writing by his eccellenciy novels group
****** DAN ALHAJI 1 ******
.
Iskace mai karfi hade da guguwa garin duk ya hargitse mutane sai neman wajen fakewa suke wasu kuma sun tsaya cak suna kalon ikon Allah rufaida ce a tsaye hankalinta a tashe ganin tasowar guguwa dake nufota tana dosowa ta dauke dan karamin hijab din dake jkinta ganin hkaa ta sake dinmucewa da sauri ta rungume jakarta ta makaranta ta rufe kirjinta.
.
duk wannan abin dake faruwa a kan idon safuwan tsye yake cikin motarsa ganin tasowar guguwar ne yasa ya faka motarsa.hijab din ko bai tsaya ko ina ba sai kan fuskarsa jin wani daddadan kamshi yaji a jikn hjab din sauri yayi ya cire shi ya bishi da kallo ga kuma kamshin jikin hijab din daya tafi da imaninsa.bude motarsa yayi ya fito ya doshi inda take da hijab din a hannunsa cikin takun kasaita nasu na ya yan masu ji da kan su kyakyawan saurayin ya karasa inda take tsaye tana ganin ya doso inda take ta sake rudewa ganin rashin hijab a jikinta tayi kamar ta taka da gudu ya karaso ya dan duka yace ga abinki da sauri ta karba ta saka cikin gaggawa suna hada ido yaji wani abu ya tsirga masa cikin jikinsa.
.
Take ya yardewa kansa ya sani matar da zai aura wacce ya dade yana mafarkin samu a zuciyarsa yace lalle kin amsa sunanki na mace ya nisa yace daga dukkan alamu daga makaranta kike ga kuma hadari na haduwa ga kuma ana wuyar mota ko zaki zo na rage miki hanya?ta girgiza kai cikin sauri ta fara tafiya cikin sarsarfa ta fara tafiya ya sake cewa da kin daure kin shigo na rage miki hanya kar ruwan nan ya sauko (hmm wai shin ana abun dole ne?) tayi har da ido tace a'a nace maka na gode Allah zai kawo min motar da zan shiga kafin ruwan ya sauko
bin ta yayi ya ringa mata magiya har ta fara jin haushin sa ta ci gaba da tarar motar ba ko wacce tazo a cike
shi kuma bai daina mata magiyar ta zo ya rage mata hanya ba dole hakan ta hakura ta shiga tsakiyar matar safuwan
cikin matar ba wanda yace da kowa uffan ya juyo yace yan makaranta wacce unguwar zan kaiki?
.
Tace waccan hanyar zaka bi yasa kan motar suka ci gaba da tafiya tace mun zo ya tsaya ta sauka tace masa na gode yace sai yaushe kenan kai!.ta tsallaka kwata ba tare da ta tanka masa ba ta shige gida.ya girgiza kai ya ja motarsa yayi gaba.tayi sallama ta shiga gida ta tarrar da umminta tsaye tana kalllon hanyar kofar gida ta amsa sallamarta tace yanzu nake zancen ki ganin hadarin nan ya taso tace wallahi yau wahalar mota ake ina tsaye a titi tasowar guguwar nan ban sami mota ba
yanzu wani bawan Allah ne ya dame nina zo ya rage min hanya kafin ruwan ya sauko da har naki ganin ban samu bana hakura na shiga ya rage min ( hmmm kaji yaran kirki ba kamar maryam ba uwar son dadi) habiba ta bude baki tace kin shiga mota wani ya rage miki hanya? duk nasihar da nake miki ta tashi a banza shine kika gaya min wani ya rage miki hanya to ba yau kika fara ba ta sassauta murya tace"wallahi ban taba shiga motar wani ba yauma ganin hadari ne in Allah ya yarda bazan sake ba dan Allah kiyi hakuri"
.
Tace mutunci ki nake taya ki karewa tace to ummi afwan tace a wuce a kiyaye gaba tashi kije kiyi abinda zakiyi wanka ta fada bangaren safuwan kuma ko yinin wannan ranar tunanin rufaida ne ya zamo masa abincinsa ya kasa sakat!! bacci ma kasawa yayi sai juye juye yake yi.daga ya rufe idonsa sai ya ganta lokacin da iska ta yaye mata hijab shi komai nata burgeshi yake a haka sulainman amininsa yazo ya same shi suka fita ya akayi yau ban ganka a majalisa ba? yace labari ne dani yace to bani na sha yace wallahi wata tsintuwa nayi akan hanya yace tame? yace wata zukekiyar yarinya nayi arba da ita yace wannan ba irin wadan can bace ina ganin ma auranta zanyi yaja da baya yace aure fa kace? yace kwarai kuwa.
.
yace amma wallahi ka bani mamaki mai ka tsinta a duniyar har zaka tunkaranwa kanka tsofa sai kace wani bagidaje ai mu yanxu muka fara cin duniyar mu da tsinke safuwan yace wai kai yaushe zaka san duniyar nan ba matabbata bace mu fa bana yau bane ya mike yace kaga tafiyata ya rike gefen rigarsa yace to zaka raka ni kona sami wani? yace Allah yakai mu daren yana fita safuwan ya zauna yana tunanin shi daga yau ma ya daina neman mata rufaida ta ishe shi auran ta zaiyi Allah yasa wani bai rigashi ba dan irin su rufaida wawuson su ake.
.
WANE NE MAHAIFIN RUFAIDA?
.
malam nasiru mahaifin rufaida ma'aikacin NEPA ne aiki ne ya kawo shi garin katsina.
haifaffan garin kano ne cikin karamar hukumar gaya cikin wata unguwar kofar gabas shida matarsa habiba.
.
WACE CE HABIBA? WATO MAHAIFIYAR HABIBA
.
ita kuma tana cikin unguwar alawa nan cikin karamar hukumar alawa dake ckin karamar gayan take bayan zaman su a garin gaya ne basu dade da aure ba aka mayar da shi aiki katsina suka koma can da zama .mallam nasiru mutum ne mai kishin matarsa habiba tana da hakuri sosai funanin gaye ne kyawawa ne sosai sun haifi yar su wato rufaida bayan shekaru goma sha takwas ta sake haihuwa ta haifo dan ta wato kamal. (hausan nawa sai a slow)
.
***** DAN ALHAJI 2 *****
.
kwata kwata yayan su biyu ne a duniya wannan shekarar ce rufaida take zana jarabawarta ta fita daga secondary.
motar safuwan taja ta tsaya a kofa gidan su rufaida sulainman ya yamutsa fuske yace ina gidan? safuwan yace gashi nan a fusace ya kalle shi yace wai kai wanni irin mutum ne ka duba matsayinka na DAN ALHAJI amma ka rasa wadda zaka ce kan sai yar talaka ai kwarya tabi kwarya in tabi akusa sai ta fashe" ransa a bace yace kai wai sulainman me yasa kake yawan shiga rayuwata?
.
ita na gani ina so kuma ba wanda zai hanani abunda nake so talaka da mai kudi duk Allah ne yayi su idan ka tashi naka auran ka auro yar karuna ba ruwana ya aika yaro gidan yace kace ana sallama da can ya tuna bai san sunanta ba ya tambayi yaron yarinyan gidan nan yace sunan ta rufaida nidai ita nasani sai kaninta kamal goyansa ake yana shan nono ya dafa kansa yace ka shiga kace ana sallama da ita yaron irin masu surutun nan ne yace inji wa zanceh?
.
suna tsaye jikin mota sai ga malam nasiru nan suka gaisa yace kune masu sallama da rufaida suka amsa da eh ya nuna musu waje suka zauna yace dasu "tasan da zuwanku? suka ce A'a,yace toh a gaskiya bana son ta fara zance yanzu saboda yana so tayi karatu mai zurfi kunga ba'a hada taura biyu a baki" safuwan ya marairaice yace dan Allah baba anyi mana afuwa mu ringa ganinta ko da sau daya ne a sati sulainman ko duk haushin safuwan ya kama shi ganin yadda yake ta zuba magiya.malam nasiru ya nisa yace ba wai na bazan baka auranta bane a'a zancen ne dai bana so yanxu ni din nan dakake gani ba yadda za'ayi nayi wa yata auran da bata so shi dai magiyar yake ta yawa malam nasiru sulainman kamar ya rufe shi da duka sukayi sallama akan nan da kwana biyu su dawo zai yi shawara ya gani haka suka tafi basu ganta ba zuciyar safuwan kamar zata buga shi ko sulainman kuka ne kawai yakeyi dan takaichi suna shiga mota ya hau masifa wallahi ka bani mamaki har ka tsaya wani talaka talak ya ringa wulakan taka.kana wani lallamin sa si kace yar gwal ce nasan ko yar shugaban kasa kake so za'a aura maka ba tare da wani dokoki ba amma ka tsaya wani banza yana hura hanci shi ga mai ya yace ai kasan an ce mai abu sarki shikenan sai kayi ta zuwa ana wulakan ta ka ni ai dan rakiya ne bangare malam nasir ko malam nasir yana shiga gida ya kira ta ya tambayeta tasan wanda yaxo gurinta?
.
da sauri tace bansan shi ba yace baki san shi ba yaxo gurin ki kasan magana tayi yace to koma mene ne ki natsu kisan abinda kike kar ina tufkar dama ta hagu na warwaeewa kinsan ra ayina ina san kici gaba da karatu kenake yiwa gata wataran zaki gani dan yanzu karatun mace yana da mahimmanci sosai ba sai ta dogara da mijina ba sabo da haka ki fitar da duk wani sauraron samari ki tsaya kiyi karatun ki.amma duk da haka tunda naga wannan yaron yanace kuma daga dukkan alamu mutumin kirkine ki sanar da umminki in kina son sa sai ya ringa zuwa dan kin isa zancen amma akula sosai tashi kije safuwan kuwa ya matsu kwana biyu tayi kamar ya jawo kwanakin gani yake sunyi masa nisa haka itama duk da taba soyyaya ba son sa yake mata ziyara lalle yayi sa'a ba irin tsiyar da kawayenta su halima abdullahi basa yi mata akan wulakanta samari da take yi dan kusan duk kwanan duniya indai zata fita sai samari sun biyota taki kula su wasu suyi ta yiwa kawayenta zarya akan suyi musu kanfen a wajenta sulainman abokin safuwan ne tun suna yaranta shima ubansa (kusane) mai kudi ne su a rayuwarsu ta duniya basu san babu ba kudi ne gasu nan kamar banza ba wanda a cikinsu bashi da kamfanin kansa,sama da hudu bnda iyayensu da suke kashe musu kudi kamr kasa tare suke sheke ayar su shi yasa suleman baya son sufuwan yayi aure saboda yasan dole abotar su zata yi nakasu group ne dasu bakwai dukkansu yayan masu kudine wannan yana wane wannan duk mutumin dake zaune a unguwar yasan da zancen su
.
WANENE MAHAIFIN SAFUWAN? alhaji mu'azzam sunan mahaifinsa yana da bala in kudi na gaske kusan in baizo na daya a masu kudi ba bazai wuce na biyu ba Allah ya jarrabe shida da son safuwan ko dashi kadaine yake dashi shiyasa oho! duk abinda yayi gani yake daidaine mutane suna yawan kawo masa tsegumin dan nasa amma sai ya hau fada yana mai cewa ansa wa yaro na ido taya ake so yayi masa so ake ya takura masa shi yasa yake tabargazar sa,
.
su uwa ba harara uba ba kwaba,da wuya mutum ya kalle shi sau daya bai sake ba yawancin abkansa suna ce masa yyai kama da wani mawaki MASARI
yaci gaba da cewa ba wnai abu bane yke tafe dani ba illa tsananin so da kauna da suka yi katutu a cikin birnin zuciyata suka hanani sakat tunda na dora idona a kanki ina fatan zan sami wani gurbi a zuciyarki ko yane kona sami nutsuwa ya kura mata ido tsawon mintuna biyu da wani mayataccen kallo da har sai da yasa taji kunya ta boye idonta cikin mayafi ya sake cewa baki ce komai ba tace to ni mai zance? yac e baki da abinda zaki ce? ta tsaya kiji indai kin yarda da soyyayat kuma kin yi amanana dani to kice I LOVE YOU safuwan (mtsww i love u din banza).
** DAN ALHAJI 3 ***
.
A cikin yan mata ya rinnga yaba wa da hankalin yaudarace kawai wannan yarinyar idonta a bude yake kana ganin kalaman ta kamar wata tsohuwar yar bariki yac e ba haka bne kawai mata masu tattausan lafazi soyya ce mai karfi take shiga tsakanin su a kullum sulainman na zuga shi mai zaiyi da yar talaka,dayaga abin bana wasa bane sai da yasan yadda yayi Alhaji muaz yasan zancen zai auri yar talaka sanin halin alhaji muaz na kin hurda da talakawa ko kadan baya son ya rabe shi ya dinga fada ya zubawa idonsa toka tun da yake bai taba yiwa safuwan fada ba sai karonnan ran safuwan ya baci yace shi ita yake so ya ko haukansa ta inda ya shiga batanan yake fita ba yace kaje ka dubo ko yar wa kake so ka aura zan aura ma,
.
safuwan yayi buris da maganar yaci gaba da zuwa gurin rufaida yasa a gaba yana ta wallafo masa illolin zama da talaka kuma ya dauki alkawarin in dai ya rabu da yarinyar nan zai kara masa wasu kanfanoni annan ne HAJIYA BILKI yar katsina wan asali kenan ga kunya ga kara haba yallabai kabar yaro ya auri wacce yake so talaka da mai kudi duk Allah ne ya haliccesu kuma ba wanda yasan wada yafi mu lokacin da mukayi aure kana dashine? da na sha yasar da kayan dakina ina mana abinci na kuma sha kwana da yini anan fa yace ina wuta ya sakata?
.
ya ringa fada wai tayi masa gori a gaban yaro itama ta daka ta tashi ba wanda ya saurara a ranar dai rai ya baci sosai dan sai da hajiya tayi masa fushi sosai wato yajin aiki ya rasa yadda zai sha kanta gashi baya son bacin ran ta kona miskala zarratin amma yana ganinin indai akan ya hakura safuwan ya auri yar talaka ne sai dai ko wacce wacce.haka sabani ya ringa shiga tsakanin su har sai da aminiyar ta hajiya jamila ta ringa tausar ta akan ta rabu dashi dan zamanine hajiya bilki tace baki san halin yallaban ba yana da bala'in taurin kai nima dakika ga muna zaune lafiya dan ni dince ta makaryaci kinsan dai komai yanzu ma wani lokacin birkicewa yake yi wai shi aure zai kara yana son karawa safuwan yar uwa tunda naki haifuwa kinji fa kamar ni nake bawa kaina ni yanzu na zubawa sarautar Allah ido kowa dai ya hau kujerar naki,a majalisa su sai zuga shi suke wai kar ya aure ta tunda abbansa baya so kawai yasan hanyar da zai yi ya yaudareta ya nuna musu sam shi auranta zaiyi nina daina hurda da ko wacce yarinya najashi cikin zolaya nace har tima yace koma wace ce suka hau dariya gaba dayansu yanzu kam kusan ace tunda ya hadu da rufaida ya daina kula ko wacce yarinya sai dai abin da ba'a rasawa dan abin ko rawa shima din ya yi bala'in ragewa yana kuma ganin da zarar ya aureta zai de na gaba daya su kuma sun kudirin niyar ko ta halin kaka bazai aure taba jarabawa ta fito gaba daya rufaida tayi passing malam nasiru yayi murna sosai ya ringa sa mata albarka habiba ko baki yaki rufuwa saboda murna bayan tayi wanka ta huta ta dauki waya ta sana da safuwan shima yayi farin cikin yace aina dauka baZa ki sanar dani ba ai labari ya iso min tun dazun a hanya naci karo da lubabatu suke bani labari
.
duk makarantar keda bahijja kun zarce kowa.ina mika sakon murna kafin nazo har gida sai dai ina ganin ya kamata mu shirya wani dan kwarya kwaryan party na taya ki murna tace a'a na gode abba bazai yadda ba su bahijja basun gaya maka munyi daxun a makaranta ba? ai ya isa wani haddan mota ya shiga ya wuce yayi mata siyyaya ya hada kaya kamar hauka dan sai daya cika motar da kaya atamfofi da dai sauran kaya basai na tsaya ina ir gosu ba da dai duk masu azabar tsada sai kuma bangaren takalma da gyalluluka da yan kunnaye fashion dasarkoki har dana gold yayi parking motar a kofar gidansu yara suka ringa shigar dasu daga habiba har rufaida ba wanda bai tsorata ba suka ce kai ku tsaya ba nan gidan aka ceku kawo ba wanan ai kayan masu kudine suka ce a'a nan aka ce mu kawo da yake sun san shi mutum ne mai kyauta kusan duk yaran layin suka ce safuwan ne fa yace mukawo umminta tace maza ku mayar ke kuma dauki gyalenki kije kice kin gode ya ajiye yi azama kafin abbanki ya dawo bake ba har ni sai ta shafa ganin yara yayi sunyi kaya niki niki suna dawowa dasu ya dubeta yace meye haka?
.
tace kabari ba yanzu ba yace wannan wacce irin magana ce? a fusace yake maganar duk abinda na baki sai kice kin gode kiki karba to wallahi ina tantama akan so da kika ce kina min itama ta fusata tace ai dama ba abinka nake so ba kai....bata karasa ba ya kwallawa yaran kira yace kowa ya dauki abinda yake so ya kai gida" suka tsaya tsororo suna mamaki.
.
yadaka musu ts
awa yace ba da kunake ba nan da nan suka sawa kayan warwaso kowa yayi gida da abinda ya samu yana murna yakai wa uwarsa ita ko kafin yaran su karasa ta shige gida ya shiga matarsa ya hada wata yar karamar guguwa yayi ficewarsa daga layin,tana shiga gida ta fada kan cinyan umminta tana kuka habiba tace lafiya ? tace yayi fushi ransa ya bace sosai tace gwara hakan dan wallahi abbanki yaga wannan kayan raina in ya kai dubu sai ya baci.
.
*** DAN ALHAJI 4 ***
.
Baci dama tunda ya fara ja miki kunne na gaya miki karki yarda kikar kwandalarsa kuma na gaya miki tuntuni kwana da kwanaki bashi ba dallilin sa sati wajen uku kenan amma fa duk da haka hankalinsa na kanta tsabar zuciyace irin tasa son ta da kaunarsa yana nann daram a ransa abin sai dai ya karu itama hankalinta na kanshi itama dai tata zuciyar na mata yadda taba shi hakuri asalima tana ganin ba abinda tayi masa dole ne tabi umurnin iyayenta dan bata da kamar su duk ta damu kanta abbanta ya tambayeta cewa bata jin dadine?
.
ita koh habiba tasan akan rashin zuwan safuwanne tayi banza da ita ko tambayarta mai ya dameta bata yiba kowa ya ganshi yasan ya rame kullum zuciyarsa kamar ta fashe da yaga abin na neman tarwatsa masa zuciya waya ya dauka ya kira ta cikin sanyi murya tace "HELLO"! yace ke baki san ki yiwa mutum laifi baki bashi hakuri sai kawai ki share ni tace kai baka gane ba bani da wani laifi bacin ran iyaye na nake gudu dan ban son bacin ransu kokadan.{hmmm matan kwarai kenan amma banda na zamani}
.
maganar ta doki zuciyarsa sosai yace shikenan sankin ganni gobe tace Allah ya kaimu bai masa ba ya kashe wayar hannun yasa ya dafa kumatunsa yana tunanin maganar data gaya masa jikinsa yayi sanyi yace laalle wanan yarinyar wato dole ta guji bacin ran ubanta amma ni akanta na sakawa nawa iyayen bacin ran a kanta na dauke kafana daga gidanmu sai alhaji ya tau tsawon kwana bakwai bai sani a idonsa ba idan abin ya dameshi sai dai ya kirawoni a waya shima dakyar nake amsa maganar sa duk saboda ita zuciyata ta ringa zuga shi kawai ya dauki shawarar abokanansa idan kuma ya tuna da son da yake mata sai yaga hakan bai dace ba gwara ya bari ta zama mallakin sa yayi niyar ya share ta kar ya kuma zuwa gurin ta hakan ta faskara,
.
daukar mota sa yayi ya ratsa ta majalisa anan ma sun yaudare shi ya ki,ya zare jikinsa yace to zan tafi wajen ginbiya yana bala'in basu mamaki da shagala irin ta DAN ALHAJI yanzu yarinya karama ta dauke masa hankalinsa yafi tsohon minti goma bai sami yaron da zai aikaba yana daga idonsa suka hada ido da ita ta fito daga kusa da gidansu da kamal a hanninta yana kuka kayanda tsa sunyi mata kyau shirt da riga nena material ta yafa dan kwali a kanta ganin safuwan taji gaba daya gabanta ya fadi ba karamin dadi tajiba bata bari yagane ba fuskarta ba yabo ba fallasa ya mika hannu ya karbi kamal ya sake barkewa da kuka yamika shi tasa hannu zata karbe shi dan kwalinta ya sullube sakar baki yayi yana kallon gashinta har baya bashi da maraba dana india gashi rigar tayi bala'in fito da suran jiikinta haba ganin hakan yasa shi ya direrece ta lura da hakan tayi sauri ta shige gida har ta dawo sam bai san tana tsaye ba ya shiga duniyar tunani.sai da ta dan daki murfin motar sannan yayi firgit tace tunananin mai kakeyi haka?
.
yayi murmushi yace tunanin naya wuce naki na ga kin zama mallakina tace kar ka sami damuwa insha Allahu kamar yaune haka sukayi ta hiransu cikin faranta zuciya a hanyarsa ta zuwa gida ba abinda yake illa tunanin surar da Allah ya bata a gaskiya gani yake idan ya sameta yafi kowa sa'a ya buge siteri yace ai ni indai na sami wanan yarinyar ba kuma wata yarinyar da zata bani sa'awa a rayuwata wani tunani ya fado masa sai daya ji bugun zuciya wani tsoro ya bayyana a fuskarsa tunawa yayi anya mallam nasiru zai bashi yarsa idan yayi bincike ya gano halinsa dana mahaifinsa na kin talakawa idan ko ta bincike ne a gaskiya bazan sameta ba a halin irin na mahaifinta mai ra'ayin rikau saboda duk wanda ya kwana ya tashi cikin unguwarsu ba wanda bai san tabargazar da sukayi da shi da abokinsa ga kuma halin da yake ciki shi da alhaji har yanzu yana kan bakarsa ta bai yarda ya aureta ba ko jiya sai daya dada jadda masa akn ya samo ko yar wacece indai ya amsa sunansa na mai kudi yanuna masa indai bai aureta ba zai iya shiga wani halin tatshin hankali yana gama wannan tunanin duk saiya ji ransa ya baci ji yake kamar zuciyarsa zata fashe ta warwatse gaba daya a daddafe ya ringa tukin har yazo gida d kyar yana shiga cikin gidansa firiji ya zarce ya bude ya dauko kwalban barasarsa bai tsaya tsiyayawa ba kwalbar ya daga ya tittila a cikinsa sai da ya tabbatar da ba komai a cikin kwalbar sanan ya jefar ya samu waje ya zauna idonsa ya kada yayi jajawur saboda tsabar bacin rai.
*** DAN ALHAJI 5 ***
.
ya saka wata kara yace DAN ALHAJI kace ka komo ruwa kenan? yace tsindim dan jiya zuwa yau tima ta shayar dani da. suka bushe da dariya" safuwan yace inna son ganinka akwai magana yace gani nan zuwa dama ina kan hanya zuwa gidan ke neni da mubashar suna gama wayar sulaiman ya daki kujera yace waya ce maka ana yiwa bariki fitar gaggawa mubashar yace DAN ALHAJI kenan, sulainman aa guje ya fada kan DAN ALHAJI yana cewa WELCOME TO BARIKI (Allah ya sawwaka dai) safuwan ya saki wata wawar dariya yace aini yanzu na zama bokan bariki yau wata goma dai na barta firij ya nufa ya balle kwalba ya tuntula safuwan yace ba'ayi bani ba mikomin haka dai suka ta yin kayan shirme shirme , mubarshi yace ya mutumiyar safuwan?
.
yace tananan da ai a kanta nake cewa zamuyi wata muhimmiyar magana ni fa ina ganin aurena da ita ba mai yuyuwa abne sulainman ya karkata hula ya ce kai kace kai da kan ka mutu ka raba kai da ita ku shawota can kai da ita kai da nasan iskancinka baka rabo da halin ka ka tsya muyi magana ya kakr gani yanzu za'ayi yace wannan maganar da muka gaya maka a majalisa itace abinyi ya nisa yace nifa yarinyar kwarjini takeyi min kasan duk tsawon lokacin da mukayi ban taba tabata ba ko da hannunta ba kuma kasan ban taba sati da yarinya ban san taba.a gaskiya ina son yarinyar dan haka bana son taba mata rayuwa tace to dan gidan rufaida ai ka zuba ido kanta kana kallonta kana hadiyar yau kana gani wani zai zo ya dauke ta tsawon minti goma ba wanda yayi magana yace to ni ya zanyi na shawo kanta?
.
suka hada baki suka ce ya kake yi da sauran yan matanka" munarshir ya kama kunnensa ya rada masa wata magana yace kwarai da gaske suka dau dariya gaba daya suka tafa gaba daya sulainman yace kabar min komai a hannu na kai dai ka dauke kafarka kwana biyu ka kuma hakura da yi mata waya ko da kuwa ta kiraka a waya ka kaheta ku dai ku bani lokaci dana daukar maka za kaga aiki da cikawa ya girgiza kafadarsa yace Allah ya kaimu gaba dayan su suka amsa da ameen ni dai nace allahumma a'a kwana biyu bata ji duriyarsa ba hankalinta ya tashi soasai ko ta name shi a waya baya dauka ta ringa turawa da message amma shiru ba amsa ba karamin tashin hankali ta sake shiga ba abin duk ya biya dameta ta ringa tunani anya lafiya kuwa ita dai a iya sanin ta ba abinda ya shiga tsakanin su shihowar wani yarone ya katse ta daga tunanin wanda ya zame mata abincinta a kullum yace "Assalamu alaikum wani ana sallama da rufaida inji wani a waje dakwa tayi kamar bata jiba umminta tace baki ji abinda yace bane? tace iye iye? tace ana kiranki a waje ki leka ki gani mana tace jeka kace wane ne?
.
yarobya dawo yac sulainman ne abokin safuwan wani tashin hankali taji ya dada karuwa ta tabbata ba lafiya ba.tana fita ganin sulaiman yasa ya taji wani faduwar gaba ta karasa inda yake suka gaisa duk ta matsu taji halinda safuwan yake ciki yace baki tambayeni mutumin kiba? tace shine abinda nake so ji yace to mutumin an binciko file dinsa ta dafa kirjinta tace bashi da lafiya mai ya same shi? wallahi zazzabi ne mai zafi ya kamashi ko abinci baya ci a gaskiya zazzabi bai kama shi da wasa ba shine naga ya dace na zo na sanar da ke dan kar kiji shiru tace hakan yayi kyau na gode shi kuma Allah ya bashi lafiya yana gida ne ko .......?
.
yace a'a suna da likitansu a gida shi yake buba shi gashi bansan gidan su ba inji ta sulainman yace gidansu ba boyayye bane ko kuma kar na baki wahala kawai ki gaya min ranar da zaki sai na zo mu tafi tsaya na baki lambata idan kina da bukatar hakan sai ki neme ni tace ba damuwa in haka ta taso na neme ka sukayi sallama ta shige gida ta sanar da ummin ta safuwan bashi da lafiya sosai shine abokinsa yazo ya gaya mata habiba tace aiya shi yasa kwana biyu baya zuwa Allah ya bashi lafiya tace ummi dan Allah ki barni naje na duba shi tace kin san dai bazan mu tunkari abbanki da wannan maganar ba ta sake sasaauta murya ummi har naje na dawo ba tare da ya sani ba tare da halima abdullahi ta raka ni hakan yayi kyau sai ki shirya ku tafi nan da nan ta shirya cikin wani leshi madan karen kyau gashi ta tsara kwalliya mai daukar hankali tayi kyau sosai abinka da kyakywa ta sake tsokano shi ita da kanta da ta duba madubi sai data firgita gashi kayn fitet ne ta dauko mayafi ta yafa tana fitowa umminta tace baza ki tafi a haka ba ita kanta kyaun rufaida ya firgita ta duk dacewa kamar su daya sai dai ta fita haske.ta koma daki ta kuma duba madubi ta tabbatar umminta tayi gaskiya kamar ta cire sai wata zuciyar taba ta shawarar dora after dress akan kayan ta after dress mai ratsn ja gashi jan less ne ta saka zaka zata wata yar india ce tafito tace ummi haka yayi?
.
tace ko kefa to je ki daki ki dauko min wannan karamar jakata ta dauko ta mika mata ta dauko kudi naira dubu uku tace ki sai masa kayan dubiya tace mai zan sai masa? tace abinda kika gaya dace ta rataya jakarta tace sai na dawo habiba tace af! kin kira habiba a wayar kin ji tana nan?
*** DAN ALHAJI 6 ***
.
Na manta bari in kira ta ta dauko wayar ta a cikin jakarta ta kira halima sau uku shiru wayr taki shiga ummi kin ji wayar taki shiga ina ga maysalar bata da cajine bari naje gidan suna gani tace to dai dan bata anan ki dawo kar ki tafi ke kadai kuma ku kula da kanku ku tsare kan ku ku kila da mutuncin ku ku dawo da wuri kafin ya dawo tana zuwa ta tarar gidan su halima a rufe jikinta yayi sanyi tasan uma idan ta koma gida shikennan babu tafiya gashi ta matsu taga yadda jikin nasa yake da dade tana tunani ko ta koma gida ummi baza ta barta ta tafi ita kadai ba uma gashi batsan ranar dawowar su halima daga garinsu ba indai kika ga sun kulle gidan gaba daya to sun fita gari ta kuma dada sanar da ita sun kusa tafiya gashi bata da wata kawa da umminta ta yarda da ita bare ta dauke ta,
.
sai kawai ta ynke shawarar tayi tafiyarta tana isa bakin kasuwa tayi masa siyayya ta kira sulainman tayi masa kwatancen inda take akayi sa'a lokacin suna gidan safuwan da suka tsara yadda za suyi inta zo a zuciyar sa sai ya ji tausayinta amma ina shedan ya rinja yeshi wani hadaddan lemon kwali suka bude suka zuba wasu kwayoyi masu sa maye suka rufe suka mayar firij ya sami wani shinfideden bargo ya lullubu ya kwanta a kan gado ba wanda zai ce ba mara lafiya bene.ayya Allah sarki rufaida,bai fi awa daya ba ta dawo hayyacinta a gigice ta tashi ta ganta akan gadon sa wata kara ta saka marar misaltuwa hade da wasu zazzafan hawaye suka ringa fitowa mata tayi zinbir ta mike ta dau kayanta tasa shi kuma ya zuba mata ido yana kallon kyakykyawan surar da Allah yayi mata a cikin mata da banbanci duk iya neman mata irn nasa bai taba gamuwa da irin taba ko tima bata kama kafartaba ya kudiri niyyar kota halin kaka sai ya mallaketa a matsayin matarsa cikin rudani ta juya ta kalle shi tasana mara misaltuwa da tsiya wacce baza dada son komai kama dashi ba tace
.
KA CUCE NI!!! KA YAUDARENII!!! KA BATA MIN RAYUWA!!!! KA CUCI IYAYENA!! KA DAU ALHAKINSU!! KA ZALINCESU!!! ALLAH YA ISA!!
.
kukan da keyi ya sake tsanan ta tacu gaba da cewa sun dauki shekaru da dama suna tarbiya ta amma sa'a daya ta tashi a banza cikin kuncin zucita tace Allah ya isa! tsakanina da kai yadda ka sani cikin takaicin rayuwa in Allah ya yarda kai ma haka zaka kare da sari ta fice daga dakin ta nufi hanyar fita waje
duk tausayinta ya dame shi da na sanin da bata da amfani tashi yayi ya ringa zagaya dakin ya rasa abinda yake masa dadi can hangin jakarta da hanzari ya dauka ya bita ya kwalla mata kira amma ina ko kallo bai isheta ba motarsa ya hau ya bita har titi ya tsaya dai dai inda ta tsaya yace ga jakarki ba tare da kallon shiba tasa hannu ta fisge tayi gaba bitaa yayi da kallo yana cewa ta shiga ya kaita gida yana kallo ta tayi wata mota tayi tafiyarta ta bar tsaye sai ga sulainman nan suka tyaya suna tambayar sa ya DAN ALHAJI da fatan ka rubuce ka wanke ko kallon su baiyi ba yaja motarsa ya barsu a nan tana shiga gida ta tarar umminta na bacci lallabawa tayi ta shiga bandaki ta gama abinda zatayi tata gyara fuskarta sannan ta koma dakin ummi tayi sallama tace ta dawo tace yaya jikin nasa tace da sauki ummi tace ninaji a jikina dk ba dadi shine na kwanta ina kuma halima?
.
tace ta wuce gida ita sauri take wai zasu tafi garin su yau kwana da kwanaki tana cikin bacin rai ta kasa gayawa kowa ta bar abin a zuciyarta yana damuntako baccin arziki batayi ga wani sauyi da take ji a jikinta ta kara razana.kullum sai yayi mata waya data gaji ta babbalata ta watsar duk wani abu da tasan inta kalle shi zata tuna da shi ta rabu dashi kullum yazo sau hudu ko biyar taki fita duk umminta na lura da hakan tace wai ke me yaka hakan to?
.
da taga hakan gudun kar ta takura mata sai taji abinda yake faruwa idan yazo sai tayi kamar ta fita sai ta shige wani daki a sororon gidan ta kifa kanta tana kuka bata zata umminta ta ganta bata shigo daukar itace ba karamin faduwar gaba tayi ba tace me kike yi anan? kuma kukan me kike yi? zaki gayamin abinda yake faruwa ko sai ranki ya baci na lura lura da ke tun ranar dakikaa je duba yaronan kike cikin kunci to me ke faruwa in baki gaya min ba wazaki gayawa? ko dole akace ki saurareshi? ai dama ke kika ce kina sonsa cikin shekar kuka tace ummi ba komai ji nayi bana son sa akwai wani abu haka kawai baka ce baka son mutum sai da dalili shike nan dga yau idan yazo sai kin boye a nan nba kawai kice bakya nan rufaida inkin huce inda rabo sai ku shirya tashi ki shiga gida ta bita da kallo tana murmushi a zuciyarta inadai fada ne irin na saurayi da budurwa nawa akayi aka shirya ta dauki itacen ta tashiga gida itama kawana biyu a tsakanin haka laulayi ya bayyana tashin zuciya da tsirtar da yawu amai da sauran sauransu Rufaida ta fara hankalin habiba ya tashi data lura da halin da yar take ciki tace ke! gaya min gaskiyar abinda yake faruwa dake? yau rabonki da ganin al'adar ki wata nawa?
.
*** DAN ALHAJI 7 ***
.
Tayi shuru ta sake zare mata ido cikin fada tace zaki gaya min ko saina ci miki mutinci cikin raway murya tace wata biyu batasan lokacin data makureta ba tana cewa ni zaki bawa kunya duk irin tarbiyar da muke miki a banza ashe duk wannan abin da suke akan idon mallam nasiru cikin tsawa yace saketa aikin gama ya riga ya gama cikin wata mahaukaciyar tsawa ya sake cewa zaki sake ta ko sai kinyi kisan kai tana sakinta ta fadi a sume cikin gigita akayi asibiti da ita bayan an gama aune aune da dube dube da kuma bugun zuciya da suka gani suka kira mallam nasiru.suka tabbatar masa tana da ciki na wata biyu da kwana goma sannan matsalar duk sanda wani abu ya faru wanda zai fadar mata da gaba zata iya rasa tunaninta in dai ta razana suka sallameta suka bata magunguna a haka suka bar asibitin a sabule bayan sun je gida ne ta tambayita wanda yayi mata ciki bata boye musu komai ba a lokacin a lokacin habiba ta sha fada dan me ta bar ta taje buba wani saurayi?
.
to iyaye mata ayi hattara akan irin wannan tabargazar kobuba saurayi ko zuwa gidansu ko a gaiyace ki party koh gidan aboki,to dai yan mata ayi hattara iyaye musa ido akan shige da fitar yayan mu yan mata a guji karbar abuna shi kona ci a wajen samari,ayi hattara mutunci daya ne idan ya zube rayuwarki ta shiga ibtila'i dan Allah mu kula Allah ya kare mana har kukan dan kan daru YANCIN KU GIDAN MAZAJEN KU.
AMEEN!!!!}
.
gidan Alhaji muazzam ya nufa yayi sa'a ya same shi aja yo masa sallama da shi ba dadewa yana tsaye wanda ya aiki yafito yace wai waye yace kace bako ne yake son ganinsa ya ske dawowa yace an ce ka shigo wani falon alfarma aka shiga da shi yana shiga ya tabbatar alhaji ba karamin mai kudi bane amma hakan bai sa zuciyarsa ta karaya yaji tsoron fadin abin da yake tafe dashi ba suka gaisa yace na zone na sanar da kai cewa dan ka safuwan ya yiwa ya ta fade saboda haka har ciki ya shiga zirbir Alhaji ya mike yace au ta haka kuma ka bullo? kana ganin hakan zai sa na yarda ya aure ta? to tsaya na gaya maka har yanzu ina nan kan bakata ka nemi wannda ya yiwa yarka ciki tun da wuri kuna sakin yayan ku kamar awaki sai sun dauko muku abin kunya ku rasa yadda zakuyi ku ringa kame kame idan kun sami warsali sai ku lika masa kawai in so kake a taimaka maka a baka kudin dazaka zubar sa a baki ba sai kazo kana soki burutsu ba duk wannan maganganun nasu kamar da almara da yake malam nasiru yana tsaye jikinsa sai tsuma yake dan tsananin bacin zuciya tashi yayi ya dauko kudi masu yawan gaske dan a kalla za suyi dubu dari biyar ya mika wa malam nasiru ya fisge ya yayyaga su ya watsa wa Alhaji yace karya kake kace zaka siyi mutuncin yata baka da kudin da zaka girgizani.
.
"hmmm toh mata masu kwadayi a kiyaye,cikin zafin nama yayi kan malam nasiru ya ce kan har ka isa ka zo har gidana kaci min mutunci hajiya bilki data shigo taga Allah yayi kan mallam nasiru ta shiga tsakanin su da sauri shi ko nasiru ko zagesu Alhaji yaci gaba da fada sai naga wanda ya tsaya maka a garin nan ko wayene wallahi baka isa ka jada niba kawai talauchi yana damunka zaka zo kayiwa mutane hauka ga kanan babban mahaukaci kana ganin yata ko ta rasa wanda zata aura zata auri dan kane? zan bari ta saurareshi ne kaine baka isa da danka ba amma nina isa da yata banza shashasha banZa, ya ringafizgewa yana ki bar nina nuna masa matsayina ta juya tace da mallam nasiru dan Allhah fita kayi tafiyarka kayi hakuri ya fita yana cwa da kin bar shi ya dau raina tunda bani da galihu ta zaunar da shi tace kaga abinda nake gaya maka ka barshi ya auri wacce yake so kaga yanzu ya jawowa mutane abim kunya yace au ke kin yarda shi yayi mata?
.
kunya kuma su suka ji tunda ba a jikin sa cikin yake ba duk abinda namiji yayi adone kuma sai na dau mataki a kansa zai sa yazo har gida yaci mutunci na sai na sa an daure shi ya raina kansa hajiya bilki tace haba yallabai a cuce shi a hana shi kuka kasan fa duk abinda ya fada gaskiya ne kawai dan bashi da kudi a danne masa hakki, a fussace yace ke tunda kina da kudi basai ki tsaya masa ba wannan ai maganar banza ce kina ganin abinda mutum nan yayi min ya nuna kudi a kaaa an yaya gasu gutsi gutsi baza su taba moruwaba tace ai bai rama ba na riga na cuceshu ya harzuka yace walllahi ran ki zai baci saboda tashi ki ban waje ya sake daka mata tsawa ta mike ta fice ya zauna yana ta kunfar baki yana hada gumi yana ganin tunda yake bawanda ya taba ci masa mutunci irin wannan zaune suke a majalisa suna ta shewa duniya tayi musu dadi mallam nasiru ya hango dan marakin zuciyarsa ta kuma yi masa zafi tafiya yake kamar zai fadi har ya karaso kusa da inda suke ya tsaya jikin wata bishiya da aka sare cikin daga murya yace kai safuwan wainwayo yayi da sauri kiran da yaji kamar daga sama ganin malam nasiru yayi a tsaye yana ganinsa ya taso cikin faduwar gaba haka kawai yaji bugun zuciyarsa yana karuwa.
** DAN ALHAJI 8**
.
Yana karasowa inda yake ya sunkuya zai gaishe shi yace dakata daga wajen ubanka nake naje dan mu sami masahaal akan abinda kayiwa rufaida har ciki ya samu shine ya nuna min bashi da mutunci kafin ya sake wata magana safuwan yace ya za'ayi kaje wajen sa o shi yayi mata cikin?? malam nasiru yace rashin kunya zakayi min har kana da bakin fadamin wannan maganar yace an fada maka kai kake niyyar zagin ubana to wallahi kar ka yarda ka zagar min uba yace idan na zage shi me zakayi? yace rama masa zanyi uba bai fi U.
.
kafin ya karasa mallam nasiru ya kai masa mari fau!! yan majalisan ganin haka suka taso da sauri shi ko safuwan ganin haka yana juyowa shima ya kai masa wani wawan mari anan da nan mallam nasiru yayi sauri ya kauce kaucewar da zaiyi yaci tuntube ya fada kan wata reshen bishiya yana fadowa kansa ya fashe kafin wani lokaci mutane sun taru kowa na fadin albarkacin bakinsa,wasu nace wa shi ya tura shi wasu nacewa tuntube duk yabi ya rude ganin halin da malam nasiru yake ciki nunfashin sa sama sama wasu na cewa ya mutu wasu na cewa da ransa aka dauke shi akayi asibiti duk wanan abinda yake faruwa akan idon iyatu a kusa da gidan su rufaida take aiki gidan wani wai Alhaji kabiru tana gani malam nasiru ta dauka fa da sauri ta nufi gidan sa tana shiga ta tarar da habiba zaune tana bawa kamal nono ta labarta mata batasan lokacin da ta ajiye kamal din ba ta dauki mayafi bata tsaya daukarsa ba tayi waje da gudu ba takalmi rufaida ta rufo mata baya suka bat iyatu a tsaye yaro an dagwar dashi yaga fitar yan gidan su ya daga ido yaga baisan iyatu ba ya barke da kuka tasa hannu ta dauke shi ta ringa rarrashin sa yaro yaki bi sutayi da shi suna isa wajen da abin ya faru suna kokarin tsallaka titi lokaci da ake kokarin sa shi a mota jini yana tsituwa habiba ba tare data duba titi ba ta tsallaka mai mota yana tayi mata horn rufaida tace wa ummi ga wata katuwar mota nan tsaya ta wuce ina motar nan tazo tabi ta kanta take ko shurawa batayi ba.tab!
.
Ana wata ga wata ga kuma wata Allah ya sawwaka dai,ana barin wajen da aka sa mallam nasiru a mota kallo ya koma titi gawar habiba kwance ita ko rufaida tunda ta kwallara wata uwar kara ta nufi wata hanya (abinda likita ya fadi ya tabbata) mutane suna ta habiba ba wanda ya kula da ita iyatu na karasawa da kamal a hannunta taga abinda ya faru jikinta ma rawa yake tana ta kuka tana cewa itace matar mutumin nan dya fada kan bishiya mutane sunyi jugun jugum sai ga motar data dauki malam nasiru ta nufi gidansa dashi kafin su karasa asibiti ya cika a ranar mutane unguwar da dukkan wanda abin ya faru a idonsu koya jiyo labari ba wanda bayi kuka ba alhaji kabiru ne komai ke hannunsa banda kukkan ba abinda yake shi da matarsa sun shaku sosai anyi zaman mutunci aka sitirtasu aka sallace su aka kai su makwancinsu bayan dowowarsu ne kowa ya nutsu aka tuna ba'a ga rufaida ba mutane da yawa sunce tare suke lokacinda abin ya faru iyatu ce ta bada shaidan hakan kmal sai kuka ya ke yana dube dube mutane yana neman uwarsa gashi ba'a ga yayarsa ba karamin tada hankali mutane yake ba alhaji kabiru ne ya dauke shinyayi waje dashi yana rarrashinsa har bacci ya daukesa jikinsa yayi zafi sosai saboda kukan daya dade yanayi Allahu Akbar! Alllah ya jikan malam nasiru da malama habiba
.
Gashi ba wanda inda yan uwasa suke ba irin bakin cikin dasu alhaji kabiru da abokan aikin sa ba suyi ba rufaida ko jin wanda ya ga mai kama da ita ba'ayi ba mutane unguwa sunce sai sun dauki mataki akan safuwan wasu nace wa abar shi da Allah tunda yanzu ina mallam nasiru da mai dakinsu da yar tasu da abin ya faru saboda ita wannan kawa ibtila'i ne daga Allah yan sanda ko tunda abin ya faru suka tsar keyar safuwan Alhaji duk ya rame yayi baki hajiya bilki ko tunda taji abin daya faru da iyayen rufaida bata cikin hayyacinta tana kwance a asibiti jininta ya hau sosai safuwan ko in ba kyakyawan sani kaya masa ba baza ka gane shi ba yan sanda sun hana ganin shi ko Alhaji ma sau daya ya ganshi.kamal har ya fara sabawa da mutanen gidan alhaji kabiru ba irin sabon da basu yi da Alhaji ba barcine kawai yake rabasu kullum zai tafi kasuwa sai da dabara suke rabuwa wani lokacin ma boye shi akeyi sai nono ko dama ba'a kara bashi ba tunda dama ya isa yaye gashi Allah ya jarrabi Alhaji kabiru da hajiya naja son sa Allah ne ya basu dama basu taba haifuwaba kusan shekara ashirin da aure Allah bai basu haifuwa ba yaro yasake wani girma da wayo Allahji muazzamu duk wa babba wanda yasan mai fada ajine ba wanda bai gani ba akan a bashi safuwan hakan ta gagara saboda duk wani abin da yake makama da shi gaba da gabanta Alhaji kabiru yafi shi idon ko batun kudi ne yayi masa fintinkau ba yadda baiyi ba akan suyi masahalaha da alhaji kabiru abin yagagara yaune ranar zuwa kotu duk wani wanda abin ya shafa ba wanda bai halattaba yan kallo ko kamar kasa ba wanda ke jin tausayin safuwan ko mahifinsa kusan mutane unguwar su murna suke suna cewa ai dama gaba da gabanta duk iskancin da yaron kayi ubansa baya kwabarsa.
** DAN ALHAJI 9**
== == == karshe == == ==
.
Komai yayi daidai dan tunda abin ya faru ko kare a cikin unguwar ba wanda yaje masa jaje hakan yan uwansa wannan abin ba karamin tayarwa da alhaji muaZzam hankali yayi ba duk sai yaji ya tsanni halayensa yasan shi ya jawa kansa halinsa na wulakanta talakawa ga irinta nan tun daga yanzu hatta yan uwansa sun tsane shi lokaci daya ya gane kuskuransa ga kuma dana sani da yake tayi akan malam nasiru ga shi cikin lokaci kankani ya bar masa duniya gashi ya rataya akan dansa kai! duniya abin tsoro ce daga wannan lokacin yasan lallai ya yarda kaki naka duniya taso shi kaso shi duniya taki shi gashi dai ta faru akan Alhaji muaZzamu ya gani tun kafin aje ko ina duk kowa ya natsu ana sauraron fitowar mai shari'ah waje ya cika makil can tsayin wasu yan mintuna sai ga shi mai shari'a ya fito kowa ya tashi ana fadin kotu ya zauna sannan kowa ya zauna waje yayi tsit ba wanda ya sake ko tari sai can ga wani mai sayar da doya ya doso get din kotun ganin mai gadin baya wajen ya zagaya ya hango mutane da yake babbar kotu ce wajen kotun biyar ce ya fito yana a sayi doya wani mai tsaron kotu number 2 yace ka bar wajen nan ba wajen talla bane mai shari'a ya shigo banza yayi masa yaci gaba da fadin a sayi doya mai shari'a ya daka tsawa yace waye mai mana tallan doya anan wai?
.
yan sanda sukayi kansa da yake mai taurin kai ne sai ya zagaya yaci gaba da tallansa mai shari'a yace aje a shigo da mai doyar nan b bata lokaci suka cika aikin su kafin su shigo dashi ya tsaya zai yimusu taurin kai ya sha kulki kotu mao shari'a yace kai na ce maka nan wajen talla ne kuma ba anje an yi maka magana ba? saboda kai dan taurin kai ne kaki maza ku ajeshi sata daya ya durkusa yace dan Allah yallabai kayi hakuri yace an kara maka sati biyu ya sake cewa wallahi talla na fito ban barwa iyalina na komai ba yace sati uku shigo ku tafi dashi ya tsaya ya sake cewa dan Allah ayi hakuri alkali yasake cewa idan baka shige ka tafi ba in ka sake magana sati hudu ya sake cewa in kun kulleni yayana da matata zasu shiga damuwa alkali ya sake cewa kar ka kara magana sai ko cewa yayi tunda ka dauke ni ta karkarewa yai ya ringa cewa asai doya! asai doya! asai doya! ba wanda abun bai bawa dariya ba amma ba hali mai shari a ya mike yana cewa ya shiga cember aka yi gaba da mai doya a na ganin mai shari a ya tashi mutane suka shiga dariya har da tsuntsire wa shi kansa alkalin da ya shiga camber fadawa yayi kan kujera yana dariyar mai doya yace lallai wannan dan iskan kauyene bayan komai ya lafa an bar kowa yayi dariyarsa ya gyatsr mai shari a ya sake dawowa yaje yasa akayi tsit aka kira wata shari a sannan sai tasu safuwan lauyan malam nasiru mai suna mustafa dauda sai mai kare safuwan shine ya mike mai suna bala ali aka shigo da safuwan alhaji muazzam rudewa yayi ganin muguwar ramar da dansa yayi bashi ba har sauran mutane da suka san shi sun san yana cikin damuwa mai tsanani mai sharia yace ina safuwan?
.
yace gani yace kotu tana tuhumar ka akan silar mutuwar mallam nasiru da batan yarsa wacce kayiwa fyade kayi mata ciki" yayi shuru mai sharia yace kotu tana sauraron ka yace a gaskiya nasan ni nayiwa rufaida fyade a sakamon yaudararata da abokina sulainman yayi yaje gidansu yace bani da lafiya duk dai yasan maganganun daya gaya mata ta yarda da hakan ta amince akan inta sami lokaci zata neme shi a waya ya dauketa ya kai ta ta dubani muna zaune ta bugo masa waya ta sanar da shi inda zasu hadu ni kuma naji haka ni da mubarshir muka sami lemon kwalba muka sa kwayoyi muka bata shine nayi abinda zanyi da ita ba tare da sanin taba ban sani ba ko a lokacin cikin ya shiga lauyan mallam nasiru ya mike ya roki ai maaa uzuri yayi wa safuwan sasu tambayoyi aka basa lauya mustafa yace mallam safuwan ina ganin zaka fi kowa sani ina ma ba naka bane kai kasan yadda ka same ta? yace a gaskiya a cikakkiyar budurwa na same ta bata taba harka da wani ba mai sharia ya dakatar dasu yayi ya dan rubuce rubucensa yace an gama da wannan yace sai tuhuma ta biyu maibya faru tsakanin ka da mallam nasiru? yace tsakanina da mallam nasiru yazo ya same ni a majalisa mu muna zaune muna hira law mustafa ya sake mikewa yace da kai da wada wa? lauyan safuwan ya mike yace ai wannan tambayar bata cancanci wannan lokaci ba law mustafa yace ai ko dole ne ya lissafo wadanda suke wajen dan dukkanin su muna bukatansu anna law bala ali yace ba lalle ne yasan su gaba daya ba law mustafa yace akan me bazai san suba bayan kullum tare suke law bala yace ina rokon kotu ta duba wannan tambayar bazai yiyu ya iya lissafo suba saboda yana cikin rudani law mustafa yace ba wanda zai manta tunda tare suke shedancinsu da abokin tsiya dana arziki ba'a nemansu mai shari'a ya buga abin hannunsa yace kotu tana san safuwan ya lissafo abokansa dake wajen kuma kotu nasan su bayyana nan da mako biyu safuwan ya fara lissafosu sulainman,auwal,musbahu,nura,ali,da mubarshir habib nurandi,hashim,muhannai,auwal,musa da sunusi nasidi kai harta ni abba sanda ya kirani yace suke wajen.
.
ci gaba da yadda ku kayi da mallam nasiru bayan ya kirawo ni na durkusa zan gaisheshi yace bashi ne ya kawo shi ba daga wajen ubana yake ya sanar da shi abinda na yiwa yarsa amma da yake bashi da mutunci sai ya ci mutuncinsa nace shi yayi maka? ai bashi yayi mata fyaden ba gurina zakazo kuma wallahi har ka yarda ka zagan min uba shi ne ya kai min mariya mare ni na juya zan rama........
safuwan yasa kuka mai karfi sannan yaci gaba da cewa ina kai masa mari ya kauce yaci da baka ya fada kan bishiya kan sa ya fashe muka dauke shi mukayi asibiti da shi kafin mu karasa ya mutu kukan da yake ya sake tsananta ta cikin shashshekar kuka yace wallahi bani na kashe shi ba alkali yace ya isa sai kuma tuhuma ta uku ina rufaida? ya shiga yin kuka mai tsanani marar misaltuwa yace wallahi bani da masaniyar batan ta kuma har ga Allah nima inaa bakin cikin rashin ganinta kuma ina addu'ar Allah yasa a gan ta dan ni har yanzu son tada kaunar ta suna nan a dashe a zuciyata duk wannan abu da ya faru Allah yayi shi ya faru kuma nine sila mai shati'a yace na daga shari'a zuwa ashirin da uku 23 july a koma dashi gidan maza da sauri ya dafe kansa da hannunu biyu lokaci guda ya ji wani bugun zuciya kafin yan sanda su karaso inda yake har ya fadi kasa babu wata gaba da take motsi a jikinsa lokaci daya alhaji shima ya kwalla wata kara shima ya fadi kasa tsawar ce ta gigitani biron dake hannuna ya fafi kasa.ALHAMDULLILAH
shin za'a ga rufaida kuwa? idan an ganta a wani hali za'a sameta?, shin ya hukunci safuwan zai kasance?
ku saurareni a littafi na biyu da kuma littafina mai fitowa nan gaba mai suna..........
,
GODIYA da yabo sun tabbata ga Allah subahanahu wata ala mai kowa mai komai tsira da aminci su tabbata ga annabi muhammad (s.a.w) da alayen sa da sahabbansa sa masu girma da daraja.
.
KARSHEM DAN ALHAJI LITTAFI NA 1 SAI KARASHEN ZUWA MASU MAKONNI IN MAI DUKKA YA KAIMU
.
Jinjina ga marubucin wannan littafi M. A Gana, Allah yakara basira..
.
sai ni kuma jabeer rabi.u idris dana kawo muku ke cewa ku huta lafiya
whatsapp 07034488635..........
Download Ďan Alhaji Littafi Na Daya Complete
0 Comments
Thank you for this comment