[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [10:52PM, 10/18/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 41����
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Shi kuwa Dauda da ya riga ya san tarkon da ya
dana fadi ya ke ba laifin ki ba ne,ba laifin ki
bane laifin mata ta ne tin da sanadin ta mai
nakasa kamar ki ta sami lasisin ci mun
mutunci......Sumayya ta harzuga ta ce nakasa
gare ni a zahirance amma a zuci kafi kowa
nakasa,shashasah mara mutunci,dabba na
tausayawa Bilkisu,in har haka maza su ke
gwara na mutu ba aure....ta na gama fadan
haka ta shige ciki da saurin ta,Bilkisu hauka ne
kawai ba ta yi ba,kawai yayar ta na zagin mijin
ta,ta kashe wayar ta sake kira,Dauda ya daga
ya shiga shirya ma ta karyar yanda aka yi.!
Sumayya kuwa ta na shiga daki hijab da zani
kawai ta iya dauka ta sa,silifas ne kafar ta,ta
fito ba ta ma san inda ta dosa ba,ta na ji Sadik
na fadin laa Aunty Sumayya ta fita,Dauda ya ce
kin ji ma ta fita ko?me Bilkisu ta ce oho......
Tafiya ta ke tana kuka,wani irin sanyi ke busa
ta gashi hijab kawai ta sa ba ta maida rigar
sanyin ta ba. Da sanyi yayi sanyi,iska na kada
ta gashi ba ta da ko sisi dole ta ja gefe,ta na
kakkaura,ta na rawan sanyi.
Ba kamar kullum ba,dan yawan na su yau ya
sha bambam,dan a kalla mun dirga bikes kusan
ishirin,sai da su ka cika sannan su ka tsaya
kofar gidan su Moh,ba tare da bata lokaci ba
ya fito da shigar sa cikin bakaken kaya tin daga
sama har kasa,hatta hamlet din sa baki ne,ga
katan jacket da ya rufe shi ruf ba a kanin fatar
jikin shi ko kadan. !
Kai tsaye su ka dauki hanya,Abuja su ka
nufa,Ba su kai ga nisa ba ya hange ta sai
rawar dari ta ke,kuma da alama kamar kuka ta
ke,ya so ya dake ya wucewar sa,amma ina ya
kasa,kawai sai ganin shi su ka yi ya ja ya tsaya
gaban ta dan haka dole kowa ya tsaya...
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [10:56PM, 10/18/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 42����
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Kuka ta ke ba kakkautawa,sai jin karar bike ta
yi gaban ta,ta dago a hankali ta bi su da
kallo,ganin yawan su da shigar su gashi duk
fuskokin su rufe cikin hamlet ya firgita ta...ta
dan yi baya,Moh ne ya sauko daga na sa bike
din,ya cire hamlet din sa ya na duban ta,tuni
ta waye shi,hankalin ta ya dan kwanta.....haka
sauran ma duka su ka ciro na su,daya daga
cikin su dake groups din bike riders ne ba su
Shamo kadai ba, cikin rashin fahimta ya ce me
ya kawo tsayuwar mu?Shamo ya nuna ma sa
Sumayya ta tare da fading if am nt mistaking
kayan Moh ce.........daya ya ce ka na nufin..kan
ya karasa Moh da idanun sa ke kan fuskar
Sumayya, a hankali muryansa a sanyaye, ya ce
ku wuce kawai,zan biyo ku. Ba musu dan su
Shamo sun san za a yi haka,su ka maida
hamlet din su su ka yi gaba...
Gaban ta ya tsaya ya na nazartar ta,daga
bisani ya ce what is wrong?me ki ke yi a nan?
maimakon ta bashi amsa sai ta dada fashewa
da kuka,mutane da ke wucewa sai kallon su
suke,bare Moh unguwar su ce ba wanda be
San shi ba. Ganin haka Moh ya aje hamlet din
sa kan bike,ya matso kusa da ita ya na
shhhhhsh!!!kar ki tara min jama'a mana,kamar
wacce aka zuga,sai ma dada rera kukan ta ta
ke.
Moh ya daga kafada ya sauke tare da fadin
shikenan cry all you want.....cry ur hrt out. Ya
sa hannu a aljihu ya fidda hanky ya mi ka ma
ta. Ta karba ta na kokarin goge hawayen,amma
ta kasa tsada su. Sai da su ka kai kusan minti
goma sha biyar ta na sharbar hawaye,ya
jingina jikin bike din sa kafafun sa harde hannu
cikin aljihu ya na kallan ta. Sai da ta yi mai isar
ta,ta koma sai ajiyar zuciya kawai ta ke. Moh
ya taso ya na cire Jacket din jikin sa,wani irin
iska mai sanyi ce ta buso su,sai da Sumayya ta
girgiza,idanun sa kan ta,ya karasa gare
ta,Jacket din sa da ya ciro ya rage da ga shi sai
rigar sa ta ciki lng slip ya daura kafadar
Sumayya ta hagu,ya zagayar da ita ta bayan
ta,ta sauka bisa kafadar ta na hagu,ya ma ta
kamar mayafi,a hankali Sumayya ta dago
idanun ta da ke cike da kwalla su ka shiga na
sa yayin da ya sakar ma ta murmushin da ta ji
shi har ran ta,ya ce even when you are crying
you are beautiful too....
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: HASKEN IDANIYA 43
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Yana fadar hakan, sai Sumayya ta sami kanta
tana mai Murmushi cike da kunya, ta yi saurin
kasa da idanun ta yayinda ta ke kokarin gyara
rigar sanyin da ya yafa ma ta dan kuwa ta na
bukatar shi. Moh na duban ta ya ce yauwa
now shez smiling...... Ta sa tafukan hannun ta
biyu ta rufe fuskar ta. Hakan da ta yi sai ta
burge shi,shi kam ya na san diya mace mai
kunya,dan kuwa ita kunya ado ce,kuma yaji su
shamo na fadar cewa duk mace mai jin kunyar
ka to na yin ka kenan.........
Ya na san jin dalilin da ya sa ta kuka,amma ya
san ba zai wuce sokonci da sakaci irin na
Sumayya ba,dan kila takaici ya rufe shi in ya
ji,dan haka ya share tare da tambayar ta ina
ne gidan ku?ya kamata ki tafi kan ki zama
kankara,mu je na raka ki.....
Kai a kasa Sumayya ta ce ai ba nan kusa ba
ne,gyadi-gyadi ne fa....ya gyada kai,tare da
fadin owk ina zuwa. Waya ya fitar ya na
kira,bayan an daga ya ce Mallam shehu, ka na
ta ina ne?eh Muhammad ne....jin ya fadi sunan
sa na asali da bakin sa ya sata dagowa da
sauri...ta ce Muhammad ko de shi ne
Muhammad din da ta gani a wayar ta......?ta
saki baki da hanci ta na kallan sa kasancewar
waya ya ke ta sami damar kare ma fuskan shi
kallo........
Wayar ya kare ya na fadin toh ka zo yanzu ina
jiran ka,eh titin baya ne. Ya aje wayar ya na
kokarin sawa a aljihu,ko da ya kalle ta,ya ga da
gaske kallan na shi ta ke sai ya kashe ma ta
ido ya ce ko na mi ki ne yan mata? sai sannan
ta ankare da kallan sa da ta ke,kunya ya cika
ta yayinda ta yi saurin dauke kai,ta na dada
dukunkuna cikin rigar sanyin sa. Ya
murmusa,wani sanyi ne ya buso shi duk yanda
ya so da daurewa sai da ya girgiza,hannu ya
tura cikin aljihu ya na dan huro iska ta baki
san...ta kasan idon ta ta ke kallan sa,ol her lyf
ba ta taba ganin wanda ya ke zame ma ta
haske kamar wannan bawan Allah da ke gaban
ta ba,duk kukan da bakin cikin da ta kwaso
yanzu yanzu ya sa ta sami sanyi cikin zuciyar
ta,ba tin yau ba Muhammad ya ke zama
waraka na matsalolin ta,duk lalacewar shi,ya
zame mata madafa a yan kwanakin da ta san
shi,ko ba komai in him ta na samin hasken
idaniya....HASKEN IDANIYA TA.......me ki ka ce?
ya tambaye ta dan yaji kamar ta yi magana..
Ita ma din ba ta san sanda ta furta ba,dan
maganar zuci ta ke,sai kawai ta girgiza tare da
fadin ba komai. Moh ya gyada kai tare da fadin
yanzu driver zai zo ya maida ke gida,na san ba
za ki iya hawa bike ba.....
Zaharaddeen $homar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [00:04, 10/21/2015] Khadija Sidi: HASKEN
IDANIYA 44
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Sumayya ta yi saurin cewa da ma ba na
hawa.....cikin zolaya Moh ya ce dama ba zan
dauke ki ba ni ma,ba na daukan
mata,musammam mace mai kuka!!! Yanda ya
fadi maganar sai ya qara burgeta, ta dan kalle
shi yanda ta ga murmushi kunshe a bakin sa ta
san zolayar ta ya ke,ta dauke kai tare da fadin
TCH irin kan ka ake ji.....hakan da ta yi ya
bawa Moh dariya,dariya yayi sosai,shi kan shi
ya yi mamaki wai shi ke zolayar mace,har
kuma ta na sashi dariya....ya kara yin wani
dariya....da sauri Sumayya ta ce kai ka yi?cikin
rashin fahimta,fuskar sa cike da fara'a,ya ce
me fa?ni na yi me?ta ce dariya.....pls do it
again....yana ma kyau dama kana dariya!?......
Wani abu ne sabo ya lullube Moh,be san sanda
ya ce ah ah kin manta ke ki ka yi......Gosh
lady......! now you got me blushn......ya kau da
kai shi a lalle so ya ke ya daure fuska,dan ta sa
ya ji nauyi for d fast tym a rayuwar Moh ya ji
kunya.!
Sumayya ta lura da hakan,yanda ta ga kuma ga
murmushin amma a dole so ya ke ya sha
kunu,ya wani kau da kai ya bafe.....ba ta san
sanda ta bushe da dariya ba,ta na ka yi dariyar
ka kawai,surru ne ba mai ji....
Maganar ta ta ya bashi dariya,be san sanda ya
sake sa dariya ba,ya juyo su na kallan juna,dan
dariya idanun ta har wani kyalli ya ke ya ciko
da ruwa,dariyar ta ta ta burge shi matuqa,ya
tsaya ya na kallan ta,sam ba ta lura ba,sai da
ta yi me isar ta ta ankare da kallan ta da ya
ke,ita ma din kallan sa ta yi kafin ta yi kasa da
na ta idon,ta ji ya ce I love it wen you look at
me way.......ta yi shiru ta na kallan kasa,karar
tsayuwar motar da su ka ji ya su kallan wajan
da sauri. Moh kamar ya maida Baba Idi dan
kuwa ya dade be tsinci kan sa a yanayi mai
dadi kamar wanda ya shiga kasencewar sa tare
da Sumayya.
Lokaci daya baisan sanda fuskarshi ya daure
ba, kamar bashine yake dariya dazuba. Ba
yanda zai yi ya ce ga wanda zai kai ki gida a
Yanda ya saba magana a daure haka ya mata
magana.....malam Shehu ya fito ya na karam
bani Oga gani,ya na magana ne ya na kallan
Sumayya. Moh ya ce Mallam Idi kaya na za ka
kai gida.....Mallam idi ya ce to ina kayan na
sakasu a mota. Moh baisan sanda ya saki
fuskaba, Moh na murmushi ya ce Mallam idi
kayan nan yafi karfin dauka,ga ta gaban
ka....kunya ya cika Sumayya ganin yanda
Mallam shehu ya kalle ta ya na aw toh toh eh
gaskiya ba batun dauka,ran ki ya dadi ai sai mu
tafi....Moh ya ce jeka mota ni zan sa kaya na
da kai na. Mallam idi ya wuce mota ya na toh
toh ai sai na je din,ya koma mota ya zauna.
Sumayya ta kalli Moh irin kallan ayya mana,shi
kuwa ko aji kin sa,ya bude ma ta bayan mota
ta tashi tana cilla qafa ,sai da ta shiga ta zauna
ta fara kokarin ciro ma sa rigar sanyin shi,ya
dakatar da ita ta hanyar fadin am sure ba ni za
ki bawa ba,kin fi ni bukata,take kia of your
slf,nd cry no more,owk?ta girgiza kai,ta ce
nagode. Murmushi yayi ya ce ni ne da godiya
you made my day......ya rufa motar,Mallam idi
ya ja mortar,sai da su ka fara tafiya ta juyo ta
ga har lokacin kallan motar ya ke,ba ta san
sanda ta daga ma sa hannu ba,haka shi ma ya
tsinci kan sa ya na daga mata.
Moh kenan.......
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: HASKEN IDANIYA 45
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Hannusa a aljihu har sai da su ka kurewa
ganin sa sannan ya saki ajiyar zuciya,when it
comes to Sumayya,shi kan shi ya na mamakin
kan sa. Gida ya koma dan kuwa ba ya ji zai iya
bin yan uwan sa,first tym da za a yi tafiya mai
nisa ba tare da shi ba kenan.
Sai da su ka dauki hanya sosai sannan ta
gaishe da Mallam shehu. Ko da su ka dauki
hanya sosai sai ta tashi daga mafarkin da ke,ta
komo rayuwar ta,gaban ta ya shiga dukan uku
uku. Har kofar gida ya aje ta su ka yi
sallama,Sumayya ta shige ciki.
Ta na shiga ta tadda Gwaggo a tsakar gida sai
cika ta ke ta na batsewa,ganin Sumayya tuni ta
rufe ta da duka,Sumayya ta na na shiga uku
me na mi ki!!!!!?ina Gwaggo jibgar Sumayya ta
ke ta na muguwa,azzaluma,almura ke kin ki
auruwa shi ne za ki je ki kashewa yar uwar ki
aure!!!?
Abbu ne ya fito da sauri ya kwaci Sumayya
Hannun Gwaggo,ta na mallam ka bari na dake
ta na huce,yarinyar nan idan ta kuntata ma ka
bakin ciki ya miji talaka!!!!!yanzu Bilki ta kira ni
ta na kuka ta zayya na min yanda ta ci
mutuncin mijin ta gaban yara,kuma Bilkin ta na
ji,mara mutunci da na kira Daudan ma na har
da kwallan sa.
Sumayya na kuka ta buye bayan Abbu fadi ta
ke wlh Abbu ba haka ba ne,wlh Abbu mijin
Bilkisu ba dan mutunci ba ne.....wani kukan
kura Gwaggo ta yi za ta damko Sumayya,Abbu
ya yi saurin tura ta baya,ya na ke!!ke dalla
matsa,kar ki sake ki kara taba ta,wannan wani
irin masifa ne wai Huwaila?kin yi bincike kin ji
abun da ya faru ne?kin ji ta bakin diyar ki?
kawai sai ki yanke hukunci haka ake?ke
Sumayya wuce ciki,anjima ki zo ki min bayani.
Sumayya ta raba ta shige dakin su jiki na kyar
ma. Gwaggo ta yi kwafa,wlh wannan yarinyar
da ana bada sadaka da tuni na ba ta ita na
huta,dan na cire buri akan ta. Cikin takaici
Abbu ya ce ana bayarwa,sai ki ba da Ita din
mu gani,Allah ya wadar na ka ya lalace....
Gwaggo ko a jikinta, ji take kamar ta tattara
Sumayya tayi kyauta da ita, Sumayya ta shiga
daki tanata kuka,tana baqin chikin wannan
rayuwar data sami kanta aciki, lokaci daya ta
tuna cewa duk abinda yayi farko yanada
qarshe, kuma ta tabbata akwai hikima akan
hakan da Allah yayita, sabida Allah duk abinda
yayi yanada hadafin yinsa, fatanta Allah ya
bata ikon chinye wannan jarabawar, tana tsaka
da tunini saiga Abbu ya turo qofa, ya nemi
ixinin shigowa,Sumayya tayi sauri ta tashi
xaune, tace ya shigo Abbu ya shigo ya nemi gu
ya xauna ya nemi bayanin yanda abin n ya
faru, anan Sumayya ta bashi labarin komai
dalla dalla. Abbu baiyi mamaki ba Dan ya
Dade da jin halin dauda Amma ba halin fada,
tunda huwaila ba yarda takeyiba, anan ya qara
yiwa Sumayya nasiha, akan ta kare mutuncinta,
ya saka mata albarka ya fita.....
Yinin ranar Sumayya a daki ta wuni tana
tunanin rayuwarta, a daddafe tayi sallah tazo
ta kwanta, wayarta ta tashi xata dauko,
juyowan da xatayi taji wani qamshi, Wanda
yasa ta riqa jin qirjinta yana bugawa, amma
bata gane ko wane irin qamshi bane, jin
qamshin ya sanya ta farin ciki, ta lumshe ido
batasan daga ina qamshin yake fitowaba, daga
kan da xatayi, sai taga rigar Moh daya bata a
sakale gefenta, tasa hannu ta janyo rigar sai ta
fahimci rigar ce take qamshi, wani murmushi ta
saka, lokaci daya ta manta da baqin cikinta,
miyasa Moh yakeso ya xama HASKEN
IDANIYANTA.!! Duk lokacinda ta ganshi takan
manta ko ita wacece,! batasan lokacinda ta
dunqule rigarba ta dora a fuskanta tana
shinshina tana murmushi.......
***********
A bangaren Moh kuwa, yana isa gida ya fada
daki, ya kwanta yana kallon wutar dakin, xahiri
ita yake kallo, amma kuma xuciyansa yana
chan gun Sumayya, yana tariyo kukanta, da
kuma dariyanta, hadi da murmushinta, wani
juyi yayi ya dunqule hannu, wannan yarinyar
komai tayi kyau take, shez beauty by nature,
Wayanshi ya dauko, ya fara Neman number
Sumayya, sai yaya ba number ta aciki, sai
lokacin ya tuna number ta yana dayan
wayanshi, kuma wayan yana chikin aljihun rigar
da ya baiwa Sumayya.!
Wani murmushi yayi, ya kira Malam Idi,
Kazo ka kaini gidan da kai min kayana....!
Bai jira amsaba ya kashe waya.
Malam Idi ya sake masa waya, yace yaje dauko
Alhaji ne a airport sai idan ya dawo, hakan yasa
ya haqura har Malam Idi ya dawo.
Ya sami kanshi yanason ya chanxa tufafinsa
daga qananan kaya, idan kaga Moh da shadda
sai ranar sallah, shima dai Alhajin sa yake
matsa masa, ya sakashi gaba yasa dole ya saka
kayan.
Haka ya dauko kayan sa na sallah ya saka, ya
feshesu da turare,
Baisan dalilin da yasa ya saka wannan kayan
ba.....
ya jira Malam Idi har ya dawo, yana xuwa ya
shiga mota suka wuce sai unguwar su
Sumayya. Yau Moh ne a mota, Wanda duk
Duniya idan xaije xaman bike dinsa yake tafiya,
Sai Gashi a qafar gidan Sumayyar shi............
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [00:17, 10/21/2015] Khadija Sidi: HASKEN
IDANIYA 47
Na khadija Sidi & Hauwa M. Jabo
Malam Idi yace to Muhammad gamu a gidan,
Moh ya kalleshi, Malam Idi ya xa'ayi naga
kayana!?
To saidai a sami yaro ya kirata ko!? Ya daga
kafada irin duk Yanda kayi daidai ne.!
Mlm Idi ya sami yaro a ka aika kiran Sumayya,
Yaro yace ana sallama da Sumayya, Gwaggo
tace yaro Sumayya kodai lele!? Yace nidai
Sumayya aka cemin. Kuma yaro kace chikin
wata babbar mota suke ko!? Yace eh irin na
chikin TV dinnan na american film. Gwaggo ta
riqe baki, tace to kace tana xuwa, bayan yaro
ya fita Gwaggo ta leqa waje ta hango motar
saida taji jiri, Dan yayanta suna da samari
masu kudi amma ba mai irin wannan motan.!!
Aranta tace badai Sumayya ba, wannan farin
jini saidai lelena,
Waxai biyo wannan gurguwar tayi tsaki ta koma
ciki.
Lele... Lele... Ki fito ana Neman ki. Lele cike da
mamaki, nemana kuma!? Eh ki fito yar albarka.
Cike da mamaki ta fito batasan tayi
appointment da kowaba, ki dan gyara fuskatki,
Dan naga da babbar mota yaxo.!
Lele kuwa ta shiga shiri kwalliya take kamar
me, , ta fesa turare kala kala ta chanxa tufafi,
Sumayya tana xaune tana kallon ta. Har ta
qare ta fito Gwaggo ta fara mata kirari, lele
anata yanga ana daukar kai, ta fita, waje......
Tana xuwa Moh ya fito daga chikin mota, ta
kalli Moh ita kanta tasan wannan guy yafi
qarfinta, Dan saida tadan rude da ganinsa. Ta
daure tana Dan kwarkwasa, tace sannu fa. Ya
kalli mlm Idi yace nan kuwa ka kawo min
kayana.!?
Mlm Shehu yace yallabai ai idan ma ka kalli
wannan zakaga sunyi kama, nama dauka itace
saida naga wannan mai lafiyace, waccan kuma
batada lafiya,
wani kallon banxa Moh yayiwa mlm Idi saida ya
rude Dan yasan halin Moh....
Kayan nawane Mara lafiya!? Allah ya baka
haquri,
Moh yace masa ni kayana nakeso. ya naga
wannan. Ya nuna lele da hannu, sai lokacin
Moh ya daga kai ya kalli lele, lallai tayi kama da
kayansa sosai.
yace ina kayana!?
Ta kalleshi cike da mamaki, tana wani fari da
ido, tace kayan ka kuma!? Yace eh kayana.!
Sai Mlm Idi ya matso kusa da ita yace mata
mai Dan cilla qafar nan muke nema, Amma
Moh baiji ba. Tace au.... Ta tabe baki wai gurin
adda kazo.!?
Allah dai yasa ba sata ta makaba naji kana
fadar kayanka....
Moh ko kallonta bai qara yiba, bare yaji mi take
fada, ta shiga gida harga Allah Moh ya mata,
tace Gwaggo nikam naje naji yana kayanshi,
inaga adda ta mishi sata ne ya biyota, Gwaggo
tayi salati, ta gwalawa sumayya kira,
Taje wanda tayiwa sata ya biyota karbar
kayansa...
Lele tace walhy Gwaggo guy din ya hadu,
yanxu idan yace yana sona haka xai riqa kallon
yayata a matsayin barauniya kenan.....
Gwaggo tayi tsaki ni wannan yarinyar, ni kam
wata rana saidai naji sammaci, ta qara
gwalawa sumayya kira, sumayyah ta fito tana
cilla qafa kije wanda kika yiwa sata yazo karban
kayansa!.
Ta dafe qirji, kaya, Gwaggo tace kya tanbayeni,
kije kya gani.
Sumayya jiki a mace, ta cilla qafa ta fita, Moh
ta gani a tsaye ya saka hannu aljihu yana mata
murmushi......
Ku biyo tagwayen marubuta,
Sai kuma ranar......
Sidiya & M. Jabo..
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: HASKEN IDANIYA 48
Na khadija Sidi & Hauwa M. Jabo
Wani wawan murmushi ya sake mata, tuni
tsoro da fargabar da taji suka kawar a
xuciyanta, ta matso kusa dashi tana murmushi,
shima murmushin yake mata, shikam Idi kallon
ikon Allah yake wai Muhammad ne yake kula
wannan gurguwar.!
Tana xuwa ta kalleshi daga sama har qasa,
bata taba ganinsa da wannan kayan ba, kullum
kayan bike rider ne a jikinsa, ko kuma qananan
kaya, yau kam kayan mu na hausawa ya saka,
ta gaidashi chikin fara'a. Ya amsa yana kallon
ta, Moh yana kallonta ya rasa da me xai fara.
Yace nayi mantuwa ne a wannan jacket Dana
baki Dazu, akwai phone dina a ciki, shi xaki
bani.
Ta mai lau da ido, Wanda ita bada wani
manufa tayiba, amma saida Moh ya rude, ya
wani chije gefen bakinsa, shi kadai yasan mssg
dinda ya karba lokacinda ta masa wannan
kallon, aranshi yace ita komai nata daban
yake.........
Tace OK bari na dauko maka. Ta juya tana
chilla qafarta, ta shiga gida, shi kuwa ya bita da
kallo. tana isa taga Gwaggo da lele a tsaitsaye,
da alama ma lebenta sukayi, batace dasu
komaiba ta wuce daki ta dauko rigar, ta fito,
lele tace yauwa, kin gani ko!? Gwaggo kince ba
sata ta masaba sabida kin hango yana
murmushi ko. Nace miki sata ta masa, Dan
wallahi da bakinsa yace min kayan shi, kuma
fuskarsa a daure, alamar ranshi a bace yake
kenan. Gaddama ce ta kaure tsakaninsu, ita
lele tanason ace satar tayi Dan ta sami hanyar
cusha kanta gun Moh..
Ita kuwa Gwaggo bada wata manufa tace ba
sata tayiba....
Hmmm a banxa lele idan dai Moh ne ya hadu
da wacce ta fitama, su yar baqa duk an kawo
jiki amma basu sami fuskaba, shidai Sumayya
kawai yakeso.!!!
Ta fito ta miqo masa rigar ya karba yace ai
rigar ta xama taki daga yau. Yana magana
yana kallon ta, yasa hannu a aljihu, ya Ciro
wayanshi ya miqa mata rigar.
Gwaggo kuwa da lele suna chan sun labe suna
leqen Sumayya suga satar da tayo.
Amma basu gane komaiba, gwaggo ce ma mai
fadin ba sata bane, kuma ba soyayyyah bace,
wannan Dan gwalisar ai yafi qarfin Sumayya.
Lele baqin ciki ya turnuqeta ko magana ta kasa
tayi.....
Moh ya kalli Sumayya ya kanne mata ido,
bakice yayi kyauba. Ta boye fuskanta chikin
tafin hannunta. Tadan jingina jikin motar,
fuskanta a boye tace yayi kyau sosai......
Sumayya kin xama HASKEN IDANIYATA. Dago
kai tayi ta kalleshi, sabida abinda take sakawa
kenan a xuciyanta wato ya xama HASKEN
IDANIYANTA......
Ta qara murmushi tace, ka ganka, kamar wani
ango.! ya Dan duqar da kansa daidai fuskarta
ya qara kanne mata ido, yace angon Sumayya
ko!? Kunya ta kama sumy Tace laaaa, nidai ba
haka nake nufiba.!! To mi kike nufi!? Shiru ta
masa.
Basu dade sosai ba, sabida shi Moh yanason ya
kasance tare da Sumayya, amma kuma yakan
rasa mi Xai ce mataba, barshi yayita kallon ta,
idan tayi dariya yace tana burgeshi idan tayi
kuka yace still tayi kyau........
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [11:12PM, 10/22/2015] Auntie M.Jabo: HASKEN
IDANIYA 49
Na Hauwa M. Jabo & khadija sidi
Ya kalli Sumayya yace, u make my day. Ta dago
ta kalleshi Tace ko daxu kace min haka. Dariya
ya saka sosai yana wani jefa kai baya., ya nuta
daxuma da xa'a kawo ta ya fada mata
hakan....
Duk lokacinda Moh yake dariya sai Sumy ta sayi
ta kallonsa.
Bada son ransuba suka rabu da juna.......
******************
Alhaji habeeb mahaifin Moh yana xaune a tare
da hajiya bushra yana bata labarin cigaban da
yake Dada samu, tanata jin dadi, Moh ne ya
shigo gidan, daga hajiya bushra har Alhaji saida
suka miqe tsaye, Dan mamakin kayan jikin
Moh, hajiya ta kalli mijinta, cike da al'ajabin da
suka gani,
Muhammad lokaci daya suka hada baki, suka
kira sunanshi.
ya juyo ya kallesu, murmushinsa na kullum ya
musu, sannu da dady ya hanya!? Nan ma
mamaki Dan Alhaji yayi tafiya yakai nawa
amma Moh, daidai da rana daya bai taba ce
masa ya hanya ba,bare sannu da xuwa, sai
yau. Cike da mamaki Yace lafiya lau
Muhammad.
zonan.!
Yaje gun iyayensa, suka fara tambaya daga
ina!? Yace na fita garine, hjy bushara tace da
wannan kayan!? Kodai daurin aure kaje!?
Kallonsu yayi da idonsa, kawai naji na saka
kayan hausa ne,. sukam mamaki sukeyi. Bai
tsaya wani magana ba yace bari na shiga ciki.
Ya miqe haka suka bishi da kallo suna murna,
lallai Muhammad ya qara hankali........
hajiya tace wai ina xancen yarinyar nan!? Alhaji
ya kalleta irin bai gane wacce take nufiba, ta
gidan Alhaji Yusuf. Au wa take da suna.!?? yar
farar nan ko!? Tace Lallai yaka mata mu
hadasu Dan yarinyar akwai natsuwa ga kuma
hankali ga uwa uba kyau....
Alhaji yace badai yanxuba, mu bari sai ya qare
karatun ko ya kika gani!? Tunda ya kusa, tace,
To idan aka mata mijifa Alhaji!? Haba bayan
munyi magana da shi Yusuf din, kuma yace an
bamu. Hajiya bushra washe haqora tayi tana
dariyar jin dadi xata kai ga jika.....
********
Sumayya bata bar gofar gidan ba saida Moh ya
kure mata, tana murmushi ta cillo qafarta, ta
shigo gida, ko sallama bata qarasaba lele tace
adda wai waye Wannan??. Ya bar miki kayan
nashi da kika daukone!? Ina kika sanshi,
Sumayya ta kalleta tace kekam lele rashin
kunyar ki yayi yawa.! Ways gaya miki kayansa
na dauka? Ko kin taba ganni nayi satane, a
fitsarance tace waya sani ko kin sato na
Wannan, dan ya kulaki, ai kinga wannan shi
daban yake,..
Gwaggo dai kam tsaye tayi tana kallon ikon
Allah. Ita koma miye idan dai xai saki hannu
abin farin cikintane, Gwaggo tace ke lele ba'a
son rashin kunya ba yayarki bace.!!
Daga lelen har Sumayya furucin Gwaggo ya
daure musu kai, wai YAYARKI.........
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [11:12PM, 10/22/2015] Auntie M.Jabo: HASKEN
IDANIYA 50
Na khadija Sidi & Hauwa M. Jabo
Gwaggo taci gaba, sannan ina ruwanki da
gunda ta samoshi, tunda dai ta bayyana ba
sata ta masaba ai shikenan, Ke Sumayya wuce
abinki.
Lele ta saki baki tana kallon abin al'ajabi,
tunda ta tashi a gidannan bata taba ganni
Gwaggo ta shigarwa Sumayya fada ba, koda
tanada gaskiya kuwa, farko ta dauka ma ba yar
gidan bace, sai daga baya.,
Sumy ta cilla qafarta ta wuce daki, Gwaggo taci
gaba da aikin ta ba tareda ta kalli leleba,lele ta
cika tayi fam, Jiran Gwaggo takeyi ta qara
magana ta sauke mata gwangwon masifa....
Humm Gwaggo ko dago kai batayiba, bare ta
qara magana, ita kam duk gunda ta fadi
rataya, burinta ta a kawo mata mai dan maiqo
ta lasheeeeee.....
*******************
Moh kwance a daki, ya kasa gane kansa sai
tunanin Sumayya yakeyi, kansa ya dau xafi. A
fili ya fada dama haka soyayyah take!? Inason
tsananin son yarinyar nan, I love her much.....
haka sumy ta riqa masa gixo a daki, ya ganta
tana dariya, ya ganta tana murmushi, ya ganta
tana kuka, ko wanne tayi kyau take masa,
girgixa kansa yayi, yayi wata yar siririyar qara,
lumshe idonsa yayi, kai Duniya Moh ya hadu,
nima ya tafi da imanina,
" banga laifin su yar baqa da suke yaqi
akansaba"
saida sidiya ta taboni tace jabo xaifa fara
sana'ar sa, mugudu kada kice na gudu na
barki, sai lokacin na dawo hayyacina,
Ashe har Moh ya nufi Dan akwatinsa, ya bude
ya dauko farar powder sa yana shaqawa, ai
tuni muka baiwa rigar mu iska......
*************
Chikin dare guraren 12 na dare Gwaggo ta kira
Sumayya wajen daki, hankalin Sumayya ya
tashi, Dan bata manta jibgarta da akayi Dazu
da safeba.....
Jikin ta ya fara bari, ke ki natsu muyi magana,
Gwaggo magana take qasa qasa, fuskanta a
sake, wai waye ta ganku dashi Dazu,!??
Sumayya cikin tsoro walhy Gwaggo Dan skull
dinmune, Gwaggo tace ke kada ki mayar dani
mutuniyar banxa, dan makarantar kune shine
yake miki wannan kallo yana wani mar mar da
ido, kamar bebin roba, ke bakiga wani kallo da
yake mikiba!?
Ko motsi kikayi fa sai ya duba yaga minene! Da
gani wannan sonki yakeyi, ki saki jiki hanyar
arxiki ce ta sameki, idan xaki min bayani kawai
kimin, Sumayya ta daure tace Gwaggo waya
baki Wannan labarin!? Tace da idona na gani,
ai inanan labe xaure. dariya ce taso ta
kubcewa Sumayya, amma ta hadiye dariyar wai
Gwaggo batajin kunyar fadar lebe tayi..
Anan Sumayya ta baiwa Gwaggo labarin Moh,
amma ba wani soyayyah tsakani, Gwaggo tace
ke wallahi sonki yakeyi ta rungume Sumayya
Ashe dai Xan ci arxikinki Sumayya...
wannan qatuwar motar wallahi ban taba ganin
irintaba.
Sumayya kam mamaki ya isheta daga ganin
sarkin fawa sai miya tayi zaqi......
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [11:12PM, 10/22/2015] Auntie M.Jabo: HADKEN
IDANIYA 51
Na khadija Sidi & Hauwa M. Jabo
Ita kam yau koba komai tasha albarka gun
Gwaggo, abinda tunda tayi wayo bataji daga
bakin Gwaggo ba, sai yau.
Ssai kace ba Gwaggo bace kullum chikin
hantararta,da muxgunamata, da toxartata,
gaban qannenta, Wanda hakan ya haifar mata
mummunan raini mai yawaa gurin qannenta,
amma yanxu kamar xa'a wuce gurin........
Kamar kullum, Tana sallan ta na dare, wayarta
tayi qara guraren 2 na dare, ta dauko kamar
ba xata budeba Dan tasan saqo chikin dare sai
dai Airtel , haka ta daure ta buda ga
mamakinta sai taga daga Muhammad ne, ta
maimaita sunan Muhammad..!!! bata kawo
Moh arantaba ta bude kamar haka.... " U r
such a nice person 2 think of,
like the way I'm thinking of u now.
Missing u my Sumy." . Wani murmushi ta saka,
Wanda batasan lokacinda ta sakeshiba, ta
maimaita mssg din yafi sau 10, MY SUMY. sai
murmushi takeyi, tanason ta bashi amsa amma
ta kasa, ta rasa yanda akayi ta bari Moh ya
shige mata rai haka farat daya, guy dinda
akace yana shaye shaye, qirjinta ne ya buga
sosai, cocaine yakeshi fa!!
Wata xuciyar tace Ki baiwa kanki lafiya
Sumayya, soyayyah da wannan yaron ba naki
bane, ta ko ina yafi qarfin ki, kinga....
Ya fiki kudi,
Ya fiki kyau,
Ya fiki lafiya,
Ya fiki.... Ya fiki..... Ya fiki..... Haka tayita lissafa
abubuwan da ya fita dasu,
Tachije gefen bakinta, irin batada mafita
dinnan..
Tayi ajiyar numfashi, amma dan ya fiki komai ai
yanasonki ko.!? wata xuciyar ta bata amsa,
kuma bake kika nemeshiba, haka dai Sumayya
tayi t tunani har bacci ya dauketa.....
****************
Chikin qanqanin lokaci Moh yayi ginin da ba
Wanda xai iya rushe wannan ginin nashi a
xuciyar Sumayya.! Soyayyah ce da shaquwa
akeyi a gurin,
Ya koya mata sonshi da qaunarshi da tattalinsa
da qarfi da yaji, dukda shi ba wani maye baye
a soyayyah, amma dukda haka yayi nasara., ta
xama yar gata gun Gwaggo, duk da Moh ba
wani sakin kudi yake musuba, amma Gwaggo
ta amince matuqar xai rabata da Sumayyah
kuma tasan dole ne sai ta lasa......
Lele kuwa tun daga ranar ta daina yiwa Sumy
magana, ko Sumayya ta mata magana bata
amsawa, ita ala dole Moh take so. Moh dai kam
yayi farin jini kowa so yakeyi.
"Harda su zainb khalifa koda ita yar baqa akwai
kwashe kawashe, inaga xamu hadata da
garbati..!!"
**************
Moh ne da Sumayyah maqale da waya suna jin
juna, sunyi akan xaixo gurinta, tun bai qare
wayan ba yace gashi a qofar gida..
Koda Sumayya ta fito saiga Moh kuwa, yayi
kyau iya kyau, yace yanason yayi magana da
Gwaggo, ta masa iso ya shiga chikin gida gurin
Gwaggo.......
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [11:12PM, 10/22/2015] Auntie M.Jabo: HASKEN
IDANIYA 52
Na Hauwa M. Jabo & khadija sidi
Moh ya shiga ya gaida Gwaggo karo na farko
tun haduwarsu da Sumayya, Moh ya cewa
Gwaggo yanason Sumayya ta rakashi wani
gurine, Gwaggo ba musu ta amince, dukda
Sumayya bataso hakan ba, amma kuma baxata
iya gaddama da Gwaggo ba.
Ya ijiye mata farare qal, bandir daya, Gwaggo
garin karbar kudin saura kadan ta fadawa
Moh.
Har xasu fita Gwaggo ta kwalawa Sumayya kira,
ke shashasha ko yar hoda baki iya shafawaba
bare Jan baki, ke wallahi anyi bilijis " villages"
da lele tana nan datagyaraki, kullum gakinam
wata bilijis " villages " dake, yanxu haka xaki
tafi da wannan uban hijabin kamar wata
tantabara.... nidai kam Allah yasa kada wannan
yaron ya gudu,
Sumayya murmushi kawai tayi, ta wuce, tabar
Gwaggo tana sunbatu....
Sumayya da Moh a mota, dukda tayi sabo dashi
amma still akwai kunyar Fulani tare da ita.
Park suka nufa sun iso Sumayya da hijabinta
tana cilla qafa shi kuwa Moh cike yake da farin
ciki, kamar yafi kowa jin dadi a rayuwa..! Daka
ganshi kasan Bashida,
Sun sami gu sun xauna wayarta ce tayi qara
alamar mssg ya shigo, ta dauka ta karanta sai
tayi murmushi,.
lokaci daya ran Moh ya baci, mi yasata
murmushi bayan suna tare,.!!??? haka kawai
yaji yanason yaji mi take yiwa murmushi. yayi
yayi ya daure, amma ya kasa daure wa,
ta sowa yayi yaxo gabanta hannun sa a cikin
aljihu, ta dago kai ta kalleshi, sai ta masa
murmushi amma ya kasa maida mata
murmushi Y!??
Sumayya ya kira sunan ta saida yaji wani
duuuuum a qirjinta yanayin yanda ya kirata, ta
dago ta kalleshi, idonsa sun chanxa kala, tace
na'am ? Shiru yayi, sai ya tsuguna gaban ta,
Sumayya waye ya turo miki mssg!?? mi yace
kike yiwa murmushi?? Shi kanshi baisan ya
mata wayannan tambayoyinba kuma baisan
miyasa yace wayeba! Maimakon yace wacece...
Ta kalleshi tace miyasa kakeson kaji!? Tana Dan
murmushi, Dan ta Riga ta gano cewa kishi
yakeyi, fuskanta a sake, tace wani ne wai na
masa yanason yaxo gidan mu anjima shine.......
Katseta yayi da qarfi saida ta rude, lokaci daya
ya koma Moh dinta ta sani mugu a skull, Moh
dinda baya dariya, saida taji tsoro, hannu ya
miqa mata fuska a daure, ta gane mi yake nufi,
ta miqa masa wayar, ya lalubo inbox dinta
amma kuma sai yaga last mssg, an rubuta
sunan Gwaggo kamar haka, "YAR ALBARKA,
KIZO MIN DA MAI DAN MAIQO MAIQO." Baisan
lokacin da ya saki dariya ba.
Ya daga hannu kamar xai laquto hancinta sai
kawai ya laquto iska. tace miye na daure fuska
Dan nace wanine!? Ya kalleta ya sauke kafada
yace, nothing. Ta kanne mai ido tace kodai
kishi yakeyi!? tsura mata ido yayi, kadaina
kallon Sumayya kada ka kamu da sonta ba
ruwana.!
Ai saidai Sumayya tayi haquri Dan already
Muhammad ya kamu da son nata. Kallon juna
sukeyi ba ko gyafta Ido,
Chan dai Sumayya ta kawar da kanta, Moh
yace, au har ta gaji da kallon Muhammad din
nata....???
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [11:23PM, 10/22/2015] Auntie M.Jabo: HASKEN
IDANIYA 53
Na khadija Sidi & Hauwa M. Jabo
Tace waya gaya maka Muhammad dinta ne,?
ya wani zare Ido, to Muhammad din waye!?
Tace na Sumayya ne. gaba daya suka saka
dariya, cike da nishadi.... Ai nasan Sumayya
kayan Moh ce ko!? Tace Of course, kamar
yanda Muhammad yake kayan Sumayya.
Tafada cike da murmushi, Ya maimata sunan
Muhammad, tafi kowa iya fadar sunanshi.!
Suna xaune wani yaro matashi yaxo ya miqawa
Moh wani gwali, waya ce a ciki, iPhone...... ya
bude wayarta ya cire sim dinta ya saka a cikin
iPhone din ya miqa mata, ta kalleshi irin
minene!? Yace ta karba wayace na karbo miki!
Ko bai isa bane, murmushi tayi, ya isa
mana.......
Moh sau da yawa idan yana waya da Sumayya
sai yaga kamar bashi bane, wai shine yake yiwa
mace dariya yake biye mata, duk abinda tace
sai yaji hakan ya masa koda ya sabawa
ra'ayinsa burinsa kullum ya ganshi tare da
ita........
Yadai kake kallon ta haka!? Dan firgit yayi, ya
kalleta, tayi murmushi ta kashe mishi ido,
Sumayyah.! your smile act as medicine in my
sickness.....
So please always smile...
Murmushi suka ma juna kin xama HASKEN
IDANIYATA Sumy..!
Tana Dan juya wayan, wayanda saidai ta hango
a gurin skull mate, wai yau wayarce a
hannunta.
Haka suka qare soyewarsu suka tafi gida, saida
suka kusa kaiwa, ya tuna saqon Gwaggo, yace
wai miye mai Dan maiqo maiqo
!? Dariya ya bata tayi dariya sosai, tace ni
banasan miye mai Dan maiqo maiqo ba, dan
kawai kada yace xai siyo,
Kallonta yayi irin bai yarda da amsar data
bashiba, parking din motar yayi, ya fito yaje
gun wani shago, ya tambayi mai shagon, mlm
Dan Allah miye mai Dan maiqo maiqo!?? mai
shagon ya masa bayani, ya dawo ya shiga tuni
yayi kwana yaje ya siyo ma Gwaggo kaji da
kayan kwalam kaka kala......
Sun iso gida tare suka shiga, Muhammad
baisan dawar garin ba ya miqawa Gwaggo Leda
yace ga mai Dan maiqo maiqon Gwaggo..
su Gwaggo kam anji kunya, amma tasa hannu
ta karba tanata godiya....
Ya fito xai tafi sumayyah ta rakashi kenan yayi
karo da lele lokaci daya ta rude ta fara
karairiya, Sumayya dai kallon ta kawai takeyi,
adda keji ciki Xan rakashi, Sumayya batace
komaiba, hannu ta daga ma Moh sukayi
sallama, lele kuwa ta shiga gaba tana kada jiki,
amma a banxa Dan Moh ko iniwumarta bai
kallaba bare ita., tace please Bross xan bika ka
saukeni a shingai bakery's, ko dago kai baiyiba
yace bansan gurin ba.! tace laaa kana dan gari
amma baka saniba, no problem broo muje xan
Muna maka, ya shiga mota, suka kama hanya,
anan lele ta fara surutai, wallahi broos ka
hadu, addata tayi dace, baice mata komaiba.
Amma yanda nake ganinka mai class ka wuce
soyayyah da gurguwa...!!!!
Birki ya taka da qarfi saida kanta ya bugi
gaban motar, ba tare daya kalletaba da ln voice
dinsa yace get out a sanyayeee....!
Xatayi magana ya daka mata tsawa da qarfi I
said get out..........
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: ����HASKEN IDANIYA 54����
Na khadija sidi & Hauwa M. Jabo
Jikin lele yayi sanyi ga wani tsoro daya kamata,
ta juyo ta kalleshi shima ya dago Ido ya kalleta.
taganshi kamar bai taba dariya ba a Duniya, sai
lokacin ta qara jin tsoro, Dan gaskiyar magana
bata taba tunanin haka yake daure fuskaba,
duk da haka bataji rashin sonsa ko qunarsa a
cikin xuciyarta, ta bude motar ta fita tun kamin
ta qarasa fita ya ja motar da qarfi, Allah yasota
bata fadiba, dama Moh bike rider ne, an iya
isqilanci kala kala da rayuwa....
****************
Hutu ya qare an koma makaranta,
Moh ne da gang dinsa su shamo. Kamar dai
yanda suka saba Moh ne a gaba suna bin
bayan shi, mai gadi kuwa yana hangosu ya
wanqale gate yana daga musu hannu, Dan
shima yana yinsu sosai..
Signal kawai sukaga Moh ya saka, alamar xai
tsaya, suka tsaya dukansu, waya ya dauko
daga aljuhu ya cire helmet dinsa, yana
murmushi ya fara waya, tunda suke basu
taba biyo hanya wai dan an kira Moh ya tsaya
daukar wayaba, sai yau, Sumayya ce ta kirashi,
sun kai 30 mnt suna magana, shamo ranshi
yayi matuqar baci akan wannan gurguwar ana
yarfasu, yace ma Moh zamu shiga ciki, Moh
hannu kawai ya daga mishi, ko kallonsa baiyiba
yaci gaba da soyewarshi...
************
Ta fito Daga gun photocopy, tana cilla qafarta,
sai kuwa suka hadu da hameeda, ta rave ta
bata hanya ta wuce, amma humaida da
tsokana, tace nidai bansan miyasa Allah yake
hadani hanya daya Da wannan matsiyaciyarba,
aseeya tace, Allah kuwa, kauce kada ta goga
miki asara dangin asara. Sumayya batace
komaiba ta wuce sai kuma ta tuna da Moh yace
ta daina bari ana rainata, sai taja ta tsaya, har
xata juyo sai kawai ta wuce, hijabinta humaida
ta janyo. Kowa yasan mi ake qunshewa a cikin
hijabinan oho.!? da gani bayan gurgunta akwai
wata na kasa a ciki, suka saka dariya, juyowan
da Sumayya xatayi ta wanke humaida da mari,
tasssssss. Saida aseeya taja baya tana mamaki,
humaida ta riqe kunci tana xare ido, ta nunata
da yatsa, bari kiji na gaya miki, shiru shiru ba
tsoro bane gudun magana, na dauka kinada
hankali, Ashe bakida hankali, to wallhy a shirye
nake da duk kika min sai na rama,
Daga baya gayun da suka ga yanda abin ya
faru suka saka tafi, Raf Raf Raf...... dama sun
tsani humaida Dan bata kulasu, wani guy yayi
ihu yace dole kayan Moh, yana daga mata
yatsa, Sumayya dagowa tayi ta kallishe ta
masa murmushi, har xata wuce sai kawai ta
hango Moh tsaye ya rungume hannuwansa
yana murmushi, Sumayyarsa ce ta xama
strong kamar yanda yake buqata.... gurin moh
ta nufa, shima ya nufota suna yiwa juna
murmushi, humaida kam ba Marin da aka
mata yafi mata ciwoba, irin ganin Sumayya tabi
Moh suna murmushi, yafi mata ciwo..aseey
tace gaskiya yarinyar nan ta wulaqantamu kalli
Marin da ta miki sabida Allah, kuma wallahi kin
maru, wata harara ta dalla mata, aseey tayi
shiru, karta sauke haushi akanta.......
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [9:31PM, 10/23/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 55����
Na khadija Sidi & Hauwa M. Jabo
Sun kawo daidai joint din student, tace ni xan
tafi labry akwai assignment dinda aka bani,
Moh yayi shiru Dan tunda ya shigo skull dinnan
bai taba rubuta assignment ba, bayason ya
barta ta tafi, amma kuma yagane Sumayya
serious student ce.....
Su james ne xaune suna gulma, wannan
gurguwar Allah na tsaneta,
shamo ya kwashe da dariya....! Kai.! kayan
Moh dinne zaka tsana,!?.
Son yace Ai kuwa dai kaya, Dan Wannan itace
ainihin kayan..
suka kwashe da dariya, son yace seriously na
tsani kayan nan nashi. James yace ba ruwana
yana wani daga hannu irin ba hannunsa a
wannan xance.! Shamo yace Kun gane yarinyar
baby ce, amma kuma na banxa tunda bata iya
tafiya...
Moh kawai suka gani tsaye gabansu hannuwa
cikin aljihu,amma ga dukkan alamu baiji hirar
tasuba, Moh ina kayan naka, yayi wani
murmushi, na kaisu labry,
James yace Sumy kayan Moh, yace kai, nagafa
kanason ka haura gidana! Suka kwashe da
dariya, ai duk makaranta nan ba Wanda ya isa
ya haura gidanka, ai Wannan kayan Kane Moh,
wani murmushi yayi ya lashe bakinsa, yadan
cije lebensa, ya daga kai ya kalli sama, yace,
inason son Sumayya sosai, ta xama HASKEN
IDANIYATA....
Sukam kallonsa suke anya wannan yarinyar ma
mutum ce,? yakamata su binciko gidansu da
sauransu, Dan dole su taimakawa abokinsu,
Dan ga dukkan alamu yana cikin wani hali, sun
ci gaba da hiransu, amma Moh baya tare dasu,
dama yakanyi hakan bare yanxu da ya xama
busy a tunanin Sumy.
**************
Alhaji jiyafa naje gidan alhj Yusuf, naga
yarinyar, Allah munyi dace da suruka ta gari,
duk tafi yaran gidannan natsuwa da hankali,
uwa uba tarbiya,ni inaga a fara maganar auren
tun yanxu, kaga yana kammalawa sai a daura
auren. tunda kaga shi Muhammad din bawai
kula mata yakeba, mune xamu masa auren,
amarya kawai xa'a akawo masa, alhj ya cire
hula ya Sosa kai, kina ganin hakan yayi!? nidai
hakan yamin gaskiya, yaronnan bawai yasan mi
yake damunsa bane, kuma Nasan ko ance yaje
gun yarinyar tadi ba xuwa xaiyi ba. Saidai ma
na riqa sa hajiya rukayya tana turo min ita
weekend ko xasu qara ganin juna su daidaita,
tunda ita yarinyar tanasonsa sosai.!!
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [9:43PM, 10/23/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 56����
Na khadija sidi & Hauwa M. Jabo
OK hajiya hakan xa'ayi, duk yanda kikace, ya
kanne mata Ido, tayi murmushi, tsoffi na
soyewa, Allah ya kaimu lokacin,
yanxu zanyi magana da Yusuf din sai muji
yanda xata qare, idan yaso ita yarinyar sai ta
kammala karatunta a gidansa,
Hjy bushra ta washe baki, burinta taga auren
Muhammad....
***************
Iyayen Sumayya sunsan da xaman Moh, sunyi
magana da Abbu, Abbu ya xaunar da Moh ya
Muna mishi cewa Sumayya fa batada lafiya,
yana gani gurguwace, shin xai iya auren ta a
haka, Moh yace ai yaji ya gani,
duk qannenta sunsan da xaman Moh, sunsaan
yafi qarfinsu, lele kuwa kullum cikin shiri take
akan yanda xata bullowa Moh ya sota amma ba
nasara, Dantsoronsa ma takeyi yanxu, amma
kuma ta kamu da sonsa ba kadan ba.......
Tafe take tana cilla yar qafarta a hankali, har ta
kawo aji ta shiga ta xauna, Malaminsu yaxo aka
fara karatu, kamar daga sama saiga Moh ya
shigo, malamin ya tambayeshi lafiya!? Yace
naaxo na duba kayana ne, to ka bari idan mun
qare karatu sai kazo ka duba ko, Moh wani
kallo ya masa kawai yasa kai a ajin, ya fara
raba Ido saida ya hangota ya wani hade hannu
ya cije baki ya kanne mata ido,ga kayana sir,
ya juyo ya kalli malamin, gun Sumayya ya nufa
daga gefenta yaa xauna, yana mata murmushi,
ta kasa daure wa itama ta maidamata, tuni ya
dauke mata hankali, har malamin ya kamasu,
mlmin ya koresu daga ajin, dukda ranta ya
sosu, amma kuma batason ran Moh Yana baci,
bayan sun fito anan ne, takece masa ya daina
xuwa ajinsu Dan kusan kullum Moh ko yanada
lecture haka xai kashe nashi yaje nasu
Sumayya, idan ta masa magana yace bashida
lecture, all over Moh ya zama Sumayyah, komai
nashi Sumayya, humaida tayi baqin ciki har ta
gaji abokansa ma haka.......
**********
Hjy bushra tama hajy rukayya magana, akan ta
tiqa barin surukarta tana zo musu weekend
Dan a saba da juna, a fara xumunci tun yanxu,
ai kuwa tuni ta amince.
Ranar farko data fara xuwa gidan, suna xaune
a Palo, Moh ne ya shigo ya daga musu hannu,
ya wuce baima kula da wata baquwa a gidan
ba, ya nemi hanyar shiga dakinsa Muhammad
zonan, hajiya ta kirashi, bakaga qanwarka
bane!? Ka ganta Tazo mana weekend ne.!
Waiqo da kansa kawai yayi, ba tare da jikinsa
ya motsaba, ya kalleta, ya ganeta sarai, Tana
cikn list din mutanenda ya tsana, kallon ta yayi
Ido cikin Ido, yace waye ita!? Hjy tace yar gidan
Alhaji Yusuf ce, har ka manta da ita!? Yace No
ban ma Santa bane, yaci gaba da tafi yar shi,
kunya ta kama hajiya, tayi yaqe kinsan yayan
naki miskiline, sai kinyi da gaske, tunda dai
yanason ki ai da sauqi sunkuyar da kanta tayi
kawai, Dan taji bala'en kunya...,
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [10:09PM, 10/23/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 57 ����
Na khadija sidi & Hauwa M. Jabo.
Wasa wasa hajiya bushra sunyi maganar aure,
sunkai kudin aure da kayan aure, amma Moh
duk bashida labari, sunsan halinsa, sunsan
bashida matsala da mace, zai amince da ita
kawai. Sunachan suna bidirinsu har an saka
ranar aure.........
Bangaren Lele kuwa, abin Duniya ya isheta,ta
kasa danne son Moh azuciyanta, kullum wutar
sonshi Dada ruruwa take a xuciyarta, gashi idan
yaxo gidan ko kallon ta bayayi, tayi gaba da
Sumayya har ta gaji, ta daina Dan Sumayya ta
Dade da ganeta, amma banxa takeyi da ita,
gashi Gwaggo ta daina goyon bayanta, tunda
yanxu Sumayya na bata mai dan maiqo maiqo
daga qarshe lele ta shirya yanda xatayi......
Adda bani wayarki na saurari qur'ani Dan Allah.
Sumayya kallon ta kawai tayi cike da mamaki,
qur'ani ta maimata, Dan bata taba jiba, lele
bayan music ba abinda takeyi da waya sai
chatting. Ba musu ta miqa mata ta kuwa danna
hd phone ta kunna qur'ani, Sumayya xuciyanta
daya, lele Abu na farko da tayi shine daukar
number Moh....
sai ta saka wayan silent, dan taji dadin aikinta,
ta masa mssg kamar haka,...
inason ganinka yau.!
Ko minti daya ba'ayiba reply ya shigo,
OK xan shigo yanxu,
ta tura masa da
ba yanxuba sai da yamma kuma ba gidaba,
Yaturo mata da
ok inane!?
Ta tura masa da,
mu hadu a day 2 day villa.
Ya turoda
ban San gurinba saidai naxo gidan na dauke ki
mu tafi,
sai ta tura mai da.
No xan maka kwatance,
kiranta yayi amma taqi receiving, Sumayya ta
juyo ta kalleta lele an kiranine!? Qirjin Tanee
ya buga tace Aah!? Tace OK a jikina naji kamar
an kira, lele banxa ta mata irin batajinta
qur'ani take saurare...
Taqi receiving saida ya tsinke ta masa msg
ina cikin mutane, ta tura masa address da
komai,
Tace wayar ba chaji xata iya mutuwa ko wane
lokaci so qarfe 4:30 mu hadu a gurin,
yace,
ok,
Moh bai kawo komai a ranshiba baimasan cewa
gurin hotel bane........
Lele haka tayita game da wayar da sauraren
karatu har chajin wayar Sumayya ya qare
tassss..
Kuma taqi fada mata ba chaji, Dan kada ta
nemi chagi da wuri, sai Chan tace adda wayar
ta daukefa. Ta karba ba tunanin komai ta sami
yaro ta aikashi aka kai mata gun chaji, lele ta
Chaba ado Naji da fada, ta fito,
Gwaggo aaah lele manyan mata se ina kuma,
wallahi Gwaggo yanxu Fatima Isma'el ta kirani
na rakata lunching, to yar kirki mai farin jini
daga Allah, a zomin da abinda ya samu...
Ta fita Tana fita sai wani boutique ta sami wata
arniyar rigar bacci, ta siya ta wuce take ta
kama daki ta shige...
Waya tama Moh amma ta Kira yakai sau goma
yaqi dagawa, sai ta masa SMS tace Sumayya ce,
wayana ya mutune.!
Sai ya kira taqi dauka, ya mata SMS Sumayya
gani a gurin. Qirjinta ne ya buga rassss yau ake
yinta sai yanxu ta fara jin tsoron abinda take
shirin aikatawa..
OK ina zuwa ta tura masa, ta kira Gwaggo, tace
ta ba Sumayya, aka baiwa Sumayya, adda
yanxu Bross Moh ya kirani wai ki sameshi a
day 2 day, ya kira wayanki a kashe, wai room
16c l, itama Sumayyah batasan gurinba, lele ta
mata kwatance, Sumayya xuciya daya tace to,
kuma batayi mamakin ina ma ya sami number
taba, Dan tasan Moh akanta komai xai iya yi,
Ta shirya ta saka hijabinta ta fito, Gwaggo tace
Sai ina hajiya!? Tace Muhammad yakeson
ganina, ta tabe baki, shine xaki tafi mishi
haka!? kamar wata mai ciwo, ke wai bakiga
qanwarki yanda take dandashewa, tayi chas
chas da ita, koda ke dince an kwana biyu, Allah
dai yasa kada yaron nan ya gaji da halinki ya
gudu, ya barni da tagumi, murmushi kawai
tayima Gwaggo ta fice, koda taje gun mai
chaji ya kulle shagonsa tsaki tayi taje ta shiga
mota xata gurin....
Lele ta masa SMS kaxo room 16C
Moh yadanyi mamaki kadan, mixai kaisu daki,?
amma sanin tsarkin Sumy yasa bai damuba
baima kawo komai a ransaba, ya wuce kai
tsaye. Dakin ya nufa ya gwangwasa jikinta a
sanyaye ta saka arniyar rigar bacvinta wacce
ilahirin jikinta a waje yake ga lele itama a dire
take dan kuwa lafiyyar macece...
Ta bude masa ya shigo ta kulle qofa ya
juyowan da zaiyi suka hada ido, qasa yayi da
idonsa da qarfi, tunda Allah ya halicceshi bai
taba ganin mace a hakaba sai yau,,!!
Baya ya juya zai fita amma me, qofa a kulle,
juyowan da xaiyi sai lele ya gani gabansa,
kallon ta yayi daga sama har qasa, tsikar jikinsa
ce ta tashi, ya runggume hannayensa ya
jingina jikin qofar Yana kallon ta.
Gwangwasa qofa akayi, ga dukkan alamu
Sumayya ce.........
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [8:09PM, 10/27/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 58����
Na khadija sidi & Hauwa M. Jabo.
Wani murmushi lele ta masa mai rudar da
mutum, yadago mayun idonsa ya kalleta lokaci
daya kawai ta rikide ta zamo masa Sumayyarsa.
runtse Ido yayi da sauri, ta matso gabanshi,
tana kaririya, Bross ka saki jiki, ba Wanda
xaisan hakan ta faru, bross wallahi ina tsananin
sonka da sha'awar ka, inason ka xama nawa..!
karo na biyu aka qara qwanqwasa qofa, ya
bude idonsa a hankali, dama kayan data saka
sai a hankali, wata yar jelace aka sa aka daure
gaban rigar, tuni lele ta kwance jelar, ga
dukiyar fillo a tsaitsaye suna ma Moh
murmushi, dagyar ya iya lalubo numfashinsa,
abinda bai taba ganiba, kuma bai taba faruwa
dashiba, Bross ka amince dani Dan Allah.!
jikinsa ta fada, ta rungume shi..... Ya kasa
motsi, tace Gani cikakkiyar mace mai lafiya mi
xakayi da gurgugurguwa!!
gashin kanta ya janyo da qarfi ya wurgar da ita
gefe..
ba'a qara kwankwasa qofaba.
Ta miqe tsaye tana murmushin karuwanci, ita
kanta da ganin idon Moh ta gane sabon
shigane, tazo daidai shi,tana kallon idonsa da
suke rudar da ita, kasan me!? Wallahi summa
tallahi adda Sumayya tana nan gurin, idan har
baka biya min buqata naba yanxu xan kirata
nace mata kana nemana, wani kallo ya mata,
aranshi yace waisu mata dama haka suke,!?
Tsaki yayi shi kanshi ya san ya sami chanji
ajikinshi dakewa kawai yayi, ya miqa mata
hannu, bata gane mi yake nufiba sai kawai ta
tashi ta fada qirjinsa, qara tureta yayi daidai
nan aka qara gwangwasa qofa, muryar
Sumayya yaji tana cewa ba kowa acikine!?
Tabbas yanxu ya tsinke amma ya dake, shi
kansa baisan dalilin da yasa yaji tsoroba, ya
kalli wannan shedaniyar yarinyar ya kalli qofa,
ya juwo da qarfi, wani wawan mari ya xabga
mata saida ta fadi...
Daidai nan ita kuma Sumayya ta juya tana cilla
qafarta Dan tasan ba kowa a dakin, xata sauka
qasa taqara dubashi, lele tana kallonsa sai taga
yana taba wando har taji dadi a ranta, cewa
wata qila xai mata...... Sai kawai taga ya Ciro
belt dinsa, ya nannade a hannu ya fara xabga
mata, wani wawan ihu ta saka, charaf a
kunnen Sumayya , birki taja tana yan juye juye,
muryar kamar muryar lele, jeem tayi ta kasa
kunne ko xata qara jiyo ihun, amma batajiba..
Moh hannu ya Dora akan lebensa alamar ta
masa shiru, ta kuwa toshe baki da hannu, tana
marmar da manyan idonta, haka yayita
suburbudarta tun bata ihu har ta fara ihu har
ta daina ihu, saida ya mata lilis....
Sannan ya kalleta Ido cikin Ido ya daura dayar
qafarsa akan gadon ya duqo dakansa daidai
ita, ya miqa mata hannu,wannan karon ta gane
me miqa hannun nasa yake nufi, ta masa nuni
da gefen gado, bai daina kallon taba, bai janye
hannunsa, ta fahimci sai ta dauko masa, ta
tashi tana kuka tana dingishi ta dauko key ta
miqa masa, koda ta juyo xata bashi sai ta
ganshi ya saka hannu a aljuhu yana kallon
qofa, haka taje ta bude masa qofa, ya fito, tayi
sauri ta kulle Dan kada adda Sumy ta ganta.....
Lele kuka takeyi kamar ranta xai fita, ga kunya
ga rashin biyan buqata......!!
Ya fito ya gangaro qasa ranshi a bace, ga wani
iri da yakeji a jikinsa, chan ya hango Sumayya
tana Dan waige waige, gurinta ya nufa da
sauri, ranshi a bace yake kamar me, amma
suna hada Ido da Sumayya sai ya saki
murmushi, ya matso daf da ita ya sunkuyar da
kansa daidai fuskarta yana kallon ta, Sumy You
dont know effect u hv on me, bcz evry time I
see u my heart begins to smile!
Murmushi ta qara masa tana son rufe fuskarta.
Ya nemi gu ya xauna,ganinta har ya mantar
dashi wata lele, tace sorry ka kira waya na a
kasheko!? Bata jira ya bata amsaba ta fara,
Allah lelece ta karbi wayan ta saurari qur'ani
har chajin ya qare,
Itama take kirani tacemin kace na sameka
anan gurin, kuma naje dakinda tace kace naje
amma sai Naji dakin a kulle kamar Number 16c
ne kace ko,!? na gwangwasa ba kowa, Ashe
ma yanxu kake xuwa. Tadan turo baki irin na
shagwaba, ka sa naje ina buga dakin mutane,
kasan ma miye, nafaji qamshinka a gurin,
amma dai Nasan xuciyata ce take raya min
haka, tunda yanxu kake xuwa ta qarasa tana
kallon sa......
Ido ya saka mata yana kallon ta,
Duniya komai Sumayya tayi burgeshi takeyi, ya
fahimci duk plan din lele ne, ya qurawa
Sumayya ido sosai, lokaci daya shaidan ya
tariyo masa lele tsiraranta tana murmushi as in
Sumayya ce ya gani a hakan, dafe kai yayi da
qarfi ya runtse ido iya qarfinsa yace
Noooooooooooooooooooooooo!!!!!!!
Saida Sumayya ta firgita, ga Moh da loin voice,
saida mutane suka Dan kalleshi, ya duqar da
kansa da qarfi yana girgixawa ...
Sumayya ta duqo da kanta yanda xaiji abinda
take fada, cikin rada, tace masa, idan mutum
ya tuna wani Abu na bacin rai, ko masifa,
koma na miye, ba Noo xai cebe ,INNALILLAHI
WA INNA ILAIHI RAJI'UN..!! xai fada, xai sami
peace of mind.! Ka gane,
Oya repeat it. INNALILLAHI WA INNA ILAIHI
RAJI'UN..!!
Dago kai yayi ya kalleta, idonsa sun ciko sosai
sunyi jaaa.
Tace oyaaa said it...... Ina saurare tana Dan
juya hannu alamar ya maimaita, kamar yanda
malama take yiwa dalibai yara idan tanason
suyi karatu. Kallon ta yake sosai, ta qara
maimaitawa INNALILLAHI WA INNA ILAIHI
RAJI'UN..!!
Shima ya maimaita INNALILLAHI WA INNA
ILAIHI RAJI'UN..!!
Tafa wa tayi, raf raf raf!!! tace bravo dear na.!
Ya kalleta sosai baisan sanda ya maimaita
abinda taceba BRAVO DEAR.!! Yana kallon ta
sosai yace Thanks so much for being there on
my side, & supporting me all through.
Sumayyah Without U my lyf would have been
incomplete...
Please kada ki barni, I really really love u
Sumayya...
Dan siririn hawayenn da suka maqale masa ne
suka gangaro a fuskarshi, sauri yayi ya kawar
da kansa kada ta gani, amma ina ta riga ta
gani, "ko nida sidiya mun gani, muka kalli juna
Muna mamaki wai Moh ne yake ma Mace
gwalla......."
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [8:37PM, 10/27/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 59����
Na Hauwa M. Jabo & khadija Sidi
Duk da ranshi a bace yake amma kuma Sumy
dinsa sayi making day dinsa, sun soye sosai ita
dashi, da kalamai masu dadi da faranta ran
juna, Sumayya na burgeshi yanda har yanxu
kunyar shi takeji. Wani lokaci sai ya kalli abarsa
yayi murmushi.......
sai daf da maqreeb take cewa kaga an kusa
sallah, ni xan wuce gida, kai kuma kamin kaje
gida ka sami wani masallaci nan kusa ka sauke
farali, koya ka gani, !? kallon ta yayi, komai
nata daban yake, shi kam rabonshi da shiga
masallaci tin ranar sallah da dad dinsa ya
matsa masa akan sai yaje sallan Idi, sai yau da
Sumy dinsa tace ya tafi, kuma dole ya tafi, yace
duk yanda kikace haka xa'ayi, murmushi kawai
ta masa, suka rabu, yaso ya sauketa gida,
amma ba hali tunda tace aje masallaci...
Moh da kayan shi kenan.!
haka yayiwa Gwaggo siyayyah Dan ya gano
Gwaggo akwai son mai maiqo maiqo.
shiyasa duk xaixo sai ya siyo mata mai maiqo
maiqo.......
Kamin Sumayya ta shiga gida saida ta cilla
qafarta ta karbo wayarta....
Chan da dare, saiga Gwaggo, ke kiramin lele,
har yanxufa bata dawoba, wayata babu ko sisi
a ciki, Sumayya tace ina tafi hala!? Tana
qoqarin janyo wayanta, Nidai naga ta shirya
tace min xata gurin ko hotine ko lanchin ne,
kamar lanchin tace min, kesan duk dadewar ta
bata wuce 9 amma fa har 11 bata dawoba,
Sumayya ranta daya, Dan batasan abinda ya
faruba, ta kira lele, ta kira yafi sau goma,
sannan daga warshe aka dauka, tana dauka lele
ta fashe da kuka,
Dan Allah adda ki yafemin wallahi sharrin
shaidan ne, wallahi adda nima ban San na
aikataba Dan Allah Ku yafemin adda, kuka take
kamar ranta xai fita, Sumayya bata gane
komaiba, tace koma miye dai yanxu kiyi sauri ki
dawo gida, Adda Baxan iya hada ido dakuba,
Adda gara na mutu wallahi.!! ta qara fashewa
da kuka, tsawa Sumayya ta daka mata, ke
dawo gida yanxu yanxu kinji na gaya miki
Gwaggo tana jiranki, ta kashe waya, Gwaggo
tace minene!?
Sumayya tace kukafa take, wai mu yafe mata
baxata iya hada ido damuba, Gwaggo tsaki taja
kira ki bani shashashar yarinyar, aka qara kira
ta dauka, Gwaggo tana karba ta fara masifa ke
sutubi "stupid " kina ina har yanxu?? Sai taji
muryar yarta duk ta dishe, sai jikinta yayi
sanyi, sai ta dawo rarrashi, haba lelena, ki
dawo gida wallahi duk mun yafe miki, ai ba
halin ki bane. Wannan ma nasan mistag "
mistake " aka samu, ki dawo kinji, ita lele
abinda take nufi daban, su abinda suke nufi
daban,
haka ta dawo gida, ta kasa hada Ido da
kowanne, Sumayya dariya take mata batasan
abinda ya faruba, tace idan dai nice, ki saki
jikinki kawai,
Kawai lele Abu daya xan gaya miki, qirjin lele
ya qara bugawa,
tace lele, kiji tsoron Allah. duk abin da xakiyi ki
tuna Allah yana ganinki, kuma ki sani ba
mutuncin ki bane a matsayinki na YA MACE ki
aikata abinda kika aikata yauba.. kinga misali
shi namiji idan yayi Mara kyau ba'a cika ganina
akan DIYA MACE dukda cewa duka ba kyau,
amma dai na mace yafi muni, dan nata a
bayyane yake, fadawa jikin Sumayya tayi tana
kuka, tana dada roqon qafara,
Sumayya dai tayita lallashinta da mata wa'azi
har tayi bacci, abinka da Wanda yaci na jaki,
kamin asuba lele zazzabi ya rufeta sosai, ita
lele duk gani takeyi akan Sumayya tasan mi ya
faru.......su lele ansha kunya ga na jaki.....
Moh kuwa bayan yayi sallah ya wuce gida, yana
xuwa gida yasha tea, ya kwanta haba sai
tunanin lele ya farayi, yana ganinta tsirara tana
masa murmushi amma kuma maimakon yaga
fuskar lele fuskar Sumayya yake gani, qirjinta
yake hangowa a cike,tsikar jikinsa tana tashi,
lallai mace bala'e ce, dafe kai yayi xai qara
wani ihun.
Sai ya tuna radar da Sumayya ta masa a
kunne, sai yayi sauri yace
INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN.!!
Yayita fada saida ya tsinci kansa da ba wata
damuwa tare dashi, aranshi yace ai ma
innalillahi..... Tafi wannan powder, jin yanda ya
sami natsuwa lokaci daya, da powder ce sai
ciwon kai da gushewar hankali,
Afili ya fada, Sumayya ke rahamace gareni. Kin
xama HASKEN IDANIYATA, Baxan barki ba duk
rintsi duk wuya....
***************
Lokaci yaja, masoya suna bararrakar
soyayyarsu, hankalinsu kwance ba wata
damuwa tare dasu, kamar ma sunfi kowaa
farin ciki da dacewa da juna.
Lele kuma tayi bala'en natsuwa, amma har
yanxu akwai son Moh a rayuwar ta, girmamawa
take yiwa Sumayya kamar me, Moh kuwa bata
qara bari sun huduba.....
Hajiya bushra da Alhaji xaune a Palo suna
tattauna yanda bikin da daya tilo xai kasance,
an tanadi gida Naji da fada, na nunawa tsara,
"Dan nidai jabo Dana shiga nida sidiya har
yawu saida ma xubar Dan kyau da tsaruwa.......
Moh ne ya shigo ya gansu kamar suna lissafi,
ya gaishesu, Dan Sumayya a hankali tafara
chanxa rayuwarsa, ya xama na kirki kirki,
amma kuma idan ta kama yana harkarshi...
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [8:49PM, 10/27/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 60����
Na khadija sidi & Hauwa M Jabo
Dady yace Muhammad zonan, ba musu yaxo
ya xauna, dady yace ki masa bayani,hjy tace
kamasa dai, ko wane sai ya kasa magana, sai
Moh ya dago da voice dinnan nashi mai sweet,
yace idan bakuda bayanin fada ni ina dashi,
suka ce yi naka to,
yace dady Dana qare karatu xanyi aure. Dama
shi moh haka yake, bai cika yin doguwar
maganaba, idan ba sign yayiba to maganar
bata wuce biyu ko uku, da kayansa Kawai yake
magana sosai,
Suka kalli juna, cike da mamaki Aure.!!!?? suka
saka dariya, hajiya tace ai maganar da muke
son mu maka kenan, shima dan murmushi
yayi, yace gud dady,
hajiya bushra tace ai maganar aure kada Kaji
komai, mun Riga munyi komai an siyo kayan
aure, hatta gidan da xaka xauna mun tanadar
maka, bari ma ka gani, ahj ya janyo laptop
dinsa slim da ita, mai tambarin apple, ya
kunna ya nunawa Moh, sai lokaci daya farin
cikin Moh ya bayyana, ya fara hangoshi shida
Sumayya a cikin gidan suna lovewa. Wata
dariya yayi. Duk saida sukayi mamakinsa,
Daddy na gode, gidan yamun sosai, wayar shi
tayi qara ya tashi, ina xuwa, dady, yaje
Sumayya ce ta kirashi, hjy bushra tace ka gani
Nasan Baxa mu sami matsala ba, kaga ma da
kanshi yace yanason auren, kuma ga gidan ya
masa, alhaji sai jinjina mata kai yake yana
murmushi, kaga yanda yake farin ciki, ta daga
hannuwa sama, Allah mungodema, ai Nasan
da gudu da yaga yarinyar xai amince da ita,
bari na nemo hotonta na nuna masa ita idan
yaxo.....
Moh ya dawo hjy tace dama mun Riga mun yi
komai Muna jiran kawai ka qare ne ayi bikin,
Sosa kai Moh yayi, yace thanks oooo.....
Hjy miqa masa wayar tayi, nasan ka Santa,
amma qara dubanta ka gani, Nasan xata maka,
munyi komai hatta sadaki da kayan aure mun
kai kai ina gaya maka hadda........ Bata
qarasaba ya katseta da miye wannan!? Yace
humaida ce!? matarda muka xaba maka, gata
mai kyau ita mai kyau, Ku haifomin jikoki masu
kyau... Ta fada tana dariya, Tsaya wa yayi yana
kallon mamarshi tana xuba, dady dai yayi shiru
yaji yanda xata kaya,
Maaamaaa.,!!! Ni bana yin wannan qazamar.
Hjy baki ta sake! Kamarya bakayinta, yace
banayinta maaaaamaaaaa, I hate her sabida
batason kayana,ta tsani kayana, nima na
tsaneta, hjy cike da mamaki tace wayanni
kayan naka ta tsana!!?? Muhammad Dan ta
tsani kayanka tunda bakai ta tsanaba ai da
sauqi.....
Miqewa tsaye yayi, yace dady.! maaamaaa!!
bana yin wannan yarinyar Sam,
Sumayya nakeso kuma ita xan aura..........
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [9:07PM, 10/27/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 61����
Na Hauwa M. Jabo & khadija Sidi
Hajiya cike da mamaki tace waye Sumayya
kuma,? Kuma waima wane kayanka ta tsana da
baka sonta!?
Maaaaamaaaaa, Sumayya itace yarinyar da
nakeson na aura, mun Riga munyi alqawarin
aure da ita, kuma dad nata ya bani ita, sabida
haka ni banayin humaida sabida batayin
kayana itama.!
Hajiya ta kalli alhaji, yau xasuga abin kunya,
Muhammad yana son ya kunyatasu, basu taba
tunanin cewa Muhammad yana kula maceba
bare har yasan soyayyah,
Alhaji ya gyara xama yace ai kuwa bakin
alqalami ya Riga ya bushe Muhammad, auren
humaida ba fashi, saidai ka hada biyu ka aura
amma baxai yi ka watsa mana qasa a ido
ba.....
Sabida haka Sai dai ka hada su biyu xaka aura
kuma humaida xa'a fara aure, sannan ita
Waccan da kake nufi..
Ya daga ido ya kalli iyayensa, dady.
Maaaaamaaaa, miye mata biyu!? Dady kokai
baka auri mata biyuba sai ni!? Kaima ka auri ta
biyu mana...!
Hajiya bushra tace kai banason shashanci, yaqi
ya auro mata biyu, kai wuce daki xamu
nemeka, alhj ya kalli matarsa yace ki barshi mu
qare magana mana, tace mayi daga baya, taji
yaro yana mata xancen kishiya,
Bayan ya wuce nan suka fara neman mafita,
sun tattauna sosai, sannan suka tsaya akan ya
kawo musu yarinyar su gani! Dan sun san halin
Muhammad idan bayason Abu bayasonsane,
yanxu lallabashi Kawai xasuyi ya auresu duka,
ya kuma gaya masu Waye babanta wata qila
ma mu hada business dashi, .
Su Fatima da xainb suka shigo, anan hajiya
take ce musu, kunji yayanku wai yanada wacce
xai aura,
laaa, habadai, mama, kai.....!!! Nasan Matar
bross dole one in town ce ya samo, Xee tace
nasan ma xatayi gashi, kuma tabbas yar
gayuce, kila ma irinsa ce bata magana, haka
sukayi ta surutai, heeee shine lokacin yake
tambayar kayan make up, ke sistoo inaga itace
ya siyowa takalmi last time, haka sukayita
surutai su kadai suna imagine din Matar
Moh......
***********
Moh da gang dinsa sun dawo skull, kamar
yanda suka saba, sun rako Moh gida ya musu
hannu xasu wuce sai ga Alhaji habeeb ya
tsaidasu, sun gaidashi chikin ladabi,
Kai jamilu, wace yrinya ce Muhammad yakeso!?
James ya sosa kai, dady nima bansantaba,
amma tambayi shamo ko ya Santa! Waye
shamo kuma!? Shamsu dady, tsaki yayi yace
duk kunbi kun bata sunayenku, ya juyo gun
shamoo, kai shamsu wacece wannan yarinyar,
shamo shima ya kasa fada, kai ko ba wata da
yake nema, mune yakeyiwa, amma yace kamar
Sumayya sunanta ko.!?
Suka kalli juna, son yace dady wata skull mate
dinmu ce yakeso, kuma wllhy dady gurg.......
Shamo yace mishi kai......
Yace miye!? Wallahi ba ruwanmu,
Dady yaga dai ba kanta, yace kai Kunsan gidan
su yarinyar ne!? Shamo yace no dady nidai
bansan gidan ba.
Kuma fa lokacin shine kan gaba gurin nemo
Gidan su Sumayya, lokacinda sukace ba mutum
bace,
Son yace ni na sani dady.
Dady yace Ku kuini gidan su yanxu
Su Kansu suna jin tsoron abinda xai biyo baya,
dady mota Kawai ya shiga yana jiran su kaishi
Gidan yarinyar!
Haka suka shiga gaba dady yana bayan su,
kamar yanda suka saba gudunsu sukeyi kamar
walqiya, tin dady yana musu horn alamar su
rage har ya gaji yariqa binsu, yaga yanda ake
bude musu hanya duk gunda suka dosa, har
suka kai qofar gidansu Sumayya,
Dady yanata kalle kalle ko xai hango babban
gida a gurin, amma duk gurin ba wani gida
daya mai kyau, mai nuna alamar kudi,
Kamar daga sama dady ya hango motar
gidansa ta tsaya, sakake yayi yana kallo, Moh
yaga ya fito cike da murmushi, sai kuma wata
gurguwa tare dashi, tana cilla qafa.
Dady aranshi yace wato Muhammad yanxu ya
qara natsuwa harda guragu yake taimakawa
kenan......
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [10:21PM, 10/28/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 62����
Na khadija sidi & Hauwa M. Jabo
Dukda dady ya tsani talakawa, amma sai yaji
dadi ganin dansa yana taimakon guragu.
Moh bai kula da dady ba, Dan hankalinsa yana
kan Sumayya, har ta shige gida, son ne yace
dady ga gidansu Sumayya nan, yana nuna
Gidan da yatsa, dady ya kalli Gidan a
walaqance, wato nanne gidansu yarinyar, dady
yace haba ba banxa naga Muhammad da
gurguwa, Ashe ba taimakonta yake yiba qanwar
budurwarsa ce, to wallahi bai isa ya auro mana
yar talakawa ba, dangin guragu, wata qila ma
asibiti ya kaita, mike yace no dady bafa qanwar
budurwarsa bace, gurguwar fa itace
Sumayyar.......
Dady kam bai yarda da abinda kunnensa
yajiyo masaba, yace mi kace? .
James yace gurguwar ce Moh yakeson ya
aura.!!!
Da qarfi dady yace WHAT!??? .
charaf a kunnen Moh, ya juyo sai yaga baban
shi da abokansa, fuskarsa a sake yaje gurin su,
dady ya kallesa rai a bace, Muhammad mi
kaxoyi anan!?
Yace dady na sauke kaya nane, dady ya kalli
su James kunce gurguwar ce shi kuma, shi
kuma yace kayan sa, kumin bayani manaaaaa...
Ya fada yana daga murya,......
James yace dady ai Sumayyar ce yake cewa
kayan shi, gurguwar,!?
Moh yace dady eh itace Sumayyar,
Wankeshi yayi da mari, saida Moh ya rude,
tunda ya girma yayi wayo iyayensa basu taba
dukansa ba sai yau...
Ya dago ido ya kalli dady ya kalle abokansa,
yaji Marin matuqa, yasa hannu a aljihunsa ya
wuce ya barsu a nan tsaye, motar ya tayar
kamar xai tada gari,
Dady kuwa yasa aka kira masa baban Sumayya,
yaron da aka aika yace wani mutumine mai
kudi, da babbar mota Gwaggo suruf tace kace
yana xuwa, kamin ta fadawa abbu saida ta leqa
ta hangosu, fuskar dady a turnuqe, tace shiko
wannan waye? karaf idonta asu shamo, ta dafe
qirji, ga wasu Manya manyan yan sanda a
bayansa, ta jinjina kai, su wayannan yan
sandan ma ba masu kaki bane, sunyi kama
dana xuwa kama barayi, dama tace abbun
baya nan, Dan taji tsoro.
Taxo ta fada ma abbu ana Neman sa tayi masa
bayanin yanayin mutanen da suke Neman sa,
Abbu ba wata damuwa ya fita abinsa,
Alhj habeeb bai tsaya komai ba, ya fara da
tambayar Muhammad ne yake Neman wata
yarinya anan!? Ko yar wajen kace!? Abbu ya
amsa da eh Sumayya ba,...
Dady ya gyara tsayuwa, ya fara xuba masa
kashedi, abbu yanata bashi haquri ya qare ya
wuce abinsa su mike suka dafa masa....
Duk abinda akeyi a idon Gwaggo, abbu na shigo
wa ta fara masifa qarshe ta dire akan
Sumayya,
Ai ni nasan ba Wanda zai kwashi wannan baqar
mayyar, mai shegen baqin jini, wallahi Sumayya
da nasan ke xai Haifa da lokacin chikin ki da na
jiqa kanwa da gishiri nasha chikin ya xube,
miye amfaninki, yuzilis"useless"kawai....
Sumayya dai batace komai ba.
Tayi xaune ta takure tana sauraren Gwaggo....
Ran Maxa ya baci Moh yana xuwa gida sai
lokacin ya tuna keys din dakinsa suna gurin
Sumayya data kwace lokacin da suke soyewa...
Palo ya xauna yana huci ko minti 30 ba'ayiba
sai ga dady ya shigo kamar xai fadi Dan
masifa,ga babbar Riga, yana xuwa ya fara
masifa hajiya bushra ta fito qannen Moh suka
fito akayi curko curko...
Wai yaronnan ya rasa yarinyar da xai dauko sai
diyar matsiyata, kuma gurguwa...
GURGUWA!??? .Lokaci daya duk suka maimaita
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [10:27PM, 10/28/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 63����
Na Hauwa M. Jabo & khadija sidi
Ya kalli hjy bushara yace Wallahi gurguwa,
qannensa sun sha jinin jikinsu, Dan ko a
mafarki basuyi tunanin haka xata faruba..
Hjy bushra gaskiya ta muta yawa, sai kallon
Moh takeyi, Moh kuwa ko a jikinsa, sai kada
qafarsa yakeyi yana kallon TV abinsa, dama ba
isashiyar tarbiya gareshiba, Dan an sangartashi,
so ba wani girmamawa tskaninsa dasu, Dan ma
Sumayya ta Dan gyara shi yanxu....
Alhj ya qare bala'en sa ga haushin Moh yaqi
tankashi, ya wuce dakinsa,
Hajiya bushra tazo tana tambayar sa
Muhammad wai da gaske gurguwa ce
yarinyar!? .
Ya dago arnan idonsa da suka kada sukayi
jaaa, ga Marin da dady ya masa a idon tuni
idon ya kunbura yace maaaamaaaa, Sumayya
nakeso kuma ita xan aura, tace ni ba shi nake
tambayarka ba, nace da gaske gurguwace, yace
of course, la'ilaha illallahu Muhammadu
rasullullahi....... Muhammad da gaske gurguwa
kakeso!?
Haba Muhammad! .
Duk matan duniyar nan ka rasa wacce xaka so
sai gurguwa, .maaaamaaaa gurguwar ce ta
mini..
Qannensa suka labe gefe suna kallo suna
mamaki, dan wannan abin yaci uban
tunaninsu...
Hjy bushra kam rarrashin danta takeyi, akan ya
haqura da gurguwar ya auri humaida,
Maaaaamaaaaaa banason ta,
Waye bakason?.
Ita wannan da kika fada. Humaida, yace eh,
Tashi yayi ya fita bike dinsa yahau yabi hanya
baisan ina xai nufaba yayi tafiya ba adadi
sannan ya dawo ya biya Gidan su Sumayya ya
karbo key dinsa, bai nuna mata komai ba ita
ma bata nuna masa komai ba, Dan ko helmet
dinsa bai cireba key kawai ya karba ya wuce
abiinsa .
****************
An buga sama an buqa qasa, akan Moh ya
haqura da auren Sumayya amma yaqi haqura,
iyayen sunyi fada suka dawo rarrashi amma
Moh ko a jikinsa, ahj haheeb kuwa ya baiwa
abbu tsoro akan ya jawa nakasashiyar yarsa
kunne amma ina..
Sumayya ko ajikinta, Dan Moh yariqa yayi nare
nare a chikin xuciyarta, yayi tasirinda idan dai
ba mutuwa ba ba abinda xaisa ta barshi,
soyayyah kenan........
Lokacin da aka saka na auren Moh da humaida
ya matso amma kuma still Moh baya tare da
ra'ayin su...
Hajiya wallahi da yaronnan ya kunyatani gara
na salwantar da rayuwar gurguwar nan!.
Hajiya ta to she baki, kisa alhaji??? Ban goyi
bayan kisaba, ina ma laifin ka saceta sai bayan
aure a dawo da ita,
No kasheta xanyi....
Hajiya kam jikinta yayi sansanyi musamman
yanda tasan halin mijinta, idan yace xaiyi Abu,
to sai yayi wannan abin itadai fatanta ayi
wannan auren kada suji kunya..
Moh ne ya shigo, ko kallonsu baiyiba Dan baya
yinsu yanxu tunda basayin Sumy dinsa.
Dady ya kirasa, amma Moh ya masa banxa,
saida hajiya bushra tace wai baka ji ana kiranka
ne!? Sannan ya tsaya ba tare da ya juyoba,
Da muryar nan tashi yace maaaaaamaaaaaa go
ahead,
Dady ne ya taso da kansa yace xa'a daura
maka aure da humaida, 20/5 dn ni Baxan bari
Dana ya auri nakasashiyiba.....
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [10:54PM, 10/28/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 64����
Na khadija sidi & Hauwa M. Jabo
Ina mai gargadinka akan ka gaggauta barin
yarinyar nan, wannan shine gargadina dakai na
qarshe Muhammad, kazo ka auri humaida, kai
kamaji, idan har baka amince da auren
humaida ba to
WALLAHI WALLAHI BANI BAKAI, BANI BAKAI... .
Sannan ina mai tabbatar maka da cewa na
cireka daga jerin yayana matuqar kaci gaba da
xama da wannan nakasashiyar yarinyar yar
iskar yarinyar Wani juyowa Moh yayi da qarfi ya
daga hannu yace
ENOUGH DADY.....!!!
Idon Moh sunyi qanana sosai, ya kalli dady
yace, Kana da right na fadar duk abinda kaga
dama akaina but not my Sumy, dady inason
Sumy, kuma sai na aurta matuqar inada
numfashi itace HASKEN IDANIYATA, .
Dady ya qufula, ni kake gayawa haka
Muhammad, Moh ya sauke kafada irin kai kaso
hakan,dady ya dago hannu xai wanke Moh da
mari, Moh ya riqe masa hannu, ya kallesa ido
cikin ido, kanada right ka dakeni lokacinda
nake chikin jerin yayanka, amma banda yanxu,
ni ba danka bane. Kai ka fadi hakan yanxu
right!? .......
Ya saki hannun uban ya wuce dakinsa, yana
shiga waya ya dauko ya kira Sumayya.!!
Assalamu alaikum..
Muryanta da yaji ta mantar dashi komai,
bashida abinda xai fada mata, sai kawai yace
bye ya kashe wayan...
Maganganun dady dinsa suka riqa dawo masa
akai, ransa yayi mugun baci gani yake duk akan
humaida ake masa wannan, yaso ya shaqi
powder amma sai ya fasa yaci gaba da fadin
innalillahi.....,...raji'un, kamar yanda
Sumayyarsa ta umurceshi,
Har saida ya sami natsuwar xuciyansa....
*********..
Sumayyah taje hospital gaida wata skull mate
dinta da ta sami accident ta karye, anan ta
hadu da wani Dr. Mai shegen naci ya biyota
wai yana sonta, xai gyara mata qafarta xata
koma daidai, Sumayya kam bata kulashiba Dan
xuciyanta ba kowa Sai Muhammad dinta...
Bangaren Dady kuwa ya Riga ya kammala
yanda xa'a kashe masa Sumayya.
Sumy cillire suna tare da Moh zaune wani guri,
suna hira, Moh ya qura mata ido sosai,
Ta kalleshi ta xare masa ido, wai me kake
kallona ne!? Tadan murguda masa baki, saita
dada burgeshi, murmushi kawai yayi yazo
gabanta ya tsuguna, a qasa ya zana I LOVE U
SUMAYYAH..
Dariya tayi tace miyasa kake son Sumayya!???
Ya kalleta Sumayyah I have no reasons of
logical thinking as to why I luv u, All I know is
dat, my heart is happy, my mind afloat & my
eyes satisfied when I'm with u........
Murmushi ta masa ta kanne ido, lallai
Sumayyah tayi dace, ji yake kamar ya hadeta
kawai taxama shi, ya huta da missing dinta...
Sun fito dag skull, sai Moh ya biyota daga baya
ba tare da ta saniba,
Wasu motocine suka shigo lokaci daya, Moh ya
hangosu sun dunfari Sumayya, tuni ya qara ma
bike dinsa wuta, yana kawowa ya ture Sumayya
ta fada chan chikin rame, shi kuma motar
sukabi ta qafarsa da hannunsa suka
wuceeeee........
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [6:34PM, 10/30/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 65����
Na khadija sidi & Hauwa M. Jabo.
Motocin da suka kade Moh kuwa tuni suka
gudu, Dan ba halin take Sumy Dan ta fada cikin
rame, ta cillo qafarta da sauri, taxo tana kuka
tana kiran sunansa, ta duba gaba da baya ba
kowa, kuka takeyi kamar ranta xai fita, Moh
kuwa tuni ya suma a gurin,
Moh koda yake hawa bike bai tafa faduwaba,
Allah ya masa baiwar iya bike....
Chan Allah ya kawo wani dattijo, Sumayya ta
tsayar dashi tana kuka tana Neman taimako ya
kaishi asibiti, anan ta masa bayanin yanda abin
ya faru, ya kalli Moh wannan ba yaron Alhaji
habeeb bane,!?. Tace eh shine baba..
Tuni yayi waya da yan sanda yasa aka kai Moh
asibiti, sannan yayi waya ya gaya ma aljh
habeeb.
Alhj yaji tsoro, shida ya aika akashe Sumayya
xasu kashe masa da....!!! ya kira wayanda
yasaka aikin suka masa bayani, ya gane cewa
Muhammad ya ture Sumayyah, aka kadeshi, sai
kawai ya gane ba laifinsubane, haushi da
tsanar Sumayya suka qara dasuwa a
xuciyansa..
**********
Dady da hjy bushra Sunje asibiti anan Dr. Yace
qafarshi ta sami rauni ana buqatar kudi masu
yawa, a masa aiki, ko a fitar dashi waje idan ba
hakaba Moh baxai tashiba har abada, xai rasa
qafarsane..
Hannunsa da sauqi Dan baima kariyeba, kawai
yaji mummunan rauni ne.. sai wasu gurare
daya Dan qoggoje...
Uwa da da sai Allah, hajiya ta rude matuqa, da
daya tilo azo a rabata dashi, sai kuka take
abinta, shima aljh yaji tsoro, amma sai ya
dake, bayan likita Ya qara masa bayanin
raunukan da yaji, da kudinda ake buqata
amasa aiki, sai alhj yace saiya gana da yaron
tukuna, da fatar dai yana iya magana,!? Likita
Yace yana magana sosai,...
Yana shigowa Moh na ganin su, ya kulle
idonsa, anan dady ya gaya masa abinda likita
yace, sannan xai biya kudi da sharadin xai bar
sumayyyah.....
Bude idonsa yayi a hankali, Dagyar yake iya
magana, yace dady idan har sai na bar
Sumayya xaka biya min kudin, wallahi nafison
na tabbata a hakan, matuqar Sumayya xata
xauna dani...
Ran dady ya bace matuqa, ya jiyo ya kalli
hajiya, kinji ko,!? Kinji ko.!? Ta bata hannu irin
kayi haquri dinnan, To wallahi ba hannuna
aciki, kuma kema ban yafe mikiba idan har kika
bada kwandala akan aikinsa, hatta ruwan
gidana ban yarda Muhammad yashaba,
matuqar yana tare da wannan gurguwar, hjy
tayita roqonsa yayi haquri amma yaqi....
Qarshe yasata gaba yace ta wuce su tafi, tana
kuka tabar hospital din, suna isa gida ya tattara
sauran yaran fateema da zainb ya gargadesu,
duk wacce ta kuskura taje asibiti duba
Muhammad bashi ba ita..
Sumayya ta rude iya rudewa ta sami likita, ta
masa tambaya anan yake gaya mata adadin
kudinda ake buqata, taje gida ta saida wayarta
da duk wani Abu da tasan tana dashi, amma
ko kwatar kwatar kudinda ake buqata basu
kaiba, tamasan kudin a kudin mota ma xasu
qare....
Alhaji Nifa bazai yiwuba, idan ka hana
nabiyawa yaronnan kudin aiki baxaka hana
naje nayi jinyarsaba, danane fa.!!! So kake
Duniya ta xagemu,? ke bakiga abinda ya
manaba,? yarasa wacce xai aura sai gurguwa,!
sannan ya watsa mana qasa a ido yaqi
xabinmu......
Ahj yace ki barshi gurguwar tayi jinyarsa mana,
saida suka kai ruwa rana sannan Alhaji ya
amince, tayi jinyarsa amma gwandalarsa idan
ta bayar Allah ya isa, idan kuma ya gane bakin
auren ta.....
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: 6:35PM, 10/30/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 66����
Na Hauwa M. Jabo & khadija Sidi
***********
Sumayya ta gayawa iyayenta abinda ya faru,
sun jajanta musamman abbu, Dan yace ma
xaixo ya dubashi da jiki....
Gwaggo kuwa saida tayi masifa kamar me, wai
qaddarar Sumayya ce take binsa, Tunda yace
yanason Sumayya ya fara samun matsala....
Hajiya bushra xaune ta tsurawa kyakyawan
danta ido, ya Dan rame kadan, kallonsa take
wai akan mace haka ta faru dashi, abinda bata
taba tunaniba, Ashe duk yanda mutum yake,
Mara magana da rashin kula mutane, xai sami
wacce yakeso haka.. tsaki tayi daidai nan
Sumayya ta shigo, kicibis sukayi ido hudu da
hjy, inda hajiya ta ganeta ta hanyar cilla qafar
da takeyi.
aranta tace yarinya kyakyawa abarson kowa a
fuska, amma na banxa tunda a nakashe
take.......
Gaisuwar da ta mata ya dawo da ita daga
tunanin da takeyi. Hjya bushra hararar ta tayi,
keee.... waye ke!? Dukda ta ganeta.
Ita kuma Sumayya tana qoqarin gaida hjy,.
Ta amsa a daqule, ana tambayarki kina
gaisuwa, nace waye ke!? .
Sumayyah Ta tsuguna gabanta chikin ladabi,
nice Sumay...... Batama bari ta qarasaba, tace
Munafuka, dama kece mayyar da kika cinye
mani yaro ko!? Allah ya isa tsakanina dake,
tashi ki bace min da gani yar iskar yarinya,
Allah ya isa tsakaninmu, da idonta kamar na
mujiya, Allah ya isa tsakanina dake wallahi.
Sumayya kuka ya kubce mata musamman jin
kalmar Allah ya isa daga mahaifiyar
Muhammad dinta... ta tashi ta cilla qafarta, ta
fita, fitarta yayi daidai da bude idon Moh, ya
juya chan ya juya chan, baiga kowa ba sai
mamanshi...
Ya Dan daure fuska, Dan baya sake musu
fuska, maaamaaa naji qamshin Sumayya ne..
Hararar sa tayi qamshi kodai wari, ina gurgu
yaga qamshi,!
Maaaamaaaa ina Sumy dita wallahi naji
kamshinta, tace aljanar yaxo na koreta, ya juyo
ya kalli uwar, maaaamaaaa ki kirawomin ita
mana.! Banxa tayi dashi, iya qarfinsa ya fara
kiran SUMAYYAH.! SUMAYYAH..!!!!!!!
Tuni ya cika gurin da kiran Sumayya, hajiya
bushra taga da gaske yake, dan har likitoci sun
fara xuwa ana lafiya.!? Amma ko a jikinsa
Sumayya yake kira, saida aka kira masa
Sumayya sannan yayi shiru,
Hjy baqin ciki ya isheta, ta tashi tabar dakin,..
Ya kalli Sumayya murmushi ya mata, amma ta
kasa maida mishi, saima kukan da ta qara
fashe dashi..
Ya rasa mi xaice mata, tayi shiru gashi ba halin
ya tashi, bare yazo gabanta ya tsuguna, ya
bata haquri,
Sumayyah.!! yanda ya kira sunanta, sai ta ji ya
banbanta da na ko wane lokaci, tausayinsa ya
kamata, tanajin haushin kanta ya xa'ayi
bashida lafiya tazo tana mai kuka, dago idonta
tayi, cike da hawaye, ya kalleta ido chikin ido,
ta qara kyau, amma kamar tadan rame.....
Moh dama ba gwanin maganaba bare ga ciwo,
yace ki kasance tare dani kawai. Hakan xai iya
zama magani gareni.!
Sumayya tace dan Allah Muhammad ka
haqura dani, kabi iyayenka...
Wani fito da ido, yayi, Sumayya bakyasona ne!?
Ko Dan kinga na sami nakasa ne!?
Tsohe bakinta tayi, wallahi ba haka nake
nufiba, kawai dai mu haqura da juna yafi.
Akaina ka rasa duk wani gata naka kalli yanda
kake shirin dawowa...!
Ya kalleta, idan dai har ina numfashi a Duniya,
Baxan taba barinka ba Sumayya, saidai idan ke
kika barni..
Sonki nakeyi Sumayya, kallonsa tayi, batasan
lokacin da ta masa murmushi ba,
Yace look at Her..... Tana hawaye tana
murmushi, yanda yayi maganar sai ya bata
dariya,.!
Yace + dariya again.batasan lokacinda tace,
Muhammad Kaine HASKEN IDANIYATA,dukkan
alama maganar xuci ce ta fito waje..........
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [6:35PM, 10/30/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 67����
Na Hauwa M. Jabo& khadija sidi
*********.
Su shamo sun sami labarin abinda ya faru da
Moh, dukda Moh ya daina yinsu, tunda ya gane
basason kayansa, ya dauke musu kai, baya
harka dasu Sam,dama idan yana skull to yana
gun Sumy, ko yanada lecture idan dai Sumayya
na skull din haka xai bita yaje gurinta. Tayi
fada har ta gaji, haka idan an liqa result saidai
yaje yana kallon na Sumayya badai bashiba, shi
dama nashi su shamo suke duba masa.....
Moh shi yake haska group dinsu, ganin ya
dauke musu kai, suma sun kama Kansu, Dan
bawai kudi aka fisuba, kawai Moh yafi
kwarjinine, a duk gurinda suka shiga...
Sunxo asibiti, nan ma Moh ya dauke musu kai,
dukda sunji haushi amma suka daure, sukayi
ya jiki suka wuce...
Humaida kuwa yanda labari ya sameta, Moh
yayi accident har ya rasa qafarsa, da hannu,
Ba shiri taje ta cewa mamanta wallahi baxata
aureshiba, ta fasa auren, iyayen kuwa ba musu
sukace, shikenan, Yanxu dai ta bari idan an
dauko xancen auren sai kawai ace an fasa,
yauwa ammi dama akwai wani guy da muka
hadu, wallahi ammi guy dinnan ya hadu, uwar
ta shafa kan yarta, karki damu duk yanda
kikeso haka xa'ayi, humaida yar gatace gaba da
baya .....
***************
Sumayya ce ta shigo asibiti kawowa Moh abinci,
Dan tun da hakan ya faru, ita take kawo masa
abinci, kuma haka yake chin abinsa, tunda Moh
yake bai taba chin tuwon masara ba, sai
xamanin Sumy, kunu da qosai haka take kawo
masa ya cinye abinsa, sabida uban ya hana a
bada ko kwandala nashi, hatta abinci yace idan
aka ciyarda Moh a kudinsa Allah ya isa, tana
tafe tana cilla qafarta, da ganinta kasan tana
chikin damuwa, kicibis tayi karo da wannan Dr.
da yace yana sonta, murmushi ya mata, tamai
yaqe, sun gaisa sama sama, ya tambayeta mi
taxoyi asibiti!? Tace tanada mara lafiya ne,
yayanta ne baida lafiya..
Eyyah, Allah ya qara lafiya, muje na masa ya
jiki, Sumayya har chikin ranta taji dadi, xaije
duba Muhammad dinta, sai ta dan sake mai
fuska, suna tafe tana bashi labarin yanda
accident din ya kasance.
Har suka shigo, fuskanta a sake, shi kuwa
wannan Dr. sai dadi yakeji ta kulashi zai cimma
burinsa insha Allah.!
Sallama tayi, Moh ya amsa kamin ya qare
amsawa sai yaga mutum tare da ita yanata
murmushi, tace kaganshi nan, Dr, yace Allah ya
qara lafiya, sannu yayan mu.!
Wani kallo Moh yayi wa Sumayya, wato yana
nan kwance ba lafiya, tana kula mutane ko, ita
kuma ta sake mai murmushi...
Dama a kwance yake rufe idonsa yayi, dan ya
fahimci wani Abu a idon Dr. Din. har Dr. Ya
qare surutansa, Moh baice masa komai ba, ko
bude ido ma baiyiba, xuciyansa sai tafasa
takeyi wai yayan mu, tabbas ce masa tayi
yayantane bata fadi cewa shi saurayinta neba
kenan, Dan ta ganshi kwance,.......
Wani abin daya qara baiwa Moh haushi shine
Sumayya da ta raka Dr. Da xai wuce, ji yayi
kamar ya kamota ya shaqeta Dan bakin ciki.
Bayan sun fito da Dr, yace tazo office dinsa
akwai bayani, xuciyanta daya ta bishi, office
dinsa, duk tunaninta akan Muhammad dinta
xai mata magana,
ya fara,
Sumayya tun haduwar mu ta farko na gaya
miki abinda yake damuna game dake, inasonki
ne, kuma matuqar kika amince kika aureni to
xan gyara miki qafarku ki dawo lafiya lau
kamar ko wace mace mai yanci...
Dago kai tayi ta kalleshi, rai a bace, haba Dr,
na dauka maganar Dan uwana xaka min, ni
wallahi daka gyaramin tawa qafar gara ka
gyarawa Muhammad tashi..!¡
Murmushi yayi Dan gani yake kamar ya fara
samun nasara,
Miqewa yayi yaxo gabanta ya Dora hannun sa
akan nata,
Subhanallahi, miye haka Dr.!??..
Ta fada tana ture hannunsa, ta miqe tsaye, yi
haquri, shima ya tashi tsaye, wato tun ranarda
kikaxo duba qawarki, idan baki mantaba kin
baiwa wata Aron hijabinki tayi sallah, wallahi
tun lokacin na hango surar jikinki, sha'awarki ta
kamani, ke ko baki aureniba, sau daya ma idan
nayi dake, wallahi xan gyara ma Dan uwanki
qafarsa, ya riqo hannuwanta, wankeshi tayi da
marii...
Ni ba yar iska bace, kuma ba'ason taimakonka,
wawa kawai, ta cilla qafarta xata fita janyota
yayi jikinsa da qarfi, dai dai nan aka turo qofa,
gashi ya riqeta gam, Moh ne saman keken
guragu........
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un abinda ya fada
kenan....
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [12:02AM, 11/1/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 68����
Na khadija sidi & Hauwa M. Jabo
Sumayyah tana kiciniyar ta qwace kanta, sai ido
hudu sukayi da Moh, Dr. Ya saketa da sauri,
Sumayya kuwa ta tsinke, Moh qoqarin juyawa
yayi amma ya kasa, dan ba hannu daya, dama
tunda sumayyah ta fita raka Dr. Ranshi ya
sosu,harma dai da yaga fuskarta dauke da
murmushi, ya kasa haquri, tuni ya sami wani
lebara yace ya kawo shi. Lebaran mai surutu,
da kanshi yagaya ma Moh yaga Sumayya tare
da Dr. Isa, a kwatancen da Moh ya masa
lebaran qara gane Dr isa ne, kamin su isa
lebaran yake baiwa Moh labari, ai Dr isa
mutumin banxa ne, har fyade yake yiwa yan
mata, sau da yawa anso a koreshi amma
xamansa likita mai haxaqa yasa aka barshi,
amma wallahi bashida kirki, gaban kowa yana
iya taba mace, Allah dai ya wadaran Dafta "Dr."
Isa, Moh saurarensa kawai yake baice masa
komaiba, har suka isa yaga abinda xai harzuqa
xaman lafiyar xuciyanshi, dama shi tun bayan
fitar Sumayya da Dr hankalinsa bai kwantaba.
Ashe abinda Sumayya takeyi kenan!?
Ya manta da abinda lebaran ya gaya mishi
sam, Idonsa suka kada sukayi jaaa, zuciyanshi
sai wani tafar fasa take, ran Maxa ya baci, ya
manta Sam da yanayin qafarsa, lebaran kamin
ya hankalto Moh ya miqe tsaye yana qoqarin
tafiya,kikaji raqaqaqa, qafarsa tayi qara, wata
axaba yaji wacce bai taba jin irin taba, lau yayi
zai fadi daidai nan Sumayyah ta fito a office din
Dr. A rude, taga Moh a atsaye kamin ya fadi
takai gunsa ya fadi a jikinta, xafin taka qafar da
yayi, yasa numfashinsa ya dauke, ga wani
radadi da yakeji a xuciyansa, koshi ya isa ya
sumar dashi, ganin Sumayya a qirjin wani,
likitoci sukayo kansa, suna fada miyasa aka fito
dashi...!
Haka aka kaishi daki da sauri, gashi ba wani
kulawa yake samuba, tunda asibitin ba wani
mai kyau bane, asibitin gwamnatine,
Sumayya kuka take kamar ranta xai fita, tana
safa da marwa har saida aka tabbatar da
dawowar numfashinsa....
Sumayya ta shigo idonsa a rufe ko bacci yake
ko idonsa biyu ohooo...
Ta xauna gefen sa tana kuka, tana masa
bayanin yanda komai ya faru, Moh ko motsi
baiyiba, nan ta qara tsorara, a hankali ta
kama hannunsa, ta hada da nata ta matse
GAM.!! Sai anan ne ya motsa yatsunsa, tayi
sauri ta sake masa hannu, ta kira sunansa,
Muhammad.!!!
idonsa biyu gyaleta kawai yayi, Dan idan akwai
abinda ya tsana a Duniya baikaitaba,
maganarta axaba take qara masa, ji yake
kamar ya shaqeta ya shaqe kanshi duk su
mutu a huta...
haka ta qare xaman ta, ba xancen cin abinci,
ta wuce gida Dan hado masa abincin dare.
***************
Son kwance yana juyi, abokinsa Moh yake gani
kwance chikin wani hali, son akwai tausayi,
sannan duk chikin gang din su shi yafiyin Moh,
bala'en sonsa yake kamar wani mace, ya kasa
zama yana tunanin hanyar da xaibi ya
taimakawa abokinsu, xunbur ya miqe ya hau
bike dinsa sai asibiti, ya kawo daidai gate, yaga
wata yarinya tana masa hannu alamar ya tsaya,
yasan fuskarta amma baisan ko wacece ita ba,
sai ya tsaya, anan na masa bayanin kanta taji
labarin accident dinda Moh yayi,shine tazo ta
dubashi,
amma abinda yafi bata mamaki kamar Moh,
amma yana kwance wannan hospital din..!
Son baice mata komaiba kawai yace ta biyoshi,
Ya nuna mata gurin Moh ta shiga gaidashi,
Shi kuma son kai tsaye gun likitan da yake
duba Moh ya nufa, sunyi magana akan xai
bada kudi a masa aiki, sannan xa'a chanxa
masa asibiti, nan likitan yake cewa lallai kam,
Dan kuwa idan qafar Moh ta qara sati daya
saidai a gutsireta. ..
Hankalin son ya tashi matuqa, Amma miyasa
dady bazai biya masa kudinba!???
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [12:22AM, 11/1/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 69����
Na Hauwa M. Jabo & khadija Sidi
Son bai jira wata wata ba yaje banki ya Ciro
kudi, Amma kudin bai kaiba, ya kawo wa likitan
yace ayi amfani da wannan daga baya xai kawo
sauran, daidai nan kilishi ta shigo tace xan
bayarda ragowar, nawa ake buqata!?? Likatan
ya gayamata tace a jirata xata ciro ta kawo...
Cikin 20mnt saiga kilishi ta dawo ta kawo kudin,
da yake ita khadija amma dai kilishi ake
kiranta, yar saurauta ce, gaba da baya,ga
dukiya Allah ya hore mata, ga kyauta, so
abinta baya tsole mata ido, da taimakonta aka
chanxawa Moh asibiti, chikin awa daya, son ya
kira hjy bushra ya gaya mata an chanxawa Moh
asibiti, ya bata number daki da komai....
Ba shiri hjy bushra ta iso asibitin, taxo kicibis
tayi karo da likitan da xai yiwa Moh aiki, likitan
yace dama ana buqatar sa hannun iyayensa ko
matarsa, anan hajiya ta saka hannu ba tare da
tasan cewa son ya biya kudin aikin ba, ita gani
take kamar dady ne ya biya, Dan jiya har kuka
ta masa akan ya barta ita ta biya, amma yace
idan ta biya bakin auren ta, kuma Allah ya isa,
yanda hajiya bushra takeson aure, ai baxata
aikata abinda xaisa auren su ya lalaceba... !!!
*****************
An shiga da Moh a masa aiki, kilishi, tana xaune
itada son da hajiya bushra, duk sun xuba uban
tagumi
Wato Allah ya jarabci kilishi da son Moh na
mutuwa, amma bata taba fadawa kowaba,
sabida jiji dakai irin na yayan sarakuna, ita
kawai butinta taga Moh ko daga nesane, idan
ta ganshi takanji sanyi a ranta, so batada
matsala, kwana biyu data daina ganinsa anan
ne ta sami labarin cewa yayi accident, shine
Taxo dubashi, kilishi kenan, kilishi masoyiyar
Moh....
An masa aiki chikin nasara da taimakon son da
kilishi,
Ana fitowa dashi hjy bushra ta dauki waya cike
da murna ta kira dady tana masa godiya, ta
kuma gaya masa an buqaci a saka hannu ta
saka, nan ya balbaleta da bala'e akan miyasa
tasa hannu, nan ma saida ya mata Allah ya isa,
sai lokacin ta fahimci Ashe bashi ya biya kudin
ba, daidai nan son ya shigo, hjy cike da
mamaki, tace yauwa, sanusi zonan, yaje kanshi
a qasa, tace wai ya akayi akayiwa Muhammad
aiki!? Anan ya gaya mata shi ya biya kudin, da
kilishi, waye kilishi kuma!?
Yace wata skull mate dimu ce,
Hjy bushra tayi ta saka musu albarka hadda
hawayenta, najin dadi......
**************
Sumayya bayan maqreeb kamar yanda ta saba,
ta dawo kawowa Muhammad dinta abinci,
dukda ranta a jagule yake, sai sauri take tana
yar cilla qafa, Dan ta makara yau, sabida
Dagyar ta sami mota, amma me!?? ba Moh ba
labarin sa, taje gun likitan da yake duba Moh
shima akace bayanan, anan ta xauna jiran
likita, da abinci har guraren 10 na dare, sannan
ta tafi gida cike da mamaki,
Gobe ma haka Taxo ba likita ba labarinsa anan
ta fara tsinkewa, to ina Moh ya tafi!? yama
xa'ayi ace an sallami Moh bata saniba.!? Kodai
iyayensa suka dauke shi, ta dauko tsohuwar
wayarta, wacce ta daure da gyaure, ta nemi
number Moh, dukda tasan baxata samuba,
amma saida ta kira, bata shiga, duk inda take
tunanin taga moh taje bata ganshiba.......
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [12:43AM, 11/1/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 70����
Na khadija sidi & Hauwa M. Jabo
Sumayyah duk ta rude, ta qara fita hayyacinta,
wasa wasa har aka wuce sati daya, ta sami
likitan anan akace an chanxashi, kuma taje gun
Wanda aka chanxa, shikam ko kallon ta baiyiba
bare ya saurareta....
Tun tana boyewa a gida, har ta fara kuka chikin
dare.
Ranar abin ya cita ya cita, ji take kamar ta
hadiye numfashi ta mutu, ba abinda yake mata
dadi, baci ba sha, tayi kukan xuci kamar me,
tayi hawaye, dama Sumayya akwai qarfin hali
da boye damuwa,
Amma ranar takai bango, kukane ya kubce
mata mai sauti, har saida lele ta farka daga
bacci, Taxo gunta, adda lafiya!? Sumayya
batasan lokacinda ta fada jikin leleba, taci
gaba da kukanta mai sauti, mai tsima zuciyar
duk mai saurare, nan lele tayita bata haquri,
har ta danyi shiru, lele tayita tambayarta
minene, anan Sumayya dai ta fadawa
qanwarta, Dan tayi ajiyar maganar har ta gaji...
Lele tayi shiru, chan tace adda zan
taimakamiki, xan nemo miki Muhammad duk
inda yake, tashi xaune Sumayya tayi tana goge
hawaye, ta kalli lele, tace lele banason a.....
Bata bari ta fadi abinda xata fadaba, ta toshe
bakin Sumayya, tace wallahi adda baxan
maimaita kuskuren Dana aikata bayaba. Trust
2me, kuma kema yanxu kinsan na natsu ba
kamar Daba.., ko bakiga na natsuba,!? tana
kallon Sumy.! tace, kin natsu lele.! ta fada tana
Dan murmushi......
Haka kuwa lele ta baxama Neman Moh, tashin
farko taje asibitin da Sumy tace an kwantar da
Moh, tayi tambaya akace an masa transfer,
likitan daya dubashi ma an chanxa masa gun
aiki, tasa aka nuna mata likitan da aka chanxa
dana farkon, taje gunsa, tamai mar mar da ido,
tuni ya rude, yaga yar beuty dama lele gwanar
kwalliya ce, Kuma ga baiwar kyau da Allah ya
mata...
Ta kasheshi da dadin baki, tuni ya nemo file
din Moh, da asibitin da aka maidashi, da
komai, ta bashi number akan xai nemeta...
Daga nan ta wuce asibitin da likitan ya gaya
mata, tayi bincike har ta gane dakin Moh,
amma baxata iya shigaba, Dan baxata iya
hada ido dashiba, tana tsaye bakin qofa, saiga
kilishi da son sun shigo, ta gaishesu, son yake
cewa tayi kama da Sumayya, lele tace kamace
kawai, ta tambayi, son Dan Allah nan
Muhammad yake jinya,?? Kilishi kuwa daure
fuska tayi, ta dauka lele gurin Moh Taxo, son
yace eh nan ne amma yana Hutu yanxu saidai
ki bari xuwa anjima ki dawo.
Kilishi sai hararan lele takeyi.. Lele ko a jikinta,
tayi godiya ta wuce gida..
Cike da farin ciki taje ta sami Sumayya ta gaya
mata ta samo gurinda aka maida Moh,
Sumayya batasan lokacinda ta rungume lele ba
dan murna,
Gwaggo take tambaya mine ake ta murna
haka!?? lele tadan bata labari sama sama,
Gwaggo ta fara bala'e, akan Sumayya ta fita
harkan moh, duk ta tsiyatar dashi, ta barshi ya
huta mana,, ita kuma da Allah ya ijiye haka
tayita zama a tsiyatance,
Ta juyo gun lele, ke kuma lele Wannan shine
pos & los "first & last" dinki, kada ki qara shiga
harkar wannan Mara arzikin. Kema kwana biyu
na daina gane kanki, ba wani dan maiqo maiqo
da yake shogowa. haka dai tayita masifa....
Sumayyah cike da farin ciki, dukda tana
fargabar abinda xai biyo baya haduwarsu da
moh, amma ta dake, Ta tafi asibitin da lele ta
gaya mata, tunda ta shiga qirjinta yake
bugawa, kamar ta fasa amma kuma ta dake,
takai daidai qofar shiga amma kuma sai taja ta
tsaya, daidai qofar shiga ta hango mace tana
baiwa Moh abinci a baki....
sandarewa tayi agun, haka ta riqa dawowa da
baya da baya, ta kama hanyar fita, sai kuma ta
dawo, karo na biyu, anan taji maganar macen
tana cewa Dan Allah Muhammad ko xaka
hadamu da Sumayya ne. Wallahi na yarda ka
auremu mu biyu, inasonka, wasu hawaye suka
sauko akan fuskarta, tajuya da qarfi, tabar
gurin, ta samu gu ta xauna tana hadiye rai, tayi
kamar minti goma a gurin, sannan ta qara
komawa, Wannan karon direct ta shiga dakin,
kilishice ta riqe hannun Moh, tana shiga
Kalmar da taji Moh yace SHIKENAN NA AMINCE,
kilishi ta sunbuce hannun Moh....
Karaf dukansu suka hada ido da Sumayya....
Sai gobe Kuma idan mai duka ya kaimu....
Kuci gaba da haquri wallahi yau saida na qare
typing duk ya goge, saida na sake yin wani..
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: Auntie M.Jabo: 🍃🍃HASKEN IDANIYA 71🍃🍃
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo
Kilishi murmushi ta sake ma Sumayya, yauwa
gara ma da kikaxo, ta saki hannun Moh da
sauri tazo tana sannu da xuwa yaya Sumayya,.!
Sumayya kallon ta tayi, wato irin ya amince da
ita har ta fara ce mata yaya….
Taso ta nuna bacin ranta, amma da yake
Sumayya akwai qarfin hali, da qarfin xuciya, da
hangen nesa, sai kawai ta dake,
Moh kuwa ido ya saka mata yana kallon ta,
lokaci daya missing dinta ya bayyana a
fuskarshi Automatically dayaga Sumayyah sai
yayi murmushi…..
Sam ya manta da abinda ya faru a
asibiti,ganinta ya mantar dashi komai…
Tazo kusa dashi ta xauna, batace komaiba, nan
dai kilishi da guntun kishinta ta fita ta basu
waje….
Sun dauki tsawon lokaci a haka, kunyarsa
takeji, ta duqar da kanta taba wasa da yatsun
hannunta, ba mai magana cikinsu..
Moh, yayi qoqarin tashi xaune, yana Neman ya
sauko qasa yazo gaban ta. da sauri Sumayya ta
tashi tsaye ta hanashi saukowa, Taxo gabansa
ta tsuguna, ta kasa kallonsa…
Ya bude baki xaiyi magana sai kuma ya tsaya,
kallon ta yake sosai, kwalla ce ta fito chikin
idonsa, har suka gangaro saman hannun
Sumayya, Sai lokacin ta dago kai tayi ta
kalleshi, itama hawayen ne suka gangaro a
fuskanta..
Yace No Sumayyah, don’t cray please.!!!
Ido cikin ido suke kallon juna, Moh yanason ya
sauko qasa amma ba hali, yace” Sumayya ki
yafemin, please kada ki qara nisanta na kinji.
nasha azaba lokacinda banajinki kusa dani, kinji
Sumy na”
Itakam mamaki abin ya bata, Dan itace ya dace
ta bashi haquri bashiba, amma ya dage yana
bata haquri hadda Yan matan hawaye,
Nan ma itama ta shiga bashi haquri, ta
maimaita masa abinda ya faru,ba wai hakan
takeba, hannu ya Dora akan leben sa, alamar
tayi shiru bayason wannan xance, an Riga an
gaya masa waye Dr, isa, son yayi masa bincike
akansa kuma ya gane ba laifinta bane, ” burina
ki daina fushi dani kinji.!
Murmushi tayi tana jin dadi, nan ta gaya mishi
ai ba fushi tayi dashiba, tamai bayanin Taxo da
yammar ranar, bayanan,ta kuma gaya masa
lele ta taimaka mata ta nemo mata gurin da
aka maidoshi, a ranshi ya jinjina lele…!!!
Sun fahimci juna dama ba Wanda xai iya shiga
tsakaninsu.
Tana tsugune gabanshi son ne da kilishi suka
shigo ganin Moh, yana murmushi ya basu
mamaki, ran kilishi ya sosu, itada sai tayi awa
hudu xaune tana mai magana, amma bata
wuce samun kalma biyu kai ko bude idonsa
bayayi bare yasan da xamanta, amma wai
shine yau hadda qoqarin saukowa qasa… Kilishi
na mutuwar son Moh.
Son dai kishi yake da Sumayya amma ya boye,
sun gaisa, son yace wato Moh mu ake yiwa
yanga ko.!? sabida sumy Taxo hadda qoqarin
saukowa akan gado ko?.
Dariya Moh yayi, wacce rabon da yayi irinta,
anyi sati nawa, yace naga kayana dole da
wareee…
Kuma daga yau sunana Muhammad not Moh,
ka gane ai…. Sumayya tafison Muhammad,
nima nafison sa ya fada yana kallon
Sumayyah,, kilishi dai kam ta xama yar kallo,
anya xata iya xama cikin wayannan masoyan!?
Dama haka yake son Sumayya!??
Lallai tanada aiki.. Sai hadiye yawun qarfi da
yaji takeyi..
Daurewa tayi tace yaya Sumayya lallai kinada
matsayi,..
Wallahi yau nayi awa daya ina masa magana
akan ya riqa chin abinci, kinga hannun sa
bashida lafiya, baya iya chin abinci da kansa sai
an bashi, amma kamin ya yarda na bashi sai
muyi awa daya baya kulani, yauma na
lallabeshi akan ya riqa ci koda sau biyu ne
arana, amma saida yakai fiye da awa daya
sannan yace min ya amince, lokacin ne ma kike
shigowa, sumayyah a ranta ta maimaita NA
AMINCE, sai lokacin tayi hamdala da batayi
mummunan xargi akan suba, yanada kyau
kullum mu kyautawa yan uwan mu xato kamin
mu xartar da hukunci….
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [11:01PM, 11/1/2015] Auntie M.Jabo: 🍃🍃
HASKEN IDANIYA 72🍃🍃
Na khadija Sidi & Hauwa M. Jabo
Yanxu gashi bawai xancen auren da taji yana
fada bane yace ya amince, Ashe abincine,
murmushi tayi, to amma miyasa kilishi tayi
kissing hannunsa.!?
Moh yace “Sumayya mi kike tunanine ko baki
yafe mini bane?.”
Tadan wayance tace laaaa, ba komai, ranar dai
kowa yaga chanji a gurin Moh, sabida ya saki
jiki, yana magana hattta hjy bushra saida tayi
mamakinsa, tanata washe baki, amma tana
kantarawa Sumayya harara……
**************
Moh, saida ya share sama da wata uku a
asibiti, sannan ya sami sauqi, da yake yana
samun kulawa sosai a asibitin, Wanda kilishi ke
bada kudin sabida axabar sonda takewa Moh,
ba tareda ya saniba burinta masoyinta ya sami
lafiya, dukda kullum gani take xai aureta,
amma idan taga yanda yake ma Sumayyah
soyayyah gaban uban kowa, sai tasha jinin jikin
ta, Allah sarki kilishi, abar tausayice akan son
Moh….
qafarsa ta ware ko ina Yana takawa da ita,
kamar bashiba…..
Yaune aka sallami Moh daga asibiti, sai ina
kuma!?
Baxai dumfari Gidan ubansaba, Dan ya riga ya
koreshi, Gidan su son ya nufa, kilishi qarfi da
yaji ta xama qawar Sumayya, Dan ba yanda
xatayi, Sumayya tana yawan baiwa kilishi
shawara hakan yasa take qara burgeta…
*******
Moh da Sumy suna ci gaba da soyayyah, anan
ne Moh xaice kawai lokacin aure fa yayi, aure
kuma waxai daura masa aure!? shiryawa yayi,
ya karbi kudi a hannun son ya tafi sokoto, karo
na farko da Moh ya shiga motar kasuwa a
rayuwanshi, sai rayuwar mutane tana bashi
tausayi, yanda suke yin komai a quntace, har
yakai sokoto tunanin sa daya, ya xa’ayi wannan
qasa tashi ta sami ci gaba irin na sauran
qasashe, !??.
Ba hanya mai kyau,.!! ba Sana’a ga Al umma,
abinda ya bashi mamaki da haushi, ganin
bayan motar da ya shiga ta cika, sai wani gato
majiyin qarfi, yazo yana roqon direba ya
sallameshi, ya bashi 50naira, gaton yanata
godiya, idan da ace, qasarmu tanada ci gaba
wannan gaton baxaka ganshi anan ba, yafi
qarfin xama nan. Yanxu minene mafita a
qasata Nigeria!??.
Da wannan tunanin Moh ya isa sokoto….
Yaje Gidan qanin baban shi, mamaki sukeyi
matuqa, tunda suke basu taba ganin
Muhammad a gidan ba Sai yau, wasu ma basu
sanshiba a dangi,.
Moh ya fadama uncle dinsa abinda ya kawo
shi, yanason ya nema mishi auren Sumayya,
uncle kuwa ba musu ya amince, ya baiwa uncle
din kudin motar da zaixo kano, amma yaqi
karba, ya saka ranar da xaixo kano Dan nema
masa auren Sumayyah,
Moh yaje ya sami abbu ya gaya masa xa ‘azo
neman auren Sumayya gurinsa rana kaxa lokaci
kaza….
Uncle nasiru ya cika alqawari, Dan kuwa ranar
yaxo kano shida abokinsa, da wani abokinsa da
yake nan kano, aka nemi auren Sumayya abbu
ya amince yace shi tin tuni ya baiwa
Muhammad Sumayyah…
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [11:19PM, 11/1/2015] Auntie M.Jabo: 🍃🍃
HASKEN IDANIYA 73.🍃🍃
Na Hauwa M Jabo & khadija sidi
An saka ranar daurin aure, ba dadewa, Moh,
yayi iya abinda yake dashi a kudinda suka rage
masa a account dinsa, da kuma taimakon son,
Ya kama gida haya, ba laifi dai, Amma dai
wannan Gidan ko yan aikin gidan su Moh sunfi
qarfinsa, bare shi kanshi Moh din…
Ko gurinda yake parking din bike dinsa yafi
qarfin gidan da xai xauna, Amma ko a jikinsa
dukda yaso ya shayar da Sumy jin dadi Amma
Allah bai nufaba, su Moh an San wani Abu
tawakkali…
Yayi qoqari ya dinkawa Sumayya tufafi daidai
gwargwadon abinda ya rage masa,..
Sumayya da Muhammad xaune a zauren gidan
su,
Sai kallon ta yake, yace “Sumayya, inasonki
kinji,” dariya ta masa, a rayuwa yanayin
maganar Moh Yana burgeta, sabida baisan
yanda xaiyi magana doguwaba, duk yanda yayi
magana baya wuce kalma uku, itace ma take
samun sa Yana mata magana mai Dan tsawo,
yace “dariya kike min ko!?” Kin kusa xama
matata dai, ya kalleta, Sumayya tace na’am. Na
Dade ina tunanin wannan ranar, ranar da xa’a
daura min aure dake, ki xama matana, kulle
fuska tayi tana dariya, suna xaune saiga lele
tana hango Moh ta koma da gudu….. murmushi
kawai Moh yayi. Dan yasan abinda yasa take
guje masa,
**********.
Gwaggo xaune tana yan hade hadenta,
keeee.!!! ta gwalawa Sumayyah kira, ta fito
tana cilla qafa, ke shashasha, ke bakisan yan
dabarun mataba, haka xakije masa kamar kunu
Mara sugar.! Sumy bata gane abinda Gwaggo
take nufiba, nan Gwaggo ta xaunar da ita ta
riqa durka mata maganin mata,
Gwaggo tace, Ina gaya miki wannan abin shine
darajar ki, dan ma mijin bashida komai ne, da
Wanda xan hada miki wallahi kullum sai ya
sallameki, Sumy kam kunya ta isheta.
Gwaggo duk a tunanin ta maganin mata shine
darajar mace, amma batasan cewa ba haka
bane, akwai abubuwa da dama da ya mace
take buqata a gidan mijinta, mace ta gari dole
ta xamo mai tsabta, iya girki, biyayyah ga
mijinta, sannan ta xamo mai godiya ga duk
abinda ya mata, uwa uba ta xama expert a
gurin kwanciya, dan da yawa mata kunya, ko
tsoron miji kada a rainasu yakesa basa biyawa
majaxensu buqatinsu, ai da xarar an daura
aure ba xancen raini, ki baiwa miinki haqqinsa
kawai.!!! xakiga wata Matar ta hada komai,
kyau, girki, tsabta, amma gun kwanciya ba
bayani, to lallai akwai matsala, dole kiji oga
yana miki dan tsaki da safe, Dan gamsuwa..
kuma duka wayannan abubuwan dole a hade
mace xata hadasu, bawai tanada daya, batada
dayaba, to mace idan ta hada wayannan xata
xama mowa a gurin mijinta….
amma itakam Gwaggo qoqarin matse Sumy
kawai takeyi, bawai gaya mata wayannan
abubuwan ba da sunada matuqar muhimmanci
duk wata ya mace tasan da haka…
Sumayyah Tasan idan taqi sha ma masifa xai
xama, haka ta daure ta riqa dirka…
Gwaggo tace, Yanda kika tsufa a gida,ai saida
yan hade hade, ko qanneki da basu tsufaba na
musu wannan, kinga kullum lfy lau gidajen
maxajensu Sumy batace da ita komaiba….
****************.
Ranar assabar itace ranar da xa’a daura
auren. SUMAYYAH & MUHAMMAD,
Son,ya gayyato duk abokansu, an taru daurin
auren fiye da tunanin Moh, fuskar shi kamar
tekun madara, yasha fararen kaya da babbar
Riga ke hadda hula, da ganin yanda yakeyi da
babbar rigar, kasan bai sababa, sai dariya yake
yau Sumayya zata xama tashi..!! .
Kamar daga sama saiga motar yan sanda guda
biyu, dady ne cikin motar shi,tare da yan
sandan, ya fito ya yan sandan suka Mara masa
baya, suka wuce dakin da ake daura aure…..
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [9:37PM, 11/3/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 74����
Na Hauwa M. Jabo & khadija sidi.
Dady yana shiga, yaji ana karanta fatiha,
alamar an daura aure, ya kalli liman rai a
bace, yace wallahi ka warware auren nan
Maxa, liman ya kalli Dady, yace sai kace wani
jahili, ai aure kam ya riqa ya dauru, saidai ka
nemi Muhammad yaronka, kace ya saki
Matarshi idan yaga dama, amma aure an
daura, kuma ya dauru. Dady ya rude kamar
wani mahaukaci, wato har an daura auren.!!!
ya gyara babbar Riga, yace ma yan sandan ku
kama abbu da uncle nasir ya nuna su da yatsa,
sannan aje akama nakasashiyar yarinyar nan...
dama da yan sanda mata akazo, aka turaso
cikin gida, su kamo Sumayya, amma kuma
koda suka shiga, Sumayya ta tafi gurin kitso,
anan akace saidai a tafi da uwar amarya,
Gwaggo ta zazzaro ido, wallahi ba inda xani, ta
kalli yar sandar tace wallahi yanxu sai na kulle
gida na suburbudeki, ni xa'a nunawa baqin
kaya, yar sandar ta fito da bindiga, ta matso ta
kama hannun Gwaggo, nan Gwaggo ta fara ihu,
tana Neman taimako, yayanta suka taso, yar
sandar ta daga bindiga sama, tace, duk Wanda
ya matso wallahi xan harbeshi, Gwaggo kuwa ta
fara tsinewa Sumayya, nidai wannan ya ban
haifoki da arxikiba, wallahy da nasan haka xaki
xame min dana jiqa kanwa da madaci na zubar
da cikinki, wane irin bala'ene wannan!? Hatta
ranar bikin aure sai gaddara ta biyoni,
Sumayya bakida amfani gareni, haka tayita
masifa kamar sumy tana gurin, har aka fito da
ita, waje...
yan daurin aure suka tsaya kallon ikon Allah,
kowa ya kasa gane mi yake faruwa...!!
Moh, baisan mi yake faruwa ba, yana chan
yana gaisuwa da jama'a. Wani yake bashi
labari, da sauri yaxo Gwaggo yayi karo da ita
an janyota, tana ihuuuuu...
dai dai nan ya kalli yar sandar da take qoqarin
dura Gwaggo a mota, ya finciko yar sandar ya
wasketa da mari biyu masu lafiya, saida ta
fadi, bindigar hannun ta ma ta fadi, ya dauki
bindigar ya riqe, yayi qiqarin fitarda Gwaggo
daga motar, sai harare harare takeyi, ta shiga
gida tana kuka, yau an musu wulaqancin da
ba'a taba masu irin saba, Gwaggo saida tayi
kuka Dan baqin ciki, kuma ta quduri aniyar
raba auren, dan baza akai Sumayya gidan Moh
ba.......
Moh, Yana ganin Gwaggo ta shige gida, ya nufi
gurin da akace dady dinsa yana chan, da
xuwan sa, yaga an fito da uncle Nasir da Abbu,
Dady yana biye dasu yana muxurai, yana
kawowa yayi tsaye gabansu cike da rashin
kunya da rashin tsoro, lokaci daya fuskarsa ta
koma Moh bike rider dinsa Nada... kayan bike
rider ne Kawai babu a jikinsa., ya kalli yan
sandan yace ku kwancesu, cike da gadara da
isa y fadi hakan, da yake shi dansandan yasan
Moh da gang dinsa sarai, Dan anyi ta kawo
qararsu, ba adadi har duka suna musu, ba
musu, ya kwance su uncle.
Dady ya fara yiwa police din fada, Moh yace
masa sheeeeeeeeeeee... Ya Dora hannu akan
lebensa, alamar Dady yayi shiru, kamar tsafi
kuwa, Dady yayi tseeet, ya kalli yan sandan
yace kuna iya tafiya, ba musu suka kama
hanya, dady yana musu masifa da Turanci,
yace sai sun biyashi kudinsa... Moh ya daga
bindigar dake hannun ya riqeta sosai, yace
Alhaji Habeeb, yau baice Dady ba, nine
bakaso!? To yau xan bar Duniya Dan ka
gudanar da rayuwar ka yanda kakeso, alhj ya
rude ganin bindiga a hannunsa, ya tuna
abinda ya faru kwanaki, saura kadan ya rasa
qafa, ya fara Dan Allah kayi haquri, wallahi
bakai bane, nakasashiyar yarinyar nan ce
banaso..!! Moh yayi murmushi, yace Alhaji
Habeeb, duk Wanda bayason kayana, nine
bayaso, Sumayya is mine, idan har ina
numfashi dole na rayu da kayana... Dady
mamaki yake yanda Muhammad yake fadin
sunansa, yansanda ne sukaxo daidai nan Moh
ya harba bindigar.....
Kuyi haquri wallahi na chanxa wayane,so
keyboard din Wannan wayar namin wahalar
typing, xuwa gobe idan na gyara xaku jini naso
koda page biyu nayi amma nafi awa biyu ina
rubuta wannan kunga kuwa akwai sauran
ayyuka, xuwa gobe dai. ...
Sidiya & M jabo
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [4:22PM, 11/4/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 75����
Na Hauwa M Jabo & khadija sidi
Ganin Moh ya harba bindigar, sai kuma ya
Dora akanshi yana qoqarin harbawa, Dan
sandan daga baya ya bige bindigar ta fadi ya
dauke, Alhaji habeeb tuni ya Rude, yan
daurin aure kuwa haka suka zama yan kallo,
abu kamar film, rayuwar Moh ta jagule.... Dady
ya bata masa rana gaba daya, wannan itace
ranar farin cikinsa,amma ya masa Wannan
Karen aikin...!!!!
Dady kuwa ba kunya ya buga babbar rigarsa da
yan sandansa ya wuce, hawaye ne suka
gangaro a kumatun Moh, ran maza ya baci.,
tunanin sa wane hali Sumayyarsa take ciki
yanxu, uncle nasir ya dafa kafadarsa ya jashi
cikin wani daki, ya rarrasheshi, amma saida
Moh yayi kuka mai sauti, har yana sarqewa,
Ashe akwai abinda xaisa Moh, kuka!? gaba
daya ya rasa mi yake damunsa, ji yake kamar
ya mutu Dan baqin cikin, sabida yasan idan
sumayyah taga wulaqancin da akama
mahaifiyarta, ranta xai sosu. sai dunqule
hannuwa yakeyi, "nida sidiya muka matsa gaba
Dan kada ya makemu." yana wani girgixa kai,
cocaine ne kamar yake motsa masa, Dukda ya
Dade baishaba, wani fizge fizge yakeyi, zunbur
ya miqe, uncle ya riqishe, ya kasa masa
magana, ya saka hannunsa ya cire hannunsa
daya riqe hannunsa dashi...! ya fice, mike yayi
karo dashi, kanada baby kusa.!? Mike yace
wallahi babu. ya wuce, gun su James a gurin
shamo aka samu. Ya karba ya shiga mota
dama glss din motar dark ne, so ba mai
ganinsa, ya shaqi powder sosai, har saida
hankalinsa ya gushe matuqar gushewa.!!!
sannan yayi baya da kansa, ya girgiza da qarfi,
yayi baya da set din ya kwanta. har mutane
suka qare watsewa yana cikin Motar, chan yaji
ana bubbuga qofar...
Abbu ne, yazo gurin sa, baiso budewa ba dan
bayason yaga halinda yake ciki, amma haka ya
daure, ya bude masa. Abbu ya kallesa yaga
yanda idonsa suka kada sukayi jaaaa, kuma sun
kunbura sosai, Moh bai bari sunyi ido biyu ba.
Abbu, har ya qare yiwa Moh, fada akan abinda
yayiwa mahaifinsa dazu, Moh bai daga kai ya
kalleshiba, ya qare ya wuce.......
Sumayyah ta dawo daga gurin kitso, tana cilla
qafarta, tana shigo wa bilki, ta kalleta tace yar
qaddara da hasara, tayi wani Dogon tsaki,
Sumy taji haushin Wannan Kalmar, ta kalleta
bilki lafiyan ki kuwa!? Tace kyaji bayani, ta
wuce abinta, dama bilki batason Sumayya tin
abinda ya faru da mijinta kwana ki...
Sumayyah taga kowa jugun jugun, a ranta tace
kardai an fasa daurin auren ne!! Tace Gwaggo
na dawo, Gwaggo tace sai ki nemi gu ki zauna
muyita zama, Dan wallahi idan dai ina
numfashi baxa'akaiki gidan Muhammaduba....
Gwaggo ta fashe da kuka, yau bakiga
wulaqancin da uban sa ya a kaminiba, wai nice
har cikin motar yan sanda!!! Duk akanki
Sumayyah, kinji harbe harbe, kamar yan boko
haram sun kawo xiyara a unguwar. wallahi
saida na hango yan wuta yau.. ta qara
fashewa da kuka, nan dai lele ta qara yiwa
Sumayya bayani har abinda Abbu ya basu
labari a waje....
Sumayya tayi shiru batace komaiba, ta gama
sadaukarwa, chan kuma tace Gwaggo, Kiyi
haquri.... akan zamana gaddara gareki.! nasan
tunda na girma ban taba amfanar dake
komaiba, kullum kina shaqar baqin cikina,
Gwaggo nayi burin kyauta ta miki, amma
banida halin yin hakan...
Yana daga cikin dalilin da yasa na qara dagewa
nayi karatu dan Kawai na sami na kaina, na
riqa kyauta ta miki, Dan nima sami albarkarki
kamar sauran yan uwana.....
ta fashe da kuka, Gwaggo ki yafeni,! kuma
insha Allah ko Bayan rayuwar ki bazan je Gidan
Muhammad ba, matuqar hakan xai fatan ta
miki, Gwaggo Dan darajar manzon Allah ki
yafemin wannan chin mutuncin da toxarcin
Dana janyo miki, ta fada jikin Gwaggo tana
kuka mai tsima xuciya.......
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [10:28PM, 11/4/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 76����
Na khadija sidi & Hauwa M. Jabo
Jikin Gwaggo yayi sanyi matuqa, abinka da d'a,
da mahaifi, kuma dama duk abinda Gwaggo
xata ma Sumayyah bata taba ce mata uffan
ba, sai ta qare ta bita har daki ta bata haquri,
ita kanta Gwaggo tasan duk yayan ta ba Wanda
yake mata biyayyah kamar Sumayya, kumaa ba
Wanda yake mata bauta kamar ita,
amma kullum cikin muzguna mata take kan
abin Duniya....
Kiyi shiru Sumayya, na yafe miki.. dama
bakimin komaiba wallahi, kuma insha Allah xa'a
kaiki dakin mijinki, yau dinnan kuwa, Allah ya
miki albarka. Sumayya tace Aah Gwaggo
wallahi na haqura da Muhammad har
abada.....
qannenta sunyi zaune suna kallonsu, duk
haushin Sumayya sukeji banda lele, Gwaggo
tace idan dai Nice na haifeki, kuma kina min
biyayyah a matsayina na mahaifiyarki kamar
yanda kikeyi ada, to ki shirya anjima akaiki
dakin mijinki... haka dai aka samu Sumy ta
amince xata, shima da amincewar Gwaggo.....!!
Da yamma aka shirya amarya aka kaita gidan
mijinta, wayaga Sumayya a gidan Moh...
Mohammad Moh, kuwa yasha cocaine yakai
sau biyar, so gaba daya ya rikide, Sam ya fita
daga cikin hankalinsa, son dai daya ga abin
nashi bamai qarewa bane, sai ya jashi a motar
daya kwanta ya tsaya a hanya ya mai Dan
siyayyah abinda xasu buqata, yakaishi gidansa,
koda yaxo har Sumayya tayi bacci, anan Palo ya
ijiye Moh, ya wuce abinsa........
*****************
Sumayya da asuba ta farka sai Kawai taga Moh
kwance a Palo, a ranta tace haka Muhammad
yake kwanciya a warwatse kamar wani
mashayi.!!? lokaci daya ta tuna hirar Guyz a
bus, sauri tayi ta kawar da Wannan tunanin a
xuciyanta.
tayi qoqarin tayar dashi yayi sallah, amma ina
kamar gawa haka yake, banbancinsu da gawa
shine shi yana numfashi, gawa kuma batayi,
haka ta haqura taje tayi sallah, ta dawo, anan
palon ta kwanta tana kallon Moh, jin abin take
kamar a mafarki, wai itace gidan mijinta, abin
qaunarta... amma ina ba mafarki bane gaskiya
ne,
Gidan ba laifi, Abbu ya mata kayan daki daidai
shi, lele ma duk kayan da tana taronta ta
baiwa Sumayyah su...
Har guraren 8 bai tashi ba, ta hada musu abin
karyawa, taxo tayi ta tayar dashi, dagyar ya
bude ido, jiyojin kanshi duk sun fito, yayi wani
kala dashi, ya kasa bude idon duka sabida
nauyin da suka masa, Sumayya ta kira sunan
shi, Muhammad.! Ya bude idon duka ya
kalleta, kadan ya rage tayi fitsari a zaune,
sabida idon sun kunbura, sunyi kamar jini, jaaa
sosai, duk xagayen farin yayi jaaa, Dan bacin
rai da kuma ccn dinda yasha, ta matso kusa
dashi cike da tsoro, tace bakada lafiya ne,? Ta
taba goshinsa, rufe idonsa yayi, Dan ya Dade
yana irin wannan mafarki... tashi kayi sallah,
kaga har lokacin ta ya wuce....
Sumayyah! Ya kira sunanta, Tace na'am da
gaske kece!? Tace eh mana, yanxu ke matata
ce!? Ta rufe fuska da hannuwanta, xanen
hannunta yake kallo, baisan Miye shiba, amma
ya mata kyau, kuma har cikin ranshi ya masa
kyau, Kawai yaji yanason ya taba zanen, ya
shafa hannunta a hankali, Dan baya wani iya
daga hannunsa... janyota yayi jikinsa a hankali,
ya ringumeta sosai, shi a nashi tunanin koda
mafarki yakeyi atls yadan taba abar
qaunarsa.....
Dagyar ta samu ya gane ba mafarki yakeba, ya
tashi yayi sallah amma ya kasa tashi!, da
taimakonta, ya tashi yayi arwula, yayi sallah,
anan dai ta gane yayi Shane, daga yana yinsa
amma bata ce masa komai ba, ya qare ta kawo
mai breakfast, kwata kwata ba abinda yake
iyayi, hatta hannunsa dagyar yake iya dagawa,
haka dai ta bashi abinci abaki har ya cinye tas
ba tareda taciba, ta fahimci yaji yunwa....
*************
Saida Moh, yayi kwana biyu sannan ya dawo
daidai...
Sumayyah tayi gayun ta cikin wasu kaya masu
kyau, kuma sun kamata sosai, ta fito daga Palo
ta shigo daki, Moh ya xauna yana kallon ta, sai
yanxu yake gane cewa lele ma ba komai bace
gaban Sumayya, komai nata need, daidai
buqatar mabuqaci, sosai yake kallon ta, ta
kashe mai ido, tace yadai!? Yama kasa magana
sai murmushi da yake sake mata, miqewa yayi
yaje gurinta ya kamota ya xaunar da ita, karo
na farko dayaga Sumayyah ba hijabi, bayan
sonda yake mata yasan akwai diriii, Dan duk
abinda yaji su shamo suna fada gurin
hadaddiyar mace Sumayyah tanada shi, ya
tsuguna gaban ta kamar yanda ya saba, ya
kamo hannuwanta da suka sha qunshi, kuma
qunshin ya mata kyau sosai, yana wasa dasu,
yace, Sumayyah ke bakya mamaki.!??
Tace mamakin me!?
Yace mun xama mata da miji mana, kunya taji
ta dugar da kanta amma kuma ya riqe mata
hannuwa, so ba gurin boye fuska, yace, still
kunya kikeje, ya turo baki, nifa mijinki
ne,banason wannan kunyar, nan ma kunya ta
dadaji, yanda Moh yake mata shagwaba, ta
rasa bakin magana, tadan cije gefen bakinta,
karaf a idon Moh, yace bari na tayaki cijewan,
dariya tasa, Noo banaso..! amma ina Moh ya
kusa bakinta,..
"haka sidiya ta janyo min hijabi da qarfi, jabo
mu fita mu basu wuri, zasu fara abin mata da
miji nace to har ina tuntube"
A ranar Moh ya mayar da Sumayyah cikakkiyar
mace, bayan Sumayyah ta gayamai anayin
sallah raka'a biyu...
Hummm..!! Su sumy anshigo system, ga dure
dure da shaye shayen da Gwaggo tama Sumy ,
ga Moh ba saban ba, Dukda bai wani iya
harkar sosaiba, amma saida taji jiki, da yake ba
sai an koyama mutum ba, su Moh ma an shigo
system.....
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [11:08PM, 11/5/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 77����
Na khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Duk sammakon Dana tsula gidan su sidiya,
amma koda naje sidiya ta saki baki tanata bacci,
haushi ya kamani bayan na gaya mata tun 6 na
safe xamu tafi gidan Sumayyah dan Muga
yanda suka tashi, amma ina sai 10 muka isa,
haushi kamar ya kashe ni, Dan naso naga yanda
Moh xaiyi da kayan shi....
Mun isa gidan a Palo mukayi karo da Sumayyah,
tana cilla qafa, sidiya tsaki tayi, har sun fito,
nace kamar ba'ayiba ko!? Sidiya tace ya xamu
gane tunda cilla qafa takeyi, haka muka
haqura...
Moh ne ya fito a daki da sauri.. Sumayyah nace
kije ki kwanta mana, duqar dakanta tayi, ta
wuce kitchen abinta, ya biyo bayanta ya
rungumota ta baya, haba Sumy, kije ki huta kin
gaji da yawa, tace waya gaya maka na gaji!?, da
sauri ya juyo da ita yana fuskantarta da gaske
baki gajiba?? ta gane mi yake nufi, Dan jiya da
dare tamai ihu, qarshe tace ta gaji Dan Allah
yayi haquri...…
Sidiya ta kalleni tayi murmushi, jabo an raya
sunnar ma'aiki, nace naga alama...
Yaqi sakinta ala dole ta gaji, ita kuma sai aikinta
takeyi, ya fake da ta gaji yana yan tabe tabensa,
duk a hankali yakeyi, tayi mai banxa kamar
batasan yanayiba, abinka da sabon shiga, har
saida ta qare hada abin karyawa, ta kawo
sukaci...
Sun qare kenan suna xauna Moh ba sabon ba,
maimakon ya bari Sumy tayi shagawa, shi yake
shagwabar, wai bayansa yana ciwo ta masa
tausa, haka baiwar Allah nan da nata jikin taje
tana masa tausa,
Sallama sukaji,
Sumy tayi sauri ta gyara amma Moh ya kamata
ya qara rungumeta, ya amsa sallamar yace a
shigo, Sumy sarkin kunya tana qoqarin kwace
kanta, amma ina, sai ido hudu sukayi da
kilishi...
Ran kilishi yayi matuqar sosuwa, ji tayi kamar ta
hanbare Sumayyah, taje ya rungumeta.!! a
rayuwar kilishi tanason Moh, ko mai sunan shi
taji sai tayi murmushiDan qauna, kullum zikirin
kilishi Moh, dama haka Allah yake abinsa, yakan
sanya qaunar junan mu a zukazatan juna, ya
sanya qaunar Moh a xuciyar Kilishi, shi Moh
kuma Sumy yakeso, Moh ko kallon kilishi
baiyiba, ta gaisheshi, bai amsa mataba, saida
Sumy tadan xungureshi, tace ana gaisuwa.!
sannan yace yauwa, kilishi dai kam tana ganin
Abu, gata da naci, tasan bayayinta amma ta
nace, ko ina sarautar da jiji dakai yake
ohooo....!?
Moh ko a jikin sa, gyara kwanciyarsa yayi wai
taci gaba da masa tausa, Sumayyah gyaleshi
tayi, taci gaba da magana da kilishi, haushi yaji
ya tashi ya shige daki,
Moh kenan, still da bashida komai a
talakancensa amma yana jin kansa, haline kawai
irin nashi....
Kilishi ta kawo ma Sumayyah yan kayayyakin
buqata, da kudi, amma Sumayyah taqi karbar
kudi, har saida taga Kilishi kamar tana hawaye,
sannan ta karba, itadai Kilishi taanason tayiwa
Moh hidima, ko xata samu shigaaa.....
Chan Moh ya qalawa Sumayyah kira, tana tashi
kilishi taje gun da Moh ya ijiye takalminsa, tasa
gyalenta ta goge masa.! tama takalmin kiss har
sau biyu, ko haka ta tsaya an biyata, kaji
soyayyah irin ta Kilishi....
Achan daki kuwa dagyar Moh ya bari sumy ta
dawo gun Kilishi, ta nuna mai wulaqanta Dan
Adam ba kyau, musamman mutumin da yake
qaunarka......
Kilishi dai kam anji jiki, cike da haushi ta fito,
amma kuma bashi xai hana ta qara dawowa ba
koba komai ta samu natsuwa ganin Moh da
tayi........
Sumayya da Moh, soyayyah suke narka, abinka
da sabon shiga....
Matsala daya da take damun Sumayyah, wacce
da Sam bashida ita itace, yawan fushi, ga fada,
Abu kadan zai fara fada, kamar ya cinye
mutum, hatta Sumayyar shi ma bai bartaba, ko
kuma ka ganshi shi kadai ya xauna yanata fada,
kamar wani xararre, Sumy bata kulashi Sam,
Dan tasan kusan duk akanta ne hakan ta faru
dashi....
**************
Result ya fito, Moh ya fara Neman aiki, amma
me!? duk inda yaje aka kalli result din sai a
masa dariya, sabida a result dinsa bai wuce ya
sami lebaranciba, Dan bashida maraba da
Wanda baije skull ba, Sam result dinsa bashida
amfani, idan ma sunce xasu daukeshi aiki, to
xai xama sabida sunsan babansa mai kudi ne,
sai suce sai ya kawo kudi masu yawa, shi kuma
bashida kudin, haka xai haqura,
zainb qanwarsa, a sace take sammasa kudi yana
samun abinda xasuci shida Sumayya, Dan wani
lokaci sai sukai yamma basu karyaba....
A haka har Moh ya saba da axumin litanin da
alkhamis sabida chan jin rayuwa da ya sami
kansa a ciki.
haka sukaci gaba da rayuwarsu, cikin qinci da
wadatar xuci...,
Sumayyah tana iya bakin qoqarinta na ganin ta
faranta mijinta rai, girkinnan daidai aljihunsu
amma tana bashi lokaci Dan yayi dadi, haka
kwalliya ma ba'anarta a bayaba, Dan ta kula
Moh yanason kwalliya, idan ta saka Jan baki, sai
ya lashe shi hankalinsa yake kwanciya, Dan
kayan mu na mata, a talakance, tana hada abin
ta tasha, duk Dan ta samu albarka gurin
mijinta, ganin cewa basuda bai hanata
farantawa mijintaba...
Sau da yawa Moh yakan yita masifa shi kadai,
har abin ya shafi Sumayya, ya juya mata baya
har a shinfida, amma koda xata farka, xata
ganta cikin faffadan girjinsa ya rungumeta baya
iya fushi da ita na awa daya.....
*************
Suna xaune suna labari, Sumayya xata gaya mai
tanada ciki, ya kalleta, ya xare ido..
Ciki, Sumy,!?/ kuma ni na miki shi!? Duk wannan
sunbatun na murna, kajishi, wa xai mata ciki
idan bakaiba."
Murna a gurin Moh ba'a magana, yanxu kullum
maganarsa daya baby...
sai ya xauna yayita shafar cikin yana daura
kansa a cikin, yayita surutunsa shi kadai Sumy
na masa dariya....
Wata rana Sumayya ta dawo daga skull tana cilla
yar qafarta, sai ta hadu da kilishi, sun gaisa,
Dan sun Dade basu haduba, anan Kilishi take
gayawa Sumy xatayi aure qarshen wata..
Allah sarki kilishi an barwa Allah, kowa xata
aura!? Nidai nasan xuciyar ta na gurin Moh,
Sunyi musanyar number kuma Sumayya tayi
mata alqawarin xatazo mata bikin...
Sumayyah itama result dinsu ya fito, duk tafi
kowa result mai kyau a Dptm dinsu.....
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: ����HASKEN IDANIYA 78����
Na khadija sidi & Hauwa M. Jabo
Kasan cewar result dinta yayi kyau, Ba jimawa
Sumayyah ta sami aiki, saidai Moh sabida
kishinsa bazai iya bari tayi aiki a guraren da take
samun aikiba, Dan har office xa'a bata...
Daga qarshe haka ta bige da teaching....
Dan Cikin Sumayyah ya taso har ana ganinsa a
hijab, cikin har yana motsi, Moh ya kwallafa
rayuwar shi a cikin nan, kamar me, har
sumayyah takanyi kishi da cikin wani lokaci,
wata rana da yamma sumy tana cilla qafa, sai
kawai ta cilkata saman ruwan santsi ya
kwasheta ta fadi, kuma ta fadi saman cikin,
anan dan cikin mai wata shida ya xube, Moh ya
Dora burin Duniya da wannan cikin, Dan baqin
ciki, hadda yan hawaye yayi, Dan shi abin
mamaki yake bashi wai xai sami yaro shima.......
Moh asalin Dan farine, bayan jiji dakai da
yakedashi cike yake da mahaukaciyar wauta...
********
Wata rana Sumayyah bayan ta fito daga ajin da
take bayar da karatu,suna zaune a staff, taji
ana cigiyar ma'aikata na computer, wayanda
suka iya computer sosai, ai kuwa Sumayya ba
shawara ba komai ta rubuta sunan Moh, dan
tasan mijinta a gurin gurune, bayan ta koma
gida take bashi lavari, amma Moh ido bude yace
baxai yiba, haka ta lallaba kayanta, sannan ya
tafi, shi dole ya gaji da wulaqanci.
bayan practice da aka musu Moh ya samu
karbuwa, sosai....
Wannan yayi sanadiyar Dan farfadowar Moh,
yana samu daidai gargwado a aikin sa, ga
matarsa malamar secondary....
Sumayya duk ta dauki albshinta sai tayiwa
Gwaggo siyayyah, sauran ta saka dashi, hatta
abinda ita kanta bataci takan siyawa Gwaggo
shi, Dan samun albarka iyaye, kuma a hakan
Gwaggo take karbewa tayita saka mata albarka,
burin Sumayyah kenan.....
*************
Hjya bushra xaune ta xuba uban tagumi,
batasan duniyar da danta yake cikiba.!!, tanason
ta taimaka masa amma uban ya hana, tayi fushi
har ta godema Allah, Fatima ce ta shigo da wata
calendar a hannunta, maaamaaa kalli, humaida
ce tayi aure da wani yaro, hajya tayi tsaki, ba
dole tayi aureba tunda sunji shiru, ni wallahi
banga laifin su ba, ai ma sun mana mutunci..
Fatima tace ke maaaamaaaa wallahi bakya
ganewa, ta harareta ina xan gane kuwa,
Dariya Fatima tayi, tace muma dai 'ya'ya ne,
kuma dole a somu tunda mu ake gani yanzu,
idan kuma muma an fitarda damu daga yaya sai
mu kama gaban, mu....ta fada tana dariya,"
abinsu ya xama tsokana, hjya bushra kullum ta
xauna xancen Moh, idan lokacin dawowarsa
yayi, sai kaji tace da yanxu ya shigo ya mini
kaza, wani lokaci sai ta fashe da kuka, shiyasa.
Yaran har suke zolayar ta." hajiya bushra tace
bace min da gani, sakarya kawai, tace yi haquri
maaamaaa, xannuna miki abinda nakeson
nunawa, hjy ta daure fuska, banaso..!!
Allah m serious maamaaa.
Tace kinga humaida on 12/February, tayi aure,
sannan lokacin broos yana asibiti ne, auren
Bross 20/may aka daura shi kinga kenan tun
Bross yana asibiti suka yiwa yarsu aure, hjy
bushra ta gyara xama, ke da gaske?? Wallahi
kuwa duba ki gani, nan hjy ta shiga lissafi, ai
kuwa,ta fara zaginsu, sannan tace sai an biyasu
sadakinsu da kayan auren su, ta kalli Fatima, ki
kalli kayan da muka kai musu, akwati set 6 ko
wanne set daya guda 7 ne a ciki, haka suka
kaisu gidan su humaida, set din atamfa da jaka
da takalminsu da sauran kaya daban..
qananan kaya ma haka,
Hatta kayan bacci set daya aka kashe,
Million nawa na kashe a kayan auren nan.!!?
keni ba kudin ba, kayan ma nakeso wallahi,
Fatima tace wallahi kuwa, komu aka baiwa muka
saka ai mun more tunda kunce gurguwa baxata
sakasuba...
Fatima wallahi xan bata miki rai, ki tashi ki bani
guri..! Fatima kam dariya ta saka, ta wuce ta
bar hjy xaune tana sunbatu, bari alhaji ya dawo
wallahi sai an karbo kayannanm....
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: [11:40PM, 11/5/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 79����
Na Hauwa M. Jabo & khadija Sidi
***************
Wata rana Sumayyah zaune a staff dinsu, ana
hira, mata dai idan an hadu hirar dayace...
sumayyah batace musu komai ba, Dan ita kam
bata taba sayen maganin mataba, ita take hada
abinta kuma Moh dinta yana gamsuwa iya
gamsuwa, kuma duk basuda effect...
Chan wata tace malama Sumayyah yadai,!?
wallahi ki daina duqunqunewa cikin hijabi
maxan yanxu sai kana nuna musu kaima da e
yane...
Sumayyah murmushi kawai tayi mata, Matar
tace xakiga murmushi idan kikaga wata a
gidanki.! maganar ta baiwa sumayyah dariya,
wai kishiya......
Chan taji wata tana ta bada nata labari, Wanda
ta aura dai kamar basonshi takeba, so bata
sakin jiki kada ya rainata da sauransu...
Saida suka qare Sumayyah ta kirata daban, tace
mata, ke kuwa bakyason mijin kine!? Tace
wallahi anti Sumayya sai a hankali, Dan har
yanxu bana iya sakin jiki dashi, gani nake kamar
xai rainani.....!!!
Sumayya ta kame ha6a, haba khadeee, Keda
nake gani wayayyiya,Amma kike wannan
magana!?
To bari na gayaya miki, da an riga an daura
aure, xancen raini ya qare.. ki saki jikinki, ki
nunawa mijinki qauna, duk wani Abu da kikasan
xai faran ta masa rai ki masa, ki xama gwana a
girki, tsabta, qamshi, yan kayan matsunnan
haka nan xaki riqa sakasu, kina fuske wa abinki,
Shagwaba nan kina masa..
,ta xaro ido, shagwaba anti!? Habadai xanje da
class sai naje ina masa shagwaba!? Ai sai rainin
ya xarce na kullum. Sumayyah ta gyara xama,
to bari na gaya miki khadee, matuqar baki
biyawa mijinki buqatarsa wallahi xakiga yanda
bakya so, kina xaune kin harde ke marason
raini, sai kiji yana xancen amarya!? ta qara
zaro ido, amarya kuma!? , Allah ya rabamu da
kishiya
! Au, bakyason raini ai dole ya dauko wacce xata
riqa masa abinda yakeso, wai mi kike nufi
khadeee!? Kina nufin haka xai xauna dake kina
daure masa fuska, sannan yaci gaba da xama
dake a hakan!?
Shifa namiji haka yake kamar qaramin yaro! Duk
yanda kikayi dashi haka xaiyi, amma fa idan
kina kyauta ta masa.... Yana samun far in ciki a
gurin ki ai kinga ba yanda xai hango wata,
khadee ta washe baki, kenan Dana Riga masa
ba xancen kishiya, na tsani kishiya, Sumayyah
tace banceba, amma gaskiya mafi yawan matan
da ake yiwa kishiya laifinsune, sai kiga mace ta
harde a gida wai ita hajiya, batason raini, ko
kuma kiji tana cewa mun tsufa mun barwa yara,
a kuwa dole miji ya dauko yarinya wacce xata
kama abarsa tayi asawaki da ita.. Khadee ta
kwashe da dariya, kai anti Sumy wai asawaki,
Sumayya tace eh mana, kinyi asawaki Kema sai
ya lashe miki, kinga anyi one one, ga lada ga
sweet, khadee tace daji lasar nan xatayi sweet
anti, Sumayyah tace kedai kika sani.. anti yau
xan fuske nace yamun, Sumy ta kalleta Keda
bakya son raini kuma!? Ta kwashe da dariya,
anti Sumy ci gaba da dai. Sumy tace Yauwa,
kinga yan kayan baccin nan, ba qaramar rawa
suke takawa ba gurin mai gida, xaki samu kala
kala, ba manya manya masu aljihuba, wayanda
suke nuna jikinki duka, daidai aljihunki, ya
hango twins dinki lafiya lau, khadee ta tabe
fuska, to ai anti abin nawa duk sun xubem.
Sumy tace ko sun xube Kiyi yan dubaru, akwai
kayan baccin da xasu dago miki su, idan kinje
kasuwa duk xaki samu,
kin ganni nan, wallahi bana wasa da kayan
bacci, Dan nasan suna daukar hankalin mijina, a
hankali xaki kula da wane abune yakeso
wannene bayaso, bawai sai kin tambayeshiba,
yau da gobe xaki fahimci haka, khadee tace
lallai anti Sumayya Ashe ke gwanace, yanda kike
xuba hijabi nan na dauka u don't know anything
walla...
Sumy yayi murmushi, ai darajar mace kenan ta
rufe Al 'aurarta saiga Wanda ya halatta ya
ganta, kinganni ko, wallahi mun Dade da mijina
kamin aure, amma daidai da rana daya bai taba
ganinaba, kullum da hijab dina, da mukeyi aure
ko, sai komai nawa ya xamo masa baqo, idan
ina tafiya kallona yakeyi, kullum yana
marmarina, khadee tayi shiru tana kallon ikon
Allah, Ashe wannan cilliren tana cilla love a
gurin mijinta, ai ke anti Sumy baki ba kishiya
har abada, dariya Sumayya tayi, kedai Bari,
kinsan namiji sai a hankali basuda tabbas....
Amma dai anti idan haka kike masa ya miki
kishiya ai ya yaudareki...
No khadee, wasu maxan sunada sha'awa mai
yawa, idan anyi rashin Sa'a suka auri macenda
batada sha'awa sosai, kinga akwai matsala, dole
ya nemo qari, idan dai ba so kake ya aikata
xinaba.
Haka wasu Maxan matansu basa gamsar dasu,
irin haka kinga dole namiji ya nemi qarin aure, a
ganina ma idan yayi auren ya miki adalcine,
Dan xai iya sakinki, wasu maxan kuma ra'ayine
kawai yakesa su qara auren,
Wasu kuma suna qara aure ne Dan matan su
basason a rainasu, Sumayyah ta fada tana
kallon idon khadee.. Khadee tace ai anti Sumy
xan cen raini ya qare,
Sumy Tace yanxu naji xance..
Yau xanje na fuske na gwada asawakin a hankali
har na saba,
Yauwa khadee na...
Yar shagwabar nan, da Dan tsokana nan dai,
kawai kuyi wasa, ki riqa hada jiki dashi idan
kuna zaune body contact yanada muhimmanci
sosai,
Sannan gun kwanciya ki sami turare kala daya,
Wanda sai lokacin kwanciya xaki fesashi, ina
tabbatar miki duk duniyar da yaje idan yaji
wannan qamshin sai abarsa ta harraka, zai tuna
dakene, a gida kiyi amfani da turare dubu,
amma gun kwanciya daya is ok, khadee tace
anti bani address din gidanki mana.!?
Sumayyah tace address kuma!?
Eh mana, wai nazo kina koya min abubuwa,
sumayyah cikin xolaya tace Keda bakyason raini,
tace anti share xancen raini Dan Allah dole nazo
gidanki, na kwashi lectures, anan sukayi sallama,
khadee ta tsaya tana kallon Sumy tana cilla qafa
amma bata wasa cilla soyayyah take...
...
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: ..
[11:52PM, 11/5/2015] Auntie M.Jabo:
����HASKEN IDANIYA 80����
NA khadija sidi & Hauwa M. Jabo
Sumayyah ta koma gida, duk a gajiya take da
sauri ta shiga kitchen Dan tasan Muhammad
dinta ya kusa dawowa, abinci mai sauqi ta
masa, ta hada masa zobo, abinci dai dai na
masu rufin asiri, Dan yanxu alhamdulillah Moh
ya fara samun sauyin rayuwa kadan, aikinsa
yana samu sosai, kullum burinsa ya faran tawa
Sumayyarh rai...
Ya dawo a gajiye taje ta tarbo abinta, tayi
kissing dinsa a kumatu, ya turo mata baki, ni
nan nakeso!
Tayi murmushi ta masa a bakin, ya qara turo
baki ba irin shiba, irin wannan xo na nuna
miki,tasan Wanda yake nufi, sai ta xille, shiko ya
daure ala dole yayi fushi, ta kawo mai zobo da
ruwa yaqi sha, baxakasha ruwanba!? Ya
murguda baki,hmmm. Sarkin rigima, ta gane
abinda yakeso saida tamai kiss dinda yakeso
sannan yayi dariya, Moh yana tsula shagwaba a
gurin Sumy dinsa, rayuwarsu abar son kowa,
tamai ya mata, suna faran ta ran juna, amma
fa sun sha wahalar Duniya...
bayan ya qare cin abinci, sunyi sallah sun huta,
tace saura Abu daya, ya gane, yace bacci ba,
tace karatu dai, ya turo baki, gaskiya yau
alkhamis, kuma duk Duniya ranar alkhamis
hutune, ba'a karatun islamiyy....
Ta gane bayason karatunne yau dajin yace
bacci, Dan haka yakeyi, idan bayason karatu,
daga yace cikinsa na ciwo sai yace, zuciyanshi na
tashi, ko yayi baccin qarya,
Tace to mu muna karatu ranar alkhamis,
waima! duk lokacinda mukayi Muna karatu
bakasan cewa ba'a karatu ranar alkhamis ba sai
yau!? Kanne mata ido yayi, ya janyota, ni
gaskiya matana nake buqata, tace ka bari mu
qare karatu, daxu ina xaune, nayi imagine din
wani style, zaiyi sweet sosai, amma da sharadin
sai ka iya karatun jiya, idan kuma baka iyaba ya
wuceka, yace wallahi baki isaba, sai anyi shi,
yanda ya fada ya bata dariya sosai, ya tsaya
yana kallon ta, a Duniya yasan yayi dacen mace
saliha,
Shiyasa Manzon Allah(S. A. W) yace" Duniya
gurine na jin dadi kadan, Wanda yafi kowa jin
dadin Duniya shine Wanda ya sami mace saliha"
tace ya kake kallona, ya Sosa kai, ina tunanin
abinda kikace ne, dariya tayi, tace yanxu dai iya
karatunka xaisa ka ga wannan abin,basai kayi
tunaninsaba...
Ta tashi ta cilla qafa taje ta dauko littafai, ya
daure fuska, ya naga hadda tajweed!? gaskiya
yau ba tajweedi, tace kadai manta yau akwai
tajweed, ya murguda baki, tace oho dai, ta
xauna Qur'ani suka fara yi, ya iya surar data
fada masa kaf ya haddace, " suratu shamsu" ce,
Moh daqiqine, amma gudun kada yaji kunya
gun Matarshi, yasa ya sayi wasu littafan idan
yaje aiki, daya samu lokaci haka xai xauna
yayita bita har ya iya,
Moh baiyi islamiya ba, a yanda ya bata labari,
sun fara karatun Islamic amma ya daina xuwa,
aka kawo musu Malami a gida shima ya daina
xuwa, shi yasa Sumayyah daga Alifun, Ba'un ta
fara mishi, Dukda yadan iyasu amma ya manta,
har yanxu an kai ga karatun surori.....
Fiqhu ma sunyi nisa, sira da yake tarihine, da
yawa take mishi,
Ita ta koya mishi sallah, gabaki daya Moh bai iya
komai na ibadaba, ta sauyashi ya xama na kirki,
shi yasa bay tana danasanin barin iyayensa ba,
duk wahalan da yasha, da yaga Sumy sai yaji
wahalan ta gushe,
Tace yauwa mijin Sumayya,
Yanxu sai muyi fiqhu, shima ya biya bai wuce
guri biyu yayi kuskureba,
Gurin tajweed ne ake kai ruwa rana, Dan bai iya
qalqale qalqalennan ba...
Dagyar ya samu aka qare karatu....
Ya Sosa kai,yace yanxu xamuyi ko sai Anjima, !?
Tace minene!? Yace style dinda kikace mana!?
Ta daure fuska tana tattara littafai, nifa wasa
nake maka, ta wuce daki, kuuut.!! Wallahi baki
isaba, ya kuwa bita ya riqeta, sai ta nuna masa
style dinda tace zaiyi sweet, Sumayyah tayi
dariya har cikin ta yayi ciwo, qarshe dai sun
raya sunnar annabi....
***********
Bikin lele ya matso anata hada hada,
Gwaggo kuwa batayi qasa a guiwaba Dan gyaran
da tayiwa lele yafi na Sumy , Dan tasan lele sai
a hankali, Sumayyah dama ta shiga dashe Dan
Kawai bikin yar uwarta, haka ta karbi kudin a
dunqule ta kaiwa Gwaggo, tace ga nata
gudummuwa, Gwaggo taji dadi kamar me, dan
duk cikin qannen Sumy ba Wanda ya kawo,
irin abinda Sumayyah ta bayar, kuma duk sun
fita arziki,
Ankai amarya dakinta,
A hanya Sumayyah taji ana tadin wai wani jirgi
yayi accident kuma duk an mutu sai mutum 7
suka rayu.
Tanata Allah sarki.!!
Bayan ta dawo gida a gajiye, ta tarar da
Muhammad dinta yayi bacci, tamai kiss a
kumatu ta qara lullubeshi, wanka ta shiga tayi,
har zata kwanta sai ta tuna taga TV a kunne,
Moh bai kashe ba, taje sai taga ana labarai,
anan ta tuna ance jirgi ya fadi, Bari ko xata gani
a labaran.
Tana nan xaune chan sai taga an nuno jirgin ga
gawawaaki nan xube, abin gwanin ban tausayi,
Aka hasko wayanda suka rayu karaf sai taji ance
ALHAJI HABEEB GALADIMA..
ta qara dubawa ana nunoshi sai taga Dady.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai ta
furta.......
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: ����HASKEN IDANIYA 81����
Na khadija Sidi & Hauwa M. Jabo
END.........
Dady yana cikin wayanda sukayi hadarin jirgin
saman, gaba daya fuskanshi ta chanxa ,
Sumayyah da gudu tana cilla qafa taje ta ta
tayarda Moh, daga bacci, bata ma tsaya mishi
bayaniba, janyoshi kawai tayi, tana nuna mishi
TV tana kuka, karaf idonsa suka kai ga
mahaifiyansa kwance, duk fuskanshi rauni,
runtse ido yayi da sauri, dan har cikin
xuciyansa yaji wani radadi, ya dauka ma ya
mutu, ya dungule hannu iya qarfinsa,
Sumayyah ta xaunar dashi, anan yaji sauran
Labaran, Sumayyah na kuka tace, yanxu xaka
tafi, ko sai gobe??? Yace ina kuma xan tafi!?
Tace gun Dady mana,!!
Kallon ta yayi, yace Allah ya bashi lafiya,
addu'ar ma fito masa tayi amm baiyi niyyan
fadaba.
Ya tashi ya juya ya koma daki, kwanciya kawai
yayi amma ya kasa bacci, Sumy kuwa alwula
tayo, taxo tana qoqarin tayar dashi, yayi sallah,
akan Allah ya baiwa Dady lafiya, amma Moh
yace baxai yiba, tayi rarrashi duk abinda tasan
xaisa yayi ta masa amma yace baxai yiba
qarshe wata tsawa ya daka mata, saida biron
sidiya ya fadi, na kalli sidiya nace yadai,
mutumin fa yadau xafi tace ko xamu gudune,
naje kin cika tsoro......
Sumayyah jiki a sanyaye tayi nafiloli, tayiwa
Dady addu'a sosai, akan Allah ya bashi lafiya...
Gari ya waye, Sumayyah ta tayar dashi, yana
wani shan qamshi, batace dashi komaiba, ta
hada mai breakfast ta wuce aikinta, shima ya
tashi ya wuce aikinsa, a office sai jaje ake
masa, kamar ma baisan abinda yake faruwaba,
yanata fuskewa, a ransa yake tunanin dama
ashe sunsan mahaifinsa,!?
Moh lokaci daya yana son ya rikida ya Moh
dinsa nada, dagyar ya qare aiki, ya koma gida,
Sumy ya tarar xaune da ganin ta tana cikin
damuwa,
Tamai Sannu da zuwa, ta karbi jakar hannunsa,
tasan abinda yafiso idan ya dawo, tamasa kiss,
murmushi yayi ya rungume kayan shi yayi
kissing din kanta...
A rayuwarsa duk damuwar daya shiga idan
yaga Sumayyah komai xai yaye,baya iya fushi
da ita, ta riqa ta zama HASKEN IDANIYARSA.
Bayan Hutu da chin abinci, yace yau ba
karatune!? Tayii murmushi tazo kusa dashi ta
xauna, haba Muhammad.! Da idonka kaga
halinda Dady yake ciki, amma hankalinka
kwance baka tunanin komai, mahaifinka nefa.!!
Kallon ta yayi, yace yau ba karatun kenan,!??
Murmushi tayi, ba karatu, yauwa to xoki mini
tausa yau nasha aiki a office, bata masa musu
ba ta tashi ta cilla qafarta ta wuce daki,
tanamai tausar tanaci gaba da masa maganar
Dady, Sumy tanata magana batasan Moh yayi
bacci ba, haushi ya bata yanda mutum xaiga
iyayensa cikin wannan halin yaqi damuwa.....
Itakam tana yiwa Dady addu'a, ko ba komai
shine sanadin xuwan farin cikinta Duniya wato
Muhammad dinta....
**********
Wasa wasa saida Dady yayi wata daya, yasa a
nemo masa Moh, amma Moh ya bace bat,
Sumayyah tayi rarrashi har ta gaji,akan ya tafi
amma yaqi, har abinda basu tabayiba saida
sukayi, wato gaba, yayi gaba da ita na kwana
biyu akan ta matsamai da maganar
mahaifinsa.....
Alhaji yaga aya hadda hadisai..!! sabida yanxu
ya dawo bashida hannu ko daya, duk
hannuwansa sun guntule, sannan qafarsa ta
hagu ta kar kace, so bazai iya tafiya da itaba,
yayi kuka shida matarsa har sun gode Allah.!!
Sumayyah tana xaune a staff room saiga
khadee sun khadee take bata labarin cewa
yanxufa komai xam xam, Ashe ba xancen raini
anti Sumy, wallahi ina gaya miki komai yi masa
nakeyi, hatta wanka tare mukeyinsa, kai anti
Sumy kin ceci rayuwata, da sweet ya barni,
garin shirmena, Sumayyah tayi dariya, to sai ki
qara dagewa, khadee tace bazan manta dakeba
anti Sumy, sukace gaba da hirarsu dai....
Sumayyah dagan nan gidansu ta wuce, ta tarar
da Gwaggo ta xuba uban tagumi, Gwaggo
lafiya !?
Ke wallahi Sumayyah na gaji, kullum mijin lele
sai ya Nada mata Dan Karen duka, bakiga
yanda ta dawoba,
Ita kuma bilki tace matan banxa yake kawo
mata a gida, idan tayi magana sai yace idan ba
xata iyaba ta qara gaba, ita waccan mai sunan
mamana, ko maganarta ba'ayi Dan har
mantawa nake da ita, yanxu fa su hudu suke,
tace kullum nema yake daya tayi wani Abu ya
sallameta, ya dauko wata, gashi tace baya basu
komai, a tsiyace ke maxan nasu duk nosen ne "
Nonsense " sun xama yuzile " useless,
Sumayyah dai ta baiwa Gwaggo haquri, kici
gaba da musu addu'a, tsaki tayi, wallahi rabon
da naci mai Dan maiqo tin Wanda kika kawo
min kwana ki, Allah dai ya miki albarka
Sumayyah, ni har kunyarki nakeji wolla, dariya
Sumy tayi, Gwaggo ni kike jin kunya? nandai
suka tattauna d'a da mahaifi ta wuce gida.
****
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
[1:58am, 2/28/2016] ☄Zaharaddeen☄Shomar☄: HASKEN IDANIYA 82 THE END
****
Tana clss tana bada karatu, saiga wani mutumi
yaxo gunta, ta fito tana cilla qafa ya mata
bayanin abinda ya kawo shi, tace xataxo amma
ba yanxuba sai ta gayawa mijinta, ta karbi
address din gurin sukayi sallama...
Tana komawa gida tace Moh yazo ya rakata
wani guri, ba musu ya amince, sun shiga
asibitin, Moh Sam bai kawo cewa gun
mahaifinsa xa'azoba.
Suna tafe tana addu'a akan Allah yasa kada su
hadu da kowa, wanda Moh ya sani ya gane,
har kuwa suka shiga cikin dakin basu hadu da
kowaba, suna shiga ta tsaya bakin qofa...
Hjy bushra ta miqe tsaye, Muhammad!!!
Rabonta dashi yafi shekara daya,
Moh juyowa yayi da qarfi xai fita, curus yaga
Sumayyah tayi tsaye ta rungume hannuwa ta
kafamai ido, wajenta ya nufo xai janyeta ya
bude qofa, saida yazo daidai ita zai janyeta, ta
dagaa mai hannu...
Tace wallahi summa tallahi idan har ka fita nan
dakin direct daga nan gidanmu xan wuce,
bazan xauna da mutuminda baya qaunar
iyayensaba, fuskanta a daure take magana, ya
dago ido ya kalleta, maganar ta yake jinjinawa
wai xata barshi.!!! yama rasa bakin magana,
ita batasan cewa sune suka barshi ba,!?
matsowa tayi kusa dashi ta riqe hannunsa tana
cilla qafarta, ta janyoshi ya kuwa biyota kamar
raqumi da akala saida tazo daidai gun
mahaifinsa, ta saki hannunsa, ta juya xata fita
hjya bushra ta kirata, hjy taje gurinta tana
kuka, Sumayyah ki yafemana mun gyamaceki
mun....
Alhj ne ya kira Sumayyah ta juyo tare da hajiya
suka tafi gurin alhj, alhj da hawayensa shabe
shabe a fuska yana kuka yana roqon Sumayyah
da Moh qafara..
Sumayyah kunya ta isheta tana ba komai
Dady.. duk gurin saida akayi kuka amma banda
Moh, ganin Sumayyah tace ta yafe shima yace
ya yafe, Sumayyah ta roqarwa mijinta gafara,
alhj yace ya yafe masa tuntuni,
Anan dai aka shirya har Moh ya dan saki jiki.....
Bayan kamar sati daya da shiryawarsu, alhj ya
nemi Moh akan yaci gaba da gudanar da
business dinsa, anan ma saida aka kai ruwa
rana, Dan Moh yaqi aminta, dagyar ya amince
ya karba shima da sa bakin Sumayyah... .
**********
Moh........
Bayan an shirya hjy bushra take bashi labarin
irin wulaqancin da su humaida suka musu
baice komai ba....
Saman bike dinsa, gudu yake,kamar yanda ya
saba, gidan su humaida ya nufa, yayi sallama
babanta da mamarta duk suna Palo xaune,
anan suka fara washe baki na munafunci,
Muhammad Kaine a gidan mu!? humaida.! Ya
jikin baban naka!? Humaida.! Zo ga
Muhammad, Moh ya cire helmet dinsa ya riqe
a hannu, ya saka dayan hannunsa a aljihu,
yace naxone karbar kudi da kayan da su hjy
sukace sun kawo na aurena, tsuru tsuru sukayi,
daidai nan humaida ta fito daki da yarinya a
hannu, yarinyar sai dalalo yawu takeyi, irin
golayen yaran nan ne ta Haifa mijinta yace
badai gidansa xa'ayi rainon wannan goluwarba,
tuni ya koro humaida gida da takardar saki.....
Moh yace kuna jina, sukace kaya kan basu
saidaj a ma kayan kudi xamu biya, Moh yace
ba kudi muke buqata, Dan munada su, kayan
nake bugata, nanda kwana hudu ina buqatar
kayan a gidanmu....
Ya fice abinsa, yar yarinyar da take hannun
humaida tace babaa, Moh ya juyo yaga shi
take kallo, yazo gurin yarinyar ya kalleta yaga
halittar ta, ya mata kiss a kumatu, ya shafa
kanta tanata dariya ya wuce abinsa...
Ko haka aka bar humaida taga aya......
**************
Bayan shekara 17.
Wata yarinta ce kyakyawa ajin qarshe ta shigo
ta hijabi a jikinta, tana shigo wa ta tube hijabin
wai Allah, ta fada tana Neman gurin xama, alhj
Habeeb ne ya kwala mata kira, ta xun buro
baki kaifa wallahi ka cika rigima yanxu xakace
sai na karanta maka news paper...
Yace ke ja'irar yarinya, gwalo ta masa, yau
saidai ka karanta jaridar da kanka, TV xan
kalla, hjy bushra ta fito, wa yake yiwa mijina
wulaqanci.!? Rufaida ta kwashe da dariya
wannan mijin naki ai saike, wazai iya, zoki
karanta mai jarida, ni bazan iyaba, ta karbi
jarida tana karanta mishi,
Wata yar yarinya kimanin 14yrs ta fito tana ya
mutsa fuska, na rainin wayo, wannan tsohon
Yana takura mana.! har kunya nakeji na nuna
shi as my grandfather, Moh ne, ya shigo sai ki
kasheshi a daina cewa kakanki gurgune,
Ta toshe baki laaa, Abbah wasan kaka da jika
mukeyi fa.. alhj habeeb ya kwashe da dariya,
yarinya taji tsoro, axo a karanta min news
paper.
Yace kagansu duk sun rainamu
saina mammakeku, suka saka dariya su biyu
lokaci daya sukace, da wane hannun xaka
makemu!? Sumayyah ce ta shigo tana cilla
qafarta, taje tana yiwa mijinta Sannu da xuwa,
ta rungume shi tamai abinda yakeso, ta karbi
jakar hannunsa, rufaida ta kalli hjy bushra a
hankali tace, nifa kunya nake ji idan naga
mamee tana wani rungumar Abban mu, Ashe
Sumayyah tajita, tace to sai ki hanani ringumar
mijina...
Gaba daya aka saka dariya, .. Rufaida aranta
tace hajiya bushra naji da gurgun mijinta,
Abbah yanaji da yar cilliren Matarshi...
Rayuwa ta sauya Sumayyah ta fito gari tana
cilla qafarta Dan gurguntarta bamai gyaruwa
bace.,duk tafi yan uwanta daukaka, alhj ya
gane cewa nakasa daga Allah ne, Dan gashi
yanda Allah ya mayar dashi, Gwaggo kuwa tuni
ta sadaukar ta daina kwadayi, kilishi ma ta
barwa Allah ta rungumi mijinta...
TAMMAT BI HAMDILLAH..
Mun saudaukar da wannan littafin ga duk wani
mutum da Yakeda nakasa a jikinsa, hakan
bawai Allah bayason su bane ya halicce da
nakasa, saidai Dan ya nuna ikonsa akan komai,
kuma ya xama abin jarabawa ga bayinsa.!!.
Allah yasa mu amfana.
Muna jiran gyaranku yan uwa..
Hauwa Muhammad Jabo
& Khadija Sidi (Salma Ateeku)
Muke muku fatan alkhairi sai mun hadu a
sabon littafina ni jabo mai suna........
Duk mai buqatar littafan jabo
Www.hauwajabo.blogspot.Com
Www.jabohauwa.WordPress.Com
Face book group: Auntie M. Jabo Books.
����NAZARI AKAN HASKEN
IDANIYA.����
Na Hauwa M. Jabo
& Khadija Sidi (Salma Ateeku)
* Muna godiya Ga masoyanmu da Suke bibiyar
littafin daga farko Har qarshe...
*Kunga dai yanda rayuwar Sumayyah ta
kasance, da itace qasqantacciya a gidansu,
amma daga qarshe duk Ta fi yan uwan ta
daukaka Saboda haqurinta....
* Sumayya ta gyara Moh,
Ya bar shaye shaye, nd closer to his lord.
He will be losing saboda ita,
Amma shi zaiga kamar hez wining sabida a
gurinsa hakan rahamane..
*Sis din Sumy za ta yi tunanin za ta iya jan
ra'ayi Moh,saboda kyau da bude jikin ta,
Amma zai zama duk a banza,
Kunga kenan ba sai kin fitar da tsaraici za a
sokaba, Sumy kullum cikin hijabi take amma
itace star a gurin Moh,
So bawai sai ka bude jikinka xa'a sokaba, yan
mata masu saka kayan tsiraici Ku gane
wannan....
*Sannan kuma nakasa ba ta hana a so mutum,
dan kunga yanda Moh ya mutar ma Sumayyah
bayan ita gurguwace..
In Allah ya baka mai son ka shikenan,
Kunga cewa Cos Moh is perfect,
Sumayya opposite din sa ce, amma haka yaso
kayan shi, Ilimi kawai ta fi shi..
*Babban abunda ya sa Moh shan wahala
bijirewa iyayen sa ne da yayi, Dan kuwa Duk
wanda yayi haka sai ya wahala a rayuwa, shi
hakkin iyaye daban yake.
*Kunga yanda Sumayyah ta xauna da Moh cikin
wahala, kunga kenan ba sai ana da kudi mace
za ta gyara kan ta ba, wasu matan idan mijinsu
talakane, haka xasu ta xama basa qoqarin
gyara Kansu,
Kunga Sumy Wit d little tins da ta ke da,su
kananfari da kissa haka ta tafiyar da mijinta.
*Illar sangarta yaya, sabida lokacinda yaqi
karatun Islam da basu biye masa ba da ba
hakaba, saboda rashin ilimin Islam yake kawo
rashin sanin darajar iyaye, Wanda hakan yasa
Moh yabar iyayensa akan mace, ita kuma
Sumy lokacinda mahaifiyarta tace bazata gidan
Moh ba ta amince Dan tasan darajar nata
iyayen.
* Mijin sis din Sumy zai gwada ma ta iskanci,
wanda sis dinta ta na takama ta auri mai
kudi,kunga kenan ba kudi ba,miji na gari shi ne
rayuwa, Allah ya baiwa ko wa miji nagari.
Ina amfani garin san kudi ka auri kwarto?
Wanda Ya kasa hakuri har sai ya kai ga yayar
Matarshi,
Iyayen da sukeda kwadayi irin su * * Gwaggo
taga illar auren kudi, dan ga abinda ya janyo
mata nan kullum taqumi da zullumi...
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Download Hasken Idaniya Littafi Na Daya
0 Comments
Thank you for this comment