[2/3, 4:40 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




🅾1⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```


_The price of success is hard work, dedication to the job at hand, and the determination that whether we win or lose, we have applied the best of ourselves to the task at hand._



*Shafin Masoya*


_ASEEYA ABUBAKAR IMAM_
_HAUWA AUWAL TSOHO_
_SAUDAT ABDULLAHI SAJ_
_HAFSAT IBRAHIM QUEEN HAFCY_
_NABEELA DIKKO_
_'YAR FATHER_
_AMEENA SANI MANI_
_FATIMA UMAR ABDULLAHI (MUMMY YUSUF)_
_FATIMA LAWAL UMAR ROGO_





```SHIMFIDA/TSOKACI```



Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin halittu, wanda bai Haifa ba kuma ba a haife shi ba, wanda yake da mulki cikakke kuma tabbatacce. Tsira tareda amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) dangaban goshin Allah, wanda duk wanda ya kaucewa tafarkinsa ya bata. Tareda iyalan gidansa da sahabbansa hadi da duk wanda ya bi tafarkinsu ya zuwa ranar tsayuwa.



Godiya fiye da a kirga zuwa ga mahaifiyata, wacce ba zan taba buda littafi ba face na sankamamata godiya kan dawainiya da wahala da take yi a kaina, tabbas ba domin mahaifiyata ba, da maikaratu ba za ka san waye _ZAINUDDEEN ZAIN_ ba, ina rokon ubangiji da ya yafe mata kurakuranta, ya kuma sa aljanna ce makomarta. Ubangiji ka kareta daga sharrin duk wani mai sharri. Amin.



Masoyana, kuma naku daban ne, banida baki da zan iya furta godiya zuwa gare ku kan gwarin guiwa da nake samu daga wurinku, ina mika godiya kan addu’o’I da fatan alkhairi da kuke yi zuwa gare ni. Inaso kuma kusan cewa, ina yin ku sosai da sosai. Irin ana tarennan, kun dai gane.



Wannan labarin kirkirarre ne, duk da cewa jigon labarin ya faru da gaske, duk abubuwan da za su fito a labarin kirkira na yi. Labari ne na wata baiwar Allah da ta shiga gararin rayuwa, tun kuruciyarta har ta kai shekaru  31, an aurar da ita ne ga wani mutum da ke zaune a garin Maiduguri mai suna QASIMU, ita matar mai suna SAJIDA, haifaffiyar garin Kalgo ce da ke jihar Kebbi. Tun tana da shekaru 16 aka aurar da ita, duk da a lokacin tanada wanda take so sosai, a haka aka tankwarata, ita kuwa ta yi biyayya ga mahaifanta duk da rayuwarta ba ta so ba. Bayan aurensu da malam QASIMU, wulaknci kala-kala, sai ya dinga biyowa baya, duk abinda ta yi, ba ta burge shi, har dukan ta yake yi, a haka har suka haifi ‘ya’ya guda biyu: BILKISU ita ce babba inda take da shekaru 14 sai ‘yar karamar mai suna AMISHA inda take da shekaru 4, kafin AMISHA SAJIDA ta haifi da namiji, wanda rashin kulawa da take samu daga mijinta ya zama ajalinsa, wanda shi ne dalili da ya sa, a lokacin da ta haifi AMISHA, dole ta jajirce wurin ganin ta kula da ita yadda ya dace.



Dalilin Qasimu na wulakanta matarsa kuwa, shi ne, saboda shi ma da wacce yake so, amma a gida aka tilasta sa kan lallai sai ya aureta,  shi ne yake wulakanta ta da zimmar ko zai rage radadi da raunin da aka yi wa zuciyarsa.


SAJIDA kuwa, ba ta sarye ba wurin kokarta janyo hankalin maigidanta zuwa gareta ba duk da ba ta son sa, amma ina, abin sai gaba yake yi, duk da sun ajiye ‘ya’ya kuma ga shi sun fara manyanta.




Kwatsam suna a haka, ‘yan Boko Haram za su kawo hari a garin nasu, wanda zai yi sanadiyyar bazamarsu cikin jeji da basusan ina za su nufa ba, za su hadu da masifu da dama a cikin jejin, haka za su koyi darussa su kuma hadu da mutane da dama.



Ya wannan abin zai faru, ina kuma za su tafi? Duka amsoshinku suna cikin wannan littafin mai suna; *’YAN GUDUN HIJIRA* _labarin Sajida_




***FARKO***




Lokacin damina ne, ga shi da misalin karfe biyar na maaraice, kuma da alama akwai alamun hadari duba da yadda giragizai ke shawagi a sararin samaniya, da kuma yadda suka lullube rana har ma za ka yi zaton dare ne ya shigo, iska mai sanyi wanda ke kadawa a hankali kadai ya isa ya saka mutum nutsuwa. Abin ka da gari mai yawan jama’a sosai, garin MAIDUGURI. Duka wannan yanayi mai dadi tareda kwantar da zuciya bai hana hawaye zuba ba daga idanun SAJIDA, zaune take cikin gida da ke dauke da daki kwaya daya wanda suke zama ita da mijinta QASIMU da ‘ya’yansu guda biyu BILKISU da AMISHA. Sai zabgar hawaye take har da shessheka a kukan nata, sai kokarin sharbar majina take daga hancinta, amma ina abin ya fi karfinta, tana tsakiyar ratsa kuka, ta jiyo kukan Amisha daga dan karamin dakinsu wanda ko kyaure ba ya da, ga labulen dakin ya yi datti kamar wanda aka dauko daga juji, jin kukan diyarta mai shekaru hudu a duniya, ya kara jefa ta cikin wani sabon kuka wanda har sauti ya fara bayyana, ta tsinci kanta cikin halin rashin iya motsawa balle ta je ta rarrashi diyar tata, wacce rabonta da ta saka abinci a cikinta tun garin kwaki da ta sha da safe. Cikin shesshekar kuka ta tada kanta sama, a ranta tana cewa, ya ubangiji kana ganin halin da muke ciki ni da ‘ya’yana, ka kawo mana dauki…tun bata kammala addu’ar ba sai ta ji shigowar BILKISU daga sallamar da ta yi kafin ta shigo. Fuskarta cike da hawaye ta tada kai ta kalli ‘yarta BILKISU da take kira da MAMANNE kasancewar sunan mahaifiyarta take da, “me ke faruwa naga kin dawo cikin damuwa, MAMANNE?” ta fada muryarta na rawa cike da alamun kuka ga kuma tausayi cikin muryar. “Sani mai shago ne ya ce ba zai sake bamu bashin garin kwakin ba, wai saboda ba ma biya, ya ce yana biyar mu bashin sama da shekara, kuma wai bai ga alamun za mu iya biyanshi ba, shi ba zai yarda mu kashe mashi shago a banza ba” ta fada sai ta karasa cikin kuka. Cike da tausayi ta janyo ta a jikinta ta rungume sai rusar kuka suke. Ita tunaninta daya ne, yanzu yarannan nata a haka za su kwana cikin yunwa da wahala.




Suna a haka, sai suka jiwo ana, sallama, jin bakuwar murya, sai suka yi sauri suka share hawayen da suka cika fuskokinsu, suka amsa sallama tareda yi wa mai sallamar iso, sai ga wata mata ta shigo, daga ganinta kasan irin matannan ne masu wadata, duk da ba za ka kira ta mai kudi kai tsaye ba, malama AISHA sunanta kamar yadda ta sanar da su bayan da ta gabatar da kanta.




“dama ina tsaye ne lokacin da ‘yarki ta zo neman bashi wurin mai shago, shi ne na biyota bayan naji abubuwa da ya fada a kanku, nasan tabbas kuna bukatar taimako, ga wannan” ta mika musu, awara tareda dankali da aka soya, sun sha yaji da albasa ga kabeji a ciki, ta kuma ce da su; “ku kwantar da hankalinku, duk abinda ubangiji ya yi, mai kyau ne, wata rana duk wannan talaucin zai gushe. Idan kin aminta, zan dauki diyarki aiki a gidana, sai ta dinga kawo maku abinci daga wurina, kuma na dinga biyant duk karshen wata”



Sai da ta yi ajiyar zuciya na tsawon lokaci, kana ta aminta, ba tareda ta ko yi tunanin shaidawa mijinta ba, domin tasan ba zai taba goyon bayan haka ba. Duk da ba zai taba taimaka musu ba ta ko wacce hanya.




“kinada aure ne?” inji malama Aisha ta fada a dai dai lokacin da ta kai idanunta tana kallon farfajiyar gidan da ya sha shara sosai, ga tsafta, amma gidan ba tsari ba kuma kulawa daga maigidan. “eh inada miji” “Allah ya sawwaka”



Nan ta shida mata cewa za ta zo da safe domin ta kai su su ga gidan, daga baya sai su saka ranar fara aiki, ta kawo kudi ta basu, ta ce ga wannan ku sayi kayan abinci, domin ai mutum ba ya zama da yunwa.




Ta yi mata rakiya har kofar gida, ta dawo ta kira AMISHA suka zauna suka saka awarar da dankalin cikin kwano, wanda har ya fara lamba, suka zauna su uku suna ci, su dukansu fuskokinsu cike da tausayi sai da aka fara kiran magariba, suka samu suka karasa ci, bayn sun wanke hannuwansu, AMISHA ta fara zabga musu surutu. Murmushi kawai SAJIDA ta yi ta ce “lallai AMISHA ba ki da kunya, wato dazu yunwa ce ta sa sai rusamin kuka kike yi, yanzu kuma za ki zo ki dameni da wannan surutu naki?” suka share da dariya, nan ta umarce su da su dauki butoci domin su yi salla lura da lokaci ya rigaya ya yi.




SAJIDA mace ce baka ga ta doguwa mai kakkauran jiki, tanada alamaun kirar karfi, ga ta da zuciya mai kamar maza, tanada kirki sosai ga addini kuma ga tausayi, nan da nan hawaye sun fito daga idanuwanta, ba kyakkyawa ba ce, haka ba zaka kira ta da mummuna ba, haifaffiyar garin KALGO ce da ke jihar KEBBI, aure ne ya kawota garin MAIDUGURI hannun QASIMU.



Da suka idar da sallah, ta kira Bilkisu ta aiketa da kudin da malama AISHA ta basu, domin ta siyo musu kayan abinci. Fitar BILKISU da kamar minti biyar sai ga hadari dauke da iska ya taso, kan titi sai guduwa mutane ke yi, wadanda ke cikin gida kuwa sai ta kansu suke yi, domin irin iskannan ne mai masifar karfi wanda har itace yake kayar wa.




Wanne hali BILKISU take ciki?
SAJIDA fa wanne yanyi za ta shiga?
Ina QASIMU da har yanzu bai dawo gida ba tun fitar sa da safe?



Duk amsoshin suna cikin shafi na gaba, labarin har yanzu bai fara ba.




DR. ZAIN
[2/3, 4:40 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾


🅾2⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```




_A common mistake that people make when trying to design something completely foolproof is to underestimate the ingenuity of complete fools_




*Shafin Masoya*



_M. D. R. Arrigasiy_
_Fiddausi Sodangi_
_Ayush Iliyasu_
_Amra Auwal_
_Sayyada Maryam_
_Madara_
_Zeety_





***CI GABA***



Iska ake ta famar zabgawa mai dauke da masifar karfi tareda wani sanyi wanda ke saka mutum kakkarwa ba tareda ya nufa ba, haka kake jin iskan dauke da sauti mai firgitarwa, sai daukar bugun kwano yake daga kan dakuna yana yawo da su a sararin samniya da farfajiyar garin MAIDUGURi, itace kuwa haka suke faduwa kamar ma’askin dare ya hau kan mace mai gashi. Mutane kuwa sai kokarin ceton rayukansu suke yi ta hanyar neman hanyar wucewa gida, cikin gudu, garin gaba daya sai ya yi duhu, ko tafin hannunka ba ka iya gani, wutar PHCN kuwa tun kafin iskan ya kawo aka dade da daukewa, kasancewar masu hasashe sun tabbatar da yiwuwar iskan zai yi barna.



Hankalinta a tashe, ta rungume AMISHA sai zabgar kuka take yi, a ranta tana cewa wannan masifa har ina, yunwa da talauci ga shi sun janyo na yi asarar diyata, wayyo ni SAJIDA na shiga uku…kalaman ta take ta maimaitawa ke nan a zuciyarta, cen ta jiwo rufin dakinsu ya fara babbakewa, iska ya fara daukarsa, cen sai ji ta yi fuuu! Iska dauke da kasa na shigowa cikin dakin nasu ta sama, kasancewar rufin dakin iska ya dauke shi, ganin haka, ta kalli AMISHA da ke rungume a kirjinta, ta tada kanta ta kalli saman dakinsu, kawai ta sunkuyar da kai wani sabon kuka ya soma daga dan karamin bakinta, kasancewar wannan lokacin kukan ya kwaceta har sautinsa ya bayyana. Ba ta san lokacin da ta buda baki ba ta ce; “QASIMU! Wai kana ina ne, ya za ka tafi ka bar mu cikin wannan masifar? Oh! Ni ‘yasu, yanzu wanne hali BILKISU take ciki?” ta fada a daidai lokaci da take kokarin nemo malullubi da za ta rufe jikin AMISHA da shi, ganin yadda take kakkarwa ba ko tsayawa.




BILKISU kuwa, kasancewar inda aka aiketa ba nisa da gida, har ta rigaya ta siyo juyowa da za ta yi ne iskan ya taso, inda idanuwanta suka cika da kasa, ta rafka kuwwa, mutane da ke guduwa domin neman mafaka suka bangajeta ta fadi, ga ta a kasa ‘yan abubuwan da ta siyo sun watse sai lalube take kasncewar idanuwanta suna a cike da kasa,  ga kuma matsanancin duhu da iska mai karfi bugu da kari ga sanyi, mafi muni kalar tufafin da ke jikinta, kan talauci wani hijabi ne da yanzu shekarunsa sha tara, na mahaifiyarta ne take sakawa, shi kadai suka mallaka, idan mahaifiyarta ta dawo daga lalurarta sai ita ma ta dauka ta fita, idan kuma fita ta kama su a tare, a haka take fita dole ba hijabi a jiki, har ‘yan unguwarsu na mata sharri, _mai hijabin da ya girmemata_ a jikinta kuwa zani ne, wanda ta yi daura gaba da shi, wannan ya bai wa sanyi damar ratsa jikinta yadda ya dace, musamman ma da hijabin ba kauri, saboda ya sha ruwa kuma ga huji wurare da dama a jikinsa.



Da laluben ta samu ta tattara wasu daga cikin kaya da aka aiketa ta siyo, ganin ta tattara sai ta nemi wata rumfa ta shiga ta tsaya, a lokacin tana gani idanuwanta sun fara budewa daga kasa da ta cika su. Iskan ya kwashi awanni hudu ana yin sa daga bisani aka sauko da ruwa masu matsanancin karfi, ganin iskan ya tsaya, kuma ga ruwa ana laftawa da har sun dauki awa daya da kusan rabi ana laftawa ba ko alamar tsaiko ko sassauci, Bilkisu ta ratsa ta cikin ruwan a guje ta nufi gida. Isar ta gida gaba daya jikinta a jike har kana ganin kwancin mamanta a kirjinta duk da daura gaba ne a kirjin nata kuma ga shi ko bra babu, cikin kakkarwar sanyi, ta yi tsaye, a lokaci daya ta sake kayan da mahaifiyarta ta aiketa ta siyo, ganin yadda mahaifiyarta da kanwarta ke shan kashin ruwa zaune cikin daki, kasancewar rufin dakin da iska ta dauke. “innalillaahi wa inna ilaihi raaji’un” ta fada a dai dai lokacin da take saka kuka tareda shekowa ta rungume mahaifiyarsu, wacce ita kuma ta rungume AMISHA da sunan hana ruwa su doketa



“inna, ku taso mu tafi” ta fada tana kokaarin jan hannun mahaifiyarta




“rufa muna asiri, so kike mahaifinki ya dawo bai tarar da mu ba mu jawo wa kanmu masifa? Kiyi hakuri, komai dan lokaci ne, wata rana wannan sai dai ki ba yaranki ko jikokinki labari”



“rayukanmu ne fa cikin hadari Inna, muna fa da damar hana faruwan haka, amma muna gani za mu jefa rayukanmu cikin hadari? Kalla fa kiga AMISHA karama ce sosai, so kike wani ciwo ya shige ta da har sai ta rsa ranta, nasan abinda kike nufi, kila ki ce wai za ki fita ba tareda izinin Baba ba, mutumin da bai kiyaye dokokin ubangiji da ke kansa ba, me ye laifi idan an saba masa? Kuma wannan abu ne da ya danganci rayuwa, addini ma ya aminta da ki fita kan hakan.”



“yimin shu, ki bari mu duka mu mutu, a nan din, ya fi mu fita mu mutu a wani wuri da ba dakin mijina ba”



Bilkisu ta koma gefe, sai kallon karamar kanwarta take yi cike da tausayi, hawaye kuwa dama sun saba da shawagi a lallausan kumaatunta.



Ta mayar da hankalinta ya zuwa mahaifiyarta, sai kallonta take irin kallon da ita kan ta ba ta san wanne iri ba ne, na tausayi ne, na haushi ne ko na kauna ne, oho, ita dai kawai ta kura mata idanu.



Haka ruwan suka ci gaba da sauka, har zuwa ukun dare, dama ba wasu tufafi suke da ba, ganin lakar da ya zagaye dakin nasu, haka ta rage tsayi kasancewar ruwa sun dketa duk ta side, ta rasa ina za ta ajiye ‘yarta wacce sai kakkarwa take kuma tuni jikinta ya fara zafi, ganin haka hankalinta ya tashi sosai, a kidime take yin komai, domin ta san idan ma rashin lafiya ne yarinyar take fama da shi, tau cikinta ta yi, domin Babanta ko sisinsa ba zai saka ba wurin nemamata lafiya.



Ganin mahaifiyarta a kidime, kuma lura da yadda hankalinta ya fi komawa kan ‘yarta karama, sai Bilkisu ta dakata daga tarkata kwanuka da take yi, ta matsa kusa da mahaifiyarta ta taba jikin AMISHA, ai kuwa sai da ta ja daga baya, ta ce; “umma! Kin ga abinda nake gaya maki ko, yanzu ina amfnin badi ba rai? Ga shi kin jawo wa Auta ciwo, kila ma pneumonia ce, tashi mu je asibiti”



“ke BILKISU, asibiti cikin darennan? Hala su ma’aikatan asibiti injimumuka ne da za’a tarar da su a wannaan lokacin, hudun dare fa ta kusa”



“ranar a Islamiyya, malaminmu ya gayamuna cewa, ma’aikatan asibiti sukan yi musanyar lokutan aiki, wasu kan yi da safe wasu da rana wasu kuma cen suke kwana suna aiki, kinsan sha’anin lafiya, ko da yaushe takan kama mutum ya nemi zuwa ganin likita, tunda ciwo ai ba sanarwa yake yi ba Inna, ki daure mu tafi, rayuwarta za ta iya shiga wani yanayi idan muka jinkirta.”



Nan ta yi ajiyar zuciya mai tsayi sosai, sai ta suri AMISHA wacce sai rawar sanyi take yi, ba ko mayafi a tare da ita ta fito cikin tsalelen dare karfe uku da mintuka, bayanta kuwa BILKISU ce da hijabi da zanen da ke a jikinta duka sun jike sun kame sosai a jikinta, har yanzu kukan SAJIDA take yi tana tafiya cikin sauri, hannunta daya a kan yarinyar dayan kuwa shi ne dauke da ita.



Suna zaune ne a unguwar Bulaburin sai suka nufi asibitin TH wato UNUVERSITY OF MAIDUGURI TEACHING HOSPITAL wacce wasu suke kir da TH wato teaching Hospital ko COSTIN kai tsaye. Haka suka ci gaba da tafiya, har suka karaso a gada ta GWANGE, ruwa sai wucewa suke yi ta karkashin gadar da karfi dauke kuma da sauti, suka wuce gadar suka karaso GWANGE suka wuce ta police station, abin mamaki duk da matsala da ake fama da ita na hare-haren BOKO HARAM, sam ba su hadu da jami’an tsaro ko daya ba, suka wuce suka karaso MARAZINE HOTEL da ke kusa da TH. Isowarsu TH suka tarar da  kofar a bude inda mai gadi yake ciki abinsa yana ta sharar barci. A ranta tace oh! Wacce irin kasa ce wannan muke ciki? Suka shiga daga ciki, ga parking space bayan da suka wuce ta gefen hagu daga round about da ke cikin asibitin ganin sai ta rasa ina za su nufa, ganin labour ward, duk da ba karatu mai zurfi ta yi ba, tasan cewa layin masu haihuwa ne, hakan ya sa ta ci gaba da dubawa, har idanuwanta suka kyalla mata inda aka rubuta A&E wato accident and emergency a upstairs, hakan ya bata damar kara kaimi suka taka ta matattakalar suka isa, abin mamaki sai ta tarar da masu aiki a zaune sai faman fira suke, ga roaster a gabansu dayar ce rike da biro inda dayar ke dube –dube a cikin wayarta, dayar kuwa tana zaune tana saurar surutu, ta fahimcii hakan ne sandiyar su suna da wuta, kasancewar an tada gen.



Gaba daya suka mayar da hankali wurinta, “‘yaruwa lafiya?” dayar ta fadacikin damuwa. Kuka na kokarin kwace mata ta yi musu bayanin komai, cikin sauri, dayar da ke rike da biro, ta taso ta karbi ‘yar, jin yadda jikinta ya yi zafi, kuma ga kakkarwa da take yi, yasa ta yi sauri ta shiga da ita wani daki da ke da gado kwaya daya, ta kwantar da ita, bayan ta nemi pulse na ta ta kara bincikar me ke damunta sai ta fito ta sami mahaifiyarta, ta ce da ita; “haba ‘yaruwa ke wacce iri ce, za ki bari ‘yarki ta sha kashin ruwa haka? Ga shi yanzu saura kiris ta rasa rayuwarta, ga ki da alamun mai hankali, amma kina irin wannan, diya `fa rahama ne, kuma ansan uwaye musamman mata da kauna hadi da nuna kulawa gun diyansu”


“ki yi hakuri ranki ya dade, wasu lokuta abubuwa sukan faru, amma mu mutane ba ma da ikon hana faruwar haka, amma da ikon Allah haka, ba za ta sake faruwa ba”




“Allah ya sa; ina mahaifinta?”




Nan idanuwanta suka faar fiki-fiki, cikin rawar murya ta ce “ya yi tafiya ne, amma gobe zai dawo”



“zo” suka shiga ta mata wasu allurai guda biyu, sai ta rubuta mata wasu magunguna ta ce idan safiya ta waye sai ki siyo, a dinga bata, inda za ki sayo za su maki bayanin yadda za ayi amfani da shi, amma ki dinga kulawa don Allah”




Suka yi godiya, suka kwana nan asibiti, a rayuwar SAJIDA, ba ta taba kwana a wuri lafiyayye ba irin fakon asibiti, duk da tayi kwanan ne bayan da suka kammala sallar asuba, har rana ta fara fitowa kafin suka samu suka fito daga asibitin, sai godiya suke yi wa wannan nurse din kamar su yi mata sujada kan jin dadi, da suka fito daga sibitin sai suka biya wurin wata mai sayar da kosai kan hanya suka siya daga ragowar kudin da malama AISHA ta ba su, suka nufo gida.




QASIMU kuwa, da ya dawo da safe ya tarar da abinda ya faru da dakinsa, ya kuma tarar da matarsa tareda ‘ya’yansa ba sa nan, ya ce “kutumar uba! Wato shegiyar matarnan abin da za ta min ke nan? Wato idan ba na nan wurin maza take zuwa ta kwana? Ai ko za ta dawo ta same ni.”



Shigowarsu gidan, a hannun BILKISU leda ce dauke da kosai mai zafi, SAJIDA kuwa tana dauke da AMISHA, zumbur ya mike ya ce da ita, “gidan uwar wa kika fito?”





DR. ZAIN
[2/3, 4:40 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




🅾3⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```



_And in the end, it's not the years in your life that count. It's the life in your years._





*Shafin Masoya*

_Ummyn Yusrah_
_Star Nucy 360_
_80k_
_King boy Isah_
_Mlife_





***CI GABA***




Jikinta na rawa, ta mayar masa da amsa; “wallahi AMISHA ce ba lafiya, duka ruwan jiya a kanmu suka kare, shi ne muka fita cikin dare muka kai ta asibiti, domin duba lafiyarta, ka ga magunguna da aka rubuto likita ta ce a siya mata,” ta fada a dai dai lokacin da take kokarin nuna masa takardar maganin, AMISHA kuwa sai sharar barci take rike a kirjin mahaifiyarta.



“yimun shiru munafuka, dama ai ina ankare da ke, wato duk idan ba na nan fita yawon banza kike yi? Abin ma bai isa ki fita ke kadai ba, har sai kin tafi da yarana, lallai yau za ki ci ubanki”



“haba baban Bilki ya za ka je fe ni da wadannan munanan kalamai, ko halin diyarka ba za ka duba ba? Kalla fa yadda take faman cira da makyarkyata. Kuma idan lalaci zan je, da yara masu wayau zan fita? Me yasa ko da yaushe ba ka tsayawa ka dinga yi wa kanka adalci? Na san fadan da kake yi, duk bai wuce kokarin tserewa biyan kudin magani ba ne, kar ka damu, ni ban dora maka biyan kudin ba”.


“lallai SAJIDA hantsarki ta ja ruwa, wato ni nake magana kina mayarmun?” ya shareta da mari sai da ta fadi, tare da AMISHA, nan ta farka saboda jikinta ya doki kasa sosai. Ya bita da shuri, yana bugu  a kasa, AMISHA kuwa sai faman rusa kuka take yi cikin radadi, sai da BILKISU ta yi sauri tazo ta dauke ta ta koma gefe, itama tana rusa kuka, haka ya daketa iya son ransa, ya kama hanya ya fita, ba tare da ya ko kula da me za su ci da safe ba.



Ba mai kokarin rarrasan wani daga cikinsu, a haka suka sha kukansu na wani lokaci, kana suka ci gaba da sabgar rayuwarsu, cen suna tsakiyar cin kosai da suka sayo daga kan hanya, sai ga muryar malama AISHA tana masu sallama, bayan da suka karba tare da yi mata marhaba, ta sami wuri ta zauna cikin sakin fuska, duk da ta so ta Ankara da damuwa da ke shimfide a fuskokinsu, amma a haka suke karfin halin boyewa, har da yi mata murmushi ita ma. Suka taya mata kosan, ta nuna musu ta ci abinci kafin ta fito, suka yi- suka yi ta ci ko kadan; amma ta kekasa kasa ta ki. Da suka kammala, ta sanar da su cewa ta zo ne domin ta nuna musu inda gidan nata yake, sai su saka ranar da za ta fara zuwa aikin. Ai ko nan suka yi cirko-cirko suna kallon juna ita da ‘yarta, lura da yanzu ta gama shan duka daga lusarin kidahumin mijinta da sam bai san darajar ‘ya mace ba.  A zuciyarta ta yanke shawara, sai dai ya yanka ta, amma ba za ta fasa tura ‘yarta aikatau ba, domin ba za ta bari yunwa ta illata su ba, kuma ba za ta je yawon bara ba, haka ba ta da wani jari da za ta dinga juyawa, ba ta san lokacin da hawaye suka subuce mata ba. Malama Aisha ce ta ce; “subhanallah! Me ke faruwa malama SAJIDA naga kin fashe da kuka?” “ba komai, wani haki ne ya fadamin a idanu” “amma da mamaki, domin duka idanun naki biyu naga suna fitar da ruwa” “yawwa ku tashi muje sai ki nunamuna gidan naki” “to” kawai ta fada tare da mikewa.




Ba su zame ko ina ba si unguwar Danori, ta nuna musu gidanta inda take zama, daga ita sai ‘yarta FATIMA, mai kimanin shekaru sha biyar, wacce ke SS1 yanzu. Fatima fara ce kum gata da tsayi sosai, ba ta da jiki, wanda har ya sa ko shape ba za ka iya hango wa a jikinta ba, amma kirjinta cike yake da mama, duk da kananan shekarunta, tana gane karatu sosai a aji, haka tana mayar da hankali sosai a bangaren karatun addini, hakan ya sa ta zama mai ladabi da biyayya sosai a wurin mahaifiyarta, har ta kai ko kara mahaifiyarta ta ajiye, ba za ta tsallaka ba.



Shigarsu gidan, ita ta tarye su cikin murna na girmmawa, su BILKISU kam an sha kallon farfajiyar gida, domin ita ta dauka ko a turai ne take.



Tun daga kofar gidan, gida ne da ke dauke da ginin zamani, bayan electronic gate da yake da shi, aka sanya wata wire da ta zagaye wasu flowers na roba, wadanda ke fitar da launuka daban-daban na haske, a tsakiyar flowers din kuwa da suka zama kamar carpet a wurin, manyan itace ne na giginya, suma duka na roba ne, da kuma kalar nasu haske daban, shi yasa yara ke misalta gidan da Gidan Haske. Daga shigowarka gidan kuwa, ko mai gadi babu, kasancewar gate din da remote yake aiki, haka za kaayi tafiyar sama da minti talatin idan da kafa ne kafin ka iso harabar inda mutane suke, a gefe, parking space ne, sai dayan gefen da ke dauke da natural grass carpet, wanda masu bashi ruwa daban, nan FATIMA ke wasa da abokaninta, idan ka wuce wannan play ground, za ka zo ne inda aka zagaye kamar lambu, shuke-shuke kala-kala, su guava, lemu, mango da dai sauransu, shi yasa wurin a ko da yaushe dauke yake da sanyi, sai kuma kujeru da aka jera a tsakiyar itacen, inda ake shakatawa, daga nana kwai wani floor da aka yi wanda ta shi za ka iya shiga ainihin gidan, ta babban parlour da sauran dakuna.


Sai ta ce da su “kunga gidana, kuma nan nake so diyarki ta dinga yin aiki, saboda na yaba da hankalinta, kuma na yarda da tarbiyyarta”


“Ba abin da za mu ce maki sai dai godiya, ubangiji Allah ya biyaki, ke kuma BILKISU, kar naji ko nagani kin yi rshin kunya gareta, yi nayi bari na bari, duk yadda kikasan kina bani girma, ita ma haka nake so ki girmama ta”


“insha Allahu inna, zan kiyaye”



“game da tahowarta, kullum, driver zai dinga daukota kuma shi zai dinga mayar da ita”


“Muna godiya”


A nan suka ci abincin rana, bayan sun sha kallo a TV suka dawo gida.


Sai dai aka yi rashin sa’a, domin kuwa QASIMU, ya fi awa daya da dawowa daga yawonsa na banza, da sunan yunwa yake ji, ya dawo gida ne domin ya ci abinci.




Har yanzu labari bai fara ba



DR. ZAIN
[2/3, 4:43 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




🅾4⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```





_The world is moving so fast these days that the man who says it can't be done is generally interrupted by someone doing it_








*Shafin Masoya*


_Feenah Baby_
_Maryam Adamu_
_Maryam Mrs Isma'il_
_Khadija Muhammad Wani_
_Firdausi Feedo_






***Ci gaba***





“dama ai nasan taurinn kanki, ba zai bari ki yi mani biyayya ba, wato a duk lokacin da na fita, sai ki dauki, la’antattun kafafuwanki kema ki fita iskancinki ko? Don ubanki, zo yau sai kin gayamani, gidan uban da kika fito” ya fada a dai dai lokacin da yake kokarin zare belt daga dan zugaggen kunkurunsa. Ganin haka jikinta ya kwashi bari, domin ta san muddin belt dinnan ya fito daga gidansa, ba zai koma  ba har sai jikinta ya yi jina-jina. BILIKISU kuwa tuni ta fara kuka, domin tasan yau ba mahaifiyar tata kadai ba, har ita sai tayi gashin bai da ruwan zafi.





“don tsabar iskanci ina maki magana, kina wani kallona kamar wata saliha, na ce gidan uban wa kika fito?”  ya fada yana zare idanu.





Jiki na rawa, ta ba shi amsa. “dama jikin AMISHA ne ya yi, tsanani, shi ne muka koma domin a duba lafiyarta”




“da izinin wa kika fita?”




“naga ba ka kusa ne, kuma wannan abu ne da ya shafi, lafiyar diyarmu, shi ne naga ya dace na kaita”




“oh! Wato kina so ki nunamin cewa ni bansan daraja ko hakkin ‘ya’yana ba kenan, ke ce wacce tasan darajar ‘ya’ya? Dakata! Ba ma wannan ba, ina abin da kika dafa yau, ni yunwa nake ji”




“sai da tayi shirun kusan minti daya, sai sake-sake take yi  ranta, yawu ma idan ta yi yunkurin hadiyewa, a haka suke subuce mata, ta kalle shi ta ce; “gidannan mun fi wata shida rabonka da ka kawo mana ko magi, kuma duk sana’a da na dauko, kai ke cinye jarin, duba ka gani, kalli ‘ya’yanka, ko yara da ba sa da uba, ba za su wulakantu kamar yadda ka bar ‘ya’yanka ba, na ji ni ba ka so na, ban damu ba, domin saninka ne nima tilstani aka yi, amma tunda har ka ji har ka iya haihuwa da ni, ai ya kamata ka kula da yaranka…” saukar belt kawai ta ji a tsakiyar kanta, kfin ta maido da hanklinta ya dora mata duka a bai, sai dukan ta yake da belt, kasancewar belt din da karfe a jikinsa, ya farfasa mata jiki, sai kuka take yi, shi kuma sai zaginta yake yana rusa ashar. Shi ne bai barta ba, har sai da ya ga ba ta motsi, ya dawo kan BILKISU ya zabgamata belt, ganin zai illatata tayi makota a guje, ko da ta fita ta tarar da mutane sun taru, amma sai shakka suke na shiga gidan, domin kuwa sun san matsawar suka shiga fadan zai dawo a kawunansu. Haka ta ratsa cikin taron jama’a da ke wurin a gigice tana rusa kuka tareda sosa wurare da ya zabgamata belt. Nan ta fara fadin “ya kashe mamarmu…” jin haka jama’ar da ke wurin suka runtuma cikin gidan, ai ko suka tarar da ita a kwance ba ta ko motsi, a dayan gefe kuwa, AMISHA ce sai faman zabgar kuka take yi, daga cikin wadanda suka shigo gida, akwai maza da mata, sai wata mace ta yi kanta domin ta tabbata ko mutuwa ta yi, shi kuwa QASIM sai fadar yake “wa ya kawo ku cikin gidana, wallahi ko mutum ya fita, ko na illata shi” jin haka, wani saurayi majiyi karfi, ya tinkaro shi ya fara shar mashi mari, yana cewa, “idan iskanci kake takama da shi, saninka ne mu munfika, idan kuwa hauka ce a kanka, to wallahi mune maganinka..” ya ci gaba da dukansa, sai da mutane suka rike shi. Sai fadar ke  bar shi ya koyamasa hankali. Matar da ta je duba SAJIDA ta tabbatar da ba ta mutu ba, nan suka zuba mata ruwa, zuwa wani lokaci ta farfado, tare da jan wata doguwar sheda.




Wata mata ta ce da ita; “wai ke me kike ciki ne da ba za ki rabu da wannan mahaukacin ba, ke fa kyakkyawa ce, amma ji yadda kika lalace, kalli ‘ya’yanki ki gani, ba tarbiyya kadai ba, har ilimi rasawa za su yi, gaskiya ki sake tunani”




Inda wasu na tausaya mata, wasu kuma suna yi mata fada, a haka dai suka barta, shi kuwa gogannaka tuni ya fita kan kunyar duka da ya sha daga saurayin unguwwa.




Tsawon lokaci tana sharar kuka, tare da jinyar rauni da miki da mahaukacin mijinta ya mata. Tana cikin kuka ta jiyo sallamar wasu maza a bakin kofar gida, wanda ya sa ta share hawayen da ke riganganiyar kwarara daga idanuwanta, cikin sifar tausayi ta kalli, BILKISU da ke gefenta itama tana sharar kukan. Ta dauko tilon hijabin da suke bani-bani ita da diyrta. Ta suri takalmi da sun fi shekaru shida har sun sude kan dadewa, kuma kafar daban-daban, ta fita domin ganin su waye a kofa. Isar ta sai ta ga wasu ne daga unguwar tasu, wasunsu ma ta san su sosai, bayan sun gaisa da ita, suka shaida mata cewa, sun zo ne domin su gyara mata rufin dakinta da iska ya dauke. Saninta ne wannan ba karamin tashin hankali ba ne idan QASIMU ya dawo, domin ba shakka ba zai rasa bin da zai fada ba, ga wannan gyaran. Amma a haka ta ba su dama su shigo suyi aikin musamman da suka sanar da ita cewa, taimako ne daga kungiyar unguwar, dam sukan taimakawa duk wanda irin haka ta faru da shi. A ranta tan cewa, sai dai duk abin da zai faru ya faru, amma ba zan bari diyana su wulakanta cikin zafin rana, ko ruwan sama ba, musanmamn da yake yanzu lokacin damina ne, ga masifar zafi ga shi ko da yaushe ruwan sama zai iya sauka.




Suka fara shigowa da kayan aiki, suka kawo langa-lang (kwano) suka jibge katakai da kusoshi, wasunsu rike da hammer wasu rike da bar ta cirewa ko gyaran kusa, da dai sauran kayan aiki, su da yawa ne shi ya sa suka kammala aikin cikin lokaci kankane, ai ko nan ta dinga yi musu godiya kamar za ta rusuna.




Bayan sun wuce, cike da murna suka gyara dakin nasu ita da BILKISU, inda AMISHA take shimfide kan tabarma tana sharar barci, duk da jikinnnata har yanzu da alama zazzabi. Da suka kammala, ta aiki BILKISU domin ta yo masu cefane, kasancewar sun samo kudi daga gidan Malama Aisha. Da ta dawo suka dora abinci, tuwon dawa da miyar kuka.
(ayi hakuri, wanan layin missing up ne, amma a hakan ma zai karantu)



Ai ko cikin gudu da murna ta je ta siyo abubuwan da aka aiketa ta siyo.



Sai murna suke yi ita da ‘ya’yanta ganin yadda aka gyara musu dakinsu har rufin nashi ya dawo sabo. Suna cikin murna sai ga sallamar driver ya zo daukar BILKISU, nan suka yi sallma da mahaifiyaarta ta tafi.




Wucewarta da kamar mintuna hamsin sai ga QASIMU ya dawo, kallo daya za ka masa kasan cewa yana cikin magagi na maye, tafiyarsa kadai ma ta isa ta fassara haka. Daga shigowarsa, ya ce; “ina yarannan suke ne, ki fiddomin da su, akwai wani dan siyasa da ya yi sanarwa cewa, duk wanda yake da ‘ya’ya marayu, ya kawo su a gani, za a dinga daukarsu zuwa kasashe domin su dinga yin aiki, sai a dinga biyan mahaifinsu ko mahifiyarsu  wasu kudade, kinga dama ce muka samu ta mallakar kudi, ko ba komai wannan talaucin nasan ya ishe ki….” “tabbas ban taba sanin baka da hankali ba sai yanzu, shekaru nawa muke cikin talauci da ukuba da kangi, sau nawa a rayuwarka ka taba tunanin kawo muna dauki ta hanyar da ya dace sai yanzu da ka ji wai kudi za ka samu? Wato duk abinda kai ba za ka amfana ba, ba za ka yi shi ba? Tau ka karkade kunnuwanka da kyau ka ji; kyaleka da nake yi, ba wai tsoronka nake ji ba, ina kyaleka ne saboda kai shugaba ne a kaina, tunda ka kasa fahimtar haka, inaso kasan cewa ni ba lusara ba ce, da zan mika wa ‘yan siyasa ‘ya’yana ba, wadanda ko kadan ba sa tausayin talaka, wannan da kake gani, suna amfani da ku ne domin su cinma burinsu, kodai ta hanyar yin tsafi da ‘ya’yanku, ko su sayar da su hannun kafurai arna a kashashen waje a dinga zina da su ko ayi tsafi da su. Talauci ai ba hauka ba ne, wallahi idan har ka ga ka dauki daya daga cikin ‘ya’yana, sai idan kashe ni ka yi”




Har ya so ya tada fada, ganin yadda ta cije, dole ya hakura, har zai fita, sai ya kyalla idanuwansa ya hango rufi da aka yi musu. Sai ya kada baki ya ce;



Har yanzu lbarin bai fara ba



08034840276

DR. ZAIN
[2/3, 4:43 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾



🅾5⃣




Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```




_Remembering that you are going to die is the best way I know to avoid the trap of thinking you have something to lose._




*Shafin Masoya*


_Banida baki da zan yi wa masoyana da kuma mabiya wannan littafin godiya, ina alfahari da ku duk inda kuke haka ina yabawa hadi da godiya kan addu'o'i da fatan alkhairi data gareku. Allah ya bar mu tare._




***CI GABA***




“ina kika samo kudin gyaran wannan rufin?”



“ba ni na gyara ba, dama a unguwa akwai kungiya ta taimakon kai-da-kai, su ne suka tausaya wa halin da yarana suke ciki, suka zo suka yi mana wannan gyaran”




“sun baku wasu kudade ne?”



Cikin ranta ta yi wani bahagon murmushi mai dauke da takaici, a ranta tana ewa, ba shakka, duk wanda Allah ya jarabta da auren miji jahili wanda bai san me ake kira hakkin aure ba, yana cikin damuwa, wato shi ba ya da tunani idan ba a bashi kudi ya salwantar ba? Sai tace “a a! ba su bamu ko sisi ba.”




Ya rafka tsaki ya wuce, har da gunaguninsa.




BILKISU kuwa, bayan an gabartar da ita ga sauran ma’aikatan gidan, tun daga masu baiwa flowers ruwa, har masu aikin girki da sauransu, sai kuma aka nunamata gidan da kuma inda za ta yi aiki, wato goge-goge na bangaren FATIMA, hakan yasa  aka kawota wurin FATIMA domin su ga juna.




BILKISU wankan tarwada ce, irin yarannan ne masu tsayi sosai, amma ita tana dan da kaurin jiki, gata da tsawon gashi, sosai ta biyo mahaifiyartaa a fuska, amma ta dara mahaifiyarta kyawu nesa, tanada dogon hanci ga dan tsukakken baki, sai dai muryarta ba siririya bace, tana dan da kauri, idanuwanta ba farare ne gaba daya ba, sunada ratsin ja, ko saboda yawan kuka da take yi ne oho! Tana dan da sauri wurin magana, sai dai akwai kaifin tunani da saurin fahimtar abu ko karatu.




Da sukaa ga juna, ta tsunduma aiki, ita kuwa FATIMA ba abin da take yi illa assignment da aka basu  aji, tana assignment din tana satar kallon BILKISU ita ma din dai satar kallonta take yi.




Da ta kammala aikin sai ta kirata suka zauna suka fara fira, a cikin firar ne take tambayar ta wacce makaranta take, inda ta sanar da ita, cewa tun kammala JSS3 nata karatunta ya tsaya, kasancewar dama mahaifiyarta ce ke daukan nauyin katun nata, ga shi kuma mahaifiyar yanzu ba jari ko kudin da za ta kula da karatunta.



“yanzu idan za a saka ki makaranta za ki koma”



Bayan ta saki murmushi, na jin dadi ta amsa “sosai kuwa, banida buri irin in yi karatu mai zurfi har na zama lawyer, idan har na sami damar komawa makarannta ba karamin farin ciki zan yi ba”




Itama sai da ta saki nata murushin sai ta ce da ita, “kya iya tafiya, naga ba sauran aiki”



Ta je dakin Malama AISHA ta tarar da ita sai karatun Jarida take yi, ta shaida mata cewa ta kammala har FATIMA ta sallameta, za ta koma gida ne, “haba BILKISU komawa gida tun yanzu? Sai ka ce wacce ake kora, ba za ki tsaya kiyi wasa ba?” shirun da tayi kanta a sunkuye shi ya nunawa malama AISHA cewa hankalinta yana gida, sai ta jawo hannunta, ta zaunar da ita parlour ta shiga ta dauko mata abinci dafaffe da kuma kayan abinci wadanda ba  a dafa ba, tace, kuci wannan, wannan kuma ku dinga dafawa, a kai-a-kai. Ta kira driver ya dauki kayan ya kai su a mota, suka tafi.



Da gudu ta karasa cikin gida tare da rungueme mahaifiyarta, da ke zaune kan wata tsohuwar tabarma da gaba daya ta side, tana yi wa AMISHA wasa. “kar ki ballamin kafa! Gara ke da sauran kuruciyarki” “wallahi inna dadi nake ji, kinga yadda suke son jama’a kuwa? Ni inda ma cen ne gidanmu, wallahi da na ji dadi…” “kowanne rai da kike gani BILKISU yanada kaddara da ubangiji ya dora a kansa, wayonsa ko dabararsa duk ba za su yi tasiri kan tsarin ubangiji ba, ko ai mu din ba mantawa da mu ya yi ba, kuma bamusan me ya tsara a kanmu nan gaba ba” “ba rashin godiya nake yi ba, kawai ina nuna farin cikina ne”



A dai dai lokacin ne driver ya fraa shigowa da kaya cikin gida, wanda ya sa BILKISU ta mike zumbur domin gaba daya ta manta cewa tare da driver suka zo. Bayan sun saka kayan gaba daya cikin gida, suka yi sallamaa da shi ya wuce.




FATIMA kuwa; daga fitar Bilkisu kai tsaye ta nufi dakin mahaifiyarta, inda ta tarar da ita zaune a parlour tana kallon tashar MANARA TV, cikin nutsuwa ta mayar da hankalinta ya zuwa ga ‘yarta, saboda jin irin sallamar da ta yi, tasan da magana a tafe da ita.



Cikin sakin fuska a kalleta ta ce, “kar dai kice har kin kammala assignment da naga kina rubutwa?” bayan ta saki murmushi, ta ce “na jima da kammalawa” “sannu agogo sarkin aiki, wasu lokuta sai ki dinga tunamin da mahaifinki, shima lokacin yana raye, ba ya wasa da aiki ko kadan, kinzo ki tayani kallo ne, duk da nasan ba son tashoshin da ake yin wa’azi kike yi ba” “a a! ba kallo na zo taya ki ba, nazo ne muyi wata magana” “inajinki, me ke tafe da ke?” “dama kan BILKISU ne, kinga tana da kuruciya har yanzu, kuma da lokaci, me zai hana ki sakata makaranta, ko ba komai taimako ne kuma ga alama z ata yi ambition mai kyau, saboda na dan tattuna da ita, har ta nunamin mastalolin da suka hana karatunta ya ci gaba, kinga mu da ubangiji ya yi wa budi, hakkinmu ne mu taimakamata tunda munada ikon yin hakan” tayi ajiyar zuciyaa na wasu lokuta kana ta kalli diyarta da ke zaune daga kasan kujera kusa da kafafuwanta, inda ita kuma take kan kujerar, sai ta shafo kanta cikin murmushi, hawaye suka zubo mata a lallaausan kumatunta, a ranta tana tunawa da kokarin kwatanta halayyar wannan yarinyar da ta mahaifinta, ga tausayi da son taimakon talaka. Sai ta ce da ita. “kar ki damu, dama ai saboda irin wadannan ne ubangiji ya wakilta mu akan wannnan dukiyar, kuma da ikon Allah zamu taimaka mata, zan je gidansu ajuma, in yaso da safe idan mahaifiyarta ta amince sai na je naga principal naku muyi magana, tunda kinga yanzu har kun dauki sati biyu da komawa, zan kokaarta nagani ko zasu yimaani wannan alfarmar” “nagode Mama” “ai ni ya kamata namaki godiya, ni da kika kawowa aikin lada har a daki”.






08034840276

DR. ZAIN
[2/3, 4:43 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




🅾6⃣




Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```




_I learned that courage was not the absence of fear, but the triumph over it. The brave man is not he who does not feel afraid, but he who conquers that fear._





*Shafin Masoya*



_Tabbas ba zan iya mika dokacin godiyata ba gareku masoyana da mabiya wannan littafin, ina jin dadin yadda kuke nuns kulawarku gare ni, kuma inaso ku San da cewa lafiya lau nake wiki ne ya rike ni kwana biyu, kuma dama on weekends ba na posting. Allah ya bar mu tare_






***CI GABA***




Sallamar malama AISHA ce ta katse raha da SAJIDA ke yi cikin ‘ya’yanta a daidai lokacin da suke cin abinci, bayan sun idar da sallar magarib, da kusan minti ashirin da wni abu. Cikin murna Bilkisu ta tashi ta tarye ta har da hadaawa da rungumarta. “sannu da zuwa, ke ce a gidan namu, ba ko sanarwa” SAJIDA ta fada, a daidai lokcin da take kokarin mikewa tareda neman ruwa daga Randa da ke kusa da ita, domin wanke hannunta. Bayan ta wanke hannunta, suka shiga gaisawa da malama AISHA, lura da akwai magana da ta kawo ta, sai suka shiga cikin daki, suka bar yara nan a waje domin su karasa cin abinci. AMISHA kam sai kokarin zabga loma take yi, ga shi an dade ba a hadu da miyar sure ba ga manshanu, da kamshinsa zai doki hancinka tun daga nesa, bugu da kari, SAJIDA gwana ce a tuka tuwon masara.



“naga kamar kina tafe da magana, shi yasa na ce mu shigo daga ciki”



“haka ne, akwai magana mai muhinmanci da ke tafe da ni. Ba sai na tsaya dogon sharhi ba, kinsan wa cece ‘yarki; wato BILKISU, kinsan irin halayya da kaifin basira da ubangiji ya bata, haka kina sane da irin burinta a rayuwa, na kokarin ganin ta yi karatu har ta kai wani matsayi da za ta zama abin dubawa a idanun mutane. Ba wannan ba ma, saninki ne a wannan zamani, idan har mace za ta koma gefe ta jefar da karatun zamani musamman a baya, tau ba ita kadai ba, hatta rayuwar ‘ya’yanta abin tausayi ce, domin yanzu zamani ya kawo, da mazaje sam ba su san me ake kira aure ba, ba su san ko kadan ba me ya dace da yaransu ko matansu, kawai abin da suka sani shi ne kawunansu. Karkashin wannan nake gani, ya dace ki saka hannu wurin ceto rayukan zuri’arki daga shiga gararin rayuwa. Inaso karkashin umarninki, na saka BILKISU makaranta. Dama naji ta kammala JLC nata, kinga yanzu ba wani nisa aka yi ba daga shiga SS1 sai na tuntubi malaman makarantarsu FATIMA, sai na sakata a makarantar, kinga ko ba komai rage wata wahala ce”




Ta yi doguwar ajiyar zuciya, kana ta ce; “ban ki ta taki ba, amma inada tabbas kan duk makaarantar da ‘yarki take, ba karamar makaranta ba ce, mu da ko na koko da kyar mukan samu, ina mu ina sakata irin wannan makarantar, na biyu, mahaifinta, lusarin mutum ne, ba zai bari na saka ta makaranta ba, domin hatta wannan aikin da take yi a gidanki, ban bari ya sani ba…”




Ta katse ta ta hanyar dafa kafadarta. “kalle ni SAJIDA, matsawar za ki biyewa wannan mijin naki, ba shakka rayuwar yaranki za ta taso a halaka, kiyi tunani, Allah ya sawwaka, yanzu ace ubangiji ya dauki rayuwarki, ya kike tunanin rayuwar yaranki ta taso? Wa zai kula maki da su? Nasan kina sane da ko kusa QASIMU ba zai kula da tarbiyyarsu ba, sai dai ya lalata tarbiyyar, idan za ki farka, yanzu y kamata ya yi ki farka ki aikata abinda ya dace”




Ta fashe da kuka wanda har sautinsa ya kasa boyuwa daga bakinta, ta kalli malama AISHA, ta sunkuyar da kai, a kwakwalwarta, ta fara hasaso yadda rayuwar yaranta za ta kasance da ace ba ta raye. “haka ne abin da kika fada na baki dama, ai yanzu ke matsayin mahaifiya ce ga BILKISU, kiyi duk abinda ya dace”




“yawwa! Na ji kina fadar ba kwa da kudin biya mata zuwa makaranta, hmm! Ai ina sane da shi ne dalilin da ya hana ta ci gaba da karatu, duka ta sanar da FATIMA, kuma ni banada niyyar ki biya ko da kwandala wurin karatunta, yanzu hakkin wannan ya dawo kaina, ni zan yi, kawai abnida nake bukata daga gareki, shi ne ki kula sosai da zuwanta makarantar ki dinga kuma bata kwarin guiwa. Sai ki kirata, ki sanar da ita yadda muka yi yanzu.”



“mamanne!”



“na’am inna” ta fada tareda tasowa cikin sauri, daga inda suke zabga fira ita da kanwarta, kasancewar sun jima da kammmala cin abinci. Daga shigowarta, ta nemi wuri kan tabarma ta zauna, dama dakin tabarmi biyu ne kadai a ciki, wacce suke kwana ita da kanwarta, sai wacce mahaifiyarta ke kwana a kai, domin QASIMU ba kullum yake kwana gida ba, duk da tabarmin sun tsufa, ba za ka ga datti a kansu ba.



Ta kwashe duk abinda ya sa ta kirata ta gaya mata, ai ko nan ta bige da murna, har da nunawa a fili. Ta dawo ta shaidawa kanwarta, suka ci gaba da firarsu, bayan Sallar isha malama AISHA ta koma gida.



Komawarta gida ta sanar da FATIMA yadda suka yi da mahaifiyar BILKISU. Nan FATIMA ta buge da murna, tana fada a ranta, cewa, tabbas za ta yi abokiyar zuwa makaranta. Nan ta koma dakinta ta ci gaba da karatu, inda mahaifiyarta ta buda startimes ta fara kallon Sunnaah TV. Washe gari, ta bi su FATIMA zuwa makarantarsu, domin ta zanta da principal. Da yake Rubby makaranta ce da dalibai ke fita a kalla 7:30am, inda duk dalibin da ya kai 7:45am ya makara. Kasamcewar tanaso ta gana da principal sai ta fita tun kafin 7:20am, bayan sun saukar da FATIMA ta nufi assembly ground da ke harabar makekiyar makarantar, kai tsaye ta nufi office na principal din, wanda daga shigarka, sanyin AC ke kokarin ya ratsa bargon jikinka, haka kamshin turaruka kala-kala za su dinga kawo zungura a kusurwowin hancinka. Zaune ta tarar da shi sai faman dube-dube yake a wani katon littafi da ya ajiye a gabansa, a idanuwansa kuwa wani medicated tabarau ne da ke taimaka masa wurin  karanto kalmomi da ke jibge cikin littafin. Sallamarta ce ta mayar da hankalinsa ya zuwa bakin kofa. Office din nasa kai kace wani katon parlour ne, domin har da kujeru three seaters da two seaters aka kawata shi da su, a matsayin parlour da zai sadaka da ainahin office din da shi yake aikinsa, wannan parlour din da shi yake taryar baki ko guntun conference meeting. Bayan ya amsa sallamarta ya rufe littafin tareda dagowa da fuskarsa domin ya ga wa ke sallama, nan ya buge da murmushi ya ce; “manya, yau ku ne tafe? Ai da kin aikomin, sai nazo” ta buge da dariya, “kai dai principal ba ka gajiya da tsokana, ina ni ina tadowa da shehin malami” shima ya buge da dariya, bayan sun gaisa, ta gabatar masa da abinda ke tafe da ita. Da farko ya so ya nuna abin ba zai yiwu ba, amma da ta roki alfarma, ta kuma nuna maa yarinyar za ta iya cinma ‘yan ajinnasu, sai ya aminta, sai ya turata ya zuwa ga Vice Principal Administartion, dauke da rubutu, na nuna gansuwarsa kan a baiwa BILKISU damar zowa tayi karatu a mataki na biyu a makarantar gaba da primary, wato SS.



Da ta kai wa vice takarda, sai ya umarce ta da ta zo da yarinyar gobe, domin a mata interview, bayan ta rubuta entrance exams, ta nuna ba laifi.



Washe gari suka zo da BILKISU, ta rubuta entrance exams, bayan awa biyu aka kammala makin na jarabawar, ga mamaki sai ga shi tafi duk sauran da suka rubuta cin maki mai yawa, aka mata interview, malaman sai sake baki suke yi suna kallaonta yadda take zuba turanci, kamar wata da ta fito daga ingila, hakan ya sa vice ya gayamata cewa za abata science class, nan ta katse shi, ta nuna masa cewa ita lawyer take so ta zama, don Allah su taimaka mata. Sai suka barta a Art class, wanda dama shi ne ajinsu FATIMA.



Nan aka bata house (red house), aka kuma bata damar cewa ta fara zuwa makaranta daga gobe, cikin sauri Malama AISHA ta biya kudin makaranta da na uniform da na litattafai, da yake dama makarantar su suke dinkawa yara uniform, haka su suke siyar musu da textbook duk a cikin kudin makarantarsu. Ta karbi uniform, da textbook, da sport wears da sunan on wednessdaya za ta fara shiga aji.



Tun da misalin karfe bakwai na safe take tsaye a kofar gidansu, a jikinta farar riga ce da iyakanta kugunta dauke da dogon hannu, rigar ta sha ado da tambarin makrantaar da aka rubutawa ruby ta ko’ina, sai guntun skirt da zamu iya kira da ash colour duk da kala din da surki, wanda iyakarsa guiwarta, wanda ya sa dole take kame-kame cikin kunya, sai dan hijabi da iyakarsa wuyanta. (ohh! Mu nasara da yahudu sun hallakamu, ace har uniform iyaye ba zamu tsawatar ba, wannan shiga ta yahudawa haka.) takalminta kuwa bakake sai farin socks da ta yi kokarin rufe tsiraicinta da shi ta amfanin jawo shi har kusa da guiwa. A hannunta kuwa dan wane basket ne, da aka cika da abinci da za ta ci a lokacin break fast.



Cen sai ga mota ta tsaya daf da ita, FATIMA kuwa sai sakar mata da murmushi take yi, cikin murna bayan ta gaida su ta shiga motar suka nufi makaranta.



Har yanzu labrin baai fra ba



08034840276

DR. ZAIN
[2/3, 4:46 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾



🅾7⃣



Na





*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```





_The paradox of courage is that a man must be a little careless of his life even in order to keep it_






*Shafin Masoya*




Aisha Alto
Asiya Lame
Maman Ahmad
Ililee
Mr Smiles
Ummie Zuru



***CI GABA***







Cikin mota suke fira, inda FATIMA ke sanar da ita darussa da za a gabar musu da su  idan suka shiga a aji, za su gabatar da civic education first period sai economics sai government, inda take gayamata halayyar kowanne daga cikin malaman. Da suka karaso makaranta suka nufi assembly ground kai tsaye, ba da dadewa ba, prefects suka fara tsara yadda za su shiga layin assembly tareda kula da su, inda ake bincikar masu zowa da datti ko wata kwalliya da ba ta dace ba, bayan sun fitar da kamar mutum biyar suka umarce su da su rusuna na kneel down a cen bayan layin assembly, kafin malamai suzo su yanke musu hukunci. Zuwa wani loakci sai ga malamai sun fara zowa, da principal ya karaso, bayan national anthem da ‘yan wasu abubuwa da aka gabatar. Sai principal ya yi dan jawabi cikin harshen turanci, aka sallami kowa ya wuce aji domin gabatar a karatu, su kuwa wadanda aka tsare aka sakasu aiki a matsayin horo.




SS1B shi ne ajinsu, bayan sun shiga sun zauna, sai surutu suke zabgawa, inda wadanda suka lura da akwai bakuwar fuska a ajin, sai dandazo suke yi domin sanin wacece ita, FATIMA kam har ta gaji da amsa tambayoyinsu, cen sai ga malamarsu Victoria ta shigo, da yake ita ce mai daukar su civic education, bayan sun gaidata, ta shiga kai tsaye cikin darasi. Da ta gama jawabinta sai ta fara yi musu tambayoyi, inda BILKISU tafi amsawa, dalilin da yasa Victoria ta kirata da friend kenan, shi kuma ne dalilin da yasa ‘yan ajin nasu, musamman masu kwazo a ajin suka fara daukan ta a matsayin kishiya. Haka malaman suka dinga yabawa kokari da kwazon BILKISU, sanadiyyar yin bakin jininta kenan a ajin.




Bayan kada kaaraurwar tara wato breakfast, cikin sauri suke fita daga ajin domin halartar wurin cin abinci, inda suka taru a bangarori daban-daban na makarantar, ko wa ya baje abinda ya zo da shi daga gidansu domin tarfawa cikinsa. BILKISU kasancewar batasan kowa a makaranta ba, ta je wurin FATIMA tareda abokaninta domin su ci abinci tare, cikin sakin fuska FATIMA ta tarye ta, su kuwa abokanin na FATIMA sai wani kallon mai bisa ruwa suke yi mata, suna ganin gaba daya wannan ba ajinsu ba ce. Ko magana ta yi musu sai su dinga fura iska a hanci suna tada kai, duk da haka BILKISU ba ta kula su ba, a haka ta koma gefe ganin ba su ba ta fuska ba, ta bude dan abincinta na talakawa dumamen tuwon masara da miyar kuka ta fara ci.




A wurin cin abincin ne, kawayen FATIMA ke tambayar ina kuma ta rungumo wannan local girl haka? Ta yi musu bayani gaba daya. Ai ko nan suka far mata da fada, “wato saboda rashin hankali shi ne za ki jangwamowa kanki wannan? Irin su ne ke zowa kai tsaye su raba diya da mahaifiyarta, ki tsaya nan wai ku masu taimako, hala an gaya muku ubangiji da ya halicci kowa ba sai da ya leka zuciyoyinmu ba kafin ya raba muna arziki, wallahi wasu talakawa da za a yi su masu kudi, da anga tsiya”. Suka tafa hnnu suka sheke da dariya, ita kuwa FATIMA ko kallo ba su isheta ba, domin kacokam hankalinta na gefen BILKISU da sai satar kallon juna suke yi. Da suka kammala cin abinci suka fara zagayawa suna yawo, dalilin da ya sa FATIMA ta kira BILKISU ke nan domin ta nuna mata makaranta, su kuwa kawayen nata sai tafiya suke suna sukar BILIKISU cikin habaici da kalmomi masu zafi. Ita kuwa ko a jikinta, domin sai fada take yi a ranta, “tankawa, yabawa, biyar bashin matsiyaci”  suna tafiya suna fira har lokacin komawa aji ya yi. Da suka tashi daga makaranta, ‘yan ajin nasu sai hararta suke yi, ita kuwa ko kallonsu ba ta yi ba, FATIMA kuwa bakin ciki kamar ta kuwwata, domin lokaci daya ta ji BILKISU ta kwanta mata a rai,musamman kyawawan halayyarta, ga shi kuma duka kawayenta ba wacce ke son ta. Ta yi nisa da tunani, cen ta jiyo horn na motar gidansu, cikin sanyin jiki su duka biyu suka shiga motar, kusan minti biyar ana tukin motar ba wanda ya furta ko harafi daya, cen BILKISU ta nisa ta ce, “na rasa wanne irin bakin jini muke da shi, ni da mahaifiyata, duk inda muka je sai kiga ana kyamar mu, hatta mahaifina ya tsane mu, ga shi first day dina a makaranta na fuskanci matsalar tsana, anya kuwa ba laifi muka yi wa ubangiji ba, zan tambayi mahaifiyata, ta yi wu a danginmu akwai wanda ya tafka zunubin da har mu an tarfa muna” ta fashe da kuka. Ganin haka FATIMA ta janyo ta ta dora kanta kan kafadarta ta fara rarrashinta, driver da tun shigarsu yake sauraren wakar Sani Sabulu, wakar Dikko na Gotomo, ya juyo cike da tausayi, ya ce, “ke BILKISU kar ki kara fadar haka, kinsan wasu yara ba sa da tarbiyya musamman idan suka ga ‘ya’yan masu arziki ne su, sai kiga suna wulakanta na kasa da su, ba su san da cewa, ubangijinnnan da ya basu arziki bai manta da sauran ba, sun manta mahaifansu ba wani abu suka yi wa uabngiji ba har ya ji bari ya biya su ta hanyar azurta su, ki ci gaba da hakuri, duk wanda ya sha wulakanci a inda yake neman abincinsa, ba shakka yana dauke da dimbin lada, ki kyalesu su kwashi zunubi” FATIMA ce ta karbe zancen, “haka ne, ai kamata ya yi ki tsaya kema ki nuna musu ke mutum ce, da me suka fiki? Kin fa fi mafi yawansu kyawu ga ki da ilimi da saurin fahimta, wanda shi ne dalilinsu na je fa maki karan tsana, sai ki bullashe kema tunda ba yadda za su iya da ke, kudin da iyayensu ke biya su kike biya, tau me ye bamabnci?” ta kara fashewa da sabon kuka, ita kuwa sai rarrashinta take yi, har suka karaso daf da kofar gidansu, duk da da kyar mota kan shiga unguwar, haka da reverse ake fita. Suka yi sallama ta shiga gida, da zinmar zuwa marice za ta zo.




Shigar ta gida ta tarar da mahifiyarta a daki, cikin sakin fuska da gaida ta, ta je ta canja kayan jikinta ta ajiye kan tabarma ta fiddo da wata ‘yar guntuwar toka da suke wanka da kuma wanki da ita, ta ajiye kan uniform nata. Sai ta fita ta suri buta domin ta yi alwala. Mahaifiyarta kuwa, sai kokarin gyara shinkafa take yi wacce za ta dora kan wuta, ajuma da maraice. Inda AMISHA sai wasa take a kusa da ita.




Bayan da ta kammla sallah, ta je ta wanke uniform nata, ta fita ta yo cefane da za a yi amfani da shi domin tuwon maraice, da ta dawo suka shiga fira da mahaifiyarta inda take tambayarta game da rayuwar makaranta, ita kuwa tana ba ta amsa, har aka fara kiran la’asar. Bayan ta kammala salla ta suri takalminta da dan tilon hijabinsu ta nufi ind take aiki. Mahaifiyarta kuma ta fada aikin abincin dare.




Bayan sun gaisa da malama AISHA, kai tsaye ta wuce lungun FATIMA, ta fara yi mata aiki, tana aiki suna fira har ta kammala, ta fito ta sami malama AISHA a parlour inda suka yi bankwana ta wuce daf da magariba. Aka kammala sallar magariba, lokacin hadari ya kankama har an fara iska mai dauke da sanyi da kuma kamshin ruwa, cen an fara kiran la’asar sai ga QASIMU ya shigo da abokaninsa guda biyu, ASHCO da LIVER, su duka uku sun sha giya sun bugu, sai surutu suke da su karan kansu basusan me suke fada ba. Cikin murna SAJIDA ta tarye su kasancewar ba bakon abu ba ne a wurinta mijinta ya shigo gida a buge, ta shimfida musu tabarma a waje duk da da alamun hadari, ta kawo musu abinci, ita kuwa suka wuce yin sallah ita da yaranta. Sai kyakkyewa QASIMU ke yi inda abokaninsa ke yaba wa girkin matarsa, har da sude hannu suna santi, sai labarai suke bai wa junansu kala-kala. Da suka kammala ta zo ta dauke kwannan ta kai wurin wanke-wanke ta ajiye, juyowar da za ta yi sai aka fara yayyafi, dalili da yasa ta canjawa kwannan wuri ke nan, ta rugo daki domin taga lafiyar yaranta, cike da mamaki, sai taga QASIMU na nunawa abokaninsa inda za su kwanta.




Ta yi tsaye tana kallonsa cike da mamaki irin ta ma rasa me za ta gaya masa, saboda gaskiya ta mata yawa, ta kalli su abokanin nasa ko a jikinsu su ala dole ga su za su kwanta da iyalin wani amma ko a jikinsu, ta kalli yaranta, AMISHA har ta fara rawar dari, BILKISU kuwa itama kallonsun kawai take yi. Budar bakinsa ya ce “ki zo bayan ASHCO ki kwanta, ke kuwa BILKISU da AMISHA ku kwanta tareda LIVER ni sai na kwanta ta cen ko a kasa na kwanta ai ba damuwa, yana fadi yana tangadi da kokarin watsi da hannuwa.




Bakin ciki ya lullubeta, take zuciyarta ta kawo a makogwaro, a ranta tace bari na nunawa mutuminnnan ba mashayi ne kadai mahaukaci ba. Cikin ruwan ta fito ta nufi inda suke daka, ta dauko tabarya ta nufato dakin……..




Har yanzu labarin bai fara ba




08034840276

DR. ZAIN
[2/3, 4:47 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾








🅾8⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_





® *PEN WRITERS ASSOCIATION*





```QUOTE OF THE DAY```







_Always acknowledge a fault. This will throw those in authority off their guard and give you an opportunity to commit more._







*Shafin Masoya*


Zainab Jibril
Umaima Jibril

(My biological sisters)





***Ci gaba***



Daga shigowarta ta tarar da ASCHO shi har ya kwanta ya ragamata inda za ta kwanta ita, shi kuwa LIVER yana kokarin gyara inda zasu kwanta Shi da AMISHA da BILKISU, gogannaka kuwa yana tsaye yana kallo, a tsarinsa sai sun kwanta kafin shi ma ya kwanta. Daga shigowarta bata yi wata-wata ba ta fara musu da duka tim-tim-tim! Dalilin da ya sa suka fito daga dakin kenan a gurguje, suna “ke ya kina harkar yawa, wannan ba yi ba ne..” suna fada cikin maagagin maye. Ta ce “idan kai jahilin mahaukaci ne, bari na nunamaka ni mahaukaciya ce da ko lasisi banida, in ba jahilci ba, iyalinka wai za ka ce wani katon banza ya zo ya kwanta su hada jiki a shimfida daya, shaye-shaye hauka ne hala? Ku kuma imbanda jahilci da hauka da rainin hankali wai har ku biye wa wannan tsarin saboda tsabar lalacewa, ai ko a yahudawa ba za a sami masu irin wannan aikin ba…” su duka hudu sai dukansu ruwan sama ke yi, ita kuwa sai faman zuba take yi, tana fadan tana kara jin haushin abin, cen QASIMU ya kada baki yace, har yanzu dai cikin mayen yake, “ke nan gidana ne ni keda ikon in tsara duk yadda na so ba wata shegiya da ta isa ta hana ni, da zan gina gidan, Naira nawa kika bani?” Ya fara zarar belt daga kugunsa. Wasu hawaye suka fara kwaranyomata, ta rasa hawayen me ye, na zama mijinta jahili, mahaukaci, marar kishi, lusari, wawa, dakiki ko me? Ta kalle shi ido cikin ido ta ce “QASIMU wallahi bari in gaya maka, kalle ni da kyau, zan iya daukar irinka biyu ba tareda na gaji ba” ya kalleta ya tabbatar ko a jeji suka hadu ba abinda zai iya yi mata. “ko ka dawo cikin hayyacinka ko in illtaka da wannan tabaryar, ku kuma ku fita gidannan tun kuna kalluwa ko in muku raunin da har makiyanku sai sun tausaya maku” jin haka suka kwashi kunyarsu sumu-sumu suka nufi waje cikin ruwan sama da iska, sa’arsu daya iskan ba karfi. Ya juyo ya kalleta sai haki take kamar wacce ake yi wa kidan tauri a ka, gaba daya ya tsorata domin bai taba ganin ta shiga yanayi irin wannan ba, ta kalle shi ta ce. “idan ka ga dama ka iya shigowa, idan kuma abokaninka za ka bi ga hanya cen” ya dubi ruwannan kara karfi kawai suke yi, ya nufi daki, sai makyrakyatar sanyi yake yi, ta ajiye tabarayar ita ma ta nufi dakin a fusace.



Ta tarar da yaranta suna cikin damuwa, ta gyara musu inda za su kwanta, inda ta shimfida dayan tabarmar domin su kwanta ita da mijinta.



Su ASHCO kuwa, daga fitarsu sai sabbatu suke suna fadan, kai wannan matar akwai masifa, ita ko irin wayewarnan ta zamni ba tada, amma fa gaskiya ta iya girki kawai dai ’yar masifa ce. A haka har suka karaso inda za su kwana, gaba daya tufafin jikinsu sun jike su kuwa sun sha kashin ruwa sosai har da makyarkyatar sanyi su ke yi.



Har yanzu dai QASIMU kallonta kawai yake yi, ya kuma tabbata a buge ba abin da zai iya a jikinta, sai kawai ya ci gaba da mitarsa, ita kuwa ta ci gaba da rarrashin yaranta, musamman BILKISU da ta lura hankalinta ya tashi.



Washe gari bayan sun iyar da sallah suka dauko kur’ani suna karantawa kamar kullum, har zuwa wani dan lokaci suka dora Karin kumallo, ba da jimawa da kammala Karin nasu ba sai ga driver ya iso, sun fahimci hakan ne, sanadiyyar har cikin gidansu FATIMA ta shigo, bayan sun kammala gaisawa da mahaifiyarta, ta suri littfanta da dan kwandonta wanda ke dauke da abincin da za ta ci dama ta jima da shiryawa suka fice.



Kamar kullum; yau ma ita ce zakara a bayar da amsoshin da malamansu ke tambayarsu a cikin aji, wanda shi ne dalilin kara tunzurar da mahassadanta.



Da suka tafi cin abincin tara, haka suke nuna kyama gareta a fili, dalilin da ya yi sanadiyyar FATIMA ta shigar mata fada, har suka bata da abokaninta. Sai fada suke; yanzu kan ‘yar talakawa kike fada da mu? Hala kin manta inda muka fito, kin manta shakuwa da muka yi da ke? Ta amsa musu , “idan dai haka ne zaman tare, ba shakka ba inda wannan tafiya za ta kaimu sai ga halaka, shin mun manta cewa da mai kudi da talaka duka bayin Allah ne? ku dakata nai muku tambaya, shin mu da iyayenmu suka mallaki dukiya, wata gwaninta suka yi wa ubangiji ne ta sanadiyyarta ya basu dukiya? Shi talaka daga sama ya fado ne ko kuwa an gayamuna cewa ubangiji bai san da zamansa ba? Kar mu manta, shi fa ubangiji a ko da yaushe kan aiki yake haka mutum ba wanda aka kammala halittarsa, ta yi wu, mu iyayenmu masu kudi ne, amma mu a talakawa ubangiji ya rubuta za mu kasance, ba wanda ya isa ya canja hakan, ta yi wu ita da take diyar talaka dama cen mai arziki ubangiji ya halicceta. Duk yadda muka ga mutum mu daina wulakantashi.”



Wasu daga cikinsu jikinsu ya yi sanyi, inda wasu suka buge da tsaki suka suri jakunkunansu suka wuce aji duk da cewa da sauran lokaci, a cewarsu, su ba za su saurari wa’azinta ba, bayan wasunsu sun rafke da Kabbara.



BILKISU kuwa hawaye sai faman kwarara suke daga kumatunta, ta kalli FATIMA ta ce, “bai dace ki bata da abokaninki ba a kaina, abinda suke fada gaskiya ne, ni diyar talakawa ce, su kuma diyan masu kudi ne, sun fi dacewa da ke ba ni ba da kika sani a kankanin lokaci…”



“kada ki kara furta komai, ashe dama za ki iya juyamin baya tun tafiya ba ta yi nisa ba? Duka zama ko mu’amala da ba ta ubangiji ba ba ta da amfani ko wacce iri ce kuwa, da suke da kudi, a aji ai kin fisu kokari, kinga kuwa ba ko’ina ba ne kudi suke abin azo a gani.”


Suka rungume juna suna faman kuka wanda sam ba ka jin sautukansu.



Zuw wani lokaci, suka wuce aji domin daukar darasi. A cikin aji sai harararta abokaninta suke yi, inda ita kuwa BILKISU ta sha jinin jikinta kamar wacce aka dorawa kan bindiga a ka, dalili da yasa malamai da dama suke tambayrta ko lafiya kuwa.



Da aka tashi daga makaranta suka nufi gida kowa ya shiga sabgar rayuwarsa.



Da misalin karfe shida na yamma bayan tasowarta daga Islamiyya ta tarar da taro a unguwarsu, da kyar ta samu ta kutsa tsakankanin jama’a ta shiga gida. In da ta tarar da mahaifiyarta sai kokarin izar wuta take da kokarin dubawa ko abincin da ta dora ya kusa ya nuna. “me ke faruwa Inna naga taro a unguwa, har da masu waka maza da mata”? “’yan siyasa ne suka zo wai campaign, nima saurin da kika ga ina yi domin na halarci wurin ne, na ji me suke tafe da shi”. “Hmm! Inna kenan; wadannan mutanen fa ko kusa ba sa tausayin talaka, ba abin da ke gabansu face su yi amfani da kuri’ummu su jefa mu rana, ki duba duk rana da yunwa da muke sha a layin zabe da barazana da muke fuskanta daga makuwwata siyasa, karshenta sai kiga sun zo sun manta da mu ko su dinga wawasar dukiyoyinmu, ba za su sake dawowa ta kanmu ba, sai lokacin da siyasa ta gabato, amma saboda wautarmu mun kasa mu fahimta” wani ajiyar zuciya SAJIDA ta yi tare da kallon ‘yarta wacce kullum take yi wa kallon mamaki, saboda fasaha da masifar zurfin tunani da ya yi katutu a kwakwalwarta. “ba shakka haka ne, amma ai yanada kyawu mu halarci wurin, ko ba komai za mu ji alkawaruka da za su yi, idan ma ba su cika ba ohonmusu” “Allah dai ya kyauta”. Ta shige daki ta shirya ta fito taya mahaifiyarta aiki. Da suka kammala, suka fita tare domin saurarar me ‘yan siyasa suka zo m,asu da shi na alkawari.


Har yanzu labarin bai fara ba


08034840276

DR. ZAIN
[2/3, 4:47 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




🅾9⃣





Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```





_Life is 10 percent what happens to you and ninety percent how you respond to it._








*Shafin Masoya*




Zainab Idris Makawa
Fiddausi Sodangi
Menu gee
Chuchu
Queen Mermu
Nafee Anka
Asy Khaleel
Aunty Baraka
Hauw Auta







***CI GABA***




Haka unguwar ta cika makil da dimbin jama’a kama tun daga maza tsofaffi zuwa mata, ga samari ga yara kanani, a cen dayan bangaren kuma motoci ne da aka cika bayansu makil da na’urori masu amsawa da fitar da amo, sai wakoki ke tashi na ‘yan takara, har wasu wakokin ba ka ma jin me ake fada sanadiyyar wasu wakokin na shiga ta cikinsu.



A bangare daya kuwa, wani minbari ne aka kafa wanda ke da fadin daukar mutum uku kacal, inda nan duka wanda zai yi wa mutane magana yake takawa ya tsaya.



Fitowar SAJIDA da BILKISU suka yi dai-dai da wanda ke magana a lokacin, shi ne dan takarar gwamna a karkashin jam’iyya mai adawa



Nan ya shiga zayyano musu alkawaruruka na abubuwan da zai yi musu idan suka zabe shi a matsayin gwamnansu. Wannan shi ne dalili da yasa sai kuwwa mashaya ke yi suna fadar “sai ka yi” duk da ana amfani da amsa amo mai karfin gaske, a sama-sama kake iya jiyo zantukan masu magana kan mimbari saboda wurin ya cika makil da jama’a kuma suka kasa yin shiru.



Kusan magariba, aka fara watsin kudi, wanda shi ne dalili da ya hautsina wurin gaba daya, aka fara sare-sare fada kazami ya kaure wurin nan aka fara aika wasu barzahu kan ‘yan kudi kalilan, ganin haka SAJIDA ta suri ‘yarta suka fada wani gida, su kuwa ‘yan kuwwar siyasa sai faman daga takubba sama suke yi suna kokarin kai wa juna sara ko suka.




‘yan takaran kuwa tun da suka watsa musu kudin suka bar wurin, wasunsu ma har sun jima da fita unguwar.



Kai talakan Nigeria, yaushe za ka san ciwon kanka?



Zuwa lokaci mai tsawo, ana dauki ba dadi tsakanin wadannan jama’a da mafi yawansu abokai ne, tuni wurin ya cika da jini, haka kasar wurin ta fara rufewa da gawarwakin baraden siyasa, cen sai ka fara jiwo jiniya ta motar ‘yan sanda, wanda ya yi sanadiyyar wasu suka ranta a na kare, wasu kuwa suka tsaya. Isowar motar, ba su yi wata-wata ba suka fito cikin sauri, suka fara duka da kama duk wanda suka gani, inda su kuma baraden siyasar suka fara mayar da martini na dukan da saran.



Har bayan isha ana wannan dauki ba dadin



Gaba daya unguwar ta rude, wasu da dama a gidajensu ko abinci ba a daura ba.


SAJIDA kuwa ba ta sami damar fitowa daga inda suka labe ba sai da misalin sha dayan dare har da mintuka, gaba daya hankalinta a tashe kasancewar ta baro AMEESHA ita kadai a gida, sai faman zubar hawaye take. Cikin sauri har da hadawa da gudu take tafiya inda take janye da hannun BILKISU sai faman tuntube take, amma ko ta tsaya ta duba, kasancewar hankalinta ba ya kanta. Daga shigowarta gida sai faman duba take inda za ta ga AMISHA, shigowa da za ta yi a daki sai ta tarar da ita tana barci, ashe tun da ta bar ta tana barci ko farkawa ba ta yi ba, dalili da ya sa ta yi ajiyar zuciya kenan tareda karasawa cikin dakin. Saukar mari kawai ta ji a kumatunta har sai da ta fadi cikin firgita da razana, waigowa da za ta yi sai ta ga QASIMU tsaye tuni ya zare belt dinsa daga tsugaggen kugunsa, kafin ta motsa daga faduwar da ta yi, ya fara shauda mata belt din, ya bugamata a ka ya buga a bai ya buga a jiki, ta rasa ta ina za ta kare duka. BILKISU kuwa sai faman kuka take tana fadar “ka yi hakuri” nan ya jawo ta ya maka a kasa ita ma ya shiga dukanta, kukan da ta ke yi mai dauke da sauti mai kara, ya farakar da AMISHA.



“don ubanki ina kika fito? Wato halayyar nan taki ba za ki taba sauya ta ba ko? Da zarar na fita sai ki suri kafafuwanki la’antattu ki fita? Babbar matsalar ma ko sisi ba kya kawowa, yanzu da a ce fitar nan da kike yi kina dawowa da wani abu ai da ba matsala. Dakata ma don uwarki ni da abokanina za ki yi wa Bura uba ranar ko?” yana fada yana zabga mata belt a wuya, BILKISU sai kokarin karemata take yi.



Ya dake su son ransa, kana ya fita wurin yawonsa na dare.


BILKISU ce ke rarrashin mahaifiyarta tana kokarin share mata jini da ke tsiyaya daga jikinta. Cen AMISHA ta fara ihun yunwa take ji, dalilin da yasa mahaifiyar ta tuna tun kammala girki da ta yi fa kafin magariba suka fita, sallar magarib da isha duka suna a kansu. Cikin sauri ta tafi inda ta ajiye abinci ta debo mata suka suri buta ita da BILKISU suka yi alwala suka yi sallah bayan sun kammala Sallah ne suka ci nasu abincin, da misalin sha biyun dare.



Haka suka ci gaba da jinyar juna, barci ya kasa zo musu. Cen kusan biyun dare ta jiwo shigowar maigidanta, duk da ba abin mamaki ba ne a wurinta amma dai yau abin ya taba ta, ya shigo sai mashalo yake yana tangadi na masahaya, tun daga nesa za ka jiwo shi yana warin giya sai faduwa yake yana tashi, da kyar ya samu ya dafa kofar shigowa gidan, kasancewar gidan ba kyaure ya shigo kai tsaye. Ya zube a bakin kofa sai faman zuba amai yake yi, da ya kammala amansa ya fadi nan sai barci, ga shi ane-ane cikin amai jikinsa duk kasa ce ga wasu uban takalmi a kafafuwansa.



SAJIDA kuwa kuka ya dawo mata sabo, ta tada kai sama, ta ma kasa furta addu’ah, ta kalli yaranta da gaba daya sun yi barci, ta sake kallon inda QASIMU ya bige da barci, wani bakin ciki ya sake dasuwa a zuciyarta hawaye kuwa suna rigangar sauka daga kumatunta, kawai ta ci gaba da karatun kur’ani da dama shi ne ya hanata barci.



Tun da asubar fari ta tashe shi ya je ya yi sallah, ama kamar kullum ya hauta da masifa. “wai shin rami daya ne za a saka mu? Ince kowa da nasa ramin? To me ye na damuwa da lamurrana? Wai ke ustaz, wa ya san mugun ta’adin da kike yi, mu za a ci da burga? Mu za a nunawa tsoron Allah, mu da muka ga manyan malamai irinsu…” kawai ya sake bigewa da barci, har da minsharinsa. Ta tada yaranta suka tafi yin alwala ita kuwa ta ci gab da lazumi.



Har yanzu labarin bai fara ba, amma saura kiris mu shiga labarin
[2/3, 4:52 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾



1⃣0⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```





_A musician must make music, an artist must paint, a poet must write, if he is to be ultimately at peace with himself. What a man can be, he must be_








*Shafin Masoya*


'YAR BABA
FATIMA SANI IDI
MINISTAN MATA





***CI GABA***




Da misalin karfe uku ne na rana, amma za ka dauka tsakiyar dare ne yadda gaba daya sama ta canja, haske ya kaura daga garin Maiduguri, wani iska mai dauke da sautin ban tsoro kawai ke tashi kuma yana dauke da kura wacce ta yi sanadiyyar kwashe duk wani mai tafiya kan titi ya nemi wurin fakewa.


Cen ruwa masu tsananin karfi suka fara sauka na tsawon lokaci, sai zuwa bayan isha ruwan suka dauke. Daga nan sanyi ya gauraye garin gaba daya, sai daidaiko kake hango mutane masu wucewa kan titi, inda ruwa suke kwararnya a indaruruka kamar a bakin kwarya.



Tun lokacin gaban SAJIDA yake yankewa yana faduwa, gaba daya hankalinta ya tashi, sai faman taslima take yi da kokarin karanto ayoyin kur’ani domin ta kwantar da hankalinta, amma abin ya ci tura. Dalilin da ya sa ta saka a jikinta cewa ba shakka a wannan daren akwai mummunan abu da zai faru.



Kan tabarma suke zaune ita da yaranta, inda take kokarin koyar da su karatuka da suka koyo daga aji a Islamiyya. Shigowar QASIMU ba ko sallama cikin dakin ya mayar da hankulansu ya zuwa bakin kofa, sai haki yake yi, idanuwansa kuwa kamar wanda aka bai wa gashi aka kwace, ba ko takalmi a jikinsa, gaba daya hankalins a tashe, wannan yanayi ne da ko matarsa ba ta taba ganinsa ciki ba bare yaransa.



Ganin haka ta mike tsaye cikin kidimewa da tsananin tsoro, a fuskarta kuwa alamomin tambaya ne a shimfide wadanda ke bukatar sharhi da fashin baki. “me ke faruwa” ta fada muryarta na rawa, yawun bakinta suna kokarin subucewa makogwaronta.. ya kasa furta komai, sai kokarin nuna bakin kofa yake yi, yana so ya yi magana amma kamar wanda aka sakawa rodi a makoshi. Ganin haka sai ta nufi bakin kofar domin ta ga ko wasu ne suka biyo shi. Abin mamaki, har ta fito a tsakiyar gida ba kowa, kuma gaba daya unguwar tsit ba hayaniyar cewa biyo sa aka yi, hakan ta sa ta ci gaba da tafiya har ta karaso kofar waje, ta leka garka. Amma sai ta fara shinshinar ba lafiya, ksancewar a lokacin ba zai kai karfe goma na dare ba, amma gaba daya ba kowa kan titin, illa sai wani sanyayayyen iska da ke kokarin ratsa mutum, wanda ya yi sanadiyyar kara fitowarta da kyawu domin ta ga me ke faruwa. Fitowar da za ta yi, sai ta jiwo karar bindiga Taaa! Ai ko nan ta fadi dirsham, da rarrafe ta fada cikin gida, gabanta sai dukan uku-uku yake yi kamar zauciyarta za ta fito daga makwancinta. A rikice ta fado daki, ta janyo yaranta ta rungume a jiki. Bakinta na rawa ta ce “’yan…b..b..ko haram..ne” ai ko nan BILKISU ta kara shigewa a jikin mahaifiyarta. QASIMU kuwa ya koma cen gefe cike da tsoro sai kallon matarsa yake yi ya kasa furta komai.



Cen sauti mai masifar firgitarwa ya tashi, wanda yayi sanadiyyar hatta ginin gidansu sai da ya fara girgizawa yana zuba, cikinsu kuwa sai kugi da rura yake kamar wadanda ake yamutsawa, AMISHA ta fashe da kuka mai tsananin sauti, inda BILKISU ke kokarin rarrasarta da kuma kokarin dafe bakinta domin ta daina fidda sauti, SAJIDA kuwa sai faman kallon yaranta take yi, inda gogannaka ya fara fitsare wandonsa, cen sautin bindiga ya fara tashi, sai Taa! Taa! Kake ji ta ko’ina har sai ka rasa sanin daga ina sautin ke fitowa.



Cen suka jiwo an shigo gidansu, ai ko suka kara narkewa a juna, shi QASIMU tuni ya mutu daga inda yake a kwance, idanuwansa kadai ke motsi sai zuciyarsa da ke bugawa, amma sam hankalinsa ya fita daga gare shi kan tsoro da firgici. Suka shigo dakin nasu kai tsaye. ‘yan boko haram din su biyu ne, kowanne rike da bindiga AK47 rataye a wuya da wani mariki mai tsayi, a jikinsu duka kakin sojoji ne sai dai sun rufe kawunansu da rawani, haka sun rufe bakinsu, dalilin da ya sa ba zaka iya fayyace su ba ko da kuwa ka san su karti ne majiya karfi ainun, sai a kugun kowanne daga cikinsu, Bam ne sai wukake manya guda biyu, a kafadarsu kuwa harsashi ne a ake yi wa hadi da bindigar da suka dauko. Kallonsu kadai ya isa ya sakaa mutum ya kidime ya rasa ina zai dosa ya rasa me ke masa dadi.



Cikin murya ta firgitarwa suke tambayarsu, ina maigidanta, sai a lokacin suka lura ashe QASIMU tun shigowar wadannan ‘yan boko haram din ya shige cikin kwamacala ya rufe kansa da kayan da ke kusa, makyarkyata da yake yi kan tsoro ita ta ankarar da ‘yan boko haram din cewa fa da mutum a cikin kayan, wanda ya sa daya daga cikinsu ya shuri kayan, sai ga QASIMU ya fado tim har da kuwwa cikin rauni, ya kalle shi ya ce “shege maza na a jeji kai kana nan sai sharholiya kake yi da mata ko” ya fada dai dai lokacin da ya kai wa SAJIDA Kallo. “tuba nake ranka ya dade..” ya share shi da mari, ya ce “dan shegiya” ya iza keyarsa ya sake kai masa shuri da mari duk a lokaci daya. Nan SAJIDA ta kara matse yaranta a jikinta, sai zubar hawaye take yi.



Dan boko haram din ya juwo, ya ce “lallai yau dole mu dandana dadin da kake sha kai ma, matar nan taka za ka bamu muji dadi da ita, idan mun gama kuma za mu tafi da ita inda muke zama mu ci gaba daga inda muka tsaya. “haba yallabai, ai ba sai ka gayamin ba, wallahi ku tafi da ita na baku halak, ga diyarta nan ma idan ita bata ishe ku ba duka ku hada ku tafi da su, nidai ku yimin rai, kar ku taba lafiyata ko rayuwata”



Jin haka dan boko haram din ya juyo cike da mamaki ya kalli QASIMU ya sake kallon SAJIDA, sai ya ce da shi; “kai wanne irin lusari ne da ba ya kishin iyalinsa, duk inda muka je sai munsami mazaje na kokarin kare iyalansu daga fyade ko muzgunawa amma kai da kanka kake bayarda matarka, ba ka da kishi ne?” yallabai ai banga amfani yin jayayya inda baka da karfi ba, a ganina ai wauta ce” “ko kuma wauta ce ka kiyin yunkurin ceton matarka ba”

“don Allah kar ku ketamin da mutunci, ku tafi da ni na aminta, amma ku barmin yara na don Allah, kun fa ce musulunci kuke yi wa aiki,amma wannan aikin naku sam bai yi kama da na musulmi ba, ba aikin musulmi ba ne yin fyade ko satar matan mutane ba, hasali ma musulunci ya yi fada da wannan mummunar halayyar. Don Allah ku ceci rayuwar yara na”



Nan dan boko haram din ya shareta da mari ya ce “ke! Lallai wuyanki ya yi kauri”



Suka janyo QASIMU a gabansu suka dora wuka a wuyansa suka yanka, inda su kuwa suke kuka kamar rayukansu za su fita. Daga yanka shi suka nufato su SAJIDA, ganin sun banbare AMISHA daga jikinta, wani sabon karfi ya shigo ta, ta mike tsaye idanuwanta suka rufe, ta suri dayan dan boko haram din da tandara a kasa kaji Kumm! Kansa ya fado a kasa, sai jini ke fita ko motsawa bai yi ba ya mutu, ganin haka dayan ya yo cikinta, kafin ya karaso shima ta yi cikinsa suka fara kokawa, ya dauke ta ya buga a kasa, ganin haka BILKISU ta fita a guje ta dauko tabarya, ko da ta dawo yana kan mahaifiyarta yana kokarin cire mata tufafi, ta saita da kansa ta maka masa tabarya, kafin hankalinsa ya dawo ta sake maka masa, ya fadi, mahaifiyarta ta mike, ganin yana motsi ta amshi tabaryar ta ci gaba da maka masa, har sai da ya daina motsi. Ba shiri ta goya AMISHA ta ja hannun BILKISU suka fito a guje daga gidan, fitowarsu suka hango an tara jama’a nesa da su sai harba bindiga ake yi kowa ya kwakkwanta a kasa, dalilin da yasa suka sudada kenan a hankali suka hau hanyar jeji suka fara gudu ba kama hannun yaro.



Labarin zai fara a shafi na gaba


08034840276

DR. ZAIN



[2/3, 4:52 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾



1⃣1⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```




_Do not think about the past_

_Accept the Present._

Think for the Future, and _face tomorrow with a sweet and beautiful smile._









*Shafin Masoya*


*YAN GUDUN HIJIRA FANS*




***CI GABA***




Sai gudu suke faman zubawa kamar wadanda kafafuwansu za su cire, a bayanta Amisha ce ta goyo, inda ta rike hannun Bilkisu da hannunta daya, sai faman zabga gudu suke yi, duk inda suka yi nisa da gudu sai su waigo suga ko ana biyar su ta baya. Sautin bamabamai kuwa da na bindiga su suke kara musu kaimi wurin gudu da ganin sun tserata da rayukansu. Sai gudu suke wani sa’in su fada rami kasancewar ba wuta kuma ba hasken wata, wani sa’in su gwaru da kafafuwansu da manyan duwarwatsu da ke kafe a cikin kasa. Amisha kuwa kuka ne kadai nata, gaba daya Sajida ta jike da zufa sharkaf kamar wacce aka zubawa ruwa a jiki, gashi kaffuwanta duka sun fashe sai zubar jini suke, amma a jikinta ba ko alamar gajiya ko nuna kasawa a haka ta ci gaba da gudun ceton rayukan yaranta da tata rayuwar. Bilkisu dole ta jure duk da ta gaji, amma gajiyar ba ta nuna a jikinta ba.



Su ne ba su tsaya ba, har sai da suka tabbatar da cewa sun daina jiyo sautuka da karar bamabamai da harbin bindiga. Sai haki suke kamar wadanda zuciyoyinsu za su fito daga makwancinsu. Suka tsaya cak a tsakiyar jeji, ta duba gabas da yamma kudu da arewa ba mutane ba alamun mutane, ta tada kanta sama, ta ga ko taurari babu, a kunnuwansu kuwa sautuka ne na kwarin jeji da ke fitowa daga nahiyoyi daban-daban da ramuka da suka cika jejin, danye batak ciyawa da ta kawata kasar jejin.



Ta kalli yaranta, kawai ta fashe da kuka, ganin haka sai Bilkisu ta rungumeta Amisha dai har yanzu faman kukan take, tun mahaifiyar na rarrasarta har ta gaji ta bar ta. Sai ta tada kanta ta ce; “ya ubangiji kana kallon hali da yanayi da muke ciki, munsan da cewa ba mantawa da mu ka yi ba, ya ubangiji ka kawo muna dauki, ka kalli yanayin wadannan marayu da nake tareda su ka yi jinkai gare mu” ta sake fashewa da kuka.



Nan suka ci gaba da tafiya cikin sunkurun jeji ba tare da sanin ina za su nufa ba. Sai ketan ciyawa suke, saboda tun shigowarsu jejin ba kan hanya suke ba, sun shigo ne a guje su kawai abinda ke gabansu shi ne su tserata da rayukansu. sai da suka tabbatar hankalinsu ya kwanta kafin suka sami karkashin wata itaciya ta dorawa suka zauna, dole ta cire hijabin da ke jikinta da tun lokacin da suka fara gudu yake a wuyanta, ta shimfidawa yaranta, bayan ta laluba ta tabbatar ba mugayen kwari a wurin, ita kuwa ta kishingida a jikin icen. A haka ta zama maigadin yaran, inda su kuwa suka bige da barci. A rayuwarta sai sake-sake kala-kala take yi.



A cikin gari kuwa, da ‘yan boko haram suka ga wadanda suka tura a gidan su Sajida ba su fito ba, sai aka tura wasu su uku domin su gaya musu cewa su fito an kammala operation za a wuce ne masauki, shigar su gidan, suka tarar da gawarwakin mutanensu biyu da gawar Qasimu, cike da mamaki suka tsaya kan gawarwakin, daga bisani suka tura dayansu ya sanar da shugaban tawagar, ya hadashi da wasu masu aikin daukar gawarwakin wadanda aka kashe, suka zo suka kwashi mutanensu suka fita. Da za su bar garin wasu saman motoci Hilux wasu kuwa kan Babura sai harba bindiga suke a sama suna kabbara wasu kuwa suna ihu. A haka har suka fita daga garin.



Haka jama’ar gari suka wayi gari cike da bakin ciki da zullumin abinda ya faru cikin dare, in da kowa idanuwansa sun yi jawur kamar wuta sanadiyyar rashin barci da kusan duk mazauna unguwannin da abin ya shafa ba su sami runtsawa ba.



Malamai kuwa tun kammala sallar subahin suka shiga yin nasihohi domin kokarin kwantarwa wadanda aka dauki yara ko mutanensu da hankali. Sai jiyo kara ka ke yi ta amsa kuwwa daga masallatai daban-daban.



‘yan jaridu kuwa sai kokarin neman labarai suke daga jama’ar da abin ya shafa.


Sajida kuwa har safiya ta waye ba ta rumtsa ba, sai gadin yaranta take yi, ko motsi ta ji sai ta tashi ta duba ko me ye tafe. Kasancewar ba ruwa, dole taimama ta yi, ta yi sallah. Duk da gajiyar gudu da rashin kwanciyar hankali, Bilkisu da Amisha suka farka a lokacin sallar subahin, kasancewar mahaifiyarsu ta saba musu da tashi a lokacin. Bayan sun iyar da sallah, suka tashi suka ci gaba da tafiya cikin jeji, da ba su san ina za su nufa ba. Kuma iya inda kallonsu ya tsaya, ba abinda suke hangowa sai shirgegen jeji da dimbin ciyawa kore kuma danye shar.


Ita ce a tsakiya, inda ta riko Amisha a hannun dama, ita kuwa Bilkisu tana daga gefenta na hagu. Sai tafiya suke ba mai cewa kowa uffan, tun suna tafiya cikin dungun safiya har rana ta fara ketowa har ta fara zafi duk tafiya suke yi, ba abinda suke haduwa da shi face, dimbin ciyawa sai yashi da manyan duwarwatsu da ke jibge cikin jejin. Cen da rana ta haura sosai kusa da tsakiya, sai Amisha ta fara neman abinci, cikin matsanancin kuka mai dauke da sauti mai karfi. Dalilin da ya sa dole mahaifiyarsu ta tsaya da tafiyar da suke yi. Ta duba gabas da yamma kudu da arewa, sama da kasa, ta ga ba abinci kuma ba mafitarsa a kusa da su, ta sunkuyar da kai hawaye suka fara rigangar fitowa suka jika gefen kumatunta. Ta tada kanta ta kalli yaranta duka biyun, nan take hawayen suka kara karfi wurin gangarowa. Ta fara dube-duben ina za ta sami wurin da ke da inuwa domin ta ajiye su. Cen ta hango icen kalgo ya yi girma sosai, sai ta ja hannun Amisha ta kaisu karkashin icen, ta cire hijabinta ta shimfida musu, ita kuwa ta shiga jeji domin ta nemo masu abinda za su ci. Bayan ta gaya musu cewar kar su kuskura su daga daga wurin.


Tana tafiya tana zubda hawaye na tunanin yanayi da ta baro yaranta a ciki, ta tsunduma cikin jeji tana neman abinda za ta kawowa yaranta, duk inda taga zugu na surkukin itace, sai ta je gun ta bincika ko za ta sami abinda za ta yanka ta kawowa yaranta. Amma har rana ta karkata daga tsakiya ba abinda ta samo.


Su Bilkisu kuwa sai faman hamma suke yi, Amisha tun tafiyar mahaifiyarta take kuka, shimfide a kirjin yayarta, inda take kokarin rarrasarta, amma abin ya ci tura. Hakan ya sa ita ma ta fara kukan saboda tausayaw kanwarta. Cen sun yi nisa cikin kukan da ba mai rarrasar wani, suka jiyo motsi da sautukan tafiya, kuma sautin sai kokarin dumfaro su yake yi. Cikin tashin hankali Bilkisu ta mike zumbur, tashin da za ta yi sai ta ga wani mutum da a shekaru zai haura arba’in, rike da kwari da baka, gaba daya jikinsa a hargitse, da alama ya kwashe kwanaki ba tareda ya yi wanka ba. Cikin rudewa ta suri kanwarta domin su gudu, sai ya yi mata alama da hannu cewa shi ba zai cutar da su ba. Sai ta tsaya. Ya karaso daf da su ya zauna. Ya yi numfashi mai tsayi bayan itama ta zauna sai ya ce; “Bauyar Allah ga ku yara kanani, me ya kawo ku wannan jejin mai matukar hadari?” Nan ta kwashe labarinsu ta gaya masa. Bayan ya sake ajiyar zuciya ya soma; “gaskiya ku tashi, akwai wani masauki da na killacewa irinku, muna tareda mutane sama da ashirin ni nake fita ina samo mana abinda za mu ci, kuma kunga idan kuna cikin jama’a hankalinku zai fi kwanciya, kai ga kuna a nan ku kadai” “ban ki ta taka ba, amma, mahaifiyarmu ta bamu umarni kan kar mu yarda mubar wurinnan har sai ta dawo” ya yi murmushi, ya ce tau shi kenan, bari na zauna na jira dawowar mahaifiyar taku” “su mutanen da za ka nemowa abinci fa?” “kar ki damu” ya fada cikin sakin fuska. Ya cire kayan farautarsa ya ajiye a gabansa, suka ci gaba da tattaunawa.



Cen sai ga Sajida ta dawo, gaba daya a jiggace, kafafuwanta burum-burum, hawaye kuwa kamar a yanzu suka fara zubowa, kasancewar duk yawon da ta yi, ba abinda ta samo, kuma ga shi lokacin har rana ta fara sanyi. Ganin yaranta tareda wani, hankalinta ya tashi, ta karaso wurin a guje, daga zowanta ta ce; “wa ye wannan kuma mamanne?” “wani bawan Allah ne Umma…” ta kwashe labarinsa ta gaya mata. Bayan ta yi ajiyar zuciya, suka gaisa. Sai ya nuna musu su tashi su karasa masaukinsu. Suka dugunzuma gaba daya ya zuwa masaukin, inda su duka ba abninda suka saka a cikunansu, sai rurin yunwa suke.



Ina za su je?
Me za su tarar?
Duka ku biyo ni a shafi na gaba.




DR. ZAIN
[2/3, 4:52 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾



1⃣2⃣



Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```





_Don’t walk as if you rule the world…Walk as if you don’t care who the hell rules the world._








*Shafin Masoya*



MATA TUBALIN AL'UMMA

GIDAN BUKI


***CI GABA***






Tun daga nesa za ka fara jiwo sauti da wasannin yara kanani, inda hayaki ke kokarin tashi ya zuwa sararin samaniya. Filin wurin an gyara shi sosai duk da cewa a kewaye da shi ciyawu ne da manyan itace, tsakiyar a share yake kuma a tsabtace. Manyan mata su ne ke kokarin gyara wuta domin gasa abinda aka kamo ko dafa abinda aka samo na abinci, inda yara kanani maza da mata ke ta zagayar filin a guje da wasanni kala-kala. Duk da Amisha na dauke da yunwa kuma ga masifaffiyar gajiya, sai da ta murmusa, alamun ta ji ndain zowa wannan wurin. Ganin isowarsu, gaba daya jama’ar wurin suka yo cincirindo suka nufato su da sannu da zuwa, inda wata tsohuwa ta gabata ta ja hannun Sajida suka wuce ta kai ta wani daki da aka zagaye da itace, sai ciyawu da aka rufe itacen da su ta yadda za su ba da kariya daga dukan rana ko saukar ruwan sama. A cikin dakin kuwa ba komai face fako, alamun a kasa ake kwanciya. A ranta tana kwatanta rayuwarta ta gida da wannan dakin, sai ta yi murmushi ta kara godiya ga ubangiji ta ce a ranta; tabbas duk halin da mutum yake ciki idan ya kasa ya yi godiya ga ubangiji ya yi butulci. Nan ta tunanmin da wakar wani mawaki wai shi ZAINUDDEEN ZAIN DR. ZAIN wakar mai suna brighter star, inda yake cewa; _‘ko a bakin kura dole ne mu gode Allah, a gunsa kadai muke nema idan muka yi salla_…..” sai ta fito domin ta janyo yaranta. Cen ta hango su zaune cikin yara suna cin abinci, ita kuwa sai ga tsohuwa ta kawo mata nata abinci. Ta koma cikin dakin domin ta ci nata, da ta kammala ta fito aka bata ruwa ta sha. Sai ta hango wasu za su tafi debo ruwa. Budar bakinta ta ce; “dama da ruwa ne nan kusa da mu?” tsohuwa ta kalleta firgigi, ta ce; “ruwa akwai su amma ba kusa ba, ko za ki bi wadancen ne?” “e saosai, domin munada bukata da ruwan gaskiya”. Ta kira yaranta suka bi wadanda za su tafi diban ruwa a rafi.



Mata uku ne a gabansu kowacce rike da abin diban ruwa, wanda aka sassaka daga ice, sai ita da ta sako yaranta a gaba tsakaninta da matan uku, sai tafiya suke yi, matan na fira inda ita kuwa hankalinta gaba daya ba ya nan, ta shiege duniyar tunani tuni.



A ranta tana cewa; dama mutane zasu iya rayuwa a kungurumin jeji haka? Tabbas na yarada duk bakin da ubangijin ya tsaga ba zai hana shi abninci ba.



Haka suka ci gaba daa tafiya har suka karaso rafin, bayan sun dauki lokaci suna tafiya. Wuri ne da ya kawatu sosai da ruwa da ke gudanawa a guje, sai ‘yan duwarwatsu da ke kafe daga ciki ruwan wadanda mutum zai iya takawa domin ya zauna ya yi wasa da ruwan ko ya diba, ba wasu ciyawu a kusa da ruwan kasancewar a bakin kogin yashi ne mai dimbin yawa wanda shuka ba za ta iya rayuwa a kai ba. Kuma abinka da jejin Maiduguri mai masifar zafin rana (lol).



Ta koma daga gefe ita da yaranta domin su wanke jikinsu, kasancewar sun jima ba su sakawa jikinsun ruwa ba. Inda sauran matan ke kokarin dibar ruwa da za su koma da su domin amfanin jama’a.



Suka kammala dibar ruwa sai suka jira su domin su karasa wanke jikinsu, da suka kammala suka dugunzuma su duka ya zuwa masaukinsu, inda suke tafiya suna fira da kokarin kwatatnta rayuwakansu na gida da na nan wurin. Har suka karaso masauki. Bayan sun ajiye ruwan, mutane suka shiga shirin yin sallah kasancewar lokacin rana saura kiris ta fadi. Da suka kammala sallah, gaba dayansu suka taru, maza a gefe daya mata a gefe daya, aka gabatar musu da wani katon akushi cike da abinci da gasassun zomaye da namun jeji daban, kowa ya zagaye akushin suka fara ci, sai ci ake yi ana fira, mazan da ba za su haura uku ba, sai matan da suke su bakwai har gami da tsohuwa, yara kuwa su tara hadi da su Amisha. Su ne ba su kmmala cin abincin ba har sai da loakci isha ya gabato.



Aka taru gaba daya wuri daya, dattijo ya ja su a sallah. Da suka idar, kamar kullum, ya gabata ya ja hankulansu ya kuma yi musu nasiha da rarrasar zukatansu kan ibtila’I da suke ciki.



Bayan ya kammala, suka taru su duka gaban wuta da aka hura domin yin fira, bangaren maza daban inda yara suke cakushe tareda mata, sai fira ake yi tsakanin juna cen sai tsoho ya gabata, ya ce yanada kyau idan da wani cikinku da yake da labari da zai fadakar da mu, ya gabata ya bayar, amma kafin mutum ya bayar da labarin da yake tafe da shi ba shakka, ya gabatar muna da kansa ko da kuwa mun sanshi, lura da a tattare a mu akwai baki.



Nan take kowa ya yi na’am da wannan shawarar.



Nan wani daga taron ya mike tsaye, shekarunsa ba za su haura, arba’in ba, duk da gemunsa yana dauke da furfura, gashin kansa ya yawaita kuma ga shi a hautsine, fari ne a jiki, amma farin ya garwayu da tsawon lokacin rashin ganin ruwa wanka, har fatar jikinsa ta rina ta fara baki, gajere ne, ba ya da kauri sosai,amma muryarsa tanada nauyi. Sai ya gabata.



Sunana Shu’aibu, an haife ni a garin Maiduguri, a nan na girma duka karatuna tun daga primary har secondary a nan na yi, haka ni ma’aikacin gwannati ne, inda nake aiki da Nitel. Inada yara biyu da matata daya.



Wata rana ce da ba zan taba mantawa ba, naje dauko yarana daga makarantar da suke karatu, yaran sun fito har sun fara murmushi da murnar sun hango mahaifinsu ya zo makaranta daukar  su kamar kullum. Kawai sai sauti da karar bindiga suka fara tashi, gaba daya mu da ke wurin muka rude, muka rasa sanin ta ina ne wannan sautuikan ke fitowa, ko da hankalina ya dawo, kawai hango karamin dana nayi, mayakan boko haram sun dauke shi tare da wasu yara, sai kuka yake yana kiran sunana, ni kuwa ba abinda zanmasa sai kuka nake yi, suka ci gaba da yin harbi ta gefenmu, mutane sai zubewa suke yi a mace, ganin haka, muka ranci na kare muka fara gudu, su kuwa suka biyo mu da mashunansu, mune bamu tsaya ba sai da muka tabbatar da cewa mun bace musu a cikin latsetsen jeji.



Kwana da kwanaki muna yawo cikin jeji, mu hadu da wannan bala’in yau gobe mu hadu da wancen masifar, duk wadanda nake tare da su su hudu suka mutu, ni kadai na rayu ya zuwa wannan ranar, har zuwa lokacin da ubangiji ya hada ni da wannan dattijon mai nagarta. (ya nuna mafaraucin da ya kawo su SAJIDA). Shi ya kawo ni nan ya bani kulawa da tsaro.


Gaba daya mutane da ke wurin suka yi tsit, kamar wadanda aka dorawa wuka a wuya.



Cen sai wata tace, “saura ka bamu labarin da ka ce zai amfane mu kamar yadda aka sanar cewa, duk wanda ya gabatar da kansa ya kuma bamu labari ko kadan ne.”



Ya girgiza kansa, ya ce “ba damuwa, zan baku labarin NUSAIBA littafin *Zainuddeen Zain dr. zain*, mai suna SAKACI”




DR. ZAIN
[2/3, 4:53 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




1⃣3⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```




_Some people are just so FAKE that if you look properly at the_

_back of their neck, you’ll find a tag saying “MADE IN CHINA”_









*Shafin Masoya*


*Online Hausa Writers*






***CI GABA***




*DANDANO DAGA LITTAFIN SAKACI*
Na *ZAINUDDEEN ZAIN DR. ZAIN*




Mota kirar camry ce yake cikinta, , mai kalar siminti,duk da cewa sauti ke tashi a motar na wakar 2pac a dai dai gabar:  A FUGITIVE MY OCCUPATION IS UNDER QUESTION WANTED FOR INVESTIGATION, EVEN THOUGH AM MARKED FOR DEATH AMA SMOKED TILL I LOOSE MY BREATH MOTHERFU…… ANY TIME I SEE THE PAPER I SEE MY PICTURE, WHEN THEY NIGGAZ GETTING RICHER THEY TRYNA GET CHA, ITS LIKE  A MOTHERFUC…..TRAP, AND THEY WONDER WHY ITS HARD BEING BLACK, DEAR LORD CAN YOU FEEL ME? STRESSED GETTING MAJOR UH…………a wakar HELL RAZOR sam hankalinsa ba ya kan wakar saboda unguwar da yake kokarin kutsawa unguwa ce da tafi shahara da rango, unguwa ce da ke makale a jikin dutsi, sai wata ‘yar karamar hanya da iya mota zata iya wucewa, a bangaren hagu da damar hanyar kwazazzabai ne guda biyu wadanda a duk lokacin damina zakayi zaton wani babban kogi ne da har kamun kifi za a iya yi a ciki saboda tsananin cika da ruwa da sukeyi. A hankali ya dinga taka motar har ya karaso daf da wani gida wanda yake a cikin rango ta bangaren hagu da yake ya dauko hanyar ne daga gabas zuwa yamma. Ganin ya kusa isa daf da kofar gidan kuma ga shi ko kusa bai hango alamun yara da zai iya turawa ba su kira masa SAKEENA saboda ya yi ta kiran wayarta bata daga ba, sai rabon idanu yake yi ko Allah zai sa ya hango wani ko wata yarinya da zai aika su kira masa ita, cen idanuwansa suka hango masa wata yarinya, ba shakka yarinyar tanada kananan shekaru sai dai cike yake da mamaki ganin yanzu iyaka sha daya da mintutuka ita kuma wannan yarinyar  da UNIFORM a jikinta na makarantar gaba da PRIMARY. Ba tareda wani inda inda ba ya daga mata hannu alamar tazo, cikin sauri ta ajiye Jakarta ta taso, tun kafin ya ci birki ya soma magana, “don Allah kinsan SAKINAR gidannan”?


                       “Eh” ta fada cikin sanyin jiki.


                        “Don Allah shiga kice ana kiranta”


                       “tau” kawai ta fada a daidai lokacin da take juyawa.


                     Cikin rabin minti sai gata ta fito, “wai ance bata nan”


                “nagode” ya fada a dai dai lokacin da yake kara yi mata kallo, wannan karon ba irin kallon da yayi mata a farko ba, yarinya ce karama sosai domin shekarunta ba zasu haura sha hudu ba, da ka kalleta kasan irin shiru shirun yarannan ne da sam basa son hayaniya sai harkar gabansu, a fuskarta akwai kwale har biyu, dark ce in complexion, gata ba tsawo, ko kusa bazaka kirata da mummuna ba haka ba kyakkyawar da za’a kira da mahaukacin kyawu ba, tufafin jikinta duk sunyi dauda har idan ka matso kusa da ita hancinka zai shaidama hakan, tanada idanu da ake kira SEXY EYES, ga muryarta sirariya da laushi, UNIFORM din jikinta kirar siminti ne wando da jacket sai farar riga da hijabi fari da sucks farare takalmi kuwa bakake rufaffu, kayan sosai sun mata kyawu sai dai cike suke da dauda. Ko kusa batada SHAPE, amma irin yarannan ne da mama ya cikawa kirji tun suna a kankanun shekaru.



             Daga gayamasa cewa bata nan kai tsaye sai ta nufi wurin da ya daga mata hannu ta taso, ganin haka sai SALEEM ya sake daga mata hannu alamar ta tsaya, cikin murmushi ta tsaya, sai ya fito daga cikin mota yazo har daf da ita, amma shi yana kan hanya ita kuma tana cikin rango, sai yace da ita “me kikeyi a nan”? ba tareda ta furta komai ba ta soke kanta a kasa tana wasa da kasa ta hanyar amfani da sirarun kafafunta.



             Sai ya ce “kodai hutawa kike yi” murmushi kawai ta sake sakar masa



              Sai ya Ce “okay ki je inda kike hutawar bari in gyara PARKING mota sai inzo in taya ki fira” har yanzu dai da murmushi kawai take biyarsa.



            A ransa yake cewa tabbas na sami bagas bari in yi sauri in yi SUBMITTING FILE din wannan kasan ni kamar RONALDO ne bana zubar da chance



                 A dai dai inda ya gyara PARKING sai ga wani mai gida yazo da tashi motar, saboda haka kokari kawai yayi ya sami wuri yayi PARKING, sai sauri yakeyi yana kokarin ya tarar da ‘yar shila, sunan da yayi mata kenan a ransa, yana iyar da gangarewa a rangon sai ya ganta tana kokarin fitowa har ta rigaya ta dauko Jakarta rataye a kafadarta ta dama.


                

             “ya akayi”? ya fada ba tareda ya tsaya ba ko nuna alamar ita yake yiwa magana ba, ganin a kan hanya akwai wata budurwa da ke kokarin wucewa, yana gudun ta gane cewa wannan karamar yarinyar yake kokarin tsaidawa ta raina shi. Kamar shirin littafi ita ma yarinyar ba tareda ta tsaya ba ta ce da shi “akwai mutum ne a wurin”



                 Sai ya ida gangarewa, har sai da ya tabbatar hankalin budurwar ba ya kansa sai ya dawo. Koda ya dawo har ta fita rangon ta fara nisa, amma sai waigowa  take yi ga alama shi takeso taji me yake tafe da shi



                   Cikin sauri ya bude motar ya yi STATER, sai ya fiddo da kansa ta tagar motar yayi mata alamar ta zo ta shigo.




                    Cikin nuna wayau tayi sauri ta shige, har yanzu da Jakarta rataye a kafadarta ta dama.



                       Budar bakinsa sai ya ce “yanzu ina zamu je?”



                          Bayan ta saki murmushi wanda a duk lokacin da tayi shi DIMPLES sukan bayyana a kumatunta, sai ta ce “gaskiya bansani ba”



Ganin yara sun fara angaje ya tabbatar cewa dare ya raba sosai, sai ya dakata da bayar da labarin NUSAIBA wato SAKACI. Aka sallami kowa, inda kowa ya nufi makwancinsa.





DR. ZAIN
[2/3, 4:53 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




1⃣4⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```




_Don't  let the world change your smile  , let your smile change the world ヅ_










*Shafin Masoya*




ASTUU
ZEE BABY
MISS UMMI
INDABAWA


***CI GABA***





Shigarsu yar bukka da aka nuna mata tun zowarsu a mfatsayin inda za su zauna, ta fara duban inda za su kwanta, ko da alama babu tabarma ko abninda zasu shimfida domin dora bayansu, ta fara kawar da ciyawu da datti da suka baibaye bukkar, kana ta cire hijabin da ke wuyanta ta shimfida ta fara kwantar da Amisha, sai ta yi wa Bilkisu ishara da ta je ta kwanta. Tsaye kawai ta yi tana kallon mahaifiyarta, har ta sami wuri cen labin bukka da jingina banta, ta mike kafafuwanta duka biyun, tana kallon inda ta shimfide yaranta. Ganin har yanzu Bilkisu a tsaye take yasa ta kada baki ta ce; “me kike yi a tsaye, ba kya jin barci ne?” “inna inajin barci, amma ai ba yadda zan yi barci na barki a zaune, kina wahala da mu sosai, gamu munzo tsakiyar jeji, inda nake tunanin ba zamu iya kubuta ba, bare ki ci gajiyar wannan wahala da dawainiya da kika sha da mu”.




Murmushi kawai ta saka, sai ta ce; “haba mamanne ya kike zance kamar wata aljihun baya, kin manta ubangiji ya fada da kansa cewa ‘inna ma’al usri usran’ ai babu wani tsanani face ubangiji ya tanadi sauki a karshensa, bature ma ai yana fadar ‘there is always a light at the end of a tunnel’ kada ki biyewa hudubar shaidan har kiyi tunanin wai a wannan jejin rayuwarmu zata kare, ina shinshino zaki zama wata abu gobe wacce kasa gabadaya zata yi alfahari da ita.” “hmm! Inna kenan, ni fa ba yarinya ba ce yanzu” “har gobe ke yarinya ce, akwai abubuwa da bazaki iya hangowa ba yadda ni nake hangensu je ki kwanta” “banajin kwana inna. Shi wancen labari na Nusaiba da alama zai fadakar musamman wurin iyaye da kuma malamai dama yan gari masu halin sakaci ga yaaransu”



Nan suka dauke da fira har barci ya sharesu, cen zuwa ukun dare, Sajida ta tashi domin ta yi nafila kamar yadda ta saba yi a gida. Ta fito a wajen bukkar, ba abinda ke shawagi a kunnuwanta sai kuka da sautuka na tsuntsaye da kuma kwari wadanda wasunsu suna cikin ramukansu, fitowarta ta nufi randuna inda ake ajiyar ruwa, ta  suri moda ta nebo ruwa ta koma cen wurin da suka yi fira, ta fara alwala, bayan ta dan kewaya. Daga kammala alwalarta, juyowa da zata yi sai ta hango dattijo mafarauci tsaye yana kallonta. Da alama tun fitowarta daga bukka yake tsaye wurin. Ba tareda ta ce da shi komai ba ta nufi bukkar da suke ita da yaranta. Ta fara sallah. Ta yi nisa cikin sallah sai Bilikisu ta farka, itama kamar yadda take yi kullum a gida ta tashi ta nufi waje, ta yi alwala ta zo ta fara tata sallar. A haka har lokacin sallar subahin ya yi, sun fahimci haka ne da suka fara jiwo kiran farko na assalatu.



Da aka kammala salla cikin jam’I, wani ya gabata ya yi nasiha ya wa’azantar ya kuma ja hankulan mutane kan cewa ita fa kaddara takan zo ne yadda ubangiji ya tsara, kuma wajibi ne kowa ya yi imani da ita ya kuma karbi duk abinda ubangiji ya zo da shi karkashinta. A haka har rana ta fara fitowa. Dai dai lokacin su kuwa mata tuni sun fara shirin abinda za a karya da shi, bayan sun wanke tukwana, yar kuwa suka shiga jeji suka debo itace a yanga, aka hura wuta aka dora tukwane. Da aka kammala abinci, aka saka shi cikin babban akushi, na maza daban na mata daban, a haka aka ci sai raha da ba’a ake da juna, gwanin sha’awa.



Haka matan suka taru wuri daya, suka wanke akussai da aka ci abinci da su, inda ya yara suka shiga gyaran wuri, su kuwa mazan suka fara gyaran wurin da ake zama, fira, cen zuwa wani lokaci sai suka taru gaba daya inda ake firar, wani saurayi ya gabata, ya fara koyar da su karatu bayan ya kammala karantar  da su tauhidi suka shiga fikihu da hadisi. Da aka kammala, kowa ya kama gabansa, inda mafarauci ya shiga jeji domin nemo musu abinda zasu ci. Suma wasu daga mazajen suka bazama cikin jeji neman abinci. Yara kuwa suka shiga jeji debo itace, inda mata suka yi rafi domin debo ruwa.



Sai tafiya suke suna fira kamar wadanda ba damuwa a tare da su, har suka karaso rafin, suka debi ruwa suka juya domin kowa mmasaukinsu, suna ciki tafiya suka jiwo motsi a gefen hanya, da farko basu kula ba saboda ganin jeji ne ba mamaki ba ne a ji motsi a surkukin ciyawo, amma jin motsin ya yi yawa, sai Sajida ta gabata domin ta shaida me ye, inda sauran matan suka tsaya cirko-cirko suna kallon me zai faru kuma mme ye ke motsi haka.



Ai ko isarta wurin, batasan lokacin da ta ce, “maciji ne” ba. Jin haka matan suka firgita suka ranta a na kare, wasu da ke dauke da ruwan suka wurgar da abin diban ruwa, wasu kuwa suka fara gudu da ruwa a kansu, gaba daya jikinsu ya jike sharkaf da ruwa. Wasu suka nufi hanyar masaukinsu, wasu kuwa suka arta a jeji ba tareda sanin ina zasu nufa ba. Sajida tana daga ciki wadnnada suka dauki hanyyar masaukinsu.



Amisha kuwa ita da Bilkisu suka bi yaran da suka tafi debo itace, idan suka debi a nan su je cen su diba, har kowa ya tara adadin da yake tunanin zai iya dauka, aka nemo bawan kalgo da wasu ciyawu kamar yodo da gijen kurciya aka rubanya sai suka daure itacen da su, wadanda basa iya azawa da kansu aka dora musu, inda sauran suka dauka, aka nufato masauki, su Amisha kuwa ‘yan rakaya kawai suka koma, saboda basuda kwarin daukar itace. Sai fira suke irin ta yara, har suka dawo masauki.



Mafarauta kuwa, wadanda suka bazama, wasu sun sami damar kamo zabbi na jeji, wasu kuma su kamo hwakkara da dai sauran tsuntsaye da dabbobi kamar damo da zomaye.



Shi kuwa dattijo da yake shi kadai yake tashi farautar haka ya nutsa cikin surkukin jeji yana neman babbar dabba da zai kawo, ai kuwa bai dawo ba har sai da ya kamo Barewa. Jikinta gwanin sha’awa.



A gigice suka karasu masauki sai haki suke yi, sai bayan hankalinsu ya kwanta ne suka fahimci, biyu daga cikinsu basu dawo ba, gani haka, hankalinsu ya sake tashi, inda wasu suka ce su basu lokaci idan basu dawo ba, sais u shiga jeji nemansu. Wata ta ce; “muna fa sane a mu matan wanda masaukin, ba inda muka sani sai rafi, ban tunanin za su iya kawo kawunansu gaskiya, zai fi mu jira mazajen su zo, sai muyi musu bayani, wata kila zasu iya gano su, amma idan muka ce mu tafi, to za a yi biyu babu kenan ko ayi haihuwar guzuma.”



Suka hada baki gaba daya, “tabbas zancenki dutse ne”



Ba da jimawa da dawowarsu ba, sai ga yara sun dawo, suka sauke itace da suka dauko, Bilkisu da Amisha suka yi sauri suka dare jikin mahaifiyarsu, ganin ba walwala a tare da su, Bilkisu ke tambayar me ke faruwa, inda Sajida ta kwashe duk abinda ke faruwa ta gaya mata, nan ta sake baki, ta ce, “shi ne kuke zaune ba wacce ta shiga jeji nemansu, idan fa muka bari abinnan ya yi tsawo to rasasu zamuyi, kun ko ga yadda wannan jejij yake dauke da hadaruruka?” kallon ta kawai Sajida ta yi, da farko bataso ta bata amsa ba, amma sai ta ce; “na yi iya kokarina mu tafi, amma na fahimci tsoron jejinnan suke yi, kitaso muje Mamanne. Nasan ke kinada zuciyar tausayi”. Suka tashi ita da ‘yarta, ta ce da sauran, “zamu shiga neman ‘yan uwanmu, idan da wacce zatazo sai ta biyo mu mu tafi” shiru ba wacce ta tanka, ganin haka suka nutsa cikin jejin.



Cen zuwa tsakiyar rana, mazajen suka fara dawowa. Aka kwashe abinda ya faru aka gaya musu. Cikin nuna dmuwa suka fara hanyar inda aka musu misalin cewa daga nan ne suka bazama cikin jeji. Fara hanya da zasu yi, sai suka hango Sajida tafe da matan duka biyu tareda Bilkisu, gaba daya sun jigata. Sauran matan cikin murna suka sheko suka tarye su, suka jawo hannayensu suka zaunar da su. Sai tambayarsu suke me ya faru da su.



Sajida ta ce, ita kawai ta gansu ne zaune a gindin wani ice suna zabga kuka.



Su kuwa sai suka shiga bayar da labarin ainda ya faru da su. Dayar ta ce; “da muka fara gudu, muka rasa ina zamu nufa, ni da ke dauke da ruwa, bansan ta ya na yada ruwan da ke dauke a kaina ba, sai gudu nake ina waigen baya, inda motsi ciyawo da nake takawa, suke kara razana ni har nake tunanin kila macijin ne, kusa da kafafuwana, sai gudu nake ina kara tsalle gudun kar ya harbe ni, ina gudu ina kuwwa, kwatsam na gwaru da ice na fadi, na tashi ba shiri a kidime, na kalli gabas da yamma kudu da arewa, ba mutane ba alamarsu, ba hanya ba alamarta, bansan inda zan dosa ba, kawai sai na ji an dafa nit a baya, na rafka ihu, waigowa da zan yi sai naga wannan bauyar Allah, da yake nasan fuskarta, sai hankalina ya dan kwanta, duk da nasan da kyar mu iya mayar da kawunanmu gida.”



Dayar ita ma ta soma, “tun lokacin da muka yanke da ayari, nake bayanta, ina cewa da ita tsaya ‘yaruwa, amma ina kamar ana sakarwa doki linzami, sai kara gudu take, ganin haka na fahimci, ta rude ne sosai, sai na ci gaba da biyarta, har ya zuwa lokacin da na tarar da ita tsaye tana kallon-kallo, na dafa kafadarta. Nima sai a lokacin na nutsu na kalli jejin da kyau, nna tabbatar ba ita ba, har ni da na biyo tan a tafka kuskure, domin ba za mu iya mayar dda kawunanmu ba a nan masauki.”



Sai taya su murna ake yi da fatan alkhairi.



Nan mazan suka dauki, abin diban ruwa suka je rafi domin debo ruwa, da suka dawo suka hannuntawa matan ruwan su kuma suka shiga aikin dafa nama da aka samo daga farauta, zuwa maraice dattijo ya dawo, aka shiga gyaran Barewa ya zuwa dare. Da aka kammala aka hada abincin kamar kullum, aka zauna aka ci aka sha.



Sai mai labarin jiya ya gabata, domin ya ci gaba da labarin Nusaiba wato daga littafin SAKACI na ZAINUDDEEN JIBRIL ZAIN DR. ZAIN.






DR. ZAIN
[2/3, 4:53 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




1⃣5⃣



Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```







_I can be so mild to give a second chance but not so stupid to give the same loyalty u took for granted_ 😬





*Shafin Masoya*




*kebbi state online writers*

*Gombe writers Association*



***CI GABA***







Dandano daga littafin SAKACI na ZAINUDDEEN ZAIN DR. ZAIN




                         “haba ke da unguwarku kice bakisan inda zamu je ba?” ya fada cikin sakar mata murmushi shi ma.


                          Kada ka bi ta wannan hanyar ta nuna masa hanyar hannun dama da zata iya sada ka da titi, saboda gidanmu ta gefen ya ke, kada wanda ya sanni ya ganni.



                           Cike da dariyar jin dadi ya ce a ransa lallai wannan ‘yar hannu ce, bazan sha wahala ba wurin cinma abinda nakeso na cinma.



                          Sai ya mike ta hanyar hagu hanyar da sam bazata taba sadaka da titi ba kasancewar ta nufaci manyan duwatsu ne sai kwazazzabai, sai da ya tabbatar cewa sun bace ta gefen unguwarsu NUSAIBA sai ya dauki hanyar da zata sada su da babban titi, haka suka hau EXPRESS wanda ya fito daga unguwar BADARIYA zuwa inda har wayau basu yanke shawarar ina zasu je ba.



                        Gaskiya ke kyakkyawa ce ya fada a dai dai lokacin da ya kafa idanuwansa a jikinta yana kokarin leko surar da ta tara, duk da cewa hijabin da ta saka yana hanashi hango abinda yake kokarin ya leko.



                         “Aji na nawa kike?” ya fada ba tareda ya kalleta ba



                            “JSS 3 nake” ta fada cikin sunkuyar da kanta a kasa



                             “Ashe kune manya a makaranta”, ya fada dai dai lokacin da yake kokarin kai hannunsa a nata hannu, ya rika hannun nata ya shafa, ya ga ko kusa bata nuna alamar ta hanashi ko tsawwaluwa a tare da ita ba, sai ya ce “gskiya hannunki yanada taushi kamar inyi ta tabinsa har gobe”.



                                 Murmushi kawai tayi ta sunkuyar da kanta



                               A ransa yace gaskiya bagas ce na samo amma babbar matsala ita ce, wannan CHILD ABUSE ne, domin ko kusa wannan yarinyar bazata wuce shekaru sha hudu ba, kai ai duk cikin Karin ranking ne a iskanci, kaga sai abokanina su SADDAM su sha labari, kuma inmusu kuri cewa ni har ‘yan shila nake harka da su.



                        Ganin yayi iya kokari domin ya hango me ta tara a kirjinta, amma hijabi ya hana, sai ya zura hannunsa ya yi amfani da gefen hannun ya shafa kirjinta, ai ko nan ya sake yimata kallo, ko kusa baiyi tsammanin zasu kai girman yadda ya ji su ba, sai ya gyara hannun da kyawu ya kara matsasu, sai ya ce, “an taba taba maki su”?




                               Tace “a a”




                               Sai yace “ko zaki bani in taba kuma insha”?



                                        Sai ta daga kanta alamar eh

                                    

                                        Ai ko nan ya kara taka mota



                                       Yanaso ya kira abokinsa KABIRU domin ya karbi makullin dakinsa amma yana tsoron dariyar da KABIRU zai ajiyemasa a lokacin da ya ganshi da wannan karamar yarinya, kawai ya cigaba da taka motar har suka fice daga garin BIRNIN KEBBI suka nufa chi GARIN TARASA, “kin taba shigowa wannan garin”? Ya fada a dai dai lokacin da ya aza dayan hannunsa a cinyarta tareda shafa cinyar na wasu lokuta.



                                 Tace “a a”



                                   Sai ya ce “ai nan ne ake kira da GARIN TARASA”



                                 Sai tace “mahaifina yakan zo nan kuwa”

                         

                                      “Ke da gaske” ya fada cike da tsoro



                                        Sai tace “ai da maraice ne sukan zo aiki, bayan ya kammala aikin OFFICE”


               

                           Bayan ya sami wuri ya yi PARKING sai ya fara taba jikinta, ya jima yana wasa da duk ilahirin jikinta (mai karatu yi hakuri saboda akwai under 18 da ke karanta novels, so bazan iya zayyano EXACTLY yadda abubuwan suka gudana ba). Har ta fita sosai cikin hayyacinta, ba abinda ke fita daga bakinta da hancinta face wani nannauyan numfashi wanda yake garwaye da dan sauti mai alamar kuka.



                            Yana cikin taba ta sai suka hango yara sunzo dibar ruwa kasancewar a bakin BOW HOLE suka tsaya, nan ya umurceta da ta dawo kujerar baya, bayan yaran sun wuce, sai suka cigaba da abinda sukeyi wannan karon har hannunsa ya kai a kasanta,sai ga wani dauke da injimi na ban ruwar fadama yazo ya debi ruwa a GALLON da zai zubawa injimi domin injimin ya sami damar tashi, ganin haka sai ya dawo a kujerar gaba ya ce tayi zamanta a ta baya, ya tuka mota suka fice daga kauyen.




Ci gabn labarin ‘yan gudun hijira



Da ya lura cewa mutane sun fara jin barci, sai ya dakata da labarin nasa, inda aka sallami kowa ya nufi bukkarsa domin ya hutu zuwa safe kuma a shiga sabgogin rayuwa.




DR. ZAIN
[2/3, 4:56 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾



1⃣6⃣



Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```






_If you play with me just remember I might sparkle everyday but I still got claws 😼_






*Shafin Masoya*



SAADATU IBRAHIM GUJIYA
MAIMUNATU MUKHTAR KATSINA
SHARIFA GAZBI
MIKAILU HAYAKI
DANMAMMA




***CI GABA***




Cigaban labarin ‘yan gudun hijira




Cen tsakiyar dare, iska ya fara kadawa a hankali, sai kara karfi iskan ke yi wanda sanyinsa da yanayinsa kan mantar da mutum a duk yanayin damuwar da yake ciki, kwatsam sai iskan ya fara kadawa da karfi dauke da sauti mai firgitarwa kuma ga kura da ke biyo cikinsa wacce ta hado da ciyawu da ba sa da karfi da ledoji. Karar kadawar manyan itace kadai kake iya jiyowa sai kuma bugawar shi iskan. Sai kara karfi iskan ke yi wanda karfin nasa ya yi sanadiyyar farkawar da yawa daga cikin mazauna bukkokin musamman da wasu bukkokin suka fara girgizawa suna neman tubekewa.



Tsaye tayi tana kallon ikon Allah, inda a gaban idanuwanta bukka ke tarwatsewa, sai dai kawai kaga mutane kwance, kariyar da suke alfahari da ita ta bukka iska ya tafi da ita. Batasan lokacin da hawaye suka fara gangarowa daga bakar fuskarta ba wacce ke da fadi, ta tada kanta, taga kusan bukka uku, duk sun tarwatse, sai ta shiga tasu bukkar cikin sauri ta tada yaranta ta fito da su ta rungume sai kuka suke yi, inda Bilkisu ta kasa furta komai, ita kuwa Amisha sai zabga ihu da kuka take yi.



Suna a haka sai ruwa suka fara sauka da karfinsu, ganin haka hankalinta ya tashi, ta kara kamkame yaranta a jiki, sai ji take, ina ma tanada ikon mayar da su a cikinta ta yaddda ba za su cutu da wannan ruwa ba, gasu a tsakiyar jeji ba malaba ba wurin buya kasancewar ko bukka daya babu a tsaye gaba daya bukkokin sun fadi.



Cen a gefe kuwa sauran jama’a ne da yara a cikinsu tuni sun fara rawar sanyi tare da kukan neman agaji, inda iyayensu hankulansu yake a tashe musamman mata da suka ga ba malaba ba mafita. Mazan ne suka dage wurin ganin sun nemo inda za asami kariya ko yaya ne, ta hanyar kokarin tada wasu daga cikin bukkokin da suka fadi, amma ina abin ya ci tura domin iskan ya ki ya bar su su kafa bukkokin. Dole suka hakura, suka tssaya wuri daya iska ya dinga dukansu a tsakiyar ruwa masu masifar sauka da karfi.



Amisha sai cira take kamar wacce rayuwarta za ta fita, ga ruwan sai kara karfi suke yi iskan kuma ya ki ya lafa, kamar wanda ake karawa karfi. Wasu ddaga manyan itace da ke zagaye da wurin tuni refukansu suka fara karyewa suna fadowa kasa, lamarin da ya kara tayar da hankulan mutanen wurin ke nan, har wasu matan suka fara fashewa da sabon kuka.



Sajida dai haka ta kara rungume yaranta, tana faman zuba kuka ganin halin da yarinyarta take ciki. Bilkisu kuwa abu biyu ne a ranta, tana tausayawa mahaifiyarta ganin yadda mahaifiyarta ke kokari wada ta tabbatar har rayuwarta za tai ya badawa domin ta ceci rayukansu, sa’annan tana tausayawa kanwarta da ta san ba cikakkiyar lafiya take da ba. Ta kara rungume mahaifiyarta ta fashe da kuka wanda karar saukar ruwa da iska suka hana ajiyo muryarta.



Cen aka yi wo wata walkiya mai haske, har sai ta sa ka ga jiri, sai wata tsawa ta biyo bayanta, wacce ta haddasa tarwatsewar kusan duk ilahiran mutanen da suka taru a wurin, gaba daya sai da kowa ya rude suka dauka ko aradu ce ta sauka a kawunansu, wasunsu har sun fara hanyar jeji neman tsira. Wasu kuwa suka saki fitstsari a wandunansu. Sajida ta kara rike yaranta cikin firgita, gabadaya hankalinta a tashe, batasan lokacin da ta ce, “ubangiji kana kallon halin da muke ciki ka agaza ka fiddamu wannan masifar”




Ruwan haka suka ci gaba da sauka ba tsaiko har gari ya waye.



Da safe duk inda ka duba idan har wurin yanada rami ko kadan ne, to ya cika da ruwa, ba inda za ka yi taku biyu ba tareda ka saka kafarka cikin ruwa ba, wasu wuraren ma ruwan har a kugu suke kawowa mutum.




Ganin yadda wurin ya koma ta yadda zai yi wuya sui ya zama a wurin, sai suka fara tafiya domin neman wani wuri da za su sauka kuuma, bayan sun dauki lokaci suna shawara a tsakaninsu.


Sai a a lokacin suka lura da cewa wata yarinya kankanuwa ta rasa rayuwarta a sanadiyyar wannan babban hadari da ya dauki lokaci mai tsawo yana zubar ruwa.



Aka yi sauri aka kawar da ita kamar yadda musuluci ya tanadar, suka nusa cikin jeji, domin neman inda za a yada zango. Sai tafiya suke cikin tabo da kuma ruwa da suka kwanta a jikin kasa, daidaiku ne cikinsu ke sanye da takalmi, gaba daya kayan jikinsu a jike sharkaf, suna tafiya har hakoransu ke gwaruwa da juna tsakanin na kasa da na sama kan masifar sanyi da ke ratsa su.



Jikin Amisha ya yi zafi kamar garwashi sai cira take kamar rayuwarta za ta fita, dalilin da ya sa, mahaifiyarta biyar taron kawai take yi amma gaba daya hankalinta ba ya wurinsu, tunanin da take, ina za ta samawar wa yarinyarta da magani.



Suka ci gaba da tafiya har tufafin jikinsu suka far bushewa, kasancewar rana ta dauki zafi sosai, kasa ma ta fara shanye ruwan da suka kwanta a kanta, suna tafiya suna duba inda ya dace su yada zango, amma duk inda suka duba sais u ga ba zai yi musu zama ba. Ganin yara sun fara kukan yunwa, wani daga cikinsu ya bada shawarar a dakata ko da a tsakiyar jejijn ne ba lallai sai ansami wuri yalwatacce ba, a nemowa yara abinda zasu ci, in ya so daga baya a nemi inda za a sauka din. Nan take aka yi na’am da shawararsa, aka sami wurii aka zauna. Maza suka runtuma cikin jeji neman abinda yara za su ci. Matan kuwa suka shiga rarrasar yara da ke kuka. Sajida ta nemi wuri ta shimfidar da Amisha ta dora kanta a cinyarta bayan ta zauna kusa da ita, Bilkisu kuwa zaune kawai ta yi, tana kallon mahaifiyarta tareda mayar da kallo ga sauran mutanen da ke zagaye da su. Duk wacce ta kalla, sai ta nutse da tausayi, a ranta tana tuno irin wahala da suke sha a hannun mahaifinsu, tana cewa “wai ko dai munzo duniya ne domin mu wahala..?”



Bayan wani lokaci, sai ga wadanda suka je fararuta sun dawo dauke da namun zomaye da damo da zabbi jeji, nan take matan suka fara gyarawa, duk da ba ruwa  awurin, a haka suka gyara sai aka hura wuta ta hanyar amfani da duwatsu guda biyu aka bugasu suka fitar da wuta, aka dinga dora naman daya bayan daya ana gasawa jan wutar, da aka gasa wani adadi, sai aka bai wa yaran domin su ci, inda daga baya aka gasawa sauran mutane ragowar, ahaka dai aka ci domin a gusar da yunwa.



Suka dugunzuma gaba daya, cikin jeji suna tafiya neman wurin da za a yi masauki.



Tafiya ta yi tafiya, har rana ta fara sanyi, cen suna tsakiyar tafiya sai suka jiwo sauti na kafafuwa a guje tafe ta bayansu, waigowa da za suyi, sai suka hango wasu majiya karfi dauke da makamai, ba mai alamar imani ko tausayi a fuskarsa daga cikinsu, sun tinkaro su a guje. Ganin haka, suka ari na kare suka fara gudu, su kuwa wadannann mutanen suka biyo su a guje da niyyar kama su. Wurin guduwa suka rarrabu, inda Sajida ta mayar da Amisa a bayanta ta goya, ta kama hannun Bilkisu kamar an ba wa yaro alawa ana kokarin kwacewa, suka dubi inda ya musu cikin jeji suka fara gudun ceton rayukansu.



Me zai faru da su?
Ina za su je kuma?
Za su tsira?
Za a kamasu ne?
Kashe su za a yi?
Za ta rabu da yaranta ne?

Duka amsoshinku na cikin feji na gaba.




DR. ZAIN
[2/3, 4:56 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




1⃣7⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_





® *PEN WRITERS ASSOCIATION*





```QUOTE OF THE DAY```






_Don't waste your time with people who seek attention they are just bored with there life._






*Shafin Masoya*



Her Excellency Hajiya Aisha Atiku Bagudu the wife of the governor of Kebbi State




***CI GABA***






Sai gudu suke yi gaba daya kaya da ciyawu da ke shimfide cikin jejin suka dinga fasa kafafuwansu, amma ko da wasa hakan bai raunana su ba, hasalima basusan ma cewa kafafuwansu sun fashe ba, sai  kaimi suke karawa hadi da gudu na ganin cewa sun tserata da rayukansu daga wadannan azzalumai da suka dafo masu. Kara da sauti na wadanda ake kamawa daga bayansu, ita ta hadddasa Karin kaiminsu wurin gudun ceton rai, Amisha duk da jiki ba lafiya kuka kawai take sakarwa, lamari da ya kara saka Sajida a halin na shiga uku, ina zan saka kaina kenan, har ta sa sai hawaye ke kokarin kwarara da idanuwanta, ta rasa me ke mata dadi. Bilkisu kuwa ba babinda take yi sai kokarin taimakawa mahaifiyarta wurin ganin cewa ta dage sosai wurin wannan gudu na ceton rai, sai waigowa take yi tana sanar da mahaifiyarta halin da ake ciki, idan sun yi kusa da su, ta sanar da ita, idan maan kama wata ko wani ta sanar da ita. A haka har aka kama da yawa daga cikinsu. Su kuwa sai gudu suke. Inda ubangiji ya cece su shi ne, da suka sami wani babban dutse suka haye. Ganin sun haye wannan babban dutsen sai ‘yan book haram din suka dakata da biyarsu din, suka fara zagayar dutsen domin su ga ko ba sojoji kan sa kafin su yi shawarar me kuma za su yi.



Sun jima suna zagayar dutsen, kafin babba daga cikinsu ya bayar da umarnin cewa su koma ainahin masaukinsu domin su ajiye wadannan da suka kama, su kuwa wadannan da ke kan dutse a zauna a tattauna a san yadda za a fatattke su har a kama su su shiga hannu. Nan take suka wakilta wasu daga cikinsu, suka kwashi wdanda aka kama din ya zuwa masauki. Saura suka tsaya suna shawara da karatun ta yadda za su bullowa wannan dutsen har su sami nasarar kama wadanda suka dare samansa.



Wadanda suka sami damar dare dutsen sun hada da Sajida da yaranta, sai mutuminnann mai bayar da labarin Nusaiba, da wasu mata guda biyu.



Dutsen akwai fadi a samansa sosai, yanada tayi kuma akwai wuyar hawa, sai dai idan ka sami hayewa gabadaya, za ka ga filinsa tamkar a kasa kake. Yana dauke da itace wadanda suka hada da Geza, Sabara, Anza da da sauran otace da galibi kan fito kan dutse. Iya kallonka ba abinda za ka iya hangowa face fili fallau har sai abin ya firgitar da kai.



Ba wani kyakkyawan shiri, duk da zazzabin Amisha ya tsananta, a haka ta shimfideta karkashin wani babban icen Kalgo, ta barta nan tareda Bilkisu da matannan guda biyu, ta kalli wannan mutumin, ta ce, “bawan Allah ya kamata ni da kai mu shiga wannan jeji mu gani ko za mu iya samun wuri mai saukin sauka kafin wadannan azzaluman su hawo, domin idan suka hawo tabbas kashinmu ya bushe, kan dutsenannan bana tunanin za mu iya tsira daga sharrinsu.” Gyada kai kawai ya yi, alamar gamsuwa, duk da cewa a ransa ba haka ya so ba. Dole ya bi ta suka fara zagayawa suna neman ta inda za su sauka kafin wadannan azzaluman su hawo ta kan dutsen. Aka bar su Bilkisu da fako, zuciyoyinsu kuwa kan bugawa kamar wadanda za su fito daga kirjinsu.



Sai tafiya suke, har suka dauki lokaci mai tsawo, ba inda suka ga dutsen ya kare ko alamar wurin da za a sauka, lamarin da ya kara tayar musu da hankali kenan, ganin sai kara nutsawa suke cikin jeji kuma kan dutse, sai mutumin ya bada shawarar cewa ya fi dacewa su koma, su dauko mutanensu ayi wannan tafiyar ta neman wurin sauka tare, musamman ganin duhu ya fara shigowa. Da farko ta so ta ki aminta da shawarar, sai daga baya ta aminta, suka juyo. Inda suka bar su, a nan suka tarar da su kuwa, hankulansu a tashe, Amisha kuwa kamar wacce ake karawa wutar zazzabi, jikinnnata ya kara zafi, ko motsi na dole kadai take iya yi, Bilkisu kuwa aikin kuka kadai take. Sai da suka yi mamaki ganin nama a kusa da sun a zomaye da bushiyoyi. Dalilin da ya sa Sajida ta tambaye su kenan, “wa ya kawo wannan?” cikin sanyin jiki, Bilkisu ta karba, “mu muka je muka nemo, ni da wannan” ta nuna daya daga cikinsu. Nan take suka gyara naman, suka hasa wuta suka ci. Bataayi mamakin hakan ba, saboda ta san yarinyarta tanada karfin zuciya, kuma tasan komai za ata iya aikatawa domin ta taimaki wasu, bare da yake ga kanwarta na neman taimako.



Bayan sun kammala cin naman, cen dare ya fara shigowa, suna tsakiyar taimama domin su sauke sallolin da ke kawunansu, sai suka fara jiwo sauti cikin Amsa Amo (loudspeaker) kamar haka; “kun nuna bajinta da har kuka iya tserewa mayakanmu, amma munaso ku san da cewa, wannan gudu naku, ba zai tseratar da ku daga hannunmu ba, saboda mun fi ku sanin jejinnan sosai, zai fi muku idan kuka sallama kawunanku, ba zamu cutar da ku ba, dama mu manufarmu mu dora kowa kan turbar Islama, a ajiye karantarwar yahudawa da nasara a rungumi sunna da Qur’ani, kar ku tsorata mu ba azzalumai ba ne, ba ma kisa, jihadi ne muke yi. Ku mika wuya, ba zaku cutu ba.”



Cike da mamaki suke kallon juna, inda zantukan sun ratsa daya daga cikin matn da ke wurin, har da cewa da su, “ya kamata mu gaggauta mika wuya tun da sun tabbatar muna da xewa ba za su cutar da mu ba, ya fi mu ci gaba da wannan gudun da sam ba tsira ko alamu  tsira a cikinsa, ku kalla fa ku gani, wuni daya kenan ba wanda ya saka ruwa a cikinsa a cikinmu, mu kalla fa muga, wanka ba a ma zancensa, abinci a jiye zancensa shima, inaga mika wuya ne kawai mafita a garemu, kunji da kunnuwanku cewa ba za su cutar da mu ba, kuma kan daular musulunci suke gudanar da lamuransu”



Ta jima tana yi wa wannan matar kallon takaici, da jin kamar ta shara mata mari ko ta jefo mata asshar, amma sai ta hadiye, wasu hawaye masu zafi suka fara fito mata, muryarta na rawa ta kalle ta ta soma. “ke yanzu har za ki dauki zancen wadannan azzaluman? Idan da gaske suke yi ke da kike talaka kila ma bakida ilimin book, me ye hadinsu da ke da har za su shigo su dagulamaki rayuwa ta hanyar raba ki danginki da yaranki da mijinki, hakan ne taimako, kuma a naki tunni haka musulunci ya tanadar ko ya koyar? Wannan amsa amo da suka yi amfani da ita, in ce itama yahudawa da nasara suka kawo ta, domin a tarihi bamu taba jin cewa kakanninmu sun yi amfani da irinta ba wurin isar da sako, bindigogi da ke hannunsu, gaba daya na yahudawa da nasara ne. tau su da ke fada da abinda yahudawa da Nasara suka zo da shi, me ye kuma na amfani da kayan Yahudawa da nasara? Tabbas akwai lauje cikin nadi. Ba sa kisa suka ce, kinga tun nan sun nuna maki makaryata ne, domin shakka banayi, ba za su rasa yin kisa a gaban idanuwanki ba, kuma kisa na wadanda basu ji ba su gani ba, ga talaka mai kokarin neman abinda zai sakawa cikinsa, ya nemi inda zai dora awazarsa. Kada kdimewa da neman mafita ya sa ki manta zaluncin wadannan azzaluman ‘yar’uwa, ubangiji da ya je fo mu a wannan halin ba shakka bai manta da mu ba kuma zai nema muna mafita, ko nan kusa komai dadewa ko a duniya ko mu ji dadin mafitar a gobe kiyama. Wannan ita ce jarabawarmu, mu kafe kafafuwanmu, mu dage damtse, ba shakka mafita na kusa, ai duk abinda ya zamo daya, to kamar ya kare ne”



Ta yi ajiyar zuciya har kunya ta kamata, tareda fitar da hawaye. Suka gabata, suka yi sallah har da Bilkisu, sai suka ci gaba d tafiya domin neman inda za su sauka, su kuma ga ko za su sami fita daga wannan jeji, da kubuta daga hannun wadannna makiya Allah da ke biyarsu.


Ganin an dauki lokaci mai tsawo har dare ya fara rabawa, ba tareda ko daya daga cikinsu ya zo ya mika wuya ba, sai suka fara hawo dutsen da niyyar kama su ko su aikasu lahira, musamman saboda sun gindaya musu sharuda da basu damar sallama kawunansu, amma suka ki. Suka biyo su a fusace. Sun jima tsaye suna kokarin neman hanyar da suka bi, kasancewar duhu ya mamaye dutsen sosai, sai sanyi da ke dukan jikin mutum dauke da wani iska mai dadi. Suna tafiya har suka karaso inda suka ci abinci suka kuma yi sallah. Kallon wutar wurin ya tabbatar musu da tabbas sun jima da barin wurin, dalili da ya sa suka kara kaimi kenan wurin ganin sun cinmusu sun tsayar da su.


Su kuwa sai tafiya suke yi, duk inda suka ga alamunsaukar dutse sais u nufaci cen, amma har yanzu ba alamun ta inda z sui ya sauka, dole suka ci gaba da tafiya, har safiya ta  waye. Tun fara tafiyarsu take goye da Amisha, inda sauran suke a gaba ita kuma tana ta baya. Dayar matar da suke tareda ita ce, ta nuna musu gaskiya ita ta gaji, kuma ba za tai ya ci gaba da tafiya ba. Jin haka suka yi tsaye suka yi rarrasarta ta nuna gaskiya ita ta gaji sai dai a yada zango a nan. Mutumin da ke tare da su ne, ya ce, “idan muka tsaya a nan, duk gudu da muka yi cikin wannan jejin za tashi a banza ne, domin inada tabbacin cewa yanzu haka suna biye da mu, zamnmu a nan kuwa dole za su riske mu, ina amfanin badi ba rai ke nan? An yi ba a yi ba kenan. Ki daure ki tashi, ki duba har da karamar yarinya da daure, muyi hakuri, su dai da ke son su zlunce mu suka jure wuya, sai mu da ke kokrin kubuta daga rayukanmu….”



Suka yi juyin duniyarnan da ita, ta ki aminta da ta tashi, suka ajiye akan za su bar tan an, suka wuce. Tafiya ta yi tafiya, ga zafin raina sai kara dukansu yake, ga yunwa na cinsu ta ciki, ga gajiya a tattare da su, amma ba mai alamun tsayawa ko nuna karaya.


Azzaluman kuwa sai tafiya suke kamar wadanda ake karawa karfi, kowannensu da mummunar niyya a zuciyarsa, yana hango irin kisa da wulakanci da z su yi wa wadannan da ke kokarin sakaa su wahala, a cikin wannan sunkurun jejin. Suka ci gaba da tafiya, suna yi suna fira da yin ba’a a tsakaninsu, har suka tarar da wannan da ta kasa tafiya, kwance a karkashin wani ice da ta kare kanta daga zafin rana.



Ganin sun zagaye ta, cikinta ya fara rura, gaba daya yawun bakinta ya kafe ta kasa motsi numfashi ma ba ta san ta ya yake fita daga huhunta ya zuwa karan hancinta ba, cikin kidimewa ta ce, “wallahi sun ganni..”



Suka zagaye ta, sai dariya suke yi, ita kuwa sai kuka take rusawa, tana so ta gudu, amma sai take ji kamar kunkunceta aka yi cikin manyan kacoci.




Me za su yi mata?

Mu hadu a shafi na gaba.




DR. ZAIN
[2/3, 4:56 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




1⃣8⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_





® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```






Never trust someone who lied to you more than twice bcz he won' change at all and will pass for a stupid girl.






*Shafin Masoya*



MATAR YAEESH FANS




***CI GABA***




Sai zagayar ta suke yi, suna yin wata dariya wacce ke kara jefata cikin tsoro da tashin hankali, ganin ta kidime sai shugabansu ya yi alama da hannu, cewar a kashe ta kawai, ya bayar da umarnin ne ganin cewa, idan suka ce su tafi da ita, za ta rage saurin da suke yi na kokarin cinma sauran, haka ba za su iya barinta da rayuwarta ba.


Nan wani ya gabata, ya caka mata wuka da ya zaro daga kugunsa, ya sake daga wukar ya caka mata, har sau uku, duk lokacin da ya caka mata wuka, sai ya juya wukar a cikinta domin ya katse hanjinta, karshe ya tunkudeta ta fadi a mace. Suka ci gaba da tafiya domin su tarar da sauran.


Su Sajida kuwa sai tafiya suke yi cikin matsananciyar zafin rana, ga yunwa ga jikinsu na wari, ga shi ba mai takalmi a kafa, kafafuwansu sun fashe, amma kamar ba su fashe ba, domin ba sa jin zafi ko zafin rana. Suka ci gaba da nutsawa cikin jeji har suka hango inda za a iya takawa a sauka daga kan wannan babban dutse, da suka share awanni suna tafiya a kai. Sai dai matsala daya, wurin da masifar hadari, wanda da zarar ka kalli wurin saukar za ka fara ganin jiri, musamman da za ka zaci wata rijiya ce za ka shiga mai gaba dubu, duk ba wannan ne tashin hankalin wurin saukar ba, irin yadda acen kasan yake da ciyawu da itace manya masu dauke da kaya, kamar su gumbi da sauransu. Wannan ya tayar musu da hankali.



Gaba daya suka tsaya bakin wurin suna kallon ikon Allah. Komai jarumtar  mutum dole zuciyarsa ta karaya, dole ya firgita, saboda hadari da ke ga wannan wurin saukar, musamman da ga alama ba wanda ya taba sauka ta wurin bare, su bi hanyar da ake sauka, su ne zasu buda hanyar.



Ganin sun yi tsaye ba wani motsi, Sajida ta ja hannun Bilkisu, ga Amisha goye a bayanta, ta fara sauka.



Cike da mamaki, mutumin da ke bayan su sai kallonta yake yi yana girgiza kansa, a ransa yana cewa. “tabbas duk duniya ba wanda yakai uwa mace son yaranta, ji wannan masifar, amma a ko da yaushe yaranta take fara kallo, ita ba ta damu ba matsawar dai yaranta za su rayu” ya girgiaza kansa yana mai jinjina mata.



Ganin abinda mahaifiyarsu ke so ta aikata, na jan hannunta domin su sauka tare, Bilkisu ta kwace hannunta, ta ce, “kar ki damu Inna, ki kula da kanki kawai da kuma Amisha insha Allah zan iya sauka, ina daga bayanki, saboda ke ba zan bari na fadi ba. Ba da son ranta ba, dole ta bar ta, ita kuwa ta kara gyara goyon da ta yi wa Amisha, ta ci gaba da sauka. Ganin ta fara nisa, sai Bilkisu ta biyo bayan ta, suna sauka, suna amfai da rike itace da ke jikin dutsen gudun kada su subuce. Mutumin ya umarci dayan matar da ta bi bayan Bilkisu, cikin tsoro ta fara bi ta bayanta, jikinta sai rawa yake yi, da ya ga ta fara nisa sai shima ya biyo ta bayansu, a haka suka dinga saukowa daga kan wannan dutsen. Cen suna cikin sauka, sai matarnan ta subuce, ta fado, haka ta dinga gangarowa ta doki nan ta doki cen har ta fado kasa, amma tun a lokacin gangarowar rayuwarta ta fita daga gareta, gawarta kadai ta isa kasa. Cikin sauri Sajida ta kalli sama, a zatonta Bilkisu ce ta fado, duk da bataji dadin mutuwar wannan matar ba, hankalinta ya dan kwanta ganin ba ‘yarta ba ce ba ta fado. Ta jima tana kallon yadda Bilkisu ke kokarin saukowa kafin ita ma ta ci gaba da saukar.



Haka suka ci gaba da sauka, har suka dauki wani lokaci mai tsawo, kasancewar dutsen yanada tsawo sosai.



Masu biyarsu kuwa, haka suka ci gaba da biyarsu ta amfani da sawu da kuma alamun wucewarsu, ba wanda za ka kalla ya nuna alamun gajiya ko yunwa a tattare da shi sai tafiya suke yi, kamar wadanda aka karawa karfi da kaimi.



Sajida ta fara sauka, kafin Bilkisu ta karaso sai mutumin da ke tare da su. Har yanzu jikin Amisha da zafi, ga shi gaba daya yawun bakinta ya kafe, ba ta iya furta komai, ga yunwa ga ciwo, su kuwa ga yunwa ga gajiya a tattare da su.



Kallon tausayawa take yiwa ‘yarta ganin yadda jikinta ya fashe wurare da dama sai fitar da jini suke, sanadiyyar saukowa daga kan dutsen, amma ko a jikinta, ita ma ta nuna alamun cewa su ci gaba da tafiya, musamman da take ganin duhu ya fara shigowa.



Suka tada kawunansu sama suka kalli ta inda suka sauka, a ranta tana cewa. “lallai ubangiji yana yadda ya so, wannan wurin da mutum zai rantse cewa ya sauka ta nan, ba zan aminta ba, amma yau ni Sajida, ni ce na sauka a nan”



Suka ci gaba da tafiya ba tareda sanin ina za su nufa ba, su dai burinsu kawai su fita daga wannan jejin.



Su kuma suka ci gaba da biyo su har suka kawo ta inda suka sauka, cirko-cirko suka yi, suna kallon ikon Allah, suna kallo da tunanin ya aka yi har suka iya sauka ta wannan wurin. Duk da sun sha training kuma suna kokarin gwada training nasu a aikace, sai da suka karaya da tsorata wurin saukowa daga wannan dutsen. Sai kara tunzura suke yi da sakawa a ransu, matsawar suka kama su, to ba za su yi musu da sauki ba.



Suka fara saukowa daga kan wannan dutsen, wasunsu, dole suka fara saukowa duk da ba da son ransu ba ne. shugabansu shi ne a gaba, sauran na biye da shi, a haka suke amfani da itacen da ke kafe a jikin sutsen gudun kar su fado, suna sauka a hankali, duk da haka sai da mutum uku suka subuce suka fado a mace. Amma sauran ko a jikinsu. Suka ci gaba da saukowa.



Har suka sauko gaba daya, suka ci gaba da biyar sawunsu, wannan karon cikin gaggawa da sauri har da hadawa da gudu, tuni suka kunna fitillunsu masu masifar haske da nan take sukan makantar da wanda duk aka cinnawa haskensu a idanu. Sai sauri suke da zinmar cinma su Sajida.



Su kuwa sai tafiya suke, a gajiye, kawai dai suna yin tafiyar ne saboda ta zame musu dole, amma gaba daya sun yanke tsammani da za su tsira.



Tafiya ta yi tafiya, duk da sanyi na dare ya fara sauka amma gaba daya zufa ke ke fita daga jikinsu, a haka suka ci gaba da tafiya ba hutu, duk inda sua ga wani ice da suke tunani zai iya zama magani, sais u tsaya su diba, ta tattauna shi a harshenta, sai ta sakawa Amisha ruwan a baki, cikin ikon ubangiji kuwa sai ga shi ta fara samun sauki.



Ganin ta fara samun sauki, sai suka sami wuri suka yada zango, suka yi amfani da damar suka yi taimama suka yi sallah, suka dan huta na wasu mintuna kana suka ci gaba da tafiya wacce su karan kansu basusan ina za su dosa ba, kawai dai su fatansu su kubuta daga wadannan azzalumai su kuma fita daga wannan masifaffen jejin.




Su kuwa sai kara sauri suke yi, da nufin cinmusu, domin sunada yakinin cewa ba nesa suke da su ba, musamman da yake sunsan akwai mata da yara tare da su, dole su bukaci hutawa, domin a zatonsu sunada yawa sosai.



Cen dare ya raba tsakiya suka fara hango hasken fitilunsu, dalili da ya sa suka shiga sabon gudu kenan, duk gajiya da suke ji ta kau a lokaci daya, suka fara gudun ceton rayukansu, wurin yunkurawa Sajida ta fadi, dalili da yasa Amisha ta rafka kara kenan, ta fashe da kuka mai karfin sauti har sai da masu biyar su suka jiyo, ai ko suka hasko inda suke, suka tabbatar su ne. suka ce da wa aka hadamu idan ba da ku ba, suka nufato su a guje. Ba tareda jiran su tashi ba Mutumin da suke tare da shi ya ranta a na kare, Bilkisu kuwa ta tada mahaifiyarta suka dauki sabon gudu na ceton rai.




Karshen rayuwarsu kenan?
Duk wahalar da suka yi nan ne karshen rayuwarsu?
Za su tsere musu kuwa?
Me zai faru da su?



Duka amsoshinku suna cikin shafi na gaba.




DR. ZAIN
[2/3, 4:57 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




1⃣9⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```





_Be the first rate version of yourself and not the second version of someone else_ 💃





*Shafin Masoya*



*PEN WRITERS ASSOCIATION*

MAMAN ALEESHA
MAMAN SADIQ
NUSAIBATH
MEENERT FARUK
AMINA GUNABI
KHAUSAR M NASEER
YAR FATHER
AUNTY MUMMY
KAMAL NO LOVE
NORDEEN AMRABAT
NABILA DIKKO
ZAINAB USMAN
DIYUART YUSUF
SHAFA SALFAZ


***CI GABA***



Cikin rashin shiri suke gudu gashi tsakiyar dare ba sa ma gcanin inda suke dora kafafuwansu. Sai kitar jeji suke yi ba shiri, har suka cinma mutumin da ke tare da su suka wuce shi a guje.  A duk lokacin da suka yi nisa da gudu sais u waigo su ga har yanzu biyarsu suke yi, su kuwa sais u kara gudu. A haka har suka cinma mutumin da ke bayansu, suka kama shi. Gani haka hankalin Sajida ya tashi matuka. Suna cikin gudu, sai kafafuwan Bilkisu suka shige cikin wasu ciyawu suka sarke, ta fadi, dalili da ya sa dole mahaifiyarta ta tsaya kenan domin ta tada ta, kafin ta sami tada ta, har sun zagaye su, ganin haka ta rungume yaranta tana fadar, “kuyi wa yarana rai, ni ku tafi da ni, amma don Allah kada ku cutar da marayun Allah”



Sai dariyar mugunta suke yi mata suna zagayar su. Cen sai babbansu ya karaso, aka yi masa hanya ya karaso ta kusa da ita, ya ce, “wannan ce ta wahalar da mu haka, tabbas yau karyarki ta kare, nag a yadda gudunki zai kubutar da ke daga hannunmu, tun farko mun baku damar mika wuyanku, da hakan ba ta faru d ku ba”



Ya bayar da umarnin a zo masa da su. Nan take aka daure hannayensu aka iza su kamar bayi, tareda mutumin da suka fara gudu, ana tafiya ana dukansu da bulala ana kuma izar su sai kace wasu bayi. Cikin mamaki taga babban nasu ya fiddo da wata waya, ya dora a kunne ya koma gefe bayan ya danna lambar da yake so ya kira, ya yi waya tad an lokaci kadan, saai ya dawo suka ci gaba da tafiya. Zuwa wayewar gari suka yada zango a wani katafaren fili mai yalwa sosai. Cike da mamaki tag a sun fito da abinci kalar wanda za a dafa kadai ko a siyo a shago, ko shago irin manyan shaguna, suka fara ci, suka basu suma suka ci, cen sai suka fara jiwo karar mashuna da mota. Ashe wayar da ya yi ya kira ne ya yi kwatancen inda suke, shi ne mutanensu suka karaso domin su wuce da su masauki.



Aka tura su cikin hilux ta baya, sauran suka shiga ta gaba, sai wasu suka hau Babura, suka buga ya zuwa masaukinsu, sai wakoki suke yi da kuwwace-kuwwace.



Sansanin wuri ne mai yawan gaske, wanda aka killace da wata gina da aka yi da laka, wacce ita ce aka yi wani gini da ita da zai ba wad an garin kariya daga masu kawo hari, haka duk wanda zai shiga garin dole tan an zai iya shiga, bayan masu fakon kofa sun aminta da ya shiga. Idan ka shigo harabara kallo dole za ka dinga mayarwa, boda yadda aka kawata wurin da gine-gine dole ka kira shi da kauye mai zaman kansa, ga mutane nan saai sha’aninsu suke yi ana kai da kawo, a ce karshen garin ma bowhole ne da ke bayar da ruwa a duk lokacin da aka bukata, wanda ake amfani da generator wurin ta yar da shi. Akwai dabbobi cikin garin kama daga shanu har ya zuwa kaji da zabbi, lamarin da ya kara nutsar da Sajida cikin mamaki ke nan.



Duk sun ga wadannan abubuwan ne, a lokacin da ake wucewa da su ya zuwa wurin shugaban wurin. Haka aka ci gaba da tafiya da su, inda yara da mata da ke cikin dan karamin garin sai kallonsu suke yi cikin tausayi. Sune ba su tsaya ba har sai da suka karaso wani katafaren wuri, wanda ga alama nan ne ake taruwa domin yin jawabi ko wani babban abu idan ya taso.




Ba da jimawa ba da tsayuwarsu, sai gad an aiken shugaba ya zo, ya sanar da wadanda suka zo da su cewar, an umarce su da su kais u inda za su watsa ruwa su wanke jikinsu su saka wasu kaya kafin shugaban ya zo ya gabatar masu da jawabi.




Cikin gaggawa kuwa aka hada su da wadanda za su sada su da inda za su yi wankan. Shi mutumin aka hada shi da wani tsoho, ita kuwa Sajida wata tsohuwa ta zo ta ja hannunta suka tafi.



Da suka kammla wankan suka canja kaya.



Sosai Sajida ta yi kyawu da tufafin da ta saka, kai ka ce dama tufafinta ne, uwa uba Bilkisu, amisha tuni jikinta ya fara sauki, ashe dama yunwa ce ta haddasa mata zazzabi. Da cikinta ya cika sai gashi ta fara surutu da tsohuwa, har da wasa, duk da hankulansu a tashe suke, Sajida ta ji dadin ganin yarinyarta a cikin wannan yanayi na walwala.



Daga cikin wadanda suka kamo su ya gabata, ya fara yi wa Sajida da yaranta bayani tareda mutumin da ke tare da su. “ajuma kadan shugabanmu zai zo ya maku jawabi, inaso ku karkade kunnuwanku sosai ku saurare ni, kada ku sake ku kalle shi ido cikin ido, haka kadda wanda ya yi magana idan ba umarni aka ba shi ba. Idan kunne ya jiya jiki ya tsira”



Ya tashi fu ya wuce, ya bar sun an sai kallon juna suke yi.



Mutumin ne da ke basu labarin Nusaiba, ya juyo ya kalliSajida ya ce, “yawwa ku bari na karasamuku labarin da muka fara a sansaninmu.” Sai da ta saki murmushi kafin ta gyra zama, bayn sun hada idnu da tsohuwa ta yi wa Amisha alama da hannu cewa ta zo ta zauna a jikinta.


Shi kuwa sai ya ci gaba da labarinsa,




DR. ZAIN
[2/3, 4:59 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




2⃣0⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```





_If you can't find the right words for certain situations just give a smile. Words have potential to confuse but a smile convinces... 😇_







*Shafin Masoya*


MANSUR SUFI
USMAN ANGO




***CI GABA***





Dandano daga littafin SAKACI na ZAINUDDEEN ZAIN DR. ZAIN


                               Fitowarsu sai tace “ka bari mu bi wannan hanyar” sai ta nuna hanyar garin MAKERA wacce take hagun JUNCTION din fitowa daga garin TARASA


                        “Okay” ya fada “akwai inda zamu je ke nan?”

                           
                                   Ta ce “eh!”


                            Ya cigaba da taka motar basu sami wurin PARKING ba har sai da suka karaso a garin MAKERA, a dai dai lokacin da aka tayar da ‘yan makaranta, makarantar da ke a garin MAURIDA wanda titi kadai ne ya raba garin da garin MAKERA, shiyasa sau da yawa wasu sukan dauka duk gari daya ne.


           

                   MAURIDA shi ke bangaren dama idan ka fito daga BIRNIN KEBBI, MAKERA kuwa ita ce bangaren hagu, galibin mazauna garin MAURIDA ARAWA ne sai FULANI da ZABARMAWA


                            Nan ya cigaba da tafiya har suka karso JUNCTION da zai iya sadaka da garin TILLI da ZOGIRMA da BUNZA idan ka cigaba da tafiya, haka zai iya sadaka da KANGIWA da su BUI idan ka bi barauniyar hanya, a dama kuma sai BIRNIN LAFIYA da su ARGUNGU.


                                Sai suka bi hanyar dama sukacigaba da tafiya har suka wuce wani dan kauye wanda tanan ne zaka iya daukar barauniyar hanya zuwa garin BUI da su GIGANE suka sami ‘yar karamar hanya sai suka yi PARKING na mota, ya dawo ta SEAT na baya, sai suka cigaba daga idan suka tsaya, kasancewar kafin su tsaya ya rigaya ya gaya mata cewa ta cire wandonta na makaranta, bayan ‘yan wasanni da yayi da ita sai suka fara, suna cikin yi kwatsam sai ga wata bakauya ta zo ta wuce, tabbas ta hango me sukeyi kasancewar kan hanya suka yi PARKING amma sai ta kawar da kanta kamar sam bata ga me ke wakana ba, asali ma sai kara sauri takeyi, wanda saurin shi ya kara tabbatarwa da SALEEM cewa lallai ta gansu.

                         Ganin haka sai suka kammala a gurguje duk da cewa ko kusa SALEEM bai gamsu ba, ita NUSAIBA da zarar ka kalle ta zaka fahimci haka, nan sukayi sauri ta dawo ta gaba, suka dauki hanyar dawowa gida, suna gudun kar bakauya ta gayawa ‘yan garinsu a illata su.


                             Sai gudun fitar hankali yake yi a dai dai lokacin da ya hau babban titi da zai sadaka da MAKERA zuwa BIRNIN KEBBI, kasancewar titin yana a tsakiyar fadama ne, a gefukansa kakan ga masu sayar da kankana da dankali da dai sauran kayan gwari irin su timatir da albasa. Saurin da yake yi shi ya hana ya tsaya duk da NUSAIBA ta bukaci hakan domin tana so wai ta siya kankana.


                                Sun jima da baiwa MAKERA baya har sun wuce JUNCTION na garin TARASA suka karaso dai dai inda ‘yan sanda ke tsayawa, sai ta ce, a makaranta ance mukawo dari biyar, wai za a buga wasu takardu, ba tareda ya ce komai ba a ransa ya ce, yanzu idan na bata kudinnan ta yuwu karshen haduwarmu kenan, tunda ga shi ta gayamin cewa batada waya.


                                 Sai ya juyo ya ce da ita, “dari biyar kawai kike bukata”?, tace “eh”, sai ya ce “ba damuwa, kibari gobe sai in baki”, “ki gayamin inda zamu hadu”, sai ta ce da shi “kawai ka zo makarantarmu dai dai sabon titi da akeyi na makarantar horar da sojoji, da zarar an tadamu tara sai mu fita”, “okay ba damuwa” kawai ya fada. Tareda girgiza kansa.



                                 Da suka karaso daf da unguwarsu inda zai ajiye ta, sai ta ce da shi, “ko zaka iya zowa unguwarmu da daren yau ka ga idan da dama sai mu fita?”, sai ya ce “ba damuwa zanzo idan aka kammala sallar isha, mu hadu dai dai inda na ganki a kofar gidansu SAKEENA”.


                          Nan ya buga mota ya fice.


                           Ba tareda ya koyi sallar isha baya zo inda sukayi alkawari ya fake, tun bayan magariba yayiwa abokinsa ali magan kan cewa zai zo da budurwarsa saboda haka ya ajiye masa makullin dakinsa inda idan ya zo zai ganshi, sai faman latsal wayarsa yakeyi bugun Samsung note 5, a kusa da shi sai ya ji motsi, dagowa da zaiyi sai yaga nusaiba ce, duhu ya jima da sauka shiyasa ya kasa gano fuskar karamar kanwarta da ke tareda ita wacce iyakanta shekaru takwas zuwa tara, a hannunta bokiti ne kamar da alama ruwa zasu tafi diba. Murmushi kawai ya sakanmata, sai yace wannan fa, kanwata ce ta fada, tareda yi masa dariya a dai dai lokacin kuma take wasa da bokitin hannunta, wallahi anhanani fita ne, shi yasa na dauko bokiti nace ruwa zan debo domin inzo in shaida maka, gudun in barka tsaye kayit jiran tsammani, bayan ya saka murmushi sai ya ce ba komai, si kanwarta tace da shi, yaya ka bani dari biyu ina so in kashe a school gobe. Kash ya fada sai ya fidda yar dubu daya ya ce da ita kin gani wannan ce kadai nakeda banida canji, idan na baki ita kuma gida zaki ci duka, ki bari gobe zan ba nusaiba ta kawo maki, cikin nuna aalamar jin dadi ta ce ba damuwa. Sai ya juya ya wuce, bayan ta kara jaddada masa zancen da sukayi na haduwa a safiyar gobe.



                ‘yan kudin da ke hannunsa duka suka kare a dare, kasancewar mutum ne mai masifar kyauta ga kokarin saka kati a waya,, sai ya kasance a aljihunsa ko aho bai kwanta da shi ba.



                Kashe gari da ya laluba yaji ba ko sisi a jikinsa, sai ya sake komawa barci kashi na biyu, kasancewar baya so ya hadu da nusaiba ba tareda ya cika mata alkawarinta ba.


               Da misalin goma da mintutuka na safe sai ga kiran abokinsa rayyanu a waya, ya shaida masa gashi kan junction na tashar kola yazo ya karbi jersey da zasuyi wasa da ita gobe da maraice, kasancewar yafi kowa saurin fita fili sai ya zo da su, cikin sauri ya taso daga shi sai t shirt sai wando na sport wanda da kadan ya wuce guiwarsa, sai sauri yakeyi, duk da sauti ke tashi a kunnuwansa na wakar ZAINUDDEEN ZAIN mai taken juyin rayuwa dai dai verse three inda yake cewa

“ RAYUWA GUDA CE DAN UWA IDAN KA GANE
MAMA TA FADA A FARKO SAI YANZU NA GANE

IDAN KANADA SHI KAINE ABOKI NA KOWA
IDAN KA RASA A MAKA KALLO NA WAWA

NAI NADAMAR ABUNDA NA AIKATA CEN A FARKO
SHEGIYA RAYUWA TA KASA TAIMANI KARKO


UBANGIJI KAMIN AFUWA KAMUN LAMUNI
ZUNUBAN DA NA AIKATA YA ALLAH GAFARCE NI

MALAM KOMAI KAKE GANI FA DA LOKACINSA
KOMAI SHAKIYANCIN MUTUM AI DA MAGANINSA

NI DALIBI NE NA RAYUWA NA WA’AZTU
GASHI DUK NA KAKKABE NADAWO GIDAN RUBUTU

‘YANUWA MU DAUKI DARASI A RAYUWATA
KOMAI KYALEKYALI NA DUNIYA FA ZAMU BAR TA

KUNCE BANA IYA HAUSA HIP HOP WANNAN ME NENE
GASHI NAYI DALLA DALLA KOWA MA YA GANE”


               Yana tafiya yana yin wakar gashi ya iya sosai kamar shi yayi ta.


               Kanar a mafarki sai ya hango tafiyar NUSAIBA daga nesa tana kokarin nufato hanyar da yake kokarin ficewa daga, tun kafin ta karaso kusa da shi ya tabbatar ita ce, har yau din cikin duda take

                 “Ina zaki je ya fada?” cike da daukin son jin me zata bayar a matsayin amsa



Cen sai aka kira su, dalili da ya katse wannan labari ke nan da yake ba su


DR. ZAIN




[2/3, 4:59 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




2⃣1⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```




_Do not think about the past_

_Accept the Present._

Think for the Future, and _face tomorrow with a sweet and beautiful smile._









*Shafin Masoya*



*YAKI DA RASHIN GASKIYA WHATSAPP GROPU*





***CI GABA***




*Cigaban labarin ‘yan gudun hijira*




Shiru har zuwa maraice, har dare ya soma ba labarin kira daga shugaba, dlili da ya sa suka tafi sabgoginsu kenan, shi ya baiwa Sajida damar zagayawa sosai a sansanin domin shaidawa idanuwanta halayya da yanayi da mazauna wurin suke. Ba shakka taga abubuwa da dama  wadanda suka sanya imaninta ya karo, tausayinta ya karu, haka tsammaninta da kuma jajircewarta da idanuwaanta suka kara budewa. Yanayi da ta ga wasu mata musamman hankalinta ya tashi, yadda gaba daya an kawo su an jibge, akwai abinci sosai, har asibiti akwai cikin wannan sansanin, amma rayuwarka ba za ta tafi yadda kake so ba, shuwagabannin sun fake da musulunci suna zaluntar mazauna wurin, idan ka motsa a kafurta ka, a kasheka kai tsaye, idan ma me ka yi, sai a ce shari’ah ko haddi za a tsayar a kanka. Kuma abin haushi da yawa daga cikin wadannan mabiya boko haram din ba musulmai ba ne, ta fahimci haka, lura da da yawa daga cikinsu ba sa sallah, wasu kai tsaye zaka ga cross a wuyansu. Wannan lamarin ya bata mamaki matuka.


Cen bayan isha sai ga dan aiken shugaba, cewar yana neman su Sajida, da yake su kadai aka kawo a ranar.


Suka gabata a gabansa, kamar dalibai sun zo diban karatu  a gaban malami. Ya fara musu jawabi irin nasa: “nan da kuka zo, kun fito ne daga biladi kufrin ya zuwa biladi Islam, inda za a baku kulawa karkashin kaantarwar addinin musulunci wanda shi kadai ne mafita gareku. Cen inda kuke, yahudawa sun cakuda kafircinsu da al’adunku kun zama ‘yan bidi’ah kuma mushrikai fasikai, nan zamu musuluntar da ku, mu shayar da ku romon musulunci zalla domin gobe kiyama ku samu rabo……..”


Bayan ya kammala jawabinsa, sai ya ce “idan da mai tambaya zai iya yii ko guntun jawabi”



Dama tun fara zancensa, bakinta yake rawa tanaso ta furta zance. Sai ta mikar da hannunta, alama tanaso tayi magana. Aka bata dama, sai ta mike.


“kace zaku bamu kulawa karkashin karantarwar musulunci, naga mu duka ba wacce take muharrama a gareku, me yasa kuka killace mu, ko shima wata karanatrwa ce ta musulunci da bamusan da ita ba? Iya namu karatu, kisa kaba’ira ce da ubangiji ma  ba ya yafe maka gaba daya idan ba kaffara ka yi ba ko masu hakki suka yafe, ku naga kun mayar da kisa kamar numfashi, ko kunyi shi ba kwa damuwa, me hakan yake nufi? Dazu da nake zagaywa, naga mayakanku da dama cikin tantuna tareda mata da aka kamo wasu wurare da alama zamntakewa suke kamar ma’aurata, wannan kuma musulunci ne? abubuwa da dama misali wayar salula kalar tufafi kai har kalar abinci da kuke ci, duka na yaudawa ne da kuka ce karatun da suka zo da shi haramun ne, shi haramun din ba ya aiki ne a kanku? Wadnda wannan hare-hare naku ke shafa, galibi mata ne da yara kanani sai kuma wasu da gaba daya a rayuwarsu ba sa boko, su mnayan masu bokon sunada tsaro wasunsu ma kamar tare kuke da su, idan da gaske boko kuke yaka, me yasa hakan ke faruwa/ dama shi jihadi akan yi shi ne ta hanyar kama yara da mata azo a buya tsakiyar jeji……..”


Kafin ta karasa wani ya shareta da mari, har sai da yatsunsa suka kwanta a kumatunta, nan Bilkisu ta fashe da kuka. Wanda suke tareda shi tuni ya sha jinin jikinsa, ya fara bari, domin ya fara shinshino mutuwa kusa.


Ya sake sa kafa ya shureta, ta fadi a gigice, ganin haka, sai shugabansu ya tada hannu alamar ya dakata. Ita kuwa ba ta damu ba ta waigo ta kalle shi, ta ce. “ni fa ba daren da jemage bai gani ba, idan aka cire daren mutuwarsa, kuma aka yi sa’a ko yanzu kasuwa ta waste dan koli ya dade da cin hajarsa, ba dukana ya dace kayi ba, zai fi kyau idan ka bani hujjoji ta hanyar amsa tambayoyina, domin hakan da ka yi, ya nuna bakada amsa ga tambaya ko daya daga cikin tambayoyi da na yi maku”


Shugaban sai ya karbe zancen, “tun farko mun sanar da ku mu zamu kula da ku karkashin karantarwar addini. Da kike zancen jihadi, ai yaki dan zamba ne, dole sai ka hada da dabaru idan kanaso ka cinma burinka, haka lokaci na zuwa da zamu fito gaba da gaba da ‘yan bokon. Kan mata kuwa, ai ba lalata muke yi da su ba, aurensu muke yi, dama mata biyu nake da, yau dinnan za  aurar min da ke na cika ta uku”


Ya yi alama da hannunsa cewa akira jama’a domin su shaida auren. Cikin mintuna kadan aka tara jama’a.


Tayi murmushi, dalili da yasa shugaban nasu ya tabayeta kenan, “ko kinada abin fada”

Ta ce “sosai kuwa ni keda abin fada”


“ki gaggauta kinga jama’a sun taru”


“a karatu da mukayi a Qurani, idan mace mijinta ya rasu za ta yi idda ne na tsawon wata hudu da kwana goma (Bakara aya ta 234) da cewar _kuma wadanda suke mutuwa daga gare ku suna barin matan aure (ma’ana wadda mijinta ya mutu ya barta) matan suna jinkiri da kansu wata hudu da kwana goma……._


Haka ya zo a Bukhari hadisi mai lamba 1280 da mai lamba 1281 da kuma lamba 5334 ya zo a Muslim 59/1486 ya zo a Abu Dawuda 2299 a Tirmizhi 1195 a Nasa’I 3533 cewa iddar mace tsawon wata hudu ne da kwana goma idan mijinta mutuwa ya yi yaa barta.


Haka akwai wannan zancen har wayau a Bukhari 313 da kuma 5341-5343 a Muslim 66/938 Abu Dawuda 2302 da 2303 Nasa’I 3536 ibn Majah 2087.


Ba nan kadai ba ka duba Bukhari 5336 da 5338 Muslim 1488 da 1489 Abu Dawuda 2299 Tirmizhi 1197 Nsa’I 3540-3543.


Da yake ku malami ne, bana bukatar na sanar da ku cewa haramun ne aure a kan idda.


Ya kwashe da wata dariyar keta, sai ya ce “ ai ba kan idda zamu aureki ba, wa ya gayamaki akwai idda a kanki, kar ki manta fa, ke ganimar yaki ce a wurinmu”


“ganima kuma?”

Ta fada cike da mamaki.


“haba malam, jiya ne fa cikin dare yaranka suka kamo mu, a lokacin da muke kokarin ganin munsami malaba, ba wanda ya gwabza yaki da mu, bare mu zama ganimar yaki, ku daina yin ta’awili kan zantukan ubangiji da ma’aikinsa, kawai domin ku biya bukatunku. Muna ciki gida aka zo aka kashe mijina gaban idanuwana”


“tau kingani, ki ganimarmu ce, kika gudu, ga shi kin dawo hannunmu”, ya fada yana kallon taron jaama’a da suka zo shaidar wannan mugun aure.


Nan ya wakilta wani ya zama waliyyi gareta, aka yi nema aka bayar, aka yanka sadaki dubu, dari, ya biya nan take, aka yi khduba aka daura aure. Duk a gaban jama’a, ita dai Sajida gaskiya ta yi mata yawa, ta kasa furta ko oho. A ranta tana mai cewa, “wallahi da na bari ya yi lalata da ni gara naa rasa rayuwata, wannan ai gara yahudanci da kasan fyade ne za a maka, da wannan zina da sunan daurin aure”


Mutane suka watse, wasu mata suka ja amarya har tantin da ango yake zama, Bilkisu sai kallon mahaifiyarta take, inda Amisha ita ma kllon take baa tareda ta fahimci me ke faruwa ba.


Shigowarsa dakin ta sa matan gaba daya suka tashi suka fita, aka bar bilkisu sai Amisha, ya ce “tau sai ki salami yaran naki ko”


Ta ce. “yaraa ba inda za su je, me kake nufi ne, wannan ba fa aure ba ne, hanya ce ta zina, ina ka taba ganin an yi aure haka? Sai kace auren Aladu?”


Ya harzuka, amma sai ya hadiye abinda ke ransa, ganin haka sai Bilkisu ta fita waje, amma sai ta tsaya kusa da tantin tana sharar kuka. Amisha kuwa sai taa kara matsewa a jikin mahaifiyarta ganin yadda mahaifiyar ta fara daukan zafi, ta fahimci cutar da ita ake so ayi.


Gaanin haka ya zaburo, ya rarumi Amisha daga jikinta, da kyar ya kwace ta ya wurgar da ita, har sai da sautin buguwa da kanta ya yi a kasa ya girgiza mahaifiyarta, inda ta doshi wurin da take a guje cikin matsanancin tashin hankali.




09039951083

DR. ZAIN
[2/3, 4:59 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




2⃣2⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_





® *PEN WRITERS ASSOCIATION*





```QUOTE OF THE DAY```






_We waste time looking for the perfect lover, instead of creating the perfect love._






*Shafin Masoya*


*AMEESHA*
*HALIMA MUHAMMAD*




***CI GABA***







Tana zubar hawaye ta rungumota da zinmar ta rarrasheta, amma sai ba ta ji ta koksa ba, ko motsi batayi ba, sai jini da ya bata mata jiki wanda ke fita daga inda kanta ya yi mummunar fashewa. Ganin haka hankalinta ya kara tashi. Ta sake fashewa da wani sabon kuka, wanda ya sa gaba daya ta ji kamar  ba a jikinta take ba, idanuwanta suka rufe, zuciyarta ta fara zafi. Shi kuwa gogannaka, sai cewa yake, “ki ajiyeta kizo, kinsan hadisi yana fadar duk mace da mijinta ya kirata ta ki ta zo, ya kwana yana fushi da ita, mala’iku zasu kwana suna tsinemata” gaba daya jin surutunsa take kamar ana kara rura wutar da ke tafasa a zuciyarta. Ta juwo da karfi ta yi kukan kura tayo cikinsa, ta kama wuyansa. Ya tunkudeta ta fadi yana fadar “kinada hankali kuwa?” Ta sake mayar da kallonta inda Amisha ke kwance a mace,zuciyarta ta sake rufewa, ta sake kawo masa wawa, ya zame ya kaimata naushi a baya, ta fadi, ta sake tasowa tayo cikinsa, ya sake kai mata naushi a fuska, har ya fasa mata baki, amma ko a jikinta, miki da tunanin rasa yarta ya makautar da ita. Sai yowa take yi cikinsa, shikuwa yana kaimata duka, a duk lokacin da ya daketa, ai ta fadi gaba daya fuskarta ta kumbura tana fitar da jini, amma ko kadan jikinta bai mutu ba, har sai da ya gaji da kansa, da ta kam shi, a wuya sai shure-shure yake yana neman mafita, amma ina ba zai iya kwatar kansa ba hannun Sajida saboda haka kirarta take kamar basamudiya ga tsayi ga kaurin jiki. Ta shake shi har sai da ya mutu, ta wurgar da gawarsa cen gefe. Ta yo gefen ‘yarta ta cigaba da kuka na wani lokaci mai tsawo.



Cen tana kuka ta tuna, matsawar safiya ta waye aka tarar da danyen aikin da ta aikata, tabbas ita da ‘yarta sai dai buzunsu, domin kuwa kashe su za ayi, sai ta leko kofar tantin, ta yi sa’a kuwa Bilkisu na zaune kusa tana faman zabga kuka, ta soke kanta a tsakanin kafafuwanta. Ganin haka sai mahaifiyarta ta je kusa da ita ta dafa ta, cikin firgita ta waigo. Ganin mahaifiyarta ce, sai ta rungumeta cikin sabon kuka.


Ta ce da ita; “ajiye kukan, abinda ke gabanmu yanzu shi ne, muyi kokari mu nemi ta inda zamu fita daga wannan wurin, domin na kashe shugabansu” cike da tsoro ta kalli mahaifiyarta da ke magana jikinta na rawa. “ina Amisha” zancen da ya fara fitowa daga bakinta kenan. Bataan lokacin da ta sake fashewa da wani sabon kuka ba, tana so ta gayamata me ya faru da kanwarta amma kuka ya hana, ganin haka, Bilkiu ta mike zunbur ta shiga tantin, ai ko sai ta fadi kasancewar ta kasa rike kafafuwanta, nan ta fara kuka tamkar an baiwa yaro alawa an kwace, har da ajiyar zuciya. Saai jijjigata take, a tunaninta zata farka, amma ina.


Cen Sajida ta shigo cikin tantin ta fara rarrasarta tana fadar “ki taso mu tafi kafin azzalumannnan su Ankara da ta’asar da nayi, kar gudunmu da kwnakin da mukayi muna shan wuya a jeji su tashi a banza, kinsan matsawar wadannan mutanen suka fahimci me ya faru, sai dai gawarmu”


Budar bakinta, ta ce, “gaskiya umma bazan iya barin gawar Amisha a nan ba”


“ka jimin karanbanin banza, kinaso ki gayami cewa kin fi ni son ta ne? akwai abubuwa da ke faruwa wadanda mutum ba yadda ya iya dole ya rungume su yadda suka zo, wannan kaddara ce ba mu muka tsara ko muka zabi rayuwarmu ta zo a haka ba, tsarin ubangiji ne kuma shi ya fi mu sanin dalili da ya sa ya aikata hakan akanmu, inada tabbaci ubangiji ya mana tanadi da zamu yi farin ciki da shi. Ki zo mu tafi, karshen rayuwarta kenan, babu wani abu da zamu iya yi a kai, abinda take bukata daga garemu shi ne addu’ah”


Ta yi ajiyar zuciya ta mike, daf da zowa bakin kofa, saai ta tsaya, ta juyo ta kalli mahaifiyarta da ke kallon inda gawar Amisha take kwance tana zabgar kuka, ta ce; “inna! Kinada hanya da zamu fita ne daga wannan gari, ki duba fa dazu da muna zagayawa, ko ina cike yake da tsaro mai tsanani da rana ma ke nan, bare da dare, ni fa ina jin tsoro”


Ta yi murmushi ta karaso kusa da ita, ta dafa kafadarta, ta ce “Mamanne kenan, a duk lokacin dabawa ya yi yunkurin aiwatar da abu, kada ya sake ya kalli hadaruruka da ke cikin abinda zai yi, ya kalli ina yake so ya tafi kawai, a lokacin ba abin da zai hana shi isa inda ya dosa, ba shakka bansan hanya ba, amma ke a tunaninki za a rasa wadanda suka san hanya? Kar ki manta akwai tsofaffi a gidannan wadanda sun yi shekaru da dama, dole a cikinsu akwai wanda ya san hanya. Zo muje” ta fada dai dai lokacin da take jan hannunta ya zuwa kofar fita.


Fitowarsu daga kofar da kyaurenta wani labule ne shudi, amma yanada kauri sosai, suka yi kicibis da wani mai aikin tsaro yana zagayawa a cikin garin, sun fito ne a daidai lokacin da yake wucewa ta kan layinsu, rike yake da bindiga AK47 wacce ke make da alburusai si aljihun rigarsa da na wandonsa da suma suke dauke da alburusai da ‘yan bamabamai.


“ina zaku cikin wannan daren?” ya fada yana mai jiran su bashi amsa


Cikin debe damua a fuskarta, ta amsa masa, “dama wannan yarinya ce ta kasa barci tazo ya samemu da mijina, kasan yau aka dauramuna aure, shi ne ya fusata yace in maidata dakinta ko ya yanka ni”


Ya fashe da dariya, ya ce “tabbas wannan karamin aikin shugaba ne, ke yarinya kina kukan rashin mahaifiyarki ne? je ki kai ta kafin ya jiwo zancenmu ya hada da ni ya yanka” ya wuce abinsa. Nan ta kara sauri, hart a karaso inda tsohuwar da ta kai ta inda ta yi wanka lokacin da suka zo. Da kyar ta samu ta tadata, saboda a hankali take tadantan gudun kar yara da ke kwance a dakin su farka. Tashin tsohuwar ta so ta yi magana sai Sajia ta rufe mata baki, da ta gane Sajida sai ta mike zaune, bayan ta sake bakinnata ne tsohuwa ke tambayarta, me ya kawota wurina cikin wannan tsalelen dare. Cikin rashi sanin inda za ata soma, ta kalli bilkisu da tun shigowarsu hankalinta yake tashe, kamar wace za atura a rami da ranta, sai ta cewa tsohuwa. “iia, nasan dai kinsan duk anda ya taimaki wani, shima ubangiji zai taimake sa, ba dogon suturtu nazo muyi ba, akwai babban al’amari da ya faru kuma ke kadai ce za ki iya taimakamani, ni da wannan marainiyar” “me ye ya faru ‘ya ta?” ta fada cike da son jin amsa daga Sajida. “iya….ta yi shiru, hawaye suka fara sauka daga kumatunta ta kasa furta komai. Ganin haka tsohuwa ta dafa kafadarta ta ce, “kar ki ji komai gayamin matsalarki, insha Allah zan sharemaki hawayenki” “ki taimakemu ki unamuna hanyar guduwa daga wannan garin, wallahi matsawar muka kwana a garinnan to da safe kisan gilla za a yi muna” “kisan gilla kuma? Ke da kike auren shugaban wannan garin gaba daya, wa ya isa ya tabaki, haba ‘ya ta” ta fada tana kokarin janyo ta a jikinta “bazaki fahimta ba ne” “ai sai ki fahimtar da ni” “na fa kashe shugaban, kashe ‘yata ya yi ni kuma bansan me ya faru ba, kawai naga gawarsa a hannuna” ta sake fashewa da wani sabon kuka, a wannan karon hard da sauti.


“lallai kin aikata babban aiki” ta yi shiru na wani lokaci mai tsawo, sai ta kalli Sajida ta kalli Bilkisu, cikin tausayi ta mike tsaye, ta ce “ku biyo ni.”


Suka biyota, ta shiga gaba suna biyarta bayan sun fito daga tantin, duk inda za su bi sai tsohuwar ta leka sai ta ce da su su dakata, ida tag a ba kowa sai ta fara wucewa daga baya sai ta yi musu alama da hannu cewa su zo, sais u biyo bayanta ahaka har sukayi nisa da tafiya cikin garin. Saura kiris wani ya gansu, sai suka shige wani tantani suka labe da ya wuce suka fito suka ci gaba da tafiya. Haka suka ci gaba da tafiya har suka karaso a wani tanti sai tace su shiga ciki, da suka shiga, tsohuwa ta tayar da wani saurayi mai kimanin shekaru sha tara, cikin firgita ya tashi, ganin tsohuwar ce, sai ya yi shiru, ya mata alama da hannu cewa lafiya. Ba tareda ta bashi amsa ba, ta jawo hannunsa suka fito, suka ci gaba da tafiya, har suka karaso wurin wata Katanga, daya bayan daya sukaa dare katangar, amma kafin su hau katangar sai da tsohuwa ta yi musu bayanin cewa, ita ba za tai ya biyarsu ba, domin za ta tsayar da su ne, haka idan ta bisu za a zargi wani abu, kawai su tafi, shi kuwa saurayin ashe dama jikanta ne, tamasa alkawarin wata rana za ta fitar da shi, shi ne take gayamasa cewar lokacin ne ya zo.


Ta yi bankwana da su ta kuma yi musu fatan alkahairi. Dadi a zuciyar Sajida kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha.


Ai ko suna kammala tsallakewa suka fara gudu na fitar hankali. Abinka da mutum mai zurfin tunani, ashe Sajida ta debo makudan kudi daga tantin shugabansu, bayan kudin sadakinta da aka damka mata a hannu, ta daure su a zane cikin leda, da su take gudu a jikinta. Bilkisu da saurayi ma sai aikin gudun suke yi.



Shin su rayuwarsu kullum a gudu suke?
Ina kuma za su dosa?
Duk amsoshinku na a shafi na gaba




DR. ZAIN
[2/3, 5 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾



2⃣3⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```






_On average, women say 7,000 words per day while men manage just over 2,000 words._








*Shafin Masoya*




*MUGIRAT MUSA*



***CI GABA***





Ba zancen tsayi ko wasa, saboda sun rigaya sun san cewa matsawar suka tsaya aka tarar da su a wannan karon ba zanncen kamu ba ne, kisan gilla za a yi musu, duk gudun da suka dauki kwanaki sunayi zai tashi a banza kenan.


Sai ketar jeji suke yi a kidime hankulansu a tashe, idan suka dauki kamar awa biyu suna gudu sai su tsaya su huta, a haka har safiya ta waye suna kan gudu. Ganin hasken rana ya bayyana, ya sa suka tsaya suka yi taimama suka yi sallah, ba tareda sun tsaya doguwar addu’ah ba suka cigaba da aikin gudu.


A gari da suka fito kuwa, dama shugaabannnasu shi ke bayar sallah, da lokaci subahin ya yi aka ga bai fito ba, aka dan kara minti goma, ind wasu ke tunanin auren da ya yi e ya hana shi fitowa sallah da wuri, aka gabatar da wai ya jagoranci sallar.


Da suka ga har ga shi safiya ta waye ama ba shugaba ba alamunsa, kasancewar duk safiya yakan hau mimbari ya yi musu irin huduba da ta kamace su. Ganin haka, sai wani ya je kofarsa ya dinga yi sallama, ganin ya dau lokaci mai tsawo yana sallama, amma sam ba alamun za a amsa, ya sa yazao ya sanar da saura mutane, sai wani na kusa sosai d shugaban, ya zo ya shiga dakin, ai ko nan ya yi tsaye ya sha jinin jikinsa, yana cikin dakin ya yi kira da babbar murya, cewa “ku zo ku ga abinda na gani” nan sama da mutum biyar sukaa rugu cikin dakin. Sai kallon gawar shugabansu suke yi wacce hart a fara kamewa sosai, a gefe kuwa gawar Amisha ce, da ke kwance cikin jini. Nan take wani daga cikinsu, mataimakin shugaban ya bada umarnin a kawar da gawar ta shugaban ayi mmata sutura, ita kuwa Amisha ayi wurgi da gawarta cen cikin jeji. Ya fito ya hau mimbari ya soma jawabi.


“saninku ne duk mai rai mamaci ne, kuma a iya zamanku na wannan garin kun shaidi adalci daga garemu ta hanyar baku kulawa yaddda adini ya ce a baku, amma kamar kullum ita musiba haka take bibiyar mumini har ya zuwa ranar da zai hadu da ubangijinsa, jiya annoba ta sauka a wannan garin namu da ta yi sanadiyyar salwantar rayuwar shugabanmu, tabbas kaddara gaskiya ce, haka daukar fansa ma gaskiya ce. Mu ke fita domin takara, ama yau mu aka zo har gidanmu neman magana, to walahi inason ku shaida, ba za mu kyale wannan cin fuska da akaa yi muna ba, za mu duki fansa, idan na ce fansa, ina nufin fansa da ake kira fansa. Ba wadannan kadai ba da ke da hannu a cikin abin d ya faru ba, hatta asu alaka da su a wannan garin sai mun nunamuku azabar da zasu sha kafin wadanncen su shigo hannu”


Ya yi alama da hannu cewar wasu su gabata a gabansa, sai ga wasu karti biyar majiya karfi wanda kowannensu idan ya yi kashi a jeji ya umarceka da ka korewa kashin kuda bazaka bari kuda su taba masa kashi ba kan masifar karfi, ga kowannensu kato a kirar jiki, kuma duka bakake wulik, fuskokinsu kamar sai da aka zabo, ba mai alamar imani a cikinsu ko tausayi. Ya ce da su. “kunsan halina, bana bukatar na yi maku dogon sharhi kan ni waye. Bana tausayawa wanda ya saba umarnina,kuskure kuwa ba ya cikin kamus dina, inaso ku kawomin wannan matar da ta aikata wannan aikin, bandamu da wadanda take taredasu ba, ita kadai nakeso ku kawomin, kuma a raye, bandamu ba yadda zaku jagalgalataa ba, nidai ta zo hannuna a raye kawai, ko da kuwa gunduwa-gunduwa kuka yi mata. Ku saurara, da zarar awa 48 ta shude baku kawota ba, kada wanda ya yi gigin dawowa wannan garin, ba sai na gayamuku hukuncin da zai hau kanku ba.


Cilin sauri suka dare Babura masu tsayi sosai na tayoyi, irin Babura da a kaashen waje kadai ake kera irinsu, da suka fito daga garin sai suka raba hanya, kowa ya dauki hanya daya domin yunkurinsu na cinma su Sajida. Kowannensu ya baiwa babur nasa wuta ya noshi jeji ba tsaiko.


A garin kuwa suka ci gaba da lamuransu na shagalin nada sabon shugaba, wanda ya soma nashi dokoki da tsare-tsare bayan sun kawar da gawar shugaba da ya mutu. Ana tsakiyar shagali, ya sake hawa mimbari, sai mai kira ya yi kira, dalili da ya sa kowa ya halarta ke nan, a wannan wuri da kusan nan ne magama da wurin taro a duk lokacinda wani abu ya faru, ko kuma ake da wani sako da za a gaya musu.


Cikin bacin rai yake magana, inda ya yi umarni d a gabatar masa da duk wani wanda ke da alaka da Sajida aa garin, cikin kankanin lokaci aka gabatar masa da mutumin da ke basu labarin Nusaiba. Jikinsa sai rawa yake yi. Shugaban ya yi umarni da a kaimasa shi a dkin tuhuma. Dakin tuhuma, daki ne da ake ajiye masu laifi omin a bincike su kan wai laifi da ake zarginsu,  a tarihin garin ba wanda ya taba shiga dakin tuhuma ba tareda rayuwarsa ta salwanta ba. Haka suka ja shi yana kuka suka shiga da shi wannan dakin da ake zaluntar marasa karfi.


Cen sai ga shugaban ya shigo dakin, suka dora mutumin kan kujera inda suka daure hanneyensa ta baya, shi kuwa yana a zaune, suka kuma daure shi ta gabansa da kafafuwansa a wuri daya, yada ba zai iya motsawa ba, a gefen hagunsa da damarsa, karti ne rike da manyan karafuna masu tsini sosai.


Aka gabatarwa da shuban kujera a daf da wannan mutumin, ya kalle shi ido cikin ido, ya ce, “kar ka wahalar da ni ba bata lokacina nazo yi ba, ya aka yi suka gudu suka bar ka baya, ko kai sai a daren yau ka shirya naka gudun”?


Bakins na rawa, hawaye na rigangar fita daga idanuwansa yake magana, “wallahi bansan komai ba gameda wannan abu da ya faru, ya ma zan iya sanin wani abu, tun da aka kammala daurin auren, aka turamu ya zuwa wani daki, wanda munada yawa a cikinsa, kuma ko fitsari zaka fita, jami’ai naku har biyu ke rakayar mutum, kan haka ne da fitsari na kwana a marata gudun kar na aikata laifi, wallahi ko da wasa ba zan yi gigin aikata kisa ba, bare irin wannan kisa, ai idan na yi shhi, kaina ne na kashe. Yallabai wallahi bansan komai ba”


Zaumbur shugaban ya mike, sai da ya fara tafiya ya kai bakin kofa, saai ya daga hannunsa sama, ya saukar, ganin haka wadanda ke a gefen dama da hagun wannan mutumin sai suka girgiza kawunansu. Daga fitar shugaban, sai daya aga cikinsu ya yi amfani da wannan karfen da ke hannunsa ya caka masa a kirji, har sai da ya fito ta bayansa, yana nishin fitar rai, dayan ya dubi kansa ya faskara masa wannan katon karfen, har sai da kwanyarsa ta bayyana, ya mutu b atareda ya ko shura ba.


Suka duki gawarsa suka yadda a jeji.


Su Sajida kuwa sai faman gudu suke yi, saurayin da tsohuwa ta hada su da ne ya bukaci su tsaya domin su huta. Cike da jin haushi Bilkisu ta kalle shi, ta ce, “malam ba ka da hankali ne, kallemu ka gani, munyi kwanaki muna wannan gudun, idan muka biyemaka, duk gudun da muka yin a kwanaki ya tashi a banza kenan, domin tarar da mu zasuyi, abinda muka aikata kuma na tabbata ba za su taba yafemana ba, ina amfanin badi ba rai kenan, tafiyar da ba fashi fa zaman baya ba ya yi mata, kawai mu ci gaba da gudu har ya zuwa inda zasu tabbatar mun kubuta daga wadannan azzaluman sai muyii hutun dalili”


Ya kalleta sai haki yake, “anya kinada tausayi kuwa a zuciyarki, tun cikin dare fa muke gudu gashi har rana ta fara kaifi, kike kum zancen mu ci gaba da gudu, sai kace gudun famfalaki”


“hmm! Samari kenan, ai wannan ya fi gudun famfalaki domin gudun ceton rai ne” Sajida ta fada. “ka daure kar ka bada maza mana, kalli fa mace ce, kuma sa’ar kanwarka, idan har zata iya jure wahala kai matashi ai ya kamata ka tabuka fiye da ita”


Ya yi shiru na wani lokaci, sai ya kalli Bilkisu ta ke masa kallon haushi da ganin ya tsaida su.


“Inna idan ya gaji mu bar shi nan idan ya huta, sai ya tarar da mu gaba, kar ki manta fa, ba za su taba tsayawa ba har sai sun ga sun cinmuna, kuma burinsu a kanmu ba mai kyau ba ne”


Jin haka, saurayi ya mike zumbur, suka ci gaba da aikin gudu, cen suna cikin gudu, suka jiyo sautin babur ta bayansu, dalili da yasa suka shige kenan cikin sabarru domin su boyewa ko waye ma tafe. Suna cikin boyon suka hango daya daga cikin wadannan kartin ya zo wucewa ta kusa, da su, ashe ya jima yana biyar sawunsu ne, da yazo inda suka shiga boyo sai ya ajiye babur din ya fara duban ko zai gansu. 


Ganin haka sai Sajia ta yi wata dabara, suka bar Bilkisu nan a boye, sai ita da saurayin suka zagayo ta bayan wannan katon, shi kuwa sai duba yake ko zai gan su.


Sajida ta je kan jikin babur nashi ta daauko wasu karafuna guda biyu manya, duk tana yi ne cikin sassarfa gudun ya jiwo motsinta.

Cen yana cikin dubawa, sai ya hango duhun mutum, ya kara matsawa wurin, ganin ya dosata gabadaya ta kidime ta mike tsaye, kafin ta gudu, ya yi caraf ya kameta, ya ce, “ku daina wahalar da kawunanku, ba a tsira a hannunmu sam” ya fashe da wata mahaukaciyar dariya, ya dauko ta kamar jinjira ya dora a wuyansa, Bilkisu sai kuka take tana kiran Inna zo ki kubutar da ni.


 Ya fito daa ita daga cikin surukin sabaru daa kalage, ya ajiyeta, ya fara tambayarta ina mahaifiyarta, ta yi shiru taki amsa masa, ganin ba zata amsa ba ya shara mata mari, har sai da bakinta ya cika da jini, ta fashe da kuka ta dafe bakinta,


“za ki yi magana ko sai na ill………


09039951083

DR. ZAIN
[2/3, 5:00 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




2⃣4⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```




_A beautiful face will age and a perfect body will change ,but a beautiful soul will always be beautiful.._









*Shafin Masoya*



*Asiya Abubakar Imam*


***CI GABA***




….illata ki?” ya fada yana mai zaro idanunsa ya zuwa gareta, ganin haka ta tsorata har ta fara ja da baya, ta amfani da jikinta tana motsawa kasancewar ta fadi a sanadiyyar mari da ya kaftamata.


“da fa ke nake magana”


 Ta kara tsorata sai kuka take tana ja daga baya, bai Ankara ba shi kuwa ji kawai ya yi an kawo masa bugu a ka da karfe, juyowa da zai yi aka kara buga masa, ya yi tangal-tangal kamar zai fadi, amma zai ya jure ya yo cikinsu, ganin haka suka zaude, ya kawo duka ya sami saurayi a baki, nan take bakinsa ya fashe, karfen da ke hannunsa ya fadi. Ganin haka, kafin ya mike Sajida ta yo cikinsa ta sake bugamasa karfen da ke hannunta a ka, sai ya fadi rica! Ganin haka saurayi ya mike cikin sauri ya kama mata, suka ci gaba da dukansa har sai da suka tabbatar ba ya motsi.


Bilkisu kuwa inbada kuka ba abinda take yi sai kokarin taba bakinta inda ya mata rauni.


Ganin sun kawar da wannan katon, Sajida ta zauna, ta mike kafafuwanta ta tada kanta, sama hawaye suka dinga fitowa daga idanunta kamar birgaggen famfo, ta dinga wasu addu’o’I a zuciyarta kawai dai zaka ga bakinta yana motsi. Bilkisu ta rarrafo ta kwanta a jikin mahaifiyarta, inda saurayi yake tsaye a kansu, duk da shima a jigace yake, ya tausaya musu matuka.


Budar bakinsa, ya ce, “yanzu me ye mafita?”

Sajida ta kalleshi, gaba daya hawaye sun jika fadaddar fuskarta, idanuwanta sun yi ja sun kumbura kan masifar kuka, gashin kanta gaba daya ya yi taushi kan azaba da zufa da ta jika shi, kafafuwanta kuwa burum-burum kan masifar kura. Ta ce, “kaga wannan? Kadan ke nan daga musibu da muka shiga cikin wannan *GUDUN HIJARA* da muka tsinci kawunanmu a ciki, yanzu zamu ci gaba da gudu ne, har ya zuwa inda ubangiji ya sada mu da mafita ko wata sabuwar jarabawar.”


Suka mike suka ci gaba da tafiya, har dare ya fara yi, ganin haka suka tsaya suka yi salloli da ake biyarsu, saidai suna tsakiyar rama sallolin sai ga ruwa un fara sauka, da suka kammala sallar sai suka nemi wuri domin su buya, kasancewar fallau jejin yake, dole suka hakura a karkashin sabara, ruwan a dukansu, sai cirar sanyi suke, amma a yada suka iya, suka sha kashin ruwan a sama da awa biyar kuma masu tsananin karfi. Da ruwan suka tsaya, duk da da barci a idanuwansu, haka suka cigaba da tafiya, da yake sun galabaita kuma sun jigata, ba sa iya gudu.


Ba tareda sanin ina za su nufa ba, sai tafiya suke ba abinda ke zukatansu irin yau su gan su sunn tarar da wani gari, amma kamar su debe tsammani, domin har safiyar Allah ta waye, ba gari ba alamrsa, dole suka ci gaba da tafiya a haka, suna tsoron su tsaya wadannan azzaluman su tarar da su, ga shi kuma yunwa sai dibarsu take, ita gajiya ba a ma maganarta domin  yaddda suke jan kaffuwansu kadai a yayin tafiyarsu ya isa ya bayyana maka hakan. Ganin sun gaji sosai, kuma ga rana ta fara, zafi, ta kuma lura da yaran yunwa suke ji, sai suka ratse kan hanya, suka nemi wani katon dutse, suka zauna cikin kadarkonshi, suka nemi wuri suka gyara, yadda zasu sami kariya daga zafin rana ko saukar ruwan sama, ta hanyar amfani da itace da ciyawu. Sai  ta umarce su da su zauna su huta, ita kuwa ta shiga jeji domin ta nemo musu abida za su ci.


Ba ta sami dawowa ba sai zuwa maraice, inda ta zo musu da bushiya kwara hudu, wadanda ta yi amfani da baki ta yanka, kasancewar ba abin yanka. Dama kafin  ta dawo sun shiga jeji su debo itace, da idan Allah ya sa ta dawo da abin farauta sai a gasa.


Haka suka gyara inda za a gasa naman, suka tara itace masu girma guda hudu sai ciyawa mai dan yawa, suka kafa wasu itace masu dan tsayi guda biyu sai suka gilma wani ice kwaya daya, wanda a jikinsa suka dora duka bushiyar da suka gyara guda hudu. Aka samo duwatsu na kankara guda biyu, suka dinga bugasu har suka fitar da wuta, wacce ta kama ciyawar, suka ci gaba da hurawa har wutar ta kama sosai. Suka ci gaba da gyara wutar har naman ya gasu gaba daya, suna yi suna fira. Aka saukar da nama suka ci. Ganin dare ya fara, kuma ga shi suna jin kishi na ruwa, Sajida ta ci gaba da tafiya cikin kadarkon har ta tarar da inda ruwa suka taru sosai, ta sha, ta wanke jikinta, daga bisani, ta zo ta kai su suma suka sha, suka wanke jikinsu, ganin haka sai suka nemi wuri kusa da ruwan suka kafa ‘yar bukka.


Haka Sajida ta ci gaba da kulawa da su, tana kuma amfani da damar tana jan kunnuwansu musamman domin su fahimci juriya da yadda da kai su ne sinadarin kowacce rayuwa. Haka suka dauki sati daya a wurin, ganin ruwan sun fara raguwa, sai suka tattara  nasu ya nasu suka ci gaba da wannan makauniyar tafiya, da basusan ina suka fuskanta ba.


A garin ‘yan boko Haram din kuwa, da awa 48 suka shude, shugaban ya ga wadanda ya tura basu dawo da Sajida ba, sai ya tura wasu, ya ce, ya basu umarnin su zo masa da su Sajida da kuma wadanda ya turan su biyar gaba daya, wannan karon ko a raye ko a mace.


*GARIN MAI DUGURI*

Aisha kuwa hankalinsu a tashe tun lokacin da suka ji cewa unguwar su Sajida sun kwana cikin tashin hankalin harin ‘yan boko Haram, hakan ya sa ta ajiye a ranta cewa za ta je domin ta ga wanne hali suke ciki. Safiya na wayewa, ta shiryawa Fateema kamar kullum, driver ya dauketa har zuwa unguwar su Bilkisu kamar yada aka saba, amma sai suka tarar da taro a unguwar, mutane sun rufe hanya kama daga masu zowa duba halin ‘yan’uwansu sai masu zowa ganin me ya faru, tun da uwar safiya. Ganin za ta iya makara zuwa makaranta, ta umarci driver da ya kaita makaranata, ta tabbata Bilkisu ba za ta yi fashin zuwa makaranta ba, suka isa makaranta, ana tsakiyar assembly amma hankalinta na kan gate na shigowa makaranta ko Allah zai sa ta kyalla ido ta hango Bilkisu, amma har aka gama aka sallamesu ba Bilkisu ba alamunta. Ana  koyar da su a aji, amma sa hankalinta ba ya gun har malamai suka fahimta suka  tambayeta, da tambayar ta yi yawa sai ta gaya musu damuwarta, su tausayamata ainun musamman da yake lbari ne da kusan kowa ya ji abinda ya faru.


Da aka tashi makaranta, ta zo ta sanarda mahaifiyarta cewa Bilkisu ba ta je makaranta ba, kuma ta tabbatar da lafiyarta kalau, ba za ta yi fashin zuwa makaranta ba. Dalili ke nan da ya kara tada hankalin mahaifiyarta. Suka shirya suka nufi unguwar su Bilkisu.


 Da rana ne, hakan ta sa taro da suka tarar da safe bai kai wannan ba, domin wannan har yara kanani da mata kake gani, dalili da ya sa suka ajiye motarsu kenan nesa, suka taka ya zuwa gidan a kafa, sai kutsa jama’a suke yi su shiga wannan kutsu su fita wancen har suka karaso ta kofar gidan, suka samu suka shiga, abin mamaki, suka tarar ba kowa a gidan, suka fito suka tambayi wadanda suka tarar a bakin kofa labarin su Sajida, wani saurayi ya basu amsa da “ba wanda ya gansu tun jiya, illa dai shi Qasimu munsami gawarsa da aka yi wa kisan gilla ta hanyar yanka shi”.  Nan take hawaye suka zubo mata, Fatima kuma ta kamkame mahaifiyarta a jiki, kamar wacce ake shirin kwacewa.


Cikin sanyin jiki suka dawo gida. Sai zullumi Aisha ke yi tana tuno irin wahala da Sajida ke sha da kuma irin jajircewarta, ta tabbata mace ce da za a amfana da ita, gashi yanzu ba wanda yasan duniyar da ta fada, ko boko haram sun tafi da ita, ta sake zubowa da sababbin hawaye a lokacin da ta tuna basira da hazakar Bilkisu da kuma burinta a rayuwa.


Kullum sai sun je unguwar suna neman wanda ya ji labarin su Sajida, amma shiru babu.


*JEJI*


Suka ci gaba da tafiya ba tareda sanin ina zasu ba, tun safe har zuwa dare, suka dan huta na wasu awanni kana suka ci gaba da tafiya cikin surkukin jeji mai dauke da hadaruruka da musibu.



DR. ZAIN
[2/3, 5:04 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾





2⃣5⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_





® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```




_it a rayuwa tamkar alawa ce, dadinta ba ya dorewa_









*Shafin Masoya*



Kyautar Allah fans





***CI GABA***





Sai kara nutsawa suke yi cikin surkukin jeji, tun saurayi na nuna alamun kasawa, har shima tafiyar ta bi jikinsa, ba ya bukatar su tsaya hutawa. Wasu lokuta su sha kashin ruwa, wasu lokuta kuma zafin rana ya gasa su, su shiga wannan kwararon su fita wancen, a haka har suka dauki wajen kwanaki biyar suna kitar wannan jejin.




A bangaren ‘yan boko haram, wadanda aka turo su bi bayan wadanda aka aiko domin su kama su Sajida kuwa, suka ci gaba da dubawa har Allah ya sa suka tarar da ragowar hudun zaune a karkashin wani katon ice, suna tattaunawa kan yadda zasu bullowa wannan lamarin lura da lokacin da aka diba musu ya rigaya ya kare, kuma ga shi basu sami kamo su Sajida ba. Hango motoci da Babura, suka fahimci me ke faruwa, tabbas farautarsu aka turo. Sun rigaya sun san da cewa ba tausya musu za a yi ba, saboda haka suka yo cikinsu da zinmmar su yi fada da su, sukaa shiga dukansu. Ganin haka, wadanda suka zo a mota da Babura, suma suka mayar da farmakin, fada mai tsanani ya kaure tsakaninsu, inda suke kokarin kawowa juna sara da suka, idan wannan ya saro wannan sai wannan ya goce shima ya kai masa duka ko wawa ko sara har suka dauki lokaci mai tsawo suna fafatawa, sun jima juna rauni sosai, daga karshe suka sami kashe mutane hudun bayan suma sun kashe musu mutum uku.




Suka dauki gawarwakinsu suka bai wa wasu daga cikinsu, suka saka a mota suka umarce su da su kai wa shugabansu, inda su kuma sauran suka ci gaba da farautar su Sajida.



Daga isar su a garin nasu, suka jibge gawarwakinsu a tsakiyar filin da ake taruwa, nan take aka sanar da shugaban cewa wadanda ya tura sun dawo. Ya zo ya shaida aikin da suka gabatar. Ya jinjina musu, ya kuma kara jaddadawa mutanen da aka tara cewa, ba wanda y isa ya kubuta a hannunsa, kuma wannan shi ne karshen duk wanda zai saba umarninsa ko ya nemi ya ha’ince sa kamar yadda yake fada. Ya kara da cewa tabbas su Sajida ma za su shigo hannu, kuma zasu dandana daga mafi munin azaba kafin a raba su da rayukansu. Jawabansa, suka sanyaya jikin duk wanda ya halarci wurin, kama daga ma’aikatansa har su wadanda aka tsare a garin. A fusace ya koma tantinsa domin ya ci gaba da tsara wurare da zasu kai hari. Sauran jama’a suka ci gaba da sabgogin rayukansu.



Su Sajida kuwa suka ci gaba da tafiya, har kafafuwansu suka kumbura jikinsu ya jigata gabadaya yanayin jikinsu ya canja, amma sai tafiya suke hakan, ga masifar yunwa ga kishi na ruwa, wanda ta kai sai su dauki kwana biyu ba tareda sun hadu da abinda za su ci ba, ruwa ma sai idan sun yi sa’a ne an yi ruwan sama sai su samu su sha daga garesu, abinci kuma da kyar suke samun zomo ko bushiya su kama, wani lokacin kan rashin wuta danye suke cin nama gudun kar rayuwarsu ta salwanta.



Wata rana suna tafiya, da maraice, sai wani iska mai karfi ya taso, dalili kenan da ya sa suka nemi wurin fakewa karkashin wani katon ice, mai dauke da wani katon kogo, iskan sai kara karfi yake yi, kuma ga duhu na kara shigowa abinda ya yi sanadiyyar tashin hankalin Sajida ke nan, musamman ganin Bilkisu ta gaji sosai, kasancewar yau kwana biyu kenan suna tafiya ba tareda sun huta ba.



Suna zaune a gindin icen, duk da icen kato ne, amma a haka iskan ke wujijjiga shi kamar zai fado, suna zaune, sai suka ga hayaki na fitowa daga cikin kogon, sun lura da hakan ne a lokacin da suka fara jin wani masifaffen zafi na fitowa ta daga kawunansu, dubawa da zasu yi sai suka hango hayaki na fitowa daga kogon. Cikin tsoro suka tashi suka ja daga baya, amma kamar wadanda aka ba wa umarni sai suka tsaya suna kallon yadda hayakin ke fita, zafin sai karuwa yake yi, abinda ya fi basu mamaki shi ne, yadda wannan iskan bai shafi fitowar hayakin ba, sun yi zaton wuta ce ke kokarin fitowa ko kamawa a jikin icen.



Suna tsaye nesa da icen, sai suka ga wani katon maciji da girmansa ya ninka Sajida sau biyar ya fito daga kogon, ai ko fitowarsa zafin ya karu, a jikinsa launuka ne na shudi da ruwan dorawa da ja, ya wuce da sauri a saman iska. Wannan ne ya haddasa su duka suka fadi, kamar tunkudasu aka yi, kowannensu ya kasa magana ko motsi kan tashin hankali na ganin wannan shirgegen maciji da ko a mafarki ba wanda ya taba ganin irinsa a cikinsu.



Ya jima yana wucewa kan masifar tsawo, duk da ya wuce, zaka ga alamun launukan ta wurin, haka hayakin ya jima kafin ya bar fitowa.



Ai ko kuzarinsu na dawowa, suka ce kafa me naci bambaki ba, suka ranta a na kare, sai gudu suke suna kokarin waigowa domin su tabbatar da cewa ba biyar su yake yi ba, duk da gajiyar Bilkisu, ita ce gaba a gudu sai Sajida a bayanta. Sun dauki lokaci mai tsawo suna gudu, domin sune basu tsaya ba har sai da sanyin asuba ya fara sauka, suka sami wani kogo a jikin wani dutse suka shiga, sai haki suke yi kamar rayukansu zasu fita.



Sun jima suna zantawa kan wannan abin al’ajabi da suka gani. Kana suka rama salloli da ke kan su, suka sami wuri suka kwanta domin su rage gajiya da ke tattarre da su, tun da subahi suke barci har rana ta fadi ba su farka ba, kamar hadin baki, sai cen cikin dare, Sajida ta farka, ta fito daga kogon ta duba yanayinsa a waje, ta dan zagaya, inda ta ci karo da ramun wasu tsuntsaye, nan take ta ja daga baya, ta dawo ta tad yaranta, da suka wartsake, ta shaida musu abinda ta gani, cikin farin ciki suka biyo ta bayanta, ta nuna musu ramin, ta yi amfani da kara ta saka a ramin, fir! Tsuntsayen suka farka, jin motsin farkawarsu, su Bilkisu suka karaso ta kusan su, suka dinga kama duk tsuntsun da ya yi yunkurin guduwa, a haka har suka kama adadi mai yawa, suka dawo makwancinsu, suka fige, inda lokacin da suke aikin fiigar ita da mahaifiyarta, shi kuwa saurayin yana cen yana kokrin nemo itace da za a gasa wadannan tsuntsayen.



Da ya kawo suka hura wutar kamar kullum ta hanyar amfani da duwatsu, musamman da yake daren ranar ya zo da sanyi, sun ji dadin hura wutar sosai, dalili da ya sa kenan duk da sun kammala gashin sai da suka dade suna karo itace domin su duma jikinsu da wutar, har zuwa tsakiyar dare.  Suna so su yi barci amma sun rigaya sun yi barci mai tsawo sosai, shi ne dalili da ya sa suka buge da fira mai tsawo. Inda idan wannan ya bayar da labari, wannan sai ya bayar da nasa, sai raha suke yi sun dariya tsakaninsu



Nan Sajida ta ce, “ku bari na baku labarin KARSHEN ZALUNCI labarin kawo karshen ta’addancin sarki RUSKINANU na littafin ARTABON SARAKAI mai KARAGAR TSAFI wanda ya mallaki maganin mutuwa KUWWATUL KITAAL.”



“Maganin mutuwa fa Inna? Hala akwai maganin mutuwa ne?”




“ba ki ji na ce mulkinsa ya zo karshe ba, shi ke nunamaki ita mutuwa ba ta da magani, wata hanya ce da duk ratsen mutum dole sai ya bi ta wurin, gata ba ruwanta da sarki ko talaka, batasan yaro ko babba ba, batasan namiji ko mace ba, batasan nagari ko dan banza ba, idan ta kira ka kuma ba wanda ya isa ya hanaka zuwa”



“shi wannan sarkin kuma waye shi?”



“kina nufin baki karanta labarin ARTABON SARAKAI ba, na ZAINUDDEEN ZAIN DR. ZAIN?”



“ban taba jin littafin ba”


“taff! Ashe kuwa jirgi ya bar ki tasha”



“inna tau me zai hana ki bamu labarin daga farko?”



“inda nake da niyyar baku, yafi dacewa da halin da muke ciki, zai kara muku karfin guiwa na sanin cewa uangiji bai manta da mu ba, yana sane da halin da muke ciki”



Nan saurayi ya kara gyara zama, sai ya nisa ya ce, “amma ba a wannan zamani aka yi wanann sarkin ba, tun daga sunansa da kuma aikin da naji ya yi, na mallakar maganin mutuwa?”



“sosai an yi shi ne sama da shekaru dubu goma, ya yi mulki na zalunci fiye da tunanin mutum, ga shi jarumi mai masifar karfi, ga tsafi ga mulki ga shi da ‘ya ZABZABATU mummuna amma ga masifar karfi da dabarun yaki, da bokansa AJAMALU da kaf a lokacin duniya ba kamar shi a tsafi. Ga rashin imani da rashin tausayi”



“zan so ko naji karshen wannan sarkin,  RUSKINANU ne kika ce sunasa ko?” saurayi ya fada.



Sajida ta gyara zama sai ta fara.





DR. ZAIN
[2/3, 5:04 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾



2⃣6⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```



_yanzu suka dora tasu tukunyar, tuni tamu ta tafasa_










*Shafin Masoya*


*YAN GUDUN HIJIRA FANS*




***CI GABA***






Dandano daga littafin *KARSHEN ZALUNCI*





Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah makadancin sarki, wanda ya bai wa musulunci girma da martaba a sama da duk wani addini, shi ya halicci komai da kowa kuma shi kadai ya dace a bautawa, gagara misali ne a lamuransa wanda buwayarsa ta zarce misali. Ina kara gode masa kan baiwa da ya bani, har na tsintsi kaina cikin dandazon marubuta masu rubuta abin da al’umma za ta amfana ko ta nishadantu, ina rokonsa da ya datar da ni da gidan aljannarsa Firdausi ameeen.



Salati nayo gun Muhammad (SAW) Bakuraishe jikan Abdul-Muddalibi dan Aminatu manzon gaskiya wanda kaunarsa ta mamaye zuciya, kuma tafiyarsa ba za mu ki binta ba, muna rokon ubangiji da ya sadamu da tozali da shi a yinin gobe kiyama a gun shan ruwan Alkhausara ya bamu mu sha da lallausan fararen hannayensa ameeen.



Tsira da aminci ubangiji ka dada gun iyalan gidansa, wadanda suke masoya a gare shi, tare da zaratan sahabbansa wadanda farin cikinsa shi ne nasu, wadanda suka bayar da rayukansu fansa gare shi, tare da duk wanda ya bi turbarsu ya zuwa ranar tsayuwa.




Ina mika godiya ga mahaifiyata wacce ko da wasa ba zan buda shafin godiya ba ba tare da na bata nata sakin layi ba, ita ce jigo da silar duk wani ci gaba nawu, ina rokon ubangiji da ya kare ta daga sharrin masharranta ya kuma datar da ita da gidan aljanna.



Masoyana na nesa da na kusa, banida baki da zan gode maku, musamman a dan karamin littafi irin wannan, amma naso ace zan iya bude zuciyata, da na nuna muku yadda soyayyarku ke shimfide a huhu da ruhi da kahon zuciyata, irin kun dai ganennan ana tare.




*TSOKACI*



Wannan  season din, wato *KARSHEN ZALUNCI* ci gaba ne na _KUWWATUL KITAAL_, idan maikaratu bai manta ba, mun karanto season one _(KARAGAR TSAFI)_ season two _(KUWWATUL KITAAL)_ wannan shi ne season three *(KARSHEN ZALUNCI)*. Kar maikaratu ya damu ko da wanne season ka fara za ka iya fahimtar ina labarin ya dosa, amma idan baka karanta season one ba kafin ka fara wannan season na uku yanada kyau ka nema a shawarce, akwai lambata a jikin littafin, idan aka nema zan turo.



Idan maikaratu bai manta ba a karshen season one, su _JAUHARANU_ da _WALKINANU_  sun shiga hannun dakarun _SARKI SAMAKATUL BAHAR_ har aka killace su a cikin keji, domin yara su zo su dinga kallonsu a matsayin tsuntsaye, sun yi yunkurin su kubutar da kawunansu amma, a banza domin duk wani tsafi da suka sani sun yi amfani da shi amma abin ya ci tura, dole suka hakura suka ci gaba da zama a keji, abinci ma sau daya suke gani a wuni, hakan ta sa suka rame sosai har sai sun ba ka tausayi idan ka kalle su, labarinsu kuwa, dole aka rufe aka ki sanar da _SAMAKATUL BAHAR_ gudun hukunci da zai dauka kan mazauna garin kafin su _JAUHARANU_.



A karshen season two kuma mun ji yadda _GIMBIYA ZABZABATU_ da mahaifin _WALKINANU_ wato _WASHMANU_ suka sha alwashin karbo su tareda dauko ita _KARAGAR TSAFI_, tambaya a nan ita ce, _BAHARUL MAUTI_, gari ne da ke a karkashin ruwa kuma yana dauke da hadarurruka bila adadin, me zai faru da su _ZABZABATU_? Za su sami damar dauko _KARAGAR TSAFI_ kuwa? Za su kwato mutanensu kuwa? Cikin labarin komai zai warware.



Wannan season zai fi karkata ne gun fassarar mafarkin da _ZABZABATU_ ta yi har sau shida a season two, wanda zai dauke mu ya zuwa tarihin wani jarumin gaske, wanda sam baisan tsoro ba, kuma ga shi addininsa ya bambaanta da na su, sunan jarumin _AMJAD_, yana zaune ne a kasar _HERA_ da ke nesa sosai da kasar _FARETU_.



Ta yaya fassarar mafarkin zai alakanta da wannan jarumin? Ya halin su _RUSKINANU_ wanda ya mallaki *KUWWATUL KITAAL* maganin mutuwa? Duk za mu ji a wannan littafin da ikon Allah.




Wanne addini ne ake yi a kasar _HERA_? Duk za mu ji a cikin labarin.



*FARKON LABARIN*


Kasar _HERA_ kasa ce da ke dauke da wasu al’adu wadanda suka sabawa mafi yawa daga cikin kasashe, kasa ce wacce ta tara jarumai da manyan masana a fannoni daban-daban, kasa ce wacce ta hada da mafarauta da masu ilimin likitanci, amma duk wadannan a kan koyamaka ne gwargwadon inda matsayinka ya fada, misali wadanda za su zama jarumai dole ne su fito daga gidan jarumai, ko gidan sarauta, dan matsafi duk yadda ya kai ba za a bari ya koyi yaki ba, haka wanda za a koyawa tsafi dole ya fito daga gidan bokaye, haka sauran, doka ce diyan talakawa su koyi wani abu a kasar idan ba sana’a ce ba, kamar kera makamai ko wani abu da ya danganci aikin kwadago. Wannan dokoki da ke shimfide a kundin kasar, shi yasa kasar ake kallonta da tsaurin ra’ayi inda talakawan ke kallon gaba daya ba a masu adalci, duk da haka kasar tana kula da bai wa na gaba girmansa, duk da tana cike da zalunci suna nuna soyayya tsakanin junansu.



Kasar suna bautar duk sarkin  da ke kan mulki, duk wanda ya ki sai ya biya da kansa. A haka abubuwa suka ci gaba da tafiya a kasar, har aka haifi jarumi _AMJAD_, sai dai aka yi rashin sa’a, domin mahaifinsa _SUMAIRU_ talaka ne sosai wanda ke sana’ar kera makamai.



Tun haihuwarsa, mahaifinsa ya ga abubuwan al’abi dangane da shi, mahaifiyarsa ta rasu ne sanadiyyar haihuwarsa, amma tun haihuwar ta sa, abubuwa suka fara canjawa mahaifin, idan da naira dubu yake samu a wuni, sai ya dawo samun dubu goma, wannan shi ya bashi damar kulawa da dansa ta hanyar siya masa duk abinda yaro ke bukata, a haka har ya kai shekaru takwas, a makaranta kuwa idan ana koyar da shi sai kayi zaton ya ma fi malamansu sanin abun, bayan kaifin basira da rikon abu ba mantuwa akwai shi da zuciyar jarumai, wanda kan haka har ake ganin ko ba ya da tausayi ne, karami ne amma akwai matsanancin karfi, wannan jarumta ta shi ita ta sa gaba daya sa’anninsa shayinsa suke yi, kai har na gaba da shi na tsoronsa duk da kananan shekarunsa.



*Note:* _duk seasons da nake kawowa online, ina katse su ne daga asalin yadda na rubuta su, saboda haka ba komai ne nake sakawa online ba, ainahin labarin, idan zan fitar a kasuwa zan sanar sai a nema, domin ko kashi talatin na labarin ban sake ba._




DR. ZAIN
[2/3, 5:04 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾



2⃣7⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```



_kyawun budurwa asanta da kunya_









*Shafin Masoya*


Jega Village




***CI GABA***





*Cigaban labarin ‘yan gudun hijira.*




Tana kawowa nan da labarinta, suka yi shiru gaba daya, sai kallon juna suke yi cike da alamun tambayoyi a fuskokinsu, da ta fahimci tambayoyi suke so su mata kan labarin KARSHEN ZALUNCI ta ce, “kar wanda ya min tambaya cikinku, idan labari ne zan ci gaba da baku shi a duk lokacin da muka sami lokaci, a halin yanzu mu mayar da hankalinmu kan yadda zamu sami fita daga wannan jejin mai dauke da hadaruruka”



Suka girgiza kawunansu alamar gamsuwa da zancenta. Kana suka shiga shirin daukar hanya na wannan tafiya da ba a san ina za a dosa ba, kawai dai titi ne mafarkinsu.



Haka suka cigaba da tafiya shiga wannan ramin fita wancen, shiga wannan hadarin fita wancen, har rana ta yi zafi sosai, ganin haka suka sami wuri suka labe cen cikin wani katon rango da ya samu ta sanadiyyar ruwa da ke saukowa daga kan falalen dutsi. Nan suka yi sallah, suka dan sami abinda suka sakawa cikinsu, kana suka ci gaba da tafiya.



Har zuwa faduwar rana suna tafiya, ba gari ba alamunsa, da rana ta fadi, suka tsaya suka yi salla, sai suka hura wuta domin su duma jikinsu. Cikinsu sai kiran ciroma yake, kaancewar sun dauki lokaci ba tareda sun ci komai ba. Duk da haka cikin walwalaa suke firarsu, duk da ana cewa wai yunwa ba ta da sabo.



Ganin sun nutsu, sai ta ci gaba da basu labarin KARSHEN ZALUNCI.




*DANDANO DAGA LITTAFIN KARSHEN ZALUNCI.*




Kamar yadda muka sanar jarumi Amjad ya taso ne hannun mahaifinsa wanda yake sana’ar kere-kere, hakan ta bashi damar sanin makamai sosai da amfaninsu da kuma sanin yadda ake sarrafa su, da yake kasar Hera kasa ce da ta haramtawa duk wani dan talaka koyon dabarun yaki, Amjad bai samu damar shiga makarantar koyon yaki ba, amma a haka yake labewa yana kallon yadda ake koyar da fada  azuzuwan da ake koyar da jarumai, idan dare ya raba tsakiya sai ya dinga bitar abinda ya koya, hakan ta bashi damar zama gwani wurin iya sarrafa takobi, da iya harba baka, domin zai iya harba baka, har tayi tafiya tsawon kwanaki uku. A karfi kuwa sai ya dauki giwa komai girmanata ba tareda wahala ba, duk wannan abin da ke faruwa da Amjad, masarauta ba ta sani ba, amma mahaifinsa ya san komai, duk da da farko yana masa fada daga baya ya dinga karfafamasa ta hanyar kera masa makamai nashi na kansa musamman.




Jarumi Amjad da ya girma sai ya zama wani saurayi mai kyau sosai mai kwarjini a idanun mutane haka a zuciyoyin ‘yan mata.




 Wata rana suna tafiya da abokaninsa cikin jeji suna yawon farauta, kwatsam sai wasu dakaru na makociyar kasarsu suka tare su da niyyar illata su, dakarun za su haura dari, su kuwa su biyar ne kadai, ganin mutum dari sun zagaye su, gaba daya hankalinsu ya tashi, sai rawar jiki suke yi, Amjad ne kadai tsaye a kafafuwansa, su duka dauke suke da makamai banda Amjad domin shi kadai ne daga gidan talakawa, kuma a dokar kasar ba a bari talaka ya koyi fada, a cewarsu bai dace da shi ba. Ganin abokaninsa sun tsorata, ya zare takobi daga hannun daya daga cikin abokanin nashi, ya tinkari wadannan dakarun, ya fara saransu yana sukarsu, su kuwa sukai masa kawanya. Suka fita batun abokaninsa suka yi wo kansa da niyyar illata shi, suka zagaye shi sai kawo mashi sara da suka suke yi, yana gocewa shima yana kokarin kai musu sarar, cikin kankanin lokaci ya illata su gaba daya. Cike da mamaki abokaninsa suka fara kallonsa. A kan hanya suke tambayarsa, ina ya koyo irin wadannan salallai na fada, yaki ya sanar da su.




Da suka dawo gida, ya tafi bakin aiki a kasuwa domin komai ba su kamo ba ranar, ya je wurin mahaifinsa domin ya gani ko da aikin da zai taya shi, su kuwa abokanin nashi suka wuce makaranta, domin an umarce su da su zo karatun maraice, shigarsu ajin da dan wani lokaci aka fara masu darasi. Daya bayan daya suke fitowa domin su fafata da malamin nasu, kasancewar yana so ne ya gwada hazakarsu, har ya zo kan wanda Amjad ya yi amfani da takobinsa, wurin tarwatsa dakaru dari. Daga zare takobinsa, sai malaminsu ya fara kallon takobin cikin mamaki, bayan sun kammala darasi, sai ya kira shi ya ce da shi, “me ya faru da takobinka, na ganshi da jini na mutane, kuma da alama ka fafata ne da mutune da dama?” nan ya fara rabon idanu, yasan idan ya yi karya, fille masa kai za a yi domin shi ne dokar kasar. Dole ya kwashe labarin gaba daya ya sanar da malaminsu, sai da malamin ya dade yana tunani kafin ya nisa ya sallameshi.




Amjad na kan hurawa mahaifinsa wuta shi kuwa yana kokarin narke darma da zai kera wani takobi, kusan faduwar rana, sai ga dakarun sarki sunzo cikin sauri, suka jajibi Amjad, mahaifinsa ya yi yunkurin shiga tsakani, suka tunkude shi, ya fadi, shi kuwa Amjad ya rigaya yasan laifin da ya yi, kuma yasan idan ya yi yunkurin fada da su, gaba daya zuri’arsu za’a shafe daga doron kasa. Ya bi su har fada. Suka gurfanar da shi gaban sarki.




Wani da ke gefen daman sarki ya matso ya fara magana, “Amjad dan Sumairu, an kamaka da laifin taka dokar kasa, ta hanyar nuna salon  fada, wanda ‘ya’yan masu mulki kadai keda wannan damar, me za ka ce?”




“ba shakka hakan ta faru, amma ranka ya dade, da ban aikata haka ba, da yanzu diyan manyan dagatai a wannan kasar sun rasa rayukansu, mumfita farauta ne, dakarun kasar Jaiha suka zagaye mu da niyyar illata mu, ganin abokanina duka sun shiga tashin hankali, shi ne na karbi takobin daya daga cikinsu na ceci rayukanmu”



“ba shi ne bayani da nake so kayi muna ba, muna so musan wa ya koyar da kai salon fada?”




“ba wanda ya koyar da ni fada ranka ya dade”



“ina aka taba yin fada, har illata mutum dari kuma kace ba koyar da kai aka yi ba, idan ka batamuna lokacin kaa san hukuncinka”




Nan ya kwashe duk yadda aka yi ya iya fada ya sanar da su. Bayan fada ta dan yi nazarin zantukansa, suka kuma auna maganganun sai suka yanke masa hukuncin kora ta har abada daga garin, domin hukuncinsa kisa ne, amma ganin taimako ne ya yi, kuma ba koyar da shi aka yi ba shi ne aka sassauta masa aka kore shi kawai daga garin. Mahaifinsa yana kuka, dole ya bar shi ya tafi.




Wadanda suka raka shi, ba su rabu da shi ba har sai da suka fita da shi iyakar kasar. Ya duba hagu da dama gabas da yamma ba a binda idanunsa ke gani illa faifan jeji wanda ke cike da sunkuru da falalaen duwatsu manya. Nan ya ci gaba da tafiya har ya kawo inda hankalinsa ya kwanta, ya tsaya a nan ya shiga jeji ya saro manyan itace, ya kafa ‘yar rumfa da sunan daki, inda zai dinga kwana.




DR. ZAIN
[2/3, 5:04 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




2⃣8⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```




_sammako ake bugawa idan ana so a Kama fara_









*Shafin Masoya*


MRS. ISMA'IL
SISTER NAJA'AT
AMEESHAH
MARYAM HAMZA FUNTUA




***CI GABA***




*Cigaban labarin ‘yangudun hijira*




Su duka suka yi shiru, sai kallon juna suke yi. Bilkisu ta nisa ta kalli mahaifiyarta ta ce, “lallai wadannan sunada tsattsauran ra’ayi, wane irin dokoki ne a wannan kasar da ke kokarin haramtawa talaka motsawa da taka tasa rawa wajen nuna gwannta ko hazakarsa, talakawa ai mutane ne, kuma da yawansu zaka tarar sunada baiwa wacce ma ta fit a ‘ya’yan masu kudin, amma duk sai a kange su a hanasu shiga inda zasu nuna baiwar tasu, sai kiga kasa ta kasa cigaba”




A duk lokacin da Bilkisu ke magana, sai kaga mahaifiyarta ta kashe kunne tana saurara, saboda hikima da ke kunshe cikin zantukanta. “haka ne mamanne, amma ai ko a wannan zamanin idan kika duba kusan duk daya ne da kasar HERA”




“haba Inna, daya fa?” ta fada cikin zazzaro idanu.




“eh! Sosai, ba bambanci. Ki duba  kiga yanzu ko aiki za ka je nema, idan ba dan masu hannu da shuni ba ne kai da wuya ka samu, sai kiga talaka da kwalinsa mai kyawu amma ‘ya’yan masu mulki za a dauki mukamin da ya dace da na talakan a basu, sai su dare kujerar su kasa tabuka komai, kullum sai a ga kasa na ci baya. Idan kika dawo bangaren damar karatu, wato daukar nauyin karatun dalibai, sai kiga dan talaka ya cancanci a fita da shi kasashen waje ya je ya yi karatu, amma sai a dauki wannan damar a baiwa yaran masu mulki, su je cen su yi ta aikata masha’a karshenta su dawo ba karatun su kawo wata mummunar akida. Kinga kuwa ba bambanci, gara ma su kasar HERA sun nuna doka ce, da wadannan da ke aikatawa a dunkule.”




Saurayi ya yi ajiyar zuciya, yanaso ya furta zance, amma zantukan Sajida sun rigaya sun gamsar dole ya yi shiru. Ganin sun fara gyara zama da niyyar su kara hutawa, ta dube su ta ce, “me kuke nufi? Babu amfanin badi fa ba rai, da muguwar rawa, kuma gara kin tashi. Zaman baya ba ya yi wa tafiyar da ba fashi. Kar mu bata rawarmu da tsalle, kada mu yi jifar gafiyar Baidu, kada wahalarmu ta tashi a iska, idan muka sake jiki muka zauna, su fa masu biyar mu, ba sakewa za su yi ba, ba za su tsaya ba har sai sun tabbatar da mun shiga hannunsu, idan har su da ke yunkurin kama mu, basu huta ba, babu dalilin mu mu tsaya hutu. Mun fa dade muna tafiya, inada yakinin inda zamu nufa dole kusa da fita hanya ne.”




Suka tashi cikin tsalelen dare, suka dauki hanya, duk da yunwa a taredasu, jikinsu da kwarinsa. Sajida ce a baya inda saurayi ke gaba, ita kuwa Bilkisu a tsakiyarsu.




Suka ci gaba da tafiya cikin jeji, ga sanyi ga duhun dare ga sunkurmin jeji, ba abinda ke shiga kunnuwan mutum irin kuka da sautuka na tsuntsaye da kwari da ke kwance a ramukansu. Cen suna cikin tafiya suka hango haske na wuta a dokar jejin, alamun akwai mutane kusa da gun, suka ci gaba da tafiya, duk da sun dauki lokaci mai tsawo suna tattaunawa kan su  is da gun ko su ratse daga kan hanyar, gudun su fadawa zago bayan gara suke gudarwa. Jiwo sautukan na mutane ya sa Sajida ta umrce su da su bi ta gun, amma idan sun kusa kai sai su labe, domin su shaida abinda ke faruwa, idan ‘yan boko haram ne, sai su canja hanya, domin ta yiwu ba su ba ne, sai  su nemi taimako. Duka suka amince da hakan.




Haka suke jan jiki a kasa, da suka karaso daf da taron gudun  hango su, suka sami wuri suka labe, amma suna gani da jin duk abinda ke faruwa.




A tsakiyar filin wani ne tsaye kyam, zaka gan shi wani dan fyarat da shi, duk tsananin sanyinnan da ake yi shi ba riga a jikinsa, hakan zata baka damar ganin layu da karhuna da ke zagaye a wuyansa da hannayensa da kugunsa. A cen gefensa wasu ne a zugunne kowannensu sai bari yake yana rawar kafa, kamar wanda ake tunzurawa. Shi kuwa sai kirari yake yi wa kansa. A cen dayan gefe kuwa makadi ne da ke buga ganga yana zuga wannan dan taurin, shi kuwa yana ririta hadi da dada kansa.




“ni ne kafiri da ba ya sallar safe, ni ne na Salima duk wanda ya ji haushina zai mutu. Ni ne kafirkafir da ba kafiri ba amma nafi kafiri kafirci. Yau ina wanda yace ba ni ba ne na aikashi lahira nan take. Ni ne dakalin majina a hauni a zame na hau mutum na zauna daidai. Ni ne murucin kan dutsi ban fita ba sai da na shirya, ni kuturwar uwa ce, zama da ni ya zama dole. Ni ne lange-lange mai ramar keta, ni ne…tsufa da ni ya zama dole, Allah ya kashe mijin kyaklkyawa, ana jana’iza muna kai kaya. Yaro ka ja da mu, mu ja da iyayenka…….”




Sai kalamai yake wadanda ke kunshe da shirka da kuma habaici.




Bilkisu ta kalli mahaifiyarta, ta ce “wadannan kuma su waye? Amma dai Inna kafirai ne, naji yana fadar ba ya sallar safe”





“Wadannan ‘yan tauri ne da ke fitowa farauta” ta fada a lokacin da take kokarin mikewa tsaye




“inna ya ke nan, yanzu wurinsu za mu je ko mu ratse hanya, ni fa na tsorata, ji wadannan adduna da sanduna da suke dauke da su.”




“mamanne kenan, akwai makami da zai daga maki hankali ne yanzu, ke da kika ga bindiga, kikaga takobi da gariyo da adda da hargi, wadannan makaman zasu daga maki da hankali? Harbi a wutsiya ai ya fi kuskure, kuma kwai a baka, ai ya fi kaza a akurki. Su muka gani, kuma tabbas su dole gari Zasu nufa, idan ma bazamu bi su ba, ai ya kamata muje su doramu hanya”




Suka mike suma suka bi bayanta, suna tafiya a tsorace, ita kuwa hankalinta a kwance, har suka karaso daf da taron. Ganinsu, sai makadin ya dakata da kidan nasa, hankalin kowa ya koma kansu, lura da shi makadin da ya dakata da kidan, kallonsu ya dinga yi. Kai tsaye Sajida ta shiga tsakiyar filin saurayi da Bilkisu kuwa suka riketa gam. Ta fara magana da murya mai karfi.



“Assalamu Alaikum ya ku taron wadannan mafarauta,ku yi sani yau ba farautar namun jeji kuka yi nasara ba, kun yi nasarar farautar wadanda ke bukace da neman agaji ne, kunyi farautar marayun Allah ne wadanda suka shiga musiba da ibtila’in rayuwa. Mun kwashe kwanaki muna gudu cikin wannan jejin muna neman tsira sai yau ubangiji ya sadamu da ku. Mu ‘YAN GUDUN HIJIRA ne, da mayakan boko haram ke farauta ruwa a jallo, ku taimaka, ku tafi damu a garin da zaku isa ko ku nunamana hanya inda zamu isa kowanne gari ne cikin sauki. Aikin lada ba ya kadan, ku taimaka, ku ceci rayukan marayunnan”



Ta fada cikin kuka, tana nuna su Bilkisu.




Gaba daya mafarautan da ke wurin suka yi shiru, tausayi ya kamasu ya kuma dabaibaye zuciyoyinsu. Nan wani daga cikinsu ya gabata ya soma “mun ji zamu taimaka muku, amma ba zamu iya tafiya tareda ku ba, saboda jiya muka shigo jejinnan farauta, ko zamu koma gida kuwa ba yanzu ba, zamu bar ku ku kwana, tun da safe sai mu doraku kan hanya da za ta sadaku da gari mafi kusa, ai ba nisa, ba zai kai tafiyar wuni daya ba ma.”




Kan murna kamar su zuba ruwa a kasa su sha, nan Sajida ta dinga yi musu godiya, inda hawaye suka rinjayeta kan murna sai kuka take. Nan aka kawo musu abinci, da yake mafarautan basu kafa tantuna ba, dole a kasa suka kwana a fili, sanyi kuwa kamar zai kashe su bayan sauro da ke yayyakar naman jikinsu.



Allah sarki, haka suka kwana, har safiyar Allah ta waye, bayan sun yi salla suka ci abinci, da rana ta fara fitowa, aka nuna musu hanyar da za ta sadasu da gari mafi kusa, suka kama hanya, bayan sun yi godiya kamar su rusuna.





Shikenan wahalrsu ta kare, ko da saura?
Wanne gari ne wannan da zasu nufa?
Me zsu tarar?
Idan sunje garin, ina kuma zasu nufa?

Duka amsoshinku suna cikin shafi na gaba. Yanzu labarin ya fara hawa hanya.



08034840276 call
09039951083 whatsapp


DR. ZAIN
[2/3, 5:05 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




2⃣9⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```







_namu allaxiy da amanu yake tafiya, budurwa kuma anfi so a Santa ne da junta_






*Shafin Masoya*



AMYRAN MD
ASTUU



***CI GABA***






Haka suka cigaba da tafiya sai fira suke yi cike da farin ciki kasancewar an sanar da su cewa ba za su dauki lokaci suna tafiya ba kafin su isa gari mafi kusa.



Sai a lokacin suka sami damar kallon yanayi na jikinsu. Ita dai Sajida a jikinta riga ce da aka bata ta saka a daren amarcinta na aurenta da shugaban boko haram na garin da suka fito, sai hijabi shima duka a garin aka bata shi, hijabin dark blue ne ga tsawo har yana ja a kasa, shi ke hana a hango kalar atamfar da ke jikinta, atamfar ruwan shudi ce, amma tanada ratsi da aka mata na kwalliya ta kaloli irinsu ruwan dorawa da baki da surkin fari. Itama rigar doguwa ce amma iyakarta guiwa, bata matse jikinta ba, sai zani da aka yi da sifa irin ta skirt. Sosai kayan sun yi mata kyau. A kafafuwanta ba takalmi, domin a wurin gudun ceton rai, ta wurgar da su. Gaba daya kafafuwanta sun bice da kura haka jikinta burun-burun kamar wacce ta yi wanka da Hafdi (toka ta wutar murhu) haka gaba daya jikinta ya yi datti sosai, wasu wurare  kafarta duk ta fashe da jini kan ratsa ciyawu da kuma gauruwa a duwrwatsu.



Bilkisu kuwa a jikinta wata riga ce da aka bata itama kasancewar auren mahaifiyarta ne, rigar irin dinkinnnan ne na kasar Parkistan, rigar amba colour ce amma tanada ratsi kwalliya na fari a gaba da shudi, sai wando mai fadi da ya tsuke a karshen kafarta. Sai wani dankwali da ta rufe kanta da shi, shudi. Ba ta da hijabi a jiki, haka a kafarta ba takalmi. Ita ma duk ta yi datti ga kafafuwanta duk sun yi dauda a gefen jikinta rigaarta ta yage kan matsifar keta jeji a lokacin da suke gudun ceton rayukansu.



Saurayinda ke tare da su kuwa. Wata polor shirt ce a jikinsa, ruwan siminti, wacce a wuyan rigar, aka kawata shi da bakar kwala, a kugunsa kuwa jeans ne baki, wana da zarar ka kalle shi, za ka san ya dade a jikinsa ba tareda ya ga ruwa ba, duk da bakin da yake da shi. Shima dai ya wurgar da takalminsa kan masifar gudu. Haka wasu wurare a jikinsa, sai jini ke fita saboda raunuka da ya samu wurin kokarin ya kubutar da rayuwarsa.



Haka suka cigaba da tafiya. Sajida ta ce a dan saurayin da suke tareda shi, “sai tafiya muke yi, bawan Allah amma har yanzu bamusan waye kai ba, bamusan daga inda ka fito ba, haka bamusan ya aka yi ka fado hannun wadannan azzaluman ba.”



“haka ne” ya fada bayan ya yi murmushi tareda juyowa, da yake shi ne gaba, “nima ai bansan labarin komai game da ku ba”




“hmm! Labarinmu ba wani abu ba ne mai birgewa ko sha’awa ba, labari ne da tun farkonsa har karshe yake dauke da bakin ciki, kunci, takaici, nadama, tashin hankali da fadi tashi. Labari ne da ba wanda zai so ya ji  an ce wani wanda ya sani ya afka cikinsa.”



Ya girgiza kansa, ya ce, “duk wannan labarin a kanku ya kare? Ikon Allah, zan ko so naji wannan labari naku”



“kar ka damu, za ka ji labarinmu, insha Allah, yanzu dai ka fara bamu naka labarin muji, ko ba komai domin musan da wa muke tafiya.”



“da farko dai sunana Mustapha, ni haifaffen garin Borno ne, a unguwar GRA, lafiya lau muke zaune da mahaifiyata da mahaifina suna nunamin kauna fiye da komai, kasancewar ni kadai suka mallaka, ni din ma sun jima da aure kafin ubangiji ya basu ni, inada kaka daya, ita ce wacce ta zo ta tada ni daga barci, ta hada ni da ku, ina matukar kaunarta ta yadda hatta rayuwata zan iya badawa domin na fansheta. Ina karatu a jami’ar Maiduguri, inda nake karanta biology a 300level. Wata rana nazo ziyarar kakata a unguwar da take nan bayan TH, shigata gidanta ke da wuya, sai muka jiyo sauti na bindigogi da tashin bamabamai, da kuma kara da kuwwar jama’a, hakan tasa  muka rufe ko’ina na gidan, muka kasance cikin tsoro. Mun jima a wannan yanayin, da muka ji sautin ya lafa sai na bude kofa domin mu ga ko sun tafi, budewa da za mu yi, sai muka ga gaba daya kan titin mayakan boko haram ne dauke da mugayen makamai, muka yi yunkurin juyowa cikin gida, daga nesa wani yace, idan kuka kuskura kuka juya sai na watse muku kwanya da wannan bindigarar, dole muka tsaya, cike da tsoro, suka zo suka kama mu. Tun ranar muke hannunsu, mun sha wahala iri-iri da sunan wai horo ne suke bamu na zama sojojin boko haram. Kullum babu abinda suke koyar da mu fiye da falalar jahadi da kuma lada da ke kunshe cikin kashe makiya addini. A wurinsu duk wanda bai koma jeji ba ya jaddada jahadi ko ya kafa daular musulunci, tau shima kafiri ne da jininsa ya halatta. Sun sha koyar da mu, falala da yadda ake kunar bakin wake da sauransu. Abu daya ke dauremin kai game da su, wasu lokuta sai kiga turawa ne ke kawo musu abinci da makamai, wasu lokuta kuma sai kiga bakaken fata ke kawowa amma kuma daga gani kasan ba kudinsu ne ba, domin wanda yake zaune a jeji, ina yaje ya nemo kudi da zai sayi bindigar da kwaya daya zata haura dubu dari biyu. Nayi tunani naga daga cikin masu wannan ikirarin na boko haram, zaki ga talaucin kansu kadai ya ishe su, ya za ayi wanda yake da talauci, ya iya samun kudin sayen bindiga mai masifar tsada, kuma ya  sayeta,  kuma ya dawo jeji ya tare, wa zai ciyar da shi?”



“Mustapha ke nan, ai duk mai hankali yasan wadannan yan boko haram din, daukar nauyinsu ake yi, matsalar da yawa daga cikinsu jahilai ne kan addinin, wasu ma sai ka tarar ba musulmi ba ne, ana amfani da su ne kawai domin a lalatawa musulunci suna. Akwai labari na wani bawan Allah da ya ce, su biyar aka taba turawa a kasar Misra wato Egypt domin su nemo ilimin addinnin musulunci su zo su dinga bayar da fatawowi domin su rikita addinin musulunci, hakan ta faru har ga Mai Tatsine, wanda turawa ke daukar nauyinsa, da asirinsa ya tashi tonuwa aka fahimta, kuma ashe ba musulmi ba ne, hakan takan faru, saboda kafurai sun fahimci cewa musulunci shi ne addinin gaskiya, basuda wata hanya da za su dakushe addinin sai ta hanyar kirkirowa da irin wadannan abubuwa na rudani da zasu dinga shafe hasken musulunci su dinga jingina su ga addinin musulunci”



“Allah dai ya kyauta”



Suka ci gaba da tafiya. Su ne basu iso gari mafi kusa ba sai da maraice. Tun daga nesa suke hango hayakin girki na tashi, ga kamshin kauye da ke kokarin dumfaro hancinsu, sai kuka na jakai da shanu. Daga nesa suke iya hango kalar bukkoki da dakuna da wannan kauyen yake da , duk da tun daga nesa za ka iya fahimtar cewa kauyen ba ya da girma amma akwai ruhegu (wurin ajiyar abinci kamar su damma da sauransu ko buhuhuwa) sosai a garin, wanda zai tabbatarwa mutum da cewa, wannan garin tabbas na manoma ne. ganin sun fara hango gari, suka kara sauri, kamar zasu ruga aguje. Amma da suka karaso daf da garin, sai Sajida ta umarce su da su tsaya. Da suka tsaya cike da mamaki suna kallonta, sai ta umarce su da suyi addu’ah da ake yi kafin a shiga gari. Suka yi addu’ah suka shiga garin da kafar dama. Duk wannan abin da ke faruwa, kusan magariba ne, domin saura kiris rana ta fadi.



Shigarsu garin duk inda suka biya sai kallonsu ake yi, irin kallon tabbacin cewa wadannan baki ne, da suka ga abin ya ki ci ya ki cinyewa, sai Sajida ta nufi wasu da ta gani zaune a gindin wani ice, ta yi musu sallama, suka amsa, sai take tambayarsu ko za su iya nunamata gidan maigari ko mai unguwar garin, ganin yadda suke kallon ta ya tabbatar mata da basa jin Hausa, ta yi musu fulatanci, nan ma ba wanda ya iya mayarwa. Ta gwada yin turanci, shima ba wanda ya amsa. Nan idanuwanta suka raina fata, taji gaba daya murnar da take yi ta koma ciki. A ranta tana mai cewa, yanzu duk wahalar da muka sha ta tafiya ba mai jin yarenmu. Ta kalli Mustapha da Bilkisu, taga dukkaninsu suna cikin damuwa ne. ta yi ajiyar zuciya suka ci gaba da tafiya, suka nemi wuri suka zauna, domin su yi shawarar me kuma zasu yi, ya zasu yi da wadannan da basajin Hausa.



Suna zaune karkasin ice da suka zauna, sai suka jiwo an fara kiran sallar magariba, dalili ke nan da ya sa suka sauya shawara, Sajida ta nuna su tafi masallaci, idan suka tafi, dole dayan biyu ta faru, kodai su sami wanda ya iya yarensu ko kuma su tarar da mai gari a masallacin.




Suka dugunzuma su duka uku, zuwa inda suke jiwo sautin kiran sallah na fitowa,da suka karaso masallaci, suka debi ruwa suka yi alwala, Mustapha ya shiga masallaci aka yi jam’I da shi, inda su kuwa suka tsaya daga waje suka bi jam’i. daga kammala sallah mustpha ya mike ya fara jawabi da kokarin yin bayanin ko su waye. Amma har ya kammala bayaninsa, ba alamun ko da mutum daya ne ya fahimci me yake so ya fada, ganin haka, sai ya fara yin yaren kanuri, amma ba alamun an fahimce shi. Ganin haka ya fashe da kuka su Sajida ma da ke wajen, sai kuka suke yi. Dole ya fito ya tarar da su. Suka nemi wuri cen nesa da masallacin suka zauna.




Aka kira sallar isha, suka zo aka yi salla da su. Aka sallame, suka koma wurin da suke zaune, suka zauna. Har mutane suka fara watsewa daga masallaci suna zaune. Wasu ma idan suka biyo za su wuce, sai su dinga basu sadaka, inda Sajida ke nuna su ba sadaka suke so ba. Har dare ya fara kamawa suna zaune garin da ba wanda ke jin yarensu, ga su ba sa jin yaren ‘yan garin su kuma.



Me zai faru?
Ya za su karata a wannan garin?




Amsoshinku na shafi na gaba





DR. ZAIN
[2/3, 5:05 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




3⃣0⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_





® *PEN WRITERS ASSOCIATION*





```QUOTE OF THE DAY```





Duk laifi na kura ne, bacin satar zare








*Shafin Masoya*




Duk mabiyi wannan labarin




***CI GABA***





Suna zaune suna zullumi, ba tareda sanin me za su barkata ba, kasancewar gaba daya hankalinsu a tashe yake. Cen sai Mustapha ya ce da su, “tun da lamarinnan ga yadda ya zo, ya kamata ace tun da safe munkama hanya ya zuwa gari na gaba ko ubangiji zai sa mu dace da wadanda zasu fahimci me mukeso mu fada. Wannan abin ya yi yawa, ace gaba daya kazo garin da ba mai jin yarenka.”




“haka ne” Sajida ta fada. “wannan zai nuna muna buwaya da gagara ta ubangiji, ya kuma kara nunamuna kudurarsa kan komai. Mu kalli kwanaki da muka share muna gudu a cikin jeji kadai, kuma ga shi muka tarar da wasu suna rayuwa a wani wuri da sam ma ko yarenmu basaji, tabbas ubangiji girmansa ya zarce tunani”




Suka yi ajiyar zuciya, suka ci gaba da tattaunawa. Suna cikin fira sai Bilkisu ta ce, “Inna ya kamata mu shiga garinnan ba zai yi wu ace ba wanda zamu samu da zai fahimci abinda muke so mu fada ba, ace duk garinnan ba wanda ya yi yaki da jahilci na boko ko wanda ya dan yi karatun addini da zai dan fahimci larabci”





“haka ne” inji Sajida. “amma kinsan da cewa karatu na kauyuka a fannin boko basu yi karfi ba, ki kalla gaba daya fadin garinnan ba zai yi wu a gina musu makaranta ba saboda yaransu ba zasu haura nawa ba, malamai nawa za’a kawo musu, bacin ga wurare cen da ya dace a tura malamai anki, kan karatun addini, a kauye fa akwai matsala, zaki tarar da liman ko ahdwari ba ya iya karantawa, fatiha ma da kyar yake iya karantawa saboda karancin ilimi, ta ya kike tsammanin irin wannan ya iya larabci ko waninsa? Birni ne fa ilimi ya yawaita har kike ganin da yawa an iya turanci an iya larabci, kauye tuni an manta da su, su suke da bukatar a bawa kulawa ta fannin addini da karatun zamani, amma ina shuwagabanninmu sun yada su. Wallahi idan za ki je wasu kauyuka sai kinyi kwalla, wasu ma da ke da makarantu, azuzuwansu ba sa zaunuwa saboda gabadaya rufin azuzuwan sun tashi, ba kujeru ga allon rubutu ya lalace, a takaice dai azuzuwan ba sa zaunuwa, tau ya kike tunanin a iya karatu a cikin su, bangaren malami kuwa, sai kiga makaranta wacce kusan kauyuka shida ke kawo yaransu karatu, amma malami daya ke karantar da su, gayamin injimi ne da zai iya ba su ilimi yadda ya kamata? Ko kiga malami yana zaune yana jiran wai sai yara sun dawo daga jeji kafin su zo makaranta, haka har lokaci ya kure. Ko kiga malami shi karn kansa yana bukatar a ilmantar da shi, amma shi ne wai headmaster. Gayamin yadda zasu iya samun ilimi? Bangaren addini kuwa sai dai mu dora hannu a ka muce ‘innalillahi wa inna ilaihi raji’un’ domin yadda kauyuka ke tura yaransu almajiranci kana dubawa kasan da lauje cikin nadi.”




“lauje cikin nadi fa?” Mustapha ya fada yana mai kallonta cike da daukin jin me za ta fada.




“Eh! Lauje cikin nadi kuwa” ta fada tana mai kara gyara zama. “ ka duba ka ga, galibi lokutan da ake tura yara almajiranci, lokaci ne da aka girbe albarkar abinci bayan damina, sai su tura yaran da sunan karatu saboda kar yaran su ci abincin da suka noma, idan lokacin noma kuma ya yi, sai kaga yaran sun koma gida wasu domin taya iyayen aikin jeji. Ka kalli yara da ake turowa, wasu shekaru uku wasu hudu, haba gayamin yadda yaro da ba ya da kwanciyar hankali abinci ma ba ya da tun tashinsa da safe hankalinsa na wurin me zai ci yau, ina zai sami abinda zai sakawa cikinsa. Yaro kankani da wurin barci ma ba ya da sukuni saboda zasu haura su dari suna kwance a wuri daya, ga rashin wanka, cututuka su biyo baya, ga haduwa da marasa tarbiyya tun suna kanani. Gayamin yadda malami kwaya daya zai iya ba wa yara sama da dari biyu tarbiyya. Duk ba nan gizo ke sakan ba, wasu ta nan ne ake lalata su, wasu su koyi shaye-shaye wasu su koyi fashi da sauran ta’addanci. Ki kalli yanayi na karatu da kuke yi ku da kuke a gaban iyayenku, sai ku kwashi ilimi har ku sauke alkur’ani, su kuwa su dauki shekaru ko baki basa iya tadawa.”




Bilkisu ta nisa ta kalli mahaifiyarta, ta ce, “tabbas inna haka ne, amma fa gwannati nada laifi”




“mamanne ke nan, gwannati bazata rasa laifi ba, amma kina sane da kashi 99 laifin iyayenne, ai ba hakkin gwannati ba ne kula da tarbiyyar yara, nata hakki ta bayar da hanyoyin inganta rayuwa da tsaro da walwalar al’umma. Laifinta anan shi ne; ta kasa tsayawa ta inganta makarantun tsangaya na almajirai, ta dauki malamai ta dinga biyansu, su kuma su dinga karantar da yaran a kuma hana su yawon bara, domin wannan yana kada kimar musulunci a idanun kafirai”





“Alla dai ya yi muna jagora”  Mustapha ya fada.




Suka ci gaba da fira da kuma tattaunawa kan matsalolin ilimi, cen suna tsakiyar fira,sai ga wai mutum yazo kusa da su. Kafin ya karaso sai Mustapha ya ce da su. “ga limamin gari nan tafe…”




“y aka yi kasan shi ne liman?”




“kun manta a masallacin na yi salla?”




Yana karasowa sai ya yi musu sallama, suka amsa. Sai ya soma. “hal yastadi’u ahadukum attakallumu fil arbiyyah” (ko da wanda ke iya magana da larabci a cikinku?) cike da jin dadi kamar wacce za ta tashi sama, Sajida ta girgiza kai ta ce “na’am! Kai fa anta, wa kaifal umur” (eh! Muna jin larabci, ya kake ya lamura) “ bi khairin. Ra’aitu hazassabiyu yatakallamu ba’ada an tahaina minasswala, ka’annahu yuridu an ya kula lana shai’un muhinmun, fahimtu zalika hina baka lamma ra’ana la nafhamu luggatallazi yatakallamu bih” (da alkhairi, naga yaronnan yana zance cikin masallaci bayan da muka kammala sallah, kamar yana so ya sanar da mu wani abu mai muhinmanci, na fahimci hakan en, lokacin da ya fashe da kuka da ya fahimci ba ma jin yarensa)




Sajida ta kalli Bilkisu da Mustapha, hawaye suka cika idanuwanta, ta kalli liman, ta sunkuyar da kanta kasa, sai ta ce “na’am ya imamu, ladaina khabarun, walakinnahu dawilun jiddan, walaisa ladainal waktul aan, la khabarnahu laka, walakinnal aan nu ridu musa’adataka an turshidana ila dariki ayyi baladin allazi arafta iza ataina bihi sa najidu assayyarah ila baldati Kebbi. Asaabatna musibati Boko Haram, madaina ayyaman narkudu wa nabta’idu anhum, hatta ataina ila baldikum haza. Sa’idna” (Eh! Imamu munada labari, amma yanada tsawo sosai, ga shi bamuda lokaci, da mun labartamaka shi, amma yanzu muna bukatar taimakonka, ka dora mu kan hanyar duk garin da ka san cewa idan muka tafi cen zamu sami mota da za ta dauke mu zuwa jahar Kebbi. Musibar Boko Haram ta far muna, munduki kwanaki muna gudu muna kokarin nisanta daga garesu, har muka karaso wannan gari naku. Ka taimakemu)




Ya kalle su cike da tausayi sai ya ce, “antumul aan duyufulliy, wala yumkuni li an utrikakum fi hazihillaila, indalikuu ma’iya ila baiti” ya fada a dai-dai lokacin da yake kokarin juyawa. (ku bakina ne a yanzu, bazai yiwu gareni ba na bar ku ku tafi cikin wannan daren ba, ku biyoni muje gidana)




Suka biyo ta bayanshi, suna tafiya yana yi musu tambayoyi suna bashi amsa. Duka da larabci, har suka karaso bakin wani gida wanda ba ya da kyaure, amma a zagaye yake da gini na laka, wanda aka yiwa babbar kofa, sai ta ciki da dauke da kofa uku, na matan aure sai bangaren rahegu da kuma inda ake bayawa a yi wanka. A dayan bangare kuwa wurin turke dabbobi ne, ya cika da awaki da tumaki, sai shanun noma guda biyu da jaki kwaya daya. Ya yi saallama, aka amsa sai suka shiga daga ciki, ya kira matansa guda uku, ya gabatar da su Sajida gare su, ai ko nan suka tausaya musu, sai kallonssu suke yi cike da mamaki. Tabbas kallo kadai idan ka yi zuwa ga su Sajida dole kaji tausayi ya ratsa ka. Aka shimfida musu tabarma, cen bakin dakin amarya, aka kawo musu tuwon gero (tuwon hatsi) da kunu, miyar batso aka kawo musu wacce ta ji man shanu, har yana dukan hancin mutum. Suka ci suka sha, suka bige da fira, bayan imamu ya ja Mustapha ya nuna masa inda zai kwana. Tun da subahin suka fita sallah, da aka iyar da sallah, suka dawo gida, imamu ya shirya kayansa na zuwa jeji, sai ya dawo gun Mustapha ya ce su je su yi wanka, zasu tafi ne wurin mai gari, suka yi wanka, aka kawo musu kari, da yake lokacin rana har ta fito. Suka ci, sauka dugunzuma ya zuwa wurin mai gari.





Da suka zo sai liman ya gabatar da su ya kuma sanar wa maigari da labarin da suka bashi kan kansu. Cike da mamaki, mai gari ke kallonsu. Ya tausaya musu, daga bisani, ya hada su da wasu dogarawa nashi, saman jaki domin su rakaye su gari na gaba. Haka suka ci gaba da tafiya tareda wadannan dogarawan, har suka karaso gari na gaba, aka yi sa’a a garin akwai masu Babura, kai tsaye gidan maigarin garin suka isa da su, suka mika masa takarda daga maigarin garin da suka fito, bayan an karanta, ya hada su da masu Babura domin su kai su babban birni.




Wannan wane birni ne zasu isa?






DR. ZAIN



[2/3, 5:05 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




3⃣1⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_





® *PEN WRITERS ASSOCIATION*





```QUOTE OF THE DAY```





_komai kake gani da lokacinsa_








*Shafin Masoya*



Equity FM




***CI GABA***





Suka ci gaba da tafiya kan Babura har suka karaso garin Biu. Suka ajiye su a nan, suka koma kauyensu, su kuwa suka nemi mota domin ta kai su gari na gaba, da ya ke a garin da suka fito ambasu gudunmawa ta kudi da zasu yi guzuri da su, hakan batasa Sajida ta manta da kudi da ta debo ba daga garin da ta kashe shugaban boko haram da kuma kudin sadakinta da ke a leda a jikinta.


Shiga wannan garin fita wancen, har ubangiji ya kado su a garin Adamawa a unguwar Dandu. Ganin maraice ya karaso ta ja yaranta ta nufi guest inn da ke kusa da su ta kama musu kudin daki biyu, shi Mustapha ta kama masa daya, inda ta kamawa kanta da Bilkisu daya, suka yi wanka, kasancewar tufafin jikinsu su kadai ne suke da, dole su suka mayar a jikinsu, hakan ta sa dole da aka kammala sallar Isha suka fito neman tufafi da zasu saka a jikinsu. Suka nufi wani babban shagon sayar da kaya da ke unguwar AT unit. Suka siyo kaya kala biyu-biyu da zasu dan yi amfani da su. Suka dawo masaukinsu.



Sun jima a dakin da su Sajida suke, sai fira suke yi, da kokarin zantawa kan abubuwa da suka faru da su a jeji. Budar bakin Bilkisu sai cewa ta yi, “Inna me ya sa bamu gabatar da kawunanmu gun sarki ba ko wasu masu fada aji a gwannati? Na tabbata da bazamu kashe kudi haka ba, kuma hankalinmu zai fi kwanciya”



“bamusan tsarin garinnan ba, kuma da uwar maraice zamu sallamawa sarki ko gwamnati? Sai ma mu tafi a karyata mu ko a dinga yimuna kallon mabarata, tunda  alhamdulillahi munada ‘yan kudi a jikinmu, kuma na tabbata ko ina ne a kasarnan zasu dauke mu su kaimu, ai gara mu tsara abu yadda mu mukaga ya yi mana dai-dai. Banida niyyar komawa Maiduguri, garinmu Kebbi zan je a garinmu na Kalgo wurin iyaye na. ko ba komai a cen za ki sami gata da bakisamu ba tun haihuwarki.”




Jin haka, Bilkisu ta waigo ta kalli Mustapha da tun lokacin da Sajida ta fara magana ya yi shiru, sai ta ce, “ya zamuyi da Mustapha? Na tabbata bazai so ya rabu da iyayensa ba.”




“haka ne, kuma ba wanda zai raba shi da iyayensa.”



Ta kalli Mustapha ta ce da shi, “kanada lambar mahaifinka ko mahaifiyarka?”



“eh! Inada lambobin duka daga cikinsu” ya fada.



“shi kenan, je dakinka ka kwanta” ta fada a dai dai lokacin da take kokarin mikewa daga kan gado da take zaune.



Ya tashi jiki ba karfi ya wuce dakinsa, inda su kuma suka rufe nasu dakin suka fara kuka na rashin Amisha da suka yi.




*MAIDUGURI*



Haka malama Aisha ta ci gaba da zuwa neman Sajida da yaranta a duk unguwa da ta ji cewar an ga wasu *‘yan gudun hijira* haka kullum kunnuwanta na kan redio idanuwanta kuna na kan talabijin kullum, ko Allah zai sa ta jiwo labarin inda Sajida da yaranta suke. Amma ba su ba labarinsu, ta kai sanarwa gidajen redio da talabijin amma kamar an shuka dusa. Hakan ta sa, sai dais u nemi wuri ita da ‘yarta Fatima su darji kuka son ransu.




Iyayen Mustapha kuwa, tun batan Mustapha da kakarsa, suka shiga tashin hankali, da har abin ya zamewa mahaifinsa kamar hauka, domin sai kaga shi kadai yana sambatu marasa ma’ana. Dole sai da aka tashi tsaye da neman magani kafin ya fara dawowa hayyacinsa. Kullum cikin mikin rashin dansu suke.




*ADAMAWA*



Haka suka kwana cikin bakin ciki da bacin rai duk da sanyin AC da ke dukan jikinsu, Mustapha a farke ya kwana har aka fara kiran sallah a kunnuwansa. Da suka kammala sallah, har ta fara lazimi, barci ya kwasheta, haka Bilkisu, kamar hadin baki shima Mustapha barcin yake yi, sune ba su farka ba sai zuwa sha dayan rana, suka shiga suka watsa ruwa, ganin Mustapha bai zo ba, ta tabbatar mata da lallai, barcin ne bai sake shi ba, ganin haka sai ta je ta tada shi, ta umarce shi da ya je ya yi wanka domin fita zasuyi. Suka dawo nasu dakin suka jira shi, da ya kammala wanka ya zo ya same su, a sababbin tufafi da suka siyo jiya su duka uku suka fita. Sune basu fita daga Taxi ba sai a unguwar wuro chakke, suka nemi inda ake sayar da waya, aka ce da su ba a sayarwa a nan, hakan ta sa dole suka nufi kasuwa, a kofar kasuwa ce suka sami masu sayar da waya, da suka saya, suka sake hawan mota ya zuwa ofishin MTN suka sayi layi, aka mata register da kyar suka mata, saboda rashin ID card. Suka fito bayan ta sayi kati ta saka. Suka dawo masaukinsu, bayan sun biya wani restaurant sun ci abinci.



Daga dawowarsu, sai ta ce da Mustapha ya saka lambar mahaifinsa a wayar, ya saka, sai ta kira, kiran farko kuwa aka daga.



“Assalamu Alaikum”



“wa alaikumussalam”


“barka da wuni”



“yawwa barka”



Don Allah ko kai ne Alhaji Kabiru?”



“eh! Ni ne Alhaji Kabiru, lafiya, da wa nake magana?”



“lafiya lau, sunana Sajida, a halin yanzu ina cikin garin Adamawa a cikin birnin Yola”



“tau malama Sajida me ya faru ne?”



Ta kwashe duk bayani da ya kamata ta yi masa ta yi, ta kuma sanar da shi cewa suna tareda yaronsa Mustapha. Cikin rawar murya da kadadi ya bukaci da ta bashi ya ji muryar yaronsa. Ai ko da ya tabbatar da cewa yaronsa ne, murna ba a ko iya bayyanawa.


Da ta karbi wayar, mahaifin ke cewa zasu zo shi da mahaifiyar Mustapha domin su dawo da yaronsu gida, bayan ya mata godiya kamar ya rusuna kasa. Inda ta nuna ba damuwa zasu jira su, amma su kokarta su taho yau.



Ya sanar da mahaifiyar Mustapha komai, da farko taso ta musa zancen ta zata wasa ake so a musu da hankali, amma da ya tabbatar mata da cewa ya ji muryar Mustapha sai ta aminta, ko wanka bai bari tayyi ba, ya kira driver ya ce ya zo ya kai su garin Yola.



Suka kama hanya, kasancewar hanyar ba kyau, dole sai da suka yi zagaye ta Gombe kafin su shigo garin Yola, wanda ya sa tun karfe daya basu iso ba sai  sha daya da mintuna na dare.



Murna a wurin Mustapha da mahaifansa ba a cewa komai, dalili kenan da ya kara sa Sajida ta fashe da sabon kuka, ganin yadda suke nuna jin dadin haduwa da junansu.



Alhaji Kabiru ya jaddada godiyarsa ga Sajida kamar ya rusuna.




Sajida ta sanar da shi cewa, dama ta kirashi ne domin da safe suke shirin wucewa a garin Kebbi. Kebbi fa? Alhaji Kabiru ya fada cike da mamaki” ba fa gari ba ne da ke kusa, akwai nisa sosai, naji labarinku, ya kamata a ce kun huta sosai kafin ku wuce”



“Alhaji, ai babu daren da jemage bai gani ba, idan ka cire na daren mutuwarsa. Zaman hutu ba ya da amfani musamman idan da kaya a kan mutum. Kuna cikin farin ciki saboda kun hadu da yaronku, ni kuwa na rasa ‘yata a wannan tafiyar, kuma na dauki shekaru ban saka iyayena a idanuna ba, bare na ji muryarsu, ko na rungume su yadda kuka rungumi juna, ka ko ga babu hutu a wurina. inshaAllahu gobe zamu wuce tun da asubar fari.”




Da ya ga alamun batada niyyar fasa tafiyar dole ya hakura da rarrasarta, suka kwana nan ita da mahaifiyar Mustapha da Bilkisu, shi kuwa Alhaji ya kwana a dakin daa aka kamawa yaronsa Mustapha.




Ko karyawa basu yi ba, tun daga kammala sallah, Alhaji ya dauke su ya zuwa Adamawa sunshine da kansa. A hanya ya dauko makudan kudi ya bata, ta ce bazata karba ba, ita aikin Allah ta yi masa, ya nuna ai ba saboda mayar masa da yaronsa ya sa ya bata kudi ba, ya bata ne domin ta tallafawa marainiyar da ke tareda ita, gudun su shiga halin kakanikanyi domin batasan ya zata tara dda gida ba. Jin haka ta karba, kudi tsaba har dubu dari biyu da hamsin, ta yi godiya. Suka shiga mota, basu jma ba motar ta tashi. Dalili da yasa alhaji kabiru ya buga motarsa kenan ya zuwa Maiduguri da kansa, su kuwa su Sajida suka nufi Birnin Kebbi.



DR. ZAIN
[2/3, 5:06 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
----------------------------
_based on true life story_
                      🐾




3⃣2⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR.ZAIN_





_dedicated to: Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar Boko Haram_




*PEN WRITERS ASSOCIATION*





```QUOTE OF THE DAY```



komai na rayuwa ubangijinmu ya Riga  ya tsara
Tun daga kukanmu har muzo mu dara




*SHAFIN MASOYA*


Farida Gusau








***CI GABA***





Motar, mota ce kirar Sharon wacce ke dauke da mutum goma sha daya har driver, a gaba mutum biyu sai a tsakiya mutum hudu haka a kujerar baya mutum hudu ne a zaune. Sajida ce a gaba tareda Bilkisu, kasancewar sun rigayi kowa zowa, kuma hankalinta ya fi kwanciya idan ta zauna da yarinyarta.


Sai tafiya suke yi cikin motar, in da driver ya saka musu waka da suke cashewa da ita, waka mai taken *Rayuwa tana faruwa sai ta wuce kamar ba a yi ba* wacce Zainuddeen Zain ya yi tareda wasu mawakan Kebbi, a dai ai in da yake cewa.


_Dakata malam kaji na gayamaka halin rayuwa_
_Tamkar alawa ce, zakinta ba ya dorewa_

_Tun kana yaro kankani jikinka babu quality_
_Sai dai a ja hannunka garka a kaika titi_

_Abubuwa da dama ba ka iya yiwa kanka_
_Idan aka dauke ka baka so kuma ka yi kuka_

_Tufafi ma da kansu, mama ce zata sa ma_
_Yara manyan gobe, in ka manta na tunama_

_A hankali.., sai ga shi ka fara girma_
_Ka fara tara budare, su Asiya da Teema_

_A dinga duba bakin gatari, in an yi sara_
_Za aji dadin saran sosai in an yi gyara_

_A hankali malam, sai ga shi ka fara tsufa_
_Muryarka ta canja tafiya hadi da sifa_

_Kafin ka Ankara, rayuwarka sai ta kare_
_A kaika kushewa a barkka cen ka tare._




Haka wakar ta ci gaba da tafiyaa, har ta kawo in da Zainuddeen Zain ke cewa:



_Tsakanin samu da rashi ubangijinmu shi ya tsara_
_Dole sai wani ya rasa kafin ka zo ka dara_

_Mulki, kasaita ubangiji ya bada_
_Ya hore dawakai da kilisai ga masu fada_

_Ka manta komai, kai riko gagam ga duniya_
_Ba ka tari, ba rashi gaka da lafiya_

_A hankali a haka rayuwa take ta tafiya_
_Talakawa kana kallonsu cen kasa da fariya_

_Mulkin sai ubnagiji ya kwace ya bai wa waninka_
_Sai kayi magana ba wanda za ya ji ya bika_

_Haka ne halin rayuwa, juyi-juyi dan’uwa_
_Wani sai ka gan shi tsaye cak kama da kainuwa_

_Karamin mai wayau nesa ai ya fi mahaukaci_
_Komai zai zo maka da sauki, mahakurci_

_Kwatsam a haka rayuwarka sai ta kare_
_A kaika kushewa a barka cen ka tare._



Haka dai wakar na tashi a motar, su kuwa suna fira kala-kala, in da wasu ke firar sha’anin gabansu kamar kasuwanci da sauransu.


Cen bayan motar gaba daya, wata mata ce da gaba daya shekarunta bazasu haura ashirin da biyar ba, amma kan masifar ganin bone, gab daya fasalinta ya canja, zaka yi zaton ta haura shekaru hamsin a duniya. Zaune take tun shigarta motar ba wanda ta cewa ko kanzil, illa sai kokari kara rungume yaranta guda biyu da take yi a jiki, duk ba wnnan ne abin kallo ba, irin yadda cikin da ke jikinta har ya bayyana.


Ganin shirunta ya yi yawa, wata mata da ke kusa da ita ta kalleta tace da ita “baiwar Allah, tun shigowar mu a motarnan kike ta zullumi da kokarin rungume yaranki kamar wacce za a kwacewa, kallon yanayinki ba shakka ba za ki rasa labari da zaki bamu ba domin amfaninmu”.


Jin wannan magana da ta fito daga matar da ke kusa da wannan baiwar Allah, ya sa hankalin da yawa daga jama’ar da ke cikin motar ya dawo kan su domin jin me wannan matar za ata fada a matsayin labari rayuwarta.



*LABARIN NA’IMA*


“Sunana Na’ima” ta soma bayan ta share hawaye da suka gangaro a farar fuskarta. Tana magana da shesshekar kuka a tattarae da ita, kuma irin kuka da ke ratsa duk zuciyar mai imani. “muna zaune da mijina maisuna Jamilu a wani kauye da ake kira Minchika. Fulani ce ni gaba da baya haka maigidana Jamilu. Sana’ar maigidana ita ce, kasuwanci, ni kuwa ina sakar hula da tabarma. Wata rana da misalin karfe biyar na safiya muka fara jiwo kara da kuwwar mutane, hakan ta sa dole muka tashi ba shiri, domin mu tabbatar da abinda zukatanmu ke yi muna zargi na cewa mayakan boko haram ne suka yi wa garinmu tsinke. Hakan ta sa dole ni da mijina muka koma a guje domin mu dauko yaranmu guda biyu,dayan shekarunsa biyar”, ta fada a dai-dai lokacin da take dafa dayan yaro da ke kan cinyarta daya, “sunansa Sani, sai dayan yaronmu da shekarunsa biyu, sunansa Ahmad” ta fada a dai-dai lokacin da take kara rungumashi a jikinta, hawaye kuwa suka ci gaba da ganagarowa daga idanunta ya zuwa kumatunta. “Ba shiri muka fito, Ahmad na goye a bayana, in da Sani na rike shi a hannuna, shi kuwa Jamilu yana ta bayanmu sai gudu muke yi, a haka a gabanmu muke ganin yadda ake kama mutane ana yankawa dalili da yasa muka kara kaimi kenan wurin gudu domin mu tserata da rayukanmu. Wurin gudu kasancewar akwai dandazon masu so su tserata da rayukansu, muka rasa Jamilu, na so na koma na nemashi, amma na kasa, domin ina tsoron na koma, rayuwar yarana ta salwanta, dole muka ci gaba da gudu na neman tserata da rayukanmu, har muka fado cikin jeji. Fadi nan tashi cen tsawon kwanaki tara muna yawo cikin jeji, ba ruwa isassu, ba isasshen abinci ba tsaftar jiki bugu da kari gani dauke da ciki na wata har shida. Ga yara sai kuka suke yimin kan yunwa, wasu tsofaffi da muke tareda su, suka rasa rayukansu kan wahala, haka wasu yara da muke da su suka mutu. Wata rana muna cikin tafiya, Allah ya nufa muka karaso wani kauye, kamar hadin baki mu shida ne har yarana, ko sunan garin bamu fara tambaya ba, sai ga jirgin sama ya fara yimuna aman ruwan alburusai da bama bamai, ai kuwa nan hankalina ya tashi, na fara kallon yarana zasu mutu, ga shi bamusan wanne hali mahaifinsu yake ciki ba, nan muka runtuma cikin jeji gudu ya dawo sabo” ta fyace majina da ke kokarin fitowa daga hancinta, ta hanyar amfani da gefen zaninta, ta ci gaba. “wurin gudu, Ahmad ya bata, dole na ci gaba da gudu da goyon Sani ni kadai cikin uwa jeji ga tsohon ciki. Fadi tashi har na kawo wani kauye inda ake saka mutane a tsallake da su a jirgin ruwa, musamman wadanda irin ibtila’inmu ya far musu. Cikin ikon Allah a nan naga Ahmad, a  hannun wani bawan Allah, na karbi abina bayan na yi masa godiya. Aka saka mu a jirgin ruwa aka tsallaka da mu, a haka har Allah ya kawo ni garin Yola. Zuciyata bata mutu ba, kan haka ban tsaya kada girmana ko mutunci na ba wurin yin bara, sai na nemi aikin wanke-wanke wurin wata mai sayar da abinci a unguwar Demsawo, na dauki kwanaki ina yi mata aiki, na tara ‘yan kudi, sai na dawo a unguwar Jambutu na ci gaba da kamawa wata mata dahuwar abinci a nan, kwana biyu da na tara kudi masu dan tsoka, sai na ce bari na nufi garin Kebbi, ko ba komai, munada ‘yan’uwa a cen kuma gari ne da ke da zaman lafiya sosai. Kunji labarin rayuwata a takaice.”



Tana kawowa nan, hatta driver sai da ya yi kwalla, Sajida kuwa ajiyar numfashi kawai take yi.


Wata a cikin motar, sai ta kada baki ta ce, “wai dama akwai mutane masu irin wannan rayuwar? Gaskiya kun ga ibtila’in rayuwa, Allah dai yasa kaffara ce a gareku, shi yasa bahaushe ke cewa, ‘ko a bakin kura, ya kamata mutum ya godewa ubangiji’, domin duk musiba da ka shiga, idan ka ji halin da wani yake ciki,sai ka tausaya masa dole.”


Juyowa kawai Sajida ta yi domin ta kalli, mai magana, ba taredaa ta furta ko kalma daya ba ta sake mayaar da fuskarta kan titi ta ci gaba da tuno abubuwa a suka faru da ita a lokacin da take karkashin kasimu.


Da suka kammala tattauna matsalar matar, sai wani da ke zaune a kujerar tsakiya, ya ce, “idan da wanda ke dauke da labari irin wannan ya bamu, ko ba komai zamu kara jin tsoron Allah mu kuma godemasa kan ni’ima da ya bamu komai kanakantanta kuwa.”


Gaba daya suka ce haka ne kuwa. Ganin haka, sai wani matashi da iyakarsa shekaru ashirin da uku ya gayara murya ya soma.



DR. ZAIN
[2/3, 5:06 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾




3⃣3⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_





® *PEN WRITERS ASSOCIATION*





```QUOTE OF THE DAY```




_Allah ne kadai ya san karatun kurma_









*Shafin Masoya*



Wannan shafin naku ne masoya a duk in da kuke a fadin duniyarnan ina godiya da irin addu'o'i da fatan alkhairi da nakesamu daga gareku. Haka ina godiya da shawarwari da kuke bani Allah ya bar mu tare.



***CI GABA***







*LABARIN SHU’AIBU*



“Sunana Shu’aibu, ni haifaffen garin Bunza ne da ke karkashin jihar Kebbi, a unguwar Fulani aka haife ni nan garin Bunza, a nan na tashi na yi wayau har na girma, lura da ban mayar da hankalina kan kiwo ba duk da cewa ni Fulani ne gaba da baya, ya sa mahaifina ya tura ni karatu a garin gashwa da ke karkashin jihar Borno. Nan na yi karatu har na sauke alqur’ani, ina karatun litattafai, kafin na mallaki karfi da hankalin kaina, na kasance ina yin bara gida-gida domin na sami abin da zan ci domin in rayu. Da na mallaki karfin kaina, sai na dinga yin sana’ar dako a kasuwa, a lokutan da ba ma yin karatu a makaranta, nakan je kasuwa domin na sami abin  da zan tallafawa kaina. Bangaren iyayena kuwa, tun lokacin da suka kawo ni karatu, bansake ji daga garesu ba, hasali ma su da kan su ko sau daya basu sake komawa ta kaina ba, tun abin yana damuwata, har ya bi jikina, yanzu banajin komai kan hakan. A in da muke kwanciya kuwa, zamu haura mu dari, kuma ga wurin matsattse wan da dole wasu sai dai su gwamu da wasu kan rashin yalwar wurin kwanciya, bayan wari na daudar jikinmu, numfashi ma kadai a gauraye yake, wanda shi karan kansa wata mabuda ce ta shigowar cututuka daban-daban. Wata rana da ba zan taba mantawa da ita ba, muna aiki da maraice a kasuwa, kusan lokacin magariba, na daukowa wata mata kaya da ta siyo tana gaba ina biyar ta daga baya, muna karasowa bakin kofar kasuwa, sai muka fara jiwo kara ta bindiga, mutane sai guduwa suke yi suna kokarin tserata da rayukansu, hakan ta sa mutane sai gwauruwa suke da junansu a halin fita daga kasuwar, sai faduwa mutane suke yi, ana take wasu, wasu a nan wurin suka rasa rayukansu. Ganin haka, na yada kayan matar da ke dauke a wuyana, na bi jama’a aguje da ke kokarin ficewa daga kasuwar domin su ceci rayukansu. Sai gudu muke yi, irin gudunnan  na idan ba ka yi ka bani wuri, bugu da kari ga duhu sai kara shigowa yake yi, mune bamu tsaya ba har sai da muka kai tsakiyar jeji, kuma ga masifar duhu, saboda mun dauki awa biyar muna gudu, ba tsaiko. Muka tsaya tsakiyar jeji mu hudu ne, wata mata na tareda mu, sai wasu tsofaffi maza gudu biyu. Matar kuma gata dauke da tsohon ciki. Amma a haka take gudu kamar ba ciki a tattare da ita. Nan  muka yada zango cikin jejin da bamusan sunansa ba, bamusan a ina yake ba, bamusan ina zamu nufa ba. Muna tsakiyar hutawa aka fara ruwa masu masifar karfi, dama tun da maraice munga alamun hadari, ba alamun ruwan zasu sauka, saukarsu kawai muka ji,dalili kenan da yasa muka fara sassarfa muna neman in da zamu labe domin mu buya daga shan kashin ruwan sama. Da kyar muka sami wani kwazazzabo mai zurfi muka shiga, duk da bai bamu cikakkiyar kariya daga shan kashin ruwan ba, ya taimaka wurin rage karfin ruwan daga dukan jikinmu kai tsaye. A lokacin ni ba ta kaina nake yi ba, na fi tausayawa matar da ke tare da mu, musamman yadda naga tana cira tana rawar sanyi, a duk lokacin da na kalleta na kuma kalli tsohon cikinta, sai kawai naji hawaye na kwaranyowa daga idanuwana. A haka ina tsaye har ruwan suka kammala sauka gaba daya, kallon da nake wa matar ya sa gaba daya banajin dukan ruwan. Wani abin tausayi, shi ne, wadannan tsofaffin da muke tareda su, a kalla kowannensu zai haura shekara saba’in, wannan shi ne dalili da ya kara tsayar da mu cikin jeji tsawon makwanni muna shan azaba da ganin bone. Domin kamar hadin baki, su duka biyu, suka kamu da rashin lafiya mai tsanani, ban yi zaton zasu rayu ba. Haka ni da wannan matar muke shan wahala wurin kulawa da su, musamman da yake tsofaffi da suke da bukatar kulawa ko ba ciwo bare ga dalili. A rayuwata, ban taba haduwa da mace mai dakakkar zuciya mai karfin hali irin matar da muke tareda ita ba. Duk da cikinta tsoho ne, bazaka gane hakan ba, yadda take tafiyar da lamura gata da sanin ya kamata. Haka nake fita farauta na nemomana abin da zamu ci, in da ita kuma take kokari wurin ganin ta gyara duk abin da na kawo ta sarrafa shi ya zama abinci, tsawon makwanni a jeji. In da muka tashi tukuru domin ganin mun nemawa wadannan tsofaffin magani. Da muka lura cewa sun sami sauki sosai, sai muka tashi daga masaukinmu in da muka mayar da shan kashin ruwa tamkar yin wanka.”



Gaba daya wadanda ke cikin motar hankulansu suka dawo kansa, wasu sai sharan hawaye suke yi, in da wasu ke ajiyar zuciya. Wasu kuwa suka bige da mamakin, wai dama akwai mutane masu irin wannan rayuwa a duniya. Shi kuwa mai tukin motar sai ya kunna musu wakar ZAINUDDEEN ZAIN mai taken ALAMJIRI wacce suka yi da wani mawaki dan Katsina da kuma Ranking Boy dai-dai in da yake cewa;




_ya baro uwa ya baro uba duk a kauye_
_Fadi-nan-tashi-cen burinsa safiya ta waye_


_Ina za ya dora kansa, ba sukuni a barci_
_Ba sutura mai kyawu, walla ba abinci_


_lafiya ta kaurace daga garesa_
_Babu kwanciyar hankali babu walwalarsa_


_sama da su dari suke kwanciya a daki_
_Malami guda daya ba ya dora su tafarki_


_iyaye da gwannati ya kamata duk mu lura_
_su ne fa suke girma su zamemna lalura_


_tun suna kanani tarbiyya sun kasa samu_
_mu duba abinda ke faruwa a makotanmu_


_kula da yaranmu wajibi ne ai a kanmu_
_Idan muka kula kuma lada ai zamu samu_


…………………………………………..


Haka dai wakar ta ci gaba da tafiya, sautin na tashi a hankali, ta yadda ba ya hana kowa ya ji zancen wani. Shu’aibu ya ci gaba da labarinsa.



“muka ci gaba da tafiya, tsawon kwana daya muna tafiya cikin jeji tun da muka baro in da masaukinmu yake har Allah ya kawo mu wani kauye, munsami kulawa sosai daga mutanen kauyen, kwana daya muka yi a garin sai ga mayakan boko haram sun yi wa garin kawanya. Suka zagaye mu, sai suka yi magana da wata amsa amo, cewar, idan mu mazajen mun aminta mu shiga yakin da suke yi su kuwa matan su bi su su tafi da su, da suka ga alamun ba za a amsa musu ba, suka shigo garin, haka suka dinga kama mutane suna yankawa ba imani, ba kokkotawa. Su kuwa matan suka dinga kama su, da sunan wai ganimar yaki. Ganin haka, na kaikaici idanuwansu na ranta a na kare, in da wasu mutum biyu suka biyo ni, da suka tabbatar da cewa ko shekara aka yi bazasu iya kama bahillace a jeji ba da gudu dole suka sallama suka koma wurin jama’arasu. Kun ji rabuwa ta da tawagar da muke tareda su. Nasan ba shakka ba jinina ba ne, amma naji rabuwa da su tamkar rasa wani bangare na rayuwata. Wanda har yanzu mikin yana tare da ni, musamman na matarnan mai ciki. Yanzu Allah kadai yasan halin da take ciki. Ni kuwa da na tabbatar na tsere musu a gudu na nemi wuri na zauna domin in sami karfin tafiya da ci gaba da neman hanya domin in koma asalin garina wato Bunza a jihar Kebbi.”



Gaba daya motar kowa ya yi shiru ya sha jinin jikinsa. Shi kuwa shu’aibu ya ci gaba da labarin ibtila’in da ya same shi sanadiyyar Boko Haram.


Kwanci-tashi har na fado garin Mubi, in da a nan ma harin Boko Haram ya tarar da mu, dalili kenan da yasa dole na yi kaura, na yi amfani da ‘yan kudi da na tara ta hanyar dako na shigo mota ya zuwa garin Yola. A Yola na sauka a wata unguwa da ake kira Anguwan Tana, a nan ne na hadu da wasu samari masu kirki, duk da talakawa ne, sun bani kulawa sosai yaddda ya kamata. Nan na dinga zama, duk da safiya nakan fita neman kudi, idan na sami aikin lebaranci ko dako nakan yi, a hankali ina tara kudi, har na sami guzuri da na tabbatar zai kai ni garina na Bunza a jihar Kebbi. Shi ne na shiga mota domin na koma gida.”



Yana kawowa nan ya yi shiru, suma dai wadanda suke cikin motar shiru suka yi kamar wadanda aka umurta. Cen wani tsoho da ke zaune daga tsakiya ya kada baki ya ce; “wasu lokuta mutane na bani mamaki musamman wadanda suke tura yaransu yawon almajiranci, sai ka ga an tura yaro almajiranci tun bai ma mallaki hankalin kansa ba, wani ko wando bai iya dorawa ba, baisan hagu bare damarsa ba amma a haka za a tura shi almajiranci, abin takaici sai a kaiwa malami shi, ba abincin da zai ci, ba kudin kula da lafiyarsa ba ko sutura a tatter da shi, mafi mamaki sai kaga lokcin da ake tura su almajiranci sai bayan an kammala girbe abinci ne. idan muka kalli garuruwa da suke dauke da ‘yan ta’adda galibi zaka ga sun fi yawan masu yawon bara ne da sunan almajiranci, yaro tun yana kankani zuciyarsa ta mutu da bara, ta ya zai girma ya nemi na kansa ko ya tsaya da kafafuwansa? Allah dai ya kyauta”




Ya fada bayan ya ja dogon tsaki. Nan dai suka ci gaba da tattaunawa, driver kuwa sai sharar gudunsa yake yi, idan ya canja wannan wakar ya saka wannan.




DR. ZAIN
[2/4, 7:52 PM] Dr.  Zain✍🏾: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾





3⃣4⃣







Na





*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_






® *PEN WRITERS ASSOCIATION*





```QUOTE OF THE DAY```



_People will stare..._

_Make it worth their while._









*Shafin Masoya*



_Sis Naja'at_
_Aisha_
_Fatima_
_Zainab_

Kawayena na kaina




***CI GABA***






 Haka suka ci gaba da tafiya cikin motar idan wannan ya bayar da nasa labarin, wancen ya bayar. Kwanci tashi har suka karaso garin Gusau, dole suka lallaba gudun kar su hadu da masu garkuwa da mutane. Suka karaso Sokoto, suka ci abinci suka karaso Kebbi.



Duk da cewa ta dauki lokaci mai tsawo batazo garin ba, fasali na garin bai rikitata ba. Aka saukar da su a tashar sir Yahayya Memorial Hospital Birnin Kebbi, kasancewar suna tareda wani tsoho da ta yi wa alkawarin cewa zata taimake shi, basu nemi motar zuwa garin kalgo ba, sai ta tsayar da wasu jama’a ta tambaye su in da sansanin *‘YAN GUDUN HIJIRA* yake. Aka sanar da ita cewa sansanin guda biyu ne, akwai daya da yake a bayan Oando bye-pass kenan, sai daya da ke unguwar malala quarters hannun riga da sabuwar makabarta. Ganin na malala quarters ya fi zama kusa da su sai suka nufaci cen. Ita da Bilkisu da dan tsoho, suka gangara gangaren malala cikin keke napep, duk in da suka ga taron jama’a sai su tsaya su tambaya, a haka har suka kawo daf da kofar gidan.



Gida ne da ba shafar siminti a bulon ginin haka ba fenti ba kyaure kai kofa ma babu, akwai fadi da gidan ta ciki amma duka kofofin dakunan ba wacce ke da gambu duka labulayya ne aka rufe kofofin da su. Gida ne da cikinsa akwai mutane sama da dari biyu, kama tun daga kananan yara ya zuwa manya maza da mata.



Da maraice suka isa gidan wurin karfe biyar da minti arba’in da wani abu, suka yi sallama da masu gidan, sai wata mata da ake kira Hauwa’u ta fito. Sajida ta yi mata bayanin daga in da suka fito. Bayan matar ta nisa, sai ta ce da su, gaskiya ita ba ta da damar karbar shi tsohon a gidan, amma tana zuwa, fitowa da zata yi bayan ta shiga cikin gidan, sai ta fito da wani saurayi dogo baki da shi mai suna Sani. Ta bar shi da su nan tsaye ta koma cikin gida.



Sajida ta sake kwashe labarinsu da ya dace ya sani ta gayamasa, ta kuma nuna abin da ya zo da su nan shi ne domin su taimakawa wannan tsohon ya sami wurin da zai fake. Sai da ya dauki lokci mai tawo kafin ya fara magana. “gaskiya ba za mu iya barin shi ya zauna nan ba” “saboda me ke nan?” Sajida ta fada cikin mamaki da son jin me zai fito daga bakinsa. “saboda nan da kike gani, duka iyalinmu ne kadai, ba wani wanda ba ya da alaka da mu duk yawanmu da kika gani kuwa, eh! A halin yanzu gwamnati ke biya muna kudin hayar wurinnan, amma asali mu muka saka kudin jikinmu, na matsananciyar shan wuya muka biya hayar gidan, kinga wani wanda ba muharramin matanmu ba bai dace ya zauna a cikin gidanmu ba. Kinssan duniya kumaa ta wuce tunaninmu, yanzu bamuda tabbasa cewa ku ‘*YAN GUDUN HIJIRA* ne da gaske, domin ba rubuce yake a fuskokinku ba, haka bamusan halin shi wannan dattijon ba. ‘yar’uwa naji labarin da kika bayar, amma ki sani muma mun shiga musiba da irin wannan hali da kuma kuka shiga, saboda haka nasan ‘yan boko haram ba zasu yi kasa a guiwa ba har sai sun cinma burinsu, hakan kuma zasu iya yi ta kowacce hanya. Kuyi hakuri”



Ta yi ajiyar zuciya mai tsawo a ranta tana kokarin neman mafita, amma ina duk abinda ta yi yunkurin tunawa, sai ya tafi kamar kura da ke kan taga. Kawai sai hawaye suka fara fitowa daga idanuwanta, ta kalle shi, ta ce “malam Sani ka ce sunanka ko? Gaskiya ka bani kunya, ai shi taimako idan zaka yi baka tunanin sharrin shi wanda zaka taimaka, annabi cewa fa ya yi, muyi wa muminai zaton alkhairi, ko don tsufan wannan bawan Allah ai zaku taimaka masa, duka saura kwana nawa ya bar muku duniyarku, zancen matanku, wannan ai duk ya isa ya yi jikoki da ku. Ba shakka baka shiga ibtila’I da muka shiga ba, domin da ka shiga kuwa, da da gudu ka amshi wannan aikin ladan. Amma ai gari da yawa maye ba ya cin kansa. Ku zo mu tafi” ta fada dai-dai lokacin da take jan hannun Bilkisu a fussace.



Tsoho na daga bayansu suna tafiya cikin sauri, cen tsohon ya ce “yarnan dakata, kije zuwa in da zaki tafi, ni zan iya kula da kaina, duk abinda ya dace zan aikata ku tafi kawai kada na batamaku tafiya”



Ta kalleshi cikin bacin rai kamar zata shiga jikinsa ta dake shi.



“baba bari na tambaye ka, wa ka sani a garinnan?”


“yata ba wan da na sani”



“shi ne kake so muyi kisan kai ta hanyar barinka kai kadai, ai ko da ba mota ta hadamu ba, kai ka isa ka haife ni sosai, kana ganin ba hakki ne a kaina na taimake ba, annabi ya fada yana daga cikin kyawawa ayuka a girmama mai furfura, gashi baba kanka duka farin gashi ne, idan kuma lada ce baka so mu samu sai ka sanar da mu domin mu tafiya”



“ba haka nake nufi ba yata, kawai dai naga wahala ta maku yawa, kuma naji kina fadar har garin kalgo zaku tafi.”



“kar ka damu baba, mudai gama da matsalarka. Garin kalgo duka minti nawa ne daga nan Birnin Kebbi”



Suka ci gaba da tafiya har suka karaso bakin titi.




Suka tari keke napep suka hau, ta ce ya kai su government house. Ya ajiye su a in da ake parkin motoci ta waje, ta taka ya zuwa gate din gidan, in da ta yi kicibis da masu tsaron kofar, kama da ‘yan sanda sai sojoji da kuma civil defence. “me ke tafe da ku?” daya daga cikin masu tsaron kofar ya fada, in da sauran suka kora musu na mujiya, ai kallon su suke yi kasa da sama. Ta kwashe labarinsu ta gaya musu. Cikin yi musu kallon uku saura kwata, daya daga cikin masu tsaron kofar ya ce, “gwamna ba ya nan ku tafi” “tau don Allah ina zamu sami mai kula da walwalar al’umma?” “shima ba ya nan, ku tafi aka ce” “malam ya da haka kake wani korarmu kamar wadanda suka zo bara? Hakkinmu ne fa muka zo mu taimaka su saukar amma kake mana haka?” “bara wa ya sani ko barar kuka zo, ke wallahi ko kubar kofarnan ko rayuwarku ta baci”




Ta yunkura ta yi magana, tsoho ya ja hannunta ya ce “yata zo mu je”



Suka tafi, suna tafiya tana mita da fada, har suka kawo Diamond bank suna tafiya  tsoho ke gayamata.



‘yata ai wannan kadan kika gani, halin masu gadi kenan, sai azo neman gwamna da magana mai muhinmanci amma wadannnan su hana, suna zaluntar gwamnati suna zaluntar talakawa suna zaluntar kawunansu.”


Suka ci gaba da tafiya ba tareda sanin ina zasu nufa ba. Daf da bakin first bank a round about ta central mosque suka hau keke napep. Bilkisu dai bata ce komai ba. Suka nufaci dayan sansanin “*YAN GUDUN HIJIRA* da ke bayan Oando. Nan ma aka gaya musu kamar yadda aka gaya musu a malala, dalili kenan da ya sa suka nemi wuri suka zauna domin ganin ya ya dace su bullowa lamarin. Gata ta iso jaharsu ta dauka komai zai saitu, amma wankin hula na so ya kai ta dare. Suna cikin zantawa suka jiwo kiran sallar magariba.




Suka tafi a massallaci da ke kusa, tsoho ya shiga masallaci ya yi sallah, in da suka tsaya daga waje suka yi sallah. Daga kammala sallah tsoho ya tarar da su a bakin masallacin, suka ci gaba da tafiya, har suka karaso kan titi da ke hannun riga da sabuwar tasha. Suka jira abin hawa, basu samu ba, sai suka ci gaba da tafiya har suka karaso kan babban gate na sabuwar kasuwa ta gaba, in da gobara ta yi barna. Duka suna tafiya ne, suna neman mafita ta hanyar tattauna shawarwari. Daga karshe suka yanke shawarar zasu tafi da shi a unguwar badariya su nema masa in da zai zauna, da suka karaso unguwar badariya a keke napep aka saukar da su dai-dai ‘yar kassuwar badariya, suka nemi gidan mai unguwa aka nuna masu, suka tafi suka yi magana da shi suka kwashe labarinsu suka sanar da shi, ya dauki alkawarin zai kula da tsoho da ikon Allah. Da akayi isha suka yi sallama da maigari ita da Bilkisu suka nufaci garin kalgo, bayna ta kawo kudi har dubu ashirin ta bai wa tsoho, ta ce ya tanka jalli da su ya sami sana’a ya dinga yi da zai dinga kula da kansa.



Badariya gari ne da ke da kafaffen tarihi, amma a halin yanzu unguwa ce a cikin Birnin Kebbi, kasancewar gine-gine sun tarar da su. Mutane ne da a zamanin baya sun fi shahara da farauta da noma, Hausawa ne, amma sune surke da Fulani da Zabarmawa. Wan da ya sa suka zama kamar tanti na kasuwanci da kuma harkar gini saboda hadewarsu da Birnin Kebbi.



Kai tsaye a tashar da ke Haliru Abdu keke napep ta ajiyesu, suka tari mota da zata kai su Kalgo. Cikin mintuna kadan motarsu ta tashi.




08034840276

DR. ZAIN
[2/24, 7:48 PM] Dr.  Zain✍🏾: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
                    🐾



_last page_



3⃣5⃣







Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_





® *PEN WRITERS ASSOCIATION*





```QUOTE OF THE DAY```





_Mulki da kasaita ubangijinmu shi ya bada_







*Shafin Masoya*




Yan Gudun Hijira Fans
MATA TUBALIN AL'UMMA


***CI GABA***






Daga saukarsu daga keke napep a farkon titi daga round in da zai sadaka da babban filin wasan kwallo na Haliru Abdu, wanda ya fi shaahara da Haliru Abdu mini stadium Birnin Kebbi, in da ta fuskarsa ne ake samun motoci da zasu dauki mutum ya zuwa bunza, kalgo jega minna kamba da dai sauran gruruwa. Nan wata mota ta tsaya gabanssu tun kafin su karasa in da motoci ke taruwa. Suka yi sauri suka shiga motar, kamar yadda mai motar ya umarta, a cwarsa doka ce daukar mutum kan hanya, amma su aikaatawa suke ba ruwansu. Daga shigarta ta tambaya, nawa ne kudin motar, ya ce da su naira dari-dari zasu biya. Ya buga mota suka ci gaba da tafiya. Daga ita sai Bilkisu a motar, sai wani dan saurayi da ya ce shi a Federal University Birnin Kebbi za a ajiye shi FUBK. A kan hanya ya dauki wasu da zasu tafi kalgo, har dai motarsa ta cika, mutum biyu a gaba sai mutum hudu a baya.


Sai fira ake yi cikin motar, in da Sajida ba abinda ke ranta irin tunanin halin da zata trar da gida, anya kuwa ma zasu shidata? Batasan lokacin da hawaye suka fara kwaranya daga idnuwanta ba, sai ji kwai tayi Bilkisu na kokarin sharemata. Dalili ke nan da ya mayar da hankalin wata mata da ke kusa da su ‘yar kimanain shekar 29, amma zaka yi zaton ta haura shekaru arba’in kan galabaita da shan wahala. Budar bakin wnnan matar ta kalli sajida ta ce, “bauyar Allah, komai fa ya yi zafi, to maganinsa Allah sarki, kin ganni nan, ba musiba da ban fada ba, babu tashin hankali da ban gani ba a rayuwa, amma dole na jingine komai gefe, na kurawa sarautar ubangiji idanu na yi wa kaina fada domin na gina kaina da kaina. Ba abin da kuka zai haifar maki, face mutuwar zuciya” cikin sanyin jiki Sajida ta juyo ta kalli wannan matar da take fara sol duk da ba kyakkyawa ba ce, sai ta kada baki ta ce, “ke kuwa boyar Allah wacce musiba kika shiga haka? Ki sanar da mu wata kila mu amfana muma mu sami izina daga labarinki.”


*LABARIN SHAMSIYYA*


Bayan ta nisa, sai ta soma.


“Sunana Shamsiyya, ni asalin ‘Yar garin Wamakko ce, da ke cikin jahar sokoto, mahaifina da mahaifiyata duka haifaffun sokoto ne, amma yanayin aiki yasa a garin Tambuwal aka haife ni, nan nayi karatu na primary da secondary, haka jami’a a  Usman Danfodio University Sokoto nayi karatun diploma. Bansami aiki ba, kasancear yanayi na kasa idan ba wanda ya tsayamaka, kai talaka sai dai ka yi hakuri, duk da kyawun takarduna kuwa, a haka na sha yawun neman aiki ba dare ba rana, har na gaji dole na saduda. Kan haka mahaifina ya sakani a gaba akan tilas sai na fiddo da mijin aure, ni kuwa ba mai tara samari ba ce, wanda nake so kuma na bincike shi bai shirya ba, kan haka na sha tsangwama da barazan daga mahaifana kan lallai zasu aurar da ni ga duk wanda suka ga dama, na sha kuka har idnuwana suka kumbura, har kuka ya zama tamkar  wani bangare na rayuwata. Haka na ci gaba da kokartawa na gani ko zan iya taimkawa Jamilu saurayina domin mu samu mu yi aure, amma abin ya ci tura, kasancewar shima kamar ni baisami aiki ba, sai ya yi lebaranci kafin ya sami ya kula da mahaifansa da kannensa guda uku. Wannan ya sa na shiga damuwa matuka. Kwanaki da mahaifana suka dibamin akan lallai na fidda miji, suka cika, hakan ta sa suka sake zaunar  da ni suka bincike ni kan zancen, na kasa basu magana da zata gamsar da su, hakan ta kara tunzurar da su, suka ce tabbas zasu hadani da wani wai Alhaji Rabi’u da ke nan Tambuwal, tsoho ne da zai haura shekaru saba’in, amma mai kudi ne sosai, ni kuwa a lokacin shekaruna 25. Na ci kuka sosai, tun da safe na sami Jamilu, na sanar da shi abinda ke faruwa. Ranar kamar ya yi hauka, ya rasa me ke yi masa dadi, a haka ya rarrasheni ya nuna na kwantar da hankalina, bamu isa mu canja kaddarar Allah ba, shi dai yanada tabbaacin cewa yana ji a jikinsa, shi zai aure ni. Zantuknsa sun kwantar mani da hankali, amma sun kasa fahimtar da ni cewa gaskiya yake fada, domin ni sai na dauka cewa nafi son shi ne, hakan ta sa na koma gid sai kuka nake yi ba ko kokotawa. Sai na share kwana biyu ba tareda na sakawa cikina komai ba, duk na yi baki na rame. Kwatsam ina cikin daki ina sharbar kuka kamar kullum, ga mahaifina ya shigo dakin da nake, shigowarsa, ya wurgomin katuka na gayyatar daurin aure ya fice abin sa, na yi maza na dauko, katukan sun kai kimanin dari biyu. Dubawa da zan yi sai nag a anrubuta. ‘Iyalan gidan Malam Kasimu tsoho da na Malam Sani Kahutu na gayyatar mal,malama….zuwa daurin auren ‘ya’yansu…..’”ai sunana da na hango wai za a dura aurena da Alhaji Rabi’u, ya sa cikina ya murda gaba daya yawun bakina ya tsinke, abin mamaki saura kwana uku a daura auren namu. Hakan ta sa na tashi a gigice, na yo garka, na tarar da Jamilu na sanar da shi, cikin kidimewa ya rushe da kuka, ya gayamin ai ya dade da fara ginin da zai sakani, kum ya sayar da dabbobinsa da dama har ya hada da yawa daga lefe da zai aiko gidanmu, duk gudun kar wannan ta faru. Nan muka zanta kan ina zamu sami mafita, na nunamasa mafita daya ce, kawai yazo mu gudu, in da ya nunamin illar aikata hakan, ya nuna kamar bijirewa umarnin iyayenmu ne idan hakan ta faru, ya ce na ajiye hankalina wuri daya mafita bazata gagara ba. Na faufaye, har na fara gayamasa maganganu marasa dadi, ina fadar dama nasan ni ke sonsa ba shi ke sona ba, duk yadda zai kwantarmin da hankali ya yi, amma na ki na saurare shi. Karshen ganina da shi kenan, domin da asubar fari na saci kudin mahaifiyata nayo kudin mota da su na zo garin Jega, na jima a nan Jega ina harkar sayar da abinci ina tara kudi, sai daga baya na dawo nan Kalgo, in da kasuwanci na ya girma, bayan sana’ar abinci har atmafa ina sayarwa da sauran kayayyaki”


*CI GABAN LABARIN ‘YAN GUDUN HIJIRA*



Nan Sajida ta nia, ta ce “kin taba tunanin wanne hali shi Jmilu yake ciki? Ba kya tsoron a yi tuninin shi ya boyeki har a cutar da shi? Kin yafe mahaifiyarki ne da ko sau daya baki koma garinku ba tsawon shekaru hudu? Allah ya kyauta” sajida ta fada, a dai dai lokacin da  take cewa driver ya ajiye su a unguwar Tudun Tasha.



Aka ajiye su suka yiwa sauran fatan alkahiri su kuwa suka nufaci wasu mutane da ke zaune gefen titi ta hannun dama, bayan sun yi masu sallama, suka gaisa da su, sai Sajida take tambayarsu ko Allah yasa sun san unguwa da ake kira shiyar Huci. Inda wani saurayi ya nuna ya sani, haka ya yi musu bayani sosai, kyam tayi tana kallonsa, da ya fahimci ba in da suka sani, sai ya ce su biyo shi, haka yana gaba suna bayansa, har suka karaso a shiyar Huci, suka yi masa godiya ya koma, ita kuwa ta sake tambayar wasu bayin Allah kan gidansu, kasancewar garin ba babba ba ne, nan take  aka nuna mata.



Gida ne da ba kyaure  tare da shi, ginin na laka ne ta gaba, amma sauran katangar gidan duk da darni aka yi amfani aka zagaye shi, ba shakka ta dauki shekaru masu tsawo bata zo ba, amma fasalin gidansu bai canja mata ba, nan kawai ta fashe da kuka, ta rasa kukan me take yi, kukan bakin ciki na abubuwa da suka faru da ita, ko kukan dadi na ga shi ta dawo gida.



Suka kutsa kai sukayi sallama, yara kawai ke guje-guje a farfajiyar gidan da ya sha shara tsaf, a cen gefe kuwa wata tsohuwa ce zaune kan tabarma abinci kusan kala uku a gabanta, sai kokarin kiran jikokinta take kan su zo su ci abinci. Zumbur ta mike duk da jikinta na rawa, a haka ta tako da sauri, tana fadar “muryar wa nake ji haka? Sajida ke ce kuwa?” ta fada a daidai lokacin da ta rungumota tana kuka, ita ma sajidar ta fashe da kuka, ta kara rungume mahaifiyarta. “inna wannan wacece kuma?” “mahaifiyata ce” wannan ya sa kakar Bikisu ta saki sajida ta juwo ta rungume Bilkisu, cikin muryar kuka ta ce aje a kira mahaifinta.



Da ya shigo ta gabatar da Sajida gare shi, nan ya fara fashewa da kuka, yara da mata da ke gidan sunsan Sajida a labari, amma sai yau ubanguji ya nufa suka ganta. Nan ta kwashe duka abinda ya faru da ita ta gaya musu, mahaifanta suka bata hakuri, ta tambayi saurayinta, aka sanar da ita cewa, ya rasu da jimawa. Bayan ta yi kuka na wani lokaci aka nuna mata in da zata zauna ita da diyarta.



Kwana biyu da ta nutsu ta tambayi kalar sana’ar da ta fi ci aka sanar da ita, ta fara a hankali, ta kuma saka yarinyarta karatu a BICE da ke garin Birnin Kebbi domin ta ci gaba da karatunta.



Haka dai Sajida ta zama hamshakiyar ‘yar kasuwa mai kudi sosai cikin shekaru biyu in da da bisani ta auri wani danmajalisa da ke Aliero, bayan ta tura ‘yarta karatu jami’a domin ta karanci law.




Alhamdulillahi, nan wannan labarin ya tsaya. Littafina na gaba sunansa *KANGIN BAUTA* _KAFIRCIN TURAWAN YAMMA_ amma kafin na fara sakinsa zamu sake sakin *ARTABON SARAKAI*




08034840276
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_



Download Ýan Gudun Hijira Littafi Na Daya Complete