AlJANAR FATIMA
littafin Kingboy Isa
Ebook created by Shuraih Usman
Published at www.hausaebooks.com.ng
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Part 1-2
NA. 👑 KING BOY ISAH 👑
👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽
*بسم هللا الر حمن الر حيم*
_*YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH MAMALAKIN KOMI DA KOWA WANDA YA DAI-DAI
TA GABOBINA*_
_*TSIRA AMINCI KA DADAWA FIYAYEN HALLITA ANNABI MUHAMMAD S.A.W SHUGABAN
HALITTA CIKA MAKON ANNABAWA*_
_*INA ROKON ALLAH A KAN RUBUTUN NAN DA ZAN FARA ALLAH KA IYA MINI KA BANI KAIFIN
BASIRA DA HIKIMA ALLAH KASA NA RUBUTA ABUNDA ZAI AMFANE MU DUNIYA DA LAHIRA,
AMIN.*_
💃🏻 GA WATA SABOWA ZAMANI MAI YAYI SABUWA.
Bazan manta da ku ba domin kun zama My blood.
Bazan barku ba domin in na barku na bar kaina.
Bazan ki yaban ku ba domin yaban gwani ya zama dole.
Bazan hana ku ba dole in mika shi gare ku littafin baki daya sadaukarwa ne gare ku MY BLOOD duk yan Kungiyar
Zamani writers association ®Z.W.A banga kamar ku ba bakwa taba nuna banbanci
❤😍
💃🏻 ```Bazan taba mantawa da ku ba masoyana a duk inda kuke alherin allah ya kai muku kuna a heat na.
Bari in fara rubuto ku🤦🏻♂ Kash! Nawan in na fara rubuta ku bazan idasaba har karshen littafin ga ruwa biro na
kadan ne. Ilove you my fans```
A Cikin kado anguwar hausawa dake babban birnin tarayya Abuja.anguwa ce mai lunguna gata da tarin bishiyoyin
mangorori hankan ne yasa anguwar take da inuwoyi hakan ta haifar wa da wajen duhu dan daga ance ma karfe 6 tayi
to sai an haska fitila tsabar duhu in dai ba farin wata ba. Anguwa ce mai tarin jama'a, ko ta ina ka duba mutane ne
kowa na uzurinsa. Akwai masu saide-saide da yan shaguna da irin tsofafin nan masu saida kayan makulace na yara.
Wata yarinya ce sanye da doguwar farar riga wacce ta koma baka dan tsabar datti, Yarinyar fara ce kallo daya zakayi
mata ka gane hakan saidai dauda ta masheta baka. Gashin kanta mai tsayo ne amma rashin gyara yasa duk ya fara
cicirewa tsabar datti gashi duk ya barbaje mata a fuska sai ta dage shi tukun take iya ganin gabanta.
Duk mai tausayi yaga yarinya to dole tausayinsa ya lunku a kanta. Domin tayi kalar ban tausan. A hanakali take
tafiya har ta isa bakin kofar wani shagon saide-saide. Bakin kofar shagon taje tayi tsaye ta dan yace gashin da ya
lilube mata fuska tana kallan cikin shagon. Shi kuwa mai shagon a lokacin ya dan duka daukar wani abu. 'Da
dagowar shi duka hada ido da ita sai ji yayi gabansa yayi mugun faduwa.
Nana take yanayinsa ya canza kalo daya zaka mishi ka gane ya fusata ainun!, "Ke uban me zan baki iyee?, haka jiya
ma kika zo kika min tsaye a kofar shago kina wani nuna min ciki da baki, gaki yau kin kuma Dawowo uban me zan
miki".
Dayan hannuta ta daga ta dage baki hade da nuna yatsar ta cikin bakin tukun ta sauke shi ta nuna cikin ta kamar dai
yanda tayi mishi jiya. Wanda duk me hankali in ya gani zai gane tana nufin yunwa take ji tana bukatar abinci,
Shima kuma kanshi ya fahimci hakan.
Download Aljanar Fatima Littafi Na Daya Complete
1 Comments
Tnx
ReplyDeleteThank you for this comment