jan zuciya.
Zai wuya kaji kukan Sultana,dan mai matukar hakuri ce sai in tana jin yunwa.

"Mtsww.
Dankwali ta figa tare da fita waje ta batta a kan gado tai kitchen.
Da kallo ta bita tare da fara ta6e baki halamun kuka.
Da abincin ta dawo a hannunta tare da dangwarar wa.

"Daga yau abinci zaki fara ci dan bazan iya wahalar dama kunu ba kullum.
Kamar wacce taji kawai sai ta kara sa kuka.
Kai ta dungure mata tare da mika mata abincin da karfi da yaji yarinya tana kuka.

"In banda bakar mugunta a tafi dake man a barni naci amarcina amma aka barki ban haifa ba ni da reno.
Kukan da suka ji ne yasa da uban da yaran da gudu suka karaso cikin gidan,jin hayaniyarsu yasa da sauri ta finciko Sultanan ta hau rarrashi yarinya na bangarewa.

"Mey ya sameta irin wannan kukan tun a titi nake jiyo wa.
Wayen ce ta fara cikin rashin gaskiya.
"Wai fa dole sai dai na bata abinci shine dan na hana dan akwai yaji take wannan ihun.

Karbarta ya yi yana goge mata baki tare da  kallon Jamilan da tuhuma.
Yasan Sultana bata ra'ayin abinci,
"Toh ina kununta?
Tashi tayi tare da fad'in
"Bari na kawo.

Da harara suka bita shi da da Saifu,dan sarai ya tsani Auntyn nan tasu dan muguntar da take musu a sati kwai da tafiyar Umma.

Kamar kullum yau ma ya dakko Sultana tare da yi mata shimfid'a yana had'a rai,dan tun dazun ta bashi haushi.
Ido ta sa mishi,in ranta yai dubu toh ya 6aci,a kaf yaran tafi tsanar Sultana,dan akanta kullum ba ita ba miji sai lallashin ya'rshi.

Wani kallo yai mata kamin yaja musu bargo dan har yanzu Sultana bata dawo normal ba kamar da.
Dan haka yau da safe yana fita aiki ta hau huce wa bisa kansu da duka da tsawa.

Sultana Saifu ya dakko dan sam bata da nauyi sukai gidan Aunty Rabi.
Hawaye ta goge,dan duk tana jin komai tun fitar uban,tanan kam tasan yara sunyi maraicin uwa.
****

Yau da gobe ya wuce wasa,da iyayinta ta tasamu kan Kabir har yake kulata, agabanshi sosai take kula da yaran har ya zamana ya saki jiki da ita akan tana kula mishi dasu fisabilillahi.

Sai dai in aka ce ba idonshi mugunta ta rinka yinta kenan har sai Aunty Rabi ta zagawo tukunna.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

4_Ita batta a duka,amma bata hanasu abinci sai randa abin ya motsa.
Sai Aunty Rabi tayi kamar ta fad'a mishi sai ta bari,duk a kullum Saifu na kawo karar basa son Aunty Jamila muguwa ce.

Band'akin waje ta shige kusan awa guda tana wanka,Nass dake tsaye tuni ya fara kukan  kashi yake ji,ga foo amma yasan ta musu gargadi da kashin foo sai ya hau shadda,sannan basu ba shiga na d'aki.

Tsoron duka yasa ya tsaya sai matsewa yake yana kuka.
Tashi Saifu ya yi tare da dakko mishi foo ya ajiye mishi tare da cire mishi wando da nufin ya zauna akai.

Sauri yake dan ya cire, sai dai tuni har ya fara saka a wando,amma duk da haka sai ya zauna a foo din cikin sauri.
Karasa cire mishi wandon Saifu ya yi ya matsar yana kallon band'aki jin bud'e kofar Aunty Jamila.

Baya ya yi ganin ta waro ido waje tare da fad'in
"Kan uban chan..kashi ne haka Nasir?
Da sauri Saifu ya ce
"Kiyi hakuri Aunty Jamila.
Buta ta ajiye tare da waiwayen neman abin duka.
Tashi Nass din ya yi da sauri ya 6oye a bayan Saifu tare da sakar kuka.

Takalminta na danko ta cire ta hau maka mishi yana kuka tare da rirrike Saifu kan ya cece shi.
"K'auce koh kuma na had'a da kai shegu kawai.
Kare Nass yake yana bata hakuri amma taki hakura,tuni ta hau jibgarsu gaba d'aya tana mai zagin uwar su, ganin su Saifu na kuka yasa Amjad d'aukar Sultana dake cinyarshi duk suka sau kuka.

Hijab Aunty Rabi ta d'auka tare da saurin zaga wa.
"Wallahi sai ka wanke, ni zaku had'a wa wannan kazantar?.. D'auki maza ka shiga band'aki ka zuba mishi rawa ya wanke kai ka dawo kuma ka gyara min wajen nan...
"Haba Jamila,wane irin rashin imani ne wannan?.. Nawa ma Nasir yake da har zaki ce ya wanke kashi?..

Hannu ta daga mata.
"Ni fa bana ciki da wannan kinibibin wallahi da munafurci,jakarsu ce ni? Wallahi bazan wanke kazantar wannan kartin yaran ba..
Hawaye Rabi ta goge,
"Ni zan wanke musu toh.

Baki ta ta6e tare da fad'in
"Ke ki ka jiyo,amma ni dai bazan sa hannuna a kashin nan ba.
Juyawa tayi gun da su Amjad suke tare da nuno su da takalmin
"Kuma kumin shiru kamin nazo yanzu naci uwar...

Shiru tayi tare da saurin hullar da takalmin ganin yadda Kabiru ke huci a gabanta tamkar kububuwa.
"Mey ya dawo dashi iyanzu?...
Kan ta karasa tunani tuni ya wanke ta da mari.

Jin ihun Jamilan da faka takalmi yasa Rabi fitowa daga band'aki.
"Ashe bakida mutunci?.. Muguwa azzaluma..wallahi yau sai na fanshe dukan da yarana suka sha a gunki..
Ganin takalmin bazai mishi ba ya hau jibgarta da hannu yana surutai.

"Kayi hakuri Baban Saifu ka batta haka dan Allah..
"Barni da ita Aunty Rabi,ashe kema kina sane da irin muguntar da take baki ta6a fad'a min ba sai Saifu dake min complain kullum..
"Kayi hakuri bazata kara ba..
Samu tayi ta fisge tare da yin d'aki da gudu ya bita, ganin zai cimmata ta shige band'akin d'aki ta rufe.

"Ki fito tun wuri ki san inda dare ya miki,dan wallahi yau sai kin barmin gida,irin haka yasa naki jinin kara aure dan bakar mugunta irinta *MATAN UBA* dana shata.
Mita yake har Aunty Rabi ta gama gyara Nass ta wanke wajen duk suka rukunkume uban suna kuka.

"Mu dai bama son Aunty Jamila Abba..
Tsugunawa ya yi tare da goge musu hawaye.
"Nima bana sonta,yau zata tafi kunji?..
Sultana ya kar6a tare da jijjiga ta.
"Yi hakuri Ummata.

Hawaye Aunty Rabi ta kara goge wa, banda rashin imani a yaran nan ina abin duka,marayun Allah wanda ya dace a tausaya musu.
Nawa Nass yake? Bata jin har yanzun ya kai shekara uku.

Daga uban har yaran tausayi suke bata,dan haka da sauri tai hanyar waje tana goge hawaye.
Bata jin a iya tashin yaran nan ta ta6a jin Halima ta duke su haka,kar kara ita batta a zan ma duka,karshe su bata hakuri ya kare.

Kai ta girgiza, mutuwa bata barin wani dan wani,tasani da tuni ta bar Halima da yaranta.

Kaya ya sauya musu tare da tambayar sunci abinci?
Kai suka kad'a
"Eh.
Saifu ne ya ce
"Har yanzu Mama bata dawo ba Abba,da itane bazata daki Nass ba,in ta dawo sai ta rama mana koh?

Kai ya kautar tare da goge hawayenshi,
"Hakane,nima bazan sake yarda a dukar min ku ba Saif,wannan ma Allah zai maganinta,muje mu tafi unguwa.
Jaddada mata ya sake kan wallahi in ya dawo ya sameta tai kuka da kanta.

Yana fita kuwa ta had'a y'an chanjin hannunta ta arce Kano.
****

Kuka yake ma Umma da tazo yana tsara mata muguntar da Jamila take ma yaran,
"Umma dan rashin imani Sultana ma bata bari ba,babban abin kuma yadda take maka wa Halima zagi alhalin tana chan a makwancinta.

"Shin Umma wai duk *MATAN UBA* haka suke ne a duniya koh kuwa ni tawa jarabawarce haka?..
Ban fa manta irin azabar dana sha gun su Tabawa ba,shi yasa tun farko naki auren nan.

Hawaye Umman ta goge.
"Ka yi hakuri Kabiru, amma ba duka aka taru aka zama d'aya ba,ni kaga a gidan wani nake,balle na ce zan zauna da kai,kai kuma kaki rabuwa da yara balle na tafi dasu chan Kano,amma kam tabbas Jamila taban mamaki.

Kuka sosai Jamila tayi jin ya ce bazai iya zama da ita ba.
Rantsuwa take akan bazata kara ba shikam ya ce sam,dama chan ba sonta yake ba,haka yaranshi.
Haka tana ji tana gani aka kwaso kaya da saki d'aya.

Makaranta yasa Nass dan ya rinka bin su Saifu da Amjad,domin ragewa kanshi aiki,in zai tafi aiki sai ya kai Sultana gidan Aunty Rabi,da haka suke rayuwar su har ranar da Aunty Rabi suka zo tashi an ma mijinta transfer.

Kuka sosai tayi ita da yaran,dan koh ba komai sun shaku sosai,toh dadinta d'aya Kano suka koma.
Tun bayan tashin Aunty Rabi ya fara fuskantar matsala ta inda zai bar Sultana dadinshi d'aya anyi hutu lokacin,dan haka ya tarkatasu suka tafi Kano hutu.
***

"Dole dai abinda ba'a so din Kabir shi za'a yi,hakura zakai ka kara auren koh dan kula maka da yaran.
Kai ya dago cike da marairaita.
"Dama jiya mun shawarta da ita Mahaifiyar marigayiya,kayi hakuri ka auri Fatima,inaga ita dake halalin Halima ce dole ta rungumi yaranta.

Tsam ya yi,shawarar tayi,sai dai yana tunanin yadda zai iya zama da Fatima a shimfid'ar Halima.
"Wannan ne fa kawai maslaha,hakuri kawai zaka yi.

Gidan abokinshi yaje wanda kusan tare suka tashi,shine babban abokin shawarar shi in yazo Kano.
"Kabi shawarar Umma kawai,ina ga wannan ne kawai mafita,dan ba wanda zai rikesu sama da y'ar uwar mahaifiyarsu.

"Ka duba nawa zaman mana,kaga zaiyi wuya ka gane yaran Sumayya dana y'ar uwarta da aka min auren huce haushi da y'ar uwarta.
Kai ya jinjina,dan yasan yadda abin yake,bai manta kiyayyar da yayar Sumayya ta gwada ma abokinshi ba karshe aka raba auren aka bashi kanwarta ita ta tafi ta auri wanda take so.

"Ni kuwa kasan rabona da yaran nan naka na kusa shekara takwas,tun fa haihuwar Sumayya na farko.
Murmushi abokin yayi.
"Lalle kam yanzu sun girma sosai,suna islamiya yanzu kila ka gan..

Shiru ya yi dan jin sallama had'i da kukan Farida tsakaninta da Allah kuka take.
Daga kitchen Umman ta leko dan jin kukan rabin ranta Farida.
Direct wajen Abbansu ta nufa fuska rufe da dankwalin kanta da ya ware,had'i da hular da jaka da takalmi hijab a hannu.

"Mey ya faru uwar bankaura?
A gabanshi ta zube tana shura kafa cikin shagwa6a,tsaki Abban nasu ya d'an yi,yasan mud'in bai tambayi mey ya faru ba ta dinga wannan abin.

"Toh ya isa,yi shiru,ke Aisha mey yasa Farida kuka?
Dariya Aishan take harda ta keta,ganin hakan yasa ta kara jiniyar shagwa6ar tata tana mey hullawa Aisha hijab d'in hannunta.

Cikin sigar lallashi ya ce
"Kyaleta, fad'a min mey aka miki yayata?
Ikon Allah Abban Saifu ya tsaya gani,yasan daga shi har abokinshi akan yara sam basu da zafi,halinsu d'aya shi yasa abota tazo d'aya.

Kukan ta bari tare da had'iye guntun,
"Abba dazun fa kace mana kana da d'aurin aure a garin nan yafi a kirga koh?
Kai Abban ya kad'a mata,
"Eh hakane,mey ya faru?
Zama ta gyara tare da cigaba.

"Abba shine,shine fa tun fa daga layin islamiyarmu Abba nake ganin taron samari da y'an mata duk sunyi kwalliya har nazo layin nan samari ne duk da matansu a tsaye..
Kai ya sake kad'a mata halamun yana ji.

Cigaba tayi da fad'in
"Toh Abba fisabilillahi ba dole nai kuka ba tunda mu ka ki mana aure kana kallo yadda samari suke ta karewa a garin nan suna aurensu sunkusa su kare...

"Mtsww...
Tsaki Abban ya yi,tare da kok'arin neman abin duka,ganin haka da sauri taja baya tana kara kukan,ita fa har ranta da gaske take,sai dai jin tayi karo da mutum yasa ta juya tare da barin kukan,
haka kawai kuma suna had'a ido taji kunya ta kamata,dan haka da sauri ta mike tare da sanya gudu cikin kunya.

Dariya yai sosai,sai daga bisani shima Abban abin ya fara bashi dariya yana girgiza kai.
"Farida!..Farida!!..
Kai ya sake kad'awa
"Farida ake fad'a maka, uwar bankaura,har kullum jinta take yarinya,in ta kwa6a ma shirme sai kaji kamar ka sa kuka.

Kai Baban Saifu ya kad'a
"A'a da fa gaskiyarta,kar suna kallo ai ta aure samari su su tashi a tutar babu.
Dariya ya sake yi.
"Toh yanzu kai in ka tsareta kila kalmar auren kawai ta sani in dai Farida ce.
Kai ya jinjina
"Lalle sun kam girma,mashaAllah.

Ita kwa kitchen ta shige gun Umman,itama dariya ta samu tana yi lokacin da Aisha ke bata labarin.
Kan Aisha tayi da zummar kai mata duka tai bayan Umma.

"Kyaleta Faridee na,zo nan,ke ai naki saurayin special ne,kina a zaune zai zo har inda ki ke ya d'auke ki ku tafi gidan ku.
Da sauri ta ce
"Allah Umma?
Kai ta kad'a mata
"Da gaske.
Tsalle ta sa tana murna,sai Umman ta girgiza kai.

"Allah ya nunan ranar girmanki Farida.
Ba musu ta ce
"Amin Umma.
"Toh maza kuje ku cire kaya ku nutsu ku sanya hijab ku kai ma su Abbanku da Uncle d'in Kaduna abin sha.

Kai suka kad'a, da gudu kuma suka nufi d'aki dan yin yadda ta ce.
"Yauwa,toh ke rike faranti da kofuna,ke kuma d'auki kunun ayar nan,ku shiga da sallama,sannan ku durkusa ku sake gaishe shi.

Kai suka kad'a.
Dan haka a nutse suka isa parlourn kai a kasa kamar gaske suka gaida shi,da fara'a ya amsa yana tambayar su makaranta har suka tashi.
Binsu ya yi da kallo ganin suna tafe amma suna dukan kafad'ar juna sai ya kad'a kai.

"Abokina kana shan drama a gidan nan.
Kai ya kad'a
"Sosai kuwa,mud'in Farida na gidan nan.
Da wannan suka cigaba da abinda ya kawo shi.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

5_Da shawarar Abokinshi yabi ta umma,haka duk dangi sun yaba da shawarar,dan haka kawai sai aka d'aura auren da zummar in zai koma su tafi da amarya Fatima tunda dama bazawara ce kusan tare akai musu aure sai dai ita a shekara biyar auren ya mutu dan bata haihu ba shi kuma miji dama yana da matarshi, uzzura da gori ne ya kar auren ta dawo gida.

*A KADUNA*

"Fatima.
Kai sinke ta amsa.
"Dan Allah ki rike min yara da amana,ki sani tamkar nauyi Allah ya daura miki bisa kanki,ki rike min su tamkar naki..

"InshaAlla zaka sameni da rike su tamkar nawa.
Murmushi ya yi tare da mata godiya.
Da dare duk suna zaune suna kallo Sultana na a cinyarta tayi bacci.
Kallo su Saifu tayi,sunyi kane-kane a cinyar baban nasu d'aya da remote Nass yai bacci.

Tana jinjina irin sangartar da akai wa yaran,a ganinta yanzu ai sun kai minzalin barin zaman cinya.
D'aya bayan d'aya yake dibansu tana taya shi duk suka kwantar da yaran a d'akinsu,ganin ya dau Sultana sun fita yasa ta bishi da kallo.

D'akin ta bishi,ga nan Sultana ya shinfid'e ta shi ya shiga wanka.
Kaya ta cire tare da maye gurbinsu dana bacci ta d'ane gado.
Fito wa ya yi sanye da jallabiya yana goge ruwan kanshi da towel.

Kallon mamaki yake mata ganin har ta kwanta ba koh wanka.
Murmushi ya yi tare da zama dan shafa mai.
Halima kam ta daban ce,dan haka ya kasa had'a ta da kowacce d'iya mace wajen kunya da kawaici da iya ado sassanya.

"Kiyi alwala muyi sallah.
Kai ta dago tare da kallonshi,ganin ya juya baya yasa ta tashi tare da shiga bayi.
Sun idar amma ya kasa tashi sai lazimi yake,chan har ta gaji ta tashi tare da kwanciya.

Allah yaga tun aurenshi da Jamila take haushin dama ita ya aura,ta sani Ya Kabir abin son kowacce Y'a mace ne barin ita data jima a son dama shine mijinta.
Bayanshi take kallo da wani irin siga,yau Allah ya mallaka mata shi cikin ruwan sanyi.

Murmushi tayi ganin ya tashi yana nad'e sallaya,binshi take da ido komai yake yinshi cikin nutsuwa da birgewa.
Shi kam tunanin ta yadda zai iya kebanta da kanwar Halima yake shi yasa yake ta  sininki.

Satar kallonta yake,ganin haka yasa ta rufe ido kamar mai yin bacci.
A dirare ta zauna a gefen gadon tamkar ma shine amaryar.
Ganin zaman bazai yu ba sai ya gyara filo tare da jingina yana dan leken ta.

Gaba d'aya data rufe ido sai ta juye mishi Haliman.
Da sauri ya d'auke kai tare da janyo Sultana ya d'aura bisa hannunshi yai mata filo tare da tofeta da adu'a.

Tsam tayi tana kallon wani ikon Allah,karamin tsaki tayi tare da juya baya tana gunguni ciki-ciki,yaji, koh bai jiba sai Allah,shi dai tuni ya tsunduma a baccinshi.

Warai ta tashi,da halamun wannan tafi Jamila Bariki,ita tai ma yaran wanka,ta basu abinci gwanin sha'awa har suka tafi makaranta.
Tun yaran basa sake wa da ita da baban nasu har suka ware in banda Saifu,da sannu duk ta siyesu da halaiyar da koh a da bata da ita.

Yanzu kam ya aminta yaranshi sun samu madadin karamar uwa,shi kam Saifu har yanzu bai sake da ita ba,dama kuma tun zamanin mamansu ma baya shiri da Fatima.

Sau tari baban yakan sauya mishi harce da turanci in tana wajen dan yasan bata jin turanci ita islamiya tayi tun a jss3 ta rufe zuwa,dan haka da yaga yana kama kai ya tambaye shi mey ya faru,kullum amsar d'aya ce
"Nothing..
A haka har aka shafe shekara.

Samun promotion nashi a baya ya kawo bud'i sosai a rayuwarshi,aciki harda daga wa daga Kaduna zuwa Abuja.
Abu na farko da ya fara shine sauya musu makarantar yaran masu kud'i, dan yana ga koh kobon shi zata kare toh fa zai bawa yaranshi ilimi mai kyau.

***
Shekara d'aya ta shud'e lafiya ba tare da wani abu ba,wanda shi yai dai-dai da shekara su biyu da aure, abu d'aya ne da ya fara fuskanta shine sam yaran basa ra6ar Fatima har Sultana,in dai yana nan koh kiranta tayi yanzu zata fara kuka.

In ya tambaye su kuma yanzu zasu fara raba ido babu mai fad'in dalili.
A boye-a boye ashe take sau musu dan hali,ita ba duka,a'a, mintsini da jan kumatu su Jan kunne sune aikinta.

Sannu a hankali sai ya fara ganin wani sabon sauyi,mud'in suna d'aki tare da Fatima toh kowanne yaro zai nemi waje yai ladab babu mai ra6arshi har Sultana.
Dan kam zasu riketa dan ma kar taje suna yi suna kallon gefen Fatima.

Ranar suna zaune a parlour sai zuba take mishi ya kanya, shi kam d'aya bayan d'aya yake karewa yaran kallo,akan Amjad ya dire kallonshi.
"Kai Amjad,zo nan..
Da mamakin shi sai yaga ya kalli gefen da Fatima take yana sissinke kai.

"Amjad baka ji Abba na kira ba...
Da sauri yaron ya tashi jiki na 6ari yai gun Abban.
Baki sake yake kallon yaron, duk sun fara zama wasu dolaye mud'in a gaban Fatima ne.

Kallon Fatiman ya yi,da sauri ta sau mishi murmushi.
"Mey ya samu kumatunka naga ya kumbura?
Cikin sauri ya girgiza kai tare da fad'in
"Ba komai.
Kai ya girgiza.
"A'a Abbana,fad'a min mey ya kumbura ma shi?

Saifu ya kalla,shi kuma ya kalli gun Fatima,yana kallo ya kad'a mishi kai halamun ya ce ba komai.

Shiru kawai ya yi,amma tabbas yasan da wata a kasa,yana fatan ba zargin da yake bane.
Dan ba wannan bane karo na farko ba,ya ta6a ganin bayan kunnen Sultana ma a kwarzane,sannan cinyar Saifu tayi ja.

"Gobe yaran abokina zasu zo hutu su biyu daga Kano,gashi a goben nake son tafiya Jos work shop,toh zan jira su zo sai na tafi jibi in Allah ya kaimu.
Kai ta girgiza,
"Allah ya nuna mana.
Yaran ya kalla,da mamakin shi sai yaga duk suna neman kuka.

Hannu ya mika musu,duk sai suka kasa tahowa in banda Saifu,dan haka da kanshi ya tashi tare da daukan Sultana.
"Kuzo muje naji mey ke damun sojoji na.
Hannunsu ya kama,duk da yana kula da yadda Nass da Amjad ke kallon gun Fatima.
"Common boys..

Chakulkuli ya fara musu,a hankali suka fara warewa suna dirka dariya,take sai suka manta da hudubar Fatiman suka bishi d'aki.

Kwafa tayi bayan ta gama bin bayansu da harara.
"A hankali zan saita ku wannan rawar kan naku da 6aci duk sai kun daina.
****

"Ku shigo man ku ka tsaya a bakin kofa.
Juya wa yaran sukai tare da kallon bakin kofa jin muryar Abban.
"Saifu,kuzo ga yayyenku nan su Farida,
Tashi sukai da nufin isa gun shi Fatima ta fito a d'aki duk sai suka tsaya banda banda Saifu da ya karasa.

"Kuzo man.
Yake ta fara da fad'in
"A,har sun iso?
Kai ya kad'a mata yana kallon yaran,abin har ya daina bashi mamaki ya dawo bashi tsoro.
Ta yaya in sunga Fatima zasuna haka?

"Ku karaso.
Katseshi tayi,dan haka sai ya kauce su Farida suka shigo.
Duk iyayin Farida da Aishan da murnar zuwa Abujan duk sai suka yi sanyi.

Akalla yanzu za suyi shekara 10,zuwa tara,dan duk sun shiga Js1.
"Ku zauna yanzu zan dawo,ku kuzo muje kan suci abinci Amjad.

Da sauri har sun rigashi fita a parlourn, yana ji Fatima tana cewa Sultana
"Kema tafiya zakiyi kawas?.
Mota ya bud'e musu,yau kam dole yaji dalili gun yaran.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

6_Yara kam fur kowa yaki magana,sai Saifu ke kwata magana sai Amjad yai saurin girgiza mishi kai.
Kai ya kad'a, koma meye yasan gaskiya zatai halinta wataran.

Washegari da kuka suka rabu,duk ya sake damka amanar yaran a hannun Fatima,zai iya cewa wannan ne karo na farko da zaiyi tafiya ba tare dasu ba.

Bayan fitarshi ta juyo da kamar gaske a gaban Abbansu tana lallashi, yana bata baya ta maka musu tsawa.
''Ku wuce mu shiga ciki ya'yan mai.
Kai Farida ta dago tare da kallonta,sai harara take maka musu jiki na 6ari suka wuce banda Saifu da bai daina kukan ba.

Bayan su suka bi,kowa ya zauna ya nutsu yana maida kuka.
Kan Saifu ta dawo cikin zare ido,
"Kai ba zaka rufen baki uban d'an taurin kai?
Juyawa mata baya ya yi yana cigaba da kukanshi,a razane ta juyo tare da nufo gunshi,kamin ya yi kwakkwaran motsi ta damki kumatunshi tun karfi ta hau murdewa tana kuma marin bakinshi da d'ayan hannun.

"Rufe min baki,shegun yara sarakan y'an 6acin tsiya...
Aisha Farida ta zungura da kafad'arta cikin rad'a
"Wannan muguwa ce wallahi Aisha...
Zungurarta tayi da halamun tai shiru,harar inda Fatima take tayi,ganin yadda Saifu yake kuka take Jan kumatunshi da mari wai sai ya yi shiru.

"Mtsww"...
Tsaki taja tare da juyawa d'akin da aka sauke su rai 6ace,ji take tamkar taje ta shigar ma Saifu.
Cika Saifu tayi tare da juyo wa jin tsakin,da kallo ta buta har ta shige d'aki ta rufo kan ta dawo kan Saifu.
"Bazan lamunci wannan ta6arar ba wallahi, dakaku zanyi tunda Abban naku ya kauce.

Kai ta dungure mishi tare da juyawa tana makawa su Amjad harara da sukai tsuru-tsuru.
"Sauran ku,yau na sake naji muryar wani wallahi sai mutum yaji jiki.
Kasa sukai da kai,tana shiga d'aki da gudu sukai wajen Yayan nasu tare da rungumoshi cikin lallashi suna hawaye.

Hannu Sultana ta kai fuskarshi tana goge mishi hawaye tare da girgiza mishi kai yayinda hannu d'ayan ke bakinta tana tsota.

D'akin su Farida suka nufa,duk da ido suka bisu Faridan harda guntun hawayenta.
"Allah ya isanka,azzaluma kawai.
Kallonta suke jin yadda take zafin Fatima.
"Ni fa Aisha tun jiya naji na tsani matar..
Hannu ta sa tara da rufe bakin Faridan
"Ba ruwana Allah,ki rufa mana asiri.

Gun yaran suka je tare da lallashin Saifu,
"Dama haka take muku?
Kai Amjad ya daga.
Tuni suka fara basu labarin Fatima Farida harda hawaye.
"Toh mey yasa baku fad'i ma Abbanku ba?
Shiru suka yi suna kallon-kallo.

Kan wani lokaci har sun ware dasu Farida.
Yunwa ce ta fito dasu,guntun abincin safe suka ci tare da fita tsakar gida yin ball.
Farida kad'ai take yi,da hannu take wa Saifu wai ya shigo suyi.
D'aki ya koma tare da sako takalmin ball ya fito sai wage baki yake.

Ganin haka yasa Amjad ma dakko nasu ya mika wa Nass sai dillika dariya suke
Farida kawai ke ci,dan haka aka raba gida team nata daban na Saifu daban,da taci d'aya shima zai dage yaci.
Yau d'aya sun zage suna wasa cikin kwanciyar hankali dasu Farida.

Sama-sama take jiyo ihu cikin baccinta,dan haka tuni baccin ya fara mata kaura bata ma da lokacin tashi balle ta d'aura abinci har 12 saura.

"Meye haka kuma?
Juyawa sukai jin muryar Fatima cikin tsawa,da sauri Nass ya hullar da ball din dake hannunshi jiki na 6ari.
"Hakuri Aunty.
Hararar su Farida tayi tare da jan tsaki ta juya,itama tana hura hanci ta bita da harara.

Anyi ball ciki ya rarake,tuni kowa ya fara russuna.
"Ni fa yunwa nake ji wallahi Aisha.
Hamma Saifu ya yi.
"Me too"
"Me too"
Nass ma ya ce
"Me too".
Dan tsaki tayi,tare da kallon agogo.
"In a gida ne ai tuni mun jima da cin abinci,wannan ai mugunta ne.

Tsaki ta kara yi tare da kallon Sultana wacce ta zuba mata ido hannu a baki tana tsotsa.
"Kema kina jin yunwa koh Sultana?
Kai ta kad'a
Saifu ta kallo.
"Je ka ce ma Auntyn ku muna jin yunwa.

Da kamar mai jin tsoro,chan dai ya nufi d'akin yana kwankwasawa sai yaji ta kofar ta bud'e,Farida ya kallo,da kai ta mishi halamun ya shiga kawai,kai ya kad'a kamin ya tutsu.
Su da suke a parlour ma sai sa sukai saukar marin, dan haka rike da kunci ya fito yana hawaye.

"Anki a baku d'in, yunwar ta kashe ku.
Rai Farida ta had'e jin ta fito tana sababi.
"Ai dama guntun na safe na ajiye a matsayin na rana,tunda kun cinye au kunci rabanku sai kuma na dare..
Da sauri Farida ta amshe
"Dare kuma Aunty?
Harara ta maka mata kan ta ce
"Eh har dare,koh da magana?

Baki Faridan ta ta6e tare da kau da kai gefe.
Kofarta ta turo tare da jan tsaki.

"Kaima naka iya ja mata Allah ya isa ne, amma ace duk girman nan naka ka tsaya kuka,toh wa zai tarewa kannenka fad'a?
Shiru ya yi kamar mai nazarin zancen.
"Ni ba ma wannan ba,mey zamu Ci yanzu?

Dube ta fara,akan Corn flakes
ta dire,da sauri ta tashi tare da nufar kan dining din ta dakko da madara da sugar.
"Abu mai sauki,musha corn flakes kawai.
Kofuna ta d'akko kowa ta zuba mishi,da wannan suka samu suka cike wani gurbin,sai daren kuwa ta basu indomie.

Washegari.
Har sha d'aya bata fito ba ga Sultana acici ta fara kukan yunwa tun corn flakes da suka kora dazun.
Kallo Saifu tayi,sai ta tuna da marin da ya sha jiya,dan haka da kanta ta tashi tare da nufin taso ta.
"Ke Farida wallahi fa ba ruwanmu.
Harara tai mata kan ta tura kofar d'akin Fatiman.

Bacci take hankali kwance, dan haka sai ta kai hannu kan filon tare da fara bubbugawa.
"Aunty!.. Aunty!!!.
"Mtsww"..
Tsaki tayi,tuni Faridan ta had'e rai, duk da tana karamar amma ta tsani tsaki.

"Ke..
Kallota tayi rai had'e
"Mey ki ja zo yi min har d'aki?
Kai ta kautar dan jin warin bakinta na yawun bacci da sauri.
"Abinci Sultana zata ci naga shiru ba'a daura ba ne shine nazo tada ki.
Tsaki ta sake yi tare da juya mata baya wanda da sauri Farida ta kai hannunta hanci halamun toshe wa.

"Kinji Aunty...
A zabure ta mike tare da yarfo mata zagi.
Ciki-ciki ta ce
"Allahumma yahdiki.
Da ido ta tsareta
"Mey ki ka ce?
Kai ta k'autar hannu bisa hanci.
"Ni ba abinda nace.
"Toh wa ki ke rufewa hanci?
Baya taja tare da sauke hannun.

"Kefa dama tun jiya naga take-taken baki da kunya,toh bazan d'aura ba,wanda yaji yunwa ya fita ya daura...
Kwanciyarta ya sake yi hakan yasa Farida ta6e baki tare da fita.
"Yau fa ake yinta,nifa badan ina tsoron Umma ba da wallahi na sau rashin m.

Gunta Sultana tayi tare da fad'in abinci.
Baya ta bata tare da goyata,
''Zaki sha corn flaks?
Kai ta girgiza mata tare da fad'in
"Abinci.
Aisha ta kallo,
"Ba mun iya dafa shinkafa da miya ba?
Kai ta kad'amata
"Toh muje in da miya mu dafa,dan ko ni yunwa nake ji.

"Um-um Farida,ni fa ba ruwana,wannan matar in ta zaune ki wallahi babu mai kwatarki.
Baki ta ta6e tare da kallo Saifu.
"Zo ka nunan inda kayan miya yake,ina ruwana da ita,mai warin bakin kawai.

Kitchen ta nufa,cikin sa'a kuwa akwai guntuwar miya a tukunya ta jiya da taiwa cikinta su ta basu indomie.
Rishi ta girgiza, cike yake da kalanzir,wannan bata matsala dan ta iya kunna wa.

"Ina ashana?
Da sauri Saifu ya kawo mata,
"Yauwa.
"Dakko tukunya babba.
Nan ma da sauri ya shiga store tare da kinkimo katuwa irin ta cin gidan su.
"Yauwa.. Saura ruwa, da gishiri,in ya tafasa sai a wanke shinkafa a zuba,ai na iya.

Aisha ce ta leko,ganin tilin shinkafar da Faridan ta debo zata wanke.
"Ke Farida,Allah wacce Umma take auna mana bata kai wannan ba,bari ki gani.
Ragewa tayi,tare da rage ruwan,
"Eh na tuna,in ta tsotse sai a kara har sai an ta6a in ta fara fashewa,wallahi na tuna.

Risho suka kure,dan haka tuni ruwa ya tafasa,ana watsa shinkafa ana matsawa gefe dan yadda ruwan ke tafasa.
Da taimakon Aisha dai shinkafa ta had'u kasa duk ruwa,haka suka yad'e aka watsa a faranti tare da juye miya gaba d'aya da nama suka dawo parlour.

Sai murna suke har yaran yau kam sun shiga kitchen da kansu sunyi girki.
Hankali kwance yau suka saki jiki da su Farida sai da sukai nak duk an 6ata parlour da watsin shinkafa ta fito jin hayaniyar tai yawa.

"Kanbu...
Duk suka juya jin muryarta,
"Meye hakan?
Parlourn take nuna musu kowa yai shiru.
"Wa ce gwanar girkin?
Shiru ba amsa,cike da tsawa ta sake tambaya
"Aunty ke fa ki ka ce wanda yake jin yunwa ya shiga ya d'aura, shine gaba d'ayan mu muka shiga dan duk yunwar muke ji..

"Toh naji rasai,kinfi y'ar gida koh?
Kai ta dauke tana girgiza kai.
Kitchen ta nufa,sai gata rike da tukunyar miya a hannu ba komai cikinta.
Duk ido suka sa mata yadda ta sa musu.
"Kun san Allah tunda har ku ka shanye miyar nan gaba d'aya toh wallahi kunci rabonku har na dare.

Ido Farida ta waro,kan ta kai kallonta ga agogo,
"Har dare kuma? Karfe d'aya fa Aunty.
Tsaki tayi tare da juya wa kitchen din,tsintsiya ta dakko.
"Ku tabbatar kuma kan na dawo a d'aki kun share min wajen nan tass wallahi, in ba haka ba jikin kowa zai fad'a mishi.

Wannan ba wani abu bane gin su Saifu,dan haka da sauri Amjad ya d'au tsintsiya ya hau shara Nass ya yi kitchen.
Da yamma tai wankanta ta tafi makota,ganin lalle da gaske take basu da abinci yasa dole corn flakes suka d'akko dan sha.

Binsu tayi da kallo ganin yadda duk suka zuba mata ido,gaba d'aya corn flakes din bai fi Sultana tasha ba ya kare.
Duk haka suka hakura suka barma Sultana dan har ta fara kukan yunwa.

Sallar magriba suka yi,gaba d'aya sun kafawa TV ido ciki na kiran Chiroma,a jima kad'an Farida ta kalli agogo tayi tsaki.
Gwangwanin madara Nass ya dakko,kan ya wuce d'akin su duk suka bishi ido.
"Kai,wallahi Aisha har Abujan nan ta isheni, tunda muke mu Umman mu bata ta6a barin mu da yunwa ba.

Kallonta Saifu ya yi.
"Ai dan ba step mom naku bace,muma da Maman mu tana nan bazata hanamu ba.
Kallon sukai gaba d'aya da tausaya.
Amjad ne ya amshe,tare da fad'in
"I hate step moms,dan mugaye ne I swear Farida.

Aisha Faridan ta kalla,tana shirin basu amsa Nass ya fito rike da school bag d'inshi da gudu.
"Na tuna,akwai sauran biscuit namu da Abba ya sai mana guda 3.
Kar6a Faridan tayi,kamin cikin harara ta ce
"Da ka san da wannka barmu da yunwa? Toh debo mana kofuna.

Manya ne biscuit d'in, dan haka dasu sukai maganin yunwar daren ranar tare da fashaka da madara sai da sukai nak suka kora da ruwa.
A faranti suka juye sauran madarar,duk Farida suke kallo cikin readyn wawaso suna dariya amma tayi sama da ita.
"Ku tsaya a deba ma Sultana sai ayi wawar.

Kai suka kad'a, dan haka a murfin madarar ta bata kan ta ce musu
"Ready?
Da karfe suka ce
"Yessss.
Tana ajiye wa suka hau wawaso hannu baka hannu faranti suna dariya.
Ita kam Sultana gaba d'aya ta kafa kai a murfin kan kace kobo duk sunyi dumu-dumu da madara.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

7_Farantin Saifu ya d'auke da guntu, tuni suka hau kewaye parlourn yana gudu suna binshi.
Bud'e kofar parlourn ne yasa kowa ya yi poster.
D'aya bayan d'aya take kallonsu,ta ma rasa mey zata ce,da gudu Sultana ta 6oye a bayan Farida tana raba ido.

"Bala'i"...
Kai Farida ta kautar tare da fad'in a hankali
"Ki gani akan ki.
Kan su Saifu tayo, da gudu duk suka jeru bayan Farida suna had'e rai.
Tsaye tayi tana kallonsu,tabbas in batai da gaske ba sai yarinyar nan tasa yaran nan sun daina tsoronta.

"Wane d'an uban ne yasa ku dakko min madara ku shanye?
Hanci Farida ta fara hurowa duk suka yi shiru.
"Ba magana nake muku ba?
Nan ma shiru,sai tashin kukan Sultana data fara.

Gyale ta tu6e tare da cin damara ta nufi gaban kayan kallo tana cirar waya.
"Yau hannuna ya daina ciwo,da waya zan cid'a ku...
Gudu suka sa gaba d'aya tare da nufar d'akin su Farida suka kulle suna dariya.

Bugu take wai su bud'e.
"Ashe bamu da wayo in ma mun bud'e.
Zagi ta narkowa Farida,da sauri ta amshe tare da fad'in
"Wallahi ba uwata sai dai taki...
Da sauri su Amjad suka kallota,
"Mun shiga uku,Aunty ki ka zaga?
Mukullin ta cire tare da hararar su,
"Wa ya fad'a ma uwa tafi uwa? Sai dai in na fita ta kasheni.

"Ni dai Farida kinja mana masifa wallahi, yanzu haka kila gobe ma ta sake hanamu abinci.
Hararta tayi.
"Tama isa,kashe mu zatai kenan?.
Shiru sukai jin yadda take narko ashar kan wallahi in har ta kamasu na lahira sai ya fisu jin dad'i.

Hararar kofar Farida tayi,kan a hankali ta ce.
''Wannan anyi mahaukaciya wallahi,mtsww.
Su dai kowa yai tsuru-tsuru banda ita da Saifu.
Ranar sai a d'akin gaba d'aya suka kwana.
****

Kuka take mishi ido duk hawaye tare da mishi kallon tuhuma,
Tafiya yake da zummar rarrashi sai ta daga mishi hannu halamun kar ya karaso mata tana mai cigaba da kukanta mai tsuma rai.
A furgice ya tashi tare da fad'in
"Halima"...

Ko'ina yake kallo na d'akin hotel din gabanshi na fad'uwa.
Kai ya dafe da d'ukkan hannunshi biyu,tabbas mafarki yake,in kuma zai tuna wannan ne karo na uku da yai mafarkin Halima tana mishi kuka,na farko tun aurenshi da Jamila tana fad'in yaranta.

Gaba d'aya sai hankalinshi ya koma gida,ya sani da kila yaran basu a lafiya.
Tashi ya yi tare da nufar band'aki kawai ya dauro alwala ya tada nafila,yana mai rokon Allah yasa yaranshi suna a koshin lafiya.
****

A ABUJA.

Tun asubar fari ta tadasu sallah,dan in da sabo sun saba su sallah bata wuce su sabon Umma.
Duk zaune suke wannan ya kalli wannan wanchan ya kalli wannan dan yunwa dake addabarsu banda Sultana dake bacci.

A dan kwana biyu har sun fad'a.
Har 7 na safe suna zaune,chan dai suka bige da fira Amjad na kallonsu.
"Ni fa yunwa kamar ta kasheni Aunty Farida..
Kalloshi tayi tare da fad'in
"Yanzu ya zamuyi toh?
Nass ne ya ya ce
"Muje irin na jiya muyi break fast da kanmu.

Tsam tayi,kamin ta girgiza kai,
"Toh bari na leka in bata nan sai mu fito.
Kai suka kad'a mata.
Kamar barauniya take sand'a har kofar d'akin Fatima ta leka tana bacci,a ranta ta ce
"Muguwar Allah sa tayi sallah ma.
Har zata wuce taga key ajikin kofar,dan haka da sauri ta koma tare da rufeta ta waje da mukullin dan ma kar ta fito.

"Ku fito na kulleta.
Gaba d'aya suka duru kitchen d'in da zummar daura koma meye suka ja suka tsaya.
Baki sake Farida ta ce
"Kai,lalle matar nan.
Bin store din suka kara yi yadda tasa mukulli ta datse shi.

Kitchen din suka kalla, dan mugunta babu wani abu da zasu juya ya basu abinci su ci sai kwanika da da jerin filasai.
"Yanzu Aunty Farida mey zamu ci?
Kallo Amjad din tayi da har ya fara hawaye.

Duk d'aki suka koma sun zuba tagumi ido ya kad'a yai ja dan yunwa.
A zabure Faridan ta mike tare da fad'in
"Na tuna..
Duk suka bita da kallo ganin ta nufi jakar kayan su.
Kud'i ta ciro na dari bibbiyu tana wage baki.

"Aisha guntun chanjin mu da Abba ya bamu kin tuna?
Baki itama ta wage tare da kad'a kai.
"Toh mu fita mu sai wani abu sai muci.
Gaba d'aya suka wage baki tare da kad'a kai suka mike.
Da kuka Sultana ta mike,dan haka sai suka sunkumeta suka bud'e gate suka fice.

A gun mai shayi suka dire yana soya kwai.
Dari biyar ta fitar,
"A bamu biredi na duka.
Da sauri Sultana ta nuna kwan da yake soyawa ta ce
"Ni wannan.
Kallota tayi tukunna ta kalli kud'in hannunta.

Gaba d'aya dubu da dari uku ne har na biredi,mai biredin ta kalla.
"Soya mana kwai wanda zai ishemu mu duka da biredin dari biyar sai muyi ta ci koh?

Kai suka kad'a mata suna lashe baki cikin murna.
Kowa biyu ya soya mishi tare da zuba musu a leda.
"Gaba d'aya kud'inku 8,60.
Bashi tayi,tare da kallonsu.
"Toh da mey zamu had'a?

"Tea man Aunty Farida,sai dai ba madara da siga Aunty ta kulle.
Kai ta kad'a, kamin ta kalli mai shayi.
"Nawa madara guda shida irin wannan?
"2,10 ne.
Kai ta kad'a.
"Siga fa?
Sai ya ce babu,tare da nuna musu kanti a gefe inda zasu samu.

A kanti suka kaso sauran chanjin dan ganin bournvita da suka yi kan suka koma gida.
Kitchen suka koma tare da daura ruwan zafi mai yawa,a nufinsu suyi ta sha.

Brush suka yi,kan suka dawo.
A baje suke kowa da kofi da an sa mishi kwai a tsakiyar biredi ga katon tea flask cike da wani ruwan na anjima, tuni suka fara kawo network har suna kwasar dariya.
A zabure ta mike tare da fita,sai yanzu ta tuno da kofar Fatima da ta rufe jin bugu.

Tana bud'ewa ta zuba da gudu,dan tasan in ta rikota sai ta Allah.
Wajejen 11 suka leko jin karar tvn parlour.
Zaune take ta hakimce tana kwasar lafiyayyen abincinta hankali kwance tana bin wakar tv.

Fito wa sukai bayan Farida ta ce kar wanda yai dariya.
"Chips" ne lilli6e da ga nan shayi mai kauri tana korawa.
Kai ta dago tare da kallonsu har sunyi wanka abinsu suna kallonta.
Murmushi tayi,ita a tsammaninta kallon za suci suke mata.

"Dama kun koma,dan wallahi kunsha madarar break d'in ku ban girka da kowa ba,dole kuji ajikinku yau.
Waje suka samu tare da zama gaba d'aya a kujera d'aya kusa da Faridan.

"Ke kuma Farida ki ke kowa?
Kallota tayi a yatsine.
"Bari kiji koh yaran gidan nan bana fad'a suna fad'a wallahi, ki saita nutsuwarki kamin ki bar gidan nan koh na saita ki...
"Sannu uwata.
Kai ta kawar.
"Mey ki ka ce?
Rai ta had'e tare da fad'in
"Ni ba dake nake ba.

Abincinta ta cigaba da ci tana fad'in
"Karamar marar kunya.
Haka suna kallonta dan rashin imani ta cinye tass harda dariyar mugunta tai d'aki.
Kwaikwayar tafiyar Faridan take suna dirka dariya,dan mugunta yau ma tana wanka ta fuce tare da kulle kitchen gaba d'aya.

Lalle Fatima akwai karfin hali.

Sai bayan la'asar ta aiko dan makociyarsu da abinci flask d'aya baifi nacin mutum uku ba.
Da harara tabi abincin, dan haka ba wanda ya ta6a.
Yauma sai bayan magriba ta dawo duk wani abu nasu ya kare,dole abincin suka ja suna cikin ci tazo lokacin Farida sun wanko hannu dan barwa Nass da Sultana.

Dariya take harda rike ciki ganin yadda sukai la'asar dan mugunta.
Tsaki Farida tayi,dan tazo wuya a tsanar matar nan.
"Ke,da wa kike?
Cike da harara ta ce
"Da ke nake.
Tana murguda baki.
A tunzure ta nufota,dan haka zuruf ta mike tsaye tare da kama kugu.

Mari takai mata sai ta kauce.
"Dole ma ki bar gidan nan gobe..
Da sauri ta amshe
"Ai ba gidan ki bane ba inda zani.
Chafkota tayi ta fara duka itama tana ramawa da Allah ya isanta.

Cikata tayi tare da fad'in
"Ni ki ke jawa Allah ya isa.
Baya taja tare da fad'in
"Eh,muguwa kawai azzaluma kawai,ai bari Uncle ya dawo wallahi duk sau na fad'a mishi abinda ki ka mana tun tafiyarshi...
Shiru tayi ganin ta sake yin kanta tai d'akin yara da sauri ta rufe.

Kai ta kad'a, kamin ta juyo kan sauran.
"Uwarku ku ke kallo koh mey?
Jansu Aisha tayi tana bata hakuri,sai da suka tabbatar sunzo d'aki tukunna Saifu ya ce
"Mudai ba uwar mu ba sai taki,kuma an fad'a muguwa...

Da sauri suka rufe duk da ba tahowa tayi ba.
Uwa dai uwa ce,amma sai taji wani iri,duk da abinda ya haifota shi ya haifo tasu uwar.
Tsanin mamakin abinda ya faru ranar kusan kwana tayi tana neman abinyi.

Washegari

Kowa kasa fito wa ya yi,musamman su,dan Farida tasha kwata fita suna had'a ido.
Ga bakar yunwar data addabesu,ga kudi ya kare,ga ta tsare hanya balle su san nayi.

Dan mugunta har goma taki barin parlourn, ga Sultana da Nass sai kuka suke amma ta maze.
Sha d'aya tabar parlourn, dan haka da sauri Farida ta shige d'akin yara.
By


Feenat Ja'afar
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

8_Kuka ta tarar sunayi har Aisha,duk in ka gansu gwanin ban tausayi barin Sultana,sai ta sa hannu a baki kamar ta hakura sai ta cire taci gaba da yi.
Duk wata dabara ta kare musu,dan haka har Faridan kuka suke,chan dai tai shiru.

"Kuzo muje makota sai muce su bamu tunda yauma babu abinci.
Kai Saifu ya kad'a
"K'awar Aunty ce,wallahi itama muguwa ce,ga Abba ya hanamu yawo.

Shiru tayi,sai dai ganin Sultana tayi wajen tea flaks yasa wani hawayen ya zubo mata.
Dakkowa tayi da zummar a zuba mata shayi tsautsayi ta fad'i har flaks ya fashe sai ta sau wani kukan.

"Kuzo mu fita inba haka ba wallahi kashe mu zatai da yunwa.
Jiki babu karfi suka fito tare da zama a parlourn har yanzu fasasshen flaks din na hannun Sultana tana ja dakyar, yau dai iya wayyon Farida ya kare.
Da sauri ta fito daga d'aki tana yake hakora, hakan yasa Nass da Amjad da Aisha da gudu sukai hanyar d'aki har suna gware.

"La,ashe sun fita,amma suna dawo wa zan ma flashing in yaso sai ka kira.
Kit ya kashe lokacin da yake jan jakarshi a harabar airport d'in ya isa mota.

Juyo wa tayi kan su bayan ta sauke wayar tana kallon tsagerun cikin da basu motsa ba.
Kan flaks din ta dire na hannun Sultana,itama duk tayi tsuru-tsuru kana ta6ata zata sau kuka.

Ganin ta nufosu yasa da sauri ta cika flaks ya fad'i tare da yin gefen Farida.
"Kan uba..
Tashi sukai tsaye ganin ta daga flaks din tana karkad'awa.

"Ki ka fasa min flaks Sultana?
Kai ta hau kad'a mata daga bayan Faridan tana kuka.
"A'a ba kuka ki ke ba wannan, yanzu ne za kiyi na gasken gaske...
Bayan Faridan tayi Sultanan tana kank'ame Faridan tana ihu amma sai d ta fincikota.

Kunne ta murd'e mata kamin ta sau mata rankwashi sai kwa ta kara sakar kuka,bai isheta ba ta kama gefe da gefen kumatunta tana ja tun karfi tana mata kashedin in ta kara ganinta da flaks a hannu sai ta cire mata kumatu...

Shiru tayi jin an hankad'a ta,tafiya tayi kamar zata fad'i ta rike kujera baki sake.
Huci yake,gaba d'aya sai ya dawo mata sak babanshi in ya fito a babu wargi suna yara.
"Saifu"..
Cike da mamaki ta kira shi yayinda yake lallashin kanwarshi yana harararta cike da tsana.

"Ni ka hankad'e?..
Banza yai mata yana huci.
Da sauri Farida ta dan bugeshi tare da fad'in
"Kai ka ce eh din,wallahi in ta dake ka mu had'u mu mata dukan tsiya muguwa kawai.
Kallo Fatiman ya yi,yau da gobe sai Allah,dan haka nan take ya ce.

"Eh an ture ki rama in kin isa.
Kallonshi take,kawai sai ma abin ya bata dariya,jin dariyarta yasa su Amjad lekowa.
"Wallahi yau a gidan nan zanga dan uban da zai kwace ka a hannuna...
Da sauri Farida ta ce

"Hmm dallah chan,Allah zai kar6eshi,kuma nima wallahi ina tsaye baki isa ki dakeshi ba bayan kin hanamu abinshi ba...
Kan ta karasa tuni har tai kan Saifu marainin wayonta,marinshi take yana dukanta Farida ma ta shiga amma saida taci karfinsu ta kai Saifu kasa.

Yadda kasan Allah ne ya aikota haka ta, hau ruwan cikin Saifu tana jibga ta fuska ta jiki tamkar wani babba tana maka mishi zagi da fad'in yau zatai maganinshi.

Tun Farida na dukanta har taga ba ji take ba ganin hakan yasa da gudu sauran suka rufar mata Farida na fad'in su cije ta,sai dai ina,suna kawo hakori tana makewa.
Yanzu kam har ta galabaitar da Saifu ya ma daina ramawa sai kokarin shid'ewa da yake jini na fita ta hancinshi amma taki daina dukan dan jin har yanzu yana fadin Allah ya isa.

Tashi Farida tayi tare da nufar kitchen tunda taga baji take ta hannu sai ra shiga neman madoki.
Allah ya bawa Nass sa'a ya kamo fatar bayanta da hakori tare da sau mishi chafka iya karfinshi yana kuka.

Da halama taji zafi,dan haka sai ta sau Saifu ta juya tare da mangare Nass iya karfinta a fuska,da sauri ya cikata tare zubewa ya dafe inda ta make.
Bai isheta ba shima tabi kanshi da duka tana fad'in
''Ni ka ciza?
"Yau sai na zubar ma da hako...

Shiru tayi jin saukar wani zazzafan duka a goshinta,kan ta dago taga waye an kara kwad'a mata muciya, tuni dan azaba ta daga Nass tare da juyawa da zummar chafkar mai d'ukan suka ji ansa salati da karfin tsiya.
Gaba d'aya suka juya har Sultana da Amjad da Aisha dake jijjiga Saifu ya tashi suna kuka.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

9_Jakar dake rike a hannunshi ya hullar cikin sauri tare da fara tattare hannun rigarshi jikinshi har wani 6ari yake tare da juyawa ya dannawa kofar sakata.
Take ya sauya kama tamkar ba uncle din Abuja ba.

Da sauri Farida ta hular da muciyar dake hannunta tare da matsawa ganin itama Fatiman na matsawa lokacin da Abban su Saifu yake kusanto su a sukwane.

Neman guduwa take jiki na 6ari,sai dai taku uku kwakkwara ya fard'o ta.
Kamar yadda ta haye kan yaran tana jibga shima haka yai mata tare da dage wa iya karfinshi yana mari da kai mata naushi a duk inda ya samu.

Duka yai mata na fitar hankali yadda yasan bazata iya koh motsi ba kamin ya kyaleta ya rarrafa ga Saifu da baya motsi.
"Saifullah,
Jijjigashi yake hawaye na digar mishi amma ba koh motsi ajikin yaro.

"Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un...Saifu.
Farida ya kallo da sauran yaran,da sauri ya ajiye Saifun ya karasa gun Nass dake yunkurin amai daga kwance ya kasa ya dago shi shima baki fashe.

"Farida...
Jiki na 6ari ta ce
"Na..na.. na'am.
"Yi sauri ki dakko min Nass,Aisha ki dakko sauran ki ku fito ku sameni a mota.
Da sauri sukai yadda ya ce shi kuma ya kinkimi Saifu.

Har zai tada mota yai saurin komawa tare da cire mukulli ya kulle Fatiman dake a kwance cikin jin jiki.
Kallon yaran yake yadda aka dukufa kansu barin ma Saifu da ake neman cechar ranshi.

Da sauri ya fuce tare da yin kwana yadda ba mai kallonshi kawai ya sau kuka.
Irin azabar da yasha a hannun *MATAN UBA* bai manta ta ba dai-dai da second.
Kai ya duk'ar hawaye na zuba yana adu'ar Allah ya ceci yaran.

"Abba...
Fuska ya guge kamin ya dago tare da k'akalo mata murmushi na dole jin muryar Sultana ta dafa shi.
Ganin Amjad na tahowa yasa ya rike hannunta tare da cewa su tafi.

Anyi nasara Saifu ya kawo wuta,har sun mishi dressing na ciwon da yaji shi da Nass ana musu karin ruwa.
Waya ya ciro tare da kiran d'aya daga y'an office nasu.

"Ina son ka aika min y'an sanda majiya karfi mata gidan da nake,ka had'o da maza biyu dan Allah masu zafi...
"Subhanallah, lafiya Kabir?..
Kai ya kad'a kamar yana kallonshi,
"In zan samu kamin yadda nace zan ma bayani daga baya,kamin nan dan Allah ka kawo su asibiti suga wani abu.

Wayar ya kashe bayan ya fad'a mishi asibitin tare da kallon yaran da suke kallonshi,ita kam Farida da Aisha jin zancen y'an sanda har sun fara raba ido suna kallon juna.

Amjad ne ya riko hannunshi tare da fad'in
"Ka ce su kama Aunty Abba su sata a cell har abinci itama su hanata Abba.
Kai ya kad'a mishi tare da kallonsu d'aya bayan d'aya, gaba d'aya a kwana uku duk sun fad'a har su Faridan.

"Kunci abinci kuwa ma yau?
Da sauri Sultana ta girgiza kai halamun a'a.
Le6e ya cije tare da girgiza kai,har in yabar Fatima a haka yasan bazai huce takaici ba,dole a nina ta yadda ta azabta yaranshi.

"Kuyi hakuri Farida,bari na kai ku kuci abinci,ina zuwa naga su Saifu...
Kuka ta sa,tare da girgiza kai,
"Mu dai gida zamu tafi, a kaimu Kano gun su Umman mu.

Da kallo ya bita, sai ya hau kad'a mata kai.
"InshaAllah,kuyi hakuri zan kai ku da kaina.
Ba'a jima ba sai gasu sun iso.
Y'an sanda 4 biyu mata biyu maza tare da abokinshi,matane wasu kitika-kitika tamkar dangin samudawa a dire da ganin su kasan ba wasa.

D'akin su Saifu ya kaisu.
"Ku fara duba ga wannan kamin mu wuce ga inda zamu..
"Innalillahi, Kabir accident sukai ne?.. Subhanallah.
Kai ya kad'a yana murmushin takaici.
"Ku biyoni kawai.
D'an sanda d'aya suka bari tare nurse a gun su Saifu.

Kofar ya bud'e tare da fad'in su shiga.
Bin bango suka samu tana yi cike da cije le6e fuska a kumbure.
"Officers ina so a tafi da ita ai mata duk hukuncin da ya dace ga wanda yai yunkurin kisa ta hanyar duka,ina si ku lakad'a min ita sai inda karfinku ya kare wallahi koh nawa ne zan biya.

Kasa ta koma tare da sanya kuka tana bashi hakuri.
"Subhanallah, a'a Kabir,kar ayi haka,a dai yi sasanto matarka fa?..
Ido ya sa mishi,kamin ya kad'a kai.
"Kaji mey nace kuwa Nasir? Yarana ita tai musu duk wannan aika-aikan ciwon ba wani hatsari,dan haka bani da guntun alaka da ita aure na saki.

Bayanin yadda ya sameta akan su Saifu yai wa y'an sandan, tun kan aje ko'ina tuni matan suka fara sakar mata mari
"Wuce da kafafunki..
"Dan Allah Ya Kabir ka yi hakuri kar su tafi dani,wallahi kasheni zasuyi...

"Mey ku ke jira da ita officers? In ta kama a kashe ki wallahi zai fi min dad'i Fatima.. Nayi imani da Halima na raye irin hukuncin da zata sa a miki kenan dan irinki annoba ce a gari..

Juyawa ya yi tana kiranshi cikin kuka.
Kai Nasir din ya sunkuyar,ganin ya fuce hakan yasa shima yabi bayanshi jiki a sanyaye,hakan yasa da fatattaka suka tsamota a gidan tare da hullata motarsu.

Da kallo yaran suka bi motar har suka bar ganinsu.
Gun cin abinci ya kaisu,a hankali suka fara zamewa suna d'aura kai bisa table din kan a kawo abinci.

Cike da tausayawa yake kallonsu ganin yadda sun ma kasa cin abincin sai Aisha dake chaka a hankali.
"Ummata bud'e bak'i in baki abinci kinji?
Kai Sultanan ta girgiza mishi tare da lafewa a jikinshi baki a hannu.

Ajiyar zuciya ya yi,duk ci irin na Sultana amma yau ba kanta.
Su Farida ya kallo,
"Kuyi hakuri Farida kuci kar yunwa tai muku illa.
Kai ta duk'ar tare da zubawa abincin ido wanda yasha kaji,sam na abinda ke ranta duk kuwa da kaunarta da dajjaja.

"Amjad kai fa?
Kai ya dago tare shima girgiza wa.
"Tea Abba zansha ni.
Kai ya kad'a tare da aikawa a kawo kofi hud'u harsu Farida da farfesu.

"Tashi Ummana kisha tea kinji?..
Hannu yakai bisa kanta da sauri jin zafi k'au.
"Subhanallah, Sultana.
Kallonshi tayi ido lumshe.
Da sauri ya dakko kofin tare da fiffitawa ya fara bata sha uku ta fara amai.

Kan ya yi kwakkwaran motsi Farida ma data dau shayin ta fara.
"Ya ilahi...
Gaba d'aya rikice wa ya yi ganin Faridan na kuka ita da Sultana,ba yadda ya iya dole su ma asibitin ya mika su dan yadda zazzabi ya rufe Farida da Sultanan.
****

Reras yake kallonsu an jere mishi su a gado hud'u kowa da drip,kukan ma ya kasa zuwa mishi,lalle yasan ba karamin azaba suka sha gun Fatima ba.

Tashi ya yi tare da fita waje yana danna waya.
"Abba ina zaka tafi?
Juyo wa ya yi tare da kallon Amjad,
"Ba inda zani Amjad waya zan ma Umma jirani yanzun.

Chan bayan bishiya ya nufa tare da jingina yanajin yadda wayar ke ringing.
"Assalamu Alaikum...
Shiru ya yi,sai da ta sake kamin ya ce
"Umma...
Kuka yasa mata kamar wani yaro,dan haka tuni ta rude ta fara tambayar lafiya?

"Umma Fatima y'ar uwar su Tabawa ce,itama tabi sahun su duk sun kassarani Umma..
"Subhanallah Kabiru,mey tai maka?
"Umma Fatima itama bata da imani,wallahi yanzu dai ki yarda dani duk *MATAN UBA* mugaye ne,kiris ya rage ta kashe min su Saifu Allah ya kawo ni...

"Kayi hak'uri Kabiru ka bar kuka,InshaAllah ina bisa hanya zuwa gobe kar ka mata komai...
"A'a Umma,ba sai kinzo ba,dan tuni nai mata hukunci dai-dai da laifinta,Umma na had'ata da hukuma...

"Kai,kai Kabiru,bai kai haka ba,yanzu kai hak'uri a sunto ta InshaAllah muna kan hanya.. Kai hak'uri.
Hawaye ya goge tare da fad'in sai ta zo.

D'akin ya koma tare da jan kujera ya zauna yana kallonsu.
Ilahirin fuskar Saifu da Nass duk a kumbure.
Kai ya kautar jin hawaye ya taho mishi.

Gefen Farida ya dawo,bacci take fuska duk tayi fayau sai dogon hanci.
Yanzu mey zai ce da abokinshi in wani abu ya samu ya'rshi?
Kai ya girgiza tare da shafa kan Sultana.
By


Feenat Ja'afar
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

10_"Abba"....
Dagowa ya yi da sauri jin muryar Nass,da sauri ya tashi tare da isa gareshi.
"Sannu Nasir, ina ke maka ciwo?...
"Abba ina Saifu? Aunty zata kashe shi fa.
Hawaye ne ya cika mishi ido,da sauri ya kawar da ido tare shanye su.

"Juya ga nan Saifu yana bacci..
Kai ya juyar inda ya nuna mishi dan gaskatawa.
"Ina ke maka ciwo?
Juyowa ya yi tare da kafe Abban da ido.
"Abba ina Aunty Fatima?
Murmushi ya yi tare da shafo kanshi.

"Tana chan an kulleta a cell,daga yau ta bar mana gida gaba d'aya..
Da mamakinshi sai yaga ya fara murmushin murna.
Gun Farida ya juya sai yaga ta zuba musu ido halamun itama ta tashi.

"Kin tashi Farida?
Kai ta kad'a tare da goge hawaye.
"Sannu,ina ke miki ciwo?
Kai ta girgiza halamun babu.
Nurse ya kira ta cire ma Faridan ruwa ya kare har ta zauna.

Ko'ina take dubawa ba Aisha ba Amjad.
"Ina Aisha uncle?
Kallota ya yi ganin tana neman kuka.
"Sun tafi da Amjad gidan Uncle Nasir, kar ki damu da safe zasu dawo.
Kai ta sunkuyar tana goge hawaye.
Chan ta sake fad'in
"Zanyi sallah..

Kallota ya yi da mamaki,sai ya kad'a kai.
"Sister dan Allah a taimaka mana da abin sallah da hijab.
Kallonta yake yadda take rama sallolin dake a kanta har ta idar,lalle ne abokinshi yai ma yaran tarbiya ba kad'an ba.
Dakyar ya zuba mata abinci tare da tilasta mata taci.

Shi kam Saifu sai chan dare ya farka da kuka yana kiran Abba.
Attendance d'in dake kula dasu ne ta farka kamin Abban nashi ya farka.
"Ga ni nan Abba nah,sannu.
Dakyar yake iya bud'e idon dan duk sun kumbura dan duka.
****

Washegari
11 na safe a Abuja tai ma su Umma dan asubanci sukai ta kasa nutsuwa.
Sanarta asibitin da suke ya yi,lokaci kad'an sai gasu sun iso tare da yayan Fatima da Umman Fatiman wato kakarsu su Saifu.

Ba karamin al'ajabi sukai ba da ganin su Saifu a wannan hali,hakan yasa Umman su Fatiman kuka da yin tir da halin Fatima.
"Wannan shi ya dace da ita Kabir wallahi ka min dai-dai.
"Ko ni ne a matsayinka wallahi sai in da karfina ya kare kan wacce tai ma yarana haka...

"Haba Uzairu,ka yayyafawa wutar ruwa man ba wai ka kara hurata ba,Fatima jinin ku ce koh dan haka ai mata hak'uri..
Da sauri yayan Fatiman ya katse Umman.

"Wallahi Umma in Kabir yai hak'uri toh tabbata an maka Fatima kotu ta yadda zata amshi hukunci dai-dai da laifinta,kila ta hakan sauran y'an baya masu hali irin nata su hankalta in sunga ana daukar mataki...
Dagowa Ummansu Fatiman tayi tana kad'a kai.

"Wallahi Umman Kabir ina bayan Kabir d'ari bisa d'ari, a yau nai nadamar zaman Fatima a zuri'ata,ni dai bani ta gado ba a wannan mugun halin da rashin imani,na sani da in da marigayiya Halima ma ce bazata ta6a wannan mugun halin ba...

"A'a Ummansu Uzairu,hannunka baya ta6a ru6ewa ka cire ka yadda,kuskure duk muna yi,ni dai in anbi ta tawa a sinto Fatima Kabir...
"Kiyi adalci Umman Kabiru,ki d'auka baki da alaka da Fatima kuma ta aikata hakan a jikokin ki wallahi nasan sai inda karfinki ya kare.

"Dan haka yadda Fatima ta manta alakar dake tsakanin yaran nan da mahaifiyarsu wallahi nima na manta ta,kuma ina rokon Allah ya bi ma yaran nan hakkinsu da ta ci.

Kai ya Uzairu ya kad'a
"Amin Umma,kema Umman Kabir ki manta wata alaka kawai Fatima ta karbi hukunci,na tabbatar a gaba zai zame mata izina da y'an baya.
Shi dai Kabir yai shiru yana jin su,dan sam bai tunanin iyayen Fatima zasu mara mishi baya ba.

Kwana biyu suna jinyar Saifu da Nass,tuni Farida da Sultana aka sallamesu sai dai rikicin gida da take musu kullum.
Dan haka ana sallamar su a ranar suka tattare da yaran suka nufi Kano ba wanda yabi takan Fatima.
*****

A Kano kowa tir yake da halin Fatima na wannan irin rashin imani da ta girka, sai dai wasu suna fad'in bai dace a barota a hannun y'an sanda ba zasu iya lahanta ta.

Har gida ya kai su Farida yana mai bawa abokinshi hak'uri a bisa abinda ya faru.
"Ta su Farida mai sauki ne abokina in har da dubi yaran nan,na rasa wani irin zamani muke ciki wanda mata suke daura kishin su bisa yaran da ba nasu ba har su iya danne imaninsu su aikata haka.

"Wanda zai iya haka ga yaro tabbas zai iya kisan kai,duk in anyi duba da taka rayuwar a hannun *MATAN UBA*.
Murmushi ya yi dan tuna baya da irin tashi ukubar da har kullum yake ganin ba wanda yasha irinta hannun *MATAN UBA*.

"Sai dai wani hanzari ba gudu ba.
Kai ya dago yana duban shi.
"Duk tsiya taci daraja d'aya a hannunka Kabir,ka daure kayi afuwa koh ba komai yanzu nasan ta d'an d'ana kud'arta,ba dan halinta ba dan Halima dake a matsayin jinin..

Ido ya rufe tare da jingina kai a kujerar,fad'in Halima yasa duk yaji wani iri,ba dan yaso ba sai dan irin tausarshi da abokinshi da Umma sukai ta mishi yasa a saki Fatima wacce tuni aka wuce da ita asibitin gwamnati dan galabaita.
****

"Umma"...
Faridan ta kallo tare da amsawa.
"Wallahi ina tausayin yaran uncle, ban ta6a ganin muguwa irin Fatima ba sai a makaranta.
"Umma har muka taho kullum suna fad'in sun tsani step Moms nasu,har nake ganin wani iri.

Murmushi tayi tare da kad'a kai.
"Basu ji dad'in su bane Farida,dan haka har abada baza su daina tsanar  *MATAN UBA* har sai randa suka dace da tagari wacce zata goge tabon y'an baya.

Tsam Faridan tayi tana tunani,duk da shekarunta bai kai ta samo musu mafita ba amma a ranta gani take da ita ce bazata ta ta6a musu mugunta ba kamar yadda Ummansu bata ware waye y'arta a tsakanin ita da Aisha.
By



Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

*ASALIN LABARIN*

11_Kabir yaro ne na biyar ga Malam Yusufa,asalin su y'an kauyen Rano ne kamin kakansu Kabir ya dawo cikin Kano yai aure.
Yara 16 ya mallaka suna rasuwa har Allah ya kawo Yusuf da Nasir suka zauna su biyu rak.

Mahaifin Kabir Malam Yusuf yana da mata uku,yayinda Nasir kaninshi yake da guda d'aya, kusan duk tare akai auren,sai dai shi Malam Yusuf koh shekara ba ai ba ya sake aure saboda iya rashin zama irin na Tabawa uwar gidanshi.

Masifa sosai ya gani lokacin da ta riski har an kai k'walla na amaryarta.
"Wallahi Isubu ka sai wa kanka bala'i da masifa a gidan nan mud'in ka kara auren nan.
"Bacin ga jaraba mey zai sa aure shekara guda kawai wai zaka kara koh haihuwa ban ba...

"Ke Malama ki fa dakata min..
"Bazan dakata ba Isubu, ba haka ka ke so ba?
Kai ta kad'a
"Toh ka samu.
Kallonta yake yana mai wani tunani cikin ranshi.

Shin ya ma akayi ya lalumo Tabawa a matsayin matar aurenshi?
Hala ya makance ne lokacin da bai gano rashin tarbiya irinta gidan su ba ya auro ta?...
"Eh kalle ni da kyau,Tabawa ce d'aya da ka sani..

Kai ya girgiza kamin ya juya da zummar fita yana fad'in
"Allah ya kyauta...
Tsakar gida ta fito tare da fad'in
"Ya kyauta maka, macuci kawai.
Kai ya kad'a tare da fita waje rai na kuna,tabbas dole ma ya jawo auren nan ayi a gama koh zai samu sukuni.

Duk yadda Tabawa takai da iya masifa amma amarya sai da ta shigo gidan Malam Isubu.
Lami ba tazo da mutunci ba tunda taga take taken uwar gida Tabawa,dan haka amarci kad'an aka ci Malam Isubu ya koma y'ar gidan jiya.

Kullum acikin raba fad'a ake tsakanin Tabawa da Lami,abu sai ya had'e mishi goma da ashirin.
Dan haka sai ya zabi zaman shago in da ya bud'e a kwanar gidanshi.
Bashi ba sake dawo wa sai in dare ya raba yasan kowa tana d'akinta.
***
 
Shekaru biyar ya jure,dan a yanzu fad'an ya dawo na yara tunda kowacce ta haihu konika yara biyu-biyu duk mata.
Karafkaf yaran ba wanda ya bar halin mahaifiyarta,dan haka su ma tun suna yara suka fara cin kai a tsakaninsu.

"Ni abinda nake gani Malam Isubu ka nema wa kanka sauki kamin masifar gidan ka ta sa ma ciwo.
Tashi ya yi daga kishingid'en da yake a kan bujukura a zauna.

"Ta ya-ya Malam Nura?
Zama shima ya gyara tare da tofar da guntun goron dake bak'inshi.
"Ina yarinyar nan da take kawo d'an b'uka shagonka ka siyar wa Ummanta?

Kai ya kad'a tare da fad'in
"Eh naji,Y'ar wajen Malam Kabiru...
Baki ya washe tare da fad'in
"Eh ita.
"Kai ya kaga tarbiyar yarinyar?
Murmushi ya yi tare da sunkuyar da kai.
"Ba laifi gidan kam akwai tarbiya,barin ma yarinyar...

Baki Malam Nura ya washe tare da fad'in
"Kawai ka nemeta,in dai har kun daidaita ina ganin zata iya zame maka waraka a gidan dan tana da hankali na yaba.

Tsam Malam Isubu ya yi yana dan murmushi, ba tun yau ba yaji yarinyar ta shiga ranshi,sai dai ganin abinda ya kawo ta kawai take shi yasa bai maida kai ba.

Shawara ya ce zaiyi,duk shi ya aminta har cikin ranshi da yarinyar.
Kan wani lokaci har magana tayi nisa tsakanin Rukayya har an kai kayan tambaya da sadaki.
****

"Alhamdulillahi dai,dan nima na haifa Tabawa balle ki min gori,yadda ki ke da biyu mata nima haka na haufesu,da ma maza ne kyayi da dalili...
"Oho dai,na fad'a miki ya'yan ki su kiyayi ya'yana koh na...

"Toh kaji,ana ta cin kan ne?..
Shiru sukai tare da juya wa jin muryar mai gidan.
Karasowa ya yi yana mai cigaba da mita.
"Ku kwantar da hankalinku, dan kunyi na kud'inku saura nawa.

Kallon-kallo suke da rashin fahimta.
"Mey kenan haka ke nufi Malam?
Ledar hannunshi ya ajiye da ba wanda ya iya amsa daga yaran har iyayen.

"Aure zan kara nan da mako hud'u masu zuwa.
Baki suka saka tare da zuba mishi ido.
"Atoh,kuma ji da wai,dan ban ma yi niyar fad'a muku ba sai ranar aure sai dan kawai hakkin ku sani.

D'akin Tabawan ya shige inda a nan yake da kwana.
Sai bayan ya wuce Lami ta kalli Tabawa tare da fad'in
"Lalle da bala'i Tabawa a gidan nan.
Shiru tai mata ita tama rasa bakin magana.

Bala'i dai bana yasha shi bibbiyu ne akan auren,dan haka sai yafi lokacin Tabawa ita kad'ai.
Takai ta kawo har abinci a gidan bai da kaso duk dan wai ya sadudu,shi kam koh a jikinshi,dan aure kam ba fashi.
By


Feenat Ja'afar
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

12_Jiya amarya ta tare,kan y'an kwanan amarya su kauce sunga abu gun su Tabawa,dan mai kid'an kwarya suka kira ta kad'a musu 'Ladi mai kid'an kwarya asha kid'a asha dad'i ari'.
Da an buga sai su sa shewa tare da habaici suna kiran y'ar mai tallan d'an b'uka da fura.

Ango ne ya shigo da babbar malum-malum yana ta washe hak'ora bayan kowa ya watse.
D'akin Tabawa ya fara shiga da zummar yai mata sallama sai ya tarar da Lami ma tana d'akin.

Mamaki ya gagara barinshi har yau na yadda lokaci guda Lami da Tabawa suka dinke kamar basu bane kajin nan sarakan fad'a.
Kowacce taci daurin 'ture ka ga tsiya' a gaban koshi suna aika mishi harara.

Baki ya washe tare da fad'in
"Ashe ma kuna tare a nan..
Banza suka mishi tare da juya mishi keya kowacce.
Yau ranar farin cikinshi bazai biye musu ba balle su 6ata mishi wannan daren.

"Toh dama sai da safe nazo muku, ga nan balangon ku ga na yara.
"Mtsww aikin banza kawai..
Murmushi ya yi tare da kad'a kai.
"Koyi komai yau dan bazan biye ku ba.
"Allah bamu alkairi..
Tsaki Lami ta kara.
"An dai ji kunya wallahi Isubu, ji yadda ka ke wani 6ari tamkar sabon ango.

Baki ya washe mata tare da fad'in
"Ku dai mu kwana lafiya..
Waje ya yi ya barsu suna cizan yatsa.
"Wallahi ya ma mayarmu wasu bi ta chan Tabawa.

Kwafa Tabawan tayi tare da tashi ta bud'e balangon.
"Wato ita nasan kaza ya kai mata mu ya raina wa hankali.
Kwata Lami tayi tare da fad'in
"Toh kawo in bakya ci ni zanci.

Rai 6ace Tabawa ta kallota.
"Ke ma fa ba mutunci ya gama ratsa ki ba.
Shiru sukai jin an ta6a butar karfe.
"Yi shiru..
Shiru Tabawan tayi suna kasa kunne.

Balangon suka gama cinyewa kamin aka hau goge man ajikin kaya cikin sauri jin muryar Malam na y'ar dariya an ajiye buta.

"Muje muji,ji wata munafukar dariya da yake.
Gida ne na kasa mai d'auke da dakuna uku, d'akin Lami da Tabawa a jere sai nashi dake kallon nasu da yanzu ya dawo na amarya.

Cikin sand'a suke bin bango har suka iso kofar d'akin amarya suna kasa kunne.
Sallamar idar da sallah suka ji Malam ya yi,da sauri Lami ta zunguri Tabawa nufin ta matsa mata Tabawan tana doke hannun Lamin halamun tai shiru.

Dan tsaki Lami tayi da zummar komawa d'ayan gefen basu nufa ba suka ji Malam ya daga labule da sauri suka hau kame-kame har suna yin gware.
Kai ya kad'a tukunna ya ce
"A'a, kuyi zamanku dan kofa zan kulle na koma ciki.

Salin alin kowa tai d'akinta da borin kunya,kai ya kad'a tare da tura kauren ya kulle yana tur da wannan jahilci na su Lami.

Komai ya sauya wa Malam tun bayan aurenshi da Rukayya,dan ita mai kunya ce da kawaici, duk da tana fuskantar tsangwama gun su Lami in har ba Malam.
Ga jarabar fitsara da ashar da yaran gidan ake koya musu su mata duk tana dauke kai.
****
Bayan wata biyu da biki.

Da gudu ta fito daga d'aki rike da baki tai gefen rijiya inda suke wanke-wanke ta fara kela amai.
A razane Lami ta leko dan ganin waye mai aman.

Ido ta zaro ganin amarya Rukayya ce,tasan Malam a d'akin Tabawa ya kwana tasan asubanci yake ya fuce, dan haka da sauri ta banku d'akin ba koh sallama.
Duka ta d'ad'a mata a cinya ganin ta baje sai jan minshari take ga yara a kasa duk sunyi fitsari d'aki na zarni.

A zabure ta mike rike da gun da masifar waye wannan, ganin Lami tuni ta sauya fuska da zummar magana ta rigata.
"Kin baje baki sai minshari ki ke ja ga nan amarya ta kwaso mana magana a gida.

Zani ta gyara tare da daukar dankwali cikin rashin fahimta.
"Ban gane ba fa..
"Dama tun wanchan watan na ce miki tayi tsallaken wata biyu kin ki yarda gashi nan toh.

Fuska Tabawan ta yamutse tare da tofar da yawun bakinta a bangon d'akin.
"Dan Allah ki min yaren da zan gane..
Da sauri ta katseta da fad'in
"Ciki toh gare ta..

Yafico ta tayi jin wani k'ak'arin aman suka hau leke.
Da baya Tabawa ta dawo tare da dafe kai.
"Shi kenan mun kad'e Lami in har ta haiho namiji.
Tsaki Lamin tayi tare da saurin fad'in
"Ji wani mugun baki gun Tabawa?
"Ni muje muga mey ake ciki...

Shiru sukai ganin Rukayyan zata wuce.
Hannu Tabawa ta cije kamin ta ce
"Wallahi yadda ki ka san na shako ta haka nake ji Lami.
"Ki ajiye wannan yanzu musan abinyi tun kamin ya girma.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

14_"Subhanallah Rukayya da gaske baya motsi kam..
Kai ta kawar gefe ganin yadda Inna ke jijjiga yaro amma ba halamun zai motsa.
Ido ta rintse tare da tuno da wannan ayar ta 'ALLAZINA IZA ASABATHUM MUSIBATUN QALU INNALILLAHI WA'INA ILAIHIRRAJI'UN'.

Hawaye ne ya zubo mata wanda bata ma san ya taru ba,a hankali ta cigaba da karanta Innalillahi acikin zuciyarta tana kallon Inna dake dabarar su ta tsofi.
"Inna ya rasu fa,ki daina wahala...
Kai ta dago cike da tausayin y'ar jakar tata.

Ganin zata kara karyar mata da zuciya yasa da kanta ta tashi tare da fita band'aki rike da buta jin Inna na kiran su Tabawa.
Kuka ta fara yi a band'aki, koh ba komai UWA UWA CE,koh ba sabo akwai kauna ta musamman.

Haka tana ji tana gani aka kira Malam sukai ma yaro sutura shima harda hawayenshi.
Kukan dasu Tabawa suke ne wiwi ya fara damun jama'a, dan haka ido kawai Rukayya ta zuba musu cike da wani abu a ranta.

A d'aki suka kule suna ta tuntsiririn dariya ta yadda ba mai jin su.
"Kai Tabawa kin iya shawara,da yanzu muna kwasar bakin ciki a gidan nan na ganin yaron nan..
Baki Tabawa ta rufe mata ganin inuwar wani.
"Waye nan?

Tashi Lami tayi tare da lekawa da sauri amma ba kowa.

***
"Kiyi hakuri Rukayya, nasan kinyi tawakkalli,InshaAllah ba da jimawa Allah zai sake bamu wani.
Kai ta duk'ar tana dan murmushin kunya,duk da a zahiri hawaye ke neman zubo mata.
Tashi ya yi ganin Inna na neman shigo wa.

Sannu a hankali duk sai ta fidda zargi har ta gama wanka lafiya.
Fatan ta Allah yasa mai ceto ne,Allah kuma ya basu wani nagari mai albarka.

Allah kuwa ya amsa,domin koh wata uku batai ba da gama wanka tasan tana da shigar ciki.
Rokonta daya Allah ya inganta koma mey zata haifa.
Allah cikin ikon shi sai gashi wannan karan ba tayi laulayi ba,dan haka ba wanda ya farga da cikin har ya girma.

"Zo Tabawa,muje daga ciki...
Binta tayi ba musu har d'aki,
"Anya zargina ba gaskiya bane kuwa?
D'aurin zani ta gyara tare da fad'in
"Na mey fa?
"Ciki man Tabawa.. Koh ke har yanzu baki da basirar gane mai ciki a ido?

"Mtsww.
Tsaki Tabawan tayi,
"Wai wane irin ciki bayan muna gidan nan koh tari bata ta6a ba balle amai?
Hararar ta tayi,
"Wallahi kina da abin haushi Tabawa,wa ya fad'a miki dole sai anyi amai ake ciki?
Baki ta ta6e tare da fad'in
"Oho.

"Amma ke baki ga yadda kullum take runduma riga da katon mayafi a tsakar gida ba?
Kai ta girgiza
"Ai kin san sanyi ne,dan haka ki bari muga ai dai dan duma ne zai baiyana.
Da wannan suka zuba ido ma Rukayya duk wani takunta,sai dai sun kasa tantancewa,dan tayi kiba ba laifi.
****

"Sannu da zuwa Malam..
Tashi tayi daga kan abinda take tana murmushi ta isa gareshi dan amsar kayan hannunshi.
Shima baki har kunne yake kallonta,a kullum yana dad'a yaba wa tarbiyar Rukayya shi yasa tafi sauyuwa cikin zuciyarshi.

"Yauwa Rukayya,sannu da gida.
Kai ta duk'ar cike da y'ar kunya.
Kwafa Lami tayi a hankali tana aika harara cikin duhu ta nufi d'akin Tabawa.
"Idan da abinda naki jinin na bud'i ido nagani toh bai wuce shegiyar nan ba Rukayya.

Baki Tabawa ta ta6e,
"Ni ai bazan iya sanya ido ina ganin wannan kinibibin ba ne shu yasa duk ran girkinta magriba take min a d'aki.
Kwafa Lamin ta sake,
"Ni ba ma wannan ba,yadda haihuwa ta tsaya mana a gidan nan yanzu ita tafi komai tsaya min a rai.

"In dai har abinda nake zargi ne wato ciki ne da yarinyar nan toh na yarda ita ta sa mana hannu haihuwa ta tsaya.
Tsam Tabawa tayi,
"Lalle Lami akwai ki da hangen nesa, ni sam ban ta6a kawo haka ba.
"Toh meye abin yi yanzu? Dan ko ni na k'agu naga na tara yara musamman maza.

Baki Lamin ta ta6e tana mata kallon tara saura kwata.
"Lami nasan abin yi,kawo kunne kiji.
Daurewa tayi tare da mika mata,a hankali fuskarta ta fara washe wa zuwa dariya.
"Kai amma Tabawa ke dai dusa ce wallahi.
Rai Tabawan ta had'e tana dubenta.

"Eh mana,in ba dusa ba ace tun da kina da wannan a hannunki ki ka bari muna shan wahala?
"Yi hak'uri baizo min ba ne.
Tsaki Lamin tayi tare da zama
"Yanzu yaushe zamu je gidan?
Tunani ta fara
"Yanzu dai bata gari,kuma ni ban san wajen ba,amma duk randa ta dawo sai muje.

Da wannan suka rufe chapter har su na fad'in in sunje mey zasu ce Mai yankan wuka ya musu.
****

A hankali ciki na girma tana cigaba da boye kayanta har yai wata 6,gaba d'aya ya gama bin jikinta,yanzu kam ba sauran 6oye,dan haka yau daga ita sai riga da zani ta fito sai dankwali a kai taci d'auri.
Da Lami ta fara ka'ro a gaban randa ta daga kai tana shan ji ka ke kwat-kwat na shigar ruwa.

Da azama ta cire mod'ar a bakinta cikin kwarewa, tuni ta hau tari tana mai kallon cikin Rukayya ba koh kiftawa.
Murmushi tayi tare da kad'a kai,lalle tasan haka zata faru dan ma Tabawa bata gida.
Har ta wuce tana binta da kallo ta d'au buta ta shige bayi.

Mod'ar ta dangwarar tare da shiga d'aki jiki na karkarwa.
Tabbas ta san ciki ne da yarinyar nan amma gidahuma Tabawa ta batar su,gashi yanzu har ya girma.
Ranar har Tabawa ta dawo tana sincewa tana d'aurawa.

Hakan yake itama ga Tabawan, tana shanya ta shigo cikin ne ya fara mata barka da zuwa,dan haka tafiya take bata koh kallon gabanta idonta na kan cikin har tana neman fad'uwa dan tuntu6e da buta.
Kai ta sake kad'awa dole ne tasan irin zaman da zatai dasu Tabawa.

Tun daga wannan lokaci suka kasa zaune suka kasa tsaye,dan dabara ta kare gashi kawar Tabawa bata dawo ba balle suje neman taimako,dan haka kawai sai suka sa ido suga a haife.
****

Tun jiya take jin dan milmil tana daurewa ganin Malam na gida,sai dai yadda yana fita ciwo ya taho gadan-gadan yasa ta fara fita a hayyacinta.
Cike da cije le6e ta leko tare da kiran babbar y'ar Tabawa.

"Ladidi d'an kira min Malam dan Allah.
Gaba d'aya suka sa mata ido har yaran,take su Lami suka gano yanayinta,d'aki ta koma tana rike baya.
Yaran suka ce su fita wasan su kar wanda ya sake ya kira Malam.

Harda tafawarsu cikin murna tare da saurin bin bayanta.
A durkushe suka sameta har ta fara nishi da halamar dai haihuwar bana da sauki tazo.
"Subhanallahi..
Da sauri sukai kanta.
"Haba Rukayya, kina naguda amma ki gagara sanar mu?

Le6e ta cije tare da zame hannun Lami cikin karfin hali.
"Ku fita zan iya.
Ido Lami ta kannewa Tabawa,da sauri ta ce
"A'a baza ayi haka ba.
Shiru tayi jin d'aya ta bayanta ta rike mata hannu yayin da Lami ke kok'arin duba fitar yaro.

"Kinga har kai ya kusan fita,yi sauri kiyi ta nishi..
Bata da zabi, illa tai kok'ari taga yaron ya fita koh ta huta da azabar rikon Tabawa.
Kai Tabawa take girgiza wa Lami cikin keta ita kuma tana kanne mata ido.

A kalla goshin yaro har ya fito amma dan bakar mugunta tun karfi Lami ta sake dannashi ciki ya koma kira take
"Yauwa kara yin nishi da karfi.
A karo na biyu yaron na danno kai tana mayarshi tun karfi cikin karfin hali da rashin imani.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

16_Bakin ciki kam sun ganshi,koh suna kan ganin shi,dan fa yaro mai kuka Allah ya bawa Rukayya, dan haka in ya fara challara kuka koh bacci ka ke sai ka mike,hakan yasa a kullum suka ji kukan wata irin tsanashi ke sake shigar su.

Dan haka suka daura daga inda suka tsaya tun bayan suna da yaro yaci sunan Kabir.
Karan nan bata sakacin barin d'aki ba kowa,dan kullum Raliya na gidan koh ta turo Ummilo har ta kusa arba'in.
****
FARIN KOMAI.

Duk'e suke a gaban mai yankan wuka kawar Tabawa tana bashi bayani.
"Yanzu mey ku ke so ai da ita? Dan banga halamun za'a iya aika yaron nan lahira ba koh uwar.
Lami Tabawa ta kalla,ita kuma tana kallon mai yankan wuka.

"Allah ja zamanin ka so muke daga yau yaji bai kaunar kusantarta balle har ta kai ga an sake samun rabu,ta yaro kuma ka barmu dashi,a fara da uwar,sannan mu a dawo mana da haihuwar tata kanmu ni da Tabawa.

Dariya ya yi tare da kad'a kai.
"Aikin farko mai sauki ne,kai a wajena shi yafi komai sauki na juya kan miji akan mata.
Baki suka wage tare da kad'a kai na mugunta.
Tarikice ya basu tare da fad'in yadda zasuyi amfani dasu.

"Wannan dai ku tabbatar kun sanyata a kofar d'akinta, ba mu'amula ba shi da kallon d'akin ma sai dai a mafarki koh in ta sake gida.
Tafawa suka yi suna jinjina mishi cikin murna.

Yau ta Rukayya ta fara fita yawon arba'in, dan haka tana fita suka kulle gida tare da yin yadda mai yankan wuka ya umarta.
"Bakar mayya,daga yau ke da ganin miji sai dai a d'akin wasu.
Gud'a Tabawa tasa,tare da gyara wajen kamar ba ayi komai ba.
****

Jim tayi tana tunani a d'aki, ta rasa gane kan Malam,in zatai lissafi toh yau kusan watan ta guda da taga Malam ya sako kafarshi d'akinta.
Ba ma wannan ba,koh girki tayi sai dai ya ce ta kai d'akin Lami koh Tabawa koh kuma ta shinfid'e a kofar su.

A da koh Kabir ke kuka in ya shigo da azama zai isa isa ya d'auke shi koh a hannunta ne ya kar6e shi,amma yanzu sai dai ya tsaya daga nesa yana fad'in ta kula dashi man.
Koh in ya gansu a waje ya kar6eshi.

Yau da gobe sai Allah,dan haka tun baya damunta har ya fara.
Dan haka ta nemi shawarar Raliya,ita kuma ta ce ta tuntu6e shi koh laifi tai mishi.
Hakan tayi,sai dai da mamakinta sai ya ce shi ba abinda ta mishi,asalima ya nuna har kullum baida sama kamarta.

A zaure suke,ganin ta fara hawaye tuni ya hau lallashi,garin haka har ya sada ta da kafad'arshi, kamar an ce Lami leka sai kwa tai katari da hakan.
Kai ta gyad'a tare da koma wa ciki.

"Lalle mun yanka ta tashi Tabawa.
Kallota tayi tana shar6ar miyar kuka.
"Mey kuma ya faru?
Leka wa tayi sai ga nan Rukayyan ta shiga d'aki tare da kullowa rike da mayafi ta fuce.

"Innalillahi...
D'akin Lami ta koma tana doka salati,
"Wai meye Lami?
Cikin kud'ima ta ce
"Tashi ki ga,zama bai ganmu ba.
Yadda taga su Malam ta sanar wa Tabawan tare da sakon kaunar da yake isar mata.
"Kinga gashi ya ce ta fito kila ya kaita wani waje su had'e.

Kwanon abincin ta dangwarar tare da kallon Lami ba koh kiftawa.
"Mey zamuyi toh yanzu?
"Mun kad'e kawai in dai Malam ya kad'aita da jarababbiyar matar nan..
"Kinga,tashi zaki yi mu nufi gun Mai yankan wuka mu kora mishi bayani..

Hannu ta hau lashewa tana kad'a kai da kallon yaransu wanda suka zuba musu ido.
"Ya zamuyi da yara?
Tsaki Lami tayi,
"Ni in zaki fito ki fito,da a ina muke barin su?

Sunje suka kora mishi bayani, dariya ya yi tare da gyad'a kai.
"Ai nayi mamakin ku da banji kunce ai musu farraku ba,ta yadda koh kallonta kar ya kaunata,ai in zaka sha giya toh kasha ta dubu.
Kai Lami ta kad'a
"Ayi ta zama mujiya a idonshi.
Wani kallo ya musu tare da mika hannu

"Nafi son na rika fa jin dumus saboda dad'in aiki.
Guntun kud'in gadon Tabawa suka bashi,
"Dan Allah ai mana mai zafi Mai yankan wuka.
Kai ya kad'a,tare da dakko wata gwalba mai dauke da wani bakin turare mey kamshi mara dad'i.

"In har kullum zaku na sanya mishi wannan a kayanshi na yau yafi na gobe yawa,toh haka a hankali kinta zai rika hau hawa har a wayi gari bai kaunar ganinta.
"Sannan daga zarar turaren ya kare toh komai zai iya faruwa,koh dai ya saketa,koh kuma in ya cigaba da ganinta abin ya shafi kowa,aciki kuwa harda ku..

Ido suka zaro.
"Kamar ya mai yankan wuka?
Murmushi ya yi tare da dauke kai.
"Toh meye amfanin zamanta bayan matsala ce? Kawai daga nan ta kara gaba kar ya shafe mu.
"A'a Tabawa,
Kallo Mai yankan wuka tayi.
"Meye mafita in har ya kare bata fita? Nasan kasan wata hanya koh sauya tsari sai ayi.

Kafad'a ya daga,
"Ni dai na gama bayani,in kuma har na sauya toh ba lalle ku samu abinda ku ke so ba,dabara ta rage taku ta yadda zata fita kan turare ya kare,a kuma adana kwalbar ta hanyar binneta,in har kunyi wannan.

Da hannu ya nuna musu halamun komai ya kare.
Ido Tabawa ta hau zarowa tana kallon Lami
"Toh in kuma ba'a adana kwalbar ba mey zai far...
"Malamai ku tashi ku ban waje wasu na jira.
 
Hannu Lami ta yafito ta halamun ta tashi kawai su wuce.
Da harara ya bisu,
"Bai dame ku bane in har ba'a adana ta ba..
Juyo wa Tabawa tayi jin abinda ya ce.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

17_Tsafi dai wai gaskiyar mai shi,sannan asiri ya wuce wasa,a hankali Rukayya ta fara ganin sauyi mai gaba daya gun Malam,in har ta fuskance shi kamar ganinta ne ma baya kaunar yi a gidan.

Yaronta yai wata shida,rarrafenshi a ko'ina acikin gidan,tun daga wannan lokaci ya fara fuskantar cin zali wajen y'an uwanshi da iyayen su.
Amma abinka da yaro gobe ma zai rarrafo ya sake zuwa gare su,sai dai in taji kukanshi ta dakko abinta ta goya kawai.
***

"Raliya abin nan ba fa na karau bane,wallahi kullum Malam kara tsanar ganina yake a gidanshi, ga tsangwama da habaici da nake kwasa gun matanshi, ga bakar azaba da ina ji ina gani ake gasawa yaron nan..

Kuka ta fashe dashi tare da girgiza kai
"Wallahi nayi iya bawa Malam hak'uri ya ma fad'a min mey na mishi yaki Raliya.
Dafata tayi cike da tausayawa.

"Tabbas nasan kina hak'uri Umman Kabir,amma ki kara akan na da,InshaAllah in na koma zan sanar da Abban su Uzairu in yaso ya tuntu6e shi muji koh wani abun ne...
Shiru tayi tare da dan tunani.

"Amma anya Umman Kabir abin nan baiyi kama da aikin asiri ba?
Dagowa tayi tare da zuba mata jajayen idonta,
"Ni nasan su Lami zasu iya komai koh dan yadda Malam ke nuna miki so..
Katseta tayi ta hanyar girgiza kai.

"Ban kawo wannan ba Umman Uzairu, nafi kawo laifi na mishi tunda bai kin Kabir.
"Ni dai kawai ki sanar da Abban Uzairun tunda kila ya fad'a mishi laifin.
Kai ta kad'a tana mai kallon yadda duk tabi ta rame duk akan Malam.
***

"Turaren nan fa baifi a kwakkafeshi ba a yau da gobe Lami amma kinga yarinyar nan mayya taki tafiya.
"Ina fa tsoron maganar Mai yankan wu....
"Rukayya! Rukayya!!..
Shiru sukai tare da kasa kunne jin kwala kiran da Malam ke wa Rukayya cikin tunzura.

Da sauri suka mike tare da lekawa.
"Fito nan tsakar gida.
Ido jajir ta fito halamun yanzu ma kuka ta d'ika.
Tsugunawa tayi kai kasa tare da fad'in
"Gani Malam...
"Munafuka rufe min baki..

Dagowa tayi,suna had'a ido ya kautar da fuska da sauri duk ya sauya kama.
Ido su Tabawa suka had'a tare da komawa d'aki suna murna jin ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba yasa suka nutsu tare da fito wa cikin marairaita.

"Haba Malam,wannan irin fad'a makota suna ji kayi hak'uri haka.
Harara ya sakar musu
"Hak'uri ya wuce wanda nake yi da ita tuntuni? Koh ba kwa gani ne?
Kai Lami tai saurin kad'a wa tare da fad'in
"Muna gani Malam,amma mey tai maka yanzu?

Kai Rukayyan ta dago dashi tare da zuba ma Lamin ido.
"Toh wai dan rashin mutunci irin nata shine ta kai karata gun Nasir wai bata san mey tai min ba duk na sauya.
Ido Tabawa ta zaro
"Kai Rukayya, toh meye ma na kaiwa kara gun kaninshi?

A tunzure ya ce
"Toh nagaji,ki tattara kawai kije sai na nemeki.
Ido ta rintse hawaye ya zubo shar, nan take ta karanto ayar yayewar mudiba.
Bazata so ta tona abinda take fuskanta ba a gidansu,amma yanzu ankai ga6ar da dole a sani.

Tashi tayi tare da kad'a kai
''Kayi hak'uri Malam,zan tafin,Allah ya huci zuciyar ka.
Tsaki ya yi tare da juyawa yana fad'in
"Na dai fad'a miki,kar kuma na dawo na sameki...
Da kallo ta bishi har ya kulle zauren.

Gudar su Lami ce ta sanya ta dawo da kallonta gare su.
Murmushi tayi musu tare da shigewa d'aki jin suna fad'in
"Y'ar gaban goshi yau sai a kara mai,a tafi tafiya ta har abada...

Ido ta sake rintsewa tare da sakar kuka.
"Allahumma ajirni fi musibati...
Ranar tayi kuka har sai da taji ba dad'i, karshe ta hau tattare abin amfaninta na waje tana kaiwa d'aki.
D'anta ta dakko wanda y'ar Lami ta mangareshi ya fad'i yana kuka.

Goyashi tayi tare da yafa mayafi ta sawa kofarta kuba ta rufe.
Har ta bar gidan su Tabawa basu bar yin dariya ba da ya6a mata habaici.

Da daddare har shago Babanta ya samo Malam Isubu kan zuwan Rukayya gida ba laifi inji ta.
A wulakance suka rabu da dattijon,dan gar da gar ya ce shi koh sunan Rukayya bai kaunar ji,dan haka yama sauwaka mata kar a dameshi.

Jiki a sanyaye ya dawo musu da bayani.
"Duk yadda akayi yaron nan ba a hankalinshi yake ba Inno, dan ba haka Isubu yake ba sam,ya sauya.
Shiru tayi tana kallon Rukayya dake hawaye.
"Kin tabbatar ba wani abu ki ka mishi ba koh Ru..

"Dan Allah Inno ya isa,koma meye yafa sauwaka mata,toh mubar tone-tone kawai.
Shiru tayi tare da bashi hak'uri.
Wannan ne silar barin Rukayya gidan Malam Isubu.
*****

Tunani yake duk da surutun da Lami take shatata mishi ba koh shan numfashi.
"In har tunani na yai dai-dai toh a watan nan Yaron nan Kabir ya shekara biyu koh Lami?
Ras taji gabanta ya fad'i, amma sai ta wayence tare da fad'in
"Hakane Malam,mey ya faru?

Tashi yai tare da barin cin abincin
"D'ana zan kar6o a gunta ne,nasan iyanzu kam an yaye shi,bazan iya rayuwa babu shi kusa ba..
Baki sake ta bishi da kallo har ya fuce ya bata guri.
Kwafa tayi tare da girgiza kai.

"Tabawa..
Kira ta kwalla mata, dan haka a yatsine ta amsa dan tuni an dawo gidan jiya tun fuskantar da kowa ya yi yana zagawa shi kad'ai wajen mai yankan wuka.
"Meye?.
Tsaki tayi tare da fad'in
"Malama in zaki shigo ki shigo,dan wallahi wuta bata mutu ba a gidan nan.

D'akin ta shigo dan jin ba'asi, dan haka tuni ta kora mata bayani.
"Yanzu ma nasan chan ya nufa,dan koh abinci bai gama ci ba ya tsame hannunshi.
Tsam Tabawan tayi
"Ni fa na zata tunda muka binne kwalbar nan zai manta ta har d'anta ashe ba haka abin yake ba.

Baki ta ta6e,
"Atoh,in ma zamu manta komai mu tashi tsaye toh,in ba haka ba ya kar6o yaron nan da sannu zai maido da uwar ma.
"Kin manta sun kwashe kaya ne?
"Tabawa baki san meye so ba ne.
***

"Kiyi hak'uri Rukayya kar ya tara mana mutanen unguwa kawai ki bashi yaron nan.
Sake kank'ame Kabir din tayi tana girgiza wa Inno kai cikin kuka
"Ni nasan muguntar gidan ne Inno, ina nan ma ya aka k'are bare sun san ba idona...

Kuka ta sake saka tana ita dai ko mey zaiyi bazata bayar ba.
A tunzure Babban ya shigo rai 6ace.
"Ki wuce ki kai mishi yaron nan tun kamin na sa6a miki Rukayya..

Kai ta dago cikin tsoro ganin Baban a haka,bata jin ta ta6a ganinshi haka,dan haka tuni ta mike jiki na ka'rkarwa rike da Kabir shima da ya fara kuka yana kiran Umma.

A duhu ne,amma duk da haka yana jin kukanta yai saurin dauke kai daga gareta yana huci.
Duk da a zahiri ji yake tamkar ya lallaso Rukayyanshi amma wani abu ya hana.

"Dan Allah Malam kayi hak'uri ka bar min Kabir nai alkawarin kaishi kullum shago...
"Bana so,d'ana kawai nake so.
Ba yadda ta iya,dole ta mika mishi Kabir ganin Babanta ya fito.

Kuka take Kabir nayi ganin ana nema a rabashi da Umman shi a cikin daren,kam ya riketa yana janshi yaro na rike Umman shi.
Dan haushin Rukayyan da sauri ya fincikoshi tare da had'owa da gyalenta a hannuKabir da kamar ya shid'e gun kiran
"Umma.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

15_Gaba d'aya suka bi jaririn da ya fad'o da kallo tamkar wanda aka hankad'o shi daga cikin,sai dai da halamun baya motsi.
Cike da murna Lami ta kallo Tabawa tare da nuna mata jaririn da baki halamun aikin su ya yi kyau.

"Saura mabiya Lami,dakko muciya,koh kuma muje daga nan na duba yaran nan shiru daga kiran Malam,sannu Rukayya.
Hannun Lami ta kamo sukai waje cikin murna.

Ido ta sa yaron,ganin baya motsi yasa ta kai hannu tare da dan ta6awa.
Ido ta rintse sai ga nan hawaye na malala,shikenan shima ya tafi.

Hannu ta bata tare da tafawa,cikin rad'a-rad'a ta ce
"Kai wallahi Lami ba ki da imani.
Dariya ta sa tare da itama da fad'in
"Har na kai ki?
Dariya suka kara sawa.
"Ni fa badan-badan ba wallahi itama mu karasata tabi jaririn kawai tunda kinga bazata lafa ba a gaba ma namiji zata sake haiho wa.

Kai ta kad'a, dan haka katuwar mociya ta dakko tare da rike hannun Lamin suka koma d'akin.
Kukanta kawai take duk da kwa irin azabar da take ji dan wahalar data sha.
Da ido tabi su ba wani guntun karfi a gareta.

"Riketa mu fito da mabiyar kar tai mata illa.
Da sauri Tabawa ta bawa Lami muciyar tare da yin baya da zummar rike ta.
"Bud'e bakin?
Kallonsu kawai take ta kasa koh motsin hanawa.
"Kinga Tabawa bud'e min bakin ki ga.

Ba musu ta dakarkare tare da wage bakin Rukayyan tun karfi Lami ta turmutsa muciyar ciki tana tura wa.
Yunkurin amai take numfashinta na sama amma Lami na sake tusawa har wani cije hakora take dan mugunta.

"Innalillahi... Lami?
Gaba d'aya suka juya tare da sakin Rukayyan ita kuma ta zare muciyar.
"Kasheta ku ke so kuyi koh mey?
Harara Lamin ta sau mata,yadda ta tsani Raliya haka ta tsani mutuwar ta.

Ledar hannunta ta mika wa yarinyar da suka zo da ita tare da cire gyalenta taci damara dashi cikin sauri ta tutsu cikin d'akin.
A hankali ta zaro mabiyar tana ta yi ma Rukayyan sannu.
Tsaki Lami taja tare da hullar da muciyar ta fita waje dan haka da sauri Tabawa tabi bayanta.

Dago Rukayyan tayi wacce sai maida numfashi take dan azaba,kai ubangiji ya rabamu da rashin imani.
Harda hawayenta dan tausayi.
"Taya zaki yarda su Lami su karbi haihuwar ki da hankalin ki?

Kuka tasa tana mai nuna mata yaron dake shinfid'e a kasa,da sauri ta juya tare da ganinshi,bacin mabiya da ta iya fidda wa ba abinda ta sani,shima an koya mata ne dan gudun haihuwar gida ba kowa.
"Ummilo..
Yarinyar da suka zo ta kwalla wa kira.

Zata shigo ta ce ta tsaya,tai gudu ta kira Marka ingozoma makociyarta.
Duk da ta fidda rai a yaron amma hakan bai hana tasa Raliya d'aura shi a zani ba daga kishingid'en ta ruko abinta.
Wajen ta fara gyara wa tana mai tir da halin mugunta.

"Yauwa Marka bissmillah..
shigo wa tayi harda y'ar jakarta mai d'auke da sabin reza da zare.
"Au,ki ce har an haihun ma Raliya?
Kai ta daga tare da fad'in
"Duba mana yaron nan Marka dan Allah.

Hannu Markan ta kai zata karbi yaron sai Rukayyan ta girgiza mata kai tare da fad'in
"Ya mutu fa Marka.
"Eh duk da haka bata dai ta duba mugani dan kamar kirjinshi na bugawa...
Kai ta kad'a tare da mika mata ba dan wai ta yarda da zancen Raliya ba.

Kai ta kawar da sauri ganin yadda Marka ta tashi tsaye ta rike kafar yaron duk biyu ta yadda kanshi na kallon kasa tana dan dukan bayanshi kad'an.
Ido ta rintse,har cikin ranta ji take kamar Marka ita take bugu, dan haka tuni ta fara kuka tana fad'in

"Marka ki bari,
"Ki bari dan Allah..
Ganin taki daina wa yasa da dan karfi ta ce
"Dan sonki da Allah Marka ki bar dukanshi haka,yafa mut..
Jin muryar kukan jaririn ciki-ciki muryarshi a dan shake ne yasa tai shiru tare da kallonsu.

Da sauri Markan ta juyo da yaron dai-dai tana dariya ita da Raliya,ganin haka yasa itama sakar ajiyar zuciya tare da kara sakar kuka.
"Inaga yasha wahala ne gurin fita har gashi yasha ruwa,tabbas gwara da aka duba da munbi ta taki shikenan.

"Bari ki ga,dole na zuko ruwan nan da ya sha,Raliya bani abu kusa da abin kuskure baki.
Waje Raliya tayi tare da yin yadda Marka ta ce.
****

"Kai wannan shegiyar Raliyal wallahi Lami ta kwafsa mana,kila da tuni mun fasa kuka biyu yanzu.
Kwafa Lami tayi,
"Ki bari kawai,tunda munyi nasarar wannan ma d'an ya tafi da sauki sai musan nayi daga...

"Inyaaaaa....
"Ke yi shiru Lami kamar kukan jariri nake ji..
Tsaki tayi tare da gyara zama
"Wane jariri kuma a gidan nan?
Kai ta kad'a
"Sai dai a makota wan..
"Inyaaa...
Wani kukan suka saka ji wanda yasa Lami yin shiru tare da kasa kunne cikin zaro ido suna kallon juna.

A zabure suka mike har suna gware.
Samu sukai Marka na zuko ruwan kad'an-kad'an wanda hakan ke sa yake wage murya wajen ihun murya ta bud'e.

Chak suka tsaya tare da zubawa jaririn ido wanda ke bud'e hannuwa yana sake chanyara kuka tun karfinshi.
Duk kallonsu suke yadda suka kame,baki Raliya ta ta6e tare da sanya hannu bisa hanci tare da sakar bud'a iya karfinta.

Lami ce ta fara juyawa, tukunna Tabawa ta d'aura a bayanta.
Hannu tasa bisa ka da nufin kwalla ihu da sauri Tabawa tasa hannunta tare da damke bakin tun karfi.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

18_Kukan Kabir ne yasa su yin shiru tare da fito wa a d'akin Lami cike da al'ajabi.
"Kai shiru Kabiru, daga yau damu zaka saba..
Tabawa ce ta kalli Lami cikin hasken farin wata,da sauri Lamin ta ta6e mata tare da daga kafad'a.

"Ba dai Malam da gaske kar6o yaron nan kayi da tsohon daren nan ba?
Harara ya sau mata,
"Laifi ne dan na kar6o koh mey?
Kai ta girgiza da sauri,zatai magana Tabawa ta riga ta
"A'a ba haka take nufi ba,kawai dai sai muka ga kamar bai kamata ka amsa ba sai ka bar mata ya girma chan wajenta.

A tunzure ya ce
"Banyi ra'ayi ba toh,na dawo dashi in zaku rike min shi toh,in baza ku iya ba zan kaishi chan Rano a min rainon shi.
Da sauri Lami ta zungureta ganin zata sake magana.
"A'a Malam baza ayi haka ba muna gidan nan..

Karasawa tayi tare da mika hannu.
"Kawo shi ya zauna cikin y'an uwanshi zancen Rano bai taso ba.
Kafad'a Kabir ya make halamun bazai je ba yana cigaba da kukan shi cikin jan zuciya.

"A'a kyaleshi muga zuwa gobe,in zan fita sai na barshi da ku a hankali zai saba da kowa.
Waje ya koma dashi sai kuwa yai shiru a zatan shi gun Umman zai maidashi dan yaga sunzo layin ga gidan yana hango shi.

Shago ya bud'e mishi tare da dakko mishi biscuit mai ya'ya, hularwa ya yi tare da kara sanya kuka yana fad'in Umma har lokacin yana nan rike da gyalen tamau a hannu.
"Toh yi shiru zan kai kaji Kabir?
Ajiyar zuciya ya fara,sai a lokacin ya kula da gyalen hannunshi.

Kar6a ya yi a hankali tare da jefa shi cikin shagon yana tsuka,ganin haka yaro ya sake sakar wani kukan yana nuna mishi gyalen Umman.
Shagon ya rufe tare da komawa dashi gida,tuni ya kara jinyar kukan shi ganin an dawo gidan da ba na Umman ba.

Kalloshi yake yadda yake jan ajiyar zuciya cikin bacci.
Fitilar kwai ya matso da ita yana mai kare mishi kallo,kamar su d'aya dashi,sai dan abinda ba'a rasa ba na mahaifiyarshi.
A gefenshi ya kwanta,yau dai d'aya yaji d'umin yaron shi mafi sauyuwa cikin ranshi.

Washegari har yazo fita shago bai tashi a bacci ba dan rashin yin bacci da wuri jiya.
Jin ya kira Lami ne yasa ya fara motsi.
"Ni zan fita,dan Allah in ya tashi a bashi abinci shima,naga kuma ya yi fitsari.

Kai ta kad'a kamar gaske.
"Toh a dawo lafi...
"Au,kaga ma ya farka.
Kallo Kabir din yai wanda yasa musu ido daga kwancen kamar yana tuno inda yake.
Murmushi yai mishi tare da isa gurinshi ya shafa kanshi ya fuce.

Yunkurin tashi yake yana ta6e baki halamun zaiyi kuka,harara Lami ta sau mishi tare da karasa wa gareshi.
Kai ta dungure mishi tare da jan kunnenshi tun karfi da sauri ya saki wata razananniyar kara.

D'akin yaran gidan suka nufa jin kukan Kabir din kowacce baki duk koko da maikon kosai a hannu sunyi dumu-dumu.
"Kamar kai ka sakar min fitsari a katifa dan iya shege.

Tabawa ce itama ta shigo,ba imani gaba d'aya suka hau ja mishi kunne iya karfi da nuna tsana.
Shid'ewar da ya fara ne yasa suka sarara mishi tare da fitarshi tsakar gida.

Lalle da wuya na kisa da a dan kwana biyu zata kashe Kabir.
A gaban Malam kowa nannan yake dashi kamar su had'iye, yana bada baya su hau mishi mugunta daga su har yaran, karamar yarinyar Lami kad'ai ke tausaya mishi,sai dai bata da wayon da zata hana.

Sau tari yakan dawo ya riski yaron na kuka koh ajiyar zuciya ta in yaci mugunta,da yai magana sai suce sam har yau yaki ya saba dasu,kowa ya daukeshi sai kuka.
Amma fa shi in ya daukeshi zaiyi shiru ajikinshi har yai bacci.

Abinci kuwa tare za'a had'a mishi da yayyenshi gaba daya,wani sa'in kamin yai kwakkwaran loma biyu sun kwakwashe,sai dai ranar ya wuni kukan yunwa, su kuma su wuni dukanshi kan sai ya rufe musu baki yai shiru.

Kan aje ko'ina yaro duk ya rame yai baki,sam bazaka zata Kabir bane fari mai kyau da sumar kai.
Gaba daya koh bacci yake shi kad'ai zai dinga razana shi kad'ai.
****

Wasan kasa yaran suke yana kallonsu daga gefe ya zauna yai tsiru shi kad'ai tamkar maraya marar gata yai duku-duku dashi.
Tsaye take tana karewa gidan kallo,kowa yana harkarshi cikin walwala da sakin jiki cikin gata banda shi.

Sallama take shirin yi sai ta dakata ganin da jan jiki ya isa wajen yaran dake wasan kasa da zummar ai dashi.
Dagowar da Indo zatai y'ar Lami ta biyu ta ganshi a gun ta sau mishi harara tare da daka mishi

"Dalla matsa daga wajen mu shege kawai..
Mari ta kai mishi tare tureshi tun karfinta yai baya tare da fad'uwa yana kuka.
Su Lami ta kallo,sarai sun juyo sun gani,maimakon taga suyi magana sai ma dariya da suka saka tare da d'auke kai daga gare su.

Hawaye ne ya zubo mata na tsabar tausayin Kabir,a hankali ta karasa shiga ba tare da tai sallamar ba,dan a ganinta daga su har yaran ba wanda ya chan-chanci amancinta.


Dagoshi tayi tana mai kad'e mishi jiki tana bashi hak'uri.
Da harara suka bita har ta fuce dashi sa6e akafad'a.
''Munafuka kawai.
Baki Lami ta ta6e,
"Ke ta isheki kallo ma,ni fa na fara gajiya da bautawa d'an nan Tabawa,a kullum ta duniya ji nake ina kara tsanar yaron wallahi. 

"Ki bari kawai Lami,wuya ma kad'ai ta ishe shi karasa wa a gidan nan,dan wallahi baki fini tsanar yaron ba.

Ranar a gidan Raliya ya wuni tai mishi wanka,a ranar yaci mai kyau,sai ga Kabir ya ware suna wasa da Uzairu d'anta.
Dan haka da Ummilo yarinyar makotansu ta mayarshi da kuka suka rabe, dan yasan ya dawo gidan azaba.
****

"Ya ki ka tarar shi da ki ka je Umman Uzairu?
Murmushi ta k'akalo tare da fad'in
"Lafiya lau,a nan ma ya yini.
Shiru tayi tare da sauke ajiyar zuciya.
"Ya rame koh?
Da sauri Raliya ta girgiza kai.
"Ba wata rama da ya yi fa Umman Kabir,ki kwantar da hankalin ki.

Murmushi tayi hawaye har ya taru a idonta.
"Ba gaskiya bane wannan Umman Uzairu, kina so ne kawai ki kwantar min da hankali, amma a yadda nake mafarkin yaron kullum nasan ba kalau yake ba,ina ji ajikina.

Shiru Raliyan tayi,tasan kawai ta fad'a ne,amma ba wanda zai ce Kabir yana lafiya koh da kuwa makotansu Tabawa ne,sai dai kowa na tsoron su ba mai ta6a yi musu fad'an basu kyautawa Kabir.

Dan haka sai ta dafata tare da fad'in
"Kiyi ta sa shi cikin adu'ar ki Umman Kabir,InshaAllah ina ji a jikina a gaba Kabir zai zama wani ni,a yanzu dai dole kiji,ki kuma ki ji, ki gani ki kau da kai.
"Ki sa a ranki wuya bata ta6a kisa,InshaAllah Allah zai kare miki shi a duk inda yake.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

20_Washegari tun asuba ya tashi dan himma,gaba d'aya ya gama cika ruwan gidan yai shara tukunna ya shiga ya watsa ruwa ba koh sabulu.
Kallonshi Abban yake yadda yake tattare gidan cikin sauri kamar kullum.

Suna had'a ido ya dauke kai,har kasa ya tsuguna tare da mishi ina kwana,kai kawai ya kad'a tare da fita da sauri.
Duk da har akasan ranshi ji yake tamkar ya ce yaje ya kwanta kamar kowa ya huta,sai dai bai isa ba.

Kok'arin fita yake sai ganan Tabawa da sauri ta fito har tana tuntu6e
"Wato kamanta dukan da kasha jiya koh?
Kasa yai da kai.
Kubar kofar zauren tasa tare da kullewa,
"Yau zanga karyar taurin kai.

Binta yai da kallo ido fal hawaye,samu yai ya zauna dan ya rasa na yi,ga sai karar mota da babura yake ji wanda shi ke nuna mishi lokacin makaranta ya yi.

Yau dan mugunta dan ma kar ya fita ba yaron da ya fito siyan kosai duk dan kar yaje makaranta.
Tashi ya yi ganin turmi,duk da katangar kasar bata da tsayi sosai amma shi nashi tsayin bazai kai ba.
Dan haka turmin yasa tare da danewa ya haura ta katangar.

Ba karamin ciwo yaji ba a gwiwa, amma dake abinda rai ke so ne shi koh ajikinshi haka ya tafi gidan su Uzairu yana dingishi.
Har kullum Umman Uzairu na mamakin son makaranta irinta Kabir.

Gyara mishi ciwon tayi tare da bashi uniform yasa ta zuba musu abinci suka ci harda zuba musu na tara.
Da suka dawo sai wai wayen masu gini yake yi yadda suke jidar kasa suna mikawa na sama yana laftawa.

"Kabir,
Juyo wa ya yi jin muryar Ahmad
"Mu tafi man ka tsaya.
Wuce wa sukai amma tunanin masu gini yana a kasan ranshi.
Kasa shiga gidan ya yi bayan yaje ya sauya kayanshi a gidan Umman Uzairu, haka kawai ta raya mishi yaje wajen masu gini.

Kallon yadda suke,dan haka sai ya karasa wajen mai bada umarnin.
"Nima zan iya...
Wai wayo wa ya yi,sai dai ganin Kabir da bai ma fi shekara 7 ba sai abin ya bashi dariya.

"Haba yaro, wane kai wannan aikin sai dai kai wasa dai...
Shiru ya yi ganin Kabir din ya wuce tare da daukar kwa6a66iyar kasar da aka fara zubawa ya daga yana nishi ya daura a kai shi kad'ai.
Gaba d'aya baki suka saka suna kallon yaron,lalle sa kai wai yafi bauta ciwo.

Dan haka mutumin baida bakin hana Kabir,sai dai yasa ana zuba mishi rabi yana mikawa.
Ganin washegari gari ma ya dawo shi da Ahmad, sai ya ce a'a sai yaga Babansu tukunna.
Dan haka ba musu ya kaishi gun Abba,bai samu matsala ba,dan take ya ce ai jikinshi ne.

A kwana biyar har ya saba kullum sai yazo dan Ahmad fur babanshi ya hana shi,yau aka gama gini dan haka sai kirgo kud'i y'an sile-sile ya bashi.

"Ga kud'in aikin ka Kabiru,ka burgeni sosai,ina matukar son yaro mai zuciya.
Kallon kud'in yake yana washe baki,
"Na gode,in za'a sake ma zan zo har inda ka ce ka ke.
Da gudu ya nufi gidan Umman Uzairu yana murna yau an bashi kud'in aiki.

Kallonshi take cike da mamaki,lalle wani abu sai Kabir,
"Umma ki ajiye min har na tara dashi zan dinga siyan littafi na siya mana gida na siyawa Umma ma.
Fara'arta ce ta yawaita, har ba tasan hawaye ya tarar mata ba.

"Allah yasa Kabir,Allah ya amsa.
Murmushi ya yi tare da kallon Uzairu da ya shigo.
"Ka ga ka ki zuwa gashi har an bani kud'in aiki.
Da sauri Uzairu ya ce
"Wai Umma?
Nuna mishi tayi tana musu dariya.

"Ai Umma Uzairu rago ne bazai iya ba wai.
Kai Uzairu ya kad'a
"Tab,naje kaina ya lo6a,kai dai kaje kai tayi ni bazan iya b...
Shiru ya yi jin sallamar Umman Kabir.
Da sauri Kabir din ya juya tare da isa wajenta da gudu.

Hawaye ya fara kamar kullum in ya ganta,yau ba labarin gidan su Tabawa sai labarin aikin da ya yi aka bashi kud'i.
"Umma nuna wa Ummata ta gani.
Ajiyar zuciya ta saka,lalle bata isa dakushe Kabir ba,sai dai a ganinta yai kankanta da aikin gini.

"Toh Kabir Allah yasa kafi haka.
Baki washe,sai Uzairu ya ce
"Amin zaka ce.
Kai ya kad'a tare da fad'in
"Amin toh Umma.
Tsarabar da ta kawo ta basu,cikin murna harda kayan sallah da littafi da pencil harda jakar makaranta ta buhu shi da Uzairu.

"Na gode Umman Uzairu, ubangiji ya baki lada,ina farin ciki idan nazo gidan nan naga Kabir a farin ciki.
"A kullum bani da adu'a sai ta Allahu l ya taimake shi da sauran yaran musulmai.

Murmushi tayi.
"Yi wa kaine ai Umman Kabir,kema kina ta fama da kan ki ya kamata ki hakura da fita haka tunda kin kusa haihuwa.
Kai ta kad'a
"Kamar kin san akan zuwa gun Kabir yau ma sai da muka kai ruwa rana da Malam,na rasa mey Kabir ya tsare mishi fur yaki jinin na ce zani gunshi.

Murmushi Raliya tayi.
"Ki bishi a hankali kin san maza kila yadda ki ke zata ba haka bane.
Kai ta girgiza,
"Kishi kawai yake da Kabir nake gani.
Baki tai ta bata har dai ta gamsu ta bar maganar.
****

Yau Jumma'a,su Kabir har an shiga primary 3, da wuri aka taso su dan ganin jiya nad'ar da yaci ta tsayawa a gun masu gini yasa yau ya wuto gida yana cire kayanshi.
Shigarshi ke da wuya duk suna tsakar gida har yaran.

Indo ke gaban rijiya tana diban ruwa,yayin da Hafsa ke wanke-wanken kayanta.
''Yauwa,zo ka karasa min dan wahala.
Kallota ya yi,sai dai ya karasa tare da kar6ar gugar hannun nata.
"Kabiru wai makarantar da dad'i ne?

Hafsa ya kallo ganin ita ce sai ya saki jiki.
"Eh,ni kinga yanzu har ajina uku Allah Hafsa ki shiga.
Kai ta kad'a tana mishi murmushi.
"Ni da ban iya komai ba Kabir.
Ruwa ya zuba yana kok'arin bata amsa yaji Lami na duka mata tsawa.

Shiru tayi rai a jagule, sai dai tsugunawar da zaiyi yaji an kwada mishi abu a gadan baya.
Dagowa ya yi dan azaba yaga Indo na kok'arin kwad'a mishi ice
"Ni zan saka abu ka tsaya yin fira?
Kai ya kad'a tare da kok'arin kaucewa ya manta da bayanshi rijiya ce.

Taga-taga yai zai fad'a da sauri ya dafa Indo,tuni gabanshi ya fara fad'uwa ganin bai fad'a ba.
"Lalle ma yaron nan?
"Toh mey ki ke jira dashi da ya rike ki?
Kallo Lamin suka yi,da ka ta nuna mata halamun ta hankad'a shi,batai wata-wata ba kuwa iya karfinta ta hankad'a shi.

Kai ya buga tare da sakar ihu da karfi ya kank'ame gugar da Allah yasa a kulle take.
Ahmad da yazo nemashi yaga abinda ake neman yi wa abokinshi sai ya juya da gudu shagon Abban su Kabir din.

Hafsa yake kira ganin yadda kafafunshi ke cikin rijiya hannunshi rike da igiyar guga,ga nan inda ya bige har ya fara jini.
Da gudu ta rike gugar ta waje tana kiranshi.

Daga yaran har iyayen dariya suke mishi har wacce ta hankad'a din.
Ganin Hafsa na kok'arin ciro shi yasa su Tabawa suka taso tare da kok'arin kunce igiyar suna ihu shi da Hafsa akan kar su hullashi.

Dukan hannunta Lami take tana fad'in
"Idan baki cika ba wallahi zan hulla ku tare.
Kai take girgiza musu
"Wallahi Lami mutuwa zaiyi, ku taimake shi kar ku kunce.

Guga taki kuntuwa dan haka da sauri Tabawa ta dakko wuka,tuni makota suka lelleko ta katanga masu iya bada hak'uri suna yi amma iya karfin su suke yanka igiyar suna dariyar mugunta.

"Da wannan basirar tazo mana ai da tuni ka manta da fad'a shege mai taurin rai...
"Hafsa...Hafsa dan Allah,dan Allah ki janyo ni...
Bata da cikiken karfin janyoshi,dan tamau Lami ta riketa tana ji tana gani suka sau igiyar Kabir yana ihu yana komai suka tsunduma shi.

"Wayyo Kabir Lami,dan Allah ki cikani na tsamo shi...
Lafiyyen mari ta dauketa dashi tare janyeta a gun gaba d'aya suka juya da zummar barin bakin rijiyar sai sukai poster.

Ahmad suka gani tare Abban su Kabir sun shigo a sukwane.
Kan suyi kwakkwaran motsi har shima ya karasa jin Hafsa na Kabir ne a rijiya Abba ya tsunduma kanshi cikin ba koh gargada.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

21_A kansu gaba daya aka raja'a dan cecen ransu wanda dakyar aka samu masu hakan rijiya da karafan unguwa suka fiddo su kank'ame da Kabir duk sunji ciwo.

"Ban san da mey zan kira abin nan ba likita,abu daya na sani kawai ku yarda tsautsayi ne.
Abban Uzairu likita ya kalla tare da kad'a kai.
"Allah rufa asiri toh,amma tabbas sunyi mummunar buguwa, barin ma uban,dan shi yaron sai nake ga tamkar ma wanda aka sanya shi ciki intentionally.

"Dan in ka duba gaba d'ayan shi ya tafi in banda ciwo da yaji keya, wannan kuma baida alaka da fad'awa rijiya dan direct ya shige.
Ajiyar zuciya likitan ya yi tare da fad'in
"Any way,a barshi a tsautsayin,amma gaba asa ido.

******
"Kiyi hak'uri Umman Kabir, mu kuma gode Allah da ya cece su.
Hawaye ta goge tare da kad'a kai tana kallon gefen Abban Kabir din dasu Tabawa da sai kuka suke.
Ta sani a duk rintsi dama baza'a rasa burbushin kauna ta Allah acikin kowacce rai ba,balle kuma iyaye.

Bata ta6a zatan Malam zai iya sadaukar da ranshi ga d'anta d'aya tilo ba.
Kai ta d'auke tare da goge hawaye...
"Hafsa...Hafsa...dan Allah ki janyo ni kar ki bari su jefa ni...
Gaba d'aya d'akin suka juyo tare da kallon Kabir dake ihu farkawar shi kenan ido a rufe.

Kai Umman ta dago tare da kallon gefen su Lami da sukai saurin mikewa.
"Na sani wallahi, na sani jefa Kabir akai da gangan dan na samu labari a bakin Ahmad...
Hannu Umman Kabir tasa ta rufe ma Umman Uzairu baki tana girgiza kai.

Daya bayan daya suka fara zamewa suna barin dakin ganin Kabir din ya bud'e ido.
"Sannu Kabir,Allah ya kara cecen ka.
Ido ya sa ma Umman Uzairu mai magana, kamin ya jiyo kan Ummanshi,suna had'a ido ya saki kuka.
"Yi shiru Kabir,yi hak'uri.

"Umma su Tabawa ne suka kashe ni fa...
Duk kuka suka sa har shi jin maganarshi cikin shesshekar kuka.
Kanshi ta shafo tana girgiza yarinyar bayanta.
Umman Uzairu ce bashi amsa
"Basu kashe ka ba Kabir,baka mutu ba..
"InshaAllah Allah na tare da kai.

Umman yake kallo,dan haka da sauri ta kad'a mishi kai halamun haka ne.
Labari ya fara basu suna kuka yana yi,wannan irin rashin imani har ina?
Tsam Umma tayi,
Tabbas a duniya bata da makiya sama dasu Lami,amma dole hakkinta ne ta sanya Kabir binsu da y'an uwanshi.

Ta sani da wata rana sai labari,wata rana koh an ce suyi baza suyi ba.
Lalle yanzu ta dau hanya bisa ga rayuwar Kabir,tana kuma rokon Allah yasa Kabir shi zai nuna wa su Lami Aya.
Har aka sallame su kala Abban Kabir bai ce ba,hakan ne yasa suka gane tabbas shirin mai yankan wuka har yanzu yana rike da Malam.

Sai dai daga wannan rana da abu ya faru Allah ya yaye wa Kabir duk wani digon tsoro nasu acikin rai.
Daga ranar ya daina duk wani aikin bauta cikin gidan a ciki kuwa harda diban ruwa a rijiya.

In zasu kwan dukanshi ci kanku bazai ce ba,dan tuni in da sabo yaci ya saba,zuciya har ta kekashe.
In kuwa a yaran gida ne sai inda karfinshi ya kare daga kan Indo har kasa.
Dan haka tanan ba karamin y'anci ya kwata ba,dan sai ya zamo gaba daya yaran na shayinshi,dan in ta fagen fad'a ne toh da duk'kan karfinshi ya ke aika musu duka.

Matsalar kafa Malam ya samu,dan haka sai da dingishi yake iya tafiya.
Yanzu abin ya zama sai gaba yake sake yi a harkar rayuwar gidanshi,shi ya zama matan, yayin da su Lami suka zama shi,duk abinda da suka ce akan Kabir,toh fa shi zai aikata.
****

Yau da gobe sai Allah,ga nan Kabir an zana jarawar karshe ta primary cike da nasara.
Gun aikin gini kuwa tuni shima ya zama kwararre,dan ba abinda zasu sa shi bazai iya ba,dan haka tuni ya zama yana samu sosai ta hanyar gini.

K'ak'karfa ne,dan tun kan aje ko'ina jikinshi har ya fara murd'ewa,sam in ka ganshi ba ka ce Kabir bane dan shekara goma sha uku.

"Umman Uzairu... Umma..
"Kira suke maka mata cike da murna su uku.
Fito wa tayi tana amsawa rike da hannun Halima wacce ke kukan bacci.
"Mun dawo,har mun rubuta..
Baki ta washe tare da fad'in
"A lalle mashaAllah, ubangiji yasa an gama a sa'a.

Baki suka had'a tare da fad'in
"Amin
"yanzun sai ta sakandere koh?
Kai Kabir ya kad'a cikin farin ciki.
"Eh Umma,Jss1 zamu tafi kuma.
Kai ta jinjina.
Halima ya kallo wacce ke mishi dariya,dan haka da sauri ya karasa tare da cire alawa yasan ita takewa ya mika mata.
"Ka ganta tun dazun ta dameni da bacci,na kwantarta nan kuma ta ki.

Kumatun ta yaja cikin wasa,alawa na baki ta fara bangala mishi dariya.
"Yauwa,kema ki girma a saki a makaranta koh Halima?
Kai ta kyad'a kamar ta gane mey yake nufi.
"Ubangiji ya taimaka.
Murmushi yai,kamin ya ce
"Anjima zani gun Umma ma na sanarta.
Murmushi tayi suka fita shi da Ahmad.

"Yanzu Kabir in munci boarding ya zamuyi?
Murmushi Kabir din ya yi
"Ni ina son boarding Ahmad,sai dai koh na fad'a wa Abba ba kulani zai ba,ga Abban Uzairu nasan baya son boarding da muguntar wai da ake,kuma da kud'i ma dan ni da Uzairu ne,ni kuma wanda na tara ba yawa dan dashi na biya na wannan jarabawar.

Kai Ahmad ya jinjina.
"Sai mun had'u anjima.
Gida ya shiga yana daga ma Ahmad kai halamun toh.
***

"Abba takaddarmu ce ta gama primary zamu shiga secondary mun samu day,ma'ana ta jeka ka dawo.
Kai Abban ya juyar mishi dashi,kawai bai son yaga Kabir na ra6arshi,wani irin haushin yaron yake ji.

Jin shiru yasa ya sunkuyar da kai,bai san abinda yasa sam Abba ya tsaneshi ba.
Su Tabawa dake sauraro ta janyo Lami d'aki.
"Jiya a gidan Tasallah ina jin irin muguntar da danta yake fad'a ana yi a makarantar kwana,yaron duk rauni jikinshi ina ji yana cewa ta jeka ka dawo zai koma shi dan wahalar ta kwana.

Tsam Lami tayi
"Toh mey ki ke so ayi?
Gyara zama tayi
"Yauwa,mey zai hana mu sanya baki a aika wanchan gawa taki ramin a lallasa mana shi achan?
Dariya suka sa harda tafawa.
"Eh lalle yau Tabawa kin kawo shawara.

Bakin kofar Hafsa ta bari da sauri jin zasu fito.
Baki har kunne suka isa wajen Malam,Kabir yana ganin su yasan za'a mishi wata tsiyar.
Dan haka tashi ya yi jiki ba kwari zai bar wajen yaji sunce
"A zauna man Kabir..
Baki sake yake kallon su,sai ya kallo Hafsa dake girgiza mishi kai halamun yace bai yarda ba.

Yadda suke murmushin shi yasa yasan da mugunta suka zo.
"Amm Malam.
Kallosu ya yi yana amsa wa.
"Mey zai hana ka kai Kabir din makarantar kwana tunda naga yana da son karatun zamanin.
Cike da mamaki Abba da Kabir din suke kallonsu.

"Eh wallahi Malam a kaishi,mun goyi baya...
"Kabir..
Da dan hankali Hafsa ta kira shi,ganin yadda take girgiza kai yasa Lami ta mako mata harara.
Sai yai murmushi tare da zama,tsam ya karanci abinda suke nufi,dan haka jin Abba ya yarda sai ya musu godiya.

Hararar shi Hafsa tayi bayan ta biyo shi waje sai yai mata murmushi
"Kai baka san tarko aka d'ana maka ina ta cewa kace baka yarda ba amma sai da ka amince.
Murmushi ya yi tare da kad'a mata kai
"Kar ki damu Hafsa,ba abinda zai faru,nima ina son boarding,kawai dai ki dage kema ki fara karatu koh primary 2 a saki tunda kin iya abinda nake koya miki.

Kai girgiza,
"gaskiya nai girma yanzu da makaranta,shekarata 15 fa Kabir.
Rai ya had'e
"Wa ya fad'a miki? Akwai wanda suka fiki Allah kar ki biyewa su Indo kiyi ta yawon tallar nan Hafsa.
Kai ta kad'a mishi,
"Toh zan fad'awa Abba,koh Abban su Uzairu.

Da taimakon Abban su Ahmad su Kabir suka samu gurbi a makarantar kwana ta boy's and girl's,shi kam Uzairu fur ya ce sai Day,da wannan abotar Ahmad da Kabir ta kara kulluwa.
Sai ga su Tabawa harda tara mishi kanzo su a dole wuya zata kashe Kabiru a boarding.
Da murmushi kawai yake bin su,dan duk ya gano shirin su a kanshi.

"Umma gobe zamu tafi ki min adu'a.
Murmushi Umman tayi
"Adu'a kullum ina kan yi maka Kabir,ubangiji yasa aje a sa'a, amma ni sam ba dan ka nace ba bana kaunar makarantar kwana dan yadda ake fad'in muguntar su.

Dariya ya yi bawa Nafisa abinci ta dan cije shi tana dariya.
Hannu ya yarfe yana mai kallonta.
"Tafiya zanyi naga wanda zaki na cizo kullum in ya zo.
Dariya tayi.
"Ina zaka Yaya?
Kallon su Umman take,tun yanzu zaka gano kaunar juna ta y'an uwan taka a tare da yaran musamman Nafisa da Kabir.

"Makaranta zan tafi Nafi, sai na jima zan dawo.
Kuka take neman yi ya hau lallashi,ita ta wa zai na kawo mata alewa take.
Da zai tafi Umman ta dakko mishi abinda ta mishi.

"Gashi Kabir,ubangiji yasa a fara a sa'a,ka kula da amana kawai da karatun ka.
Kai ya kad'a yana duben abin,
"Kai Umma na gode, kamar kinsan bani da kayan y'an gayu su cabin da peak,sabulu ma duk bakud'in nawa ya tafi a littafai da jaka da sabin kaya.

"Dan ma wannan karan Abba yai min uniform har biyu da akwati..
Murmushi tayi tana kad'a kai
"Allah ya cigaba da ganar shi,a kullum kai ta sa shi a adu'a kar kaga laifinshi.
Kai ya kad'a
"InshaAllah Umma,bari na biya gidan Inno kar na amsa quarry dan I know her.

Murmushi Umma tayi,tana jin dad'i taji Kabir na d'an yaren turawan nan.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

 22_Da dad'i ba dad'i haka Kabir da Ahmad suke daurewa har suka ci karfin karatun su.
Ganin ba abinda ya ragu jikin Kabir sai ma waye wa da kara kyau da yake shi yasa suka sanya Abba cire hannu a karatun Kabir,ba musu ya daina cin kwandalarshi,yanzu kam kud'i ba matsala ba ce sai dan abinda ba'a rasa ba,dan a kanshi Ummanshi ta fara dinki.

Da duk karfinta take neman kud'i dan cika burin d'anta na yin karatu mai zurfi.
Sosai harkar gini take kai mishi har ya samu ya tallafawa Abbanshi da yanzu kasuwar bata kai mishi,sai dai har ya bashi abinda zai bashi bazai ce mishi kanzil ba.

Da ya kaiwa Umma kukan shi magana d'aya ce
"Kai hak'uri, watarana sai labari...
Har ga Allah ya gaji da zuwan watarana d'in nan da har yanzu bata zo ba.

Sun gama secondary cikin nasara da kyaututtuka na yabo ga Kabir masu tarin yawa.
Kowa yai murna dan har gida makota suke zuwa ganin kyauta da a unguwa ya zama zakaran kwajin dafi.

A ranar su Tabawa sunyi da na sanin aika Kabir boarding, a ganin su banda nasara ba wata wahala da yaci achan,tai ma Tabawa Allah wadai da wannan shawara gashi ya zama d'a tamkar da dubu.

Shekarunshi goma sha tara,dogo ne mey kirar karfafa, a yanzu kamaninshi sunfi fito wa na sak da Abba.
Fari da sumar kai kawai ya lakato na Umma dake da jinsi na fulani.

Zai wuya ka ce bai kai 25 ba a lokacin dan sam bai d'aukar wargi,dan gayu ne mai ci da guminshi har ya tallafa.
In dai zai samu,toh burinshi ya wadata ran mutum uku,
Ummanshi,
gidan su Uzairu
,sai kuwa Abanshi in ka had'a Hafsa,sauran kam tun Umma nayi har ta hakura ta zuba ido,dan in ba ta dalilin Abba ba yadda ya tsani *MATAN UBA* ba mai cin kwandalarshi.
****

"Kiyi magana cikin na uban waye...
Baki ta turo tana guna-guni,Kabir da ya shigo yai tsaye jin zancen cikin Indon.

Shiru sukai tare da zuba mishi ido.
Tamkar kabewar dake kan kabari ne shi a yanzu a idonsu wai bakin cikin mai taushe.
Handsome, matashin yaro mai ci da kuruciyar shi.
Kallonshi kad'ai a garesu babbar aya ce dake sa suyi shiru.

Dan haka baki kowa yaja ya tsuke har ya shige inda nan ne d'akin shi na Ummanshi na da.
Tsam ya yi cike da mamaki,a ganinshi wannan ai ba abin tada hankali bane dan Indo ta kara ciki.
Shi shaida ne yadda samari har a cikin zaure yasha kicibis dasu suna lalume Indo.

Sannan in bazai manta ba yasha jin an kama Indo da wani a rufar kasuwa ba so d'aya ba ba biyu ba...
Sam ya rasa dalilin da ya kasa jin tausayin Indo a cikin ranshi sai tsanar su.
A kullum in ya rintse ido yakan tuna hankad'a shi rijiya da tayi ne tana dariya.
Hmm,abin da aka gasa kam wai shi ya ga wuta.

Ajiyar zuciya ya yi tare da fad'in
"Allah ya kyauta.
"Kabir"...
Kofa aka kwankwasa.
Amsawa ya yi tare da tashi ya bud'e mata jin muryar Hafsa.
Murmushi yai mata tare da bata waje ta shigo.
Murmushi ita ma tayi tare da zama.

"Ya akayi sisto?
Murmushi ta sake yi tare da girgiza kai,jin tayi shiru yasa ya zauna kusa da ita yasan da magana.
"Uhmm.
"Aure nake son yi nai nisa da gidan nan da bakin cikin cikin shi Kabir,bazai yu na zauna barikin gidan nan tabi ta kaina ba Allah...

Kuka tasa tana mai tir da halin y'an uwanta.
"It's Ok..
Lallashinta ya fara.
"Yunus dama ya matsa ya turo ina ki,dan ina tunanin karatuna dana fara.
Kai ya kad'a
"Banki taki ba,amma zanso ki tuntu6i Yunus akan cigaban karatun ki,Jss2 ki ke.

"Koh ni a kullum burina kiyi nisa da dabi'ar y'an matan gidan nan, ki bi Allah ki rike mutuncinki,auren Allah sa shi yafi alkairi, amma zanso ki idda makaranta koh kina gidan miji.
Kai ta kad'a.
"Zan tuntu6e shi,koh kuma kasa baki naga yana yaba mutuncinka a gidan nan.
Kai ya kad'a.
"InshaAllah zanyi kok'ari.

Taje kai ya yi yana fesa turare.
"Yanzu sai ina?
Murmushi ya yi tare da fad'in
"Gidan Umma zani,tukunna zan biya naga budurwa ta Halima.
Dariya suka sa suna kok'arin fita,
"Wannan had'in Allah sa ya tabbata.
D'aki ya datse yana fad'in
"Amin sisto.

"Bye..
Hannu ta daga mishi tare da fad'in
"Ok,bye..
Yana fita kusan gidan gaba daya suka d'au tsaki.
"Tusa kai ba kwarjini, wallahi kinji asara marar kishin y'an gidan nan.
Kallo su tayi tare da Indo mai magana.

''Ji da abinda ke a gaban ki,dan asara ke ki ka ganta...
Shiru tayi ganin ta zaburo zata nufe ta.
"Wallahi kar ki kuskura ki shafan kazamin jikin nan da yaga maza turum...
"Ki kiyayeni Hafsa wallahi.

Tsaki Hafsan tayi tare da jan mayafinta ta fuce,
"Asara kawai,yawun bacci.
Kwafa Indo ta kuma yi tare da koma wa,
In da sabo ta saba da yadda Hafsa ke wanke su musamman in sun dawo a bariki.
In dai zasu kawo toh ta ciki mai sauki ne,yanzu za'a hararrameka in ka fad'i waye uban a hau lalarsa daga baya su murtsike cikin.
****

"Nan A.B.U nake hari Umma InshaAllah.
Kai ta kad'a
"Allahu ya taimaka Kabir,ga dan uwanka(Uzairu) ya ce shi ba rana wai sana'a zai fara.
Kai ya kad'a
"Hakan ma yana da kyau,a hankali zaiyi ne.

Tsakar gida ya kalla ganin Fatima a zaune.
"Yau banga budurwar ba Halima.
Murmushi tayi tare da fad'in zaka ganta bada jimawa ba..
Sallamarta ne yasa suka dubi waje gaba d'aya.
Daga yanayinta zaka gane ranta a dagule yake,sai dai tana yin arba da Kabir ta sau fuska tare da sunkuyar da kai tana murmushi.

"Uhmm,budurwata kinyi kyau fa.
Hannu tasa ta rufe fuska bakin nan yasha kan ta kile.
Dariya Umma tai musu tana kad'a kai jin tsokanar Kabir din.
"Toh ni kam Umma haka za ai auren kullum ana kunshe min ido.

D'akin su ta nufa tana dariya,ita har ga Allah da gaske kunyar Kabir take.
Gidan Umma ya nufa duk da yana d'ari-d'arin zuwa,dan tun girmanshi suke y'ar tsama da mijin Umman.
Wai komai na Umma a Kabir yake karewa,maimakon ta kula mishi da yaranshi.

Duk murna suke na ganin shi musamman Nafisa ta zama y'an mata y'ar gayu.
***

Da taimakon Umma da kud'in gini ya bi Ahmad suka samu kurbi a jami'a inda ya zabi bangaren zane koh dan gini wanda zanensu shine burinshi yayin da Ahmad ya zabi bangaren kasuwanci.
Anyi auren Hafsa inda aka kaita Zamfara.

Bayan wuya kam sai dad'i,gashi yanzu har sun kammala.
Aminin Abban su ne ya bashi yarinyarshi
Ahmad ya aura,kamin su gama akai rikicin auren kan matar bata sonshi, da dad'i ba dad'i har ta samu ciki,da wannan aure ya mutu ta auri mai sonta,haushin wannan yasa sirikin Ahmad din ya fanshe wa Ahmad da kanwarta Sumayya Umman su Farida.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

23_"In har zakuji ta tawa toh da kun daina wahalar da kan ku a wannan yaron yanzu kuyi ta yaran nan su samu mazan aure Tabawa,kullum sake dakko muku magana suke amma ku ta abu daya ku ke kullum ba nasara..

Lami ta kallo jin bayanin Tasallah,kuma fa da gaskiyar ta,dan duk wata kadarar su a Kabir ta kare na ya ta6e yaro sai gaba yake.
"Nima ina jin bakin cikin abin nan fa Lami,mu rabu da yaron nan kawai Mai yankan wuka ya hau aikin su Indo yaje chan ya karata.

Da wannan suka ajiye makamen su akan Kabir na asiri,tunda sun san yanzu kam Kabir sai kallo daga nesa.
****

Kai ya taje,shi kad'ai kawai ya tashi da wani farin ciki tun mafarkin Halima da ya yi tana mishi y'ar kunyar nan.
Ya sani da a da kam da gaske wasa yake,amma yanzu tabbas yasan yai nisa cikin son Halimatu,dan haka yau wankan nata ne.

Gidan ya shiga tana a tsakar gida ta daga madubi tana ta kallon gefe da gefen fuskarta cikin fari irin na masu iya yi.
Kallonta yake,matuka abin ya fara bashi dariya,ganin yadda ta dage tana tsatso kyanta a madubi.

"Oh ni Raliya,yanzu Halima har yau kwalliyar nan bata kare ba?
Madubin ta ajiye tana ma Umman
"Nayi kyau?
Kai ta girgiza,tare da niyar juya wa ta kula da Kabir a bakin kofa.
Magana take shirin yai mata halamun tai shiru zai shigo,Halima ta kalla wacce ta cigaba kyalinta,sai ta girgiza kai tare da yin ciki.

Waka ta dan fara rera wa tana dan rufe ido kamar wai tana jin kunya.

 _'Kalaman juyan baya_
_'da kayi su sai naji kunya'_
_'Akan kwa bana sanya ka hu_...

Shiru tayi tare da waro ido ganin yadda ya hard'e hannu yana mata murmushi, juya wa tayi da sauri tare da rintse ido cikin kunya,tabbas tasan ya jima a nan wajen.

Tashi tayi tana gyara gyalenta cikin satar kallonshi,ganin yana takowa yasa tai saurin sadda kai kasa tana murmushi tare da fad'in
"Ya Kabir..
Shiru ya yi bai amsa ba,dan haka sai ta dago a hankali.

Madubin ya dauka yana dan gwada yadda tayi cikin tsokana.
Kau da kai tayi tana dan dariyar kunya,akanta kam shi zai komai in Halima zatai murmushin kunyar nan.
"Nayi kyau?
Gyale tasa ta rufe fuskarta wai ita a dole kunya.

Kai Umma ta kad'a da ta fito,
"Na rasa ina zata tafi awa a zaune kyali,ashe saurayin ne zai zo zance.
Kai ya girgiza,lokaci ya yi da za'a ajiye zancen wasa,amma bari ya fara ta Ummanshi yaji.

"Dama gun Umma zani,tunda bata wajen zuwa ni kam Umma ki ara min ita ta rakani,amma ta sanya nikabi tunda kwalliyar tawa ce..
"Umma nima zani..
Kallo shi sukai Khalifa da ya shigo dan autan su Halima.

Dariya Umman tayi
"A ba ruwana, kunfi kusa,a gaida min Umman da kyau,amma Halifa da kai hak'uri..
"A'a Umma,yazo muje dashi karin dan rakiya.

Duk sabon su da juna a yau sai kallo sai murmushi, tamkar wasu masoyan nan masu kunyar juna.
"Matar...
Kai ta kawar jin sunan da yake kiranta tun yarinta tana murmushi.

"Uhmm.
Kai ya kad'a.
"Ni fa na shirya,koh yau a daura mana aure..
Dariya ta dan sa,a zatan ta har yanzun wasan ne..
Sai dai jin har a gaban Umma yana fad'in shi fa tare zasu koma Kaduna in zai fara aiki yasa ta hau kunya.
Ya Kabir a kullum shine mafarkinta,shine burinta tun zamanin yarinta.

Zata iya cewa daga tausayin rayuwarshi ya rikid'e ya koma 'so' sannu a hankali.
A kullum burinta ta aure shi koh dan share mishi hawayen da su Tabawa suka dasa mishi.
Tana fatan tai silar dai daituwar lamarinshi shi da Abba.

Abu kamar wasa a hankali magana ta zama babba,kowa yai na'am da had'in, duk a lokacin ba wata babba bace daga ita har Fatima, amma aka sanya su lalle sai Kaduna.

Rayuwar aure suke mai cike da so da tattalin juna.
Halima mai matukar hak'uri ce da k'au da kai,hakan yasa zai wuya ka ga sun sa6a,kullum cikin farin ciki yake har takan mantashi rayuwar gidan su Tabawa har suka samu Saifu.

A wannan lokacin ne Abban su Farida aka aikashi Jigawa,silar rabuwar shi da Abokin shi Kabir sai daga baya ya dawo Kano.
*****

"Sai fa kana yi kana manta baya kamin zaka iya daure wa kai musu wani abin Abban Saifu.
Murmushi ya yi tare da kwantar da Saifu.
"In na ce zan iya manta abin da kwasa a gidan nan Halima ba mai yuwa bane.

"Naga rayuwa duk da nasan kin riski wani abin wani kuma sai labari.
"Maman Saifu har yau ina neman wanda yasha irin azabar da na gani gun *MATAN UBA* amma banga ba.
"Dani da Abba har yau dinnan sai kallo daga nesa,tun tashi na ban san tararrayar mahaifi ba sai tsana karara.

Da yai ta tuno wa Haliman na hawaye wani abin ma sai yau taji,a ranar ta kara tsorata ga sha'anin *MATAN UBA*..
Tamkar karamin yaro haka yake mata kuka yana tuna mata da baida kamar su Lami a sahun makiya.

Nata hawayen ta shanye tare da janyoshi gareta.
"Abban Saifu gashi yanzu sai labari,ka yafe musu tunda a kalla suna ganin Aya akan su Indo.
Murmushi ya yi tare da girgiza kai.
"Zan yafe musu duk randa suka tabbatar min da zasuyi abu daya,wanda na tabbatar baza su iya ba,sai dai su dauwama da zunubi.

Kai ta kad'a, kamin a hankali ta janye maganar suka dawo wata.
"Ni na fa matsu da auren nan na Nafisa yazo mu tafi.
Murmushi ya yi.
"Toh ku auren da ba amarya ma ina zaiyi dad'i.

Dariya tayi tare da kad'a kai.
"Yaki hak'uri a gama biki su tafi ba,ni fa sam bana son American nan yaya gani nake kamar mutum in ya zauna zai dau al'adar su.
Kai ya girgiza mata,
"Toh ya za ayi,kinsan Nafisa kuwa yadda take ji da wannan mijin dan zasu zauna a America?

Dariya suka sa tare da girgiza kai
"Nafisa gidan fafu,chan karyar zata karu.
Dariya sukai yana kad'a kai.
Har cikin ranshi yasan zaiyi missing Nafisa y'ar kanwarshi tsoka d'aya cikin miya.
Bayan sun dawo a bikin Nafisa ya jona masters nashi Zaria.

Sau biyu su Tabawa na kwata zuwa ana katari baya gari,dan haka sai yadda sukai da Halima haka zata cika su da sha tara ta arziki amma babu gwaninta,daga karshe har gida yaje yai musu kashedi kar ya kara ganin kafarsu a garin Kaduna.

A hankali yai ta samun bud'i da dad'i babu dad'i suna zaune da Halimenshi da yaran su,har kawo lokacin da mutuwa tai musu yankan kauna.
Yaso ya jiyarda Halima dad'i dan a ganinshi tare sukaci zamanin wuya,ga nan dad'i yazo babu ita.
****

*WAIWAYE*...

"Abba wai Aunty Fatima ta dawo?
Saifu ya kallo tare da cire farin glass din idonshi.
Kai ya kad'a mishi,
"You know.. Ba wai ita zaku duba ba,ku duba Maman Saifu sai mu mata afuwa.

Shiru sukai suna duben shi.
"Amma Abba bazata dawo ba koh?
Murmushi yai tare da saurin kad'a kai
"Ta tafi har abada,yanzu ni ne Mama,ni ne Abba..
Fuska suka washe harda dariya dan murna banda Saifu.

Kallo Saifun ya yi ganin yadda ya zuba TV ido,tvn ya kalla,sauran ma duk sun maida hankali gun film din 'Cinderella'
Rai Saifu ya had'a tare da fad'in
"I seriously hate them..
Da sauri Nass ya ce
"Step-Moms ba? Kalli Cinderella..
Dan tsaki ya yi yana kara volume.

Jiki a sanyaye ya kalle su,da gaske kuma suke,dan a haka ji suke kamar su shiga suje su mak'ure step mom na Cinderella.
Amjad ya kallo jin ya ce shima
"Me too..

Jingina ya yi tare da kallon su,tabbas sai ya yi da gaske,dan karara yake ganin kin *MATAN UBA* a idon yaran shi sama dashi kanshi.
In har ka cire Sultana da shan hannu ke a gabanta tana musu dariya.

Tun daga ranar suka zama y'an lele,abinda suke so shi za ayi,mace kuwa koh ta office suka ga tana yage wa Abban su baki yanzu zasu hau hararar ta suna Abban yazo su tafi.
Ya sani da koh dan lafiyar yaranshi zai hak'ure da rayuwar aure,dan gaba daya ya tsorata da lamarin auren duk da jiki da jini sai a hankali.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

24_"Wayyo dad'i, dama ni ce wallahi Ummahani.
Harar ta tayi.
"Dallah,dan baki san meye auren bane,dan wallahi ni dai karatu nake so...
Hawaye Umma Hanin ta goge,ita kam sai fad'i take dama ita ce.

"Ke baki da wayo,da ni ce?
Kai ta kad'a
"Tuni na yarda.
Lissafi ta fara mata.
"In fa za'a miki aure ke y'ar gata ce.
"Kinga gadon ki ma ke dai za'a siya miki,a siya miki kayan kitchen, TV,kujeru,ga kayan lefe duk ke kad'ai, kije kiyi ta abinci kina share gidanki ki fesa turare..

Tsaki Ummahanin tayi jin yadda Farida ke kara bata haushi,sauran kam marasa wayo y'an uwanta sai fad'in
"Eh man,ai bata da wayo,koh ni ce yarda zanyi Allah.
Tashi tayi ta bar musu wajen ganin baza su gane ba.

Ita kam Farida har ta dulmaya tunanin gata a gidanta ta share ta shiga kitchen tana yiwa mijinta girki,har haskowa take yaran su sun dawo tana musu wasa.
Murmushi tayi tare y'ar murna,
"Allah zanyi abu in an min aure Aisha..
Tsaki Aishan tayi tare da bud'e sabon shafin littafin HAMIDA.

"Aure?
Da sauri ta ce
"Eh mana,koh bakya so?
Baki Aishan ta ta6e tare da fad'in
"Allah kiyaye,kuma zan fad'awa Umma na ce baki da aiki sai zancen aure.
Da sauri ta warce littafin hannun Aishan.
"Ni kuma sai na nuna mata har yanzu kina nan da karatun nan na littafin soyayya.

Tsere suka fara cikin hostel din tana ta bata bazata fad'a ba tana zille mata.
Hutu suka yi na Junior waec da suka zana.
Cike da murna aka dawo gida harda hawayen anyi missing Umma.
****

A gaban mirrorn dakinsu suke sai mangaje juna ake wajen yin kwalliya suna dariya.
Dankwali Aisha ta dakko tare da fara daurawa cikin kwarewa tana murmushi.
Ita kam riga da skit na english wear ta sanya masu ruwan zuma tana taje gashinta.

"Gaskiya kin kwafsa Farida..
Baki ta turo tana d'aura ribbon.
"Ke ni fa bazan iya rayuwar zani da d'aurin wahalar nan ba,sai dai in ki fasa zuwan dani.
Kwafa Aisha tayi tana yafa gyale.
"Amma wannan ai iskanci ne,ya ma za ai ga ankon aure ki wani sanya k'ananan kaya?

Ribbon din ta cire da sauri tare da hullarwa a gaban mirror
"Toh na fasa zuwa..
Kofa ta bud'e tare da fita waje,da sauri Aishan tabi bayanta tana kwala kiran Umma wacce tasan ita kad'ai zata sata dole.

"Umma..
"Oho dai,na ce ba zani ba,dama in kaje banda cin rai mey ka ke diba a gidan auren...
Fitowar Umma ne yasa tai shiru tare da turo baki.
Da sauri Aisha ta ce

"Yauwa Umma,ji wani wulakanci gun Farida dan Allah..
Magana take kamar zatai kuka tana kallon Faridan dake mata gwalo.
"Mey tayi? Ke fa Allah ya yi ki da mita Aisha...
Buga kafa Aishan ta fara cikin shagwa6a.

"Toh naji,mey tayi?
Nuno Faridan tayi
"Ki kalla fa Umma,tsakani da Allah wai bazata sa ankon Ummahani ba da wannan yan duniyar kayan zata..
Magana Umman zata yi Faridan itama ta hau shura kafa.

"Yi hak'uri muje zan d'aura miki,amma ke ce yau baki da gaskiya Farida,kuma koh ni bazan barki ki fita da wannan kayan ba.
"Wayyo Umma,na tsani zani,sai da na fad'a mata taje tasa aka mana,haba,mutum yaki waye wa,ana yayin skirt mu aganmu da zani?

"After all ma ni fa ban iya d'aurawa ba kin sani Umma..
Kamota Umman tayi da sigar lallashi.
"Toh naji ayi hak'uri muje ni zan d'aura miki nace,a bar...
Sallamar Abba ne yasa Umman tai shiru jin yana fad'in
"Bissmillah"..
Cikin sakewar fuska tare da nuno Farida da halamun ta rufe gashinta.

Hijab din Umman ta shige gaba daya jin har an shigo.
"Umman su ga bakin Abuja..
Baki Umman ta washe ita da Aisha ganin Abban Saifu dasu Saifu suna fad'in
"Sannun ku da zuwa.
Tuni kamshin turaren su ya bad'e parlourn.

Jin sannun taki ta kare yasa Farida dan yaye hijab din ta yadda fuskarta zata baiyana.
Ilahirin parlourn ido suka zuba mata ganinta cikin hijab din Umman tana kok'arin yayewa Umma na sake tura ta ciki amma saida ta fiddo fuskar.

Daya bayan daya take binsu da kallo har ta sauke kallonta kan uncle din Abuja,yake ta musu kamar yadda taga suna mata kan da sauri ta sauke tare da komawa ciki tana dan tura Umman halamun su tafi d'aki Umman na yake cikin jin iskancin Farida.

Kai Uncle din ya kad'a jin Umma na fad'in
"Haba Farida..
Murmushi ya yi tare shima da fad'in
"Farida"...
A hankali.

Da hijab ta fito ita da Aishan da Umma sai wani sinke kai suke.
Cike da ladabi suka gaishe shi daga zaune su ma su Saifu suna gaida Umma.
Kowa yaran kallon kowa yake yadda ya girma,sai dai ita Farida tafi mamakin girman su Saifu a shekara 4 kawai.

Hannu ta daga ma su Saifun halamun 'Hi' ganin suna gulmarsu suna murmushi shi da Amjad.
Ganin hakan su ma suka daga musu.
Sultana take kallo ganin yadda ta zuba musu ido tana murmushi hannu a baki.

Murmushi tai mata har hakoranta masu d'auke da wushirya suka baiyana.
 Hannu ta miko mata tare da fad'in
"Sultantee" a hankali.
Kabir dake kallonsu da mamakinshi yaga Sultanan ta mike zuwa gun su Faridan.

Tashi sukai tare da bin Umma kitchen, su dai su Saifu da suka ganeta sai kus-kus suke yi.
Bayan sun ajiye suka sake komawa kitchen, jimawa kad'an sai ga su sun fito Farida rike da hannun Umman suka nufi d'akinsu.

Tamkar y'an biyu haka suka fito komai iri d'aya gyale a hulle a kafad'a, da Umma ta gyara sai Faridan ta sake sauke wa tana zunguro baki,suna ji Umma tana fad'in
"Eh dai kuje tunda ta yarda tasa.

Mayarda Sultana sukai tare da yi ma su Saifu sallama.
"Abba sai mun dawo,
Cewar Aisha.
Kai ya kad'a yana zira hannu a aljihu tare da fad'in
"Ku tabbatar magriba bata muku a hanya ba.
Kai Aishan ta kad'a tare da kar6a hannu biyu.

Shima Abban su Saifu ciro wa ya yi tare da basu,
"Gashi ku kara toh.
Kai suka girgiza suna kallon Abba.
Abban ya kalla,sai ya ce
"A'a, ba ruwana.
Yana dariya,dan haka sai Aisha ta kar6a tare da fad'in sun gode.

Tashi sukai gwanin ban sha'awa kansu daya,sai dai kaurin jiki da daya tafi daya.
Da kallo suka bisu ganin suna dan dukan kafad'ar juna kamar yara cikin tsokana.
Kai Kabir ya girgiza tare da murmushi.

"Lalle kam abokina har yau su Farida basu girma ba.
Kai Abban ya kad'a shima yana binsu da kallo har suka fice
"Ai bana tunanin yaran nan zasu girma,barin ma dai Farida.
Murmushi ya yi yana tunanin abinda ya kawo shi.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*  ©Feenat Ja'afar. 2017.  ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).  25_Su Abdallah su Saifu su ka bi d'akin su wanda suka dawo a islamiya. Ajiyar zuciya ya sau tare da kora ruwa tukunna ya kallo Abba.  "Bana 6oye maka komai abokina,koh munyi nisa ina da hanyar samun shawara kamar kullum yau ma nazo ma da ita. Zama Abban su Farida ya gyara tare da bawa abokin nashi nutsuwar shi.  "Wato na raka shekara hud'u ba tare da nai sha'awar kara aure ba a rayuwata har yau din nan tun bayan rasuwar marigayiya. Kai ya kad'a mishi tare da fad'in "Hakane.  "Bazan ce maka ina jin dad'in zaman haka ba,amma dai nasan ina manage in har nai la'akari da yara na 4 duk a karkashina ba mai tallafa min. "Komai na ya zama koma baya, dan latti na koye shi,dan dole sai na tabbatar kowa ya shirya kamin na sama mana abincin breakfast nima nayi na sauke su school tukunna ni na nufi office.  "Ka sani da bani da sauran yadda ga mata,duk da akwai wata colleague na da take shige min amma ni anshani na warke gaskiya. "Toh yanzu kullum Sultana bata da aiki sai na ita ma tana son Momy kamar na y'an class nasu.  "Takan min kuka wataran, har nake tunanin koh zan yardewa Zubii ne bisa sharad'i.. Ajiyar zuciya ya yi. "Amma kasan mey? Kai Abban su Farida ya kad'a. "Ranar farko da su Saifu nai latti ban dakko su ba suka dau taxi har office a lokacin Zubii ta tsayarni.  "Zo ka ga yadda suke dallah mata harara wanda ba shiri nai mata sallama muka wuto gida. "Tun a mota Saifu ya fara fad'in shi ya tsaneta ba ma yason kara ganinta dani.  Dariya yai, "A lokacin nai dariya,domin yadda kasan ni ne d'an Saifu Baba, haka ina ji ina gani na fatattaki Zubii duk da gargadi da nake sha a office na yawan latti na wanda nake tsoron kar ya shafi aikina.  Shiru ya yi tare da sunkuyar da kai yana furzar da iskar bakinshi. Ajiyar zuciya Abba ya yi. "Matuka ina ganin kok'arin ka abokina,dole zaka samu matsala tunda ka hana kanka sukuni.  Kai ya dago da zummar tambaya sai ya kad'a mishi kai halamun eh mana. "Rayuwa ba'a taru an zama d'aya ba,dole bazaka dauwama a haka ba har karshen rayuwa, in su Saifu basu bukatar uwa nasan gaba Sultana zata nema,dan mace sai mace   "Ka cire shakku,ka ruki Allah ya baka mafi alkairi InshaAllah zaka ga dai-dai. Kai ya kad'a halamun ya gamsu. "Toh yanzu meye shawara? "Dan fa tuni na cire Zubii cikin tsarina dan yanzu abinda yarana suke so haka za'ayi.  Jim Abba yai yana murmushi, "Eh toh,akwai shawara da ni nake gani zata bulle, amma ina son ka samu Umma kaji mey zata ce game da shawarar in yaso sauran mey sauki ne..  Zama Abban Saifun ya gyara cikin zumudi. "In har zata bulle min da yarana ina maraba da ita... Kai Abba ya kad'a, kan dalla-dalla ya fara zayyano mishi shawarar yana sauraron shi har sai da ya kai aya.  Kai Kabir ya fara girgiza wa, "A dai sake wata,haba, ina ni ina... "A'a, ka tuntubi Umma na ce in tai na'am toh ka zurfafa tunani akai,dan wannan a gani na shine kawai hanya daya mafi sauki. Shiru yai yana kallon wani waje,ya sani da zai yi wuya abokinshi ya bashi shawarar da zata cuce shi,dan haka sai ya yarda a zai tuntubi Umman. *****  Shiru itama Umman tayi tana duban wani gu cikin tunani,hakan yasa ya gane batai na'am ba. Murmushi ta fara tare da dubenshi, "A gaskiya da na auna koh ni wannan shawarar tai min dari bisa dari Kabiru,sai dai fatan Allah yasa ta bulle, ya kuma sa wannan shi zaifi zama mafi alkairi ga yaran.  Ajiyar zuciya ya yi,har ga Allah shi dai wannan abu bai mishi ba koh kad'an. Sai dai da mamakinshi da ya shawarci Nafisa sai ta fara dariya tana kiran great. "Wallahi bros shawara ce wannan mai kyau ka duba,a hankali a gaba zaka gane alfanunta.  Sun fa sashi a tsakiya, Hafsa,Umman Uzairu,Nafisa da Umma kowa bak'inshi yazo d'aya da na abokinshi,dan haka sai yaki komawa tare da 'Istikhara' ta kwana uku,hud'u amma kullum yana jin abin a ranshi, dan haka sai ya koma ga abokinshi dan sanarshi yadda kowa ya ce da kuma Istikharan da ya yi.  Murmushi Abban ya yi na jin dad'i, kamin yai magana Kabir ya katse shi. "Toh amma abokina ni fa abin ne sai nake ganin kamar... Da sauri Abban su Farida ya tsayarshi, "In har kayi na'am, toh wannan ba wani sabon abu bane koh abin assha, believe me,a gaba zaka gode Allah ka kuma gode min,dan nasan kayana.  Shiru ya yi yana hasko abin,sai yaga duk wani bankwara kwai. Dan haka jiki a sanyaye ya fita,sai dai har cikin ranshi ya kasa nadamar hakan. ****  "Kai,ina..A gaskiya da sake,wai an bawa mai kaza kai. Kai ta girgiza tare da d'auke kai tai kicin-kicin da fuska. "Wannan ba shawara ba ce,a gaskiya batai ba,tab..  Kallonta yake yana mamaki,yau wai Sumayya ke musu dashi? "Sumayya? Ido ta rufe tare da girgiza kai. "Abban su Sumayya koh gaskiya? A gaskiya da duba a lamarin nan dan kaf a gidan nan Allah bani da wata y'a da ta isa aure har za'ai min sadakar ta balle Farida,tab ka dai sake lale..  "Ni fa ba musu na tambaya ba,dan tuni na riga na bashi Aisha,in kina ganin Faridan ita ce taki kuma ta gaban goshin ki,naji tayi k'ank'anta,amma Aisha nada kaurin jiki ai...  Tashi tayi tare da girgiza kai "Daga Aishan har Farida nawa ne,ban ware ba,na kuma ce basu isa aure ba wallahi, ka fa sake shawara. A tunzure ya mike,sai dai ganin ta fara hawaye yasa ya rage murya. "Nu nake iko da yarana ba wani ba,kar ki bari tun yanzu yarana su fara bijire min dan bazan...  "Wayyo Allah na shiga uku... Da sauri suka juya jin ihun kukan Aisha a bakin kofar hannu bisa kai. Tsawa Abba ya doka mata,dan haka tuni ta farke da kuka iyakar iyawar ta tana fad'in ita bata so.  A tunzure Abba yai yo kanta Farida da ta fito jin ihun Aishan ta kare, "Dan Allah Abba kai hak'uri.. Umma ya kalla wacce ke goge hawaye,da sauri ya nuno Aishan. "Baki da ikon hanani abinda nayi niya, wallahi na rantse kamar nayi na gama..  Waje ya fuce,da sauri Umman ta zauna akan gado da6ar hawaye na zubar mata,ganin haka da sauri Aisha ta cika Farida ta nufi gun Umma gwiwa biyu tana kuka.  "Wallahi ni Umma bana son aure yanzu,dan Allah ki taimakeni ni bana so karatuna zanyi Allah.. Ido Farida take rabawa, ganin Ummanta yau na kuka,tun tashinsu bata jin ta ta6a ganin sa6ani tsakanin iyayen nasu sai yau.  Hawaye ta hau goge wa Umman "Ni fa ban gane abin da ake nufi ba Umma? Auren ake wa kuka? Dama babu kyau? Cike da sauri ta ce "Rufe min baki,ku mey ku ka sani?... Shiru tayi tare da goge hawayenta ta kallo su.  "Farida.. Ido ta zuba mata. "Idan ki ka sake ki ka nuna kina son auren nan wallahi ni da ke ne a gidan nan,dan naga halamun ba hankali gareki ba har gwara Aishan tasan ciwan kanta. Shiru tayi kawai tare da zuba wa Umman ido tana tunanin wani abu. By   Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

26_Kukan Aisha ta daina jin Umman batai na'am ba ta tashi tare da zama a d'ayan gefen gadon tare da daura kanta kafad'un Umman tana jan zuciya.
Hannu Umman takai fuskar Aishan.
"Yi shirun ki Aisha.

Kasa shiru Faridan tayi tare da fad'in
"Amma Umma...
Da sauri Umman ta kallota
"Ki ce toh kawai Farida,in kuma kuka na ki ke so ganni bari nai tayi...
Da sauri ta hau girgiza kai tana goge ma Umman fuska duk da ba komai a kai itama kamar tai kukan.
"A'a nayi shiru yi hak'uri Umma.

Kanta itama ta daura a d'ayan gefen kafad'ar Umman,ita dai an mata daya,ga samu ga kuma kwanan yunwa,amma tasan tunda Umma bata so toh kila akwai wani abin da babu kyau acikin aure.

Abba da ya dawo yai tsaye yana kallon su tare da girgiza yana murmushi ganin dramar Umman tasu,jin sautin murmushin nashi yasa suka juya,Umma na ganin shine tai kicin-kicin kuma.

A gefen su shima ya zauna yana kallonsu barin Umman da taki yarda su had'a ido.
"Bari naga Umman taku in yaso naji meye matsalar.
Kai suka kad'a tare da tashi ganin Abban ya sakko harda murmushi.

Fita sukai sai ya kulle kofar tare da zama gefen Umman sai ta kara matsawa,bai zuciya ba ya sake matsawa yana murmushi.
"Haba Summy..
Kai ta kawar jin ya kira sunan dake sata dariya.

"Toh naji amini afuwa a fad'a min meye matsalar.
Kamar wata su Farida haka take turo mishi baki kadan-kadan irin na shagwababbu.
"Ina jin Summy..
Murmushi kuwa tayi kamar yadda yai dan shi.

"Ni dubawa nake so kayi yaran nan ba abinda suka sani game da aure ne barin ma Farida kar taji labari.
"Koh fa 15 ba wacce acikin su ta kai ka duba wannan lamarin.

Kabli da Ba'adi ta fara kawo mishi yai shiru tare da zuba mata ido yana murmushi sai da ta kai aya ta dire tukunna ta hau kunkuni.
"Kuma ma..kuma ma fa...
Cike da murmushi ya ce
"Kuma mey?
Shiru tayi tana murza yatsunta.
"Shekarunki nawa aka miki aure ne ni na ma manta dan tuna min..

Inda-inda ta fara mishi na kan ta dakarkare ta ce
''Sha takwas.
"Saboda Allah fa Summy?
Kai ta kawar dan sarai tasan ta zuluka.
Hannunta ya kamo tare da rike su kam ya had'a suka zama (15).
"Shekarun ki goma sha biyar aka kawo min ke gidan nan da wasu watannin,ki ka haihu a shekara daya da rabi.

Shiru tayi dan tasan haka zancen yake,dan haka yaci gaba.
"Nana Aisha(R.A) tana y'ar shekara (6) aka aura mata ma'aiki (S.A.W),sannan ta tare a shekarunta (9) a gidanshi...
Magana zatai ya girgiza mata kai.

"Ina kai ki tukunna.
Shiru tayi tare da sauraron shi.
"Har yau bana jin a kauye an daina wannan al'adar ta aurar da yara da sun fara sanin kansu daga shekara 10,11,12,har zuwa sama.

"Naji zaki ce min ne y'an da dana yanzu ba d'aya bane,amma kiyi duba a birni nan ana aurar da yara wanda basu kai shekara 15 ba Allah nasha gani Sumayya.
"Ki min alfarma kar ki tsorata yaran nan,aure bai kashe ki ba,ba rage ki da komai ba.

"Kinfi su sanin waye Kabir, ya rayuwarshi ta kasance har zuwa yau din nan..
''Zan so a abinda na yarda dashi jinina ya nuna wa Kabir da ban-banci,zanso ki barni nai amfani da damar ganin yaran shi dasu Aisha sun saba in yaso in sunje su dauke ta kamar kawa ta inda ba matsala.

"Na yarda dake Sumayya,hakan yasa na yarda da yarana kaf ciki babu mai iya kwata halin su Tabawa koh Fatima.
"InshaAllah bazanji kunya ba,na yarda dasu zasu iya.

Ajiyar zuciya tayi,dan haka sai ya cigaba da kwarin gwiwar shi.
"Ki taimakeni ki tayani wannan jihadin, ina so su gane akwai banbanci daga yaran har Kabir,dan Allah ki min alkawarin wannan.

Kai ta girgiza,
"Ka bani zuwa gobe zan duba lamarin.
Murmushi ya yi tare da kad'a mata kai.
"Koh nan da sati ne na baki.
Kai ya dungure mata.
"Ashe a gunki yaran nan suka koyi daru ban sani ba.
Kai ta sunkuyar tana dariyar kunya.
****
Washegari ma duk sukuku suka tashi.
Duk sunyi tsumu akan gado kowacce na tunani.
Chan dai Farida ta ce
"A gaskiya kin luza wallahi Aisha.
Harara tai mata tare da gyara kwanciya.
"Ni nasan mey ranar chan na karanto a littafi ai Farida,ina da wayona Allah bazan yarda ai min wannan abin ba da kankanta ta.

"Ba ma wannan ba,haka kawai sai a min aure ba soyayya ba komai ban san miji sai ka ce auren da...
Katseta Farida tayi a dan tsorace jin bayanin Aisha.
"Meye toh a auren dan Allah fad'a min abin tsoro ne?

"Zaki tsara ke ba iyayi ba?
Kwafa tayi
"Allah yasa Abba yai miki toh.
Kai ta girgiza da sauri.
"A'a wallahi nima ba amin ba tunda abin tsoro ne, ji muguwa.
Duka ta kaiwa Aishan tana turo baki

"Uhmmm
Gyaran murya Umma tayi ganin kofar su a bud'e tare da kwankwasawa.
Tashi sukai ganin Umman tare da yin shiru.
Zama tayi tare da musu murmushi.
"Yau ba wanda naga ya fito tun bayan gama breakfast dinku lafiya duk gidan shiru?

Kai kasa Aisha tayi,yayin da Farida ta girgiza kai
"Lafiya Umma.
Kai ta kad'a tare da gyara zama.
"Tambaya nake son muku kowa ta bani tata amsar.
Kai suka kad'a tare da bata nutsuwarsu.

"Aisha..
Cikin sanyi ta amsa.
"Ina so ki fad'a min mey ki ka fuskanta a game da aure?
Kai ta duk'ar da sauri gabanta na fad'uwa,hakan ya nuna wa Umma ta san takan abin ita.
"Ina jinki.
Ido suka sa mata ita da Farida,sai ta hau in ina tana susar keya.

"Ni fa..Umm..nima ban sani ba.
Murmushi Umman tayi,da sauri Farida ta zungureta.
"Allah Umma karya take ta sani..
Rai Aisha ta had'a
"A ina na sani.
K'yaleta tayi tare da kallon Umman.
"Ni na sani na fad'a miki?

Dasauri Umman ta kad'a mata kai halamun ta fad'a.
Zama ta gyara ta fara lissafi,
"A islamiya malamin mu ya ce 'aure sunnar Annabi ce,ya ce duk wanda yai aure ya haihu da yawa ranar gobe kiyama annabi zaiyi alfahari da zuri'arshi dan ta kara yawan al'ummar shi.

Kai Umma ta kad'a tana murmushi dan jin anzo wurin.
"Ina ji.
Da sauri ta cigaba
"Yauwa,daga nan sai taru a daura aure da mijin ai party koh walima daga nan sai a kai amarya gidanta.

Kai Umma ta sake jijjiga mata halamun tana ji,ita kwa tsakaninta da Allah ta dage tare da ci gaba.
"Yauwa,sai tai ta aiki tana biyayya inji malamin mu duk macen da bata biyayya a wuta za'a sata hakane koh Umma?

Cike da kaguwa Umman ta kad'a kai sai ta cigaba.
"Daga nan sai ta haihu,tai ta haihuwa har ta daina in yaran sun girma..
Tsayarta Umman tayi,
"Toh ya zata samu cikin tukunna? I mean a in btw auren da haihuwar
Kai Aisha tai kasa dashi halamun wai kunyar Umma take ji.

Ita kam ido ta zubawa wani waje halamun tunani,chan da sauri ta ce
"Na tuna Umma..
"Bayan anyi auren tana shara,dafa abinci,da sauran su.
"Toh daga nan fa?
Cewar Umma,
Kallon Umman take da halamun tambaya.

"A'a sai ta samu ciki man Umma ta haihu ai na fad'a,
Kai Umma ta kad'a halamun gamsuwa.
"Na ji,shine na ce taya zata samu cikin?
Cikin cire shakku ta ce
"Idan mijinta yana bata abinci man tana koshi kullum sai cikin yai katoto kamar haka..hakan nan
Nuna musu take halamun girman cikin da nata cikin.

Hannu duk biyu Umma tasa tare da dafe goshinta cikin takaici tana kiran
"Ya Ilahiii...

"Mtsww..
Tsaki Aisha tayi tare da harararta.
Gaba d'aya kallonsu tayi ganin Umma kamar ta sau kuka tare da dagawa Aisha kafad'unta halamar tambayar mey tayi?
Ita iyakar gaskiya ta fad'i ba ragi, dan haka sai ta ce

"Umma mey nayi? Koh ba haka bane?
Dagowa Umman tayi tare da daga mata kai halamun haka ne.
Kallon Aisha tayi cikin farin cikin ta fad'i dai-dai.
"Dalla ba gashi ba na fad'i dai dai,da har da min tsaki dan ke kin kasa.
Baki ta murgud'a tana kallon Umma da ke kok'arin tashi jiki a sanyaye ta fice.

Lalle zata kwari yaran nan in har tai la'akari da rashin yardar Aisha wacce tasan komai, gefe d'aya ga Farida mai son auren amma ba abinda ta sani sai iyayi.
Amma mamakinta da abin haushi ma bai wuce na malamin islamiya ba.

A ganinta wannan bayanin su yafi chanchanta su sanar da kamar dai Farida ma'anar aure ace ta sani ba wai manufofi ba.
Zama tayi tare da sakar ajiyar zuciya.

Tabbas Aisha tasan komai,dan tasha kamata da karatun littafi,tasan koh a chan zata iya fuskantar wani abu fakacin Farida uwar y'an shirme ita dai batta a shakiyanci da iyayi.

Dan haka dole wacce tasan takan aure ita za aiwa.
Kai ta jijjiga cike da zancen zuci.
"Aisha yafi chan-chanta kam,tunda Abban nasu ya dage.
Da wannan ta rufe in Abban yazo su yanke shawara kawai a bawa Uncle Kabir Aisha.
By

Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

28_Gidan su Uzairu suka je jin yana kukan rabashi da Rukayya da sukai har tai aure ta hayayyafa a wani waje.
A hankali irin ukubar da Kabir yaci yake sauraro har izuwa randa Allah yafi karfin su Tabawa ya tsaya da kafafunshi.

"Lalle ka ga rayuwa Kabir,ka ga ukuba,ka ga jarabta iri-iri a duniyar nan.
"Na gode Allah da ya rayaka har ka zama wani daban cikin yarana kamar yadda naso tun farko.
"Duk hukuncin da zaka d'auka akan su Tabawa bazai gamsar dani ba mud'in ban gansu a kurkuku ba Kabiru.

Kai ya girgiza mishi.
"Kayi hak'uri Abba,wannan ba komai bane in har kaji dayan laifin,na sani ga duk DAN ADAM(sis Ruffy) bai isa tsallake KADDARA shi ba,a yanzu bana ganin su Tabawa a gabana sai ku kad'ai.
"Dole na gode Allah da ya nufa duk wani sihirinsu ya warware komai.

Kai ya kad'a,
"Na sani,amma matuka su Tabawa sun cuce ni ba kad'an ba.
"Allah ka bi ma kowa hakkin shi kawai.
Kai suka kad'a tare da fad'in
"Amin.
"Bana bukatar na koma kusa dasu sam,a barni a nan kawai.

Murmushi Kabir ya yi,yau farin cikin har yaso yai mishi yawa.
Dan haka yana fita ya nufi gun masu gini dan gobe su je su fara foundation na ginin.
A yau d'aya farin cikin shi ya dawo sabo fil.
Dan haka daga nan gida suka dawo gun Umma.

"Umma da gaske.
Kam ya rungume Umman yana mata hawayen dad'i.
Dagoshi tayi itama idonta fal hawaye.
"Alhamdulillah, mu gode Allahn da baya bacci Kabir,na gode Allah da yasa yau komai ya kare.
Kai ya jijjiga mata yana washe baki.

"Insha-Allah a gobe nake so a fara zuba katangar da zata raba gidan Abba da nasu Tabawa a fara gini.
Kai ta girgiza mishi.
"Ba za ai haka ba Kabir.
Murmushi ya yi.
"Wannan ne babban adalcin da zan iya musu Umma,dan ba dan mu ba da tuni gidan ma sun bari.
****

Baki har kunne da daddare ya isa gidan abokinshi,ya ma kasa barin gari ya waye.
"Alhamdulillah toh,sosai nai maka murna,ubangiji yasa karshen wahalar kenan abokina.
Cike da farin ciki ya ce
"Amin abokina.
Sun jima tare tukunna suka dawo batun aure.

Jim ya yi yana murmushi kai a kasa.
"Farida"...
Kai Abba ya kad'a.
"Eh Insha-Allah, Farida ce matar.
Kai ya jijjiga.
"Amma ta yarda koh? Ta yarda da auren tsoho?
Murmushi Abba ya yi tare da kad'a kai.
"Farida bata da matsala,asalima murna take bisa za'a mata aure,abu daya na sani sai kayi hak'uri dan Farida yarinya ce koh auren bata sani ba.

"Abu d'aya nake fata shine ta rayu a gidan ka ta yadda zata gama wayonta a cikin iyalinka wanda tanan komai zai fara.
Kai Kabir ya kad'a.
"A gaskiya samun aboki irin ka tun yarinta zai matukar wuya.
"Duk rintsi,duk tsanani,duk dad'i kana tare dani.
"Na gode da wannan kyauta,na gode da wannan karamci.

Kai ya kad'a.
"Kar kaji komai,a yanzu dai mun zama daya,abu daya na sani yanzu na girma maka,dan siriki nake remember.
Hannu ya bashi tare da tafawa suna dariya.
"Lalle aboki ka ban aiki,yanzu ta yadda zan fara da su Saifu nake tunani.
Kai ya kad'a,
''Insha-Allah komai zai zo da sauki.

Da sauri Aisha dake la6e ta koma ta corridor ta shige d'akin su.
A gaban madubi ta samu Farida sai tazar kai take ta kama tashar gata cikin gidanta.
Duka ta d'ad'a mata a hankali,dan haka a furgice ta kallota tana sosa gun.

"Lalle wallahi an gama dake na rantse Fadila.
Ido ta zaro.
"Mey aka min?
Zama Aishan tayi tana kad'a kai.
"Tab,wallahi an cuce ki,kin san wa aka baki?
Kai ta girgiza tana kallonta.
Dariya ta fashe dashi tare da fara mata wakar
  _'Yarinya an cuce ki an had'a ki da tsoho,tsoho sa'an Abban ki shi zaki aura_'.

Tsaki tayi tare da tashi,
"Toh meye abin dariya? In zaki fad'a min ki fad'a min ni waye tsohon?
Dariya ta sassauta tare da gyara zama.
"Wallahi kin tashi a aiki,kin san wa Abba ya baki da ki ka yarda?
Kai ta girgiza har ta fara tsorata.
"Waye dan Allah Aisha?.

"Uncle din Abuja fa..
Shiru tayi tare da kafe Aishan da ido,kan ta nufa har ta kwalara kara mai karfi tare da doka tsalle ta rungume Aishan cikin murna.
"Ki ce Abuja za'a kaini? Wayyo dad'i...

Baki sake Aisha take kallonta cike da mamaki.
"Anya Farida kina da hankali kuwa? Koh ba kiji abinda na ce ba?
Kai ta girgiza mata cikin murna.
"Naji sarai,toh meye aciki?
Galala take kallonta,da gaskiyar Umma,lalle Farida d'anya ce sharaf.

"Uncle dan gayu ne,ga yaranshi y'an gayu masu kyau,ga garin ma na y'an gayu,ranar naji Abba na mishi murnar ya koma sabon gida irin na y'an gayu,toh meye aciki? Allah ba'a cuceni ba...

"Lafiya kuwa?
Abba ne a bakin kofa jin ihun Faridan.
Nutsuwa tayi tare da dakko gyale ta yafa tare da bud'e mishi tana sunke kai kasa.
"Lafiya Abba,kawai ban san nayi bane..
Harara Umma tayi tare juyawa d'akinta tana fad'in
"Ta tsorata ni wallahi, ina band'aki na fito.

"Kin girma fa Farida,dan aure za'a miki,dan Allah ki nutsu.
Kai ta sunkuyar tana fad'in
"Toh Abba na daina.
Kai ya kad'a,
"Yauwa ki kintso kizo ga Uncle din ku na Abuja ku gaisa.

Kasa ta kara yi da kai wai ita kunya,yana bada baya tai saurin komawa ciki.
"Uncle ne ashe Aisha dazun yazo,Abba ya ce muje mu gaisa.
Kallon baki da wayo Aishan take mata tana dariyar keta.
Tsam tayi,tare da sa hannu biyu ta rufe fuskarta halamun kunya.
"Aisha kunya fa na fara ji,ya zamuyi?

Baki ta ta6e,
"Baki ma fara ba,sai kin shiga daga ciki,kizo muje dan bacci nake ji.
Kai ta kad'a harda gyara gyale a mudubi, hannunta Aisha ta janyo kamin ta bar gun suka fuce.
Shi kad'ai ne a parlourn ba Abba,dan haka kai a sunke suka tsuguna tare da gaishe shi a tare.

Murmushi yai yana duben su,abin ma sai yaso ya bashi dariya ganin yadda suke wani sunke kai.
A hankali ta dago da zummar satar kallonshi sai karaf suka had'a ido.
Dan haka da sauri tai kasa da kai tare da sake janyo gyale ya rufe mata fuska tana kunshe murmushi.

Kallonsu yake,har ya ma rasa mey zai ce dasu dan rashin abin fad'i.
Kai ya kad'a, tare da fad'in
"Aji nawa yanzu ku ke Farida?
Gefen gyalenta ta rike tare da zungurar Aisha yana kallonsu,da sauri Aishan ta ce
"Jss3 muke.
Kai ya kad'a tare da fad'in
"Good".

Shiru sukai,sai dai yana kallon yadda suke dan kus-kus ta kasa duk da baya jin komai.
Murmushi ya yi,ganin kamar sun takura yasa ya ce
"Toh ni zan tafi,kuyi ma Abban ku magana.
A tare suka mike suna fad'in toh.

Yana kula da yadda suke zungurar kafad'un juna halamun musu suke,yana kallo Faridan ta dan juyo tana magana wa Aisha,ganin yana kallonsu sai ta kara sakar gyale da sauri suka kule corridor.

Kai ya kad'a yana yar dariya mai sauti.
Lalle ya sani da aiki a gabanshi ba kad'an ba.
Dan wannan wani sabon raino zaiyi ba wai zaman aure ba in har yai la'akari da shekarunta dana Saifu ba wani nisa su ka bashi ba.
Sannan har yau rainon Saifu yake da k'annenshi ta fagen yarinta.

Murmushi ya yi,amma koh ba komai yarinyar tana burgishi da wannan dan rawar kan nata,yasan za ai ta buga drama a gidanshi da Farida.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

29_Tun daga wannan ranar ya dage da tsantsara ginin Abbanshi da yake so a gama kamin hutun su Saifu ya kare.
Da shawarar Abba yake zuwa wai fahimtar juna gun Farida,sai dai fa kullum daurewa yake amma gaba daya gidan ma wani iri yake mishi,barin ganin Umman su Faridan sai yaga kamar girma ya fad'i.

Yau ma kamar koyaushe daga shi sai ita a parlour kanta kasa kamar kullum tana murmushi.
Allah yaga tana son kwalliyar Uncle da turarenshi,har mamaki take in Aisha na tsokanarta akan zata auri Uncle tsoho.

Kai ta dago dan sake karyata Aisha,da sauri ya fara danna waya ya bar kallonta.
Sarai yasan da kallonshi take dan haka sai yaki dagowa.
A ranta fad'i take
"Aisha bata san kyau da tsufa ba,in za'a batta zata ce Abban su yafi Uncle tsufa Allah,dan Uncle dan gayu ne barin yanzu da ya sanya suite tamkar balarabe ya zamar mata.

Ga dan sagen nan da wani hasken kyau na fulani da jin dad'i da ya k'awata fuskar.
Murmushi tayi tare da dan duk'ar da kai tana murmushi, kallota ya yi a dan sace ta cikin farin glass nashi,komai irin na Farida na burgeshi,barin wannan y'ar kunyar da yanzu ta koyo takan bashi dariya in ya ke6e.

Murmushi ya yi tare da kad'a kai,tare da fadin "yarinta dad'i
A zuciyarshi.
Kai ta sake dagowa da zummar sake kare mishi kallo sai karaf suka had'a ido,ganin yadda ya tsareta da idanu yasa da sauri ta janyo gyalenta tana rintse ido tana yarfe hannu halamun ya kama ta.

Kai ya girgiza yana murmushi, gaba daya wata dabi'ar ta Farida irin ta yarintar Halima ce musamman wannan yar kunyar shakiy'ancin.
Gyran murya ya yi tare da gyara zama.
"In munyi tafi Abuja dake zaki cigaba da karatun ki a boarding koh day ki ke so?

Kai ta dago tare da kallon wani waje halamun tunani yana kallota ta gefen gyalen.
A dan sace ta kalloshi tare da fad'in
"Kowanne ina so..
Kai ya kad'a,wani sa'in ba laifi ashe Faridan.
Ita kam tunaninta dama ta ce 'Day', dan in ta tafi boarding wa zai na share mata gida da bawa su Sultana abinci?

Kai ta girgiza halamun babu.
"Bani ruwa in ba matsala...
Kalloshi tayi tare da kallon ruwan,a gabanshi yake tasan hannu kawai zai mika ya dakko,sai dai ta tashi a hankali tare da tsiyaya mishi kai duk'e ta bashi.
Har ya kar6a ta kasa tashi jin ya ce ta tsaya.

A durkushen take kallon yadda yake dan zukar ruwan yana latsa waya,tuni har ta fara mamakin wannan sarauta ta uncle,ruwan ma sai an mishi gayu?
Tana nan tsugune har ya shanye tare da bata kofin ya mike.
"Hope kin fara shiri koh?
Kai ta duk'ar tana girgiza kai.

"Toh in kina da bukatar wani abu ki min magana dan ina son mu koma tare ne dan chuku-chukun makarantar ki.
Kai ta kad'a mishi idonta a nashi,dan haka sai ya d'au mukullinshi tare da daga mata hannu halamun bye.

Murmushi ta k'akalo tare da dan daga mishi nata yatsun tana yake,
"Ki ce ma Umman ku na tafi toh,ga nan na bar miki wani abu koh zaki nema dan abin yi.
Kai ta daga,tare da fad'in
"A gaida su Sultana..Na gode.
Cikin sanyin murya.
Murmushi ya yi tare da kad'a kai ya juya.

Jiki a sanyaye ta koma ta rasa dalili.
D'akin Umma ta kwankwasa jin an ce ta shigo ta shige, a bak'in gado ta sameta tana shirya wasu kaya wanda tasan duk nata ne na biki.
Kud'in ta ajiye mata tana dan ta6e baki halamun kuka,dan haka sai Umman ta bar abinda take ta zuba mata ido.

Tun ranar chan Umman ke fushi da ita,bata so tai aure Umma bata so ba,dan haka kasa ta zube tare da daura kanta ta sau mata kukan shagwa6a.
Aikinta ta cigaba da yi ta manna mata,sai dai jin tana
"Toh ni har na daina murna,ki ce wa Abba kawai a fasa auren.

Murmushi tayi,tare da dagota ba koh hawaye sai matse ido take.
"Za kiyi kukan gaske yarinya,ba rawar kai ba?
Kwafa tai mata tare da fad'in
"Bana kin aurenki, tausayinki kawai nake ji Farida..

Kafe Umman tayi da ido.
"Tasayin mey toh Umma? Koh kema dan an bani tsoho ne ki ke tausaya min irin na Aisha?
Kallonta kawai take,sai tai murmushi tare da kad'a kai.
"Baza ki gane ba,ke dai Allah sa ya tausaya miki...
Ido ta zaro cikin tsoro tare da fad'in
"Wa din Umma wai Umma?

Kai Umman ta girgiza.
"Ba kowa su6utar baki ne kawai.
Ajiyar zuciya tayi tana taya Umma aikin, kad'an-kad'an take duben y'ar tata tana murmushi, wani sa'in har mamakin rashin wayo irin na Fadila take,batta a bankaura da rawar kai amma sam ta rasa rashin wayo irin nata na yaran yau in tai la'akari da yadda duniya ta dawo.

Dole zata daure ta cigaba da zamawa su Farida k'awa har sai ta koya mata dawar garin,yanzu dai tasan bazata fahimci komai ba.
Murmushi tayi tare da kallonta jin yadda take tsara shirmenta na auren.
****

Wata guda ya debe ana aikin bangaren Abba tare da tatsa katanga a tsakanin gidan da inda su Tabawa suke dan cike umarnin Abban.

Ta bangare biyu kowa ya kid'ime da shirye-shiryen auren uncle da Farida.
A yadda suka tsara ba wani taro sai d'aurin aure da tafiya da amarya kawai.

A cewar Uncle shi ba abinda yake da bukata dan komai ya shirya shi cikin sabon gidanshi tamkar da mace a ciki.
Abu d'aya ya ce zasu iya kara mata kayan kitchen in tana da murad'i.

Kallon Farida Umman take,ganin yadda ta kama tasha,tun jiya tana fuskantar ta yadda duk tai la'asar,ga dai kayan lefe amma koh murna bata yi,fatan ba Aisha ba ce ta sanarta komai.

Takan rasa ta ina ma zata fara?
Koh dan irin gyaran nan da iyaye ke wa yaransu Umma ta kasa dan tausayin Farida..

Ido ta sa masu ganin sun fashe da kuka ita da Aisha suna kallonta.
Da rarrafe Farida ta zo gare ta tare da kwanciya bisa cinyar Umman.
"Ni fa sai yanzu na gane bani da wayo,Allah Umma bana son na barku.

Kai ta girgiza mata,
"Ai zaki na zuwa kar ki damu,kowa da haka ya saba.
Kuka take ita dai in ta tuna kwana kad'an za'a maidata Abuja da zama.
Dakyar ta rarrashe su ita da Aishan sukai shiru.
*****

Kowacce tai tagumi tana tunanin rabuwa da y'ar uwarta gobe iyanzu.
Duk baki suna waje in banda su,dan haka tashi Aisha tayi tare da rufo kofar da mukulli ta dawo kusa da Farida.

"Kin san mey Farida?
Kai ta kad'a fuska a maraice.
"Kawo kunnenki kiji wani abu da dabarar yi.
Kunne ta bata,tiryan-tiryan ta fara zaiyano mata abubuwa tana zaro ido gabanta na fad'uwa.

Da sauri ta kallo Aishan rai had'e.
"Ke uncle d'in an fad'a miki d'an iska ne wai?
Harara Faridan ta sau mata,
"Toh shikenan in baki yarda ba wallahi haka na karanta.
Jim tayi,da sauri ta fara kad'a kai.
"Gaskiya ban yarda ba,wannan ai iskanci ne ma.

"Mtsww..
Tsaki Aisha tayi tare da harararta.
"Wa ya fad'a miki iskancin ne? Toh wallahi zakiyi bayani.
"Ba aure ba?
Kwafa tayi tare da kad'a kai
"Zaki ce Aisha ta fad'a miki...
Ido ta fara warewa yana raina fata,
"Dama haka ne auren?
Baki Aisha ta ta6e
"In banda Umma da ta hanani ai da tuni na fad'a miki.

"Kai,ina,uncle bazai haka ba Allah Aisha, tab...da kwa nai mishi ihu wallahi..
"Mtsww..
Wani tsakin Aisha ta kara,
"In zaki nutsu ki ma nutsu wallahi.
Gaba daya ta tsorata ta,dan haka tuni ta fara neman hanyar bullewa.

Murmushi take mata jin abinda take karanta mata wanda a ganin su shi zai bullar musu.
Hannu ta bata tare da tafawa suna dariyar keta.
"Ba mai miki wayo in kinyi haka Allah.

Kus-kus dinsu suke su kad'ai ba mai jin kansu, duk da a zahiri Faridan na jin dan fad'uwar gaba in ta tuna da bayanin Aisha.
Da wannan suka kwanta zuwa gobe d'aurin aure.
 
***
Washe gari
 *RANAR D'AURIN AUREN UNCLE da FARIDA*
Kusan wannan auren ya kusa da farkon shi dan ya tara jama'a.
Y'an aikinsu na Abuja da Kaduna kusan duk sun halarta harda Aunty Rabi.

Yai farin cikin auren,in yai la'akari da yadda karan nan Abbanshi ya sanya albarka ya kuma tako har kofar gidan su Farida.
Dan haka baki har kusan kunne yake washe shi,haka ya dinga bi yana nuna wa y'an aikinshi Abbanshi suna gaisawa.

Matsala daya ya fara fuskanta ita ce ta tuburewar su Saifu tun jin zai yi aure a yau,yai lallashin abanza amma Saifu da Nass sai kuka suke,yasan zasu ware in har suka ga wace ce amaryar,dan haka sai ya kyalesu ba tare da ya sanar su ba.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

27_Murmushi Abban ya yi jin shawarar Umman,kai ya kad'a.
"Banki taki ba Umman su,amma ni ina da tawa shawarar in har kin aminta.
Kai ta gyad'a
"Ki kira min yaran nan tukunna.
Ba musu ta tashi tare da kwankwasa d'akin su Farida,ciki ta shige tare da zama.

Kallonsu take d'aya bayan d'aya kamar yadda su ka sa mata ido.
"Aure ba abin ki bane,dan baida wani aibu acikin shi Aisha..
Kallo Umman Aishan tayi, tuni har idonta ya fara kawo ruwa.
"In karatu ne ana iya yi a gidan miji, sannan ga dimbin lada dake cikin shi ga na biyayya ga iyaye.

"Ki ma Allah Aisha kar ki bani kunya a gaban Abban ku komai ya ce kiyi na'am...
Bata jira mey zata ce ba ta ce su biyo ta.
Kai sunkuye tana hawaye Abban ya kallo ta,
"Aisha wannan ya nuna min bazaki iya sharen hawayena ba tun yanzun da nake so ki share koh?

Kai ta girgiza tare da fad'in
"A'a.
"Toh meye matsalar?
Umma ta kalla hawaye na zubar mata.
"Ni zaki kalla kar ki kiji komai ki fad'i matsalarki.
Kai ta sunkuyar tare da fad'in
"Kai hak'uri Abba,wallahi bana son aure yanzu Farida ke so,dan Allah Abba kar amini dole.

Kuka ta fashe dashi sosai,dan haka sai Abban yai tsam.
"A'a, ni fa ba muyi da kai zaka tsaya tambayar ra'ayi ba Abban su,kowacce ka isa da ita,itama Aishan fad'a kawai take.
Kai Abban ya girgiza.
"A'a Sumayya, a bi a hankali.
Farida ya kallo da take harar Aisha,ita tun a d'aki jin Umma ta ce ba komai a aure take Allah-Allah Aisha ta amince.

"Farida..
Abban ta kallo tare da amsawa.
"Kin shirya amsar tayina na aure yanzu?..
Kai ta kad'a da sauri duk da tana kallon yadda Umma ke girgiza mata kai halamun ta ce a'a.
"Umma yanzu fa ki ka ce 'Aure ba abin ki bane,dan baida wani aibu acikin' koh?
Banza Umman ta mata,dan haka sai ta dawo kan Abba dake mata murmushin jin dad'i.

"Ni Abba ka min Allah ina so in dai za'a bani kayan d'aki da komai zan zauna,meye aciki? Ina so Allah..
Kai ya kad'a yana kallon Umma da sai harara take mako wa Farida,
"Toh Alhamdulillah, na gode Farida,zan miki komai kar kiji komai har kayan kitchen.

Aisha ta riko tare da fad'in
"Wayyo dad'i"
Cikin murna.
"Na gode Abba,wayyo Allah Aisha.
Hawaye Aishan ta goge tana kallon Umma da kamar ta rufesu da duka gaba daya dan haushi,sai ta marairaice mata.
"Abba yaushe za'a daura toh?

Gaba d'aya ido suka sa mata har Umman,ita kam koh ajikinta Abba ta zubawa ido jiran amsa,basu nufa ba suka ji Abba ya kece da dariyar jin tambayar Farida,dan haka da sauri Umma ta ce
"Tashi ki bar wajen nan marar hankali kawai..
Tashi sukai har da dan tsallen murnar Farida,ita kam Aisha dariyar mugunta ta fara mata.

"Lalle muguwar d'anya ce ke wallahi Farida.
A gado suka zauna tana lissafin abin yi.
"Naji dai wallahi nafi ki wayo yarinya.
Dariya Aisha tayi.
"Wai,wallahi har na hasko ki a gidan miji, zai debi abu.
Zama ta gyara.
"Bama wannan ba,tukunna kinsan wa za'a aura miki da ki ka amince?

Baki ta ta6e
"Oho,ni dai aure kawai.
Kai Aishan ta kad'a.
"Za kiyi bayani, sai kinje zaki gane abinda nake gudu wallahi..
"Za muyi anko kuwa Aisha?
Harara ta sau mata.
"Au baki ma jin abinda nake fad'a kenan?
Kallonta tayi,
"Mey ki ka ce? Banji ba ina lissafi.
***

"Ka kara lale Abban su,ka duba abinda Farida take shi kad'ai ya isa nuna ma ba abinda ta sani sai hauka wallahi..
Karasa wa tayi tana goge hawaye.
Murmushi yake yana duben Umman.
"Bana jin munyi haka dake Sumayya,dan haka kar ki maida min hannun agogo baya.

Tayi takaici tai komai amma agun Abba aure kamar anyi an gama.
Dan haka sai ta sa musu ido har Faridan taga iya gudun rawarsu.
****

Kwance yake a rigingine bisa gado ya zubawa fankar dake kad'awa a sama ido.
Tabbas tarin arziki da yake samu a yanzu baiyi ba mud'in ya kyale mahaifinshi a gidan kasa na shekara da shekaru.

Juyi ya yi jin hawaye ya taru bisa idonshi.
Sai yaushe ne zai ga soyayya mahaifi a gareshi? Sai yaushe?
Har yau d'in anan ba abinda ya sauya zani daga abinda yake fuskanta,ya sani da a iya kuriciyarshi bai ta6a sa6a ma mahaifinshi ba,ina ma ya ra6e shi bare ya sa6a?

Kai ya girgiza, amma har yau d'innan baya yarda ya kalleshi balle ya mishi maganar arziki.
Tamkar an tsikareshi sai ya mike
 tare da goge hawayen ya nufi band'aki tare da gyara fuskarshi ya rufo d'akin hotel d'in.

Tun ba yau ba ya sai kangon makotan Abbanshi,a kullum yakan kwata rushe gidan yai na zamani amma Abban bai nuna ya aminta koh a'a.

"Bissmillah..
Gidan ya shago da masu ruguje gini,ba kowa a gidan sai halamun kofar su lami a rufe.
"Daga nan d'akin nake so a fara zuwa katangar kangon nan tunda a had'e suke.
Kai suka kad'a mishi tare da fita dan bawa wanda yake cikin motar umarni ya fara aiki.

Kan kace meye tuni d'akin dake a matsayin na Umma na da yai flat tamkar ba ata6a yi ba.
Kamin yamma hatta kasar motar ta kwashe ta matsar chan gefen kangon.

Kallon gidan yake,ba karamin fili yai ba da aka had'e da makotan.
Juya wa zaiyi sai dai yaja ya tsaya ganin kwalba an tono ta har ta dan fashe, dan haka a hankali yasa leda tare da karasa tono ta,sosai ya kad'u ganin kasanta da wata laya nannad'e cikin fata.
Jujjuya ta ya fara,in banda wari ba abinda take tai bakikkirin da ita.

Juya wa yai da zummar fita sai ya tsaya tare da gyara farin glass idonshi ganin wata bakar kwalba na yalki da laya a gefenta.
Kamar kar ya duba,sai dai ya kasa daurewa tare isa wajen ya fiddo da handkerchief a aljihunshi tare da rufe hannunshi ya bankad'o su.

Kai ya kawar tare da yin bissmillah ya dakko layar da kwalbar sai wari take yana jujjuyawa yana yamutsa fuska.
Tamkar an jeho su haka suka shigo gidan ganin manyan motoci a kofa.
Suna yin ar'ba suka fara inda-inda,sai dai idon su na kaiwa kan kayan da motar ta tono suka hau raba ido.

Ido ya zuba musu,gaba daya a yanzu koh a y'an aiki bai tunanin zai iya d'aukar su Tabawa dan munin kamanin su agunshi.
A yanzu tsantsanin kallonsu ma yake dan  yadda duk suka zama wasu zararru in sun ganshi,dan haka da sauri ya d'auke kai tare da fita da kwalbar daga gidan.

Ba wacce ta iya magana sai da ya fuce,dan haka da sauri Tabawa ta d'aura hannu bisa kai tare da runtuma ihu.
"Shikenan asiri ya tunu,wallahi Lami kwalbar nan ce da layar da mai yankan wuka ya ce mu sata tare da kwalbar ta aikinshi yau ya tono ta.

Kasa magana Lami tayi tana zufa,tasan yau kam karya ta kare,kila in Malam yazo ya dankara musu saki tunda ba makawa sai an fasa kwalbar nan..

"Yanzu meye abinyi Tabawa?
Kai ta girgiza
"Mu bishi muga inda zai hullar sai mu dawo mu binne.
Fita sukai da sauri,sai dai ba Kabir sai kurar motarshi.

Gidan Umma ya nufa a inda nan ne su Saifu suke mata hutu.
Kallon ikon Allah suke lokacin da k'anin Nafisa ya kunce layar.
Baya su Saifu sukai da sauri dan ganin kai kamar na miciji da korayen ido duk ya bushe cikin layar.

"Ban fa yarda da abin nan ba Umma,kamar yadda naga ganin abin su Lami sun kasa sukuni.
Ajiyar zuciya Umman tayi,tare da fad'in
"Allah kyauta.
"Amin.
Kai Aliyu ya dago.
"Yanzu ya za ayi dasu Ya Kabir?

Umma ya kallo,sai ta ce ya fita ya sa musu kalanzir gaba daya bayan ya fasa kwalbar.
"Abba meye wai?
Nass ya kallo tare da kad'a mishi kai.
"Ba komai Nass.
Saifu ya kallo,
"Je ku shirya mu fita in da abinda kuke so ga Sultana naga ta shirya.

Tashi sukai tare nufar d'akin Umma.
"Yau na yanken shawarar tunkarar Abba Umma a wannan karan koh zan san laifin da nai mishi dan nasan yau da matsala dan na rushe wani bangare na gidan...
Shiru ya yi jin karar wayarshi, duba wa ya yi,Abban Uzairu ne,dan haka sai ya d'auka dan yasan yanzu ba jimawa suka rabu.

"Kabiru kana ina?
Cike da mamaki ya kalli Umma dan koh sallama Abban Uzairu bai mishi ba.
"Ina gidan Umma Abba,lafiya?
Cike da dauki ya ce
"Kazo gida yanzu inda hali kaga wani abu.
Wayar ya ajiye yana kallon Umma.

"Kai Umma ba lafiya ba,duk yadda akai nasan Abba ne yaje gida yaga abinda nasa ayi.
Shiru sukai,
"Kaje dai kaji koh lafiya, Allah rufa asiri.
Tashi ya yi ganin su Saifu.
"Ku jirani na dawo koh?
Kai suka girgiza
"Muje dai Abba mun shirya.

Jama'a suka samu a gidan makil ga nan ihun Abba yana fad'in sai sun fito mishi da Kabir.
Karasawa sukai ciki,da sannu ya fara fitar da jama'a yan kallo yana kutso wa ciki.

"Abba..
Chak ya tsaya da bugun kofar d'akin da su Lami suka kulle ya bari,a hankali ya juyo tare zuba wa Kabir din ido wanda ke hawaye.
Abban su Uzairu Abban ya kallo da halamun tambaya, da sauri ya daga mishi kai.

"Yaya shine Kabirun ka..
Baki sake ya sake kallon Kabirun dake murmushi yana mai gode Allah da ya nuna mishi wannan rana.
A hankali suka fara isa ga juna bakin Abba na ka'rkarwar kiran Kabiru har suka had'e.

Daga sama har kasa yake kallon Kabir din shima yana hawaye.
"Kabiru na ne yanzu haka?
Hannun Abban ya riko yana jijjiga mishi kai,
"Sannu Kabiru,Allah ya raya min kai duk rintsi.

"Azatona ka mutu dan tun hullaka rijiya na daina ganin ka na kuma kasa komai a kai,kai hak'uri Kabiru,ba laifina bane...
Kuka yaAbban yanai.
Juyawa ya yi tare da nuna wa Abba su Saifu yana murmushi halamun nashi ne.

"Ikon Allah.
Hannu ya mikawa su Saifu,dan haka da sauri suka karasa ganin Abban su a jikin shi,sun sani da kullum in sunzo Kano bai musu magana sai kallo da ido.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

33_Tana d'aki lokacin da suka dawo,tun daga bud'e kofar su suka fara kallon parlourn yadda yake diddika kamshi a gyare tsaf-tsaf kamar kullum.
D'aki kowa ya nufa a gajiye har Uncle din,sai Sultana da ta nufi d'akin Faridan ganin bata ganta ba.

"Anya wannan gyaran d'akin na john ne kuwa Nass?
Kallonshi Nass din ya yi shima yana mamakin yadda aka dame musu gado ba irin yadda john ya saba ba.
Kafad'a ya daga halamun shima bai sani ba.

Duk mamaki suke har Saifun,sai dai shi sai ya bari a ya sake iyawa ne kawai,dan haka ba wanda ya kawo Farida ce tayi.

Fito wa tayi jin muryar uncle din tai mishi sannu da zuwa kamin ta wuce da Sultana d'akinta.

Kamar kullum kowa ya d'au abincin shi ya nufi dining dan ci.
Jin shiru sai dariyar Sultana daga d'akinta yasa Uncle din sanya Nass ya mika wa Farida nata ya kira Sultana.

Tashi yai ba dan yaso ba ya d'auka tare da kwankwasa kofa yana kallon Abban,dan ka'idarsu ce dole a baka izinin shiga kan ka fad'a.
Farida ce ta bud'e, ganin ita ce yasa kawai ya mika mata tare da kawar da kai yana kiran Sultana ta fito.

Kar6a tayi tana mishi murmushi kamar yadda Umma ta ce,shi kam ganin Sultana ta taho yasa ya bar kofar yana chunno baki.

Chokali Uncle din ya ajiye bayan gama kallon su din ya dafe kai da duk hannu biyu.
Ya sani tun ranar da suka fita ya ja musu kunne suka daina maganar Farida,duk da yaji dad'in ba wanda ya sake tada zancen mey yasa ya aurota amma yana kula sun fita a sabgarta ma gaba d'aya sai kallon tsana da harara.

Kai ya dago jin Nass na kiran Sultana ba iyaka dan haka sai ya kallota.
Kafad'a ta make musu rike da abincinta a hannu halamun d'aki zata bi Farida su ci.

Ajiyar zuciya ya saki tare da girgiza kai.
"Bari taje...
Jin haka yasa da sauri ta kara mai zuwa ga Farida tana murna.

Yau a d'akin Sultana tai wanka bayan ta ma Sultanan nata.
Ganin ba wasu kayan kyali sai farar powder kawai,dan haka sai tajata suka koma d'akinta.

A nan ta tsantsara Sultana tare da sanya mata kayanta riga iya gwiwa blue mai flower pink dan lokacin fitar su ya yi na yamma.
Riga da skirt itama ta sanya na attamfa pink da ratsin blue,sai zamo sunyi kusan anko da Sultanan.

Dankunne kawai tasa blue mai kamar barima tare da daura dankwali.
Ta mudubi take wa Sultanan dariya ganin yadda take kallon yadda take mirza jan baki,dan haka sai ta juyo tare da shafa mata suna dariya.

Kofa aka kwankwasa,da sauri Sultana taje ta bud'e.
Uncle ne cikin kanan kaya sai ka ce dan saurayi sai kamshi yake.
"Wow...my princess,ke ce kuwa?
Dariya take mishi jin ya fara kod'a kwalliyarta tana gyad'a kai.

Kofar ta bud'e gaba d'aya ta yadda  Farida ke iya ganin su.
A yau kad'ai wani irin kyau yaga Sultanan na sake yi har bai san ya ciro waya tare da daukarta ya juya yadda suka bawa Farida baya ya kyalla musu selfie suna dariya ba shi da Sultanan.

Ajiyeta ya sake tare da daukarta ita kad'ai,tuni gwalli ya motsa sai karkacewa take karawa yana mata yana dariya.
Farida ya kallo wacce ke kallonsu itama baki washe,ai sai yanzu ya tuna d'akinta suke,dan haka a hankali ya ce

"Oh! Farida sorry.
Kai ta kad'a, duk kowa na gidan gwanin sha'awa yake a idonta ita barin Sultana.
"Zamu fita,ba wani abu koh?
Kai ta girgiza,kamin ta ce
"Sai abu d'aya.
Tsayuwa ya gyara tare da gyara farin glass dinshi.

"Ok,mey fa?
List din ta dakko bisa mirror tare da dan dukowa ta mika mishi da hannunta biyu.
Glass ya gyara yana mai sake kallon cefenan nata,a dan sace ya kallota,hankalinta kwance take murmushi.
Kamar ya ce mey zatai dasu sai dai ya basar.

"Dama Uncle ni bana son abincin wajen nan ne kullum,tunda na iya sai mu siyo gobe na fara.
Dariya ke kok'arin subuce mishi,har ga Allah mugun yarintar Farida yake gani,dan haka sai yake ganin kamar fad'a take amma ai tayi k'ank'anta da iya girka duk abinda ta lissafo mishi.

Kok'ari ya yi ya danne tare da fad'in
"Shikenan?
Kai ta girgiza mishi halamun ba shikenan ba,sai dai kamin yakai ga magana ta langwa6e kai cikin shagwa6a tare da fad'in
"Nima so nake naje ne fa Uncle.

Tsayuwa ya gyara tare gyara glass din shi,tamkar wata Sultana in taso mishi shagwa6a haka ta dawo,dan haka da sauri ya basar tare da fad'in
''Ok...

Dan tsalle tayi kad'an tare da d'aukar gyalen da ta fito dashi cikin murna.
Ganin yana kallonta yasa sai ta dan nutsu tare da sauke kai tana murmushin kunya.

Murmushin shima ya yi tare da fita rike da hannun Sultana dan haka da sauri ta lankaya gyalen a kafad'a ta fito dan bin bayan su.

A mota suka tarar dasu Saifu duk sun shassha mur ganin Farida da gyale.
Kasa hakura Saifu ya yi,dan haka da sauri ya tambayi Abban da ita zasu tafi ne?
Faridan ya kallo yadda itama ta zuba mishi ido,da mamakin Saifu sai yaga Abban ya daga kai halamun eh.

Kofa ya rufo da karfi yana harararta lokacin da suke kok'arin shiga gaba ita da Sultana tana murmushi.
Horn ya yi aka bud'e musu gate yana kok'arin d'aura belt.

Faridan ya kalla da ainashin gyale a gefen kafad'a daya kamar yadda yaga y'an mata nayi sai yai murmushi tare da dauke kai ya fita daga gidan.

Da kaya niki-niki suka dawo kusan duk list din Farida harda su lunch boxes na yara da na manya da jakunkunan su harda su kitchen apron.
Wani abin ma bai san amfanin da zai musu ba amma Farida ta jido su,shi dai adu'ar shi d'aya Allah kad'e mishi asara.

Da kanta ta shiga kitchen tana jere kayan,na fridge ta sa,na store ma haka.
Bayan sunyi sallar isha'i ita da Sultana ta cire kayanta tare da sanya sassauka suka nufi kitchen.

Kaza ta gyara jin shiru basu dawo ba ta silala ta juye a roba mai murfi tare da sanyata cikin freezer..
***

Washe gari week end,wanda a ka'idar gidan suna yin bacci ne har sai randa yunwar cikin su ta taso su.
Gari na waye wa ta fito tare da shiga kitchen aka d'aura apron.

Fridge ta bud'e tare da ciro daskararriyar silalliyar kazarta ta jiya har tai kankara.
Store ta shiga tare da dakko tukunya ta ta fara aiki.
Farfesun kazar ta fara had'awa bayan ta gama yanke albasarta bisa copping board da tafarnuwa ta watsa.

A greater ta jajjaga komai gudun kar ta tashi kowa a bacci ta nan zuba,duk wasu items da take da bukata na karin dand'ano tasa tukunna ta d'aura bisa gas.
Kan kace meye tuni kamshin 'Chief Faridee' ya fara bud'ad'e gidan bayan an zuba kayan kamshi.

Gefe tayi da wannan, tukunna aka d'aura tea tare da binciko kayan citta dasu kanumfari da sauran kayan kamshin tea da Umma ta sanarta tasa ta watsa ta rufe dan ya dahu.

Parlour ta koma tare da dakko bread wanda suka siyo jiya mai yanka-yanka ta koma kitchen tare da fara mayarshi hadadden 'Sandwich' ta jere su bisa wani dish dogo mai kyau yadda kana hango su ta ciki gwanin kyau.

D'ayan wani warmer ta dakko shima mai ruwan garai ta juye farfesun kajinta aciki a hankali taje ta jere su da tea flaks,cups,plates da sauran abin bukatar kowa tukunna ta hau gyaran gida.
 
Tsaf ta gama komai,tukunna ta koma d'aki tare watsa ruwa dan gajiya.
Sultana ce ta fara tashi,dan haka sai ta mata wanka tare da mata shiri cikin kaya masu sauki suka zauna a parlour suna dan tad'in su.

Amjad ne ya fito yana shasshako kamshi-kamshin abinci a parlourn yana kallon su Sultana.
Murmushi tayi mishi,kamar ya mayar mata sai dai ya kautar da kai tare da neman waje ya zauna yana dube-dube.

A hankali sauran ma suka fara fito wa suna muzurai na yunwa da shakar kamshin parlourn, duk suka zauna suna dan gulmarta da baki da hannu,kitchen Nass ya leka,sai gashi ya fito yana girgiza wa Saifu ksi halamun baiga komai ba,a jima kad'an ayi hamma mai tsaki nayi duk tana kallon su.

Juya wa sukai jin bud'e kofar Uncle d'in da shima ya fito jin corridorn shi ya cika da kamshi iri-iri yana kalle-kalle.
"Sorry guyz,yunwa koh?
Kai suka fara kad'a mishi suna hamma.

"Ina kwana Uncle..
Kallota ya yi tare da amsawa itama yana bata hak'uri tare da fad'in su tafi cin abinci kawai tunda an makara.

Kallo uncle din tayi tare da yin murmushi.
"Ai tuni ku muke jira na gama komai yana bisa table.
Kallon-kallo yaran suka fara tare da kallon Abban nasu yadda ya zuba mata ido.

Ganin ba mai motsi yasa ta kama hannun Sultana tare da nufar hanyar dining din ta yaye labule abincin suka baiyana.
Tana yaran kowa na zungurar kowa suna kus-kus.

Shikam Uncle din kallonta yake yadda take bubbude komai cikin nutsuwa,bata sake kiransu ba sai kamshi abinci da ya kira uncle dan gaskata hancinshi.
Zama ya yi tare da lelleka abincin yana mata yake ganin yadda take loda mishi.

Zama tayi tare da kallon yadda ya dau sandwich daya ya kai baki yana kallon yaran.
Ido ya lumshe,dan haka da sauri ta waro ido ta zata koh bai mishi bane.
Ido ya bud'e tare da sauke ajiyar zuciya yana kiran yaran da hannu cikin sauri halamun su taho.

Kamar kwa masu jira da sauri suka mike har suna dan had'a kafad'a.
Murmushi tayi tare da zuba ma kowa tana tura mishi.
Tsit ka ke ji daga uban har tsagerun ya'yan an dukufa ana aika d'a'amu ba k'ak'kautawa.
Wa yaga su Uncle
*d'an hakkin da ka raina*😹
By

Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

34_Ruwa ta debo a roba kamar yadda taga Umma nayi in Abba yasa hannu a abinci tare liquid soap ta miko wa uncle tana murmushi.
Hannu ya sud'e yana kad'a kai,
"Bravo alaiki Farida...
Baki ta washe tare tatsa mishi soap din ya wanke hannu yana kallon yaran masu kokawa da kasusuwa.

Dariya suka sa bayan Nass yai musu wani tsurkun suna kallon Farida da ta fara kwashe plates na gaban Uncle ta nufi kitchen.
Da fara'a ya kallo su duk a zatan shi abinci ne ya kwashe su.

"Hala yai dad'i?
Kai Nass ya kad'a lokacin da yake yagar cinyar kaza.
"Not bafad'in
..
Duk kallo Nass d'in sukai jin a yau har ya sauya wa Abban suna zuwa Dady cikin santi,dan haka tuni suka kece da dariya harda kyakyatawa.

Dariyar su ne ya fito da ita,da mamakinta har Uncle d'in suke dariya yana kad'a harda basu hannu suka tafa.
Murmushi take tare da zubawa Uncle din ido,ba karamin kyau yai mata da dariyar tashi ba,a dan zamanta na sati ta fuskanci yana da kyakkyawar alaka tsakaninshi da yaranshi dan matuka yana ji dasu tamkar tsoka daya cikin miya.

Wani sa'in sai ta ga kamar ma ya maida su abokanshi cikin aminci.
Ina ma zasu ra6a ta itama ta zama Family kowa ya sota kamar yadda suke son junan su.

"Kar ki damu,kiyi tayin yadda Umma ta ce zasu so ki..
Murmushi tayi tare da kad'a kai jin zancen zuciyarta ta karasa garesu.
Murmushi Uncle din ya dawo yi ganin Faridan,a hankali kowa ya tsagaita tashi suka ci gaba da abinda suke.

Ba laifi,dan ta samu sassaucin hararar da suke mata da kallon tsana,abu d'aya ne dai har yau sun kasa kar6a shine matsayinta na 'Stepmother'.. Dan kuwa koh a gabanta d'aya ya tuna wa saura yanzu zasu fara yatsine fuska suna kiran 'No way..

Abu d'aya ta fara fuskanta shine shegen cin da su Saifu suka kowa harda na keta a kwana biyu kawai.
Yanzu zata gama abinci sai ana cikin ci su riga kowa cinye wa sai su hau fad'in a kara.
A d'aukin girkin take,dan haka tashi ta kara wani bai bata matsala haka zasu cinya tass.

Murna take a yau lahadi gobe zata fara halartar makaranta dan Uncle ya bata uniform sun siyo school bag da duk abin bukatar ta,dan haka gobe sai bin su Saifu.
Kowa yana kallo amma ita da Sultana suna kitchen sai agigin fere dankali take mai yawa tana zubawa a ruwa.

Sai da safe tai musu ganin takwas har ta gota bata kwanta ba.
Duk da kallo suka bita har ta kule kowa na aiyana abu cikin ranshi.

Kofa aka buga mata lokacin da take kok'arin kwanciyar,tashi tayi dan jin bugun kamar na Sultana,bud'e wa tayi,ita ce kuwa rike da karamin pillown ta sanye da kayan bacci.

Murmushi tayi mata tare da fad'in
"Can I stay with you tonight?
Waje ta bata ganin yadda take langwa6e mata kai halamun roko, da kwa dan gudunta ta shige tana murnar yau zata kwana tare da Farida.

Ajiyar zuciya tayi tare da
"Thank God da na iya had'a yaran baturen nan,da iyayin y'an gidan nan ya barni a baya..
Kofa ta rufe tare da juya wa tana k'akalo murmushi.

Da gani ita Sultana fira tazo,ita kam daukin tashi da wuri yasa sai bacci ke fusgarta amma tana biye wa Sultanan da sai zuba take mata kamar kanya.
Chan dai wajejen tara da wani abin taja bargo tare da ce ma Faridan.
"Good night..

Ranar ce ta farko da suka fara had'a kwana ita Sultana,dan haka tun asuba da tashi sallah itama ta tashi tana binta.
Kitchen suka wuce suna idarwa koh koma wa ba suyi ba.

Da dan kwarafniyar Sultana ya ja hankalin Uncle wanda suka dawo a masallaci ya tsaya,su kam su Saifu bacci fal ido suka wuce d'aki.

Yankan 'chips' ya samu suna yi suna a gaban sink suna dariya a tsaye,yayin da ta bawa Sultana kujera ta hau ta tsaya itama hannunta na cikin ruwan dankalin.

Hannu ya hard'e tare da jingina yana kallon su.
Kayan bacci ke a jikinta na riga da wando cotton fari da mitsi-mitsin flower jajaye wandon da kad'an ya wuce gwiwa yayin da hannun rigar yake mai tattara da jan zare kamar shimi harda su 'breast curve'.

Dan dad'in aiki zanin da ta dauro ta cire gefe tare cire karamin gyalen ta ci damara dashi ta bar gashin haka,dan haka daga inda yake yana iya kallo tumin d'aurin da tai wa gashin da ribbon fari.


Murmushi yai musu ganin Sultana na dan yarfa mata ruwan dankalin tana kautar da fuska suna dariya.
Ilahirin surarta ya fara karewa kallo.
Kusan da kad'an tafi Saifu tsayi da dan kaurin jiki.

A zahiri surar girma ta baiyanar mata dan tuni ta fara cika mai fusgar hankali irin na cikakkun mata.
Ajiyar zuciya yai tare da saurin juya wa ya bar kofar ganin tunani ya fara kaishi wani gurin dan haka sai ya barsu nan.

 'French toast' da chips ta had'a musu cikin nutsuwa dan ta rage aiki jiya.
Ganin kullum tea ake sha,dan haka yau sai ta dama musu tapioca na cikin garar ta ruwa-ruwa tasha madara.

Da sannu kowa cikin 'lunch box' nashi ta sanya mishi 'french toast' da chips din da dan ketchup.
Sai tapiocan a cikin dogon bottles din masu kama da karamin flaks na yara ta rufe su kamar jakunkuna.

A gaggauce tai wa Sultana wanka ta buga d'akin su Saifu itama ta shiga kamin ta dakko goggun kayan su ta ajiye.
Make-up dai-dai dai-dai ta musu ba wani jan baki sai powder kawai da wet lip komai iri guda har style na gashin su parking a tsakiyar kai.

Jin hayaniyar y'an gidan halamun sun fara fitowa yasa ta kamo hannun Sultana suka fito.
Sucks suke sawa a parlour,duk da kallo suka bisu ganin tana musu 'Hi'.
Yake kawai suka mata kowa ya cigaba da sabgar gabanshi.

Dining ta wuce tare da zuba ma kowa chips nashi a plate da 'ketchup' a gefe da kwai soyayye tare da tapioca a cup.
Corridor take kallo ganin har yanzun Uncle bai fito ba,gaba d'aya ta k'agu taga an gama ta isa makaranta.

Hanyar ta sawa ido jin bud'e kofarshi,turaren shi ne ya fara baiyanar dashi a gare su yana daura link na hannunshi.
Matuka yai mata kyau yau a cikin dogayen kaya farare har yafi na ranar Jumma'a kasantuwarshi ma'abocin k'ananan kaya.

"Sorry guys...
Kai duk'e yake fad'i rike da briefcase nashi a gefen hannu.
Murmushi tayi tare da kok'arin jan kujera ta zauna.
"Bissmillah...
Ya fad'a yana gyara d'ayan bangaren link d'in.

"Good morning Dady..
Murmushi ya yi jin sunan da suka k'ak'aba mishi,hannu yakai tare da ruko kumatunta yana fad'in
"Morning sweetheart..
"Ina kwana Uncle..
Kai ya dago tare da amsa wa yana kallonta.

Tai shar cikin uniform din sun mata charas kamar an auna ta ba wai kallo kawai ba.
''Farida...
Murmushi tayi tana zama
"Na'am ina kwana.
Zama yai yana dan basar da kallonta tare da amsawa ganin yadda yaran suka sa musu ido kirrr.

Murmushi yai musu dan haka sai kowa ya cigaba da ci kawai.
Bayan kowa ya gama ta sako hijab nasu iya dan kirji rataye da jaka sai ta nufi kitchen tare da debo lunch boxes din.

Galala suke kallonta barin ma Uncle da yaji wani bankwarakwai har da shi ya tafi da nashi office koh zai ji yunwa.
Dariya Nass ya saka,dan haka sauran ma sai suka fara har uncle din ganin Dady ma ya zama dan makaranta.

Yake ta hau musu,amma ji take tamkar ta sa kuka dan ganin ita a dole tayi gwaninta.
Kai Uncle ya kad'a, shi yasa yake ganin yarintar ta,in banda haka ina shi ina lunch box a office?
Shi kam Saifu cewa ya yi ya wuce wannan level d'in ai sai dan primary koh nursery ba shi dan Jss1 ba zai shiga 2.

Taji dad'i da Amjad ya kar6a ba musu,ita kam dama Sultana murna take dan kullum tana ganin kowa lunch box nashi ita sai dai in an tashi break suje shop it da su Saifu.
Har a mota dariya suke,sai dai da mamakin su da zata fito dasu ta fito har mota.

Sun hau hanya Uncle din ya fuskanci yake kawai take musu,dan haka a hankali ya sau karatun Qur'ani wanda yake sa yaran shiru dan dole.
Har suka zo makaranta kanta na bisa hanya.

Kowa ya fita har Sultana,dan haka ita karshe,duk lunch boxes din uku ta d'auka har nata tare da barin na Uncle a motar zata fita.
"Farida..
Juyo wa tayi fuska a sake tare da kallonshi.
"Na'am Uncle.

"Kin gane ina zaki nufa koh?
Kai ta kad'a tare da yin kasa da kai tana murmushi.
"Zan bi su Saifu..
Kai shima ya kad'a yana dan murmushi hannunshi bisa stirrri.

Fita zata sake yi ya sake fad'in
"Farida..
Zama tayi tana dubenshi,dan haka sai ya ciro kud'i tare da mika mata.

"Gashi in zaku shop dan su Saifu total ake min every month kan na kamin na saki ciki.
Murmushi tayi tare da kad'a kai
"Bana son musu..
Baki sake ta kar6a ganin yadda ya tsareta.
"Na gode.
By

Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

35_Office ya wuce yana murmushin abinda Farida tayi,a kalla koh ba komai yasan da abin dariyarta yaranshi da sannu zasu sake su amsheta a matsayin uwa a gaba tunda har takan sa suyi dariya.

Parking ya yi yana kok'arin fita ya hango jakar lunch box nashi da ta ajiye,kai ya girgiza tare da fita.
Yasan yau in dai ya dau lunch box har office sai ya gaji da tsiya gun Nasir,dan haka kofar ya rufe.

Yau dai kusan tare suka zo Nasir,bayan sun zauna yake mishi wai
"Na y'ar mitsila (Feedoh daughter😘).
Dariya suka sa tare da tafawa.
"Yau ana makaranta an shiga SS1.

Kai ya jinjina yana dariya,
"Lalle ka tsinci dami fa a kale mutumina, auren yana ban sha'awa na yarinya da tsohon saurayi..
Dariya uncle din yasa yana kad'a kai
"Baka da dama Nasir.
Ana fira ana aiki,galibi da dabi'ar Farida ne har suka tashi break.

"Coffee fa yau ba inda zai kaini,dan sosai nake jin yunwa bari nai order.
Murmushi Uncle din ya yi dan tuna wa da tsarabar Farida.
"Kasan mey?
Kai Nasir ya kad'a,
"Ranar fa Farida tasa muka jido lunch boxes har ina mamakin mey za ai dashi sai dai nai shiru.

"Yau kawai mun gama break sai ga ta da lunch boxes wai ga nawa koh zanji yunwa ji kamar dan primary..
Dariyar keta ya fara mishi tukunna ya fara fad'in
"Ka ga dan gatan y'ar mitsila, a tarairayi yaran ka a tarairaye ka..

Kai ya kad'a jin tsiyar Nasir.
"Amma kasan mey?
Kai Nasir din ya girgiza.
"Y'ar mitsila fa ta bada mamaki fa...
Zama ya gyara jin fara zuwa gurin.
"Na mey fa?
Kai ya jinjina,
"Allah nake fad'a maka ta bani mamaki a ranar farko da naci girkinta har yau din nan da sabon salo na daban duk ta iya a fagen girki.

Ido Alhaji Nasir ya zaro..
"A kai haba?
Kai ya kad'a
"Fiye da zaton ka.
Cike da zolaya ya ce
"Toh kar fa muje kallon kitse muke wa rogo y'ar mitsila ta san komai fa.

Kai ya girgiza yana fad'in
"Kai haba,bar wannan wajen..
Dariya yasa tare da fad'in
"A'a toh a dakko min girkin y'ar mitsila na ta6a.

Kallonshi yake da mamaki.
"Wai da kana nufin na shigo da jakar lunch box?
Kai ya girgiza
"Ina yanzu sai a mana dariya.
Tashi Alhaji Nasir din ya yi.

"Toh kawo ni na dakko,muke shigo da order ma,meye ne aciki? Kai anya nima bazan dau wata y'ar chukul din ba nima ta mayarni yaro...
Dariya suka sa,lalle Alhaji Nasir akwai shakiyi, haka ya bashi mukulli yaje mota ya kinkimo jakar lunch box har office nasu.

"Bissmillahi..
Bud'e wa ya fara d'aya bayan d'aya yana kallonshi.
Dariya yasa ganin abin ciki,sai dai yai mishi kyau a ido dan haka sai ya dau French toast ya gutsura yana kok'arin zuba tapioca.

"Kai,lalle ne,a kalla tai ma maganin yunwa.
Murmushi ya yi yana kur6ar coffee shi dai.
"Toh shi wannan breadin da mey tayi shi? Allah ya min dad'i..
Kallonshi ya yi lokacin da yake jujjuya french toast din hannunshi.

"Breadi koma?
Kai ya kad'a mishi dan bak'inshi ya cika da tauna.
Tashi ya yi tare da zuwa ga table d'in Alhaji Nasir din yana leka abin.
"Ka d'au d'aya kaji yai dad'i fa..
D'auka ya yi yaci d'aya, a hankali ya janyo kujera ya zauna cin mey duka,iya dariya Nasir yasha ta,lalle y'ar mitsila ta iya kiwo.
****

Ita kam kamin ta samu su Saifu har sun shige cikin taron y'an assembly, dan haka itama sai tabi sahu tana karantar tsari da yanayin makarantar ta masu hannu da shuni,kowa ka gani kwas dashi dan gayu.

Iya dubenta bata ga su Saifu ba sai Sultana da tai mata bye-bye ta tafi class.
Dan haka a matsayinta na sabuwar zuwa sai ta tsaya inda-indar in da zata dosa.

Juya wa tayi sai ga nan wata kusan za suyi sa'anin juna da ita tana takun y'an gayu da iyayi.
Da dan fara'rta ta tare ta da tambayar ina zata dosa musamman da kayan hannunta.

Kallon banza ta mata tana yatsina tare da wuce wa ba koh magana.
Juya wa tayi tana kallon yadda take tafiya kamar bazata taka kasa ba.
Harara ta doka mata tare da fad'in
"Ji ka'fa kamar ta agwagi dalla...
Chak yarinyar taja ta tsaya tare da juyo wa.

Kai Faridan ta d'auke tare da had'e rai ganin tana taho wa.
Daga sama har kasa ta karewa Faridan kallo tabbas bata da makusa ta fuskar shigarta da tsayuwarta.
Kallota tayi ganin yadda take kare mata kallo tana taunar cingam sai ta dauke kai.

Murmushi yarinyar taga tayi da mamakin ta,kan ta farga ta miko mata hannu tare da fad'in
"Friends?...
A takaice ta kalleta, kyakkyawa ce daga gani y'ar masu kud'i ce, sai dai ita sam batai mata ba balle har tai kawance da ita...

Kai ta d'auke tare da kin kulata,tasan Umma tasha fad'a musu shasha ce mai taunar chewing gum a titi koh karuwa,dan haka bata ga abin kawance anan ba.
"Allah kiyaye nai kawance da mai cin chewing gum a titi..

Dariya yarinyar tasa tare da cire chewing gum din ta hular tare da fad'in
"Ok,fine,kiyi ta tsayuwa na fasa nuna wa..
Juya tayi,ganin da gaske tafiya zatai ga duk an watse yasa ta tsayarta.

"Toh rakani dan Allah..
Juyo wa tayi tana murmushi kamin ta kar6i wani kayan suka tafi,duk sai taji bata kyauta ba da ta ce mata mai kafar agwagwa dan haka a hankali ta ce mata
"Sorry..

Kallota tayi da halamun mai saukin kai ce ba yadda tai tsammani ba sai dai ta shafeta a rawar kai.
Murmushi tai mata tare da fad'in
"It's ok..
Ajin da zata ta tambayeta,da mamakinta sai taji ajinsu d'aya ma ashe.

Kamin zuwa break duk ta gama karantar halin wacce ta kira kanta da Laila,dan haka sai ta yarda suka kulla kawance dan daga gani zatai saukin lamura.
Ita kwa Laila kawai Farida mata tayi dan tana son mutum marar daukan raini.

Sultana ta hango da halamun nemanta take,dan haka da sauri ta karasa tare da taryarta.
Inda zata samu su Saifu ta kaisu ita da Laila,dan haka har cikin abokanshi taje tare da mika mishi nashi ta kauce.

"Wace ce Saif?
Yana hura hanci ya ce
"Wai ita Step-mom namu ne..wai fa...
Dariya abokan suka sa tare da sake kallo Farida.
"Kai amma an cuci Step-moms,kalleta fa na fita tsayi kuma ma y'ar secondary...

Kwafa Saifu ya yi dan jin anzo wajen.
Koh shi ya masifar raina girman Farida a matsayin step-moms,balle kuma in ya tuna akidarsu ta tsanar duk wata wacce ta amsa sunan  step moms barin ma ace tasu,dan su fa ansha su ne sun warke.

"Wow,French toast Saif..
Kallo su ya yi yadda suka fara hakar abinda ta kawo yana ta6e baki.
"Amma kun more zaku ci dad'i a gidan ku..
Kallosu ya yi yadda suke ci suna fad'in yau ba zuwa shop,yaje kawai.
****

Sai ya zamo daga wannan lokacin daga Uncle din har yaran kowa baijin kunyar daukar lunch box barin ma Saifu da yanzu a dalilin zuwa da lunch box yanzu abokanshi sun mayarta kayan wata karya kowa ka ganshi da ita a rataye,tanan dai Faridee ansau✔

Uncle kam yanzu har ya saba ya dau briefcase da lunch box a hannu ya shiga office har wani alfahari yake.
A nan za'a had'u in snacks ta zubo ai taci ana mishi tsiyar y'ar mitsila,dan haka yakan ce ta kara yawan abin akwai maciya a office.

Zama da Laila kowa yasa ta fara koyan wasu abubuwa na daga dabi'ar ta aciki kuwa harda wannan gwalangwazon da yanga karfi da yaji.
Ga kullum da snacks din da zata koya gunta dan duk su masu burin girke-girke ne,dan haka zani ce ta tadda muje.

 A class suke wanda kusan watan ta guda kenan da fara zuwa makaranta.
Zaune suke sunyi tagumi jiran teachern Biology ya dawo har sun gaji period nashi ya kusa fita bai dawo ba.

Duk tagumi suka zuba Laila na bankad'a text book na Biology ita da wata y'ar yarbawa suna duba abubuwan ciki duk da ba nasu bane ita ta taho kawai dashi.

Farida ta zungura da sauri tana nuna mata abu a jiki suna kallon y'ar yarbawa.

"Ga baby acikin womb Farida wai...
Diagram din ta zuba wa ido tare da gyara zama.
"Toh anan yanzu ta ina zai kutso wannan katon kan nashi?

Dariya y'ar yarbawa tayi,kamin ta kai hannunta kan layin
"Ta nan man.
Harararta sukai,dan haka tuni ta fara basu bayani suna waro ido.

Farida Lailan ta kallo,wacce tuni har ta fara gyara mazaunin hijab nata tana had'iyar yawu jin bayani daga bakin y'ar yarbawa dalla-dalla.

Kan ka ce mey tuni har ta tsure ta fara zufa,kallo kawai katon kan yaron take amma ace wai ta jikinta zai hudo ya fito.
"Mun shiga uku Farida.
Kallo su y'ar yarbawa tayi ganin yadda sukai tsuru-tsuru suna kallon juna tare da fad'in
"I see,da kun zata aman baby ake koh mey?

A tunzure Laila ta ce
"Kinga Malama tafi,tafi dalla, gaba daya kin tsorata mu da wani bayanin ki na karya da gaskiya,dau littafin ki.

Baki ta ta6e tare da bar musu wajen suna jimami.
"Farida..
Tsuru tai mata kamar 6ere a buta.
"Ni har ma na fara tsoron nai aure wallahi Farida.
Da sauri ta ce
"Nima fa..
Shiru tayi,dan shaf ta manta bata fa fad'a wa Laila Uncle ba dadynta bane kamar yadda ta ce mata su Saifu k'annenta ne.

Hannunta ta kamo tare da fita waje suna leka wa.
"In fad'a miki gaskiya?
Kai Lailan ta kad'a, sai ta duba gefe da gefe tukunna a hankali ta ce
"An fa min aure ni...
Baki sake take kallonta ba koh kiftawa.

Dariya ta sa iya karfinta harda da rike ciki,dan haka da sauri ta rufe mata baki dan kar wani yaji.
"Kar ki fad'a dan Allah sai suna tsokanata an bani tsoho.

Dariyar Laila ta daina tare da kafeta da ido.
"Wai dan Allah da gaske ki ke Farida?
Tsaki ta danyi a takaice,
"Allah serious da aurena, amma kar k fad'a fa.
Baki ta saka jin ta rantse,
"Toh waye mijin?

Ba musu ta ce
"Uncle..
Cike da rashin fahimta ta ce
"Wane uncle?
Ido cikin ido ta ce
"Dadyn su Sultana man...
Rai Lailan ta had'e
"Malama kar ki rainan hankali,ba kin ce su Saifu k'annenki bane?

Tsaki tayi tare da fad'in
"Eh man,yaran uncle ne ai,koh kin ta6a ji na cewa uncle Dady?
Kai ta girgiza cike da yarda da maganarta.
"Shikenan Farida ke ma kin kusa haihuwa Allah tunda aka miki aure.

Ido ta zaro,da sauri ta kad'a tare da fad'in
"A'a wallahi,ba yanzu ba sai na sake girma,haka kawai wannan ai saina mutu in ya 6ullo Allah,kinganni fa.
Jinjina mata ta fara,
"Ya yi momcyn su Saif,ai dole ne ma na kai ki karo course gun sister wallahi yadda zaki mamaye zuciyar Uncle kam ba cikawa.

Dariya suka sa,
"A'a, wani irin course kuma? Allah sa na girki ne..
Chaii,Faridan matsala.
By

Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

38_Kofa aka kwankwasa, dan haka sai sukai shiru jin sallamar uncle.
Tashi tayi tare da bud'ewa tana murmushi ganin yadda shima fuskanshi a washe.
"Ku fito in ta gama..
Kai ta kad'a mishi,dan haka sai ya juya rike da hannun Sultana wacce ta taho.

"Uhmmm...
Kofar ta rufe tare da juyawa ga Laila da ke narke wa a gado.
"Ke fa?
Cike da shakiyanci ta ce
"A min aure nima kawai...
Dariya tasa tare da hulla mata gyalenta,
"Samo mijin ni zan sanar wa sister ta miki..

Tashi tayi tana yafa gyale suna dariya har suka fito.
A mota suka tarar su da Sultana sai dariyar shakiyanci Alhaji Nasir yake ma Uncle din shi kam sai murmushi da kad'a kai.
Jin sun iso yasa suka saita kad'an.

"Ina muka nufa Laila...
Kallon hanya take tare da kallo Farida tana fad'a mishi unguwar.
Kafad'arta Farida ta zungura suna kunshe dariya.
Mudubin ya gyara duk yana kallon su harda mata rad'a.

Kai ya girgiza yana murmushi har suka iso gidan Auntyn Laila.
"Uncle bari na rakata..
Kai ya kad'a mata yana kallon Nasir dake shafar hab'a yana kallon Lailan.
"Toh kawarmu, mun gode..

Murmushi tayi tana kallon Alhaji Nasir, ganin abinda yake yasa ta duk'ar da kai tana murmushi suka wuce.
"A gaskiya zan ratso,dan fa naga gida Kabir..

Kalloshi ya yi bayan su Laila sun shige,
"Bar wasan nan dan Allah,ka rabamu da Mom Nour kalau,dan tsaf zata zaune y'ar mutane..
Dariya suka sa Nasir harda kyakkyawa.
***

Da fara'a Auntyn Laila ta kar6i Farida dan tuni har tasan wace ita a gun Laila.
"Aunty bari mu wuce suna jirana..
Kai ta kad'a tare da tashi sukai mata rakiya.
"Nima fa sister da zaki taimaken aure zaki min.

Lailan suka kallo tana turo baki,dan haka sai suka sa dariya.
"Abu mai sauki Laila,zan kira Abba yaji komai sai a dai daita.
Ido ta waro tana fad'in
"A'a na yafe wollah...
Dariya sukai sa mata har Auntyn ta koma ita kuma ta sake fita dan raka Farida.

Da dariya suka fito,ganin su Uncle na kallonsu yasa suka dan maze har ta bud'e mata kofa ta shige.
"Bye-bye...
Yatsunta ta dago mata tana murmushi,kamin Faridan ta daga har Nasir ya dago mata.
Dan haka da sauri Lailan ta sauke nata tana mishi murmushin kunya.

Kai Uncle ya kad'a tare da tada mota yana dariyar shakiyancin Alhaji Nasir.
Har suka sauke shi a gida yana sa su dariya barin Farida,sai ta ga tamkar wani joker.

Hanya take kallo cikin jerin solar dake bisa kwaltar tana murmushi d'auke da Sultana bisa kafarta a gaban motar.
Uncle din ta kallo a dan sace,tukinshi yake amma cikin nishad'i abinshi.

Kai ta duk'ar tana murmushi tare da d'aura ha6arta bisa gashin Sultana tana sakar ajiyar zuciya.
Kallota yai a takaice yana tuki.
Ya rasa wani irin nishad'i yake aciki a daren yau,kawai sai ya ta'alaka da barkwancin Nasir ne,dan haka shima sai ya sau ajiyar zuciyar yana kallon hanya dauke da murmushi.

****

Sun shafe kusan term harda dauri,iyanzu dai ta yarda da batun Umma sai dan abinda ba'a rasa ba.
Dan sannu a hankali yaran ta fara daina ganin tsanarta a tare dasu sai ketar cin abinci kawai in sun so mata mugunta.

Tayi waya,dan haka bata da matsala ta gida,takan kira Ummanshi su sha fira,haka yakan bata Abbanshi su gaisa yai ta sa mata albarka.
Koh da suka samu hutun term yaje Kano dubo Abba dasu Umma tare da su kwanan su suka juyo.

Kawancenta da Laila kuwa yasa ta koya mata kallon Indian films da sauran film na soyayya,dan haka iyanzu ta gama yadda da tabbas tana son Uncle sosai.
***

"Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un..
Da sauri ta fito a kitchen jin maganar uncle da dan karfi da ludayi a hannu tana zaro ido.
"Baida lafiya ne?..
"Uncle lafiya?
Kallota ya yi lokacin da yake sauran waya,a hankali ya sauke wayar yana danna kiran Ummanshi.

"Ina zuwa Farida...
A kunne ya sanya,tana ringing no answer.
Har zai sake kira yaga kiran kaninshi mai bin Nafisa.
Tabbas ta tabbata,dan haka kawai sai ya kallota.

"Rasuwa akai ne a Kano..
Hannu ta d'aura bisa.
"Na shiga uku,waye?
Ganin zata fasa mishi kuka yasa saukar da hannun nata.
"No ba ke bane,mijin Umma ne ya rasu..
Kai ta kad'a,
"Aiya,Allah sarki,Umman ka?

Kai ya kad'a mata yana yin hanyar d'akinshi.
A nan parlourn ta zaune sai dan kallon corridor take.
"Ki bishi ki ga kawai.

Tashi tayi da nufin yin hanyar d'akin sai dai tana ta tunanin shiga.
Duk gigiwarta bata ta6a shiga d'akin ba kusan wata uku da zuwanta gidan.
Duk da koh wannan zuwan Umma sai da taja kunnenta kan gyaran d'akin mey gidan da sauran abubuwa tace bata yi.

Kofar ta tura dan sallamarta jin yana waya cikin lallashi yana kuma had'a kaya.
"Kiyi hak'uri Nafisa,ni dai ki bi a hankali dan Allah ki bar kukan haka nan..
Tsaye tayi tare da zuba mishi ido jin yadda yake lallashin ta wayar kamar yai kuka.

"Nafisa?...
Tunano sunan tayi,dan haka sai ta dan ji wani iri.
"Yauwa Farida,zan tafi Kano Insha-Allah gobe zan dawo sai mu tafi gaba daya.
Agogo ta kalla,goma da wani abu na safe.
"Yanzu uncle?

Kai ya kad'a..
"Ummata ne Farida,ki fad'i ma su Saifu in sun dawo a islamiya kar suga bana nan.
Kai ta kad'a cikin marairaita.
"Toh,Allah ya ji kanshi,ka mawa Umma sannu.
Kai ya kad'a yana fad'in
"Amin..

"In sun dawo ki sanar ma musu bana son kowa ya fita,sannan magriba tana yi ki rufe ko'ina.
Kai ta sake kad'awa tana mishi fatan alkairi.
"Koh breakfast bakai ba Uncle.

Murmushi ya yi ganin yadda tayi,kawai sai ya samu kanshi da riko hannunta cikin sigar lallashi.
"Kar ki damu,sai na dawo..
Kai ta kad'a har ya fuce kamin ta kallo hannun nata bisa fuska,hanci takai tana lumshe ido jin kamshin Uncle din tana murmushi.

D'akin take kallo a tsare kamar na mace sai dai a tsari da akwai gyara.
Komai Navy blue da fari gwanin ban sha'awa kamar a turai.
D'akin ta jawo tare da fita parlour.
By

Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

36_Kai ya girgiza tare da sakar labulen yana murmushi ganin yadda suka rukunkume juna suna murna.
"Ashe zaki gane kwatance?
Harara ta dan sau mata tare da fad'in
"Kin dai bani wahala,jiya fa nai ta bulayin neman gidan sai da koma school na nemi alfarmar address naki d numbern gidan kamin nazo yau.

Parlour ta bud'e mata tana fad'in
"Sorry sorry.
Shiru tayi tana dan mata halamun uncle din yana nan?
Kai ta girgiza, dan haka da sauri ta ce
"Wow, kinga gidan ki kuwa kawas?
Murmushi tayi tare da janta d'aki.
"Mu shiga daga ciki ke dai.

"Allah kin dace a gidan,ga shi kin dace da sugar dady..
Harararta tayi jin an sako uncle,
"Ke ni barni munyi fad'a..
Ido ta zaro tana cire gyale.
"Da uncle din?
Baki ta cinno tare da 6ata rai kamar gaske.

"Toh ki sauke,dan rule number one na Aunty ta ce ba'a saurin fushi da miji Hajiyata.
Baki ta ta6e tare da fad'in
"Da budurwanshi fa yake ce ma dorling a gabana fa,ki gane mana..

Shiru tayi tana nazari,
"Shi ya ce miki budurwanshi ne?
Kai ta girgiza halamun a'a.
"Amma harda fad'in wai sunyi missing nata kinga irin dariyar ma da yake mata tukunna?
Kwafa tayi tare da girgiza kai.

Dariya Laila ta sa,
"Lalle ana Son uncle da yawa abin harda kishi haka?
Juyo wa tayi tana yatsine fuska.
"So kuma? Kamar ya?
Harararta Lailan tayi da kallon kar ta raina mata wayo.

"Ni ina gane so ne ta hanyar in kana kishin abu yarinya,abinda ya had'ani da Fahad kenan muka 6a6e,dan ina son sanshi da yawa a time din.
"Amma kila fa koh wata y'ar uwanshin ce fa ki bincika.
Tunani tayi na zancen Lailan,da wannan tasa ta basar da zancen Feenah dorling suka fito parlour.

Abin sanyi ta dakko mata suna fira Uncle ya fito yaci ado cikin k'ananan kaya sai kamshi yake.
Duk'awa tayi tare da gaishe shi,dan haka da fara'rshi ya amsa yana tambayarta y'an gida sai wani duk'ar da kai take cikin wai kunya.

Farida ya kallo wacce ke murmushi kamar ba ita ba ce dazun.
"Bari zamu fita kila mu dawo tare da Alhaji Nasir ayi abinci damu.
Kai ta kad'a tana murmushi,
"A dawo lafiya.
Fita ya yi yana kad'a kai.

Da sauri Laila ta juyo tare da zungurarta,
''Kai wallahi na fasa auren yaro k'awata sai Sugar Dady,dan Uncle dinki ya had'u Allah da gani zai iya love...
Harara ta sau mata da sauri tare da fad'in

"Bana son iskanci fa..
Dariya ta sa tare daga kafad'a
"Seriously kinsan ni bana 6oye abu a rai ai ba muna-muna tsakanin mu kawas,koh hardani cikin kishin?
Shiru tayi tare da kafeta da ido.

"Kenan nima ina son Uncle wai?
Kai ta kad'a mata tana dariya.
"Of course, in har kina kishin shi toh believe me,you're in love with him Hajiyata...
Tsam tayi tana murmushi, kenan da gaske itama tasan so?.

Da wannan suka shiga kitchen d'in a tare aka fara baje basirar iyawar k'awayen biyu dan uncle da abokinshi.
Flasks uku suka batse da abinci iri daban,ganin fruits yasa Laila ta ce suyi juice da haka ake sace zuciyar mutum inji Auntyn ta.

Kan kace mey tuni gida ya bud'ade da kamshin abinci.
Flasks uku suka batse da abinci iri daban da abin sha mai sanyin cikin y'ar kula doguwa.
Da ido kawai su Saifu suke binsu ganin irin iyayin da yau ake zubar wa cikin gidan dan sarai sun san Laila da Farida a school.

Uncle din ne ya fara shigo wa lokacin suna parlour Laila na fad'in ita gida zata kar ai mata fad'a dare ya yi.
"Kiyi hak'uri uncle yana zuwa sai mu tafi mu kai ki har gida..
Shiru tayi tare da amsa sallamar,da hannu yake mata nuni da wai ta dakko mayafi.

Tashi sukai har Lailan tare da ajiye Sultana a kasa wacce ta d'aura kanta bisa cinyarta sukai d'aki.
Mayafansu suka dakko tare da dawo wa parlourn lokacin Uncle ya dawo yana fad'in
"Bissmillah..

Zungurar juna suke suna kunshe dariya ita da Lailan,ganin su Uncle din sai suka nutsu tare da karasa wa suna musu sannu da zuwa.
Ko'ina suke kallo gwanin sha'awa ga nan kamshin delicious ya bud'ade ko'ina.

"Sannun ku da gida..
Zama sukai shi da Alhaji Nasir din dan gaisawa da amarya y'ar mitsila da yaran.
Uncle ta kallo a kai sa'a shima ya kallota,dan haka da ido take nuna mishi dining halamun wai ta zuba?

Alhaji Nasir ya kallo yana sosa keya, shi kam duk yana kula dasu,dan haka kai kawai ya gyad'a mata.
Tashi tayi tare da nufar
dining din.
"Laila..
A hankali ta kira ta kamar kiran munafukai dan haka sai ta juya.

Da hannu take yaficota halamun tazo,kai duk'e ta tashi tare da isa wajen dan taya ta tare da mata rad'an tafiya zatai.

"Mun zuba Uncle..
Juyo wa ya yi tare da fad'in
"Ok,sannun ku..
Alhaji Nasir ya yafico suka nufi dining din yana kallo Laila.
"Yauwa Uncle,dama tun dazun dama Laila take son ta tafi na ce ta bari mu kaita in ka dawo.

Kai ya kad'a cikin murmushi
"Mun gode Laila da ziyara.
Cike da kunya tana murmushi ta kad'a kai suka koma d'aki suna dan zungurar juna ta kafad'a tare da satar kallon su Uncle duk suna kallonsu.

Kai Uncle din ya kad'a suna dariya shi da Nasir.
Yarinta dad'i.
Ganin haka yasa su Saifu ma suka bar wajen Sultana kuma tabi su Farida.

"Kai mutumina kayo babbar sa'a, irin wannan garar ai koh Momyn Nur(Matarshi) albarka.
Dariya suka sa suna cigaba da aika d'a'amu.
"Wato ina wani tunani..
Kai Uncle din ya dago yana murmushi.

"Anya bazan jarraba kawar taku ba...
Dariya Uncle yasa yana kad'a kai.
"Ni dai ba ruwa na in girma ya fad'i..
Lemo ya kora yana lumshe ido.
Gaskiya ya dan fara yadda da batun Nasir na ya tsinci dala a kale.
Murmushi ya yi yana kad'a kai.
Ga koshi,ga kuma kwanan yunwa.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

39_Washegari jirgin safe ya biyu suka tattara suka tafi gaisuwa ma Umma.
Kwanan su hud'u suka dawo dan islamiya ga kuma hutu ya kusa karewa.

Kwana goma kenan da rasuwar mijin Umma.
Yau suna makaranta har lokaci ya gifta ba Uncle ba dalilin shi,gashi tayi kiran har ta gaji ba answer.
Su Saifu ta kallo wanda suke dan tsaki kad'an halamun zafin rana.

Sultana ta jawo tare da fad'in su fita kawai sai ga nan kiran Uncle din.
"I'm sorry,ku hau abin hawa please in kunzo zan bashi gamu hanyar gida naje dakko Feenah ne a airport nai latti in kunzo...

Dum taji gabanta ya fad'i,sai dai ganin su Saifu sun sa mata ido yasa tai yake tare da kashe wayar.
Dubu kawai gareta a cikin jaka,fur mai taxi ya ce sai dai ta fita ta kar6o kamin su Saifu su fita dan baza su shanya shi ba.

Sako kanta kenan cikin parlourn da niyar yin sallama taja ta tsaya baki a sake.
Sanye take da cikin suit na mata bakake mai wando ta yafa gyale iya kafad'a kamar hijab.

Rungume take da Uncle bisa kafad'arshi ya zagayeta da hannunshi biyu daya a kanta yana ta aikin lallashinta da fad'in
"Shhh,it's ok...
Ji tai numfashinta na sama,dan haka da sauri ta rufe ido lokacin da Feenah ta dago tana kad'a ma Uncle kai halamun toh taga Faridan

Ido suka had'a,dan haka da sauri ta koma da baya tare da nufar inda ta fito ido taf hawaye tana had'a hanya,kiris take jira tasau kuka.

"Ina kud'in Farida?..
Saifu ne yake tambayarta ganin tai tsaye a kansu tana kallon wani waje.
"Farida...
A tunzure ta kalloshi lokacin da hawaye ke saukar mata cikin karfi ta ce
"Ban sani ba kai,kaje ka kar6o...

Gaba d'aya yaran suka kallota harda mai taxi cikin mamaki,dan haka a tunzure Saifu ya fito tare shiga gidan yana hararar tsawar da tai mishi suka ci karo da Uncle din a bakin parlour dan haka sai ya kar6o ya dawo.

Hawayen ta goge,tare da d'aukar jakarta da ta Sultana da lunch boxes nasu sai ga Saifun a tunzure ya mika wa mai taxi kud'in yana warto jakarshi.
Ido ta rintse,bai dace kishin Uncle ya shafi yaran ba,dan haka da sauri ta bud'e ido tare nufin bawa Saifun hak'uri har ya shige.

Da sauri ta bi bayanshi tana fad'in
"Saifu...
Banza yai mata yana tafiya cikin sauri.
"Saifu...
A masife ya juyo tare da fad'in
"Meye?
Ido ta zaro ganin yadda ya yi,jin tai shiru kawai sai ya wuce yana

"That's why I hate step moms,I hate them all..
Shiru ya yi ganin Uncle din da Feenah a tsaye duk suna kallonsu.
Kuka ya saka tare da nufar gefensu ya shige parlour da gudu.

Farida Uncle din ya kallo yana k'ank'ance ido cikin 6acin rai,da sauri yabi bayan Saifu,ganin haka yasa ta sunkuyar da kai tare da sakar kuka.
D'aya bayan d'aya suke wuce wa suna shiga parlourn su Nass harda harara.

Ita dai Nafisa kanta ya kulle,shin Farida bata san wace ita ba koh mey? Dan kishi take ga kwance a fuskar Faridan,dan haka take ta fahimci meye silar ganin kallon da Faridan take mata itama ta shige.

D'akinta ta nufa,yau d'aya taji gidan ya mata zafi daga zuwanta.
Dan haka sai ta zauna a bakin gado tare da sakar sabon kuka tana tuno da Feenah bisa kafad'ar Uncle.

"Toh wacece wannan y'ar gayun da uncle ke rarrashi?..
Zuciyarta ne tai tambayar,dan haka sai ta tsaida kukan ta hau tunani.
Iya zamanta da Uncle bata ta6a sanin yana da wata y'ar uwa mace ba balle ta ce yana da muharrama.

Koh gidan Abbanshi suka je shi kad'ai suke samunshi sai Umman Uzairu da ya musu d'aki d'aya a gefen gidan kan a gama nasu ginin...
Kai ta dago jin an kwankwasa d'akin tare da murd'a wa.

Doguwa ce mai dan kaurin jiki fara da gani ta gaji da waye wa.
Murmushi ta sau mata tare da rufe kofar ta shigo.
Hawaye ta goge itama ta k'akalo mata murmushin.

Cikin nutsuwa ta tako tare da dan d'osa na wa a gadon ta zauna yadda suke dan gogar juna.
D'akin Feenah take kallo,jin shiru yasa Faridan ta dan saci kallonta.

Murmushi Feenah tai mata sai ta ga kamar Uncle ne ya yi.
"Nice room..
Kai ta kautar tana dan jin sanyin yadda ta yabi d'akinta.
"I'm sorry Aunty nah..
Kallota ta sake yi,duk sai taji wani bankwarakawai jin babba ta ce mata sorry.

Kai ta sunkuyar cikin jin kunyar matar.
"Laifin Bros ne da bai fad'a miki wace ce ni ba may be.
Dagowa tayi baki sake tare da maimaita
"Bros?
A hankali.
Kai Nafisan ta kad'a halamun taji tana murmushi.

"Bama kama koh?
Kasa tai da kai da sauri tana kad'a mata kai.
Ji tai dama kasa ta rabe ta shige ciki dan kunya.
"Tabbas basa kama amma tsayinsu d'aya da farin fulanin Umma da suka gado wanda sai yanzu ta kula da hakan.

Murmushi Feenah tayi tare da kad'a kai ganin yadda Faridan take.
Cikin sanyin murya ta ce
"Ina yini..
Dariya Feenah tasa,oh yau taga y'ar mitsila da kishi,dan haka take yadda kishi ba ruwanshi da girma koh k'ank'anta.

"Na same ku lafiya?.
Kai ta kad'a har yanzun taki yadda su had'a ido.
"Ya hakuri?
Hannun Faridan ta kamo tana murmushi, farad daya har ta shiga ranta.

"Mun gode Allah Farida..
A hankali tana dan janta da fira har ta dan sake kamin ta batta ta kimtsa ita kuma ta nufi inda su Uncle suke.
Kitchen ta nufa da zummar d'aura musu abu mai dan sauki kad'an ganin ba kowa a parlourn.

Tana cikin aiki Feenah ta shigo tana dan mata murmushi.
"Sannu mu barki ke kad'ai..
Juyo wa tayi tare da murmushi tana girgiza kai
"Ba komai.
Karaso wa tayi tare da fad'in
"May i?
Tare da nuno girkin da hannunta.

Kai ta hau girgiza mata tana fad'in ta barshi ta huta kawai.
Ba dan taso ba ta fita a kitchen din ta nufi inda aka sauketa ta cire kaya.
Kitchen din suka leko,dan haka sai ta bar abinda take ta kallo su,daga Uncle din har y'an mazan kowa baida walwala in banda Sultana.

Ci kanki ba wanda ya ce mata har suka bar kofar kitchen din sai Sultana dake mata bye-bye tana murmushi halamun fita zasuyi.
Kai ta kai kasa har ido ya cika da kwalla ganin irin kallon tuhumar da Uncle ke mata sannan da kallon tsanarta cikin idon su Saifu.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

41_Sun kai kusan minti biyar daga uncle din har yaran ba wanda kwakkwaran motsi sai kallon-kallo a tsakani.
Wani lokaci a chan baya ya tuno lokacin da Fatima ke lugude akan Nass Faridan na kok'arin rafka mata mociya a ka.

Ido ya rintse tare da fad'in
"Ya Qadir..
Kai ya dafe tare da zuba wa su Saifu ido wanda su ma shi suke kallo kamar masu neman abinyi.
"Ke nan da gaske dama Umman Farida ba Mom nata bane Dady?

Kallon Saifun ya yi zuru ba amsa,dan haka sai ya wage baki tare da kai halamun ba ita ba ce..
Zuru yai mishi..
"Ok ka sani kenan Dady?

Nass ya kallo,kan yai motsi Amjad ya dauro tashi.
"Da gaske kena. akwai step Moms masu kirkin Umman Farida Dady?
Duk ido suka zuba mishi da son jin amsa kamar yadda ya sa musu?

Kenan wannan ne gyaran da Feenah ke fad'i ya gano koh mey?
Tunani yake,dan haka da sauri ya kad'a halamun shi din ne..
Toh amma meye laifinshi aciki meye laifinshi?
A ina ya...
"Dady...

Kallosu ya yi,ashe fa amsa suke nema..
Yake ya yi tare da fad'in su ci abinci in ana cin abinci ba'a magana..
Natan kowa yaci tare da ture na siya gefe.

Ita kwa tana zama ta ciri wayanta tare da danna kira.
A hankali ta furta
"Umma..
"Na'am Farida,kun tashi lafiya?
Kai ta kad'a kamar tana ganinta.
"Ina kwana Umma...
Shiru tayi bayan wannan, dan haka tuni Umman ta gano akwai wani abu,dan batajin da wanda zai fad'a mata Farida da halinta.

"Kinyi sanyi Farida,koh ba lafiya?
Murmushi ta k'akalo tare da girgiza kai tana hawaye.
"Ba bu Umma...
Jim Umman tayi,zuwa chan ta ce
"Farida ki kara hak'uri kinji, kiyi hak'uri..
Kuka ta sa mata tana girgiza kai.
"Umma dabarata ta kare kan su Saifu,ni har naji auren bana yin shi.. Ki taimakeni..

Kuka take,dan haka tuni ta rikita Umman,ta sani abu ne mayuwaci da zai sa Farida kuka koh da kuwa a bata mata.
Tana da hak'uri da barkwanci,zai wuya ka ga kukanta sai dai murmushi kullum kamar gonar audiga.

"Na sani Farida,na sani,amma ki gane hakurin ki shi zai sa su sake fahimtar gaskiyar ki halin ki a gare su,sannan duk tsiya kar ki yarda ki daga muryar ki sama da ta Uncle dinki kinji?

Hawayen ta goge dan tuna yanzu,
"Umma kiyi hak'uri na furta,in ba haka ba ba zan ji dad'i ba.
Duk abinda ya faru ta karanto wa Umma
"Umma ai banyi fitsara ba koh?
Jim Umman tayi kamin ta ce
"Kinyi hankali Farida,tabbas wani abin sai hanjinki,ki koyi rike sirrin gidan ki tun yanzu ba komai zaki na fitar wa ba.

"Yanzu ina so in har sunci toh na yau ya wuce,bazan hanaki kwatar y'anci ba,amma kiyi a hankali,ki sa ido za kiga sauyi Insha-Allah..Hawayen ta goge tana mai fatan haka har sukai sallama.

Yunwa take ji,dan haka sai ta fita bayan ta wanke fuska,amma duk da haka zaka fuskanci tai kuka.
Duk suna a parlour banda Uncle din.
Kowa kok'ari yake ya kalle ta.

Abin kai yau harda kwashe plates nasu sun kai kitchen.
A dan sace ta kallosu, duk kallonta suke har Sultanan duk inda ta motsa.
"Koh baku koshi bane?
Kai suka d'auke da sauri tare da girgiza mata halamun sun koshi.

Kujera ta jawo tare da zama dan karyawa, sosai taji dad'i da ta ga abincin siyan basu ci ba,amma duk da haka taki ta ware kamar da.
Ga ciwo da mararta take mata.
Bud'e kofar uncle din taji da halamun takunshi da kamshin turarenshi ta maze.

A kanta ya tsaya yana yiwa yaran magana da baki suna girgiza kai.
Kanta duk'e bisa kofin tea duk da tasan yana kanta amma taki ta dago.
"Gobe Feenah zata dawo,in akwai abinda ki ke bukata in kun gama sai mu fita shopping..

Kofin ta sauke kasa tana kok'arin kai hannu bisa abinci,dan haka a takaice ta  amsa da babu.
"Babu..
Fita zaiyi, amma sai ya zauna bisa kujera shi da yaran,ba mai magana sai karar TV har ta gama.

Kayan ta kwashe sai Sultana ta tashi tare da bin bayanta.
Yau daya har ya tsoraci fushin Farida,dan haka Allah-Allah yake gobe tazo Feenah ta bashi shawara.

Har dare bata bin ta kansu,sai ma d'aki da suka kule ita da Sultana bayan sun dawo a islamiya.

Washegari kamar kullum ta had'a wa kowa lunch box nashi har na uncle din kamin su fito.
Fuskarta suke kallo,a sake take sai dai har yanzun ba wata walwala.

Kujera kowa ya ja tare da zama.
"Ina kwana uncle..
Murmushi ya yi tare da kad'a kai, jin yai shiru yasa ta kalloshi a takaice.
Ganin yana murmushi yasa ta sake yi koh baiji bane.
"Oh sorry,Lafiya, hope kin tashi lafiya?
Kai ta kad'a tare da fad'in
"Uhmm.

Har aka gama suka tafi tamkar wasu kurame sai kallon-kallo kawai har suka zo makaranta.
Kamar kullum kowa ya fuce sai ita bayan ta sauke Sultana.
"Farida..
Kiranta ya yi ganin zata fita.

"Na'am,
Juyo wa tai tana kallonshi,
Kud'i ya mika mata kamar kullum ta ce na jiya ma yana nan.
Kai ya kad'a, dan haka sai ta sake yunkurin fita da sauri ya sake fad'in
"Farida..

Bata motsa ba,haka bata juyo ba,dan haka sai ya samu damar fad'in
"I'm sorry...
Har ranta taji kalmar, dan haka a dan sace ta kalloshi har sai taji kunya babba ya ce mata sorry.

Kai ta d'auke ba yabo ba fallasa, dan haka bazai gane ta hak'ura koh a'a ba ganin ta fita tana daga mishi yatsunta kamar kullum.
Murmushi ya yi tare da tada mota har ta wuce rike da hannun Sultana yana kallonsu ta mirror kamin ya wuce.
****

"Yau fa na fuskanci yake kawai ka ke tun zuwan ka office.
Pen ya kad'a tare da sakar ajiyar zuciya.
"Koh y'ar mitsila ce?
Murmushi ya yi tare da kad'a kai.
"Ka bari kawai,tun jiya yarinyar nan ta d'auke  wuta kamar wata babba Allah ta iya fushi.

Gemu Nasir yake shafawa yana dariya.
Jin yai shiru yasa yaci gaba.
"Kuma kasan irin fushin Halima yarinyar nan gareta mai sa kai nadamarnan koh baka shirya ba...

Dariya ya kece da ita harda kykakyatawa yana fad'in
"Anzo wajen,saura kad'an.
Ido yasa mishi da rashin fahimta,dan haka da sauri ya daga mishi hannu.
"No zaka fahimta gaba kad'an tunda har ta fara yanayin Halima.

Pen din ya ajiye tare da girgiza kai.
"Haka ka ke ai da an magana sai ka kauce hanya,shawara nake nema ni ba shakiyanci ba Nasir..
Dariya shi dai yake tayi yana kad'a kai,dan haka kawai sai uncle din ya sa mishi ido.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

42_Wanka kawai tayi ta shiga kitchen tare da ciro markad'e ta hau abinci.
Haka kawai taji tana son Nafisa dan haka koh gajiya bata bi ba ta hau girki.

Hayaniyar yaran taji,wanda ke nuna sun dawo kenan daga dakko Feenah,da fara'arta ta fito dan tararta.
Waya ta shigo tana yi halamun tana sauraren d'ayan bangaren.

Murmushi tayi tare da ajiye jakarta tare da fad'in
"Hon...I want a divorce..
Da sauri uncle ya kallota har yaran da Farida,da sauri ya warce wayar ganin zata kara magana ya harareta tare da kashe wa.

D'aki ya ce su Saifu su tafi ganin tana nemar mishi kuka,dan haka sai Faridan ma ta juya duk da tana iya jiyo su daga kitchen.

"Ba dan haka na baki waya ba,in kuma so ki ke muyi fad'a toh bissmillah.
Kukan tasa tana fad'in
"Bros banzo kasar nan dan na koma ba,na gaji da gafara sa banga kaho ba,Ummanshi ta rasu bama kasar, Abba ya rasu,kwana goma kamin nazo har an mata da yazo..

"Mey muke nema da bamu samu ba?
"Koh kud'in da suke diddika mishi yake zaunarshi baya tunanin a kasarshi anfi bukatar mu?
"Burina zama likita na zama,amma ba burina na bautawa masu jan kunne ba,kasata nake kishi,nan nake da burin taimako amma sanda ya murkusheni na fara bauta musu...

Ido kawai Uncle yasa mata yadda take magana ba koh shan numfashi cikin masifa.
Tunaninshi wai dama mata in an ta6o su basu iya fad'a bane kamar Farida koh kuma hali ne yazo d'aya?

Murmushi ya yi tare da tashi ya nufi kitchen,
"Bani ruwa Farida..
Juyo wa tayi duk tana jinsu,dan haka ba musu ta bashi da cup.
Wala Allah in ta kora na sanyi taji sa'ida.
Kofin ta mika mishi bayan ta shanye ya sake kara mata wani.

A dan sace ta kallo shi tana goge fuska halamun taji kunya.
"Sannu toh..
Fuska ta marairaice dan haka da sauri sakko tare da tsugunawa a gabanta tare da riko hannunta.

"Ki gane Feenah ba wai ina bayan Salis bane,at least ki bashi dama ta karshe tunda ya ce zai gyara,sannan ki saurara gobe ne yai alkawarin har yara zasu taho, ina rokonki kibi a sannu ki kuma cire batun saki,ban son ji.

Kai ta kad'a,
"Ji yadda little Hali ke kuka a waya Feenah ba kyau fa zalunci..
Fuska ta marairaice,
"Raina ya 6aci shi ne dalilin baro masa ita amma kar ka tona kasan raina kamar nai tsuntsu dan na mata yayen dole...i'm sorry..
Kunne ta kama kamar yara in sunyi laifi.

Murmushi ya yi zai magana sai ga nan wani kira ya sake shigo wa.
"Kar ka damu ka nutsu ka bari goben ku karaso,tana nan a guna.
Feenahn ya kallo yana nunota da hannu ya tashi.

Jin shiru yasa Faridan fito wa d'auke da flaks tana mata murmushi.
"Aunty sannu da zuwa..
Murmushi tayi tare da kad'a kai,
"Sannu Aunty Farida,ya aiki?
Kai ta kad'a tana tashi da konawa dan had'a komai.

Da dare bayan ta nutsu tana a d'akinta ya kwankwasa.
"Dazun muna magana a mota bamu karasa ba.
Kai ta kad'a tare da zama.
"Yauwa,nima yana raina abin gwara da kazo.

"Bros,da farko kai kuskuren dasawa yaran ka tsanar *MATAN UBA* wanda har ya zamana ta zama dabi'arsu ya kuma bi jikin su suke musu kallon duk d'aya.
Kai ya kad'a yana jinta.
"Na biyu baka kaunar kwa6arsu wai dan kar Farida ta sarar su in na fahimci dalili..

"A duk abu na na nan duniya bros akwai mai kyau akwai marar kyau,bazai ta6a yiwu wa ace duk MATAN UBA na duniya halin su d'aya da su Tabawa da Jamila ba,ya kamata ka koyar da k'anka da yaran ka haka.

"Farida yarinya ce,wacce bai ma dace ace tun yanzun ta iya rike ragamar k'anka da yara kamar su Saifu fa,but thank God,yarinya ce mai zuciyar manya,in har ka kyalla da kyau zaka gano son faranta wa iyalan gidan fal cikin ranta ka kula da kyau.

Tabbas duk wani kuskure na Uncle a yau ta k'ak'kabe mishi tass wanda ya duba yasan yai kuskure.
Parlour suka fita ta sanar wa su Saifu duk abinda za suyi in har Farida sun fito tare.

D'akin Faridan ta kwankwasa ta amsa tare da bud'e mata ta shigo.
 Kusa da ita ta zauna tare da riko hannunta tana murmushi,
"Zan ari bakin Bros da su Saifu na sake baki hak'uri, and su ma yanzu zasu baki believe me..

"Farida..
Kallota tayi ganin ta zama serious sosai dan haka sai ta nutsu.
"Kamin nan ina son na baki wani tarihi,ta yu zaki fahimci wani abu daga ciki na abinda yasa zaki kara d'aura belt naki ki kuma bawa Uncle da yaranshi tabbaccin akwai MATAN UBA na kwarai a kusa.

Ido ta sa mata,dan haka tun daga haihuwar Uncle ta fara bata tarihin kalubalen da ya fuskanta a hannun su Tabawa har girmanshi.
Kuka take da idonta jin wai duk wannan masifar Uncle ya ganta a hannun su Lami.

Dafata tayi itama tana goge hawayen tuno da rayuwar yayan nata a hannun MATAN UBA
"Farida 'abin da aka gasa wai shi ya ga wuta' inji y'an iya magana,hak'uri da juriyarki ita zata sanya ki fidda wa Bros tambari da ya buga nasu Tabawa,bai da laifi in anbi ta wani bangaren,dan ance in maciji ya sare ka in kaga tsumma ma gudu ka ke.

Kai ta jijjiga,
"Insha-Allah zan basu mamaki,Insha-Allah daga yanzu zasu ga banbanci,dan na kara tsanar mugu tun daga jin labarin su Tabawa.
Murmushi tayi tare da fad'in
"Na gode Farida,nasan zaki iya,Allah zaya sanya miki hannu soon.

Murmushi tayi ta kad'a kai.
"Muje parlour.
A zaune suka same su duk sun sanya Uncle d'in a tsakiya.
"Oya,ga nan Aunty Farida ku bata hak'uri.
Kallota tayi da sauri.
"Aunty basu fa min komai ba..
Kai ta jijjiga
"I know,amma sai sun bada.

Kallosu tayi tana musu da kai halamun su bata
"Kiyi hak'uri..
Cewar Amjad, kan yai shiru Nass ma ya bayar sauran Saifu dake ma Feenah yake.
Y'ar hararashi tayi duk Faridan na kula,dan haka sai tai murmushi, abadan bata tunanin Saifu zai iya fad'in tai hak..

"I'm sorry Aunty Farida,daga yau baza mu sake komai ba sai yadda ki ka ce...
Ido ta waro waje baki sake tana kallonshi yayin da shi kuma yake kallon Feenah halamun ya yi yadda ta ce toh.

Wonder shall never end,'Aunty Farida?
Ido ta karkad'a ganin Saifun ya matso tare da kama kunne yana sake fad'in sorry yana kallon Uncle dake murmushi ganin Faridan nayi.

Saifun ta kamo tare da cire hannunshi daga kunnen tana dariya.
Kamar gaske shima Saifun sai ya fara yana sissinke kai,dan haka sai ta dungure mishi kan da sauri ya tafi kamar zai fad'i ta riko shi suna dariya.

Eh lalle ya gano inda ya gaza,ya gano ta inda ya 6ata,dan haka sai ya kallo Feenah tare da lumshe mata ido yana duk'ar da kai halamun ya gode,kan itama ta rausayar tana murmushi halamun he's welcome.

Uncle din Farida ta kallo tana murmushi, bayan duk sun nutsu har yaran sun tafi d'aki dan bacci,kai ta sunkuyar ganin shima ya kallota,a yau wani lamari taji yana zarya cikin kwanyarta game da Uncle wanda ta tabbatar shi ake kira da 'Kauna' dan tausayin rayuwarshi.

Yanzu waye zaice Uncle shi yaga wanchan rayuwar ta baya? Tasan yanzu sai tarihi..
Lalle ta gode Abbanta da ya bata Abban su Saifu,in har ita ce Farida Ahmad ita kwa zata shayar da uncle mamaki har sai ta matar dashi ya ta6a rayuwa a hannun su Lami.

Kan ta sake dago wa still idonshi a kanta,da sauri ta sake yin kasa dashi cikin kunya tana murmushi,duk Feenah na kallonsu tana girgiza kai, lalle da wani babban aiki a gaba,ja kuwa.
By

Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

43_A kitchen suke suna had'a breakfast harda su Saifu da Aunty Feenah yau koh bacci basu koma ba daukin zasu ga yaran Feenah.
Abinda su ka yi su Saifun ke miko wa Farida lunch boxes nasu tana jera wa cikin nishad'i suna tad'in su.

Su kansu yaran a yau wani farin ciki suke ji a dole sun taya Farida shiga kitchen duk da taimakon Feenah.
A mota ma haka,kowa ka gani yana cikin nishad'i.
Dan haka Uncle tuki yake yana musu murmushi dan jin dad'in yau.

Kamar kullum ya sauke su kowa ya zago yana mishi peck kamar wasu larabawa gwanin sha'awa su na fita.
Juyo wa yai bayan ya gama da y'an mazan yai ma Sultana a goshi yana jan kumatunta tana dariya.

Ido Faridan ta sa musu, kullum zai ma kowa amma nanda ita.
Sauke Sultanan tayi tare da kallonshi kamar yai mata amma ya kasa.
Ba tare da ta kawo komai na ita ta kai baki tare da mishi bisa gefen kumatun shi.

Waje tai ta barshi baki sake suna mishi bye-bye ita da Sultana suna murmushi.
Hannu ya daga cike da kallon Faridan,da halamun ita koh a jikinta ma kamar ba ita tayi ba har suka wuce.

Tuki yake yana tunanin Farida,tabbas ta sauya,dan a da bata mishi koh da bai mata.
Mudubin gaban motar ya kallo tare da ta6o kuma tun yana murmushi, kai ya kad'a, a hankali ya sau sassanyan kid'a tare da sakar ajiyar zuciya har ya isa ga office.
Hmmm,Uncle something! Something!!...😜

Ita kam har Laila sai da ta zuba mata ido tana kallo ba koh kiftawa ganin yadda take murmushi ita kad'ai tana lumshe ido.
Iska Lailan ta furzar tare da fari da ido ta ambaci
"Ya Rabbi...
Kallota Faridan tayi tana murmushi,ganin ta tsareta da ido yasa ta ce
"What?

"Uncle...
Ido ta zaro tare da fad'in
"What?
Kai Lailan ta dungure mata tana hararata.
"Wannan murmushin na Uncle ne for sure..
Wayence ta fara tana dan harararta.
"Very funny..
Tare da bud'e littafi tana kicin-kicin da fuska.

Baki Lailan ta ta6e tare da gyara zama..
"Ki ma yarda mata wallahi u r in love,cos wannan shegen murmushin '6aunar' naki ban yarda dashi ba yau.
Kallota tayi tare da yin dan jim,aji ta kallo,tasan revision ake dan haka bata sa ran da zasu samu first period, dan haka da sauri taja ta waje.

Hannunta duk biyu ta rike tare da marairaice mata.
"Yes i'm in love Laila,buh I don't think Uncle na sona ni k'awata taimaka.
Karasa wa tayi tana sauke kai kasa cikin marairaita.
A dankalin gefen ajin Lailan ta zaunar su rike da hannun juna.

"Anya Farida kina yin yadda Aunty ta ce kuwa?
Baki ta turo gaba tana kunkuni,dan haka da sauri Laila ta hararota.
Hannunta ta sake damka cikin marairaice fuska
tana fad'in
"Yanzu komai ki ka ce zanyi i swear Laila..

Zama Lailan ta gyara tana fari da ido cikin iyayi.
A sannu ta hau mata iyayi tana zayyano mata harda irin taryar da Auntyn ta ke wa mijinta da irin sallamar da take mishi.

Fuska ta yatsine da dauri tai da ita kamar taga abin amai.
"Yook, dan Allah kar ki sani amai, wannan ai kazanta ce,ina ma laifin kumatun tunda dama yana ma su Saifu.

Harara Laila ta sau mata tare da ture hannunta tana kok'arin tashi ta riko ta.
"Zancen gaskiya zan iya komai banda wannan, gaskiya tsantsani nake...
A tunzure Laila ta ce
"Tsantsano y'ar kayan haushi kawai..

Baki Faridan ta turo,
"Eh naji ke ce komai ke in kinyi aure kije kiyi tayi..
Tsaki Laila tayi tare da tashi,
"Cikani toh yar nema.
Tashi tayi tana mata magana ita kuma tana toshe kunne halamun bazata ji ba.
****

Rike suke da little Halee mai sunan Maman su Saifu a hannu daga Faridan har su Saifun kamar su mayarta ciki.
"She's pretty..
Murmushi Uncle ya yi su da Feenah da maigidanta.

"Aunty Feery bani ita dan Allah,I loved babies..
Ido ta zaro tare da fad'in
"Really?
Kai suka kad'a har su Nass,kamin suka fara fad'in
"Me too..
"Me too,
"Me too.
Dariya parlourn kowa yasa jin yaran da santin babies kowa na fad'in me too.

Baki Halima ta yage musu cikin dariyar yara tana kallonsu ,hakan yasa Farida itama murmushi tare da fad'in
"Me too..
Dariya parlourn kowa yasa jin yaran da santin babies kowa na fad'in me too.

Faridan su Saifu suka kallo,yayin da ita kuma ta kallo Uncle tana murmushi.
Ido ya zuba musu barin ma Faridan,kai ta dauke tare da daurawa su Saifu babyn ganin Feenah na mata tsiyar sai ta sullu6o musu.

Da dare ya ce mijin Feenah ya ce tazo su tafi hotel tunda sunzo da yara ga d'akin d'aya ne amma fur Uncle yaki.
"Matan su kwana d'akin Farida,sai Irfan ya kwana gun Saifu gadonshi yana da girma.

Uncle din ta kallo ganin kitika-kitikan yaran Feenah, wannan ai sun cinye mata gadon in sun kwanta.
Kamar Feenah ta gano tunaninta tai saurin kad'a kai.
"Ai na manta akwai d'akin ka ma Bros, Hon,mu kwana tunda gobe ne zamu wuce Kano.

Daga Uncle din har Faridan Feenah suka sa wa ido baki sake,murmushi mijin nata ya yi tare da koma wa d'aki shi da yaran dan su dakko kayan su zuwa d'akin Farida.

Ido Feenah ta kannewa Uncle din tana dariya ta wuce tare da dago wa Farida hannu
"Sabhahul khairr..
Yake ta mata har ta shige,Uncle din ta kallo ganin su kad'ai aka bari.
 Keya ya dan sosa tare da dauke kai.

"Ba damuwa ki zo muyi sharing nawa akwai space.
Juya wa ya yi ya batta nan tsaye tana jinjina kwana d'akin Uncle.
Drawer ta bud'e bayan ta fito a wanka tana wa yaran Feenah yake dake kallonta.

Su har yanzun mamaki suke wai wannan ita ne matar Uncle din su.
Murmushi suka mata ganin ta d'aura hijab bisa kayan baccin ta dau waya tana musu sai da safe.
Kai suka kad'a tare da kwanciya suna dan kus-kus.

Ra6e-ra6e ta fara,anya bazata kwana parlour ba kawai?
Kai ta kad'a tare da murmushi da zummar juya wa taji bud'e kofar  Feenah.
Yake ta mata ganin tana kallonta,
"Au baki kwanta ba Faridee?

Magana zatai taji takun Uncle sanye da jallabiya,corridorn ta sawa ido,dan haka ganin su tsaye yasa shima ya sa musu ido.
Kitchen Feenahn tayi tana kunshe dariyarta rike da feeder a hannu.

Ruwa shima ya dakko yana ma Feenahn yake,da mamakin su sai ta nemi waje cikin parlourn ta zauna tana sake fad'in sai da safe.
Yake Faridan ta mata tare da wuce wa tana kallon Uncle din har ta kule corridor.

Feenah ya hararo wacce ke kunshe dariya ta mike.
Da kai ta nuna mishi halamun ya wuce kawai ba gardama.
Kai ya girgiza yana murmushin yadda ta mayarsu kamar yaranta.

A bak'in kofa ya samu Faridan wacce ganinshi yasa ta kule ciki.
Iska ya furzar tare da kad'a kai, yau Feenah ta kwaso mishi aiki kawai.
D'akin ya murd'a tare da bin bayan Faridan har wata fad'uwar gaba yake ji a yau.
Wa yaga 'Tijara,wai dukan Miji da asubar fari.😹
By

Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

44_A tsaye ya sameta tsakiyar d'akin tana raba ido,juya wa ya yi tare da sanya mukulli a kofar ya dan kallota.
"Ki zauna man..
Yake tai mishi tana sake k'arewa d'akin kallo.

Ruwa ya tsiyaya a cup yana sha tare da kallonta ta gefe ido ganin har yanzu taki zama.
Tunaninta d'aya labarin da Aisha ta bata,gana y'ar yarbawa ya isa ta guji kwana d'akin Uncle..
"Farida..

Kalloshi tayi cike da tausayin kanta,toh mey ma yasa bata ce zata kwana a kasa bisa d'akinta ba?..
"Ki kwanta man..
Yake tai mishi ganin yana daukan pillow zai d'aura bisa kujerar gefen gadon mai hannu d'aya.
"A'a Uncle bari ni na kwanta achan d'in..

Galala yake kallonta ganin da sauri ta rarumo pillow,
"No ki kwanta a gadon yau kawai nan zai min..
Murmushi tayi a dole ita ta samo dabara,
"A'a, ai ya ma kad'an 2sitter ne ba matsala zan kwanta.

Kai kad'a yana kallonta da mamakin yadda take d'ari-d'ari dashi a yau.
Gadon ya haye ta yadda zata samu ta shigo ta tsukukun wajen.
Yake tai mishi tare da ajiye pillow ta zauna rike da waya.



Akan photon su ta tsayar da idonta wani tafkeke yai kyau duk da a nesa take kalloshi.
Sauka ya yi tare da isa ga fitila zai kashe ya kallota.
Kwanciya tayi tare da damke ido kamar wanda yasata baccin dole.
Kai girgiza tare da murmushi ya kashe fitilar.

A hankali ta fara bud'e ido rike da waya a hannu duk ta takura cikin hijab d'in.
Dan haske ta gani masu kyalkyalin blue da pink bisa gefen gadon cikin bed lamp.
Satar kallonshi tayi taji yana adu'a tare da tofe ko'ina ya juya.
Cikin sand'a ta tashi tare da cire hijab din ta ajiye gefe tana huci.

Wayar ta ajiye tare da fara itama adu'ar kamar yadda ta saba ta kwanta.
Juyi tayi sai lokacin ta tuno da pad din dake like a jikinta,dan haka sai ta sau ajiyar zuciya tare da yin hamdala tana murmushi.

Juyo wa yai kad'an dan ganin koh tai bacci yaji shiru,idonta a kanshi,dan haka su na had'a ido tai saurin tamke nata.
Murmushi ya yi tare da da yin rigin gine yana bud'e Gallery.
Hotonan Sultana yake kallo wanda ya ta6a d'aukan ta a d'akin Farida.

Murmushi yake tare da shafo fuskar Sultanan ganin yadda tai kyau ranar.
Na gaba yake yana duba sauran,a hankali ya dawo baya kad'an tare da yin jim ya zuba wa wayar ido.

Dariya suke shi da Sultanan sa6e da ita bisa kafad'arshi yai musu selfie ga chan Farida a bayan su tana musu dariya.
Zooming yai yana mai sake kallota tai tsaye rike da k'ugu tamkar tasan zata shiga tai kyau.

Bangaren Faridan ya kallo,idonta rufe halamun bacci na son d'aukanta.
Murmushi ya yi,yarinyar tana matukar burgishi ya rasa dalili,barin ma a y'an kwana biyun nan...
Ajiyar zuciya ya yi tare da ajiye wayar ya kwanta.

Ido ta bud'e tare da zuba mishi ido,murmushi tayi tare da rufe idon tana gyara kwanciya,a hankali har bacci ya fara fizgarta.
~~
Hannu take nuno mishi tana murmushi halamun jinjina a karon farko tun aurenshi da Farida yau yai mafarkinta.
Tako wa ya yi ganin tana kok'arin juya wa ta barshi amma tai mishi nisa,dan haka sai ya soma kiranta.

"Halima!..Halima bari kiji kar ki tafi ki barni....
"Halima!..
"Halima"...
Zaune ta tashi jin tamkar a mafarki ana mata rad'a.
Wayarta ta lalubo tare da tashi ta haska shi ganin d'akin dulum.

A zahiri ma kama sunan Haliman cikin baccin shi yana dan mutsu-mutsu kad'an da kai.
Fuska ta yamutse tare da mai mata kalmar
"Halima kuma?
Cikin mamaki.

Tabbas tasan mafarkin Maman su Saifu yake dan jiya taji Aunty Feenah ta ce little Hali takwarar Maman su Saifun ne.
Uncle din ta kallo jin yai shiru yasa da sauri ta kashe wayar ta kwanta.

Mike wa ya yi halamun ya farka a mafarkin tare da jan douwar ajiyar zuciya.
Agogon waya ya kalla kusan ukun dare da wani abu.
Kai ya girgiza tare da sauka ya shige band'aki.

Tana kallonshi yadda yake jero nafila tare da kwararo adu'o'i wanda yawanci na Halima ne.
Tun tana iya kirgawa har wani sabon bacci ya sureta.
Washe gari tana ji yana tashinta da nufin tai sallah yana fita ta sake sabon juyi dan sam jiya bacci rabi da rabi tayi.

Kallonta yake bayan ya dawo daga masallaci ba bu halamun tai sallah, dan haka tuni ya gano a halin da take.
Har zai juya ya fuskanci a takure take dan haka sai ya dakko bargo tare da rufa mata ya rage karfin a.c yana dubenta.

Sosai mafarkin yau ya tsaya mishi a rai,tun rasuwar Halima yakan yi mafarkin tazo mishi babu walwala barin ma lokacin auren su Fatima.
Jingina yai da pillow,amma yau na daban ne,dan matuka ya gano wannan zuwan na daban ne.

Murmushi ya yi yana kallon hoton sun dake manne a bango.
Tabbas mutuwa mai yankan kauna ce,dan ta raba shi Halima rabuwa ta har abada.
Ya sani da har kullum baida madadin Halima a duk a aurenshi.

Har yanzu ita ke da mulkin birnin masarautar zuciyarshi,
"Farida...
Kai ya kad'a.
Yasan nata ba so bane,tana burgeshi ne kawai domin aksar wasu halayenta sukanyi shige da na Halimenshi musamman ta fuskar fara'a da hak'uri,shagwa6a da yarintarsu mai ban sha'awa.

Yana zaune yau koh baccin ya kasa koma wa sai tunanin Habibiyarshi yake a juma ya kallo Farida.
Ya kwata ya tasheta ganin lokacin shiga kitchen nata ya yi amma sai ya bari,yasani tana da matukar kok'ari dan haka yau d'aya ya bari ta huta har sai ta motsa dan kanta dan yasan revision suke.

Juyi tayi duk a zaton a gadonta take wanda take sakata ta bararraje,kallota ya yi jin a hankali tana adu'a da halamun har yanzun baccin bai saketa ba.
Murmushi yai yana kallon yadda duk gashinta ya yamutse gwanin kyau ribbon yai gefe guda.

A zabure ya sakko ganin zata sake wani juyin wanda daga shi sai dai tajita a tiles da sauri ya daddafe hannu yai mata k'awanya yadda ta zamo rabi a kujera jikinta rabi a hannunshi.

Ido ya zuba mata,jin ta wani iri yasa da sauri ta bud'e ido sai warai a nashi.
D'akin ta karewa kallo a hankali ta tuno inda take dan haka da sauri ta mirgina kan kujerar tana dubenshi.

Tabbas da taci kasa ba da ban uncle ya taro ta ba.
Murmushi yai mata,dan haka itama sai ta mishi tare da kallon agogo.
Ido ta zaro tare da kallonshi ganin ya zauna,a zabure ta mike tana kiran
"Ya Rabbi,wayyo..
Ribbon din ta gyara tare da yayimar hijab nata cikin sauri zata fita.

Da kallo ya bita har ta ta sa ta fuce,dan haka sai ya bi bayanta.
Kitchen ta nufa tana kukkunna wutar parlourn jin wai yau har su Saifu sun rigata tashi ga nan hayaniyar su.

Ja tai tsaya da tsanin mamaki baki sake,Uncle ta kallo wanda shima ya karaso ganin ta tsaya ya kallo Feenah da ke fadin
"Surprise...
Murmushi tayi tana bin komai da ido, lalle yau da ta tafka lattin da bata ta6a ba har 7:10am tana bacci.

Karasa wa tayi cike da jin dad'i tana fad'in
"Kai Aunty amma na kin taimake mu,gaba d'aya na sha'afa da bacci yau...ina kwana.
Murmushi tayi tare da amsa wa tana dago wa Uncle yatsu dake musu murmushi.

"Yanzu kije yau na hutarki har lunch kuje ku dawo.
Murmushi ya yi tare da juya wa dan shiga wanka.
Kwarai taji dad'i, duk da taki yarda amma ganin Feenahn taki bata yasa ta zari tsintsiya tare da fita parlour.

Jim tayi,yau dai d'aya ya kamata ta gyara d'akin Uncle dan koh ba komai chan ta kwana,dan haka sai ta nufi chan ta hau gyara jin yana a band'aki.

Fita take kok'arin yi ta tsaya tare da kurawa hoton ido,tsaye suke shi da Maman su Saifu yaran na zaune kan kujera da tsohon cikin Sultana.
Juna suke kallo cike da so da kauna suna murmushi rike da hannun juna.

Kai ta dauke daga hoton,haka kawai taji tana dan kishin Maman su Saifu dan tasan ita kad'ai ta mallaki son Uncle abinta har ta koma gashi har a bacci yana ta sururunta.
Waje tayi dan isa ga d'akin Sultana,da mamakinta yaran Feenah shima sun hutarta wankan Sultanan har tasa uniform.

Cike da marmarin zaman su tare da iyalan Feenah suka rabu dan isa ga Kano,dan haka sai aka d'aura daga inda aka tsaya in har ka d'auke jituwar su dasu Saifu da ta kara karfi,ta Uncle kuwa iyakarta da d'akinshi gyara shine kawai cigaba.
***

Sunyi hutu,wanda daga shi zasu shiga SS2,duk da mai tsayi ne amma Uncle kad'ai yaje duba mahaifan nashi ganin Aisha ta kawo musu ziyara yau.

"Yanzu ya zamuyi Saifu? Ga nan John bai dawo ba balle yai mana refilling ga yau uncle zai dawo miya kawai gareni..
Tunani suke na gas da ya kame gashi ba kero ba hot plate dan ba wuta,mai gadi ya je gida ya dawo.

Yaran ta kallo,tasan iyanzu yaci duk su fara jin yunwa barin su Saifu acici.
Fuska ta washe tare fad'in
"Idea..
Tashi tayi duk suka bita da kallo har ta isa gun dining.

Gwangwanin madara ta girgiza tana murmushi da kallon su Saifu dan tuna wa da wani lokaci chan baya zamanin Fatima.
Cornflakes ta zuba wa kowa tare da jerawa a faranti ta bawa kowa nashi.
Dariya suke dan tuno musu da baya gashi Aisha a gurin.

Guntun dake ciki ta juye a plate tare da dawo wa cikin yaran tana kunshe dariya,a hankali suka fara tariyo baya suna gyara zama.
"Ku tsaya a deba ma Sultana sai ayi wawar..
Kai Sultana ta girgiza tana dariya,dan haka sai ta ce

"Ready?
Kallon juna suke suna dariya ganin a hankali tana tuna musu da rayuwar da sukai da ita chan baya dan haka da karfi suka ce "Yessss.
Kai ya sako cikin gidan har zai bud'e parlourn ya bari yaje ga window in da yaga labile a dage yana lekensu sanda ta ce ready.

Tana kwa ajiye plate din aka hau wawaso hannu baka hannu bisa faranti suna kyalkyala dariya.
Dariya shima ya fara ciki-ciki yana kallon Faridan yadda suka zama basu maraba  da yaran wajen wawaso.

Tsayuwa ya gyara ganin Sultana ta d'auke farantin tana gudu tana lasar guntun sauran sun d'aura a bayanta ta zille musu su na dariya.

Farida ya kallo,wacce
tsuguna tare da dafe baya tana maida numfashi cikin murmushi.
Ido ya zuba mata, tabbas wannan shine mafarkin Halima a kullum tun tana raye, yaranta kawayenta.

Yau ga nan Farida ta maye gurbin in da ta tsaya.
Dariya take harda rike ciki tana nuno gefen su Sultana,dan haka sai ya kallo gun,Nass ke jan plate Sultana na ja,kan ya farga ta kai hakori zata sa cizo yai sauri ya cika shine suke dariya.

Faridan ya sake kallowa, lalle hasashenshi na dangantata da Halima bai fad'i ba,dan yasan d'aya ce tamkar da dubu koh a yara sai an tona.
A hankali ya sau ajiyar zuciya tare da furta
"Bravo Farida...Bravo alaiki wa Jazakillah...

Hmmm.
Lalle *Tuna baya shine roko*.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

47_Tsaye yake a bakin gate na makaranta ya zuba ma gate din ido.
Murmushi yake ganin yadda suka sanyata a tsakiya kowa kok'ari yake ya bata labari suna dariya.
Sosai ta sake fito mishi cikin uniform din wanda yasha shan tela (shape) da hijab iya kafad'a.

Duk yaran sun fita haske,amma a yau gani yai ta fisu haska wa barin na in tai murmushin nan.
Kai ya d'auke daga kallonta ganin sun karaso kusa.
Yau da gobe kam a gareshi wai ta wuci wasa,ya yi surrender,ya kuma amshi lalle ya kamu da so a karo na biyu.

Kalloshi tayi bayan sun shiga tana mishi  murmushi ganin idonshi kir a kanta.
Wayan cewa yai tare da kallo su Saifu yana tambayar su karatu.
Murmushi tayi tare da kallon hanya kawai.

Da nacin Nasir Abbanta ya ce ya yarda ai auren amma ya kasance wani term,zo ka ga murna gun Laila da Alhajinta kamar mai auren farko.

"Hajiyata soyayya tayi a rayuwa,kar kiji yadda nake ji na a sama dan kulawar Baby..
Dariya Faridan ta sau,
"Wollah in kince babyn nan ba karamin dariya yake ban ba.. Ina ma laifin Alhaji..

Hararar ta tayi tana tsuke fuska.
"An fad'a miki mu irin ku ne?
Hararar ta rama tare da fad'in
"Meye damu?
Kafad'a ta daga..
"Kiyi kallo yarinya,in nai gaba zaki biyo bayana ne,a soyayya ba fulako mud'in da so Hajiyata..

"Ya kirani Baby na kirashi Baby,meye aciki? Duk acikin so ne..
Tsam tayi tana tunanin zancen Laila,tabbas tayi iya kok'arinta ganin Uncle ya sota amma abin ya faskara..

Dafata Laila tayi,
"Ni na saki kuka?
Kallota tayi da sauri,hannu ta kai bisa kuncinta jin damshin hawaye.
Murmushi tayi tare da girgiza kai
"Koh kad'an, ba ke bane...
Hannunta ta ruko.
"Toh waye?

Kuka ta sa mata ba k'ak'kautawa, dan haka tuni ta rud'e ta hau lallashi.
"Ni sai dai naga ana ta so amma ni banda ni ba dole nai kuka ba,Uncle bai sona Laila..
Tsam Lailan tayi.
"Wa ya fad'a miki? Believe me, yana sonki sosai.

Murmushi tayi tana goge kwalla.
"Fad'a kawai ki ke,amma ke kanki kin shaida baya min duk yadda Alhaji Nasir yake miki a gaban ko ma waye, a ganina shi ne so mai cike da tsantsar kulawa..

Hannun Lailan ta kamo.
"A da bana damu wa Laila,amma yanzu ina damuwa in har naga irin naku salon,matuka yana burgeni, nakan ji ina ma zan samu koh rabin hakan gurin Uncle..

Kai ta girgiza,
"Nasan bani da ranar samu,dan yadda yake nuna kula a su Saifu haka yake min,babu wani dan maganar soyayyar nan in a romantic way fa Laila.

"Ni yadda na fuskanta kusan dani da mai dawainiya da gidanshi duk d'aya nake,sassanyan kalam nashi fa shine
'Farida,sannu da aiki..
'Farida kin tashi lafiya?
'Farida na gode..

Murmushi tayi,
"Ina jin ciwo,amma ban sanar wa da kowa ba hatta Umma,ke ma zance ne ta ratso kawai na furta..
Rungumota tayi cike da tausayin kawar tata ta fara lallashi.
"It's ok..

Bayan ta nutsu ta fara fad'in
"Amma fa baby yasha fad'a min Uncle na matukar sonki Farida,har yakan ce naku salon na burgeshi sau tari in yazo tad'i..
Murmushi tayi tare da girgiza kai.
"Hmm,fad'a kawai ki ke,dan ranar chan na gama tabbatar wa bana gaban Uncle.

"Har d'aki fa na kai mishi shekaran jaka jiya da ruwa amma Uncle yana gama sha kin san mey ya ce?
Kai ta girgiza tana kallonta.
Kwafa tayi tare da kad'a kai.
"Wai na gode Halima..

Ido Laila ta zaro
"Wace ce haka?
Baki Faridan ta ta6e..
"Momyn fa su Saifu..
Dariya Laila ta sa..
"Toh meye ba ta mutu ba?
Harararta tayi tana turo baki.
"Eh amma ta bar mishi sonta har yanzun, ranar fa yana bacci yana ta sururunta dan so..

Dariya sosai Laila tayi,
wanda har yasa ta kule,Allah bata jin tana da tsananin kishin Uncle sai ranar da ya kirata da Halima..
"I love him wollah Laila,har mafarkinshi nake,amma ki duba shi ta machacciya ma yake ba ni ba.
Da kalar tausayi ta karasa tana duk'ar da kai.

Kamin Laila tai magana an kwankwasa d'akin..
Uncle ne,dan haka tuni taji bata son tashi.
Ido ya kura mata ganin yadda take k'auda gefe tabbas halamu ya nuna tai kuka.
"Ga nan Nasir yazo..
Kai ta gyad'a kawai,dan haka cike da mamaki ya juya.

Tare suka fito duk suna zaune a parlourn har Uncle.
Ido ya sawa Faridan ganin taki kalloshi suna gaisawa da Nasir.
"Baby nah...
Kasa Laila tai da kai ganin Uncle tana murmushi.

Duk ido suka sa musu daga Farida har Uncle din ganin yadda Nasir ke kashe Love a gabanshi.
"Jiya d'aya amma na kasa sukuni har sai yanzun da nai arba fa,amma ke kamar ma ba kiyi missing na ba fa My sugar...

Uncle Farida ta kallo ba koh kiftawa wanda ya sau baki yana kallon Nasir,tabbas yasan da biyu yake,sai dai suna had'a ido da Farida yai saurin yake mata hak'ora.
Kitchen ta wuce bayan ta yake mishi nata kamar ta d'aura hannu a kai ta sau ihu..

Tashi yai yana hararar Nasir dake mishi dariyar keta yai kitchen, dan haka da sauri ya dawo kujerar kusa da Laila aka hau tad'in soyayya ba ruwan su.
Ruwa take jera wa faranti ya shigo kitchen din dan haka sai tai tsam jin kamshin turarenshi.

Tako wa yai tare da isa wurin da take ya tsaya tare da tayata dakko kofuna.
A dan sace ta kalloshi idonshi bisa kanta.
So yake ya tambayi mey ke damunta amma ya kasa.
"Sannu da aiki..
Sosai ta kalloshi ido cikin ido,wannan shi ne kawai kalmar da zai fad'a mata?

Kai ta d'auke cike da takaici tana kad'a mishi kai.
Farantin zata d'auka sai ya rike halamun zai d'auka.
Hannun nashi ta sawa ido jinsu bisa nata tare da sake kalloshi.

Dan janye wa yai bayan ya kula yana fad'in
"Oh! Sorry..
Kar6a yai tare da fita bishi da kallo,plates da serving spoon Laila ta shigo tare da ruk'unk'umota ta baya cikin murna.
Tare suka fita su Uncle har sun isa dining suka isa dan zuba musu.

Kallota ya yi,
"Ku kunci ne?
Kai ta kad'a halamun eh.
Da sauri Nasir ya amshe.
"Laila bata ci ba,dan haka ku zauna sai nafi ma ci in ina kallonta.
Murmushi Faridan tayi,a zahiri ba suci ba dan ta su Saifu take su ci su tafi islamiya.

Nasir zata zuba wa ya girgiza kai
"A'a bani na fara zuba wa Baby da kaina ku kuci naku..
Galala Uncle ke kallonshi ganin wannan rawar kan abokin nashi yana dan kallon Farida.

Dai-dai da ruwa in Laila zata dauka tuni zaiyi sauri ya mika mata cike da kulawa suna ma juna murmushin so.
Kasa Farida tai da kai sai chakalar abincin take da chokali ta kasa ci.

D'aki ta kule dan takaici bayan ya tafi rakasu.
Kan ta farga har hawaye ya hau sintiri bisa kuncinta.
Iyanzu tana da muradin taga ana gwada mata so irin na Laila,amma bata tunanin zata samu.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

49_Murmushi ya yi tare da kai hannu bisa lallen yana fad'in
"Oh,sorry,ya zugin?
Kasa ta zamo tana murmushin kunya tare da kad'a kai halamun ya daina tana mai jawo abinci ganin lokaci yana ta sake ja.

"Abinci Uncle kar ya huce..
Sakkowa ya yi yana jijjiga kai tare da zama a gabanta baki ya ki rufuwa.
"Ni fa yunwar ma bana ji tun kiran Abba na farko da batun nan a karo na biyu.

Kai girgiza tana mai bud'e plate din tana murmushi,
"Ni zan fara fesawa Aunty Hafsa a waya kuwa gobe in Allah ya nuna.
Murmushi ya yi yana mey kallon agogo.
"Nasan yanzu Feenah sun tashi,bari na riga ki..

Murmushi tayi tare da debo abincin a chokali ta mika mishi bisa hannunshi halamun ya kama lokacin da yake sauraron ringing na wayar.
Wayar ya nuno mata tare da nuno bak'inshi halamun ta sa mishi jin Feenah ta d'auka.

A sannu take bashi a baki kamar wani yaron goye yana fesa wa Feenah labari cikin murna.
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kai tana sake debo wani tare da mika mishi,bazata ce ga a yanayin da take ciki ba a yau.

Abu d'aya ta sani shine tana jin wani shaukin so da kaunar Uncle ta ko'ina bisa 6argo da jinin jikinta,dan haka abincin ma a da style take bashi tamkar mai tsoron kar ya kware.

Dariya ya saka jin iskancin Feenah bayan da ya bud'e baki ya amshi wata lomar yana jijjiga kai halamun ya gode.
Murmushi tayi tare da sake debo wani dankwalinta na neman fita sai ta cire ta ajiye gefe tare da dagowa zata bashi ya kware.

Ido ta zaro tare da saurin ajiye chokalin ta hau tsiyayo ruwa tana mishi sannu,tarin ya dan sassauta tare da bud'e baki idonshi bisa kanta tana bashi ruwan bayan ta dan kara tsayinta kad'an daga tsugune.

"Uhmm..uhmm
Gyaran muryar Feenah ne cikin waya yasa ya gano ya bar mutum.
Baki yai saurin cire wa a kofin yana fad'in
"I'm sorry..
Ita dai bata san mey suke fad'i ba taji dai kawai ya ce
"Abinci ne" yana kallonta yana dariya.

Famfon bayi ta wanko hannunta tare da sake zama jin har yanzun wayar bata kare ba ta fara cire nama tana ware k'ashi gefe.
"Uhmm..
"Of course..
"I see..
Kawai yake fad'i a takaice yana kallon Faridan.

Murmushi tayi tare da mika mishi naman bisa baki ba musu ya bud'e tare da amsa.
Lumshe ido tai tana mai yin murmushin jin sautin dariyar tashi ita kad'ai ta isa ta sata a nutsuwa.
Kai ta dago zata mika mishi taga yana duba wa halamun kud'i ya yanke.

Ido ya zuba mata a hankali ya bud'e bakin ta sanya mishi yana dubenta.
Plate din ta turo mishi halamun ya karasa tunda ya gama tana murmushi.
Da sauri ya girgiza kai tare da nuna mata hannunshi halamun ba wanki.

Bakin ya bud'e mata halamun ta cigaba da bashi da kanta.
Murmushi tayi cikin kunya tare da yin kasa da kai tana bashi a hakan kai duk'e.

Yatsun ya riko tare da kai naman baki yana kallon lallen,jin hakan yasa ta dago tana dubanshi.
Baki ya kara kaiwa ya bud'e kamar zai cijeta tai saurin rintse ido tana murmushi,murmushin shima ya yi tare da zamewa ya kwantar da kanshi bisa cinyarta.

Idon ta bud'e tare da sauke su bisa fuskarshi,lalle ne ba sai an sanarta yana a farin ciki ba yau,koh kuwa ya manta a inda yake.
Dan haka kai ta k'auda tare da murmushin kunya jin hannunta bisa bak'inshi.

Tad'i yake mata,wanda aksar na Ummanshi ne da Abban shi sai kuwa yarintarshi.
Kamin su farga har lokaci ya ja ba kad'an ba wajen saurarenshi.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

48_Shirye-shiyen bikin su Laila suke,dan haka duk sun shiga busy ganin term ya kusa karewa.
A gidan Uncle kam yanzu hatta yara sun fara fahimtar akwai wata a kasa.
Dan rimi-rimi suna a cikin walwala da yai mistake na koh suna ne yanzu zasu kasa gane kan Faridan.

Tun abin bai damun Uncle har ya fara kulewa da sabon halin Farida.
Haka kawai shi ba wai da gangan bane yake danganta ta da Halima,ya rasa dalilin da yasa a yanzu komanta in tayi sai yaga kamar irin na Halima ne, a nan toh zai sa6a suna sai a samu matsala,karshe sai su Saifu zasuyi mishi sasanci.
 ***

"Koh ni bana tunanin nayi irin d'aukin nan naki fa Laila..
Murmushi tayi tana duben lallen da ake tsantsara musu.
"Ba zaki gane ba,duk da ina jin fargaba amma ina a farin cikin zama ta Baby Allah kuwa gobe.

Dariya sukai,kai Faridan ta kad'a.
"Ina tausaya miki Maman Nurr, kar tai miki sallama da luguden kin kwace mata Baby..
Dariya suka sake sawa harda tafawa.
"Allah nima ina dan tsoron matar,dan sam bata da fara'a,dad'in ki d'aya an raba mazauni sai kashe love lafiya.

Fari tai idonta tana murmushi,
''Ki bari kawai Hajiyata,har na haskoni wollah..
Kai Faridan ta girgiza tana cije le6e na mugunta.
"Zaki tsara,wallahi za ki yi bayani ne muna gefe..
Harararta tayi,
"Wa ya fad'a miki kowa ma irin ki ne?

Kai Faridan ta dungure mata tare da fad'in
"I see,muna nan ai.
Sun had'e sosai,ga gyaran jiki ga lalle.
Tun dazun suka je saloon wash&set tunda sun sa mai.

Sai dare kusan tara ya d'akko ta a gidan Auntyn su Lailan sai cije le6e take wai farcenta zafi inda lalle ya shiga tana yarfe hannu.

Parking yai chan gefe tare da kunna fitilar cikin motar yana mamakin raki irin na Farida.
"Ina ne?
Hannu biyun gaba d'aya ta nuno mishi tana shisshitu.

Iya dubenshi shi baiga komai ba sai kyakkyawan bakin zanen da yasha jan rani.
Kamar wacce aka mintsina haka ta dan zabura jin zugi tana shisshitu kamar wacce taci yaji tare da marairaice fuska tana duban hannun.

Hura mata ya fara da iskar dake bakinshi yana fad'in sannu a hankali.
Shiru ta danyi tare da zuba mishi ido yadda ya rirrike hannun nata yana hura su tuni sai ta kama tasha tana murmushi.
D'agowa ya yi jin shiru,suna had'a ido tai saurin fad'in

"Ahh,shhhh zafi..
Hurawar ya cigaba da yi sai kwa tai shiru suna duban juna cikin murmushi,a dan jima ta hau shisshitu yana fad'in sannu.

Mota ya tada duk da haka hannun yana bisa fuskarshi yana dan fiffitawa.
Murmushi take tare da dunbenshi cikin sassanyan kallo,sosai take jin dad'in nuna kulawar Uncle a yau.
Juyo wa ya yi ya dan dubeta da sauri ta d'auke kai

"Ya daina?
D'ayan hannun ta bashi wanda ta hau yarfe wa dan shakiyanci tana fad'in
"Wannan ma..
Murmushi ya yi mai cike da sauti yana kallon hanya tare da hura wanda ta bashi.
"Gayu da wuya,but i like it dan yai kyau.

Ido ta sa mishi tana murmushi, jin tai shiru yasa ya kallota cike da jin dad'i, a hankali ta janye hannun daga nashi cikin kunya tana sissinke kai tana murmushi ganin sunzo gida.

Kallota ya yi shima yana murmushin, lalle yau da halamun an manta da y'ar mitsila ake tare hala?
Horn yai yana mai kunna fitilar motar tare da yin baya ya jingina a kujerar kan a bud'e tana dubenta kasa-kasa.

Sarai ta kula,dan haka fur taki kalloshi har aka bud'e gate sai ya kad'a kai yana murmushi.
Duk daga parlour suka fito suna tutturo baki ga halamun Sultana tasha kuka.

"Oh,i'm sorry Sultantee,rungumota tayi ganin ta saka sanya kukan tana fad'in sai jiranta take bata dawo ba ta d'auka ta 6ata ne..
Dariya suka sa har uncle din
"Allah Aunty Farida na dad'i kin fa jima ga kukan Sultana.

Kallo Saifun tayi tana sake basu hak'uri.
"Ban san zamu jima ba haka nima duk fa na gaji nai kewar ku yau kawai.
Da kallo ya bisu ganin sunbi bayanta tana sa6e da Sultana a baya ba ma wanda yake ta tashi wato Farida da ce tasu yanzun.

Kai ya kad'a yana murmushi, jin dad'in yaranshi tabbas nashi ne,dan haka yake kara jin Faridan a chan kasan ranshi a kullum barin ma dai yau.
Bayan su ya bi,a parlour ya tarar su Sultana na shafa gashin da yasha wanki sai kyalli yake tana fad'in yai kyau suna mata dariya.

Sosai kam yai kyau gashi ya kara tsayi sai walwali yake anyi baya dashi.
"Mu fa yunwa muke ji mun kasa ci tun dazun muna jiran ki.
Ido ta waro,
"Haba Saifu,kuma in ban dawo ba fa koh bana nan ba fa kyau jira...

Ido suka sa mata har uncle din
"Ina zaki?
Ganin yadda suka zira mata ido yasa tai saurin gyara zancen.
"No ina nufin in nai tafiya fa.
Kai su ka kad'a,
"Ai tare muke tafiya ma.
Yake tayi tana jijjiga kai halamun haka ne.

Tashi Uncle din ya yi jin ana mishi waya ya ciro a aljihu.
'Uzairu'.
Daga wa yai tare da sallama suka gaisa,sanarshi yai ya kira Abba shi zai tafi gida ne za suyi magana.
Tashi yai yana mai kiran Abban yana musu halamun su ci kamin ya dawo.

Shiru Uncle din bai dawo ba har yaran suka tashi ta kai Sultana ta kwanta bai zo yaci abinci ba.
Har zata wuce itama d'aki sai ta kasa,haka kawai ta raya mata ta kai mishi in yaso ta duba koh lafiya.

Kwankwasa wa tai,jin ya ce yes yasa ta dan tura a hankali rike da faranti mai d'auke da plate da ruwa da cup.
A hankali ta ajiye tare da kok'arin fita ganin yana waya sai yai mata da hannu halamun ta tsaya.

"Umma..
Shiru yaji,dan haka sai ya sake karyar da murya.
"Amincewar ki kawai muke bid'a Umma wannan karan dan Allah ki cika min burin nan..
Shiru ya yi tare da daina fara'r da yake jin kukan Umman, dan haka da sauri ya fara bata hak'uri.

"Umma ban san zai 6ata miki ba dan Allah kar ki min haka zamu hak'ura har Abban,amma ki daina kuka..
"Na amince ne Kabir, wannan ne ya sani kuka ba komai ba,ubangiji yasa ai damu..

Zirif ya mike cike da farin ciki ya toshe baki,kamin ya farga har hawaye ya zubar mishi.
Adu'ar da yake kwararowa Umman ne yasa Farida gano akan  mey ake wayar dan haka tuni itama ta doka tsalle ta dire tare da isa ga inda yake cikin murna.

Wayar ya sauke,kamin Faridan ta ankara cilak ya dagata sama yana sanarta Ummanshi ta yarda zata koma wa Abbanshi.
Kai ta gyad'a mishi tana sanarshi ta fahimta suna dariya cike farin ciki.
Sauketa ya yi tare da ruko hannunta ya zaunarta bakin gado shima ya zauna.

"Na fi kowa farin ciki a yau Farida da naga wannan ranar da su Umma zasu sake zama a inuwa guda,ina a farin ciki.
Kai ta gyad'a mishi itama bakinta yaki rufuwa.

"Nima Uncle nai farin ciki sosai,tun ranar da Aunty Feenah ta bani tarihin rayuwar ka da tasu Umma nake da burin naga sun koma tunda mijinta ya rasu,nasan Abba zai sake sonka a yau su Tabawa sai su mutu.

Ido ya sa mata yana murmushin jin dad'i, kamin ta farga har rungumota dan murna suna dariya,tuni aka ture batun kunya murna ta mirtsiketa.

Sosai ya yake murnar dan haka ba rukon wasa yai mata ba,a tare suka sau ajiyar zuciya suna dariya.
Chan ta dago tare da tuna mey take tana sinke kai tare da satar kallonshi.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

51_Jarkar Farida ta daga tana lekawa,
"Ke kamar na jiyan nan Allah akwai dad'i kamar shayin larabawa.
Dariya Laila tayi,
"Eh shine,kiyi ta sha toh dan har mun fito ta biyo mu dashi wai ya zama ruwan sha na koh sassaken 6aure koh mey ne?.

Kai Faridan ta daga abinta sai kwakwand'a take kamin ta sauke
"In ma sassaken darbejiya ne akwai dad'i chakwai..
Harararta Lailan tayi,
"Ji ta agun,bakin naki ne chakwai din ai ni dai ba ruwana..
***

7:50pm
Uncle ne tare da angwaye sau hud'u suka shigo jin har ya shirya su amare na kule a d'akin Farida.
Nasir bakin nan har kunne sai dariyar keta yake wa Kabir lokacin da suke zama.

Waya ya dakko tare da danna kiranta yana murmushi yaji an bud'e kofar d'akin Faridan.
Ido ya sawa kofar jin taku kwas-kwas ana fad'in
"Hello...

Murmushi ya yi tare da fad'in
"Hi sweetheart...
Wayar ya kashe jin dariyarta,
Sultana ce sanye ita da yar Auntyn Laila da farin gown na yara tana jan kasa.
Tashi yai tare da ware hannu ganin ta taho da gudu ya dagata suna dariya ya dire.

Matuka sunyi kyau da make-up sosai sun kwaskwareta su na bayan amarya gashin nan yasha gyara.
"Ina Auntyn ku?..
D'aki ta nuna mishi tana rad'a mishi wai su ma sunyi wai kyau.
"Really?

Kai ta daga mishi.
Sautin murmushin su da kamshin amare ya fara ziyartar angwayen da karar takalma cikin takun 'yan gayu kwas-kwas.
Dan haka duk ido suka sanya ma kofar barin ma kar ango da Uncle suji labari.

Karasa mike wa ya yi a ranshi yana kiran
"Tsarki ya tabbata ga shugaban halitta...
Murmushi tayi tare da dan sunkuyar da kai.
Mike wa Nasir yai tare da fad'in
"Charkwai mad'agwai..
Dariya suka sa da abokan ango dana amarya banda Farida da Uncle da suka lula duniyar musayar kallo da digar da murmushin so Faridan na dan saukar da kai.

Sanye amaren suke da net brown mai flower bakake da ratsin green kadan na zaiba head ma baki yasha nad'in Turai 'yar adu'a da stones brown.
A yau koh ke baka ce a cikin su kin saje da farare dan make up sai walwali suke.

Ita ta dafo amarya wacce tai wankan green itama bakin nan yaki rufuwa.
Da kafad'a Nasir ya zungureshi,a wayance ya dauke kai yana murmushi tare fara mirza hannun Sultana.

A dan sace ya sake kallota ganin zasu ratsa su wuce ta kusanshi.
Kalloshi tayi,matuka yai mata kyau shima dan ya sake sabuwar shiga da wannan farin tabaron gadon wanda a ganinta shine sirrin kyaun Uncle ta ido.

Kai ta duk'ar tana murmushi tare da fad'in ma su Sultana
"Common.. Common.. Common..
A hankali,da dan gudunsu kwa suka nufe su Sultana na rike hannunta.

Ajiyar zuciya ya sau,tamkar ya janyo baya ace yau ne auren su,dan shi a ganinshi ta ninka kowacce kyau dan ita kad'ai yai tozali da ita ya makance bai tantance sauran ba.
Binsu sukai a baya har yanzun yana dan kallota ya basar har suka isa ga waje.

"Ku sako min amaryata nan da driver d'aya ba kari kafata kafarta.
Nasir suka kallo jin shakiyancin shi suna dariya.
Dasu Sultana da ita kad'ai suka rage,dan haka a dan sace ta kalloshi lokacin da yake bud'ewa su Sultana baya suna shiga.

Juyo wa yai ya kallota,yau d'aya yaji wani kishi na sanya gyale a gefen kafad'a kamar yadda ta saba.
Bud'e mata gaba ya yi,kamar wani sirikinta yau sai wani sissinke masa kai take da munafukin murmushin nan nata.

Rufe wa ya yi a hankali suna kallon juna.
Zaga wa yai ya shiga ganin har sauran sun tada sun wuce.
Juyawa tayi tana ma su Sultana magana akan yadda zasuyi kamar yadda suka tsara.

Kai suka gyad'a mata,dan haka sai ta juyo tare da fad'in
"Good..
Kallota ya d'an yi ganin tana gyara zaman gyalen da warwaron hannunta.

Iska ya furzar yana karya kan mota kamar ya ce lullu6e ko'ina koh a fasa zuwa.
Ya sani da ana zuwa kan kowa bisa matarshi zai dawo dan ganinshi wai tafi ta kowa.😜
By

Feenat Ja'afar.
In anjini chilu, gobe ina da islamiya da walima  sai jibi..
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

_😍😘Ga masoya labarin *MATAN UBA*  I would thank you from the bottom of my heart..❤ but for you, my heart has no bottom😜_...

_Amma fa a gareni ni abadan babu kamar *KIYAYYA* duk da *SAKEENA* na fara daga nan sai *DAN YAU*._
_Yayin da a gare ku wasu suke fad'in  *BARIKI IYAWA* yafi su, wasu su na fad'in a'a *A BAKIN AURENKI* dai._
_Wa'azi ne gare ku kishiyoyi,zan so ku rike a Ranku *BA KISHYA BA CE* 'yar uwa ce in har mun rike wannan kalmar ta *KADDARA CE* daga Allah koh da kuwa Kaddarar ta zama *JUYA* ce  mudin *RABO IN YA RANTSE*_ sai ta zauna...📋✍🏼.

Jumma'@ Mabrook..
Love you all😍.

50_Sannu a hankali bacci ya dan fara fusgarta tana gyangyad'i dan yau ba karamin gajiya tai ba ga aikin gida ga yawon gyaran jiki.
Murmushi yai tare da dan tashi a hankali daga kafafun nata ya dakko pillow.

A bisa lallausan center carpet din da suke ke kai ya ajiye pillown tare da kwantarta kamar wata babyn da ake lalla6awa dan kar ya tashi ya lullu6a mata bargo.
Ajiyar zuciya ta saki tare da gyara kwanciya.

K'afa ya tankwashe tare da zama kamar mai d'aukan karatu yana mai kare mata kallon.
Murmushi ya yi,a hankali ya mika hannu tare da gyara gashin da ya zubo mata garin gyaran kwanciyar ya mayar baya.

Ya dan jima a haka yana kallonta,ya sani da in zai kwana bazai gajiya da kallon Farida ba wanda yake ganinta a baccin ta kara k'awatuwa mishi.
Murmushi ya sake,a hankali ya furta
"Sleeping beauty"..
 
Agogo ya kalla,ba dan yaso ba ya shiga bayan gida dan watsa ruwa shima dan ya kwanta dan gobe yasan akwai jigilar d'aurin auren su Laila.
Cikin nutsuwa yake shirya wa, a hankali ya kan kallota,na jijjiga kai ya yi,na murmushi ya yi har ya gama.

Maimakon ya hau gado ya kwanta sai kawai ya samu kanshi da komawa ga Faridan ya matsar da faranti,a hankali ya sanya kanshi bisa matashin da take yana jan bargo dan kar ta tashi.

Ido ya sa mata jin yadda har numfashi suke had'awa dan kusanci.
Murmushi yau tare da kai hannu saitin bakinta ya zagaye su y'an chukul dasu,daga karshe sai 6àrawo bacci ya sace shi kan ya farga a hakan.

Kiran sallah ne ya tada shi ba dan baccin ya ishe shi ba ya bud'e ido bisa fuskarta bak'inshi dauke da adu'ar tashi a bacci.
Murmushi ya yi tare da tashi jin zai makara ya gyara mata bargo.
Su Saifu ya taso a gaggauce jin an tada ikama.

Ita kam juyi ta ta sake da halamun bacci yanzu ta fara taji ana sallama a wani gun na sallah.
Tsam tayi ido rufe duk da ta kawo wuta abubuwa suna dawo mata na jiya daki-daki.

Ido ta bud'e ta bud'e da sauri tare da tashi tana karewa d'akin kallo,tabbas anan ta kwana.
Gado ta kalla,bata ga halamun an kwana kai ba dan komai yana nan bisa inda yake ga kuma bargo tare da ita.

Gefenta ta kalla,kenan Uncle nan ya kwana?
Tunani take mey ya faru kamin tai bacci,abu d'aya ta iya tuna wa tad'in uncle, dan haka da sauri ta sanya kanta cikin bargon tana leka wa.
Kan ta fito dashi tare da sakar ajiyar zuciya ta furta
"Thank God.

A gaggauce ta mike tare da ninke bargon ta mayar inda yake ta dau farantinta ta fuce dan ma kar ya sake ritsata dan haka koh da ya dawo sai fankon d'aki babu 'yar mitsila.

Murmushi ya yi yana duben wajen tare da tuno jiya,tabbas girma ya kare,dan ya gama zubewa,sannan gaskiyar Nasir da ya ce ya saki jiki yaci duniyar shi da tsinke.
Kai ya kad'a,yana mai aiyana
"Komai yazo karshe..
****

10:02am ya fito yasha farar dakakkiyar shadda mai sirfani yai harda babbar riga kamar ma shine angon.
Duk ido suka sa mishi har yaran wanda su ma sukai shigar shadda da zuwa d'aurin aure.

Murmushi yake yayin kallonta ganin yadda ta zuba mishi ido itama tana murmushi.
Ba tun yau ba ya gano duk randa yasa manyan kaya Farida naso, ya gane hakan ne ta yawan kallonshi da murmushin ta.

Sosai itama tai mishi kyau,barin yadda tai baya da gashin nan sai ta dawo mishi babbar mace mai aji.
Kasa tai da kai cike da kunya tana murmushi rike da serving spoon.

"Wow!.. Dady kayi kyau sosai.
Murmushi yai musu yana fad'in
"Really?
Kai suka jijjiga da sauri Nass ya ce
"Kamar kaine angon...
Dariya suka sa yana kallon Farida da ke dan sato kallonshi tana tayasu.

"Sabhahul khair ya Dady..
Sultana ya kallo yana murmushi,kumatunta ya kamo yana fad'in
"Habibtee Sultantee.. Ya ruhii,kaifa halik?
Dariya tai tana fad'in
"Alhamdulillah..
Peck ya bata yana fad'in
"MashaAllah zan kara kud'in islamiya..

Dariya suka sake lokacin da Faridan ta dawo bangareshi domin zuba mishi tana murmushi
"Ina kwana Uncle..
Kai ya daga yana sake kallonta.
"Lafiya lau,ya ki ke?
Kai ta kad'a mishi tana had'a mishi tea.

Murmushi ya yi tare da kallo su Saifu
"I'm so happy today...
 Da sauri suka had'a bakin fad'in
"Umma zata koma gidan Grandpa right?
Farida ya kallo yana murmushi jin har ta rigashi.
Gira ta daga mishi tana barin wurin dauke da murmushi.

Kai ya jijjiga musu baki ya ki rufuwa,ya sani da kowa zaiyi murnar wannan komen duk wanda ke yinshi.
Dan haka sai yai musu albishir d'in ana gama bikin su Uncle Nasir zasu tafi Kano,dan haka da farin ciki aka gama cin abinci har suka fuce gun d'aurin aure.

Da yamma tare da amarya suka dawo gidan Faridan da tsiraren kawayensu wanda suka gayyata a auren dan shirin dinner.
"Oho,in zaki sha ki sha dan Allah na gaji da dure-duren nan na Aunty.
By

Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

53_Yana kallon su Saifu ya ce
"Ku kai kayan mota..
Bangaren Farida ya kalla a dan sace.
"Ku kar6i nata ma..
Kan ya gama har ta nufi hanyar waje janye da katuwar jaka.
Uncle din suka kallo.
"Dady zamu jima ne dama?
Yawu ya had'iya yana mai sake kallon jakar Faridan da ta fuce.

"A'a, ana gama d'aurin aure zamu dawo dan Monday zan koma office..
Kai suka kad'a tare da janyar jakar Sultana suka bi bayan Faridan.
Tsam yai shi kad'ai a parlour.
"Anya yarinyar nan ba wani abu take shirya wa ba kuwa?
Ya sani da bata ta6a tafiya da irin katuwar trolley haka ba in zasu.

"Ka ce an fasa tafiyar kawai kai kad'ai zaka.
Kai ya kad'a, haka za ayi kawai.
Waje ya fita,da mamakin shi har ita ake dilka dariya a cikin motar,sai dai suna had'a ido ta juya baya tare da 6ata rai tana kallon wani bangaren.
Dan haka sai ya kasa fad'in sun fasa su koma din.

Maimakon haka ma sai ya shiga tare da tada mota yana duben yadda ta juyar da kai gefe.
"Kwana uku kawai zamuyi,dan kowa ya zauna da shiri..
Shiru nan ma bata tanka ba,dan haka sai ya sake shan jinin jikinshi.

Su na sauka Kano a gidan Umma suka yada zango har Faridan.
Sosai ta sake suna ta fira kamar yadda ta saba in sunzo hutu fur taki kallon inda yake har ya fuce kama d'aki.
Sai bayan magriba ya dawo duk suna tsakar gida har su Saifu ana ta labarin bikin Laila.

D'aki ya shiga a zaton shi koh tana ciki.
"Ka dawo?
Juya wa yai jin Umma,
Kai ya kad'a,
"Tun dazun naje gun Abba ne.
Kai ta jijjiga.
"Umma ina Farida?
Karasowa tai ciki,
"Ai sa6ani ku kai,bata jima da fita ba kanta ke ciwo shine ta tafi nayi ta bari kazo ma ta ce za kuyi waya.

Yake yai yana kad'a mata kai.
Abinda bata 6a kenan tafiya ita kad'ai sai dai su kaita, ya sani da zafin na yau biyu ne harda na barin bikin Laila.
"Umma bari na koma gun Abba toh duk yadda mukai dashi zan dawo kiji batu.

Yana fita ya jingina da mota tare da fidda waya yana nazari,iska ya furzar tare da kad'a kai ya hau dailing numbernta.
Karfi da yaji so yarinyar nan take ta sa shi cikin tension wanda a da bai cikin shi.

Dan tsaki ya yi tare da cire wayar a kunne jin ba'a d'auka ba ya sake dailing.
Tsam yai bayan jin ba'a dauka ba.
A abu da yawa Farida zai yi wuya yaga fushinta sai wannan, ya rasa meye in ya kira ta da Halima yake kona ranta haka?

'Kishi ne'
Fad'in wata zuciyar.
Kai ya girgiza,yanzu kenan wannan ne ita nata salon kishin?
Murmushi yai yana girgiza kai har hakoranshi suka fito.
Da ma zata gane irin matsayin da ta taka a zuciyarshi ne mai shige da Halima wanda har yasa yake kasa banbanci dame ya kirata,Halima koh Farida?

Ya sani da daga yanzu ta daina fushi dan ta ciro tuta.
Mota ya shiga.
Shi kanshi bazai ce ga ranar da kamu da son Farida ba,ya sani da tun a baya tana matukar burgishi barin yarintar ta.
"Koh shine son?
Zuciyarshi ya tambaya, dan haka kai ya kad'a dan yarda daga haka son ya girma.

Wanda a yanzu bai jin zai iya rayuwar nisa da Farida.
Dole ya sauke komai ya gurji rayuwarshi kamar yadda Nasir yasha fad'a mishi.
Murmushi yai tare da tada mota ya karya kan mota inda zai sada shi ga 'yar mitsilarshi.

Nasir ya kira sai dariyar keta yake mishi jin bayanin shi.
"Ba fa abin mamaki bane,dan nasha fad'a maka tuni kazo wurin ka kasa kar6a ne kawai,amma 'yar mitsila ta damko wuyanka tamau.
Murmushi yai yana kad'a kai.
"Ni mamakina a yaushe hakan ta kasance ne Nasir,na kasa sanin rana koh lokaci.

Dariya ya sa mishi harda kyakkyatawa.
"A'a wannan abu na Allah,wai budurwa da jika 😹..
"Lalumo dai,ni nayi nan,a gaida 'yar mitsila.
Kai ya kad'a yana dariyar shakitancin Nasir.
***

"Ni abinda ban gane ba Farida wannan uwar jakar da ki ka kin kimo ta lafiya dai koh?
Umman ta kallo tare da turo baki.
"Ni fa na gama zaman Abuja,bazan koma ba yaji nai..
Galala Umma ke kallonta,kan ta farga Umman ta sau dariya.

"Yaji?
Kai ta kad'a tana kai ayaba baki.
"Ba ke ki ka ce na yarda na taho ba,sauran maganar mayi a nan..
Rai Umman ta had'e
"Ke bana son iya shege fa,zatona kin girma ashe har yanzun yarinta na nan bisa kanki..

Ayabar ta ajiye ta hau kukan shagwa6a.
"Allah Umma da gaske nake ni fa yaji nayi,gaba daya Uncle baya sona kune baku sani ba har yau komai Halima,duk randa ta motsa mishi haka zai ta ce min wata Halima da nai magana ya hau fad'in shi ba haka ya ce min ba.

Ido Umman ta sa mata yadda mitar ta ta kare a kan Halima,in ta fuskance 'yar tata ba ma rashin halartar bikin yafi kona ranta ba kamar wannan.
Murmushi tai tare da kad'a kai, lalle kowa da nashi salon kishin,dan haka hannunta ta riko tana murmushi.

"Toh naji bai kyauta ba..
"Amma Farida ina ke ina kishi da wacce bata ma duniyar?
Baki ta zunguro tana kunkuni.
"Toh naji,in fad'a miki wani abu?
Kai ta kad'a har yanzun baki a d'ane.
"Uncle yana sonki hakan yasa yake danganta ki da Halima saboda ita ce kawai yafi so..

Baki ta saka tana kallon Umman.
"Koh ya ta6a kiranki da sunan Fatima koh Jamila?
Kai ta girgiza da sauri tana kallon Umman.
"Yauwa,toh ki gane kina da matsayi gareshi irin na Halima a yanzun shi yasa yake kasa banbance ku.

"In kuwa kinga mutum na kishin ka toh ki tabbatar yana matukar sonki shi yasa bai son wani ya ra6eki koh da kuwa ta kallo ne,dan haka ki d'auka so ne yasa yai miki haka a gun dinner.
Tsam tai tana tunanin maganar Umman har Aisha tazo suka kule d'aki Umma na karanta mata dabarun zaman gidan miji.

"Toh ta ya Aisha zan tabbatar yana sona kamar yadda Umma ta ce?
Zama Aishan ta gyara tana bata darasi.
"Ga hanyoyi da yawa da zaki gane mutum na sonki,kin ki kar6a ne tun da,da tuni an wuce wurin...
Shiru sukai lokacin da wayar Faridan ta hau kara lokacin da Uncle ya kira.

Aisha ta kallo tana nuna mata wayar,kai ta girgiza halamun kar ta dauka.
Dan haka sai ta ajiye Aishan na fad'in
"In dai yana sonki zai sake kira,in baki d'auka ba zai damu..
Dan haka har yai 2 missed call taki d'auka tana murgudawa wayar baki kamar Uncle din ne.

"Toh daga nan fa Aisha mey zanyi?
Murmushi Aishan tayi,tuni fi'ili ya tashi ta hau zayyana mata abinda zasuyi koh Uncle yazo biko.
Da wannan ta tashi tai wanka tare da da sauya kaya.
***

"Bissmillah man...
Maganar Abba suka jiyo a parlour lokacin su na d'akin Umma,da sauri suka leko da kai cikin sand'a.
Baya sukai da sauri Faridan na zaro ido had'i da dafe kirji.
"Uncle?..
Kai Aisha ta jijjiga tana dariya,cikin rad'a ta ce
"Ba na fad'a miki ba..

Leka wa suka sake yi,da sauri suka komar da kai ganin uncle din na dan satar kallon corridorn kamar mey son ganin wani abu.
"Muje..muje.
D'akinsu suka shige da sauri tare da rufo kofa.
A gaban mirror Aisha ta tsayarta ta hau gyarata har dasu powder.

"Toh meye hakan kuma?
Harara Aishan ta sau mata lokacin da ta tuje dankwalin kan nata.
"Ki sa ido,koh a haka zaki je koh powder babu in an ce Uncle yazo?

Galala take kallonta, dan haka bata bi ta kanta ba ta cigaba da gyarata kamar wata 'yarta a gaban mirror.
Zama sukai da sauri jin an kwankwasa d'akin.
Abba ne,dan haka tashi Aisha tai tare da bud'e wa.

Da dan gudu Faridan ta nufe shi dan murnar ganinshi yana mata murmushi.
"Ki je ga chan mai gidan ki a parlour zai tafi,ki taho da abin sha.
Kai ta kad'a mishi tana duk'ar da kai wai ita kunya har ya kauce.

Aisha ta kallo,da sauri ta doka tsalle har da bawa Aishan hannu su ka tafa.
Shi da Abba ne a parlourn, dan haka a nutse su ka shigo kai a kasa rike da faranti da abin sha da Umma ta jera musu.
Ido ya sa mata tukunna ya d'auke kai yana ma Abba yake.

Gaishe shi Aisha tayi yana tambayarta makaranta lokacin da Faridan ke tsiyaya mishi ruwa a kofi.
Duk sai ya ji yau ya bala'in takura a gidan abokin nashi kuma siriki barin ganin Faridan.

Murmushi yake lokacin Abba na tayashi murnar su Umma.
Tashi tai tare da dan duk'awa rike  ruwa a hannu zata bashi,kalloshi tai ta gyalen yana iya kallo gashin da aka gyara a gefe.

Yake yai mata tare da mika hannu zai kar6a,a hankali kamar mai yin rad'a ta ce
"Ni fa bazan koma ba.
Ido ya sa mata, a hankali ya bar murmushin baki sake ya marairaice fuska.

Ruwan ta sa mishi a hannunshi tare da juyo tana wa Abba murmushi shima ta bashi kamar ba ita ba.
Yake yai wa Abba ganin sun tashi yana mai kai ruwa baki,a san sace ya kallosu zasu shige Aisha na dan mangarar kafad'ar Faridan itama tana ramawa kamar yadda suk saba tun yarinta.

Ruwan ya ajiye tare da kallo Abba yana jijjiga mishi kai ba wai dan ya gane mey yake nufi ba.
Wannan shine ga koshi,ga kwanan yunwa 😜.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

54_"Kashe wayar da sauri dan koh ya kira yaji a kashe kinga mun kara mishi tension..
Marairaice wa Faridan tai tana langwa6e kai
"Uncle ne fa,Allah har naji tausayin yadda yai dazun.
"Mtsww...
Tsaki Aishan tayi tare da warce wayar ta kashe tana harararta.

"Baki shirya kwatar y'ancin bane ina ga 'yar dad'i Uncle..
Kai ta girgiza da sauri.
"Ni fa tausayi kawai na ce miki nake ji kar ki min fassara.

Hakan kwa akai,koh da ya tashi tafiya duk da Abba ya ce a kira suyi sallama ya ce a'a zai kira kawai dare ya yi.
Har ya gama komai ya kwanta yana tunanin gashin kumar Farida.
Wayar ya sake gwada wa har lokacin a kashe,ba yadda ya iya dan haka a hakan ya kwana da abin cikin ranshi.

Washegari ma a kashe,dan haka tun tara ya isa gidan Umma achan suka karya ya jira duk suka shirya.
"Dady kaimu gidan su Aunty Farida..
Sultana ya kallo yana murmushi,kamar mai jira da sauri ya kad'a mata kai.
"Ok,muje toh.

A mota Saifu ya ce
"Ta huce Dady?
Juyo wa yai kad'an yana tuki ya kalloshi tare da kad'a kai.
"Ku tayani lallashi ta ce baza fa ta bimu mu koma ba,just imaging.
Ido suka zaro
"Ina d'in Dady?

Ajiyar zuciya ya sau tare da furzar da iska.
"Gidan mu..
Dariya suka fara kunshe wa,dan haka da sauri ya juyo yana dan duban su tare da koma wa yana kallon hanya tare da fad'in
"Ya Rabbi...Please Guys,be serious..please.
Kai suka kad'a mishi.

Su na isa ya kallo su,yake suka mishi,sai yai ajiyar zuciya, yana fatan in taga su Saifu a wuce wurin su wuce jibi gida.
A waje ya tsaya su kuma shige dan ai mishi iso.
Abba ne ya fito da halamun fita zaiyi.

"Kullum tamkar bako ka ke,koh zanyi wa kowa iyaka da gidana banda kai abokina.
Murmushi Uncle din ya yi lokacin da suke shiga.
Daga su Saifu har Faridan ba wanda ya gani,dan haka sai ya fara ware ido.

Magana Abban yai ma Umma tare da cewa uncle zai je baya ya dawo,Umma ta tafi fad'o ma Faridan ta shirya zasu fita inji Uncle.
Yaran ne suka fito sai ware ido yake yagan su tare.
Da ido yai musu halamun ta huce?
Kai Saifu ya girgiza yana marairaice fuska halamun bata huce ba.

Iska ya furzar, toh mey take so ya mata?
Kusa dashi Saifu ya dawo ya zauna.
"Dady ga shawara..
Zama Uncle din ya gyara yana kallonshi.
"Idan budurwata
 ta 6ata rai abu uku nake ta huce har tai dariya..

Kai Amjad ya hau kad'a mishi yana fad'in
"No..
Amma sai Saifun ya hararoshi halamun mey a ciki?
Hannu Amjad yasa tare da dafe kai jin Saifu ya tuni asiri.

Ido Uncle din ya zaro da sauri.
"Saifu? Budurwa fa?
Dan matsawa Saifun ya yi yana sosa keya tare da kad'a kai halamun eh.
"Oh no..
Ido Uncle ya k'ank'ance tare da fad'in

"How old r you?..
Yake Saifun ya yi yana kallonshi kamar ka ce kule yace chass.
"I'm 14..
Baya Uncle din ya yi yana rufe ido tare da dafe kai ya furta
"Saifu...

Matso wa Saifun ya yi yana dariya tare da dafa hannun Uncle din
"Common Dady, I'm only trying to help you out,amma shikenan ba ruwana.
Ido ya sa mishi,dan haka da sai abin ma ya bashi dariya.

Wai Saifu da budurwa? Ya ilahi.
Sosai yai dariya,yasan yaranshi tamkar abokai suke gunshi,wannan ba wani abu bane dan Saifu bai boye ba,amma shi dariyarshi kamar Saifu mey zai iya fad'i ma budurwa?

Fatanshi Allah ya tsare mishi su,dan yanzun ne yake da kalubalai tunda har sun fara sanin wannan.
Magana yake shirin yi sai ga nan su Faridan sun fito,zama ya gyara yana kallon fuskar Faridan.

Gaisuwa kawai ya samu,duk da ba karamin kyau yai mata ba dan da farko har ido ta zira mishi Aisha ta zungureta kamin ta saita kai tana chunno mishi baki.
"Muje koh?.
A dirare ta kalloshi kamar gaske tare da tashi ta fad'awa Umma.

Tare suka fito Uncle din yai mata sallama suka fita.
Yau Uncle harda bud'e mata kofa ma'ana ta shiga,yake tai mishi sai ta bud'e baya ta shige sai Nass ne ya shiga.

Tuki yake in banda dariyar su ba abinda ka ke ji da ya tsomo baki sai ta gimtse fuska.
Iska ya furzar yana yana girgiza kai,shi gani yai ma kamar yaran suna a bayan Faridan,dan ba mai sako shi cikin firar har suka isa gidan Abba.

Duk sun fuce sai ita ta rage bayan ta fidda Sultana.
"Farida..
Juyo wa tai a dirare tare da sa mishi ido.
"Subutar baki ne fa..
Marairaice mata ya yi tare da karkata kai
"I'm sorry...
Yake tai mishi tare da saurin gimtse wa ta fuce.
"Farida..Farida.

Koh waiwayo wa batai ba ta isa ga yaran suka shige gidan Abba.
Iska ya furzar, yarinya karama tana wasa zuciyarshi?
Kwafa ya yi,yasan abin yi.
Motar ya kashe tare da shiga gidan ranshi duk ba dad'i.

Sai dai ganin su cikin walwala tare da su Abba yasa ya sake jin Abban sai sanya wa iyalanshi albarka yake ganan Farida kanta kasa tana murmushi tare da fad'in
"Amin Abba.
Bangaren Umman su Uzairu suka nufa ita da su Saifu.

Murmushi Abban yai yana mai kad'a kai
"Kayi dace Kabiru,iyalin ka yarinya ce,amma tana da hankali sosai musamman in naga kusancinta da yaranka nasan akwai kyakkyawar mu'amula a tsakanin su,Allah yai albarka.

Murmushi ya yi yana kallon bayan su su Faridan dake tsakiyar su Saifu suna magana kasa-kasa tare da kallo Uncle din halamun dashi suke.
"Amin Abba,ya k'afa?
Kai ya jijjiga,
"Alhamdulillah, maganin da ka aiko yana min dad'i in na shafa,Allah kara bud'i.

Murmushi Uncle din ya yi yana kad'a kai
"Amin Abba.
Shiru sukai kamin daga bisani ya ce
"Ni fa Abba yau da daddare nake so in son samu ne a mayar da auren nan gobe Umma ta tare hankali sai yafi kwanciya.

Murmushi Abban yai yana gyad'a kai,
"Mey Umman naka ta yanke? In ta aminta duk yadda kai dai-dai ne Kabiru..
Baki ya wage yana murmushi.
"Itama haka ta ce Abba,naji dad'i bari Abban Uzairu yazo a tsara komai kawai.

Da murna ya nufi bangaren su Umman Uzairu.
Bayan sun gaisa baki yaki rufuwa yake sanarta abinda suka yanke.
Murmushi tayi tare da kad'a kai.
"Allah yaso Kabir,ubangiji ya nuna mana,naji dad'in wannan lamari tun kwanaki a gun Abban ku.

Su Farida ya kallo wanda suke murnar jin da abinda yazo,ido ya sa mata yana murmushi ganin yadda take juya hannunta cikin magarya ta kasa sha.
Alfarmar komen su Umma yasa ta mayar mishi kanta duk'e.
Tashi Umman tayi dan kawo musu ruwa su Saifu ta kira suka bita amsar magarya wai su bar ma Faridan wanchan.

Matsowa yai kusa da ita yana dan kallo waje yana murmushi.
"Ba koh tayi.
Kai ta dago tare da turo baki ta janye kwanon ganin zai tsoma hannu.
Fuska ya marairaice,
"Wai dama baki hak'ura ba har yanzun?

Kai tai saurin girgiza wa tare da fad'in
"Eh,ba zan koma ba ni ka matsa kar Umma ta shigo.
Ido ya sa mata ganin yadda take k'au da kai halamun baza ma ta kalleshi ba.

"Amma na ce kiyi hak'uri fa Farida,kina da rigima fa..
Kalloshi tai da sauri,
"Koh?
Kai ya girgiza,
"A'a, ba wannan ba,yanzu fad'a min meye matsalar sai na gyara?
Kai ta girgiza halamun bazai iya ba koh ta fad'a.

Da mamaki ya kallota.
"Mey yasa toh?
Ido cikin ido ta dubeshi,ba zato ya ji ta ce
"Saboda ba ka sona...
Baki ya saka yana kallonta da mamaki.
Jin ta kwafsa yasa da sauri ta gyara.
"I mean baka damu dani ba,amma ban ce ni dole a soni ba fa...

Murmushi ya yi yana kallonta,sai yanzun ya gano bakin zaren.
Matsawa ya sake yi kamar mai neman shige mata,dan haka da sauri ta ja baya rike da kwanon magarya tana sake chunno baki.

Kwanan yai saurin riko wa yana kallonta ganin yadda take kautar da fuska gefe.
Juyo wa tai tare da kallonshi,kam ta sake riko kwanon da hannu biyu yana ja tana ja kamar wasu yara yana murmushi.

Da karfi taja har tana ciccije wa dan haka sai ya taho tare da sakar magarya ta zube a tsakar ledar.
A tare suke bin magaryar da kallo wacce ke tsere bisa ledar d'aki.
Kalloshi tai,dan haka sai ya daga mata kafad'a yana ta6e baki halamun ba ruwan shi.

Fuska ta hau shagwa6e wa kamin ya farga har ta sa mishi kukan karya tana nuna magaryarta.
Ido ya zaro yana mai kai hannu bakinta halamun tai shiru yana kallon waje halamun kar aji.
Da sauri ya fara tattaro mata yana zuba wa a kwanon tare da fad'in
''Shhh,i'm sorry,bari na kwashe
Cikin rad'a.

Kukan ta tsaida tana kunshe dariya tare da mishi gwalo,jin ta daina yasa ya dago,da sauri ta sake d'aye baki tana nuna sauran magaryar tare da fad'in
"Ummma...
A hankali cikin rad'a ya ce
"Farida,I said i'm sorry...
Yana kallon kofa jin wannan karan mai sauti tayi.

Da sauri ya hau tattare wa yayin da ita kuma take kunshe dariya ganin yadda ya dukufa cintse magarya da ya juyo zata sake sakar kukan shagwa6a tana nuna magarya tare da kiran Umma.

"Lafiya kuwa?
Kai suka daga da sauri ganin Umma dasu Nass a bakin kofa kowa rike da kofi da magarya aciki.
Faridan ya kallo da dan harara kad'an ganin tana kallon Umman Uzairu.
"Umma magaryata fa ya zubar min.

Uncle su Umman suka kalla yadda yake tsincewa yana dan harararta halamun ta tara mishi jama'a.
Murmushi Umman tayi tare da girgiza kai ta juya ta bar wajen,a ranta sai jinjina wa Uncle yake,wato auren yarinya sai ya sa ka dawo yaro.

Kai ta kad'a tana dariya tuno yadda ya dukufa tsina, lalle aiki ya samu manya.
Sosai take son Farida,dan fa abinda 'yarta ta kasa gashi ita tana yi aciki kuwa harda kula da su Saifu.

Juya wa tai tare da sake kallo bakin kofar jin dariyar su Saifu suna kallon cikin d'akin, kai ta girgiza itama tana yin tata kasa-kasa cike da jin dad'i, fatan ta Allah yasa farin cikin iyalin Kabir ya d'aure.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

55_Gaba d'aya ya tattara tare da mika mata daga ita har yaran yana dan hararar su tare da kunshe tasa dariyar yana zama.
Faridan ya kallo wacce ke dariya, kai ya kad'a,koh ba komai yaji dad'i da a dalilinshi take dariyar.

D'ukawa Sultana tayi tare da juye tata magaryar a ta Farida tana dariya ta zauna.
D'aya bayan d'aya suka zo suna juyewa tare da zama suna dariya.
Circle suka had'a,dan haka sai ta turo kwanon tsakiya dan kowa ya iya samu ya sha.

Murmushi ya yi tare da kai hannu zai d'auka ta dan janye tana murmushi.
Kai ya langwa6e mata,dan haka sai ta dawo dashi kowa ya fara sha suna tara kwallo a gefe cikin kofi.

"Dady ka shuka mana bishiyar magarya a gidan mu muna ci kullum akwai sweet..
Dariya suka sa ma Nass har Uncle din Farida yana kad'a kai.
"Toh Abbana,kar kaji komai,amma kamin nan koh taro min shi kar ya wuce zazzau..

Hularshi ya cire tare da bawa Amjad ya tare bayan Nass da ita suna dariya.
Faridan ya kallo lokacin da take sanya wa Sultana a baki tana shirin cizonta cikin wasa tai saurin janye hannun tana yarfe wa.

Murmushi ya yi tare da kallon hannun yana mai jin wani abu na tsirga mishi bisa jini da bargonshi.
Farida tabbas farin ciki ce a cikin gidanshi Allah ya bashi kyauta dalilin wuya da yaci da yaranshi a baya.

Tabbas lokaci ya yi da ya dace ya cike sauran gurbin da ya rage bai cike ba.
A dan sace ya kallota cikin wani yana yi,tai mishi kyau sosai cikin attamfa mai riga da skirt tasha d'aurin turai 'yar adu'a pink dan haka sai ta haska mashi ita tamkar Zahra kusa da wata.

Kai ya kad'a tare da sake sanya hannu dai-dai ta kawo nata har hannun nasu na karo da na juna.
Yatsan ya riko yana kallonta cikin wani yana yi.
Da sauri ta kallo su Saifu duk hankalin su baya kansu sai daga kai duke suna cilla magaryar tana fad'awa bakin su Sultana na musu dariya.

Kiciniyar kwace wa ta fara ya rike yatsun kam kamar zai cire su.
Kan farga har ta tsuguna tare da kaiwa hannun nashi hakori tuni ya cika da sauri yana yarfe wa.
Yake tai mishi tare da 'yar harara tana sanya magaryar a baki.

Kai ya jijjiga yana kallonta tare da kai wajen da ta cija bakinshi yana dariyar zai kamata ne.
Fari tai da ido tare da lumlumshe mishi ido tana murmushi.
Magarya ya hullo mata guda d'aya dan haka da sauri ta bud'e ido tare da ware su kanshi.

Su Saifu ta kallo tare da daga mishi gira,da sauri ya daga mata kafad'a halamun ba shi bane.
Kai saukar yana kok'arin diba ta hullo mishi itama d'aya.
Dago wa yai tare da shima daga mata gira,dan haka da sauri ta daga kafad'a itama halamun ba ita ba ce.

Tsaye tayi tana musu murmushi ta window bayan taga komai,kila da yanzu ita ce tare da iyalan nan masu matukar ban sha'awa ba dan zuciya data rinjayeta ba.
Hannu ta kai tare da goge hawayenta,ta nufi cikin d'akin da sallama.

Tuni tamkar anyi ruwa an d'auke haka kowa ya gimtse fuska suna ganinta har Uncle din.
Kasa tai da kai,tuni taji ta sake muzanta,kunya ta rufeta,ta sani da taci amanar 'yan uwan taka tsakaninta da Kabir tun ma kamin a tsallako 'yan uwantakar da koh a musulunci babu kamarta.

'Uwa d'aya, uba d'aya ya wuce wasa,amma tai fachali da wannan ta muzgunawa yaran 'yar uwarta halaliya.
Hawaye ta goge tare da sake kallo su.
Da mey ta karu yanzun?
Ribar mey taci bayan wannan?

Kai ta girgiza dan tasan babu,sai ma tsangwama da take samu a gidan miji kawo a gun Umma da 'yan uwanta..
Yau ki manin shekaru 5 da wani abu ba wanda yake jin kanta in har ta cire Umman Kabir.

"Mtsww...
Tsaki Saifu ya yi tare da dauke kai,da harara sauran yaran ma suka d'auke kai daga kallonta har Uncle din kamar kullum in sun ganta a gidan in banda Farida da yau d'aya taji tausayin Fatima ganin yadda take hawaye.

Juyawa tai tare da fashewa da kuka,a kullum tsantsar tsanarta take gani gun Kabir da kuma iyalanshi,ga hararar da Umman Uzairu ke kwad'a mata.
Anan ta zube tare da fara magana cikin kuka.

"Umma duk d'an Adam ajizi ne,abu sama da shekara biyar amma kullum babu sauki duk da na nemi gafara amma anki a yafe min.
"Da wanne zanji? Da rayuwar kuncin gidan Kamal koh da tsanar dangina?

Tashi Farida tayi tare da fito wa duk suka bita da ido.
Barin wajen Umma tayi tare da zirar buta ta shige bayan gida dan haka tuni Fatiman ta sake sanya kuka abin tausayi.
Shiru tai tare da juyawa jin an dafata ta baya ido duk hawaye yai jajur.

Murmushi tai mata tare da kamota ta tashi tsaye.
"Dan Allah Farida ki basu hak'uri koh zan samu saukin wani abun,ta yuwu in Yaya Kabir da su Saifu suka hak'ura kila su Umma su gafarta min dasu Ya Uzairu..

Kuka tasa tare da rufe fuska da hijab tana cigaba da neman afuwa.
D'aya bayan d'aya suke zamewa suna bin bayan Uncle din i zuwa bangaren su Abba.
Da kallo Farida take binsu har suka fuce basu koh waiwayi Fatima ba dake rizgar kuka.

Parlourn Umma Faridan ta jata tana mai fad'in ta daina ya isa haka.
''Insha-Allah Aunty Fatima zasu yafe miki,har su Umman ma kamin mu koma,kiyi hak'uri ki bar kukan haka.

Kallon Faridan take tana murmushi hawaye na zuba.
"Na gode Farida,na gode.
Murmushi tayi tare da girgiza kai,
"Ba komai..
"Ki batta Farida,a rayuwa Fatima baki ga komai ba ma,ba mugun hali bane junin ki?

Kwafa Umman tai,
"Yanzu ki ka fara gani,sai yanzun ma na gane dalilin da yasa Allah ya hanaki haihuwa Fatima,dan ta yuwu su ma zasu iya dibar wannan rashin imanin naki da kiga girka...

Kai Farida ta girgiza da sauri tare da fad'in
"Subhanallah... A'a Umma kar kice haka dan Allah gudun kar muyi sa6o..
Hawaye Umman ta goge tare da fad'in
"Astagfurullah, amma ni na san koh Halima bazata yafi Fatima in da zata dawo..

"Zata yafe,zata yafe Umma,dan ansha fad'in min cewa mai hak'uri ce,a yanzu kuwa yafiyar ku shine nata Umma,dan Allah Umma abin nan ya wuce,matuka Aunty Fatima tai nadama..

"Na sani da duk iya muguntar Aunty Fatima bai kai digo a na abinda su Tabawa suka girka ba,na sani,Umma kema kin sani..
"Amma da wacce ta ta6a neman gafara?
Shiru Umman tayi,dan haka sai ta girgiza kai
"Nasan babu.

"Dan tunda nake a duniya ban ta6a jin marasa imanin su Tabawa ba,ban ta6a ganin su ba,ba kuma na fatan naga fuskar mugaye Umma,dan nasan munana ne zasu iya bani tsoro...

Murmushi Umman tayi,da sannu tai ta bata hak'uri Fatima na yi,tsakanin D'a da uwa sai Allah,dan haka kamin ta bar gidan Umma ta yafe.
By

Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

56_Koh da ta shiga bangaren Abba ba wanda tai ma magana har dare bayan an mayar da auren su Abba da Umma.
Sosai suke a cikin farin ciki a yau da ganin wannan rana kar ma dai Kabir yaji labari.
Bakin nan yaki rufuwa tamkar gonar audiga.

Tashi Umma tayi ta shige chan kwal d'aka jin tsiyar da Kabir ke mata wai an d'aura, yanzu ta zama amaryar Abba a karo na biyu.
Dariya yaran suke mata,dan haka sai filancin ya motsa tare da tashi ta shige chan ciki.

Tara ya shigo har yaran sun fara bacci ita kad'ai da Umma ke tad'in su jefi-jefi.
Murmushi ya yi tare da fad'in
"Muje koh?
Kai ta duk'ar tana mai  kad'awa.
Fita yai yana ma Umman sai da safe.

"Umma dan Allah ki kara musu fad'a kamin nazo goben,Allah ba dad'i ne dan koh ba komai jinin su ce tunda halalin Maman su ne.
Kai Umma ta kad'a
"Ai kin san Saifu ne matsalar,in dai yaji kamar sauran ma sunji ne,chan dama ni bana son abinda ake ma yarinyar nan amma babu mai sauraro na ne.


"Sultana mai zata bini tayi bacci gobe da daru.
Murmushi Umman tai mata.
"Ai fa,
Har kofa ta rakota tana mai shi mata albarka kamin ta koma.

Kallonshi tai lokacin da ya kai hannu yana mai bud'e mata kofar yai wanka cikin k'ananan kaya kamar yadda yafi so sai kamshi yake.
Murmushi tayi tare da shiga.
Dole kullum tai ta gani yana zama yaro.
Dan ita a tashinta zata iya kirga sau nawa taga Abban su da k'ananan kaya ya sa.

Ajiyar zuciya tayi tare da jingina tana shakar sanyin a.cn mai had'e da kamshin uncle, tuni taji ta fara jin kasala kamar mai jin bacci.
Kallota yai fuska d'auke da murmushi.
"Ya akai ne Farida?
Juyo wa tai tana murmushi tare da dan girgiza kai halamun babu komai.

Kai ya kad'a tare da kallon hanya yana murmushi.
"Yau ina a farin ciki..
Kalloshi ta dan yi tare da kad'a kai.
Shima sai ya kad'a kan tare da fad'in
"Hala azumin magana ki ke?
Murmushi tai tana girgiza kai.

"Koh baki huce ba,ummm Habebtee Farida...
Kalloshi tai jin sunan har cikin ranta da mamaki.
Kallonshi take,shin da gaske ita Habebteen shi ce?
Dan kallota yai yana murmushi har hakwaranshi na bayyana.

"Koh da ja?
Kai ta k'autar tare da yin kasa dashi tana mamaki
Uncle ne kuwa?
Sake d'agowa tayi tana kallonshi,har yanzun murmushi yake mata yana kallon hanya.

Juyo wa yai harda kanne mata ido d'aya, dan haka da sauri ta d'auke kai tare da kallon d'ayan bangaren tana murmushi.
Kai ya kad'a lokacin da yake yin kwana,hannunta ya kallo tare da kai nashi ya riko d'aya tare da damke shi cikin nashi.

Ido ta rintse da sauri tare da jin buguwar zuciyarta ya karu.
"My Feery..
Ya Rabbi, ido ta sake tamke wa.
Wai dama Uncle haka yake koh dan yau yana jin farin ciki?...

Ido ta bud'e jin ya d'an matse hannun tare da fad'in
"Uhmm..
Zama ta gyara tare da fad'in
"Uhmm.
Ita ma
Kai ya kad'a lokacin da yake kok'arin yin parking a gefen tafkeken wani gu ta baya.

Kallota yai yana murmushi.
"Zan samu rakiya?
Kasa tai da kai,duk sai taji kunya ta fara sakko mata barin wannan kallon Uncle din na kasa-kasa.
Fita sukai tare da zago wa dan nufar wajen da take ganin tsirarin mutane aksar kamar dama an tanada domin masoya ne ga nan sai tad'in soyayya ake ana aika ice cream.

Murmushi ya yi tare da dan zuwa ya zunguri kafad'arta da tashi kamar yadda yaga su na yi da Aisha in sun so gulma.
Kallonshi tayi tare da kau da kai tana murmushin kunya,Allah yau Uncle sai ka ce wani su Saifu da halamun wasa yake ji,dan haka sai ya kara mata kunya.

Tare suka fito rike da leda a hannunshi ita ya bata robar 'Fan ice' babba ta rike sai musayar murmushi ake.
Gaskiya ta yarda da hasashen Umma Uncle na sonta duk da ba kai ga furtawa ba.

Mota suka shiga,da sannu ya gyara parking din zuwa chan gefen jama'a gefen royal tree tasha kwalliyar fitilu sai walwali suke.
Kai ta duk'ar tana murmushi ganin yadda ya jingina a kujera yana kallonta.

Ajiyar zuciya ya sau tare da kar6an na hannunta ya bud'e.
"You know..
Tsam tai tana dan sauararen tad'in shi nason irin wannan lokacin da ba wani haske sai na farin wata da kyalkyali irin wannan.

Kai ta dago tare da dubanshi,Allah sakawa Abba da ya bata Uncle a matsayin miji, ta gode Allah da ya bata alfaharinta da mafarkinta.
Tana son Uncle, ta sani ba kad'an ba..
Kai ta duk'ar tana murmushi, ina ma zasu dauwama a haka tasan bazata gaji da sauraron shi ba har gari ya wanye..

"My Ferry..
Ido ta lumshe tare da saita nutsuwarta jin buguwar zuciyarta,a hankali ta juyo tare da bud'e ido bisa kanshi.
Yau kalamanta sun tsaya chak! Wanda ta rasa dalili.
Ice cream ya miko mata a chokali tare da nufar bakinta dashi.

Kai ta kautar tana murmushi tare da kad'a kai.
"Oh! common..
Juyo wa ta sake yi,dan haka bai kasa a gwiwa ba ya sake mika mata.
Bakin ta bud'e mishi kad'an,cike da so ya sa mata yana murmushi shima yana sha.

Hannu ya kai tare da kunna waka cikin baitin 'wait for me' a slow motion.
Kalloshi ta dan yi,batai tunanin Uncle najin waka balle ma ta soyayya.
Zama ya gyara tare da sake mika mata yana murmushin bin baitin cikin nutsuwa yana kallonta.

Ido ta sa mishi,ga dad'in ice cream ga dad'in wakar Uncle, ga kuma dad'in wajen da yanayin shi.
A hankali lokaci ya fara ja jama'a na watsewa sun lula a duniyar masoya.
Ringing na wayarshi ne yasa ta k'auda kai tana murmushi. 

Kallonta yai lokacin da ya daga yana murmushi
"Maj'nu ina ka baro Lailan taka?
Dariya yai kad'an mai sauti yana mai nuno mata wayar dan haka tuni ta gane da Nasir yake.


Ido ya sa mata yana ma Nasir dariya ganin yadda ta matso tana fad'in
"Uncle ka ce Laila...
Kai ya kad'a ganin yadda take zumud'i.
"Toh a bamu Lailan aro  Maj'nu..

Dariya suka sa tare da mika mata ganin yadda take washe baki da sauri ta ce
"Kawas..
Daga chan Lailan ta amsa da
"Hmmm,bawani kawas nai fushi..

Kai ta karkatar tare da yin kallar tausayi kamar Lailan na kallonta.
"Ayya,kiyi hak'uri tawan, tunda nazo wayanki a kashe fa..
Daga chan Laila ta ce
"Eh na rasa wayana zan turo miki numbern ta nan yanzun yaushe zaki dawo?

Uncle ta kallo wanda ya jingina yana kallonta.
Baki ta turo tare da fad'in
"Ba rana...
Har suka gama ta bashi bai d'auke ido akanta ba.
Wayar ya kashe yana sake dubanta.

"Meye ba rana?
Baki ta chunno gaba tana dan gunguni.
Zama ya gyara tare da riko hannayenta duk biyun ya kira ta.
"Mey ki ke so nayi a wuce wurin mu koma jibi?
Shiru tayi tare da juyar da fuska gefe.

"Kina sona kuwa Farida?
A bazata tambayar tazo mata,dan haka sai ta juyo ta k'ura mishi ido kamar yadda ya yi mata.
Kai ta girgiza halamun A'a.
Ido ya zaro tare da fad'in
"Mey yasa?

Baki ta chunno gefe tare da fad'in
"Saboda baka sona ni ma..
Baki ta datse da sauri jin ta kwafsa tana dan rintse ido.
Murmushi ya yi tare da sadda kai kasa ganin lokaci yaja goma saura yasa ya tada mota.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

57_Har suka isa kofar gida kanta a gefe sai dai ta dan juyo in taji yana furzar iska tare da sauke ajiyar zuciya in ya kallota.
Kalloshi tayi tare da fad'in
"Na gode,sai da safe.
Murmushi ya yi tare da dakko ledar ya mika mata.

Hannu ta kai zata kar6a ya kautar yana murmushi, ido ta sa mishi,sai murmushi ya yi amma ya kasa ya ce Farida ina sonki,wannan ce babbar matsalarshi.
Kai ta juyar tana masifa ita kad'ai cikin zuciyarta.

"Ni ina ganin fad'in ana son mutum kamar kauyanci ne ma a fad'i Farida...
Juyo wa da tsabar jin wani abu ya tokareta mata makoshi dan haushi.
"Uhmm.
Kawai ta ce ta sake dauke kai.

"Kin san dalili?
Shiru tai,sai dai ta girgiza kai halamun a'a.
_"Cos I love you without knowing how?..when?, or from where?_..
"Dan sometimes I can’t see myself when I’m with you nakan ji wani yanayi haka nan like.. You know... Amm.. ban ma dai san ya zan ce ba ki fahimta.

Ido ta karkad'a,toh koh dai ya d'auka da Halima yake ba Farida ba? Mamaki ya hanata magana sai ido ta yadda koh kiftawa ba tai baki a sake.

Kai ya kad'a mata yana murmushi har hakoranshi na baiyana.
"Akwai wata rana da bazan manta ta ba,kila ke kin manta..
Da karin bayani take kallonshi,dan haka sai ya ce
"Na tuna miki?
Kai ta sunkuyar tana murmushi..

Dan haka sai yai ajiyar zuciya tare da jingina,
"Ranar da ki ka zo ga Abban ki kina kukan aure ki ke so kar samarin su kare kin tuna?
Gyale tasa ta kirifce fuskarta dan tuna wa suna dariya wai ita kunya.

Ajiyar zuciya ya yi tare da fad'in
"A ranar naji how I wish ni saurayi ne da na ce ni ina nan zan jira ki Farida cos idan ina tunanin a ranar na had'u da son Farida may be,domin daga wannan ranar nake tuna ki har nai ta murmushi ni kad'ai.

Tun tana iya jinshi tana murmushi fuska rufe da gyale har ta fara hawaye dan dad'i wanda ya kaita da soma shesshekar kuka kad'an kamar ana busar sarewa.
Shiru ya yi tare da daina murmushin ya matso tare da yaye gyalen wanda tasa ta rufe fuskar dashi.

"Farida..
A dan rikice ya kira ta ganin kukan gaske take yana fad'in akan maganar da yake ne bata so?
Kai ta girgiza,
"Ok ni ne bakya so?
Kai nan ma ta sake girgiza wa tana kallon fuskarshi kai da ganin kukan kasan na shagwa6a ne da jin dad'i.

"Ok,ok toh mey ya sa ki kuka?
Baki ta d'aye tana ta6e bakin hawaye na zuba.
"Ba..ba..bana so fa ka daina fad'a ne uncle..
Baki bud'e ya ce
"Mey d'in ne baki so na daina fad'i?
Baki ta sake 6arewa tare da fad'in
"Kana sona uncle, ka cigaba nake so..

Tsai yai yana dubanta ganin yadda take ta6e bakin,dariya ya fashe mata dashi harda kyakkyatawa.
Kukan ta daina tare da zuba mishi ido tana kallo ganin yadda yake dariyar yana sake goge mata fuska, kan ya zata har ta sau mishi cizo dan haushi.

Hannu ya hau yarfe wa yana fad'in
"Ok,ok I'm sorry..
Jawota yai tare da mata dabaibayi.
A tare suka sau ajiyar zuciya yana mai sake jaddada mata kaunarshi kai ba kace Uncle Kabir bane.
Ba dan sun so ba suka rabe sai dan yadda dare ya shigo.

Tana shiga d'aki Aisha tana waya,da sauri ta haye gadon tare da kwalla ihu tana tsalle bisa gadon.
Da sauri Aishan ta kashe wayar tana fad'in
"Are you crazy?
Baki ta toshe da sauri tare da tare da zama ganin Abba da Umma na turereniyar shigo wa jin ihun da tayi.

"Kuna da hankali kuwa?
Da sauri ta nuna Aisha,
"Ita ce Umma..
Ido Aishan ta zaro,
"Karya take wallahi Umma ita ce..
Kai Abba ya girgiza tare da juya wa yana fad'in
"Allah ya nunan ranar da zaki girma Farida..
By

Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

58_Washegari tun tashin su taci karo da text message nashi mai tsuma rai,dan haka koh da tai wanka sai ta samu kanta da tsaya wa kyali a gaban madubi duk da sai anjima zata fita.

"Aisha..
Galala Aishan ke kallonta,
"Nayi kyau dan Allah?
Daga sama har kasa ta kallota sai washe baki take.
Dan haka sai ta girgiza kai tare da ta6e baki.

"Ban san yaushe har ki ka bada gari ba Farida? Mey ya fad'a miki da har ya siye imaninki daga fita jiya?
Ido ta lumshe tare da fad'in
"So"...
Baki sake Aishan ke kallonta, 'So'?
Ido ta bud'e tare da jijjiga mata kai tazo ta zauna.

"Ban isa karyata son da Uncle jiya ya gwada min ba Aisha, Uncle karshe ne ban ma san na yafe ba..
Kai ta kad'a tare da fad'in
"I see..
Murmushi Faridan tai.
"Ba zaki gane ba,abu d'aya na sani ina matukar za bala'in son Uncle Aisha..

Ido ta rintse da karfi tana murmushi tare da damke hannu a kirji.
"Ya ilahii...Wollah i love him,I really love him Aisha..
Baki sake da mamaki take kallonta,dan haka jin shiru yasa ta bud'e ido.

"Oops..
Iska ta furzar tare da fari da ido tana fad'in
"Ya Allah..meye kuma?
Kai ta girgiza tana kallonta.
"Farida yaushe ki ka san so?
Baki ta chunno tare da tashi ta koma gaban mirror tana fad'in
"Uncle ya koya min..
Kai Aishan ta hau kad'awa
"Umm! I see..
***

"Mun fa zama 'yan kallo Lami.. A gidan nan tun bayan tonan asirin nan Malam ya juya mana baya,koh bangarenshi ya sanya sharad'in kar muje sai ya neme mu..
Tsaki Lamin tayi.
"Ke wannan ne ma a gaban ki?
Kai ta jijjiga.

"Har kullum baki da hankali Tabawa,wato ba ma ta auren da yai ki ke ba sai ta wani abu chan.
"Shin bakya tunanin irin daular da Kabir yake ciki a yanzu ga dawowar Rukayya?
"Shin ba zakiyi tunanin ta yadda muma zamu kwashi rabon mu ba tunda gaba daya sun sallama lamuran mu?

Tsam tayi,
"Kuma fa hakane Lami,yanzu ya zamuyi? Dan tun bayan mutuwar 'Mai yankan wuka' muka rasa na kwarai sai kud'in mu da ake ci,ga jarabar mazajen yaran nan har nakan rasa abin yi..
Shiru Lamin tayi.
"Ga dabara..
Da sauri Tabawan ta gyara zama tana washe baki.

"Muje muna kuka wajen malam din in har ya yafe toh zai iya tausar Kabir din har mu ma ya samu yana yaga mana rabon mu..
Baki ta yage duk ya 6aci da jan goro,
"Kai Lami akwai kwakwalwa,kyanta yanzu muje tunda 9 tayi ai ya tashi a bacci kamin Kabirun yazo mu kasa.

Kai ta kad'a tare da yayumar gyale suka fuce zuwa kewayen Abba mai gate wanda aka sanya katanga a tsakanin su ya zamo su suna a tsohon gida.
Kari yake a parlour

Kai ya juyar gefe jin zuciyarshi na tafasa,kai kana gani kasan kukan ba na Allah bane.
"Tabawa..
Cikin shessheka ta amsa.
"Zai fi mana kyau idan ku ka nesanta kan ku da zuwa inda nake, domin ganin ku na sake sanya min tsanar ku ne kawai..

Ido suka waro suna kallon juna.
''Haba Malam,duk tsiya fa har yanzu mu matan ka ne...
Da sauri ya juyo a masife,
"Au shine alfaharin ku?
Kai suka girgiza da sauri.

"Toh na sauwake muku auren nawa dama alfarmar makiyin naku kuke ci har ku ka kai iyanzu kuna a matsayin mata na..
"Innalillahi.. Haba Malam,daga neman gafarar?

Waje ya nuna musu tare da sake 6ata rai
"Ku 6acen da gani,sannan ya zama rana ta karshe da zan sake ganin kafafunku cikin kewayen nan dan yau Rukayya zata taro,amma in baku ji ba naga sake ganin kafar wata cikin gidana na sallama muku wanchan..

Sallamar Uncle ne yasa yai shiru ganin shi da akwati guda biyu ta Umma,tuni sukai ladab tare da sunkuyar da kai kasa harda fad'in
"Sannu Kabiru,ina kwana?
Abban ya kallo ranshi had'e
"Da wani abu ne Abba?

Kai ya girgiza tare da fad'in
"Na ce su bar min sashe sunki tashi,sannan ka zama shaida na sake su bana son kuma wata mu'amula ta gama ni dasu ta fanin zama a inuwata koh taka.

Tuni ya sake tamke fuska ya kallosu
"Toh mey ku ke jira anan?
Murya na rawa suka ce
"Hak'uri muka zo bayar wa,kuskure ne..
Murmushi ya yi tare da kad'a kai
"Ok ya yi kyau,amma zan sanar ku in har na sake ganin kafar d'ayar ku a cikin gidan nan Tabawa za kusha mamakina ne.

Ido suka waro.
"Dan Allah kai hak'uri..
Waje ya yi tare da ajiye jakar,dan haka da sauri suka koma kan Malam da ya cigaba da yagar kazarshi da Umman Uzairu ta dafo mishi tamkar ba mutane a gabanshi.

"Zaku fita ne koh na cika umarnin Kabir?
Juya wa sukai jin maganar Uzairu shima rai had'e, yadda ya tsani mutuwarshi haka ya tsani su Tabawa,dama kiris yake jira ga kwa dama ta samu.
Jiki a salu6e suka tashi su na mai sake bawa Malam hak'uri Uzairu ya rakasu har waje.

"Kabir ya bani damar koh baya garin nan in naji koh naga kun shigo gidan nan na sanya a d'aure mishi ku 'yan sanda..
Da sauri suka juyo har Lami na hararar shi
"Kai kuma a suwa?
Murmushi ya yi tare da kad'a kai
"Zaku gane a suwa in kun kwata sake shigo mana gida.

Gate din ya tura tare da barin su baki sake.
"Lami da gaske fa suke ba zasu bari aci arziki damu ba,ki duba kiga wannan gida ga sanyin a.c ga cima mai dad'i..
"Mtsww..
Tsaki tai mata tare da harara ta koma gida cikin konar rai.
By

Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

60_Washegari duk jikinta yai sanyi tana had'a kaya kamar kullum in sun zo zata koma.
Tashi Aisha tayi tare da isa gun akwatinta ta zuge ta dawo tare da mika wa Faridan.

Jujjuya wa tai tana kallonta da halamun tambaya ganin littafi hud'u.
"Mey zan dasu?
Zama tayi tare da murmushi.
"Ki karanta su,da ajiye wa nai sai na samu bibbiyu na baki copy d'aya akwai abubuwan da zai taimake ki sosai aciki ba wai littafi bane na soyayya.

Bankad'a su tai dan fahimtar abinda ke ciki,duk dabaru ne na zaman gidan miji harda na girki.
Murmushi tai ido cike da kwalla tare da kallo Aishan ta rungumeta tana fad'in
"Allah barmin ke 'yar uwa kwatan jikina...

Tureta tai tana harararta suna dariya
"Ke fa bakki M,kwata ce ma?
Kai ta girgiza tana goge hawaye tana dariya.
"Allah ina sonku, sai naji kamar kar na tafi..
Harara ta sau mata.
"Sai ka ce gaske.
Dariya sukai tare da tayata ta gama su na firar su cike da son juna.

Kallota ya yi lokacin da suka d'au hanya ta juya su na dariya ita da su Sultana.
Kai ya kad'a yana murmushi tare da kallo hanya.
Kalloshi ta dan yi tare da gyara zama tana mishi murmushi,a dan takaice ya kallota tare da fad'in
"Hi..
A hankali kamar bai son su Saifu su ji.

Kai ta kai kasa tana murmushi,kamin ta dago a dan sace ta kalloshi tare da daga mishi yatsunta halamun
'Hi'.
Kai ya gyad'a yana murmushi,tun yana iya jiyo hayaniyar su Saifu a hankali ita ta bingire bacci,dan haka kowa ya gyangyad'a suka bar Uncle da tuki.

Ajiyar zuciya yai tare da furzar da isa hannunshi bisa stirrn mota bayan ya kallota yadda take bacci hankali kwance fuskarta na kallo shi.
Juyi tai taji duk ta takure dan haka a hankali ta fara dan  mutsu-mutsu halamun tana son space dan haka sai ya rage gudun tare da gyara mata kujerar tai baya dan ta kara jin dad'in baccin.

A gajiye suka sauka,dan haka kowa d'akinshi ya nufa dan ware gajiya.
A parlour suke suna kallo ga katon plates na fruits a tsakiya ana ci.
Waya yake da Umma yana murmushi,
"Duk kowa lafiya, ya Abba?

Ajiyar zuciya yai tare da jingina kai yana 'yar dariya mai sauti,ba sai an fad'a ba kai kasan jin iyayen nashi guri guda ke sa shi farin ciki.
Farida ya kallo wacce ke latsa waya tana murmushi halamun wata gulmar ake guntsa mata ta 2go Laila.

Murmushi yai tare da fad'in
"Za taji Umma,na gode.
Wayar ya ajiye tare da fad'in duk Umma na gaida su.
Kai ta dago tare da kad'awa
"Muna amsawa,dazun ai munyi waya ta kira taji mun sauka..
Murmushi yai tare da kallo su Saifu da suka raja'a a kallon TV wata mata a asibiti ta haihu suna fad'in.

"Wow! She's so cute...
Tvn Farida ta kalla,koh ita jaririyar tai mata kyau.
Kallo Farida Nass ya yi yana turo baki
"Aunty Farida kin ce fa kin zama Mom namu koh?
Kai ta kad'a tana kallonsu ganin yadda ya zunguro baki.

"Toh ki je asibiti muma ki samo mana baby mai kyau muna so,Sultana ta girma...
Ido ta zuba musu jin sauran ma sun hau kad'a kai su na fad'in
"Eh kam,ki haifar mana baby mu ma.. 

Kallo Uncle din tayi dan jin mey zai ce tana raba ido.
Ha6a Uncle din ya hau shafawa yana kallon Faridan da wata siga yana murmushi,
"Dady ma yana so koh Dady?
Wayen cewa tare da gyara zama yana fad'in
"Eh..sosai ma Nass..ai..amma toh..

Farida ya kallo,
"Amma ita fa Momyn naku tana so?
Faridan suka kalla duk cike da son jin ta ce tana so.
Yake tai musu tare da kad'a kai tana basar da uncle
"Baby ai na da kyau..
"Toh samo mana..
Amjad ta kallo tuni har ta fara marairaice wa ganin yadda suke fad'in su kam a samo musu k'ani Sultana na fad'in K'anwa.

Uncle ta kallo,sai da ya dai daici yaran basa kallo ya kashe mata ido d'aya yana yana dariya.
Yawu ta had'iye tun karfi jin cikinta na wani irin kulululu da sauri ta d'auke kai.
Ba fa a nan gezo ke sakar ba..
Zama ta gyara tare da sake kallo Uncle din sai wani kakkane mata ido yake.

Kai ta d'auke da sauri,
"Haihuwa?
Zama ta sake gyara wa tana tunano diagram din nan cikin biology har ta soma zufa.
Su Saifu ta kallo,har musu aka fara na wai sunan da za a sawa babyn in yazo.

"Na'eem..
Kai Nass ya girgiza wa Amjad
"A'a Nawwas.
"A'a Suhaif dai..kunga Saifu da Suhaif,ya zama kamar takwara na.
Dariya suka sa har Uncle d'in in banda Farida dake yake musu hak'ora.
Kamar an mintsileta da sauri ta tashi tana fad'in
"Ina zuwa..
Ta kule d'aki.

Dariya Uncle ke ke kunshe mata tare da girgiza kai yana cije le6e,sarai ya fuskanceta da yanayin da ta shiga tun fara zancen,hakan kuwa da ta nuna ya sake tabbatar mishi da 'yar mitsila yanzu ta san dawar garin...

"Dady kai fa?
Ajiyar zuciya ya sau tare da furzar da iska,a hankali ya ce
"Farida..
Baki su ka saka tare da zuba mishi ido suka maimaita
"Farida kuma Dady?..
Kallosu yai ashe fa yai katofara,dan haka da sauri ya wayence tare da fad'in

"No.. I mean..
Kai ya dafe tare da rintse ido tare da bud'ewa yana musu murmushi.
"Sorry guys.
Sultana ya kallo tare da fad'in
"Sultanate fa? Mey ki ke so a sa ma babyn?

Baki ta yake tare da fad'in
"Sultana 2..
Gaba d'aya suka sa dariya Uncle harda janyota.
"That's my princess.. Nima baby girl nake so..
Baki mazan suka had'a gun fad'in
"Nooo Dady Boy...

Kallosu yai yana murmushi tare da tsaida su
"Ok,ok,i know boys...
Tsit tai tana jiyo su duk karad'in su daga cikin d'aki tana tunani ta inda zata fara.

Laila ta kira har ta kusa tsinke wa kamin aka d'auka cike da dariya.
''Yar mitsila ta Uncle..
Rai ta 6ata tare da chunno baki,
"Wace ce kuma 'yar mitsila?
Dariya Lailan tayi,daga cikin wayar tana iya jiyo dariyar da Alhaji Nasir ke taya Lailan yana fad'in ba ruwan shi fa.

"Ke man..
Dan tsaki tai tare da fad'in
"Na fuskanci wani rawar kai ki ke ji.
Dariya ta hau mata,sai da taji ta fara masifa ta tsagaita.
"Dad'i ta miki,ni gani nan a tension.

Waje Lailan ta sauya tana jiyo Nasir na fad'in gulma koh?
Komai ta koro mata da ya wakana duk ta wani marairaice fuska.
Tsam Lailan tayi.
"Ke ni fa ba haihuwar nan ba yanzu ba planing ma zanyi na shekara uku..Tab,sai mun taho.

"Ke mata shawara fa nake nema,kin kwa san yadda nake ji? Da  fa kwarin gwiwa ta nazo garin nan amma ana kiran haihuwa duk ta sace..
Dariya Lailan tayi.
"Ke ware wallahi, bana ciki da kinibibi,tunda kin shirya cire komai ki bawa su Saifu k'ani...

"Wayyo ni,kinga ma dariyar da Uncle din yake wallahi ta mugunta ce ma kamar,ina fa jiyo su wai toh zan haifi 'y'an biyu a raba gardama,ji kamar wata akuya...
Shiru tai jin an kwankwasa kofa.

Agogo ta kalla kusan goma,zai wuya ace su Saifu ne koh Sultana,dan taji shiru tasan sunyi bacci..
Shiru tayi ganin Uncle ya turo kofa ya shigo.

Yawu ta had'iye tana jiyo Laila na fad'in in ba zakiyi magana ba sai da safe.
Mike wa tai tare da waro ido tana kallonshi.
"Un..Uncle.
Kofar ya rufe tare da juyo wa yana kallonta.

"Magana naji ashe ba kiyi bacci ba?
Kai tai saurin jijjiga wa tana raba ido.
"Ok.
Kofin hannunshi ya nuno mata tare da fad'in
Zan samu tea kuwa mai dan d'umi please?
Kai ta kad'a tana gyara hannun rigar baccinta mey kamar shimi halamun ta gama shiri.

Dariya ya d'an kunshe ganin yadda sai kakkare wani guri take da hannu tana jan riga.
Kofin ya mika mata halamun tazo ta amsa.
Yawu ta had'iye tare sunkuyar da kai tana kad'a mishi.
Ganin ta tsaya inda-inda yasa ya karaso tare da ajiye wa kan mirror ya juya.

Ajiyar zuciya ta sau tare da rufe ido tana fad'in
"Thank God...
"Ki kai min d'akina please hot one fa..
Ido ta bud'e da sauri tare da kallonshi,kai ya dauke tare da fita yana jijjiga kai.

Hannu ta d'aura bisa kai,Uncle bai ta6a mata haka ba sai yau,goma fa?
Ka'fa ta hau bugawa had'i da sa kukan da ba hawaye tana ta6e baki.
"Wayyo Ummata..
Text taji ya shigo ga hoton Laila bisa screen din,dan haka da sauri ta d'auka tare da bud'ewa.

"Ki ware fa Hajiyata,naji tun yanzu kin fara rawar murya...
Hulla wayar tai kan gado tana goge zufa,ganin hakan bazai mata ba yasa ta zari zani da hijab ta d'aura bisa rigar jikinta tai kitchen cikin sand'a.

Tafi minti biyar tana tsaye a bak'in kofar Uncle d'in ta kasa shiga,sai tayi kamar ta kwankwasa sai ta koma gefe.
Jahadi tai,da nufin ta kwankwasa kawai sai ta ajiye ta gudu in yaso in ya bud'e sai ya d'auka.

Kai ta kad'a tana murmushin jin shawarar zuciyarta.
Farantin ta ajiye tara da dagowa da zummar bugawa taji an bud'e kofar.
Kam ta tsaya baki sake rike da hannu a kame tana kallonshi.

"Oh,sorry.
Hannun ta mayar tare da rufe baki tai kasa da kai.
Ciki ya koma yana mai bata hanya halamun ta karaso ciki da tea d'in,ba dan taso ba ta d'auka tare da ra6awa ta gefenshi ta shige zuciya na dukan tara-tara jin ya maida kofa ya rufe.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

61_Fuska ta marairaice mishi rike da faranti a hannu.
Murmushi ya yi tare da wuce wa bisa kujerar d'akin ya zauna yana latsa waya tare da satar kallonta.

"You know a said mai zafi nake so and kin hutar min shi a tsaye da ki ke hala na had'o da kaina?..
Kai ta girgiza da sauri tare da karasowa taja stoll na gefen gun tana dan kallonshi kad'an ya d'auke kai.

"Gashi..
Dagowa yai yana kad'a kai tare da d'aukan cup din ya kai baki dan haka da sauri ta juya da niyar guduwa yai saurin cire kofin a baki har yana kok'arin ya kwareshi.
"Uhm-um,wait..
Chak ta tsaya tare da saurin rintse ido tana yarfe hannu.

"Ai ya huce, sam ma ba zafi...
Juyo wa tai tana langwa6e mishi kai cikin marairaice fuska.
Kai ya jijjiga mata yana mika mata kofin
"Yes,zo ki ta6a kiji sam ba zafi..
Baki ta chunno kamar ta sau mishi kuka..
"Ki sani ba a iya miji gardama koh kiwa...
Hudubar Umma ce ta fad'o mata rai,dan haka sai tai saurin gyara fuskar tare da zuwa gareshi.

"Wani zan sake?
Kai ya girgiza mata da sauri.
"Nop,kawai muje na rakaki ki dumama min zaifi kamar dare ba?
Kai ta kad'a kamar kadangaruwa tare da amsa ta daura bisa faranti suka nufi kitchen.

Gas ta kunna tare da yin yadda ya ce duk ya bi ya takureta kamar wanda zai koma ciki.
Juyo wa tai tare da d'aurawa a farantin da zummar ta bashi ta tsere sai ya rigata fita a kitchen.
Juyo wa tai tare da fadin
"Oop..Uncleee..
Tana dan buga kafa.

D'akin ta tura,iyanzu tun tana jin buguwar zuciya har ta dan daina sai abin da ba za'a rasa ba.
Rashe-rashe ta sameshi bisa gado har jallabiyar ya cire halamun yai shirin kwanciya dan haka sai tai tsaye a kofa.

"Tea d'in nan samu kuwa?
Katseta yai,dan haka jiki a sanyaye ta karasa gadon tare da ajiye farantin ta mika mishi kofin.
Kafad'a ya make tare da fad'in
"Ba ki ga hannu na a bargo?
Ido ta waro,dan haka sai ya bud'e baki halamun ta bashi yana nuna mata gefen gado halamun ta zauna.

Kai ta langwa6e mishi kamar ta sau kuka,bacci take ji amma tunda tazo d'akin Uncle har ya baje.
Tana ji tana gani haka ta zauna tare da daukan kofin ta juya tare da diba a chokali ta fara bashi.

Kai ya d'auke da sauri yana hihitu halamun ta kona mishi baki ya rufe bakin da hannu, dan haka da sauri ta ajiye tea din tare juyo wa tana neman cire hannun da fad'in
"Oh! I'm sorry..
Tana hurawa halamun ya huce cikin kid'ime wa.

Dariya ya kimtse tare da fad'in
"It's ok,ki bani ya huce.
Kai ta kad'a ita duk zatar ta da gasken kona shi tai,dan haka koh da ta kara diba har furawa take kamar zata bawa yaro tukunna ta bashi.

Murmushi yake yana kallonta tare da amsar tea da chokali ba koh kiftawa ita kam ta dage tsakaninta da Allah bashi take tana gyara hijab dake biyo hannunta.
"Ki cire hijab din ya takura ki..
Kai ta kad'a, dan kam ya takuratan,dan haka ba tare da ta kawo komai ba taja ta cire yana kunshe dariya.

"Koh ke fa..
Murmushi tai tare da cigaba da bashi sai wani lullumshe mata ido yake yana bud'e baki tana bashi har ya kare.
"Thanks...
Kai ta kad'a tare da kok'arin tashi yai saurin fad'in

"Kai,Ya Allah,na gaji sosai musamman nan dan tuki...
Galala take kallonshi ganin yadda yake marairaice mata fuska,kamin tai magana ya rigata fad'in
"Tausani kad'an my Ferry...kin iya?

Ido ta zaro,da sauri ta girgiza kai tare da fad'in
"A'a ban iya ba...
Murmushi ya yi tare da jijjiga kai.
"Good.. Hawo na gwada miki toh..
Baya ya juya halamun rub da ciki yana cije bakin karya yana rufe idi tare da fad'in
"Wash,na fa zaunu sosai a mota.

Hannu ta aza bisa kai tare da 6are baki kamar ta sau ihu,lalle yau tasan karya ta kare...
"Uncle dinki ne fa? Ki mishi duk cikin lada ne ba abinda zai faru ki tuna ranar chan...
Hannun ta sauke jin wata zuciyar tai mata tuni tana karkad'a kai da murmushi halamun ta tuna.

Juyo wa yai tare da bud'e ido d'aya daya a manne ya kallota.
"Zan samu?
Kai ta kad'a tana gyara d'aurin zani tare da tattare wa,ta ma rasa ta ina zata hau gadon sai inda-inda take.
Juya wa yai yana murmushi ciki-ciki tare da sanya fuskanshi pillow ya rufe yana mata dariya har ta hawo.

Durkushe tai sai ta mika hannu sai ta dauke bisa bayan nashi tana k'auda kai gefe had'i da rintse ido.
Jihadi tai ido rintse ta fara tausashi yana dan fad'in
"Oh..yauwa,nan ma..
Yar harara ta sau mishi tare da da yin inda ya nuna.

Cike da murya kasa-kasa ya ce
"My sweet Ferry...
Baki ta chunno tare da dannawa da karfi harda cije le6e..
"Yauwa dorling..
Da wayo da wayo ta kusa minti 10 tana abu daya har ta kosa karfinta duk ya tafi a tausa yana fad'in bai isa ba.

Chan dai taji shiru ya daina sambatun, a hankali ta leka fuskarshi da fatan Allah ma sa yai bacci ta gudu kawai ganin sha d'aya har ta gota mata a d'akin.
Ajiyar zuciya tai tare da furzar da iskar dake bak'inta harda fad'in
"Thank God..
Ido rufe.

A hankali ta ta fara janye jiki tana cije le6e kamar munafuka zata sauka a gadon taji an chafko hannunta.
Hannun ta kallo da sauri ido waje,a yadda yake har yanzun haka yake fuska bisa filo.
"Dama ba bacci yake ba?
Kanta tambaya tana kallonshi  yadda ya rikota kam.

Kamin ta samo amsa har ya juyo tare da jayota gaba d'aya ta fad'o inda yake baki bud'e a tsorace tana kallonshi.
Ido ya bud'e kad'an tare da dubenta.
"Wa ya sallame ki?
Kai langwa6ar tare da marairaice  mishi fuska.
By

Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

62_Ido ya komar ya rufe tare da mata dabaibayi kam ta inda ba hanyar gudu.
Tun tana sa ran ya saketa har ta hak'ura ta sau jiki jin ya saki ajiyar zuciya kamar mai bacci.

Ido ta sa mishi da sannu tana kare mishi kallo,a hankali ta ji ta fara zurmuwa har tana sake gano kuruciyar shi a yadda ya rufe idon.
Sosai ya koma Ummanshi,kai in batai karya bama sai ta ce yafi Umma kyau da tsarauwa ga gayu kuma.

Kasa tai da kai kamar yana kallonta tana murmushi, a hankali ta sake dagowa,sajen shi take kalla,Allah Uncle kam ya yi a gareta ba karya....
Warai ya bud'e ido tare da sauke su bisa nata.

Ido ta waroganin yadda yai mata bazata ya kamata tana kallonshi,dan haka da sauri ta tamke ido kam-kam ganin yana mata murmushi.
"Abin ma harda sata?
Ido ta bud'e tare da mishi kallon neman sani jin ya ce sata.

"Eh man,na kallo na,koh ba ke ba ce?
Kai tai saurin jijjiga wa halamun ba ita ba ce.
Murmushi yai tare da gyara kwanciya su na facing juna,ido ta rufe dan ganin haka.
Hannu ya kai bisa gashin kanta yana murmushi.
"My yori-yori..

Murmushi tai tare da sake sadda kai kasa.
A hankali ya make murya cikin wakar yori-yorin ya fara fad'in
  _" Love love, mh mh mh;love love ..._
Ido ta bud'e tana dan dariyar jin baitin.
Murmushin shima ya soma tare da riko ha6arta ya sake fad'in

_"well, am with you ma love love.. Uhm,nobody can love you the way I do,am with you my lova lova..._
Dariya ta sanya harda kyakyatawa da gyara kwanciya tana kad'a mishi kai shi kam sai sake zakulo baitin da ya iya yake rero mata tana dariya tare da fad'in yaci gaba.

Ido ya manne tare da fad'in
"Nawa zaki biyani ladan yi?
Kai ta langwa6e tare da shagwa6e mishi fuska,kai ya girgiza tare da sake gyara wa yana fad'in

  _" Same thing, same thing way dey make me feel like say you go be my wife_
_"Na the same thing wey been dey make others dey say I dey waste my time_..
Kai ta jijjiga tana dariya halamun ya cigaba,murmushi yai tare da sake fad'in

_"Na because I dey respect you girl,spending for you every night and day I dey pray for you, because of you I dey fly like butterfly.._
Nan ta kakare ya ya fara lalubo sauran ya rasa ganin yadda take dariyar.

Ido ya zuba mata shima yana murmushi, akan yaga farin cikin 'yar mitslilarshi ya koyo wakar masoya sosai koh dan irin moment din nan..
Hannu yakai yana gyara mata gashi cikin murmushi yana kallonta.

Dariyar ta tsagaita tare itama da kallonshi ido cikin ido tana murmushi, so d'aya ne, ta kuma tabbatar tana ma Uncle shi,a yanzu da ya warar ta yai mata tuni da hakan.
Kasa jurewa ya yi,karshe dole ya sadaka da jikinshi lokaci guda suna sauke ajiyar zuciya.

Bai sai iya lokacin da ya dau yana mai dakon son Farida ba,abu daya zai iya fad'i shine ta dawo da farin ciki da ya rasa tun bayan rasuwar Halima da ma yaran shi...
Wal nepa suka d'auke wuta,dan haka da sauri ta sake kankamo shi tana rintse ido.

Murmushi yai tare da kok'arin zameta tana fad'in
"No..
"Ok..
Waya ya lalubo tare da haskata tai langwas kamar ba ita ba ce dazun mey dariya duhu yasa tai ladab.
Dan tashi yai a hankali ta sake riko shi kam halamun kar ya batta.

Kai ya jijjiga mata tare da fad'in ba inda zashi john zai kira.
Ido ta sake rufe wa har ya kira John tare da sanarshi ya kunna mishi inji yana mamagi ya amsa.
Kallota yai yana mai kashe wayar lokacin da haske yazo na halamun an kunna.

Murmushi ya yi tare da rad'a mata
"Yori yori..
Ido ta bud'e tana murmushi tai lakwas.
"Jirani kad'an ina zuwa..
Kai ta kad'a mishi tare da zamewa bisa pillow.

Alwala ya dauro tare da fito wa tana sissinke mishi kai.
Guntun ruwan alwalar ya san yarfo mata yana murmushi.
"D'auro alwala kizo ki tayani sallah..
Kai ta dago lokacin da yake zira jallabiya,dan haka sai ta kad'a tare da nufar bayan gidan itama tai kamar yadda ya umarceta ta fito.

Kai da gwiwa ta had'a lokacin da suka idar yana mata tambayoyi kamar yadda Sunnah ta koyar tana bashi amsa.
Murmushi yai tare da fad'in
"Mumtaz..
Kai ta sake sanya wa ta dan duk'ar bisa cinyoyinta tana murmushin kunya.

Tashi yai har ya gama shiri tana nan a nad'e ta kasa tashi.
Waya ya dakko bisa bed site yana kad'a kai had'i da murmushi ya kunna bed lamp nashi kamin ya juya,kai ta sunkuyar tana murmushin ganin ya ganota.

Wajen makunnar wutar d'akin yaje tare da kashe wa ya zama d'akin yai dan dim na bed lamp kawai.
Hannu ya mika mata tare da fad'in
"Uhmm..
Dago wa tayi ta zata abu zai bata taga ya miko mata hannu,tuni so ya rinjayi kunya sai ta mika mishi nata a hankali ya dagota da dan nishin shi.

"Kai,kina da nauyi ashe?..
Murmushi tai kai kasa,a hankali ya kai hannu tare da zame hijab din yana fad'in
"Ba kin ce yana daminki ba?
Kai ta sake duk'arwa ba amsa.
A hankali yana janye hankalinta har ya zaunarta bisa gado shi kuma ya kwanta tare da yin filo da kafafunta.

Yau wannan kunyar da ta danno kai fa?
"Oya,saura ke?
Kad'an ta dan kalloshi tare da fad'in mey ne?
"Yori-yorin..
Kai ta girgiza mishi halamun bata iya ba..
Hannunta ya riko tare da fad'in
"Mai alya fa?
Murmushi tai tana kallon wani waje.

A hankali ya furta tare da gyara kwanciya yana mai riko hannayenta masu guntun lalle yana kaiwa baki.
Ido ta lumshe jin ya soma gasa mata rai da kyawawan lafuzan nan nashi dake sata murmushi ba dan ta shirya ba.

Da sannu kidan ya soma sauya,a hankali rawar ma ta sauya,tun kana iya jiyo murmushinta da sannu ya maye rera waka cikin baitin kukan ta ga Uncle..
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

63_Juyi tayi da niyar janye bargo daga fuskarta jin dan zafi dan sosai babban bargo ne ya rufe ta har kai tana dan cije le6e.
Fuska ta dan yamutse tare dan bud'e ido tana 6are baki halamun kuka ganin d'akin wayam halamun masallaci yaje.

Hawaye ne ya zubo mata tare da fad'in "Wayyo Ummata..
Ta sani da kiran Umma zai sa ta zo dan cecarta tasan da yanzun ta iso tun jiya...
"Ana son mace kar ta zamo raguwa dan a gaba haihuwa zatai dan haka komai sai kun d'aure...

Hudubar Umma ce ta fad'o mata kai lokacin da take kok'arin kurma kuka sai tai shiru tare da kok'arin tashi tana hawaye.
Inata-inata ta tattare na tsere zuwa d'akinta.

Band'aki ta shige ido na zubda kwalla ta kule cikin kwarmin wankanta koh ta samu sa'ida da ruwan d'umin heatern band'akinta.
Lalle ne in dai wannan ne girman da Umma ke fadi toh kwa wannan girma da wuya yake.
Tana nan cikin ruwan har wani gyangyad'i ke kwasarta ciki tana rufe ido.
***

"Dady mu tafi bacci nake ji...
Nass ke dan ta6o shi ganin yadda ya zaune yaki tashi kamar kullum su tafi in yaje ya yi lazimin achan.
Ajiyar zuciya ya sau,Allah ya gani har tsoron arbawa yake da Farida a yau.

Alo tsiya alo danja ce ya sani,dan haka ya tsokano fad'a.
Yawu ya had'iye tare da kad'a mishi kai da fad'in
"Ok.
Saifu ya kalla da har ya bingire yana neman koma wa a masallacin ya tashe shi suka wuce.

Kofar ya rike tare da murd'a wa a hankali yana tura kanshi dan ganin koh ta motsa gadon wayam.
Band'aki ya tura nan ma ba kowa,dan haka sai ya sake fita dan zuwa yaga halin da take zuciya na mishi d'ari-d'ari ya tura d'akin nata nan ma wayam.

Band'aki ya tsaya jin ba motsi ciki yana kasa kunne a hankali ya ce
"Farida..
Ido ta bud'e cikin 6acci tare da fad'in
"Uhmm..
Ajiyar zuciya ya saka tare da gyara tsayuwa.
Jin shiru yasa ya sake kiran tare da dan buga kofar.

Watsake wa tai da sauri tare da fad'in kar fa ya shigo dan Allah.
Kai ya kad'a tare da fad'in
"Toh yi hak'uri kin tashi?..
"Uhmm..
Jim yai tare da sake mata wata tambayar,komai ya ce sai ta ce
Uhmm kawai,dole karshe ya hak'ura ya koma d'aki dan sanin abinyi.

Kofar ya turo lokacin tana ruku'u cikin sanyin jiki.
Gado ya samu tare da zama a gefe dan jiran ta idar rike da kofin ruwa da abu dunkule a hannunshi.
Ido ya sa mata jin tai sallama,gaba d'aya tausayi ta bashi dan bai zaci hakan ba ma.

Kai ta duk'ar tana goge hawayen 6aci tare da ta6e baki,dan haka da sauri ya sakko lallashi tare da bata ruwa da maganin tasha sai sake narkewa take dakyar ya samu ta koma bacci.

Ajiyar zuciya ya sau bayan ya gama lalla6en ya ja mata bargo tare da had'a tagumi yana kallonta.
Murmushi ya yi,Farida kam daban ce,dan duk yadda yai tsammani sai ta bashi mamaki har ta wuce tunaninshi.

Iska ya furzar yana sake gyara mata bargon,sai yanzun hankalinshi ya kwanta ganin har ajiyar zuciya ta dan sau halamun baccin yai dad'i.
Wuta ya kashe mata tare da sauke labulayen d'akin ganin gari ya fara haske kar hasken ya dameta.

A hankali ya rufe kofar tare da nufar d'akinshi dan kimtsa chan yau koh baccin da ya saba bai koma,a jima kad'an ya leko ta.

Mika tai baki na dan motsa wa jin dama-dama sosai.
Ido a hankali jin kamar ana kus-kus kusa da ita ta kallo gefen.
Sultana ne da Nass duk sun tsaya bisa kanta suna kallo,ganin ta bud'e ido yasa suka sau murmushi kamar dai gadinta aka sa su.

Murmushin itama ta musu tare da kok'arin tashi Nass ya fuce yana kiran ta tashi.
Tare ya shigo da yaran rike da plate a hannunshi Saifu rike da mopper Amjad da tsintsiya.
Baki ta saka tare da kallon hannun kowa.

"Sannu Aunty Farida,ya cikin naki?
Galala ta kallo Uncle din baki sake da halamar tambaya, yake yai mata tare fad'in
"Sannu,ya cikin?
Kai ta kad'a musu kawai tana sauke kai kasa.

Brush tayi suka fita dan jiranta kan table ita da Sultana.
Tare da suka fito cikin shiri kamar ba ita ba suna dan dariya shar dasu.
Abincin ya cigaba da zuba ma su Saifu yana dan sato kallonsu tai da kai kasa.

Parlour suka zaua bayan sun gama cin abincin jin su Saifu sunce yau zasuyi komai sai cikinta ya daina wai ciwo,kai ta kad'a musu ganin suna tattare kayan zuwa kitchen.

Uncle din ta dan kallo a sace lokacin da yake goge saman table din da farin gyalle.
Kai ta sunkuyar da sauri ganin ya kallota, tunanin yadda Uncle ya iya lauya wayo take tun daga jiya har fad'i ma su Saifu ciwan ciki take.

Kai ta girgiza tare da kad'a kai tana kallon yadda suke aiki.
Murmushi tayi,lalle aiki ya samu maza.
By

Feenat Ja'afar.

Ayi hak'uri Insha-Allah gobe dayawa zanyi har sai angaji😁
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

64_Da yamma sai gasu sun shigo da Nasir harda Laila a tare lokacin tana d'aki,jin muryar Lailan yasa ta tashi tare da bud'e kofa da sauri suka kank'ame juna cikin murna.
"Dallah cikani na ma manta ya akai nazo..

Fuska ta marairaice mata kamar gaske.
"Haba kawas,yi hak'uri koh baki zo ba gobe da za'a kaini.
Kofar suka rufe tana fad'in
"Ba wani nan..
Kai ta langwa6e mata,da gaske duk tai sanyi sai kam ka zata ba lafiya.

Gyale Lailan ta cire tana ajiye shi gefe,ido Faridan ta sa mata.
"Kinyi kyau sosai k'awata..
Murmushi tai tare da fad'in
"Aure wasa ne Hajiyata?
Harara ta sau mata suna dariya,
"Ba wasa bane,ina angon?

Hannunta ta kamo tare da fad'in
"Maj'nu nah zaki ce,Baby ba yana parlour da Uncle..
Kai ta dungure mata,
"Allah baki da kunya..
Ramawa tai tare da fad'in
"Kunyo.. Meye dan na ambaci habibena a gaban ki?

Ido ta sa mata tare da girgiza kai
"Babu.. Kawai dai ina tunanin ina ma ni ce,sosai fa nake kunyar Uncle Allah Laila..
Baki ta ta6e tana sake gyara zama.
"Cire kunya yarinya ki murji amarcinki,yes kowa ma yana wannan kunyar amma ni? Tab,wallahi ta ranar nai na ware...

Dariya suka sa harda tafawa,
"Muguwa K'awa, wollah baki da dama ne..
Kai ta kad'a da sauri tana fad'in
"Kwarai kuwa,gwara nima na fito a dama dani.
Kai ta kad'a suna dariya.
"Wallahi duk kinyi fa wani la'asar.
Hannu ta kai bisa ha6a tana dan kare ma Faridan kallo cikin shakiyanci.

"Uhm-uhmm,su kawas koh dai?..
Harara tai saurin sau mata.
"Koh dai mey? Ni ban san iskanci fa..
Dariya Lailan ta sa ganin yadda take turo baki gaba..
"Ayya,yarinya ta zama momma ashe...

Shiru tai tare da tashi ganin ta rarumo filo zata kwad'a mata ta kauce tana dariya.
Tsaf 'yar gari Laila ta zauna harda sabuwar lecture kai ka ce wata babbar macen ce da tsabar iyayi.
Tun tana daukan wasa har dai ta ware ta hau tsintar na tsinta dan tasan a yanzu dai batta kamar Laila duk garin nan.

Parlour suka fito in da dariyar shakiyancin Nasir kad'ai ke tashi.
"Na 'yar Mitsila ba dama ne..
Shiru yai jin kofar Faridan za'a bud'e, murmushi Uncle din yai yana mai kallon kofar.
A tare suka fito fuskar su dauke da fara'a, dan haka tuni suka dauke hankalin gogan nin nasu.

Dan duk'awa tai tana gaida Nasir din kai duk'e, amsawa yai yana musu murmushi,Uncle din ta dan saci kallonshi kanta a kasa tana murmushi, kir idonshi a kanta,dan haka Laila ta dan zungura halamun su tafi.

Da kallo Uncle din ya bita ganin yadda da suke dan kus-kus har suna had'a kafad'a halamun suyi shiru lokacin da zasu shiga kitchen.
Kai ya girgiza,ya zama tamkar al'adarta ture kafad'ar juna,ba kad'an kuma yake mata kyau ba dan a ganinshi komai tayi na burge wa ne..


"Farida..
Kafad'arshi Nasir ya ta6a ganin ya lula yana murmushi..
"Farida?
Kai Nasir din ya kad'a,
"Eh man,tamau ka kasa sukuni tun ganinta ka bari mu sabbin aure muyi..
Murmushi ya yi tare da girgiza kai.
"Nasir naka da dama..
Dariya yasa sosai har su Farida dake kitchen ta girgiza kai.

"Kai Laila mijin nan naki ya fa iya dariyar mugunta Allah..
Dariyar ita ma ta sa mata tana kok'arin d'aura tukunya.
"Barmin Baby, da wannan munafukin murmushin da kuke saka ina kallo ai gwara mu..
Murmushi tayi tare da girgiza kai.

"Ni ina su Saifu ne?
Kallota tai lokacin da take yanka musu fruits tare da fad'in
"Islamiya suka tafi..
Kai ta kad'a tare da cigaba da abinda take tana fad'in
"K'awata kin san mey?
Kai Faridan ta girgiza
"Sai kin fad'a.

Ajiyar zuciya Lailan ta yi.
"Allah ban tunanin Momyn Nur zatai sauki ba haka,kin san kuwa har yau ita ke aiko min abincin safe da rana har dare?
Ido Lailan ta dan waro
"Ke dan Allah fa?
Kai ta kad'a
"Sosai,ga yaran na sona zuwansu biyu in zasu tafi k'ananan sunyi ta fad'in zasu zauna dani.

"A da gani nake bazan iya sake wa da yaran miji kamar yadda ki ke yi da su Saifu ba,amma a yanzu Allah ina son su,koh dan ina son Dadyn su ne?
Murmushi Faridan tai tare da kad'a kai
"Zai iya yuwa, dan kinsan hausawa na fad'in mai son uwa yaso d'anta,kina son ubansu su ba kya son su I don't think da gaske ki ke.

Jim tayi tana kallon wani waje.
"A yau kad'ai na sake jin kaunar y'an gidan nan Laila,dan bansan dalili ba,haka kawai nake jin wani sabon lamari ga Uncle mud'in idona yai katari dashi,ina son su,kamar yadda sosai na san su na sona.

Ajiyar zuciya Lailan tayi.
"A yanzu ne nake tunanin mey *MATAN UBA* suke kwasa a jikin yaran mazajen suin har sun musu mugunta Farida?
Murmushi tai tare ture plate din fruit din ta janyo wani.
"Har kullum tambayar da nake ma kaina kenan Laila,amsa d'aya nake iya bada wa,shine tsagwaron mugunta ce da rashin imani ba wai kishi ba.

Kai ta kad'a mata cikin gamsuwa da bayaninta.
"Allah dai ya kyauta.
Kai Faridan ta kad'a tare da fad'in
"Amin kam..
Fruit din suka d'auka bayan Laila ta zuba shinkafa bisa wuta ta gyara gyalenta su ka fita.

Na su uncle suka ajiye tare da yin d'aki da nasu Laila.
Da kallo suka bisu har suka kule.
"Wato abokina matuka ina mamakin dabi'ar Laila da Farida..
Murmushi yai yana daukan abarba.
"Na mey fa?
Zama ya gyara shima ya d'auka.

"Yara ne,amma matuka masu hankalin manya,ga wayo,a fagen soyayya kuwa..
Ayaba ya tauna yana gyad'a kai.
"Kar ma dai Lailata taji bayani,dan taci sunan nata Laila....
Dariya Uncle yai tare da girgiza mishi kai..
"Eh sosai,a lambun itatuwa ba,na san wannan.

Dariya yasa yana girgiza kai
"No,believe me,da gaske nake,Laila kam hmm,ba a cewa komai,amma ba karamar farar sa'a nai da tsinto ta ba cikin mata dubu..
Abarba ya gatsa yana lumshe ido dan zagi,dan haka sai uncle din ya jinjina kai yana mishi murmushi.

A ganinshi shi yafi chanchanta ya ce haka,dan a yanzu gani yake mata suna suka tara,in har zai iya cire Halima,toh Farida ta sha gaban tunaninshi..
Murmushi yai yana gyad'a kai, kowa dai da nashi gwanin,dan haka abin ba'a cewa komai.

Kwanika suke tattare wa har su Saifu bayan su Laila sun tafi sun gama cin abinci har takwas tayi.
"La,an fara wrestling..
TV su Saifu suka kalla,dan haka tuni hankalin su yai gun suka nufi parlour tare da barin su Uncle a kitchen.

A dan sace ta kalloshi tana mika mishi plate bayan ta wanke yana dauraya suka had'a ido.
Kai ta d'auke tare da kallon cikin ruwan kumfar tana murmushin kunya ganin kallon da yake aiko mata.

Plate din ta sake kai duk'e, murmushi yai tare da had'o wa da hannunta ya rike kam,dan haka sai ta kalloshi.
Kasa ta sake yi da kanta,wannan kallon bata iya jure shi,dan ba karamin kunya yake bata ba amma shi koh a jikinshi.

Kamin ta farga ya koma ta bayanta tare da sanya hannunshi duk biyu ya riko hannunta mai rike da soso suna wankewa a tare.
Ido ta rufe jin numfashin shi kusan saitin kunneta.

Kanshin ya d'aura bisa wuyanta tare da sakar ajiyar zuciya, a hankali kamar mai rad'a ya ce
"My yori-yori..
Ido ta sake tamke wa sosai tana buguwar zuciyarta na dad'uwa da sauri da sauri.

"Dady kar ya wuce ka fa..
Murmushi yai tare da dan juya jin muryar Nass ya dan daga murya dan yaji..
"Bari Nass mun kusa mu gama ku cigaba..
Ido ta dan bud'e tare da wara su kan hannunsun,a hankali ta furta
"Uncle yara fa..

"Ina suke?
Shiru tai tana wanke plate din da yake dirza soson hannunta a kai.
Tun tana takura kanta har ta dan sau jiki a haka su ka gama tare da fita ta barshi yana d'auraye hannu ta gudu parlour inda su Saifu sai ihu suke na fad'in
"1,2,3 ya cinye..
Cikin ihu gaba d'aya hankalin su yai kan wrestling.

Fito wa yai yana goge hannu da karamin towel yana dan hararota kad'an tai tsakiyar su Saifu ta zauna.
Murmushi ya yi tare da kad'a mata kai.

Kowa yai d'aki dan  bacci,daga wanka ta fito ta mirza mai kad'an da turare cikin sauri duk dan tayi ta kwanta ta zira kayan bacci.
Gado ta d'ane tare da jawo bargo sai ta tuna bata kashe fitila ba,dan haka sai ta zame bargo da niyar sakkowa taji an dan kwankwasa d'akin.

Ido ta waro tare kasa kunne,kamin tai kwakkwaran motsi har an turo kofar.
Yawu ta had'iye tun karfi ganin Uncle rike da kofi a hannu yana kallonta ganin yadda take raba ido ya 6era a buta.

Kofi ya nuno mata cikin dan kama kai
"Zan samu tea please?..
Fuska ta fara marairaice wa tana kallonshi ganin ba da wasa yake ba dan haka a hankali cikin ranta ta furta
"Wayyo ni Ummata...
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

65_Tana tutturo baki ta isa d'akin tare da tura wa.
Kai ya dago yana dane-danen waya ta tsaye a gefe rike da farantin tana dan kau da kai gefe ita a dole bata son shiga d'akin.

Kai ya kad'a tare da sake kallon wayar yana latsawa.
"In ya huce zaki koma ki dimamo irin na jiya fa..
Kalloshi tai,dan haka sai ta ajiye gefen tare da sake tsayawa.
Amma dake Uncle din namijin duniya ne da sannu yasa ta zauna.

Kallota ya yi,
"Daga yau ma tea din ya dawo dan kullum 10:30pm dot nake son ya iske ni tunda abin haka ne..
Fuska ta marairaice,
"Uncle mey nai ni..
Kai ya d'auke yana kur6ar tea d'inshi,dan haka sai ta saita tare da sakar fuska.

Tashi tai da nufin fita jin ya shareta yai saurin fad'in
"Wa ya sallame ki?
Kalloshi tai fuska a marairaice tana sake zama.
Duk ya d'auke mata wuta, dan haka ba dan taso ba tai shiru har gyangyad'i ya fara surarta ta zame nan.

A dan jima ta farka ta tashi ta zauna,in taga bai ma kallonta sai ta koma.
Kai ya girgiza tare da ja mata bargo,abin nata ma abin dariya.

Washegari ma haka har ta kwanta goma ya kwankwasa ta bud'e tana hammar karya da murza idanu halamun bacci take.
"Shayi,koh kin manta?
Wata hammar ta sake ta karya duk yana kula da ita,abin har dariya yaso bashi sai dai ya gimtse.

"In kin ware ina jira..
Da kallo ta bishi tana chunno baki ganin wannan kuturin sanaben irin na Uncle.
D'aki ta koma tare da zarar hijab ta d'aura bisa kayan baccin ta nufi kitchen.

Mika mishi take harda wani munafukin murmushi wai duk dan ya batta tunda ta sau fuska.
Murmushi yai tare da amsa yana girgiza kai,shi wai Farida zatai wa wayo.

Sha yake yana dubanta jun yadda take mishi tad'in daga term din nan sai SS3.
Murmushi ya yi tare da gane inda ta dosa.
Dan haka sai ya fara biye mata har da su dariya.

Ajiyar zuciya yai yana kallonta,kallonshi ita ma take tana murmushi, ganin abin yai yawa yasa ta dukar da kai da dan kunya,murmushi yau tare da fad'in
"My yori-yori uh uh..

Sato kallonshi tayi kai duk'e tana murmushi,
"Uncle wai meye ne yori-yori?
Shayin ya kwankwad'e gaba d'aya jin anzo wurin yana murmushi ya ajiye kofi.

"Biya na baki bayani..
Zama ta gyara tare da dunkule hannunta ta mika mishi tana murmushi.
"Gashi toh..
Murmushi yai tare da kallo hannun, hannunshi ya mika mata halamun ta bashi tana kunshe dariya.
Yi tai kamar ta bashi abu duk da ba komai a cikin hannun tana dariya.

Tafin hannun nashi yake kallo ta biye mata yana fad'in
"Uhmm,duk wannan ni kad'ai?
Kai ta jijjiga tana dariya,hannun ya hau jujjuya wa kamar gaske.
"Amma abin yai kyau..
Kai jijjiga
"Toh a fad'a min..

Kallota yai dauke da murmushi.
"Kawo kunnenki ban son kowa yaji.
Matsawa tai ba tare da ta kawo komai ba ta mika kunne.
Kamar mai rad'a ya fara mata magana a hankali, tsit tayi tare da nutsuwa idonta rufe tsawan lokaci.

Dago wa yai yana kallonta,dan haka sai ta bud'e ido tare da kau da kai tana murmushin kunyar jin abinda ta tambaya.
Tabbas da tasan wannan ce ansan da bata tambaya ba kayan kunya.

''Kin gane bayanin?
Hannu tasa tare da rufe fuskarta wai ita kunya tana fad'in
"Uncle..
Dariya yai tare da fad'in
"Koh ke ba ita ba ce?..
Juya wa tai tare da sanya kanta jikin katifar ta rufe fuska tana murmushi.
Kai ya kad'a tare da murmushi.

A hankali ya fara janta da fira, tun bata iya magana har ta ware jin labarin su Aunty Feenah zasu dawo Kano.
"Yanzu nasan Little Haly ta sake girma mai kyau da ita.
Kai kad'a yana murmushi.
"Ki daure ki haifo muku taku mey kyaun tunda su Saifu ma naso.

Ido tai mishi kir a waje.
"Na haihu kenan?
Kai ya jijjiga.
"En,mey ki ke gudu?
Kai ta sunkuyar,
"Azabar haifan babyn,da ana siya sai mu siyo na huta..
Ido ya sa mata,jin yai shiru yasa ta kalloshi, dariya yasa harda kyakkyatawa,lalle har yanzun da sauran Farida.

Kallonshi take tana yake baki,har ga Allah da gaske take,in dai ana siyar wa gwara a siyo ta huta da fitar da ta jikinta.
Kai ya kad'a tare da tsagaita wa.
"Halima da kanta take haifuwan su Saifu a gida ma ba babu mataimaki Farida..

Ido ta zaro tare da wage baki,dan haka da sauri ya jijjiga mata kai halamun yes.
"Wani sa'in sai dai nazo na tarar har ta yanke cibi kamin ta kira makociyarta Aunty Rabi taimako.
Kai ta jijjiga, lalle yar baiwa ce..
"Jaruma ce koh acikin mata Halima,nasan kuma yana da nasaba da hakurinta...

Baki ta chunno jin yadda yake kwad'a Haliman kamar wani ita ta rage mace d'aya jaruma a duniya sai kwad'ata yake.
Tuni dan halin ya motso na kishi,har kullum ta rasa mey yasa take kishin Halima koh da kuwa cikin mata ne.

Kalloshi tai yadda yake murmushi yana dad'a lissafo mata wacece Halima da jarumtarta.
Baki ta sake turo wa,dole ta dage dan sai tafi Halima jarumta,tuni taji tsoron haihuwar ma ya fuce akanta dan kishin yadda yake kwad'a Halima...

Shiru yai tare da zuba mata ido ganin yadda take chunno mishi baki.
Dan harshe ya dan cije,ashe fa ya kwafsa.
Yafi kowa sanin yadda Farida ke ji in ya ambaci Halima,ya kuma rasa dalilinta na yin fushi a kullum.
Murmushi ya yi tare da girgiza kai,komai na Farida daban yake,in banda haka mai ya kai ki kishi da matacciya?

Baya ta juya tare da jan jiki sosai tai kan filo ta kwanta tana gunguni.
Kai ya girgiza,
"Farida matsala...
Gadon ya haye tare da kiranta tai mishi banza.
"Oh,common mana, jarumta fa na ce kawai ba komai ba kan Halima..

A tunzure ta tashi tare da fad'in
"Nima zanyi fin nata,ba ita kad'ai ne jaruma ba amma tun dazun ka ke ta kod'a min ita..
Baki ta saka tare da sakar kukan 6aci.
Galala yake kallonta da mamaki,kan ya farga har dariya ta subuce mishi,dan haka tuni ta sake tunzura tare da kok'arin sauka dan barin mishi d'akin ya ruko ta.

"Ok,ok,toh naji,i'm sorry,shikenan?
Kai ta girgiza halamun ba shikenan ba tana chunno baki kuka ba koh hawaye.
"Ai ke in anzo kanki karshe ce believe me,dan sunanki jarumar mata a fagen jarumta wane Halima..

Kalloshi tai da y'ar harara jin zai zurma ta.
Kafad'a ya daga da fad'in
"Sosai.
Har ranta kwa taji dad'i jin ya zama serious.
"Sai dai fa da matsala..
Ha6a yake shafawa yana mata kallon kasa-kasa.

Ido ta zaro,
"Matsalar mey?
Matso wa yai tare rad'a mata,kai ta d'auke tare da k'auda kai tana sinke kai,in dai zata zama jarima yanzun ai tana ga ba abinda zai gagara,dan haka cikin sauki yasha tunaninta cikin ruwan sanyi.

Kallonta yake yana murmushi tai bacci, lalle ne Farida kam bata da wayo,abu kad'an zaiyi wayonta ya kare.
Kai ya jijjiga tuno rigimar tata da yadda komai ya kare sai ya sake murmushi har hakoranshi na bayyana,bargo ya gyara mata kamin shima rufe ido.

Tun daga ranar ya samo lagon kayarshi,yanzu zai 6atar da tunaninta daga baya ya hau dariyar keta in ta tuna yadda take zurmuwa.
Burinta a yanzu zata iya haifar baby koh da yanzu yazo zata nuna jarumta koh dan son su Saifu da ita da suke ma Baby.
****

Sun koma makaranta,dan sanabe
chan karshe suka maida bencinsu su biyu ita da aminiya Laila,a cewarsu yanzu sun fice ajin yara dan haka wuce nan.

A yanzu basu da burin da wuce ganin sun faranta ran mazajen nasu da iyayi irin nasu had'i da shawarwarin juna,dan haka tuni suka sake dinkewa ana baje wa su Nasir bajakolin iya yi.

Su Uncle abin nema ya samu,wai matar direba ta haifi mota😜
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

66_Zaune suke a parlour ita da yaran su na kallo,a dan jima su kalli kofa halamun dai da wanda suke jira zai zo anyi hutun makaranta sannan ba islamiya.
Cike da farin ciki suka mike jin sallamar Uncle baki har kunne dan murnar zuwan bakuwar tashi.

Zai wahala in baka sani ba ka ce wai tafi Uncle a shekaru,dan ita mai karamin jiki ce ga kuma wayewa da ilimi da ta samu wanda shi zai banbanta ta da sauran 'yan uwanta.
"Aunty Hafsa..
Da murnar su yaran suka tare ta lokacin da ta sako kai parlourn.

Da murnarta ta tare su tana mai kallon Farida da murmushi.
"Sannun ku da zuwa..
Hand bag nata ta kar6a lokacin da take kok'arin since goyon dake bayanta sukai mata chaa a ka kowa na kok'arin amsar babyn.

Kai ta girgiza tana murmushi ganin yadda har Uncle din sun mamaye babyn sai fad'i suke
"She's so cute..
Farida na dariya.
Matuka iyalan Kabir sun burgeta,duk da wannan ne haduwarta da Farida na farko sai dai a waya,amma ta gano su na da kyakkyawar mu'amula da junan su.

D'akinta ta sauke ta,dan sosai ta san mahimmancin wace ce Hafsa gun Uncle a yau ganin yadda bak'inshi yaki rufuwa har kowa ya tafi su na a tare firar yaushe gamo.

Ajiyar zuciya yai yana kallonta.
"Har kullum ina alfahari dake sis ta yadda ki ka jajirce gun karatun ki,i'm so proud of you,ina fatan na kira ki chief Nurse watan wataran.
Murmushi tai tare da gyara zama.
"A kullum kai ke karan gwiwa Kabir har na zama abin da a yau na zama,na gode, Allah ya bar mana zumunci.

Kai ya kad'a yana murmushi,
"Amin sister,ni ne da godiya.
Kai ta kad'a.
"Gaskiya kai dacen mata mai tsanin son yaran ka,sannan matuka tana hankali in ka cire 'yar yarintar dake tare da ita wanda yai dai-dai da wayonta,sosai nake ganin kok'arin yadda muke zumunci a waya, a waye take batta duhun kai.
Kai ya kad'a yana murmushi.

D'akin Faridan ta shiga bayan sunyi sallama da Uncle din.
A goye ta tarar da babyn nata Farida na dan jijjiga a hankali halamun tai bacci.
Murmushi suka sakar ma juna.
"Har yanzun baki kwantar ba Farida,kar fa ta saki ciwan baya.

Murmushi tai tare da girgiza kai,
"Ai bata da nauyi,goyon ke min dad'i ne..
Kai ta kad'a tana jinjina a gidan wa ya fi wani son yara,uncle din? Koh Farida koh su Saifu?.
Tasan dai a yau 'yarta tasha kauna da d'auka.

"Kullum ina cewa Uncle in mun samu dugun hutu muje Sokoto ashe zaki rigamu zuwa sai dai gaba.
Kai ta kad'a tana murmushi
"Yana fad'a kam,ga nan bikin Saliha ya kusa in ta gama secondary Insha-Allah,dan su ma sun kagu su zo toh karatu.

Kai ta sunkuyar tana murmushi.
Ganin firar Farida ke so taki tashi yasa ta ce
"Kawo ta ki ga,kije ki kwanta kema.
Keya ta sosa cike da kunya ta sinto babyn,ta dan jima tana sinke-sinke kamin tai mata sallama ta fita.
Kai Hafsan ta girgiza tana murmushi tare da sauya wa babynta pampers.

D'akin ta tura tare da shiga tana leken shi.
Harara ya dan sau mata lokacin da yake gyara labule ganin iska na kad'owa na hadiri.
Marairaice wa tai tare dan karasa wa tana ajiye farantin shayi.
"Mey nai kuma my boo nah?..
Sake harararta yai kamin ya janyo window.

"Wato kin samu Hafsa ni kin manta ni koh? Na zata achan zaki kwana..
Murmushi tai tare da cire hijab da zanin da ta d'aura a kai.
"Toh bari na koma,dama firar bata kare ba ita ta koroni..

Zani ta dau tana chunno baki kamar gaske ta juya zata koma ya chafko ta yana fad'in
"Ba ki isa ba kuma wannan,in an shigo min ba'a fita kin sani..
Baki ta sake chunno mishi tana gunguni ya hau mata chakulkuli kad'an tuni ta ware tana dariya ta zille zuwa katifa ya biyo ta.

Ajiyar zuciya yai tare da yin filo da kaffafunta.
"Sosai nai farin cikin zuwan Hafsa a yau,dan rabon da tazo nan tun lokacin Fatima,matuka ina sonta da burin kyautata mata iyakar iyawa na Farida..

Kai ta kad'a tana murmushi sai ya cigaba.
"Hafsa kad'ai ke kaunata a lokacin da sauran 'yan uwana ke burin sun kuntata mini..
"Hafsa kad'ai ke iya sharing na kwanon abincinta dani Farida a lokacin da bani da rabo acikin abincin gidan mu..

"Hafsa ce kad'ai za'a dakeni,a tsangwameni a cikin yayuna ina kuka tazo tana lallalashina itama tana kuka tare da fad'in
"Kabir kai hak'uri,bani da karfi da na rama maka.. A yayin da sauran 'yan uwan nawa ke murna da dariya in har sunga kukana..

"Wallahi Farida Hafsa ce kad'ai a wanchan lokacin zata iya fad'awa wuta ta tsamoni dan so in har su Tabawa sun hullani dan so..
Ido ya rintse yana tuno wata rana achan baya,ranar da bazai iya goge wa cikin rayuwarshi ba.

Ranar da yake ihu yake komai tare da roko na Allah da annabi amma babu mai jinshi,maimakon haka ma dariya suke suna mai turereniyar hankad'a shi cikin rijiya in banda Hafsa dake ihun taimakonshi ba hali.
Hawaye ne ya zubo mishi ido rufe,da sauri tasa hannu tare da taro su itama tana hawayen.

Ido ya bud'e, sai ta hau kad'a mishi kai.
"A yanzu hawayenka masu matukar tsada ne Uncle balle har ka zubar min su kan wasu chan wanda basu chanchanta ba su Tabawa.
Murmushi yai mata tare shima da kai hannu yana goge mata nata.

"Basu nake ma kuka ba my yori yori.
Kai girgiza
"Kaunar Hafsa gareni ce ta sani kuka,na san koh yanzu ina da 'yar uwa shakikiyata mai kaunata a bangaren Abba da muke da jini..

Kai ta kad'a mishi tana murmushi.
"Ka d'auka toh d'aya ce tamkar da dubu,dama da wani taron na yuyu gwara d'aya kwakkwara Uncle.
"And na san watan watarana su Tabawa zasu iya kwaso kafa su iso gare ka,toh ina so daga yau ka barmin komai a hannuna,ka manta da ka ta6a rayuwa da wasu chan wai su su Tabawa.

"Yanzu kana da Umma,Abba,su Saifu,Aunty Hafsa dasu Aunty Feenah masu kaunarka..
"Bayan haka kana da Farida,koh ni kad'ai na isa na maye maka gurbin su Indo da ka rasa believe me.

"Cos you're my heart,my soul,my world,my Jannah,my treasure..
Murmushi tai tare da jaddada mishi
"You're my everything..

Murmushi yai tare da janyo fuskanta ya had'a tare da nashi yana sauke ajiyar zuciya, in da Farida a kusa yasan ba shi babu shiga cikin bakin ciki zata wanke zuciyarshi ne tass.
Ya gode Allah da ya bashi Farida madadin Halima,domin in ana neman *Mar'atus saliha* a garshi zai daga hannun Farida sama ya nuna,domin ga ta a gareshi.
By


Feenat Ja'afar.
Ai  min afuwa jiya na ce zan turo shiru,na fita ne anyi rashi ma Auntyn mu, thanks.
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
        (admin
   Arewa hausa novels
       Novels villa
     Duniyan novels
   Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
          And
Cool novel, makeup and cooking)

      WHATSAPP NO:
    +2347039625239
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

67_Kwanan Hafsa shida ta tada ballin gobe zata tafi dan kwana uku tazo musu sun hanata tafiya,wasa-wasa sai da tai kwana takwas kamin ya batta ta tafi yana mata tsiyar koh Yunus ya motso kambun sa?
Murmushi kawai ta musu amma ba wai dan ta gaji da zaman gidan ba,yara take tunani da ta baro ga zata Kano.

Ba karamar tsaraba suka jido mata ita da yaranta, barin Farida kayan baby na mata sai jida take ma babyn Hafsan su kayan wasa.
Ido ne kawai nata,dan so kam ta ganshi gun Kabir da iyalanshi,bata jin koh Fatima dake a jininta tai mata rabin karar da Farida tai mata,dan haka cike da kaunarta ta baro gidan da sake son d'an uwan nata Kabir.
***

"Tashin hankali, wannan ai koh Makkah ki ka je sai haka irin wannan tsarabar Hafsa,lalle duniya tana gidan Kabiru..
Kai ta kad'a kanta na bisa waya tana latsawa, sai dai jin abinda Tabawa da Indo suka fad'i yasa ta dago kai da sauri baki sake tana kallonsu.

"Ku ma za kuje ina?
Harararta Lami tayi tare da fadin
"Abuja gidan Kabir,koh ba komai ai wannan ma nashi ne kuma jininshi ne..
Baki Indo ta yage tana kad'a kai
"Kwarai kuwa,dama wallahi dama kawai nake nema na rokeshi kud'in jari dan ni kwarjini yake min..

Murmushi Hafsa tai na takaici..
"Baza ku ta6a sauya wa ba daga inda nasan ku,a kullum ku duniya ku ke hange ba wai lahira da mugun abinda kuka shuka ba..
"Ban tunanin har yanzun baku saduda ba,wato ku ba ma ta neman gafarar abinda ku ka mishi ku ke ba sai ta abin duniya?

Le6e ta cije
"Na gode Allah da ya wareni cikin ku sannan ya banbanta ni da dabi'ar ku wallahi, ba da ban Kabir yai mun tuni ba da sai na ce wallahi ina da na sanin kasantuwa ta acikin ku...

Mari Lami ta dauketa dashi tana huci.
"Wawiya kawai,toh bari kiji duk lalacewa ta baki isa sauyani daga uwarki ba,da wanda zai ce bai son duniya? Koh ke ba kwadayin bane ya kai ki mu za kiyi wa bakin cikin zuwa?..
Hawaye ke zubo mata dafe da wajen marin,sai da ta kai aya kamin ta tashi ta sa6a yarinyarta ta hau tattare kayanta dan takaici.

Gidan su Abba ta koma jin duk sun chako mata da fad'in
"Eh ki kwashe yar bakin ciki,wanda zamu samo sai yafi wannan, ki zuba ido.
Kamar kullum in tazo Kano da kukan bakin cikin y'an gidan su take koma wa sokoto, amma yau dake Umma na gida dama takan je mata ita da Kabir tun da sun saba anan ta gama hutun ta ta koma.

Sunfi sati su na neman address na Kabir a Abuja sun rasa wanda zasu tuntu6a,su Indo kad'ai ke shiga sashin su Abba a dalilin zuwan Umma,toh ba fuska balle su tambaya, ga kacha-kacha sukai da Hafsa sunyi imani bazata basu ba.

"Ga dabara..
Tabawa suka kallo gaba d'ayan su.
"Ke Fatsima tunda kina da waya ki kira Hafsa a zuwan bata hak'uri sannan ki ce munji munyi nadama ta baki adireshin zamu mu bashi hak'uri, in ta kama ki kawo har kukan karya zanyi mata nasan ita akwai wayo.

Shewa suka sa harda tafawa har yaran.
"Tinkiya ta na siyar jiya dan nasan in munje zan maida har kud'in rago, na fad'a wa Murtala sati biyu zamuyi koh wata dan haka dama bai bani ci balle sutura dole ya barni zuwa cin arziki yaki,karshe wai na zabi daya.

Shewa suka sake yi suna dariya
"Toh ke mey ki ka ce?
Baki ta ta6e
"Wannan kaddararran auren wallahi kud'i yafi min shi,tuni ma na ce na zabi tafiya Birnin tarayya Habuja..
Dariya suka sa suna fad'in tai musu dai dai,harda mai fad'in itama in dai ta samo dayawa sakin nata mijin zatai ta kama gida.

Haka kwa akai duka kira Hafsa,duk da bata yarda dasu ba amma jin yadda suke rantsuwa da Allah yasa ta yarda sun gane gaskiya,karshe harda sake musu nasiha zata kashe waya suka sake makale murya akan ta basu address na Kabir koh su Indo su wakilta su nemo musu gafara.

"A'a Tabawa,bai kamata daga dawo wata su na su diba su je ba..
Da dad'in baki sai da ta bayar tana mai fatan Allah sa da gaske su Tabawa sun shiryun.

Kwana biyu da haka kuwa sukai shiri su biyar dan wai masu kud'i basa son yuya balle ya'ya, dan haka suyi hak'uri sauran duk abinda suka samo tare za'a raba.
Da wannan aka nufi Abuja koh su Umma ba wanda ya sani.

****
Waya yake mata yana tuki tana y'ar dariya mai sauti tare da fad'in
"Me too..
Shiru tai tana saurarenshi tare da barin abinda take tana fad'in
"Ok Sugar...
Wayar ta cire a kunne tare da kaiwa baki ta bata dogon kiss tana mishi dariya.

Kai ya kad'a tare da fad'in
"Yauwa,sai na iso..
Wayar ta ajiye bayan sunyi sallama ta cigaba da juye abinci a flaks tana murmushi yaran zo dan cire kayan Jumma'a wai za su wasa jiki a backyard.

Dariya suke ma su Saifu dake nuna kumatun Nass wai yafi kowa kiba tana kad'a musu kai suka fuce.
Koh ita kanta Uncle fad'i yake wai shi kam ya iya kiwo, sai sake cika mishi ido take da kyau.
Murmushi tai dan tuno Boo din nata,tasani duk inda yake toh yana gaf da dawo wa gare su dan 5 tayi..

Windown kitchen din ta leka ta inda take jiyo hayaniyar su Saifu.
Murmushi tayi tuno da lokacin baya suna ball tare,kai ta kad'a, yaushe zatai tunanin zata zama Mom nasu Saifu a lokacin, murmushi tayi tare da sakar ajiyar zuciya ta ambaci
"My boo.
By

Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

68_Sallama akai,dan haka sai ta rufe tare da fita jin muryar John na fad'in ta leko wai gidan suke nema wasu daga Kano.
Gyale ta dakko tare da fita tsakar gida kowacce da kullin kayanta.

Da fara'a ta ce su shigo jin sun ce dangin su Kabir ne daga Kano ta zata koh yan Rano ne.
Kalle-kalle suka fara suna zungurar juna jin sanyin a.c da kuma kyaun parlourn.

"Humm,Aljanar duniya,ji wannan alatu ni Tabawa...
Zungurarta Lami tai halamun tai shiru kar aji ganin Faridan ta nufi kitchen kashe gas.
"Ji matar tashi,wannan ai ya haifeta ashe da gaske?
Hannu Lami ta kai bakinta halamun suyi shiru man.

Da fara'a ta sake fito wa d'auke da faranti da kofuna da abin sha,tuni suka hau yage baki..
"Ya ku ka zauna a kasa? Ku hau kujera please..

Baki suka sake wangale wa kamin duk suka d'ane bisa kujera,duk da yarinya ce Faridan amma ba karamin kwarjini tai musu ba dan ta gaji da gayu ta ko'ina, dan haka tuni suka sake raina kansu.

Zama tai suka gaisa,tuni suka hau bata labarin irin wahalar da suka sha gun neman gidan kaf kud'in su ya kare.
Yake tai musu tare da tashi ta koma kitchen, haka kawai taji basu wani kwanta mata na sosai duk Sonta da dangin Kabir.

Abinci ta zubo a plate yaji naman kaji da akai wa Pepper chicken da fried rice tai shar da vegetables tai green.
Wasu ta bawa tare da koma wa dan debo wa sauran da basu samu ba Uncle ya shigo.

Cike da mamaki yake duben su kowacce ta shiga taitayinta kai duk'e.
Da mamaki ya shiga kitchen jin Farida na waya tana fad'in
"Bari zan kira ki nai baki...

Baki sake yake dubenta,hala bata gane su waye ba?
Juyo wa tai jin takun shi,murmushi ta sau mishi tare da bashi dan peck tana mishi sannu da zuwa.
Kai kawai ya kad'a.

"Ka ga bak'i koh?
Kai ya kad'a mata.
"Kin gane su kuwa?
Kai ta girgiza tana murmushi tare da jera sauran plates din bisa babban faranti kanta duk'e.
"Su Tabawa ne f...
Da sauri ta dago tare da kallonshi,a hankali annurrin dake bisa fuskarta ya fara 6ace wa,ido cikin ido suke kallon juna,dan haka sai ya daga mata kai halamun

"Yes,su ne..
Farantin ta ajiye tare da yin parlourn a sukwane har wani 6ari jikinta yake ya d'aura a bayanta.
Cinyar kaza Tabawa ta d'auka zata kai baki kamar mayunwaciya Faridan ta baiyana.

" Toh ya'yan *al beit beiti Abouna*,kar
 ki soma,dan wallahi in ma kinci sai kinyi amanta anan wajen makira algungumai kawai...
Gaba d'aya suka juya tare da kallo mai maganar, a tunzure ta karaso tare da kwace kazar hannun nata ta warce plate.

Ido rufe tana yarfa musu ruwan bala'i.
Sim-sim kowacce tai kasa kamar yadda ta ce a daga mata kujera.
"Ni? A gidana?
Kai ta girgiza
"Wallahi ba bu fuskar tar6arku balle har ku ci abincin da na girka...

Lemon ta janye,da sauri ta dago tare da fad'in
"Ina sauran?
Ido suka hau raba mata,shi dai Uncle ya hard'e hannu sai neman dariya yake ganin yadda Faridan ta haukace musu.
Window ta nufa ta bayan backyard tare da zuge wa ta kwad'a kiran su Saifu da karfi

"Boysss...
A tare suka had'a bakin fad'in
"Yes Mom..
In sun ji irin wannan kiran..
Kallon-kallo su Lamin suka fara,su duk a tsammanin su Maigadi ta kira dan basu ga yai siffar masu mutunci ba,dan haka tuni suka fara bada hak'uri su Saifu suka diro.

Tuni suka had'e rai,dan ba mai sanar su sun san sarai su Tabawa ne.
Su Tabawa ta nuno musu,
"Ku chaje min su su fito da lemo ukun nan yanzun matsiyatan banza.

Jaka suka zuge tare da miko wa su Saifun suka warce suna galla musu harara.
Kujera Uncle yaja ta dining ya zauna ganin dramar Farida da yaran sai tuttoshe hanci suke wai wari ma suke.
"Dan Allah Hajiya ki saurare mu, mu fa gafara muka zo nema..

"Gafara?
Kai suka daga da sauri
"A gun wa kenan?
Uncle su ka kallo a dan dirare,
"Gun mai gidan..
Zama tai bisa d'aya daga kujerun parlourn tare da hard'e k'afa d'aya bisa d'aya rai had'e
"Ni ce mai gidan nan in dai nan ku ka zo,ku fad'i komai ina sauraro..

Kabir suka kallo,dan haka sai ya ciro waya ya hau latsawa tare da had'e rai, dan haka dole suka koma ga Faridan duk da itama ba sauki.
"Toh Hajiya mun sani,dan Allah ki bashi hak'uri ya yafe mun gane kuskuren mu..

Kallonta take tana murmushi,
"Ke ce Lami koh?
Kai ta kad'a da sauri tana wangale baki,
Kai Faridan ta jijjiga,
"Naga alama,dan ance dama kinfi kowa karfin hali.
Kafa ta sauke tare da gyara zama.
"Za a yafe muku toh,kar kuji komai..

Da sauri Uncle din ya dago yana kallonta da mamaki,tashi tai tare da ciro phone nata ta seta recording tare da sake zama.
"Yauwa Hajiya,Allah kara girma..
Murmushi tai,kai kana gani kasan na mugunta ne.

"Za a yafe magana ta wuce har abada in har zaku cika sharudd'i na guda d'aya..
Zama su ka gyara tare da fad'in
"Toh Hajiya,muna ji in dai za'a yafe d'in za muyi komai..

Kai ta kad'a har yaran da uncle su na mata kallon mamaki.
"Yauwa,ina so a yanzu muje ga hukuma,ku sanar su cewa
  _'Ni Lami da Tabawa,mune muka shiga d'akin kishiyar mu muka turmushe jaririnta na fari har lahira lokacin da take wanka a band'aki...

A razane su ka kallota,har Uncle din wanda shi harda mike wa ya karaso jin wani sabon al'amari..
Kallon-kallo su Tabawan suka fara tare da tsananin mamaki a fuskokinsu.

San haka sai ta murmushi tare da kad'a kai ta tashi,
"Nasan kowa tunaninshi ina na san wannan acikin ku koh?
Baki sake suke kallonta ba koh kiftawa.
Uncle ta kallo,
"Wallahi su Lami su suka kashe yaron Umma na farko da hannun su Uncle,koh nayi karya?

Su Tabawa ta kallo hawaye na zubar mata,tsit sukai ba mai magana sai kallon-kallo wanda shi ya tabbatar wa da Uncle gaskiyar lamari kenan.
Ido ya rintse tare da fad'in
"Ya Rabbi..

Cigaba tayi,
"A gun kaka(Mahaifiyar Abban su Farida) naji zuwan mu Kano bayan Aunty Feenah ta sanar ni komai,a ranar naje gunta Uncle in bazaka manta ba har na kai dare,a ranar ganin unguwar su d'aya dasu Tabawa nasan bazata rasa sanin halin su ba take sanar ni taji da kunnenta Lami da Tabawa su na zancen su suka kashe jaririn Umma ranar zata shiga musu gaisuwa tarar su a d'aki suna maida zancen.

"Ta ce tai saurin barin kofar dan jin Lami na fad'in waye nan? Tai gun rijiya.
Hawaye ta goge tare da kallon uncle,
"Koh Abbanmu bata sanar wa ba,haka nasan Umma ma bata san silar mutuwar babyn ta ba,nima amana ta bani,amma a yau dole ce tasa na furta a gaban su,dan banga abin 6oye wa ba tunda sun aikata...

Le6e Uncle fin ya dan cije tare da gyad'a kai,kallo su Tabawan ya yi,da sauri su ka d'auke kai zuwa kasa,dan tsabar takaici sai ya nufi d'akinshi jin hawaye na neman zubo mishi jin wannan rashin imanin.

Kok'ari tai taga ta daina hawayen tare da yin murmushin takaici.
"A gare ku shima Kabir d'in ai mataccece ne,tunda kun kashe shi a ranar haihuwar shi,sannan kun sake kashe shi a rijiya mai ga6a da yawa.

"Indo,ina Indo take?
Kai Indon ta dago jiki a sanyaye,
''Sannu Indo kinji,Kabir ya fito da ikon Allah,da ku sauran y'an uwan masu murnar an hulla Kabir ya mutu.
"Su Tabawa ya rayu ba tare da ciyarwar wani shegen acikin ku ba,sai mey yai saura kuma?

Shiru sukai kai kasa,murmushi tayi tare da zubar da hawaye su Saifu suka matso lallashinta.
Kai ta girgiza

"Abu d'aya ne baku sani ba a kan Kabir a wanchan lokacin, na san da baku wahalar da kan ku ba gun lalle sai kun halakashi..

"Domin Kabir dashe ne na Allah,dashen da koh babu ban ruwa sai ya yi tsiro..
"Kabir muruci ne,murucin ma na kan dutsi,wanda ya gagari tona sai dai kallo,dan bai fito ba sai da ya shirya.

"Shin zaku iya abinda na lissafa ku sake maimaitawa a gaban hukuma haka?
Tsuru-tsuru sukai,tasan ba wanda zai iya,dan ba wai sunyi kama da masu tuban gasken ba.

"Munji duka mun d'au laifin,duk laifin Lami ne,ita ce mai bada wannan shawarar wallahi Hajiya bani ba..
A tunzure Lami ta kallo Tabawa,
"Au haka zamuyi da ke?
"Koh a kashe jariri kin d'anne yaro hanci kawai nasan na matse mishi..

"Koh kuma waye ya d'akko wuka ya yanka igiyar gugar Kabir ya fad'a rijiya? Sai yau nake da laifi banda ke koh?
A tunzure itama Tabawan ta hau fad'in
"Ai yarki ce Indo ta fara hankad'a shi karasawa kawai nayi..

Kallo Faridan su Saifu sukai lokacin da take saving recording din tana murmushi dan fahimtar mey tayi lokacin da ta kunna magana rau rau na fita kamar lokacin ake yinta.
By

Feenat Ja'afar

*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

69_Har komai ya kare suna kallonta baki sake cike da tsoro.
"Dan Allah Hajiya kiyi hak'uri, mun san munyi kuskure dan Allah..
Kai ta kad'a,
"Kuskure?
Kai suka daga suna sake kaskantar da kai.

Murmushi tai tare jijjiga kai
"Kalmar da na tsani ji kenan,'kuskure'.. Dan haka bani bukatar ku sake min second d'aya cikin gida yalla..
Kofa ta nuna musu rai a had'e, dan haka tuni suka sake kaskantar da kai Tabawa harda kuka dan tayi imani aka kai maganar gidan kaso za a kai su.

Ganin zasu 6ata mata lokaci tasa su Saifu su fitar musu da kaya sannan su kira mata Baba mai gadi da John ya taho da bindiga..
Zuruf suka mike ba shiri jin batun bindiga kowa ya kama hanyar waje su Saifu na kiran su
''Murderers kawai"..

Wajen ta fito tana fad'in
"Ku gane fiskokinsu Baba,idan ku ka sake ganin d'aya cikin gidan nan ka harbe min su,tsofin banza kawai.
Parlour ta koma ganin su Saifu da su John su fitar dasu a gidan.
Air weak ta dau tana feshe d'akin dashi tana tsaki,tabbas da gaskiyar su Saifu, ai sai yanzu taji warin da suke fad'i.

D'akin Uncle ta tura tare da shiga,a rigingine ta sameshi ya kurawa fanka ido,jin ta shigo yasa ya juyo tare da kallonta.
Murmushi yai mata,dan kaf yana jiyo komai har fitar su Tabawan.
Karasa wa tai tare da zama tana mishi murmushi tare da mika mishi wayar hannunta.

"Zan so a sada su Tabawa ga kotu Uncle tunda mun samu cikakken sheda sun fad'i da bak'in su,barin irin su cikin Al'umma babban hatsari ne,wallahi da ni wata mey fad'a ajin ce a nan kasar sai na kafa dokar duk *MATAN UBAN* da suka kashe,koh suka illata yaran kishiyoyinsu a kama su a d'aure su ai musu rataya ta inda kamin su mutu sai sun wahala..

Murmushi yai mata tare da da dan tashi ya zauna yana fuskantar ta,hannunta ya kamo ya rike,yadda take maganar ya tabbata da gaske take har zuciyarta,shi kuwa baya jin koh kashe su Tabawa akai zai sa ya huce takaicin abinda suka shuka a doron kasa.

"Ni ai nai gaba Farida,koh a haka Allah ya barni nasan ya nuna ma *MATAN UBA* nah aya..
Ido ta sa mishi.
"Ki kalle su man,a tsiyace, ki kalle ni,a wadace,abu d'aya na sani na hadithn hausawa da ya tabbata cewa
 'Duk wanda ya ce d'an wani bazai kyau ba,toh nashi bazai ba.

"Na gode Allah,da a hankali yake wanke min zuciya da farin cikin rayuwa..
"Farko na samu ilimi,na samu yara da mata masu tsananin kaunata da farin cikina.
"Koh koma war su Umma babban farin ciki ne a gareni da zai sa na shafe su Tabawa a rayuwata.

"Ba wai naki ta taki ba,amma ina mai tabbatar miki koh gidan kaso su Tabawa suka shiga ba shi zai sa na yafe su ba,a game da yaron Umma kuwa zan tuntu6i Abba,duk abinda ya zartar ba zance kanzil ba,a bangarena shari'ar Allah nake jira,dan nai imani tachan zata fi kyau da dad'in gani a gareni.

"Just focus ahead and stop westing ur time on those Jagaliyar su Tabawa chan da nasan koh a 'yan sharar gida na baki su ba zaki kar6a ba,ki d'auka daga yau mun wuce gurin.

Kai ta jijjiga tana murmushi
"Sosai kai musu nisa, Insha-Allah baza su sake gigin zuwa ba nasan,dan haka ba mai 6ata min ranka sanya shi inuwa your Highness..
Kai tai dashi kasa tana lumshe ido tare da sanya kan bisa hannun nashi kamar wacce ke a gaban sarki.

Murmushi ya yi tare da sauke ajiyar zuciya, Farida kad'ai ke iya gano lagon shi a saukake koh da iya ya 6acin rai.
Ha6ar ta ya dago yana murmushi had'i da kallonta idonta rufe.
A hankali ta bud'e su bisa kanshi tana murmushi.

Koh da su Umma suka ji murmushi kawai tai,take Abba ya ce shi sai ya doka su kotu akan wannan sunyi Shari'a.
Kai Umman ta kad'a mishi kawai,dan tasan wata Shari'a kam sai a gaban Allah,dan haka ta ce bashi da alaka dasu ya barsu kawai da fitowar rana da fad'uwar ta,amma fa bazata yai yafiya ba.
****

Lokaci na tafiya dan gashi har su na kok'arin zana jarabawar fita a secondary.
Abu d'aya ne yanzu burinta shine ta samu baby,dan haka duk karshen watanta zatai ta pt ne amma shiru ba bayani.

Da ta kawo wa Laila zancen zata fara fad'in
"Sai mun zo,ji wata kaddara fa? Haka kawai kina a wannan lokacin kina damun kan ki dan su Saifu na so?
Kai ta girgiza mata.
"Ba zaki gane ba ne Laila,Uncle ma naso, nima kuma ina son nuna mishi ni jaruma ce sosai dan da kaina zan haihu..

Dariya Lailan tasa kamin ta hararo ta,
"Lalle aiki ya kwa samu mata,a hakan zaki haihu da kankin?
Baki ta turo tana had'e gira,
"Eh man,ki sa ido tunda ke ba kya so..
Baki ta ta6e,
''Eh wallahi bana so sai nayi shekara uku..

Kai ta gyad'a mata tana mata kallon kar ki rainan wayo.
"Ke ni fa yanzun ma ba wai na yarda dake bane,dan wallahi kin sauya...
Harara ta kwad'a mata,
"Wallahi bana son wulakanci Mata,ji wani fata dan Allah? Ki tafi ma mu sauya waje karatuna ke a gabana.

Baki Faridan ta ta6e,
''Ke dai ki ka sani, amma gaskiya nake fad'a miki kin sauya,ki je a bincike..
Littafi ta rarumo da nufin kwad'a mata ta zille tare da mike wa tana mata dariya.
"Insha-Allah kin rubza ma..
Waje ta sauya da sauri ta bar Laila da tsarguwa,dai dai da Auntyn ta jiya haka ta ce anya Laila kuwa?

Ido ta fara rabawa tare da fara lissafi, tabbas karatu ya shige mata gaba har bata san ma tai tsallake ba a wata.
A zabure ta mike tare da yin gun Farida,tashi tai tana
"Wasa nake miki fa yi hak'uri kawas..
Hannunta ta rike tare da fad'in

"A'a mu bar karatun nan wallahi na tsargu nima..
Ido Faridan ta waro
"Da mey ki ka tsargu?
Gyalenta ta bata tare da fad'in
"Ke dai muje chemist,pt strip zan anso.

Kai ta girgiza mata
"In fa ni ce wallahi da wasa nake miki,ina san wani kamanin mey ciki?
Kai Lailan ta gyad'a tana fad'o wa Nasir a waya zasu chemist ya fad'a ma uncle.

Asubar fari ta doko mata kira koh sallaya bata nad'e ba tana kuka,tana jin Nasir na tai hak'uri zai san abin yi.
Ido ta zaro jin abinda ta ce,toh meye abin kuka ita gashi ido rufe nema take?

Amma tai mamaki,tunda tasan Laila tai planing, dan haka sai ta ce
"Ina ya'yan anguryar da ki ka had'iya guda hud'un toh? Ba kince na planing bane inji Auntyn ki?

Kukan ta bari,kamin daga bisani ta sau mata tsaki cike da masifa cikin kuka ta ce
"Ban sani ba din in baki da abin fad'i..
Kit ta kashe wayar ta bar Farida da waya a kunne baki sake,toh ita ta kar zomon koh mey?

Uncle ne ya shigo,
''Lafiya dai koh?
Kai ta dago tare da kad'a wa.
Abinda ya faru take sanar mishi duk ta marairaice.
"Mu nan nema muke dama wajena yazo tunda ita bata so..

Dariya yai tare da zama ganin yadda take fatan dama ita ce.
"Ni da kinbi ta tawa ki daina ptn nan,a hankali zai zo ne in baki damu ba.
Kai ta kad'a ba wai dan ta d'auka ba.
Dan tana sake wuce wata ta sake zirar pt.

Tsaki tai tare da furzar da iska tai flushing ta fito tana turo baki.
Dariya ya soma mata,dan haka kawai sai ta sau kukan 6aci hannu rike da strip.
"Negative..
Kai ya kad'a har lokacin yana mata yar dariya dan haka sai ta sake ta6e baki ta sau mishi mai sauti.

"Ok,I'm sorry,zo na gani..
Kafad'a ta make mishi tana cigaba da kukanta na 6aci,kai ya kad'a, amma yasan ba karamar raguwa za ai ba duk randa aka ce yau Farida a labor room.
Dariya yai tuno da zazzabinta na ranar yadda aka rika daga da ita akan allura kad'ai ma tukun azo batun labor.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.
2017.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).

71_Kusan kullum tana kan hanyar gidan masu jigo har ranar suna,duk da sun mishi huduba amma basu sanar ma su Farida mey suka sa ba sai ranar,sosai tai murna jin wai Uncle dinta ne ya samu takwara shi yasa akai musu bazata.

A cewar shi ta dalilin shi yasan Laila har aure ya dauru gashi harda rabo,ga aminta da a yanzu ta juye musu zama y'an uwanta tamkar ta jini,dan kowa kazo nazo ne dan haka sai suka had'a family.
***

Ajiyar zuciya ta sau tana murmushi, wani sa'in har mamaki take yadda Uncle ke kashe lokaci gaban mirror koh dare koh rana yai ta shafe-shafe da fesa turare a kuma goga na gogawa.
Koh ita bata wannan kyallin musamman duba ga dare ne yanzun.

Juyo wa yai yadda ta tankwashe kafa a tsakiyar gadon tare da daura pillow a cinyarta tare da riko riko ha6a da dukkan hannunta biyu halamun tagumi har lokacin idonta a kanshi sai wani lullumshe su take tana murmushi ita kad'ai halamun tai nisa.

Karasa wa yai tare da murza yatsunshi biyu a kusan fuskanta sukai kara,da sauri ta kalloshi a dan furgice.
"Hala na sauya miki kamanni?
Kai ta girgiza tare da duk'ar wa tana murmushin.

Hayo wa yai tare da d'auke hannunta a tagumin yai pillow da kafafunta tare da janye pillown tare da fad'in
"Gani toh..
Murmushi tayi tare da kad'a kai.
"Yau tun a bacin ki na fuskanci sai fara'a ki ke da magana a bakin nan..

Yatsa ya kai bakin tare da lakato shi,dan haka sai ta kau da kai tana murmushi, tabbas yau da farin ciki ta tashi wanda tasan baya rasa nasaba da mafarkin da tai a wayewar yau.
"Uhmm..
Kalloshi tai jin ya ta6ota.

Sanar shi tai yau ma sake mafarki tai ta haihu shi yasa tana ta farin ciki kamar a gasken ma ta samu.
Jim yai yana dubenta ganin yadda take sanarshi har kaman babyn da ta gani cikin mafarkinta.
Murmushi yai mata tare da shafo fuskanta,a hankali annurin fuskan nata ya soma dishashewa.

Tamkar wacce zatai mishi kuka haka ta marairaice mishi idon har ya cika da kwalla tana dubenshi.
"Uncle anya zan haihu da gasken?
Ido ya zuba mata ganin hawayen ya zubo da tambayar bazatan da tai mishi.

Mike wa yai tare da kwanto da kanta bisa kafad'arshi yana lallashi dan har ta bashi tausayi a yau.
"Don't worry My,Insha-Allah a gaske ma kin kusa,believe me..
Luf tai ido lumshe tana tunani,a kalla yanzu da gama secondary nasu sun shekara dan babyn Laila ba inda bai tafiya da kafanshi.

Tasan tai hak'uri, kamar yadda Umma da Uncle din ke sanarta a kullum.
Wannan karan har Feenah sai da tai checking nata kamar yadda ta matsa su ganta koh da matsala komai normal.

Yanzun ma abu d'aya ne tai hak'uri yake sake jaddada mata.
Kanta ya dago da hannunshi biyu jin har lokacin hawayen take ya kura mata ido taki bud'e idon.

Cike da nutsuwa ya fara mata abinda ya san lalle zata ware har hawayen k'afe.
Tsit kam ka ke jinta kuka ya kare sai love.
Fuskarshi ya cire a natan tare da had'e goshin su guri d'aya su na sauke ajiyar zuciya a tare ido rufe.

Shi kad'ai yasan kan kayanshi,dan haka a ruwan sanyi yake iya sanyaya ta koh da kuwa zafi ta hau,dan haka wataran takan kira shi da *'Mahboob*' dan a gareta karshe ne.

Hakan take gareshi, duk randa za'a kunnoshi koh ya shiga matsala ita kad'ai ke iya laluboshi har ya dawo saiti, dan haka ita ma in ta motso toh a ranar ta bar yori yori ta koma *'Mahbooban*' shi zallah kawai...

Kwanto mishi tai had'i da murmushin kunyar tuni wai ya samota wai.
Da sannu guguwar son ta motso musu dan haka murmushi su kawai ke tashi mai sauti tana 6oye fuska jin yadda yake mata rad'ar wani abun da halamun dai yau 'yar kunyar ya motso mata.
****

Hutu ake,chan Kano su Saifu ya mika su wannan karan dan ma su Umma hutu sai murna suke,dan haka gidan daga shi sai 'yar mitsilarshi,hakan yasa ya dawo tamkar gidan indiawa dan so.

A kitchen suke yau sai kusan goma suka tashi yin breakfast.
Duk yai mata dabaibayi duk wani motsi tare suke kana ganin su kasan ana kara'in honeymoon a gidan.
Kwai ta d'akko su na dariya ganin yadda ya dai-dai ta hannun nasu zai fasa.

A hankali ta soma tattare fuska jin wani karni da taji na kwan ya bugeta.
Daurewa tai su na kad'awa jin zuciya na taso mata da sauri ta zame tare da nufar gun sink da dan gudunta tana toshe hanci ta fara aman ruwan da ta sha dazun.

Da sauri ya nufota yana fad'in
''Farida..
Fuska ta fara yamutse wa rike da ciki jin dacin bakinta.
"Koh dai baki da lafiya?
Kai ta girgiza mishi hanci toshe,
"Dan Allah rufe kwan nan ban son ji at all..

Galala yake kallonta,dan haka da sauri ya rufe tare da riko hannunta sukai parlour har ta soma zifa.
Kalloshi tai jin yai shiru,kir yai mata yana murmushi ba koh kiftawa,dan haka sai ta dago mishi gira halamun lafiya?

Hannayenta ya riko gaba d'aya still bakin nashi yaki rufuwa.
"Farida..
Ido ta zuba mishi tana kallo.
"I think fa you're pregnant...
Ido ta zaro waje da sauri tare da fad'in
"Mey ne?

Kai ya kad'a mata yana murmushi,
"Jirani na dakko waya..
Da kallo ta bishi kai d'aure tana sake maimaita
''Pregnant?
Baki washe ya dawo tare da zama kusa da ita hannunshi bisa nata yana kiran Feenah.

Ido kawai ta zuba mishi jin yadda yake ma Feenah bayani suna dariya.
"Bata wayan Bros, Insha-Allah ma kwarnafi ne ya kwanta dis time.
Wayan ya bama Farida yana fad'in
"Insha-Allah..

Bayan sun gaisa take tambayanta last da tai period.
"2month karshe da 6days..
Jim tai tare da fad'in
"Dama kina wuce 2month d'in?
Kai ta girgiza mata tana kallon Uncle dake washe baki yana kallonta.
"A'a 2 month ne..
"Ok..

"Ya yanayin temperature naki? I mean akwai zazzabin dare haka koh zafin jiki?
Kai ta jijjiga da sauri,
"Akwai,na dan jima ma ina yi kusan 1month ba sosai ba..
Kai Feenah ta kad'a,
"Bayan tashin zuciya mey ki ke ji kuma?

Ba komai ta ce,dan haka sai ta ce ta bata Uncle din suyi magana.
Bashi tai tana mai laluba ciki,a hankali ta fara murmushi tana mai fatan da gaske ne.

"Ok,da girman kujerar ki Doc, yanzun kuwa.
Wayar ya sauke yana mata murmushi.
"Ta ce muyi pt koh muje asibi...
Zumbur ta mike tun kamin ya gama magana tana gyad'a kai.
"Akwai guntun strip d'aya a toilet da na ajiye tun kwanaki.

D'akinshi suka nufa tare da fatan bai expire ba.
Band'akin ya jawo tare da fad'in ta auna su gani bayan sunga bai ba.
Idonta a kulle ta fito tana mika mishi wai ya duba.

Ido yake zaro wa yana kallonta lokacin da take jiran tsammani ido a waje.
"Anya kuwa akwai?
Ido ta sake bud'ewa,
"Line nawa ya yi?
Da sauri ya sake duba wa kamin ya kallota har ta fara cije yatsa tana yarfe hannu cikin marairaice wa.
"2 ne..

Ido ta zaro tare da fad'in
"2 fa?
Kai ya jijjiga mata,kan ya farga har tai saurin kar6a cikin murna tana duba wa.
Tsalle ta buga da sauri cikin murna tare da rukunkumoshi tana fad'in
"Positive Uncle ka kalla I swear..
By

Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION(NWA).

72_Murna kam an shata, tuni aka fesawa Nasir,ita ma ta sau wa Laila kira.
"Wayyo ni,har na hasko idon ki wallahi a labor room ana push!!! Kina wayyo Uncle ka ceceni.
Dariya suka sa kamin tai saurin fadin
"Allah ya sauke,sai ka ce wata ke? A gida nima zan haihu ni kad'ai dan in nuna ma Uncle nima jarumar ce.

Dariya Laila sanya harda kyakkyatawa.
"Muna nan ai,maji magani.
Wayar ta sauke bayan sunyi sallama tana ta shafa ciki tana murmushi,
"Umma...
Ummanta ne ta fad'o mata,tabbas duk sonta da cikin bazata iya cewa wai
"Umma ina da ciki ba..
Ido ta rufe da duk hannunta biyu kamar Umman na ganinta wai ita kunya.

Aisha ce ta fad'o mata, dan haka sai ta maka kiranta tasan bazata iya jure wa ba dole a sani a gida.
Ihun da Aishan ta sanya ne yasa itama ta sanya su na tsallen murna,tana fad'in da gaske har Umman ta riske ta.
Tana jiyo lokacin da ta fad'a ma Umman tai kit ta kashe wayar da sauri tana dariya,wai ita ne da kunyar Umma.

Tun a mota ya fesa wa su Saifu da ya dakko gidan Feenah bayan sun d'au hanya.
Irin murnar da suke ne yasa ya fara murmushi, ya rasa wa yafi wani d'aukin cikin,shi? Koh Farida? Koh kuma su?
Kai ya girgiza,ba zai iya kwana ba,dan haka a ranar ya juyo sai bayan magriba suka isa Abuja.

Tare da Laila ya tarar su da mai sunan shi a zaune a parlour nan wai koya mata yadda zata kula da kanta take har lokacin labor.
Laila har baki ta bud'e ganin yadda suka tasa ta tsakiya sai ka ce sabuwar halitta kowa so yake ya ra6eta.

"Dan Allah Mom Farida ki haifo mana boy..
"No,girl..
Dariya suka sanya jin Sultana ta amshe da sauri,
"Yaushe zai girma toh kamar haka,hakan nan..
Saifu suka kalla ganin yadda yake kwata cikin shi.

Kai ya Uncle din ya girgiza yana musu dariya ya wuce d'akinshi,yasan in ya biye ta tasu yasan baza su barshi ba a wannan shakiyancin nasun.

Kula kam tana ganinshi da kauna gun yaran da Uncle kan cikin,haka kawai in taso zata sanyo zani tai cikin karya ta fito parlour su tasata gaba suna dariya.
Laulayi take ta6awa na mai wahala ba,ita dai batta a k'wadayin fan ice da tuwon laushi,kullum flask nata na a gidan Laila,dan ita bata iya cin nata.

Bikin Aisha aka sa wata biyar,dan haka sosai suke daga kan ba zuwa Kano nan da 5month.
Daga karshe ta kale tamkar ta hak'ura, ganin haka yasa ya ce ranar tazo suje wani gu cikin karamar motar shi.

Kamar wasa ya fara koya mata,kan sati har ya bata gwaji, abinka da mai rawar kai a hankali hannu ya fad'a.
***

"Uncle kar muyi haka,dan Allah kabarni naje,nai alkawarin kula da kaina ba yawo, kullum in na gida please...kaji? Haba my booo...
Kai ta langwa6ar gefe rike da hannunshi kamar zata sa mishi kuka.

Ajiyar zuciya ya sau tare da furzar da iska yana kallonta.
"Wannan ne babban matsalar,amma dayar matsalar ma zata iya sanya wa kin san aki tafiyar.
Baki ta turo tare da sanya kuka ba hawaye tana fad'in

"Haba Uncle dan Allah,koh sati d'aya ne dan Allah..
Ido ya zaro..
"Sati?
Kai ta kad'a da sauri
"Eh sati kad'ai dan Allah.
Murmushi ya yi tare da zame wa ya kwanta.
"Koh ba ni ba yarana ma sanin kanki baza su iya sati baki kusa da su ba,balle azo kaina...

Kuka ta fashe dashi na gasken tana buga katifa har da shura kafa ga nan ciki a gaba.
Basarta ya yi,dan fa abinda bazai iya bane wannan, ta tafi ta barsu wai har sati.

Kuka sosai take tun yana iya basarta har sai da zuciya ta debe shi ya jawo ta,ture shi ta fara tana mai cigaba da kukanta.
Ta ma yaya za a ce a bikin Aisha ace bazata ba?
A kanta aka fara haihuwa?

Kyaleta ya yi ganin yadda take daddagewa tana ture shi,dan haka sai ma ta sauka tare da bud'e kofa da sauri ta fice yana kiran ta.
Sauka ya yi tare da binta,dan haka da sauri ta rufe kofa,kofar ya tura tare da shiga har ranshi ya soma 6aci.
Dan haka tuni ya rufe ido ya fara fad'an dan ya ce ta hak'ura shi ne har zai jawo tai ma kanta illah?

Kukan ta bari tare da fad'in
"Eh dan ni banga dalili ba gaba d'aya cikin biyun..
"Akaina aka fara ciki? Koh kuma da Maman su Saifu bata nan basu rayu ba?....
Baki ya saka cike da mamaki yana kallonta,sai da ta dire aya ta hau sauke numfashi.

"Ni ki ke fad'i ma haka Farida?
"Ni ki ke sanar ma son ranki kawai dan na ce ki tsaya?
Shiru tai kanta kasa tana goge ido,tabbas zuciya ta jata har ta fad'i ba dad'i.
Dan haka sai ya kad'a tare da juya wa ya fuce kawai ranshi 6ace.

Burus tai mishi,a ganinta in nuna tai fushi zai batta ta tafi,ranar sai a nan ta kwana.
Washegari kowa rai a dagule ya tashi har yaran su ka zo breakfast su na dan kuskus ganin yadda take dan kallon bangaren Uncle lokaci-lokaci ranta ba dad'i.
Ji take kamar ta dubu shi amma ta kasa dan fa fushi take.

A shirye ya fito hanunshi bisa kwalarshi yana gyara wa,bai kalleta ba ya ce
"Guys,maza ku samoni mota nayi latti..
Agogo suka kalla,tabbas zai iya ci har ya gama su tafi,sai dai ganin yadda yake sauri yasa suka kwankwade shayin tare da binshi su na mata sai sun dawo.

Da kallo tabi shi yadda ya nuna ba ma ai ruwanta ba a gun,kai ta d'auke cikin kunar rai da takaici taga lunch box nashi bai d'auka ba.
Dauka tayi da sauri da zummar mika mishi yana kallonta yai gaba ya batta tsaye rike da ita baki sake.

Baki ta ta6e tare da koma wa ciki tana masifa ita kad'ai
"Wannan ai fad'an ma rashin gaskiya ne..
Zama tai a kujerar dining din tana hararar kofa.
Abincin nashi ta kallo,har tea ta had'a mishi da komai,dan takaici kawai sai ta sau kuka a gun.

Waya ta d'auka tana kuka tana tsara wa Umma abinda akai tun jiya har yau da hanata zuwan da ya yi.
"Ban san baki da hankali ba har yanzun Farida ba sai yau...
Baki ta saka tare da daina kukan.
"Akan wannan maganar shi ne har zaki nemi mishi rashin kunya yana yabonki sallah?

"Umma ce wa fa..
"Ki rufe min baki,yana y'ancin hanaki zuwa koh baida dalili kuma dole kiyi biyayya tunda mijinki ne..
"A shirmen ki ma wa ya fad'a miki hakan zai sa ya barki? A kalla kiyi ta rarrashi a matsayin ki na matarshi kina da hanyoyi da yawa ba wai wannan rashin hankalin ba..

"Ki tabbatar baki sake sa6a mijinki ba,balle ki fad'a mishi magana da yaranshi, yasan da ba Haliman ai,dan haka ki tabbatar yana zuwa kin bashi hak'uri...
Kuka sosai take,dan haka kit Umman ta kashe wayar.
A ganinta akan gaskiyarta take na meye zai fita yin zuciya?.

Kayan ta kwashe,duk da sosai taji ciwon yadda bai ci abinci ba ya fuce amma ba yadda ta iya zata bashi hak'uri, kuma bikin ta fasa ma zuwa.
Wayarta ne tai ruri,Laila ne,kamar mey jira da sauri ta d'auka.

"Mom twins ga maigida na gaishe ki..
Murmushi tai cikin sanyin murya tai magana.
"Lafiya kuwa?
Tabbas Laila na bata shawara wacce take bullar mata,dan haka sai ta sanarta har yadda sukai da Umma.

Kwafa tai mata cikin jin haushi.
"Wallahi har kin ban haushi ba kad'an ba...
"Wannan ai ba abin tada jijjiyar wuya bane,cikin kissar ki zai aminci miki ba sai an kai ruwa rana ba..
"Ina mamakin da karamin abu irin wannan yake gagarar ki wataran Farida.

"Abu na karshe ya zama na karshe gare ki da miji zai fad'a kina fad'a, haba Hajiyata,ba aji mu bane wannan,sannan duk tsiya kar ki sake barin d'akin mijinki wai dan ranki ya 6aci,ki danne har washegari ba'a raba shimfid'a da miji koh anyi fad'a sam ke baki ma da wayo Allah..

Ajiyar zuciya ta sau,tare da jijjiga kai,
"Toh ya zanyi,wallahi ji na nake a sama ne da naji ya hana,yi hak'uri ki ban mafita..
Duk yadda zatai ta tsara mata tare da fad'in ta tabbatar kuma ya hakuran.

Iska ta furzar tare da sauke waya ta kallo lunch box din,murmushi tayi tare da shiga kitchen ta juye mishi har nata tare da zirar mukullin mota tai office nasu bayan ta sake kimtsawa.

Wayarshi ta kira,su na tsaka da zancen su ya gani,sai ya danna reject.
Wayar ta sauke tare da mayar da gyalenta saman kai kawai ta kutsa office din tana gunguni.
Tambaya tai wata Sakteria ta nuna mata office d'in.

Tana ji yadda suke kallonta su na kus-kus din madam din Boss ne.
Kwankwasa wa tai,daga ciki Nasir ya ce 'yes', dan haka kawai sai ta tura da sallamarta.
Baki suka saka suna kallonta rike da lunch box da waya da keys a hannu.

Nasir ya kallo tare da sake kallonta jin tana gaida Nasir din.
Karasowa zatai ya tashi da sauri tare da fad'in su fita kawai ya rike lunch box sai wani kakkareta yake halamun kar a ganta.
Mota ya bud'e suka shige da sauri ya rufe tare da kallota rai 6ace.

"Mey ya sa baki ce zaki zo ba na fito koh baki ga da maza a ciki ba?
Baki ta turo tare da fad'in
"Ba ka ki d'auka ba,shine na shigo..
Ido ya sa mata ya ma rasa abin fad'i ganin yadda ta tsare shi da ido.

Ya bud'e baki zai magana tai saurin rukunkumoshi tare da fad'in
"Na tuba toh,please forgive me bazan sake ba har na jiya ma.
Ajiyar zuciya yai jin yadda take mutsu-mutsu wai ya ce ya yafeta.
By


Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION(NWA).

75_Yau kam mata ansha daga,dan sai wajen goma ta sauka,muryar nan har ta dashe dan mita da karad'in a yafe mata.
Dan haka tun abin na ba wa su Laila dariya har ta karya musu zuciya barin bayan ta haihun.

Kuka ta sa bayan an nuna mata wai mey ta haifa koh tana a hankalinta ta rufe ido kam.
Ranar lalle ta sake sara wa mata,ta sara wa iyayen da suka haifo ta duniya..
Ta kuma sara wa Halima mai haihuwa ita d'aya babu dan tayi,lalle jaruma ce ta kuma ajiye makamanta akanta.

Hawaye Uncle din yake goge mata tare da jera sannu,sannu yafi a kirga idonta rufe tana jijjiga mishi kai kawai.
D'akin hutu aka garata bayan an gama kimtsa ta aka kawo musu baby,zo ka ga yadda take make kafad'a tana chunno baki wai bata daukan babyn sai ta huce.

Murmushi Uncle ya yi kawai tare da fad'in su kyaleta.
Ba kowa daga shi sai ita bak'in nan har kunne,burinshi su Saifu su karaso da Nasir yaje d'akko wa.
Babyn take satar kallo lokacin da yake nuno mata yana fad'in sun samu Sultana 2 sai k'au da kan karya take tana make kafad'a tare da k'au da kai a ganinta ita ta sanya har jarumtar k'are.

Murmushi ya yi tare da juyo da babyn inda ta juyar da kan ya fara make murya da tamkar wai babyn ke mata roko da kirari a gareta na jarumar uwa.

  _"Dear Mom.. Forget Superman, Batman, Spiderman and all the other comic book heroes. They should make a movie about you 'Supermom'. Thanks Mom,thanks for being the hero,warrior in my life.._

_"Thank you for being so wonderful,I love you Mama.Please ki d'auke ni naji d'umin ki.._
Fuska ya marairaice mata tare da fad'in
"Please..
 
Murmushi tayi tare da rintse ido,wani dad'i take ji yayin duk wani zugi taji yana raguwa had'i kaunar manna babynta jikinta.
Hannu ta kai bisa yatsun babyn tana dan ja babyn na mutsu-mutsu,Uncle ta kallo tana murmushi sai ya lumshe mata ido had'i da shafo fuskarta.

Kofa a ka bude cike da murna suka shigo.
Baraden nasu ne su ma bakin nan har kunne cike da burin arbawa da baby..

Tashi yai tsaye dan basu waje tuni duk sun mamaye gadon Faridan ta matsa chan karshe kowa hannunshi bisa baby su na yabawa sosai.
Ajiyar zuciya yai tuno da lokacin baya sanda Halima ta haifo Sultana.

Kai ya sunkuyar yana murmushi, a'a yau ba Halima ba ce,Farida ne,rayuwa mai sauyi-sauyi..
"Dady..
Kai ya dago jin Nass ya kira shi tare da fad'in yazo wai yaga babyn na musu murmushi tasan sun zo..

Murmushi ya yi tare da matsawa ya tsugunna a gaban su nan suka lalace har kusan sha d'aya dakyar su ka hak'ura su ka tafi gida.
Washegari aka sallame su sukai gida.

Sai ga nan su Farida ana rokon Umma yafiya,ta sani haihuwar ta ne kad'ai ba tai ba amma ta bata ciwan kan da koh Aisha bata bata ba.

Kaka har mamakin yaran da Uncle take ta yadda tun yana kawaici har ta kai ta kawo a ranar kam parlour ta koma ta barsu da yaran ganin d'aukin babyn ba na karau bane har Faridan tai bacci.

Haka washegari dakyar ya lalla6a su musamman Sultana sukai makaranta, ya kuma sha mamaki da aka tashi yaje wai ba su Saifu.
Da mamaki ya kira aka sanar mishi ai sun karaso.
Kai ya kad'a yana murmushi, lalle yaran da gaske suke.

Fur da dare baby tai ta kuka har sai da Faridan itama ta sau kukan jin da ta fara bacci mai dad'i kaka zata tayarta baby na kuka.
Gyangyad'i take a zaune bisa gadon kaka na gyara ma babyn parmpers Sultana ta leko.

Kai kakan ta girgiza,
"Dama har yanzun ba kiyi bacci ba har sha biyu?
Murmushi tai mata tare da kallon babyn tare da sa hannunta a baki ta koma.

***
Tashinta kenan ta nufi band'aki tana hamma dan baccin dake idonta jin ana kiran assalatu.
A gaban gadon ta tsaya baki sake dan kula da ba baby a gadon sai shinfid'a.

"Na shiga uku...
Zazzage shinfid'ar ta fara da sauri gabanta na fad'uwa ba baby ba halamunta.
"Wayyo Allah,kaka..kaka..
Juyi kakan tai tare da amsawa,
"Kaka baby,na shiga uku an sace min baby kaka ki taimake ni..
A zabure kakan ta mike tare da watsakewa.

"Ke bana ciki da shirme..
Tashi tai ganin harda su daga zanin gado tana kiran babyn ta.
"Subhanallah.. Naga karfe biyu ma mun tashi,bari na duba koh ta mirgina chan bayan gado..
Hannu ta hau yarfe wa tana kuka,da sauri tai waje tare da yin d'akin Uncle.

"Wayyo Allah,naga ta kaina uncle..
A zabure ya mike jin kukanta, kasa ta zube tare da mimmike kafa hannu bisa kai tana mishi kuka dan haka da sauri ya sakko.

"Lafiya? Mey ya faru?
Jijjiga ta yake tana nuna mishi waje.
"Baby..ban ganta ba an sace min ita..
Galala yake kallonta,jin hayaniyar Kaka yasa da sauri yai wajen tare da isa d'akin, sama da kasa babu jaririya.

Waje ya nufa tare yin bak'in gate a kulle maigadi ya hau tuhuma yana mai tabbatar mishi ba wanda ya shigo koh ya fita.
Parlourn ya koma gabanshi na fad'uwa ya nufi inda yake jiyo kukan Faridan kaka na bata baki.

D'akin Saifu ya tura sai gashi ma ya fito jin haya niya.
D'akin su Nass ya koma ya bud'e duk baccin su suke dan haka tuni ya sake rud'ewa ya soma zufa.

"Toh waye zai d'au baby gida a kulle su na bacci?
Tunani yake,dan haka baida mafita tunda bata gidan kawai ya doka kiran police kan su basu ga fa babyn su ba.

Baba mai gadi ne yazo yana sanarshi wai baiga magen shi ba,dan yasha jin ance kuliya na cin jarirai..
Kuka Faridan ta sake kurmawa jin bayanin Baba maigadin tana fad'in ita dai kawai babynta za'a biya ta wallahi.
By

Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION(NWA).

76_Kuka sosai ta rika musu ba da ban karar gen ba da ba abinda zai hana tada kowa na gidan akan ita fa sai an fito mata 'yarta,haka kurum,yaushe ma ta dawo a nakudarta?.

Dan haka ba shiri Uncle yabi shawarar maigadi na duba bayan gidan koh za a ga kuliya duk da shi sam hankalinshi bai d'au abin ba,tayaya kuliya ma zata sungumi d'an mutum?
Sai dai borin Farida yasa ya d'au torchlight suka hau zaga gida.

Chak ya ja ya tsaya tare da fad'in
"Baba na tuna ba mu duba d'akin John ba..
Kai Baban ya kad'a, dan haka da sauri suka nufi d'akin sai ga nan kuliya kwance gefen katifar John tana bacci halamun ya manta ya rufo kofa da ita.

Parlour ya koma,iyanzu kam abin ya fara bashi tsoro ba mamaki ba?
Ga sabon dagun hankalin shine kukan Farida..
Waya ya ciro jin har an shiga sallah ya hau kiran Nasir wala Allah koh zai samu mafita ganin police kam shiru.

Laila ce ta d'auka gabanta na fad'uwa ganin kiran, tambayarta yake Nasir ta ce ya shiga alwala lafiya?
Kai ya kad'a tare da fad'in
"No,ba komai..
"Yauwa gashi nan ma.
Halin da suke ciki ya sanar mishi dan haka tuni ya hau salallami.

"Ka tabbatar har su karkashin gado kun duba da ko'ina?
Kai ya kad'a mishi tare da fad'in
"Ba fa inda bamu bincika ba a gidan nan Nasir,abin yana matukar d'aure min kai..

Jim yai tare da fad'in
"Toh koh Aljanu ne?..
Da sauri Uncle ya ce
"Aljanu kuma?
Ihu Farida ta sake tare da burburwa yana tai hak'uri tana mak'e kafad'a.
"Bari Nasir zan kira..
Wayan ya kashe tare da koma wa dan lallashinta har Saifu ya taso su Amjad duk sunyi chirko-chirko.

Tunaninshi koh dai ya sanar dasu Umma?
Kai yai saurin girgiza wa,toh mey zai ce ma?

Jim kaka tai tana dan tunani,
"Ni kam ka binciki wajen Sultana?
A tare su ka kallota har Faridan,da azama Uncle ya mike dan tuno wa da kwana biyu tabbas baya rufeta ta baya.
Kofar ya murd'a a hankali duk suka d'auru bayanshi su na leka wa tamkar sunzo sata.

Kwance take a rigingine tamkar wata teddy haka ta aza babyn a kanta a rub da ciki babban yatsanta na bakinta yayin da dan karamin ta sanya wa baby,da tai motsi in taji yatsa ta hau tsotsa da haka suke baccin su daga babyn har momman.

Juyo wa yai tare da kallon Farida wacce ta sau ajiyar zuciya mai karfi tana rintse ido.
Kai kakan ta girgiza, ta rasa ya akai tun da hankalinta bai kawo nan ba?
Lalle sha'anin y'an gidan nan sai su,dan haka su na shiga ita ta juya dan zuwa alwala.

A gefen gadon Uncle din ya zauna tare da kallon wannan dabara ta Sultana ita kam baby kamar ta samu sucker sai sha take.
Hannu ya kai da zummar d'auke baby sai kwa ta challa ihu,dan haka da sauri ya janye hannun yana ganin ikon Allah ganin
ta sake raruma ta hau sha.

Murmushi Fatidan tai tare da zama itama,jin kukan babyn yasa Sultanan fara motsi dan haka sai ya hau tashinta.
Ido ta bud'e ganin yadda suke kallonsu yasa ta kallo babyn,baki ta wage tare da musu yake sai ya d'auke babyn ta tashi.

Fad'a zai fara mata tai narai-narai zata sau kuka Faridan ta hau lallashi.
Sanar su take babyn ke kuka shine fa ta d'akko ta ganin su Mom Farida kar ta tashe su a bacci shine ta taya su raino.

Ajiyar zuciya yai tare da kad'a kai,ita kam Farida mamaki take da wayon Sultana, koh ma dai meye tasan dominta tayi.
Ta sani da tun haihuwarta take sake ganin so ga iyalan gidan da babynta,dan haka koh da ya bata babyn suka fita nan ta zauna tana feeding nata Sultana na taya ta har su ka dawo a sallah.

Uncle ne ya soma dariya tare da gwada ma yaran borin da Faridan ke yi dazun su na dariya,kai sai fa yanzu ta fara jin kunya.
Sallamar su Laila ne yasa suka saki baki su na kallon juna,shaf ya manta bai sanar musu an ganta ba.

Sosai sukai dariya lokacin da ake maida zancen yadda abin ya kasance sai tsiya suke ma Faridan.

Kaka kam tana ganin wani abu wai shi fi'ili a gidan Uncle.
Wanka wannan yanzu zata hau karad'in kiran Uncle din yazo kaka zata konata ya taimake ta.
Haka zai zo bakin kofar band'akin yana fad'in
"Kiyi hak'uri.. Umm,uhmm kaka a dan sassauta mata dan Allah..

Shiru take musu har ya gama rokanshi ya fuce sai fa tai mata.
Dan haka kullum wanka da kuka ake shiga a hakan ma tai ta jan hankali ruwan na huce wa.
***

Iska ta furzar ganin wannan kwalliya da taki karewa a gun Laila da Aisha.
Mike wa tai su ka sake zaunarta dan haka nata ido.

Sosai tai kyau ita da iyalan nata a yau kowa na yaba wa,dan haka tuni aka hau watsa selfie da y'an taron suna da babynta Leema.

A kunne Nass ke rad'a mata Uncle na kira a bayan gida wai ta taho da baby,dan haka sai ta bashi babyn ta ce gata nan zuwa.
Tamkar ango shima ya sha farar shadda ta manyan kaya bakin nan har kusan kunne yana daukansu da yaran.

Murmushi take tana gyara ma baby showel ya sake daukanta a hoto,a ganinshi bata ta6a mishi wai kyau ba irin na yau daga nan ya kira su Aunty Feenah da su Hafsa.
Suna kam ya kayatar matuka.

Watan su d'aya suka nufi Kano dan samun hutun su Saifu daga nan ta karasa wankanta chan.

Wannan farin zuwanta Kaduna gun Momynta ba tare da Aisha ba sai Sultana,sosai zaka fahimci da rashin sabo a tsakanin su,dan daga murmushi sai y'ar fira jefi-jefi.

Abu d'aya da ya bata mamaki bai wuce sakewar fuskar mijin momyn nata ba wannan karan,dan ita da gani take kamar ma bai son tazo gidan shi.
Shi kam ganinta nasa yaji haushin da fa yanzun ya'rshi ce da Abbanta bai mishi fashin mata ba karon farko.

Uwa uwa ce,dan haka a dan sati sosai ta ja 'yarta ta rage wani filakon,ganin hakan har da mata kukan ita tun aurenta bata ta6a zuwan mata ba.
Murmushi tai tare da fad'in zata zo ne watan wataran.

Cike da tsaraba Uncle ya dakko su suka dawo Kano daga nan Umma ta dasa a inda ta tsaya na gyaran d'iyar tata.
By

Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*

©Feenat Ja'afar.

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION(NWA).

77_A mota suke bayan sun dawo a gidan Aunty Rabi sun kai mata yini da Aunty Feenah.
Sai d'an kallota yake yana shafo ha6a da murmushi.
Kai ta sunkuyar dan wani abin har kunya ma yake bata a yau.

Sosai ita kanta tasan ta tsatso kyau da gyaran jikin Maman Juwairiya,ga nan kitso yiri-yiri da bai saba gani ba Umma ta sanya dole an yaryara mata shi harda na gaba,ga nan kunshi sak dai sai ta dawo kamar ba Momyn su Saifun ba.

Parking ya yi su Saifu sukai gaba da baby yayin da ya jingina yana sakar ajiyar zuciya.
"A gaskiya ki fa shirya,ni in son samu ne gobe ma mu wuce..

Kai ta langwa6e tare da marairaice mishi fuska kamar zatai kuwa.
"Kai My Boo,wata uku na zata zanyi kamin na koma ni fa nai missing su Umma fa.
Harara ya sau mata tare da fad'in

"Kwanan ki nawa da barin gidan ki?
Marairaice wa ta sake tare da fad'in
"Wata na fa kachal..
Murmushi ya yi tare da fad'in
"Itakillah Mom Saifu fa,wata amma kina neman kari? Baby Leema 2month take fa..

Baki ta dan turo kad'an tana gunguni ya matso tare da gwara mata goshin shi ta rike gun tana 6are baki.
Bakin shima ya 6are tare da tayata,dan haka sai suka fara dariya.

Wani waje ya kallo,a hankali fara'r dake fuskarshi ta fara raguwa tare da jan jiki ya koma set nashi ya zauna.

Juya wa tai dan ganin mey ya gano?
Su Tabawa ne tsaye ita da Lami su na nuno motar su halamun basu dai san su na ciki ba dan glass din mai duhu ne na ciki kawai ke iya hango na waje.

Murmushi tayi tare da girgiza kai,a kullum ta duniya Allah sake kaskantasu yake ta sani da hakkin mutum babban abu ne mud'in bai yafe ba.

Uncle ta kallo tare da kai hannunta ta riko nashi,ta sani da duk da su Tabawa basu a gabanshi amma tabbas in dai zai gansu toh fa zasu tuna mishi baya ne mey sa shi a 6acin rai.

Ajiyar zuciya ta sake saki,ta gode Allah da bai sa ta ari halin su Tabawa na *MATAN UBA* ta lakawa ruhinta ba.
Uncle din ta kalla,mutum har mutum mai matukar kamala da suffar kwarjini,ga kud'i ga lafiya da tsabar kyawun kama da jin dad'i da Allah a yanzi yai mishi baiwar su.

Su Tabawa ya kalla lokacin Indo ta fito,kai ta girgiza, tabbas the difference is clear,lalle ne duk wanda ya ce d'an wani bazai kyau ba toh fa lalle nashi ne bazai kyau.
Hannunshi ta sake rintse wa cikin nata tana jijjiga kai.

Ina ma *MATAN UBA* zasu gane abinda ta gano na game da sirrin rike da ta gano da tai imani daga yau an daina samun mugayen *MATAN UBA*.
Domin ta duba,aksar duk wanda hakan ta same shi kamar Kabir d'inta Allah yakan daga darajarsu ya martaba su sama da kima, ya kuma kaskantar da irin su Tabawa da d'iyan su.

Har kullum tana mamaki idan har aka ce *MATAN UBA* na cin zalin yaran kishiyoyinsu takan dasa ayar tambaya
Shin *kishi* ne koh mey?

Murmushi tayi tare da girgiza kai,
"Ba kishi bane,in har kishi ne matuka tana kishin Uncle ta yadda bata bukatar wata mace ta ra6ar mata abinta.

Abu d'aya ta bari wanda shine take ganin dalili su ne abu uku=
*Hassada*
*Mugunta* da kuma
*Rashin imani*.
Tana ganin wannan ita ce cutar da ke damun zukatan *MATAN UBA* irin su Lami..

Murmushi tai har hakoranta suka baiyana gareshi,cike da nutsuwa ta fara mishi kirarin da tasan in ta fad'i yakan dara koh da bai yi shiri ba.

"Gaba dai gaba dai Uncle na Farida Dadyn Saif da Amjad, Nass,Sultanat da Leema,wallahi kai makiyanka nisa nisa na har abada..

"Allah ja min zamanin ka,lalle ne kam mai laya kiyayi mai zamani, mai zamani kiyayi mai Allah,ka rugasu dan ka rike Allah..wai Aradu maganin shagalalle..

Dariya yasa sosai jin wannan kirari tamkar wata marokiya a gaban sarki,take yaji kuncin ya yaye,tuni maye gurbin da farin ciki.

Kai ya girgiza tare da fad'in
"Farida..
Kai ta karyar kasa tana murmushi tare da fad'in
"Yes your Highness..
Murmushi ya yi tare jinta lungu da sako na zuciyarshi.

Allah yai mishi baiwa, da Ni'imar ababe da yawa,ya gode,ba kuma zai gaji da gode sarki Allah na da ya sanya rawarshi har tai kyau haka.

Zaga wa tayi tare da bud'e mishi mota tana mai sake kaskantar da kai a gareshi tamkar wata driver, tuni kuwa ya fara jinshi bisa sama.
Motar ya kulle suka jero zasu wuce su Lami da suka sau baki gun kallon su.

Kasa suka zube da sauri ganin wani dan banzan kwarjini da yai musu har basu san sun furta ina wuni ba baki na ka'rkarwa.
Gefe yai da kai,sai Farida ke kallo su tare da rausayar da kai halamun ya amsa.

Da kallo su ka bisu har su ka shige gidan su Umma su na tad'in su cike da kwanciyar hankali tamkar ba mahalukai su ka wuce ba a gun.

Jiki a salu6e su ka tashi tare da shiga gida,sun sani basu isa tambayar gafara ba,dan a kullum sharad'i d'aya ke taka musu burki, sun sani da baza su iya zuwa ga hukuma ba su ce su din masu laifi ne ba.

A ganin su da kunyar duniya gwara ta kiyama,dan haka sun yarda su zauna a haka duk tabbas wataran hakan zai iya kumbura zukatansu,dan fa ga koshi ne,ga kuma kwanan yunwa.

*Karshe*
Lalle ne kam dama ai wata Shari'ar sai a lahira.
Ina rokon Allah ya yafe min d'ukkan kurakuran da nai a wannan labarin nawa na *MATAN UBA*
Ina rokon Allah da ya isar min da sakona inda nake da bukatar ya isa dan *MATAN UBA* su fahimci ina na dosa.

Nafisa Bashir Tanko,(Feenat Ja'afar) ke muku fatan Alkairi.
Ubangiji ya gyara zukatan mu da aikata khairan.


Download Matan Uba Littafi Na Daya Complete