*_maman Al-ameen CE_* 👌👌👌
*INDO BALA'I*

🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀



_bismillahirrahmanirraheem,ina rokon Allah yabani ikon farawa cikin sa'a nakuma gama cikin sa'a,ameen_





Page 1/2

*_Na Maman Al-ameen momcy_*



Tafe take tana tsalle tana waka tana cilla ledar dake hanunta,wani gida ne ginin laka naga tashiga ko sallama babu tahau kwala kira


Inna! inna!! inna!!!


Wata yar dattijuwace tafuto daga wani daki tana kai indo kekam bansan sanda zakiyi hankaliba ko sallama babu sai kwalamun kira kk to ina aikan danamiki


Turo baki tayi tace gashichan

Inna tace to maza sai kitashi kije kidibo ruwa ko,kai inna dan Allah daga dawowa ta daga kasuwa ko hutawafa banyiba,

Inna tace to ahikenan inbaki dibo ruwanba naga da abunda za'a dafa abincin kici

Tana turo baki tadauki bokiti tafuta

Wasu yarane su biyo suna tafiya da alama aika suka futo da kwano akansu,amma ban hango meye acikiba,

Daya daga cikin yaranne yace laaa hasan kaga INDO bala'i tafuto ,dayan yace laa wlhy itace kai mutsokaneta mu gudu,
Aikuwa sukabi ta suna sanda itakuwa tafiya takeyi sam bata lura dasuba saiji tayi sunce INDO bala'i suka ruga aguje ai aje bokitin tayi tabisu dagudu tayi nasarar kama daya Wanda shine me kwano akansa kyawawan Marika tabashi tareda buga masa naushi abakinsa tsabar azaba saida yasake kwanon dake kansa yafadi kasa ananne nayi nasarar ganin abunda ke ciki garine ciki da alama nika suka karbo aikuwa yakife acikin lallausan kasar garin ga baki yafashe sai jini yake ,

Dukda haka batasakeshi cewa take ayo nisa arkace ko yau sai kasan uwar datasa ka tsokaneni ehee Dada wanka masa mari tayi yafara bata hakuri dakyar muryarsa take futa tsabar azaba


Wani mutumine yazo wucewa yaga yadda INDO ke sanbadan yaro yanufota dakyar yakwace yaron ahanun INDO tareda tambayar meyamata ,cikin huci INDO tace katambayeshi mnh,kallon yaron yayi yace mekamata cikin kuka yaron yace wai dan muncemata INDO bala'i

Hantsilowa INDO tayi zata kara kai masa duka mutumin ya tareta tana cewa oh sake maimaitawa kayi ko,

Hakuri mutumin yadinga bata dakyar tahakura tadauki bokitinta tayi gaba,

Dazumar d'ayan ma  sai tabishi ta dakashi

>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *tushen labari*




Mallam bala shine asalin mahaifin INDO Wanda suke zaune akauyen tsamiya su biyo mahaifinsu yahaifesu,shida kaninsa suntashi cikin gata dukda bawani hali sukedashiba sai rufib asiri babansu dankasuwane yana zuwa birni yasaro yazo kauye yasayar ahaka har ciwon ajali takamashi yarasu ,bala da kaninsa aminu mahaifiyarsu na kula dasu sosai dukansu suna makaranta arabi da boko dake kauyen bala shiya rike kasuwancin babansu suna samun naci Dana makaranta kasancewar yakai matsayin samartaka, shi kuma aminu baya zuwa kasuwar ,lokacinda aminu yagama secondary yanemi yayanshi yaturashi birni yakaro karatu shi kuma dama tunda yagama becigababa yamaida ahankali kan kasuwancinsa,haka kuwa akayi yatura kaninsa aminu birni dan karatun jami'a

Bayan tafiyar aminu birni yayansa bala yahadu da harira suka kulla soyayya ba jumawa sukayi aure amma tinda suka yi aure harira ba labarin haihuwa ko bari bata tabayiba


Shikuma aminu yana chan birni sai karatu yake harya kammala degree na daya yashiga tabiyu




Harira tana kulada gwoggwo wato surukarta mahaifiyarsu bala


Bayan aminu yagama degree dinshi ta biyu yadawo gida kafun aiki ya samu ,sosai matar wansa ke kula dashi shima kuma yana darajata sosai,

********************
Bayan shekara biyu aminu yadibi takardunsa yatafi birni Neman aiki ,cikin ikon Allah yasamu aiki awani company ,yakanje gida duk weekend ahaka yana samun kudi yana ajiyewa haryatara na fili yasaya yayi gida, bayan anbashi manager a companyn,yahadu da dawa ta yar babban mutum acikin garin kano,sukayi aure ,bayan auren su dashekara daya ta haihu namiji akasamasa sultan ,

Bayan aihuwar sultan da shekara daya matar bala wan aminu tarasu,bayan rasuwarta da kamar bazai sake aureba daga baya yahaduda hadiza ya aura ,itama saida tayi shekara shida Allah yabata aihuwa ta haifi diya mace akasamata Aisha taci sunan mahaifiyarsu suke kiranta da INDO


Ba yanda aminu beyiba kan yayansa yayarda yakoma kano kasancewar gdnsa babbane kuma part biyu ne aciki manya manya ga boys quarters dayayi abangare dabn ,Sam bala yaki yarda yakoma kano, acewarsa yafison mahaifarsa da kasuwancinsa akauyensu,



Lokacin sultan na yaro yakanje kauye amma tinda yagama primary yakoma waje da karatu,achan yakammala karatunsa tindaga secondary har degree dinshi,



Lokacin kuma INDO anshiga primary ,tanada shekara goma sha biyu tana primary 4,kasancewar ba asata da wuriba,


Amakaranta INDO batabarin kowai indai aka tsokaneta zata rama bata barin ta kwana gashi Allah yayita da karfi,harda maza buguwa take,saidai kuma Allah ya zuba mata kwakwalwa ,mallam ai sunaji da ita saboda kokarinta amma akan fadarta suke batawa,


Mahaifiyar sultan Wanda yakekiranta da mami tasake aihuwa ta haifi shukhra Wanda kusan sa oi ne da INDO


*******************cigaban labarin....

_Kubiyoni_



*INDO BALA'I*
🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀


Page3⃣~~4⃣



_na maman Al-ameen momcy_





Indoce zaune tanashan kunu da kosai nakaryawa inna tafuto daga daki tace yanzu INDO har yanzu baki gama shan kokonnanba so kike ki makara ko,turo baki tayi tace to inna ba yanzu zangamaba,

Wucewa inna tayi tacigaba da aikinta dantasan da takara magana yanzu gwoggwo daga daki zata amsa antaba mata mesunanta ,

Zainabce kawar INDO Wanda ake kiranta da *Abu*    tashigo itama da shirinta na namakaranta ,chab INDO bakima gama shiryawaba kinsanfa muna jarabawar chanja ajinefa gskya ki aje kokonnan mutafi karmu makara,

INDO tace toke banda abunki akwai mallamin da ya isa yahanani shiga jarabawa ne inda kijirani nakarasa kijirani ,zama Abu tayi tace to kiyi sauri,saida tashanye kafun tatashi suka tafi asoron gidan suka hadu da baba  ,yace ah uwata har anfuto ,INDO tace eh baba Abu tagaida baba,baba yaciro kudi yace toga muttala ayi tara,INDO takarba da murnanta tana yiwa baba godiya suka futa,ai kuwa suna isa makaranta suka samu har anshiga jarabawa,da confidence dinta tawuce aji Abu nabinta abaya itadai tana dan tsoron,saboda tasan sunyi latti,

Mallam idine yace ke INDO daga ina kuke sai yanzu kuke zuwa makaranta bacin kunsan kuna jarabawa,hawayen karya INDO ta kirkiro tana matse ido ,wlhy innatace ba lafiya shine natsaya nayi aiki kumama.....kwai sai tafashe da kuka kamar dagaske ,mallam idi yaji tausayinta yace kiyi shiru Allah yabata lpy sai kuyi sauri kurubuta dan ankusa abuga,


Ai dasauri INDO tayi cikin aji Abu tabi bayanta suka fara jarabawar ba wuya suka gama sukayi submitting suka futa dayake daya zasuyi kowa yagama gida zaitafi ,

Suna futowa INDO tace Abu muje gonar mallam lado musaci masara,

Abu tace kai INDO bakyajin tsoro kinsan fa sai yakai kararmu wurin megari ,INDO tace da Allah ja ke kinada matsala towaye me tsoron megari da Allah mallam indaki kizo muje,haka Abu tabuta sai gonar mallam lado,masarar da tayi da wacce batayiba haka sukayita balla insun bude sukaga batayiba sai su jefar ,aikuwa sun acikin haka saiga lado yanufo gonarsa suna ganin haka suka aune dagudu damasararsu ahanu kowa ta rike nata ,binsu yayi amma yakasa cinmisu kasancewar ya dan tsufa bashida karfin binsu ,haka yadawo cikin gonarsa yaga irin barnan dasukamishi,

Ai mallam lado beyi wata wataba yabi bayan su dan yagane yaran dama bayau suka fara masa barnaba ,inyakai kara iyayensu suce ayi hakuri,

Gidan megari yanufa yaje yakora masa bayanin abunda su INDO yar mallam bala suka masa

Megari yatura akirawo iyayensu ,mallam balane zaune da buta ahanunshi yana alwala gwaggwo kuma nagefen dakinta ta shinfida taburma tanadan shan hantsi,

Sallama akayi baba ya amsa yakara sa alwalarshi kafun yafuta ,tinda yaga dan aiken megari yasan INDO tayi wani abunne,dan aike yace dama megari yace anasan ganinka,
Mallam bala yace to bari tashiga nafuto sai muje ko,

Yana shigowa gwoggwo taga fuskarsa ta chanja tace uhmm ai nasan ba kalauba yauma sharrin aka kumayi wa jikata ko,ai tana ganin baba yafuta itama tadauki mayafinta tayi hanyar waje ,dan Aiken takalla tace tofa daga ina? baba bece komaiba ,dan aike yace megari ne yace akirashi ,tace injidai lapiya ?yace aa dama mallam ladone yakai karar yar gidannan INDO sunyimasa barna agon.....ai kafun yakarasa gwoggwo ta haushi da masifa oh mukam munshiga uku eh jikata ita kadai ke laifi agarinnan ko to bazai yiwuba muje wajen megarin tama rigasu baba yin gaba sai surutai takeyi ita ala anyiwa yar jikanta INDO sharri,



Suna isa megari yakora musu bayani akan laifin da yarsu tayi,baba yana kokarin bawa mallam lado hakuri gwoggwo tace ai ba maganar bada hakuri ni banyarda INDO tashiga masa gonaba ,to mema zatayi da masararsa yarinyar data tafi makaranta mezai kaita gona tatashi tatafi tanata masifa ita antaba jikanta,baba kam hakuri yabawa mallam lado tare da bashi wani Abu yarage asara,



Su INDO kam gidansu Abu sukayi suka gasa masararsu suka Nada acikin su kasancewar innar Abu bata gida,




Saida suka cinye sukasha ruwa suka futo ,aikuwa suna futowa INDO taga yaron daya tsokaneta ranan aiwuf ta chafke yaro tahau tilansa ,saida damasa na jaki tabarsa suna shigowa gidansu baba yana tsakar gida inna kuwa tana kicin tana aikinta duk bonbomin gwoggwo batacemata kalaba ,

Suna shigowa baba yace zonan ,yanda taga baba ya bata rai tasan cewa lado yakawo kararsu gida,dukawa sukayi kusa da baba ,yace daga ina kuke yanzu INDO tace baba daga makaranta muke bata auneba taji saukar mari baba yadaka mata sawa daga ina kuke tatsala uban ihu saida gwoggwo taji daga daki aikuwa tafuto,

Tana masifar wayataba INDO, dasauri taje taja INDO agaban baba tana masifa me tayi masa baba bece komaiba yatashi yayi waje,


*********

Sultan ne zaune a falon sa shukrah tashigo yaya wai kazo inji dady,juyowa yayi ya harareta ke baki iya sallama bako,

Tace yi hakuri yaya,yace to wuce kice ina zuwa,

Bayan shukhrah tafuta yadauki wayarsa yazo kiran da dady ,dadyne da Mani zaune afalon sai shukhrah ,

Sultan yace gani dady ,dady yace eh dama sonake tinda baka fara zuwa aikinba kuma ga shukhrah tasamu Hutu to sonake muje kauye muyi  ziyara gobe saboda haka sai ka shirya ,yace to dady Allah yakaimu ,

Shukhrah kam sai murna takeyi zataje kauye ,mami tace kekuma irin wannan murna haka in dady yace yafasa bandakefa,dariya tayi tafada jikin dady dady yace ai autana kinsan dole aje dake ai ,


Bangaren sultan kuwa haka kwai yaji bayason zuwa kauyennan ,kwai dai bazai iya cewa dady bazeje bane,kuma ga asobitinsa ba akarasa aikinba kuma zasu tafi ,haushin zuwa kauyen yadanji amma sayya daure yahada kayansa ,




******INDO kam ranan batafuto adakin gwoggwo ba dantasan in tafuto kuwa zata jibgu agun baba,

Hardare tana dakin bata ko lekoba har bacci yadauketa ,



Washegari da tingoma su sultan suka iso tsamiya driver yakawo su dan sultan ba gwanin yin driving bane,saboda besababa inyayi tuki waje kadan saiyaji yagaji,


Adai dai kofar gidan sukayi parking suka suka shiga cikin gidan driver kuma yanata futo da kayan da suka Zo dashi a but
.
Da murna inna takarbesu tashinfidamusu tabarma sannan takawo musu ruwa,

Bayan angaggaisa ,inna tace kedai banwayekiba baki taba Zuwa kauyen ba ,shukhrah tayi murmushi dady yace ai makaranta ne yake riketa yanzu sunyi hutune nace to bari na kawosu ita da yayanta suyi Hutu ,kafun agama masa aikin asibitinsa,inna tace ayya ace likitane fa ,mami tace eh Shikuma abunda yazaba knn





Baba yace gashi kunzo kakar naku kuma tafuta tashiga makota

Berufe bakiba gwoggwo yashigo ,tana fadin to yau mutanen birni ne akauye tafada tana dariya irinta zolaya


Sultan yace eh mune mnh ko ba aso zuwanmubane,gwoggwo datakaraso kan tabarman tana shirin zama tace wuuuu wane ni ince banason ganin jikokina ,

Da gudu ta shigo cikin gidan  da Abu ahanunta ,KO lura dasu batayiba takutsa ta tsakaninsu ta yi dakin gwoggwo....

*Maman Al-ameen ce*👌



*INDO BALA'I*
🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀



5⃣&6⃣




_Na maman Al-ameen momcy_,




Ai kuwa gwoggwo na ganin INDO tayi daki aguje tasan da wani Abu ai sai ta Mike tabi bayanta dakin

Shikam baba da takaici yagama isarsa ko kallon inda take beyiba, dadyne yace Aishace haka


Inna tace itace
Momy tace to meye kuma tashigo gida aguje haka kamar wacce akabiyo


Baba yace yawuci wani abun taje tayi,yarinya kullum cikin nema wa mutane magana take daga taje gonar wane tamasa barna sai kaji ance tafasawa dan gidan wane kai ko baki ko kaji ta gurda wani haka kullum muke fama da ita kuma ko a makaranta ma haka ake kawo kararta,ni wallahi nama rasa yanda zanyi da yarinyar nan,
Sultan lokaci daya maganganun baba suka bata masa rai wai anrasa yaya zasuyi da ita bata bugu bane ai ambartane wani haushi aransa yace inama atare suke ai da tayaba wa aya zakinta daduk wannan iya shegen bazatayiba


Dady yace to meyasa baza Ku dinga daukar mataki akantaba karfa wataran daje tajawo wa mutane abunda yafi karfin bada hakuri fa

Baba yace ai bakasaniba kaga ko uwarta bata isa tayi magana ba sai gwoggwo tataso akan mutane koni ban isa dukar INDO ba sai gwoggwo tahau masifa wataran ma harda kuka wai ana zalinta mata jikanta


 Momy tayi ajiyar zuciya tace amma bekamata kuwa abarta akan wannan tarbiyyarba dan kokadan hakan bashida fa ida tinda ya macece kuma girma takeyi yakamata ace ana girmane ana hankali kuma duk rintsifa gidan wani zataje to ahaka....momy bata gama maganaba saiga gwoggwo da INDO sunfi to ,


Gwoggwo tayi murmushi tace cha nayi tafuto tagaida iyayenta da yayanta

Zama sukayi INDO najikin gwoggwo ,tace ina wuninku,dady da momy suka amsa ,gwoggwo tace to baki gaida wannakiba,

Sai asannan taluradashi bakaramin kwarjini yayi mataba ,yanda taga yawani murtuke fuska yasa tawano turo baki,taki gaidashi,


Gwoggwo tace iy bazaki gaidashi ba,INDO tace to mutun yana wani bata fuska ne Zan gaidashi yaseen bazan gaidashi ba ,

Wani irin curin takaici da haushin tane ya wurgu a zuciyar sultan ,aransa yanacewa zanyi maganinki kuwa kafun inbar garinnan,


Gwoggwo tace toga kanwarki sai kuje kudanyi hira kallon kallon shukhrah da INDO keyiwa juna ,INDO tayi murmushi tace to kanwata tashi muje yawo ,gidansu kawata nan makota ,shukhrah tamike suka futa ,tin asoron gidan INDO kecewa shukhrah ke wai hala haka wannan yayannaki yake baya dariya yawani murtuke kamar Wanda akayiwa mutuwa,

Shukhrah tace ke niba ruwana bakisan yaya bane baya wasa da yara kuma inkikayi masa laifi suka yakeyi,


INDO tace wa yake duka ,shukhrah tace to innayi laifi ko agaban mamyne yana dukana wallahi,
INDO tace lallai ai wallahi nikam yabigeni sai na rama dan bazan barshi yaci zalina abagas ba kam ehe,



Shukhrah tace ke yaya fa yanada karfi wallahi bazaki iya ramawaba,   adai dai nan sukashigo gidansu Abu


INDO tagaida innar Abu dake tsakar gida tace inna Abu fa ,inna tace tace tana daki baban ta yamata duka wato indo awarar yaro kuka diba kuka guduko,ai kema dakije kihadu da babanki dannasan daga gidannan gidanku suka nufa,indo tace ai ni banmaci awararba kuma rashin kunya yaro yamana muka daki banza kuma muka dibi na banza tana maganar tana shigewa dakin Abu


Shukhrah kam binta tayi itama cikin dakin,inna kuwa addu'ar shiriya kawai tayi mata,



Agida kuwa INDO na futa aka kawo karanta tabigi yaro kuma ta dibarmasa awara,baba be iya yace komaiba sai tashi dayayi yafuta waje,gwoggwo tace oh nikam naga takaina ace yarinya duk garinnan ta tsole musu ido kodan sunga yafisu kyau ne yarinya kamar yar larabawa suke mata hassada,sai asannan sultan yayi magana OK kaka keso kike kibata yarinya ko to bazeyiwuba bari baba yashigo da mingama Hutu tare zamu wuce da ita kano


Gwoggwo tace eye Mara kunya wato nine banmata tarbiyyaba sai Kaine ka iya ko ,oh Ku yan birni akwai wata tarbiyyanema daku



Momy tace yi hakuri gwoggwo, bama inda zata wasa yake miki ,tace ai damainanankan bawanda zai tafi mun da jika kalan kije chanma kuyita zalintarta ahakama inasa ido ake mata balle abayan idona
.
Mikewa sultan yayi yakoma mota yasauke sit yakishingida yana ganin yaran kauyen yanda suketa wasa cikin kasa da dauda ,aransa yace ba doleba cututtuka yadinga shigar yara,

Indo da shukhrah yahango duna dawowa, futowa yayi yajingina jikin moto yanajirar karasowarsu danso yake yafara takawa INDO burki akan shashancin datakeyi ,

Shukhrah indo tataba tace ke kalli wannan yayanki Wanda baya dariyarnan yanda yadada murtukewa ko annuri babu afuskarsa shukhrah tace ke haka yayafa yake ko agida baya dariya amma wataran yakanyi murmushi wa mamy ,suna isowa daida jikin motar yace ke kuzonan ,shukhrah ya kalla yace yawo ko,zatayi magana amata wani kallo dayasa tasha jinin jikinta,
Kallon shukhrah yayi yace wuce zamu hadu a gida ,

INDO dabece tawuceba zata wuce yace ke zonan ,juyowa tayi tagallamasa harara ta murguda masa baki tashige gida da gudu.... ..


*INDO BALA'I*
🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀



 9⃣&🔟




_Na maman Al-ameen momcy_






Cikin masifa gwoggwo tace fadamun wayadake nace ko,INDO cikin kuka tace bawannan bane mekama da mayuñnan Wanda baya dariyarnan yayan wanchan shukhrah nibanmasan sunansaba,

Gwoggwo tace shegen yaro meya miki Shikuma daga zuwarsa?
INDO tace ba innace tabani tuwon su baba nakai mishiba dakiba to shine inazuwa dakin yafara dukana wai harda cewa sai yakashenima,


Gwoggwo ai sai tafara salati la ilaha illallahu yanzu kaikuma yaronnan ahaka birnin taku take daga ganin mutun kace zaka kasheshi yau naji dan iskan yaro tana magana tana tafiya ,duk wajen daga inna har mamy ba Wanda yakalli inda suke balle yayi magana dan zuwa yanzu momy tagano halin gwoggwo akan INDO

Sultan da dama duk yanajin abunda sukeyi yayiwa dakin key yayi kwanciyarsa,haka gwoggwo taje tagama masifarta da zage zagenta tahakura tatafi,dan tasan ai yana cikin dakin yanajinta


Su dady da baba suna dawowa sultan yasamu baba akan maganar tafiya da INDO, aikuwa baba ya amince dama shima yana tinanin hakan aransa,




Da asuba indo najin tafiyarsu baba masallaci ta futo ta lallaba sai dakin baba,dan daukar mataki akan abunda sultan yamata,

Aikuwa tana shiga taga system dinshi a kunne da alama yana amfani dashinema yaje sallar aikuwa tazauna tadinga shige shige batamasan inda take shigaba saida tayi nasarar gogemasa komai na laptop dinshi kafun tatashi lafuta adakin ,



Sultan yana dawowa daga masallaci yadauki laptop dinshi da niyyar cigaba da abuda yakeyi ,kwae sai yaga laptop arufe yabude yaduba komai babu aciki ,gashi duk tsare tsarenshi na asibinda zaibude aciki suke kuma akan abunda yakeyi knn yabari yatafi sallah ,duk kololuwar bacin rai yakai kuma yatabbata INDO ce ba kowa ba tataba masa
Kwafa yayi ransa yayi matukar baci
*INDO BALA'I*
🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀


Page 1⃣1⃣&1⃣2⃣




_Na maman Al-ameen momcy_




Su mamy duk kayansu driver yakaimusu mota ,futowarsu kawai yake jira su tafi,


Gabadaya sunyi sallama ,gwoggwo harda yar kwallarta wai Aminu yaki zaman kauye,


Dady da mamy duk sunshiga mota ,INDO da shukrane tsaye ajikin mota suna sallama da Abu,

Baba yafito dakaya ahanunshi dama lokacin gwoggwo takoma cikin gida ,

Mikawa indo yayi yace toga kayanki maza kushiga manah jiranku zasu yi tayi,
.damamaki indo takalli babanta tace baba kayan meye kuma"

Yace kayanki mnh tare zaku tafi ai kije chan kiyi rashin ji kiga kosu yan birnin zasu barki"

Fashewa da kuka tayi tafada jikin Abu dukansu sai sukasa kuka,

Baba yace shukhrah shiga mnh ,shiga motar shukhrah tayi itama jikinta duk yayi sanyi,

Mamyma sake cikin mota sai tadanji tausayinsu,

Babane yamatso yabude motar yaja indo ajikin Abu yasata amota yarufe ,aikuwa indo sai takara kaimin kukanta sosai tajeyi baba kan gida yakoma dan sauri yakeyi yatafi kasuwa,

.bakaramin kuka Abu tayiba musamman dataga tashin motar su indo ai saurayi gida tacigaba da kukanta ba kakkautawa,

Ahanya indo tin mamy da dady na kokarin bata hakuri har suka hakura duka rabu da ita ,daga karshe bacci menauyi yayi awun gaba da ita,




***sai misalin karfe daya suka iso garin kano daidainan kuna indo tafarka idonta  ya sauka cikun garin kano,

Kallo taketayi duk inda akawuce saitakalla amma bata magana saboda haushin kowa takeji,


Saida suka iso gate din gidan taga anbude musu tankamenen gate din gidan ,tahangi cikin gidan mamaki yakamata sosai ganin irin girman gidan da haduwarsa,

Ai saitaji tasake ranta lokaci guda ganin harda kayan wasa ga bishiyoyi harda na mangoro ai sai tasaki murmushi ita kadanta,

Bata karasayin mamaki ba ma said a suka shiga tsantsarerren falon gidan ,ai tuni INDO tasaki baki tana karewa falon kallo yanda yahadu ga wani kamshi natashi afalon ,dama INDO akwai San kamshi da tsafta ai saitaji gidan yaburgeta sosai,

Mamy dake tsaye tana kallon yadda indo ke murmushi tana kallan gidan abun yabata mamaki sosai,mamy tace wa shukhrah datazube akujera ta dibo gajiya kuhaura sama manah keda momy(INDO) kuyi wanka ,

Shukhrah tamike indo tabi bayanta suka haura sama ,mamy ma bayansu tabi tashiga bedroom dinta,


Bedroom din shukhrah yaburge INDO sosai ,musamman cikin toilet dinta ga ruwa ga komai ka kayan kamshi ai haka indo tadage tayi wanka sosai tawanke gashinta da baya kitsiwa tsananin yaukinsa da tsayinsa kullum saida ta daureshi,



Tana futowa tashafa mayukan shukhrah masu tsada da kyau, sannan tagoge kanta,shukhrah dale cire kaya zata shiga wanka tace INDO aida kinbari munje wanke Kai saloon dabaki jika kankiba"
INDO takalleta kawai tacigaba da abunda takeyi ,powder kawai tashafa sai ruwan tirare datayi ajikinta ,tasaka wani riga da skrt na atamfa acikin kayanta,sai tayi kyau sosai,dama tayi alola kwai sai tayi sallarta,itama shukhrah tana futowa tashirya cikin Riga da skt amma na kanti,tayi sallah kafun takalli INDO databaje agado tanasonyin bacci tace sister tashi muje muci abinci mnh kobakyajin yunwane ,tashi tayi suka futo falon,daidai Shikuma yanashigowa falon ,

Ido 4sukayi da indo amma sai yakauda kansa kamar begantaba ,shukhrah CE tace  yaya sannu da dawowa,be kalletaba yace kuma sannunku dadawowa,


INDO kuwa ko kallanshi batayiba balle yasa ran zata gaidashi,wucewa yayi dakin mamy basujima suka futo tare ,


Mamy tace shukhrah yayato bakuci abincinba ,shukhrah tace mamy jiran ki mukeyi,to ai gani sai muci ko,tayi maganar tana karasowa dinning din,
Shima karasowa yayi yaja kujera yazauna sukafara cin abincin,har cikin ranasa yaji dadin ganinta a gidan dan tabbas zai gyara mata zama kam,



Suna gamacin abincin indo tace ita bacci tajeji tahaura sama,itama shukhrah haka tayi ,tunda suka kwanta basu tashiba sai kusan magrib ,



***washegari dukansu ne zaune agaban dady harda sultan,dady yakalli INDO yace mamana ni a wani class kkne a skull"

Tace dady iam going to primary 5"
Dady yace to ashema class dinku dayada shukhrah sai Ku cigaba dayi tare ,kuma mindayma hutunku zai kare saikifara. zuwa,

Dady yakalli sultan dabayace komai yace sai kuje skull din ranar Monday din kayima regtration,sultan yace to dady yabar falon,sukuma suka cigaba da hirarsu da dady dan mamy tana kicin tana shirya breakfbreakfasts,


____________Ranar Monday shukhrah tagama shirinta na makaranta ,itakuma indo kayan gida tasa rigada wando na shukhrah sunyimata kyauma sosai,
Afalo suka sameshi yanashan coffee ,shukhrah tace yaya mun shirya" indo kuwa batacemasa kalaba,saida yakarasa shanye coffee dinshi kafun yamike yadauki makullin mota sukabi bayanshi suka shiga mota,



Ko a skull INDO tabashi mamaki sosai yanda ake mata tambayoyi na interview take bada amsa,

Sosai sai taburgeshi akaro Na farko amma Sam be gwada a fuska ba, saida yagama mata komai kafun suka futo ,ahanya yabiya da ita kasuwa yasa yamata komai na makaranta kafun yadawo mota yasameta harta fara bacci,


Ido yazubamata yana ganin kyawunta ga farinta haryaso yayi yawa,dama ba dan kwali akanta sai mayafi data yafa gashinta yadan yanko ta fuskarta sai tayi kama sai da indiawa,

Aransa yace dubeta kamar mutumiyar kirki,tada motar yayi suka wuce gida ,yanayin parking tabude idonta taga har sun iso gidanefa Ashe,

Bude motar tayi zata futa yariko hanunta tareda murda mata hanun bakaramin zafi tajiba ,yace ke ina bakida kunya baki iya gaida manyaba ko ,dakike shirin futa nizandauka miki kayan, ita sai asannan ma talurada kaya agefenta,

Sakemata hanun yayi tareda yimata winning idan yasake shigowa bata gaidashi ba,

Itakuwa diban kayan tayi tafuta idonta yagama cika da kwalla dan yayi matukar bata haushi aranta tace kuma gaisuwarne bazanyiba naga abunda zaiyyi"





_ayi hakuri ba yawa amma insha Allah zanyi kokarin yin muku typing meyawa 2days iam always busyne wlhy_


*_maman Al-ameen CE_* 👌
*INDO BALA'I*
🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀


*_page_* 1⃣3⃣



_Na maman Al-ameen momcy_





Da kananun magana tashiga cikin falon ,mamy CE kadai afalon tana kallon labarai A TV,tace oh kekuma meye akamiki wayatabaki ko sallama babu sai kananun surutu dakiketayi"INDO tazauna kujera kusada mamy tace to ba wannan boss din bane wai saida muka dawo yahauyimun masifa wai bana gaisheshi kijifa mamy to wai mamy dole sai nagaisheshine?

Mamy tace aa badolebane amma ai yayankine dole kina girmamashi,kingane daga yau kina gaisheshi kinji ko,

Turo baki tayi tace to mamy shima sai yadena bakin hali

Mamy tace to wani bakin hali kuma yamiki? taturo baki tace to momy shifa kullum baya dariya saidai yadinga wani batarai fuskarsa kullum a daure,

Mamy tace to ai bayason kurainashine kingane"
Tabe baki tayi tatashi tahaura sama,

Duk yadda sukayi da mamy akan idon sultan sukayi Dan yashigo falon mamy taganshi sarai tayi shiru,

Karasowa cikin falon yy yana murmushi dan dariya ma taso bashi wai boss,
Mamy tace tofa kaji abunda kanwarkatace ,murmushi yayi yace kyaleta mamy ta kusa  tayi hankali ai dolenta,

Murmushi mamy tayi tace kadai bita ahankali,shikam futama yayi dan zaije asibitinsa,


_____saida tashiga daki tabude ledodin da tashigo dashi harda unifom da safa da sandal sai littattafan makaranta extercise book da su biro da pencil kai komai dazata bukata saida yasayamata,tadanji dadi har cikin ranta,



________washegari tin 6:00am suka tashi sukayi wanka suka shirya ,uniform din bakaramin kyau yayiwa INDO ba ,rigane da skrt iya guiwa light blue din riga da black sikat,sai Dan karamin black hijab,

Saida tadaure gashinta da ribbon kafun tasa hijab din akai,


Dakyar mamy tasata tayi break wai ita batasan su makara dan lokacin kusan seven ya wuce kuma 7:30 suke shiga class,

Shukhrah tace to mamy driver ne zaikaimu ko yaya,mamy tace kuje kutambayeshi mnh,

Kallon INDO shukhrah tayi tace kije kitambayo mnh yaya kingafa karmu mamakara gwara ke ma new comer ce,

Indo tace ke wallahi kinada matsala sai shegen tsoro tana maganar tana tafiya,

Saida taje kofar dakinsa saitaji kamar tajuya ,saikuma tafasa tayi cnoking bell din ,saida tayi sau biyu ana uku yatashi ya bude ,tashigo tana tura baki,tace yaya wai inji mamy kazo kakaimu skull karmu makara dan Allah, ko kallanta beyiba yace nine driver dinku,???

Tace aa yaya ,

Yace to kije driver yakaiku,

Haushi yabata tajuya zata futa adakin yace zonan,yaci sa'a batayi musuba tajuyo din tadawo din,

Kallonta yayi sosai kafun yamikamata hankicif yace goge janbakinnan,

Takalleshi dakyar ta karba ,ta goge samasama ,tamikamasa ,
Kallon ta yakuma yi yace matso ,

Kusa dashi tamatsa yakarbi hankicif din ya riko face dinta yafara goge mata fuskarta da bakinta dayasha jambaki,

Sosai taji haushin gogemata jambakinta dayayi tayi,ga bata musu lokaci dayayi ,

Kallonta yayi yace tashi kije,


Batasan yaya akayiba ta wulla masa harara daidai kuwa yadago da idonsa yakalleta,dasauri tanufi kofa tafuta ,kwafa yayi yatashi yadauki makullin motar sa yafuto,



Tada mota yayi yafara musu hon


Ai dasauri shukhrah tadauki Jakarta tafuto,saida ta gaidashi kafun tabude motar zata shiga yace ina *HUMAIRAH*???


Zaro ido tayi alamun batagane wa yake fadaba ,yalura da haka yace kije kikira Aisha


Komawa tayi tasameta har tacire hijab wai ita tayi fushi ,shukra takalleta tace wai inji yaya wai kozo mutafi,ko kallon shukra batayiba tace kije kicemasa ninafasa zuwa skull din yau,


Komawa shukra tayi tafadamasa abunda INDO tace,
Bude motar yayi yafuto fuskarnan ba alamar wasa yashiga falon.




*_Maman Al-ameen CE_* 👌




_____
*INDO BALA'I*
🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀


1⃣4⃣&1⃣5⃣



_Na maman Al-ameen momcy_





Yana shiga falon tana zaune akujera har tacire hijabdinta harda dankwali ,bata auneba taji anwani figota ko hijab din bata daukaba bare dankwalin ,saida yakaita har bakin motar kafun yalura da ba dankwali da hijab akanta ,wani wawan tsawa yamata ,ina hijab dinki da dankwalinki eyeeee

Bata ko kalleshiba kanta yana duke dan yayi mugun bata mata rai kuma bata amsamasaba,

Wani tsawan ya aikamata keeeee badake akeyi ba ko,


Ko kallansa nanma batayiba takoma falon tadakko hijab da dankwalin amma btasaba tdai rikesu ahanunta,tabude motar tashiga aranta tana kulla tsiyar dazata masa,


Harsuka isa skull din ba Wanda yayi magana,




_____koda akatashima shiyazo yadaukesu,har lokacin fuskar INDO ba wani annuri,yalura da haka saikuma yadanji tausayinta,aranshi yace dukda dai yarinyace amma gwara tasan abunda yakemata zafi tin yanzu,


Koda suka iso gida shukhrah CE tafara futa tayi cikin gida,INDO ma zata bude tafuta yariko hanunta ,lokaci daya yaji wani yarrrr ajikinshi,daurewa yayi besake hanunba yace *Humairah*!

Dasauri tajuyo suka hada ido tantana bala'in San sunan dama tin akauye ta kan cewa Abu tana cemata humaira,

Taji dadin sunan har cikin ranta amma saita turmutse fuska tana kallonsa, shima kallonta yakeyi,yace humaira kinajina duk abunda kikason ba aso kidainashi duk wani abunda kikasan za'a miki fada akai kidainashi plsss, banason abunda zaisa ina dukanku ko yawan yimuku fada kinjiko,

Hawayene sharrrrr a idonta ,saiyaji tausayinta kuma sosai,da hanunsa yagogemata hawayen yace iam sorry my 6ter,yasakar mata murmushi,


Atare suka futo amotar suka shiga falon ,mamy da shukhrah saida sukayi dariya, ganin dazufa sukayi fada amma yanzu sun shigo tare,sultan har yana sakar mata murmushi,


Sultan yace mamy meye yabaku dariya haka,shukhrah tace yaya ai kune kukasamu dariya,

Harara yawatsamata yace to meye abun dariya, mamy tace ai dazun munga anata hucine yanzu kuma saimukaga kun shirya har ana murmushi,

Murmushi yakumayi yace mamy ai humaira idan tanaso muzauna lapiya kimata fada tadaina abunda banaso,yakareshe maganar yana wucewa dinning dan yanajin yunwa sosai,dukansuma dinning din sukaje amma banda INDO datawuce daki,


Saida tayi wanka tasa wasu riga da wando na kanti da mamy tasayomata tayi kyau matuka ga kamshin dake tashi ajikinta medaukar hankali,


Dakamar baza tafutoba chandai tafuto fuskarta har yanzu atamke,tinda tanufo dinning din yake satar kallonta duk mamy na lura dashi,


Zama tayi batacewa kowa komaiba tafara serving din kanta ,dakyar take dibar abincin tana kaiwa baki ,sultan duk sai yaji ba dadi yasan shine silar rashin kuzarinta,amma tawani fannin dadi yaji dan atunaninsa ko tafara nutsuwa ne,



shukhrah ta kalleta da sigar tsokana tace oh indo mukuma meye namu aciki da aka hada damu,


Wani harara tawatsa mata tace ke bafa wasa nake dakeba kingane kuma kar kisake cemun INDO "


Mamy tayi murmushi tace to ai ba ita takar tsomonba,

Kallon shukhrah sultan yayi yace eh karki sake cemata INDO dagayau kingane ko,


Ita inyayi maganama haushi yake bata kwai sai ta dauki plate din abincinta tabar wajen,

Mamakine yakamashi yadda takeda zuciya haka



Shima tashi yayi yatafi part dinshi,wanka kwai yayi ya kwanta agadonsa sai yanajin wani Abu akan indo Wanda shi kanshi besan meye ba,


Itakam indo tana gamacin abincin ta futa ,cikin bishiyoyi gidan tanufa,aikuwa tadale bishiyar mangoro tadinga balla tana zubarwa akasa ,hakama na gwaiba shima saida tadinga batawa kafun tasauka,

Tadibi Wanda zata diba tabar sauran awajen,futowanta daga garden din keda wuya sukayi kicibus dashi,yafuto daga part dinshi,

Wani kallon tuhuma yabita dashi tare dacewa ke kuma ubanme zakiyi dawannan danyen abun da kikaje kika kwaso eyee

Kallon shi tayi babu alamar tsoro atareda ita tace sha zanyi,hanu yamika yace bani sunan bazakishaba,aikuwa tace bazata bada ba,

Hanunta yakama yamurdeta yakarbe mangiron yajuyesu a dustbin din dake kusa dashi,yace wuce kibani GU anan,


Kallonsa tayi tace wallahi saina rama duk abunda kakemun ,ta murgudamasa baki tayi cikin gida,

Shikam kafewa yayi agun dan yarasa meyasa duk sanda yatabata saiyaji jikinsa gabadaya yamutu,



Komawa part dinshi yayi,danjinshi yakeyi gabadaya ba kwari ajikinshi,


Aikuwa INDO dama alabe take tacikin falo sotake taga ina yanufa ,

Ai sai tafuto da ruwanta cikin cup tadaidaici daidai bakin kofarsa yanda tasan zaibi tasheka ruwan takoma dagudu,






_______shikam dama tinda yashiga bacci yayi nasarar daukarsa befarkaba saida yaji ana kiran sallar la'asar

Dasauri yatashi yashiga bathroom yayi alola yafuto dasauri zaije masallaci aikuwa be auneba santsin tiles Dana ruwa yayi nasarar zamardashi awajen har kasa yakai.....




*_maman Al-ameen CE_* 👌
*INDO BALA'I*
🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀


1⃣4⃣&1⃣5⃣



_Na maman Al-ameen momcy_





Yana shiga falon tana zaune akujera har tacire hijabdinta harda dankwali ,bata auneba taji anwani figota ko hijab din bata daukaba bare dankwalin ,saida yakaita har bakin motar kafun yalura da ba dankwali da hijab akanta ,wani wawan tsawa yamata ,ina hijab dinki da dankwalinki eyeeee

Bata ko kalleshiba kanta yana duke dan yayi mugun bata mata rai kuma bata amsamasaba,

Wani tsawan ya aikamata keeeee badake akeyi ba ko,


Ko kallansa nanma batayiba takoma falon tadakko hijab da dankwalin amma btasaba tdai rikesu ahanunta,tabude motar tashiga aranta tana kulla tsiyar dazata masa,


Harsuka isa skull din ba Wanda yayi magana,




_____koda akatashima shiyazo yadaukesu,har lokacin fuskar INDO ba wani annuri,yalura da haka saikuma yadanji tausayinta,aranshi yace dukda dai yarinyace amma gwara tasan abunda yakemata zafi tin yanzu,


Koda suka iso gida shukhrah CE tafara futa tayi cikin gida,INDO ma zata bude tafuta yariko hanunta ,lokaci daya yaji wani yarrrr ajikinshi,daurewa yayi besake hanunba yace *Humairah*!

Dasauri tajuyo suka hada ido tantana bala'in San sunan dama tin akauye ta kan cewa Abu tana cemata humaira,

Taji dadin sunan har cikin ranta amma saita turmutse fuska tana kallonsa, shima kallonta yakeyi,yace humaira kinajina duk abunda kikason ba aso kidainashi duk wani abunda kikasan za'a miki fada akai kidainashi plsss, banason abunda zaisa ina dukanku ko yawan yimuku fada kinjiko,

Hawayene sharrrrr a idonta ,saiyaji tausayinta kuma sosai,da hanunsa yagogemata hawayen yace iam sorry my 6ter,yasakar mata murmushi,


Atare suka futo amotar suka shiga falon ,mamy da shukhrah saida sukayi dariya, ganin dazufa sukayi fada amma yanzu sun shigo tare,sultan har yana sakar mata murmushi,


Sultan yace mamy meye yabaku dariya haka,shukhrah tace yaya ai kune kukasamu dariya,

Harara yawatsamata yace to meye abun dariya, mamy tace ai dazun munga anata hucine yanzu kuma saimukaga kun shirya har ana murmushi,

Murmushi yakumayi yace mamy ai humaira idan tanaso muzauna lapiya kimata fada tadaina abunda banaso,yakareshe maganar yana wucewa dinning dan yanajin yunwa sosai,dukansuma dinning din sukaje amma banda INDO datawuce daki,


Saida tayi wanka tasa wasu riga da wando na kanti da mamy tasayomata tayi kyau matuka ga kamshin dake tashi ajikinta medaukar hankali,


Dakamar baza tafutoba chandai tafuto fuskarta har yanzu atamke,tinda tanufo dinning din yake satar kallonta duk mamy na lura dashi,


Zama tayi batacewa kowa komaiba tafara serving din kanta ,dakyar take dibar abincin tana kaiwa baki ,sultan duk sai yaji ba dadi yasan shine silar rashin kuzarinta,amma tawani fannin dadi yaji dan atunaninsa ko tafara nutsuwa ne,



shukhrah ta kalleta da sigar tsokana tace oh indo mukuma meye namu aciki da aka hada damu,


Wani harara tawatsa mata tace ke bafa wasa nake dakeba kingane kuma kar kisake cemun INDO "


Mamy tayi murmushi tace to ai ba ita takar tsomonba,

Kallon shukhrah sultan yayi yace eh karki sake cemata INDO dagayau kingane ko,


Ita inyayi maganama haushi yake bata kwai sai ta dauki plate din abincinta tabar wajen,

Mamakine yakamashi yadda takeda zuciya haka



Shima tashi yayi yatafi part dinshi,wanka kwai yayi ya kwanta agadonsa sai yanajin wani Abu akan indo Wanda shi kanshi besan meye ba,


Itakam indo tana gamacin abincin ta futa ,cikin bishiyoyi gidan tanufa,aikuwa tadale bishiyar mangoro tadinga balla tana zubarwa akasa ,hakama na gwaiba shima saida tadinga batawa kafun tasauka,

Tadibi Wanda zata diba tabar sauran awajen,futowanta daga garden din keda wuya sukayi kicibus dashi,yafuto daga part dinshi,

Wani kallon tuhuma yabita dashi tare dacewa ke kuma ubanme zakiyi dawannan danyen abun da kikaje kika kwaso eyee

Kallon shi tayi babu alamar tsoro atareda ita tace sha zanyi,hanu yamika yace bani sunan bazakishaba,aikuwa tace bazata bada ba,

Hanunta yakama yamurdeta yakarbe mangiron yajuyesu a dustbin din dake kusa dashi,yace wuce kibani GU anan,


Kallonsa tayi tace wallahi saina rama duk abunda kakemun ,ta murgudamasa baki tayi cikin gida,

Shikam kafewa yayi agun dan yarasa meyasa duk sanda yatabata saiyaji jikinsa gabadaya yamutu,



Komawa part dinshi yayi,danjinshi yakeyi gabadaya ba kwari ajikinshi,


Aikuwa INDO dama alabe take tacikin falo sotake taga ina yanufa ,

Ai sai tafuto da ruwanta cikin cup tadaidaici daidai bakin kofarsa yanda tasan zaibi tasheka ruwan takoma dagudu,






_______shikam dama tinda yashiga bacci yayi nasarar daukarsa befarkaba saida yaji ana kiran sallar la'asar

Dasauri yatashi yashiga bathroom yayi alola yafuto dasauri zaije masallaci aikuwa be auneba santsin tiles Dana ruwa yayi nasarar zamardashi awajen har kasa yakai.....




*_maman Al-ameen CE_* 👌
*INDO BALA'I*
🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀



1⃣6⃣&1⃣7⃣





_Na maman Al-ameen momcy_





Bakaramin faduwa yayiba akan kafarsa,dakyar yaja kafarsa yakoma cikin dakin azaune yayi sallah, aikafin ya idar da sallah kafa ta kumbura sundum abunka da jikin hutu,





Shiru shuru mamy bataga yashigo ba ,kuma gashi har anyi magarib anyi isha ,kuma tasan ba futa yayiba,
Shukhrah ta kwalawa kira lokacin har dadyma yadawo ,shukhrah tace gani mamy ,mamy tace kije kudubomun yayanki ko yana daki idan yananan kice masa yazo muyi dinner,

Koda shukhrah taje saura kiris itama tazame daruwan da INDO tazuba,
Tayi mmkin ganin kofarsa abude danbaya taba barin kofarsa abude,


Ahankali tashiga da sallamarta ,amma be amsaba ,yana kwance ya lulluba ,idonsa alumshe kamar me bacci amma ba baccin yakeba azabace kawai datamasa yawa dan har zazzabi ta shigeshi,


Shukhrah tace yaya ahankali yabude idonsa ,tace wai mamy tace kazo muyi dinner, girgiza mata Kai kwai yayi ,

Ai da sauri shukhrah tajuya taje tafadawa mamy yadda tasameshi,ba bata lokaci mamy tanufo dakin shi,

Yananan kwance  alullube,

Har bakin gadon mamy taje tazauna tadan yaye bargon tataba wuyansa taji zafi sosai,shikam alokacin ma magana tagagareshi,


Mami ganin hakan yabata tsoro ,wayarsa ta dauka tabincika number salim abokin aikinsane a asibiti, tasanar dashi ba bata lokaci salim yazo,

Sai adaidai nan yadan iya yabude baki yace kafata zaka dubamin plsss, ba musu salim yabude bargon,kafarnan tayi jawur ta kumbura, mami tace kaikai a ina kabuge kafar haka,be boye mataba yafadamata faduwar da yayi,


Mami tahau masifa ko masu mopping ne basuyi dakyauba,ruwan zafi salim yadiba yadauki dan karamin towel ya tsoma acikin ruwan ,ya manna wa kafar ,ai besan lokacinda ya saki wata kara ta azababa,mami tatausyamasa wlhy,


Saida salim ya dindima kafar sosai kafun yashafa masa maganin bugs akafar ,yakuma yimasa allurar zazzabin jikinsa,

********


INDO shiru shiru bataji yashigo ba ,har cikin ranta taji dadi dan tasan hala hakan ta ne yacimma ruwa,


Shukhrah CE tashigo tasameta kwance agado hankalinta kwance,

Tace waike bakisan yaya baida lapiya bane bazaki je kidubashiba,dasauri tace dagaske meya sameshi?

Shukhrah tace kafarsa CE tabugu KO tafiya baya iyayi,

INDO tace ayya muje inganshi,


Koda sukashiga dakin shi yananan kwance har bacci yadaueshi,aranta tace madalla gobe kakara taba INDO,


_______saida yayi kusan kwana uku kafun yafara futowa har lokacin kafar bata gama sabewaba,dan har dingisa kafar yakeyi,


Futowarsu knn zasu tafi skull Shikuma yafuto daga part dinshi, INDO tana juyowa sukayi ido biyu kawai sai tasakar masa murmushin mugun ta tareda yimasa gwalo tashige mota,

Murmushin takaici yayi yana tuna hukuncin da zaiyi wa INDO




_______kusan wata guda kenan abubuwa sun faru dayawa ciki harda gama primary dasu indo sukayi har anyimusu join jss 1


Duk har wannan lokacin bedauki matakin komai akantaba,itakuma tasake dan atinaninta ko ya mantane,





Zaune suke su duka afalo suna hira ,INDO kuma na game awayan mami yashigo fuskarnan atamke,yakalli shukhrah yace kudibo littattafanku nagani,yafuta,


Tashi shukhrah tayi tadauki nata tabibayansa part dinshi, ba laifi tana kokari,yace kikara kokari kinji ko tace to yaya,yace kikiramun humaira,




Tanazuwa tame ta zaune tana game dinta ko motsawa batayiba balle tayi
Niyyar tashi,


Shukhrah tace wai kije inji yaya" saida tagama nata damuwar kafun tatashi,tadauki jakar makaranta tafuta,

.ko sallama batayiba tashiga, wani irin kallo yamata yace baki iya sallama bane taturo baki,

Girgiza kai yayi dantariga tashigo hanunsa sai kuwa yayi furnished dinta.. ....





*_maman Al-ameen CE_* 👌
*INDO BALA'I*
🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀



1⃣8⃣&1⃣9⃣


_Na maman Al-ameen momcy_





Batarai yayi kamar betaba dariyaba yace bude littattafanki kimun bayanin abunda ake muku a skull


Saida ta turo baki kafun ta bude math tafara masa bayani yayi matukar mamakin ganin kokarin ta,har cikin ransa yaji dadi amma beyarda yabayyanana,sai ma Dada daurewa dayayi,


Saida tagama da littafan tass takalleta da sigar rashin kunya tace to nagama"

Shi har yama mance da tana karatu badan tayi maganaba dan yashagala da kallonta yadda dan karamin bakinta yake motsi yana matukar tafiya da hankalinsa,


Kallonta yayi da rinannun idanuwansa yace oya kingama KO to saura kuma nayi furnished dinki"
Zaro ido tayi tace to menayi kuma"?

Yadan saki murmushin mugun ta yace idan maybe ya manta to uwar d'a ai bazata mantaba ko"


Kallonsa kwae takeyi dan ita ta manta netayi,saida yashiga toilet yayi wanka bayan yayiwa kofar key yacire key din,



Saida yagama shafe shafensa yasaka wasu kananun kaya sunkarbi skin dinshi sosai,

Yadauki wayarsa yacigaba da chart abunsa ko kallon inda take beyiba,ahaka har bacci yayi nasarar daukarsa,


Tun INDO najirar yacemata tatafi har talurama yayi bacci ne abunsa,ranta yayi mugun kaiwa kololuwa abaci,


Tafi awa zaune agun danshi baccinsa yakeyi hankali kwance,

Tin tana jure zaman hartakasa hakuri,ga idonta abushe ba alamar nadama acikinta,



Tinowa tayi time din dayacire key din tagan kamar agaban rigarsa yasa a pocket dinshi,dasauri tamike kamar anzabureta ta haye kan gadon dan dama shi chan dungun gadon yakwanta ,ahankali takematsawa har ta iso kusa dashi, hanunta takai aljihun rigarsa talaluma amma babu,

Saitafara kokarin duba aljihun wandonsa,bata ankaraba taji yarike hanunta,dukda haka be bude idoba,kokarin zamewa takeyi amma tagagara,bude idonsa yayi ahankali yadaura akanta wani irin kwarjini tamasa,zuba mata ido yayi kanta ko dankwali babu gashinta yasakko haryana rufe mata ido dan bata daure gashinba,sai alokacin yalura da kirjinta da dan irgen dangi datafara,wani irin shork yaji tindaga kansa har kafarsa, besan lokacin daya janyota tafado kan kirjinsaba,gashin kanta yafara shafawa lokaci daya tasaukar masa da lasala ajikinsa,


Besan yaya akayiba yakai hanunsa kirjinta yafara dagulata yama manta dawa yake tare jiyake kamar dawata babba yake tare,

Bakaramin razana INDO tayiba dan a islamiyar dasu ke zuwa anfara musu lecture akan idan mace danamiji suka hadu da kuma yadda aure yake dadai sauran su, bakaramin rudewa tayiba ,gashi yadda yake murzata har zafi takeji sosai,hawayen da takeyine yasauka afuskarsa Wanda duminsa yayi nasarar dawomasa davtinaninsa ,hankadeta yayi da jikinsa tareda Neman tsarin Allah daga sharrin shedan,itakam sauka tayi agadon kuka yaci karfinta batada burin dayawuce yabude mata kofa tatafi,


______mamy ma taji mamakin har yanzu INDO batadawoba ,sai kuma tace ko dai yana mata lesson ne dan tayarda da Santa 100% shi yasa ko zargin wani Abu batayiba,



Saida yagama sauke numfashi kafun yashiga toilet yafuto, yatsaya daf da ita yace kinaso kitafi ,dasauri tadaga masa kai yace to tashi kishiga toilet kiwanke idonki kuma kitsayar da kukannan dan inkika futo da kukannan to bazaki tafi ba, ba musu taje tawanke idonta yabata hankicif dinsa tago fuskarta tsab kamar batayi kukaba kafun yabude mata kofa takwashi littattafanta ,

______yakamata muleka gwoggwo muji wani hali tashiga da akatafi da INDO.....






*_maman Al-ameen CE_* 👌
*INDO BALA'I*
🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀

2⃣0⃣&2⃣1⃣



_Na maman Al-ameen momcy_



*_Hakika naji dadin adduo'inku agareni fans ,ba abunda zance agareku sai godiya ,nagode sosai kuma cikin ikon Allah nasamu lapiya nagode Allah yabar zumunci,ana mugun tare ai🤝_*





Tinda gwoggwo taga ta wuni bataji d'uriyar INDO ba tahau damun inna wai ina INDO ne,inna tace mata taje aika,taga har wuni guda kusan magrib ba labarin indo ai tuni tarude ma inna adaidai nan kuwa baba yashigo baboye boye yafadamata INDO tatafi birni, bakaramin rudemusu tayiba dakyar baba yatausata yacemata ai baza ta dadeba zata dawo,ahaka ta hakura,

_____tinda indo tafuta sultan yarasa abunyi yanajin motsin wani Abu aransa amma besan meye bane,kwanciya yayi rub da ciki yakura wa silin ido yana tinani Wanda nikaina maman Al-ameen bansan tinaninda yakeyi ba daga karshedai naga ya lumshe idonsa,


****indo kuwa tana komawa daki tawuce dan bakowa afalo ko kallon shukhrah dake kwance agado batayiba ta watsa littattafanta kan gadon tashige bathroom, wanka tayi tafuto saida tagama shafe shafe tasaka wasu riga da skrt na kanti,

Tafada kan gadon ta lumshe idanuwanta ahankali abunda yafaru dazu itada sultan yadawo mata ba karamin haushin hakan tayiba,tsaki tahauyi mtswww mtswww shukhrah dake gefenta tanason yin bacci tsakin indo yahanata,

Tace haba INDO meye kuma haka kinzo kinata wani yima mutane tsaki, meyasa shi yayan bakimasaba ai naga bani natabakiba dazaki zo kina Neman hanani bacci anan"


Mtswww tsaki INDO takumayi tace toke atinaninki bazan iya yimasa tsakinbane ko tsoron sa nakeji akacemiki"

Shukhrah tace oho wayasani"shiru INDO tamata danbatason magana tana tinanin matakin dazata dauka akan sultan,



____,,___washe gari su INDO duk sun shirya tafiya makaranta kowa yana dinning banda sultan ,INDO ce dakofi ahanunta tanadan kurban tea din ahankali kamar bazatashaba ,mamyce tafara tashi tayi dakinta, shukhrah ma tamike yace amma kinsan yau munada test amma ko tea din baki gama shaba kinata wani yanga wa mutane nidai bari na dakko jakata kigani inbakigamaba tafiyata zanyi,

Shukhrah tana tashi indo tatashi tashiga kicin tadibo gishiri ahanunta ,tadawo dinning, karamin flask dake kan dinning din tajawo Wanda tasan na coffee din sultan ne budewa tayi tajuye gishirin aciki ta dakko suger ma meyawa tazuba tamayar tarufe tacigaba da kurbar tea dinta,
Sultan ne yashigo fuskarnan amurtuke kanshi tsaye dinning ya nufo yaja kujera yazauna ko kallanta beyiba haka itama tajuya kai tacigaba da damuwarta,

Cup yadauka yajawo plask yatsiyanyi coffee, cikin  ji dakai yakai cup din baki, aiyana kurba yawatsar tareda kwarewa yahau tari,dai dainan mamy tafuto, indo kam ko kallo be ishetaba,mamy takaraso dinning din tana fadin subhanallah meya faru kuma"tari yakeyi kamar zaiyi aman hanjinsa,public toilet dake wajen yashiga dakyar yadinga kwarara amai,
Mamy kuma sai tahau tambayar indo meyafarune,?INDO tace batasaniba tashima tayi tawuce daki tadakko jakarta suka wuce skull ranta fall da farin ciki,

Shukam saida yayi amai har ya galabaita kafun yafuto, akujerar falon yakwanta saida yayi kusan awa kafun yadawo daidai ,mamy dake zaune agefensa tarusa tagumi tana tinanin neyasameshi,tayi saurin matsawa kusa dashi tace wai meyasamekane sultan???

Dakyar yafadamata abunda yaji acikin coffee din, yace mamy kinsan sugar ma basonakeba kuma akahada harda salt,

Mamy tace to tayaya ma suger da gushiri suka shiga coffee dinka,masu aikin gidannan sun tafi hutu,ni dakaina yau nahada breakfast a gidannan to yaya akayi har haka tafaru kuma,
Shikam sultan yagano INDO CE tazuba amma afili be gwadawa mamy ba,


***daidai lokacin tashinsu INDO a skull nayi yatsinci kansa dasan zuwa dakkosu ,key dinsa yadauka yatafi, adaidai kofar makaranta yagansu atsaye suna jiran driver,shukhrah ce tafara ganinsa tace la humaira yayane yazo daukarmu,itama ta koyi cemata humaira kodan saboda yan skull dinsu karsu rainasu suji tanace musu INDO,

Jutawa indo tayi dasauri tacikin Glass din motarsa sukayi ido biyu,kau da kanta tayi,shukhrah ce tafara tafiya tabude gaba zata shiga yayi saurin cemata shiga baya,ba musu tabude baya tashiga ,INDO kam saida tagama yanganta kafun tazo tabude baya zata shiga,yayi saurin tada mata tsawa ke ni driver dinkune dazaki shiga baya come on shiga gaba ,batayi musuba tabude gaba tashiga tareda buga murfin motar, bekulataba,


Saida suka iso gida shukhrah tafuta itakuma tana kokarin bude kofar tajita arufe ,beko kalletaba saima wayarsa dayaketa dannawa,shukhrah kam ko tsayawa batayiba tayi gaba abunta,


Wani tsaki taja mtswww, sai asannan yajuyo yakalleta fuska adaure yace ke ubanwa kikewa tsuka........






*_maman Al-ameen CE_* 👌
*INDO BALA'I*
🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀


2⃣2⃣&2⃣3⃣

_Na maman Al-ameen momcy_





*_hakika inajin dadin comment da akeyi akan wannan littafi (INDO BALA'I) kuma da Allah fans acigaba da comment insha Allah muma zamu kara kokarin mu akan nada saboda comment dinku shiyake karawa manah karfin gwuiwa._*


 


Zubamasa manya manyan idanuwanta tayi tana kallonsa batama da niyyar bashi amsar tambayarsa,kallon da take masa tayi mugun sakar masa da kasala,besan lokacin dayamatso daf da itaba har numfashin su na haduwa dana juna,cikin sanyayyar muryarshi yace Aisha"!

Yadda yakirata dasunanta na asali kirjinta yayi matukar bugawa

Takara kuramasa ido yace meyasa bakyajin magana Humaira"? Meyasa kullum kikeda burin batamun raine eyeh"?

Yakama fa kigane fa yanzu girma kikeyi kuma anfanin girma hankali kobahakabane"

Hanunta yarike yace dan Allah idan kinason muzauna lapiya plsss kidingajin maganata Dana kowama kinji ko?

Yalumshe rinannun idanuwansa ya bude ahankali yace humaira meyasa kika samun salt and sugar a coffee plsss ?so kikeyi namutune,

Sai alokacin ta girgiza masa ,yace to idan har bakyason inmutu plsss kidaina karki sake kinji "


Tayi shiru ,yace baki amsamunba kinji?

Ahankali tace naji ,amma nima kadena yimun mugunta tayi maganar kamar bazatayiba,yadda bakinta yayi motsi yayi bala'in tafiya dashi saida yarufe idonsa yabude ,ga wani Abu dayake masa motsi aransa amma besan meye ba,


Yatsansa yadaura akan lips dinta yace idan har kema kindaina namiki alkawarin zamu zauna lpy dake insha Allah,



Shuru tayi ta wani turo baki kamar zatayi kuka ,chankuma tace toni kabudemun intafi yunwa nakeji,"
Shi dariyama tabashi amma saiyadanyi murmushi yace to saikinyi smile kafun kitafi,

Murmushi tayi tace to nayi ,shima murmushi yakumayi yace to kinmun alkawarin zamuci abincin tare kinga yau munshirya ko?

Tsabar ta gaggauta ta tafi tace masa eh,yayi dariya ya mata signa ,yabude motar dasauri tafuta ,

Shima futar yayi yabi bayanta ,

Afalo tasami mami da shukhrah har tacire uniform dinta,

Mami tace yammatana kekuma a ina kika tsaya ?turo baki tayi tace yayane yacemun in tsaya mnh kumafa gashi yunwa nakeji amma yaki yabarni natafi,

Mami tayi murmushi tace to jeki cire unifom kizo kici abincin, aranta kuwa mami tafara gano wani al-amari tsananin sultan da INDO,


Saida tacire uniform dinta tafuto tanufi dinning, daidai sultan yashigo ko lurada da mami beyiba yabita dawani shu'umin kallo yace idan kinyi serving dinmu kikawo mnh falo muji kinji,


Yawuce falo sai alokacin yaga mami datakura masa ido tanason gano wani Abu atare dashi,

Yace mami dama kinanan, tace eh ina nan ,kusada ita yaje yazauna ,


INDO kuwa saida tagama ra'ayinta kafun ta zuba abincin a flate tadawo falon,a tsakiyar rugg din falon tazauna batacemasa komai ba,tafaracin abincin ta,

Dayagafa haikan bazatayi masa maganaba,
Yataso yazauna kusa da ita yace to kuma bazakice nazo muciba,batako kalleshiba yadauki cokali shima yahau cin abincin,,


Sosai mami taji dafin hakan dan dama dad dinsa yadade da yimasa magana akan yafuto da matar aure amma har yagaji da magana bekawoba hasalima shi ko budurwa bashida ita,tin alokacin mami tayanke shawarar fadawa dad dinsa abunda tagani.........




*_maman Al-ameen CE_*👌
*INDO BALA'I*
🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀

2⃣4⃣&2⃣5⃣


_Na maman Al-ameen momcy_





```Gaskiya naji dadi sosai gameda yadda kukanunamin kulawarku agareni,akwai wadanda sukabini ta PC da adduo'insu akwai kuma wadanda suka kirani awaya nagode nagode Allah yabar zumunci ameeeeeen```😍







________koda dady yadawo mami ta koramasa bayani ,bakaramin dadi dady yajiba atinaninsa hakan ai zaikara wa muzuncinsu kaimi shida dan uwansa,

Tin alokacin yakira dan uwansa yasanardashi amma sun zaunar sai sungama S.S.C.E sai ayi bikin,shima Aminu wato baban INDO yaji dadi sosai ,



Sultan kam adaren ranar kusan kwana yayi beyi bacciba dan dayatuno da indo besan daliliba sai ya tsinci kansa cikin farin ciki, yana rintsa idonsa sai yadinga ganin dan karamin bakinta yana mitso bakaramin burgeshi yakeyi ba,





____yadda ya kwana itama INDO haka ta tsinci kanta da ganin kyakykyawar fuskarnan tasa yana sakar mata wannan killer smile dinshinnan,ita kadai sai tayi murmushi,

Da kyar itakam bacci yayi nasarar daukarta sabanin sultan shikam sai da akakira sallah asuba yatashi yaje yayi sallah yadawo kafun wani bacci me dadi yadaukeshi,




_____yau takasance weekend kuma sunyi Hutu a islamiya,zaune suke duka a waiting falo ,shukhrah na daurewa indo gashinta bayan itama INDO tadaure mata nata ,jiran yayansu kawai suke yashigo su tambayeshi zasuje wanke kai ,


Daidai nan yashigo falon yauma kamar kullum fuskarsa amurtuke ba annuri ,idanuwansa suka sauka akan gashin INDO ,saida yadan rintsa idonsa yabude shi besan dalili ba komai nata yana burgeshi amma banda masiifarta,


Zama yayi akujera chan nesa da nasu,shukhrah ce tace yaya ina kwana,lafiya kwai yace atakaice ,indo ta tabe baki aranta tace madalla ai bakece sarkin gaisuwaba oho miki nidai bazan gaidashi ba ma balle ya dizgani,


Wayarsa yake dannawa amma jifa jifa yakan saci kallonta harsuka gama ,Sai da sukaje daki shukhrah tace to ke bakitambaya mnh ba kumafa ahizaibamu kudin wanke kanfa ,INDO tace to ke meyasa baki tambayeshiba?

Shukhrah tace to ke bakiga yanda yaya yashigo bane fuskarsa adaure ni gskya ina tsoron yimasa magana,

Mtswww INDO taja wani tsaki tace ke wlhy kinji jiki da shegen tsoron wlhy ,tayi maganar tareda ficewa adakin,sultan dake zaune afalon dama Sam be so tafiyarta afalonba tinda tafuto yake satar kallonta kasa kasa wai kartagane tarainashi,


Kan kujerar dayake tazauna agefenshi dan har jikinsu na haduwa tace bosss plss kabamu kudi zamuje wanke kaine  kaji"

Lumshe idonsa yy ahankali ya budesu yace naji tashi kuje Ku shirya kuzo nakaiku ,tsalle tayi tafada jikinsa ta manna masa kisss awuya  tace yawwa my bosss thank u ta ruga da gudu tayi sama ,jingina jikinsa yayi idonsa alumshi dan mutuwar zaune yayi,abunda vesaniba mami duk tana ganinsu dan futowarta daga dakinta kenan taga INDO tazo wajen shi,karasowa falon mami tayi jin motsinta yadawo dashi hankalinsa, ahankali yabude rinannun idanuwansa yadaurasu akan mami,mami tadanyi murmushi tace wai yaushe zaka bude asibitn kane?

Da kyar yabude baki yace mami sai dady yadawo zansameshi mutsara yadda zamuyi celebrated din ko?mami tace eh hakanma yayi,


Tashi yayi zaifuta mami tace au kaga na manta kanwarkafa tana zuwa yau " yace wata kanwata kuma mami? Tace *ANISA* mnh yau zatadawo kasarnan kuma tace agidannan zata sauka plss idan ta iso zakaje kadaukota a airport, to kawai yace yayi ficewarsa,

Be jimaba yashirya cikin kananun kaya farin t-shirt da bakin wando sunyimasa kyau sosai sai kamshi yake zubawa,



Afalo yasamesu sun shirya ,INDO tasha ado kayan sun karbeta sosai atamface doguwar riga yayi matukar zama ajikinta,sai kanshi take zubawa,


Kallonsu yayi yace muje ,ammafa har lokacin fuskarnan adaure ,


Awani makeken wajen gyara yatsaya shukhrah tafuta itakuma indo takalleshi tace to boss ai bakabamu kudin ba ko?

Kallanta yayi yaciro kudi meyawa yasaka mata ahanu yace idan kuka gama kujirani zanzo namaidaku gida sannan saura kuma ayi rashin ji"


Ko godiya batayiba ta bude motar ta futa suka shiga cikin wajen itada shukhrah, binbayarta yayi da kallo hatta tafiyarta burgeshi takeyi,murmushi yayi yaja motarsa yayi gaba,



______Anisa kuwa jirginsu yasauka a Nigeria takira mami tasanarda ita mamy ma takirashi tasanar dashi yaje yadakkota daidai kuma lokacin da zaije ya dakko su INDO a saloon kenan, yadai amsa wa mamy da to amma shi har cikin ransa ya tsani yarinyar saboda rashin kunya da rashin tarbiyyarta,


A kofar wajen yasamesu ,saida suka shiga yafara tafiya INDO taga yanabin hanyar da ba na gidaba ai sai takasa shiru dan yunwa takeji gida kwai takeson zuwa,tace boss ina kuma zamuje,be kalletaba yace saidake zanyi,

Daidai nan suka iso airport ,chan yahango Anisa atsaye da trolley dinta ,kusa da ita yatsaya yayi perking yafuto,tana wani yatsina fuska tace welcome" be amsa ba yace muje ko,


Shiga motar tayi ,INDO tajuyo takalleta suna hada ido tawatsawa INDO harara aikuwa itama INDO batayi wata wataba ta gallamata harara,tareda Jan tsaki mtswww, lokaci daya kuma takejin wani kololuwa da haushin Anisa aranta....




*_maman Al-ameen CE_*👌




Download Indo Bala'i Littafi Na Daya Page 2