*🌚GANTALALLIYA🌚*
*WRITTEN📝*
*BY*
*DEEE*❤
*STANDARD WRITER'S ASSOCIATION*
True life story.
1-5
Wata zukek'iyar bakar mota kirar benz E350 na hango ta karyo kwana, wani dankareren gida ta tsaya, yana matsa horn mai gadi yataho da gudu ya bude gate, sannu da zuwa yakeyimas bai tsaya ya sauraresa ba ya wuce inda ake parking motoci.....
Maigadin yana rufe kofar yabi bayan motar da sauri, kan ya isa har mutumin dake cikin motar ya fito, gaishesa yayi tare da yimasa sannu da zuwa.....
"Yawwa sannu sabo, madam tana ciki ne ko tafita" yake tambayar mai gadin, daidai lokacin dayake bude kofar bayan motar yana dauko jakar sa.
"Ai ranka shi dade baka dade da fita ba wata mata tazo naga sun fita tare, kuma har yanzu basu dawo......." daga mishi hannu yayi rai abace yace "shikenan nagode zaka iya tafiya"
Yana shiga cikin gidan, tundaga bakin kofa yafara karo da shirgi kalakala, tsaki yayi ya wuce dakinsa, wanda yasameshi a yanda ya fita ya barshi, wani takaici ne ya rufeshi, kamar yayi kuka, ga yunwa daya kwaso.
Da kansa ya kyara dakin sannan ya fito kitchen domin yasamu abinda zaisa a bakinsa. Yana shiga idonsa ya kai kan gas cooker din, tayi dak'al dak'al, dagani tunda aka siyeta bata taba ganin ruwa ba, haka ya daure ya dauko wata yar karamar tukunya, itama seda yadaurayeta sannan ya dora ruwa, wanda baima san abinda zae dafa ba.
Fridge din ajiye kayan miya ya bude don yaga ko zae samu ragowar miya sai ya dafa farar shinkafa, yana budewa ya rufe da sauri, dan tsabar wani wari daya doshi hancinsa, nan take yaji amai ya taho mai, da gudu ya kashe wutar gas din yayi waje da sauri....
Tun a kofar kitchen din yafara sakin aman, ga wani jiri dayake dibarshi, haka yayi yagama, da kyar ya gyara wajen yayi dakinsa, toilet ya fada ya sakarwa kansa shower, sannan yasamu ya dan ji dadi.
Yana fitowa ya suri key din mota yayi waje, ba motar daya dawo da ita ya hauba yanzu, wata jar mota ya dauko an lullubeta da bakin tinted, yana fita bai tsaya a ko ina ba sai a chicken castle....
Anan yasamu yaci sakwara da miyar agushi, ci yake kawai amma zuciyarsa babu dadi. Yana gamawa ya koma gida, misalin karfe 6 na yamma, amma bata dawo gidan ba, sai yayi tunanin ya kirata a waya sai kuma ya fasa.
Kwance yake akan gadonsa kamar mai bacci, amma kuma ba baccin yakeyiba illa tunane tunane da suka shige mishi kai.
Ba ita tadawo gidan ba sai goma saura yan muntina....
Buzubuzu ta shigo gidan, daganin tafiyarta kasan babu nutsuwa atare da ita, gashi sai taunar chew gum take kai kace ba mace ba, bama wannan ba, shigar da tayi ma kadai ya isa kasan wacece *BINTU MATAR SADIQ.*
Dakinta ta wuce tayi wurgi da jakar hannunta tana "washhh!!! Nagaji wallahi" kayan jikinta ta cire ta wurgarsu a tsakiyar dakin,ta dauko wata doguwar rigar bacci,wacce inbanda tsami babu abinda takeyi, amma haka ta tafka abinta ko ajikinta...
Kan hargitsetsen gadonta ta hau ta kwanta abinta, wayarta ta dauko takira wata kawarta, saidai bata dauka ba, haka ta gaji ta ajiye ta ja bargo ta shige....
Shikuma tunda yaji shigowarta yakasa daurewa seda ya tashi ya biyota har dakin nata. A fusace ya shiga kamar wanda zai daketa sai dai yana zuwa yaji gabansa yayi wani irin mugun faduwa,a sanyaye ya karasa gabanta..
"Haba bintu! Ina kika tafi kika kai dare haka batare da kin sanar dani ba" shiru tayi kamar ba da ita yake ba, seda yasake magana ta dago a fusace "haba malam kafa takura min nidai wallahi, nadawo ma ko sannu da zuwa baka min ba sai tambayar daga ina nake, to unguwa naje koda magana ne? Girgiza mata kai kawai yayi kafin yace "Allah ya baki hakuri" tsaki taja "aikin banza kawai, nikatashi kafitar min adaki bacci nakeji" bata jira cewarsa ba taja bargon ta koma.
Salalo salalo yatashi yafita adakin, dakinsa yakoma ya kwanta yana tunanin, wai maiyasa bintu take mishi kwarjini ne? Meyasa idan yayi yunkurin yimata fada yake kasawa ne? Meyasa kuma yake masifar sonta? Da wannan tunanin har bacci ya kwashesa amma bai samu amsar tambayarsa ba....
To nima dai na matsu nasan wannan dalili😜
Written📝
By
*DEEE*❤
08177892239
*🌚GANTALALLIYA🌚*
*WRITTEN*📝
*BY*
*DEEE*💘
*OMG!!! FROM WHERE I AM GOING TO START SELF?😍 AM OUT OF WORDS😷 FAN'S I FEEL LIKE LAUGHING😃 AND CRYING😭 AT THESAME TIME❣ BABU ABINDA ZANCE DAKU SAI GODIYA, NAGODE ALLAH YA BAR ZUMUNCI YA BAR SODA KAUNA, KUMA INA MUKU FATAN ALKAIRI NANKIN BANINKI YANDA KUKE MIN*❤❤❤
*Maman Nawal! wannan page din na sadaukar miki da shi😘 nagode da kulawarki, so da kaunarki agareni, Allah ya barmana ke*❤
True life story.
5-10
Kirayekirayen sallar asuba ne ya tasheshi, toilet ya nufa ya doro alwala ya fito yazura farar jallabiyarsa ya nufi masallaci...
Ita ko gwanar ko motsawa batayi ba, tayi d'ai d'ai, sai sharar munshari takeyi. Seda yadawo ya biya dakin nata, a hankali ya bude kofar, a hankali ya soma kiran sunanta "bintu!bintu kitashi kiyi sallah, inyaso sai ki koma baccin" cikin masifa ta tashi "ohh ni bintu Allah ya hada ni da jarababben miji, kai kenan baka so kaga ina hutawa seka zo ka takuramin, ina ruwanka da sallah ta" daurewa yayi yace "haba bintu, kefa musulma ce, yakamata ki dinga kiyaye addininki, abinda kikeyi kwatakwata bai kamata ba" Allahu akhbar!! Kace yau yan wa'azin ne suka tashi, to idan wa'azi kakeji katafi kayiwa wayanda suke bukata, nikam bana so ehen" zaisake magana tace "kaga malam, kai bakayi taka sallar ba? Kwarai kuwa ninayi sallah" to kaje Allah ya bada lada, nikam sena tashi zanyi bacci bai isheni ba" tana gama fada tasake komawa ta kwanta.....
Cikin takaici yabar dakin, a zuciyarsa kuma yana fadin Allah ya shiryi bintu.
Bai dade da fita daga dakinba wayarta tayi kara, da sauri ta mike tana shewa ta dauka "uwar dakina ya akayi, nakiraki kafin na kwanta jiya baki dauka ba, lfy? Hmm kedai bari, wannan dan jarabar ne, ina dawowa ya tsareni wai senayi masa girki" da sauri bintu ta mike "wai kina nufin har yanzu baki fara juya shi ba" tabe baki saratu tayi, wato kawar bintu" bari kedai bintu, ai narasa wanna irin mutum ne, amma karki damu zamuyi maganinsa kwannan nan"
"Yazama dole ma muyi maganinsa, yau zanje wajen hajiyarmu, daga nan kuma zan leka gidan suna kinsan nafada miki yar wata makociyar mu ta haihu, idan nadawo zanzo har gida" to ba damuwa.... Sukayi sallama
Tashi tayi ta shiga kazamin toilet dinta, fuskarta kawai ta wanke da ruwa, sai bakinta data kuskure tafito, kitchen ta nufa, dan rabonta da abinci tun na rana, ruwan tea ta tafasa ta soya kwai na iya cikinta, tafito ta nufi kan dinning tana ci...
Shima sadiq daya koma dakinsa wanka yayi yayi shirin tafiya office.
A kan dinning yasameta baiyi niyyar cemata komai ba,dan yau tunda ya tashi yake jin haushinta, dan babu abinda yafi damunsa illa rashin sonyi sallarta, zai bude kofa kenan tace "sadiq ina son magana da kai" tsayawa yayi a inda yake batare da ya juyo ya kalleta ba yace "ina jinki sauri nake zan fita" seda ta kurbi ruwan tea tace "mukullin motar ka nakeso zaka bani, yau da ita nakeson fita"
Jiyayi kamar ta buga mishi guduma akansa,gaskiya bintu ta rainashi dayawa, yakamata yafara nuna jarumtakarsa akanta, ko zata shiga taitayinta, dakewa yayi yaci magani "ai ba daga gidanku kika zo da ita ba" da sauri ta mike ta kalleshi cike da mamaki "Sadiq nikake fadawa haka" juyowa yayi ya nunata da yatsa yace "angaya miki hakan, bintu bari kiji nafada miki, iskancinki yafara isata, bakida aiki sai gantali, babu ranar da zata fito ta koma ga ubangijinta baki fita ba, bamakidamu da tambayata ba, kuma sai sanda kika ga damar dawowa, to wallahi yau karna sake nadawo gidan nan naga bakya nan, k'azamar banza kawai shaaa shaaa shaaa" yafita ya barta a wajen, bintu kuwa mutuwar tsaye tayi, duk bala'in ta kasa cewa komai tayi, dan dama bokan ta yace duk sanda sadiq zaiyi mata irin wannan hargagin, karta sake ta tanka mishi, dan komai zai iya faruwa...
Takaici ne ya rufeta takasa karasa breakfast din da takeyi, seda ta tabbatar ya fita daga gidan tace "aiko kayi kadan ka hanani fita wallahi, kuma zanyi maganinka ne"
Dakinta ta wuce, cikin sauri tashiga wanka, nan da nan ta fito,komai bata shafa ba ta zura doguwar rigar atamfa, ko d'an kwali bata daura ba ta yafa kyale kawai, ta suri key din mota tayi waje...
Gudu kawai take zabgawa a titin kamar zata tashi sama, aiko batayi aune ba ta bugawa wani mai keke napep, amma cikin icon Allah baiyi komae ba, illa bomber motar ta daya sauka, aiko tsayawa tayi tafito tana ta dureduren ashar, shima mai napep din futowa yayi ya duba bayan kekensa yaga ba abinda tayi yace
"Allah ya taimakeki,wlh da sai kin biya ni" wani ashar din bintu tasake k'undumawa, tacire mayafin kanta taci dammara "wallahi baka isaba sai ka biyani motata, dan iskanci sai kuzo Ku shiga gaban mutum, wlh bazan dau asaraba. Mutane aka cika sai kallonta ake tana ta zagezage, hakuri ake bata amma sam tace bazata hakura ba,alhalin kuma itace mara gaskiya, reader's kuji karfin hali fa.😆
Wani mutumi ne yaga ana ta hayaniya, yayi parking aka bashi labarin abinda yake faruwa,yace mai napep din yatafi zai biya, yayi masa godiya yatafi.
Bakaniken sa yayiwa waya, cikin yan muntuna kuwa ya iso aka gyara mata motar, me makon tayi godiya secewa tayi "Allah ya taimakeku wlh da kunga bala 'i " tafigi mota tayi gaba. Mutane kuwa sai Allah waidai suke da irin su bintu.
Gidansu ta nufa, tabawa hajiyarta lbrn abinda Sadiq yayi mata yau da safe, da sauri hajiyan tace "shi Sadiq dinne yace haka" bintu ta gyada kai "to lallai gobe senayi miki hadin zuciyar kare, da kaina zan doka uban sammako naje barikin sojoji, idan sun yanka kare subani zuciyar, akwai wani hadi da wata aminiyata tafada min, indai akayisa, to sai yacce kikayi dashi, babu boka babu malam, kedai duk abinda zaice kiyi mishi shuru, gobe zanxo da kaina in kawo miki"
Rungumeta bintu tayi tace "yawwa hajiyata, shiyasa nakesonki, kina kawo wuta" suka kwashe da dariya, hira suka sha Sosai, sai yamma likis bintu tafara shirin tafiya
"Hajiya bari in tashi inje in shirya, zani gidan suna" Jakarta ta bude ta dauko dubu goma ta mikawa hajiya, ta amshe tana godiya, sukayi sallama...
Sadiq kuwa tunda yaje office kasa aikata komai yayi, tunani ne fal akansa, ga wata uwar rama dayayi, dayaga hakan bazai samu wata mafuta bane yasa ya tattara aikin ya ajiye ya nufi gidansu...
Yana shiga falon wani kamshin abinci mai dadi ya doshi hancinsa,da kyar ya hadiye yawun bakinsa, yayi sallama baki na rawa,jin shuru bawanda ya amsa mishi ne yasa yawuce kitchen kansa tsaye...
Khadija yatarar tana ta soya kayan miya da alama jolof zatayi, sallama yayi ta amsa da fara'arta "yaya Sadiq yau Kaine a gidan" murmushi yak'e yayi mata, dan gaba daya hankalinsa yana kan tukunyar dataketa faman juyawa "ehh nine nazo dije, tunda ke bazaki taba iya daukar kafa kizo inda muke ba"
"Yaya kasan halin ummana, sam bata son na matsa nan da cen, daga makaranta sai gida" tabe baki yayi"to yar umma, ina Umman taki take naketa sallama" yanzu ta shiga nan makota barka,amma tace bazata dade ba, kozaka zauna na kirawo maka ita? ah'ah ba sauri nake ba, bari na zauna a falo na jirata" ya fice, ita kuma ta cigaba da girkinta....
Zama yayi a falon yana kallo amma kamshin girkin khadija ya cika mishi ciki, jiyake kamar yaje yace tai sauri ta kawo mishi... Yana wannan tunanin kuwa sai gata dauke ta tere ta hado mishi, tunda ta shigo yake Allah Allah ta ajiye yafara ci....tun kafin ta gama ajiye masa ya karba ya ajiye agabansa, bude kulan yayi, jolof din couscous ne, yaji vegetables, da kaji..
Bai tsaya zubawa a plate ba yasa cokali yana ci,ciyake hannu baka hannu k'warya,dan yau ko tea din daya saba sha a office, bai samu yasha ba.
Khadija kuwa binsa take da kallo,sai a lokacin taga uwar ramar da yayi, tunani tafara yi a zuciyarta, meya ramar da shi haka? Kuma meyasa yake irin wannan cin abincin kamar wani dan kauye? Nan da nan taji tausayinsa yakamata "dagani akwai abinda yake damun yaya, koma meye Allah ka yaye masa" tafada a zuciyarta kafin tace "yaya sadiq kaci a hankali, idan bai isaba akwai wani" kunya ce ta kama shi,dan yama manta tana wajen, amma ya dake yace "cemiki akayi ina jin yunwa sosai ne? tashi ma kibani waje" dariya ce ta taho mata, ta tashi da gudu ta bar falon..
Seda ya cinye abincin tasss!!!! Yasha lemonsa mai sanyi, yakora da ruwan sanyi, wata nutsuwa ce ta saukar masa, take wani bacci mai dadi yayi awon gaba da shi.....
Bintu kuwa tana komawa gidan taga bai dawo ba,dadi ya kamata, batawani sakeyin wanka ba, kayan jikinta kawai ta sauya ta dau kwalliya tayi gidan suna....
*WRITTEN*📝
*BY*
*DEEE*💘
08177892239.
*🌚GANTALLIYA🌚*
*WRITTEN*📝
*BY*
*DEEE*💘
*⚜🇦rewa 🇼riters🇫orum⚜*
*• Follow us on facebook*~ _
www.facebook.com/Arewa-Writers-Forum-294302397727161/
*Dedicated to DEEE💘 NOVELS GROUP❤ THANK YOU FOR THE LOVE*😍
11-15
Baccinsa yakesha bilhaqqi, har aka fara kiran sallar magariba, bashida niyyar farkawa, khadija ce ta fito ta duba shi, tasameshi shameshame, rike baki tayi tana "ikon Allah, wannan ko lafiyarsa kuwa?
Sallamar ummansu ce ta dakatar da ita,bata amsa sallamar ba tace "yauwa Alhamdulillah! Umma zokiga abun mamaki" karasowa ummansu tayi tace "au wannan kuma yaushe yazo? Rike k'ugu tayi tabata labarin abinda yafaru tun zuwansa "umma nifa ina ganin akwai abinda yake damun yaya, kalla fa yanda ya rame, kamar wanda ya tashi daga cuta"
Umma batace komai ba, illa karewa sadiq kallo da tayi, tabbas itama ta hango akwai wani abu, amma batace komai ba, tashinsa tafarayi "sadiq! Sadiq! Tashi maza katafi masallaci gashi cen anata kiran sallah" da sauri ya mik'e " ah umma kin dawo, yaushe kika dawo bansani ba" yafada atare "kaje kayi sallah nace, inka dawo mayi magana" ta wuce dakinta khadija ma tabi bayanta...
Bayan yadawo daga masallacin ne, yasame su afalo,khadija ta dora kanta a cinyar umma sai zuba shagwaba takeyi, "yaya kadawo? sannu da zuwa, khadija tafada tana kallonshi, umma ma tunda ya shigo idonta akanshi yake "ehh dijen gala nadawo" kukan shagwaba tasaka "umma kinji yana cemin dijen gala koh" d'aga mishi dan yatsa tayi "au dama zuwa kayi kasamin y'a kuka kenan, batace maka bata son sunan nan bane" zama yayi yana fadin "tuba nake nadena"
Har k'asa ya tsugunna ya gaida mahaifiyarsa, bayan sungama gaisawa ne ya lura da irin kallon da umma kemasa, sunkuyar da kai ya dungayi yana jin kunya, dan yasan halin mahaifiyarsa akwai ta da lura, yanzu haka tagano akwai damuwa a tattare da shi.
Gyaran murya umma tayi tace "nikam sadiq rashin lafiya kayi ne haka" dammm! yaji gabanshi ya fadi "emmm aaamm mai kika gani umma?
"Gani nayi duk ka rame kamar wanda yatashi ajinya" sosa keya yayi yace "wallahi umma aiki ne yayi min yawa a office, ko abinci bana samun damar ci sosai, shiyasa na dan rame"
"Au kadan rame? Anya sadiq kana kallon madubi kuwa? Kaga uban dogon wuyan da ka ajiye kuwa, gawani uban gashin baki daka tara, abinda nasan kwata kwata da bakayi, to waima shin ita bintun tana ina take barinka kake futa baka ci abinci ba?
Yak'e yayi "umma ai bintu tana iya bakin k'okarinta taga naci abinci, nine dai bani da lokaci, har fada itama mukeyi da ita akan k'in cin abinci" tunda yake magana umma take harararsa, dan daga yanayinsa tasan karya yake mata "toh sannu shugaban k'asa sarkin aiki"
Sosa k'eya yayi yace "wallahi kuwa umma, amma zan dauki hutu,nasamu nadan huta nima" gyada kai umma tayi "Allah ya taimaka, yanzu ai seka tashi katafi gida kar bintun taga kayi dare ko? Ehh haka ne kam umma, nima yanzu nake niyya"
Amma a cikin ransa yace "wannan GANTALALLIYAR bama sai idan tana gidan ba" mikewa yayi zai tafi khadija tace "yaya ka tsaya kaci abincin dare mana" kamar yace zai zauna, amma sabida umma yace "ke madam na cen ta hada min favorite dina, intake jira nasani" *kuji karya k'iri k'iri*😆
Kallo kawai umma tabisu dashi yayi musu sallama yafita, yana dama karya koma gidansa, yazauna tare da mahaifiyarsa da kanwarsa...
Yana fita umma tace "Allah ya kyauta, amma nidai nasan akwai abinda sadiq ya boye min" karaf khadija tace "umma ko fada sukayi da anty bintu" atsawace umma tace "nidai banfada ba,kuma Karna sake jin kinfadi haka" kiyi hakuri umma" naji, d'agani ninaje nayi sallah...
Bangaren sadiq kuwa yana komawa gida dakinsa ya nufa, dan yasan kozai mutu bintu bazata zauna a gida bata futa ba, ruwa ya watsa yadawo yayi sallar isha'i, seda yadade a sujjadarsa ta karshe yana rok'on Allah ya shiryi matarsa, Allah yakawo ranar da bintu zata dena abinda takeyi su zauna lafiya, harga Allah babu wata mata dayakeson zaman aure da ita irin bintu, duk matan da suke binsa har office suna cewa suna sonsa gaba daya basa gabanshi, son da yakewa bintu Allah ne kadai yasani, gashi tana wahalar dashi,shiyasa kullum addu'arsa Allah ya shiryeta ya daidaita tsakaninsu... Da haka har bacci ya daukeshi baiji shigowarta ba.....
Ita ko bintu *GANTALALLIYA* ana cen gidan suna duniya tayi dadi,abincin da aka kawo mata na suna,tuwon shinkafa da miyar taushe, sai waina da sunasir,kadan taci, tafaki ido,ta bude Jakarta ta dauko wata katuwar bakar leda ta juye tuwon, waina da sinasir, ta zura su cikin jaka, tasake dauko wata ledar ta juye miyar taushen tayi fuska, sai yak'e takeyi....
Ashe duk abinda takeyi wasu mata biyu suna kallonta daga baya, d'aya ce tafara gani ta tabo d'ayar "laaaaa kinga wata mata, wanka iya wanka tayi, hada gwal ajikinta, amma tana juye abinci a leda, kodai irin matan nan ne masu aro kaya? Seda ta kare mata kallo tace "ai bintu GANTALALLIYA ce matar sadiq, mijinta abokin mijina ne, bakaramin mai kudi bane, amma bata da aiki sai yawo gida gida, biki kam ko ba,a gayyaceta ba setaje,tadebo abinci, dan bata girki a gidanta, ga k'azantar masifa,rowa kuwa ba'a cewa komai, da ta bayar da abu ta gwammaci ya lalaci. Shiyasa ma ni bana shiri da ita dan bata da kamun kai ko kadan" jinjinawa d'ayar tayi tace "Tabb gaskiya mijinta yana fama" jiyowa bintu tayi ta kallesu suka wayanci suka dau wata hirar... Ba ita ta baro gidan suna ba sai bayan sallar isha'i, daga nan tayi gidan aminiyarta hajiya turai.....
Afalo ta sameta ta dora kafa daya kan daya tana waya, ko sallama babu, tana ganinta suka kwashe da shewa "ahayyye chasss! Suka kwashe da dariya, hajiya turai ce tace "shegiyar ashe kina tafe" cire mayafi bintu take kokarin yi tace "ina tafe wallahi, daga gidan suna nake"
"Ya gogan naki kuwa" tabe baki tayi kafin tace "ehmm waya san mishi ne, ai baki san ma wani sabon salon iskanci ba? Gyara zama hajiya turai tayi tace bani nasha" wai yau ni sadiq zaicewa karna sake na fita daga gida, bama wannan ba, nace yabani makullin motarsa wai ai ba daga gidanmu nazo dashi ba" dariya hajiya turai ta kwashe da shi kafin tace "mena fada miki, ai seda nace kizo mukoma wajen lud'iya kika k'i, gashi nan, ai kadan kika gani a aikin namiji, saura yayi waje dake , koya auro wata matar yayi banza dake" wani uban ashar bintu ta zunduma tana "aiko bai isa ba wlh, nafi k'arfinshi.....ni wlh lud'iyan ne tsoro yake bani, shiyasa bana son komawa, gashi sai dare ake zuwa" wani kallo hajiya turai ta watsa mata "to ai sai ki zauna namiji yaita wahalar dake, kwanaki da mukaje, ke kanki baki ji dadi ba,ki juya shi yanda kike so, amma yanzu gashi asirin yafara karyewa ke zai fara juyaki, ke da bakinki kika fada mijinki baya wasa da addini, kuma kinsan irinwayannan idan ba tashi kikayi a tasayeba kezakiyi kuka da idonki" shuru bintu tayi,hudubar hajiya turai tana ratsata, tuni ta amince mata "to yanzu ya kike ganin za'ayi? Shawara ta rage taki, ni ko yanzu kikeso ashirye nake"
"Kibari dai sai gobe, akwai wata aminiyata ma da mijinta yake kawo mata matasala, inyaso sai muje tare" murmushin k'eta tayi tace "ahh to, kuyara ne, bakwa ganewa, mazan yanzu saida bin bokaye" suka tafa suna dariya....
Ba ita tabar gidan hajiya turai ba sai tara da yan muntuna, daga nan ma seda ta biya gidan saratu ta labarta mata yanda sukayi da hajiya turai, bakaramin dadi taji ba, dan ita mijinta ba k'aramin kulle yake mata ba, gashi tana son fantamawa....
"kice zan fara fantamawa nima bintu" saratu tafada tana murmushi" kehh ai wannan lud'yan ya iya aiki, kawai ni tsoro yake bani, gashi sai dare ake zuwa" ke dallah manta dawani tsoro, indai da biyan buk'ata ai shikenan" rausayar da kai bintu tayi tace"ahhh akwai dan nagani,shikadai hajiya turai take bi, bakiga yanda takeyi da mijinta ba, yan uwansa kuwa tuni ta rabashi dasu" gwalalo ido saratu tayi tace "wani abun sai manya" suka k'yalk''yale da dariya "keh bari nadena biye miki natafi gidana, rabona dashi tun safe, inna biye miki kwana zamuyi" dariya saratu tayi tace"laaaaa ni ko abinci ban kawo miki ba" aiko zubo min natafi dashi dan yunwa nakeji wallahi, dama nataho da wani abinci daga gidan suna, sadiq yaci, dan nasan yana cen yana cika yana batsewa, yunwa taci ubansa" kai bintu amma baki da adalci, yanzu bazaki iya yimasa girki bama" tabe baki tayi "ke kika San wannan, niko baya cikin tsarina, kinga tashi muje kizuba min natafi goma ta wuce"
Kitchen suka shiga, saratu ta dauko wani k'aton flask,ta cika shi da shinkafa, ta sake dauko wani matsakaici ta zuba miyar kaji, hannu bintu tasaka cikin tukunyar ta dauka wani katon hak'ark'arin kaza tafara ci.....
Sun fito saratu zata rakata bakin motarta sukayi kicibus da mijin saratu yana rufe gida, ko kallon inda yake bintu batayi ba saifama take da k'ashin kaza, balanta yayi tsanmanin zata gaidashi, ita ko saratu a tsoraci take, cikin sauri sukayi sallama da bintu ta koma ciki......
Tun daga bakin k'ofa yafara mata balbalin masifa "keh wannan yar iskar kawar taki sau nawa zance kidena kawo min ita cikin gida, yar iskar mata ta mayar da aurenta ba abakin komai ba kullum tana yawon bin gidajen mutane,inma banda shedaniyace ita karfe goma ta wuce amma ko ajikinta, to wallahi kifada mata karnasake ganinta a gidana, inba haka ba.....kafin yakarasa ta katseshi "inbahaka ba me? Kaga bashir kafa takura min, dan kana da gida shine ba dama wani nawa yazo sai kayi magana, idan tak'amar ka gida, kaje gidan bintu kagani seka raina kanka" ta shige ta barshi a wajen, da karfi yace "Sena raina kaina da k'azantarta ba,keda bakinki kikacemin kawartaki akwai k'azanta" bata ce masa komai ba ta wuce daki ta kwanta...
Bintu kuwa ba ita ta isa gida ba sai shadaya saura, tana shiga tafito da kayan abincinta, a kitchen ta tsaya ta dau plate tayi dakin sadiq...
Tana shiga ta banka kofar da karfi, wanda duk baccin da sadiq yake seda yatashi a furgice, dan jiyayi kamar a mafarki "enyeeee!! Wato har kasamu nutsuwar yin bacci baka ga dawowata ba, lallaima sadiq, yanzu idanma wani abun ne yasameni shikenan ko ajikinka ko?
Goge idonsa yayi yana hamma "nina aikeki? Kokuma da izinina kika fita? Dan haka ko meya sameki ke kika siya da kudinki"
Zunbura baki tayi tace "duk dai wannan abinda kakeyi nasan yunwa kakeji, ga abinci nan nakawo maka daga gidan suna, cikaji yayi dadi wallahi" wani mugun kallo yayi mata kafin yace "ke yanzu rayuwar da kika daukarwa kanki tayi miki daidai, duk kayan abincin danake kawowa gidannan bazaki taba iya zama kiyi min girki a matsayina na mijinki ba, yanzu ko kunya bakiji ba kikawo min abinci daga gidan suna, bintu wai ke wace irin macece dan Allah?
Seda ta dura ashar tace "Ehh lallai namiji ba dan goyo bane, yanzu naje gidan sunan abani abinci nakasa ci nace sena kawo maka, amma zaka tsaya kana min dogon bayani, to wlh ka kori gaba"
"Nace bazanci ba,ke da kika dauko ki dauki abinki ki futar min daga d'aki" ba musu ta tattara kayanta "kayiwa kanka, dan wallahi nasan yunwa ce take nuk'urk'usarka, abinci ne inbaka ci yanzu ba kaci da safe, dan yunwa ba kanwar uwar kowa bace girki kuma idan kana so kaci na gidanka seka dau yar aiki, nikam ba baiwarka bace" tana karasa maganar ta gutsuri waina ta fice taja kofar da karfi......
Shiko sadiq kamar TV yamayar da ita, tana futa yace "anya wannan matar ita kadai ce kuwa? Inalillahi wa inna ilaihirraji'un" yaita maimaitawa....
Reader's kuyimin hakurin rashin jina dawuri yau, nima nadan taba GANTALI naji abinda bintu takeji.😜
*DEEE*💘
*🌚GANTALALLIYA🌚*
*Written📝*
*BY*
*DEEE💘*
*⚜🇦rewa 🇼riters🇫orum⚜*
*A. W. F*
*I.G:Arewa writers forum fans*
*• Follow us on facebook*~ _
www.facebook.com/Arewa-Writers-Forum-294302397727161/
بِسْــــــــــــــــمِ اللَّهِ الرَّحْمَ الرَّحِيْم.......
The Heart that believes and fears ALLAH Shall always have Peace & Contentment. May you and ur Family remain peaceful & contented forever. May Allah fulfil all our needs, may HE accept all our duas, remove our difficulties and Protect us from Shaytaan and all Evil..... Alhamdulillah it's Friday, remember the Sunnah's of the day, especially reciting Surat Al-Kahf.....
JUMMA'AT MUBARAK FAN'S🌹
True life story
16-20
Tsabar takaici ne yahana shi bacci, juyejuye kawai yakeyi har aka kira sallar asuba.. Bayan yadawo daga masallaci aka mishi waya a wajen aiki akan yayi sauri yazo shugabansu yana nemanshi. Hankali atashe ya shirya ya tafi, dan daga jin kiran babu lafiya....
Hajiyar bintu kuwa sammako ta doka, taje tasamo zuciyar kare da sauran kayan hadin da aminiyarta ta fada mata. Tana zuwa gida tagama hadasu tayi gidan bintu....
Sallama taketayi amma shiru ba'a amsa ba,"gidan kamar bakowa,kodayake mai gadin yace min bata fita ba" hajiyar bintu tafada tana kara cusa kai cikin gidan, dakinta tashiga tasameta sai baccinta takeyi hankali kwance...
"Ba shakkah yarinya, harma damar bacci kika samu miji yana miki iskanci ko? To tashi" ta kai mata duka,a furgice ta mike zatayi bala'i, a zatonta sadiq ne, sai kuma sukayi ido hudu da hajiyarta "laaaaa hajiya yaushe kika zo? Bansani ba, wato ke bintu har yanzu kina nan da wannan shegen baccin naki ko"Sosa kanta tayi, mai kama dana mahaukata "wlh hajiya gajiya ce,ban kwanta da wuri ba"
"To tashi maza, ba zama ne yakawoni ba, kinga wannan garin" tafada tana nuna mata wani kullin abu abakar leda "a cikin abinci zaki zuba mishi yaci, yanaci... Hmmm ko uwarsa bata isa ta rabashi da ke ba, dukiyarsa kuwa komai zakiyi da ita bai isa yayi miki magana ba" karbar kullin bintu tayi tace "to hajiya nagode fa, amma ba anan take ba,sadiq fa yasan ba girki nakeyi a gidannan ba, dan wlh anfi wata rabon danayi abinci Sadiq yaci,karfa yagane"
Dariya hajiya tayi kafin tace "bintu bana son shiririta fa, ai yanzu dole zaki tashi ki gyara, kiyi masa girki mai dan banzan dadi, kinayi kina kisisina sai kin tabbatar yacinyeshi, zakizo kibani labari"
"Huuu hajiyata shiyasa nake sonki, Allah ya barminke kidade kiyi lasting" dariya tayi tace "bari natashi natafi, dan yau zanje kauye" kauye kuma? mezakiyo a kauyen haka" kiwona zanje nagano kwana biyu ban lek'a ba" to kya gaidasu inkinje" ta dauko dubu hamsin a dakin sadiq ta bata "gashi kinyi kudin mota" ta amshe tasa a jaka sukayi sallama..
Yana zuwa office aka bashi takardar sallama, sakamakon baya tabuka komai inyaje aiki, kansa ne ya dunga sarawa jiri ya dunga dibarsa, tabbas yasan shi mai laifi ne amma bakowane ya janyo hakanba illa bintu, hakuri ya dunga bawa shugaban nasu amma sam yaki ko sauraronsa, haka ya hakura ya tattara yabar office din...
Gidansu ya wuce, zuciyarsa tana masa zafi, tabbas bintu ta cuceshi, itace silar rashin kwanciyar hankalinsa, gashi takara sashi cikin wata matsalar, yarasa aikinsa...
Da sallamarsa ya shiga, umma ce kadai zaune a falon tana karanta hisnul muslim, seda ta karasa addu'ar datakeyi ta amsa sallamar da yayi, gefenta yazauna a kasa ya sunkuyar da kai jiki a sanyaye ya gaidata, amsawa tayi tana kallonshi, kafin ta ankara kwallar dayake boyewa ta zobo...
"Subhanallah,sadiq lafiya meya faru? Bai ce mata komai ba sai takardar hannunsa daya mik'a mata, da sauri ta bude ta karanta "inalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni fi musibati, wa akhlifli min kairan minha!!!
"Umma bakin ciki suke min, banyi musu komai ba umma, hassada ne da bakin ciki dan sunga ina samun cigaba, shine suka kai sukata wajen manya na.....yana fada yasake raushewa da kuka "kayi hakuri Sadiq, Allah yana tare da masu hakuri, duk abinda kaga yasamu mutum, to dama Allah ya shiryo hakan, babu wanda ya isa yayi maka abinda Allah bai shiryo maka ba, Allah ya mayar maka mafi alkairi, ka dage da addu'a Allah zai kawo maka mafuta kaji" jikinsa ne yayi sanyi da jin nasihar mahaifiyarsa, jiyayima duk duniya an dauke mishi damuwa....
Magana yakesonyi amma sallamar khadija ta dakatar da shi, da gudu ta shigo ta haye cinyar umma "ohhhhh ni amina, zata balla min kafa" dariya tayi tace "ummana bazan karya ki ba" kallonta sadiq yake tayi, yana jin dama shine ita, bata da wata damuwa. Umma ce tace "bakiga yayanki bane" da sauri ta mike tayi wajenshi "yaya sadiq ina wuni, ina anty bintu,kaki ka kawo mana ita ko? Shafa kanta yayi "kanwata zan kawo muku ita, ta kwana ma" tsalle ta dungayi kafin umma tace "kije ki cire uniform dinnan kici abinci zamu unguwa" da murnarta tayi daki jin zasuje unguwa...
"Umma dan Allah kibani khadija natafi da ita tayi mana kwana biyu" zaro ido tayi "nikuma abarni nikadai kenan ko" marairaicewa yayi "dan Allah umma, kinga yanzu kullum ina gida, zan dunga kaita skull ina daukota, dan Allah karkice a a" tausayinsa taji tace "shikenan na amince,amma baxata dade ba? Na yarda umma"
Tashi tayi tabi khadija dakin, samunta tayi tsaye agaban drowa tarasa wanna kaya zata sa "yayanki yace ki shirya zakije ki musu kwana biyu" tsalle ta dungayi tana murna "au dadi ma kikeji zaki tafi kibarni ko" tsayawa tayi "ah ah ummana,kingafa bantaba zuwa gidan yaya na kwana ba, shiyasa nake jin dadi" to ai shikenan... Umma dakanta ta shirya mata kayanta tsaf ta fito suka tafi....
Bintu kuwa tunda mahaiffiyarta tabar gidan ta tashi da kanta tayi gyaran gidan da kanta, tass ta gyare ko ina tasa ruraren wuta sai kamshi gidan yake kamar bashi ba, abun mamaki har dakin sadiq ta shiga ta share ta goge ta wanke toilet, abun se wanda yagani...sedae fa tanayi tana tunanin waje, dan kafarta har k'yaik'ayi take mata yau bata taka kobakin gate ba....
Girki ta d'and'asa mai shegen dadi, dan dama wajen girki bintu ba daga nan ba, yine bazatayi ba, sabida tasa kanta a Gantali...
Suna hanya khadija sai surutu take yimishi, shiko zuciyarsa tana tunanin, Allah yasa bintu bata fita gantali ba, Allah yasa ganin khadija yasa ta rageyimasa wayansu abubuwan,dan baya son khadija ta fuskanci wani abun, dan akwai ta da surutu... da wannan tunanin suka karaso gidan...
Tun daga tsakar gidan yakejin wani kamshin abinci mai dadi, mamaki ne ya cikashi,kasa daurewa yayi yace "khadija kina jin kamshin danake ji kuwa? Lumshe ido tayi tace "inaji yaya, na matsu naje naci girkin anty bintu" murmushi kawai yayi,dan shi bai yadda bintu ke girki ba, azatonsa ko a makotane...
Shi kansa mai gadi ba'a barshi baya ba, seda yayi zaton anya kuwa bintu ce ke girki....
Suna shiga sadiq yaga falon ya chanza mishi, ga wani kamshi dayake tashi, rufe idonsa yayi yasake budewe, yana budewa sukayi ido hudu da bintu, ta tsala kwalliya, tasha doguwar rigarta ta atamfa, ga wani irin daurin dan kwali mai hawahawa, ga kamshi dayake tashi a jikinta, jiyayi kamar ya rungumeta, amma ganin khadija ne yasa yafasa...
Da murmushi ta karaso inda suke tana mishi sannu da zuwa, mamaki bai gama kasheshiba seda yaga tasa hannu ta karbo jakar kayan khadija dake hannunshi, kasa cewa komai yayi sai kallo, ita ko duk tana sane dashi,a zuciyarta tace "zaka sani ne" juyawa tayi kan khadija tana "khadija yau kece a gidanmu, ina umma? Cikin fara'a khadija ta amsa"tana gida, tace tana gaisheki" shafa kanta bintu tayi kamar mutuniyar arziki "ina amsawa, mushiga ciki ki huta ki ci abinci ko? Kama hannunta tayi sukayi cikin falon...
Sadiq kam jiyayi wani son bintu yana ratsa shi, azatonsa ALLAH ne ya amsa addu'ar sa, bai san makirci ne aka shirya shi ba.... D'akinsa ya wuce yagansa fesfes, toilet ya shiga don ya watsa ruwa, kafin ya fito bintu ta baro khadija a dakin tabiyo shi....
Abakin gadon ta zauna, yana fitowa ta mik'a mishi wani karamin towel na goge jiki, dadine ya kamashi, tuni ya nemi damuwarsa yarasa...."wai bintu ko anya kece kuwa, naga duk kin chanza, kodai wa'azi kika jiyone" harara tayi mishi"haba my1, ai ba kullum ake kwana a gado ba, nima yau nayiwa kaina fada,naga yakamata na zauna na kula da gidana,da mijina" zama yayi kusa da ita "ko kefa, yanzu bakifi jin dadi ba, rabon dana ganki a irin wannan yanayin tun kina amarya, gaskiya naji dadin chanzawarki bintu" rufe fuskartatayi da hannu "nidai kashirya muje kaci abinci nasan yunwa kakeji" wani farin ciki ne yasake rufeshi, shiryawa yayi suka fito sai zalayarta yakeyi...
Khadija suka samu harta gama cin nata abinci, dan dama seda bintu ta zuba mata tayi dakin sadiq...
Tana kwarkwasa tana yanga tasamu sadiq ya cinye tasss abincin data zuba mishi... Yana gama ci tajashi suka tafi daki suka bar khadija tana kallo a falo.......
*Asalin Labarin*
*DEEE💘*
*🌚GANTALALLIYA🌚*
*Written📝*
*BY*
*DEEE💘*
*⚜🇦rewa 🇼riters🇫orum⚜*
*A. W. F*
*I.G:Arewa writers forum fans*
*• Follow us on facebook*~ _
www.facebook.com/Arewa-Writers-Forum-294302397727161/
*Agaskiya babu abinda zan iya cewa da masoyana sai godiya, Nagode! Nagode!! Nagode!!! Godiyarma ta gode, bantaba sanin cewa haka nake da masoya ba sai jiya,kodayake dama mutum baya gane masoyinsa, sai wani abu yasameshi! More especially SADNAF Novels Group,nagode da addu'arku, Allah ubangiji yabar so da kauna, wayanda suka kira ni awaya, da wayanda suka bini da addu'a ta prvt gaba daya babu abinda zance daku sai Allah ubangiji ya biya muku bukatunku na alkairi, masu aure a cikinku Allah ya dauwamar daku a cikin gdn mazajenku da farinciki mai dorewa. Irina kuma marasa aure Allah ubangiji yabamu mazaje nagari! Ameen yah Rabbi!!!*
Ina kuke mutanen AREWA WRITER'S FORUM???? WANNAN SHAFFIN NA SADAUKAR DA SHI DOMIN KU, ALLAH YAKARA HADA KAWUNANMU❤
True life story
21-25
Mahaifin Sadiq dan asalin garin Bauchi ne, rasuwar mahaifinsa ne yadawo dasu garin mahaifiyarsa wato kano, sakamakon takurawar da dangin mahaifin sadiq sukayiwa mahaifiyarsa hajiya Amina... Sadiq ne danta na fari, tundaga shi kuma Allah bai bata wata haihuwar ba, wannan dalilin ne yasa dangin alhaji sunusi, wato mahaifin sadiq suka takura mata, har Allah ya karbi ransa lokacin sadiq yana dan shekara hudu.....
Kobayan rasuwar alhaji sunusi basu kyaleta ba,abun nasu sai kara ta'azzara yake, shiyasa ta yanke shawarar tattara dukiyar da mijinta yabar musu ta dawo mahaifarta...
Koda tadawo garin kano a gidan wani kanin mahaifinta ta sauka, dayake itama marainiyace gaba da baya, babu yanda kanin mahaifinta baiyiba ta zauna dasu amma taki tace kawai ya nemo mata gida matsakaici ta siya... Hakan ko akayi ya nema mata gida a unguwar maidile suka koma ita da danta... Ragowar kudin hannunta kuma ta bawa kanin mahaifinta tace ya hada ya dunga juya mata....
Akwana atashi hajiya amina tana cikin kwanciyar hankali ita da danta Sadiq, wanda babu abinda yanema yarasa, yana karatunsa boko da isalama...
Lokaci ba wuya nan da nan ya kammala secondary dinsa, batare da bata lokaci ba cikin sa'a yasamu admission a jami'ar bayero university kano.....
***************
Bintu yan asalin garin kano ne,mazauna kofar mata, su biyu ne a wajen iyayensu, shamsiyya ce babba sai bintu, tundaga kan bintu hajiya dije ta tsaida haihuwarta, a cewarta ya'ya' biyu sun isheta...
Kaf kofar mata babu wanda baisan rashin mutunci irin na hajiyarsu bintu ba, sbd bakin cikin halinta ne yayi sanadiyyar rasa ran mijinta malam suleman, duk wani hali na bintu wajen mahaifiyarta ta dauko shi, dan tun tana yarinya ta dorawa kanta yawon masifa, ko makaranta bata zuwa sai dai gantali...
Ita kam shamsiyya yarinya ce kamila mai sanin yakamata, dan har fada takewa bintu akan ta dena yawo, ta dunga zuwa makaranta, amma taki ji, intaji ta ishetama ta zazzageta, hajiyar bazata ce komai ba....
Bayan shamsiyya ta kammala secondary dinta ne wani yafito yana sonta da aure, tako amince mishi, amma hajiya da bintu suka ki yarda, wai dan talaka ne, duk da suma bawani arzikin ne dasuba amma basa son hada jini da talaka...
Sam shamsiyya taki amincewa da maganarsu, tace arziki na Allah ne, taji ta gani tana son shi a haka....haka suka rabu da ita akayi bikin aka kaita gidanta dan karami, hajiyar bintu sai ALLAH wadai da gidan takeyi....
Bayan bikin kuwa ita da bintu babu wanda yasake waiwayar shamsiyya... Itama shamsiyya duk sanda zata zo bazata samesu a gd ba.... Seda sukaji labarin auwal mijin shamsiyya yafara samun arziki ne suka fara zuwa gidan...
Nanfa hajiya tafara tunanin dora shamsiyya a hanyar malamai,amma sam shamsiyya tak'i amincewa, illa ma duk sanda suka zo mata da zancen bin bokaye sedae taitayi musu wa'azi, su kuma su hadu su zageta tass, har akwai sanda bintu tace "hajiya anya wannan yar kice ta cikinki kuwa? Tsaki hajiyar tayi tace "ki rabu da ita, indai na miji ne,da kanta zata tashi ta nemi taimako" wannan ne yasa hajiyarsu bintu dena bi takan shamsiyya, duk abinda zasuyi ita da bintu suke abinsu.
Haka rayuwar bintu da hajiyarsu ta kasance, kullum cikin rigima suke da mutane, hatta masu adaidaita sahu basu kyale ba, dan sai adaidaita ya dauko su daga uwa duniya subashi naira hamsin ko talatin, inya ki yarda ma suk'i bayarwa sun kwammaci yayi musu Allah ya isa, wani zubin kuma yan rabon fada ne zasu biya....
Wata rana bintu taje gdn wata aminiyarta hajiya turai,wacce suka hadu a kasuwar rimi asibiti,tunda hajiya turai taga bintu taji tana sonta, batayi k'asa a gwa ba tayi mata mgn, dayake bintu akwai ta da son mutane, gashi taga hajiya turai ruwan masu kudi ce, tuni ta washe mata baki suka gaisa, hajiya turai take tafadawa bintu tana burgeta, sukayi exchanging numbers, tare da yiwa juna kwatancen gdn su.... Tundaga ranar suka kulla, a sati idan bintu bataje gdn hajiya turai sosai ba taje sau uku ko hudu.....gdn hajiya turai gdn dan ko wacce shegiya ne, duk da kasancewarta matar aure, amma wannan bai hana ta mayar da gdnta na shedanci ba, dan harda yan daudu a gdn, mijinta kuwa sai yacce tayi da shi....
Haduwar hajiya turai da bintu ne yakara tabarbarewar tarbiyarta, dan wata ran ma a gdn take kwana kotakai dayan dare tana gantali. Hajiyarta kam ko a jikinta bare ta tsawatar mata...
Watarana misalin karfe 9 na dare, bintu ta baro gdn hajiya turai, tanata zabga uban sauri, gashi bata samu abin hawa ba, ta hango wani adaidaita a tsallaken titi ta tafi da gudu, daidai lokacin wata mota ta sharo da gudun gaske, saura kadan yayi gaba da ita yayi sauri ya taka burki......
Futowa yayi da sauri yana bata hakuri, seda takare mishi tanadi sannan ta wuce ta hau adaidaita ta wuce.... Shikuma tsayawa yayi yana kallonta, maimakon tabashi haushi, amma burgeshi ma tayi,da sauri yakoma cikin motar ya dunga bin adaidaitan daya dauketa.... To wai waye wannan, wanda masifar bintu ce ta burgeshi?
Sadiq ne, bayan ya kammala karatunsa a bayero,cikin sa'a yasamu aiki a immigration office.... Gaba daya ya chanza,kudi sunfara zamar mishi, kyansa ya kara futowa, duk da bakine amma har wani haske yayi najin dadi....
Adaidai kofar gidansu adaidaitan ya tsaya da ita, ganin ya tsaya ne yasa sadiq shima tsayawa,naira saba'in bintu ta dauko ta wurga mishi, shiko yace bazai yarda ba kudinsa yafi haka, hayaniya suka farayi duk sadiq yana kallonsu, seda yaga abin bana karau bane yasa, yafito ya karasa inda suke...
"Abokina lafiya dai naga kuna ta hayaniya" bayani mai adaidaitan yayi mishi" ya dauko dubu daya ya bashi, zai bashi chanji yace yaje kawai....bintu kuwa, kunya ce ta rufeta, dan tunda take bata taba jin kunya irinta yauba, zatayi magana sadiq ya katseta, dan shi azatonsa talauci yasata yin haka, bai san tsabar rashin mutunci bane....
A lokacin sadiq ya shaida mata shifa har ga Allah sonta yakeyi, itama bintu tuni taji ya kwanta mata, dan dama irinshi takeson aura, shiyasa duk samarin dasuke zuwa wajenta take wulakanta su,intaga kafiya naci ma tafito da ruwan sanyi a roba tayima wanka dashi, acewarta bakayi wanka ba,har suka gaji suka dena, yazamana babu wanda yake zuwa wajenta, sai yau da Allah ya hada ta da sadiq... Bayan sun daidaita, ya dauka kudi wanda bansan nawa bane ya dank''a mata ya tafi....
Tana zuwa gd ta samu hajiya bata nan, soke kudin daya bata tayi, ta nufi makotansu cin awara...
Shikam Sadiq tun a hanya yake godewa Allah ya samu irin matar dayakeso, yar talakawa, wacce zai zauna da ita batare da wata matasala ba... Yana zuwa gd ya iske ummansa zaune a tsakar gida da yaran makota, dayake Allah yayi ta da son yara, zama yayi ya labarta mata tun farkon haduwarsa da bintu, itama taji dadi, takuma ce zata gaggauta gayawa dangin mahaifinsa, dama gobe takeson zuwa kauye daga cen seta biya, dan itama bata son sadiq ya dauko masu auren yar masu kudi....
Bintu kuwa hajiyarta nadawowa ta labarta mata,ta kuma nuna mata kudin daya bata, cikin hanzari hajiyar ta zari mayafi suka tafi wajen malam, a cewarsu sabida yanzu sai yan bakin ciki zasu hana....
Koda mahaifiyar sadiq taje tasanar musu, sukayi mata alkawarin suna nan zuwa, anan ne ta tarar da yar kanin baban sadiq sunyi hatsarin mota ita da mijinta gaba daya sun rasu, sai yarsu guda daya Khadija, yar kimanin shekara goma sha biyu, bakaramin tausayawa yarinyar tayi ba, shiyasa ta roki arzikin abar mata ita tasata a makarantar boko data islama, cikin sa'a kuwa kakarta ta amince, dan dama bawani karfi gareta sosai ba.
Bayan ta dawo, sadiq yaji dadin ganinta da khadija, dan tun yana karami yakeson kanwa, shiyake kaita makaranta insuka tashi kuma sutaho da yaran makota,sbd lokacin yana wajen aiki, bakaramin shakuwa sukayi ba, dan khadija yarinyace mai shiga rai....
Akwana atashi maganar auren sadiq da bintu tana matsowa, cikin nasara kuwa su bintu suka rufe bakin mutane, koda akaje bincike babu wanda yafadi wani ai'bu akansu,har akayi aure aka gama lfy....
Aka kai amarya gidanta mai kyan gaske a unguwar shagari qtrs, babu abinda aka kai bintu dashi, dan Sadiq yace subar komai zai siya, tunda suka cinye amarcinsu bintu tafara nunawa sadiq halinta, dan duk maganar da zai gaya mata sai abinda taga dama takeyi, abun bakaramin damunshi yakeba, uwa uba gantali, gazanta, rashin yin girki........ Seyayi yunkurin yimata fada sai yakasa, gashi baya son bata mata rai gashi yak'asa sanar da kowa halinda yake ciki, shikadai abun yake damu......
*Cigaban labarin........*
Masoyana kuyi hakuri da wannan kafin Allah ubangiji ya kaimu gobe, zakujini a cigaban GANTALLALIYA... Asha karatu lafiya.....
*DEEE*💘
*🌚GANTALALLIYA🌚*
*Written📝*
*BY*
*DEEE💘*
*⚜🇦rewa 🇼riters🇫orum⚜*
*A. W. F*
*I.G:Arewa writers forum fans*
*• Follow us on facebook*~ _
www.facebook.com/Arewa-Writers-Forum-294302397727161/
True life story
26-30
Basu suka futo ba sai gabannin magariba, shima dan tana so ta fice daga gidanne, shi ko sadiq yaji dadin yanda bintu tayi mishi yau, dan rabon da yasamu hakkinsa na aure a gunta harya manta, sai yau dayake ta hada mugunta....
Ko wankan tsarki batayi ba,tasaka kayanta,"sena dawo" kawai tace mishi, ta fice abinta,shiko kamar wani soko kawai yabita da kallo... Tashi yayi,jiyayi jikinsa duk ya mutu, da kyar ya iya shiga yayi wanka, yafito da niyyar tafiya masallaci, falo ya iske khadija har yanzu tana ta kallonta hankali kwance...."kanwata oya atashi aje ayi sallah ko" to kawai tace mai, amma bata da niyyar tashi, dan lokacin period takeyi... Yana gama gaya mata ya fice massalaci,seda ya hada da sallar isha'i sannan yadawo gidan...
Khadija ya tarar ta hada kai da gweiwa tanata kuka, da sauri yakarosa inda take ya dago kanta "sis lafiya, meyasaki kuka? A shagwabe tace "ba kune ba kunfita kunbarni nikadai a gida, sai tsoro nakeji, ni ka mayardani wajen ummana"
"Haba sister, daga zuwanki kuma, kiyi hakuri, anty ki taje gidansu hajiyarta batajin dadi, nikuma idan naje sallar magrib sai anyi isha'i nake dawowa, am very sorry kinji kanwata" gyada kai tayi, shikuma sai share mata hawayenta yake yana ta faman rarrashi....
**********
Tana fitowa, gidan saratu tayi,takoyi sa'a kuwa mijinta bai dawo ba, mayafi kawai ta yafa sai yar posarta, sukayi gidan hajiya turai... Suna zuwa falon cike yake da matan banza da wani dan daudu da suke kira jiji....jiji yana ganin bintu yataso yana wata rausaya kamar irin karuwar macen nan "ahayyyyye chassss!!! Suka fada atare suka juya suka hada duwawunsu.....
*Waiya zubillah! Wallahi tallahi reader's wannan labarin ba karya bane, abinda wasu ballagazazzun matan sukeyi kenan, suna da aure amma basu dauke shi abakin komai ba.. Kawai na dan chanza wayansu abubuwan ne,kuma wannan danake fada muku wallahi nasanta farin sani, halinda ta daukarwa kanta kenan, Allah ka shiryemu kafi karfin zuciyoyinmu*
"Ta gidana wannan fa, naga itama kala ce fa" yafada yana nuna saratu, yana wani irin taunar chew gum, da fariii da idanuwa "to ai jiji kinsan bana hurda da kananan mutane, duk mutane na yan hannu ne" suka sake kwashewa da shewa irin tasu ta yan duniya "shiyasa kike burgeni ai,Ku shiga hajiyar tana ciki, bari naje na samo muku wani abu kudan taba,dan yau gidan yayi albarka komai ya kare" bintu zatayi magana, saratu tarugata "laaaaa ka barshi mana ai bama zama zamuyi ba" a fusace jiji ya juyo "kantarancen!!! Wacece wannan take maidani namiji, wlh kinci sa'ar wannan uwar tawa, da sena tsinka miki mari" hakuri bintu ta dunga bashi sannan ya wuce yabarsu a wajen...
"Ke Sara meya kaiki, sufa basa so ace musu namiji, dan haka daga yau idan zakiyi mishi magana, ki dungayi kamar da mace kike magana" tabe baki saratu tayi"nidai muje muyi abinda yakawomu kafin abban daddy yadawo" Jan hannunta bintu tayi suka nufi dakin hajiya turai....
Daidai lokacin suka ga wani babban alhaji yafito daga dakin, gaishesa sukayi, seda sukayi dan gaba, bintu taradawa saratu "mijinta ne fa wannan" rike baki tayi "yanzu mijinta yana nan, aketa wannan bidirin? Bintu tace "kadan kika gani" suka cusa kai cikin dakin...
"Ahhh har kun karaso? Yage mayafi bintu tayi ta zauna abakin gado "wallahi kuwa hajiyata, ai kitashi kawai mutafi, dan ni nayi maganin matsalata, wannan kawar tawa kawai zamu kai, dan tana cikin matsi, yanzu haka ma a tsoraci take kar mijinta yadawo" shek'ewa da dariya turai da bintu sukayi, suka tafa hannu"kice sabon shiga ce" kallon saratu bintu tayi "emmm bawani sabon shiga, tana son buga ronse dinta tana masifar tsoron mijinta" seda turai tayi wani murmushi kafin tace "ke waya fada miki ana tsoron na miji? Inma zaki saki jiki kidena, tun wuri kidena, kici duniyarki da tsinke, bari na tashi muje mu nema miki mafuta yarnan" ita ko saratu gaban ta faduwa kawai yake,tasan duk inda mijinta yake yanzu yakoma gida, a fili kuma murmushin yake kawai takeyi....
Basu suka bar gidan hajiya turai ba, sai karfe tara saura kwata, koda suka isa wajen bokan nasu, seda suka jira yagama da wata mata sannan suka shiga.... D'akine mai shegen duhu, gashi babu fitila, sai wata wutar itace daya hada, hakoransa kawai suke iya gani, ga uban hayaki dayake tashi, tunda suka shiga wajen, gaban bintu yake faduwa, dan duk bokayansu babu irin wannan,saratu kuwa rawa kawai jikinta yakeyi, tanata matse cinya, dan wani futsari ne yake shirin zubo mata.... Hajiya turai kuwa harwani kirari takeyi mishi, shikuma sai jin dadi yake yana gyada kai,dan a duniya yana son ayi mishi wannan kirarin,saidai bakowace ta iya ba sai wacce ta cika shu'uma wajen bin bokaye...
"Hajiya turai ce ta juya ta kalli saratu "ki nutsu kiyi masa bayani, karkisake kiyi kuskure, dan zaki iya shiga matsala" jiki na rawa tafara yimasa bayani, tana gamawa ya shek'e da dariya, juyawa bayansa yayi ya dauko wata yar karamar tukunyar k'asa,ya dora akan wani kan rago, yace taje ta dauka, jiki na rawa, fitsarin data fara matsewa yasoma zubowa, daukowa tayi hannunta kamar zai fita daga jikinta sabida tsabar rawar dayakeyi, tana dauka yasake dauko mata wani kulli, nan ma jiki yana rawa taje ta amso ta zauna....
"Ki zuba garwashin wuta, a cikin wannan tukunyar, kizuba wannan turaren a ciki, sai kin tabbatar ya kusa dawowa gida zaki turara, sai kin kusan gamawa zaki kirawo sunansa sau uku, sannan ki zuba wannan ruwan ki kashe wutar,kina kashewa kifasa tukunyar, yafada yana kara mik'a mata wani ruwa a cikin kwalba....yak'ara da cewa, karki sake kibari tukunyar nan ta fashe bakiyi wannan aikinba, idan ba haka ba, abun kanki zai koma...
Karba tayi ta hadasu waje daya, sannan ta bude posarta, ta dauko kudin ciki gaba daya ta dora mishi, akan wani waje da yace ta dora...
Godiya sukayi mishi gaba dayansu, suka tashi suka tafi,suna kan hanya ne saratu take cewa"ni yanzu yazanyi da wayannan kayan, niba jaka ba? Bintu tace "karki damu, zan baki tawa ki juye, kedai kiyi hankali kindai ji abinda yace miki" seda suka kai hajiya turai gida suka ajiye, saratu sai godiya take zabga mata, dan ji take harta fara juya bashir mijinta, kamar yadda taga aminanta sukeyi,dan abun yana burgeta, musamman yanda bintu take gantalinta son ranta, sadiq baya iya cewa komai...
Jaka bintu ta bata tasaka abubuwan da boka yabata, takawota har kofar gida ta ajiyeta ta wuce.... Ashe tunda suka shigo kan layin bashir yake kallonsu, dan tun kafin takwas yadawo ya tarar saratu bata gida, yayi imani da Allah bintu ce tazo ta dauketa suka fita, amma dan ya tabbatar da zarginsa ne yasa, ya dauki daddy da tabarwa yar akinta, yasamu bayan wata bishiya ya labe,yana ganin bintu ta tafi kuwa yataso da sauri yayo kofar gidan..
Koda saratu ta tura kofar gidan taji ta a rufe, sai tayi tunanin kodai bashir bai dawo bane? Aiko bata karasa tunanin taba taji saukar belt a gadon bayanta,a gigice ta juyo, ya sake dauketa dawasu tagwayen mari, tuni tasaki futsarin daya matseta, jakar hannunta ta subuce akasa.........
Kubiyoni a page nagaba muji yaya saratu zasu kwashe da bashir, tukunyar da boka yabata zata fashe kuwa ko kuwa????
*DEEE*💘
*🌚GANTALALLIYA🌚*
*Written📝*
*BY*
*DEEE💘*
*⚜🇦rewa 🇼riters🇫orum⚜*
*A. W. F*
*I.G:Arewa writers forum fans*
*• Follow us on facebook*~ _
www.facebook.com/Arewa-Writers-Forum-294302397727161/
*Inasonku masoyana, abin kaunata, abun alfaharina, wallahi banma San da irin kalmomin da zanyi muku bayanin yanda nake kaunarku ba a zuciyata, duk da jiya na dan samu wata yar matsala danaji wasu sunacewa ai marubuciyar GANTALALLIYA ta cika girman kan masifa, wallahi ba girman kai bane, abubuwane sukayi min yawa, hasalima saukin kai ne dani idan kun fahimceni,shiyasa bana samun damar yiwa wasu daga cikinku reply, amma kaina bisa wuya Kuyi min gafara, zan yi iya bakin kokarina nabawa masoyana lokacina. Sannan Akwai wayanda suka tambayeni akan suna son sanin takaitaccen tarihina, to suma ina basu hakuri akan rashin samun lokacin dabanyi ba nafada musu, amma ina musu albishir dama sauran masoyana da suke so suji takaitaccen tarihina, zan bude group,zan tura links din a groups da dama, zan saka ranar danakeda isseshen lokaci, kowa ta tambayeni abinda takesonji game dani Naoge.*
Dedicated to ummu salma wannan shafin nakine kekadai ban hadaki da kowa ba, nagode da kaunar da kike nuna min a koda yaushe I❤you dear.
True life story
31-35
Dukanta ya hau yi kota ina, amma duk wannan bai dameta ba,hankalinta yana kan Jakarta, maganar boka tana ta fado mata...sunkuyawa tayi zata dauki jakar, ai ko bashir ya fuzgeta yayi wani cilli da ita, jikake tasss, tukunya ta fashe.... Da gudu ta isa wajen jakar, tana budewa taga tukunya tayi rugurugu, ihuu tasaka tana "shikenan bashir kacuceni, ka kasheni da raina" shiko mamaki ma ta bashi, gawani haushinta dayakeji, wato shi da tayiwa laifi bai fadi haka ba, sai ita daya fasawa waya, dan azatonsa wayarta ce ta fashe a cikin jakar, magana yafari cikin zafin rai
"Kinga saratu, nagaji da wannan iskancin naki, tunda ni ban isa nafada miki magana kiji ba, sai abinda kawarki tace miki, kitafi gidanku, nasakeki saki biyu" yana karasawa yaja daddy suka shiga gida ya kulli....
Ita ko sai faman ihu take tana bashi hakuri, amma ko kallo bata isheshi ba... Seda ta gaji dan kanta, ta mike,da hartayi hanyar gidan bintu, sai kuma ta sake shawarar gwanda ta tafi gdn iyayenta, dan ita yanzu haushin su bintu takeji, duk sune suka sakata cikin wannan masifar, tana zamanzamanta da mijinta, gashi sun janyo mata, sukuma kowacce tana zaune da mijinta lafiya... Da wannan tunanin tafita titi harta samu abun hawa ta hau, duk da ba ko sisi ajikinta, kawai ta hau sukayi gaba...
*DUNIYA KENAN, HAKA TAKE, WANI INYAYI RAWA AN BASHI KUDI, WANI INYAYI DUKA ZAICI... INA KIRA GA MASU KWAIKWAYON MUGUWAR DABI'AR WASU, KUNGA YANDA DAI SARATU TA KARE GARIN HANGEN RAYUWAR WASU, KADA KACE LALLAI KINGA/KAGA ABINDA WANCE TAYI KICE SAI KINYI, WALLAHI TALLAHI KEDA KIKA KWAIKWAYA SAI KINFI KOWA SHIGA CIKIN MATSALA, ALLAH YA KYAUTA YA SHIRYI WAYANDA SUKA KAUCE HANYA AMEEEN YA RABBI!!!*
Tana shiga gidan sadiq tasamu a falo yana jiranta, dan tun dayaci girkin nan yakejin inba bintu ba zai iya rayuwaba, har khadija tagaji da jiran dawowar bintu tagaji tayi baccinta, shiko kasa rintsawa yayi yana jiran dawowarta...
Yana jin shigowarta ya mike da sauri ya nufota zai kai mata runguma, da sauri ta daga mishi hannu "ahhhh tsaya tsaya! Wannan kuma wani sabon salo ne zaka wani taho da saurinka zaka rungumeni, kaga malam, ka kama kanka"
"Haba swthrt, kefa naketa jira tundazu nakasa bacci, ai kya bari ko tausa ne mushiga nayi miki tunda kince a gajiye kike" seda ta kalle shi ta watsar kafin tace "naji muje, amma kafin nan ina jin yunwa, akwai abinci a gidan? Sunkuyar da kai yayi murya k'asak'asa "aiko mun cinye abincin nida khadija" zaro ido tayi "na zauna na shek'a girkina, sannann kucinyemin kaida wata yar iskar kanwarka, to seka san yanda zakayi kasamomin abinda zanci"
"Karki damu swthrt, yanzunan zan miki" hartayi gaba seta dawo "minti goma nabaka, in bahaka ba rai zai baci" bata jira cewarsaba ta shige dakinta "shikuma ya shiga kitchen,sai rawar jiki yakeyi. Jolof din taliya yadafa mata nan da nan yayi ya gama, shiga dakin yayi, kan gado yasameta, daga ita sai underwear dinta data ja sama... Durkusawa yayi yace "swthrt gashi nagama" yana ajiyewa ya zauna abakin gadon, jikinsa sai rawa yakeyi,tashi tayi ta zauna ta kalli abincin ta kalleshi "kici kiji abincin yayi dadi wallahi swthrt" tsaki tayi tace "haka ake kawo abinci a garinku babu ruwa, ba dan lemo"
"Yahakuri swthrt,mantawa nayi" yafada bashida niyyar tashi "zaka tashi kaje ka kawo min ko sena bata maka rai" tafada a dan tsawace, da sauri ya mike ya nufi fridge, seda yafita yake tunanin, meyake faruwa dashine bintu take tayi mishi haka ne, gashi wani masifar kwarjini take mishi, haka yaita sakar zuci harya dauko ya kai mata....
Zama yayi a gefenta, seda tagama cinye abincin, tasha ruwa, tasha lemo, tabi lafiyar gado, shiko yabita da tausa "swthrt ban fada miki wani abu daya faru dani ba" a gatsine tace "meye"
"An sallameni daga wajen aiki fa dazu, ina so in fada miki naga kinata sauri zaki fita" da sauri ta mik'e zaune "da gaske kake sadiq, kana nufin yanzu kwatakwata kadena aiki, baka da aikinyi" cigaba yayi da matsa mata kafa "wallahi kuwa swthrt, amma karki damu, haka Allah yayi, Allah ya taimaka ma ina da gidajen haya da shaguna, ga gidan gonata na nan dana kauye, in sha Allah kasuwanci kawai zan fadayi"
"Ehh haka ne, Allah ya rufa asiri" tana fada ta koma ta kwanta "karfa kidamu swthrt, babu abinda zaki nema da kike samu a wajena kirasa, sedai kawai yanzu abinda yarage nayi, na sami hanyar dazan fara juya kudadena" bata ce masa komai ba, dan tafada duniyar tunani ne kawai, aranta ta dunga fadin
"Sadiq yarasa aiki, tabbb, aiko zamana dashi yazo karshe, me zan zauna inyi,, tunda yanzu bawasu kudine zasu dunga shigomasa ba, yar fantamawar nan danake samu inayi, da ankwana biyu zan dena, dan wallahi idan kudi basa shigowa, wayanda yake tak'ama dasu ana kwana biyu idan muka cinyesu shikenan fa,sunana sorry, gwara tun wuri nasan inda dare yayi min, tunda yanzu akwai wasu yan kudi a wajena, kwara naje hajiya turai, tarakani wajen bokannan nata, yasamomin wani karamin alhajin, naje na aura, dan bazan iya zama gidan da babu naira ba"
Haka taita tunaninta har bacci yayi awon gaba da ita, shima sadiq baisan sanda baccin ya kwashesa ba awajen...
Washegari tunda asuba khadija ta tashi tayi sallah, sannan tayi muraja'ar qurani, hartayi ta gama ba taji fitowar daya daga cikinsu ba, hartayi wanka tayi shirinta cikin uniform din makaranta, amma babu alamar zasu tashi, gajiya tayi ta nufi dakin, kofar tafara bugawa, seda ta buga wajen sau biyar sannan sadiq ya farka, tasowa yayi ya bude kofar ya ganta a tsaye,gaisheshi tayi ya amsa sannan tace "yaya tundazu nake jiranku baku tashi ba, gashi zanyi late a scool" fitowa yayi daga dakin "am sorry sister, bamuyi bacci da wuri bane shiyasa, kinyi breakfast? Banyi ba"
To ki shiga kitchen ki hada abinda zakici, bari nayi sallah sena kaiki" zaro ido tayi "yaya yanzu bakuyi sallah ba,shine kuketa bacci, tabbb, ni bazanma iyayin bacci ba, batare danayi sallah ba" shan kunu yayi "keh! Ki kiyayeni, zaki wuce kiyi abinda nace miki ko kuwa? Wucewa tayi simsim kamar munafuka, shikuma ya juya yana "yarinya sai shegen surutun tsiya"
Tana gama yin breakfast, shima ya fito sanye da jallabiya "oya tashi muje" mikewa tayi, tana son tambayar bintu, tanajin tsoron karyayi mata masifa, haka taja bakinta tayi shiru ya kaita ya ajiye... Har ya dawo sarauniyar tashi bata motsa ba, ragowar abincin da khadija ta rage ya zauna ya cinye...
Zama yayi a falon ya kunna TV yana kallo, sai misalin 11 saura bintu ta futo daga dakin tana hamma, tawani ci daurin kirji kamar jakar kauye,kan dinning din tayi, ganin kwanuka da kofunan shayi ne ya tabbatar mata anci abinci "sadiq waya ci abinci anan" tafada tana ajiye kofin data d'aga "khadija ce dama dazan kaita skull, shine ta soya doya da kwai, ragowar shine na hada tea nasha"
"Inyee, wato ita khadija data tashi seta yi iya cikinta dana dan uwanta ko,wato ni bare, zata dawo tasameni ne a gidan" ta jawo kujera ta zauna "kiyi hkr swthrt,nima bada ni tayi ba,wanda ta ragene naci" dallah cen ni rufemin baki, wato kai mai kanwa, katashi kasama min abunda zanci"
Da hanzarinsa yatashi ya shiga kitcen, itama doya da kwan yayi mata yakawo mata, ya hada mata shayi mai kauri ya tura mata gabanta.....
Saratu kuwa koda tazo kofar gidansu, seta fashewa mai adaidaita da kuka, tana ya taimaketa bata da kudi, shiko yace baisan zance ba seta biyashi kudinsa, dan basuyi da ita taimako zaiyi mata ba, seda suka fara hayaniya har kaninta ya jiyo ya futo, dayake shagonsa yana kofar gidan..
"Ahhh lafiya meyake faruwa ne? Malam!!!!! Bai karasa ba saiyaga ashe yarsa ce "yaya saratu, daga ina kike a tsohon daren nan, ina daddy da babanshi" kuka ta fashe da shi "Sameer bani dari uku nabiya wannan mutumin kudinsa kafin mu shiga ciki" komawa yayi cikin shagon ya dauko d'ari biyu da talatin "kinga wallahi ita kadai ta rage min" ya mikawa mai adaidaitan "abokina dan Allah kayi hakuri da wannan, wallahi sukenan dani" fuzga yayi ya shiga machine dinsa yakad'a yayi gaba...
Seda suka dauki yan muntina kafin mahaifinsu yazo ya bude kofar, haskesu yayi da touch light, sukuma suka danna kai cikin gidan "tofa, saratu daga ina kike a wannan tsohon daren ina maigidan naki da takwarana? Kasa cewa komae tayi sai kuka "malam lafiya kaida suwaye? Innarsu saratu ta fada tana futowa daga dakin "futo kiganewa idonki" futowa tayi, tana ganin saratu ta rafka salati, saratu kuwa durk'ushewa tayi akan gweiwoyinta tana "kuyafemin inna, bashiir ya sakeni saki biyu"
"Inalillahi wa inna ilaihirraji'un!" Suka fada dukansu atare,mahaifinsu ne yace saratu, ki fada min gaskiya, me kika aikata har bashir yayi miki saki biyu a tsohon darennan, nasan bazai taba aikatawa ba haka kawai" share hawayenta tayi, ta kwashe komai tun farkon haduwarta da bintu, har izuwa yanzu da aka dank'ara mata saki biyu tafada musu...
Takaici ne ya cika su gaba daya, daki babansu ya shiga ya dauko wayar redio yafito yayi mata tsinan nan duka, innaru kuma kuka kawai takeyi,Sameer ne yaketa bata hakuri,duk da shima nashi ran yayi masifar baci...
Dan dakuwa saratu ta daku, dan harkasa ihunma tayi, seda yagaji dan kansa ya kyaleta "kin cucemu saratu, kin watsa mana kasa a ido, tunda aka daura min aure da mahaifinku bantaba futa bada izininsa ba,barema harnaje wajen boka, kanwarki tana cen a gdnta lfy da mijinta da yayanta, dukda itace karama amma Allah ya ruga bata miji da wuri, harseda ta haifi yaya biyu sannan Allah ya baki miji, amma gashi kinkasa zama a matsayin da Allah yayi ki, shikenan, sai kizo muzauna a gidan kici uwar dazakici.....takarasa tana fashewa da kuka, ranar haka suka kwana kowa da abinda yake sak'awa aransa, saratu kuwa nadama ce fall cikinta...
******
Bintu tana gama breakfast sega jiji da tawagar yan daudunsa, da kyar mai gadin yabarsu suka shigo, dan sadiq yataba yimishi warning inyasake bari yan daudu suka shigo masa gida to abakin aikinsa, to ba yanda ya iya tunda sun kira bintu agabansa tace su shiga. Suna rausaya kamar bishiyar zogale suka shiga falon ko sallama babu sai shewa, itama tashi tayi tana gyara daurin kirjinta "shegiya jiji, kice keda tawagarki ne" wani fari yayi da ido "Ehh wlh uwar dakina, ai cewa nayi gwara muzo har gida musameki, dan zuwa da kai yafi sak'o" jinjina kai tayi "kwarai kuwa inajinki" dama wannan yar uwar tawa ce zatayi bikin zagayowar haihuwarta, shine nace bari muzo mu rok'i arziki, zamuzo muyi a nan, sbd gdn hajiya turai yayiwa jama'armu nisa, to munyi dace ma ga mai gidan yana nan, kobashine kawun namu bane? Yafada yana kallon sadiq daya kasacewa komai illa kallo "Ehh shine, babu damuwa jiji, ai ke ta gidana ce, yaushene abun? Jibi jibi ne "ahhh kice muna da chasu" wlh kuwa uwar dakina" to muzamu wuce, yacce ake ciki mayi waya"suka mike, "kutsaya ina zuwa" ta kalli sadiq "kadan basu wani abun suyi kudin mota" mikewa yayi yana fadin to, dakinsa ta shiga ya k'irgo dubu ashirin yakawo musu "Ahhh ayi haka babban yaya, to godiya muke"seda tarakasu har bakin gate sannan ta dawo...
"Swtrt bari naje na dauko khadija a skull" harararsa tayi"to sarkin kanwa, saura kaje ka zauna, nima wanka zanyi na fita" fita yayi ya nufi makarantarsu, akasan wata bishiya yasameta kowa ya baje ya barta, ga rana da yunwa duk sun addabeta.......
*DEEE💘*
*🌚GANTALALLIYA🌚*
*Written📝*
*BY*
*DEEE💘*
*⚜🇦rewa 🇼riters🇫orum⚜*
*A. W. F*
*I.G:Arewa writers forum fans*
*• Follow us on facebook*~ _
www.facebook.com/Arewa-Writers-Forum-294302397727161/
Wannan shafin na sadaukar dashi ga dukkan readers/mosoyan littafin GANTALALLIYA, wayanda nasani, da wayanda bansani ba, Nagode da kulawarku da soyayyar da kuke nuna min,da addu'oinku gareni, Allah yabarminku❤
True life story
36-40
Kusa da ita ya karasa, a hankali ya kira sunanta "khadija" dagowa tayi a furgice, idanunta sun kad'a sunyi jawur "yaya tundazu naketa jiranka kak'i zuwa da wuri kowa ya tafi ya barni" tana karasawa ta rushe da kuka,baice mata komai ba, jan hannunta yayi suka nufi mota, seda suka shiga ya hau rarrashinta har suka isa gida...
Da gudu tafito daga motar ta nufi cikin gidan, bintu tasamu a falo sai faman waya take, da taga wayar ba mai karewa bace, ta shiga daki ta tube uniform din, tasaka doguwar riga, tadawo falon, lokacin tasamu ta gama wayar "anty sannu da gida" tace mata tana murmusawa "yawwa sannunki" ta fad'a da kyar "anty ya jikin hajiya kuwa" da sauri bintu ta kalleta "jikin hajiya kuma, wacce hajiya kenan?
"Jiya yayana yace min kinfita hajiya ba ta jin dadi, inata jiranki harnayi bacci baki shigoba, yauma harna fita baki tashi a bacci ba, amma jikin nata da sauki ko? Kallonta kawai takeyi kafin tace "shi sadiq dinne yace miki haka" dai dai lokacin yayi sallama ya shigo "yawwa sadiq, shine jiya dan nafita buk'ata ta,zakayiwa mahaifiyata karyar rashin lfy" shiru yayi baice mata komae ba,illa kallon khadija dayakeyi, itakuma khadija mamaki ne ya cikata, musmman yadda taga bintu ta rufe sadiq da masifa kuma yakasa cewa komai...
"Ina magana kayi shiru,munafuki, dama so kake hajiyata ta mutu ko, to wallahi bari kaji, sedai uwarka ta mutu ba dai..... Keh! Ya isheki duk iskancinki dazakiyi, kiyi amma karki sake kisaka mahaifiyarmu, idan ke baki da tarbiyya to mu munada..... Bata karasa ba sadiq ya dauketa da mari...
"Khadija ashe bakida kunya, a gabana kike fadawa matata haka, wallahi kinyi na farko kinyi na karshe, idan kika sake kwatanta irin haka, wallahi ranki seyayi masifar baci" dafe kumatunta tayi tana hawaye "haba yaya, ina hankalinka yatafi, a gabanka kanaji ana ciwa umma mutunci ka kasa cewa komai, to wallahi idan kai zaka dauka, nibazan dauka ba" tana karasawa ta shige daki, sadiq kuma sai wani huci yakeyi...
Kan bintu ya juya yanata bata hakuri "dalla ni ka rufe min baki, masoracin banza kawai, yarinya karama tafi karfinka, to wallahi yau koka dauketa ka mayar da ita gidansu, ko kuma ni na fita na barmuku gidan"
"Haba bintu, meyayi zafi haka,wallahi ita zata bar gidan, yanzunnan zan mayar da ita" ya wuce daki fuuuuu.... Duk abinda suke cewa tanajinsu daga daki, tana jin sanda sadiq yabar falon ta dau waya...
Hajiyarta ta kira ta labarta mata komai "hajiya nifa wannan yar iskar kanwar tasa tana neman ta ruguzamana shiri, amma nace ya kaita gida" daga cen bangaren kuma hajiyar tace "kinyi daidai,amma duk da haka zataci ubanta,bazamu barta haka ba, tunda naga alamar yar shishigi ce"
"Hajiya nifa inama tunanin zamana da sadiq ya zo karshe wallahi" zaro ido tayi "akan me,so kike ki tonawa kanki asiri nima ki tona min, d'an abinda muke samu, idan kika rabu dashi ina muka kama, ki kwantar da hankalinki, zanyiwa tufkar hanci"
"Hajiya ba wannan bane damuwata" nanta kwashe komai akan rasa aikin sadiq, dakuma shawarar data yanke, da sauri tace "haba bintu, ina wayon naki yake, ya kike abu kamar ba nonona kika sha ba, ai bakiga ta rabuwa da sadiq yanzuba, bayana da dukiyoyi da kadarori ba" bintu tace "Ehh"
"To sai kin tabbatar komai nashi yadawo hannunki sannan zaki buk'aci yasakeki, kinga da zarar ya sakeki kinada madafa, wallahi da anganki da kudinki miji ma ba wuyar samu zaiyi miki ba"
"Huuuu hajiyata, agaskiya kinkawo shawara, ni ai ban kawo haka ba, kinga kuwa yanzu yadda yake rawar kaf'a akaina, komae nace shiyakeyi, yanzu zan sameshi, a hankali zan karbe komai nashi, hajiya hatta gonarsa ta kauyensu sena karbeta, motocinsa kuwa yau dinnan zan karbe mukullan nakawo ki ajiye su a wajenki"
"Yawwa yanzu naji batu, da ai shirme kikeyi,ke idan son samu nema, gidan dakuke cikima, kisamu ki karbe takardun, yana baki takar saki musa shi a kasuwa...
"Ba saikinfada ba hajiya, kibari dai sena zo, naji yafito, nima gani nan zuwa gidan yanzu" ta kashe wayar, duk maganganun dasukeyi a kunnen khadija, mamakine yacikata, a zucuyarta take cewa "dama haka bintu take azabtar da yaya, to wallahi nayi alkawarin,bazan taba bari ta cuci yayana ba, idan da boka ta dogara, ni da Allah na dogara, in sha Allah sena lalata duk wani shiri nata" daidai lokacin sadiq ya shigo dakin...
"Keh mara kunya, ki tattara kayanki yanzunnan zan maidaki gida, tunda baki da kunya, kuma ki shirya abinda zaki fadawa umma, dan sena gaya mata abinda kikayi" bata cemasa komai ba, ta dauko jakar kayanta ta fito, a tsaye suka sami bintu a falo
"Sadiq ina buk'atar mukullayen motocin gidannan" tafada tana hara rar khadija "ki bude bedside dina,suna ciki ki dauki wadda zaki fita" wani wulakantaccen kallo tayi mai "Ehh nasan inda suke ai, hada na hannunka nake buk'ata"tafada tana nuna key din hannunsa "ok da wannan kikeson fita? To gashi, bari nina dauko wani" yafada yana mik'a mata key din, karba tayi "kaga,ku hau napep kaje ka kaita ka dawo, kullum seka fita a mota ne" baice mata komai ba ya juya ya kalli khadija datayi mutuwar tsaye "wuce mutafi"
Fita sukayi ya tarar musu napep suka dauki hanya... Harsuka isa gidan abin bintu yana ran khadija, tunda take bata taba ganin shedaniya irinta ba... Suna shiga suka samu umma tana bacci,kamar a mafarki taji sallamarsu,rungumeta tayi "ummana nayi missing dinki sosai" itama Umman rungumeta tayi "nima haka khadija ta, gidan duk babu wani dadi, dama yanzu naketa tunanin na kirashi yadawo min dake" sadiq ne ya katse hirar tasu "umma barka da yamma,ya gida"
"Lafiya lau, ya bintu" gaban khadija ne yafadi dataji an ambaci bintu "tana nan qalau, tana gaidaki" bana amsawa, tunda taki zuwa ta gaidani" sunkuyar da kai yayi "zatazo umma, aiyukane sukayi mata yawa,yauma naso muzo tare, to wannan mara kunyar yarinyar tayimata rashin mutunci" zaro ido tayi tana kallon khadija "bangane rashin mutunci ba"
Kwashe komae yayi ya fada mata, amma seya boye laifin bintu "ita khadija ce tayi haka" gyada kai yayi "wallahi kuwa umma, shiyasa na tattaro ta nadawo da ita, tunda tace bazata taba yin shiru ba"
"Ehh kayi gaskiya, gwara daka dawo da ita, kuma keda zuwa gidannan kunyi sallama, tunda rashin kunya neyake kaiki" kuka tafarayi "wallahi Allah umma....rufe mun baki mara kunyar banza, na hanaki shegen surutunnan amma kink'i ko, to zanyi maganinki, tashi kibani waje" ta mik'e da gudu ta shiga daki tanata kuka...
"Kayi hakuri sadiq, yarintane yake damun yarinyar nan, idan kaje gida kabawa bintu hakuri dan Allah" mik'ewa yayi yana fadin "to umma bakomai, zataji in sha Allah" ya wuce ya koma gida....
Basu dade da fita ba ta kwashe mukullayen motocin gaba daya da takardun tayi gidansu, hajiyar ta bawa tace ta ajiyesu a wajenta, dan kada wata matsalar ma ta taso mishi yace zai siyar,nan fa hajiya ta dage tanata bata muguwar shawara, akan kartabar Sadiq da komai, seta tabbatar ta yasheshi tass sannan ta dage yasaketa.....
Data gama da gidan hajiyar gidan hajiya turai ta nufa, ranar ita kadai tasamu a gidan babu kowa, nanfa bintu tasake kwashe komai itama tafada mata, hajiya turai ta jinjinawa shawarar da hajiyarsu bintu ta bata
"Gaskiya hajiya tayi miki dabara, dan wallahi ko tsinke kada kibarshi dashi, kinga kina futowa, wallahi kodan abin hannunki da gudu za'a aureki" seda tayi shewa tace "bari kedai, wallahi ni dan saurayi ma sabon jini nakeson aura,inji dadina son rai" suka tafa hannu "aikuwa zaki samu,idanma kina so akwai wani yaro, bakigansa ba ya hada komai, gashi bawani shekaru ne dashi ba, tuntuni nake harinsa, sedai ni kinsan bana son harka da kana nan yara ne,gashi bawani kudi kake samu ba,sedae su suci naka, da tuni na d'ana shi wallahi" gyara zama bintu tayi "haba hajiya, ai ni kawai yanzu zaki had'a mu nafara d'anawa, dan abari ya huce, sheke kawo rabon wani,idan kudi ne, karyaji komae, wallahi indai zanji dadi babu matsala" suka sake tafa hannuwa, hajiya turai kuwa take ta dauko waya ta kira number, bugu biyu ya dauka
"Hajiya turai tamu, idan naga kiranki to tasamu" seda tayi dariya tace "aiko samu ne babba ma kuwa, kaidai kawai kaxo gida ina nemanka yanzu" da sauri yace "to gani nan hajjaju"
"Yanzu zaki ganshi, dan nasan kina ganinsa angama, irin namijin da kikeso ne, yafi mijinki komae" d'aga gira tayi "wa? Nifa kidena cewa mijina, dan ni tuni nadena daukar kaina a matsayin matarsa, nagama yayinsa,sabuwar rayuwa kawai hajiya"
Suka kwashe da dariya "wai ni ina kawarki saratu" tabe baki tayi "waya sanmata ne, ni tunsanda muka rabu kota kirani taji yanaje gida, shiyasa na watsar da ita"
"Badai tasamu kan mijinta ba, kirabu da ita, zata nemeki ne inta dagule mata, dan naga ba fitacciya bace" daidai lokacin Small daddy ya shigo gidan, wato yaron da hajiya turai ta kira...
Dogo ne sosai, fari,yana da dan kauri, ga pinks lips dinsa, dagani bai wuce shikaru ashirin da biyar ba.. Falon ya shiga yazauna, kiranta yayi a waya ya shaida mata ya iso..
"To kitashi ki sauya wannan kayan, kisaka kananan kaya, dan komae naki ya futo, sannan ki boye mishi shekarunki, kinsan yaran suma sunfi son yara, sannan ki tabbatar mishi auren dole akayi miki so kike ki kashe auren kifito ki aure shi, yanajin haka kekuma zaki samu abinda kikeso"
Fitowa sukayi, bintu sanye take da wasu matsatsun riga da wando, rabin kirjinta duk sunyi waje, kai babu ko dan kwali, sai juya duwaiwaka takeyi tana turo kirji gaba, ita a dole seta jawo hankalin small daddy... Waiyazubillah abinda batayiwa mijinta na sunna, amma gashi a banza tanayiwa wani dan iska😭😭 Allah ka shiryemu...
Tunda suka zo suka zauna idonsu akan bintu yake, dan gaba daya tatafi dashi...itama bintu hakan, jitake kamar ta janyosa jikinta, gaba daya ya kwanta mata...hajiya turai tace "to small daddy,wannan kawar tawace, zan hadaku, sunanta bintu, gata dai, zan tashi nabaku waje, setayi maka bayani, na yarda da kawata bata da wata matasala...
Tana futa bintu ta koma kusa da small daddy tazauna,sai kwarkwasa takeyi "sannunka, kamar yanda hajiya tayi maka bayani, sunana bintu, matar aure ce ni, amma auren dole akayi min tunda yarintata, yanzu idan zaka amince dani, zan kashe aurena, nafito muyi aure da kai idan zaka amince" tunda take magana yake binta dawani kallo irin na haramci "bintu ai duk namijin daya kalleki, zaiso kasancewa dake har abada, abu dayane zai hana ki aurenki yanzu"
"Mainene shi? Kudi, gaskiya banida kudin da zan iya aurenki, bani dawata sana'a makaranta nakeyi"
"Karka damu small dad, kudi ba matsala bane, indai kana sona karkaji komai, komai kakeso zanyi maka" atake yakai mata wata runguma, tuni tayi accepting, tun a wajen suka fara tambadewa....
*Deee💘*
*🌚GANTALALLIYA🌚*
*Written📝*
*BY*
*DEEE💘*
*⚜🇦rewa 🇼riters🇫orum⚜*
*A. W. F*
*I.G:Arewa writers forum fans*
*• Follow us on facebook*~ _
www.facebook.com/Arewa-Writers-Forum-294302397727161/
*Wannan shafin na sadaukar da shi ga HAJIYA HINDATU, a gaskiya babu abinda zancemiki sai fatan alkairi akodayaushi, samun mace irinki a wannan lokaci abune maikamar wuya,mai halin yan aljanna, Allah ubangiji yaraya miki yaranki yasa kifi haka Ameen ya rabbi I heart you dear, muna mugun tare❤💯*
True life story
41-45
Sundade suna aikata ba daidai ba a falon hajiya turai, harseda suka gaji dan Kansu sannan suka rabu da juna..small daddy ne ya kalli bintu yace
"Gaskiya bintu ke duniya ce, ina ma ace tuntuni nasanki, wallahi da babu macen da zan kula barema harna kusanceta, gaskiya kin hadu"
"Karka damu small da, ai yanzu muka fara, kaidai kawai ka rike alkawari, duk sanda nake buk'atarka zan nemeka, kaima kuma, duk sanda kake da buk'ata ta ka kirani kawai"
Da kyar suka rabu da juna, tashiga ta dauko Jakarta, dubu ashirin ta mik'a mishi tace yayi hakuri, batasan zasu hadu yauba, yana karba sukayi sallama ya wuce, ita kuma ta koma dakin hajiya turai...
"Gasiya hajiya small dad ya hadu, na dade banji dadi irin na yau ba, ashe da cutar kaina nake danake zaune da sadeeq bai iya tabuka komai ba"wani dan iskan murmushi turai tayi
"Ai nafada miki, yaron ya san takan mace, sai dai kuma bana so kiwani dade dashi, kawai kid'ana kiwuce wajen, tunda bawani kudi zaki dunga amsa ba,saidai shi yaci naki"
"Wallahi hajiya na yarda yaci kudin, indai zai dunga biyamin buk'ata ta, ke nifa bari nafada miki, wallahi ko hajiyata bata isa tarabani da small daddy ba, ni idanma duka dukiyata yake buk'ata wallahi zan mallaka mishi, indai zai kasance tare dani"
"Lallai bintu small daddy yatafi da ke, to Allah ya barku tare, indai kina sonsa ai ba matsala"
Suna gama hirarsu bintu tayi shirin tafiya gida, tafe take a hanya tanata tunanin small daddy.... A d'aki ta iske Sadeeq ya zuba uban tagumi,yana jin shigowarta ya mik'e da sauri
"Swthrt sai yanzu, ina kika shiga haka duk hankalina ya tashi banganki ba?" Ko kallon inda yake batayiba ta wuce ta ajiye Jakarta, ta zube a gado..
"Haba swthrt ina magana...kaga kayimin shiru, dan Allah ka fita kabani waje nagaji"
"To kiyi hakuri barinayi miki tausa" dak'a mishi tsawa tayi "kaga kafita nace bana son surutu" tana fada ta koma ta kwanta, shikuma yafita yabar mata dakin yayi nashi dakin...yana futa ta mik'e ta sa key ta rufe kofar, ta koma ta dau waya, missed calls din small daddy tagani rututu, da sauri ta kirashi suka kusan kwana suna waya...
Bangaren su Umman sadeeq kuma,tunda yatafi tabi khadija daki tana mata fad'a
"Wato khadija kinzama mara kunya ko? Matar yayannaki zaki kalla kice mata bata da tarbiya"
"Ummana wallahi dan bakisan meyake faruwa bane, sam anty bintu bata kyautawa yaya,yanda na kulama saitayi fuciwarta se sanda taga dama zata dawo, Allah umma yaya yana cikin wani hali, idan shi yana jin tsoronta,mukuma bai kamata muzuba musu ido ba taita azabtar mana dashi, kalli fa yanda yadawo kamar wani tsoko, to wallahi sema kinga yanda yakeyimata, kamar ita takawosa duniya, dazuma ina ji tana waya da hajiyarta wai zasu...... Keh rufe min baki,ina rabaki da surutu kina cigaba ko, ina ruwanki da rayuwar da yakeyi da matarsa, ko ance miki ana shiga tsakanin miji da mata ne, khadija kifita a idona fa, tohm"
Takarasa maganar a tswace, khadija kuma sai kukan rashin fahimtarta da umma batayi ba takeyi, a ganinta da umma zata yarda sai su had'a kai su ruguza duk wani shirin bintu. Tunani ta shiga yi, bayan umma tafita daga dakin, cen kuma ta tsaida kukan datake yi, wata dabara tafado mata, a fili tace "yawwa hakan zanyi kawai, dan wallahi ko umma zata kasheni wlh sena lalatawa bintu komai, kuma asirinta seya tonu" tana fada ta mik'e tayi kitchen, dan yunwa takeji....
Akwana atashi bintu sun shak'u da small dadi sosai, dan har mota ta bashi, a cikin motocin sadeeq, sauran kuwa duk ta siyar, sai ta hannunta datake amfani da ita, shikuma sadeeq ko oho, idan wata yar futa takama shi, saidai yahau adaidaita sahu, ya zama mijin tace, duk abinda bintu tace mishi shiyake, gaba daya duk yabi ya lalace, yarame yayi bak'i,bashida wajen zama sai wajen masu gyaran machine din unguwarsu, mutane kuwa duk sanda yafito andunga nuna shi, masu zagin bintu sunayi, masu Allah ya shiryeta, wasuma tsine mata sukeyi,dan babu wanda baisan ita ta jefa shi cikin wannan halinba....ita kanta ummansu sadeeq tafara damuwa da halin da danta yake ciki, babu yanda ta iya tunda tasan anruga an asirce mata danta, addu'a kawai takeyi, takuma saka malamai sutayasu da addu'a Allah ya karya abinda sukayi.....
Haka rayuwata dunga tafiya, a kwana a tashi khadija ta kammala karatun secondary dinta, tayi kyau ta girma ta zama cikakkiyar budurwa, dan babu ranar daxata futa samari basu biyotaba, sai dai ita bata ko kallon inda suke, barema harta kulasu...
Wata rana ne, da yammaci umma ta aiketa ta siyo musu kuka, sanye take cikin hijabi iya gwewarta,tana tafiya cikin nutsuwa, harta isa gidan tasiyo, tana kan hanyarta ta dawowa ne, wani mayen saurayi ya dunga binta,babu yanda baiyiba akan ta shiga motarsa yakaita gida amma tak'i, shima kuma yak'i dena binta, harseda tashiga gida...
Dukda ta shiga gidan bai tafi ba,tsayawa yayi yarasa tayanda zaiyi yasamu ta fito,yana tsaye saeyaga wani yaro, "yawwa dan yaro dan Allah shiga gidannan kace ana sallama da yarinyar data shigo yanzu" dayake yaron yaga fitar ta yasan khadija yake nufi "tab, ai malam idanma zaka hakura ka hakura, indai khadija ce, wlh bama zata fito ba,bare harta saurareka" yana gama fad'a yayi gaba, dan saurayin yasake binsa da gudu
"To dan Allah kayi min sallama da wani nata, ko yayanta ko mahaifinta"
"Mahaifinsu yarasu, yayanta kuma yayi aure bama anan yakeba, sai dai mahaifiyarta" da sauri yace"Ehh dan Allah ka kira mahaifiyarta kace tayi bak'o" yaron ya amsa masa da to "ya shiga ya sanar da sakon, umma tace ya shigo daga ciki, yana fita yafad'a mishi, cikin jin dadi ya dauko kudi ya bashi sannan ya shiga gidan.........
Ina bawa masoyana hakuri akan rashin jina da bakuyi jiya ba, ayyukane sukayimin yawa, gibema bazakujini ba,sai Allah ya kaimu jibi, saboda zanyi tafiya zuwa maradi, in Allah ya kaimu lafiya zakujini jibi in sha Allah kutayana da Addu'a Nagode.
DEEE💘
*🌚GANTALALLIYA🌚*
*Written📝*
*BY*
*DEEE💘*
*⚜🇦rewa 🇼riters🇫orum⚜*
*A. W. F*
*I.G:Arewa writers forum fans*
*• Follow us on facebook*~ _
www.facebook.com/Arewa-Writers-Forum-294302397727161/
*Happy, Happy Birthday! Sister bilki I hope the day has been blessed with the presence of those you love most, and many magical moments! On your birthday, today, I wish you a year with loads of fun, excitement and beautiful memories.*
*Happy Birthday!once more again I hope its filled with love, laughs, and family..🎉🎊♥*
Dan ALLAH ina rok'on wayanda suke biyoni private na tura musu novel, dan ALLAH kuyi hakuri ku dunga tambaya a groups, karkuga bana responding, wallahi abubuwan yawa suke min, karku dauka wulakancine wallahi ba haka bane,Allah yasa kun fahimceni.😊
Wannan shafin sadaukarwane ga dukkanin masoyana na DEEE FAN'S CLUB ina godiya da soyayyar da kuke nuna min, nima ina sankon sosai da sosai, ALLAH ya barmu tare one Love❤
True life story
46-50
Cikin falon umma tayi mishi iso, seda suka gaisa, sannan yafara yi mata bayanin abinda yakawo shi
"Hajiya ni sunana usman surajo,dama ina hanyar dawowa daga kasuwa ne naga wata yarinya data shigo yanzu, to nayi kokarin ta tsaya muyi magana amma tak'i yarda, hakan yak'ara tabbatarmin da tarbiyyarta,, shiyasa ta k'ara burgeni,naji bazan iya ba senazo har gida nasami manyanta"
"Gaskiya ne,naji dadin yanda kayi, dan yarinyar nan duk saurayin da zai tsayar da ita a titi bata sauraronshi, watakila hakan dakayi, kasamu kudaidaita, amma kafin nan,kai dan ina ne?
"Ni dan asalin garin kano ne,ina tare da iyayena a unguwar taludu, kwanan nan nafara kasuwanci a kasuwar kwari, ina saida atampopi da lessina, shiyasa banyi aure ba tuntuni, amma tunda yanzu Allah yabani Sana'a kuma Alhamdulillah ina samun alheri, shiyasa hankalina ya jikkita kan aure, hajiya in har zaki bani yarinyarki, wallahi a shirye nake"
"To naji duk bayananka, sedae wani hanzari ba gudu ba,zan kira yayanta,zan fada mishi komai, inyaso seyayi bincike akai, yanda mukayi, seka dawo rana ita yau in Allah ya kaimu"
"To babu komai hajiya, amma dan Allah ina neman alfarma, kidan turo mun ita mu gaisa yanzu, kafin nadawo"
"To ba komai bari na turo maka ita" tashi tayi ta shiga ciki, a zuciyarta kuma sae yabon halin saurayin take, dan ita yanayinsa ya burgeta.... Da kyar ta lallaba khadija ta tafi wajensa, da sallama ta shiga tana tura baki, waje tasamu nesa dashi ta zauna
"Ina wuni" tafada tana turo baki "lafiya lau yan mata, ya gida" yafada yana kallonta yana murmushi "lfy" kawai tace ta sunkuyar da kai, shuru sukayi na yan muntina, kafin ya miko mata wayarsa yace
"Gashi,dan Allah ki taimaka kisaka min number ki,zamu dunga gaisawa kafin nadawo lokacin da hajiya tace" seda ta ja lokaci, sannan ta karaso inda yake ta karbi wayar, tana fara saka mishi number wayarta kira yashigo wayar.....
Ganin hoton mai kiran ne yasata zero ido, da kuma sunan dayakejiki, a fili tafada "Anty bintu! Kasanta ne" tafada tana nuna screen din wayar, har kiran ya tsinke,jikinsa ne ya hau rawa, gumi yafara keto mishi, cikin en'ena yace "ehmmm ammm wata abokiyar kasuwancina ce" a fusace tace "abokiyar kasuwancinka shine zaka sakamata sweet love" kasa ce mata komai yayi, itakuma hawayene suka dunga bin kuncinta, a fili ta dunga fadin
"Yanzu Anty bintu har saurayi gareta tana matsayin matar yayana,wannan wacce irin masifa ce, wallahi dole na tashi tsaye na farfado da yaya daga wannan masifar da bintu ta jefa shi, tun kafin ta kwaso wata cutar tazo tasaka mishi, dolenema ya rabu da ita koyanaso kobaya so" ta k'arasa maganar cikin d'aga murya....
"Haba khadija, kiyi a hankali mana, bakya tunanin idan mahaifiyarku taji hankalinta ya tashi.....kayimin shiru, mayaudarin banza mayaudarin hofi, ba hada kai ba ake haduwa a ci amanar yayana, nima kaxo zaka yaudareni, to Allah ya tona maka asiri, kuma sekayi nadama, Allah bazai barka ba" ta fashe da kuka
"Dan girman Allah khadija ki tsaya ki saurareni, wallahi sharrin zuciyane, amma wallahi nayimiki alkawarin daga yau babu ni babu bintu, amma sena fara tayaki kin cika burinki, wallahi Allah khadija da gaske nakesonki, bani da burin cutar dake a zuciyata, tunda naganki naji wani masifaffen sonki,ki taimakeni, zanyi miki bayanin komai kafin mu bullowa hanyar da zamu kwatowa yayanki hakkinsa"
Shiru tayi da kukan kafin tace "kayi alkawari zaka taimakeni mu ceto halinda yayana yake ciki" matsowa yayi kusa da ita "wallahi Khadija nayi miki alkawarin zanyi iyakacin bakin kokarina"
"To shikenan, kaga yanzu kar umma taji abinda muke cewa, kaje kawai saimuyi waya gobe, inyaso ko wani wajen ne ma hadu mu tattauna"
"To babu matsala Allah ya kaimu" sukayi sallama, koda ta koma umma taga yanayinta ya chanza, bata kawo komaiba,a tunaninta haduwarne bata sonyi.....
To wai waye wannan saurayin ne?
Small daddy ne, saurayin bintu, ko ince kwartonta, tunda suka hadu da bintu, kud'ad'en datake bashi, sune ya hadasu ya fara kasuwancinsa, dan motar data bashi ma siyar da ita yayi, yakuma sake karbe ta hannunta,dan komai ya buk'ata babu gardama take bashi.....tunda yafara kasuwancinsa yafara dauke mata wuta, dan sai sunyi zasu hadu, seya kawo mata uxuri, dan neman hanyar da zae rabu da ita kawai yakeyi,dan soyake ya gyara rayuwarsa...... Ita kuma bintu ba karamin tashin hankali ta shiga ba,kullum cikin kiransa take, wani lokacinma har kuka takeyi, gidan hajiya turai kuwa hartagaji da kai mata k'ara, dan babu abinda take cemata se "kawai ki manta dashi" sabida haka ne yasa ma ta daukewa gidan hajiya turai wuta, kullum tana kofar mata wajen hajiyarta....
Da tunanin khadija ya tafi gida, yana kuma danasanin tambadewar da sukayi da bintu, gashi yanzu yazo yana danasani, yayi imani da Allah komai zaiyiwa khadija bazata taba ganinsa da mutunci ba,gashi Allah ya jarrabeshi da sonta, yayi alwashin gobe seyafadawa khadija komae, tun farkon haduwarsa da bintu har karshe ko zae samu sauki a ransa...... Da wannan yakarasa gida, saedae kasa bacci yayi, daya rufe idonsa yake ganin khadija.....
Washegari da asubar fari khadija ta tashi, tunda tayi sallah bata koma ba, zama tayi tana ta tunanin abinda bintu takeyi, a zuciyarta ta dunga fadin "anya kuwa bintu zata shiga aljanna? Haka taita tunaninta harta gaji ta shiga kitchen ta had'a musu abinda zasuyi breakfast....
Suna cikin cin abincinne umma tace "khadija, idan kingama abinda kikeyi, zan aikeki gidan yayanki, tun jiya nake kiranshi a kashe, kuma bance kije kiyi rashin kunya ba, kinjiko? Seda ta hadiye abinci bakinta "to umma"
Daidai lokacin da suka gama ne kiran small daddy ya shigo, da sauri ta mik'e ta bar falon, seda suka gaisa sannan yace mata karfe nawa zasu hadu, ta fad'a mishi ummanta zata aiketa gidan yayanta, seyace to zaizo ya dauketa sae suje, bata amince ba,seda kyar ya shawo kanta ta amince....
Karfe 12 na rana daidai yazo ya dauketa suka tafi,suna tafe a hanya ya kwashe komai tun farkon haduwarsu da bintu yafad'a mata, babu abinda ya boye mata.... Wani nauyi kanta yayi tunda yafara magana, wani bak'in ciki da tsanar bintu da hajiya turai suka taru a zuciyarta, harma dashi small daddy yabata haushi ba kad'an ba, sedai bata nuna mishi ba..... Nesa da gidan ya ajiyeta yace taje ta futo yana jiranta, tana fita kuwa kiran bintu ya shigo wayarsa,kamar karya dauka sai kuma ya dag'a, yana dagawa tace
"Haba Cwt, menayi maka ne inata kira tun jiya kak'i dauka, meyake faruwa ne? Tabe baki yayi sannan yace "wlh baby ina cikin wani matsala ne, zan zo na dauke ki anjima, nafada miki koma menene kinji karki damu" sauke numfashi tayi "to Cwt senajika" ta kashe wayar tana jin dadi....
Khadija kuma tunda ta shiga gidan ta ganshi kamar kango, hatta mai gadi an sallameshi, babu mota ko d'aya, mamaki baigama cikata ba seda ta shiga falon taga babu kujeru babu kayan kallo, sallama ta dungayi taji shiru, gidan harwani amsawa yakeyi, ga k'ura ko ina, k'asan tail's dinma duk shatin kafafune sabida tsabar k'ura.... Dakunan ta hau dubawa amma bataga kowa ba, hakanne ya tabbatarmata babu kowa, haka ta futo tayi wajen motar small daddy...
Gaya mishi yanda ta tarar da gidan tayi, baiyi mamaki ba,dan yasan halin bintu, gida suka nufa,nan itama ta bashi labarin abinda tasani daga cikin halin bintu, hada zancen saida kadarorin sadeeq.... Bak'aramin tausayawa sadeeq yayi ba,ya kuma cemata karta damu, in sha Allah komai zai daidaita.....
"To yanzu ya kake ganin za'ayi, ta ina zamu fara" seda yadanyi tunani sannan yace "yanzu dai ta kirani tace tanason gani na, kuma nace mata ina cikin matsala,abinda za'ayi shine, anayin magariba zankirata mu hadu, zan langwabemata nace, wasu kayan kudi ne akayimin tallansu, idan har na siya ba karamar riba zanciba, amma kudine babu, kayan zasu kai million 1 da rabi.....kinga zata fara tunanin hanyar dazata samu kudin, na tabbata yanzu bata da su a hannu, idan ta fara wannan tunanin, nikuma sena bata shawarar ta dauko mun duka takardun gidajen sadeeq dana gonakinsa, sai mu sami lawyer na karya mu raina mata hankali dan naga bawani ilimine da ita ba ba ganewa zatayi ba, ina tunanin wannan shine plan na farko, yayi ko?
"Gud, abinda kafada yayi daidai, amma a ina zamu sami wanda zai hau lawyer? Kar aje a sami problem fa" murmushi yayi kafin yace "uhmm karki damu, ina da wanda zaiyi bashida matsala" daidai lokacin suka isa kofar gidan ya ajiyeta ta shiga gida, shima ya yi nasu gidan........
Deee💘
*🌚GANTALALLIYA🌚*
*Written📝*
*BY*
*DEEE💘*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*OMG!!! FROM WHERE I AM GOING TO START SELF?😍 AM OUT OF WORDS😷 MEMBER'S DIN PML A GASKIYA BABU ABINDA ZANCE DAKU SAI GODIYA DA FATAN ALKAIRI, ALLAH TUNDA NAFARA RUBUTA NOVEL BANTABA GANIN MUTANE MASU SON JUNANSU DA HADIN KAI IRIN NAKU BA, ALLAH UBANGIJI YAK'ARA MANA SO DA KAUNAR JUNANMU, MUGUN JI MUGUN GANI ALLAH YA TSARE MU DA K'UNGIYAR MU🙏🏻 AM PROUD OF YOU GUY'S😍.*
*DEDICATED TO MY 2 LOVELY💕 SISTERS, BEELKEEY SHUWERH AND SUHANA, NO NEED FOR DOGON TURANCI, YOU KNOW I HEART♥ YOU GUY'S, AND I REALLY APPRECIATE WHAT YOU DID TO ME, I WILL NEVER FORGET YOU IN MY LIFE😍 ANA TARE #ONE❤.*
TRUE LIFE STORY.
51-55
Tana shiga ta tarar da umma tana bacci, band'ak'i ta shiga ta yi alwala tayi sallah, har yamma tayi sosai, taga umma bata da niyyar tashi, d'akin ta koma ta soma tashinta.
"Umma kitashi haka, yamma tayi fah" a hankali umma ta bud'e idonta "a'a yaushe kuma kika dawo"? Zama tayi tana fad'in "tund'azu fa nashigo nasamu kinata bacci"
"Wallahi kinga, ina gama karatu bacci ya kwasheni, ya kukayi da yayan naki to"? Gyara zama tayi "ai umma babu wanda nasamu a gidan, kuma gidan a bud'e amma bakowa" tashi zaune umma tayi "bangane babu kowa gidan ba,kuma a bud'e"
"Uhmm umma wallahi da gaske, duk d'akunan nan babu kowa, kuma umma kinsan me"? Girgiza kai tayi, kafin tace "inajinki" k'asa tayi da murya "umma wallahi gidan kamar k'ongo haka yadawo, falon nan babu komai, sai datti, mai gadin ma da alamu an sallamesa"
Salati umma tayi, a zuciyarta kuma tace "kardai abinda khadija tafada min kwanaki gaskiyane, to inma haka ne gaskiya akwai matsala, dole ne nacigaba da taya yaron nan da addu'a, dan wannan matar tasa akwai alamar tambaya akanta...." Tab'atan da khadija tayi ne yadawo da ita daga tunanin da ta tafi "ummana tunanin me kike? Kodai na b'ata miki rai ne"?
Murmushin yak'e tayi "a'a khadija, bakomai, zan cigaba da kiransa, ko zan samesa" hira suka d'an tab'a kad'an,amma duk zuciyar umma babu dad'i, itama khadija kawai gata nan dai, haka dai har aka kira sallar magrib suka tashi.......
B'angaren small daddy kuwa, yana komawa gida wanka yayi, ya shirya cikin k'ana nan kaya, wayar bintu yakira, bugu d'aya ta dauka, tana d'agawa tace "Cwt ka shirya ne?" Wani haushinta ne yakama shi, amma dan kar plan dinsu ya ruguje ne yasa ya daure yace "Ehh ki shirya, yanzu zanje wani campani, ki je kiyi mana booking d'aki a prince hotel, yau kwanan dadi zamuyi" wani dad'i ne yakamata, dan tayi missing dinshi "to shikenan Cwt bari na shirya" d'if ta kashe wayar ta saki shewa, shikuma haushinta kawai yakeji....
Suna gama wayar tayiwa hajiyarta sallama tace gida zata koma, hajiyar ce ta tsaidata da magana "wai nikam bintu bazakiyi sauri ki d'ibo takardun gidajen sadeeq bane, kinga dai yanzu way'anda yasa haya duk kin kori mutanen ciki, ki dauko takardun tunda komai yana hannunki kawai mu siyar, tun kafin uwarsa, da wannan figalalliyar kanwarsa sugano halin da ake ciki"
"Hajiya siyarfa da gidajen nan ba abune mai sauk'i ba,shiyasa kikaga nayi shiru da zancen, sai munsami lawyer da shaidu" tsaki hajiyar tayi "yo wannan ae abu ne mai sauk'i, dan dai lawyer da anbasu cin hanci ai shikenan" mik'ewa tayi ta rataya Jakarta "To hajiya, kedai karki damu, komai yana hannuna, bari naje innazo gobe zamuyi magana" bata jira hajiyar tace komai ba ta fice, ita kuma hajiya sai mita takeyi "ni na rasa meyake damun yarinyar nan kwana biyu , d'an kud'in datake kawo minma tadena, kodayake yanzu fa babu abun, tunda mijin bawani aiki yakeyi ba, shiyasa nakeso tayi ta siyar da komai, yasaketa ta huta amma ta tsaya shiririta, Allah dai ya kyauta" ita kadai tayi kidanta tayi rawarta, kafin itama ta zari mayafi tayi nata *gantalin.*
Tana fita tasamu napep ta hau, kai tsaya gidanta ta nufa tasamo abin kud'in da zata siyar, dan inbanda d'ari biyun dake Jakarta babu ko sisi.... Tana isa ta tadda sadeeq ya fito daga toilet, ko kallo bai isheta ba ta wuce d'aki, dube dube ta hauyi, dan tarasa ma mai zata siyar, komai na gidan ta had'a ta siyar, dakin sadeeq ta koma ta hau bincike, cikin sa'a kuwa ta ga wani sabon agogon hannunsa wanda kud'insa zai kai dubu dari da hamsin, daukewa tayi tasa cikin zaninta, dai dai lokacin sadeeq ya biyota d'akin "madam mai kiketa nema ne?" Bata ce masa komai ba sai tsaki datayi ta fice abinta, kallo kawai yabita da shi, duk lokacin da bintu takeyi mishi irin wannan abun, yana jin wani iri a ransa, saidai yaji yakasa komai, hasalima jiyake yana kara sonta..... Fita shima yayi, yaje wajen masu gyaran machine ya zauna, dan yanzu bashida wajen zuwan da ya wuce nan......
Tana fita taje kasuwar sabon gari ta saida agogon dubu tamanin, daga nan ta wuce Prince hotel ta kama musu d'aki, kiran small daddy tayi tasanar dashi numbar d'akin, daga nan tashiga toilet domin yin wanka, dan rabonta da wanka kwana biyu kenan.....
Shiko Usman (small daddy) yana fitowa daga gida, direct gidan wani abokinsa saifuddeen ya nufa, nan ya kwashe komae game da bintu ya fad'a mishi, yakuma rok'esa akan yanaso yazo su hadu su ceto sadeeq da dukiyars daga hannun bintu, cikin sa'a ya aminta, yakuma ji tausayin sadeeq, yana la'antar hali irin na bintu, da tsari da irin su.......
Yana gamawa da abokinsa, yanufi prince hotel, akan gado yasameta, daga ita sai wata matsiyaciyar riga, wacce da ita da babu duk d'aya suke, yana shigowa ta tafi da gudu ta d'afe jikinsa "haba cwt, yazaka gujeni kwana biyu, kasan halin dana shiga kuwa?" Janyota yayi suka zauna kan gadon " babyna ban manta dake ba, wallahi wata matsala na shiga ne" d'ago kanta tayi " cwt wanne irin matsala ne wannan dakaketa fad'a, yakamata yau nasan matsalar nan" marairaicewa yayi "kinsan nace miki inaso nafara business, to wani mutumi danayiwa magana kwanaki, shine yanzu yace akwai wasu kaya da zaibani, amma kud'insu naira million 2 ne, inhar nasiya zan samu ribar datafi haka, shiyasa nashiga neman inda zan samu kud'aden nan bana so wannan business din ya wuceni, gashi har yanzu bansamu ba, hakura zanyi kawai ba rabona bane" mik'ewa tayi zaune tana nazari "haba cwt, meyasa baka sanar dani ba, kasani kozanyi wani abu akai" zaiyi magana tace "shikenan,yanzu dai banda kud'i, kuma banida wani abun kudin da zan siyar, sai takardun gidajen mijina da na gonakinsa, tun tuni naso nasiyar da su muyi aure, amma senayi tunanin dole sai da shaidu, karnaje akamani, tunda ba suna nane jiki ba"
"Baby kintabbatar takardun na gidajen mijinki ne?" Girgiza kai tayi alamar "Ehh"
"Akwai wani abokina lawyer, yana da kirki sosai, zai taimaka mana sosai, yanzu zan kirashi a waya muyi magana, amma Kafin nan, wanna gidan zamu fara siyarwa?" Da saurinta tace "Cwt dukkansu zamu siyar, kaga idan nabaka kud'in, ragowar sai muyi aurenmu, koba haka ba cwt?"
"Wowww u r d best babbyna, naji dadi, inko mukayi haka ko? Munayin aure zamu bar k'asar nan, zansami wani na dorashi kan kasuwanci na, mukuma munacen munajin dadinmu" lumshe idonta tayi "karka damu cwt, nidai idan zaka kasance tare dani, wallahi nikuma zan mallaka maka duk abinda na mallaka a duniya, yanzu ka kira shi abokin naka" wayarsa ya dauko ya kira saifuddeen, yasa a hand's free sukayi wayar kamar yanda suka shirya plan din,batare da bintu tagane komae ba, hasalima dad'ine ya cikata dataji lawyer yace gobe suzo da takardun office su sameshi.......
DEEE💘
*🌚GANTALALLIYA🌚*
*Written📝*
*BY*
*DEEE💘*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Dedicated to Fati Azaland, shafinnan naki ne kekadai ban had'aki da kowa ba,no need for long easy you knw i❤you💯 #one love♥ ana mugun tare.*🤝
TRUE LIFE STORY.
56-60
Basu suka bar hotel d'inba sai misalin sha d'ayan dare, dai dai kan kwanar gidanta ya ajiyeta, sukayi sallama akan gobe zai dawo ya d'auketa suje office d'in lawyer....
B'angaren ummansu sadeeq kuwa, kasa bacci tayi, juye juye kawai takeyi tanata tunane tunane, a zuciyarta take cewa "gaskiya gobe dole naje gidan sadeeq da kaina, na ganewa idanuwa na abinda khadija tafad'a min d'azu, yaro gaba d'aya ya canza, baya ko wai wayar inda muke" haka taita tunani har bacci b'arawo ya sace ta.....
Washe gari misalin karfe tara na safe, bintu tagama harhad'a takardun, kiran small daddy kawai take jira, tana zaune bakin gadonta ne wayarta tayi ringing, da sauri ta d'auka a zaton ta shine, sai taga bak'uwar number, d'auka tayi ta kara a kunne, "Hello waye" abinda tace kenan, daga can b'angaren kuma taji ance "haba bintu ai kya bari mu gaisa ko?" Yatsina fuska tayi "inajinka malam, dan ina da abunyi" D'if taji an kashe wayar, taja tsaki ta ajiye, bayan y'an muntina taji wani kiran yasake shigowa, ta d'auka wanda yakira d'azu ne, tana dubawa taga small daddy ne, da sauri ta d'auka, "hello cwt kataho ne?" Gyaran murya yayi kafin yace "Ehh baby, nakusa k'arasowa kifito yanzu" yana fada ya kashe wayar, aransa yace "zaki ci ubanki ne, bake y'ar iska ba," itakuma fitowa tayi, ta bar sadeeq bawan Allah sai baccin wahala yakeyi......
Kwanar da suka saba had'uwa ta sameshi dai dai lokacin ya k'araso, tabud'e gidan gaba tashige, suka nufi office d'in lawyer.....
Umman sadeeq kuwa kasa d'aurewa tayi, suna gama breakfast, tacewa khadija "khadija, nifa yanzu zantafi gidan sadeeq da kaina, dan wannan shirun nashi yafara damuna" cikin mamaki tace "umma keda kanki kuma, kibari mana ni na koma nagano miki" girgiza kai tayi "a'a kibarni naje na ganewa idona, zuwa da kai ai yafi sak'o" dariya tayi kafin tasake cewa "to shikenan hajiya umma, amma zan rakaki" kallonta tayi "babu Inda zanje dake, ki zauna kiyi mana girki kafin nadawo, sarkin son yawo,nima ba zama zanyi ba" dariya ta sakeyi "kai ummaa, to naji shikenan, idan kindawo dan Allah zanje gidansu hauwa, sai mitar bana son zuwa gidansu take min" mik'ewa umma tayi, to sedai nadawo d'in, karki sake kije ko ina sena dawo" ta amsa da "to umma, ki gaida min da yaya"
Fita tayi cikin sa'a tasamu abin hawa ya kaita gidan sadeeq, tundaga bakin gate tafara gasgata maganar khadija, tana shiga ciki, taga gaba d'aya gidan ya chanza mata, kamar ya shekara babu mutane, sallama ta rink'a dokawa amma shiru, sai cen sadeeq yafito yana hamma, wacce dagani ta yunwa ce, kallonshi ta tsaya yi kamar bata tab'a ganinshi ba, yana ganinta shima mamaki ya cikashi "ahhh umma kece da safiyar nan, Allah yasa dai lafiya?" Kasa cemasa komai tayi sai kallo, tsugunnawa yayi ya gaidata, asanyaye ta amsa
"Sadeeq wai meyake damunka kwana biyu, kadena lek'o mu, nakira wayarka har nagaji da kira kullum akashe, jiya na turo 'yar uwarka, bata sameku ba,ba kai, ba ita bintu, shine nace to bara nazo da kaina naji meyake faruwa?"
"Wallahi umma lafiya k'alau, bintu ce dama bikin wata k'awarta ya tashi, to bani da kud'in bata tayi anko da gudun mawa, shine na siyar da wayar na bata" sakin baki tayi "Ehh lallai yayi kyau, sukuma motocin gidan, da kayan falon ina kuka mayar dasu, naga gidan wayam!"
"Suma duk mun siyar dasu umma" salati tasaki da sallalami "yanzu sadeeq sabida rashin hankali,duk sai kud'auki kayan gidan ku siyar, to yanzu meye amfanin haka?" Sunkuyar da kai yayi "to umma duk kud'ina sun k'are, yanzu haka zancen danake miki, abinda zamuci babu a gidan" kasa cewa komai umma tayi, sai kallon k'urrilla da take mishi, shikuma kunya ta cikashi, umma ce ta katse shirun dacewa "to wai shin ina gidajen hayarka, da gidajen gonarka, koda kud'in bakayi wayansu abubuwan ba,mekakeyi da su?" Shiru yayi baice komai ba,seda tasake magana yace "umma duk suna hannun bintu, ita take kula dasu" runtse ido tayi ta bud'e "kana nufin takardun gidajen naka da komai suna wajenta?" D'ago kansa yayi "to umma meye dan na bata? Bintu tacika yar halak, babu macen da zata iya zama dani banda aikinyi a wannan zamanin, amma bintu bata tab'a nuna min wani abuba, tana zaune dani da dad'i babu dad'i"
"To waima yanzu ina take ita bintu, kobata tashi daga baccinbane?" Tafad'a cikin fad'a "nima tunda nashi bansata a idona ba, inaji tafita unguwa"
"Ehh lallai sai yau na tabbatar da maganar khadija, bintu ta shanyeka ta mayar da kai sha-sha-shaaa, sai yacce tayi da kai ko? Wato da safiyar nan harta fice ta barka kayi gadin gidan, jibi yanda kadawo" tafad'a tana nunashi da yatsa, "kalla gidanka kamar k'ongo, to wallahi tayi kad'an ta mayar min kai wani su-su-su, wanda tayi taje ita da Allah, amma wallahi tayi tagama, dole na d'auki mataki,kuma tun wuri idan ta dawo ka karbo min takardun gaba d'aya ka kawo min dakanka a yau d'in nan, bazaiyowu taje ta siyar dasu ba, kana nan zaune, tunda ta mayar da kai sha-sha-shaaa, to ni nafi k'arfinta wallahi"
"Haba umma, gaskiya bazan iya cewa bintu haka ba, idan nayi haka ai banmata adalci ba, yanda bintu take nuna min kuma dan zata kula min da gidajena,, shikenan kuma se kice na karb'e, ai seta cema nasa mata ido dan naga dukiyata ce" mamaki ne ya cika umma, tunda take da sadeeq bata tab'a fad'ar magana ya k'etare ba,koda kuwa ransa baya so, amma gashi akan wata ya fara musayar yawu da ita, duk da tasan aikin asirine ba'a hayyacinsa yake ba, amma abin yayi mata ciwo "Abubakar sadeeq! Tunda na haifeka, bantab'a saka ka abu ka k'iyiba, amma yau akan matarka kasakawa idanunka kwalli kagaya min k'iri k'iri bazakayi ba, ba laifinka bane, laifin matarka ne, taje ita da Allah, dan bazan tab'a yafe mata ba, kaikuma zanje nacigaba da tayaka da Addu'a Allah ya kub'utar da kai daga sharrinta, dan bintu ba alheri ce a garemu ba baki d'aya, kayi hakuri sadeeq, koni ko khadija bazamu sake zuwa inda kake ba, kaima bama buk'atarka dakazo inda muke, tunda kazab'i farincikin matarka akan nawa" ta k'arasa maganar hawaye na zubo mata, shima sadeeq kasa cemata komai yayi sai hawaye ne suke zuba a idanunsa, zuciyarsa tana wani irin rad'ad'i,shi kanshi abinda yafad'a baiji dad'insa ba, amma bazai iya fad'awa bintu abinda ummansa tace ba. Jin yayi shirune yasa umma tashi tayi tafiyarta, bai cemata k'ala ba, illa tana fita ya dunga buga kansa da bango yana kuka.....
Haka umma ta tafi gida ranta ab'ace, kwashe komai tayi tafadawa khadija, itama bataji dad'i ba, tace "amma Umma meyasa zaki ce karya sake zuwa inda muke? Ba kya tunanin abun zaiyi mishi yawa, umma kinsanfa ba laifinsa bane" tana fad'a ta fashe da kuka "nasan ba laifinsa bane, b'acin rai ne yasa nafad'i haka, amma zan dage da addua'a, in sha Allah, komai zai dai dai ta.......
Su bintu kuwa, da suka isa office din saifuddeen, bayan sun gaisa yace ta kawo takardun, small daddy ta mik'awa ya karb'a ya bashi, seda ya bisu d'aya bayan d'aya ya karanta sannan yace, "naga takardun, gidaje shida, filaye hud'u sai gonaki biyar, yanzu zaku bar wayan nan takardun, tunda jiya kace min mai su yarasu ko?" Ya fad'a yana kallon small daddy "Ehh rasuwa yayi, wannan itace iyalinsa, gadonta ne,tunda iyayensa sun rasu" ya fad'a yana nuna bintu "to babu damuwa, zaku barsu a nan, zan kaisu a chanza sunan a saka sunanta, dan gudun kar asami matsala wajen siyarwa" wata takarda ya bawa bintu yace ta rubuta sunanta tayi signing, karb'a tayi tana rawar jiki tasa sunanta tayi signing, yace sudawo nanda sati d'aya, dan mai Chanza sunan ya tafi hutu, amma nanda kwana biyar zai dawo, godiya sukayi masa, bintu harda bashi dubu biyar, baiyi niyyar karb'a ba, amma small daddy yayi mishi signal da ido ya amshe yana godiya suka fito suka kama hanya.....
"Amma cwt abokinka d'in nan yana da kirki wallahi, naji dad'in yanda yayi mana, kaga yanzu nanda sati d'aya sai mu saka komai a kasuwa ko cwt?" Kallonta yayi, yayi wani murmushin mugunta "Ehh baby, amma kafin nan, kisan yanda zakiyi sadeeq yasakeki saki uku, dan ni wallahi harnafara kishinki" kallonsa tayi cikin jin dad'i tace "karka damu cwt, dan dai saki ai kamar anyi angamashi ne, dan dama ni tuntuni na yanke wata alak'ar aure tsakanina dashi, ko kwana bamayi tare" daidai lokacin yakawota kofar gidan hajiyarsu ya ajiyeta sukayi sallama.......
Tana shiga ta kwashe labari ta bata, rangad'a gud'a hajiyar tayi tace "kice mun kusa mufaso gari" fari tayi da idanu "hmm bari hajiya, sai ma kinga wanda zan aura wallahi, ni yanzu hajiya bama wan nan ba,taya ma zan sa sadeeq ya sakeni, kinsan tunda yaci wannan abincin yake mutuwar sona, anya ko zai sakeni ta dad'i?"
"Gaskiya dai kam bazai sakeki ta dad'i ba, tashi zakiyi yanzu muje wajen mai hantiti yayi wani abun akai, yakuma kau da tunaninsa akan takardunsa, tunda yasan suna wajenki........
DEEE💘
*🌚GANTALALLIYA🌚*
*Written📝*
*BY*
*DEEE💘*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
This page is for you, Hawwe my twin sister👭 Thanks for always being there for me😍 much love sister❣.
True life story.
66-70
Ruwa aka yayyafa mishi, masu mishi firfita nayi, da k'arfi numfashin shi ya ke fita, addu'a limamin masallacin ya dunga tofa mishi, a hankali yafara bud'e idanunsa da sukayi ja jawur, mik'ewa yayi zai tashi da sauri mutane suka ririk'e shi....
Kallon su yakeyi d'aya bayan d'aya kamar wani zararre sai zare jajayen idanunsa yake yi. Da k'arfinsa ya fara magana "mai yake faruwa da ni ne? Me nayi kuka rurruk'e ni? Ku cikani na tafi gidana matata tana jirana" mamaki ne ya cika mutanen wajen, liman ne ya wakilta wa'yansu maza biyu yace su rakashi gida, rurruk'o shi sukayi suka nufi gidansa.....
Khadija kuwa tana ganin hayak'in ya gama fita ta tattara kayan gaba d'aya tasami wani buhu tasa ta k'ulle ta koma ciki ta zauna jikinta yanata rawa, dan abinda ta gani ya furgita ta sosai, zaman ta keda wuya taji ana buga k'ofar gidan, mik'ewa tayi da sauri ta nufi gate d'in, har zata bu'de sai kuma ta tsaya "waye ne" ta fad'a da k'arfi, daga wajen kuma akace "mune ki bud'e mai gidanki ne ba lafiya" dan azatonsu matarsa ce, da sauri ta bud'e k'ofar taga sadeeq shame shame, seda suka shigar da shi har falon sannan ta rakosu ta rufe k'ofar tana musu godiya.....
Da gudu ta koma falon ta zauna kusa da shi "sannu yaya, ya jikin?" Shi dai baice mata komai ba sai kallo, tashi tayi ta d'ibo ruwa ta kawo ta bashi a baki ya sha, yana gama sha yace "shiga d'akin bintu ki kirawo min ita" da sauri tace "yaya kana nufin bakasan bata gidan nan bane ko kuwa mantuwa ce kayi?" Shuru yayi na d'an wani lokaci kafin ya dafe kansa, dan wani irin ciwo yakeyi mishi, kallonsa tayi tace "yaya lafiya?" Runtse idonsa yayi "sister zo ki kaini d'aki na kwanta, jiri nakeji" tasowa tayi ta ruk'o hannunsa ta kaishi d'akinsa ya kwanta ta futo itama ta nufi d'akin datake kwana intaje gidan.....
Waya ta d'auko ta kira numbar small daddy, sai dai yayi rejecting bai d'auka ba, ajiye wayar tayi ta fara tunani kalakala, can setaji kiransa ya shigo, da sallama ta d'auka bayan sun gaisa ne ta sanar da shi komai, ya jinjina k'okarinta sosai, amma tace mai dan Allah tana son su k'ara kwana hud'u, sabida sadeeq bai gama dawowa cikin hayyacinsa ba, dole zata sake bincika gidan kozata gano wani sihirin,sannan tana so ayi mishi saukar al Qurani, ya shaida mata bakomai, ai shi yayi alk'awarin zai taimaka mata, tayi mishi godiya sukayi sallama....
*WASHEGARI*
Ko sallar asuba bai iya fita ba sabida tsabar ciwon da yakeji a jikinsa, khadija ce ta shiga d'akin ta tada shi yayi sallah, ta fita bakin layin ta siyo musu k'osai, dayake akwai y'an chanji a hannunta, dan babu komai na ci a gidan, in banda
Lipton sai ragowar shugan daya sha gari da shi jiya..... Ruwan tea ta had'a ta kawo mishi har d'aki da k'osan da ta siyo, a baki ta dunga bashi, ya ko ci sosai, tana kwashe flask d'in shayin ne da kofinan zata kai waje taji yace "sister jiya kinji shigowar bintu kuwa? Ko saida kikayi bacci ta dawo?" Ajiye kayan hannunta tayi ta zauna "yaya ai bata dawo ba, dana gaji da jira na rufe gidan na kwanta" cikin zafin rai yace "kinyi daidai khadija, dan wallahi dama bintu ta kaini wuya, nagaji da iskancinta...." Yafad'a yana maida numfashi, ruk'o hannunsa tayi "yaya kayi hak'uri kaga baka da lafiya" shuru yayi baice komai ba, ta mik'e ta bar d'akin......
Gyara gidan tayi tasss! Ta share ko ina ta gog'e ta kunna turaren wuta, k'amshin turaren dayaji ne yasa shi fitowa daga d'akin, a kwance yasameta kan kujera ta rufe ido amma ga dukkan alamu ba bacci takeyi ba, sunan ta ya Kira "khadija" bud'e idanunta tayi batare da ta mik'e ba, seda ya sake kiranta ta tashi ta zauna "na'am yaya ka fito" dai dai lokacin shima ya sami waje ya zauna "yaya ya jikin naka?"
"Alhamdulillah naji sauk'i, yanzu bana jin komai" murmushi tayi tace "to Alhamdulillah yaya harnaji dad'i" kallonta yayi yace "au shiyasa kika zo nan kika kwanta cike da damuwa, to naji sauki ai" ya k'arasa maganar cikin zolaya, nutsuwa yayi yasake kiran sunanta, itama ta maida hankalinta gaba d'aya kansa, yafara magana kamar haka....
"Khadija tunda nake a duniya bani da wani d'an uwa na jini daya wuce ke, bani da abokin shawara daya wuce umma, khadija ina cikin damuwa sosai, kuma babu wanda yakamata nafad'awa damuwata face keda umma, sai dai nakasa aiwatar da hakan, khadija kasancewarki ke yarinya ce, amma Allah yayi ki da wayo da zurfin tunani, yau zan fito fili nafad'a miki duk damuwar da take damuna kozaki iya kawo min mafuta, dan ni nayi iya tunani na, amma banga wata mafuta ba, amma dan Allah kafin nan, ina so kiyi min alk'awarin bazaki fad'awa umma ba, wannan maganar ta tsaya iya ni da ke"
"Yaya nayi maka alk'awari umma bazata ji wannan maganar abakina ba" nan ya zayyane mata duk abinda bintu takeyi mishi, tun wanda yake iya magana'a da har wanda yazama saidai ya zuba mata ido kawai, yana fad'a yana hawaye "khadija ni abinda yake bani haushi yake bani mamaki, idan nayi yunk'urin d'aukar mataki sai naji na kasa, idan nayi yunk'urin sakinta sai naji duk duniya idan babu ita bazan iya rayuwa ba, duk da irin abinda take min, tasa na mallaka mata komai nawa, kiduba kiga duk irin tarin dukiyoyina amma yanzu bani da ko tsinke, komai na gidan nan ta kwashe ta siyar inaji ina gani bani da bakin magana,ni kaina nasan inna fita nunani akeyi, yanzu ki duba kiga, bata kwana a gida ba, a sunan matar aure, wannan wace irin rayuwace, wallahi nagaji khadija sakinta nakeso nayi, amma ina neman shawarar ki a matsayinki na yar uwata dan Allah sister karki ce karna saki bintu, wallahi muguwace nagaji da zama da ita, ta cuceni ta azabtar dani" ya k'arasa maganar cikin kuka, itama kukan takeyi, a zuciyarta kuma tace "Allah sarki yaya, wannan kadai kasani, bakasan bintu har d'an iska ne da ita a waje ba, da kasan wannan ya kenan" a fili kuma tace "yaya kayi hakuri, ko wanne dan adam dama da irin jarawabar da Allah yakeyi mishi, irin taka jarabawar kenan, dan haka ina son ka share bintu, ka manta ta cikin ranka, infact kaddara ma baka tab'a saninta ba a rayuwarka, duk da nasan abune mai wahala ka manta, maganar saki kuma yazama dole ka rabu da ita ni kaina bana jin dad'in abinda takeyi, gaskiya bakayi sa'ar mata ba, mu jirata muga dawowarta,amma ka dage da Addu'a in sha Allahu komai zai wuce, amma bana so kasa damuwa aranka kaji yayana" share hawayensa yayi
"Nagode sister, in sha Allah zan tayin addu'a ita kuma zamuga iya gudun ruwanta, amma dan Allah sister ki zauna a nan karki tafi ki barni ki zauna tare da ni zanji dad'i"
"Tohm Yaya I will stay with you for a long, amma yau ina so inje wajen umma in karb'o kud'i, musiya kayan abinci, dan babu komae a gidan"
"Tohm sis, amma dan Allah karki dad'e kinji" smiling tayi tace "bazan dad'e ba yaya"
*3Days Latter*
Suna zaune suna cin abinci a falo ne bayan sallar isha'i, wayar khadija tayi ringing, ganin small daddy ne yasa ta mik'e da sauri ta bar falon, k'asa tayi da murya "goben da k'arfe nawa zaku taho" daga can b'angaren yace "bayan sallar la'ar, kin tabbatar komai noms ko?" Waigawa bayanta tayi "Ehh babu komai kudawo, nagama shirya komai" ya amsa da "to shikenan" sukayi sallama ta kashe wayar ta dawo falon tana dariya....
"Kedawa kikayi waya naga sai faman fara'a kike, kodai kinyi saurayi baki fad'a min ba?" Rufe fuska tayi tace "ni yaya bawani saurayi, Hawwe ce ta kirani muka gaisa" hara rarta yayi yace "emmm Hawwe ko? Shine ba'ayi wayar gabana ba aka tashi" shiru tayi mishi batace komai ba.
Washegari da safe suna breakfast yake cewa khadija "sister nifa yanzu naji k'arfina yadawo wallahi, ba kamar yanda nakejin kasala kwanakin baya ba" washe baki tayi "to ai haka akeso yaya, ni nasan can d'inma wasa kake da addu'a, duk da ba haka ba" kallonta yakeyi cikin burgewa, dan khadija ta iya magana "haka ne sister, gaskiya har ga Allah ina wasa da addu'a sosai, amma na dena, zan dage sosai, dan inajin ajikina akwai abinda yake damuna sosai kwanakin baya, amma tundaga zuwanki nafara samun chanji, gaskiya na gode sister Allah ya baki miji na gari" kallon shi tayi suka had'a ido tayi saurin d'auke idonta, dan duk sha k'uwar da ke tsakaninta da Sadeeq tun tana yarinya tana masifar jin tsoronshi "bakomai yayana, idan banyi maka ba wazanyi wa?" Nan suka sha hirarsu cikin kwanciyar hankali.....
Sallama sukaji ana ta zabgawa daga waje, a tare suka amsa, khadija tayi saurin mik'ewa ta bud'e k'ofar,hajiyar bintu tagani yarkace yarkace, gaisheta khadija tayi bata amsa ba ta chusa kai cikin falon, bin bayanta khadija tayi, "hajiya sannu da zuwa, yau kece a gidan namu?" Sadeeq ya fad'a yana sunkuyawa "Ehh nice, naji y'ata shiru kwana biyu, nayi kiran duniya wayarta a kashe, shine nace bari inzo ingani, tana d'akinta ne?" Ta fad'a tana nuna d'akin "hajiya ai yau kwanan bintu hud'u kenan bata gidan nan, ni kaina bansan inda taje ba, nayi zatonma ko tana gida ne" cikin masifa tace "zancen banza zancen hofi, kana nufin kace yau kwana hud'u bakasan inda bintu take ba,amma shine zaka zauna ka mik'e k'afa ko ajikinka, ko da yake ka d'auko wannan karuwar k'anwar taka kuna iskancinku a cikin gidan shiya........ "Dakata hajiya, kada ki sake jifar k'anwata da irin wannan mugun sunan, ki bar gani ke surikata ce, wallahi ina iyayin komai akan k'anwata" yafad'a cikin zafin rai "eyyyyy dole kace haka sadiq, wato borin kunya kakeyi ko, to wallahi bari kaji, mintuna goma na baka ka nemo min inda ka kai min y'ata, ko yanzu kajika a kotu,kuma wallahi sena tona muku asiri,kai ko kunya bakajiba kana lalata da yar........ Hannu ya d'aga cikin zafin rai zai k'wada d'a mata mari khadija tayi saurin ruk'e shi "au da marina zakayi, lallai ka cika mara kunya, wallahi da kasake hannunka ya zo fuska ta da ka ga karyar rashin kunya, munafukan banza muna fukan hofi, oooooo kunji kunya wallahi" ta fada tana ihu, sadeeq kuwa zuciyarsa ce take wani irin tafasa, juyawa khadija tayi ta had'a hannayenta tace " yaya dan Allah na rok'e ka kabani izinin yin magana, dan ALLAH yaya karkace nayi shiru, so nake na tabbatar mata bamune fasukai ba ya'rtace fasuka" d'aga mata kai kawai yayi alamar tayi magana, matsawa tayi ta fara magana....
"Tunda nake a rayuwata ban tab'a aikata zina ba, haka zalika yayana, muntaso cikin tarbiyya da kulawar mahaifiyarmu, bamu tab'a tsallakewa umarninta ba, sai yau akan wata banza, yar iska, *Gantalalliya* jahila, wacce batasan darajar iyayenta ba data mijinta, anyi mana k'azafi mafi muni a rayuwa, ni banma tab'a ganin jahilai dabbobi marasa kunya irinku ba a duniya,to wallahi bari kiji hajiya, kinyi k'arya ki shigo har cikin gidan yayana kice zaki kiramu da fasukai, dan ko ba mune fasukai ba yar kice fasuk'a" tafada tana nuna hajiya da yatsa, daga hajiyar har sadeeq kallon mamaki sukewa khadija da sukaji ta ambaci karuwa,dan shidai saeeq a iya saninsa bintu bata karuwanci, barta dai da gantali, k'azanta rashin son yin sallah da sauransu, k'arfin hali hajiyar tayi tace "ke yar iska, a gidan ubanki kika ga bintu tana karuwanci, wallahi sai kinyi nadamar wannan Kalmar dan ubanki" tana gama fad'a tayi hanyar fita, da sauri khadija ta shawo gabanta....
"Nafad'a bintu ce karuwa, a karuwar ma k'azamar karuwa mai bin maza tana da aure" sadeeq ta kalla tace "yaya ina so ka gafarce ni akan abinda kaji suna fitowa daga bakina, kwata kwata banyi niyyar fad'a maka ba,dan gudun bacin ranka, dan babu abinda yafi tashin hankali akan ace matar ka ta sunna tana bin wani d'an iskan da babu abinda yafika dashi, yaya tunda ka auri bintu ba kai takeso ba, kud'inka takeso, wannan shed'aniyar uwar ta tace da wata aminiyarta hajiya turai suke bin bokaye aka juya maka hankalinka, kake kyaleta tayi duk abinda taga dama baka iya cewa komai, a karshe data yi sanadiyyar rasa aikinka shine tafara shirin rabuwa da kai, yanzu haka ta ta tattara filayenka gaba d'aya ta kai ta siyar, amma Allah bai bata nasara ba" tayi shiru da maganar kafin ta cigaba hajiyar bintu tace "karya kike munafuka, wallahi duk sharrinki ya k'are akanki, y'ata ce dai dole a fito min da ita a yau dinnan, babu wani wayan cewa da zakuyi" cikin d'aga murya khadija tace 'yar ki tana Kaduna ita da d'an iskanta" wayarta ta d'auko ta kunna musu duk recording din wayar da bintu sukeyi da small daddy, tun farkon had'uwar su, harta zuwansu Kaduna, murya kuwa radau tafito, dan duk wanda yasan muryar bintu yanaji zai gane ita ce,nan khadija ta kwashe duk labarin ta da small daddy tafad'a babu abinda ta rufe, mutuwar tsaye sadeeq yayi gumi sai keto mishi yakeyi, a zuciyarsa kuma yace"yanzu abin bintu ashe ba iya gantalinta bane hada bin maza, lallai khadija tayi gaskiya da tace dole na saki bintu" khadija ce ta dafa shi yadawo daga tunanin dayake "yaya kayi hakuri, nasan na b'ata maka rai, banyi niyyar kasan wannan maganar ba,dan nasan kowaye haka tafaru da shi bazai ji dad'i ba,dole ce tasa na fad'a dan na tabbatarwa wannan jahilar matar mu ba fasukai bane, mu ya'ya ne masu tarbiyya, ba irinsuba jahilai kawai" dai dai lokacin bintu ta fad'o cikin falon.......
To kubiyoni kuji ya zata kasance ne.......
DEEE💘
*🌚GANTALALLIYA🌚*
*Written📝*
*BY*
*DEEE💘*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
Wannan page d'in Sadaukarwa ne ga dukkanin masoya littafin GANTALALLIYA da wany'anda nasani da way'anda bansani ba, a kullum ina alfahari daku, kodayaushe idan na tuna da ku ina jin farin ciki a zuciyata, ina sonku fiye da yanda kuke sona, ina muku fatan alkairi fiye da wanda kuke min, babu abinda zan iya cewa da ku sai godiya, Allah ubangiji ya barmu tare🤝. My love for you is like a ring; it has no beginning and no end.❤
True life story.
71 To 🔚
Hajiyar bintu ce tayisaurin cewa "yauwa Alhamdulillah, ga bintun nan tazo, gwanda da Allah ya kawo ki yanzu, wan nan figalalliyar yarinyar ce zata lak'a miki sharri wai kina Kaduna keda saurayin ki" tafad'a tana nuna khadija " ai ba
sharri akayi mata ba hajiya, inbanda ba kya tsoron Allah kiji wan nan muryar kice sharri ne" khadija ta fad'a a gadarance "wai meyake faruwa ne, nifa bangane mai kuke nufi ba" bintu tafad'a cikin masifa, babu wanda yayi magana, shidai sadiq a tsaye yake kamar wani gunki, dan tsabar takaici ma ya kasa magana, Khadija ce ta matsa gab da bintu tace,
"Hmmm! Munafuka macuciya, jahila, muguwa azzaluma, banza kuchaka kazamar banza karuwa kawai..... D'aga hannu tayi zata kaiwa khadija mari sadiq yayi saurin rik'e hannunta ya zabga mata mari har sau biyu, sai a lokacin yasamu damar magana,
"Ke kin isa kice zaki saka wannan kazamin hannun naki ki tab'a min k'anwa, wallahi baki isaba, kinyi kad'an, kuma bari kiji in gaya miki, duk abinda kikeyi Allah ya toni asirinki, macuciya azzaluma maciya amana, kin bani mamaki wallahi bintu, duk abinda nake miki ba kya gani, seda kika cuceni kika rabani da 'yan uwana, duk inda na fita kowa kallona yakeyi, masu tausayina nayi, masu zagina nayi, kece silar rasa aikina, amma duk wannan bai dame ni ba na cigaba da zama dake da zuciya d'aya, ashe ke duk ba haka bane daga gareki, wallahi Allah ya isa tsakanina da ke bintu, bazan tab'a yafe miki ba, ki fitar min daga gida na sakeki saki Uku" wata 'yar iskar dariya tayi tace "to sai me dan ka sakeni, aikin banza, dama me kake tsinana min a gidan in banda tsiya da talauci babu abinda kake fama da shi, Allah ya isarka kuwa babu abinda zatayi min tunda ba ubana bane kai..... Sallamar da akayi ne tasa ta dakata da magana.
Small daddy ne da abokinsa saifuddeen, tunda bintu ta shigo dama khadija ta tura mishi tex tace suzo, da kyar bintu ta had'iye yawun bakinta tace "meya kawo Ku nan? waya kirawo ku?" Ta jero tambayar a tare "saurin me kike bintu, kwantar da hankalinki mana, zakiji koma menene" khadija ta fad'a tana dariyar mugunta.
Small daddy ne ya zube a gaban sadeeq ya ruk'o k'afafunsa "Dan Allah Dan annabi d'an uwana ina neman gafararka akan hurda da na dungayi da matarka, wallahi b'ata ne da rud'in shaid'an, ina rok'on gafararka na tuba ka yafe min wallahi nayi nadama" ya fashe da kuka, tausayi ya bawa sadeeq ya d'ago shi yana cewa "abokina baka da laifi, ga babbar mai laifi, dan ba'a shed'anin namiji sai dai mace, tun farko ita ta bada kai bori ya hau, ita ta jefaka cikin wannan masifar, dan haka ni bakayi min komai ba na yafe maka" rungumeshi yayi yana godiya har seda sadeeq ya dakatar da shi.
Bintu kuwa ita da hajiyarta jiki sai rawa yakeyi, nan da nan suka shiga tashin hankali, mussaman bintu datayi niyyar fantamawa da dukiya, a zuciyarta tace "ashe guy dinnan raina min hankali sukeyi, wannan fa shi ake kira anyi ba'ayi ba"
Small daddy ne ya amso takardun a hannun saifuddeen ya mik'awa Sadeeq, yayi mishi bayanin duk plans d'in da suka had'a, wani hawayen farin ciki ne suka dunga zubowa sadeeq, dan a tunaninsa bintu ta dad'e da siyarda komai nashi, karb'a yayi yana dubasu yaga ko duk sune, mamaki ne ya sake kama shi dayaga harda gidan da suke ciki taso ta siyar, a fili yace "lallai bintu kin cika mara imani, yanzu har gidan da nake ciki kikaje ki siyar, wallahi bintu bazan tab'a yafe miki ba, nagodewa Allah da wa 'yan nan bayin Allan" ya fad'a yana nuna su small daddy "dan haka yanzu tun wuri kija uwarki kubarmin gida bana buk'atar sake ganinku a rayuwata" kuka ta farayi had'e da dariya tana "kun kyauta, cwt kaci amanata, bazan tab'a yafe maka ba, dama duk abinda mukayi da kai shiri ne ko?" Ta kwashe da dariya tana "wallahi shiri ne yayi ashe, wallahi shiri ne, shikenan sun sa yasakeni ya kwace takardun gidan ban siyarba, da na sani ashe da tun tuni naje na siyar, ashe shiri ne" ta janyo hajiyarta "hajiya mutafi kawai shiri ne sukayi" hajiya da ta fuskanci bintu ta fara zarewa ta rushe da kuka tana "dan Allah Ku taimaka min, wallahi haukacewa zatayi, Ku rufa min asiri, yanzu ina na kama" khadija ce ta dakamata tsawa "malama kija mahaukaciyar 'yarki kutafi, babu abinda zamuyi muku, ai kad'an ma kuka gani, hauka kuwa yanzu tafara shi, nan gaba tsirara zata fara yawo a titi, kafin kema kifara naki" ruk'o k'afar khadija tayi, tayi saurin hankad'ata, kuka take tana su taimaka mata amma babu wanda yaji tausayinsu, a k'arshema korar kare sadeeq da khadija sukayi musu, haka nan hajiyar bintu taja ta, ita kuma sai faman cewa take "dama shiri ne suka shirya min" haka suka tafi gida tana ta fad'a, hajiya kuma sai faman kuka takeyi tana ta shiga uku......
Rungume khadija yayi yana ta yi mata godiya "sister am out of words, wallahi kin taimakeni a lokacin da nake buk'atar taimako,badan ke ba, Allah kadai yasan halin da zan shiga nan gaba" kallonshi tayi ido cikin ido tace "you deserve brother, idan banyi maka ba, wazanyi wa? Ka godewa Allah sannan ka godewa Usman (small daddy) da friend dinshi saifuddeen" sakinta yayi yaje har gabansu yana ta godiya, saifuddeen ne ya dakatar da shi "wannan ba komai bane yaya, yanzu an ruga anzama d'aya, fatanmu shine Allah ya kiyaye gaba, sannan shawarar da zan baka yanzu, ka dag'e da addu'a, dan yanzu bamu san irin sharrin da mahaifiyar bintu zata cigaba da binka da shi ba, sannan tunda baka wani aiki, ina neman alfarmar kabani gidan gonarka na nan garin, zan dunga kula maka dashi, tunda nima bani da aikinyi, nasamu abinyi nima, gidanjen kuma asamu wasu abasu haya, kaga a hankali zaka maida arzikinka" amincewa sadeeq yayi yakuma nuna jin dad'in shawarar daya bashi, nan saifuddeen ya gabatar da usman a gunsa akan maganar auren khadija da yake sonyi, yaji dad'in hakan, amma yace zasuyi magana da ummansu......
Sallama sukayi musu, sadeeq ya rakasu har bakin gate yanata musu godiya, koda ya dawo cikin gidan yasami khadija tana sallah, da ta idar ya tambayeta sallar me takeyi, dan ba lokacin sallah bane, ta shaida mishi sallah tayi ta sake mik'a godiya ga ubangiji, sannan yayi musu tsari da dukkanin masu nemansu da shi, dad'in hakan yaji shima yaje ya d'auro tashi alwalar yayi sallah,ya mik'a godiyarsa ga ubangiji mad'aukakin sarki.......
"Yaya kaga yanda Allah yake ikon shi ko, ka duba kaga tun ba'a je ko ina ba har Allah ya fara saka maka"
"Ai dama Allah ba azzalumin bawa bane, kuma komai yayi farko zaiyi karshe, yanzu ita gashi nan ta fara zaucewa, meye ribarta a nan?"
Dariya khadija tayi tace,
"Ribarta shine ta haukace, ai wallahi kad'an ta gani, saura wannan uwarta ta"
Ta fad'a tana dariya sosai "yaya yanzu tunda an riga an gama komai, yakamata mu tattara mu koma gida mu sanar da umma"
"Nima tuna nin da nakeyi yanzu kenan, muyi sallar isha'i sai mu tafi ko?" Ta amsa da " to"
Sunayin sallar isha'i suka shirya suka tafi gidan umma..... Akan sallayarta suka sameta tana wuridi, seda suka jira ta idar, bayan sun gaisa ne Sadeeq ya kwashe komai da komai ya fad'a mata, babu abinda ya b'oye mata...... Salati umma tayi hada kukanta tana,
"Sadeeq kai kuma irin taka jarabawar kenan, Allah ya saka maka, yayi maka sauyi da mafi alkairi, ke kuma khadija Allah yayi miki albarka ya baki ladan ceton d'an uwanki da kikayi, tabbas zaman mu da ke ba k'aramin alkairi bane, sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, khadija bana son aurenki da wannan yaron usman"
Daga khadija har sadeeq sukayi saurin kallonta da sauri, sadeeq ne ya daure yace,
"Amma umma sabida me, naga ai yace ya tuba yayi nadama,kuma wallahi umma da gaske yake, na yaba da hankalin shi"
"Sadeeq dama tun kafin kuzo min da wannan maganar, nayi niyyar raba khadija da shi, tun bayan tafiyarta gidanka, nasa Malam liman yayi min bincike akan shi, ashe yaron manemin mata ne, ya lalata yaran mutane dayawa, a karshe ya koma bin wata matar aure, wacce ta ke masifar ji da shi, kud'i kuwa bata jinsu, konawa ya buk'ata ta bashi, sai da kuka fad'a min yanzu na gano ashe bintu ce matarka, to gaskiya bazan so ace khadija ta auri wanda yayi lalata da matan banza ba, koma ba haka ba, yayi tarayya da matar yayanta a waje , wannan maganar kawai a ajiyeta,abinda yayi ALLAH ya biya shi, sabida ayi haka dama Allah ya had'a su, amma ni gaskiya bana son maganar auren shi da khadija"
Gaba d'ayansu abinda umma ta fad'a ya shige su, sai dai khadija bata ji dad'in hakan ba, sabida tayi mishi alkawarin indai suka shawo matsalar zata aure shi, yanzu kuma da wanna ido zata kalle shi, duk irin k'okarin da yayi, sadeeq ne yayi magana wadda yadawo da ita daga tunanin datake,
"Haka ne umma, sai da kika fad'a na gane hakan nima, shikenan wannan ba wani abu bane, ni zan same shi nayi mishi bayani yanda ya kamata" khadija dai bata ce komai ba, umma ce tace "bari in tashi in shiga nan mak'waftan, tun da rana suka aiko min anyi haihuwa d'an ba rai ban samu naje ba, sai yanzu, ga abinci can khadija kije ki d'auko muku, sai na dawo"
Ta fad'a tana mik'ewa... Har umma ta fita khadija bata motsa daga inda take ba, dan tunda umma tayi maganar rabuwarta da Usman taji duniyar ta dena yi mata dad'i...... Sadeeq ne ya lura da hakan, gab da ita ya matsa ya mintsini kafarta tayi saurin d'agowa.
"Sabida umma tace bazaki auri usman ba, shine hankalinki ya tashi ko?" Sun kuyar da kanta tayi bata san sanda hawaye suka zubo daga idanunta ba, "subahanallah! Khadija, kardai kice min soyayyar usman ta shiga zuciyarki" ya fad'a a gigice, a hankali ta fara magana "yaya ban tab'a jin ina son usman ba, tausayinsa nakeji, da kuma alk'awarin da nayi mishi, yaya Usman yana sona sosai, baka tunanin idan ya rasa ni zai iya komawa gidan jiya"
"Ki kwantar da hankalinki sister, ni zan yiwa usman bayani yanda zai fahimta, nima saida umma ta fad'a naga bai dace ace kin auri wanda yayi tarayya da matar da nake aure a da ba, kiyi hakuri, kuma kita addu'a Allah ya kawo miki wanda ya fishi kinji sistona?" Gyad'a kai tayi tana share hawayenta, ta mik'e ta nufi kitchen ta zubo musu abinci sukaci.......
Bayan kwana biyu sadeeq ya nemi usman yayi mishi bayani kamar yanda ummansu tace, hakuri ya ruk'a bashi tare da nasihohi, duk da ran usman baiyi mishi dad'i ba amma yaji dad'in yanda Sadeeq yayi mishi bayani, bayan sun rabu ne Usman yaje yasami abokinsa saifuddeen yayi mishi bayanin yanda sukayi da sadeeq.
"Abokina kaga abinda nake fad'a maka ko, wani lokacin sai kaga kamar bak'in ciki nake maka, yanzu me bin mata ya amfana maka, gashi dai ka tuba ka dena amma ko ina shaidar da ake bayarwa akanka, kullum ina maka fad'a kai kana ganin ai waye wane, ga irinta nan ai, kana ji kana gani yanzu abinda baifi k'arfinka ba seya so yafi k'arfinka, sa'arka ma bai kwace motar da kud'ad'en da bintu take baka ba, kayi hakuri kawai, dama ba komai mutum yake samu a duniya ba, wan nan ya isa ya k'ara koya maka hankali" kuka usman yakeyi sosai yace,
"Wallahi saifuddeen ban tab'a nadamar shed'ancin danayi da mata ba sai yau, gashi dai na tuba har ga Allah amma mutane bazasu dena jifana da wannan sunan ba, yanzu inaji ina gani na rasa khadija, yarinya mai hankali da tunani ga iya magana, lallai rayuwata tazo k'arshe" yasake fashewa da kuka, saifuddeen ne ya jawo shi yaita rarraahin sa yana sakeyi mishi nasihohi har yasamu zuciyarsa ta fara hucewa........
*Bayan wata hu'du/ five months later*
Khadija ce kwance kan cinjar umma tana tsife mata kai, sadeeq ya shigo a gajiye, sallama yayi suka amsa, sukayi mishi sannu da zuwa, umma ce tace "to ya kasuwar, dagani yau ka gaji" dayake yasa haya a gidajensa, kud'ad'en kuma yafara kasuwanci a kasuwar kwari, dan yanzu shagunan sa biyu, babu abinda baya siyarwa danginsu atamfofi da less mayafai, harma da takalma, kuma abun ya karb'eshi sosai. "Ehh wlh yau nagaji sosai" dariya tayi tace to ai sai ka watsa ruwa kazo ga abinci" sauke numfashi yayi yace "ai umma sena fara ci wankan nan zai samu" dariya ce ta kwacewa khadija, yayo kanta zai buga ta b'oye bayan umma yace, "umma yarin yar nan fa nema take ta raina ni" dariya umma tayi tace "ah to ba dole ta raina kaba, ka fito da mata kayi aure ka k'i wai kai tsoro" shiru yayi baice kamai ba, dan shi a duniya ya tsani ayi mishi maganar aure, a karshema ya tashi ya bar musu falon, khadija ta sake kwashewa da dariya, umma tayi mata nuni da tadena tace "nayi shiru"
Washegari sadeeq zai tafi kasuwa khadija kuma bata tashi bacci ba umma tace "sadeeq niko ina so muyi wata magana inba sauri kake ba" gyara zamansa yayi yace "haba umma,komai saurina ai na tsaya naji uzirinki" itama gyara zamanta tayi tace
"Sadeeq ina so ka bud'e kunnenka sosai ka saurareni, kaga kai kullum girma kakeyi babu aure, nayi nayi da kai ka fidda mata kak'i, na zabo maka cikin y'an matan unguwar nan kace bakaso, to ni yanda na fuskanceka tsoron kada abinda ya faru da kai yasake faruwa kakeyi, to na yanke hukuncin had'aka da khadija, tunda itama tak'i tsaida miji, dan ba zaiyowu ba muyita jerawa da Ku a gida d'aya ba,shekarunku sunata tafiya, barema kai" tunda yaji ta ambaci khadija, yaji kansa ya d'aure d'agowa yayi yace,
"Umma naji duk batunki, amma wacce khadija kike nufi?"
"Au wace khadija kasani bayan ta gidan nan, khadija dai khadija nake nufi, ita nakeso ka aura, dan naga babu macen da ta dace ka aura in ba ita ba, kaima hankalinka yafi kwanciya, tunda dai tsoron matan kake, khadija kuwa bazata tab'a cutar da kai ba" shiru yayi yana nazarin maganar umma, kafin yace "to umma ALLAH ya tabbatar da alkairi" dai dai lokacin khadija ta fito daga ita sai sleeping dress, gashinta duk ya tashi, kallo d'aya yayi mata ya kau da kansa, dan duk rabin cinyarta a waje yake, kusa da umma taje ta zauna tace
"Yaya ina kwana" bai kalle ta ba yace "lafiya lau Dije an tashi?" Hamma tayi tace "Ehh yaya harzaka fita ne?" Ya amsa da "Ehh" yana fad'a ya mik'e yace "umma na tafi sena dawo" ya fice kafin suce "Allah ya dawo da kai lafiya" khadija ce ta kalli umma tace
"Umma yanaga yaya wani iri ne yau, ko dai zancen da baya so kikayi mishi?" Kallonta tayi tace "kwarai kuwa khadija, abun ya isa haka, kema ki nutsu ki saurareni nayi miki naki bayanin" gyara zama tayi tace "to umma" umma tayi mata bayani kamar yanda tayiwa sadeeq, kukan shagwaba khadija tasa,
"Umma ni gaskiya bazan auri yayana ba, taya ma zan kalleshi a matsayin miji, nidai umma dan Allah ki bar wannan maganar, idan auren kikeso nayi ALLAH zan fito da miji very soon, amma yanzu ni ace na auri yaya" tasake rushewa da kuka, umma tajawota jikinta
"Haba Auta ta, yanzu ba kya so ki taimaki yayanki, kinga fa duk duniya kinfi kowa shak'uwa da shi, ke kadai zaki zauna da shi tsakani da Allah, kinga dai yanda ya sha wahala a baya, shiyasa yake tsoron sake auren, amma idan kece nasan ba zaiji komai ba,inkuma kinfiso ya sha wahala shikenan seya auri wata" da sauri khadija ta rufe bakin umma,
"Umma na amince, bana so na sake ganin yaya a irin wannan halin, zan aure shi umma" umma ta rungumeta tana "Allah yayi miki albarka khadija, naji dad'in maganarki" itama kara makakkale jikin umma tayi tace "umma dan Allah zanje gidansu hawwa anjima"
"Au zakije ki bata labari ko?" Rufe fuska tayi tace "a'a umma, mun dad'e bamu had'u bane" tabe baki umma tayi "to ai bani zaki tambaya ba,kiyiwa yayanki waya, inya barki to saikije, in ya hana ni ba ruwana" turo baki tayi tace "kai umma, nidai dan Allah kice inje ba sena wani gaya mishi ba" tashi umma tayi tace "aikuma sai kiyi" ta tafi ta barta a wajen.......
Bayanda ta iya dole ta kira shi, dan tana son zuwa gidan su hauwa, d'aki ta shiga ta d'auki wayarta ta kirashi, bugu biyu ya d'auka yace "dijen gala ya akayi" kasa cewa komai tayi, seda ya sake magana tace "yaya dama umma ce tace in tambayeka, ina so zanje gidansu hawwa"
"A ina ne gidan"
"A 'yan kaba ne" zaro ido yayi yace "yanzu har 'yan kaba zaki, gaskiya ban yarda ba" marairaicewa tayi "dan Allah yaya, bazan dad'e ba"
"To naji, kije, amma idan kin yarda ki zauna har sena tashi daga kasuwa na biyo na d'aukeki" da sauri tace "na yarda" sukayi sallama ta kwasa da gudu taje ta fad'awa umma, Umman ko taji dad'i dataji yace zai zo ya d'auketa.......
Shirinta tayi tsaf taci kwalliyarta cikin riga da skert na atamfa, ba k'aramin kyau tayi ba, ga kamshi da takeyi kamar wata amarya, umma tayiwa sallama ta fita sai gidansu hauwa.....
Tana shiga suka gaisa da antyn su hawwa, ta shiga d'akinsu, tana shiga ta samu sadiya ma tana gidan, aiko suka kwashe da ihu, hawwa tace "shine ko ki fad'a mana zaki zo" zama khadija tayi tace "ai idan na fad'a miki ma ba yarda zakiyi ba" ta juya wajen sadiya tace "inyeee su Sadybaby ashe kina nan"
"Wallahi nima ban dad'e da zuwa ba, kinga kamar had'in baki" suka kwashe da dariya, suka sha hirarsu, khadija ta basu labarin had'in da akayi musu da sadeeq, dan dama bata da aiki sai basu lbrn yayanta, suka tayata murna sosai, hawwa tace,
"Wayaga su Dije a gidan sadeeq, anayin first night, shikenan zata k'ara jin tsoronshi" Sadiya ta dora da "dama yaya, bare anyi abun" suka kwashe da dariya, itakuma tace "wlh bana son iskancinku, zaku fara ko" suka sake saka dariya kafin hawwa tace "bari naje na kawo mana abinci, kar sadeeq yazo yace na bar mishi amarya da yunwa" ta fad'a cikin zolaya, ta wuce ta kawo musu abinci sukaci suka k'oshi, karfe biyar daidai sadeeq ya kira khadija yace ta kwatanta mishi gidan, tana mishi kuwa cikin y'an mintuna ya k'araso, su hawwa suka rakota sai zolayarta sukeyi......
Suna tafe a hanya babu wanda yacewa wani k'ala, har suka isa gida, da sauri khadija ta bud'e mota zata fita setaji a kulle, juyowa tayi ta kalleshi yace mata "fita mana" tsunkuyar da kai tayi bata ce komai ba, yace mata juyo ki kalle ni," da kyar ta iya d'aga kai ta kalle shi, yace "ina so ki fad'a min tsakaninki da Allah kina so na?" Daaaam!!! Taji gabanta ya fad'i, kasa cewa komai tayi yasake magana "ina magana kinyi shiru, ko umma batayi miki bayani bane?" Cikin rawar murya tace "Ehh tayi min"
"To ina sauraronki, ki fad'a min gaskiya, kar kiji kunya ki cuci kanki, idan ba kya sona, ki fad'a min, ni nasan yanda zanyi da umma"
Rufe fuskarta tayi da hannunta tace "ina sonka yaya" shima lumshe idonsa yayi ya bud'e, wani dad'i yaji ya ratsa shi dayaji abinda ta fad'a, shima yaji wani sonta yana ratsa shi, bai san sanda yace "ina sonki khadija" kunya ce ta lullub'e ta tace "yaya futsari nakeji, bud'e min in fita, seda ya kwaikwayi maganarta sanan ya bud'e mata ta fita da gudu, shikuma ya dungayi mata dariya.......
Cikin y'an watanni aka d'aura auren Sadeeq da Khadija, y'an uwansu na Bauchi gaba d'aya sun hallara, amarya khadija kuwa tayi kyau harta gaji da kyau, dinner biyu ma akayi, k'awayenta su hawwa, Sadiya, Billy, Asmeey pinkey, fatima dasu Maman junior sunyi mata kara ba kad'an ba, dan tunda aka fara bikin suka hidima, ranar da za'a kai amarya gidanta tayi kuka kamar ranta zai fita, dan jikin umma ta makale tana,
"Ummana babu abinda zance dake, sai Allah yasa kigama da duniya lafiya, kinyi min Duk abinda yakamata uwa tayiwa d'iyarta, umma Allah yasaka miki da gidan aljanna, ALLAH ya biyaki ummana, zanyi kewarki" itama Umman kuka takeyi tace "khadija Allah yayi miki albarka, Allah ya baku zaman lafiya keda mijinki, ya jikan iyayenki, kinyi min ladabi kinbini, kema babu abinda zance dake sai fatan alkairi, Allah yasa ki shiga gidan mijinki a sa'a" da kyar aka rabasu, aka kai khadija cikin mota sai faman kuka takeyi, su hawwa da Sadybaby sai rarrashinta sukeyi.......
Fad'ar tsaruwar gidan ma b'ata baki ne, dan sadeeq sabon gini yayi,irin tsarin ginin turawa a nasarawa GRA, acewarsa sabuwar amarya sabon gida sabuwar rayuwa, dangin mahaifiyar khadija da dangin mahaifinsu sai jinjinawa umma sukeyi, dan ko 'yar da ta haifa iya abinda zatayi kenan.....
Kowa ya watse saura su hawwa da su Sadybaby, dan sunce sai sun siya baki zasu tafi, ango sadeeq ya zo da abokansa, bayan an siya baki ne sukayi shirin tafiya, khadija ta ruk'o hawwa gam tana karta tafi, da kyar aka samu ta saketa tana kuka, hawwa tabi kunnenta ta rad'a mata "nasan abinda kike tsoro, kiyi hakuri, gobe zan dawo" suka wuce suka bar amarya da angota......
*Wai ina labarin bintu ne?*
Tun ranar da sadeeq ya saketa suka koma gida, ta runga hauka tuburan, ta dunga d'auko komai tasamu ta jefawa hajiyarta, harta fasa mata ido d'aya,hajiya ta sha kuka, ta shiga gida gida mak'otansu neman taimako, kowa yak'i sauraronta, haka ta hak'ura, saida ta tuna da 'yarta shamsiyya, tacire kunya taje har gidanta, ta gaya mata komai, taji tausayinsu sosai, tace zata taimaka su kai bintu gidan mahaukata, hajiya tayita godiya neman gafararta tace ba komai..... Tana komawa gida ta iske bintu tayi kashi ta zauna tana ci kamar abinci, da sauri hajiya ta nufi inda take, ta d'auki tabaryar dake gefenta ta buga mata, anan take hajiya ta fad'i tace ga garinku, bintu kuwa ta hau kanta da duka harseda ta gaji ta koma gefe tanata dariya.....
Shamsiyya kuwa koda mijinta ya dawo ta sanar da shi halin da ake ciki yace basuga ta zama ba, suka tashi suka nufi gidan, tundaga kofa suke jin wani irin wari, suna shiga suka tarar da gawar hajiya, ga bintu a gefe sai hauka take, kuka shamsiyya tasaka tana "inalillahi shikenan ta kasheta" hak'uri mijinta ya dunga bata, suka sanar da jama'a akayiwa hajiya sutura aka kaita gidanta na gaskiya, ita kuma bintu suka mik'ata gidan mahaukata, gari ya d'auka bintu ta haukace ta kashe babarta. *Gani ba wane dai ya ishi wane tsoron ALLAH*
Itakuma hajiya turai da nata asirin ya tashi tonuwa, y'an fashi ne suka shigo gidan mijinta yayi tafiya ta kawo kwartonta, suka buk'aci kud'i seda suka k'arbe mata gwalgwalnta kaf suka said bundiga suka harbe k'afa funta duka biyun, mijinta yadawo yaji labari, shima da taimakon addu'a asirin datayi ya karye, ya dank'ara mata saki uku, takoma gidansu ba ciwon k'afa, har tsutsa takeyi, seda taci wuya ta gane Allah da girma yake san nan ta mutu.
Koda saratu taji labarin abinda yafaru da su, tayiwa Allah godiya daya sota da rahamarsa tun wuri, dan ita yanzu suna zaman lafiya da mijinta.....
Shima small daddy, wata yasamu tagama jami'arta ya aureta, suna zaune lafiya....
B'angaren su khadija amarya kuwa, shak'uwa da soyayya ce mai k'arfi tasake shiga tsakaninsu, nan nan sadeeq yakeyi da ita kamar kwai.....
Shekara d'aya da aure ta haifo jaririnta santalele mai kama da sadeeq, yaci sunan baban sadeeq sunusi, suna kiranshi da sultan, rayuwa dai ta sauyawa sadeeq, jinsa yake kamar sabon mutum, sai yanzu yasan yayi aure, farincikinsa ummansa, khadija sai d'ansu sultan......
ALHAMDULILLAH ALA KULLI HALIN, DUKKAN YABO YA TABBATA GA ALLAH UBANGIJI MAD'AUKAKIN SARKI, DA YA BANI IKON FARA WANNAN LITTAFI LAFIYA, YAU KUMA NA KAMMALA SHI LAFIYA, ALLAH INA ROK'ON KA KA YAFE MIN DUK WANI LAIFI DANA AIKATA A CIKIN WAN NAN LITTAFI, KASA WAY'ANDA SUKE KARANTAWA SU FAHIMCI SAK'ON DANA KE SON ISARWA, KA BASU IKON AMFANI DASHI.....
INA MIK'A GODIYA GA DUKKANIN MASOYANA BAKI D'AYA DA SUKA BANI K'ARIN GWEWAR RUBUTA WANNNA LITTAFIN.....
UP
UP
UP
UP
UP
PURE MOMENTS OF LIFE WRITER'S, INA MIK'A GODIYA TA GAREKU, ALLAH YA BARMU DAKU YA HAD'A KAWUNAN MU, MORE ESPECIALLY, SUHANA, FATY AZLAND,BEELKEEY SHUWER AND SADNAF. MY LOVE FOR YOU IS ENDLESS❤.
Sai kunjini cikin sabon novel d'ina😊.
For more information and corrections call, 07033406410. or WhatsApp, 08177892239.
DEEE💘
Download Gantalalliya Littafi Na Daya Complete
0 Comments
Thank you for this comment