Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
        (admin
   Arewa hausa novels 
       Novels villa
     Duniyan novels 
   Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
          And 
Cool novel, makeup and cooking) 

      WHATSAPP NO:
    +2347039625239
TUN KAFIN AURE💐1
Motsi kadan sai ta daga labule ko zata ga
shigowarsa amma shiru. Dawowa tayi falo ta
shimfida abin sallah don tana gudun kada ya
dawo ya shige daki bata sani ba. Tayi raka'a
takwas duk biyu tayi sallama ta sake tashi ta
daga leka wajen, wannan karon ruwa akeyi
kamar da bakin kwarya tayi ajiyar zuciya...daya
daga cikin lokutan amsar addua kenan sai ta
koma kan abin sallar ta fara addua. Tana yi tana
kuka bukatar tata bata wuce Allah Ya shirya
mata Junaid ba. Jin alamar shigowar mota gidan
yasa tayi saurin kashe fitilar falon ta koma gefe
ta tsaya. Bata dade ba taji ya bude kofar a
hankali ya shigo da sanda kamar wani barawo.
Mamaki ne ya kamata yadda yake da key din
kofar bayan ta rufe ta sannan ta kwashe duka
keys din. Yana kokarin hawa sama ne yaji ta
haske masa fuska da touch light din
wayarta....wane dan kut....maganar ce ta
makale a bakinsa ganinta a tsaye fuskar nan
kamar bata taba dariya ba. Duk da a buge yake
amma sai da gabansa ya fadi.
Saukowa yayi yace Mommy ina wuni...wunin
uwarka Junaid? Nace wunin uwarka. Matsowa
tayi ta cire hannu ta kwada masa mari har sau
uku sannan ta koma ta zauna idanunta cike da
hawaye.
Bai iya cewa komai ba don yasan bashi da
gaskiya. Yana kallo tana masa kukan nan da ya
tsana har cikin zuciyarsa yake jin abin. Mommy
ya kira ta a hankali bata ko kulashi ba sai da
tayi mai isarta ta tashi ta haska masa agogon
bango. Karfe nawa yanzu ta tambayeshi. Hudu
da minti ashirin ya bata amsa kansa a kasa. Mu
je kayi wanka kawai tace masa. Ba musu ya hau
sama tana bayansa yana tangadi amma yana
iyaka kokarin dannewa wai kada tace ya sha
wani abu. Suna zuwa kofar dakin tace idan kayi
wanka kayi alwala ka sauko ina jiranka.
Daki ta wuce ta kalli maigidanta da yake ta
uban minshari ta ja dogon tsaki. Ita kam kudi
bai zamu musu komai ba sai silar watsewar
tarbiyar yaronta. Allah Yasa ma yaran basu da
yawa su uku ne. Babbar Nafisa tayi aure itama
mai bin Junaid din
Hamida tana gidan mijinta. Shi kadai namiji ya
zame mata jarabawa a gidan duniya. Mijinta
Senator Rufai Bukar ya rike mukamai da dama
har zuwa lokacin da ya fara siyasa yanzu haka
karo na biyu kenan da aka sake zabarsa sanata.
Ko kadan bashi da lokacin iyalinsa saboda tafiye
tafiye idan yana kasar kuwa daga office sai
bacci. Baya taba bincikar halin da yaransa ke
ciki amma duk karshen wata zasu ji alert mai
kauri a account dinsu. Gaba daya lalacewar
tarbiyar Junaid bata gabansa. Alwala ta sake
sannan ta tashe shi ya sauko suyi sallah a kasa
tare da maaikatan gidan tunda ana ruwa.
A falon kasan ta tarar da shi yana nafila tace
cikin takaici ko kunya baka ji ka gama aikin
sabo ka zo ka tsaya gaban Allah kana neman
biyan bukata. Masu aikata laifi bisa kuskure ma
suna tsoron haduwa da Allah amma kai naka
lamarin kana sane kake takewa. Alhaji dake
saukowa daga bene a lokacin yace ni kuwa bana
so yaro yana kokarin shiryuwa kina sagar masa
da gwiwa... Alhaji kenan ta fada tana shimfida
abin sallah wallahi ina dada baku shawara kai
da Junaid kuji tsoron Allah. Akwai ranar kin
dillaci ranar da dukiya bata da wani amfani.
Daga mata hannu yayi to malama naji zan masa
fada ince dai shikenan ko.
*********************
Hafsi! Hafsi!! Hafsi!!! Dagewa tayi ta sakar mata
duka a baya. A gigice ta dago kai Ummati lafiya
kika doke ni. Kujera ta jawo ta zauna kusa da
aminiyarta, naga kin zurfafa a tunani ne. Tunda
ansa rana ya kamata ki rage tunanin Saif haka.
Ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a cikin
randa. Ke ko tunanin exams kike? Nima da tawa
'yar brain din ban tsorata ba sai ke. Ajiyar
zuciya Hafsi tayi ta kalli kawarta Ummati wai
kinsan ya mukayi da Saif kuwa jiya? Me ya faru
ta tambaya cike da zumudi. Ita dai soyayyar
Hafsi da Saif tana burge ta. kamar abin arziki ya
nuna min hotunan wasu abokansa da sukayi da
matan da zasu aura sai daga baya yace ai tunda
ansa rana muma yana son muje muyi. Dadina
dake sokonci kin manta mun taba hirar dake
lokacin da muka ga na Aliya Yunusa duk muka
ce muna so. Ke kanki kin yaba da kyan da suka
yi. Gara da kika ce yabawa kinsan ko da wasa
bazan iya tambayar Mama ba ma balle Baffa.
Bazasu taba barina naje ba shiyasa ma na cire
abin a raina, amma ina fada masa haka da fushi
ya tashi rai a bace.
Ummati ta dafa kafadar Hafsi bari mu fito daga
exam dinnan sai muyi shawara. Karatu suka
cigaba har malamansu suka shigo ajin aka fara
jarabawa.
Suna tsaye a bakin gate din makarantarsu
Health Technology dake cikin birnin Kanon dabo.
Ummati ta zunguri Hafsi tana waigowa ta danyi
murmushin yake. Kana ganinta kasan tana cikin
damuwa. Ke na samo mana mafita fa. Nan take
hankalinta Hafsi ya kwanta har suka samu
adaidaita sahu suka tafi gida.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 2
A tsakar gida ta tarar da mamanta tana dinki.
Bayan sun gaisa Mama ta tambayetajarabawa.
Alhamdulillah tayi sauki sosai. Hmmm kinji ki
wai tayi sauki sosai to a bita da addua dai. In
sha Allah ta bata amsa tare da shigewa daki.
Tunani kawai take yi na yadda zata gabatar da
plan din da suka yi da Ummati idan ba haka ba
sai dai Saif yayi hakuri. Amma tasan halinsa
sarai na fushi. Gado ta fada tana juyi. Idan
akwai abinda ta tsana bai wuce fushin Saif dinta
ba. Ina ma dai yayi hakuri har zuwa lokacin
aurensu sai ayi kowanne hoto yake so ta fada a
ranta.
Sauransu jarabawa uku su gama makarantar
gaba daya sai dai har yau ta kasa fadawa
Mama. Hafsi ta rasa me yake mata dadi domin
kuwa daren jiya da Saif yazo baram baram suka
rabu. A cewarsa bai taba tambayarta komai ba
sai wannan ta gagara yi masa. Da bacin ransa
tayi bacci 'yar wayar daren ma da suke yi yaki
kiranta da ta kira kuma yaki dauka.
Shewar Ummati ta jiyo tare da kannenta Amira
da Anisa. Da sauri ta fito ta jawo hannunta suka
koma daki. Ummati ta kalle ta to sarauniyar
masoya yau kuma me ya faru? Tunda naji
muryarki kamar zaki yi min kuka nasan an taba
zuciyar. Ba kya ma tausayina wallahi naga abin
har dariya yake baki. Plate din abincin da Hafsi
ta zuba amma tunani yasa ta kasa ci shi
Ummati ta dauka tana ci...bakinta cike da abinci
tace bana tausayinki zan zo yau. Ai don nasan
Baffa yana gida yau ba aiki ne ba bari zaiyi ki
fito ba. Ni fada min me ya faru. Hafsi ta zauna
kan dadduma tace akan zuwa daukan hoton nan
ne fa. Kwarewa Ummati tayi tana kokarin yin
magana. Amma dai ke anyi banza wallahi Hafsi,
ina ce tun last week muka rufe zancen nan.
Ajiye plate din tayi ta tashi ina zuwa...ganin
zata fita Hafsi ta bita da gudu tsaya don Allah
ina zaki. Ko sauraronta bata yi ba ta shige
kitchen wurin mama. Mama kinga Hafsi
ko...dago kanta tayi daga tsintar waken da take
yi me tayi miki kuma ku da ba kwa rabo da
fada. Wai nace mata ranar da muka gama
exams tunda ta safe gare mu ranar tazo muje
daukan hoto shine tace wai bazata ba. Mama
tun shekaranjiya nake mata magana tana kin
bani amsa shine nace bari nazo kawai na fada
miki. Kun fiye shirme ke da yar uwar taki meye
abin fada a nan. Kinsan halin Baffanku sarai
baya son fice fice ba gaira babu dalili nasan
abinda take tsoro kenan. Ummati wadda ta
zauna a kasa tana taya ta tsintar waken tace
Mama dama wai na tarihi nake son muyi ranar
tunda kinga ni Bauchi zan....karasa mana bauchi
zamu kaiki ko. Tashi tayi zata gudu Mama tace
ba komai zan fada masa ranar da ku ka gama
din sai kuje kuyi hoton shikenan ko. Nagode
nagode nagode abinda ummati take ta fada
kenan har ta fita daga kitchen din. Ita kuwa
Mama dariya take sai dai bata san me yaran ke
kullawa ba.
********************
Kwance yake kan makeken gadonsa yana zukar
wata irin taba mai kauri da tsaho, bai ankara ba
kawai sai ganinta ya yi a tsaye bakin gadon. Ah
sis saukar yaushe...harara ta galla masa kafin
ta fizge tabar. A jikin wandonsa ta kashe ta ai
kuwa ba shiri yayi ihu tare da mikewa yana
kokarin cire dogon wandon. Sis don mugunta sai
ki kona ni me nayi miki kuma daga zuwanki. Ko
da ya cire wandon saman gwiwarsa ya fara
alamun tashi. Ta zauna ai kadan ma ka gani
wutar can tafi wannan. Jin yanayin maganarta
yasan mommy ta kai shi kara wurinta ne. Daure
fuska yayi yace to idan kinzo ganewa idonki ne
kinyi sa'ar gani sai ki fita....rayuwa kowa da
tasa so please let me be. Duk ranar da na gaji
ke zan fara sanarwa. Yana gama magana ya
shige toilet tare da banko kofar da kafa daya.
Har zuciyarta taji sautin ta mike a sanyaye.
Zuwan Junaid America certificate kala kala ya
samu banda na school harda na shaye shaye,
neman mata da tsabar kin ji. Baya ganin kowa
da gashi ciki kuwa harda mahaifin nasu da ya
dage sai dansa yayi karatu mai tsada.
Dakin mommy ta shiga ta zauna a gefen gado
tayi tagumi tana jira mommyn ta idar da sallah.
Ya dai Nafisa kunyi magana da kanin naki. Hmm
mommy ai lamarinsa sai addua kawai ta fada
tana tabe baki. Nan ta labarta mata yadda suka
yi. Mommy tace to ni dai na gaji zan sanar da
Hajiyan Dangi halin da ake ciki kafin yaron nan
ya dauko mana magana. Zaro idanu Nafisa tayi
cikin tsoro tace Hajiyan Dangi....wai .
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 3
Cike da murna Hafsi ta kira Saif ta sanar da shi
an bata izini a gida amma sai ta gama exams.
Yayi matukar farinciki da jin hakan. Hafsi
kyakkyawa ce ga kyan jiki. Tun farkon
haduwarsu yayi ta fama da samarin da ke sonta
kala kala Allah Ya taimake shi ta zabe shi kuma
yayi saa mahaifinta bashi da wasa wurin sa ido
akan lamuran 'ya'yansa. Duk da kasancewarta
ba fara ba saboda babanta mutumin maiduguri
ne amma yanayin fatarta mai kyau ne kamar
'yar hutu. Duk wanda ya kalle ta sai ya kara
saboda haka Saif yake godewa Allah da wannan
tsaleliyar budurwar take sonsa.
'Yan ajinsu suna ta faman rokonta su tsaya ayi
hoton tarihi ciki kuwa harda Ummati amma ita
duk hankalinta yayi gaba. Gefe ta jawo kawar
tata. Ummati wai kin manta da abinda ke
gabanmu ne yau kin tsaya sai hira kike yi. To
sarkin azarbabi ko dan jan aji ai kya yi masa
yasan kema kina ji da haduwa. Ki bari muyi
sallama da mutane cikin mutumci. Da kyar Hafsi
ta bari sukayi hotuna sannan suka wuce gida.
Cike da doki tayi wanka ta debo kayan sallarta
da wasu kaya masu kyau har kala hudu ta zuba
a leda. Tana cikin shiryawa Saif ya kirata. Tana
dauka ya suma magana.
(Matar baku shirya bane? Na kusa karasowa
gidanku fa)
Ji tayi gabanta ya fadi don bata fada masa da
yadda aka barta ba. Kashe murya tayi cike da
shagwaba.
( Saif kada ka zo please Baffa zaiyi fada. Ka jira
mu a bayan layin su Ummati idan ka iso yanzu
zan fito nima.)
(Ai duk yadda kika ce haka za'ayi matar. See
you soon)
A gaggauce ta fito ta ce Mama zan je gidansu
Ummati daga can zamu wuce. To Allah Ya
kiyaye amma don Allah banda bude jiki gaban
mai hoto. To kawai ta amsa tana sauri ta fita.
Hafsa! Taji mama ta kira ta ....a hankali ta juyu
tace baki karbi kudin hoton ba da kudin mota ko
duk saurin ne. Da gudu gudu ta koma ciki ta
karbi kudin tayi godiya sannan ta fita.
Tana zaune gaban motar Saif suna ta hira sai
dai gaba daya ta kasa sakin jiki sosai saboda
basu gama fita daga unguwarsu ba. Karshe dai
fakewa tayi ta duba kasan takalminta ta
sunkuyar da kanta har sai da taji sun hau titi
sosai. A gaban wani sabon gidan hoto da ake ji
dashi a kano Treasures suka tsaya. Zata bude
kofa ta fita Saif yace haba matar ai nine mai
bude miki kofa daga yau, tunda gashi nayi sa'a
kin shiga motata. Ummati da ke baya tayi shewa
lallai ma Saif wato ni ko oho. To Allah bazan
fito ba sai nima wani cikin ku ya bude min ai
nima ina da nawa rabin ran. Dariya duk suka yi
sannan suka shige ciki. Zama suka yi a
reception ya gama magana da receptionist
sannan yayi joining dinsu kafin azo kansu. Wai
Saif yau babu aiki ne ka fito yanzu? Matar
kenan Lukman na bari ya kama min kafin mu
gama. Dayake aikin sa kai ne ba. Da haka nan
nace ka zo a wannan lokacin cewa zaka yi aiki
aiki. Ledar hanunta ya kala yayi saurin dafe kai
kinsan har na manta ba taho da kayan canjawa
ba. Bata fuska tayi don Allah da gaske kake?
Dariya yayi mata sannan yace ina son
shagwabarki matar kinga yadda kika yi kyau
kuwa...buga kafa tayi a kasa ni fa da gaske
nake yi Saif....nima da gaske nake yi Hafsah ya
kwaikwayeta. Zanyu kuka fa dariya yakeyi sosai
sanan ya tashi ke wasa nake yi suna mota just
give me a minute.
Bayan ya dawo suka shiga aka bar ummati tana
jiransu idan an gama na masoya sai ayi na
kawaye kamar yadda ta fada.
Suna shiga mai hoton ya ce da Hafsi cikin
hausar da bata gama zama a bakinsa ba zaka yi
cire wanan veil ko yana nuna mayafinta. Saif ta
kalla da alamar tambaya yace ta cire akwai
wanda zasuyi nan gaba da mayafin. Nan fa aka
rinka hotuna kala kala...babu wanda jikinsu baya
taba na juna tun Hafsi tana dan jin kunya har ta
saki jikinta. Sunyi kusan kala goma suna canja
kaya dama ga ta gwanar kwalliya da daurin
dankwali. Mai hoto yace da Saif, Alaji ba zakiyi
na english wears ba amarya? Dariya Hafsi tayi
tace kaji min mutum baza muyi ba. Saif yace ni
nayi tunanin zaki zo dasu fa matar. Juya masa
idanu tayi mai hoto yana kallonsu wannan sai
bayan biki. To na yarda ya amsa mata sai tana
shirin daukan mayafinta sai kawai taji saif ya
cire mata dankwali ya kuma fizge mayafin ki
dan baza gashinki sai muyi a haka a madadin
kananan kayan tunda naga wannan rigar ta
kama ki yadda yake maganar wani kasa kasa.
Daure fuska tayi sosai Saif meye haka ya zaayi
nayi hoto a haka. Ita saboda ma yanayin rigar
bata yadda sunyi hoto da kayan ba mayafi ba.
Fitted gown ce a jikinta wadda ta bude daga
kasa. Saman kuwa ya kama mata kirji sosai
gashi gaban yana da dan zurfi ana ganin saman
kirjinta.
Shi kanshi Saif ya kadu da ganin surarta banda
mai hoto da yake gefe yana ganin bati. Please
matar ko daya ne ki bari muyi please, please.
Bata son bata masa rai amma ba karamin
haushi taji ba. A haka ta bari aka yi guda daya
da kyar ta tsaya gabansa bayanta a jikin kirjinsa
ya sakalo hannuwansa duka biyu ya ta gaban
cikinta. Wani irin yanayi duka suka tsinci kansu
shi da kansa yace ya isa guda dayan.
Da rashin fara'ar nan aka dauke su tare da
Ummati wanda zasu nuna a gida. Bayan an
wanke musu ya bada wayarsa aka tura masa.
Ita Hafsi dama tata wayar ba wata mai tsada
bace tace bata so. Wanda aka wanke ma cewa
tayi ya rike duka a wajensa. Ganin duk ta bata
rai bayan sun shiga mota yace Ummati ta bata
hakuri. Ko da ummati taga dalilin fushin duka ta
kai mata a baya shegiya Hafsi irin wannan pose
haka ko ni da Lawal bamuyi irinsa ba. Hawayen
da take kokarin boyewa ne suka sakko ba shiri.
Saif na gani ya tsaya da ribas din da yake shirin
yi da mota.... matar don Allah kiyi hakuri nima
sai da nace muyi abin duk ya dameni. Bani da
niyar wulakanta ki, ummati ki sa baki mana.
Haka suka yi ta bata hakuri har ta dena kukan
amma a zuciyarta ba karamin tsanar kanta tayi
ba da ta biye masa irin wannan runguma haka
kamar an shafa fatiha. Ga wani bakon feelings
da takeji tunda ta hada jiki da Saif abinda ko
hannunta bai taba rikewa ba. Anya tayi wa
kanta adalci kuwa. Da wannan tambayar a ranta
suka isa unguwarsu.
Kamar yadda suka tafi yanzu ma a bayan layi
suka sauka. Haka ta shiga gida sukuku kannenta
suka karbi hotunan da tayi da Ummati suna
gani. Baffa ne ya kula da yanayinta Hafsa me
ya faru ne duk kinyi wani iri. Kago murmushi
tayi Baffa kaina ke ciwo. Daki ya shiga ya samo
mata magani Mama tace sannu ai abin ne da
yawa ga karatu, kinyi jarabawa sannan kuma
baki huta ba kin sake fita. Ai zan baki hutun
kwana biyu kafin ki cigaba da tayani dinki kinga
sun taro. Baffa ya harareta nifa na gaji duk kin
mayar min da yara teloli. Kowa dariya yayi
harda Hafsi da ta kakalo ta dole.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 4
A hankali yake tuki kamar yana tausayin kasa.
Fitsararrun matasan Abuja ne suka cika wurin
maza da mata wanda abin takaici 'ya'yan
musulmi ne mafiya yawan cikinsu. Kallo ne ya
koma kan hadaddiyar motar da ya shigo da ita
tun kafin a gane waye a ciki. Wuri ya samu yayi
parking yana fitowa aka fara ihu da tafi
Juni! Juni!! Juni!!!
Junaid ji yayi kansa ya kara fashewa. Sanye
yake da wani matsatstsen jeans baki da bakin
takalmi mai kyau. Farar riga ce a jikinsa mai
dogon hannu amma bai balle maballi ko daya ba
ana ganin bakar singlet din da yayi zanzaro da
ita. Hannunsa wani agogo ne mai tsada ga
bandana ya daura a kansa wanda ya tara gashi
ya aski gefen hagu da dama. Kana ganinsa kaga
yaron da ke ji da kudi, kyau da tsabar rashin
tarbiya ko rashin sanin ciwon kai.
Junaid Rufai Bukar kenan dan senate president
din Nigeria wanda yake fantamawa son ransa
saboda kudi da kuruciya da ke cinsa.
Tun shigowarsa harabar club din take kallonsa
kamar tsohuwar mayyar da ta kwana da yunwa.
Tana son namiji mai kyau a rayuwarta gashi tun
da ta fara zuwa club din bata taba ganinsa ba.
Yana ta gaisawa da maza da mata tana binsa
da ido har ya shige ciki. Itama binsa tayi ta
sami wuri a gefe ta zauna don matan da sukayi
kansa suna da yawa. Sai da taga an fara rawa
ta je kusa da shi suka gaisa. Amma ke bakuwa
ce ko ya tambaya yana mika mata cup cike da
juice wanda aka sirka da kayan maye. Yes ta
bashi amsa. Matar ta hadu don ba ya kirata
yarinya ba, yasan da kyar idan bata girme shi
ba. My name is Tilly beauty...sunan ya dace da
ke kuwa. Ni suna na Junaid. Hmm amma naji
ana kiranka Juni. Cire glasses dinsa ya yi kana
mata wani shuumin kallo Juni friends dina ke
kirana. Nima ina son zama daya daga cikinsu.
Then you can call me Juni. Haka hira ta balle
tsakaninsu karshe da suka fara buguwa da kyar
suka karasa daya daga cikin dakunan da ake
bayarwa haya a cikin club din.
Ganin baccinsa yayi nisa ta dauki kayanta ta
saka ta kare masa kallo gaskiya Juni yana da
kyau ga kudi...just what she needed. Takarda ta
samu ta rubuta sunanta da phone number ta
ajiye masa sannan ta fita. A waje ta hadu da
kawarta Rosie suna haduwa suka tafa. Aiki yayi
kyau Rosie sai munji daga gareshi. Shegiya Tilly
baki da kyau fa Rosie ta fada tana dariya.
*******************
Da kyar ta samu Baffa ya barta taje gidan
yayarta Hadiza kwana uku bayan ta gama
exams. Suna kitchen sai hira suke yi Saif ya
kira Hafsi a waya. Tashi tayi ta koma daki
Hadiza tana ta yi mata tsiyar ta gudu kada aji
hirarsu.
Kan gado ta kwanta sannan ta amsa wayar.
(Hello matar kin wuni lafiya?)
(Lafiya kalau ya aiki?)
(Ba dadi gaskiya. Ni missing dinki nake yi sosai
yau.)
Yar dariya tayi domin itama kwana ukun da basu
hadu ba tun ranar da suka je daukan hoto bata ji
dadi ba. Babu abinda yafi damunta kamar yadda
ta kwadaitu da son sake jin ya taba ko da
hannunta ne. Ya Allah Ka kara tsare mana
imaninmu.
(Ina gidan Yaya yanzu amma anjima bayan
laasar zan tafi.)
dadi yaji har ransa domin kamar yadda take son
kasancewa tare dashi abin yafi daga wurinsa.
Karshe dai yace zaizo ya dauketa.
Bayan ta idar da sallah ta zauna gaban mudubi
fuskar nan tasha fenti. Hadiza ta kalleta Hafsi
amma dai kinsan bai kamata ki fita da irin
wannan adon kan titi ba ko. Saurin mikewa tayi
to yi hakuri Yaya na yau ne kawai nayi shaawa.
Saif na zuwa yayi mata waya tayi sallama da
yayarta wadda har kudin mota ta kara mata.
Tana rufe gate din gidan ta tsaya ta feshe
jikinta da turare mai kamshi abinda bata saba ba
domin tasan rashin dacewar mace ta tsaya
gaban saurayi tana kamshi irin wannan banda
zunubi a addinance. Sai dai ita kanta ta rasa
gane dalilinta na yin hakan. Annabi SAW yayi
gaskiya da ya fada mana cewa shaidan yana
gudu a jikin mutum kamar yadda jini yake gudu.
Shi aikin sabo da kadan muke farawa sai a
hankali ya zame mana jiki. Mu kiyaye don Allah
da yadda muke langabewa jikin maza ayi hoto
wai da sunan pre-wedding pictures. 'Yar uwa
idan baki aure shi ba meye makomar rungume
rungumen da ku ka yi duk da sunan wayewa?
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐5
A mota Hafsi ta sami Saif yana jiranta. Tana
shiga wani kamshi mai dadi ya bakunci hancinta
tare da sanyin AC. A kunyace ta zauna tare da
gaishe shi. Matar kinyi kyau sosai ga kamshi
mai dadi da kike yi. Fari tayi masa da ido har na
kai ka kamshi Saif? Har kin fini ya bata amsa
yana dariya.
Yana tuki suna hira bata ankara ba taji ya kama
mata hannu ya dora akan gear ya hada ya rike.
Tana kokarin kwacewa ya matar kina son muyi
accident ne kike neman canza min gear? Cikin
muryar shagwabar da ta saba magana tace da
hannuna fa ka hada Saif. Au hannunki ne ma ba
nawa ba. Naka ne mana amma ba'a gama baka
ba sai an daura aure. Ku mata komai sai an
daura aure ne? Ko kin manta ansa mana rana.
Ai yanzu abinda ya rage tsakaninmu kadan ne.
Suna shiga unguwar ta fada masa su bi ta
bayan layinsu Ummati sai ta sauka. Ba musu
layin suka shiga da yake a tsuke yake ba
mutane sosai. A nan Saif ya sami damar
kebewa da Hafsi don a gidansu akwai idon
jama'a. Rikota yayi ya hanata fita....matar ni fa
duk kin rikita min lissafi tun ranar saturday da
muka yi hoto. To yanzu me kake so ayi.
Wayarsa ya dauko yana nuna mata pictures din.
Hafsi ta sami tarbiya daidai gwargwado kuma
shima Saif din ya fito ne daga gidan mutumci
sai dai koyi da tarbiyar nasara yasa idanunsu ke
neman rufewa. Ganin hotunan yasa suka fara
shiga wani yanayi. Yadda ya riketa kamar ba zai
saketa ba yana kokarin hada bakinsa da nata
itama kuma bata yi yunkurin hana shi ba.
Tun shigowarsu layin Mal Aminu ya gane motar
sai dai bai gane yarinyar da ke gaba ba saboda
yadda take ta kokarin rufe fuskarta. Ganin
motar ta shige wata kwanar ba hanyar gidansa
ba yasa yayi mamaki kamar ya wuce sai yaga
anyi parking dinta a karkashin bishiyar darbejiya
shiru ba'a bude kofa ba. Karasawa yayi ya
tambayeshi gidan wa yake nema tunda dai a iya
saninsa gidansa yake zuwa a unguwar.
Jin ya fara kissing dinta jikinta yayi sanyi
hankalinta gaba daya ya tashi. Ashe akwai ranar
da zata aikata irin abinda take ji a labari tana
ganin bakin masu aikatawa. Wai a zamanin
yanzu a haka ne kawai masoya zasu nunawa
junansu kauna. Wazu hawaye taji sun zubo
mata. Hankalin Saif ya tashi...matar kiyi hakuri
wallahi rudin shaidan ne amma bani da mugun
nufi a kanki. Yana cikin share mata hawaye
suka ji an bude kofar gefen da take
zaune.....idanu ta bude a tsorace ganin waye a
tsaye cikin rawar murya tace BAFFA!.
*******************
Yau ma a cikin maye ya shigo gidan anyi sa'a
ma wurin shabiyu da rabi na dare ya shigo. Fito
ya shigo yana yi yana karkada keys din
hannunsa. Kamar daga sama yaji
kira...Junaidu....ba don namiji bane da gabansa
sai ya fado kasa yadda ya mugun tsorata. Cak
ya tsaya kamar gunki. Don ubanka juyu ka
kalleni. Mommy da ke zaune a gefe shiru tayi.
Babu wanda baya tsoron Hajiya Ramatu. A kano
take aure a gyadigyadi wurin da aka fi sani da
dangi, shiyasa ma ake kiranta da Hajiyan Dangi.
Tsawa ta daka masa bazaka zo ba ne. A hankali
ya dawo ya zauna a kan kafet. Hajiyan Dangi
doguwar macece kamar mahaifisu ga jiki. Ita
kadai ce mace a gidansu kuma ita ce babba.
Allah bai bata haihuwa ba sai dai ta rike yara da
yawa daga danginta har na mijinta. Cikinsu
harda Senator Rufai kaninta. Mace ce mai riko
da addini kuma mai sa ido akan tarbiya. Yanzu
Junaidu wannan wannan rayuwar ka daukarwa
kanka? Tana magana ta soma hawaye gidan
malamai manyan mutane muka fito amma
saboda giyar kudi na dibanka kana neman lalata
rayuwarka. Ta kalli Mommy yanzu sai da
lamarin ya baci haka kika sanar dani. Mommy
dai hakuri ta ba ta. Bandanan kansa Hajiyan
dangi ta fizge. Gobe kaje ka aske wannan
shegen kan kuma kazo ka nuna min. Ko ci
kanka bai ce mata ba haka ya tashi ya basu
wuri. Yana shiga daki tabarsa ya kunna ya fara
busa hayaki kai ka ce bakinsa salansar mota ne.
A haka Junaid ya tuna bai yi sallar laasar,
magriba da isha ba. Tsaki ya ja tare da mikewa
ya nufi toilet. Haka ya yi alwala irin yadda
kwakwalwarsa ta karanta masa sannan yazo ya
fara ramuwar sallolin da bai ma san abinda yake
karantawa ba.
A dakin da take sauka kuwa Hajiyan Dangi ce ta
yanke shawarar ba zata koma kano ba sai
kaninta Rufai ya dawo daga Australia sunyi
magana akan Junaid. Babu abinda taki jini
kamar yaro yaki ya rinka keta dokokin Allah ba
tare da an dauki mataki akansa ba.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐6
Jikinta ne ya hau bari kamar wadda akayiwa
wanka da ruwan sanyi a watan december. Iya
karfinta ta sa ta fito daga motar har tana ture
baffan nata. Da gudu ta tafi gida kafarta ko
takalmi babu. Saif kasa motsi yayi a cikin motar
ya sunkuyar da kansa. Baffa bai ce masa komai
ba ya juya ya nufi gidansa.
Yadda ta shigo a firgice yasa Mama saurin
tashi. Hafsa lafiyarki? Me ya faru? Me ya sami
yayarki? Ko daya cikin tambayoyin bata amsa ba
durkusawa kawai tayi a gabanta tana kuka.
Amira ce ta kula da kafarta ta dama tana jini.
Mama kinga kafar Hafsi jini take yi. Subhanallahi
ke ko hatsari ku ka yi a hanya ne? Ana magana
kinyi shiru kamar wata bebiya. Cikin Hafsi har
wata kara yayi da jin sallamar Baffa. Bai jira an
amsa ba yaja hannun Hafsi zuwa dakinsa.
Garammm ya banko kofar har gaban su Mama
ya fadi. Ihun Hafsi kawai suka ji tana bawa
Baffa hakuri. Tuni Mama ta karasa bakin kofar
dakin tana bugawa. Su Amira kuwa sai kuka don
tun suna jin kukanta har murya ta dashe. Babu
irin magiyar da Mama bata yi masa ba amma
yaki budewa.
Baffa ya bude kofa Hafsi na kwance a kasa
Mama ta shiga dakin hankali a tashe. Baffan
yara me ya faru...ke Hafsa me kika yi? Da kyar
Baffa ya iya fada mata tana ta kuka. Ita kam
Hafsi hawayenta ba na zafin duka bane kawai.
A yau tayi dana sanin abinda ta aikata. Tayi
Allah wadarai da maza da matan da basa jin
komai lokacin da suke hada jikinsu da juna alhali
babu aure a tsakaninsu. Yau ina ranar son
zuciya da biyewa shaidan da mukarrabansa
wadanda suke tallata irin wannan watsewar da
sunan wayewa. Mama da bata zagi yau duk
wanda yazo bakinta dankarawa 'yar tata take yi.
Tashi ki bani wuri mara mutumci tasa kafa ta
haure ta. Jiki a sanyaye haka ta fita tana share
hawaye.
*******************
Yau kwana biyu kenan Junaid yana wasan boya
da Hajiyan Dangi da mommyn sa. Tun sallar
asuba yake fita sai tsakar dare yake dawowa.
Hajiyan Dangi lamarin ba karamin bata mata rai
yake ba. Sai da ta cika sati a gidan Senator
Rufai ya dawo. Bayan ya huta cikin dare
wuraren karfe tara yaje dakin da yayar tasa ta
sauka.
Hajiyarmu babbar Hajiya zama da tashi cikin
girma. Kirarin da ya saba yi mata kenan yau ma
bayan yayi sallama tun kafin ta amsa ya fara.
Murmushi tayi tana kallonsa Rufai bazaka girma
ba. Ai indai ina ganinki bazan girma ba Hajiya. A
kan kafet ya zauna kusa da ita. Bayan sun gaisa
tace Rufai kayi min laifi gaskiya. Nasani Hajiya
kiyi hakuri don Allah. Lamarin Junaid ba karamin
bata min rai yake yi ba amma na rasa yadda
zanyi da yaron nan. Dole ka fadi haka mana
tunda aiki yafi maka akan rayuwar iyalinka,
wannan karon cikin fushi take maganar. Kana
gefe kana turowa yara kudin da yafi karfin
aljihunsu dama me kake tsammani ga yaro da
kudi. Shiru yayi don sam baya iya mata musu
kuma ma yasan gaskiya take fada masa. Tace
to ni na yanke shawara ayi masa aure kawai.
Tun zuwana garin nan yaron nan yake gudu na.
Anya zaka iya haduwa da Allah akan yadda kayi
wasarairai da amanar da Ya baka na yara? Ni
bama wannan ba Rufai kaga Allah Ya baka
matsayi a cikin al'ummar kasar nan kuma ni da
kai munsan ba iyawarka bace tasa ka samu.
Zabi ne kawai na Allah saboda haka ina dada
baka shawara kamar kullum ka tsaftace
dukiyarka. Ka kiyaye haram don ita kadai zata
wargaza duk wani al'amarinka. Kafin ta gama
magana idanun senator sun cika da kwalla.
Dukiya kam suna kai suna wasa da ita son
ransu. Ya Allah Ka bamu ikon gyarawa ya fada
a zuci.
Gyara zama yayi to Hajiya wa kike jin za'a aura
masa? Sayyada ta bashi amsa a takaice.
Sayyada ya maimaita shima ban gane ta ba.
Bama ka santa ba. Yar wajen Atika ce kanwar
Baba(maigidanta). Tun da ta gama secondary
ta dawo hannuna bana ma zata gama Buk.
Yarinyar tana da hankali da nutsuwa kuma bata
daukar wulakanci shiyasa nake ganin zata
taimaka wajen shawo mana kan Junaidu. Har
zuciyarsa yayi murna. Yace Allah Ya shige mana
gaba kuma don Allah a taya mu addua.
Junaid yasha fada wurin mommy karshe tace
yaje ya bawa Hajiyan Dangi hakuri. Yana zuwa
bakin kofar dakin yaji maganar da suke yi da
babansa. Wata dariya ce taso kubuce masa...wa
yaga Junaid da auren dole. Ai ko zai dena
holewarsa a waje zancen aure bai ma taso ba.
Juyawa yayi a hankali tare da yankewa kansa
shawarar barin garin a washegari daidai lokacin
da yaji Alhajinsu yana cewa idan Hajiyan Dangi
zata koma kano zasu tafi tare.
Batul Mamman
TUN KAFIN AURE💐7
Tamkar mujiya haka iyayenta suka mayar da ita.
Babu mai kula ta sai kannenta suma a tsorace
don sun fuskanci su Mama fushi suke da ita
kada abin ya shafe su.
Zaune take kan abin sallah tana addua bayan ta
idar da sallar walha. Idanunta duk sun shige ciki
ga ramar da tayi saboda rashin cin abinci.
Sallamar Mama taji ta dago kai a hankali ta
amsa. Ko kallonta bata yi ba ta shige tana
tashin Anisa ta sha magani saboda ta kwana da
zazzabi. Mama ina kwana, an tashi lafiya? Kau
da kai tayi amma har zuciyarta tana tausayin
Hafsi. Ta kuma yarda kaddara babu yadda bata
zuwa ga bawa domin duk cikin 'ya'yanta ita ce
mutum ta karshe da zata yi tsammanin zata
aikata abinda tayi. Auta tashi ki sha magani kinji
ta fada tana shafa kanta...mama baki ji Hafsi
tana gaishe ki ba ne. Tsaki tayi naji...karbi ki
sha sai ki koma baccin. Ficewa tayi ta koma
dakin Baffa ita ma kukan tayi na tausayin halin
da yara harma da manya ke fadawa a wannan
zamanin.
Fitar mama kenan Amira ta fito daga toilet ta
tsugunna gaban Hafsi. Wai ni don Allah me kika
yiwa su Baffa ne Hafsi? Anisa dake kwance
tace yanzu ko gaisuwarta ma Mama bata amsa
ba. Share hawaye tayi babu komai ku dai cigaba
da taya ni addua. Tana gama magana ta tashi
ta tafi dora girki don yau duty dinta ne. Ko da ta
fita kannenta shawara suka yi karshe suka kira
yayarsu Hadiza a waya aka sanar da ita abinda
ke faruwa.
*******************
Juni ba wayarka bace take ringing tun dazu.
Tsaki yayi ya sha giyar dake hannunsa kyale shi
Old Man dina ne. Ai tun shekaranjiya dana bar
Abuja yake nemana wai ni zaiyi wa aure...what
a joke. Chuks ya kalle shi ku fa hausan nan
haka kuke sai ku auri yarinya ku sakata a family
way at a very young age. Chai, its disgusting.
Karshe ta sami VVF wurin haihuwa kuyi mata
saki.
Hannu Juni ya daga masa kai Chuks dakata
bana son wulakanci. Gara mu aure muke yi da
wuri kai at what age ka fara having sex. Wata
irin dariya yayi har mutanen dake cikin club din
suka fara kallonsu...my friend I was 13 fa. Wata
yarinyar neighbour dinmu ce na ma girmeta. Ita
ta koya min. Juni yace ka gani ko ashe kune
manyan 'yan iskan. Kun iya bibiyar kananan yara
amma idan musulmi sunyi aure sai ku ce child
molestation. Hypocrates kawai.
Abeg no insult me Juni.....ai kaine ka fara zagin
hausawa nasan karshe kan musulmi zaka koma.
Ha! Kai ai baka son islam Juni you drink like a
fish and sleep with every prosti...kafin ya karasa
Junaid ya kai masa naushi a baki. Kan kace
kwabo bakin Chukwuma ya fara jini nan yan
uwansa suka tarar wa Juni ashe akwai 'ya'yan
hausawa. Cikin karamin lokaci sai fada ya kaure
tsakanin musulmi da kishiyoyinsu na wani
addinin. Ana ta fashe fashen kwalaben giya.
Karshe dai sai da police suka shigo cikin lamarin
duk aka kama su.
Tilly na kwance akan gado tare da wani
hamshakin dan kasuwa taji waya. tayi mamakin
ganin sunan Juni ta dauka cike da farinciki. Nan
yayi mata bayanin yadda suka yi da police
amma jin ko dan waye kuma ya jika su da kudi
sun sake shi. Karshe dai yana bukatar account
number dinta zai turo mata da kudi ta biyoshi
Lagos. Ko sallama bata yiwa mutumin da suke
tare ba ta tashi bayan taji alert....lallai Juni na ji
da kudi.
*******************
Cikin kuka Mama tayiwa Hadiza bayanin abinda
Hafsi tayi. Itama kukan take...wallahi Mama
yanzu irin wanan masifar ake fama da ita. Ana
zance ana shafar juna karshe inda kaddara ayi
ciki. Mama tace abin ne ba kama ba don ni na
haifi Hafsa ba amma wallahi nayi mata shaidar
alkhairi. Allah Yasa mufi karfin zukatanmu. Amin
Mama amma don Allah kuyi hakuri don idan
muka nesanta kanmu da ita sai tayi wani abin
ma babu wanda ya sani.
Hafsi da Ummati suna ta shawarwari Hafsi tace
kinsan har yau babu waya ko text din Saif. Idan
na kirashi ba waya a kashe abinda ya kara
batawa Baffa rai kenan don shi so yake a sanar
dashi a matso da bikin. To aje gidansu mana
don bai isa ya jawo mana jangwam ya tsallake
ya barmu a ciki. Ke ummati kila a tsoro yaji. Ai
ni dadi na dake shegen son saurayi. Ni wallahi
daga yau kara kama kaina zanyi har sai anyi
aure.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 8
Juni dear....yes Tilly ya amsa mata yana daga
kwance. Jin tayi shiru ya taso ya dafa bayanta
Tilly ya akayi ne? Ko akwai abinda kike so ne?
No tambayarka kawai zanyi. Nawa ne kudin
hotel dinnan ne per night? N150,000. Wage baki
tayi ko wane kwana daya? Eh menene wai duk
kin wani rude. Gani nayi kudin da yawa kuma
gashi yau kwanan mu hudu banda abinci da
kudin da kake kashewa a club. Wani shekeke ya
kalleta kin ma raina ni to ko don ban biya ki
naki kudin bane...yana gama magana ya mike
daga shi sai gajeren wando ya jefo mata
cheque. Ganin kudin dake jiki dubu dari biyar ba
shiri ta rungume shi tana ta murna. Hmm kudi a
kasar nan yana hannun masu shi suna kashewa
kadangarun bariki da kayan maye wani lomar
tuwo ta gagare. Masu kudi a rinka cin halal dai.
*******************
Hajara tana kwance tana chatting da kawayenta
a group taji shigowar messages. Tana dubawa
hotuna ne kamar bazata bude ba don bata da
data sosai sai ta bude daya. Zumbur ta mike ta
bude sauran. Babu shakka ita ce a duka
hotunan biyar. Wadda ta turo cewa tayi ga wani
style din pre-wedding pictures. Nan da masu
cewa sunyi kyau da masu zaginsu. Wani gumi
ne taji yana karyo mata lallai baa shaidar
mutum, yarinyar da kullum take shigar mutumci
ita ce a haka. Tsam ta tashi ta dauki mayafi ta
sauka kasan gidanta wurin makociyarta. A'a
Hajara shigo mana ina kitchen...a sanyaye ta
karasa dama wani abu zan nuna miki a waya.
Maimakon kiyi min forwarding, menene mu gani.
Ruwan ruden tuwon da take ne ya fallatso mata
a hannu da gefen fuska saboda tsabar rudewa.
Na shiga uku ni Hadiza me zan gani haka.
Hajara tace a group na gani shiyasa na nuna
miki don nasan wace Hafsi. Muciyar ta karba
ganin yadda hannun Hadiza ke rawa ta karasa
mata tuwon. Daren ranar bata yi baccin kirki ba.
Mijinta zai tafi office ya ajiyeta a gida duk da
bata fada masa abinda ke faruwa ba yasan babu
lafiya.
A falo ta hadu da Baffa zai fita ta gaishe shi.
Lafiya dai Hadiza irin wannan sammako ko duk
saurin ki taya ni cin kosai ne. Murmushin karfin
hali tayi. Baffa akwai wasa sai dai baya sake wa
yara suyi yadda suke so. Ganin bata biye mishi
ba ya mike muje ciki. Mama na shafa mai suka
shigo dakin. Hadiza lafiya kuwa...nan taji tsoron
nuna musu hoton sai dai tasan yadda irin
hotunan nan ye kawo a social media. Wasu
mutanen basu da aiki sai ture turen abinda bai
shafesu ba karshe su kunna wuta mai wuyar
kashewa. Wayar ta mika wa Mama shima Baffa
ya zauna kusa da ita yana gani. Hankalinta bai
tashi ba sai da taga 'yarta babu ko dankwali ta
shige jikin namiji sai kace kanin uwarta ko na
ubanta. Nan take numfashin Mama ya fara
sama sama dama ita haka take idan ranta ya
baci. Haka ta fita daga ita sai daurin kirji ta
shiga dakin 'yan matan. Wayar chaja ta fizgo
daga jikin bango ta fara tsula mata. Hafsi ji tayi
kamar a mafarki ana dukanta tayi saurin tashi.
Yaya Hadiza ta gani sai kannenta. Cikin rashin
fahimtar laifinta ta fara rokon gafara. Sai a
lokacin Baffa ya shigo ya dakatar da dukan.
Kyaleta haka ku zauna. Wayar Hadiza ya bata
hoto daya ta kalla ta kama kafar Mama tana
kuka...don Allah ku yafe min wallahi bazan kara
ba. Ki ma kara mana don ubanki...wai ni dame
muka kuskure miki ne Hafsa. Lokaci guda kin
fara taka rawar gangar shaidan. Wai ma yaushe
akayi wannan hoton? Shiru tayi ba amsa. Nace
yaushe akayi hoton nan...lokacin...lokacin.
Hadiza ce ta katse ta lokacin me? Uhm lokacin
da muka ce miki zamu daukar hoto da ummati.
Nasan za'a rina cewar Baffa. Dama nasan da
taimakon wani a lalacewar da kika soma yi.
Amma wallahi ba a gida na ba. Gidansu
Saifullahin zani in nunawa mahaifinsa, ki kwana
cikin shiri aurar dake zanyi cikin kankanin lokaci
mutuniyar banza. Nan dai ya hada duka yaran
nasa sun sha fada da nasiha. A dakinsa kowa
yace da Mama ta tabbatar ta tuntubi Hafsi ko
babu wani abu da ya shiga tsakaninsu domin shi
yanzu ya tsorata da halin yaran zamani.
Batul Mam
TUN KAFIN AURE💐 9
Wani irin kuka ne mai tsuma zuciya take yi
tunda Mama tayi mata wannan tambayar. Wai
ko wani abu ya shiga tsakaninsu??? Lallai ta
jawo wa kanta tunda an fara zargin ko
lalacewar tata ta kai nan. Gabadaya filon ta
gama jika shi da hawaye dadin bakin cikinta ma
rashin duriyar Saif. A wannan yanayin Ummati
ta shigo itama kukan take yi don a falo Mama
da Maman Ummati suka hada su ana ta fada
gadon itama ta hau suka jeru kamar masu gasar
kuka. Iyayensu sunyi fushi sosai. Tayi nisa da
tunani kamar daga sama taji wayarta na ringing.
A firgice ta tashi don tasan ko waye me kiran.
Ringtone dinsa daban ne....ummati ce ta doke
mata hannu da sauri tana kokarin dauka. Ta
galla mata harara to banza mara zuciya..duk
abinda ya samemu a dalilinsa sai yau zai wani
nemeki. Cikin muryar data dashe saboda kuka
tace bafa ki san me ya same shi ba. Don Allah
ki bani wayar Ummati. Ni wallahi haushi kike
bani mtww karbi ni ta dangwara mata wayar ta
koma gefe. Ba zancen fita don iyayensu mata
suna falo ana ta maida zance.
(Matar ina kika shige ina ta waya.)
Kaji rainin hankali yau fa kwanansu shadaya
bata samunsa a waya(kai zan yiwa wannan
tambayar. Sai da kaga matsala ka guje ni Saif)
kuka ne yaci karfinta.
Shima a hankali yake magana( kiyi hakuri ni
kunyar sake haduwa dake da kuma Baffa nayi.
Matar ina tsoron zama sirikinsu har abada Baffa
bazai dena ganina da wannan tabon ba)
Wani irin faduwar gaba taji (me kake nufi? Baffa
fa sun taho gidanku tare da baban ummati)
(Nasani na kuma nayi musu bayani. Tun ranar
da ya ganmu na sanar da umma don bana son
rufafa a maganar aure. Kunya tasa na guje ki
don naci amanar Baffa. Kiyi hakuri muyi rabuwar
arziki amma bazan iya aurenki ba.)
Yana kashe wayar wani kuka ya kwace mata
har su Mama suka shigo. Ummati suka fara
tambaya tace bata san me ya faru ba. Kasa
fada musu tayi tana ta kuka. Gajiya suka yi da
tambayar aka kyaleta. Sai da Baffa ya dawo ya
sanar da Mama yadda sukayi mahaifin Saif yace
aure ba fashi tare da basu hakuri shi kuma dan
yace bazai iya sake kallonsa ba. Zai fadi haka
mana tunda yaso gurbata mana rayuwar
yarinya. Suna ta maganganu Hafsi na jinsu daga
daki tana kara tsanar kanta da abinda tayi.
******************
Junaid mutum ne mai son jindadi, bashi da
magana sosai sai ta zama dole. Ko kadan baya
daukar raini wannan kuma hali ne ya tarar da
dukiyar da ya taso cikinta. matashi ne dan
shekara 30 ga tsaho ga kyau ga fatarsa mai
kyau saboda tana shan hutu. Gashin kansa da
saje kuwa a kwance yake don kudin da ake
ajiyewa don gyara shi daban ne. Yana son kula
da gashin kansa ko kadan baya son abinda zai
bata shi.
Yana kwance kan kujera kansa a cinyar Tilly
tana fara shafa masa kai. Doke mata hannu yayi
yana magana kasa kasa ki dena taba min kai I
hate it. Dan tabe baki tayi to yi hakuri naga ko
wanka baka yi ba meye abin bacin rai don na
taba? Tashi yayi ya bude fridge ya dauko lemon
gwangwani ya fara sha. Ki shirya muje party
amma bana son wannan faratan naki kamar
mayya ya juya mata baya ji yadda kika kusa
kwashe min baya. Yi hakuri Juni ta fada tana
murmushi bari na cire su nayi wanka.
Lallai ma yarinyar nan wallahi kinyi kadan abinda
ya fada kenan lokacin da ya fito daga wanka ya
kama Tilly tana satar masa kudi. A fusace ya
karaso gabanta tasha mari hagu da dama. An
fada miki bani da hankali ne? Kumatu ta rike
tana kuka ni ka mar Juni? Ke 'yar waye da
bazan mareki ba? Barauniya kawai get out of
my room. Kafa yasa yana kai mata duka tana ta
ihu. Da kyar ta rarrafa ta fita ya jefo mata
jakarta waje ta ce zaka san ni kayiwa haka Juni
sai na bata maka rayuwa. Ta mike da kyar tana
dingisawa mugu ko kudina bai bani ba duk
kwanakin nan dana yi.
*******************
Dai dai yake kallon mutane kowa da budurwarsa
ana ta sha'ani. Shegiya Tilly da nasan haka take
ai da tun wuri na nemi me rako ni nan. Kai da
wa kake magana Juni? Shafa kansa yayi zancen
zuci ne ya fito fili birthday boy...Imi dan wani
gwamna ne abokin Junaid ne tun suna
secondary duk watsewarsu tare sukeyi. Ina babe
din da na ganku tare ne jiya? Tilly barauniya? Ai
na bata takardar sallama dazu....sata fa tayi min
don rainin hankali. Imi da buduwarsa suka fashe
da dariya ai abokina ka fiye kwashe kwashe ne.
Ya rungumo yarinyarsa ya Simy akwai wata a
kasa ne kada yayi kwanan kadaici yau. Kai kyale
ni kawai. Maybe na tafi portharcout gobe. Dont
worry I will pay bana son ganinka so quite.
Wayarta ta dauko ta mika masa ga hotunan
wasu nan duk kawayena ne idan ka zaba kayi
min magana. Bakin ruwan suka koma ana ta
wasa da raye raye shi kuma yana kallon 'yan
mata kala kala a wayar. Tsaki yayi zai kira Simy
ta karbi wayarta sai kawai yaci karo da hoton da
ya daga masa hankali. Zuciyarsa ce take bugu
da sauri da sauri...he wants this girl at all cost
abinda kawai yake fada a ransa kenan.
Batul Mamman
TUN KAFIN AURE💐 10
Jikinsa har tsuma yake bai taba ganin macen da
ta sace masa zuciya ba kamar wannan. Fatansa
daya wannan saurayin daya rungumeta ba
mijinta bane. Tura hotunan yariyar yayi daya
gani a wayar ya tashi da sauri ya je wurin da Imi
da Simy suke ta rawa yana mata liki da dubu
daya. Janyo hannunta yayi suka fito daga wurin
rawar Imi ya jawo wata suka cigaba. A irin
wannan rayuwar ana tafka kazanta da tsabar
rashin kishi. Muna mantawa akwai ranar da
zamuyi accounting for every second da muka
rayu a duniya.
Rawar ta cigaba da yi a gabansa ganin hakan ya
sake janta suka kara nisa da mutane. Yarinyar
nan nake son duk wani information a kanta. Ta
dan nutsu ta kara kallon hoton wai wannan kake
nufi? Eh mana are you blind? No...sai tayi dariya
sorry. Gaskiya Juni bansan....katse mata
magana yayi kada kice baki santa ba. Kudi ya
dumbuzo daga aljihunsa ya damka mata a
hannu. Ki nemo min duk abinda ya dace ...ya
sake kallon hoton...my God she is so pretty.
Kallonsa tayi Juni wannan fa pre-wedding
pictures ne. Maybe ma anyi auren don na kusa
wata da ganinsu. A wani group aka saka na ma
manta wadda tayi sending. Ai sai ki sake
sending ki tambaya. Look Simy bani account
number dinki. Washe baki tayi yanzu kayi
magana. Zan nemo ta ko tana gidan miji ne sai
tazo ta kashe maka kishi...kanne masa ido tayi
ta tafi. Simy 'yar shekaru goma sha tara
karamar yarinya ce da iyayenta suka kyaleta
take irin rayuwar da take so saboda yanayin
aikinsu. Tana abinda taga dama babu me
tsawatar mata a cewar su kuruciya ce ke
damunta. Wai kuma yar musulmi kenan babu ko
tsoron mutuwa.
******************
Kallon 'yan uwanta take ana ta hayaniya. Kanta
har wani sarawa yake don ciwo. Wai nan lefenta
aka kawo shine har yanzu mutane basu gama
tafiya ba. Dakinsu ta nufa kai tsaye wata
kakarta tace ai tunda kika dawo bamu watse ba
ki tsaya ki kalli abin arziki. Ai ni kam wannan
miji yayi ina ma ina da sauran kuruciya. Dariya
duk aka sa Hafsi ko sai hawaye. Auren da zaayi
ba dadin rai. Abinda komai Baban Saif ne yayi
don yace shi ba karamin mutum bane aure ya
zama dole. Shi kuma Saif kamar bai taba cewa
yana sonta ba alaqar tasu yanzu ba yabo ba
fallasa. Da gaske yayi nadamar abinda ya aikata
sai dai kunyar iyalin Baffa yasa har ransa baya
son ayi auren. Allah Yaso shaidan baici galaba a
kansu ba da da wane ido zai tsaya a gaban
mahaliccinsa? Ko matasa nawa ne ke tuna irin
wannan a lokacin da suke matse 'ya'yan mutane
suna aikata haramun?
Ita kanta Hafsi tana tsoron rayuwar da zasuyi.
Da wane ido zasu rinka kallon juna. Ba don
zuwan Baffa ba da kila shikenan. Rayuwa kenan
wasu na nadama wasu kuwa zuciya ta gama
bushewa a aikin sabo. Tir da wannan rayuwa ta
shaye shaye da zinace zinace. Ya Allah Ka kara
shiryamu Ka bamu wadatar zuci.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 11
Da gaske Simy ta shiga neman yarinyar hoto
don Juni dubu dari da hamsin ya saka mata a
account yace cikon sai bukata ya biya. Hoton ta
fara turawa groups uku da take tsammanin daga
nan aka turo don ta manta inda ya fito. Sai
bayan kwana hudu ya kebbi tayi magana tace ai
saurayin yayan kawarta ne a kano suke. Jin
haka Simy tayi saurin cewa ai yarinyar da
makotansu ne sun dade basu hadu ba tana
neman address dinta ne. Nan dai ba wani dogon
bincike yar kebbi ta turo da number din Zainab.
Mata mu rage tallata sirrinmu a social media
don Allah.
Kamar akan kaya yake a lagos din sai dai kuma
dole ya tsaya don Imi yana nan Simy ba tafiya
zata yi ba. Yana cikin restaurant din hotel din
da yayi masauki tayi masa waya ta shigo. Nan
yayi mata kwatance suka hadu. Sai da ta cika
cikinta da abinci wanda ya kasa ci don dokin jin
abinda zata fada masa. ta sanar dashi yadda
suka yi da yar kebbi cikin tsananin farinciki ya
kankameta sannan ta bashi number din Zainab.
Tana ta dariya Juni lallai yarinyar nan ta tafi da
imaninka idan akwai saura. Ke me kike nufi? Ya
daure fuska...ni duk iskanci na bana hadawa da
izgilanci ga addini fa. Ga wayarki ya mika
mata..zan ciko miki kudinki anjima. It was nice
doing business with you Juni. The pleasure was
all mine ya bata amsa.
Dakinsa ya koma ya hada kayansa. Bayan ya
gama ya kira number din Zainab. Kamar gaske
sallama ya fara yi mata ta amsa duk da taji
bakuwar murya.
Dan gyaran murya yayi( Zainab ce ko)
(Eh, wa ke magana)
Shiru yayi yana tunanin karyar da zaiyi ( ina
yayanki ango to be?)
( ya Saif ya fita)ta bashi amsa.
( suna ta shirye shiryen biki ko)
Mamaki ta fara yi dai amma tayi shiru (eh
amma fa still bangane ka ba)
( ina printing din cards na biki ne a nan kusa da
unguwarku shine nake son nuna masa sample
don kiran kasuwa).
Sai a lokacin ta dan saki rai tayi masa
kwatancen gisansu kamar yadda ya bukata ba
tare da ta kawo komai a ranta ba. Yarinyar
kamar mara wayo ya fada shi kadai, ba wani
bincike ta turo da address.
Scrolling waya yayi ya nemi sunan Oldman ya
kira. Senator Rufai yayi mamakin ganin sunan
Junaid yaron da number dinsa da suke da ita
gaba daya basa samu sama da sati biyu. Hakuri
Junaid ya bashi tare da sanar dashi zai tafi kano
wurin Hajiyan Dangi itama ya bata hakuri.
Senator Rufai murna yayi sosai. Yana matukar
son dansa lalacewar yaron kawai ke damunsa.
******************
Kano ta dabo tumbin giwa yau tayi babban
bako. Junaid Rufai Bukar ne yake tafiya cikin
nutsuwa don yau manyan kaya ya saka tare da
aski wanda gashin na zuba zuciyarsa na kuna.
Hatta faratansa yaje wani salon a lagos 'yan
mata sun gyare shi. Shadda yasa light blue anyi
mata dinki mai kyau kansa harda hula. Idan ka
ganshi sai kasa shi cikin mazan kwarai sai dai
abin ba a fuska yake ba.
Yana tafiya maaikatan airport na binsa a baya
ganin sunansa yan maula sun rude. Motar da
babansa ya turo ce ta karaso gabansa aka saka
masa kayansa a cikin booth. Kudin ya basu
masu yawa tunda bai san zafin nema ba. Kowa
sai murna...Tilly dake bayansa wadda baisan ma
jirgi daya suka biyo ba tayi murmushi tasan ba a
banza yayi wannan shigar yazo kano ba. Sai ta
rama wulakancin da yayi mata a lagos. Wayar
Rosie ta nema ta sanar da ita ta shigo gari.
Gyadi gyadi yace da driver din ya kaishi . Dreba
ya shafa kai yallabai ai Alhaji ya gina ma
Hajiyar gida a hotoro ai kusan shekararta biyu a
can. Shima Juni kai ya shafa don yaji kunya.
Rabonsa da zuwa sada zumunci 'yan uwansu na
kano ya kwana biyu.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 12
Tun kafin ya iso Hajiyan Dangi tasa su Sayyada
yi masa abinci. Kusan tafi iyayensa murnar
zuwansa ma tunda mommy tayi mata waya ta
sanar da ita yana hanya. Alkawari ta daukarwa
kanta da yardar Allah yaron nan sai ya shiryu.
Ita da kaninta kawai iyayensu suka haifa,tunda
bata da nata 'ya'yan nasa sune natan. Idan ta
bar dan uwanta ya cigaba da sangarta danshi
lallai taci amanar mahaifiyarsu.
A falo ya risketa tana karatun Al-Qurani cikin
murya maidadi take karanta suratul Sajda. Wata
irin nutsuwa da kwanciyar hankali yaji yana
ratsa masa zuciya ya kasa karasawa cikin falon.
Sai da ta kai karshen aya ta ajiye tare da yi
masa nuni da ya karaso ya zauna. Bayan tayi
addua tace Junaidu dan gudun hijra ka dawo?
Murmushi yayi tare da sosa keya. Yi hakuri
Hajiyana bazan kara ba. Kallonsa kawai take yi
hatta tafiyarsa irin ta babansu ce. Kamar su ta
baci. Inama ace yayi koyi da halayen Malam na
kwarai.
Haka ta kira 'yan matan gidan nata suna
gaisawa dashi. Wai Hajiyan Dangi ta iya kiwo ya
fada a ransa. Ba don yunwar yarinyar hoton nan
bace kawai a ransa ai da yasan yadda yayi a
sami 'yar rage dare ko da daya ce. Wani shegen
murmushi yayi, Hajiyan Dangi dake gafe tana
kallonsa tayi tana murmushin...sai na gyara
maka zama yaro.
*******************
Ko kafar gida Hafsi bata zuwa yanzu Saif dinma
Baffa ya hanashi zuwa a cewarsa sa hadu idan
an daura aure. Duk abin duniya ya isheta gashi
dai zata auri wanda take so amma babu wannan
farincikin ko kadan a ranta. Duk surutunta yanzu
ta zama wata abar tausayi. Yan uwanta kuwa
sai shirye shirye suke yi hankali kwance.
*******************
Ya kusa awa biyu a gefen gidan sannan yaga
fitowar wanda yake jira. Tabar hannunsa yayi
saurin kashewa ya tada mota ya bishi a baya.
Yinin ranar duk inda Saif yayi Junaid na binsa a
baya ba tare da ya sani ba. Takaici ne ya
isheshi don kuwa baiga alamun anzo gidan da
yake nema ba. Karamin tsaki yayi ganin sun
kusa karasawa gidansu Saif din. Horn ya rinka
matsa masa kamar hauka dole Saif ya tsaya
yayi parking. Wannan takun kasaitar ya dinga ya
har ya isa kusa da motar Saif. Ganin bai sanshi
ba sai ya mika masa hannu su gaisa. Kin karbar
hannun Juni yayi daya tuna yadda suka
kankame abar sonsa.....abar sona??? Ya tambayi
zuciyarsa. Sannu dai, Saif ko? Eh ya amsa masa
fuska a sake...Saif akwai fara'a. Shiru yayi don
bashi da abin fada abin har ya fara isar Saif.
Ban fa gane ka ba wa kake nema ne? Hoton
cikin wayar ya nuna masa idanun Saif har wani
kankancewa suka yi don tsabar bacin rai. Yayi
imani ko mutum daya bai turawa hotunan ba
kuma Hafsi ko wayar kirki bata da ita shiyasa
ma bai tura mata ba. Juni ya katse masa tunani
I want her kuma zan iya biyanka ko nawa ne ka
kaini wurinta. Ikon Allah....kai kuma daga ina?
Kana ma da hankali kuwa? ba ko kunya balle
tsoro kake fada min hakan. To bari kaji na fada
maka this coming saturday zata zama
mallakina. Kasa karasa magana Saif yayi saboda
tsabar takaici ya tsaya yana magana da
kwancen hauka. Shafa kai Juni yayi plan dinsa
is working. Sai kuma ya yamutsa fuska tunda
baka jin lallami kasani cewa nan da ....sai ya
dubi agogonsa kamar 20 minutes yarana zasu
dauko min ita su kai min ita hotel. Wani mari
yaji a kuncinsa kamar wuta kafin ya dawo
hayyacinsa kuwa Saif ya shiga mota ya tayar.
Shege ya fada yana shafa kunci amma fa marin
da zafi...kodayake its worth it.
Bayan Saif yabi har kofar gidansu Hafsi. Yana
tsaye a can gefe ya hango wani dattijo mai cike
da kamala ya fito sunyi magana da Saif. Yasan
bai wuce barazanar karyar da yayi ba Saif din
yake fada shi kuwa bukata ta biya dama plan
dinsa yaga gidan kuma ya gani. Sauransa jin
sunanta duk da a zuciyarsa ya rada mata suna
pretty.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐13
Wallahi Baffa kamar mahaukaci fa yake magana
kuma nayi tunanin da gaske yake. Gyara
tsayuwa yayi to Saifullahi ai kadan ma kuka
gani. Illar irin wannan abin dama ba na lokaci
daya bane. Me zaku fadawa yaranku idan suka
ci karo da hoton nan gaba? Shin kuna da bakin
tsawatar musu bayan sun san borin kunya kawai
kuke yi. Allah Ya kyauta ka tafi gida kawai in
Allah Ya yarda babu abinda zai faru. Saif kallon
Baffa kawai yake yi don yaga kamar bai yarda
da abinda ya fada ba. Shi kadai yasan abinda ya
gani a idon yaron nan. Jiki a sabule ya juya ya
tafi.
********************
Wannan tafiyar kasaitar yake yi har ya shigo
gida yana dan fito don yau zuciyarsa fes take.
Tunda yazo kano bai sha giya ba sai taba da
shisha suma duk a waje saboda sa ido irin na
Hajiyan Dangi. Tsohuwar nan akwai hana ruwa
gudu. Turus yayi da ya ganta zaune a kan
gadonsa. Fuskar nan babu fara'a koma waje
kayi sallama ka shigo kamar dan arna kana min
fito kamar mai kiwon kare. Haba Hajiya ai
dakina ne kuma nasan babu kowa a ciki meye
na sallama kuma. Ashe baka san cewa akwai
aljanu da malaikun Allah a ko ina ba. Don baka
ganinsu hakan ba yana nufin babu su ba. A duk
lokacin da zaka shiga wurin da babu kowa sai
ka ce Assalamu alaina wa ala ibadullahis salihin.
Ai na iya Hajiya bafa complete jahili bane ni.
Naji koma dai kayi. Fita yayi yayi mata
kyakkyawar sallama ta amsa sannan ya shigo.
Cire kaya ya fara yi yana wurgi dasu tace maza
ka gama ka tsince min su ga tsintsiya nan ka
share dakin. Me??? Ni din Hajiya? Kai mana
Junaidu ko kana jin saurayi kamar ka zan bari a
share masa daki. Ni wallahi bacci nake ji duba
fa ki gani na dawo da wuri shadaya bata yi ba.
Ta mike Allah sai ka gyara dakin nan idan ba
haka ba zaka ga yadda zanyi da kai. Tana fita
ya fada gado sai dai bai gama gyara kwanciya
ba ta dawo. Yauwa kayi sallah kuwa?... .au
kwanciya kayi ko to tashi ta fada tana dukansa
da slipas din kafarta. Dole ya mike Hajiya bana
so fa. Sallah kuma nayi don nasan ina da
ayyuka a gabana shiyasa ma tun da Baba yazo
muka je muka yi sallar asuba ina dawowa nayi
duka sallolina ya kare maganar da murmushi.
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun shi kawai take
fada. Junaidu lalacewar taka har ta kai haka?
Shiyasa ka gagara shiryuwa mana. Ta share
wasu zazzafan hawaye dake sauko mata. Ashe
baka san cewa wutar masu barin sallah daban
take ba? No Hajiya nifa nayi ko bakiji abinda na
fada bane. Bakin gado ta zauna Junaidu babu
wata sallah da zaka yi ba a lokacinta ba da
gangan Allah Ya karba. Harma gara lokacin ya
wuce maka bisa kuskure sai ka rama. Ita fa
sallah kariya ce daga aikin sabo da alfasha.
Rayuwa da mutuwa gaskiya ne Junaidu, azaba
ko rahmar kabari gaskiya ne, wuta da aljanna
ma gaskiya ne. Maganar Hajiyan Dangi da
hawayenta sun taba masa zuciya har bai san
lokacin daya dora kansa a cinyarta ba yana bata
hakuri. Junaidu ka kiyayi Allah sai Allah Ya
kiyaye ka. A yau alkawari daya nake nema a
wurinka shine na tsayar da sallah. Nayi miki
bazan kara bari naji kiran sallah na kasa tashi
ba. Ta shafa kansa Allah Yayi maka albarka.
Amin
******************
 Ummati ana ta rawar kai biki ya gama matsowa
da kyar aka barsu zuwa salon don ko gyaran jiki
Hafsi bata yi ba. Wannan kuma duk yana cikin
punishment din da aka tanadar musu a gida
saboda laifin da sukayi don a cewar Maman
Ummati itama haka zaayi mata tunda bakinsu
daya.
Sai da Saif yayi jan ido sosai sannan kanwarsa
Zainab ta fada masa gaskiya ita ce garin
binciken waya taga wadannan hotunan a
wayarsa ta tura wayarta, daga nan kuma ta tura
wa kawayenta. Da belt ya zane ta tana ihu tana
bashi hakuri. Ko da mamansu taji dalilin dukan
Allah Ya kara tace musu duk su biyun. Ke banda
gulma me ya kaiki bincika masa waya....bayan
zainab ta koma daki da kuka Maman tace gobe
ma ka sake daukan yar mutane kuje yin hoton
rashin kunya....istigfar ya rinka yi a zuci. Allah
Yasa daga wannan bazasu fuskanci azabar Allah
ba. Don kam shi da Hafsi sunyi nadama sosai.
Batul Mamm
TUN KAFIN AURE💐 14
Duk abinda yayi niyyar yiwa Pretty kamar yadda
ya saka mata suna maganganun da Hajiyan
Dangi tayi masa yasa duk jikinsa yayi sanyi.
Washegari bai bari ya makara sallar asuba ba
domin kafin lokaci ma yayi setting alarm. Suna
dawowa ya shiga dakin Hajiyan Dangi. Har ka
manta yadda ake sallama ne? Ba shiri ya fita
yayi sallamar ya jira tayi masa izini ya shigo. A
kasa ya zauna cike da ladabi tace yau dannan
nawa akwai magana a bakinka. Fadi inji Allah
Yasa alkhairi ne. Shafa kai yayi alkhairi ne
Hajiya. To ina jinka. Wai yau shine da jin kunya
abin ya bashi mamaki... dama yarinya na gani
ina son aura kuma idan da hali da wuri nake son
auren. Allah mai girma da daukaka ta daga
hannu sama ta yabi Allah SWT sannan ta kalle
shi. A ina take kuma ya sunanta? Nan fa daya
yace a ransa, sai kuma dabara ta fado masa.
Nasan gidansu dai amma banyi mata magana ba
domin mafi son ki fara nema min izini. A'a wai
kuwa Junaidun da ta sani ne wannan? Yau
komai a hankalce yake yi. Allah Yasa bata yi
masa zancen Sayyada ba itama yarinyar bata
sani ba da yazo ya bata kunya. Kwantar da
hankalinka bari na fadawa Baba sai musan
abinyi zuwa karshen sati. Sanin cewa nan da
kwana uku zaa daura mata aure Junaid ya fittike
mata shi lallai yau yake son taje. To naji bari dai
na fada masa tunda da kanka ka zo da
maganar. Tana fita yayi ajiyar zuciya yarinyar da
har yanzu baiga zahirinta ba yake tunanin
aura....sai dai kuma irin yadda yake jinta a
ransa yasan da gaske yake burin rayuwa da ita,
baya jin zai taba iya yarda wani ya shiga
tsakaninsu.
Sai bayan laasar Hajiyan Dangi ta shirya tare da
wata yar uwarsu Gwaggo Mairo suka nufi
unguwar sabontiti inda Junaid yayi musu
kwatance a matsayin gidansu Pretty. Karba ta
mutumci da karramawa Mama tayi musu bayan
sun gama gaisawa ne Hajiyan Dangi ta gabatar
da kanta tare da fadin dalilin zuwansu. Mama
tace kuma nan gidan yaron ya fada muku? Nan
ne domin ya kwatanta min gidan ta waje sosai
Hajiya ta bada amsa. To Hajiya ni dai banda
yaran nan biyu da suka gaisheku bani da wata
'yar sai Hafsa wadda asabar dinnan zaa daura
mata aure. Babbar kuwa shekararta uku ma da
yin aure. Shiru Hajiyan Dangi tayi sai Gwaggo
mairo ce take ta basu hakuri tace nasan
yaronnan kam ba kananan yake nufi ba zamu
sanar dashi yayi hakuri. Hajiyan Dangi ta fiddo
kudi a jakarta tace gashi a bawa amarya. Allah
Ya sanya alkhairi. Mama taki karba itama
hakurin ta basu. Hajiya sai ta ajiye kudin a kan
tebur. Suna kofar fita Hafsi ta dawo daga salon
duk a gajiye. Har kasa ta durkusa ta gaishesu.
Ko baa fada ba Hajiya tasan wannan ce Hafsar
da danta ya gano. Lallai ya rude don yarinyar
tana da kyau. A sabule suka fito don ba haka
aka so ba. A tunaninta indai yayi aure wasu
daga cikin ayyukan barnar da yake aikatawa
zasu ragu ko ma ya bari gaba daya.
Tun a mota ta kira shi domin taga missed calls
dinsa da yawa sai dai bai dauka ba. Suna isa
gida Sayyada ta sanar da ita ai ya tafi masallaci
ne. Dadi ne ya cika mata zuciya sannan ta shige
daki. Cike da doki ya shiga dakin yana ta washe
baki. Har zuciyarta take tausayinsa... junaidu
yarinyar nan ashe ranar asabar za'a daura mata
aure. Kayi hakuri ka nemi wata. Mikewa yayi
hakuri fa kika ce Hajiya. To ma baki basu kudi
bane? Ai wallahi da sunga kudi magana zata
chanja. Murmushi tayi zauna Junaidu. Ina so ka
sani ba fada ta bace Annabi SAW yace babu
kyau wani ya shiga cikin cinikin wani ma balle
harkar neman aure. Ai ba'a hada nema akan
nema. Abu daya zaisa ka iya nemanta sai dai
indan wancan yace ya fasa. Wani irin bacin rai
yaji a ransa idanunsa sun kada sunyi ja. Fita
yayi fuuu ya buga mata kofar daki har sai da ya
tsorata ta. Allah Ka shirya mana ta fada a fili.
Jan mota yake a guje kamar zai tashi sama.
Baya ganin gabansa ma da kyau. Club ya shiga
ya tayar da kura kafin ya tsayar da motar. Idanu
duk a kansa ya shiga. Waiter na shirin zuba
masa giya ya sunkuce kwalbar yana kafa kai.
Sai da ya bugu sosai ya jawo hannun wata
yarinya suka fita tare yana tangadi. A waje ya
dauko wayarsa ya bata yana lumshe idanu kira
min oldman. Waye kuma oldman? Ki dduba za
zaki gani a wayar. Ringing biyu ya dauka sai
yayi mamakin jin muryar mace ta sanar dashi
wurin da dan nasa yake ya daga masa hankali.
Yana ajiye wayar ya kira Hajiyan Dangi ya fada
mata. Nan tayi masa bayanin abinda ya faru
sannan ta sanar da maigidanta inda Junaid
yake. A can abuja kuwa Mommy Senator Rufai
ya tasa yace mata gobe zamu kano.
Batul Mamman
TUN KAFIN AURE💐 15
Hajiya da maigidanta sun rasa yadda zaayi a
dauko Junaid saboda Baba baya iya tuka mota
idan dare yayi. Suna ta shawarwari ne suka ji
karar motar sa. Da sauri suka fito motar duk ya
buge ta a hanya har fitila daya ta lotse. Haka
suka kama shi yana ta tangadi sosai suka shiga
dashi dakinsa. Hajiyan dangi sai kuka take jin
yana ta sumbatu yana cewa ko a aura masa
pretty ko ya saceta ta karfi. Haka Hajiyan Dangi
ya zauna dashi har yayi bacci shi kuma Baba ya
kira senator Rufai ya sanar dashi halin da ake
ciki.
Jirgin karfe 7 na safe suka biyo shiyasa kafin
karfe 9 sun iso kano. Motoci uku ne suka je
tarbar maigirma senate president da matarsa
Hajiya Salama.
Gyadigyadi suka nufa gidan Hajiyan dangi.
Mommy tana ganin Hajiya ta soma kuka. Bana
son irin haka Salama baki san hawayen iyaye
cuta ne ga 'ya'yansu ba? Share idon tayi tace
kinga irin yadda nake fama da yaronnan ko. Ni
fa har cewa nayi baban nasu ya dena saka
masa kudi a account amma yaki. Hajiya tace
abar maganar nan yanzu bari mu gani ko ya
tashi. Su hudu iyayen suka dunguma zuwa dakin
da Junaid yake mahaifinsa ya bude kofar ya
tarar dashi a kwance yana ta busa taba. Kwarai
yayi mamakin ganinsu ya tashi da
sauri...mommy na sannu da zuwa. Hannun daya
kawo zai tabata ta doke tare da jan tsaki. Yasan
fushi take yayi murmushi kawai ya kalli
babansa. Oldman ya hanya? Wannan karon
Hajiya ce ta doke masa baki. Uban naka kake
kira oldman kuma junaidu? Dole kayi ta ganin ba
daidai ba a rayuwarka tunda iyayenka ma basu
da kima a idanunka. Da ace ka maida hankali
kan addini da kasan cewa iyaye sun fi karfin
wasa. Duk zama suka yi Senator Rufai ya cire
hularsa yasa hannuwansa ya dafe kansa. Ya
rasa yadda zaiyi da Junaid fitinarsa kullum
karuwa take. Hajiyan Dangi ce ta labarta musu
dukkan abinda ya faru game da yarinyar da
Junaid yace yana so mai suna Hafsa. Ya
maimaita sunanta a ransa yafi a kirga. Baya jin
komai game da maganganun da suke yi.
Hankalinsa ya tafi can tunanin yadda zai mallaki
yarinyar nan mai suna Hafsa.
A wace unguwa suke? Ita ce kalmar da yaji
daga bakin mahaifinsa. Da sauri yace sabontiti.
Shi kuma wanda zata aura fa? Nan ma Junaid
ya bada amsa. Alhaji zaka nema min aurenta?
Wallahi nayi maka alkawarin zan shiryu indai na
aureta. Hajiyan dangi tace Rufai me kake shirin
yi ne? Shima Baba cewa yayi hala ka manta
haramcin neman aure akan na wani? Mommy
dai binsu ta rinka yi da ido don itama bata san
me mijin nata yake nufi ba.
Batul Mamman
TUN KAFIN AURE💐 16
Senator Rufai dai bai iya basu amsa ba ya fito
ya shiga mota kafin a tayar Junaid ya fito da
gudu ya shiga shima. Yana zama senator yace
sai ka kwatanta wa Bulus hanyar gidansu yaron.
Yaron kuma Alhaji? Ba nema min auren zaka yi
ba? Junaid just do as you are told kaina har
ciwo yake. Ba gobe ne daurin auren ba? No sai
saturday.
Gidan ya fara cika da 'yan uwa da abokan arziki
yan daurin aure da biki. Da gudu ya shigo gidan
har yana zubar da abincin dake hannunsa wata
yayarsu ta janyo shi. Adnan saurin me kake yi
ne haka? Yauwa yaya ina baba? Ya amsa yana
ta haki. Wannan mutumin da ake nunowa a tv
na gani a waje sun zo a cikin motoci masu kyau
sai wani mai bindiga yace babanmu suke nema.
Kai mai bindiga fa kace...eh wallahi amma na
hango na tv din mai kudi ne fa. Jin kamar yana
shirme Zainab ta leqa wajen da kanta ai kuwa
babu karya wasu jeeps ne guda uku duka bakake
amma ta tsakiyar tafi kyau. Ga mutane sun sha
suit kowa rike da bindiga.ba shiri ta koma cikin
gida ta nufi dakin baban su sai dai a hanya suka
hadu har Adnan ya isar da sako. Shima dai
mamakin yayi ya matsa wurin daya daga cikin
guards din yace shine mai gidan. Yana kallo
yaje wurin motar tsakiyar sai ga wasu mutane
su biyu sun fito. Ba ko shakka senate president
ne Rufai Bukar yasha wata ash shadda kana
ganinshi kaga kudi da tsantsar jindadi. Dayan
kuwa saurayi ne kyakkyawa amma fa kayan
jikinsa kamar anyi wasan kura dashi. Guard din
yace ciki zamu shigo. Nan Alh Bashir yace to
cikin hanzari yayi musu jagora. Suna shiga
jamaa sai binsu ake da ido har falon sa. Maman
su Saif ta bi bayansu. Ganin waye bakon ta fito
da sauri ta bada kudi a siyo lemuka da ruwan
roba.
Alh Bashir ya sake gaishe da senator sai yayi
mamakin ganin da kansa ya taso ya bashi
hannu. Bayan sun gama gaisawa yace ni sunana
Rufai Bukar. Ranka ya dade ai tuni na ganeka ni
sunana Alh Bashir. Senator ya kalli Junaid dake
zaune kan kujera ba zaka gaishe shi ba. Nan
take ya sauko ya gaishe shi. To nasan zaka yi
mamakin ganina tare da dana a gidanka ba tare
da an sanar da kai ba. Haba ranka ya dade ai
nasan dole ce ta sa. To akan maganar yarona
ne Junaid... ..haka dai senator ya labartawa
Alhaji komai na halayyar dansa da Hafsa da ya
gani yana so. Ikon Allah kawai yake fada sannan
yace idan na fahimci inda zancen ya dosa so
kake Saifullahi ya hakura kenan. Hular kansa ya
cire ya dago kai idanunsa da kwalla Alhaji ina
tsammanin Allah baiyi maka jarabawar haifar
dan da....kai Junaid ku fita. Suna fita ya cigaba
da magana wadda sai da hawayen da yake
kokarin boyewa suka zubo. Junaid yaro ne me
hazaka tun kuruciya amma yanayin aiki da
jindadin kudi yasa na sangarta shi. Yaronnan ya
janyo min magana fiye da yadda baka zato ga
shaye shaye ga....da dai sauran aikin sabo. A
bisa amana nake fada maka sirrina Alhaji
wallahi wallahi mulki da kudi jarabawa ne sosai
daga Allah. Ban farga da munin share lamuran
yarana ba sai da naji waazi daga bakin wasu
malamai kamar su Daurawa, Kabir Gombe dasu
Dr Sani Rijiyar lemo. Nasan nayi barna mara
iyaka har ina tsoron ranar mutuwata. To a yau
bani da burin daya wuce yaron nan ya shiryu ina
ganin wannan zai zama sanadiyar samun rahma
a gareni. Da gaske mutumin nan kuka yake
Alhaji Bashir ya fada a ransa ganin hawayen
senator. Naji dukkan bayaninka ranka ya dade
amma yarinyar ba tawa bace. Na sani kuma
nasan haramcin nema akan nema. To idan haka
ne ko zaka yarda na kira mahaifinta dashi yaron.
Ai mai nema ke bi kayi mana jagora gidansu
kawai.
********************
Baffa don Allah ka yafe min nasan nayi kuskure
wanda bana fatan sake maimaitawa. Hmm
Hafsatu kenan ki sani kaza tana taka danta ba
don bata sonshi ba sai don ta koya masa
hankali. Hakika muna cikin wani zamani da ake
tallata zina kamar kayan miya, wanda bai siya
ba ma kallon banza ake masa. Amma ina so ke
da ku ma...ya kalli Amira da Anisa lallai ku tuna
wutar Allah mai radadi ce kuma baya bata da
kadan. Sai ka aikata abu ka manta ma dashi
watarana ya dawo ma lokacin da baka
tsammani. Ki je na yafe miki Allah Ya yi muku
albarka. Da farinciki suka tashi dukkansu balle
ma Hafsi zuciyarta fes fes. Suna fita Alh Bashir
ya kira Baffa ya sanar dashi zai zo gidansa da
baki nan da lokaci kadan idan yana gida.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐17
Sakin baki Baffa yayi yana kallon Alh Bashir,
Senator Rufai da Saif. Wane irin rainin hankali
ne suka zo masa dashi. Gyara zama yayi ya
kalli Alh Bashir...yanzu kana nufin ranar asabar
da wani zaa daurawa Hafsa aure ba da
Saifullahi ba? Wai ni Alhaji me kuke nufi da ni da
iyalina ne? Akan hoton da yaron nan ya sa
Hafsa taje suka yi babu abinda banyi mata ba
karshe kuma sai kawai kace min daban yana
son aurenta kuma ka amince. To kai ma ka
amince ne? Ya tambayi Saif. Sunkuyar da kansa
yayi kasa. Shi kam kunya tasa har zuci baya
son auren nan don bazai juri haduwa da
mahaifinta yana tuna ranar da ya kama su a
mota ba.
Zuciyarsa har neman tafasa take don a yadda
yake ji a ransa ko gyada aka dora masa a kan
kirji tsaf zata soyu. Ina amfanin dan cikinka ya
dauko maka abin kunya. Ba don hoton nan ba
sam bazai damu ba idan Saif ya fasa auren
Hafsi. Senator Rufai da yake gefe yana kallon
abinda ke faruwa a falon yayi dan gyaran murya
don ya fuskanci kwata kwata kudinsa da
mukaminsa baiyi wa Mal Aminu kwarjini ba.
Kallon da ya yiwa Baffan hafsi yasa yayi
shiru...malam tun a gidansu munyi magana dasu
yaron yace indai ka amince to zai iya hakura da
ita. To a wane dalili ne wai zaku mayar dani
karamin mutum irin haka? Ko don ba 'yarka bace
shine zaku rinka juya min ita kamar waina.
Bakin Baffa har kumfa yake yana magana ba
karamin bacin rai ya shiga ba kila kudi senator
ya basu shine suke neman yi masa wannan cin
kashin. Senator Rufai yayi masa bayanin halin
da dansa yake ciki da tsoron karin lalacewarsa
sai baffa ya kada baki yace wato lalataccen
danka kake so ya shiryu sanadiyarta ko? Idan
kuma abin ya faskara ya dora min ita akan
turbar lalacewa fa? Haka yayi ta fada karshe
yace ni dai gaba daya na fasa bawa kowa Allah
Ya hada kowa da rabonsa.
Abin da senator yake ta kokarin boyewa game
da jikinsa ne ya faru don kuwa yana tashi
kirjinsa ne ya fara ciwo sai jiri ya debeshi ya
fadi. Baffa ko kallonsa baiyi ba don a tunaninsa
na karya ne tunda yaga kudi bai dauke masa
hankali ba. Saif da Alh Bashir kuwa da sauri
suka yi kansa Alh Bashir a tsorace yace haba
Aminu taimaka mana. Idan mutumin nan ya
mutu a gidan nan wallahi duk sai an daure mu
ko a yanke mana hukuncin kisa.
*******************
Alh Bashir da Mal Aminu ne tsaye gaban gadon
da aka kwantar da Senator Rufai bayan yasa
iyalinsa sun dan basu wuri. Da kyar yake
maģana yace nasan a dalilina kun sami sabani
amma bisa amana zan fada muku sirrina. Hakika
duk wata kujerar iko a kasar nan is addictive
maana idan aka hau ba'a son sauka indai ba ta
sama za a hau ba. Magudin siyasa da hadamar
kudin talakawa duk munayi. Ina tsammanin ma
shiyasa Allah Yake jarrabarmu da lalurori da
kala kala da 'ya'ya marasa da'a. Yasa hannu ya
share hawaye. Ina matukar son Junaid ganinsa
nake tamkar mahaifina saboda kamaninsu. Duk
abinda ya zama a yau laifina ne saboda yadda
na sakar masa yake facaka da kudin talakawan
kasar nan. Tun farkon abin mahaifiyarsa ta fara
hanawa ni kuma ina ta ganin kamar lokacinsa
ne. Maganar tasa sarkewa tayi saboda tari Mal
Aminu ya rirrike shi. Sai da abin ya lafa ya
cigaba da magana. Muna cikin wani lokaci da
yaran da ka tsaya da kyau wurin tarbiyarsu ma
baci suke balle wanda aka sakewa. Masifu sunyi
mana yawa duk a dalilin nesanta kanmu da
mukayi daga Allah da koyarwar Annabi SAW.
Mal Aminu ya dan tabe baki don shima sheda ne
akan rashin adalcin kasarnan da yadda yake
ganin tarbiyar yara yanzu a matsayinsa na
malamin sakandire. Ji yayi senator ya rike masa
hannu wanda hakan ya dan tsorata shi. Sati
biyar kenan da likita ya tabbatar min da cewar
inada ciwon zuciya kitse ya lullube ta. Babu
wanda na fadawa sai ku biyun nan da na hadu
daku a yau. Likitan ya tabbatar min ko dai na
cigaba da rayuwar shan magani ko na mutu.
Subhanallahi Alh Bashir ya fada.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 18
Hakika mutuwa abin tsoro ce musamman ga
irinmu masu aikata sabo muna sane. Kamar
yadda na fada a gidanka Alhaji waazi naji yayi
matukar razana ni. Ina tsoron mulki yanzu, ina
tsoron kudi, ina tsoron haduwa da Allah akan
laifukana sannan ina tsoron samun kamasho
daga laifukan Junaid tunda laifina ne abinda
yake yi. Akan yarinyar nan ya dawo gida da
guduwa yayi. Akan ta yayi min alkawarin
shiryuwa shiyasa kaga na dage. Idan har na
mutu yana wanan rayuwar kabari zai min kunci.
Kuka ne yaci karfin senator sai dai su uku
mazan akwai hawaye a idanunsu. A wannan
zamani hanyoyin dulmiyar da bayin Allah akwai
yawa ga bayyana sabo saboda rashin tsoro. Mal
Aminu yace zan amince amma sai anyi masa
gwaje gwajen cutuka saboda lafiyar Hafsa. Ko
sau daya kada yazo gidana sai na tabbatar da
lafiyarsa sannan zaa fara maganar aure. Abu na
karshe zamu rubuta yarjejeniya kai Alhaji ka
zama shaida duk ranar da ya koma ga miyagun
halayensa bayan aurensu kun amince kotu ta
raba auren idan yaki shiryuwa. Na yarda na
amince kawai senator yake fada. Ba zai iya fada
musu mugun mafarkin da yayi yaga kansa cikin
wuta yana ta shan azaba ba a dalilin dukiyar da
suke wadaka da ita. Abin tamkar gaske ya gani.
Mutuwar abokinsa washegarin mafarkin wani
wanda yayi gwamna karo biyu sun shiga sun fita
ya zama minista shi ya kara tada masa hankali.
Gawar abokin nasa bakikkirin kamar an shafa
gawayi gashi yaransa suna ta murna harda party
ranar da yayi bakwai wai giwa ta fadi. Sosai ya
tsorata har baya iya baccin kirki. Uwa uba kuma
yaga yadda hukumar kama masu watanda da
arzikin kasa su cinye a cikinsu tasa mutane a
gaba. Wannan tonon asirin ma na duniya ya ishi
bawa mai tsoron Allah.
*******************
Kuka take sosai a daki tunda Baffa ya sanar da
ita abinda ke faruwa. Duk gidan al'amarin bai
musu dadi ba Mama tana ta mita. Hafsi tayi
fushi sosai da Saif da ace wani abu ma ya faru
tsakaninsu haka zai fasa auren karshe duk
wanda ta aura yaci mata zarafi. Yanzu duk
farincikin da take baffa ya yafe mata ashe hoton
nan bazai fasa jawo mata sabbin masifu ba
kullum.
Ummati ce ta shigo da sallamarta Hafsi ni fa
ban gane zancenki ba a waya. Rungume
aminiyarta tayi tana kuka tana sake mata
bayani. Ummati ta kalleta yanzu shi dan sanatan
kin ganshi? Ke wa yake ta tashi ko sunansa ma
ban sani ba. Ai kinji dadi Lawal baizo kun yi
naku hotunan ba. Wannan hoto bai zo min da
komai ba sai sharri. Ummati rarrashinta kawai
take tana tuna yadda Allah Yasa ta auna arziki
bata riga tayi hoton ba. A da suna wa abin
kallon wayewa sai dai yanzu sunyi karatun ta
nutsu. Duk wani hani ko umarni a musulunci
akwai alkhairi mai kyau a tare da shi.
*******************
Da sassafe Junaid ya tafi asibiti. Sam daren jiya
baiyi bacci ba tunda Hajiyan Dangi ta sanar
dashi yadda mahaifinsa yayi dasu Baffa. Ya
tabbatar ba wani abu Baffan ke tsoro ba sai HIV
da sauran dangin cututtukan da ake kamuwa
dasu ta wannan hanyoyin.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐19
Kwanaki uku kenan tana binsa yanzu ta gama
gano gidan da yayi masauki abinda ya rage
mata yadda zata sami damar yi masa abinda
bazai taba mantawa ba har abada. Idan ka bari
motar nan ta bace mana bazan biyaka ba
yau...dreban taxi din ya kara gyara mirror din
gaban mota yadda zai ganta da kyau. Mace har
mace sai dai babu alamun mutumci a tare da
ita. Kallonta yake yana hadiyar yawu saboda
irin shigar da tayi ta matse dukkan jikinta ga
kamshi kamar wadda tayi wanka da turare. A
bakin gate din wani asibiti yayi parking inda
yaga motar da suke bi ta shiga. Tafiyarta kamar
da gayya don ta tada hankalin maza...a
zuciyarsa dan tasi Allah Ya isa yayi mata shi ba
aure ba kullum yana yawo da ita a gari.
Junaid ya kara kyau saboda shaye shayen da ya
dena yan kwanakin nan. Bayan sun gaisa da
likitan ya sanar dashi irin tests din yake so ayi
masa wanda suka hada da HIV da hepatitis.
Haka ya zauna aka debi jinin yasa kida a
kunnensa yana jiran result. Ba karamin farinciki
yayi ba ganin komai is negative. Tabba ba
kowacce mace yake muamala da ita ba kuma
yana amfani da hanyoyin kariya amma dai
gaskiya ya tsorata. Ana bashi result dinsa wani
tsalle yayi da ihun murna. Yana fita Tilly ta fito
daga inda ta boya tabi layin ganin likita. Da kyar
da salon bugun ciki taji abinda ya kawo Juni
asibitin. Allah Ya kama ka Juni boy sai ka gane
baka da wayo a hannuna.
******************
Baffa da Mama sun yanke shawarar Hafsi ta tafi
gidan kanwar mama dake aure a Funtua har sai
yaji makomar Junaid. Haka ta tafi ba musu ita
duk abinda zai sa su manta da laifinta na baya
nema take shiyasa suka yi shawara da ummati
kan cewa bazata musa musu zancen auren dan
senator Rufai ba. taso kwarai taga ko waye
Junaid dinnan sai ta hakura ganin iyayenta basa
yi mata zancensa.
A gajiye Tilly ta shiga gidan aminiyarta Rosie.
To mutanen banza daga ina kike tun safe ba hi
ko hello. Harara ta galla mata Ke ni bani abinci
kizo muyi magana akwai gist fa. Rosie ta washe
baki hala kin samo hanyar bi ta kan wannan
shegen dan sanatan? Fadi ki kara Tilly ta amsa
tana fari da ido. Yanzu dai cikina is empty.
Wata gyatsa tayi me kara sannan tasa kafa ta
ture plate din abincin can gefe. Tana sakace
hakori tace Rosie yar mutan Gaya kina ji na. Ni
da tun dazu na matsu ki gama cin abincin, to ya
akayi? Nan ta bata labarin yadda ta bishi asibiti
da test din da yayi. Ni bansan me ya faru dashi
ba these days amma naga baya zuwa wuraren
shakatawa. Da na yanke shawarar na biya
doctor din su fada masa yana da HIV to sai nayi
tunanin kada yaje wani ya sake aga negative.
Tunda ta fara magana Rosie take dan tunani. Ke
banza magana fa nake. Ki fada min yadda zanyi
ya aureni mu kwashi namu national cake din. Ai
ki kwantar da hankalinki sister. Ki bani two
months kawai sai muje gidansu. Two months
kuma? Yi min bayani mana. No ki bari idan har
naga titin da nake so mubi mai billewa ne zaki ji
komai. Ke dai ki cigaba da sa ido don mu
tabbatar da inda yake ko yaushe.
*******************
 Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah. Senator
Rufai ya mayarda Alh Bashir wani abokin
shawara don har yau Mal Aminu bai gama
sakewa dashi ba. Alh Bashir yasha fada masa
idan har suka dage zasu iya sawa ya aikata
alkhairi a ragowar tenure dinsa. Shi kuwa Junaid
a kano ya cigaba da zama wurin Hajiyan Dangi
ya rage shaye shaye sosai. Har mamaki yake
bai taba ganin Hafsi da idanunsa ba amma sai
bin dokoki yake saboda ita kamar wanda aka
asirce.
Saura sati uku bikinsa da Hafsi ta dawo kano.
Baffa kam sai da yaga result din tests har daga
asibitoci biyar ya gamsu tare da bawa Junaid
damar yazo ganin Hafsi.
******************
Ba wata kwalliyar kirki tayi ba don ma yayarta
Hadiza ta matsa mata ne. A falon gidan Baffa
yace su zauna yadda mutane zasu rinka
wucewa. Hafsi murmushi tayi daya fadi haka
lallai laifi Allah kadai ke yafewa duka amma
mutane abu kadan sai yasa su tuna baya. Tun
kafin ta daga labulen falon gabanta ke faduwa
wanda ta rasa dalilin hakan. Da wannan
muryartata mai kamar shagwaba tace Assalamu
alaikum. kamar a dauke masa wutar jikinsa
Junaid me cika idon yan bariki ya kasa amsa
mata. Ido kawai ya bita dashi.....you are so
beautiful,so pretty. Kin shigowa tayi ganin
yadda ya rude saboda ganinta. Tsoronta daya
kada ta shigo ya nemi taba ta. Karaso mana
Hafsi ko....ya fada yana daga gira daya.
Sunkuyar da kanta tayi kasa baka amsa min
sallama ba ai. Dan bata fuska yayi ke da
gidanku. Anyway wa alaikum salam. Tana zama
ya tashi daga inda yake ya dawo kujerar kusa
da ita. Wallahi kin hadu sosai ma kuwa. Can't
wait to have you. Gabanta taji ya fadi anya
wanan ne Baffa ya aminci ta aura. sai ma a
lokacin ta kare masa kallo. Don kyau dai yana
da shi amma wani gashi ta gani ya danyi tsini
daga tsakiyar kansa ga wani wando me fadi irin
wanda black americans na ghetto suke sawa.
Rigar jikinsa kuwa itama me fadin ce ta dan
sauko masa. Nan take taji ta tsane shi bare da
ta kalli wani kwantareren takalminsa. Yanzu fa
sai ace duk kayan nan masu tsada ne ko ta
fada a zuci.
Ganin yadda take kare masa kallo yasa yayi
shiru shima yana dada kallonta. Can daya ji
shirun yayi yawa yace yah nayi miki ko? Firgigit
ta kalle shi bata fahimci zancen sosai ba kawai
sai tace masa a'a. Ya zaro ido me kika ce?
Kinsan yadda mata ke rububina kuwa? Ganin ya
dauki wata hanyar sai ta katseshi da gaisuwa.
Bayan yan mintuna tace zata shiga gida.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐20
Ke kada ki raina min hankali mana. Ya daga
zuwana zaki ce wani zaki shiga gida. Ya kara
kankance ido irin na 'yan duniya ko kina son
nayi miki irin abinda wanan matsiyacin yayi miki
ne a wadannan pictures din? Gyara zama tayi
tana kallonshi. Kaddai ace a hotunansu da Saif
ya ganta. Tasan ance a hoto ya ganta amma
bata da details din abinda ya faru. Da kyar tace
wane hoton kake nufi ne. Wata babbar waya da
bata taba gani ba ya dauko ya nuna mata
hotunan. Gabanta ne ya fadi a tsorace ta mike
wallahi ni ba yar iska bace idan ma abinda ya
kawo ka kenan. It was my first and it will be my
last in sha Allah. Tafi ya rinka yi tana magana
eyye! eyye yarinyar ta iya turanci ashe. Kunya
taji ta kamata shi kuwa ya cigaba da magana.
Kar ki damu fa Juni has done worst amma
tunda naga babanki yana pretending kamar ke
saint ce ba komai shiyasa ma zan aure ki. Daga
nan har muyi aure zanyi kokarin dena kula wasu
matan sai ki dage ki koyi jan hankalina. Da wuya
ake impressing din Juni. Yana gama magana ya
tashi ya good night Hafsi Hafsi. Daga bakin kofa
yayi blowing mata kiss. Sai da ya fita taja wani
numfashi. Lallai akwai matsala ina ita ina
wannan mai zubin 'yan iskan.
*********************
Fuska ba annuri ya shigar mata daki ba ko
sallama. Junaidu abin ya motsa ne ka shigo min
daki kai tsaye. Dafe kai yayi oh sorry Hajiyata
raina ne a bace. Dan murmushi tayi tana nuna
masa wurin zama. Zo nan dan Hajiya bani
labarin yadda kuka yi da Hafsa. Kara zumburu
baki yayi wai don rainin hankali baki ga yadda
take min wani irin kallo ba. Hajiyan dangi dariya
tayi ya bita da ido me kuma ya faru kike min
dariya? Yo dannan banda abinka ji irin shigar da
kayi kamar wani tsohon dan tasha. Duk kayan
jikinka sunyi maka yawa. Lah Hajiya gayun
kenan fa. Black americans hadaddu ai irin
shigar nan suke irinsu ice cube, snoop dog,
kanye west da....kafin ya kara magana ta daga
masa hannu dakata haka. Yanzu don Allah zaka
iya kawo min sunayen Annabawa ko Sahabbai
goma? Ka rasa wanda zakayi koyi dashi sai
makiyan musulunci? Kaji tsoron Allah Junaidu
ka gyara rayuwarka. Yanzu dubi wani gashi a
kanka kamar juji kuma nasan kana sane ka tara
shi. Kana girma kana kara cin kasa. Bakin nan
na Junaid kam yayi tsine saboda yadda yake
zumburo shi..dan me zaayi masa fada. Sai dai
kuma maganar ta dan shige shi. Ya mike zai fita
daga dakin Hajiya kiyi hakuri da yardar Allah
zaki ga na zama salihin mutum ko, yanzu ma ai
kinsan Juni yayi sanyi. Filo ta jefe shi dashi ya
gudu don yasan ta tsani Junin nan da ake
kiransa.
*******************
To baiwar ciki ina nan ina ta nema miki mafita
wurin Juni ke banda ci babu abinda kika iya.
Tilly ta hadiye naman da ke bakinta da kyar kin
dai sanni tun farkon haduwarmu ina da son
abinci musamman idan akwai nama. Rosie ta
bata fuska to naji mayya amshi ki karanta
wannan. Dafe kirji Tilly tayi me zan gani haka?
Aure zaiyi, ai wallahi uban kuturu yayi kadan. Ni
fa banda kudinsa shima kansa ina so. Wata
takardar Rosie ta mika mata tace to wanan
kuma fa. Ci...ci...ci me? Mun shiga uku Rosie ya
akayi kika bari ciki ya shige. Rosie ta dakatar da
ita tsaya kiji ai cikin nan shine license dinki for
now. Ke dai ki saurare ni da kyau kinsan tunda
muke bamu taba yin babban kamu irin haka ba
dole mu rike wuta.
****************
Nafisa da Hamida sai shirye shirye suke dan
uwansu zaiyi aure. Kashe kudi suke kamar babu
talauci a nigeria har sai da mommy tayi
magana. An hada lefe na gani na fada a cikin
gidan daga baya Senator ya yi musu gine mai
kyau babu abinda bai saka ba yace a nan zasu
zauna har sai yaga kamun ludayin zaman nasu
don bai gama yarda da dan nasa ba.
A kano ma su maman Hafsi suna nasu shirin
duk da sun san Senator Rufai da iyalinsa ba
tsaransu bane amma dai suna gudun gori ace
sikau suka kai yarsu.
Ranar karbar lefe tazo dai dai da sati daya kafin
biki Hafsi bata sake ganin Junaid ba shima bai
neme ta ba don yasan ta kusa shiga hannunsa
wannan yatsine yatsinen da take masa dole ta
ajiye a gefe.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 21
Yan uwa da abokan arziki sun cika gidan. Yan
ganin kwal uwar daka ma suna nan zaune suga
irin abinda zaa kawo wa Hafsi.
Akwatuna ne ake ta shigowa dasu gidan har
goma sha takwas. Hajiyan Dangi ita ce tayi
jagora ta nuna musu kayan. Akwati set biyu
guda sha biyu na amarya ne komai na ciki me
tsada ne harda set din gwal uku. Sai daya na
baffa, na Mama, na 'yan uwanta sai kuma
wanda zaa bawa yan uwa da abokan arziki.
Dukkansu shake suke da kaya. Ga kudin dinki
dubu dari biyu. Wai a haka ma don kada su zake
da yawa ne. Ranar bakunan mata sunyi magana
har sun gaji kowa da abinda take fada. Mama
dai dubu hamsin baffa ya bata na tukwici shima
don su fita kunya ne. Wata yayarsa ta kira ta
fadawa tare da dora nata dubu goma. Yayar da
yake tana da dan rufin asiri ta kawo talatin
itama Hadiza ta kawo goma suka cike dari.
Hajiyan dangi mace mai kwarjini da kamala tace
ko kwandala ba zasu karba ba yar da aka basu
ma sun gode. Suna fita aka hau bude buden
akwatuna ana kallon yadda ake wasa da kudi a
kasar mu.
*******************
Hafsi tasha gyaran jiki sai sheki take ga lalle
wanda mai lallen ma Hamida ce ta turo ta har
gidansu. Ummati tace Allah Yasa kuyi zaman
lafiya naga kamar basu da raina mutane. Haka
akayi kamu a wani makeken filin senator wuri
ya dauki mutane. Idan kaga Hafsi kamar wata
yar tsana saboda mai kwalliyar ma tafiyayya ce.
Tayi kyau har ta gaji. Su ummati ma da
kannenta baa barsu a baya ba. Itama Batul
Mamman sai wani shishshige musu take taga
kudi.
Ranar dinner wasu kaya da mama ta kure basira
ta dinka Hafsi ta saka. Ummati tana zuge mata
zip din rigar Hamida ta shigo da wata riga da
skirt na lace ne ko material gashi nan dai abin
mai daukar ido golden brown. Tunda aka fara
biki ta likewa su ummati sun zama kamar
kawaye. Kayan hade suke da takalma da head
and veil. Hafsi ta bata rai ni fa wanan zan saka
mama ce ta dinka min. Hamida ta marairaice
haba matar yaya anko yake son kuyi da kansa
ya bayar aka dinka miki. Suka shiga ban baki ita
da Ummati amma sam Hafsi taki yarda har
zancen yakai kunnen mama. Nan tayi musu
sulhu gobe idan zaa kaiki sai kisa nawan zan ga
mai hanaki amma yau dai ki saka na angonki.
Maman ummati tayi dariya to yar shagwabar
Mama gobe dai zanzo da bokitin share hawaye.
Taro yayi taro wuri ya cika da mutanen da suka
amsa sunansu a naija. Yan mata anyi dinkunan
rashin mutumci suna tafiya kamar sanduna babu
lullubi. Matan aure sai hura hanci wai kar a
raina su. A mota aka tsayar da hafsi har Junaid
ya iso. Ko da ya fito da shaddarsa golden brown
bata gane shi ba. Duk da yasa hula ta kula yayi
aski, ya gyara fuska gaba daya ya canja. Shima
kallonta kawai yake har ya karaso. A kunnenta
ya rada mata ni kada ki cinye ne da kallo, it has
been three weeks, kin kara kyau kema. Cak ta
tsaya saboda yadda yayi kusa da ita. Ana fara
musu alamar su shigo cikin hall din taji yana
kokarin kama mata hannu. Kokarin fizgewa tayi
shi kuwa ya matse hannun ga zobba a hannun
har ta fara jin zafi. A hankali tace kaci bashi
wallahi. Ya sassauta rikon suka shiga.
Dinner tayi kyau kuma ko liki baayi ba wannan
kuma dokar Hajiyan dangi ce. Tilly da aminiyarta
Rosie ma sun sami shiga a wurin daukar hoto
Junaid ya gansu. Tsoro ne ya kamashi ya hau
adduar kada tayi masa wani haukan a wurin don
bai ma tsaya tunanin yadda suka sami katin
shiga ba. Bayan sun dau hoto ta bashi wani
envelop congrats Juni boy. Hafsi ta dan kalle ta
Tilly tace amarya mun dai rigaki lasar zumar
muna fata tayi miki dadi yadda....junaid ne ya
katse ta get out...ba musu ta kama kawarta
suka fita don idanunsa sunyi jazur tasan halinsa
sarai. Babu wanda ya kula sai Hafsi kowa na
shaanisa.
Dreba ne a gaba sai Ummati baya kuma Junaid
da Hafsi don ya nace shi zai mayar da ita gida.
Tayi kokarin daurewa ta kasa can kasa kasa
tace wace wannan matar ne. Dama ransa ya
gama baci gashi yana son dena shaye shaye
babu ko taba a aljihunsa ya harareta idan zaki
bude baki kiyi magana ki bude sai wani kasa
kasa kike da murya kamar wata mumina.
Ummati ta juyu don taji me yace...zare mata ido
yayi ke bana son gulma me kike kallo. Ba shiri
ta juyar da kanta. Tooooh wannan ne mijin da
Hafsi zata zauna dashi. Hafsi dai shiru tayi tana
kallon fuskarsa. Sai tayi da gaske akan wannan
mutumin. Abu daya ta sani dai da yana cikin
farin ciki kafin yaga wannan matar. Babu ko
sallama suna zuwa gida suka fita yace da dreba
yaja motar su tafi.
Daki ya shiga hankalinsa a tashe yana tarrabin
abinda ke cikin takardar da Tilly ta bashi.
Juni boy
Nasan kana cikin farin cikin auren da zakayi
gobe nima ina taya ka murna. Sai dai ina me
tabbatar maka gobe zanzo Abuja a tawagar
amarya. Ga wedding gift nan.
Luv Tilly
Bude daya takardar yayi gumi ya karyo masa
ganin reult ne dake tabbatar da Tilly na da ciki
har wata uku.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 22
Ko kayan jikinsa bai canja ba ya fita zuwa hotel
din da abokinsa Imran yayi masauki. A waje ya
tsaya yayi masa waya. Sai a karo na uku ya
dauka ya sanar dashi yana wurin parking ya fito.
Suna hada ido Imi yace yace ya mutumin you
sounded worried fa. Me ya faru ne? Envelop din
Junaid ya mika masa. Imi ya rinka dariya bayan
ya karanta harda hawaye a idonsa. Can ya daki
kafadar junaid...haba mutumina kada ka bada ni
mana. Yanzu har akwai wata chick da zata ce
kayi mata ciki ka yarda? Matan nan fa sun fi mu
tsoron faruwar hakan tunda su ke da wahala.
Wani abin kawai take so. Fuskar Junaid babu
sauran kwanciyar hankali uhm uhm Imi aure fa
zanyi kuma Allah Ya sani ina son yarinyar ina
kuma son gyara rayuwata. Kaima Allah Ya baka
tagari. Kayya yaro gigin soyayya ke dibanka bari
romon ya kare zaka neme ni ne. Bayan ina
kallo dazu amaryar taka ta murguda maka baki.
Kansa ya shafa yana dariya da irin tsokanar
fada ne yaga tana kulashi shiyasa yake mata
haka a fili yace Kai kam kamar ana kada maka
gangar shaidanu..ya ina cewa zan shiryu kana
min mugun baki. To yi hakuri na Hafsa Imi ya
fada yana dariya...yanzu dai ka manta da
wannan yarinyar kada ma ka sata a rai. Idan ta
sake nemanka kaci ubanta da kyau wallahi zata
kyaleka. Kada ma ka fara bata kudi don sai tayi
blackmailing dinka. Nan suka yi ta shawara sai
wurin ukun dare Junaid ya koma gida.
******************
Bacci sam yaki zuwa idanun Hafsi sai tunani
take kala kala. Wannan Junaid din dabiunsa na
bata tsoro( wai ma don ya rage!) Gashi haka
hankalinta bai kwanta da matar da ta bashi
envelop ba. Maganar Tilly duk ta tsaya mata a
rai wai sun rigata lasar zumar.....ehew abin
kyankyami ma zancen ta fada a fili tana
yamutsa fuska. Anya ba yan is...sai tayi shiru
zargi babu kyau don haka mafitar ta daya shine
ta mike ta dauro alwala ta tayar da sallah. Haka
tayi ta nafila har asuba tana addua sannan ta yi
bacci.
Sai wuraren goma na safe ta farka. Shima
Hadiza ce ta tasheta da dundu...to kasa ana
shirin fita daurin aure kina kwance kina bacci
hankali kwance. Mutssika idanu tayi ta
mike...ina ummati ta tafi Yaya? Debo miki ruwan
zafi kiyi wanka. Kinsan dai baffa yace karfe biyu
zaa bar kano so kiyi da jiki kafin a dawo daga
daurin aure. Ta kalli agogon wayarta...Allah
sarki nan da mintuna arbain da bakwai kin zama
matar aure. Cikinta taji yace kulululu da gaske
abin yazo. Kuka tasa wa Hadiza inama basuyi
wadannan hotunan ba tun kafin aure da yanzu
Saif ta aura. Ummati ta ajiye bokitin hannunta ki
gode Allah baa daura dashi ba don yadda aka ce
Junaid yayi bayan yaga hotonki da kila a gidan
auren zai biyo ki ko ma ya kashe auren. Hadiza
tace kyale ta ummati ai tasan wani baya auren
matar da ba tasa ba.
Kayan da mama ta dinka da aka hanata sawa
daren jiya su tasa ai kuwa tayi kyau sosai.
Katon mayafi ta yafa ga kamshi ko ta ina.
Taro yayi taro don manyan mutane na kusa da
nesa sunzo bikin dan manya. Junaid yasha
cream shadda harda babbar riga da brown din
takalmi da hula maroka suna ta sanaar su. Daga
karshe dai Liman ya daura auren Junaid Rufai
Bukar da Hafsa Aminu Garba.
Mijin Hadiza ne ya bugu ya sanar da ita an
daura auren kan sadaki dubu dari gida ya cika
da guda da hayaniya. Wata 'yar makarantarsu
tace gaskiya Hafsa Aminu kinyi saa muma Allah
Yasa mu a danshinku. Yan Amin kuwa suka
amsa.
Ansha koke koke lokacin dasu Hajiyan dangi
suka zo daukar amarya. Mama kasa daurewa
tayi ta kulle kanta a daki. Baffa ma yana mata
nasiha yana sharar kwalla. Bai taba tunanin zata
yi auren nesa ba, aure ma irin na gidan Senator
Rufai Bukar. Motoci har wajen layinsu Hafsi.
Cikin motocin kuwa harda wadda Rosie da Tilly
suka dauko haya suka bi ayarin kai amarya. Don
karfin hali har mutane uku suka dauka aka dauki
hanyar abuja.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 24
Dakata Imi zanyi maganinta da kaina. Cheque
ya bata na dubu dari biyu. Idan na sake ganinki
duk abinda ya faru dake ki kuka da kanki. Suna
jan mota ta fita ta tari taxi don yau Rosie bata
biyo ta ba saboda laulayi daya fara damunta.
Murna take sosai don wannan cheque din sabon
makami ne a gareta.
Daki aka bawa Hafsi da kawarta sauran yan biki
suna wani masaukin. Nafisa ta tafi da yayarta
Hadiza gidanta ita kuwa Hamida ta nace tare
zasu kwana da amarya kafin washegari a kaita
side dinta.
******************
Wani sabon kukan Hafsi da Ummati suka dasa
lokacin da aka fito rakasu bakin motocin da zasu
mayar dasu kano. Yanzu haka zata zauna da
mutanen da bata gama sanin halinsu ba. Ga
uban gayyar wato Junaid ko doriyarsa bata sake
ji ba tun a wurin dinner. Kamar yasan tunaninsa
take sai gashi ya fito da kananan kaya a jikinsa.
Yau ma yayi kyau tunda kayan ba oversize
bane. Har kasa ya durkusa ya gaishe da
gwaggwaninta dasu Maman Ummati. Hadiza ta
rungumota tana ta bata baki akan ta dena kuka
haka. Kyaleta Hadiza na gulma ne fa kuna tafiya
zata sake. Harararsa tayi yace ai gara ki nuna
musu halin da kike min. Hajiyan dangi ta kama
hannun Hafsi rabu dasu zan miki maganinsu.
Anisa ta Amira ma sunyi nasu kukan da
alkawarin zuwa idan anyi hutu. Haka dai suka
rabu abin tausayi ana janye Hafsi daga jikin
Ummati.
Bayan duk sun tafi aka dawo falo. Hajiya da
mommy suka yi musu nasihohi da fatan alkhairi.
Nafisa da Hamida suna gefen amarya suna kula
da masu dada share wurin kafin su kaita. Sai da
aka gama fadan Junaid yace to Allah Ya saka
da alkhairi amma yaushe zaku bani matata?
Mommy ta cire takalminta ta jefa masa to
tsohon mara kunya ai gara ka nuna hali. Ya dafe
kai Hajiyan dangi tana duba masa...yauwa
Hajiya duba ki gani ko kan ya fashe. Hafsi kuwa
dariya tayi har sauti ya fito yace kinci bashi
Hafsi Hafsi. Nan suka zauna ana ta raha sai
kawai suka ji sallama.
Mata ne biyu sunsha hijab daya sai kuka take
dayar tana bata hakuri. Dif Junaid yayi ya dena
dariyar da yake saboda ya gane mai muryar.
Zuciyarsa ke bugun uku uku yaji yawon bakinsa
ya kafe. Itama Hafsi ta gane yarinyar ko baa
fada ba tasan akwai matsala don ta kula da
yadda ya kidime da ganinsu. A fusace ya
kallesu ubanwa yace ku shigo har nan? Wai ma
waye ya baku izinin shigowa.
Mommy da Hajiya cikin rashin fahimta suke
kallonsa. Junaid kana hauka ne zaka ga baki
kayi musu irin wannan tarbar? Rosie ta kiyi
hakuri Talatu an gama cutarki shine zaa ci
mutumcinki saboda baki da galihu. Mommy tace
ku zauna muji abinda ya kawo ku. Tilly harda
fyace majina ai yafi kowa sanin dalilin
zuwanmu. Idanun Junaid kamar an bada masa
yaji yayi kanta yana sirfa mata zagi.
Kana tabata zansa a kulleka mara mutumci
kawai. Daga kai yayi suka hada ido da Senator
Rufai. Alhaji wai me ke faruwa ne? Yace ku
zauna muyi magana. Su Rosie aka wani rakube
a kasan carfet ita da Tilly. A bakin gate na
gansu suna fada da security yarinyar can ya
nuna Tilly tana ta kuka. Ganin haka na tsaya
aka kirasu tayi min bayani. Cheque ya dauko
daga aljihunsa ta mikawa Mommy. Kingani kudin
daya bata jiya wai taje a zubar mata da ciki.
Kinga goshinta inda ya fashe lokacin da yake
dukanta ta fadi. Kamar anyi masa wanka da
ruwan zafi haka yake ji. Me tilly ke nema ne a
tare dashi? Kokari yake su hada ido da Hafsi ita
kuwa idonta na kasa tana kuka a hankali. Salati
su Hajiya suka hau yi tace lalacewar taka har ta
kai ka bada kudin yin kisa. Kuka ne ya kwace
musu ita da Mommy. Junaid yana ta basu
hakuri. Hafsi ta mike zata shige daki don taga
zancen kamar ba nata bane. Dawo dawo ai gara
kada a munafunce ki Hafsa. Senator ne ya
kirata ta dawo ba musu. Ya maida kallonsa ga
Junaid. Ka san yarinyar nan? Eh na santa amma
wallahi ban dake ta ba. Rufa min baki
shashasha. Kullum yadda zaka zubar min da
mutumci yake nema. Ko tsoron mutuwa baka yi.
Ke ya daka ma Tilly tsawa ta dago a firgice
garin yaya kika amince masa. Ta kara jan
majina ta fara bada labari. Ni ina sayar da kati
ne kusa da wani club da suke zuwa a gidan
wannan yayartawa nake da zama shine ya
biyoni wai yana sona. Rannan rannan sai
kuka....Rosie tace kudin kati yace taje ta karba
shine yayi mata fyade. To ganin cewa danka ne
bamu daga zancen ba.
Wallahi Álhaji karya suke duk karuwai
ne....bakinsa yaji Hajiya ta make. Rufa mana
baki. Rosie ta cigaba to da mun hakura sai
kuma ga ciki shine muka neme shi kawai jiya
sai yazo har gida ya bata cheque ita kuma ta
karba don taga bana nan.
Hafsi tayi saurin daga kai tace ba kece kika zo
wurin dinner ba kuwa daren jiya? Junaid yace
yauwa Alhaji wallahi kaga itama zata min sheda
wurin dinner ta biyoni ba raping dinta nayi ba.
Mommu tace Hafsa kada ma ki fara kare masa
don bakisan waye Junaid ba. Duk abinda akace
yayi zan yarda. Allah wadaran iskanci yau
mahaifiyarsa ma taki yarda dashi.
Senato Rufai ya kalli dansa cikin bacin rai yace
ka taba ganinta? Eh ya amsa masa. Muamala ta
shiga tsakaninku? Shiru ya kasa magana. Ya
daka masa tsawa kai kurma ne. Hawayen da
yake boyewa ya sauko yace eh. Innalillihi wa
inna ilaihi rajiun. Koda ba auren so suka yi ba
amma ace mijinka yana neman mata akwai
ciwo. Hafsi duk auren ya kara fice mata a kai.
Senator yace to ke zaa kaiki asibiti a sake miki
gwaji idan ya tabbata da gaske yayi wa Junaid
wani mugun kallo zamu jira ta haihu a aura
maka ita. Mikewa yayi a fusace su Hajiya suka
bi bayansa.
Batul Mamman
TUN KAFIN AURE💐23
Tunda suka hau hanya basu tsaya ba sai a garin
Abuja. Motar da Baffa ya hado da kayan da yayi
wa 'yarsa ita ce ta karshe cikin jerin motocin.
Duk girman gidan ba duka motocin bane suka
sami shiga ba saboda yawansu. Shima gidan
cike yake da mutane gashi basu iso da wuri ba.
Dakin mommy su Hamida suka kai Hafsi. Ita dai
kanta a kasa taki dagowa ta kallesu. Mommy
cike da murna tace nasan kun gaji ga magriba
ta kawo kai a kai su masauki suyi wanka aci
abinci sai su shirya akwai wata dinner din karfe
takwas. Hafsi ta kankame hannun ummati sai
Nafisa tace mommy wanan fa aminiyarta ce
tare zasu zauna kafin anjima ta dan kanne ido ai
sai kamarsu ta Junaid ta kara fitowa Hafsi tayi
saurin dauke ido.
Suna idar da sallar magriba akace Hafsi ta shiga
wanka. Komai na toilet din daban yake...oh su
Hafsi a toilet din matar sanata. Tana fitowa
Hajiyan dangi ta tarar suna hira da mommy sai
ta kasa fitowa. Hadiza da Nafisa wadanda tuni
jininsu ya hadu kamar sun dade tare suka fara
mata dariya. To yan nema da girmanku kuna
tsokanarta ko. Fito kinji Mamana ni da nake so
nan da yan watanni nazo yi miki wankan jego.
Ai Hafsi ji tayi kamar ta nutse a kasa Mommy
tace Hajiya banda kwacen 'ya fa. Fita suka yi
aka hau shirin amarya. Kwalliyar yau tafi ta
sauran events din. Suna gamawa kowacce ta
dau ado jiki da fuska aka fito. Motar da tafi
kowacce kyau daga tsakiya wani abokin Junaid
ya bude mata kofa ta shiga ya rufe. Taso kwarai
Ummati ta shigo sai kawai taga angon nata ya
bude kofa ya shigo. Ko tari bata yi ba don ganin
yadda yake mata wani irin kallo. Ganin abin yayi
yawa tace ya dai? Kamar ya, ya bata amsa. Ta
dan turo baki kallo dai idan yayi yawa kuma zai
shiga babin haramun. Yayi yar dariya Hafsi Hafsi
kenan malaman karya. Wa ya fada miki kallon
miji ga matarsa yana ciki. Yadda tayi da bakinta
yasan sarai murguda masa shi zata yi. Yarinyar
nan akwai tsiwa. Yace to basai kin murguda min
baki ba idan kina son kiss, you just need to ask.
Sakin baki tayi tana kallonsa lallai ma mutumin
nan..dole ta fasa ta kara hararsa. Yayi dariya
sannan yace karamar mara kunya kawai.Hular
kansa yasa ya rufe fuskarsa. Idan mun isa ki
tasheni jiya banyi baccin kirki ba. Ko kula shi
bata yi ba ta juyu tana kallon garin da bata taba
tunanin zuwansa ba nan kusa.
Nicon Hilton suka shiga. Manyan mutane da
dama sun halarci taron. Su mommy ma da
sauran matan manya sunzo amma shadaya suka
koma gida. Sai wurin shabiyu da kwata mommy
tayi wa Junaid waya kan su taho gida haka
saboda Hafsi da suka yi zaman mota.
Ummati da Hafsi suna ta hira kafin motar da
zasu shiga su karaso gabansu idon Hafsi yakai
kanta. Tabbas matar da tazo wurin dinner dinsu
ta kano ce. Matsowa tayi gaban Hafsi tana
tafiya duk jikinta na girgiza amarya mun sake
haduwa ko. Ga naki gift din nasan Juni boy da
rowa baiyi sharing nashi dake ba. Wai wacece
matar nan ne ta tambayi kanta? Tana mika
hannu zata karba Junaid ya doke hannun. Da
bomb ne ma haka zaki karba ko ya fada yana
zare mata idanu. Mota na tsayawa yaja
hannunta ya tura ta ya kalli ummati kema shiga
zan biyo abokina. Yana rufe musu motar kafin
su fara tafiya Hafsi taji yace cikin daga murya
what the hell do you want? Suna tafiya a
zuciyarta Hafsi ta kara yarda akwai wata a kasa
tsakanin Junaid da yarinyar nan.
Ka zama uba ga abinda ke cikina. Ka rabani da
rayuwar da nake ciki. Maana ka aureni.
wadannan ne amsoshin da Tilly ta bawa Junaid.
Imi dake ta yiwa Junaid horn ya shigo su tafi ya
fito daga mota ganin yadda abokin nasa ya rude.
Ya mutumina wannan ce akuyar dake neman
daga maka hankali? Ai ka barni da ita na farfasa
mata jiki kawai. Yana magana ne yana kokarin
dauko wani katon dutse cikin wadanda akayiwa
wurin ado dasu. Imi baya daukar raini shiyasa
Junaid ya tabbatar yana daukan dutsen nan jikin
Tilly zai dire shi.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐25
Rigar jikin Junaid ta gama jikewa da gumi
saboda tashin hankali. Yana ganin iyayensa sun
shige yayo kansu ita da Rosie sam ya manta da
Hafsi a falon. Ke don ubanki me kike nema ne a
tare dani? Idan ciki ne dake ki sa a ranki har
abada Junaid bazai taba zama uba ga abinda ke
cikinki ba.
Hafsi tana jin furucinsa ta nemi hanyar barin
falon rasa wurin shiga tayi don bazata bi su
mommy ba a wannan yanayin da suka tashi.
tana turo kofar dakin da take tsammani ma na
masu aiki ne taji yo Tilly tana dariya...haba Juni
boy ai kowa yaci tuwo dani miya ya sha. Ni ka
zane a lagos daga na fadi abinda baiyi ma dadi
ba. Rosie ta dan dake ta to banza rage
muryarki. Ta maida kallonta ga Junaid ai kai
karamin dan iska ne don giyar kudi ce ta kaika
tashar iskanci mu kowa, ta nuna kanta da Tilly
wahalar rayuwa ce ta kawo mu kaga dole mu
fika rashin imani. Tsayawa yayi ya rasa yadda
zaiyi dasu. Ya juya ya fita daga falon tare da
buga kofa da karfi har sai da gaban Hafsi ya
fadi.
Masu aiki ya tarar a barin nashi ya ma manta
wai shara akeyi da sauran gyare gyare. Get out
ya fada cikin karaji har su Nafisa suka fito daga
ciki ita da Hamida. Sauri tayi ta dafa masa
kafada Junaid what is wrong? Ban sani ba
wannan karon hawaye yake sosai. Ku fita
wallahi ko wani yaji ciwo. Ba shiri duk suka yi
waje shi kuma ya shiga sabon bed room dinsa.
Bai taba tunanin first day dinshi da Hafsi zai zo
masa a haka ba. Tsakani da Allah yake sonta
don a yadda ya tsara ma kansa ma bashi da
niyyar takura mata. A hankali zai bita ya koya
mata sonshi don yasan yanzu baya gabanta.
Gashi yar tsiwarta da fadan da suke suna burge
shi. Drawers ya rinka budewa kamar mahaukaci
yana neman kayan maye ko yaya ya gusar
masa da hankali ya manta da bacin ransa.
Wata taba dogowa ya dauko wacce Imran ya
kawo masa tsaraba daga Italy. Kujera ya hau ya
rufe idanunsa. Yana kunnawa yaji an fizge ta
daga bakinsa yayi saurin bude ido. Hajiyan dangi
ce tsaye kansa fuskarta jike da hawaye. Haba
dan albarka. Yanzu ashe akwai wani maganin
bakin cikin rayuwa bayan ambaton Allah da
karatun Quran ko sallah? Ashe duk abinda ake
fada maka bayan kunne yake bi. Bakin gado ta
zauna dora kansa a kan cinyarta ya saki kukan
da yake ta kokarin boyewa. Kyale shi tayi yayi
mai isarsa har yayi shiru don kansa. Bai tashi
daga kan cinyarsa ba yace Hajiya sai da nake
son na canja halayyata kuma sai wannan
masifar ta taso min? Kul ta ce masa tana
girgiza masa kai. Allah sarki ne mai dinbin
rahma da jinkai ga bayinSa. Shekararka nawa
kana saba masa Yana hakuri da kai? Meye baka
sha ba da aikin neman mata duk sai yanzu don
Ya jarrabe ka kake neman kara fadawa ga
halaka. Shin ka sani ma ko silar shiga aljanna
ce wannan jarabawar? Dago kansa yayi yana
kallonta. Hajiya wallahi yarinyar nan karuwa ce.
Na rantse miki da Allah ita ta fara nema na a
club. Abinda ta fada duk karya ne ya dan
sunkuyar da kansa maganar cikin dai bazan
karyata ba kila da gaske ne.
Kayi hakuri ka daure kaci jarabawar nan. To
Hajiya zancen Hafsa fa? Ya zanyi da ita idan
taki ni. Murmushi Hajiya tayi ,kasa Allah a ranka
yarona komai zaizo da sauki. Hafsa tayi min
yanayi da mutanen kirki idan ka nuna mata kai
mutumin kirki ne sai kaga Allah Yasa ta zauna
da kai lafiya.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐26
Neman Hafsi aka rinka yi a cikin gidan an rasa
ina ta shiga. Mommy sai kuka take ko don taji
zancen ciki ne ta gudu. Wata mai aiki mai suna
Amaka ce ta tafi bakin gate ta tambayi
securities din wurin ko sunga fitarta. Kusan awa
biyu ana abu daya har Hajiyan dangi da Junaid
suka shigo gidan don ta matsa masa akan yazo
ya nemi gafarar iyayensa. Ganin gidan a
hargitse Hajiya tace Salma me ya faru ne haka.
Mommy cikin kuka tace bamu ga Hafsa ba
Hajiya. Kinga har babansu ya fito nemanta.
Tunda akace Hafsi ake nema Junaid ya dena
gane me ake fada. Na shiga uku Mommy ta
gudu. Tilly da Rosie dake zaune a gefe ko a
jikinsu. Ya nufo su cikin tsananin fushi ku sa a
ranku indai banga matata ba wallahi kun gama
ganin farinciki a duniya. Banzaye Matsiyata,
karuwai....kafin ya kara magana Amaka mai girki
ta fito daga dakinta da gudu. Madam amariya
dey for my room. Bangaje ta Junaid yayi ya
shige dakin. A daidai lokacin Senator ya fito
yana waya da IG na police kan a baza masu
nemanta. Me zai fadawa Mal Aminu? Duk
kudinsa mutumin kwarjini yake masa sosai.
A kwance ya sameta kan gado tana ta rawar
sanyi. Hafsi me ya faru ya fada yana shirin taba
ta. Doke masa hannu tayi da kyar don wani
zazzabi ne ya kamata sosai bayan tayi kuka mai
isarta. Zuciyarta a cushe take da tsananin
bakinciki. Badon abinda tayi ba tun kafin tayi
aure tasan Allah bazai hadata aure da mazinaci
ba.(don ma bata san yayi shaye shaye ba).
Ganin yadda ta hade fuska ga wasu hawayen
sun taro a jajayen idanunta. Kasa ya sunkuyar
da kansa kiyi hakuri Hafsi ki bari na taimaka
miki ki tashi naga kamar ba kya jindadi.
Harararsa tayi tayi tsaki a hankali zata mike. Ke
ba kya gajiya da harare harare ne , wata rana
sai na tsire miki ido. Duk da suna tare da
damuwa da bacin rai amma sai da duk sukayi
murmushi. Nafisa ce ta fara shigowa sannan su
Mommy suka biyo baya. Hajiya tace mamana
duk kin samu cikin damuwa tun dazu ana
nemanki. Sai a lokacin suka kula da idanunta.
Mommy ta zauna a bakin gadon. Kiyi hakuri yata
nasan duk abinda zan fada zakiyi tunanin ko don
bani na haifeki ba. Hafsi ta share hawaye ba
haka bane mommy. Hamida tace wai ni me ya
faru ne shi yazo yana mana fada dazu mun
shigo kuma ance ana neman ta.
Babu wanda ya bata amsa. Mommy da kanta ta
taimaka wa Hafsi ta tashi. Zazzabi ne a jikinki
ko? A'a kaina ne kawai kuma zai dena idan
nasha magani. Mommy tace ku zama shaida
idan har yarinyar nan tace bazata zauna da
Junaid ba sai an raba aurensu. Hajiyan dangi
zancen bai mata dadi ba ta kama hannun danta.
Muje Allah Ya kyauta.
Kwanaki uku bayan zuwan su Tilly jikin Hafsi ya
warware sosai ga kulawar da take samu daga
wurin iyayen Junaid. Hajiyan dangi taso komawa
kano amma dole ta zauna har a shawo kan
matsalar data kunno kai gidan. Su Nafisa kuwa
kowacce ta koma gidan mijinta. Kirikiri aka hana
Junaid ganin Hafsi gaba daya gidan ya masa
zafi. Addua da yawan sallah yanzu kamar sabon
limami don tsoronsa baya wuce a raba shi da
Hafsi.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐28
Fizgo ta yayi har jikinsu yana haduwa da juna.
Bata yi attempting ta gudu ba ta dai ki yarda su
hada ido. Thank you kawai ya ce mata a daidai
kunnenta a hankali ya fice daga dakin. Tunane
tunane ta rinka yi barkatai game da feelings
dinta akan mijin nata. Karshe dai ta tabbatar
tausayinsa kawai take ji. Sai kuma ta koma
tunanin yadda zata yi da su Tilly. Ita dai bazata
je tace karya suke ba kanta tsaye don tsoronsu
ma take ji. Dadin abin ma tunda suka kawo
kansu gidan ai sun san abinda suka taka. Ita a
wa taje ta karyata su ace garin yaya ta sani. Da
kunya aji amarya tana labe.
Tana ta tufka da warawara ita kadai har Hajiyan
dangi ta dawo. Bayan sun gaisa tace kiyi hakuri
na barki aikin jira ko. Ba komai Hajiya. Flask din
kunun ta kalla au ina Junaidu? A nan na barshi
fa zai sha kunu. Ya sha ya fita inji Hafsi. Kan
wata kujera ta zauna tace Hafsatu. Naam ta
amsa. Kin sanar da iyayenki abinda ya faru
kuwa? A tsorace ta dago ido. Wallahi ban
fadawa kowa ba. A'ah kwantar da hankalinki ai
tambayarki nayi. Munyi shawara da su Rufai ne
yace zaije har kanon ya sami babanki ya sanar
dashi. Domin idan akwai cikin nan dole mu tsaya
yarinyar ta haihu mu karbi dan. Gashi ma dai
ana tunanin gara suyi aure saboda gori a nan
gaba. Ko kadan ba haka muka so ba amma
bazamu yi wata barnar ba don mu boye wata.
Idan har kinsan bazaki iya zama da Junaid ba a
haka kada kiji kunyar sanar dani. Ta dan gyara
zama. Nasan iyayenki ma bazasu taba yarda ba.
Kuma bazanga laifinsu ba ko nice abinda zanyi
kenan.
Duk maganganun da Hajiya take Hafsi ta gane
so suke suji ko zata bukaci a raba aure. Ko
kadan bata so iyayenta ma su san maganar. Ai
idan auren ya mutu wani kashin kazar zata
shafa wa kanta. Dama ummati ta fada mata a
groups din whatsapp babu irin abinda baa fada a
kansu. Da masu zagi da masu kiranta karuwa
ma. Ai auren rufin asiri ne gareta sosai. Dan
murmushi tayi cikin kunya tace Hajiya in sha
Allah zan zauna.
Har ranta taji dadi kuma tayi mamakin saurin
amincewar Hafsi. Allah Yayi miki albarka Ya
baku rayuwa mai albarka duniya da lahira. Ta
kama hannayen Hafsi ta rike. Mungode sosai
kuma zan kara jan kunnensa aka neman lahira
da gudun duniya. Har hawaye Hajiya tayi tace
bari na tashi na sanar da su Salma don su
kunyarki ma suke ji. Baki ga baban naku bai
neme ki ba. Yace bai san yadda zaiyi ya kalleki
bane.
Ranar da Hafsi ta cika sati su Nafisa suka zo
gidan zasu yini. Hira suke sosai da Hafsi kamar
sun dade da sanin juna. Suna nan zaune Junaid
ya shigo dakin. Rabon da su hadu tun a dakin
Hajiyan dangi. Wata doguwar riga ce fitted a
jikinta kanta ba dankwali Nabilan Nafisa tana ta
jagwalgwala mata kai wai zata mata kitso. Yana
yin sallama tayi saurin sunkuyar da kanta. Sis
ina ta nemanku ance min kunzo sai Amaka ce
tace kuna nan. Hamida ta ce ai yanzu mu Hafsi
ce yar uwarmu. Ka zama dan karo ko Yaya?
Nafisa tace Hafsi baki gaishe shi ba. Kafin ta
amsa yace kyaleta bashi take ci. Nabilatu na
kice kike ja min kan mata haka ko? Ku kuma duk
kun kyaleta sai ta tsige mata gashi. Dariya duk
suka yi kaji mai mata donma kayi saa tana mata
gyaran gashi. Yace nasan dai kara kike musu to
baa yiwa dangin miji haka sai su raina ki. Filo
nafisa ta jefa masa. Sannu kanwa uwar hadi tun
yanzu zaka fara nuna hali. Ke Hamida dauko
min 'yata mu tafi kai kuma ka zauna ka gyara
mata. Nabila sai ihu take da Hamida ta dauko
ta...ni kichu kichu anti. Tanayi tana dukan
Hamida.
Sai a lokacin tayi magana. Don Allah Hamida ku
kyaleta. Ganin basu saurareta ba ta dauki hijab
dinta zata bisu. Kafin ta gama sun fice harda
rufo kofa.
Suna fita harda tafawa. Bawan Allah Ya Junaid
duk ya zama abin tausayi. Kiri kiri anki kai masa
matarsa gidansa. Nafisa tace nasan fushi su
Mommy suka yi amma ai zasu bari ta koma. Ko
ba komai yanzu da kudi Junaid bazai kara bin
wasu matan ba a waje. Abinda ya wuce kuma
Allah Ya yafe mana baki daya. Amin Ya Allah.
Batul Mamman💖
.TUN KAFIN AURE💐27
Hajiyan dangi ce kadai ke shiga sabgar Junaid.
Shiyasa kullum yana dakinta. Hafsi kuwa dakin
da aka bata kusa da na Mommy ne ko fita bata
yi. Ranar laraba tana zaune a daki duk shirun ya
isheta ta fito zata dakin Hajiyan dangi don yau
bata leko sun gaisa ba. A bakin bene suka hadu
Hajiya tace ina zuwa mamana? Ta dan sunkuyar
da kai, dama gaisheki zanzo yi. Tayi mata
murmushi to bazan amsa gaisuwar a nan ba.
Karasa dakin ina zuwa. Zanje wurin babanku ne
muyi magana.
Ba musu ta karasa sauka. Sai dai kuma bata
san ina ne dakin Hajiyar ba gashi ba damar ta
koma sama ta tambaya. Wani corridor tabi tana
tafiya sai ta jiyo maganganu daga dakin. Babu
shakka wadannan matan ne ke maganar. Kamar
ta wuce sai ta tsaya daf da kofar. Daga ciki ta
jiyo daya daga cikinsu tana magana da fada
fada...kai banza so nake kawai kayi karyar kaine
babana. Ka sami wasu da zaku zame min iyaye.
Wallahi babbar harka zan baro mana idan kuka
yi kuskure kuma Allah kashimu ne zai bushe. Sai
wata tace ke komai akayi dake sai kinyi hauka
ki rage muryarki mana. Wannan karon sai da
Hafsi ta hada kunnenta da kofar take jin me ake
fada.
Bayan dayar ta gama wayar tace ni yanzu Rosie
ya zanyi idan suka kaimu asibitin ayi min test.
Gashi kece mai cikin bani ba.
Hasbunnallahu wa niimal wakil. Ashe karya suke
babu wani ciki. Bata san dalili ba amma har
ranta taji dadin wannan zancen. Rosie tace kada
ki damu Tilly nasan yadda zamuyi da komai. Ke
dai idan kika yi kokarin yaudarata idan kika
shigo gidannan sai na koya miki hankali, itama
wannan matsiyaciyar amaryar tasa sai nasan
yadda nayi aka saketa ko ta nemi sakin da
kanta. Ni bani maganin nan na kara sha naji
cikina ya fara ciwo ciwo. Gara shegen yayi ya
bare kowa ya huta. Tilly ta kalleta ki hakura ki
haifeshi ni yanzu da ko shege ne ina so. Ai
tunda likitan nan yace mahaifata ta lalace nake
jin son haihuwa. Rosie ta tabe baki...wanan dai
sai suck away in kin matsu kije gidan marayu.
A sanyaye Hafsi ta cigaba da tafiya. Wata mai
aiki ta gani ta tambayeta dakin Hajiya ta nuna
mata. Tana shiga ta tarar dashi zaune kan
carfet yana shan wani abu a cup. Ganin tayi
turus ita bata shigo ba ita bata fita ba yayi dan
murmushi mai cike da bakin ciki. Hafsi Hafsi ko
na fita ne don ki sami sakewa? Dan kwarin
gwiwa da samu data tuna cikin ba nasa bane ta
shigo. Ina kwana ta fada tana dan durkusawa.
Ajiye kofin yayi yana kallonta cike da mamaki.
Hala ta manta abinda ya faru a kwanakin da
suka wuce. Kai fa ka fiye kallo kuma na fada
maka babu kyau. To ranki ya dade na dena
daga yau. Rufe idanunsa yayi ya dauki cup din
kununsa ya cigaba da sha. Jin wani daddadan
kamshi kusa dashi yasa ya bude idon. Hafsi ce
zaune a kasa kusa dashi. Tayi yar ajiyar zuciya.
Junaid, bata taba kiran sunansa ba sai yau
shiyasa yaji wani dadi. Sai ya wayance. Ke mijin
naki kike kira haka ba ko yar alkunya irin na
matan hausawa. Komai bacin rai baya rabo da
wasa. Kafin tayi magana yace kina hararata fa
zan...sai ya kashe mata ido daya tsire miki ido
zanyi. Ai kayi kama da mugaye dama. Ya mike
tsaye ni din? Ashe baki da ta ido yar nan. Yadda
ya rike haba yasa tayi dariya. Duk da yana tare
da damuwa ya koyawa kansa hakuri. Har yana
tsokanarta. Wani serious look ta gani a tare
dashi. Yace Hafsi Hafsi why are u being nice to
me? Ta dan kalle shi, saboda i believe you.
Bangane ba ya fada cikin rashin fahimta. Bazan
miki karya ba nasan Tilly kuma cikin jikinta
maybe nawa ne. Na sani ta bashi amsa. Na dai
yarda ba...ba raping dinta kayi ba. Tana gama
magana ta mike zata gudu.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐29
Hannun kofar ta kama amma saboda yadda take
hanzarin fita sai ta kasa budewa. Hijab din ma
saboda karar jan kofar da Nafisa tayi a baibai ta
saka shi. Duk abinda take idanunta na kansa
don tsoro take kada ya karaso inda take. Wani
irin kallo ya rinka yi mata ko kifta ido baya son
yi. A hankali taga yana matsowa inda take.
Cikinta har wani sauti yake bayarwa saboda
yadda ta kideme. Da kyar ta iya cewa nifa bana
son kallo. Bai dakata ba da tafiyar sai da yazo
gabanta. Da zaa taba kirjinta sai anji bugun
zuciyarta da sauri da sauri. hannunta ya kama
ya jawota ciki ya zaunar da ita kan kujerar
gaban dressing mirror. Ji yadda jikinki ke bari
kamar kinga wani dodo ko irin kinzo yi min sata
na kama ki. Yadda yake maganar ne ya sata
dan guntun murmushin yake. Shiru tayi tana
tsoron kada Hajiya ko Mommy wani cikinsu ya
shigo dakin tunda suna shigowar kullum. Ganin
yana neman cire mata hijab ta fara kokawar
rikewa. Ya kalleta ya sha kunu wai ni da jikina
ki rinka rufe min. sai anyi magana ki rinka wani
abu kamar wata malama. Ta zumburo masa
baki, to yanzu me kake so ayi. Da faraarsa yace
ki cire na gyara miki gashinki ko baki ji me Sis
ta fada ba. Tayi masa fari da ido ai da ka sani
salon ka bude sai ka rinka gyaran gashi. Gaba
daya ta ruda shi da yadda tayi masa fari da ido
har ya kasa magana. Tana ta surutu ita daya
sai gani tayi yana kici kicin cire mata hijab. Ihu
ta fara masa wallahi idan ka matso zan bude
murya. Ganin duk a tsorace take yayi dariya duk
wanda ya shigo taimakonki sai ya tayani cire
miki hijab din, bari ma na kulle kofar kinsan leke
dakin newly weds hatsari ne. Yana zuwa bakin
kofar duk cikinta ya gama durar ruwa sai kawai
taga zai fita daga dakin...take care Hafsi Hafsi.
Murmushi ta sami kanta da yi bayan ya kulle
kofar ta fada gado ta kwanta.
Hajiyan dangi suka gani a dakin Mommy suna ta
hira. Suna zama Mommy tace dama jira nake ki
fito Nafisa. Lafiya dai ko Mommy? Ta
tambayeta. Eh to wannan makociyar taki nurse
nake son ki kira tazo gida tayiwa yarinyar can
test a tabbatar da cikin. Hamida tace Mommy
ana yin scanning fa dashi ake fadar EDD. Nafisa
ta buge mata baki to banza wa ya fada miki we
are intrested muji lokacin haihuwar. Hajiya tace
kunga ni ku nutsu idan kinje gida ki fada mata
ko zuwa gobe ne sai kuzo tare. Amma abinda
Hamida ta fada gaskiya ne. Idan anyi mata
gwajin sai ayi scaning din. Nafisa ta mike bari
naje na fada musu don su zauna cikin shiri.
Hafsi tana fitowa zata dakin Mommy ta ga
Nafisa tana dawowa daga dakinsu Tilly.
Hannunta Nafisa taja suka shiga wani karamin
falo. Suna zama Nafisa ta ce Hafsi what do you
think of Junaid? Kasa ta sunkuyar da kanta.
Tana jin nauyin Nafisa sosai don ma ita din tana
da wayewa ta iya jan mutane a jiki. Ta dan taba
ma Hafsi kafada ina jinki kanwata. Jin ta sake
yin shiru tace nasan Junaid ya taba rayuwa
mara kyau irin ta 'ya'yan masu kudi marasa
kwaba amma duk irin halayensa he is not a
rapist. Kuma a irin ji da kansa na da fa banda
yanzu, bazai kula mai kati ba. Ko da wasa
bamuyi tunanin zaiyi aure ba nan kusa amma sai
gashi yana ganinki ya canja sosai. Banda degree
yana da masters har biyu amma yaki aiki sai
kashe kudi. Sai gashi jiya Alhajinmu yace yayi
masa maganar yana son fara aiki. Hannayen
Hafsi ta kama ki daure ki zauna dashi don Allah
na tabbatar he will be a better person. Ganin
Nafisa na hawaye Hafsi ta suma kuka itama.
Cikin kukan ta fadawa Nafisa abinda taji daga
dakinsu Tilly. Murnar Nafisa har zuci tace kada
ki fadawa kowa da sannu asirinsu zai tonu.
Scanning zan kaita shegiya gayyar tsiya. Har
suna da guts din shigowa gidan nan. daga nan
suka zauna suna tattauna yadda zasuyi karshe
Nafisa tace idan kin amince zanyi magana a
kaiki wurin mijinki. Dammmm zuciyarta tayi don
tsoro.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐30
Washegari gari da safe Nafisa tazo da Mariya
nurse. Ita tayi musu jagora zuwa dakin su Tilly.
Senator Rufai tun da suka zo gidan zama ya
gagare shi ko kadan baya kaunar haduwa dasu
gashi bazai iya korarsu ba har sai sunga yadda
al'amarin zai kasance.
Tun daren dama Tilly ta gama tsorata Rosie
tace ki kwantar da hankalinki nifa abu irin
wannan baya tsorata ni. Zamu sami mafita cikin
ruwan sanyi. Ko da su Nafisa suka shiga dakin a
kwance suka tarar da Tilly , Rosie tana rirriketa
tana ta amai. Laulayi dai kamar gaske. Nafisa ta
kawar da kai gefe dama bata sanar da Mariya
ainihin alaqarsu ba. Ita ko sunansu ma bata sani
ba. Ta yi mata kallon banza ki tashi za'ayi miki
test. Rosie ta yi kalar tausayi to bari na taimaka
mata ta gyara jikinta. Mariya tace ai fitsari
kawai nake bukata ma idan kun shiga ga
wannan robar ta mika mata irin sample bottle
din asibiti sai ku kawo min a ciki. Kadan ma ya
isa. Nafisa tace kiyi mata na jini kawai ance yafi
nunawa. Nan da nan suka hada ido a tsorace.
Tilly ta fara hawaye don Allah kuyi hakuri bana
son allura. Nafisa tace ke da zaki haihu meye
abin tsoro a allura. Mariya tace ki bari kawai
muyi na fitsarin idan bai zama clear ba sai na
debi jinin. Rosie ce ta kamata tana tafiya a
hankali har suka shiga toilet suka rufo kofar.
Tilly ta gyara jikinta tana tsaki ta sassauta
murya kinji waccan yarinyar wai blood test? Idan
ta shiga hurumi na bazan mata ta dadi ba. Rosie
ta rufe mata baki sai an ji mu. Ungo ni ta mika
mata robar data cika taf da fitsari. Kamar ta
rike kashi haka Tilly ta karba ta fito ta ajiye a
gaban Mariya.
Duk suna kallo ta saka PT strip din a cikin robar
ta fito dashi ya nuna layi biyu alamun ciki.
Mariya tace ai kinga ma Nafisa ya nuna basai
munyi na jinin ba. Nafisa a ranta tayi kwafa
dama tunda suka shiga toilet tare tasan akwai
abinda zasuyi. Ta kalleta harda dan guntun
murmushi sannu Allah Ya raba lafiya. Yanzu
gobe zan kaiki asibitin da nake zuwa sai ayi miki
ultrasound gara mu gani kila ma biyu ne babies
din. Nafisa dai dariyar da take harda ta mugunta
suka fice ita da nurse.
Suna rufo kofar Tilly tace na shiga uku ya zanyi
ne Rosie gobe asirina zai tuno. Kwantar da
hankalinki kamar tsumma a cikin randa. Wannan
yar kwailar matar tasa zamu kullawa. Idan zai
aureki ai gara ki zauna ba kishiya muci karenmu
ba babbaka Talatu. Suka tafa sannan tace akwai
dan taimako daga wurin malam fa sunansa
makalemata. Idan lokaci yayi zan baki ki yi
amfani dashi.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐32
Wani irin radadi ne ya ziyarci kafafunta duka
biyun ta runtse ido ko motsi ta kasa yi saboda
duk wurin pieces din glass ne. Tilly kuwa
kwanciya tayi wanwar a kasa tana kwarma
wayyo cikina, wayyo ta kashe min da na shiga
uku. Rosie tace kiyi hakuri Talatu ki mike tsaye.
Hafsi ta kallesu tana cewa sannu amma duk
kafafunta sun kone saboda zafin abincin harda
cikinta don karamin mayafi ta yafa sanin cewa
babu ma aikata maza da ake bari su shigo cikin
gidan. Ga plate din da ya tarwatse wasu duk
sun soke mata saman kafafunta. Duk da haka
bata damu ba ta duka tana son taya Rosie ta
daga Tilly tsaye. Hannunta taji Tilly ta make
tana kara sautin murya. Muguwa azzaluma don
kawai ina da cikin mijinki shine kike son zubar
min dashi. Wallahi duk abinda ya sami dana kotu
ce zata raba mu. talakar banza.
Wawan mari Talatu taji an dauketa dashi.
Mommy ta sake daga hannu Hajiya ta riketa yi
hakuri Salma muji abinda ya hadasu. Rosie cikin
kukan makirci tace Talatu ce ta fito zata sha
iska tace dakin yana tayar mata da zuciya. Tana
fitowa wannan yarinyar ta nuna Hafsi, mommy
kuwa ta make hannun karki sake nuna min
yarinya da yatsa wallahi. Rosie ta share ta
cigaba da magana kawai tana ganin Talatu sai
tace mata zanga yadda zaki haifi dan shege a
gidannan. Tray din da plates din da ke kai duk
ta tura mata a ciki. Hajiya ko kadan bata
gaskata zancen ba ganin yadda Hafsi ke kuka
tace mamana me ya faru. Hafsi ta fadi iya
abinda ta sani. Mommy ta kama hannunta su
koma falo ayi maganar.
Sai a lokacin suka kula da yadda jini ke bin
kafar Hafsi ta dama Mommy tace maza a kira
mata Junaid yazo ya kaita asibiti.
Da fara'arsa ya shigo falon. Mommy daga nasa
yarki dafa min indomie sai ace in kaita asibiti.
Ko ta kitse albarka. Gunjin kukan Tilly yaji daga
bayansa ya juya da sauri lafiya? Rosie hade rai
ka tambayi matarka da take son zubar wa
Talatu da ciki. Yace au ashe sunanta Talatu ai
na zata Tilly ne. Muryar Mommy yaji tana
kiransa. Ya zan aika a kira ka sai kazo kana
wani zancen daban. Ka dauko key mukai
yarinyar nan asibiti nace. Ya kalle Hafsi duk
fuskarta hawaye yayi saurin karasawa gabanta.
Me ya faru Hafsi garin yaya kika ji jiwo?
Mommy tace ka tashi mana ka zauna kana mata
tambayoyi.
Suna shiga motar Nafisa na isowa Hajiya tace
ta debo su Rosie su taho tare. Amma ta taho da
security don kada su zama su kadai. A motar
Junaid kuwa Mommy tana ta balai ya dauko
musu masifa har gida. In Allah Ya yarda sai
cikin ya zube. Ga Hafsi nan ki saki jiki kiyi ta
zuba masa 'ya'ya tunda su yake so. Hajiyan
dangi ta gama waya da senator ta sanar dashi
halin da ake ciki sannan ta dubi mommy tana
bata hakuri. Junaid kuwa banda sannu babu
abinda yake fadawa Hafsi. Hawaye ne wani ke
bin wani a idanunta don ita kadai tasan me take
ji musamman a cikinta. Ga babban mayafi ta
yafa wani karin zafin a cikin.
Suna isa asibiti Junaid daukarta yayi don ganin
yadda kafar taki dena jini. Emergency aka shige
da ita da Tilly. Kururuwa kawai Tilly take yi ita
tasan danta ya mutu. Ai kuwa basu dade ba
nurse ta fito tace Tilly tayi bari. Nafisa ta rike
baki cike da mamaki wato don sunji yau zaayi
scanning suka bullo da wannan abin. Dariya tayi
tana gyada kai sai tayi maganin mutanen nan.
Junaid yana tsaye doctor ya zare glass dinda ya
shige kafar Hafsi yana ta mata sannu. Bayan an
gama cirewa ansa plaster ya lura ta kasa
kwanciya da kyau yace Hafsi akwai inda yake
miki ciwo bayan kafar ne? A hankali ta daga
kanta tace cikina. Fatar ta daye. WHAT???
Shima ya gama tsorata yayi saurin cire mayafin
ya nunawa doctor din. Da almakashi ya yanke
barin rigar daya kwanta akan cikin yace yi
hakuri fatar bata cire ba. Ya dauko magani zai
saka mata Junaid ya karba don tuni ya kule da
kallon da yake mata. Dr bai ma san me yake ba
ya nuna masa yadda zai shafa ya fita.
Ba karamin tausayi ta bashi ba yana shafawa
tana runtse ido duk hawaye. Sai da ya gama ya
duka yana hura mata cikin tuni ta hadiye kukan.
Ya dago kansa sannu kinji Hafsi rabin raina.
Ashe tsautsayi ne yasa nasa ki girki. Amma me
ya hadaki da waccan. Fada masa komai tayi
yace ba komai. Allah Yayi mana jagora.
Dr Sunusi yana fita Nafisa ta ja shi suka yi
magana tace dr ina jin yarinyar nan cikin karya
gareta. Yace ya akayi kika sani tace yar
uwarmuce ce daga garinmu ina jin karya take ta
matsu ne ta haihu sai tayi ta kiran cikin karya
gashi kwanaki tayi bari baa wanke cikin ba. So
nake don Allah kayi mata wankin ciki zan biya
ko nawa ne. Bani da burin da ya wuce Talatu ta
sami haihuwa. Ta dan matse hawaye. Dr Sunusi
yace ba komai Hajiya ki kwantar da hankalinki.
Yana fita Nafisa tace shegiya ai karen bana
shike maganin zomon bana.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐31
Senator Rufai ranshi duk a bace da aka sanar
dashi result din test din. Ya kalli Hajiya ni yanzu
ya zanyi da Hafsatu? Duk irin abinda ya faru
kafin a bashi aurenta gashi kuma baaje ko ina
ba rayuwarsa ta baya tun kafin yayi aure tana
dawo musu. Hajiya tace ni dai idan zaka dauki
shawarata Rufai kabari yarinyar nan ta tare.
Kullum mu kwana mu tashi da ita bata san
makomar aurenta ba ai kaga ba dadi. Irin
wannan ne idan iyayenta suka sani lamarin sai
ya baci fiye da yanzu. Mommy tace anya Hajiya
a bar shi da yar mutane kuwa? Bafa kowacce
mace bace zata yarda ta zauna da mutumin da
yake da da a waje ba. Wata ko dan kishiya bata
so bare dan kafin fatiha. Senator yace to ku
bani zuwa wata asabar din sai a kaita. Kisa su
Hamida su tambayeta irin kalar motar da take
so ma. Mtsw Ya danyi tsaki yaron nan bai min
adalci ba wallahi. Gara tun da sauran mutumci
na naje har gida muyi magana da babanta.
Zaman dakin duk ya isheta tana ta canja
tashoshi babu wani abin kallo ta mike ta daga
labule tana kallon waje. Tun jiya da su Nafisa
suka zo da nurse bata sake fita daga dakin ba,
Nafisa dai ta fada mata zasu dawo ta kai Talatu
scanning. Tun dazu take jiran zuwansu ko ta
sami abokin hira. Su mommy suna iya kokarinsu
wurin debe mata kewa sai dai kuma suna cikin
damuwar maganar cikin nan. Tana dan
tunaninta ne ta kalli kasa suka hada ido da
Junaid. Wani abu ne ya ratsa mata zuciya har
kafarta. Murmushi yayi mata tayi saurin sakin
labulen. Ta koma ta zauna bakin gado. Meyasa
take saurin rikicewa ne akan Junaid..abinda
take tambayar zuciyarta kenan.
Meyasa zata masa rowar kyakkyawar fuskarta
ne. Su Hajiya suna masa gashin kuma gashi
yanzu yana cikin jindadin kallonta ta gudu.
Girman laifinsa yasa ya danne zuciyarsa bai
dami iyayen nasa akan a bashi matarsa ba.
Itama yana jin nauyinta sosai a ransa. Ina
amfanin badi ba rai? Karamar yarinya tana masa
kwarjini saboda ya zubar da girmansa a waje.
Ga su Rosie sunyi kane kane a gidansu. Fasa
shiga gidan nasa yayi ya koma main house. Mai
aikatan gidan suna ta gaishe shi ya haye sama
da sauri. Addua yake kada kowa ya ganshi a
hanyarsa ta zuwa dakin Hafsi.
Rub da ciki tayi tana karanta wani littafin tarihin
Annabawa da Hajiya ta bata taji an bude kofar.
Duk a zatonta Nafisa ce tayi saurin juyuwa
babbar yaya ina ta jiranki tun dazu yau bani
da....kallon da yake mata bayan ta juyu yasa
tayi shiru. Ya zaka shigo min ba sallama? Ni da
dakin matata har sai nayi sallama? Ya kara
kallonta ita duk kayan jikinta suna mata kyau.
Dinkin yau ma riga da skirt ne fitted sunyi mata
kyau sosai abinka da yar Mama tela. Ya jawo
kujerar dressing mirror banda gulma duk wannan
kwalliyar kice babbar yaya kike jira? Fada min
gaskiya dai ni kika yiwa wannan kwalliyar ko.
Bargo ta jawo ta rufe jikinta da sauri ni ba kai
nayiwa ba. Kan gadon ya dawo ya zauna a
gefenta ya rage murya are you sure? Har fa
zuwa kika yi bakin window don na ganki kuma
na gani. Daga cikin bargon tace ni Allah ba kai
nayiwa ba. Ji tayi kamar ya tashi daga kan
gadon sai dai kuma har fuskarta ta rufe yace
malaiku na jinki kina cewa yar miji kika yiwa
kwalliya ba shi ba. Yau littafinki sai cika da
rubutu amma fa daga na hagun. Muryar nan ta
shagwaba ta fara yi ni ba haka nake nufi
ba...kafin ta karasa magana taji ya daga bargon
daga wurin kafafunta ya shigo ciki. Hannuwansa
yasa ya danne duka sides din don kada ta bude.
Tuni idanunta suka raina fata, they were so
close suna shakar numfashin juna. Ya kashe
mata ido daya ina jinki wa ma kika yiwa wannan
kwalliyar? Ki fadi abinda nake son ji sai na fita
salin alin. Kanta a kasa tace kai. Malama ni
banji ba fa. Ta sake cewa kai a hankali. Bari na
sake matsowa kusa kila zanfi ji. Da karfi tace
kai nayiwa. Good girl to ki dan bani chance
mana na yaba kwalliyar. Bata ankara ba taji ya
janyota ya rungume. Yana shafa mata gashi a
hankali. Wata ajiyar zuciya yayi Hafsi Hafsi ki
tayani addua yau nayi interview har biyu ta
neman aiki. Nasan nayi laifi da yawa shiyasa su
Mommy basu da time dina amma don Allah zaki
zama friend dina kuma special adviser dina.
Dago kanta tayi tayi masa murmushi eh. Thank
you so much. Ya mike yau zaki min girki? Ban
iya ba ta bashi amsa. Au kin manta da malaikun
ne? Itama mikewar tayi na iya, me zaka ci?
Kallonta ya sake yi gaskiya kayan nan naki fa
suna...kodayake ba komai ki dai rufe jikinki kafin
kije kitchen din. Indomie da kwai nake so ina
sonta sosai. Idan kin gama ki kirani. Wayarta ya
dauka yasa mata number dinsa. Duk ta tsufa
anma dena yayin irinta. Itama Gwaggo Zainab
ce ta siyo mata irin second hand dinnan. Ki taho
dashi daki zanzo na karba. To kawai tace ya
fita. Tayi tsaki meyasa idan taga Junaid take
zama wata wawiya ne. Ko dan jan ajinma sai ya
nemi ya gagareta.
Kasa ta sauka babu kowa sai masu aiki ta dafa
masa indomie biyu da daffafen kwai biyu. Tana
shiga kitchen Rosie ta hangota ta koma daki da
sauri ke Tilly tashi mu jirata a hanya. Akan tray
ta dora zata fito wata mai aiki tace madam bari
na kai miki Hafsi tayi dariya ai ba nauyi Chinwe
nagode. Tana tafiya kamar daga sama Tilly tazo
ta bangaje abincin ya zube a kasa plate din ya
fashe kawai sai ji tayi Tilly na ihu wayyo Allah
cikina.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 33
Tana kwance suna hira cikin nishadi nurse din
ta dawo. To angama komai ina kudina? Rosie ta
dauko dubu ashirin a jakar Tilly ta mika mata. Ki
dai tabbatar babu wani cikin wadanda suka
kawo mu babu wanda ya shigo. Nurse Talle ta
washe baki tana murna ta ce angama ranki ya
dade. Bata dade da fita ba Dr Sunusi ya shigo
dakin tare da wata nurse din. File ya bude yana
dubawa, ya dan dago kai kece Talatu Jibo ko?
Eh ta amsa da kyar tana ta rike ciki ita a dole
mara lafiya. Yanzu likita na rasa baby na kenan?
Kiyi hakuri mana ki dena kukan Rosie ta fada
tana rarrashinta. Dr yace ya naga kina rike ciki
ne ko bai gama fita bane? Saurin sakin cikin tayi
ya fita duka ni dai ku sallameni kawai na tafi. Ya
kalli nurse din kinga ki gyara min dakin can
zanyi mata wankin ciki, ya maida kallonsa ga su
Tilly. Ai kada ki damu idan nayi miki wankin
cikin before you know it zaki sami wani. Yadda
kike rike cikin nasan akwai saura. Wannan karon
kukan gaske ta saka masa kayiwa Allah likita
kada kayi min wallahi cikin baya ciwo ko kadan.
Yace ai dalilin wankin kenan idan akayi bari ba
ciwo nan ma akwai serious problem. Tana kuka
yace a kawo wheelchair a kaita dakin da zai
mata a can.
Kankame Rosie tayi bazata tafi ba. Rosie tace
kiyi hakuri Tilly kada asirinmu ya tuno. Saboda
tsabar kwadayin daya kawo su Tilly tana ji tana
gani akayi mata D and C. Likita dai yasha zagi
ta uwa ta uba.
Sai dare aka sallamosu duka a gidan suka hadu
da Hamida suna jiransu da Senator. Ko daki
basu shiga ba Rosie tace yallabai munyi waya
da kawu na baban Talatu yace gobe zaizo gari
don na fada masa abinda ya faru. Anyi mata
fyade kuma anyi sanadin zubar da cikin. Wallahi
maganar nan har yan jarida sai na fadawa.
Kowa kallonta kawai yake tana rashin kunya
Senator ya hanasu magana a cewarsa dansa ne
ya ja masa. Tana gamawa yace idan sunzo
goben zaa daura musu aure da Junaid. Yana
gama magana ya juya zai haye sama zuciyarsa
na kona saboda bacin rai. Ta sake cewa ita
kuma wadda ta zubar da cikin idan zaayi adalci
sai a saketa ko a dau mataki. Hamida tace uban
kuturu kuma yayi kadan in fada miki. Hafsi mutu
ka raba da Junaid. Hajiya tace ku wuce ku tafi
gidajenku Allah Ya bamu alkhairi.
Junaid da Hafsi basu san abinda ke faruwa ba
saboda ya wuce pharmacy da ita neman wani
magani. Ac ya ware mata ya ja mayafinta can
baya yadda cikin zaisha iska. Motar ko radio bai
kunna ba yana ta kallon yadda Hafsi take ta
zumbure zumbure. Yasan itama laifinsa take
gani ya jawo musu masifa har gida an rasa
yadda zaayi dasu saboda gudun abinda zaije ya
dawo tunda babansa dan siyasa ne. Tarkace da
yawa ya siyo mata na kwadayi bayan ya siyo
maganin. Ganin bata da niyar kula shi yace
Hafsi Hafsi kiyi hakuri akan abinda ya faru.
Bansan dalilinta nayi miki sharri ba amma zanyi
maganin abin. Tsautsayi ne ya kaini ga saninta
amma kisa a ranki wallahi bazan aureta ba don
nasan ko wacece Tilly. Cikin takaici yake
maganar Hafsi tayi biris dashi. Ba komai ke
damunta ba face yadda aka kasa gano karyarsu
kuma ita bata da wani shaida akan abinda taji.
Tasan Nafisa ta yarda da ita amma idan basuyi
wani abun ba suna kallo Senator zai sa Junaid
ya auri wannan matar. Wai ma ya akayi suka
yarda bari tayi ne? Ko dai da cikin gasken? Ita
ta gama zama confused. Har ta fara kokonto
akan abinda kunnenta ya jiye mata
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐35
Washegari wayar Junaid ce ta tasheta daga
bacci da asuba. Ko da ta dau wayar sai taga an
rubuta J dear. Lallaima wato har wani saving
sunansa yayi a haka. Ta daga cikin muryar
bacci tace waye ne waya da asussuba kamar
me karbar bashi. Murmushi yayi yana shafa
kansa ai zaki biya bashi ne Hafsi Hafsi amma
not now. Yanzu dai ya kika kwana? Ya jikin? Da
sauki ta ams itama murmushin take. Wani son
Junaid takeji yana ratsa ta. Amma babu yadda
zatayi yanzu sai sun kawar da su Talatu daga
gidan.
Karfe 9 na safe aka sanar da su Mommy zuwan
baban Talatu Mal Jibo da kannensa biyu.
Senator ta tayar daga baccin da sai bayan
asuba ya sami runtsawa saboda tunani.
Doguwar riga ya saka ya mike. Ki aika a kira
min Junaid tun jiya ban sanar dashi maganar
auren ba saboda kada ya daga min hankali. Shi
ya jawo matsalar nan so he has to deal with it.
Mommy tace amma yallabai baka ganin kara
dulmiya shi zamuyi kaga baya sonta kuma basu
da kamanin mutumci. Hannu ya daga ya dakatar
da ita...haba Salma duk shi baiyi tunanin haka
ba sanda yake bin duk macen da ya gani. Ai duk
rayuwar da mutum yayi kafin aure indai ba Allah
Ya kare ba sai kiga tana bibiyarsa. Ko kadan ita
dai abin baiyi mata dadi ba amma dole tayiwa
mijinta biyayya. Haka suka sauka kasa ya fita
wani falo ya tarar dasu a zaune sun kusa cinye
duk abinda aka kawo musu na tarar baki. Bayan
doguwar muhawara Senator Rufai wanda rashin
son tonon asiri yasa babu wanda ya iya sanarwa
halin da ake ciki cikin abokansa da yan uwa ya
tsayar da magana akan zaa daura auren Junaid
da Talatu nan da sati biyu. Mal Jibon karya yace
ranka ya dade ni dai gara a daura auren nan
asabar mai zuwa saboda kada ya lallaba ya
sake banka mata wani cikin. Wata irin tsawa
Senator Rufai ya daka masa ya mike
tsaye...kada ka dauki saukin kaina a matsayin
shashanci mana. Ina binku ne a hankali kawai
don in tayaku sayawa yarku mutumci. Idan kuka
shige gonar da ba taku ba wallahi ina da karfin
da zansa duk a neme ku a rasa. Duk abinda
nake yi saboda girman Allah nake yi so be
careful , be very careful. Yana gama magana
ya fita Tanimu yace kai baaba kaji yadda hantar
cikina ke kadawa kuwa. Baaba yace ai sai da
nayi dana sanin magana ma. Wallahi idan Rosie
bata biyamu da kyau ba jikinta ne zai fada mata.
Kaga yadda yake muzurai kuwa. GG dake gefe
yace ai ni na fiku tsurewa yadda yace zai batar
damu gani nake kamar ya gama gane mu ma.
Baffa ya dauki wayarsa dake faman ringing tun
yana sallar walha ya duba sai yaya sirikinsa ne.
Bayan sun gama gaisawa Senator ya labarta
masa dukkan abinda ke faruwa a gidan nasa.
Mal Aminu dai yau ya rasa bakin magana
saboda takaici yanzu irin gidan da Hafsan sa ta
tare kenan. Senator ya cigaba da bashi hakuri
da neman shawara. Mal Aminu duk yadda ransa
ke kuna yace dole ayi abinda ya dace don a rufa
asiri kuma shi yanzu kullum Junaid yana kiransa
kuma ya yarda da irin shiryuwar da yake ji tare
dashi. Haka suka yi ta shawara Senator yace
idan ba damuwa ko zaku iya zuwa zuwa Jumaa
kai da Alh Bashir saboda bani da wanda zan iya
tonawa sirrina. Lallai rayuwa babu yadda bata
zuwa ga bawa. Allah Ya kara rufa mana asiri.
Daga nan Senator ya nemi dansa ya sanar dashi
shawarar daya yanke. Junaid mikewa yayi cikin
rudani yana daga murya...wallahi wallahi Alhaji
bazan auri Tilly ba, karuwa ce fa.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐34
Yadda tayi zurfi a tunani yasa Junaid kare mata
kallo. Wayarta ce ta hau tsitsi shi ya dawo da
ita daga dogon tunaninta. Da sauri ta dauka
ganin baffanta ne. Tana masa sallama yace
Hafsa ya jikin? Dazu babanku yayi min waya
kinji ciwo. Ince ko babu wani mugun
rauni..dariya tayi ashe kana sona dai Baffa. Yayi
dan gyaran murya kaniyarki wasa nake dake ne.
Ta sake wata dariyar baffa babu ciwo sosai
glass ne ya shige min kafa amma an cire. To
sannu Allah Ya kara sauki, amma ki rinka kula
kinji ko. Ga Mamanki duk ta damu itama. Sun
dade suna hira da mama da kannenta kowa
yana mata sannu. Bayan ta gama wayar yace
yanzu tun dazu ina magana kina share ni sai da
kika ji muryar su baffa kika yi dariya ko. Yadan
bata fuska kamar zaiyi kuka Allah Sarki Junaid
babu mai sonka. Har tissue yasa yana goge ido ,
bata san lokacin da dariya ta kubuce mata ba.
Wayarta ya dauka yana juyawa. Ni na gaji da
ganin wannan toy din. Idan munje gida kizo ki
karbi sabuwar dana siya miki. I hope you will
like it.
Bayan yayi parking din motar Hafsi ta bude zata
fito yace tsaya ina zuwa. Zagayowa yayi ga
mamakinta sai kawai taji ya dauketa. Yau karo
na uku kenan yana daukarta. Tana ta mutsu
mutsu ya ajiyeta kada wani ya gansu ya share.
Da kafa ya tura kofar motar bai tsaya ko ina ba
sai a side dinsu dake bayan gidan. Ajiyeta yayi
ya bude kofar ya sake daukanta, kan doguwar
kujerar falo yasauke ta ya duka hannunwansa
duka biyu a gwiwoyinsa yana ta nishi. Wai Hafsi
haka kike da nauyi...anya baki kai buhun
shinkafa biyu ba kuwa. Filon kan kujerar ta jefa
masa wallahi bani da nauyi. Kuma ma ai bance
ka daukeni ba. Ya sami wuri kusa da ita ya
zauna tare da janyota jikinsa. Gaskiya yarinyar
nan idan kika hau kaina buzu na zaa dauka.
Mintsini yaji a gefen cikinsa tace ya fa isheka
ko don kaji ina shiru. Ya kama gefen cikin ke
dama haka kike? Don kin kone a ciki nima
nakasa ni zakiyi. Ya danyi murmushi me kama
da na mugunta kinsan fatar cikinki zata fi dadin
mintsini ko. Tana jin haka tayi saurin tashi sai
ta fada jikinsa saboda zafin da kafarta tayi.
Rungumeta yayi sosai hmmm su Hafsi wayon ki
dan ji dumin jikina shine kika wani fado min a
jiki. Maganar da tayi niyar yi ce ta makale mata
saboda kunya data kama ta. Zata bashi hakuri
taji ya hade bakinsu wuri daya. Cikin kankanin
lokaci suka tafi wata duniyar sai dai basu dade
ba suka ji bugu a bakin kofa tare da sallamar
Hamida cikin daga murya.
Tsaki yayi ya amsa mata tare da mikewa. Tace
Yaya munji shigowar motarka amma har yanzu
Hafsi bata shigo gida ba. Wani tsakin yayi gata
nan zuwa kill joy sim dinta zan saka a sabuwar
waya. Hafsi dai gintse dariya tayi don yadda
taga yana bin Hamida da harara bayan ta rikota
zata taimaka mata su koma cikin gida.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 36
Senator Rufai yace Allah Yasa magajiya ce sai
ka aureta. Yau kaine kake kiran wata karuwa?
Ka manta irin kukan da mahaifiyarka ta rinka yi
lokacin da kake bibiyar matan banza. Yau gashi
a sanadiyar hakan Junaid wasu yan iska suna
neman bata min suna. Duk rayuwar da nayi a
politics ina taka tsantsan saboda abokan gaba.
Hajiyan dangi dake zaune a gefe ta dago kai
cikin fushi lallai ma Rufai ashe duk abinda kake
ba saboda lahirar mu kake yi ba. Dama saboda
mutumcin siyasa kake yi. To wallahi ka sa a
ranka duk abinda ya sameka kai ka jawo tunda
babu abinda kake don Allah. Mommy dai kuka
take don abin yayi mata yawa. Hajiya tace
Junaidu? Ya amsa mata cikin kuka. Ina so kayi
wa babanka biyayya hakan shine shaidar ka
shiryu. Kuma da yardar Allah zaka ci jarabawar
da Yake yi maka. Tashi ka tafi Allah Yayi maka
albarka. Yana fita mommy ta hau rokon a janye
maganar aure. Yace kun kasa fahimta ta ne
Hajiya. Nasan ina son kare mutumci na amma ki
duba ki gani indai yayi mata cikin da gaske kada
su sami abin tozarta shi nan gaba. Bani da burin
da ya wuce naga iyalina suna zaune cikin
kwanciyar hankali amma hakan bazai taba
yiwuwa ba sai mun toshe duk wata kofar da
wani zai iya samun damar daga mana hankali.
Senator yayi iya kokarinsa wurin ganin iyalinsa
sun amince da auren don a iya tunaninsa da
haka ne kawai zaa iya toshe bakin su Talatu.
Kamar wanda aka jefo daga sama kawai ganinsa
tayi a cikin dakinta. Yar tsiwar data yi niyar yi
masa saboda ya shigo mata daki ba sallama ma
kasawa tayi saboda wata irin runguma da yayi
mata. Cikinta ne ya soma zafin wurin da ta kone
ta fara neman ya sake ta. A kunnenta taji yana
magana cikin muryar kuka har hawayensa na
sauka a kafadarta. Hafsi please dont ever leave
me. Dole ta hakura ta tsaya har ya gaji don
kansa sannan ya ja hannunta suka zauna a
bakin gado. Kansa ya dora kan cinyarta sannan
ya fara magana. Alhajinmu yace lallai sai na
auri Tilly. Dama tasan haka zata iya faruwa sai
dai tayi shiru ganin kamar bai gama magana ba.
Na fada masa karya tayi min amma yaki yarda.
Hafsi ke kadai kin isheni rayuwa ina tsoron
hadaki da kwararriyar yar bariki. You are too
innocent bazaki iya kishi da ita ba. Gashin
kansa ta shafa indai Alhaji ne ya baka umarni to
don Allah kayi masa biyayya. Kada ka manta
aljannarka tana tare da farin cikin iyayenka a
kanka. Tana gama magana yaga ta share kwalla
yayi tashi zaune kingani ko tun yanzu kin fara
kuka. Sai kuma ya kashe mata ido ko dai kishi
ne ya motsa. Kyakkyawan rankwashi ta sakar
masa ya dafe kai yarinya baki sanni ba ko. Sai a
lokacin ya kula ashe daga ita sai wani towel iya
gwiwa. Yayi wata dariya yau zaki gane nima
mugu ne. Towel din ya kama daga daidai kirjinta
yana ja tana ja. Muryarta na rawa tace zan
maka ihu fa? Ai idan kika ji mace tana zanyi ihu
ba yin zata yi ba. Besides ba zaki so a shigo a
ganki a haka ba. To naji ta ce masa, don Allah
kayi hakuri bazan kara ba. Kallonta ya rinka yi
cike da so yace come here. Sake rungume ta
yayi yana shakar kamshin jikinta. Shima kansa
yana mamakin yadda yake iya kasancewa da ita
kuma ya iya hakura ba tare da ya nemi biyan
bukatarsa ba. Ya amince wannan shine true
love.
Haka suka kasance suna nunawa junansu
kulawa har ranar asabar ta zagayo wadda ranar
Baffan Hafsi da Alh Bashir zasu iso abuja kuma
ranar ne auren Junaid da Talatu Jibo Aka Tilly.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐38
Rosie tace dadina dake ba kya cin ribar abu. Kin
fiye rashin hakuri kamar gudawa. Ki zuba ido
yau a jikinki zai angwance. Ki dai sha kaya da
kyau don ki kara kama shi a hannu.
Hamida ana ta rawar kafa kamar ita ce zata
tare. Nasihohi da adduoi Hajiya da mummy suka
yi wa Hafsi. Hamida taja hannunta masu aiki
suka bi bayansu da akwatunanta. A ciki suka
tarar da Nafisa da yaranta 'yan mata biyu Ummu
mai sunan mummy da Husna. Suna ganin Hafsi
suka kankameta suna murna. Nafisa tayi musu
tsawa ku sake ta mana haka kada ku kayar da
ita. Husna yar shekara biyar tace Mama Hafsa
ni a nan zan zauna tare da ke ko. Hamida tace
asheUncle Junaid zai kore ki kuwa. Ai ku da
gidan nan sai nan da wata tara. Hafsi ta
sunkuyar da kai kasa cike da kunya. Haka suka
zauna suna ta hira. Ko kadan basa barinta tayi
kewar yan uwanta saboda yadda suke janta a
jiki.
Tun daga bakin kofa yake jin kamshi mai dadi
sai dai zuciyarshi wani irin kunci take masa.
Yana shigowa falon yan uwansa suka fara
tsokanarshi. Nafisa tace to ya isa haka ku tashi
mu tafi. Duk suka yi mata sai da safe suka fita.
Dama tun shigowarsa Hafsi bata yi masa
magana ba saboda yadda su Hamida ke
tsokanarta. jin bashi da niyyar kawar da shirun
dake tsakaninsu tace masa ina yini. Lafiya ya
amsa a takaice. Can ya sake cewa tashi mu
shiga ciki muyi sallah ko. Dadi hakan yayi mata
ta kara tabbatar da cewa Junaid ya fara maida
hankali a lamuran addini. Fuskar nan tata a rufe
ta bi bayansa. Suna shiga yaji hakurinsa ya
soma karewa yace mata kiyi alwala ina zuwa
nayi mantuwa a mota.
Cike da damuwa yake tuki ya rasa abinda ke
masa dadi. Ace ya rasa abinda zaiyi ta tunani a
yau sai Tilly, Why ??? Gidan ya nufa yayi saa
suna zaune a falo. Mamaki karara a fuskar Tilly
yace hado kayanki ki sameni a mota. Yana fita
suka sa shewa da dariya. Tilly ta yi saurin
dauko jaka ta watsa kaya kadan a jakar ko
sallama babu ta fice. Rosie ta koma daki tana
cin farar kasa wadda ta zame mata abinci
yanzu. Mayen cikin yaki zubewa ita kuma tana
tsoron wankin ciki.
Kusan awanni biyu kenan da fitarsa amma taji
shiru. Tun tana sharewa har ta kasa hakuri.
Lekowa tayi wajen gidan babu daya daga cikin
motocin da yake shiga. Komawa tayi ta zauna
tana ta sake sake. Gajiya tayi ta tashi tayi sallar
isha da nafila ta zauna kan darduma tana
karatu.
Hotel ya kama musu don yasan babu mai bashi
mukullan gidan da Alhaji ya kama masa kafin
ayi masa wani ginin inda zai iya hada matan
biyu. Tilly ansha gyara ciki da waje. Ta nuna
masa salo salo na kwarewarta a fanin
shegantaka. Wayarsa ce tayi kara wurin
shadayan dare. Har ya fara bacci Tilly ta dauka
taga ansa H dear. Kashe wayar tayi gaba daya
tayi tsaki sannan da dariyar mugunta. Yarinya
yau zaki bushe ta fada a fili..
Saroro ta tsaya kallon wayar. Yanzu ita Junaid
ya kashewa waya? Ko tayi masa laifi ne? A falo
ta kwana ranar tana kuka ita wannan wace irin
rayuwa ce daga wannan sai wannan kullum. Ta
yanke shawarar idan bai dawo ba da safe zata
sanar da iyayensa.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐37
Hafsi da Ummati sun kusa rabin awa a waya
suna ta shawarwari don yanzu kam Hafsi tasan
bazata iya zama haka babu abokin shawara ba
duk da cewa su Hamida suna iya kokarinsu.
Yayarta Hadiza ma ta bugu sun dade suna
magana. Tana wayar Nafisa ta shigo da wata
karamar jaka a hannunta ta zauna kan kujera.
Hafsi ta gama waya suka gaisa. Nafisa tace
kanwata kinga yadda Allah Yake ta jarrabar mu
da abubuwa kullum ko? Yauma hakuri dai zan
kara baki. Da yar shawara kadan. Kinga
wadanan kayan masu tsada ne amma fa idan
kika sha baza ayi asarar kudin tara ba. Suna
gyara mace sosai sannan ki rika shan fruits
musamman kankana. Akwai kunun aya ma da
ake hadawa da ita da cucumber, dabino,
kaninfari, citta da kwakwa. Zan hada miki da
kaina kafin anjima. Munyi magana da Mommy ke
zaki fara tarewa sannan bayan sati daya talatu
ta tare amma gidanta daban ne. Kiyi iya
kokarinki ki zama tamkar karuwa kema a wurin
mijinki kinga ya san wasu matan so raba shi da
irinsu sai kin dage sosai. Kan Hafsi a kasa duk
kunya ta kamata ta kasa magana. Nafisa ta
nuna mata yadda zata yi amfani da kayan data
kawo mata. Ke ni ki dena jin kunyata bazan taba
bari matan banza su rabaki da mijinki ba. Tunda
kika auri Junaid kin gama mana komai.
Talatu yar gidan Mal Jibo mai faskare amaryar
Junaidu dan sanata. Kirari ne Rosie da ke zaune
kan kujera take wa aminiyarta. Tilly tace yanzu
fa dole inyi ta amsa sunan Talatu sunan dana
manta dashi tun a kauye. Suka tafa sanan rosie
ta miko mata kullin magani. Ga wanan kawata ki
shafa hannu ne ki taba shegen. Wallahi zaki
sha mamaki don watarana ma sai ya gundireki
idan ya fara like miki. Wata shewa suka yi tace
Rosie ba kyau. Gara tun wuri na fara kiranki
Samiranki kada ayi subutar baki a gaban
surukai. Hakane, yanzu dai zan kira shi yazo a
sunan kina zubar da jini sai ki fara gwada
saarki. Bikin ma da akace muyi a garinmu zasu
sha mamaki don sai munyi kara'i. Sake tafawa
sukayi sannan Tilly wadanda sun koma dakin da
Rosie ta kama musu ta dauki waya ta kira shi.
Tun safe ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda
tsananin farinciki yau Hafsin sa zata tare. Ya
fito daga wanka yaji karar waya a zatonsa ma
Hafsi ce don tun dare take tsokanarshi da
flashing. Tsaki yayi kamar tana gabansa daya
ga number din Tilly. Yana dauka Rosie ra
kwarma ihu tace yazo Tilly tana ta zubar da jini.
Wani tsakin yayi ya ajiye wayar ya cigaba da
shiryawa. Sake buguwa suka yi har sau biyar
sannan ya dauko a wulakance yace gani nan
zuwa. Cikin gidansu ya shigo ya fadawa Mommy
inda zashi. Ta tabe baki sai ka dawo. Kada dai
ka dade yace to. Shi har a ce masa kada ya
dade yadda yake zumudin nan.
Suna jin tsayuwar motarsa Tilly ta kwanta a
kasa tana wai wai. Kudi ya jefa mata yana mata
kallon banza gashi nan nasan abinda kike nema
kenan. Ganin bashi da niyar taimaka mata ta
tashi ta mike ta riko shi. Juni boy ka saki jikinka
mana ai an riga an daura. Ina jiranka anjima
kazo mu tafi namu gidan don a sannu zansa ka
manta wannan kwailar. Hankadeta yayi har ta
fadi kamar zaiyi magana ya fasa ya fice. Rosie
dake kitchen ta fito da sauri tana mata sannu.
Tilly tace aikin banza maganin naki baya komai
ji yadda ya ture ni.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐39
Wani azababben ciwon kai ta farka dashi lokacin
da taji bugun kofa. Sai bayan asuba bacci ya
sace ta, dan goge fuska tayi ta bude kofar.
Amaka ce dauke da tray ga wani a kasa shima
duk kwanukan abinci ne a ciki. Tace Amariya
goodmorning...Hafsi ta dan saki fuska ta amsa
tare da daukar tray din kasan suka shigo dashi.
Amaka tace Madam say make you tell me wetin
you wan chop for lunch. Hafsi tace what? Ita fa
bajin pidgin english take ba. Ta dai gane lunch
ta ce mata ta tafi kawai zata shigo. Har shabiyu
tana jira ganin dai bashi da niyar dawowa gashi
wayoyinsa duk ta kasa samu ta fito ta tafi main
house. Babu kowa a falon sai akwatuna guda
uku daga bakin kujera. Dakin Hajiya ta fara
leqawa ta ganta tana daura laffaya. A'a mamana
keda kike amarya me ya fito dake kuma. Nima
shirin komawa Kano nake yi yanzu Rufai nake
jira yazo muyi sallama sai a kaini iyaport. Hafsi
tayi dan murmushi tace Hajiya bana son ki tafi.
Allah sarki Mamana bakya so naje na gyara
nawa auren ne? Tare fa aka kawo mu dake
gashi muna neman wata daya. Wasu hawaye
masu zafi ne suka sauko mata Hajiya a rude
tace haba Hafsatu kada ki karyar min da zuciya
mana. Ki kara hakuri in Allah Ya yarda zaku
sami zaman lafiya da Junaidu. Kirawo min shi
mu yi sallama sannan ki goge idonki kada yace
na taba masa mata. Kanta a kasa tace baya nan
Hajiya. Dan bata rai tayi ina yaje kuma daga kai
masa amarya. Mummy dake tsaye a bakin kofa
tace garin yaya kika bari ya fita amarsu. Har
kasa ta kai ta gaishe da mummy sannan soma
kuka. Duk hankalinsu ya tashi aka suna
tambayarta ko lafiya. Da kyar tace musu bai
kwana a gida ba. Sai suka fara salati. Mummy
ta dauki waya ta kira shi aka yi sa'a a kunne
wayar take.
Tilly ta kalli wayar bari na daukar maka Juni
boy. Kasan yau rana ta ce so duk mai kira yayi
hakuri. Ba musu ya mika mata batare da yasan
mai kiran ba. Hello ta fada bayan ta amsa
wayar. Mummy a dan razane tace wacece?
Ahhh tuni ta gane muryar jarababbiyar babar
tashi. Tace matarsa ce Talatu don Allah a dena
kira yana bacci ne idan da sako ki fada na gaya
masa. Yadda take maganar a ladabce shi yasa
Junaid ta kara lafewa jikinta yana mata
cakulkuli please ki ajiye wayar anjima na kira.
Karaf maganar sai a kunnen mummy tace
Junaid da karfi. Tilly bata bare yaji ba ta ajiye
wayar ba tare da ta kashe ba tana ta dariya
please baby ka bari kaga jiya baka barni na
runtsa ba.
Jefa mummy tayi da wayarta tana kuka mai
tsuma zuciya. Maganar Junaid ta tabbata
karuwa ce yarinyar nan. Suna tare bansan ko a
ina ba amma suna tare. Hajiya tace inna lillahi
wa inna ilaihi rajiun. Anya zan iya komawa kano
kuwa salma? Yarona yana cikin matsala.
Mummy tace ki tafi hajiya ai tsuntsun daya ja
ruwa shi ruwa zai daka. Rashin jin maganar
iyaye yasa ya kwaso mana balai. Bari na tado
Yallabai wallahi a nemarwa yarinyar nan saki tun
wuri. Ni bazan iya kallon Safiya ba ina kallo
dana yana wulakanta musu 'ya.
Tunda suka fara magana Hafsi ke kuka Mummy
ta jawota ta rungume. A haka senator Rufai ya
samesu. Bayan anyi masa bayanin abinda ke
faruwa yace su kwantar da hankalinsu zaisa a
nemo shi duk inda yake a kasar.
Wasa wasa sai da suka yi sati biyu a hotel suna
shan soyayya. Hutu ya ratsa su da kyau don
daga ci sai kwanciya. Ko kadan baya son Tilly
amma ji yake idan ya rabu da ita komai na iya
faruwa. Kashe mata kudi yake kamar hauka tana
karbewa. Rosie master planner ma an manta da
ita .A rana ta shabiyar Senator yasa aka yi
freezing dukkanin accounts din Junaid.
Matsayinsa yasa har aka nuna masa statement
of account din dan nasa. Ba karamin barnar kudi
yayi ba a iya kwanakin da baya gida. Senator
Rufai ya shiga rudani sosai yadda junaid yake
neman kara lalacewa.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐41
Dakinsa ya shiga ya lalube duk wuraren ajiyarsa
ya dauko kudi masu yawa. Yana zuwa wurin
parking yaga convoy din Alhajinsu dole ya tsaya
suka gaisa zai fita. Senator Rufai bai nuna
damuwa ba yace Junaid kafin ka tafi ina son
ganinka. Tsaki yayi wanda har uban yaji
sautinsa. Tilly ta kira shi ya kai sau ashirin kada
yaje taki binsa ko yau ta hana shi kusantar ta.
Yana zaune gaban iyayensa Alhaji ya fara masa
nasiha mai tsuma jikin mai imani. Mummy ce ta
fara lura da yadda hankalinsa ko kadan baya
tare dasu. Duk zancen senator ta bayan
kunnensa yake bi. Tana kara kiran wayar yace
Alhaji bari nake yanzu dai matata ce so don
Allah ku dena daga hankali idan baku ganni ba.
Mummy tace Kana da hankali kuwa Junaid ? Bai
amsa ba ya mike mummy ba nisa zanyi ba ga
keys din gidan ashe suna dakina can zamu
zauna. Fita yayi ko waige babu. Ba mummy ba
hatta senator yau idanunsa sun kawo ruwa.
Ashe da gaske ne idan mutum baya tsarkake
dukiyarsa yaran da aka ciyar da ita albarkarsu
tana tawaya? Allah Ya dora masa son Junaid
har baya son laifinsa. Gashi yau dukiya da dansa
sun zame masa silar rashin kwanciyar hankali.
Kullum tunaninsa baya wuce kada dansa ya
jawo masa abin kunya saboda shi dan siyasa
ne. Daga yau zai guji abin kunya saboda shi
musulmi ne. Haka suka yi ta saka da warwara
kafin daga karshe Senator ya yanke shawarar su
dage da addua har Allah Ya kawo musu mafita.
Duk yadda take kokarin boyewa kana ganin
Hafsi kasan bata da nutsuwa da kwanciyar
hankali. Son Junaid take sosai gashi tana
missing din irin wasannin da suke na tsokana.
Wataninta biyu a gidan Nafisa hakan ya zama
wata uku rabonta da Junaid. Iyakar alkhairi tana
samu wurin iyayen wanda bai damu da ita ba.
Senator ya siyawa babanta mota ya canja musu
gida. Duk sai da aka hada da ban baki Mal
Aminu ya karba. Itama Hafsi dubu hamsin ta
bawa Ummati saboda bikinta saura wata biyu.
Hafsi da Hamida suna zaune tana ta yiwa
hamida tsiyar ciki Nafisa ta shigo falon da
faraa. Big sis ta samu ne hamida ta tambaya.
Kwarai kuwa yanzu Alhaji ya ce muje ayiwa
Hafsi passport dukkanmu zamu umra. Farin ciki
mara misaltuwa ya bayyana a fuskarta. tana ta
godiya ga Allah. Ta samu damar zuwa yin addua
sosai game da Junaid.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐40
Maaikan daya daga cikin bankunan da Junaid ke
ajiya bisa umarnin senator Rufai suka gano
masa atm machine din da yake amfani dasu
wurin cire kudi. Duk a area daya ne hakan ya
bashi tabbacin Junaid yana garin Abuja a
sheraton hotel don shi yafi kusa da wurin atm
din. Ba tare da ya sanar da iyalinsa ba ya tura
ayi masa bincike a hotel din da ma wasu
wuraren shakatawar dake kusa da wurin. Cikin
ikon Allah bayan kamar awa biyu da tafiyar yan
aikin aka kira Senator aka sanar dashi Junaid
yana sheraton din harda room number aka bashi.
Damuwa da bakin ciki sunsa hafsi wata irin
rama. Bata cin abinci sai abu mai ruwa ruwa.
Kullum hakuri kawai suke bata. Karshe Nafisa
tace gara ta tafi d ita gidanta saboda ta rage
kadaici. Haka ta hada kaya suka tafi. A cän
kano yaya hadiza ce kawai tasan abinda ke
faruwa ita ma nafisa ce ta sanar da ita. Hadizan
ce ta hana a fadawa iyayensu tace zata zo
garin karshen wata idan maigidanta zaizo
conference don haka kawai idan ta tafi baffa
fada zaiyi yace Hafsi bata dade ba baya son
yawo. A gidan nafisa ita da yaranta koda yaushe
suna tare da Hafsi. Hatta abinci tare suke ci
shiyasa bata da lokacin tunani da kuka sai ta
shiga daki kwanciya.
Kwanaki biyu bayan an yi freezing account dinsa
yaje atm ya dawo ya dubi Tilly dake rawa a
tsakar daki. Naje atm fa duk machine din yayi
rejecting dinsu. Ta rage sautin kidan tare da
hade rai me kake nufi to? Ka duba a na wasu
areas din mana. Ya zauna bakin gado naje wuri
biyar fa. To ai sai kaje banki don yau dole sai ka
biya ni. Hannunta ya kama ya zaunar da ita.
Haba Tilly bafa call girl kike ba. Yanzu aurenki
nake so banga dalilin biyanki ba duk kwana. Ki
bari gobe naje na karbo keys din gidan sai mu
koma can. Na gama gajiya da abincin hotel ga
rashin abinyi. Hararsa tayi sai yaji gabansa ya
fadi....Hafsi ce mai yawan yi masa irin wannan
kallon. Ko sau daya baiyi mata waya ba gashi
har yayi sati uku rabon da ya ganta. Tace kai
malam dakata min, kudi fa sai ka bani ka tashi
kaje banki kawai. Ya sauke murya kinga tym fa
tilly gashi yau friday dole sai monday zan iya
zuwa. Amma ina da cash a gida if you cant
wait. Da yake akwai ta da hadama tace jeka ka
dawo ina jira. Zan fita nima kafin ka dawo.
A kwance ta tarar da Rosie tayi amai har ta
gaji. wani matsatsten wando tasa da karamar
riga sai dan karamin mayafi shaidar ita
musulma ce. Gidan duk yayi kura saboda sanyi
ita kanta Rosie duk ta rame tayi baki. Abinka da
hasken bleaching. Lafiya Rosie me zan gani
haka tana magana tana toshe hanci. Cikin kuka
tace Tilly da kina duniyar nan? Kwana nawa
babu ke babu labarinki ko wayata ba kya dauka.
Irin sakayyar da zaki min kenan? Na gama
kashe kudi na tas a kanki duniya ta samu kin
sani a shara. Tilly ta zauna can gefe. Yi hakuri
bana son juni ya zargeni ne. Me ya sameki?
Yunwa Tilly yunwa. Gashi na kasa girki saboda
rashin kuzari. Tilly ta kalli cikin da ya fito sosai
ko don rosie ta rame ne oho. Su shege manya
ashe ana nan baa rabu ba. Ai na dauka tuni kin
koma harka. Maganar ta sosa ran rosie sai ta
dake dai. Me nema dole yayi hakuri. Wata
yarinya mai sayar da plantain Tilly ta samu kusa
dasu ta gyara gidan ita kuma tayi abinci. Bayan
Rosie ta dan dawo hayyacinta Tilly tace na fa
shiga problem kawata. Maganin nan kamar ya
fara loosing effect dinsa. Kinga yau motsi kadan
sai yace zashi gida to gudun kada naji a jikina
na bari ya tafi. Idan akwai sauran sa ki bani.
Cikin takaici ta kalli Tilly, lallai samun duniyar
dan tsako. Dama nasan dole ce ta kawo ki
wurina. To bani dashi ki koma halinki ya zaunar
dake. Tilly ta mike aikin banza biyanki fa zanyi.
Nan ta jefi rosie da kudi gashi nan dubu hamsin
ne. Karyarki tilly har kin isa ki wulakanta ni. Har
kin manta duk abinda nayi miki a rayuwa? Idan
kika ci amanata Tilly nima zanci taki. Tilly ta ja
tsaki da wannan kayan a gabanki...to naji duka
sai nasan kina yi. Haka suka yi ta fada kafin da
kansu su sauko don tilly bata da niyar barin
gidan ba biyan bukata.
a firgice ya shigo gidan Mummy har tsoro taji.
Junaid dama kana nan? Baka neman iyayenka
da matarka. Ya gaisheta ta kau da kai lallai
yaron nan bama ka da kunya. Yace mummy kiyi
hakuri. Ina oldman? Baki ta bude oldman kuma
Junaid? Hala abin ya naka ya dawo. To bari kaji
in fada maka wannan iskancin bazan sake dauka
ba. Yace kiyi hakuri mummy Alhaji nake nufi.
Ina dayar to? Dama ita yake son tambaya amma
ya kasa. Ban sani ba ta bashi amsa tare da
mikewa ta haye sama. Tana hawa ta kira Bulus
maigadi tace kada ya bari kowa ya fita sai
Alhaji ya dawo.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐42
Sau uku tana katse wayar tare da yin tsaki. Ya
kalleta fuskar nan babu fara'a. Ya rasa dalilin
zamansa da ita don ko kadan baya sonta. Bashi
da sukuni indai ba kusantarta yayi ba shiyasa
take gara shi sosai. Parties kala kala yake
dawowa ya tarar ta shirya a gidan samari da
yan mata su taru su hole. Idan yayi magana
kuwa ranar sai ya kusa kuka zata bashi
hakkinsa. Yana dai zuwa gaida iyayensa idan ta
gadama amma zancen Hafsi tace ko zuci yayi
zata sani kuma tayi rantsuwa ranar sai dai
hawayensa su kare bazata bashi kanta ba.
Kallon wayar yayi waye ke kiranki? Mtsw rosie
ce duk ta dame ni tana son na taimaka mata da
kudi. Ina wanda na baki last week baki bata
bane? Ta kara yin tsaki kasan gayyar tsiya na
rasa me take da kudin. Yace to bari idan na fita
zan kawo ki bata. A ranta tace kyayi kya gama
bazan bayar ba don yanzu kam yadda yake
yawan hade mata rai tasan magani ya fara ja
baya kuma da kunya ta koma gidan rosie. Wata
biyu rabon da taje kudin da take karba ma
account dinta yake shigewa..
Rosie ta kalli wayarta da katon cikin dake
gabanta. Kudin abinci ma yanzu gagararta yake
amma Tilly taki taimakonta. Gidan da ta tare ma
bata sani ba bare tabi sawu. Shawara daya ta
yanke ta neme malaminta a warware abinda
takewa Junaid ya dawo hayyacinsa ya koreta.
A kasa mai tsarki hafsi da sauran iyalan senator
Rufai Bukar sun dage da yawan sallah da adduoi
don nemarwa Junaid shiriya. Shi kanshi senator
da ya dage da istigfar ba karamin mamaki yayi
ba yadda yake jin canji game da al'amuransa.
Idan Junaid ya dawo garesu dole su koma a
nemi ilimin addini sosai.idan da asiri a jikin
junaid to harda sakacinsa ta bangaren addua.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐44
Junaid yace kowa ya tuba don wuya fa ba lada.
Imran na dariya yace ai wallahi da lada tunda
nayi nadama kuma dai ai ba bari saida nazo
gargarar mutuwa ba. Yanzu dai abar zancena
wane mataki zaka dauka game da Tilly? Gaskiya
i cant say for now matsalar tafi yawa idan na
ganta. Ita kuma dayar ina sonta sosai amma na
rasa me ya hanani nemanta. Bayan dan tunani
Imran yace na sama mana mafita. Cikin zakuwa
yace wacce? Kana ganin zaka iya hakura da
mace indai babu aure a tsakaninku? Jimm yayi
na dan lokaci. Tilly ta zame masa jaraba yace in
sha Allah. To indai haka ne ka kira ta yanzu a
waya. Junaid ya dauko wayar ya kira. Imran
yasa speaker kafin ta dauka yace kayi mata saki
uku yanzu ka yanke ala.....hello? Juni boy ina ka
shiga ina ta jiranka. Imran ya zungure shi yana
magana kasa kasa. Saketa mana...a dan
tsorace yace Tilly na sakeki saki u..u..uku. wata
irin kara suka je imran ya kashe wayar yace to
tura mata text don a sami shaida. Jiki ba kwari
ya tura Imran yana masa dictating abinda zai
rubuta. Yana tura send Junaid yayi wata ajiyar
zuciya. Imran yace idan har bazaka iya ba ka
barni na biyoka gidan. No ka barni kawai ina
zuwa zan koreta.
Hafsi tana ta juya waya a hannunta ta kasa
bugawa. Tun a kano Ummati ta bata shawara
yanzu ma ta sake kiranta taji ko ta kira tace
mata yanzu zata kira. Sai da ta tattaro dukkan
courage dinta ta kira. Wayar tayi ringing har ta
katse bai dauka ba. Kamar tayiwa ummati Allah
Ya isa. Gashi ta zubar da ajinta kuma babu
biyan bukata. A lokacin da take wayar Junaid da
Tilly fada suke kowa murya a sama don bai ma
ji karar wayarsa ba. Nishi take kamar wata
kumurcin maciji Juni boy baka isa ba na rantse
maka. Ni zaka yiwa wannan rashin mutumcin,
saki har uku? Duk da bashi da kwarin gwiwa
sosai yace ki fita kawai kafin na kira security.
Daki ta shiga da gudu ta barbada dan sauran
maganin a hannunta. Saboda kuka bama ta
ganin gabanta sosai. Duk duniya babu wanda ya
isa ya raba mu. Tana yin kansa cikin zafin
nama ya tureta bai san lokacin da ya fara
karanta La haula wala quwata illa billah. Zafi
sosai jikinsa yayi sosai har yáji kamar kafarsa
bazata iya daukarsa ba. Tilly kuwa kan wani
muzurunta ta fada daya tureta. Wata kara
muzurun yayi tare da yakushin tilly. Hannunta
mai magani a jikin magen duk ta shafe masa
shi. Ihu tasa sosai tana kuka ganin abinda tayi
na shiga uku shine na karshe maganin. Wani irin
kallo taga muzurun yana yi mata tare da biyota.
Tuni tilly ta dago jirgin badai maganin yana yi
jikin kowacce dabba ba. Tsere suka sa ita da
muzurun tana gudu yana binta juni help me
please. Ko dago kai baiyi ba yadda yake jin jiri
na dibarsa. Tilly dai kitchen ta shiga ta rufo
kofa tana numfarfashi. Muzuru kowa yana ta
meoww daga bakin kofa yana karta iya karfinsa.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐43
Kwanansu hudu da dawowa bayan sunyi sati
uku a kasa mai tsarki Hafsi ta taje kano tayi sati
biyu. Sun sha hira da ummati ta fada mata halin
da take ciki. Gashi dai ta kara kyau ga hutu
amma babu nutsuwa a tare da ita. Bikin dake
gabanta ne duk yasa ta dan manta da halin da
take ciki. Ansha shagali don ummati ita kadai ce
mace a gidansu. Duk kayan da ta saka da ma
wasu abubuwan Hafsi ce tayi mata. Idan aka
tambayeta mijinta kuwa sai tace yayi tafiya ne.
Haka suka sha biki aka kai amarya gidanta.
Bayan an gama biki Alhaji ya turo mata da kudin
jirgi tana zuwa mota na jiranta suka wuce gidan
Nafisa.
Ya kusa rabin awa yana jiran Imi a kofar super
market din sai ga Tanimu wanda yazo gidansu
a matsayin baban Tilly yana bin wata mata da
kaya niki niki a baya. Tabbas shine don ga uku
ukun bakinsa nan. Rufe motar yayi ya fito ya
karasa inda Tanimu yake shirin lodawa matar
kaya a booth dinta. Assalam alaikum....ai kafin
kace kwabo Tanimu ya zura da gudu don kuwa
ko a mafarki baya jin zai manta wannan fuskar.
Ita kuwa matar kyawun Junaid duk ya dauke
mata hankali kana ganinta kasan tana da aure.
Wani fari ta rinka yi masa da ido da kwarkwasa.
Hafsi ce ta fado masa, gabansa ya fadi. Ya rasa
dalilin da yasa baya iya bude bakinsa ya nemeta
ko ma yayi zancenta. Hango Tanimu yayi zai
tsallaka titi ya bishi da gudu. Wuyan rigarsa ya
kama ya fizgo shi. Tanimu duk ya gama rudewa
don bai manta yadda senator yace zai iya sa a
batar dasu idan suka yi masa karya. Gwiwoyinsa
a kasa ya daga hannu sama yallabai kayi min
rai wallahi sani suka yi. Junaid yace meye
alakar ka dasu? Ya cigaba da magiya faci nake
a tsallaken titin gidansu kuma ina hada su da
maza. Dama dai yasan matan banza ne amma
dai baiyi tunanin iyayen karya ta kawo ba. Sam
baya jindadin rayuwarsa yanzu kullum jinsa yake
kamar an kulle shi a cikin kwai. Imi yaji ya taba
shi ya Juni meke faruwa ne? Junaid ya kalli
Tanimu dake zaune gabansa ya fadawa Imran
ko shi waye. Imran ya kira waya ba dadewa ta
shiga suna zaune police biyu suka zo yace a tafi
da Tanimu har ya fadi inda sauran suke.
Yallabai ai ba sai an dake ni ba muje na nuna
muku su duk abokai na ne. Keyarsa suka tasa a
gaba suka tafi shi kuma Imi ya dawo motar
junaid ya zauna. Wai meyasa kaki yarda mu
hadu a gidanka ne? Wani zafi jikinsa yake yi
yace Imran ina cikin problem sosai, wallahi na
tsani rayuwata. Ba abinda ke min dadi....yanzu
fa ina shiga gida da naga matar nan babu
abinda nake so kamar kusantar ta. Tun ana abu
da marmari yanzu ya koma kamar cin tuwo. Ita
kuma idan ba kudi ta gani ba ta rinka gara ni
kenan. Imran yace ai laifinka ne, tun a wurin
bikinka nace ka barni nayi maganinta kaki.
Yanzu kuma gaskiya na tuba...junaid yayi yar
dariya Allah Ya kara shiryamu. Amin dan
uwa...ai in fada maka wata shegiya ce. Au
wallahi na tuba fa. Hmmm yarinya na dauko
bayan an gama abu sai da nayi kwana biyu
bansan inda kaina yake ba saboda na kasa
fitsari. Wani mugun ciwo tasa min in takaice
maka labari sai da aka yi min aiki a Germany.
Abinda ya gabata Allah Ya yafe mana amma ni
da mace sai matata insha Allah.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐46
Ruwa Hafsi ta diba a wata roba taje falo ta
kwance dankwalin kanta ta jika shi tana goge
masa jiki. Nafisa taje tana bude buden dakuna
har taga kayan junaid. Riga kawai ta saka masa
suka fice. Ihun Tilly suka ji tana kada ku barni
da muzurun nan. Sai da drebansu ya sha wahala
kafin ya iya kulle muzurun a kitchn dama ta
taga ya shiga. Bakin Tilly duk jini don ta sha
faratansa masu tsini suka tausaya mata ta shiga
motar tare dasu. Asibitin kudi suka je inda aka
yiwa junaid gwaje gwaje likita ya tabbatar babu
abinda ke damunsa sai yawan tunani da bacin
rai. Mummy da senator ma sun zo ana yiwa Tilly
dressing din ciwukanta. Babu wanda ya kula ta
a cikinsu suka wuce wurin Junaid.
Washegari sai wurin shadaya na safe Junaid ya
farka. Koda ya bude idanu iyayensa ya gani da
yan uwansa. Hajiyan dangi ma tazo daga kano.
Yunkurin tashi yayi yaji hannu ya danne shi ta
baya Juni ka kwanta jikinka ba kwari fa. Na
shiga uku ce ta subutu daga bakinsa. Don har
zuciyarsa saida ta kada don yanzu tilly tsoro
take bashi. Yace me kike a nan ba na sake ki
ba? Wani murmushi mummy tayi har kana ganin
hakoranta, ita kuwa Tilly me kumburarriyar
fuska tace dont mind him zafin ciwo ne yake
damunsa. Imran da yake asibitin tun safe bayan
ya kira wayar hamida ta dauka yace ke bana
son iskanci...sai yayi saurin rufe bakinsa Allah
na tuba. A gabana yayi mata saki uku wallahi
kuma harda text ma shaida. Karya yake Mummy
don Allah kada ku rabani da Juni. Nafisa tace
idan ma joni ne ke da shi har abada. Kuma idan
baki fita ba Allah security zan kira miki. Ta kalli
su Hajiya tace ai a kwance muka ganta tana
wani tsafi muzuru na lasheta kamar maye. Duk
shi yaji mata ciwo. Tilly cikin kuka da daga
murya tace wallahi karya ne bana tsafi. A jikin
Juni nayi niyar shafa maganin shine na fadi ya
goge a jikin mage. Subhanallahi dama asirce shi
kike yi. Saurin rufe bakinta tayi jin baram
baramar da tayi. Tana girgiza hannayenta da
kanta tace ba haka nake nufi ba wallahi.
Hamida ce ta bude kofa zata tura Tilly waje sai
ga muzuru ya shigo ji kake yana meooowww da
yaga Tilly. Bayansa nurses biyu ne da wani cikin
masu gadi sun biyoshi da gudu. Jikin Tilly ya
dafe yana zazzare idanu harda wani lafewa a
kafadarta. Ita dai mutuwar tsaye tayi ko motsi
ta kasa. Maigadin yace kuyi hakuri muna binsa
yana gudu kamar yasan inda zashi ne. Imran
dariya har kasa ta kaishi yace no ka barshi
kawai ga matarsa nan ya nuna Tilly dake
hawaye ba kakkautawa. Tausayi ta bawa hajiya
tace don Allah a raba ta dashi. To dai jikin Tilly
kamar me wasan kura da kyar aka rabasu don
sai da aka yiwa muzurun allurar bacci ya fado.
Tana ta godiya nan ta fada musu duk sharrin
data kulla ita da Rosie ta roki gafarar su. Hafsi
da ke can gefe akan kujera Tilly ta kalla tace
kema sharrin dana yi miki babu ma cikin kawai
so nayi ya sake ki.
Nan dai kowa yace ya yafe Nafisa tace ina
kudin da kika karba wurin Junaid. Sai lokacin ma
ta tuna cikin kankanuwar murya tace yana
drawer a gida. Nafisa ta sha kunu to babu ke
babu su don har atm din Alhajinmu ya sata yana
baki kudi. Daga nan ki san inda dare yayi miki.
Hajiya tace to kuzo mu tafi gida don a kawo
musu abinci. Hafsi ce kan gaba Hajiya tace ni
bana son gulma zauna wurin mijinki kinji ko.
Kamar tayi kuka duk suka fice. A bakin kofar ta
tsaya taki juyuwa ma ta kalleshi. Kusan minti
goma tayi a haka har kafaŕta ta fara sagewa shi
kuwa Junaid dama kyaleta yayi don yaga iya
gudun ruwanta. Yana kallonta ta sa nauyi a
wannan kafar idan ta gaji ta canja. Murmushi
tayi don ta fara bashi tausayi.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐45
Da kyar ya mika hannu ya dauko wayarsa don
ya kira imran. Kansa ne yake juyawa saboda
tsabar ciwo ga zazzabi da ya rufar masa lokaci
guda. Missed call din Hafsi ya gani take yaji
zuciyarsa tayi masa sanyi. Kiranta yayi amma
har wayar ta kare ringing bata dauka ba.
Tsaki tayi ganin me kiran ta wurga ta kan gado
tare da tayar da sallah. Husna ce ta shigo dakin
jin waya tana ringing ta dauka ta fita Maama ga
wayar Mama Hafsa tana ringing. Nafisa ta ajiye
remote din hannunta ta kalli Husna. Yanzu wa
yace ki dauko mata waya? Maama sallah take
yi. Kinga an sake kira ma. Nafisa ta karba ganin
sunan Junaid tayi saurin dauka. Tana jin
muryarsa ta mike tsaye Junaidu kana ina?
Jikinta har rawa yake yace sis kece? Sautin
kukansa taji yace i need you please. Kizo gidana
yanzu. Kwalawa Hafsi kira tayi ki fito muje
gidan Junaid Hafsi ina jin akwai matsala don
maganar da yake ma ya dena. Hafsi najin haka
itama kukan ta fara suka dunguma waje driver
ya kaisu unguwar maitama inda gidan Junaid
yake. A hanya ta kira mummy ta fada mata
itama duk ta rude don tasan ko ba a fada ba
dan nata yana cikin matsala.
A falo suka tarar dashi yana ta rawar sanyi ga
gumi ya gama wanke shi har rigarsa ta jike.
Nafisa tace da drebansu yazo ya dauko musu
shi asa shi a mota. Hafsi tace bari a rage masa
kaya jikinsa yayi zafi sosai. Ina ne kitchen ma,
duk ta rude tayi nan tayi can. Nafisa ta nuna
mata da hannu tana dago kan Junaid.
Wata irin faduwar gaba taji lokacin da taga Tilly
kwance muzuru yana bin jikinta yana lashewa.
Ko motsin kirki ta kasa yi don duk inda ta motsa
sai ya yakushi wurin. Yanzu ma cinyarta
muzurun ke lasa. Auzubillahi minash shaidanir
rajim. Abinda ya fito daga bakinta kenan. Tilly
cikin kankanuwar murya tace taimake
ni...muzuru ne ya dare kan fuskarta yana lasar
mata baki saboda ta motsa bakin.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐47
Dole ta ajiye fushin ta koma kan kujera ta
zauna. Tana zama ya soma dariya ai na zata
kinyi short service ne shiyasa kika dogare a
tsaye kamar soja. Dan turo baki tayi tana
harararsa... shafa kansa yayi yace God how i
missed that. Hafsi don Allah dan dawo nan ki
zauna. Kujerar gaban gadon ta kalla daya nuna
ta kawar da kai gefe sai hawaye. Kamar tana
kara masa ciwo da kukanta ya taso a hankali ya
dawo kusa da ita akan wata doguwar kujera.
Janyota yayi ya rungume ba tare da yayi
magana ba sai saukar hawayensa taji a
wuyanta. Tayi saurin dago kanta kukanta ya
kara tsananta. Fuskokinsu ya hada suna kallon
juna yana shaqar daddadan kamshin jikinta. Ki
yafe min Hafsa, ki yafe...bakinsa ta rufe da
hannunta daya wanda yasha lalle mai kyau tace
Allah Ya yafe mana baki daya. Hannun nata ya
zare ya cigaba da magana. Nasan na zalunci
kaina da irin rayuwar danayi adopting tun kafin
nayi aure. Na janyo ma kaina da duk wanda ya
rabeni bacin rai da bakin ciki. A yau nayi dana
sanin duk wani shaye shaye da bin mata dana
yi, rashin kyautatawa iyaye da keta dokokin
Allah. Kuka Junaid yake sosai da sauti Hafsi ta
kara rungume shi sosai tana share masa
hawaye. Kasan lesson din dana dauka a
rayuwarmu? Ya girgiza kai tace Allah Yana bawa
bayinsa chance din tuba da dama don baa
makara da tuba sai an mutu. Kaddarar aurenka
tasa nayi abinda ban taba tunanin yi ba kaima
kuma kabar abinda kake yi. Ni bazan dauki fushi
da kai ba don idan Allah Ya yafewa bayinSa
baya rike su ko Ya cigaba da kamasu dashi. Ni
da kai duk da sauran musulmi duk muna bukatar
inganta imaninmu mu tsayar da zukatanmu wuri
guda a hanyar neman lahira. Kudi ba hauka
bane face wani nau'i na jarabawa daga Allah.
Sai dai munyi rashin saa da yawa cikinmu
musammam 'ya'yan musulmi idan muka ganmu
ko iyayenmu a madafan iko a kasar nan sai
muyi ta barna da dukiyar da ba tamu ba. Yace
hakane kuma gashi da sanin iyayenmu muke yi.
Zanyiwa Alhaji magana kinga duk abinda nayi a
da bai taba hanani kudi ba. Nagode da Allah Ya
hadani dake Allah Ya yi miki albarka tace amin.
Dago fuskarta yayi yana kokarin kissing dinta ta
sake sunkuyar da kai. Au bayan duk kin gama
zance ni shine zaki wani sunkuyar da kai kasa.
Dama fa na gano ki tun dazu abinda kike jira
kenan shiyasa kike ta wani shige min jiki.
Hararar nan mai burge shi tayi masa ta tashi da
sauri. Kada ka manta ni amarya ce samuna sai
anyi da gaske. Yanzu ma don baka da lafiya ne.
Yayi mata murmushi me kashe zuciya Hafsi
Hafsi tawa Allah Ya barmu tare.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐49
Kana ganin Hafsi kaga amarya sai zuba kamshi
take. Hamida ta kalli agogo tayi dariya kinga
Hafsi karfe takwas ta wuce ki tashi ki tafi wurin
mijinki don yau babu mai raka ki. Sunkuyar da
kanta tayi kasa don kuwa mummy na falon.
Mikewa tayi itama tana dariya rabu dasu kinji
Hafsa ni sai na raka ki da kaina. Ba shiri Hafsi
ta tashi da gudu ita kuma mummy ta haye sama
tace bari kiga ni na tafi wurin nawa tsohon. Ku
kuma kowacce ta tashi ta tafi gidanta a barni na
huta. Tana bace musu Nafisa tace to nidai
nayiwa Hadiza alkawarin kaiki da kaina so wuce
mu tafi. Haka suka je side din Junaid ana ta
hira. Hamida na sallama ya bude yana wani
harare harare sai yanzu kuka ga damar kawota.
To sai da safenku yaja hannun hafsi ciki. Nafisa
tace yaro kaci bashi mu kwana lafiya.
Kallon dakin take wanda ya kawatu da kayan
more rayuwa kala kala. Zauna mana Hafsi Hafsi
ko kauyancin ne ya motsa. Ta sha kunu yau
wacece bakauyar eyye. Toooohhh ni kike
zarewa idanu? Duk mace mai zarewa mijinta ido
fa hukuncinta.......mamaki da jindadi ne suka
ziyarci zuciyarsa da gangar jikinsa lokacin da
yaji ta hade bakinta da nasa. Sai da suka jima a
haka ya rinka kokarin su hada ido taki. Kaji wani
sabon salon gulmar kina wani kasa da kai kamar
mutuniyar kirki. Ita kanta tayi mamakin abinda
tayi. Ya kama fuskarta da hannayensa
biyu...Hafsi ki fada min abinda zai karasa cika
min farinciki na. Kunnensa ta kama tace I love
you J dear. Tana gamawa ta hada da cizo a
saman kunnen sannan ta gudu. Binta da zaiyi
yaji an buga musu kofa ga wayarsa dake aljihu
tana ringing. Hafsi ta dawo tace ni na ga ta
kaina. Menene ya tambaya a firgice ta nuna
masa hanyar kofa. Kullum aka kawoni sai wani
abu ya faru. Kanne mata ido yayi kaga su Hafsi
ke kuma kina bukatar kadaicewa da mijinki ko.
Dundu tayi masa har yayi kara sannan ya duba
mai kiran wayar. Ya nunawa Hafsi kinga ma sis
ce. Yana dauka tace fito falo kai da Hafsi.
Hankalinsu duk ya gama tashi ta dauki mayafi
suka tafi falon. Suna ganin Tilly Junaid ya kama
hannun Hafsi zo mu tafi don yau bansan dame
tazo ba. Muryar Senator suka ji yace duk su
zauna. Sai a lokacin Hafsi ta gane baby ne a
bayan Tilly. Nafisa tace a bakin gate muka
ganta securities din wurin sun hanata shigowa.
Mummy tace shine kika kwaso mana ita ko.
Wasikar da Tilly ta bata ta mikawa Senator ya
karanta sannan aka bawa kowa ma ya karanta.
Hafsi tana gamawa taje ta rungume Tilly cike
da tausayawa tace Allah Ya jikanta. Amin Hafsa
nagode don Allah ku yafe mana. Kowa jiki yayi
sanyi aka ce an yafe. Mummy tace to yanzu me
ya kawoki? Cikin kuka ta fadi matsalarta harda
labarin rayuwarta dana Samira wanda ta sani.
Duk mai imani zaiji tausayin yadda aka yiwa
marayun mugun riko musamman Tilly wadda
kanin babanta ya bata ta kakarta kuma ta
karyata zancen sai da aka ganta da ciki suka
koreta.
Bayan ta gama bada labarin senator yace kinyi
karatu ne. Tace eh abinda ya fara sasu bin
maza kenan neman kudin makaranta. Yace to
ina takardunki? Tace suna gidan da aka koro
mu. To gobe kije ki dauko da murna tace to ta
sunkuya zata kwance goyon senator yace ah ah
ki tashi yanzu zansa dreba ya kaiku asibiti a
duba lafiyar yaron. Tayi musu godiya ba adadi
Hafsi ta karbi Abdallah ta rungume tana kuka.
Tilly tace musu sunanta Safiya yaron kuma ga
sunan da mahaifiyarsa ta zaba amma baa yi
masa radin suna a kunne ba. Junaid yace
khudba aka cewa. Senator ya miko hannu
alamun a bashi yaron. Hafsi ta mika shi Senator
Rufai yayi masa Khudba. Sannan dreba ya kaisu
asibiti inda suka kwana.
Junaid ya kalli fuskar Hafsi bayan sun idar da
sallar nafila yace to yau dai Allah yayi ga Hafsi
Hafsi ga Junaid a daki daya saura me? Yadda
yake mata wani irin kallo tace saura karatu ko.
Eh haka ne fa ya mike tsaye zai cire riga bari ki
sha darussa kala kala. Can na jiyo dariyarsu
suna cike da farinciki.
Washegari kamar yadda yayi alqawari a gaban
iyalinsa yace ko bayan ransa su kula da karatu
da rayuwar Abdallah. Visa ya tura su aka yi saar
samu saboda sunan senator cikin sati daya aka
gama komai ya tura su Saudia inda ya samawa
Safiya Jibo aiki a Nigerian embassy dake can.
Tayi musu godiya kamar ta ari baki da sake
basu hakuri akan laifin da suka yi.
******************
Kowa a gajiye saboda yadda taron yayi jamaa
Hafsi bata samu kanta ba sai can dare ta dauki
baby Rufai junior suka shiga dakin Junaid. Tana
shiga ya rungumeta cike da farin ciki haba
maijego ya zaki min rowar matata da baby na.
Tayi masa kiss a kumatu sorry my dear J kaga
akwai mutane a gidan kuma duk saboda mu
suka zo. Yace haka ne ya karbi junior to yi sauri
ki min tausa kada su mama suce me nake miki.
Kayi ka gama kai da tausar i just came to say
goodnight. Haka zaman su ya cigaba cikin farin
ciki da kwanciyar hankali. Watan Junior shida
Hafsi ta fara wani laulayi ga bikin Anisa da
Imran abokin Junaid.
Bayan shekara 25
Rahma ce zaune tana koyawa Al-Amin auta
assignment amma rabin hankalinta yana kan tv
zaa fara musabaqar karatun alquran na duniya
baki daya. Ana zuwa kansa ta fara kabbara har
su Junior, Ummi da Aisha suka fito. Ta kalli
yayyen nata tace kunga Yaya Malam. Duk zama
suka yi suka bada attention basu san sadda
iyayensu suka zo suka zauna ba. Karatu yake
da murya mai tsuma zuciyar mai sauraro. Ga
larabci tamkar balaraben gaske. Lokacin da ya
gama gaba daya falon ya kaure da kabbara.
Hafsa ta kalli yaranta zuciyarta sai hamdala
take tace to ku tashi muyi sallah mu taya shi
addua. Junaid ya mike da sauri Mama Hafsi
nine first ina fata zaki bani kyauta. Al amin yayi
saurin tashi Allah nine first yau Abba don tun
dazu nayi alwala. Sauran yayyen ma suka tashi
kowa yace yau yayi alwala da wuri. Junaid yace
kaga yan nema da baban naku kuke tsere? Duk
dariya suka yi Hafsi tace zo nan babana yau
kyautar taka ce. Junior yace mama dama yau
tun safe kike nuna mana wariya akan wannan
dan kalen. Filo ta jefa masa duk suka tashi yin
nafila su taya Abdallah Muhammad adduar
samun saa. Bayan sun idar Junaid yace kullum
kyautar mama kuke so to nima ga tawa. Tickets
ne na zuwa saudia. Zamuje umra tare da taya
Abdallah murna ko baiyi na daya ba zaman nasa
ma abin alfahari ne gare mu. Nan da nan gidan
ya kaure da murna.
Safiya ta cire glasses din idonta ta share
hawaye. Ina ma Samira nada rai ta ga danta
gaban manyan malaman musulunci. Mijinta
Muhammad Aswadiy yace mata cikin harshen
larabci ki cigaba da yi mata addua Safiyya.
Allah shine mai gafara da jin kai. Nagode sosai
Abu Musab ta fada tare da murmushi.
Shekararta biyu a saudia suka yi aure bayan
rasuwar matarsa. Ta sanar dashi komai na
rayuwarta ya ce Allay shine mai gafara da
jinkai. Tare ta hada Abdallah da yaransa uku ta
rike. Bayan ya shiga ciki ne Safiya ta tashi tayi
sujjada tana kuka tace Ya Allah Ka yafe mana ni
da Samira da dukkanin musulmi ka sakawa
iyalan Alh Rufai da mijina Muhammad da
alkhairi. Amin
Alhamdulillah👏🏾
Batul Mamman💖
[5/31, 6:17 PM] Fatima Bello: TUN KAFIN AURE
💐48
A tsorace ta shiga compound din da dakin Rosie
yake cike da zulumi. Bata san da idon da zata
kalli kawar tata ba bayan irin sakayyar da tayi
mata ta mugunta. Yan matan gidan masu
zaman banza ne suke binta da ido lokacin da ta
shigo gidan. Ai dole su kalleta fuskarta har ta
canja kama. Gata kai babu ko dan kwali yar
hular gashin data saka ma tuni muzuru ya tuge.
Kofar dakin ta kama zata bude taji a rufe ta fara
bugu iya karfinta. Rosie don Allah ki bude nice.
Nasan ban kyauta miki ba amma don Allah ki
yafe min. Tambai mai gidan ce ta fito tare da
sauran matan duk suna ta kallonta Tambai ta
koma daki ta dauko wani abu cikin katon
mayafinta ta mikawa Tilly tare da wata takarda.
Kiyi hankuri fa kawarki ta mutu kwana biyu da
sunka shige. Wani ihu ta fasa tare da yin zaman
dirshan a kasa. Ta bude zanin baby ne yake
bacci. Kuka take iyakar karfinta Rosie ki yafe
min wayyo Allah na mun tuba. Allah Ka yafe
mana. Ta kankame jaririn Tambai da sauran
mata suna bata hakuri. Sai da ta gaji don kanta
ta mike tace yaushe ta rasu. Wata mata tace
mata yau kwana biyu kenan. Yunwa ce ta
kasheta ga nakuda ta wahala kafin ta haihu.
Wata kuma tace ke baki da imani ba kece kika
auri dan sanata ba amma ko sau daya baki zo
ba. Haka suka gama cece kucensun kowacce ta
koma dakinta. Tambai ta mika mata mukulli tace
ki kwashe kaya don kudin haya ya kare. Tana
bude dakin wasu hawaye masu zafi suna saukar
mata. Ta kalli baby din da ya kura mata ido tace
ka yafe min dana na kashe maka mahaifiya
amma daga yau nice mamanka. Sunana na
gaskiya bama talatu bane sunana Safiya. Ta
bude takardar tana karatu tana kuka.
1/1/20..
Assalam alaikum Talatu, idan kin sami takardar
nan to hakika rai yayi halinsa. Ya yar uwata
munyi rayuwa tamkar tumaki marasa alkibla.
Nice ma sanadiyar lalacewarki bayan kin baro
gidanku a dalilin fyade da kanin babanki yayi
miki aka karyata ki. Nima wahala ce ta kawoni
ga wannan rayuwar a dalilin maraici kamar
yadda kika sani. Sai dai kuma duk tsananin
rayuwa ba hujja bace ta iskanci. Nayi nadama
mara iyaka kuma naje wurin malam ya warware
abinda aka yiwa Junaid. Ki rokeshi da duk
wanda kika san muamala ta hada mu ya yafe
min. Kema ki tuba don Allah.
Hawaye ta share tace na tuba nima nabi Allah
da manzonSa.
Ga abinda Allah Ya bani nasan dai aikin da
wahala ki taimaka ki bashi tarbiyar da mu bamu
samu ba. Ki koya masa tsoron Allah da
azabarSa. Na saka masa suna Abdallah bawan
Allah. Allah Yasa muna da rabon rahmarsa.
Ashhadu an lailaha illallah wa ashhadu anna
muhammadar rasulullah.
Yar uwarki
Samira Jafaru.
Nima a gefe saida nayi hawaye. Talatu au na
manta Safiya ta rungume Abdallah tana ta kuka.
Allah Ya gafarta miki Samira Allah Ya jikanki.
Haka ta zauna tayi yan kwanaki har dan abin
hannunta ya kare. Ga Abdallah ba abinci. Karfe
tara na dare Tambai tasa samari suka yi boli da
Safiya da kayansu. Babu abinda ta dauka sai
kayan jikinsu ta goya Abdallah suka fita daga
gidan. Yanzu ina na nufa ta fada a zuciyarta.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐49
Kana ganin Hafsi kaga amarya sai zuba kamshi
take. Hamida ta kalli agogo tayi dariya kinga
Hafsi karfe takwas ta wuce ki tashi ki tafi wurin
mijinki don yau babu mai raka ki. Sunkuyar da
kanta tayi kasa don kuwa mummy na falon.
Mikewa tayi itama tana dariya rabu dasu kinji
Hafsa ni sai na raka ki da kaina. Ba shiri Hafsi
ta tashi da gudu ita kuma mummy ta haye sama
tace bari kiga ni na tafi wurin nawa tsohon. Ku
kuma kowacce ta tashi ta tafi gidanta a barni na
huta. Tana bace musu Nafisa tace to nidai
nayiwa Hadiza alkawarin kaiki da kaina so wuce
mu tafi. Haka suka je side din Junaid ana ta
hira. Hamida na sallama ya bude yana wani
harare harare sai yanzu kuka ga damar kawota.
To sai da safenku yaja hannun hafsi ciki. Nafisa
tace yaro kaci bashi mu kwana lafiya.
Kallon dakin take wanda ya kawatu da kayan
more rayuwa kala kala. Zauna mana Hafsi Hafsi
ko kauyancin ne ya motsa. Ta sha kunu yau
wacece bakauyar eyye. Toooohhh ni kike
zarewa idanu? Duk mace mai zarewa mijinta ido
fa hukuncinta.......mamaki da jindadi ne suka
ziyarci zuciyarsa da gangar jikinsa lokacin da
yaji ta hade bakinta da nasa. Sai da suka jima a
haka ya rinka kokarin su hada ido taki. Kaji wani
sabon salon gulmar kina wani kasa da kai kamar
mutuniyar kirki. Ita kanta tayi mamakin abinda
tayi. Ya kama fuskarta da hannayensa
biyu...Hafsi ki fada min abinda zai karasa cika
min farinciki na. Kunnensa ta kama tace I love
you J dear. Tana gamawa ta hada da cizo a
saman kunnen sannan ta gudu. Binta da zaiyi
yaji an buga musu kofa ga wayarsa dake aljihu
tana ringing. Hafsi ta dawo tace ni na ga ta
kaina. Menene ya tambaya a firgice ta nuna
masa hanyar kofa. Kullum aka kawoni sai wani
abu ya faru. Kanne mata ido yayi kaga su Hafsi
ke kuma kina bukatar kadaicewa da mijinki ko.
Dundu tayi masa har yayi kara sannan ya duba
mai kiran wayar. Ya nunawa Hafsi kinga ma sis
ce. Yana dauka tace fito falo kai da Hafsi.
Hankalinsu duk ya gama tashi ta dauki mayafi
suka tafi falon. Suna ganin Tilly Junaid ya kama
hannun Hafsi zo mu tafi don yau bansan dame
tazo ba. Muryar Senator suka ji yace duk su
zauna. Sai a lokacin Hafsi ta gane baby ne a
bayan Tilly. Nafisa tace a bakin gate muka
ganta securities din wurin sun hanata shigowa.
Mummy tace shine kika kwaso mana ita ko.
Wasikar da Tilly ta bata ta mikawa Senator ya
karanta sannan aka bawa kowa ma ya karanta.
Hafsi tana gamawa taje ta rungume Tilly cike
da tausayawa tace Allah Ya jikanta. Amin Hafsa
nagode don Allah ku yafe mana. Kowa jiki yayi
sanyi aka ce an yafe. Mummy tace to yanzu me
ya kawoki? Cikin kuka ta fadi matsalarta harda
labarin rayuwarta dana Samira wanda ta sani.
Duk mai imani zaiji tausayin yadda aka yiwa
marayun mugun riko musamman Tilly wadda
kanin babanta ya bata ta kakarta kuma ta
karyata zancen sai da aka ganta da ciki suka
koreta.
Bayan ta gama bada labarin senator yace kinyi
karatu ne. Tace eh abinda ya fara sasu bin
maza kenan neman kudin makaranta. Yace to
ina takardunki? Tace suna gidan da aka koro
mu. To gobe kije ki dauko da murna tace to ta
sunkuya zata kwance goyon senator yace ah ah
ki tashi yanzu zansa dreba ya kaiku asibiti a
duba lafiyar yaron. Tayi musu godiya ba adadi
Hafsi ta karbi Abdallah ta rungume tana kuka.
Tilly tace musu sunanta Safiya yaron kuma ga
sunan da mahaifiyarsa ta zaba amma baa yi
masa radin suna a kunne ba. Junaid yace
khudba aka cewa. Senator ya miko hannu
alamun a bashi yaron. Hafsi ta mika shi Senator
Rufai yayi masa Khudba. Sannan dreba ya kaisu
asibiti inda suka kwana.
Junaid ya kalli fuskar Hafsi bayan sun idar da
sallar nafila yace to yau dai Allah yayi ga Hafsi
Hafsi ga Junaid a daki daya saura me? Yadda
yake mata wani irin kallo tace saura karatu ko.
Eh haka ne fa ya mike tsaye zai cire riga bari ki
sha darussa kala kala. Can na jiyo dariyarsu
suna cike da farinciki.
Washegari kamar yadda yayi alqawari a gaban
iyalinsa yace ko bayan ransa su kula da karatu
da rayuwar Abdallah. Visa ya tura su aka yi saar
samu saboda sunan senator cikin sati daya aka
gama komai ya tura su Saudia inda ya samawa
Safiya Jibo aiki a Nigerian embassy dake can.
Tayi musu godiya kamar ta ari baki da sake
basu hakuri akan laifin da suka yi.
******************
Kowa a gajiye saboda yadda taron yayi jamaa
Hafsi bata samu kanta ba sai can dare ta dauki
baby Rufai junior suka shiga dakin Junaid. Tana
shiga ya rungumeta cike da farin ciki haba
maijego ya zaki min rowar matata da baby na.
Tayi masa kiss a kumatu sorry my dear J kaga
akwai mutane a gidan kuma duk saboda mu
suka zo. Yace haka ne ya karbi junior to yi sauri
ki min tausa kada su mama suce me nake miki.
Kayi ka gama kai da tausar i just came to say
goodnight. Haka zaman su ya cigaba cikin farin
ciki da kwanciyar hankali. Watan Junior shida
Hafsi ta fara wani laulayi ga bikin Anisa da
Imran abokin Junaid.
Bayan shekara 25
Rahma ce zaune tana koyawa Al-Amin auta
assignment amma rabin hankalinta yana kan tv
zaa fara musabaqar karatun alquran na duniya
baki daya. Ana zuwa kansa ta fara kabbara har
su Junior, Ummi da Aisha suka fito. Ta kalli
yayyen nata tace kunga Yaya Malam. Duk zama
suka yi suka bada attention basu san sadda
iyayensu suka zo suka zauna ba. Karatu yake
da murya mai tsuma zuciyar mai sauraro. Ga
larabci tamkar balaraben gaske. Lokacin da ya
gama gaba daya falon ya kaure da kabbara.
Hafsa ta kalli yaranta zuciyarta sai hamdala
take tace to ku tashi muyi sallah mu taya shi
addua. Junaid ya mike da sauri Mama Hafsi
nine first ina fata zaki bani kyauta. Al amin yayi
saurin tashi Allah nine first yau Abba don tun
dazu nayi alwala. Sauran yayyen ma suka tashi
kowa yace yau yayi alwala da wuri. Junaid yace
kaga yan nema da baban naku kuke tsere? Duk
dariya suka yi Hafsi tace zo nan babana yau
kyautar taka ce. Junior yace mama dama yau
tun safe kike nuna mana wariya akan wannan
dan kalen. Filo ta jefa masa duk suka tashi yin
nafila su taya Abdallah Muhammad adduar
samun saa. Bayan sun idar Junaid yace kullum
kyautar mama kuke so to nima ga tawa. Tickets
ne na zuwa saudia. Zamuje umra tare da taya
Abdallah murna ko baiyi na daya ba zaman nasa
ma abin alfahari ne gare mu. Nan da nan gidan
ya kaure da murna.
Safiya ta cire glasses din idonta ta share
hawaye. Ina ma Samira nada rai ta ga danta
gaban manyan malaman musulunci. Mijinta
Muhammad Aswadiy yace mata cikin harshen
larabci ki cigaba da yi mata addua Safiyya.
Allah shine mai gafara da jin kai. Nagode sosai
Abu Musab ta fada tare da murmushi.
Shekararta biyu a saudia suka yi aure bayan
rasuwar matarsa. Ta sanar dashi komai na
rayuwarta ya ce Allay shine mai gafara da
jinkai. Tare ta hada Abdallah da yaransa uku ta
rike. Bayan ya shiga ciki ne Safiya ta tashi tayi
sujjada tana kuka tace Ya Allah Ka yafe mana ni
da Samira da dukkanin musulmi ka sakawa
iyalan Alh Rufai da mijina Muhammad da
alkhairi. Amin
Alhamdulillah👏🏾
Batul Mamman💖
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
        (admin
   Arewa hausa novels 
       Novels villa
     Duniyan novels 
   Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
          And 
Cool novel, makeup and cooking) 

      WHATSAPP NO:
    +2347039625239



Download Tun Kafin Aure Littafi Na Daya Complete