Ajininsa yake 1-01
Posted by ANaM Dorayi on 07:24 AM, 03-Nov-15
Under: Ajininsa yake
__________________ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
________
Rabe jikin daya daga cikin bishiyon da suka yi wa
filin sukuwar kawanya. Jikinsa kayan mkrntar
firamare ne. Farar riga da koren wando. Gaba-
daya hankalinsa tattare ya dora bisa dawakan da
ke zuba tsere kamar za su tashi sama. Babu
abinda yake tunani, illa ina ma shine bisan dokin
da yayi wa saura fintankau?"
Jama'a suka hau ihu, don taya mai dokin daya zo
na farko murna. Shi ma ya kwasa a guje.
Yana isowa bai ma san ya jefar da jakar
littattafan sa ba. Ana ture shi, yana turawa, sai
da ya kutsa ya ta6a jikin saurayin daya zo na
farko.
Kamar an sanya shi al-janna, haka yake ji cikin
ran sa.
Wasu rukunin dawakan ne za su taso yanzu, shi
yasa duk jama'a suka koma inda suke.
Haka shima ya nemi wata bishiyar ya kuma
ra6ewa jikin sa na tsuma, tamkar na 'yan dambe.
Caraf!
Ya ji an cafke kunnunwan sa 2, a firgice ya juyo,
su kai ido 4 da mahaifinsa. Ido warwaje ya daga
hannayen sa sama, amma ya kasa cewa komai.
"Ba za ka daina bata min rai ba Naseer?
Makarantar kenan?
Ya 6ata rai kwarai, manyan idanuwan sa suka
kada jajir!
Haka ya tsurawa Baban sa ido.
"Zo mu je mkrntr, jikinka ne zai gaya maka,
tunda kai kunnan kashi gare ka, ni ma ba zan
fasa ba!
Ina jakar ka?
Ya shiga dube-dube,"Au jakar ma ba kasan inda
take ba?"
Ya maka masa duka a keya,"Wuce mu je ka nemo
jakar, dan banzan yaro marasa jin magana!"
Yaja kunna sa suna tafiya har suka yi karo da
jakar,"Duka ka dauko ta!"
Ya sa hannu ya dauko, a haka suka shiga. Cikin
mota, kunci kamar Naseer zai yi bindiga sabo da
kunburi."(L.E.A Primary School) da ke kusa da
ofishin "Yan-sanda na Tudun Wada Zaria nan
suka shiga shugaban makaranta.
Ya tsura masa ido ya-ce,"Ba za ka bar Babanka
ya huta bane Naseer! Kai wane irin yaro ne?" Ya
juya gefe ya tura hannunwan san a aljihu.
Hedimasta ya dankwafar kan sa ya ce,"Rage
tsawonka, ka kuma cire hannayen ka daga
aljihu!"
Ya durqusa yana huci, saboda tsabar zuciya,
kirjinsa na bugawa muraran kowa na gani."
Malam Balarabe ya ce,"Zane min shi za ka yi a
gaba na in gani.
Idan kuma ba za ka iya ba, ni zan dauki bulalar
in hukunta shi bar ni da shi.
Ya ce,"nan da nan ban zuwa Hedimasta, sai na
ga jikin Naseer yayi rudu-rudu.
Ina bulalar take? Miko min ita nan!"
Hedimasta ya jawo dorina, Baban sa ya cire masa
riga da karfin tsiya yana kallo aka rinka tsala
masa dorina dai-dai har goma sha biyu.
Amma Naseer ko gezau bai yi ba, balle ya fidda
hawaye.Takaici kamar ya kashe Malam Balarabe,
ya ja kujera ya zauna, ya ce,"Ban san yadda zan
yi da wannan yaron ba, shi kadai gare ni, amma
gaba d'aya ya buwayeni."
Hedimasta ya ce,"Sai addu'a, yaran yanzu addu'a
ce ke ladabtar da su, don haka ka yi tayi masa
ita.
Babu komai, ka na iya komawa ka bar ni da shi
kawai.
Ya karkada kai cike da damuwa, yasa aljihu ya
labubo Naira 2 ya dora bisa tebur ya ce,"Ga
kudin tarar sa nan don na san da wadancan ya
shiga mota ya je filin sukuwar."
Ya ce,"To shi ke nan.
Allah ya shirya mana."
Ya mike yana fadin,"Amin.
Ya mika masa hannu suka yi Musabaha.
Ko ta kan Naseer bai sake bi ba, ya sa kai ya
bar ofis din.
Hedimasta ya duba shi ya ce,"
"Naseer!"
Ya sunkuyar da kai kasa, ban tanka ba."
Haba Naseer, ka na da kokarinka, kaf ajinku
babu mai kwakwalwar ka, amma ka zauna cikin
aji, sai ya gagare ka?
Kai kullum hankalinka na filin Sukuwa.
Idan ba kayi karatu yanzu ba, sai yaushe za ka
yi?"
Ko alama kai ba ka koyi da abokanka, ba ka
tausayin mahaifinka.
Kodayaushe shine zarya filin sukuwa yana kamo
ka.
Ka yi wa kanka fada Naseer, ka ga yanzu aji 6
ka ke, a gantale, a gantala dai ka kusa zana
jarabawar shiga sakandire, idan ba ka maida
hankali ba, ka na ji ka na gani abokanka za su
wuce su bar ka anan.Yanzu abinda na ke son ka
da shi, shine ka maida rigan ka, ka wuce aji, ka
ga sauran minti 10 a fito (Break), sai ka zo ka
amshi kud'in ka.
Ga su nan aje su waje na. Idan ba ka zo ba,
wannan zai tabbatar min cewa ka gudu ne.
Tashi ka wuce."
Ya mike ya maida rigarsa, bayan sa rudu-rudu
da zanan bulala.
Kai tsaye ya wuce ajinsu.
Malamin da ke cikin ajin yace , "Sai yanzu ka ke
zuwa?" Yayi shiru yana hura hanci.
Ya ba shi rankwashi 2 masu kyau, sannan ya-ce
ya je ya zauna.
Ya taho a kunbure ya tsaya gaban bencin baya,
inda ya saba zama.
Kallon sauran yaran kawai yayi, suka hau
matsawa ya sami wuri ya zauna. Ya ci gaba da
kunci, bai ko sauranon Malamin turancin da ke
ajin har aka kada Break tara. Malam ya fita,
kowa yayi waje, sai Naseer kadai ke zaune yana
tunanin yaya za'a kare wasan da ya baro ana
yi? Wani yaro dai-dai tsawon sa wankan tarwada
ya shigo, ya zauna kusa da shi.
"Naseer, ashe ka zo?
Ya dube shi ido jazur!"
"Eh,
Ya kura masa ido ya-ce,"Yau ma dukan ka aka
yi?"
"Ban sani ba!"
Ya fada cikin fushi.
Ya-ce,"Ai na gaya maka, kar ka je, amma ka ki
ki, don na san dole ne Babanka zai zo nan ya
bincika."
Ya nuna shi," Kar fa ka dame ni Sageer, meye
ruwan ka!
To!"
Ya mikie ya-ce,"Allah ya ba ka hkr. Ni zan je
wajen masu abinci, in sayo maka gyada ne?"
Ban ci!"
Ya amsa, bai kalle shi ba.
Sageer ya wuce abin sa.
Tsaki yayi, ya jawo jakarsa ya fidda littafin sa da
biro yayi ta zana dawaki suna tsere, ko alama
bai yi tunanin ya je ya amso kudin sa ba. Duk
da cewar Hedmasta ya-ce idan bai zo ba, to ya
san ya gudu ne.
Kuka yake ta ji, ta bayan tagar ajin da yake
zaune. Kwarai kukan ya dauki hankalinsa, don
haka ya mike ya leka.
Wata 'yar yarinya-ce rabe take ta gurshashan
kuka ba ji, ba gani.
Akalla za ta kai shekaru 8 ko fin haka.
Ya sanya mata ido, duk tayi zufa, majina sharaf-
sharaf, nan take tausayin yarinya ya lullube shi.
Ta tagar yayi tsalle, ya diro gaban ta, don haka
ta dube shi a firgice.
"Ke da wanene?
Ta kasa magana, saboda kuka da ya ci karfinta.
Ya kamo kafadun ta, ya-ce,"An ce wa ya duke
ki?"
Cikin muryar kuka ta amsa,"Kudi na ne suka
fad."
Kudinki?"
Ta amsa da ka.
"To ina yan-uwanki?
Ko ba ki da su?"
Da ka tasa ke amsawa.
Yayi dan shiru, ka-fin ya-ce,"Ki yi shiru, zo nan
ki zauna ki jira ni.
Ya jawo hannun ta, suka zagayo barandar ajinsu
ya zaunar da ita," Zauna nan ki jira ni."
Ta zauna tana share hawaye.
Wasu na sake zubowa.
Kai tsaye ofishin Hedimasta ya nufa.
A kofa suka yi kicibi6.
Hedimasta ya-ce,"Ai na dauka ka yi halin naka
ne.
A jinku da za ni yanzu, shigo ka amsa."
Suka shige tare, ya jawo dirowa ya dauko, ya
mika masa." Ana tashi kuma, ka zo nan kafin ka
wuce gida."Can kasan makoshinsa ya amsa da
"To."
Ya fice.
Malama Abu da ke zaune ta ce ,"Ina son yaron
nan, amma bai son karatu, ga shi da kokori.
Hedimasta ya ce,"Ke ko ni wallahi akan dole na
ke dukan sa, saboda baban sa tausayi yake ba
ni, koma yana son yayi karatun."
Ta ce,"Yara ai sai hkr, Allah dai ya shirya mana."
Ya ce,"Amin."
Shi kuwa wajen yarinyar nan ya koma, har
yanzu tsiyayar hawaye take yi.
Ya kamo hannu ta yana fad'i,"Har yanzu kukan
ki ke yi?
Ta so mu je ki zabi abinda ki ke so ki ci."
Ya ja ta zuwa wajen masu abinci.
Can ya hadu da Sageer."
Ina ka samo wannan?"
Ya ce,"Kudin ta ne ya suka fadi, shine take
kuka, kuma bata da kowa anan.
Zo ki zaba, me ki ke so?"
Kankara kawai ta nuna.
Ya siya mata, sannan ya kara mata da aya mai
siga da gyada mai gishiri.
Ta ce,"Na gode.
Ya kamo ta suka dawo da Sageer.
Nan bisa baranda suka zauna su 3 tana ta shan
kankara ta."
Ya sunan ki?"
Ya tambaya ta.
Ta-ce,
"Zahra Umar.Ya ce,"Wane aji ki ke? Ta amsa,
"Aji uku." Ya ce,"To maza ki cinye, ki koma aji.
Ya juya suka ci gaba da hira da abokan sa.
Labarin wasan da ya baro ana yi, shi yake ba
Sageer.
"Abinda ke hana ka karatu kenan Naseer, kai
kullum hankalinka ka akan polo yake.
Ya gyara fuska, don shi Naseer akwai iya tsare
gida tamkar wani babba, ya ce,"Kowa ya dame
ni akan Polo, ni kuma ina so, burina in ganni ina
sukuwa, kamar Yakubu Jah-Jah. Yau ba karamin
burgeni yayi ba, sai da na kukkutsa na ta6o
shi."
Ya ce,"To ai komai dan lkc ne Naseer. Ina
amfanin kullum sai an yi maka bulala? Dubi jikin
ka, ko'ina ta6on bulala ne, sam ba ka jin
magana Naseer." Ya ce,"Ban ji din idan ka yi
min iskanci yanzun nan, zan kwashe ma hakori
wallahi, ka kuma sake magana, ka gani."bai ce
kala ba, ya juya ya ci gaba da murza gyad'ar sa,
yana afawa baki. Naseer ya juyo kan Zarah, sai
ya ga wayam!
Tuni ta kama gaban ta. Yayi dan shiru, kome
yake tunani? Oho.
Ya dubi Sageer, ya ce,"Yaushe Zarah ta gudu?"
Yayi banza da shi, yana ta jan gyadarsa.
Tsaki yayi shi ma, ya mike ya haura aji ta taga.
Yara cike da ajin ga littattafin sa da biro, amma
babu wanda yayi gigin ta6awa, don sun san
kayan Naseer ne.Yana zama ana kada
kararrawa. Muryar Sageer ya ji ta taga yana
cewa,"Dama ana tashi ka yi tafiyar ka, kar ka
sake ka neme ni!"
Ya ce,"Kai din banza, wa zai neme ka?
Mts!
Ya dauke kan sa daga kallon sa.
Shi ma tuni ya bar wajen ya nufi ajin su."
Karfe sha biyu da rabi aka tashi.
Naserr ya fito rataye da jakarsa, babu abinda ya
tsinana da littafin sai dai dan banzan zanen
dawakai.
Yana tsaye bisa barandar yana kallon yara na ta
wucewa.
Can sai ga Zarah a gujeni ta za ta wuce." Da
sauri ya kwala mata kira,"Zarah!"
Ta dawo gunsa da fara'a ta,"Sai ku gudu, babu
sallama?"
Ita dai dariya ta sani. Sai gobe kenan?" Ta ce,"
Eh."
Ya ce, shi kenan, amma ki dina gudu, kar ki fadi
kin ji?"
Ta ce,"To." Bata saurari komai ba, ta juya ta tafi
a hankali, kamar yadda ya ce. Ya kasa dauke
idonsa a kanta, har ta sha kwana.
Kawai ya ji kaunar sukuwa. Ya sakko daga
barandar, ya nufi ofis din Hedimasta, yana fadi
a ran sa,"Shi kuma wancan dan rainin wayau,
wai sai na je gun sa, kafin in tafi gida.
Mts!
Ya ja tsaki.
Fuska murtuke ya shiga ofis din.
Kaf Malaman da ke ofishin, sai da suka tanka
masa.
Ba su ishe shi kallo ba ma, balle ya tanka ma
su.
Gaban tebur ya tsaya, yana kallon
Hedimasta.Shine ya yi masa magana,"Manya!"
To akama hanya, kar ayi kwana ko'ina sai gida.
Ka ji ni da kyau?"
Ya juya manyan idanuwan sa ya ce,"Uhm
"
Gobe kuma 7 da rabi ka same ni anan.
Kama hanya ka wuce."
Ya juya ya ce a ransa,"D'an rainin wayau!"
Malama Abu tayi kiran sa.
Ya matsa wajen ta ya tsaya.
Ta kare masa kallo sannan ta ce,"Ayi kokari, a
zo, makarantar gobe don Allah."
Ya murza ido ya amsa,"Ai zan zo."
Ya wuce tana kallon sa.
Yana fita ya saki tsaki,"Wannan matar, wata
rana sai na tara ma duwatsu wallahi!"
Bai nemi Sageer ba, ya kama gaban sa.
Dai-dai wata kwana yahango Malamin
turancinsu, wanda ya rankwashe shi da safe, ya
rabe jikin kwanar, ya waiwaga bai ga kowa ba.
Yasa hannu ya dauki katon dutse, ya wulwula
masa.
Kau!
Malami ya ji saukan dutse bida ga keyar sa.
Ya dafe keya yayi ta neme-neme, amma bai ga
kowa ba. Cikin hanzarinsa ya dawo kan kwanar,
ba kowa a wajen.
Makale yake jikin wani gida, yana hango Malam
na ta murza keya yana kwafa.
Sai daya bar wajen, sannan ya fito ya dafe a
guje.
Ya kusan isowa gida, ya ci karo da wasu yaran
'yan makarantarsu suna tafe su hudu sun gara
kwallon nan sama,Babu bata lkcn kwallo ta
haura katangar mutane, ta fada cikin gidan.
Yara suka tsaya suna kallon Naserr.
Ya gyara fuska ya ce,,"Ku shiga ku dauko mana."
Guda ciki ya ce,"Malam kar ka raina mana
hankali ma na, ba kai ka jefa ta ba?"Yana rufe
baki. Mai-gidan na fitowa da kwallon a
hannunsa. Suna kallon yasa wuka ya yanka ta 2,
ya jeho musu, ya juya cikn gida abin sa.
Me Naseer zai yi?
Ba dariya ba.
Yaro mai kwallo ya ci kwalar Naseer,"Wallai sai
ka biya ni kwallo na!" Haka sauran yaran suke
ta fadi, duk suka yayyame shi.
Wani dan murmushi yayi yace,"Malam ka sake
ni girma da arziki.
Idan ka yaga min riga, kaf hakorinka kaf, sai na
kwashe ma su." Ya ce,"In ka isa.
Allah ya tsine min!" Koda Naseer ya dunkule
hannu, sai kwaf!
Bisa hancin mai kwallo.
Nan take jini ya tsinke. Dambe ya kwaure da
abokan mai kwallo. Su 3, amma ba su ishi
Naseer komai ba, haka ya ringa wuji-wuji da su,
ya na jefarwa. Mutane suke fara taruwa, aka
raba, binicike ya tabbatar da Naseer ne bai da
gaskiya.
Amma bakin sa yaki mutuwa, saboda haka
samari 2 suka cukuikuyo shi, har gida da yaron
nan jini na ta fita ta hanci. Hayaniya Malam
Balarave ya ji zauren gidan sa, don haka ya fito
yana tambaya ko lafiya?
Ganin Naseer da gayyar yara. Shi ya tabbatar
masa Naseer ya sake dauko masa wata
maganar. Akai masa bayani, dole Malam
Balarabe ya biya kudin kwallo.
Sannan ya kai wanda aka fasawa hanci kemis
aka wanke masa da magani, kuma ya kai shi har
gidan su, saboda gudun tashin hankali.Naseer
na zaune, ya kunbura suntum, da gani ya sha
fada wajen mahaifin sa. Malam Balarabe ya
shiga tsakar gida ya zauna bisa tabarma ya sa
wa Naseer ido.
Ya kada kai, ran sa bace ya ce,"Kai
jama'a,"Naseer ko kauye zan maida ka ne?
Wannan fitina, ta ishe ni! Jin muryan sa yasa ta
fito da daki.
"Ka dawo Malam?"
Ya ce,"Na dawo Mairo.
Zo ki zauna ki ji." Ita ma ta zauna a
tabarma."Naseer ya ishe ni, zan maida shi
kauye, ya je can yayi noma, tunda karatun ma
ba son shi yake ba, sai dan bazan daukan
magana." Ta ce,"Malam ka ce ya kara lalacewa
kenan.........."Ya katse ta,"To ya ki ke son in yi?
Karatu fa Naseer ba yin zai yi ba, ai gara ya
koma can yayi Noma."
Ta ce,"Wannan mai kunnen kashi ne zai yi
noma?
Bai yi karatu ba, sai aikin wahala? Malam, barin
Naseer a gaban mu, shine mafi alkhairi a gare
mu, don ko banza ba mu gan shi ba a
makaranta ba, in ka je filin Sukuwa za ka gan
shi.
Duk rigimar da zai kwaso, zai fi kyau ya kwaso ta
a gaban mu.
Da ka dauke shi ka kai wurin da bai sa ba, ba
kuma shakkar su yake yi.
Mu yi ta yi masa addu'a.
Allah zai duba mana."
Malam Balarabe yayi shiru, jin ka fin ya sauke
numfashi ya ce,"Ya ci abinci?"
Ta ce," Ina fa.
Ai ka san yadda ya kumbura, ya dankare anan,
haka zai yi ta zama, idan ba Sageer ya shigo
gidan nan ya daga shi ba.
Ya ce,"Allah ya shirya.
Ta ce,"Amin.
**********
Satin nan tsaf! Naseer na zuwa mkrnt kamar
abin ya dore a haka. Kuma kodayaushe aka fito
tara. Zarah na tare da shi, ya siya mata
wannan, ya siya mata wancan.
A 'yan kwanakin nan sosai ta saba da shi, don
har gida tana ba Innar ta labarin Naseer.
Ba karamin mamaki Naseer ya ba kowa ba,
ganin bai ta6a jera kwana biyar cur, yana zuwa
mkrnt ba.
Yau litinin yayi shirin mkrnta, sai dai zuciyar sa
bata raya masa ya je makarantar ba.
Kai tsaye bakin titi ya nufa, ya shiga motar
sabon gari. PZ. Daga can ya karasa filin sukuwa
a kasa. Baban sa bai neme shi ba, don ya ga
abin yayi sauki wancan satin, saboda haka
shima yayi zamansa a runfar sa da ke kasuwar
Tudun Wada, inda yake siyar da kayan miyan sa.
Naseer kuwa can ya wuni, domin wasan da yake
son gani ba a fara ba ma, sai 10 na safe. Gab
da sallar azahar ya dawo gida cike da farin ciki,
don yau sosai ya sha hannu da mutuminsa
Yakubu Jah-Jah.
Umman sa ba tayi masa magana ba, duk da
cewar ta fahimce ba makaranta ya je ba.
Bayan ya ci abinci, yayi Sallah. Nan ya gungura
bisa tabarma yayi ta barci har karfe uku da
rabi.
Umman ta shi, ta tashe shi ta ce yayi sallah, ya
tafi Islamiyyar sa.
"Sai ka ki zuwa mkrnta yau?" Inji Sageer. Ya
ce,"Ban je din ba, sai me?"
Ya ce,"Sai me kuwa? Hedimasta na nan yana
jiranka." Ya ce,"Kar ya rage min rai. Sageer yayi
dan murmushi ya ce,"Ba ka ma san wani abu
ba, na je ajin ku neman ka, sai na ga yarinyar
nan Zarah ta sha kuka, ta gaji, wai bata gan ka
ba.
Ni ne ma na rarrashe ta, na je na siyo mata
kankara da gyada.
Tun da yake magana, ya sanya masa ido har ya
kare.
Hankalinsa tashe ya ce,"Inna lillahi. Wallahi
mantawa na yi." Ai kuwa ta sha kuka, har da
'yan mangwaron guda 2 a hannu, na yi na yi ta
sha mangwaron ma, ta ki wallahi.
Nan da nan ran sa ya 6aci ya fada tunanin
Zarah.
Can ya nisa ya ce,"Gobe zan je mkrntr. Ya
ce,"Da dai ya fi.
Suka isa Islamiyya suka shiga aji.
Fadan sa biyu da yara ka fin Malam ya shigo
cikin aji.
Washe gari Naseer ya je makaranta, kuma Zarah
ya fara nema a jin na su, ka fin a shiga asanbili.
Tana tsaye bisa barandar ta hango shi tafe.
Da gudu ta sauko ta kama shi, tana murna.
"Zarah!"
Ta dube shi,"Jiya ban zo ba ko?"
An ce ki na ta kuka."
Ta ce,"Inna ce ta ba ni mangwaro ta ce,"In sha
daya, in kawo maka daya.
Ina ta neman ka, ban gan kaba."
Yayi dan murmushi, ya ce,"Kuma sai aka ce ki yi
kuka?
Kar ki sake kin ji?"
Ta ce,"To.
Tana lalubar Jakar ta.
Mangwaron ta dauko ta mika masa,"
Ga shi nan, na boye maka shi a jaka ta.'a
Ya amsa yana fara'a sosai,To na gaode, idan kin
koma gida, ki cewa Inna na gode."Ta amsa da
,"To."
Tana fadi ana kadawa, don haka ya ja hannun
ta zuwa layin su, ya sanyata a layi har yana ba
na kusa da ita gargadinka kar su sake su ture
ta.
Da (Break) tare suka yi kamar yadda suka saba.
Koda aka tashi, sai da ya tsallakar da ita titi,
sannan ya dawo suka wuce tare da Sageer. Har
cikin ran Naseer, yayi alkawarin ba zai sake
fashin mkrnt ba, sbd Zarah, kar ta neme shi, ta
rasa, hankalin ta ya tashi ta yi kuka.
Ranar laraba ya je mkrnt, ya nufi ajin su Zarah,
aka ce masa bata iso ba tukuna. A asambili bai
gan ta ba, har aka fito break. Ya shiga damuwa
kwarai, dn haka ana tashi, ya binciki wadanda
suka san gidan su.
Ya samu, suka dunguma tare da Sageer da
sauran yaran.
A gangare gidan su yake, suka tsaya a zaure.
Baban ta ya ritsa su, sai ya wucr cikin gidan. Ya
ce,"Lafiya yaya aka yi?"
Naseer ya ce,"Ba mu ga Zarah a mkrnt bane,
shine mu ka zo mu duba ta.
Cike da fara'a ya ce,"Ayya!
Zarah yau babu lafiya, zazza6i take yi.
To ku shigo mana, shine za ku tsaya a zaure ku
na leke?
Ka yaro ho!"
Suka bi bayan sa har dakin Innar Zarah.
Tana kwance, anyi mata shimfida a bakin kofa,
an daga labule don ta sha iska.
Malam Umar ya ce,"Ku shigo, ta nan a kwance.
Ina A'in take ne?"
Zarah ce ta gaya masa tana bayi.
Su Naseer suka shigo suka zauna gefe suka,
gaishe ta, bata iya amsawa ba, wai kunya sai
6oye fuska take yi.
Innar ta ta shigo tana fadin Baki mu kayi?" Ya
ce,"Yan makaranta ne, suka zo duba autar
ki."Ta ce,"Ah! Sannun ku da zuwa." Suka gaishe
ta, ta amsa tana zama kusa da Zarah, hakan ya
ba Zarah damar hayewa jikin ta, tana mata
rada.
Cike da fara'a Innar ta ta dube su,"Wanene
Naseer din? Ya sunkuyar da kai, yayin da Sageer
ke nuna shi. Ta ce,"Kullum sai an ba mu lbrn
Naseer. Ya tare fada, ya siya min wannan, ya ba
ni wancan.
Ashe babba ne.
Ajinka nawa?"
Ya ce,"Shidda 6,."
Ta ce ,"Ashe ma ka ku san gamawa.
Lallai Zarah za ta yi kewa, don shekaran jiya ne,
ba ka zo ba ko?
Nan ta ishe ni da magana, Inna yau Naseer bai
zo mkrnt ba.
To mun gode Naseer.
Allah yayi ma ku albarka."
Duk kunya ta rufe shi da kyar ya ce,"Amin.
Malam Umar ya ce,"To an gode, sai ku tashi
kowa ya tafi gida ko?" Kar aga kun dade ba ku
koma gida ba. Mun gode." Suka mike suna
fadin,"Allah ya kara sauki." Iyayen ta suka ce
"Amin."
Sun fice, jim kadan wani yaro ya dawo cikin 'yan
rakiyar Naseer.
Wani kulli leda ne ya shigo da shi,." Wai ga shi
in ji Naseer.
Ya aje gefen Zarah ya ruga a guje.
Inna na ta dariya. Ta kwance bakar ledar, kullin
gugguru da gyada ne a ciki da aya soyayya. Ta
kada kai ta ce,"Allah sarki yaro, shi kuma jininsa
da na Zarah ya hadu.
Malam Umar ya ce,"Shiririta ke nan.
Ko ina ne gidan su?
,"Oho."
Ita kuwa Zarah tuni ta fara diban abin ta tana
ci.
Kwana 2 Zarah na kwance a gida.
Kullum sai Naseer ya je gidan da safe da
yamma. Hakan yasa iyayenta suka san Naseer
sosai.
Innar ta ke cewa"Lallai Zarah Allah ya ba ki
yaya daga sama."
Shi yasa da ya zo, sai ta ce, "Zarah ga yayanki
ya zo." Ko barci take kuwa za ta tashi. Sai dai
Zarah ta warke ta koma Mkrnta, sannan
hankalin Naseer ya kwanta.
A dalilin Zarah. Naseer ya nutsu a mkrnta, ko
sau daya baya fashi, duk da cewar bai bar Polo
ba, domin duk asabar da lahadi in dai akwai
wasa, toh yana can. Ba karamin mmk ya ba
kowa ba. Iyayensa na ta murna, suna yiwa Allah
godiya, duk da dai rigimar sa ta neman magana,
tana nan babu abin da ya sauya.
Naseer kam bai iya zama na cikakkiyar awa 3,
sai ya nemi abokin dambe.
Duk sa'o'insa tsoronsa suke yi, sbd karfinsa,
balle kananan yara.
Ganin ya nutsu a mkrnt, yasa Hedimasta ya
nada shi (Labour prepet). Sosai yake gudanar da
aikinsa, don ba sauki, ga yara.
Zarah ko ajin su kuskuran kallon banza, babu
mai yi mata shi, sbd kanwar Naseer ce.
Kokarinsa da komai, sai ya nuna shi babba ne,
ke sawa yana kara kwarjini a idon kowa.
Allah yayi masa kyau, surar jikinsa kaf bai da
makusa.
Shi ba fari bane, kuma ba baki bane,."
Sannan ya zarce wankan tarwada.
Wasu manyan idanuwa da Allah yayi masa
farare sol!
Su ke sawa duk wanda ta kallai, sai tayi
sha'awar sa.
Ubangiji yayi wa Naseer wannan baiwa.
Wanda adalilin haka ne kawai yake shiga ran
jama'a su kamu da kaunar sa.
Yau suke zana jarabawar share fagen shiga
karamar sakandire (Common Entrance). A
kwalejin Alhuda-huda. Sun yi, sun gama cikin
sa'a kowa ya koma gida.
Ranar litinin suka taru a mkrnt, kamar yadda
aka bukace su.
Hedimasta ya raba masu satifiket da
Testimoniya, sannan ya sallame su, sai ranar da
jarrabawa ta fito, za'a neme su.Suna fitowa,
ana tashi tara. Naseer ya kama hannun Zarah
ya kai ta siyen kayan kwalama. Daga nan aji ya
zagaya da ita, yana ba yara kashedi da gargadin
NI duk wanda ya kuskura ya ta6a masa Zarah,
musamman zai zo mkrntr kuma kashin mutum
ya bushe, idan ya kama shi.
Shi dai Sageer bin sa kawai yake yi, yana dariya.
To wa zai ta6a ta? Bayan Naseer sunan ya gama
firamaren ne kawai, amma kodayaushe yana
can, sai ya tabbatar da Zarah ta yi break, an
koma aji, sannan ya kama gaban sa.
Idan ya ga dama ya zauna rumfar Baban sa,
idan bai yi ra'ayi ba kuma ya buga yawon sa,
musamman idan akwai wasa a filin sukuwa.
Kwalejin jeka, ka dawo ta gwamnati da ke
kufena, ita Naseer ya samu, yayin da Sageer ya
sami kwalejin Alhuda-huda.
Karatu ya kankama, hakan bai hana Naseer kula
da 'yar kanwar sa ba.
Kullum safiya a bakin kofar mkrntr su take
samun sa yana zaman jiranta, sai ya danka
mata kudin tara da dukkan abinda ya ci ya rage
mata, sannan ya wuce." Bai hada wata 3 ba,
gaba daya a mkrntr sunan sa yayi tambari, ko
dama shi ne shugaban ajin su watau (Monitor)
Tun daga Malamai har manyan da ke gaba da
shi, sun san Naseer da kokari da rashin ji.
Babu damar manyar sa su ta6a shi, ana fita
wajen mkrnt, zai tara masa duwatsu.
Suna ji suna gani Naseer ya gagare su, ba'a
dade ba, ya zama abokin kowa, suna kiran sa
HUKUMA.
Ba wanda bai san Naseer Hukuma ba, har
shugaban mkrnt (Principal). A yau da aka kawo
masa Naseer gaban sa da laifin rufewa Malamin
su kofa.Principal ya dube shi da kyau ya
ce,"Mece ce hujjar kullewa Malaminka kofa?"
Yana daga durkushe kyar! Ba alamar tsoro ya
ce,"Duk ranar da babu asanbili, karfe 7 da rabi
yake rufe mana kofa, duk wanda ya zo bayan
wannan lkc, sai dai ya zauna a waje.
Darasin English ya wuce shi kenan. Shi yasa na
gaya kowa yayi kokari yau ya zo da wuri, sai
kuma ga shi yau Malam bai zo ba, sai takwas
saura kwata, dalilin da yasa kenan na rufe kofa,
don shi ma ya makara.
Principal ya tsura masa ido, yana mamaki,"A ina
ka ta6a jin an rufe wa Malami kofa?"
Ya sosa keya ya ce,"A kufena." Nan da nan
Principal ya shaka,"Iskancin ka ya zo kaina ne?
To na lura ba ka da tarbiyya, sbd haka bayan
sajen ya hukunta ka, za ka koma gida ka huta
sati 2, idan za ka dawo kuma da Babanka."
Naseer yayi shiru, ko ajikin sa, shi nan take ma
yake tunanin zai sami isasheshen lkcn zuwa filin
Sukuwa. Yana tsaye garau!
Sajen yayi masa bulala goma masu kyau.
Aka mika masa takardar hutun cewa aji."
Ga wata sanarwa!. Zan tafi Saudiyya, sati 2 zan
yi idan Malama ya sake rufe ma ku, kofa ku aika
min da sako daga can zan sa masa (Road
block' .
Duk suka dau ihu........
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Ajininsa yake 1-02
Posted by ANaM Dorayi on 09:40 PM, 03-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_____________Ya
daga hannanyensa sama, ya ce,"Sai na dawo!"
Suka ce,"Hukuma!" Hukuma!!"
Ya ce,"Ko ba'a rarrashe ta ba, hakuri take don
U........in karasa?" Ihu kawai suka yi.
Shi ya jawo hankalin Malamai.
Nan take aka firfito da su waje, duk aka ce su
zube sajen yayi masu biyar-biyar.
Shi kuwa Naseer aka tasa keyar sa ana dukan su
suna ihu."
Abar mana Naseer! A bar mana Naseer!!
Karfe tara da kwata ya dawo gida, lkcn Baban sa
ya riga ya fita.
Umman sa ta ji motsin bude dakin sa da ke
zaure.
Ta leko, don ganin wa ke taba kofar, Sai ta gan
shi.
Fuska yamutse ya ce,"Koro ni aka yi."
Ta ce,"Ka biya kudin mkrnt Naseer, me zai sa a
kore ka?"
Yayi dan shiru, ka fin ya ce,"Laifi na yi Umma.
Ta tsura masa ido, ta ce,"Haka dai, kullum kai ba
ka girma Naseer, balle ka yi wa kanka fada.
Laifin me ka yi kuma?Kai tsaye ya gaya mata
abinda ya faru.
Ta kame ha6a ta ce,"Tirk'ashi! Allah ya shirye ka.
Zaman gida ka fi so ko? To ai shi ke-nan, sai ka
yi ta zama ranka na maka dad'i." Ta juya ta shiga
cikin gida abin ta. Ya tura kofa ya shige d'aki, ya
watsar da littattafansa gefe, ya kwanta ringigine
bisa 'yar katifarsa yayi shiru, can ya ja d'an tsaki
ya ce,"Komai dai ni ne mai laifi, mutum ya raina
mana wayau, sai a k'yale shi?
Mts........."
Ya ci gaba da kuncin rai, wai kullum shine mai
laifi. Da yamma Baban sa ya dawo. Mairo ta
mayar masa da abinda ya faru. Yayi shiru bai iya
cewa komai ba. Suna zaune k'ofar gidan su
Sageer, shi din ke masa fad'a.
Naseer 6ata lokacin ka ka ke yi. Wallahi ina gaya
ma wannan maganar ka na ganin ihun banza
nake, ba za ka gane kuskuren ka ba, sai nan
gaba. Shi karatu ko na k'wana d'aya ya wuce ka,
ai an cuce ka, balle na sati 2. Amma fa sai ka
yarda."
Ya ce,"Me zai faru, idan ban yarda ba? Ya
amsa,"Me kuwa?" Kawai ina gaya ma gaskiya ne."
Ya nuna shi ya ce,"To ashe kai ne babban mai
6ata lokacin sa. Ni nan da ka ke gani, ba'a raina
min wayau. Gidan su Zarah za ni, za ka?"
Ya hahare shi ya ce,"Ban zuwa.." Kar ka je, sai
me?"Yayi banza da shi.
Ya mike ya wuce abin sa.
Sageer ya bi shi da kallo, ya kad'a kai ya ce,"Ina
tausaya ma Naseer.
Allah ya shirye ka." Shi kuwa gidan Zarah ya je
suka sha hira cikin gidansu da Innar ta gab da
kira magariba, sannan ya koma gida.
**************
Washe gari da safe 7:30, kamar yadda ya saba
fitowa yana tsaye gefen titin Kongo, wanda ta
mik'a har (W.T.C). Jar T.Shirt ce a jikin sa da
wandon Jeans. Nan ya saba jiran Zarah, don bata
kud'in tara.Zuwa can ta doso, kayan makaranar
nan sun sha guga, sai d'aukan ido suke yi tamkar
yadda ita kanta Zarah ke d'aukan hankalin
jama'a, sbd tsabar kyau da kullum take kara yi.
Kayataccen murmushi suke wa juna, sai da ta zo
gab da shi, ta ce,"Yayana, ban gane ba, ina
uniform?" Ya tura hannayen sa aljihu ya ce,"Ga
su nan a jiki na."
"Wai ba za ka makarantar bane ko yaya ne?"Ya
zura mata ido yadda take motsa bakin ta, yake
burge shi,"Huta na ke yau." Ta ce,"Wasa da
karatu Yaya na?" Gaskiya ni ma zuwa na bai da
amfani, mu je gida kawai ni ma in cire." Yayi
d'an murmushi ya ce,"Ki na so in yi miki bulala
kenan? Ita ma murmushi tayi,"Ka san Allah, sai
na had'a ka da Inna. Ya sanya mata ido, ya
kasa cewa komai." Ka na ta kallo na, magana na
ke."
Ya ce,"Yau fuskar ki tayi min kama da hasken
zara, sai na tuna ashe zarar ce."
Ta dan shagwa6e fuska,"Kai yayana, maganar
makarantar na ke. Ka koma gida ka sayo
uniform, ka wuce makaranta, idan ba ha ka ba
Inna za ta ji
" Ya ce,"Don Allah ki share."
"To me ya hana ka zuwa?"
Ya ce,"Hmm......laifi na yi."
"Wane irin?"
"Ke dai zo mu je in raka ki, na gaya miki a
hanya.
Suka wuce ya na labarta mata.
Ta dube shi,"Kai yayana, saboda Allah me yasa
haka?"
Ban kyauta ba ko?"
Ya tambaya. Ta ce,"Gaskiya ba ka kyauta ba,
don wanna 6ata Record ne. Don Allah kar ka
sake.
Ya numfasa ya ce,"An gama.Kuma sai da ki ka
fad'a na gane ban kyauta d'in ba.
"Tayi 'yar dariya, yana kallonta,"Yayana, kai
kullum ba ka sanin ka yi laifi, sai na fad'i?
Amma in na ce ka gyara, sai ya gagara."
Ya dan ja ya tsaya,"Me ki ka ce in gyara, ban
gyara ba?" Ita ma ta tsaya,"Da kana gyarawa,
yaushe za'a ba ka hutun dole? Yadda yayana ke
so na, ya kamata ace komai na ce, ta zauna.
Yanzu ni ka ga babu yadda za'ayi in tsallake
maganar ka."
Yayi murmushi, suka ci gaba da tafita, yana
tad'in,"Komai ki ka ce, ba na tsallakewa, ke ce
ba kya ganewa." Ta dube shi kamar yadda yake
kallon ta, ta ce,"Na sakar ma yayana." Suka yi ta
tafiya har kusa da mkrnt, sannan ya ja birki ya
ce,"To bari in bar ki anan, amma Zarah hak'uri
za tayi, yaya bai da kud'in (Break)."
Ta shagwa6e a gaban sa,"Ni a'a.
Allah ni na saba kashe kud'in yayana."
Ya d'aga lallausan gashin girar sa, bak'i wulik!
Yana kallon ta.
'Yar dariya yake yi mata.
Ita kuwa shagwa6ar ta take,"Allah ni ma zan
koma gida!"
Ya laluba aljihu, ya ciro Naira 20 ya mik'a mata.
Ta amshe tana fad'in,"Dama tsoka na ce?
Shi kenan ni ma ba zan rage maka abinda na ci
ba."
Ya ce,"Har kin isa. Ki na son bulala kena." Ta yi
murmushi ta ce,"To na gode, sai na dawo. "Ya
ce," A dawo lafiya." Ta juya ta shiga cikin 'yan
mkrnt, tana tafe tana waigen sa, shi kuwa yana
tsaye, ya kama tafiyar ta k'ule masa.Ya sauke
numfashi, ya juya ya dawo gida. Sati 2 suka
cika. Naseer zai koma makaranta. Malam
Balarabe ya ce bai san zancan bin sa
makarantar ba. Ran Naseer ya 6aci, ga shi yana
son komawa makarantar, don kar Zarah ta ce
shine bai son zuwa. Sageer ya samu a karo na
farko ya rok'e shi, su je ya rarrashi Baban sa
yayi hak'uri, su tafi makarnta gobe tare. Abin ya
ba Sageer mamaki k'warai, kuma yayi farin cikin
jin hakan.
Saboda haka babu 6ata lokaci, suka same shi da
daddare. Sageer yayi ta rok'o a madadin
Naseer. Malam Balarabe ya ce,"Sageer ni na
haifi Naseer, amma ko alama Naseer bai san
mutuncina ba, bai san mahimanci na a gare shi
ba.
Tun da abin nan ya faru, ban iya cewa da shi
k'ala ba, sbd takaici da 6acin rai, amma Naseer
bai san ya durk'usa gaba na ya ce Baba ka yi
hak'uri akan abin da na aikata ba. Sai yanzu ne
zai ce in zo muje makaranta? Me zan ma sa?
Bayan ba ni da amfani a gun sa? Sageer ya kara
duk'awa ya ce,"Baba ka yi hakuri, ka yafe
masa." Ya ce,"Naseer yaro ne?" Shekarunsa
goma sha takwas, yayi hankalin da zai san 6acin
ran iyayensa.
Babban kuskur ne a gare shi.
Amma shi komai yayi, sai ya d'auka dai-dai ne.
In banda tsageranci, menene na rufewa Malimin
ka k'ofa, don shi yana rufe ma ku? Ashe za ka
iya rufe min gida, duk ranar da na yi dare a
waje. Ka kiyayi duniya Naseer, ranar da za ta
koya ma hankali sai ka gwammace ba ka zo
cikinta ba."
Ya k'ara sunkuyar da kai ya ce,"Ka yi hak'uri
Baba, in Allah ya yarda ba za'a sake ba."Sageer
ya ce,"Baba, ka amince goben za ka d'in?" Ya
ce,"Ya zama dole, tunda ka sa baki Sageer, don
ka fi shi hankali, da ace yana koyi da kai, ai da
ba haka ba.
Ni dai bn ma sa mugun baki ba, iyakata da shi
add'ur Allah ya shirye shi. Amma daga yau in ya
sake d'ebo rigimarsa, ko alama ba ni a ciki. Kar
ma ku dunfaro ni. Ina fatan kun ji abinda na
ce,"Sageer ya ce,"Insha Allah."
Ya ce,"Allah ya kai mu goben.
Allah yayi maku albarka." Suka amsa da "Amin-
Amin."
**************
Washe gari Malam Balarabe ya maida Naseer
makaranta. A gaban (Principal) da sauran
Malami Naseer ya d'auki alk'awarin ba zai sake
sa6awa dokar makaranta ba.
Shugaban makaranta ya ce idan ya sake korarsa
za su yi, don fitinar sa ta ishe su.
Malam Balarabe yayi ta ban hak'uri, sannan aka
sallame su. Malam Balarabe yayi gida. Naseer
yayi aji. Akwai Malami a cikin ajin, don haka a
salihin sa ya shige. Sauran d'alibai na ta
bayyanar da farin cikin su bisa fuskokin su. Bai
kula kowa ba, ya wuce mazaunin sa, ya zauna a
d'aure.
Malam na bada baya, duk suka yanyame
shi"HUKUMA! HUKUMA!!" Ya dube su ya
ce,"Yawa ku ke, kowa ya zauna, in ba ku wani
labari." Suka zauna sauraron sa.
Ya mike ya zo gaban allo ya tsaya.
"Gata nan, gata nan ku!" Suka ce,"Ta zo mu ji
ta!" Ya ce,"Da Naseer ne da Englishi Master,
wata rana sun fita farauta, sai Naseer ya kafa
Malam, ya na da A B C D.
Englishi Master zai k'wace, dambe ya kaure.
Naseer ya kada Malam, ya na da A B C D a
gwafa, ya auna masa koda ya mike, sai ya rubta
wa Naseer SUSPENSION."Gaba d'aya suka d'au
dariya da tafi har da masu fito, ya ce,"A
saurara!
Sati 2 Naseer ya dawo, amma da sabon
alk'awari." Ya kame kamar soja, hannun sa ma
dama saitin kunne sa, ya ci gaba,"Na d'auki
alkawari ga makarantar kufena. Zan zama mai
ladabi da biyayya. Zan maida hankali ga
karatuna, zan tabbatar da ci gaban ta, idan ba
haka ba, kora ce!"
Ta yadda ya aje salon kalmar k'arshe KORA ce!
Shi yasa duk suka d'auki tafi,"Yayi! Yayi!! Allah
ya bar mana HUKUMA!" Ya ce,"Hukama na
ofishin principal, sbd haka kowa ya d'auki
wannan alkawarin, kar fushinta ya kama shi." Ya
d'auki alli ya rubuta bisa allo.,"Ya ce,"Wannan
shine Nationar Anthem d'inmu.
Suna ta hayaniya. Malamin Geography na tsaye
yana kallon su, sai dai suka gan shi tsulum! Ya
karasa shigowa.Da turanci yake magana,"Meke?"
Naseer ya ce,"Ba komai." Ya aje alli, ya wuce
wajen zaman sa.
Malam ya dubi allo ya karanta abinda Naseer ya
rubuta, ya dube su da kyau ya ce,"Wa ya
rubuta wannan?"
Baba wani 6oye-6oye Naseer ya d'aga hannu.
Ya ce,"Ya mik'e tsaye.
Tsaf!
Ya tashi fuska d'aure. "Menene wannan?" Ya
k'ara kirnewa, ya ce,"Sabon alk'awari ne, New
testament ba." Dariya ta kubce masa, yayi d'an
murmushi, ya ce,"Naseer ba ka ji ko?" Ya dan
duk'a ya ce,"Allah ya shi taimaki Malam!"
Suka d'auki dariya. Malam ya ce,"K'wana 2 ba
na ganin ka, ina ka je?" Ya amsa"Saudiyya."
Ya tsira masa ido, yana kad'a kai,"Hajji ko
umrah?"Ya ce,"Umrah." An dawo lafiya? Ina
tsaraba?" Ya nuna allo ya ce,"Ga ta nan kuwa."
Malam d'aurewa yayi ya ce,"To ka share." Ya
k'ara duk'awa ya ce,"Allah shi taimaki malamin
binciken yanayi."
Ya fito yana na tafawa, ya d'auki abin share allo
ya share."Malam an share." Ya ce,"Ka ci gaba da
tsayuwa anan." Ya dubi d'alibai ya d'aga gira ya
ce,"Soja kenan a fakaice." Nan ya ci gaba da
tsayuwa har darasi ya k'are , kuma hakan bai
hana shi abinda yake so ba, duk da cewa ya san
tsayuwar ma horo ce aka ba shi.
Naseer kam sai addu'a.
**************
Sannu a hankali. Malamai da iyayen Naseer
suna hak'uri da shi. Har ga shi gobe ake sa ran
za su fara rubuta jarabawar su ta karshe watau,
(WAEC). D'in su. Da yammacin wannan lahadin
ce. Naseer ya d'auki wankan sa yayi tsaf!
Cikin gogaggen yad'in sa ruwan madara yayi
kyau sosai, dan shi Naseer akwai son gayu, ga
kuma tsafta.
Zai yi wuya ka gan shi a yamutse. Kayan sa
kuwa duk inda zai nemo guga, sai ya nemo, sbd
babu yadda za'ayi ya sanya kaya ba guga. Ya
dan goge sandal d'insa bak'i, kai tsaye ya wuce
gangare gidan su Zarah. Bai nemi Sageer ba,
saboda ya san zai yi wuya ya fita yawo, saboda
karatun jarabawa.
Yana cusa kai cikin zaure, idanuwan sa suka
nuna masa wani abinda bai ta6a jin fad'uwar
gaba ba, sai akansa. Zarah ke tad'i da wani
saurayi, wanda ita ma a yau d'in nan suka
had'u da shi.
Sarai Naseer ya san saurayin a nan layin sarki
yake, sai dai ko gaisuwa bata ta 6a had'a su
ba.Nan take kishi ya lullube shi, mahaukacin
kishi kuwa, don sai da ya ji zuciyar sa ta kulle,
ta tattaro ta dawo iya wuya. Duk da cewar bai
ta6a furtawa Zarah kalmat so ba, illa iya ka
komai take so, shima shi yake so.
Tana ganin sa,tayi sauri ta rufe fuska da
hijabinta, har ya wuce cikin gida, bata bude ba,
haka kuma babu wanda ya tanka ma wani.
kujera ya ja tsakar gida, suka gaisa da Inna,
tana tsakar alayyahu. Ya jawo faranti yana
tayata."Amma gaba d'aya hankalin sa bai jikin
sa." Lafiya Naseer?" Ya ce,"Lafiya lau Inna, me
ki ka gani?" Ta ce,"Na ji ka yi shiru ne, ko anyi
fad'an da su Umma ne?" Ya kada kai,"Babu
komai wallahi." To duk tunanin jarabawar ce?"
Ya ce,"Jarabawa ai mun gama da ita. Insha
Allahu babu abinda zai gagara."
Ta ce,"Allah shi yarda Naseer, ai ba na haufi
akan dan nawa." Ya mika mata alaiyahun da ya
tara a hannunsa, ta karfa tana yankawa.
Zarah ta yi sallama ta shigo, suna hada ido, ta
rufe fuska da hannayen ta, ta fad'a daki. Ya
ce,"Ki fito kawai, yau bulala za ki sha." Inna ta
ce,"Yakamata, haka kawai ana zaune k'alau, za
ta fara jawo mana samari, wai shi nan auran ta
zai yi, ba yaudara ya zo yi ba."
Shi d'in ya fad'i haka?"
Inna ta ce,
"Eh,
ai sai da Babanku ya fita, ya tsare shi a zauren.
Zuciya ta k'ara shak'e shi, da kyar ya
amsa,"Inna Zarah ai yarinya ce, kuma karatu za
ta yi."
Ta ce,"Ni ma shi na gani, amma Malam ya ce
tunda da gaske yake, sai ta tsaida shi, tana
gama karatun, ayu da shi, idan Allah ya
nufa.'Kyar yake kallon Inna. Zarah ce ta d'auke
masa hankali da ta fito, tana fad'in,"Yaya na ina
wuni?" Ya maka mata harara. Tayi murmushi, ta
zauna kusa da shi,"Me na yi yayana?
Wannan harara ta bata min fuskar ka, dan yi
murmushi mana, haba Big Bros." Ya dubi Inna
fuska daure, "Kin ji yadda yarinyar nan ta raina
ni ko?" Ta ce,"Kai ka kyale ta." Ta d'auke
alayyahunta ta shige kicin. Shi
kuwa hararar Zara ya ci gaba da yi.
Ta sanyaya murya, ta ce,"Ba ka ga yadda ka yi
ba, me yasa?" Ya ce,"Karatu za ki yi, ko tara
samari?" Ta ce,"Salis ne kawai yayana, don Allah
ka yi hak'uri." Ya ce,
"Zarah! Zarah!! Zarah!!!
Ta amsa."
"Na'am."
Sau nawa na kira ki?" Ta ce,"Ina jin sau 3 ne."
Ya k'ara dubanta," Ki na ma ji ne?"
To shi ke nan." Ki saurare ni."
Ya mik'e yana fad'in."Inna na wuce!"
Ta lek'o ta ce,"To Naseer, agaida su Ummah."
Yayi waje. Zarah na bin sa."Yayana, me zan
saurara na ce?" Ya juyo cikin zaure, ya ce,"Ai ba
ki tabbatar da ko sau nawa na kira ki ba, it
means hankalinki ba a waje na yake ba. Saboda
haka ni zan yi wa tufka hanci, don hankalinki ya
tsaya waje 1."
Ya sa kai ya fice ya bar ta cikin duhu. Yana ji
tana kiran sa, amma kishin daya mak'ure masa
wuya, ya hana shi amsawa.
Bayan sallar isha'i, gidan su Sageer ya nufa. Ya
yaye labulen dakin ya shiga. Kwanon abinci
Sageer d'in, ya bude zai fara ci." Me ka ke yi?"
Ya ce,"Abinci zan ci, zo mu ci mana." Ya ce,"Don
Allah ka rufe abincin nan, ka taso ka raka ni nan
layin sarki." To ka za mu ci abinci mana!"
Kar in rasa wanda zan je nema ne.
Don Allah ta so mu je." Sageer ya rufe abinci, ya
sanyo takalaman sa, ya rufe dakin sa, suka
wuce layin sarki, ba tare da ya san me za su je
yi ba.Kawai Naseer ya ce,"Wani zan je gani."
Suna zauna da abokan sa 2, labarin yarinya
Zarah yake ba su, lokacin da Naseer suka iso
tare da sallamar har da Musabaha, kamar abin
arziki. Naseer ya dube shi ya ce,"Ah! Kai ne
Salees ko?"
Ya ce,"Eh ni ne, lafiya?" Ya ce,"Ita ta kawo
hakan. Na san ba sanni ba, amma watak'ila da,
da rana na zo, da ka gane ni. Well kar mu je da
nisa, kawai gargadin ka na zo yi akan yarinyar
nan Zarah. Ban som in k'ara ganin 'yar k'afan
ka a gidan su. In kunne ya ji........"
Ya juya zai wuce. Salis ya dafo k'afarsa ya
ce,"Dakata mana. Kalle ni, idan ka na takama
kai dan Tudun wada ne, ni ma kazalika haifaffen
Tudun Wada ne, saboda haka karan daji bai isa
ya budewa karan gida ido ba."
Naseer yayi dan murmushi ya ce,"Allah ko?" To
lulaba da kyau ka ji, wannan ba kare ba ne,
kura ce, don uban kare karyar sa."
Sageer ya rik'o shi yana fad'in." Naseer! Dama
rakiyar da ka ce in zo yi kenan, Meye haka?"
Abokan Salis ma suka taso." Me ye haka ku ke
yi? Don Allah ku bari, yawa ne. Zaarah sai
wanda ta za6a, sbd ha..........."
Wani wawan mari Naseer ya tsinkawa, mai
maganar. Shi yasa yayi gum da bak'in sa. Salis
na ganin haka, shi ma ya ware. Sageer ya kamo
Naseer ya ce,"Naseer, kada ka kuskara ka dauko
wannan fitinar! Ka ga k'ofar gidansu ka zo, duk
inda aka je, kai ne mai laifi!
Ya ce,"Da shi na ke magana, daya sanya min
baki?" Yana rufe da baki, ya ji saukan naushi.
Cikin zafin nama Naseer yayi kukan kura, ji ka
ke yi dim! Ya sakarwa Salis naushi a mukamuki.
Nan take kamar almara. Salis ya fad'i a sume.
Abokan Salis suka rude. Sageer ma ya firgice, ya
rinka jan Naseer, yana fad'in,"Ka gani ko?" Ka
ga irin ta ko?"
Su kuwa abokan Salis cikin gida suka shige,
neman taimakon jama'a."Ka zo mu tafi Naseer!"
Yana jan sa, yana tirjewa,,"Babu inda za ni!" Ka
kyale ni. Duk abinda suka ga dama su yi!"
Ya ce,"Haba Naseer! Me yasa kai zuciyarka bata
kulla maka alkhairi ne? Dubi fa abinda ka aikta?
Ka na zaton iyayensa za su kyale ka ne? Wallahi
da na san abinda za ka zo ka yi aikata kenan.
Sam da ban biyo ka ba, ba za ka ja min masifa
ba wallahi! Ya dube shi da kyau, ya ce,"Sageer!
Bi tannan, in bi ta can, idan ka kuskura muka
had'u, sai na fasa maka baki!
Yana sa aya ya wuce, ya bi ta inda ya nuna,
suna jin abokan Salis na fad'in Ga shi can zai
gudu!
Sageer ya shafa a guje, ya tsere. Shi kuwa
Naseer ja ya yi, ya tsaya har gayyar jama'ar
suka zo gunsa.Me yayi maka, za ka kashe shi?"
Ya ce,"Ku zuba masa ruwa, ya farfad'o, sai yaga
maku."
Samari suka yi caa! Za su rufe shi da duka,
mahaifin Salis ya hana, don tuni ya tura daya
daga cikin abokan Salis din ofishin 'Yan sanda.
Ana ta kwaranniya, ga Salis a kwance shame-
shame. "Yan sanda 2 suka iso, nan take suka
wuce da Naseer da laifin yunk'urin kisan Kai,
kamar yadda aka shaida ma su. Salis dai sai da
ya hau gadon asibiti a daren nan, sannan ya
farfado.
Wuyan sa a kage, bai iya juyawa ta gefen da
Naseer ya naushe shi.
Kai tsaye gidan su Naseer, Sageer ya nufa. Yana
ta hak'i, kamar ran sa zai fita.
Malam Balarabe da Mairo, suka firgice.
"Menene Sageer?" Ya ce,"Ba lafiya Baba, ina
zaune Naseer ya ce in zo in raka shi layin sarki.
Ashe fad'a za shi yi. Wallahi Baba ban sani ba, a
takaice dai ya naushe masu yaro ya fad'i, suma
yayi mutuwa yayi? Allah kad'ai ya sani, ya zo
ma mu gudu, ya ki. Can na baro shi, ban san
halin da ake ciki ba!"
Mairo salati da d'auka, shi kuwa Malam
Balarabe cewa yayi,"To ba shi kenan ba, ka
koma gida abinka, ka yi kwanciyar ka.
Tsuntsun daya ja ruwa, shi ruwa zai yi wa
banzan duka.
Idan sun so ma, kar su bar shi da rai, babu
abinda zai dame ni."
"Baba...." Ya katse shi,"Babu ruwanka na ce! Ka
wuce gida abin ka, idan kuma kai ma can d'in
za ka sake komawa, to Bismillah!
Amma ni Balarabe ba ni a cikin wannan
maganar." Tuni Umma ke tsiyayar
hawaye,"Sageer mu je, ina ne, suke fad'an?" Ya
ce," A layin sarki ne." Malam ya ce,"K'ofar zaure
ban ba ki izinin takawa ba.
Yauwa." Ya sa kai, ya koma d'aki. Umma ta
koma bisa tabarma, ta tallabe kai ta
ce,"Wannan yaro, wannan yaro. Allah ka shirye
shi.Sageer ya tsuganna ya ce,"Umma ki yi
hak'uri, ki daina zubda masa hawaye." Ta dube
shi cike da damuwa ta ce,"Bari fad'i Sageer, ya
zama dole in yi hawaye, don bansan masifar da
Naseer ya jaji6o mana ba wannan karon. Me ya
had'a su da yaro?" Ya ce,"Ni ban san
takamaiman zancen ba, amma na ji wai yana
masa gargad'i akan Zarah."
Ta ce,"Zarah? To shi me ya dame shi da
saurayin Zarah? Auranta zai yi?"
Ya amsa,"Bai ta6a yi min magana a kanta ba,
sai dai bn san abinda ke cikin ran sa ba a game
da ita." Ta sauke numfashi ta ce,"Dubi wannan
abin kunya, akan budurwa, ya je yana haukan
banza, idan ya kashe d'an mutane, ya yake son
mu yi da ran mu? Yanzu kai Sageer ka yi
hak'uri, ka koma ka bincika mana halin da ake
ciki ka ji?"
Ya ce,"Ya zama dole Umma, bari in tafi. Allah
shi kyauta."
Ta ce,"Aamin."
Ya mike ya fice.
Nan ta ci gaba da zama a kunci, tana mai
tsananin al'ajabin halayen Naseer, kamar ba su
suka haife shi ba, don ko 1 bauko halayyar su
ba. Ta nisa face,"Kuda, ya haifi zuma.
Allah ka shirya mana!
Tsaye Sageer yake a cikin jama'ar da suka taru,
suna ta maida labarin fad'an da aka yi karya da
gaskiya.
A nan yake jin Naseer na hannun "Yan sanda a
anan caji ofis da ke kusa da su.
Jikinsa na rawa, ya bazama ofishin. Cike yake
daga waje, daga ciki kuwa abokan Salis suke ta
bada bayanan yadda abin da ya faru
(Statement).
Shi kuwa Naseer yana tu6e, a bayan kanta. Yana
isowa, mai magana lkcn ya ce,"Yauwa ga shi
nan, tare suka zo, amma shi raba su yake yi,
yana ta jan sa, ya k'i tafiya.Sai da ya sumar da
shi." Dan sanda ya ce, wa Sageer shi ma ya
fad'in abinda ya sani.
Tiryan-tiryan ya maida wancan, dan sanda ya
ce, ya dubi mahaifin Salis ya ce,"Duk mun ji
bayanin kowa, kuma hakan ya tabbatar mana
Naseer na da laifi dumu-dumu, saboda haka za
mu tsare shi a
a nan a bisa laifin tada husuma, har zuwa lkcn
da Salis zai sami sauki.
Sajent!"ya amsa,"Sir!" A wuce da Naseer cikin
Cell."Sageer ya d'ora hannu a ka yana
fad'in,"Inna-lillahi-"Wa-Inna-ilaihir raji'un!"
Insfesta ka yi hkr, ka ba ni shi beli. Gobe za mu
fara (Exams), ka ga za ta wuce shi."
Dan sanda ya gyara fuska, ya ce,"Ya san da
jarabawar, ya je neman fad'a? Bata dame shi
bane, da ta dame shi, karatu yakamata ya
zauna yayi, ba fad'a akan budurwa ba. Saboda
haka babu, har sai Salis ya bar asibiti. Kuma
gaba d'aya abinda aka kashe a asibitin, za'a
kawo (Bill) nan, shine zai biya. Na gama da ku."
Sageer ya na ji, yana gani, aka wuce da Naseer
ko gezau bai nuna a fuskar sa ba.
Har goma da rabi na dare. Sageer na aikin
rok'on a ba shi Naseer akan beli, amma dan
sandan nan ya k'i, anan iyayen Salis suka bar
shi, kuma da gani akwai wata 'yar muna-muna
tsakanin insfesta da iyayen Salis.Sha d'ayan
dare, ya bar wajen ya koma gidan su Naseer,
har sun kulle k'ofar gida, ya buga. Malam
Balarabe ya bud'e, ya shigo ya kwashe kaf!
Halin da ake ciki ya fad'i. Malam ya balbale shi
da fad'a,"Me yasa ka ke wahalar da kanka akan
wanda bai san ciwon kan sa ba? Shin ba cewa
nayi ka tafi gida abinka ba? Yanzu k'arfe nawa
ne?" 11 ta wuce, kai ma so ka ke ka 6ata wa
naka iyayen rai ko?
Ya karkad'a kai."To maza ka wuce gida, da safe
kuma ka shirya ka tafi jarabawar ka, kar ka
saurare shi!
Maza sai da safe."
Ya juya ya tafi, ran sa in yayi dubu toh ya 6aci.
Abu 1 yake wa Naseer bak'in ciki, gobe ba zai
samu zana jarabawa ba.
Washe gari karfe 7:30 Zarah ke k'arasowa bakin
titi, sai dai yau babu yayanta a wajen, kamar
yadda kullum safiya shine mutum na 3 da ke
faranta mata rai, daga iyayenta, sai shi.
Don haka ta tsaya shiru cike da mamakin me ya
hana yayanta zuwa yau? Ta kusan minti 5r a
tsaye, sannan ta wuce jikinta duk ya mutu.
Kuma ko alama zuciyarta bata cikin sukuni har
na rashin ganin Salis jiya da daddare, kamar
yadda yayi mata alk'awari.
Ta fe take tana zancan zucci fad'i take,"Ina ka
ke yayana?" Zarah." Ta ji an k'wala mata kira.
Ta waiga gefen da aka kirata, firgici. Bak'in get
din ofishin "Yan sanda ta hango Sageer tsaye da
kayan makaranta.
Da sauri ta tsallako. Hankali tashe, ta
tambaya,"Ina yayana ne?" Ban gan shi ba yau."
Cike da damuwa ya amsa,"Ai yayan nan naki,
sai a hankali.
Yana nan ciki."
Ta k'ara ware ido ta-ce,"Ban gane yana nan
ba?"
(Police Station)Na ga ka nuna!
Ya ce,"Eh mana.." Hankalinta ya k'ara tashi,"Wa
ya kawomin shi?" Bata jira ya bata amsa ba, ta
wuce, ya biyo ta, yana fad'in,"Wallahi tsautsayi
kawai, jiya ya je wajen wani wai shi Salis, suka
fara gardama akan ki, sai fad'a. Kin san halin
yayan naki, k'ashi daya ke gare shi, yana dukan
sa, ya fad'i a sume."
Tun da yake magana, ta rage sauri. Yana sa
aya, ta juyo ido cike da kwalla ta ce,"Shi da Salis
suka yi dambe? To saboda me?"
"Oho!
Amma a kan ki ne Zarah. Naseer bai son Salis
na zuwa gun ki, gargad'in da na ji yana masa
kenan.
Abin ya kai su ga dambe."
Ta tsura masa idanuwanta da suka cika tam!
Da hawaye, ta ce," Za'a bar ni in gan shi?"
Ya amsa,"Ban sani ba. Ni ma yanzu na kawo
masa abinci, mu je mu gani.
Suka shige cike, da k'yar aka sake yarda su gan
shi,don bai jima da komawa ba. Ana fito da shi,
suka yi ido 4 da Zarah, sai ya juya, ya koma ciki
da saurinsa. Kamar za ta burma ciki, ta bi shi,
kira take,"Yayana! Yayana ka zo mana, in gan
ka!" Dan sanda ya ce,"Yan mata, ihunki fa yayi
yawa wajen nan. Hala saboda ke aka yi fad'an?"
Bata iya cewa da shi komai ba. Sageer ke jawo
ta waje. Zarah, ki yi hak'uri ki tafi makaranta, ni
ma yanzu zan wuce."Insha Allahu na san zuwa
anjima, za'a bada belinsa.
Yi hak'uri."
Tayi tsaye tana share k'walla." Zo mu je." Suka
fito bakin titi. Sageer ya tare mai mashin, ya
yana fad'in,"Ki wuce Zarah, kin ga lokaci yana
kurewa." Ta ce,"Zan ta fi." Mai mashin ya ja,
suka tafi. Yana waigen ta, yana nuna mata
alama da hannu ta wuce, har suka yi nisa.
Tsaye kawai take kikam! Ta rasa na yi.
Tunanin ta, me ya kai Naseer fad'a da Salis?Nan
take ta samo amsar. Wani ni'imamman farin ciki
ya lallube ta.
In banda abin yayana, ai sai ya gaya min kai
tsaye, menene na fad'a da Salis? K'walla suka
cika idanuwanta, tana kallon ofinshin "Yan
sanda,"Ba zan iya zama cikin aji ba, kai kuma ka
na tsare a nan yayana. Ta goge kwalla ta
kwashe sauri sauri sai gida.
Babu ko sallama, ta fito dakin. "Ke! Lafiya?"
Innar ta, ta tambaya, kuka ta fasa,"Inna 'Yan
sanda sun kama yayana! Ta dafe kirji a firgice ta
ce,"Me yayi?" Bakinta na rawa, ta mayar da
abinda ya faru. Inna ta d'auki salati, kan ta ya
d'aure"To ki yi shiru, bari Baban ki ya fito
wanka. Kai yara babu hankali, koma dai menene
cikin zuciyarsa, ai sai yayi hakuri, menene abin
fad'a?."
Shigowar Malam Umar yasa tayi shiru,."Me ya
faru? Inna ta amsa,"Naseer ke hannu 'Yan
sanda. Wai jiya sun yi fad'a da yaron nan daya
zo gun Zarah jiya, har sumar da shi." Ya ce,"To
saboda me?"
"Oho!"
Yayi dan tsaki ya ce,"Yara ba sa jin magana,
menene abin fada anan? Ko shi ma sonki yake
yi?"
Ta sunkuyar da kai ta ce,"Nima ban sani ba."ya
ja tsaki. Inna ta ce,"Idan ma sonta yake, me zai
kai shi, fada in banda abin Naseer. Shi ma ya
san babu yadda za'ayi mu hana shi, mu ba Salis
in har ya furta.
Allah shi kyauta.
Yanzu yaya za'ayi Malam?" Ya ce,"Bari in shirya,
in je in ga Baban na sa, sai a san abin yi.
Ke kuma ga shi kin makara.
Ki bata sauran 20 din nan, maza ta je ta hau
mashin ya kai ta.
Ya fice daga dakin. Inna ta dauko 20 din ta
bata,"Tana bayan mashin hankalin ta na ofishin
'Yan sanda.
Haka suka wuce tana kallon wajen har suka
k'ule.
Malam Umar ke wa su Malam Balarabe sallama
a k'ofar gida. Tare da Mallam Lawal mahaifin
Sageer.
Bayan sun yi Musabaha, sun gaisa sai ya
ce,"Magana na ji babu dadi, shine bari in zo in ji
yadda aka yi?"
Malam Lawal ya ce,"Zaman nan da ka ganmu
nan, rarrashi kawai na ke yi.
Malam Balarabe ya ce babu ruwan sa a ciki.
Sannan baban tashin hankali, na je ofishin, don
in yi belin sa." Yan sandan, suke gaya min
iyayen wancan yaron, sun ce kara za su kai
kotu, wai da wuk'a ya zo, yana neman kashe
shi."
Da wuk'a?
Ya ce,"Sharri ne kawai, don Sageer ya gaya min
tare suka je, kuma babu komai a hannu Naseer.
Dukan sa kawai yayi, ya suma. Shi kuwa Naseer
tun yana yaro haka Allah yayi shi da karfin
tsiya.
Malam Umar ya kada kai cike da damuwa,
"Wannan al'amarin bai yi dadi ba. Su kuma bai
kamata su yi haka ba. Menene amfanin yin
sharrin?" Malam Balarabe ya amshe,"Laifin su
ku ka gani? Karan banin da ya kai shi,ya ta6a
masu yaro. Shi zai fidda shi. Saboda haka kar ku
wahalar da kan ku, ku kyale shi, su koya masa
hankali."
Malam Umar ya ce,"Ba kuwa za'a kyale shi ba."
To wallahi babu hannuna acikin, kun ji kuma na
rantse.." Ya ce,"Shi kenan Malam Balabare,
amma ina tabbatar maka, bai kamata ka yi
saurin rantsuwa ba. Tunda abin ya zama haka,
mu sai mu je ko?
Ya fad'i yana kallon Malam Lawal, duk dacewar
ba su taba sanin juna ba, sai yau.
Ya ce,"Taso kawai mu tafi." Rai 6ace suka bar
wajen, tamkar yadda ran Malam Balarabe ke
bace.
Ya jima a zaune, yana tunani da tambayar kan
san "Yaushe Naseer zai daina bata min rai?"Ya
ce,"Taso kawai mu tafi." Rai bace suka bar
wajen tamkar yadda ran Malam Balarabe ke
bace. Ya jima a zaune, yana tunani da tambayar
kan san."Yaushe Naseer zai daina bata min rai?"
Ya kada kai ya ce,"Allah ka shirya min." Ya
mike, ya shiga gida, ya mayar wa Umma zancan
kai Naseer kotu inji iyayen Salis.
Idanuwanta suka kada, cike da tashin hankali ta
ce,"Wannan sharri ne, na san Naseer bai jin
magana, amma bai ta6a daukan makami ya hari
wani da shi ba.
Gaskiya Malam bai kamata ka tsame hannunka
daga maganar ba."
A fusace ya ce,"To ai sai ki dauka ki maida min.
Ya ja tsaki, ya bar gidan, ya wuce kasuwa. Ya
bar Mairon, kamar ta aza hannu bisa kai tayi
kuka.
Duk iya kokarin da su Malam Umar suka yi, don
ganin su kwantar wa iyayen Salis hankali, don
su janye kudirin su, sam sun ki sauraron su, shi
mahaifin sa ma ya ki yarda su gan shi ido da
ido.
Abokan Salis din ke gaya masu, an ma riga an
shigar da kara.
Takarda kawai suke jira a aiko ofishin 'Yan
sanda...........
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp
08168575100
Ajininsa yake 1-03
Posted by ANaM Dorayi on 11:44 AM, 04-Nov-15
Under: Ajininsa yake
___ NA ZULAIHAT SANI KAGARA___________
Al'amarin bai masu dadi ba ko alama.
Karfe 11:30 duk suka koma gida. Inna na zaune,
duk tunani ya addabe ta.
Malam Umar ya shigo. Yadda ta lura ran sa a
6ace yake, yasa nan da nan ta gane ba ayi
nasara ba.
Hannu ta a kunci, ta ce,"Ya dai Malam?"
Ya jinjina kai ya ce,"Ai komai ya kwa6e A'i.
Iyayen Salis sun kai shi kotu."
Kotu?"
Me yayi zafi? Shi Salis din rauni yayi sosai?"
Ya ce,"Ko alama, duk da dai ban gan shi ba,
amma an ce ya bar asibitin.
Abin ma dasharri ya zama, wai dawuka ya je
kashe shi......."
Da sauri ta katse shi,"Wannan karya ne. Naseer
bai daukan makami, bar shi dai da saurin duka
ga karfi." Ya ce,"Babban abin tashin hankali ma,
shi Malam Balarabe ya ce, ba ruwan sa ciki.
Saboda haka al'amarin sai addu'a
. Mu jirar ranar da za'a shiga kotu.
Ni takaici na yaron nan jarabawa suke yi.
Mts!"
Yayi tsaki, ya kardada kai.Ta ce,"To yaya zai yi?
Ba dole yayi hkr ba. An san abin akwai 6acin rai.
Allah shi kyauta."
2:15 Zarah ta shigo gida a dokan ce, duk a zaton
za ta ji an ce yayanta ya baro ofishin 'Yan sanda,
sai ma ta ji wani labari sabo. Ta ha de kai da
guiwa, hawaye na ambaliya.Inna ta ce,"Hak'uri
za ki yi Zarah, haka Allah yaso, fatan mu kawai
Allah ya takaita abin. Tashi ki zubo abinci ki ci."
Ta girgiza kai,"Ba zan iya ba Inna. Ya za'ayi wa
yayana sharri, wanna ai zalunci ne."
To ya za'ayi? Tun da ya riga ya bi shi, har gidan
su ya ta6a shi, ai bai da mafita, sai dai Allah.
Allah ya isa.
Wallahi!
Kuma Salis din zai zo ya same ni!"
Ta tashi fu......... ta wuce.
Daki ta nufa ta kifa bisa gado, tana murzar ido
hawayenta bai yanke ba.
***************
Bayan sallar La'asar. Inna ta gama shirinta tsaf!
Ta tsaya kan Zarah da ke zaune bisa sallaya,
tunda ta idar da sallar, "Tunda nayi-nayi da ki
tashi ki tafi Islamiyya, kin ki motsi, ni zan tafi
layin Labadiya in yi wa Umman Naseer jaje. Sai ki
kula da gidan, ga miya can na dora, idan kuma
kin ga dama abincin na ki yana nan a kicin din."
Ta sa kai ta fice, ba tare da Zarah ta ce, wani
abu ba. Minti 10 bayan tafiyar Inna sai yaro yayi
sallama, ya shigo ya ce ana kiran Zarah inji Salis.
Da ita yaron ke magana, don haka ta ce,"Ka ce
tana zuwa."
Ta mike da hijabin da tayi sallah ta fito.
Salis na cikin zaure ya sha wankan la'asar, yayi
adon shadda bulu.
Fara'a kawai yake yi, ita kuwa jikin bango ta ra6e,
fuska daure. Ya dan matso yana fadin "Yan
matan da ta dace da sunanta, ya sanyin
la'asar????Ta dirka masa harara. Ya ce,"Wai!
Me ya faru?"
Ta gyara tsayuwa cikin fada ta ce,"Salis kar ka
sake zuwa guna!
Ban da lokacinka, ban da lkcn mai lakacin ka!
Saboda haka ka fita harka ta kawai, idan ka na
son kanka da arziki!"
Ta juya za ta wuce, da sauri ya ce,"Me ya faru
Zarah? Ke da ake neman kashe ni, saboda son da
na ke miki? Labarin da na zo in ba ki kenan, ya
za ki min haka?" Ta juyo ta nuna shi,
"Sharrin da ku ka k'ulla masa a kanka zai kare!
Kuma da yardan Allah, sai ya fito, ba zai mutu a
hannun Alk'ali ba!"ta shige gida, ta bar shi sototo
cikin duhu,"Me yarinyar nan take nufi? Ta san
fadan da muka yi kenan?
O.K, shi ma take goya wa baya, ba ni ba.
Shi ta fi so kenan?" Ya huta, ya ce a fili,"Zan yi
maganin sa kuwa.
Kuma ba zan daina son ki ba."
Ya fita, ya bar gidan ran sa 6ace."
Haka Zarah ke cikin kunci, har zuwa dare babu
abinda ta iya kaiwa bakinta.
Sallamar Sageer, ita suke amsawa yanzu. Ya shigo
duk suna tsakar gida zaune, ya tsugunna, ya
gaida su Inna.
Sannan suka gaisa da Zarah." Sai na dawo na ji
sabon labari.
Wallahi-wallahi Baba karya suke yi. Naseer bai je
da komai ba a jikinsa."Ya ce,"To yau muke tare
da Naseer? Duk iya kiriniyar sa na sani. Kawai
sun san yana jarabawa ne, shi yasa suka ja
maganar, don ya rasa. Sun kuwa yi a kansu. Idan
kuma har son Zarah yake yi, ni na ba shi ita
duniya da lahira. Za ta jira shi har ya sami
madafa.
Ba shi kenan ba? Na ga wani dan kusun uwar da
zai sake zuwa min k'ofar gida."
Ba k'aramin farin ciki ya ratsa zuciyar Zarah ba.
Suka kalli juna da Sageer, yayi mata murmushi,
ta yi sauri ta rufe fuska.
Yayin da Inna ke fad'in,"Ka gama magana
Malam. Allah yasa rabon sa ce."
Sageer ya ce,"Amin.
Ni zan wuce (Police Station) din, in gan shi."
Zarah ta mike,"Baba ni ma in je?"
Me za ki yi a can Zarah? ki yi zaman ki kawai,
wurin nan ba wajen zuwanki ba ne."Ta
marairace,"Zan gaishe shi ne Baba,
kuma......kuma........"
Kuma me?"
Inna ta tambaya.
Ta kwanto jikinta, ta 6oye fuska. Babanta ya
ce,"Ba fa za ki ba. Ki ba Sageer sak'on ko
menene a kai ma sa." Haushi ya kama ta, ta
tashi ta shige daki. Sageer yayi masu sallama, ya
fita.
Yana tsaye gaban kanta aka fito da Naseer. Da ka
kalli fuskar sa, za ka san ya fad'a, saboda bai
saba da wajen ba, ga k'yamar k'azantar da ke
wajen, shi yasa bai iya cin abinci sosai. "Ya aka
yi?" Ya ce wa Sageer.
Ya amsa, "Lafiya lau. Daga gidan su Zarah na ke
duk suna gaishe ka.
Zarah ma ta so biyo ni.
Babanta ya hana.
Ni da abinda na ke son in gaya ma ka, ko an je
kotun nan, kar ka amsa laifin da ba ka yi ba."
Ko na amsa, menene?
Sun dade ba su min sharri ba." Ya ce,"To wai kai
son Zarah ka ke, ko menene dalilin yin haka?"
Ya juya lafiyayyun idanuwan sa, ya amsa,"Me ka
fahinta?" Ya dan kada kai,"Naseer manya.
In kasan haka ne, sai ka gaya mata kawai,
menene na 6oye-6oye?"
Ya ce,"Ai Zarah yarinya ce, bai kamata in kasa
mata hankali ba.
Ina sa uniforma, tana sa uniform, sai ince ina son
ta?
Da sunan me?
Don kowa ya san ban isa aure ba.
Da fa hankalina sarai. Su Baba ne suke ganin
banda shi."
Yayi d'an murmushi, ya ce,"To ai duk ta kare,
tunda sun gano ka.
Har Babanta ya ce,"In har son ta ka ke. Wallahi
ya baka ita."
Yayi jim!
Yana masa duban mamaki, Ni zaka zolaya?" Nace
wallahi, ka ce zolaya? Maganar da aka yi ta yanzu
a gaba na.
Zarah ma na zaune.
Yayi 'yar dariya, kafin,"Yaya Zarah ta yi?" Tsaf!
Fuskar ta, ta nuna min kai take so.
Ai kun shak'u da Zarah Naseer, dole mata so ka.
Ba ka ga yadda take rawar jiki, ta zo nan ba, aka
hana ta.
Tun jiya hankalin ta yake tashe."Ya lumshe ido,
shiru yana tunanin zucci, kafin ya bude. Dan
sandan da ke tsaye ya ce,"Lokaci yayi." Ya bude
ido sosai,"Ka ce mata, kar ta damu, lafiyar ta
lau, komai zai wuce Insha-Allahu." Dan sandan ya
ce,"Mu je ciki Yalla6ai."Naseer ya dube shi a
dage, ya ce,"Kai ne yalla6ai, ranka ya dad'e yace
Sageer.
Sai da Safe."
Can a mak'oshin ya amsa, don har cikin ran sa
yana bakin cikin ganin Naseer a wannan wurin.
Ya fito ya nufi ciki da tunani. Karatu kawai yake
yi, amma zuciyarsa na cike da tausayi Naseer,
ganin har za'ayi jarabawa 4.
Shi Naseer bai sami ko daya ba, abin ya dame shi
kwarai, don bai da abin yi ne kawai.
******************
Abin kamar wasa, sai da Naseer ya kwashe
kwanaki 3 ofinshin "Yan sanda, sannan takardar
sammacinsa ta zo. Ranar juma'a aka fara
sauraron shari'ar. Malam Balarabe dai babu
ruwan sa, don haka bai ma je kotun ba, su M.
Umar ne da mahaifin Sageer su ka je.
Sageer kuwa yana makaranta, amma gaba daya
hankali sa bai jikinsa. Balle kuma Zarah, wacce ta
fi kowa kunci na ta na tsare.
Tayi iya kar k'ok'arin ta, don ganin ta jure zaman
ta cikin makaranta kamar yadda Babanta ya
tilasta mata tafiya.
Amma sam ta kasa.
Bata fahimtar komai, kwance take kawai bisa
tebur, zuciyar ta na zugin tunanin wane hukunci
za'a yanke wa yayanta?
Saboda Salis ya sha alwashin sai ya sa an d'aure
Naseer, dalilin juya masa baya da Zarah tayi tashi
guda.
Naseer tsaye gaban Alkali, babu fargaba ko
shakkar wani abu, yana saurare aka gabatar da
k'arar sa, tare da laifin da ake tuhumar sa. Alkali
ya tambaye shi,"Ka ji laifin da ake tuhumar ka?"
Ya ce,"Ran ka ya dade, na ji."
Ya ce,"To ka amince da hakan, ko ka na da abin
cewa?"
Naseer ya amsa."
Ban amince ba, ni ban ta6a fad'a da makami ba.
Kawai dukan sa na yi, ya suma."Wani Lauya da
ke zaune tuntuni, cikin rukunin lauyoyin da ke
zaune, yayi fit!
Ya mik'e tsaye ya ce,
"My Lord,
Sunana Barista Usman, ni ne Lauyan mai kare
wanda yake k'ara, watau Salis.
Ina da 'yan tambayoyin da na ke son yi wa
Naseer."
Alkali ya ba shi umurni.
Nan take, yayin da su Malam Umar da M.Lawal
suke cike da fargabar wannan shari'a, gain har
lauya su Salis suka d'auka.
Lauya ya matsa kusa da Naseer, suka k'arewa
juna kallo, sannan ya ce,
"Ranar lahadi daya ga watan nan da muke ciki,
da daddare ka je k'ofar gidan su Salis, ko zan san
abinda ya kai ka can?"
Naseer ya amsa,"Gargad'i na je yi masa, akan
k'anwata Zarah, don ba na son ya rinka zuwa
gunta." Ya ce,"Wane irin gargadi ne da za ka bi
mu2m har k'ofar gidan sa, ka rufe shi da duka.
Sai da ya daina numfashi, sannan ka yi k'ok'arin
da6a masa Wuk'ar da ke jikinka?"
Hankalin Naseer ya k'ara tashi, idanuwan sa suka
kad'a jajur!
A fusace yake magana,"Ba haka bane!
Tare da aboki na Sageer muka je, na yi masa
gargadi da baki, na ce kar ya sake zuwa wajen
Zarah.
Shi ya fara kai min duka, duka 1 na yi masa, ya
fad'i sumamme.
Abokan sa 2 na wajen, kuma suna gani!
Lauya yayi d'an murmushi ya ce,"Malam Naseer.
Lokacin da ka yi wa Salis lilis!
Har ya suma ka yi iya k'ok'arin ka, don ganin ka
dank'arawa Salis wuk'a.
Amma ba ka sami nasara ba, sbd abokan sa da
suka fi k'arfin ka.
An kira 'Yan sanda sun zo wajen, har suka tafi da
kai ofishin su.
Amma abin mmk, babu wuk'ar nan a tattare da
kai.
Ko za ka gayawa kotu inda ka 6oye ta?"
Ya k'ura Lauya ido, kamar shi ma ya sumar da
shi yake ji, ya jima kafin ya ce,"Had'iye ta na yi."
'Yan kallo na ta dariya.
Alkali ya ce kowa ya natsu.
Sannan ya ce,"Nan a kota ka ke Naseer, ka kula
da harshenka."
Barista Usman ya gyara zaman kot d'insa, ya
ce,"Kowa ya san wuk'a bata had'iyuwa gare ka,
amma kowa ya ji da bakin ka ka ce tare da
abokin ka Sageer ku ka je k'ofar gidan su Salis.
Bincike ya nuna Sageer ya gudu kafin 'Yan sanda
su zo.
Menene dalilin gudun sa?"Ya kad'a kai tare da
fad'in,"Ni ma ban sani ba." Lauya ya dubi Alkali
ya ce,"My Lord, dole Naseer ya ce, bai san dalilin
gudan abokin Sageer ba, domin shi ya mikawa
wukar ya gudu da ita kafin isowar 'Yan sanda.
My Lord, kudirin Naseer ya kashe Salis da ya sami
damar yin hakan, sbd haka na ke rokon wannan
kotu mai adalci, da ta daga sauraron wannan
k'ara zuwa 27 ga wannan wata da muke ciki, don
ba ni damar tattara shaidu na, wadanda za su
tabbatar wa kotu wannan tuhuma da ake wa
Naseer gaskiya ne.
Na gode."
Ya koma kujerar sa ya zauna.
Zuciya kamar ta kashe Naseer.,
Kiri-kiri an lauya magana, ta zama sharri har ana
neman jawo Sageer ciki Ba shi kad'ai ba, hatta
Malam Umar haka zukatan su ke tafasa, shiru
kawai suka yi suna sauraron jawabin Alkali.
"Kotu za ta ci gaba a wannan watan kamar yadda
lauya ya buk'ata.
Sannan kotu ta buk'aci a kawo mata Sageer a
wannan ranar.
Shi kuma Naseer za'a aje shi a ruman har zuwa
wannan ranar."
Al'amarin daya fari a kotu, ya daga hankalin
kowa, hatta Malam Balarane da ke ikirarin babu
ruwan sa cikin rigamar da Naseer ya jefa kan sa.
Sai dai bai fito fili ya bayyana damuwar sa ba.
K'ala bai ce wa su M.Umar ba, har suka k'are
bayanan su.
Shiru na tsawon sakwanni bai tanka ba.
M.Umar ya ce,"M. Balarabe ko ba za ka ce komai
ba, ai ko tofa 'yar addu'a, don samun al'amarin.
Ya dube shi tsakar ido ya amsa,"Naseer ba ya
buk'atar addu'a, sai hukunci.
Damuwa ta 1 ce, yaron nan da aka jawo shi cikin
fitinar da bai ci ba, bai sha ba.
Shi kad'ai ke buk'atar addu'a.
Ubangiji Allah ya ku6utar da shi."
M.Lawal ya ce,"Insha-Allahu baki dayan su za su
ku6uta, duk da dai mu ba mu da k'arfin d'aukan
lauya, ai Allah na nan, za mu gaya masa ya duba
mana.
Ni zan k'arasa gida M. Balarabe, kuma ina ba ka
shawara fushin farko ba na ka bane.
Ka sani bakin mahaifi dafi ne ga 'ya'yansu, yayin
da suke cikin fushi da su.
Saboda haka ka sanya wa ranka ruwan sanyi, mu
rungumi k'addara.
Ya mik'e, ya na k'ara fad'in,"Malam Umar ni zan
wuce, sai yadda hali yayi kenan?"Ya ce,"To Allah
ya jishe mu alkhairi, ya kuma sauka mana
wahala."
Ya amsa da amin, duk suka yi Musabaha.
Ya wuce ba tare da M.Balarabe ya k'ara tofa
wani abu ba.
Bayan tafiyar M.Umar, ya dube shi, ya ce,"Malam
Balarabe ka yi wa girman Allah, ka sanya wa
ranka cewar wannan abu mukaddari ne daga
Allah, babu makawa sai ya faru." Ya ce,"Shi fa
Allah baya d'ora wa bawa abinda ya fi k'arfin sa,
sai abinda shi bawan ya d'ora wa kan sa.
Idan yayi taka tsan-tsan da rayuwar sa, yana
kiyayewa, sai Allah ya taya shi kiwo.
Shi yasa Ubangiji ya ce,"Idan kun ga sharri, to
daga gare ku ne, sai ku binciki kan ku.
Amma shi ya ce yana 1 daga cikin imani yarda da
k'addara mai kyau ko maras kyau.Na yarda cewa
Naseer shi ya jawo wa kan sa, sai dai kai ina son
ka yarda da cewa kaddara ce Allah ya dora
maka, babu makawa sai ka ga wannan 6acin ran,
amincewar kuwa shine ka daina fushi da Naseer,
ka taya mu addu'a Allah ya ku6utar da su."
Yayi shiru kamar ba zai tanka ba, tsawon lkc.
Sannan ya sauke numfashi ya ce,"Na ji Malam
Umar, na kuma gode. Allah ya bar zumunci,
amma kar ka manta, na yi rantsuwa ba zan yi
kaffara ba."
Malam Umar ya mik'e rai 6ace, ya fice daga
rumfar Malam Balarabe.
Babu Sallama.
Malam Balarabe ya bi shi da kallo, kawai na
tausayin su ya lullube shi, ya kad'a kai, ya ce a
ran sa,"Naseer na da gatan sa, amma shi bai san
hakan ba.
Allah ka shirya."
Haka hankali Sageer yake tashe, jin cewar shi ma
ana buk'atar sa a kotu da laifin shi ya gudu da
wuk'ar da ake zargin Naseer ya je kashe Salis da
ita.
Bai san lokacin da ya kawo kan sa gidan su Zarah
ba.tana kwance ruf da cikin, gefen tabarma da
suke tare da Innar ta,har ya gama gaisawa da
Inna Zarah bata iya dagowa ta dube shi ba, sbd
jin muryar sa ma k'ara dagula mata lissafi yayi,
wasu sabbabin hawaye suka cika idanuwan ta
tam!
Kayan makaranta ke jikinta, don bata iya cire su
ba, tunda ta dawo ta sami yadda shari'ar ta kaya
a kotu, ido jajur!
Sageer ya dubi Inna,"Yanzu mecece mafita
Inna?"
Gaba 1 tausayi yaran ya gama kashe mata jiki.
Ya nisa ta ce,"Mafita 1 ce Sageer, ita ce addu'a
wajen Allah.
Ka kwantar da hankalin ka.
Insha Allahu za ku ku6uta.
Kar ka damu ka ji?"Ya ce,"Shi kenan Inna. Allah
ya taimake mu." Ta ce,"Amin." Ya sauke
idanuwan sa, inda Zarah ke kwance, yayi kiran
ta,"Zarah! Bata amsa ba, ya ci gaba,"Kiyi hak'uri
Zarah." Dasauri ta mike cikin sassarfa, hawaye na
zuba ta nufi daki. Dai-dai k'ofa ta tsaya tana
fad'in,"Sai Allah ya tsinewa Salis!wannan sharri
yayi yawa.
Insha-Allahu sai ya ga k'arshen sa!"
Ta juya cikin d'aki da gudu.
Sageer ya ce,"Yaya za mu yi Zarah? Sai hak'uri
kawai."
Ya juya kan Inna,"Bari in koma Inna, ki gaida
Baban. Gobe asabar. Insha Allahi zan je in ga
Naseer d'in." Ta ce,"To Allah shi kare."
Ya amsa da
"Amin."
Ya mik'e ya bi Zarah d'aki. Can yayo ta
rarrashinta har suka shirya tafiya gidan yari gobe,
ganin Naseer, ba tare da sanin su Inna ba, don
kar su hanata.
Karfe 10 na safiyar asabar a k'ofar gidan yari tayi
masu. Sun jima suna neman yadda za su yi, a
bar su ga Naseer d'in, kafin suka sami
amincewar hukumar gidan mazan. Suna zaune
cikin wani d'an d'aki wanda za'a iya cewa ofishin
gandirebobin ne, aka fito da shi.
Bak'in k'ofar yayi tsaye ya sanya wa Zahar ido.
Kwanaki 5r kenan, amma ji take tamkar shekaru
5r ne.
Rabon da ta sanya shi a ido. Tausayinsa yasa
take ganin ya rame, ya dishe kamar ya shekara
yana ciwo. Hawaye kamar fanfo, suka tsunke
mata.
Naseer ya juya da sauri cikin 6acin rai ya ce wa
gandiroban,"Maida ni ciki!"
Ko kafin Sageer ya ce wani abu, har Naseer ya
kai bak'in k'aton gate d'in da ke k'argame a
bakin babbar k'ofar da za ta kai ka ciki.
Gandiroba na biye da shi,"Ba ka son ganin su
ne?"
"Eh!"
Ya amsa ba tare da ya waigo ba.
Gandiroba ya bud'e get, yayin da Sageer ke
k'arawa wajen,"
Naseer!
Naseer magana na ke so mu yi! Ya shige ciki, aka
rufe, sannan ya juyo ya ce,"Idan za ka zo, ka zo
kai kad'ai, ban da Zarah!
Ya wuce cikin sassarfa ya bar wajen.
Sageer yayi tsaye, yana kallon sa, har ya daina
ganin sa.
Ya tako a hankali inda Zarah ke durk'ushe, kanta
cikin guiwa.
Ya ce,"Zarah!
Taso mu tafi." Da kyar ta mik'e, gaba 1 Gandiroba
da ke wajen, babu wanda bai kalle ta ba, wasu
ma dariya ta ba su, ganin yadda Sageer ke jan
hijabinta, tana jefa k'afa kamar makauniya.Daya
daga cikin su da ke zaune gaban wani katon
tebur da alama yana daya daga cikin manyan
wajen.
Tsam!
Ya mik'e ya nufo su, abinka da yare kuma babu
musulunci, yana zuwa ya rungumo kafad'un
Zarah ya shiga rarrashin ta,"Kin kuwa san yadda
ki ke da kyau, ki ka zauna ki na kuka? Don
wannan tsohon mai laifin, ya ce bai son ganin
ku?"
Da sauri ta kwace kafad'un ta, ta balla masa
harara." Tsohon mai laifi?
Yayana ba tsohon mai laifi bane,sharri aka yi
masa, kuma Allah zai fitar da shi! Tuni ta bar
Gandiroba nan a tsaye. Sageer ya biyo ta. Dariya
suka ci gaba da yi, abinda ya k'ara hassala
zuciyar Sageer. Gudun mai zai faru, idan ya
tanka, shi yasa ya rufawa Zarah baya, suka bar
harabar wajen.
Tafe suke. Zarah na koken,"Kiri-kiri yayana ya ce
baya son gani na, me yasa?" Ya ce,"Ai ba zai so
ganin ki a yanayin da yake ciki ba. Ba zai so ki
rink'a kuka ba Zarah.."
Ta ce,"Ba wani Sageer, akwai abinda yayana ke
nufi." Bai nufin komai, yakamata ki gane, ba
kowane zai jure ganinsa a haka ba.
Kawai ki manta Zarah, addu'a kad'ai za ki taya
mu."
Ta sauke numfashi ta ce,"Yadda yayana ke so na,
haka na ke son shi Sageer, ya kuwa zama dole in
yi kuka, tunda yana cikin wani hali. Na san
yayana jarumi ne, komai zai iya jurewa, amma
zama cikin wannan shegen gidan rayuwar kunci
zalla cikin sa.
Salis ya bi son zuciya zai kuma ga 6acin ta yarda
Allah."
Dai-dai suna tsayuwa bakin titi. Sageer ke
fad'in,"Zarah yayenta kenan, soyayyar ta d'aure
min kai. Shi kuma Salis ai har da kishi, ga mari ga
tsinka jaka. Kin fa san mu maza mun fi ku zafin
kishi, illa iyaka na mata ne ya fi bayyana. Dole
Salis ya rasa na yi, tunda kin ce ba ki tare da shi.
Yayan ki, ki ka fi so ko?"
Ta saci kallon sa tana d'an murmushi ta ce,"Kai
wanne ka ke ra'ayi?" Yayin da wata bus ta tsaya
gaban su. Ya ce,"fad'a 6ata baki. Shiga mota
kawai mu isa gida." Suka shige cikin mota, ta
sauke su inda suke son sauka. Sageer ya biya
kudi.
***************
Washe gari Sageer na tare da Naseer a gidan
yari, kuma ya samu nasarar ganin sa. Zaune suke
suna nemar wa juna mafita.Gaba d'aya hankalin
Naseer a tashe yake kuma ya fi karkata ga
k'aunar jefa Sageer cikin maganar da babu
hannun sa a ciki. Saboda haka ya dage yana
fad'in,"Koda wasa Sageer kar ka kuskuara ka
amince da laifin da ake so a k'aga ma. Don na
lura Lauyan nan, shegen kan sa ne. Saboda haka
ka lura da laffuzan da za su fito bakin sa. Sannan
ka ba shi amsa."
Ya ce,"Ni ma d'in kai na fi ji Naseer, na san ka
ba ka da tsoro, don girman Allah kar ka fad'i
abinda zai 6ata ran Alkali, a zo kuma abubuwan
su k'ara rikicewa."D'an murmushi yayi." Ai taka
tsan-tsan na ke yi, sbd ba na son Zarah ta
dauwama a kuka, ba don haka ba, da tun
shekaranjiya na amsa da wukar na je, ka ga Alkali
ya huta, take a nan zai yanke hukunci."
Naseer kenan, to Allah dai ya fida mu lafiya. Bari
in lalla6a gida, me zan cewa mutuniyar?" Ya
ce,"Ka gaya mata idan har ta san tana sona, to ta
daina min kuka, lafiya lau na ke, damuwa ta 1
ce, yanayin da take na rashin kwanciyar hankali.
Muddin kuwa ta natsu, ta maida hankalin ta a
makaranta, shakka babu, ni ma zan sami
nutsuwa.."
Suka mike yana fad'in,"Zan isar da sak'on insha-
Allahu.
Sai mun had'u a kotu." Ya wuce Sageer na tsaye
na kallon sa. Gandiroba ya bi bayan sa. Kafin ya
fice, ya juyo suka had'a ido,"Ka gaya mata ta ci
gaba da lissafin kud'in (Break) d'in ta Insha
Allahu da na fito, zan biya su."
Murmushi Sageer yayi ya ce,"Zan fad'i." Yasa kai
ya fice, tare da ,mai tsaron sa. Sageer ya sauke
numfashi cike da tausayin abokinsa, sannan ya
fito yana fad'in cikin ran sa, "Da yardar Allah sai
ka bar gidan nan."
27 ga wata kotu ta cika mak'il!
Kasancewar litinin ce masomar aiki, ko nasara na
tsoronki. Ci gaba da shari'ar su Naseer aka fara
saurara. Gaba d'aya kowa ya hallara har da
shedun da lauyan Salis ya ce zai gabatar.
Ba wasu bane, illa abokan Salis da aka yi abin
akan idanuwan su, amma maimakon su fad'in
gaskiyar lamarin, sai suka goya wa k'arya baya,
suka tabbatar wa Alkali tabbas Naseer ya sumar
da Salis, sannan yayi k'ok'arin da6a masa
shar6e6iyar wuk'a.
Bayan Alkali ya gama sauraron shedun lauya, kai
tsaye yasa aka shigo masa da Sageer cikin akurkin
kotu.
Bayan yayi rantsuwar zai fad'i gaskiyar abinda ya
sani. Alkali ya tambaye shi, Me ka sani a game
da fad'an Naseer da Salis?"
Ya gyara tsayuwa, ya fed'e bayani kamar yadda
ya faru. Alkali ya ce,"To ina wukar da ka tsare da
ita?" Ya kad'a kai, fuska yamutse ya
amsa,"Naseer bai je da wuk'a wajen ba, balle har
in gudu da ita. Hasali ma, Naseer bai ta6a yawo
da makami ba." Yana sa aya. Lauya ya mik'e,
"My Lord!
Ina da 'yan tambayoyi ga Sageer."
Na take ya sami izini." Gaban Sageer ya tsaya
suka kare wa juna kallo, kafin ya ce,"Hujja 1 na
ke so ka gaya min, menene dalilin gudan ka, ka
bar k'ofar gidan su Salis?"
Sageer ya amsa,"Gidan iyayen Naseer na je, don
sanar masu halin da ake ciki." To da ka garzaya
ka sanar wa iyayen na sa, sun zo wajen?"
Yayi shiru, na 'yan dak'ik'ai, sannan ya kad'a
kai,"Ba su zo ba."
Me yasa?"
Lauyan ya tambaya cikin sauri.
Gaban Sageer ya ci gaba da fad'owa, kamar ma
ba zai ce komai ba, saboda tsawon shirun sa, ya
nisa a natse ya ce,"Cewa suka yi babu ruwan
su." Lauyan ya gyara tsayuwa ya ce,"Ah!
Naseer ba d'an su bane?
Don me za su ce ba ruwan su? Nan kam Sageer
ya kasa amsa wannan tambayar, ya aje kai k'asa,
idawuwan sa suka cika da k'walla.
Barista ya dai-daita zaman kot dinsa, ya dubi mai
shar'ia ya ce,
"My Lord!
Bayanan Sageer sun nuna a fili ko a gidan su
Naseer ya ishe su, sun kuma tabbatar da zai
aikata abinda ake tuhumar sa da gasganta min
binciken da na yi cewar har kwana 2 yau, babu
mahaifin Naseer a cikin kotun nan. Ya mai girma
shari'a.
Iyayen Naseer ma sun tabbar da d'an su zai
aikata laifin,My lord, banda wannan ya dade
yana dauko wa mahaifin sa magana, wanda shine
babban dalilin da yasa ya tsame hannunsa akan
d'an sa. Bincike ya nuna ko cikin makaranta
Naseer bai da biyayya, domin har makaranta ta
ta6a korar sa na sati 2.
My Lord!
Ga shedu na na ga hujjoji na na, ga kuma
k'wafin shedar koran Naseer daga makaranta na
sati 2.
A tunani na sun isa su tabbatar da cewa Naseer
shaharrare ne wajen aikata laifuka iri-iri.
Saboda haka ina rok'on wannan kotu mai adalci
da ta duba ta fidda wa Salis hakkinsa, na neman
kashe shi da Naseer yake shirin yi.
Na gode."Ya mik'a takarda. Aka mik'awa
Alkali.Sannan ya koma mazauninsa ya zauna.
Kotu ta yi tsit! Yayin da Alkali ke duba takarda.
Can 6angaran 'yan kallo inda su Malama Lawal
da M. Umar ke zaune, tuni ransu ya gama 6aci,
da ka dube su, ka san akwai tashin hankali a
tattare da su. Zaune kawai suke, amma
zukatansu babu abinda bata sak'awa.
Alkali ya dubi Naseer da ke tsaye cikin akurkin
tuhuma, cikin madubin idon sa fari sol ya ce da
shi,"Ina fatan duk ka ji bayanan da suka gabata.
Ya ce,"Ka ji Me za ka k'ara a kai?"
Ya amsa,
"Babu."
Ya ce,"Duk ka amince da abubuwan da aka fad'i
kenan?"
Kai tsaye Naseer ya amsa,"Dole duk abinda aka
fad'i, ya zama gaskiya, saboda ni ba ni da wani
sheda sai Allah, domin haka babu amfanin
wahalar da kotu, duk hukuncin daya dace sai ayi
min."
Na amince da kowane irin adalci da mai shari'a
zai min."
Alkali shi kan sa, sai da kalaman Naseer suka sa
shi ya jima yana yana kallon sa. Haka su M.Umar
ke kallon Naseer cike da tausayi. Sun sani dole
dama haka za ta kasance, sai dai kawai addu'ar
Allah yasa hukuncin ya zama mai sauki.
Bayan kammala rubucen-rubucen Alkali, sai ya
yanke hukunci. Bayan ya karanto dokokin kundin
shari'a, sai ya zarce da cewa,"Kotu ta yankewa
Naseer d'aurin wata 3 a gidan yari, ko tara ta
3000. Haka kuma shi zai biya kud'in asibitin da
Salis ya kwana, wanda a yanzu haka (Bill) yake a
hannun kotu, na naira dubu biyar da d'ari biyar
da hamsin 5,550.
Shi kuwa Sageer taimakawar da yayi wajen
ta'addancin, kotu ta ba shi tarar 1500, ko sati 2
gidan yari, tare da gargadin mai tsauri, idan har
aka sake kamasu da laifin irin wannan. Kwarai za
su had'u fushin hukuma.
A karshe ina jan kunnunwan Naseer da Sageer da
cewa kar wanda ya sake nemaan wani da fad'a.
Tare da fatan dokar kasa za ta zama abar biyayya
ga kowa.
Nan take ya sallami wannan shari'a ya kama
wata.Waje aka fito da su Naseer, duk jama'ar su
suka biyo su, yayin da gayyar su Salis da Lauyan
su suka wuce cike da farin cikin samun nasara. A
nan take su M.Lawal da M. Umar suka had'a
kud'i 1500, don biyan kud'in tarar Sageer, shi
kuwa Naseer suna ji, suna gani aka wuce da shi
gidan yari, don babu yadda za su yi.
Gaba d'ayan su babu mai adadin kud'in tarar sa
da na asibitin Salis, jimliar dubu takwas da dari
biyar da hamsin, kamar su zubda hawaye,
saboda 6acin rai. Shi kam Sageer sai da ya zubda
hawayensa, a haka suka nufi kasuwa, runfar M.
Balarabe suka sheda masa yadda shari'a ta kaya.
Kawai kad'a kai yayi, ya ce,"Allah yasa ya zama
darasi a gare shi."
Malam Lawal ya ce,"Yanzu matsalar kud'in
asibitin nan da aka ce sai an biya. 8,550." Mala,
Balarabe ya ce,"Ai da ma Alkali ya maida su
dauri. Wa zai biya?
Ni dai bn da wannan adadin kudin.
Dukkan su shiru suka yi na 'yan dak'ik'ai, kafin
M. Umar ya ce,"Allah ya rufa asirin, ni zan
k'arasa gida."Balarabe ya mika masa hannu,"To
ka gaida gida, Allah ya saka da alkhairi.."
Amin."
Yake fad'i, yana mik'ewa tsaye. Suka yi sallama
da Malam Lawal, ya fito ya bar su tare da Malam
Balarabe.
Gida ya nufa, lkcn 10:15 na safiya. Inna na
zaune tsakar d'aki cike da tunani, har wani
gyangyad'i takaici ke son d'ibar ta. Sallamar M.
Umar ta sa ta, ta wartsake."
Ka dawo?"
Ya k'araso cikin d'akin yana fad'in,"Na dawo."
Ya zauna rai 6ace, yayin da take masa sannu da
zuwa, ya amsa,"To yaya, me ake ciki?"
Ya ce,"Anyake hukunci. Wata 3 zai yi gidan yari
ko tarar 3000.
Sai kuma kudaden asibitin da suka ce sun kashe,
5550. Kin ji yadda aka yi. Shi kuma Sageer da
yake na sa babu yawa, mun had'a kud'in mun
biya tarar.
Inna ta aje numfashi, ta ce,"Yanzu shi Naseer din
gidan yarin zai yi?
Ya amsa,"To yaya ki ke so a yi?
Ba mu da adadin kudin nan A'i.
Dama ace 3000 ne kawai, da sai ayi 'yan buge-
buge a samu. Amma babu komai. Allah zai rufa
asiri, zan yi iya kokari na mu gani."
Ta ce,"Sati mai zuwa zan amshi adashina 3500
ne, sai in hakura da tafiyan kauyen, zan ba ka a
harhada mu ga abinda za'a samu." Ya nisa kafin
ya ce,"Allah ya kai mu lkcn. Ni bari in koma
kasuwa."
Ya mike ya fice Inna na fadin,"Idan Zarah ta
dawo zan leka wajen gidan su Naseer din in yi wa
Umman ta sa jaje.Ya ce,"Sai kin dawo." Ya fice ya
bar ta da jimami. Tamkar d'an cikin ta take jin
Naseer a zuciyar ta, sbd yadda ya kular mata da
Zarah lokcn da take buk'atar kulawar. Watau
sa'ilin yarintar ta.
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Ajininsa yake 1-04
Posted by ANaM Dorayi on 10:59 AM, 06-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_____________
Karfe 3 ta gota, awa 1 bayan dawowar Zarah
daga makaranta, amma har yanzu tsiyayar
hawaye take yi. Tunanin ta me take da shi
wanda za ta siyar, don taimakawa iyayen ta
wajen fiddo Naseer daga gidan yari! Tsaf!
Ta mike ta nufi d'an akwatin kayanta ta bud'e, ta
za6o tsala-tsalan ciki, watau k'arshen adakar.
Kala 6 ta aje su bisa gado, ita ma ta nemi wajen
ta zauna ta ci gaba da tunanin adadin kudin da
kayan za su bayar. Can cikin zuciyar ta kuwa,
tsabar kewar yayanta ke addabar ta. Ji take
tamkar sun shekara goma rabon su da juna.
********************
Cikin kwanaki 3 bayan yanke shari'a Umman
Naseer tare da taimakon su Malam Lawal da M.
Umar da Inna suka had'a kud'ad'en da kotu ta
buk'ata, watau Naira 8,550. Suna biyan kud'in
kai tsaye kotu ta aika da takardar umurnin sakin
Naseer.
Yana fitowa yayi arba da su M. Umar da abokinsa
Sageer. Da sauri suka nufo juna Sageer, ya
rungume shi suna yi wa juna barka tare da nuna
tsananin godiya ga Ubangiji, sannan ya juya
wajen su M.Umar ya gaida su. Su ma cike da
farin ciki su ke, fuskokinsu tsaf, suke d'auke da
fara'a suka amsa gaisuwar sa. Daga nan gida
suka wuce da shi.
Umman sa na jin sallamar su, ta mik'i da
hanzarin ta, amma kuma sai ta kasa aiwatar da
komai, haka ta tsaya kame da ha6a tana kallon
Naseer. Kwarai ta tausaya masa ganin ya sauya
ba kad'an ba.
"Malam!"
Ta kwala wa Malam Balarabe kira, yayin da su
Naseer ke karasowa daf, da ita.
Ta koma bisa tabarma ta zauna suka zauna suna
fad'in,"Sannu Umma."
Ta ce,"Kai ne abin sannu, manya d'ibar fari. Allah
ya shirye ka." Ya sunkuyar da kai, dai-dai lkcn
Malam Balarabe ya fito daga d'aki. Sageer ya
gaishe shi, sannan ya ce,"Su Baba na nan zaure."
Bai saurari gaisuwar Naseer ba, yayi gaba abin
sa, ya nufi zaure.""Ku shigo mana M.Umar! Kun
tsaya daga nan kamar bak'i?"
Ya koma ciki suka biyo bayan sa. Umma ta k'ara
baza tabarma kowa ya zauna suna 'yar raha.
Bayan gaisuwa. M.Lawal ya ce,"Malam Balarabe
babu wato doguwar magana tsakanin ka da
Naseer, face ka sanya wa ranka ruwan sanyi,ka
yafe masa laifin da yayi maka, tunda Allah ya
tak'aita wannan wahalar. Shi kuma tun a hanya
mun jajja masa kunne, yayi alkawarin ba zai sake
maimaita laifin makamacin wannan ba. Ina fatan
za ka karbi tuban sa ka sanya masa albarka?
Malam Balarabe yayi d'an jim, sannan ya dubi
abokan sa ya ce,"Hakika kun nuna min kauna
tsakani da Allah, kuma wanda na yi imani ko
banda rai za ku iya rike min iyali na. Saboda haka
ba ni da wata kalmar godiyar da zan muku, illa in
ce Allah ya saka maku da mafificin alkhairi, ya
bar mana zumuncin da ke tsakanin mu, har zuwa
gidan aljanna. A game da Naseer kuwa, ni na
yafe. Ubangiji ya shirya mana dukkan zuri'a baki
d'aya.
Kowa ya ce,"Amin.
Kan Naseer na sunkuye, kuma har cikin ran sa
yana jin tausayin iyayen sa, sai yanzu yake
nadamar ta6a Salis da yayi. Sai dai ba laifin sa
bane, kaunar da yake wa Zarah, ita ta kai shi ga
aikata abinda zuciyar sa ta sak'a masa. Amma in
kwana dubu yana wannan bayanin, iyayensa ba
za su ta6a daina ganin laifin sa ba, Musamman
Abban sa. Ya sauke numfashi, na jin dadin
furucin Baban sa.
Tsam!
Ya taso ya tsungunna gaban sa, ya ce,"Abba na
gode." Ya dube shi a raunane ya ce,"In kunne ya
ji, gangar jiki ta tsira Naseer. Ka sani kullum
shekaru na tafiya suke yi, za'a wayi gari wata
rana ace babu ni, shi yasa kodayaushe kokarina
ka dan sami ilimi dai-dai gwargwadon k'arfi na,
amma kai hankalinka ba shi a nan.
B'acin rai na kodayaushe, idan na tuna cewa ba
ka sami rubuta jarabawar ka ba, ga shi ance
saura guda 3 a kammala ta.
Wannan babban rashi ne, don ko banza sai wata
shekarar za ka sake wanda ya kamata ace katafi
wani mataki na gaba. Haka Allah ya so."
Wannan dogon jawabi ya sanyaya jikin kowa, duk
sukai shiru na 'yan dak'ik'ai kafin M. Lawal ya
ce,"Lokaci kam an 6ata shi.Amma babu wuya a
wurin Ubangiji, wata shekarar za ta zo ne, sai ya
sake. Allah dai ya kai mu dai rai lafiya."
Suka ce,"Amin."
Malam Umar ya muskuta, ya ci gaba,"Akwai wata
magana da na ke ganin zai yi kyau in fade ta
wannan zaman, don kowa ya zama shaida. Allah
ya sani, ba ni da abinda zan yi wa Naseer in iya
saka masa akan hidimar kuluwar da yayi wa
Zarah, wanda shine silar kullawar zumuncin mu,
face in ba shi auran Zarah.
Don samun d'oruwar zumuncin mu. Ina fatan
kowa zai amshi wannan kyauta tawa da hannu
biyu. Saboda haka Naseer, ga Zarah nan matar
ka ce insha Allahu.
Za ta ci gaba da karatu har zuwa lkcn da Allah ya
hore mana d'an abin yi. Haka kuma ina son kowa
ya shaida ko bayan raina, ban ce a tada wannan
magana ba, koda za'a sami wani akasi ta
6angaran Zarah, wanda ba na fatan faruwar
hakan, ban jin Zarah za ta iya juya wa yayanta
baya. Ko akwai kuskure a zan ce na?
Gaba dayan su farin ciki ke bayyane bisa fuskokin
su, musamman uban gayyar wanda yake jin
tamkar an tsunduma shi a al-janna.
Kiris ya rage ya riga iyayen sa magana. Sageer
yayi sauri ya toshe bakin sa. Umma ta ce,"Kyale
shi mana mu ji abinda zai ce maras kunya, dama
tunda aka fara maganar bakinsa ya k'i rufuwa.
Ai sai mu kyale shi, ya amshi auran da kan sa."
Da sauri ya mik'e, yana dariya yayi zaure. Sageer
na bin sa, yayin da iyayen ke masa dariya.
Malam Lawal ke fad'in,"Yaya za ki maida shi
kamar mace? Ai mata aka sani da wannan
kunyar.
Gaskiya abu yayi dadi, kuma mun amshi wannan
babbar kyauta taka.
Allah ya sanya duban albarkun tare da fatan ran
mu ya kai had'e da koshin lafiya."
"Amin."
Duk suka amsa Malam Balarabe ya mik'awa M.
Lawal hannu su kai Musabaha,
"Mun gode!
Mun gode!!
Allah ya bar zumunci.
Malam Umar ya ce,"Naseer d'a na ne, ni kad'ai
na san irin gudumuwar daya bai wa rayuwar
Zarah, na kuma fahinci dalilin fadawar sa
wannan fitinar.
Zarah yake so, ni kuma naba shi. Allah ya
tabbatar mana."
Umma kan ta farin ciki ya hana ta cewa k'ala, illa
ta amsa da amin, ta zarce ta sawa abin albarka
cikin zuciyar ta, sun dan jima suna hirararrakin
raha, kafin suka yi sallama suka fito.Naseer da
Sageer na cikin dakinsa su ma suka fito suka yi
rakiya tare da k'ara godiya, sannan suka dawo
d'aki. Bisa katifa Naseer ya zube a ringine.
Sageer ya zauna kusa da shi ya ce,"Yanzu ba
washe hak'ora ba, mice ce shawarar ka?" Ya juya
ya dube shi." Ta me? Ya ce,"An ba ka Zarah,
wane shiri za ka yi na dogaro da kanka, don ci
gaba da kulawa da ita?"
A natse ya taso, ya dube shi kafin ya nisa, ya
ce,"Akwai fa sauran aiki, amma ai Allah na nan,
shi yasan yadda za'ayi ko?
Haka ne,
sai dai yakamata kai ma daga (Next year) ka dai-
daita jarabawar ka, don na san ka da shiririta
akan karatu. Wani lkcn har da laifin ka."
Ya kwada masa harara, ya ce,"To zigziglar
baturan ilimi!
Cewa na yi ba zan sake (Exams) d'in ba ko yaya?"
Ya ce,"Ka ji tsiyar ka, sai ana maganar arziki, sa
ka fand'are. Ni bari in wuce gida, tun kafin mu
hau rimi mu fad'o karyayyu."
Ya mik'e zai fice, "Naseer ya janyo hannun
sa,"Kai banza ne Wallahi, duk ka 6aci da bakar
zuciya, yanzu kuma me na yi? Ya sanya masa ido
suna kallon juna. D'an murmushi Naseer yayi, ya
saki hannun sa cikin damuwa ya ce,"Je ka ma
kawaia anjima idan na yi wanka, zan fito mu je
gangare." Ka wuce kawai, kar ka biyo min."
"Me yasa?"
Ya ce,"Shi yayi saniya, d'an rainin wayau. Kasan
in yi maka rakiya, amma ba ka san in ba ka
shawara, ka ji ba.
Ka tafi kai kad'ai, ba Zarah bace? Kun
san.............."
Ya katse shi, saboda fizgo shin da yayi, ya zauna
dabas!
"Bani shawara Sageer, me ne zan yi?
Faskare ko dako?
Yasar masai ko kuwa in fara turin kura?"
Ya ce,"Ko wanne ka d'auka yayi, idan ma gatse
ka ke min, ina son ka sani duk sana'a ce, kuma
da su mutane da yawa suke ciyar da iyalan su.
Sana'ar hannu aba ce mai kyau, wanda duk me
yin ta, ya wuce raini.
Sai anjima."
Ya ce,"Tsaya mana,
ai ka fad'i gaskiya Malam Sageer. Ba gatse na ke
yi ba. Yanzu menene abin yi? Ya ce," Akwai
shagon da na yi magana zan rinka zuwa koyon
d'inki. Nan shagon Alh. Hassan, idan ka na so, ka
zo mu rink'a zuwa tare.
Me ka ce?"Kai tsaye ya amsa,"Dai-dai wallahi.
Yaushe za mu fara?" Ya ce,"Ka ga ranar
Wednesday za'a gama (Exams),zuwa alhamis ko
juma'a, sai mu fasa kawai." Ya ce,"Dole a fasa ko
a sami na auran Zarah. Komai zan iya yi, sbd ita,
don jin ta nake tamkar rai na. Anjima za ka raka
ni d'in ko?
Yayi d'an murmushi,"Shi yasa ka yi saurin amsa
min? To bn zuwa, ka je kai kad'ai, kafin laifin ka,
kai kad'ai.............."
Umma ce ta katse hirar da ta kwala wa Naseer
kira. Ya mik'e yana naushin kafad'ar Sageeer. Jim
kad'an ya dawo da kwanon abinci.
Sageer ya ce,"Umma har ta gama abinci k'arfe
11?" Ya ce,"A'a, waina ce Abba ya bada kud'i,
maimakon ta kira ni, mu siyo shine ta shiga nan
gidan wainar ta siyo da kan ta."
Sageer ya kad'a kai, ya ce,"Su Umma na son ka
Naseer, ka yi wa Allah ka rink'a gudun 6acin ran
su."
"To, na ji."
Haka ya fad'i yana bud'e wainar, komai yayi.
Suka fara ci, sai dai Sageer ya lura kamar Naseer
bai son yin magana, don haka ya tambaya,"Me ka
yi?"
"A'ina?"
Shi ma ya tambaye shi. Ya ce,"Kamar wani abu
ya dame ka?"
Ya dube shi da kyau, ya ce,"Har yanzu babu
wanda ya fahimce ko ni wanene, shi yasa aka
min kallon maras ji. Alhali ni ina son duk abinda
zan yi, ina da dalili na.
Kuma wallahi ina tausayin iyayena. Amma abinda
ke ba ni haushi, ku ba ku fahimtar halaye na A
JINI NA SUKE. Sannan shin wai ma, me na ke yi
na 6atanci, wanda ya taka shari'a?"
Sageer yayi shiru, yana kallon sa. Naseer ya kad'a
kai, manyan idanuwan sa suka fara kad'awa, ya
sanyaya murya,"Amma tunda kai ma ka na ganin
ina sa6awa su Abba, yanzun nan zan je in nemi
gafarar su, ni kuma zan nemawa kai na mafita,
duk da na san cewa ban aikata komai ba, don
ran su ya 6aci.
Sageer nisa ya ce,"To ka yi hak'uri, idan magana
ta bata yi maka bane."
"A'a,
ka fad'i dai-dai, abinda ka fahimta ne tsakanin
ka da Allah so ba matsala na gode, mu ci abinci
kawai." Suka ci gaba da cin abinci, suna hirarraki
har suka kammala. K'arfe 12 Sageer ya koma
gida, ya bar Naseer tare da su Abba yana sake
neman gafarar su.K'arfe 4 bayan sallar la'asar,
ya fito fes! Cikin k'anana kaya. Shagon aski ya
fara shiga, aka yi masa, gaba d'aya ya k'ara
tsaftacewa kamar wani ango. Daga nan gidan su
Sageer ya nufa, yana zaune bisa dakali ya na
karatu. Naseer ya jira shi, ya mayar da littafin ya
kulle k'ofa, suka wuce gangare. Cikin zaure ya
tsaya ya dubi Sageer ya ce,"Zan iya shiga gidan
nan kuwa?" Ya ce,"Me yasa?" Kunyar Inna na ke
ji............."Bai gama zancensa ba, sai ga Inna ta
kawo cikin zauren. Take nan Naseer ya daburce,
tsanananin kunya ta kama shi tamkar bai ta6a
sanin Inna ba. Shi kan sa ya rasa dalilin hakan.
Hannun sa a k'eya yana ta sosawa,"Sannu Inna.
"Dukkan su suka ce. Bakin ta har kunne ta amsa.
"Allahu Akbar Naseer, yanzun nan gidan ku na
nufa in duba ka.
Sannun ku!"Suka tsugunna suka gaida ta, ta
amsa, sannan ta zarce da fad'in,"To ku shiga.
Zarah tana nan a ciki, sai na dawo." Suka amsa,
"Adawo lafiya." Amin." Ta wuce tana fad'i.
Su kuwa ciki. Suka yi sallama, kamar su take jira,
domin kuwa ta zuba adonta da wani material
ruwan hoda da farin furanni. Ko ba'a tambaya
ba, adonta ya nuna tsaf, tana cikin farin ciki irin
na bege. Amma maimakon ta tarbi yayanta
kamar yadda ta saba, sai ta kasa, saboda wata
sabuwar kunyarsa da ta mamaye idanuwanta,
masu sa yayan nata neman zarewa.
Sallamar kawai ta iya amsawa, ta k'ara sunkuyar
da kai, ta d'ora idanuwanta bisa tiran da take
gyaran wake. Kujeran tsakar gida suka ja suka
zauna, sannan Sageer ya ce,"Zarah, yau kuma ba
za'a kalli yayan bane?"
Sageer ta duba fuska cike da murmushi,
"Ina ruwanka?"
Ya ce,
"Au,
haka ne?
Saboda na kawo miki shi ko?
Ba laifin ki bane.
To ya ki ke?"
Ta ce," Lafiya lau, ya mutan gida?" Ta amsa,"Su
ma k'alau suke. Yau dai kuka ya k'are ko? Ga
yayan ki nan. Allah ya taimake mu ya fito."Ta
ce,"Allah ya kare na gaba." Amin, sai ki yi masa
fad'a ya rink'a danne kishi." Ta karkad'e kai. Duk
suka fara dariya,"Kin goye bayan sa kenan?" To
babu ruwa na, kinfi kowa sanin halin yayan ki."Ta
ce,"Akwai k'arya k'ashin wuya ko? Ai ya bada
darasi, ka ga babu mai sake kwatantawa.
Suna ta k'yalk'ya dariya. Naseer kamar ya lashe
ta, sai lkcn ya fara magana, "Kinyi min dai-dai
my sister, jarumta adon namiji, kuma ai kishi
halas ne, duk wanda ya shige maka hanci, ka
daddage ka fyato shi, har sai ya balle k'ashin
wuya. Idan ya suma, ya farfad'o ya gane
kuskuren sa ko tawan?" K'ara aje kai tayi k'asa
tana murmushi.
Sageer ya ce,
"Ok,
irin na ku tsarin kenan?
Lallai jiki magayi, gara shi da ke mai kukan tsiya."
Wasa na ke Sageer,ai yayana yayi min babban
laifi.
Shekaru nawa mu ke tare da shi? Koma dai
menene, sai ya gaya min, ba wai ya je ya jawo
mana tashin hankali ba. Babu wanda ran sa bai
6aci ba akan abinda ka aikata.........."
Ta d'an dube shi a raunane ta ci gaba,"Don
girman Allah yayana ka rink'a gudun abinda zai
rik'a 6ata wasu Abba rai."
Gaba d'ayan jikin Naseer yayi sanyi, ta jefa shi
cikin damuwa.
Yayi d'an shiru kafin ya numfasa."
Ya ce,"Na ji Zarah.
Insha Allahu ba za'a k'ara ba. Kuma na rok'i su
Abba sun ce komai ya wuce.
Ina fatan ke ma za ki min afuwa, ki d'auka cewa
kishin ki ne yayi min yawa har idanuwa na suka
rufe ruf!
Ba na ganin kowa a gaba na, balle ya gaya min in
ji. Ki yi hak'uri, kin ji?"
Ta d'an rausaya kai tana murmushi,"Ya wuce,"Sai
harkar soyayya ko?"
Kunya ya bata sosai, ta rasa madafa. Sageer ya
ce,"To in d'an jira daga zaure ne? Yadda ka so."
In ji Naseer ya sanya hannu cikin tiran da ke cike
da wake ya shiga taya ta. Ta ce,"Yimin
wulank'anci, don na rako ka."
Zarah ta amshe,"Kyale shi Sageer, yi zaman ka ai
kai yayana ne."Maigida na ke, komai sai da izini
na." Ta ce,"Haka ka ke gani, amma ni na san
sabon yayana ya fi power, don haka ka bi shi a
hankali.
Ya dubi Sageer ya ce,"Allah ko? To sannu yaya
ina yini?" Sageer dokar masa kafad'a, suka ci
gaba da hira cikin farin ciki.Daran wannan ranar
Naseer bai iya barci ba. Ba waai k'aunar Zarah
ke masa tuk'uk'i ba, don wannan ta dad'e masa
cikin zuciya. Ammamaganar da ta zame masa
sabuwa, ta kuma hana shi sukuni, ita ce maganar
da kowa yake masa, watau ya rink'a gudun
abinda zai rink'a 6ata wa iyayensa rai. Ko Inna
da ta dawo, ta same su a gidan. Sai da ta fad'i
wannan maganar sbd haka abin yayi matuk'ar
tsaya masa a rai.
Kuma ya rasa mafita, domin shi a ganinsa bai
aikata komai ba, don ran su Abba ya 6aci, akan
gaskiyar sa yake kuma ko a yanzu ba don kotu ta
shiga tsakanin sa da Salis ba, da Salis ya gane
shayi ruwa ne, madara ake zuba masa yayi kauri.
Duk da cewar Baban Zarah ya share masa
hawaye kuma ya hana Salis zuwa wajenta.
Wannan ba zai hana shi k'wato hak'k'in sa ba.
Amma magana ta kau, tunda kotu na tsakani.
Ya juya rigingine, ya numfasa,
"Mece ce mafita a waje na ni Naseer?
Na san ba ni da hak'uri, amma ai sai anyi min na
ke ramawa. Sai kuma a rink'a ganin laifi na." Ya
ja tsaki, ya kada kai mai cike da takaici. Har aka
kira assalatu idonsa 2, ya fito yayi alwala, suka
fita masallaci da Abba.
Bayan cin abincin safe, ya fito k'ofar gida yayi
shiru a tsaye, kusan layin yayi tsit! Saboda duk
wani yaro daya isa zuwa makaranta, ya riga ya
tafi. Duk kadaici ya dame shi, ga yawan tunani,
don haka ya kulle d'akin sa yayi wa filin sukuwa
tsinke. Mutane 2 kawai ke cikin filin, can nesa da
shi suna wasan kwallon Golf. Wata kujera mai
zaman din-din-din ita ya samu ya zauna.
Maganganu barkatai suka yi ta zuwa, suna
wucewa cikin zuciyar sa, musamman wacce ta
hanashi barci jiya.
Rana ta fara yin zafi, ya zamana filin babu kowa
cikin sa, sai Naseer da ke jingine da kujera ya
d'aga fuska sama idauwan sa gaba 1 na rufe,
kawai damuwa ta sanya shi kasancewa cikin
wannan yanayin tsawon lkc, kafin ya fara tsinkar
karar kofatan doki.
A natse ya bude idanuwan sa. Ya juya ya dubi
gefen da yake jin tafiyar dokin. Wani matashi ya
hanga, ya sakar wa doki linzami, in ba ka yi, ba
ni wuri, sukuwa yake yi, babu kama hannun
yaro. Naseer ya saki ido, kaf hankalinsa ya koma
ga mai sukuwa. Nan take damuwar sa ta kau
daga zuciyar sa.
Mai dokin nan shi kad'ai yake atisayen sa.
Sai Naseer da ke masa kallon kauna da
sha'awa."Zagaye karo na 3 kenan zai yi wa filin,
wanna karon k'ure dokinsa matuk'a, babu 6ata
lkc, doki yayi ta haniniya ya d'aga shi sama, yayi
watsi da shi tamkar yadda aka shek'e dussa a
matankad'i. A guje Naseer ya mik'e ya nufi inda
matashin ke kwance shame-shame a sume. Ashe
ba Naseer kad'ai ya ga wannan tashin hankali ba,
har da wasu masu ababen hawa da ke tafiya
bisa titi.
Kasancewar filin yana gefen hanya ne.
Nan da nan suka kawo masa d'auki, inda tuni
Naseer ya fara ceto ran sa, ta hanyar rage masa
wasu kayayyakin da ke jikinsa, kamar su hular
kwanon da ke kan sa da sauran su.
Daga nan aka shiga neman ko za'a samu wata
sheda a jikinsa, wacce za ta bayyana ko shi
wanene da insa ya fito.
Cikin aljihun sa Naseer ya zak'ulo wayar
hannunsa, don haka ya fara neman wace lamba
zai kira.
A dalilin bai san kan wayar ba, dannawa na farko
da yayi, sai ga sunan Yakubu Jah-Jah ya baiyana
watau(Dillied numbers) ya shiga, ma'ana Yakubu
Jah-Jah, shine na k'arshen wanda matashin ya
kira a wayar sa.
Kai tsaye Naseer ya kira lambar. Babu jimawa
kuwa ya d'auka,"Hello bros, ka same ni a gida
kawai!"
Naseer ya ce,"Bai mai wayar bane, dama mu na
son mu shaida maka ne, ya fad'o daga doki,
kuma yana cikin wani hali sbd haka ka hanzarta
zuwa nan filin sukuwa."
Cikin tashin hankali Jah-Jah ya
amsa,"Subhanallah!
Ga-ni nan zuwa Insha-Allahu!
"Naseer ya dubi sauran jama'a, ya ce,"Na sami
wani ya-ce yana zuwa yanzu, ina jin d'an-uwan
sa ne." Yana rufe baki,wanda ya ruga neman
ruwa, ya dawo da ledar (purewater), aka bud'a
ana ta fesa masa.
Amma har ya k'are saurayin bai farfad'o ba.
Suna nan jugun-jugun!
Cike da tausayin saurayin."
'Yan-uwan sa suka iso cikin wata mota k'irar
(Honda Civic), nan da nan suka sa shi a mota,
d'aya daga cikin s ya hau dokin yayi gaba da shi,
jama'a kowa ya kama gaban sa, amma shi
Naseer yana tare da su Jah-Jah da shi suka iso
(Zaria Clinic) kuma da shi aka yi ta kai kawo har
majiyacin ya sami natsuwa bisa gadon asibiti.
Likita na duba shi.Yayi matuk'ar auna arziki, don
babu karaya a jikinsa, sai 'yan raunuka da rashin
farfad'owar sa. Sun d'an natsu hankalinsu kowa
ya bar wa Allah al'amarin sa. Naseer ya matso
kusa da Jah-Jah ya mik'o masa waya da wasu
kudad'e kusan dubu hudu da d'ari biyar, ya
ce,"Ga kayayyakin sa, ni na aje sbd sha'anin
mutane, wani da zuciya 2 ya kan zo taimako."
Yakubu yasa hannu, ya amsa tare da duban
Naseer,"Gaskiya ne, kuma mun gode Allah ya
saka da alkhairi. Ya sunan Malamin ne?"
Ya ce,"Naseer suna na."
Fuska cike da fara'a ya ce,
"Ah!
Ashe takwarar maras lafiya ne. Shi ma sunan sa
kenan, kuma k'ani na ne, uwa d'aya uba d'aya."
Ikon Allah, to Allah ya ba shi lafiya, ni zan
k'arasa gida." Ya amsa da amin.
Ya mik'a masa hannu, suka yi sallama. Sannan
yayi sallama da kowa har da iyayen su Yakubun
da ke wajen, ya tafi. Cike yake da al'ajabi tare da
tausayin takwaran na sa.
A lokaci 1 yana jin dad'in had'uwarsa da
mutumin da yake burge shi a duniya, sbd wasan
tseren polo, watau Yakubu Jah-Jah. Tuni ya
mance da damuwar da ke ran sa, ya tsunduma
tunanin yadda zai yi ya k'ulla zumunci da su
Yakubu.
Don shi ma ya sa mu ya kutsa cikin wasan polo,
wanda ya jima cikin mafarkinsa. Yana tafe, yana
addu'a Allah ya cika masa burin sa, idan akwai
alkhairi, babu wanda bai ji lbrn abubuwan da
suka wakana ba, iyayen sa, Sageer tare da Huril-
aininsa Zarah. Haka yake kiranta(Huril-aini),
watau sanyi idaniya.
**************
Da yamma bayan sallar la'asar can ya nufa, ya
tarar da takwaran nasa ya farfad'o, kuma
Alhamdulillah, ya d'an murmure, yana amsa
gaisuwa sosai. Yana isa. Yakubu ya gabatar da
shi ga k'aninsa, domin tuni yake da lbrn irin
gudumuwar da Naseer ya bayar. A nan ya kai
magarib, suna ta hira da Yakubu Jah-Jah.
Washe garei k'arfe 10, ya isa asibitin, bai iske
kowa ba, sai takwaran sa Naseer. Bayan sun
gaisa, ya tambaye shi jikin sa. Ya ce,"Ah jikin an
gode Allah." Zauna mana." Ya ja kujera ya zauna,
yana fad'in"Kai kad'ai ne? Ina yayan na mu?" Ya
ce,"Ka san shi ya kwana, so ya koma gida, ya
d'an huta, sai Mama, ta d'an zaga ne."
Ya ce,
"Ok.Sun d'an yi shiru, na 'yan dak'ik'a kafin
Naseer da ke jingine da filo ya ce,"Ai na ji sauki,
ni yau ma na so a sallame ni, amma yaya ya
hana, wai in dai bari zuwa gobe a tabbatar da
komai Normal." D'an murmushi yayi,"Gaskiya ne,
gara dai ka d'an kwana biyun." Ya ce,"Wallahi
sam na rasa dalilin da yasa hawan doki bai
amshe ni ba, fad'owa ta ta 3 kenan fa."
"Ah!
Haba dai? To saboda me?"
"Oho!
Ni abin ma har ya fita min a rai ko dama yaya ke
matsa min, wai yana son na gaje shi. Ni ina zan
kai wannan wahalar?" Naseer ya kad'a kai cike da
fara'a, "Ni kuma ka san wani abu! Bala'in son
hawan dokin nan na ke yi. Tun ban da wayau na
ke zuwa kallon sukuwa, ai na sha yin hannu da
yayan na mu, ba dai zai gane bane." Ya ce,"Ka ce
za ka zama mutumin yaya sosai, domin shi ido
rufe yake neman masu sha'awar wasan polo."
Zuciyar Naseer tayi fes!
D'oki ya mamaye zuciyar sa.
Ina yanzu Yakubu zai zo ya ce su tafi fili, ya koya
masa sukuwa? Bai gama tunanin sa ba.
Maman ta fito bayi.
Naseer ya tsugunna ya gaida ta, ta amsa tana
mai jin dad'i a ran ta. Kuma kwarai take yaba
Naseer cikin zuciyar ta, tun jiya da ta fara ganin
sa. Wannan
A JININ SA YAKE!
Farin jini ga kowa, duk inda ya kutsa. Allah yayi
wa Naseer wannan kwarjinin. Da ita suka ci gaba
da hira, babu zato sai kiran sallar azahar suka ji.
"Wai har k'arfe 1 ta yi.,"Naseer ya duba
agogonsa, ya fad'a. Ta ce,"Ai babu wai a ciki.
Lokacin ne ya gangaro irin na k'arshen zamani
komai a gurguje, shi yasa kafin D'an-Adam ya
farga, ya cinye lkcn sa a duniya cike da dogon
buri fal zuciyar sa, domin shi yana ganin kamar
jiya aka haife shi.
Mutane k'alilan suke gane kanana alamomin
k'arshen duniya, suna ta tabbata a fili, har su
kan yi k'ok'arin su gyara halayen su, su koma ga
Ubangiji.
Amma da yawa daga cikin mu. Yanzu ne suke
bude sabon faifan cin duniya da tsinke, ta ko
wacce hanya.
Ubangiji ya shiryi zukatan mu ta yadda za mu
gane cewar mun fa kusan zama abin tausayi.
Kwarai mahaifiyar su Yakubu ta kashe jikin
yaran, kowa numfashi ya sauke Naseer ya
ce,"Allah yasa mu dace." Suka ce,"Amin."
Ya mik'e ya ce,"Bari in yi sallah in koma gida."
Shi ma dayan Naseer d'in, ya sakko yana
fad'in,"Mu je ni ma in yi sallar." Suka fita tare, ita
ma Mama alwalar ta shiga yi.A harabar asibitin
suka had'u da Yakubu na fakin. Gun sa suka
nufa suka yi masa barka da zuwa, sannan suka
gaisa da matarsa da ke tare da shi. Shi ma
masallacin ya bi su. Uwar gida kuma ta wuce
cikin asibitin.
Fitowar su masallaci, babu 6ata lkc k'anin Yakubu
ya fesa masa lbrn hirar da su kayi da Naseer,
baki har kunne ya jawo kafad'ar sa, ya ce,"Haka
na ke so Naseer A. Daga yau na sanya maka
Naseer A.
Wannan kuma ya zama B, tunda ragon maza ne.
Insha- Allahu wasan polo kamar ka iya shi. Zan
koyar da kai sukuwa, idan har ka mai da
hankalin ka kwarai, to kuwa zan ba ka mamaki.
Yaushe ka ke son fara zuwa koya?"
Wannan albishir ba k'aramin kid'ima Naseer yayi
ba, ji yake tamkar an biya masa aikin hajji. Bakin
sa ya k'i rufuwa,"Ai ni ko yanzu ka ce in zo mu je
da gudu zan bi ka yaya, domin ni a rayuwa ta, ba
ni da burin da ya wuce min in zama d'an wasan
polo." Yakubu ya ce,
"To yanzu yadda za'a yi, gobe idan Allah ya kai
mu, aka sallami takwaranka, bayan sallar la'asar,
sai mu had'u a fili.
Har wannan kalalan ma sai ya hau ba kyale shi
zan yi ba." Suna dariya Naseer B ya ce,"Kai yaya,
tunda dai ka sami wani Naseer d'in, ba shi kenan
ba. Sukuwar nan fa da zan iya da tuni ina
Kaduna ana fafatawa da ni..............."
"Shiru don Allah!
Nan ka fi auki wajen maida zancen.
Doki kuwa hawan shi ya zama dole yaro." Suka
shiga yi amsa dariya, yadda suka ga ya marairece
baya son hawan doki.
******************
Abin nema ya samu wajen Naseer, mafarkin sa
ya tabbata gaskiya. Yau ga shi a filon sukuwa
bisa doki ana koya masa sukuwa.
Abin ya ba su Yukubu mamaki ganin yadda
Naseer ke sakarwa doki linzami kamar ba hawan
sa na farko ba kenan." Lallai za'a da Naseer,"
Haka Yakuba Jah-Jah ke fad' a zuciyar sa.
Nan take ya dorawa Naseer kyakkyawan zato.
Nan suka wuni filin sukuwa, sai gab da kiran
magarib suka dawo.
A daran ranar, suna tare da Sageer bisa hanyar
su ta zuwa wajen Zarah. Sageer ke fad'in,"Gobe
ne fa za mu fara zuwa shagon koyon d'inki."
Naseer ya ce,"Taf, ai ni gobe tun safe Jah-Jah ya
ce in fito, zai yi wuya zuwa na koyon d'inkin
nan." Sageer ya dube shi,"Ka fasa kenan?"Ya
ce,"Zan iya cewa hakan, don ka san da abin
nema ya samu a guna." Amma kuwa bai kamata
ka fasa ba, kuma a ganina sukuwa ba za ta hana
ka koyon wata sana'ar hannu ba."
Da wutsiyar ido ya kalle shi, ya ce,"Ita sukuwar
ba sana'ar hannu bace? Idan na kware. Yakubu
yayi min hanya manyan su. Allah ya taimake ni, a
na haye." Ya ce,"Haka ne.
Allah ya tabbatar da alkhairi. Ina ganin ma dai
zan bar ka anan, bari in wuce shagon, in yi masa
tuni, ina nan zuwa gobe."
Sarai Naseer ya gane ya yi fushi ne, amma ya
share, ya ce,"To, sai mun had'u." Take nan
Sageer ya yanke hanya, shi kuwa Naseer ya mik'e
zuwa gidan su Zarah.
Zarah na ta wanke-wanke, yayin da Inna ke
tankad'an garin tuwo. Sallamar Naseer suka
amsa, ya shigo da fara'ar sa mai tattare da
albishir cikin zuciyar sa. Sau guda Zarah ta kalle
shi, ta maida kai bisa aikin ta.
Innar ke fad'in,"Ah, d'an Inna." Ya k'araso gabn
ta ya tsugunna,"Sannu Inna, ina yini?" Ta amsa
tana duban sa, sannan ta tambayi mutun gida?
Ya ce suna lafiya.
Ta ce,"To yaya an je sukuwar?" Ya amsa,"Na je
Inna,
kuma Yakubu ya yaba da kamun ludayi na.
Sai a taya ni da addu'a. Allah ya tabbatar da
alkhairi." Ta ce,"Insha-Allahu za mu yi maka d'an
Inna.
Allah yasa ka na da rabo ciki.
"Kullum yana jin dad'in kalaman Inna, kuma har
da hakan ke k'ara masa soyayyar Zarah cikin ran
sa.
Ya amsa da,"Amin Inna."
Sannan ya dubi inda Zarah ke aiki, kanta sunkuye
yake, dad'e duniya bata san da shigowar sa ba,
amma gaba daya hankalin ta ya taru ya koma
inda Naseer ke tsugunne.
Ya juya kan Inna ya ce,"Inna kin san wani abu!
Zarah ta daina gaishe ni, ko sannu da zuwa bata
min, ni ba yayan ta bane? Bata da kunya ko
Inna?"
Murmushi Innar ta yi kafin ta ce,"Wannan kuma
ai tsakanin yaya da k'anwar sa ce, ni na shiga?"
Ta sunkuci kwanon garin ta tayi kicin, ta bar
Naseer nan yana kallon yadda Zarah ke kwad'o
masa harara.
Yana ganin Inna ta shige kicin, ya sunkuci kujera
ya nufi gunta ya zauna.
"Baki da kunya ko? Ni ki ke harara?"
Ta aje kai k'asa, ta ce,"Na ji ka na min sharri ne,
ni ce bn gaishe ka?"Ya ce,"Ai da, da zarar na
shigo gidan nan, ke za ki fara tarba ta.Ni kuma
abinda na fi so kenan kodayaushe in rink'a ganin
fara'ar ki. Idanuwanki suna duba na. Da kin san
irin farin cikin da ki ke sanya ni, da ba ki daina
ba.
To wai ma sbd me ki ka sauya?" Akaikace ta
dube shi,"Ni ina zan sani, ni ma haka kawai na ji
ba ni iyawa."
Ya ce,,"Ni kuwa na san dalili, in fad'i?"
Ta ce,"Fad'i mana."
Ya dubi hanyar kicin.
Inna ta raja'a bisa aikinta.
Sannan ya duk'o k'asa-k'asa ya ce,"Saboda Baba
ya ce ke mata ta ce, ko ba haka bane?" Bata
dube shi ba, ta amsa,,"Yaushe Baban ya fad'i
hakan? Ai ni bn da labari." Murmushi yayi ya
d'an yarfa ruwan d'auraya, don ta zolaye shi,
yayi jim, yana kallon yadda ruwan ke gangara
bisa kyakkywan kuncin ta.
Take nan zuciyar sa ta d'auki zugi, sbd tsabar son
da yake wa Zarah. Jin yayi shiru yasa ta bude
shi.
Yanayin da yake zahiri ya nuna ya shagala, d'an
murmushi ta yi, da gangan ta tsunduma kwanon
da ta wanke cikin ruwan daurayar, ruwan ya
fantsale har bisa fuskar sa.
Yayi lallausan ajiyar zuciya, sannan ya lumshe
ido, ya bud'e a natse yake fad'in."
"Kin rama ne?
Kamar ma ba ita ta aikata ba, ci gaba ta yi da
aikin ta. Ya d'auraye kwanon ya kife mata shi."Ba
ki ganni a doki ba yau." Ta ce,"Na gan ka mana."
Ya k'ara duban ta, kamar yaya? Biyo ni ki ka yi?"
Ta karkada kai," A raina na ke ta aiyana ka, ka
tsere Yakubu Jah-Jah.
JUMAT KAREEM
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Ajininsa yake 1-05
Posted by ANaM Dorayi on 11:18 AM, 06-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
.
." Ya ce,"Wane ni, rufa ni ki saya." Ta ce,"Ai na
san yayana ba shi da wasa, yau da gobe za'a kira
ka Jah-Jah.
Ta d'an dube shi,"Ko ba haka ba?"
Yana murmushi ya amsa,,"Komai ya fito bakin ki
alkhairi ne, Insha Allahu don haka nace haka d'in
ne." Ta ce,
"To Allah yayi yagora."
Ya ce,"Amin."
Ta jima da gama wanke-wanken yana yi mata
d'auraya. Amma suka ci gaba da zama wajen
suna hirar har gob da kiran magariba. Sannan ya
sallami Inna ya koma gida.
Sati 2 sun yi wa Naseer yawa, domin a cikin 'yan
wad'annan kwanakin ya kasance sai Yakubu yayi
da gaske yake tsere masa bisa doki.Ba k'aramin
mamaki ya ba kowa ba, musamman Yakubu da
k'anin sa Naseer B. Haka ya burge abokinsa
Sageer da Zarah, ranar da suka ziyarce shi a filin
sukuwar, don ganin yadda atisayen ke tafiya.
Tabbas Naseer gwarzo ne kuma Allah yayi masa
baiwa cikin jinin sa.
Safiyar lahadin yau, ita ce ranar da Yakubu ya
ajiye, don gabatar da Naseer ga uban gidansa a
Kaduna, sbd sosai ya tabbatar da Naseer ba zai
ba shi kunya ba.
Tsaf! Naseer ya kammala shirinsa, ya fito cike da
albarkar iyayensa.
A k'ofar zaure suka had'u da Sageer tare suka
gangaro har zuwa marabar da za ta kai Sageer
shagon da yake koyon d'inki. A nan su kayi
sallama Naseer ya wuce gidan su Zarah. Suka yi
sallama da juna, don bai iya wucewa, ba tare
daya salleme ta ba.
Nan ma ya sami k'arin addu'a daga iyayen ta.
Sannan kai tsaye d'an acaba ya aje shi k'ofar
gidan Yakubu Jah-Jah da ke Tudun-Jukum.
Babu 6ata lkc suka damki hanyar Kaduna, cikin
motar Yakubu.
A cikin tafiyar awa 1 kacal!
Suka iso k'ofar katafaran garejin siyar da motoci
wanda yake d'auke da sunan (DABAI MOTORS'!
Cikin kallon tsoron da Naseer yayi wa garejin, yayi
zaton akalla akwai sababbin motoci na gani, na
fad'a sama da 200.
Domin kuwa motoci ne fululu!
Wannan na zagin wancan.
Yakubu yayi masa jagora zuwa 6angaren ofishin
wajen inda suka fara magana da sakataran sa,
wanda a fili ya nuna sun jima da sabawa da
Yakubu.
Nan take ya sada su da ogan sa.
Tare da sallama suka shiga k'aton ofishin daya
amsa sunan ofis.
Kyakkywan Alhajin wankan tarwada na zaune
bisa lafiyyar kujerar sa. Sanyin A.C na ratsawa ta
ko'ina cikin ofishin gwanin dad'i.
Cikin fara'a da walwala ya amsa sallamar su,
sannan ya ce,"Yakubu kun iso?
Bismillah ku zauna mana."
Kujera 2 da ke gabn d'in, su Yakubu ya jawo ya
nuna wa Naseer ya ce ya zauna.
Duk sun natsu a zaune.
Shi dai Naseer haryan muzurai yake yi irin na
bak'unta.
Sun kwashi gaisuwa cikin girmamawa, haka shi
ma Alhj ya amsa yadda yakamata.
Daga nan Yakubu ya ce,"Alhaji wannan shine
Naseer, ina fatan babu wata matsala."
Yakubu ya amsa,"Insha Allahu ba na haufi a kan
sa, sai dai ka gani da idon ka.'a
Murmushi Alhj yayi, sannan ya ce ,"To shi kenan,
ina son k'arfe 2 mu had'u a fili."
Ya juya kan Naseer ya ci gaba,"Naseer, ka saki
jikin ka, za mu had'u k'arfe 2 a fili, don ganin
yadda ka ke gudanar da sukuwar ka.
Ba wani abu. Sai mun had'u d'in ko?"
Ya ce,"Shi kenan Alhj. Na gode."
No problem." Alhj ya fad'i yana jawo dirowar
gaban sa. Makullai ya d'auko, ya mik'awa
Yakubu,"Don Allah ka tabbatar da su Musa sun
dawo da dawakan nan guda 3 akan lkc. Kuma a
ba su abinci a kyale su su huta."
Ya ce,"To Alhj. Muna iya tafiya ko?" Ya ce,
"Yes,
ai ina ganin babu wani abu, idan ma akwai.
I will call you."
Ya amsa da,
"O.K Sir."
Suka mik'e suna fad'in,"Mun bar ka lafiya," Sun
kai k'ofa.
Alhaji ya sake kira,
"Naseer!"
Ya juyo da sauri tare da amsawa.
Ya ce,"Kar fa ka ji komai, cikin ranka, tunda
Yakubu ya yarda da kai, ni ma na amince da kai.
Kawai gwaji ne, don in gani da ido na."
Naseer yayi murmushi, kafin ya ce,"Babu komai
Alhj. Ai gwaji dole ne a ko'ina haka k'a'idar take
na gode kwarai."
Shi ma Alhj murmushin yake yi, yana duban
Naseer, sannan ya ce,"K'arfe 2 insha Allahu."
Yakubu ya janyo kafad'ar Naseer yana
fad'in,"Allah ya kai mu lafiya."
A haka suka bar ofishin.
Cikin mota bisa hanyar su ta zuwa bargar
dawakin Alhj. Naseer cike yake da farin ciki tare
da doki cikin zuciyarsa.
Kwarai ya k'osa karfe 2 tayi su hadu da Alhj a
filin sukuwa.
Yakubu ya dube shi ya ce,"Ka ga oganmu ko?" Ya
amsa,"Kwarai na gan shi, da gani kuma Alhj zai yi
saukin kai."
Ya ce,"Kwarai kuwa. Alhj Basheer Rufa'i Dabai
kenan. Wanda ya gaji d'umbin arziki daga
mahaifinsa Alhj. Rufa'i Dabai. Su 2 ne shi da
kanwar sa, ita tana Jordan tare da mijin ta. Yayi
aiyukan gwamnati da dama. Daga baya ne ya aje,
ya ci gaba harkokinsa na kasuwan cin da ya gada.
Bayan wannan garejin motocin, yana da wani a
Mando, wanda ake siyar da manyan motoci zalla.
Yayi k'arfi sosai a harkar polo, dan kusan zan iya
ce maka duk Arewa babu club din da ya kai na
sa ingattatun dawakan polo.
In dai ana maganar polo, idan aka ce maka
(DABAI RIDERS), to anyi maka kankat! A gaskiya
na ci gajiyar Polo kuma babu abinda zan cewa
Alhj. Sai Allah ya saka masa da alkhairi. Shi ya kai
ni Makka, yayi min aure, ya ba ni gida. Sau 3
yana can zamin mota. Da zarar ya ga ta tsufa, ta
soma ba ni matsala, zai sa aban wata. Saboda
haka na ke son ka kwantar da hankalinka, ka
natsu ka nunawa Alhj Jarantakarka. Insha Allah
wata rana za kayi dariya.
Naseer ya cire tagumin daya zabga, ya sauke
numfashi, kafin ya ce,"Lallai yayaka mori Polo.
Allah yasa muna da rabo muma.
Kuma yarda Allah ba zan ba ka kunya ba." Yayi
yar dariya ya ce,"Ai na sani kai ne Naseer Jah-
Jah."
Ya ce,"Me ake nufi da Jah-Jah?" Alhj. Ya soma
lak'aba min.
Da zarar na hau d'oki, shi kuma ya shiga yi min
kirari kenan,
Jah! Jah!!
Mu je Yakubu!
Ina jin dad'in kirarin Alhj, Sannu a hankali sunana
ya zamana ba'a kiran sa zalla, sai an lak'aba Jah-
Jah."
Ya ce,"Gaskiya ne, ba kai kad'ai ba, ni kaina
kirarin yayi min, tun ina yaro k'arami na ke
begen sunan."
Dariya Yakubu yayi.
Shi kuwa Naseer tambaya yake," yayansa ba sa
yin Polon?"
Ya amsa,
"Ai 'yar sa guda 1 ce a duniya, tana ma can
Jordan tare da k'anwarsa can take karatu.
Kawai tausayin Alhj ya ji ya kama shi.
Shi yasa ya ce," Allah Sarki, yanzun duk dukiyar
nan 'yarsa 1?
Allah ke nan." Ya ce,"Wallahi kuw.
Oh, har ta shiga jama'i. Nusaiba sunan ta, ni na
ke kiran ta Baby N. Tana ce min Jah-Jah, kamar
ita ta rad'a min sunan. Gaskiya yarinyar na da
tarbiya ga ilimi. Shekarunta 15 ta sauke Kur'ani,
ga sanin harshen larabci ko yanzu ma abinda
take karantawa kenan a can Jordan din "Arabic
and Islamic Studies)."
Naseer ya nisa, ya ce,"Amma ya kyauta daya
banbanta da wasu masu kudin ko kuma in ce
wasu 'yan boko ma sun maida kan su tamkar
Yahudawa, saboda takamar abin duniya." Ya
ce,"Ai Allah ya taimake shi,"Ubangiji ya k'ara
shirya mana zuri'a."
Naseer ya amsa da Amin."
Ba k'aramin mmk Naseer ya sha ba bargar
dawakin Alhj Basheer, domin dakawai 12 ke
harbin iska, sun kai sun kawo a girma da koshin
lafiya. Ya kubu ya zaga da shi ko'ina tare da
gabatar da shi ga jama'ar da suka iske a wajen.
Daga bisani Yakubu ya bude wani k'aton falo
mai kunshe da kayan alatu, kuma da gani an
tanade shi ne, don hutawa da gudanar da taro.
Anan suka zauna. Yakubu ya ci gaba da gudanar
da aiyukkan sa, kamar yadda Alhj ya umurce
shi, ko kuma ana iya cewa ya saba yi a
kodayaushe.
K'arfe 2 bayan salar azahar. Su Naseer na filin
sukuwa, ba jimawa Alhj Basheer ya iso cikin
tsaddadiyar Jeep din sa. Bayan sun kwashi
gaisuwa, sai suka rankaya wajen da wasu yara
ke rike da dawakai guda 2. Naseer ya hau 1.
Alhj ya ce Musa daya daga cikin yaran sa ne, shi
ma ya hau 1. Suka dai-daita sahu, kafin Yakubu
ya hura usur, watau ya ba su umurni tashi. Alhj
Basheer ya sha mmk, domin Naseer yayi wa
dokin Musa Fintak'au!
Wanda shi ma Musan yana 1 daga cikin wanda
suke taka rawar gani a (DABAI RIDERS).
Alhj ya dubi Yakubu, ya ce,"Za'a da Naseer,
gaskiya shi ma yana Jah. Kuma kawai yaron ya
shige min rai, tunda ku ka tafi, na ke ta tunanin
sa." Yakubu yayi murmushi, ya ce,"Haka
ne,"Naseer na da hazak'a ba k'aramin mmk zai
bayar ba, nan gaba, idan ya k'ara gogewa."
Yana rufe baki. Dokin Naseer na isowa. Ya ja ya
tsaya gaban su Alhj.
Alhj da kan sa ya rik'e masa, ya sauka,"Good!
Sukuwa tayi yadda ake so Naseer. Saura mutum
1 na ke so ku kara.
Ina Dogara?
Yakubu kira shi ya hau doki."
Kowa ya san Dogara, shi yake rufa wa Yakubu
baya, kuma shine na 2 cikin wadanda Alhj
Basheer ke ji da su ko'ina."
Amma ko alama gaban Yakubu bai fad'i ba, da
kiran Dogara. Domin yana da yakinin Naseer zai
iya karawa da shi kan sa Yakubu."
Don haka kai tsaye ya kwala wa Dogara kira.
Daga gefen da suke tsaye.
Ya baro sauran, ya iso gun su Alhj.
Alhj ya ce ya hau dokin da Musa ya sauka.
Cikin ji da kan sa ya kama doki ya d'are, kamar
yadda Naseer yake tsaf!
Bisa na sa.
Suka ja sahu. Yakubu ya bada umurnin tashi.
Kowa ya baza wuta, suka sakar wa dawakai
linzami. Me zai faru? Kafin wani lkc Naseer ya
6ace 6at!
Sai k'ura.
Duk Jama'ar wajen shewa suke yi.
Alhj kuwa rungume hannayensa yayi ya kasa
cewa komai, amma cikin zuciyar sa ba karamin
alfahari yake yi ba da samun Naseer.
Musamman ganin Yakubu ya fara manyanta,
yana buk'atar hutu nan d'an lkc k'ank'ani.
Bai gama tunanin dogon burin da ya d'ora akan
Naseer ba, Naseer din ya iso cikin sassarrafa ya
diro.
Yakubu ya rungume shi. Duk Jama'ar wajen
suka yayyame shi ka dauka gasa ce ake yi.Alhj.
Ya kamo kafad'un sa, ya juyo sosai ya dube shi,
bakin sa har kunne. Alhj ya mik'a masa hannu,
suka yi musabaha, sannan ya ce,"Welcome to
DABAI RIDERS.Daga yau ka zama Naseer Jah-
Jah." Dai-dai lkcn da Dogara ke k'arasowa
wajen, gaba d'aya jikinsa babu kwari kamar an
zare masa laka. Duk 'yan wasan da ke wajen sai
hannu suke ba Naseer suna taya shi murna don
haka shi ma Dogara yi mika masa ya
ce,"Congrats."
"Na gode."
Inji Naseer yayin da shi tuni Dogara ya bar
wajen dauke da wata irin hassada cikin zuciyar
sa.
To ai dama haka D'an-adam yake, tara ne bai
cika goma ba.
Duk inda ka kai ga dumbin masoya, dole ne ka
sami wanda a rayuwa ba ka yi masa ba.
Wani lkcn kuma zai iya zama hassada.
Muna iya cewa zuciyar Dogara ta shiga wani
garari na musamman take yanzu akan Naseer,
ganin yadda Alhj yayi maraba da shi, domin
burin sa duk lkcn da Yakubu ya zama tarihi a
(DABAI RIDERS), to shine zai maye gurbinsa. Sai
ga shi da rana tsaka wani ya zo daga sama
kuma take yanke Alhj ya kira shi da Jah-Jah.
Suna mai tsada da muhimmanci a gun Alhj
Basheer.
Lallai Naseer yayi wa Dogara shigar sauri a bisa
dukkan alamu kuma ya zama kishiryarsa, sai dai
ce Allah ya tsare sharrin shaid'an.
Ba kankanin farin ciki Naseer yake ciki ba, a
tarihi rayuwar sa kaf!
Yana jin ba shi da wata rana da ta fiye masa ta
yau. Don haka ne ma yake ganin ba shi da wata
kalma wacce zai yi wa Yakubu godiya da ita,
balle Ubangiji daya nufe shi, ga kai wa wannan
matsayi da ke cikin ran sa, ga cimma wannan
matsayi da ke cikin ran sa tun yana yaro
karami.
Saboda haka ya kara kaimi fiye da ko wace
rana, don ganin ya ba maras da kunya.
*******************
Kafin shekara 1 Naseer ya wuce duk inda
tunanin mai karatu zai kai a duniyar wasan
polo. A kowane lungu gabas da yamma kudu da
arewacin Nijeriya. Dole ne ka ji sunan
Naseer
Jah-Jah
a bakin masoyan wasan tseren polo. Wannan ba
karami matsayi ya samawar Naseer ba a cikin
zuciyar Alhj Basheer.
Wanda ta kai ga akan dole Dogara ya sakar wa
Naseer ragamar (DABAI RIDERS), ya tattara
kayan sa ya canza sheka, don ba zai iya ganin
irin gatan da riritawar da Alhj Basheer yake wa
Naseer ba.Ana iya cewa ko Yakubu bai sami
irinta ba. Domin ko kafin Naseer ya hade
watanni 6 a wasan Polo. Alhj Basheer da kan sa
ya nemi sanin mahaifin Naseer kuma ba 6ata
lkc, ya kulla zumunci da shi mai karfi gaske.
Sanin mahaifin Naseer Malam Balarabe, ba mai
karfi bane, shi yasa Alhj ke yawan yi masa
alkhairi akai-akai. Kwarai a halin da ake ciki
yanzu Malam Balarabe yana alfhari da Naseer
kuma yayi imani a polo abincin Naseer yake. Shi
yasa Allah ya shimfida masa so da kaunar
sukuwawan da shi a da yake ganin ba karamin
saba masa yake yi ba.
Sai dai duk da haka yana yi wa dan sa huduba
da kar ya mance da ci gaban karatunsa, kamar
yadda kullum Sageer da Zarah tare da iyayen ta
ke masa matashiya akan gyara jarabawar sa,
don ci gaba da karatunsa na gaba. Amma shi
dan gogan ya riga ya raja'a akan abin da ya sa
gaba, Kuma yake da buri a kan sa. Ko alama
baya waiwaye, wanda hausawa ke wa kirari da
adon tafiya.
Inda ya sa gaban sa, kawai can yadosa bil hakki
da gaskiya.
A yan tsakanin ne kuma Sageer yayi nasara
samun gurbin karatu a (poly) da ke Gaskiya,
Tudun-Jakun Zariya, a fannun kasuwanci
(Businees Admin).
Baba 6ata lkc, ya kama karatun zango-zango,
kuma abn mmk duk tare da gudumuwar aljihun
Naseer karatun na Sageer ke tafiya.
Bayan haka bai daina zuwa wajeb dinkinsa ba, a
halin yanzu ma ya kware babu irin dinkin da ke
gagaran sa, ta nan ma baya rasa taro sisi, duk
da dai ogan sa, bai yaye shi ba. Yana nan tare
da shi.
Haka al'amuran suka rinka tafiya dai-dai da
yadda Allah ya shirya wa kowa rayuwar sa.
Soyayya tsakanin Alhj Basheer da Naseer kuwa
kara shiga ran Alhj take yi tamkar yadda Naseer
ke kara fito da (DABAI RIDERS) a duniyar Polo
ciki da Wajen Najeriya, watau kasashe
makwantan mu.
Tuni Yakubu ya sakar wa Naseer kambunsa
gaba 1, yana mai alfaharin shi ya kawo wa Alhj
gwarzon Da, wanda yake ganin ma ya na taka
rawar da shi bai taka rinta ba.
Shi yasa kullum kirarinsa da babbar murya yake
masa,
"NaseerJah-Jah!"
*****************
. BAYAN SHEKARu BIYU.
A cikin shekarun biyun nan, ba sai mun tsaya
dogon surutun irin tambarin da sunan Naseer
Jah-Jah yayi a duniyar Polo ba.Musamman a
cikin garin su da unguwar su, idan aka yi
la'akarin da irin kwarjinin sa tun farko, balle
yanzu daya kasance duk wanda ya dube shi, ya
san yana hutawa,kuma yana kan lokacinsa,yayi
fad'i, ya yi zabgege, ya k'ara fari da ka ganshi,
ka ga d'an wasan motsa jiki. Maganar kyau da
iya shiga irin ta sutura, abin ba dama, domin
Naseer ya dad'e da gogewa wajen iya tsafta.
Don haka ya zarce wa tsara.
Ya zama abinda bature ke kira (TALK OF THE
TOWN), wato abin hira a gari.
Ta yadda ya tsara rayuwar sa. Abin ya na da
ban sha'awa, saboda babu girman kai, babu
wulakanci kuma abin hannu sa bai tsokane
masa ido ba. A duk lokacin da yake gari, za ka
ga samari na yawan sintiri gidansu.
Can kuma 6angaren tauraruwar sa, komai tafiya
yake dai-dai da ci gaban da aka samu, domin
kusan a yanzu Naseer shine ragamar karatun ta.
Bai kyashin kashe ko nawa ne a dangane da
hidimar Zaran sa.
Wani abin sha'awa da ya fi kowa, a cikin
gidansu yake shirin fitar da wani gini mai bn
mmk. Kasancewar gidan k'aton gaske ne, ko
dama rashin kud'i ne yasa yake a wulak'ance.
Tuni aka fitar wa iyayensa 6angarn su. Shi kuma
na sa 6angaran aka shimfida filat mai d'akuna
3. Ba shi da buri daya wuce ya tsara wa Zarah
abubuwan da zai fiddo ta daga cikin tsara,
tunda ga shi Allah ya ce su huta."
Kwatsam!
Allah da ikonsa sai ga takarda daga k'asar
Ghana zuwa (DABAI RIDERS), suna neman izinin
d'aukar Naseer haya na wata 1, don gudanar da
wasa a wata kungiyar wasan Polo da ke can
Ghana.
"Al'amarin yayi wa kowa dad'i.
Musamman Alhj Basheer da Yakubu kuma babu
6ata lkc.
Alhj ya amince masa da tafiyar, babu wani
sharad'i ko wata tsatstsaurar doka.
Ranar tafiyar sa, yayi sallama da kowa, sannan
ya nufi gidan su Zarah. Tana zaman jiran sa,
kamar yadda ta san yana tafe. Kallo daya yayi
mata, ya gane hankalin ta a tashe yake, ya
karkade kai ya ce,
"Wai ke ba za ki daina wannan kuncin ba?
"To ko in fasa ne?"
Ta ce,"Kasan ban isa in hana ba."
Da sauri ya tari numfashin ta."
Kina ganin ba ki isa ki hana tafiyar nan ba?
Lallai za ki sha mamaki, idan aka wayi gari gobe
ki ganni a garin nan.Me zan samo a Ghana,
wanda ya wuce farin cikin ki?
Look Zarah!
Ina ganin ke har yanzu ki na daukata a
matsayin yayanki ne, ba ki san cewa akwai
banbnci ba.
Wallahi, kin ji na yi miki rantsuwa ko? Muddin
ba ki saki jikin ki akan tafiyar nan ba, zan fasa
ta, kuma babu wanda zai sani dole. To kila ko
su Abba su cika min ido.
Ta numfasa ta ce,
"Wai!
Ai kuwa na gode Allah, tunda akwai su Abba,
don na san zai wuya inji sanyi a raina, bayan na
san yaya na zai bar ni tsawon wata 1, "Alhali
ban saba ba."
"Dan murmushi yayi, kafin ya ce,"To ai ba zan
bar ki haka kawai ba, kin ga wannan?
Sabuwar wayar ki ce dalilin siyan kawai don
murinka sanin halin da muke ciki ne,
kodayaushe. Amshi nan."Ta saki baki tana kallon
kwalin rantsatstsiyar wayar da aka ce tata ce a
lkcn 1, kuma tana tambayar kanta yaushe
yayana ya siyo min NOKIA ta hannu na?"
"Kin amsa na ce, ki ka baje min ido, ki na kallo
na." Tasa hannu ta k'arba,"Amma dai yayana ka
na son kashe kudi, ita wannan Sabis d'in bai
zuwa Ghana ne?"
Dariya ta sake ba shi, ya ce,"Ina jin hakan a jiki
na, zuciya ta na gaya min tana gargadina da
cewa kai Naseer kar ka bar Nijeriya, ba tare da
ka sakewa k'anwar ka sabuwar waya ba, don ka
san ta hannunta ta shekara."
Zai iya kasancewa ta fara bada matsala. To kin ji
dalili,
da a sami matsala,
gara ayi wa tufka hanci.
Ko me ki ka ce?"
Ta d'an rausaya kai cike da mamakin yayanta,
ta ce,
"Godiya kwando-kwando yayana.
Allah ya k'ara bud'i."
Bai amsa ba.
Wayar sa ta hau ruri, ya jawo ta cikin alhu ya
duba lambar. Alhj Basheer ne, kamar yadda
yake a rubuce cikin wayar (Alhaji). Ya dube ta ya
ce"Mintu 2, "Sannan ya danna Ok."
Suna magana da Alhj.
Amma ita Zarah kallon sa take yi, kasancewar
hankalin sa ba ya gunta. Sai ta sami damar kare
masa kallon da ta jima da mancewa da ranar da
ta yi masa irin wannan kallon.
Nan take zuciyar ta, ka karan ta mata ba
k'aramar sa'a ta yi ba, da samun Naseer.
Kwarai ta tantance Naseer watanne, tamkar
yadda take Zarah.
Anya kuwa 'yan mata za su kyale mata Naseer
d'in ta ita kad'ai, yadda ya shiga yana fita gari
da kashashen duniya da irin wannan baiwa da
Allah yayi masa???"Nan da nan kishi ya rufe ta,
idanuwanta suka fara kad'awa, sannan kafe
suke tana kallon sa, ba tare da ta san tana yi
ba.
Kusan minti 2 da kammala wayarsa. Shi ma yayi
zurun yana maida martani.
Ganin idanuwan ta sun fara ja, shi yasa ya
murza yatsunsa biyu, suka yi k'ara bisa fuskar
ta. Cikin kunya ta sunkuyar da kai. Sai kuwa
tambaye yake,
"Menene?"
Ta ce, "Ba komai."
Kin san Allah, ban yarda ba, kuma ba zan bar
wajen nan ba, sai kin gaya min ko menene ki ke
tunani." Ta riga tasan halin yayan na ta, don
haka ta d'an dube shi, ta ce,
"Mata na zuwa kallon polo a Ghana?"
Tambayarta ta d'aure masa kai, kuma take ya
gane me take nufi. Amma sai ya nemi sanin
dalilin tambayar ta,
"Me ya sa ki ka ce haka?"
Sannan ba ki ta6a tambaya ta hakan ba, sai
yau?
Shiru tayi, ta rasa bayanin da za ta yi, don ita
ma ba'a son ranta tayi masa tambayar ba.
Jin tayi shiru tsawon 'yan dakikai, shi ya sa ya
ce,
"Zarah, dube ni nan."
A karkace ta dube shi, jim ta sauko ido.
"Zarah, son ki ba karya bane a ciki rai na.
Kar ki mance, tun bn san me zuciya ta ke nufi a
game da ke ba, har na gane so da kaunar ki na
ke yi.
Ma"anar tun yarinta, har zuwa sanin ciwon kai
na, ban jin akwai abinda zai cire min soyayyar ki
Zarah. Don kin jima cikin raina shekaru masu
yawa.Saboda haka ki kwantar da hankalinki, ni
yayanki nai miki alkawarin har abada ke kadai
ce, ba kari balle maganar canji. Kin ga zancen
mata na zuwa kallon Polo ko ba sa zuwa, duk
ba matsala da ta shafe mu bace.
Kin amince?"
Kad'a kai tayi, ta d'an nisa kafin ta ce,"Na gode
yayana, amma maganar k'ari, ka na nufin babu
zancen kishiya?" Da sauri ya amsa,
"Nufe na kenan Zarah.
Kin isheni rayuwar dauniya, domin komai na ki
yayi min yadda ra'ayina ke buk'ata."
Wannan karon ta kalle shi ido ciki ido, sannan ta
ce,
"Ban ji dad'in wannan maganar ba yayana, don
ka shigo hurumin da ba na ka ba.
Wannan hukunci ne na Ubangiji, wanda bai
kamata ko ma ince bai halasta ko wane D'an-
adam yayi shishshigi a cikin sa ba.
Ka ga dai........."ya katse fuska daure,
"Me ki ke nufi?
Na yi miki k'arya kenan?"
Ta ce,"Ban ce ka min karya ba,
amma magana ta gaskiya, duk macen da aka yi
mata alkawarin ba za'a yi ma ta kishiya ba, ta
yarda ta amince.
A hakikanin gaskiya ta yaudare zuciyar ta.
Don shi aure al'amari ne na Allah, tamkar
haihuwa da mutuwa.
Ubangije ne kadai ya san yadda ya shirowa
bawan sa rayuwa.
Shi yasa na ke ganin bai halasta masoya su
rinka yi wa junansu ko wane irin alkawari a
hurumin da ba na su ba.
Ina fatan yayana ya fahimce ni....?
Tun da take mgn, yake kallon ta, sai dai laffuzan
ta kawai ke sosa masa rai.
Bai kamata ta ki amincewa da shi ba,
don shi hakikanin gaskiyar sa ya fad'i.
Kenan duk son da yake nuna mata karya ne.
Nan da nan ya hassala.
Mikewa yayi ya sungumi jakar sa da ke gefe ya
ce,
"Allah ya sa mugana."Ita ma ta mike,"Yayana
fushi ka yi?" Tuni ya kai kan sa tsakar gida.
Inna na zaune kofar dakin Malam Umar can ya
nufa. "Inna na fito."
To dan Inna.
Allah ya kiyaye, ya tsare mana kai duk inda ka
ke." Sai ga M.Umar ya fito wanka, yayin da
Naseer ke amsawa da "Amin Inna."
"Har ka fito?"
Inji M.Umar.
Ya amsa,
"Eh,
"Baba."
"Madalla-madallah,
to Allah ya ba da sa'a.
Sai a kiyaye da ibada, ita ce gaba da komai, ka
ji?"
Ya ce,"To Baba na gode.
Na bar ku lafiya."
Ya wuce suna ta sa masa albarka, kafin Inna ta
ce,
"Ke ba za ki k'ar6ar masa jakar bane, ki raka
shi?"
Ta wuce da sauri ta bi shi, tana fad'in,"Kawo
jakar yayana."
Kamar ma bai ji ta ba, ya shige zaure abinsa.
Da gudu ta karaso zauren, haba yayana, bai
kamata ka yi saurin fushi haka ba." Ya juyo a
fusace, har ta ji tsoro a zaton ta duka zai ka
mata, ganin yadda ya nuna ta yana fad'in
"Ki koma!
Allah kar ki biyo ni, na gaya miki!
Kin ji ko?"
Ya juya ya fice daga zauran.
Tayi tsaye cikin zauren shiru, idanuwan ta suka
kawo kwalla.
Menene abin fushi a bayanin da ta yi?
Don dai ba'a son gaskiya?"
Ai kuwa wannan maganar haka ta ke yayana, ko
ka ki, ko ka so ba zan yaudari kai na ba.
Alhalin na sani kai mijin mace 4 ne."
Ta fad'a a ranta.
Wanda ya k'ara birkito mata da wani salon kishi,
har ya tilasta mata tsiyayar hawaye.Kusan minti
2 tayi a tsaye, sannan ta goge fuskarta da kyau
ta dawo cikin gida.
Daki kawai ta shige, ranta in yayi dubu, a 6ace
yake.
Shi ya sa ma ko sake kallon sabuwar wayar daya
kawo mata ma bata yi ba, illa iyaka, ta bar nan
tsakar daki, har Inna ta shigo ta gani.
*********************
Kwana 2 kenan da tafiyar Naseer Ghana, amma
babu motsin sa. Ko alama Zarah bata cikin
sukuni, kuma yayan na ta ya bata mamaki.
Wannan irin fushi haka, daga gaskiya?
Zaune kawai take cikin ajin su, duk sauran
dalibai na ta harkokin su a dalilin tashi (Break)
din da aka yi.
Amma ban da ita.
Tunani ya addabe ta, ko alama ta kasa tantance
me shirun Naseer yake nufi?
Shin yana son ya nuna mata cewa dole sai ta
yarda da ra'ayin sa ne?
Ko kuwa so yake ya tilasta ma ta sakin na ta
hangen?
Ta nisa tana mai tsananin kewar yayanta,
saboda ta tabbatar da shi ma yana cikin
yanayin da take a halin yanzu, kuma ta yarda ta
amince ko bayan sun yi aure, ya ce zai k'ara
wani, ba wai ya na nufin ya daina son ta bane.
Son ko wacce mace, na tasiri ne a zuciyar
mijinta dai-dai da yadda ta zauna da shi.
Duk da dai akan sami akasi ta ko wane 6angare,
a sami rashin jituwa tsakanin ma'auranta, idan
ba'a kai zuciya nesa ba, sai ka ji ana cewa a
rabu. Amma magana ta gaskiya, ita ce so yana
tafiya dai-dai da rikon amanar zaman tare.
Yarda da juna, kyautayawa ta kowace fuska,
hakuri da juriya.
Duk ma'auratan da suka mallaki wannan,
shakka babu za su ci ribar zamantakewar auren
su. Musamman mu mata da muke zama a
karkashin mazajen.
Sai ki ga ko mata nawa ya ajiye, ba zai ta6a
daina ganin kimar ki ba, a idaunsa.
Sai dai miji butulu maras tsoron Allah.
Zarah ta yarda ta amince da wannan, saboda
haka take ganin ba za ta iya sakar wa Naseer
jayayyar da suke yi ba.
Kan ta a kife yake bisa tebur yayin da take
rattafo wannan dogon tunanin.
Sallama kawai ta ji bisa kanta, ta dago da suri
ta dubi masu sallmar.Wasu kyawawan 'yan
mata su 3 ta gani a tsaye, suna mata murmushi.
Ta zauna sosai, ta ce,"Sannun ku."
Dukkansu suka amsa, kafin guda ta ce,"Don
Allah tambaya muke?
Ta ce Allah yasa na sani.."
Ta ce,
"Ke ce Zarah?"
"Eh
ni ce."
Mai magana ta ci gaba,"To ni sunana Lubabatu,
sai kawaye na.
Wannan Hauwa'u, waccen Maryan, dukkan mu
muna S.S.3.
Muke,......
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Ajininsa yake 1-06
Posted by ANaM Dorayi on 02:00 PM, 07-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
.may be ko ki na ganin mu anan."
Ta karkada kai.Bisa teburin Lubabatu ta haye,
kafin ta ce,"Dama abinda ya kawo mu, kin gane?
Kawai ance yarinyar da Naseer Jah-Jah zai aura
tana cikin school din nan.Shi yasa muka ce ya
zama dole mu ganki, sbd mu Fans d'in sa ne.
Ina fatan kin gane.?
Zarah ta dube su dai-dai ta ce,"Na gane kuma na
gode."Maryam ta ce,"Kuma wallahi kun dace, dan
ke ma kin mana."
Hauwa'u ta amshe,"Gaskiya ne, amma duk da
haka kin yi da ce, so handle him with care, kin
san yaron yana kan lkcnsa."kan Zarah ya d'aure,
ta rasa ta cewa ko dama ita ba mai yawan
magana bace ko cikin ajin su, ba da kowa take
magana ba.
Shi yasa 'yan ajin suke ganin kamar tana da
girman kai.
Saboda kyan da take da shi.
Alhali ba haka bane, haka Allah ya halicce ta.
Jin tayi shiru, yasa Lubabatu ta diro daga tebur
ta ce,"To mun gaishe ki, mu za mu ari na kare.
Muna S.S.3, in case ko za'a gaisa."Maryam ta
amshe,"Ai ko bata zo ba, mu ya zama dole mu
rinka zuwa muna duba ta, a madadin sa, kin san
an ce ya fasa
"Ghana.
" Haka."
Inji Lubabatu,
"To sai kin sake ganin mu."
Ta ce,
"Shi kenan,
na gode,"
Suka wuce ta bi bayan su da kallo har suka bar
ajin.
Tagumi ta zabga, tunanin ta ya dawo sabo, don
'yan matan sun firgita ta kwarai.
Ashe ma anan kusa da ita tana da abokan
hamayya bata sani ba?Shine Naseer yake son ya
cusa mata wani ra'ayin da ba shi yuwuwu ?
Bayan bata ma san meke faruwa a wasu wurare
ba.
Tsoro ya kama zuciyar ta, ba na wasa ba.
Shi yasa ta aje a ranta, zai yi wuya Naseer ya
kasance na ita kad'ai har abada, kamar yadda shi
yake hasashe.
A susuce ta kasance zuwa tashi gida.
Ko a gidan ma tunanin ta bai sauyawa ba.
Saboda ya kamata ace ta san halin da yayanta
yake ciki a k'asar Ghana.Kwanan sa 5, babu
bayani.Abin ya gagari zuciyar ta, ga shi har su
Inna sun fara tambayarta labarin yayan na ta.
Cikin shagon d'inki ta iske Sageer da safiyar yau
lahadi.abin ya ba Sageer mmk kwarai, jin cewa
wai Naseer bai kira Zarah sa ba, tun tafiyar sa.
Alhalin shi kusan kullum sai sun gaisa da shi.
Don haka ya tsare ta da tambaya," Kin masa laifi
ne kafin ya tafi?"ta ce,
"Eh
toh,
k'ila a wajen sa zai iya zama laifin
, domin ko a ranar ransa 6ace ya tafi."
Nan take ta warware wa Sageer komai.
Dariya Sageer yayi, sannan ya karkada kai, cike
da mmkin abokinsa.
Sanin hali, yafi sanin kama.
Sageer ya dade da sanin halin abokin sa, wani
fandararran mu2m ne, mai tafiya akan ra'ayin
sa.
Wannan AJININ SA YAKE.
Saboda haka ya ce mata,
"To ai ke Zarah yakamata ki yarda da aboki na,
don kin san yana son ki sosai, kuma na san babu
yadda za'ayi yayi miki alkawarin da ba zai iya
cikawa ba."Ta ce,"Saboda Allah Sageeer da
mutuwa, da haihuwa, da aure duk na wanene?"
Ya ce,
"NaAllah."
Ta ce,
"Don me mu2m zai yi katsalandan a ciki?
Sai kuma an sami akasi, sannan a fara "Wallahi-
tallahi, ita ta lik'e min?"
Don haka ku ke yi ku maza, da zarar za ku k'ara
aure, sai ace wa uwar gida "Wallahi ta nace sai ni
ne.
To ba za'ayi haka da ni ba Gaskiya.Sageer ya
kama ha6a ya ce,"Zarah kenan, shi yasa
mutumin naki ke cewa sbd lafuzan ki yake k'ara
son ki.
Yanzu tunda abin ya zama haka, ga lambar da
yake kirana da ita, sai ki kira shi."
Tuni take kallon sa, baki sake, yana yin, shiru ta
ce,"Wai ka na nufin yana kiran ka?""Kwarai kuwa
kodayaushe sai yayi min tsiya, idan na ce masa
ban sami zuwa na duba masa ke ba.
Kin san sha'anin School, ba time.amma ki yi hkr,
ga lambar."
Ta ce,"Kyale kawai Sageer, ai dai har ga Allah
gaskiya na fad'i.
Da kan sa zai neme ni."
Ta juya ta fito daga shagon, Sageer ya biyo ta,
yana magiya.Sannan ta tsaya ta amshi lambar,
suka yi sallama ta koma gida da mmkn
Naseerrrrrrrr......!!!watau shi a dole da gaske
yake yi ko?"
"Eh
mana."
Inji wani 6angare na zuciyar ta.
Su Lubabatu suka fad'o
mata, take nan wata kwakwalwar ta mai kaifin
hankali, ta gaya mata,"Kin san Allah, kar ki
amince, gara ki tsaya tsaka-tsaka, idan tayi ruwa
rijiya, idan bata yi ba masai!"Da daddare ta
kasance ita kad'ai ta rage, bata yi barci ba,
wannan kad'ai ya tabbar mata da lallai son
yayanta.Wasi-wasi kawai take yi, ta kira shi?
Ko ta share kawai?
Ina ta kasa daurewa.
Laluba wayar ta tayi, ta loda lambobin a ciki ta
hau kira.
Amma har ta kaste, bai dauka ba.Nan fa abin ya
kara damunta.
Fushi masoyi, akwai dalili.
Ko dai kishi, ko kuma anyi masa kwakkwaran laifi.
Kafin safiya ta amsa laifin ta, na kin amincewa
da furucin Naseer.Kwarai yana son ta, kuma
watakila alkawarin da yayi mata, ya kasance
tabbatacce.Ko karin safe bata yi ba, ta nufi
shagon masu kayan waya.Sabon layin Etisalat ta
siyo, hada da katin 200, ta dawo gida ta dannan
sabon layin cikin wayar ta.
Sannan ta loda katin da ta siyo suka shige.Sai ga
ta da bonus na naira 100, take nan kudi suka
zama 300,. Bata jira komai ba ta nemo lambobin
da take son dauka tun jiya.
Bugu daya, ta juyo muryar da take ta kewa
kwanaki 6 kenan. Sai dai tayi matukar mamaki jin
ya ce,"Kanwata kenan."Jikinta yayi mugun sanyi,
a lkcn guda kunya ta mamaye idanuwanta, don
haka ta kasa cewa komai, ta bar shi da kiran,
"Hello!
Ba za ki magana ba?
Yi hakuri ki ce wani abu,
inji."
Hawaye suka cika fal!
A idonta kafin ta ce,"Ai ka nuna min iyakata,
me ka ke so ince?"
Tana jin hucin murmushin sa kafin ya ce,
"Ina zaton kin daina so na ne,
shi yasa na hkr.
Amma na amsa laifin,
tunda Sageer ya min fad'a.
Yanzu kashe in kira, kar kudin su k'are.
Kafin ma ta kashe.
Shi ya kashe.
Jimawa kadan wayar ta, ta dauki ruri, ba 6ata
lkc.
Ta danna
O.K,
"Ban ta6a tunanin za kai min haka ba yayana,
amma ba komai rayuwa ce."
Ya ce,"Zancen dai ki ke so aci gaba da yin sa, ni
kuwa tuni na watsar dashi, tunda ba ki yarda
ba.Ni Naseerr na sharo ta ko?
Ko kuma yaudarar samarin zamani ta zo gare ki
kenan."
Muryar sanyaye ta amsa,
"Ban fad'i haka ba, ranka ya dade."
Ai inda kasa nan ake gardamar kokowa.
Ga fili,
ga mai doki."
Ya ce,"
"Ni
Jah-Jah
zan gwada sukuwa ta,
wacce ta sha ban-ban da ta kowa.
Insha-Allah sai na ba ki kunya."Ta ce,"Ni kuma?
Sai dai 'yan matanka a sake masu kiran kan su,
wai fans din ka."
Kan sa tsaye bata amsa,
"Ke ki ka san wannan, amma ina gargadin ki da
ki kiyayi zargi da surutan 'yan karan kad'a miya.
Masu ara su yafa. Alhalin ni bn ji ba, balle in
gani.
Muddin kika cigaba da sawa ranki cewa fans
dina 'yan mata na ne, ina me tabbatar miki
zuciyar ki za ta buga akan aikin banza."
Aikin banza yayana?"
"Eh mana.......
"Wai kai a'a, ashe fa kishi ne ko?
Ki na son yayanki kena. To na gode, sai dai don
Allah ki rinka daurewa.
Naseer na ki ne.
Jah-Jah kuwa na fans ne a filin sukuwa.
Kin amince da ni?" Ta ce,"Uhm...."
Ya ce,"Ban amsa sosai inji, ba uhm...... Ba."
Ta yi dan murmushi ta ce,"Na amince."
To ya su Inna da Baba?"
"Suna gaishe ka. Ni ba zan tambayi Ghana ba,
don tai min ba dai-dai ba."
Dariya ta ba shi, shi yasa ya ci gaba da tsokanar
ta, suna hawa suna sauka."
*******************
Wata guda da kwana 2,"Naseer ya dawo gida
Najeriya, bayan ya kammala aikin da aka dauke
shi haya a k'asar Ghana.Kamar kar su bar shi
ya dawo, sbd iya aikin sa da kwarewar sa
wanda yasa ba k'aramin masoya yayi ba a can
maza da mata.Kaduna ya sauka daga Abuja,
inda Alhaji da kan sa tare da Yakubu suka
dauko shi a filin jirgi.
Bargar dawakin Alhj suka wuce.
Naseer ya warware gajiya, sannan aka maida
bayanai akan kudaden sa da suka shigo ta banki
Naira dubu dari shida, sun jima da shiga akaunt
din sa.Alhj Basheer bai bukatar ko sisi daga
hannun Naseer, maimakon haka ma take nan ya
mika masa kyautar makullin mota, don nuna
farin cikin sa ga manya-manyan lambobin yabon
da Naseer din ya dawo da su, wadanda za'a aje
tarihi a ofishin Alhj.Naseer kuka ne kawai bai yi
ba, sbd murna da farin ciki.
Bayan sallar azahar suka koma (Dabai Motors),
inda Alhj ya nuna wa Naseer motar sa. (Honda
civic) ce mai kofa 1, kowa sai taya Naseer murna
yake yi.Shi kuma Naseer Yakubu ne kawai cikin
ran sa,
don komai Allah yayi Yakubu ne sila.
Tankinsa cike da mai, yana gaba Yakubun na bin
sa a baya akan hanyar su ta dawo wa
Zariya.Allah ya kawo su lafiya, kowa ya nufi
unguwar su.
Arziki kashi, abin har daure wasu Umma kai
yayi, wai yau Naseer din su ke jan motar kan
sa.
Ba abin mamaki a al'amarin Ubangiji,
Don shi yake fitar da mai arziki daga talaka.
Idan kuma ya ga dama ya fitar da talaka a jikin
mai kudi.
Shine kuma mai bada baiwa da hikima, mai
daukaka mu2m duniya ta sanshi har yayi sunan
da wani mai mulkin bai yi ba.Shine mai rufawa
bawa asiri ta yadda ba wanda ya isa ya tona
masa, har jama'a su rinka ganin shi wani abu
ne.Ubangiji gare ka muke neman rufin asiri.
Ya Allah ka amsa!...Amin ya Allah (ANaM)
Allah ya kam ya rufa wa Naseer asiri, yayi masa
baiwa, ya kuma daukaka shi ta yadda jama'a
suke masa kallon mai kudi a halin yanzu.
Shi yasa abin ya k'ara rikita Zarah, lkcn da ta
fito ta ga yayanta a mota, kwarjininsa ya zarce
misali.komai kyau yake wa Naseer, shi yasa ta
kwana addu'ar Allah ya sa zancen Naseer ya
tabbata gaskiya.
Don bata jin za ta yarda da duk wani kalubale
Naseer na ta ne, ita kadai.
Washe gari banki ya fara shiga, bai gushe ba.
Sai da ya turawa Yakubu Naira dubu hamsin
cikin
(Account)
din sa, sannan ya fitar da wasu Naira dubu
hamsin din.
Ya nufi shagon siyar da atamfofi, ya zo6o tsala-
tsala guda 6 'yan dubu bibbiyu.
Ya za6o Engilsh guda 2 ya had'o da shaddoji
kala 6, masu kyau.
Sannan ya koma 6angaren kayan sanyawa na
maza.
T.Shirt da wanduna Jeans da Shirt masu dogon
hannu, nan ma ya kwasa iya yadda yake so.
Yana barin nan gidam su Yakubu, ya wuce
sashin mahaifiyar sa, nan ya shiga da atamfofi
kala 2 cikin leda.
Bayan sun gaisa, tayi masa lale da dawowa daga
Ghana.
Ledar kaya ya mika mata ya ce ga tsarabar ta
nan.Kai tayi farin ciki ta kuma sa albarka kwarai
da gaske.Yana kokarin tashi, sai ga sallamar
Yakubu, ya shigo.
"Naseer!"
Yayi kiran sa ya ce,"
Na'am yayana. Ina kwana?"
Ya amsa, lafiya lau.
Ai yanzu na fita zan fito da mota a wanke, sai
naga taka motar a waje, kuma dama wajen ka
za ni.
Sako na gani an aiko min a waya, wai an
min tiransifar dubu
hamsin daga,
(Account)
dinka."
"Dubu hamsin?"
Hajiya ta sake maimaitawa.
Ya ce,
"Wallahi hajiya."
Naseer ya ce,"Haba yayanmu, kamar wasu
kudin kirki?"
Ka cancani haka ne shi yasa, kuma ni ba ni da
abinda zan saka maka da shi,
don komai na samu, kai ne sila."
Ya zauna hannu kujerar da yake kafin ya ce,
"Naseer kenan, to Allah ya bar kauna.
Hajiya sai a tayani godiya.
Ta ce,"Dole, ka ga ni ma ga tawa tsarabar.
Allah yasa a kare da iyaye lafiya.
Ya ce,
"Amin
, Hajiya."
Ina takwara na ne? Halan bai tashi barci ba?"
Yakubu ya ce,"Kamar kuwa ka sani, yana can
yana barci."mik'ewa yayi, suka yi sallama da
hajiya suka fito tare da Yakubu,
shi ya wuce sashinsu, don yin wanka.
Naseer kuwa waje ya fito,
ya bude mota ya dauko wasu kayan a wata
babbar leda, ya nufi dakin da ke kofar gidan,
yana kwankwasa.
Zuwa can aka bude cikin fara'a Naseer ke
fadin"Ka na huta wallahi."
Ya dan duba shi,
ba tare da ya ce komai ba, ya juya ciki.
Naseer ya biyo shi, "Watau ba ka ma tashi barci
ba?
Ya murtsuke fuska da hannayensa, sannan yayi
mika, kafin ya ce,"
Na gaji ne."
Ba aikin fari, balle na baki ka ke fadin ka gaji.
Jiya ma ina ta sa idon ganin ka, sai na ji shiru,
wayar ka kuma na kashe."
Ba wata walwala a fuskar sa,
"Ban da caji ne, jiyan nima na so zuwa, lkc ne
bn samu ba."
Ya ce,"
O.k,
to ga tsarabar ka.
Ya mika masa ya kar6a, sai kawai ya wurga bisa
katifa, yana fadin ,
,"Na gode."
Abin ya daure masa kai, har ya kasa cewa wani
abu.
Haka suka danyi jim shuru kafin Naseer ya
mike, "bari in karasa gida." "to sai anjima". yace
yana kwanciya a katifa.â bakaje kaga mota ta
ba, ko bakada labari ne?" ya dago fuska daure
yace "Oh, naji, mancewa nayi." ya mike suka
fito. Ya kare wa motar kallo, zuciyarsa ta kara
shiga wani garari, har yana tambayar kansa, "Da
ya motar nn tawa cefa." Ya kada kai kadan yace,
"Allah ya sanya alkhairi." yace, Amin. Ni zan tafi
sai yaushe zaka bullo ne?"Da kyar ya amsa, "zan
kira ka idan zanzo." Kukan wayarsa ya juyo daga
daki, don haka ya juya da sauri ya koma dakin,
yabar naseer tsaye ba tareda sunyi sallama ba.
Yana shigewa yaga ya turo kofarsa. Sam-sam
ran Naseer baiji dadin abinda takwarar sa yayi
masa ba. Shiyasa har ya bar wajen, yana
tunanin me ya faru tsakanin su? Don bai taba
ganin irin wannan fuskar ba awajen takwaran
na sa balle yayi masa irin abinda yayi masa yau.
Da wannan tunannin fal, ransa ya gama raba
tsarabar sa gidansu zahra da gidansu sageer.
Kowa nata murna, yanasa albarka. Ya dawo gida
karfe 12 dai dai na rana. Malam balarabe na
zaman jiransa. Yana shiga ya hau fada, "ina ka
shige saboda Allah? Bayan tun jiya na gayama
sammako zamuyi zuwa kaduna nan! Karfe 12
yanzu, yaushe kakeso muje mu dawo?" Yace "yi
hakuri Abba, ban san rana tayi haka ba. Ka
gama shirin ne?" Yace "tun yaushe nake zaman
jira? Tuwon girma, ai miyarsa nama. Wallahi
sammako naso muyi wa Alhj, don nuna masa
farin ciki na." Umma tace, "mallam ai gara ku
tashi da wannan maida zancan da kukeyi."
Gaban umman ya zube ledoji guda hudu,duk
kayayya ki ne. Umma ta zazzage su. Wai!
Haihuwa me rana, Kamar tayi kwalla saboda
murna. Haka Abba yayi zugum, yna alajabi. Da
ya tuna irin wuyar da naseer ya basu a can
baya, sai ya nisa yace,"Allah abin godia ne mai
shiryar da wanda yaso a duk lokacin daya so
din. Allah ka kara shirya mana ." Murmushi
naseer yayi, kwarai ya gane dalilin adduar Abba.
Ya dubi umma itama shi din take kallo, fara'ar
sa ta karu. Umma tace "me akayi?" Yace ba ayi
komai ba umma. Baki gama abinci bane." Abba
yace, "ba wani abincin da za'aci, tashi mu tafi,
ko kuma inbi ta haya." Ya mike, ya kwaso
takalma yayi waje ya cigaba da fadin. "Ai gidan
Alhj Basheer ba bako na bane." Umma tace,
"kaga, tashi ku tafi. Allah ya kiyaye hanya." Da
sauri ya tashi, yabi shi suka damki hanya.
Alhj na ofis lkcn da Naseer ya kira shi a waya.
Ya shaida masa zuwansu, don haka kai tsaye
can suka wuce. Malam Balarabe ya zuba godiya
kwarai da gaske. Abin yayi wa Alhj basher dadi,
shi yasa ya ce ba za su tafi ba, dole sai sun
wuce gidan sa sun ci abincin rana ko dama cin
abincin yake shirin tafiya. Lokacin da Naseer ya
yo masa waya, ya ce suna tafe.
Tare suka rankaya gidan na su.
Suna falon baki, akai ta shigowa da abubuwan ci
da sha iri-iri.
Tare suka ci, suka sha suna hirar duniya.
Sai misalin uku da rabi, suka baro kaduna.
************
Cikin wata guda, ginin da Naseer ke yi a cikin
gidan su ya kammalu tsaf! Gwanin ban
sha'awa, kowa ya ga tsarin da aka yi wa ginin
nan, dole ya ba shi sha'awa.
Bayan haka kuma sun yi shawara da Sageer
akan bude shagon dinki, don haka Naseer yasa
Sageer ya nemo shagon haya, ya biya kudin
shekaru 2.
Babu 6ata lokaci aka gyare shi, aka zuba
kekunan dinki guda 2 da na aiki (Design) tare da
na yin zig-zig. Sageer ya koma can ya samu
mataimaka, kafin ya kammala karatun sa,
wanda bai wuce wata 3 su fara jarabawar
karshen ba, ta kammala Diploma.
Shi kuma dan gogan fafitukan shirye-shiryen
auren sa ya ci gaba da yi, don ita ma Zarah,
wata 5 suka rage mata ta gama sakandire.
Manyan akwatunan sa (Set) guda ya kusan
shake su da kaya na gani na fada, na burgewa
gaba dayan su, sai sharholiyar su suke yi, ba su
da matsala, duk da cewar kusan kullun sai
Zarah, ta amshi bakin 'yan mata a makaranta
masu zuwa ganin ta, wanda akasarin su, su
Lubabatu suke yi masu jagora.
Abin ya daina tada mata hankali, ta daina wasi-
wasi. Zuciyar ta ta sami sukuni.
Domin ta hakikance Naseer na ta ne ita kadai,
don bata ta6a gani ko jin yana neman wata ba,
Masu karyar su 'yan matan sa ne, sun gaji sun
daina, saboda rashin ganin fuska. Kirsa iri iri
naseer na gani a wajen wasu yam matan
marasa kamun kai da hakuri. Su kan mance
mijinka, idan Allah ya kawo shi, kana
kyakkyawan zaman ka zaizo ya sameka.
"(Karshen zubar da aji kenan a waje na, kuma
ina ganin ko a al'adar bahaushe. Saurayi shi ke
zuwa tad'i, koda kuma had'in iyaye ne.
"Ma'ana iyayenki suka ba shi ke, su kan ce ne
ya zo ya ganki, ba wai ke za'a ce ki je ki gan shi
ba. Mata kuna da kima da martaba mai yawa.
Don Allah ku rika zama kamammu a
kodayaushe, domin komai yawan da ake cewa
kun yi, har ana muku kirarin kamar Janpa a jos.
Wallahi babu wanda ya isa ya je gidan ku ya
d'auko ki, dole sai ya bi ta yadda shari'a ta
tsara."
Ba wai da ganin saurayi, kina son sa ba, kita
binsa kamar yadda wasu yam matan sukeyi a
wannan zamani. Watanni uku bayan dawowar
naseer daga Ghana, ranar litinin da safe yana
office din Alhj Basheer kamar yadda ya bukaci
ganinsa a wannan lokaci. Alhj ya dube shi irin
wanda ya saba yi masa irin na kauna yace
"Naseer ya maganar karatun ka ne? Diploma
gareka ko degree?" Naseer ji yaji tambayar Alhj
tadan sa shi al'ajabi, sai dai zuciyarsa bata raya
masa komai ba, don haka yayi dan murmushi
yace, "Alhj sakandire kawai na gama". Shima
Alhj mamaki ne ya kama shi, fuska a yamutse
yace, "why? Kuma shine tuntuni baka koma ka
ci gaba ba?" Shiru Naseer yayi a dalilin bashida
wata hujjar badawa. Shi yasa Alhj yaci gaba da
cewa, "gaskia banji dadi ba, amma ba matsala,
ka kawo min takardunka, ka zabi ko wacce
makaranta kake son zuwa." Naseer ya shafa
keya, shi kan sa nauyin ya fadin abinda yasa
yake ji. "Ai ban....ban ma samu yin jarabawar
ba. Take nan tausayi ne ya lullube Alhj Basheer,
don babu abinda yazo zuciyar sa, illa matsalar
rashin kudi, saboda haka bai nemi sanin dalili
ba. Kai tsaye yace, "Anyway, tunda abin ya
zama haka, sai kaje ka binciko lokacin da zaa
fara biyan kudin jarabawar. Zan baka ka biya,
ka rubuta. Idan (result) ya fito zaa san abinyi.
Gaskia ban taba zaton haka ba, da tuni na
tilasta maka ka koma school. Shi ilimi ai baa
wasa dashi, domin wata fitila ce, wanda hasken
ta bai taba dushewa har abada. A kowane lokaci
zai yi maka amfani." Naseer ya kara sunkuyar
da ido yace "Na gode Alhj. Ina ganin ma an
kusan fara biyan external insha Allah zan biya."
Yace "bance ka biya ba, ka kawo min yawan
kudin nace, ni zan ba ka. Murmushi yayi kafin
yace , "to Alhj nagode. Bari in karasa wajen
Yakubu." Ya amsa, "To, shike nan. Yauwa, gobe
in Allah ya kaimu zan tafi Abuja, 'yar waje na
zata dawo daga jordan, zan dauko ta a (Airport).
Koda yake bka san ta ba. Nusaiba sunan ta, ta
kare digiri din ta bana. (Arabic and islamic
studies)." Naseer ya numfasa yace "tayi kokari,
nayi mata murna. Allah ya kai mu lafiya."
"Amin, amin. Kana iya tafiya, shike nan."
Zaharaddeen shomar
Whatsapp 08168575100
Ajininsa yake 1-07
Posted by ANaM Dorayi on 08:04 AM, 09-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
.Ya mike ya sallame shi, ya fito Alhj ya raka shi
da kallo.
Yana rufe ofis din, ya dan kada kai.
Haka kawai Allah ya sanya masa kaunar Naseer.
Bai ki kodayaushe su kasance tare ba, sosai yake
jin sa cikin zuciyar sa, tamkar dan daya
haifa.Wani lokaci har ya kan tambayi kan sa ko
don ba shi Da namiji ne? To ai kuma yana da
yara masu yi masa hidima a ko'ina, tun kafin
zuwan Naseer,amma bai ta6a jin wanin su a cikin
ran sa, kamar yadda Naseer ya kama zuciyarsa
ba.
Komai zai iya wa Naseer dai-dai yadda zai yi wa
Nusaiba 'yar cikin sa.
Kawai ya kan danne wasu abubuwa ne, saboda
kar sauran yaran sa su ce ana nuna masu
bambanci ko su fa zargin wani abu.
Washe gari k'arfe 2 na yamma Alhj Basheer ke
tsaye wajen tarbar fasinjojin a filin jirgin sama na
tarayya Abuja.
Bayan wasu 'yan mintocin jirgin da ya taso daga
Jordan ya sauka.
Daya bayan daya fasinjojin da ke ciki suke fitowa.
Jimawa kadan wata tsaleliyar budurwa ta fito
saye da doguwar riga da dan karamin farin hijabi,
wanda gaba daya tsayinsa bai zarce kafadunta
ba.
Wankan tarwada ce sosai, fatar ta ke ta walwali
ga kyakykyawar fuska mai dan fadi.
Hakan ya dai-daita zaman siririn hancinta da
tsarraren baki.
Tana da wadatar idanuwa fa gashin ido da gira.
Dan matsakaicin tsayi gare ta, sai dai za ta dan
d'ara Zarah kadan,
tofa! Mekuma yakawo wannan zancen? Maji ma
gani...
jaye take da wata jaka ruwan toka mai
matsaikacin girma ga kuma karama rataye a
kafadarta.Tun da suka hango juna. Su kai
musayar murmushi har ta karaso fara'ar ta ta
kara karuwa take yi, tana isowa ta saki jaka ta
rungume mahaifinta,
"Abba na!"haka lallausar muryar ta ke fadi,
tamkar Zarah ce ke magana.
.*****Tinani**** kodai..........uhm banda
shishshigi ANaM...
saboda kwarai yanayin sautin muryar su, yayi iri
daya.Alhj ya dago ta bakin sa har kunne ya
dube ta,"Yar gidan Abba kenan,
"To ya hanya?"
Ya su Antinki?"
Ta ce,"Lafiya lau Abba na.
Ina Ummi?"
"Bata zo ba?"
Umminki na gida, ta so zuwa, amma kin san ta
so lazy,
you know?"
Wai kuma ta fasa saboda tafiyar mota'¿
Ta kayata fuskarta da lafiyayyen murmushi,
"Lallai Ummi, ko kewa ta ma bata yi ko?"
Ai shi ke nan."
Ya ce,"Ba ga Abbanki ba? Duk na kosa ki dawo
my baby, kullum na dubi kofar ki a kulle, sai inji
raina sam ba dadi."
Ta kara kwantar da kanta bisa kafadar sa,"Ni
ma haka, na yi Missing din ka Abbana."Cikin jin
dadi ya rungumo kafadarta, ya ce,
"To mu je mota,
direba na jira."
Dai-dai lkcn da aka kwarara sallama, duk suka
duba suna amsawa."
Wani kosashshen matashi ne, cikim adon
bakaken (Suit).
Yana da tsayi sosai, don ya kare Alhj Basheer."
Ga fadi da alamar hutu,
shi ba fari ba, fara'a sosai bisa fuskar sa, yayin
da ya dan duka yana fadin
"Ina yini Baba?"
Tuni Nusaiba ke kame da baki, tana masa kallon
mamaki, ido waje.
Alhj Basheer ya amsa."
Lafiya.
Da ga ina?
Ban shaida ka ba._?
Ya ce,
"Dama.............."
"A jirgi mu ka hadu Abba.
Wai sunan Sa Ibrahim."
Nusaina tayi saurin taran numfashin sa.
Alhj Basheer ya dan tsuke fuska yana dubn ta,
"I see,
ina mota ki same ni can."
Ya juya kan Ibrahim ya ci gaba,"Ka gaida gida."
Ya kara rankwafa ya amsa,
"To
Abba na gode."
Ya wuce ran sa bai masa dadi ba."
Yana bada baya.
Ibrahim ya dan runtse ido ya fada a hankali
"Yes!"
Ta ce,
"Don me za kai min haka?"
Ya ce,"Shi yasa ki ka fito da sauri kenan."
Bai kamata ka zo kai tsaye wajen Abba na ba,
haka kawai daga gani na a jirgi.
Ya ce,
"Oh,
duk bayanin da muka yi, fita suka rika yi suna
bin iskar jirgi?"
Haka bai dace da ke ba, yakamata ki amince da
cewar da gaske nake yi."
Cikin damuwa ta ce,"Ina cewa na gaya ma
sunana, na ba ka (Address) da lambar waya,
sai me?
Karshen amince kenan a zato na."
Tsararren bakin ta kawai yake kallo, sansanyar
muryar ta na sa shi dogon tunani.
Ya shafa kai, ya numfasa ya ce,
Fakat!
Kin kare magana.
Mu je in raka ki,
kar Abba ya ga kin dade."
Ta ce,"
Na gode."
Ba sai ka raka ni ba, ina jin kunyar Abba."
Amma yakamata in ce da shi Allah kiyaye hanya.
Ko kuwa?????""Ta juya, ta ja jakar ta, ba tare da
ta amsa ba.
Biyo ta yayi da sauri, yana fad'in
"Please, da zarar kin sanya layin ki, ki yo min
(Flashing)
don in san kin maida layin, ina fatan za ki
taimaka?
Ta tsaya cak!
Ta ce,
"Ni ma ka taimake ni ka koma, zan kira din."
Ya kare mata kallo, kafin ya ce,
"Promise?"
"Na yi."
"TO Allah ya kiyaye hanya, ki ce wa Abba a
sauka lafiya, kin kankane min shi."
"Dan murmushi ta yi ta wuce abin ta.
Shi kuwa nan yayi tasye yana kallon yadda take
takawa har ta fice daga wajen."
Yayi zazzafan ajiyar zuciya, ya so ace ta dan
sake waigowa ya kara ganin kyakkyawan fuskar
ta, amma ina,
hakan bai samu ba.
Shi yasa ya jima ya na wasi-wasi, yana ganin
kamar bai sami kar6uwa ba.
Alhj Basheer ke zaune a cikin lafiyayyar motar
sa (KIA).
Ko alama fuskar sa babu walwala.
Isowar Nusaiba ma yasa ya kara tsuke fuskar.
Tana karasowa jikin but, ya dago mata shi ta
bude, ta jefa jakar ta ciki, ta rufe.
Sannan ta iske shi a ciki.
"Mu je ko Abba."
Bai amsa ba, yayi wa mota key, ya fito harabar
aje motoci.
Ya dauki hanya.
Shiru suka yi na 'yan dakikan, ran Alh.
Basheer na sosawa akan al'amarin daya gani
wanda yake ganin yakamta yayi wa tufkar hanci
da gaggawa, don cimma burinsa.
Buri kuma!!!! Baridai inyi tanbaya a nan, friends
kunsan burinsa? Inna jiran amsarku wadda ita
zatazama matakin dorawa daga wannan page,
idankuka Marubuciyar tabamu baki daya ta
hutashshemu kenan!! ANaM Dorayi ***Smile***
Haka zalika ran Nusaiba yake kuntace....domin
ba'a son ranta Abban ta ya ga Ibrahim ba,
saboda bata gama tantance shi cikin ranta ba.
Musamman jin cewar yanada mata daya da yaro
daya. Shirunsu yayi yawa kuma, abinda Nusaiba
ta lura kamar ran Abbanta a bace yake, ba
yadda ta fara ganin shi ba, don haka ta nemo
abin cewa. "Abba na". Ta kira shi. "Uhmm!"
Tace, "Ummi taki zuwa dauko ni, abin yana ta
ban haushi." Da wutsiyar ido ya kalleta, "Ni ba
wannan matsalar ta dameni ba." "Meya dameka
Abba?" Yayi dan jim, kafin yace, "me kike tunani
gameda Ibrahim?" Kunya cike da idon ta, ta dan
sunku yar da kai, tace "Abba, Ibrahim a jirgi
kawai muka hadu." Yace, "wannan ba itace
amsa ba, zaka iya ganin mutum yanzu take nan
ya shiga ranka, shi yasa na tambaye ki menene
raayinki akansa." Tayi shiru, jin tayi shiru, yasa
ya c igaba. Kar kiji kunya, ki gaya min komai
Nusaiba, kin san ni mahaifinki ne, kuma ke
kadai ke gareni, kuma ina alfahari da ke.
Saboda haka ki warware min komai, menene
raayinki akan Ibrahim?" Tadan cire kai ta dube
shi, tace "banda wani raayi akan sa tukuna,
saboda kasan komai sai da shawara da tunani."
Yace "hakane, amma zanso ace kin gaya mun
wani abu." Tace, "bansan komai a gameda
Ibrahim ba, illa ya gaya min shi dan gidan Alhj
Abdul Mutallib Kazaure ne.Shahararren dan
kasuwan nan na kano. Garkuwan kazaure. Shi
maaiksaci ne a (Nigerian Embassy Jordan),
yanada mata daya da da daya." Alhj ya kada kai
yace, "Nusaiba." Ta amsa "Naam Abba." Yace,
"idan nace ki aje Ibrahim a filin jirgi, tunda a
jirgi kawai kuka hadu, zaki iya?" Kai tsaye ta
amsa, "me zai hana Abba? Kaban umurni, in
ketare, mecece hujjata a matsayinka? Biyayya a
gareka dolene Abba, muddin ban sabi sharia ba,
saboda haka na aje Ibrahim, ban san abinda ka
hango min ba." Ya kare mata kallo, sannan ya
aje numfashi. Shi yasa yake son Nusaiba kamar
ya hadiye ta. Yace "yar albarka mai kaifin
hankali da sanin matsayin na gaba." Musamman
iyayenta da take jin su sosai cikin ranta.
Abbanta ma yafi shiga ranta, ba kadan ba,
saboda yadda ya nuna mata kauna da soyayya,
tun tana yar mitsitsiyar ta. A lokacin data
mallaki hankali kuwa, sun kasan ce abokan
shawarar juna, babu abinda ya dami Alhj
Basher, zama yake da abar sa, ya war ware
mata duk abinda ke cikinsa. Walau farin ciki ko
akasin hakan. Balle ita da take a matsayin mai
karancin shekaru, bata zar tar da komai sai
abban ta yasani. Hakan ba kankanin tattalin
kaunan dake zukatan su yayi ba. Mika hannu
yayi, ya dauko nata, yadan matse shi, kafin yace
"Nusaiba na gode Allah daya bani ke daya tal!
Amma ki ka zama tamkar dubu. Kinsan dalilin
cewa ki aje Ibrahim?" Ta kada kai tana dubansa.
Yace, "miji na zaba miki.". ****Uhm*** anxo
gurin, amma banan gixo ke sakarba!!!!! Haka
kawai taji gabanta ya fadi, sai dai kuma ta rasa
dalilin bayyanar murmushi a fuskar ta har da
wata bazawarar kunya data sauka cikin
idanuwanta, masu kyau da haske. Aje kai tayi
kasa taci gaba da murmushin. Abinda ya kara
faranta ran Abbanta kenan. Ya Kara runtse
yatsunta, yaci gaba da cewa, "Naseer yaro ne
dan mutunci. Dan babban gida. Ba wai ina nufin
babban gida irin na wannan zamanin ba, kamar
yadda mutane suka maida rayuwa akan tarin
dukiya shine mutunci da babban gida. A'a ina
nufin kyan asali, addini,da dabiu na gari, wanda
yakan samo asali ne daga tarbiyar iyayen
babban gida.
Aunty Zulyma ta hutashsheku!! Ammafa......
Uhm! Muje zuwa wai Mahaukaci ya hau kura....
Baki nan aka kawo min Naseer, yana min wasan
polo, a maganar nan yanzu da nake miki, ya
zama wani jigo a harkar wasan polo abin
alfahari. Allah ya sanya min so da kaunar Naser
fiye da tunaninki, wanda har ya kai ni ga son
hada zuria da shi. Sai dai bani da kowa sai ke
Nusaiba, shi yasa nake rokon ki da nuna min isa
da ke kuma biyayya ta karshe da zaki min, ki
amince da zabin da nayi miki" Wasu kwallane ke
cike fal! Cikin idanuwan ta, wadanda ita kanta
bata san dalilin taruwar su ba. Daga bisani ne ta
fahimci cewar kalaman Abbanta na karshe, su
suka tara mata hawayen da suke neman sauka
bisa kuncin ta. Jin yayi shiru, yasa ta dube shi,
duba na aminci da girmamawa, tace Abbana
kaban mamaki daka ce kana rokona, kenan kana
kokwanto akan ba zan maka biyayya ba. Ai...."
Hawaye shar shar! Bisa kuncinta. Shiya hana ta
karasa zancen ta. Tasa hannu tana sharewa
wasu na kara fitowa kamar ma kukan naso yaci
karfin ta. Hankalin Alhj Basheer ya tashi
matuka. Fuskar sa ta nuna karara, "ba haka
nake nufi ba bebina, kin ga dubeni. Ki dubeni
nace" Ta dago idanuwanta jajur! Ta kalle shi,
yayi sauri ya goge hawayen ta sannan ya dawo
da hankalin sa ga tukinsa, bakinsa na fadin,
"wannan maganar ta wuce. Yanzu gaya mun
yaya kikaji daga ambatar sunan Naseer?" Tace
"Abbana ai tun ina yar yarinya raayinmu daya
dakai, balle a yanz dana mallaki hankalina,
nasan cewar ba zaka taba kai ni inda zan cutu
ba. Dadin dadawa kuma a shariance, matsayin
dana ke yanz na wacce bata taba yin aure ba.
Hakkin Kane ka zabar min miji na gari wanda
kake min hangen farin ciki da kwanciyar hankali.
Don haka Abba ka daina roko na, kace mun
Nusaiba na baki umurni kawai, ni kuwa inbi."Bai
san lkcn daya fashe da dariya ba,yana fadin,
"Bebina gime a hug!" Ta matsa kusa da shi
sosai, tayi kwance bisa kafadar sa kunshe da
murmushi bisa fuskarta." Allah yayi miki
albarka."Insha Allahu yadda ki ka faranta min
rai, haka ke ma zaki kasance cikin farin ciki."
****Uhm! To Allah ya amsa?****
Ta k'ara makale masa ta ce,"Amin Abba
na........." Ta ja sunan Abban yayi tsawo, don jin
dadin sa. Haka suka kasance har isowar su
Kaduna." Labarin Naseer yake bata. Jaruntakar
sa da kwarewar sa akan wasan polo.Haka kuma
bai 6oye mata karancin karatun sa ba. Take nan
suka zakulo yadda za'a warware wannan 'yar
matsalar.
Ko alama Nusaiba bata yi kama da Hajiya
Zulaihat ba, watau duk kyanta a wajen Abban ta
ta samo shi.
Ita fara ce sol! Tana da manyan kyau, ma'ana
da ka dube ta, za ka gane kyakkyawa ce.
Sa6anin Nusaiba, ita kananan kyau gare ta,
kana kallon ta, tana qara kyau, ba za ka ta6a
ganin sauyi ba.
An riga anyi sallar magariba, lkcn da suka iso
gida. Tana rafka sallama. Ummin ta ta fito,
"Oyoyo, bebin Ummi!
Nusaiba ta cunno baki,"
Ba wani."
Ai wallahi Ummi......."
Rungume ta tayi, shi yasa ta kasa k'arasawa.
Ummin ke cewa,
"Yi hakuri, jiki na ne na ji yayi min nauyi, shi
yasa ban biyo Abban ki ba. To ya hanya?" Ta
ce,"Lafiya lau.
Su Anti na gaishe ki."Ta ce,"Kyale Antin nan ta
ki, wai a waya take min shegantakar da ta
saba." Tayi 'yar dariya ta ce,"Zan cen Anti bai
wuce na amarya. Na dai ce mata ta bari sai an
rangado mata, sannan ta sami bakin magana."
Yauwa, na gode da ki bata amsa, sannan
sallamar Alhaji." Kin ma tsaya ki na hira da ita
ne, bayan ta ki zuwa dauko ki."
Dukan su dariya suka yi." Abba na ai rike ni
tayi."
To kwace ki gudu kawai, kar tayi miki wani dadin
baki."
Ta ce,
"Yanzu kuma Abba."
Ta suri jakar ta nufi dakin ta.
Ummi na fadin,
"Au, zuga ki yayi?"
Ta juyo dauke da murmushi, ta kada kai ta
wuce abin ta.
Hajiya Zulaihat tayi wa Alhj sannu da zuwa.
Ya amsa, tare suka haye sama."
Nusaiba na shiga dakinta, ta yar da jaka,
ba6ata lkc ba, bayi ta shige, jimawa kadan ta
fito da alwala, tayi sallolin ta.
Ta jima bisa sallaya tana lazimi har zuwa kiran
isha'i, ta mike ta ci gaba da sallah. Bayan ta
idar, sannan ta cire kayan jikin ta, tayiwanka ta
nufi.
Madubi da ke shirye tsaf!
Da kayan kwalliya iri-iri, ta ja kujera ta zauna."
Daddaga kayan da ke wajen tayi, duk sababbi
ne aka zuba mata.
Dan murmushi tayi, ta fada a ranta,"Ummi na
kenan."
Ta shafe jikin ta da (Lotion), sannan ta mike ta
nufi Wadirof, ta janye murfin gilas din, haka tayi
tsaye wangame da baki.
An cire wadirof din ta tsadaddun kayayyaki kala-
kala.
Wani farin ciki ya sake kama ta, a lkcn guda
zuciyar ta ta kara kamuwa da tsananin son
iyayenta.
Ta shiga dubawa, gaba daya ta rude ta ma rasa
wace riga za ta sanya."
Domin duk wacce ta d'aga, sai taga ta fi ta farko
kyau. Da kyar ta iya dai-daita zuciyar ta, ta
dauki wata 'yar kanti ruwan hoda, doguwa mai
karamin hannu ta sanya.
Gaban rigar akwai ado na furanni farare
kanana, su suka kara wa rigar kyau.
Da ta koma jikin madubi kuwa, ka rantse da
Allah sbd jikin ta kadai aka yi rigar, ita kanta ta
tantance hakan.
Gashin kanta da ke sake, shi ta kama tana
daurewa da wani dan karamin (Ribbon) da ke
makale jikin rigar.
Bata kammalaba Umminta ta budo kofa ta
shigo,
"Ke!
Wai ba za ki fito cin abinci bane,
iyayen gayu?"
Da sauri ta tarbi Umminta ta rungume,
"Allah sarki Ummina, na gode da kaya."
Ta dago ta,
"Gaskiya kuma kin yi kyau bebin Abba. To mu je
ki ci abinci. Abbanki ya ce idan kin gama, ki
same shi daki." Bakin ta har kunne ta
amsa,"Minti 2, Ummi gani nan." Ta wuce dauko
mayafin rigar. Ummi kuwa ta fice daga dakin."
Akan tebur, daga ita sai Umminta, domin shi
Alhj Basheer bai damu da ya ci abinci bisa tebur
ba, ya fi son akai masa cikin dakin sa ya ci.
Abinci kala-kala, kowa ya za6i abinda yake so
ya ci.
Nusaiba ta yayyafita, saboda kosawa tayi ta ji
kiran Abban ta.
Tana mikewa. Ummi ta ce,"Ke ba dai kin koshi
ba?
Ta nuna hanyar sama ta ce,
"Abba na kira can za ni."
"Cewa yayi ki ci ki, koshi kafin ki je."
Cikin doki, ta ce,"Na koshi ummi, idan ma zan
kara, na kara a wajen Abba na."Ta sumbaci
kuncinta ta haye sama da gudu. Ummin ta, ta
raka ta da ido har ta kule." Ta aje numfashi,
tana karkada kai. Tabbass tayi kewar 'yar diyar
ta, tilo tamkar dubu."
Sallamar Nusaiba Alhj Basheer ya amsa.
(Laptop) ce a gaban sa, yana ta 'yan dube-
duben ajiyar sa. Koda shigar ta, kwarai ta ga
dakin ya sauya mata.
Ga wasu bakin makamakan hotuna guda 4 da
suka kara kayata kafcecen dakin, daya kai
girman wani falo.
Uku daga cikin hotunan Alhj Basheer ne tare da
Naseer rike da wasu kofuna tare da wasu
kyaututtuka.
Dayan kuwa Naseer din ne shi kadai, ya da wani
katon kofi sama, dariyar da yayi ta kara
kwarjinin fuskar sa. Kai tsaye gaban hotunan ta
tsaya ta zuba ido.
Domin ko alama bata tantama wannan shine
Naseeerrrrrr!!!!......."
Ba wai son sa bane take ya kamata, a'a
kwarjinin sa ne ya debi hankalin ta har ta ji
faduwar gaba, kuma ko alama bata ji tana kin
sa ba.
Tana kokarin kaucewa hotunan, ta ji hannun
Abbanta ya rungumo kafadar ta, ya lika ta
kuibinsa.
Ta dan sauke numfashi kadan, ta ce,"Hotunan
ko sun yi kyau."
Yayi dan murmushi ya ce,"Allah ko?
To ki canka waye a tare da ni? Cikin
zolaya t amsa,
" Bebin ka of course."
Ya ja hancin ta ya ce,
"Stop joking."
Ba ni ce a tare da kai ba Abba?"
A hoto na ce,
kin sani sarai,
come on,
gaya min."
Tayi 'yar dariya,
"Uhmm...........jarumun dan wasan polon nan da
aka kawo ma ka shi, lkcn da ba nan.
Ya ma sunan sa?"
Ta tambaya, tana duban sa.
Haka shi ma yake kallon ta kafin ya ce,
"Sunan sa ya 6ace miki kenan?
Maganar Abba bata da muhimmanci ko?"
Ta kada kai,
Wasa na ke,
ai da shigowa ta na gane Naseer ne."
"To yaya ki na son sa?????"""""
Da sauri ta bar wajen, ta koma bisa wasu
kujerun farin karfe na alfarma ta zauna.
Kunya ce mai karfi ta kamata.
Shi ma ya tako a natse ya zauna gefen ta."
Wannan shine zabin da na yi miki, ina son ki
gaya min yayi, ko bai yi ba?" Kan ta a kasa, ta
amsa, "Yayi Abba."
Ki na son sa?"
Tayi shiru jim.
Sannan ta kalle shi,"Ummi ta ce kana kira na."
Wannan shine kiran, ki ga mijin da na za6a miki,
sannan in tabbarar da ki na son sa.
Ki gaya min."
Abba na ce yayi."
Ba yayi ba,
ki na son sa?"
Alhj fa ya tasa ta gaba, ita kuma duk kunya ta
rufe ta, da kyar ta cije ta daure ta amsa,
"Eh!"
Ta mike a guje, ta bar dakin.
Alhj Basheer ya bi ta da kallo yana dariya,
sannan ya numfasa yayi hamdala ga Allah.
Kai tsaye Nusaiba dakin ta shige, ta fad'a bisa
gado, ta nutse cikin katifa.Ta jima a kife, kafin
ta birkito ta tsirawa fitlun da ke cunkushe suna
lilo a saman tsakiyar dakin ido.
A zahiri su take kallo, amma ko alama ba kyan
tsarin bane cikin ran ta.Zuciyar ta yamutse take
da tambayoyi masa yawan gaske a game da
za6in da Abban ta yayi mata."
Shin waye Naseer?
Wane irin sani Abban ta yayi masa?
Duka zahiri da badini?
Ya za kai kar6e ta, idan ya ganta?
Watakila shi ma hoton na ta ya gani, kamar
yadda ita ma ta gan shi...................
Ta sauke numfashi, ta fada a ranta,"Allah ka sa
aure na da Naseer alkhairi ne."
Ta yunkura ta tashi zaune,
"Yar jakar hannun ta da ta yasar bisa gadon tun
shigowan ta, ita ta jawo gaban ta, ta bude zif
din ta dauko wayar ta.
Ta mike ta koma jikin wata dirowa, wacce jerin
akwatuna ke bisa kanta." Ta jawo ta tsakiya, ta
binciko (Sim card) na ta, na gida Najeriya ta
dawo bakin gado ta zauna. Sannan tayi aikin
maida shi cikin waya. Jimawa kadan ta nemo
wata lamba mai dauke da sunan KAUTHAR. Ta
kira babu wani bata lokaci aka sada ta da
kauthar. Can ta tsinkayi ihunta, "ba dai kin iso
ba! Cike da faraa tace, "tun yaushe? Ai muna
shigowa kaduna, ana sallar magrib. Zaki zo
goben?" "Me zai hana? Allah ya kaimu goben
lafiya." "To shike nan ki gaida momi." "Zataji".
Sukayi sallama. Tana cire wayar daga kunnanta,
kiran wata bakuwar lamba ta shigo. Tayi zuru
tana kallon wayar a yayin da tuni zuciyar ta ta
aiyana mata mai kiran wayar. Nan da nan
gaban ta yayi mugun faduwa. Hannun ta ya hau
rawa,bata sami motsawa ba sai da kira ya
katse, sannan ta sauke numfashi. Bata gama
numfashibba wayar ta sake daukar ruri.
Hannunta bai daina rawa ba illa ma karawa da
yayi a hakata danna OK, cikin kasala ta kanga
wa kunnanta, murya sanyaye tace, "hello! Ya
numfasa ya amsa, "baki da alkawari. Haka
mukayi da ke? Ta numfasa, yasa ta zama mara
gaskia a zahiri,don haka ta amsa laifin ta, "Ayi
hakuri, ban .... Ya katseta."baki damu dani bako
Nusaiba? Ni kuwa ko alama na kasa sukuni,
gaba daya lissafi na a dagule yake. Nasan ba
zaki gasgata ni ba. Amma zaki sha mamaki idan
nace miki gani a kofar get din ku." Ai kuwa bata
gasgata abin da taji ba don sai data mike
zumbur tsaye tace, "kace me? Dan murmushi
yayi jim, yadda ta firgita, "tsoro kikaji? Tace,
"dan Allah da gask kakeyi? Yace "ai ba karya a
son da nake miki. Kawai na kira babana don
nace masa na iso sai ya cemin shima yna nan
Abujan yazo wani (conference) na kwana biyu,
shine yace in jira shi mu wuce kano tare. Ina
zaune a masauki tunannk ya addabeni ban san
lokacin dana bugo mota na taho ba, ki fito ina
nan waje." Shiru tayi ta rasa meke mata dadi? A
lokaci guda tausayin shi ya dirar mata a zuciya
ya bi ko ina a jikinta. "Me zance da bawan
Allahn nan? Ta tambayi knta. "Hello! Kina kan
layi kuwa? A firgice ta dawo daga duniyar
tunannta ta dan nisa tace, "gaskia Ibrahim da
dai kayi hakuri zuwa gobe kadawo, a san
abinyi."
Gaba daya guiwar sa ta kwabe ya, rasa
kuzarinsa. Murya raunane yace, "Nusaiba ba
kya sona, ita kenn karshen maganar. Abinda na
lura da shi kenan tun farko. Ko kuwa saboda
nace miki ina da mata shiyasa kika zuzzu ke
mun? Ba yaudarar ki nakeson yi ba ina gaya
miki gaskia ce tsakani da Allah. Mata ta batayi
min komai ba shekarun mu uku da aure. Kawai
Allah ne ya jarabce ni da sonki. Tsananin so mai
tada hankali. Nusaiba da kinsan halinda zuciya
ta tashiga tun daga lokacin da kika bar ni a
(Airport), ya zuwa yanzu da baki ce in dawo
gobe ba. Pls ki tausaya min ki fito, in sake ganin
kyakkyawar fuskar ki ko nasamu barci yau." Ba
karamin dafa mata jiki kalamansa sukayi ba,
kwalla fal idanuwanta, sai dai babu abinda ta
iya yi, domin bata ma san wa zata dunfara ta
nemi izinin sa ba. Kana dan siririn hawaye ya
gangaro bisa kuncinta, kafin tace, "duk abinda
kake nufi ba haka bne Ibrahim. Kaga dazu Abba
yayi mun fada yanzu kuwa babu yadda zaayi
insake zuwa ince masa gaka nan, ka sake biyo
ni. Shi yasa nace ka hakura zuwa goben zan san
yadda zan bullowa alamarin. Kaji? Don girmn
Allah kayi hakuri. Ka nemo layin Antina nasan
zata kwantar maka da hankali ka......... Ji tayi
dim!din! Din alamun an kashe wayar. Da bayata
fadi bisa filo, me zatayi? Ba kuka ba. Gaba daya
lokaci guda taji Ibrahim na ratsa ko ina cikin
jikinta, sabd tsabar tausayinsa. Rike hannayenta
kawai taji anyi, gaban ta ya sake faduwa da jin
muryar umminta, "ke! Nusaiba menene? Ta
tarairayo ta, ta tashi zaune.Da sauri ta rungume
Ummin." Na ce menene? Tayi shiru, don bata da
abin cewa.hasali ma ba'ason ranta Ummi ta
riske ta a wannan yanayin ba." Bebin Abba na
ce menene?"Tana kudundune ta amsa, "Ba
komai ummi." Ta ce,"Karya ki ke yi. Haka kawai
ba za ki hau kuka ba,
akwai dalili."ta dago mata fuska,"Dube ni nan."
Tayi zuru, kwalla na diga." za6in Abbanki ne, ba
kya so?"Da sauri ta kada kai,"A'a Ummi. Allah
ba haka bane. Ta ce,"Nusaiba, sanin kan ki ne
Abbanki ba zai cutar da ke ba, haka kuma ba
zai so ya ganki cikin irin wannan damuwar
ba.idan kin san bakya son Yaron nan, to ki gaya
min gaskiya, in rarrashi Abbanki ya hakura da
wannan abu.
Shi yana can daki, yana ta murna yana sa miki
albarka, ke kina nan ki na ta koke?
Bebi na,
ke kadai gare mu,
ba za mu so wani ciwo ya kama mana ke ba,
har mu rasa ki.
Menene gaskiyar magana?"ta goge hawaye,
kalaman Umminta suka sanyaya zuciyarta.
Ta dube ta ta ce,"Ummi wallahi duk abinda da
na gaya wa Abba na, gaskiya ne."
To menene dalilin kuka?
Ta sunkuyar da kai kasa, ta warware mata
labarin Ibrahim. Ummi tayi shiru, kafin ta nisa
ta ce "Lallai Ibrahim abin tausayi ne, amma bai
kamata ki kwanta ki na koke-koke ba, sai kiyi
addu'a.Allah ya sanya masa hakuri."Ta ce,"Ni
dai ko, Ummi ki gaya wa Abba na gobe, idan ya
zo, ya kira shi,
ya ba shi hakuri.
Ya gaya masa ina da wani."
Ko ba haka ba?".......
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Ajininsa yake 1-08
Posted by ANaM Dorayi on 08:10 AM, 09-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
.Ta shafa kanta ta ce,"Haka ne Bebina,
to ki daina kuka. Naseer yaron kirki ne, don ya
fito daga gidan mutunci. Sai ki ci gaba da
addu'a.Allah ya tabbatar da alkhairi.
Yadda ki ka faranta mana rai.
Insha-Allahu ke ma za'a faranta miki.
Allah yayi miki albarka."Amin Ummina." Ta ce,
tana dubanta. Ummi tayi murmushi, ta dan kama
ha6arta ta ce,"Ila gadan! Insha-Allahu. Inji
Nusaiba fuska sake.Ma'ana ta ce,"Sai da safe."
Ta amsa da "In Allah ya yarda."
Ummi ta mike ta bar dakin, tana waigen
'yarta.Wata ajiyar zuciya tayi, ta koma da baya ta
sake kwanciya.
"Allah gani gare ka, ka za6a min wanda ya fi
zama alkhairi."
Idonta kuri, ta kasa barci.ko alamar sa ma bata
ji.ji take kamar son Ibrahim yana neman ya
rinjaye ta."
Zakakan kalaman sa sun yi ta zuwa, suna dawo
mata a rai, irin labaran daya rinka zuba mata a
jirgi.
Idan ta rufe ido, shi take gani.
A karo na farko daya zauna kujerar da ke gefen
ta, ya yi mata sallama." Assalamu-
alaikum.............!
Kawai ta kan tsinci bakin ta yana sake amsa
sallamar, ba tare da sanin tana yi ba.
Dare ya tsala, ta rasa me zuciya ta ke da
Ibrahim?
Don haka tayi wuf, ta mik'e ta nufi bayi, ta
shiryo lafiyayyar alwala, ta fito ta nufi sallaya.
Hijabinta da zani, ta daura ta dora hijabi, tayi
niyyar nafila.
Bayan ta kawo raka'a 2 masu kyau, sannan ta
zauna ta dukufa addu'an Istahara.
Sai da ta kammala, sannan ta sami nutsuwa
cikin ranta.
Ta sake mikewa ta kawo wutiri, kafin wani lkc ta
soma jin barci.
Nan bisa sallayar ta, barci mai nauyi ya dauke
ta....
Tana ta tsala kuka, kofar wani tsalelen gida mai
kyan gaske, ba za ta iya sanin tsawon lkcn da
tayi tana zuba kukanta ba, mai tsuma zuciya da
ban tausayi. Kafadar ta, ta ji an dafa, wata
sansanyar murya ta kira sunan ta
"Nusaiba!,
Ta dago idanuwa jajur!
Ta dubi mai kiranta.
Naseer ne dafe da kafadar, suka zuba wa juna
ido.
Jim!
Sannan ya ce,"Taso mu shiga ciki."
Ba musu, ta mike, yana jaye da ita har bakin
kofa. Ja tayi ta tsaya cak! Tare da shirin fizge
hannun ta. Cikin sauri ya sake kamo ta,"Kar ki
k'i shiga gidan ki Nusaiba, ki sa ni ke uwar
'ya'yana ce. Ba a son raina............."
"Nusaiba!
Ke Nusaiba, ki tashi asuba tayi...Cikin mafarkin
muryar Umminta ke kwala mata kira.
Firgigi! Ta tashi, hawaye ne sharkaf a fuskar ta,
nan da nan ta kawo salati tare da share
hawayen, sannan ta amsa kira." Na tashi
Ummi."*****Allah Sarki***
Ta dafe goshi, jikinta tamkar an mata shegen
duka, da kyar ta mike ta nufi bayi, ta fito da
alwala, don sallatar asubah.
Tana ta lazimi bisa gadon ta.
Amma tunanin mafarkinta take yi. Menene
musabbabin kukunta? Babu abinda ta kawa wa
ranta, illa watak'ila Ibrahim ne zai zame mata
k'arfen k'afa.
Idan son shi ya hanata yi wa iyayenta biyayya,
ai ya cutar da ita. Naseet dai ta gani kiri-kiri,
amma ta kafe ta k'i shiga gidan sa. Nan da nan
ta daga hannu sama."
"Ya Allah na roke ka, kar ka kawo min ranar da
zan yi musu da iyaye na. Allah ka musanya
wannan kuka nawa, ya zama farin ciki a gare ni.
Allah ka daidaita zuciya ta akan tsananin son
za6in su Abba.
Ya Allah ka amsa, don albarkar da ka yi wa
Manzonka. Muhammad (S.A.W)." Haka ta koma
ta kwanta, ranta cunkushe har wani 6arawon ya
sake dauke ta.
Kamar a mafarki ta ji rurin wayarta, ta bude ido
cike da mamakin ba irin barcin daya dauke ta
mai nauyi gaske. Ta dauko waya ta duba.
Abban ta ne.
Da sauri ta dauka."
"Abba na!"
Ya ce,
"Duk gajiyar ce?
To ki zo mana in gan ki,
kafin na fita."
" 'Yar kunya ce ta sata murmushi,"Yi hakuri
Abba,
gani nan."
Ta diro da sauri, tayi bayi ta wanke baki da
fuska.
A gurguje ta sauya kaya, ta fice.
Lokacin kafe 9 dai-dai.
Da gudunta ta haye 6angaren Alhjn, ta tura kofa
tare da sallama.
Ya amsa yayin da take takowa cikin sauri tana
fadin,
"Kaifa asbahta ya Abba!
Shima fara'a yake yi, har ya iso inda yake
zaune. Ita ma zama tayi, ta yada kai bisa
kafadarsa."
Abba ina kwana?"
Lafiya lau."
Na ce duk gajiyar
ce har karfe 9 ban ga Bebina ba?"
Ta ce,"Barci ya sace ni." Ya ce,"Ummanki ta
gaya min sak'onki, kar ki damu, zan kira shi ya
zo yau, don in yi masa bayani kin ji?
Sannan ina ganin ma tare za mu fita, mu je ki
za6i irin motar da ki ke so.
Akwai sabbabin shigowa kala-kala, sai kin darje
Bebina."
Bakinta har kunne, ta k'ara langwa6e masa,"Na
gode Abba na."
Amma in tamabaye ka mana Abbana?"
Ya ce,"Me zai hana?
Ta ce,
"Shi Naseer wacce yake hawa?
Ya ji dadin tambayar ta, domin kawari yana son
ya rink'a jin zancen Naseer a bakinta."
Ya ce,"Uhm........... A halin yanzu dai (Civic)
yake hawa."
Ta dube shi da sauri "Abba sirikin (Dabai
Motors) ke hawan (Civic)?
Dariya yake yi, kafin ya ce," Kina da gaskiya, da
ni tunanina, sai zai fara angwaci, zan canza
masa.
Amma tunda haka ki ka ce, za'a bari ku je tare
ku Za6i irin daya.
Ya yi miki hakan?"
Ta gyada kai,
"Yayi Abba,
mun gode."
Tana shiru Hjy Zulaihat na shigowa da tiran
kayan abinci Alhjn. Nusaiba ta mike da sauri ta
amsa, ta kai bisa shimfidar da yake zama, don
cin abinxin.
Bayan ta gaida Ummi. Suka baje nan suka karya
tare.
Suna hira. Hjy Zulaihat bata bar dakin Abba ba,
sai 10:30, ta koma dakin ta, don yin wanka."
Tana shiga, wayar ta da ke ta faman ruri ta
katse.
Kai tsaye can ta nufa, ta dauka, ta duba (Missed
call) 5, duk lamba 1, wacce Ibrahim ya kira jiya."
Ya salam!
Ta fadi ido rufe Da sauri ta kira." Allah ya ba ki
hakuri, wayar ma ba za'a daga ba?"
Murya sanyaye ta ce,"Wallahi ba ni a dakin, ina
can wajen Abba na ne, ka hakuri, ka ji?
Sanyi ya ji cikin ransa, ya ce,"Ya zan yi, so ya
kama ni, ai sai yadda akai da ni.
Za ki sami fitowa ko sai gobe?"
Tace,"Maida wukar, gani nan fitowa."
Tana jin saukan numfashin sa ya ce,"Don Allah
kar ki dade,
na k'osa."
Ta aje waya, ta nemi wuri gefen gado, ta dan
raba hankali tayi shiru, ba tare da ta fahimci
dalilin shirun ta ba.
Can ta nisa, ta mike a natse, ta gyara zaman
mayafinta da kyau, ta baro daki ta koma wajen
Abbanta."
Suna nan tare da Ummi. Kai tsaye ta shaida
masu Ibrahim ya dawo. Ya dube ta da sauri, ya
ce,"Je ki ce ya shigo, ku same ni a falon baki."
Ta juya ta fiti cikin hanzari.
Zaune yake cikin mota (Camry), yayin da ta
budo get ta fito. Suna hada ido, zuciyar sa ta
hau bugawa, tamkar za ta tsaga kirjin sa. Cikin
kuzarinsa ya fito, baki har kunne. Da sallama ta
karaso gunsa. Ya amsa." Sannu da zuwa."
"Ke ma sannu da fitowa.
Ya mutan gida?
Ya jin dadin ki?
Tayi d'an murmushi,"Duk suna lafiya, amma jin
dad'i, ai ku ke da shi."
Kallon ta kawai yake yi, zuciyar sa kamar anyi
masa albishir da aljanna.
Wani kayatacen murmusji yayi, kafin ya
ce,"Wane jin dadi zan yi, bayan har yanzu ban
kama dahir ba?
Jiya zuciyata kamar za ta k'one, sbd tsabar
rashin ganin ki.
Me yasa za ki min haka?, So na ne ba kya yi ko?
Ta dan yi shiru jim.
Sannan ta ce,"Ba haka ba ne, amma yanzu mu
shiga ciki.
Abba ya ce yana son ganin ka."
Ya fadada fara'arsa cike da jin dadi ya ce,
"Rana kawai za'a sa mana,
mu je in ga Abban."
Yana kulle mota, jikinsa har rawa yake yi, haka
ta sa ma sa ido, tausayin sa zalla cikin ranta."
Ta wuce, ya biyo bayan ta, tayi masa jagora
zuwa falon baki.
Falon ya shiryu, iya shiryuwa.
Shi kan sa masaukin ya kayatar da shi.
Ta nuna masa kujera, ya zauna, kafin ta ce,
" Miniti 2."
Ya ce,"1 na ba ki."
Ta wuce tana dan murmushi.
Jimawa kadan, ta dawo dauke da tire cike da
ingantattun abincin karin safe, ta dire a gaban
sa, ta ce,"Abba ya ce," Ka yi (Break-fast), ga shi
nan zuwa ku gaisa."Ya ce,"To, na gode kin kuwa
san rabo na da abinci?, Ta dan dube shi yayi da
take harjada masa abubuwan cikin filet, ta dan
kada kai,"Tun wanda na dan ci jiya a jirgi."
Ido waje ta ce,"Kai haba, me yasa? Ya
ce,"Tunaninki kawai, sannan abinda ki kai min
jiya, ko alama bai min dadi ba.
Shima ya taimaka wajen hana ni cin abincin
dare.
Ina son ki Nusaiba, so mai ban mamaki, domin
ni ban ta6a zaton zan so wata 'ya mace, kamar
yadda na so mata ta ba.
Sai ga shi tashi guda, kin rikita ni Nusaiba, har
ina neman zarewa.
Allah yasa yadda ki ke zuba min abincin nan, ki
zabu min shi a cikin gidana."
Ba ta ce komai ba, domin kalaman Ibrahim
nema suke su kidima ta.
Kai Nusyy mene abin kidimawa a wannan
kalaman! Nima idan nadage zan iyasu...
Koya kukace?
Aje masa tayi a gaban sa, ta mike a hankali ta
ce,"Don Allah ka ci da yawa, bari inje in dawo.
Don me?"
Please!
Ki zauna,
kan dole ta zauna, saboda a gaskiya bata son
yadda Ibrahim ke cusa mata ra'ayin sa, tana
tsoron kar a wayi gari ta kama da tsananin son
sa, wanda zai iya wahalar da ita, kafin ta manta
da shi.
Tsit!
Tayi a zaune,
ba eh,
balle a'a.
Shi yake ta ba cikin sa abinci, wani lkcn ya kan
yi santi da gangan, don tayi dariya, amma ina!
Sai dai tayi murmusji, ta kauda kai,
Bayan ya kammala, ta tattara kayan, ta dauka,
yana fadin "Ki cewa Mama na gode da (Break-
fast)
Ta dan juyo, ta dube shi ta ce, "Zan fadi."
Ta sa kai ta fice.
Shiru yayi, yana mamakin kansa, domin shi
abinci, idan ba na matar sa ba, duk gaibu ne.
Ba wani sakin jiki ya ci shi yadda yakamata.Yayi
kasake yana tunanin tsiyar da Ummansa take
masa." Da kafin kayi auran. Abincin wa ka ke
ci?"
Uban 'yan gulma!
Kada kai yai, yana wani bazawarin murmushi.
Hannun sa daya yana shafar cikin sa har da
wata gajeruwar gyatsa.Sallamar daya tsinkayo
ce, ta sa ya dai-daita sahun sa.
Yana amsawa, yana ganin Alhj yayi sauri ya
mike tsaye, yana masa sannu cike da
girmamawa."
"Zauna mana."
Inji Alhjin.
Sannan ya zauna,
suka ci gaba da ganawa."....
Nusaiba tare da Umminta suke hira a babban
falo. Bayan wucewar minti 20,. Alh. Basheer ya
dawo, ya cewa Nusaiba,"Ki je ki sallame shi,
mun gama magana."
Ta mike ta nufi falon baki, ilahirin jikinta a mace
yake, sbd tsabar tausayin Ibrahim.
Koda ta iso bakin kofar, haka ta tsaya kusan
minti 3, kafin ta tura kofar ta shiga.
Bai iya amsawa ba, kan sa a saye cikin guiwa.
Zuciyar ta, ta k'ara raunana.
Suka zauna shiru tsawon lkc, kafin tayi karfin
hali, ta katse shirun."
"Ibrahmin don girman Allah, ka yi hakuri kaji,
mu yi addu'ar Allah ya sa hakan shine ma fi
alkhairi a gare mu."
Ya dago ya dube ta, ido jajur!
Ya ce,"
Na yi Nusaiba, ni zan koma."
Nan da nan idanunwanta suka kawo kwalla,
murya raunane ta ce,"Bana so in yaudare ka ne
Ibrahim shi yasa, don Allah kar ka dauki
wannan abu da wata fuska."
Ya kada kai, ya ce,"Hakan ya na da kyau
Nusaiba, babu 6oye-6oye ko rufa-rufa.
Abba yayi min kalamai ma su dadi da kwantar
da hankali, sai dai kin san abinda rai ke so, bai
ta6a samun nutsuwa lkc guda, muddin zuciya
bata sami abinda take bukata ba.
Na san zan shiga wani hali Nusaiba.
Domin son ki ya riga ya shige ko'ina a jiki na."
Ka barwa Allah komai." Ya ce,"Na bari kuma ina
taya duk wanda ya same ki murna, saboda ba
k'aramar sa'a yayi ba.
Amma zan so ace ki dan yi (Saving) lamba ta,
mu rink'a gaisawa, kafin auran ki ya tabbata.
Zan sami wannan taimakon?"
zan yi (Saving), amma da sharadin gaisawa
kawai."
Da k'yar ya mik'e tsaye, ya sanya mata ido,"To
na gode............... Ya ci gaba da kallon ta,
fuskar dauke da 6acin rai a bayyane.
Shi yasa ita ma ta kasa kallon sa.
Kamar zai sake cwa wani abu, sai kuma ya kasa.
Ya juya da suri ya fice daga falon.
Ya dan jima da fita.
Nusaiba na zaune tana ta sharar kwalla, kafin ta
samu hawayen suka tsaya.
Ta mike cikin hanzari, ta bi shi.
A zatonta ma ba za ta same shi ba, amma tana
tura kofa, ta gan shi zaune da hankicin yana
share fuska.
Kirjin ta ya ci gaba da har6awa, ta tsaya jikin
kofa ta ce,"Allah ya kiyaye hanya,
idan ka yi waya da Madam, ka ce ina gaisheta."
Can k'asan mak'oshin sa ya amsa,"Za ta ji."
Tare da sawa mota makulli, ya bata wuta, bai
saurari komai ba, ya bar wajen.
Nusaiba na tsaye sai da ya 6ace ta dawo cikin
hanzari.
Babu kowa a falon k'asan, don haka ta nufi
6angarenta.
Kai tsaye shirin wanka tayi, dan lkcn kankani, ta
kammala wankanta, ta tsala kwalliya da a
tamfarta mai kyawun gaske.
Kwanciya tayi shiru, tana tunanin abubuwa
masu yawa.
Duk da dai bata son ranta ya na sako mata
Ibrahim, sam ta kasa fidda tausayin a ranta.
Ta lumshe ido ta dawo da hoton Naseer cikin
zuciyar ta,"Me yasa na ke ta faman kuka,
ban son shiga gidan ka?
Ta kasa ba kanta amsa, saboda ba ta ma san
me ranta ke nufi a game da Naseer ba.Ita bata
kin sa,
ita kuma bata wani zazzafan dokin sa take yi ba,
duk da ta hakikance za6in Abbanta ingantace
ne.
Amma kwarai mafarkinta na rikita ta, shi yasa ta
ke masa fassara kala-kala.
Cikin duniyar tunanin ta ne, ta jiyo kwakwazon
Kausar.
"Ahalan-wa-sahalan!
Larabawan Jordan!
Tayi wuf ta diro daga gado, tayo waje, suna
kicin tare da Ummi suna gaisawa, can ta nufa
suka nufi juna suka rungume. Kausar na da
surutu, ga zak'in murya tare da saurin magana.
Suka dubi juna.
Kausar ta juya kan Ummi,"Ummi wallahi
yarinyar nan tana jin dadinta, wai mai karatu ce,
ta dawo kamar fanke!
Suna dariya, ta bata amsa,"A'a kin manta
alkubus ne?
Ta ce,"Ananandai, kin kalli madubi kuwa kin ga
wadannan kumatun?
Ta tamabyeta,
tana ta6a mata kumatu.
Ta doke hannunta tare da fadin,
"Ban sani ba,
masharranciya.
Ni don Allah zo mu je, 'yar sa ido.
Suka wuce rike da hannun juna.
Ummi da dariya ta kada kai."
Kausar kenan!"
Daki suka fada, ta wurgar da jaka gefe, ta zube
bisa gado.
Ina can tunanin ki ya isheni cikin aji, wawan
lakcaran nan, ya ki sallamar mu."
Nusaiba ta zauna gefen ta, ta ce,"Ai ka ji halin
Dan-Adam. Yanzu da bai zo ba, sai ace ya ki
zuwa, don rashin kishin kai."
To kuma sai ya shiga lokacin mu?"
Ke manta, don Allah ina tsaraba ta tukuna?
Dan murmushi tayi,
"Ni in gaya miki tun jiya da na jefar da jakar ko
ta kanta ban sake bi ba.
Ita ce can?"
Ta fadi tana nunuwa.
Mikewa ta yi ta tanyo ta," Ina fatan kin kawo
min turarukan nan?"
Bude dai ki gani." Ta wurgo mata dan makulli.
Tasa ta bude dan kankanin kwadon da ke
makale jikin zif din.
Ta wangame Jakar. Su 2 suke fiddo kaya kala-
kala na sawa, turaruka , mai iri-iri, a goguna da
dukkan kayan kyale-kyalen mata.
Kausar ta darji na darza, ta maida jakar ta.
Bayan sun kammala da tsaraba.
Nusaiba ta kira Mariya 'yar yarinyar da ke masu
aiki, ta kawo wa Kausar abubuwan kusa da ba
ka za6in ta. Da kofi jus a hannun ta, ta dubi
Nusaiba ta ce,
"Bebin Abba kenan, to yanzu kuma sai me?
Ta dan ta6e baki, ta ce,"Sai me kuwa?
Zama tare da Abba na, gani ga shi."
Tayi 'yar dariya, ta aje kofi k'asa,"Magulmaciya,
ai karyar korar samari, ta kare.
Dole yarinya ta tsaida na aure, ko mu samu
wani Sugar Daddy mu mik'a masa."
Ta zungura kafadar ta,"Aniyar ki ta bi ki. Kin san
ma me ke faruwa?"
Sai kin feshe ni."
Ta dan karkace kai, ta bata labarin Ibrahiim
yadda suka hadu a jirgi.
Ta kwa6e fuska ta ce,
"Amma guy din yayi, sai dai ya dan kwafsa,
tunda yana da mata.
Ajinsa ya sauko."
Ya sauko?"
"Eh,
mana,
kin san fa ni duk harkar kishiya ba ni a ciki."
Dariya ta bata,"Ke bakin kishinki zai hallaka ki,
ina ruwanki da ita?"
Ai ni duk inda ta fadi, sha ne, ni dai rokona
Allah ya hada ni da na gari.
Aje wannan maganar, da alama so ya kamaki."
Eh,
ya kamani,
sai dai abin ba zai yiwu ba."
Ta dan ware ido."
Don me,
bayan ki na sonsa?
Matar ce jaraba?"
Ta dan nisa ta ce,"Abba na ya za6a min miji."
Mai-maita don Allah?"
Na ki maimaitawa, kada Allah yasa ki ji."
Na ji abin ne kamar a oldings days.
Me yasa Abba yayi maki haka?"
Ya ga shi ne ya fi dacewa da ni,
kin kuma san Abba ba zai kai ni gidan wahala
ba."
Ta kada kai tare da yamutsa fuska,"Ni kuwa kin
ga inda za'ayi daga dani kenan.
Abar ni in darje, in za6i wanda ya kwanta
min."ta zuba mata ido, kafin ta ce,"Kausar
kenan.
Kawata kaza kanki da motsi."
Ta ce,"Allah ya isa,
banza!
Ta 6alla mata harara, ta juya tare da sakin
wawan tsaki.
Don na mutu a tausayinki, shine zaki wulakanta
ni.
Allah yasa mai duka ne, Abba bai sani ba,
kullum yayi ta jibgarki, kamar 'yarsa."Ta sa
dariya, ta sa hannu ta jayo ta,
"Kawalli kenan.
To huce, ki ji wani dan bayani...........Ta katse
ta,"Ba wani bayani, kawai ki gaya wa Ummi ke
ga wanda ki ke so.
Kar fa ki manta, wanda ba ka so, ko kallon sa
ba ka so yi balle aje ga biyayyar aure. Amma ke
na ga alama za ki yi wasa da rayuwar ki."
Ta ce,"Ba haka bane kuma zan so ki dan natsu
ki fahimci abin da zan ce."
Ina jin ki."
Ta ce,"Na dade ina wani nazari akan auratayya a
wannan zamanin.
Ta yadda aka maida aure abin wasa ko kuma
ince don wani jin dadin bukata, sa6anin ibada
kamar yadda ya zo daga Manzon mu.
A zamanin da can kamar yadda a kakanin mu
suke ba mu labari, sai ranar da aka kai ki dakin
miji, sannan za ki san wanda ki ka aura, haka
shi ma mijin, a lkcn zai san ki.
Amma abin mamaki sai ki ga sun zauna lafiya.
Mutu ka raba. Da tafiya tayi tafiya, anyi karatun
boko, wai an waye, sai aka ce wannan tsarin
auran dole ne.
Aka soke wannan tsari, aka ce abar kowa ya
aure za6in sa.
Sai ga shi a lkcn auran za6in abubuwan sun
rikice.
Aure ya zama wasa, an maida saki ba a bakin
komai ba.
Wallahi wani auran ko Shekara ba'ayi za'a fara
sa, in sa.
Wani lokacin ma ki tsince su a kotu.
Shi yasa a nawa ra'ayin, ban ta'allaka soyayya
zalla ba a cikin zama aure.
Dole sai da addini,
"Kyan asali,
"Tarbiya.
"Hakuri,
"Juriya, da sanin me zai je, ya dawo?
Wannan shine abubuwan da kakaninmu suka
rinka dubawa wajen auratayya.Ina son ki
sani,abinda babba ya hango. Yaro ko yahau
rimi, bai zai gano shi ba.
Ita kuwa zuciya a kodayaushe kyale-kyale tafi
so, duk wanda ya biye mata kuma, karshen
al'amarin ba zai yi kyau ba.
Saboda haka Abba yayi dai-dai da yayi min zabi.
Ubangiji Allah ya taya shi zabi.
Abu na gaba da na ke so ki yi koyi da shi
kawata, shine kar ki hakikance wa ran ki dukan
abinda zuciyar ki ta bukata.
A kodayaushe ki fi rinjaye bisa za6in Allah."
Kausar ta numfasa ta ce,"In yi miki ta Indiya,
Vah! Lak lak shukran, mere dost! Tana
murmushi ta amsa, " Ki na nan da Indiyancin ki,
na dai ji shukran godiya ce, wannan larabci aka
sata.
Na ce da kyau, godiya dubu-dubu kawata. Ai kin
yi nasiha, na kuma gamsu Pyar ho gaya." oh ba
za ki daina Indiyanci ba kenan, me ki ke nufi?"
A sannu a sannu za'a so juna. Wai ma waye
gayen da yayi sa'a haka? Ta ce," Ban san shi ba,
hotonsa kawai na gani a dakin Abba, shi yake
gaya min dan wasan Polon sa. Yaro ne mai
hankalu kuma ya fita gidan mutunci...
Comment dinku yana karamin Karin gwiwa, so
keep it up
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Ajininsa yake 1-09
Posted by ANaM Dorayi on 04:39 PM, 09-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
.
Sunansa Naseer."
Tayi fit, ta ce,"Naseer Jah-Jah!"
Ke ba fa Yakubu Jah-Jah ba.
Naseer aka ce ta ce, tun yaushe tutar Yakubu ya
sauko, ai yanzu Naseer shi ke jah.
Ki na nufin shi Abba ya za6a miki?"
Ta zura mata ido,"Kin san shi ne?"
Ta miko hannu,"Ke dai ban hannu tukuna."Ta
bata suka tafa, jikin Nusaiba ya k'ara sanyi,"Don
Allah san shi?"
"Ba dole ba, ni da na ke bin Daddy kallo. Sai
yanzu na k'ara yarda da maganar ki, komai
babba ya hango.
Yaro bai iya ganinsa ko ya hau abinda ya fi rimi
tsawo.
Naseer na shan yabo wajen kowa, sannan kowa
na son sa.
Lallai Abba ya san abinda ya dace da ke."
Dan lumshe ido tayi, ta ce a hankali,"Masha-
Allah."
Sannan ta bude suna duban juna,"Kin ga abinda
na ke ke gaya miki ko?"
Yanzu me ya rage?"
Kawai mu jira lokaci, biki mu guwangwaje, ranar
ni kai na sai na hau doki.
Shi kan sa Jah-Jan dole ya daga min kafa.Ta
bata hannu suka tafa.
Nusaiba ta ce,"Kin ga yanzu dole a nemo kayan
aiki, ina littafan hausa? Ta ce,"Suna nan, amma
fa na aje na Momin Zariya ban karan ta su
yanzu."
Don me?"
Wasu maganganu tayi akan 'yan (Flashing) ya
bata min rai, kai tsaye na buga waya na zagi
banza."
Inna-lillahi wa-inna-ilaihir-raji'un! Ki zage ta? Ta
figo jakar ta tana fadin,"Bari ki gani, kullum
yawo na ke da littafin, koda musu zai tashi in
nuna shaida."
Ta jawo shi, ta ta bude mata wajen, ta karanta.
Tana gamawa ta dube ta.
"Amma kuwa Kausar kin ba ni mmk. Yanzu ke
saboda Allah ina hankali a cikin irin wannan
(Flashing) Haka kawai ba sa ki aka yi ba, ki
dauki waya ki hau (Flashing) sama da goma sha,
har dan cajin mutum ya kare.
Menene amfanin sa?
Ke ko ni da ne ke kawar ki, na yi miki haka,
dole na kure ki, ki zage ni.
Ai babu abinda ya fi kona rai a game da harka
waya irin (Flashing), saboda ba ka san a wane
yanayi mutum yake ba, watakila ma cikin jama'a
yake, balle wannan da aka ce har cikin dare yin
sa ake yi.
A gaskiya ban goyi bayan masu wannan dabi'a
ta Flashing)
babu iyaka ba.
Kar kuma kin mance, su masu hulda da jama'a
ne, ke ki na (Flashing), wata can na yi, ko ma
ince wasu, ai kin ga dole abin yayi masu yawa
har su ji zafin abin."
Ta kwada mata harara, ta ce,"Suyita jin zafin
mana, mu muka sa su rubutun? Ta ce,"Ayya
kawata.
Ban so ki kasance cikin irin mutane masu ci,
suna share baki ba.
Ma'ana duk mutumin da zai miki abinda za ki
amfana da shi.
Ya fi gaban wannan furucin da ki ka yi. Ba
karamin kuskure ki ka yi ba, da ki ka ce kin zage
ta.
Domin Manzon mu Annabi Muhammad (S.A.W)
ya ce,"Kada ku kasance cikin wadanda za su
tashi ranar gobe kiyama suna matsiyata, alhalin
sun yi ibadar su daidai. An tambayi.
Mai girma da daukaka, wanene matsayin
lahira?"
Sai ya ce,"Shine wanda zai zo da aikinsa cif-cif!
Amma ya ha'inci wannan, ya zalunci wancan, ya
shiga hakkin wannan.
Sai ya kasance an debe ladarsa, an biya su, har
ta kai ga ba shi da sauran lada, daga nan za'a
fara diban zunubansu ana dora masa.
A karshe zai tashi a tutar babu. Wa-iyazubillahi!
Saboda haka ki daina daukn irin wadannan
abubuwan na shiga hakkin jama'a a kankanin
zunubi.
Ubangiji bai yafe hakkin wani har sai shi wanda
aka zalunta ya yafe, ina fatan kin fahimce ni? Ta
sauke tagumi ta ce,"Duk jiki na ya yi la'asar.
Allah ka tsare mu da tashin matsiyatan lahira.
Bari ma dai ki gani."
Wayarta ta dauko,"Me za ki yi?
Ta ce,"Neman afuwa."
Dan murmushi tayi,"Ina son ki wajen daukar
nasiha. Nemo ta mu gaisa. Daga nan mu nemi
shawarwari."
Cikin dan kankanin lokaci waya ta sada su da
Momin Zariya. Jimawa kadan ta dauka tare da
sallama. Kausar ta amsa,"Na san ba za ki gane
ni ba Momi, amma an ta6a kira na fadi wata
magana maras dadi akan maganar da aka yi sbd
'yan flashing.
Gaskiya na yi tunani na ga abinda na yi bai da
ce ba in kira ki, in ba ki hakuri.
Momi ta ce,"Haka ne, kuma har ga Allah ya
wuce. Rashin fahinta ke sa wa mutane ke ganin
ba'a kyauta ba. Amma da an san irin kashin da
'yan flashing ke yi, da irin ku ba su zage mu ba.
Bayan wannan wai har kiran waya ayi hankali
tashe, ace don Allah ki bugo anyi mutuwa.Jiki na
rawa zan kira, wai sai ki ji ana kyalkyar dariya.
Menene wannan?
Yanzun saboda Allah don ka kira mai irin
wannan marasa hankali, wanda bai san inda ke
masa ciwo ba. Ka yi laifi?"
Ta nisa ta ce,"Tafdi!
Lallai wannan rashi hankali ne, abinda kuwa ya
raba mutun da dabba kenan hankali.
Hakuri za ki yi Momi aikin jama'a ki ke yi, dole
ki rinqa ganinsu iri-iri..
Tayi murmushi,"Wannan ya zama dole, ban
kwana da kowa, ban tashi da kowa.
Duk wanda ya gyara, ya sani, haka duk wanda
ya 6ata, ya sani.
Shi Dan-Adam ai tara yake, bai cika goma ba,
babu wanda zai ce ya wuce zagi a doron kasa.
Saboda haka ni duk wanda ya zage ni, na yafe
masa, ni ma ina rokon wanda yake ganin na
6ata masa, to ya yafe mi. Saboda halin rai."
Kausar ta cika da al'ajabi, har ta rasa ta cewa.
Jim kadan ta ce,"Ga kawata Nusaiba, za ku gaisa
ta ma kusa aure, sai ki bata shawarwari.
Nusaiba ta amsa, ko dama sifikar a bude take,
tana jin komai.
Bayan sun gaisawa.
Momi ta kara da cewa,"Shawarwari suna nan
jibge, cikin littafai. Idan mai karatu ya natsu, zai
fahimta, ba wai dadin lbr kawai ba.
A karshe sai ince bayan hakuri, a kara da juriya.
Jurewa kwaramniyar aure, shi ke sa wa zama ya
dore irin na iyaye da kakkanin mu. Allah yayi
yagora, ya zaunar da mu lafiya da mazajenmu."
Ta ce,"
Amin.
Mun gode
Momi.
Don Allah zan tambaye ki, ina fatan ba za ki yi
fushi ba?"
Ta ce,"Allah yasa na sani.
Don Allah shekarunki nawa?
Kuma 'ya'yanki nawa?
Ta ce," Bana ina da shekaru arba'in da daya 41.
'Ya'yana takwas 8,, sai daya da Allah yayi wa
rasuwa.
"Wai, lallai Momi kin mika, to Allah ya raya su,
rayuwa mai amfani, ya jikan wanda ya rasu.
Mun gode."
Ta ce,"Amin, ni ma na gode."
Kausar ta daga murya,"Sai anjima Momi, ni suna
na Kausar!
"To Kausar, ke kuma yaushe ne auran na ki?"
Ta ce,"Da saura Momi, karatu na ke yi." Shi
kenan Allah ya za6o na gari. Sai Anjima."
Amen.
Suka kashe waya.
Nusaiba ta budi Kausar,"Kin ji ko?" Ta ce,"Borin
kunya kawai na ke yi, ashe sa'ar Momina na
zaga. Daga yau Insha Allah ban sake ba.
Ta ma yi wani littafi TARKON AMANA, ban
karanta shi ba.
Amma gobe zan shiga kasuwa."
Tana dariya, kawai suka tsinkayi kiran sallah
cikin masallaci dake like da gidan."
Wai azahar ce tayi,? Inji Kausar. Nusaiba ta
ce,"To da zauna nan kina zagin mutane, sai dai
ki ji wuf a kabari. Ta shige bayi ta bar ta da
kwakwazo,"
Banza!
An dai yafe min, ko dama da wa da na zaga??"
*******************
Shi kuwa Abba bayan kammala shirin sa, misalin
sha dayan rana ya bar gida bai zame ko'ina ba,
sai Zariya.
Malam Balarabe na zama jiran sa kamar yadda
ya shaida masa ta waya cewar yana tafe, don
gabatar da wata magana. Shi kan sa da ya iso
gidan su Naseer, ya ga sauyi.Koda ya shiga ciki
kuwa abin ya ba shi mmk. Kuma Naseer ya kara
burge shi, ganin yadda ya gyara gidan su
gwanin sha'awa, cikin falon da aka sauke shi.
Nan ma komai ya ji dai-dai k'arfin samun
Naseer, hakika kowane ya zo, za'a fita kunya. An
kuwa fita kunyar Alhj domin tarba ta
musamman aka shirya masa, duk da cewa
Naseer kan san bai san da zuwan Alhjn ba,
kuma Abba bai gaya masa ba.
Saboda lkcn da Alh. Basheer ya yo waya.
Naseer bai gida.
Bayan natsuwar su, su biyu a cikin falon. Alh.
Basheer yayi gyaran murya, ya fara gabatar da
abinda ke tafe da shi, "Na san zakayi mmkn
zuwa na, ba saboda zumuncin da ke tsakanin
mu ba.
Amma watakila dalilin zuwa na, ya ba ka mmk.
Sai dai a hakikanin gaskiya, ba abin mmk bane
ga shirin Ubangiji, domin shiya hada ni da
Naseer kuma ya sanya min kaunarsa.
Kaunar tayi yawa Malam Balarabe, har na ji ina
son hada zuri'a da ku.
Ma'ana 'ya ta Nusaiba na ba Naseer."
Gaban Malam Balarabe ya fadi ba kadan ba,
sannan ya rasa a wane yanayi yake?
Ana wata ga wata kenan, ya ma rasa wane,
bayani zai yi?
A matsayi da girman Alh. Basheer, ya d'auki 'ya
ya ba su, ai kar6a ya zama dole, don ko
mafarkin bai ta6a gigin tunanin wannan abu ba.
Kwarya ta bi kwarya...........Inji hausawa.
Allah mai iko. Bakin sa har kunne ya ce,"Kai!
Kai!! Kai!!! Alhaji wannan sako da girma, yake,
mun gode, Allah ya saka da alkhairi, ya taya mu
rik'e amana."ya ce,"Amin, sauran magana kuma
Naseer ya je su ga juna, domin jiya ta dawo
daga Jordan, ta kammala karatunta." Ya
ce,"Madalla, kawari Naseer ya gaya min
shekaran jiya har yake ce min ka yi masa
maganar makaranta, ka na son ya ci gaba.Na
ce,ai shi ya tsaya shishirinta da yanzu ya gama.
Sai dai akwai wani hanzari, ba gudu ba Alhj,
wanda ya zama dole in fade shi. A hakikanin
gaskiya akwai wata yarinya da aka ba Naseer
tuntuni, jira ake ta gama sakandirinta ayi auran.
Bana ma za ta gama. Ka ji abinda ya sanya ni a
damuwa, ban kuma san yadda za'ayi ba?"
Shi kansa Alh. Basheer zancen ya motsa
zuciyarsa, jikin sa yayi sanyi jin shiru yana dogon
tunani. Amma ko alama ran sa bai jirkita da
wani bakon tunani ba, tsabar kaunar Naseer ke
nuna masa babu wata matsala. Ya dubi Malam
Balarabe ya ce,"Ai Naseer mijin mace 4 ne, so
ina ganin ba wata matsala, na riga na ba shi
Nusaiba, ya hada duka ya aura, na dauki nauyi
komai. Allah ya taya shi riko bisa adalci."
Fafdi! Wace irin kauna kuwa Alhj ke wa Naseer?
ko alama Malam Balarabe bai san irin ta ba.
Ashe akwai sauran irin su Alh. Basheer a
duniya?
Ya karkada kai ya ce,"Ba ni da bakin godiya Alhj.
Bari dai in kira Maman shi, ta taya ni."
Ya mike da rawar jiki, ya leko ya kwalawa
Umma kira. Ta amsa, ta same su a falon saye
da bakin hijabin ta, gefe ta zauna. Sannan
Malam Balarabe ya mayar mata da bayani. Ita
kan ta, ta ji dadi fuskar ta, ta nuna karara, sai
dai tunani dan gogan take yi, jin cewar bai ma
san da zancen ba.
Da wace fuska zai dauki al'amarin? Bata da
amsa tilas, Naseer ne zai fayyace komai.Wannan
tunani shi ya sace mata guiwa. Bayan ta gama
murna da godiya ga Alh. Can ta koma kuryar
dakin ta tayi zaune gefen gado tana jujjuya
al'amarin cikin ranta. Tare da tambayar kan
ta."Wane irin bayani za mu yi wa iyayen Zarah?
Ta nisa ta ce,"To ya Allah kai ka shiryo wannan
al'amari, ina rokonka ka sanya mana fahimtar
juna."
Tana gama addu'ar ta, ta jiyo kiran Malam, ta
amsa.
Ya ce ta zo Alhj zai koma.
Ta yo waje, nan tsakar gida ta iske shi, suka yi
sallama tare da kara kwarara godiya.
Hannu ya zura aljihu, ya debo kudin da shi
kansa bai san ko nawa bane, ya mika mata.
Ta kada kai ta ce,"Alhj ai mu ne za mu bada
tukuici.
Ya dubi M.Balarabe." Malam,
Naseer d'anta ne ko d'a na?"
Ya amsa yana murmushi,"Ita ma ta san dan ka
ne Alh. Ya juya kan ta,"Amshi na ce, ba ruwan
ki da zancan Naseer."
Ta sa hannu ta kar6a tare da godita mai tarin
yawa.
Bata gama rufe baki ba.
Naseer ya bugo sallama, ya shigo, suna amsa
masa.
Bakin sa har kunne,
"Ah!
Alhaji,
na ga motar ka a waje.
Ai ban san za ka zo ba, da ban fita ba."
Ya ce,
"Ai wajen Malam na zo,
shi yasa ban ce ma zan zo ba."
Ya dan duk'a yana gaishe shi.
Bayan ya amsa, ya k'ara da cewa,"Ni zan koma
kenan."
Suka wuce. Naseer ya taka masa zuwa, zaure.
ya sallame shi, ya dawo ya bar su tare da
Malama Balarabe.
Umma na ta k'irgan kudaden ta 'yan d'ari
biyar-biyar sabbabi dubu tara da d'ari biyar.
A bisa dukkan alamu dubu goma Alhj ya so
bayarwa,
sharrin sababin kudi ne, d'aya tayi munafunci
ta like can jikin 'yar uwanta a aljihu.
Naseer na shigowa. Ya amshe su yana fad'in,"Su
Umma kenan, ina nawa kason?
Ta ce,"Ba ga su nan a hannun ka ba,
diba mana." Ya zauna gefenta,"Zarah fa
zan siya wa Cakulet." Ta fige tana fad'in komai
Zarah, bakin ka bai ko gajiya." Yayi 'yar dariya
"Umma ke ma fa kullum sai kin tambaye ni ita,
me yasa na ki bakin bai gajiya?"
"Ban sani ba."
Ni kuwa na sani, son ta ki ke yi."
Ta mike ta wuce
uwar daka, don adana kudinta, ta bar shi nan
yana mata dariya. Kafin ya ce,"Yanzu ma cewa
tayi
in gaishe ki. Na baro Inna shirye-siryen, dambu
na ce su aje min, zan koma in ci. Za ki ci,in zo
miki da shi?"Ta fito kofa, ta
ce,"nagode.......Sallamar Malam ta hana ta k'ara
wani abu." Ya tafi? Ya amsa." Ya tafi. Kai ba mu
wuri. Magana za mu yi." Ya cewa Naseer yana
kallon sa.
Ya kwashe makullai, ya wuce Sabon bangaransa,
ya bude ya shige yayi kwanciyar sa, don hutawa
kafin la'asar ya fita filin sukuwa.
Yana bada baya. Malam ya zauna kamar yadda
Umma ke zaune zugum. Yai dan jim, kafin ya
numfasa ya ce,"Yanzu ya ki ke ganin za'a 6ullo
wa a'amarin nan?"
Gada daya na rasa na yi." Ta ce,"Kai, ko ni?
Ta yadda za'a fahintar da iyayen Zarah, shine
magana."
Cikin damuwa ya ce,"Ashe dai kin fahince ni.
Wallahi Alhj ya cika min ido, sannan ina
ganin girman sa da mutuncinsa, babu yadda
za'a yi in ce masa wannan abu bazai yuwa ba.
Ta ce,"Malam, ai iyakar kauna ce wannan.
Duk wanda ya dauki dan sa ya ba ka, shakka
babu ya gama da kai. Balle irin wadda muke
ganin
matsayin mu bai kai ace mun je neman aure
gidan
Alhj ba,sai ga shi da kan sa ya kawo mana.
Kar6a ya zama dole, idan akwai abinda ya wuce
dole ma,
du ya wajabta a kan mu. Ina gani ka fara zuwa
ka
sami Malam Lawal ka shaida masa ka nemi
shawararsa,ya nisa ya ce,"Haka din za'ayi. To
shi dan gogan fa? Ta ce,"Je dai ka gama da
babbar magana.
Ya mike yana fadin,
"Yanzu kuwa." Ya fice ya barta da zabgegen
tagumi.
Damuwar ta daya, yadda za'a shawo kan iyayen
Zarah, da ita kan ta.
Bus din da M. Balarabe tare da M.Lawal ke ciki,
ita ke tafiya bisa titin da zai kai su Sabon gari.
Suna zazzaune gidan gaba. M.Lawal ke fad'in
"Malam Balarabe na ka kwantar da hankalin ka.
Wannan ba wata maganar zafi bace, abu ne na
fahinta, na kuwa san M.Umar ba shi da matsala,
zai fahimci komai."
Ya ce,"To ita yarinyar fa?
Ba ka ganin ba za ta yi zaton da man can
Naseer na neman yarinyar bane?
Ka san fa mata."
Ya ce,"Ina baka, ka na roko, kai kuwa.
Na daina Allah ya kaimu lafiya.
"Shi kenan abin cewa.Cikin kankanin lkc suka
sauka a kasuwar mata.
Da kafa suka gangara wajen cinikin sa, inda yake
gyaran kekuna na hawa. Tun daya hango su
yake fara'a har suka iso. Suka yi musabaha tare
da
yiwa juna sallama.Cikin shagon da yake tara
kayan aikinsa nan ya baza ta6arma, suka
zazzauna.Jikinsa na rawa, ya fice minti 3 sun yi
yawa, ya dawo da sassanyan ruwan leda (pure
water), ya aje a gaban su, ya dauko ya mikawa
gudu-guda,"Ku sha ruwa don Allah.
Kai sannan ku da zuwa. Kun dauko rana."
Malam Lawal ya ce,"Gaskiya yau ana zuba
rana."
Bayan sun kammala da ruwan sanyi, sun gaisa,
Malam Lawal yayi gyara murya, ya ce,"M.Umar
wata magana ce gagaruma ke tafe da mu, shi
yasa ka gan mu cikin ranar nan face-face.
Ina kasuwa M.Balarabe ya zo min, hankalinsa
tashe yake ya gaya min Alh. Basheer mai gidan
Naseer ya zo dazu har gida, ya same shi yake ce
masa yana son hada zumunci, saboda kaunar
da yake wa Naseer, watau ma'ana ya ba shi
'yar sa ya aura.
Yayi masa bayanin akwai wacce aka ba shi
tuntuni, amma ya ce babu komai sai hada 2, shi
zai dauki dawainiyar komai. Hakika na san
gaskiya hankalin M.Balarabe a tashe yake, don
bai san yadda zai fuskance ku da zancen ba.
Hatta shi kansa Naseer din bai san halin da ake
ciki ba. Saboda shi Alhj bai gaya masa ba, kai
tsaye wajen Malam Balarabe ya zo.
To shine na ce ba mu ga ta zama ba, dole mu
zo mu baka hakuri, don Allah don son Annabi,
kar wannan abu ya kawo wani sa6ani, a bar shi
a shirin Ubangiji.
Don Allah.............
Da sauri Malam Umar ya dakatar da shi da
hannun sa, kafin ya ce,"Haba Malam Lawal
wanna ai abin farin ciki ne, domin kuwa na
tabbtar da kauna ce da yarda ta sa Alh. Basheer
ya kaddamar da wannan al'amari, shi kuwa
Naseer ya cancani a taya shi.
Murna, saboda ya sami gatan da ba kowa ke
samu ba.
A matsayin na na uba ga Naseer, ina mai
tabbtar ma ku da cewa ni ne zan amshi
waliccinsa ranar dauri auransa a kaduna.
Allah ya nuna mana ranar lafiya.
Malam Balarabe kar ka ji komai akan wannan
abu.
Ina mai murna tare da farin ciki, addu'ar mu
kawai.
Allah ya taya shi rikon su bisa adalci.
Suka numfasa, kalaman Malam Umar sun
matukar gamsar da su.
Malam Balarabe ya ce,"Mun gode kwarai da
gaske.
Sauran Zarah a rarrasan mana ita.
Idan ma zai yuwu, ka turo min ita ni in rarrashe
ta da kai na."
Yayi murmushi,"Babu damuwa, kar ka dora
wani tunani akan Zarah, zan mata bayani,
Zata fahimta Insha Allahu.
Yaushe ne Alhjn ya ce ranar bikin?"
Ya ce,"Ai ina ganin hadawa za'ayi rana , don mu
kawai yake sauarar mu gama kimtsawa.
To shi kenan.
Allah ya kai mu lkcn."
Suka amsa da amin."
Sun dan jima, suna hirarraki akan al'amarin,
sannan suka yi sallama, suka koma.
Malam Umar bai kawo tunanin komai ba, ya
dorawa ransa, illa addu'ar Allah ya za6a mafi
alkhairi.
Idan kuma auran ya tabbata, to Allah ya zaunar
da su lafiya.
************
Misalin karfe 1:30 na rana Naseer ya farka
barcinsa, yayi alwala yayi sallah.
Bai ci abincin Ummansa ba, don ya sa Inna ta
aje ma sa dambu.
Yana kokarin ficewa.
Abban sa yayi kiransa falo. Can ya iske Umma a
zaune, yana shiga ta ce,"Ka ga abincinka a
kicin? Ya ce,"Ban shiga kicin din ba, kin ma san
na gaya miki Inna za ta aje min dambu."
Ta ce,"Yayi kyau." Abba ya ce,"Naseeer, ban
hankalinka nan.
Alhj Basheer ya ce, ya ba ka auran 'yar sa,
saboda haka ka je ku ga juna, ka yi masa
godiya.
Insha-Allahu da na Zarah za'a had'a, na ma
riga nagayawa Malam Umar, mun gama
magana."
Tun daya fara magana, idanuwan Naseer ke
kafe, yana kallon Abbansa.
Gaba daya tsigar jikinsa ta mike, wani abu ya
taso ya toshe masa makoshi, da kyau yayi iya
cewa,"Abba ai ba mu yi wannan maganar da shi
ba, maganar makaranta kawai mu ka yi, na
kuma gaya maka.
Ina ni, ina neman 'yar Alhaji?Gaban Umma ya
fad'i, ganin yadda Naseer ke magana hankalinsa
tashe. Kan ka ce kwa6o, kyawawan idanuwan
sa, sun kada. Abba ya ce,"Kwantar da hankalin
ka Naseer. Na san akwai maganar Zarah a
gaban ka kuma ka na sonta.Duk na shaidawa
Alhj.
Ya amince a hade.
Ina rokon ka Naseer da ka dubi girman Allah, ka
dubi so da kaunar da dan tahalikin nan yake
nuna mana. Ka kar6i wannan kyauta da hannu
bibiyu. Ka je ku gaisa da yarinyar nan, sannan
ka yi wa Baban ta godiya.."Umma ta
amsa,"Alhaji ya gama maka komai Naseer, ka yi
hamdala ga Allah daya hada ka da mai son ka.
Sannan ina son ka sani, idan ka amshi wannan
kyauta, mu ka daraja, idan kuwa ka butulce.
Wallahi-wallahi ka tozarta mu Naseer.
Sanin kan ka ne, matsayin gidan Alhj ya fi karfin
mu, sai ga shi Allah ya kai ka wajen.
Babu abinda ya dace kai, illa ka kara kusanci da
yi wa Allah godiya ta hanyar amsar wannan
magana cikin farin ciki da zuciya daya.
Ka ji?
Ya dube ta jim, kafin ya ce,"Na ji.."
Ya mike ya ci gaba da fadin,"Ina zuwa."
Abba ya ce,"Ina zaka, ba'a gama magana ba."
Bai ce komai ba, ya dawo ya zauna.
Yaushe za ka Kadunan?
Gobe."
"A'a
yau ya kamta ka tafi.
Menene na jira sai gobe?
Ko kuwa Umman shi?
Ta ce,"Haka ya kamata.
Shi ma zai ji dadi, zai kuma san ka dauki abin
da mhinmanci.
Ya ce,"To Abba."
Ya ce,"To je ka ci dambun, daga can ka wuce
kawai.
To din dai ya sake fadi, ya mike yayi waje har
wani jiri yake gani.
Umma ta bi shi da kallo, ta juyo kan Abba ta
ce,"Naseer da mata 2, wannan mahaukacin
Yaron."
Ya ce,"Sai anyi da gaske.
Fuskar sa akwai alamar tambaya.
Kar kuma ki mance halin dan ki, akwai kafiya."
Ta ce,"Allah zai tsare.
Shigowar Sageer kenan cikin shagon dinki, daga
makaranta yake, kamar tare suke da Naseer,
yayi fakin a sikwane ya shigo.
Ido jajur, bakinsa na rawa,
"Sageer zo!
Ya juya,
ya koma mota.
Nan da nan shi ma Sageer ya sami kan sa cikin
faduwar gaba.
Motars ya same shi ya hade kai da sitiyari."
Menene Naseer?
Ya dube shi zufa sharkarf jikinsa, ya ce,"Alhj ya
kashe ni.
Da na san duk abinda yake min ba saboda Allah
bane, da tuni na rabu da shi."
Cike da tsananin mmk Sageer ya ce,"Me yasa ka
ke wannan maganar?"
Dazu da safe ya zo kai tsaye ya sami Abba ya ce
wai ya ba ni 'yar sa in aura.
Me yasa?
Don me?
Wai kuma Abba ya amsa masa, maimakon ya ce
ba zai yuwu ba kawai.
Yanzu saboda Allah me su ke son in gaya wa
Zarah?
Kai ni gaba 1 ma ban ji ina wannan ra'ayin ba,
don haka ba zan aure ta ba.
Su da suka kar6a, sa san yadda za su yi."
Yana maganar sa. Sageer na kallon sa, shi kan
sa zuciyar sa ta girgiza, saboda Zarah da ke
tsakani, amma da yayi tunani nan da nan yayi
amfani da kwakwalwarsa,"Yanzu ka na nufin
babu zaancan Zarah!
Wai in hada su 2 ayi biki gaba 1, sbd an gaya
masa yawon kida za ni!Dan murmushi yayi ya
ce,"In don haka ne Naseer, ai babu laifi, za ta
fahimce mu. Amma magana ta gaskiya. Alhj
kauna ya nuna maka.........
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Ajininsa yake 1-10
Posted by ANaM Dorayi on 04:42 PM, 09-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
.Cikin zafi ya katse shi,"Sageer fita a motan nan!"
Ba zan fita ba Naseer....."Ka fita na ce ko?
"Ba zan fita ba Naseer, me yasa kai kullun ba ka
son gaskiya? Ko kuwa ka na nufin dole sai na
goya ma baya, mu kwance wa iyayen mu zani
kasuwa?
Ba haka rayuwa take ba Naseer, ina kuma mai
tabbatar maka cewa ba karamin kaunar ka Alhj
yake yi ba, tunda har ya ce ka hada su 2, ka
aura.
Ya kamata ka duba wannan, idan ma ba ka
dauke shi a hakan ba, sai ka duba darajar su
Abba, su duka amshi maganar."
Wani mahaukacin kallo yake masa. Wanda ya
nuna Zahiri lallai kura tayi lafiya, da tuni ya
kashe masa baki, ya gama sarewarsa kaf, sannan
ya ce,"To na ji Baba na, sai anjima ko?"
Sageer ya karkada kai cikin murya mai taushi, ya
ce "Naseer, Zarah na da tunani, tana da hankali,
domin ta ta6a yin wasu maganganu wajen nan,
wanda yasa ka ga na hakikance za ta fahimce
mu.
Ka ban izini in je ni kadai in yi mata bayani, zan
dawo ma da amsa."
Ya nuna shi,"Ban aike ka ba! Babu kuma
ruwanka a cikin wannan maganar. Fita-fita kawai!
Yayi jim, suna kallon juna, sannan ya ce,"Naseer
saurin fushi ba naka bane, ka bi maganar nan a
hankali tare da dogon tunani kafin ka yanke
hukunci. Auran mata 2, a lokaci daya, ai na dan
gata ne, yaushe rabon da ka ji anyi irin sa?
Kamar Naseer ya kwarma ihu yake ji, saboda
bakin cikin Sageer ya ki fitar masa daga mota.
Zuciyar sa na ta kara tafarfasa.Sageer na hada ka
da Allah da Manzonsa ka fita a motan nan, ka ki
ko? Ya ce,"Ai ita kanta wannan motar Alhj ne ya
ba ka ita, menene damuwar ka akan zama na a
cikinta? Zuciya ta shake shi tamau! Idanuwansa
suka kara firfitowa jajur! Ya ce,"Haka ne, ka kuma
kyauta da ka tunasar da ni.
Saboda haka ga ta nan ka maida masa abar sa."
Cikin za fi ya hankade murfin motar, yayi waje.
Ganin haka yasa Sageer ya fito ya tarbe
shi,"Zancan bai kai haka ba Naseer. Tunda na
gaya ma gaskiya ba ka yarda ba, shikenan. Ta
Malam bata wuce amin.
Ka yu hakuri ka koma motar ka." Ya ce,"Ka san
Allah sai ka maida ta, ka ga daga nan ya ba ka
tukuicin 'yar, ba shi kenan ba.
An raba gardama?
Ransa bace ya ce,"Allah ya tsare ni. Ka san ba
haka na ke ba, ba kuma zan zama ba."
Uban tsaki ya ja.
Sageer na kallo, ya tsare dan aca6a ya dare, ya
bar shi nan yana kwala kira.
Jingina yayi da motar rungume da hannayen sa,
yana kada kai.
"Rigima sabuwa, me yasa su Abba suka kar6i
maganar nan, ba tare da sun shawarci Naseer
ba? Kodayake suna ganin sun isa da shi ne.
Yakamata Naseer ya gane hakan." Ya numfasa ya
ce,"Allah ka dai-daita, idan da alkhairi." Ya bude
mota ya shiga, ya ja ya maida ta gidan su
yayimusu bayanin yadda suka yi da Naseer din.
Nan ya tafi, ya bar su da hannu a kunci cike da
zullumi me zai je, ya dawo?
Filin sukuwa mai mashin ya aje Naseer, ya fiddo
kudi ya mika masa, yayi gaba abinsa, shi kuwa
waje ya samu ya zauna, ya rasa abinda ke masa
dadi a duniya.
Abin kamar a mafarki yake ganin sa. Zuciyarsa na
yi tayi masa saka iri-iri, yana shigewa.
Wucewar minti 15 da zaman sa, wayarsa ta
buga.Da kyar ya ciro ta. Ya duba lambar. Abba
ne ke kiran sa. Kawai yasan Sageer ya je gidan
kenan, don haka ya maida wayar aljihu, ya ki
dauka.
Mikewa yayi ya sake neman dan aca6a ya dare
suka yi wa Tudun Jukun tsinke. Yakubun da ya je
nema, bai dawo ba, amma Naseer B yana nan,
don haka bayan sun gama gaisawa da mutan
gidan, dakin Naseer B suka zube a katifa.
Naseer B ya kare masa kallo, kafin ya ce,"Ban ga
motar ka ba?
Ya ce,"Gida na bar ta." Ya ta6e baki,"Aca6a ka ke
son hawa?
Jin dadi." Yayi shiru bai tanka ba.
Wai baka da lafiya ne? Na ga kana yi kamar mai
ciwo?"
Ya kada kai, ya ce,"Masifa ce ta same ni."
"To fa, wacce irin masifa?
Bai 6ata lkc ba, ya warware ,masa halin da ake
ciki. Take, yanke Naseer B ya turnuke da bakin
ciki.
Hassada ta kama shi, yayi kasake tamkar mai
tunanin abin kirki."
"Taf!
Lallai Naseer wawa ne, abin farin ciki ya sa me
shi, amma ya ce masifa."
Auran jari?
Mutum ya sami wannan, ai ya haye. Mts........
Ya ja dogon tsaki,"Da ni na sami haka, ko ma
wace yarinya na ke nema, ai don uban ta dole ta
daga min kafa, ta nemi wani mijin, yaushe zan
tsaya bata lokaci na auran su su 2?
Wani wawan tsakin ya kuma mamaitawa, sannan
ya ce,"Yanzu kai ina mafitar ka?
Ya ce,"Wallahi ban sani ba, ni dai yarinyar nan
ban ta6a ganin ta ba, kai koda ma na ganta, ba
za ta yi min ba, tunda ina da wacce na ke so.
Ni abinda ya fi bata min rai, wai kai tsaye Abba
ya samu.
Ai da sai ya kira ni ya ce Naseer 'ya ta ta rasa
miji don Allah ka aureta. Zan maka komai.
Ka ga ni na san bayanin da zan masa.Naseer B
ya zazzago idanuwan munafunci ya ce,"Gaskiya
ne.
Ai dama idan ka ga irin haka, kwantai yarinya
tayi, ake neman kai da ita. To yanzu kai zama za
ka yi haka kawai, ba za ka ta6uka komai ba?
Kamar yayi kuka yake kallon sa, domin hawaye
ne tamke a idonsa,"Me zan iya yi B? Bayan na
gaya maka. Abba yayi ruwa, yayi tsaki kamar su
za su zauna da ita.
Mts!
Ya kama baki yana kada, kada,"Amma ka ban
mmk. Shi kenan an maka auran dole.
Sabon yayi kenan, namiji da auran dole. Na ga ko
matan ma ba yarda suke yi ba.
Wata ta sha fiya-fiya, wata ta banki kalanzir,
koda yake Malamai sun ce yin hakan mutuwar
kafirci ne. Sannan kai ma na ka na lokacinka ai
ba za ka mutu saboda 'yar Alhaji ba.
Amma ina ganin ai za ka iya daukan jaka, ka bar
masu garin, sa gane kuran su."
Ya dube shi da kyau ya ce,"Ka na nufin in yi
tafiya ta kawai?"
Sosai ma."
To Zarah fa?
Ai ita ina son ta ba zan iya barinta ba." Ya
ce,"Ita ma ta hada na ta komatsan ku sa kai."
Takaici ya kara lullube shi ya buga tsaki ya
ce,"Abin kuma ya zama iskanci.
Ba fa Indiya ka ke kallo ba, wannan zahiri na ke
gaya maka.
Ina za ni da 'yar mutane?
Ya ce,"Idan kuwa mafita ka ke nema, dole cikin
biyu ka dauki daya, ko ka hakura da su duka,
ko ka aure su gaba daya har da wacce ba ka
son.
Ka kuwa ce ba ka son ta, yaya za'ayi ku zauna
tare?
Ransa ya kara baci ya ce,"Yaya za'ayi kuwa? Kai
ka na da mafita, amma suna da kamar wuya.
Ka dan nemo mai sauki ne, zai fi.."
Mai sauki bai wuce ka yi tafiyar ka, ka ba kwana
2. Alhj zai ji haushi, ya soke zancan. Idan ka
dawo, a nemi Abba gafara, ka ga shi kenan,
waccan magana ta tashi, dole a bar ka da Zarar
ka. Wallahi ta ma fi dacewa da kai, duk da ban
ga waccan ba."
Ya nisa ya kwanta a katifa rigingine, sakwan 2,
bai ce kala ba.
Yana zancan zuci ya kafin ya ce"Yau din nan zan
6ace masu kuwa.
Ya 6alla masa harara, ya ce a ransa,"Ai sai ka
6ace, tunda a wajen ka masifa ce ta same ka.
A dakin yayi sallar la'asar, duk irin kiran wayar
da Abba ke yi, babu wacce ya amsa.
Kira na karshe daya shigo, shine na Zarah,
misalin hudu da rabi, shi ma bai dauka ba, don
bai san ma ta inda zai fara yi mata bayani ba.
Take nan ya kashe wayoyinsa duka biyun.
Karfe biyar dai-dai Yakubu ya dawo, su biyun
suka fito tarbar sa,"Bakin sa har kunne ya fito,
"Ah! Jah-Jah.
Dama ka na nan?
Ban ga kafafuwan ka ba?
Yayi dan murmushi ya ce,"Tana gida."
Jaja ya miko masa hannu su kai musabaha,
Yakubu ya ce,"Congrats!
Sai na ji daddan lbr wajen Alhj.
You're so lucky Naseer.
Nusaiba akwai hankali ga natsuwa.
Ka zama dan gata, mata 2, lokaci guda.
Allah ya tayaka rikon su.
Yake yayi, domin tumi zuciyar sa ta kara firgita.
Watau Alhj har ya fara shela 'yar sa tayi miji.
Lalai zai ji a salansa.
Bai ce komai ba.
Ya ce,"Na gode yayanmu.
Amma yayanmu ai ina ganin kamar bn isa rike
mata 2 ba."
Ya ce,"Why not, kai ba namiji bane? Babu
abinda zai gagare ka, dukkan su a karkashin
ikon ka za su zauna, illa iyaka ka sa ido akan ko
wacce, ka fahimci halin ta.
Sannan ka yi iyakar yin ka, ka tabbatar da cewa
babu gutsiri tsoma a cikin gidan ka.
Daga karshe kai karan kanka ka tsaida adalci.
Shakka babu gidanka za'a zauna lafiya.
Ko dama na gaya maka Nusaiba bata da
matsala.
Kafin in taho ma, na je mun gaisa ina mata
tsiya, ta gudu.
Ya dafa kafadar sa, ya ci gaba," Ka yi sa'a
Naseer. Alhj na kaunar ka.
Ka rike masa amana, ka ji? Da kyar ya hadiye
miyau, don ya fahimci Yakubu ba zai gane ba,
saboda haka yayi masa ta 'yan duniya, ya
washe baki ya ce,"To na gode yayanmu.
Dama zan wuce kenan sai gobe."
Ya ce,"Allah ya kai mu. Ina fatan ka shirywa
wasan mu da (Kano Horses) jibi?
"Sun aiko da takarda ne?
Duk dazu Alhj ke shaida mi."
Ba matsala, kullum a shirye mu ke." Yayi
murmushi, yana masa kirarin ,"
Jah-Jah!
Ba wani bayanka."
Su kayi sallama.
Yakubu ya shige gida."
Naseer ya dubi Naseer B, ya kwa6e fuska ya
ce,"Yayanmu ya shagala.
Ka ji Alhj Feshi ya ke yi 'yar sa ta yi miji."
Dariya yai cikie da hassada,"Zai sha mamaki."
Manta kawai.
Ni zan wuce,sai mun waya."
Suka wuce yana taka masa, jimawa kadan ya
sami dan aca6a ya hau, yayi gaba.
Naseer B yasa hannaye aljihu, yayi hucin zafi, ya
ce a ran sa,"A sauka da nauyi.
Gara6asa ta wuce ka Yaro."
Ya juyo ya dawo gida ran sa cike da tunanin ko
shi ma ya koma Sukuwan ne?
Dan aca6a ya aje shi kofar gidan su Zarah. Ya
sauka ya shiga zaure, ya dau lkc cikin zauren
yana tunanin iska. Da kyar yayi karfin hali ya
shige tare da sallama.
Amma da ka dube shi, za ka tabbatar babu
kuzari a tare da shi. Inna kadai ke tsakar gida a
zaune. Ta bi shi da kallo, tana fadin,"Ka kyauta.
Kuma sai ka bar ni da dambu cikin kula.
Ya karaso gefenta ya tsugunna ya gaishe ta.
Bayan ta amsa, ta ci gaba da fadin,"Me ya hana
ka zuwa tun danbun na da mutuncinsa?
Nan da nan idanuwansa suka fara ja."
Ina ba zan iya cin sa bane, shi yasa." Ta ce,
"Don me?
Ita rayuwa ba shirin Ubangiji bace? Kar ka damu
kanka dan Inna, kai dai ka roki Allah ya sanya
alkhairi.
In don ta Zarah ne, na riga na yi mata bayani,
na kuma kwantar mata da hankali.
Ita fargabar ta daya ce.
Wulakanci take gudu.
Nace........
Yayi fit!
ya katse ta,"Inna ni fa ban so, su kyale ni
mana.
Ko kuwa ana auren dole ne?
Ni babu abinda ya dame ni da kudin Babanta.
Ga wacce na ce ina so, kowa ya san maganar
nan, ai bai kamata Abba yayi haka ba.
Saboda haka ni gas...............
Yi min shiru don Allah.
Me yasa ku yaran yanzu ba ku da kawaici ne?
Sai ku ce dole-dole abinda ku ke so, shi za'ayi?
Abba bai da iko da kai ne?
Na ce su iyayenka ba isa da kai ba ne?
Ya sunkuyar da kai, saboda kunyar da nauyin
Inna kawai, ba don wai jawabinta ba. Sam bai
ratsa zuciyarsa ba, balle ya saduda. Ta sassauta
murya,"Haba dan Inna, yanzu kai ka na ganin
yadda Alhj ya taso da girman sa da komai, ya
tunkari Abbanka da wannan maganar, har yana
da abin cewa bayan wannan? To ina son ka
sani, ba haka dattijo yake ba, kuma Abba yayi
abinda ake so, kamar yadda Alhj ya nuna halin
girma.
Abu na karshe, shine ka ba mara da kunya, ka
nuna wa duniya ka fito gidan mutunci, ka yi
kawaici irin na mutan da, ka amshi wannan
kyauta da zuciya daya.
Ai Malam ya jima nan yana jiranka har ya sa
Zarah ta kira ka a waya, amma ka ki dauka.
Ko dama bayanin da zai maka kenan, kai dan
mu ne, duk ci gaban daya same ka, muna farin
ciki da shi.
Allah ya taya ka rikon su bisa adalci.
Inna sarewa kawai take yi, domin shi a wannan
lkcn tunanin sa wane gari zai 6oye.
A neme shi, a rasa?
Abuja tayi masa kusa, sai dai Lagos ko Fatakwal.
Shi yasa jawabin Inna ko ince nasihohinta, ba
dayan da ya ji.
Ko da tayi shiru ma, sai da ta sake
maimaitawa,"Ka ji ko dan Inna?
Sannan ya dawo hayyancin sa, ya dan daga kai
ya ce,"Na ji Inna."
Ta ce,"To shi kenan, tashi ka shiga daki.
Zarah ta kawo ma abincin."
Ya mike ya shiga dakin.
Zarah na zaune bisa kujera, tana sauraron
komai.
Daga shigowar sa, suka hada ido, gaban sa
kawai ya ji ya fadi.
Da sauri ya kauda kai, ya hanzarta zama.
Shiru suka yi, kowa ya rasa mai zai ce wa dan-
uwansa.
Inna ta kwala kira.
Zarah ta amsa, ta tashi ta fice, bai ko iya cira
kai ya dubi fitar ba, illa wani tukuki da ransa ke
yi, ko alama ba shi da ra'ayi daya da su
Abba.."Sallama tayi, ta shigo da kayan abinci a
tire, ta aje gaban sa.Ta bude kula ta dauki filet
da cokali za ta zuba. Wata shakakkiyar murya ta
ji ya ce,"Kar ki zuba."
Ta dube shi idanuwan nan jajur!
Suke ta ce,"
"Don me?"
Ba zan iya ci ba."
Ta ce,"Zan gaya wa Inna."
Ya dauki murfin ya rufe kular ya ce," Je ki gaya
mata din."
Ta koma da baya ta zauna dirshan!
Ta kare masa kallo, tayi dan murmushi ta
ce,"Kai yanzu mece ce matsalarka?
Abincin ma ba za ka ci ba?
Ko zaton ka za ka sami matsala ta waje na?Ta
dan kauda kai kafin ta ci gaba,"Ina jin na ta6a
gaya ma wannan maganar, har ka yi fushi.
Alkawarin a hurumin da ba na mu ba, kuskure
ne.
Ga shi ba'a je ko'ina ba, ta fiya ta sauya salo,
sai dai ina baka tabbacin cewa ina tare da kai a
ko wane yanayi, ni ce uwargida."
Ya watso mata gwalagwalan idanuwan sa jajur!
Ya nuna ta da yatsa,"Yanzu na gane ba kya
sona, tunda ba kya kishi na.
To ina son ki sani, ganin nan da ki ke min,
sallama na zo miki, domin gaba daya na hakura
da auran."Ban gane sallama ba? Ya ce,"A zaton
ki zan auri yarinyar nan ne? Ban jin zan iya, na
kuma lura babu wanda zai fahimce ni, balle ya
goya min baya.
Babban abin bakin ciki, wai har da ke. Shi yasa
na hakura da auran gaba daya.
A yau din nan zan bar ma ku garin, sai ku nemi
wani miji."
Tayi dan murmushi, yana lura da ita.
"Wannan zancan 'yan dirama yayana ka ke yi.
Maganar kishi kuwa, ai babu wani kishi daya
wuce na bin iyaye.
Ni gaskiya na ke gaya maka yayana.
Muddin ka ce za ka aikata wani abu wanda
zuciya ta shirya maka, to ina mai tabbatar maka
da na sani ne zai biyo baya.
Zai yi kyau ka sami lokaci ka yi tunani kafin ka
yanke hukuncin.
Idan kuma ba ka yarda ba, to ni din ma ina iya
cewa na hakura.
Wata kila hakan shine mafi alkhairi.."Zuru yayi
mata, yana kallo, ta . Sannan ya ce," Ci gaba
mana." Ta ce,"Ai na gama, sauran za6in na ka
ne." Ya ce,"Ina lura da ke har wani murmushi ki
ke yi, watau magana ta busa ce, shi yasa ki ke
rattafo wadannan kalaman.Tuni na gaya miki
za6i na, na hakura da auran, meneme ma 6ata
lkcn wa'azinki? Tunda ba shi zai sa na so
yarinyar nan ba?
Da muguwar rawa, gwamma kin tashi, ina
kakkaucewa, kowa yana jawoni da wa'azi.
Alhali masu wa'azin ba su za su zauna da 'yar
ba.Kin fi kowa sani na, idan na tsani abu sam-
sam ba na waiwayar sa, haka kuma in na so shi,
kamar zan mutu na ke ji, saboda tsabar kauna.
Haka jini na yake, babu mai iya canza min shi.
Ina son ke ma ki yi tunani akan magana ta.
Ni zan wuce, watakila ban iya mancewa da ke."
Tsoro ya fara kamata. Me Naseer ke naman
jawo masu? Tabbas ta fi kowa sanin halin
yayanta, na kafiya akan ra'ayinsa.
Amma maganar da aka ce iyaye na ciki, ta fi
gaban a zauna ana jayya da ita.
Idanuwanta suka raina fata.
Take nan suka kawo kwalla, a raunane."
Ta ce,"Yayana saboda ni ka ke son bijirewa su
Abbba?
Ba ka yi min adalci ba, domin ni har ga Allah ba
zan bijerwa iyaye na, saboda kai ba.
Komai son da na ke maka, zan hakura.
Balle wannan maganar mai sauki, ka hada mu,
ka aura menene a ciki?
Lallai gata ya yi maka yawa, ka je din duk
abinda ka ke so, ka aikata dai-dai ne."
Bai ce uffan ba, ya mike yai waje abin sa. Babu
kowa a tsakar gidan, don haka ya kara sauri, ya
bar gidan.
Zulumi bisa zulumi.
Tunani. Haka Zarah ta kasance har bayan sallar
isha'i. Haka abin ke daurewa Inna kai.
Ita gani ma ta rinka yi kamar Naseer wasa yake
yi.
Malam Umar na shigowa, ta maida masa
bayani.
Bai 6ata lkc ba, ya sake shura takalmansa ya
nufi gidan su Naseer.
Ya jaddawa Malam Balarabe halin da ke ciki da
irin shirin da Naseer ke kullawa zuciyar sa.
Al'amarin ya daurewa su Malam Balarabe kai,
har yayi fushin da bai ta6a yin sa ba, domin a
gaban Malam Umar ya ce," Idam kuwa har
Naseer yasa kafa ya bar garin nan, har abada
ban yafe masa ba.
Malam Umar bai ji dadin wannan kalami ba.
Yayi rarrashin duniya.
Malama Balarabe ya ki sakkowa, sai ma kara
tafasa zuciyarsa ke yi, ransa 6ace ya dawo gida.
Al'amarin ko alama bai yi dadi ba.
Haka Umma ke ta wahalar tunani cikin ranta, ko
bata furta komai ba, fushin da ke zuciyar ta, ya
ishi Naseer.
Karfe 11 dare, ko gyangyadi ba wanda yayi, don
sun hakikance Naseer ya aikata abinda zuciyarsa
ta shirya masa.
Tunanin Malam Balarabe, shine bai san da wane
ido zai kalli Alh. Basheer ba, balle abinda zai ce
da shi?
Ya zuwa yanzu ya ci ace Naseer ya je sun gaisa
da yarinyar nan,Me Alh. Basheer zai dauka cikin
ransa? Lallai ko alama Naseer bai daraja shi ba,
bai kuma ta6a tozarta shi ba, irin na yau. Kawai
hawaye Umma ta gani suna zuba daga idon
Malam Balarabe.
Hankalinta ya kara tashi, muryar ta na rawa ta
ce,"Don Allah Malam ka daina zubda masa
hawaye, bakin da ka yi masa ma kadai ya ishe
shi."
Bai iya cewa komai ba, ya goge hawaye.
Ta sake cewa,"Kwanta ka sami barci, ka barwa
Allah komai."
A cikin dakin shirun da suka yi, na juyayi suka
tsinkayi motsi kamar ana ta6a k'ofa.
Umma ta ce,"Malam ba ka kulle k'ofar gidan
bane?"
Ya ce,
"Oho,
ni ban sani ba, amma ina ganin kamar na
kulle.."
Motsi na ke ji."
Malam Balarabe ya mike a hankali, ya bude
kofa ya fito.
Umma na biye da shi.
Naseer suka gani rataye da jaka, yana sanda zai
fice.
Umma ta ce,
"Naseer!
Ya tsaya cak!
Bai juyo ba.
A zaton sa sun yi barci, don ba su ji shigowar sa
ba.
Abba ya ce,"Dama ka daina sand'a ka saki jikin
ka, ka yi tafiyar ka yadda ka saba, babu abinda
muka isa mu yi ma ka.
Maganar barin gari kuwa, in ka so ka koma
bangon duniya ka zauna.
Ba zai ta6a damu na ba, saboda ba ka da wani
amfani a gare ni."
Sai dai ina son ka san wani abu.
Duk inda za ka je, ba za ka ta6a ganin alkhairi
ba.
Ka aje wa ranka har abada na sallame ka, kar
ka yi tunanin ka na da iyaye.,
Alh. Basheer kuma ina iya zuwa gobe, in ba shi
hakuri. Ka na iya tafiya, in kulle gidana."
Tsaye yayi, ya kasa cira koda kafa daya ce.
Ilahirin jikinsa babu inda zufa baya ratsawa.
Umma ta ce,"Ka wuce ka tafi, ka bar mu a
tsaye."
Jakar da ke kafadar sa ta zamo ta fadi k'asa,
saboda tsabar rashin kuzari, yasa hannu ya
d'auko ta, ya juya a hankali ya koma
6angaransa, ya bude ya shige.
Malam Balarabe, ya wuce, ya kulle kofar gida.
Suka koma dakinsu.
Labarin zuciyar Naseer abin ba'a cewa komai.
Kansa cikin guiwa tamkar ya hadiye zuciya, ya
mutu.
Yanzu shikenan ya tabbata za'ayi masa auran
dole?
Bai san lokacin daya daddage ya kwarma ihu
ba,
"Dole!
Umma ta tashi zumbur!
Tana fadin,
"Subahanallah!
Menene wannan?Abba ya ce,"Menene kuwa,
daya wuce mahaukacin dan ki."
Ta nufi kofa tana budewa.
Ya ce,
"Me zai dame ki?
Ki kyale shi ya hadiyi zuciya ya mutu.
Kafin safiya, sai in tabbatar daya cika dan
halas."
Allah Sarki uwa!
Bata saurari Abba ba, tayi waje can sashin
Naseer.
K'ofar falon wangame take, tana zuwa, ta cusa
kai.
Shi kadai yake madedewar sa tsakar falo, ya
dunkule waje daya tamkar mai tsananin ciwon
ciki."
Ta isa da sauri ta cicci6o shi, fadi take,"Naseer!
Kai Naseer tashi ka ji."
Da kyar ta samo hankalinsa yayi zuru, yana
kallonta.
Naseer ka na hauka ne?
Daga abin arziki, sai ya zama na tsiya?
Kai ba Yaro bane Naseer, ka yi hankali da za ka
gane muhinmancin mu a gunka.
Amma ka ke kokarin aikata abinda Yaro karami
ba zai yi shi ba.
Yau har kuka sai da Abbanka. Yayi a kanka, me
ka ke zaton zubdar hawayensa zai haifar maka?
Yau ko ba ka son yarinyar nan, ai ka dubi
girman Babanta daya ce ya ba ka ita.
Sannan ka dubi darajar mu iyayenka da mu ka
amsa. Ban ta6a tunanin za ka yi mana haka ba
Naseer.
Don a zota na ka yi hankali, ka daina shirmen
baya.
Ka sani in har Alh. Basheer ya sami labarin ba
ka son 'yar sa, ran sa ba zai masa dadi ba,
wannan kuma shine karshen cin mutunci da
tozarci a idon jama'a.
Saboda haka yanzu na ke so ka bani amsa, shin
ka amince za ka auri yarinyar nan?
Ya dube ta a yamutse, kwalla ne sharkaf bisa
kuncinta. Jikin sa ya k'ara sanyi, zuciyarsa ta
raunana, bakin sa na rawa ya ce,"Umma ki
share hawayen nan, komai ya wuce.
Zan je Kaduna gobe."
Ta ce,"Ta so mu je ka roki Abban ka gafara, ran
sa 6ace yake da kai.
Yayi kuka, yayi maka baki.
Hakan bai dace ba,
kuma masifa ce babbab a gareka."
Ya mike suka fito tare, suka sami M.Balarabe
zaune yana juyayin takaici.
A natse ya aje guiwoyinsa a k'asa gaban Abba,
"Abba ka yi hakuri, ka yafe min."
Ya cira ido ya dube shi,"Me zan ce da kai
Naseer?
Ka riga ka ban kunya, rashin zuwan ka Kaduna
a yau, wata magana ce a lullube. Na kuwa san
tuni Alhj ya gane nufin ka.
Ban yi zato ba,ko ba son yarinyar nan, kamata
yaui ka bi umurnina.Idanuwansa suka kara ja.
Tabbas yarinya baya son ta, idan ma ana
maganar, ji yake kamar ana k'ara dasa masa
kiyayyar ta cikin zuciya.
Kawai daurewa yayi, ya k'ara k'asnk'antar da
murya, ya ce,"Abba na yi kuskure, amma zan
gyara, ka yi hakuri don Allah."
Ya ce,"Taashi ka koma dakin ka, komai ya
wuce.,
Sai dai ina son ka sani, hankali na ba zai ta6a
kwanciya ba har sai ka amshi kyautar Alhj da
zuciya daya.
Ka so ta kamar yadda mahaifinta ya kaunace
ka."
Da kamar wuya. Wai gurguwa da aure nesa.
Abinda yasa shi yake jinjina kai kenan.
Ya ce,"Insha Allahu gobe zan je Kaduna." Kullin
da ke zuciyar Abba ya dan warware, ya dube
shi da kyau ya ce,"Je ka kwanta.
Allah ya kai mu goben lafiya.."
Ya mike yana fadin,"Amin.
Umma sai gobe."
Ta amsa masa.
Ya wuce sa shin sa."
Karfe takwas na safiya.
Sageer ke sallama tsakar gidan su Naseer.
Umma ta fito daga kicin tana amsawa."
Sageer, in ce dai lafiya ko?
Ya ce,"Lafiya lau Umma.
Jiya da daddare Naseer yayi min waya ya ce zan
raka shi Kaduna."
Ranta yayi fari sol!
Ta ce,
"To madalla."
Suka gaisa, sannan ya wuce falon su, ya gaida
Abba.
Shi ma ya ji dadin abin.
Take nan zuciyarsa ta yarda da Naseer.
Daga nan sashin Naseer din ya wuce.
Kofar a bude, yayi sallama ya shiga.
Yana zaune saye da bugaggiyar shadda, ruwan
ganye mai duhu.Duk da fuskar sa babu walwala,
kallo daya za kai masa, ka tabbatar da yayi kyau
ba kadan ba.
Safa yake sawa a lkcn da ya amsa sallamar, ba
tare daya kalle shi ba.
Haka kuma daga nan bai sake cewa da shi
komai ba.
Shi ma Sageer din shiru yayi yana kallonsa, ya
gama sanya safa, ya janyo bakaken takalmansa
koba, ya sa.
Hular sa da ke gefe, ya mika hannu ya dauko,
ya riqe ta a hannu.
Mu je ko?
Ya cewa Sageer,
yana duab sa.
Ya ce,
"Dora hular mana."
Ya dora. Sageer yayi dan murmushi, ya ce,"Ko
yau ka ke angwanci, iyakar ta kenan.
Babu makusa na Zarah angon Nusaiba."
Fuska daure ya ce,"Ka yi shiru, ya fi alkhairi
akan zancan da ba za ka faranta min rai ba."
" 'Yar fara'a yayi. kafin ya ce,"Naseer kenan.A
zatona maganar ta wuce, sai zancan shagalin
biki za mu sa a gaba?..
Zaharaddeen Shomr
Whatsapp 08168575100
Ajininsa yake 1-11
Posted by ANaM Dorayi on 11:36 PM, 11-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
.
.Ya ce,"Biki kuma shine a gaban ku, tunda Naseer
ya bi umurni.
Za ku rabashe na ke gaya ma, bikin 'yar (Dabai
Motors) tilo.
Amma zuciya ai dole a bar wa mai ita ko?
Sageer bai son jin maganar, don haka ya ki
tankawa, haka bai hana shi Naseer din yayi shiru
ba,"Ba ka ce komai ba?
Yakamata ka ce wani abu, magoya bayan karya."
"Karya?
Karya ce mana.
Ni kuwa na fi son duk abinda za'a yi, a rinka fede
gaskiya komai dacin ta.
"A'a ba dama ka nuna ra'ayinka, sai ayi ma baki,
da zarar an sami matsala kuma, ace ban kyauta
ba.
Ko ba haka bane?
Ya ce,"Haka ne, amma a iya sani na, rakiya
Kaduna ka ce zan ma, ban san dalilin wannan
musayar ra'ayin ba.
Tunda za ka Kaduna.
Ina ganin maganar ta k'are, a ba shi a ka amince
kawai,. Idan ka gama shirin ina kofar gida."
Ya mike ganin zai fita.
Naseer ya sha gaban sa, amma kafin ya ce wani
abu. Umma ta sawo kai cikin falon.
Ita ma haka tayi tsaye, tana kallon su cirko-cirko,
kamar zakaru na fada.
Sageer yayi sauri ya kar6i katon filas din silba da
ke hannun ta.
Ta ce,"Menene?
Hada baki su kayi,"Babu komai Umma."
Naseer ya zarce da fad'in"Anya kuwa za mu tsaya
karyawa kuwa?
Ta ce,"Ya zama dole, ai da sauran lokaci, don nan
da Kaduna, in Allah ya yarda nan da nan ne.
Ga ruwan zafi nan, zo ka kwaso sauran abincin."
Ta fice. Naseer ya dubi Sageer ya ce,"Zauna in
kwaso."
Ya zauna yana fadi cikin ran sa," Dan rainin
wayau."
Tire ya dawo da shi, ya aje, kofuna ne, sai
soyayyen dankali da kwai ga biredi a ledar sa.
Cikin daki ya shiga ya kwaso gwangwanayen
madara da Bonvita.
Babu wanda ya tanka wa wani.
Ya gama hadawa, ya mika wa Sageeer na shi.
Cikin zaman kuramen suka kasance zuwa wani
lkc.
Shirun Sageer kuma ya dami Naseer, don haka ya
ce,"Rabo na da abinci tun karin safiyar jiya.
Kamar bai ji shi ba, ya ci gaba da kurbar
shayinsa Naseer ya dube shi a dage,"Ina magana,
ka na banza da ni.
Ni na fi ka iskanci Wallahi.
Ya kwado masa harara, ya ce,"Dama ni ba dan
iska bane, kai ma ka san wannan. Allah daya
hada ni da kai, shi zai raba ni da kai, in huta."Ya
ja dogon tsaki,"Sai me, sai me kuma?
Mts...............Ya aje kofin, ya mike," Ka same ni
waje." Ya ce,"Ko kuma na same ka Kaduna ba,
na lura duk ka kosa."
Ficewa yaui, bai tanka masa ba.
Cikin mota haka suka zauna dunkum!
Sageer ke tukin, abin yayi masa dai-dai, domin
gaba daya ya tattara hankalinsa ga tukin, shi
kuwa Naseer tunanin sa me zai cewa Nusaiba?
Ta yaya zai fuskance ta?
Yadda ba za ta gane komai ba, don gudun wata
matsala?
Wadannan tambayoyi sun sa shi yana jin kamar
ya ce wa Sageer su juya.
Amma babu hali.
Ransa ya kara kuna, ya cika da kunci.
Zarah ce kadai za ta iya share masa zuciya, ga
shi tana makaranta, babu halin daukar waya,
balle ya kira ta, ya dan ji sanyi a ransa.
Saboda haka ya bude sakwanin (Text) din ta, yayi
ta karantawa.
Kawai ji yayi Sageer na fadin,"Ina mu ka nufa
ne?
Ya cira kai, ya duba, suna cikin Kawo.
Ya duba agogansa k'arfe 10:30am.
Ofishin Alhj suka nufa. Bai jima da isowa ba,
lokacin.
Suna ta musayar fara'a, har suka zauna.
Gaisuwa cikin mutunci da girmamawa suka yi wa
Alhj.
Shi kansa Alh cikin jin dadi yake a yanayin da ya
ga Naseer, tun daga shigar da yayi ya zuwa
dauko abokin sa da yayi.
Abin ya burge shi.
Hakan kuma ya nunar ,masa da amincewar
Naseer dari bisa dari.
Wani dadin farin cikinsa, shine samun goyon
bayan Nusaiba da mahaifiyarta, baya dawowarsa,
yayi masu bayanin s 2 ne 'yan matan da Naaseer
din zai aura lokaci guda.
Shi yasa yake cikin nishadi, zuciyarsa kamar
gonar auduga.
Cikin kunya Sageer ke cewa." Da tun jiya muka so
zuwa, to ni ina makaranta, shine nace yayi
hakuri, yau mu zo in taya shi godiya.
Gaskiya mun ji dadi Alhj.
Mu kuma ya ba mu Ikon rike amana."
Alhj ya ce,"To Amin.
Ni ma na ji dadi,."
Ya maida kallon sa kan Naseer ya ci gaba,"Akwai
gida a (Hanwa Low-cost) nawa, shi zan ba ku, ku
zauna.
Akwai motoci guda 2, su ma sai ranar tarewa
za'a tare da su. Sannan kar ka manta da
maganar da mu ka yi akan makaranta, ina
jiranka."A lokacin da yake kara nuna kaunar sa ga
Naseer.
Shi dan gogan tunaninsa daban ne.
Domin kuwa cikin ransa yake saka wadannan
kalamai,"Lallai Alhj dan siyasa ne.
Ai na dade da sanin wannan wayon masu kudi.
Da za'ara 'ya'yan su sun rasa miji, sai a sami
wani mai yunwa a lika masa, a ba shi gida da
mota.
Shi kenan an kama shi a hannu, sai yadda aka yi
da shi.
Allah ya hada ka da Naseer, mu je a siyasar."
Kayataccen murmushi yayi, suna kallon juna da
Sageer kafin ya ce,"Ban san avinda zan ce ba
Alhj. Na gode."
Ya fadi yana dan rankwafawa, Sageer ya taya shi
godiya.
Bakin Alh. Basheer baya rufuwa, ya ce,"Kauna ce
Naseer, kar ka ji komai ni Babanka ne.
Yaya sunan ita waccan 'yar tawa?
Ya shafi keya, ya ce,
"Zarah."
Yayi murmushi ya ce,"Ashe kanwata ce, shi ke
nan ga Nusaiba ga Antin Jordan.
To Allah yasa albarka."
Sageer ya ce, amin.
Suka yi shiru na 'yan dakikai, kafin Alhj ya lura,
kamar kunya duk suke ji, don haka ya ce,"Za ku
karasa gidana ne?
Sageer ya amsa,
"Eh."
Ya ce,
"O.K.,
to ku na iya tafiya, zan kira Nusaiban, in gaya
mata ku na tafe." Sageer dai ke magana,"To mun
gode." Suka mike, suna k'ara godiya, suka yi
waje.
*******************
(Go slow) ne ya 6ata masu lkcn bisa hanyar su ta
zuwa unguwar Rimi, sakamakon mutuwar wata
babbar mota akan titi.
Naseer ya ja dogon tsaki, saboda takaicin zaman
da suke a mota, ga rana ta fara zafi.
Sageer ya dube shi ya kauda kai.
Tuntuni yake son yi masa magana a kan
alkawuran da Alhj yayi masa, watau gida da
canjin mota, amma yayi shiru, saboda yana
gudun 6acin rai. Shi yasa ko yanzu da ya ci birki
da yin dogon tsakin sa, kallon sa kawai yayi, ya
kyale.
Da kyar da ji6in goshi suka sami wuce dogon
cunkoson motocin.
Sannan suka fada titin da zaikaisu kayatacan
gidan Alh. Basheer.
Nusaiba ma gab da kammala shirin ta, lkcn da
Baba Mai gadi yayi sallama ya kira Mariya mai
aiki, ya ce ta gaya wa Hajiya bak'i sun zo.
Sama Mariya ta haye ta shaidawa Ummi, ita
kuma ta umurce ta da kira mata Nusaiba.
Jimawa kadan Nusaiba ta shigo, ita kanta Ummi
sai da gaban ta ya fadi, saboda tsabar iya adon
Nusaiba,Komai ta sa yana amsar jikin ta. Wani
lallausan farin les ne ke jikin ta, wanda aka yi wa
ado da zare kalar samaniya.
Shi yasa hatta abin wuya, da 'yan kunnenta, kalar
samaniya ne. Haka nan warwaraye, sai bungus
din su da ke hannunta na hagu. Haka takalmin
kafar ta suke irin daya da gyalen da ta yafa,
wanda gaba daya ta tattara launanin farin ciki, ga
duk wanda ya kalle ta.
Tamkar yadda ko wace zuciya ke a ji a duk
lokacin da samaniya tayi luf-luf!
Cikin wannan launin mai sanyaya idanuwa.
Ummi ta dafa ta ta ce,"Naseer ya iso, ki maza ki
kai shi babban falo, a kai masa duk abinda ya
dace.
Ta ce,"To Ummi." Tana kallonta. Ki tafi mana, ko
sai na ce kin yi kyau? To kin yi kyau Bebin Abba."
Da sauri ta juya cikin hanzari ta bar dakin dauke
da murmushi, bisa fuskarta.
Ummi ta kada kai ta ce,"Allah sarki Bebin Abba.
Allah yayi miki albarka.."
Su Naseer na tsaye jingine da mota, inda suka yi
fakin a harabar aje motoci. Nusaiba ta danno,
tana takawa d'ai-d'ai. Gaba dayan su sai da suka
rasa kuzari.
Kwarai Nusaiba tayi wa Naseer kawarjini a idonsa
har yasa jikinsa yayi sanyi, sai dai cikin zuciyar sa
Zarah ta riga ta kame, ko alama bai ji wani
matsugunni da zai aje Nusaiba ba.
Sallama tayi masu, tana dan murmushi, suka
amsa ta ce.
"Kuyi hakuri, ku na ta tsayuwa ko?
Sannun ku da zuwa."
Sageeer ya ce,
"No,
kar ki damu.
Ai ba mu wani dade ba.
To ya ki ke?
Ta ce,"Lafiya lau.
Ku k'araso ciki mana."
Ta fadi tana duban Naseer ido cikin ido. Kwarjinin
Naseer ya zarce na yadda ta ji, a ganin sa na
farko a hoto, shi yasa tayi saurin kauda idonta.
Bismillah!
Ta wuce suka biyo bayanta
zuwa babban falon gidan,
wanda ba kowa ke shigar sa ba.
Naseer da Sageer, sun ga launanin abubuwan
rayuwar duniya cikin falon nan, kai ka rantse ba
za'a ta6a barin duniyar ba.
Bayan sun zauna, ta gaishe su cikin kunya da
ladabi.
Abin ya burge Sageer, yanayin yadda ya ga
Nusaiba.
A na shi gannin, bai ga wani abin ki ba. Shi kuwa
Naseer ba dole bane ya so wannan yarinya, duk
da tana ingattatun abubuwan bukata. Shi abin
daya sani Zara yake so, ita ya za6a, ita kuma
yake son ya aura ya zauna da ita iya rayuwarsu."
Bayan sun kammala gaisawa, ta mike tana
fadin,"Minti 2,." Sageer ya ce,"Mun baki."
Ta fice tana fara'a.
Suka kalli juna jim.
Sageer ya fara murmushi.
Naseer ya kauda kai. Nan da nan ya hadiye
murmushinsa, ya gyara zama a kujera.
Ya fara lissafin zuci. Da sallama ta sake shigowa,
dauke da dogon tire fari, shake da kayan lashe-
lashe da shaye-shaye.ta aje masu.ta zuba
(Drinks)' kala-kala, ta koma ta aje gaban sa, "Ku
sha ruwa."
Sageer ya ja robar Swan, ya dauki kofi,"Mun gode
Malama Nusaiba." Ta koma gefe ta zauna.
Sageer ke ta magana." To, ga fa aboki na Naseer.
Ni kuma suna na Sageer.
Ya ki ka gan shi? Ya dan sadda kai kunshe da
murmushi ta ce,
"Dai-dai."
Yace kin tabbata, yadda ki ka yi mana dai-dai,
haka shi ma yayi miki? Ta gyada kai, tare da
fadin "Na'am."
A karkace Naseer ke kallon ta, tana amsawa, ya
numfasa, kamar wanda zai fadi wani abin kirki.
Duk da yana son yayi mata magana, amma
rashin sanin abinda zai fadin, yasa shi yayi shiru,
kamar ba shi ba.
Saboda haka ya bar Sageer , yana yi masa tad'in.
Ya ce,"Gaskiya mun gode da fatan Allah ya sanya
albarka a cikin abinda za'a kulla.
Sannan wani hanzari ba gudu ba.
Abba yayi miki bayanin akwai uwargida ko?
Ta ce,
"Eh."
Ya ce,"Ina fatan za ku hade kan ku kamar Ya da
Kanwa. Zarah babu ruwan ta, kuma tana da
hakuri da hankali. Koda aka gaya mata zai aureki,
addu'a kawai tayi, tare da fatan samun hadin
kan ku."
Hankali kwance ta ce,"Insha Allahu babu matsala,
domin shi shirin Ubangiji kullum alkhairi ne ga
bayin sa, idan ka ga akasin hakan to laifin daga
mu ne 'Yan-Adam.
Saboda haka ni ma ina mana fatan alkhairi tare
da fahintar juna."
Sageer ya jinjina kai, ya ce,"Amin.
Naseer ka ji, ko kuma in bari in ba ku wuri ku
gaisa."
Ya dan muskuta ya ce,"Ina jin ma idan ma za
kayi zaman ka, babu damuwa, ai ni da kai ba
bambanci.
Duk abinda ka fadi tamkar ni ne na fade shi."
Ya riga ya gano shi, don haka ya ce,"Haka ne,
amma waka a bakin mai ita, ta fi dadi, ko
Malama Nusaiba?
Ta ce,"To ni me zan ce?
Ya mike ya ce,"Bari dai na jira ka a mota.
Malama a fito lafiya."
Ta ce,"Kuwa ba ka zauna shiru kai kaidai a mota.
Ta mike, "Zo mu je." Ta fice ya bubbuga kafadar
Naseerr, sannan ya bi bayan ta.
Wata kofa ta bude, sai ga su a wani matsaikaicin
falo. Ta ce ya zauna ta kunna masa T.V. "Wane
( Channel) Ka ke so? Ya ce,"Bar min labarai, na
gode."
Ta fita, jimawa kadan suka dawo tare da Mariya,
dauke da kayan abinci da na sha, ta aje masa."
Duk ni kadai?
Tayi murmushi," Duk kuma na ke son ka cinye."
To na gode."
Ta sa kai ta fita.
Sageer yayi kishingide a kujera, ya cigaba da
kallon sa.
Tana sallama babban falon. Naseer na daukan
waya, "Yaya B, ya aka yi ne? Ka na wane gari ne
yanzu?
Ya ce,"Tafiyar nan bata yuwu ba B. Sai dai mun
hadu, ka ji labari. Ina ma Kaduna a halin
yanzu.......
Takaici yasa Naseer B, ya kashe wayar sa. Jin
shiru. Shi yasa shi ma ya cire ta a kunnan sa.
Ya gama 'yan latsen-latsen sa tsawon lokaci,
kafin ya dubi inda Nusaiba ke zaune. Kanta a
sunkuye yake, don haka ya ci gaba da hararar ta.
Jikinta ya bata ana kallon ta, saboda haka ta dan
dago ba zato suka hada ido.
Yayi sauri ya janye na sa...................
______________________________
Masu karatu, yaya za ta kaya ne? Wace badakala
za ta faru a wannan labari? Ga Naseer Ga
Nusaiba, cikinsu wa zai ci gari? Na yi gaba a
dangaraman jirginmu na (MAIZAR AIRLINE). Mue
je zuwa, wai mahaukaci ya hau Kura.
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Download A Jininsa Yake Littafi Na Daya Complete
0 Comments
Thank you for this comment