[9/15, 5:47 PM] prince_s_square: 💧💧 *MATAR ABDALLAH.!* 💥
                True life story.!



*HASKE WRITER'S ASSO..*
Home of expert & perfect writer's.

 
*MALLAKAR : FEEDOHM💞*
  Wattpad:Feedohm

*BISMILLAHIR RAHMANUR RAHIM..*

01

     Duk'ar da kai nayi cike da jin kunya yayin da wani sashe na zuciyata ke cike da farin ciki. Tabbas abun alfaharine ace namiji kamar Abdallah ke son ya aureni, Idan akace na fitar da mace mai sa'a a layinmu ba abinda zai hana na fitar da kaina!

  "Tunanin me kike Muhibba? Ko Abdallah bai maki bane.?  Maganarsa ta katse man d'an gajeren tunanina..

  Cike da kunya nace "Ba tunani nake ba."

  "To me kike? Ya kuma jeho man tambaya.

Ban bashi amsa ba ya cigaba da fad'in "Ki aje duk wani tunani kin ji ko Muhibba?Ki fahimce ni banzo gurin ki da wasa, ba tsakani da Allah nake son aurenki, kuma bana bukatar daukar dogon lokaci, Idan da san samune bikin mu bana so ya wuce nan da nan da wata d'aya.."

  "Da sauri haka.? na fad'a a hankali

  "To meye a ciki? Kin san dae na fad'a maki ina da mata wadda duka auren mu da ita bai wuce shekara uku ba."

  A sanyaye nace "Amma me yasa kake son sake aure ya Abdallah.?

  Takaici ya fito k'arara a fuskarshi wanda bansan lokacin da nace "Kayi hakuri idan tambayana ya b'ata maka rai "

  "No baki bata man rai ba Muhibba, Duk lokacin da aka man maganar matata ina jin matuk'ar takaici wanda bana iya b'oyewa.."

   Duk'ar da kai nayi cike da tausayinshi, to me ke sashi takaici? ko ba auren soyayya sukayi bane da matar shi?

  Kamar yasan me nake fad'a a raina yace " Bansan dadin aure ba Muhibba, Nayi nadamar auren da nayi a baya duk da dai auren soyayya mukayi."

"Banyi sa'ar mata ba Muhibba dan girman Allah ki bari muyi aure cikin gaggawa."Ya sake fad'a cikin k'unar rai

  Cikin tausayawa nace "Kayi hakuri Ya Abdallah komae mai wucewa ne, kuma dama mu mata dole sae anyi hakuri damu , domin muni ne garemu.."

  "Banda ke Muhibba ina da yak'inin idan na aureki na yi sa'ar mata, Bazan boye maki ba kin fi matata komae! Komae fa nake nufi, Kyau ,hankali, sura, tarbiyya da ilmi Muhibba."

  "Na fita fa kyau ya Abdallah? Amma naga kaima ka fini komai Ya Abdallah shin me yasa kake son auren munannan mata ?Na fad'a cike da rashin wayau

  Yar dariya yayi ya shafa sumarshi kafin yace "Haske kawae na fiki Muhibba amma kin fini kyau sosae, kuma banda abunki skin dinki kala ce mafi tsada a duniyar mu.."

  Tab'e baki nayi don nasan kawae fad'a yayi don naji dad'i na gyara wuyan hijab dina ina kallon Baffa dake alwala bisa dankali sannan nace "Zan shiga gida Ya Abdallah magriba ta k'arato.."

  Cikin sauri ya rik'o hannuna nayi saurin fizgewa ina banka mashi harara nace "Ni dae ka daina rikeni gaskia, kasan dae haramun ne "
 
  Lumshe ido yayi tare da had'e hannunshi guri d'aya yace "Afuwan Matar Abdallah, Bazan kuma ba.."

  Murmushi nayi na juya a hankali ina waigenshi sae da nakai bakin zaure sannan na tsaya don ganin yana niyar tayar da jibgegiyar motarshi.

  Banbar gurin ba sae da dena ganin kurar motarshi,Cikin gida na shige da gudu na isa bakin murhu inda Umma Jamila take tana saka danwake na tsugunna ina washe baki nace "Umma Jamila kinsan Abdallah Aliyu?

  Kai tsaye tace "Mijin Hasna kike nufi.?

  Washe baki na kuma ina fad'in "Shi Umma Jamila "

  "Ina kika ganshi? Me ya had'a ki dashi Muhibba? ko aikenki yayi shi yasa naga kin dad'e."

  Rufe fuskana nayi da tafin hannu nace "Umma Jamila shi zan aure."

  Dariya ta saki har da tab'a hannu sae da tayi mai isarta sannan tace "Allah ya baki lafiya Muhibbata. Tashi ki dauko barkono ki daka man "

  Turo baki nayi nace "Umma Aisha Wallahi da gaske nake shi yace yana sona, kuma dama shekaran jiya ya tsayar dani muna dawowa daga islamiyya...

  Katse maganar tayi tana fad'in "Tashi ki daka man barkono Muhibba, Kin san dae bana son k'arya ko? Banda baki da wayau ma idan akace Abdallah zai aureki sae ki yarda? duka yaushe yayi auren da har zai kuma wani?

  "Na fi matar shi komae fa kuma baiyi sa'ar mata ba yace." na fad'a cike da jin haushinta

  "Kin fita rashin wayau ba!

  "Kai Umma Jamila shi ya fad'a man yanzu"

  Kallona tayi sosae kafin ta girgiza kai a hankali tana fad'in "Tashi ki je ki man abunda na saki "

  Mikewa nayi ina tura baki a raina nake fad'in "Dama nasan Umma Jamila sae ta k'aryata ni, k'ila ma bak'in ciki take man, Yo eh mana k'ila bak'in cikine tunda Baffa na bai kai Abdallah komae ba "

   Kamar mahaukaciya na saki dariya tare da dukan kaina nace "Lallae banda hankali ya za'ayi uwa ta man d'iyarta bak'in ciki?Ba bak'in ciki take ba jin haushi ne." Na bawa kaina amsa

**

  A razane ta mik'e tare da d'aga mashi hannunta na haggu ta kawar da kai gefe guda "What are you saying Abdallah? Ni zakawa kishiya? kama rasa wacce zaka had'ani kishi da ita sae banza yar talaka? karka manta waye kai Abdallah! sannan karka manta da dukiyata kake rayuwa."

  "Ba kishiya zan maki ba Matar Abdallah, Baiwa zan sayo maki, kin san meye matsalarmu da zaran ta buk'atarmu ta biya zan sallameta ki yarda dani no one can snatch me from you."

  " Enough Abdallah."

  Rungumota yayi sosae a jikinshi tare sa sassauta murya yana fad'in "Abdallahn ki kike wa tsawa Matar Abdallah? Kema kin san dalilin aurena kuma bazan auro maki wacce bara ta maki biyayya ba yar talaka ce."

Banza ta mashi tare da tureshi daga jikinta ta zauna sosae bisa kujeran tana jefa mashi harara, Ita kam da zata iya babu da ta haihu da Abdallah, amma matsalar bara ta iya wahalar ciki ba sannan ta zo ta haihu duk ta bud'e ga kuma wahalar kula dasu. Anya bara tace su hak'ura da son yaran ba? Ita kam duk yarda ta kai da son yara bai kai yarda ta tsani kishiya ba.

   "Understand me Hasna, Ina matuk'ar son yara kema haka, kuma bara ki iya haifa mana su ba, ki barni na aureta mana ba zan maki wani abu negative ba."

  Lumshe ido tayi a hankali tabbas bara ta yarda ta haihu ba don bata shirya tsufa ba sannan ta san suna matuk'ar buk'atar yara ita da Abdallahn ta, Meye ma idan yayi auren? ta dai san Abdallah nata ne babu wanda ya isa ya kwaceshi hannunta haka babu macen da zai so bayanta

"Na yarda ka aureta but under two conditions."

Hannunta ya sak'ale cikin nata a hankali yace "What are the conditons Matar Abdallah.?

  Hannunta ta zame cikin nashi tare da d'ago kai tana kallonshi "Kasan ina sonka kuma ina kishinka ko Abdallah?

  Gyad'a kai yayi yana jefa mata mayan kallon dake kashe mata gangar jikinta.

  "First tun daga kan neman aurenta har zuwa inda zata zauna ni ce zanyi komae."

  "Kin hutar da Abdallan ki." Ya fad'a dauke da lallausan murmushi

Harara ta zabga mashi kafin tace "Second ba wani relationship da zai shiga tsakaninku sae da sanina."

  "Hasna?Last condition yayi tsauri Matar Abdallah." Ya fad'a a hankali.

  "That my conditions Abdallah, Idan bai maka ba zamu iya zuwa gidan marayu mu dauko ko yara nawa muke buk'ata." Ta k'arashe maganar tare da mikewa tsaye

  Maidota yayi jikinshi tare da sake mata lallausan murmushi yace "Ina zaki? Na yarda."

  Murmushi ta sake itama sae dae bai kai zuci ba, dan janyeta yayi jikinshi ya mike ya nufi fridge ya dauko kwalbar wine tare da glass cup guda d'aya ya aje sannan ya zauna, Sumba ya kai mata a goshi sannan ya tsiyaya ya kai bakinta, babu musu ta shanyeta tas tare da komawa ta kwanta jikinshi tana fad'in "Abdallah, I'm in the mood."

  Chak ya dauketa bai direta ko ina ba sae bisa tattausan gadonsu yana romancing d'inta..

#Feedohm..
💧💧 *MATAR ABDALLAH.!*💥
                   True Life Story.!

                              💥

*®HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
   *Wattpad:Feedohm*

  (Note: Those that follow me on my old wattpad account i've change an account due to some problem so i no longer use tah.!)

*02*

        Haka rayuwar ke tafiya cikin dan lokaci kad'an Muhibbah ta d'auki son duniya tare da yarda ta d'aurawa Abdallah, bata da wani tunani ko zance da ya wuce Abdallah har ga Allah take sonshi kuma take gurin aurenshi tare da kyautata mashi.

   A Bangaren Abdallah kuwa ko sau d'aya bai tab'a jin kaunar Muhibbah a ranshi ba, asalin duk wata k'auna da soyayya da zai nuna mata tsantsar yaudara ce, gurinshi kawae ya aureta ta wa matarsa bauta sannan ta haifa mashi yaro ko d'aya ne ta fita ta bashi guri.

  Cikin d'an lokacin iyayen Abdallah na k'arya suka shiga maganar yayin da aka tsayar da maganar aurensu wata biyu kacal shima sae da Baffa ya dage sannan, don su a san ransu wata d'aya kawae suke buk'ata.

  Yauma kamar kullun bayan ya dawo da company ya iske Hasna na ta tattara wasu daga cikin kayanta na sawa wad'anda basu sha wahala, rumgumeta yayi ta baya yana shakar kamshin gashinta dake jik'e da ruwa da alama daga wanka ta fito murya k'asa k'asa yace "Princess Wad'annan kayan fa?

  Juyowa tayi gaba daya tana kallonshi sae wani lullumshe ido take, a hankali tace "Amarya nake tsintarwa lefe."

Dariya ya sake sosae tare da janyota jikinshi yace "Wow Matar Abdallah gaskia kin kyauta amma karki saka wad'anda kika san ina sonsu."

Sumba ta kai mashi a kumatu tare da zagaye waist d'inshi da hannu ta lafe sosae jikinshi sun dad'e a haka sannan wayarshi ta fara ruri sae da ta katse sannan ya d'an jata gefen gado tare da lalubo wayar ya duba "Hibbah ce Princess." Ya fad'a had'e da kwanciya rigingine

Binshi tayi ta kwanta saman kirjinshi a hankali tace "Call her zan so naji muryarta yau."

Kanne mata ido yayi yace "She has very sweet voice fa, amma duk da haka bata kai Matar Abdallah ba."

  Sosai ta b'ata rai ya ja hancinta yana fad'in "Sorry My Princess wasa nake muryata kamar tsohon rak'umi take kullun a shak'e."

Dariya ta sake harda kwalla kafin tace "Baka da kirki Abdallahnah."

  Kiran Muhibba ya kuma shigowa k'aro na biyu ya saki tsaki ya dauka yana fad'in "Yan matana ina niyar kiranki kika kuma kira hope kina lafiya."

Cikin sanyin murya tace "Assalamu Alaikum dae Ya Abdallahna."

  "Afuwan Ameen wassalam."Ya fad'a tare da murgina Hasna ya daura kanshi saman kirjinta yana kallon cikin idonta

A hankali ya kuma fad'in "Ya dae Hibbah naji kinyi shiru ko akwae matsalane.?

Kamar yana kallonta ta girgiza kai a hankali tana murmushin da ya fito da dimple dinta.

  A hankali tace "Ya Abdallah,jiya kace zaka zo kuma ba ka zo ba."

"Au ban zo ba ashe?Fad'a man kinyi kewata ne.?Ya fad'a murya can k'asa

Gyad'a kai tayi kamar tana gabanshi

  "Shine kike man shiru ko? yarinya bata son ganin Abdallah."Ya k'arashe maganar cikin sigar tsokana

  Cikin sanyin murya tace "Kai Ya Abdallah."

  Murmushi yayi mai sauti yana shafa fuskar Hasna "Kai Yanmatana."Ya fad'a yana kwaikwayon muryarta.

Sosae take buk'atar ganinshi don haka ta kwantar da murya tace "Dan Allah zaka zo yau.?

"Kina son ganina.?Ya sake k'waik'wayon muryarta

Dan murmushi tayi kafin tace "Ina kewarka sosae Ya Abdallah, Jiya na sa ran ganinka amma ban samu ba."

   "To yi hakuri kin ji ko? Yau zan shigo me kike so na zo maki dashi."Ya karashe maganar cikin sigar jan hankali

  Kamar mai rad'a tace "Ba komae."

"Ban yarda ba sae kin fad'a."

"Allah ba komae, kae kawae nake son gani."

  Fizge wayar Hasna tayi cikin jin haushin yarda ya dage sae magana yake mata, canza murya tayi tare da kanga wayar tace "Network fail."

Dariya ya sake yana girgiza kai "Shine zaki k'arbe wayar ko?ko dae kin fara kishine.?

  "Dole nayi kishin Abdallahna mana, amma ba ga ko wace sakaran mace ba."

Shafa kanta yayi a hankali tare da tufkeshi guri guda kafin yace "Princess kin rage ice cream dinki na jiya.?

  A Hankali tace "Me za'ayi dashi Abdallanah.?

"Hibba zai kaiwa." ya fad'a kai tsaye

"A siyar mata wani mana Abdallah, na fara shan wancan." ta fad'a a hankali tare da gyara mashi sumarshi da tayi yawa

  "No, Ki k'ara mashi ruwa da sugar bara ta gane ba kin san gida babu,  zan siyar mata chocolate idan na fita."

**

Muhibba kam jin ance network fail yasa ta aje wayar don har ga Allah bata kawo komae ba a ranta sae ta dauka mtn ne, kallo Rauda tayi dake tufke mata kai tace "Tashi ki rakani na karb'o d'inkina don Allah."

  Harara ta sakar mata tana fad'in "Kitson fa.?

Marairaicewa tayi tace "Da daddare a ida Rauda, Ya Abdallah ne zai zo kuma su nake son sawa sannan ina so na tsaya gurin habibu mai shago na sayar mashi fura da youghurt na dama mashi nasan da k'yar idan ya ci abinci yau."

  Tab'e baki rauda tayi tare da tureta ta mike tsaye tana fad'in "Ke Muhibba! Uban wa yace maki bai ci abinci ba yau? mutumin dake da kudi da mata ta ya zata barshi da yunwa tun daga safe har yanzu? kin ganki ko.?

  A hankali tace "Allah da gaske nake Raudah, sam matarsa batta da kirki."

  "Shi ya fad'a maki haka? ki iya bakinki fa."

  "Shi mana, wallahi tausayinsa nake ji , kinga baya samun kula gurin matarshi dole nice zan kula dashi."

Hmm kawae tace ta kyaleta, a haka har suka je shagon d'inkin suka k'arbo sannan ta tsaya ta sayi fura da youghurt har da coconut suka koma gida.

Cikin d'an lokaci kad'an ta gyara zaurensu ta fesa wankanta da sababbin kayanta, ta yi kyau ainun kamar ita tayi kanta sae zabga uban kamshi take.

"Umma nayi kyau ko.? ta fad'a tare da juyi a gaban Umman

  Murmushi ta mata tana fad'in" Bansan wa ya koya maki rashin kunya ba Muhibba."

Ringing din wayarta ya katse masu firan ta fita da sauri tana fad'in "Umma na tafi Ya Abdallah ke kirana."

  "Allah ya shiryaki."Umman ta fad'a ganin tana niyar fad'uwa saboda masifar sauri

Tabarma ta dauka ta shinfid'a a zauren tare da fita ta nufi inda ya faka motarshi, yana ganin ta tunkaro gurin ya fito daga motar ya jingina da ita ya hard'e hannu yana aika mata da wani irin kallon da ke k'ara narkar da zuciyarta.

  Duk'ar da kai tayi har ta iso kusa dashi dauke da murmushi, cikin sanyayyar murya ta mashi sallama, Bai amsa ba sae leken fuskarta da yake yana murmushi.

Tana jinshi don numfashinshi a kumatunta yake sauka, turo baki tayi tare da juyar da kanta gefe guda tana fad'in "Ama mutun sallama amma bara ya amsa ba."

Salon da tayi maganar ya sashi sakin yar siriyar dariya yana fad'in" Idan ma ban amsa ba ai laifinki ne Hibbatah."

A shagwabe tace "Laifina kuma ya Abdallah."Ta karashe maganar tare da d'ago fararan idanunta ta sauke a fuskarshi

Lumshe ido yayi yana fad'in "Tubarakallah."

  Juyar da ido tayi gefe guda yayin da kaunarshi ke neman kassarata, ita kam bata jin zata iya rayuwa babu Abdallanta.

  "Ina wuni."Ta fad'a a hankali tare da tura yatsanta na tsakiya a baki

Kallonta yayi yarda take tsotsan yatsan hankalinta kwance, Bata ankara ba taji ya kamo hannun tare da turawa bakinshi, a rud'e ta fuzge tana kallonshi cike da tambayoyi kala kala.

Kafin tayi magana yayi saurin fad'in "Ina so ne nasha madaran dake cikin yatsunki da kullun kike tsotsa sae kuma naji ashe dauda ce cike dasu, don har wani tsami tsami suke."Ya k'arashe maganar tare da yatsina fuska yana tab'e baki kamar gaske.

  Bata san lokacin da ta kai mashi duka ba tana turo baki, Kaucewa yayi yana dariya had'e da kama kunnuwanshi.

  Juyawa tayi ta fara tafiya tana hararanshi k'asa k'asa yayin da ya bi bayanta yana mata dariya, cikin zauren ya sha gabanta har lokacin dariya yake, ya marairaice murya yana fad'in "Haba mana ya zaki taho ki bar Abdallanki? Nayi laifi ayi hakuri amma ai zan iya gyara laifina ko.?Ya k'arashe maganar yana leken fuskarta

  Banza ta mashi, jin yana neman kamo hannunta yasa ta d'ago tana hararanshi yayin da yayi saurin saki yaja baya yana dariya "Ni kike harara Hibbah?

A Hankali tace "Amma ai nace maka ba kyau ka dinga tab'ani ko.?

Waro ido yayi cike da duniyanci yace "Zan sake jin taste din yatsunki ne kawae fa, sae na gyara laifina."

  "Kai Ya Abdallah.! ta fad'a har da d'an murmushinta

Dariya ya mata a haka suka yi firansu ta dauko mashi furan ya dan sha ba sosae ba sannan ya mike ya dauko mata ice cream da chocolate din da ya kawo mata, Karb'a tayi tare da godiya sosae sannan ya tafi..

#Feedohm
#Much love Haske writer's

[9/16, 5:29 PM] prince_s_square: 💧💧 *MATAR ABDALLAH.!*💥
                   True Life Story.!

                              💥

*HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
   *Wattpad:Feedohm*

03

     Ko da ya koma gida ya iske Hasna zaune ta zabga uban tagumi, kusa da ita ya samu ya zauna yana dariya k'asa k'asa da farko shareshi tayi sae da taga yak'i cewa komae sannan ta sakar mashi harara tana fad'in "Dariyar meye haka Abdallah?

Dariya ya kuma saki yana fad'in "Muhibba ce tayi man kwalliya amma wallahi tun kakarki na budurwa aka daina yayin atamphar da ta saka."

Dariya ta saki sosae tana tab'a hannu "Abdallanah baka da dama."

  Tsayar da dariyar yayi tare da dafe kai yana fad'in"Kinga ki shirya muje mu gano Ummana batta da lafiya na manta tun jiya Salis ya fad'a man."

Daure fuska tayi tace "Gaskia baran je Abdallah."

"Why?

  "Duk lokacin da naje gidanku kasan dae wuni nake ranar ina amai ko?Wane dalili kuma kake so na fad'a maka Abdallah.? Ta fad'a kai tsaye tana kallon cikin idonshi

Dariya yayi mai sauti yana kallonta kafin yace "Well ai ba laifi bane Matar Abdallah."

   Daga haka ya mike ya shiga d'aki yayo wanka, cikin d'an lokaci ya shirya cikin shadda blue da ta asha aikin hannu, Abunka da farin mutun sae tayi bala'in k'arbarshi ya fito sae k'amshin turare yake.

  Da sauri ta sha gabanshi tare da bashi kyakykyawar sumba a kumatu tana fad'in "Abdallanah sarkin kyau."

  Kanne mata ido yayi yace "You are sure?

    A hankali tace "Absolutely."

Lallausan murmushi ya sakar mata kafin ya zagayeta ya wuce, da sauri ta janyo hannunshi ta langwabe kai tana fad'in "What about dinner.?

"I'm not hungry."

  "But.."

Hannunshi ya daura saman lips d'inta yana fad'in "Shii....Yau abincin Ummana nake son ci, kin san ita ba ragguwa bace da kanta take girkawa."

Sam bata fahimci yab'a mata magana yayi ba da Momynta yake ba tunda acan gidansu basa girki sae dae masu aiki su masu, don haka ta saki lallausan murmushi tana fad'in "Ka taho man dashi kasan nima ina son girkin Umma Abdallah"

  Dariya ya saki sosae ba tare da yace komae ba ya wuceta yayin da ta bi bayanshi har parking space sannan ta juyo.

  Ita kanta tana mamakin irin son da takewa Abdallanta ko dan yana da kyau ne? Dan murmushi ta saki tabbas samun mutun kamar Abdallah sae an kuka ta tabbata da ace Abdallah D'an masu kud'ine ita kanta bara ta tab'a samunshi ba amma sae Allah yayo shi talaka.

  ***

  *ASALIN LABARIN..*

A cikin garin kaduna unguwar Sarki GRA unguwa ce ta masu tarin dukiya, walau ma'aikantan gwamnati ko yan'kasuwa.
HASNA matashiyar budurwa k'yak'yawa ajin k'arshe da ubanta d'iyar wani hamshak'in mai kud'i, Yarinya ce yar gata d'iya ga wani hamshakin dan kasuwa Alhaji Ahmed tarau da mahaifiyarta Hajiya Nafeesa, ita kadae Allah ya ba iyayenta don haka ta tashi cikin gata  da sangarta don ko wanki Underwears d'inta bata iyawa..tun daga primary school har degree a k'asar india tayi abunta sannan ta dawo gida tana aiki k'ark'ashin campany mahaifinta..

Tun tana k'arama ta tashi da son mutun mai kyau don ita komin talaucinka indae kana da kyau babu ruwanta sannan zata ja ka a jiki sosae tare da yi maka d'awainiya, Ita ko cikin k'awayenta bata alak'a da mummuna komin kud'in ubanka.

  A Bangare Abdallah kam tun suna yara Babansu ya rasu sae Ummansu da suka tashi gurinta cikin kulawarta ta soyayya tare da tarbiyyar islam, Su ukune gurinta, Yaya Salis ne babba wanda shi baiyi makaranta ba sae motar haya da yake ja zuwa lagos sae Abdallah wanda da k'yar ya gama karatun pharm a zaria amma ba aikin yi don haka yake sana'ar achaba a cikin garin sae auta Hafsah dake SS1 yanzu.

Tunda suka tashi suka iske mahaifiyarsu Aisha bata da wata sana'a da ta wuce saida k'osae a bakin titi kuma da wannan sana'ar ta rik'esu su duka ukun ta basu tarbiyya dae dae gwargwado..

  Makwabtansu kam Kawunsu ne Dalha  ma'ana k'anin babansu shima talaka ne sosae yana sana'ar nik'a sannan yana da wata makirar mata Naja da yara biyar duka mata, babu wata shak'uwa tsakaninsu da gidansu Abdallah saboda gani suke su Abdallah sun fisu cigaba.

  Abdallah Saurayi ne d'an shekara 31 dogo sosae sannan yana da cikar mazantaka da k'ira ta jarumai, Farine sosae kamar bature yayin da yake da yalwatacciyar suma da ta kwanta lub lub a kanshi, yana da doguwar fuska dake d'auke da manyan idanu farare tas da gashi zagar zagar, sannan yana da yalwatacciyar gira mai cike da bak'in gashi, Hancinsa siriri ne sae labbanshi yan madaidaita masu tudu bak'ak'e sae siririn sajanshi yake kewaye da fuskarshi.

  Dae dae gwargwado yana samu a sana'arsa ta acab'a kuma yana rufawa kanshi da mahaifiyarshi  hakan ne ma yasa baka tab'a gane talaucinsa..

Had'uwasu tasamo asaline lokacin da ya kawo mai gadin su hasna unguwarsu a machine yayi parking a jikin gate d'in su yaje samu canji ya sallameshi..

Yana dawowa ya iske an yarda mashin din gefe guda yayin da Hasna ke tsaye rik'e da marfin motarta da alama ita ta saka aka yardashi, da azama ya matsa yana fad'in"Wannan wane irin wulak'ancine da bara a iya bari na dawo ba na d'auke kaya sae a yar man da machine.?

  "Anje an yar.." Sae dae cak maganar ta tsaya lokacin da ta daura idonta a fuskarshi..

  Dan karamin tsaki ya sake tare da matsawa yana k'ok'arin ta da machine din k'asa k'asa yake fad'in "Wannan rashin sanin darajar d'an adam ne."

  "Sallau kama mashi mana ya tada." Ta fad'a ba tare da ta sani ba

  Da gudu maigadin ya matsa ya kamawa Abdallah suka tashe shi, Yana k'ok'arin tada machine d'in ta matso tana fad'in "Kayi hakuri fa."

  A hasale yace "Idan banyi ba dukanki zanyi hajiya.?

Yar dariya tayi tana fad'in "a'a kai ko mana, kayi hakuri ba da ganga machine d'in ya fad'i ba, na zo wucewa da motor ya d'an zungureshi."

Tab'e baki yayi yana kallonta sannan yace "Ban cika son k'arya ba hajiya, Na aje machine a k'ofar gidanku kuma kin yar kuma sae me.?

  "It's by fluff Allah." ta fad'a a hankali

  "Al right." Ta ji ya fad'a har lokacin machine d'in yak'i tashi

  "An b'ata maka machine ko? Kayi hakuri fa."Ta kuma fad'a tana satar kallonshi

A Hasale yace "Hajiya ki shiga gida da Allah."

  Sam bata ji haushi ba asalima burgeta yayi, haka tacigaba da mashi nacin mashi magana, wata ya bata amsa wata kuma ya shareta, ganin machine d'in yak'i tashi yasa ta hau nacin ya shiga motarta ta saukeshi gida da safe za'a kawo mashi machine d'insa.

Da k'yar ta samu ya shiga ta kaishi har gidansu sannan ta karb'i numbershi, wanshekare tun da safe sae ga Yaron babanta da mota wae ance ya kawo mashi  instead of machine d'in, sam k'in k'arba yayi har sae da tazo da kanta.

Sun ja lokacin kafin soyayya mai k'arfi ta shiga tsakaninsu yayin da ta karb'i takardunsa ta bashi babban matsayi a campanyn Babanta bata sha wahala ba iyayenta suka amince dashi duk da yake talaka saboda dama ba masu k'yamar talakawa bane.

Duk wani party da club na manyan yara haka zata d'auki Abdallah su tafi, sosae take jawa kanta mutunci domin duk cikin friends d'inta babu mai saurayi kamar Abdallanta haka idan akaje batun gayu sae dae a gani a jikin Abdallanta ba dae ya gani ya kwaikwaya ba, haka musamman zata bada oder kayan sawarshi daga india domin kawae yayi zarra..

  Tabbas Abdallanta yayi ZARRA Ballantana ma da k'yawu da hutu suka k'ara kwanciya tare dashi, Duk da da yawan yan mata abokanta suna bala'in sonshi amma sanin halin Hasna yasa babu wacce tayi gigin furtawa..

  Cikin d'an lokaci kad'an ta koya mashi bak'ak'en dabi'unta yayin da ya d'auki shan minti ,shan shisha, shan sigari da shan giya ba wani abu ba, Zuwa club kam har idan bara taje ba shi ke matsa mata sae sunje..

  Duk abubuwan da yake ko kad'an bai tab'a bari Ummanshi ta fahimci wani abu ba har aka fara maganar aurensu yayin da Kawu dalha ya shige mashi gaba atunaninshi zai d'an samu wani abu shima.

Dai dai da naira d'aya da za'a kashe gurin bikin Hasna ce ta bashi ya bayar, sae dae sadaki ne kawae tace ya nema da kanshi, A Haka har aka fara shiryayen biki yayin da ta d'auke shi ta kaishi ya zab'i gidan da zasu zauna cikin gidajen babanta.

  Shagali sosae akayi don tun ana sauran sati biyu bikin suka fara zuwa abuja ana party har zuwa ranar da aka daura aurensu aka kai amarya gidan mijinta.

   Daddare ango ya shigo tare dasu Fahad wanda dama fahad tun suna k'anana suke tare shi kadai ne be canza ba,

  Allah yasa alkhairi yama amarya sannan ya juya ya tafi donshi har ga Allah baya kaunar Hasna ko kad'an

   Bayan abokansu sun gama sharholiyarsu suka masu bank'wana....Amarya da ango kam ansha amarci cike da kaunar juna.

  Haka suka cigaba da murje soyayyarsu yayin da gidansu ya zama kamar wata k'aramar bariki don kowa yana da damar da zai kawo friend dinshi daga maza har mata cikin gidan sae dae basa zina kawae asha firane ayi d'an shaye shaye a wuce, sannan basu d'auki tab'a jikin wani jinsi wani abu ba indae ba private area bane.

  Watansu biyu da aure ta fara rashin lafiya, bayan sunje asibitine suka fahimci tana dauke da ciki sati 6, Tun asibitin ya fahimci tana cikin tashin hankali har suka iso gida, ko parking bai gama ba ta fice ta shige falo, sae da yayi parking sannan ya shiga ya isketa sae safa da marwa take tsakiyar falon don haka ya riko kafad'unta yana fad'in "Me ke faruwa Princess? Me yasa yanayinki ya canza.?

  "Bana son haihuwa Abdallah." Ta fad'a kai tsaye tare da juya mashi baya

Zaro ido yayi a d'an tsorace yana kallonta domin har ga Allah shi mutun ne mai tsananin son yara, a hankali ya juyota suna fuskantar juna "Bakya son haihuwa baki d'aya koko bak'ya son haihuwa dani Hasna.?

  "Idan akwae wanda zanso na haihu dashi A duniyarmu Abdallah bai wuce kai ba! Kawae baran iya wahalar ciki da rainon yaro bane Abdallah." Ta fad'a idonta cike da k'wallah

"Me yasa Hasna? Dan Allah karki mana haka wallahi ina son yara sosae."Ya fad,a muryarshi na rawa

  Kuka ta saki a hankali tana fadin "Nima ina son yara Abdallana, amma gaskia mamana ta sha wahala sosai gurin haihuwana sannan mutane da yawa suna fad'ar wahalar dake tattare da ciki ni kam dae baran jura ba Abdallah."

  "Enough Hasna, kawae dae kice bara ki haihu da talaka ba irina." Ya k'arashe maganar cikin matsanan cin fushi.

  Rungumeshi tayi da sauri tana kuka,lokaci guda zuciyarshi ta karye tabbas shima yasan daukar ciki da rainonsa ba abu mai sauki bane sannan yana da yak'inin Hasnarsa bara ta dauki wahala ba, zagayeta yayi da hannunshi a hankali yace "Ya kike so ayi Hasna? Kiyi hakuri ki haifi wannan sae musan yarda za'ayi daga baya."

  Cikin kuka tace "Baran iya bwla Abdallah, dan Girman Allah muje a zubar dashi, wallahi zan d'auko maka yara ko nawa kake so gidan marayu."

  "Yarana nake so nima Hasna."Ya fada a hankali tare da d'ago idanunshi da sukayi jawur yana kallonta

  Sun dauki lokaci sosae kafin ta shawo kanshi a zubar da ciki shima sae da Momynta ta kirashi sannan ya yarda, da kanta momyn ta dauki Hasna ta kai aka zubar da cikin sannan suka saka aka juyar mata da mahaifa...

#Feedohm
#Haske writer's...[9/18, 10:07 PM] prince_s_square: 💧💧 *MATAR ABDALLAH.!*💥
                   True Life Story.!

                              💥

*HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR: FEEDOHM(Fiddausi Musa)💞*
   *Wattpad:Feedohm*

 

*04*

   *CIGABAN LABARIN.*

  A Haka rayuwa ta cigaba har bikinmu ya zama sauran kwana biyar gashi har lokacin ba'a kawo man lefe ba. Hakan  yasa hankalina yayi masifar tashi tunda nasan indae za'ayi aure unguwarmu to ana sauran sati uku ko biyu ake kawo masu lefensu amma ni har yanzu nawa shiru..

  Ina zaune zugum cikin d'aki yayin da maryama k'awata ke ta faman tsokana na wae fargabar auren ce tasa nayi zugum haka..

  Ajiyar zuciya naja ina fad'in "Barni Maryama, kinga har yanzu shiru babu lefe, kina ganin kuwa hakan bara ya jawa Umma surutun jama'a ba yarda aka zuba ido ana jiran aga abunda za'a kawo man."

Kamar tana jira tace "To ki kirashi man Muhibba, sae ki ji yaushe zasu kawo, kinsan kowa da yarda suke hidimansu, wata kila sae ranar d'aurin aure za'a kawo maki."Ta k'arashe maganar tare da hura iskar bakinta

  Jim nayi kad'an, don har ga Allah ina jin nauyin kiran Abdallah na mashi maganar lefe, to amma ya zanyi? don haka na dauko wayata a hankali tare da dialing numbershi sae dae har sae da ta kusa katsewa sannan aka d'auki wayar.

K'irjina ne yayi masifar bugawa jin muryar mace na fad'in "Larindona (Yar raino da yarabanci)  ya akai? Abdallanah dae bacci yake, amma k'ya iya fad'ar abunda kike buk'ata sae a aiko maki dashi yanzu."

  Jim nayi ina jinjina kalmar Larindo, duk da bansan me take nufi ba amma na jita har a raina, sannan me wannan matar ke nufi da tace idan akwae abunda nake bukata na fad'a mata? ita a wa?bayan bata da wani matsayi a gurin Abdallanah.

  "Larindona kina jina kuwa.? Ta sake fad'a da alama tana jin d'ad'in fad'ar sunan.

  "Kiyi hakuri da Abdallah nake son magana idan ya tashi k'ya fad'a mashi."Na fad'a kirjina na dukan uku uku.

Yar' dariya ta saki kafin tace "Ki d'auka da Abdallah kike magana Larindo."

K'itt na kashe wayana ina kallon maryama dake latsa wayarta, a sanyaye nace "Meye Larindo Maryama?

  Dariya tayi kafin tace "Ina zan sani Muhibba? wata k'ila ba kalmar hausa bace."

**

Abdallah kam dake kwance bisa cinyar matarshi yana dariya k'asa k'asa, yana jin an kashe wayar yasa shi k'wacewa yana hararan Hasna cikin soyayya kafin yace "Zaki kashe man aure ko.?

Itama hararan ta sakar mashi kafin tace "K'arya nake ba Larindon bace.?

  Hancinta ya ja sannan ya d'auki wayar yana fad'in "Bara na kirata naji me take bukata, nasan dai bai wuce maganar lefe ba, Shegiya kamar tana yawo tsirara."

  Bata ce mashi komae sae dae dariyar da ta saki, ba har yayi dialing Number Muhibba. Duk da tana ganin kiran amma sae taji shakkun d'auka don haka har ta yanke ba'a dauka ba, sae da ya kuma kira karo na biyu sannan ta d'auka ba tare da tayi magana ba..

Sallama ya mata kamar yarda tace bata son wani hello...

Jin muryarshi yasa ta d'an samu natsuwa har da sakin murmushi tana fad'in "Ameen wa'alaikassalam, Barka da wuni Ya Abdallah."

  "Me kike yi na kiraki baki dauka ba Muhibba? ko har an fara ja man ajin ne tun yanzu."Ya fad'a cike da zolaya

Dariya tayi mai sauki kafin tace "Kai Yaya Abdallah wane irin aji kuma? ni da zan zauna k'ark'ashin ikonka? kawae na kasa dauka ne a zatona ko Yayata ce ta sake kirana."

A hankali yace "Oh Hibbatah ba dae har kin fara jin tsoronta ba?

  Dariya kawae nayi ba tare da tace komae ba.

"Kin kira ina bacci kiyi hakuri kin ji ko? Fad'a man me kike buk'ata yanzu.? Ya fad'a cikin sigar lallashi, wanda har sae da Hasna ta ture kanshi a jikinta tare da balla mashi harara, dariya ya mata tare da kanne mata ido guda.

  Cikin jin nauyi tace "Uhm dama maganar.."Cak tayi shiru ta kasa cigaba jin maganar tayi nauyi bakinta

  A hankali yace "Menene Hibbah? Fad'a man kinji? ko akwae wanda zaki fad'awa bayan ni.?

  Girgiza kai tayi kamar yana kallonta lokaci guda idonta ya ciko da k'wallah jin su gwaggo mari na maganar lefen a tsakar gida, a hankali ta mik'awa maryama wayar don ita har ga Allah tana jin nauyin tambayarshi wani abu..

  Jin muryar maryama na fad'in "Ina wuni Yaya Abdallah?

  Ya sashi b'ata rai sosae sannan yace "Kina lafiya? Menene da Ita bara ta iya fad'a man ba sae ta saka wani.?

  Tab'e baki maryama tayi sannan tace "a'a maganar lefene taji shiru, kuma ga mutane nata tsegumin ank'i kawowa har yanzu."

Kai tsaye yace "Ga k'anwata kuyi magana da ita." Tare da kangawa Hasna wayar a kunne ya mayar da kanshi a k'irjinta ya kwantar..

  K'arb'a tayi cikin izgilanci tace "Lefen kuke buk'ata yanzu.?

  Kallon Muhibba tayi a ranta tana tambayar, wannan wane irin tambayar rainin wayau ce? amma a zahiri cewa tayi "Ko bamu fad'a ba kun san dae dole mu sa ran zuwanshi Yar'uwata."

  "To ku cire.! Domin mu a al'adarmu sae amarya tazo gidanta muke d'aukar lefenta mu bata..don bara mu yarda mu zubo kaya ba sannan azo ana  yan' d'auke d'auken da akewa lefe."

"Turk'ashi! To ku ina ruwanku da abunda za'a dauka a ciki? injin dae hak'k'in amarya ne lefen.? ta fad'a a hasale

"Fad'a man wace aya ko hadisi yace dole ama amarya kayan lefe? Kindai ji abunda na fad'a kuma babu canji. don haka ki koma ki fad'awa mara kunyar amaryar da ta saki kiranshi cewa bara a kawo ba."

  Tabbas maganar ta mata zafi don har ga Allah ita irin mutanan nan ce mara sa d'aukar raini, cikin k'ullafa tace "Amma wannan k'anwar Abdallah anyi shegiya mara mutunci jaka..! Wallahi duk ranar da muka had'e sae na yaga mata rigar mutunci..  Uban wa yace mata mu talakawane? Uban wa ya fad'a mata muna jiran banzan lefensu?koko an fad'a mata a tsirara muke yawo? Ke Muhibba wallahi har Abdallah idan muka had'e sae na keta mashi rigar mutunci don baran d'auki iskancin ko wane shege ba."

  Kuka Na saki kamar raina zai fita jin abunda Maryama ke fad'a, yayin da zuciyata ta tsarge da tausayin kaina da har na yarda na fad'a cikin masu kudi...

Wannan wane irin wulakancine? Duk abunda K'anwar Abdallah ta fad'a babu abunda banji ba, Tausayi sosae na bawa maryama don haka ta dawo kusa dani tana k'ok'arin tsayar da masifarta tare da rungumeni tana fad'in "Kiyi hakuri kinji Muhibba..Mutumci kam k'anwar Abdallah batta dashi amma ai ba duka aka zama d'aya ba, maganar lefe kuma ki barta kinji ko? Akwae wani less da Babanmu ya sayar man dubu 46 naci bikinki dashi, kin ga sae na baki ki saka ranar d'aurin auren kinga zasu fahimci bamu rasa suttura ba, Albashshi idan sun baki lefen sae ki k'arb'a daga baya kin ji ko."

Maryama ta dad'e tana lallashina kafin ta samu nayi shiru sannan ta fita taje tawa Ummana bayanin cewa Su Abdallah sun ce sae ankai amarya suke bata lefe a al'adarsu..

Murmushi Umma tayi sannan tace "Babu laifi Maryama ai kowa da nashi al'adar, ki ba k'awarki hakuri karta damu nasanta bata da hankali sosae,  Allah yasa hakan ya zama alkhairi, Ni kuma bara nawa mutane da Baffanta magana."

  Maryama ta dawo tana fad'a man yarda sukayi da Umma, na d'an ji sanyi sosae tunda Umma tace akwae masu al'adar haka, don haka na d'an saki raina sannan na amince da zan k'arb'i Less d'in maryama na saka tunda nan gida ba'a man d'inki ba a lefe muka dogara..
 
  Maryama d'iyar mai kudi ce sosae a k'asan layinmu, tunda muka taso a tare muke, kuma yan gidansu na bala'in sona haka itama..

**

Tunda wannan abun ya faru ban kuma ganin Abdallah ba haka ko waya bayya kirana nima kuma na d'anyi k'ok'arin shareshi sae dae sam na kasa don har ga Allah Son Abdallah nake fisabillah, Ana gobe za'a d'aura aure na kira wayarshi amm har ta k'ari ringing bai d'auka ba.

Maganar kud'in da zanyi hidima dasu kuwa a ranar da muka gama waya naga an turo man dubu hamsin (50000) Ta account d'ina duk da sunan macene HASNA AHMED TARAU hakan bai hanani cigaba da amfani da kud'in ba don nasan daga gareshi suke.. 

  Sae bayan minti kamar talatin sannan ya kira a lokacin muna gidansu maryama domin acan nake zaman sitting d'ina da friend d'ina.

  Cikin sauri na dauki wayar muryata na rawa nace "Nayi maka laifine Abdallah.?

"Ina k'ofar gidanku ki fito kinji ko.? Ya fad'a cikin sanyin murya da alama na bashi tausayi

  Da sauri na mike na fice ba tare da na fad'awa kowa ba, na iskeshi inda yake aje motarshi, da sauri na doshi gurin don har ga Allah babu kunyar kowa a zuciyata, Abdallana kawae nake son gani a lokacin..

  Ina k'ok'arin tsayawa gabanshi nayi uban tuntub'e na tafi luuu  zan fad'i yayi saurin tareni tare da dawo dani jikinshi yana kallona cikin kulawa "Fad'a man meye matsalarki ? Ina hankalinki ya tafi da kike neman fad'uwa? baki san amarya tsautsayine da ita ba? Ko duk wajen kallona ne kike neman fad'uwa.?

  K'asa nayi da kaina ina k'ok'arin zame jikina daga nashi amma sae yak'i sakina sae kallon jan lallen dake yatsun hannuna yake don haka na janye hannuna da na dafe k'irjinshi dashi tare fizge jikina daga nashi

  Gani nayi ya bud'e man k'ofar motarshi yana fad'in "Ki shiga mu matsa anan naga akwae mutane ko."

  Ban musa ba na shiga ya rufe sannan ya zagayo ya tada motar tare da barin layin unguwarmu, inda na fito ya dosa har sae da yayi d'an nesa da gidansu maryama sannan yayi parking tare da juyowa ya zuba man ido..

K'asa nayi da kaina sosai, yasa hannunshi ya d'ago hab'ata yana kallon cikin idona"Na maki laifi ko Muhibbatah.?

Kamar zance eh sae kuma na girgiza kai a hankali idona yayi rau rau.

  Hannuna ya kamo yana murzawa a hankali kafin yace "Kiyi hakuri kinji ko Hibbah, wallahi ba'a san raina hakan ya faru ba tafiya ta kamani sae yau na dawo."

  A Hankali nace "Amma me yasa baka fad'a man ba Ya Abdallah? Kasan dae zan damu ko? Hawayen da nake k'ok'arin b'oyewa suka zubo.

Waro ido yayi soaai tare da rungumoni jikinshi yana bubbuga bayana a hankali ba tare da yace komae ba, Duk yarda naso na k'wace daga jikinshi sae na samu kaina da kasawa sae ma k'ara lafewa da nayi ina shakkar daddad'an k'amshin turarenshi...

Mintina kad'an ya d'ago fuskana yana jefa man wani tattausan kallon dake k'ara narkar da zuciyata, a hankali yasa yatsanshi yana sharen hawayen da yayi sauran kafin yakai bakinshi ya bani wata sassanyar sumba a kumatuna, hakan yasa na k'ara rikicewa da soyayyarshi lokaci guda na shiga wani irin yanayi mai wuyar fassarawa..

  Na tabbata ya lura da hakan shi yasa shi kiran sunana cikin wata irin siga "Muhibbatah."

Dago idanuna nayi ina kallonshi k'asa k'asa kafin nayi magana yace "Kiyi hakuri kinji ko, Ina matukar kaunarki.. ni kaina nayi kewarki sosae hakan yasa ina dawowa na kasa samun sukuni sae da nazo gurinki wallahi ko gida banje ba."

  "Da gaske kayi kewata.."Na fad'a a hankali cike da jin dad'i

Hannuna ya daura saman zuciyarshi yayin da ya zuba man ido cikin kauna yana fad'in "Ban tab'a yin ko da minti d'aya ba tare da tunaninki ba Muhibba."

  Lumshe ido nayi ina jin yarda zuciyarshi ke bugawa, tabbas na yarda Abdallana na man wani irin so na musamman tare da k'auna..

  Katse man tunani yayi ta hanyar fad'in "Kin san me na fi tsana a duniyarmu Muhibba.?

Girgiza kai nayi a hankali sannan yace "Bana son hawayenki Muhibba, Na tsani wanda zai saka Muhibbata hawaye kamar yarda na tsani kaina yanz.."

  Da sauri na rufe mashi baki da hannu ina girgiza mashi kai , Hannun ya janye ya kai mashi sumba yana fad'in "K'umshinki yayi kyau Muhibba."

Murmushi kawae nayi tare da janye hannuna na mayar cikin hijab...

Mun dad'e muna fira sannan duk a tunanina zai man maganar lefe amma sae naji shiru nima ban mashi ba,har muka gama firan ya rakani har bakin gate d'in su maryama ya tafi..

#Feedohm
#Haske Writers...
[9/18, 10:12 PM] prince_s_square: 💧💧 *MATAR ABDALLAH.!*💥
                   True Life Story.!


                              💥


*HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
   *Wattpad:Feedohm*


  *05*


     Cikin ikon Allah ranar asabar da misalin k'arfe sha d'aya da rabi na safe aka daura aurena da Abdallah akan sadaki naira dubu hamsin. Bayan an dawo ne tsegumi ya tashi wae sam auren bayyi mutane sosae ba, don duk a tunanin jama'a za'a ga manyan mutane daga jahohi daban daban amma sae aka samu akasin haka, wasu ma fad'i suke wae kamar babu yan uwan Abdallah shak'ik'ai a gurin daurin auren dan basu ga masu kama dashi ba ko ta jini daga abokai sae mutanen azik'i...

  Nikam babu abunda ya shalleni bare ya dameni, gani nake don ba'a ga mai kama dashi ba sae ace babu danginshi a ciki? koko sae ya fad'awa jama'a wannan yan'uwana ne.? A raina kam na hak'ik'ance ko da Abdallah shegene babu abunda zai ragu a cikin zuciyata..

  Maryama ta shigo ta mik'o man Peak da markad'ad'd'ar cucumber tana fad'in "Mutane munafukaine wallahi."

  Nasan itama maganar ta jiyo don haka nace "Me kuma akayi Maryama?

Boye man tayi wata k'ila bata so raina ya b'aci don haka tace "Ke ba komae, Ki had'a kisha bara naje na shigo dasu Shatu yanzu suka iso kuma basu san gidan ba."

  Hannunta na janyo ina dariya "Kisa yaro ko su Amina su shigo dasu wallahi bana son rabuwa dake."

  Tsaki ta saki tana harara tace "Ke ni bana son gulma k'ya ma fad'i wanda baki son rabuwa dashi amma bani ba."

  Dariya nayi ina fad'in "Kayyasa Maryamata akwae ki da banzar fassara."

Itama dariyar tayi ta fita tana fad'in "Ki tashi ki sake wanka k'awata."

*

  Bayan an gama daurin Aure Abdallah kam gidan Ummarshi ya nufa, Ya iske zaune tsakar gida tana wanke wanken kayan da ta gama sana'a dasu, kusa ita ya tsugunna yana nannad'e babbar rigar da ya sha..

Da murmushi ta kalleshi kafin tace "Ka ganka kuwa Abdallah kayi kyau sosai yarda kasan sabon ango."

Shima d'an murmushi yayi kafin yace "Ina Wuni Ummana?Baki san angon bane Umma, domin daga daurin auren Mahmud nake."

"Ba dai Mahmuda da na sani aka daurawa aure Abdallah? Me yasa baka fad'a man ba, ai da ko addu'a na masu ko banje wa mamarsu walima ba."

  Goro ya fiddo da dabino ya mika mata yana fad'in "Ba sae kinje ba Umma daga nan ma k'ya iya masa addu'ar samun abunda ake buk'ata."

Ba ta kawo komae ba ta k'arba  tace "Allah yasa alkhairi Abdallah, ya Albarkacesu da zuri'a d'ayyaba, yaya wajen su Hasna da fatan tana lafiya.?

  "Lafiya lau Umma." Sun d'an tab'a fira sannan ya mata bank'wana ya tashi...

  A waje ya iske Kawu dalha yana nik'a yayi bad'a bad'a da garin masara fuskarnan tayi fari tas sae idanunun da ake gani.

  A Hankali ya matsa yana fad'in "Barka da wahala Kawu dalha ka ganka kuwa? wallahi kaje kayi wanka in ba haka ba sae an bar kawo maka nik'a."

  "Barka kadae mijin hajiya, nagode Allah da gumi na ake nema ba wata ke bani ba, shege mai matattar zuciya."Ya bashi amsa ba tare da ya kalleshi ba

  Dariya yayi mai sauti ya fiddo da goro ya mika mashi yana fad'in "Haba kawu meye na fad'a kuma? Ka ga ni ba fad'a nazo ba  goro na kawo maka don nasan dae bara ka iya saya da kud'inka ba."

Hannu ya saka ya karb'e yayi k'asa da kai yana fad'in "Abdallah Abdallah nima ai ba fad'a nake nema ba, Kaine da shegiyar magana amma komai ya wuce, Dan Allah zan samu d'ari biyar anan kuwa..?

Dariya yayi sosae yace "Ai ba kud'i hannuna Kawu, suna gurin Hajiyata, Yau bata bani ba."

Daga haka ya shige mota ya barshi yana binshi da harara cike da takaici, shi kam daga nan direct gidanshi ya nufa ya iske Hasna da friends d'inta maza da mata sae cashewa suke abunsu, tana ganinshi ta ruga da gudu tare da rungumeshi, d'agata sama yayi yana girgizawa tare da rawa ta yan bariki..

Sun dad'e suna sauke buhun bariki kafin ya nufi d'aki da ita suna dariya, bisa gado ya jefata tare da rage kayan dake jikinshi shima ya kwanta ya janyota jikinshi yana shafata

"Angon Larindo.."Fad'a tana shafa dukkan jikinshi

   Lumshe ido yayi kafin ya damke hannunta ana fad'in "Me kika tanadar man yau Princess.?

"Me kake so? ta fad'a tare da narkewa jikinshi sosae

  Murya k'asa k'asa yace "Kinsan dae yau ranar amarcin mu ta biyu ko? Ki shirya man kanki kin ji ko.?

  Sumba ta kai mashi tana fad'in "Kullun a shirye nake Abdallanah."

Zaune ta mike tana fad'in "Oh na manta na fad'a maka na shirya mana big bash to celebrate our 2yrs anniversary da daddare, Ina fatan Larindo zata je."

  Bata rai yayi yana fad'in "Ba sae taje ba Princess wallahi b'ata mana guri zasuyi."

   A Shagwab'e tace "Abdallana ina so friends d'inmu su ganta please."

  "Kayan da zata saka fa.? Ya tambaya har lokacin fuskarshi ba walwala da alama baya son zuwan Muhibbah.

  Lumshe mashi ido tayi tace "Akwae wata gown d'ina da nasa a partyn zee sae na bata ta saka ko.?

  Murmushi yayi yace "Shi kenan Princess. I love you much."

  Sumba ya kaimata tare da mirginawa ya tashi zaune jin wayarshi na ringing cikin aljihun rigar da ya cire.

  Dan karamin tsaki ya sake ganin Kalmar LARINDO na yawo a screen d'inshi, don haka ya dauka a dak'ile tare da fad'in "Larindona.!

Duk da bata san me kalmar ke nufi ba amma bata son sunan a ranta, a hankali tace "Ya Abdallanah."

  A dak'ile ya kuma cewa "Menene Larindona?

  "Bakomae dama kira nayi naji ko kana lafiya don naga tun jiya da muka rabu bamu sake magana ba."Ta fad'a cikin sanyin muryarta

  Tsaki ya saki har tana iya juyoshi kafin yace "To nagode."

  Zuciyarta ta karye jin tsakin da ya saki, sae taji sam bata ji dad'i ba wata kila matarshi ce ta b'ata mashi rai tunda dama tasan dole ranar yau ya samu rashin d'aa gurin matarshi yarda bata da kirkin nan..

  Lokaci guda tausayinshi ya d'arsu a ranta yayin da taji idonta na niyar zubo da k'wallah, ita kam idan akwae abunda ta tsana bai wuce b'acin ran Abdallanta ba. A hankali tace "Wani abu ke damunka ne Ya Abdallah, dan Allah kayi hakuri ka daina sawa kanka damuw.."

  Kitt taji an yanke wayar, A Hankali ta kwantar da kanta bisa cinyar Maryama tana share kwallan da suka gangaro

Gwaggo Habi ta shigo ta kamata suka shiga gurin Baffanta inda ya mata nasiha sosae tasha kuka sosae barema yarda Baffan ke rok'anta tawa mijinta biyayya kamar baiwarsa.

  Daga nan gurin Ummanta aka nufa da ita inda ta jiyo su saratu matar k'anin Baffa suna gulma wae da sukaje zasu jeran kayan a BQ aka basu suka jerasu wae k'anwar Abdallah tace gyara ake wa bangaren amaryar idan an gama an mayar mata da shi can.

  Ita dae kam bata damu ba duk da ta d'an ji ba dad'i, a haka har Umma ta gama mata nasiha suna kuka su duka biyun.

  Motoci biyu suka kawo Alentra guda sae honda civic itama guda d'aya, A Haka aka sakata tare da mutanen da suka sawwak'a sauran kuwa sae dae suka hau abun hawa suka biyota, Kuka sosae take har aka iso tangamemen gidan Abdallah gidan da ya tafi da imanin duka mutanen dake gurin.

Sashena aka nufa dani inda yake dauke da ciki da falo guda sae d'an k'aramin toilet a cikin falon, Tsakiyar gado a ka ajeni sae maryama da su hafsatu dake zagaye dani ko wane da abunda yake sak'awa.

  Ba'a bamu abinci ba sae wajen k'arfe takwas da rabi sannan suka kawo farar shinkafa da manja da yajin k'uli k'uli.

  "Kutmar Ubancan wae me mutanan nan suka mayar damu ne.? cewar Maryama tare da d'aukar bokitin da aka kawo abincin ciki ta fita, nikam kuka na saki don har ga Allah abun ya tab'a man rai

Tana fita na janyo wayata na kira Abdallah amma sae da ta kusa katsewa sannan aka d'auka ana fad'in "Larindo me kuma kuke buk'ata? Jinja ko k'arin barkono ko gishiri.?

  Yanke wayar tayi ganin Maryama tsaye tare da Abdallah a bayanta, kifar da kanta tayi jikin pillow ta cigaba da kukanta, Duk mutanen dake gurin suka bar d'akin yayin da ya tako a hankali ya tsaya bakin gadon yana kallonta.

Tab'e baki yayi tare da zama gefen gadon ya d'ago fuskarta ya d'aura a cinyarsa, murya k'asa k'asa yace "Muhibbatah kiyi hakuri nasan kun fi k'arfin cin shinkafa da manja amma restaurant d'in da aka bada abinci a maku shine ya kama da wuta yanzun nan kuma an nemi kayan miya an rasa shi yasa aka dafa maku."

  Ba tace mashi komae ba sae zamewa da tayi daga cinyarshi ta cigaba da kukanta k'asa k'asa

  "Muhibbatah." Ya kira suna cikin k'warewa da yaudara

  Cak kukan nata ya tsaya yayin da yasa hannunshi ya zame mata gyalen da ta rufa dashi, a hankali ya cire mata dankwalinta yana yawo da hannunshi cikin gashin kanta.

  Cikin rad'a yake fad'in "I'm sorry Muhibba, Na karbi laifina kin ji ko yanzu zan je na kawo maku abinci da kaina though bana jin dad'i amma baran bari ran Muhibbata ya b'aci ba."

  A hankali ta d'ago tana kallonshi tare da kai hannu zata share hawayenta amma yayi saurin rik'e hannun yayin da ya kai hancinshi yana goge hawayen dasu...

  A Hankali tace "Me ya sameka?

  Tsayar da hancin yayi a kusa da idonta a hankali ya motsa bakinshi yayin da lips dinshi ke jingine da kumatunta yace "Fever."

  Idanunta ta waro tana kallonshi cike da tausayi lokaci guda ta kai hannunta wuyanshi idonta cike da k'wallah tace "Amma baka fad'a man Ya Abdallah."

  Murmushi ya sakar mata yana fad'in "Karki damu Muhibbanah, Is normal ai Love Fever ne.."

   Lumshe ido tayi har ya k'are goge mata sannan ya bata  tattausar sumba a kumatunta ya narke mata idanu.

  A hankali ya tashi tsaye yana lulluba mata gyalenta a kai, K'asa yayi da kai a hankali yace "Ban tab'a ganin halitta mai k'yawu irin ta Muhibbata ba, gaskia kin had'u."

 
  Shiru tayi ya kuma ya ja mata hanci cikin tsokana yace "Kin san menene kuma?

A Hankali ta girgiza mashi kai tana kallon k'asa tare da wasa da yatsun hannunta, kama hannun yayi ya zauna kusa da ita yayin da jikinshi rabi yana gogar nata cikin wata irin murya yake fad'in "Komae na Muhibbatah mai kyau ne shi yasa nake matuk'ar kaunarta."

   Dagowa tayi tana kallonshi, dauke da lallausan murmushin da ya fito da dimple d'inta, yasa hannu a dimple d'in yana mai da mata martanin murmushinta.

  Sumba ya kai mata tare da juyawa ya fad'in" Bara na k'arb'o maki kaya sae ki shirya zanzo na d'aukeki anjima kin ji ko."

  Tana so ta tambayeshi ina zasu sae dae kuma ta kasa don kullun Abdallanta kwarjini yake mata, Yana fita Su Maryama suka shigo suna fad'in wae ance su shirya za'a mayar dasu gida don babu wanda zai k'wana a gidan amarya.

  Kuka ta saki tare da kiran Abdallah wannan karan shi ya dauka yana fad'in "Larindona har sun shiryane.?

Cikin kuka tace "Dan Allah karsu tafi Abdallah, ka barsu zuwa gobe mana kamar yarda akewa ko wace amarya Abdallah."

  "Haba Muhibba ai yanzu an bar k'wana gidan amarya kiyi hakuri kinji ko?

  "Gobe kawae Abdallah." Ta fad'a cikin kuka

  Cikin sanyin murya mai cike da rauni yace "Kina so ki shiga hakkina ko Muhibbah?Baki son ina da bukatarki bane yau Muhibbah?Kiyi hakuri ki su tafi kinji ko, karki shiga hakkin Abdallanki, Na maki alk'warin zan mayar maki da darenki farin dare.! Zan cika maki shi da soyayya da k'auna mai tarin yawa."

  Shiru tayi tana saurarenshi lokaci guda zuciyarta ta k'arye, tabbas bara ta shiga hakkin Abdallanta ba..

  A hankali yace "Muhibbah..Baki yarda da Abdallanki ba? Shi kenan na hakura ki ce su dawo."

  A raunane tace "aa Ya Abdallah na yarda da kai."

Murmushi yayi mai sauti yana fad'in "Yauwa Muhibbata shi yasa nake matukar k'aunarki ba kamar Hasna ba."

Itama murmushin tayi...
Tana ji tana gani suka watse suka barta k'walam, tabbas tayi kuka sosae har wata yar yarinya ta shigo d'auke da kaya cikin leda tana aje tana fad'in "Gashi ance a kawo maki sannan ki shirya da wuri anjima kad'an zaaje partyn."

#Feedohm
#Haske writer's
#Much Luv Momma Hafsat (Xoxo)...

 ðŸ’§ðŸ’§ *MATAR ABDALLAH.!*💥
                   True Life Story.!

                              💥

*©HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
   *Wattpad:Feedohm*

*07*

  Kofar na kalla yayin da k'irjina yayi mummunar bugawa, Abdallana ne da wata ba indiya hannunsu a sark'e yayin da suka saka wani tsadadden yadi ruwan kwae kala daya, ko mak'iyinsu a lokacin idan ya kallesu dole ya yaba k'yawunsu.

Tashin hankalin da nake ciki na d'azu ya bar ni, sae wani sabo dake niyyar dirar mikiya a cikin k'ahon zuciyata "Wannan Yar'uwarsa ce amma ba dae matarsa ba." Wani sashe na zuciyata ya tunatar dani.

  Gani nayi matar ta tsaya cak tare da kallon Abdallanah, ta shagwab'e murya tana fad'in "Yanzu nan har ciki zan taka da k'afata Abdallanah."

  Lumshe mata ido yayi tare da sumbatar goshinta ya d'agata sama kamar jaririya ya fara takowa da ita a hankali idanunsu na sark'e da juna.

  "Hoooooooo.." Gurin ya d'auka tare da tab'i ana rungumar yan'mata.

  Bansan lokacin da na rik'o hannun Budurwa Fatima ba ina k'ak'k'arwa "Wacece waccan kar dae kice man MATAR ABDALLAH ce"na fad'a muryata na rawa tare da niyyar d'aukewa.

  Dan murmushi tayi a hankali tace "Hasna kenan MATAR ABDALLAH."

  "MATAR ABDALLAH fa kika ce? amma ai ba haka take ba."Na sake fad'a ba tare da nasan na fad'a ba

  Murmushi ta man tare ta wuce daga kusa dani ta zauna cikin kujerun dake zagaye da gurin.
Kujeran dake kusa dani ya zauna sannan ya d'aurata saman cinyarshi tare da sumbatar goshinta kafin ya juyo gurina yana kallon cikin idona.

Murmushi ya sakar man ganin yarda nake k'yarma don a lokacin da za'a auna jinina tabbas bsbu abunda zai hanashi hawa.

  Kamar mai rad'a yace "Meet MATAR ABDALLAH Larindo."

  Had'iye miyau nayi cikin wahala lokaci guda jikina yayi mutuwar bazata, ban iya ko da motsa hannuna ba bare na dube baki nayi magana, ita kam juyowa tayi tana kallona sama sama, kafin ta sakar man murmushi da na kalleshi matsayin tsantsar rainin wayau tare da mik'a man Hannu guda alamun mu gaisa.

   Da k'yar na danne zuciyata dake niyyar fitowa na daga hannuna dake k'yarma na mika mata, Kamar garwashi haka nake jin hannun nata yayin da idona yayi jawur k'irjina kam na tabbata ko mutanen dake waje zasu iya juyo bugunsa.

  Murmushi ta kuma saki tana fad'in "I'm MATAR ABDALLAH nice to meet you."

  Cikin k'yarma nace "Nima MATAR ABDALLAH ce.."

Dariya ta saki cike da rainin wayau "Tace wae nima MATAR ABDALLAH ce" ta fad'a cikin izza da cin fuskar

  Kafin ta janye hannunta daga nawa tana kallon Abdallah ta d'age mashi gira d'aya saitin kunnenshi ta matsa yayin da bakinta ke motsi cikin a hankali tace "Really wae MATAR ABDALLAH ce.?

  Tab'e baki yayi tare da jujjuyar da kai yana kashe mata ido.

"Ya Rabbi."Na fad'a lokacin da naji wani katoton abun na neman tarwatsa zuciyata, tabbas wannan abun akwae cin fuska da wulakanci a ciki, lokaci guda hawaye ya fara sintiri saman fuskata, yayin da nake saka bayan hannuna ina gogewa kamar wata zautatta.

  An d'auki lokaci ba tare da nasan me ake ba, har sae da Abdallah ya d'an zunguro k'afata tare sa duk'o da kaishi saitin fuskata yana fad'in "Eat mana."

  D'agowa nayi ina kallon Plate d'in robar dake gabana wanda ke dauke da K'ugun kaza soyayya sae Kai da K'afafu da yan hanji da aka soya da kwai guri guda aka luliye.

  "Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un."Abunda na fad'a kenan yayin da wasu k'wallan masu zafi suka fara wanke man fuska...

  Tashi nayi da niyar barin gurin amma Abdallah ya maidoni yana jefa man wani irin kallo, ban san lokacin da na fizge hannuna ba na fice daga hall d'in ina hawaye yayin da mutanen gurin suka d'auki ihu tare da sowa banda Budurwa Fatima da ta biyoni da Abdallah.

  "Muhibba." Yake kira amma sam banyi tunanin juyowa ba don bana tunanin zan iya sauraren abunda zai ce man.

Budurwa Fatima ta sha gabanta cike da tausayi don tunda ta ga Muhibba ta ji ta kwanta mata a rai

      "Should i say something to you.? ta fad'a tana kallona

  Dae dae lokacin Abdallah ya iso yana jefa man wani irin kallo wanda ta kasa banbance shin kallon soyayyane ko na kiyayya koka tsabar wulak'ancine..

  "Me ke faruwa Muhibba? Where are you going.? ya fad'a kamar mai rad'a tare da kamo hannuna biyu

  Ban Kalleshi ba sae dae nace "Sake man hannu Abdallah."

  Janyoni yayi da karfi na fad'a k'irjin, bansan lokacin da na tureshi ba da k'arfi tare da sakin kuka mai cin rai...

  "Muhibbata."

   Cikin tsawa nace "Don't ever call me Muhibbarka, I'm ignominy Abdallah.."Na k'arashe maganar cikin matsanancin kuka.

  "Listen Please and tell me what's wrong."Ya fad'a a hankali.

  Cikin tsawa nace "You're asking me what wrongs.?

  Shiru yayi yana kallona yayin da na zuba mashi manyan idona da sukayi jawur ina kallonshi, Wani takaici tare da tsanarshi ya man dirar mikiya cikin tsawa na cigaba da fad'in "Da fari Abdallah bayya k'aunar Matarshi sannan MATAR ABDALLAH batta da ladabi, batta da biyayya, batta da tarbiyya, bata iya soyayya ba, bata iya kula da miji ba, bata iya girki ba, bata iya magana ba, MATAR ABDALLAH mummunace, MATAR ABDALLAH k'azamace, Muhibba Tafi MATAR ABDALLAH komae.!

  "Muhibba."

"Enough Abdallah, Wad'annan ma duk sun isa bana son sake jin wani mummunar ak'idar matarka domin na fahimce komae a yanzu, I'm Ingominy Abdallah duk abunda kukayi a hall din bai isheku ba sae kun nunawa duniya Muhibba Yar talakawace ta hanyar bata kai da k'afafun kaza a ranar aurenta.! bakuyi kuskure ba domin yar'talakawa ce amma ba wulak'antatta ba."

  Kallonta yake kamar bai fahimci me take fad'a ba" Ban fahimceki ba Muhibba, Make it clear please."

  Wani tuk'uk'in bakin ciki ya tasowa mata yayin da ta fashe da matsanancin kuka tana kallonshi .

  "Believe me Muhibba ban san me aka kawo maki ba, wallahi is'nt my fault." Ya k'arashe maganar muryarshi na d'an rawa.

  Cikin tsawa tace "Whose fault Abdallah ?Nasan bai wuce ka ce MATAR ABDALLAH  ba ko.?

  Bayan hannunta ta saka ta share hawayenta, a hankali tace "You broke my truth Abdallah."

  Lumshe ido yayi yana saurarenta lokaci guda ya budesu yana kallon Budurwa Fatima "Ki tafi da ita gida Tee gani nan zuwa." Ya fad'a tare da juyawa ya koma hall d'in sanyaye, Har ga Allah bai lura da abunda aka kawo mata ba sae yanzu da tayi magana, tabbas ba'a kyauta mata kuma sae ya fad'awa Hasna bata kyauta ba, Tausayinta yaji karo na farko a d'an zaman da yayi da ita..

   Kuka take sosai yayin da Budurwa Fatima ke ta lallashinta cike da kulawa, ganin ta d'an rage kukan yasa tace "Mu tafi Muhibba tun kafin mutane su fito."

  Girgiza mata kai tayi tana fad'in "Zan hau machine ki barsa kawae."

  "Me yasa Muhibba.?

  Kai tsaye tace "Gidan mu zan tafi."

  Dan murmushi tayi kafin tace "Ince kina da mahaifi da mahaifiya Muhibba? kuma na tabbata basu barki haka ba sae da suka maki wa'azi kafin ki taho, Idan kin koma ya zaki ce masu? Meye laifin mijinki anan? Kin san yana da mata kika aure sa sannan kuma kin san yana sonta? Kawae don ya rungumeta a gabanki shine laifi?

  Girgiza kai tayi yayin da take ganin abunda suka mata matsayin cin fuska da tozarci, Babban bak'in cikinta bai wuce abunda aka bata ta ci ba.
Lokaci guda ta tuna da maganganun babanta, da k'yar ta iya tsayar da zuciyarta har ta yarda ta koma gidan Abdallah, sun dad'e da budurwa fatima don har sae da suka dawo wajen karfe d'aya sannan ta mike ta mata bank'wana ta tafi..

  Ita kam ta gagara ko da zama yayin da tunaninta ya tafi gurin Abdallah da matarsa, Tabbas sun wulak'anta ta sun nunawa duniya ita yar talaka ce, Amma me yasa Abdallah ya mata k'arya haka?

  Jin an turo k'ofar d'akin yasa ta kwanta da sauri tare da k'udundunewa guri d'aya, Bakin gadon ya zauna yana kallonta babu yabo babu fallasa kafin ya kira sunanta cikin wata irin murya ...

  "Muhibba, Though nasan ba dole bane ki fahimceni amma wallahi duk abunda ya faru banda masaniya akai."Ya fad'a cikin raunin murya

  Da sauri ta mike zaune tana kallonshi, lallae Abdallah ya mugun raina mata wayau, shin me ya dauketa?

  "Kenan ku yan biyune Abdallah."

  K'walla na hango cike da idonshi, yayin da ya narke murya yana fad'in "Wallahi Muhibba tun jiya da na sha wani fruit da Hasna ta bani nake jin kaina kamar bani ba, Tabbas nasan anje party amma wallahi bansan me ya faru ba acan, ki fahimceni dan girman Allah ki man uzuri, na tabbata  kece mace ta farko da ta tab'a fabimtar Abdallanta sannan ta samu gurbi na musamman a zuciyar Abdallah."Hawayen idonshi suka gangaro saman fararen kumatunshi

  Tabbas ina kaunar Abdallah, lokaci guda zuciyata ta narke yayin da tausayunshi yaman dirar mikiya.

  Muryashi na rawa yayin da hawaye suka cigaba da zuba yake fad'in "Dan girman Allah kiyi hakuri Muhibba baran iya jure fushinki ba."

  Da sauri na d'aga mashi hannu nima ido cike da k'wallah don har ga Allah baran juri ganin hawayen Abdallana ba "Na fahimceka Abdallah kuma insha Allahu zan tayaka addu'a idan ma wani abu aka maka da yardar Allah zai kare, dan Allah ka daina hawayen nan wallahi zuciyata bara ta dauka ba Abdallah."

  Kamar d'aukewar ruwa hawayen suka dauke yayin da ya janyoni jikinshi a hankali yake fad'in "Allah ya maki albarka Muhibba, dan Allah karkiyi fushi dani komae rintsi ki saka a ranki Abdallanki bara ya tab'a muzguna maki ba muddun yana cikin hankalinshi."

  Gyad'a kai nayi tare da lumshe idanu yayin da na hakikance da maganar Abdallah, ashe mugun halin matarshi har ya kai ga asiri? Lallai kam dole na tashi tsaye da addu'a don wata rana ni zatawa.

  Duk abunda ya fad'a na bak'in halinta ya dinga dawo man a kai, indae hakane gaskiyar Abdallah bata da hali mai kyau, Amma me yasa Abdallah yace matarshi mummunace? ni kuma yau na ganta ta fini kyau da komae, kasa daurewa nayi na kalleshi.

  "Banyi tunanin haka zanga Matarka ba."Na fad'a cikin raunin murya

  Shafa kaina yayi tare da kwanciya saman gadon ya janyoni a jikinshi, cikin kunnena yace "Me yasa Muhibba?Fad'a man ya kikayi tunanin ganinta."

Kai tsaye nace "Mummuna kamar yarda kake fad'a man."

"Kin dauka bata kai haka muni ba ko.?

  "Naga tana da k'yaune."

A Hankali yace "Ni kam ban tab'a ganin kyaun ta ba Muhibba, watak'ila ko don bana sonta shiyasa, amma a gurina kin fita komae Muhibbata."

  Kamar an tsikareshi ya mike yana fad'in "Ina zuwa Muhibbata."

  Binshi nayi da kallo har ya bar d'akin yayin da na koma na kwanta cike da tunani kala kala, sam bana fargabar yarda darenmu zai kasance da Abdallah don har ga Allah ban san ya daren amarci yake ba tunda lokacin ban wuce shekara 17 ba, a nawa haukan kawae na kwanta a jikinshi yana shafani shine auren kuma ban tab'a saurayi ba sae Abdallah sannan ba karatun littafin hausa nake ba don haka sam bansan rayuwar aure ba. Ina zaune jiran Abdallah har bacci ya kwasheni bai dawo ba ..

#Feedohm

  💧💧 *MATAR ABDALLAH.!*💥
                   True Life Story.!

                              💥

*©HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
   *Wattpad:Feedohm*

*08*

**
    Wani mugun kallo ta watsa mashi tare da d'aga mashi hannun tana huci "Dakata Abdallah! kana so ka fad'a man cewa kaji haushi mun bawa amaryarka Kai da k'afafu.?

  Cikin sanyin,murya yace "Yes.! Kuma baki k'yauta ba Hasna."

  "Ai dama baran tab'a k'yauta mata ba." Ta fad'a kamar idanunta zasu fad'o k'asa

A Hankali ya taka har kusa da ita, murya k'asa k'asa yace fad'in "Duk abunda muka mata a hall din bai isheki ba Hasna? Har sae kin k'ara da wannan? kin wulakanta ta cikin bainar jama'a.? A tunaninki zaki burge Abdallah? duk da bana k'aunarta amma Mahaifiyata ta hananeni da tozarci."

  Kallonshi take sama da k'asa kafin tace "Ba kai da k'afa ba Abdallah har da kugu ai na bata, meye na tozarci a ciki? ko ka manta kasha fad'a man yar' talakawa wace? kuma na tabbata ko gidan Ubanta abunda take ci kenan koko ta wuce haka? Fad'a man Abdallanah."

  "Wait Hasna..Yes Yar'talakawa ce amma ba wulak'antattu ba, ko an fad'a maki takalawa wulak'antattu ne? baran daina fad'a maki baki k'yauta ba Hasna kuma banji dad'i ba."

  Kasa cewa komae tayi sae kallon da ta bishi dashi. Ganin ya juya yana niyyar barin d'akin yasa ta sha gabanshi idonta cikin nashi tace "Me kake nufi Abdallanah?

  "Kin fi kowa sannin Abunda nake nufi Hasna."Ya bata amsa babu yabo ba fallasa..

  Wani bahaggon kallo ta bi shi dashi kafin ta kamo dukkan hannayeshi cikin nata ta langwabe kai tana fad'in "Meye haka Abdallanah? akan wannan yarinyar zakayi fushi da Hasnarka.?

  Shiru ya mata tare da janye hannunshi ya zauna kujeran dake kusa dashi, binshi tayi ta tsugunna gababshi tare da d'aura kanta saman cinyarshi, cike da k'issa tace "I'm sorry Abdallanah."

Lumshe ido yayi tare da d'agota ya zaunar da ita bisa cinyarshi yana sinsinar wuyanta a hankali yace "Ki fahimci me nake nufi MATAR ABDALLAH, idan wannan yarinyar ta ga muna wulak'antata tabbas zata gane abunda yasa na aureta kuma bara ta yarda ta biya mana buk'atarmu ba, dole mu lallab'ata har mu samu abunda muke so shikenan sae muyi zamanmu daga ni sae ke yar'mu ko yaronmu."

  Idonta a lumshe tace "Na fahimta Abdallanah kayi hakuri."

  Murmushi ya sakar mata tare da sumbatar wuyanta yana fad'in "Ina kazar amarcina.?

A Hankali ta mike tana rangwad'a ta fita daga d'akin ta nufi kitchen ta dauko wata katuwar leda da tray ta dawo ta aje gabanshi tare da komawa ta zauna tsakiyar gadonta ta lullib'e kanta da mayafi tana murmushi..

  Da tattausan murmushi ya mik'e ya zazzage kazar ya nufi gadon shima

***

  Muhibba kam tunda asuba ta tashi sae kalle kalle take a tunaninta Abdallah ya dawo, sae da ta tabbatar da ba kowa d'akin sannan ta tab'e baki ta nufi toilet tayo wanka tare da d'auro alwala ta fito tana goge kanta da d'ankwalinta..

  Jagwab ta zauna bisa gado tare sakin d'an k'aramin tsaki tana turo baki , a hankali tace "Kayan ma bara a iya bawa mutun ba, yanzu to dan Allah me suke so na saka koko nayi ta zama da kaya kala d'aya har Abdallanah ya shigo ya iskeni haka? bayan Maryamata ta fad'a man cewa amarya k'walliya take sosaae."

  Dariya ta sake tunowa da komin tsiyarsu dole su bata kayanta yau, don haka ta mike ta saka hijab tare da shinfid'a d'ankwalinta ta kabbara sallah don ko abun sallah ba'a kawo mata ba.

   Sae da tayi azkar d'inta ta karanta AlQur'anin wayarta sannan ta mik'e ta bud'e d'akin ta leka waje jin masallacin kusa dasu sun sallame sallah kuma tana so ta hango Abdallanta ko da daga nesa ne...

  Wani lallausan murmushi ta saki tare da tallabe kumatu ganin wani ya turo kofar yana k'ok'arin shigowa kuma a tunaninta Abdallanta ne ya dawo daga masallacin, ganin mai gadin gidan ne yasa ta b'ata fuska sannan ta koma d'akinta tana fad'in "May be ya makara bai tashi ba bara na tada shi ko a gida sae yayi tunda mosque sun gama."

  Wayarta ta dauka tayi dialing numbershi cikin sa'a ya dauka sae dae baccin dake idonshi ya hanashi magana.

"Ya Abdallah ina kwana."Ta fad'a har da russunawa kamar yana kallonta

  "Larindo."Ya fad'a cikin muryar bacci tare da k'ara rungume Hasna dake baccinta hankali kwance .

  Dan murmushi,ta sake tace "Bacci kake ko? ka tashi kayi sallah to."

  "Sannu d'iyar liman ba yanzu ba."Ya fad'a har da d'an tsakinshi yarda bara ta ji ba.

  Cikin sanyin murya tace "Sae yaushe Ya Abdallah? kar fa lokacinta ya wuce."

  Banza ya mata tare da yanke wayar yayi jifa da ita ya koma baccinsa, Ita kam mamaki ya hanata barin inda take yayin da ta saki baki tana kallon wayar.

***

Tunda daga ranar sae da akayi kwana biyar Muhibba bata kuma ganin Abdallah ba, ko ta kira wayarshi batta shiga yayin da kullun da za'a kawo mata abinci mai rai da lafiya tare da kaya kala d'aya na sawa .

  Abun yayi bala'in d'aga mata hankali don haka ta yanke shawarar shiga cikin gidan taji ko lafiya, Hijab ta sanya ta fita daga d'akinta ta ja kofarta.

  A sanyaye ta turo kofar babban falonsu had'e da yi Sallama tayi tsaye tana jiran a amsa ta shiga domin ta na d'an jiyo dariyar mutane k'asa k'asa.

  Ta dad'e tsaye tana jiran a amsa amma shiru babu amsa haka har lokacin tana jiyo dariyar da alama hankalin mutanen dake ciki baya ga k'ofar don haka ta d'aga labulen ta shiga cikin sanyin muryar ta kuma yin sallama.

  Cak ta tsaya ganin Abdallanta goye da matarshi suna ta dariya abunsu yayin da yake zagaye falo da ita, Lokaci guda hawaye suka cika mata ido yayin da zuciyarta ta karye, a sulale ta juya ba tare da sun lura da ita ba, da gudu ta koma d'akinta ta fad'a saman gado ta saki kuka mai masifar cin rai "Ashe ma yana cikin gidan" Sam ta kasa fahimtar Abunda Abdallanta ke shirin aikatawa.

  Kuka take na tausayin kanta da rayuwar da zata fuskanta a gidan mutumin da ta d'auki son duniya ta daura mashi "Anya Kuwa Abdallah na sona? amsar da ta kasa gano wa kenan, a tunaninta indae yana sonta bara ya tab'a banzar da ita haka a matsayinta na amaryar da ko sati bata k'ulla gidanshi ba.

  Ta dad'e tana tufk'a tana warwara yayin da zuciyarta ta kasa banbance halin da take ciki, sam bata so ta kiran Ummanta ta d'aga mata hankali,

  "Maryama." ta fad'a kafin ta dauki wayarta kira Maryama

  Ringin d'aya Maryama ta dauka tana fad'in "Amaryar Abdallah, fad'a man an baki lefenki? Yaya zaman naku? ina fatan k'awata tayi k'iba sannan tana samun farin ciki gurin Abdallanta."

  Kuka ta saki a hankali tana sauraren Maryama, Hankalin Maryama ya tashi tace "Menene Muhibba? Me kika kewa kuka? Fad'a man da sauri, ko wani abu danginshi suka maki eyeh?

A hankali ta fad'a mata duk abunda ke faruwa daga zuwanta har partyn har abunda ya faru da kuma yanzu da ta shiga gidan.

  "Kan ubancan amma ke banza ce Muhibba."

  Kukanta ya tsananta jin maryama sae uban bala'i take mata maimakon ta lallashe, sae da maryama tayi masifarta mai isarta sannan tace "Bara nazo gidan wallahi sae na yage masu rigar mutunci daga Abdallah har shegiyar matarshi."

Ba'a d'auki lokaci ba kuwa sae ga Maryama, a harabar,gidan tayi cibus da Abdallah rige da hannun matarshi da alama fita ma zasuyi, wani tuk'uk'in bak'in ciki ya tokareta ta tunkaresu cike da b'acin rai...

  Yana hangota ya had'e rai tare da k'ara rungumo Hasna jikinshi, Itama Hasna kallon maryama take cikin rashin sani tare da k'ara lafewa jikinsa sosae.

  "Su,Maryama ne."ya fad'a babu yabo ba fallasa don har ga Allah bayya son k'awancen maryama da Muhibba saboda maryama tafi Muhibba hankali da wayau kuma zata iya canzawa Muhibba tunani.

  "Ba su maryama bane, su innarsu Maryama ce."Ta fad'a kamar idonta zai fad'o kasa saboda tsabar harara

Wani banzan kallo ya mata kafin ya bud'e bakinshi da niyyar mata magana amma tayi saurin d'aga mashi hannunta sama tana aikin zabga mashi harara "Dakata, ka adana kamalanka Abdallah don basu nazo ji ba idan kana son fad'ar wani abu ka iskeni har inda nake ka fad'a amma yanzu Maryama tazo ta fad'a maka nata bawae ta saurareka ba."

  A zafafe hasna ta sakeshi tana kallonta cikin tsabar raini da wulak'anci "Ke wacece.?

  "Idan na bar nan K'ya iya tambayar munafukin mijinki idan ya gulmar ta zame maki jiki.! sannan ina so ki kama banzan bakinki har lokacin da zan bar nan."

   Daga hannu tayi da niyar marinta tana fad'in "How dare you."

  Da sauri ta rike hannun tana girgiza kai had'e da murmushi tana fad'in "Kai.. kai.. MATAR ABDALLAH.! Maryama ce gabanki ba Muhibba ba, wallahi kika bari hannunki yayi gigin tab'a jikina sae na keta maki rigar mutunci anan gurin kuma agaban munafukin mijinki."

Kamar an dasa Abdallah haka yake tsaye yana kallonsu thou dama shi ba mutun ne mai son rigima ba shi tsoronta ma yake kamar,Haka tsoron Maryama yanzu dake gabanshi don har ga Abdallah fitinarta ta shalle tunaninshi, maganarta ta doki dodo kunnenshi

  "Sannu munafuki dole ka tsaya kana kallona, to ka sani mata muka kawo maka ba baiwa ba Abdallah, sannan kaine kace kana sonta ba l;ika maka ita akayi ba, kuma gidan talakawa ka ganta ba gidan wulak'attatu ba, ka fad'a man dalilinka na wulak'antata? koko dama munafunci yasa ka aureta akwae wata k'ullaliya cikin zuciyarka? Ka yaudari kanka Abdallah kuma kaci amanar K'awata kuma wallahi sae kayi nadamar Abunda ka aikata."

  A Hankali yace "Idan tashin hankali ya kawoki maryama dan girman Allah ki fitar man daga gida."

  "Wallahi ban fita tunda k'asar ba gadon uban wani bace."ta fad'a kamar idonta sae fad'o k'asa

  "Baran ce Muhibba ta bar gidanka ba, sannan baran sa Muhibba ta wulak'anta aurenta ba, ba kuma zan saka ta sab'a maka ba Abdallah, sae dae bazan yarda a wulak'anta man yar'uwa ba domin ba k'awa kadae na dauketa ba Yar uwa tace. Kai Abdallah bara ma kaji idan kaga na bar gidan nan yau to wallahi sae an bawa Muhibba lefenta don ita ba shegiya bace da zata dinga zama da kaya kala d'aya, sannan sae an bawa Muhibba yan'cinta na girki da Miji domin itama MATAR ABDALLAH ce.!

  "Idan ba;ayi ba fa? ak'wae uwar da zaka iya.? Hasna ta fad'a cikin b'acin rai da tashin hankali

  "Idan ba'ayi ba kika tambaya? Kar ayi ki ga zan bar gidan koko  zaku samu kwanciyar hankali a gidan, Kuma dan uwarki ki rufe man baki tunda ba gurinki nazo ba, banza juya dake mai yankakkar mahaifa...!

Turk'ashi...

#Feedohm
 ðŸ’§ðŸ’§ *MATAR ABDALLAH.!*💥
                   True Life Story.!


                              💥


*©HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers


*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
   *Wattpad:Feedohm*

*09*

        *This Snippet goings to DarlingSlimzy and PharmLawysat.I pray to Allah to expose your enemies,i pray that Allah deny them what they want, humiliate them, let them see no peace anywhere in this world, protect all of us that need protection and guides all our affairs. Amin*

***
  Hayaniyar da Muhibba tajiyo yasata fitowa da sauri, Tun a falo ta fara  jiyo kamar muryar Maryama kuma ta tabbata babu abunda bara ya iya faruwa ba idan maryama ta iske Abdallah. Ta sani sarai Maryama batta da hakuri kuma bata jure komae k'ank'antar wulakanci da cin mutunci daga gurin kowa, balle ma ace Muhibbarta aka tab'a..

  Cak ta tsaya ganin Maryama rike da k'walar rigar Hasna yayin da Abdallah ke k'ok'arin rabasu, muryar maryama taji tana fad'in " Ance maki juyar ko ba ita bace? ki fad'a man idan akwae shegen da yasa ki yanke mahaifarki? uban wa ya sani ma ko dan baki haihuwa yasa Abdallah auren Muhibbar."

  Cikin k'yarma ta fara kiran sunan "Maryamar."

  Ita kam ko saurarenta bata yi ba ta cigaba da fad'in "Munafuki da dad'in baki ya saye zuciyar k'awata ashe duk munafurcine."

  Kuka ne ya ci k'arfin Hasna ta kai hannu ta kaiwa Maryama duka a kai ta goce da sauri.

   Muhibba ta k'araso tana kuka tana jan Maryama"Dan Allah ki bari Maryama banna so."

  "Barni Muhibba."Ta fad'a a hargitse

  "Na shiga uku, dan girman Allah ki zo muje maryama ki daina nace ."Ta k'arashe maganar cikin matsanan cin kuka.

  Gani tayi Maryama ta zub'e k'asa yadda kasan yar bori sae juyi take tana birgima tare da wata irin kuwwa tana fad'in "Sae ni Sarkin Aljanu zanzakitu, me yasa aka b'atawa god'iyarmu rayi? ba zamu yarda ba, sae mun kasheku..Hoooo."

  Baya Abdallah ya ja yayin da Hasna ta koma bayanshi cike da firgici,Ita kam Muhibba iya rud'ewa ta rude don bata tab'a tunani ko jin ance Maryama na da aljanu ba sae yau,"to ina ta samesu? na shiga uku kar dae ace sanadina Aljannun maryama suka fara bayyana."

Adadin kukanta ya karo yayin da tayi ta maza ta duk'a ta rike maryama gam tana tofa mata addu'a

  "Duk ke kika janyo komae Muhibba."Abdallah ya fad'a sae raba ido yake

  "Munafuki ba ita ta janyo ba kaine.! duk abunda kuke muna binku a baya kuma muna kallonku! harta abunda kuka bata gurin party mune muka cinye bayan kun tafi, kuma sae mun kasheku."A ka fad'a cikin wata irin razanannar murya

  "Sae mun kashe ku idan ba'a bata hakkinta ba."A ka kuma fada cikin tsawar gaske

  Sosae su duka suka razana amma hakan baisa Muhibba sakin Maryama ba sae ma k'ara rik'eta da tayi duk da tana tillar da ita gefe guda

  "Hoooo Baku ji bane..Ina lefenta.?

  Cikin k'yarma Abdallah yace "Wallahi lefenta nanan kuma za'a bata hak'k'inta don Allah kuyi hakuri."

  Hasna kam da gudu ta fad'a d'aki ta shige can k'uryar gado ta nannad'e don har ga Allah bata taba ganin aljanu sun taso ba kuma tana da bala'in tsoro

  Bin bayan Hasna yayi cikin k'yarma yana fad'in "Muhibba dan Allah ki mata addu'a su tafi,sanna ki basu hakuri ki kaita d'akinki bara na dauko lefen na kawo sae a raba maku k'wana, ai shikenan ko.?

  Tashin hankalin da take ciki bai bari ta basu amsa ba sae addu'a take har ta samu Maryama ta yi shiru sannan ta mikar da ita da k'yar tana tangad'i suka isa falonta, ta k'wantar da ita bisa doguwar kujera ta koma ta rakub'e sae addu'a take don har ga Allah ta tsorata amma bara ta iya bari Maryamarta ita kadae ba da babu abunda zai hana ta fice da gudu tun lokacin da aljanun suka taso ..

Abdallah kam iya rud'ewa ya rud;e Allah ma yaso sun had'a lefen sae dae wasu kayan duk tsofaffine na Hasna yayin da Hasnar aka sake mata sabbi, Da sauri suka fara cire tsaffin suna musayarwa da sabbi sannan ya dinga kinkimar akwatunan guda uku yana fita dasu daya bayan daya har ya kai falon Muhibba sannan ya dawo

"Tashi mu tafi Hasna."

K;walalo ido tayi tana share hawayenta "Ni kam bazan je Abdallah, wallahi tsoro nake ji."ta fad'a tare da k'ara lafewa k'arshen gado

"Ni kadae zanje to."

"Kai kadae ka aurota ai, kaga ka tafi don Allah ka samu ta bar gidan, ka masu duk abunda take buk'ata ni kam ba inda zanje."

Juyawa yayi a sanyaye ya koma ya toge bakin kofa yana raba ido "Muhibba ga lefen nan dan Allah kiyi hakuri da abunda ya faru."

  Ba tace komae ba ta share hawayenta tana kallon Maryama da har lokacin ke sheme tana gurnani.

  "A tale mana kayan."Su kaji ta fad'a kamar wata tsohuwa

  Da sauri Abdallah ya fara zazzage kayan tana daga kwanceta idonta ya juye tana kallo, sae da aka gama bud'e komae sannan tace "Leshi bai isa ba, haka material, sannan sae an k'ara adadin takalmi da jikka da turare..."

  "Duk za'a karo, dan Allah kuyi hakuri."

Dariya ta saki da k'arfi ta mike tana layi har ta isa gurin kayan sannan ta sheme zaune ta ware k'afafu tana kallonshi k'asa k'asa "Maganar k'wana."

Muhibba ya kalla a d'an tsoraci yana rike da labule yace "Yarda kika ce muhibba."

  "Yarda tace uwar wa? yarda dae nace, A bata sati d'aya sannan ka dinga k'wana biyu biyu haka na rab'a."Ta sake fad'a cikin kuwwa.

  Kafin ta daka mashi tsawa tana fad'in "Fice mara mutunci..."

Bata rufe baki ba ya fice da sauri yana kallon baya, bai tsaya ko ina ba sae d'akinsu a can ya iske Hasna har lokacin kwance bata motsa ba inda ya barta shima hawan gadon yayi ya lullube da bargo yana fad'in "Hasna dan matso kusa dani."

  Murginowa tayi ta k'ank'ameshi sae raba ido suke, a hankali tace "Ya kukayi da ita.?

Cikin rad'a ya fada mata duk abunda ya faru yayin da ya k'ara da fad'in "Zan san yarda zan hana Muhibba fad'a mata komae kafin na samu na rabasu in ba haka ba buk'atarmu bara ta tab'a biya ba."

Miyau ta had'e tana fad'in "Ban tab'a ganin tashin hankali ba irin na yau Abdallah."

"Nima wallahi hasna, ashe dama haka aljanu suke? Ya sake fad'a a hankali tare da rufe kanshi da,bargo..

**

Abdallah na fita Maryama ta juyo tana kallon Muhibba dake rakub'e sae zufa take tace a hankali tace "K'awata tashi mu shigar da kayan d'aki."

A firgice ta kalli Maryama sae raba ido take ta kasa cewa komae

  "Ke dalla Maryama ce."Ta kuma fad'a tana hararanta

  "Maryama."Ta fad'a tare da saurin rungumeta ta saki kuka tana fad'in "Sannu Maryama kinji."

A Hankali "Sannu da akayi me? ke k'awata ba wasu aljanu k'arya nake, idan ban masu haka ba baran iya k'watar maki yancinki ba, baki ji yarda na yanketa ba idan da na tsaya nasan sae taji inda nasan an yanke mata mahaifa kuma sae Abdallah shima ya tuhumeni kila ma har aje a fad'awa Abbana kuma kinga ba wanda yace man an yanke mata mahaifa sharrine kawae na mata."

Ware ido nayi ina kallonta kafin ta hanbareni tana fad'in" karki dauka ni ce zan k'watar maki yanci a'a na yau ne kadae ke zaki k'watarwa kanki dan wata rana idan na kuma k'aryar Aljanu asirina zai tonu."

  "Da gaske dama ba wasu aljanu Maryama?duk wannan abun da kikayi?

Harara ta balla mata "Banza boarding fa nayi, ko kin tab'a jin ance maryama na da aljanu, wallahi k'arya nake, amma fa naji fad'uwar da nayi har yanzu hannuna zafi yake.."

  "Lallae Maryama." na fad'a tare da kai mata duka a baya, ta saki k'ara tana dariya sannan ta mike tana fad'in "A K'aro leshi, A k'aro.."

Dariya na saki ina jinjina iskanci irin na Maryama, tabbas nasan bata jin magana amma ban tab;a tunanin zatayi k'aryar aljanu irin haka ba,..

  Kayan muka d'auka da k'arfi muka shigar dasu d'aki, sannan ta bud'e tana fad'in  "Bara na k'ara kallo nayi maza na fita don Wallahi mamana bata san na fito ba tana wanka na taho don bak'in ciki bara ya barni na jira ta fito ba, Idan naje gida na kiraki akwae magana sosae da zamuyi."

Gyad'a kai nayi ta cigaba da bincika kayan d'aya bayan d'aya, Tabbas kayane na gani na fad'a sae da ta gama kallo sannan ta mayar dasu takulle tana fadin "Kiyi hakuri na zagi mijinki Muhibba, sannan idan ya shigo ki ce ya daura maki shi sama sae munyi waya."

Bata jira komai ba ta fice yayin da na bita da sauri amma kafin na isketa har ta fice daga gidan "Allah sarki Maryamata." Na fad'a ina goge yan k'ananan k'wallan da suka zubo man..

  Ina Gab da shiga sashena naji Muryar Abdallah daga bayana yana kiran sunana"Muhibba."

Ban juyo ba haka ban amsa kiran ba sae dae na tsaya cak ina sauraren abunda zai fad'a, hucin shi naji a bayana yana fad'in "Bazan lamunci zuwan Maryama gidana ba."

Da sauri ina juyo ina kallonshi cikin rashin fahimta, yayin da ya gyad'a man kai yace "Yes karta kuma zuwa gidana nake nufi, idan ke baki san Wacece Maryama ni na sani."

  "Ni kam nasan wacece Maryamata Abdallah."Na bashi amsa ina kallon cikin idonshi

Murmushi yayi mai sauti kafin yace "Ok! amma ki sani Muhibba kadai na aura banda Maryama kuma karta kuma zuwa gidana."

  Idona ya ciko da k'walla nace "Bazata yiyu ba Abdallah sae dae idan bana cikin gidan nima"

  Bai ce komae ba ya juya da niyyar tafiya yayin da na bishi da sauri ina fad'in "Kawae don tazo ta fad'i gaskia shine laifinta gurinku."

  "Ta fad'i gaskia koko tana neman kashe maki aure."Ya fad'a tare da juyowa yana kallona babu yabo ba fallasa

  "Maryama bata tab'a kashe man aure Abdallah."Na bashi amsa cikin jin haushin zancensa

  "Yarinya kenan, To bara na fad'a maki gaskiar wacece Maryama gurinki don ki sani, tun ranar da kika had'ani da Maryama mu gaisa Maryama ta fara neman soyayyata sannan take neman hanyar da zata rabamu dake, Ke hatta ranar daurin aurenmu Sae da Maryama ta sameni tana kuka da rok'on na so ta na aureta itama a baya, Kinsan me ya had'asu da Hasna kokowa yau?

  Bance komae ba sae binshi da kallo da nake a firgice sannan ya cigaba da fad'in "Bayan ta shigo ta ganni ina k'ok'arin shiga mota shine ta tareni tana rok'ona na sota har take fad'ar Hasna juyace batta haihuwa haka kema sam bata san Hasna na jinta ba shine fa Hasnar ta shak'ureta har kika jiyosu, tana ganinki ta mayar da maganar wae tazo k'watar maki yan'cine har aljanunta suka tashi don karki fahimceta."

"Abdallah."

"Shiii kiyi tunanin Makomar aurenki Muhibba, sannan bazan boye maki ba Idan har Maryama zata cigaba da zuwa nan gidan gurinki to ina mai tabbatar maki zan sota wata rana domin itama tana da kyau da kuma diri kuma zan aureta sannan bana da ra'ayin mata uku kinga kenan ko ke ko Maryamatah."

 

#Feedohm💧💧 *MATAR ABDALLAH.!*💥
                   True Life Story.!

                              💥

*©HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
   *Wattpad:Feedohm*

   *Congratulation Ummu Subay'a for the Completion of GIDAN BATURE, Allah yasa mu amfana da abunda ke cike, Reverence to MA'U BATURE.*

*10*

  Wani razannannen kallo take bishi dashi har ya dasa aya, lokaci guda da taji kanta na bala'in juyawa, yayin da bugun zuciyarta ya tsananta, firgice tace "Mene?

Tattausan murmushi ya sakar mata had'e da gyad'a kai yana aika mata da wani irin fitinannen kallo.

"Maryamatah take son Abdallanah." Ta fad'a a hankali tare da mayar da kanta k'asa, hawaye suka balle mata kamar bud'ewa fanfo.

  "Ya rage naki Muhibbah." Ya kuma fad'a tare da juyawa yana murmushi k'asa k'asa

  Finciko hannunshi tayi da k'arfi tare da nuna mashi d'an yatsa, cikin tsawa take fad'in "K'arya kake Abdallah! wallahi Maryama bara ta tab'a cin amanata ba, wannan d'aya daga cikin munafurcinka ne."

  Yar dariya ya sake yana fad'in "Baki da wayau Muhibba kina saurin yarda da Mutun."

  Cikin k'unar rai tace "Kamar yarda na yarda da kai ko Abdallah? To ma meye idan Maryama ta soka? Ba kai ba, Idan da Maryama za tace na ciro zuciyata na bata to wallahi babu abunda zai hanani na damk'a mata ita! bare ma kai Abdallah? meye don na barwa Maryama kai? Wallahil azim idan kaga maryama ta daina zuwa gidan nan sae dae idan bana cikinsa ko da kuwa zaka sakeni sau talatin ka auri Maryama sau tis'in."

  Kallonta yake da mamaki don baiyi tunanin haka daga gareta, cigaba tayi da fad'in "Ina tantama akanka Abdallah, bana tunanin dan Allah ka aureni ba Abdallah.! Fad'a man me yasa ka aureni?

  Murmushi yayi mai sauti sannan yace "Yes.!dan ki haifa man yara na aureki Muhibba."

  Hawaye masu zafi suka zubo mata a hankali ta saka bayan hannu ta share tana kallonshi "Da tun farko ka fad'a man gaskiyarka,babu abinda zai hanani aurenka Abdallah saboda ina k'aunarka matuk'ar k'auna, me yasa ka munafurceni?Me yasa ka yaudareni Abdallah?

  Bai ce mata komae ba sae binta da yayi da kallo, a hankali ta juya tana fad'in "Banda zuciyar da zance ka rabu dani Abdallah."

  Dariya yayi k'asa k'asa yana kallonta "Ko kema da taki Manufar Larindo.? ko kema kud'in Abdallah suka janyoki Muhibba? Fad'a man gaskia? kinga kenan ki bani in baki babu wanda za'a cuta."

  Bata ce mashi komae ba ta juya ta shige d'akinta yayin da ta jingina da kofar tana fitar da kuka mai cin rai, Sae yanzu abubuwa da dama suka dinga dawo mata game da Abdallah.
"Allah ya isa Abdallah, ka cuceni wallahi bazan tab'a yafe maka ba."

Durk'ushewa gurin tayi tare da d'aga hannu sama tana fad'in "Ya Allah kai ka had'ani da Abdallah kuma kafi kowa sanin Hanyar da zaka rabani dashi, Allah na rokeka ka cire man son Abdallah."

  Maganar Maryama ranar d'aurin aurensu ta fara dawo mata "kar dae ace yan'uwan Abdallah basu da masaniya akan aurenmu? in kuwa haka ne tabbas Abdallah ya zalunceta, kuka ta kuma fashewa dashi yayin da ta mike zumbur ta fad'a d'akinta.

**

  "Umma naje gidan Muhibba d'azu, kuma kinsan me sun bata lefenta Umma, kaya masu kyau da tsada."Ta fad'a tana kallon Umman Hibba dake d'auraye kayan da suka gama cin abincin rana

  Murmushi Umman tayi tace "Masha Allahu Maryama, Ya wajen ita Muhibbar? injin tana lafiya.?

  Dariya tayi sosae tana fad'in "Kinganta kuwa Umman? wallahi tayi kyau tayi b'ul b'ul da ita yarda kika san kazar turawa, Umma hankali a k'wance kamar ba ita ba, sae murna take tana tambayata ina Umma wae, ni kuma nace kin ce zaki zo wata rana."

Dariya Umman tayi sannan tace "Kin kuwa mata karya Maryam, ina ni ina zuwa gidan Muhibba? ke dae Allah ya nuna mana naki kema Maryama nan ne ni da kaina zan kai d'iyata har d'akin mijinta sannan kuma na dinga zuwa ina duba lafiyarta."

Dariya Maryama tayi cike da jin dad'in kalaman Umman sannan ta rungumeta har tana niyyar tuntsirar dasu k'asa tace "Shi yasa nake sonki Ummarmi."

  Tureta Umma tayi tana hararanta "Shine zaki kayar dani k'asa ko?

   Ta k'yalk'yale da dariya "Yi hakuri Umman, bara na kira maki Muhibbar ku gaisa to."

Girgiza kai Umman tayi tana murmushi tace "Barta duka yaushe ta bar gidan da zanyi waya da ita Maryama.?

  "Kai Umma kenan ba kiyi k'ewar autar taki ba."Ta fad'a tana dariyar shak'iyyanci.

  "Ni da nake da Maryama a kusa dani, me zai sani k'ewar wata Muhibba?

  "Kai Umma, kenan idan nayi aure kuka zaki dingayi kina kiran Maryamata ki dawo, to kawae bara na auri Baffa kinga bara kiyi k'ewata ba."ta k'arashd maganar cike da shakiyyanci har da far fara idanu.

  Duka Umma ta kai mata tana hararanta "Tashi ki ban guri Maryama, Allah ya shiryan ku."

  Sun dad'e suna fira da umma yarda kasan Uwa da d'iya,sannan Maryaman ta tashi tama Umman bank'wana ta tafi gidan.

**

  Ruwa ta tsiyaya mashi a glass cup ta mika mashi sannan ta zauna bisa hannun kujeran tana kallonshi dauke da murmushi "Now fad'a man menene Abdallanah?

  Kallonta yayi na yan'mintuna kafin yace "Muhibba nake so ta dawo wancan d'akin." ya nuna d'akin da suka ajewa yaransu.

  Tsaye ta mike tana kallonshi "Ta dawo cikin gidannan kake nufi Abdallah? Bara ta yiyu ba gaskia."

  "Me zai hanata yiyuwa Hasna?Kawae kayanta zata d'auko kinga kenan ta yiyu." Ya fad'a tare da janyota ya daura saman cinyarshi yana shak'ar k'amshin turarenta.

  "Impossible Abdallah.!

"I will make it to be Possible Matar Abdallah." Ya fad'a dauke da dariyar dake nuna alamomi da yawa

   Harara ta watsa mashi "Wani lokacin idan kana abu kana manta waye kai Abdallah? Nan gida nane Abdallah idan ka manta ina so ka tuna."

  Murmushi yayi yana kallon cikin idonta kafin ya kai mata sumba a lips yace "Hakane gidan MATAR ABDALLAH ne ba gidan Abdallah ba kuma daga MATAR ABDALLAH har abunda ta mallaka dukkansu k'ark'ashin Abdallah suke don itace ta ga Abdallah ta k'yasa ta yarda da duk wani conditions nashi, ba Abdallah bane ya ganta ya k'yasa! kinga kuwa dole ta bi abunda Abdallah yake buk'ata, ai kin fahimci abunda nake nufi yanzu? Ya k'arashe maganar tare da bata k'yakyk'yawar sumba a wuya ya mike yana murmushi ya nufi d'akinta:

  Yana shiga d'akin ya iske Moh Bala zaune dirshan tsakar d'akin yana shan wine abunshi kamar d'akin matarshi , wani banzan kallo ya watsa mashi yana fad'in "Duk falo bai isheku iskancin ku ba har sae kun shigo d'aki.?

  Dariya Moh Bala yayi yana fadin "Sorry Abdallah na duba fridge d'in falonku babu mai sanyi shine na shigo nan na samu ko laifine a yafe man."

  "Ba laifi bane Moh Bala."Hasna ta fad'a lokacin da take shigowa d'akin tare da rungumar Abdallah ta baya ta k'wantar da kanta.

  Zamewa yayi ya d'auki towel ya fad'a toilet yayo wanka, lokacin da ya fito basu d'akin don haka ya samu damar shiryawa cikin k'ananan kaya T shirt fara sae blue din jeans ya fesa turare ya fita, a falo ya gasu Hasna na zaune busa kujera yayin da Moh Bala ke zaune saman hannun kujeran suna ta dariya abunsu.

  Yana fitowa ta sake tattausan murmushi ta mike tare da rungumeshi tana kallonshi "So cute Abdallanah."

Lumshe ya sake mata tare da sumbatar goshinta  ba tare da yace komae ba ya janye jikinshi
ya fice yana d'aga mata hannu

  BQ ya wuce ya tura k'ofar a hankali d'auke da sallama, hangota yayi k'wance tsakar falon da hijab jikinta ta dunk'ule guri guda , lumshe ido yayi ya k'arasa kusa da ita ya tsugunna yana kallon fuskarta.

  Murmushi ya saki ganin yarda ta dunk'ule guri guda tare da saka yatsanta d'aya baki tana tsotsa.

  A Hankali ya kira sunanta "Muhibba."

Dan juyi tayi ta d'aura hannunta saman cinyarshi tare da turo baki tana fad'in "Ni baran kuma yin magana dake ba Maryama sae ki fad'a man da gaske bak'ya son Abdallahna." d'an siririn hawaye ya ga sun gagaro a cikin idonta.

  Murmushi ya kuma saki tare da kai hannu ya share mata hawayen yana zagaye girar idonta da yatsanshi d'aya.

  Daukarta yayi cak ya direta bisa doguwar kujera yana murmushi mai sauti kafin ya kai hannunshi ya d'auki wayarta dake yaje gefe guda ya d'an duddu ba sannan ya aje mata kusa da ita.

  Har ya kai bakin kofa ya kuma dawowa tare da sumbatar goahinta yana fad'in "I'm so sorry Muhibba."

  Yana fita daga BQ din ya dauki mota ya wuce gidansu, sun d'an tab'a fira da Ummansu tana tambayar ya Hasna.

  "Alhamdulillah." Ya fad'a tare da cigaba da fad'in "Umma munje asibiti game da matsalar rashin haihuwarta an bamu magunguna sosae kuma insha Allahu za'a dace don jiya mun koma likitan yace ko da yaushe zata iya samun haihuwa."

  Washe baki Umman tayi tana fad'in "Alhamdulillah Abdallah, gaskia nayi farinciki sosae Allah yaa k'ara lafiya ya albarkace ku da zuri'a ta gari."

  "Ameen Umma."

  "To ko zakaje da Aisha ta dinga taimaka mata da abubuwa davl yawa tunda kaga ba komae zaka sa yan aiki su maka ba, amma idan Aisha ce zata mata komae."

Dan murmyshi yayi yace "A'a Umma ai ta ma samu wata yar' budurwa da zata dinga taimaka mata da komae."

  "Kana ganin zata mata komae ba matsala Abdallah.? ta fad'a cikin kulawa

Murmushi yayi yace "Ba wata matsala Umma don yarinyar na da hankali sosae."

Sun dan dad'e suna fura da Umman sannan ya mik'e ya mata sallama tare da aje mata dubu biyar suyi cefane, daga nan Unguwar su Muhibba ya wuce yayin da yayi parking dai dai k'ofar gidansu Maryama ya fito tare da kiran Number Maryama'

  Ringing d'aya ta d'auka tana fad'in "Assalamu Alaikum, sunana Maryama da wa nake magana.?

  Dariya yayi mai sauti kafin yace "Meye na sauri Maryama? ki fito gani a bakin gidanku."

Bai jira abunda zata ce ba ya yanke wayarshi, ita kam Maryama har ga Allah bata dauki muryar Abdallah ba ta dad'e tana bala'in "Don rainin wayau kawae sae a kira mutun ace ya fito kamar wani ya ajeka."

Mamanta ta kalleta tare da girgiza kai tace "Komae naki,l na bala'i ne Maryama, yanzu meye laifi don anzo wajenki?

Turo baki tayi tana fad'in "Amma ai tun kafin sati idan mutun zai zo ya kamata ya fad'a maka ba sae yazo ba amma wallahi idan naje naga ba dai dae ba sae na ya gawa mutun rigar mutunci."

  Mikewa tayi tana bala'i tare da d'aukar hijabi ta fita "Kam bala'in nan me ya kawo Abdallah gurina? ta fad'a tare da d'aure fuska ta rik'e kugu ta isa gabanshi tana girgije girgije

  "In jin lafiya ka kirani.? Ta fad'a tana harare harare

Lallausan murmushi ya sakar mata yana fad'in "Ko sallama bara ki ma Abdallah ba Maryama."

  Harara ta balla mashi tana fad'in "Yinta ba dole bane amsata kadae na dole Abdallah, kai ni wallahi haushinka nake ji Abdallah don da za'a bani bindiga babu abunda zai hanani bingigeka wallahi."

  Yar siriyar sariya ya sake yana fad'in "Na san da haka shi yasa k'awarki tace nazo na baki hakuri tukun."

  "Tace kazo koko gulmarka ta kawoka Abdallah? Fad'a man me kazo yi gidanmu? ta fad'a har lokacin bata daina harare hararenta ba

  Hannunshi ya had'e cikin aljuhu yana jefa mata wani mayen kallon sannan yace "Afuwa nazo nema gurin Maryamarmu."

  "Idan gulma ma ta kawoka kaji da ita Abdallah." Ta fad'a tana hararanshi
 
  "Ko daya, ni dae hakuri nazo,l  na baki akan abunda ya faru jiya, don Allah kiyi hakuri nasan nayi laifi."

  Kallonshi tayi ta d'an saki ranta tace "Ita Muhibbar ka bata hak'urin?

  Ware ido yayi yana kallonta "Me zai hana na bata hakuri Maryama?kawae tace bara ta hak'ura ba sae idan ke kin hak'ura."

  Dan sanyi taji a ranta don irin mutanan nan ce masu masifa da saurin sauka lokaci guda a hankali tace "Duk da baka k'yauta ba amma ba komae kace mata na hak'ura, amma dan Allah Abdallah karka cutar da ita kaga yarinya ce sosai ."

Murmushi ya mata tare da fiddo da wayarshi ya d'an duba wani abu kafin ya mayar da ita Aljihu yana fad'in "Nagode Maryama ni zan tafi idan naje gidan kiraki sae kiyi magana da Muhibban kiji yarda mukayi da ita."

  "Bakomae nagode a gayar man da ita"Da haka ta juya ta shige gida abunta..

#Feedohm💧💧 *MATAR ABDALLAH.!*💥
                   True Life Story.!
                              💥
*©HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers
*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
   *Wattpad:Feedohm*
*11*
     Cikin k'wana d'aya aka gama k'washe man kayana aka mayar dasu cikin gidan, k'ofar d'akina da aka bani tana kallon dining area kuma shiga ciki da falone sae toilet a ciki sae dae daga ganin tsarin d'akin kasan na yarane tunda a bangon d'akin anyi zanen yan cartoon.
   Har ga Allah banso hakan ba don bana bukatar zama cikinsu, maganar Abdallah kam na tattarata na watsar sae dae soyayyarsa dake addabar zuciyata haka kuma na kasa yarda da kalamansa na don na haihu ya auro ni gani nake aikin asirine ko kuma don ya muzguna man yasa shi fad'in haka, don haka maganar na nan daram a zuciyata, kuma ko ma hakan ne a ranshi ni bana da gurin barinshi har abada domin wata irin kauna nake masa mai tsanani wadda har zuciyata bata iya hango laifinshi sae ta samu abun kareshi..
Tunda na dawo sam bansa Abdallah ko matarshi cikin idona ba sae dae kullun safiya wata yarinya zata kawo man abinci da abunsha haka rana da dare.
  Cikin kwana biyu na rame sae dan hasken da nayi wanda nasan shima na wahalane.
  Kad'aici ya isheni na kira number Maryama don tunda ta tafi bamuyi waya da ita ba kullun na kirata wayar batta shiga bansan dalili ba, yau kam nayi sa'a ta shiga sae dae har ta gama ringing bata dauka ba don haka na mike na shiga towel don dauro alwalar magrib..
  Fitowa daga toilet nayi ina yarfe hannuna tare da goge fuskana, Jin k'arar motar Abdallah yasa nayi saurin matsawa jikin window ina kallonshi.
Gabana yayi mummunar fad'uwa ganin hannunsa sargahe dana Matarsa, a hankali na juyar da kaina gefe guda tare da barin gurin a sanyaye na dauki abun sallah na shinfida sae dae har ga Allah zuciyata tuk'uk'i take.
  K'amshin turarensa  ya tabbatar man da ya kusa dani, ina tsaye na kasa kabbara sallah na juya a hankali ina kallon baya na sae dae sam babu Abdallah babu dalilinshi, wasu hawaye masu dan karan zafi suka zubo na saka gefen hijab d'ina na goge, tabbas da nasan haka ake aure da wallahi da banyi sha'awar yinsa ba baki d'aya, sae dae ban sani ba ko dan banyi sa;ar miji bane.
  Muryar Abdallah naji a bakin k'ofa yana fad'in "Yan matana."
Ban juya ba don zato nake ko zuciyata ce ke yaudarata don haka na mike a sulale na sanya hijab d'i  jikina tare da duk'awa zan gyara abun sallah
Hannu naji a bayana nayi saurin d'agowa a firgice. Lumshe ido nayi ganin Abdallah ne yayin da zuciyata ta d'anyi fari.
  "Shine kika man shiru ina magana ko? ya fad'a cikin sanyin murya.
Juyawa nayi na nufi bakin kujera ina k'ok'arin d'aukar dank'walina ina fad'in "Ban san kai bane."
  K'arbe d'an k'walin yayi ya ja hannuna har gurin kujera ya zauna sannan ya zaunar dani gefenshi hannunshi cikin nawa yace "Har yanzu fushi kike dani ko Muhibba? ko baki iya tarbar miji bane? ba d'an hug bare kiss ko?
  Girgiza kai nayi a hankali idona cike da k'wallah "Wane irin hali Abdallah ke gareshi?Shin wulakancine koko tsabar duniyanci ne? taya ma zai tambayeni Hug da kiss bayan duk wulak'ancin da ya man k'wanaki? ko dae ya manta ne?
  Dago kaina yayi ya rike da hannunsa yana fad'in "Wae menene kike ta faman daurewa? kinga Abdallah bayya fushi dama kin saki ranki domin ko wani ke fushi Abdallah bai cika ganewa ba."
  A Hankali na mike yayi saurin maidoni yana kallona, cikin sanyin murya nace "Sallah zanyi Ya Abdallah."
  Shiru yayi don shi kanshi baiyi sallan ba, yayin da na mike na nufi abun sallah, har zan kabbara na juyo a raunane ina kallonshi "Kai kayi Sallan ne Ya Abdallah?
Girgiza kai yayi yana mugun murmushinshi, wanda har lokacin na kasa fassara wannan murmushin
  "Kazo muyi mana tare sae kama jam'i."Na fad'a a sanyaye
  Girgiza kai ya ku ma har lokacin fuskarshi d'auke da murmushi "Kiyi abunki ni banayi." ya fad'a kai tsaye
  Cikin mamaki nace "Meyasa?
  Babu kunya yace "Banyi niyya bane, sae zuwa anjima idan nayi niyya nayi karki damu kinji ko? ke dae kiyi abunki yar gidan liman."
  K'walla ya cika man ido yayin da tausayinshi ya d'arsu a zuciya, muryata na rawa nace "Dama sae anyi niyya ake sallah ya Abdallah inji Farillah ce.?
  Murmushi yayi mai sauti sannan yace "Komai ai saida niyya MATAR ABDALLAH."
Lumshe ido nayi a hankali tare da kabbara sallah sae dae har ga Allah yin sallah kawae nake amma wani sashe na zuciyata cike yake da tunanin wace irin rayuwa ake a gidan Abdallah, in kuwa haka ne ya zamar man dole na d'aurashi hanyar gaskia ko da kuwa zan gamu da wulakanshi da tozarci a rayuwata.
  Ina gama sallah na koma bisa kujera na zauna yayin da idona ke zubar da k'wallah wanda yanzu sun zame man jiki ko da yaushe cikin kuka nake, ringing d'in wayarshi naji a kusa dani na kai dubana ina kallon wayar don ni sam ban ma lura da ita ba.
  Gabana yayi mummunar fad'uwa ganin tank'amemen hoton Maryama tana murmushi a bisa screen d'inshi yayin da sunan MARYAMATA ke yawo a sama, Ido na fiddo sosai ina kallon number tabbas babu tantama Maryama ke kiran Abdallah
  Ya Allah."Na furta yayin da bugun zuciyata ya tsananta kafin lokacin hawaye sun gama wanke man fuska.
  Maganganun Abdallah suka fara dawo man a zuciya, tabbas indae hakane Maryama ta cuceni, ta ci amanata,  ta ci amanar taren mu, taya ma za'ai Maryama taso Abdallah bayan ta fi kowa sanin irin son da nake mashi..
  Ban san zuwan Abdallah ba sae dae hannunshi da na gani ya d'auki wayar yana fad'in "Oh maryamata har 2missed call kuma? am sorry,,lemme call her Allah yasa bata ji haushi ba."
  A razane na d;ago ina kallonshi da rinannun idanuna yayin da ya zauna bisa hannun kujeran da nake yana kiran Maryama ya saka speaker har ina iya jiyo wayar na ringing.
Ringing d'aya ta dauka had'e da sallama "Assalamu,Alaikum Abdallah, Barka da dare"
Murmushi yayi ba tare da ya kalleni ba yace "Ameen wassalama Maryama, Kin kira ko? kiyi hakuri bana kusa ne kinji ko.?
Dariya tayi tace "Kai Abdallah ba fa wani abu zance kayi ba meye na saurin bada hakuri."
  Shima murmushin yayi yana fad'in "Nasan halin Maryamata da saurin fushi kinsan ni kuma yanzu lallab'aki nake."
  Cire Speaker d'in yayi ya juyo yana kallona muka had'a ido har lokacin k'wallah ke gudu a fuskana tabbas Maryamata ce ko tantama bannayi akan itace domin ko a mafarki baran tab'a manta muryar Maryama ba.
  Ita kam Maryama jin abunda yace tayi wani banbara k'wai ta tab'e baki tana fad'in "Kai dai ka sani Abdallah, yanzu kana ina ne? idan kana gida ka bani Muhibbar na kira wayarta a kashe."
  A hankali yace "Ina gida mana Maryama, Kizo mana."
  "Nazo nayi me Abdallah? ni dae Dan Allah ka bani ita."Ta fad'a cikin k'osawa da zancensa
  Kai tsaye yace "ki ganni mana Maryamata ko bara ki ji dad'i ba."
Dan karamin tsaki ta sake tana fad'in "Shin zaka ban itane koko na yanke wayata? kasan dae ba kud'in banza na saka ba bare na tsaya fira da kai."
  "Karki damu bata kusa dani."Ya kuma fad'a harda sumbatar wayar
  Yanke wayar tayi tana fad'in "Dan iska kawae ko uwar wa yake sumbata kuma."
  Ko a jikin Abdallah duk da yasan ta katse ya cigaba da fad'in "No karki man na fi son gani gaki ki naji tattausan lab'b'anki saman fuskana"
  Shiru yayi sannan ya cigaba da fad'in "Kinga Pearl ko kinyi a nan idan na zo sae kin rama man abuna."
  A rud'e na fizge wayar tare da tandarata a k'asa ina wani irin tuk'uk'in kuka, Kamar mahaukaciya na bi wayar na tattake ina fad'in "Me yasa kike son mijina Maryama? Me yasa dan Allah bayan kinsan ni baran iya maki haka ba Maryama, shin bakiyi tunanin ni bazan tab'a so maki miji bane? Haba Maryama me yasa zaki man haka?Inna lillahi wa jnna ilaihir raju'un, Wannan wace irin Jarabta ce.?
Da murmushi a fuskarshi ya kalleni tare da kallon wayar yana fad'in "Shine zaki yar man da waya ko Muhibba? to ma fad'a man meye laifin wayar a ciki ko itane ta sumbaceni ba Maryamarki ba."
  Wani lafiyayyen mari na sakar mashi ina kallon cikin idanunshi "Ab...
  Hannunshi ya daura saman bakina da murmushi a fuskarshi yace "Karki kirana sunana har sae na fanshe wannan marin MATAR ABDALLAH, sannan sae ki daura daga inda kika tsaya."
  Kafin na bashi amsa ya daukeni cak tare da jefawa saman gado...
Ganin yana niyar fitar man da sutura yasa na kuma rud'ewa ina kuka tare da fad'in "Ka daena Banna so Abdallah, banna so nace ."
  Bai saurareni ba don kamar k'ara tunzurashi nake ya fara murzar jikina cikin k'eta da mugunta.
  Ihu nake tare da kiran sunan Allah ina rok'anshi ya saurara man amma sam bai san abunda nake ba har sae da ya rabani da budurcina ta k'arfi da yaji sannan ya d'ago yana kallona da rinannun idanunshi yana murmushi "Kin had'u Larindo, kinga inda rabo zuwa nan da wata tara kin juye sae kuma a k'ara gaba."Ya fad'a har da tofar da yawu gefe..
  Kuka na saki da k'arfi yayin da azaba ke dandak'ata nace "Allah ya isa Abdallah, wallahi bazan taba yafe maka ba a rayuwa, ka cuceni ka zalunceni sae Allah ya saka man, tsinannen la'annan Allah."
Dariya yayi ya mik'e tare da fizgar towel d'ina yana fad'in "Kinji nace ki yafe man Muhibba?
  Kuka na cigaba dayi da karfi ina matse cinyoyina ji nake kamar ana saka man barkono a jikina sunan Ummana na fara kira ina kuka sannan na cigaba da fad'in "Allah ya isa tsinannen insha Allah sae Allah ya man sakayya tun a duniya, mugu."
  Tattausan murmushi ya sake lokacin da yake daura towel a k'ugunshi yana fad'in "Ki dinga jam'i Matar Abdallah, tsinannu, la'anannun Allah kuma mugaye, karki damu ni kam na yafe maki tuni don baki kai na rik'eki a rai ba bare a zuciyata."
  Har ya juya ya kuma juyowa tare da jefa man wani irin mahaukacin kallo yana fad'in"Matar Abdallah ki taimaka ki wanke Abdallahn ki yau mana."
  Turo kofar da akayi ana fad'in "Wae me kake haka ne Abdallah? ko wari ma baka ji ya isheka? ka fito ka ci abinci mana ko...."
  Maganar ta mak'ale tana binshi da kallon lokaci guda ta juyo tana kallona tare da kallon Abdallah.
#Feedohm💧💧 *MATAR ABDALLAH.!*💥
                   True Life Story.!

                              💥

*©HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
   *Wattpad:Feedohm*

*12*

 
  Kallona take tare da kallonshi lokaci guda tana so ta gasgata abunda take zargi. A rud'e ta mayar da kallonta gareshi tare da nunoni tana fad'in "Na shiga ku me ka mata Abdallah?

  Dan murmushi ya saki yana fad'in "Dama na biya sadaki don tazo taci abinci ne kawae Matar Abdallah?Abunda nake maki shi na mata itama."

   Wani irin ihu ta saki yayin da ta nufoni a guje bata yi wata wata ba ta haye bisa gadon tare da haye ni tana duka kamar wata zautacciya, ni kam banyi tunanin rama wa ba bare na kare dukan nata illa wasu mahaukatan hawaye suka cigaba da sintiri saman fuskana domin har ga Allah abunda Abdallah ya man ya fi nata ciwo da k'una..

  Fitilar glass d'in dake gefen gadonta ta raruma tana fad'in "Wallahi sae na kasheki sae na kashe duk wanda ta yarda yayi alak'a da Abdallanah bazan tab'a yarda wani ya shiga tsanani da Abdallanah ba."

Rumtse ido nayi gam ina jiran mutuwa ta don zata fi man sauk'i akan halin da nake ciki, Shirun da naji yayi yawa ne yasa na bud'e idona na sauke a kansu.

    Abdallah naga ya dauke matarshi daga jikina cak  ya bar d'akin da ita kamar wata jaririya..

   Nikam komawa nayi ina kwanta tare da cigaba da kukana, ganin kukan bara ya man ba yasa na mike da k'yar na shige toilet..

  Da k'yar na gyara jikina sannan na dawo nayi zaman dirshan ina fitar da wasu masifa tattun hawaye, ina jin wayata na ringing amma ko gurin ban kalla ba bare nayi tunanin d'auka don bana jin zan iya magana cikin halin da nake ciki yanzu.
 

  A bangaren Abdallah bai sauketa ko'ina ba sae tsakiyar master bedroom d'insu k'irjinsa ta daka a haukace take fad'in "Why Abdallah? Abdallah Why."

  Banza ya mata tare da turata bisa kujera yaje ya sakawa d'akin keys sannan ya shige toilet abunshi ya dad'e cikin sannan ya fito daure da towel kamar mahaukaciya ta sha gabanshi tare da sakin mahaukacin kuka tana fad'in "Me yasa Abdallah?

Murmushi ya saki yace "Banyi broken conditions d'inki ba da gangan Matar Abdallah, asali ma banna da feelings a kan Larindo, She just slap my preety face kuma kinsan Abdallah bayya dukan mace that was the only purnishment da zan iya bata kiyi Hakuri."

  Bata daina kukanta ba don har ga Allah tana tsananin kishin Abdallah, matsowa yayi sosae kusa da ita tare da had'e fuskarshi da tata yana kissing duk inda ya san hannunshi ya tab'a a fuskarta

Ni kam yarda naga rana haka naga daren ranar yayin da ya zame man bak'in dare a rayuwata.

  "Dama wannan daren Abdallah ya man alk'awali? babu ko tantama baran tab'a manta wannan daren ba a rayuwata kamar yarda ya fad'a."

  Ban bar gurin ba har sae da naji kiran sallah ta asuba sannan na mike a sanyaye na shige toilet na sake wanka na dauro alwala ina fitowa na iske Abdallah tsaye bakin k'ofar d'akin daga shi sae jallabiya, d'auke kai nayi na taka a hankali na isa inda abun sallah ya ke na shinfid'a

  Fuskarshi dauke da murmushi yace "Baki iya gaisuwa ba ko Muhibba.?

Idan abun sallan ya amsa to nima na amsawa Abdallah, takowa yayi ya tsaya bayana sannan ya saka dukkanin hannunshi ya juyo dani yana kallon fuskana tare da sumbatar lab'b'ana "Kuka yana bala'in k'ara maki k'yau Muhibbatah, dan Allah duk lokacin da zakiyi kuka ki taimaka ki kirani don ba k'aramin sani nishad'i yake ba."

  Juyar da kaina nayi cike da takaicinsa shin wane irin mutun ne Abdallah?Anya ma kuwa yana da imani a zuciyarshi? taya zai kalleni yace kukana nishad;i yake sakashi? wato bai da damuwa a duk yanayin da nake ciki?

  Aljihun jallabiyar shi ya laluba ya fiddo da takarda tare da kama hannuna ya saka a ciki yana fad'in "Kinsan dai kece da miji yau ko? so ga bill d'in abincin MATAR ABDALLAH dan Allah kiyi sauri ki had'a komae zuwa k'arfe tak'was zamu fita."

  Wasu hawayen suka fara sintiri a fuskana yayin da ya sakar man tattausan murmushi ya fice daga d'akin

   "Ya Rabbi."na fad'a tare da bin bayanshi da kallon sannan na lumshe idona cike da tausayin kaina.

  Na dad'e ina tsaye kamar gunki kafin na kabbara sallah, ina sallamewa na janyo wayata  na duba naga missed call din maryama kusan 18. sae d'an k'aramin text da ta turo man " _Muhibba kina lafiya kuwa baki d'aukar wayarki? karki damu anjima zan shigo kin ji ko?_ "

  A Hankali na girgiza kai wani zazzafan kishi na neman hargitsa man k'wak'walwa

   "You broke my truth Maryama." Na fad'a had'e da share k'wallana na jefar da wayar saman gado yayin da na zame saman abun sallah.

  "I don't want you Maryama, You broke my truth,Me yasa ne Maryama? shin babu wani d'a namiji sae wanda nake so ne? Haba Maryama "Na fad'a hawaye na bin kumatuna

  "I hate you Maryama."

Na dad'e ina kuka tare da surutai sannan nayi lamo kamar mai bacci, sam banyi tunanin fita daga d'akin ba bare har naje na girka masu abinci, ina kwance a nan kusan karfe 7 da rabi aka turo k'ofar da karfin tsiya, ban juya ba don nasan bara ya wuce Abdallah ba

  "Wane iskanci ya hanaki fita ki had'a mana breakfast har yanzu? ko kina nufin ba ki iya girki bane? Muryar Hasna ta daki dodon kunnena

  Ko alamun naji me take fad'a banyi ba na gyara kwanciyarta yadda baran hangota ba.

  A harzuk'e ta matso kusa dani tare da sa kafarta ta hakadani tana fad'in "Dan iskanci ma bacci kike ko? Gidan uba an saba da wahala ,wato an shigo gidan hutu bara a huta ko? to wallahi ke da ki huta sae dae in kin bar nan gidan ."

  Tashi nayi zaune ina kallonta don har ga Allah zan iya hakuri da Abdallah saboda ina k'aunarshi amma bazan iya hakuri da MATAR ABDALLAH ba ita kanta da ta san halin Muhibba da batayi tunanin shiga harkata ba domin hak'urina kawae ga Abdallah yake shi kad'ae zan iya d'aukar duk wani wulak'anci da cin mutuncinsa..

  Ta kuma harzuk'a tana kallona "Wae bak'ya jin ana maki magana ne? koko kurma ce ke? Ki tashi ki je ki had'a man break fast tun kafin na wulak'anta ki."

  Dan murmushin takaici na sake tare da mik'ewa tsaye ina girgiza kai, har ga Allah bana so ta kaimu inda batayi zato ba.

  Ko a tunaninta mik'ewar da nayi breakfast d'in zan had'a mata ? sae cewa tayi "Sinasir nake so da green soup sae kunun gyad'a da farfesun yan ciki."

"Kan ubancan to ai ko baiwar Ubanki ce bazan maki abunda kika lissafa ba Matar Abdallah." Na fad'a ba yabo ba fallasa

  "What?How dare you." Ta fad'a cikin tsawa

  Ganin na haye gado yasa ta fita da sauri tana maganganu k'asa k'asa, mintina kad'an sae gasu sun dawo da Abdallah da alama ma bacci yake ta tadoshi, sam ban tashidaga gadon ba sae ma gyara kwanciya da nayi abuna ya matso har kusa da gadon kamar kullun fuskarshi d'auke da murmushi yana fad'in "Me na fad'a maki d'azu Muhibba? Me yasa bara ki mata biyayya bane?

  Banza na mashi na matsar da k'afana gefe guda, zama yayi gefen gadon yana kallon k'irjina a hankali ya kai hannu da niyar tab'awa sae kuma ya janye ya shafi wuyana.

  "Zazzabi ke ki ne Muhibba? Ya fad'a jin jikina da d'umi

Nikam lumshe ido nayi don nasan lafiyata lau haka yanayin jikina yake.

  "Tashi ki je ki had'a mana breakfast Muhibba."Ya sake fad'a ba yabo ba fallasa

  Mik'ewa nayi a sanyaye don bana jin yana daga cikin halin k'warae yin gardama da mijinka ko mai ko munin halinsa, har na kai bakin k'ofa na jiyo muryana na rawa nace "Ai bansan kitchen d'in ba."

  Murmushi naga yayi ba tare da ya kalli Hasna ba ya mik'e ya nufoni tare da jan hannuna muka fita, bai sake ni ko ina ba sae cikin kitchen d'insu sannan ya bud'e wata k'aramar k'ofa yana fad'in "Duk abunda zaki buk'ata yana a nan ciki, kiyi sauri ki gama tun kafin tayi fushi dake."

  Bak'in ciki yasa na saki kuka ina fad'in "Idan tayi fushi dani sai menene ya Abdallah? kaga wallahi ba dan ita zanyi girkin ba."

  Murmushi yayi mai sauti yana fad'in "To dan wa zakiyi Larindo?

  Lumshe ido nayi nace "Saboda darajar aurena."

  K'yak'yk'yawan murmushi ya saki ya matso kusa dani cikin kunnena yace "Naji dad'i da kika san darajar aurenki Muhibba! and I'm so thankful to Baffa da ya baki ilmin marin mijinki kuma."

  Da sauri na kalleshi tare da ja baya haka shima baya ya ja ya ware hannayenshi yana murmushi tare da kanne man ido daya yace "Ko zaki ce man bashi ne ya baki wannan ilmin ba? to ko dae Maryamata ta ce.?

  Kuka na saki da k'arfi ina fad'in "Baffana bai bani mummunar tarbiyya ba Abdallah."

   " To Maryama ce? ya kuma tambaya yana murmushi

  A hankali na juya mashi baya ina goge hawayena don tabbas indae zaka cigaba da biyewa zancen Abdallah babu abunda zai hana zuciyarka fitowa.

  Kunun gyad'a na masu sae doyar dana soya da miyar k'wae sannan na shiga d'akina na fito da sababbin coolers na zuba a ciki sannan na kai dining area na aje na koma d'akin na k'wanta abuna

  Cikin bacci naji kamar ana jan k'afata na bud'e ido a hargitse ina kallonshi yayi wanka cikin manyan kaya sae kamshi yake zabgawa, ya sakar man murmushi yana fad'in "Kin had'a breakfast kuma kin tafi baki tsaya kin ci ba."

  Mayar da kaina nayi na kwantar babu yabo ba fallasa nace "Na k'oshine."

  Murmushi ya saki mai sauti yace "Ko dae kin barbad'a wani abu a cikine Larindo?Fad'a man ba wanda zaiji."

  Kalmar Larindo ni kam ta fara isata na d'aure na girgiza kai cike da takaicin shi..

  "To meyasa bara ki ci ba."

  Tambayarta ta fara isa ta don haka nace "Azumi nake ai."

  Ware ido yayi yace "Azumin me? kin sha Ramadan ne?Huh fad'a man a farko watan ko tsakiya ko k'arshe kika fara menstruation a lokacin.?

  Banza na mashi na kawar da kai gefe guda ni kam na rasa wane irin mutun ne Abdallah.

  Tallabo fuskana yayi ya had'e da nashi yana fadin "Wae nikam Larindo har nawa zaki rama ne? na san dae bai wuce biyar ba ko.?

  Kuka na saki na mike na fice daga d'akin da sauri naje dining area na dauki cup na zubo kunun gyad'ar sannan na dawo na iske shi yana nan inda na barshi hannunshi cikin aljuhunsa.

  Murmushi ya saki ganin na kafa cup din ina shan kunun sannan ya fice daga d'akin ya barni cike da takaicinsa.



#Feedohm💧💧 *MATAR ABDALLAH.!*💥
                   True Life Story.!

                              💥

*©HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
   *Wattpad:Feedohm*

        # *Ina rabaku da SO ke/kai dae kayi addu'a kar Allah ya jarabceka da SON wani/wata*

*13*

  ***

   *Wata Uku..*

   Haka rayuwa ke tafiya babu yabo ba fallasa a gidan Abdallah, yayin da duk wani aiki da wahala suka tattara suka koma a kaina, a lokacin ne harta yar' aikin gidan sae da MATAR ABDALLAH ta kora wae a cewarta gidan ya cika..

  Abdallah kam sae na sharari sati ban sanya shi a idona ba, lokaci guda na rame nayi haske kamar bani ba, haka babu abunda ya k'ara shiga tsakanina da Abdallah.

  Maryama kam tayi kira na har ta gaji amma sam nak'i d'aga wayarta daga baya ma a cikin blacklist,

  Da ta fahimci nayi blocking kiranta ranta ya b'aci sosae abunka da mai zuciya sae  ta kasa daurewa yayin da ta turo man text tana fad'in "Kina nufin kinfi K'arfina yanzu ko Muhibba? Ko baki fad'i ba na fahimce ki tunda gashi Maryama na kiraki dan iskanci  bak'ya d'auka? to ko gwamna kike aure baki isa ki wulakanta ni ba kuma insha Allahu daga yau ba zaki k'ara ganin kiran Maryama ba balle kiyi tunanin ganin k'afar Maryama gidanki."

  Ko da naga text d'in shareta nayi naci gaba da harkar gaba ni don  hakam ma dad'i ma hakan ya man don na rabu da ita cikin sauki ba tare da b'acin rai ba..

   Daga baya ne na kira Ummana shine take fad'a man cewa  wae Maryama ta tafi k'asar Cairo karatu "Allah ya taimaka" Kawae nace tare da kawar da zancen Maryama

    Sae dae nayi mamaki da naji Maryama bata fad'awa Ummana abunda ke faruwa tsakanin mu ba ko da yake nasan duk sab'anin da muke samu da Maryama bata yarda ta fad'awa wani ba to wae ma da wane ido zata kalli Ummana ta fad'a mata cewa saboda tana son Abdallah na sab'a da ita...

  Kuskure na d'aya dana aikata shine na k'asa fad'a wa kowa halin da nake ciki a gidan Abdallah, ciki kuwa har da Ummana wadda ya kamata ace ta kasance abokiyar shawarata.

  Yau kam Alkubus na dafa da miyar agushi, tun da na fara girka miyar naji sam bana buk'atar k'amshin da miyar ke yi, da k'yar na k'arasa ta, sannan na jera komae bisa dining table na koma kitchen domin d'auko coconut drink da nayi.

  Ina ajewa naji k'amshin turaren Abdallah a bayana, a hankali na juya ina kallonshi don nayi bala'in kewarsa, k'amshin turarensa ya dake ni sosai, na toshe hancina da sauri ina k'ok'arin kewaye shi wuce...

Janyo hannuna yayi ya dawo dani  gabanshi yana k'are man kallo sama da k'asa"Fad'a man gaskiya baki yi kewar Abdallanki ba tsawon wata d'aya ba ki ganshi ba? kuma ko ki nemeshi ko.?ya fad'a d'auke da tattausan murmushi yana leken fuskata.

  Gumtse bakina nayi da hannu ganin amai na niyar taso mani tare da ina girgiza mashi kai a hankali ina kallon shi k'asa k'asa da idona da ya kad'a yayi jawur..

  Tattausan murmushi ya kuma saki tare da janyo ni jikinshi ya matse sosae yana kallona, lokaci guda zufa ta fara keto man, na fara k'ok'arin ture shi amma sam yak'i sake ni sae murmushi ya ke abunshi.

  Da k'yar na bud'e bakina dake cike da yawu nace "Ya Abdallah ka sake ni dan girman."

  Murmushi ya kuma saki ba tare da yace komae ba ya saka hannunshi d'aya ya bud'e cooler dake bisa dinning d'in ya kai hannu ya gutsuro alkubus d'in ya kai bakinshi yana lumshe ido

Cikin kunne na ya rad'a man "Like mother like son, banbancin ke mutun ne shi kuma flour ne amma ko?It's so delicious."

  Kafin nayi wani yunk'uri na shek'e da wani irin amai kamar yan' cika zasu fito waje, a tunani na zai ture ni daga jikinshi amma sae na samu akasin haka yayin da ya k'ara matse ni jikinsa sosae ya zauna bisa kujeran yana kallona..

  "Sannu ko? ya fad'a k'asan mak'oshi..

   A hankali na d'ago ina kallonshi muka had'a ido yayin da yake cin alkubus dinshi hankali kwance kamar ba amai nayi a jikinsa ba haka kuma bara kayi tunanin shine ya man magana ba.

  A sanyaye nace "Kayi hakuri."

  Tattausan murmushi ya saki yana fad'in "Dama bak'ya lafiya ne?

  A Hankali na girgiza kai ina k'ok'arin mik'ewa sae dae jikina a sanyaye yake ko tsayuwar kirki bazan iya ba, komawa nayi na k'wanatar da kaina a k'irjin shi yayin da zuciyata ke cigaba da tashi.

   Kallona yayi ya sakar man murmushi sannan ya rufe cooler abincin ya ture tare da d'aukata cak ya nufi d'aki dani, Ni kam kallo nake binshi dashi har ya dire ni da k'arfin tsakar dakin.

  Bayana ya d'an bugu sosae na saki yar' k'ara ina kallonshi a raunane..

   Murmushi ya saki yace "Da zafi ne?

  A hankali na gyad'a kai har lokacin ina kallonshi.

  Duk'owa yayi ya lakuce man hanci yana kallo na k'asa k'asa sannan yace "Haka naji zafi lokacin da kika man amai a jiki."

  Murmushi ya kuma saki yana fad'in "Kinsan me nafi tsana.?

  Still girgiza kai nayi tare da mayar da kaina k'asa ina k'ok'arin mayar da hawayen dake niyyar zubo man.

  "Na tsani amai Larindo." Ya fad'a dauke da murmushi

  Da sauri na kalleshi cikin sanyin murya nace "Kayi hakuri ba laifina bane."

  Murmushi ya kuma saki yana fad'in "Amma banda naki ai Muhibba.?

  Kai tsaye wani sashe na zuciyata yace "K'arya kake Abdallah." yayin da na kalle shi da sauri ya gyad'a man kai tare da sake man murmushi

  "Karki zurfafa tunanin a cikin lamarin Abdallah, ki tashi kije ki gyara jikinshi zan kira likita ta duba man ke don nasan ba'a amae haka kawae sae da dalili shi yasa ma kika ji nace ban tsani aman ki ba don bana so kiyi tunanin soyayya ta saka.."

  Mik'ewa yayi ya bud'e man toilet sannan ya fice daga d'akin, Nikam lumshe ido nayi na bi bayanshi da kallo har ga Allah ina son Abdallah haka babu abunda nake tunanin zai rage man sonshi a zuciyata.

  A Hankali na tashi na shiga toilet d'in na gyara jikina na dawo na zauna bakin gado sae sak'a nake ina warwarewa..

  Muryar Hasna naji a bakin k'ofa tana fad'in "To amma dole ta fito ta gyara inda ta b'ata ko Pearl?

  "Kar ki damu Matar Abdallah zan gyara."Naji ya fad'a cikin sanyin murya

  "Kai kuma? a'a gaskia bara ta yiyu ba, ta dai fito ta gyara tunda ba wani ya mata ba."

  "Shin nace ki gyara ne? Ya fad'a yana murmushi

  "Amma taya wata zata yi amai kai ka gyara Abdallah, frankly..

Daga mata hannu yayi yana kallonta da tattausan murmushi a fuskarshi, a hankali yace "Enough Hasna mu shiga please."

  Turo d'akin a kayi suka shigo su uku ne da wata bak'uwa wadda alamu sun nuna malamar asibiti ce,

    Tab'e baki Hasna tayi ganin Abdallah ya nufo kusa dani yana fad'in "Bismillah Madam, Allah yasa hasashe na ya zama gaskia."

  Zuwa tayi ta duddubani sannan ta juya tana kallon Abdallah da murmushi tace "Da alama fa Abdallah kamar amaryar taka ta kusa zama Mama."

  Da sauri muka kalleshi baki d'aya yayin da ya dawo da kallonshi gareni tare da kafeni da ido..

  Muryar Hasna naji tana fad'in "Sae ki kawo man maganin da zan fara amfani dashi ko."

   Kallon ta nayi tare da tunanin shi ko itama batta lafiyane? Saukar lallausan hannun Abdallah naji saman nawa, ido na na bi hannun ina kallonsa yayin da na lumshe idona, tausayin kaina da tausayin abunda ke jikina ya kamani lokaci guda! shin ya zaya tashi a gidan Abdallah?shin zai zama kamar nice mara yan'ci da galihu? koko Abdallah zai so shi? Wasu zafafan hawaye suka silalo fuskana ..

   Ji nayi Abdallah ya rungumo ni jikinsa sosae tare da zagayeni da hannunshi duka biyu, ina jin lokacin da Hasna ta saki tsaki ta ja hannun Malamar asibitin suka fita.

  A Hankali yace "Nagode Muhibba."

  K'amshin ya kuma dakar man hanci naji wani sabon aman na shirin fitowa, da k'arfi na tureshi jikina na fara k'warara aman a tsakar dakin

  Wani irin kallo ya bini dashi kamar kullun fuskarshi d'auke da murmushi sae dae wannan karon murmushin ya banbanta dana kullun..

  "Sannu."

  Duk'ewa nayi ina rike da cikina tsawon mintina, jin shirun yayi yawa yasa na d'ago a wahale ina kallonshi, shima kallo na yake, mayar da kaina nayi saman cinyata na tsawon yan' mintina sannan na mik'e a hankali

  Cikin sauri ya mike tsaye ya zagayo da hannunshi saman kafad'ata tare da rik'o dayan hannun cikin nasa, a hankali ya rik'eni sosae ya nufi hanyar toilet dani, a bakin k'ofar ya tsaya ya sake ni yana fad'in "Sannu kin ji ko? bara naje na wanke jikina  nima dan Allah ki kula sosai kin ji ko.?

  Kallonshi nake cike da mamakin shi, kallonshi da murmushin shi duka ya canza yayin da komae yake man cikin sanyin rai.



#Feedohm💧💧 *MATAR ABDALLAH.!*💥
                   True Life Story.!



                              💥



*©HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers



*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
   *Wattpad:Feedohm*



        # *Kuyi Hakuri kwana biyu na jina shiru da kun kayi, Tafiya ce ta kamani na dawo kuma naji wani K'azamin Labari..*
  #I'm Still alive..



*14*



  ***


  Ina kwance naji alamun shigowarsa, Sam ban jiyo ba sae ma lumshe idona da nayi kamar mai bacci..

  K'afafuna ya gyara ya mayar man dasu bisa gadon sosae, sannan ya rangwafo tare da leko fuskana, ina jin lokacin da ya saka hannu ya shafi ciki na sannan ya kaiwa goshina sumba yana fad'in "Thank you Muhibba."

  Shima kwanciya yayi a baya na ya janyoni bisa k'irjinsa yana shafa bayana a hankali, duk abunda yake ko nuna naji me yake banyi ba har sae da baccin gaske ya k'washe ni..

  Ko da na farka yana nan mak'ale dani na dan juya na kalli fuskarshi da alama shima baccin yake, a hankali na zare hannunshi daga jikina ina k'ok'arin tashi amma sae yayi saurin maido ni tare da matseni sosae a k'irjinsa,  idonshi a lumshe yake fad'in "Karki k'ara tunanin zaki sake motsi ba tare da sanin Abdallah ba, Fad'a man me kike so da kike k'ok'arin tashi bayan yanzu kikayi baccin.?

  Mayar da idona k'asa nayi a hankali nace "Sallah zanyi."

  Tattausan murmushi ya saki sannan ya ware hannunshi na fita a hankali na sauka daga gadon, har na yo alwala na dawo yana nan k'wance inda na barshi, na d'an saci kallonsa na ga baida alamar tashi yayi sallah..

  Lumshe ido nayi a hankali nace "Kai bara kayi sallah ba Ya Abdallah.?

  Murmushi ya saki sannan yace "Kabarin mu d'ayane? to yau ma banyi ni.."

  Da sauri ya bud'e idonshi ba tare da ya k'arasa zancen sa ba, Muryarshi na rawa ya cigaba da  fad'in "Ina nufin yau kam nayi niyya don jam'i ma zan mana."

  Girgiza kai nayi a hankali bansan lokacin da murmushi ya sub'uce man ba, da sauri ya mike ya fad'a toilet d'in yayo alwala har lokacin ina nan tsaye ina jiransa..

  Ga mamakina Abdallah ya ja mu sallah yarda ya kamata kamar wani liman, Sae da ya sallame sannan ya juyo yana kallona d'auke da murmushi yace "Karkiyi tunanin don farin cikin ki nake anan, saboda unborn d'ina nake."

  Murmushi nayi nace "Ni dama ai bance don ni kake ba."

  "Good." Ya fad'a tare da mik'ewa, har ya kai hanyar fita ya juyo yana fad'in "Kina buk'atar wani abu ne.?

  Girgiza kai nayi tare da mikewa na nannad'e abun sallah.

  "Ban yarda babu abunda kike so ba Larindo." Ya k'arashe maganar yana kallon cikina

  Banza na mashi na juyar da kai ya kuma fad'in "Idan ke bak'ya son komae na tabbata Unborn d'ina yana bukatar wani abu."

  Kai tsaye nace "Sae ka tambayeshi ai."

  Ware idanu yayi ya tako gabana tare da  duk'awa ya riko kuguna ya kai kunnensa jikin ciki na, banji me ya fad'a ba sae dae naga ya d'ago yana sakar man murmushi sannan ya mike  ya fice ba tare da yace komae ba..


 **

 A hankali yace "Wae Umma idan mace na da ciki me tafi buk'ata ne.?

  Da mamaki ta kalleshi, farinciki fal a fuskarta tace "Abdallah wa ke da juna biyu.?

  Murmushi yayi yana fad'in "Hasna ce Umma jiya Nurse ta zo ta dubata saboda yawan aman da takeyi."

  Tab'a hannu Umman tayi tare da d'aga kai sama ta d'aga hannunta tana fad'in "Alhamdulillah, Masha Allah."

  "Abdallah har wata nawa ne? Allah mun gode maka, tana dai lafiya ko.? Ta fad'a cike da tsantsar murna...

  Cikin murmushi yace "Wata uku ne Umma."

  "Masha Allah."

 "Umma to yanzu me kike tunanin ta fi so, don wallahi tun d'azu take rigima wae yunwa take ji kuma bata fad'i me take bukata ba."


 Murmushi tayi tace "Allah sarki baiwar Allah, dama dole haka ta kasance tunda na farko ne sannan banda abunka Abdallah ai ita da kanta zata fad'i abunda take bukata saboda kasan kowa da kalar nashi laulayin karka damu kaji ko? gobe da safe zan shigo na dubata sannan zan saka Aisha ta d'an mata kayan kwad'ayi irin na masu juna biyu yau."

  Kamar yayi kuka yace "Yanzu Umma haka za'a barta yau bata ci komae ba?

 "Sae hakuri Abdallah, masu juna biyu sun gaji haka ka ji ko? insha Allah da cikin ya d'anyi k'wari zata koma dae dae, amma yanzu bara na tashi na saka mata d'an wake tunda ina da wani yaji mai dad'i wata k'il ta soshi."

  Lumshe ido yayi yana fad'in "Yauwa Umma."

Bata wani jima ba ta gama d'an waken ta zuba mashi a wani k'wano tare da k'ulle mashi yajin ta saka a leda ta bashi da k'ullallan man gyad'anta..

  "Mun gode Umma."

  "Ka gaishe man da ita ka ji Abdallah,ka ce ina mata sannu da jiki, ka kula da ita sosai ka ji ko?

  Murmushi yayi ya na fad'in "Insha Allahu Umma."

  Ko da ya koma gida Hasna ya iske zaune a falo da sauri ta tare shi tana fad'in "Ina kaje Abdallah tun d'azu nake nemanka kuma wayarka sae ringing take baka d'auka ba."

  Murmushi yayi tare da janta suka zauna bisa kujeran yana fad'in " Gurin Umma naje na k'arbowa Larindo Dan wake."

  Bata rai tayi tana fad'in "Itane tace maka tana son d'an waken.?

  A hankali yace "A'a naga dai sae amai take kuma da alama bara ta iya cin abincin ba."

  Tab'e baki tayi ta juyar da kai yayin da ya sa hannu ya juyo da ita cikin lallashi yace "Fushi kike da Abdallanki Pearl.?

  "Kiyi hakuri kin ji ke da kike da yaro a sanga ko kin manta ita ba kawae wahalar haihuwar ce tata amma yaro ai na Matar Abdallah ne, ki yi hakuri na kula da ita kar taje ta zubar man da yaro, da ta haihu ta baki yaronki shikenan fa, kin ji ko Hasnata.?

  Banza ta mashi ya daura kanshi a k'irjinta yana fad'in " Abdallanki fane? Kuma kin san bazan iya jurar fushinki ba, Kiyi hakuri kin ji ko? Look please, fad'a man ma Kin fara shan maganin da Nurse ta baki.?

  Turo baki tayi tare da gyad'a kai, ya kai mata sumba yana fad'in "Nace fa kiyi hakuri ko? Ko zaki ci d'an waken me."

  A hankali ta gyad'a mashi kai tare da turo baki tace "Kasan fa yau ne birthday d'in Deebah shine kayi tafiyarka ka barni ko?


"Oh Matar Abdallah Allah na manta." Ya fad'a cikin sigar lallashi

  A shagwabe tace "Ka tashi kaje ka shirya to."

  Janyeta yayi daga jikinsa tare da sumbatar hannunta ya shiga kitchen ya dauko plate biyu ya zuba d'an waken tare da tura mata d'aya gabanta yana fad'in "Sauko ki ci kin ji ko? Bara na kai mata nata sae na shirya kafin ki gama ci."

   Yajin ya zuba mata a gefe tayi saurin Fad'in "Abdallah masu ciki basu cika son yaji da yawa ba, a rage shi gaskia kar Unborn d'ina yayi jan ido."

  Ware ido yayi yana fad'in "Da gaske.?

  Gyad'a kai tayi sannan tace "Huh."

  Hannu ya saka ya kwashe yajin ya bar k'adan sannan ya dauka ya nufi d'akin dashi, a zaune ya iskeni ina danna wayanata ya aje plate d'in gabana tare da duk'awa yace "Sannu kin ji ko.?

  Dagowa nayi na kalleshi tare da kallon plate din da ya aje, Wani farin ciki ya kamani ganin abunda ke ciki..

  Da sauri na kai hannu na janyo Plate din sosai tare da saka hannu ya debo na kai bakina, dad'i ya ratsani na lumshe ido a hankali nace "Nagode."

  Tattausan murmushi ya saki yana fad'in "Ki godewa Unborn d'inki."

  Bance mashi komae ba na cigaba da cin abuna ko rabi banci ba yajin ya k'are, na d'ago a sanyaye nace "Yajin ya k'are."

  Tab'e baki yayi tare da murmushi lokaci guda yace "Sae ki saka maggi ko."

  "Yajin dai." Na fad'a cikin shagwabar da bansan ina yi ba...

  Gani nayi ya kafeni da ido nayi saurin mayar da kaina k'asa yayin da ya saka hannu ya d'ago fuskana yana langwabar da kai..

  Lumshe ido yayi tare da sumbatar bakina sannan ya mike a hankali yana fad'in "Yajin dai ko Muhibba? Bara na k'aro maki kinji ko."

  Bin bayanshi nayi da kallo har ya fita sannan na mayar da kaina bisa cinyarta ina kallon cikina, wasu hawaye masu zafi suka zubo man wanda na rasa dalilinsu...


  A falo ya iske Hasna na cin abun ta hankali kwance ya duk'a zai dauki yajin tayi saurin kamo hannunshi tana fad'in "Mene zakayi dashi Abdallah.?

  "Tana buk'ata ne Hasna."

 A shagwabe tace "Ni dae banna son yaro mai jan ido, Yauwa Abdallah kaga yanzu Deebah ta kirani wae ta ji mu shiru."

 Hannu ta saka ta shafa kirjinsa tare da janyoshi ya zauna sosae ya jingina da jikinta sannan ta shafi cikinsa ta langwabe kai tana fad'in "Ba ci abinci ba ko Abdallanah? Oya bud'e bakinka na baka abincin Umman mu don banna so naga ka zauna da yunwa gaskia."

  Debo dan waken tayi ta tura mashi a baki ta saki lallausan murmushi tana fad'in "Yayi dad'i ko Abdallanah? Gaskia yau sai munje mun gayar da Ummanmu."

  Murmushi ya sakar mata tare da lumshe ido, sae da ta gama bashi d'an waken sannan ta saka lips dinta ta lashe duk inda d'an waken ya b'ata mashi, a hankali ta d'ago idonta a lumshe tana fad'in "Muje na wanke Abdallanah."

  Tattausan murmushi ya saki sannan ya mike suka shige ciki, sae da shiryashi cikin k'anan kaya sannan itama ta shirya cikin wata had'ad'd'iyar doguwar riga ruwan kwae ta sumba ci kumatunshi tana fad'in "Kayi k'yau Abdallanah."

  Murmushi ya sakar mata sannan ya ja hannunta suka fita har ga Allah ya manta da abunda yazo d'aukarwa Muhibbar, a haka suka isa gaban motar ya bud'e mata.

 Tsaye tayi tana kallonshi a shagwabe tace "Ni banyi kyau ba Abdallanah."

 Ware ido yayi ya rungumota jikinsa yace "Ai dama can MATAR ABDALLAH mai k'yau ce ko ba'a fad'a ba."


  Ni kam jin k'arar tada mota yasa nayi saurin lek'a da sauri, "Ya Allah."
 


#Feedohm💧💧 *MATAR ABDALLAH.!*💥
True Life Story.!

💥

*©HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
*Wattpad:Feedohm*

*15*

***

Zamewa nayi k'asan d'akin yayin da na had'e kaina da guiwata, wani azababben kishi ya turnik'e ni ji nake kamar zuciyata zata fito saboda masifar zafi, Kuka ma nake so ya fito ko naji sanyi amma na kasa...

"Allah sarki Ni anya nayi kaina adalci? Anya ban zalinci kaina ba? Inna lillahi wa'inna ilaihir raj'un."

Da k'yar na samu hawaye ya fara fitowa daga idona "Meyasa nake son Abdallah bayan bashshi da wani hali da ya kamata ace na soshi? Anya zuciyata ta mani adalci kuwa.? Ya Allah ka cire mani Son Abdallah! Ya Allah ka rabani da Abdallah."

Hawaye sosae ke fita daga idanu na, lokaci guda tunani da kewar Maryama ya d'arsu a zuciyata "Allah sarki maryama, duk duniyar mu babu wanda zan fad'awa damuwa ta sama dake, Me yasa kika yarda soyayyar wani ta raba tsananin mu, Sam bai cancanci ya samu gurbi a zukatan mu ba Maryama, Me yasa Maryamata.?

"Anya kuwa hakan zata Faru Maryama?

Zabura nayi kamar zautacciya ina fad'in "A'a Maryamata."

Wani sashe na zuciyata ya fara gargad'i na tare da tunatar dani abubuwa da suka faru a baya "Ayya kuwa Maryama?

Wasu hawaye suka fara man sintiri kamar b'allewar fanfo tunina ya tsaya cak lokacin da na tuna sadda muna y'an yara wani yaro d'an ajin mu yace yana sona, da nak'i kulashi ya koma gurin Maryama a ranar da ya fad'a mata yana sonta sae da ta janyo shi har gaba na ta mashi zagin rashin mutunci sannan ta tura k'eyarshi har gurin malan tace d'an iskane so yake ya rabata da Muhibbarta...

"Anya zata man haka? Me yasa banyi magana da Maryama ba? Kuka sosae na sake lokacin da na tuna irin k'aunar da Maryama ke man, tabbas nasan soyauya da kishin Abdallah ya hanani tunanin abunda Maryama zata iya da wanda bara ta iya ba...

Da sauri na janyo waya na na fara k'ok'arin kiran number Maryama amma sam bata shiga, Ummana na kira nace ta k'arbo man number da Maryama ke amfani da ita yanzu..

"To." kawae ta bini dashi tare da yanke wayar abunta

Sallamar da naji a falo yasa na mike da tare da goge fuska na na fita, Idan banyi kuskure ba Budurwa Fatima ce tsaye tsakiyar falon sargahe da jikkarta taci k'ananan kaya da k'arin gashin doki.

Fad'ad'a fara'a ta nayi duk da k'asan zuciyata cike yake da k'unci ina fad'in "Yau kuma bak'i ne a gidan? Sannu da zuwa, ki zauna mana."

Da fara'a ta amsa "Aiko dae mune, ko ba'a so zuwan na mu bane?

"A'a ke kau ai BAK'ON KA HASKEN KA, ki zauna mana dan Allah, duk da dai kinyi rashin sa'a Matar gidan batta nan yanzu suka fita." Na fad'a dauke da murmushin yak'e.

Dan murmushi ta saki tana fad'in "Ai ba komae ke da ita ai duk d'aya ne, Ya kike amaryar mu? ashe an samu cigaba an baro BQ an dawo cikin gida."

Dan murmushi nayi tare da nace komae ba don har ga Allah bansan me zance mata ba, asali ma ni ban cika son ana zancen abunda ya shafi aurena da zama na ba, wuce wa nayi na d'auko mata ruwa da lemo na kawo mata, ina k'ok'arin zama ta janyo hannuna tana murmushi tace "Ni fa gurinki nazo Hajiyata kuma naga alamar kamar baki so zuwan nawa ba, Ya kike ciki ke da angon naki? Allah dae yasa an samu cigaba? wae shin an raba maku kwana kuwa.?

"Ikon Allah."Na fad'a a zuciyata ni kam bana son karan bani abunda bai shafeka ba ka shiga ciki, shin ina ruwanta da yarda nake da mijina bare raban k'wanan mu.

"Kunyata kike ji kikayi shiru, ko bak'yason na tambayeki ya Abdallan ki yake a gurin kwanciya? To sha kuruminki bazan tambayeki ba ke da kanki zaki bani labari wata rana indae muna tare." Maganar ta ta doki dodon kunnena.

Nikam har ga Allah magannanun Budurwa Fatima son fara ita..

Duka ta kaiman a cinya tare da rik'o hannuna tana fad'in "Sweetie mu bar maganar tunda bak'ya so, yanzu dae gurinki nazo."

"Allah dai yasa lafiya.? Na fad'a babu yabo ba fallasa tare da zame hannu na daga nata

Dariya tayi sannan tace "Kinga lafiya lau wallahi, dama wata k'awata tace man ta ganki a gurin Party kuma kin burge ta sosai shine ta bani 50k na kawo maki k'ya sha sweet da irin y'an kayan mu na mata."ta k'arashe maganar tare da kanne ido guda.

"Sae kuma a kayi rashin sa'a ni banna shan sweet bare kayan ku na mata ."Na fad'a babu yabo ba fallasa don babu wata hujjar da macen da ban sani ba zata man k'yautar kudi har haka gaskia in ba dae tana da wata mummunan k'udiri a kai na ba, duk da nasha jin Maryama na fad'in wasu mugaye mata na amfani da kud'i su saye mutun har su b'ata mashi rayuwa a banza sannan maganganun Budurwa Fatima sun yi matuk'ar d'aure man kai.

"Kai Muhibba idan bak'ya son sweet ai bak'ya rasa abunda zakiyi da kud'i ba, tunda naga ba wani kud'i kike samu ba sannan kayan mu na mata kam ai dole ki sha su in ba dae har yanzu ba'a fara sha'ani ba da Abdallan.?

Maganarta ta daki dodon kunnena na kalleta da sauri, tabbas ta fara bani tsoro duk da mana bai kamata nayi saurin yarda da mutun irin budurwa Fatima ba..

Kai tsaye nace " Ni ce nace maki ina son kud'in koko Abdallan ne yace maki baya ban kud'i?

"Ko baki fad'a ba ai nasan basu ke dake ba tunda daga yanayin gidanku kam, kuma nasan Abdallah dai ba baki zaiyi ba, Ko da yake ina maganar kud'i ma? ai ki samu ya kula ki tukun."

Mik'ewa nayi tsaye ina kallonta tare da girgiza kai nace "Ikon Allah! to budurwa Fatima ni kam sae anjima don bana tunanin akwae wani abu mai amfani da zan kuma saurara kam."

"Ko? Ke kam baki san duniya ba Yarinya! anyway zan aje maki kud'in a hannuna don baran iya mayar mata ba don banna so ta raina maki aji, duk lokacin da kike buk'atar su k'ya neme ni." Ta fad'a tare da mik'ewa tsaye tana gyara jikkar ta

Bance mata komae ba na wuceta abuna yayin da hankalina ya koma gida biyu, Shin me Budurwa Fatima ke nufi da maganganunta? Me yasa komae sae tayi k'ok'arin saka Abdallah ne a ciki? Me ya shafeta da lamarin mazana da mijina? Dan k'aramin tsaki na sake tare da karkatawa ga Number da Umma zata turo man, ina shiga wayata na d;auka kuma na iske Message d'in Umman...

Duk da naji dad'i amma zuciyata bugawa take da na tuna masifar da zansha gurin Maryama, bare ma ace ita ne ke da gaskia,

Ringing d'aya ta d'auka had'e da sallama kamar ko da yaushe ta had'a da fad'in "Sunana Maryama da wa nake magana, don naga bak'uwar number ta nigeria ni kuma yanzu kun san dae ina Cairo."

Cikin sanyin murya nace "Maryama."

"Kan uban can Muhibba wane d'an iska ya baki numberta kuma? owo kin gama cin amarcin kin tuna da Maryama banza ko? to uban me zan maki yanzu bayan duk iskanci da wulak'ancin da kika man ke da mijinki.?

Kuka ya k'wace man nace "Maryama ki tsaya ki ji mana."

"Naji me? ke wallahi kin san dae banna son iskanci ko?

Cikin kuka sosae nace "Maryama da gaske...

Sassauta murya tayi tana fad'in "Kamar kuka kike ko Muhibbatah kin san dai wasa nake maki ba bala'in gaske bane ko.?

Kamar tana ganina na gyad'a kai tare da kiran sunanta

A rud'e ta fara fad'in "Menene Muhibba? ki bar kukan dan girman Allah ki fad'a man me aka amaki? Abdallah ne Ko? Yi shiru mana kinji Muhibba."

Tausayinta ya kamani yayin da naji tsanar kaina da ta Abdallan da ya rabani da Maryamata lokaci guda...

Kamar tayi kuka tace "Ko bak'ya lafiya ne Muhibba? don Allah ki man magana mana kin ji?

Jin shirun yayi yawa yasa tace "Shikenan kiyi shiru kin ji ko? Ranar monday zan dawo na ganki Muhibba, babu amfanin zamana nesa dake muddun zaki dinga shiga damuwa, Dan Allah kiyi shiru."

"Kiyi hakuri Maryama."Na fad'a muryata na rawa

"Wae menene Muhibba?Dan Allah ki fad'a man matsalarki."

"Babu komae Maryama kawae nayi kewarki ne sosae Maryama, kuma nasan na maki laifi don Allah kiyi hakuri."

A raunane tace "Banyi fushi ba Muhibba ki daina kukan kinji ko? Zan dawo ai?

"Ba sae kin dawo ba Maryama, anjima da daddare zan kiraki."

"Shikenan Muhibba ki kula kin ji ko."

Gyad'a kai nayi tare da yanke wayar, Allah sarki Maryamata...

**

Sae isha'i sannan mutanen gidaj suka dawo a tunani zai lek'o gurina amma sam babu alamunsa,

Wani sashe na zuciyata ya hanane da maganar Maryama yayin da nayi niyyar bazan tambaye shi komae ba, asali ma baran sake tada maganar ba...

Kamar yadda Ummansu Abdallah ta fad'a wanshekare da marece sae gata da leda gari yayi zafi kusan rabi, A lokacin na fito zan d'auki ruwan a frigde d'in falo naji sallamar ta...

Juyawa nayi na kalleta lokaci guda naga tsantsar kamaninta da Abdallanah aje robar ruwan nayi na matsa sosae na duk'a har k'asa tare da amsa sallamarta

Kaina a k'asa nace "Ina wuni.?

Cikin fara'a ta amsa da lafiya "Lafiya lau Alhamdulillah, Ya muka sameku.?

Allah sarki ashe Umman ta san da zamana, cike da jin kunya nace "Alhamdulillah Umma, dan Allah ki zauna."

Dan murmushi tayi sannan ta d'an rab'a gefen kujeran cikin jin nauyi, lemo na d'auko mata da ruwa na zuba mata a cup na d'uk'a ha ,k'asa na mik'a mata.

Girgiza kai tayi tace "Alhamdulillah nagode kin ji ko, Allah ya maku albarka, Ni kak ke kad'ae ne a gidan ."

A Hankali nace "a'a suna ciki."

"Taimaka ki masu magana dan Allah, Ya jikin Hasnar?

Bansan ma ni bata lafiya ba kawae dae nace mata "Da sauki."

Mikewa nayi na je nayi knocking a part d'in Abdallah don na tabbata suna ciki..

"Who is there.?Ya fad'a a hankali cikin sanyin murya

Shiru nayi don wannnan ne karo na na farkon tunkarar d'akinshi

"Hasna.?ya kuma fad'a

A Hankali nace "Muhibba ne."

"Ohk."

"Assalamu Alaikum zan iya shigowa? Na fad'a cikin sanyin murya tare da tsayawa bakin d'akin

"Mata da d'akin mijinta wa ya isa hanata shigowa? shigo mana Matar Abdallah."

Gabana ke fad'uwa na tura kofar a hankali na shiga, turus nayi ganin kwalbar giyar dake gabanshi

A Firgice ace "Na shiga uku.! Me kake sha Ya Abdallah? Allah yasa ba giya bace?

Murmushi ya sakar man yana fad'in "Giyane ko kema zaki sha Matar Abdallah.?

Fitowar yar budurwa daure da d'an guntun towel ya katse man abunda nayi niyyar fad'a.

Dukan k'irji na ya tsananta yayin na kasa furta kalma ko d'aya.

"Meet my ex-friend Matar Abdallah." ya fad'a tare da nuna matashiyar duburwa da da hannu...

#Feedohm💧💧 *MATAR ABDALLAH.!*💥
True Life Story.!

💥

*©HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
*Wattpad:Feedohm*

*15*

***

Zamewa nayi k'asan d'akin yayin da na had'e kaina da guiwata, wani azababben kishi ya turnik'e ni ji nake kamar zuciyata zata fito saboda masifar zafi, Kuka ma nake so ya fito ko naji sanyi amma na kasa...

"Allah sarki Ni anya nayi kaina adalci? Anya ban zalinci kaina ba? Inna lillahi wa'inna ilaihir raj'un."

Da k'yar na samu hawaye ya fara fitowa daga idona "Meyasa nake son Abdallah bayan bashshi da wani hali da ya kamata ace na soshi? Anya zuciyata ta mani adalci kuwa.? Ya Allah ka cire mani Son Abdallah! Ya Allah ka rabani da Abdallah."

Hawaye sosae ke fita daga idanu na, lokaci guda tunani da kewar Maryama ya d'arsu a zuciyata "Allah sarki maryama, duk duniyar mu babu wanda zan fad'awa damuwa ta sama dake, Me yasa kika yarda soyayyar wani ta raba tsananin mu, Sam bai cancanci ya samu gurbi a zukatan mu ba Maryama, Me yasa Maryamata.?

"Anya kuwa hakan zata Faru Maryama?

Zabura nayi kamar zautacciya ina fad'in "A'a Maryamata."

Wani sashe na zuciyata ya fara gargad'i na tare da tunatar dani abubuwa da suka faru a baya "Ayya kuwa Maryama?

Wasu hawaye suka fara man sintiri kamar b'allewar fanfo tunina ya tsaya cak lokacin da na tuna sadda muna y'an yara wani yaro d'an ajin mu yace yana sona, da nak'i kulashi ya koma gurin Maryama a ranar da ya fad'a mata yana sonta sae da ta janyo shi har gaba na ta mashi zagin rashin mutunci sannan ta tura k'eyarshi har gurin malan tace d'an iskane so yake ya rabata da Muhibbarta...

"Anya zata man haka? Me yasa banyi magana da Maryama ba? Kuka sosae na sake lokacin da na tuna irin k'aunar da Maryama ke man, tabbas nasan soyauya da kishin Abdallah ya hanani tunanin abunda Maryama zata iya da wanda bara ta iya ba...

Da sauri na janyo waya na na fara k'ok'arin kiran number Maryama amma sam bata shiga, Ummana na kira nace ta k'arbo man number da Maryama ke amfani da ita yanzu..

"To." kawae ta bini dashi tare da yanke wayar abunta

Sallamar da naji a falo yasa na mike da tare da goge fuska na na fita, Idan banyi kuskure ba Budurwa Fatima ce tsaye tsakiyar falon sargahe da jikkarta taci k'ananan kaya da k'arin gashin doki.

Fad'ad'a fara'a ta nayi duk da k'asan zuciyata cike yake da k'unci ina fad'in "Yau kuma bak'i ne a gidan? Sannu da zuwa, ki zauna mana."

Da fara'a ta amsa "Aiko dae mune, ko ba'a so zuwan na mu bane?

"A'a ke kau ai BAK'ON KA HASKEN KA, ki zauna mana dan Allah, duk da dai kinyi rashin sa'a Matar gidan batta nan yanzu suka fita." Na fad'a dauke da murmushin yak'e.

Dan murmushi ta saki tana fad'in "Ai ba komae ke da ita ai duk d'aya ne, Ya kike amaryar mu? ashe an samu cigaba an baro BQ an dawo cikin gida."

Dan murmushi nayi tare da nace komae ba don har ga Allah bansan me zance mata ba, asali ma ni ban cika son ana zancen abunda ya shafi aurena da zama na ba, wuce wa nayi na d'auko mata ruwa da lemo na kawo mata, ina k'ok'arin zama ta janyo hannuna tana murmushi tace "Ni fa gurinki nazo Hajiyata kuma naga alamar kamar baki so zuwan nawa ba, Ya kike ciki ke da angon naki? Allah dae yasa an samu cigaba? wae shin an raba maku kwana kuwa.?

"Ikon Allah."Na fad'a a zuciyata ni kam bana son karan bani abunda bai shafeka ba ka shiga ciki, shin ina ruwanta da yarda nake da mijina bare raban k'wanan mu.

"Kunyata kike ji kikayi shiru, ko bak'yason na tambayeki ya Abdallan ki yake a gurin kwanciya? To sha kuruminki bazan tambayeki ba ke da kanki zaki bani labari wata rana indae muna tare." Maganar ta ta doki dodon kunnena.

Nikam har ga Allah magannanun Budurwa Fatima son fara ita..

Duka ta kaiman a cinya tare da rik'o hannuna tana fad'in "Sweetie mu bar maganar tunda bak'ya so, yanzu dae gurinki nazo."

"Allah dai yasa lafiya.? Na fad'a babu yabo ba fallasa tare da zame hannu na daga nata

Dariya tayi sannan tace "Kinga lafiya lau wallahi, dama wata k'awata tace man ta ganki a gurin Party kuma kin burge ta sosai shine ta bani 50k na kawo maki k'ya sha sweet da irin y'an kayan mu na mata."ta k'arashe maganar tare da kanne ido guda.

"Sae kuma a kayi rashin sa'a ni banna shan sweet bare kayan ku na mata ."Na fad'a babu yabo ba fallasa don babu wata hujjar da macen da ban sani ba zata man k'yautar kudi har haka gaskia in ba dae tana da wata mummunan k'udiri a kai na ba, duk da nasha jin Maryama na fad'in wasu mugaye mata na amfani da kud'i su saye mutun har su b'ata mashi rayuwa a banza sannan maganganun Budurwa Fatima sun yi matuk'ar d'aure man kai.

"Kai Muhibba idan bak'ya son sweet ai bak'ya rasa abunda zakiyi da kud'i ba, tunda naga ba wani kud'i kike samu ba sannan kayan mu na mata kam ai dole ki sha su in ba dae har yanzu ba'a fara sha'ani ba da Abdallan.?

Maganarta ta daki dodon kunnena na kalleta da sauri, tabbas ta fara bani tsoro duk da mana bai kamata nayi saurin yarda da mutun irin budurwa Fatima ba..

Kai tsaye nace " Ni ce nace maki ina son kud'in koko Abdallan ne yace maki baya ban kud'i?

"Ko baki fad'a ba ai nasan basu ke dake ba tunda daga yanayin gidanku kam, kuma nasan Abdallah dai ba baki zaiyi ba, Ko da yake ina maganar kud'i ma? ai ki samu ya kula ki tukun."

Mik'ewa nayi tsaye ina kallonta tare da girgiza kai nace "Ikon Allah! to budurwa Fatima ni kam sae anjima don bana tunanin akwae wani abu mai amfani da zan kuma saurara kam."

"Ko? Ke kam baki san duniya ba Yarinya! anyway zan aje maki kud'in a hannuna don baran iya mayar mata ba don banna so ta raina maki aji, duk lokacin da kike buk'atar su k'ya neme ni." Ta fad'a tare da mik'ewa tsaye tana gyara jikkar ta

Bance mata komae ba na wuceta abuna yayin da hankalina ya koma gida biyu, Shin me Budurwa Fatima ke nufi da maganganunta? Me yasa komae sae tayi k'ok'arin saka Abdallah ne a ciki? Me ya shafeta da lamarin mazana da mijina? Dan k'aramin tsaki na sake tare da karkatawa ga Number da Umma zata turo man, ina shiga wayata na d;auka kuma na iske Message d'in Umman...

Duk da naji dad'i amma zuciyata bugawa take da na tuna masifar da zansha gurin Maryama, bare ma ace ita ne ke da gaskia,

Ringing d'aya ta d'auka had'e da sallama kamar ko da yaushe ta had'a da fad'in "Sunana Maryama da wa nake magana, don naga bak'uwar number ta nigeria ni kuma yanzu kun san dae ina Cairo."

Cikin sanyin murya nace "Maryama."

"Kan uban can Muhibba wane d'an iska ya baki numberta kuma? owo kin gama cin amarcin kin tuna da Maryama banza ko? to uban me zan maki yanzu bayan duk iskanci da wulak'ancin da kika man ke da mijinki.?

Kuka ya k'wace man nace "Maryama ki tsaya ki ji mana."

"Naji me? ke wallahi kin san dae banna son iskanci ko?

Cikin kuka sosae nace "Maryama da gaske...

Sassauta murya tayi tana fad'in "Kamar kuka kike ko Muhibbatah kin san dai wasa nake maki ba bala'in gaske bane ko.?

Kamar tana ganina na gyad'a kai tare da kiran sunanta

A rud'e ta fara fad'in "Menene Muhibba? ki bar kukan dan girman Allah ki fad'a man me aka amaki? Abdallah ne Ko? Yi shiru mana kinji Muhibba."

Tausayinta ya kamani yayin da naji tsanar kaina da ta Abdallan da ya rabani da Maryamata lokaci guda...

Kamar tayi kuka tace "Ko bak'ya lafiya ne Muhibba? don Allah ki man magana mana kin ji?

Jin shirun yayi yawa yasa tace "Shikenan kiyi shiru kin ji ko? Ranar monday zan dawo na ganki Muhibba, babu amfanin zamana nesa dake muddun zaki dinga shiga damuwa, Dan Allah kiyi shiru."

"Kiyi hakuri Maryama."Na fad'a muryata na rawa

"Wae menene Muhibba?Dan Allah ki fad'a man matsalarki."

"Babu komae Maryama kawae nayi kewarki ne sosae Maryama, kuma nasan na maki laifi don Allah kiyi hakuri."

A raunane tace "Banyi fushi ba Muhibba ki daina kukan kinji ko? Zan dawo ai?

"Ba sae kin dawo ba Maryama, anjima da daddare zan kiraki."

"Shikenan Muhibba ki kula kin ji ko."

Gyad'a kai nayi tare da yanke wayar, Allah sarki Maryamata...

**

Sae isha'i sannan mutanen gidaj suka dawo a tunani zai lek'o gurina amma sam babu alamunsa,

Wani sashe na zuciyata ya hanane da maganar Maryama yayin da nayi niyyar bazan tambaye shi komae ba, asali ma baran sake tada maganar ba...

Kamar yadda Ummansu Abdallah ta fad'a wanshekare da marece sae gata da leda gari yayi zafi kusan rabi, A lokacin na fito zan d'auki ruwan a frigde d'in falo naji sallamar ta...

Juyawa nayi na kalleta lokaci guda naga tsantsar kamaninta da Abdallanah aje robar ruwan nayi na matsa sosae na duk'a har k'asa tare da amsa sallamarta

Kaina a k'asa nace "Ina wuni.?

Cikin fara'a ta amsa da lafiya "Lafiya lau Alhamdulillah, Ya muka sameku.?

Allah sarki ashe Umman ta san da zamana, cike da jin kunya nace "Alhamdulillah Umma, dan Allah ki zauna."

Dan murmushi tayi sannan ta d'an rab'a gefen kujeran cikin jin nauyi, lemo na d'auko mata da ruwa na zuba mata a cup na d'uk'a ha ,k'asa na mik'a mata.

Girgiza kai tayi tace "Alhamdulillah nagode kin ji ko, Allah ya maku albarka, Ni kak ke kad'ae ne a gidan ."

A Hankali nace "a'a suna ciki."

"Taimaka ki masu magana dan Allah, Ya jikin Hasnar?

Bansan ma ni bata lafiya ba kawae dae nace mata "Da sauki."

Mikewa nayi na je nayi knocking a part d'in Abdallah don na tabbata suna ciki..

"Who is there.?Ya fad'a a hankali cikin sanyin murya

Shiru nayi don wannnan ne karo na na farkon tunkarar d'akinshi

"Hasna.?ya kuma fad'a

A Hankali nace "Muhibba ne."

"Ohk."

"Assalamu Alaikum zan iya shigowa? Na fad'a cikin sanyin murya tare da tsayawa bakin d'akin

"Mata da d'akin mijinta wa ya isa hanata shigowa? shigo mana Matar Abdallah."

Gabana ke fad'uwa na tura kofar a hankali na shiga, turus nayi ganin kwalbar giyar dake gabanshi

A Firgice ace "Na shiga uku.! Me kake sha Ya Abdallah? Allah yasa ba giya bace?

Murmushi ya sakar man yana fad'in "Giyane ko kema zaki sha Matar Abdallah.?

Fitowar yar budurwa daure da d'an guntun towel ya katse man abunda nayi niyyar fad'a.

Dukan k'irji na ya tsananta yayin na kasa furta kalma ko d'aya.

"Meet my ex-friend Matar Abdallah." ya fa
d'a tare da nuna matashiyar duburwa da da hannu...

#Feedohm💧💧 *MATAR ABDALLAH.!*💥
                   True Life Story.!

                              💥


*©HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers


*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
   *Wattpad:Feedohm*


*16*

    ***

       A razane nake kallonsu baki d'aya yayin da na sandare inda nake ko k'afata na kasa d'agawa, kafin nayi wani yunk'uri na ga yarinyar a gabana tare da kamo hannu na tana fad'in "Gaskia Abdallanah kayi sa'ar mata babu ta yar wa a cikin su."

  Fizge hannuna nayi ina k'ok'arin tsayar da hawayen dake zuba daga idona kafin na fara jan k'afata da niyyar barin d'akin.

  Abdallah ne ya sha gaba na yana fad'in "Wae me ke damunki ne Muhibbah? Gaisawar ma bara ki iya ba da k'awataMuhibba? Please wae me ke damunki ne? She's just a friend of mine fa. Gaskia kina kwafsa man da yawa, Kin san Allah da Hasna ce ko.."

  Daga mashi hannu nayi ina kallon k'asa cikin sark'ewar Murya nace "Ni ba Hasna bace Abdallah, Muhibba ne ka daina had'a da ita."

  Murmushi yayi mai sauti yana kallona "Anyway fad'a man me ya kawo ki d'akina?

  Girgiza kai nayi yayin da wani abu ya tokare man mak'oshi, a hankali na juya baki na d'auke da addu'a yayi saurin kamo hannuna tare da fizgoni baya

  Bansan lokacin da na kifa mashi mari ba tare da angaza shi gefe na d'ago rinannun idanu na ina kallonshi, cikin tsawa nace "Don't ever touch me Abdallah.."


  Juyar da kai yayi yana furzar da iskar dake bakinshi, lokaci guda idonshi ya kad'a yayi jawur, Yar budurwa tayo kanshi tana tare da kamo hannun shi tana kallona mayar da kallonta tayi ga Abdallah tana tambayarshi "Matarka na da hankali kuwa Abdallah.?


  Bacin ran da na gani yanzu bai kai na marin da na mashi ba , ya tureta daga kusa dashi yana zabga mata wani irin kallo "Watch ur words Beeba." Ya fad'a cikin sark'ewar Murya .


  Tab'e baki tayi tana harara ta a hankali tace "Kayi hakuri ba ni ce na kashe zomon ba r..."

  Wata k'ofa ya nuna mata yana fad'in "Please leave."

  Kusa dani ya matso ya saka hannu ya d'ago fuskana yana kallon cikin idona, murya k'asa k'asa yace "Kishin da nake gani a idonki kad'ae ya ishe ki bak'in ciki Muhibbatah."

  Lumshe ido nayi tare da juyar da kaina na fice yayin da nake jin zuciyata kamar zata fito

  Ban bi ko ta kan Umma ba na nufi d'akina, a bakin k'ofa naji Umman na fad'in "Wannan ce yarinyar Hasna Abdallah.?


  Kai tsaye yace "Eh ita ne Umma."


  Juyawa nayi ina kallonshi a tsorace jin me yake fad'a a hankali na sulale dirshan bakin kofar d'akin tare da zuba masu ido ina fitar da k'wallah masu zafin gaske..



  "Abdallah lafiya kuwa.? Umman ta tambayeshi tana nuno ni da hannu.

  Mikewa yayi ya nufoni da sauri yana fad'in "Lafiya lau Umma da yake tana da matsalar jinnu wani sa'in sae dae kawae ki ga ta zube wata k'ila sune su ka zo yanzu."

  Kuka na saki da k'arfi ina girgiza kai "Allah ya isa Abdallah, ka cuceni, ka zalunce ni bazan tab'a yafe maka ba."

  Dariya ya saki a hankali tare da duk'awa kusa da fuskana yana fad'in "Tashi ki shige ciki tun kafin na baki mamaki Muhibbata."  sannan tofo man miyau kamar yana man addu'a.

  "Wane mamaki ne ya rage baka bani ba Abdallah.?


  "Allah ya isa kawae zan maki kin san kuma dole ta bi ki ." Ya fad'a dauke da murmushi

  "Sae me idan ka man Allah ya isa Abdallah, Ko baka man ba ni na maka Abdallah."

  "Kinga ba Ummana bace wannan k'anwar ta ce, ki tashi ki shiga ciki don bata kaunar aurena dake don bata sanki bane shi yasa har ta tsaya ta maki magana."

  "Karyane Abdallah."

    Murmushi ya saki tare da juyawa yana kallon Umman ganin hankalinta ba gurin yake ba yasa shi fizgata ya tura d'aki tare da janyo k'ofar da k'arfi ya rufe..


  Nayi kuka kamar raina zai fita tare da nadamar yarda da nayi da Abdallah, Ummana na kira cikin sa'a ta d'auka yayin da na fad'a mata duk halin da nake ciki...

 Nasan Ummana bara ta tab'a bin baya na ba wannan k'aron ma cewa tayi na dage da addu'a sannan na gyara halina wata k'il akwae abunda nake mashi wanda bayya so...

  Cikin kuka nace "Umma munafuki ne wallahi baya sona, d'a kawae yake buk'ata daga gareni sannan ko iyayensa.."

  Katseni tayi tana fad'in "A k'ul Muhibba kar na kuma jin kalmar batanci ta daga bakinki."

  "Umma.."

 Naso ta tsaya na mata bayanin halin da nake ciki amma sam tak'i saurarata illa kawae ce man take kiyi hakuri Muhibba, ki ci gaba da addu'a babu wanda ke jin dad'i a gidan aurensa, ki rik'e sirrin aurenki....

  Daga k'arshe ma kashe wayar tayi abunta...


  Da daddare ina zaune bisa abun sallah ya shigo d'auke da leda a hannu shi zama yayi gefena yana kallona k'asa k'asa.
 
  A hankali yace "Me kike rok'awa Abdallanki."

  Wani bak'in ciki ya tok'are man mak'oshi nace "Roko nake Allah ya kashe ka Abdallah."

  Dariya ya saki harda rike ciki kafin ya kafeni da ido yana fad'in "Kai Muhibbanah ai k'ya bari na ga Unborn d'ina kafin na mutu ko?
 
  Juyar da kai nayi gefe tare da nuna mashi kofa nace "Dan girman Allah ka fitar man daga d'aki Abdallah."

  Tattausan murmushi ya saki yana fad'in "Kinyi tusa ne Muhibbatah?Shine kike kora ta don  bak'ya so Abdallanki ya shaki warinta ko? karki damu kin ji ko bazan damu ba dan na shaki tusar Matata."

    Rasa abunda zan ce mashi nayi don haka na rufe bakina tare da kwantar da kaina saman cinyata.

**

  Haka rayuwa ke tafiya har cikina ya tsufa Itama Hasna kam ko ban tambaya ba nasan cikinta ita ma ya tsufan yanzu kam ina samun saukin lamuran Abdallah, bare ma da Maryama ta zo har gida ta d'an bani shawarwari haka nima idan naje gidan mu Ummana na bani shawara sosae sae dae har lokacin ban da wata hujjar da zan ce dangin Abdallah basu san ya aureni ba..

  Yau kam ina zaune ya shigo d'akin ya iske ni ina tsefe kaina, ya dad'e tsaye yana kallona kafin ya tako har inda nake ya tsugunna tare da karb'ar matsefin yana murmushi...

  Juyar da kai nayi ina fad'in "Sannu." Don yanzu ya fara fita a raina kwata kwata ko magana don ta zama dole nake mashi.

  Murmushi ya kuma saki tare da janyo ni jikinsa bayan ya zauna yana fad'in "Kin ci abinci ko.?

  Banza nayi mashi ya kai hannu ya shafi cikin tare da juyo fuska na yana fad'in " Kin bar fushin da Abdallah haka kinji ko? don a banza kike fushinki Abdallanki bai cika damuwa da fushin ki ba."

  Haka ya k'araci maganarshi ban ko kulashi ba har ya gama man tsifar sannan ya mike yana fad'in "Shine ko sannu bara ki man ba ko.?

  "Ai ba ni na saka ba."Na fad'a kai tsaye.

  Tattausan murmushi ya saki tare da jan gashin da k'arfi na saki k'ara na rik'e mashi hannun ina kallonshi.

  Kashe man ido yayi yana fad'in "Sake man hannu tunda bake kika sani ba."

   Turo baki nayi nace "Ka sake man gashi to."

  "Idan nak'i fa.?

  Shiru nayi ina kallonshi lokaci guda na mayar da kaina k'asa murmushi yayi ya saki kan tare da sumbatar tsakiyar kaina ya juya yana fad'in "Ina bala'in so naga kina kuka Muhibbata, amma sam yau kin k'i faranta ma Abdallanki rai."

  "Allah ya isa." Na fad'a tare da rakashi da harara har ya bar d'akin.


  A ranar da daddare ciwo yaci k'arfina tun ina daurewa har na kasa na fara kuka, ganin abun yak'i k'arewa yasa da k'yar na rarrafa naje na buga masu k'ofa, a tare suka fito suna tambayar waye...

  Ina tsugunne bakin k'ofar d'akin cikin kuka nace "Cikina Abdallah, Dan Allah ka taimaka man mutuwa zanyi."

  Mayar da kallonsu sukayi gareni lokaci guda kafin ya duk'a gabana ya rike hannuna a rud'e yana tambayar "Me ya samu cikin Muhibba?

  K'wantar da kaina nayi a cinyarsa ina fad'in "Cikina Abdallah, Cikina, Baya na Abdallah, Ka taimaka man kuguna zai cire Abdallah."

  Dago kaina yayi a rud'e yana fad'in "Kiyi hakuri Muhibba, ki daina kukan kin ji ko? ba abunda zai sameki insha Allahu."

  Ganin jini ya fara zuba yasa ya d'aukeni a rud'e yayin da Hasna ta koma ciki ta d'auko waya ta kira Nurse...

  Dakin shi ya shigar dani ya k'wantar saman gadon shi yana jera man sannu tare da hura man iskar bakinshi a goshi haka hannun shi na saman goshi na...

   Mintina kad'an Nurse d'in tazo, sae dae duk yarda ta kai ga k'ok'arin taga na haihu sam na kasa saboda k'arfina ya k'are gashi numfashin yaron ya fara d'aukewa cewa tayi gaskia sae dae a kaini asibiti don da k'yar zan iya haihuwa da kaina...

  Cikin tashin hankali aka tafi dani asibitin suma sunyi bakin k'ok'arin su amma dole sae an man CS Abdallah kam yayi mugun kid'ime wa har ya fara bawa Hasna Haushi...

  Hannuna gam ya rik'e lokacin da ake k'ok'arin shiga dani threater yayin da idonshi ya kad'a yayi jawur...

  Cikin kuka nace "Mutuwa zanyi Abdallah dan Allah ka yafe man na yafe maka Abdallah."

  Girgiza man kai yayi yayin da hawaye suka fara wanke mashi fuska "Bazaki mutu ki barni ba Muhibbatah."

  Da k'yar na kai hannu na na goge mashi hawayen ina murmushin azaba "Cikina Abdallah, wallahi nasan mutuwa zanyi, dan Girman Allah ka kula man da yarona karka barsa ya wulak'anta a gidanka kamar maman sa  Abdallah."

  "Nace maki baza ki mutu ba Muhibba, bara ki tab'a mutuwa ba ki barni." Ya fad'a da k'arfi tare da dafe kanshi da hannu bayan an cire hannunshi daga nawa...

  Nikam har ga Allah na yankewa kai da rayuwa saboda azabar da nake ji, A Hankali nace "Kaman alk'warin zaka kula man da yarona Abdallah."

  Ana rufe d'akin yayi zaman dirshan a bakin threater d'in tare da had'e kai da guiwa yana fitar da wani irin gurnani..

   Cikin ikon Allah aka fito da abunda ke cikina Babyboy ne mai kama da Abdallah duk da yana jariri gashi jawur dashi kamar a tab'a jini ya fito..

 Ni kam bansan inda hankali na yake ba sae da safe lokacin dana farka na iske Abdallah Zauna gefen gado na yayin da Ummana take jan carbi sae Maman su Maryama da yayar Ummana.


 A wahale na juyar da kai ina kallon Abdallah da idanunshi sukayi jawur da alama yayi kuka, A hankali na laluba gefen da nake tunanin zanji abunda na haifa amma babu shi don haka a wahale nace "Ina Yarona Ya Abdallah?

  Da sauri ya kalle ni tare da kallon Ummana lokaci guda ya mike da sauri ya bar d'aki Umma rabi ce ta matso tana fad'in "Sannu Kin ji ko Muhibba.?

  Gyad'a kai nayi ina cije baki yayin da na kuma bud'e baki a hankali nace "Umma dan Allah zanga yarona."

  Lumshe ido tayi yayin da hawaye suka fito ta matso sosae tare da dafe goshi na tana fad'in "Yana nan Muhibba ki bari ki huta sae a kawo maki shi ki ganshi."


  "Lafiyan shi lau Umma? Na fad;a tare da juyar da kai gefe guda

  Murmushi tayi wanda da gani iyakarshi leb'e kafin tayi magana wannan Nurse d'in ta shigo tana fad'in "Ya mai jikin take? Sannu kin ji ko?

  Ummana ta amsa da "Gata nan ta farka."

  "Allah ya k'ara sauki." Ta kuma fad'a

  "Ya Hasnar take."Ummana ta fad'a a sanyaye

 ,"Alhamdulillah ai itama yanzu ta sauka ta samu yaro na miji."

  Gyada kai nayi jin abunda aka fad'a tare da lumshe ido na bacci yayi awon gaba dani...

  "Alhamdulillah."Umman Maryama ta fad'a

  ***



 #Feedohm
#Haske Writer's Asso...💧💧                               💧💧 *MATAR ABDALLAH* 💥
True life story


                 💥



© *HASKE WRITER'S ASSO* 💡
Home of expert & perfect writers



*MALLAKAR FEEDOHM*

*wattpad :feedohm*



*17*

Alhamdulilah umman Maryam ta fad'a


YA Hasnar tace munfa kawo k'arshen komai dan yarinya an bata danta

idan kuna musawa ku duba karshen labarin

kunga an hutar ku jira kullum  anyinke shi

gadama
Damar ku masu jira



*London*
 Suna sauka su Hadim sunzo taran su FUJJI tana ganin Baban ta da gudu ta jeta ta fad'a masa d'agata yayi yana juyata su Maaf ko ta kansu bai biba har Akkam da yaka ta faman d'aga masa hannu Fuji tace "Abul sai kadin ga tafiya wajen wanan ummul Kaam din kana barin mu meyasa baza ka zauna awajen mum na ba.?
Saida jikin kowa yayi sanyi Fuj zaran zance awajanta ita ko Fandau daukan Akkam tayi tana cewa" a a akai yaron Ummu yazama lukuti ita Hadim dan ta badar da zancen tace "ina  mai Barnon.?
Fandau tace" Emir yana wajen Mama.
Cikin murna Hadim tace "Allah yar uwa to da magana.
Itade Fandau gaba tayi ta shige mota sai.
Hadim tace "shine my star baku gayamin ba nasan zaman da zanyi daku ai ana shide Nabil kama hannun BilAL yayi suka shiga

Fuj bata hakura ba da suka je gida ma sai sake cewa tayi "Abul meyasa kazomin da wannan. ta nuna Fandau
Nabil yace saboda ita ma Momyn kuce.
"no Dad muguwar muce.
 Hadim tace" daughter kidena fadan haka itama Momyn kuce.
Cikin tsawa Fuj tace mum Akam boy ne ta buga kafa tayi sama Hadim ta tashi ta bita wanda Fandau tasan ma lallashin taje yi
Nabil ya fara kame kame
"kin gane Mata shiyaro yana da riko amma idan tayi wayo zata dena.
Fandau tace "ayya
Sai dare Nabil ya gayawa  Hadim yanason mayarda Fuj Islamic school
Hadim fada ta fara kamar ta ari baki Nabil yace "My one nayi tunani akai sosai ba sai macce tayi boko take wayewa ba wayewa yanayine kawai yanzu kiduba Ummul Akkam ba ta taba shiga class wai dantayi boko ba amma gashinan kanta awaye yake duk inda me  kacen da jakan bai dauka ba cikin nusuwa ta fara takawa masu aiki ne suka fara cewa Yasaiyada barka dazuwa amsa musu take cikin gajiya *FUJJIRAT* kenan gwararriyar lacture a Ramad meduguri a fannin Islamic hayani yanda takeji tunkafin ta shiga gidan shi yanuna mata akwai taron samari na family agidan tunda su BilAL suna kasan gidan baya rabuwa da taron samari dan haka kawai ta janza hanya ta zagaya ta baya ta shiga bedroom dinta ta wuce saida ta wasa ruwa tasa doguwar riga ta dauki shijab dinta iya guiwa tasa dan ita tanada cikan kirji books da Heep's ga gidan su gidan tara samari dan haka kullum tana cikin shijab bame ganin su Maaruf yace kannen FUJJI ne saide ace sunyi kanwa ta 3 da iita gaku suna jida kudi dan haka duk abonkan su ba sa an su bedroom din Hadim ta shiga bata ganta ba ta fito parlour Fuhad kanin ta taga azaune yana danne danne a laptop tasan hayani yane ya koroshi a general parlor cikin murmushi yace .
"auntes dama kina ciki  ai da nasani dana shiga kin dauramin karatu .
"a a Fuhad yanzu na shigo ina mum na.?
"Tana part din ummul kaam  tasan idan tace zata ze part din Fandau dole tabi ta wayen yan hayaniyan dole ta waje ta fita ta zagaya zaune ta same su har Abul dinta
Naga Nabil yazama kato haka Hadim ma Fandau ta murje dayake ba jikin kibane dasu ba amma nayi mamakin ganin su duk kamar basu suka ciwannan shekarin ba musamman Fandau  ko Ammati yar auta baza kace ita ta haife taba  cikin nusuwar ta durkusa ta kaida su  Hadim tace "yawwa gwara da Allah ya kawoki FUJJI ki fitar da kwanin ki acikin su dan kinga su BilAL kannen ki har anyanke rana bana son ace su maza ma sunyi sunbar ki.
Shiru Fuj tayi  to yanzu ita waza ta fitarne duk maneman tafison Shamsudeen dan gidan BilAL maina amma shikuma sai jan aji sai kace ba shiya nace ta yarda dashi ba
Nabil yace "yafi mukude nasan yanzu da zannah yananan baku isa ta kai shekara 26 agida ba  kannen bayan ta suna da yara Tajuddin na miji ma yayi aure harda yara 2. 
Ahankali Fuj tace "Mum shamsudeen din yafi ko tana fadan haka ta tashi da sauri ta shige bedroom din Ammati

Su Fuj tunsuna yara da sukayi wayo Hadim da kanta ta gaya musu dukan tarishin su ko da suka san ba itace uwar su ba ba abinda yaragu ason ta sukeyiwa Hadim saima ganin kimanta da suke dan sunfi son ta ma akan Fandau komai mum dinsu

*ARANAN AUREN*
*BIKI BIKI*
*AMFANI SOYYYYA*
*AURE*
Arannan naga iyaye yan Duniya ga Naira da Naira ya hadu gaba daya patyn bikin bawan da ba ayi da iyayen ba irin ta asan da akayi ba a magana Fandau komawa tayi kamar itace amarriyan su Jidda sai tsokanan ta suke Ummul kaam amma ke za acud'a ko

Hadim da kanta ta kai Fujjirat dakin miji kuka ko ba amagana da kyar aka rabasu
Tazo ko a gida tasa Nabil agaba tana kuka yanzu shikenan bazan ji motsin Fuj ba.
Fandau sai dariya take tace "inban da abinki Aunty yau fa amare 2 kika karba nayaran ki to me dan kinfitar da guda 1
Nabil yace "my one kawai kije ki karbo yarki nifa wanan dare nake jiye mata. Ma ga Shamsudeen jimgege dashi.
Dariya Fandau ta kara yi tace aini dadina da kobe zaurin zuwa ni adaren farko uwan wani har sumarni yayi.
Nabil yace "bakomai lada zata samu amma fa afili azuci ko addua yake Allah yasa yabita asannu.
Hadim ko fiton kujera ta dauka ta dinga jifan Fandau dashi Nabil yana karewa
Hadim tace "wllh mugun bakin ki akanki dake da yarki aike ba akwai aiki agaban ki.
Tana gama fadan haka ta haye sama dama girkin Fandau ne Nabil ya kama ta suma sukayi nasa part din
Wanka Fandau tayi tafito ta sameso yana aiki a laptop ta ja tarufe tace "time dina ya shigo dan kasan bana yarda da sakin wannan *DAMAN TAWA*
"Gaskiya ne yan mata wai ke mesirrin ne kinaga duk kin sake zama wata yarinya wllh da keda yan matan dazu awajen bikin banga wani ban banci ba.

"haba kai kake manin haka amma wace Budurwan za asamu haka.

"Bani ka dai ba har abokaina sun sha gayamin basu yarda ba wai kece ki ka haifi su Maaf ba shiyasa Akullum nake tunawa da ranan haduwar mu dake zanje lawan Bor
Na sinci dami a kale ashe itace farin cikina ina godiya da my one dan ita ce dalilin haduwar mu naso nayi wasa da *DAMA TAH* na kin shawaran ta Allah yasoni da rahama
*AMFANI SOYYYYA AURE*
 kinbani yara masu albarka gashi yanzu muna shirin taran jikoki ina yarona. yana magana yana kunce igiyar rigan wankanta zatayi magana ya kifa fuskan sa kirjin ta

*Nima yanzu ya kamata nabar su haka gudun kar Gulma yayi yawa shi yasa ma ban leka gidan amarin ba*

Alhamdulilah

Sai kunsake jina jikin
*AMFANIN SOYYYYA*
wanda nasan zai k'ayata ku yabaku taurayi fiye da dama ta

(Subhanallahi wa'bihamdika Astagfirullah wa'atubu Ilaika)

*MALLAKAR FEEDOHM* 💞

*&*

*BATUL*

*DUK ME MUSU YA KARANTA DUK*  2


*KALA SAI KINYI AYI*

*B JATTKO*💧💧 *MATAR ABDALLAH.!*💥
                   True Life Story.!


                              💥



*©HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers


*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
   *Wattpad:Feedohm*


*18*


     *Wannan page din nakine MEELA ADEEL da yar kanwarki MEENARH PARROT da yan Feedohm novella,Ina K'aunarku matuk'ar k'aunar...💥*


  ***

    Lumshe ido yayi lokacin da d'an mashin d'in ya saukeshi a bakin asibitin, Kud'inshi ya ciro ya bashi sannan ya ida shige wa cikin asibitin,a bakin kofar d'akin da Hasna take yaji muryar Mominta na fad'in "Kiyi hakuri mana yanzu zasu maido maki da yaronki ba sae kinje ba."

  Cikin d'aga murya tace "A'a wallahi momy karb'oshi zanyi mu koma gida, wallahi na gaji da zama anan ita da Allah ya d'aurawa ta zauna idan ta gama jiyar ta iske takardar ta gidan ubanta."

  Lumshe ido yayi ya wuce ya shiga d'akin da Muhibbar take, yaron na k'wance gefenta sae wutsil wutsil yake abunshi yayin da ita kuma take bacci.

  Ganin babu kowa d'akin ya sashi k'arasawa jikin gadon ya zuba masu ido yana kallonsu sosai tausayinsu ya  kamashi, a hankali ya kai hannu ya dafa goshinta, kamar jira take ta dub'e idonta tana kallon shi sannan ta mayar da kallonta inda taji yaro na wutsil wutsil

  A hankali ta saki murmushi tare da sa hannu ta shafi yaron tana kallonsa ta dad'e tana kallon yaron sannan ta juya ga Abdallah.

   Cikin sanyi murya tace "Kaga yarona ko Abdallah?kaga yana kama da kai ko.?

  Gyad'a mata kai yayi tare da janye hannunshi daga goshinta ya d'aura saman bakin shi yana kallonta...

  "Tunda na haifa maka yaro zaka sake ni ne ko Abdallah.? ta fad'a muryar ta na rawa

  Da sauri ya kalleta tare da girgiza kai a hankali.

  Cikin rawar murya tace "Dan Allah Abdallah idan ka sake ni ka bar man yarona gurina nima ina sonshi wallahi na maka alk'awarin da ya girma zan mayar maka da shi kar ka raba mu yaro ne zaiyi kuka idan bana kusa."

  A Hankali ya kira sunanta "Muhibba! bazan raba ki da yaronki ba kuma bazan sake ki ba."

  "Da gaske Abdallah? ta fad'a idonta tab da hawaye

  Gyad'a mata kai yayin da shima idonshi ya cika da k'wallar muryarta yaji tana fad'in "Har yanzu ina sonka Abdallah."

  Hannunta ya rik'o gam ya saki kuka mai cin rai.


**
     Jimawa kad'an Umman Abdallah ta dawo ita da K'anwar Abdallah Aisha ganin babu yaron yasa Aisha ta tambayi hasnar "Ina yarona yake Aunty Hasna.?

   A Hasale ta ce "Ban sani ba."

  Momin Hasnar ce tayi saurin fad'in "Aisha yaronki yana can d'akin ana bashi mama, kije ki ganshi a can kinji ko." ta nuna mata d'akin.

  Umman Abdallah tace "Wae har yanzu ba'a maidoshi bane.?

  Gyad'a kai tayi tace "Eh muma dae munji shiru.?

  "To wake bashi nonon ne.?Ta tambaya tana kallon Hasnar

  Kai tsaye Hasna tace "Wannan mai aikin tawa ce ke bashi da yake itama ta haihu sae dae yaronta bai zo da rai ba."

   Gyad'a kai tayi tana fad'in "Allah sarki ashe itama tana da aure kuma tazo tana kula dake?

  Ganin sunyi shirune yasa tace "To ko zamu je mu ganta.?

 Momin Hasna ce ta fito da rafer ta dari biyar biyar guda biyu ta mik'awa Umman tana fad'in "Ga wannan kema kinyi wata hidimar dasu.

  Dariya tayi ta karb'a tana fad'in "An gode sosai wallahi, ai mu kam bamu da abunda zamuce maku sae dae addu'a Allah ya k'ara d'aukaka Allah ya baki lafiya Hasna kin ji ko.?

   Aisha kam ba tace komae ba ta juya ta nufi d'akin da aka nuna mata  ita dae har ga Allah wannan Hasna ba yi mata tayi ba haushi ma take bata, d'an k'aramin tsaki ta saki tare da tura k'ofar d'akin ganin Abdallan tsaye yasa ta d'an saki ranta ta nufi shi tana fad'in "Yaya Abdallah waccan matar taka batta da mutunci wai naje ina tambayarta ina yarona shine take man tsawa, Ina yaron Yaya Abdallah.?

  Da hannu ya nuna mata shi ta nufi yaron da murmushi ta d'aukeshi "Masha Allah gaskia dani yake kama Yaya Abdallah." Ta fad'a cikin farin ciki


  Sannan ta juyar da kanta ga Muhibba tana fad'in "Sannu baiwar Allah."

 Gyad'a kai Muhibbar tayi tare d'an k'aramin murmushi tana kallon yaron

  Maganar Aisha ne ya daketa jin tana fad'in "Gaskia Yaya Abdallah yaron na da k'yau Allah ya taimakemu baiyi kama da Aunty Hasna ba."

  Jin yayi shiru ya sata cigaba da fad'in "To wae ma Yaya Abdallah idan aka sallami Aunty Hasnar waye zai cigaba da shayar da yaron? ko wannan d'in zata biku gidan ku ne sae ku dinga biyanta tunda ita yaron nata ya rigaya ya mutu tunda dama ana haka ko kuma ita zaku barwa yaron.?

  Waro Ido tayi tana kallon Abdallah cikin, k'yarma ta mik'a hannu tana fad'in "A'a yarona nane wannan ki bani abuna dan Allah."


  Kallonta Aisha tayi tana fad'in "Ke wannan yaron Aunty Hasna ne fa, ke naki ai ya mutu ko basu fad'a maki ba.? ta k'arashe maganar tare da juyawa zata fita.


  Wata uwar zabura tayi ta wulk'ito k'asa cikin kuka tace "Nawa ne mana baki gani ba ne? ki bani abuna dan Allah."

 Da sauri Abdallah yayi kanta ya d'agata ya mayar da ita saman gadon, cikin kuka ta kalleshi tace "Ka karb'o man yarona Abdallah, ka fad'a mata wannan nawa ne bana Hasna ba kaga zata fitar man da yarona."


  Muryar Hasna taji tana fad'in "Ta ina ya zama naki? bayan naki ya rigaya ya rasu? ko kin k'ara haihuwar wani ne?ke Aisha mik'o man yarona."

  Jikinta ne ya fara rawa yayin da ta cakumi rigar Abdallah lokaci guda idonta duk suka fito waje, cikin rawar murya tace "Da gaske ba yarona bane Abdallah? Da gaske yarona ya rasu?Me yasa baka tsayar dashi ba Abdallah? Me yasa ka barsa ya tafi ya barni? Dan Allah ka dawo man da yarona Abdallah, Dan Allah kace masa ina son na ganka, Abdallah Ko gawar yarona ina son na gani." Ta k'arashe maganar cikin wani irin matsanan cin kuka

  Shi kansa k'irjinsa ke wani irin masifar bugawa yayin da ya rik'e hannunta gam sae k'yarma yake ganin jini ya fara b'ata bedsheet d'in da take yasa hankalinshi ya k'ara masifar tashi

  Numfashinta ke neman fita daga jikinta a hankali ta cigaba da fad'in "Ku bani gawar yarona Abdallah na gani, Dan Allah ka taimaka man Abdallah ban gansa ba, Ina son yarona Abdallah."
 
  Lumshe ido tayi tare da komawa ta sume, wata irin jijjiga yake mata tare da marin fuskarta kamar mahaukaci yana fad'in "Ki tashi Muhibba yaronki ne wallahi, babu wanda ya isa ya rabaki da yaronki, ki tashi Muhibba, dan Allah ki tashi..."

  Da sauri Aishan ta kalleshi tana fad'in "Me kake fad'i haka Yaya Abdallah?

  Gurin Aisha ya matsa tare da warce yaron a hannunta ya dawo ya daura shi saman k;irjin Muhibbar cikin kuka yake fad;in "Dan Allah ki tashi Muhibba, ga yaronki nan na mayar maki da abunki, ki tashi dan Allah."

  Hasna ce ta juya a fusace ta bar d'akin yayin da ta koma d'akin da Umman Abdallah ke cikin kuka take fad'in "Na shiga uku Umma Abdallah yace ba yarona bane wae na yar aikina ne kuma d'an shi."


  Cikin tashin hankali Umman ta tashi tsaye tare da rike kafad'ar Hasnar tana fad'in "Bangane ba Hasna, fad'a man me ke faruwa? kamar ya ba yaronki bane.?

  Kuka ta kuma saki da k'arfi ta durk'ushe tana fad'in "Wayyo Ummana naa shiga uku dan Allah ki taimaka ya k'wace man yarona, Umma yaron yar'aikina ce yace fa? Me yasa Abdallah ya man haka Umma? Me yasa ya ci amanata ya dinga tarayya da yar' aikina har ya mata ciki? Umma Abdallah ya cuceni ya ci amanata bayan duk irin halaccin dana masa a baya."

  "K'aryane yaronki ne Hasna tashi muje wallahi babu wani munafurcin da ya isa ya hanaki yaronki, wannan ma wane irin tozarci ne? Uban wa yace yaron na yar aikin ki ne.?

  Hannunta ta ja suka fice da sauri suka fad'a d'akin bata yi wata wata ba ta nufi kan Muhibbar tare da warce yaron ta mikawa Hasna, karb'e yaron Abdallah yayi yana kallon Umman idanunshi tab da hawaye yace "Ba yaronta bane Umma, dan girman Allah ku barwa Muhibba yaronta."

  Wani lafiyyan mari ta sakar mashi tana fad'in "Yaron matar ka zaka d'auka ka bawa yar aikinta Abdallah? Ina hankalinka ya tafi? Uban me ka shawo? Dama na dad'e ina zargin kana yan shaye shaye Abdallah."

  "Bansha komae ba Ummana, wallahi da gaske nake ba yaronta bane Umma ita ma ta sani dan Allah ki tsaya na maki bayani."

  Wani banzan kallon ta watsa mashi tana tambayarshi"Bayanin banza! dan Ubanka fad'a man waye?

  Durk'ushewa yayi yana fad'in "Na Muhibba ne kuma ita ma matata ce ma Umma."

  "Ka dae ci amanar mu Abdallah, dama Hasna ta sha fad'a man ta sha kamaka d'akin yar aikin ni ce ban yarda ba ashe dae da gaskiyarta,  Ba kayi halin Mahaifiyarka ba Abdallah "Cewar Momin Hasna dake tsaye gefe

  Idon Ummanshi ya cika da k'wallah "Idan wannan kace yaron yar' aikin ku ne to inna yaron da Hasna ta haifa Abdallah.?kenan da gaske hasna take kai fasik'i ne Abdallah.?

  Girgiza kai yayi da sauri idonshi tab da hawaye " Babu ko d'aya Ummana, Wallahi ban tab'a zina ba kuma wallahi Hasna bata haihu ba."

  "Karka mayar dani yar iska Abdallah? Ka fad'a man yaron waye waccan?

  Muhibba ya nuna tare da kanshi yana kallon su, kukan da Hasna ta saki ya dawo da hankalinsu a kanta yayin da fad'i kasa tana birguma "Na shiga Uku Momi, Abdallah ya sace man yarona kenan ya bawa yar aikina? Ummana dan Allah ki taimaka mani ya dawo man da yarona."

   Cikin tashin hankali yake kallonta "Wane yaro take magana? bayan tasan bata da yaro."

  Cikin tashin hankali Umman ta cakumi k'walar shi yayin da take sakar mashi mari ta ko'ina tana fad'in "Dan Ubanka ka fada mam gaskia Abdallah, ka fitowa da Hasna yaronta."

  Gadon Umma ta nufa ta finciko yaron tare da jefashi jikin Abdallah tana fad'in "Yaronka zaka d'auka ka bawa wata karuwa kenan Abdallah? ka bata yaronta tun kafin na tsine maka albarka."

  Maryama ce ta fad'o d'akin tana fadin "Allah Saeki Muhibbata an." Shiru tayi tana kallon mutanen dake cikin d'akin kafin ta nufi Gadon Muhibbar da sauri.



#Feedohm💧💧 *MATAR ABDALLAH.!*💥
                   True Life Story.!

                              💥

*©HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
   *Wattpad:Feedohm*

*19*

  ***

Juyowa tayi tana kallonsu da idonta da suka kad'a sukayi jawur ganin Muhibbar ko numfashi bata yi amma sam hankalinsu ba gareta yake ba, nuna Abdallah tayi cikin rawar murya tace "Me ya sami K'awata Abdallah? Ka fad'a man me ya samu Muhibba? Wallahi kar ka kuskura wani abu ya sameta don bazan tab'a barinka ba Abdallah."

  Babu wanda ya bata amsa sae Abdallah da yayi kan Muhibbar yana kiran sunanta ita kam Maryama ta fice da gudu tana kiran wata nurse da ta fito daga wani d'aki opposite dasu.

  A tare suka shigo da nurse d'in yayin da ta nufi gadon Muhibbar domin dubata amma Momin Hasnar ta tsayar da ita ta hanyar d'aga mata hannu cikin tsawa take fad'in "Ya isa haka Sister Luba karki kuskura ki tab'a ta."

  Cak Sister Lubah d'in ta tsaya yayin da Maryama ta juyi a sak'wane tana kallonta mayar da kallonta tayi ga Abdallah  da yake k'ok'arin daukar Muhibbar   jin abunda momin Hasna ta fad'a

  Cikin tsawa tace yayin da idonta ya cika da k'walla "Karka kuskura ka tab'a man K'awa Abdallah.!

  Tureshi tayi da k'arfi daga kan Muhibbar ta fice da gudu sae gata ta dawo da maza guda biyu a bayanta, cikin k'yarma ta nuna masu Muhibbar yayin da sukayi kanta,  ganin suna niyyar d'aukar ta yasa Abdallah yayi kansu cikin tashin Hankali yana fad'in"Karku tab'a man Mata."

  A harzuk'e Maryama ta juyo tana fad'in "Tun daga ranar da ka soma zaluntar ta na cireka a matsayin mijinta Abdallah."

  "Wallahi ba wanda ya isa ya fitar da ita daga asibitin nan muddun baa biya mu kud'in aikin da aka mata sae dae ta mutu a nan."Muryar Hasna ta daki dodon kunnenta

  Da sassarfa ta k'arasa kusa da ita ta cire sark'ar zinarin da ke wuyanta da yan kunnen ta damk'a a hannun Hasnar ta juya a fusace tana fad'in "Banda lokacin ki yanzu Hasna amma wallahi baki sha Maryama a banza ba, sae na tabbatar maki da bunsurun da ya tara kud'in kika d'auka a k'ark'ashin tafin hannun Maryama yake."

Mazan ta kalla tace "Ku taimaka ku d'auketa mu tafi dan girman Allah."

  Suna fita Abdallah ya bi bayansu yayin Umman shi  ta janyo shi cikin kakk'ausar murya tana fad'in "Ka fad'a man wacece waccan Abdallah.?

  Cikin tashin hankali yace "Matata ce Umma."

Lafiyayyen mari ta bashi tana fadin "Gidan uwar wa ka aureta? da sanin wa ka aureta?

  "K'arya yake Umma wallahi yar aikina ce yake lalata da ita har ya mata ciki shine yace na rufa mashi asiri, har ya kawota asibiti ta haihu yaronta ya mutu, shine ya d'auke nawa ya bata, ki taimaka mani Umma." Hasnar ta fad'a tare da k'ank'ame Yaron jikinta

  "Inna lillahi wa inna ailaihir rajun Amma Allah ya isa Abdallah! Allah ya tsine maka Albarka ashe mugun halinka har ya kai ga haka? har ya kai ga kayi zina har ka samu shege? sannan ka k'wace wa matarka yaro ka bawa karuwarka? ka ci amanata ni mahaifiyarka! kaci amanar matarka wallahi bazan tab'a yafe maka ba."

Cakumar wuyanshi tayi tana fad'in "Meye ribarka Abdallah.?

  Cikin kuka Aisha tace "Me yasa zaki yarda da abunda wad'annan mugayen suka fad'a maki Umma? Me yasa shi bara ki saurareshi ba?kenan bare sun fiye maki d'anki Umma.?

  Duka ta kaiwa Aishan tana fad'in "Ki rufe man baki dan ubanki don wallahi Hasna ta fiye man Abdallah sau dubu."

Banda hawaye babu abunda ke fita daga idanunshi a hankali yake kallon Hasna dake tsaye rik'e da yaro a hannunta yayin da ya mayar da kallonshi ga Mominta tabbas ya yarda mace bala'i ce domin tana iya kaika cikin jahannama da k'afafunka.

   Da k'arfi Umman ta turashi "Fita ka bani guri Abdallah bana son ganinka,wallahi na tsaneka, ka zubar mana da mutunci a idon duniya ka gama wulak'anta ni Abdallah, ka fita nace maka." ta k'arashe maganar cikin tsawa tare da durk'ushewa gurin tana kuka

  Juyawa yayi a hankali yana kallon Hasnar yayin da yayi kanta cikin sark'ewar Murya yace "Kin cuceni Hasna kin b'ata man rayuwa, banda zuciyar da zan ce maki Allah ya isa kawae na barki Hasna, wallahi ko da zanyi yawo tsirara sae na tabbatar da kin kwashi abunda kika shuka a rayuwarki! Bani yarona Hasna, wallahi bazan taba bar maki yarona ba."

  Sama da k'asa ta kalles hi tana fad'in "Wallahi baka isa ba Abdallah har ka mance alkawarin mu koko ka mance Wacece Hasna?Me zaka iya man banza talaka da kai? ka ci sa'a har yanzu Hasna na sonka amma wallahi da ko asibitin nan baka fita ba da k'afarka."

  Cikin tsawa yace "Ki bani yarona Hasna."
 
  "Ba ka ji bane? Nace bazan bayar ba Abdallah."Ta fad'a a tsawance

  Ummanshi ce tace "Ka fita nace Abdallah, wallahi idan baka bar mata yaron nan ba rayuwarka bara ta tab'a yin dae de ba, sae na tsine maka Abdallah ka wulak'anta ta yarda ko kare sae ya fika albarka."

   "Ko da zan fi haka tozarta bazan fita babu yaron nan a hannuna ba Umma, bazan yarda na raba UWA DA D'A ba."Ya fad'a tare da fizge yaron daga hannunta

  Yaron ya tsalle da kuka yayin da ya fita da sauri daga dakin bai ko juyo ba, Zaman dirshan Hasna tayi ta saki kuka tana fad;sin "Yarona Umma, ki k'arbo mani yarona Dan Allah."

  "Banda halak'a da Abdallah bare har na k'arbo maki Yaronki Hasna,amma kuto kadae zata iya karb'o maki yaronki."Umman Abdallah ta fad'a cikin sark'ewar Murya.

**

  Maryama kam cikin motar da tazo da ita aka saka Muhibbar yayin da ta ja Motar da k'arfi ta nufi asibitin garkuwa da ita saboda can ake dubata, cikin sa'a ta iske Dr d'in nan sun karb'eta bayan tasha fad'a sosae daga gurinsu, waje ta fito ta kira wayar Umman Muhibbar ta fad'a mata suna garkuwa sannan ta kira Mamanta itama ta sanar mata.

  Suna gama wayar sae ga Abdallah cikin gidan da jariri a hannunshi , Umman Muhibbar ta nufeshi a rud'e tana fad'in "Lafiya Abdallah? Me ya faru ka fito da yaro haka ko malullub'i babu.?

Mika mata yaron yayi ta karb'a da sauri tana fad'in "Me ke faruwa ne Abdallah?

  "Yaron Muhibba ne Umma na kawo maki."Ya fad'a tare da duk'awa bisa guiwowinsa

  Baffa ne ya fito da buta a hannunsa ganin Abdallan a tsugunne yana kuka ya sashi k'arasawa da sauri gurin yana tambayar "Lafiya? Me ke faruwa ne Abdallah.?

  Cikin kuka ya fara basu labarin Abunda ya faru tun daga farkon neman Aurenshi da Muhibbar har zuwa yau.

  Umman ce ta kalleshi tab da hawaye tare da nuna mashi kofa tace "Tashi ka fitar mana daga gida Abdallah."

  Cikin sanyin Jiki Baffa yace "Me yasa kayi haka Abdallah.?

Kuka ya saki yana fad'in "Wallahi sharrin shaid'an ne Baffa da kuma Matata Dan Allah ku yafe man Baffa wallahi komae ya canza man."

  "Dan Allah kace ya fitar mana daga gida Malan."Cewar Umma tare da juya masu baya

  Kallon Abdallah yayi a hankali yace "Da daddare ka dawo muyi magana da kai Abdallah."

  Kasa tashi yayi har sae da Baffan ya d'agashi ya rakashi har bakin kofa sannan ya dawo gurin Umman dake zaune tana kuka tana ganinshi ta saki sabon kuka tana fad'in "Yaron nan ya cucemu Malam, wallahi ya cuci Muhibba insha Allahu sae yayi kuka da idanunsa."

  "Allah kyauta." Abunda ya fad'a kenan tare da d'aukar butarshi ya nufi makewayi,

   Yaron ta d'auka ta goya ta sab'i hijabin ta, a bakin k'ofa ta ci karo da yan sanda tsaye da yaron mak'wabtansu yaron na ganinta yace "Yauwa ga Umman Muhibban ma can."

  Tana k'ok'arin Kewayesu taji wani na fad'in "Malama kece Uwar Muhibba."

  Banza ta masu duk da gabanta ya fad'i ta tsaya cak sae dae bata juyo ba.

  "Ke ce Uwar Muhibba.? ya sake maimaitawa

  "Eh."

Takarda aka miko mata ta k'arba ta dub'e wae an zo tafiyane da Maryama da Muhibbarta.

   Cikin tashin hankali ta kallesu tace "Akan wane dalili.?

  "Idan munje can an maku bayani."Ya bata amsa a dak'ile yana kallon yanayin gidan

  Juyawa tayi a fusace ta koma cikin gidan sae gata da Baffa a bayanta, mika masu hannu yayi had'e da sallama, babu wanda ya amsa ciki sae ma ce wa sukayi "Ba jiranku zamu yi ba."

  Dan murmushi Baffan yayi yana fad'in "Bayin Allah me ita Muhibbar tayi? bayan tana can k'wance gadon asibiti."

  "Ko gadon mutuwa take sae mun tafi da ita."Wani ya fad'a a tsawance

  "Bance bara ku tafi da ita ba, amma dai bata nan gidan tana asibiti." Baffan ya fad'a cikin taushin murya

  "K'arya kake."Ya fad'a kai tsaye

Shiru Baffan yayi yana jinjina kai kafin d'an sandan yace "Ina Maryam?

  Banza ya masu har sae da ya maimata sau biyar amma babu amsa a fusace ya kalli yaran da suke tare yana fad'in "Ku shiga ku bincika gidan ku fito man dasu tunda bara yayi magana ba."

  Kewaye Baffan sukayi yayin da Umman ta kalleshi cikin kuka tana fad'in "Kayi wani abu mana Malan."

  Murmushin takaici ya saki yana yana kallon ilahirin mutanen dake kewaye dasu suna kallonsu cikin sanyi murya yace "Me zanyi masu? ba kiji  wannan yaron yana k'aryata ni bane? ki barsu su shiga duk wulakancin da sukayi niyyar suyi Allah baya bacci."

  Kuka ta saki cike da tashin hankali, Yan sandan kuwa haka suka gama masu watsi da kaya suka fito sannan suka turasu mota  suka tafi dasu police station.

**

  Abdallah kam number Maryama ya soma nema amma sam tak'i d'agawa daga k'arshe ma black list ta sakashi.

Kusan zaucewa yayi yayin da ya samu gefen titi ya tallab'e kai yana sambatu sae da ya k'washi kusan awa d'aya sannan ya tashi zumbur yana fad'in "Yauwa Muhibba gidansu ta kaiki ko.?

  A Kafa ya fara takawa ya nufi gidansu Maryama sae da yayi tafiyar kusan awa d'aya da rabi sannan ya isa gidan sae shashsheka yake yayin sa k'afarshi duk tayi bororo, Bubbuga gate d'in ya fara kamar zai balle maigadin ya lek'o yana fad'in "Wane hege ne anan.?

  Dashe baki yayi yana fad'in "Owo ashe mijin K'aramar Hajiya Muhibbane, aiko yanzu su Hajiyar su ka fita ina jin kasuwa ma suka tafi, don naga har da kwand'on da zasu zubo kayan kasuwar."

  Cikin k'yarma yace "Wace kasuwa?

  Dashe baki buzu yayi yace "Ina jin kasuwar dake da hanyar sama a gefenta."

  Juyawa yayi da sauri ya tafi yayin da buzu ya koma cikin gidan abunshi, Abban Maryama ne ya fito yana fad'in "Buzu bud'e man gate zan fita."

  "Sae ina Alhaji.?

Murmushi Abban yayi yace "Baka san an k'wantar da Muhibba asibiti bane?

  "Owo shine naga su hajiya sun fita dazu da kwand'o a hannu? Aradu nasha kasuwa zasu je."Ya fad'a had'e da d'age kai sama

  "Kaga bud'e man gate banson surutu."Abban ya fad'a tare da bud'e mota ya shige

#Feedohm


Download Matar Abdullahi Littafi Na Daya Complete