[17/12 06:24] Hajara: [10/17, 11:52 AM] MMN ABDULJLL: *💔💔IN SO CUTANE 💔💔*

*بسم الله الرحمن الر حيم*

*Fasaha Online Writers.*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

          

                  1.

       💔💔💔💔💔💔

*Godiya ga Allahu (S.W.T) mai kowa mai komai da ya bani ikon fara wnn novel cikin koshin lafiya.*
*Alhamdulillah Hamdan katheeran d'ayyiban mubarakan fiih.*

*Fatan alkhairi gareku masoya aduk inda kuke ,ku ke bani kwarin gwiwa ako wani lokaci nagode kwarai da gaske Allah ya bar k'auna.*

****** ***** *****

Da d'add'aya suke fitowa, dan zuwa ganin Wannan mai sa'a da ya sace zuciyar yayarsu har ta fita ta saurareshi.

Ba ma fitar ne yafi basu mamaki ba, sai jimawar da tayi wajen zance daga cewa bari Inga waye ne in dawo.

Kanwarta mai bi mata Nusaiba,wacce kusan kansu d'aya ita ta fara zuwa ta gaisheshi, sai Fati, itama taje da sunan taje gaisheshi, daga nan sai kannenta maza Nafi 'u da Hamza .

D'an autansu khalil ne kawai baije ba .dan shi d'an ba ruwana ne.
Gulma ajali.
Hhhh gulma harda maza.

Abinne kam da mamaki dan ko Mamansu da suke kira da Ummi ma cikin mamaki take fitar 'yar tata da rashin Dawowarta da wuri.

 Ummussalma kenan 'ya ga Mal. Abdullahi.
Mahaifin Ummussalma Babban malami ne wanda yake karantar da manyan mutane da matasa.
Har islamiyya na musamman ya bud'e kusa da gidanshi dan koyar da yaranshi da na makwabta.

Cikin ikon Allah islamiyyar ta hab'aka har daga wasu anguwanni zuwa karatu akeyi .

Ummussalma wacce aka fi kira da Salma, kunnenta kuma suke ce mata Aunty Salma, itace 'ya ta uku a wajen iyayenta amma itace mace babba a gidan.
Yayyunta biyu maza ne Allah yayi wa d'ayan rasuwa Saura d'aya wadda suke kira da Ya Al-amin. Wani lokaci su ce mishi yayanmu.

Tun tasowar ta tashi da burin ta zamo likita, ita kuwa a rayuwarta babu abinda yake burgeta irin taga nurses sanye da fararen kayannan Suna bawa mara lafiya taimako.

Sosae take son karatu dan ita a rayuwarta babu abinda ya fiye mata karatunta muhimmanci.

Tun gamawanta secondary school mahaifinta yaso ya aurar da ita amma ganin yadda ta nace kan karatu kuma bata da wani tsayayye dan ita Sam bata sauraron samari dan a ganinta b'ata lokaci ne, kuma hakan zai iya hanata karatunta yadda takeso.

Babban abinda take gudu shine, kada babanta yasan tana da wani yace zai mata aure.
Shi yasa Shima babannata ya hakura da batun aurar da ita kuma ya nema mata karatu a school of nursing.

Karatu take ba wasa dan samin cikar burin ta, kuma cikin ikon Allah tana samun nasara dan tunda ta fara bata tab'a samun matsala da karatun ba.

Duk yadda wasu suke nuna mata Suna son ta, wasu ta hanyar kannenta suke bi,wasu kuma ta wajen yayanta wasu kam direct wajen Mal. Suke zuwa da bukatarsu ta aurenta, saidai yace musu sameta Su daidaita kansu dan shikam alk'awari ya daukarwa kanshi bazaiyiwa 'yarshi auren dole ba, ko wacce zai bata dama ta zab'i wanda takeso, nashi dai yayi bincike ne idan an dace da nagari Falillahil hamdu.
Idan kuma akasin haka ne sai ya bata shawarar da zai amfaneta sai kuma ya bisu da addu'a.

Samun ta a daidaitan shine matsalar dan ko kad'an bata bada fiskar da za'a kawo mata irin wnn maganar ta soyayya.
Ko yaya mutum yaso tunkarar ta sai abin ya gagara dan Allah ya bata baiwar k'warjini, ga uwa uba d'aure fiska da takeyi idan ta fita waje, ko da mutum yayi dauriya da k'arfin halin yi mata magana ma daga kallon da Zata maka zaka San babu nasara ,gata kullum cikin zumbuleliyar hijabi ,zaiyi wuya Kaga dariyarta shi yasa Yawancin mutane suke ganin zata yi wayar shaani.

itakam haka yafi mata Dan babu wanda zai kawo mata cikas a Karatunta.

Kannenta ,Nusaiba da Fatima duk suna da masu zuwa wajensu, fatimar nema Salma take hanata fita a cewarta idan auren takeso ma ta bari sai ta K'are secondary school.
Itama Nusaiba dan ta K'are ne.

Wani lokaci haushi suke bata idan taji Suna maganar soyayya, ko kuma idan aka ce wani yazo wajensu taga suna rawan Kai.

Yawancin mutane Suna gani girman kai ke damunta ko kuma dan taga tana da kyau yasa takeyin  hakan wasu kuma cewa suke mai kud'i take son ta aura.

Saidai abin mamakin masu kud'in ma ba sauraransu takeyi ba.
Abinda basu sani bama shine ita Sam a tsarinta bata son auren mai kud'i dan gani take auren mai kud'i sawa Kai damuwa ne.
Na farko gani take kamar baza ta samu attention d'inshi yadda ya kamata ba.

Ta iya yiyuwa ta zamo kamar abokiyar gabar danginshi dan zasu sa mata ido sosae ganin d'an uwansu na da kud'i.

Gani take shi dinma zai ga kamar dan kudinshi takesonshi ba dan Allah ba.

Shi yasa take da burin idan Zata yi aure ta auri talaka d'an uwanta mai rufin asiri wanda kuma zai barta tayi aikin asibiti su zauna lafiya su rufawa juna asiri.




 *Mmn Abdul and Noorain.*
[10/17, 2:32 PM] MMN ABDULJLL: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


*By Anty Rukie.(Mmn Abduljalal.)*
    

                   2.

       💔💔💔💔💔💔


*Wannan shafi nakine Ummu D'alhat Allah ya ja kwana ya albarkaci zuri'arki baki d'aya.*


******  ******** ****

Yanzu Saura shekara guda ta gama karatunta.
Kwatsam sai Allah ya had'a ta da wanda ya shiga zuciyarta lokaci guda ba tare da ta shiryawa hakan ba.

*Love at  first sight.*

Wajen bikin kawarta suka had'u dashi,wajen dinner bikin, Allah yayi zasu had'u dan ita ba mai zuwa ire iren guraren bane.

Kallo farko suka yiwa juna saida zuciyarsu ta amsa lokaci guda, tun da take a rayuwarta bata tab'a jin abinda taji game da shi, bata tab'a ganin mutumin da ya burgeta lokaci guda  kamar shi ba.

AHMAD kenan, yaro d'an kwalisa.
Maraya ne mahaifinshi duka biyu sun rasu a gidan yayanshi babba yake da zama.

D'an kasuwa ne , ya fara saida 'yan kunne daga kad'an kad'an Allah yasawa  abin albarka har ya bud'e babban shago a kasuwar jalingo. A hankali yanzu har Allah ya albarkaci sana'ar shaguna uku yake dasu.

Asalinsu yan Gassol local govt ne, Rasuwan iyayenshi yasashi Dawowa jalingo da zama gun d'an uwanshi.

Iya secondary school ya tsaya a matakin karatu, dan gidansu basu bawa karatu muhimmanci ba Sam, sun karkata ga noma, da sana'a.

Idan ka ganshi Sam baza Kayi tsammanin baiyi zurfi a karatu ba dan kud'i da wayewa Sun sashi ya goge.
Kyakkyawan saurayin dogo fari, mai d'an fad'i.
Yana da bille a fiskarshi na gado, duk yaran gidansu Suna da irin wnn billen, sosae bille ya masa kyau kamar dama dashi aka halicce shi.

Tun daga lokacin da suka had'u yake zuciyarshi na harbawa, so yake ya mata magana amma kwarjininta ya hana shi har aka gama biki aka watse.

Lokacin da zasu watse yabi bayanta dan ya samu magana da ita unfortunately sai ya ganta tare da wani Sun kama hanyar tafiya.

Hankalinshi ba k'aramin tashi yayi dan duk a zatonshi saurayinta, sai bayan ta tafi yake tambaya aka ce mishi yayanta ne, tare suka zo, da ya Al -amin da yake ba jimawa sosae za'a yi ba ya jirata suka koma tare .

Bai bar wajenba sai da ya samu cikakken adress d'inta da sunanta,  har da fatan Allah ya bada saa ango ya mishi dan yasan halinta Sarai ba lallai bane ya samu karb'uwa.

Suka k'ara da ce mishi sai fa yayi da gaske dan bata sauraron kowa idan yayi hakuri da halin wulakancinta watakil yayi nasara.

Cikin d'oki yake cewa in Allah ya yarda ma zaiyi nasara, dan yana gani itace first and last love d'inshi.

Har cewa yayi bari yabi bayansu yanzu yaga gidansu.

Cikin dariya angon yace, "Me ma sunanka? "

Kamar jira yake yace ,"Salman. "

Dariya aka ta mishi a wajen wato har ya tashi daga Ahmad ya koma SALMAN.

"To Salman, abi a hankali kada zarbabin yayi yawa kaje kuma ka rasa abunda zaka ce mata. "

Cewar wani daga cikin abokansu.
Dariya sukayi dukansu cikin sauri ya juya yana cewa "Allah ya bada zaman lafiya ango nima na tafi neman aure.

A hankali yake binsu da mota har kofar gidansu, sai da yaga Shigansu snn ya koma.

Koda ya komama babu abinda yake gani sai fiskarta duk da baiga fara'a ba kokadan a tare da ita amma shi dai ta mishi a hakan.

A b'angarenta kuma tunda suka bar wajen tunanin wnn saurayin da taji an kira shi da Ahmad yake manne cikin zuciyarta, duk wani motsi nata fiskarshi take gani, tad'inma da sukeyi da yayanta yawanci shi yakeyi dan hankalinta na kan AHMAD.

Bai kawo komai ba yayi tunanin gajiyar biki ne ya maida ita shiru shiru.

A wajen bacci ta dad'e tana tunanin shi da duk wani action d'inshi da yayi a gun haka yake mata yawo a ido kamar film take Kallo.

Kwana tayi tana mafarkinshi kamar yadda Shima hakan ta kasance gareshi.

Hakan yasa Washegari da sassafe ya je kofar gidansu yayi parking a d'an nesa da gidan kad'an yana kallon k'ofar kamar yana jiran fitowarta.

Ya dad'e a zaune a gun yana tunanin ya aika a kira mishi itane ko ya bari sai zuwa anjima.

Fitowa tayi sanye
da uniform d'inta na school of nursing farare tass wando da riga, sai babban hijabin da ta d'aura kan uniform d'in, kafarta sanye da bak'in takalmi sau ciki.

Binta yayi da Kallo ,duk da ba kwalliya a fiskarta ta mishi kyau dan kyawunta naturally ne.

Chocolate colour ce, ba za'a sata sahun farare  tass ba bata kuma cikin bakake, ba za'a sata a sahun farko na kyawawa ba amma Sassanyar kyau gareta. Baza a iya gane dirin da Allah ya mata ba dan kullum cikin lullub'e jikinta takeyi da hijabi.

Nitsuwarta yake k'ara fizgar hankalin duk wani mutumin kirki zuwa gareta.

Ji yake kamar ya fito ya mata magana amma kwarjininta ya hana shi.

A nitse take tafiya har sai da yaga ta d'an yi nisa snn Shima ya tada motarshi ya bita a hankali.

Har ya isa kusa da ita da zummar yi mata magana amma ganin  yanayin fiskarta ya dakatar dashi.

A daidaita ta tara ta shiga snn ta sanar da shi inda zataje.
Har suka isa bai daina binsu ba.

Tana fitowa tasa hannunta cikin hand bag d'inta Zata biya kud'i, sai ganin mutum tayi.....





*Mmn Abdul and Noorain .*
[17/12 06:24] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


*By Anty Rukie.(Mmn Abduljalal.)*
    

                   2.

       💔💔💔💔💔💔


*Wannan shafi nakine Ummu D'alhat Allah ya ja kwana ya albarkaci zuri'arki baki d'aya.*


******  ******** ****

Yanzu Saura shekara guda ta gama karatunta.
Kwatsam sai Allah ya had'a ta da wanda ya shiga zuciyarta lokaci guda ba tare da ta shiryawa hakan ba.

*Love at  first sight.*

Wajen bikin kawarta suka had'u dashi,wajen dinner bikin, Allah yayi zasu had'u dan ita ba mai zuwa ire iren guraren bane.

Kallo farko suka yiwa juna saida zuciyarsu ta amsa lokaci guda, tun da take a rayuwarta bata tab'a jin abinda taji game da shi, bata tab'a ganin mutumin da ya burgeta lokaci guda  kamar shi ba.

AHMAD kenan, yaro d'an kwalisa.
Maraya ne mahaifinshi duka biyu sun rasu a gidan yayanshi babba yake da zama.

D'an kasuwa ne , ya fara saida 'yan kunne daga kad'an kad'an Allah yasawa  abin albarka har ya bud'e babban shago a kasuwar jalingo. A hankali yanzu har Allah ya albarkaci sana'ar shaguna uku yake dasu.

Asalinsu yan Gassol local govt ne, Rasuwan iyayenshi yasashi Dawowa jalingo da zama gun d'an uwanshi.

Iya secondary school ya tsaya a matakin karatu, dan gidansu basu bawa karatu muhimmanci ba Sam, sun karkata ga noma, da sana'a.

Idan ka ganshi Sam baza Kayi tsammanin baiyi zurfi a karatu ba dan kud'i da wayewa Sun sashi ya goge.
Kyakkyawan saurayin dogo fari, mai d'an fad'i.
Yana da bille a fiskarshi na gado, duk yaran gidansu Suna da irin wnn billen, sosae bille ya masa kyau kamar dama dashi aka halicce shi.

Tun daga lokacin da suka had'u yake zuciyarshi na harbawa, so yake ya mata magana amma kwarjininta ya hana shi har aka gama biki aka watse.

Lokacin da zasu watse yabi bayanta dan ya samu magana da ita unfortunately sai ya ganta tare da wani Sun kama hanyar tafiya.

Hankalinshi ba k'aramin tashi yayi dan duk a zatonshi saurayinta, sai bayan ta tafi yake tambaya aka ce mishi yayanta ne, tare suka zo, da ya Al -amin da yake ba jimawa sosae za'a yi ba ya jirata suka koma tare .

Bai bar wajenba sai da ya samu cikakken adress d'inta da sunanta,  har da fatan Allah ya bada saa ango ya mishi dan yasan halinta Sarai ba lallai bane ya samu karb'uwa.

Suka k'ara da ce mishi sai fa yayi da gaske dan bata sauraron kowa idan yayi hakuri da halin wulakancinta watakil yayi nasara.

Cikin d'oki yake cewa in Allah ya yarda ma zaiyi nasara, dan yana gani itace first and last love d'inshi.

Har cewa yayi bari yabi bayansu yanzu yaga gidansu.

Cikin dariya angon yace, "Me ma sunanka? "

Kamar jira yake yace ,"Salman. "

Dariya aka ta mishi a wajen wato har ya tashi daga Ahmad ya koma SALMAN.

"To Salman, abi a hankali kada zarbabin yayi yawa kaje kuma ka rasa abunda zaka ce mata. "

Cewar wani daga cikin abokansu.
Dariya sukayi dukansu cikin sauri ya juya yana cewa "Allah ya bada zaman lafiya ango nima na tafi neman aure.

A hankali yake binsu da mota har kofar gidansu, sai da yaga Shigansu snn ya koma.

Koda ya komama babu abinda yake gani sai fiskarta duk da baiga fara'a ba kokadan a tare da ita amma shi dai ta mishi a hakan.

A b'angarenta kuma tunda suka bar wajen tunanin wnn saurayin da taji an kira shi da Ahmad yake manne cikin zuciyarta, duk wani motsi nata fiskarshi take gani, tad'inma da sukeyi da yayanta yawanci shi yakeyi dan hankalinta na kan AHMAD.

Bai kawo komai ba yayi tunanin gajiyar biki ne ya maida ita shiru shiru.

A wajen bacci ta dad'e tana tunanin shi da duk wani action d'inshi da yayi a gun haka yake mata yawo a ido kamar film take Kallo.

Kwana tayi tana mafarkinshi kamar yadda Shima hakan ta kasance gareshi.

Hakan yasa Washegari da sassafe ya je kofar gidansu yayi parking a d'an nesa da gidan kad'an yana kallon k'ofar kamar yana jiran fitowarta.

Ya dad'e a zaune a gun yana tunanin ya aika a kira mishi itane ko ya bari sai zuwa anjima.

Fitowa tayi sanye
da uniform d'inta na school of nursing farare tass wando da riga, sai babban hijabin da ta d'aura kan uniform d'in, kafarta sanye da bak'in takalmi sau ciki.

Binta yayi da Kallo ,duk da ba kwalliya a fiskarta ta mishi kyau dan kyawunta naturally ne.

Chocolate colour ce, ba za'a sata sahun farare  tass ba bata kuma cikin bakake, ba za'a sata a sahun farko na kyawawa ba amma Sassanyar kyau gareta. Baza a iya gane dirin da Allah ya mata ba dan kullum cikin lullub'e jikinta takeyi da hijabi.

Nitsuwarta yake k'ara fizgar hankalin duk wani mutumin kirki zuwa gareta.

Ji yake kamar ya fito ya mata magana amma kwarjininta ya hana shi.

A nitse take tafiya har sai da yaga ta d'an yi nisa snn Shima ya tada motarshi ya bita a hankali.

Har ya isa kusa da ita da zummar yi mata magana amma ganin  yanayin fiskarta ya dakatar dashi.

A daidaita ta tara ta shiga snn ta sanar da shi inda zataje.
Har suka isa bai daina binsu ba.

Tana fitowa tasa hannunta cikin hand bag d'inta Zata biya kud'i, sai ganin mutum tayi.....





*Mmn Abdul and Noorain .*
[17/12 06:24] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*

       *F.O.W.*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*


                3.

        💔💔💔💔💔💔

*Kun jini kwana biyu shiru ,wayar ce ta d'an samu matsala t goge min duk typing  da nayi ,so bear with pls my lovely fans.*
***      ***    ***

Ganin mutum tayi yana mikawa mai napep kud'i ,ga kamshin turarensa da ya bud'ad'e wajen.

Yana kokarin bashi canji ya mishi alama da hanu ya barshi ya tafi .

Hanun ta fara bi da kallo a hankali har ta sauke idanunta kan kyakkyawar fiskarsa.
Rass taji kirjinta ya amsa.
Shine.
To me ya kawo shi nan ?

Kallonshi ta tsaya yi ,sanya yake da shadda dark brown colour , d'inkin half jamfa ,kalar kayan ya dad'a haska fatarshi.

Hannayenshi duka biyu ya zura cikin aljihu yana kallon wani wajen .

A hankali ta juya ta kama tafiya tana jin wani irin yanayi a tattare da ita.

Ajiyar zuciya ya sauke snn ya bita da kallo, a ranshi cewa yake ashe da gaske suke cewa saiya yi da gaske zai iya  yi mata magana, dole ma ya cire fargabar da yake ji ya mata magana.

Binta yai a baya har ta shiga cikin makarantar.
Yana kallonta ta zare babban hijabin da ke jikinta, 'ya karamar farar hijabi ta bayyana ,tsawonta iya kirji.

Wani irin takaici yaji ya rufe shi.
Yanzu a haka zata tsaga cikin mutanen ajinsu ta shiga.

Yanzu haka kullum take yi ,kuma tayi yawo cikin makarantar kowa yana gane masa ita.

Take yaji wata matsananciyar kishinta lullub'eshi.

Tsaki yaja lokacin da yaga ta shige cikin class.
A bayyane yace "Meye amfanin irin haka."
Ya kuma jan 'yar guntuwar tsaki.

Ya jima tsaye gun yana ta sak'a da warwara daga k'arshe dai ya bar gurin ya tafi sabgoginshi.

Haka ta wuni da tunaninshi da mamakin abinda ya yi d'azu.

Duk abinda takeyi yana manne cikin zuciyarta ,hotonshi ke mata yawo cikin idon zuci.

***    ***  ***

Napep ne ya sauketa kusa da masallacin kofar gidansu.

Hanyarta ta shiga gida jikinta ya bata ana kallonta ,hakan ya sa ta d'an dubi  gefenta.

Karap suka had'a ido a tare kuma suka kawar da kansu.
"Inna lillahi "tace tana dafe kirjinta dake bugawa da sauri.

Sauri ta kara ta shige cikin gida tana maida numfashi.
Mutuminnan fa yana so ya mata illa.
Dan baisan yadda takeji idan ta ganshi bane da ko da wasa bazai rika zuwa kusa da inda take ba.

Bata ankara ba taji an amshe jakar hanunta ,dubawan da zatayi taga Nusaiba ce tsaye a gabanta tana kallonta tamkar maison jin wani abu daga gareta.

D'aure fiska tayi snn tace "Ya dai."

"Ke zanma wnn tambayar aunty Salma, kin shigo kamar an jefo ki ,snn kuma kika tsaya kika kurawa waje d'aya ido, me ya faru."

Nuna kanta tayi da yatsarta "Ni d'in?"

"Muje ki huta da alama gajiya tayi miki yawa likita."
Nusaiba tace ba tare da ta amsa mata waccar tambayar ba.

Tare suka shiga d'akin ta tub'e uniform ta shiga wanka amma zuciyarta fal tunani.

Bayan fitowarta Faty ta shigo mata da abincinta na rana ,duk da yamma tayi amma ta saba takan d'an tab'a kafin taci na dare.
Amma yau ko sha'awar cin abincin batayi.

Tsura mata ido Nusaiba tayi can tace "Aunty meke damunki sam ban gane miki ba."

Basar da tambayar tayi tace "Ina Ummi Faty."

"Tana d'akinta "tace gami da ficewa dan itakam ba mai yawar magana bace Nusaiba ce mai surutu ,ga san jin kwakwaf.

Ganin da tayi baza ta samu bayanin da takeso gun auntynta ba yasa "Allah ya baki hakuri ."
Ta tashi ta fita itama.

Binta Salma tayi da kallo snn ta d'an murmusa ,a hankali ta ce,"Kusasu."

Jingina tayi da jikin gado taci gaba da tunaninta.

***    ***    ***

Tsaye yake yana mamakin kanshi da kanshi.
Wannan wace irin yarinyace haka?
Kwarjininta yayi yawa.

Shawara ya rikayi da zuciyarshi.
Shin ya aika ta fito ne ,ko ya hakura sai gobe.

Dafe kanshi yayi yana magana shi kad'ai.
"kada kuma na aika ta fito na gagara yi mata magana.
Gaskiya da naji kunya yarinya karama."
Shi kad'ai ya kuma cewa kanshi "Ka tabbata zata fito d'inne tukuna."

Murmushi yayi ya kuma cewa tunda na ganki ma yayi ba sai na aika ba.

Shiga motarshi yaja ya tafi zuciyarshi fal tunanin yadda zai b'ullowa al'amarin.



*Mmn Abdul &Noorain.*
[17/12 06:24] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*

       *F.O.W.*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*


                4.

        💔💔💔💔💔💔


Halima Auwal .(Mmn Aysha)
Maryam A.I Gital.
Teemerlurv.
Khairat Up .
Mamyn Najma.
Fashuna.
Hawwer (Autar Fasaha.)
Aysha Ali Garkuwa.
Raheenat.
Aisha s.Bayero (Kalar Gayu.)
Rahmat Nalele (Samareen Bana)
Xaynab 💤(Rouky Pinky.)
Ummin Weedyan .
Dss.

*Fasaha grp nvl members muna alfahari daku ,Allah ya kara baseera fasaha da zakin hanu.*

****    ****   ****


Har Ummi ta shigo d'akin ita a tunaninta ko Salma bata jin dad'ine dan tasan ko yaya in ta dawo sai ta nemeta sun gaisa. Amma yau shiru.

"Ummulu yau kuma lafiya kika zauna cikin d'aki shiru."

Kakaro murmushi tayi snn tace "Lafiya lau Ummi sannu da gida."

"Yauwa sannu ,amma me ya ajiyeki cikin d'aki kikayi shiru haka."
Ta tambaya tana naxarin 'yar tata.

"Ba komai Ummi yau munyi wani practical ne mai wahala, na gaji da yawa ne."
Hhhhhh Practical indeed Aunty Salma."

"Sannu ,Allah ya albarkaci karatun ,yasa ya amfani al'umma."

"Amin Ummina ."
Tace tana murmishi dan sosae take jin dad'in addu'ar da Umminta ke mata ko wace rana.

Kiran sallar Magrib da taji anayi ne ya tayar da ita daga inda take zaune.

Abincin daren ma dan kada Ummi tayi tunanin wani abu yasa ta daurewa taci.
Ga kuma 'yar sa ido Nusaiba.

Haka yau ma ta kwana mafarkinshi .
Har mamakin kanta take ji ,wai ita ce ta fad'a ,ta tsunduma cikin kogin son wani wanda bai furta mata kalmar so ba.

Dauriya kawai takeyi kada a fahimci halin da take ciki har ta shirya ta fita dan tafiya makaranta.

Ko da ta fita sai da ta tsaya ta tsurawa inda ta ganshi jiya ido kamar an ce mata zai b'ullo ta ganshi.

Abinda bata sani ba shine yana daga nesa yana kare mata kallo.
Ganin tsayuwar bazata k'areta da komai ba yasa ta kama hanyar tafiya inda zata samu abin hawa.

Kokari takeyi ta yakice damuwar da ta take ciki.
Shi yasa da ta dawo daga makaranta bata yadda ta zauna ita d'aya ba gudun kar tunani ya addabe ta.
Sa hanu tayi aka karasa aiki da ita kamar yadda ta sabayi kullum.

Washegari ma haka da ta fita take ta tsammanin  ko zata ganshi amma shiru ,kwana biyu kenan take ta zuba ido bashi ba labarinshi.
Hakan yasa ta dage lallai sai ta yakiceshi daga zuciyarta,dan wasa wasa tunaninshi yana so ya zame mata matsala.

Kamar yadda ta saba yauma haka ta sauka dadai masallacin kofar gidansu .
Kallon inda ya zame mata kamar jaraba tayi dan duk lokacin data fita sai ta kalli wnn wajen .

Abin mamaki shi ta gani jingine da jikin motarshi ya zuba mata idanu.
Sanye yake cikin shigar yadi mai laushi ,milk colour ,d'inkin tazarce ,kanshi ba hula sai kwantacciyar bakar sumar shi irin ta asalin fulani,wanda ya dad'a k'awata mishi fiskarshi.

Wannan karo murmushi mai narkar da zuciya da gabb'an jiki ya sakar mata.
Tuni kuma jikinta ya amshi sakon .

"Ya Ilahi."
Ta furta tana jin yadda zuciyarta ke bugawa .
Da sassarfa ta shige cikin gidansu tamkar ana hankad'a ta.

Bata yi gigin tsayawa wani tunani ba gudun kada 'yar sa ido ta gano ta .

Da saurinta ta shige d'aki, ta jefa jakarta kan gado snn ta jinginu da jikin bango ta runtse idanunta ,jikinta har rawa rawa takeji yakeyi.

Murmushi ne ya sub'uce mata da ta tuna killer smile d'in da ya sakar mata d'azu.

Dafe kirjinta tayi tace a hankali "Ahmad zaka kashe Ummusalma."
Still idonta a rufe ,ta kuma sakin wani murmushin.

"Akwai good news kenan auntynmu."
Ta tsinkayo 'yar sa idonta tana fad'a.

Saurin bud'e idonta tayi ta watsa su kan Nusaiba ,take kuma ta daidaita nutsuwarta ,ba tare da tayi magana ba ta zare hijabin jikinta snn ta zauna bakin gadonsu tana maida numfashi a hankali.

Binta da kallo Nusaiba keyi can ta tab'e baki tace "Yau kuma da abinda aka dawo kenan."
Ganin bata kula ta ba yasa tayi sum sim ta fice daga d'akin.

Washegari kasancewar weekend ne babu inda Salma taje tana gida suna wankin kayansu dana Ummi dana khalil, dan duk weekend suke had'a kayan su wanke.
Sosae ta sake suna ta zuba hira cikin raha da kannenta dan ta kore duk wata tunanin Ahmad daga zuciyarta, saboda taga Nusaiba gab take da ganota .

Kwance take kan sallaya bayan sallar magrib ,cazbaha rike a hanunta amma kuma ba abinda takeyi dashi sai fiskar Ahmada dake mata gizo , idan ta tuna murmushnsa sai itama ta murmusa.

Ganin abin yaki barinta yasa ta d'an daki kanta tare da cewa "Wai meye haka ne."

Nusaiba da Faty da suke ninke kayan da suka wanke duk suka juyo suka kalleta.

"Me muka yi miki aunty."
Cewar Nusaiba.

Harara ta zabga mata "Ke kuma waya kasa da ke."

"Au da Faty kike , me tayi to."
Faty tayi saurin cewa "Ni kuma?"

Karamar tsaki tayi ta juya musu baya taci gaba da kwanciyarta, tunani ta shigayi ,lallai asirin zuciyarta ya kusa ta tonuwa .
"Me yasa Ahmad ya shiga zuciyarta haka .
Me takeji wnn game dashi."
Ni ko nace Na love ohhh my sisi.

Tsaki ta kuma ja wanda ya tilastawa su Faty kallonta snn suka kalli juna.
Aunty Salma dake hana su yawar tsaki yau ita ke da kanta take ta zabgawa.
Lallai akwai matsala.




*Mmn Abdul &Noorain.*
[17/12 06:24] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


     *F.O.W.*


*By Anty Rukie "Mmn Abduljalal.)*


              5.


     💔💔💔💔💔💔


Haka ta karaci kwanciyarta da tunaninta har taji an tada sallar Isha'i snn ta tashi ta bada farali.

Karatunma yanzu idan anayin shi rabi karatu rabi tunani.
Wani lokacin tana cikin karatu sai ta lumshe ido ta kama murmushi ita kad'ai.
Ah lallai abun azeemun.

Ranar sunday da dare bayan sallar isha'i tana kwance ta tashi taci abinci taki firr, ko da Ummi ta matsa mata sai cewa tayi batajin dad'in jikinta , ciwon kai zazzab'i ,ciwon ciki .
Hhhhhh kodai ciwon zuciya Madam Salma.
Ita kanta ta rasa takamammen wanda zata ce yake damunta.

Ummi ta matsa mata dakyar ta tab'a kad'an ta cire hanu ta koma ta kwanta.
Yanzu abinda take ji yafi karfin tunaninta .
Zuciyarta nauyi yake mata, ji take kamar ta fitar ta huta.

Ummi tace ta tashi su tafi asibiti nan kuma tace abin baikai haka ba.
Taje ko chemist ne su Nusaiba su rakata a bata magani nanma ta dad'a narkewa bata son zuwa.
Dama kuma sun san halinta sarai bata son magani bare uwa uba allura.
Dama haka likitocin suke ?🤔

Ga tsoron allura su kuma sun iya tsirawa mutane.😊

Ko k'arya nayi Mmn al-Mustafa?😜

Sallamar yaro ne ya dakatar da Ummi daga fad'an da takewa Salma na kin magani.

Dukansu suka amsa sallamar yaron suna maida hakulansu gareshi.

"Ana sallama da Salma inji wani a waje."

Rass Salma taji gabanta ya fad'i.
A ranta tace Allah yasa Ahmadunta ne.

"Kace batanan ."
Ta tsinkayo Nusaiba tana fad'a, dan tasan amsar da zai samu kenan daga Salma.

Abin mamaki sai sukaji tace a hankali.
"Bari inje in duba inga ko wayene."

Zuruf ta ta mike taje tana zura hijabinta.

"Kai."
Nusaiba ta kwala wa yaron kira dan har ya fara tafiya.

"Kace tana zuwa."

Galala Ummi tayi tana binta da kallon mamaki.
Suma kannenta matan da mazan duk haka abun yake a wajensu.
Salma da lafiyarta ma yaushe ta fita ta saurari wani bare kuma ba lafiya.

Sumi sumi tazo ta wuce su tayi hanyar kofar gida.

Tsayawa tayi tana leka ta  kafar gate d'in
"Hmmmmmm" ta sauke doguwar ajiyar zuciya.

Wanda take fata da muradin gani shi ta hango tsaye ya zubawa kofar fitowa ido.

Dafe kirjinta tayi ta lumshe ido tana murmushi .
Wani sanyin dad'i taji yana ratsa ko wani sassa na jikinta.

Minti biyu ta d'auka tsaye a wajen ,tunanin yadda zata fita takeyi tunda bata saba ba.

A hankali take takowa cikin nauyi da kunya .
Shiko gogan ido ya zuba mata kamar ya jawota ta iso da wuri.

Ma k'asa yace "Faruk fito gatanan zuwa."

Tana isa Faruk yana fitowa daga cikin mota.
A kunyace ta gaishesu ba tare da ta d'ago ta kallesuba.

"Malama Salma sai kika ga bak'i ba zato ko?"
Cewar Faruk.

"Hmm " kawai ta iya cewa.

"Laifi kika mana muka biyo ki fa."

"Laifi kuma ?"
Tace a hankali tana mai d'ago kanta.

Caraf suka yi 4 eyes da gogan ,ai a d'ari ta sauk'e kanta.

"Laifi babba ma kuwa malama Salma."
Cewar Faruk.

"Kin sace min zuciyar aboki , kin hana mishi sukuni ,ya gaza samun nutsuwar zuciya. Da fatar za'a taimaka a agaza a maida mishi zuciyarshi ta koma daidai."

Dad'a sunkuyar da kanta tayi tanajin ni'imtacciyar iska na shiga jikinta.

"Salman, fili dominka sai ka kokarta ka amso zuciyarka.
Faruk ya sake cewa .

Kan su ankara har Faruk ya bar wajen.

"Kaji min d'an iska ,zai tafi ya barni  da ita."
Ahmad yace a zuciyarshi yana mai bin Faruk da kallo.

Haba Ahmad kamar ba namiji ba?🤔

Salman kuma?
Ta maimaita sunan da taji Faruk ya kirashi dashi a ranta.
Ita dai da Ahmad tasanshi to ya akayi yau kuma aka kirashi da Salman.

"Uhm uhm" Ahmad ya d'anyi gyaran murya yana gyara tsayuwarshi tare da daidaita nutsuwarshi.
Yau ga dama ta samu ba sanya.

Kallonta yai still kanta a k'asa ,so take ta d'ago ta kuma kallonshi amma nauyinshi da takeji ya hana ta yin hakan.
Kokarin bud'e baki takeyi tace mishi su shiga daga ciki dan bata saba tsayuwa haka ba ,amma bakinta ya gaza bud'uwa. Gaba d'aya kunya ya gama mamayeta.



*Mmn Abdul &Noorain.*

*Wnn shafin naku ne.*

Reederh Malaysia
Mmn sadeeq
Zaa princess
Foulani cerdia.
[17/12 06:24] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*



*Fasaha Online Writers.*


     *F.O.W*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*


                 6.

       💔💔💔💔💔💔


A tsanake yafara gabatar da kanshi snn yaci gaba da bayanin abinda ke tafe dashi.
Nishad'i suke ji dukansu hakan yasa basu gaji da tsayuwar dasukayi a wajen ba.

Fitowar kannenta ne ya ankarar da ita abinda ta aikata ,sai yanzu ma ta tuna cewar bata da lafiya.
Abin al'ajabi kuma ko alamar ciwon bata ji ayanzu.

Sallamar shi tayi da cewar zata shiga gida dare yayi.
Shikam ta biya shi a hakanma tunda ta tsaya ta saurare shi, ga dukkan alamu kuma ya samu karb'uwa duk da ba sakewa tayi da shi sosae ba amma ya fahimci kunya ce ta mata yawa.

Al-amin ne ya zo shigewa yaga abinda ya bashi mamaki ,wato Salma tsaye da wani da gani kuma zance sukeyi .

Baiyi k'asa a gwiwa ba ya nufi inda suke.
Sallama yayiwa Ahmad tare da mika mishi hanu suka gaisa.Mamaki yake da kuma jinjinawa sa'a irin na wnn bawan Allah.

Bayan ya wuce Ahmad ya tambayeta "Wannan shine yayannamu?"

Kai ta gyad'a mishi alamar eh.
Snn ta kuma cewa zata shiga dare nayi.

Sallama sukayi har ta fara tafiya ya dakatar da ita.

"Gimbiya a taimaka min da phone no. Ko zan samu bacci mai dad'i."
Ya fad'a yana zaro wayar shi daga aljihu.

Dawowa tayi ta amshi wayar ta saka no. Snn ta juya ta nufi gida.
Har ta shiga yana tsaye a gun yana kallonta.

Sai bayan ta shiga ne tukun ya nemi layin Faruk yace mishi yazo su tafi.

Rufe kofar gate d'in tayi ta juya zata shige ciki taji an riko hijabinta.
A tsorace ta kalleshi.
"Yayanmu ka bani tsoro wlh."
Ta fad'a a shagwab'e.

"Sorry Ummulun Ummi, wani baban sa'a  ne wannan ,har aka fita mishi da darennan."

"Kai yayanmu ai ka bari mu shiga ciki ko?"
Ta fad'a tana yin gaba.

Binta yayi a baya yana cewa "Abinne ya ban mamaki, lallai wannan gaye mai sa'a ne."

Suna shiga ciki ta ga Ummi zaune tare da khalil tana k'ara mishi karatun Qur'ani.

Binta Ummi tayi da kallo ,ita kuma duk kunya ya gama cikata da tuna a yadda ta fita daga gidan daga cewa barin je inga waye.

"Ummulu ya jikin ?"
Ummi ta tambayeta.

"Jiki kuma ?"
Ta mayar wa ummi tambayar.

"Dama bata da lafiya ne Ummi."
Cewar Al-amin.

Kwance take anan tana kukan ciwon kai, ciki, da zazzab'i aka aika kiranta, kaga yanzu har tambayata take wai jiki kuma?"

Cikin zolaya Nusaiba tace "Ita tama manta bata da lafiya fa Ummi."

Al-amin ya cab'e zancen da cewa "Maganin ciwon ne dai yazo."
Yauwa al-amin ka canka dadai👌

Itakam tuni ta shige d'aki dan kunyar Ummi taji da gaske.

Shi kuwa al-amin sai ya k'ara da cewa "Meye sunan sirikin namu."

"Lucky."
Nusaiba ta bada amsa har da d'aga murya yadda Salma zata jiyo ta.

"Kuma fa hakane."
Al-amin ya fad'a yana dariya."

Cikin farin ciki da annashuwa Ahmad ya koma gida ,yau jinshi yake kamar ya sauke wani kaya mai nauyi, jinshi yake sakayau.
Ji yake tamkar babu kamarshi babu kuma wanda ya kaishi sa'a.

Saida ta gama juyinta kan gadonsu cikin farin ciki snn ta d'au litattafanta ta fara dubawa.

Har su Nusaiba suka shigo karatunta take yi hankali kwance cikin nishad'i ,ta kwana biyu bata karatu mai dad'i irin na yau ba.

Karar wayarta ce ta katse ta , dubawa tayi taga new no.
Jikinta ya bata cewar Ahmad ne ,sbd haka fiskarta d'auke da murmushi ta d'aga wayar.

"Na kira nace miki na isa gida  lafiya ne, na kuma miki mu saida safe."

Murmusawa tayi snn tace "Na gode ,mu kwana lafiya."

Ci gaba tayi da karatunta tayi bayan ta ajiye wayar, su Nusaiba duk sun kwanta.

Can tayi nisa da karatunta ta sake jin  wayar na ringing.

Dubawa tayi taga shi d'inne.

"Bakiyi barci ba?"
Tambayar da ya jefo mata kenan bayan ya amsa sallamar da ta mishi.

"Yanxu zanyi."

"Me ya hana kiyi tun d'azu."

"karatu nakeyi ."

"Karatu kuma da darennan ,taimakeni dan Allah kiyi baccin yanzu."

"To ai kaima bakayi yi baccin ba."

"Jikina ne ya bani bakiyi ba shi yasa na kasa yi."

"Hmm, Mu kwan lafiya ."

Tace tare da kashe wayar kamar ita ta kira.



*Mmn Abdul &Noorain.*
[17/12 06:24] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*



*Fasaha Online Writers.*


    *F.O.W*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*



              7.

       💔💔💔💔💔💔


Kamar yadda yace hakan kuwa tayi dan rufe littafan tayi ta adana su a ma'ajiyarsu.

Alwala taje ta d'auro ta yi addu'oin da ta saba yi kafin ta kwanta.

Soyayya mai karfi ya shiga tsakaninsu har ya zamanto basa iya yin kwana d'aya basu sa juna a idanunsu ba.
Sau d'aya ya tab'ayin tafiya ta harkar kasuwancinsa .
Hhh wnn lokacin sun ji a jikinsu dukansu biyu.
Kwana biyar kacal yayi amma ji suke kamar sun shekara basu had'u ba, duk da cewa basu d'aukan lokaci mai tsawo sai sunyi waya.

Daga nan kuma yace bazai kuma tafiya irin haka ba ,koma me ya taso zai tura yaranshi .
waya kuma ako da yaushe cikin yinshi suke kamar ba ita ke jin haushin Nusaiba idan ta ishe ta da amsa waya ba.
Snn kuma duk dare sai yayi ta kiranta yace ta kwanta ta huta baya so ta wahalar mishi da kanta ,baya kuma barinta sai ya tabbata ta kwantan.

Karatu kam yanzu tab'a shi dai ake sama sama ba kamar yadda ta keyi da ba.
Ita kanta ta rasa abinda yasa take biye mishi yake hana ta isasshen karatu duk son da takewa karatun kuwa. Da gaske zuciyarta ke mishi biyayya akan duk abinda yakeso ko da bata so hakan ba.


Zaune suke k'asar bishiyar mangoro dake cikin gidansu suna shan iska.

Ummi, Fati, sai kuma Salma , Ummi da Fati tsintar shinkafa sukeyi ,itako Salma jan lalle take zana wa yatsunta.

Nusaiba dake cikin d'aki tana gyara ne ta fito rike da wayar Salma ta zo ta kara mata a kunnenta .
Da hanu ta tambayeta wayene.

Kamar tana jira tace "Waye kuma banda Lucky."

Sallama tayi ya amsa ,suka gaisa tana satar kallon Ummi , Ummi ko kallonta batayiba ,idonta na kan trayn shinkafarta.

Bayan sun gaisa tace mishi yayi hakuri aiki take yi zuwa anjima zata kirashi.

Cire wayar Nusaiba tayi daga kunnen Salma ta nemi waje ta zauna.

"Yauwa aunty Salma ya kamata ki d'an takawa yayannan namu birki hakanan.
Kiran yana yawa ,atleast da dare kam ya bar ki kiyi karatu ,amma bini bini kira ,gaskiya zai wargaza mana tsari , yanzu fa sam bakya karatu kamar da."
Ta karashe maganar tana satar kallon Ummi.

"Adda magana ."
Cewar Fati ,tana hararar Nusaiba.

Itama Salma Hararar ta zabga mata snn tace "To maganad'isu ,yaushe kikaga banyi karatu ba, naga lokacin da nake karatun duk kunyi nisa a bacci."

"A da kenan, yanzu kam ina zaki barmu muyi bacci mai nisa yanzu yanzu karar waya a ishe mu kuma da kashe murya."

"Taraba state broadcasting service (T.S.B.S.)"
Cewar Fati.

Nusaiba ta amsa da "A a kin manta T.T.V. ne Taraba television."

"Kin shiga uku da gulma Nusaiba ,dan tsabar gulma har wani ina hana ku bacci ,Sa idonki dai ya hanaki kada ki min sharri."

Gyara zama tayi ta fara magana seriously "Aunty ki ture batun wasa, wlh ba gulma ko sa ido ,abinda na lura dashi nake fad'a nifa gani nake kamar Lucky bai damu da karatunki ba ,idan ya damu k'arfafa miki gwiwa ya kamata yayi ,amma kullum shike hana ki karatun ,anya wnn idan a gidanshi kike zai barki kiyi karatunma?"

"Kai Adda Nusai kamar wacce aka aiko?"
Cewar Faty.

Zare mata ido tayi "Ke ban hana ki kirana da Nusai d'innan ba, ki kirani da full name d'ina 'yar rainin hankali, kuma daga fad'ar gaskiya sai ace an aiko ni, nifa so nake auntynmu ta fito da result mai kyau amma wnn d'an wailawan yana so ya kawo mana cikas."

Ummi har yanzu bata kallesu ba balle tayi magana amma tana sauraron duk abinda suke cewa.

Itako Salma kogin tunani ta fad'a ,maganar Nusaiba fa gaskiya ce ,tunda take tare dashi bai tab'a kawo mata maganar karatunta ba ,bai tab'a tambayarta burinta idan ta gama karatu ba ,kuma ko ya kirata tace mishi tana karatu bai tab'a ce mata Allah ya bada sa'a ko ya taimaka ba, shi dai kullum maganarshi ta amince ya turo manyanshi, kuma bayaso a d'au lokaci ba'ayi bikinsu ba.
To me hakan yake nufi.

Fati ce ta matso kusa da Nusaiba tace a hankali "Munji mama Nusai, zamu gyara, uwarsu matar ubansu."

D'aga hanu tayi zata d'aka mata duka ta goce ta sake binta sai ta arce tayi cikin d'akinsu tana dariya.
Kan gado ta fad'a tana dariya tana d'agawa Nusaiba hanayenta tare da cewa "Na tuba bazan kara ba Mama Nusai."
Dariyar har kamar shaketa yakeyi .
Lallai yau fati ana jin raha.

Itama kanta Nusaiba dariya abin ya bata sai ta fad'a kusa da fati itama tana darawa.

Tsagaita dariyar Fati tayi snn tace.
"Fisabilillahi me yasa kikawa auntynmu haka, kinga bata ji dad'in abin ba wlh, nasan gaskiya kika fad'a amma dakin yi mata magana tsakaninku Ummi bata wajen."

"Hmm baza ki gane bane Fati aunty tana yiwa mutuminnan matsananciyar soyayyar da ba lallai bane da saurareni ta fahimci abinda nake nufi.
Da gan gan na mata haka ,ko ba komai nasan Ummi zata mata magana kuma in shaa Allah zata saurareta ta gyara."

"Allah ya sa to."
Fati tace.

A can waje kuma su fati na barin wajen Ummi ta d'ago ta kalli Salma.
"Ummusalma."

Kusan a firgice ta d'ago "Na'am Ummi."




*Mmn Abdul & Noorain*
[17/12 06:24] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


*F.O.W*


*By Aunty Rukie (Mmn Abduljalal.)*


                8.

      💔💔💔💔💔💔

*Gaisuwa da fatan alkhairi masoya a duk inda kuke, ina kaunarku fiye da yadda kuke qaunata*
*Gaisuwar ban girma gareki ummu D'alhat, Allah ya bar zumunci.*

*Maryam A.I Gital*
Kina raina ,Allah ya qara miki lafiya da basira.

*Ciwo lokaci guda yake shiga ,amma sauqi sai a hankali, Alhamdulillah, na samu sauqi 'yan uwa saidai fatar Allah yasa ciwon ya tafi gaba d'aya.*
*Naji jiki wollah.*


"Nasan Nusaiba bazata yi miki k'arya ido da ido ba, kai ko a bayan idanki ma banyi tsammanin haka ba , abinda nusaiba ta fad'a yana kan hanya ,muddin kika biyewa Ahmad ya hanaki karatu baki kyautawa mal.ba.
Mal. Ya yarda zakiyi kuma zaki iya shi yasa ya tsaya  tsayin daka na ganin kin yi karatunnan domin cikar burinki.
Duk da cewa tun farko aure yaso ya miki kika nuna ke karatun kikeso kuma ya biye miki.
Kina tunanin zai ji dad'i idan lokaci guda kika watsar da wahalar dayayi na ganin kin cika burin ki."

Kanta a duke tace "kiyi hakuri Ummi bazan k'ara ba."

"Baza mu takura ki ba Salma idan auren kike so yanxu ki sanar damu dan baza mu tauyeki ba kinga sai in sanar da Mal. a fad'awa Ahmad d'in ya fito."

Girgiza kanta ta shigayi "A'a Ummi wallahi sai na k'are karatun."

"Ni dai na gaya miki kika ci gaba da biye mishi kina wasa da karatun matakin da zamu d'auka kenan."

"In shaa Allah daga yauma an dena Ummi kiyi hakuri."

Fati ce ta iso ta karb'i shinkafan da suka gyara tana kallon auntyn tasu da gefen ido ,dan son gane wani yanayi take ciki.

Saida ta wanke lallenta snn ta bar wurin , tana isa kofar d'akinsu ta samu nusaiba zaune daga gefe tana kankare k'umbunanta .

Kurr nusaiba ta kureta da ido ,itako tayi kamar bata ganta saima d'an murmushi da tayi ta wuce ta .
Saida tazo ta bayanta snn ta talle keyar ta tare da cewa "wani irin kallo ne  haka kamar baki da gaskiya.

Ajiyar zuciya ta sauke dan duk a zatonta auntyn tayi fushi da itane.

"Sorry my aunty ,ciwon sub'ul da baka ne ya kamani d'azu a gaban ummi."

"Allah ya shirye ki uwar 'yan magana , Mama nusai."
Ta karashe maganar tana murmushi dan tasan ta tsokano ta.

Cuno baki nusaiba tayi "Allah zanci kaniyar Fati."

"Nawa dai zaki ci tunda ni na fad'a."

"Wane ni swt aunty ita dai da ta fara kirana da sunan."

Haka suka ci gaba da rahansu tamkar babu abinda ya faru.

Kamar yadda ta alkawarta haka ko akayi bayan yazo sun sha firarsu zai tafi yake ce mata sai tajishi anjima idan ya kirata.

"Yauwa Ahmad dama akwai wata maganar da nakeso muyi da kai."

Dawowa yayi ya zauna "Ina jin ki sweety na."

Sai da ta d'an murmusa kafin ta fara magana.
"Dan Allah Ahmad kiran daren nan nakeso ka d'an rage dan yana shiga lokacin karatuna ,bana samu nayi karatu kamar da wlh."

Tunda ta fara magana ya kafe ta da ido har ta gama .
"Karatu dai, karatu dai."
Yace a ranshi.

"kayi shiru Ahmad."

"Salman dai."
Yace mata fiskarshi d'auke da murmushi ,dan ya lura duk lokacin da aka ce mishi Salman sai tayi ta mishi kallon mamaki.

"Wai ni me yasa ake ce maka Salman ."

"To meye sunan idan ba Salman ba."

"Ahmad nasanka dashi nidai."

"A da kenan, tunda Ahmad ya had'u da Salma ya zama Salman, ina  fata kin fahimta."

"Lallaima Ahmad, to ni bansan wani Salman ba Ahmad na sani."

"Daga yau na soke Ahmad d'in Salman zaki kirani."

'yar dariya tayi "Cabb, ni Ahmad na sani kuma shi zan kira ban san wani salman ba ehe."
Ta karashe maganar harda d'an murgud'a bakinta.

Ciza lower lip dinshi yayi yana binta da kallo tallabe da hab'a fiskarshi d'auke da murmushi.

"Baka ce komai ba Ahmad."
Tuni fara'ar fiskarshi ta d'auke ,shi da yayi tsammanin ya shashantar da maganar ashe bata manta ba.

"To me kike so ince tunda rowar muryarki kike so kimin."

Marairaicewa tayi tare da cewa "Ba haka bane Ahmad ,hiran yana tsawo yana affecting karatuna, har an gane a gida bana karatu kamar da, kuma kaga ina cikin shekaran karshe ne na gamawa, ya kamata in maida hankali sosai ko dan na samu sakamako mai kyau domin cikar burina."

Tsura mata ido yayi na d'an lokaci yana nazarin kalamanta ,daga baya yace "Menene burin naki ."

"Na zama nurse of course ,naga ina taimakawa 'yan uwana da sauran al'umma idan rashin lafiya ta samesu."

"Akwai matsala ."
Yace a ranshi, dan yasan da wuya iyayenshi su amince da hakan.

"Salma me zai hana ki amince ayi aurenmu idan yaso ki kammala karatun a gidana."

Shiru tayi nad'an lokaci tana tuno maganar Nusaiba.
"Wnn idan kina gidanshi zai barki kiyi karatun ma?"

Tunowa da hakan da tayi yasa ta fara girgiza kai.
"Gaskiya Ahmad ,A'a, ka bari dai na kare karatun idan yaso ayi komai kafin na fara aiki."

Shiru yayi yana tunanin yaya danginshi zasu d'auki wnn al'amari su da sukewa karatun boko fassara ta daban musamman ga mace.
Zai jarraba sa'arsa ya gani idan har ya aureta koma me za'ayi ayi ,idan su zasu janye ra'ayinsu falillahil hamdu , idan kuma itan ce zata hakura da cikar burinta ,duk dai wnn sai ta shigo gidanshi .




*Mmn Abdul&Noorain*
[17/12 06:24] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


*F.O.W*



*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*



               9.

     💔💔💔💔💔💔


*In dedication to my swt sisto Haleema Auwal (Mmn Aysha.)*


Jin shirunshi yayi yawa ne ,ya sata shiga damuwa, dan yanzu ta dad'a tabbatar da maganar nusaiba ,Ahmad baya son karatunta ,idan ta sake ta shiga gidanshi kuma tayi ban kwana da cikar burinta.

Hakan yasa ta mike a sanyaye ta mishi sallama tun bai amsa ba dan yayi nisa a tunani ,tayi gaba abinta.

Shiganta d'akinsu ta zauna ta jinginu da bango , a ranta take cewa "Lallai nusaiba ta hango mini abinda na gagara hangowa kaina, yanzu idan yace bazanyi aikin ba hakura da aikin zanyi koko dashi zan hakura.

Tana tuna yadda za ta hakura dashi taji gabanta ya bada damm, juya kanta ta shigayi ,"bazan iya ba ,duka biyu ina so."

Ta fad'a a bayyane.

Shi kuwa Ahmad kanshi ne yad'au caji, tunani yake yi lallai idan yayi sake Salma zata guje shi akan karatunta dan ya lura ba karamin kwallafa ranta tayi akai ba ,ina mafita.

Mafita d'ayace ,itace yayi wa tufkar hanci tun abu baiyyi nisa ba ,saboda haka sai ya yanke shawarar yayi abinda zuciyarshi ta raya mishi .

Zuwa yayi ya samu yayanshi ya bashi labarin ya samu yarinyar da yakeso ya aura snn yana so aje anema mishi auranta, amma bai fad'a mishi akan tana karatu.

Yayanshi yayi farin ciki kwarai ,dama burin shi kenan yaga d'an autansu ya ajiye iyali.

Saboda haka sai ya nemi sauran 'yan uwanshi ya sanar dasu snn suka sa ranar da zasu je dan su nema mishi aurenta.

Kamar yadda suka tsara ko haka sukayi , sunje nemawa Ahmad aure gidansu Salma ba tare da saninta  ba ,duk da a wurinsu suna tunanin saida suka fahimci juna kafin Ahmad ya tunkare su da maganar.

Shi kuma Ahmad a tunaninshi so da yardar dake tsakaninshi da Salma bazai bari ta watsa mishi k'asa a ido ba koda za'a tambayeta ra'ayinta game da aurenshi.

Sun samu tarba ta mutunci da karamci daga wajen Mal. Inda bayan gaishe gaishe suka gabatar da bukatar su ta nenawa k'aninsu auren Salma.
Snn idan zai yiyu suna bukatar a gama komai cikin k'ankanin lokaci.

Duk da Mal.yaji mamakin abin amma bai nuna musu ko a fiska ba, ya dai ce musu zai ji ta bakin yarinya dan basu sanar dashi wani abu makamancin haka ba daga cikin gidan.
Snn bai b'oye musu ba ya sanar dasu salma tana karatu da kuma irin karatun da takeyi.

Nan suka shiga kallo kallo kowa da abinda yake sak'awa a ransa.

Sallama da godiya suka mishi suka kama hanyar komawa gida .

Ahmad da yakasa zaune ya kasa tsaye yana jira yaji irin amsar da zai samu daga garesu .
Ganin shigowarsu yasashi binsu yana musu sannu da dawowa.

Daga yanayin fiskokinsu ya gano akwai matsala.
Babu walwala a fiskar ko d'aya daga cikin su ukun.

Ganin yadda ya tasa su gaba yake binsu da kallo cikin rashin sukuni yasa babban yayansu wanda yake tare dashi ya fara magana cikin zafin rai.

"Ahmadu me ya had'a ka da 'yar boko? Wato bidi'a kakeso ka kawo mana cikin zuri'a ko? Ina kai ina auren likita ,kullum tana yawon zuwa asibiti bata da lokacin ka, duk 'yan matan garinnan ka rasa wacce zaka aura sai wacce ta tsofe tana yawon karatun boko.
Ka bani mamaki Ahmadu ,kai da kake namiji ma bakayi karatun boko mai zurfi ba sai mace?
To ba'a zuri'armu ba saidai idan zaka canza dangi, baza mu lamunci wnn aikin kafurcinba."
Ya karashe maganar yana huci.

Suko sauran 'yan uwan sai gyad'a kai sukeyi irin d'an uwansu is absolutely right d'innan.

D'ayan yayannashi ya cab'e zancen da cewa "Kasan duk dangin mu ba'a tab'a irin haka ba kuma akanka baza'a fara ba, gwara ma ka canza shawara ."

D'ayan ko da tausayin Ahmad duk yabi ya cika shi ganin yadda lokaci guda kamanninshi suka canza ,jijiyoyin kanshi suka tashi burd'um2 ,cikin sassauta murya yace.
" Nidai shawarar da zan baka ,kayi hakuri ka daure ka cire yarinyar a ranka dan kasan aurenta ba mai yiyuwa bane, ka nemi wata ka aura."

Babban yayan ya amshe da "Kada ma yayi hakuri in ya ga dama ,aurene dai bazai aureta ba, saidai in bana numfashi, idan ma aurenne akwai yanmata da yawa masu mutunci ,ko ni nan zan zab'a maka mace mai hankali nagartacciya wacce tasan darajar aure mai yawon banza ba."

Sai a snn ya samu bakin magana "Wai shin auren 'yar bokon haramunne?"

"Laa ilaaha illallahu ,muhammadarrasuulullahi salallahu alaihi wa sallam."
Suka had'a baki wajen fad'a.
Kadin d'ayan wannashi yace.

"kaga abinda muke gudu kam ko, zama da ire irensu babu abunda yake k'arawa mutum sai rashin kunya , yanzu akan auren farin kake sa' in sa damu .
Daga yanzu ma kenan inaga in ta shigo gidanka ,Kai Allah ya raba mu da auren 'yan boko, ko da yake ba laifin ka bane ,biye maka da akayi tun farko kayi karatun bokon shi ya baka damar yin abinda ranka keso."

Babban yayansu sune ya katse shi da cewa "Umaru ka daina b'ata bakinka ,ni nan zanyi maganin fitsararre ,aure zan mishi da 'yar mutunci ko yaki ko yaso, cikin kwanan nan zamuje nema mishi auren, idan ya ga dama kada ya hakura wnn matsalarshi ce."



*Mmn Abdul &Noorain*
[17/12 06:24] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*



*Fasaha Online writers*


*F.O.W*



*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*


              10.


       💔💔💔💔💔💔

*A friend in need is a friend indeed.*

Maryam Mazad.

*kina nan manne cikin raina a ko da yaushe.*


Tsabar bakin ciki da takaici barin gurin Ahmad yayi, danji yayi kamar ya naushi bakin yayannashi.

"Ji min mutum kamar wani ubana wai aure zaimin ,kamar wata mace."
Abinda ya fad'a kenan lokacin da fita daga gidan.

Salma kuwa tana can bata san wainar da ake toyawa ba, saida gari ya waye taje gaisheda malam yake tambayarta ko ita tace Ahmad ya turo iyayenshi.

Take taji wata muguwar fad'uwar gaba ta mata dirar mik'iya.

Dafe kirjinta tayi tana juya kai idanun ta taff kwalla, maganar ma ta gagareta.

Ganin halin da ta shiga lokaci guda yasa malam yace ta tashi taje kawai dama ya tambaya ne don yaji ta bakinta.

A sanyaye ta tashi ta tafi tana jin zuciyarta na dokawa.

A b'angaren malam kuma dama yayi tunanin bata da masaniya akan hakan dan inda ta sani ko yaya zata sanar da Ummi, saboda haka ya kudurta indai bata so ,hakuri kawai zai basu idan suka dawo.

Yaraf ta zauna a bakin gado hawaye na gangarowa daga idanunta .
Abinda Ahmad zai mata kenan, ya turo iyayenshi ba tare da izininta ba.?
Ya yakeso iyayenta su d'auki al'amarin."
Ita har kunyarsu ma ta fara ji ,gani take kamar zasu ce da saninta suka zo, ba abinda yafi damunta kamar idan ta tuna maganar da sukayi da ummi kwanaki uku da suka shige.

Lallai Ahmad ya mata bazata.
Ko me Mal. Yace musu sai Allah.

Tana cikin tunanin ta tsinkayo nusaiba na cewa "Lafiya aunty kike kuka?"

Shafo hawayen fiskarta tayi tana kallo kamar wacce taga bakon abu, ta kuma gagara yiwa Nusaiba magana.

Ganin haka yasa nusaiba fita ,tare da kiran ummi.
Tare suka shigo da Al-amin da ya shigo gaisheda Ummi ya ci karo da labarin Salma tana kuka.

"Kukan me kikeyi salma, Me ya sameki da sassafennan?"
Ummi ta tambaya tana zama kusa da ita.

"Cikin kuka tace Ummi Ahmad ya turo iyayenshi gun mal.  ba tare da sanina ba."

"Au dama bake kika ce ya turo ba?"

"Ummii."
Tace da saurin baki tana zaro idanu.

"Taya zan yanke wnn hukunci ba tare da saninku ba, wlh ni ban san zai turo ba ."

Ta fad'a muryarta na rawa tare da karin hawaye akan fiskarta.

"Toh kukan me kikeyi ba kinasonshi ba ,meye dan ya turo."

Da sauri ta sake cewa "A'a ummi ban shirya ba wlh , na fad'a mishi sai na kare karatuna, Ummi yanzu me Mal. Yace musu."

"Ina zan sani ni kuma yanzu dai zasi dawo su ji amsa kuma amsar tana gareki in eh, eh in a'a kuma sai asan yadda za'ayi."

Ajiyar zuciya ta sauke tana share hawaye, tare da bin ummin dake fita da kallo.

Mayar das kallonta tayi kan su fati da nusaiba .
Suna had'a ido ta harare ta "kallon fa ?"
Dariya tayi taja hanun fati sukayi waje tana cewa "Fati mu fita kar a huce haushin lucky akanmu."

"Ina kwana ya al-amin."
Salma ta fad'a murya k'asa² .

Murmushi yayi "Ummulu har an gama kukan?"

Kwafa tayi snn tace "Haushi ya bani yayanmu idan banyi kukan ba bazan ji dadai bane."

"Banda abinki meye abin kuka a ciki, dan ya turo ba sai a gama komai a jira idan kin kare karatun musha biki ba?"

"Hmm yayanmu baza ka gane bane ."

"To ganar dani"
Ya fad'a tare da zama kan katifa.

Gyara zama tayi ta zayyane mishi komai har da yadda ahmad yake basar da zancen karatunta in ta mishi.

Shiru yayi na d'an lokaci snn yace "Nidai shawarar da zan baki anan itace ,ki dage da addu'a ,ki roki Allah zab'in alkhairi , idan Ahmad alkhairi ne a gareki Allah ya tabbatar idan kuma sab'anin haka ne ,Allah ya musanya miki mafi alkhairi."

A ranta tace in Allah ya yarda ma alkhairi ne.
A fili kuma  tace "Amin na gode yayanmu."
Amma kuma can k'asan ranta da gaske haushin abinda Ahmad ya mata takeji.
Hakan yasa ko da ya kirata kin d'auka tayi ,duk nacinshi haka ya hak'ura ya kyaleta.

Ko da tagama shirin makaranta ta fita ma ta ganshi sarai tayi kamar bata ganshi ba tayi saurin taran napep
ta shiga ta tafi.

Toh Ahmad ka b'allo ma kanka ruwa ,da wanne zakaji da haushin su yaya babba ko kuma fushin da Salma takeyi da kai.



*Mmn Abdul& Noorain*
[17/12 06:24] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


*F.O.W*



*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*
 

                11.

        💔💔💔💔💔💔

*Assalamu alaikum warahmatullah.*
*Ina taya d'aukacin iyalan margayi Hamma Umar da kuma makaranta littafin rubutaccen al'amari alhinin rashin wnn bawan Allah, Allah ya ji qanshi yasa ya huta , mutuwar wnn bawan Allah ya shigeni ba kad'an ba,Allah ya bawa iyalanshi haqurin rashin da sukayi, Allah ya jiqan dukkan musulmi ,Allah yasa mu cika da imani*
Kullu nafsin za'iqatil maut.😭😭😭

*Ina kike Mmn Ukhty (Lubabatu kyauta ) ga taki gaisuwar ta musamman.*
*Allah ya bar qauna.*😍😍😍


Wasa² saida suka kwashi kwana biyu Salma tana mishi wasa da hankali ,gefe d'aya kuma yayanshi ya bud'a mishi wuta akan lallai sai ya rabu da ita ,dan yace ya nema mishi auren 'yar abokinshi kuma an bayar sbd haka ya cire hankali kan Salma ya rike wacce aka bashi hanu bibbiyu.

A rana ta uku ne tana zaune bisa sallaya bayan ta idar da sallar isha'i.
Babu abinda takeyi illa tunanin Ahmad dan tayi  kewarshi ba kad'an ba.

Ji tayi nusaiba ta kamo hanunta tana cewa "Aunty salma zo muje kiga wani abu.,"

Ganin yadda nusaiba take kamar bata cikin nitsuwarta yasa ta tashi ta bita.

Har suka isa kofar gida snn ta saki hanunta.

"Me kika ce zan.."

Bata ida maganarta ba taga Ahmad tsaye a gabanta ya langab'e wuya yana kallonta ,irin kalan tausayinnan.

Da sauri ta juya zata koma yayi saurin shan gabanta.
Itako sarauniyar sa eyes sai ta hard'e hannayenta tana kallonsu.

D'aure fiska tayi tabi gefenshi zata wuce ya sake tareta.
Ganin abinnata da gaskene yasa shi yin kneeling a gabanta yana kallon cikin idonta.

Kawar da idonta tayi daga kallonshi snn tace "Meye haka kuma Ahmad."

"Ki min duk hukuncin da kikaga zaki iya amma banda haramta min ganinki da magana dake.
Na yarda ni mai laifi ne amma hukuncin da kike mini ya min tsauri da yawa, kiyi wa Allah ki sassauta min."

Cikin sassauta murya idanunta sun cicciko tace "Ahmad me yasa kamin haka?
Me yasa ka turo magabatanka ba tare da sanina ba."

"Kiyi hakuri ban yi tsammanin abin zai miki zafi haka ba.
Na d'auka ko don so da yardar dake tsakaninmu sun isa susa ki hakura da abinda nayi, ki kuma amsa tayin neman auren da nayi miki, ban sani ba ashe nayi kuskure ,ni kad'ai ke ta haukana.
Ko ban fad,'a kin san sonki da k'aunarki suka sani yin hakan.

Ya karashe maganar cikin rawar  murya dan zafi biyu ne ya had'e mishi, ga barazanar yayanshi gareshi ga kuma salma tana faman juya mishi baya.

Bata san sanda ta durk'ushe kusa da shi ba ,muryarta a shak'e alamar kuka ke shirin kufce mata tace "Tsoro nakeji Ahmad."

Katse ta yayi da sauri "Tsoro ? Tsoron me?"

"Ahmad Jikina na bani idan na shiga gidanka baza ka barni na cika burina ba."

"Ai kam jikinki ya baki gaskiya dan akwai k'alubale babba ma kuwa."
Yace a ranshi .

A fili kuma ce mata yayi "Idan ba gaskiya jikinnaki ya baki bafa, idan zan barki ki cika burinnaki fa?"

Kawar da kanta tayi dan bata son kallon kurillar da yake mata yau, tamkar me mata kallon bankwana.

"Ina shakka akan haka Ahmad ,dan ban ga alamun haka ba."

"Salma ,zanyi iya kokarina naga burinki ya cika ,idan nace miki nayi alk'awari zaki aureni."

Gyad'a mishi kai tayi a sanyaye tana goge hawayen da suke zubo mata.

Shi d'inma a fakaice yake goge nashi ,sbd yana tunanin yadda za'ayi ya mata alk'awarin da cika shi ba tabbas, kuma shi duk abinda zai zubar mishi da mutunci a idon salma da 'yan gidansu baya so,dan ita d'in 'yar mutunci ce 'yar gidan masu mutunci.

Rab'a shi tayi ta wuce dan bazata iya tsayawa wani dogon zance ba ,duk jinta take wata iri jikinta yayi mugun sanyi.

Nusaiba ko saida tayi wa Ahmad sallama tabi bayan auntynta .
Suna shiga nusaiba mai bakin reza tace "Wlh lucky ya ban tausayi Fati ,har kuka fa yayiwa aunty."

"Ungo nan."
Ummi ta fad'a tana mata dakuwa .
"Dama abinda ya kaiki kenan dan ki kikawo rahoto."
Hhhhhh wa yaga BBC.

"Allah ya duba miki mama nusai ,da ya sani ma ni ya kira babu wanda zai san yayi kuka."
Cewar Fati.

"Kwa dai ji dashi ."
Salma ta fad'a a hankali snn ta shige d'akinsu.

Cikin zullumi ya koma gida yana ta tunanin yadda zai shawo kan yayunshi  su amince da auren Salma.
Hakan kuma bai hana shi kiran ta ya dad'a kwantar mata da hankali ba, saida yaji ta saki jiki snn ya kyaleta, ya d'ora daga inda ya tsaya (tunanin kenan.)

Itako salma duk da ta yarda da Ahmad da k'aunar da yake mata ,wani gefe na zuciyarta yaki yarda cewa ahmad zai iya cika mata alk'awari.
Daga k'arshe dai tayi wa kanta add'uar fatan alkhairi tsakaninta da ahmad.

Shawarar da zuciyarshi ta bashi yayi niyyar aiwatarwa, dole ne ya saki jiki da yayanshi ya daina wnn fushi da yakeyi dashi ko Allah zaisa ya dace.

Washegari ya shiga gurin yayanshi dan ya fara aiwatar da kudirin shi.
Saidai me.....?
[17/12 06:24] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers*


*F.O.W.*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*

               12.


       💔💔💔💔💔💔

*Wannan shafi zai tafi ne direct zuwa gareki my kakus (Amina Sale Muri)*
Mmn Baba, Allah ya barminke 😍

*Masoya na gode da addu'oinku ,ina alfahari daku , ina qaunarku fiye da yadda kuke qaunata.*



Yana isa yayanshi ya fara zazzaga mishi masifa, "Wato ahmad, ni ban isa da kai ba ko? kafi k'arfin in sa ka ko in hanaka kenan.
Tun yaushe nake binka kaje wajen Asiya ku zanta kaki saurarona ,kai gaka isasshe, to bari in fad'a maka da kaje da kar kaje duk sammakal aure dai ba fashi, idan yaso dan tsabar kiyayyar da kake mata idan an kawo maka ita kayi gunduwa gunduwa da ita ka kawo min  ,kaji ko?"

Amma yaya da ka barni na zab'i wata ko ba salma ba akan da ka min auren dole yanzu watakila yarinyar ma tilastata za'ayi kaga idan akayi mata hakan ba'a yi mata adalci ba."
Ahmad ya fad'a cikin sassauta murya.

"Ahmad, ba shawara ko ra'ayinka nake nema ba ,umarnine nake baka a matsayina na babban wa wanda nake mazamin uba .
Ita yarinyar da yake 'yar arziqi irin albarkace batayi musu ko ta nuna wata matsala ba sai kai da kake mai bushasshen ido."

"Ahmad bishi a hankali ka samu biyan buqata."
Zuciyarshi ta raya mishi.

"Allah ya baka hak'uri ,yaya zanje anjima da yamma."
Ahmad ya fad'a cikin tausayawa kanshi.

"Kada ma kaje in ka dama Ahmadu, gwara ka nunawa aminina da duniya cewar ban isa da kai ba ,itakam asiya ta nuna an isa da ita tunda tayi wa mahaifinta biyayya ,ba irinka ba marar jin magana da rashin sanin ciwon kai."

"Oh Allahna."
Ahmad ya fad'a cikin ranshi.

A fili kuma yace ,
"Zanma je in sha Allah."
Daga ya tashi ya fice yana jin kanshi na juya mishi.
Wato yayanshi so yake ya d'ura mishi hawan jini, idan ba haka ba meye na cewa sai yaje zance bayan ya san ba son yarinyar yakeyi ba snn qiri qiri yanaso ya raba shi da masoyiyarshi,abar qaunarshi, hasken idaniyarshi.


Zuciyarshi a cunkushe ya tafi gidan abokin yayanshi, aka yi mishi iso .
Zaune yake yana tunanin me ma zai cewa yarinyar.

Nazo zance?

Yayana ya turo ni ?

Oho ni banma san me zan ce mata ba.
Itama mai matacciyar zuciya ,ace mutum bai ce yana sonki ba a had'aki dashi ki yarda.
"Mtss ."
Ya ja tsaki a bayanne dan sauran zantukan a zuciya yake yinsu


Ni ko nace "Amma ahmadu ka cika d'an rainin sense ,me kake cewa Salma idan kaje wajenta😏

Yana zaune yaji sallamar  Asiya ta ,ciki ciki ya amsa dan sanin muhimmancinta.

Shigowa tayi hanunta d'auke da trayn silver , kwalin juice , robar ruwa sai kananan cups a kai.

Sanye take da atamfar cote d voir ,kalar brown ,ta yafa gyale wanda ya shiga da kayan ,fiskarta tasha kwalliya ,sai kamshi ke tashi a jikinta kamar anyi b'arin turare.

Gabanshi taje ta duqa ta ajiye snn ta d'an koma baya kad'an.
"Sannu da zuwa Bappa ahmadu."
Ta fad'a da 'yar siriryar muryarta kamar ta asiyarmu.
Sunan da yaran yayunshi suke kiranshi dashi kenan.

"Kaji 'yar banza ,wai baffa ahmadu kamar wani tsoho."
Ya fad'a a zuciyarshi.

🤣🤣🤣 haba ahmad tunda ake kiranka da sunan baka jinshi kamar na tsofi ba sai yau, kar kayi dai nima na soma kiranka da wnn sunan.

Bata damu da kin amsa mata gaisuwarta ba duk da ba haka ya saba mata ba idan sun had'u ko in taje gidansu, amma ita kanta tasan wnn had'uwa ta dabance.

Matsawa tayi ta jinginu da jikin kujera snn ta kuma cewa "Ina yini Baffa ahmadu."

Baisan sanda yace "Ke ni baffanki ne, ta ina muka had'u na zama baffanki."
Shiru tayi kanta a kasa.

"Hindatu kike ko wa?"
Da sauri ta d'ago ta kalleshi .
Yana nufin ya mance sunanta ma kenan, lallai abin nashi da gaskene.

A hankali tace "Asiya."

'yar karamar tsaki yaja ,snn ya kalleta a yatsine, shi sai yanzu ma ya tuna da sunan 'hindatu 'yar yayanshi ya kirata.

A ranshi yace "Ji rashin kunya wai ita nan zatazo gurin saurayi har da cab'a kwalliya idan an barta tayi abin burgewa."

Nace ina ruwanka mal. Ahmadu indai ba burgekan tayi ba, kai ka saya mata kayan kwalliyar.😏

Asiya ko tace min gane min hanya Mmn Afrah.💞


*Gaisuwa gareki masoyiyar gaskiya Maryam A.I Gital, Allah ya bar min ke.*

 luv all my fans.😍😍
[17/12 06:24] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


*F.O.W*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*


               13.

   
       💔💔💔💔💔💔

*Dedicated to my sister ,Asiya muhammad.*


Asiya kyakkyawar yarinya ce fara tass ,don ko shi Ahmad bai isa ya nuna mata farar fata ba.

Jikinta d'an daidai, dirinta daidai jikinta baiyi yawa ba baiyi kad'an ba, karyanka kace ka ganta bata burgeka ba , bama kamar idan ka kalli kwayar idonta ,dan manyan idanune da ita farare tass, kamar dai na asiyarmu.

Ga bakinta d'an dadai mai d'auke da fararen qananan haqora.

Amma shifa ahmad duka wnn ba burge shi tayi ba, shi a gurinshi babu macen da ta kai salmarshi.

"Wai ke baki da wanda kike so yake sonkine zaki buge da auren baffan qawarki?"
Ya fad'a tare da tsare ta ido sai muzurai yake mata dan yasa mata tsoro.

Jin tayi shiru  bata ce komai ba sai wasa da yatsunta da takeyi ,yasa shi yace .
"Ke duba, idan har kinsan ba san aurennan kike ba ki fito kifad'a musu bakiso kinada wanda kikeso ,dan kar ki cutar da kanki ,yanzu an daina yayin irin wnn auren na takura, kina jina?"

"Hmmm."
Tace kawai tayi shiru.

"Ki bud'i baki kiyi magana ba kiyi ta "Hmmm ba, hmmm kam sai ta iya kasheki babu wanda yasan abinda ke cikinki."

Dariya maganar tashi ta bata wai hmmm zai kasheta.
Lallai ma baffa
ahmadunnan.

Murmusawa tayi snn tace "Nikam bazan iya bijire wa iyayena ba ,bazan yi musu dasu ba ,duk abinda suke so shi nakeso."

"Kaji wawiyar yarinya zata b'ata min shiri , tana nufin tana sona kenan ,lallai iska na wahalar da mai kayan kara.
Zancen zuci.

"To ni kuma ina da wacce nakeso ba ke ba ya kenan?"

Shiru ta masa tamkar bata jishi ba.

"dake fa nake."
Ya fad'a tsawace.

A razane ta kalleshi snn cikin rawar murya tace.
"Ka bar wa Allah komai zai zab'a maka abinda yafi alkhairi."

Shiru yayi na d'an lokaci dan ta so ta kashe mishi jiki.
Can dai yace.

"Ke ma kiyi addu'ar Allah baki miji maisonki."

"Aini na dad'e da neman zab'in Allah akan samun miji managarci ,mai addini, sanin ya kamata, mai mutunta d'an adam , snn wanda zai riqe ni da amana."

Harararta yayi "To kin tabbata nine wnn mijin da kika roqarwa kanki, kina da tabbacin zan riqe ki da amana, bayan kuma hankalina nakan wata?"

Kanta a k'asa tace "In sha Allah ,dan nasan addu'a bata fad'uwa qasa banza, nikam nayi na'am da zab'in da Allah ya min."

"Kinfa kawo point yarinya addu'a bata fad'uwa qasa banza ,nima dashi na riqe tuntuni Allah ya mallaka min salmata cikin sauqi."
Zancen zuci.

Niko nace zab'in alkhairi akace ba  abinda kakeso ba mal.ahmadu.🙄

Basu wani jima ba ya musu sallama ya koma , yana komawa gida ya tarar yayanshi yadawo daga kasuwa.

Gurinshi ya wuce dan ya sanar da shi ya je gurin Asiya ya dawo.
☹wa yaga notice me.

Duk da yaji dad'in zuwan da ahmad yayi bai nuna ba, saima ce mishi da yayi, "da fatar ba rashin mutunci kaje ka musu ba."

Shafa kanshi yayi tare da cewa "A'a wallahi."

"To yayi kyau."
Yayannashi yace atakaice.

Zama yayi kamar zaiyi magana sai kuma wata zuciyar tace mishi "Bi a hankali ahmad kar ya gano ka."

Sbd haka ya tashi yayi waje danjin an dara k'iran sallar maghrib .

Yanzu daga yayannashi har salmar lallab'asu yakeyi, ya rasa wa zai tankwasa a cikinsu ya zubar da makaman yakinsa.

Sai da ya kuma zuwa wajen asiya dan ya tabbatar wa yayanshi ya mishi biyyaya.
Bayan kwana biyu yaje ya same shi da maganar.

Bayan ya gaisheshi a ladabce yace "Yaya dama nazo ne batun maganar salma."
Sai kuma yayi shiru yana d'an sosa kai tare da kallon yayannashi k'asa².

"Ina jinka."
Yayan ya fad'a yana had'e fiska.

"Dama nace tunda zan auri asiyar me zai hana itama salmar a nema min aurenta , kaga ko tana aikin tunda asiya tana nan ba wata matsala, zata kula da gidan."

Kallon banza yayan ya bishi dashi snn yace "da yake ga maigaidin gida ka samu kenan, kai ka fita ,matar so ta fita ita ku barta da gadin gida ko?
To ban amince ba.
Ashe baka fita harkar yarinyar nan ba dama.
To daga yau kar ka kuma kawo min zancenta dan har abada ba amincewa zanyi ba, gwara ka rik'e wacce muka zab'a maka hanu bibbiyu ya fi maka alkhairi.
Ba kaje ka nacewa mai vakkugo boro (Mai rataya jaka.) tazo tana juya ka yadda taga dama ba ,dan irinsu ba imanine da su ba."

Shiru yayi yana kallon yayanshi yadda ya fitittike yake zuba mishi masifa yaki ya saurareshi sam.

"wani irin kallo kake min haka ahmadu, dan ina guje maka fitina shine zaka tsaya kana min irin wnn kallon rainin .
Akwai abubuwa da dama da muke guje maka wanda kai baka sani ba, ire iren wad'annan mata masu zuwa aiki fitina ne, sai kaga ana haifa maka yara masu kamanni daban² sai kayi sa'a kasamu d'aya mai kama dakai, kuma a jibge maka su a ce duk naka ne, babu kuma yadda ka iya kayi ta d'awainiya da shegu.
To ni dai ba da ni za'ayi wnn kafurci ba kaji na gaya maka."


*Mom Sadeeq ce*😍
[17/12 06:24] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers*


*F.O.W*


*By  Anty Ruky (Mmn Abduljalal)*


                14.

        💔💔💔💔💔💔


Takaici da bakin cikine suka cika ahmad jin irin qazafin da sharri da yayanshi yake faman d'orawa salma , sbd haka ya tashi ya bar mishi wajen ba tare da ya kuma mishi magana ba.

Lallai yayanshi baisan wacece salma ba da har yake tunanin zata iya aikata irin wnn hali.

Tunani ya Shiga yi a yanzu ga irin abinda yake fad'a akanta inaga in ya aureta ,lallai akwai yaqi a gabansu daga shi har salma ,dole su fiskanci matsaloli, shi kuma ba hak'ura zaiyi da ita ba.

Haka ya ci gaba da zuwa wajen salma ,bai sake kawo mata zance turo magabata ba ,ita kuma hankalinta kwance ,gani take kamar ya hakurane sai ta k'are karatunta.

Shi kuwa yayanshi da sauran yan uwa shirye shiryen biki suka fara yi dan gani suka idan suka sake zai botsare musu yak'i auren asiya .

Tunda yaje gurinta sau biyu bai kuma zuwaba ,ita kuma bata damu ba tunda tasan ba sonta yakeyi ba.

Bai tashi sanar da salma zancen bikin shiba sai ana saura sati biyu baikin nanma dan kada taji a bakin mutane ne ta ga kamar ya munafurce ta.

Sosai ta shiga tashin hankali dan lokaci da yasanar da ita labarin k'ura mishi ido tayi ko motsi babu sai aikin kallonshi takeyi cikin razani da mad'aukakin mamaki.

Shima kanshi ahmad cikin fargaba na yadda zata d'auki al'amarin da kuma abinda zai biyo baya yake.
Ba karamar dauriya yayi ba wajen yi mata zancen , ita ma kuwa yaci ace ta fahimci hakan ko daga yadda yake in ina wajen fad'a mata maganar.

Bata anakara ba taji hawaye na mata sintiri a kan fiska.

"Subhanallah, salma kuka ? Dan Allah ki daina zaki sa na karaya, kinsanfa nace miki ba san yarinyar nan nakeyi ba ,auren had'ine,
me zaisa ki tada hankalinki, dan Allaj ki daina."

Cikin sarkewar murya tace "Me yasa baka sanar dani tun wuri ba, saida ya rage saura kwanaki kad'an?"

"saboda nima ba'a sanar dani da wuri ba tunda sunsan ina da wacce nakeso ba zab'insu ba."
Ya shararo mata k'arya.

girgiza kanta ta shiga yi "Bazan iya ba ahmad ,bazan iya ba, dole na hakura da soyayyar ka koda zata kashenine."

Cikin firgici yace "Haba salma ,me yasa zakice haka, me yasa zaki yanke wnn hukunci ."

Katse shi tayi da cewa "Saboda danginka basa sona suna da zab'insu, kuma nikam..."
Sai kuma ta fashe da kuka.

"Wa ya fad'a miki basa sonki salma, suna sonki mana tunda ai kinga da kansu suka zo nema min aurenki, da ba don kin nuna bakyaso yanzu bama da yanzu an kusan gama komai ,dan Allah kada ki min haka salma."

Cikin kuka tace "nikam bazan iya ba ahmad kishi ma kad'ai ya isa ya kasheni ,bazan iya ba."

Innalillahi to ce miki  nayi ina sonta da zakiyi kishi da ita ,uumm?"

"Ko baka santa ina dai zaka zauna da ita ."

"Ni dai ki bar wnn magana na fad'a miki ba son aurennan nake ba , idan kika ce zaki hakura dani kinaso na mutu kenan."

"Ba wani mutuwa da zakayi ."
 Ta fad'a tana jan hanci.

Ganin abinnata da gaskene ya dage da rarrashi ,dakyar ya samu ta bar kukan ,shi ma d'in daurewa yakeyi, ji yake haushin yayanshi da na asiya suna dad'a cika mishi zuciya.

Bai bar gidanba saida yaje har wajen mal.ya sanar dashi maganar aurenshi , snn ya nuna mishi yana kan bakanshi game da maganar su da Salma.

Nasiha sosae mal.ya mishi daga karshe ya mishi add'uar Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba.

Ita ma ummi da kanshi yaje ya mata bayani, addu'ar zaman lafiya ta mishi itama, tana mai tausaya musu dashi da salma.

Tun daga ranar salma take jinta wata iri.
Sosae take jin zafin abin a ranta.
Wai yau Ahmad ne zaiyi aure kuma wata zai aura ba ita ba , gaskiya abin na ci mata tuwa a qwarya.

Ranar tashin hankali.

Ranar da aka d'aura auren ahmad da asiya , daga ahmad d'in har salma cikin tashin hankali suke.

Tun safe yake neman layinta taki d'auka ,qarshema kashewa tayi.

Kwance ta wuni a ranar dan zuciyarta ke mata ciwo.
Dakyar ummi ta sata a gaba taci abinci da rana.

Ganin yadda ta sawa kanta damuwa ,ummi ta sanar da mal.halin da salma takeciki.

Nasiha ya mata mai ratsa jiki, duk yadda ta so ta daure saida tayi kuka.

Daganan ta shige d'akinsu ta kwanta tana jin yadda zuciyarta ke bugawa tamkar zata fito waje.

Har dare bata kuma fitowa ba, bata qara cin wani abinci kuma ba, fati da nusaiba duk sun shiga damuwa, sosae suke tausayawa auntyn tasu.

Har dare yana neman layin baya samu ga rashin kwanciyar hankali, dan duk wata hidima da akeyi kallon abokan shi kawai yakeyi.

Layin nusaiba ya gwada kira,ya kuwa ci sa'a ta shiga.

Bayan sun gaisa ya tambayeta salma.

"Gata kwance tun safe bata jin dad'i."
Abinda tace mishi kenan.

"Taci abinci?"

"Kad'an taci tunda rana bata kuma ci ba."

"Ina zuwa "
Kawai yace ya kashe wayar.
[17/12 06:25] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online writers*


*F.O.W*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*


                15.


        💔💔💔💔💔💔


Ba da jimawa ba sai gashi yana sallama, har cikin gidan ya shigo ya gaisheda ummi snn ya nemi ganin salma.

Kwance take bisa katifar su fati ta lumshe ido tamkar maiyin bacci amma ba barcin take ba.

Muryarshi taji yana sallama kofar d'akin.
Tsabar rud'ewa kasa amsa sallamar tayi, sai tashi da tayi ta zauna tana kallonshi da mad'aukakin mamaki.

Fati ce da tayi rigingine kan gadon salma ,ita halin da 'yar uwarta tashiga yake damunta.
Ita ta amsa sallamar tare da bada izinin shigowa.

Tare suka shigo da nusaiba, ta je ta ajiye ledojin da ta karb'a daga hanun ahmad snn ta d'auki sallaya ta shimfid'a mishi.

A hankali ta sake komawa ta kwanta ta tana gyara zanin dake lullub'e a jikinta.
Lokaci guda kuma taji hawaye na jika mata fiska.
Ita kad'ai tasan irin azabtuwar da takeyi, yanzu kuma da ta ganshi sai taji ,abin ya qaru mata.

Gaisheshi fati tayi ya amsa idonshi na kan salma.

"Ya jikin?"
Ya cewa salma.

Shiru tayi tamkar bata san da ita yakeyiba.

"Daure ki tashi mu tafi asibiti a duba ki."

Da sauri kuma muryarta na rawa tace "Ni lafiyata lau."

"A hakan, yanda kika kudundune ,kika kwanta?"

"Bacci zanyi ."
Ta bashi amsa.

"To me ya hana ki cin abinci kuma."

"Na koshi."

"ban yarda ba."

Shiru tayi mishi.

"Ta so ki d'an tab'a wnn ko kad'anne salma."
Ya fad'a cikin sassauta murya.

Jin bata amsa kuma bata motsa ba ya kaurara murya "Sauko mana."

Shiru ta kuma yi.
"Kin san Allah, idan baki taso ba d'ura zan miki, kuma ki sa wasa ki gani , zaku rik'e min ita aiko kanwarmu."
Ya fad'a yana maida dubanshi gun su nusaiba

"Sosae ma ."
Nusaiba tace.

D'an bud'e idanunta kad'an tayi tana kallonsu.

"Kunga, Fatinmu, kuzo ku rik'e min ita naga idan ba d'uran aka mata ba ba ci zatayi ba."
Ya fad'a yana nad'e hanun farar shirt d'inshi.

Wuff ta tashi  tana raba ido dan duk a tunaninta da gaske yakeyi d'uran zai mata.

"yauwa qanwarmu miqo min plate."

Da sauri nusaiba ta fita ta kawo plate.

Ita kuwa salma binshi take da kallon mamaki ya wani zo ya zauna musu tsakiyar d'aki har da tankwashe qafafu kamar mai neman gafara, har da wani cewa zai mata d'ura.

Ajiye mishi plate d'in nusaiba tayi ta koma ta zauna kusa da fati.
A cikin ledojin da ya shigo dasu ya bud'e d'aya, ya juye cikin plate d'in .
Take qamshi ya cika d'akin har yawun su nusaiba ya tsinke ,banda uwar gayyar dan babu abinda zai burge ta a yanzu.

Gasasshen nama ne ruwa² wanda yaji kayan had'i sai tiriri yakeyi.
Ya sake fiddo kwalin exotic babba mai sanyi dan har rab'a²
yakeyi.

Had'e fiska yayi yace "Sauko mana."
Su nusaiba ko sun zuba ido suna kallon drama.

"Ko dai d'uran za'ayi ne?"
Ya fad'a yana yunk'urawa kamar zai tashi.

Ai da sauri ta sauko ta zauna kusa da plate d'in tana ta fama gyara zanin da ta lullub'a dashi, kasancewar top yellow da skirt baqi a jikinta ,kuma top d'in 'yar qarama ce.sai bakar hula da ta sa akanta.

Ganin duk tabi ta takura kanta yasa shi cewa fati "Miko mata hijabi."

Miqa mata fati tayi ta amsa tasa snn ta ture zanin yayi kasa.

Kawar da kanshi yayi ya maida hankalinshi kansu nusaiba hakan ya bata damar ci kad'an ta cire hanu.
Dan dama tana tunanin yanda zata bud'e baki taci yana kallonta.

Tana cire hanu ta matsa a hankali ta kwantar da kanta kan katifar .

Da ido nusaiba ta mishi alama.
 ya juya ya kalleta.

"Har kinme?"
Da sauri tace .
"Na qoshi wlh ,ahmad dan Allah kada kace na qara.

Tausayi ta bashi yanda take magana muryarta na rawa .
Exotic d'in ya tsiyaya a qaramar glass cup d'in da nusaiba takawo.

"Amashi wnn kisha to."
Ya fad'a a tausashe.

Bata son yawar magana shi yasa ba musu ta karb'a tasha rabi, zata ajiye yayi saurin tareta da cewa .
"Yi haquri ki qarasa shi mana."
Har wani langab'e kai yakeyi.

Kafa kai tayi ta shanye snn ta maida kai zata kwanta.

"Taimakeni ki zauna ya d'an shiga jikinki tukuna salma."
Ya dakatar da ita daga kwanciyar da takeson yi.

Hakan yasa ta zama ta lumshe idonta tare da d'ora hanunta kan goshinta.
Ita matsalarta a yanzu ganinshi da takeyi shi yake dad'a tayar mata hankali idan ta tuna da yanzu mijin wata ce sai taji kamar ta kurma ihu .
Duk da taji dad'in kulawar da ya bata, tunda tasan amaryar ya baro yazo yana fama da ita taci abinci, hakan ya nuna mata da gaske ba son auren yakeyi ba.

Matsowa yayi kusa da ita cikin tausasa murya yace...
[17/12 06:25] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


*F.O.W*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*


             16.

      💔💔💔💔💔💔
*Ban manta da ku ba .*

Reedah malaysia.
Zaa princess.
Fatima (Bazamfariya)
Mmn Sa'ad.
Mmn sadiq.
Fadhilatu Ali.
Habiba Muhammad.
Ummi Aisha.
Mmn Humaira.
Amina jaji.
Ahmatallah.
Kai kuna da yawa fa masoya.
*Allah ya bar k'auna*
*Ana tare.*👍👍

"Salma dan Allah kirufa min asiri ki cire damuwa a ranki, idan kinayin haka hankali na tashi yakeyi ya kikeso inyi, dame zanji .
Abinda kin riga kin sani Salma ce a zuciyar Ahmad, to meye naki na d'aga hankali.
Kin ga saboda kin d'aga wayata da kikayi yau haka na wuni da zazzab'i ko uabinci ban iya ci ba."

Da sauri ta bud'e ido ta kalleshi, idanun duk sun rine sun kankance.
"Yanzu haka ka wuni baka ci abinci ba?"

"To ya zanyi kin min rowar muryarki ,kuma nasan idan ba kina cikin damuwa ba baza kiqi d'aga wayata ba, qarshe ma kika kasheta gaba d'aya."

"Yi hakuri."
Ta fad'a kamar zatayi kuka.

"bazan hakura ba kuma haka zan kwana da yunwa indai baki bar damun kanki da d'aga hankalinki ba."

"zan bari wlh, dan Allah kaci abinci, bari nusaiba ta kawo maka."

"a'a ni bazanci abinci gidan surakanina so kike ace bani da kunya?"

"Ba wani rashin kunya."

Basar da zancen yayi da cewa "to yaushe zaki bar damuwan naji kince zaki bari."

"Na bari ma, kaci dan Allah."

"Ban yarda ba har sai naga murmushin kan kyakkyawar fiskarnan."

Bata san sanda murmushin ya sub'uce mata ba, su ma su nusaiba dake kallonsu saida suka murmusa.

"Yauwa to,ko kefa, kinga yanzu idan na koma gida zanci abinci hankali kwance, Nusaiba ,fati, ga amanata, ko na tafi kar a barta cikin damuwa, kar abari ta kuma zama da yunwa ,snn kada kubar ciwonnan ya sake damunta."

Dariya dukansu sukayi, cikin dariyar nusaiba tace "lucky abun baiyi yawa ba?
ta ina zamu ga ciwo kuma mu hana shi kamata?"

"Ku qoqarta dai qannena."
Ya fad'a yana mik'ewa.

"Yauwa ina wayar auntynku?"

Fati ce ta bud'e bedside drawer ta miqa mishi.

Kunnata yayi yana mita ,"Waya cajinta a cike aka kasheta kawai dan a quntata rayuwar bawan Allah."

Miqa mata wayar yayi a taimakeni kada a kuma kasheta ,ko zan samu barci."

"Kai lucky", nusaiba ta fad'a tana dariya.

"Allah da gaske nake , idan banji muryarta ba baxan iya bacci ba."

Ah, lallai abin azeemunne.

Sunkuyowa yayi kusa da ita "Zan tafi salma , Allah ,qara qarfin jiki, ya yaye miki wnn zafin kishin."

Harara ta sakar mishi, ya kama kunne yana dariya.

Sallamarsu yayi ya tafi ,Salma sai binshi da ido takeyi .

Saida ya fita ta lumshe idonta ,ta yi rigingine kan katifa.

Nusaiba da fati da suka tafi rakiya suka shigo.
Suna shigowa nusaiba taje ta zauna a inda ya tashi ta wani tanqwashe qafafu kamar dai yadda yayi d'azu.

"Sauko kici ."
Ta kwaikwaiyi muryar ahmad har da wani had'e ranta.

D'an bud'e ido salma tayi ta kalleta taja 'yar siririyar tsaki.

"Kinsan Allah idan baki taso ba d'ura zan miki, fatinmu zaki tayani aiko?"
Ta sake kwaikwayon shi.

Dariya ce ta ciyosu daga fatin har salma suka shiga darawa, salma kuwa tana dariyar ta d'au pillow ta jefeta dashi tana cewa "Mara kunyar banza."

Kama baki tayi "Oh aini naga rashin kunya soyayya gaban yara ba ko kunya, ke d'in ma harda biye mishi kina wani marairaicewa da kashe murya."

"Allah ya duba miki adda nusai."
Fati tace.

"Bari ma na duba menene a babban ledan can, mutane
duk sun gama tsinka mana yawu ,da nice ke aunty ai sai na bar muku sud'i wnn uban qamshi, amma har wani yanga kike, Fati ,kin san me?
Inaga a gurin da yayanmu yake sayo mana lucky ya sayo naman nan, baki ji k'amshin iri d'aya ba, har ma da d'and'anon."
Ta k'arishe tare da jefa tsoka na biyu cikin bakinta.snn taci gaba da
 bud'e sauran  ledojin tana surutai.

Fruits ne cikin babban ledan, kama daga lemu ,ayaba, kankana, apple, abarba dss.

Fati ce tazo ta kwashe tana cewa "Bari a je a nunawa ummi tukuna buku kwad'aima."

******   ******  *****

Yana komawa gida ko hanyar d'akin amarya bai kalla ba.
Wankanshi ya shiga yayi snn ya kira salma suka sha hirarsu.

Washegari haka salma ta tashi jiki ba k'wari, da ka kalleta kasan akwai damuwa a tattare da ita.

D'akin al-amin ta leqa bayan ta gama shiryawa zata tafi makaranta , ta sameshi yana karyawa.

Gaisheshi tayi tace "yayanmu rabo na da kai tun jiya da safe."

"Na shigo da daddare ummi tace min lucky yana d'akinku,yazo dubiya.

Shiru tayi tayi qasa da kai, kiran sunan lucky da yayi yanzu har yasa gabanta fad'uwa.

"Salma."
Yace bayan ya ture kwanon d'umamen da ya gama ci.
"Na'am ."

Tace gabanta na tsananta fad'uwa dan tasan shi d'in ma dai bai wuci maganar auren ahmad zai mata ba.


*Gaisuwar takice swt sister , Halima Auwal, Allah ya qara miki lfy da kwanciyar hankali.*
[17/12 06:25] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


*F.O.W*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*


                17.


      💔💔💔💔💔💔


"Ina so ki nitsu ki bani hankalinki ki saurareni dan fahimci abinda zan fad'a miki."

Gyad'a mishi kai tayi ba magana kam.

"Kinga aurennan da kike gani, nufi ne na ubangiji , shi aure muqaddarine snn kamar yadda kike ga mutuwa ta ke d'auka idan tazo ba jinkirtawa, haka shima aure, idan lokacin shi yazo ba makawa sai anyi shi.
Babu wanda yake auren matar wani ,kamar yanda babu wanda zai haifi d'an wani, sbd haka, ki dad'a tabbatarwa kanki cewa lokacin auren ahmad ne yazo kuma anyishi akan lokacin da ubangiji ya qaddare shi.
Dan yayi aure ba shi yake nufin baza kuyi aure ba, a'a lokacine da rabo, idan da rabo kamar yaune, sai kiga anyi ya wuce.
Idan kuma kika ga bakuyi auren ba dama can Allah bai hukunta zakuyi  bane, sai ku sawa zuciyoyinku haquri da tawakkali.
Wani lokaci mutum yakanso abu matsanancin so, amma sai kiga ya zamo ba shine alkhairi a gareshi ba, mafi alkhairi yana can ta inda ba'a yi tsammaniba.
Wani lokacin kuma mutum yakanqi abu ba tare da yasan abinda yaqin shine alkhairi a gareshi ba.

Ni dai shawarar da zan baki ki sawa zuciyarki haquri da dangana, ki nemi zab'in alkhairi wajen Allah.

Bayan haka akwai abinda na lura dashi.
Soyayyar ahmad ya rufe miki ido yasa kin manta ko ince kinyi watsi da abubuwa masu muhimmanci.

Kin yi karatu kina da ilimin addinin ,bakya buqatar na fad'a miki cewa duk waraka tana cikin qur'ani.
Na fahimci ayanxu ahmad shine weak point d'inki, inda bakiyi watsi da karatun qur'ani ba yaushe damuwa zatayi miki yawa har ta sa miki ciwo.

Ki riqe Qur'ani ki samu waraka daga rabbil izzati, salma, ki daure ki cire duk wata damuwa, duk abinda kika ga ya faru da bawa dama can *Rubutaccen al'amarine*.(Aysha Ali Garkuwa)

Allah ya sa kin fahimci abinda nake nufi."

Ajiyar zuciya ta sauqe ,lallai al-amin ya haifu cikin malam, yawancin abubuwan da ya fad'a yanzu kusan irinsu malam ya fad'a mata.

Lallai tasan tayi sakaci da karatun qur'ani dan idan bata manta ba takai aqalla sati biyi bata karanta ba.

Sosae taji dad'in shawarwarin da ya bata har tanajin kamar damuwarta ya yaye.

Sbd haka ta mishi godiya .
Shi ya rakata yana bata shawarwari har ta samu abin hawa ya biya mata ta shiga ta tafi.

Daga wannan rana Salma ta koma karanta Al-qur'ani mai girma fiye ma da yadda take yi da, snn bata wasa da tashin dare tana nemawa kanta sauqi gurin mamallakin sammai da qassai.

Cikin ikon Allah kuma kashi tamanin cikin d'ari na damuwarta ya yaye, bata da wata matsala illa ta kishin Ahmad dake mintsilinta sa'i da lokaci.

Auren da yayi baisa ya daina zuwa gun Salma ba, zuwa yakeyi kamar yanda ya saba.

Ganin haka yasa wata rana ,bayan bikin ahmad da sati biyu Ummi ta k'ira salma tayi mata magana.

"Salma yanzu abinda kike yi kina ganin kina kyautawa?"

"Me nayi ummi?"

"Yaronnan ahmad ba aure yayi ba."

Dummm, taji kirjinta ya buga ,dakyar ta bud'i baki tace "eh..aure yayi."

"To me yake kawo shi wajenki kullum?"

To fa me ummi ke nufi kenan dan ahmad yayi aure saisu rabu kenan? ai shi ba son auren yakeyi ba.
Tunanin da takeyi kenan.
Ummi ta katse ta da cewa
"Da kefa nake , nace me yake kawoshi wajen ki kullum."

Nanma shiru salma tayi heart d'inta na dukan tara tara.

"Salma , ya kamata kuyi wa kanku fad'a.
Ita yarinyar ba rai ke gareta ba. , yanzu ke zaki ji dad'i ace kiyi aure ,amma kullum mijinki ya bar ki a gida yaje wajen zance?"

Wani rarass zuciyar salma yayi, mijinta yayi mata haka kam ai ya kasheta da ranta , inaa baza ma ta iya ba.

"Salma ki sani duk abinda aikata wa wani kai ma sai an maka, watakil ma fiye da abinda ka aikata. Kin so kanki da yawa salma ,kin manta fad'in manzonmu annabi Muhammad (S.A.W)

"Laa yu'uminu ahdukum hatta yuhibbu li'akhiihi maa yuhibbu linafsihii."

"Imanin d'ayanku bazai cika ba har sai ya so wa d'an uwansa abinda ya sowa kansa."

"Salma ko kin manta da wannan hadithin.
Shin idan kukayi auren ma haka zaku je kuyi ta wulaqantata kuna nuna mata ita d'in ba komai bace?

Shin ke baza ki nuna mishi yayi adalci ba ,kanku kawai kuka sani.

Ko kin manta irin azabar da Allah ya tanadarwa namiji mara adalci tsakanin matansa?

A tunaninki soyayya kike nuna mishi kenan?, sam wnn ba soyayya bace, soyayya ta gaskiya itace ka taimakawa masoyinka ya tsira daga fad'awa halaka.

Bari kiji na fad'a miki , yau koda ba ahmad bane ya aure ki, alhakin baiwar Allahn nan bazai barki ba, sai Allah ya bi mata haqqinta, saikinga sakayya ganin idonki.

Ba baki ko fata nake miki ba, ina guje miki abunda zai hana ki kwanciyar hankali ne a gidan aurenki tunda kin bada gudummawar tashin hankalin wata a gidan aurenta.

Kiyi wa kanki fad'a ,ku gyara tun abu baiyi nisa ba, ki guji d'aukan haqqi, ki kuma taimaka wa ahmad ya tsira daga halakar dayakeso ya jefa kanshi, ni dai na gaya miki."

Jiki a sanyaye salma tace" na gode ummi, in shaa Allahu zamu gyara, hakan bazata kuma faruwa ba ."

"Da dai yafi muku."

A sanyaye ta mik'e ta fita daga d'akin ummi ta shige nasu.
Sulalewa qasa tayi ta zauna dab'as, ta fara tunani.

Lallai ta yarda da maganar ya al-amin da yace ahmad shine weak point d'inta,soyayyar ahmad ya sa ta manta da abubuwa masu muhimmanci.

Lallai tayi contributing wajen cutar da matar ahmad, in itace abin ya faru da ita ya zatayi ,ina zata sa ranta ?

Ajiyar zuciya ta sauqe a fili tace "dole ayi wa tufkar hanci."

To ko ya ahmad zai d'auki zancen?

*Mom Hanan ce🥀*
[17/12 06:25] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers*

*F.O.W*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*


               18.

      💔💔💔💔💔💔

*This page goes directly to u my other half ,Nafeesat Abdussalam (Mrs Bashir Bello.)*
*LYSM.*❤❤❤


Saida ta gama tunaninta snn ta tashi ta d'au wayarta ta qirashi.

Bayan sun gaisa tayi shiru ta rasa ta inda zata fara.

Shi mamaki ne ya cikashi kasancewar Salma bata kiranshi saidai shi ya kirata ,snn kuma basu jima sosae da gama waya da ita ba, to me ya faru?

"Lafiya salma?"

"Magana zamuyi ahmad."

"magana wace iri ?"

"Mai muhimmanci."

"Lallai kuwa mai muhimmancine tunda aka qirani ,kuma ansan anjima zanzo, me ya faru ?"

"Ahmad pls kar kazo yau , in fact ma inaso ka rage yawar zuwa wajena da kakeyi dan Allah."

"Kashe zan kiraki." yace .
Tun bata kashen ba ya rigata kashewa ya kuma k'iranta.

"Salma?"
Ya qira sunanta cikin tashin hankali.

"Kece kuwa?"

"Nice Ahmad."

"Nayi miki laifine?"

"Baka yi min komaiba ahmad."

"To wa yakeso ya shiga tsakaninmu?"

"Babu kowa, so nake matarka ma tasamu lokaci da kulawarka dan tana buqatar hakan."

Bashi ba hatta ita mai maganar zuciyarta bugawa takeyi da qarfi.

"Salma kice min kin samu wanda ya fini shi yasa kikeso ki rabu dani ta wannan hanyar."

"ko kad'an ba haka bane, ahmad muna shiga haqqin baiwar Allahn nan, kasani Allah babu ruwanshi da kana sonta ko baka sonta ,iyaka dai akwai igiyoyinka qwarara akanta,.
Kamar yadda kake da haqqoqqi akanta haka itama akwai haqqoqinta da suka rataya a wuyanka, abu mafi A'ala gareka shine kayi qoqarin sauqesu ,tun kafin hakkinta ya kamaka.

Ahmad bamu kyautawa yarinyar nan, itama Allah ne ya halicce ta kamar yadda muma ya halicce mu, tana da zuciya da rai kamar yadda muke dasu.
Me yasa zamu cutar da baiwar Allah bataji ba bata gani ba.
Kayi tunani bafa ita ta kawo kanta gareka ba, kawo ta akayi, auren nan babu mamaki ita ma ba sonshi takeyi ba tayi haquri tayi biyayya ta zauna a gidanka.
Aurennan fa ya riga ya d'auru ba kwance shi za'a yi ba.
Allah kad'ai yasan abinda ke b'oye.
Kayi haquri ka yarda da qaddara , ka riqe matar ka hanu bibbiyu ku zauna lafiya zaka ga ribar hakan in sha Allah.

Cikin sauri yace "Salma kina nufin kin barni kenan?"

"Ban barka ba ahmad, ina tare dakai in shaa Allah, ni dai burina kada mu shiga hakkin baiwar Allah, Allah ya kama mu."

Sai a snn ya sauqe ajiyar heart.
"To me ya had'a hakan da zuwa gunki kuma?"

"Ahmad so kake su malam su hanaka ni suce baza kayi adalci ba?"

"To naji amma dai zanzo yauko?"

"A'a banda yau banda gobe."

Zaro ido yayi tamkar tana ganinshi, yace "Banda yau banda gobe ma, anya salma?"

"Mu daure dai Ahmad."

"Na shiga uku ni Salman salma zata kashe ni."

Dariya ta fashe dashi "Haba ahmad be strong mana, mutuwa guda?"

Shima dariyar yayi. jin yayi dariya tasan komai normal yanxu sbd haka ta kashe wayar.
Har yanzu zuciyarta bata bar bugawa ba, ita kanta ta jinjinawa qoqarinta da kanta.

Bin wayar yayi da kallo snn ya ajiyeta gefe.
Nazarin maganganun salma ya shiga yi, duk da ba a yau kuma ba a kanta ya fara jin ire iren maganar ba ,amma ta salma tafi shigarshi .
Tariyosu yakeyi d'aya bayan d'aya yana auna su kan mizanin hankali .

Tabbas ta fad'i gaskiya , zaiyi qoqari yaga ya gyara.

Kamar kullum yau ma da kusan magriba ya shiga gidan, sallama yayi ciki² kamar dai yadda ya saba, amsa mishi tayi, tayi mishi sannu da zuwa, duk da tasan ba lallai bane ya amsa, tunda sai ya ga dama yake amsa mata magana.
Ga mamakinta sai taji ya amsa ba tare da ya d'au lokaci kamar yadda ya saba ba.

Kitchen ta koma taci gaba da ayyukanta.

Can ta fito zata shige d'akinta sai ganinshi tayi zaune cikin falonta.
Bin falon yakeyi da kallo yana tunanin ,gidan da ya gina da sunan salma, falon salma , yau wata ce a ciki ba salma ba.
Ikon Allah kenan Ahmad.

Itakuwa mamaki ne ya cika ta dan tunda ta zo gidan bai tab'a shigowa falonta ba ,sai dai taji motsinshi a falonshi, iyakaci dai tana iya qoqarinta taga sun had'u da safe ko ta yaya dai ta gaisheshi, snn idan ya dawo tana zuwa ta mishi sannu da zuwa, bayan haka tana kai mishi abinci duk da ko kallon abincin bayayi hakan baisa ta fasa kai mishi ba tunda shi yake cefanowa, ita dai fatanta watarana ya sauqo komai ya zama labari.

Har tad'an wuce ta dawo, "Akwai abinda kake buqatane?"
Ta tambaya a ladabce.

*Gaisuwa gareki sister Shema'u (Mmn Doctor)Ina yinki tawan.*
[17/12 06:25] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


*F.O.W*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*


             19.
 
     💔💔💔💔💔💔

This page is specially dedicated to you my brother.
*D'alhat Musa Muhammad Dagauda.(Abu Hanifa.)*
I am very proud of u bro.

***   ****  ***

Firgigit yayi ,alamun yayi nisa a tunani.
Ya kalleta kad'an ya kauda kai "Babu."
Yace a tak'aice.

Kamar zata wuce sai kuma ta canza hanya  gurin d'an k'aramin fridge d'inta dake cikin falon ta nufa.
Ruwa mai sanyi ta d'auko da plate da d'an karamin glass cup ta kawo ta ajiye kusa dashi snn ta wuce .

Da kallo ya bita snn ya maida kallon kan ruwan da ta ajiye mishi.

Fitowa zata wuce,har yanzu dai mamaki bai barta ba , ba taganshi a falon ba sai ruwan da ta ajiye.

Zuwa tayi ta d'auka ta mayar , ga mamakinta sai taga yasha ruwan.
Murmushi tayi ta tattara tana ci gaba da jinjina al'amarin.

A gurguje ya shiga d'akinshi yayi wanka tare da alwala dan zuwa sallar magrib.
Zuciyarshi fal tunanin aikin da salma ta sa shi.
Ya dai quduri niyyar bata lokaci da kulawa saidai ya rasa ta yadda zai fara.

Sai bayan sallar isha'i ya shigo .
Falonshi ya nufa ya zauna tare da kiran wayar salma.
Yaudai yasan kewarta sai ta kusa illata shi.

Ko gaisawa bai tsaya sunyi ba yace "Da zan iya yau d'innan da fushi zanyi da ke Salma."

"Me kuma nayi Ahmad?"

"Kin fini sanin lafinki ."

"Nifa ban sani ba sanar dani."

"Da kika haramtamin ganinki yau da gangan dole kice baki sani ba."

"Oho, ai har da gobe ma."
Ta fad'a tana dariya duk da dai dauriya takeyi dan ta qara mishi qwarin gwiwa.

"Salma, har ma dad'a jaddada min kikeyi har da gobe ma ko?"

"Eh mana."

"Zamu gani goben idan da qafar ki zan zanzo."

"Assalamu alaikum."
Asiya tayi sallama tare da kutsa kai cikin falon dan sam batayi tsammanin samun shi ciki ba tunda dama ta saba kullum saidai tazo ta ajiye abincin baya nan.

"Wa, alaikumussalam, bismillah ."

Yace snn ya maida hankalinshi ga wayar da yakeyi.
Zai qara magana yaji ta kashe wayar.
Kallon wayar yayi da kyau ya tabbatar dai kashewan tayi ,sai ya sake dialing.
Shiru bata d'auka ,ba har sau uku.

Ajiye wayar yayi yana maida dubanshi kan asiya dake kofar fita.

"Zo ki zuba min abincin."
Taji yace.

Cak ta tsaya tana tunanin ko bata ji da kyau bane.

"Baki ji bane?"

Yanzu kam ta tabbata kunnuwanta sun jiye mata dadai.

Dawowa tayi tayi serving d'inshi , har taje ta kawo ruwan wanke hanu da nasha, yana zaune dafe da kanshi da hanuwanshi biyu.

Salma dai ta bashi aiki, yanzu kuma tunani yake koma zaiyi bayan wnn.

Har ta juya zata tafi ya d'ago ya kalleta.
"Ina zaki kuma?"

To fa, baffa ahmadu kam yau lafiya kuwa.

A tsanake ta dawo ta zauna a k'asa  nesa dashi kad'an tayi k'asa da kai.

Gaskiya abin fa da mamaki, yau ya canza mata da yawa, ko dai har ya sauqo ne da wuri haka.
Ko me ya canza mishi ra'ayi?

Bata ida tunani ba taji yace " ke baza kici abincin bane?"

"Yanzu zanje inci."

"Me ya faru da wann an d'in da bazakici anan ba."
😳anya bappa ahmadu ne kuwa, ko canza mata shi akayi.

Hhhh nace ba'a canza miki shi ba asiya, addu'ar kice ta karb'u ,da kuma qoqarin ummi, uwa ta gari mai sanin ya kamata da hangen nesa , da kuma baiwar Allah salma , mai jin maganar iyaye, da d'aukan nasiha ga kuma kishin kai.

"Asiya baza kici abincin ba?"

Adarare ta matso ta zuba abincin tana satar kallonshi, shiko hankalinshi ya maida kan abincin da yake ci.

Gefe ta koma tamkar wata bak'uwa ta zauna taci itama.
Tana gamawa ta tashi ta tattara tana mamakin yadda yaci abincin da yawa.

Shima duk abinda takeyi kallonta yakeyi, yaji dad'in abincinta ba k'arya ,baiyi tsammani zata iya girki kamar haka ba, amma fa shi yasan na Salmanshi sai yafi wnn dad'i.

Tana gama gyara gurin tafita.
Ajiyar zuciya ya sauk'e yana yabawa kokarin da yayi a yau.

Wayar salma yaci gaba da nema yaji ta a kashe ,duk haushi ya gama cika shi, ita ta hana shi zuwa snn ta k'i suyi magana ko ta wayar ma.

Washegari ,tana jiran taji fitowar shi taje ta gaisheshi yadda ta saba, sai taji shi ya shigo .

Gaisheshi tayi tana wani sunne kai, ya amsa yana binta da kallo, kunyarta irinta salma .
Yace aranshi.

"Ke kuma haka akeyi ,jiya kika tafi ba ko jam wala,(mu kwan lafiya)

"Hmmm ."
Tace ,kawai ba magana, sai murmushi da takeyi da tuno lokacin da yace mata hmm zai kasheta.
Yau kuma ko me zai ce mata?

"Hmmm ,ke ma inda dad'i."
Taji yace mata.
Murmushin dai ta kuma yi bata ce mishi komai ba.

"Zan fita to."

"A dawo lafiya, Allah ya bada sa'a."
tace.

Har ya fara tafiya a ranta tace bari dai ta gwada sa'arta.

"Baza ka karya ba zaka fita?"
ta fad'a a d'an tsorace.

Saida ya juya ya kalleta snn ya ce.


*08161594233*
[17/12 06:25] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers*


*F.O.W*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*

             20.

       💔💔💔💔💔💔


"kin gama abin karin ne?"

A hankali ta sauk'e ajiyar zuciya .
"Na gama."

"To kawo min."

Sauri sauri ta je ta had'a komai a babban tray.
A tunaninta zai koma falonshi, sai kuma ta sameshi a falonta.

"Nan zaki kawo."
Yace ganin tana wucewa.

Yauma zama yayi ya take abinci yayi naqq snn ya sallameta ya tafi, har da tambayarta ko akwai abinda take buk'ata.

Hakama da ya dawo saida yaci abinci ya shirya ya tafi gidansu salma.

"Haka mukayi dakai?"
Abinda ta fara ce mishi kenan bayan sun gaisa.

"Kema haka mukayi da ke?"

"Me nayi ni kuma?"
ta tambaya tana noke kai.

"Me yasa jiya muna magana kika kashemin waya kuma na k'ira kika k'i d'auka."

"Oh ayya lokacin naji kamar amarya na kusa ne shiyasa, kuma kaga bazata ji dad'i ba kuna tare kana magana da wata babu dad'i."

Harara ya banka mata, itako abinma dariya ya bata, ta shiga yi k'asa k'asa.

"Wlh, kika kuma kashe min waya zan fasa bada ratan ,ci gaba zanyi da zuwa kamar yadda na saba."

"Allah ya baka hak'uri, amma maganar gaskiya hakan bai dace ba, dan Allah idan tana kusa ka daina k'irana. Ko ni akaiwa haka bazan ji dad'i ba, kuma irin haka sai ka sa ta rika jin haushina wlh, kuma kaga maganar yawan zuwan nanma da gaske nake ,ka bada ratar atleast kwanaki biyu ko uku kafin kazo, dan itama tasan ka mutuntata."

Saida ya barta ta gama zuba zancenta yace "Idan naqi fa?"

Shiru ta mishi.
Ya kuma cewa "Auntyn asiya nace idan naqifa , me taya kishiya kishi."

Dariya ta d'an yi tace ,"nima sai naqi fitowa kalas."

"Allah, ko, to kalle ni mana ki rika bani amsa, kina magana kina sunkuyar da kai, kalli cikin idona ki fad'a idan da gaske kikeyi ."

Jin tayi shiru ya kuma cewa " ki gwada qin fitowa ki gani idan ban shiga har cikin gidan ba irin ba rannan kema kin san zan iya.
Nifa mamaki ma kike ban yanzu , kwanakin baya har da ciwo kikayi kan kishi amma yanzu ke kike taya kishiyar taki kishi akan kanki.hmm abin har da tsoro mafa ya fara bani , ko dai auren ne yasa kika rage sona salma?"

Kawar da kanta tayi gefe tanaji kamar tayi kuka ,dan ita tasan abinda take ji game da maganar auren nan nashi.

Daurewa tayi tace.
"Kaji tsoron Allah dai ka sauqe haqqin da ya rataya a wuyanka ,kuma kar ka cusa min ra'ayi nikam."

"To naji malama salma , wa'azin ya isa haka."
Ya fad'a yana tunani
a ranshi da yayanshi yasan wacece Salma da bai hanashi aurenta ba.

**** ****  ****

Zaune suke cikin falon Ahmad, suna kallon wani indian film d'in da aka sa a bollywood.

Ahmad dai kallo yakeyi amma sam hankalinshi baya ga t.vn.
Tunanin yadda al'amarinshi da Salma zai kasance kawai yakeyi.

Har ga Allah abin ya fara bashi tsoro yanzu, babu abinda yafi d'aga mishi hankali kamar idan ya tuna salma ta kusa gama karatunta amma har yanzu babu alamar yayunshi zasu amince mishi ya aureta, tsoronshi duk ranar da zata ce mishi ya turo magabatanshi.

Ita kuwa asiya kallonnata rabi da rabi ne, tana kallon film, rabin hankalinta kuwa ya karkata ga son gano abinda yakesa Ahmad nisa cikin tunani.

Yawancin lokuta takan ganshi cikin damuwa da tunani mai zurfi, duk da yana kokarin sake mata suyi hira cikin nishad'i, yana bata kulawa daidai gwargwado ,amma ko ba'a fad'a ba tasan yana cikin damuwa.

Kwantar da kanta tayi a kafad'arshi, wanda ya tilasta mishi sauqe ajiyar zuciya , dan ya manta yana tare da mutum cikin falon.

Maida kallonshi yayi kanta snn yace "Ya dai Sal- asiya."

Bata amsa mishi saima kokarin d'aga kanta da takeyi .

Kwantar da kannata dad'ayi yana mai tuhumar zuciyarshi da bakinshi wajen gaza b'oye halin da yake ciki.

A kullum mutuncin yarinyar qaruwa yake a idanunshi sbd hakuri da kuma kawaicinta.

Yasha kiranta da sunan Salma ,duk da dai ba amsawa takeyi ba, amma bata nuna mishi damuwarta ko a fiska ,har ya zamo idan ya kirata da Salma shi da kanshi abin yake bashi kunya.

Asiya bata da matsala, ga haquri ga tsafta ,kullum fes fes zaka ganta daga gidanta har ita kanta.hakan ya bata matsayi mai girma a zuciyar Ahmad, saidai yasan babu abinda zai girgiza kujerar sarautar sarauniyar da ke mulkar zuciyarshi. wato Salma.

K'ok'ari yakeyi kar damuwar da yake ciki ya shafi zamansu , amma ya rasa me yasa zuciyarshi da bakinshi suke nuna gazawarsu.

Kallonta ya kuma yi yaga ta lumshe ido tayi lamo tamkar maijin barci.

"Barci ko?"

Girgiza mishi kai tayi alamar a'a.

A sanyaye tace ina tunanin yaushe zanje inga Adda na ne.

Tausayi ta bashi yanda tayi maganar a sanyaye ,yasan ba wnn kad'ai ke damunta ,amma ya zasuyi dukansu cikin damuwar suke,  ya san yama fita damuwa dan a tunaninshi nata mai sauqi.

Yau aurensu watanni hud'u kenan da kwana shida.
Ita kanta tasan zuwa wnn lokaci an samu canji daga ahmad sosae ba kad'an ba.

Tasan haqurinta ya mata rana ya kumayi amfani, shawarwari da naseehar Addanta sun mata amfani sai dai damuwar da take gani a fiskar ahmad wasu lokuta yana d'aga mata hankali., har yakansa taso tasan taqamammen matsalarshi duk da dai jikinta yana bata damuwar bazata wuci a kan yarinyar da yace mata yana so bane.
[17/12 06:25] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers*


*F.O.W*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*


                21.


        💔💔💔💔💔💔          


Kwanto da ita yayi jikinshi gaba d'aya snn yace mata "Yaushe kike so kije ki ganta?"

Da sauri tace "ko yanzu ma."

Hancinta yaja yana murmushi yace "'Yar adda ,yanzu kam dare yayi ai, saidai gobe ko jibi ko gata ko..."

"Kaiiii...😳ta katse shi tana zaro , wnn dogon lissafi? goben dai dan Allah."
Ta fad'a a shagwab'e.

Ajiyar zuciya ya sauqe "Sai goben to in Allah ya kaimu."

"Allah ya kaimu"
 tace zuciyarta fal farin ciki.

"Amma fa tare zamuje mu dawo dan ba jimawa zakiyi a can ba."

"Ayya dai."
Ta fad'a da fiskar tausayi.

"To ba ganin su kawai zakiyi ba?"

"Har da Abba fa ,kasan shi ba lallai ne na same shi a gida ba, sai yamma yake dawowa."

"Sai nayi tunani akai idan naga zan iya."

"Zaka iya ma, naga kai d'inma sai  yamma kake shigowa."

"To kuma wa zai min girki?"

Shiru tayi ta rasa ma me zata ce mishi.

"Hmmm, baki ji bane?"

"Naji, basai ka siyo mana ba abu na rana d'aya kawai fa."

"ni kuma naki nakeson ci ya kenan?"

Da sauri tace "to zan dafa maka in na dawo."

"Huta abinki ,da wasa nake miki, Allah ya kaimu goben."

"Ameen ."Tace tana jin dad'in gobe zata je gidansu, dan tunda tayi aure bata je ba sai k'annenta ne suke zuwa mata.
Sai kuma gidansu ahmad da taje sau biyu.

**    **     **


Tafe suke ita da k'awarta faleela , paper rik'e a hanunta sai jakarta da ta rataya.
Dukansu biyu sanye suke da uniform na sch. Of nursing.

A nitse suke tafiya suna tattaunawa , hakan yasa Salma bata tari napep da wuri ba, har saida suka zo ta inda faleela zata ratse ta yi hanyar gidansu suka d'an tsaya dan su k'arasa tattaunawarsu.

Sallama suka wa juna kowa ta kama hanyarta .

"Sssssss."
Taji ake signal ,kusa da ita.
Ko alama bata nuna taji ba balle ta juya .

"ke 'yan mata."

Juyowa tayi da murmushi d'auke a fiskarta jin muryar yayanta Al-amin.

"Dama kai kake min wnn k'iran 'yan itskan."

Dariya sukayi dukansu sbd yanda ta ambaci iskan ,ta fitar da harafin s d'inne bayan ta danne harshenta da hak'oranta ta fito dashi tsakanin  tsiririn wushiryarta.
Kamar yadda qaninsu khalil yakeyi.
Halittarshi ce haka amma ko da yaushe ya ambaci harafin sai sunyi mishi dariya.

"Me kakeyi anan yayanmu?"

"Aiki mana baki gani ne?"
Ya fad'i yana nuna blocks d'in dake tare a kusa dasu ,labourers sai jida sukeyi suna kaiwa wani wajen da wasu ke gini.

Sai a snn ta lura da blocks d'in.

"Yanzu ya yayanmu haka kake d'aukan blocks d'innan masu nauyi."

"Wa ya gaya miki suna da nauyi."

"Da nauyi mana da gani ma ba sai an fad'a ba."

Ta fad'a tare da sunkuyawa tana kokarin d'aga block guda.

"Wasshh."
Tace tana yarfe hannayenta bayan ta ajiye block d'in da ba wani d'agawan kirki tayi ba sai raki .

"Madam karambani ,kin d'auka aikin da ragwayene irinki."
Ya fad'a tare da dungure goshin ta.

'yar dariya tayi tace "Gaskiya fa kuna kokari yayanmu."

"Neman halas kenan ummulu yana da wuya ."

"Aikam ,Allah dai ya biyawa duk mai neman halaliyarsa bukatunshi,Allah ya sanya albarka a sana'ar."

"Amin ummulun ummi ,muje in raka ki ,kinga sunyi nisa a aikinsu sun barni."
Ya qarashe maganar yana nuna ta gefen da yake ginawa ya bari.

"Au ginin kakeyi kenan?"

"Eh, wad'ancan suke kai mana blocks muna ginawa, gidansu oganmu ne muke renovating."

"Allah ya taimaka ."
Tace ,daga nan suka ci gaba da tafiya, har bakin hanya.

     _Two days later_

"Ummulu, an bani saqo na manta ba isar ba."

"Mik'o."
Tace tana mik'a mishi tafin hanunta.

Kallonta ya tsaya yi snn suka tuntsure da dariya dukansu biyu.

"Daga an bani saqo sai mik'o, yaushe kika zama haka?"

Dariya ta kuma yi tace
"Nayi tsammanin kud'i aka baka ka bawa baiwar Allah Salma."
Har da wani marairaicewa.

"To ba shi bane sai ki had'iye kwad'ayinki."

"Menene yayanmu."

"Oganmu ne yace in gaisheki."

😳"Oganku?"


*Slm, fans pls a rika haquri damu , masu magana ta pc da masu yi a grps, duk wanda yayi magana ban amsa ba that means ban gani bane, wasu kuma waiting yake nunawa, and masu magana a grps kuma, ba ko wani chat nake iya bi na karanta ba dan grps d'in sunyi min yawa ,idan nace ko wanne sai nabi na karanta to fa bazan samu time na typing ba, idan har kayi magana a grp ba response ka min magana personally in har na gani zan amsa, so bear with me , ina qaunarku kamar yadda kuke qaunata ,na gode.😍😍😍*
[17/12 06:25] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


*F.O.W*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*


              23.

       💔💔💔💔💔💔


"Zauna kiji salma."
Zaman tayi tana fiskantarshi.

"akwai abinda baki sani ba, ogan nan da kike gani?"

Da sauri tace nakeji dai ban tab'a ganinshi ba ai.

"Sorry, da kike ji to.
Duk mutum mai son karatu burge shi yake yi, yanason mutumin da yasan kanshi.
Tun ranar da ya ganki da uniform, kuma nace ke kanwatace , yaji kin burgeshi"

Katse shi tayi da cewa ,ni d'in ce na burge shi ,ko uniform ko kuma karatun?"

"Duka."yace a taqaice.

"Kuma idan kika sake katse ni ,zaki bar nan da rarrafe."

"Afuwan ya akhy."
Ta fad'a tana rike kunnuwa.

"Yauwa kina ji, ce min yayi ,babu yadda baiyi da qannenshi mata ba su karanci science courses, amma sam sunki ,wai da wuya , tsoro sukeji, baza su iya ba, shi kuma yayi burin a cikin k'annenshi a samu doctor ko nurse , ya musu alk'awarin ko nawa zai iya kashe musu ,amma duk sunki, abin takaicin dukansu yaran gidan su babu wanda ya karanci science."

"To shi me ya hana shi karanta ,tun da yana so?"

Harara ya galla, mata tayi saurin rik'e bakinta , "sorry yayan ummulu, mantuwa nayi."

"Baki ji me nace miki bane? K'annenshi mata yace yakeso su karanci course d'in sbd kishin addini da kuma taimakawa mata 'yan uwansu , ko kema ba hakanne ya saki karatunba?"

Gyad'a kai tayi tare da cewa "hakane."

"To shi yasa da yaga kanwar d'an gidanshi tanayi yaji dad'in abin kuma yaga zai iya bada tashi gudumawar ,kuma ba ke kad'ai yake bawa irin wnn kulawar ba, matasan unguwarsu masu kokarin karatu ma yana taimaka musu,snn ko ni nan da kika gani lokacin da nake makaranta ba k'aramin taimakona yayi ba, yanzu haka shawara yake bani da inje in had'a masters , ina fata kin fahimta?"

"Na kusa dai."

"Tashi ki bar na, tunda yau kuma kwakwalwar ta cushe."
Ya fad'a yana mikewa .

Cikin dariyar kular da shi da tayi tace "Tsaya ina da tambaya."

"Shi wani mataki ya taka a karatun, da shi da matarsa duka."

"mts bana son tambayar ganganci, mutum mai karfafawa wani gwiwa yayi karatu, shi kuma me zai jira yana da hanyar karatun."

"To kuma shine ya tsaya aikin gini ,ko yana wani aikinne?"

"Wai ance miki dole mutum idan yayi karatu mai zurfi sai yayi aikin goverment ne? ina ce iliminshi a kwakwalkwarshi take, kuma da abinda ya karanta zaiyi aiki,.
Shi wnn da kike ji babban contractor ne, yana kuma da companyn kayan aikin gini masu inganci, yana da gidan block na musamman ,gari gari ake bashi contract, har k'asashen waje yake zuwa, duk tafiyar da kika ga nakeyi tare dashi ne , dan ina d'aya daga cikin amintattun yaranshi.
Kuma kin san me ?"

"sai ka fad'a."

"Office yake dashi musamman ,government ta san da zama shi ,snn ya da motoci na d'aukan kayan aiki da blocks ba sai ma an nema a wani waje ba."

Tab'e baki tayi tace.
"Allah ya taimaka to, ka kuma ce mishi na gode."
Dan ita gani take b'ata lokacinshi kawai yakeyi wajen son fahimtar da ita ko waye mai gidanshi.

***  ***   ***

Ma sha Allah, gidan ahmad yanzu sai sambarka, komai ya daidaita ,zama suke cikin aminci.
Duk da har yanzu babu abinda ya ragu na soyayyar salma cikin zcyr ahmad, haka kuma bayan kwana biyu yake zuwa gun salmar,
Snn daga gunta ma babu wani canji.
Snn babban karin farin cikinshi kuma a iya zamanshi da Salma bai tab'a ganin ta ko yaji labarin an ganta da wani ba.
 hakan bai hana shi bawa asiya kulawa ta musamman ba.

A kullum kokari yakeyi yaga ya danne damuwar shi da kuma soyayyar da yakewa salma a gaban asiya, dan a yanzu tana da matsayi na musamman a zuciyar ahmad.

Babban abin da ya k'ara mata matsayi da k'ima a idonshi shine cikinshi da take d'auke dashi na watanni uku.
Rabo kenan.

***    ***  ***

Sati biyu da dawowar salis aka sa lokacin bikinsu.
Shirye shirye suka shigayi , tare da salma da pendonsu kanwar mamansu,sai fati, suka shiga kasuwa sukayi wa nusaiba sayayyan kayan kitchen masu kyau, dadai k'arfinsu.

Tun ana saura wata guda biki pendonsu da take kaduna ta iso ,nan ta fara gyara amarya yadda ya kamata.

Cikin kwanakin kuma Salma ta k'are karatunta bayan taci wuya ,har rama tayi.

Farin cikin ta ya gaza b'oyuwa, ba ma ita kad'ai hatta malam da ummi da sauran 'yan uwanta sunyi farin cikin kamalla karatun nan nata ,sai da fatan samun sakamako mai kyau.

Alk'awari ta d'aukarwa kanta ,duk lokacin da Allah ya sa ta k'are makarantar lafiya zata shirya walima , dan nuna tsan tsan farin cikinta da godiya ga Allah da ya bata ikon yin karatun.

Hakan ko a kayi ta fara shirye shiryen walimah ,tare taimakon ,malam, ummi, da al-amin.

Nusaiba taso ta haqura su had'a walimar da na bikinta ,tace sam, bazaiyiyu ba, walimarta daban na bikin nusaiba daban.


*Gaisuwata gareku.*
*Rakiya yakubu.*
                &
*Habiba Muhammad.*
[17/12 06:25] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*

'
*Fasaha Online Writers.*


*F.O.W*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

                24.

      💔💔💔💔💔💔

*Ina kike uwa ma bada mama, wnn shafin naki ne, uwa hana kukan talauci, uwarmu abar alfaharinmu, HAJIYA FA'IZA ALIYU BASHIR (Aunty)*

*Allah ya bada tsawon rai mai amfani.*
*Ina alfahari dake mamana.*


Yau suka tashi da shirye shiryen walima , gida ya cika da dangin Malam da na ummi, duk sunzo taya Salma murnar k'are karatunta.

Yadda aka tsara da yamma za'ayi walimar .
Wanka ta fito tana gyara fiskarta bayan ta gama shafa mai.

Fati ko tana fitar mata da sabon kayan da al-amin ya d'inka mata na fitar walima.
Nusaiba ce ta shigo tana mika mata wayarta da take ringing .

"Wayene?"
Ta tambaya tana kallonta.

Mik'a mata wayar tayi tana mita k'asa k'asa "Kullum mutum ya bata waya sai tambaya wayene, tamkar bata san sarkin nacin ne yake kiranta ba."

Bata kulata ba ta karb'a ta kara a kunnenta ita kuma ta juya ta tafi.

"Assalamu alaikum, Ahmad an wuni lfy?"

"Wa alaikumussalam, amma bazan amsa gaisuwar ba."

"Me ya faru."

"Tambayata ma kike me ya faru? Salma yanzu kina ganin kin kyauta kenan?"

"Me nayi ahmad?"

"Ina ko zaki san abinda kikayi tunda yanzu bani da wani matsayi a gunki, fii sabiilillahi a ce zakiyi walima na qare makarantar ki baki sanar min ba , me kike nufi?"

Jimm tayi ta ma rasa abinda zata ce dashi.

"Dole ki rasa ta cewa tunda kinsan baki da gaskiya."

"To ahmad me zan ce maka, naga walimar na mata ne , ko zaka turo amarya ta taya ni murna ne?"

'Yar karamar tsaki yaja ,a kufule  kuma yace ,"Idan na mata ne kuma bani da matsayin da za'a sanar dani kenan, da ba don na k'ira nusaiba ta d'auka ba har ayi a gama ban sani ba dan ban kai matsayin ba ko?"

"Allah ya baka haquri ni ba haka nake nufi ba."

"To yayane in ba haka ba?"

Kamar zatayi kuka tace "Ni dai kayi haquri."

Katse wayar yayi yana maijin haushi abinda tayi mishi.
Wato taki sanar dashi ne dan kada ya ce zai d'auki nauyin wani abu.
Mttss yaja tsaki, yasan hakan halinta ne ,tunda suke da ita bata tab'a rokanshi abu ba , snn koshi ya bata ma sai yayi da gaske take karb'a ,wani lokacin sai ya bawa kannenta sukai mata.
Duk da hakan yana qara mata daraja a wajenshi amma yaji haushin abinda tayi mishi ba kad'an ba kuwa .

Saida ta gama shiri tayi d'as da ita kamar wata sabuwar amarya .
Ta cewa fati ta kirawo mata nusaiba.

Suna cikin magana nusaibar ta shigo , itama wankan ta yiyo .
Harara salma ta galla mata, ita ko ta d'auke kanta tamkar bata ganta ba.

"Nusaiba me yasa kika fad'awa ahmad maganar walimar nan?"

Kallonta takeyi baki sake, daga bisani tace "Wai kina nufin dama baki sanar dashi ba ?No wonder yake tambayar ya yaji hayaniya , ashe bai san da maganar ba , amma dai baki kyauta ba wlh."

Har ta d'auki mai zata shafa ta sake juyowa takalli salma "Ina fata ya nuna miki b'acin ranshi kuma kema ya b'ata miki naki ran, wlh nima kin ban haushi aunty, meye abin b'oyewa a gurin abin farin cikin? Wlh in nice shi zai fara sani."

"ke ya isheni haka masifaffiya, yarinya kamar an d'auko hayarki kimin lecture?"

"Allah ya baki haquri   aunty, kinyi kyau fa kamar yau za'a kaiki gidan lucky."
Ta fad'a tana washe baki da son basar da zancen dan taga aunty nata har ra fara hawa.

Kafin ta yi magana suka jiyo sallamar friends na salma , suna shigowa suka had'a baki wajen fad'in "Wooww ,sister salma ,kinga yadda kika fito?"

Murmushi tayi tana mika musu hanu d'aya bayan d'aya suna shaking, snn suka zazzauna aka fara chapter.

"Allah ya nuna mana bikinki sister, wnn had'uwa haka ?"
Faleela ta fad'a , dukkansu cikin farin ciki suke ,kowa ta cab'a ado na gani na fad'a.

Wata cikinsu tace wlh nima nanda kwana biyu zakuzo nawa walimar, ina komawa zan fara shiri."

Kwashewa dauka sukayi da dariya "Ke da kika ce sai party, yaushe kika canza shawara?"

Cewar d'aya daga cikinsu.
"na fasa ,nima walimar zanyi ."

Fati ce ta shigo tana ce musu su fito an gama had'uwa su ake jira ,har malaman da zasuyi wa'azi sun iso.

Fitowa sukayi sai zuba k'amshi sukeyi.
Kanwar mamarsu ta kaduna ita tazo ta rike hanun salma tana cewa "Ma shaa Allah 'yata kinyi kyau."

Shadda ta saka zani da riga da d'ankwali purple colour yasha aiki , d'aurin steps tayi a kanta wanda ya dad'a fito da kyaun fiskarta sai gyalenta fari da ta yafa , takalminta silver colour sai purse da agogon hanunta , sarka da 'yan kunne ,abun hanu zobuna duka silver colour.
Simple make up tayi wa fiskarta ,daga powder, kajal sai janbaki colourn kayanta.

Canopies biyu aka kafa cikin gidan kasancewar akwai babban fili a gidan.

Sai da ta fara zuwa ta kwashi gaisuwa gun manyan malaman da aka gayyata domin gabatar da lecture.
*Hajiya Faiza Aliyu Bashir.*(Aunty)
*Hajiya Aishatu (Malama Tasalla.)*
*Malama Mamuji*

Sune manyan malaman da aka gayyata domin gabatar da wa'azi a wnn rana ta farin ciki ga k'awata Salma.
[17/12 06:25] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


*F.O.W*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*


             25.

      💔💔💔💔💔💔

*Wannan shafi kyauta ce gareku Qungiyar Khairul Umma, at large ban rage ko d'aya ba.*
*Allah ya biyaku.*


Wad'annan manyan mata masu daraja malamai ne daga qungiyar mata musulmai na Jalingo ,dake jahar Taraba .

*KHAIRUL UMMATI*
Qungiyace ta musamman wacce take bada muhimmiyar gudumawa ga musulunci da musulmai.
Aiki suke tukuru wajen ganin sun d'aukaka kalmar Allah, ba dare ba rana.
Suna sadauqar da lokacinsu, qarfinsu, da dukiyoyinsu wajen d'aukaka kalmar Allah.
Lunguna, saquna, qauyuka ,suke shiga dan yin da'awa.
Suna musuluntar da wad'anda ba musulmai cikin hikima, baseera, da ilmin da Allah ya hore musu.

Suna kuma d'aukan nauyin wanda ya musulunta 'yan uwa da dangi suka k'ishi sanadiyyar shiga addinin musulunci.
Karatu ,ci ,sha, sutura ,muhalli, wnn duk basa gazawa wajen d'aukewa masu buqata.

Ruwa da iska, zafi da sanyi , zafin rana, akwai da babu duk ba sa hana su tsayawa tsayin daka wajen ganin sun yiwa addini hidima.
Allah ka sakawa wad'annan bayi naka da alkhairi , ka biya musu buqatunsu na duniya da lahira, ka qara musu lfy, ka basu ikon cika qudurin su na alkhairi.
Ka kare su da kariyarka ,kama karesu daga sharrin dare da rana, mutum da aljan.
Ka kare su daga sharrin dukkan abin qi.
Ka kara d'aukakasu.
Ka basu ikon ida nufinsu na alkhairi.
*Ameen*

Malama Tasalla ita ta bud'e taro da addu'a tare da karatun alqur'ani mai girma.
Daga nan Hajiya Fa'iza ta fara gabatar da lecture akan muhimmancin ilimin 'ya mace.
Muhimmancin karatun likitanci ga 'ya mace a wnn zamani da muke ciki, wanda ma'aikatan asibitoci suke d'aukan ran musulmi ba a bakin komai ba , ake wulakanta musulmai, a tozarta su ,ana musu kallon banza da raini, ana ganinsu basu san komai ba, more especially mata masu ciki in anzo wajen haihuwa.

Tayi magana akan likitoci musulmai da suke biyewa colleagues nasu wad'anda ba musulmai ba wajen kin taimakawa da tausayawa ga 'yan uwansu musulmai.
Sai kaga an kawo mace mai nakuda ,tana fama, ace idan ba kud'i baza'a karb'e taba.
Ko da kud'in ma baza ta samu isasshen kulawa ba tunda musulmace kuma ba a ga maiko a tattare da ita ba.
Su kuma 'yan uwan namu musulman sai su nuna halin ko in kula ga lamari.
Shin tsoro ne ko kuma qangarewar zuciyace.

Wata ma kina gani musulmace 'yar uwarki, sai arne ko arniya ta tsaya kanta tana bata kalmar "JESUS."
Instead ke ki bata kalmar shahada.
Allah ya tsare.

Wani abin takaicin zaka ga mace tana fama ,wai dan ta d'auki lokaci bata haihu ba dan kar ta b'ata musu lokaci sai a nemi mijinta ko 'yan uwanta ace su sa hanu za'ayi mata tiyata bazata iya haihuwa da kanta ba, ke kuma 'yar uwa musulma kina gani kin yi shiru baza ki taimaka da baiwar da Allah ya baki ba.

Nasan ba duka aka taru aka zama d'aya ba ,amma masu taimakon basu da yawa.
*Sister Jamila Usman Nyaja (Mmn Al-Mustafa)* kina kokartawa, kina bawa mata kulawa ta musamman naji daga bakin mutane da dama .
Allah ya saka miki da mafificin alkhairi.

Nurses kuji tsoron Allah, ku tausayawa 'yan uwanku musulmai ,ku taimaka musu da iliminku, Lokacinku da kuma aljihunku inda hali.
Akwai lada mai tarin yawa cikin wnn aiki naku,.
Nan dai Hajiya Fa'iza ta rika kwad'aita musu lada da kuma falalar dake cikin wnn aikin.
Har Salma da sauran colleagues d'inta suna jin zasu iya bada kowace irin gudumawa ta fannin wnn karatu da sukayi.
Gaba d'aya sun kwad'aitu da falalar da ke cikin wnn aiki.

Karshe ta bawa iyaye shawara da k'arfafawa yaransu gwiwa dan su rika karanta science courses sbd mu samu wadatuwar likitoci musulmai.

Daga nan Malama Mamuji ta karb'i wa'azin inda ita kuma tayi fad'akarwar akan mata ma'aikatan gwamnati da suji tsoron Allah , su rik'e mutuncinsu da mutuncin aurensu.
Su kame kansu aduk inda suka tsinci kansu.

Su guji cin amanar Allah, da ta mazajensu.
Snn ta zayyano d'imbin azabar da tab'ewa da ke jiran duk mace mara tsoron Allah, mai cin amana , mai munafurci da annamimanci.

Wayyo Allah , kuzo kuga yanda guri yayi tsit, tsoron Allah ya Shiga zuqatan mahalarta wannan taro .

Kuzo kuga idanuna yadda nake zaro su ,ina bin aminai na da kallo, Maryam Mazad, Amina Sale Muri, Lubabatu kyauta, Salamatu Ibrahim Bawa, Ummul kulthum Aliyu Bashir, Nafisa D'ahiru,Hajara Aliyu, Sister Jamila, Sadiya sale, Jamila Mu'azu, Maryam Adamu lanko,Sadiya Ibrahim, ga kuma swt sister Halima Auwal, Ga Nafeesat (Mrs Bashir Bello.) Kai ,muna da yawa fa.
Sai zura gula gulan idanunsu sukeyi, anji maganar lahira.

Malama mamuji badai iya sa tsoro ba, idan tana wa'azi sai kaji kanka na juyawa, kwakwalwarka na amsa quwwa, tsigar jikinka na tashi, ka rika jin wani zuuuuuu irin kana gangarawa lahirannan.Lol.
Allah kasa mufi qarfin zuqatanmu.

Ana cikin wa'azi sai ganin almajirai akayi suna shigowa da kwalayen juices da snacks.

Mikewa salma tayi tana rarraba ido , can ta hango Nusaiba ,zaune tayi zugum jiki a sanyaye, alamar wa'azi ya shigeta.

Cikin sanyin jiki ta ...

Na gaji wlh☹
[17/12 06:25] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers*


*F.O.W*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*

                 26.

     💔💔💔💔💔💔

*Wnn shafi kyautace gareki Hauwa .S. Zaria, nagode da qauna Allah ya bar zumunci.*🌹

Cikin sanyin jiki ta fara ratsa mutanen har ta isa wajen nusaiba ta kamo hanunta.

Saida suka fito sarari snn suka tsaya.
Lokacin nusaiba ta lura da kayan da ake shigowa dasu, ta tambayi salma daga ina.
Itama tace bata sani ba, dalilin da ya sata nemo ta kenan.

Kafin su qare maganarsu almajiran har sun gama sun fita.
Sbd haka nusaiba taja hanun Salma tana cewa "Zo muje mu duba."

Suna fita suka ga wucewar motar ahmad, sai almajirai a gefe da suke rabon kud'i.

"Ahmad ne wlh."
Salma tace tana nuna motar.

Kafin nusaiba tayi magana sai ga wata bak'ar mota mai tinted glass tazo ta parker kusa dasu, sai sheqi takeyi.

Babu ta yadda zasuga na ciki, sai na cikin ne yake kallon su.

Kamo hanun nusaiba salma tayi tana cewa ,"Mu koma to, tsayuwar me mukeyi.

Har sun kusa kofa suka ji ya al-amin na k'iransu .
A tare suka juyo ,suka saki murmushi a tare.

"Yayanmu nayi missing d'inka yau wlh."cewar nusaiba.

"Ke kikayi missing d'inshi ko ni, tunda garin Allah ya waye ban sashi a ido ba ,inajin ma tun asuba ya bar gidan."
Salma tace.

"'yan matan ummi kunga yadda kuka yi kyau kuwa, ku tsaya na muku hoto."
Al-amin ya fad'a lokacin da ya iso dab dasu ,ya ajiye k'atuwar ledar dake hanunshi, yana kuma fiddo wayarshi daga aljihu.

D'aukansu hotuna yayi tayi wani su biyu, ya musu d'add'aya snn sukayi tare dashi.

Saida suka gama snn ya d'auko ledar da ya ajiye ya mik'awa nusaiba yace "Ku k'ara ku rabawa bak'i."

Karb'a Nusaiba tayi tana cewa "Me kuma muka samu? Na lura sai wani ji da aunty salmannan kukeyi dukanku, wlh kukayi wasa nima sai na zuciya nayi karatun." tana fad'a tana bud'e ledar.

Dariya dukansu  sukayi snn Salma tace"ki zuciyan mana muma haka muka fiso."

Snn ta juya ga ya al-amin."Yayanmu wancan bai isa ba har sai ka dad'o wani?"

"Wnn dabanne sai na dawo ana jirana."
Yace tare da barin wurin , suna kallonshi ya shige cikin mota.
Kallon juna sukayi kafin nusaiba tace "Wnn kuma motar waye?"

"Allah masani." Salma ta bata amsa.

Fitar da abinda yake ciki nusaiba tayi , hand bags ne masu kyau da k'wari diff.colours.

"Woow , duba aunty Salma ,hand bags d'innan sunyi kyau."
Cewar nusaiba.

Karb'a tayi tana dubawa.

*Congratulations Ummu Salma.*
*May Almighty Allah bless ur knowledge.*


*Curtesy.....A.M.G.*

K'ara girman idonta  tayi tana kallo snn nunawa nusaiba.
"Duba kigani."

"Waye shi?"
Nusaiba ta tambaya.

"Ina zan sani."
Salma ta bata amsa.

Rik'e ledan sukayi a tare suka shiga gida, nan suka tarar an k'are wa'azi , malama Tasalla tana addu'ar rufewa.
Fati suka tarar har ta fara rabon take away.

Robobi ,mafici, cups ,da aka manna musu stickers, suka shiga rabawa, tare da bags d'in.
Haka taro ya watse cikin farin ciki, sai fatan alkhairi ake mata.

Da dare suna had'e dukansu a tsakar gida ,duka yaran gidan suna had'e har da Malam, kamar yadda ya saba zama cikin iyalanshi idan d'alibanshi basu zo ba ,hira suke cikin raha, duk suna cikin nishad'i.

Al-amin ne ya shigo da sallama, dukansu suka  maida hankalinsu kanshi suna amsa sallamar.

Kusa da Mal. Yazo ya zauna ya gaisheshi snn ya gaida ummi da kanwarta, kannenshi suka mishi sannu da zuwa.

"Hamza zo ka tayani d'aukan wasu kaya a d'akina.
Cewar Ya al-amin, bayan ya mike yana zura takalmanshi.

Ba tare da b'ata lokaci ba sai gasu sun dawo d'auke da kaya.

Kayanya shiga fiffitarwa nan kusa da Mal.
Saida ya gama fitarwa yace "Salma ga sak'onki."

"Wnn fa daga ina ?"
Mal. Ya tambaya yana kallon kayan.

"Oganmu a gurin aikine ya bani na kawo mata."

Wani zabura salma tayi har ta tsorata pendonsu dake zaune kusa da ita.
Kamar wacce aka hankad'a ta isa gaban al-amin ta zauna tamkar wacce zatasa shi ya maida maganar da ya gama fitarwa yanzu.

Hanunshi ta kamo ta rike ,bakinta na motsi ta kasa magana sai kallon shi takeyi.

"Yayanmu."
Tace still idanunta cikin nashi, ta rasa me zata ce mishi, ta rasa ta ina zata fara,
Girgiza mishi kai ta farayi alamar maganar ki fitowa.

Kawar da idonshi yayi tare da zame hanunshi daga cikin nata, kallon da take mishin ne yaji shi wani iri ,kallon  yayi kama kwarai da na tuhuma, snn kwayar idanunta kamar suna nuna tamkar akwai wata laifi da ya aikata mata.


*Mom Afrah🌹*
[17/12 06:25] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


*F.O.W.*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljala)*


               27.


       💔💔💔💔💔💔

*Wnn shafi nakine Hajiya Aisha (Hausa novels books, na gode da kulawa Allah ya bar zaumunci.*

***   ***   ***

Kallonsu kowa yakeyi cike dason jin k'arin bayan.

Lura da hakanne yasa ya al-amin ya fara nuna musu kayan da d'add'aya.

Sphygmomanometer, na auna B.P. weigheing scale,na gwada nauyi.  thermomether, na gwada temprture, first aid box da duk wani abin buqata, sai kuma qaton text book na research.

Bin kayan da kallo salma takeyi zuciyarta na bugawa, a yau kam bata yarda da cewa kyautatawace haka kawai ba kamar yadda yayanta yake fad'a mata, a yau zuciyarta ta fara raya mata wani abin daban.

Tana gama wnn tunanin taji hrt d'inta ya buga da k'arfi har sai da ta kamo yatsun hanunshi guda biyu ta matse da k'arfi.

"Ya haka Salma?"
Ya fad'a qasa qasa tamkar baya so a jishi.

"Ya al-amin."

"Ya dai?"

Kamar nusaiba tasan abin da ke zcyr salma ta matso tace "Yayanmu hand bags na d'azu kuma daga ina?"

Saida ya d'auke kanshi daga kallonsu, sbd kaucewa kallon kurillar da salma ke mishi, yace "Duka shi ya bayar."

Kallo su salma tayi taga duk hankulansu na kan kayan snn tace , "Me yasa kake karb'an mishi kayanshi?"

Ba tare da ya kalleta yace "Sbd ba kyau maida hanun kyauta."

"Ka tabbata tsakani da Allah yake wnn abin?"

"To da tsakaninshi da dake ne? dan mutum yayi kyauta sai a tuhumeshi? Na d'azu taya murna ne ,yanzu kuma gudunmawa ne dan ki taimakawa al'umma, ko ba daga yanzu karatunnaki zai fara amfani ba? Kuma ko bai saya miki ba ina da niyyar saya miki idan aka biyani kud'in aiki na?"
Duk maganar da sukeyi a hankali sukeyi.

Sai a snn ta d'an samu relief amma hankalinta bai gama kwanciya ba.

Su kuwa sai yaba kayan suke suna sa mishi albarka , Su Hamza har da cewa tazo ta gwada B.Pn su , Fati da nusaiba kuma sukace ta gwada weight d'insu.

Ita dai binsu takeyi da kallo tana kissima abubuwa da dama a ranta.
Kallonta ta maida kan Mal. taga shi hankalinshi yana kan labarin da kanwar mamansu take bashi.
Su nusaiba ne dai suke ta jujjuya kayan kowa na fad'an albarkacin bakinshi, daga qarshe fati ta tattara ta shigar d'akin Ummi.

Har aka watse hiran Salma dai jikinta a sanyaye yake.

Sai washegari su Ummi suka matsa mata da ta mishi godiya, ba dan ranta ya soba ta nufi d'akin al-amin.

Maganar ma kamar shaketa akeyi tacewa wa al-amin ya qira oganshi ta mishi godiya.

"Zan dai baki nambarshi ki qira shi."
Yace mata .

Cikin nuna gajiyawa da zancen tace bani da kud'i a wayata, in kaima baka dashi, sai in baka saqo kace mishi na gode."

Mika mata wayar yayi yana cewa "Gashi kirashi."

B'ata fuska tayi tace "in ce mishi wacece?"

"Ummu salma "yace a taqaice.

"Nikam karb'a ka fad'a mishi saika bani in mishi godiyar."ta karishe kamar zata sa kuka, bakinnan a cune.

Karb'a yayi, yayi dialing nambar , saida ya d'auka suka gaisa snn yace mishi Ummu salma ce keson magana dashi."

Miqa mata wayar yayi ta qara a kunne.
"Assalamu alaikum."
Tace a sanyaye.

"Wa alaikumussalam."
"jin tayi shiru ya sashi cewa Ummu ya kike ya mutanen gida."

"Lfy, ina yini?"
"Lfy lau Ummu ya hidima?"

"Alhamdulillah."
Tace snn tayi saurin cewa "Ya al-amin ya kawo min saqo ,na gode Allah ya qara bud'i."

"Amin, Amin, nima na gode."
Kit ta kashe wayar ta mika ma al-amin tayi gaba.

***   ****   ****

Zaune take gaban dressing mirror tana shafa mai tamkar dole aka sata, gaba d'aya a gajiye take, ga wani irin kasala da takeji.
Juyawa tayi ta kalli   nusaiba dake kwance kan katifa tana karanta wani Hausa novel, sai sambad'a murmushi takeyi.

"Ke malama, ni ki tashi ki zo ki shafa min mai a baya, duk kin bi kin gajiyar da mutum wai yawon rabon kati, idan kikayi wasa sauran ke zakiyi, ba gyaran jiki kikeyi ba ko fatar za'a canza gobe sai kin fita dan ni na gaji, tsabar rainin wayo ma instead ki nemi qawayenki suje miki sai kiyi ta had'amu da aiki, Fatinma gobe baza taje ba."

Ajiye littafin tayi ta matso kusa da ita kafin tace "Yi haquri auntynmu, kwana nawa ne zaku gama, kuma mafa lada zaku samu, Allah ya bada ladan taku auntyna."

"Ni kar ki wani isheni da zaqin baki, shafa min a baya wlh duk a gajiye nake, yau ko d'an kwalliyar jumm'ar ma mutum bai samu yayi ba ,har yamma tayi."

Karb'an man tayi tana shafa mata  tare da cewa "A dai qara haquri dai, kwanan nan zamu fara rabon naki in da rai."

Pendonsu ne ta shigo ,tana ganinsu tace yauwa 'yan matana, shafa mata man da kyau, ko ta ina yaji kada saurayi ya tambayeta wani irin mai take shafawa."

Dariya duka sukayi snn nusaiba tace "To dan me zai tambayeta"

"saurara kiji ,idan kika ji saurayi ya tambayeki wani irin mai kike shafawa tofa baki iya shafa man bane, ina irin 'yan mata masu rataya kananan gyalen nan, sai kiji ana tambayar su wani irin mai suke shafawa, suko su ta fari da ido suna tsammanin abin kirki sukayi Ko sun burge basu san shi yasan abinda ya gani ba, bama kamar ta bayan nan sai kiga jiki fes baya kuma fari fat tamkar baiga ruwan wanka ba.

Kwashewa sukayi da dariya tare da tafawa, "kai Mamanmu akwaiki da qalqaletion, su samarin ne suka fad'i hakan?"

Dariya itama tayi,"To ku zauna dai ana fad'a muku gaskiya kuna maida abin wasa."

Sallamar al-amin ne ya katse musu hirar da sukeyi.
Ya leqa daidai lokacin da salma take fitar da kayan da zata saka.

"Ummulu, idan kin gama ki same ni a d'aki ."

"Toh."

Tace tana ci gaba da shirinta.tsaff, ta saka 'yan kunne da sarqar gwal d'in da ahmad ya bata washe garin walimar graduation d'inta, ta fesa turarenta mai sanyin qamshi snn ta kama hanyar d'akin al-amin."

Tana isa ta tsaya turuss tana kallon kofar d'akin.
Takalma biyu ta gani a kofar kuma tana da tabbacin d'ayan ba nashi bane, hakan ya tabbatar mata ba shi d'aya bane cikin d'akin.

Jin alamun motsi kuma ba'ayi magana ba yasa al-amin cewa "Waye a nan."

Da sauri tayi baya ta shiga ciki ta d'auko hijabinta babba mai hanu ta saka.

Dawowa ta tsaya bakin kofar ,haka kawai taji gabanta na fad'uwa , itafa yanxu al'amarin ya al-amin yana kulle mata kai, kar dai maganar ogannan nashi zaiyi mata.

Tuna haka da tayi ,gashi kuma bata yarda shi kad'aine cikin d'akin ba yasa ta juyawa zata koma.

"Ummu salma."
Taji shi ya qirata.

"Na'am."
Tace, tana matsowa a hankali tamkar wata mai laifi.

Sallama tayi a sanyaye, ilai kuwa muryoyi biyu suka amsa mata.
[17/12 06:25] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


*F.O.W.*

*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*

                  28.

        💔💔💔💔💔💔

*Dedicated to my swt & lovely sister Halima Auwal.*


Cakk ta tsaya bata shiga ba kuma bata koma koma ba.

"Shigo mana Ummulu."
Ta tsinkayo muryar al-amin.

Kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta shiga bakin ta d'auke da sallama.

Kallon yayannata takeyi tana jira taji abinda zai ce mata.
Shi kuwa ko kallonta baiyi ba.

Tana daga tsayen tace "Gani yayanmu."

Harara ya galla mata snn yace "Na ganki ai."

Samun guri tayi ta zauna tayi qasa da kanta, dan ko da wasa bata nuna tasan da mutum a d'akin ba bayan al-amin.

Fita al-amin yazo yi ta tashi ta bishi da saurinta.
Juyowan dazaiyi har suna cin karo tayi sairin ja da baya.

Qasa 2 yace "Baki ga mutum bane ko baki iya gaisuwa bane yau kuma."

Itama a hankali tace "Mutum a ina?"
Hararar ya kuma galla mata ,ya juya zai fita.

Mutumin dake zaune kan resting chair tun d'azu yana kallon dramar da yaya da kanwar sukeyi ,ya ce " Ina zuwa kuma ameen?"

"Sosa keya ya al-amin yayi yana 'yar murmushi yace. "Zanje nanne in dawo yanzu."

Da ido ya mata alamar ta koma ta zauna.
Komawan tayi ta zauna ta bakin kofar a darare tamkar tana jira a ce kett ta ruga. Duk haushin yayanta ya gama cikata, ko bai fad'a ba zuciyarta na fad'a mata wnn shine ogannashi.

Shiru ne ya biyo baya kafin daga baya taji ya ce "Ummu."
Cikin taushin murya.

Duk da fad'uwar gaban da taji hakan baisa ta d'ago ba balle ta amsa.
Bai damu ba yaci gaba da jera kiran sunanta ba ko gajiyawa.

Mamaki ne ya isheta jin nacin k'iran yayi yawa yasata d'agowa, a ranta tana cewa wnn akwai nacin tsiya.
Caraf suka had'a ido , ya sakar mata murmushi da yasa tajin wata irin tsinkewar zuciya .

"Subhanallah."
Tace qasa qasa.

"Haba sister Ummu , haka likitocin suke treating patients nasu, ba gaisuwa, ina magana ba amsawa, an kuma d'aure fiska , taya zan saki jiki in fad'i cutar dake damuna har a bani magani ko shawara?"

Jin haka yasa ta d'ago ta kuma kallonshi.
Giranshi d'aya ya d'aga mata tare da cewa "Yess, ko ameen bai gaya miki patient ya kawo ba?"

Girgiza mishi kai tayi ba tare da tayi magana ba.
"Ashe laifinshi ne ,tunda bai sanar dake ba. Yanzu kin shirya in fad'i damuwata?"

"Me ya hana shi zuwa asibiti ?."tace a ranta.

Katse mata tunani yayi ta hanyar cewa "Are u ready, sister Ummu?"

Shirun ta kuma yi.
Sai da ya kuma maimaita tambayar snn ta gyad'a mishi kai.

"Ok, listen attentively and look at me also."
Taji yace.

Tabd'i lallai ma, harda look at me, tunda bayani zaiyi ai kunne keji ba ido ba.
Tace a zcyrta.

"Ummu ,Kalleni dan Allah."
Ya kuma cewa.

"Fad'i ina jinka."

"Um um nisai kin kalleni."
Ya fad'a a shagwab'e.
Ikon Allah, ko dai d'an auta ne." tace a zcyrta.

Kallonnashi tayi , ya lumshe ido ya bud'esu tare da cewa "Yauwa ko kefa."

Kasa ta kuma yi da kanta.
"Kina jina?"

"umm."
Tace a taqaice.

Tun bayan kwanaki takwas da suka shige nakejin kaina yake min wani DUUUUUM  haka.

 kunnuwana kuma suke min SHUUUUUU.

Zuciyata take bugawa KIKIB  KIKIB  KIKIB.

Kina jina?
Ya tambaya yana kallonta.

"Umm."
Ta ce, snn yaci gaba da cewa.

"Snn idanuna suke min wani dishi dishi, ban cika ganin mutane sosai ba.

Allah yasa kin fahimci bayanin da nayi miki."

"Yanzu baka gani sosai kenan?"

"Yanzu kam ina gani sosai ma kuwa, saidai nasan zuwa gobe abin zai dawo."

Sakin baki da hanci tayi tana kallonshi, ba tare da ta sani ba. Shima kallonnata yakeyi babu kuma alamun wasa a fiskarshi.
Wnn wani irin kwatancen ciwo ne?

"Ya dai ummu ko baki gane bayanin bane in sake."

Sai a snn ta fahimci kallonda take mishi tayi saurin kawar da kanta.

"Da ka je asibiti wajen manyan likitoci inaga zasu fahimci bayanin."

"ke fa?"
Ya tambaya har da karya wuya.

"Ban gane irin ciwon ba."

Langab'ar dakai ya kuma yi ,"Yanzu ko d'an Bpn ma baza'a gwada min ba, kika san ko ya hau."

Tunani ta shigayi, kodai yazo ya gwadatane yaga ko ta iya aikin, idan ba haka ba wnn wani irin ciwo ne?

"Kinji."
Ya kuma cewa.

"Wnn mutumi akwai d'an banzan naci tace a ranta."

Tashi tayi ,ya bita da kallo har ta fita , ya sauqe ajiyar zuciya snn ya d'auki wayarshi ya fara danne danne.

Bada jimawa ba ta dawo d'auke da B.P apparatus a hanunta.

Kusa dashi taje ta ajiye.
"Gashi ka gwada."
Tace dashi.

 Idanunshi ya waro.
"Ni kuma ina zan iya Ummu, abinda ba aikina ba, fisabilillahi haka akeyi? Zo ki gwada kinga yamma tayi idan na dad'e za'a min fad'a a gida."

Matsowa tayi kusa da shi snn tace "Bismillah."

"Kafa zan miko ko hanu?"
Ya mata tambayar.

 Dariyace ta sub'uce mata ba shiri ,taji kamar tace mishi kai zai mik'o, dan ta fahimci akwai rainin hankali a al'amarinshi,
 kamar wanda bai tab'a zuwa asibiti ba."
Ta tuna hakan a ranta.

"Hanun rigar zaka ja."

"Zuwa ina ?"
Ya sake tambayar yana kallon cikin  idonta.

Bata san sanda ta b'alla mishi harara sbd tsabar raina mata hankali da yayi.

"ashe kema kin iya ?"
Taji shi ya fad'a .

"Me fa?"

"Irin wnn kallon da kikayi min yanzu, sai naga ya qara miki kyau."

D'aure fiskarta ta dad'a yi snn tace "Ka janye hanun rigar magriba ta kusa."

Hanun farar shaddarsa ya janye yana murmushi aranshi ko cewa yake "Lallai zaisha fama da yarinyar nan, irin wnn shan murr haka.

Abin gwajin ta d'auka ta matso kusa dashi sosai snn ta durkusa.


*Mom Hanan*🥀
[17/12 06:25] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


*F.O.W.*



*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*


               29.

     💔💔💔💔💔💔


Bin hanunta da kallo yakeyi yanda take taka tsan tsan kar hanunta ya tab'a jikinshi.
Har ta iso gun damtsen shi.
Kurawa murd'add'en  damtsen shi ido tayi .
Wnn kakk'arfa ne, dole yayi aikin gini. ta fad'a aranta.

"Ya dai Ummu?"

D'aurawa tayi taci gaba da abinda takeyi cikin k'warewa, har ta gama ta cire snn ta d'ago ta kalleshi.
"Normal, ba wata matsala."

"Kin tabbata?"

"Hararanshi tayi qasa qasa ba tare da ta amsa ba, ta tashi daga kusa dashi ta koma inda take da.

"To a bani result d'in a rubuce."

"Bani da biro da paper."
Ta fad'a fiska a had'e dan ya gama kular da ita.

"Yanzu ko sauran na makarantan babu."

Kamar baza ta amsa ba can dai tace "Sun k'are tun randa na rubuta last paper."

Tana fad'in haka ta mik'e.

"Dakata malama, ina zaki bamu gama ba?"

Kamar zata yi kuka taja ta tsaya ba tare da ta kalli inda yake ba, shiko sai kallonta yakeyi yana dariyar yadda ta had'e rai.

Bata ankara ba ta jishi yana magana dab da ita , "Na baki assignment kije kiyi tunani ko research kan ciwon da na kwatanta miki ,nd don't forget nace miki 8 days back ciwon ya fara min, but yau naji sauqi, kiyi tunani ko Allah zaisa in samu maganin ciwon daga gareki dan bana son zuwa gurin wani likita tunda nasan maganin bazai samu daga wajensu ba."

Yana gama fad'in haka ya fice yana cewa "Na barki lfy, Allah yasa research d'inki ya mana amfani, kar kuma ki manta kwanakin , takwas nace.
Ya dad'a jaddada mata snn ya ci gaba da tafiya.

Tsaye tayi tana kallon yadda yake taku cikin k'asaita tamkar wanda ya fito daga tsatson sarauta.
Saida ya fice daga gidan snn ta sauqe ajiyar zuciya tana mai hura iska ta hancinta tamkar mai fyato abu har sau uku wai ita batason qamshin tiraren shi da ya cika mata hanci, snn ta d'auki B.P.Machine d'inta tayi cikin gida.

Ko da ta koma cikin gida harkokinta taci gaba da yi duk da dai tunanin kalar ciwon mutumin yana mata yawo a kai, tambayar kanta take, shin ciwon na gaske ne koko raina mata hankali yayi.

Sai bayan sallar isha'i al-amin ya shigo, duk sun baje kan babbar tabarma suna cin abinci.

Shima nashi abincin ya d'auko ya zauna kusa da Salma da tunda ya shigo bata kalleshi ba, so yake ya fahimci wani yanayi take ciki.

Sai da ta tabbatar ya gama snn tayi qasa da murya tace "Shine ko?"

"Wa kenan?"
Ya tambaya tamkar bai gane abinda take nufi ba.

"Oganka."

"Eh shine ,me ya faru?"

Shiru ta d'anyi ,daga bisani tace "Wai da gaske bashi da lafiya?"

Kallonta yayi da mamaki sai kuma ya maze yace "Ba shi ya fad'i hakan ba?"

"Eh, shi ya fad'a, amma ni kalar ciwon ya ban mamaki."

"Waye yake rashin lafiya?"
Cewar pendonsu.

Gum al-amin yayi dan shi dai yasan lfyar oganshi qlau, baisan yaushe ya fara rashin lfyr ba.

"Ogan yayanmu."
Ta bada amsa.

"Assha,Allah ya bashi lfy." cewar Ummi.

"Amin." suka amsa baki d'ayansu.

 Fati tace
"Ko shi kika duba d'azu aunty Salma."

"Eh, shine."
Har tayi shiru sai kuma tayi murmushi mai sauti tare da cewa "Ni ciwon nashi ne ma yaban dariya wlh."

"Ciwo kuma ya baki dariya salma, ba kyau irin haka, kar kiyi haka amatsayinki likitta bai kamata ba.

"Pendo ,bari man kiji irin ciwon, wai fa kanshi ke mishi Duuuuum, kunnuwanshi kuma suke mishi Shuuuuuu, snn idanunshi kuma wai dishi dishi suke gani , tun kwanaki takwas da suka shige,
Ko me ya hana shi zuwa asibiti duk cikin kwananakin? snn abin mamaki yace d'azu idanunshi suna gani sosai saidai yasan zuwa gobe ciwon zai ci gaba. Kuji fa dan Allah.
Snn wai zuciyarshi ke bugawa kik."
Bata qarasa ba tayi saurin had'iye maganar sakamakon bugawar da tata zuciyar tayi, snn qwaqwalwarta ta fara fassara maganganunshi d'aya bayan d'aya.

Dariya al-amin yakeyi qasa qasa a ranshi yake cewa "Lallai oganshi ya iya game, ko ya wasan zata qare?"

Dariyar nusaiba ne ya dawo da ita daga tunanin  ta fad'a.
"Lallai wnn mutumi ya iya rashin lfy, kuma kwanaki takwas, kenan tun ranar da kika k'are makaranta."
Nusaiba ta fad'a cikin dariya, Fati ma dariyar takeyi amma ba kamar nusaiba ba.

Kan Salma ya kuma d'aurewa da ta tuna jaddada matan da yayi ,wai tayi lissafi ,kwanaki takwas , to lissafin me yakeso tayi.

Nusaiba ce ta sake katse mata tunaninta da cewa.
"Aunty wato rashin ganinki a hanyar makaranta ne yake tab'a ganinshi kenan."

Yanzu kam har su Ummi dariyar salma sukeyi, ita kuwa ta saki baki kamar wawiya tana kallon al-amin.
Indai haka ne nufinshi tabbas ya gama raina mata wayo, har da sata gwada B.P nshi.
No wonder yace baya bukatar zuwa wajen likita,.

"Allah yasa research d'inki ya mana amfani, kar kuma ki manta kwanakin takwas nace."
ta kuma tuna kalamanshi.

Gyad'a kanta ta shiga yi , ko ba komai nusaiba ta taimaketa, kuma ba wani research da zatayi.
To ma ba sai ya sake ganinta bane zai raina mata hankali.
K'wafa tayi ta tashi ta barsu a gurin suna ta mata dariya, dan a gurinsu komai a bayyane yake.
[17/12 06:25] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


*F.O.W.*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal*

             30.


      💔💔💔💔💔💔

*Wnn shafi kyauta ce gareku Fasaha  Grp nvls members 1,2,3,4. muna godiya da dimbin qaunarku garemu.*


Shiganta ba da jimawa ba nusaiba tabi bayanta ta zauna kusa da ita.

Kafin tayi magana Salma ta riga ta da cewa.
Nusai bakiga mutuminnan ba ,very gentle with innocent face, sam bai dace da abinda yayi d'innan ba, ya ban mamaki wlh.

Gimtse dariyarta tayi tace "Me yayi miki ne aunty, har kike cewa ya baki mamaki."

"karya mana da raina min wayo da yayi, wlh fiskarshi batayi kama da hakan ba sam."

"To idan kuma ba karyan bane kike karyata shi fa ,ki bari ki tabbatar tukun ki yanke hukunci. "

Tsaki mai qarfi taja snn tace "Ya zaki ce ba qarya yayi ba, mutum daka ganshi kaga lafiyayye ya wani  tsaya yi min kwatancen shirme, ni sai yanzu abin yake bani haushi ma. ko da yake har da laifin yayanmu ma wlh, na jima da ..

Bata qarasa ba kiran ahmad ya shigo wayarta ,hakan yasa ta dakatar da maganar da takeyi ta d'au wayar tana sauk'e ajiyar zuciya .

Shima ajiyar zcyr ya sauqe , kwana biyun da basu had'u bane duk suke ji tamkar kwanaki da yawa suka d'auka basu ga juna ba, nan ma kullum suna waya fiye da sau biyu.
Sam sun kasa sabawa da hakan .

Hiran su sukayi cikin shauqi da ishqi wanda ya mantar da Salma b'acin rai da take ciki.

_Two days later_

Kasancewar ko wani wkend suke wanki kayakinsu , hakan ya kasance yauma har da ya al-amin , suna yi suna hira cikin nishad'i da qaunar juna , su Hamza suke jawo musu ruwa a rijiya suna wankin.

Har azahar suka gama kowa yaje ya bada farali snn suka baje dan bawa ciki hakkinshi.

Saida suka gama nusaiba da Salma sukayi wanka , nusaiba sai dariyar tsokana takewa Fati dan ita zata yi musu girkin dare kasancewar time table suke dashi ,kowacce da ranar girkinta, shara, wanke wanke.

Sai bayan sallar la'asar suka fara tattara kayansu da suka bushe suka fara ninkewa.

Da na Ummi suka fara snn suka jibge nasu a d'akinsu suka shiga ninkewa.

Na al-amin suka tattara suka kai d'akinshi suna ninkewa, suka ji sallamarshi.
Murmushi yayi ganinsu duka biyu a d'akinshi kafin yace nusaiba tazo ya aiketa.

Suna fita sukayi d'an kuskus d'insu bata daiji abinda suke cewa ba, sai dariyar nusaiba taji irin na shaqiyanci ma.
A ranta take tunanin me nusaiba ta samu take wnn d'an iskan dariya.

Can taji shiru, ta dai ci gaba da abinda takeyi, har wani raba kayan biyu tayi tana cewa "Ba dariya zakiyi ba,sai kin karasa ninke kayan nan."

Tana cikin ninke kaya tana suruntanta taji abu ya tab'ata a baya,da saurinta ta juya bataga kowa ba sai hijabinta da ta gani a yashe a bayanta.

D'auka tayi ta kalla ta ajiye a kan katifar ya al-amin taci gaba  da abinda takeyi tana cewa "Nasan babu mai wnn aiki sai nusaiba."

Sallama taji a bakin kofar, wadda yasa zcyarta tsinkewa tare da mummunar fad'uwar gaba.
A gigice ta d'auki hijabinta ta saka.

Sake kwad'a sallamar akayi wanda ya tilasta mata zama yaraf akan kayan da ta ninke, tana maida numfashi tare da dafe kirjinta dake bugawa da qarfi kuma sauri sauri, sbd gane mamallakin muryar.

Saida yayi sallama na uku snn ta amsa.
Shigowa yayi ya tsaya bakin k'ofar tare da hard'e hannayenshi a kirji, ya tsura mata ido.

Kamar yadda bata kalleshi hakama batayi mishi magana ba.

Takowa yayi ya iso kusa da ita snn ya tsuguna , sun d'au lokaci a hakan bata kalleshi ba kuma batayi magana ba, kanta a qasa ,fiskarta kuma a daure kamar wacce taga ajalinta.

"Da fatar na sameki lafiya Gimbiya."
Nanma shiru ba amsa.

Wata zuciyarce take fad'a mata ta gaisheshi , ko ba komai ogan yayanta ne, kuma shi babba ne akanta.

"Ina yini ."
Tace dashi, ba tare da ta d'ago ba.

"Lafiya ba sosae ba, dan bani da tabbas."
D'an dagowa tayi ta kalleshi jin yadda ya bata amsa tamkar mai rad'a.

Wnn karo english wears ne a jikinshi, bazata iya tantance kamanninshi ba tunda ba tsayawa kallonshi takeyi ba.

Gyad'a mata kai yayi tare da lumshe ido, hakan yasata saurin kawar da kanta.

*08161594233*
[17/12 06:25] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


*F.O.W.*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*


                32.

       💔💔💔💔💔💔

Ko kallonta batayi ba ta d'au buta ta nemi waje ta fara alwala.
Hakan ya bawa  nusaiba damar ci gaba da abinda takeyi.

Saida sukayi sallar magriba sukayi addu'oinsu suka shafa snn salma tace "Nusaiba , wato munafurci kuka kulla ke da yayanmu ko, muna aiki, kika kama hanya kika fita kika barni."

"To ni kuma aunty me na sani, yayanmu ne fa ya qirani ya aikeni kuma kinji lokacin da ya kiran."

"Ba wani nan ina jinku kuna kuskus kice aikanki yayi."

"aikan yake fad'amin kenan lokacin."

"Wani irin aika ne ?"
Ta fad'a tare da tsare ta da ido.

"Haa ah, tace tana 'yar dariya "Sirri ne fa ,yace kada in fadawa kowa."

"Nice kowan kenan, in ba munafurci meye na baza'a fadawa kowa ba, mts."
Taja tsaki snn ta kuma cewa "Yauwa yaushe kuma kika taba jin na cewa mutumin nan gentle."

"Wani mutumi?" ta tambaya tamkar bata fahimci abinda take nufi ba.

"Mutumin da kika min sharri dazu a wajenshi, yaushe na ce shi gentle ne."

"Haba, aunty Salma , da bakinki a cikin d'akin nan kika ce mishi gentle with innocent face?"

"Mtss wancan lokaci ,ina miki bayani ne dan ki fahimci abinda yayi bai kamata ba, baki abin magana.
Kamar tana jira tace "tsuliya abin kashi."

Qwafa salma tayi tana cewa "Ba laifinki bane nusai."

"Banda abinki aunty salma ai kunfi dacewa da wnn dinma."

Wani wawan zabura tayi saida ta tsorata nusaiba.
"Da wa din muka fi dacewa?Amma mutuncinki ragagge ne nusaiba. Ahmad din zakiyiwa haka?
Allah ya kawoshi lafiya, dole yasan matsayinshi a gunki. Wlh kin ban mamaki."
Tsakaninta da Allah ranta a b'ace take maganar.

Kusa da kofa nusaiba ta koma snn tace "Tsakani da Allah to meye laifina dan na fad'i ra'ayina, mutumin da ya so ka ya so abinda kakeso ai shine abin so. Bayan haka ma duk wanda yasan dacewa, yaganki yaga gentle yasan kunfi dacewa, ki duba fa skin colour naku ma iri d'aya, shi kuwa ahmad wani fari fauu dashi, idan kuka had'u saiyayi fauu, ki kuma kiyi wata disshhh dake."
ta karishe da dariyar rainin hankali.

"Naji nusaiba, yanzu nasan irin zaman da zanyi da ke, snn da bakisan bamu dace ba sai yanzu kike ganin rashin dacewar, kisani duk wanda yaki ahmad ni yaki, na kuma gode da kiyayyar da kika nuna min,

"Allah ya baki haquri ,niba nufina kenan ba."
Daga nusaiba ta fad'i haka dukansu sukayi shiru.

Saida suka gabatar da sallar ish'ai snn suka bar d'akin, ba mai kula dan uwansa, Fati ko zuba musu ido tayi dan ita bata ma san wanda ake maganar a kanshi ba.

Ko da ahmad yazo, kamo hanun fati salma tayi suka fita tare, nusaiba na kallonsu tana ta dariya qasa qasa.
Saida suka fita tayiwa su ummi tad'in daramar da sukayi da salma snn tace bari taje taga ya salma zatayi.

Tana zuwa wajensu ta washe baki , "Lucky sannu da zuwa ,  "
"Yawwa kanwarmu da fatar na sameku lafiya."

"Lafiya lau ya Madam."
Ta fad'a tana satar kallon salma."

Shima saida ya saci kallonnata snn yace "tana lafiya."
Salma dai sai zabgawa nusaiba harara takeyi, itako sai janshi da hira takeyi ,harda cewa Allah ya bar mana luckynmu.

"Munafuka."salma tace qasa qasa.

"Aunty kince wani abu ne?"
hararan ta kuma galla mata snn ta d'auke kai.

"Nifa yau ban ganewa aunty salman nan ba.
Cewar ahmad yana maida dubanshi ga salma.

"Ai yaufa bazaka gane mata ba da..."

"Ke nusaiba bar nan."salma ta fada tana muzurai, sbd tsoron kada nusaiba  ta fadi wani yazo wajenta , gashi yanzu ma duk a tsarge take.

Dariya nusaiba tayi ta k'ara gaba, tana cewa "lucky, na tafi tunda an koreni."

Ita dai salma jinta takeyi wata iri tamkar ta aikata sab'o haka takeji, duk lokacin da A M G ya fad'o mata sai taji tsinkewar zuciya.

Allah alla take ta shiga gurin al-amin da ya shiga gida yanzu dan tana so suyi magana.

Suna shiga gida ta cewa Fati wuce ciki ni zan shiga gun yayanmu.

Yana jin ta kusa isowa kofarshi yayi saurin kashe wutan d'akin dan ya santa da tsoron duhu.
Tsayawa tayi tana kallon kofar d'akin tana tambayar kanta ta shiga ko kuma ta bari sai da safe.

"Kai ina bazan iya ba yau za'a yita ta qare."
Tace a ranta.

Sau uku tana sallama ,shiru ba amsa, hakan yasa ta kutsa kanta cikin dakin duk da duhun dake ciki.

Lalub'e ta shigayi har ta gane makunnin wutan ta kunna, saiga al-amin kwance bisa katifa ya rufe ido tamkar mai bacci.

"yayanmu ka tashi magana zamuyi ,ni nasan ba bacci kake ba.
jin yayi shiru yasata isa bakin katifar ta duqa ta jijjiga shi da iya qarfinta saida taga ya bud'e ido snn takyale shi.

"Ke meye haka ."yace yana wani hade rai.

"magana zamuyi."

"shine kuma bazaki iya haqura sai gobe ba zaki tasheni a bacci."

"Tunda ka tashi ba sai muyi maganar ba."

Yau ya lura a salmanta take sbd haka ya dad'a hade fiska.
"yauwa, me yasa d'azu baki qarasa ninke min kayana ba? tunda kika shigo sai kizo ki karasa."

Kama kugunta tayi fiska a d'aure tace "Ka ninke kayanka da kanka, naga dai d'azu ninkewa mukeyi ni da nusaiba, ka kirata ka turo min wani k'ato."

Waro idanunshi yayi "waye k'aton salma?"

"Ogan nawa kike cewa k'ato,  haba ummulu aiko albarkaci na ya kamata yaci ki mutunta shi."

Kamar zatayi kuka tace "Yayanmu me yasa kake min haka ne, kasan ahmad nakeso kuma shi zan aura, danme zaka hadani da wani? Yaudararshi kakeso nayi, ko ahmad din kakeso na yaudara.?"

"Ko d'aya ni bance ki yaudari kowa ba, amma ina laifin maisonka, ahmad din wani yunkuri yayi game da maganar aurenku? Tun yaushe kika qare karatun in har da gaske yake."

Katse  shi tayi da cewa "Wlh da gaske yakeyi, naga wancan karon ba tare da sanina bama ya turo, da na nuna mishi rashin amincewata ne ya dakata, kuma yace sai na yi mishi izini zai sake turowa."

"mtss, to me ya hanaki yi mishi izinin, ko kina tunanin haka za'a yi ta zuba miki ido ga kanwarki zata yi aure ke kuma kina jiran tsammani."

"Yayanmu, kasan ni ahmad nakeso, ka kuma san ra'ayina bana son auren mai kud'i kuma bana son mai mata."

Dariyar takaici al-amin yayi wato bakya son mai mata, shi kuma ahmad d'in 'yar tsana ya ajiye a gidanshi kenan, ko kuma shi d'in ba mai kud'in bane.?"

Wani marairaicewa ta dad'a yi, "Ahmad nefa, shi kasan ko yaya nema ina sonshi."

"Kije ki had'iye shi qarewar so Ummu salma."
Ya fad'a kufule.

"Dakata ma wa yace miki ogana yana da mata? Shi ya fad'a miki yana da mata?

Shiru tayi ta kasa bashi amsa dan itama tasan fad'a kawai tayi.

"Fita salma sai da safe tunda bakisan mai sonki ba."

Juyawa tayi zata fita ranta a b'ace, ya tsai da ita, "Kuma ki sani kafin ya fara zuwa wajenki saida ya nemi izini Wajen malam, kuma yayi na'am dashi, danshi ba wasa ya zoyi ba da gaske yakeyi."

Cikin takaici tabar d'akin a ranta take cewa "to wa yazo wasan?"gaba d'aya haushinsu takeji, daga al-amin, oganshi harma da Nusaiba.

Bai sake zuwa ba har akayi bikin nusaiba aka gama, sai tayi tunanin ko al-amin ya fad'a mishi yanda sukayi ne ya haqura.

Bayan biki taje ta samu Mal. tace mishi zata bi pendonta kaduna, bai hana ta ba ya bata izinin tafiya, sbd haka ta fara shirye shiryen tafiya.

Al-amin kuma yanzu sun koma normal ta daina jin haushinsa.

Ranar da zasu tafi da sassafe al-amin yace su fito zai kaisu tasha.

Sallama suka yiwa kowa,su Hamza suka fitar musu da kayakinsu.
Har sun kai bakin kofa salma ta koma da gudu tana cewa "Bamuyi sallama da auta ba."

D'akinsu Hamza ta shiga ta samu khalil   yana bacci.
Tashinshi tayi ya tashi yana murza idanu "aunty yanzu zaku tafi?"

"Eh, yanzu ne, kayi sallah kuwa?"

"nayi da muka dawo daga masallaci ne na kwanta."
Kanshi ta shafa "to na tafi kayi mana addu'a ."

"Allah ya kareku da kariyarsa,Allah ya kaiku lafiya."

"me zan siyo maka."

"Ball da canvas zaki saya min ."

"to khalilu na sai na dawo."

Da sauri ta fice ya bita a baya yana mata bye bye.

Motar ranar da ta gani wanda al-amin yazo dashi.

Tana isa aka bude mata gaba ta shiga da Bismillah, snn ta rufe kofar.

Kamshin da taji ne yasata d'agowa da qarfi....


*Ummu D'alhat ga naki*😍🌹
[17/12 06:25] Hajara: *💔💔IN SO CUTANE💔💔*


*Fasaha Online Writers.*


*F.O.W.*


*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*


               33.

       💔💔💔💔💔💔
*Dedicated to adda Ummulu (Ummu salma Ahmad Adam) a.k. a Dr U.S.A.*


Wanda ta gani a driver seat yayi matuqar razanata, kallonshi take da mad'aukakin mamaki.

A .M .G.

Ta d'au lokaci tana kallonshi snn ta waiga ta kalli bayanta , wayam ba kowa.
To ina suke.

Kallonshi tasakeyi sukayi 4 eyes, take tayi qasa da kanta.

"Ina kwana Ummu."

Wani kunya taji ya rufeta, cikin sanyin murya tace "Ina kwana."

"Lafiya lau, ya hidimar biki?"

"Alhamdulillah."

Daga nan sukayi shiru, yaja motar sai tasha.tana ta saqe saqe a ranta ,dama wnn bawan Allah ba haqura yayi ba liqimo yayi kenan.

Saida suka isa ta hango al-amin yana  jingine da wata mota.
To ina pendon kuma ?
Tace a ranta.

Qarar wayarta taji daga cikin handbag dinta, shi ya katse mata tunaninta.
Wani lafiyayayen murmushi ta saki lokacin da ta fito da wayar, ganin ahmad ne yake kiranta.

Bayan sun gaisa yake ce mata gashi a kofar gidansu, yazo su sake yin Sallama duk da dai jiya sunyi yana so ya kuma ganinta kafin tafi, yasan ko yaya zaiyi bazata tab'a yarda ta shiga motarshi ba, dan tunda suke tare bata tab'a yarda ya kaita wani waje da motarshi ba.

Wani irin tausasa murya tayi tace, "Ayya ahmad mun riga mun wuce."

"Ya kika mun haka salma, naso na qara ganinki kafin ki tafi."

"Nima naso hakan wlh."
Da sauri ya katse ta da "zanzo yanzu kafin ku tashi."

"A'ah, mun kusa tashi, ko kazo ma nasan bazaka samemu ba." itadai tsoronta kada yazo yaga wnn d'an anacen ranshi ya b'aci.

Shiru ya d'anyi snn yace "Zanyi kewarki salma ba kad'an ba."

"nima haka ahmad."

"Ki kula min da kanki, dan Allah banda fita kada samarin kaduna su gane minke su kyasa."

"Ina ,wane su salma ta Ahmad ce shi kad'ai In sha Allah."

"Allah ya yarda, salmata, Allah ya kaiku lafiya, ya tsaremin ke ,zan kira anjima."

"amin na gode sai na jika."

Daga nan ya kashe wayar.

Tunda ta fara magana a waya ya yi baya tare da kwantar da kanshi kan seat, ya lumshe idanunshi.

Har saida ta gama ya bud'esu, snn ya taso.
Tana kokarin maida wayar cikin jakarta ya sa hanu a hankali ya zare wayar.

D'an kalloshi tayi taga hankalinshi na ga wayar, ta tab'e baki tare da kawar da kanta.
Bude kofar take famanyi ta jishi a kulle , hakan yasa ta kuma kalloshi.

"Baki da kirki Ummu."
Yace ba tare da ya kalleta ba.

"fiye da sati baki ganni ba bakiji daga gareni ba amma sam baki nemi sanin halin da nake ciki ba."
Shima kanshi yasan ya fada ne kawai dan neman magana amma yasan bazata nemeshi ba koda shekara tayi bata ganshi ko ji daga gareshi ba.

A nata bangaren kallon mamaki take mishi dan duk a tunaninta ta d'auka zaiyi korafin wayar da tayi da ahmad a gabanshi zaiyi, amma ga mamakinta sai ya dauko wata maganar daban.
Taso ya kawo mata maganar ahmad ko dan ta tabbatar mishi ahmad takeso kuma shi zata aura amma sai taji akasin haka."

"Ummu na shiga wani qauye ne duba wani aiki, qauyen basu da service, shi yasa baki jini ba, amma baki tab'a barin zuciyata ba koda na second d'aya ne.
Da badon Allah yasa na dawo jiya ba saidai na dawo naji kinyi nesa dani, kin tafi ba ko sallama."
Ya dan sauqe ajiyar zuciya.
"Ko da yake dan in biki kaduna ba wani abu mai wuya bane, ai hausawa sunce garin masoyi baya nisa."

Duk surutan da yakeyi salma waje take kallo sam bata yarda ta sake kallonshi ba, ita dai ya cikata da haushi tunda bai fadi abinda ta keso taji ya fada ba.

"Ummu, ummu, ummu."ya jera kiran sunanta, jin bata amsa ba yasa yaci gaba da kiran sunanta.

"ya fara halinnashi na naci d'an anace kawai, sai yayi ta jera sunan mutum a bakinshi ko gajiya bayayayi."tace a ranta.

"Ummu salma." Sai a snn ta kalleshi amma bata amsa ba.
Kurawa juna ido sukayi na dan lokaci, daga bisani ta janye nata.

"Nagode."
Taji ya ce.
Kallonshi ta kumayi da mamakin godiyar da yakeyi.

"Nagode ,dama kwayar idanki nakeson gani dan su zame min abin tunawa a ko da yaushe.
Ta iya yiyuwa ma kallon karshe kikayi min Allah masani."

Da sauri ta kalleshi dan maganar ta dan tsoratata sbd a sanyaye yayi ta.

Suna hada ido ya daga mata gira tare da kashe mata ido, hakan yasa tayi saurin kawar da nata."

Murmushi mai sauti yayi tare da cewa "Ummun Abdul in sha Allah."
"Wannan rana tana cikin ranaku masu muhimmanci a gareni , zaiyi wuya na mance da ita."

Hanunta ta miqa mishi alamar ya bata wayarta.
Tamkar bai ganta ba yaci gaba da danne danne a wayar.

So take ta masifeshi amma bakinta ya mata nauyi.
Haka  kawai taga ya mata kwarjini, ya kuma cika mata ido.

"Ummu tsarabar me zaki kawo min?"

Kamar an sata dole tace "Duk abinda kakeso."

Kura mata ido yayi yana murmushi mai qayartarwa , ya ce "duk abinda nakeso kikace?"

Shiru tayi bata amsa ba.
"Ummu tsarabar zuciyarki nakeso ki dawo min da ita, zan samu?"
Ya qarishe maganarshi da cikin wata kasalalliyar murya.

Wani abu taji yana mata yawo ajiki wanda ya tilasta mata takure jikinta waje guda ta kuma rintse idanunta.

Kallonta yayi na dan lokaci kafin ya maida hankalinshi kan wayarta, ya budeta ya cire sim cards dinta ya kuma bude tashi wayar ya musu musanyen simcards snn ya miqa mata tashi wayar .
Saida yace mata "ga wayarki ."snn ta bude idanunta .

Kallon wayar tayi snn tace "waya ta zaka bani."

"itace ai."
Ya fadi ya kuma mika mata wayar.

Ganin taki karb'a yasa hannu ya dauki handbag dinta dake kan cinyarta ya saka wayar ciki.

Jakar tana hanunshi ya bude motar ya fita ,ya zaga ta gefenta ya bud'e mata.

Lokacin da suka fita an fara kiran sunan masu tafiya ,sbd haka ta matsa gurin da taga su ya al-amin, shiko yana biye da ita a baya.

Tana isa al-amin ya washe baki, "Ummuluna kamar mu tafi tare."

Saida ta matso kusa dashi sosae snn a shagwab'e tace "Shine kuka tafi kuka barni ni kad'ai yayanmu."

"Ah, haba dai, yanzu ke kad'ai kika zo?"
Ya fad'a yana waro ido kamar gaske.

"Yayanmu ka qware wajen iya manna wa mutum hauka."

"Me nayi ?to da wa kikazo?"

"Oho, ni ban sanshi ba."
Duk abinda sukeyi pendonsu da A M G suna kallonsu saidai basajin abinda suke cewa, sosae suka burge su dan da ganin yadda take mishi shagwaba kasan akwai shaquwa mai karfi tsakaninsu.
Ita pendonsu tuna mata da yaranta na farin da ta biyun sukayi , haka suke ,basa rabuwa suyi fada su shirya.

Har aka kirasu suna tsaye sai tsokanarta al-amin yakeyi.

Pendo ce ta fara shiga snn ita kuma tazo zata shiga.
"Ki kula kar ki zauna kusa da ko wani qato." taji shi daga bayanta.

Kalloshi tayi kad'an ta kawar da kanta , a zuciyarta tace "Gaka k'ato kake cewa wani kato."

Har ta shiga yana tsaye a gun , saida ta je ta zauna can ta   jikin window, seat nasu daya da pendonta, al-amin ne ya zo ya tsaya ta wajen , "Allah ya kiyaye hanya ummulu."

Hanunta ta mika mishi shima ya miko mata suka yi shaking tace "Kamar in fasa yayanmu, wlh zanyi kewarku fiye da tsammaninka, Alla sarki fati na,daga yanzu na fara kewarta."

"Daga baya kenan, saida kika daidaita cikin kujerar mota zaki wani ce min kamar ki fasa, kice dai zakiyi kewar ogana kawai."
Ya karishe da sigar zolaya.

"Hmmm, kace ya bani hand bag dina, indai ba gado na zaiyi tun ban mutu ba."
Dariya al-amin yayi ya zare hanunshi snn yace "wnn tsakaninku ne ,ni na isa na shiga inji kunya?.
Allah ya kaiku lafiya, pendo Allah ya kiyaye hanya."
Ya maida akalar maganarshi gurin pendonsu.

Barin wajen yayi yana jin ba dad'i.
Saida motarsu tazo tashi snn ya leko ya ajiye mata jakar kan kan cinyarta tare da wata leda mai 'yar girma yana cewa "safe journey dear."a hankali kamar mai rad'a.
Snn ya sallami pendo.

Suna tsaye a gun har motarsu ta tashi.
(safe journey salman ahmad.)😜

*08161594233*



Download In So Cutane Littafi Na Daya