Zaku iya downloading na wasu littatafan mu amatsayin ebook ta hanyar
latsa wannan blue din rubutun www.shuraih.waphall.com
GUDUN TSIRA
Littafi na daya(1)
Part A
AYARI NE NA WATA KABILA wacce
ake kira da
BANU
HANZAR.Shugaban wannan kabilar ya
kasance
Gwarzon Jarumi kuma sadauki na
gaske wanda
ake
kira da SHARWAN IBN KILYIN.Itadai
wannan
kabilar
asalinsu sun fito ne daga yammacin
birnin Kisra
ya
zamana cewa rayuwarsu taci gaba a
cikin zagaya
duniya saboda neman inda tsuro da
ruwa
yake,domin kiwon dabbobinsu da kuma
farauta.Masu
bincike da hasashe na wannan zamani
sun
tabbatar
da cewa a duniya kaf babu wadansu
mutane
wadanda suka lakanci iya kiwo da
farauta sama da
mutanen kabilar Banu Hanzar kuma su
dama can
tun farkon rayuwarsu a jeji suke
rayuwarsu tun
kafin
ma birnin Kisra ta kafu don haka kabilar
Banu
Hanzar suna habaka a yawa kumag ashi suna da
zaratan jarumai gwanayen yaki don
haka yan fashi
ko yan hari suna matukar
shayinsu.Lokacin da
kasar
Kisra ta kafu kuma ta gawurta a
zamanin wani
azzalumin sarki wanda ake kira da suna
RUGUZAN
IBN MAULAS sai ya fara matsawa
kabilar banu
hanzar da biyan haraji mai yawa akan
zaman da
sukeyi a cikin yankin kasarsa.Ba komai
ne yasa
Sarki Ruguzan yayi haka ba saboda
ganin kabilar
ta
banu hanzar take da yawa da kuma
zaratan
jarumai,yana tsoron kada wata rana
suyi tunanin yi
masa juyin mulki su karbe masa
KARAGAR

Download it for continue reading

Download Gudun Tsira Part 1