98U




 Compiled By Umar Dalha Funtua.

: *JALILA 1*

In the name of Allah the most Beneficent the most merciful.
Praise be to Allah lord of the words.
The beneficent the Merciful.
Master of the Day of judgement.
Alone we worship;Alone we ask for help.
Show us the straight way
The way of those on whom Thou has bestowed the Grace, those whose portion
Is not wrath, and who do not go astray.


   Gaisuwa tare da jinjina da fatan alkairi gareku daukacin masoyana, ina mika sakon gaisuwa gareku, dafatan kowa yayi sallah lafiya, Allah ya maimaita mana Ameen, musulmai da suka rigamu gidan gaskiya Allah ya jikansu, mu da muke da rai Allah ya sa mu gama da duniya lafiya Ameen suma Ameen.
 _Oh ina fatan me karatu yayi saurin cewa Ameen..... lol duk da nasan ke ko kai ka fada.........._

 *JALILA*

*Ayusher Muhd's Novel ke dauke da shafin na 1 daga cikin littafin Jalila.*
 *Dauke da tambarin Kungiyar Haske Writers Association*

  ***********

  Da sauri ta fito daga wanka ko mai bata tsaya shafawa ba ta zura kaya, ta rataya jakarta ta dauko safarta a hannu ta nufi hanyar waje, Goggo mahaifiyarta ce tai saurin cewa "Jalila ko karyawa bakiyi bafa."
 Tace tana kokarin sa sandal "Goggo share abinci nan in driver dinsu Safeenah ya tafi ni kadai nasan uban tafiyar da zansha in banyi wasa ba inci duka in naje makarantar."
 Tafada tare da gama saka sa sandal din,Goggo da sauri ta miko mata naira ashirin tace " ungo to in kinje kya samu wani abin kici."
 Jalilah ta amsa tare da yin waje da gudu.
 Tana zuwa motar na fita daga gidan da gudu ta karasa hanyar kofar sai dai kafin ta karasa sunyi gaba.
 Idanunta ne suka ciciko dan ta tabbatar anganta ko ta madubin mota ne, bayan yau aikin gidan ne ya mata yawa amma ko su tsaya ta, inda sabo ta saba sai dai tana kokarin kiyayewa dan kuwa makarantar da takeyi akwai nisa, duk da sudin makarantar kudi sukeyi ita kuma ta gomnati, sai dai ba nisa sosai tsakanin makarantun nasu.

 Sauri ta shiga yi dan tasan tabbas kafin ta isa sai tayi late.
 Duk hanya ba dadin tafiya sakamakon ruwan da aka sheka a daran jiya, dan ma bata sa safarta ta makaranta ba, jin yanda wata mota ta shararo da gudu yasa tai saurin matsawa, tare da bin motar da kallo, da gudu ya zo ya wuce da motarsa, wata muguwar harara ta bi mai motar dashi sannan ta ja wani tsaki juyawa tai baya taga duk yawanci mutanen baya motar suke bi da harara da alama kowa yaji haushin yanda motar ta kunno da gudu cikin layinsu, Jalila ta kara kallan motar wacce ta riga ta kule tare da kara tsaki tace " wasu dai ba kai sai na daukar kaya"

  Cigaba da tafiyarta tai duk ta gaji, har sai da ta kusa isa makarantar sannan ta tsaya tare da ciro safarta ta tsaya a gefe ta saka sannan ta dan karkade jikinta, ita nufi makarantar, mamaki tai da taga kamar motar da gani dazu.
 Motar ta gani tayi gaba, baki tadan tabe sannan ta karasa gate din makarantar.
 Sabon Malaminsu ta gani tsaye a bakin gate da alamar shine yake tarar late comers, kanta ta sunkuyar har ta isa gun.
 Shikuwa tunda ta taho yake kallanta fuskarsa a dan hade tana matsowa yace " Habiba Auwal me kenan?"
 Kallansa tai da sauri tare da cewa " Good Afternoon Sir!"
Yace "Afternoon?now?"
 Da sauri tace" Oh sorry sir Good Mor......."
 Katseta yai yace "Dama bakya zuwa school da wuri?"
 Kallansa tai tace " No sir wlh yau ma tsaytsayi ne."
 Fuska ya kara had'ewa yace " Tsautsayi a ranar farko dana fara tsayawa a gate?"
 Kasa tai da kanta tana wasa da yatsun hannunta, yace "sai ki dau dustbin kiyi picking."
 Kallansa tai dan ta dauka dukkanta zaiyi, murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace "Thank you sir"
 Shima murmushin yai yace "Last warning in har kinaso mu shirya kenan."

 Da sauri ta daga kai sannan ta dau dustbin tai gaba ta fara picking, kallansa ta juyo tai ta baya, ba shakka bata taba ganin wanda kayan Nysc sukama kyau ba irin Uncle Sagir.
 Jalila na gamawa ta wuce ajinsu, ganin ba kowa a cikin ajin yasa tai saurin juyawa ta nufi lap.
 Suna lap din chemistry ana musu practical, da sauri ta wuce gun groups dinsu, Zarah ta kalleta tace "Jalila kinga yarda idanunmu suka firfito muna tsoron kar a ce ya akai aka ganmu mu shida.
 Tace "Kedai bari nima na dauka zai ganni."
 Haka sukai ta karatu har sai da aka tashi break sannan ta samu tasai biscuit na naira goma taci ta sha ruwan fanfo sannan ta ajiye naira goman.

  Ana tashi suka fito ita da Zarah suna hira, Zarah tace " Jalila kinsan jiya sai ga Ya Amud da takardar jamb!"
 Jalila ta kalleta cikin jin dadi tace "Haba? Kice hankalinki ya kwanta dama kina ta tsoron kar ace za'a miki aure."
 Tace " ke dai bari jiya ai baccin dadi nai, dan banaji zan iya rabuwa da Nasir dina, kuma kinga shi level 3 yake a Buk."
 Jalila ta tabe baki tace " su soyayya manya, da alama kema makarantarsu zaki nema.
 Tace "sai ma kin tambaya...."
 Dariya sukai, Zarah tace " ni nayi gida ke nasan sai kin jira ko?"
 Tace eh
Dayake gidansu Zarah ba nisa da makaranta nan ta kwana, Jalila taja gefe ta tsaya kamar yanda suka saba, minti 30 ne tsakanin lokacin tashinsu dasu Safeena, abinda zai baka mamaki shine su in har suka shirya zasu taho to fa ba ruwansu da jiranta sai dai ita bata isa a tashi ta tafi ba sai ta jirasu.

 Tana nan a tsaye taji ance "baki tafi ba?
 Juyowa tai ta kalli malamin nasu wanda yanzu su yan aji shida kusan dukansu matan nan in suka zauna gulmarsa sukeyi, tace " eh sir."
 Ya dan daga littafin dake hannunsa kamar zai kwada mata, da sauri ta runtse idanunta, jin shiru bai dake taba yasa ta bude idanunta a hankali, kallansa tai ya harde hannayensa kawai yana kallanta cikin mamaki tace "ba dukana zakai ba?"
 Yace "me kikamin da zam dakeki? Dazu da kikai laifi ban dakeki ba sai yanzu?"
 Cikin mamaki tace amma naga ka daga......
 Yace "sato ke bakya zuwa school da wuri sannan in an tashi kece karshe a tafiya, me hakan yake nufi?"
 A ranta tace "ni kaina wannan amsar nemanta nakeyi."
 A fili tace " hmmm, ai......"
 Wayar da aka mai ne ta katsesu ya dau waya tare da fara tafiya, alama ya mata da hannu akan ya wuce.
 Tace " Okay Sir."
Bin bayansa tai da kallo, sannan tai ajiyar zuciya, nan ta cigaba da tsayuwa har suka iso, 2017 toyota sienna ce tai parkin a kusa da ita, tura kofar motar tai ta shiga.

  Sannan ta rufe kofar, Safeena ce wacce kana kallanta kasan bata wuce sa'ar Jalilan ba tace " Ashe kuma yau da kafa kika taho."
 Jalila ta kalleta tace " Amma Safeena dazu tsakani da Allah baku ganni ba, sannan Malam Auwal ma bai ganni ba?"
 Safeena tace " Ta ina zamu ganki? Sannan in ma munganki menene damuwarmu? Uban wa ya hanaki yin sauri?"
 Jalila ta juyo ta kalleta tace "Uban wa ya hanani yin sauri? Kwata kwata fitowata daga bangarenku minti nawa ne har kuka taho?"
 Tace "wannan damuwarki ce, naga kina wani hararata ni na saki aikin? Sannan in kinsan bakyasan kiyi late me zai hana ki dinga tashi karfe hudu?"

 Jalila ranta ya baci ta juyo gaba dayanta tace " karfe hudu? Ku karfe nawa kuke tashi, ni daga na tashi sallar asuba me nakeyi? Bangarenku nake shigowa sai na gama muku komai har abinci sannan nake tafiya na shirya, sannan hakan ma ba birgewa nake ba har zakice indinga tashi karfe hudu?"

 Sultan kanin Safeena ne ya zare earphone din dake kunnensa yace " will you please keep quiet, duk kun cika mana kunne da wani musunku."
 Ya maida earphone dinsa, tare da kwantar da kansa kan kujera, Safeena tai kwafa tace " in munje gida kya maimaitawa Mumy na abinda kika fada a motar nan."

 Jalila a ranta tace " yauma a kwai wani sabon shan wahalar kenan, ai wahala bata kisa."
 Suna isa gida motar Dadynsu Safeena na parking, Safeena ta tashi kanwarta Yasmeen dake barci, tana ganin Dadynta ta ruga da gudu ta gunsa.
 Safeena ma tai gunsa tana murmushi, daga Yasmin yai yana cewa "Baby Yasmin an dawo?"
 Sultan ne ya karaso yace " sannu da zuwa Dady."
 Kallansa yai yana murmushi, Safeena kusa hannayenta ta zargo cikin nashi tare da cewa " Dady kace da safe zaka dawo."
 Yace " Naso dawowa da safe sai dai akwai wani meeting da nadan yi ne da suppliers dinmu.
 Karasa maganar yai yana kallan Jalila wacce kullum take jiya iyau, irin yar kibar nan ko dan murmurewar nan batayi, Jalila tace " Dady sannu da zuwa."

 Yace "Jalila an dawo?"
 Ya fada tare da juya kai zuwa gun Safeena wacce ke harar ta, yace " muje ko?"
 Nan suka nufi ciki Yasmin ma hannunsa ita kuma Safeena ta rikeshi.

 Murmushinnn takaici tai tace " happy family,  wazai kalleni yace mahaifinane?"
 Wucewa tai can cikin gida inda aka dan musu dakinsu daya da bandaki a can karshen gidan aka katangesu kamar masu aikin gidan........



 *************

   A hankali ta tura kofar d’akin bayan ya amsa sallarmarta, zama tai daga gefen gadon inda yake a kwance, kallanta yai sannan ya fara kokarin mikewa zaune, a hankali cikin sanyin muryarta tace “ Hassan bazakai breakfast da mu bane?”
 Yace “Ummy banajin yunwa.”
 Idanunta ne suka canja yanayi cikin tsananin tausayama dan nata tace “ Hassan sai yaushe ne zakai yaki da wannan matsalar dake damunka? Mun kaika duk wani asibiti da ake ji dashi a duniya amma ba wani ci gaba, dole ance kaine zakai yaki da wannan matsalar da kanka ba wani bane zai maka.”

 Kallansa tai cikin tsananin tausayawa tace “ Hassan ka tausayamin ko dan halin da nake ciki.”
 Kallanta yai yace “ Sau nawa zan ce miki ki cireni aranki Ummy? Dazu da safe nagama nazari ina tunanin abu biyu ko dai na bar kasar nan na koma egypt da zama ko kuma na bar gidan nan, ina tunanin wannan shine abinda ya cancanta na muku dake da Abba.”

  Kallansa kawai takeyi cikin mamaki tace “ Kana tunanin in kabar kusa damu hankalinmu zai kwamta ne ko me?”
 Kafafunsa ya sauko ya saukesu a kasa yace “ To ya kuke so nai? “
 Tace “ ka zo muje gun likita ya sanar dakai hanyar da zakabi danyin yaki da matsalarka.”
 Yace “ Ummy please ki fita.”
  Mikewa tai dan tasan in bata fita bama ba wani abu dazai biyo baya, in har kaji yace mutum ya fita to tabbas karshen maganarsa tazo kenan, daga nan duk wani abu na duniya da zaka fada ko mai zafinsa bazai taba tanka wa ba.

 Tana fita ta rufo kofar sannan ta sauka kasa, mai gidanta ta kalla jiki a sanyaye, yana ganin yanda tai yasan ba’a dace ba, kansa ga saukar kan dinning din sannan ya dago ya kalli yaransa biyu dababba mai bin Hassan sai kuma mai binsa mace, duk yaransu ukun sun girma, dan karamar mace wato Ameera a Ss2 take.
 Sagir yana ganin yanda sukai duk jiki a sanyaye yai saurin mikewa sannan ya jawo Ummy ya zaunar da ita kan kujera yace “ Ummy kinsan jiya naje gidan Auty Nana?”
 Ta kalleshi tace “Da yaushe?”
Yace “  bayan mun tashi a makaranta, Aina tace ai zata zo mana hutu karshen satin nan.””
 Ameera da sauri tace “Ya Sagir da gaske?”
 Abba yai murmushi yace “Auta da alama kawa ta kusa zuwa.”

  Dukansu ne sukai murmushin.

  Suna cikin cin abinci ya fito rike da makulin mota, ko kallan inda suke baiyi ba yai waje, sam basu kula da wucewarsa ba dan falan babba ne sannan dining area din na bangaren kitchen.
 Mota kawai ya fada yai waje............


 *Wattpad Ayushermohd* ( _please vote and Comment_😍)
 #Oneluv
 🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *AyusherMohd*

           *No 2*

  Gudu yai ta shararawa a mota sai dayaga har ya fita daga cikin gari sannan yaja motar ya tsaya sannan ya gangara gefen titi ya kashe motar, gani nai ya fito daga mazaunin driver ya koma baya ya kwanta tare da lumshe idanunsa.

 Bai dade da fara bacci ba yai wani irin zabura, a tsorace ya farka jikinsa ya fara karkarwa, jiyai numfashinsa na mai wahalar ja, jijiyoyin wuyansa ne suka firfito kamar wanda aka rikema hancinsa da bakinsa, zufa ce ta shiga keto masa da kyar ya jawo numfashi sannan ya mike ya zauna tare da hade kafafunsa, nan da nan idanunwansa suka canza.

  Wayarsa ce datai kara tasa ya dawo hankalinsa, kallan wayar yai sunan mahaifinsa ne a jiki, idanunsa ya runtse yana takaicin wannan rayuwar tasa, shi kadai ya hana iyalan gidansu samun farin cikin rayuwa.

 Lalai yana tunanin dolene ya bar kasar nan yaje inda ba wanda ya sanshi in ma rayuwar tasa a iya nan ta tsaya to shikam zai iya cewa Alhamdulila.
 Bai dau wayar ba har sai da ta katse.

  Fitowa yai daga motar ya hau samanta yana kallan bishiyoyi da sararin samaniya.

  Ya dade a haka sosai yana tunani kafin ya sauko ya
 

 ••••••••••
A bangaren Jalila kuwa tana shiga ta tadda mahaifiyarta a zaune tana hada mafici, Goggo tana ganinta tace Jalila an dawo?

   Jalila ta shigo fuska a hade tace “Goggo yunwa.”
 Goggo tace “Yi maza ki cire kaya kici abinci kafin a kiraki daga cikin gida, ni kaina a zaune kawai nake anan amma hankalina na kanki.”

 Kayanta ta cire ta zura doguwar riga ta mikoma Goggo naira Goma sannan ta jawo kwanan abincin ta fara ci, Goggo tausayinta ne ya kamata dan dama tasan bazata taba kashe ashirin din nan ba, inda sabo ta saba wahala da rike yunwa.

 Batai nisa da fara cin abincin ba Safeena ta shigo bako sallama tace “Ke kizo inji Mumy”
 Bata kula taba sai cigaba da cin abincinta da tai, Safeena tace “ Malama ba magana nake miki ba?”
 Jalila tace “Malama taje koyo sallama.”
 Safeena tai kwafa tace “ Mumyn kike fadama haka?”
 Jalila ta tsame hannunta dan duk ma abincin ya fita akanta ta mike ta wuce ta gabanta, Safeena ta juya a kule tai hanyar cikin gida.

  Jalila ta tura kofar a hankali, Dady ta gani zaune da Yasmin a falo, suna kallo suna shan ice cream, sallamarta ya amsa yana kallanta, motsin Mumy da yaji ne yasa ya dauke idanunsa daga kanta.
 Mumy tana gaba Safeena na bayanta, bata kalli inda Jalila take ba sai zama datai kusa da Dady tare da kwantar da kanta akan kafadarda tace “ Abban Yasmeen kafadata duk ciwo take min.”
 Kallan ta yai tare da nuna tsantsar kulawa yace “ lafiya? Ko muje asibiti? Garin ya ya? Faduwa kikai?”

 Kallan Jalila tai hakan yasa ya fahimci mai take nufi, mikewa naga yayi cikin mamaki naga ya yi ma Jalila alama da hannu, takawa tai zuwa inda yake tana neman bada hakuri, wani wawan mari naga an sakar mata wanda ni kam tsananin mamaki sai da yasa na yarda pen dina, ya dora da cewa “ menene aikinki a gidan nan?”
 Idanunta ne suka fara zubar da kwalla dan tabbas taji marin har ranta tace “ duk wani aiki da akeyi a cikin gida.” Ta fada cikin kuka
 Yace “ akan me tunda kika dawo baki shigo kin fara aikinki ba har dai da kikasa ta yin aikin wahala?
 Da sauri tace “ Kiyi hakuri Mumy.”

 Mumy ta mike tare da kallansa tace “” Abban Yasmeen abin ai bai kai da duka ba, in ka mata fada ma ai ya isa.”
 Ya kalli Jalila a zafafe yace “ kece kikace kin daukema Mahaifiyarki aiki ko ba kece ba?”
 Tace “nice”
 Yace “ da haka kike tunanin zaku zauna a gidan da yake nata kuci kusha da kudin ta ba tare da kunyi aikin biya ba?”
 Hawayenta ta share tace “ kayi hakuri.”
 Mumy ta dan canza fuska tace “ sai yaushe ne zaka daina cewa gidana da kudina? Abu na ba naka bane?”
Yace “ na sani, sai dai agun wannan yarinyar da uwarta dole ne adinga tuna musu.”
Tace ka bari please matarkace dai
Kallan Jalila yai yace “Mata? Matar da bance inasoba aka likamin? Ko kuwa yar da batajin magana?”
 Jalila kam hawaye kawai takeyi, Yasmeen ce tasa kuka da sauri suka juya kanta.
  Dady yace “Auta menene?”
Ice cream dinta ta nuna wanda ya fadi a kasa, Jalila da sauri ta nufi kitchen ba ta dade ba ta dawo da kayan gyara gun, Nan ta gyara gun tas sannan tace “Yasmeen kin sanma yan kasa?”
 Tace” ni kad’an zan san musu”
 Tace “ ki bar musu tunda sun shanye wannan nan gaba karki basu kinji?”
 Kai ta daga tare da yin murmushi.

     Jalila wacce tana gyara gun Mumy da Dady suka shiga ciki ta goge hawayen da suka bata mata fuska sannan ta kalli Safeena wacce ke bakin kofa tana murmushin mugunta.
 Bata bi ta kanta ba tai kitchen, Safeena ce ta biyota tace “Mumy tace kiyi fried cus cus da miyar vegetables”
 Tace to
 Nan ta shiga aiki tana yi hawaye na zubo mata, a duk sanda aka cima Mahaifiyarta mutunci wuni take tana kuka, sai dai abin bakin cikin ba kowa bane mai cima mahaifiyar tata mutunci ba sai Mahaifinta da zuri’ar sa dan kuwa zuri’arsa zatace, a iya sanin rayuwarta bata taba ganin mahaifinta ya shiga bangaren Mahaifiyarta ba balle mu’amala ta aure ta hadasu ba, in ta tuno irin kuncin da mahaifiyarta ta shiga a dalilin rashin so ba shakka sai taji nata ba mai zafi bane, gwara ita mahaifinta ne.

 A haka har ta gama girkin, tana girkin tana gyara gidan inda ya baci, sai da ta juye musu nasu sannan ta dauko tasu samirar ta dan zuba kamar yanda aka kiyaste mata sannan ta gyara kitchen din.

 Daukar na Mamar Mumy tai ta nufi sama inda take, Sallama tai sannan ta tura kofar bayan an bata izini, a zaune take sanye da glass tana karanta wata takarda, kana shiga dakin wani sanyin dadi da kamshi ne zai ratsaka, inda ake ajiye mata abinci ta ajiye sannan ta tsugunna tace “Inna barka da gida.”
 Bata tankata ba, inda sabo ta saba mikewa tai sannan ta nufi hanyar waje.
 Muryar inna taji cikin tsantsar isarta tace “ na dauka jiya ma sanar dake in kin dawo yau daga makaranta zaki kwashi wankina ki sauka dashi kasa?
 Da sauri ta juyo tace “ yahkuri Inna wlh na manta.”
 Bata kara tanka mata ba nan ta nufi inda kayan suke ta hadasu ta fito dasu.

  Sauko wa tai tana kallan su Safeena da Sultan rike da littafan karatu da shigar uniform na islamiya zasu tafi.

 Abinda take tsananin buri kenan a rayuwarta taga an sata a islamiyya.

  Haka ta sauko ta kai wankin Inna gun Auwal dan ya kai mata sannan ta mikama Goggo abincinsu ta dawo dan gyara dakin Safeena da Sultan, tana gamawa ta koma kitchen dan daura abincin dare.

  Haka rayuwar Jalila take, daga aiki sai aiki, makarantar boko kadai aka barta sai dare bayan magrib take samun zama da mahaifiyarta.

**************

  _Washe gari_
 Yau kam tayi sa’a ba’a sata yin breakfast mai wuya ba, ta samu ta biyosu Safeena, a mota dama Yasmeen ce kawai mai magana ta kula Safeena ta kula Jalila dan ita yarinya ba ruwanta.
 Shi kuwa Sultan kamar baya cikin motar haka yake, earphone kawai yake sawa a kunnensa ya kwantar da kansa akan kujera har su isa.

  Suna zaune ita da Zarah, duk wata hira da zata fito daga bakin Zarah na Saurayinta Nasir ne, Jalila ta juyo tace “Nikam Zarah anya Nasir na sanki kamar yanda kike sansa?”
 Fuska ta canza tace “ wacce irin tambaya ce wannan?”
 Jalila xatai magana Uncle Sagir ya shigo, da sauri suka mike suka gaida shi.
 Idanunsa akanta ya fara sauka, a hankali wani murmushi ya banyana a fuskarsa.
 Sannan ya basu damar zama.
 “Mathematics” abinda ya rubuta kenan a blackboard sannan ya ruba “Quadratics Equation”
 Sannan ya juyo da hankalinsa kan d’alibai, Jalila ta dago suka hada ido da sauri ta sunkuyar da kanta tana wata da yatsun hannunta, haka ya shiga yi musu examples.

Jefi jefi yana sauke idanunsa akanta haka itama, har ya gama period dinsa sannan ya ce a hada masa assignment din da ya bada.
 Nan monitor ta mike ta hada, kallan Jalila yai yace “Habiba inasan ganinki biyoni da books din nan.”
 Kallansa tai sannan tai saurin cewa “Yes Sir”
 Tare da fitowa ta amshi littatafan.

  Yana gaba tana dan binsa a baya sai jitaj yace “ yau saboda in kama wata nazo da wuri sai tai sa’a bata makara ba.”
 Tace “wata? Ni?”
 Ta fada tana kallansa,bai juyo ba sannan bai daina tafiya ba yace “ da yau na kamata lalai da shikenan na daina amsa ko gaisuwarta.”
 Tace “ Na daina zuwa late insha Allah, sannan jiya ma tsautsayine.”
 Yace “ a tare zamu gama, kuna gama exams ni ma ina kammala aikina.”
 Murmushi tai batace komai ba.
 Yace “ me kikeyi tsayawa yi in an tashi daga school kullum?”
 Tace “ Kanena nake jira a tashesu sannan a daukosu sai su biyo ta nan mu tafi.”
 Yace “Kannenki?”
 Ita kanta taji abin ban barakwai sai dai ko ma menene ai kannenta ne, tace “eh”

Juyowa yai yace “ a wani school suke?”
Tace “Crescent International School”
 Kallan mamaki ya mata sai dai bai kara cewa komai ba sai juyawa dayai, yana tafiya yana mamaki, kannenta na Crescent ita kuma tana makarantar Government?

 Sai data ajiye mai books din sannan ta fito, tana tafe tana mamakin tambayoyin da Uncle Sagir ya mata.

  Ana tashi sun fito ita da Zarah, Zarah na ce mata ni dazu me kike nufi? Ban samu munyi magana ba........
 Nasir da ta gani a tsaye ne yasa ta dakama Jalila duka a kafada tace “ Jalila kinga!”
 Jalila ta juya ta kalli yaran dake tsaye daga gefensu tace “ yayanki ne?”
 Yace “My Nasir ne, da alama ya gaji da missing dina ne.”
 Jalila ta kalli Nasir din sannan ta kalli Zarah wata dariya ta kirkiro wanda kana gani kasan ta dole ce tace “ Ohh shine Ur Nasir?”
 Zarah ta hade rai tace “Meye hakan?”
 Jalila ta girgiza kai tace “Kije naga ya kura miki ido kamar zai daukeki.”
 Murmushi tai sannan tace “ Kawata kalleni fuskata batai komai ba?”
 Kamar zatai kuka ta daga kai tace “Eh”
 Zarah ta fara tafiya cikin canza salo, Jalila kallansu kawai take cikin mamaki, wannan ai da alama makaranta ya samu da wuri amma ta tabbatar baiba Zarah shekara biyu bama, dan ma tace a level 3 yake ne amma lalai da tace sa’ansu ne,lalai ansha yarinta shiyasa.

  Tab itakam gaskiya bataji zata iya soyaya da sa’anta, ita tafisan saurayi kamar Uncle Sagir, da sauri ta girgiza kai tace “What am I thinking? Ahhhhh lalai banida kai.”


#OneLuv💕
 🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *AyusherMohd*

           *No 3*

 Tana kallansu suna tafe suna rangaji irin na masoya, murmushi tai sannan ta koma gefe ta tsaya.
 A hankali duk aka yoye tana tsaye, ganin rana ta fara dishashewa ne yasa ta daga kai ta kalli sama, hadari taga yana haduwa abinka da damina kan kace me gari yayi daki, da sauri ta juya ciki ganin iska mai kura tana tasowa.
 Ji tai ta bugi abu, da sauri ta dago ta kalleshi.
 Idanunsa na kanta, ta matsa baya da sauri cikin jin kunya, sannan tace "Sorry Sir"
 Yace "anya yau sorry din nan zai karbu kuwa agurina? Da alama sai na hukunta mai laifin nan."
 Kallansa tai sannan tace " Wlh ban ku........"
 Yanda yake kallanta ne yasa ta kasa karasa maganar dake bakinta sannan tai saurin juyawa, dan ji take gabanta na faduwa.
 Murmushi yai sannan yace "muje in kaiki gida."
 Tace " Naam"
 Yace "Baki ji bane ko bakya so ne? Hadari ne a garin in aka fara ruwa kina tunanin yanda zakiyi kije gida? Ko su Kannen naki ne bakyasan ki tafi ki barsu?"

 Shiru tai tana dan nazari kafin tace " Nagode da kulawa Uncle Sagir sai dai in na tafi ba tare dasu ba fada za'amin."
 Kamar zai sake magana sai kuma taga ya juya ya koma ciki, tana tsaye ya fito da lema ya mika mata bai jira tace komai ba ya hau mota yai gaba.

  Da kallo ta bishi yau da mota yazo? Hmm ita kadai tasan cin zarafin da za'ama mahaifiyarta in har ta tafi.
 Tana tsaye aka fara yayyafi da sauri ta bude lemarta ta shiga, kan kace me ruwa ya tsuge, ruwa ake mai karfin gaske wanda tana cikin lemar ma amma ba tsira tai ba, komawa gefe tai ta rakube.
 Kamar motar zata tsaya sai taga ta yi gaba da gudu, cikin tsananin tsoro ta kalli motar tare da kwalla kara da karfi tace "Safeen ina nan fa......"
 A cikin motar kuwa wanda Safeena tacema Malam Auwal da alama ta tafi ganin hadari, wanda akasan ranta ta tabbatar bata tafi ba, tsabar mugunta ce.
  Haka ta rakube dan tsoro takeji ta koma cikin makarantar ita kadai, ganin a tsayen ma tsoro ya kamata kawai ta fara tafiya tana tafe tana kuka mai sauti, sai dai kasancewar karar ruwa bai sa tasan da karfi take kukan ba.

  Yana zaune a cikin motarsa daga gefen titi wanda shi dama yafisan gurin shiru inda ba mutane, shiyasa mafi akasari zaka sameshi ne a zaune a cikin motarsa ya zuge glass kawai ya kwanta.

  Jikin motar ta tsaya da taga ruwan ya dan yi sauki duk jikinta ya jike jagaf, ga lemarma sai lankwashewa takeyi saboda iska.

  Juyawa tai ta kalli glass din motar, da yake motar mai tints ce sai ta shiga kallan kanta tana kara wani kukan,sam tunaninta bai kawo mata da wani a cikin motar ba.

  Kallanta kawai yakeyi sai sharar kuka take wiwi.
 Komawa yai ya maida kansa ya rufe idanunsa kamar mai bacci.
 Kara juyowa yai ya kalleta, kuka take sosai, kamar dama neman kukan takeyi, haushi duk ya isheshi kamar a kansa take kukan, kofar mazauninsa ya bude, a tsorace ta kalli motar, kallansa tai a tsorace, sannan ta kalli motar .
 Kallan tsoro tamai tace "Hmm hmm."
 Hannunsa ya dago ya mata alama da ta matsa daga gun, tace "Ban gane me kace ba."
 Alama ya sake mata da hannunsa akan tai gaba, sannan ya maida kofarsa ya rufe, da harara tabi kofar motar sannan tace " wannan kuma wani kwarantancen dan duniyar ne? Maganarce yafi karfin yimin ko kuwa tsabar rashin mutumci ne?"

  Harara ta sake yi sannan ta juya, kallan motar ta sakeyi sannan tace "irin motar jiya"
 Taja tsaki tace " da alama duk masu hawa irin motar nan basuda mutunci."
 Sam ta manta da kukan da takeyi saboda masifa, tana tafe yayafi na digar mata tana yan mitocinta, sai da ta gama gajiya ligif sannan ta isa gida.

 Goggo kuwa duk ta kasa zama saboda tsoro ganin yanda ake ruwa ga har yanzu bata dawo ba.
 Tana shiga Goggo ta kalleta cikin tsananin tausayawa.
 Jalila fadawa tai jikinta duk da jikarta ta sa kuka, idanun Goggo suka ciciko sai kanta kawai da take shafawa.
 Jalila ta dago tana kuka tace ""Goggo Allah nasan da sanin Safeena, ai tasan ban taba tahowa ba."
 Goggo tace "Kiyi hakuri"
 Jalila tace "Goggo sai yaushe ne zaki daina cewa inyi hakuri? Gaba daya rayuwarmu ni dake a hakuri ta kare, nikam ina takaicin cewa ma Dadyne mahaifi......."
 Marin da Goggo ta mata ne yasata yin shiru, kallan Goggo tai kuncinta a rike,Goggo ta kalli hannunta cikin dana sani sannan tace " taya zaki dinga kushe abinda Allah ya hada?"
 Jalila tace "kiyi hakuri Goggo bazan kara ba"
 Hannunta ta kamo tace " na sani, na sani sosai abinda ke ranki Jalila sai dai bayanda zamuyi da hukuncin Allah, sannan komai zaiyi ko kowa zai zageshi to lalai banda ke, domin shine silar zuwanki duniya."

 Tace "Na daina Goggo kiyi hakuri."
 Goggo tai murmushi tace " yi maza ki cire kayanki."
 Mikewa tai ta shiga dan dakinsu.

Tana cire kaya tai sallah sannan ta mike tace "Goggo bari naje"
 Goggo tace abinci fa? Naga da safe ma a tsatsaye kikaci, shiyasa kullum gakinan kamar a hure.
 Tace " Goggo in na dawo naci" tace ban yarda ba sai dai ki tafi dashi can kici, ina zaki jira sai wajen magrib kici abinci?
 Jalila tai murmushi sannan tace " to in na gama ma rana zam deba inci a namu."
 Goggo tace "kin tabbatar?"
 Tace eh karki damu Goggo na

 Tana isa ta tadda Safeena a falo tana kallo, wata banzar harara ta maka mata sannan tace " da kuka taho kuka barni sai kuma gashi mai rai da lafiya yayo gida da kansa."
 Safeena tace " au da gaske kina can dama? Ni danaga ana zabga ruwa sai naga ina mai hankali zai tsaya a cikin ruwan nan?"
 Jalila tace " mai hankali kikace ai ni kuwa ina na ganshi?"
 Ta karasa maganar tana harararta, jitai ance " Uban wa ya baki damar cimata mutunci?"
 Gabanta ne yai wani irin faduwa, duk gidan ba wanda take tsananin tsoron ya mata fada irin Inna, a tsorace ta kalleta idanunta sun firfito, bakinta ne ya shiga rawa tace "In nn nna......"
 Kallanta tai sannan ta kalli Safeena tace " ke kuma Jalila matsayinku daya da zaki dinga zama tana fada miki kalamai irin haka?"
 Jalila ta hadiyi wani miyau me daci tace " in na bahaka bane......."
 "Dake nake magana?"
 Jalila gabanta sai faduwa yakeyi.
 Sultan ne ya fito daga kitchen rike da jarkar ruwa na faro yace " Inna ita Safeenar itace da laifi bai kamata ku dinga yanke hukunci ba tare da bincike ba."

 Kallansa tai tace " Sultan shiga daki"
 Baice komai ba ya wuce ciki, Jalila kuwa kamar wacce aka tsunduma a wani ruwan haka takeji, muryar Dady ne ya ratsa falon wanda maganganu Inna ne suka sa shi fitowa, da sauri yace "Hajiya ki mata afuwa ni zan hukuntata da kaina."
 Kallansa tai a wulakance tace " kai har wani hukunci zaka iya? Ka saisaita yarinyarka in ba haka ba daga ita har uwarta zasu bar gidan nan, karka kuskura ka manta gida da dukiyar wanene kake mora daga kai har su."
 Mumy ce ta rike hannunta tace " Kiyi hakuri ki bari dan Allah."
 Ta fada tare da jan hannun ta zuwa dakinta.
 Suna shiga tace "Inna sai yaushene zaki daina disga Abakar cikin yaransa? Karfa ki manta 'ya'yansa sunanan kuma suna jin zafin abin."
 Kallanta tai tace " ke meyasa bakida hankaline? Kin nace sai kin aureshi dake da mahaifinki, bakya tunanin wannan cin mutuncin da nakemai shine dalilin da yasa yake nuna miki kulawa haka?"

  Tace " Wlh Inna ke kike ganin haka Abbakar na sona kamar yanda nake sansa, dan Allah ki daina wulakantashi."
 Ta karasa maganar cikin lalashi.

A falo kuwa Dady a zuciye ya sa hannu ya fizgo Jalila ya kaita kitchen, cikin fada yace " sai yaushe ne zakiyi hankali kisan darajarsu Safeenan kikeci ke da uwarki?"
 Kallansa tai cikin rawar baki tace " Dady itace........"
Cikin tsawa yace " so kike in fasa miki baki? Ko me ta miki bazaki hakura ba? Shashashar banza to wlh ki bala'in shiga hankalinki in har kinaso mahaifiyarki dake ku zauna a gidan nan."
 Yana gama magana yai falo, yana shigowa Safeena taje da gudu da rungumeshi.



**************

   Yana shigowa cikin gidan ya tadda mahaifinsa a zaune a falo, karasawa yai ya gaidashi sannan ya fara kokarin mikewa.

 Mahaifinsa yace "Hassan!"
 Komawa yai ya zauna tare da kallansa, Abba yai ajiyar zuciya sannan yace " Baka manta badai karshen satin nan zamu koma asibiti ko?"
 Hassan ya kalleshi yace "Abba please ka hakura
 Abba cikin kulawa yace " Ka taba ganin inda uba ya hakura da dansa? Karka damu insha Allah da yardar Allah wannan matsala taka zata warware sannan zaka samu sauki cikin yardar Allah."
 Kallan mahaifinsa kawai yake shidai sun kasa fahimtarsa, mikewa yai baice komai ba zaiyi gaba.
 Kaninsa ne ya dafashi yace " Yaya kace Ameen mana ko hankalin Abban zai kwanta?"
 Ummy ya kalla wacce ke tsaye ita da Ameerah yai shiru sannan a hankali yadan motsa baki yace Ameeen.
 Murmushi sukai dukansu m, Sagir ya dafashi yace " Ko kai fa Yaya."
 Hannunsa yasa ya ture nashi daga kafadarsa yai wuce, Ummy tabi bayansa da kallo sannan ta kalli Ameera.
 Kai Ameera ta daga sannan tai kitchen.
 Faten dankali wanda Ummy ta masa ta zubo a plate sannan ta dau spoon ta fito, sama ta hau sannan ta shiga dakinsa.
 Yana zaune a kasa kan carpet ta shiga.
 Gabansa ta ajiye abincin sannan ta ce "Yaya abinci."
 Kallanta yai yace " BAna......"
 Tace " Na sani yaya baka jin yunwa dama ko da yaushe zancen kenan, sai dai Yaya ka ci ko dan Ummy ta samu sukuni a ranta."
  Yace "Naji zanci, ke kuma fita."
 Ta mike tace " to"
 Waje tai sannan ta turomai kofar.


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *AyusherMohd*

_Gaisuwa mai yawa tare da fatan alkairi a koda yaushe gareki Aunty na ta kaina.....Aunty Goggo Allah ya kareki ya ja da ranki😍 much luv Sister_

           *No 4*


   Da kyar ya tura abincin sannan ya mike ya shiga bandaki, wanka yai tare da dauro alwala.
 Jalabiya ya zura ya tada sallah, ya dade sosai akan sallayar yana mika rokonsa gurin Allah sannan ya kwanta a kasa, a takure ya kwanta , sam baisan sanda bacci yai gaba dashi ba.
 Ummy ce ta leko ta ganshi yana bacci, kusa dashi taje ta zauna tana kallansa cikin tsantsar so da kulawa da kuma tausayi, jan numfashi tai sannan ta mike ta dau tiren abincin da yaci tai waje.

  Gab da magrib yana bacci yaji kamar ana shakemai wuya, wani irin mumunan mafarki yakeyi wanda ya shiga sandarewa yana kankake jikinsa, idanunsa a runtse sai wani irin zufa da yake kwaranya daga jikinsa, numfashinsa ne ya shiga hawa da sauka, shure shure ya shiga yi saboda tsananin azabar da yake fuskanta.

  Har zai shiga dakinsa yaji alamar motsin Hassan, da sauri Sagir ya tura kofar, ganin Hassan a kankame yasa yai saurin shiga dakin, tabashi yai yana cewa Hassan! Yaya!
  A firgice ya bude idanunsa tare da jan wani irin numfashi, Sagir ya dagashi zaune yace "in kawo ma ruwa?"

  Hassan ya daga kai, da sauri ya mike ya dauko mai ruwa,  amsa yai ya lafa bakinsa, sai dayasha sosai sannan ya kalli Sagir ya mikamai jarkar.
 Sagir ya amsa sannan yace "akwai abinda kake bukata?"
 Kai ya girgiza alamar a'a.
 Cikin tausayawa Sagir ya kalleshi sannan ya mike yace "Yaya kazo dan Allah ko waje ka fita kaji iskar duniya."
 Bai kalleshi ba haka kuma bashi da niyyar amsamai, Sagir ganin haka yasa ya fita tare da ja mai kofar.

  Sagir yabi bayan kofar da kallo sannan yace "Allah ya yaye maka ya baka lafiya."

  Dakinsa Sagir ya shiga kallan kayan da ya cire dazu yai sannan yai murmushi ko a ya ta koma gida? Cikin nuna halin damuwa yace " ba ta dai jike ba ko?"
 Kai ya girgiza yace " ya za'ai ta jike ga lemar da ya bata sannan ya tabbatar tace ai zuwa za'ai a daukesu."
 Murmushi yai sannan ya dau wayarsa dayazo dayka ya sauka kasa.

  **************

    Jalila ce zaune tanacin abincin dare ita da Goggo, tunanin abinda ya faru dazu takeyi.
 Jitai Goggo ta tabata tace " Jalila wani abun ya faru ne dazu?"
 Jalila ta kalleta tace "Bakomai kawai dai ni akwai abinda na dade ina san tambayarki ne Goggo."

 Goggo ta kalleta tana neman karin bayani, Jalila tace " Bawai da wani abin bafa nake san ji Goggo, kawai dai tambaya ce."
 Goggo tace "Ina jinki."
Jalila tace " Ni Goggo baki da kowa ne sai Dady?"
 Murmushi tai tace"Ban gane banida kowa ba sai shi? Kin tabaganin wanda bashida kowa a duniya?"
 Jalila tace " To ni Goggo na kasa fahimtarki ne sam, na rasa takamaimai ke mukeyi a cikin gidan nan."
 Goggo ta tsame hannunta sannan tace " Lalai Jalila, muhallin Mahaifin naki kike fadama haka?"
 "Muhalli? Ai kowa yasan gidan Mumy ne ba nashi ba, sannan ni waye ma yasan ni 'yarsa  ce, ko suna a makaranta ni ansa nayi amfani da Auwal wato kakan Dady, dan kawai karma asan ni yar sace."

 Goggo tace" ya isa to, ke dai ba ruwanki da wannan, mahaifinki da mahaifinki ne, sannan banaji yana da laifi a harkar nan, laifin na iyayenmu ne."
 Jalila tace "Goggo dama tun can baya sanki"
 Harararta tai tace"Wai yau me kikesan ji ne haka?"
 Tace"ni dan Allah ki fadamin tarihinki Goggo."

 Hannunta ta wanke a robar ruwan da Jalila ta kawo ta dan matsa kadan tace " sai randa hankali yazo miki."
 Jalila ta dan turo baki tace "ni yau meyasa ake tacemin banda hankali?"
 Goggo tace " Ce miki akai mara hankali a cikin gida?"
 Tace "Safeena ce."
 Goggo tace "Fada kukai kenan?"
 Jalila ta hade rai tace " ni ai....."
 Goggo tace "sai yaushe ne zaki dinga hakuri Jalila? Na dauka na rokeki akan kai zuciya nesa?"
 Jalila ta kalleta tace "Yanzu duk hakurin da nakeyi bakya gani? Wlh a yanda nake ji da wata rana sai na fasama 'yar nan baki, kawai hakuri nake sawa a zuciyata."

 Goggo tausayinta ya kamata tace"kiyi hakuri, duk tsanani yana tare da sauki, shiyasa a koda yaushe nake miki fatan miji na gari, wanda ke sanki ina tunanin hakan ne kadai zai kawo salama a zuciyata da taki."
 Jalila tace "ni duk wanda zan aura sai dai in zai iya rikemin ke, dan bazan iya aure na barki ba."
 Dariya Goggo tai tace "Lalai yarinta na damunki Jalila."
 Haka sukai ta hira har suka kwanta.............

  *********
 

  Washegari.........

  Yau tana gama aiki ta shirya ta fito dan jiransu, dadi takeji yau ta rigasu shiryawa, yanda taga Dady ya fito da sauri ko gaisuwarta bai tsaya amsawa ba tasan lalai da matsala, mota taga ya shiga da sauri, sai ga Mumy ta taho da gudu tare da shiga gefensa itama, nan taga sun fita a guje.
 Baki ta tabe tace "ko ina zasu haka oho"

  Su Safeena ne suka fito,Yasmeen na ganinta ta isa gunta da gudu tana nuna mata sabon school bag din da Dadynta ya siyo mata.
Jalila tace "inyee lalai tayi kyau."
 Tafada tana kallan wata yagwalgwalaliyar jakar dake bayanta.
 Mota suka shiga, Safeena ta kalli Sultan tace "Sultan kamar akwai matsala a company dinsu Dady ko?"
 Sultan ya kalleta yace" ina na sani, in so kike kiji me yasa baki tambayeshi ba da zai fita?"
 Haushi ne ya kamata tace " Wai kai meyasa mutum bai isa yai maganar mutunci dakai ba?"

  Tsaki tai sannan ta maida kanta kan Jalila cikin masifa tace "ke kuma uban me kike kallo?"
 Jalila tace "Ba ni na kar zomon ba Hajiya."

 Safeena ta kara kuluwa, da saninta tasa kafa ta tako kafar Jalila, Jalila ta kalleta.
 Safeena tace " sry fa ban kula ba."
 Jalila ta kalli safarta wacce ta baci sannan ta kalli Safeena tace " mantawa nai ashe idanunki basa aiki."
 Ran Safeena ne ya baci tace "mene?"
 Jalila ta kalli window ganin sun kusa isa, me zata gani?
 Uncle Sagir ta gani yana parking din mashin dinsa, ga mamakinta murmushi ne ya bayyana a fuskarta, Safeena ce ta kalli inda take kallo nan idanunta suka sauka kan Sagir.
 Idanu ta kuramai, waye wannan?
 Batasan a fili ta fada ba, Jalila ta kalleta tace "Uncle dinmu ne na Math."
 Safeena ta kara kallanshi sannan tace "Driver tsaya anan mana ta sauka."
 Jalila ta kalleta ta tabe baki sannan ta sauka.
 Muryarta yaji tace "Good Morning Uncle."
 Juyowa yai ya kalleta, yanayin fuskarsa kadai zaka kalla kasan ganinta ya sashi farinciki.
 Jalila ta dan matsa gunsa kadan tace "Sir nayi laifi."
 Bai ce komai ba sai wani kallo da yake mata, gana kokarin b'oye abinda ke ransa, dan bai manta ita din dalibarsa bace.
 Ta fara wasa da hannunta sannan tace "Lemarka jiya ta samu matsala."
 Yace "ta samu matsala ko dai ba'a damu da ita ba an lalatata?"
 Da sauri tace " ba haka bane, Allah iska ce ta dinga bankareta....."

  Yanayin fuskarsa ne ya canza zuwa kulawa, yace "ba dai abinda ya sameki ko? Are u okay?"
 Ganin yanda ya damu da ita yasa taji ta kasa cewa komai, yanda take kallansa ne yai saurin juyawa ya kalli daliban dake ta shiga makarantar yace " Ki wuce cikin makaranta."maganar ya karasa tare da juyawa yana kallan mashin din.

  Jalila ta fara tafiya a hankali tana mamakin kulawar da yake nuna mata wanda ke kokarin sa zargin so a zuciyarta, anya kuwa? Karfa zuciyarta ta raya mata abinda ba haka ba, Uncle Sagir yafi karfinta, dan mata dayawa na sanshi, sannan da alama dan gidan wani ne duba da yanayin yanda yake zuwa wani sa'in a mota.
 Wata zuciyarce ta ce mata ina ruwan so da wannan?

 Juyowa tai bayan tayi tafiya mai nisa, ga mamakinta gani tai idanunsa na kanta, suna hada ido yai saurin juyawa, Jalila ta juya cikin yanayin jin kunya.


**********
 A company dinsu Dady kuwa suna isa sukaga mutane ancika a waje.
 Da sauri sukai parking Dady ya fito cikin tashin hankali, suna ganinshi sukayo kanshi.
Mumy na gefensa, cikin tsantsar tashin hankali yace " gaba daya kayanda muka adana sun lalace?"
 Cikin damuwa yace " Muje ka gani."
Store din da suke adana dukan kayan aikin da sukeyi ya bude.
 Store din acike yake da kayan ma'a dana na abinci.

 Gaba daya hankalin Dady ya tashi dan kana gani kasan lalai lalata musu akai.
 Juyowa yai yace " How can this happen? How......."


 Mumy ma hankalinta ya tashi ta kalli Dady tace "Yanzu ya zamuyi? Gashi zuwanka Abuja munyi signing da Al-Company zamu aika musu da kayan cikin satin nan."
 Wata zuface ta karyomai yace "Muje gida mu sanar ma Inna, sai muyi tunanin mafita, dolene mu san yanda zamuyi kafin nexweek."

  Hankali a tashe suka juya gida.
 Inna macece wacce tasan kan kasuwanci, dan company dinsu ya bunkasa ne harda tsananin iya kasuwancin ta, shiyasa mijinta yake girmama kalamanta sannan takeji da kanta itama.
 Har Allah ya mai rasuwa, ta dade tana juya company din da kanta duk kuwa da ganin Dadyna iya nasa kokarin a karkashinta,har sai dataga girma ya kamata tana bukatar Hutu sannan tabar Dady yakejan ragama.

 Inna wacce yanzu ne ta maida sunanta haka, dan da kowa Hajiya yake kiranta, yanzun ma Sultan ne ya sa mata hakan har kowa ya koma kiranta haka a gidan, amma daga ta fita sai dai kaji ana Hajiya.
 Tai shiru kafin tace "nawa ne a account dinmu?"
Yace "Hajiya mun kwashe rabin kudin mun sai kayan aiki, ba nakawo miki budget din ba?"
 Hannu tasa ta shafi fuskarta tace "Kudin bazasu kai musai wasu kayan ba kenan?"
 Kasa yai dakai yace "Gaba dayan mun gama shirya plan dinmu banaji ko kwata zai kai."
 Ta dade batace komai ba da alama nazari take kafin tace "Sai dai kenan mubi last option din da banaso."
 Yace "Loan?"
 Tace " dole zan duba a cikin mutanen Alhaji da nawa wanene na amana sai musan yanda zamuyi, either mu samu loan ko kuma yayi investing."

  Kai ya jinjina sannan yace "bari a kira board meeting sai a tattauna."
 Tace "No ka bari sai zuwa gobe in na samu wanda zai tallafa mana."
 Yace " To Hajiya."


 Nan ya mike ya fita, wani karamin diary ta d'auko ta shiga duba sunaye tana auna mutane.......


#Oneluv💕
[9/11, 9:43 PM] ‪+234 903 672 7766‬: 🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *AyusherMohd*

 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

 *No 5*


   Yau a staff room yai shiru yana tunanin yanda zaiyi, ya dade yana tunani dan baisan ma sanda wani staff yazo kusa dashi ba yace "Sagir mu mun wuce sai gobe in Allah ya kaimu."
 Kallanshi yai cikin mamaki sannan ya kalli agoggon dake jikin bango, lalai har an tashi da kusan minti goma ma.
 Yace "To Sai goben."
 Nan ya shiga hada kayansa shima, a tsaye ya ganta a inda ta saba tsayuwa, ya dade yana kallanta sannan ya karasa kusa da ita yace "Malamar jira."
 Kallansa tai sannan ta sunkuyar da kanta tana murmushi dama yanzu take tunanin bata ga fitarsa ba.
 Jitai yace mata "D'an zo."ya fada tare da fara tafiya,  cikin mamaki take binsa har suka shiga wani class.
 Zama yai a saman desk sannan ya mata alama data zauna daga kujerar dake gefensa kadan.
 Bata musa ba ta zauna, sai daya d'an yi shiru na wasu dakiku kafin taji yace " Jalila!"

 Yanda ya kira sunanta ne yasa taji wani abu yar wanda ya hanata amsawa sai kallansa datai, yana kallanta yace " labari zan baki."
 Nan ma batace komai ba sai kallansa data sake yi, murmushi yai sannan yace "akwai wani sokon abokina da ya taba ganin wata yarinya tun last year, ya taho shida kanwarsa zasuje gidan yayar mahaifiyarsu, sun tafe sai kanwar tasa tace "Yaya dan Allah mu tsaya musai maganin ciwon kai, tun dazu nake kai na kemin ciwo.
 Parking yai da saurin ganin chemist a tsallaken titi sannan ya fita.
 An miko mishi magani kenan zai amsa ta shigo da sauri, kallo d'aya zaka mata kasan hankalinta a tashe yake, tana zuwa tace " Dan Allah maganin ciwon kafa."
 Nurse din ne ya kalleta yace " Ciwon kafa wani iri?"
 Tace " ban sani ba kawai kafar Goggo ce ta kumbura." Tana hawaye take mai bayani.
 Wanda yazo siyar maganin ciwon kai sai duk tausayin yarinyar nan ya kamashi, zuciyarshi yaji ta shiga cikin matsananciyar damuwa na ganin yanda yarinyar nan take hawaye.
 Yace "Ku kaita asibiti mana."
 Bata ko kalleshi ba tace " Dan Allah nikam ka bani maganin da zai taimaka mata, banida kudi yanzu sai dari biyu, inya fi haka zan kawoma ko gobe ne."

  Tsananin tausayinta ya kara shigarsa kallan Nurse din yai sannan yamai alama daya hada mata maganin nan masu kyau, bayan ya bata ta mai godiya ta fita.
 Kallan Uncle take idanunta sun ciciko da hawaye, ba shakka daga baya tayi ta mamakin arhar maganin kenan Uncle siya mata yai? Dan ko bai fada ba tasan da kanshi yake, tunda dai na farko itace yarinyar, to in har abokinsa ne yaza'ai yabashi labari haka dala dala?
 Sagir yace " tundaga wannan rana Abokin nan nawa ya shiga wani yanayi akan yarinyar nan, jefi jefi yanabi ta layin nan ko zai ganta, sai dai cikin rashin sa'a bai sake ganinta ba har sai da akai assigning dinsa zuwa inda zaiyi bautar kasar sa, duk yanda yaso ya daure akan san yarinyar nan da damuwa da ita ya kasa, shine nake so ki ban shawara me abokin nan nawa ya kamata yai? Yana tsoron kar ya bari ya huce....."

  Wata irin kunyarsa ce ta kamata, kanta na kasa tana wasa da hannunta tana murmushi.
 Yace "Jalila, bakice komai ba? Ko ba kya ganin yarinyar nan zata soshi?"
 D'agowa tai cikin jin kunya tace " Ta ya zatai ta......."
 Yanda yake kallanta ne yasa tai saurin sa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta cikin jin kunya."
 Yace idanunsa na kanta "Ya zatai ta soshi?"
 Kallansa tai da sauri tare da cewa ba haka zance ba...."
 Murmushi yai sannan yace"Ya za'ai ta kasa sanshi?"
 Da sauri ta mike cikin tsananin jin kunya tai hanyar waje, har taje kofa zata fita taji yace " ba kya tunanin abokin nawa yayi rashin kunya? Duba da yanayinta na dalibarsa?"
 Bata juyo ba tace " Ai ba malami ne na dindindin ba sannan ko malamin ne banaji......."
 Sai kuma ta kasa karasawa tana murmushi, yace "wasa wasa al'adarki ce tsayawa a tsakiyar magana, gashi nikuma zuciyata so take taji me zakice."
 Cikin jin kunya ta juyo ta kalleshi sannan taj waje da sauri.

 Idanunsa ya lumshe cikin wani irin jin dadi sannan yabi bayan kofar data fita da kallo.
 Jalila kam tana tsaye ita kadai tana murmushi, lalai yau tana cikin jin dadi.
 Ganin motarsu tayi parking ne yasa tai saurin shiga dan ta hango Uncle na tahowa, ita kuma yanzu kunyarsa takeji.
 Tana shiga motar Safeena tace " Jalila ya sunan wannan malamin?"
 Jalila ta hade rai tace "Wanne?"
 "Wanda muka gani dazu da safe, yauwa wanda ya ajiye motar can." Ta fada tana nuna motar uncle Sagir.
 Jalila ta kara hade rai tace "menene?"
 Safeena tace "Meye kuwa, kawai dai burgeni yai nake tambaya."
 Jalila tace "Sai ki tambayi matarsa dan ni bansani ba."
 Safeena tace "Yana da mata?"
 Jalila ta guntse dariyarta a ranta tace "yayarki ba insha Allah."

  *************

   Hassan shi kadai a zaune a garden din gidansu, dan da kyar Ummy ta lalabashi ya fito, idanunsa a rufe sai dai ni kaina bansan tunanin me yake yi ba, ko kuna idanun kadai ya rufe.

  Daga bayansa yaji an rufe masa idanu, mikewa yai a zabure, Aina ta turo baki tace "Yaya!"
 Kallanta yai sannan yace "Meye hakan?"
 Tace "Yaya wai ni sai yaushene inka ganni zaka nuna farinciki kamar da?"
 Bai tanka mata ba sai kokarin barin gun da yai,idanunta ne suka canza, tsananin tausayinsa ya kara ratsata, sai yaushene Yaya zai dawo kamar da? Tana tsaye har sai da taga ya kulle.

 Tahowa tai daga gun jiki a sayaye, tana tura kofa taji ance "WAH!"
 Idanu ta runtse dan ta tsorata, dariya taji an kwashe mata dashi, ta bude idanunta cikin shagwaba tace "Ya Sagir!"
 Yace "Matsoraciya!"
 Tace "Naji din na tabbatar ko kaine sai ka tsorata."
 A tare suka nufi cikin falon suna tafe suna hira, Ummy tace "Haba Aina, an shigo da trolly banga mai trolly din ba."
 Tace "Ummy Yaya na hango shine naje mu gaisa."
 Ummy tace "kece ashe kika koroshi daga inda yake"
 Kusa da Ummyn taje tare da zama a kasa tace "Ummy ina wuni?"
 Ummy ta amsa sannan Aina tace "Ya jikin Yayan?"
 "Jiki Alhamdulila zance kenan? Sai fatan Allah ya yayemai larurar nan."
 Tausayin Ummy ne ya kama Sagir, kusa da ita ya zauna yace "Ummy d'anki yayi girlfriend"
 Kallansa tai tace "Haba?"
Aina ta tabe baki tace " da alama yarinyar bata da taste."
 Harararta yai tare da maka mata pillow yace " uwar sanjin gulma sai kije can ki shiga da kayanki kafin Ameera ta dawo."

 Ta tabe baki sannan ta mike tare da jan Trolly dinta.

Ummy cikin zumudi tace "a ina take Sagir?"
Yace "Makarantarmu."
 Tace "students ce?"
 Kai ya daga yana murmushi.
Ummy tace "bani labari."
 Dariya yai sannan ya mike yace "Ummy ba yanzu ba."
Tace "bama nasan ji."
 Nan yai sama yana cewa "zama na musamman zamuyi ai Ummy na."

 Da kallo ta bishi tana murmushi azuciyarta tace"Allah ya kawo randa zanga Hassan na walwala kamar haka, Allah ya kawo sanda zaimin zancen mace."

  ***********

  Inna ta dade tana nazari kafin ta zagaye sunan mutane hudu a cikin dan littafin nata.
 Nan ta kira Sani wanda ya kasance Secretary dinta ne a lokacin da take ganiyarta, bayan sun gaisa tace "Nikam ya labarin Alh Ayuba?"
 Yace "Alh Ayuba ai yana England tun shekaru hudu da suka wuce shi da iyalansa."
 Tai shiru sannan tai cancel din sunan sa tace " Alh Muhammad fa?"
 Yace "Hajiya kin manta shine na baki labari an rufe company dinsu?"
 Tace "Oh na manta." Nan tai canceling din sunansa tace "Alh Abdullahi Taura fa?"
 Sai daya danyi nazari yace " eh shi yana nan garin Kano, sai dai yayi retire daga managern banki ya fada kasuwanci."
 Tace "kasuwancin kamar ya yake?"
Dariya yai yace "Kasuwanci mai karfi, dan yanada company na motoci, yanada gidan mai sannan yanada store a nan garin."
  Murmushi tai tace "bashida wani issue na matsala ko personal life dinsa?"
 Sani yadan yi shiru yace "Ba komai a iya sanina na dai san akwai yaransa uku, sai dai akwai kananan maganganu akan babban dansa wanda inaji kamar akwai wata matsala da yake fama dashi, sai dai su suna kokarin boyewa."

  Ba tare da wani dogon nazari ba tace "yauwa na gode, yanzu ka bincika ka samomin number dinsa, cikin gaggawa."

 Yace "To Hajiya!"

 Harzata tambayeshi mutum na karshe da take tunani sai ta fasa dan dama tafisa ran mutane ukun.


  Mikewa tai ta shiga dan xagaye d'akin nata tana tuanani, tabbas tanajin ba matsala dan kuwa tasan Taura akwai mutunci sai dai tasan harka ta business bani in baka ne."

 Ta tabbatar in ta nemi taimako dole sai ya nemi wani abu itama daga bangarensu, waya ta daga ta kira Dady tace "Abakar ya situation din directors dinmu?"
 Yace "Hajiya abin dai ba dadi, duk an rasa mafita"
 Batace komai ba ta katse wayar, hoton mijinta wanda sukai ita da Mumy da mijinta ta kalla, sannan ta zauna tare da bude littafin da take karantawa, wanda jin matsalar nan ya sa ta ajiye.



  Su Jalila an shiga tarkon kauna tunda Sagir ya bayyana mata zuciyarsa, yau komai take in ta tuna kalamansa sai dai kaga tana murmushi ita kadai, yau aikin gidan ko wahala bai bata ba dan yau zuciyarta a cikin shauki take.
 Nace Hmmmmm


#Oneluv💕
[9/11, 9:46 PM] ‪+234 903 672 7766‬: 🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *AyusherMohd*

 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)


 *No 6*


  Kamar hadin baki yau Sagir da Jalila wani irin bacci sukai mai cike da mafarkin junansu, Jalila bayan tayi sallar asuba ta kalli Goggo dake jan carbi sannan ta gaisheta.
 Goggo ta amsa sannan tace "Jiya na kula a farinciki kike Allah ya kara kawo farinciki mai d'orewa a rayuwarki."

  Jalila tace "Ameen Goggo."
 Sannan ta d'ora da cewa "Goggo kidinga min addu'a inkin yi sallah Allah yasa na auri wanda yake sona nima nake sanshi wanda zai kularmin da ke."
 Goggo ta daga carbi alamar zata zula mata,da sauri ta matsa tana dariya.
 Goggo tace "wato gaba d'aya yanzu kinci idon akuya ko? Na kula kwanan nan fitsara kike ji sannan aure kikeso."
 Tace "Goggo daga cewa amin addu'ar miji sai kice aure nake so?"
 Goggo tace "bazakuwa ki daina cewa Miji ba kuwa ko?"
 Jalila tace "Goggo kice komai na a rayuwa, ni ba kawa ba in ba a boko ba, ni ba kowa ba, kedin dai kece komai na, kinga kuwa dole komai na nasanar dake."
 Goggo tadan murmusa sannan tace " kashe fitilar nan ga haske nan ya fara shigowa, kinga kar battery dinmu yai sanyi."
 Jalila ta kashe sannan ta mike tace "Na tafi bauta."
"Bauta? Kai Jalila bakida dama."
 Har takai kofa ta juyo tace " Allah ya taimakemu an daina bauta amma wasu karfi da yaji nema suke su mai dani baiwa." Ta fada tare da bude kofa, Goggo tai murmushi tare da bin bayanta da kallo, tace "a koda yaushe addu'ar miji na gari zan miki Habiba."

  Jalila na fita ta zagaya ta baya inda kofar kitchen take dan tanan take shiga wai dan kar ta tashesu daga bacci, kwanukan da akaci abincin dare ta hade guri d'aya sannan ta zauna ta soma fere dankali, tana d'aura mai ta shiga yin wanke wanke, tana zubawa tana gyaran kitchen, tana gamawa tasa tafashen naman kaza sannan ta fito falo ta fara shara, haka ta gama shara tai goge goge, tana gama abinci lokacin suke fitowa daga daki alamar tashi daga bacci, nan ta shiga dakuna ta gyara ta wanke toilet sannan ta fito ta dafa ruwan tea, ta dau bread din da aka ajiye domin su, nan ta fita.

 Tana zuwa ta fada wanka tana fitowa ta zura kaya sannan ta shafa mai, duk abinda takeyi tanayi tana duba agoggo, tana fitowa falo Goggo ta miko mata tea a kofi tace "zauna."
 Jalila ta kalli agoggo taga bakwai da ashirin, da sauri tadan kurbi shayin tadan gutsiri bread kadan tadan ci, tana jin alamar tada mota ta suri jakarta da hijab dinta.
 Goggo tace " kidan kara ci mana ai naga motar sai tayi zafi"
 Jalila tace "Goggo ai yanzu ba late a rayuwata."
 Tai waje da gudu a ranta tana cewa "ina san bari Uncle Ya ganni a cikin late comers?"

  Ta riga su Safeena ma fitowa, a cikin mota ta sa safa sannan tadan karkade sandal dinta.
 Safeena ta tabe baki tace "Jalila nikam dan Allah ki daina karkadomin disease."
 Jalila ko kallanta batai ba ta kalli madubin gaban mota ta shiga dan duba fuskarta, Safeena ta kara jan tsaki tace "Mutum sai kace wanda zaije tallar kai, sai wani iyayi akemana, ni wlh na tsani iskancin banza."

 Jalila ta kalleta tace "ke da wa?"
 Tace " tambaya kike?"
Jalila ta tabe baki tace " ba tambaya nake ba dan na kula ke kullum cikin neman masifa kike."
 Safeena ta bita da harara.

  Fuskarta ta maida jikin window tana kallan titi tare da tunanin yau da wani ido zata kalli Sagir?
 Ita duk kunya takeji.

 Yana tsayawa ta sako daga motar sannan tama Yasmeen bye bye.

 Tana kokarin shiga makaranta taga mota tayi parking a gaban makarantar.
 Jalila ta juya tare da kallan motar, kamar tasan motar nan, kara kallan motar tai sannan ta juya tare da cewa "in ma na san motar meye nawa a ciki?"

  Jitai ance Jalila!
 Tsayawa tai dan ta gane muryar mai maganna.
 Sagir yasa kanshi a cikin motar bayan ya fito, yace "Yaya godiya, zakaxo d'aukana?"
 Kallansa Hassan yai sannan yamai alama da hannu akan ya cira kansa daga cikin motar.

 Sagir ya fita tare da daga mai hannu, juyawa yai ya kalli kofar, gani yai bata gun.
 Murmushi yai a ransa yace " naji dadin ganinki."
 Shiga cikin makarantar yai fuskarsa dauke da fara'a.

 Kasancewar yau friday karamar rana ce sannan Sagir shine last period dinsu.

  Kafin ya shigo Jalila ta kalli Zarah tace "Zarah yau bakizo da sosan hoda bane?"
 Zarah ta mata kallan mamaki sannan tai dariya tace "yau kece da kanki?"
 Jalila ta dan canza fuska tace " in an tashi ba gida zani bane, ba kuma nasan inje fuskata na maiko."
 Zarah tace "sai ki bari sai an tashi sai ki nema bawai tun yanzu ba."
 Jalila tace "ana tashi nake san tafiya b........"
 Gaisuwar dataji anayi ne yasa tasan Uncle ya shigo.
 Harara ta makama Zarah sannan ta sunkuyar da kanta kasa.
 Uncle kuwa ko kallan ida take baiyi ba har ya fara lesson dinshi.
 Ganin baya kallanta ne yasa tadanji ba dadi a ranta sannan ta dago tare da kallan abinda yake koya musu.

  Har ya gama sannan ta fita, yana fita Zarah fa miko mata sosan powder da madubi.
 Jalila ta ture hannunta tace "banaso."
 Sannan ta maida kanta kan desk ta kwanta, Zarah tace "tashi mu tafi."
 Jalila tace " jeki ni sai anjima zan fita."
 Zarah ta fita tai gaba, tana kwance har aka wa watse, idanu ma ta rufe kamar mai yin bacci, batasan sanda ya shigo class din ba.
 Ya nemeta a waje bai ganta ba shiyasa yai tunanin ajin, kallanta ya tsaya yi yana murmushi, a hankali ta bude idanunta dan jin kamar ana kallanta.
 Idanunta ne suka sauka akan fuskarsa shagwabe fuska tai dan ta tabbatar kila tunaninsa da takeyi ne yasa take ganin kamar shine.
 Maida idanun tai zata rufe yace " fushi ake da ni ne?"
 Da sauri ta bude idanunta tana kiftasu, sannan tai saurin komawa ta zauna, Sagir yace " me kike a class ke kadai?"
 Batasan me ya sameta ba kawai ganintai ta wani hade rai wai ita a dole an mata laifi.
 Sagir yace "Da alama wannan Malamin yayi laifi kenan?"
 Kallansa tai fuska a hade tace " ba kai bane dazu ko kallan inda nake bakai ba?"
 Tayi mamakin canzawar ta da kuma yanda take magana, a ranta tace "Lalai Jalila wato kin zama kwarariya."

 FSagir samun kansa yai da darawa sannan yace " Nayi laifi, sai dai kin manta dazu Uncle Sagir ne  malamin student a ajin?"
 Tace "Yanzu fa?"
 Yace "Yanzu kuwa Urs Sagir ne."
 Da sauri ta sa hannu ta rufe fuskarta.
 Kallanta ya sakeyi yace " ba haka bane?"
 A hankali tace "Hakane."
 Murmushin jin dadi yai sannan yace " tunda na ganki hankalina ya kwanta dan dama Abbana zan raka wani guri, nace bari nazo na ganki."

 Kallansa tai tace "Okay, sai Monday kenan."
 Yace "Kai! Har sai monday fa ko?"
 Tace "ka manta yau friday?"
 Fuska taga ya canza yace "gashi naga alama ke ko yar wayarnan baki dashi, anya zan iya jure missing dinki har sai monday?"

  Kanta ta sunkuyar kasa tana murmushi, ajiyar zuciya yai sannan ya matso daf da ita yace "bari nai full charge yanda zan cancana battery dinA."

  Kallansa tai sannan ta maida idanunta kasa tana murmushi.
 Ido ya kura mata sosai sannan ya ce "Na tafi."
Sai dayaje kusa da kofa sannan tace "sai anjima."
 Juyowa yai sannan ya juya ya tafi.

 Ta window ta bishi da kallo, wani zazzafan so na ratsata.

 Sam ta shagala da tunani kafin ta farga ta fito da sauri,
 Tafi minti goma a tsaye taga dai ba alamar su Safeena, sannan ba alamar  ma d'alibai suna wucewa, lalai ta tsaya soyayya antafi an barta, yau tana cikin wani hali dan tasan masifa kam ba'a magana.

  Tana tafe tana dan mitocinta ita kadai..........


************

   Inna ce ta kalli Sani sannan ta kalli takardar daya kawo mata dauke da sunan Taura da number sa.
 Tace " da ka sake bincike ba wani abu game da rayuwarsa da ta kyalansa bayan matsalar yaran?"
 Sani yace "eh gaskiya ba wani abu special, sai...."
sai kuma ye " ba ma dai komai."
 Tace "da ke zaka fada?"
 Yace dama kamar yaransa maza biyu ne, 'yan biyu babban Hassan sai kaninsa Husaini, sai dai jiya sai aka cemin wai Hassan ne da Sagir sai macen.
 Inna tace " ko dai kaine ka manta ba?"
 Yace "zai ita yiwuwa inaji Husainin tun yana karami ya rasu."

 Tace " Dama ai maza biyu mace d'aya kacemin."
 Yace "hakan na sani amma nadauka 'yan biyun ne ashe wa da kani ne."
 Inna ta jinjina kai cikin rashin damuwa tace " ba wani abu bayan nan?"
 Yace "babu."
 Nan ta saka number a wayarta sannan ta anna dialing.
  Sai atai ringing hudu sannan ya d'aga.
A banngarensa yana zaune a bayan mota shi da Ummy, sai Sagir dake zaune a mazaunin driver shi kuma hassan na gefe, suna hanyar zuwa asibiti.
 Yana daga wa Inna tai sallama,Abba ya amsa sannan yace "ban gane ba."
 Inna tace " Taura nice Hajiyar grain."
 Sai daya danyi nazari na wasu dakiku kadan sannan yace "Hajiya ina wuni?" Yai magana tare da canza yanayin maganarsa zuwa girmamawa."
Inna ta amsa sannan tace " Taura ganinka nake san yi ina fatan zaka bani lokaci."
 Yace " Haba Hajiya, kina wani gari ne?"
 Tace ina kano, ina neman alfarma ganinka sanda kake da lokaci.
 Yace " yau dai inada abinyi, sai dai banaji gobe akwai abinda zanyi, a ina zamu hadu?"
 Ya fada yana kallan Ummy, tace " gida na zakazo ko nice zanzo ko kuwa a wani gurin zamu hadu?"
 Yace " a'a ba matsala ni zan zo."
 Tace "Nagode Taura zan turoma da address din gidan."
 Ya amsa da to sannan ya kashe wayar, Hassan ya kalla wanda idanunsa ke rufe kamar me bacci sai dai kowa na cikin motar yasan ba bacci yake ba, Ummy ya kalla ya shiga fada mata wacce ta kira.

 Gate din wani katon asibiti naga an bude musu, Sagir ya shiga da motar.


*************

  Jalila kam taci uwar tafiya kafin ta isa gida, duk ta gaji tayi ligib.
 Tana shiga ta tadda Mumy a bangarensu, gabanta ne ya fadi sannan ta kalli Goggo wanda kuka ne kawai batai ba amma da alama daurewa kawai takeyi.

  Mumy na ganinta tace "kin dawo daga yawon iskancin?"
 Jalila fuska ta canza sannan ta kalli Goggo wacce ta tabbatar an kare mata cin mutunci ne, tace " Mumy ban gane b....."
 Marin data kifa mata ne yasa ta kasa karasawa sannan ta rike kuncinta, Mumy tace " ce miki akai nan gidan karuwai ne? Ko me?"
 Mamaki ya kama Jalila tace " Mumy ban ga........."
 Wani marin ta kara kifa mata tace "a gidan ubanwa kika tsaya? Kungurmar munafuka? Dama kwanakin nan na kula bakyasan dawowa tare dasu Safeena saboda kina yawon bin maza."

  Cikin wata irin kakkausar murya Goggo tace " RAMLATU!"

  Kallan Goggo sukai a tare, dan Jalila bata taba ganin ran Mumy ya baci ba haka.



#ONELUV💕
[9/11, 9:46 PM] ‪+234 903 672 7766‬: 🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *AyusherMohd*

 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

 *NO 7*

  Goggo cikin jin zafin kalaman Mumy tace "Ta ya zaki kira yarinya ta da haka? Kina tunanin 'ya'yanki sunfi na wa ne? A koda yaushe ina jure komai ne badan banajin zafin abinda akema Jalila ba sai dan ina tunanin kila hakan shine zai kawo salama a zuciyarta, komai da kika gani inayi inayinsa ne domin ta, taya ma zaki kalli 'ya a gaban uwarta ki kirata da wadan nan munanan kalaman?"

  Mumy ba shakka ta dan tsorata, ta daure tace " ni kike yima fada? Kijira ni."
 Tafada tare dayin waje da sauri, tana fita Goggo ta rike kirjinta wanda ya mata wani irin nauyi, ga wani irin dum na tsananin ciwon kai daya fara sara mata, Jalila ta karasa kusa da ita tare da rungumeta tace "Goggo na."
Cikin shagwaba tai maganar, Goggo ta daure dan batasan Jalila ta gane batada lafiya tace " Karki damu, ko me za'amin indai har akanki ne zan ita jure komai."

 Jalila ta kwantar da kanta akan kafad'ar Goggo cikin tausayama kansu.
 Banko kofar da akai ne yasa ta d'ago da sauri cikin tsoro, Dady ta gani bayansa Mumy ce.
 Jalila da sauri ta mike ta tsaya a gaban mahaifiyarta alamar kareta tace "Dady kome ya faru laifi......."
 Wani wawan mari daya kifa mata sai data fadi kasa, Goggo ta d'agota da sauri tana tambayarta.
  Dady cikin tsananin bacin rai ya kalli Goggo yace "uban wa ya baki dama ki cima matata mutumci?"
 Goggo ta kalleshi tace " ni duk mutuncin data cimin bai zama laifi ba kenan?"
 Yace " Me yasa bakya abu da tunani? Ko kuwa kwakwalwarki ce bata aiki? Gidan da kike zaune,abincin da kike ci, kayan da kike sakawa, karatun 'yarki duk a cikin arzikin wa kike ci?"
 Goggo tai shiru tare da maida kanta kasa, sannan tace " duk da haka banaji tanada damar cima 'yata mutunci...."
 "Yanzu yarinya tayi laifi kina nufin tafi karfin a hukuntata ne ko me?"
 Jalila ta mike da sauri ta rike kafafun Dady tace "Dady na tuba, dan Allah kayi hakuri laifinane."
 Kafa yasa ya hankadata yace " gayyar tsiya."
 Sannan ya juya ya kalli Mumy ya dafa kafadarta yace "muje ciki ko?"
 Yi tai kamar me share kuka tace "Ba sai danace kayi hakuri ba?"
 Juyowa yai ya bugama Jalila wani kallo na takaici daga ita har Goggon sannan ya juya shida Mumy, har sun kai kofa Jalila tace " Dady me kake nufi da gayyar tsiya?"
 Wani banzan kallo ya buga mata sannan yace " idan kika sake min magana da wannan vibe din wlh sai jikinki ya gaya miki, sannan kiyi gagawar tasowa kiyi aikin daya kamata kiyi."
 Ya juya shida Mumy sukai gaba, Jalila da kallo kawai ta bisu idanunta na zubar da hawaye, kallan Goggo tai kamar zatai magana sai ta fasa, hawayenta ta share sannan ta mike ta daukoma Goggo maganinta ta mika mata tace "Goggo share kinsan halin Dady akwai saurin hawa kamar farashi, amma na tabbatar ba duk abinda ya fada yake nufi na, ai uba ubane ko?"

 Goggo ta tabbatar tannayi dan hankalinta ya kwanta ne shiyasa itama ta daure ta daga kai tace "haka ne."
 Jalila ta cire kayan makarantarta sannan ta fita.

 Yau kam tana aiki tana zubar da kwalla, itakam dole me gaskiya tana gama makaranta tace Sagir ya fito suyi aure ta d'auke Goggonfa subar wannan dan iskan gidan.

 
************

  A asibiti kuwa bayan sun shiga cikin office din wanda a saman kofar naga an rubuta Neurologist, suna shiga ya mike daga zaman da yake sannan ya saki fuskarsa yana cewa Welcome Taura.

 Abba ya karasa kusa dashi ya mika mai hannu suka gaisa, sannan suka gaisa da Sagir, Ummy tace "Dr Ahmad mun sameka lafiya."
 Yace "Lafiya kalau Hajiya ya mai jikin?"
 Kallan Hassan tai sannan tai murmushi kawai.

  Guri suka samu suka zauna ita da Sagir, shi kuma ya shiga wani dan d'aki shida Hassan da Abba.

  Hassan ne ya kwanta akan wani abu, sai naga an tura abun cikin wani inji, da alama dai scanning din brain dinsa ake san yi, mutumin yana daga zaune yana duduba yanayin kwakwalwar Hassan.
 Bayan ya gama d'aukan hoto sai ya dana wani abu sai Hassan ya fito, Nan Abba yaje ya taimakamai ya sauko.
 Guri ya bashi ya zauna sannan shima ya zauna kusa da Dr Ahmad ya kalli Hassan yace " Hassan!"
 D'agowa yai ya kalleshi baice komai ba, Dr yace " kana experiencing din wasu sababbin symptoms ne?"
 Hassan ya girgizakai alamar a'a sannan ya dan hadiyi miyau yace " Sai dai kwanan nan bana baccin awa d'aya nake farkawa."
 Dr yace "da mafarkin kake farkawa?"
 Yace eh
 Bayan su fa?
 Yace " bakomai sai yanda dama na saba."
 Yace "Haryanzu kanajin numfashinka na rikewa?"
 Kai ya daga, alamar eh, yace " kirjinka fa?
 Kai ya sake d'agawa, yace rashin san hayaniya fa?
 Nan ma ya daga kai, Dr yace "duk ba abinda ya ragu daga abinda kake ji da?"
 Hassan ya d'aga kai.
 Dr yace " tashi kaje."

 Hassan ya mike ya fito daga d'akin, Dr Ahmad yai gyaran murya sannan yace "Taura abin ne sai mun dage da addu'a sannan mun bulo mai ta yanda ya kamata, da farko dai kamar yanda ka sani har yanzu ba matsala dan gane da kwakwalwarsa, matsalar tana tare ne da zuciyarsa dolene sai mun dage inhar munasan ganin ci gaba."
 Abba yace "Ni Ahmad na rasa yanda zanyi, abin nan ko ina muka je za'ace matsalar bata kwakwalwa bace, kuma nima na yarda da hakan, tunda yana tuka mota da kansa ba tare da matsala ba sannan bai taba yimana abu na mahaukata ba, sai dai na rasa yan......."
 "Abinda ya faru dashi a baya, na tabbatar shine ya rike mai zuciya, yana zargin kansa ne akan duk abinda ya faru a wannan lokacin laifinsa ne."

  Abba ya kalleshi cikin nazari kafin yace "amma bayan abin nan ya faru yafi shekara d'aya a asibiti ba'a hayyacinsa ba, sannan bayan ya farka akace mana ya manta da abinda ya faru dashi a wannan lokacin."

  Ahmad yace "That's what we think, sai dai ina tsoron kar dai abin na nan a ransa, kawai dai yana nuna ya manta ne dan neman kwanciyar hankali."
  Jikin Abba ne yai wani irin sanyi tsananin tsoro ya kamashi yace "Ahmad ya zamuyi?"
 Dr yadan yi shiru sannan yace "akwai solution, na farko ku yarda da abinda ya tsara na mantawa dayai, karka fadawa kowa tunda nima ban tabbatar da hakan ba, sai abu na biyu ina ganin ku nemomai mace wacce zata dinga kwana dashi tana yini dashi, in kuka samarmai mace mai hankali wacce zatasoshi a hankali mekin dake zuciyarsa zai warke, ko akwai wacce yake so?"
  Abba yace " ina ma yake kallan macen bare?"
 Ahmad yace "to in wannan bazai yiwu ba sai dai in sake research in dubo wata hanya, dole dai a cikin gida maganinsa yake, sannan yana bukatar kukawar dukaninku, ta hakan ne guiltiness din dake makale a zuciyarsa sai kankare."

  Abba yai shiru kafin can yace "na fahimta sannan duk wani abu indai har bai sabama shari'a ba zan iya aikatashi indai har Hassan zai samu sauki, domin ni da matata Allah ne kadai yasan halin da muke ciki."
  Ahmad yace "Karka damu Allah na tare da mu insha Allah."

 Nan sukai sallama suka fito, Ummy ce kawai a d'akin, Abba yace "Hassan fa?"
 Tace yana fitowa waje yai, sai naga Sagir ya bishi.
 Ya karayina Ahmad godiya sannan suka fita.

 Hassan na zaune a can gefen asibitin ya kurama kasa ido yana karzar hannunsa na dama da farcen babban yatsarsa na hago, Sadiq na gefensa kadan a tsaye.

  "Inama Allah ya d'auki ransa a wannan lokacin? Babban bakin cikinsa bai wuce yanda iyayensa ke fama a kansa ba, gaba d'aya bayasan ya zama haka, sai dai ya zaiyi?"

 Sagir ne ya matso da sauri ya sa hannunsa ya tare hannun damarsa yace "Yaya!"
 Kallansa yai sannan ya kalli hannunsa wanda sam bai kula ba ashe ya karje hannunsa har ya fara jini.

  Hannun Sagir ya matsar sannan yace "I'm okay."

 Sagir cikin tausayawa yace "muje mota gasu Ummy sun fito.


Mikewa yai suka shiga mota.

  Duk yanda Abba yai akan yai bacci ya kasa, Aina? Kai ya girgiza da sauri dan yasan halin Aunty Nana, duk da yaya take agun Mumy ya tabbatar bazata yarda a aura mata Hassan ba, balle dama ta taba cewa Ummy ya kamata akai Hassan psychiatrist.

  Ummy ce tace " abinda Dr Ahmad ya fadama ne yake damunka?"
 Yace "ba abinda yacemin, baccin ne dai na kasa yi."

 Bata sake cewa komai ba dan ta riga taji komai, Hassan da Sagir na fita ta je jikin kofar dan dama ta damu tasan cikaken halin da d'anta yake ciki, sai dai koda yaushe Abba bai fada mata.
Ba shakka itakam gobe zatama Aunty Nana magana akan Aina taji.


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *AyusherMohd*

 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

 *NO 8*

   Dayake yau asabar ne takan dan samu ta koma bacci bayan sallar asuba saboda su kansu 'yan cikin gidan sai karfe 11 suke karyawa.
 Tana idar da sallah tai addu'ointa ta baje akan katifa, Goggo ta kalleta tace "daga sallah sai kwanciya? Kya bari ai gari yadanyi haske ko?"
 Jalila ta kara gyara kwanciyarta tace "Goggo bakiji baccin da nakeji ba wlh, nifa gani nake kamar ma baccin awa d'aya nai gaba daya."
 "To wai jiya me kika tsaya kikai tayi ne har sai 11 na dare kika dawo?"
 Jalila tadan tab'e baki tace "oho musu wai ko bako zasuyi ne ko me? Ni dai sunce inyi kwallima a babban falo sannan aka sani juya kujerun."
 Ta mike da sauri ta zauna kamar wacce wata sabuwar gulmar tazo mata, tace "Goggo kinsan wai Inna ce da kanta take tsaye a kaina tana sani yanda zanyi?"
 Goggo tace "to menene abin mamaki a ciki?"
 Jalila tace "inna fa nace ba Mumy ba, Goggo bakiyi mamaki ba?"
 Goggo tace "ni banga wani abu a ciki ba."
 Jalila ta maida kanta ta kwanta tace "lalai nikam jiya da mamakin abin nan na kwana, na tabbatar bakon da zasuyi mai mahimmanci ne."
 Goggo tace "ina miki magana ki tashi kiyi addu'oi amma ke gulma kike sonyi."
 Idanunta ta rufe wai ita a dole bacci takeyi, Goggo tace "yi baccin karya da kyau."
 Jalila tana jinta batai magana ba.
 Batafi minti talatin da kwanciya ba sukaji ana buga musu kofa.

  Goggo ta mike da kyar saboda ciwon kafa sannan ta kashe fitilar tasu sannan tabude kofar.
 Dady ta gani a tsaye tace "Ina kwana?"
 Yace " Ina Jalila?"
 Tace "bacci take d'anyi."
 "Bacci? Batada hankali ne?"
 Goggo tace "lafiya?"
 D'akin ya shiga yace "KE JALILA!"

 Juyi tayi dan itakam bacci take mai dadi, Dady ya kalli Goggo yace "tasheta mana."
Goggo tace "yanzu ta kwanta."
 Yace "To menene damuwata a ciki?"
Goggo ta matso jiki a sanyaye tasa hannu tadan daki kafarta kadan.

  Jalila ta dan bude ido dakyar tace "Goggo dan Allah kibarni nai bacci kona awa daya ne."
 Muryar Dady taji yace "kin tashi ko sai na dakeki?"
 Idanunta ta bude da sauri, tace "Da Da Dy......"
 Yace "will you get up"
 Jalila ta mike zaune a tsorace, tace "banyi komai na Dady."
 Tsananin tausayinta ya kama Goggo ace in kaga Mahaifinka tsoro kake ko kayi laifi?

   Yace "tashi muje, Inna nemanki take."
 Jalila ta mike tare da d'aukan d'ankwalinta ta sa a kanta.
 Yana gaba tana binsa a baya har sukaje ba maganar data hadasu.
Tana shiga taga Inna a falo, tsugunnawa tai ta gaisheta.

 Dady ya wuce daki dan bacci yakeji, Inna ta kalleta tace "na d'auka tunda jiya kinsan bako zanyi zaki zo da wuri dan tambayar abinda ya kamata, me yasa ne a koda yaushe bazaki dinga amfani da kwakwalwarki ba?"

 Jalila tace " Yahkuri Inna."
 Tace "taso."
Jalila ta mike sukai kitchen, kayan girki ta gani kala kala an fito dashi, Inna tace " inada bakon dazanyi wajen karfe 12 na safe, bayan kin gama yin abincin breakfast na gida sai ki shiga yin hidimar bakona."
 Jalila ta kalli tulin kayan girkin tace "Inna me da me za'ai?"
 Inna ta mata alama data matso, Jalila ta matsa kusa da ita, inna ta ce wannan vegetables din rabasu gida biyu zakiyi, d'aya kiyi miyar vegetables da farar shinkafa, wannan naman kazan pepper chicken zakiyi dashi.
 Wannan d'ayar naman kazan sai ki raba biyu d'aya sai ki fere dankali ki hada kiyi chicken pie, d'aya kuma sai ki saka a cikin miyar vegetables din.
 Ta kalli fruit din da ke gun tace " wannan kuma kiyi pineapple and coconut juice sai ki yanka ragowar kiyi fruit salad.
 Tashin hankali, kallanta Jalila tai, Inna tace " ki tabbatar kinayi kina kara gyara gidan, sannan kisa turaren wuta sosai, bakon dazanyi mai mahimmanci ne a garemu.
 Ki tabbatar kin kammala komai kafin lokacin.
 Ta juya ta fita, Jalila ta kara kallan kayan girki sannan ta kalli agoggon dake kitchen d'in, karfe 6:40am idanunta ne suka ciciko da kwalla yanzu ia kadai akw tunanin tayi wannan uban aiki sannan ta hada da aikin gida?

  Jitai ance "me kikeyi banji kin fara ba?"
 Lekowa tai ta ga Inna a digirgire a zaune a falon kusa da kitchen.
 Nan ta bude fridge ta d'auko kayan cikin da Mumy tace farfesunshi zata musu da soyayyiyar doya dakwai.

  Yau kam gun gajiya ba'a cewa komai a gun Jalila, dan dama tun datashiga Ss1 aka sakar mata girkin gida gaba d'aya, a da tare sukeyi da Mumy, ashe batasan training ake mata ba, data shiga Ss1 kuwa sai dai ta zauna a kitchen din tana cewa tai kaza tai kaza, wanda a yanzu indai abinci ne ko snacks ko abinsha sai dai in wanda bai fito ba, amma ba wanda ba'a sata yi ba.

Haka ta shiga aiki kamar mahaukaciya, duk mai tausayi inya ganta saiya tausaya mata.



*************


  A hankali Ummy ta tura kofar d’akin, a kwance taganshi a kasan d’akin daga can gefen gado, yana kwance akan sallaya yana bacci, takan rasa inda zata sa kanta a koda yaushe in taganshi a kwance akasa, abinda ke damunta shine inhar bacci dare zaiyi bazaki taba ganinsa akan gado ba, sannan a kasan ma kwanciya kawai yake, amma in gari ya waye sai kiga ya kwanta akan gado.

 Kusa dashi ta karasa ta dauko karamin bedsheets a gefen gadonsa sannan ta lulubamai, jiki a sanyaye ta juya ta fita.
 Tana rufe kofar yana bude idanunsa, kofar ya kalla dan tun da ta shigo ya farka, idanunsa ne suka canza launi a hankali ya maidasu ya rufe saboda tsananin tausayin da yakeji na mahaifiyarsa.

  Mikewa yai ya hau kan gado yai wata kwanciya a dukunkune, a hankali idanunsa suka zubo da wasu zafaffan hawaye.

  Ummy tana fita ta sauka kasa, kitchen ta shiga inda Ameera da Aina’u suke girkin abincin safe.
 Tace “wannan jagwalgwalo har mun gaji da jiransa, sai kace wanda ake mana abincin arziki.”
 Ameera tace “Ummy kin dage sai munyi girki da weekend kinga kuwa kome muka dafa sai kuyi hakuri kuci.”

 Ummy tace “ai na gama kula dake sam bakyasan yin girki, yanzu kuwa kinjama kanki duk asabar da lahadi ke zaki dinga yin girkin safe.”

  Ameera tace “Shikenan Ummy sai mudingacin Indomie.”
Aina tai dariya tace “Lalai Ameera, Abban zaki ba indomie?”

 Ummy ta juya tana murmushi, falo ta zauna sannan ta d’au waya ta kira Aunty Nana.
 Bayan sun gama gaisawa tace “muna nan da Aina’u munatashan hutu.”
 Aunty Nana tace “ ai gwara datazo dan nasan yanzu Ameera tafi kowa jin dadi.”
 Ummy tai murmushi.
Aunty Nana tace “ Ya jikin Hassan?”
 Tace “dama saboda shi na kiraki”
Aunty Nana tai shiru tana sauraranta.
Ummy tace “ Me kike tunanin akan yi masa aure?”

 Aunty Nana tace “Aure? Wace irin magana kike yi Hafsa? Wa kike tunanin zai aureshi? Karfa san kanku ya muku yawa.”

 Ummy mamaki ya kamata tace “ban gane san kai ba? Sai kace wani mahaukaci ko mai lalura mara warkewa ko fa nakasar jiki?”
 Aunty Nana tace “ Ni dai dan bakwasan gaskiya ne, amma na tabbatar Hassan nada matsalar kwakwalwa, kardai ku aura masa yarinya yazo yana neman kasheta.”

  Mikewa Ummy tai idanunta suka canza tace “mene?”
Aunty Nana tace “ Hafsa......”
Kashe wayarta Ummy tai sannan tai shiru tana kara maimaita kalaman Aunty Nana a ranta.
Aunty Nana irin matan nan ne da duk abinda ya fito musu a baki fada suke ba tare da sunyi nazari. Da yaya zaka fuskanci kalamansu ba.

  Ummy ta shiga d’aki jiki a sanyaye, Abba ya gama shiryawa yana fesa turare ta shigo, yanda yaga ta zauna akan gado yasa ya juyo yace “Lafiya?”
 Kallansa tai tace “ Alhaji ya zamuyi da Hassan?”

 Ajiye kwalbar turaren yai yace “keda Yaya Nana ce?”

 Kallansa tai cikin mamaki tace “ya akai ka sani?”
 Yace “ me yasa haryanzu bakisan kanki ba? In dai har naganki a wannan yanayi to nasan matsalar Hassan ne ke damunki, to in har naga yanayin ya hada da dan baccin rai to inba Aunty Nana ba waye? Ni dai nasan ba ni bane, sannan Sagir banaji ya taba bata miki ran da har zaki shiga cikin wani hali, ita kuwa Ameera yarinta ce a kanta.”

  Ummy ta kalleshi tace “jiya naji yanda kukai da Dr Ahmad, shiyasa......”
Yace “kike tunanin hadashi da Aina’u?”

  Tai shiru, kusa da ita ya zauna yace “Hafsa!”
 Kallansa tai yace “ shi aure da kike gani nufine na Allah, sannan wani baya auran matar wani, Allah ne kadai yasan abinda ya shirya akan rayuwar yaran nan, mudai abinda zamumai kawai shine mu dinga mai addu’a kamar yanda muka saba.”

  Kai ta jinjina alamar gamsuws sannan tace “yanzu zaka wuce ne? Naga bakai break ba.”
 Yace “ In naje naci acan, dan nasan thnda dai gida ta gayyacen ta shiryamin abinci, sannan ba dadi taga naje banci ba, kuma kinsan halina inhar naci abinci yanzu 11 banaji akwai abinda zan iya ci nan da awa d’aya.”

  Tace “Hakane, kai kadai zaka ne?”
 Yace “a’a da ina tunanin tafiya da Sagir to kuma ina tunanin kar taji nauyin fadar bukatun ta a gabansa, shiyasa zan tafi daga ni sai Ibrahim.”

 Tace “to sai kun dawo.”

 Ya dau hularsa ya saka sannan suka fito tare.
 Sagir na falo ana masu Ameera tsiya akan sun gaji da jiran abincin safe ya hangosu, mikewa yai yana dariya yace “Ummy zaku fita yawon shakatawa ne?”
 Harararsa tai tace “a haka ake fita ba ko mayafi?”
 Yace “ai ba komai tunda mota zaki shiga.”

 Abba ya kalleshi yace “Wato Sagir in baka zolayi mahaifiyarka ba na kula sam bakajin dadi.”
 Keyarsa ya sosa yana murmushi yace “Abba kasan nafisan kullum naga tana murmushi ne.”

  Ummy ta kalleshi tace “ Muje muga masu abinci tunda Abbanka ya mana yajin aiki yau.”

 A tare suka fara takawa suna hira, Abba ya bisu da kalli cikin jin dadi sannan ya juya ya fita.


************

  Jalila anci uban aiki duk tai wujiga wujiga ga ko abinci ba wanda ya damu taci, sai data gama jera komai sannan ta fito, bangarensu ta nufa cikin tsantsar gajiya.
 Goggo na zaune hankalinta duk yana kofa tana jiran yar tata ta shigo, ko abincin ma ta kasa ci, Jalila na shigo ta zube tare da kwanciya akan cinyarta.
 Goggo tace “zauna ki danci abinci.”
 Da kyar ta mike ta sha shayi da bread sannan ta fara kokarin kwanciya, Goggo tace “Jalila kidan jira ya tsirga miki.”

 Tace “Goggo wlh nikadai nasan me nakeji.”
 Tafada tare da kwantawa.


  Abba ya iso batare da shan wahala ba, saboda kowa yasan Hajiya, Sun shiga babban falo inda ake sauke manyan baki.

  Dady ne ya fara tarbarsu, ya zauna suka gaisa, sannan mumy ta shigo.
 Bayan sun gaisa ne sai Hajiya ta shigo.

 Taura yana ganinta ya mike, sai data zauna sannan ya gaidata.

 Mumy ta mike ta fito, d’akin Safeena ta shiga taga bata nan, na ta fito ta bude dakin Sultan, yana zaune akan computer da alama game yakeyi. Tace “Safeena fa?”

 Yace “Safeena? Ba jiya take cewa akwai inda zasuba yau da friends dinta? Inaji sun tafi ai.”
 Mumy tace “dama yau ne? Ni na dauka sai gobe ai, to kai taso ku gaisa da bakon.”
 Mikewa yai ya fito, yana gaishesu ya koma d’aki.

  Mumy tace “Inna bata nan kinsan tace yau akwai inda zasuje.”
 Inna ta kalli Taura tace” babbar yarinyar bata nan sun fita.”
Yace “bakomai Hajiya,ni ai ban masan kinada jika babba haka ba.” Yana nufin Sultan.
Tai murmushi tace “Sultan ai na biyu ne, babbar mace ce ajinta shida a secondary.”
Yace “Masha Allah, Allah ya raya.”
Tace “Ameen.

  Sun d’an bar musu falon na sama da minti talatin saboda su ci abinci.

  Sai da suka gama sannan Inna da Dady suka shiga.
 Sun d’anyi shiru kafin Inna tace “Taura kayi hakuri rashin nemanka danai har sai damatsala ta tasomin.”
 Yace” bakomai Hajiya.”
 Tace “Taura muna cikin matsala wanda company dinku ke neman fuskantar durkushewa...........”
 Nan ta zayyane masa duk yanda matsalolin ke faruwa,shima Dady na kara mai jawabi.
 Sai da sukka gama, Ta daura da cewa “shine nake neman taimakon ka.”

  Taura yai shiru kafin can yace “ba matsala indai, sai dai nima sai kun bani zuwa gobe na duba yanayin abin sannan sai musan yanda za’ai.

 Taji dadi sosai, dady yace “mungode kwarai.”
 Taura ya dau takardar ya shiga kara dubawa, yana nazari, kudi sukeso sosai dole dai ya nutsu kafin yasan abinyi, dan business ne.”

 Inna ta kara godiya, Dady ma haka.

 Bayan sun gama ne suka mike dan tafiya.

  Jalila bayan tayi wanka Goggo ta bata mafici dan takai makotansu akwai wata tsohuwa agidan da ta sa a mata.

  A gun ajiye motoci ta hango su a tsaye, da alama bakon ne, ta gabansu dole zata wuce shiyasa tana zuwa inda suke ta tsugunna har kasa ta gaishesu.

  Kallanta Taura yai ya kura mata ido, har ibrahim ya amsa gaisuwar shi bai ce komai ba.

 Ta kara kallan Taura wanda kallan da yake mata yasata yin kasa dakai tace “Ina wuni?”
 Taura yace”lafiya kalau, kece babbar yarinyar gidan?”
 Cikin halin ko in kula tace “Eh!”
Yace “Masha Allah, aji shida akace kike ko?”
 Takara cewa eh.
 Yace “Alhamdulila.”

 Mikewa tai tace “Sai anjima.”
 Taura yasa hannu a aljihu ya zaro dubu biyar, yace “gashi!”
Idanu ta zaro tai saurin cewa “A’a kabarshi nagode.”
 Kallanta yai sannan yai murmushi yace “kyauta na miki fa?”
 Tace “wlh ka barshi, na gode.”

  Kai ya daga sannan ya bita da kallo, Ibrahim ya kalla bayan sun shiga mota, yace “me zakace game da yarinyar nan?”
Ibrahim yace “ban fahimceka ba.”
Taura yai murmushi sannan yace a ransa Alhamdulila ala kuli hal......


 #Oneluv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *AyusherMohd*

 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

 *NO 9*


   Taura yayi shiru a d’aki yana nazari, Ummy ce ta turo kofar tare da sallama.
 Bai jita ba dan ya nustu sosai, kusa dashi ta tsaya tace “Lafiya?”
 Kallanta yai sannan yadan murmusa yace “ tsi wlh hankalina ya tafi tunani ne.”
 Tace “abinda kajeyi bai yiwu bane?”
 Yace “Hafsa dan zauna.”

  Zama tai kusa dashi tana kallansa, yace “ yau naga wata yarinya a gidan danaje, ban san meyasa ba naji yarinyar ta kwantamin sosai wanda nakema Hassan sha’awarta, tarbiyarta yasa nake tunanin zata kula da shi fiye da tunanin mu.”
Ummy tace “ yarinyar gidan dakaje ne?”
 Yace “eh.”
Zata sake magana Ameera ta bude kofar da gudu tace “Ummy yaya ne.......”
 Da gudu suka mike suka hau sama, yana kwance a kasa da alama fadowa ma yai ya kankame jikinsa yasa hannunsa a yuwansa wanda ya kasa jan numfashi.
 Sagir sai kokari yake gun taimaka mai, Ummy kasa karasawa tai sai kuka da take yi, Abba ya karasa da sauki yana danna mai kirjinsa, Aina’u da Ameera sai kuka sukeyi.

  Da kyar ya ja wani dogon numfashi sannan ya kallesu cikin takaicin halin da yake sa su.
 Wasu zafafun hawaye ne suka zubomai yana kallan mahaifiyarsa.
Ummy jiki a sanyaye ta karaso inda yake ta rike hannunsa tace “Hassan!”
 Bakinsa ne ya shiga rawa, a hankali yace “Ummy kiyi hakuri.”

 Kai ta shiga girgizawa tana kuka tace “Hassan please kadaina fadar haka.”
 Sagir ma jiyai hawaye ya zubo masa saboda tausayi, Abba ya sa hannu ya d’agata yace “ ku je ku barshi ya huta.”
 Haka suka fito daga d’akin hankalinsu a tashe, Abba ya zauna kusa dashi yace “Hassan meyasa kake kokarin jefa rayuwarka cikin halaka? Sau nawa zamu sanar dakai abinda ya faru a baya ba laifinka bane?dan Allah ka taimakemu ka cirema zuciyarka wannan zargin da takeyi.”
 Hassan ya juya kansa gefe kawai baice komai ba, Abba ya mike ya fita, tabbas ya yarda da maganar likita aure ne ya dace dashi, yanzu in tsakar dare ne abin nan ya faru ba wanda zai kula dashi me zai faru?

  Ummy kam kuka tai tayi, Sagir yana zaune a kasanta ya rasa ta ina zai fara lallashinta, gaba d’aya gidan a wannan rana ba wanda yai walwala.

  ***********

  Yau da daddare Abba ya gama yanke hukuncinsa dan a daren jiya bacci kalilan yai.
 Yau da safe kuwa karfe 10 ya kira wayar Inna.
 Bayan sun gaisa ne yace “Hajiya nayi dogon nazari akan al’amarin nan, sai dai ina tunanin haduwa ya kamata muyi ko in sanar dake ta nan?”
 Inna tace “Taura duk yanda ka gani.”

 Yai shiru kafin yace “Bari in sanar dake ta nan in yaso in kikai tunani sai mu hadu dan yanke hukunci.”
 Tace “ba laifi hakan yayi.”

 Sai daya danyi shiru kadan kafin yace “ me zai hana muyi yar hadin gida.”

  “Yar hadin gida?kamar ya kenan?”
 Yace “eh, ina nemawa d’ana babba auran babbar jikarkarki.”

  Mikewa tai daga zaman da take tama kasa cewa komai, yace “Hello!”
 Tace “ Taura naji, ba matsala mayi magana daga baya.”
 Ta katse wayar hankalinta a tashe.
 Da sauri ta danna number Dady.

  Yana kwance akan gado Mumy ba kwance a kafadarsa suna hira.
 Yana ganin wayar Inna ya mike tsaye yace “plm ce.”
 Mumy ta turo baki tace “share ta kawai, na tabbatar maganar aiki......”
 Bata karasa abinda zata fada ba taji yana cewa “To.”
 Yana kashewa taga ya kalleta yace “Inna na neman mu.”

 Mikewa tai suka hau sama.

  Jalila na ta aiki sanda ta gansu sun hau sama, sun nutsu dan yanda suka ganta alamar ba lafiya.
 Inna ta dade kafin ta kallesu tace “Taura ya kirani.”
Mumy tace “ya amince?”
 Tace “eh.”
 Mumy tace “lalai mutumin nan yanada kudi, wannan uban kudi da muka nema?”
 Inna ta mata kallan batada hankali, sannan ta daga waya ta kira Sani a gabansu ta sa a hands free.
Bayan sun gaisa tace “ Sani me kacemin dangane da babban dan Taura?”
 Sani yace “ bashida cikakiyar lafiya, dan akwai wanda yacemin ma kwakwalwarsa ba daidai take ba.”
 Inna tace to nagode.
Ta kashe wayar sannan ta kallesu tace “hadin aure Taura yake neman yi damu.”
 Mumy cikin halin ko in kula tace “Hadin aure da wa kenan?”
 Dady kallan Inna yai cikin mamaki, Inna tace “me yasa bakya amfani da kwakwalwarki ne?”
 Tace “to ai ni bangane da wa za’ai hadin aure...... “
Dady ne yai saurin tabata sannan ya kalli Inna yace “amma ai baiga Safeena ba.”

 Tace “nima abinda ya ban mamaki kenan daga farko, sai daga baya nai tunanin yaransa ashe fa ancemin ba hankali gareshi ba, kaga kuwa ta ya ya zai damu da sai ya ganta? Tunda shine dai kawai burinsa yaga ya sa marmai mata ne?”

 Mumy tace “hauka kenan, ta ya ya dan zai bamu kudi zai nemi hadin aure tsakanin mai hankali da mahaukaci?”

 Dady ma yace “gaskiya Inna nima ban amince abama Safeena mahaukaci ba.”
 Inna tace “me kuke tunani? Kuna tunanin nima a san raina ne?”
 Mumy zatai magana sukaji an kwankwasa kofa.
Inna tace “waye?”
Jalila tace “nice, abinci na kawo.”

 Inna tace shigo.
Shiga tai ta ajiye abincin a inda tasaba ajiyewa sannan ta gaisheta, ta gaidasu Dady sannan ta mike tai waje.

 Tana rufe kofa naga idanun Mumy dana Inna sun kalli juna, Inna ta hade rai ta kalli Dady tace “ da Taura ya kira cewa yai yanasan hadin aure tsakanin babban dansa da babbar jikata.”
 Dady yace “ to yazamuyi?”
 Tace “baka fahimceni ba kenan?”
 Yace “kamar ya kenan?”
 Inna tace “a ka’ida wacece babbar yarka?”
 Da sauri ya kalleta dan yanzu ya fahimce me take san fad’a, jiki a sanyaye yace “Jalilah.”
 Tace “wa kake tunanin Taura na nufi?”
 Dady ya kalleta sai dai bai iya cewa komai ba.

 Mumy cikin kissa tace “Yanzu Inna ta ya zamu aurana Jalila mahaukaci? Gaskiya nikam ban yarda ba.”
 Inna tace “ to sai shi Abbakar din ya duba ya gani, da company dinmu ya durkushe mu rasa kudin mu, da mu daure mu aurama Jalila yaran wanne yafi? Sannan yaushe kikaji ance miki mahaukaci ne?”

  Dady yai shiru yama rasa me zaice, can yace “amma ai suna ganinta zasusan ba yar cikin gidan nan bace.”

 Inna tace “karka damu da wannan zansa yau din nan a maga dinkuna kala kala, sannan zansa a dauko mai aiki, ai dama na dade ina tunanin cewa ta bar aikin da takeyi, kuma yaran nan tunda yana da matsalar kwakwalwa gani nake bazai zama wani abu ba, gidan kudi zata sannan in haukar ta juyo mai zai iya sakintama a ranar kaga shikenan kowa ya huta.”

  Kallan mamaki ya shiga yima Inna, tabbas wannan kalaman nata sunzo da rainin hankali sai dai bayaji zai iya bijirewa domin shima ya tsani talauci a rayuwar sa, menene dan ya sadaukar da rayuwar yarinya d’aya?

  Inna tace “in kuma baka yarda ba.......”
   Yace “Inna waec.....”
Tace “zanyima Taura magana a barta sai ta gama karatunta, sannan a gida ma banasan kowa ya sani har sai ta kammala karatunta yanda hankalinta zai kwanta.”
 Dady ya jinjina kai alamar gamsuwa.

 Haka suka cigaba da tsare tsarensu shidai Dady kome sukace yarda yakeyi.

  Kiran Taura Inna tai ta sanar dashi amincewarsu.
 Yaji dadi sosai ya ce zaizo karshen satin nan ya kawo kudi sannan su sa hannu akan contract din da sukai.

  Ummy dai batace komai ba, sai dai Abba yace “in zaije sai suje tare ta ganta.” Da haka ya rufe mata baki.

*********
  Jalila tayi mamaki sosai ran lahadi da yamma da Mumy ta nuna mata wata mata a matsayin mai aikinsu, sannan tace mata daga yau karta kara yin aikin gida.
 Abinci ma mai raia da lafiya aka aiko musu.
Yau kam cike da mamaki tabar gidan.

  Da zata tafi har dari biyu Mumy ta bata wai kudin kashewa, yanda ake ba su Safeena.

  Suna isa makaranta ta sauko tana tafiya, tunani takeyi wannan kuma wani sabon salon ne ke faruwa?

 Sam bata kula dashi ba wanda missing dinta ya sashi fitowa da wuri.
 Yana kallanta har ta wuce bata kula dashi ba, sai datai nisa yace “Jalilah!”
 Juyowa tai ta kalleshi, jitai duk damuwar dake ranta ya tafi, wani sansanyan murmushi ne ya bayyana a fuskarta.
 Tace “Uncle.”
 Fuska ya daure sannan yace “ what are u thinking?”
 Tace “Something suspicious.”
 Ganin Zarah ta taho yasa yace “See u later.”
 Sannan ya juya.
 Da kallo ta bishi dashi tana murmushi.
 Zarah ta daka mata duka a baya tace “Anya Jalila bakida crush akan Uncle Sagir kuwa?”
 Jalila ta ture hannunta tace “to uwar sa ido, in ma inada shi laifi ne?”

  Zarah tai dariya tace “in shigar dake?”
 Jalila a ranta tace na shigar da kaina tuni, amma a fili tace “ ni banasan love one side.”

 Haka suka tafi suna hira.

  Sai da aka tashe aka watse tana tsaye, sai leken kofa take ko zataga fitowarsa, sai can ta hangoshi ya taho.
 Da sauri ta juya kamar bata kallan gun, har sai daya iso.
Jitai yace “ Hajiyar tunani an cigaba ne?”
 Kallansa tai tace “Uncle kaine?”
 Murmushi yai sannan yace “bakima ji alamun na iso ba?”
 Tace “sry na tafi tunani ne.”
Fuska ya dan canza yace “anya kuwa kinyi missing dina?”

  Idanu ta rufe wai ita kunya sannan tace” sosai ma.”
 Yace “ to kunyar ita kuma ta menene? Ni bude idanunki ki fadamin meke damunki?”
 Idanunta ta bude tace “Uncle me zakace ingaka wanda ya tsaneka ya fara nuna maka yana sanka?”

  Sagir yai shiru kafin yace “ya danganta da irin tsanar da kuma irin san.”
 Tace “ da ba wanda ya damu dakai haka kawai sai kuma kaga kowa yana ma mutunci yana kula da kai.”
 Yace cikin dayan biyu ne, ko sun fara santa da gaske ko kuma suna san wani abu daga gunta.”

 Jalila tai shiru tana tunani, itakam bataji akwai na biyun, to ko santa sukeyi yanzu? Da sauri ta girgiza kai tace “tunda aka haifen basa sona sai yanzu?????

 Nima nace gaskiya kam😝

#Oneluv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

 *NO 10*



  Gabanta ya dawo yace " Me kike tunani kuma?"
Kai ta girgiza tace "ba komai."
 Ya dan canza fuska yace " inata farin ciki zamu hadu yau amma ke naga kamar har yanzu hankalinki baya kaina."
 Jalila ta sunkuyar da kanta kasa tace "Uncle wlh ba haka bane."
 Yace " to menene?"
 Murmushi ta shiga yi tana sunkuyar da kanta, yace "Murmushi?"
 Tace " a'a."
 Yace "ni to gaskiya a sanar dani"
 Kasa ta kara yi dakai tana wasa da hannunta, yace "Ahhh na kula dai dan ina malaminki ne yasa ake kunyata haka, gaskiya zansa a canzamin gun service yanda zanzo har gida kinga lokacin sai a cire kunyar."
 D'agowa tai ta kalleshi tace "a'a gaskiya."
 Yace " bakyasan in canza?"
 Tace "eh."
 Ya da n yi kasa da murya yace " kinfisan ki dinga ganina kullum?"
 Kunya ce ta kamata dan kuwa abinda take nufi kenan, bata kula ba ashe motarsu har tazo, horn taji anyi, kallan motar tai sannan ta kalleshi tace "Uncle zan tafi."
 Ta fada cikin sauri tare da fara tafiya, juyowa yai yana kallanta dan kar ga farga har ta bude mota.
 Safeena tunda ta hangosu a tsaye ta hade fuska, Jalila na shigowa ta kara kallan Sagir wanda har a lokacin idansa na kallan motar sai da suka wuce.
 Safeena ta kalleta tace "na fada nace iskanci kike zama yi a makaranta kin nemi karyatani yanzu me zakice? Zance da mai mata?"
 Jalila tace "Zance kikace ai ba a d'aki kika ganmu ba, a iya sanina kuma shine mijin auren ba ni ba."

  Safeena ta kulu tai kwafa tace "wlh zaki fadama Mumy uban me kikeyi a makaranta."
 Jalila ta juya kai tanama Yasmeen wasa.


   Suna shiga gida da gudu Safeena ta je tana kaima Mumy gulma, Mumy ta ce "ya isheni menene damuwarki dan tayi zance a makaranta?"
 Safeena tace "Mumy?"
 "Banasan gulma, karki kuskura ki kara kawon gulmar Jalila ba yayarki bace?"
 Mamaki ya kama Safeena, me Mumy take nufi?

  Ita kuwa Jalila tana cire kaya tana leke ko za'azo a mata duka ko aci mutuncinta, sai dai har ta gama cire kaya bataga Mumy ba.
 Goggo ce ta fito daga bandaki ta zauna da kyar tace "Jalila kin dawo?"
Jalila tace "na dawo kina bandaki."
"Wlh cikina ke mirdamin tun jiya, da alama yanayin cin abincin da muka samu ne yasa cikina ya hargitse."
 Jalila cikin kulawa tace "Goggo in anso miki magani ne?"
 Goggo tace "barshi kawai."
 Hijab ta zara tadau dari biyun da Mumy tabata dazu tai waje da sauri.

  Tana zuwa ta sai mata magani ta fito, a hanya taga mai d'ata shima ta siyi na hamsin, tana shiga gida Dady na shigowa.
 Sai data jira yai parking ta karasa ta gaisheshi.

 Leda taga ya miko mata yace "Gashi."
 Kallan mamaki tamai tace "ciki za'a shiga dashi?"
 Yace "a'a naki ne."
 Kallan mamaki ta mai tace "nawa?"
 Baice komai ba ya fito yai ciki.

 Mamaki ne ya kamata ta bude ledar, doguwar rigace a ciki da mayafinta, sai kayan kwalliya da turare.

 Kallan Dady ta sakeyi wanda yai nisa, mamaki ya kara kamata, me kenan?
 Haka ta shiga bangarensu tana mamaki, tana shiga ta mikama Goggo magani sannan ta ce kinga.
 Kayan Goggo ta amsa tace "daga ina?"
 Jalila tace "Dady ne ya bani."

 Shiru Goggo tai tana tunani, tabbas tafi kowa sanin halin mutumin nan, tunda aka haifi yarinyar nan ya bata dan kayan jarirai daga nan bai sake bata ko da da falan atamfa ba, sai sallah ne Mumy zata jefeta da atamfa mai arha, sai kuma wani sa'in in kayan Safeena sun tsufa sai a bata, meke faruwa?"

 Yanda Jalila taga Mumy ta nustu tana tunani yasa tace " Goggo in maida?"
 "Ba haka bane Jalila, kawai dai ina mamaki ne."
 Jalila tace "Goggo ni kaina mamaki abinda ke faruwa nakeyi, kinga an hanani yin aikin gida, sannan jiya Mumy tace wai tabada dinkuna a dinkamin, sannan Inna ma yanzu sakemin fuska take, yanzu kuma Dady, bansan me hakan yake nufi ba"

  Goggo dan kar Jalila ta damu sai tace mata "kila sun duba sunga yanda kike musu ne yasa suka sauko."
 Jalila tace "ko?"
 Tace "sosai ma."

 Murmushi sukai Jalila ta mike ta wanko musu d'ata suka fara ci, basu gama cinyewa ba aka kawomusu abinci mai rai da lafiya.

  Wannan sabbabin al'amari haka sukai ta faruwa a kwanan nan, Mumy da kanta tasa aka kwashe tsofaffin kayan Jalila aka sa mata sababbi, sannan tace ta dinga zuwa cikin gida tana kallo, sannan kafin su nemi abu an aiko musu.

 Itakam Goggo haryanzu bata daina mamakin wannan al'amarin ba, itakuwa Jalila hankalinta a kwance sai soyayya mai karfi da take kara shiga tsakaninta da Sagir.

  Kullum da daddare sai ta ba Goggo labarinsa.

  Shikansa Sagir ji yake a yanzu babban burinsa bai wuce ya ganshi da Jalila ba.



**********


  Yau Juma'a tun safe Mumy ta aika Jalila tazo, tare sukaje gun wanke kai aka wanke mata, sannan suka taho a hanya sai wani janta da hira takeyi, cikin hirar ne ta riko mata hannu tace "Jalila!"
 Jalila ta maida hankalinta kan Mumy.
 Mumy tace "Jalila kiyi hakuri abubuwan da muka muku a baya, bamu kyauta ba na nuna banbanci tsakaninki da Safeena da mukeyi, ke ce babba sai dai zuciya tasa mun tauye miki hakkinki, mun maidake kamar mai aikin gida."
 Ta kara raunana murya tace "kiyi hakuri Jalila."
 Jalila jikinta ne yai sanyi tace "ba komai Mumy sannan ni bakumin komai ba, Goggo itace za'a ba hakuri, ni dama 'yace a gunku kome kuka min dama hakkinane na 'ya inyi abinda kuka sa ni."

 A ran mumy tace 'Ya?
 Amma a fili tace "Nagode Jalila, sannan zan ba Goggon hakuri itama, inaso ki cigaba da nuna matsayinki na babba a gidan nan, karki nunama kowa ke din ba 'yata bace, da ke da Safeena duk daya kuke a gurina."

 Jalila tace "nagode Mumy."
 Haka suka isa gida cikin farin ciki.


  Goggo kuwa bayan sun fita ta fito da kanta ta kwankwasa kofar falon cikin gida, Yasmeen  ce ta bude kofar.
 Goggo tana dan dingisa kafarta da take mata ciwo, tace "Yasmeen Dadynku na nan?"

 Tace eh, sannan tai ciki da gudu tana kwallamai kira, dady ne yadan fito ba da dadewa ba.
 Goggo ta kalleshi sannan ta gaisheshi.
 Mamaki tai dataga ya amsa, tace magana nakesan muyi.
Yace ina jinki.
 Sai datai dan shiru kafin tace "meke faruwa?"
 Yace "name fa?"
 Tace "na canzama Jalila da kukai kai da zuri'arka, nasanka nasan bazaka taba canzawa dan kanka ba sai dai in dakwai abinda kake nufi damu, domin kai da kanka kasanar dani hakan." Yace "ban ganeba?"

 Tace "ka manta da bakinka kacemi kai a rayuwarka ba so, in har kuwa naga kanasan abu to lalai akwai abinda zai kareka ne."
 Dady yace " kema kinsan wannan zancene na da, sannan me ya kawo wannan maganar da yar cikina?"

  Kallan zargi tamai tace" tuni nazo na maka dan baxan taba tafema ba in har ka cutarmin da 'ya ta."

  Ta juya ba tare da ta nemi amsarsa ba, ko ajikinsa ya juyawarsa ciki.


********

  Yau tun safe ake hidima a cikin gida,Mumy ta aika aka kira mata Jalila, tare dukansu suka hadu a kitchen sukai ta aiki, Safeena kuwa tana gidan Kanin Inna a cikin gari, suna gamawa Mumy tace ma Jalila tace tai wanka a toilet din Safeena.

 Wani had'ad'en material ta dauko mata ta saka, Jalila kam yau tayi mamakin kyan da tai, dan tayi kyau sosai, Mumy da kanta ta daura mata dankwali sannan ta sa mata turare.

  Wajen azahar motar Taura tai parking a gida.
 Ummy ce ta fara futowa sannan shikuma ya kashe motar ya fito.
 Kallo d'aya zakama Ummy kasan macece mai class ba wani shigar karya tai ba sai dai kana ganinta kasan matar manya ce.
 Taura ya matso sannan ya nuna mata hanyar.

  Dady ne ya fito ya shigar dasu falon baki, sai wani washe baki yakeyi, Inna ta sauko suka gaisa, nan suka dan tattaba magana akan harkar business, Mumy ta mike ta shigo dakin Safeena inda Jalila take a zaune,tace "Jalila zo ki kai musu abinsha."
 Jalila ta mike tana cewa "Mumy kunya nake."
 Mumy ta yafa mata mayafi tana cewa "abokana Dadynki ne gaisawa kawai zakuyi."

 Haka ta fito ta amshi tiren ta nufi falon, ta rasa me yasa gabanta ke faduwa, yaye labulen tai ta shiga da sallama.

  Ummy tana shigowa ta kura mata ido, haka kawai taji yarinyar ta shiga ranta, yanayin nutsuwarta ne ya kara burgeta, Jalila ta ajiye tiren kanta na kasa dan ji take kamar kallanta akeyi.

 Kanta na kasa ta gaishesu, Ummy ta fara amsawa sannan Taura ya amsa ya daura da cewa " Ya karatu?"
 Tace "Alhamdulila."

 Yace "ance kun kusa fara jarabawa sai a dage ko?"
 Tace "insha Allah."

 Ganin yanda take tsugunne a gun yasa Ummy tace "tashi kije."
 Nan Jalila ta mike ta fita.

 Inna ta kalli Ummy tace "kun ganta?"

 Ummy tace " Mun ganta sai fatan Allah ya kaimu lokacin, sannan muna fatan bazaku mata maganar auren ba har sai ta gama karatunta kamar yanda aka tsara."

 Inna tace "dama hakan shine daidai."

 Ummy tai shiru kafin can tace "sai dai ni banasan auren dole, a matsayina na mace banasan tauye hakkin mace yar uwata, kar muje akwai wanda takeso."


  Mumy tace "in dai wannan ne ba matsala dan Jalila ba ruwanta da kula kowa, ita kunya ma bazata barta ta kula saurayi ba."

 Ummy ta jinjina kai na gamsuwa, haka suka sa hannu a takarda na yarjejeniya.......

Sannan sukai sallama.


Nace uhm hmm..........
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

 *NO 11*


  Ummy har ta sa hannu zata kwankwasa kofar Hassan sai kuma naga ta sauke hannunta sannan ta bi kofar da kallo, juyawa tai jiki a sanyaye tana neman sauka.
 Sagir ne ya fito daga dakinsa, kallan Ummy yai sannan ya matso gunta, yace "Ummy menene?"
  Tace " Sagir ashe kana ciki?"
 Ya kalli shima kofar Hassan sannan yace "Ummy in koma dakin yaya ta karfi?"
 Harararsa tai na wasa tace "kana tunanin zai barka ne?"
 Yace "sai in zauna ta karfi ince bazan fita ba."
 Ummy tai murmushi tace "karka damu insha Allah na kusa samun mai tayashi kwana."
 Cikin zumudi yace "haba?wanene?"
 Ummy ta fara sauka daga matatakalar tana cewa " watace."
 Sagir cikin mamaki yace " Aure?"
 Nan ta shiga bashi labarin abinda ke faruwa sannan ta daura da cewa " Sagir ni na rasa me yasa tunda na ga yarinyar nan nakeji kamar akwai alamun tauye hakki acikin wannan lamarin."

 Sagir yace "ba wani tauye hakki Ummy, na farko Yaya ba mahaukaci bane, ba kuma nakasashe bane, sannan a zamanin da ai mace ma ance ba sanin wanda zata aura take ba har sai anyi mata auren."

 Kallansa tai tace " hakane nima dan Abbanku sai da aka gama komai na ganshi."
 Tana fada tana dariya.
 Yace "kinji ma ko? Wow Ummy harna kosa naga yarinyar, tunda ta kwanta miki ma tabbatar yarinyar ta gaske ce."
 Ummy tace "kai sai yaushe zaka nunamin taka budurwar?"
 Yace "nan gaba kadan nafisan ne sai mun rabu ta gama makaranta sai na fara zuwa gidansu a matsayin saurayinta ba malami ba, kinga sai na kawo miki ita kiganta."

  Ummy tai murmushi tace "babban burina a duniyarnan bai wuce abubuwa uku ba Sagir, na farko naga yayanka ya warke ya dawo kamar da, na biyu naga ya samu macen da zata kula dashi na uku kuma na ganka kaima da matar da kakeso kuna rayuwar farin ciki."

  Sagir yai murmushin jin dadi yace "insha Allah Ummy duka burikan nan naki zasu cika ba da dadewa ba."

  Haka suka sauko kasa suna hira.
*****

  Kansa yaji yamai gingirin gim, gaba daya dakin yamai zafi, mikewa yai ya fito daga d'akin ya sauko kasa.

 Yana jin muryar Ummy dasu Ameera a kitchen, waje yai ya fada motarsa yai waje...........

Wani irin farinciki kwanan nan takeji, ga gida yanzu ana santa sosai, ga tsananin soyayya dake kara shiga tsakaninta da Sagir, jiya suka gama waec zasu fara neco, shine yau ta fita da kanta ta hau mota tace gidansu Zarah ta amso aran wasu litattafanta.

 Tana zaune cikin adaidaita tana murmushi suka dan tsaya saboda dan karamin go slow dake gun, gefenta ta kalla motarsa ce a gun, kallan motar tai sannan tai dan tsaki tace " irin motar wannan dan iskan."
 Kallan motar ta sakeyi sannan, da yake motar mai tint ce sannan bata ganshi ba a wancan ranar shiyasa bazata iya ganewa ba.

 Sa'a akai ya juyo da fuskarsa inda take,  kawai ya hangota tana murguda baki da hararar motar, mamaki ya kamashi dan ya tabbatar bata ganinsa bare tace wani abin ya mata.
 Har ya dauke idanunsa sai ya kara juyawa, baki ta kara tabewa sannan ta juya kanta tana yan guna guni, kai ya girgiza sannan ya juya fuskarsa.

  Jalila tana dan masifa tana cewa ai indai na kama mutumin nan ko ban mai komai ba sai na harareshi irin taimakon nan ma bai iya ba, ba kunya ranar ya mata rashin mutunci.

 Hassan kam gaba yai ya tafi can inda ya saba zama, ya kashe motar sannan ya kwantar da kansa a jikin kujera tare da kunna karatun al-qur'ani, kira'ar Malam Abdullahi Abba ne ya zagaye cikin motar.


   Jalila an samu jin dadi, yanzu kayanta kala kala, sannan haka zata zauna wani sa'in a falo itafa Yasmeen suyi ta kallansu, duk sanda suke kallan india in ana soyayya itada Sagir dinta kawai take hangowa, ba shakka bata san sanda san Sagir yai nisa a zuciyarta ba.

 Goggo najin dadin yanda Jalila yanzu ta murmure duk da ba kiba tai ba amma inka ganta zakaga ba wahala a jikinta.

  A kasan zuciyar Goggo har yau hankalinta ya kasa kwanciya da yanda su Mumy da Dady ke jan Jalila a jiki, sai dai duk sanda Goggo ta nemi Jalila data rage zuwa gunsu Jalila sai tace "Goggo Allah ba abinda sukemin sai mutunci."

  Jalila an dage sosai ana ta karatun Neco saboda Sagir yace tai karatu sosai dan yanasan yaga matarsa ta cigaba da karatu.
 Duk sanda yai wannan maganar sai Jalila ta sunkuyar da kai wai ita kunya, sai dai a kasan ranta wani dadi take ji.

  Goggo har ta gaji da labarin Sagir dan kusan kullum sai ta mata tadin shi.


  Su kuwa a bangaren su Inner company ya kara habaka saboda sun samu kudi sosai a gun Taura, yanzu company din ma yafi da karfi.
  Su uku suke tsara abin biki dan har kayan daki sun fara siya, Safeena kuma suna ta shirye shiryen kaita Egypt wai ta cigaba da karatunta.
 Sai dai ni nasan suna kokarin fita da ita ne dan karma a san da zamanta har sai anyi auren.

  A can gidan su Ummy kuwa, suma ita da Ameera da Aina'u suna zuwa siyayyar kayan lefe, sanda Aunty nana taji zancen nan har gida tazo tacema Ummy wai tayi dabara ai gwara da suka nemarmai mata ta kudi wai sai yafi daraja.
 Sanda tai maganar nan Ummy bata tanka ba dan haryau kalaman Aunty Nana na mata ciwo.

  
  Yau suke zane paper karshe ta neco, suna fitowa suka hau ihon gama makaranta.
 Jalila ma zaune itada Zarah a can gefe, Zarah tace "Jalila ni tun jiya nakesan fada miki wani abu."
 Jalila tace "menene? Fada kukai da Nasir?"

  Zarah ta juyo saitin Jalila sosai tace "Jalila tsoron abinda na aikata nakeyi."

 Jalila ta mata kallan tuhuma.

 Zarah tace "Jalila jiya Nasir ya sani yin abinda na ke ta tsoro."

  Jalila tace " me ya saki yi?"
 Idanun Zarah ne suka canza suka ciciko da kwalla tace "Jalila jiya muna tare da Nasir kinsan in zaizo kasan layinmu yake tsayawa sai ni kuma naje saboda tsoron kar yayana ya ganmu, jiya sai na ganshi a mota sai yake cemin motar babansa ce aka aikeshi, bayan mun gama hirarmu a cikin mota zai tafi sai cemin yai wai sai na mai kiss."

  Jalila cikin tsantsar mamaki tace "kiss?"

 Zarah ta runtse ido cikin dana sani tace "Jalila kinsan yanda  nake tsananin san Nasir ganin ransa ya baci dana tsaya ina tunani yasa na matso kusa dashi na sumbaceshi a kunci, shine yace shi sai na mai a baki, nan na kai bakina saitin bakinsa shine ya rikoni ya dinga tsotsar leb'ena bansan sanda na bude mai cikin bakina ba, Jalila bansan ya akai ba na kasa kwacewa sai bashi hadin kai danai, dakyar na kwavi zuciyata na fizge jikina da sauri na fito daga motar nai gida da gudu........."

  Kuka ne ya zo mata wanda yasa ta kasa karasa abinda takesan fada, Jalila kam sam tama kasa magana sai inalilahi kawai da take cewa........

  Ganin yanda Zarah ke kuka yasa Jalila ta riko hannunta tace "Zarah it's okay! Kinyi laifi babba ma kuwa sai dai tunda harkin fahimci kinyi laifi sai ki nemi yafiya a gun Allah ki kuma kiyayi aikata makamancin abinda kika aikata."

  Zarah ta rungume Jalila tana kuka, Jalila tace "Sai dai magana daya zan fada miki gaskiya ki bincike san da Nasir yake miki, so ne ko sha'awa, in so ne sai ku tuba ga Allah ku nemi kariya daga shedan in kusa sha'awa ne sai kisan zaman da zakiyi dashi."


  (_Gareku 'yan mata da samari masu irin wannan soyayyar, sai kaga saurayi yazo gun budurwa in zai tafi sai yace sai ta mai kiss ko sai ya rungumeta, ko kuma ya nemi tamai abinda bai kamata ba, wanda ke da kike aikatawa kinsan haramun ne, sannan shi da yake saki shima yasan haramun ne._

 _Dan Allah mu guji fadawa halaka saboda wani buri na zuciyar mu, Allah ya mana tsari ya kare mu daga sharrin zuciya_Ameen suma Ameen)

  Jalila na zaune itada Zarah tana kara mata fada aka aiko tazo inji Uncle Sagir.
 Kallan Zarah tai tace "Zarah ina zuwa."
 Zarah tace " Ba sai kin dawo ba dan na san ba ganinki zanyi yanzu ba."

 Jalila ta kalleta tace " har kin dago?"
 Zarah ta harareta tace " yanda kike nunawa ta ya ya zan kasa ganewa? Ba ni ba na tabbatar yawancin mutane sun sani."

  Jalila ta matso tace "da gaske? Ina nunawa a fili?"
 Zarah tai dariya tace gashi nan kin rubuta a goshinki da jan biro."

 Jalila ta dan daket tace "bansan iskanci."
 Zarah tace "daga ke har shi ai kun gama sanar ma mutane dan ni a bakin mutane ma na fara ji."

 Jalila ta dan shagwabe fuska tace " kice kowa kallona kawai yakeyi?"

 Zarah tace "ah to mu ai yan kallo ne."

 Jalila ta rufe fuskarta tace "bari in rufe fuska ta inje a haka."
 Zarah tai dariya tana cewa " u are so Naive."

 Jalila tana ta wani nuku nuku a haka har ta fita dan dama jiya ma a waje suka hadu gaban makarantarsu kadan, wani dan lungu.

 Sai data dan laleka kafin ta gangara wai ita a dole batasan a ganta.

  Sagir na kallanta yana murmushi har ta karaso, yace " me kike ta lekawa?"
 Tace "Uncle ya zamuyi? Duk fa ansan menene tsakanin mu."

 Yace "to sai akai ya?"
 Tace "qx
 Yace "nace sai akai ya?"
 Tace "hmm hmm"
 Murmushi yai yace " kin manta kin gama skul? Sannan ba yaudara ko wasa muke ba balle muce bamasan a sani, ya zakiyi in sukazo auranmu? Ko gidan mu?"

  Idanu ta zaro sai kuma ta rufe idanta da sauri, yace "oh  ni wai sai yaushe ne za'a daina min kunyar nan?"
 Sauke hannu tai tace "ni in kai wata maganar ne sai naji kunya ta kamani."
 Yace "to da alama zan tattara maganganun dake cina sai munyi aure."

 Murmushi tai, sun dade tare kafin tace zata tafi, dan yau ita kadai za'azo dauka tunda Safeena tana gidan kanin Inner tun last week tacan take zuwa makaranta.


  ********

  Abba ne ya kalli Ummy yace " ya kamata yau na sanar ma Hassan abinda ke faruwa."

 Ummy tace " ni kam tsoro nake kar abin nashi ya dawo."

 Abba yace " sai yaushe ne zaki bari a fadamai? Tun wancan satin kike sani nake jan lokaci ko so kike sai abin ya zo zai sani?"
 Tace"shikenan ka fadamai yau."
 Abba ya mike yai sama...........

#ONELUV💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

 *NO 12*


  Hassan na sa kaya yaji Abba na knocking, da sauri ya karasa sa rigarsa sannan ya murda makullin ya bude dakin.
 Abba ya matsawa ya shiga cikin dakin, kallan dakin Abba ya shiga yi yana jinjina kai, gashi dau duk lalurar dake damun Hassan amma bazaka taba ganin dakinsa da datti ba, yadan murmusa dan tabbas bai manta lokacin yana yaro ba kafin abin nan ya sameshi Hassan mutum ne mai tsafta da tsantsani, sai dai dakin bai musu karami ba? Ko sagir zai maida kasa? Dan dama saboda Hassan ne ya dawo nan kusa da dakinsa.

  Ganin Abba na ta dubs dube yasa hassan ya koma kan sofa ya zauna.
 Abba ya kalleshi sannan ya koma kusa dashi shima ya zauna.,
 Matsawa kadan Hassan yai dan Abba ya zauna daf dashi.
 Abba yai murmushi yace " Hassan yada matsawa?"
 Bai tanka ba dan dama Abban yasan ba tankawar zaiyi ba.

  Sunyi shiru sai karar fanka dake kadawa a cikin dakin, sai sanyin A.C, Abba ya rasa ta ina zai fara, can ya daure ya maida hankalinsa kan Hassan yace "Hassan!"
 Kallansa yadanyi baice komai ba.
Sai daya dan kara yin shiru kafin yace "Hassan ke kake tunani game da aure?"

  "Aure? Aure kamar ya?"
 Abba yace "baka tunanin aure?"

  Cikin rashin fahimta yace "ban fahimci aure ga mara lafiya?"
 Abba ya danyi shiru kafin yace " Hassan mubar zancen lafiya da rashinsa, kafi kowa sanin halin da mahaifiyarka take ciki a kanka, ka kuma san yanda tasha wahala akan rashin dan uwan............"

  Kallan sa Hassan yai idanunsa har sun kada, bakinsa ne ya fara rawa, hannunsa ya sa a wuyansa yana dan kakari, cikin lokaci kankani Hassan ya rikede, hankalin Abba ya tashi sosai rungumeshi kawai yai dan ya rasa ma mai zai mai.

  Da kyar numfashinsa ya daidaita sai dai zufa da ta keto masa, Abba jikinsa ya kara yin sanyi tsananin tausayi dan nasa ya kara kamashi.

  Ya dade sosai kafin ya dawo daidai, Abba ya mike zai fita, Har yakai kofa Hassan yace "Wani abu ya samu Ummy ne?"

  Abba ya juyo daga inda yake a tsaye cikin raraunar murya yace " Hassan in har ka damu da halin da muke ciki ka amince ka auri yarinyar da mukesanka da ita."

 Mamaki me ya kara kamashi yace" tambayar abinda ya samu Ummy......."
Yanzu Abba ya canza muryarsa daga alamar tausasawa zuwa dan bacin rai, yace " akwai wani abu dake damunta ne a duniya daya wuce matsalar da kake ciki? In har kanasan hankalinta da nawa ya kwanta ka yarda da auren da muke kokarin yi maka."

  Hassan shima cikin dan zafi abinda rabon da yai magana mai tsayi haka harya manta yace " Taya zaku nemi min aure bayan kunsan halin da nake ciki? Sannan ni a rayuwata kunfi kowa sanin banasan zama inba ni kadai ba, ya zakuyi kuyi tunanin hadani da wata? Bayan kunsan daga ita har ni hakkin mu zaku shiga?"

  Abba ya dan matso yace "wannan halin da kake ciki shine yasa muke tunanin ma auren kota wani hali, halin zama kai kadai, halin kin fadar in baka da lafiya, halin nunkufarci da rashin fadar matsalar ka, halin kin yima kowa magana, halin rashin kula da kanka, wannan kadan ne daga cikin dalilan dayasa mukesan ma aure."

  Hassan har zaiyi magana yaji kansa yayi gingirin gim dan gaba daya dama baya iya magana mai tsayi, mikewa yai ya shige cikin toilet ya rufo kofar.

  Abba ya juya ya fita, Ummy na tsaye a falo a kasa sai zagaye takeyi tana ganinsa ta matso tace ya kukai?
 Yace "kema kinsan bazai yarda ba daga bugu daya ba."
 Tace haka ne, yace "ke zaki mai magana gobe, dan inyaga kin damu kema kinsan zai yarda."
 Tace "amfani dani da tsauyi da kaunar da yakemin zamuyi?"
 Abba yace "ba haka nake nufina, hakan dai shi kadai ne haya."
Shiru tai batace komai ba.



  Jalila kuwa tana zaune kusa da goggo suna dan cin abinci duk ta dameta da labarin film din India data kalla mai suna Vivah tana ta fada mata yanda saurayin ciki da budurwar ke san juna can tace "Goggo kinsan abin mamaki? Matarfa ranar auransu ta kone a jikinta amma saurayin nan dan tsabar san da yake mata ya nuna shi wannan ba komai bane, Goggo a asibitin fa ya aureta......"

  Goggo tace " nikan Jalila sai yaushe ne zaki kyalemu muci abinci shiru? Bafa asan mutum na cin abinci na magana, sannan ni na rasa me yasa baki da aiki sai zancen soyayya, wani irin so kikema Sagir din nan dayasa kika koma haka?"

  Jalila tai dariya tace "Goggo karki damu yanzu tunda muka gama makaranta zaki ganshi tunda kinga gobe za'ai taron yaye mu, kinga kuwa kila ma jibi ki ganshi dan bazai iya dadewa bai ganni ba."

  Goggo ta girgiza kai cikin mamaki tace "yaran zamani wato ba kunya, sannan ya san gidan nan ne?"
 Tace "gobe zan kwatantamai."
 Goggo ta tabe baki tace " da alama dai kinfi sanshi ma."
 Jalila tau dariya tace " tab Goggo ai ni bansan wayafi san wani a tsakanin mu ba."
 Ya isheni haka nan.
 Ta fada tare da tsame hannunta dan ta rasa me yasa takejin kirjinta na mata nauyi sosai sannan sai tafi kanta na sarawa.

 Jalila tace " Goggo ki bari kawai na kusa daukeki mu koma gidan aurena."
 Harararta Goggo tai tace " to sannu, nidai na fada miki ki kiyayi kanki karkije ba shine mijinki ba."

 Jalila tai dariya tace "tab lalai Goggo kina tunanin zan kara san wani bayan Uncle? Ai nni har mafarki nayi na auranmu."
 Goggo tace "to uwar surutu ya isheni haka nan, ba wanda yasan mijinki a duniya sai Allah sai dai a koda yaushe ina miki fatan miji na gari wanda zai soki kamar ransa ya kuma kula dake kulawar da baki samu ba a rayuwarki."


  Jalila batace komai ba sai cigaba da cin abincinta datai tana murmushi dan itakam tasan mai so da kula da ita ba kowa bane sai Uncle dinta.


  ********


  Abba ne ya kira Sagir ya tambayeshi labarin jarabawa dan shi ba sanin abinda ake ciki yai ba, nan Sagir ya sanar mai ai an gama Neco.
 Yana kashe wa ya kira Inna, bayan sun gaisa ne yace mata "Inna yara sun gama jarabawa ko?"
 Tace "eh sun kammala nima dama ina jiran kiranka."
 Abba yace " sai mu hanzarta ko?"
 Tace "ba laifi ai ku muke jira."
 Yace " To Alhamdulila insha Allah jibi sai mata su kawo lefe."

  Tace "hakan yayi , Allah ya kaimu."

  Nan sukai sallama, kallan Mumy tai tace " yaushe kike tunanin ya kamata asanar mata?"
Mumy tace " duk sanda ya dace kinsan bata isa bijirema maganar mu ba tunda tasan Uwarta a karkashinmu take, sannan in muka mata barazana da rayuwar ta ba shiri zata aminta da duk abinda muka gindaya mata."


  Inna ta jinjina kai tace " hakan yayi, yanzu mu bari sai jibinbin ankawo lefe dan na tabbatar bazai wuce sati biyu ba bikin dan da alama Taura ya kosa."
 Mumy tace "mu ko yau yake so menene damuwar mu? Shiyasa ma nace Safeena ta cigaba da zama a gidan kawu daga nan ta wuce Egypt hankali a kwance."


  Inna tace " da nace kibi mijinki Abuja yau kin binsa kikai ko?"
 Tace "Inna dan Allah ki kyale Abbakar, sai yaushe ne zaki barshi yai aikinsa cikin nutsuwa?"
 Inna ta girgiza kai tace "haryanzu baki da hankali, ke wai a naki haukar har yanzu kina tunani tsabar so ne yasa yake kula dake haka? Yake kuma wulakanta matarcan?"
 Mumy tace "Hajiya."
 Inna tai tsaki tace "Ke kika sani, ni dai company din ku bazan taba yarda na barmai gaba daya ba dan kina kallan idanunsa da yanda yake aiki zakisan akwai tsantsar greediness."
 Mumy ta mike tace "  Zan sauka."

  Inna ta kalleta ta girgiza kai, tace ba da dan ina nuna mai matsayinsa ba kina tunanin zai ci. A da darajaki ne?"
 Mumy tai shiru, Inna tace "jeki ke kika sani."

  Mumy ta sauko ranta ba dadi.

*******

 Ummy ce ta turo kofarsa dan tajita ba a kulle ba, yana zaune a kasa yayi shiru sai ma ka rasa me yakeyi shi kadai kullum a zaune, ta shiga ta ajiye tiren abincin sannan ta zauna gefensa kadan tace "tunani kake?"

  Kallanta yai bai ce komai ba, tace "Dazu Abbanka yama magana ko?"
 Yanzun ma baice komai ba, tace "Hassan mu iyayenka ne wandanda duk duniya duk wani mai sanka sai dai ya biyo bayanmu, ka fi kowa sanin bazamu zabama abinda zai cutar dakai ba, bazan kuma nemi takura maka ba, sai dai abu daya zan fadama wannan auran ni na fara amincewa akai sannan shine babban burina wanda nakesan ka taimaka ka cikamin shi."

  Ta danyi shiru kafin ta mike tai waje.

  Da kallo yabi bayanta sannan ya runtse idanunsa, Ummy ya takeso yai?


#ONELUV💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*Sisters Always Ask Questions, Borrow Clothes, Tell You When Your Hair Doesn't Look Good, Always Fight but Never Drawn Apart, Love You Always, Encorage You When You Are Dawn...*
 _A Small Quote For My Sister Love You Always Ameenah😍_

 *NO 13*

A rayuwar Jalila indai tana gaban Goggo jinta takeyi kamar yarinyar goye, shiyasa duk wata tabata da shirme juyema Goggo takeyi, suna kwance zasuyi bacci duk ta isheta da neman sanin asalin labarinta.
 Goggo tace "to ya isheni haka nan yanzu sai ki kwanta ko kin manta gobe kunada taro a makaranta?"
 Jalila ta juyo inda Goggo take tace "Goggo kinsan yanzu addu'ar da nake yi yanzu?"
 Goggo tace "ya wuce shirmen soyayyarki?"
 Jalila ta girgiza kai tace "A'a addu'a nake Allah ya kara miki lafiya da tsawan kwana muyi rayuwa tare, banaji zan iya kwana d'aya a duniya in bakyanan."

  Goggo ta hade rai tace "Jalila nikam sai yaushe ne zaki girma? Na dauka in mutum ya tashi cikin wahala yana hankali amma wani sa'in in kikai wani abun sai inta mamakin ki."
 Jalila tai murmushi tace "Goggo a koda yaushe in ina tare dake ji na nake kamar yarinyar goye, kece kawata, mahaifiyata, mahaifina, sannan kuma yar uwata, Goggo yanda bana boye miki komai dan Allah kema kidinga sanar dani komai na rayuwarki."

  Kallan tausayawa ta mata dan tabbas tana ji a jikinta wani babban ciwo na cinta domin wasu sababbin canjin da take fuskata a jikinta tasan da matsala,, sai dai fatan Allah yasa abin ba babba bane.

  Jalila tace "Goggo!"
 Goggo tace "shikenan Jalila na miki alkawari a daren gobe zan sanar dake komai na kafin a haifeki, yanzu dai ki kwanta."
 Tace "yauwa Goggona, saida safe."
 Goggo ta daga kai, sannan ta zuba mata ido, kankace me Jalila ta tafi bacci.

  Goggo a dade tana kallanta har batasan sanda hawaye suka gangaro mata ba, hannu tasa ta share sannan ta gyara mata bargo ta juya ta fara bacci.

   Da safe bayan ta gama gyara bangarensu ta fada wanka, an dade ana saba jiki kai kace fatar tata zata canza, ta fito ta bude drawer dinta ta saka kayan makaranta sannan ta shiga duba sababbin dinkin da aka mata, nan ta zabi wani lace mai an karan kyau yasha duwatsu, ta fara kokarin sawa a jakar hannunta da aka sai mata.

 Goggo ta bude labule tana kokarin shigowa, kallan Jalila tai tace "ke da zaki makaranta me zakiyi da kayan gida?"
 Ta karasa shigowa da kyar ta samu ta zauna.
 Jalila tai murmushi tace "Goggo yau fa ake yaye mu."
 Tace "to sai akai ya?"

  Jalila tace "Ana gama taran ai zamu kwabe mu shiga kayan gida ai shagali."

 Goggo ta tabe baki cikin rashin gamsuwa tace " Wai yaushe aka fara haka a makarantar Gomnati ma?"

 Jalila tai dariya tace " ina kike fita balle ki sani?"

  Goggo tace "Hmm amma ai kyaci abinci ko?"
 Jalila tace " Ni bana jin yunwa sannan za'a kawo abin saidawa a makaran........."
 Kallan da Goggo ta matane yasa ta zauna da sauri tare da bude kular abincin, tea ne da bread da
 farfesun naman kai."

 Jalila ta dade kafin ta bude bread din, har goggo tace "menene?"
 Jalila tai yake tace "rayuwa kawai nake tunani Goggo, wai yanzu mune ake bamu abinci ba tare da munyi musu aiki ba, Goggo kin manta sanda muke musu wanki? Mu musu komai na gidan?"

  Goggo tace " rayuwa kenan Jalila, insha Allah wahala ta kare miki a rayuwa."
 Jalila tai murmushi sannan ta fara cin abincin, bazata cemata iyaye suna zuwa ba dan ta tabbbar zataji ba dadi, gashi ita ba lafiyar kafa ba."

Tana gamaci ta fito, Sultan ta gani yana kokarin shiga mota, tace "Sultan?"
Tsayawa yai har ta iso, tace "ina zaka?" Ta dauka cemai akai ya rakata saboda gama makaranta da zasuyi.
 Jitai Yace "In an kaiki makaranta ne zan wuce gidan kawu in amso sako." Sakon me?
 Yace " kamar wai lefe za'a kawo."

 Jalila cikin mamaki tace "lefe? Lefen wa za'a kawo?"
 Yace "ina na sani?"
Ya fada tare da shiga motar.
Jalila ta shiga tana mamaki, bikin Safeena za'ai? Amma bataji labari ba, to ko amsar kayan za'ai kawai a gidan?"
 Ganin batada amsa yasa ta share.


  Yau yan mate dinsu Jalila ansha uban kwalliya, sai iyayi akeyi.

  Haka aka fara programs kowa iyayensa da yan uwansa sai zuwa sukeyi, Jalila tana zaune dan tasan ba wanda zata gani.

  Zarah ce ta tabata tace "Jalila Yaya yazo dasu Umma."
 Nan sukaje suka gaishesu, Jalila tana zaune daga inda take tana hango Uncle Sagir, insuka hada ido sai suyi ma juna murmushi.
 Ganin Uncle ne ma yasa ta cire komai a ranta har aka gama programs.

  Nan sukaje suka canza kaya kowa yasa kayan gida suka dau kwalliya, masu waya sunata yin hotuna, Zahra ma ta zo musu da waya sai hoto ake tayi.

  Wata monitor din Jss3 ce ta shigo ajin nasu, nan ta nemi inda Jalila take ta tabata.
 Jalila ta kalleta tace " Hadiza ya akai?"
 Mika mata wata yar karamar jaka ta kwalli tai tace "gashi inji Uncle Sagir."
 Jalila ta amsa tana bude jakar.
 Kwalli ta gani ta jawo,Zahrace ta matso ta fizgi kwallin tana cewa " me muka sa......"
 Ganin waya yasa ta kalli Jalila tace " yeee!"
 Jalila ta harareta sannan ta fizge wayar tace " muga."
 Ganin Wayar ne ya sa ta kallan Zahra, hannu tasa cikin jakar ta zaro wani karamin card.
 Bude shi tai taga ansa
_To u my dear!_
 _Congratulation on your graduation, here is my small gift, hope you will accept it._
 Zarah ce ta kara amsar wayar ta bude ta, wayace mai tsananin kyau Sumsung Note 5 ce.
 Kan kice me Zarah ta fara haska Jalila wacce tai tsuru tana kallan ikon Allah.

  Fitowa tai daga ajin ta shiga nemanshi, can ta hangoshi cikin mutane.

  Tsayuwa tai dan bata san ya zatai ba, juyowa yai kawai sai hangota yai daga nesa.
 Yaune rana ta farko da ya ganta cikin shiga haka mai kyau dauke da kwalliya, sannan wannan ne rana ta biyu daya ganta ma da kayan gida a iya zamansu, na farko sanda ya fara ganinta sai kuwa yau.

  Kasa dauke ido yai daga kanta wanda har hakan yasata tsarguwa.
 Juyawa tai da sauri ta shiga class din.
 Zahra ta matso tana nuna mata hotunan da ta mata.

  Jalila kam bata kula taba dan hankalinta nakan Uncle dake waje.

  Daina hangoshi tai hakan yasa ta fito daga class din tana lekensa.
 Zarah ce ta miko mata wayar da sauri tace "Zarah Yours na kiranki."
Jalila aji abin banbarakwai, kallan wayar tai a jiki an saka MINE dariya tai sannan ta kalli zahra tace ya ake daga wa?"
 Mamaki ya kama Zahra sai dai kafin ta farga Jalila tana gwadawa kawai taga yaja hakan yasa Zahra tai tunanin iskanci take mata.

 Jitai yace "Banga kwalliyar nan ba, tunda ba'a ganni ba sai a taimaka azo inda muke haduwa."

  Murmushi tai sannan tace "to."
Kallan Zahra tai sannan tace "ina zuwa."

 Nan ta fara tafiya.


  Yau a kan mota ta ganshi, karasawa tai fuskarta dauke da murmushi da kuma kunya.
 Tana isa ta gaisheshi, yace "Irin wannan kyau haka ai sai kisa in rasa gane hanya."
 Kallansa tai tace "Uncle wannan gift din yayi yawa, bana tunanin zan iya amsa, Goggo ma fada zatamin"
 Yace " to Jalila ya kikeso muyi? Kingama skul nima na gama service a ina kikeso indinga jinki? Ke ba waya ba? Sannan ko zuwa zan dinga yi kina tunanin za'a barni nazo kullum?"
 Jalila tace kullum? Yace sosai in har bazaki amshi wayar ba sai dai ki amince kullum nazo muyi awa uku tare.

 Da sauri ta zaro ido dan tasan wannan inaa bazai yiwu ba.
Ji tai yace "bazai yiwu ba ko? To kinga kawai ki hakura."

  Jalila tace "Amma....."
 Yace "mu bar maganar nan please."

Kallansa tai dan batasan me zata ce ba..........

 Hira suka shiga yi ta masoya masu tashen soyayya, Kiran wayarsa da akai ne yasa ya kalli wayar mamaki  yai dayaga Mine a jiki dan number Jalila ce.
 Nan ya daga yana cewa wayarki na gun wa?
 Tace Zahra
 Zahra na dagawa tace "Uncle wai Jalila tazo anzo daukarta."
 Uncle ya kalleta yace "wai anzo daukarki."
 Mamaki ya kamata tace "amma nace sai bayan azahar, gabanta ne ya fadi badai wani abun bane ya samu Goggon ta?"

 Kallan Uncle tai a tsorace tace "Uncle bari naje gida."

 Zahra na tsaye kusa da motarsu, wayarta ta mika mata ta bata jakarta, nan Jalila ta sa a cikin jakar ta shiga ciki sukai gaba, addu'a kawai take Allah yasa ba wani abun bane ya samu Goggonta.


*£*£*********


  Goggo tana zaune wajen karfe 12 Yasmeen tazo da gudu wai tazo inji Inna.
Tayi mamaki sosai dan tanaji tunda take a gidan Inna bata taba nemanta ba haka kawai.

 Samun kanta tai da faduwar gaba.
 Haka ta taso da kyar saboda ciwon kafa ta karasa.

  Tana shiga falon taga Inna, Dady da Mumy a zaune.
 Faduwar da gabanta ya shiga yi ne kawai ya sa ta shiga yin addu'a dan ta tabbatar ba lafiya ba, shiga tai a hankali.
 Mumy ta mata nuni da kujerar dake gefe tace "ki zauna anan."
 Goggo ta zauna sannan ta gaida Inna ta gaida Dady da Mumy.

  Bayan sun amsa ne falon yai dan shiru.

 Goggo tace "lafiya?"

Inna tace "Gobe za'a kawo kayan lefen Jalila."

 Abin yazoma Goggo a ba zata wanda yasa tace "lefen Jalila kamar ya kenan? Dan banaji ta taba sanar dani tanada miji."

  Inna tace " ba sai ta sanar dake tana da saurayi ba, dan kuwa hakkin mahaifi ne ya zaba mata mijin da yaga ya dace da ita, sannan shi Abbakar ya fitar da nasa hakkin na yi mata miji yanzu hakkin 'ya ne tabi umarnin mahaifinta."

 Goggo ta kalli Dady da sauri tace " Abbakar me kenan?"
 Yace "hakan da kikaji shine."

 Cikin daga murya tace "da tunda aka haifeta bakasan da hakkin ta akanka ba sai yanzu? Dama wlh ni jikina yaban mutuncin da kuke mata da wani abin a kasa, ashe aurar da ita zakuyi? Mijin mahaukaci ne ko dan shaye shaye? Ko kuwa barawo ne? Ko kuma nakasasshe? Ko kuma dan fashi ne?"

 Mumy tace "ya zaki fadi haka, Abbakar fa ubanta ne ta ya za........."

 Goggo cikin tsawa tace "Ba dake nake ba."
Yanda tai maganar ne yasa Mumy tsorata dan bata taba ganin Goggo  na fada haka ba.

  Goggo cikin fada tacigaba " me ka mata a matsayinka na ubanta? Me ka mata?"
 Dady shim ya kasa magana dan bai taba ganin tana fada haka ba.

  Goggo fa mike da kyar idanunta sun canza tace " duk abinda kuke ma tunanin ku ajiye dan wlh ba wanda ya isa ya yima Jalila auren dole."

  Juyawar da zatai taji wani jiri na debanta, kan kace me tayi baya luuuu jikake tim ta fadi a kasa.

  Da sauri suka mike suna jijigata.

Jalila wacce ta shiga bangarensu da gudu taga ba Goggo jakarta ta cilar a dakin sannani ta fito ta nufi bangarensu Mumy dan tambayarsu,ganin Goggo a kasa su Dady da Mumy na kanta yasa ta karasa da gudu jikinta na bari.



#ONELUV💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*No 14*


  Dady a rikice ya nufi daki ya dauko key din mota ganin yanda Goggo take a kwance ga Jalila sai wani irin kuka takeyi.
 Jiyai ance "ABUBAKAR."
 Tsayawa yai sannan ya juyo ya kalli Inna, kallansa tai tace "ina zaka?"
 Yace "Asibiti."
 Tace "dawo ka zauna."
 Tsayawa yai yana kallan Goggo sannan ya kalli Inna.

 Mumy ce ta kalli Inna tace "Inna kingafa......"
 Kallan data mata ne yasa ta yin shiru, Jalila a rikice ta jawo gwiwarta ta iso inda Inna take tace "Inna dan Allah ki bar Dady ya kai Goggo asibiti, duk da bansan me ya hadaku da Goggo ba har take nan bangaren sai dai na rokeki da ki yi hakuri."
 Hannunta ta hada guri daga tana ta murzasu tana kuka alamar tsantsar neman taimako.

 Ganin Inna batada niyyar kulata yasa ta ja gwiwa zuwa gun Dady ta rike kafaraa tace "Dady ka taimaka dan Allah, karka manta Goggo matarka ce, sannan mahaifiyatace."

  Gani tai Dady ya kalli Inna, hankalin Jalila ne ya kara tashi ta matso kusa da Mumy ta rike gwiwowinta tace "Mumy ki taimaka min, bazan sake yima Safeena laifi ba, sannan zan cigaba da yi muku aiki, dan Allah ku taimakeni ku kai Goggo Asibiti."

  Muryar Inna ce ta katseta da cewa " kinaso a ceci ran mahaifiyarki?"
 Jalila a rikice tana kuka shabe shabe ta shiga daga kai ba kakautawa, Inna tace " akwai hanya daya mafi sauki, wanda in kika amince da ita bama kaita asibiti ba hatta kula da ita zamu samo wanda zai dinga yi, sannan asibiti duk tsadarsa zamu kaita indai zata samu lafiya."

  Jalila a rikice tace "ko me kukeso ku fada zanyi dan Allah."

 Inna tace "ki amince da auran da Mahaifinki zai miki."

 Gabanta ne ya fadi ta kalli Dady idanunta jagab da hawaye, yana ganin sun hada ido ya juyar da kansa gefe.
 Jalila tace "ban gane ba Inna."
 Inna tace "in baki gane ba sai ki bar Goggon taki ta karasa rayuwarta anan."

  Wani irin fitar da numfashi da Goggo tai shi yasa Jalila rikicewa ta karasa gunta da gudu tana kuka.
  Inna tace "kina tunani ne akan maganar? Ashe baki dauki ran mahaifiyarki da daraja ba kenan tunda kina tunanin yanda zakiyi tsakanin lafiyarta da farincikin ki."

  Jalila ta kalleta tana kuka tace "ko ma dawa zaku hadani na amince ni dai dan Allah ku kai Goggo asibiti."
 Inna tace "yanzu kikai magana, Abbakar kai Mahaifiyarta asibiti, sannan ki sani gobe za'a kawo lefenki da sa rana."

  Jalila kam kuka kawai takeyi, haka Dady da Mumy sukasa Goggo a mota Jalila ta shiga baya suka fita.

 Asibitin Standard sukai parking, Jalila kam banda kuka ba abinda takeyi, ana shiga da Goggo nurse ta nufi office din likita dan sanar da ita halin da Goggo take ciki.

  Jalila na zaune a kasan beni kuka kawai takeyi tana addu'ar samun lafiya ga mahaifiyarta.

 Dady na zaune shida Mumy, sunyi shiru suma.
Sai da suka samu da taimakon Allah numfashinta ya daidaita sannan suka shiga yi mata gwaje gwaje.

  Sai da suka gama sannan suka fito aka kira Dady.
 Likitan ce kalleshi tace "wani maganin hypertension take amfani dashi?"
 Yace "hypertension?"
 Tace "kanaso kacemin bakusan tanada shi ba?"
 Dady ya girgiza kai alamar rashin sani, tace "diabetes fa?"
 Dady yai shiru nan ma.

 Tace " menene tsakaninka da ita?"
 Kunya tasa yace "yar uwatace."
 Cikin rashin jin dadi tace "wannan wani irin abu ne? Batada miji ne? Ko kuwa neman kasheta yakeyi?"

  Dady yai shiru, tamai bayanin ciwon ta wanda ya riga ya ci jikinta sosai, tace " ta ya za'ayi ku bari diabetes har yai nisa ya ci kafarta?"
 Dady yace "ai mun dauka ciwon kafa ne na girma."
Tace "ko ciwon kafa ne na girma ai kwa gwada zuwa asibiti, da kunzo da wuri ai za'a sanar daku ba shi bane." Sosai ta nuna masa laifinsu sannan ta bashi takardar magunguna tace yaje pharmacy dinsu.


  Jalila na zaune kusa da Goggo tana kuka, ko mayafi babu a jikinta dan kwalli ne kawai a kanta.

  Dady sai da ya gama biyan kudin komai sannan ya shigo dakin, Jalila ce ta kalleshi batace komai ba.
 Dady yace "ya jikin nata?"
 Kasa amsa mai tai dan gaba daya yau tana tir da kasancewa  uba a gareta.
 Duk wani mutum mai imani bataji zai yiwa matarsa abinda dady ya ma Goggo yau.

  Dady ganin yanda Jalila ta dauke kai daga kansa yasa ya fito.
 Mumy ya tadda a zaune yace " mu tafi."
 Tace ya jikin nata?"
 Bai bata amsa ba ya wuce mota.
 Suna shiga ya kalli Mumy yace " yanzu abinda Inna tai dazu ta kyauta?"
 Mumy ta riko hannunsa tace "nima banji dadi ba sai dai kafi kowa sanin duk abinda Inna takeyi tanayinsa ne saboda mu, na tabbatar ba a san ranta itama tai haka ba."

 Shiru yai baice komai ba yaja motar sukai gaba.



  ******



  Ummy ce take ta buga mai kofar yanaji sai dai ya kasa mikewa ya bude, yana takure a gefen bandaki ya matse kansa da karfe, zufa nata karyomai, jikinsa sai rawa yakeyi.

  Ummy ganin ba alamar budewa yasa ta sauka kasa da sauri tana kwallama Sagir kira.
 Sagir na kwance a falon kasa yasa waya a gaba sai gwada number Jalila yakeyi sai dai tai ringing har ta gaji ba'a daukaba.
 Jin yanda Ummy ke kiransa yasa ya mike da sauri yana tambayarta Ummy lafiya?

Ummy a rikece ta karaso tace "Hassan."
 Yana jin haka ya hau sama da gudu.
 Aina'u da Ameera dake zaune suna hira suma suka taso da sauri.

  Ganin buga kofar bazata kara mai komai ba yasa ya shiga dakinsa da sauri ya dauko spire key ya bude.

  Hassan na takure jikinsa sai rawa yakeyi ga wani azabbaben ciwon kai dayake damunsa, Sagir ya karasa da sauri ya rungumeshi, Ummy kam zubewa tai a kasa tana maida nimfashi dan ta tsorata ganin yanzu abin da dan sauki zakaga in ka kwankwasa yana budewa, Aina'u da sauri ta karasa kusa da ita.

  Sagir ya dade yana mai addu'oi samun nutsuwa sannan shima Hassan din ya fara kokarin yi a zuciyarsa.

  Ameera kam kuka kawai takeyi.

  Hassan ya kalli Sagir idansa yai ja, kallan Ummy yai da Ameera dake kuka gaba daya tausayinsu ne ya kamashi sai dai bai nuna a fuskarsa ba, mikewa yai ya zari key din motarsa zai fita.

 Ummy ce ta riko hanunsa dayazo wucewa ta kusa da ita, sannan ta kalli su Ameera ta musu alama da su fita.
 Suna fita ta kalleshi tace "ina zaka?"
 Yace "fita kawai zanyi."
 Tace "Hassan sai yaushene zaka dainafita haka kawai?"
 Kallanta yai cikin takaicin rayuwarsa yace "To Ummy ya kikeso nai? Nace zan bar garin kin hanani? Sannan ba tun yanzu ba kukasan matsalata sai yaushene zaku daina damuwa in kuka gan ni cikin halin nan? Sai yaushe ne zaku cire abin a ranku ku saba da ganina haka?"

 Ummy tace "taya kuwa zamu cire abin a ranmu bayan kaidin jinin mu ne? Damuwar ka itace damuwarmu? Rashin lafiyarka itace tamu?"
 Cikin akaici yace "Ummy please, Please na rokeki da ki cire ni a ranki, Please ki manta dani kiyi rayuwarki yanda kikeyinta da."

  Tace " kana jin takaicin yanda nake shiga kunci saboda lalurarka?"
 Kallanta yai baice komai ba, tace "in har kanaso inyi rayuwa yanda kakeso to ka amince da abinda na fada ma."

 Kallanta yai yace "Ummy wai ta yaya zakuyi tunanin yimin aure cikin wannan halin? Wace macece zata iya zama dani?"
 Tace " in har ka amince ai zaka ganta, zakaga wace macecen ce haka dazata iya zama dakai?"

 Hassan yai shiru dan kansa har yanzu yana sarawa, yace "naji kiyi duk abinda kike ganin shine daidai."
 Ya fada tare da fita daga dakin, da kallo ta bishi dashi cikin tausayawa, dan tasan halin zuciyar danta,  mutum ne mai saukin kai, sai dai tundaga faruwar al'amarin nan ya rikede ya koma haka.


  Hassan na fita ya fizge mota yai gaba.


 Jalila kuwa da daddare Driver ya kawo musu abinci, ganin yunwa zataata lahani ne ya sa ta zuba abincin taci.
 Goggo ce ta farka daga nannauyan maganin baccin da aka sa mata, kallan Jalila tai sannan ta kalli asibitin, a hankali ta budi baki tace "Jalila!"
 Tsame hannunta tai da sauri ta isa guda da ita tace "Goggo! Kin ganeni?"
 Da kyar ta mata murmushi tace "Jalila karki kuskura ki yarda da abinda Mahaifinki ke shirin yi miki."

  Jalila ta kalli kasa jiki a sanyaye sannan ta kalli Goggo tace "Goggo abinda kikesan cemin kenan daga farfadowarki?"
 Goggo da kyar tace "Karki yarda Jalila, bazan kara bari su cutar dake ba ta hanyar da bazata kare ba, aure ai ba wasa bane."

 Jalila tace "to bazan yarda ba yanzu dai ki kwantar da hankalinki kinji?"
 Goggo ta daga kai a hankali, wani baccin ne ya kara yin gaba da ita.........



#ONELUV💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*No 15*


  Wajen karfe 12 na dare tana zaune akan kujera a kusa da mahaifiyarta ta kwantar da kanta a kusa da ita, Goggo ce ta bude idanunta a hankali tare da kokarin yin motsi da hannunta, Jalila cr ta farka wanda dama tana rike da hannun Goggo gam.
 Tace "Goggo jikin ne?"
 Goggo ta girgiza kai ta mata alama data kwanta a kusa da ita sannan ta matsa mata, Jalila tace "ya za'ai in kwanta anan Goggo? Ki bari zan kwanta a kasa."

 Goggo tace "kwanta anan mmagana zamuyi."
 Jalila ta mike ta kwanta akan karamin gadon wanda ya musu kadan, Goggo ta rike hannunta tace "Jalila duk abinda zai faru karki yarda da abinda mahaifinki ke shirin yi miki, daga shi har zuri'arsa, kinada wanda kikeso dan haka ni mahaifiyarki na baki shawarar bin zuciyarki."

 Jalila cikin sanyin murya tace "Goggo me yasa muke zaune a cikin mutanen da basa kaunarmu?basu damu da rayuwarmu ba?"

  Goggo idanunta suka canza kala zuwa damuwa da bakin ciki tace" Sunana kamar yanda kika sani Khadija, amma Kubra ake cemin, muna zaune a can wani kauye mai suna Chabai wanda yake karkashin karamar hukumar Misau a gariin  bauchi.

  Kasancewar karamin kauye ne sannan haka al'ada ta saba yarinya tun tana tsuma ake mata miji, haka zata taso har lokacin da zata isa aure a aura mata shi.
 Mahaifiyata itace mace ta uku a cikin matan mahaifina, sannan itace ta tsakiya, 'ya'yan gidanmu mu 23 ne, nice ta 5 sannan ta biyu a gun mahaifiyata, a ranar da ake radamin suna a ranar ne Mai garin mu wanda ya kasance mahaifin Habubakar yamai kamu na.

  Na taso mace marasan hayaniya dan a garin yara sa'anina har tsiya sukemin saboda asaranci irin nawa da rashin iya fada, Habubakar kuwa mutun ne dan gayu wanda tunda ya tasa yake bin yan garinmu Misau, Lagos da kano in zasu tafi rani.
 Ko sau daya bamu taba kebancewa da sunan saurayi da budurwa ba saboda shi gani yake yafi karfina, sannan sam baima fiya zama a garin ba.
 Ya yawan kasuwancinsa ne ya hadu da wani babban mutum mai kudi a garin kano, wanda suke safarar kayan abinci.
 Habubakar nada kokari da himmar yin aiki shiyasa mutumin ya amince dashi sannan yasan harkar gona sosai, ganin yana moruwa da Habubakar ne yasa mutumin ya nemi shawararsa akan sa shi yayi karatu, haka Habubakar ya shiga makaranta ba tare da ya sanar a gida ba, a aji hudu aka sashi saboda girmansa, ya dage sosai saboda shi mutum ne mai tsananin buri da san ya zama wani abun, haka ya share sama da shekara 8 a garinkano yana harkokin karatunsa da taimakon Uban gidansa.
 Sam ba abinda ya dameshi da tushensa inda iyayensa suke.
 Ni kuwa a lokacin sa'anina duk sunyi aure dan alokacin shekarata 15 duk inda naji tsiya akemin akan nayi kwantai, hakan yasa ko fita nadainayi, sannan Innata ta ma daina bani talla dan haushi ma takeji itama akan kullum ta bani tallan kunu kwantai yakeyi.

 Shi kuwa Habubakar ya zama dan gayu yana ta hidimominsa, alokacin ne kuma Mumy taji kaunar Habubakar ma ratsata saboda duk wani abu datake so kafin ta nema zakaga ya mata shi, wanda shi a gunsa ba wai so bane tsabar neman gun zama ne a gidan.
 Mumy wanda asalin sunanta Fatima ta bayanna ma Habubakar san da take mai,ba wani kokonto ya amince da ita saboda a lokacin ne ya tabbatar da arzikinsa ya tabbata.
Haka ya dinga nuna mata tsantsar kauna ba tare da sanin iyayenta ba, Fatima tayi zurfi a kaunar Abbakar wanda ya canzama kansa suna zuwa na gayu.
  Hajiya Zinaru wacce take mahaifiyarta ta mata hadin aure da dan uwanta, sai dai Fatima ta sanar dashi bata san sa ita Abubakar take so kuma zata aura.

 Alokacin ne akan san da soyayyar dake tsakaninsu, duk yanda Zinaru tai ta rabasu abin yaci tura, shi kuwa Abbakar ya dinga riricema Fatima akan kaunar da yake mata.
 Fatima taki ci taki sha ita fa sai Abbakar, mahaifinta shikam dama yana so, Zinaru kuwa ganin abin na Fatima yayi nisa dolene ta amince amma da sharadin dolene ya zauna dasu sannan ya cigaba da karatunsa, sannan duk abinda ta unarceshi dolene yayi.
 Abbakar hankalinsa ya kwanta dan yanzu yasan tabbas ya zama wani abun, Mahaifin Fatima ne yace yaje gida ya sanar ma iyayensa.
 Sam Abbakar baiso ba danshi babu komawa kauyensu a tsarinsa.
 Haka ya shirya ba'a san ransa ba yace zai taho, key din motarta Fatima ta bashi tace yaje da ita dan ya dawo da wuri.
 A yanzu shekaruna 18 duk garin har iyayena sun gallabeni gashi mahaifin Habubakar yaki yarda a hadani da wani, a lokacin akwai wani babban mutun wanda yakeda mata biyu dayaso ya aureni amma yaki.
  Haka rayuwata ta koma cikin tsangwama da wulakanci a garin, kuka kuwa nayishi har ba iyaka.
 Kwatsam ranar mahaifina ya shigo cikin farinciki yake cewa Habubakar ya dawo.
 Sam ko mikewa banyiba daga aikin da nakeyi saboda ni maganar mutunci ma bata taba hadamu ba.
 Randa Ya isa gidansu mahaifinsa ya haushi da fada ta ko ina bai ma jira maganarsa ba, sannan yace a ranar zai daura mana aure.
  Ran Habubakar ya baci sosai yace shi ba wanda ya isa ya aura mai yar kauye, haka aka turo gidanmu akan washegari da azahar za'a daura auranmu.
 Bakin ciki yasa Habubakar ya fita can bayan gari gidan wani tsohon abokinsa inda suke zama da yaje ya aika a kirani.
 Da kamar bazanje ba tsautsayi yasa na fita, haka yaran dan aiken ya kaini har gidan.

 Tsayawa nai a waje saboda bansan dakin ba.
 Habubakar ya bude kofar yasa hannu ya fizgoni ciki, ba abinda yacemin sai gefe daya koma ya cigaba da cin abinsa yana dadana waya.
 Na gaji da tsayuwa haka Yasa nace zan tafi.
 Mikewa yai yazo kusa dani yace " ni kike jira na aureki? Na miki kala da dan garin nan? Ko mijin wata kuchaka kamarki?"
 Nace "naji koma menene ni ba damuwa amma kabarni na fita."
 Dariya yai sannan ya sa abu ya rufe kofar ya koma yai zamansa.
  Kafafuwana har suka gaji suka fara rawa saboda tsayuwa, nan fara kokarin bude kofar ji nai an fizgemin hijab dina ta baya an yar a kasa, tsoro yasa na fara kuka ina matsawa.
 Dariya yamin sannan ya koma ya zauna, baifi minti biyu da zama ba mukaji ana buga kofa da karfi, muryar mahaifina da mahaifinsa mukaji suna cewa Habubakar ka bude kofar nan ko kuwa?
 Mamaki ne ya kamani da naga ya cire rigarsa ya bar vest sannan ya taso ya bude kofar.
 Yana budewa ya koma gefen kafita yana cewa Baffa kayi hakuri.
 Nikam hawaye na nacigaba dayi, ganin abinda ke faruwa yana zuwamin a baibai.
 Mahaifina na zuwa ya kwadamin mari ya fara makamin kafa, nan na hau kuka sosai.
 Mahaifinsa ma ya hau dukanshi, yan kauyenmu na waje suna gulma.
 Kuka kuwa kamar zan mutu haka na dinga yinshi.
 Kallansa nai nace "Habubakar ka hadamusu gaskiya ni wlh ba abinda nai."
 Mamaki ne ya kamani da naga ya min dariya ta kasa, anan ne na fahimci shiri ne nashi.
 Nan na shiga yin kuka, shikuwa ya dauka in yai haka mahaifina zaisa a hanashi ni, baisan suma duk sun gaji dani ba, haka suka dauramana aure bayan sallar asuba wanda tunda muke a kauyen ranarce ana ta farko da aka taba yiwa mace aure da asubahi.
 Ranar dukan da na sha ba'a magana, Habubakar kam bakin ciki kamar ya kasheshi.
 Yaso guduwa da asuba amma yaji an rufe kofarsa, haka yana ji yana gani aka hanashi fita.
 A ranar da rana aka kawoni ba tare da wasu kayan daki ba, kuka kuwa nayishi kamar in kashe kaina.
 Shikuwa bakin cikin an hadamu daki daya yasa ya huce a kaina wai ai ni matarsa ce.
 Wannan ita kadaice ranar da wani abu ya shiga tsakanina dashi, sannan itace ranar da aka samu cikin ki.

 Inna ta goge wata kwalla wacce ta zubo mata, tace haka aka sashi dole ya tafi dani, naje gida sallama sai mahaifina cemin yai duk randa na tako garin nan ba tare da Habubakar ba bazai taba yafemin ba, ya kuma fadi haka ne har bayan ransa.
 Innata ma ta kara jaddadamin hakan, haka aka sani a motarshi a dole yaja muka tafi.
 A hanya sai wayarsa yakeyi da Fatima, yana gamawa ya hau ni da masifa akan shi a duniya ba abinda ya sani sai kansa, sannan duk abinda zai aikata sai dai yai abinda yasan zai amfaneshe.

 Haka ya kaini can wata unguwa wanda ya kamamin gidan haya daki daya ya sani, sannan ya bani kudi.
 Tundaga ranar ban kara sashi a idona ba sai dai lokaci lokaci wani yaro yana kawomin kudi wanda nake sana'a.
 Shikuwa sunyi auransu da matarsa suna shan soyayyarsu.
 Gidan hayar kullum habaici sukemin akan cikin shege ne a jikina.
Cikina ya kai kusan wata bakwai abin duniya ya dameni, sai ranar kwatsam Habubakar yazo.
 Baiyi mamakin ganina da ciki ba, sai dai baice min komai ba ya ajiye abinda ya kawo ya fita.
 Ashe gidansu yaje ya sanarma mahaifin Fatima hadin auran dolen da akamai da cikin da nake dashi,  ya karasa maganar yana kuka yana cewa shi in har Fatima tace ya sakeni to ba wani kokonto zau sakeni ne.
 Mahaifinta yace a'a sannan ya sanar dashi ya daukoni ya dawo dani boys Quaters.
 Fatima tasha bori balle da taji inada ciki wanda itama a lokacin tanada ciki.
 Haka ya sata a daki ya dinga lallabata har ta yarda sannan ya mata alkawarin bazai kara shiga dakina da sunan tarayyar aure ba.
 Zinaru kuwa tasha mita sai dai ba yanda zatai saboda umarnine na mijinta.

 Wannan shine dalilina na komawa gidan, mahaifinta shine ya sa miki suna Jalila bayan an sa miki asalin sunan mahaifin Habubakar.....

 Kuka ne ya ci karfin Jalila wacce bakin ciki da takaici sukama yawa............


Goggo tace "Jalila bana ganin laifin mahaifinki domin tun farko ya nuna bayaso, iyayena sune basu damu da rayuwata ba...
 Jalila cikin kuka tace "kowa nada laifi Goggo ta ya za'a maida rayuwarki kamar rayuwar dabba?ta ya ta ya............
Kuka ne yaci karfinta wanda ya hanata magana...


#Oneluv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*No 16*

Kallansa Inna tai sannan ta zare tabaron dake manne a fuskarta, ta ajiye magazine din da take dubawa tace "Me kace?"
 Abubakar ya kalleta cikin jin shakarta yace "Inna abinda akai dazu bai daceba, bana tunanin ya kamata a sa rayuwar mahaifiyarta a tsakiya saboda neman abinda mukeso."
 Inna tai murmushi sannan tace " a yau ne ka fara damuwa da yar taka? Ko kuwa yau ne kake neman kula da matarka?"
 Yace "Inna kinsan ba haka nake nufiba."
 Tace "ya isheni haka nan, sannan daga wannan lokacin ba ruwanka akan duk abinda na sharada akan harkar bikin nan, na dauka kaine ka sanar damu da matar da abinda ke cikinta duk baka sansu? Na dauka kaine ka nuna mana Fatima da 'ya'yanta ne kadai abinda kake so?"
 Yace "Inna......"
Tace "ya isheni haka nan."

 Mumy cikin rashin jin dadi tace "Inna me yasa kike san canza maganar mutunci zuwa rashinsa? Kinfi kowa sanin Abban Yasmin ba haka yake nufi ba, ko ni banji dadin abinda kika aikata ba dazu, yanzu da tsautsayi yazo da mutuwa fa?"

  Inna tace "kin min shiru ke kuma ko kuwa?"
 Mumy tai shiru, Inna ta kalli Abubakar tace "zanyima tambaya ta farko kuma ta karshe akan harkar Jalila, da ita da company dinmu wanne kake ganin yafi cancanta a ceta?"
 Dady ya kalleta jiki a sanyaye, tace "ina jinka."
 Yace " ba dogon nazari Inna kinsan company yafi, sai dai......."
 Tace "magana ta kare, daga yanzu kuma  daga kai har Fatima sai ku bar komai a hanuna, yarinyar nan dai ba gidan yankan kai zamu kaita ba, ba gidan yan shaye shaye ko talakawa zata ba, mezaisa kudinga haka?"


  Dady da Mumy sukai shiru, can tace "ina takardar asibitin?"
 Dady ya zaro a aljihu ya mika mata, nan suka fito.

 Dady na shiga daki ya zauna a bakin gado ya shafi fuskarsa sannan yai wani irin ajiyar zuciya.
 Kusa dashi Mumy taje kusa dashi ta zauna, tasa hannunta a kafarsa.
 Hannunsa ya sa ya zare hannunta daga jikinsa yace "Fatima duk yanda naso nai tunani akan abin nan i think this is not right."
 Hannunsa ta kamo tace " let us save the company first, in komai ya daidaita sai musan ya zamuyi da Jalila, karka damu."

  Kai ya daga alamar gamsuwa, sannan ta jawoshi jikinta ta rungume.
 Shiru yai yana tunani, tabbas company dinsu shine darajarsu sai dai idanun Jalila sun tsaya mai a rai.

 *********


  Yau duk yanda taso tai bacci ta kasa, juyi kawai take tana kara karanto rayuwar mahaifiyarta, tabbas dolene yanzu ta dau damarar taimakon mahaifiyarta, insha Allahu yau ne rana ta karshe da Mahaifiyarta zata zubar da hawaye, tunda a tsawon rayuwarta ta kula rabi na bakinciki da zubar da kwalla ne, sai dai ta yaya zata temaki mahaifiyarta?

  Hawayenta ta share, kalaman Inna ne suka sake dawo mata, haka tai ta juyi har batasan sanda bacci yai gaba da ita ba.

******

 Washegari Ummy bayan anyi sallar azahar ta fito da lefe dan kara dubawa ita da yan uwanta, Ameera na ta zungurin Aina'u dan tasan Aina'u na san Hassan.
 Aina'u tai murmushi kawai ta mike tai ciki.
 Hassan kam dama tunda ya fara jin hayaniyar mutane ya bar gidan, da Sagir akai ta hidimomin.

 Bayan la'asar aka kawo lefe gidansu Jalila, yan uwan Mumy me suka karbi lefen, ganin uban kayan da aka kawo, dan akwati set biyu aka kawo masu dan karen kyau da tsada, sannan kayan dake ciki, ba'a magana, yan uwan Mumy sukai ta mata fada akan ta bark dan masu kudi yaso yar da ke zaune a gidansu a maimakon yarta, in taji haka murmushi kawai take sai tace wai ai so ba ayi masa dole.

  Haka yan kawo lefe suka tafi bayan an tsaida biki sati biyu.
 Ameera ce ta sanar ma Mumy cewa Ummy tace angon zai zo gobe dan yaga Amarya.
 Ana watsewa Mumy ta hau sama da sauri ta sanarma Inna.
 Ganin abin bai damu Inna ba tace "Inna kina tunanin Jalilan zata yarda taje?
 Inna tace " ki tura mota a daukomin Jalila zanyi magana da ita."
 Mumy tace "me zakice mata?"
Inna tace "ba ruwanki, ke dai ki yi abinda nace."

  Mumy ta mike ta fita.
 Jalila na zaune duba dan karatun da Goggo ta d'ora mata na islamiya, dan itama Goggon ba wani nisa karatun nata yai ba.
 Goggo na kwance tana bacci, dan da safe sai da aka tsaga kafarta akai mata aiki, aka daye fatar gun aka wanke.
  Amsa sallama tai sannan ta kalli kofar, Sultan ne ya shigo ya ajiye kular abinci sannan ya kalleta yace "ya mai jikin?"
 Tace da sauki Sultan.
 Yace "Inna na san ganinki."
Tace "akan me?"
 Ta fada tana kallan Goggo, ganin tana motsi yasa ta mike da sauri ta kamo Sultan suka fito, tace "akan me?"
 Yace "ban sani ba wlh, amma jiya dai naga mata sunzo da akwatuna, naji kuma ana cewa naki ne."
  Tace "Mene?"
 Shiru yai ganin yanda tai, yace " menene? Baki sani ba?"
 Idanunta ne ya ciciko tace "Sultan zaka iya zama agun Goggo naje na dawo?"
 Yace " ba matsala."
Tace"nagode Sultan, dan Allah ko ta tambaya kace mata naje gida dauko kaya ne."

 Ya daga ai.
Mota ta shiga drivern ya ja, tunda ta shiga jikinta ke rawa har suka isa.
 Haka ta fito da kyar ta shiga cikin gidan.
 Yasmeen na falo ita da Mumy, gaishesu kawai tai ta wuce.

  Inna na zaune ta shiga, sai da ta zauna sannan ta gaisheta.
 Bata amsa ba ta ajiye mata farar takarda a gabanta.
 Jalilata kalleta tace "Na menene?"
 Inna tace " duba ki gani."

 Jalila ta sa hannu ta dauka, receipt ne da aka bada a cashier, ga kuma tambarin asibitin Standard a jiki.
 Kallan Inna ta sake yi, Inna tace " Bakiyi makaranta bane?"
 Jalila ta kara kallan takardar, kudi ne zunzurutu wanda aka biya, na daki da kuma na aikin da aka mata da na treatment, sa dai bataji su a gunsu kudi ne mai yawa.

 Kallan Inna ta sakeyi dan bata fahimci me takesan nuna mata ba.
Inna tace takardar kudin da muka kashema Mahaifiyarki ne.
 Jalila tace "na gani angode Allah ya saka....."
 Inna tace " Biya zakiyi."
 Jalila cikin rashin fahimta tace "bangane ba."

 Inna tace "kina tunanin kina zaune a gidan mu, mun saki a makaranta, mun kula dake da mahaifiyarki, mun biya mata wannan kudin, sannan kice ba zakibi umarnin mu ba?"

  Jalila tace "Inna......."
 Inna ta katseta tace "yaya? Kina da kudin da zaki biya mu dai ko?"

 Idanunta ne suka kara firfitowa ta fara zubarda hawaye, Inna tace " in har kinfi karfin bin umarninmu sai mu zare hannunmu daga rayuwarku sai inga yanda zakuyi, ina fatan kinada inda zaku zauna da kuma kudin da zaki cigaba da kula da mahaifiyarki harta warke."


  Jalila tasa kuka tace "Inna dan Allah kiyi hakuri, Goggo tana neman kulawarku dan Allah ki yafemin."
 Inna ta mike tace " tashi ki fita, na baki daga yau zuwa gobe da safe inhar baki bi umarnin mu ba, zansa a koreta daga asibitin, sannan kubar gidan mu bayan kin biya kudin."

  Jalila ta zauna tana wani irin kuka mai ban tausayi, Inna tace "tashi ki fita."
Mikewa tai tana hawaye ta sauko.
Yasmeen na mata magana ko kallanta batai ba ta fito tana hawaye.
 Bangarensu ta nufa kawai ta zube akasa tana kuka, ya zatai? Uncle ne ya fado mata, da sauri ta janyo jakarta ta zaro wayar nan.
 Ganin irin kiran da yai mata yasa ta saurin danna kira, ringing take ta yi ba'a daga ba.

 Shikuwa a lokacin Ummy ta nemi ya rakata store, sai daya shiga mota ya tuna yabar wayarsa a gida.
 Sai dai ganin ba wani dadewa zasuyi ba yasa ya fita kawai.

   Kuka ta shiga yi sosai da taga bai daga ba, kira take tayi ba kakkautawa.
 Ganin ba dama ta cila wayar kan gado ta fito rike da jakarta.

 Tana tafe tana kuka, drivern na mata magana ko bi takansa batai ba tai waje.
 Tana tafe tana wani irin kuka.

  Sai da ta mike layinsu sosai, taje tsalakawa ta titi shi kuma ya taho saura kiris ya bugeta, wani irin burki yaja da karfi sannan ya kifa kansa da sitiyari.

 Jikinsa ne ya shiga karkarwa, Jalila kuwa ta dauka karshen rayuwarta yazo har ta tsugunna, ganin bai kade ta ba kawai sai taji wani irin kuka yazo mata.

  Tsananin tsoro yasa zufa ta shiga keto mai, da kyar ya iya fitowa daga motar, kusa da ita yazo yanda yaji tana kuka yasa yaji kansa na wani irin juyawa, dan tabbas ya dauka ya mata illa, dan uwansa ya hango alokacin da matsalar da bazai taba mantawa ba ta faru, numfashinsa ne ya shiga sarkewa, hannunsa yasa a wuyansa yana wani irin abu.

 Jalila ta dago, ganin mutum na neman zubewa yasa hankalinta ya tashi.
 Da sauri ta shiga yin ihun neman taimako.
 Mikewa tai zata nemo mutane, hannu yasa ya riko siket dinta.
 Juyowa tai da sauri tare da tsorata.
 Da kyar yace " ba bige nai ba?"

  Gaba daya ta tsorata dan ta dauka shi aka bige.

 Siket dinta ta fizge ta tsaya tana kallan sa.
 Mikewa yai sannan ya matso kusa da ita, matsawa ta dan yi.
 Ya kara matsowa fuskarsa a hade, kara matsawa tai cikin tsoro.
 Yace " meye dalilinki na tsugunnawa akasan motata da sa mun kuka?"
 Jalila ta kalleshi tace " motarka ce?"
 Yace "tambayarki nake?"
 Ta kara kallan motar sannan ta tuno abinda ya faru da irin mai motar, da alama duk masu irin motar nan basuda mutunci.
 Tace " na dauka ma hakuri zaka bani, tunda kasan na tsorata."

 Baya san magana amma yanda tai maganar yasa ransa ya baci yace " me? Hakuri?"
 Ta daga kai, kallanta yai, harzai sake magana sai kuma naga ya fasa, motarsa ya koma ya shiga ya fizgeta da gudu.

  Jalila ta harari motar, ta cigaba da tafiyarta tana matsar kwallarta.
 Da alama yau gaba daya ranar bakin ciki ce a gareta.



#ONELUV💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*No 17*


 A hankali ta tura kofar dakin, Tana kokarin shiga nurse din na kokarin fita, jiranta tai ta fito maimakon ta shiga sai tabi nurse din.
 Tana gaisheta, Nurse din ta tsaya ta amsa, Jalila ta matso tace " Aunty ya jikin Goggo?"
 Tace "da sauki, ya akai? Kina tsoro ne?"
 Jalila ta goge kwallarta tace " Aunty kina ganin kamar kwanaki nawa zamuyi kafin kafar Goggo ta samu sauki?"
 Tace "maybe 3 to 4weeks"
 Jalila ta zaro ido tace "da tsayi haka?"
 Tace "Umm."

 Jalila tai shiru, Nurse din tace " ba wata tambayar?"
 Jalila tace "in tabar asibitin fa?"
 Nurse din cikin mamaki tace " ta ya za'ai tabar asibitin tana cikin wannan state din? Ko asibitin kuke san canzawa?"

  Jalila ta runtse ido can tace " Aunty kudin ne......."
 Muryar Sultan taji yace "me kike anan?"

 Idanunta ta bude da sauri, Nurse din ta wuce ganin kamar bazata iya magana ba.
 Sultan ya karaso yana kallanta.
 Ya kara cewa "me kike anan?"

  Jalila bakinta ne ya shiga rawa ta kasa magana, Hannunta ya rike yace "meye hakan?"
 Kamar ya tabota kawai tasa kuka, mamaki ya kamashi can yace " Mumy ce?"
 Kai ta girgiza, yace "Dady ne?"
 Nan ma kai ta girgiza, sam bai kawo Inna ba saboda ba kasafai take shiga harkar rayuwar gidan ba, yace "Jikin Goggo?"

  Hawayenta ta share tace "Sultan ya zanyi?"
 Yace "name?"
 Tace "tsakanin rayuwata data mahaifiyata."
 Yace "wace irin tambaya ce wannan, sannan in amsa
kike so ai ke yarinya ce mai kuma lafiya, ita kuwa Goggo ba lafiya ne da ita ba."
 Jalila ta shiga daga kai tana cewa "haka ne, Goggo itace gaba da komai."
 Kallan mamaki ya kara mata, ta kakaro murmushin takaici tace "nagode Sultan."
Leda ya miko mata yace "gashi, Ni bari na wuce."

 Tace "kai kadai?"
 Yace " inada kudi a jikina, nan ya zaro dubu biyu yan dari biyar biyar, mika mata dubu daya da dari biyar yai ya maida dari biyar aljihunsa yace " gashi ko zaki sai wani abin."

 Ta amsa tamai godiya, juyawa yai ya fita, da kallo ta bishi sannan ta goge fuskarta ya tura kofar dakin.

 Goggo na zaune shiru ta shiga, Jalila ta karasa tana cewa "Goggo a zaune kike?"
 Goggo ta kalleta tace "kin dawo?"
 Tace "eh."
 Jakar hannunta ta kalla tace " baki daukon kaya ba?"
 Jalila ta bude baki tace "wayyo, wlh na sha'afa sam, ni fa dama jakar nan kawai naje daukowa."
  Goggo ta kalleta cikin zargi tace " me ya samu idanunki? Abubakar ya miki wata magana ne?"

 Ta zauna kusa da ita tace "Kai Goggo, ni ko ganinsa ma banyi ba."
 Goggo tai ajiyar zuciya tace " sai yaushe zamu bar asibitin nan?"
 Jalila tace "tab aima ki gyara zama goggo, dan wlh yanzu Nurse take cewa sati uku zuwa hudu."
 Goggo cikin mamaki tace "Wannan asibitin mai tsada? Kina tunanin zasu biya mana kudin?"
 Jalila tai murmushin takaici tace " karki damu da wannan, ke dai ki kwantar da hankalinki, kinji dai mai likita yace jiya."

 Goggo tai murmushi, Jalila ta bude ledar da Sultan ya miko mata, ruwa ne mai sanyi faru tace "ruwa kika aikeshi?"
 Tace "Allah sarki Sultan cewa nai ya bani ruwa in akwai, ashe wai babu shine naga ya fita."
 Jalila a ranta tace "dama sai a dinga kawo abinci ba ruwa."

 Haka tai ta kokarin boyema Goggo damuwarta.

 *********


   Sagir na komawa gida ya hau sama dan dauko wayarsa, ganin irin kiran da Jalila tamai yasa hankalinsa ya tashi, nan ya shiga buga mata waya shima, sai dai duk yanda ya kira No Answer kawai ake rubutamai,

  Fitowa yai ya shiga mota ya tafi makarantar su, ba ta nan, ya akai baiyi tunanin amsar address din ta ba? Wai shi yana ganin yasai mata waya, kwatancen gidansu bazai zamarmai wahala ba.
  Kai ya shafa cikin takaici, ina ne gidansu? Haka ya dawo gida jiki a sanyaye.

  Abba ne bayan Magrib ya shiga d'akin Hassan, yana zaune rike da littafi a hannunsa yana karantawa, Jornal ne.

 Yana ganin Abba ya rufe littafin sai dai baiyi motsi ba daga inda yake bai kuma yi magana ba.
 Abba ya shiga ya zauna kusa dashi, Shiru ne yadan ratsa dakin, can Abba yace " Me zakayi gobe?"
 Hassan ya mai kallan mamaki, me zaiyi? Shi daka rayuwarsa ai kullum iri daya ce, Abba ya kalleshi yace "Gobe da yamma ko bayan magrib kuje kai da Sagir ku ga yarinyar."

 Kallan Mahaifinsa yai cikin mamaki yace " inje ince mata me?"
 Abba yace "kaje ku gaisa ta ganka, ka ganta."
 Hassan yai shiru can yace " Ai wannan tun a farko ya kamata kuce naje, Abba abinda ya kamata kuyi tun farko kenan, ta ya zaku sa rana ba tare da yarinya ta ganni ba?"
 Abba yace "Hassan bakasan me nai ba akan samar maka abokiyar zama."
 Hassan ya kalleshi yace " me kake nufi?"

  Abba ya mike yace "Ka taimaka gobe kuje kai da Sagir, wannan rokone uba yake ma dansa."

 Hassan yai shiru baice komai ba, fita Abba yai tare da rufe mai kofa, shiru Hassan yai yana tunanin wannan abun, shi gaba daya ya kasa hasko rayuwarshi da wata mace, macen ma wacce bai sani ba.


  **********

  Wajen karfe d'ayan dare ta mike daga kwanciyar datai dan dama ba bacci take ba, fitowa tai daga dakin ta zauna a kasan matatakalar benin, shiru tai tana tunani, ya zatai? Gaba daya duk yanda taso ta canza shawarar dake zuciyarta in ta auna lafiyar mahaifiyarta wacce ta rayu cikin bakin cikin da namiji bataji zata iya canza wata shawarar, rayuwar mahaifiyarta itace gaba da komai a rayuwarta.

  Kanta ta kwantar akan gwiwowinta tana tunano rayuwar da sukai da Sagir da irin rayuwar da tai fa mafarkin yi dashi.
 Wasu zafafan hawaye ne suke zubo mata, a wannan rana bacci baiga idanunta ba.

 Wajen karfe 1o aka kawo musu abinci sannan drivern yace mata "Inna na jiranki."

  Ta fahimci me yake nufi, kallan Goggo tai tace "Goggo zanje na kwaso kayan, akwai abinda kikeso?"
 Nan ta fada mata abubuwan da takeso ta taho mata dashi, har zata fita sai ta dawo da sauri ta rungume Goggo idanunta na neman kawo kwalla.
 Goggo tace "Jalila menene? Badai jiya karya kikamin ba? Ance miki wani abun a gidan ko?"
 Dagowa tai tana dariya tace "Goggo kenan, kema kinsan bana iya boye miki komai a dunia, me zaisa in ki sanar dake? Inaji fa ganin kin kwanta yasa jikinsu yayi sanyi da zancen."
 Goggo tai tsaki tace " duk yanda naso in zauna dasu lafiya in har suka sake suka miki zancen hadin aure wlh sai sunsha mamaki."

 Jalila tace "ni inada ke a duniya me zaisa inji tsoro Goggona?"

 Murmushi sukai a tare, Jalila ta juya ta fara takawa a hankali, daga sanda tasa kafa tabar dakin nan ta shiga motar ta tabbatar rayuwarta shikenan ta canza, bazatai dana sanin fita daga dakin nan ba kuwa?
 Ai dana sani tun kafin ta fita tasan rayuwarta lalai tana cike da danasani, domin kuwa batasan wani irin zama zatai ba.

  Sai data kai kofa ta juyo tama Goggo murmushi sannan ta fita.
 Mota ta shiga tai shiru tana kallan waje, mutane take ta kallo kowa yana nasa rayuwar, haka har suka isa gidan.
 Sai dayai kusan minti biyar da parking sannan ta bude kofar ta fito.

 Inna ta kalli Mumy dake leken window ta dakinta, Mumy da sauri ta juyo tace "ta iso kuwa Inna."

 Inna ta kalli Dady tace " sai ka kyautata mata kai kuma, ka tabbatar bata nunama mijin nata tsana ba."
 Dady yace "to."
 Mumy ta matso tace "Dadyn Yasmeen let us try our best."
 Murmushi yai mata na dole sannan ya mike.
 Inna tace " in zaku siyo ragowar kayan gida kudinga daukanta a asibiti."
 Yace to, sannan yai waje.

 Yana isa falon tana shigowa, tsayawa tai tana kallansa, wai mahaifinta? Wanda hakkinta ke rataye a wuyansa?
 Dady ne ya matso kusa da ita, ya sa hannu a aljihunsa yace "Jalila ya mai jikin?"
 Kallansa kawai take batace komai ba, sai idanunta da sukai ja, bata amsa mai ba.
 Yace "me kike tunani?"
 Kai ta girgiza alamar bakomai tace " kawai ina tunanin yanda Allah ya rataya wa uba hakkin dansa a wuyansa ne."
 Dady yai shiru, zaiyi magana Mumy ta karaso tace "Jalila, yanzu muke shirin zuwa asibiti."
 Jalila tai shiru a ranta tace "tunda kunsamu abinda kukeso ai dole."

  Nan ta haura sama batare da tace komai ba.

 Inna na zaune sai data zauna sannan tace "YA YA? Kin yanke shawarar?"

  Jalila ta kalleta dan tana tsananin shakkarta ta daure tace "Amma kimin alkawari biyu."
 Inna tace "inajinki."
 Jalila tai shiru kafin tace " da farko zaku kula da Goggo, zaku samo mata wacce zata dinga taimaka mata, sannan na biyu karku fada mata komai har sai ta samu lafiya."

 Inna tace "duk ba matsala bane, Jalila ta kalleta a ranta tace me zata samu da take bin ta kowace hanya dan ganin ta min auran nan?"
 Dagowa tai da sauri datai tunanin wani abu tace "Inna tsoho ne?"

 Inna tace "a'a saurayi ne"
 Jalila cikin tsoro take kallanta, anya? Me suke tunani? In har ba wata matsalar mai zaisa su bar yarsu su zabeta?

  Inna tace " ki tashi ki sauka kasa, bayan kinyi aanka kinci abinci ki shirya, ance bayan la'asar zaizo."

 Jalila ta mike ta fito zuciyarta fal da tunani kala kala.
 Bangarensu kawai ta nufa ta kwanta, karar wayarta taji.
 Da sauri ta jawota, ta daga.
 Muryar Uncle ne ya daki kunnenta, ji tai wasu zafaffan hawaye sun zubo mata.
 Sagir yace "Jalila ina kika shiga haka? Ba dai wani abin bane ya faru ko?"

 Kasa magana tai, hankalinsa ne ya tashi.
Ya shiga tambayarta, can ta daure tace "Uncle yaushe zamu hadu? Akwai maganar da zamuyi dakai."
 Yace " ko yanzu ma in kinaso."
 Tace "a'a banda yau."
 Yace "nima na manta yau zan raka yayana wani gun, gobe fa?"
 Tace " to, Allah ya kaimu, zan kiraka goben."
 Haka kawai tace ta kashe wayar saboda yanda taji zuciyarta ta karye.
 Tana kashewa kuwa tasa kuka.
Shikenan Uncle, soyayyar da muke ma juna ashe anan zata tsaya.........

 Sagir na kashe wayar shima yai shiru, tabbas akwai abinda ke damunta......


#Oneluv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*No 18*


   Sake kwanciya tai, ta kwantar da kanta akan katifa, itada take burin auren soyayya? Yanzu me kenan?
 Idanunta ta bude a hankali, tana kallan dakinsu, rayuwarsu da mahaifiyarta ne ta shiga dawo mata, rayuwace wacce sukai ta talauci da tsana, sai dai a tsakaninsu rayuwace mai cike da dinbin kewar juna da shakuwa, zata iya rayuwa ba tare da Goggonta ba?
 Haka tai ta saka da warwara har bacci yai gaba da ita.

  Sai wajen karfe uku ta farka, shima mafarki ne ya tasheta wanda ya sata razana da sauri, sai dai me? Duk yanda taso ta tuno wani mafarkin tai ta kasa sam, wayarta ta dauka da sauri ta yima Sagir text.
 Uncle please mu hadu a makaranta ko na minti goma ne, i really want to talk to you.
 Ajiye wayar tai ta mike, gaskiya dole ta sanar ma Uncle abinda ke faruwa taji me zaice.

  Mikewa tai ta kalli kayan da aka kawo mata ta saka, nan tai wanka ta saka ta fito sidif sidif tai waje.
*****

 A can gidansu Hassan kuwa, Sai da Ummy ta mai magana ya kimtsa, da kananan kaya ya saka tasashi ya koma ya sako manya kaya.
 Fitowa yai daga dakinsa sanye da dakakiyar shad, cyan color wanda mukafi sani da bluegreen, shadar ta mai kyau sosai, dan shi dama bai fiya sa manyan kaya ba, daga kanana sai jallabiya, Abba ne baya gajiya da dinkamai.
 Ameera da kanta ta d'aukomai hula ta mikamai.
 Hassan kallansu kawai yake dan bayasan magana ya amsa.
 Takalmi ya saka sannan ya sauko kasan, Sagir sai janshi yake da tsokana wai kai Yaya gaskiya wannan kyan kamar ranar auranka.

 Hassan ko kallansa baiyi ba bare ya tankamai, shima Sagir din manyan kaya ya saka.
 Ummy ta jawo Sagir tace "Sagir ka taimaka kar a samu matsala, kasan halin yayan naka."
 Sagir ya daga kai yace "Karki damu Ummyna, ki bar komai a wuyana."

 Murmushi tai tace "godiya nake dan lele na."
 Haka suka fito kowa yana farinciki, Ummy ta mikama Sagir gift din da zasu kai mata.

 Aina'u na jikin dakin Ameera tana kallansu, komawa tai cikin dakin ta kwanta ranta ba dadi.

  Motar Hassan suka nufa, Hassan na shiga ya rufo kofa, Sagir ya zagawa ta bangaren kusa da driver yana cew "Yaya na dauka da Mamman zamuje saboda shi yasan gidan.

 Jiyai kofar a rufe, cikin mamaki yace "Yaya me kenan?"
 Hassan ya zuge glass dinsa yace " ka shiga motar ka Mamman ya jaka, ni daga can wani guri zanje."
 Sagir ba tare da tunanin komai ba ya juya ya shiga motar sa shida Mamman.

   Haka suka fita da motoci biyu, su Sagir na baya shi yana gaba.
 Suna tafe suna hira sam hankalinsa baikai kan wayarsa ba domin yanzu harkar yayansa ce a gabansa baya tunanin akwai wani abu da zai ratsa wanda zaiyi distracting dinsa.

  A kofar gidan Mamman yasa signal sannan aka bude mai gate ya shiga, maimakon Hassan ya shiga kawai sai yai gaba.

  suna parking Sagir ya juya baiga motar Hassan ba, mamaki ya kamashi da sauri ya fito wajen gidan yana lekawa, sai dai ba shi ba labarinsa.

 Haka suma mutanen gidan, dan tun lokacin da Mumy ta aika Jalila tazo ta karasa shiryata, taki zuwa hankalinsu ya tashi, ta fito ta duba bangarensu bata ganta ba.

 Hankalinsu yayi tsananin tashi dan sun duba ko ina basu ganta ba, Mumy kam kamar tai ya ya.
 Nan Dady ya fito nemanta.

  Can ita kuwa tana tsaye a inda suke haduwa, tana duba agoggo, taji ance bayan la'asar zaizo shiyasa take sauri Uncle yazo suyi magana ta koma kafin hudu da rabi.

  Agoggon hannunta ta kalla, karfe 4:30jiki a sanyaye ta juya, lalai yanzu wata zuciya tana sanar da ita Uncle bai damu da ita sosai ba, wata zuciyar kuma neman yi masa uzuri takeyi.

 Haka ta tako jiki a sanyaye ta tsaya akan titi dan neman adaidaita.

 Tana tsaye mota tai parkin ta bayanta kadan, kallan motar tai dan ta dauka uncle ne, batai ma tunanin motar waye ba kawai ta nufi motar.
 Shikuwa yanda tazo saitinsa ne yasa cikin mamaki yake kallanta.

  Sai dataje jikin kofar sannan tai tunanin ba shi bane, lalai zuciyarta a matse take da san ganin Uncle, baki ta turo sannan ta juya jiki a sanyaye.
 Yana zaune a ciki yana kallanta, da yake motar tint ce itakam bata ganshi ba.


 Haka ta tsaya a titi zuciyarta duk ba dadi, sai kara leka hanya take ko zata ganshi.

 Yana kallanta harta samu mota ta shiga, kai ya girgiza sannan ya kashe motar, yasa kansa akan kujera yana tunani, shikam ta ina zai fara kallan mace da sunan zance? Sannan in tsautsayi yasa matsalarsa ta tashi fa?
 shikam hankalinsa ya kasa kwanciya, ya san kuma Sagir zaisan me zaice mata.

  Haka ta samu adaidaita ta hau jiki a sanyaye, ajiyar zuciya taitayi a cikin adaidaitar har suka isa, tana kokarin biyan kudin adaidaitar su kuma suka fito daga cikin gidan.

 Motar tabi da kallo, taga mutane biyu a zaune sai dai hankalinta ba'a kansu yake ba.

 Haka ta taho a hankali ta tura gate din gidan.

  Mumy ta ganina waje itada Dady suna magana, suna ganinta suka juyo suka zuba mata idanu.

 Dady a zuciye ya fara takowa, ganin haka yasata ta tsorata.
 Hannu ya daga zai shara mata mari, da sauri ta runtse idanunta, tsayawa yai sannan ya kalleta rai a bace, yatsa ya nuna mata yace "ni zaki cima mutumci?"

 Mumy ta matso ta sauke mai hannu tace "Dadyn Yasmeen meye hakan?"
Kallanta yai yace "yanzu da badan shima dalili ya hanashi zuwa ba fa?sannan da kanin nasa bai fahimcemu ba fa?"

 Mumy ta kalleshi tace "tunda dai komai yazo da sauki ba shikenan ba?"
 Yace "in Inna taji fa? Me kike tunanin za'ace?"
 Mumy tace "sai muce mata ta ganshi sun gaisa harya tafi."

 Dady ya kalleta cikin jin dadi, wanda baisan  a ranta ba wai damuwa da Jalilan tai ba balle tace batasan a mata fada ne, tayi hakan ne dan abin ya kara karfafa.
 Jalila ta kalla sannan tace "Hassan din wani uzuri mai karfi ya tasomai a hanya bayan sun fito, dole ne yasashi kin zuwa, shiyasa ya turo kaninsa.

 Jalila ta dan tabe baki kadan, dan itakam ba damuwarta bane.
 Mumy ta rike hannunta tace "muje ciki ko?"

 Jalila tace "A'a Mumy asibiti zan koma."
 Mumy ta jinjina kai tace "bari mu kaiki."

 Jalila fuskarta dama a daure take tai bangarensu.
 Kayan da Goggo tace ta dauko mata ta dauko sannan ta fito.

 Suna tsaye suna ta wani abu wai su a dole mata da miji, ita Mumy sai wani shagwabewa take, haushi ya kara kama Jalila a ranta tace "mutum ya girma amma jinsa yake kamar yaro."
 Ta gabansu tazo ta wuce, Mumt ta riko hannunta tace "Jalila tare zamu tafi."
 Jalila tai shiru tana kallan Dady.
Mumy ta bude mata baya sannan ta shiga, ita kuma ta shiga kusa da Dady.
 A hanya tayi shiru tana kallan waje, wayarta ce ta fara ringing, da sauri ta zarota.

 Uncle? Da sauri ta daga tace "Uncle!"

  Jalila i am............
 Bata gama jin mai zai fada ba, Dady yai wani irin parking, wanda ya tsoratata, sam ta mantada mutane a motar.

 Mumy ta fizgi wayar tana cewa "Jalila me kenan?"

 Jalila a tsorace ta kalleta, sunan da ke jiki ta kalla MINE? Nunawa Dady tai ya kashe wayar yace "uban wa ya sai miki waya?"
 Idanunta ne suka firfito tai shiru.
 Mumy tace "Jalila zance kike a bayan idanun mu?"
 Jalila ta kallesu sai dai ta kasa magana, cikin salo Mumy tace "shiyasa take neman bijerawa maganarka kenan? Lalai samarin zamani sun iya siyan zuciya, da har zasusa 'da ya bijirema mahaifinsa."

 Dady cikin takaici yace "Uncle? Malamin ku ne kenan? Dama abinda kike a makarantar kenan?"

 Jalila da hawaye suka fara zubo mata tai shiru tana kallan ikon Allah.
 Dady yace "wato ina miki magana ma kinfi karfin amsawa ko?"
 Jalila tace "ba haka bane Dady."
 Mumy tace " Jalila yaushe kika zama haka?" 

 Jalila jitai hawaye suna gudu a idanunta, wannan shine a dakeka a kuma hanaka kuka.

 Haka tana kallo Dady ya zare sim din ya karyashi sannan ya cilar waje, sannan ya ajiye wayar cikin motar sa.

  Jalila tana kuka tana cewa "dan Allah dady ka barni ko magana daya muyi."
 Dady ko kallanta baiyi ba ya ja motar sukai gaba.
 Mumy tana cewa "lalai Jalila wato ya baki kima saurayinki magana?"

 Juyawa tai tana kallan window tana wani irin kukan takaici.


#ONELUV💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*No 19*


  A kofar asibitin Dady yai parking sannan sukai shiru a cikin motar, Jalila tasa hannu. zata bude kofar Dady yace "Jalilah!"
 komawa tai ta zauna tana kallansa tare da amsawa.
 Dady ya juyo yace "Fatima dan bamu guri."
 kallansa tai kamar zatai magana sai naga ta fasa, kofar ta bude ta fita sannan ta nufi cikin asibitin.

 Jalila ta kalleshi sai dai gani take kamar shiryawa sukai, Dady ya kalleta sannan yace "Habiba, na tabbatar kina ganin kamar ban damu dake ba wanda a gaskiyar magana ba haka bane, a duk inda uba yake to lalai tabbas ne yaso abinda ya haifa, kallan mamaki tamai dan tabbas da ace Goggo ba ta bata labarin yanda tai rayuwa dashi ba tabbas zata yarda yana santa sannan zata iya tunanin wani abun akamai daya hanashi nuna mata so.

 Dady ya kara kallanta yace " kinajin haushi na ko?"
 kanta na kasa batace komai ba, yace " Jalila wannan auran da za'a miki ba wai rayuwar mahaifiyarki kadai zai taimaka ba, ni kaina kin ceci ni sannan kin taimaki rayuwar yan uwanki."

 Dagowa tai ta kalleshi cikin rashin fahimta tace " Dady ba aure ne tsakaninku da Goggo?"
 kallanta yai yace "me kike tunani?"
 Tace " amsar da zaka bani ita zata bani ikon ajiye komai dake raina."
 Shiru yai yana kallanta yace "Jalila yanzu ba zancen wani aure da rashinsa bane a gabanmu, inhar kinason Inna ta taimaki mahaifiyarki dolene sai kin amince da auran nan, sannan in fada miki gaskiya ko ki yarda ko karki yarda Inna sai ta aura miki yaran nan."

 Idanunta ne suka fara zubar da kwalla tace "Dady kaine mahaifina ko Inna?"
Cikin fada yace "Wai meke damunki ne?yaushe kika fara gardama haka? kina tunanin lalabakin da nakeyi zai baki damar bijirema abinda mukesanki dashi ne? inhar kinasan farincikin uwar data sha wahalarki, kina neman lafiyarta to kibi abinda muka ce miki sannan karki kuskura ki fada mata zancen nan."

 Kallansa kawai take tana zubarda hawaye, faduwar da Goggo tai kenan su riba suka samu da rashin lafiyarta? tunda batasan dame zasuyi threatening dinta ba.

 Dady ne yace "muje."
 A hankali ta tura kofar ta fito, jitai kafafunta na rawa hakan yasa ta rike kofar motar.
 Haka suka shiga cikin asibitin yana gaba tana baya.

********
 A cikin asibitin kuwa Goggo ce tana kwance tana tunanin Jalila da bata dawo ba,Mumy ta turo kofar dakin.
 Goggo ta kalleta sannan ta gaidata, dan dama tunda sukazo gidan haka suka saba, Goggo ce ke gaidata.
 Mumy ta zauna a kan kujera sannan ta kalleta tace "Ya jikin?"
 Goggo tace "Da sauki, tare kuke da Jalila ne?"
 Mumy tace "eh suna tare da mahaifinta ne yanzu zata shigo."

 Da sauri Goggo ta canza fuska tace "me yake ce mata? ba dai zance........."
 Mumy ce ta katseta tana murmushi tace "Kai maman Jalila, ba wannan zancen bane, ai wannan maganar an ajiyeta sai kin samu lafiya, mun isa mu yanke hukunci ne mahaifiyar yarinya na asibiti?"

 Goggo ta mata kallan zargi, Mumy tace "duk rashin kirkirnmu ai bamu isa yi mata aure dai kina asibiti ba, sannan mahaifinta ma har fada mukai akan zancen nan, ya hana a kara tada shi."

 Jin hakan ne yasa Goggo tadan saki jiki har tace "mun gode kuna ta dawainiya."
 Mumy a ranta tace "Yarki dai nayi.
Amma a fili tace " Karki damu, ke dai ki kwantar da hankalinki ki samu lafiya, kinga dai irin kudin da ake narkarwa a asibitin nan."

 Turo kofar da Dady yai ne yasa ta dan canza fuska wai ita a dole fishi takeyi.

 Jalila ta shigo ta tafi kusa da Goggo ta zauna.
 Dady fuskarnan a hade yace "Ya jiki?"
 Tace "Alhamdulila."

 Kusa da ita ya matso ya ajiye mata kudi sannan ya juya.
 Mumy ce ta mike tace "Sai an kawo abincin dare."

 Goggo tace "Angode."

 Haka suka fita, Jalila ta kwanta a kafadarta.
 Goggo tace "Menene?"
 Jalila ta kara gyarawa tace " Kawai dumin Goggona nakesan ji."

 Goggo tai murmushi tace "wani abun ya faru ne?"
 Tace " me zai faru? Ni fa bangarenmu naje na kwanta, hardasu barci."
 Goggo tace "kin kyauta, ki dinga zuwa kema kina hutawa, zaman asibiti ba dadi sannan na kula bakya samun barci sosai."
 Jalila ta daga kai tana murmushi.
 Goggo ta miko mata duka kudin da Dady ya ajiye tace "irga."
 Jalila ta irga tace "ni Goggo dubu ashirinn nake gani."
 Goggo cikin mamaki tace "dubu ashirin? Me zamuyi da kudi haka? Sannan ni tunda nake a rayuwata ban taba rike kudi mai yawa haka ba."
 Jalila a ranta tace " gashi kin rike yau tunda suna san saida farincikin yarki."

Goggo tai shiru aranta tana mamaki........



***********

  A can gidansu Hassan kuwa, Sagir sai karya yai akan sunje sannan shima yayan ya ganta.
 Ummy duk ta matso dasan jin labari tace "Sagir kana tunanin ta mai?"
 Yace "kinsan halin yaya baice komai ba amma ga dukan alamu ta kwantamai."
 Ummy tai murmushi tace "ni kaina nasan zata kwantamai dan wannan inaji a jikina alheri ne atattare da ita."

 Abba yai dariya yace "Ah Alhamdulila lalai yau hankalinmu ya kwanta."

  Hassan sai wajen magrib ya dawo, yana shigowa Ummy ta fito cikin farinciki tace "Hassan ka dawo?"
 Kai ya daga kawai ya nufi sama.
 Yana shiga daki, kafin kofar ta rufo Sagir ya shigo, yace "Yaya dan Allah me ka aikata dazu? Ta ya zaka tafi ka barmu a gidan yarinya?"
 Hassan bai tanka mai ba sai rigarsa da ya cire dan dama ya gaji da ita.
 Sagir yace "Amma Yaya wlh ba dadi, bakaji yanda na ji kunya ba, gashi an hada maka abinci kala kala.

 Hassan ya juyo ya kalleshi, Sagir yace "Ya Hassan."
 Hassan ya matso kusa dashi yace " Sry." Ya juya yaja towel ya shiga toilet.

 Sagir ya bishi da kallo sannan yai ajiyar zuciya.
 Juyawa yai ya koma d'aki, dan shi yau abin duniya shima ya dameshi.

 Baiga Jalila a makaranta ba daya koma sannan duk yanda ya sake kiranta a waya sai acemai a kashe take.

*£*£*£££**

 Ta kowani bangare shirin aure sukeyi, Sagir ya dawo kasa an kara gyara musu saman, sai dai duk yanda ake shirin auren nan Amarya da Ango ko a tsikar jikinsu, dan ita tana asibiti gun mahaifiyarta, yanzu ko gidan ma bata zuwa, kayanta kala uku data taho dasu shi take ta sawa.
 Sam batasan auran sati biyu aka saba itadai kawai tasan batasan zuwa gidan ne ma bare a mata zancen.

 Kudin da Dady ya basu shi suke dan kwalam dinsu, sai abinci da ake aiko musu, kaf gidan ba wanda ya sake zuwa duba Goggo sai Sultan da yake zuwa duk bayan kwana biyu, sannan ita ko lefen ma da aka kawo basu nuna mata ba, ita kuwa dama ba wannan bane a gabanta, bakincikinta inda zataga Ya Sagir.
 Zuwanta makarantarsu uku amma ba ta taba dakar sa'ar ganinsa ba, har ta hakura.

 A yau da yazone wanda kwananta 10 kenan da zuwa gida wanda yai daidai da kwana 11 da kawo lefe.
Yau saura kwana uku kenan bikin ta amma bata sani ba.
 Tana zaune bayan sunci abincin safe Sultan yazo shi da wata yarinya wacce batakai Jalila ba, gaida Goggo yai.
 Jalila ta kalleshi tace "Sultan wannan fa?"
 Yace "itace zata dinga tayaki zama, mai kula da Goggo."
 Gabanta ne ya fadi dan tabbas ta fahimci me hakan yake nufi, yace "sannan Dady yanasan ganinki yanzu."

 Jalila tai yake tana kallan Goggo, Goggo cikin mamaki tace "Allah sarki angode, kinga yanzu sai ki taimaka inkinje gida ki huta ki bari sai gobe ko jibi kya dawo tunda kinga jikin nawa ai da sauki sosai, ni da zasu sallamemu ma da naji dadi."

 Jalila ta mike jiki a sanyaye, yarinyar ta gaida Goggo, Goggo ta amsa fuska a sake tace "ya sunanki?"
 Zulai yarinyar ta fada.
Jalila ta matso kusa da Goggo ta rike hannunnta idanunta suna neman canzawa tace "Goggo sai na dawo."

 Goggo ta jinjina kai tace "ki bari sai gobe ko jibi."
 Tace to.

 Haka suka fito ta shiga mota.

 Suna fara tafiya ta kalli Sultan tace "Sultan wani abin ya faru ne?"
 Yace "ban sani ba sai dai na tabbatar an kusa auranki tunda yanzu ma gidan da mutane, sannan naji Mumy na cewa an turo wai yau kanin Ango zaizo dan kuyi magana, tun jiya yaso zuwa to sai sukai tafiya, bandai san maganar da zakuyi ba."

  Gaban Jalila ne ya shiga faduwa, a hankali hawaye suka fara zubo mata, kanin ango? Zancen me? Ankusa bikinta? Da wa? Wad'an nan sune suka sake ingizata ta shiga zubar da hawaye.





#Oneluv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*No 20*


   Suna isa gidan ta fara gaida bakin dake gidan, duk yan uwan Mumy ne dan dama a iya tsayin rayuwarta bata taba ganin dangin mahaifiyarta ba, dan duk yawansu ba mai nemansu, sannan shima Dadyn baya kuma san su nemeshin.
 Shikuwa danginsa dama Mahaifinsa ya dade da rasuwa, sai mahaifiyarsa wacce dama ita kam bata san auransa da Goggo sai Mumy, takanzo lokaci zuwa lokaci, abinda zai baka mamaki shine, ita kadai take zuwa sai kanwarsa wacce dama ita fitsarariyace.
 Ko sau d'aya Mahaifiyarsa bata taba cewa Innan Goggo tazo suje muhalin yarta ba, Jalila na shekara 10 Allah ya d'auki ran mahaifiyar Dadyn.
 Shikadai yaje, dan sai daya dawo daga gaisuwa ya aiko mata da tsintsiya, kuka da gyada wai inji babarta sannan tasan yaje, sai Jalila data jiyo gun Safeena akan mahaifiyar Dady ta rasu.

  Kaf gidan yan uwan Mumy ne, sai ita kanwar Dadyn ita kadai.
 Abin mamaki shine taya akai tasan ana taro? Kuma me yasa itama in zata zo sai dai ta taho ita kadai? Kana ganin hakan kasan Dady ne ke sanar da ita.

 Jalila itakam gaishesu kawai takeyi, tana gamawa ta mike zatai gun Mumy wacce ta leko tana mata alama da hannu akan tazo.

 Jalila ta mike zata wuce taji an tawo mata hijab saura kadan ta fadi, kallanta tai zatai magana sai kuma ta fasa tace "Aunty?"
 Kanwar Dady wato Aunty Adama tace "Ke dama bakida tarbiya, in ba haka ba ki gaida kowa baki ko kalleni ba?"
 Jalila ta tsuguna tace "Aunty kema kinsan ban ganki bane."
 Tace "eh ni da nake a kauye ai bazaki ganni ba, tunda kaf falon nan akaina idan naki ya makance."
 Jalila zatai magana, Mumy tace "Jalila!"

 Kallan Mumy tai sannan ta amsa, ta kalli Adama kafin tai magana ma tace "tashi kije ana kiranki."
 Jalila ta mike ta wuce.
 Tana shiga d'akin Mumy ta rufe kofa sannan ta riko hannunta.
 Gefen gado ta zaunar da ita ta rike hannunta duka biyun tace "Jalila? Kinji abu kwatsam ko?"
 Jalila ta kalleta idanunta sun canza kala tace "Mumy ban fahimci abinda ke faruwa ba."
 Mumy ta rungumeta cikin murya mai rauni tace "Jalila nikaina abin nan na rasa ta ina zan fara sanar miki, dangin mijin ne suka ce suna san auran cikin gaggawa, yanzu nan da kwana uku za'a........."
 Yanda ta ture Mumyn daga jikinta ne yasa Mumyn yin shiru, Jalila bakinta na rawa tace "kwana uku?"
 Mumy tace "kiyi hakuri Jalila, sadaukarwa ce kikayi don ceto mahaifiyarki, kinfi kowa sanin Inna inhar bakiyi abinda tace ba, tabbas zata daina biya ma Goggo kudin asibiti ne, sannan zata iya korarku daga gidan nan, kinsan dai ba lafiya ne da ita ba, kar kuje garin wahala ciwon ya cita har azo ana dana sani...."

  Wasu zafaffan hawaye ne suka zuboma Jalila, ta kara maimaitawa kwana uku?
 Mumy tace " karki damu, mahaifinki ya yanke hukunci inhar akai auran kikaga ana cutar dake to ki sanar dashi shidakansa zai sa a raba auran."
  Wayyo yarinta da rashin tunani mai zurfi yasa Jalila tace "Haka yace ?"

 Mumy tace "sosai, kina tunanin zai bari a cutar dake ne?"
 Shiru tai tana kallan Mumy, Mumy ta mike ta bude drawer ta d'auko mata wani dankararen material mai duwatsu, tace " ki tashi ki shirya, kaninsa zaizo yanzu, insha Allah Jalila ba abinda zai faru dake, kidinga sa mahaifiyarki agaban komai."

  Jalila bakinta ma rawa tama kasa magana, Mumy ta mikar da ita tace "kiyi hakuri ki saka Jalila, dan tundazu akace ya taho."

 Haka ta hau saka kaya tana kuka, tana gamawa Mumy ta mata kwalliya da kanta, ta fesa mata turare sannan ta d'aura mata d'ankwali.

 Jalila tana zaune agaban madubi akai knocking, mai aikinsu ce tace mata wai yana falon baki.
 Mumy ta kalleta tace "Jalila!"
 Kallanta tai sannan tace "Mumy?"
 Mumy ta kara rungumeta tace "Jalila ki yafemin wahalar da na baki a da, ni kaina ina dana sanin yin hakan, kishi ne yasani yin komai."

  Da yake yarinyace mai kishiriwar nuna mata kulawa, jitai gaba daya jikinta yayi sanyi balle dataga Mumy na matse kwalla.
 Haka Jalila ta fito daga d'akin fa nufi falon bakin.


********

  Sagir na zaune yana waya da Abba, yace "Abba nifa kasan bansan me ake cewa ba?"
 Abba yace "kai dai Sagir sai a hankali, to inkungaisa sai kai introducing din kanka, inkundan yi hira kadan sai ka bata kudin kace na kwalliya ne da wasu hidindimo, dama ai laifinkune da baku bata ba da wuri, sannan laifin yayanka ne da bashida aboki ko d'aya a duniyar nan."

 Sagir yai murmushi yace "Abba bye na fara jiyo kamshin Amaryar mu."
 Dariya sukai a tare ya juyo yana cewa "Abba sai.........."
 Kallan da yake mata ne yasa ya kasa karasawa, Abba ya kashe waya yana murmushi.
 A hankali ta shigo falon kanta a kasa, kusa dashi taje ta ajiye tiren dake hannunta.
 Sannan ta dago dan gaidashi.

 Sagir cikin mamaki yace "Jalila?"
 Da sauri ta karasa dago da fuskarta tace "Uncle?"
 Kallan juna sukai kawai sai sukai dariya a tare, yace "Jalila ta!"
 Kanta ta sunkuyar sannan ta kalleshi tana murmushi tace "Uncle kaine dama? Ya akai kasan gidanmu?"

 Yace "woah da alama we are made for each other, kinsan ban taba tunanin ganinki ba?"
  Samun kanta tai da zama a kasan gun, fuskarta dauke da tsantsar farinciki tace "Uncle ni kaina nayi mamakin ganinka."

 Yace "wai ina kika shiga ne? Ko fishin ne yasa aka kashemin waya?"

 Tace "Uncle wata matsala ce ta hanani magana dakai."
Shiru yai yana kallanta, yanayin fuskarsa ne ya canza, ido ya kura mata wanda haryasata tsarguwa, tace " ka ganni kamar bani ba ko?"
 Idanunsa na kanta sai yanayin fuskarsa dake kara canzawa, a hankali yace "Jalila nan ina ne?"
 Tace "Gidanmu ne mana."

 Wani mugun faduwa gabansa yai ya kara kallanta, itama yanzu jikinta yayi wani irin sanyi a hankali tace "bakasani ba?"
 Bakinsa na rawa yace " ina Amar Amaryar?"

  Jalila gabanta ne yai wani faduwa hannu tasa tadan tura jikinta tai baya kadan sannan ta kalleshi idanunta sun ciciko.

Sagir ya fara girgiza kai yana cewa "U are not the one ko? Na tabbatar ba ke bace ba ko?"

 Hawaye ne suka fara zubo mata, idanunta na kansa, gaba d'aya jiyai wani irin zufa na keto mai yace "will you please tell me?"
 Jalila ta runtse ido wasu hawaye suka zubo mata tace "Uncle i am sorry."

 Sauko wa yai ya zauna a kasa sannan ya sa hannayensa ya shafi fuskarsa, kallanta yai cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa yace "Jalila kinsan waye Angon?"

 Kai ta girgiza tana hawaye tace "bansashi ba kuma bana sha'awar saninsa Uncle, kai nake so kai kadai nakeso Uncle na rasa yanda zanyi, rayuwar........."
 Tana kokarin sanar dashi rayuwar Goggonta, sai jitai yace "Yayana ne fa."

 A firgice ta bude idanunta, tace "me kace?"
 Idanunsa ya rufe sannan ya bude yace "Jalila he is my brother."

  Mikewa tai tana kallansa tace "brother? Ha kana nufin yayanka ne gidanku d'aya? Kenan zuwanka gidan nan a matsayin kaninsa kazo?"

  Sagir ya rufe idanunsa cikin takaicin abinda ke faruwa?
 Meke faruwa?
Yau me takeji haka?

 Mikewa tai da sauri zata fita.

 Jitai yace "He is someone whom i love alot."
 Tsayawa tai cak ba tare da ta juyo ba, idanunsa ne suka zubo da wasu kwalla yace "He is someone whom I respect alot."

  Yacigaba "He is someone whom I can't compare to anyone, i can sacrifice everything for his happiness."

 Jalila ta juyo da sauri tace "me kake so kace?"
 Idanu ya rufe wasu hawaye suka zubomai yace "Jalila bazan iya fad'a miko komai ba ayanzu, sai dai a hankali zaki fahimci abinda nake nufi ba sai dai bazan taba zama dalilin da zai zama silar bakincikin zuri'ar mu ba."

 Kallan mamaki Jalila takemai, sai hawaye dake ta gudu a idanunta tace " Kana san kaima kace inyi hakuri da auran kenan?"

 Sagir ya taso a hankali yazo inda take, kallanta ya shiga yi hakan yasa ta rufe idanunta tana hawaye.

 Jin batajin motsinsa ne yasa ta bude idanunta a hankali, me zata gani? Sagir ta gani gwiwowinsa a kasa.

 Da sauri ta ja baya tace "Uncle me kenan?"

  Sagir yace "That is how much he means to me."

Jalila kallan tsoro ta fara mai, tama kasa magana sam, sai kai da take girgizawa a ranta tana cewa "banda kai Uncle, Please banda kai, ko kowa zai fada Please banda kai, Please ku tasheni daga baccin da nakeyi."

  Sagir a ransa yana hango abinda zai faru inhar ya nemi bin zuciyarsa, yanzu ma da ya ya yayan nasa ya yarda? Sannan inya tuno da tashin hankalin da iyayensa ke ciki da abinda Hassan yamai a rayuwa bayaji akwai wani abu a cikin duniyar nan da zai kasa barmai, inya tuno da rashin lafiyarsa kuwa tabbas mace kamar Jalila itace best choice, sai dai kai fa?"

 Abinda zuciyarsa ke fadamai kenan, muryar Jalila yaji tace "Uncle have you ever love me?"

 Kallanta yai yana murmushin takaici, tace " me yasa kowa baya tunani na? Me yasa kowa yake san tsaramin rayuwata? Me yasa kowa yakesan ya zama nice mai sadaukarwa? Me yasa kowa yakesan yin amfani da ni?"

  Tsugunawa tai a gun kawai tasa kuka.

 Gana daya ya rasa yanda zaiyi, harcikin zuciyarsa yakejin kukanta.

  Baice mata komai ba sai tafasa da tasa zuciyar takeyi.

  D'agowa tai ta share hawayenta kawai ta meke zata fita.
 Sagir har ya kai hannu zai riko mayafinta sai ya fasa.
 Cewa yai "Jalila!"
 Kallansa tai sannan tace "zan shiga ciki."
 Yace " bamu gama magana ba."
 Tace " na fahimci me kakeso kacemin."

 Yace "Akwai sakon dana kawo miki."

 Cikin mamaki ta kalleshi, tana kallansa ya mike yaje inda yake a zaune dazu ya d'auko wata yar karamai jaka ta kwali sannan ya mika mata.
 Hannu tasa ta amsa sannan ta kalleshi, bai saki jakar ba yace "Jalila Please."
 Kallansa tai bakinta na rawa tace " zan shiga ciki."
 Sakin jakar tai, hakan yasa yai saurin mika mata yace "Yaya yace inkawo miki na hidindimo sannan yace kiyi hakuri bai samu zuwa ba rannan, da kuma yau."
 Jalila ta kalleshi kawai dan tama kasa magana.
 Juyawa yai da sauri, kallan bayansa tai sannan ta fita.

 


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*No 21*

   Tana tsaye har ya fita daga falon, jitai kanta yayi wani irin sarawa kawai ta zube agun ta zauna, yanzu kam hawayen ma sun kame, sam ta kasa yinkukan, batasan sanda Mumy ta shigo falon ba.
 Sai jinta tai tana cewa "Dubu d'ari da Hamsin!"
 Lalai mutanen nan.
 Kallanta tai sannan ta kalli kudin hannunta, jakar da Uncle ya mika mata ne, har yaushe Mumy ta shigo ta amshi jakar?
 Mikewa tai dakyar sannan ta fita itama ta baya tana layi, Mumy ko ta kanta batai ba ta fita falo, ta haura sama.

 Bangarensu ta nufa kawai ta zube a kasa ta kwanta, me ke faruwa da ita? Uncle? Dady? Mumy? Inna? Me yasa kowa yake san tsara mata abinda yaga dama? Me yas ba wanda yake tunanin farincikin ta?"


 Wasu zafaffan kwalla ne suka gangaro mata, tana nan azaune sam batasan sanda bacci yai gaba da ita ba.

 **********

  Sagir kam tana fita daya shiga mota ya ja ta da gudu, gaba daya ya rasa tunanin me ya kamata yai, ta ina zai fara iya zama gida d'aya da Jalila? Sannan amatsayin matar yayansa?

 Wani irin burki yaja, ya gangara gefen titi sannan ya kashe motar.
 Kansa ya kifa akan sityarin motar yana tunano kalaman Jalila, idanunsa ya runtse cikin tsananin damuwa, yace a fili "Am sorry, i am really sorry Jalilah."

  Kiran Ummy ne yasa ya d'ago, sannan ya daga wayar, Ummy daga can bangaren tace "My son ya kukai?"
 Ya kakaro murmushi yace "komai ya tafi daidai Ummy, sannan na tabbatar yarinyar nan zata kula da Yaya sosai."

 Tai dariya cikin jin dadi tace "kai ma ka gano hakan ko?"
Yace "sosai Ummy, she is really kind, innocent and honest, yaya zaiji dadin zama da ita."
 Ummy tace "Na gode sosai Sagir, sai mumai fatan amincewa da ita."
 Sagir ya daure yace "sosai ma kuwa Ummy."
 Tace "Ka taho ne?"
"Ina hanya zan dan tsaya wani gun ne."

 Yace "ba matsala, ka gama abinda kakeyi, sai na ganka."


  Nan ta kashe wayar tana murmushin jin dadi.
 Aunty Nana ta kalla wacce ke ce mata, wai da gaske a birni take?

 Tace "wai ke haryanzu baki yarda ba? Kindauka a kauye take?"
 Aunty Nana tace "ba wai haka bane."
 "Ko kina tunanin ba mai bawa Hassan yarsa ne ya aura?"

Aunty Nana tace "ni ba haka nake nufi ba, inadai mamaki ne."

 Ummy ta kalleta cikin mamaki tace "indai har ke yar uwata kika fadi haka ai banaji akwai wanda zai fadi haka naji haushi."

 Ta mike ta fito daga dakin tanajinta tana cewa "ke dai bakya san gaskiya......"

 Ummy ta janyo kofar ta fito dan kara duba sama, dan sunce gobe zasuzo jere, ba wani taro zasuyi ba saboda halin da ake ciki, dan sunsan ko sunce zasuyi Hassan bazai taba zuwa ba, aure kawai za'a daura a kawota da daddare.

   Bangaren ya gyaru sosai, tura kofar Hassan tai dan tasan yana ciki.
 Jin kofar a rufe yasa ta dan yi knocking, Hassan ya mike ya bude kofar.

Ummy ce ta kalleshi sannan ta shiga.
 Hassan ya maida kofar ya rufe sannan ya tako ya zauna abakin gado.
 Kallan d'akin tai tace "Hassan baka tunanin ya kamata mu canza gado?"

 Kallanta yai baice komai ba, tacigaba " wannan sofar ma ta tsufa ya kamata mu sa wani, sannan carpet din nan shima ya kamata mu canza shi, Hassan mai kake gani?"

 Hassan bai kalleta ba yace "Ummy Please ki bari."
 Tace "me? Bakaso a canza?"
 Yace "na rasa me yasa kike zumudin auran nan, Ummy bakya tsoron abinda zaije ya dawo?"

 Kallansa tai cikin mamaki tace "me kake nufi?"

 Yace "Ummy kinfi kowa sanin me nake nufi."

 Ummy yanayin fuskarta ya canza tace "Hassan please ka dingama kanka fatan alkairi, sannan ka dinga sa salama a cikin zuciyarka."

 Kallanta yai kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa, ya rasa me yasa duk basa gane abinda shi yake nufi.

  Ummy tai shiru, jiki a sanyaye ta fita daga d'akin, kallan kofar yai sannan ya runtse idanunsa dan jiya ma sam baiyi bacci sosai ba saboda matsalarsa data tashi, ta ina zai iya zama da mace a haka? Ya tabbatar daga randa ta ganshi cikin wannan halin zata gudu.


*********

  Jalila haka ta kwana a bangarensu ita kadai, abinda zai baka mamaki ba wanda yabi ta kanta sai abincin dare da aka kawo mata, sannan taje fita da safe mai gadinsu yace ai ance karta sake fita.
 Haka tanaji tana gani ta dawo ciki.

 Wanka kawai tai Mumy tazo ta d'auketa sukaje gun salon, a can ne ma ta daure ta tambayeta inda Safeena take.
 Nan Mumy tace mata tana gidan kanin Inna har yanzu, bayan alokacin ma tana Abuja gidan babban d'an Alhaji Sanusin wato kanin Inna.

 Jalila bata ce komai ba, haka aka fara mata gyaran jiki, Mumy ta barta agun suka tafi gidan Taura yin jere.
 Shikam Hassan da sassafe ya garkame dakinsa ya bar musu gidan, Sagir ma yaso gudu sai dai Ummy ce ta hanashi tace "ya kamata ace da namiji agun.

  Haka ya zauna cikin tsananin damuwa, yana bin masu jeren da kallo.

  Sai yamma aka turo aka dauketa, Mumyy ta kama hannunta sukai bangaren Safeena.
 Jalila tace "Mumy gun Goggo nake san zuwa."
Mumy tace "kiyi hakuri Jalila sai dai ki je gunta da mijinki, dan umarnin Inna da Dadynki ne."

 Tasha kuka ranar sai a lokacin tai dana sanin guduwa da batai ba daga gun salon.

  Haka ta kwana tana kuka, bacci ma sai zarar ta yai.
Abinci kuwa dama turawa kawai takeyi.

 Ba wanda ya damu da ita bare ya fahimci ranmar da tai a dan kankanin lokacin nan.

  Yau take asabar, Goggo na zaune akan gado tayi shiru tana tunani, me yasa tun jiya take tunanin Jalila? Ta tabbatar inhar lafiya bazata taba yin kwana uku bata zo ta ganta ba.

 Shiru tai ta shiga yin addu'a akan Allah yasa lafiya, sannan Allah yasa Sultan yazo ta tambayeshi.

  Jalila kam yau rufe kofar d'akin Safeena tai dan wani irin zazzabi mai zafi ne ya rufeta sam bata san hayaniya.

  Gudar da taji ne cikin bacci yasa ta bude idanunta a hankali, ba kowa a d'akin sai ita, sai dai daga falo tana jin ana guda.
 Mikewa taj da kyar ta sa saitin kunnenta a jikin kufar, duk lab'an bakinta sun bushe.
 Jitai wata ta sakeyin gudar, sai jitai ance "dalla malama yi mana shiru, sai wani guda kike kamar auran yar gata, da auran Safeena akeyi sai mu jure jin gudar nan amma kinzo kin cikamana kunne."

  Jalila tai murmushin takaici, har zata juya sai taji ance "Wai ke Fatima kin taba ganin mijin ma kuwa?"
 Tanajin muryar Mumy tace "inafa na ganshi?"
 Wacce tai magana tace "tunda ance yana da matsala na tabbatar babba ne, kila fa zaikai shekara 40 ko?"

 Mumy tai dariya tace "ina na sani? Sai ku bari sai ankai Amarya da daddare sai ku tambayeta."

 "40?"

 Gaban Jalila ne ya fadi, matsala? Meke faruwa? Duk da tasan dama bazasu taba mata auran mutunci ba amma batai tsammanin babba bane haka, da alama kenan akwai kanne dayawa tsakanin sa da Uncle?"

  A can gun d'aurin aure kuwa, Hassan dakyar ya tsaya aka d'aura auran, ana fitowa hoto d'aya ya daure akai dashi, shima wasu manyan mutanen Abba ne da bayanda zaiyi, sannan Abban na rike da hannunsa.
 Ai kuwa suna gama d'auka yai wuf ya tafi.

 Sagir kuwa, ba'a magana dan kuwa jiyai kamar an jefamasa katan dutse a sanda yaji sanarwar d'aurin auransu.

  Dole shi ya tsaya aka dinga gaishe gaishe dashi.

 Dady sai baza ido yake yaga ango amma bai ganshi ba, Sagir dayazo suka gaisa yake tambayarsa ina Angon?
 Sagir yace "Yanzun nan ya dan fita, kansa ne ke ciwo."

 Hassan kuwa yana shiga cikin mota ya rufe, jiyai gumi na keto mai ta ko ina, sam hayaniyar nan tasa gaba d'aya jikinsa ya ji gaba d'aya ba dadi.

  Idanunsa ne suka canza kala, kansa ya kwantar akan kujera ya rufe idanunsa.

 Firgigit ya farka dan baisan har yadan yi bacci ba, jiyai numfashinsa na neman d'aukewa, nan yasa hannunsa ya rike wuyansa yana kokarin jawo numfashinsa, gaba d'aya jikinsa ya kame, sai uban zufa dake karyomai, idanunsa sunyi jaa sosai, dakyar ya iya jawo numfashinsa.
 Nan ya shiga yin numfashi akai akai.

 Jinai gaba daya jikina yai sanyi, dan tabbas duk wanda yaga Hassan zai dauka ko Aljanu ne dashi ko kuma hankalinsa ba daidai yake ba, Hassan meke damunka? Abinda zuciyata ta shiga tambaya kenan? Nace masu karatu ku taimaka min.......



#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*No 22*


  Tana zaune a d'aki wajen azahar Mumy ta fara mata knocking.
 A kasan kofar take a kwance dan zazzabin dake jikinta mai zafine.
 Da kyar ta iya mikewa ta bude kofar, Mumy tace "Jalila ko wanka bakiyi ba? Naga tun jiya na ajiye miki kayan da zaki saka?"
 Jalila ta kalleta bakinta na rawa tace " Mumy....."
 Ganin yanda idanunta keyi yasa Mumy ta riketa, jitai jikinta ya d'au zafi sosai, tace "Zazzabi kike?"

 Jalila tai shiru, hannunta ta kamo tace " Muje Inna ke nemanki, in ta gama miki magana sai ki dawo ki sha magani."
 Nan ta rike hannunta suka fito, kallan banza kowa yake mata dan dama duk yan uwan Mumy ne masu tayata kishi da zuga ta.
 Haka suka shiga d'akin Inna.
 Tana zaune tana duba abu a waya suka shiga, sai data gama sannan ta ajiye ta kalli Jalila, sannan tai dialing number a wayarta tana cewa " magana zakuyi da Goggonki, ki sanar da ita baki da lafiya shiyasa ba zakizo ba."
 Kafin Jalila tai kokarin bada amsa, har Inna ta miko mata wayar sannan tasa hands free.
 Muryar Sultan taji yana cewa "Inna ina Jalilan? Gani a kusa da Goggon."
 Jalila ta daure tace "Sultan ni ce."
 Yace "Jalila Goggo na nemanki."
 Ya fada tare da mikama Goggon waya.

 Goggo na amsa tace "Jalila ina kika shiga?"
Jalila tace "Goggo zazzabi nakeyi shiyasa baki ganni ba."
 Tace "ni ai dama cewa nai ki zauna ki huta, amma na rasa meyasa yau hankalina yake a tashe, dafatan ba abinda ya faru?"
 Jalila tace "mai zai faru Goggo? Ke dai kawai kice ganina kikeso."
 Goggo tai murmushi dan hankalinta ya kwanta tace "kinsha magani?"
"Eh Mumy ta kaini an banni magani."
Goggo tace "Ayya! To ki huta sosai, kar ki damu dani."
 Jalila ta d'aga kai, idanunta suka ciciko a ranta tacce "Goggo ga yarki nan ana mata auran dole, auran fin karfi, auran mugunta, auran san zuciya...."

  Jin shiru yasa Inna ta kashe wayar sannan ta kalli Jalila, hannunta ta kamo ta rike tace "good girl, karki damu ki kula da mijinki yanda ya kamata, muma zamu kuka da Goggonki yadda ya dace."

 Jalila ta share hawayenta tace "Inna dan Allah ku kula da ita."
Inna tace " karki damu kanki, ai Goggo tamu ce, ke dai kiyi abinda muka saki."
 Jalila ta d'aga kai alamar to.
 Nan Mumy ta kamo hannunta suka fito.

 Innata bisu da kallo, tabbas dolene su kula da Goggo sosai, saboda yanzu ne zasu kara bunkasa company ta hanyar Jalila.

  Murmushi tai.........

 Haka Jalila, Mumy tasata tai wanka, tasha magani, ta sa kaya sannan suka fito tare, gefe guda taja ta zauna.
Dan bata jin dadi, daga baya ma data kula hankalin kowa baya kanta ta zille tai bangarensu.

  Kwanciya tai a inda Goggo take kwana, tana tuno rayuwar da sukai a cikin gidan.

 Kuka ta shiga yi sosai, wanda ya kara sa mata ciwon kan dake damunta, sai yamma likis tana kokarin fita, Dady na turo kofar.
 Kallanta yai jikinsa ne yai wani sanyi, yace "tundazu nake nemanki shine Mumyn Yasmeen tace kila kina nan."
Jalila ta kalleshi bata ce komai ba, kusa da ita ya zauna sannan ya kalli d'akin, yace "kina tuno rayuwa ne?"
Itadai batace komai ba, shiru ne yadan ratsa kafin yace "Jalila kiyi hakuri."
Kallansa tai cikin mamaki, yace "bazan nemi yafiya akan abubuwan dana aikata ba, domin har yanzu bana dana sanin aikata su, sannan abinda na aikata a baya sune suka sani nazama abinda na zama yanzu, sune kuma suka taimaka suka inganta rayuwar zuri'ata harda ke kanki, sai dai zan baki hakuri akan auran nan da aka miki dan kuwa na san bamu kyauta ba, sai dai ko yanzu aka dawo da hannun agoggo baya tabbas abinda zan sake yankewa kenan."

 Kallansa kawai Jalila take cikin mamaki, dan ta kasa cewa komai, Dady yai shiru kafin yace "ki taso muje a shiryaki sun ce bayan isha'i zasuzo, dazu akaso kiranki nace a barki zuwa anjima."

 Bata ce komai ba ta mike ta fita kawai, dan itakam bata san me zata cemai ba, tana koma tsoron kar bakincikin dake ranta yasa ta fadamai kalamai marasa dadi.

 Haka ta wuce bangaren Mumy, wanka aka sata ta sakeyi tai sallah,sannan Mumy  ta sata tadan ci abinci wanda cusa wa kawai tai, sannan ta bata magani, kayan da zata saka ta miko mata.

 Haka Jalila ta saka kayan nan ba tare da tace kala ba.
 Mumy ta mata kwalliya tai kyau sosai, turaruka ta fesa mata kala kala.
 Mumy ta fita dan ance motoci sunzo.
 Sagir na zaune a cikin mota gaba daya yau banda ruwa ba abinda ya shiga cikinsa, wace rayuwa zaiyi da Jalila a matsayin matar yayansa?

 Gaba d'aya shikam yasan rayuwarsa ta gama hargitsewa.
 Haka akai ta shiga motoci har aka fito da Jalila aka bude bayan motar da Sagir ya jawo wacce take ta Abba aka saka ta.
 Kanta na kasa dan a lulube take da mayafi, tunda suka fito yake kallansu.
 Jalila na zama taji yacema Mumy ina wuni?
 Gabanta ne ya fadi jin muryar Uncle, shine zai ma kaita? Me yake nufi da ita?
 Wani sabon takaici ne ya kara kamata, lalai yau ta tabbatar Uncle ba santa yakeyi ba.

 Haka suka shiga motar aka ja, ita kadai ke kukanta, wanda kukan ke taba cikin zuciyarsa.
 Haka sukai ta tafiya har suka isa makeken gidan.

  Gabanta ne ya shiga faduwa sanda akace ta fito, wai yau itace aka ma aure da wanda ko sani batai ba, ko kawayenta su Zahra basu sani ba, ko Mahaifiyarta bata sani ba.

 Haka ta fito, jikinta na kara tsuma wani sabon tsoro da fargabar rayuwarta na kamata.

 Sukam mutane kowa ko a jikinsa, Mumy na rike da ita suka shiga.

 A gidan kuwa, Ameerra da Aina'u suna zaune a d'akinsu sunyi shiru, Ameera tace "Aina'u inaji ta iso naji guda."
 Aina'u ta kalleta cikin takaici tace "Ameera me yasa iyayenmu basa duba abinda ya kamata? Kowa yasan tun ina SS1 nakesan Yaya, ni nace bandamu da matsalarsa ba tunda dai nasan ba hauka gareshi ba, me yasa ba wanda ya duba zuciyata? Ba ruwan kowa da damuwa ta?"

 Ameera tai tsaki tace "nima Allah naji haushi, ita wannan din dame ta fiki daya sa su Ummy mantawa da ke?"
 Aina'u tai kwafa tace "ni yau ma zan bi Umma mu tafi."
 Ameera ta ce "haba dai?"
Mikewa tai ta shiga toilet dan bata san jin gudar nan."

 Aunty Nana kam ta baza ido tana san ganin wacece matar Hassan, Ummy ta kalleta tace "Dan Allah karki bude mata fuska sai ta zauna."
 Aunty Nana tace "ni rikota kawai zanyi bance wani abu ba."


 Haka akai ta hawa sana ana ganin tsarin gidan, kowa sai ya yaba sai dai dayake bakin ciki suke.
 Jalila na zaune a kasa, kanta na kasa tana hawaye.
 Ummy ta d'agota tace "akaita sama.
 Nan Aunty Nana ta taso da sauri ta riketa, haka ta kaita d'akinta sannan ta bude mata mayafi, shiru tai tana mamaki dan gaskiya bata taba tunani.......
 Ummy ce ta dafata sannan ta rufema Jalila fuska tace " muje waje."
 Fita sukai a falo, Aunty Nana ta riko Ummy tace "kun tabbatar dai yarinyar batada wata matsala ko? Ko halayen banza, kinsan wasu yaran a ido baka ganewa amma a fili sai kiga wasu iyayensu ma sun gagaresu ne."

 Unmy takaici ya kamata tace " ba yanzu zaku tafi bane? Naga duk an fara watsewa."
 Aunty Nana ta tabe baki tace "ba sai kin kuremu ba."
 Haka ta sauko tana mamaki.

  Sagir kam yana maidasu gida yai cikin gari.


  Ummy na zaune sai kiran wayar Hassan takeyi, sai datai ringing har ta katse sau biyu sannan ya d'auka.
 Ummy tace "Hassan kana ina?"
 Yace "waje."
Tace "ka dawo gida dan Allah, kaga duk an watse sannan an bar yarinya ita kadai tun dazu."
Yace " to in ina nan ma me zan mata?"
Ummy tace "nidai ka dawo yanzu."
 Ta katse wayar tana kallan Abba wanda ya shigo yanzu.
   Hassan na ajiye wayar yau shiru, can ya tada motarsa ya taho gida.


  Jalila na zaune gurum ba kowa a d'akin, har ta gaji da kukan tayi shiru, sai dai fuskarta a rufe take.

 Ummy ce ta fito daga daki ta shiga dakinsu Ameera ta kalleta tana assignment, tace "Ameera tashi kije gun Yayarki kafin Hassan ya dawo."
 Ameera ta turo baki tace "inje in mata me?"

 Ummy ta hade fuska hakan yasata mikewa ba tare da ta kara cewa komai ba.

  A zaune take akan gado Ameera ta shiga, sallamarta ta amsa.
 Ameera ta shiga dakin tana cewa "ki cire mayafin kisha iska tunda ba kowa."
 Jalila tace " bakomai hakan ma"

 Ameera ta zauna akan kujera tana latse latse waya.

 Haka suka zauna shiru kamar ba kowa a dakin.

 Sai wajen karfe goma da rabi dan har Jalila ta fara gyangyadi, taji karar bude kofar dakin.

  Ameer ta mie da sauri tace "Yaya."
 Kallanta yai sannan yai mata murmushi.
Mikewa tai ta fita, Ummy ta gani a kasan beni tace "ina ya shiga?"
Tace "dakinta."
 Ummy tai ajiyar zuciya dan sai data mai magana yanzu akan lalai fa dakinta zai shiga ba nashi ba.

  Zama yai akan kujerar da Ameera ta tashi, sannan ya kalli inda take a zaune, bai damu yasan yanayinta ba, balle kamaninta.
 Ita kuwa tunda taji Ameera tace "Yaya!"gabanta ke faduwa.

  Dakin ya sake yin wani shirun, jitai wuyanta yana neman sagewa.
 Hassan ya kara kallanta, batada niyyar yaye mayafin ne ko me?
 Ba dai aikinsa bane?
 Daga inda yake yace " ki zare mayafin ki kwanta inkinyi sallah, in bakiyi ba ki tashi kiyi."

 Abinda ya fada kenan, ya mike zai fita.
 Har ya bude kofa zai fita sai idanunsa suka kalli ledar da Abba ya bashi.
 Kara maida kofar yai ya rufe, ita kuma ta dauka ya fita ne jin rufa kofa sau biyu.
 Yaye mayafin tai sannan tai wata ajiyar zuciya.

 Idanunta ne ya sauka a cikin nasa, gabanta ne ya shiga faduwa, sai dai yanda yake kallanta yasa ta kasa dauke idanunta.
 Kamar yasan fuskar nan, a ina?
 Idanun Jalila ne suka firfito, juya baya tai da sauri.

 Hassan ya matso ya d'au ledar ya mika mata.
 Ganin bata ganinsa yasa ya ajiye a kasa ya juya.

 Jalila tana jin ya fita ta juyo tare da ajiyar zuciya.

 Hassan yayi shiru a dakinsa yana tunani, ina ya santa?
 Wayar Ummy ce ta shigo, kallan wayar yai hartai ringing uku sannan ya d'aga tana neman katsewa.
 Tace "kana ina?"
 Yace "Ummy."
 Tace "in har kanason na samu bacci ka koma gun yarinyar nan, haba Hassan taya zaka bar yarinya ita kadai bako tausayi?"

 Hassan yace "Ummy kinsan fa bana iya kwana da kowa."
 Bata ce komai ba ta kashe wayar.

 Kansa ya dafa cikin takaicin wannan abin......


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*Sisters Always Ask Questions, Borrow Clothes, Tell You When Your Hair Doesn't Look Good, Always Fight but Never Drawn Apart, Love You Always, Encorage You When You Are Dawn...*
 _A Small Quote For My Sister Love You Always Ameenah😍_

 *NO 13*

A rayuwar Jalila indai tana gaban Goggo jinta takeyi kamar yarinyar goye, shiyasa duk wata tabata da shirme juyema Goggo takeyi, suna kwance zasuyi bacci duk ta isheta da neman sanin asalin labarinta.
 Goggo tace "to ya isheni haka nan yanzu sai ki kwanta ko kin manta gobe kunada taro a makaranta?"
 Jalila ta juyo inda Goggo take tace "Goggo kinsan yanzu addu'ar da nake yi yanzu?"
 Goggo tace "ya wuce shirmen soyayyarki?"
 Jalila ta girgiza kai tace "A'a addu'a nake Allah ya kara miki lafiya da tsawan kwana muyi rayuwa tare, banaji zan iya kwana d'aya a duniya in bakyanan."

  Goggo ta hade rai tace "Jalila nikam sai yaushe ne zaki girma? Na dauka in mutum ya tashi cikin wahala yana hankali amma wani sa'in in kikai wani abun sai inta mamakin ki."
 Jalila tai murmushi tace "Goggo a koda yaushe in ina tare dake ji na nake kamar yarinyar goye, kece kawata, mahaifiyata, mahaifina, sannan kuma yar uwata, Goggo yanda bana boye miki komai dan Allah kema kidinga sanar dani komai na rayuwarki."

  Kallan tausayawa ta mata dan tabbas tana ji a jikinta wani babban ciwo na cinta domin wasu sababbin canjin da take fuskata a jikinta tasan da matsala,, sai dai fatan Allah yasa abin ba babba bane.

  Jalila tace "Goggo!"
 Goggo tace "shikenan Jalila na miki alkawari a daren gobe zan sanar dake komai na kafin a haifeki, yanzu dai ki kwanta."
 Tace "yauwa Goggona, saida safe."
 Goggo ta daga kai, sannan ta zuba mata ido, kankace me Jalila ta tafi bacci.

  Goggo a dade tana kallanta har batasan sanda hawaye suka gangaro mata ba, hannu tasa ta share sannan ta gyara mata bargo ta juya ta fara bacci.

   Da safe bayan ta gama gyara bangarensu ta fada wanka, an dade ana saba jiki kai kace fatar tata zata canza, ta fito ta bude drawer dinta ta saka kayan makaranta sannan ta shiga duba sababbin dinkin da aka mata, nan ta zabi wani lace mai an karan kyau yasha duwatsu, ta fara kokarin sawa a jakar hannunta da aka sai mata.

 Goggo ta bude labule tana kokarin shigowa, kallan Jalila tai tace "ke da zaki makaranta me zakiyi da kayan gida?"
 Ta karasa shigowa da kyar ta samu ta zauna.
 Jalila tai murmushi tace "Goggo yau fa ake yaye mu."
 Tace "to sai akai ya?"

  Jalila tace "Ana gama taran ai zamu kwabe mu shiga kayan gida ai shagali."

 Goggo ta tabe baki cikin rashin gamsuwa tace " Wai yaushe aka fara haka a makarantar Gomnati ma?"

 Jalila tai dariya tace " ina kike fita balle ki sani?"

  Goggo tace "Hmm amma ai kyaci abinci ko?"
 Jalila tace " Ni bana jin yunwa sannan za'a kawo abin saidawa a makaran........."
 Kallan da Goggo ta matane yasa ta zauna da sauri tare da bude kular abincin, tea ne da bread da
 farfesun naman kai."

 Jalila ta dade kafin ta bude bread din, har goggo tace "menene?"
 Jalila tai yake tace "rayuwa kawai nake tunani Goggo, wai yanzu mune ake bamu abinci ba tare da munyi musu aiki ba, Goggo kin manta sanda muke musu wanki? Mu musu komai na gidan?"

  Goggo tace " rayuwa kenan Jalila, insha Allah wahala ta kare miki a rayuwa."
 Jalila tai murmushi sannan ta fara cin abincin, bazata cemata iyaye suna zuwa ba dan ta tabbbar zataji ba dadi, gashi ita ba lafiyar kafa ba."

Tana gamaci ta fito, Sultan ta gani yana kokarin shiga mota, tace "Sultan?"
Tsayawa yai har ta iso, tace "ina zaka?" Ta dauka cemai akai ya rakata saboda gama makaranta da zasuyi.
 Jitai Yace "In an kaiki makaranta ne zan wuce gidan kawu in amso sako." Sakon me?
 Yace " kamar wai lefe za'a kawo."

 Jalila cikin mamaki tace "lefe? Lefen wa za'a kawo?"
 Yace "ina na sani?"
Ya fada tare da shiga motar.
Jalila ta shiga tana mamaki, bikin Safeena za'ai? Amma bataji labari ba, to ko amsar kayan za'ai kawai a gidan?"
 Ganin batada amsa yasa ta share.


  Yau yan mate dinsu Jalila ansha uban kwalliya, sai iyayi akeyi.

  Haka aka fara programs kowa iyayensa da yan uwansa sai zuwa sukeyi, Jalila tana zaune dan tasan ba wanda zata gani.

  Zarah ce ta tabata tace "Jalila Yaya yazo dasu Umma."
 Nan sukaje suka gaishesu, Jalila tana zaune daga inda take tana hango Uncle Sagir, insuka hada ido sai suyi ma juna murmushi.
 Ganin Uncle ne ma yasa ta cire komai a ranta har aka gama programs.

  Nan sukaje suka canza kaya kowa yasa kayan gida suka dau kwalliya, masu waya sunata yin hotuna, Zahra ma ta zo musu da waya sai hoto ake tayi.

  Wata monitor din Jss3 ce ta shigo ajin nasu, nan ta nemi inda Jalila take ta tabata.
 Jalila ta kalleta tace " Hadiza ya akai?"
 Mika mata wata yar karamar jaka ta kwalli tai tace "gashi inji Uncle Sagir."
 Jalila ta amsa tana bude jakar.
 Kwalli ta gani ta jawo,Zahrace ta matso ta fizgi kwallin tana cewa " me muka sa......"
 Ganin waya yasa ta kalli Jalila tace " yeee!"
 Jalila ta harareta sannan ta fizge wayar tace " muga."
 Ganin Wayar ne ya sa ta kallan Zahra, hannu tasa cikin jakar ta zaro wani karamin card.
 Bude shi tai taga ansa
_To u my dear!_
 _Congratulation on your graduation, here is my small gift, hope you will accept it._
 Zarah ce ta kara amsar wayar ta bude ta, wayace mai tsananin kyau Sumsung Note 5 ce.
 Kan kice me Zarah ta fara haska Jalila wacce tai tsuru tana kallan ikon Allah.

  Fitowa tai daga ajin ta shiga nemanshi, can ta hangoshi cikin mutane.

  Tsayuwa tai dan bata san ya zatai ba, juyowa yai kawai sai hangota yai daga nesa.
 Yaune rana ta farko da ya ganta cikin shiga haka mai kyau dauke da kwalliya, sannan wannan ne rana ta biyu daya ganta ma da kayan gida a iya zamansu, na farko sanda ya fara ganinta sai kuwa yau.

  Kasa dauke ido yai daga kanta wanda har hakan yasata tsarguwa.
 Juyawa tai da sauri ta shiga class din.
 Zahra ta matso tana nuna mata hotunan da ta mata.

  Jalila kam bata kula taba dan hankalinta nakan Uncle dake waje.

  Daina hangoshi tai hakan yasa ta fito daga class din tana lekensa.
 Zarah ce ta miko mata wayar da sauri tace "Zarah Yours na kiranki."
Jalila aji abin banbarakwai, kallan wayar tai a jiki an saka MINE dariya tai sannan ta kalli zahra tace ya ake daga wa?"
 Mamaki ya kama Zahra sai dai kafin ta farga Jalila tana gwadawa kawai taga yaja hakan yasa Zahra tai tunanin iskanci take mata.

 Jitai yace "Banga kwalliyar nan ba, tunda ba'a ganni ba sai a taimaka azo inda muke haduwa."

  Murmushi tai sannan tace "to."
Kallan Zahra tai sannan tace "ina zuwa."

 Nan ta fara tafiya.


  Yau a kan mota ta ganshi, karasawa tai fuskarta dauke da murmushi da kuma kunya.
 Tana isa ta gaisheshi, yace "Irin wannan kyau haka ai sai kisa in rasa gane hanya."
 Kallansa tai tace "Uncle wannan gift din yayi yawa, bana tunanin zan iya amsa, Goggo ma fada zatamin"
 Yace " to Jalila ya kikeso muyi? Kingama skul nima na gama service a ina kikeso indinga jinki? Ke ba waya ba? Sannan ko zuwa zan dinga yi kina tunanin za'a barni nazo kullum?"
 Jalila tace kullum? Yace sosai in har bazaki amshi wayar ba sai dai ki amince kullum nazo muyi awa uku tare.

 Da sauri ta zaro ido dan tasan wannan inaa bazai yiwu ba.
Ji tai yace "bazai yiwu ba ko? To kinga kawai ki hakura."

  Jalila tace "Amma....."
 Yace "mu bar maganar nan please."

Kallansa tai dan batasan me zata ce ba..........

 Hira suka shiga yi ta masoya masu tashen soyayya, Kiran wayarsa da akai ne yasa ya kalli wayar mamaki  yai dayaga Mine a jiki dan number Jalila ce.
 Nan ya daga yana cewa wayarki na gun wa?
 Tace Zahra
 Zahra na dagawa tace "Uncle wai Jalila tazo anzo daukarta."
 Uncle ya kalleta yace "wai anzo daukarki."
 Mamaki ya kamata tace "amma nace sai bayan azahar, gabanta ne ya fadi badai wani abun bane ya samu Goggon ta?"

 Kallan Uncle tai a tsorace tace "Uncle bari naje gida."

 Zahra na tsaye kusa da motarsu, wayarta ta mika mata ta bata jakarta, nan Jalila ta sa a cikin jakar ta shiga ciki sukai gaba, addu'a kawai take Allah yasa ba wani abun bane ya samu Goggonta.


*£*£*********


  Goggo tana zaune wajen karfe 12 Yasmeen tazo da gudu wai tazo inji Inna.
Tayi mamaki sosai dan tanaji tunda take a gidan Inna bata taba nemanta ba haka kawai.

 Samun kanta tai da faduwar gaba.
 Haka ta taso da kyar saboda ciwon kafa ta karasa.

  Tana shiga falon taga Inna, Dady da Mumy a zaune.
 Faduwar da gabanta ya shiga yi ne kawai ya sa ta shiga yin addu'a dan ta tabbatar ba lafiya ba, shiga tai a hankali.
 Mumy ta mata nuni da kujerar dake gefe tace "ki zauna anan."
 Goggo ta zauna sannan ta gaida Inna ta gaida Dady da Mumy.

  Bayan sun amsa ne falon yai dan shiru.

 Goggo tace "lafiya?"

Inna tace "Gobe za'a kawo kayan lefen Jalila."

 Abin yazoma Goggo a ba zata wanda yasa tace "lefen Jalila kamar ya kenan? Dan banaji ta taba sanar dani tanada miji."

  Inna tace " ba sai ta sanar dake tana da saurayi ba, dan kuwa hakkin mahaifi ne ya zaba mata mijin da yaga ya dace da ita, sannan shi Abbakar ya fitar da nasa hakkin na yi mata miji yanzu hakkin 'ya ne tabi umarnin mahaifinta."

 Goggo ta kalli Dady da sauri tace " Abbakar me kenan?"
 Yace "hakan da kikaji shine."

 Cikin daga murya tace "da tunda aka haifeta bakasan da hakkin ta akanka ba sai yanzu? Dama wlh ni jikina yaban mutuncin da kuke mata da wani abin a kasa, ashe aurar da ita zakuyi? Mijin mahaukaci ne ko dan shaye shaye? Ko kuwa barawo ne? Ko kuma nakasasshe? Ko kuma dan fashi ne?"

 Mumy tace "ya zaki fadi haka, Abbakar fa ubanta ne ta ya za........."

 Goggo cikin tsawa tace "Ba dake nake ba."
Yanda tai maganar ne yasa Mumy tsorata dan bata taba ganin Goggo  na fada haka ba.

  Goggo cikin fada tacigaba " me ka mata a matsayinka na ubanta? Me ka mata?"
 Dady shim ya kasa magana dan bai taba ganin tana fada haka ba.

  Goggo fa mike da kyar idanunta sun canza tace " duk abinda kuke ma tunanin ku ajiye dan wlh ba wanda ya isa ya yima Jalila auren dole."

  Juyawar da zatai taji wani jiri na debanta, kan kace me tayi baya luuuu jikake tim ta fadi a kasa.

  Da sauri suka mike suna jijigata.

Jalila wacce ta shiga bangarensu da gudu taga ba Goggo jakarta ta cilar a dakin sannani ta fito ta nufi bangarensu Mumy dan tambayarsu,ganin Goggo a kasa su Dady da Mumy na kanta yasa ta karasa da gudu jikinta na bari.



#ONELUV💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

 *I am really Proud of you! Can't believe Kainuwa has reach more than 300k views on wattpad, Heart U* 💕💕💕💕💕💕💕

*No 24*



   Shiga d'aki yai ya tsaya yai shiru, tunani yake mai yai? Shi dai a iya saninsa baiga laifin da yai ba.
  Bandaki ya shiga yai wanka, zama yai shiru, ga wunya da ta fara cinsa, yau Ummy mantawa dashi tai? Ko laifin daya mata ne yasa tai fishi dashi?

  Kwanciya yai ya d'au jornal din da yake karantawa.
 Jiyai yau karatun sam ba dadi, shi yace amai aure? Mikewa yai zaune sannan ya shafi fuskarsa, makullinsa ya d'auka da wayarsa ya fito, ba kowa a falon hakan yasa yai waje.
 Yana kokarin shiga mota, su kuma suna shigowa.
 Sai daya jira sukai parking sannan ya shiga mota ya tada ta.
  Sagir ya fito da sauri yanasan mai magana, kafin ya karaso Hassan yaja motarsa yai gaba.
 Sagir yabi motar da kallo, a ransa yace "anya nama Jalila adalci kuwa?"
 Ameera ce ta bi motar sa da kallo sannan ta kalli Jalila ta mika mata hannu, Jalila tai murmushin yake sannan ta fito.
  Ameera ta kamata suka shiga ciki.
Ummi najin motsin mota ta fito, tana kallan sanda Hassan yai waje, ga Abba tun safe yau ya tafi Abuja.
  Suna isowa falon Ummy ta rike Jalila ta shigar da ita dakin Ameera tunda a kasa yake.
 Ummy ta kalli Ameera tace "Ameera dauko abinci."
 Nan Ameera ta fita, Jalila ta fara kokarin mikewa tana cewa "Ina kwana?"
 Ummy tai saurin riketa tace "Karki damu, ma gaisa inkin ware."
 Sagir na tsaye a jikin kofa yana murmushi, yasan halin Ummy ya tabbatar Jalila bazata taba wulakanta ba indai har Ummy na nan, kaf a duniya shi agunsa bai taba ganin mace kamar Ummy ba.

  Ameera ce ta shigo da tiren abincin, Ummy tace "zubo mata dankalin kadan"
 Ameera ta zuba mata ta mika ma Ummy, da kanta ta gyara mata zama sannan ta mika mata abinci, kallan mamaki Jalila take mata, bata taba tunanin zata samu kulawa haka ba, balle daga zuwanta ko sanin ta ba'ai ba.

 Haka ta dinga dan ci dan samon kanta tai da kasa yima Ummy musu, sai data gama Ummy ta miko mata magani da ruwa.
 Sai data sha, sannan Ummy tace karki kwanta kidan jira abincin ya tsirga miki kadan sai ki kwanta.

 Jalila ta d'aga kai, sannan ta maida idanta kasa.
 Ummy tai murmushi ta fita.
 Ameera ta mike ta biyota.

 Sagir na zaune a falon suka fito, yace "Ummy na!"
 Tace " Sagir sannu da kokari."
 Yai murmushi sannan yace "Ina Yaya yaje? Naga ya fita yanzu."
 Yanayin fuskarta ne ya canza, tace "yaushe rabon da insan inda Hassan zaije?"
 Sagir yai shiru dan ya fahimci yayi laifin tambayarta, Ameera ya kalla yace "Ashe kawarki ta koma gida?"
 Ta dan turo baki tace "sai yanzu ma ka kula?"
 Yace "kinsan dazu muna kan Jalila sam ban kula ba."
Ya mike yai kitchen.
 Ameera ta kalli Ummy tace "Ummy nikam dazu a asibiti, na rasa wa taje dubawa."
 Ummy tace wa kenan?

 Ameera tace "matar yaya."
 Ummy tace "ya sunanta ita matar yayan?"
 Ameera ta kalleta tace "Ja....."
 Kallan da Ummy ta mata ne yasa tai saurin cewa "Yaya Jalila."
 Ummy tace "me ya faru?"
 Sagir ne yai saurin katseta yace "to uwar gulma, ki bari ita Ummyn ta tambayeta da kanta mana."

 Ameera ta turo baki, Ummy tace "Sagir ya akai?"
Hannunsa rike da plate din da ya zubo abinci ya zauna akan dinning yana cewa "Wlh nima bansan wacece a asibitin ba Ummy, sai dai yanda hankalinta ya tashi da alama mai mahimmancice a gareta....."


 Ummy tace " shikenan, zan tambayeta."

 Sagir shiru yai ya kasa ko kai loma d'aya bakinsa, tunawa yai sanda suna zance da Jalila a makaranta yawanci in zatai abu zai ji tace ai Goggo kaza, ai Goggo kaza.

 Kallan Ummy yai da sauri yace "Ummy wannan matar data kawo Jalila itace "Mahaifiyarta?"
 Ummy tace "eh mana."
 Sagir yai shiru can yace "me suke ce mata?"
 Ummy tai murmushi tace "ina fa na sani? Dan jarida?"
A tare sukai dariya

^********^


 Jalila tayi bacci sosai dan sai azahar ta tashi, Ameera na dakin tana sa kaya sanda Jalila ta farka.
 Kallan Agoggo tai sannann ta mike da kyar ta kalli Ameera tace "Dan Allah zanyi alwala."
Ameera tace "ki shiga ga toilet."

 Jalila ta mike tai alwala, Tana idar da sallah Ameera tace mata ga abinci nan kici, Jalila tace "banajin yunwa.
 Bata sake mata magana ba, ta karasa kwalliyarta dan fita zatai ta fito daga d'akin.

 D'akin Ummy ta shiga tana zaune tana ta kiran number Abba, tun safe take ta ringing amma no answer.
 Ameera ta shigo tace "Ummy dawa zan kai sakon gidan Aunty Nanan?"
 Ummy tace " dama abin gara ne, gashi ba driver a gidan, ki duba ko Sagir nanan."
 Har ta juya Ummy tace " yayar taki ta tashi ne?"

 Tace "eh tayi sallah ma."

 Ummy ta mike ta fito tare da ajiye wayar.
 Sama ta hau dan taji alamar dawowar Hassan dazu, dakin ta kwankwasa.
 Yana kan sallaya rike da littafin Riyadul Salihin, ajiyewa yai ya bude kofar.
 Kallansa tai tace "Hassan ya jikin matar taka?"
 Kallanta yai yace "Ummy ni ai banganta ba?"
 Tace " baka ganta ba? Tana ina kenan?"
 Yace "ina na sani ni ai tun da suka fita ban kara ganinta ba."

 Tace "ko?"
 Baice komai ba sai kallan mamaki da yake mata, Ummy me take mai haka? A iya saninsa batasan abinda zai bata mai rai, sannan ko magana zatamai a cikin sanyi take mai.
 Kallanta yai yace "Ummy na kasa gane me ke faruwa, kince na amince da auran nan na amince ba tare da na musa ba, yanzu kuma gaba daya kin canza."

 Kallansa tai, yanayin fuskarta ya canza, abinda bataso dan ta kula in tama Hassan lago lago tabbas yarinyar nan zata kuntata a gunsa.
 Tace "Hassan ko kare ne aka baka shi akace ma gashi an baka shi, baka tunanin ya zama hakkinka ka kula dashi? In har kasa hannu ka amsa a iya tunani na dolene ka bashi hakkinsa, Hassan dabba ma kenan, balle dan adam, dan adam din ma mace mai rauni, yarinya karama."

  Kallanta yai baice komai ba, tace " yanzu da ace gidanku daban kenan haka zaka barta har ciwo ya mata illa?"

 Hassan ya kalleta yace "ba gaku nan ba,Ummy? Na tabbatar abinda zaku mata ni bazan mata ba."
 Tace "Hassan zuciyarka ma ta fara rikidewa?"

 Kallanta yai sannan ya kauda kai gefe, tace " a iya sanina yarona mutum ne mai tausayi da kula da abinda yake nasa da wanda ba nashi ba, Hassan yaushe zuciyarka ta fara rikidewa zuwa rashin tausayi?"

   Shiru yai jikinsa yai sanyi bai ce komai ba, tace " na haramta mata kwana a d'akinta, daga ranar jiya Hassan ko me zai faru in ganta a d'akin nan.

 Yace "Ummy...."
 Tace "zan kulle d'akinta ne ma in tafi da makullin, zan sa Ameera ta dawo da kayan sawarta nan dakin."

 Ran Hassan ya baci sai dai bai iya cewa komai ba, yana ji ta juya ta sauka, da kallo ya bitaa sannan yai ajiyar zuciya, dama ba auran ba, azomai da wasu sababbin al'amura shi ya tsana, sanda sukesan yai auran ba acemai komai ba, sai yanzu da yai auran ake san a canza mai rayuwarsa, me yasa basa duba yanayin lalurarsa tana bukatar sirri da kadaicewa?


  Ameera bata samu Sagir ba, tazo ta sanar ma Ummy, ba tare da damuwa ba Ummy tace "a kai gobe, yanzu muje sama."
 Tace "Sama kuma?"

 Haka suka shiga d'akin Jalila tasa a kwaso kayanta, tayi mamaki sosai dataga duk an d'auke kayan lefen da suka sa mata masu tsadar ciki, sai dai bata nuna ma Ameera wani abu ba, Hassan na jin alamunsu yasan me suke shirinyi.
 Fitowa yai ya sauko kasa ransa a bace zai fita.

 Jalila ta fito dan neman yarinyar da batasan sunanta ba, tanaso tace mata ta nuna mata inda kayanta suke tanaso ta dauko abu (wanka take sanyi ga batasan inda inners dinta suke ba.)

  Tana fitowa ta nufo falo tana tunanin inda zata ganta, tangamemen falon ta shiga kallo, dan dazu da yake kunya take sannan ba lafiya ce da ita ba ko kai bata daga ba, haka gidan yake? Kallan gidan ta shiga yi shi kuma ya sauko daga sama, san bata kuka dashi ba, shi kuma ransa a bace yake yana san fita.

  Tana tafe shi kuma ya taho da karfinsa ya bigeta, tsoron faduwa yasa ta riko rigarsa suka fadi a tare.

  Zafin faduwar ne yasa tai dan kara kadan, dagowa yai ya kalleta, itama kallansa tai.
 Idanunta ne suka fito dan ta ganeshi shine na jiya, wato shine angon nata kenan, kura mata ido yai sosai wanda yasa ta tsarguwa.

 A ina ya santa? Kallanta ya sakeyi, sannan ya mike tsaye.
  Haushi ya kamata duk da batajin dadi ai yaci ace ya mata sannu dan ta tabbatar yasan ta bige sosai.
 Hararsa tai wanda shi kuma daidai lokacin ya juyo da fuskarsa, hada ido sukai tana harararsa da sauri ta wayance tace "yaji ne ya shigarmin ido?" Wai ita adole bata ma kula dashi ba, magana take da kanta.

  Hassan kallanta yai sannan ya tuno harararnan an masa ita sau biyu, har ya juya sai kuma ya kara juyowa yai ya kalleta dan ya fahimceta sosai, itace takan hanyarnan da wacce ta harareshi a adaidaita.
 Oh, a ransa yace mai kuka?

 Jalila ma shiru tai tana tunanin faduwarnan, bashakka ta tuno, da sauri ta d'ago ta kalleshi.
 Mikewa tai tsaye, tana kokarin mai magana shikuma yai waje.

 Da sauri tace " ba kai bane?"
 Bai tsaya ba balle tasa ran tanka mata, kara kankance ido tai tana tunani, tabbas shine, wanda ya fadi akan titin nan.
 Zata kara magana taga harya fita, da kallo ta bishi sannan ta dan tabe baki tace "ba dai sanda ya kusa kadeni ya sanni ba?"

  Ganin batada amsar tambayarta yasa ta juya tana neman Ameera tare da rike bayanta, dan ta bugu sosai.

  Ummy tasa aka matsar da kayansa bangare guda, sannan aka jerama Jalila nata, hatta kan madubi sai da aka matsar da kayansa akasa nata.

 Ameera ta kalleta tace "Ummy kina tunanin Yaya zai  barta kuwa?"

 Ummy tai shiru, meye amfanin yi masa auran in basa tare?

 Haka suka gama sannan suka sauko.

 Jalila kam ganin ba alamar kowa yasa ta koma dakin ta zauna.


**********

  A can gidansu Mumy kuwa, Dady na kwance yayi shiru, Mumy ta shigo dakin, kusa dashi ta zauna ta sakalo hannu ta gefen cikinsa ta rungumeshi tace "Dadyn Yasmeen tunanin me kake?"

  Fuskarta ya shafa yace " Tunanin ki?"
 Tace "ban yarda ba, tunanin Jalila kake?"

 Yace "A'a why should i?"
Tace "karka boyemin komai plx, sannan kaima kaga gidan Taura ai, kasan daidai mata ne zasu samu zama a irin wannan gidan."

 Yai murmushi, tace "yaushe za'a fadawa Goggonta?"

 Yace "karki damu, ko ta sani yanzu ba abinda zata iyayi, macece mai hakuri, indai taga yarta cikin farinciki bazata iya cewa komai ba."

 Mumy ta jinjina kai, yace "ya gun Safeena?"
 Tace "suna Abujan, wai sai gobe zasuje ayi visa din."

 Yace "okay."


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)


*25*


 Tana zama bata dade ba taji anyi knocking din kofar sannan taji ance "Ameera!"
 Gabanta ne ya fadi jin muryar Uncle, wai nan fa gidansu ne ko? Sunanta Ameera dama?
 A hankali tace "batanan."
 Shiru yai shima kafin yace "Jalila dan bude."

 Mikewa tai ta bude kofar ba tare da ta bari idanunsu sun hadu ba.
 Sagir ya miko mata ledar dake hannunsa, kallansa tai bata amsa ba sannan batace komai ba.
 Kallanta shima yake sannan yace " test din ya fito, shine sukaban magunguna, dama kinada typoid ne?"


 Bata amsa mai ba ta amshi ledar ta bude, bayan magani taga yoghurt da exotic a kasa, zare ledar maganin tai sannan ta mikamai ledar kasan wanda ke dauke da yoghurt din.
 Kallanta ya sake yi sannan yace "kinsan wasu basa san shan magani da ruwa shiyasa....."

 Kallansa tai kamar zatai magana sai ta fasa, tace " Ameeran bansan inda tai ba."

  Juyawa tai tana neman rufe kofar, hannu yasa da sauri ya rike kofar, juyowa tai ta kalleshi idanunta sun canza suna neman yin kuka.
 Yace "Jalila wacece dazu a asibiti?"
 Tace " me kake so ka sani?"
 Yace "Kina nufin haka zamu zauna ko magana bakyasan ta hadamu?"
 Kallansa tai zuciyarta na kuna, sannan ta juya da sauri ta banko kofar.
 Hannu tasa ta rufe fuskarta saboda bakin ciki, wasu hawaye ne suka gangaro mata, ba santa yake ba, ta tabbatar yanzu kila kawai tausayin halin da ya ganta yakeyi.

  Sagir tsayawa yai ajikin kofar tare da kurama kofar ido kamar tana gun, sannan ya juya jiki a sanyaye.
 Yana neman fita yaji Ameera nacewa "Ya Sagir!"

 Juyowa yai ya kalleta, yana tsaye harta karasa gangarowa daga saman benan, ta matso gunsa tace "ina zaka?"
 Leda ya mika mata yace "Gashi kiba matar Yaya."
 Amsa tai tana cewa "menene ya Sagir? Sam ka canza  gaba daya yanzu bakasan magana sosai."
 Murmushi yai na dole yace "Ummy fa?"
Ta nuna sama da hannu tace "tana sama" sannan ta matso kusa dashi sosai alamar rada tace "Ummy fa ta dage sai yaya ya amince da matarsa."

 Sagir ya kalleta yace "bangane ba...."
 Tace "tana sama tana hada musu daki daya."

 Wani abu ne yaji ya harba kirjinsa me kake tunani Sagir? Abinda wata zuciyar ta tambayeshi kenan?.
kallanta yai yace "haba."
 Dakyar yai maganar, tace "Ai Ummy ta dage wannan karan."
 Harararta har sannan ya ture kanta yace "yaushe kika zama mara kunya? Wato harkin fassara zamansu a daki daya kena?"

 Tace " ko yaro dan shekara sha biyar ai yasan me ake nufi a wannan lokacin."
 Buge kafadarta yazoyi ta zille da sauri yace "Ameera? Kece kuwa?"

 Dariya tasa tace "ni ba ruwana Ya Sagir."

 Da kallo ya bita yana murmushi harta shige daki, tana shiga yanayin fuskarsa ya canza, daki daya? Wata zuciyarce ta kara cewa me kake tunani ne wai? Daga lokacin da aka daura aure ai kaima kasan abinda ya kamata.
 Juyawa yai jiki a sanyaye ya fita.


 Tana zaune tana kuka Ameera ta turo kofar, da sauri ta goge hawayenta, Ameera ta kalleta tace "jikin ne?"
 Kai ta daga alamar a'a sannan tace "Sunanki Ameera ko?"
 Tace eh, Jalila tace "ni sunana Jalila."
 Ameera tace "na sani."
 Jalila tai murmushi tace "Oh, yahkuri."
 Ameera ta kalleta tace "Ummy ce ta fadamin, sannan na gani a katin daurin aure."

 Jalila ta jinjina kai, Ameera ta mika mata ledar tace "gashi inji Ya Sagir, ah bakisanshi ba ko?"
Jalila ta kalleta batace komai ba, Ameera tace "shine kanin Yaya, daga shi sai ni, mu uku ne."
 Jalila tace "Yaya?"

 Ameera tace "Ya Hassan fa nake nufi mijinki."

 Jalila batasan sanda tai wata dariya ba wace ni kaina bansan irinta ba, miji? Mijin da sai yanzu ma tasan sunansa?

  Kallanta tai a ranta tace Husainin fa? Tace Hassan sannan tace Sagir.
 Kamar Ameera tasan me take tunani tace "ya rasu, dan uwan nasa."
 Jalila ta kalleta tace "Ayya Allah ya jikansa."
 Ameera ta ajiye ledar tana cewa Ameen.

Jalila ta dau maganin tasha.
  Jalila can tace "wanka nakesan yi kayana fa dan Allah?"

 Ameera tace "muje sama."
 Jalila ta mike ba tare da ta musa ba, Ummy na saukowa suna fitowa, Ummy ta kallesu murmushi tai sannan tace "Jalila kin mike?"
 Kai ta daga tare da sunkuyawa, tsugunawa sukaga tayi tace "Ina wuni."

 Ummy tasa hannu ta dagata sannan tace "ke da bakida lafiya?"

 Jalila kanta na kasa, Ummy tai murmushi sannan ta kamo hannunta, maimakon su hau sama sai ta riketa zuwa falo.

 Ameera ta kalla tace "Ameera asa mana abincin dare."
 Ameera tace "Ummy yau ma nice?"
 Ummy tace "ai na fada miki dama, daga kin shiga aji shida shikenan girki ya kamaki, yanzu kuwa kunyi hutun canjin aji kinga kuwa a matsayin yar aji 6 kike."

 Ameera ta shagwabe fuska ta nufi kitchen ranta ba dadi, ita kam tana ganin ya kamata a samarmusu mai aikin yin abinci amma taki, mai musu aiki ma suna gama gyara gidan suke tafiya sai kuma gobe.

  Ummy ta maido da hankalinta kan Jalila ta zauna sannan ta zaunar fa ita a gefen ta.
 Jalila ta zauna a darare, Ummy ta riko hannunta tace "Jalila!"
 Jalila ta kalleta kadan sannan ta maida kanta kasa tana kallan yanda Ummy take rike da hannunta, Ummy tace " ya jikin naki?"
 Jalila tace Da sauki.
 Ummy tai shiru kafin tace "da rokonki nake san yi."
 Jalila ta kalleta da sauri tana san jin menene, sai dai bazata iya dadewa tana kallanta ba, da sauri ta maida idanunta kasa.

 Ummy tace "rokonki zanyi akan ki saki jikinki da mu, ki maida gidan nan kamar gidan ku koma sama da gidanku, nasan zama da iyayen miji ba abune dayake da dadi ba,  abu ne mai wahala tun balle ga yarinya, sai dai mu lalurace tasa muke sanki anan gidan, sannan bawai dan mu cutar dake bane sai dan muna ganin in kina kusa damu hankalinki da namu sai yafi kwanciya."

 Lalura? Abinda yazo mata a ranta kenan sai dai batace komai ba har Ummy tace "Jalila mun miki laifi wanda nikaina nasan bamu kyauta miki ba."
 Jalila ta kalleta tace "Laifin me?"
 Ummy ta saki hannunta sannan jiki a sanyaye tace "mun miki laifi gun b'oyemiki larurar Hassan."

  Kallanta tai sannan ta tuno sanda ya fadi akan titin nan, aljanu? Hauka? Abinda ya fado mata arai kenan, Ummy tace "Hassan nada larura wanda mu kanmu iyayensa bamu sani ba, haka kawai tundaga mutuwar dan uwansa da dan kanin mijina Hassan ya koma haka, duk yanda mukaso musan matsalarsa mun kasa, munje asibitoci kala kala sai dai maganar daya ce, ba abinda ke damun kwakwalwarsa sai dai bamu san meke damunsa ba."

 Ummy ta juyo tare da goge kwallarta tace "Jalila ki yafe mana wannan laifin da muka aikata."

  Ganin Matar da ta sani a rana d'aya tana share kwalla sai taji gaba daya hankalinta ya tashi, batasan sanda tace "Bakomai na yafe muku."

 Ummy ta kalleta cikin jin dade sannan ta kara riko hannunta tace " jikina yana bani ke alhere ce a gareshi da mu kanmu, daga sanda naganki hankalina ya kwanta dake, Jalila ki daukeni a matsayin mahaifiyarki, ni kuma zan yi miki duk wani abu da uwa takema danta."

 Jalila tai murmushin jin dadi, dan haka kawai taji tanasan matar, dazu kukanta kadai yasa hankalinta tashi.

 Ummy ta kalleta tace "wa aka kwantar a asibiti?"

 Jalila ta kalleta idanunta suka ciciko, a hankali hawaye ya fara zubo mata.
 Ummy hankalinta ya tashi tace "ya isa haka nan Jalila, bazan kara tambayarki ba harsai sanda hankalinki ya kwanta da ki sanarmin."

Jalila share hawaye kawai take, Ummy ta mike tace "tashi kije dakin nasan abu zakiyi na tsayar dake."
 Jalila ta dago sannan ta mike, sama ta fara hawa, Ummy taji tace "dakin kusa da wanda aka kaiki jiya zaki shiga.
 Jalila tace to, nan ta tura kofar dakin, sanyin Ac dake kadawa a dakin da wani sansanyan turare ne suka bugeta, idanu ta lumshe a hankali sannan ta kalli dakin, yanayin kan madubin kadai yasa tasan dakin hade yake da namiji.
 Da sauri ta fito ta nufi dakin data shiga jiya, jin dakin tai a kulle, komawa tai dakin ta bude wardrobe gefe daya kayanta ne kaf, dayan kuma na namiji.

 Daki daya zasu zauna kenan?

  Inners dinta ta ciro sannan ta shiga wanka, kamar ba dakin namiji ba dan komai nashi a tsars suke, haka ta fito ta saka wata doguwar riga sannan ta kwanta agefen gadon, tana tunanin rayuwa, tabbas itakam zata fadama Ummy matsalar Goggo dan bazata iya kwana biyu ba bata ganta ba.
 Ta tabbatar Ummy zata fahimceta.


  Batasan bacci yayi gaba da ita ba, dan dama in tana zazzabi ta dinga bacci kenan, tsabar bacci ya mata dadi har da kara kwanciya, sanyin Ac din yasa ta jawo bargo.
 Bacci take hankalinta a kwance.


  Kofar dakin ya turo, gaba daya shi gidan ma baya san zama, tunda ya fita yana cikin mota a zaune.
 Sai yanzu daya gangaro gida, ganin magrib tayi, ya tabbatar Ummy yanzu zata shiga nemansa.


 Cak ya tsaya a kofar dakin yana kallan ikon Allah, tunda yake yau ne rana ta farko da wani ya taba bajemai akan gado haka, harda jan bargo?

 Ransa ne ya turnuko dan shi sam bayasan yaga wani a dakinsa, kusa da ita ya matso ya sa hannu ya fizgi bargon da karfi.

  Jan bargon da yai yasa ya hado da kasan doguwar rigarta yadan kwaye ta.
 Da sauri ta bude idanu, kallansa tai a zabure, shima idanunsa ne suka kai kasanta daya kwaye, da sauri ya dauke kansa, ita kuma ta mike zaune da sauri tana gyara rigarta tace "Malam me kenan?"

 Kallanta yai yace "Malam? Malam me kenan?"
 Bakinta na rawa tace " Umm."
 Ya hade rai yace "will you get up?"
 Kallansa tai cikin rashin fahimta, yace " bakyajin yaren?"
 Nan ma tai shiru, yace "banasan magana please tashimin daga kan gado."

 Jalila ta kalleshi tace " dan zaka ce in tashi sai ka min haka?"

 Wani kallo ya buga mata wanda batasan sanda ta mike ba, yace "a haka kika gadon?"

 A ranta tace "ahh yau ga wani irin mutum."

 Kallanta yai sannan ya kalli gadan, Jalila ta fara gyara gadan da karfi kana gani kasan na mugunta takeyi, tana yi tana dan murguda baki.
 Kallanta yai a ransa yace wannan kana gani kasan batada kunya wannan bakin sai ba fasashi wata rana.

 Jalila kuwa tana gyara wa tana cewa yo matsala ma ai basai an tambaya ba, mutum ba mutunci ai babbar matsalace.


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)


*26*


 
  Toilet ya shiga ya d'auro alwala, yana fitowa ya kalleta, tana tsaye tsuru dan itama jiransa take ya fito, ga fitsari ya matseta.
 Tana gani ya fito ta shiga ciki, kallan kofar data rufo yai ransa ya kara baci dan bakin cikinsa ya ganta a dakin nan.
 Tada sallah yai, bayan ya idar ya zauna ya fara addu'oinsa, itakam daga gefe ta dan rakube tai sallah, tana idarsa ta zauna agun tana yima Goggonta addu'a.

  Ameera ce ta buga musu kofa tana cewa "Yaya Jalila ki fito kici abinci"

 Juyowa yai ya kalleta ransa a bace, mikewa tai da sauri zata bude kofar.
 Batasan ya mike ba sai gani tai ya rigata sa hannu ajikin kofar.
 Kallansa tai yanda taga idanunsa sunyi yasa taji tsoro.
 Da karfi ya bude kofar sannan ya kalli Ameera.

  A tsorace Ameera tace "Yaya kana nan?"

 Kallanta ya sakeyi,ba sai ya mata magana ba tasan me yake nufi.
 Da sauri tace "Yahkuri yaya bansan kana nan ba."

 Jalila ya kalla, itama kallansa tai sannan ta kalli Ameera, bata fahimceshi ba sai cewa tai "me zanyi?"

 Hannu yasa ya turata waje sannan ya rufe kofarsa, Ameera ta kalla sannan ta kalli kofar tace "menai?"
 Ameera tasa hannu ta jawota tana mata alamar tai shiru.

 Suna sauka kan steps din tace "bayasan magana da hayaniya."
 Jalila ta kalleta batace komai ba, haka suka sauka kasa.

 Ummy nakan dinning tana rike da waya, kara neman number Abba takeyi amma shiru sai taita ringing harta katse ba'a dauka ba.

 Sagir ne ya ajiye kular daya dauko daga kitchen yana cewa "Ummy haryanzu Abban bai dauka ba?"
 Ta kalleshi tace "haryanzu, baka tunanin ko wani abun ya faru?"
 Zama yai a kusa da ita yace "bakomai insha Allahu, maybe ko aikin dayaje yi ne ya rikeshi."

 Su Ameera ne suka sauko, Ummy ta kalli Jalila tace "Jalila ban yarda da kici abinci ke kadai ba dan ba lalai kice dayawa ba."
 Jalila tai murmushi sannan ta zauna kusa da inda Ameera ta zauna.
 Bata kula da Sagir ne a saitinta ba, sai da Ummy ta mika mata serving spoon.
 Jalila ta amsa sannan ta kalli Sagir, idanunsu ne suka hadu da sauri ta maida kanta kasa, tana kallan plate din, ta ina zata ci abinci a nan?"

 Ta dan zuba abincin kadan, Ummy ta kalleta tace "Jalila wannan dan abincin fa?"
 Jalila ta kalleta tace "Ummy wlh haka cin abinci na yake."
 Ameera tai dariya tace "irin cin abincin Yaya kenan, hmm kunyi anko."
 Idanunta ta dago kadan ta kalli Sagir wanda yake ta juya abincin.
 Shiru ne ya biyo bayan falon sai dan karar cokula da suke tashi, Ummy ta rasa me yasa gabanta ke ta faduwa.

 Mikewa tai dan abincin da kyar take danci, ta kalli Ameera tace "ki dauko mata magungunanta tasha." Ta karasa maganar tana wucewa d'aki.
 Ameera ta mike tai daki, ya rage daga shi sai ita agun, Sagir ya kalleta yace "Ya jikin naki?"
 Bata kalleshi ba tace "na warke."

 Shiru suka karayi yace "Jalilah....."
 Ajiye cokalin tai da sauri sannan ta mike, dan batasan jin kalma daya daga gareshi, ina zata?
 Nufar dakin Ameera kawai tai, Ameera na fitowa ta kalleta tace "ina zaki?"

 Tace " hmm bandaki zan shiga."
Ameera ta mika mata maganin, amsa tai ta shiga ciki.
 Tunda ta mike yake kallanta harta shiga, idanunsa ya rufe yana neman tsari daga sharrin zuciya, shikam ya san ya hakura sai dai yana san ya warware misunderstanding dake tsakaninsu.

 *********

 Acan Abuja kuwa Abba ne ya kalli abokin nasa yace "wai kai da mukazo yin signing contract me ya kawomu nan?"
Ya fada yana kallan wani gidan da abokin nasa yai parking.
 Abokin nasa mai suna Hafiz ya kalleshi yace " abu zan amsa gun wani, yanzun nan zan fito.
 Fitowa yai daga motar yabar Taura a ciki, tsaki taura yai shi ya kosa su gama ya koma masaukinsa dan ya manta da wayarsa garin sauri.

  Sam bai kula ba sai jiyai ana kwankwasa glass din motarsa.
 Zuge glass din yai tare da kallan windown, wani irin kamshi ne ya shiga ratsa cikin motar, kallanta yai yarinyace wacce batafi shekara 28 ba, fara ce wanda har farin nata ma yasa zakasan ba cikakiyar bahaushiya bace, kana ganinta zaka san irin matan nan ne shuwa.

 Tasha kwalliya irin na zamani, kamshin da takeyi kuwa ba'a magana.
 Ya rasa dalilin dayasa ya kasa dauke idanunsa daga kanta.
 Murmushi tamai sannan tace "Yaya yace ka shigo kaci abinci."
Yace "Yaya?"
 Tace "Eh ai mijin yayatane."

  Yace "oh gidanshi ne kenan?"
 Tace "eh."
Gani yai tasa hannu ta bude lock din cikin motar sannan ta bude kofar.
 Kallanta yai, kayan da ke jikinta irin material ne mai kyalkyali, mace ce mai suna mace dan shape din ta ma abin kallo ne.
 Kai ya girgiza da sauri dan shikam mace baiga kyan da zaisa ta rinjaye shi ba.
 Kauda kansa yai daga kanta, matsowa tai saitin kunnensa tace "Please."
 Baisan sanda ya mike ba yace "muje."
Gaba tai tana wani murmushi, dan dama wannan shirin sunfi wata biyar sunayinshi, tundaga sanda taganshi a Abuja yazo shida matarsa wani taro, kayan jikin matar kadai ta kalla tasan kudi ya zauna musu, data tambayi mijin yayarta shine ta karajin irin kudin da yake dashi.
 Tun daga lokacin suka fara shirin jawoshi inda suke.

  Haryasa kafa zai shiga sai ya tsaya, juyowa yai ya kalleta yace "kicemai yai hakuri inada abinyi."
Ya fada tare da juyowa tana mai magana bai tanka mata ba.
Motarsa ya shiga ya jata da sauri.

  Ita kuwa Zaliha tana shiga cikin gida ta hade fuska, yayarta ta kalleta tace "ya ya?"
 Kai ta girgiza mata kawai sannan ta wuce daki cikin takaici.
 Yayarta ce ta kalli mijinta tace "Hafiz ya haka?"
 Yace " Taura namiji ne da bai kallan matan waje kuna tunanin daga haduwa daya zai amince?"
 Harararsa tai sannan tai gun kanwarta.


 ***********

  Abba na koma wa dakinsa ya dau wayarsa, kiran Ummy ya sau goma, sannan yaga kiran Sagir sau biya, sai sauran wanda abune na aikinsa.
 Yana shirin kiran Ummy wayar Hafiz ta shigo, dagawa yai cikin takaici yace "Hafiz bakada hankali ne?"
Hafiz yace "kayi hakuri dan Allah wlh dana shigo ciki ne matata ta dage akan sai na kiraka kaci abinci shiyasa nace Zaliha ta kiraka."
 Yace "meyasa to baka fadamin gidanka bane?"
 Yace "banasan ne kaji ba dadi, haba Taura dan Allah kayi hakuri."

 Kashe wayar yai sannan yai cilli da ita kan gado, ya rasa me yasa yarinyar ta tsayamai a ransa......


 ***********

  A can gidansu Hassan Kuwa jalila tana zaune a dakinsu Ameera, har wajen karfe 10, Ameera ta kalleta tace "ki tashi kije ki kwanta kafin Ummy tai magana."
 Jalila tai ajiyar zuciya sannan tace "bazan iya kwana anan ba ko?"
 Ameera da sauri tace "a ina? Ba ruwana wlh."
 Jalila ta kara yin ajiyar zuciya sannan ta mike, ta fito.

 Haka ta haura sama jiki a sanyaye, hannu tasa a hankali ta murda kofar dakin, yana kwance akan gado yana karatu.
 Kamar munafuka haka ta shiga cikin dakin, ko kallanta baiyi ba ya cigaba da karatunsa.

  Jalila tana tsaye har kusan minti ashirin, jitai kafafunta sun gaji nan ta matso kusa da gadon kadan, ta karasa kan kujerar dake dakin ta zauna tana dan matsar da littatafan dake jere agun.
 Jitai ance "karki kuskura ki hargitsamin abu, komai da kika gani agun a jere yake."

 Baki tadan tabe sannan ta daina taba litattafan, dama haushi yakeji dalilinta duk an canzamai tsarin dakinsa.

 Shiru ne ya kara ratsa dakin sai sanyin Ac dake kara sanyaya dakin.
 Bacci ne ya fara kamata dan har 11 ta wuce, tana zaune tana tunanin Goggonta.

 Ganin bashida niyyar fadamata inda zata kwanta yasa ta mike ta dau pillow din dake gefensa sannan tazo tana san daukan bargon dake kan gadon.
 Kafafunsa ne akai ta kalleshi tace "zan dan dauka."

 Kallanta yai yace "banaji naki ne."
Tace "a ina zan kwanta?"
 Alama ya mata da kasa da hannunsa ba tare da ya dauke kafarsa ba.

 Jalila haushi ya kamata, harararsa tai cikin takaici, sannan ta sa pillow ta kwanta a kasa, ai bayau ta saba kwanan kasa ba, dama saboda sanyi takesan luluba.
 Shikuwa bai kalleta ba sai dai ya tabbatar ta harareshi dan ya kula idanunta sun kware da harara sannan bakinta ya kware da murguda a bayan fage.

 Kwanciya tai ta lulube kafarta da zani, bacci ne yai gaba da ita.......

Kallanta yai sannan shima ya juya ya kwanta, abinda zai baka haushi bafa luluba zaiyi da bargon ba haka kawai.........

Wajen asuba ya farka, yai hamdaka da samun bacci mai kyau dayai, dan dama ba kullum abin tashi ba.
Dome light din dakin ya kunna sannan ya mike.

Alwala yai sannan ya dauko sallaya zai shimfida, kallan Jalila yai tana kwance a inda yake shimfida sallayarsa, bacci take sosai kafa yasa ya zunguri kafarta.

 Kara gyara kwanciya tai, ya kara sa kafa ya dan kara zungurar kafar tata, a hankali ta bude idanunta.
Ganin namiji tai a kanta da doguwar riga fara, tsorata tai, da sauri tai baya tare da yin ihu, tace wayyo Allah......
Da sauri ya rufota ya rufe mata baki, yace meye hakan?
 Sai alokacin ta tuna ashe fa wai a wani gidan take, sannan daki daya da namiji.
 Shiru tai sannan ta kalleshi, shima kallanta yai sannan ya mike yace " bakiji kiran sallah ba?"

 Tai shiru, dan batasan me zatace ba.
Mikewa tai ta nufi ban toilet.

 ********

 Inna ce ta kalli Dady tace "bazaka iya ba?"
Yace "ba wai bazan iya bane sai dai banga dalilin dazaisa a dauketa daga asibitin da take ba zuwa wani ba."

 Ranta a bace tace "kayi abinda na saka kawai, ko kana tunanin zan cuceta ne?"
 Kallanta yai yace "ba haka nake nufi ba."
Tace " kamaida ita Premier m, sannan kasa a gyara mata bangarenta, asa mata duk wani abu da ya kamata."

 Mamaki ya kamashi, a canza mata asibiti sannan a gyara mata bangarenta? Ya tabbatar wani abun take shiryawa na cigabanta ko na cigaban yarta.
 Bai musa ba yace to sannan ya mike ya fita.

 Shiru tai tana tunani........

#OneLuv💕

 **********
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)


*27*


   Dady na fita daga dakin ta dau waya ta kira Mumy.
 Mumy na shigowa ta kalleta tace “ki shirya muje ganin daki.”

 Mumy tace “ganin daki kamar ya?”
Inna tace “ au a aurar da yarki guda? Sannan babbar jika a gareni ina tunanin ya zama dole muje bayan an kaita muga muhallinta.”
 Mumy tai yar dariya tace “Lalai Inna, jikarki? Ni dai a kara za’a iya cewa ‘yatace amma Inna ke ai......”

 Kallanta tai fuska a d’aure tace “ me kike nufi?”
Mumy tace “Inna ai kece bangane me kike nufi ba.”
Inna ta ajiye wayarta sannan ta mike tace “ na rasa sai yaushe ne kwakwalwarki zata fara aiki yanda ya kamata.”
Mumy ta mata kallan rashin fahimta, Inna tace “nikam wacece babbar ‘yarki?”
Tace “Safeena mana.”

 Inna ta kalleta cikin takaici tace “wacece babbar yarki?”
Mumy tace “ni Inna rudani kikeyi.”
Inna ta harareta sannan ta girgiza kai cikin takaici tace “ni wuce muje ki shirya mu tafi, ni in munje gidan na miki bayani.”

 Mumy ta mike ta fita tana tunanin kalaman Inna, batagane wacece babbar ‘yarta ba, yo ai kowa yasan Safeena Qta fara haifa.
 Hart takai matattakala uku sai ta tsaya cak tace “ba dai......?
Komawa tai da gudu saman ta bude dakin Inna, tace “Inna badai so kike ki cema mutane nice mahaifiyar Jalila ba?”
Inna bata kalleta ba sai shafa man zafin da takeyi a kafarta da takeyi, Mumy cikin mamaki ta karaso kusa da ita tace “Inna?”
 Inna ta kalleta tace “ me? Kina tunanin is in possible?”
 Mumy cikin tsoro tace “Inna me kike tunani? Taya zaki canzama yarinya mahaifiyarta? Bayan mahaifiyarta nanan da rai?”

 Inna ta kalleta tace “ kina tunanin in Taura yasan gaskiyar al’amari akan ba yarinyarki bace zai yarda? Bakya tunanin zai ga yaudararsa mukai? In ya kwace kudin dayai investing a company dinmu fa saboda munyi betraying dinsa?”

 Mumy tace “to ai bai fito filli yace ‘yata yakeso ba, shidai babbar yarinyar gidan nan yace, sannan in ta sanar dasu fa kafin kije? Ni Inna wannan karan ban amince da abinda kika tsara ba.”

 Inna ta kalleta tace “shiyasa akoda yaushe nake ganin hankalinki da wayan ki na banza ne, ke wai haryanzu kina tunanin Abakar sanki yake?”
Tace “Inna zaki fara ko?”

 Tufe maganin zafin tai tace “ kiyi gaggawar tashi daga baccin da kikeyi, kada ki kuskura kiyi relying akan kowa inba ni ba, sannan kada kiyi trusting din kowa inba ni ba.”

  Mumy ta kalleta sannan ta mike kawai batace komai ba ta mike ta fito, itakam duk abinda Inna tace mata tana bi sai dai wannan karan hankalinta bai kwanta da hakan ba.

 **********

  Jalila kam da sutai sallar asuba falonsu na sama ta fito ta kwanta dan taga alamar baida niyyar mikewa daga gun.

 Wajen karfe tara ta farka, jitai jikinta ya ware, saukowa tai daga kan kujerar data ke kwance sannan ta karaso jikin kofar, hannu tasa a hankali ta murda kofar, kanta ta zuro a hankali tana lekawa, bata ganshi akan gadon ba hakan yasa tai tunanin baya dakin, tura kofar tai shiga, tana shiga ta hangoshi a kwance akan sallaya inda yai sallah, baki tadan tabe tace “kamar gaske.”

  Wucewa tai zata shiga toilet, gani tai ya fara wani abu harta je bakin toilet din, juyowa tai da sauri ta kalleshi, gani tai yana zufa sannan sai wani murkusus yake, idanunsa a rufe gam.

 Kallansa ta sakeyi tace “mafarki yake?”
Kusa dashi taje tadan sa hannu tadan tabashi, hannunta ya rike da karfe yana wani irin numfashi, sankamewa taga yanayi, tsoro ne ya fara kamata, ga hannunta ya kankame da karfi wanda zafinshi ya isheta.

 Cikin tsananin tsoro ta fara cewa “Yaya!” Dan abinda taji suna cemai kenan, Yaya! Yaya! A tsorace take kiran sunan nasa.

 Ganin zufa tana keto mai ta ko ina ga sai kara kamewa yakeyi, yanzu kam hannunta ya saki yasa hannunsa a wuyansa yana kokarin jawo numfashinsa da yake mai wahalar shaka.

 Jikinta ne ya fara rawa, ganin yanda yake sa hannu a wuyansa yasa tai saurin sa hannu ta rike nasa da karfi, a tsorace take cewa “Yaya! Yaya! Menene?”

  Ganin abin karuwa yake yasa ta fara tofamai kulhuwallahu, falaqi da nasi, dan bata iya addo’oi ba.

 Hannunta data rike nashi ya jawo hakan yasa ta fada jikinsa, da sauri ta mike, sannan ta shiga kiransa tana tabashi.

 Ahankali yai wani dogon numfashi, sannan ya bude idanunsa wanda sukai jaa.
 Idanunsa ne suka sauka a kanta tayi tsuru tsuru kamar kace mata kyaa ta ruga a guje....

  Kallanta yai cikin rashin jin dadi, dan shikam yasan abinda yake tsoro kenan, bayasan wani ya ganshi cikin wannan halin.
 Jalila kam tana nan a zaune kamar abu mara motsi har ya mike zaune, ganin yanda ta kame yasa ya mike tsaye ya zaune a bakin gado sannan yasa hannu ya shafi fuskarsa cikin takaici.
 Jalila a hankali ta juyo ta kalleshi bakinta na rawa tace “ hmm ka ka......”
 Kallanta yai fuskarsa a hade ga idanunsa sunyi jaa, wani irin tsoronsa ne ya kamata, gabanta ya shiga faduwa.
 Idanunsa na kanta yace “ ka me?”
 Kai ta girgiza da sauri tace “hm ba komai.”
 Ta juya da sauri gaban wardrobe taje ta bude ta rasama me zatayi a kai sannan ta matso gaban madubi shima ta tsaya, sannan ta bude bandaki da sauri ta shiga ciki.

 Duk abinda takeyi idanunsa na kanta, idanunsa ya sake runstewa cikin takaici, gani nai ya bude idanunsa ya mike da sauri ya dau waya da key din motarsa.

 Yana kokarin fita itakuma tana fitowa, kallan juna sukai da sauri ya dauke kansa sannan yai waje.

 Kallan kofar daya rufo tai sannan ta zauna a bakin gado tana maida numfashi kai kace gudu tai, me ke nan? Me ya faru dazu? Aljanu ne dashi? Kansa kalau kuwa? Badai wannan bace matsalar da Ummy tai magana?

 Ta dade a zaune sannan ta mike tai wanka, haka ta sa kaya jiki a sanyeye sam hankalinta ya kasa kwanciya.

  Ameera ce ta kwankwasa kofa, Jalila ta bude mata.
 Tiren abinci ta miko mata tace “ga abincin yaya, ke kuma ki sako muje kasa.”

 Jalila ta kalleta cikin sanyin jiki tace “Bayanan, sannan ni banajin yunwa.”
Ameera ta kalleta tace “yaza’ai kice bakyajin yunwa?”

 Jalila ta kalleta sannan ta koma ciki, gaba daya itakam abin duniya ya dameta, Ameera ta ajiye tiren sannan ta kalleta tace “ga na yaya nan sai kici anan, shi nasan ba yanzu zai dawo ba.”
Ajiye abincin tai ta fita.

 Jalila kam a zaune kawai take akan gado tama rasa ta ina zata fara tunanin abinda ke faruwa.

 Ganin ta rasa amsa kawai ta dauko hijab dinta ta sauko, su Ummy na cin abinci ta sauko kasa, kusa da Ummy taje ta gaisheta sannan ta gaida Sagir, Ummy tace “zauna muci abinci.”

 Jalila wacce ta fito dan sanar da ita tana san zuwa gun Goggo tai shiru tana wasa a hannunta.
 Ummy ta kalleta tace “Ya akai Jalila? Wani abin kikesan fadamin?”
 Dagowa tai ta kalli Uncle sannan ta kalli Ummy.

 Sagir ya kalli Ummy yace “ko jikin ne?
Ummy ta kalleta tace “Jikin ne?”

 Jalila da sauri tace “bashi bane.”
Ummy tace “to menene?”

 Jalila ta kalleta sannan ta sake yin shiru, Sagir ya yace “ asibitin zaki koma?”

 Kallansa tai sannan ta kalli Ummy, Ummy tace “wai haka?”

 Jalila ta daga kai, Ummy tai murmushi tace “menene to da kika kasa fada? Ki zauna kici abinci sai kuje da Sagir.”

 Kallan Sagir tai da sauri, sai dai batace komai ba.
Ummy tace “in bakya san ci anan ki hau sama kici kafin ya gama.”
Jalila tace “nagode Ummy.” Sannan tajuya tai ta hau sama.

 Zama tai a falon tai shiru Hassan take hangowa abinda yai dazu.

  Kanta ta kwantar akan kujera, Muryar Ameera taji tana kiranta, nan ta mike ta sauko ko dakin bata koma ba.

  Da zata fita Ummy ta kirata, Jalila ta juya taje gunta, Ummy ta miko mata leda sannan tace ki gaisheta, dan gwarama da kika tuna min yau kije, dan Abban Ameera inya dawo ba lalai ya barki ki fita ba, bayasan fita.”
Jalila ta amshi ledar tana godiya.

 A bakin mota ta hangoshi a tsaye, nan ta karasa kusa dashi, gani tai ya bude mata bayan motar sannan ya juya ya shiga gun zaman driver tare da kunna motar.

  Rufe kofar motar tai yaja suka fara tafiya, Motar tayi shiru sai karar redio dake tashi a cikin motar.

 Sunyi tafiya mai dan tsayi kafin can yace “Jalila.”
 Idanunta na jikin window tace “naam.”
Yace “Jalila nasan na miki laifi sai dai nan gaba zaki fahimci dalili na nayin hakka sannan na tabbatar a lokacin zaki san abinda nake nufi da kalamai na.”

 Kallansa tai sannan ta daure tace “ magana ta wuce, sai dai meke damun Yayan naka?”
 Shiru yai kafin yace “Ni kaina ban sani ba, dukanmu yan gidan ba wanda yasan meke damunshi, shikadai yasan abinda ya faru a lokacin.”
Lokacin?
Yace “ eh lokacin da su Husain da Nazir dan kanin Abba.”

 Jalila tai shiru batace komai ba, Sagir ya kalleta ta madubin gaban motar, yana tsananin san yarinyar nan haka kuma yana tsananin tausayinta sai dai duk yanda yaso da so da kaunar ta bai isa ba.....bai isa ba.”

  Dagowa tai ta kalli madubin suka hada ido, kanta ta kawar sannan a hankali tace “Uncle!”
Yace “naam.”
Har zata cemai Goggo mahaifiyarta ce sai ta fasa, tace “shikenan ma.”
 Yace “menene? Dan Allah ki fadamin.”

Shiru tai kafin can tace “Goggo nace a asibitin.”

 Yace “nayi tunanin Goggon da kike maganar ta ne amma ya kuke?ni da nadauka ai Goggon mahaifiyarki ce.”

  Zatai magana ya taka burki da karfi, juyowa yai ya kalleta yace “Jalila are u okay?”
 Tace “eh menene?”
 Yaran da suka tsallaka titin ya kalla yace “ yara ne wlh saura kiris su ja mana.”

 Shiru tai batace komai ba, gangarawa asibitin yai, parking yai sannan yace “Jalila ki yi hakuri dan Allah.”

 Kallansa tai tace “zancen hakuri da rashinsa ai ya kare, kafin ai abu ne ake neman canzashi ba bayan anyi ba.”
 Ta bude motar sannan tace “nagode.”

 So yake ya shiga amma bayasan ya kara bata mata rai.

Bata dade da shiga ba sai gatanan hankali a tashe tace “Uncle na rasa Goggo na.”
Sagir yace “ban gane ba?”

 Kuka ta saka hankalinta a tashe take cewa sunce an mata transfer zuwa wani asibitin kuma basusan sunan asibitin.”
Yace “ban gane ba?”

 Tana kuka tace “wai basu sani ba......”

 ********

  Abba kam dakyar ya samu bacci jiya, ya rasa meyasa gaba daya tunanin yarinyar da bata fi sa’an dansa ba ya dameshi.
Ai kuwa da sassafe ya fada mota da driver dinsa suka nufo kano, ko kara bi ta contracts din baiyi ba.

  Me ya sameshi? Me ke faruwa dashi?

*£**********

  Mumy ce ta kalli Sultan tace “Sultan bari muje gidan Jalila, ko zakaje?”
 Inna ce tai kakari wanda yake nuna mata ta daina, Mumy ta kalleshi tace “bari muje.”


Nan suka fito daga gidan suka shiga mota.

 #OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)


*28*

 Kasa tsayuwa tai kawai ta tsugunna agun tasa kuka, Sagir ya koma cikin asibitin ya tambayesu, yanda suka fadamai haka suka fada mai, fitowa yai gunta yace ta shiga mota tunda ai sunce wanda ya kawota shine ya dauketa.
 Tanaji tace "Dady ne."
Nan suka shiga yaja motar da gudu suka nufi gidansu, basuyi nisa da fara tafiya ba wayar Sagir ta shiga kara, Sagir ya daga tare da cewa "Ummy!"

 Ummy tace "Sagir kuyi sauri ku dawo iyayen Jalila da kakarta sunzo."
 Yace "gamunan."
 Ya juya kan motar yana cewa "jalila iyayenki suna gida."
 Hawayenta ta share tace "an fadama wa nene yazo?"
 Yace "kawai dai cemin tai iyayenki da ko kakarki ne?"

 Jalila tai shiru sai fatan Allah yasa ba wani abin bane ya faru, suna isa gidan ta fita da sauri ko motar bata rufe ba ta nufi cikin gidan.
 Da gudu ta shiga, a falo ta taradda Ameera rike da waya tana latsawa.
 Jalila ta matso tace "Ameera ina Mumy?"
Kallan ta tai tace "suna sama."

 Jalila tai sama da gudu, a falon sana ta taradda Inna, tsayawa tai sannan ta karaso a hankali, tsugunnawa tai ta gaida Inna kafin ta gaida Mumy.
An ajiye musu kayan ciye ciye a gaban su.

 Ameera ce ta hawo saman sannan ta mika mata makullin dakinta, Jalila ta mike ta bude dakin sannan tace ku shigo.

 Mumy ce ta fara mikewa, Inna kuwa sai data karema falon kallo sannan ta shiga dakin, zama tai tana kallan dakin kafin tace "ina mijin naki?"
Jalila tace "ya fita."
 Inna ta kalleta tace "rufe kofar."

 Jalila ta mike jiki a sanyaye ta rufe kofar, Inna ta kalleta ta mata alama data matso kusa da ita.
 Jalila gabanta sai faduwa yake ta matsa a hankali, ta tsugunna.

  Mumy ta kalleta tace "Jalila gun Goggo kika je?"
 Ta kalleta sannan tace "eh amma bata asibitin, ance Dady ya dauketa."
 Mumy ta kalli inna, Inma ta kalli Jalila tace "ni nasa ya dauketa daga asibitin."
 Jalila ta kalleta tace "Inna kikace in na amince da auran nan zaki kula da Goggo?"
Inna ta kalleta tace "hakane."
Jalila tace "kuma....."

 Inna tai murmushi tace " ba dai kina tunanin wani abin muka mata ba?"
Jalila a tsorace ta kalleta, Inna tace " kinsanar ma wani a gidan nan Goggo ce ta haifeki?"

 Jalila jiki a sanyeye tace "a'a amma......."
Inna tace "Jalila wacece ta haifeki?"
Kallan mamaki ta mata tace "ban gane ba Inna?"

 Har yaje zai shiga dakinsa yaji kamar ana magana a dakin Jalila bayan yasan Ummy ta rufe dakin, kuma yaga Ummy da Ameera a kasa.
 Hannu yasa kamar zai bude kofar yaji ance "tambayarki nake sannan amsarki nake so naji."
 Jalila tace "to ai Inna tambayarki gaba daya na kasa fahimtarta, bangane wanene ya haifeni ba?"
 Har ya juya zai tafi dan shi mutum ne da bai damuwa da abinda bai dameshi ba.

 Jiyai ance " abinda zamsanar dake inaso ya zama amsarki a duk lokacin da aka tambayeki, daga yau ko waye ya tambayeki mahaifiyarki ki tabbatar kince Mumy ce ta haifeki."

 Da sauri Jalila ta kalli kofar, shima da sauri ya kalli kofar, meke faruwa? Shidai a iya saninsa bai taba ji inda ake sanar da d'a mahaifiyarsa ba.

  Jalila tace "Bangane Mumy ce ta haifeni ba? Goggon tawa rasuwa tai ko me? Ina kuka boyeta? Ta fada cikin wani yanayi mai ban tausayi wanda yasa Hassan din jingina da bangon jikin kofar.
 Inna tace "ko daya, ina dai sanar dake ne hakan shine kadai zaisa mu taimaki mahaifiyarki mu kuma bata rayuwa na gari."

 Jalila jitai ta sa wata dariya mai tattare da bakin ciki da kuka, tana hawaye tace " A lokacin da za'amin auran nan kunce in na amince zaku kula da Goggona, sannan bayan na amince yanzu kunce kuma gaba daya ma in canza mahaifiyar datai wahala akai........"
 Marin da aka kifa mata ne yasa tai shiru, Inna tace " dan kinyi aure a gidan nan ne yasa kika fara tunanin yin jayayya dani? Ina magana kina magana?"

 Haryasa hannu zai bude kofar saboda ransa ya baci sai kuma naga ya tsaya, hannunsa naga ya dunkule sannan a ja baya daga jikin kofar, cikin takaici.
 Saboda nine kenan? Saboda iyayena sun nemi auranta yasa har ake neman sata yin haka.

 Labansa ya ciza sannan ya bude dakinsa ya shiga, ya rufo kofar da karfinsa na gaske.
 Wanda yasa sukaji kara, Inna ta kalli Jalila tace "mijin naki ne?"
 Jalila tana hawaye ta daga kai, Inna ta tabe baki a ranta tace hauka yake muraran irin wannan buga kofa haka? Ai kanaji kasan na marasa hankaline.

 Maida kallanta tai kan Jalila tace "shawara ya rage naki, inhar kinasan kiga mahaifiyarki kiyi abinda na saki, in kuma bakyaso ki hakura da ganinta ne wannan ya rage naki."

 Ta kalli Mumy tace "tashi mu tafi dan ba'a dadewa gidan surukai."

 Jalila tana kallansu suka mike gaba daya inbanda hawaye ba abinda takeyi, Inna ta fita daga dakin ta juyo tace "bazaki rakamu ba?"

 Jalila ta kallesu, yanda Inna take kallanta ne yasa ta mike ta fito falon.
 Tana fitowa shima yana fitowa daga dakin, rufo kofa, fuskarnan tasa a daure kallo daya ya musu ya dauke kansa, yi yai kamar bai ga mutane a gun ba ya wucesu ya sauka.

 Inna ta kalleshi sannan ta kalli Jalila bayan ya sauka tace "shine?"
Jalila ta daga kai, Mumy tace "amma yana ganinmi kamar yaga kashi?"
Inna tace "ki mai uzuri......"
Sai kuma tai shiru, kallanta Jalila tai badai sunsan matsalarshi ba? Ai a take tai tunani, haba itadai ta tabbatar da wani abun daga sanda ta iso gidan nan, ta tabbatar Bazasu taba ajiye Safeena su dauketa ba.
 Yanda take kallan Mumy ne yasa Inna tace" me kikeyi? Na dauka cewa nai muje ki rakamu."

  Zubewa akan gwiwowinta tai tana hawaye tace "Inna dan Allah na rokeki kiyi hakuri, zanyi komai amma dan Allah banda gurbin mahaifiyata."
 Inna ta kalli hanyar sama tace" me kike yi hakan? Salan wani ya ganki yace cutar dake mukeyi?"

 Jalila ta mike tana matse kwalla, Inna tace "muje."

 Haka suka sauko kasa tana bayansu.

 Ummy ta fito daga daki tace "har zaku tafi?"
 Mumy tace "eh wlh."

 Ummy ta kalli Jalila tace "Jalila ana kukan rabuwa ne?"
 Jalila ta sunkuyar dakai, Mumy tace " Ga tanan mun barmuku amana."

 Amana? Abinda ya darsuna zuciyar Jalila kenan, su basu riketa amana ba shine suke bada ita wai amana?
 Ummy taji tace "ai Jalila diyace agurina, insha Allahu yanda zan rike dan cikina haka zan riketa."

 Inna tace "mun gode sosai, Allah yabar zumunci, amma Taura fa?"
 Ummy tace " yana Abuja yau dai muke sa ransa."

 Sannan ta kalli Jalila tace "ki daina kuka dan Allah."
 Jalila ta daga kai tana share hawayenta.

 Haka suka fito Ummy ta mikoma Jalila leda tace " ki basu."
Jalila ta amsa tama Ummy godiya.

 Sai da suka shiga mota sannan tamikama Mumy tace "tace gashi inji Ummy."
Inna ta kalleta tace " ki tabbatar kinji abinda na fada miki."

  Jalila batace komai ba har motarsu, ta fita daga gidan, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata.

 Komawa cikin gida tai, wucewa dakinta tai kawai ta zauna tana kuka.
 Ummy ce ta shigo dakin, itakanta Ummy tun jiya hankalinta ba'a kwance yake ba ta nemi number Abba harta gaji, yanzu kuwa bama ta shiga gaba daya.

 Hannun Jalila ta kamo, tace "ya isa haka nan, insha Allahu bazakiyi dana sanin auranki cikin zuri'ata ba, Hassan na cikin wani yanayi ne sai dai ba haka Allah ya halliceshi ba, lalurace ta afkomai shekarun baya da suka wuce wanda muke addu'ar neman mai lafiya, da taimakon ki."

 Jalila ta kalli Ummy, Ummy tai murmushi tace "jiya a kasa kika kwana?"
Jalila cikin mamaki tace "ya akai ki...." sai kuma tai shiru, Ummy tai murmushi tace " ya miki magana?"
Jalila tace "hmm amma baifi sau hudu ba."
 Tace "Ba laifi dan banyi tunanin ma zai kula ki ba kwata kwata."

 Shiru tadanyi kafin ta kara riko hannun Jalila cikin murya mai rauni da tausayi tace "Jalila ki taimakeni."
Jalila ta kalleta jiki a sanyaye, tace "Jalila ki taimakeni gun ceto Hassan daga halin da yake ciki."

 Jalila tai shiru sai kallanta da takeyi, Ummy tace "Kiyi hakuri da duk abinda zai miki ma tabbatar wata rana zakiyi mamakin shi"

 Jalila ta share kwallarta tace "Insha Allahu Ummy."
Ummy ta jinjina kai cikin jin dadi tace "Jalila nagode sosai, sannan karki bari ya wulakantaki, inya miki ba daidai ba ki fito ki fadamai, hakan ne zaisa ya saki jiki dake."
 Jalila tai shiru, Ummy tace "Sannan inaso duk wani abu da kikeso ko ya dameki ki sanar dani, inaso mu zama daya ni dake, yanda na dauki Ameera haka na daukeki, kema inaso ki daukeni a matsayin mahaifiyarki...."

  Kalmar mahaifiya itace ta sa jikinta yin sanyi, a ranta tace Goggo kina ina????

 Ummy ce ta mike sannan tace " bari naje lokacin abincin rana yayi."
Jalila ta mike da sauri tace "bari inyi abincin Ummy."

 Ummy tace "ah hb? Daga yin aure sai girki?"

 Jalila tace " dan Allah ki barni nayi."
Ummy tace "muje muyi tare to, dan ina tunani Abbansu yau zai dawo."

 Haka suka sauko kasa abin sha'awa, sai dai zuciyar Jalila ciki take da tunani wanda take  kokarin  nemo ma kanta mafita."




#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

_ "There are three constants in life...change, choice and principles." -Stephen Covey_

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)


*29*


   Abba suna shigowa garin kano yacema driver dinsa su wuce gidansa na governor road, driver din yayi mamaki dan Abba ya dade bai ko leka gidan ba, ko yazoma sai dai yai abu minti kadan ya fita.
 Yau kam suna isa ya shiga ciki ya kwanta a falonsa, hannunsa yasa asaman goshinsa yana tunani.

 Mamman driver ya juya ya fita da mota, yana kokarin shiga layinsu shi kuma lokacin ne Hassan ya fito shima.
 Ganin motar Abba yasa ya danyi parking, Maman ya bude motar da sauri ya matso jikin window din da yake zaune, Hassan ya zuge glass din sannan ya kalleshi.
 Mamman ya gaisheshi, bai amsa ba yace "Ina Abban?"
 Mamman yai shiru kafin yace "Yallabai na gidansa na governor road."
 Kallan mamaki yamai yace " me yake acan?"
 Yace "ban sani ba wlh, kawai cewa yai in kaishe."
 Hassan ya tada motarsa yai gaba, direct gidan ya wuce ya shiga ciki.

  Kofar falon yai knocking sannan ya tura ta, Abba me kwanc akan doguwar kujerar dake falon, shima Abban jin motsin kofa yasa ya bude idanunsa.
 Hassan na tsaye a jikin kofar yana kallansa, Abba ya kalli Hassan sannan ya mike zaune yace "Hassan?"

 Hassan yana daga jikin kofar yace "me kake anan daga shigowarka gari?"

 Abba yai ajiyar zuciya yace "kawai!"
 Hassan yace "kawai? Taya Abba zaka taho nan bayan kasan Ummy dole tana jiranka? Ai tunda kake tafiya koda bana kula na tabbatar baka taba yin haka ba."

 Abba ya mike tsaye ya tako zuwa inda yake yasa hannu daya kan kafadarsa yace " kai fa?"
Hassan yace "me?"
Abbba yace "naji ni wannan karan ne kadai na tabayin haka kaifa? Kana kula da taka matar?"

 Hassan kallan mamaki yamai fuskarshi cike da mamaki yace " ban gane ba? Abba ya muna maganar Ummy kana zancen wata?"

 Abba yai murmushi yace "kai namiji ne kafin d'a na yanda nima nake namiji kafin na zama mahaifinka."

 Yanzu kam kallan zargi Hassan yama Abbansa yace "mekake nufi Abba?"

 Abba ya girgiza kai yace "nima bansani ba, kawai dai sanar dakai nai abinda nakeji."

 Hassan ya kalleshi baice komai ba, kawai ya juya zai fita.
Abba yace "sai ka maidani gida koba d'aukata kazoyi ka kaima mahaifiyarka ba? Dama kai a rayuwarka damuwarta ita kadaice abinda ka sani."

 Hassan ya kalleshi kawai sannan ya juya ya shiga motar sa, zama yai yana tunanin kalaman Abba, me yake nufi? Fada sukai da Ummy? Shifa a duniya ran Ummynsa ne kadai bayasan yaga ya baci.
 Yana zaune sai ga Abban ya bude motarsa ya shiga gefensa.

 Hassan baice komai ba yaja suka fara tafiya..........


  Su Ummy na kitchen itada Jalila suna aiki, Ameera ta tafi gidan Aunty Nana kai sako, Ummy sai mamakin kwarewa da Jalila tai a gunki take, wanda haryasa tace mata "Jalila nayi mamakin yanda kika iya girki a shekarunki."

 Jalila tai murmushi tace "ai kullum ni nake abinci a gida, daga na safe, na rana har na dare."
 Ummy tace "makarantar fa?"
Jalila tace "ina zuwa."
Ummy ta kalleta cikin jindadi sannan suka cigaba, suna cikin aikin sukaji muryar Abba yace "Amarya da kanki?"

 A tare suka juyo, Ummy ta kalleshi cikin kulawa sannan ta taho inda yake, Jalila kuwa sunkuyar dakai cikin kunya.

 Ummy ta karaso inda yake tace "Sannu da zuwa."
 Murmushi ya mata yace " yauwa."
Sannan ya juya, Jalila ce ta juyo, hada ido sukai da Hassan wanda batama san tare suka shigo ba sai yanzu, kallanta yai sannan ya dauke idonsa daga kanta.

 Itakuwa kura mai ido tai zuciyarta na raya mata meke damunshi? A haka dai gashi garau sai ta tuno. Abinda yai jiya, tace da daddare kuma sai ya rikide? Ko inyai bacci?

  Alamar kamawar dataji ne yasa tai saurin kallan tukunyar sannan ta cigaba da girkinta.
 Shikuwa Hassan sai dayaje zai hau sama sannan ya sake juyowa ya kalleta, ya suka kare da mutanen dazu?
 Tsaki yai sannan yace "meye damuwata?"
Sannan yahau sama.

  Dakinsa ya shiga kawai ya zauna akan gado.

  Ummy kuwa a daki ta kalli Abba da ya zauna akan kujera tace "gajiya ko?"
 Ya kalleta yace "a gajiye nake tilis naje gidana na governor road in huta danki ya taso ni."
 Tace "kamar ya?"

 Ya mike yana balle botiran jikin rigarsa yana cewa " bari nai wanka."

 Rigarsa ya cire ya shiga toilet da kallo ta bishi, danta? Hassan kenan dan Sagir tare suka fita da Ameera.

  A iya saninta Hassan kuma kamar abin da wuya, mikewa tai ta fito ta nufi kitchen.

 Jalila ta kalla tace "ko zaki kai mai abincin safe? Banaji ya karya."
Jalila tace "Ummy azahar fa?"
Ummy tai murmushi tace "haka yake, ni kaina ina mamakin yanda yake tauyewa cikinsa hakkinsa, kamar bai san darajarsa ba."

 Jalila tai shiru tana tunanin Goggonta wacce kullum take mata fada akan cin abinci, ashe ba ita kadai bace ga namijima da girmansa ana fama.

 Ummy ta kalleta tace "me kike tunani?"
Jalila ta girgiza kai sannan ta nufi sama, a hankali ta tura kofar, sannan ta leko kanta.

 Yana tsaye jikin madubi daga shi sai dan towel, da sauri ta maida kofar ta rufe shi kuwa yana tsaye yana kallanta.

 Tana rufewa tai ajiyar zuciya tare dasa hannunta akan kirjinta tana maida numfashi, meye hakan? Taya katan namiji zai hau cire kaya haka?

 Kara tura kofar tai tana tunanin ai dole ya sa riga tunda dai yaga tana neman shigowa, gani tai ba kowa a dakin, baki ta tabe sannan ta shiga ciki tana cewa dole ai yaji kunya ya shige toilet.


 Motsi taji a bayanta ta juya da sauru bayanta, yanda yake dazu haka yake yana neman abu a cikin drawer, idanu ta zaro sannan tasa hannu ta rufe idanta da sauri.

 Shaver zai dauka yana ganinta ya dauka yazo ya wuce kamar baisan da mutum agun ba, toilet ya bude ya shiga.

  Jin karar rufe kofa yasa ta bude idanunta a hankali sannan ta kara sakin ajiyar zuciya tana cewa "Woah! Kamar bai ganni ba?"

  Kallan kofar toilet din tai sannan ta fito, ta sanarma Ummy, suna kammala girkin Ummy ta zuba a kula ta bata tace "ki hau muku dashi sama, Jalila ta dauka ta hau sama, itakam batasan hawa saman nan kwata kwata."

  Tana shiga ta taraddashi yana ninke sallaya, ya ajiye sannan ya kwanta tare da dauko littafin da yake karantawa.

  Abincin a ajiye ta dibi nata dan kadan ta fito falo.

 Yau gidan shiru kamar ba mutane, Ameera da Sagir basa nan, Ummy na daki ita da Abba shima waccan yana daki, sai ita kadai a falo.

 Ummy kam ta kula mijin nata bayasan dogon magana, da alama akwai abinda ke damunsa, haka ta fito daga dakin ta zauna a falo itama.


  Da daddare kuwa banda juyi ba abinda takeyi, abinda ya faru dazu da safe shine ke damunta, taya zasu nemi ita da kanta ta wulakanta Goggonta? Matar da batasan so ba a rayuwarta? Matar da duk duniya ita kadai ke santa? Ita kadai ta damu da ita? Ita kadai ce gatanta?

 Hawaye ne ya shiga zubo mata, wajen karfe daya ta mike ta zauna kawaj ta fara kuka, shikam duk abinda takeyi yan jinta, dan shi sam baya iya bacci in ana mutsu mutsu a kusa dashi.

  Jin yanda take kuka ne yasa shi mikewa zaune, fitilar gefen gado dake dakin ya kunna.

 Da sauri ta koma ta kwanta tana share hawayenta.
Kallanta yai yace " inkinsan kuka zakiyi ki fitarmin daga daki, dan banga dalilin da zaisa a hanani bacci a daki na ba."

 Jalila ta dan turo baki wasu hawayen suka zubo mata, Hassan ya kashe fitilar sannan ya kwanta, mikewa tai tana neman fita, dayake dakin duhu ai kuwa ta bugu da jikin gado.

 Da karfi tace wayyo!
 Iska ya firzar sannan ya zauna ya kara kunna fitilar dakin, yace "meye......."


 Ganin yanda ta rike kafarta ne tana kuka yasa ya kalli gun, karamin dan yatsanta ta buga gashi hargun ya daga yana jini sosai.
 Dama me neman kuka, ganin ya taso inda take kawai ta kara sa kuka.

  Bai kulata ba sai hannunta daya riko ya zaunar akan gado, tissue ya warwaro dayawa ya rufe gun ciwon idanunsa suka canza zuwa jaa.

 Daga bayama gani tai ya runtse idan nasa kamar bayasan ganin jinin.

  Kallanta yai sannan yace " rike."
 Rikewa tai tana kuka, mikewa yai ya juya ma inda take baya, sannan ya dan dafa kansa.

  Kwalin tissue din ya miko mata ta amsa tana kuka, yace "will u please keep quiet?"

 Hadiye kukan nata tai tana kallan bayansa.
 Juyowa yai inda take cikin zafin rai yace "are u a fool?"
 Shiru tai tana kallansa, hannu yasa ya dagota ya rike kafadunta da karfinsa ya matso cikin zafin rai yace " me yasa sanda suke miki zancen banza baki basu amsa ba? Me yasa sanda suke neman sa ki abinda zai saki kuka baki sanar dasu abinda ke ranki ba? Nine marainin wayanki? Zakizo ki sani a gaba kina min kukan banza?"

  Idanun Jalila ne suka firfito gabanta sai faduwa yake da sauri da sauri saboda tsananin tsoronsa da ya shegeta, bare yanda ya matso daf da ita haka ba namijim daya taba mata haka, ga idanunsa sun canza, ga yanda yake mata fada, jitai gaba daya ta rasa abin cewa.

 Ya turata kan gado cikin takaici yace " kinsan ma'anar uwa kuwa? Ko dabansan meye hadinki dasu ba, kada ki kuskura ki dauki uwa a bakin wasa, no matter how they threatened u , don't u ever try that."

 Ya juya zaiyi falo, gaba daya zuwan yarinyarnan yasa ana sashi magana mai tsayi haka, wanda rabon daya yita har ya manta.

 Harya kai kofa tana kuka tace " kana tunanin nima asan raina akemin haka?"
Tsayawa yai amma bai juyo ba, tana kuka tace "batada lafiya, batada lafiya sosai Yaya!"

 Ta kara sa kuka, juyowa yai ya kalleta, kuka take sosai wanda haryasa hannu zai bude kofar yasa ya fasa.

 Komawa yai ya zauna a kan gadon sannan yace "zan kwanta."
Mikewa tai ta sa tissue din a dustbin sannan ta koma kasa ta kwanta tana share hawaye.
Kashe wutar yai dakin yai duhu sai sanyi dake kara ratsa dakin, dukansu idanunsu biyo sai juyi kawai da takeyi.
 Shikuma yana kwance rigingine.

 Can ta daure tace "yaya ya akai ka sani?"

 Bai kula ta ba hakan yasa tai shiru, can tace " bansan yazanyi ba, Goggo na sun dauketa daga asibitin da aka kaita, bansan abinda zasu aikata ba inhar banyi abinda suke so ba."

  Yanzun ma bai kula ta ba, sai dai a yanzu ya fahimci da mahaifiyarta ake sata abinda akaso, wanda yauce rana ta farko tun bayan faruwar abinda ya sameshi yauce rana ta farko daya fara tunanin yanasan jin dalilin abinda bai shafeshi ba, yanasan sanin me zata aikata akan abinda baishafeshi ba.



 #OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

_ "Sometime you will never know the value of a moment untill it becomes a memory" Dr Seuss_

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)


*30*


   Wajen sallar asuba tana bacci taji kakkari, idanunta ta bude a tsorace sannan ta mike tana neman fitilar jikin gado dan ta kunna, ji tai ta fada kan mutum a rikice tasa hanny ta taba shi.
 Kan fuskarsa ta taba, hannu yasa ya riko hannunta da karfi yana wani abu.
 Idanunta ne suka firfito saboda tsananin tsoro jikinta ya fara kyarma, da kyar takai dayan hannun nata ta samu ta kunna fitilar.

  Yanda yake yi da jikinsa ne yasa ma ta kasa kokarin kwace hannunta, gaba daya tsoro ya gama kasheta.
Tai tsuru tsuru da ido tana tabashi da dayan hannu tana cewa "Yaya! Yaya!"

    Hannunta ya saki ya sa a wuyansa kamar me shirin shake kansa, Jalila cikin tsoro ta rike hannu tana kiransa.
 Bakinta rawa kawai yake gun kiran sunan nasa, idanunta sun ciciko batama san sanda hawaye ya fara zubomata ba saboda tsoro.


  Yau abin yafi na jiya shiyasa hankalinta ya tashi gashi su biyu a daki, kuka kawai take tana jinigashi.
 Sai dan karatun data iya datake yi, idanunta ta rufe kawai dan batasan ganinsa a haka gaba daya ya canz kamar mahaukaci ko mai farfadiya ko mai aljanu.

  Kuka take tana kiransa wani sain tai karatun idanunta gam, har batasan abin ya lafa ya bude idanunsa ba.
 Addu'oi yai sannan ya kalleta, tausayinta ne ya kamashi, yarinya karama a maidata mai jinya? Hannunta da take tabashi dan ya tashi ya rike.

 Idanunta ta bude a hankali a tsorace, ta kalleshi.
Yace "kukan meye hakan?"

 Bakinta na rawa tace "Yaya?"
 Yace "mutuwa akai?"
Kai ta girgiza, yace "to meye hakan?"

 Tana kuka tace "bakomai."
Yace " meyasa baki nemi sanin wanda za'a baki ba?"
Tace "kamar ya?"
Yace "bakida 'yanci ne? Ko tsabar biyayya ce tasa? Ni naji inada lalura wanda ban isa in zabi matar da nake so ba, kefa?"

 Tace "nima."
Nima? Ta share hawayenta da dayan hannu  "ni Goggo batamasan nayi aure ba."
 Abinda ta fada kenan a ranta batasan a fili tai ba sai jitai yace " Goggo?"

 Kallansa tai sannan ta kakaro murmushi tace " hannuna."
 Sakar mata hannu yai sannan ya mike zaune yana kallan agoggo, mikewa yai ya nufi toilet ba tare da ya sake kallanta ba.

 Kallansa tai a ranta tace " ikon Allah, wato wani sa'in sai kaga Allah ya baka komai sai ya hanaka wani abun, kalli yanda ake sanshi a gidan nan, batasan ba kodan bashi da lafiya ne amma kaf gidan nan yanda suke mai sai kasan sanda sukemai daban ne, wanda ko kwana daya ko wuni mutum yai dasu zai fahimci hakan.

 Mikewa tai bayan ya fito tai alwala, kafin ta fito ya tada sallar ta fita falo tai sallarta sannan ta kwanta akan kujera, yau kam baccin bai dauketa da wuri ba tayi luff akan kujera tana jin kira'ar qur'ani mai dadin gaske wanda ta tabbatar radio ne yake aiki, tanasan taga tana karatun qur'ani ko ba kamar haka ba amma dai taga ta iyashi, in sultan na karatu a gida ji take inama itace.

 A haka har bacci yai gaba da ita.

  Hassan kam ya dade akan sallaya kafin ya kwanta.

  ***********
_Bayan kwana hudu._

  Goggo ce ta kalli lantana tace "Lantana Jalila bataso ba da ina barci?
 Lantana tace "eh."
 Goggo tai shiru "yau kwanana hudu kenan a sabon asibitin nan amma banga Jalila ba wanda na tabbata indai har da lafiyarta bazata taba iya kwanakin nan haka batazo ba, sannan ba wanda take gani abinci kawai suke aiko mata, bayan sanda zasu canza mata asibiti sai da suka sanar da ita Jalila nacan ma tana jiranta.

 Meke faruwa? Anya ba wani abun sukama Jalilanta ba kuwa? Wannan tunanin ne yasa hankalinta ya tashi, har jininta ya sake hawa, matar da ake tunanin sallamarta nanda kwana biyu.

 Goggo kira kawai take a kira mata Jalila.

*******
Itakam Jalila kalaman Hassan sune sukai ta mata yawo.
Gashi hankalinta ya kasa nutsuwa saboda rashin Goggonta, duk da yanda Ummy ke iya kokarinta na ganin Jalila ta saki jiki da gidan.
 Sagir kam baifiya ma zama ba saboda hankalinsa tashi yake inyaga Jalila.

  A hankali ta turo kofar, yana kwance a kan gado yana karatu, ta rasa mai yasa ita ko irin wayarnan taga yanayi ko yana dannata bayayi.
 Shiga cikin dakin tai ta tsaya tana dan wasa da hannunta.
 Bai kalleta ba bakuma tasa ran zai kalleta din, hakan yasa ta matso kusa dashi kadan.
Nan ma bai kalleta ba, daurewa tai tace "Umm Yaya!"

Bai kalleta ba yace "menene?"

 Tana wasa da hannunta ta rasa mai zatace, ganin batada niyyar magana yasa ya cigaba da abinda yakeyi.

 Jalila kam ganin tsayuwar bamai karewa bace gashi ita tasan zata iya fadama Sagir sai dai ta ina zata fara kebewa dashi ta sanar mai? Sannan mai zaiyi tunani? Gwara dai Hassan din tunda koma menene at least yasan wani abin na daga rayuwarta.

 Ganin haka ma sai ya mike yadau waya da key din motarsa yana neman fita.

 Cikin hanzari ta riko gefen rigarsa, tsayawa yai sannan ya juyo ya kalleta sannan ya kalli rigar tasa inda ta rike.
Tace "Hmm Yaya magana zamuyi."

 Da kai ya mata alama da yanaji, ta sakeshi sannan ta tsaya.
 Yace " in baka san me zakice ba ni zanyi gaba."

 Jalila tana gani ya juya ta kara riko rigarsa da sauri, kallanta ya juyo yai sai dai yanzu yanayinsa yadan canza yace " meke nan?"
 Tace "Yaya!"

 Matsowa ya fara yi tana matsawa baya, tsoro ya fara ratsa mata har sai da sukaje jikin gado ta fada kan gadon, gani tai ya rufo kanta, tsoro da fargaba suka kamata, idanunta suka firfito ganin namiji akanta haka.

 Idanunta ta runtse gam cikin tsoro, can taji shiru, a hankali ta bude idanunta a tsaye ta ganshi yace "2minute na baki."

 Tace "Yaya......"
Yace "will you stop calling me?"

 Magana nace kiyi ba kirana ba.
Ta daure tace "Yaya bansan ya zanyi ba."
 Ya kalleta alamar me take nufi.

Tace "maganar Goggo."
Yace "to menene nawa a ciki?"
Tace "naam?"
Yace "menene nawa a ciki da kike fadamin?"

 Shiru tai dan batasan me zata ce ba, agoggon hannunsa ya kalla yace "minutes din da na baki sun cika."

 Ya juya ya fita tana kallansa, ajiyar zuciya tai tace "Jalila u are really a fool."

 Shikam yana fita ya sauka kasa zai fita, Ummy ce ta leko daga daki tace "Hassan?"
 Kallanta yai sannan ya matso yanasan jin menene, ta kalleshi tace "ina zaka kuma?"
Yace " fita."
 Shiru tai alamar damuwa wanda yasa yace "menene?"
 Tace "Hassan na rasa meke damun Abbanka."

 Kallanta yai cikin kulawa, sai dai baisan ta ina zai fara jin matsalarta ba, yace " Me yayi?"

 Ta girgiza kai tace "bakomai, jeka kawai amma dan Allah ka dinga zama a gida kaga Ameera tunda taje gun Aina'u bata dawo ba, Sagir kuma na rasa me yakeyi yanzu sam ya rage zaman gida, ni kuma kasan dole tadingajin nauyi na, ka taimaka ka dinga zama ko da ba lalai ka yarda kuyi hira ba at least dai zataji motsinka a kusa  da ita."

 Kallanta yai kawai bai amsa ba sai cewa dayai "Abban me ya miki?"
Tace "me zaimin kuwa? Kawai dai naga ne kamar akwai abinda ke damunsa" dan tasan intacemai ya canza mata gaba daya, ya daina zaman gida, ya daina zama suyi hirar business data duniya lalai tafi kowa sanin halin Hassan, abin ne ke cinta yake damunta shiyasa ma tamai magana.

  Kallansa tai tace "sai ka dawo."
Tai saurin komawa daki, haryakai jikin kofa sai naga ya juyo ya kalli sama sai kuma ya fita.

   Jalila ta zauna a kasa ta baza tagumi, takaicin kanta duk ya isheta, sai yamma ta sauko.
 Kofar Ummy taje ta kwankwasa, Ummy ta fito sanye da hijab da alama sallah ta idar.

 Jalila tace "Ummy me za'a dafa?"
Ummy tai murmushi tace "dauko hijab dinki mu fita cefani.
 Jalila cikin mamaki tace "Cefane Ummy?"
Gani tai tunda tazo gidan bata taba gani anje cefane ba masu aiki ne ke siyowa.

 Ummy tacemata yi sauri.
Jalila ta juya zuwa sama, hijab dinta ta dauko sannan ta sauko.
Ummy ta daga waya tace "Dan Ummy ka iso?"
Yace eh, nan suka fita.

 Sagir na tsaye jikin mota yana hangosu ya fito ya bude musu baya yanama Ummy salute.
 Ta harareshi tace " Officer ka iso?"
Yace "barka da isowa."

Jalila tai dariya tana kallansu abin sha'awa, bata taba gani mace mai saukin kai kamar Ummy ba, tasan itakan Goggonta kadai ta sani sai yanzu dataga Ummy.

  Suka shiga baya dukansu, Ummy tace "Driver mu fara zuwa Wellcare.
Nan suka tafi ahanya sai hira sukeyi, Jalila kam sai dai tai murmushi sai in an tambayeta tace eh ko a'a.

  Ummy kam ta fito ne dan ta debe musu kewa da ita da Jalila, dan tasan Jalila na bukatar kulawa, ita kuma saboda gudun tunani da zargi yasa take neman abinda zai debe mata kewa.

  Haka sukaje sukai siyayya sosai, sannan suka biya shagon wayoyi, Ummy da kanta ta zaboma Jalila waya irin ta hannunta Sumsung ce Note 9.

 Jalila kam gaba daya ta rasa me zatace, dan itakam batasan ta inda zata fara magana ba.
 Sagir kam dadi yakeji ganin fuskar Jalila na dauke da murmushin da yake har zuciyarta bawai na iya baki ba.

   Haka suka isa gida sannan sukai abinci ta dau nasu ta hau sama, yau kam zuciyarta ta ragu da damuwa, sannan ta kara samun karfin gwiwar yima Hassan magana.
Bayan isha'i ya dawo ta jawo mai abinci kusa dashi, Hassan ya kalleta yace "nasha yogurt, later."

 Jalila ta dauke tasa a gefe, zama tai a kan gadon daga inda kafafunsa suke can karshen gado, ta mikomai wayarta.
Kallanta yai sannan ya amsa, yace "na meye?"
Tace "Ummy ce ta saimin."
Ya juyata sannan ya mika mata yace "to."
 Tace "bakasa number ka ba."

 Yace "me zakiyi da ita?"
Tace " In wani abin ya taso."
 Ya kalleta yace "kamar me?"
 Wayarta ta amsa tace "shekenan kawai kace dai bakasan sawa."

 Kallanta yai yace " kawo dai."

 Ta mika mai tana dan tabe baki kadan kanta a kasa, ya amsa yace "in zaki harareni ko murgudamin baki, ko tabemin baki ki tabbatar kinyishi ina kallo dan ko ban kallekiba ina sanin inkinyi hakan.

 Jalila ta kalleshi tace "ni banyi komai ba."
Wayar ya mika mata yace "yi saving."
Ta amsa tasa "Yayah."
 Sannan sukai dan shiru, can tace "Yaya me zanyi in taimaki Goggona?"

 Kallanta yai yace "zancen dazu ne?"
Tace "eh, na gane dazu na fara ma magana ne kamar i am hopeless bansan me zanyi ba, bani kuma da plan."

 Littafin sa ya dauka baice komai ba, saukowa tai kasa ta tsugunna a kusa dashi tace "Yaya dan Allah ka taimakeni."

 Littafin ya ajiye yana kallanta...........


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)


*31*



  Kallanta kawai yake baice komai ba, ta dago tace " Yaya Goggona......"
 Sai ta kasa karasawa saboda kukan daya kwace mata, kallanta yake baida niyyar tanka mata, balle ya lalasheta.
 Sai dai yanayin kukan da takeyi ya fahimci lalai she is desperate.
Yace "in kuka zakimin zan iya tashi in fita."

 Ta share hawayenta tace " bansan ta inda zan fadamaka halin da Goggona take ciki ba."
Yace "ban tambayeki wannan ba, abinda kawai nakesan naji me kike tunanin yi, sannan me kikeso nayi miki?"

 Ta mike da sauri tace "Yaya zaka taimakeni?"
 Kallanta yai sannan ya juya kansa, shiru tai kafin tace " Bansan me zanyi ba."

 Yama rasa mai zaice hakan yasa ya sa hannu zai dauki littafinsa, da sauri ta rike littafin.
 Kallanta yai tace "Please!"
Yauce rana ta farko a rayuwarta da take roko da neman taimako akan 'yancinsu, aduk lokacin da aka musu abu a da sam bata kawo komai sai takaicin yanda ake wulakantasu, amma bata taba tunanin zata kwaci kanta ba, itadai kullum fatanta tai aure ta dauke Goggonta.

 Hassan yace " in bakida abin cewa ki bari sai kin samu sai kimin magana, bance zan taimaka miki ba bare kisa ran zanyi, na dai ce ki fadamin ne kawai inji ko zan iya, i hate meddling in someone's life."

 Bata saki littafin ba tace " Ban taba tunanin nima har akwai lokacin da zan nemi taimakonka ba, ganin halayenka, sai dai kai kadai ne a duniya a yanzu da zaka iya taimako na, Yaya dan Allah."

 Yace " bai dameni ba, Ita mamar taki haryanzu suna tare da wanda ya haifeki ne?"

 A ranta tace "ina laifin kace mamanki da babanki?"
Amma a fili tace "eh sai dai bansan wani irin zama ake ba wanda maganar mutunci bata hadasu."

 Littafinsa ya kwace yace " to meye matsalar?"
Tace "naam?"
Yace menene matsalar ta koma gidansu mana."

 Jalila ta kalleshi jiki a sanyaye, kallanta kawai yai wanda hakan ya nunamai can din ma dai ba magana.

 Ya dade baice komai ba wanda har jikinta yai sanyi kafin taji yace "ki shirya gobe muje ki dubata."

 Da sauri ta kalleshi sam hankalinsa baya kanta ya maidashi kan littafi, kamar bashi yai maganar ba,
Tace "Bansan asibitin da suka canza mata ba."
Bai tanka mata ba, tace "Yaya in mun dubata sai me zamuyi?"

 Yace "later."
Tana shirin magana ma sai taga ya mike ya wuce toilet, ajiyar zuciya tai tace "kai wannan matarka ta shiga uku."
Sai tai shiru tace au ahh ashe fa nice ko?
 (Nace kila nice.......lol)

  Mikewa tai ta fito tana cewa "da alama bai fahimci ina na nufa ba, ni ba dubata nakeso ba, darajarta nakeso su sani balle har su kara tunanin rainata."

  Haka ta fito ta sauka kasa, tana san yima Ummy saida safe.

 Tasa hannu zata bude kofar taji muryar Ummy tace " wai meke damunka ne? Bansan me yasameka ba yanzu komai sai ka fara neman yin fada,  scammers ka hadu dasu ne ko me?"

 Yace " ke ce yanzu bansan meke damunki ba, bansan yaushe kika fara takura haka ba, dolene sai naci abincin......?

  Jalila ta juya da sauri a ranta tana cewa " mekenan?"

 Komawa tai sama da sauri, bayan sunyi sallah sannan taga yadanci abinci kadan, a ranta tace "in mace tayi ba wani abu amma namiji?"

 Hassan ya hau kan gado ya zauna ya dau jornal dinsa, a ranta tace "wai baya gajiya? Daga zama da karatu sai fita?"

 Wayarta ta dauka tana dan lalatsawa, lalai ta kosa gobe tayi ta nunama Goggo wayarta, amma zasu ganta kuwa? Bayan basusan sunan asibitin ba? Kallansa tai tanasan kara mai magana amma ta kasa.

  Meya faru tsakanin Ummy da Abba? Ta fada mai? Can tace "hmm wannan mutumin? Salan yace gulma naje yi?"

 Kafa yasa ya tura bargon dake kan gadon zuwa kasa.
Jalila ta kalleshi, ganin ba alamar shi yayi yasa ta dauko bargon ta na neman maidawa kan gadon, yace "in kinaso kiyi amfani dashi."

 Da sauri ta kalleshi tace "dagaske?"
Bai tanka kata ba, ta dauka tana murmushi ta shimfida, ta hau ta luluba da bedsheet ga pillow yaukam kwanciyar ta mata dadi, wayarta ta dauko tana kara latsawa.

 Haka tai ta latsa wayarta har tai bacci.

  Juyowa yai ya kalleta, gani nai ya kura mata ido daga inda yake, kamar yana nazari akan wani abu.

 Can sai naga ya gyara ya kwanta, bai dade ba bacci yai gaba dashi.


  Washegari ma Alhamdulila anyi sa'a abin nasa bai tashi ba, bayan yayi alwala yasa kafa ya dan buge ta dan dama haka yake tashinta.

 Idanu ta bude ta kalleshi, kallanta yai sannan ya mata alama data mike, Jalila ta tashi ta dauke da bargon daga gun, ga fili nan a dakin amma shidai anan yake sallah.

 Toilet ta shiga shi kuma ya tada sallah.

 Sai wajen karfe 7 ta tashi ta kasa ma baccin saboda ta matsu ya tashi su tafi gun Goggo, saukowa kasa tai dan fara aikin abinci saboda yana tashi itakuma ta gama komai sai tafiya.

  Ganin dakin Ameera tai a bude, a ranta tace "ta dawo ne?"
Dakin ta nufa ta kara tura kofar, me zata gani?
Ummy ta gani a kwance tana barci.

 Meke faruwa?
Badai fadan da sukai jiya bane haryakaisu ga haka?

 Gyara kofar tai ta juya a hankali tabar gun ta nufi kitchen.

 Aikin breakfast take amma sam hankalinta nakan Ummy, ta rasa meyasa batasan wani abun ya bata mata rai sam.

 Tana aiki har masu aikin gidan suka zo, suna fara kwankwasawa ta fita da sauri ta bude musu kofar, bataso a tashi Ummy.
Gaisheta sukai sannan suka fara aikin shara da gyare gyare, saboda girman kasan.

 Sagir ne ya fito ya hangota a kitchen tana ta aiki, tsayawa yai yana kallanta inama matarsa ce? Da yanzu zuwa zaiyi kawai ta bayanta ya rungumeta.

 Da sauri ya fara a'uziyya saboda neman tsari daga shaidan, komawa ciki yai da sauri ya zauna a gefen gado sannan ya kwantar da kansa kan pillow.

 Ummy kam sai wajen takwas da kwata ta farka, kallan agoggo tai cikin mamaki, wani irin bacci tai haka? Shiru tai tana tunanin abinda ya faru itada Abba a daren jiya.

  Bayan ya dawo tanemi ya fito falo yaci abinci, tunda haka suka saba.
 Kallanta yai yace mata "bayajin yunwa."
Tai murmushi tare da ajiye jakarsa tace "haka ka koshi a waje ne da alama."

 Ganin sun saba irin wannan abin bata daukeshi a komai ba, sai cewa yai ban gane na ci a waje ba? Me kike nufi? Gun wata naje ta bani ko me?
Mamaki ya kama Ummy tace "meye hakan? Ai kafi kowa sanin ba hakan nake nufi ba."

 Ai kuwa ya kara hawa wai ta rainashi, nan ya fara masifa ta inda yake shiga bata nan yake shiga ba.

 Haushi yasa ta fito tabar mai dakin, ajiyar zuciya tai sannan ta mike, ta fito falo.

 Tayi mamakin ganin masu aikin har sun gama shara suna mopping.
 Can tai tunanin Sagir, murmushi tai sannan ta nufi kitchen.

 Jalila ta hango tana aiki, da sauri ta karasa tace "Jalila?"
 Jalila ta juyo tace "Ummy ina kwana?"

Ummy tace "Jalila? Yaushe kika tashi haka?"
Jalila tai murmushi tace "kije ki zauna Ummy na kusa gamawa ma."

  Tace " banyarda ba bari naje na dawo dai."
Ta juya ta nufi dakinta.

  Shikansa bai samu barcin arziki ba, dan bayan ta tafi abin duniya ya dameshi, ya rasa mai yasa yake saurin hawa akan kome ta masa wanda ya tabbatar basai wani abin bane, ya rasa meke damun zuciyarsa da yanzu duk abinda Ummy tai matar da yake ganin kimmarta a rayuwarsa bata birgeshi yanzu.
 Zaliha.......
 Duk sanda wannan sunan yazomai saurin mikewa yake yana girgiza kai, bai isa ba, ta ina zai fara yima Ummy butulci? Yasan bazata taba hanashi aure ba dan macece mai class da sanin rayuwa wacce sam batasan fada balle musu, to amma yarinya sa'ar danta? How can he?

 Yana kallanta ta shigo ko kallansa batai ba ta shiga toilet, can ta fito ta bude wardrobe ta dau abu zata fita.
Yace "Hajiya! Ina tunanin zuwa Bauchi gobe."

 Tace "Adawo lafiya."
Ta fita.

 Adawo lafiya?
Ita kuwa tana fita tai kitchen gun Jalila, tare suka karasa aikin.
Jalila tace "Ummy bari na hau sama."
Ta fada tare da saurin yin saman.

 Hassan ya farka ta turo kofar dakin, kallansa tai tace "ina kwana?"
 Bai amsa ba, tace "bari na shirya."

 Ya daga kai alamar to, juyawa tai tadau towel tai cikin bandakin sanye da kayan jikinta.


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)


*32*


  Kallansa tai bayan ta fito cikin zumudi tace "Yaya na fito ka shiga wanka."
Yace "in nayi wanka me zan miki? Ko dama ke kike sani yin wanka?"

 A ranta tace "hmm wannan mutumin?"
Amma a fili tace " a'a gani nai zamu fita."
Yace "zuwa inafa?" Ya fada yana gyara gadan daya kwanta dan shi kam badai gyara muhalinsa ba."
 Jalila da sauri ta fara tayashi ta dayan bangaren tana cewa "jiya fa kace yau zamu."
Yace "yau din ta kare ne?"


 Baki tadan turo mai mutumin nan yake da ita?
Hassan ya matso kusa da inda take a tsaye, hannu yasa ta bayanta ya dauko wani littafi sannan ya koma kan kujera ya zauna.
Jalila ta tsaka sakato tana kallan ikon Allah, amma mutumin nan....
 Cikin takaici ta fita waje tana wata irin tafiya, bugo kofar tai sannan tabi kofar da kallo, dama ita tasan ba lalai ya taimaketa ba.
Da alama Uncle kawai zata fadama, haka ta zauna a kujera ta kuna Tv.
 Shikuwa tunda ta fara cika tana batsewa yake kallanta ta gefe ido, da ta fara wata irin tafiya kuwa tsayawa yai yana kallanta harya banko kofar.
Mai zan gani? Hassan naga ya murmusa sannan ya girgiza kai.
 Shikansa bai fahimci murmushin yai ba saboda rabansa dayai murmushi ko dariya har ya manta.
Amma tabas yau kam da saninsa ya kular da ita, dan ya fahimci wani sabon zumudi da takeyi.

 Ajiye littafin yai sannan ya mike ya shiga toilet, yana fitowa ya dauko jeans da shirt yana shirin sawa, baisan msi ya tuna ba sai naga ya cire ya dauko farin yadi mai shara shara ya sa.
 Bayasa hula dan haka ko dubata ma baiyi ba.
Zama yai ya bude tiren data ajiye.
Kallan plate biyun dake gun yai, kenan bataci abinci ba?

 A falo taji yunwa ta kamata ta turo kofar daki fuskarta a hade, kallanta yai sannan ya dauke kai kamar bai ganta ba.
 Ganinsa a gaban abinci yasa ta tsaya turus tana kallansa.

 Kallanta yai yace " Kin fasa zuwa ne?"
Da sauri tace "zamu?"
Kallan abinci yai sannan ya kalleta, da sauri ta matso tana dariya, duk yanda taso ta boye farin cikinta ta kasa.

 Shikam ya hade rai yana kallan ikon Allah, shi ta fara zubama sannan ta zuba nata.
 Dan kadan taci ta fara neman mikewa, kallansa tai taga shima kallanta yai fuskarsa a daure.
 Da sauri ta koma ta zauna tana kara cin abincin.

 Yana mikewa kuwa itama ta mike, gani tai ya koma ya zauna akan gado.
 Tace "Yaya na......"
 Kasa karasawa tai sai ta wayance tace "Yaya naga bakasha tea din ba, ko na kawoma ruwa?"

 Yace "later."
Juyawa tai ta fita, kallanta yai sannan ya mike ya dau key din mota ya dau wayarsa.

  Sannan ya sauka, bata falon sama shiyasa ya wuce kasa.

 A kitchen ya hangota, ita da Ummy da alama wanke wanke suke.
 Tsayawa yai yana kallansu, bai san me take cewa ba yaga Ummy na dariya.

 Matsowa yai yana san yi mata magana, kuma bazai iya ba.
 Juyawa kawai yai yana neman komawa sama, Sagir yace "Yaya kaine a falo?"

 Hassan ya kalleshi sannan ya juya zai hau sama, Jalila najin ance Yaya ta juyo da sauri tana hangoshi ta tsame hannunta a ruwan dauraya tai gunsa da sauri.
 Ko bi takan Sagir batai ba tasha gaban Hassan tace "Yaya ina zaka?"
 Kallanta yai yace " fita ma inzanyi sai an tambayen?"

 Tace "au yahkuri, in fito?"

 Juyawa yai ya fita waje bai bata amsa ba, da  gudu ta haura sama ta dauko hijabinta, da wayarta.
  Da gudu ta fito ta sauko, Sagir kallanta kawai yake, Ummy da mamaki ya sa ta tsaya tana kallansu, Jalila ta karaso gunta tace "Ummy zamu fita, na tafi karya fasa."

  Ummy mamaki yasa ta kasa ma magana, yau Hassan ne zai kai wani unguwa?
Kallan Sagir tai da sauri wanda yai shiru yana kallan Jalila wace yaga ko kallansa batai ba tana zumudin fita da miji.

  Ummy tace "Sagir ka ga Hassan?"
Kallanta yai ya kakaro murmushi yace "naganshi Ummy, ni kaina mamaki nake."
Ummy ta fadada murmushinta tace " Sagir da alama Hassan ya fara canzawa, ko?"
Sagir ya jinjina kai yace "sosai Ummy."

 Ummy ta juya cikin tsananin farin ciki.

 Jalila kam da sauri ta bude gaban mota inda yake ta shiga.

 Tana hakki, Hassan ya kalleta yace "meye hakan? Gudu kikai?"

 Tace " tsoro nake karkai zuciya."

 Hassan ya tada mota ya ja, suna tafi motar shiru ba komai sai sanyin AC din da ya kunna, ita ta dinga nuna mai hanya da suka shiga unguwar.

 Suna zuwa kofar gidan tace "nan ne, amma yaya kana tunanin zasu nuna mana inda Goggon take?"

 Bai kula taba yai  horn, mai gadin gidan ya fito da sauri ya leka ganin Jalila yasa ya koma ya bude.

  Shiga sukai yai parking, sannan ya kashe motar ya kalleta yace "ki shiga."
Juyowa tai ta kalleshi tace "in shiga?"
Yace "ko ni zan shiga?"
Tace "a'a ban dai fahimceka bane, ba tare zamu ba?"
 Yace " a yaushe mukai hakan dake?"

 Jalila ta tsaya tana kallanshi tace "Yaya kaifa kace zaka taimaken."
Yace "a yaushe kenan?"
 Jalila yanayin fuskarta ya canza tace "Amma....."
Yace " ki shiga ku gaisa, in kuka bakida niyya mu juya."

 Kallansa tai tama rasa me zatace " Hassan ya dau wayarsa yana duba abu."
 Idanunta ne suka ciciko ta bude motar ta fita, ta nufi gidan zuciyarta a dagule.
 Amma mutumin nan anyi mara mutunci.

 Shikuwa yana kallanta har ta shiga.

 Dady na zaune yana hada wasu takardu yana waya ta tura kofar tare da yin sallama.

 Dady ya juyo jin muryar Jalila.
A daidai lokacin Mumy ta fito ita da Yasmeen, Mumy na rike da plate dake dauke da kayan marmari.
Da yake yau asabar ba aiki.


 Kallanta sukai sai suka zubo mata ido, Yasmeen ta rugo da gudu ta rungumeta tana mata oyoyo.
 Jalila ta kalleta tace "My Yasmeen ya makaranta?"

 Yasmeen ta rike hannunta tana zuba mata shagwaba, nan Jalila ta dauketa.

 Dady ya kalleta yace "Jalila! Kece?"

 Mumy ma tace "Jalila shigo mana."
Jalila ta shigo jiki a darare ta zauna a kasa, tana gaidasu.

 Mumy ta amsa sannan tace "banyi tunanin ganinki ba daga aure."
Jalila ta kalleta sannan tai kasa dakai ita duk ta rasama me tazo yi.

 Knocking din kofa sukaji, Dady ya kalleta yace " bake kadai bace?"
Kallan kofar tai da sauri tana cewa "eh tare muke."

 Mamaki tai dataga Dady ya mike da sauri yana kallan Mumy yace "yi maza kinsanar ma Inna."
 Mumy tai sama da gudu.

Jalila ta tsaya kallan ikon Allah, Dady ya bude mai kofa.
Hassan ya kalleshi sannan yace "sannu."
Dady ya washe baki yace "shigo mana."
Hassan ya shigo tare da zama akan kujera.

 Dady ha zauna a dayar kujerar yana cewa "ai bamu san tare kuke ba, ke kam Jalila bakyaji akan me da kika shigo baki sanar mana ba?"
Hassan ya kalleshi sannan ya kalli sama wanda yaji alamar saukowar mutane.

 Matan biyu daya gani a gidan su yau ma su ya gani.
 Kallan Dady yai yace " tanata damuwa akan rashin lafiyar mahaifiyarta shiyasa nace bari muzu."

 Turus Inna da Mumy sukai akan kasan beni, Jalila ma da sauri ta kalleshi, Dady yace "naam? Me kake nufi?"

 Hassan ya zubawa su Inna ido yace " Jalila a ina Goggon take? Dan nasan bata cikin su."
Ya fada yana nuna su Mumy da kai.

 Inna wace ranta yakai koluwa gun baci, ta kalli Jalila tana jiran me zatace, Jalila kuwa tayi mamakin kalamansa dan bata taba tunanin haka zai bulo musu gatse gatse ba.

 Hassan ya kallesu yace " Ina wuni?"

 Inna bakinta na dan rawa tace "Lafiya."
Hassan ya mike ya kalli Dady yace " dan Allah a ina take? Ina sauri ne."

 Dady baki na rawa ya kalli Mumy da Inna yace "tana primer."
Yace "wani dakin?"
Dady ya kalli Mumy yace "wani dakin ne ma?"
Tace "hmm...."
Hassan ya kalli Jalila yace "muje ko?."

 Jalila tai sakato tana kallan ikon Allah.
Ganin yana neman fita yasa ta mike da sauri kar a rufeta da duka tai waje.

 Suna shiga mota ya ja yai gaba.

 Jalila ta zubamai ido tana nazari akansa, can tasa wata dariya tace "Yaya kaga idon Inna kuwa?"
Kallanta yai yace "wacee hakan?"

 Jalila tace "kaka ta? Ahh ba kakata ba kakar su Yasmeen."

 Hassan bai kula ta ba ya juya yana tuki, ita kuwa in ta tuno yanda sukai sai ta kara sa dariya.
A haka har suka isa, suna shiga ya nemi a duba musu sunan Goggo.

 Nan wata nurse ta wuce dan nuna musu dakin, Hassan ya kalleta yace "ina mota."
Da sauri ta riko rigarsa ta kasa tace "mota?"
Kallanta yai, tace "dan Allah kuje ka gaidata. Batasan anmin aure ba fa?" Ta fada tare da canza fuska xuwa tausayi......


#Oneluv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)


*33*


  Hassan ya kara kallanta yace “kina nufin in shiga ciki?”
Ta daga kai, ya kara kallan asibitin, batasan nan ma dakyar ya shigo ba?
Jalila ta kalleshi tace “Yaya!”

 Kallanta yai sannan ya fizge rigarsa ya juya.
 Binshi tai har jikin motar ta tsaya a jikin kofar inda yake tace “Dan Allah yaya kazo muje.”
Kallanta yai yace “ wai meke damunki? Ana abu dole ne?”

 Tace “i am really scared”
Kallanta ya sakeyi, tace “bansan a wani hali zan sameta ba, bansan me zance mata ba in ta tambayeni, Yaya dan Allah kazo muje.”

 Oh God! Wannan wace irin yarinya ce? Yace “to in naje ta tambayeki wanene ni me zaki ce?”

 Kallansa tai sannan tai shiru, yace “ki je ki fito in kuma in barki anan ne sai ki zauna sai dare.”

 Jalila ta kalleshi tace “zan zauna anan din.”
Yace “ ur choice.”
 Sannan ya kalleta yace” zan rufe kofa.”

  Jiki a sanyaye ta matsa daga jikin motar, ya ja yai gaba, ta glass din mota ya hangota tana tsaye inda ya barta.

  Bazai iya shiga ciki ba dan shikadai yasan memory din da yake dawomai in ya shiga cikin asibiti gun marasa lafiya.

  Jalila ta juya jiki a sanyaye, tana shiga nurse din ta tareta tace “ina yayan naki?”
Jalila ta kalleta tace “a ina Goggon take?”
Nan tai gaba Jalila ta bita a baya.

  Goggo na zaune akan gado, ba laifi kafar tata ta samu sauki sosai, tana shiga tai gunta da gudu ta rungumeta ta saki wani irin kuka.
Ita ma Goggon kuka ta saka, sun dade a haka kafin Goggon ta daure tace “Jalila ina kika shiga?”

 Jalila ta dago ta zauna kusa da ita tace Goggo na.
Goggo tasa hannu ta share mata kwalla tace “ kukan ya isa hakanan, me ya faru? Ko jikin naki ne?”

  Jalila ta kalleta tana girgiza kai tace “ba komai Goggo na, ya jikin naki?”

 Goggo ta kalleta kallon tuhuma tace “Jalila kin tabbatar? Dan nikam tsoron mutanen nan nakeyi.”

Hassan har ya fara tafiya naga yayi kwana da motarsa ya dawo asibitin, bude kofar motarsa yai ya fito sannan ya nufi asibitin.
Nurse din tana ganinshi ta taho inda yake, tace “ ka dawo?”

 Hassan yace tana ina? Nan Nurse din ta fara tafiya yana binta a baya.

 Suna taka steps din gaba daya kawai takawa yake, suna zuwa second floor yaji kansa ya fara juyawa, da sauri ya rike bango, sannan ya tsaya ya rike gefen zuciyarsa.

 Wani irin numfashi yake fitarwa, juyawa yai da sauri ya sauka kasa, nurse din ta juyo kawai taga bayanan.

 Hassan ya sauka da sauri ya shiga mota ya ja ya rufe ya fita da gudu.

  Sai da yai nisa sannan yai parkin ya kifa kansa akan sityarin motar yana maida numfashi.

  Jalila tai murmushi tace “Allah Goggo ba komai, kawai dai ina bakin cikin laifin dana miki ne.”
Goggo tace “laifi?”
Jalila ta kwantar da kanta akan cinyarta tace “ ni dai ki yafemin Goggo na.”
Goggo ta shafi kanta tace “ba abinda kika min Jalila, na tabbatar ko da kin min ba daidai ba sai dai a rashin saninki ko kuma tirsasaki akai, kawai dai inaso kisan ke kadai ce dani a duniya”

  Jalila ta share kwallar data gangaro mata tace “ tsoron sanar dake nakeyi.”

 Goggo tace “ko menene ki fadamin.”
 Jalila tai shiru can tace “zan fada miki amma sai kin warke an sallameki.”
 Goggo tai murmushi tace “ shikenan, da alama akan Sagir ne.”

 Jalila tai murmushin yake batace komai ba.

 Haka ta zauna makale da Goggonta, Lantana na gefe tana kallansu gwanin sha’awa.


*************




Su Hassan na fita Inna ta matso kusa da Dady ta daga hannu ta sharara mai wani wawan mari, da sauri ya kalleta dan sam baiyi zatan abinda zatamai ba kenan.

 Mumy ta matso da sauri ta tsaya agan Inna tace “ Inna menene hakan?”
 Inna cikin takaici tace “Uban wa yace ka fadi inda take?”
Dady ya kalleta ransa a bace takaicinsa agaban Yasmeen dan wulakanci.

 Mumy ta kalleta tace “Ta ya bazai fada ba bayan yaran yasan komai, da alama Jalila ta gama sanar dashi duk abinda ke faruwa?”

 Inna cikin kunar rai ta zauna akan kujera tace “Akace bashi da hankali?”

 Mumy ta zauna kusa da ita tace “dama
Bakiyi bincike ba?”

Inna tai shiru kafin tace “ muna cikin tashin hankali, idanun yaran nan ba tsoro ko fargaba a ciki sannan da alama baya ragama wanda ya tabashi, me kuke tunanin zai faru in yasan abinda akama matarsa? Sannan canjen da mukai muka bashi Jalila a maimakon Safeena?”

  Mumy ta kalli Dady tace “Dadyn Yasmeen!”

 Dady ya kalli Inna wacce ke kallansa yace “ hakan bazai faru ba, ni da kaina zan sanar da ita karta kuskura ta sanar dashi komai, kuskuren sanar dashi Mahaifiyarta datai ya isa.”

Inna ta jinjina kai tace “u have to take care of her, in ba haka ba ni zan bulo mata ta bayan gida, zan sata dana sanin da bata gaba yi ba daga ita har uwarta.”

 Dady yace “insha Allahu baza’a sake ba.”
Mikewa tai ta hau sama.

 Tana tafiya ya mike a zuciyd ya shiga dakinsu.


 Mumy ta bishi da sauri tare da rungumeshi ta baya tace “Darling.”
Hannunsa ya zare yace “meye hakan? Kina abu kamar yarinya?”

 Ta kara kankameshi tace “Dadyn Yasmeen am sry.......”

 Kallanta yai kamar zaiyi fada, da sauri ta sumbaceshi...........

 *************

  Ummy ce ta kalleshi tace “ ina zakaje da har kake san in wakilceka akan taron da yake da mahimmanci?”

 Yace “Abuja zan koma dan akwai abu mai mahimmanci da nake sanyi.”

 Ummy ta kalleshi tace “yafi wannan mahimmanci?”
Abba yai shiru yana duba abu a computer sa.

 Ummy tace “ ni na kasa gane abinda bazaka iya fadamin ba”
Cikin zafin rai yace “wai meke damunki ne? Dolene ko wani abu na rayuwarta sai na sanar miki?”

  Da karfi ya budo kofar wanda ya sa suka kalli kofar a tare, kallan Abba ya shiga yi idanunsa sun canza sosai.

  Yanda yake kallan Abban ne yasa Ummy ta matso da sauri ta sa hannu ta riko hannunsa tace “Hassan meye hakan? Taya zaka banko kofa haka bako sallama?”

 Idanunsa na kan Abba haryanzu wanda gaba daya Abba ya gama shan jinin jikinsa.
 Hassan ya daure yace “mekenan?”

 Ummy tace “ mekenan kamar ya?”

 Hassan bai kalli Ummy ba idanunsa nakan Abba yace “me Ummy tai da har kake mata fada haka?”

 Ummy tasa hannu da karfi ta turashi waje sannan ta fito itama, ta rufo kofar sannan ta kalleshi tace “muje.”
Ta fada tana jan hannunsa, dakyar ya hau saman sannan ya kalleta cikin takaici yace “Ummy me kika mai yake fada haka?”

 Tace “ ba abinda yamin nice namai lefi shiyasa yakemin fada akan abinda nai.”

 Kallan ta yai dan shikam bai yarda ba, to ko laifin ma tamai taya zai hauta da fada haka? Ummy ta kalleshi tace “Ina Jalilan?”

 Yace “Ummy kin tabbatar ba abinda ya miki?”
Tace “sau nawa kake so na fada ne? Ina tambayarka Jalila, badai ajiye ta kai a hanya ba?”

 Yace “Tana nan, kawai ya wuce dakinsa.”
Zama yai a bakin gado yana tunani, dolene ko wani abu na rayuwata sai na sanar miki?
Kallaman Abba ne ya sake dawo mai, meke faruwa?

 Ummy tana sauka ta koma dakin, Abba ya kalleta yace “me kika cemai? Tace “ kome nacemai bana tunanin nima ya zama dole in sanar dakai.”

 Abba ya matso kusa da ita yace “Ciwon sa fa? Ya tashi?”

 Ummy ta kalleshi tace “ kaje ka duba.”
Ta matsa daga kusa dashi.

 Abba yai shiru yana tunani sannan ya koma ya zauna agefen gado.

  ***********

  Bayan magrib yana zaune yana karatu, naga ya rufe littafin ya sauko zuwa mota.

 Kallo daya zakamai ka fahimci yana cikin bacin rai tsantsa.

 A asibitin yai parking sannan ya fito, duk yanda yaso ya duba Nurse din a reception din bai ganta ba.

 Kawai komawa yai mota ya zauna, ya kwantar da kansa akan kujera.

  Jalila kam sunata hira da Goggo taga isha’i tayi.
Wayarta ta dauko tana dubawa ko zai kirata, ta ina zai kirata? Bayan bashi da numberta? Itama haka.

 Ajiyar zuciya tai sannan ta ajiye wayar.

 Goggo ta dau wayar tana kara kallo tace “gaskiya wayar nan tayi kyau ta birgeni, mahaifiyar Sagir ce?”

 Tace “Hmm.”
Goggo tai murmushi tace “ karki damu ina warkewa zansa ya turo ai auran.”

Wani film akeyi a tv dake dakin, saurayin ta na waje yana ta jiranta ita kuma bata sani ba tana cikin gida suna ta hirar su
 Mikewa  tai ta dau hijab dinta tace “Goggo ina zuwa.”

 Ta fito, tana tafe tana cewa kai inaa.... ta ya zai zauna jirana? Au ko bai san inda nake ba na tabbatar zai sa a nemi ni.

 Tana fitowa kawai ta hango motarsa, mamakinne ya kamata ta karaso gun motar a ranta tana cewa “ kai.... ba shi bane, kanta tasa tana leka motar.”

  Hassan na kwance ya bude idanunsa, gani yai ana leko cikin motar, tunda akwai haske fitulun waje.

 Hassan ya zuge glass din motar yace “ meye hakan?”
Tace “kai!!!! Kaine da gaske, me kake anan?”

 Yace “ me nake kuwa, bakisan wannan shine hubby dina ba?”
Tace “zama a mota?”

 Bai tanka mata ba yace “ muje?”

 Tace “bari nama Goggo salama, Yaya bazaka shiga ba?”

 Kansa ya kawar gefe.

Ta fita ta ma su Goggon salama, goggo ta bita da kallo tana tunanin tabbas akwai wani abun, Jalila bazata taba zuwa ta tafi a aranar ba.

 Jalila ta shiga mota ya tada suka fara tafiya, yanda taga yanayin fuskarsa ne yasa tai shiru dan taga ba alamar wasa.

 Can ta kasa daurewa tace “Yaya nagode.”

 Bai kalleta ba yace “ 4 wat?”
Tace “ taimakon da kamin.”

 Shiru sukai sai tafiya kawai da yakeyi, can tai murmushi cikin sanyin murya tace “ at first tsoronka nakeyi, later sai na fara fahimtar ka, yau kuma na ga wani side naka na daban.”

 Hassan bai kulata ba sai da aka dade yace “ kina tunanin adan karamin kwanakin da mukai ne kike tunanin kin fara sanina?”

 Tai murmushi tace “a’a bansanka ba, sai dai na fahimci abu daya.”
Juyowa yai ya kalleta, yana jiran abinda zatace.

 A ranta tace u are kind, amma a fili dariya tai tace “na fahimci kana matukar san Ummynka.”

 Kansa ya dauke daga inda take ya cigaba da tukinsa.

 Tana san sanar dashi matsalar Ummy sai dai tana tsoro.......


#Oneluv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)


*34*


 Yana tafe yana tunanin kalaman Abba har suka iso gida, parking yai sannan ya maida kansa ya kwantar a jikin motar.

 Jalila ta fita daga cikin motar, sannan ta juyo ta kalleshi, ganinsa tai bashida alamar ma fita.
 Komawa tai cikin motar ta zauna tace "Yaya! Bazaka shiga ba?"

 Bai kalleta ba bashi kuma da alamar bata amsa, Jalila ta kalleshi tace "Yaya?"
 Idanunsa ya bude ya kalleta yace "Nikam bakinki baya shiru ne?"

 Kallansa tai ta rufe bakinta da labanta, yace " jeki, ko dole sai tare zamu shiga?"

 Jalila ta mike sum sum tai waje, ita kanta mamaki take, tana da surutu sai dai ba'a ko ina ba, a gaban Goggonta kadai take magana san ranta, amma ta rasa me yasa yanzu ta saki jiki da Hassan har take magana haka dashi, duk kuwa da dizgatan da yake.
    Rufe masa motar tai ta tako zuwa cikin gida, tana kokarin bude kofa shi kuma ya turo kofar zai fita.

  Tsayawa sukai suka kalli Juna, Jalila ta matsa ta bashi hanya.
Sagir ya kalleta yace " ki shiga."

 Ya fada tare da rike da matsa mata, kallansa tai sannan ta tako ta shiga.
 Har zata wuce taji yace " kinga Goggon?"
 Ta kalleshi ta daga mai kai alamar eh, murmushi yai tare da cewa "Alhamdulila."
 Bata amsa mai ba ta wuce ciki, dakin Ummy ta nufa ta kwankwasa mata kofa.

 Ummy na kwance dan zazzabi ke neman rufeta tace "shigo."
Jalila ta murda kofar dakin ta shiga, Ummy na kishingide akan gado Jalila ta shiga.

 Tace "Ummy ina wuni?"
Ummy ta kalleta tace "kun dawo?"

 Jalila ta matso tace "eh, amma Ummy lafiya dai ko na ganki a kwance"

 Kallanta tai tace "kai na kemin ciwo."
Da sauri Jalila ta matso tace "Sannu Ummy, kinsha magani?"

 Murmushi ta sakar mata tace "kar ki damu daga nayi bacci zai ware."

 Jalila ta tsaya tana kallanta cikin tausayawa, tabbas abinda ya faru jiya ne kila yake damunta.
  Daurewa tai tace "Abba fa?"
Ummy tace "dazu ya tafi Abuja."

 Jalila tace "Ummy ko dai in kira Yaya akaiki asibiti?"

 Hannunta ta kamo tace "Jalila karki fadama Hassan banajin dadi."
Jalila cikin mamaki tace "Ummy me yasa?"
 Tai murmushi tace "Tun yana karami bayasan yaga ko ya ya ne banda lafiya, in kuwa ya sani to ya dinga kuka kenan, yanzu kuwa da ba lafiya gareshi ba inya sani abin nashi karuwa yake."

 Jalila tace "to a kira Ya Sagir."
Ummy tace "Jalila karki damu, daga na kwanta shikenan."

  Jalila tai shiru kafin tace "bari nai sallah."
Nan ta fito zuwa sama, baya dakin nan tai alwala tai sallar isha'i sannan ta sauko zuwa kitchen.

 Duk da batajin dadi Ummy sai data musu jollof din taliya wacce tasha kayan ciki.
 Jalila ta dau nasu takai sama sannan ta dawo gun Ummy.

 Hassan kam ya dade a mota kafin ya fito, kofar dakin Ummy ya murda dan yana san ya tabbatar da gaske Abban yayi tafiyar?

 Ummy na kwance da alama bacci take, ita kuma Jalila na zaune a kasan carpet ta daura kanta akan gado, itama da alama bacci ya fara dan daukarta.
 Tsayawa yai yana kallansu, yanayin kallan da yake musu ba irin kallan daya saba bane, yau kallo ne yake na jin dadin ganin Ummy da Jalila.

  Yana neman juyawa yaji Ummy tace "Hassan!"
Juyowa yai ya kalleta, tace "zo ka dauki matarka ku tafi."
 Yace "in dauketa kamar ya?"

Tace " Badai dan rashin tausayi tashinta zakayi ba?"
Yace "Ummy tanada kafa fa?"
Ummy ta mai alama da hannu akan yai shiru sannan ta mai alama da dayan hannun akan ya shigo.

 Shigowa yai fuskarsa a daure, a hankali tace "dauketa, da alama baccin yanzu ya dauketa, kuma da karfi ya dauketa."

 Hassan ya kalli Ummy sannan ya kalli Jalila dake bacci, ta karamai alama da hannu akan ya dauketa.

 Cikin takaici yasa hannu ya dauketa kamar yarinya.

 Jalila kam yana daukanta taji alama sai dai muryar Ummy dataji tace "to sai da safenku."
Yasa ta fahimci Hassan ne sai ta kara rufe ido dan batasan ta ina zata fara kallansa ba.

 Hassan ya juya ya fita, Ummy ta kallesu cikin farinciki sannan ta kalli gefen gado, Abinci Jalila ta ajiye mata da ruwa da paracetamol wanda ta tabbatar a cikin magungunanta ta dauko mata.

 Murmushi tai sannan ta hadiye maganin kawai ta kishingida.

 Hassan haka ya hau da ita steps din har yaje kofarsu, kallanta yai yaga tana kif kif da ido, hannu yasa ya bude kofar sannan ya shiga ciki.

 Gani nai yayi hanyar toilet da ita ya bude kofar, yana neman shiga, Jalila kam jin ya sake bude kofa yasa ta bude ido ta kalleshi.
 Ganinshi tai yana neman shiga toilet da ita, da sauri tace "Yaya ina zaka kaini?"

 Yace "au kin tashi?"

 Tace "ina zaka kaini?"
Yace "kamar Ummy cewa tai in kaiki bandaki in taimaka miki kiyi wanka."

 Da sauri ta fara kokarin kwace kanta tana cewa "wlh banji tace haka ba.

 Sauke ta yai a ciki sannan yace " me tace to?" Yafada tare da tare hanyar toilet din.

 Jalila ta kalleshi tace " cewa tai sai da safenku."
 Hassan yace "hmmm bakiji farkon ba kenan, ni kuma na ji."

 Kallansa tai batace komai ba, fitowa yai yasa hannu yana neman rufe kofar.
Da sauri ta rike tana cewa "yaya menai? Naga lafiya muka dawo."
Yace " idanki biyu kikasa ma daukeki?"
 Tace " ba idona biyu ba Allah daga baya na farka."

 Yace " da kika farka fa?"
Tace "yahkuri wlh ni kunya naji."

 Kallanta ya tsaya yanayi.
 Kanta ta maida kasa tana kara rike kofar, can ta saki dan kara ta rike hannunta tace "wayyo hanuna."

 Kallanta yai yace "hannu?"

 Jinginna tai da bango tana dan murza hannun, sakin kofar yai ya shigo yana cewa "menene?"

 Da sauri tai waje da gudu tana dariya.


 Tsayawa yai kawai yana kallan ta, lalai yarinyar nan.

 Dariya ta shiga yi tana cewa "yaya wai harka shiga?"

 Hassan ya hade rai ya fara nufo ta, ganin yanda idanunsa suka canza yasa ta tsaya cikin tsoro tanayin baya.

  Sai dayaje daf da ita sannan ya zauna akan gado bai ce mata komai ba ya dau littafinsa.
 Kallansa tai jiki a sanyaye tace " Yaya bakai dinner ba."

 Kallanta yai yanzu ma baice komai ba, tai shiru ta zauna a gefen gado daga karshe.

 Shiru ne ya ratsa dakin kafin can yace "Jalilah!"
 Kallansa tai da sauri, yauce rana ta farko da ya kirata da sunanta cikin wannan muryar, murya ba mai dauke da zafi ko fada ba.

 Idanunta na kansa yace " Jalilah Please take care of Ummy."
 Idanunta na kansa tana kallansa ta daga mai kai alamar fahimta sannan tace " Insha Allah."

 Haryanzu idanunsa na kanta yace " Nagode."

 Kanta ta sunkuyar sannan tace "nima na gode Yaya da taimakon da kamin."

 Yace " me kika ce ma Goggon taki?"

 Ta kalleshi da raunanan ido tace " ban iya cemata komai ba, bansan ta ina zan bulo ba, bansan me zan ce mata ba."

 Ta karasa magana tana share kwalla, kallanta yai yanasan lalashinta sai dai bai san ta ina zai fara bama.
 Kansa ya dauke daga gunta, wayarsa ya dauka ya dubo sunan Abba.

 Rabon daya kirashi harya manta, sai dai shi Abban ya nemi shi.
Dialing yai yana kallan agoggo, goma saura.
 Yanajin wayar har ta gama ringing bai dauka ba, idanunsa ne suka kara canzawa ya sake kira, tana daf da katsewa Abba ya daga cikin mamaki da shakka.

  Kallan Abokinsa yai sannan ya mike daga falon ya fito waje.
Ya daga yana cewa "Hassan!"
"Abba kana ina?"
Jalila ce ta kalleshi da sauri, Abba yace "nayi tafiya ne, baka tambayi Ummynka ba?"

 Hassan yace " na dauka akan tafiyarne kukai fada?"
Abba cikin mamaki yace "Haka tacem?" Yana mamakin kiran da Hassan yamai da kuma mamakin yanda yake tambayarsa, duk da Hassan na tsananin san Ummy bai taba shiga maganarsu ba, me ke faruwa?"

  Hassan harzai sake magana sai kuma ya kashe ya cillar dawayar gefen gadon.

 Jalila tai shiru tana kallansa, mikewa tai tai shimfida dan yanda ta ganshi tasan da matsala.

  Bata dade da kwanciya ba bacci yai gaba da ita.

 Hassan kam ya dade kafin ya mike ya sauko kasa.
Sai daya leka Ummy yaga tana bacci sannan ya juya ya koma sama.

 Jalila ya kalla wacce ke bacci, daga gefen gado ya kwanta har bacci ya daukeshi.

  Yanda jikinsa ke kadawa da yanda yake abu kamar maiyin kuka yasa cikin baccinta ta farka.

 Da sauri ta kunna wayarta sannan ta kunna fitilar dakin.

  Bakinsa sai kakkarwa yakeyi, da sauri ta karasa kusa dashi ta kamo hannunsa.

  Ganin yana neman fadowa daga kan gadon yasa ta rungumeshi tana hawaye tana kiran sunansa.

 Idanunta a runtse, hawaye kawai ke zuba.

  Ta kankameshi, sun dade a haka kafin nimfashinsa ya fara daidaituwa.

 A hankali ya bude idanunsa ya zubasu akanta, hawaye kawai take tana kiransa.
 Yanda ta rungumeshi ne yasa ya kara kallanta sannan yace "Jalila!"

 Idanunta ta bude ta kalleshi, bakinta na rawa tace "Yaya?"

 Yace "wannan rikon fa?"

 Sakeshi tai tana kallansa, ya kalleta yace "baki iya addu'a bane sai kuka da kiran sunana?"

 A hankali tace "banyi islamiya ba."

 Kallan mamaki ya mata da tausayawa, sannan yace " kukan fa? Are u worried about me? Or are u scared?"

 Kallansa tai bata iya cewa komai ba.

Agoggo ya kalla, karfe biyar saura, mikewa yai ya nufi toilet har zai shiga sai yace " forget what I just said."
 Sannan ya shiga, ajiyar zuciya tai sannan ta sa hannunta shafi fuskarta.


**********
 A abuja kuwa, Abba ya kalli Abokinsa Hafiz yace " sry muna magana yarona ne ya kira."
 Hafiz yace " to yaya? In sanar da ita ne ko ka fasa?"

 Abba yai shiru kafin can yace "bari dai sai zuwa gobe, in na sake yin nazari."
Hafiz yai dariya yace "nazarin me? Bayan abinda ranka ke so ne sannan ba haramun bane?"

 Abba yai shiru yana tunanin yanda idanun Hassan sukai alokacin daya shigo, can yace "sai dai goben."
Hafiz yace shikenan Allah ya kaimu.

 Nan Abba ya fito, yana neman fita gate yaji muryarta tace "Ba gaisuwa?"

 Juyowa yai da sauri ya kalleta, gani nai ya hadiye wani yawo, Zaliha tayi kyau iya kyau kamar mai shirin zuwa dinner doguwar riga ce a jikinta ba dankwalli balle mayafi.

 Gashin kanta kawai ta saukar wanda yasa gyara.

 Bakinsa na rawa yace "Zaliha ko?"

 Ta dan kashe mai ido sannan ta matso inda yace tace "badai sunan ma an manta ba?"

 Yai dariya yace " ina zan manta?"

  Tace "muje ciki mu gaisa, bana iya jurar tsayuwa."

 Nan yaga ya juya tana gabe yana binta a baya, komai na jikinta motsi yakeyi.


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*Thanks for all your comments, it really give me strength 💪🏼lol.....Really Love u 💕 *

*35*

   Abba yaje shiga falon ya tsaya yana kallanta, meke faruwa dashi? Me yasa baya iya controlling din kansa? Juyawa yai da sauri yana neman fita, hannunsa yaji ta kamo.
 Kallanta ya juyo yai cikin bacin rai sai dai yana kallanta yaji ya kasa cewa komai.
 Tace "Tafiya zakai?"

 Yace "a'a."
Haka taja hannunsa har cikin falon sannan ta zauna a gefen da yake.
Tace " Sai naga kamar na takura ma."
Yace "kamar ya kenan?"
Ta dan shagwabe fuska tace " gashi nan ka hade rai."
Da sauri yace " ba hade rai nai ba, kiyi hakuri."

 Murmushi tai sannan ta zubo mai juice a cikin cup ta mikomai tace " gashi."
Amsa yai yana kallanta yana sha, can yace "Zaliha inaji ya kamata na tafi."

 Kanta ta kwantar akan kafadarsa ta sakala hannunta  cikin nasa tace "da wuri haka? Ni anya ka damu dani kuwa?"

 Taura bakinsa na rawa yace "damuwa dake din danai shiyasa kika ganni anan garin, nabar tarin aiyukan dake gabana."

 Murmushi ta saki sannan tace " nikaina mamakin yanda zuciyata ta kamu da kaunar ka nakeyi."
 Washe baki yai yace " nikaina ban taba tunanin hakan zai faru dani ba."
 Haka tai ta jansa da hira tana kara dirkamai juice din abarba da kwakwa da suka hada wanda suka hadashi da rikaken maganin da aka basu.

 Sai dare sosai ya tafi shima harda wani kwallarta wai batasan ta rabu dashi.
Haka ya lalabata ya tafi, da yaso barin garin washe gari amma dole ya hakura sai jibi.

 Yana fita ta shiga dakin Yayarta da gudu tace "Aunty !"

 Kallanta tai ta mata alama da tai shiru, nai tai shiru ta matso kusa da ita tace "Aunty gaskiyar malamin nan kinga yanda ya mato kuwa?"

Auntyn tai dariya tace " an fadamiki barno gabas take? Sanda malamin yace mu koma gida zaizo da kansa me nace miki?"
Tace "ai ni ban dauka abin zaizo da sauki haka ba."

 Tace " kedai kiyi abinda malam yace karki kuskura ki nemi jin rayuwarsa da matarsa ko 'yayansa har sai mun amso dayan maganin."
Tace "To Aunty zan kiyaye."
Nan ta fito tana murmushi, dolene ta fara rubuta abubuwan da take bukata intayi aure da irin wayar da takeso, da motar da takeso da gidan da takeso.
Dan bataso a wuce wata daya basuyi aure ba.

  Taura kuwa yana shiga hotel dinsu yai sallah sannan ya kwanta akan gado yana kara tunano abinda ya faru dashi, yaushe zuciyarshi ta koma budurwar zuciya? Me zai cema Ummy? Sagir? Ameera? Has......... goshinsa ya dafa dan ya tabbatar akwai gagarumar matsala babba in Hassan yasan halin da ake ciki, dan tabbas shikansa tsoron abinda zai biyo baya yake.

 Baisan sanda ya dau waya ya kira Zaliha ba, nan ya baje sukai ta hira har sha biyu sannan ya kwanta.

  *********

  Jalila kam batai baccin safe sosai ba dan karfe takwas ta sauko danyima Ummy abinci, dankali ta fara firewa bayan ta saka tafashen naman kaza, tana suya tana dan kara gyara kitchen din har masu aikin gidan suka iso.

  Bayan ta gama suya ne tadan tafasa indomie tai awara da ita sannan ta jera akan dinning.
Dakin Ummy ta nufa ta kwankwasa.

 Ummy ta taso ta bude mata, Jalila ta rusuna ta gaisheta sannan tace "Ummy ya jikin?"

 Ummy tai murmushi tace " Jalila na warke, na barki da aiki ko?"
Tace "kai Ummy wannan ne aiki?"

 Ummy ta riko hannunta suka fito falo tana cewa "Hassan fa?"
Tace "bacci yake sanda na fito."

 Ummy ta dan tsaya sannan tace "Jalila haryanzu a kasa kike kwana?"
Jalila ta sunkuyar da kai saboda kunya sannan tace "Ummy yaya ya fara canzawa, yanzu yana amsawa in namai magana."

 Ummy ta jinjina kai cikin jin dadi tace "na gani Jalila, ai tunda ya fita dake a mota nasan Hassan ya fara canzawa, ko Ameera bai taba fita da itaba a motarsa."

 Jalila tai murmushin jin dadin yanda taga Ummy na farinciki.

 Ummy ta kara rike hannunta tace "Jalila nagode sosai, nagode har bansan yanda zan miki godiya ba, nasan kina shan wahala da kuka da Hassan."

 Jalila ta sunkuyar dakai tace "Ummy ki daina fadar haka dan Allah."
 Ummy ta jawota ta rungume tace "Jalila mu dauki junan mu a matsayin uwa da yarta, mu ajiye surukantaka a gefe."

Ta dagota tana kallanta tace "Ameera bata fiya zama muyi hira ba, saboda makaranta in ta tafi tun safe sai uku da rabi sannan islamiya karfe hudu, tana dawowa assignment da gajiya su hanata zama ayi hira, Sageer kuwa shine ma muke hira dashi shikuma kinga namiji ne, balle kuma ince Hassan."

 Tai ajiyar zuciya tace "inaso mu dauke junan mu da mahimmanci."

 Jalila ta daga kai cikin jin dadi tace "To Ummy insha Allah."
 Haka suka karasa dinning, Ummy ta bude kulolin sannan tai murmushi tace "inama Hassan zai sauko muci abinci dukan mu?"

Jalila ta kalleta, Ummy tace "later, mu bi abin a sannu, kar san zuciyata yasa mu rikita komai."
Jalila ta daga kai tare da cewa to Ummy.

 Ummy tace kizo ki kaimuku naku, Jalila tace "ke fa? Ke kadai zaki yi breakfast?"
Tace "Sagir na nan nasan ya kusa fitowa."

 Jalila ta zo ta zuba musu ta hau sama dashi.

 Tana tura kofar yana kokarin saukowa daga kan gado da alama tashinsa kenan, Jalila ta ajiye tiren sannan tace "Yaya ka tashi? Ya jikin?"

 Kallanta yai sannan yace "Ummy fa?"
Ta dago tana cewa tana falo, ya mike ya nufi toilet.

  Tana gyara gado ya fito, dayan bangaren ya karasa yana tayata gyarawa, kallansa tai tace "yaya barshi, ka zuba abinci."
 Bai tanka mata ba har ya gama sannan ya zauna ya mike kafa yace "zo ki zubamin, tunda kin damu sai naci yanzu."

 Jalila tana murmushi ta matso ganin zata wuce yasa ya shiga kokarin janye kafarsa daya mike, ita kuma da sauri ta taho yana kokarin janye kafar ita kuma bata kula ba tai tuntube, tahowa tai zata fadi ta gaba, da sauri yasa hannu dan tareta, duk da haka sai da shima ya kai kasa, ta fada kansa kif.

  Hannunta na hagu ya bugi bango, da dan sauri tai kara, da sauri ya kalleta yace "Jalila? Menene?"

 Kallansa tai tace " bigewa nai."

 Harararta yai yace " raguwa, shine harda wani kara haka? Ni da kika danneni fa?"

 Ta dan dago ta kalleshi, yace "sai yaushe za'a dagani?"

 Da sauri ta murgina gefe sannan tadan hade rai kadan, ya kalleta yace " karki ma fara shirin yin pretending I won't fall for it twice, ki zubamin inci ko ki dauke abincinki."

 Jalila bata san sanda tai dariya ba tace "au in ban zuba ba sai kaki ci?"
Yace "Ehem, kina wasa ne?"

 Tace "a'a ina na isa in hana dan Ummy abinci?"

 Ta fada tana zubamai a plate, kallanta yai bayan ta gama zubawa sannan ya fara ci.

 Itama ta xuba taja gefe tana ci, batai auni ba taji yace " yaushe zaki koma?"

 Kallansa tai tace "Ina.....?"
Sannan ta kara fadada dariyarta tace " Gun Goggo?"

 Bai kalleta ba, da sauri ta tsame hannunta ta matso inda yake tace "Yaya da gaske?"

 Kallanta yai sannan yace "me kike shirin yi? Yanzun ma pretending din faduwa zakiyi dan in tare ki?"

 Kallansa tai tana dariya sannan ta matsa daga matsowar da tai tana cewa "wlh dazu faduwa nazo yi."

 Bai kalleta ba, ta jawo kwananta kusa kadan tana cewa "Yaya yaushe zamu? Yau? Gobe?"

 Tea yadan kurba sannan yace " yanda kika damu da Mahaifiyarki me yasa kike tsoro?"

 Har tayi shiru kamar bazata amsa ba kafin tace "a haka na taso, daga ni har Goggo bamu da daraja bare matsayi."

  Idanunsa na kanta yana dan nazari kafin yace "ki binciki mahaifinki, banaji akwai igiyar auranta akanshi."

 Jalila ta kalleshi tace " To yaya, ni tsoro nake karma su kara dauke Goggon."

 Kamar bazai tanka mata ba sai taji yace "sai ke ki dauketa kafinsu su dauke ta."

 Da sauri ta kalleshi tace "kamar ya?"
Abincinsa ya cigaba da ci, yana gamawa ya mike yai toilet, shiru tai tana nazari kalamansa wanda bata fahimta ba sam.........


*******

 Inna ce ta kalli Mumy tace " waccen sokon yaje gun Jalilan?"

Mumy tace "Inna wai dan Allah meyasa kike haka ne? Karfa ki manta mahaifin jikokinki ne."

 Tai dan tsaki tace "ni tambayarki nake yaje ko baije ba?"
Tace "wai tayaya zaije gidan sirikansa yana namiji?"

Inna tace " ta yaya zaije? Ki tashi ki sanar dashi in har shi ya kasa zuwa ya ja mata kunna ni zan yi abinda ya dace, tun kafin zance yakai gun matar Taura har yaje gunta"

 Mumy tace to ta mike ta sauko fuskarta a hade.


*******

  Zaliha zaune a cikin mota tana jiran Abba wanda ya fita siyo musu abu ya dawo, ta sa hannu ta dau wayarsa, ba security hakan yasa kawai ta bude ta shiga gallery tana kallan hotuna, ba wasu pictures bane a ciki yawanci na aikinsa ne, sai Matarsa da ta gani wace ta riga dama ta santa, sai Ameera data gani daga baya wace taga tsantsar kamar matarsa a fuskarta.

 Maza biyu ta gani sunsa kaya iri daya da alama basu ma san sanda aka musu hoton ba saboda kallon wani gun da sukeyi, dayan fuskarsa a hade ba alamar dariya da alama labarin ba burgeshi yai ba, dayan kuwa fuskarsa a sake take.

 Kurama wanda ya hade fuskar ido tai, waye wannan haka? Waye haka??????


 Nace kece inaji kika koma haka😏

Ajiye wayar tai tare da kallan titi, ita ba tsarin soyayya a ranta ba kuma ta tunanin soyayya shine abunda ya dace da ita, abu daya ta sani a rayuwa ta ganta a katan gida a katuwar mota da waya mai masifar tsada, to komai ya biyo bayan wadannan.....


#OneLuv💖
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)



*36*

 
  Ameera ta kalli Aina’u tace “dan Allah kizo mu tafi tare.”

 Aina’u ta maida kanta ta kwanta kan gado tace “dan Allah kimin uzuri, kema kinsan bazan iya zama a gidan ku kamar da ba.”

 Ameera ta dan hade rai tace “kin san da haka me yasa ke da kike yar uwa har kika bari bare ta aureshi in har kinsan kina sanshi?”

 Aina’u ta mike ta zauna akan gado tace “Ameera ni kike so in kai kaina gunsa?”
Tace “daga baya kenan, kema tun farko kinso rigima kinfi kowa sanin Halin Aunty Nana da yanda ta daura buri akanki, me zaisa ki wani fito da zancen wai kinasan yaya?”

 Aina’u ta kafe ta da ido cikin rashin jin dadin kalamanta, Ameera ta mike tace “ in ba so kike zumuncinmu yai rauni ba ki cire wannan zancen, ki ajiye shi a cikin dakin nan, na rokeki da Allah.” Ta karasa maganar tare da shiga toilet.

 Aina’u ta bita da kallo tasan gaskiya ta fada mata amma duk da haka sai dataji zafinta.

 Komawa tai ta kwanta cikin takaici.

 Ameera na fitowa ta kalleta sannan ta bude kofa ta fita falo ba tare da ta mata magana ba.

 ***********

  Jalila tana zaune a falo tana kara tunanin kalaman Hassan, haka ta sauko tana girkin rana amma tana kara maimaita kalaman a ransa, me yake nufi? In ta dauketa ta kaita ina to?

 Batama san Ummy ta shigo kitchen din ba sai ji tai ta tabata.


Kallanta tai da sauri tace “Ummy!”
Ummy tai murmushi tace “tunanin me kike haka? Kin kunna fanfo yanata zuba?”


 Jalila ta kashe fanfon da sauri tana cewa “wlh ban kula ba sam.”

Ummy ta karaso ta dau cabbage ta fara yankawa tana cewa “ Hassan ne?”
Da sauri tace “ba shi bane.”
Tace “Nice?”
Jalila ta tsame hannunta tana cewa “ke kuma Ummy?”
Tace “eh mana, kinsan dan Adam ajizine, to ko Sagir ne?”
Tace “wlh ba kowa Ummy kawai abu nake tunani.”

 Tai murmushi tace “ to ki rage yawan tunani haka, in kin kasa fahimtar abu ki tambayi wanda ya saki a duhu ko kuma ki nemi wanda zai fahimceki.”

 Kai ta daga cikin jin dadi tace “nagode Ummy.”
Sannan ta ce “ina zuwa.”
Da gudu tabar kitchen din ta haw sama, tana hakki ta shiga cikinn dakin, yana kwance kamar me bacci ta shiga.

 Kai ya girgiza kawai ba tare da ya kalleta ba, dan yasan in ba ita ba waye zai banko mai kofa haka?
Jalila ta isa kusa dashi tana hakki tace “Yaya!”
Idanunsa a rufe sai dai yadan yi motsi da hannunsa daya yake kan goshinsa, ta kara gyarawa sannan tace “Yaya dan Allah me kake nufi? Naga ni ba gida ba, ba yan uwa ba, in na dauketa in kaita ina?”
 Ta karasa maganar tana hakki.

 Bai bude idanunsa ba yace “ni zaki tambaya?”

 Ta sa gwiwowinta a kasa sannan ta sunkuyo jikin gadon tace “ yaya tunda kai magana na tabbatar da abinda kake nufi,, shiyasa naketa tunani har Ummy ta bani amsa.”
 Yanzu kam jin an anbaci Ummy yasa ya bude idanunsa ya dan kalleta, yace “tace me?”
“In tambayi wanda ya sani a duhu in har bangane ba.”

 Ya gyara kwanciyarsa tare da juya mata baya yace “ ni ai banine na saki a duhun ba.”
 Mikewa tai ta dawo ta bangaren daya juya tace “ Yaya kaine fa kace in dauketa kafin su dauketa.”
 Yace “sosai haka nace.” Ya fada yana kallanta.

 Tace “to ai shine ban gane ba.”
Yace “baki gane ba ko kwakwalwarki bata aiki yanda ya kamata?”

 Baki tadan turo jin wannan bakar maganar, ya kalleta yace “na nawa kike ci a skul? Na tabbatar double number kike dauka.”

 Fuskarta a dan hade tace “double din ai kala kala ne, ni na farko farko nake dauka.”

 Yanzu ma bai san bakinsa ya dan murmusa ba, sai kallanta dayai yace “ what’s the difference?”
Tace “ mai daukan double number akwai yan 10’s akwai 20’s akwai 30’s har 50’s ma akwai kaga kuwa ba daya bane.”

 Kai yadan jinjina kadan sannan ya sakala hannayensa tare da maida hankali kanta yace “ and?”
Tace “ mene?”
Yace “ u.”
 Shiru tai tana dan kumburo baki sannan ta mike tace “Yaya ni danazo magana daban ka canza ta zuwa wani.”

  Hannunsa yasa yadan bugi gefen sa wajen saitin cikinsa, kallansa tai sannan tace “in zauna?”
 Da ido ya mata alamar eh, nan ta zauna tana kallanshi, ganin yanda ya kafeta da ido ne yasa tai saurin dauke nata idanun.

  Hassan ya kalleta yace “ me yasa kika aureni? Bayan baki sanni ba?”

 Dagowa tai ta kalleshi, yanayin idanunta suka canza, yace “am sry let me change the question, me yasa kika bari aka miki auren dole? Last time da na tambayeki baki bani amsar da ya dace ba.”

 Jalila idanunta ne suka ciciko tana kallansa tana wani murmushin wanda kana gani kasan na damuwa ne ta dan rangwada kai gefe kadan tace “ ya zanyi? Bayan rayuwar mahaifiyata na hannunsu.”

 Yace “ kin taba ganin rayuwar wani a hannun wani dan Adam irinsa?”

 Bakinsa tasan rufe da labanta kafin ta kalleshi tanna share hawaye tace “she is too sick, wanda hakan ya tsoratani, sunce in ban aminceba bazasu taimaketa ba, how can i.......”

 Hawaye ya cigaba da zubo mata, idanu ya zuba mata kafin yace “sai yaushe ne zaki gama?”

 Ta kalleshi tana hawaye tace “mene?”
Da kai ya mata alama da fuskarta.

 Ta share hawayenta tana cewa “ na gama.”

Gani tai ya mike ya zauna, sannan ya sa kafafunsa ta daya bangaren ya saukar kasa kamar mai shirin sauka sannan yace “ sai a fara canza mata asibiti, inda suma bazasu ganta ba kafin ta samu lafiya cikake.”

  Da sauri ta kalleshi, tace “Yaya!”
Cikin wani yanayi ta kira sunan wanda kana ji kasan kira ne na jin dadi da ba zata.”

 Mikewa yai tare da bude wardrobe, gaba daya ita kam ta kame a zaune tana mamakinsa, a yanda ta ganshi bata taba tunanin mutumin nan zai mata rana ba, ta dauka itace ake san ta taimakeshi batasan itace wacce za’a taimaka ba, sannan batasan zai ata rana a dan karamin zaman da sukai ba, sai gashi tana ganin side na halayensa kala kala, wanda ta tabbatar zaman taren da sukai, su kwana tare su tashi tare shine yasa ta fahimci hakan, lalai taga hallaci daga gunsa, da gun Ummy.

 Batasan tayi nisa a tunani ba sai jitai yace “sai yaushe zaki fadama Ummy?”

 Tace “ bansan in kara mata damuwa.......”
Da sauri tai shiru tare da juya kai, takowa yai a hankali zuwa inda take, yasa hannu ya juyo da fuskarta yace “Damuwarta?”

 Yawo ta hadiya sannan ta mike da sauri ta matsa daga inda yake.
 Hannu yasa a gefen cikinta ya jawota yana kallanta da idanunsa wanda suka canza.
 Gabanta ne ya shiga faduwa, tana kallansa.

 Dayan hannun yasa ya juyo da fuskarta saitinsa yace “ tambayarki nake.”

 Jalila idanuna suka firfito tace “ hmm.”
Saketa yai yana neman fita, da sauri tasha gabansa tace “Yaya Please!”

 Kallanta yai yace “ in bakyasan in tambayeta ki fadamin meke faruwa?”

 Jalila ta kalleshi tace “ wlh bansani ba nima, ranan nan ne na fita naji Abba nadan fada.”

 Yace “yace me?”

 Jalila tace “Yaya dan Allah.....”

 Cikin zafi yace “ bani hanya”

 Jikinta ne yai sanyi ta kalleshi sannan ta sanar dashi abinda ya faru, ta daura da cewa “Yaya dan Allah karka nuna ka sani, dan Allah.”

 Gani tai a hankali idanunsa sun rikede, a hankali tadan matsa baya kadan, tana tsoron kar ya mazge ta.
 Gani tai ya dau key din mota a zuciye yayi waje.

 Biyoshi tai da sauri, sai taga ya fita waje.

  Komawa tai kitchen gun Ummy tana cewa “Ummy yahkuri na dade.”

 Ummy tai murmushi tace “bakomai, dama kinyi zamanki, Hassan ne ya fita?”

 Tace Umm kawai dan batasan me zata ce ba daga nan......



#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

" *Sending you smiles for every moment of your special day...Have a wonderful time and a very happy birthday!*" .......Phertyn Uwani😂 (El-Mustapha)

*37*


  Haryasa key ya ta da motar sai ya kashe motar ya kwantar da kansa jikin kujera tare da rufe idanunsa.

 Idanunsa ya bude wanda yanzu ya kara kadawa yai jaa sosai, wayarsa ya dauko ya kira number Abba.

  Bayan sun gama yawo shi da ita yai parking din motarsa a gaban gidansu.
 Zaliha ta kira number yayarta a waya tace "Aunty mun dawo."

 Tace "to bari in fadamai ya fito."
Hafiz ta kalla wanda ke faman hada takardu tace mai "Taura yana waje."
Wasu takardun ya dauka ya fita, Taura na ganinshi ya kalleta yace "ki shiga ciki bari muyi magana."
Tace "a'a ku gama magana ni ina jiranka anan, banasan rabuwa dakai yanzu."

 Taura yai murmushi sannan ya fita, tsayawa sukai da Hafiz suna tattauna wani abun.

 Ringing din waya ne yasa ta kalli inda ya ajiye wayarsa, Eldest Son abinda taga an rubuta kenan.

 Eldest? Tuno hoton maza biyun nan tai, ta tabbatar wanda ya maze din nan shine babban, murmushi naga tayi sliding ta daga wayar, a kunnenta ta kara.

  Hassan shiru yai kafin can yace "Abba?"

 Zaliha tadan sake murmushi tace "Bayanan."

  Gani nai Hassan ya bude kofar motar ya fita yace "waye"

 Gaban Zaliha ne ya fadi dan batasan ya akai ta tanka mai ba.
Cikin tsawa yace "waye nace?"

Bakinta ta shiga motsawa dan ta kasa magana, raban dataji tsawa ace ita akema har ta manta.
 Hassan cikin tsawa da karfin gaske yace " kin fadamin ke wacece ko sai nazo nan na fasa miki baki."

 Zaliha ta kalli inda Taura yake a rikice tace "Bari ba........"

 Yace "ina mai wayar?"
 Da sauri ta bude motar ta taho inda Taura yake jiki na rawa ta mika mai wayar.

 Yana ganin sunan Hassan gabansa ya fadi, kallanta yai cikin takaici yace "Meyasa kika dagamin waya?"
Tace "bansani ba nima...."

 Matsawa yai daga gun sannan ya kara wayar a kunnensa yace "Hassan!"

 "Hassan? How can u call my name as if ba abinda ke faruwa"

 Abba yace "Ya akai? Ina wani meeting ne Secretary gun ce ta dauka."

 Hassan fuskarsa ta kara hadewa yace " Wacece wannan? Abba me kakeyi a garin Abuja? Ba dai......"

 Kasa karasawa yai saboda kansa da yaji yamai nauyi, Abba a rikice yace "Hassan? Hassan jikin ne?"

  Idanunsa ya runtse cikin takaici yace " Abba ko ka manta wacece Ummy a gareka? Ta yaya zaka yi mata haka?"
Abba a rikice yace "Hassan ba haka bane ka tsaya kaji."
Cikin takaici yace " Wallahi Wallahi Abba in dai ina numfashi a doron kasa bazan taba bari ka tozarta Ummy ba, sannan kayi gaggawar gayawa wannan yarinyar dan na tabbatar muryar yarinya naji, wallahi in har bata shiga hankalinta ba har cikin gidan ubanta zanzo in lahantata, in yaso a kamani."

Ya kashe wayar cikin takaici sannan ya saki wayar kasa cikin wani irin bakin ciki ya saki wani irin kara tare da tsugunnawa.

 Jalila da Ummy dake kitchen suka fito da gudu saboda karar da sukaji, da sauri Ummy ta karasa kusa dashi tace "Hassan! Menene?"

  Idanunsa na runtse bashi koma da alamar dagawa, Ummy ta kalli Jalila a rikice wacce itama gaba daya hankalinta ya tashi, tace "Jalila kira Sageer a daki."

Da gudu a juya, bata kwankwasa kofar ba saboda rikicewar da tai itama ta bude kofar.

 Yana kwance daga shi sai singlet da gajerar wando, yana ganinta ya mike zaune da sauri, juyawa baya tai da sauri tace "Uncle kazo, yaya....."
Ai yanajin tace yaya ya sauko da sauri ya zari goduwar riga ta fito, shima ya fito bai ma karasa sa kaya ba sai a falon.

  Yasan nanan a tsugunne duk yanda Ummy tai ta dagashi yaki, Sageer na zuwa ya dagashi da kyar, kallan Ummy Hassan yai idanun sa jawur kai kace garwashi.

  Ummy batasan hawaye na zubo mata ba tace "Hassan lafiya?"

  Idanunya rufe kawai dan takaici, wato ita tana nan ta dauka mijinta na aiki ashe mata yake bi? Tun yaushe ya fara? Badai zina yake ba?


  Sageer ya kalleta yace "Ummy akaishi daki."
Ta matsa tana share hawayenta, hannunsa ya zare daga jikin Sageer sannan yace "take care of Ummy zan karasa da kaina."

 Sageer ya kalleshi har yai gaba, Jalila tabi bayansa da sauri.

 Ummy kam jingina tai da motarsa tana share hawaye, Sageer yace "Ummy muje ciki."

Kallansa tai tace "Sageer kaji karar da ya saki? Bai tabayin irin haka ba, ina murna ya fara samun sauki, Sageer meke shirin faruwa?"

 Sageer yai shiru tausayin Yaya da Ummy ya hanashi cewa komai, ta share hawayenta sannan tace " Sageer kaje gun Dr kajii ko da matsala."

 Sageer yace "To Ummy, amma muje ciki ki zauna tukun na."

Hassan na shiga ya zauna a kasa jikin gado ya jinginar da kansa a jikin gado.

 Jalila ta tsaya a bayansa ta rasa ta ina zata fara mai magana, ta dade a tsaye dan tayi wajen minti ashirin kafin ta juya jiki a sanyaye, hannu yasa ya riko hannu ya riko hannunta ta baya.

 Juyowa tai da sauri tana kallansa, haka suka tsaya hannunsa na rike da nata ba kuma wanda yana wani magana, har na tsawon minti goma sha biyar, kafin ta tsugunna jin kafarta na dan zafi, ji tai ya saki hannunta.

 Kallansa ta sakeyi sannan tace "Yaya jikin ne ko wani abun ne ya faru?"
 Bai kalleta ba, sai dai yanzu ya mike daga kasan da yake ya zauna akan gado.

 Sannan ya kalleta, idanunta na kansa ta kara cewa "yaya!"


 Kallanta yai sannan yace " are u worried about me? Or are u scared?"

 Ta kalleshi tace "Yaya dan Allah kadaina min tambayar nan, dan bansan me zance ba."

 Yace "okay, jeki to."
Tace "naam?"
Yace "ba fita zakiyi ba na tsayar dake?"

 Kallansa ta sakeyi tace " Yaya."

 Kallan daya mata ne yasa ta mike tai waje jiki a sanyaye.

 Zama tai a falon tana tunanin abinda ya faru yanzun nan, ya riketa sannan yace jeki, mekenan? Itakam tana kasa ganeshi wani sa'in.


**********

A Abuja kuwa Abba na gama waya ko kallan Hafiz baiyiba ya fada motarsa yai gaba hankali a tashe, kayansa kawai ya dauko a dakinsa sannan yai check out ya fito tare da ajiye motar.

 Airport ya nufa dan hankalin sa a tashe yake, yana zuwa yai sa'a akwai jirgin da zai tashi karfe 3:00pm zama yai yana jira sai dai zuciyarsa ta kasa nutsuwa.

 Lokaci nayi kuwa ya mike da sauri, ba nisa daga Abuja zuwa kano a jirgi kan kace me sai gasu sun sauka.

 Bai tsaya neman Mamman ba kawai ya hau taxi zuwa gida.


  Ummy na kwance a falo, tayi shiru tana tunanin Hassan, tana jiran dawowar Sageer daga gun Dr.
 Jin an taba kofa ne yasa ta mike da sauri dan ta dauka Sageer ne.

  Da sauri ta bude kofar tana cewa “Sageer me Dr din ya.......”

 Ganin Abba yasa ta tsaya da maganar tana kallansa, kafin tace “ Sannu da zuwa.”

  Kallanta yai jiki a sanyaye yace “Yauwa, sannan ya fara kokarin shiga ciki.”
Hannu tasa ta amshi jakarsa tai gaba fuskarta ba walwala.

 Kallan falon yai sannan ya kalli hanyar sama, kafin yace “ina mutanen gidan?”
Tace “Ameera tace sai jibi zata dawo, Sageer ya fita.”

 Yace “Jalila fa?”
Tace “Tana sama.”

 Yace “Hassan fa? Ya jikin nashi?”

 Kallansa tadanyi kamar zata fadamai sai tace “da sauki.” Sannan tai gaba.


 Ba abinda yakesan ji ba kenan, so yake yaji ko wani abun ya faru dashi, sai dai baisan ta ina zai fara ba shiyasa yai shiru.

 Ummy tana ajiye mai jaka ta juya zata fita, har takai kofa yai sauri yace “ kinje taron kuwa?”
Kallansa tai tace “banje ba.”

 Yace “Naga kamar bakya farinciki da dawowata.”

 Wani murmushin takaici tai kafin tace “banasan musu ko fada dakai daga dawowarka, mu bar maganarnan, kai wanka kafin ma shiryama abinci.”

 Kallanta yai hartabar dakin, zama yai a bakin gadon sannan ya sa hannayensa ya rufe fuskarsa.


  Jalila kam ganin hankalinta ya kasa kwanciya yasa ta mike ta kara turo dakin a hankali.
Yana zaune yasa farcensa yana karzar bayan hannunsa, idanunsa nakan bango yana tunani, idanunsa da fuskarsa a hade suke.

 Jalila ta shigo ciki, har taje kusa dashi bai san tazo ba, hannunsa ta kalla taga yana ta karza har yaji ciwo ga jini nan.

 Kallan tsoro tamai sannan tasa hannunta agun dayake karza, tana kallansa.

 Dagowa yai ya kalleta sannan ya kalli Hannunta sannan ya kalli nasa hannun, sake kallanta yai sai dai yanzu idanunsa sun canza.

 Idanunta ne suka ciciko tace “Yaya wani abun ne yafaru ko? Menene dan Allah? Ko akan abinda na fadama ne?”

  Hannunsa ya janye sannan ya mike daga kan gadon zai nufi toilet.

 Tace “kayi hakuri dan Allah, laifinane dana sani ban tsaya naji abinda suke cewa ba, sannan dana sani ban fadama abinda ke faruwa ba, kayi hakuri dan Allah, it’s all my fault.”

 Tafada tare da share kwalla.

  Juyowa yai ya kalleta kanta na kasa, tana share hawaye, ya dade yana kallanta kafin yace “ ba akanshi bane, sannan in ma shine ba laifinki bane laifinane tunda ni na matsa miki sai kin fadamin.”

 Kallansa tai sannan tace “ akansa ne ko?”

 Kai ya girgiza mata alamar a’a sannan ya shiga toilet.

 Kallansa tai sannan tai ajiyar zuciya tace “Goggo ya zanyi? Inaji nayi laifi ga wanda zai taimakeki, na tambatar da ban fadamai ba kila yau zai dauke ki daga asibitin sai dai da alama wannan bakin nawa ya ja min........




   **************

 Inna ce ta kalli Dady tace “Abakar!”

Kallanta yai sannan ya amsa, tace “ sai yaushe zaka gidan Jalila?”
Yace “so nake sai Taura ya dawo, naji ance yayi tafiya.”

 Tace “meye damuwa ta da haduwarka da Taura?”

Dady yai kasa dakai yana cewa “ai kinga ya kamata mu sake mai godiya da taimakon daya mana.”

Inna tace “wace godiya bayan abinda muka aikata yana neman wargajewa saboda shirmanka.”

 Dady yace “Inna ni......”
“Dalla rufemin baki, so kake kace ba laifinka bane? Ka tabbatar ka lalabata da mijin nata, dan kafi kowa sanin dayan plan dinmu da mukesan sake bude wani branch dinmu, ka kuma tabbatar inba da taimakon Taura ba abin nan bazai yiwu ba, ya kamata kasan abinyi, kafin ni insa hannu, kasan in nasa bazata ma kyau ba.”

 Dady yace “To inna.”

 Ta kalleshi sannan tace “tashi kaje, ka kuma tabbatar kaje gun Jalila, dan a yanda na ganta da yaran nan ina tsoro karta fadamai komai, wannan yaran idanunsa kadai zaka kalla zaka fahimci ba kara  a idanunsa balle ya mana.”

 Yace “to sannan yai waje.

 Shiru tai tana sake wani tunanin, yanzu me ya dace tayi??????

(Nace “ kya tambaye ni😏”)

*********
 Sageer ne ya kalli Dr yace “kana nufin hakan alamu ne na samun nasara?

 Dr ya kalli Sageer sannan ya jinjina kai yace “Sageer kasan Hassan yana dauke da trauma ne wanda shikadai yasan abin da kuma faruwar abin, tunda abin ya faru ka taba gani yayi ihu ko fada da karaji?”

 Sageer yace “a’a sai dai zafin rai, rashin magana da kadaicewa, sai kuma rashin nuna emotion na farin ciki ko na tsantsan bakin ciki a fuskarsa, a koda yaushe fuskarsa a hade take wanda yake nuna alama ta bakin ciki ba alama na canji.”

 Dr yace “Good, yau kuma fa?”

Sageer yace “ yau yayi kara sannan kana kallansa kasan ransa a bace yake wanda bacin ran ne da alama yasashi yin karan.”

 Yace “Very Good, ka gano improvement?”

 Sageer yace “na fahimta Doctor, a da yana fada sai dai bawai da jikinsa yakeyi ba, ko zuciyarsa yanayi ne da fuskarsa da bakinsa.”

 Yace “Very Good ka fahimceni yanzu?”

Sageer ya daga kai cikin gamsuwa da jin dadi yace “nagane Dr, na kuma gode sosai.


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)



*39*



  Fitowa tai jiki a sayaye, abin duniya duk ya dameta ga tsoron abinda zai fito daga bakin Dady da takeyi.

  Tana sauka kasa taga Ummy, Ummy ta nuna mata hanyar falo tare da mika mata tiren dake dauke da juice da cup, Jalila ta amsa tare da yin murmushin dole sannan ta nufi falon.

 A gefen kofar da zata shiga da ita falon taga Sageer a tsaye, kallansa tai da idanunta wanda suka cika da taoro, yace "Jalila, menene wai?"
 Kai ta girgiza mai alamar ba komai, zata shiga yankara kasa da murya yace "Jalila?"
Juyowa tai ta kalleshi, yace "Bakyasan ganin mahaifinki ne? Naga tunda na fada miki yazo naga fuskarki ta canza."

  Murmushin yake tai sannan tace " bakomai, nagode."
Kawai ta shiga, dan batasan me zatacemai ba.
 Abba na falon suna ta magana ta shiga bakinta dauke da sallama.
 Abba da Dady suka amsa, Dady ya kalleta cikin farin ciki yace "Jalila!"
 Jalia tace "naam sannan ta karasa ta ajiye tiren a gabansa ta gaisheshi.
Abba ne ya mike yace "yanzu ba abin business kazo ba, uba ne yazo ganin yarsa, kaga bai kamata na shiga tsakani ba, later mayi magana."

 Dady ya mike yana godiya har ya fita, kallan Jalila yai wacce ke tsugunne a inda ta ajiye juice din, Dady yace "zauna mana."

 Ta gyara zamanta tana kallansa, gabanta sai faduwa yake.

 Dady ya zauna sannan ya kalleta yace "hmm ya gidan?"
Tace "lafiya, wani abun ne ya samu Goggona?"

Yace "wani abun? Kamar me kenan?"
Tai shiru ta kasa magana, yace "dan uba yazo ganin yarsa sai ya zama sai akwai matsala?"

 Jalila ta kalleshi tace "a'a ba haka bane."

 Yace "Jalila ni mahaifinki ne, ki daina dararewa da ni."

 Ta kalleshi kawai bata ce komai ba.

 Matsowa ya danyi kusa da ita yace "jalila magana nakesan muyi."
Kallansa tai cikin tsoro, yace "Nikam ya kukai da mijin naki?"
Tace "wani mijin?"
Yace "wanda kukazo tare mana, badai wani abun kika fadamai ba ko? Naga kamar baiji dadi ba ranar."

 Jalila ta kalleshi gabanta na faduwa ta kasa magana, Dady yace "amma yasan Goggo ce ta haifeki ko?"
Jalila ta daga kai alamar eh, Dady yace "ya fadama wani ne?"

 Tace "ban gane ba?"
Yace "ya fadama wani kamar mai gidan nan cewar Goggo ce ta haifeki?"
Jalila tai shiru, yace "ba dai duk wani sirri na gida kin fadamai ba?"

 Jalila ta kalleshi yanzun ma batace komai ba, ya kalleta ransa a bace, badai duk wahalar da wulakancin da ya hadiye ba lokaci daya wannan yarinyar zata zo ta ruguzamai? Dan ya tabbatar in har Taura ya kwace kudin daya basu tabbas Inna korar sa zatasa ayi daga company din.

 Kallan Jalila yai rai a bace yace "Wai Habiba ba magana nake miki ba? Sai dai ki kalleni? Ko kema munafircin uwar taki zaki koya?"

  Jalila cikin tsoro ta kalleshi, hannunya daga a zuciye zai kai mata mari.
 Jiyai ance " da alama sararka kenan?"

 Juyowa tai da sauri ya kalli mai maganar, Jalila ma kallansa tai kawai sai ji tai hawaye sun zubo mata.
 Karasowa yai cikin tafiyarsa ta isa sannan ya kalleta yace " tashi."

 Mikewa tai tana kallansa, yace "bakiji me nacemiki ba ne da zaki zo?"

 Tace "me kace?"
 Yace “sau nawa zan ce miki ki canza tone in zakiyi magana? Meyasa bakyayi da confidence?”

 Kallan juna sukai, hawaye ya gangaro mata, juyawa yai ya kalli Dady wanda yai tsuru tsuru.

 Hassan ya kalleshi yace “ gobe zanzo muje dakai asibiti inda aka kwantar da mahaifiyarta, a gabanka zakasa hannun sallama mu amsheta.”
 Dady yace “me kake nufi?”

 Yace “abinda zuciyarka ta baka, u don’t deserve to be a father nor a husband.”

 Kallan Jalila yai yace “wuce mu tafi.”

 Kallan Dady tai gabanta na ci gaba da faduwa, Hassan ya kalleta ya mata alama data fara fita, nan ta fita tana waiyaye.

Tana fitowa daga bangaren falon taga Sageer a tsaye a jikin bango.
Yana ganin ta fito ya matso da sauri yace “ Jalila”
 Hawayenta ta share sannan ta kalleshi, yace “menene?”

 Kallansa tai kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta juya tai gaba, Sageer yace “Akwai abinda ya faru ko? Naga yaya ya shiga kuma shi bai fito ba.”

 Juyowa tai ta kalleshi sannan ta juya kawai ta hau sama da gudu.

A falo kuwa

 Hassan ya kalli Dady yace “me ka samu, na saida yarka dakai?”
 Dady yace “me kake nufi?”
Hassan yace “yanda kai da manyanka iyayen gidannka kuke nunawa, kunayi ne kamar kun samu wani abu sosai wanda yasa kuka bada yarku.”

 Dady ya kalleshi yace “Hassan ta ya zaka ce haka? Kana so kace rashin so ne yasa muka aurar da ita?”
Yace “sosai, inba rashin so ba kun taba tambayar ya mijin nata yake? Wasu halaye gareshi? Me nene aikinsa? Ya mu’amalarsa da jama’a take? Duk kunyi wannan tambayar? A matsayinka na uban yarinya?”

 Dady ya kalleshi yace “Inna tayi bincike ita ce tasan mahai.......”
Ya katseshi rai a bace “wacece ita? Menene matsayinta agun Jalila?”

 Dady yace “bangane ba?”
Hassan yamai wani kallo yace “ karka manta gobe zanzo in banzo ba jibi zanzo, in kuma har kukai tunanin yin abinda bai kamata ba, zan baku mamaki.”
Ya juya bai jira mai zai ce ba ya fita.


  Dady haka ya fito gaba daya kansa yayi nauyi, Sageer ne kawai a falon yamai sallama ya fita, yana cemai ya gaida Taura.


Mota ya shiga yai gaba.

  Sai daya je kofar gida sannan yai parking a gefen mota ya kashe motar ya fito yana tunanin abinda zai fi mai mahimmanci, danshi rayuwarsa itace gaba da komai, mai zaiyi dan cigaban sa?


Hassan kam yana haura beni kansa na wani juyawa da kyar ya kai kansa daki yana shiga ya kwanta.

 Jalila na falo tana ganinsa ta taso dan dama ta kasa ko zama ne.
Yana shiga a shiga dakin itama, akwance ta ganshi akan gado, taje kusa dashi tana san mai magana sai dai ganin idanunsa a rufe tasan bayasan magana, balle ya juya mata baya.

 Ta dan dade a tsaye kafin ta fito.

 Karfe tara tai shimfida ta kwanta, shikam tunda yai sallah ya sake kwanciya bai sake ko motsawa ba balle ta samu damar magana.

  Shikam takaicin abinda ke faruwa a gidansu ne yake damunshi, meke damun Abba? Meyasa ita wannan rayuwarta take a cude? Meyasa abubuwa ke faruwa haka? Yau ce rana ta farko dayai fada da magana mai tsayi haka, gaba daya kansa wani irin sarawa hakeyi, ya dade sosai kafin bacci ya daukeshi.

  Jalila kam ta dade a kwance kamar tana bacci, me suka fada da bata nan? Taya uba wanda ya haifeta zai dinga mata haka? Hawayenta ta share data tuno rayuwar da mahaifiyarta tai, lalai bazata bari Goggo ta cigaba da zama dasu ba.

 Juyawa tai saitin da Hassan yake, ta haska wayarta, ganinsa tai a dukunkune ta mike ta dan rage A.C din dakin sannan ta matso inda yake, kansa baya kan pillow din, in dagashi? Ganin yanda ya kwanta a takure.

 Hannu tasa a hankali ta daga kansa ta daura akan pillow din sannan ta juya ta kwanta.

 Shikam tana tabashi yaji ta, har sai data kwanta idanunsa na bude juyawa yai shima saitin da take kwance, duk da ta kashe hasken dakin ba ganinta yakeyi ba, sai dai ya samu kansa da tsurawa gun ido kafin ya maida idanunsa ya rufe.


  *************

 A kasa kuwa, Ummy ce tasa kayan baccinta ta sa hijab tana neman fita daga dakin.
Abba ya kalleta yace “ina zaki?”

Tace “Dakin Ameera, ni kam kamar munyi kuskure da mun sani dakin can mun gyarashi.”

 Kallanta yai yanda take mai magana kamar bawani abu na sabani a tsakaninsu.

 Abba ya kalleta zaiyi magana wayarsa tai kara.

Kallansa tai tace anama waya, ta juya ta fita.

 Zaliha ce, kashe wayar yai gaba daya sannan ya mike ya fito daga dakin.

 Dakin Ameera ya shiga, Ummy tana kade gadon ya bude kofar, kallansa tai tace “ya akai? Ko akwai abinda kakeso?”

 Abba ya kalleta sannan ya shigo ciki ya zauna akan gadon yace “ Kinsan gwara kiyi fada?”
Tace “fada kamar yaya?”

 Yace “wannan abinda kikeyi it really scared me, gwara ki nunamin ranki ya baci in ma hakuri ne na baki.”

 Tace “ munyi fada dakai ne?”
Kallanta yai, tace “ kai da Hassan ne kukai fada akai na wanda ni banaso, sai dai ya zanyi? Banaso naga kuna irin wannan akaina, tunda nake dakai na taba hanaka aure?”

 Yace “ kece kuwa kike da yanda zakiyi tunda akanki akeyi, ke kadaice kike da dama hana fadan, sannan maganar aure nasan tunda nake dake ban taba sha’awar kawo wata mace gidana ba, yanzun ma ni kaina bansan meke damuna ba.”

 Ummy ta kalleshi tace “ saboda kanasan ta shine ka hauni da fada waccan zuwa akan zaka koma Abuja, sannan yanzu kace bakasan meke damunka ba? Ni mubar wannan maganar, ni matsalata da damuwa ta akan Hassan ne, dan Allah ka daina barin yana sanin abinda ke faruwa a tsakaninmu, kafi kowa sanin halinsa in har yasan ina cikin damuwa, banaso Sageer ko Ameera ma susan wannan maganar, na rokeka da Allah, in aure zakayi kayi, wannan ra’ayinka ne sannan rayuwarka ce amma Please karka bari yarana su shiga wani hali a dalilin abinda kakeso.”

  Abba ya runtse idanu cikin takaicin abinda ya dade yana ginawa, wato farin cikin gidansa na neman wargajewa a dalilinsa.

 Ummy ya kalla cikin wani yanayi na tausayawa sannan yace “Maimuna ina cikin wani hali........”

 Yanda yai maganar ne yasa ta tsaya tana kallansa sai dai tausayinsa ne ya kamata, dan bazata taba manta irin wannan muryar ba daya zo mata da ita a can baya shekaru masu yawa, a lokacin kalmar nan sai data sata kuka mai yawa, yanzun ma hannunta tasa akan nashi sannan ta zauna a gefensa tace “ In kanasan ta ka aureta, in dai shine matsalar, ni zanma Hassan magana, sai dai kafi kowa sanin baka isa ka zaunar da ita a gidan nan ba, in har baso kake danka ya mata illa ba.”

 Kallanta yai cikin rauni yace “ba santa ne matsala ba, ni gaba daya abinda ke damuna ne matsala, n rasa a yaushe na fara santa, a yaushe naji in banganta ba bazan iya rayuwa ba, na rasa a yaushene na fara amsa mata akan duk abinda tazomin dashi.”


 Ummy ta kalleshi cikin mamaki tace “me kake mufi?”

 Ya kalleta yace “kizo mu kwanta, banajin dadin abinda mukeyi, me kike tunanin zai faru in Hassan ya ganki anan? D’a nane sai dai duk duniya nafi shakkarsa akan kowa, sannan shikuma indai akanki ne ba abinda bazai yi ba.”

 Ummy bata musa ba ta mike sukai daki, kwanciya sukai, tace “baka fadamin matsalar ba.”

 Yace “gobe zan gaya miki mike faruwa wanda na kasa ganeshi.”

 Ummy tace “Allah yaa kaimu.”

Nan sukai bacci............

Sageer kam gaba daya ya kasa bacci, daga bayama mikewa yai ya zauna akan gado ya kunna fitila yana tunani, anya bashine sillar komai ba?

 Gaba daya tausayin Jalila ya hanashi rintsawa......
******

A can gidan Inna kuwa, Inna sai kiran wayar Dady take bai dauka ba, yana kallan kiranta yaki dauka, sai data kira sau hudu sannan ya daga yace “gashinan zuwa.”

Ajiye wayar yai ya koma mota, dan ya gama tunanin mafitarsa, yasan kuma yanda zai buloma abinda ke faruwa dashi..........



#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)



*40*

Washegari......


 Jujuya cokali kawai takeyi a cikin cup din tea din, jefi jefi tana kallansa ta kasan ido tanasan mai magana, shikuma yana zaune a kasan yanacin abincinsa kamar ba wani abu dake damunsa.

 Can dai ta tattaro dauriyarta tace "hmm yaya nace......"
Kallan daya mata ne yasa ta maida bakinta ta rufe tare da kallan cup din ta cigaba da juya cokalin.

  Yana gama ci ya mike ya shiga toilet, wanka yai sannan ya fito.
 Kallansa tai ta ganshi daga shi sai towel dake daure a kasa, da sauri ta juya baya tare da rufe fuskarta da tafin hannunta bai bi ta kanta ba harya saka kayansa, sannan ya dawo gaban madubi yana shafa mai, yana gamawa ya fefesa turare.
 Jalila ta juyo ta kalleshi, matsowa kusa dashi ta danyi kadan tace "Yaya bakacemin komai ba."

  Bai tanka mata ba ya dau wayarsa da makullin mota ya fita, tana tsaye ya rufo kofar.
Kallan kofar tai cikin mamaki a fili tace "mekenan?"

  Takaici ne ya kamata ta zauna a bakin gadon dabas tama rasa me zata ce.

 Hassan yana sauko kasa ya sa hannu ya kwankwasa kofar dakin Abba.
Bude kofar Ummy tai sannan ta kalleshi, tace "Hassan kaine?"
Ya gaisheta sannan ya kafa leka dakin yace "Abba fa?"
Tace "yanzun nan yadan fita waje gun garden waya zaiyi."
Waya? Waye ya kirashi?
Ummy ta kalleshi tace "Hassan!"
Kallanta yai fuskarsa ta fara canzawa, tace "Please Hassan ka dinga sama zuciyarka salama, ka dinga hakuri, Abbanka namiji ne yanada hakkin auran duk wacce yakeso..........."

 Juyawa yai bai jira ta gama magana ba yana neman tafiya, tace "Hassan magana nake."
Ya juyo ya kalleta yace "Yahkuri Ummy abu zanyi ne cikin gaggawa."

 Kamar zata sake magana sai ta fasa, ta bishi fa kallo, Allah sarki Hassan tafi kowa sanin irin kaunar da yake mata.

 Garden ya nufa, Abba na tsaye yana waya ya karasa gun, kallan Abba yai kallan zargi, Abba yace "Hafiz Please ka barni tukunna."
 Bai kara jiran yayi wata magana ba ya katse layin, Hassan ya kalleshi kamar zaiyi magana sai kuma ya gaisheshi.

 Abba ya amsa yace "Hassan."
 Kallansa yai yace "kai da wanene haka?"
Yace "business ne ba wani abun ba uban yan zargi."
 Hassan ya juya kai sannan yace "me kaba iyayen Yarinyarnan a maimakon auranmu?"

 Abba ya kalleshi cikin mamaki yace "Hassan menene?"

 Hassan yace "bakomai, kawai dai so nake nasani, dan na tabbatar give and take kukai da rayuwar ta."
 Abba yai shiru kafin can yace "Bakasanta ne ko me? Ko wani abun ne ya faru?"

 Shiru yai baice komai ba, kamar kuma zai saie magana sai ya juya zai tafi, Abba ne yace "Company dinsu ne ya ke neman yin Bankrupt shine na taimaka musu."

 Hassan ya kalleshi sannan yace "yarinyar fa? Have u take care of her?"
Abba yace "kamar ya kenan?"
Hassan ya kalleshi yace "Abba ina dai sone a komai zakayi ga dinga tuna wacece Ummy a garemu."

 Abba ya kalleshi yace "Hassan just pray for me, wlh nikaina bansan meke damuna ba."

 Hassan yai shiru yana kallansa, Abba yacigaba "yanzu zan fada mata abinda ke faruwa itama, Hassan kafi kowa sanin family na are above komai na rayuwata ciki kuwa har da ni kaina, kasan yanda zan iya sadaukar da komai saboda su, sai dai i feel like there is definitely something wrong with me, na rasa yanda zanyi in cire yarinyar daga raina, as if samin ita akai a ciki."

 Hassan kallansa yake, sai dai yasan mahaifinsa tabbas wannan kalaman daga zuciyarsa suke fitowa.

 Kallansa yai yace " nafahimceka sai dai bansan meyasa zuciyata take blaming dinka ba, bawai baka iso kaso kowa bane sai dai Ummy doesn't deserve this treatment."
Abba cikin takaici yace " Ba so kadai bane a raina Hassan, mata nawa nake hulda dasu? Zance ba macen da ta taba burgeni ne? No kawai na riga nasa Ummynka ne beyond every woman, sai dai wannan karan it look like obsessed, inaji kamar dolene sai na sami yarinyarnan ko ta wani hali ne."

 Hassan zaiyi magan, Ummy wacce hankalinta ya kasa kwanciya gani take kamar yanzun ma fada sukeyi yasa ta biyoshi, jin kalaman Abba ne yasa ta tsaya tana jinsu, sai dai yanzu kam idanunta ne suka zubo da kwalla, muryarta na rawa tace "it look like akwai babbar matsala a tare dakai"

 A tare suka juya suka kalleta, Ummy ta karaso tace "just one month, ka bamu one month, ka daina kiranta sannan mu dukufa da addu'a musa nalamai ma su maka, in har a wata dayan nan dukda haka bakaji santa ya ragu a ranka ba ni na amince ka aureta."

 Ummy!" Hassan ya fada yana kallanta, tai murmushi tace "in har a wata dayan kaima ka amince dani, karka nemeta sannan ko ta nemika ko a wayyane karka daga ko ka canza number"

 Abba yace "na amince."
Hassann ya kallesu yana sanyin magana, Ummy tacee "Hassan please."

 Idanunsa ya runtse, Abba yai murmushi tare da dafashi yace "Hassan bakasan dadin da nakeji ba, sauki ya fara samuwa da alama wannan auran rahama ne a gareka damu baki daya."

 Hassan ya kalleshi sannan ya kalli Ummy, juyawa yai sannan yace "Shikenan Ummy tunda ke kikeso, sai dai ni ba one month ba ko shekara kikaba Abba bazan aminceba."

Ummy tai murmushi tace "nagode my eldest."

 Juyawa yai yabar gun, mota ya shiga sannan ya fita daga gidan.


 Jalila kam ta dade a zaune kafin ta dauko tiren abincin.

 Akan dinning taga Sageer yana breakfast, da alama ma fitowarsa kenan dan tea yake hadawa.

 Yana ganinta ya kura mata idanu har ta iso inda yake, gaisheshi tai, idanunsa na kanta yana nazarin fuskarta ya kasa amsa gaisuwar.

 Kallansa ta sakeyi, yanzu kam ita kanta ta fahimci da abinda ke dakunsa dan duk fuskarsa ta canza,  tace "Uncle bakada lafiya ne?"

   Flask din ya ajiye sannan ya zauna yace "a'a me kika gani?"

 Tace bakomai, wuceshi tai ta ajiye tiren abincin, kallanta yai yace " Yaya fa?”
Tace “ya fita.”

 Shiru yai sai binta da kallo da yakeyi.

 Jalila ta ajiye sannan ta fara dauraye kwanukan da sukai amfani dashi.


***********

 Hassan na fita ya hau titi yana tafe yana tunani, meyasa yarinyarnan bata iya fita a ransa? Ya rasa me yasa in yaji ko yaganta cikin damuwa hankalinsa baya kwanciya.

  Daren jiya ya tuno wajen karfe uku da rabi, kansa dake ta sarawa ya hanashi bacci, jin kamar ana kuka da magana, mikewa yai ya kunna fitilar gefen gado.

 Jalila ce da alama mafarki take, kusa da ita yaje ya zauna yana kallanta, alamar kuka takeyi tana magana kasa kasa, kunensa yasa kusa da bakinta dake motsi.
“Dady, Mumy, Inna na kuyi hakuri karku kori Goggo dan Allah, na daina, na daina......”

Abinda take cewa kenan, hankalinsa da tausayinta sune suka kara ratsahi, addu’oi ya mata sannan ya kamo hannunta ya rike yana kallanta.

 Ya rasa me yake tunani a sanda yake kallanta, meke faruwa dashi? Is he feeling guilty? Tunda yasan dalilinsa ne yasa aka mata auran dole? Sai dai abinda yakeji ya banbanta...... ya dade sosai har sai dayaji anata kiraye kirayen sallah sannan ya mike yai alwala.

 A kofar gidansu yai horn ya shiga, Mumy da Dady na zaune a falo, Yasmeen na gefe tana shan chocolate tana wasa aka sanar dasu zuwansa.
Ba Dady kadai ba har Mumy sai da gabanta ya fadi, ta kalli Dady da sauri tace “ Dadyn Yasmeen meke faruwa? Cikin rawar baki yace bansani ba nima wallahi.” Yafada yana tuna kalaman Hassan badai zuwan dayace zaiyi yau ko gobe ba shine yai?

 Mumy ce ta bada umarnin akan a shigo dashi, ita kuma tai sama da sauri.

 Inna na zaune tana jiran Dady wanda tun jiya take sa ran ganinsa amma baizoba haryanzu.

  Shigowar Mumy ne yasa ta kalli kofar ta dauka Dady ne, ganin Mumy yasa tace “ya akai kuma?”

 Mumy da sauri tace “Inna yaran ya dawo.”

Tace “yaro? Sultan?”

Da sauri tace “bashi ba, mijin Jalila.”

 Inna ta kalleta da sauri tace “ya dawo ina?”

 Mumy tace “yana gidan nan, bansan dame yazo ba.”

 Inna ta mike hankali a tashe tace “gidan nan?”

 Mumy tace “yana falo.”

 Inna ta dau mayafi ta fito, mumy ta biyota a baya tana cewa “Inna badai wani abun ya sake faruwa ba?” Itadai Inna batace komai ba, har suka isa kasa.

 Dady na kasan beni da alama jiransu yakeyi, Inna na saukowa yace “Inna.”

 Kallansa tai tace “badai jiyan kwafsawa kai ba?”
Dady yace “kwafsawa kamar ya?”

 Haushi ya kamata tace “ wuce muje, koma menene let’s hear it together.”

 Nan sukai falo? Hassan na zaune akan kujera suka shigo su uku.
 Kowa ya samu guri ya zauna, Hassan ya gaishesu sannan ya kalli Inna wace itama kallansa take, ya kalli Mumy da Dady wanda suma hanyace “ zuwa nai mahaifin Jalila ya rakani inda mahaifiyarta take, zai sanya hannun sallamarta.”

 Inna ta kalleshi sannan ta kalli Dady wanda a ransa yace Oh My God! Wannan wani irin yarone? Ya gama hargitsamin plan dina.

 Dasauri ya girgizama Inna kai alamar ba shi bane.
Inna ta kalli Hassan tai dariya tace “Hassan taya za’a sallami mara lafiya? Bayan ba warkewa tai ba?”

 Yace “eh wannan damuwarmu ce, dan in aka sallameta hannuna zata koma.”

 Mumy d Dady da Inna a lokaci daya sukace mene?

 Hassan ya kallesu yace “menene abin mamaki? Ba mahaifiyar matata bace? Banaji cikinku akwai mai hakkinta.”

Inna tace “mene?”
Yace “ why? Bazai yiwu ba? In bazai yiwu ba bari na kira Abba na sanar dashi, ina tunanin kamar zamu amshi kudin mu.”


“kudi?” Hassan ya daure dan kansa wani irin sara mai yakeyi, ya mike ya kalli Dady yace “ina mota.”

 Ya juya ya fita alamar wai yana jiran Dady a mota.

Inna tabi kofar daya fita da kallo, sannan ta kalli Dady, takaici da bakin ciki ne suka kamata.

 Dady yace “Inna ya zamuyi?”

 Cikin takaicinsa da bakin ciki tace “dalla wuce kaje ka rakashi, ko so kake company dinmu ya mutu?”

 Dady ya mike ya fita.

 Inna takaici ya kamata tace “lalai ba yaran nan bane bashida hankali nice banda hankali dana kawo babban makiyi har cikin gidana da kaina......”

  Dady ya shiga mota Hassan yaja suka tafi.

  A asibitin premier sukai parking, ya zaiyi?Gashi bayasan asibiti, gashi yabar Jalila agida sabofa bayasan su nemi wulakantata.


#Oneluv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)



*41*

  Tsayawa yai shi bai fita daga cikin motar ba sannan baiyima Dady magana ba, Dady kam wanda yake a zaune yana nazarin yaran ya kalleshi yace “muje?”

 Hassan ya fito daga motar sannan ya tsaya yana kallan asibitin, babban matsalarsa bawai shigar bane, zai iya shiga reception ko gun da ba marasa lafiya kamar office, sai dai daga yayi bangaren dakuna na marasa lafiya hankalinsa yake tashi, shiyasa kwanaki yana fara hawa saman beni yaji gaba daya hankalinsa da tunaninsa na neman gushewa.

 Da kyar ya daure suka nufi reception din, nan yamusu bayanin abinda sukeso, suka turasu wani office, nan ma sunyi cike cike, suka rubuta kudin da za’a basu, Hassan ya biya, suna fitowa ya kalli saman benin sannan ya kalli Dady dabara ce ta fadomai yace “kaje ka sanar da ita, ka kuma nemi yafiyarta sai ku fito tare ni ina mota.”

 Dady ya kalleshi a ransa yace “lalai wannan yaran bashida tarbiyya, ina sirikinsa amma ya maidani dan aike? Kamar wani masinjansa,  ko driver? Yana tsaye har Hassan ya fita sannan yai kwafa ya hau saman.

 Goggo na zaune tana shafa mai a hannunta, yau kam jikin da sauki, lantana na tattare kwanukan da aka kawo abincin safe zata maidasu gida.

 Dady ya turo kofar ba ko sallama, Goggo ta kalli kofa, ganinsa sai dayasa gabanta faduwa, ya shigo fuskar nan a hade ya tsaya yana kallan dakin, kallan Lantana yai yace “ke dan fita.”

 Lantana ta mike tai waje, Goggo ta kalleshi tace “ina kwana?”
Dady bai amsa ba yace “ hankalinki ya kwanta?”
Tace “da me fa?”
 “A haka in aka kalli fuskarki ba wanda zaiyi tunanin zuciyarki akwai hassada, bakinciki da tsantsar munafirci.”

 Goggo cikin mamaki tace “me kake nufi?”
Yace “sai ki taso ki zo kibi mijin yarki da kikasa ya daukeki daga gunmu.”

 Goggo cikin mamaki tace “mijin ‘yata kamar ya kenan?wace yar tawa?”
Yace “ni banda lokacin munafircinki, ki taso ki fito, in kuma bazaki iyaba ki cigaba da zama.”

 Goggo gaba daya kanta ya daure ta kasa gane me yake nufi, kwallama Lantana kira yai yace “zo ki kwashe kayan nan an sallameta.
Goggonta mike tsaye tadan dosana kafarta tace “Wai Abubakar me kake nufi ne? Ni na rasa me yasa kullum kai burinka ka jefeni da sharri.”
Cikin takaici yace “sharri? Ai kece kike bina da sharri dan na tabbatar badadan ke ba da tuni Inna ta bani company dinsu, amma saboda tana ganin naci amanarsu na kawoki, daga ke har ‘yarki banda bakinciki me kuke tsinanamin? Da na dauka yanzu zan moreta sai gashi yau ta wargaza komai, ni ki wuce mu tafi dan ganinki ma bakin ciki yake sani.”

   Goggo kallansa kawai take zuciyarta na wani irin kunna, tace “nikam menene matsayina agunka? Ma dauka ni matarka ce.”

 Wata irin dariya yai wanda yasa ta kallansa cikin wani yanayi, yace “mata? Wa? Kedin? Kema kinsan ni ba sa’an auranki bane ko a can baya bare yanzu, ni ba wani aure ko makamancinsa tsakaninmu, ina zaune dake ne kawai saboda yarki da tazamarmin dole.”

  Goggo ta share kwallar ta tana neman yin magana ya fita yana cewa “kuma ki sauko yanzu.”

 Lantana ta shiga saukar da kaya kasa, dady ya nuna mata motar Hassan, nan aka bude boot din mota aka sasu, itakam Goggo ta dade tana kuka, nurse tazo ta kara dubata sannan ta taimaka mata ta sauko, shigowar Lantana na karashe suka sauka tare.

  Tsayawa tai tana kallan motar, Hassan ya taho da sauri gunta sannan ya kalleta.
Kallansa tai cikin mamaki tace “wanene?”
Hassan ya kalleta sannan yace “bari na kira kuyi magana da Jalila.” Dan baisan me zaice ba.

 Matsawa yai ya kira number Sageer.

 Sageer na daki lokacin da Hassan ya kirashi, yayi mamakin kiransa ya amsa da sauri yana cewa “yaya lafiya?”
Hassan yace “Sageer ina Jalila?”
Yace “tana sama dazu ta hau.”
 Hassan yace “please ka dan kai mata waya.”

 Yace to sannan ya mike ya fito.

 Jalila tafito daga wanka kenan ta zura wata doguwar rigar atamfa, dan dama kwalliya bata dameta ba saboda ba barinta ake tana yi ba, sannan bama wani iyawa tai ba, balle hankalinta ma ba’a kwance yake ba bare tai tunanin yi.
Mai kawai ta shafa ta dan shafa hoda tasa turare, dan kwalimta kawai ta yafa akanta, ta zauna kenan ta dau wayarta taji knocking.

 Mikewa tai ta bude.

 Ganin Uncle ne yasa ta tsaya tana kallansa, shima kallanta yai sannan ya mika mata waya yace “Yaya ne.”
Amsa tai bata rufe kofar ba ta juya zuwa ciki tana cewa “Yaya!”

 Yace “yauwa.” Tana jiran ya sake magana kawai taji sallamar Goggo, jikinta na rawa cikin rawar baki tace “Goggo.”
Goggo tace “jalila?”

 Jalila hawaye ya zubo mata tace “Goggo kina ina?”
Tace “gani a kasan asibitin ance wai wani ne ya zo daukana shikuma naga bansanshi ba, shine ya kiraki, kinsanshi ne?”

 Jalila tana kuka tace “ki biyoshi Goggo, ke kadai ce?”
Tace “a’a mahaifinki nanan.”
Jalila tace “Goggo dan Allah karki nuna bakinsanshi ba, ki bishi zai kawoki inda nake.”

 Cikin mamaki Goggo tace “inda kike? Kedin bakya gida?”
Jalila tace “inkinzo zan sanar dake komai.”

 Goggo tace to, sannan ta kalli Hassan ta mikamai waya, baice ma Jalila komai ba kawai ya katse wayar.

  Jalila ta juyo inda Sageer yake tana hawaye, tace “Uncle!”

 Shikam hankalinsa ya tashi ganin tana kuka yace “menene? Wani abun ya faru ne?”

 Gani yai tana dariya tana kuka, tace “Uncle, Yaya ya daukomin Goggona.”

 Tsayawa yai sai dai yanzu baisan me zai kwatanta abinda yakeji ba, yai murmushi yace “duk da bansan meke faruwa ba, it look like abin farinciki ne, sannan alama ce ta shakuwa na shiga tsakaninku, tunda gashi har yasan abinda ba wanda ya sani, sannan lafiyarsa ma nasan samun kusanci dake ne yasa, uhm congratulation, Allah ya barku tare.”

 Ya juya jiki a sanyaye da kallo ta bishi zuciyarta na tausayamai, ta tabbatar Uncle na santa sosai bawai ya rabu da ita bane dan kansa sai dai zumunci da kaunar da ke tsakanin shi da yayansa.
Hawayenta ta share sannan ta zauna abakin gadon tana tunanin me zata ce ma Goggo?

Hassan kam Goggo na shiga mota ya kalli Dady yace “Allah yasa akwai kudi a jikinka”
Dady yace “babu, menene?”

 Hassan ya sa hannu a aljihu ya dauko 1000 yace gashi ka hau mota dan gida zan wuce daga nan.”

 Dady yace “mene? Kai ni na haifi Jalila fa, bawai dan aikin gidansu bane, wai me yasa......”
 Ganin Hassan yai ya shiga mota kamar ma badashi yake ba yaja yayi gaba, ran Dady a bace yabi motar da kallo.

 Hassan kam jan motar yai sukai gaba, Goggo da Jalila na baya, suna fara tafiya Goggo tace “meke faruwa? Ya akai Jalila tabar gida?”

 Hassan ya dan shafi kansa dake ciwo yace “ Jalila zata miki bayani, zaifi cancanta ta miki bayani da kanta.”

 Goggo tai shiru tana addu’a aranta, Allah yasa Jalila ba wani mugun abu ta fada ba, sai dai kallan Hassan yasa wannan ya tafi daga ranta.

  Kallan tangamemen gate din da aka bude yasa Goggo ta kara cewa “tana cikin nan?”

 Yace “eh.”

Kallan gida take har yai parking, da gudu Jalila wacce ke tsaye a waje ta taho bude kofar inda Goggo take a zaune.

  Kallanta Goggo tai sannan ta kalli gidan zatai magana Jalila ta rungumeta ta saki wani irin kuka.

 Hassan ya juyo ya kalleta, me yasa ta fita kuka ne? Shifa bayasan kukan nan.

 Kallanta yai yace “ kuka zaki tsaya yi ba zaki taimaka mata ku shiga ciki ba?”

 Ta share hawayenta tana cewa “Goggo muje.”

 Hassan ya fito ya wuce ciki bai jira su ba, a falo ya taradda Ummy da alama fitowarta kenan, kusa da ita yaje yace “Ummy ina Abba?”
Tace “yana falon sa.”

Yace “Ummy muje akwai maganar da zamuyi.”

 Kallansa tai cikin jin dadi tace “da alama Hassan dina yanzu bakinsa na kokarin yin magana akai akai.”

 Hassan ya juya ya kwankwasama Sageer kofa ya fito, yace “muje.”

 Nan suka shiga kofar falon Abba.
Yana zaune rike da qur’ani dan suna shigowa Ummy ta dauko ta mikamai itakuma da bata sallah tadau littafin addu’oi.

  Shigowar su ne yasa ya kai aya sannan ya ajiye ya kallesu.

  Zama sukai Abba yace “lafiya?”
Ummy tace “Hassan ne zaiyi magana.”

 Abba ya kalleshi yace “Hassan!”
Zama yai sannan ya dansa hannunsa na haggu akansa dake ciwo yace “tare nake da bakuwa.”

 A tare sukace “bakuwa?”
Hassan yace “eh, tunani nake boys quarters din mu zansa a gyara sai na maida ita can.”

Abba yace “naji ba wai wannan bace maganar, wacece bakuwar? Itace tambayarmu.”

 Hassan yace “mahaifiyar Jalila.”

 Abba cikin mamaki yace “me kake nufi? Taya zaka dauko mata a gidan mijinta da arzikinta da komai ka kawota boys quaters?””
Hassan yace “bansan ta ina zan fara bayani ba, sai dai ita zatayima Ummy kudan bata lokaci kadan, abu daya zan iya fada, wacce kuka sani a matsayin mahaifiyarta ba ita ta haifeta ba, ban kyauta ba na kawota ba da saninku ba sai dai wannan ne kadai solution din da yazomin”
Ya mike saboda kansa dake ciwo ya fita.
 Abba yace “meke faruwa takamaimai? Ni na kasa ganewa.”

Ummy ta dafashi tace “ mu jira kamar yanda yace, na tabbatar yana da dalilinsa, kasan Hassan mutum ne da baya shiga abin mutane, tunda kaga ya shiga wannan i am sure da dalili.”

 Sageer ta kalla wanda yai shiru yana tunani, tace Sageer taimaka muje mu shigo da ita, sai mu sata a dakin Ameera inyaso gobe sai a gyara can din.”
 Nan suka mike suka fita.

A waje sukaga Goggo ta tsaya tana cema Jalila, “nifa bazan shiga ba sai naji inane nan.”

  Jalila ta daure tace “ Goggo dan Allah mu shiga wlh zan fada miki.”
Goggo tace “Jalila.”
Jalila ta rike hannayenta tace “ Goggo gidansu mijinane.”

Goggo tace “me? Miji? Miji kamar ya?”

 Sageer har zai fita ya tuna Goggo fa ta ganshi ta kuka san sunanshi, kallan Ummy yai yace “Ummy bari na dan shiga toilet it’s urgent.”

 Dariya tai tace “to a fito lafiya.”
Ya juya da sauri, yana cewa gwara mu mata bayani kafin ta fada cikin mutane.

 Ummy tana turo kofar taji Goggo na cewa “Jalila aure kamar ya? Aure bansani ba? Auran dole aka miki?”

 Cikin mamaki Ummy a karasa tace “meke faruwa? Bangane aure mahaifiyarki bata sani ba, meke faruwa Jalila?”

 Jalila ta kalli Ummy idanunta fal tace “Ummy.”

Ummy ta kalli Goggo sannan ta kalli kafarta dake ciwo, tace “muje ciki sai muyi maganar a nutse.

 Goggo bata musa ma Ummy ba suka shiga ciki.

#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

_Should i start with sending my special greetings? Special greetings to u all my fans, thanks alot for the love and support, a sincere thanks to you all from the bottom of my heart 💕Luv u all._

*42*

 Ummy ta zauna akan gadon kusa da Goggo akwai abubuwan da takesan ji, sai dai ta tabbatar matarnan ba lafiya ce ta isheta ba, dan ga kafartanan.
Kallan Goggo tai tace “ki kwanta ki huta dan Allah karkiyi tunanin komai har sai hankalinki ya kwanta.”

  Goggo ta kalli Ummy tace “Hajiya ta ina zan kwantar da hankalina, aure? Bansani ba?”
Ummy ta kalli Jalila ta mata alama da ta fita, sannan ta kalli Goggo bayan Jalilan ta fita tace “ sai yanzu na fahimci me yasa yarki batada walwala duk kuwa da yanda naso ta saki jikinta da gidan nan, na fahimci an cutar dake, an munafurceki, sai dai bayanda za’ai a maida hannun agoggo baya, ki nutsu ki kwantar da hankalinki, inkin huta anjima sai muyi magana, sai kiji abinda ya faru nima naji abinda ya faru, amma yanzu ko saboda ‘yarki da kwanciyar hankalinta kiyi hakuri, lafiyarki itace abin dubawa a wannan lokacin.”

  Goggo kallanta kawai take tana mamakin yanda mace mai kudi, mai aji, mai kyau haka take magana cikin sanyi da nutsuwa, da alama Matarnan macece mai tsananin imani, da kaunar jama’a da sanin darajarsu.

 Kasa musama Ummy tai ta daga mata kai alamar fahimta, Ummy tace “nagode, ga toilet nan in zakuyi amfani dashi.” Ta fada tana kallan Lantana.

 Goggo tace “Angode.”
Ummy tai waje ta turo kofar.
A waje taga Jalila a tsaye, murmushi ta mata tace “me kike anan?”
 Jalila ta kalleta da idanunta da sukai raurau tace “Ummy kiyi hakuri, sannan nagode....”



Ummy tai murmushi tace “wanda zakima godiya daban bani bace.” Sannan ki barta ta huta zuwa anjima, amma meke damunta?”
Tace “hawan jini da diabetes.”

 Ummy ta kalli kofar dakin cikin tausayawa sannan tace “shikenan mu barta ta huta.”
Jalila ta daga kai alamar to sannan tai hanyar sama.

 Hannu tasa tana neman bude kofar dakin, tsayawa tai tana rike da hannun kofar amma bata bude ba, tana tunanin abinda zata cemai, da wani bakin zata fara mai godiya?

 A hankali tai ajiyar zuciya sannan ta tura kofar, a kwance ta ganshi kamar mai bacci, kusa dashi taje ta tsugunna tana kallansa, hawaye ne yazobo mata wanda batasan ya diga akan kuncinsa ba, a hankali ya bude idanunsa.

 Kallanta yai tana share hawayenta, a hankali ya ke magana yace “Menene? Wani abun ya faru ne?”
 Hawayenta ta karasa gogewa da sauri sannan ta girgiza kai tace “bakomai.”
Yace “and why?”

 Tace “bansan me zance maka bane, kawai sai naji hawaye....”
Idanunsa ya lumshe kansa na sarawa yace “ it looks like it’s ur hobby.”
Tace “kukan?”
Ya lumshe ido kawai, kallansa tai sannan tace “bakajin dadi ne?”
Bai tanka ba sannan bai bude ido ba, hannunta tasa a kansa wanda ke mai ciwo kamar zai tsage, jin zafi rau akan tai, da sauri ta kai hannu wuyansa, nan ma zafi a rikice tace “Yaya bakada lafiya, zazzabi ne a jikinka, jikinka zafi.”

 A hankali ya bude idanu yace “why? Are u worried about me?”

 Da sauri tace “sosai ma, ka tashi muje asibiti.” Ta fada tare da mikewa tana kokarin dagashi, hannu tasa ta riko hannunsa tana neman dagashi.

 Jawo hannunta yai, ta fada jikinsa, shiru ne ya ratsa dakin, ita kuma zuciyarta na harbawa da sauri da sauri, a hankali ta kalleshi, idanuwansa a rufe suke, sai cewa yai “ sai yaushe za’a daga ni?”
 Ta kalleshi ta kalli kanta data danneshi, neman dagawa tai sai taji hannunsa na rike da ita gam.

 Tace “to ai.....”
Idanu ya bude a hankali ya kalleta, a hankali tai kasa da idanunta.
 Saketa yai ta mike ta zauna a gun, bata tashi ba tace “Yaya dan Allah muje asibiti.”
Yace “bana zuwa asibiti, sannan ni nasan jikina kawai nayi abinda bansaba bane shiyasa, karki damu.”

 Idanu ta kuramai bayan ya maida idanunsa ya rufe, a hankali tana kallansa tace “Yaya nagode, ban taba tunanin wannan ranar ba.”

 Bai tanka mata ba, idanunta ne suka ciciko tace “Kayi hakuri Yaya nagode sosai har bansan ta ina zan fara ba.”
Yace “hakurin me?”
A ranta tace “da na dauka kai mutum ne mara tausayi da mutunci.”

 A fili tace “for everything.”

 Idanunsa ya bude a hankali sannan ya kalleta, itama kallansa takeyi, sai dai da sauri ta maida idanunta gefe.

 Yana kallanta yace “ya zakiyi?”
Tace “name?”

 Idanunsa na kanta tana kallansa taga ita yake kallo ta dauke idanta da sauri, yace “ya zakiyi insu Ummy sun tambayeki?”

 Tace “ bansan ya zanyi ba, wata zuciyar na sanar dani in fadi komai, wata kuma na tunanin abinda zai faru da Dady dan na tabbatar Inna bazata barshi ba.”

 Kamar bazaiyi magana ba, dan harta mike zata nemomai maganin zazzabi ragowar tata wanda takaima Ummy taji muryarsa yace “ kiyi abinda ya kwanta miki a rai.”

 Juyowa tai ta kalleshi tace “In na tuno abinda yama Goggo tundaga haduwarsu zuwa yanzu, sai naji kome zai sameshi bazan damu ba sai dai bansan meke damuna ba, I wish nima inada dauriyar zuciya ko rabin taka ce.”

 Alama yamata da hannu akan ta matso, matsowa tai gunsa, ya mata alama data kara matsowa, nan ma ta matso takai kunnenta saitin bakinsa, a hankali yace “in fada miki sirrin?”
 Kai ta daga da sauri, yace “kisa Goggonki a saman komai.”

 Abinda ya fada kenan yai shiru tare da juya mata baya ya rufe idanunsa, tsayawa tai tana kallansa me yake nufi? Tace “yaya!”

 Shiru yai baice komai ba, itama shiru tai tana tunanin me yake nufi.
 Ta dade a tsaye kafin ta daukon mai maganin, ta dauko ruwa a karamin fridge din dake dakin, tazo kusa dashi tace “Yaya tashi kasha magani.”

 Bai bude idanunsa ba, ganin bashi da alama ne yasa ne ta kara cewa “Yaya Please, ko in fadama Ummy?”
 Idanunsa ya bude yace “wato kina neman kiyi amfani da weakness dina ko?”

 Dariya tai tace “ inkaki tashi yanzu sai na sanarma Ummy.”

 Yace “eh lalai kinga gadon bacci na...”

 Ta kuntse dariyarta tana nunamai gadan da yake kwance akai, harararta yai sannan ya mike zaune ya fizgi ruwan hannunta ya mikamata dayan hannun ta. Zubamai maganin tana dariya.

 Sha yai sannan ya kwanta.


**********

 Ummy na shiga falon Abba ya kalleta yace “meke faruwa? Nifa na kasa gane abinda ke faruwa.”
Tace “ni kaina bansani ba sai dai na tabbatar Hassan yasan me yakeyi, kafi kowa sanin halinsa a da can inyai abu ma to akwai dalili, daga baya kuma da matsala ta faru gaba daya ma yadaina shiga rayuwar kowa inba tasa ba, kaga yanzu dayai abin nan kasan zuciyata dadi takeji dan na fara ganin Hassan dina na da na shirin dawowa.”

 Abba yai murmushi yace “na fahimta sannan nasan wanene Hassan, sannan ni koma menene ya faru ba wani abun dan ni dama ita na gani sannan ni ita na zaba, ko da a lokacin zasu nunamin wata ba lalai zuciyata ta amince da ita ba.”

  Ummy tai murmushi itama tace “ maybe suna tunanin sun cuceta ne da alama sunyi bincike akan Hassan..........”

 Karar wayar hannunta ne yasa ta kalleshi, kashe kiran tai sannan ta kalleshi, yace “ Sim dina na wayarki ne?”
Tace “eh, da na cire sai kuma nai tunani kar san zuciyata yasa wasu dasuke nemanka ko na taimako ko na aiki suyi ta nemanka, shiyasa nasa Sim din a wayata.”

 Shiru yai tare da maida kansa gefe can yace “Kiyi hakuri.”
 Tace “ kadaina fadar haka, kaddara ce ta zo mana, sai dai mu roki Allah akan ya taimakemu yasa mu wuce kaddarar nan.”

 Abba yai shiru bai sake cewa komai ba......


*********

 A can gidan Inna kuwa, Dady cikin takaici ya dawo gida, bakin cikinsa ko waya bai fita da itaba bare yasa a zo a daukeshi, rabansa da taxi haryamanta amma haka yahau ransa a bace.

 Yana isa gida ya wuce daki cikin zafin rai, Mumy dake kitchen tana bada umarnin abincin da za’ai ta taho da sauri ta shiga ciki.

 A tsaye ta ganshi tace “Abban Yasmeen lafiya?”

 Juyowa yai rai a bace yace “ kinsan yaran nan......” sai kuma yai kwafa.

 Ta matso da sauri tace “ya kukai? Yadauke Goggon Jalilan?”

 Yace “ya dauketa mana, yaran nan yana abu kamar shine gaba dani, kinga yanda yake wulakantani, amatsayina na uban matarsa?”

 Mumy tai shiru can tace “nikaina yaran nan yaban tsoro, wai garin yaya kukaba Jalila yaran nan? Bakusanshi ba? Na dauka kunyi bincike.”

 Cikin masifa yace “bincike? Abinda Inna ke bada umarni mu ina mukaga ta cewa?”

Mumy tai tsaki tace “ai gashi nan ta ja mana masifa, ita kanta yanzu abun ya dameta, gashinan abinda take tunanin samu ma ba samu zatai ba, wanda take dashi ma yana neman wargajewa.”

 Dady yace “wai yaran nan ni zai kalla yacemin wai inada kudi a jikin? Sannan ya mikon wai 1000 wai na hau mota shi bazai kaini ba?”

 Mumy tace “mene?”
Yai kwafa cikin takaici yace “ni nama rasa ma me zance, kamar ni????”

 Mumy ta rungumeshi tace “cool down Dadyn Yasmeen, zamu san mafita, bari Mu sanar ma Inna.”

 Yai tsaki cikin takaici, tace “Safeena ta kira, ta isa Paris lafiya.”

 Yace “Wai paris taje dama?”
Tace “eh can Inna tasa a nemar mata skul.”

 Yai shiru baice komai ba....

Inna gaba daya tunda Hassan ya fita ta kasa tsaye t kasa zaune gaba daya ta kasa samo mafita, cikin takaici ta kira Sani tacimai mutunci akan kin yimata binciken daya kamata akan Hassan kawai yacemata bashida lafiya alhalin bai bincika wani irin ciwo na kwakwalwa yake ba....


************

Kuka Zaliha take sosai tana cema Yayarta ita wlh kome zata yi tayi amma itafa kawai ta aura mata Taura in ba haka ba wlh barin gidan zatai ta shiga duniya...

 Hankalin yayarta ya tashi tace “ kar ta damu dan dole zata koma Niger.”


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*43*

Inna tana zaune tananin mafita Mumy ta banko kofa da sauri, Inna ta kalleta tace "naga sanda hankali zai ratsaki ki daina buga kofa haka, yarki ta kai a mata aure amma haryanzu inkina wani abu kamar karamar yarinya."

 Mumy ta zauna da sauri tace "ni Inna ki bar fadanki zuwa anjima yanzu akwai matsala."
Gaban Inna ne ya fadi ta kalleta tace "Abakar ya dawone?"

 "Ya dawo sai dai yaran ya dauke Goggo"
Inna tai shiru hankalinta ya tashi, ta kalli Mumy tace "yanzu kenan da alama sunsan komai ko?"

 Mumy tace "me zai hana? Shiyasa Inna ni dama na kasa gane dalilinki na......."
Wani kallo data mata ne yasata yin shiru, Inna tace "kinsan menene yake bakantamin rai?" Bata jira amsartaba tace " rashin wayau da auna tunaninki, daga ni har mahaifinki munada saurin tunani da kwakwalwa amma ke ni bansan ina kika dauko ba, da farko kince yaran ubanki zaki aura yaran da ko A bai sani ba lokacin, dole da ganin bamuda wani da bayan ke yasa muka jure, sannan kikasan wannan yaran ya munafirceki ashe har aure gareshi, amma tsabar rashin kwakwalwa kika dage ke sai shi, sannan abin bakin ciki duk yanda nai dake akan kiyi aiki a company din da muka gina nida mahaifinki amma kinki, kin dage sai dai mijinki yai, sannan yanzu kice me?"

 Mumy tai kasa dakai sannan tace "Inna wai dan Allah sai yaushe ne zaki amince da Abakar daro bisa dari? Mutumin nan na miki ladabi wanda ko ni bana miki, sannan ya a sona san da ba wanda yakemin irinshi..."

 Inna tai tsaki tace "ni tashi ki bani guri nasan mafitar data dace damu dan zamanki anan bakomai yake karamin ba sai bakin ciki."

 Mumy ta mike tai waje rai a bace....

Inna tai shiru tana tunani kafin ta dau waya ta kira Abakar.
Yana zaune a falo Mumy na gefensa itada Yasmeen, Sultan na daki yana ganin kiranta gabansa ya fadi ya kalli Mumy yace da alama Inna tagama shawara.

 Mumy tace "muje tare."
Yace "karki damu ki zauna bari naje."
Nan ya mike yai sama.........


**********

Inna ta tashi tayi wanka, Ummy ta kawo mata kayanta tace ta saka, dan itakam ta kula kayan dake jikinta da wanda aka dauko a leda san ba magana, itada Jalila ne sukaje BQ dan ganin yanayin gun.

 Jalila ta kalli Ummy tace "Ummy kije ciki zan gyara."

 Ummy tai murmushi tace "Jalila ko dai ince masu aiki gidannan sundinga kwana ne?"

 Jalila tace "saboda me?"
Tace "da alama aikin gidan ya karu, sannan zai yi yawa, tunda akwai bangarensu ina tunani gwara mu tambayesu, in zasu dinga kwana to, in kuma bazasuyi ba kinga sai mu samo wasu."

 Jalila tai shiru can tace " Ummy gani, ga Lantana ina tunanin ba wani abu."

 Ummy tai murmushi tace "baki fahimceni ba kenan."
Jalila ta mata kallo mai alamar tambaya tace "ban....."

Ummy tai dan dariya tace "so nake kibama Hassan kulawa 80% dan na kula ina hanaki kula dashi."
Jalila da sauri ta juya tana tattare kaya dan kunya, Ummy ta sake dariya tace "ko nayi sankai?"

 Jalila tace "a'a kawai ta cigaba da aikinta.

 Ummy ta kalleta tana murmushi, Lantana ta kira suka gyara gun, Ummy tace "gobe sai a siyo gado da kayan bukata a sa a ciki, wai gadan ciki ya tsufa, da Jalila zatai magana Ummy ta harareta wanda yasata yin shiru.


 Sageer kuwa a daki hankalinsa duk ya tashi tabbas Goggonta ganshi a lokacin dan har gaisheta yayi, to amma tagane tsakaninsu? Malam Sagir ashe da raban zan ganka.

 Kalaman Goggo ne suka dawo mai, ajiyar zuciya yai cikin tashin hankali yace " ba zama bane ya dace dani."

 Mikewa yai ta budo kofar dakinsa a hankali ha sako kai, yana leke.

 Bakowa a falon, komawa yai ciki ya zauna yana tunanin abinyi, can ya daure ya fito a hankali yai falo, Ummy na zaune rike da littafin addu'oi ya shigo.

 Ta kalleshi tace "Sageer fitowarka kenan, tun rana sai yamma?"

 Yace "Ummy ina matar Yaya?"

 Tace "Jalila? Tana BQ suna aiki, ta dage sai na taho, ya akai? Nemanta kake?"

 Yai murmushin dole sannan yace "eh, bari naje can."
Ummy tace "to, amma Sagir karka tambayeta maganar mahaifiyarta, da magrib in anyi sallah za'a zauna a falon Abbanka."

 Yace "to Ummy sannan yai waje.

 Tana kwashe shara ya tsaya a bakin kofar yana kallanta.

 Kallansa tai sannan ta matso inda yake jiki a sanyaye.

 Kallan dakin yai, ya kalli Kofar Toilet inda Lantana ke wankewa.

 Yace "Jalila!"

 Yace "Uhmm"
Shiru suka danyi dan they are uncomfortable in suna tare ba kamar da ba.
Can ya daure yace "Goggonki, sanda mukaje asibiti....."

 Sai a lokacin itama abin yazo mata, ta kalleshi da sauri tace "Ta ganka ko?"
Yace "kin manta har gaisawa munyi?"

 Tai shiru tana kallansa, yace "Jalila, zaki iya mata magana? Dan banasan kowa yasan abinda ya faru a baya."

 Jalila ta kalleshi tace "ince me? Ince Goggo yayan Uncle nake aure? Ko ince Goggo karki fadama kowa irin san da nakema Kanin mijina? Ko ince Goggo da naso Uncle ashe kanin mijinane?"

 Yace "Jalila ya kikesan juya maganar da na fada ne? Me yasa bakya yima kalamai na kyakyasar fahimta?"

 Idanunta ne suka ciciko tace "Uncle ni to ya zanyi? Me zance? Kamar yanda kake tsoron matsala ta afko a dalilinka, matsalar da zata sa hankalin iyayenka su tashi ni kaina a yanzu bana san ace nice silar wargaza farinciki Ummy da Abba, dakai kanka da yayanka, Uncle bansan....."

 Kasa karasawa tai saboda kuka dake neman zuwa mata dan muryarta ta fara rawa.

 Sageer yai shiru yana kallanta cikin tausayawa yace "Nafahimceki Jalila, na kuma gode da kaunar da kikema Family na, Please ko Goggonta tambayeki kawai kice mata sunane yazo daya, mu barshi kawai a haka."

 Ta daga kai, kawai dan batasan itakam me zata kuma cewa ba...

Bayan sun gama aiki tai wanka a toilet din ta maida kayan jikinta ta hau sama.

 Yana kwance yana bacci ta shiga a hankali ta dau kaya ta saka, sannan ta matso kusa dashi ta sa hannunta akansa, jin ba zafi yasa tai murmushi.

 Da alama yau ma ciwon nasa da sauki, dan bacci yake hankalinsa a kwance.

*********
  Bayan magrib kuwa Ummy ta kalli Jalila bayan sun gama girki tace "Jalila inkin kaima Goggon ki ajiye sannan ki kaita falon Abba zamuyi magana."
 Tace to, sannan ta dauki Abincin Goggo, tana shiga dakin ta zauna kusa da Goggo tare da kwanciya a kafadar ta tace "Goggona!"

 Goggo ta kalleta tace " kin gama gudun?"

 Jalila tace "gudun me?"
Goggo ta tureta daga kafadarta tace "kindauka bansan guduna kike ba? Kar na miki tambayoyi? Shiyasa tunda kika fita kikaki shigowa?"

 Jalila ta tuntsire da dariya tace "ni? Wlh ba haka bane aiki mukeyi ne bakiga Lantana ma batanan ba?"

 Goggo tace "ba wani."
Jalila fa kara kwanciya a kafadarta tace " Ummy tace inkaiki falon Abba, anan zakiji komai."

 Tace "kaini dan ni kaina so nake naji."

  Nan suka fita tare, sai data kusa kaita falon, suna tafe tare sai ga Ummy tace " Jalila barta zamu shiga tare."
Ta matso kusa da kunnenta tace "ki je ki lalabo mijinki."

 Jalila ta kalleta, Ummy tai murmushi sannan ta nuna mata sama da kanta.

 Jalila ta kalli saman sannan ta nufi matatakalar, anya zai fito kuwa? Gashi bashida lafiya.

 Kofar dakin ta tura ta shiga, yana kan sallaya yana karatun kur'ani.

 Zama tai a bakin gado tana jiransa, bai dade ba yakai ayar karshe ta cikin suratul maryam, yana neman dauko wata surar ne dan izu daya yake yi a duk tsakanin sallar magrib da isha'i tai saurin cewa "Yaya!"

 Tsayawa yai bai fara wata surarba sannan bai juyo ya kalleta ba, tace "Yaya za'ayi maganar."

 Ya juyo yace "magana?"
Ta kalleshi tace "maganar nan.... ba Abba yace sai anjima ba?"
Yace "and so?"

Tace "shine za'ayi yanzu ka sauko."

Yace "in me?"
Tace "ka sauko, muje tare."

 Yace "kinsan me kike cewa? Nine zan sauko inje inda kowa zai zauna ayi magana?"

 Kallansa tai tai raurau da ido, yace "ki tashi kije, ni ba nayi nawa part din ba? Saurab ya rage naki."

  Haryanzu kallansa take da idanun kafin tace "Yaya Please"

 Juyawa yai ya bude kur'ani zai dora daga inda ya tsaya.

 Da sauri ta sauko ta bayansa ta rike gefen rigarsa ta kafadarsa.

Juyowa yai yace "wai........"

 Bata jira me zaice ba tace " yaya dan Allah ka taimaken, ba wai wani abu zakace ba, inka zauna agun ma ya isa."

 Yace "in zauna?"

 Tsugunawa tai ta gefensa tace "Dan Allah yaya."

 Hade rai yai ya juya, tace "kan ne?" Ya mata shiru, tace "yahkuri yaya, na sani ina takura maka, sannan ina takura maka da neman yin depending akanka akan komai na rayuwata, kayi hakuri nasan bana kyautawa."

 Ta mike tai waje, a falo ta tsaya tai ajiyar zuciya sannan tace " who do u think u are?"

 A hankali ta fara sauka daga matatakar, jiki a sanyaye.

  A falo kuwa Abba da Ummy na zaune daga bangare daya, Goggo na dayan bangaren Jalila ta shigo.

Tana shigowa Sageer ya shigo, tunda ya shigo Goggo ke kallansa, inata san fuskar nan? Abba ne ya katseta da cewa "yaki saukowa?"

Ta daga kai alamar eh.
Jiki a sanyaye ta zauna a kasa kusa da Goggo.

 Sageer ya zauna a kasa kusa da Abba.

 Falon ya dan yi shiru kafin Abba yai gyaran murya yace "Sannu da zuwa mahaifiyar Jalila, muna baki hakuri akan abinda ya faru wanda mu kanmu bamusan takamaimai abinda ke faruwa ba, sai dai ina neman sanin dalilin dayasa ba wanda yasan da zamanki a gidan, sannan dalilin dayasa aka munafircemu mu dake akan auran nan, Jalila yar muce a yanzu shiyasa nake san sanin menene ke faruwa takamaimai."

 Goggo tace "nagode da karamawa, sai dai a yanda nasan mutanen nan ba damuwa sukai damu ba ina mamakin yanda akai suka kawo Jalila cikin gidan karamci irin wannan."

 Abba yai murmushi yace "mun gode da karamawa, Jalila inaso ki sanar damu abinda ke faruwa."

 Jalila ta kalli Abba, ta kalli Ummy sannan ta kalli Sageer.

 Ummy tace "duk wani abunda kika sani muke sanji, wannan shikadai ne abinda zaisa musan abinda ya dace muyi, kada ki munafurcemu, kada ki munafirci mahaifiyarki."

 Jalila ta kalli Goggo.

 Turo kofar da akai ne yasa suka kalli kofar, Hassan ne ya shigo.

 Kallan Jalila yai wacce itama kallansa takeyi, a hankali wani murmushi ya bayyana a fuskarta wanda yana ganin haka ya dauke kansa daga kallanta sannan ya nufi can gefe ya zauna akan kujera shi kadai.

 Goggonta kalleshi, wannan shine na dazu......


********

Inna ce ta kalli Dady tace "take all the blame."

Kallanta yai cikin mamaki yace "ban gane ba?"
Tace "kace kaine kai komai, dama matarka ce da yarka, kaga kome kai dama kaine me hakki akansu, wannan shikadaine hanyar dazamu kwaci company dinmu."

  Dady yace "ni na kasa fahimta, kenan nine na shirya duk abinda ke faruwa?"
Tace "eh ko dama nice na shirya? Ina naga matsayi? Matar data tsufa????

Dady yamata wani kallan tsantsan mamaki........


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*44*

  Jalila tai ajiyar zuciya sannan ta kalli Goggo tace "sanda na sameki a bangaren su Dady akwance ba lafiya........................."
Haka ta kwashe komai ta sanar dasu, gaba daya falon yayi tsiy saboda tsananin tausayin abinda kunnuwansu yakeji, Hassan na zaune ya kwantar da kansa a saman kujera, idanuwansa na lumshe kai kafe bai san me ake cewa a falon ba, sai dai gaba daya zuciyarsa a karye take da abinda kunnuwansa keji, wannan wace irin rayuwa yarinyar nan tai? Wani irin rashin imani ne hakan? Hannunsa ya matse guri guda cikin tsananin takaici.

  Jalila ta karashe maganar tana kuka tace Goggo banasan wani abu ya sameki shiyasa na kasa fadamiki, sannan suma sunce min karna sanar dake.....

 Goggo tana kallanta idanuwanta na zubar da kwalla ta jawota jikinta ta rungume Jalila ta saki wani kuka mai ban tausayi, Goggo tana hawaye tana shafa bayanta tana cewa "kiyi hakuri Jalila duk nice na ja miki abinda suka miki."

Ummy ma gaba daya hankalinta ya tashi, tausayin su ya kamata.

 Sageer kam ba'a magana dan baima san hawaye yana gangaromai ba, sai dayaji ruwa a kuncinsa, ya goge da sauri yana kallanta.

  Ummy ta kalli Abba wanda yai shiru yana nazarin abinda ke faruwa, kenan bayan yaga Jalila yace yanaso su bawa dansa a matsayin matar Hassan shine sukai bincike akan Hassan, da sukaji bashida lafiya shine suka hadashi da ita, to ina asalin yar tasu? Dan ya fahimci akwai wata.

 Kallan Jalila yai yace "ya isa haka Jalila, su ne suke tunanin sun cutar dake suna ganin sun yaudare mu, amma ni da matata basu yaidaremu ba ko kadan dan ni dama ke nagani sannan ke kika kwantamin a rai, haka itama ke ta gani sannan ke kika kwanta mata a rai, anci mutuncin mahaifiyarki a matsayinta na wacce ta haifeki ta shayar dake sannan ta reni bai kamata ko menene ba a aura da 'ya bada sanin mahaifiyarta ba."

 Ummy cikin zafin rai tace "ai muma sun ci mutuncinmu taya zasu nuna mana sune suka haifeta bayan mahaifiyarta daban, tayana dan rashin imani zasu aurar da yarinya mahaifiyarta na kwance ba lafiya? Sannan suyi amfani da rashin lafiyarta gun sata tayi abinda sukeso?"

 Goggo ta share hawayenta tace " duk nice suka raina, nice suka maida abin zuba shara, nice basa ganin mutunci, nagode sosai da kaunar da kuka nuna ma yarinyar nan, ko ba'a fada ba na san akwai kulawa mai karfi datake samu a gidannan fiye da gidan da za'a kirashi da sunan gidan mahaifinta."

  Abba yai ajiyar zuciya yace "yanzu tunda nasan meke faruwa bazan barsu haka ba."

 Ummy ta kalleshi da sauri tace "me zakayi?"
Ya mike cikin takaici yace "don't u understand what's happening? Sun daukemu a matsayin joke ne, kenan sun maidamu fools, duk abinda suka tsara shi muke bi."

 Ummy ta kalli Hassan wanda kamar ma baisan abinda ake a falon ba, sannan ta kalli Abba tace " ni kuma ina ganin ka kyalesu kawai."

 Abba yace " In mun kyalesu kina tunanin zasuyi dana sani?"

 Goggo ta kallesu tace "amma dan Allah inada tambaya, me ka musu ne da harsuke tunanin ko za'a mutu sai sun kawo Jalila cikin gidan nan?"

 Sageer ya kalli Abba yace "Abba ni kaina ina wannan tunanin."

 Abba ya kalli Ummy yace " kasuwanci......."

 Ummy tamai alama dayai shiru, yace " yanzu ke Jalila kiyi hakuri, nasan an shiga hakkinki, sannan an shiga hakkin mahaifiyar data haifeki, kuyi hakuri wannan harda laifin mu."

  Goggo da sauri tace "ba laifinku bane, masu laifin daban, zan iya yafe duk wani abu da za'amin ko na wulakanci ko na tozarci amma bazan yafemusu ba akan abinda sukama Jalila, tayaya zasuyi amfani dani wajen ganin sun sata abinda sukeso? Yanzu da ace mugun hannu ta fada fa???? Ta fada cikin raunaniyar murya.

  Hassan ya bude idanunsa ya kalli Jalila wacce ke kuka tana zaune kusa da Goggonta.

  A hankali ya mike kawai yabi ta bayan kujera yai hanyar waje.

  Jalila ta kalleshi, shima kallanta yai sannan ya dauke idanunsa da sauri.

  Ummy ta mike tace "Hassan ya akai?"

 Yace "bakomai...."
Kawai yai kofa, kallan Abba tai cikin wani yanayi, hannunta ya yadan dafa alamar ba komai.
Sannan ya kalli Goggo wacce gaba daya ita da Jalila tausayi suke bashi, yace "Sageer kai dasu Jalila ku shiga ciki, ni zanyi magana da mahaifiyar Jalila."

 Sageer ya mike ya fita, Jalila ta mike ta fito.

Abba ya kalli Goggo yace " garin yaya kika bari aka maidake kamar baiwa? Ko bakida yan uwa ne?"

  Tace "inadasu sai dai a matsayin babu suke."
Ummy tace "kamar ya?"

Tace "bayan anmin auren dole da Abakar aka umarceni da karna kara tako garin sai dashi tin daga lokacin ban sake zuwa ba, dan banida darajar da zai kaini."

 Ummy tace "kamar ya? Baki sake neman mahaifiyarki da yan uwanki ba?"

 Tace "ina zan nemisu bayan umarni mahaifina ya bani....."
Abba yace "wani umarni ne hakan?"

Ummy tai saurin cewa "Auranki fa?" Dan ta fahimci rashin ilimin addini ne ya sa ta dauka biyayya takeyi.

Goggo tace "ban sani ba nima dan rabona dashi tun ranar da aka kaini, lokacin Allah yai dabon Jalila."

  A tare sukace "me?"
Goggo tai kasa dakai tana murmushin takaici.

 Ummy tace "Goggo muje kici abinci ki kwanta."

 Abba ya kalleta cikin mamaki dan akwai tambayoyin da yake san jin amsarsu.

********

 Jalila na fitowa ta nufi hanyar sama, Sageer da sauri yace "Jalila!"

 Tsayawa tai bata juyo ba tana share kwallarta, Sageer ya matso ya mika mata handkerchief kallansa tai kamar zata karba sai kuma naga ta fasa, kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa  tace "nagode." Kawai tace ta juya ta hau saman.

Tsayawa yai yana kallanta cikin tsananin tausayi, har saida tai kwana sannan ya juya zuwa dakinsa, yana shiga ya zauna a bakin gado yana tunani, haka rayuwarta take? Shiyasa ashe ake barinta a makaranta ita kadai? Shiyasa sukasata a government?

*******
 Ummy ta taso tazo kusa da ita, suka fita tare, ina saurayin Jalila? Ta tabbatar Jalila.......... tunowa datai a inda tasan Sageer ne yasa ta kalli Ummy da sauri tace "ya sunan mijin Jalila?"

 Ummy tace "Hassan!"

 Goggo tace "wanda na gani dazu fa?"
Ummy tace "Sageer? Kaninsa ne."
Goggo tace "kaninsa?"

Ummy ta daga kai alamar eh, Goggo a ranta tace "to ko ba shi bane?"

Dakin Ameera ta kaita sannan tace "kici abinci ki kwanta, dan Allah karkiyi tunanin komai, Jalila yanzu 'yatace bazan kara bari wani abu ya sameta ba, sannan mu zamu san abinyi, ke dai ki kwantar da hankalinki ko dan lalurarki."

 Goggo ta riko hannun Ummy tace "Nagode, nagode har bansan iya godiyar daya kamata nai miki ba."

Ummy tai murmushi tace "muma mungode, da kika fahimcemu, yanzu sai kisama auransu albarka."

 Tace "insha Allah."

Nan ta shiga ciki.....

Ummy ta bita da kallan tausayi.

Jalila kam kamar zata shiga ciki sai kuma ta fasa, zama tai a falo kawai tana kuka ko kwanwutar bata kunna ba.

  Shima zama yai a kasa ya kwanatar da kansa akan kujerar dakin, wace irin rayuwa yarinyar nan tai? Amma duk da haka akwai laifinsa a ciki, ya tabbatar dabadan shi ba da baza'a mata auran dole haka ba, wadan nan tunani sune suke tayimai zirya a ransa, tarinta yaji hakan yasa ya kalli kofar falon.

  Mikewa naga yayi ya jingina kansa da jikin kofar, sheshekar kukanta yaji wanda yasashi rufe ido cikin tausayawa.

 Jin kukan yake har zuciyarsa, a hankali ya bude kofar.

  Dayake makunin fitilar falon a kusa da kofar take kawai sai ya kunna ta.

 Haske ne ya baibaye falon, da sauri ta dago.

  Jingina kansa yai da jikin kkatangar falon yana kallanta tare da sa hannunsa na hagu cikin aljihunsa.

  Kallansa itama takeyi, sun dade a haka kafin ta sauke idanunta kasa.

 Yace " yau ma hobby din naki ya motsa ne?"

 Ta kalleshi da idanunta da suka sha kuka, yace "a rana kuka nawa kikeyi?"

  Baki tadan motsa tanasan magana, yace " in zakiyi kuka kiyi a gurin daba kowa, dan ni ba hobby dina bane sauraransa."

  Ya juya bai rufe kofar ba ya zauna akan kujera, me yasa yace haka? Shi dayaje dan ya lalasheta?

  Mikewa yai yai sallar Isha'i, ganin batada niyyar shigowa yasa yaki mikewa daga kan sallayar, yana jiranta.

  Kofar yake lekawa, yaga ba alama.

  Pillow ya janyo yasa kansa akai yana kallan kofar.

  Abincin su ya kalla, bataci abinci ba, shiru yai yana tunanin shigowarta.

  Yana nan a kwance har karfe 10, baisan sanda bacci yai gaba dashi ba.

 Jalila kam bayan ya juya kawai ta kwanta akan kujerar tana yan mitoci, kasan baka damu da hawayena ba me yasa dazu kazo? Nikam Yaya me yasa baya magana mai sanyi? Tadan turo baki ta kwanta tana tunanin rayuwarsu.


  Batasan bacci ya dauketa ba, sai karfe 11 ta farka, batai isha'i ba ya akai bacci ya dauketa?

 Da sauri ta sauko daga kan kujera ta nufi dakin, a kwance ta ganshi a kasa, batai mamaki ba dan taga yanayi, kawai ta wuce toilet.

 Tai alwala tazo tai sallah, jitai cikinta na karar yunwa, ta zo ta bude abinci zataci, gani tai ba alamar taba abincin, baici abincin dare ba kenan?

 Kadan ta zuba a plate ta faraci.

 Lomarta uku taji kakarinsa, wani sankamewa yakeyi, da sauri ta ajiye abincin ta matso inda yake.

  Gaba daya ya sai juye juye yake, yana girgiza kai alamar a'a, ga zufa tanata keto mai.

  Hannunsa ta riko tana tabashi, Yayah! Yayah!
Gaba daya ba alamun yanajinta, kansa ta kwantar a kan cinyarya dan murkususun dayake yasa kansa ya sauka daga kan pillow din, tasa hannu ta rike kansa dayan hannun kuma tasa a saman kirjinsa tana dan tabashi tare da kiran sunansa.

  Can kuma sai tadanyi kulhuwalahu da falaq da Nasi sai tadan tofa mai.

  A hankali taji ya daina motsumutson.

 Idanunta na kansa ya ciciko saboda da tausayinsa, wannan wani irin abu ne ke damunshi? Me ya sameshi  abaya?

A hankali ya bude idanunsa, daidai lokacin kwalarta ta zubo ta zubu saiti idanunsa, wanda yana rufe ido ta zubo a bayan idansa.

  Idanunsa ya sake budewa ya kalleta, dayan hannun data rike kansa dashi ta saki ta share hawayenta sannan ta kalleshi tace "Yayah!"

 Idanunsa ya lumshe yana kallanta kamar yanda take kallansa cikin sansanyiyar murya mai kamma da rada yace "sai yaushe ne zaki daina saurin kuka?"

 Tace " kukan ne bakaso nayi?" Itama a hankali tai maganar tana kallansa.

 Mamaki ne ya kamata dataga ya daga kai alamar eh, tace "meyasa?"
 Ya dan girgiza kai kadan yace "ban sani ba nima, sai dai I don't like it."

  Kallansa tai tare da neman zare hannunta daga kan kirjinsa.

 Hannu yasa ya tsayar da hannu yana kallanta yace " yanzu kukan me kikeyi?"

 Tace "meyasa kakesan sani?"
 Yace "Hmm kawai, saboda sai naji ne zansan abinda ya dace nai."

 Hannunta ta nemi janyewa tana cewa "me ya faru dakai? Duk sanda kake abin nan kamar wani abu kake tunani."

  Shiru yai bai bata amsa ba, kafin can yace " izinki nawa?"
Tace "mene?"
Yace "tambayarki nai, so nake nasan karatunki, na kula kamar bakiyi nisa ba."

 Tadan sosa wuyanta da dayan hannun tace "bankai izu ko daya ba, a gida Goggo tadan koyamin na sallah."

  Idanu ya kura mata, wanda yasatai saurin juya kai yace "bakyajin zafin mahaifinki?"

  Tai shiru kafin tace "inaji, inaji sosai da har wani sa'in ganinsa ma banaso."

 Yace "kenan ko me ya faru bazakiji haushi ba?"
Tace "me zakamai?"

  Mikewa yai daga kan cinyarta sannan ya saki hannunta yahau kan gado....
 Da sauri ta taso tace "me zakayi?"
Yace "bakomai, fada kawai nai."

 Jalila ta kalleshi alamar rashin gamsuwa.........

********

Dady kuwa yana saukowa daga gun Inna ya shiga daki kawai ya hau hada kayansa, Mumy ta shigo da sauri zatai magana taga yana hada kaya, a rikice ta rike hannunsa tace "Dear menene?"

 Ture ta yai yace " menene? Da alama karshen zamana dake yazo."

 Da sauri ta rungumeshi tace "menene? Kafi kowa sanin bazan iya rabuwa dakai ba, Inna ce? Itace?"

 Yai shiru wai shi a dole ransa ya baci.
Da sauri ta fito ta nufi dakin Inna da gudu rai a bace.........

#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*45*


  Da karfi ta banko kofar dakin Inna, lokacin Inna na zaune tasa hannu tayi tagumi tana tunanin abinyi, yanda Mumy ta banko kofar ne yasa ta zabura ta kalleta tace "Lafiya?"

 Mumy cikin bacin rai ta zauna a gaban Inna tace "Inna so kike kiyi ajalina?"

"Ajalinki kamar ya kenan?"
Tace "in ba so kike in mutu ba taya zaki nemi halakamin aure? Sanin kanki ne yanzu kinsan bazan iya rayuwar ba Abubakar ba, a da ma da 'ya'ya basu hadamu ba na kasa rabuwa dashi bare yanzu."

 Inna ta katseta cikin fada tace "me ya fadamiki?"
Tace "ba damuwa ta bace da duk abinda kike tunani sai dai kiyi abinki ke kadai, dan wallahi bazan bari wani abu ya sameshi ba, in kuma so kike mu bar miki gidan to....."

 Mamaki ya kama Inna ta kalleta cikin wani yanayi tace "Fatima ni kike fadama haka? Ni wacce ma sadaukar da komai dan ganin farincikin ki?"

 Cikin masifa tace "kika sadaukar dame? Me kika sadaukar? Duk abinda kikeyi ba saboda kanki kikeyi ba? In har saboda nine ai da kin daraja Abakar kin bashi company din kamar........."
Marin data kifa mata ne yasa Mumy yin shiru, ta kalleta tare da rike kuncinta.

 Inna ta kalli Hannunta dake rawa, dan ita kanta batasan ta mareta ba, cikin dana sani tace "Fatima......"

 Mumy ta mike tsaye tana kallanta, hawaye sun cika mata ido tace " in har bakyasan in bar gidan nan ki ajiye duk abinda kike shirin yi." Ta juya tanaji tana kiranta bata amsa ba tai waje.

 Inna ta bita da kallo jiki a sanyaye.....

 Shikam Dady tana fita yai wata dariyar mugunta yace "Inna i am sry sai dai kin riga kin makaro akaina 'yarki da kikafiso a duniya zata iya juya miki baya."

  Yanajin alamun bude kofar ya shiga kokarin zuge jaka, Mumy na shigowa ta sa hannu da karfi ta fincike jakar sannan ta rungumeshi tace "Dadyn Yasmeen me yasa baka tunani na in zaka aikata abu?"

 Yace "tunanin naki ne yasani yanke wannan hukuncin, taya zan zubarma kaina mutunci? Bayan nasan ina zubar da mutunci na naki na zubar? Da ace kome zai faru zai tsaya akaina ni kadai bazai shafeki ko yaranmu ba wlh ba abinda bazan iya ba, amma ta yaya zan yarda in zubar da mutuncinki dana 'ya'yanmu."

 Dagowa tai tana kallansa tace "to kamin alkawari ko me zai faru bazaka sake tunanin rabuwa dani ba."

 Yace "na miki, yanzun ma ba'a san raina nake shirin tafiya ba."

 Ta kara kankameshi tace "barni da Inna bazan kara bari ta wulakantamin kai ba"
Ya shafa kanta yana wani murmushin mugunta yace " taya zan yarda na zama sillan fada tsakaninki da mahaifiyarki?"

 Tace " ba kaine silla ba dan dama na gaji da yanda take ma kamar wani bawanta."

  Nan ya sumbaceta a kunci yace "i luv u Zarah."

 Ta sakarmai murmushin so......
Nace ansha kauna😏

Inna kuwa Mumy na fita ta ture littatafan dake kan tabir din gabanta cikin takaici tace "Abakar how dare you!"

  Kwafa tai tace " kana tunanin ka samu abinda kakeso? Inji wa?"

 Ta sakeyin wata kwafa........

********

  Zama tai a kusa dashi a kan gado yana kwance yana tunanin Zaliha, ji yake zuciyarsa kamar zata fashe da rashinta.

 Ganin baimasan ta zo bane yasa tasa hannu ta tabashi.
Kallanta yai sannan ya kakaro murmushi yace "Yaushe kika shigo?"

Tace "me kake tunani?"
Kallanta yai jiki a sanyaye, murmushi tamai sannan ta kauda kai, a hankali yace "I am sry, i am really sry."

  Kallansa ta sakeyi tace "me kake tunani game da mutanen nan?"

 Ya mike ya zauna yace "amsar kudinmu zamuyi, inyaso company din nasu ya nukushe."

  Tace "ayi haka kuwa?"

Yace " baki kula da rainin hankalin da suka mana ba? Sannan yarinyar nan da mahaifiyarta, gaba daya ba tausayi a harkarsu, Hajiya taban mamaki duk da nasan macece wace kanta yake a waye amma i didn't expect that from her."

  Tace "na sani sai dai in muka duba abin ta wata fuska zamuga mu taimakonmu sukai, da farko dabadan sun yaudaremu ba da bamu san wacce zamu aurana Hassan ba, in muka duba saukin da muka dade muna nema akansa yanzu gashi abinda likitoci da dama suka kasa yi yarinyarnan a ciki wata daya ta mana, duk da bawai ya warke ne ba sai dai canjin daya samu nada yawa."

 Abba yai shiru yana kallanta zuciyarshi na dana sanin abinda ya aikata mata, yace "yanzu me kike tunani?"
Tace "just live them."
Yace "kina nufin duk abinda sukai ya tashi a banza?"
Tace "ko daya sai dai ina tunanin mu barma Allah, yanda suka cutar da Jalila da mahaifiyarta Allah bazai barsu ba, mu murikesu, gatan da basu samu ba mu basu, mu jira hukunci Allah akan su."

  Abba yai shiru sai kallanta kawai da yakeyi, tace "kallan fa? Shawarar batai ba?"
Yace "akoda yaushe in kina abu sai na dinga yin wani tunani, sau dayawa akance mata basukai maza zurfin tunani ba, sannan sai kaji namiji na ta aibata mace, in naji haka a koda yaushe sai insan Allah yamin baiwar da ba ko wani namiji yama ba, samunki a matsayin matata yana daya daga cikin abubuwan da nake alfahari dasu a rayuwata."

  Kallansa tai sannan tai murmushi tace " Kasan abinda yaban mamaki? Ban taba tunanin Hassan zai sauko kasa ba wlh, kasan kawai nama Jalila zancen ne amma a raina nasan bamai yiwuwa bane?"

  Abba ya kalli yanda taketa farinciki yace "ni kaina nayi mamaki, kinsan rabon da Hassan ya shigo falona kuwa harya zauna ya dade haka?"

 Tace " kasan ya sauko ya gaida baban Jalila ran nan?"

 Abba yai murmushi yace "da alama yanda nai dace da mata haka Hassan yai dace, sai muyi addu'a Allah yaba Sageer mace shima ta gari."

Tace "insha Allah."


Washegari.

Dakin Sageer ta nufa tasa hannu tai knocking.

 Yana kwance akan gado ya taso ya bude mata.

 Kallansa tai cikin kulawa tace "Sageer lafiya? Naga baka fito ba."

 Ya kalleta yace "Ummy...."

  A rikice ta kalleshi tace "menene? Bakajin dadi ne?"

 Yace "a'a kawai dai..."
Tace "na kula ma gaba daya yanzu kadan canza, Sageer menene ke faruwa?"
Yace "kai Ummy wacce canzawa?"

 Tura kofar tai ta shiga dakin, binta yai ciki da sauri yana cewa "Ummy."

 Hannu tasa ta zuge labulen dakin ta zauna akan kujera.

 Ya matso yana cewa "Ummy!!!"
Cikin shagwaba ya kirata, ta harareshi tare da hard'e hannayenta tace " In baka fadaminba ba inda zani."

 Dariya ya saka sannan ya zauna a kasa kusa da ita yace "shikenan sai muyi hira."
Tace "Sageer dan Allah meke damunka? Sai yanzu na fahimta sam da yake banda nutsuwa ban kula da canzawar dakai ba."

 Yace "Ummy wlh ba komai, muje na tayaki aikin kitchen kafin sirikarki ta sauko."

 Kallansa tai sannan tai murmushi ta mike ta fito, yabiyo ta.

 Dakin Ameera ta kalla tace "bari in nakai musu breakfast sai mu gaisa."

 Shima dakin ya kalla sannan ya matso yace "Ummy me kukai da Abba akan su?"
Tace "Goggonta zata zauna anan kamar yanda Hassan yace, su kuma su suka sani."

 Sageer yai murmushi zaiyi magana ya hangota a kitchen.
 Tsayawa yai yana kallanta, Jalila ta juyo jin motsin mutane, kallan Ummy tai sannan ta matso fuskarta dauke da fara'a tace "Ummy ina kwana?"

Ummu ta kalleta cikin jin dadi tace "Jalila kin tashi lafiya?"
Tace "lafiya kalau Ummy."
Sannan tadan kalli Sageer a hankali tace "Ina kwana?"
Sageer yace "kin tashi lafiya?ya yaya?"
Lafiya kawai tace.
 Ummy tace "Jalila naji dadin ganinki haka kamar ba abinda ya faru."

 Jalila tai kasa dakai tana murmushi, a zahiri itakam ganin Goggonta yasa takejin kamar duk wani abu daga baya kenan, sannan ta rasa me yasa takejinta haka.

 Sageer ya zauna a falo su kuma suka nufi kitchen, suna aiki suna yar hira, Ummy tace "Hassan abin nashi na tashi sosai yanzu?"
Jalila tace "ba sosai ba sai yai kwana biyu zuwa uku lafiya."

 Ummy tai murmushin jin dadi ta kalli kular data suko dashi ta bude, kallan Jalila tai tace "jiya bakuci abinci bane?"
 Tace "yayane baici ba, inaji bacci ne ya daukeshi."

 Ummy tace "ba matsala tunda ya fara bude zuciyarsa nasan komai zai daidaita a hankali."

 Jalila ta kalleta cikin rashin fahimta tace "bude zuciya?"

 Ummy ta dauko kukar tana cewa " eh mana akanki ba."

Jalila tace "ni?" Ta fada cikin mamaki da alamar tambaya, Ummy bata tanka mata ba ta cigaba da aiki.
 Jalila tai shiru tana nazarin abinda Ummy ke nufi, ba dai so take tace wai Hassan ya fara santa ba? Tab shi wannan har akwai zuciyar soyayya ma a ransa?lalai Ummy.

  Haka suka gama ta kaima Goggo ya zauna suka gaisa da dan hira, Ummy na shigowa ta mike ta dawo kitchen ta dau nasu.

 Sageer na zaune kan dinning shi kadai yana cin abinci, waya yakeyi da alama da Ameera yake waya dan yana cewa "In bazata biyoki ba sai ki dawo kindai san ran monday zaku koma makaranta."

 Jalila ta wuce ta hau sama, a hankali tasa hannu tadan murda kofar, tadan fara kokarin budewa a hankali.

 Jitai an jawo kofar da karfi har ya hado da ita data rike kofar, ta taho ciki da dan gudu ga tire a hannunta.

 Da sauri ya rike tiren yana kallanta.
Daidaita tsayuwarta tai sannan tace "yaya irin wannan fizgar kofar fa?"

 Yace "ke kuma irin wannan bude kofar fa? Kamar wata munafuka? Ko laifi kikai?"yai maganar da alamar tuhuma.

 Da sauri ta ajiye abin hannunta tace "laifin me? Ni wlh ba laifin danai."

 Baisan yanzu ma bakinsa yadan motsa ba yace " kin tabbatar?" Ya fada tare da matsowa.

 Da sauri tai baya tana cewa "ni wlh banyi komai ba, kawai dan na murdo kofa a hankali."

  Yadan kalli idanunta yace "why do i have this kind of feeling?"

 Tace "ikon Allah, dama dai fada kakesan yi, daga shigowata?"

  Ya zauna akan gado yana cewa " ramawa nai."
Tace "me nai da zaka rama?"

 Bai tanka taba ya dau littafinsa tare da gyara zama, ido ta kuramai a ranta tace "so? Hahh lalai Ummy wannan mutumin nan?"

  Bai kalleta ba yace "kallan fa?"

 Ta dauke idanta da sauri tace "sauko kaci abinci."

Yace "banaci."
Tace "bakaci jiya da daddare fa?"
Yace "shiyasa ai bazanci yanzun ba."
Tace "ban gane ba???"
Ya shareta.

 Ta matso tana neman amsar littafinta, wani kallo ya mata yace "littafin kike san amsa ko rikeni kike sanyi?"

 Da sauri ta matsa baya tace "rike ka kamar ya?"

Yace "kamar yanda kika saba."

 Mamaki ne ya kamata tace "kaima ai kana rike ni."
Wai meke damun mutan nan? Jiya da daddare kamar bashi ba.

 Kallanta yai kamar bazai yi magana ba sai jitai yace "inma na rikeki ai ke matatace."

 Mamaki me ya kamata ta saki baki tana kallan ikon Allah, shikuwa kamar baiyi maganar ba ya cigaba da karatunsa.

 Tace "dan Allah ka sauko kaci abinci."
Yace "Allah bazan ci ba."
Tace "bangane hakan ba."

Mikewa ma taga yayi ya ajiye littafib ya nufi toilet, mamaki ne ya kamata ta bishi da kallo.
Haryaje zai shiga toilet sai taji yace "inkin gama ki shirya muje a siyoma Goggo kayan dakinta da abin bukata." Ya shiga ciki yana cewa jiya dana jira kizo muci ai shareni kikai kema kiji ko da dadi......

Duk da taji dadin abinda yace sai dai wulakancin daya mata yasa tama rasa abinyi.

  Da kyar tasha ruwan tea, duk kuwa da tanajin yunwa amma takaici ya hanata, wai Allah bazanci ba, kalmar nan ta bata haushi.

  Tana nan a zaune ya fito daga wanka daure da towel, da sauri ta juya baya.

Ko kallan inda take baiyi ba ya fara shiryawa.

  Yana gamawa ya dau key yace "ina jiranki a mota."yai waje.

 Da kallo ta bishi tai tunanin jiya bayan ya warke, kamar ba shiba yana mata magana a hankali, to yanzu me ya sameshi kuma? Ramawa? Me tamai?

 Haka ta mike tai wanka duk ranta ba dadi, ta fito tana kokarin sa bra a saman towel din jikinta ya turo kofar.

  Idanunsa ne ya sauka a kanta, zaro ido tai tana kallansa, da sauri tasa hannu ta rufe kirjinta.

 Ganinsa tai ha fara matsowa inda take, idanu ta runtse tana tsoron abinda zai biyo baya, sai dayazo daf da ita har tana jiyo numfashinsa yasa hannu cikin wardrobe ya dauko abu, kallanta yai yace "Wallet."
 Ya fada tare da nuna mata wallet din, ya juya ya futa.

 Wani nanauyan numfashi ta saki........


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*47*


  Hankalinsa ya kasa kwanciya, fitowa yai daga motar tare da dan matsowa kadan da kofar shiga yadan leka ciki kadan.

 Security din dake gun ne ya kalleshi yace “Yallabai shiga zakai?”
Hade rai yai ya juya jikin motarsa, hannayensa ya hada yana dan hadasu da waresu, kafin ya koma cikin mota ya dauko wayarsa.
 Mintinsu sha biyar kenan da shiga, me sukeyi haryanzu? Ko alert bai gani ba bare yasa ran sun biya.

 Wayarsa ya dauko ya danna number Ameera.
Sukuwa suna ciki Jalila kome Ameera ta dauko indai taga kudi sai ta maidashi, Ameera ta tsaya tace “to nidai bansan me kikeso mu siya ba, duk abinda na dauko sai ki maida.” Ta karasa maganar tana kallan kwandon nasu da bakomai a ciki sai atamfa kwaya daya.

 Kiran Hassan ne yasa ta kalli Jalila tace “Yaya!”

 Jalila ta kalleta bayan ta amsa kiran, Ameera tace “Yaya....”
Yace “me kukeyi haryanzu? Badai shirme kuka tsaya yi ba?”

 Tace “a’a Yaya, ni narasa me zamu siya ne, duk abinda na dauko sai Yaya Jalila tace wai yayi tsada sai ta maida.”

 Hassan ya kashe wayarsa baijira ya gama jin abinda zatace ba.

 Tahowa yai ya shiga ciki, security din ya bishi da kallo yana yan kunkuni, inkasan shigowa zakai gulmar ta menene? Tun dazu ka tsaya kamar mai jira.

 Hassan na shiga ya sake kiran Ameera ya tambayeta inda suke, ta sanar dashi.
 Yana isowa ya bugama Jalila kallan harara sannan ya kalli Ameera yace “ina kayan da kika zaba?” Nan ta shiga daukowa tana sawa a cart din, mamaki na kara ratsata, bata dade a gidansu Aina’u ba yaushe har yayanta ya koma haka?

  Jalila na tsaye tana kallansu sai zuba kaya sukeyi a cart din har sai da ya cika sannan suka nufi gun biyan kudi.

  Tana can gefe suka biya kudin sannan ya kalleta ya nuna mata ledoji, matsowa tai ta dau leda biyu manya itama Ameera tadau biyu suka nufi kofar fita.

  Yana kallanta da yanda ledojin suka mata nauyi dan kamar ma janta sukeyi, kallanta ya sakeyi sannan ya kalli ledar ji yake kamar yaje ya amsa sai dai inaaa bayaji zai iya yin hakan, balle agaban Ameera.

  Taje kusa da motar bata kula da saman interlocks din daya dago ba, jitai tayi tintibe da sauri yasa hannu ya riko cikinta.

  Ajiyar zuciya tai dan ta tsorata ga kayan da suka kara rinjayarta.

  Juyowa tai ta kalleshi kawai sai tai dariya tace “yaya  wlh na tsorata, har na hango kaina ya bugu da jikin motar.”

 Jawota yai ta mike daidai sannan ya kalli gun datai tuntube, lalai mutanen nan basuda hankali tayaya bazasu gyara gun ba? Fuska a daure ya kalleta yace “meyasa bakya kallan kasa in kina tafiya? Da bana kusa ko da banyi hanzarin kamoki ba me kike tunanin zai faru?”

 Ta kalleshi jikinta yai sanyi tace “wlh ban......”

 Gani tai ya wuceta rai a bace, ledar hannunta ya amsa ya sa a boot din motar sannan ya bude ciki ya shiga.

 Ameera ta ajiye nata itama ta shiga baya sum sum.
Jalila ma jiki a sanyaye ta shiga, to laifinta ne? Itama ai da saninta bazata bari ta fadi haka ba.

 Harya tada motar ya fito daga ciki ya nufi gun secuydin.
Kallansa yai fuskar nan a daure, security din ya kalleshi yace “Yallabai da wani abun ne?”

  Shiru yai yana tunani, menene damuwarka da har kazo nan zakai fada akan su gyara gun da yarinyarcan zata fadi? Menene damuwarka Hassan.

 Bai tanka mai ba ya juya, security din ya bishi da kallo yace “yau ni kuma ina na samo wannan?”

 Hassan ya bude motar ya shiga dya rufota da karfi yaja motar da gudu suka bar gun.

 Shiru motar tai ba wanda yake magana, sai sanyin Ac dake ratsa cikin motar.

 Jalila ta kalleshi taga ba alamar wargi, tai gum.

 Can ta sake kallansa nan ma taga ba alama tai gum.

 Sunyi nisa sosai sai tace “Yaya kashanye yoghurt dinka?”

  Bai tanka mata ba sai dai yasa hannu ya miko mata ledar, ba haka taso ba, ta daure ta sake cewa “kasan yaya sai da muka shiga cikin store din nan naji cikina yana wani kara?”

 Nan ma baiko tanka mata ba, ta amshi ledar ta ajiye a kusa da ita sannan ta kalli Ameera datai shiru tana danna wayarta.

 Itama jan bakinta tai bata sake cewa komai ba.

 Suna isa gida Ameera ta fito da sauri saboda tsoron kar reshe ya juye da ita.

 Jalila ta zauna ba alamar fita, kallanta yai yace “me kikeyi?”

 Tace “Yaya kaima kasan ba kaifina bane, tuntube nai sannan wlh bawai kula bane banayi”

 Yace “kinji nace wani abun?”
Tace “bakace ba amma......”
Ya katseta “sauka inkuma bazaki shiga ciki ba sai ki kulle motar inkin gama zaman.”

 Kallansa tai ranta yadan sosu ta fito daga ciki ta duba boot ta dauko ragowar ledojin sannan tai ciki.

 Kallanta yai harta shiga ciki sannan ya dan saki huci yace “ ba saboda ke raina ya baci ba saboda kaina ne.”

  Idanunsa yadan rufe da hannunsa kafin ya fito daga motar.

  Ummy najin motsin shigowarsu ta fito daga dakinta tana cewa “Jalila kun dawo?”

 Ameera ce ta taho da gudu ta rungumeta, Ummy tai dariya tace “Auta saukar yaushe?”

 Ameera ta kalli Jalila tace “tare muke dasu Yaya Jalilah.”

 Ummy ta kalli Jalila wacce ta karaso tana cewa “da ita muka je ai Ummy.”

 Ameera ta kalli Ummy cikin zumudi tace “Ummy kinsan waye ya kaimu?”
Ummy ta kalleta, Ameera ta kara matsowa tace “Ummy karkiyi mamaki.........”

 “Hassan kun dawo?” Abinda Ummy tace ne yasa Ameera saurin boyewa abayanta, Hassan yace “eh Ummy.”
sannan yace “Abba fa?”
Ta nunamai falo tana kallan Jalila wacce tana tsaye yazo ya wuce kamar baiganta ba.

 Hassan ya wuce falo, Ameera ta kalli Ummy da sauri tace “Ummy kingani? Ummy yaya ne yake magana haka.”

 Ummy ta kalleta tace “naji hajiyar magana, akwai baki a dakinki kije ku gaisa.”

 Ameera tace “baki? Su waye?”

  Ummy bata tanka mata ba ta matso kusa da Jalila tace “Jalila wani abun ya faru ne?”

Jalila tai yake tace “bakomai Ummy, Kinga kayan da Yaya ya sai mata.”

 Ummy ta kalli ledar tace “basai kin ciro ba, angode Allah ya saka masa da alkairi.”

 Jalila tace “Ameen.”

 Muryar Abba sukaji yana kiran Ummy.
Ummy ta falo, Jalila kuma ta dau leda tai dakin Ameera.

 Hassan na zaune kusa da Abba ta shigo, ta zauna sannan ta kallesu tace “d’a da uba ne suke hirar yaushe gamo?”

 Abba yai murmushi yace “nikaina ina jiran wannan lokaci, lokacin da Hassan zai zauna dani muyi hirar duniya.”

 Hassan bai tanka musu ba, Ummy tace “wani abun ya faru ne?”
Yace “a’a kawai dai sirikarsa ce ta nemi mu barta ta tafi tana kunyar zama gida daya da sirikinta da mu.”

 Ummy tace “hakane munyi laifi da bamuyi wannan tunanin ba, sannan bamu tambayeta ra’ayinta ba.”

 Hassan ya kalli Ummy yace “Ummy ita so take takoma kauye nikuma ina ganin hakan ba solution bane.”

 Tace “mekake tunani?”
Yace “gwara a nemarmata gida anan ta zauna karami, can yayi nisa.”

  Murmushi tai ta kalli Abba tace “gaskiya kam yama Jalila nisa wanda zai sata damuwa.”

 Kare tsuke fuska yai yace “Ummy me kike.....”
Katseshi tai tace “ ni ba da komai nake nufi ba.”
Abba ya kalleta yace “wani abun kike tunani?”

Tace “a’a shawararce naga tayi, me zai hana a gidan da ka siya kwananan wanda ke tarauni a maidata can? Naga gidan karami ne sannan ga yarinya ma mai kula da ita.”

  Abba ya jinjina kai yace “hakan ma shawara ce, kinga Allah ne yasa bamu sa haya ba dan har an fara tambaya, Hassan sai ka dau Jalila kunduba gidan sai a sai abunda ya kamata.”

 Yace “to.”

 Bai jira wani abu ba ya mike, yanasan yama Abba godiya sai dai bakinsa bazai iya furatawa ba, harya kai kofa ya juyo yace “Ummy na hau sama.”
Tace “to Hassan.”

  Ya juya ya fita, Ummy ta kalli Abba tace “ Ya kagani?”

 Murmushi yai yace “ tunda na dawo kullum Hassan sai ya bani mamaki, lalai dolene muje muyina doctor godiya ba shakka shawararsa itace babban magani a tattare dashi.”

 Ummy ta sake yin murmushi.....

Jalila kuwa tana shiga daki inda Goggo take ta hau nuna mata kaya, Ameera kam tana gefe tana mamaki, kenan mahaifiyarta ce ta asibitin nan? Me yasa a lokacin bata nuna mata itace mahaifiyarta ba? Goggo ta kalli Jalila tace “Jalila garin yaya kika barshi ya kwaso kaya haka? Kudi fa aka sa aka siya.”

Ameera tai dariya tace “Goggo ashe ke tayo, shiyasa takasa bari na dau kaya ko daya wai tsada, sai da yaya yazo.”

 Goggo ta kalli Ameera tace “ke kuwa yar nan ina zan kai kayan nan?”

Jalila ta kalli Goggo wani abu ya tsirga mata na tausayi, tunda Goggo take bata saka kaya masu tsada haka ba, ba ta tana samun kaya kwatan yawan wannan ba, gaba daya kayanta.......”
Idanunta ne suka ciciko ta kalli Goggo tace “yaya ya fadamin abinda kikace.”

Tace “ya sanar dake?”

Jalila ta daga kai, Goggo ta riko hannunta, Ameera tai saurin fitowa daga dakin.

 Goggo ta kalli Jalila tace “Jalila kiyi hakuri, nasan burinki ma shirme nasan ganin mun zauna tare bayan kinyi aure sai dai ko a da can jinki nakeyi dan bazan iya zama da sirikina ba.”

 Jalila ta daga kai alamar ta fahimta dan batasan tai kuka.
Goggo ta kalleta tace “shiyasa a koda yaushe ake cewa Allah ba azallumin bawansa bane, Jalila ban taba tunanin zakiyi aure cikin gata irin wannan ba, gaba daya mutanen gidan nan zuri’ace ta albarka, dolene mu gode ma Allah akan baiwar daya miki ta samun dangin miji irin wannan.”

 Jalila ta kalleta idanunta suka zubo da kwalla, Goggo tai murmushi tace “nikam wannan yaran kanin mijinki.....”

 Da sauri Jalila tace “oh Ya Sageer? Oh Goggo kinsanshi ne?”

Kallanta tai taga ba wani alama ta wani abun tace “a’a na dai ganshi a asibiti.”
Jalila tace “oh haka ne.”

 Sundanyi hira kafin ta mike ta fito.

 Tunda ta shiga daki taganshi a kwance ta fito ya dawo falo ta zauna, yunwa ce ta sata shiga dakin a hankali ta dauko tiren abinci ta fito falo taci ta zauna tana danne danne a waya, daga baya ma ta sauko kasa sukai girki ta koma gun Goggo sukai hira da Ameera.

Abincin ranarsu ma data kai taga yana kwance ta diba ta fito falo taci ta koma kasa sai da suka gama abincin dare ita da Ameera sannan ta dauko nasu ta hawo sama.

  Yanzu kam a kasa ta ganshi kan sallaya yana karatu, gefe ta koma ta zauna tana sauraran kartun nashi, tana lumshe ido saboda dadi, tana bala’in sha’awar taga tana rera karatunn qur’ani haka.

  Hassan na nan zaune har aka kira isha’i sannan yai sallah, itama tai.

  Sai binshi take da kallo tanasan tamai magana amma ba fuska.

 Mikewa tai ta zubo mai abinci tace “Yaya ka sauko kaci abinci.”

 Kallanta yai yace “ban dade dacin na rana ba.”

 Ta mike daga zaman datai a kasa ta matso kusa dashi jikin gado tace “Yaya dan Allah menene? In laifi na maka dan Allah kayi hakuri.”

 Idanunya kura mata, a ransa yace “me kika min? Haushin kaina nakeji da duk abinda zanyi tun dazu sai naji kina raina, haushin kaina nakeji nasan na ganki kusa dani, haushin kaina nakeji na rashin sanin abinda ke damuna a kanki.”

 Jalila ta kalli yanda ya kafe ta da ido kana gani kasan tunani yakeyi, tace “Yaya?”

 Littafinsa ya dauka baice mata komai ba.

 Tsayawa tai shiru kafin ta zauna taci abincin nasa data zuba, kadan ta iyaci dan ya mata yawa.

 Har dare Hassan bai kula ta ba, itama haushi yasa ta dauke kai daga kansa tai kwanciyarta, kankace me bacci yayi gaba da ita.

  Kwanciya yai ta saitinta yanda yana hangota daga kan gado, ya kura mata ido, what are u to me?

  Gani yai tayi juyi ta juya mai baya.
Mikewa na ga yayi ya dau pillow dinsa ya kwanta akan kujera yanda zai ganta dan kusa da kujerar take shimfida.

 Ajiyar zuciya yai ya kalli bargon data shimfida yace “wannan bazai sata ciwon baya ba? Kullum kwana a kasa? Gata ba jiki ba?”

(Nikuwa nace waye ya sata🤨)

 Ya dade a haka yana kallanta har bacci ya daukeshi.

  Yauma Alhamdulila bai farka da ciwo ba, wajen asuba ya farka, da sauri ya mike yana mamakin kansa anan ya kwana? Ahh wai Hassan hankalinka daya kuwa?

Alwala yai sannan yazo kusa da ita, ya saba sa kafa ya tasheta yau sai gani nai ya sunkuyo yasa hannu yadan bugi kafadarta tare da cewa “Jalila?”

 Idanu ta bude cikin bacci ta kalleshi, mikewa yai.

 Ta mike itama tai alwala...........

  Tunda ta tashi take jinta ba dadi, ba sabon abu bane tasan period dinta ne ya kusa, ita kuma gashi duk sanda zatai al’ada sai tasha azaba na ciwon mara, a gida Goggo sai ta sata tasha dauri, ko ta siyo panadol......


***********

Inna ce tasa aka kira mata dady, yana zama mumy ta shigo taja ta zauna.
Inna tace “Fatima meye hakan? Magana zamuyi.”

Mumy tace “kome zakuyi kuyi agabana, sannan nima magana nazo fadamiki.”

Inna ta kalleta tace “maganar me?”
Tace “kiba Abubakar mukamin Chairman na company ke kiyi resigning, dama ai kin dade kina cewa zaki bani ke kuma ki sauka.”

 Inna ta kalleta cikin tashin hankali sannan ta kalli Dady wanda shima yai alamar wai mamaki, tace “Abakar kai ka zigata?”

Da sauri Dady ya kalleta yace “Menene hakan? Ce miki nai inasan shugabanci na company din? Meyasa kike neman sa Inna taga kamar nine nake saki abu? Banasan irin wannan abun.”

Mumy ta kalleshi tace “Dadyn Yasmeen.”
Ya hade rai yace “Taya zaki yanke hukunci ba tare da kin sanar dani ba?”

Tace “gani nai....”

Inna ta kalleshi lalai yaran nan me? Ce miki akai inasan shugabanci?????

Tai wani murmushin takaici.......

#Oneluv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*48*


  Ummy ce ta kalli Jalila tace "Jalila lafiya? Naga tau kamar bakyajin dadi?"
Tace "lafiya ta kalau Ummy."
Ummu tace "da ina tunanin ko in dau Goggo da Ameera muje dakanmu mu siyo kayan gidan muje a saka, kamar zaifi dan nasan halin Hassan bazai shiga  gun kayan ba, kinga kuma ke kadai abin bazai yiwu ba, sai da babba."

 Jalila tace "to Ummy."
Ummy tace "ko kinfiso kije da kanki? Ko mu tafi tare?"

Da sauri tace "a'a wlh Ummy hakan yafi, ni me na sani a wannan harkar?"

 Ummy tai murmushi ita kuma bataso subar Hassan shikadai dan Abba ya fita duba wani aiki.
 Jalila tace "me za'a dafa da rana?"
Ummy tace "komai ma duk abinda miki."

Jalila tai murmushi sannan tace "to Ummy nagode Allah ya saka da alkairi."

Ummy ta kalleta cikin kulawa tace "Hassan fa?"
Jalila tace "yana daki."
Ummy tace "nasan yana daki ai haryanzu bai sauko ba?"

 Jalila tace "Ummy kema harkin gane? Ni na rasa me namai."
Ummy ta guntse dariyar dake neman zuwa mata tace " da alama dai kin mai babban laifi tunda har nima na gane."
 Jalila tai ajiyar zuciya tace "na kasa gane me namai, kuma shima ya ki fadamin."

  Ameera da ta fito tasa dariya tace " ba kunya?"
Jalila ta kalleta sannan tai saurin mikewa, sai yanzu ta fahimci bai dace ba.
Ummy tasa hannu ta rikota ta makama Ameera harara tace "to uwar sa ido, menene damuwarki? Ni bana sirikanta da ita 'ya ta ce."

Ameera ta kara yin dariya tace "hmm nayi shiru ai."

 Ummy ta kalleta tace "kicema Goggo ta shirya zamuje wani guri."

 Ameera tace "ina zaku bani?"
"Ko shirya dake zamuje kema, in muka sai kayan farko sai ke da Lantana da Goggo akaiku gidan ni da Sageer sai mu karasa siyan abinda ya kamata."

 Ameera tace to, tai ciki da sauri.

Haka suka shirya Jalila na kusa da Goggonta, Goggo sai tambayarta take wai ina zasu? Itakam Jalila cewa kawai take nima ban sani ba Goggo.

 Haka suka fito Sageer ya daukesu a mota, Jalila ta baishi da kallo duk ya canza da dai ba haka tasan Uncle ba, mutum ne faran faran dasan tsokana, yanzu kuwa ya rage sannan duk yadan rame.

 Tana tsaye har motar tasu ta bar gidan sannan ta dawo ciki.

 A falon kasa tadan kwanta dan mararta ciwo take mata daurewa kawai takeyi, mikewa tai can ta hau sama dan tana san shiga toilet.

  Hannu tasa ta bude kofar dakin dakin ta shiga, yana zaune a kasa yana cin abinci da alama baima dade da tashi ba.
Tana shigowa ya kalleta, itama kallansa tai ta tsaya sannan tace "Yaya ka tashi?"

 "Umm, dazu." Ya fada idansa na kanta, ta dan tsaya kafin tace "hmm su Ummy sun fita tare da su Goggo."

 Yace "okay."
Tadanyi shiru kadan sannan tace " duk tare suka fita."
Yace "nagane, kina nufin daga ni sai ke kenan ko?"

 Tace "hmm can gidan zasu."
Yace "duk na fahimta."

 Juyawa tai ta nufi toilet kafin ta kara juyowa tace "Yaya!"
Ya kalleta tace "abincin bai huce ba?"
Yace "me kikesan ji? Da alama wadannan maganganun naki akwai abinda kike san ji."

 Tace "bakomai." Ta shige toilet.

 Da kallo ya bita ya dade kafin yacigaba da cin abincin.

 Tana fitowa yana gama cin abincinsa, tadan tsaya a jikin kofar saboda ciwon da mararta yakeyi gashi daga bayanta yake tahowa.

 Da kyar ta taka ta zauna akan kujera tadan tukunkune.

  Mikewa yai daga kasa ya juyo ya kalleta, bai kawo komai a ransa ba ya dauka dai kwanciyar tai ko toilet din data shiga ne ya sa ta.

 Komawa yai ya zauna ya dau littafi, dan nishin datai kadan ne yasa ya juyo da sauri ya kalleta.

 Yace "Jalila!"

 Dagowa tai ta kalleshi a hankali tace "naam."

 Ganin haka yasa ya sauko da sauri yazo kusa da ita inda take a kwance, kusa da inda kanta yake ya zauna sannan yasa hannu ya dagota.
 Kallanta yai itama ta kalleshi yace "menene?"

Tace "bakomai yaya..."
Yace "menene kikeyi to hakan?"

 Tace "me nayi?"

 Idanu ya kara kura mata sannan yace "menene? Karkisa na sake tambayarki."

 Ta kalleshi tace "marata"
Yace "ciwo?"

Ta daga kai alamar eh.

 Yace "kinayi ne ko yau ne kika fara?"

 Tace "inayi dama."

  Shiru yai yana kallanta yace " menstrual pain?"


Kallansa tai sannan ta saukar da idanta kasa.
Yace "ko muje asibiti?"
Tace "a'a yaya zai daina zuwa dare."

  Idanunta tadan runtse dan abin karuwa yake yi.

  Sa hannu yai ya dagota ya kawota jikin gado yace "kwanta."
Kallansa tai sannan ta kwanta.

  Zama yai kusa da ita yana kallanta, ita kuma idanuwanta a runtse suke tasa hannunta kan kasan cikinta.

  Wayarsa ya dauko ya shiga google ya rubuta how to relieve menstrual pain.

 Nan ya shiga dubawa, kallanta yai sa hannu ya gyara mata kwanciyarta zuwa rubda ciki.
 Juyowa tai ta kalleshi yace "menene?"

 Kai ya girgiza alamar ba komai sannan ta gyara kwanciyarta.

  Shiru yai yana tunani, massage lower back and abdomen? Ta ina zai iya?
Mikewa yai tsaye da sauri ya koma kan kujera ya zauna dan jin yanda zuciyarsa ke bugawa da sauri.

  Jalila kam abin ne ya kara motsawa juyawa tai ta kara dukunkunewa tana dan nishi kadan.

 Kallanta yakeyi sai dai hankalinsa duk ya tashi.
Ya mike ya taso kusa da ita ya gyara mata kwanciyarta zuwa na dazu, idanunta ne suka ciciko ta kalleshi tace "yaya hakan bayamin dadi."

  Yace "na sani daurewa zakiyi."
Tace to sannan ta gyara kanta tana runtse ido.

  Jitai hannunsa akan kasan bayanta inda yake mata ciwo, kallansa tai, ya kalleta shima fuska a hade yace " ki kwanta ba wani abin zan miki ba."

 Shiru tai ta kwanta, janye rigarta yai yana neman kaita wajen kirjinta, da sauri tasa hannu ta rike sannan ta kalleshi.

 Kallanta yai idanunsa na kanta ya sa hannu ya zare mata hannunta, shiru tai tana kallansa.

  Sai dayakai rigar saman cikinta sannan ya tattareta a gun.

 Hannu ya saka a bayanta yana mata tausa da hannayensa suka biyun.

 Idanunta ta rufe gaba daya jikinta yai sanye, Hassan kam tausa yake mata sai dai daurewa kawai yakeyi.

 Kallanta yai yace " kinajin sauki? Naga haka suka rubuta haka akeyi."
Ta daga kai idanunta a rufe dan bazata iya kallansa ba.

  Hassan ya cigaba da yi mata, tun tanajin abin har bacci yai gaba da ita.

  Ganin alamar bacci takeyi yasa ya kalleta, kusa da ita ya matso ya sa hannu akan gefen fuskarta yadan shafa kadan, meyasa kike sani yin abubuwan da ban taba tunani ba?

  Ganin motsin idanunta sun canza da alama nauyin baccin nata ya fara raguwa, komawa yai ya sa hannu ya cigaba da yimata.
Sai can ya tsaya ya kalleta tana bacci hankalinta a kwance, murmushi yai wanda shikansa bai sani ba.

 Sannan ya mike ya cire kayansa ya daura towel ya shiga wanka.

  Bai dade ba dan yana tunanin karta tashi, a hankali ya bude kofar ya fito ya zo zaisa kaya.

 Wayarta ce tai kara da sauri ya matso ya dauka, number Ummy ce ya daga a hankali yace "Ummy."

 Cikin mamaki tace "Hassan?"
Sageer dake kusa da ita ya kalleta, Ummy tace "Hassan kaine? Ina Jalilan?"

 Yace "bacci takeyi bata danjin dadi ne."

 Da sauri tace "lafiya? Me ya sameta?"
Yace "ba wani abun bane Ummy sako ne?"

Samun kanta tai da wani murmushi tace "a'a bakomai kace kartai abinci ta kwanta ta huta."
Yace to ya kashe wayar.

 Da kallo yabi wayar sannan ya kalleta, me nakeyi hakan?

Ajiye wayar yai ya zo ya saka doguwar riga ta jallabiya sannan ya zauna akan kujera ga dau littafi wanda ya kasa karanta ko layi daya.
 Sai kallanta da yakeyi, duk motsin datai a kansa.

 Can ya daure ya koma ya maida kansa kan littafin, motsinta yaji, ya mike ya zauna a bayanta ya dan fara yi mata tausa a gun.

 A hankali ta bude idanunta kallansa tai, yace "kin tashi?"

  Da sauri ta kalleshi tace "yaya, bansan nayi bacci ba wlh yahkuri."

 Mikewa yai tsaye yace "ya jikin?"
Tace da sauki sosai, yace "ki tashi ki sake wanka amma yanzu kiyi da ruwa mai zafi, sannan kisha ruwan tea black ne."

 Tace "to."

 Juyawa yai da sauri ta riko rigar jallabiyarsa.

 Juyowa yai ya kalleta, yace "menene?"

Tace "yaya nagode, sannan kayi hakuri."

  Shiru yai yana kallanta, yace "kin gode dame?"
Tace "taimakon dakamin."
Yace "karkiyi tunanin wani dalili ne yasa na taimakeki, I really hate naga wani bashida lafiya, ko wanene na gani cikin wani hali ko ba ke bace zan taimaka mai."

  Kallansa tai jiki a sayaye sannan ta sakar mai rigarsa, ai dama batace dan ita special bace, me yasa wai yaya baya magana da sanyi?

 Ta dan saukar da idanunta tace "nasani, duk da hakan nagode, sannan kayi hakuri da laifin da bansani ba."

 Ya sake kallanta yace "nagane tashi kiyi abinda nace, kina mace amma bakisan menene zai taimaki lafiyarki ba, na rasa me yasa gaba daya baki damu da kanki ba."

 Jalila ta kalleshi tadan canza fuska zuwa shagwaba tace "to ni ya zanyi?"
Yace "ba ni zaki tambaya ba."
Ya juya ya zauna.

 Mikewa tai tana mamakin yanda taji sauki, dan ta saba in har ta fara da safe to fa sai dare, in kuma da daddare ta fara sai safiya.

 Dan ma tayi sa'a tanajin yanayin nan ta sanar ma Ameera ita kuma ta bata pads, ta boye a cikin basket na laundry din dake cikin toilet din.

 Ruwa mai zafi tasa ta gasa jikinta ji tai jikinta ya sake warewa ta tsaya a toilet din, sanye da toilet, taya zata fita? Shiyasa fa daga ta tashi takeyin wanka in kuma batai da wuri ba sai ta bari ya fita takeyi, tunowa tai jiya daya ganta tana sa bra.

  Shiru tai tana tunani, ta kalli kayan data cire wanda tasa a ciki basket din laundry.

  Ganin ba yanda zatai ne yasa tadan bude kofar kadan ta leko kanta.

 Shikuma yana jin alamun bude kofarta ya kalli gun.
Suna hada ido ta komar da kanta.

 Mikewa yai dan ya fahimceta.

 Agoggo ya kalla, yaga azahar tayi ya mike ya tada sallah.

Ita kuma tana komawa ciki ta jingina da kofar toilet din, massage din daya mata dazu ta tuno, da sauri ta girgiza kai.

 Sake lekowa tai taga yana sallah, a hankali ta fito tazo jikin wardrobe ta bude ta zura hijab.

  A cikin hijab din tasa bra sannan ta zura skirt ta sa riga sannan ta cire hijab din ta matso jikin madubi ta  shafa mai sannan ta fesa body spray da turare.

  Kallansa tai yana zaune akan sallaya ta lalaba tai waje.
 Tana sauka ta hada tea kamar yanda ya sata tasha, sannan ta koma kitchen ta bude fridge ta dauko nama zata sa tafashe.

 Bayan ta fita ne yai tunanin yanzufa sai ta tafi sa abinci ko?
Mikewa yai ya sauko kasa, kitchen ya nufa, ya taka ciki ya shiga.
Raban da Hassan ya shiga cikin kitchen shikansa ya manta, ko magana zaiyi sai dai ya tsaya daga falo, ko kofa.

  Juyowa tai jin motsin shigowa, kallansa tai cikin mamaki tace "yaya!"

 Me zance? Abinda zuciyarsa ta tambayeshi kenan.
Hade rai yai yace "ruwa zaki bani."
Tace "ruwan sama har ya kare?"
Yace "a'a ba sanyi ne."
Cikin mamaki ta mikomai robar ruwa tana cewa ko na kashe fridge din?

 Mikamai ruwan tai yasa hannu zai amsa, kan hannunta hannayensa suka taba, kallansa tai shima ya kalleta.

 A hankali ta zare hannunta ta dan juya.
Ya amshi ruwan kafin yace "me kike? Ke da ba lafiya ba?"
 Tace "abinci zanyi kaga ba kowa a gidan."

Yace "dan ba kowa sai akace mara lafiya yai abinci?"

 Ta juyo tace "ba haka nake nufi ba, kaga sanda zasu dawo ne a gajiye zasu dawo."
Yace "in ance bakya kula da lafiyar ki kice ba haka ba, to Ummy ce tace karkiyi."
Ya juya ya bar kitchen din.

 Da kallo ta bishi, tadan yi ajiyar zuciya tace "oh ni, yanzu ma laifi na sakeyi?"

 Maida namantai cikin fridge din sannan ta fito.
A falo ta sameshi tace "Yaya!"

 Ya kalleta yace " kin warke ko na kaiki asibiti?"

 Tace "Allah na warke har mamaki nakeyi."

Ya juya ya hau sama.

 Shiru tai tare da binsa da kallo.


*******

Ummy kuwa tana kashe waya ta saki wani murmushi, Sageer ya kalleta yace "Ummy wani abun ne?"
Tace "a'a bakomai, kawai dai abin ne kemin dadi, dan na tabbatar yanzu Hassan ya fara san matarsa."

 Sageer ya kalleta wani abu ya ratsomai, ya daure yai murmushi yace "ai Ummy ki daina damuwa na tabbatar Yaya zaiso Jalila yanda bakya zato, tanada halayen da zaija ra'ayinsa."

 Ummy ta jinjina kai cikin jin dadi tace "sosai ma, na yarda dakai Sageer."

A tare sukai murmushi Ummy tace "ya kukai da Goggo dazu?"

 Sageer yace "ai bakiga kukan datake ba nidai har na taho tana kuka akan itakam da munbarta ta koma kauye ina ita ina wannan gida haka?"

Ummy tai murmushi tace "Sageer in na tuno abinda mutanen nan sukayima Jalila da mahaifiyarta sai naji kamar bai kamata mu kyalesu ba."

 Yace "hakane Ummy koni abin na damuwa, bansan haka tai rayuwa ba."
Ummy tace "nikaina, sai dai mu barma Allah komai."

 A ransa yace "bansani ba Jalila, bansan haka kikasha wahala a rayuwa ba, i am really sorry......."


*******

 Suna saukowa Dady ha kalli Mumy yace "mumyn Yasmeen me kikeyi hakan?"

Rungumeshi tai tace "ba sai ka shiga maganar nan ba, wannan shikadai ne hanyar da zaisa Inna tadinga ganin girmanka."

 Dady ya dago ya kalli sama, inna ya gani a tsaye tana kallansu, murmushi ya mata sannan ya kankame Mumy tare da sa kansa a wuyanta.

 Inna ta dunkule hannunta sannan ta juya, snake yanzu kake nunamin abinda ke boye a kasan zuciyarka, u really try na yanda ka boye fuskarka a cikin mask ba wanda ya fahimci abinda ke tattare da ita.

 Tace sai dai ka makaro dan kana tafin hannuna wlh.

(Nace damuwarki😏)

#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯
Written By : *AYUSHER MUHD*
✔️ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_💡)
*49*
Goggo tana zaune tana kara bin gidan da kallo, hawayenta yaki tsayawa, ashe alheri ne a dukulle a tattare da sharrin da aka jefesu dashi.
Ba wani katon gida bane, falo daya ne babba sai 2bedrooms a cikin falon da toilet daya.
Sai tsakar gida kato wanda za'a iya ajiye motoci kananan guda biyu.
Ameera da Lantana dake sa labule ta kalla tama rasa ta ina zata fara, ashe a rayuwa akwai rana irin wannan? Shiyasa mutane ke cewa Allah yasa muci darajar 'ya'yan mu, a da bata fahimtar abinda ake nufi da hakan amma yanzu ta gane dalilin fadan hakan, in kai a rayuwa bakai sa'ar abokin zama ko iyaye ba sai ka nemi sa'a akan 'ya'yanka.
Hawayenta ta share, ko mahaifiyarta da mahaifinta nada rai?
Haka su kai ta aiki, itama tana tayasu, sai yamma su Ummy suka dawo, sun siyo abin kitchen, tv set, toilet, abinci da sauransu, dama zuwan farko aka siyo kujeru, gado da labulaye.
Haka suka taho musu da gashashiyar hanta da juice suka ci suka sha, Ummy ta nunama Goggo kawai komai ta samu tayi. Hamdalla bawai taita kuka ba, hakan yasa ta saki jiki sukaci abinci tanata godiya.
Sai wajen Magrib suka kammala komai, Ummy tace su tafi, sai asa ranar tarewarta.
Goggo tai shiru tana tunani, Ummy ta matso tace "lafiya? Ko kina tunanin zama ne gaba daya?"
Goggo tace " indai hakan zai samu nafisan hakan, dan maganar gaskiya kunyar gidan nakeyi.
Ummy tace "shikenan ai ba wani abu bane, in har hakan yafi kwanta miki a rai, sai dai kamar ba'a gama jan wutar gidan ba, sannan bamu siyo generator ba."
Goggo da sauri tace "hakan ma ya isa, ba sai anja wutar ba dan acan gidan ma bamu samu wannan darajar ba ni har na rasa ta inda zan soma yi muku godiya."
Ummy tace "dan Allah ki bari, yanzu bari mu barku anan, sai nasa yanzu Sageer ya samo katuwar fitila kafin a gyara wutar gidan, kayanki kuma gobe in Jalila zata zo sai na bada a kawo miki."
Goggo ta kamo hannun Ummy cikin wani irin yanayi na farinciki tace " nagode nagode, sai dai dan Allah ina da alfarma daya dazan nema."
Ummu tace "menene?"
Goggo tace "Jalila tana bala'in san makarantar addini ta islamiyya, bansani ba ko da yanda zakuyi ku taimaka mata."
Ummy tace "basu sata a makaranta ba?"
Tace "basu sata ba, karatun da nake dashi kadan shi na koya mata."
Ummy tai shiru tana tunanin wannan muguntar kafin tace "shikenan zan sanar ma mijinta, hafizi ne na karatu dan da wuri ya sauke alqur'ani zan ji shawarar da zai yanke."
Goggo tace "nagode sosai."
Haka suka fito sukabar Goggo da Lantana a gidan, sai da suka sai katuwar fitila suka kai musu sannan suka fito.
Ummy a hanya ta kalli Sageer tace "Sageer akwai iyayenda in basuyi wasa ba alhakin 'ya'yansu shine dalilin da zaisa su shiga wuta."
Sageer yace "Ummy nikam haryanzu kwakwalwata na mamakin irin wannan mahaifin, wanda san kansa yamai yawa da har baya damuwa da halin da 'ya'yansa suke ciki."
Ameera ta kalli Ummy tace "Ummy nikam dan Allah kumin bayani, wai ya akai Goggo ta zama mahaifiyar Jalila, Mumy fa? Nifa gaba daya na rasa meke faruwa tun jiya nakesan yin tambaya."
Ummy tasa yatsa ta ta tura goshita tace "gulmar me kike sanji? Magana daya dai wannan ce mahaifiyarta me kike nemanji bayan wannan?"
Sageer ya sa dariya yace "Ummy in Ameera batai gulma ba ai ba Ameeran bace."Cikin shagwaba tace "Yaya Sageer haka zakace? Harda wani in banyi gulma ba?"
Ya kara sa dariya yace "To yahkuri ba gulma ba."
Ummy ta kalleta tace "ba wani tayi hakuri, ai dama uwar gulma ce da san jin komai."
Ameera ta kara shagwabewa tace "Ummy Allah ni abubuwan da nakeso in tambaya dayawa fa amma tun yanzu kunsa na kasa."
Ummy tace "sai ki hadiye gulmarki inkin samu Abbanki sai ki tambayeshi."
Tace "shikenan ai nasan Abbana bazai min haka ba..."
Haka sukai ta zolayarta suna dariya cikin farinciki har suka isa gida.
********
A can gida kuwa Hassan tunda ya shiga daki ya zauna a bakin gado yai shiru yana tunani, tabbas gaba daya rayuwarsa ta canza a 'yan kwanakin nan, gaba daya yarinyar nan taki barin zuciyarsa.
Abu daya ne ya fara zuwa♀️😘😏😘🤺😘🤺😛😘😘 mai badai santa kake ba?
Da sauri ya girgiza kai yace "so? Ni? Yarinyar nan?"
Kai ya sake girgizawa alamar ba haka ba yace "tausayine."
Tausayi akan me? Ka tabbatar shi kadai ne? Damuwar da kakeyi fa in abu ya sameta?
Tambayar dake tamai yawo a zuciya kenan, shiyasa ma gaba daya daga ta shigo sai yai gamar yana bacci, ko ya dau littafi wai a dole karatu hakeyi ko ya dau wayarsa....
Ita kuwa daga baya ta sauka falon kasa ta zauna.
Bayan tayi sallar isha'i ne Abba ya dawo, ta gaisheshi ya amsa fuska a sake bai dade da dawowa ba su Ummy suka dawo.
Tanajin dawowarsu ta tashi da sauri tazo taryarsu.
Ummy ta kalleta cikin kulawa tace "Jalila jikin ne?"
Tace "na warke Ummy gashi banyi abinci ba."
Tace "nina hana kiyi, bakida lafiya wake ta abinci?"
Sunkuyar da kanta tai, Ummy ta amshi ledar hannun Sageer tace "ga shi kije kuci da Hassan muma munyo namu tsarabar."
Jalila ta amsa tace "angode."
Ta fada sannan ta leka bayan Ummy, Ummy tace "tana can."
Jalila ta sunkuyar da kai tace "tam."
Ameera ta matso tace "ya jikin?"
Jalila tace da sauki.
Ummu tai gaba Ameera ma tabita, ta kalli Sageer tace "Sannu da zuwa."
Kallanta yai yace "ya jiki?"
Tace "na ware ba wani serious bane dama."
Ya kalleta cikin kulawa yace "Sannu Allah ya kara sauki."
Tace Ameen ta juya, da kallo ya bita.
Kowa daki ya shiga da ledarsa dan duk sun gaji.
Jalila ta wuce sama.
Tana shiga ta sameshi a zaune, yana ganinta ya dau littafi wai karatu yake.
A ranta tace ko gajiya bayayi.
Ta matso dan dama ta dauko plate daga kasa, ta bude tace "yaya sauko Ummy ta kawo mana abin dadi."
Kallanta yai yace "menene abin dadin?"
Ta bude kedar ta ciro ledar juice sannan ta ciro foil paper ta bude, kaza ce da kuma daurin kundu wanda yasha hadi na musamman.
Juyowa tai ta kalleshi, kallanta yai sannan ya sauko fuska ya zauna, dandai yunwa yakeji amma da cewa zaiyi bazaici ba.
Kallansa tai batasan yanda zata raba musu ba gashi plate daya ta dauko, kallansa tai shima kallanta yai tace bari na dauko wani plate din.
Ta fada tana kokarin mikewa, hannu yasa akan hannunta data dafa kasa zata tashi, kallansa tai, yace "muci tare."
Tace "naam?"
Yace "me? Dama ba haka kikeso ba?"
Tace "nakeso kamar ya kenan?"
Yace "duba ki gani, kinsan mu biyu ne a dakin nan kika dauko plate daya, yimin bayani meyasa kikai hakan to?"Jalila ta kalleshi kamar zatai magana kawai sai tasa dariya tace "lalai Yaya, yanzu nace zan dauko plate ka hanani sannan kace nice nakeso."
Yace "to ba hakan bane?"
Tace "wlh ba haka bane, ni na....."
Yanda ya mata da fuskarsa ne yasata ta kasa magana alamar bayarda zaiyi da duk abinda ta ce ba.
Bismilla tai tasa hannu tana cewa "shikenan tunda an dakeni an hanani kuka."
Bai tanka mata ba yasa hannunsa, a tare suka fara ci, itadai kunya take, shikam wani irin sanyi yakeji a ransa, yana kallanta yasa hannu cikin plate din, a kann hannunta yasa hannunsa.
Dagowa tai ta kalleshi, kallanta yai sannan ya kalli hannunsa, yace "yanzu nine nasa hannuna ko kece?"
Tai dariya sannan ta kalli hannun nashi tace "to hannun waye a sama?"
Ya kalla yace "nawa ne sai dai me yasa nakeji a jikina kamar dauramin akai?"
Tace "me? Daurama?"
Dariya ta fara yi tana kallansa, samun kansa yak da shagala gun kallanta, wanda har bai san ganin yanda take dariya yasashi sakar murmushi ba.
Tsayawa tai da dariya tace "Yaya! Kasan kayi murmushi yanzu?"
Fuska ya hade tare da zare hannunsa da sauri yace " a ina nai murmushin?"
Tace "wallahi kayi yanzu, baka san kayi ba?"
Juya kansa gefe yai yace "u are mistaken."
Tai shiru tana kallansa kafin tace " mistake nai? Amma na tabbatar naga kayi murmushi."
Yace "are u sure ba hakan kike san gani ba?"
Tace"wannan karan bazan musa ba, dan ina san inga ka yi murmushi kullum fuskarka a daure take."
Ya kalleta tare da daukan cup din juice yasha.
Haka sukaci abinci tare sannan ta mike ta wanke hannu ta sauka kasa dan kai plate.
Tana fita ya saki ajiyar zuciya yace "Hassan?"
Gaban madubi ya koma ya kalli kansa, a hankali naga yanayin fuskarsa ya canza zuwa tashin hankali, yasa hannu ya bude drawer karshe ta jikin madubi.
Wani littafi ya dauko ya bude tsakiyar hoto be ya bayyana, kallan hoton yai cikin wani yanayi sannan yamaida hoton ya rufe ya runtse idanunsa, bancancanci farinciki ba, ban kuma cancanci inso ko a so ni ba.
Mikewa yai ya dafa kansa dake sarawa........
Gaba daya ranar bai sake magana ba har ta gaji ta kwanta dan ba alamar fuska.
Washegari ma da Ummy tace ya kaita gidan Goggo bai musa ba ya jira ta suka fita tare, yana kaita kofar gidan baijira me zatace ba yai gaba.
Da kallo tabi motar tana mamakin abinda ya faru, ko a mota duk yanda taso suyi magana kin yarda yai.
Shikuwa yana ajiyeta yaja mota yana tunani.
Jalila kam tana shiga gidan Goggo ta saki baki tana kallan iko Allah, ta shigar da kayan data taho dashi, nan suka zauna suka hau hira cikin farin ciki.
Lantana ma ta zauna sukaita hira.
Goggo cikin hira ne take tambayarta wanda ya kawota.
Jalila tace driver dinsu ne ya kawoni, Yaya ya fita ne.
Goggo tace "Allah sarki, na dauka shine ince bai shigo mun gaisa ba na mai godiya."
Jalila tace "zaizo shima."
Haka sukai ta hira suna tuno rayuwar baya da yanda sukasha wahala, Goggo tanata kara nuna mata ta kula da mutanen nan dan tabbas sun musu hallacin da basu taba tunani ba.
Jalila jefi jefi tana tuno abinda yaya ya mata yanzu da zata sauko, ta fito ta kalleshi tace "Yaya baza......"
Gano tai ya dauke kai yana neman wucewa.
Tsayawa tai dagalo tana kallan ikon Allah kafin ta shigo.
Meya sameshi?
Sai bayan magrib yaro ya turo ta fito, tana fitowa taga Mamman, jikinta ne yai sanyi ta bude bayan mota ta shiga tayima Lantana da Goggo sallama akan sai ta dawo.
Haka suka hau hanya, ta kasa daurewa tace "Mamman ina Yayan?"
Yace "wlh Hajiya bansani ba, waya yamin yace in daukoki."
Tace "okay."
Haka suka isa gida taitama Ummy godiya da Abba.
Kafin ta hau sama.
A daki ta sameshi yana karatu, sallamarta kawai ya amsa shima baiko kalleta ba, Jalila ta daure tace "Yaya na dawo."
Yace "naganki."
Shiru tai a tsaye kafin ta nufi toilet, tai wanka ta sa kayan bacci sannan ta fito ta dau bargo ta shimfida tana cewa "Yaya bacci nakeji, yau da alama na zama kasa, ko dan banyi baccin safe bane? Ina ta zumudi?"
Bai tanka mata ba, tai dariya tace "hmm basa banba, ni fa da agida bansan ma wani baccin safe ba amma yanzu jin dadi yasa har in banyi ba sai naji wani iri."
Bai tanka mata ba hakan yasata yin shiru, ta sa bargo ta kwanta, bata dade ba bacci ya dauketa.
Juyowa yai ya ajiye littafin ya kura mata ido, idanunsa ne suka canza kala a fili yace " Jalilah! Jalilah!"
Sannan yai shiru, mikewa yai ya shiga toilet ya watsa ruwan zafi sannan ya zura riga, harzai wuceta ya tsaya, sai kuma ya koma ya zauna kusa da ita.
Hannu yasa a gefen fuskarta yana kallanta cikin wani yanayi.
Cikin wata raunaniyar murya yace " nasan i am hurting u, sai dai kafin kiji zafin abinda nake miki ni na ji zafi, duk sanda na wulakantaki inaji a jikina sai dai bansan ya zanyi ba, Jalilah bansan ya zanyi ba banasan naga na dawwama a koda yaushe a cikin kuntata miki."
Shiru yai yanajin wani abu a kirjinsa kafin yace "Jalila Husain......."
Ya runtse ido a hankali wasu hawaye naga sun zubomai masu zafi, hannunsa yakai kan labanta.
Idanunsa ya sake rufewa a hankali ya shiga matso da kansa ya sumbashi bakinta, bakinsa ya bari a kan labanta.
Idanunta ta bude, me zata gani?
Shima idanu ya bude suka kalli juna, da sauri tasa hannu ta tureshi, ya mike tsaye da sauri.
Tace "Yaya!"
Yace "bargona nakesan dauka sanyi nakeji."
Tace "bargo?"
Bargo a.......
Ta kasa karasawa, yace "bargo a me?"
Tace "bakomai, nagane tun jiya kaki kulani, yanzu kuma gashi kanamin magana."
Yace "yanzun ma bakiji me nace miki ba? Bargona zaki bani."
Tace "to in na baka in shimfida me?"
Ya kalleta taya zaiyi yace mata shi kwanan kasan ne bayaso?
Ya hade fuska yace "sai ki kwanta akan gado ni sam laushin katifa samin ciwon baya take."
Da sauri tace "haba? Da gaske na kwanta?"
Ya kalleta sannan ya dau bargonsa ya kwanta akasa.
Murmushi tai sannan ta hau kan gado tana dariya jin dadi.
Can kuma tace "yaya badai barmin kai ba?"
Yace "barmiki? Bakiji me nace ba?"
Tace "oh naji."
Ta kwanta tare da juya baya.
Shiru tai kamar mai bacci tana tunanin abinda ya faru yanzu, hannunta takai kan labanta ta shafasu, shima kwanciya yai yana tuno abinda ya faru, me yakai shi? Baisan ya akai yaji a lokacin sumbatarta yakesan yi ba.
Ahhh kansa ya shafa yace "Hassan!"
#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*50*


   Yana cikin barci wajen karfe uku taji ana wani irin numfashi sama sama, yanzu kam ta riga tasan shine da sauri ta sa hannu ta danna waayarta sannan ta kunna fitilar dakin, yau a rufda ciki ta gashi ya tukunkune daga can gefe hannunsa nakan wuyansa gaba daya zufa ce take keto masa, mikewa tai da sauri tazo kusa dashi.
Hannuntasa ta janye hannunsa daga kan wuyansa, idanunta sun ciciko tana kiran sunansa.

  Amma ina, hannunsa ya fizge daga gunta ya rike kansa dake wani irin sarawa, Jalila ta ga yau abin nasa dayawa dan har pillow ya dauka ya danne kansa dashi.

  Cikin tsoro da tausayinsa yasa ta janyowshi ta rungumeshi ta baya tare da sa kuka tana cewa "Yaya! Yaya dan Allah kandaina......."

  Jitai jikinshi duk yanata ketowa da zufa, sakeshi tai da sauri ta kure karfin AC din dakin sannan ta dawo a rikice ta kara janyoshi tana kuka.

  Yau abin ya dade dan ita kawai data rungumeshi ta kifa kanta a jikinsa bata sake dagowa ba.

  A hankali numfashinsa ya dawo, ya bude idanunsa, ganinshi yai a jikin Jalila tanata kuka.
  Shiru yai cikin takaici abinda ke faruwa wanda gashi duk sanda abin ya tashi sai yasa Jalila kuka haka.

  Mikewa ya fara kukarinyi, idanunta ta bude ta daukeshi a kansa, da sauri tace Yaya?
 Zama yai sannan ya jawota kusa dashi, jiki a sanyaye take kallanshi.

  Bata an kara ba taji ya rungumeta tsam, ya kwantar da kansa kan kafadarta.

  Bakinta na rawa tace "Yaya!"
"Let's wait like this for a moment......" cikin wata murya mai sanyi ya fadi hakan, shiru tai ta kasa motsi.

  Can yasa hannu a bayanta kamar me lallashi yace " sai yaushene zaki canza hobby dinki?"

 A hankali tace " to ya zanyi duk ka canza lokaci daya, ga....."
 Yace "are u worried about me or are u scared?"
Tace "zaka fara ko Yaya?"

  Shiru yai kafin ya saketa ya kalleta yace "irin wannan kure mana AC haka fa?"
Ta tashi ta dau remote tana cewa, zufa kaketayi shiyasa na kunna.

 Ya kafeta da ido yace "kin tabbatar dan ni kika kunna?"

 Tace " ban gane ba???"
Yace "a'a to haka kawai dan ina zufa sai a kure AC haka?"
 Ta kalleshi tace "nikam ko dan ka kwanta a kasa ne?  Naga ka dade lafiya."
 Kallanta yai sannan ya girgiza mata kai yace "ko daya."

 Ta kalleshi bayan ya mike daga gun tace "Yaya nikam dan Allah meke damunka? Mafarki kakeyi? Ko.......?"
Sai kuma tai shiru, yace "ko aljanu gareni?"

 Da sauri tace "ba haka nake nufi na...."

  Ruwa ya dauko yasa sannan ya dawo ya kwanta, kallanta yai da take dukushe a gun yace "Hajiya zan kwanta."

 Tace "Hajiya? Lalai Yaya matar da bata taba zuwa hajj ba, batama iya karatu sosai ba itace Hajiya."

  Juyowa yai ya kalleta sosai yace "daki shiga islamiyya ku dinga zuwa da Ameera da kuma ki zauna a gida wanne yafi?"

 Tace "in zauna a gida kamar ya?"
Tai tambayar tana kallansa, juyawa yai baice komai ba.

 Da sauri ta kalleshi tace "da ka koyamin a gida?"

 Idanunsa ya rufe da sauri tare da harde hannayensa, ta sako kanta tace "Yaya dagaske?"

  Bude idanunsa yai, sam baiyi tunanin ganinta daf dashi haka ba, idanunsa ne ya sauka a nata, da sauri ta mike tsaye ta hau kan gado ta kwanta tare da saurin kashe fitilar dake jikin gadon.

  Kwanciya tai tana dan ajiyar zuciya a hankali.

 Dakin ne ya baibaye da duhu.
 Tana kwance sai dan juye takeyi, can tace "yaya kayi bacci?"

Shiru yai baice komai ba sai dai yana jinta, tadan sake ajiyar zuciya kadan.

  Muryarsa taji yace "baki taba tambayata dan uwana ba, bayan duk wanda yaji sunana Hassan ya tabbatar inada Husain."

 Juyowa tai ta kwanta akan tafukan hannayenta ta jiyo ta saitinshi, duk da duhu ya sa bata ganinshi tace "taya zan tambayeka abinda ka kasa fadama kowa?"

  Shiru yai dan harta dauka bazaice komai ba sai taji yace " shekararsa 10 kenan da rasuwa."

 Zatai magana taji yace "tare suka rasu da dan kanin Abba, Sudais wanda yazo gidannan karatu."

  Jalila yanzuma hartace "sh........"
Ya kara katseta yace "karkice komai kijini kawai."

 Shiru tai tana kallangun da yake.
Yace " karki kunna fitila."

 Tai shiru, tare da kallansa, Hassan yana kwance yace "they died because of me......"

 Ya fada tare da runtse idanunsa da karfi yana jin wani abu na tokare mai zuciya.

 Wasu zafaffan hawaye ne suka zubomai, yace "He is a bright person, mutum ne mai tsananin hakuri, a koda yaushe cikin fara'a yake Jalila..........."

  Nauyin da zuciyarsa taci gaba dayi, ga numfashinsa na seizing ne yasa yai shiru, saukowa tai da sauri har tana buge kafa ta matso kusa dashi.

 Tace "yaya!"
Ta dauka abin ne ya tashi.
 Jinta a kusa dashi ne yasa yasa hannunsa dan jin a inda take, a durkushe a kusa dashi ya jita.

  Hannunta ya riko sannan ya kwantar da kansa akan kafafunta dake a durkushe.
Da sauri ta kalleshi.
Hannunta ya riko.

 Kallansa tai zuciyarta na bugawa da sauri, a hankali tace "karka cigaba yaya inhar zuciyarka bazata iya dauka ba, sannan bansan menene yafaru tsakaninku ba amma na tabbatar ba............"
Yanzu ma katseta ya sakeyi, yace "don't comfort me."
Shiru tai, yace " nikaina bansan meyasa nakesan fadamiki abinda ban fadama kowa a duniya ba, sai dai ina alakanta hakan da zaman da nai dake sannan da yanda nasan komai naki."

  A hankali ya lumshe ido zuciyarsa na kunna, yace "later....."
Kai ta daga tace " later Yaya.... sanda kaji zaka iya."

  Kansa ya kara gyarawa, shiru tai sai jikinta dayai sanyi, zuciyarta na bugawa da sauri.

 Ya dade a haka kusan minti ashirin kafin yaji an fara kiraye kirayen sallah, ita ta dauka ma bacci ne ya daukeshi, ga kafarta ta fara zafi.

 A hankali ya dagata sannan ya mike ya kunna wutar dakin.

 Haske ne ya baibaiye dakin, kallan juna sukai, ya dauke kai ya shiga toilet.

 Yana shiga ya kalli kansa a madubi, yanzu kam ya tabbatar ya fara san yarinyar nan, garin yaya? How can i??? Ya furzar da wata iska.

  A inda ya barta anan ya ganta, ya kalleta yace "me kike anan?"
Da sauri ta mike ta fara ninke bargo tace "bakomai."

 Kallan fuskarsa tai, tanaso taga canji a tattare dashi, kallanta yai yace "kallan fa namenene?"

 Ta mike rike da bargo tace "bakomai, ba kai na kalla ba."
Yace "then?"
 "Uhmm yauwa toilet na kalla."

  Sallaya ya shimfida batare da ya kalleta ba, ta mike da sauri ta shiga toilet.

  Tana rufe kofar tai ajiyar zuciya tace "meke damun yaya? Ya tone din maganarsa ta koma ta da?"

  Shima tana shiga toilet ya kalli kofar toilet din sannan yai ajiyar zuciya shima, ya tadda sallah.

  Pad ta canza ta fito, yana sallah ta fito, zama tai a bakin gado tana dan lekashi.

  Yana idar da sallah ya bude qur'ani, jitai yace "taso."
Da sauri ta taso tace "gani."
Ya kalleta sannan ya kalli kasa, da sauri ta zauna a kasan carpet, tana kallansa.
Ya kalleta fuska a hade yace a ina kika tsaya?
Tace can karshe, ta fada tana neman taba qur'anin, da sauri ya rike hannunta sannan ya kalleta, itama kallansa tai dan batasan me tai ba.

  Yanda yaga tana kallansa ya fahimci batasan ma metai ba, yace "ba asan taba qur'ani izu sittin in mutum na fashin sallah."
 Kunya ce ta kamata, ta kalleshi.

 Sake mata hannnu yai sannan yace can kasa ina?
Tace "a ikira."

 Kallan mamaki ya mata kamar zaiyi magana sai ya fasa.

 Nan ya bude ya yafa biyawa, tana zaune a gefe tana biyawa.
Sura daya sukai yace "sai gobe kuma."

 Kallansa tai tace "nagode Yaya."
Bai amsa mata ba ya fara karatunsa, mikewa tai ta zauna akan gado, can dai ta fito falo ta kwanta sai bacci.

  Hassan kam ya dade yana karatu kafin ya kwanta akan sallayar, bacci yai gaba dashi.



************

  Inna ta kalli Mumy wacce ta kirata tace " Abakar ya tafi gun aiki?"

 Tace "eh."
Inna ta kalleta tace "haryanzu fishin kikeyi dan nace mijinki yace shine yai komai?"

 Ta kalleta tace "Inna dan Allah Abakar yaci darajar jikokinki."
Tace "kamar ya?"
Mumy ta kalleta tace " ki barmai company din nan dan Allah, karfa ki manta yanda yake kokari ganin komai ya tafi daidai, sannan mijinki yarka ne fa? Sai yaushe ne zaki maidashi d'a?"

 Inna ta kalleta tai murmushi tace "a koda yaushe in kina abu mamaki yake bani, ke wai sai yaushene zaki fahimci wanene Abakar? Sai yaushe ne zaki gane ba saboda ke yake zaune agidan nan ba, ba saboda ke yakemin ladabi ba?"

 Cikin takaici tace "ko ma saboda me yake tare da ni bai dameni ba, tunda ni haryanzu ina sanshi kuma banasan 'ya'yana su rabu da mahaifinsu."

 Inna tai shiru tana kallanta, wannan fa bazata fahimci komai ba, tace " to naji, sai ki shirya muje gidan mu basu hakuri, in kuma ni kadai zanje ba laifi bane."

 Da sauri ta kalleta tace "da gaske?"
Tace "eh, sannan ki bar maganar bashi company din zuwa wani lokacin, in komai ya daidaita zan nadashi a matsayin shugaba ni kuma nai resigning."

 Da sauri mumy ta taso tazo ta rungume inna tace "godiya nake Inna ta."

 Inna ta kalleta kawai, cikin murna ta fita.
Inna ta bita da kallo tace "i know she is naive but I don't expect her to be foolish, ta bari yaranan duk ya gama lalatata da dadin baki."

  Tai kwafa sannan tace "bari na gama tallafo company din, in na ma da Taura zan dawo kanshi.


*********

  Ummy ce ta kalli wayar hannunta wacce aketa kira tana rejecting, Sageer wanda kecin abinci yace "Ummy wai waye yaketa kira haka?"

 Ta kalleshi kawai tai murmushi dan batasan me zata ce ba, Zaliha ce, sam bama ta gajiya da kiran wayar.

  Ummy ta kalleshi tace "ya maganar takardun naka?"

 Yace " gamunan dai muna jira basu bamu ba."

Haka suka gama yin break, ta kalli hanyar sama tacema Sageer yau da alama bacci mai nauyi sukeyi naga shiru.

  Sageer ya kalli saman shima sannan yai yake yace "da alama kam, sai dai Allah yasa ba ciwon yaya bane ya tashi."

 Da sauri ta kalli Sageer tace "kasan Sageer tsabar naga Hassan yanata canzawa sam ina mantawa?"
 Da sauri ta nufi hanyar sama.

  Jalila bata dade da tashi ba ta kalli agoggo da sauri ta mike cikin mamakin baccin da tai, a hankali ta tura kofar dakin, Hassan na kwance akan sallaya yanata bacci ta wuce toilet.

  Wanka tai ta fito a hankalita zura riga da skirt ma atamfa,tana shafa hoda taji knocking.
 Da sauri ta kalli Hassan sannan ta taho gun kofar.

 A hankali ta bude, Ummy ta gani, Ummy ta kalleta tace "Hassan fa?"

 Tace bacci yakeyi.

 Ummy tai ajiyar zuciya sannan tadan ja baya, Jalila ta fito ta kalli Ummy sannan ta gaisheta.

 Ummy ta kalleta tana murmushi tace "sry Jalila wlh na dauka ko matsalar Hassan ne ya tashi."
Jalila tace "a'a Ummy bacci ne ya daukeni wlh banmasan lokaci yayi haka ba."

 Ummy tai murmushi sannan tace "hakan yayi ai ki fito ki dauko muku breakfast."
Tace to, Ummy ta juya, komawa cikintai ta fesa turare dannan ta yafa dankwalinta ta sauko.

 Tana fita daga dakin ya bude idanunsa sannan ya maidasu.
 Sai dayai sama da minti biyar sannan ya mike ya shiga toilet.
Meyasa batacema Ummy komai ba?

 Har ya  zauna sai kuma ya fito dan yanasan jin ya ake ciki akan maganar yar iskar yarinyar nan.

 Bakowa a falon sanda ta sauko, Ummy ta jiyo a kitchen da sauri ta karasa ciki.
 Ba ita ta gani ba, ashe Sageer ne yake dauraye kwanukan da yaci abinci.

 Ta gaisheshi sannan ta karasa kusa dagun kadan tace "da ka barshi zan wanke."
Ya kalleta ba tare da ya sake aikin ba yace "yaya fa? Jikin nashi ne?"
Kai ta girgiza mai tace "ba shibane bacci ne kawai ya daukeni."

 Yai ajiyar zuciya sannan ya cigaba da wankewa, ta sake cewa "dan Allah ka barshi nayi."

 Muryar Umny taji tace "barshi Jalila indai Sageer ne."

Jalila ta fito Ummy na cewa "matar Sageer ta huta dan akwaishi dasan yin aikin girki da wanke wanke, kinsan da har shara yake tayani."

 Jalila ta kalli inda yake tai yake tace "lalai akwai kokari."
Ummy ta kalleta tace "Jalila bakida wata kawa ne ki hadasu?"

 Da sauri ta kalleta, Sageer ne ya fito hannunsa rike da plate yace "Ummy!"
 Kallansa tai tace "menene? Da kacemin da wacce kakeso yanzu kuma naji shiru, kaga kwara ni na mike tsaye."

 Tai maganar cikin zolaya, Jalila ta kalleshi.

 Ummy tasa dariya tace "meye hakan?"
Hannunsa ya kalla ya ganshi rike da plate, dariya shima yasa yace "Ummy ai duk kece."

 Jalila ce ta kalleshi itama tai dariya, Hassan wanda yake saukowa daga kan steps ya tsaya yana kallansu cikin jin dadi, Ummy ce ta fara hangoshi.
Tace "malam Hassan ina zaka bakai breakfast ba?"

 Ya karaso kusa da ita yace "ba fita zanyi ba."
 Sageer ne ya kalleshi yace "Yaya."
Kallansa yai yace " mikakeyi da plate?"

 Yai dariya yace "Ummy ce take neman tadamin hankali."
 Ya kalli Ummy, dariya tai sannan tace Wani abun kake so?"

 Jalila ta kalleshi, gani tai ko kallanta baiyi ba, a hankali ta mike ta shiga kitchen.
Sageer ya biyota, wanke wanken ya karasa ya dauraye hannayensa ya fito, har yaje kusa da kofa sai ya juyo kamar zaiyi magana sai kuma ya fita.

 Da kallo ta bishi sannan ta fara hada kayan abincinsu.

 A falo kuwa Hassan ne ya kalli Ummy yace "ya maganar yarinyar nan?"
Tace "dazuma tayita kira ina rejecting."
Yace "sim dinshi na gunki ne?"
Tace "eh."
 Yace "in har bata daina kira ba zuwa dare kimin magana, ni zan mata magana, in ta kama ma sai inje har gidansu naci mutuncinta."

 Ummy tai dariya tace "Ba sai ankai ga haka bama, insha Alla, Allah na tare damu."

  Jalila ce ta fito rike da tire.
Ummy ta kalleta tace "Jalila! Goggo tace ya kamata a saki a islamiya, shine nace zan fadama." Takarass maganar tana kallan Hassan.
Itama Jalila shi ta kalla, hartace "Ummy ai......"

 Hassan ne yai saurin cewa "karki damu da wannan Ummy, zansan yanda za'ai."

Jalila ta kalleshi jiki a sanyaye tai sama.
Ummy ta kalleshi tace "kai Hassan! Wannan magana kamar ranka na bace?"
Ya kalleta yace " haka kika gani?"
Tace "bani kadai ba har ita Jalilan, kalleta ka gani mana.

 Juyawa yai ya kalleta, jiki a sanyaye take taka matattakalar.

 Shiru yai tare da kura mata ido.
Ummy ta kalleshi sannan tace " kaje kuyi breakfast."
Ta fada tare da mikewa.

 A hankali ya mike shima ya nufi saman, taje bude kofar, ya sa hannu ya bude mata.
Juyowa tai ta zuba mai ido.....
Shima kallanta yake.......


#OneLove💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*51*

 Kallanta yai yace "bazaki shiga ba?"
Juyawa tai ta shiga dakin, ta ajiye tiren sannan ta kalleshi tace "Yaya abinci."

 Bai kalleta ba yace "sai nayi wanka."
Ya fada tare da nufa ciki,, da kallo ta bishi tana mamakin halayensa.

 Harta bude zata zuba sai kuma ta maida murfin kular ta rufe.

 Hannu tasa ta janyo littafin da yake karantawa ta dauko, ta bude cikin littafin.
 Ajiye littafintai sannan ta kalli hanyar toilet, ta mike ta fito falo.
Tv ta kunna tai shiru tana tunanin abinda ya faru tsakaninsu a daren jiya.

 Kalamansa na kara dawo mata, meya faru a can baya? Wanda yake hanashi bacci? Yake hanashi shiga mutane? Yake hanashi murmushi? Yake hanashi zama cikin yan uwansa?

  Shiru tai tana tunani, da alama shima yanada painful past wanda yafi nata.

  Yana fitowa daga wanka ya shirya, ganin bata dakin ga motsin karar TV a falon yasa yasan tana can, sai dai bazai iya kiranta ba.

 Zama yai akan kujera yana kallan kofa yana jiran shigowarta, dan yunwa yakeji.

 Jalila kuwa ta shiga tunani sai can ta dawo daga tunanin nata, ta mike ta bude kofar, a zaune taganshi tana shiga suna hada ido, yana kallanta yai saurin dauke kai.
Ta shigo ciki tace "Yaya ka fito shine ba magana?"
 Bai kalleta ba yace "inyi magana ince me?"

 Ta kalleshi tace "kacemin ka fito in taso."
 Ya kalleta yace "gashinan ai ban kiraki ba kin taso."

 Tace "lalai yaya, to bari nakoma sai ka kirani." Tai maganar cikin zolaya.
Yace "nidai kafin ki koma bani abinci naci inyaso sai ki koma."
 Ta kalleshi tadan canza fuska tace "ba kara ma kenan? Bari na fadama Ummy to nace kace ba sai naci abinci ba."

  Baisan sanda ya dan murmusa ba yace "yaushe kika koma haka?"

 Matsowa tai tace "yaya wlh yanzu bakinka ya motsa, wallahi yau na gani sosai."
 Tsuke fuska yai yace "yau menene ruwanku da dariyata?"

Tace "ni kuwa nake da ruwa yaya, bakasan yanda abin ke damuna ba, kome fa zakace fuskarnan a tsuke kake fada."

 Kallanta yai yace "bakyaso?"
Ta daga kai da sauri tace "sosai ma, wani sa'in in tone din maganarka ya koma cold sai jikina yai sanyi."

 Kalaman Ummy ya tuno data fadamai dazu, kallanta yai yace "magana zaki tsaya yi bazakiban abinci ba?"

 Ta dan turo baki ta nufi inda ta ajiye abincin, a ranta tana cewa what am I expecting?

Zubamai tai tace "ka sauko."
Yace "yanzun ma kin manta da plate din ne? Dan muci tare?"
Cikin shagwaba tace "yaya Allah fa ba haka bane."
Yace "shagwaba kika koma?"

Ta kalleshi tace "yaya wai meyasa kakemin haka?"
"Menai?"
Ta kalleshi kamar zatai magana sai kuma tai shiru, a ranta tace "rannan kamin kiss bance komai ba,  jiya ka kwanta a cinyata bance komai ba amma kai komai nai sai ka fassara."

 Mikewa taga yayi ya wuceta ya zauna a inda ta zubamai abincin.

  Kallanta yai tana tsaye hannu yasa ya jawota, ta zauna a kusa dashi.
Kallansa tai tana mamaki tace "Yaya!"
Yace "wai ni yaushe nake yayanki ne? Kin kama suna kin rike kamar ke kika samin?"

  Baki tadan turo sannan ta zuba abinci a nata plate din, gani tai yasa spoon dinshi cikin plate dinta.
Da sauri ta kalleshi yace "ba haka kikeso ba?"
Tace " bangane ba....?
Bai kara mata magana ba yacigaba da ci, kallansa ta tsaya yi tama kasa ci, sai can ya kalleta yace "kin koshi ne?"
Spoon din ta maida ciki ta cigaba daci ta mamakin wannan abu.

  Yana gamawa ya dau key ya bar dakin baice mata komai ba, baki ta saki tana kallan ikon Allah.

  Saukowa yai kasa ba kowa a falon, yai hanyar waje.

 Mota ya shiga kawai ya fita, Jalila ta dade a zaune kafin ta kwaso kwanuka ta fito.

Ganin bakowa a falon ta wuce kitchen ta wanke kwanukan, tasan Ameera na skul, da alama Ummy na daki.
Sageer fa? Bude kofar daki taji da sauri ta kalli gun.
Sageer ne ya fito sanye da kaya da hula da alama fita zaiyi.

 Kallanshi tai shima ya kalleta, da sauri ta dauke kai ta juya zata koma kitchen.
Yace "Jalila?"
Tsayawa tai a inda take sannan ta juyo ta kalleshi.
Ya matso inda take kadan ya kalleta yace "ina making dinki uncomfortable ko?"
Kallansa tai ta girgiza kai alamar a'a sannan tace "a'a
Yai murmushi yace "kiyi hakuri Jalila."
Tace "Uncle sai yaushe ne zaka daina bani hakuri? Bazance ban taba jin zafin abinda ya faru ba, dan da naji zafinka sosai sai dai a yanzu ko kadan banajin zafin ka, na fahimceka, nasan dalilinka."

 Kallanta yai yace "nagode Jalila, nagode da fahimtar da kikamin."
Ta kalleshi tace "Ummy tace duk ka canza, ni kaina nasan ba haka kake ba, Allah yasa banice sillar canzawarka ba."

Ido ya kura mata kafin yace "ko kadan Jalila, inma akwai dalili to bazai wuce zuciyata ba wanda kuma basai kin damu da ita ba, zata daina da kanta."

 Kallansa tai tace "Uncle!"
Yace "kidinga cemin Sageer kawai, hakan shine daidai a matsayinki na matar yayana."

 Shiru tai kafin tace "saidai na kiraka da Yaya sageer yanda Ameera ke cewa."

Yace "hakan yayi, nagode Jalila sannan Please let us take it to our grave, kar kowa yasan abinda ya faru."

  Zatai magana sukaji muryar Ummy tana cewa "Sageer fita zakai?"
Da sauri ya juya dan baiji karar kofa ba, Jalila ma ta kalleta.

Ummy ta kalleshi tace "menene?"
Yace ba komai, na fito ne banganki ba nake tambayar matar Yaya.

Tace "ina ciki ina addu'oi.

 Yace "Ummy zanje gun Abban."
Tace "to Allah ya bada sa'a."
Yace "Ameen ya fita."

 Ummy ta kalli Jalila tace "Jalila!"
Jalila ta matso tana cewa " Ummy nikam banga Ameera ba."
Ummy tace "sun koma skul yau dama hutu ya kare."

Tace "oh shiyasa, naji gidan shiru."
Ummy tai dariya tace "wlh kuwa, Jalila gidan namu is so boring."
Jalila tai dariya itama tace "muma haka gidan yake, Sultan kullum yana daki yana game ko jin kida, Safeena kuma tana gun Mumy ko suna kallo ita da Yasmeen, Inna na sama, Mumy kuma itama ko tana falo ko daki, dama gun Goggo nane muke zama muyi ta hirarmu."

 Ummy tace "sanda kowa yake zama, bacci da kallo ke me kikeyi?"
Tace "aiki, girki, ko wanki."

 Ummy tace "hmm da alama ya kamata ki kara samun hutu a gidan nan, yanda kikai aiki acan ba hutu yanzu duk sai ki fanshe hutunki gun mijinki."

 Jalila tai dariya tace "ai nan gidan ba aiki Ummy."

 Tace "ba wani nan, ina mijin naki?"
Cikin kunya ta girgiza kai.
Ummy tai ajiyar zuciya tace "Haryanzu baice miki zai fita?"
Tace "eh, yanzu ma fa....."
Sai kuma tai shiru tare da sa dariya.

 Ummy ma tai dariya tace "Jalila bansan ke ba amma i am sure Hassan na sanki, idanunsa kadai sun tabbatar da hakan."

 Jalila ta kalleta sai dai batace komai ba.

 Ummy ta dafata tace "Jalila godiya, kina sani farincikin dana dade bansamu ba, ganin Hassan na samun sauki yasa kullum zuciyata nakejinta tass, shikansa mahaifinshi yanzu hankalinsa yafi kwanciya har yake fita aiki ya dade haka."

 Jalila ta sunkuyar da kai a ranta tace me nayi? Ummy tace "mungode Jalila, sai dai ki kara hakuri sannan ki kara kula dashi, insha Allahu bazaki tabba dana sanin auran Hassan ba."

 Dagowa tai ta kalli Ummy sannan ta daga kai alamar to.

  Hassan na fita yaje bakin wani shago yai parkin, fita yai ya shiga ciki.

 Mai shagon ya tambayeshi abinda yakeso, Hassan yai shiru kafin yace "kawai abashi abunda ya dace."
Cikin mamaki mai shagon yace "abinda ya dace kamar me kenan?"
Gidan mamar matata zankai, ya fada tare da dauke kai.

 Mai shagon ya guntse dariyarsa sannan yace "katan din juice fa?"
Hassan yace dame?
Yace sai ka hada ko da kayan tea ne.
Hassan yace "samin to."

Nan mai shagon ya laftamai kayan tea dan kana kallan motarsa kasan da akwai kudi, ya sa mai juice kala uku a bayan boot ya cafki kudinsa.
Hassan na fita yace "Alhamdulila Allah ya kara kawoka."

 Hassan ya shiga mota yai gidan Goggo.

 Ya dade a waje yana tunanin abinda zaice kafin ya shiga.

 Almajirai yasa suka shiga da kayan.

 Goggo na zaune tana jin radio ana hada musu wuta a waje ya shiga ciki.

 Tanaganinsa ta mike fuska dauke da fara'a tana lale lale.
Ya zauna ya gaisheta ta amsa cikin farinciki, shidai yai shiru.

Kowa ta tambayeshi sai dai yace "lafiya."

 Data gama tambayar tai shiru shima yai shiru.

 Can yace "ba wuta ne? Naga kamar da wuta a layin?"
Tace "gyarawa sukeyi yanzu, Hassan mungode sosai sosai, Allah yayi albarka ya inganta rayuwa."
Yace Ameen

 Shiru suka karayi kafin ya mike yace zai tafi.

 Tace "da wuri haka?"
Yace "eh."
Tace "to mungode."
Tana fitowa waje tai karo da kayayaki, nan ta kara mai godiya har ya fita.

 Mota ya shiga yai ajiyar zuciya, sannan ya tada kota ya juyo gida.

  Jalila kuwa bayan ta gama komai a kasa, ta daura abincin ran.

Yana shiga yaji motsi a kitchen, lekawa kitchen din yai, hangota yai tana aiki, yanka vegetables takeyi, tsayawa yai daga inda yake ya kura mata ido, gaba daya yanayin fuskarsa ya canza.

  Ya dade yana kallanta har itama jikinta ya bata ta juyo.

 Ganinsa tai a tsaye da alama ya tafi tunani, ta matso tace "Yayah!"
Kallanta yai yaganta a gabansa, tace "yaya naga kana......"
Da sauri ya wayance yace "kallan yanda kike aiki nakeyi, kin tabbatar kin wankesu kafin ki fara yankawa dai ko? Dan naga kamar baki wanke ba."

Cikin mamaki ta kalleshi, juyawa yai ya fita, da kallonta bishi,, yanzu kam ranta ya sosu, me yake nufi?

 Haka ta cigaba da aikin ta ranta a bace, dan bakin cikin har kwalla ce tadan zubo mata.

 Shikuwa yana hawa sama ya bude drawer ya dauko hoton Husain yana kallo, a fili cikin wata murya yace "Husain ya zanyi? Nasan bai kamata ba, bai kamata nai sha'awar rayuwa ta jin dadi da wata ba, ban cancanci yin farinciki ba, ban cancanci a soni ko inso wani ba sai dai bansan meke damuna ba, Husain i am really hurting her, wanda nakeji kamar na fita jin zafin abinda nake aikata mata."

"Zuciyata na kwadaitamin yin rayuwa da ita, zuciyata na san ta kyautata mata, inasan ingana cikin farinciki, Husain inajina  kamar bani ba."

 Yai shiru tare da rutse idanunsa, ya koma ya jingina da jikin drawer din, a ransa yace "Husain zan sanar da ita komai, dan abinda zuciyata ke rayamin kenan, in har na sanar da ita zan barta tai deciding abinda taga ya dace, inhar tana tunanin rabuwa dani shine mafita shikenan, in kuma....."
Sai yai shiru, tare da kara runtse idanunsa,shiru yai ya dora hannunsa akan goshinsa yana tunanin abinda ya faru a baya.

 Baisan hawaye sun zubo mai ba.


**********
Mumy ce ta kalli Dady bayan ta amshi hular dake kansa tace "Dadyn Yasmeen! Inna ta yarda."
Yace "dame?"
Tace "bazata daurama laifin abinda ya faru ba."

 Yace " meyasa kike takurama kanki? Nacemiki bakomai, zan iya yin komai indai a kanku ne."

 Ta ajiye hular ta rungumeshi tace " karka damu, na fadama it's my turn to protect you"

 Kallanta ya shafa sannan yace " nine ya kamata nai protecting dinki ke da yarana."
 A tare sukai murmushi......


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

Thanks alot for the love 😍May Allah Subhanahu Watta'ala always help and guide us👏🏻

*52*


  Yanajin motsin shigowarta ya mike ya maida hoton sannan ya fito daga dakin, da kallo ta bishi tace "yaya!"
Ko kallanta baiyi ba bare tasa ran zai amsa mata, saukowa kasa yai ya zauna a garden.
Ita kuwa ganin yanda ya giftata ko kallanta baiyi ba tace "me kuma nai? Ni Habiba?"

  Abba ne ya dawo, yana sauka daga cikin mota ya hango kan Hassan, gunsa ya nufa.
 Jin motsin tahowar mutum yasa Hassan juyowa.
Ganin Abba ne yasa ya juya yana kara tunani, Abba ya karaso ya zauna daf dashi.

 A hankali yace "sannu da zuwa."
Abba yai murmushi yace "Eldest me kake tunani? Naga ka dade banganka anan ba."

 Hassan yai shiru sai dai ya kalli Abba.
Abba ya sa hannu a kafadarsa kamar abokinsa yace "Mata ne?"
Da sauri ya kalleshi.
Abba yai murmushi yace " na canka kenan."

 Yai saurin cewa "a'a ko kadan."
Abba yai dariya sannan ya sauke hannunsa daga kafadar Hassan, yadan yi shiru.
 Hassan bai kalleshi ba yace "ina yarinyar? Ka daina tunaninta?"

  Abba shima yana kallan kasa yadan hade hannayensa gu daya yadan matsa, yace " ba kamar da ba."
Hassan ya dan kalleshi yace "kana tunanin santa kake?"
Abba yace "yanzu gaskiya kakeso na fadama ko kuma abinda nasan zai kwanta maka?"

  Hassan yace "gaskiya!"

Abba yadanyi murmushi kadan yace " inayi sosai, sai dai kamar yanda mahaifiyarka tace zanyi kokari ganin na cireta a raina, dan ina ji a jikina ni kaina ba san daya kamata nake mata ba."

 Hassan yai shiru kafin ya jinjina kai yace " nagode Abba da kake kokarin cire ta aranta dukda abin ba mai sauki bane."

 Abba ya riko hannunsa yace "kasan yanda hankalina ya tashi? Lokacin da naga kana fada akan abin? Nayi tir da zuciyata nayi dana sani wanda bazan iya misaltamaka ba."

  Hassan ya kalleshi sannan yace "bansan nima sanda na hau haka bane....."

 Abba ya kalleshi yace "naji dadi a kasan raina, at least inada wanda nasan zai hanani, kaga kamar Sageer na tabbatar bazai dage akan abinda nakeso ba, balle Amira, kai kuma ba lafiya ce dakai ba, balle ka hanani abinda zuciyata ke neman jefani, sai dai bansan har jikinka yayi sauki haka ba ina can ina shirme."

 Ya karasa maganar jiki a sanyaye.

 Hassan yai shiru kafin yace "Abba a koda yaushe ka dinga tuna wacece Ummy a garemu, in har wannan tunanin na zuwa maka na tabbatar ba abinda zai gifta zuciyarka."

  Kai ya jinjina yace "ni kaina bansan ya akai zuciyata ta nemi kawomin shirme haka ba, bayan nasan irin kaunar da kakema Mahaifiyarka, bayan kai din kaine rayuwata."

 Hassan ya kalleshi cikin wani yanayi na tausayawa.

  Can ya dauke kansa da sauri saboda kwallar dake neman taruwarmai a ido, ya juya kansa da sauri.

 Abba ya sake dafa kafadarsa yace "ya ya? Fada kukai da matar taka shine kai yaji?"

 Hassan ya kalleshi sannan ya dan murmusa kadan.
 Cikin tsananin mamaki Abba yace "Hassan murmushi kai?"
Yace "wa? Ni?"
Abba yace "sosai ma kuwa, na tabbatar kayi murmushi yanzun nan.
 Hassan ya mike da sauri, Abba ya jawoshi ya zauna ya riko hannunsa yace "nagode Hassan."
 Hassan ya kalleshi yace "name?"
Yace "na komai ma, kai d'a na ne wanda na haifa sai dai ban taba alfahari da komai a rayuwa ba kamar ka."


  Jiki a sanyaye yake kallansa kafin yace "bancancanci samun wannan matsayin ba."
Abba ya dan harareshi yace " in tuno ma?"

 Da sauri Hassan ya mike dan ya fahimci abinda yake nufi yai hanyar ciki, Abba na cewa "in ban tuno ma ba na tunawa matarka."

 Da sauri ya shiga ciki, Abba ya bishi da kallo cikin tausayawa, har idanunsa suka dan canza,  ya juyo tare da dan runtse ido yace "Alhamdulila!"

  Tana kasa taga hawansa sama, da kallo ta bishi, shigewa yai.

 Bata hau sama ba sai bayan magrib, dan sunatare da Ameera da Ummy bayan ta dawo daga makaranta, bayan magrib din ma Ummy ce tacemata dare yayi.
Ameera tai dariya tace "kai Ummy ba kara?"
Ummy tasa hannu tadan kwadeta tace "zaki fara ko?"

  Mikewa tai ta hau sama, Ummy ma ta mike tace "ke kuma sai kiyi ta zaman gulma.
Ameera tace "bari na jira Ya Sageer ya dawo muyi hira, tunda dai ni kowa ya watse ya barni."

 Ummy tai tafiyarta tana cewa "bari ma na kirashi naji naga ya dade bai dawo ba."

 Jalila tana hawa sama ta ganshi a kwance, yau ba karatu yake ba sai dai a kwance kawai yake shiru, ta shiga da salama.
A hankali ya amsa wanda ita kanta bataji ba, shiga ciki tai tana kallansa.

 Yaci abinci, a ranta tace yau ba jira?amma rannan harda jin haushinsa.

 Hartana neman zama a kan kujera sai ta juyo ta fito falo ta zauna, ta kunna Tv.

 Shiru tai tana tunani, meke damunshi? Ko bashida lafiya ne?
Da sauri ta mike ta shiga dakin, tazo jikin gado tace " Yaya? Bakajin dadi ne?"

  Kai kawai ya girgiza mata alamar a'a idanunsa a rufe.
Tai shiru kafin ta juya, har zata fita sai kuka ta shiga toilet.

 Tana rufo kofar ya mike, ya kalli kofar toilet din.
Mikewa tsaye yai ya dau makullin mota ya dau wayarsa.

 Tana fitowa ya kalleta ya mika mata hijab dinta, kallansa tai tace "me?"

 Gani tai yayi gaba, da kallo ta bishi tace "yau maganar ma wahala take?"
Fitowa tai dan ta fahimci ta biyoshi yake nufi.

  Haka ya fita, tana kokarin fita Ameera ta fito jitai tace "Amarya sai ina?"
Harararta tai tace "inda kika aikeni, kicema Ummy zamu fita."

Da gudu Ameera ta taho tace "ina zaku? A daren nan?"

 Jalila ta in fada miki?
Tace eh ina? Ta fada tana matso da kunne Jalila tai dariya tace "inda Ameera ta aikemu."
Tai saurin yin waje tana dariya, dan tana tsoron karta dade a tsaye tai laifi.

  Yana cikin mota harya tada ta bude gefensa zata shiga yace " shiga baya."

 Komawa tai baya ta shiga tana yan kunkune, tana rufe mota yaja suka fita.
Suna fita motar Sageer na shiga gidan.

 Tafiya yake, ba mai magana a cikin motar, ita kuma haushin ce mata dayai ta shiga baya yasa batai magana ba.

  Kanta ta sunkuyar, jin alamun an tsaya yasa ta dago.

 Gidan Goggo? Kallan gidan tai sannan ta kalleshi cikin mamaki.

 Kashe motar yai sannan ya kwantar da kansa jikin kujera.
 Jalila cikin mamaki tace "gidan Goggo?"

Shiru yai har tana tunanin bazaiyi magana ba, cikin wata murya taji yace.

  " Jalila?"
A tsorace tace "naam."
Shiru ya sakeyi na wasu lokuta kafin yace " Zan fadamiki abinda ke damuna, abinda na aikata wanda a koda yaushe dana saninsa shike hanani sukuni, a duk sanda na tuno da abin ko cikin bacci ne nakan ji kamar nima na mutu, nakanji gaba daya duniyar ta zamarmin bakinkirin, nakanji komai na cikin duniyarnan ba abinda yake birgeni, zan sanar dake a gaban gidan mahaifiyarki idan harkinga bazaki iya zama dani ba, sai ki bude kofar ki shiga gida gun mahaifiyarki, in kuma har........."

 Sai yai shiru, dan bayasan yasa ransa akan abinda bazai samu ba.

 Shiru ne ya kara ratsa cikin motar, ita kam Jalila tayi tsuru tsuru.


 " Abdullah Taura shine mahaifina, tunda ya tafi karatu kasar Egypt suka rikeshi ya fara musu aiki a can, gaba daya mutum ne mai tsananin san aiki, hakan yasa ba ruwansa da mace balle aure.

 Ganin yanda bashida niyyar yin aure yasa mahaifinsa ya masa kamun mata, wacce take 'yace ta abokinsa.
 Amininsa ne tare suka taso, yanada 'ya'ya dayawa sai dai duk maza ne su uku ne mata.

 Babbar yarinyar Uwargidan ce, su kuma biyun matarsa ta tsakiya ce ta haifesu, dan matansa uku.

  Babbar tanada mijinta sai aka bashi ta tsakinyar mai suna Hauwa'u suna kiranta da Jidda.
 Daga can aka sashi ya dawo, yana zuwa ya ganta ya aminta da ita akai aure a sati biyu da zuwansa dan dama sun shirya komai, anayi ya dau matarsa suka koma garin Egypt.
 Bazaka taba tunanin auran hadi ne tsakaninsu ba dan suna kula da kaunar juna.

 Basu dade da aureba Allah ya bata ciki.
 Irin girman cikin yasa hankalin Taura ya tashi, ba shiri ya ajiye takarda akan yana bukatar hutu mai yawa suka taho.
 Gidansu ya kaita dan hankalinsa da nata sai yafi kwanciya.
 A lokacin da suka iso dama ana ta fama da bikin kanwarta, ganin yanda Yayarta ke shan wahala yasa sam hankalinta ya tashi, tana kuka muraran aka kaita gidan miji, haka aka gama biki lafiya ta tare, aka dukufa da mata rubutu da kula da ita, saboda cikin yasata ta kumbura sosai.
 Taura a koda yaushe yana gidan, kai abin makulashe, magani da duba jikinta, har Allah ya kawo lokaci.


  Satinta daya tana nakuda wanda ya kara wahalar da ita, aka dauketa aka kaita asibiti aka bata gado.
A wata ranar asabar aka yanke hukunci yi mata tiyata dan abin yaki karewa.
Kanwarta a rikice tazo asibitin dan labari ya kai mata, kuka kamar ranta zai fita, haka aka shiga da ita tiyata tana rike da hannun kanwarta.
 A dakin tiyata ana zaro 'ya'yan nan biyu ana kokarin yi mata dinki tace ga garinku nan.

  Tashin hankalin da suka fuskanta a asibitin nan ba'a magana.
Kowa ka gani hankalinsa a tashe yake, haka duk sanda aka kalli jariran nan biyu sai an zubar musu da hawaye.

 Haka aka kaita gidanta, Taura kamar zaiyi hauka, dauriya kawai yakeyi ba magana, dan inya tuno da jariran yaran nan wadanda ko ganinta basuyi ba sai aji hankalinsa ya tashi.

Kanwarta ita ke kula dasu dan ko gidanta bata koma ba, dayake mijinta shima na gida ne, a karshen layin ma ya kama gida.
Jin ance ta koma gidanta yasa tace itakam dasu zata tafi, duk yanda akaso ta hakura amma taki, kuka ma tasa tace itakam abarta dan bazata iya barinsu ba.
 Haka aka hakura ta tafi dasu, sai Taura ya hadata da kanwarsa wacce take shekara 14 suka tafi tana taimaka mata.

 Gaba daya Taura ya canza, kullum sai yaje ganin yaran nan hankalinsa ke kwanciya, kowa ya gansu bazai taba cewa basuda uwa ba dan sosai take kula dasu, kowa jinjina mata yakeyi dan yarinyace sannan ko haihuwar fari batai ba.

 Duk wani bukatunsu Taura ya dauke musu, sannan ya kasa komawa ma gun aikinsa.
 Har yaran nan suka shiga shekara guda, suka fara tafiya, kowa ya gansu abin sha'awa."

 Hassan yai ajiyar zuciya yace "A wata rana mahaifinta da mijinta sunyi tafiya sukai hatsari wanda ya dauki rayuwarsu.

 Taga tashin hankali ga mutuwar miji ga kula da yara biyu, sannan gashi batasan tanada karamin ciki ba.
 Gashi duk yanda akai yaran nan su barta taji da abinda ke damunta sunki dan su itace mahaifiyarsu ita kadai suka sani.
 Ita ma ta nemi a barsu, haka ta sha wahalar wannan lokaci duk ta rame ta fige.
 Taura tsananin tausayinta yasa ya umarci dauke yaran sai dai kuka tasa ta nemi a barmata wai mijinta ya tafi kar a rabata da 'ya'yanta.

  Haka ya bar mata su, har Allah ya kawo mata nata haihuwar ta haifi danta namiji aka sa mai Sageer."

  Ajiyar zuciya yai yace "Kin fahimci labari na kashe na farko?"

 Jalila wacce idanunta ke zubar da hawaye tace "Kune yaran kanana, sannan wacce ta rikeku wato kanwar mahaifiyarku Ummy ce???"

  Hassan yace "eh, Ummy ce."

 Haka muka taso mu uku, sai dai nu biyu mun girmi Sageer da shekara biyu, dangin mahaifinsa suka daukeshi saboda takaicin yanda take kula damu.

 Haka muna kuka aka tafi dashi, bayan mun dawo gidan mahaifanta ne aka yanke shawarar hada auransu.
 Da harta ki amincewa sai dai ganin za'a kwacemu yasa ta amince.

  Tunda take bata taba nuna tanasan akawo mata danta ba, duk kuwa da kowa yasan zuciyar uwa.
 Haka Abba ya daukemu muka koma Egypt, zamansu zama ne na kara bawai na aurataya ba, har a hankali suka fahimci mahimmancin junansu.

  Shekararmu takwas a garin muka dawo nigera, na taso da tsananin kaunar Ummy wanda ko hawaye ko damuwa naga tanayi sai na yi tayin kuka, ganin yanda take zama tai shiru wani sa'in tana kallan hoton Sageer yasa nai ta kuka nace a dawo Nigeria adauko mana shi.

  Tundaga lokacin Ummy ta ajiye hoton ta daina daukowa, shima Abba ganin haka yasa ya ajiye aikinsa muka dawo.
Husain nada magana sannan akwai saukin kai, muna tsananin san Ummy sai dai shakuwar dake tsakanina da ita daban ce.

 Muna dawowa nace Abba na yaje ya dauko Sageer.
Haka mukaje suka hanamu, gashi a kauye suke sun tubure akan dansu bazaiyi agola ba.
 Sai da Abba ya daukeni mukai zuwa kauyen nan sau kusan goma kafin su amince.

 Haka suka bamu shi muka kawoma Ummy shi, tayi kuka sosai dan bata taba tunanin za'a bata shi ba.

 A kuma lokacin ta dauki alkawarin bazata taba banbantamu da Sageer ba."

 Cikin tsananin mamaki Jalila ke jin wannan labarin, to meyasa Uncle yace bazai ko dan abinda su Hassan suka mai bazai iya musu butulci ba? Saboda daukoshi da sukai?

 Hassan yai shiru kafin ya dan runtse idanunsa, wani abu na ratsashi.........


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)



Trauma is defined by the American Psychological Association (APA) as the emotional response someone has to an extremely negative event. While trauma is a normal reaction to a horrible event, the effects can be so severe that they interfere with an individual's ability to live a normal life. In a case such as this, help may be needed to treat the stress and dysfunction caused by the traumatic event and to restore the individual to a state of emotional well-being.

 Some common sources of trauma include:

Rape
Domestic violence
Natural disasters
Severe illness or injury
The death of a loved one
Witnessing an act of violence e.t.c.

Idan muka duba abinda ke rubuce a sama, zai bamu damar cikaken fahimtar matsalar Hassan, Trauma na ganin mutuwar kaninsa da yake tsananin so sannan da Guilty na laifin da yake tunanin shine sanadiyar yin hakan, kafin na fara rubuta matsalolin Hassan sai danai bincike akan matsalar cutar Trauma wanda ke damunsa, na dauko bayanin sama ne saboda mu fahimci matsalarsa musan me ake nufi da wannan kalma ta Trauma, akwai mutane dayawa dake dauke da wannan matsalar sai dai bama damuwa da abinda ke damunsh saboda rashin sanin matsalarsu, wasu cikin bacci zakaga suna razana, wasu kansu ke daukar zafi, wasu duk sanda sukaga jini, duk wadannan na faruwa ne a yayin da sukai karo da wani mumunan abu wanda ya taba ayuwarsu yakan hanasu yin rayuwa yanda ya kamata.
Allah ya mana mai kyau ameen.....

*54*

  A hankali ya dago ya kalleta, itama ta bude idanunta.

 Kallansa tai sannan tai saurin saukar da idanunta kasa, ta zame daga jikinsa ta koma ta zauna akan kujera, karamin gyaran murya yai na burin kunya yace " zaki shiga ku gaisa da Goggo?"

 Bata kalleshi ba tace "a'a."
Tada mota yai sukai gaba, shiru ne ya ratsa motar ba wanda ya sake magana.

 Sunyi tafiya sosai, kafin ta daure tace " Yaushe kuma Ya Sageer din ya dawo?"

 Yace "Sageer? Bayan abin ya faru ne hankalin su Abba ya tashi shine suka nemi alfarma akan a dawo dashi, ko hankalina dana Ummy zai kwanta, dakyar dai suka amince."

 Ta dan kalleshi tace " Yaya na kasa fahimtar abu daya, me yasa kafi damuwa da Ummy kadai? Dan na kula yanda ka damu da Ummy baka damu da Abba ba."

 Kallanta yai sannan yace "haka kike gani?"
Tace "bani kadai ba hakan ne ma."
Shiru yai har kamar bazaiyi magana ba sai yace " Abba a koda yaushe in na ganshi nakanji tsananin tausayinsa, nine sillar rasa dansa da kuma dan kaninsa sai dai yanda yake nunamin so shine ke damuna, i have to be cold to him saboda ya rage damuwa dani, dan ban cancanci kaunar da yakemin ba, inasan ya rage san da yakemin ne saboda ko daga baya inyasan abinda ya faru bazai dameshi ba."

  Jalila ta kalleshi kawai sai jitai tayi dariya, kallan mamaki ya mata yace "dariyar menene?"
Tace "yaya, wallahi rashin sakarma mutane fuska da zama cikin mutane yasa gaba daya tunaninka daban ne, kana tunanin wai abinda kakemai na zafi zafi shine sai sa ya rage sanka? Ko ya rage damuwa dakai?"-

 Hassan ya kalleta cikin mamaki, tace "ashe ma gwara ni."
Fuska ya hade yace "gwara ke me?"
Tace shikenan.

 Shiru yai baice komai ba ta kara cewa "tab lalai yau naji abinda ban taba ji ba."

 Harararta ta yai yace "zaki cigaba ko?"
Ta rufe bakinta tace "bance komai ba."
Haka suka isa gida, suna isa suka shiga ciki, Abba na kallansu ta glass din falonsa, murmushi yai na jin dadi tare da godiya ga Allah.

  Suna shiga daki ta shiga toilet tai wanka saboda fashin sallah da takeyi, sannan ta fito ta dau bargo zata shimfida, kallanta yai yana zaune akan gadon yace "ki dawo nan ki kwanta yau ma a kasa zan kwana."

 Tace " a'a ka kwanta."

 Kallanta yai tace "in na kwana yau gobe ma anan zan kwana."
Yace "sanda na matsu da gadon sai na tureki na kwanta."

 Tadan hade rai kadan tace "bari na dau hijabina na tafi gidan Goggo kafin ma a tureni inji ciwo."
 Murmushi yai yace " wannan dai neman magana kike, matar dana kaiki har kofar gidan kikace bazaki iya rabuwa dani ba?"

 Baki ta bude cikin mamaki tace "a yaushe akai hakan?"
Yace "musawa zakiyi kenan?"

 Ta matso kan gadon wai ita a dole an ba ta mata rai ta kwanta tare da juya baya tace " wallahi na kula duk abinda banceba sai acemin nace."

  Kallan bayanta yai ya tuno abinda ya faru a mota, kallanta yai yace "to ko mu sanar da Goggo laifin da mukai?"
 Juyowa tai ta kalleshi tace "laifin me?"
Yace "na fitsarar da mukai......"

 Da sauri ta mike tasa hannu ta toshemai baki tace "yayah."
Kallanta yai sannan ya zare mata hannun data rufemai baki yace "yanzu yanda kika hau kaina me kike nufi?"

 Da sauri taja baya tace "wai ni yaya....."
Yace "wai a yaushe na zama yayanki ne?"

 Baki ta turo tace "to ni me kakeso nacema?"
Yace "oho amma ni bansan yayan nan."
 Tace " to naji ka daina tsokanata."

 Fuska ya hade yace "a yaushe na tsokaneki? Bakiyi rashin kunyar bane? Ko yanzu baki hau kaina ba?"

 Tace "kaine fa ka jawoni kamin kiss sannan yanzu bafa kanka na hau ba."

 Kansa ya juyar gefe yace "ni? Kin tabbatar bake kika fara ba?"
Ta saki baki tace "yaya tanan ka bulo? Su biyu fa kenan kana min haka."

  Murmushi ya sake yi.
Da sauri tace "yaya kayi murmushi wlh."

 Shiru yai yana kallanta sai dai yanayin fuskarsa ya canza yace "Jalila!"

 Gyara zama tai a hankali tace "naam."

 Yace "nagode."
Kallansa tai cikin mamaki, yace "zan sanar ma Abba komai, ko tsanata zaiyi ko hukuntani zaiyi zan dau komai, nagode da kika budemin zuciyata kika nunamin rayuwar daya kamata nai."

  Kallan rashin fahimta tamai tace "ni?"

  Yace "kin tabbatar zaki jure ganina a kasa?"
Tace "kamar ya?"
Yace "duk girman gadon nan sai na sauka?"
Tace "tare zamu kwana?"
Yace "ba haka kikeso ba dama?"
Tace "yaushe nace?"
Yai ajiyar zuciya yace "yanzu abinda na gani kenan kin fada a fuskarku."

  Tai tagumi tace "oh ni."

  Kwanciya yai ya dau littafinsa yace "ba abinda zan miki in ma shi kike tunani, tunda dai har kikai fitsara a gidan goggo ai kwana tare ba zai zama issue ba."

 Jalila tai dariya tace "wallahi yaya na fahimci kawai so kake kai ta zolaya ta."

 Bai amsa mata ba ya fara karatu, kwanciya tai daga can karshe tace "wai yaya mai kake karantawa haka kullum?"
Yace "kawai karantawa nake nai ta tisawa ina san dauke tunani daga raina."

 Shiru tai tana kallansa, yace "inkingama kallan nawa sai kiyi bacci."
Da sauri ta rufe idanunta a haka har bacci ya dauketa.

 Bargo ya ware ya luluba mata sannan ya kura mata ido yana kallo, Jalila! Jalila! Nagode da amincewa da kikai dani.
Murmushi ne ya sake bayyana a fuskarsa, sannan yai shiru yana tunanin Abba da Ummy dasu Sageer, gobe zai sanar dasu komai ya kuma nemi yafiyarsu, kome zasumai gani yake zai dauka tunda tana tare dashi.

  Sai can ya kwanta yai bacci, bacci mai dadi yai wanda shikansa bai sani ba,bai farka ba sai biyar saura, wanda raban dayai irin baccin nan ya dade, addu'oi yai tayi da neman yafiya har gari yai haske kafin ya dawo ya kwanta, yaso tashinta tayi karatu amma yabarya saboda ganin yanda take bacci.


*********
Wajen karfe 9 suna aiki da Ummy a kitchen akai sallama, Sageer dake kallo a falo ya bude kofar, mamaki ne ya kamashi ganin Inna da Mumy.

  Inna tace "Taura harya fita?"

Ya daure ya gaisheta kafin yace "yana nan."

 Tace "ko zaka sanar dashi?"

 Muryar Ummy yaji tace "Sageer wanene?"

 Sageer yace " Matar gidansu baban Jalila ce."

  Ummy tace "matar me?"

 Yana kallansu yace "kishiyar Goggo."

Ummy tace oh Sageer akwai tsiya, kallan Jalila tai wacce tai tsuru tsuru, Ummy ta dafata tace "kin manta a inda kike ne?"
 Kallan Ummy tai sannan tai murmushi tare da girgiza kai.

 Ummy tace "shigo dasu mana." Sannan ta wanke hannu ta fito, a falo suka zauna.

  Ummy ta karaso suka gaisa duk jikinsu a sanyaye.

 Inna ta daure tace "Hajiya dan Allah a mana magana da Taura."

 Ummy ta kalli Sageer tace "Sageer kira Abbanka."

 Mikewa yai ya nufi falonsa.

 Aiki yakeyi sanda ya shiga nan ya sanar dashi, Abba yace yana zuwa.

 Jalila kam aikinta ta cigaba, tanaji harsanda Abba ya shigo.

 Inna ta gaidashi kamar irin itace karama, Mumy ma ta gaisheshi.
 Zama yai yace "lafiya? Da safen nan?"


Inna ta murmusa tace "dama munzo ne muyi bayani."
Yace "bayani?"
Tace "munsan kunsan komai akan abinda muka aikata."
Yace "sai akai yaya?"

Tace "laifinane, sai dai ina baka hakuri, muci darajar marigayi karka kwace kudinka."

Abba ya kalleta kamar zaiyi magana sai yace "Sageer yima yayanka magana."

Inna najin haka gabanta ya fadi, ita kanta Mumy hankalinta ya tashi tace "ai ba sai yazo ba, hakuri mukazo badawa."

 Abba yace "na sani kuma na fahimta, matarsa ce wacce kuka wahalar kuka nemi tozartawa, hakkinsane ya yafe muku ko yaki, sannan ita yarinyar ita zaku ba hakuri ba ni ba, idan har yarinyar da mijinta sun yafe muku banaji ni inada matsala."

 A ran Inna tace nasan Jalila batada matsala, babbar matsalar yaran nan......

  ***********

  Kallansa tai tace "me kake nufi RAM?
Yace "haba Safeena ke sai yaushe ne zaki bar gidadanci? Baki kula duk mutane ba wanda yakesan harka dake ba saboda kauyancin da kike nunawa?"

  Shiru tai tana kallansa kafin tace "To ya kakeso nayi wai?"

Yace "ki tashi dalla ki canza wannan shirmen na jikinki kisa wando da riga ki bar ragowar a hannuna, ni zan maidake fitaciya a skul din nan."

Kallansa tai cikin gamsuwa sannan ta kike........


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯
Written By : *AYUSHER MUHD*
✔️ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_💡)
*55*
Sageer ne yamai knocking, yana zaune a kasan carpet yayi shiru yana nazarin dayake damunsa.
Mikewa yai da sauri yace "shigo mana."
Sageer ne ya shigo ya kalleshi yace "yaya ashe ka tashi?"
Yace "na tashi tun dazu, inzo ne?"
Mamaki ne ya kama Sageer ya girgiza kai yana murmushi yace "baki kayi."
Cikin alamar mamaki yace "baki?"
Yace "eh daga gidan su Jalila."
Da sauri yace "Goggo ce?" A ransa yana fatan badai ta gansu ba? Da sauri yace inta ganmu sai tazo? Shikanshi ya fahimci wannan bai bada ma'ana ba, kafin yai magana Sageer yace "matar gidansu babanta ce da yarta."
Cikin rashin fahimta yace "bangane hausar ba."
Sageer zai sake magana Hassan ya kalleshi, bai san sanda ya sa dariya ba yace "Tab amma lalai Sageer matar gidansu babanta?"
Mamaki ne ya kama Sageer yaya ne anya kuwa?
Hassan ya fahimci yanayin da Sageer ya shiga sai ya dan hade rai kadan ya matso kusa dashi kafadarsa ya dafa, yace "Me kake tunani?"
Sageer yai murmushi yace "kawai ina mamaki ne, banaji tunda nake na taba ganin kana dariya haka ba."
Yace "ni kaina na dade banyi dariya haka ba, kai ne yanda kai maganar ne banma san sanda dariya ta zomin ba."
Sageer ya kura mai ido cikin jin dadi, yana hamdala aransa.
Hassan ya juyarmai da kansa gefe yace " muje."
Murmushi Sageer yai sannan suka fito, tare suka sauko.
Ummy tana zaune a falo ta hangosu, tunda suka taho ta zuba musu ido cikin jin dadin ganinsu tare, karasowa sukai Hassan ya hade fuska gam, ya zauna daga kusa da Ummy.
Sai daya gaishe da Abba ya gaisheta sannan ya kallesu ya gaishesu a wani irin yanayi da inhar kana gurin sai ka dara.
Sageer ya juya kai yana guntse dariyarsa, Inna ta amsa cikin fara'a tace " sannu Malam Hassan, ina Jalilan tamu?"
Bai amsa mata ba yace "Abba ance inzo nayi baki."
Abba yace "bakin a sunan naka ne amma gun matarka sukazo."
Hassan ya juya bai ganta ba, Ummy tamai alama da tana kitchen, kallansu yai yace "ayya, wani abun ne ya faru?"
Inna ganin yanda yai magana yasa hankalinta yadan kwanta tace "Hassan nasan zakuyi tunanin cutarku mukai muka yaudareku sai dai maganar gaskiya ba haka bane, duk laifin nan nawa ne, ganin yanda Taura ya taimakemu ne yasa nai zauna nai tunani, Safeena bata dace da sirikar Taura ba, yarinyace mai san jikinta, gashi bata iya ko girki ba, ni kuma ina tun.........."
Hassan ne ya katseta yace "Tambaya nai kawai wani abun ne?"
Inna ta kalleshi, Mumy tai murmushi tace "ba wani abun bane, ita Inna tana tunanin bata kyauta ba gun yaudarar da muka muku shine mukazo neman yafiya, da neman taimako akan karku kwace kudinku."
Hassan ya kalli Abba yace " kudi na Abba ne ra'ayinsa ne ya kwace ko ya barku, ita kuma Jalila da mahaifiyarta da kukama laifi su zaku nemi yafiya agunsu ba mu ba, sannan na tabbatar wannan neman yafiyar bawai anzo yinshi bane saboda zuciya ta saduda anzo ne saboda ana san duniya."
Ya kalli Abba bai jira amsarsu ba yace "Kafin su nemi yafiya a gunka ina tunanin me zai hana a kudinmu na company dinsu mu sai share dashi? Kaga muma ya zamana munada iko akan su, saboda ni gaba daya mutanen nan basumin ba."
Ummy ce tai saurin tabashi, ya kalli su Inna ya kalli Mumy sannan ya kalli Abba yace " duk wani tunani da kukeyi akan mutanen nan sun wuce nan, ku duba abinda sukama Goggo da Jalila."Inna tace "munsani abinda muka aikata bai dace ba."
Hassan yace " Ina shi mutumin yake?"
Mumy tace "mutumin wa kenan?"
Sageer yace "mahaifinta? Bashine ya dace ya fara zuwa ba?"
Mumy tai saurin cewa "yayi tafiya ne."
Hassan yace " ohhh!"
Inna ta kasa dakai tace "na sani mu masu laifine agareku sosai, sai dai ya zamuyi? Shi mahaifinta bai taba nuna ya damu da ita ba, bai taba nuna mana damuwarsa akan matar data haifeta ba, sai dai yana neman yanzu na sakar mai ma company din, to ni ina tunanin kudinka dake ciki......."
Abba yai shiru yana kallan Inna wato a wayau tana nunamai ba fa sune masu laifi ba tsohon tane, ai in suka fahimci hakan sa dau mataki akanshi.
Sageer ya kalli Abba yace "dama ai duk mai laifin mahaifinta ne."
Abba yai shiru yana kallanta, tana ci gaba da bayani, akan yanda Dady ya banzatar da Jalila da Goggo.
Hassan kam mikewa yai ya bar falon.
Me Ummy zata gani? Gani tai ya nufi kitchen mamaki ne ya kamata sai dai wani farinciki ne ya shiga ratsata.
Cikin kitchen din ya shiga, tana vegetables a tukunya ya shiga.
A bakin kofa ya tsaya yana kallanta, juyawa kawai take amma hankalinta na falo, jin alamun mutum yasa ta kalli bakin kofa.
Hassan na ganin ta juyo ya shigo kitchen din da sauri kamar ma wai baisan tana ciki ba.
Kallansa tai da sauri ta matso cikin zumudi tace "yaya ya kukai? Sun tafi?"
Yace "ke meya hanaki zuwa?"
Tace "kawai, banasan ganinsu."
Yace "kin tabbatar ba tsoro ne ya hanaki ba?"
Tace "ba wani tsoro ni kawai........"
Kai ya shiga jijigawa wai alamar ya fahimta irin na wulakancin nan.
Tadan kalleshi fuskarta a hade tace "kaifa? Abu ka shigo yi?"
Ya kalleta yace "me? Kina tunanin gunki nazo?"
Tace "bance ba." Tai maganar cikin sanyin jiki.
Yace "ah to gwara dai ki fuskanci reality."
Baki ta dan turo ta juya ta cigaba da suya, Hassan ya kalleta hankalinsa ya kwanta ya dauka ganinsu ya sata cikin wani hali.
Fridge ya bude yadan sha ruwa kadan dan karta gane, yanayi yana kallanta amma yaga ko kallansa bata sakeyi ba.
Da karfi ya buga murfin fridge din, juyota tai ta kalleshi.
Yace "wani irin fridge ne wannan? Daga sakeshi sai ya tafi?"
Tace "anya kuwa ba kai ka buga shi ba, naga ne baya haka."
Hassan ya kalleta yace " akan me zan nemi hucewa akan fridge? Laifi akamin?"
Tace "ina na sani?"
Juyawa yai ya fita yana cewa "ke dai da kike tsoro sai ki karashi zama a ciki."
Tana neman magana ya fita, haushi ne ya kamata ta kashe gas din ta biyoshi.
Yana shiga falon itama tana shiga, da Sageer suka fara hada ido, tai saurin daukewa sannan ta karaso.
Hassan na zama yaga shigowarta, murmushi yai a ransa ta shiga ta zauna a kasa daga gefe, ta gaida Inna da Mumy.
Inna cikin sanyin murya tace "Jalila ki yafemana abinda muka aikata miki."
Mumy ma tace "kiyi hakuri Jalila, bamu kyauta ba."
Kallan Hassan tadan yi taga ko kallanta ma bayayi tace " ya wuce."
Kallanta yai, itama ta kalleshi, ta maida kanta kasa, ganin zaman nasu ba so ake ba yasa sukaitama Jalila dasu Abba godiya, dan Abba yace zaibar kudin zuwa wani lokaci.
Haka suka fito suka shiga motarsu suka tafi.Abba na shirin barin falon Hassan yace "Abba!"
Abba ya kalleshi yace "Hassan da magana ne?"
Hassan ya daga kai yace "dukanku, magana zamuyi."
Ummy cikin mamaki ta kalleshi, shima Abba kallansa yai.
Jalila ta juya zata fita, da sauri yace "Jalilah."
Cak ta tsaya saboda yanda ya kira sunanta, ya kata alama data dawo falon.
Komowa tai ta zauna, bayaji zai iya jawabin nan ba tare datana kusa ba.
Falon yadanyi shiru, Sageer na zaune shima, Hassan ya fara da cewa "Abba kayi hakuri ka yafemin, duk wani hukunci da zakamin zan dauka ko menene shi kuwa, sai dai ina neman yafiyarka a gareni."
Jikin Abba ne yai sanyi yace "rabuwa kakesanyi da matarka?"
Hassan ya kalleshi yace "Abba Husain...."
Ummy ce ta kalleshi da sauri tace "Hassan."
Kallan Ummy yai ya saki wani sansanyan murmushi yace "Ummy nine sanadiyar mutuwarsu."
Ummy da Abba a tare sukace bangane ba???
Jalila kam Hassan kawai take kallo sai idanunta da suka ciciko da kwalla.......
Hassan yace " a ranar sunan Ameera............"
Nan ya kwashe komai ya sanar dasu, gaba daya falon hankalinsu ya tashi najin abinda ke faruwa, sai dai Hassan nakaiwa karshe bai jira amsar wani daga cikinsu ba ya tashi da sauri ya hau sama, Ummy na kiransa ko juyowa baiyi ba.
Jalila ta mike da sauri tahau sama, yana shiga itama ta shiga.
A bakin gado ta ganshi yana neman zama, hannunsa ta riko da sauri tace "Yaya"
Da sauri ya jawota jikinsa ya rungume tsam, zuciyarsa na wani irin bugawa, yanda ya kankameta ne yasa tai shiru, cikin wata irin murya yace "Wani hali Abba zai shiga? Yaji dansa ne yai sanadiyar......"
Kasa karasawa yai saboda raunin da zuciyarsa ke neman yi, Jalila tace "Yaya wanda bai sanka ba inya ganka zaiyi tunanin zuciyarka rike take gam, ba tausayi a cikinta, sai dai wanda ya zauna dakai a hankali zai fahimci zuciyarka cike take fam da tausayi."
Yace "ke tausayi hakan yai miki kama?"
Tace "sosai zuciyarka saboda tsananin tausayinta ne yasa take zargin kanta da aikata laifin da ba ita ta aikata ba."
Hassan yace "ya isa haka nan Jalila, na san kina fadar hakan ne dan hankalina ya kwanta, please keep quiet."
Shiru tai sai dai haryanzu bai saketa ba, Sageer wanda hankalinsa ya tashi ya taso da sauri ya gansu a haka a cikin dakin, juyowa yai jiki a sanyaye fuskarsa na dauke da murmushi a ransa.
Yana saukowa Ummy tace "Sageer ina Hassan din?"
Yasan yanda Ummy ke tsananin san Hassan, yace "karki damu Ummy matarsa na gunsa."
Komawa tai ta zauna ta kalleshi, yace "Abba fa?"
Tace "ya shiga daki."
Sageer ya zauna a kusa da ita yace "Ummy kinsani ko kema sai yanzu?"
Ta share kwallarta tace "bantaba sani ba, Sageer Hassan haka yai shekara sama da 15 cikin zargin kansa?"
Sageer cikin tausayawa yace " Ummy ni nama rasa me zance."
Shiru sukai suma........
Hassan kam ya dade manne da ita kafin daga baya ya saketa, kallanta yai sannan yace "na matseki ko?"
Tai murmushi tace " to ni yanzu yaya wace amsa kakeso na baka?"
Zama yai a kan gado sai kuma ya kwanta baice komai ba, harta juya zata sauka saboda girkin da ta kashe taji yace " Jalilah!"
Juyowa tai ta kalleshi sai dai sanyin jiki yasa ta kasa amsawa, yace " kina tunanin hankalin Abba zai kwanta?"
Tace "shima Abba zai fahimci ba laifinka bane ba."
Yace "nagode."
Kallansa tai sannan ta fito.
********
Dady ne ya kalli Mumy yace "ya kukai?"
Tace "ni wlh gaba daya na kasa fahimtar takamaimai abinda ya faru a gidan."
Dady haushi ya kamashi, amma ya murmusa yace " amma kina tunanin sunji haushina?"
Tace " ai dukanmu ma ko kamanta Goggo na gunsu? Na tabbatar sunsan komai."
Dady yai dan tsaki a ransa yace dolene ya je ya lalaba Jalila ai dama ba mai shiga tsakanin jini? Yana zuwa zaisan yanda zaiyi ta yafemai......
#OneLuv💕
*_🗯JALILAH!!🗯_*
Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on wattpad : *Ayusher Mohd*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_💡)
*Gaisuwa gareki BillynAbdul akoda yaushe ina miki fatan alkairi arayuwarki......*
*56*
Damuwa da rashin sukuni suka saka hassan gaba, gakuma jalilah tafice tabarsa shikad'ai a d'akin, jiki a sanyaye yasakko daga gadon, yad'auki wayarsa da key yafice.
****
Su Ummy nazaune haryanzu a parlor itada Sageer, bai kalli inda sukeba yafice da sauri, dan kunyar had'a ido yakeyi da Ummy.
Da sauri Ummy ta yunk'ura zata bishi amma Sageer ya rik'e hannunta da sauri, juyowa tayi ta kalli sageer d'in, idonta harya fara tara kwallah, Sageer ya girgiza mata kansa,
"A'a Ummy kibarshi"
Ummy ta kalli hanyar daya fita tace "Yaza kace Na barshi Sageer? bakaga a yanayin daya fita bane?".
Sageer ya kalleta yace "Nagani Ummy hakan ne ma yasa nace ki barshi, addu'a kawai zamu mai."
Shiru Ummy tayi takasa magana.
Fad'uwar Abu dasuka jiyo a kitchen ya sakasu juyawa su duka suna kallon kofar kitchen d'in, sai kuma suka tafi kitchen d'in a tare.
Shigowar su tasaka jalilah dake tsuggune tana kwashe fasashshen kofin daya silmiyo daga hannunta wanda ya fashe haryasa su Ummy sukajiyo yasata d'ogowa tana kallonsu.
Da sauri Ummy ta k'araso gareta tana fad'in "bakiji ciwoba ko jalilah!?".
Kai jalilah ta girgiza mata alamar a'a sannan tace
" a'a Ummy, banji ciwoba".
Ganin haka sai Sageer yajuya yafita.
Jalila tad'an bishi da kallo, kafin tadawo da kallonta kan Ummy dake mata magana.
"Jalilah mijinki fa?".
K'asa tayi da kanta cikin kunya tace " Ummy yana d'aki".
"Baya d'aki gaskiya, dan yanzu yafita nama zata kema kina d'akin aii? Sam ban kula da saukowarki ba."
Cikin d'an zaro ido waje na alamun tsorata Jalilah tace, "Ummy yanzufa nafito, nabarshi a d'akin a kwance, naga kuna magana ne da ya Sageer, shiyyasa na taho nan banyi magana ba".
K'aramar ajiyar zuciya Ummy ta sauke, sannan tace,
"Amma a wanne hali kika barshi? Ni na kasa ganewa."
Jingina sosai Jalila tad'an karayi da fridge din dake bayanta, tareda murza tafin hannunta na dama.
"Ummy ki kwantar da hankalinki, babu wata damuwa wallahi, wannan fitarma k'ilan akwai zaman cikin ne ya isheshi".
Ajiyar zuciya mai k'arfi Ummy ta sauke, sannan tak'arasa inda Jalila take tsaye, hannunta datake murzawa ta kamo, dan zatonta ko Jalila taji ciwone da kofin data fasa".
"Ummy babu komai fa, ba ciwo najiba".
Murmushi Ummy tayi, "ai nazata ciwone kike boyemin, bara nataya ki mu k'arasa girkin".
Da sauri tace "Ummy kibarshi na k'arasa dan Allah kije kawai ki huta".
"A'a, muk'arasa kawai, kafin mijinki yadawo".
Shiru jalilah tayi saboda kunya, a tsanake suka gama komai, Ummu dai tausayin Hassan duk ya dameta, sai da taga sun kusa gamawa sannan tafito Jalila ta k'arasa.
Babu kowa a falon, Sageer ma ya shige d'akinsa. Ganin haka sai Ummy tanufi wajen Abbah, dan duba halin dayake ciki.
Bayan jalilah ta kammala komai ta d'auki abincin su ta haye sama.Ajiye tiren tayi, sannan ta d'an gyara gadon dasuka bata d'azun, gefen zuciyarta na tunanin ina Yaya yaje? itadai tasan lafiya lau tafita tabarsa, to miya fasu ne?.
Haka taita 'yan tunane tunanenta harta kammala, tashiga toilet tayo wanka, a gaggauce tafito ta shirya, dan batason Yaya yashigo ya ganta ba kaya kamar rannan.
Babu maganar kwalliya a tsarin jalilah, tasaka doguwar riga ta material, d'as takama jikinta, ta d'aura d'an kwalinta simple, harta bar jikin mirror sai kuma tadawo, ta d'auki turare tana fesawa, abisa tsautsayi kuwa ta fesowa fuskarta, sai cikin idonta Na haggu.
Karamar kara tasaki, tareda saurin rufe idon da hannu daya, dayan hannun kuma tana yarfawa tare da kiran "wayyo Goggona".
A haka Hassan yashigo dakin ya sameta.
Kallo yabita dashi, ganin yadda take tsalle-tsalle taki tsayawa waje daya saita bashi dariya, amma bai yiba ya zauna bakin gadon tareda ajiye key da wayarsa agefe.
Jalilah batasan dashiba, dan kokad'an bataji shigowar saba, sai tsalle-tsallen ta takeyi tana shiiiiii da baki, har yanzu hannunta dafe da idon, d'ayan kuma tana yayyarfashi, lokaci-lokaci takance "wayyo Gwaggona, Goggo kizo na makance".
Tausayi tafara bashi, yabita da kallo daga sama har k'asa, sai yanzu yalura da gwangwanin turaren dake k'asa a yashe, da alama shine tasama idonta.
Da sauri ya mike ya matso kusa da ita, sannan yakai hannu yariko hannunta datake yayyarfawa.
Tsorata tayi, tace, " Wayyo Allah na, wanene?".
Bai bata amsaba, suka je kusa da gado ya zauna, jawota yayi ta fad'o jikinsa saman cinyarsa.
Jiyayi wani mugun shock ya shigesa, har sai da yad'an rintse idonsa. Itakam jalilah k'amshin turarensa yasa tagane shine, dan haka saita nutsu, tabar mutsu-mutsun datakeyi.
Hannunta data rufe idon yajanye, ya kwanto da kanta saman k'irjinsa, yasaka hannunsa d'aya ya bud'e idon da k'yau, d'ayan kuma ya tallafo kanta sosai, sannan yafara hure mata a hankali, idon yayi jawur kuwa.
Yanda yake matanne yasakata yin luf ajikin sa, gakuma k'amshin turarensa mai dadi tana shaka.
Ya dad'e yana hura mata idon, sai da ya tabbatar ya huce sannan ya daina hurawar, amma yaki sakinta.
Bud'e idon tayi ahankali ta saukesu akansa, ganin ita yake kallo saita d'anyi k'asa da idanunta, a hankali ta furta "Na gode yaya".
" Uhhm".
Kawai yace mata, sai kuma ya k'ara hura mata iska a fuska.
Ta bud'e idon sosai tana kallonsa.
Da ido ya nuna kanta dake kwance a k'irjinsa, sai kuma yace, "A nan zaki kwana?".
Baki ta d'an turo gaba, ta yunk'ura zata tashi, amma saita kasa, saboda har yanzu yana rik'e da ita.
A shagwabe tace, "to taya zan tashi? bayan kamin d'aurin goro".
Firicin nata yasakashi sakin guntun murmushi, ya janye hannunsa batareda ya tanka ba.
Kanta kawai ta cire daga k'irjinsa, amma bata tashi a cinyarsa ba tace "Yaya wai ina kaje?"
"idan kin gama more cinyar itama saiki d'aga, idan kuma zaki biyane to?."
Baki takuma turowa, ta yunk'ura zata tashi tana k'unkuni
Harta mik'e yarik'o hannunta ya dawo da ita.
"Ah ah, mikuma nai?"
Hannunsa duk biyu yasaka ya zagayeta dasu, yakawo bakinsa kusada kunnenta."kina son sanine?".
Juyowa tayi ta kallesa da sauri, amma batace komaiba, saboda gabanta dake faduwa.
Ya huramata iskar bakinsa a fuska, yana kallon idonta dayay ja yak'ara d'an girma.
Yace "kin tabbatar ba saboda ki zauna kika sa turare a idan naki ba?"
Kallansa tai ta hade fuska tace "Yaya wai......."
Kauda kanta tayi, zuciyarta tana mamakinsa....
Barakai k'arshen tunanin taba taji yasaka hannun damarsa yadawo da fuskarta saitinshi.
Kafin tasamu damar magana taji bakinsa kan labanta.
Waro idanunta tayi saboda mamaki, shima ya waro nasa sosai kamar yanda tayi, sannan yahad'e bakin nasu sosai.
***********
Ummy kuwa koda tashiga d'aki sai ta tadda Abba zaune yana duba wasu takardu, shiru tayi nad'an wani lokaci tana nazarinsa, kafin tayi sallama. ya d'ago idanu yad'an kallrta ya amsa sallamar tata.
Suka d'anyi shiru zuwa 2minutes. Abba yakatse shirun da fad'in "Hassan fa?".
Sanyi Ummy taji aranta kafin tace, " yana lafiya. dama zan sanarma lokacin salla yayi".
Kansa ya jinjina mata, ya ajiye takardun hannunsa yamik'e zuwa bathroom. ita kuma zama tayi abakin gadon tana binsa da kallo, takasa tantance yanayin dayake ciki gaba d'aya. babu dad'ewa yafito, baiko kalleta ba yace, "naje masallaci".
"Adawo lafiya".
Ummy tafad'a tana mik'ewa tashiga toilet d'in domin d'auro alwala itama.
**********
Tunda suka dawo inna takasa zaune takasa tsaye, maganar family d'in Taura kawai take juyawa a zuciyarta, gakuma dadyn jalilah a gefe daya zame mata k'ayar kifi a mak'oshi, Tarawa wace hanya zatabi 'yarta ta fahimci manufarsa.
K'aramin tsaki taja, kafin ta zauna tareda d'aukar wayarta tana dannawa alamar akwai abinda take nema.
" humm" tafad'a tarefa ajiye wayar tana mik'ewa, sai kuma tace, " dukanku nasan hanyar dazanbi nai maganinku aii"
Ni dai nace, "humm".
************
Sun kai adadin wasu mintuna Hassan na baje kolinsa, kafin yacire bakinsa yana guntun murmushi.
Jalila kam kunya tasakata sinne kanta a jikinsa, sai kuma ta zame ta sauka daga cinyarsa takoma kan gado, bai ce komaiba shima yamik'e bayan yakai dubansa ga agogon dake d'akin.
Kallonta yad'anyi ya kauda kai, yanayinsa ne ya canza ya kalleta yace "Jalilah! Har yanzu Abba baice komai ba, kinganshi ne?
Shiru tayi tana kallonsa, shikuma yacigaba da tafiya.
Saida yakama k'ofar toilet d'insu zai bud'e sannan yajiyo muryarta tana cewa "amma Yaya kaimafa nakula matsoraci ne, a haka kamar....."
Kallan daya mata ne yasa tai dif tana sinne kai, fuska ya hade ya nuna kansa da d'an yatsa "ni ne matsoracin?"
Dariya tayi kawai, amma batace komaiba.
Ya jinjina kansa sannan ya ida bud'e k'ofar yana fad'in "lokaci zai nuna a gane wanene matsoraci tsakanin ni da ke yarinya"
Bataji miyaceba sosai, Dan acikin toilet ya k'arasa sauran maganar, babu dad'ewa yafito yana gyara hannun rigarsa alamar yayo alwala, itama alwalar ta tashi tai, dan dazu tai wanka, ita dama bata dadewa intana period.
Lokacin data fito shi harya fara salla, itama saita shinfid'a abin sallah abayansa ta fara tata.
Bayan sun idar ta kalleshi yana zaune inda yai sallar, yayi shiru alamar yatafi duniyar tunani, a wani halin Abbansa yake ciki?
Daurewa tai cikin k'arfin hali tace "Yaya nakawo abinci"
Kansa ya jinjina mata batareda ya kalleta ba ta mik'e tana cire hijjabin jikinta, kafin ta d'akko tiren ta dire a gabansa, yauma bayan tagama zuba masa, harta janyo wani plate d'in zata zubama kanta yarik'e hannun, daga ita harshi suka kalli junansu a tare, sai kuma yasaki ya ture plate d'in gefe, ya d'auki d'ayan spoon d'in yasaka a inda tazuba abincin.
Sai da yafara ci sannan itama tafara cin, babu mai magana acikinsu, har sukai rabin abincin.
Sai can jalilah tace, "Yaya mizai hana ka fara gwada shiga masallaci cikin mutane yin jam'i?"
Ido yad'ago yad'an kalleta, baice komaiba har suka kammala, har ta d'auka bazai ce komai ba. tana tattare kwanikan taji yace "Kina tunanin zan iya?"
Kallansa tai jiki a sanyaye, yace "a koda yaushe inaga taron mutane sai naga kamar lokacin da mutane suka taru akan su Husain."
Shiru tai kafin tace "banyi tunanin hakan ba n......"
Yai saurin cewa "I won't stay like this forever, nagode da shawararki sallah cikin mutane tafi lada."
Kallansa tai cikin jin dadi tace "tam Yaya."
"Humm" ya fad'a yana mik'ewa, kayan jikinsa yafara k'ok'arin cirewa, dan haka Jalila tayi saurin d'aukar tiren tafice.
Binta yayi da kallo, ya d'an saki guntun murmushi, sai kuma ya lumshe idanunsa, ahankali ya furta " kin cancanta jalilah ".
Ni kam danake labe nad'an dara kad'an.😅
*************
Har washe gari Abbah baice komai gameda zancen da Hassan yay masaba, wannan ne yakuma saka Hassan cikin matuk'ar damuwa, amma kasancewar Jalila a gefensa zuciyarsa tana d'an rage nauyi.
Ita kanta Ummy shirun na Abba ya dameta, duk da bai canza fuska ba, amma yanda ya share maganar sai lamarin yake nuk'urk'usarta.
Sageer ma daya kasa daurewa sai da ya tambayeta mi Abban yace gameda maganar jiya.
"Sageer baice komai ba fa, nikaina abin ya dameni, gashi bansan wane hali Hassan yake cikiba, naga har yanzu matarsa bata fitoba".
Ya sageer ya ja ajiyar zuciya, sai kuma yace "insha ALLAHU babu abinda yafaru Ummy, bara muga zuwa 9 idan bata sakkoba sai a bincika"
Ta kalli Sageer cikin jin dadi tace to Sageer.
Ummy batace komai ba tacigaba da aikinta, amma zuciyarta sai sak'e-sak'e take mata akan Hassan da kuma shirun Abbah. tare sukayi komai da Sageer.
*************
Safeena ta kalli RAM tace "ina ne nan din?"
Yace shiga ki gani, tura kofar tai, yan mata ne da maza kowa yasha kaya na duniyanci suna ta cashewa.
Da sauri ta kalleshi tace "menene hakan?"
Yace "baki gane ba? Wannan shine rayuwa ai."
Ta kallesu sannan ta kalleshi da sauri ta juya da gudu tana girgiza kai, yanda taga mata na rungume maza ba kunya? Ina zata iya shiga tai abin nan?
Daki ta shiga ta fada kan gado tana kuka da kiran sunan Inna da Mumy da Dady..........
Nace hmmmmm
#OneLuv💕
*_🗯JALILAH!!🗯_*

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on wattpad : *Ayusher Mohd*


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)


*57*

  
  Har 9 tawuce babu jalilah babu labarinta. Su Ummy suka kammala aiki tsaf itada Sageer, ko ya Ummy taji motsi saita waiga, azatonta jalilah ce.
 Shi kansa Sageer hankalinsa yafara tashi, yana daurewane kawai saboda karya k'ara tada hankalin Ummy.

A can kuwa bangaren su jalilah ciwon Hassan ne ya motsa, saboda damuwar daya kwanta dashi a zuciyarsa, akan shiru da Abba yai akan maganar su Husain, gani yake maganar tazama gaskiya shine silar barinsu duniya, shiyyasa Abba yake fushi dashi, dama Jalilah tana fad'an bahaka bane saboda kawai ta kwantar masa da hankali.

Cikin dare sau biyu ciwon natashi, shi yasa sam jiya basuyi wani barcin kirkiba, sunayin sallah da asuba kuma suka kuma kwantawa dansu rage barci.

Dama Hassan jiya a k'asa ya kwanta, duk yanda Jalilah taso yadawo saman gado bai dawo ba.
  Bayan sunyi sallar asubahi ma a k'asa ya kwanta akan sallayar dayai sallah, can cikin barci Jalilah tadinga jiyo kakarinsa, a zabure ta mike cikin tsoro ta kalli inda ya kwanta.

A razane ta sakko kusa dashi ta tsugunna agabansa, hannuwansa daya rik'e wuyansa itama ta rik'e tana kiran "Yaya! Yaya! Innalillahi please Yaya katashi."

  Gaba daya ya canza, abin ya tsorata ta, yau kam ciwon yamafi na kullum tsanani, dan jikinsa har rawa yakeyi, kansa tad'aga ta d'ora a cinyarta tana kuka da tofa masa abinda tasani, tun tana d'aukar lamarin k'arami sai taga yawuce tunaninta, da ciwon yayi kamar zai lafa saikuma jikinsa yafara rawa yakuma damk'e wuyansa yana jawo numfashi da k'yar.

  Tanaso tatshi taje takira su Ummy amma takasa, bazata iya fita tabarshi shi kad'aiba, dabara ce tazo mata data hango wayarta, da k'yar tamik'a hannu ta d'auka, tashiga laluben number Ummy.

 Jikin Ummy har rawa yakeyi wajen d'aukar wayar. Saboda ganin number Jalilah, Sageer nazaune gefenta, yayinda Abbah ke shirin fitowa daga d'aki.

Tana gama jin maganar Jalilah ta jefa wayar a kujera, bata tsaya sauraren tambayar da sageer kemataba, ganin haka shima Sageer yarufa mata baya zuwa sama, dan ya fahimci  ba lafiya ba.

 Gaban Abba ne yafad'i yabi saman da kallo cikin matuk'ar tashin hankali, badai jikin Hassan bane, da sassarfa yabi bayansu shima.

Sun tarada Jalila tanata  kuka har yanzu, gata rik'eda Hassan tana kiran "Yaya katashi!".

 Gaba d'ayansu suka rufu akansa kowa yana masa addu'a, Ummy kam tama kasa addu'ar, kuka kawai takeyi, hakama Jalila.

Ganin halin da Hassan ke ciki cikin kidima Abba yakira Doctor, a gaggauce yamasa bayani akan halinda Hassan d'in yake aciki, yana kashe wayar ya matso kusa dashi tare da riko hannunsa.

 Babu dad'ewa saiga Dr, Abba na ganin kiransa ya fito da sauri, lokacin ciwon yafara lafawa, sai numfashi da yake fitarwa sama-sama,  har yanzu kuma kansa nakan cinyar Jalilah dake share sauran hawayenta, da taimakon Abba da Sageer suka maidashi kan gado, doctor yafara aikinsa....


 ***********
Mumy ce ta kalli Dady tace "Dadyn yasmeen kayi shiru? ko kafasa zuwan"

Kallonta kawai yakeyi, amma yakasa cewa komai, yarasa miyasa suka damu da zuwansa gidan Taura itada inna, kodai wani k'ullin sukai masa ne? sukeso yaje ya afka.

Hannunsa Momy ta kamo ta kwantar da kanta akan kafadarsa, juyowa yai yana kallonta, kafin ya d'an saki iska a bakinsa.

"Wai shin menene dalilin da yasa kika  damu da zuwana gidan taura ne haka?"

Gaban Momy yad'an fad'i, ita kanta tarasa gane dalilin Inna nason Abakar sai  yaje gidan Taura, duk da dai tamata bayani a dunk'ule, amma anya babu wata kullalliya a zuciyar Inna kuwa? Itakam sam Inna inta fadi abu akan Abakar hankalinta baya kwanciya, tasan Inna sarai hankalinta nakan company dinta.

"Ya akai? Naga kinyi shiru?

"Uhm ba shiru nayiba, amma  nima ina ganin zuwan naka yanada muhimmanci, musamman idan kahad'a bayanan dana maka guri guda, akan abinda aka mana agidan, kuma nasan duk akan komawar Gwaggon tane, a ganina kawai kace kanason gwaggo tadawo nan gidan dazama kawai, ni wlhy nama amince tadawo d'akin Safeenah yanzun, kaga sai a gyara kafin ta iso, idan kuma za a canja mata kayan d'akinme to, duk fa wannan takamar da mukeyi dan munada company namu na kanmu mukeyi ni sam idanun mijin Jalila yanda yake kallanmu hankalina bai kwanta dashi ba, na tabbatar Innama hakan ne yasata fadar cewa kaje din, ai daga Jalila har Goggon naka ne."

Zuwa yanzun kam zuciyarsa tagama yarda akwai wata akasa, wato sai yanzu akasan da Jalila tasa ce?

Yace, "ita inna tayarda da hakan?" Yai maganar cikin zargi.

Da sauri tace "sosaima, itamace tabada shawarar hakan, aganina tahanyar goge laifinmu ne kawai zai hana Taura karbe kud'insa koda kuwa dansa yaso yin hakan, dan wannan dan nasa ni yafi bani tsoro, dafa zai tambayi kana ina cewa yayi wai Inashi mutumin?"

Dady ya cije lebansa, daya tuna ma rainin hankalin da Hassan yamasa randa sukaje asibiti, wai ka fito da kudi kuwa? Ya tuna sanda ya miko mai 1000, kamar shi??

Momy takatse tunaninsa da fad'in "kagani zuwan naka yanada muhimmanci kaji Darling? koba komai zaka lallaba Jalilah, ai komin lalacewa naka naka ne, mu fa kosamun damar kebancewa da ita bamuyiba."

Dady yai shiru kafin can yace "Shikenan, babu damuwa, zanje din, amma kafin natafi zan shiga wajen Inna inji miya kamata nafad'ama Jalilah idan naje, kinsan yarinyar tana jarabar son uwarta, sam bata damu da ni dana haifeta ba.

Mumy ta kalleshi, jawota yai jikinsa ya rungume ta a ransa yace wato yanzu dalilin 'yata shine na samu 'yancin roko? Da ai komai sai dai a yanke min hukunci, danasan mijinta kafin aurenn lalai dana dade da canza shika.......

*********

 Alhmdllh komai ya dai-daita, Hassan yadawo dai-dai, amma kallo d'aya zaka masa kahango idanunsa da sukai ciki, har wata yar karamar rama yayi.

Tun d'azun idonsa nakan Abba, kallonsa yakeyi ko kiftawa bayayi. ita kanta Ummy ganin kallon da Hassan kema Abban nasu yasata maida kallonta kansa, tasan soyake yace wani Abu, amma Abba sam bashida alama.

Hannun Abba Hassan yakamo, yarik'e sosai acikin nasa, wannan yasaka Abba maido gaba d'aya hankalinsa kan Hassan, ya zubamai ido cikin wani yanayi da shikadai ya san me yake nufi.

Wasu hawaye masu matuk'ar zafi suka ziraro daga gefen idonunsa.

"Abba nasan ban cancanci a yafe min ba, ni kaina nakasa yafema kaina wannan laifin, nasha addu'a inama tun sanda nayi jinya nima nabi bayan su Husain, na roki Allah akan inhar mutuwata shine mafi alkairi ya daukeni, sai dai da alama ba yanzu ba......"

 Ya kara kallan Abba da idanunsa da suka canza yace "Abba kamin dukkan hukuncin dakaga yadace dani kaida Ummy, duk hukuncin da kukamin bazan taba ganin tsaurinsa ba, Ummy! Abba dan ALLAH Ku hukuntani ko nima zuciyata xata samu sukuni.


Kasa karasawa yai saboda gaba daya zuciyarsa ta yi rauni, hannu yakai yarik'e wuyansa yana k'ok'arin janyo numfashi.

Lokaci d'aya Abba da Ummy sukai kansa, Jalilah  kam fita tayi daga d'akin tana kuka, shi kansa sageer yakasa jarumta dan tuni shima kwalla tacika masa idonsa har suna neman zubowa.

  Addu'oi Ummy da Abba kemasa, ahankali numfashin yafara dai-daita, Sageer yamik'o gorar ruwan daya d'akko, Abba ya taimakama Hassan yatashi zaune ya jingina da fuskar gadon, bayan yasaka masa fillo.
  Ummy tabashi ruwan yasha sosai, kafin ya janye bakinsa.

Idonsa yayi jajur, kalle-kalle yafara yanason ganin Jalilah amma bata d'akin.

Ummy Ce talura da hakan, ta juyo tana fad'in "Sageer! Jalilah fa?".

Shima waige-waige yafara, kafin yace, "inagafa tafita".

Abba yace, "Sageer jeka kirata".

Yace "To Abba"

Afalo ya isketa tacusa kanta a cinya tana rusar kuka, tausayi tabashi ya kura mata ido, murya a sanyaye yace "Jalila"

Shiru kamar bata jishiba.

Ya sake cewa "Jalilah!"
 Batare data kalleshiba tace "Naam." Cikin muryar kuka ta amsa.

"Kizo inji Ummy."

Abinda yafad'a kenan yajuya yakoma cikin d'akin. saida ta goge hawayenta sannan tamik'e tabi bayansa.

 Tunda tashigo Hassan ya kura mata ido, a hankali ya lumshe idanunsa, garin yaya ya bari yarinyarnan ta gama kama zuciyarsa? Ummy tajawo hannunta ta zaunar kusada ita tana lallashi.

Bayan wasu 'yan mintuna Abba yai gyaran murya, har yanzu hannunsa nacikin naHassan.

Cikin kakkausar murya yace "Hassan!"

Abba yakira sunansa cikin muryar damuwa.

Kallonsa kawai Hassan yayi amma bai amsaba.

Abba ya kalli Sageer yace "Sageer zauna anan."
 Gefensa kadan ya nunamai, Sageer ya zauna kusa dashi.

 Abba ya kalli Hassan yace " me kake san ji Hassan? Me kakeso kaji daga bakina?"

 Hassan ya kalleshi yace "Abba!"
Yanda ya kira sunansa sai da Ummy ta juya kai saboda kwalla, Abba ya sa hannunsa akan kafadarsa yace "kasan me yafi damuna akan abinda ya faru?"
 Hassan ya kalleshi, Abba yace "gani nake duk nine mai laifi ba kai ba, alamace ta ban nuna ma kulawa ba, ban nunama duk kaddarar data samemu mu dogara da Allah ba, sannan ban nunama duk wani abu daya faru ka sanar dani ba, ban nunama ko me ya faru bazai zama laifine ba."

 Hassan kallansa kawai yakeyi kafin ya juya kansa gefe, tare da runtse idanunsa, Abba yace " baka taba tunanin ko baka fita waje ba su sai sun fita kuma sai ajalinsu ya kama a gun? Hassan ina karatunka? Har ka bari zuciyarka ta damaimaiye da zargi? Ta hanaka walwala? Ta hanaka sukuni? Ta maidakai gaba daya wani mutum wanda baza'ai magana dashi ba? Ta maida ma baccinka nightmare?"

  Hassan ya kalleshi yace "Abba ni na jaa su....."

 Abba ma idanunsa ma gaba daya sun canza kala ya sa hannu ya jawoshi ya rungumeshi yace "Ko kaine hakan ta faru dakai, ace misali dukanku ne ajalin ya kama akanku alokacin, ace bare ne wanda yasaku kuka hau titin, bazanso ya zargi kansa ba har tsawan wannan lokacin bare kai dana, Hassan babban abinda yafi damuna shekarun daka diba kana zargin kanka."

Sageer ya riko hannun Hassan rungume juna sukai a tare suka saki kuka, Abba ya kallesu sannan ya kalli Ummy.

 Murmushi tamai tare da jinjina kanta alamar hakan yayi.

 Jalila kam na kwance a cinyarta tana share kwalla, a yaushe Hassan ya zama haka a rayuwarta????



**********

   "Wai zaliha wacce irin rayuwa kika saka kankine? nifa nace ki kwantar da hankalinki, sai Taura yadawo hannunki, kima bar damuwa darashin d'aga wayarki dayakeyi. nifa nama fara zargin kodai wayar tasace tafad'i? Dan nasan aikinmu ba k'aramin aiki bane dazai bar jikinsa dawuri haka"

"To amma Anty idan kince wayarsa fad'uwa tayi miyasa har yanzu bai sake zuwaba? tunfa daga d'aga wayar wannan d'annan nasa shikenan ba labarinsa, Dan ALLAH kibarni naje gidan nasa kamar yanda nafad'a miki tun farko"

"amma dai Zaliha bakida hankali ko? shin kin manta sharad'in aikin nan ne? Sannan da kankifa kika sanarmin bak'ak'en maganganun da d'ansa yamiki awaya, ko an fad'a miki Na daina sonkine dazan bari a illata minke abanza? kodai sake shawara amma ba wannanba".

"To Anty yazanyi?"

Lakwai abinda zamuyi kuwa, kibani nanda kwana uku, zanyi tunanin mafita"

"Shikenan Antyna, shiyyasa nake matuk'ar k'aunarki wlhy" ta kwanta akan cinyarta.

Murmushi Anty tayi, batace komaiba ta shafa kanta, Dan halinsu d'aya babu wani banbanci.


***********

Tun bayan fitarsu Abba Jalila ta duk'ar dakai tana murmushin jin dad'in kalaman Abba, ga fuskar Yaya tanuna shima yasamu nutsuwa yanzun.

Kad'an tad'ago idonta tasaci kallonsa, saitaga Ashe shima d'in ita yake kallo, murmushi takumayi tareda kauda kanta gefe.

Muryarsa can k'asa yace taji yace "Jalilah!"

Kasa d'agowa tayi ta kalleshi, amma ta amsa da "na'am".

Shirune yaratsa d'akin Jalilah  tana wasa da yatsun hannunta, shikam Hassan idonsa k'yam akanta, ko k'yaftawa bayayi, jinsa yake tamkar wani sabon mutum, bayanin Abba yasaka zuciyarsa ta  k'ara bud'ewa, dan Abba ya dade da shi bayan su Ummy sun fita yana kara nusar dashi da nunamai ba laifinsa bane, zuciyarsa ta kuma rage nauyi sosai, wata nutsuwa ta musamman ke ratsa dukkan sassan jikinsa, harma yana tuhumar kansa miyasa bai fad'ama su Abba gaskiya ba a duk tsawon shekarunan? miyasa yasaka ummynsa mai sonsa da da k'aunarsa aciki k'uncin damuwa har wannan shekarun, tabbas ya yarda *JALILAH!* alkairice a rayuwarsa, Dan itace ta bashi k'arfin gwiwar canja komai, yafirzo k'aramar iska daga hancinsa...

Jin yayi shiru sai Jalilah takuma d'ago idonta, karaf suka kalli juna itadashi, tafin hannunta tasa tarufe fusakar tana k'aramar dariya.

Shikuma ya lumshe idanunsa yana gyara zama.

Tashi tayi zata barmasa d'akin yai saurin rik'o hannunta dukda jikinsa babu k'arfi sosai.

Gabamta yad'an fad'i tana jira taji ya janyota amma sai taji shiru.

"Dawo ki zauna to, magana zamuyi".

Rintse ido tayi, kusan 1minute sannan tadawo ta zauna, shima zamansa  yagyara sosai yadawo kusada ita....

Jalilah!
Kallansa tai yanda yake kallanta yasa tai saurin sauke idanunta, gani tai kawai ya koma ya kwanta akan cinyarta, ya juyo da fuskarta saitinta.

 Kallansa tai tare da zaro ido, yace " dazu ba haka kika min ba? Na tabbatar dana bude idona a haka na gani." Ya fada tare da sa hannunta akansa.

  Kallansa tai tare dayin murmushi tace "tunda ka gani menene na sake gwadawa?"

 Yace "abinda kika fada nakesan ki maimaita."

 Ta dan juya kai tace "ni namanta ma me nace."

 Murmushi taga yayi, ta zubamai ido batasan a fili ta fada ba sai jitai yace " haba? Kinasan kiga ina murmushi?"

  Da sauri ta kalleshi ashe datace murmushi na masa kyau a fili ta fada.

  Kallanta yai yace "badai kina kara sona bane inkika ga ina murmushi?"

  Da sauri ta kalleshi tace "naam?"

 Yace "me? Bakya sona?"

  Bakinta na rawa tace "ni bance ba."

 Ya kara gyara kwanciyarsa yace "basai kin fada ba kukan da kikai ya bayyana min."

 Kallansa tai da sauri, da gaske? Abinda zuciyarta ke tambayarta kenan......




***********

"Ya kukayi da mijin naki?".

Innace mai maganar tana tattara wasu takardu waje d'aya.

Momy tace, " ya amince inna, k'ilama zuwa gobe yaje ya dawo da ita".

"Humm, Ku azatonku zata dawo cikin sauk'i? kokuwa ita Jalilan kuna tunanin zata amince cikin sauri?".

"To amma inna kinsan da hakan miyasa kikace yaje d'in?".

"Kallonta inna tayi da k'yau, kafin tasaki guntun murmushi "Shi dai yaro yarone, aii sometimes bana banbance tunaninki dana Safeenah dama kisamin ido kiga inda na dosa, tunda ke kullum naki hasashen daban, ke ba komai a gabanki sai wannan mijin naki da ba abinda zai tsinana miki."

Tabe fuska Momy tayi, "to nidai Dan ALLAH koma miye dai kika shirya banason yataba mutuncin Abakar, dan nikam bazan dauka ba."

Sosai inna ta kalleta kafin tace, "bazai ta6aba, tashi kije 'yar gatan miji".

Kuma had'e fuska Momy tayi, kafin tatashi, tasan bak'ar maganace inna ta fad'a mata, itakam koma miza'ayi saidai ayi, bazata bari a wulak'anta mata mijiba ehe.


Nace, "humm".


*************

#OneLuv💕
[11/30, 2:49 PM] ‪+234 803 668 9121‬: *_🗯JALILAH!!🗯_*

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on wattpad : *Ayusher Mohd*


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)


*58*

Alhamdulillah zuwa yanzu nutsuwa tazoma hassan, dan a kwanakin nan ko kad'an ciwonsa baya tashi.

Abba da Ummy sunma rasa wani irin farin ciki zasuyi, ga wata k'aunar jalilah dasukeji har cikin jininsu, yarinyar tazamarma zuri'arsu alkairi.

Ummy ta kalli Abbah dake zaune yana kallon labarai, fuskarta d'aukeda murmushi tace, "wlhy bansan wane irin alkairi zamu yima yarinyar nanba mu nuna mata jin dad'inmu akan sauyin rayuwa data kawo a duniyar Hassan".

Kallonta Abba yayi shima yana d'an murmushin, kafin ya maida kansa ga TV "gaskiyane, yarinyar ta cancanci kowanne irin alkairi, Dan ko'a mafarkina bantaba kawo zamu sami wani cigaba ba akan ciwon Hassan, dubi dai irin shekarun damuka d'auka muna famar bin likitoci na kasar nan da kuma na ketare, sosai nake jin dadi da alfahari da auran yarinyar nan."

"Ta cancanci a k'aunaceta kam....."

Maganar Ummy ta katse saboda jin wayarta na ringing .., daga ita har Abba wayar suka kalla, cikin damuwa Abba yace "ina ganin kawai acire layinnan, idan takira taji baya aiki ai dole ta hak'ura ko?"

"Ba cirewa nak'iba, muhimman mutane dake da number d'inne damuwa ta kuma kaga aii suna kira ai, amma kai yakakeji yanzu gameda ita? dan Allah zuciyarka kadai zaka duba karka damu dani ko su Hassan."

Shiru yai yana kallanta kafin yai mata murmushi ya kamo hannunta yace "Hummm....Alhmdulillah, dan kaso mafi yawa yaragu, yanzu sai lokaci-lokaci ma nake tunota, sabanin da danakejinta har raina, lalai ba shakka na tabbatar yanzu wani abun sukamin, sai dai Allah ya rabamu da sharrin mutane ni........

Ummy ta kalleshi tare dayin yar dariya kadan tace
"miye nak'in k'arasawar to?"

Shima Abba yar dariyar yayi "Ummyn Hassan, yanzu da  Hassan zai yajini ai sai an samu wata yar karamar matsala, shi da bai had'a damuwar ummynsa data kowaba."

Ummy tai murmushi tace "Kaima kasan Hassan tun yana yaro haka yake, zan iya ajiye Husain nadan shiga ko toilet amma shi yana tsaye a kofa yana jirana, ko ina zani yana biye dani, sannan kaima kasan yanda Hassan ke tsananin kaunarka, na tabbatar abinda yake zargin ya aikata shine dalilin dayasa yake neman janyeka daga jikinsa saboda in kasani kar abin ya wahalar dakai."

Murmushi ya mata shima sannan ya saki hannunta yace "na sani, sannan ko da wasa ni ban dauki abinda yakemin a matsayin haka ba, tunda ni nasan yanda ya damu dani, tsautsayine dai da kaddarar data afka mai, Allah ne kadai yasan yaro dan shekara goma sha ya yai rayuwarsa a wannan dakin...."

  Ummy tai shiru cikin tausayi tace "sai nakeji duk laifin nawa ne, kamar nice ban kula dasu yand......"

 Kallan daya mata ne yasa tai shiru.......

Yace "mu ma wadanda suka rasu addu'a mu kuma mu nemi cikawa da imani."

 Tace "hakane Allah ya jikansu da rahama, amma zaka fadawa mahaifin Sudais ne?"
Yace "su da basa kasar? Sai dai insun dawo mayi maganar."

Nan ta jinjina kai tare da kara maidakai kan Tv din da yake kallo.


*********

Bayan sun kammala had'a breakfast Ummy tabar Jalila ta karasa sauran dan dama haka suka saba, tana cikin shirya abincin a dinning Sageer ya fito, sotake yau Hassan yafito ayi breakfast d'in dashi, shiyyasa bata d'iba musuba, ta shirya komai a kan dining.


 Tsayawa yai yana kallanta yana jin dadin yanda ta canza musu gida, dan da a koda yaushe matsalar Hassan sai ta maida gidan kamar ba kowa, amma yanzu kam Alhamdulila.

Ji tai ance Jalila!"
Juyowa tai ta kalleshi tace "Un.... Ya Sageer ina kwana?"

 Murmushi yai sannan yace "Jalila mungode, mungode sosai da farincikin dakika kawoma family dinnan wannan shine abinda naso ki fahimta a waccan ranar, Yaya shine yafi cancanta da samun irinki, amma dan ALLAH ki gafarceni, da. nakula har yanzu kinkasa sakin jiki dani a gidanan, bansan ko har yanzu kina fushi daniba, ni kanin Yaya ne haka kawai zakisa a ranki kinga........."

'Dagowa tai ta kallonshi, wannan yasakashi yin shiru batareda ya k'arasa maganar bakinsaba, ta gyara tsayuwarta tana kallonsa sosai, idonta ya fara tara hawaye tace "Yaya sageer nafad'a maka tuni komai ya wuce agareni, kuma zuwa yanzu na fahimceka, bani yakamata ka godemawaba, kaine ka cancanci a godema, domin ka sadaukar da farincikin ka saboda d'an uwanka, samun irinka a wannan rayuwar sai an tona, kazama mai rama alkairi da halacci, ta share kwallar data zubo mata akan kumatunta sannan tacigaba
"Ya Sageer ka cancanci kowanne irin godiya, amma kayi hak'uri da rashin sakin jikina agareka, nasan ahankali komai zai zama labari insha Allah, kaima Allah na tabbatar bai manta dakai ba zai baka mace tagari wacce tafini komai sannan mai sanka da k'aunarka".

Kallanta yai tare da sakin murmushi wanda har hakoransa suka fito yace "nagode Jalilah, sannan dan Allah ina rok'on wata alfarma agareki".

Kallansa ta sakeyi tace "ina jinka, Allah yasa bai fi karfina ba."

Sageer ya kalleta yace "Jalilah inason koda wasa kar dan Allah kar wanda yasan wata alak'a tataba shiga tsakaninmu, sannan dan Allah ki kuma nika kulawar dakikema Yaya akan tada, kullum burina yadawo normal mutum kamar kowa, inga yana farinciki, yana shiga jama'a, yana mu'amullah acikin mutane kamar kowa."

Kanta ta gyad'a a kunyace, tace "Allah ya bani iko Ya Sageer, zanyi iya k'ok'arina kai ma sai kai naka, har cikin rains ina tsananin tausayin halin da Yaya yake ciki nima, dan babu abinda yakai k'untatar zuciya a rayuwa, mutum bacin ran yini d'aya yashiga ya yake tsintar kansa, bare tsawon shekaru irin haka"

"Gaskiyane, mucigaba damasa addu'a, inaji ajikina zaki sauya komai insha Allah, nima kicigaba damin addu'a Allah  yabani wadda zata tallafeni irin haka."

Tausayi yabama Jalila, dan haka takuma k'asa dakanta, karka damu Ya Sageer dan Allah kaima ka dawo yanda kake da mai walwala, dan Ummy ta bani labarin bahaka kakeba abaya, duk da bazata nunama ba na tabbatar abin na damunta."

 Murmushi yai yana k'ok'arin barin wajen, "karki damu, zan canja insha Allahu."


"ALLAH yasa" itama tafad'a tana fara tafiya domin duba Hassan.

Da sauri Hassan yakoma baya dan karta hangoshi, tun farkon maganar tasu yana tsaye, amma basu ganshiba, saboda sun juya masa baya, yaje yana kokarin shiga falon yaji suna zancenshi, fuskarsa dauke da murmushi ya tsaya a bayan bango yana jikinsu, a hankali kunnensa ya dinga juyo mai hirarsu.

  Yana zaune bakin gado Jalilah tashigo cikin d'akin da sallama.

Bai kalletaba amma ya amsa, da 'yar fara'arta takaraso inda yake tace "Laa Yaya ashe katashi? nifa wai hawowa nai na tasheka."

 "Na tashi!"

Haka kawai yace ba tare da ya kalleta ba, kallon data masane yagane shima maganar tasa tafita da tsauri, amma saiya dake.

Jalilah batayi zuciya ba tace "Yaya mai zai hana yau kazo kaci abinci tareda Ummy da Abbah, kodan kakuma saka zukatansu cikin nutsuwa?"

Yanzu kam bashida zabi. daya wuce kallonta da kyau, yarasa wane irin mahaukacin so zuciyarsa takema Jalilah, baikamata yaji zafin maganganunsu da Sageer ba, musamman idan yai dubi da sadaukarwar dasukayi suduka agareshi, yadad'e yana mamakin yanda kokad'an Jalila bata sakewa da sageer dan Sageer mutum ne mai faran faran yasan sageer da saurin sabo da yawan barkwanci.

Ashe akwai abinda ke tsakaninsu, ya akayi haka ta faru? tayaya iyayensa suka aura masa budurwar k'aninsa? shin basu sani bane? Da wani ido zai kalli Sageer? Ace shi da yake babba bai barma kaninsa abu na sai shine kanin nasa zai barmai? kai amma yasan babu yanda za'ayi Abbah ya aura masa wadda yasan Sageer na nema amatsayin matar aure kuma, to meke faruwa.......?"

Girgiza hannunsa da jalilah tayine yakatse masa tunanin nashi.
Tace  "Yaya lafiya kuwa?"

Baice komaiba, amma yamik'e tsaye, gani tai yanufi hanyar fita, sai da ya bud'e k'ofar sannan yajuyo ya kalleta yace "kona koma na zauna ne?"

Da Sauri tamik'e tana murmushi tace "a'a Yayah ina fa."
 Karasowa tai kusa dashi a hankali tace "Nagode."

"Da akayi me fa?"

Yai maganar yana karasa fita daga dakin.

Ta biyoshi tace "daka amince."


"Hmm" kawai yace, yacigaba da tafiyarsa.

Suna sakkowa kuwa saiga Abba da Ummy suma sun fito.
  Hassan ya karasa kusa dasu ya gaishesu, duk cikin fara'a suka amsa masa, Sageer ma dake zaune a falo yataso, gaishe da su Abba yafarayi, kafin ya gaida Hassan shima.

Cikin danne abinda ya tokare mak'oshinsa ya amsa, harda mik'ama Sageer d'in hannu tareda daga kafadarsa, a tare suka mike suka nufi cikin falon.

Ummy da Abba suka bisy da kalli cikin jin dadi,  haka suka k'arasa kan dining suka zauna, Jalila ta shiga ajiye musu plate, kowa ka kalla fuskarsa a sake take.



Abba da Ummy kuwa cikin mamaki suke da kallon Hassan daya ja kujerar dining ya zauna, alamar yau taredasu zaiyi breakfast.

Cikeda jin dad'i Sageer yace "Yaya yau zakaci abinci damune?"

Kansa ya jinjinama Sageer din.

Gaba d'ayansu farincikin ya bayyana a fuskokinsu, Ummy harta kasa boyewa ta furta " Alhamdulillahi ala kulli halin".

Abba ma abinda yafad'a a zuciyarsa kenan.
Sageer kam harda d'an rungume Hassan saboda jin dad'i, Ummy tace "inama Auta tana gida yau taga abinda take buri a rayuwa?"

 Jalila ai murmushi tace "Ameera yar makaranta."


Hassan ya juya yana kallon Jalilah da itama jin dad'in yasakata taketa murmushi, ganin yanda dukkansu suke farinciki, sai itama takema nata dangin irin wannan fatan wataran.

Kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru.

Abba ne yalura da hakan, yace "Jalila taho mana ki zauna."

A kunyace ta matso zata ja kujerar kusa da Ummy, Ummy tace "Malama Jalila zauna kusa da mijinki, nima bakiga a kusa da nawa nake ba?"

 Da saurin tai kasa da kanta saboda kunya, Ummy ta kalli Sageer tace "wanda yasan gauro ne sai yai sauri ya kawo tashi matar."

 Sageer ya kalleta sannan ya kalli Abba cikin shagwaba yace "Abba kaji Ummy ko?"

 Abba yace "gaskiya kar a sake cema d'ana gauro inba haka ba kuma yanzu nai zuciya namai aure."

  Kallansa Sageer yai yace "aure?" Ya matsa daga gun Abba da sauri.

 Tuntsirewa da dariya sukai yanda ya matsa din, Hassan ya kalleshi cikin wani yanayi da shikansa baisan wani iri bane.

Yaukam cikin far in ciki sukayi break d'in nan, dukda Hassan baya magana, kuma koda komai yafito fili dama har yanzu bawai yana yawan magana baneba, baikuma saki jiki dasuba gaba daya, amma abinda yazama dole yayi magana akansa yanayi.



Bayan sun gama Abbah yafita aiki cikin tsantsar farim ciki.

Suko duk a falo suka zauna suna hira, harda Hassan, dukda shikam ko k'ala bai ceba a zaman nashi, amma yana saurarensu, gaba daya hankalinsa nakan abinda yaji, kodai zuciyarsa ce take kara mai? Kodai ba wani abu tsakaninsu? Kallansu yai yana nazarin su, soyake yagano abinda ke faruwa? suna son juna har zuwa yanzu kokuwa? Su kuwa basusan dawan garinba, damage itama jalilan bawani baki take sakawa a hirarba, k'arfin hirar Sageer  da Ummy ne, dan Sageer ya iya barkwanci, sai dai daga anyi abin dariya zata sa dariya.


 Wajen karfe 12 Hassan ya mike ya hau sama, Ummy ta bishi da kalli cikin jin dadi.
Jalila ma bata dadeba ta mike tahau sama, a kwance taga shi kamar mai bacci.

  Toilet ta shiga ta fito sannan ta kara kallansa, kamar bacci yake kamar kuma ba bacci yake ba, kamar tai magana sai kuma ta jona wayarta a charge kawai ta fito.

Sunkai tsawon lokaci suna hirar, har karfe biyu tai Ameera ta shigo.

 Tana shigowa ta baje a falo wai ta gaji, Ummy tace tashi malama ki wuce kitchen.
har agogo yanuna 2, Ummy tace, "Ameera tashi kishiga kitchen, yau kece zakiyi abincin rana, kullum sai dai kici ki kwanta."



''Wayyo Ummy, nikad'ai zanyi?yanzu fa na dawo daga makaranta."



Ummy tace "to kedawa zakiyi? Tunma kafin rana tamiki kitashi kije ki d'ora, dan abbanku da wuri zai dawo yau, inya dawo baki gama ba kinga sai ki bashi amsa."

Ameera ta shagwabe tare da kwanciya akan kujera tace "Ummy wlh....."
Kallan da Ummy ta mata ne yasa tai shiru ta mike tsaye kamar zatai kuka.
"Karki damu, tashi muje natayaki kinji Ameera". Jalilah tayi maganar tana dafa hannun Ameera.

Cikin murna tace "yauwa matar yayana"

Hararta Ummy tayi "Jalila kiyi zamanki, taje tayi ita kad'ai, zauna ki huta".

Jalila tace "Ummy bangajiba aii, bara na tayata yanzun nan sai kiga mun gama."


Bata bari Ummy tasake maganaba taja hannun Ameera suka tafi kitchen da sauri.
Ummy tabisu da kallon sha'awa da tsantsar k'auna.


********

  Tunda Abba yafito daga gida Zaliha kebin motarsa abaya abin da zai baka mamaki a ina tasan gidansa?tun jiya da yamma tashigo garin, a hotel ta kwana, yau kam da farar safiya tazo unguwar tasu take jiransa, guri tasamu tayi parking tana dakon fitowar Abba daga gida. tana hango an bud'e gate tafara addu'ar ALLAH yasa shine, ganinsa kuwa tasaki wata ajiyar zuciyar dan dad'i, haka taita binsu abaya har zuwa office.

Yana zama a kujera yayinda Secretary d'insa kemasa bayani akan wasu bak'i, dakuma wasu abubuwan da suka faru a jiya sukaji ana knocking d'in k'ofar.

Atare suka kalli k'ofar Abba yace, "munada bak'ine?".

Yace "a'a gaskiya Alhaji, amma bansaniba ko shigowarmu nan suka zo"

"OK, jeka gani to".

Yana bud'e mata, batajira komaiba taturo kai cikin office d'in tana yauk'i, sanye take cikin wani shegen leshi, daya gama had'uwa, ga d'inkin yayi mata k'yau sosai tamkar zata fashe saboda matsetan dayayi, takawo siririn gyale ta d'ora a kafad'a, bak'amar fad'uwar gaba Abbah yajiba azuciyarsa, saida ya had'a da addu'ar " Hasbinallahu wa ni'imal wakil".

   Ganin haka Secretary din yafita, dan hannu zaliha tad'aga masa alamar yafita.

Yanda kasan gunki haka Abba ke zaune yana bin Zaliha da kallo, harta k'araso inda yake.

Mai makon ta zauna akan kujerar dake gaban desks din, saita zauna a saman desk d'in kawai tana juya idanu "haba myT! babu fad'a miya kawo gaba kuma?".

Yanda tayi maganar cikin matuk'ar salo, dole Abba ya tsirama labbanta dasukasha janbaki ido, bai iya cewa komaiba sai ajiyar zuciya ya sauke, jiyake kamar yajawota jikinsa, amma ya daure yana ambatar dukkan addu'ar datazo bakinsa, yana neman d'aukin ubangiji yafiddashi akan wannan masifa daya tsinci kansa aciki.


***********


#OneLuv💕
[11/30, 2:49 PM] ‪+234 803 668 9121‬: *_🗯JALILAH!!🗯_*

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on wattpad : *Ayusher Mohd*


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)
Day

*59*



Ummy tabi Sageer da kallo, yanda ya ajiye waya da sauri yamik'e bayan yagama ansa kiran da'aka masa, sama yahau da sauri, Hassan na kwance ya shiga bai ko jira ya amsa sallamarsa ba, yasan Jalila na kasa.

 Hassan na kwance yana tunanin abinda ke faruwa tsakanin Sageer da Jalila yaji shigowar mutum.

 Sageer ya matso ya masa bayani, ai bai bi takan Sageer ba naga ya sauko da sauri ya dau key din mota ya fita "Ummy ina zuwa" abinda ya fada mata kenan a sanda ya ganta a zaune.



Kafin ta amsa masa yafice, tad'anji zanyi aranta, tunda yau ga Hassan zai fita harda fad'in yana zuwa, tamance shrkarun daya d'auka bai Sanar mata zai fitaba.

Sageer na saukowa yaga har ya ja motarsa ya fita, motarsa shima ya shiga yana tunani, ya bishi ne?



Can kawai yaja motar sa shima ya fita.

***********


"Alhajina kayi shiru, kobakayi murna da ganina baneba?".

Abba ya had'iyi yawu da k'yar, kafin yace, " bahaka baneba zaliha, kawai nayi mamaki. ganinkine, musamman idan anyi la'akari da safiyane, dolene kayi mamakin ganin Wanda yake Abuja a Kano a irin wannan lokacin".

Cikin salonta Na yaudara tace, "Alhajina kamanta da maganarnan ta Malam ba haushe dayace garin masoyi baya nisa........


.......baya nisa kam, balle idan kaci karo da ballagazar mace, wadda batasan muhimmancin dunk'ulalliyar zuri'a ba, narasa wane rukuni zan sakaki acikin jinsin d'an adam....."

  Daga Abba har Zaliha a rikice suka juyo suna kallonsa.

Bakowa baneba face Hassan.

Yauce rana tafarko daya taba shigowa company d'in Abba ballema office d'insa, dukda yasan inda company d'in yake, amma yanzuma bisa jagorancin Sectary d'in Abba yazo, yanaji ajikinsa dama wataran sai zaliha tabiyo sawun Abba tunda batasamu yanda take soba.
Sai gashi kuwa, tunkafin ayi nisa saigata tazo d'in, hasashensa yazama gaskiya.

Bak'aramin tashin hankali Abba yashigaba, hakama Zaliha dake zaune, dan sarai tagane Hassan d'in, shine taga hotonsa a wayar Taura shida k'aninsa, tun ama hoton ta shaida wannan guy d'in bazaiyi mutunciba, balle tundaga waya dashi Taura ya dauke mata kafa.

Hassan yakatse mata tunani da fad'in "Bakiji gargad'in dana miki bane ko kuwa wanda na miki ne ya miki kadan?

 Zaliha ta kalleshi idanunta suka firfito, a hankali ya fara takowa har inda take yace "zaki sauko daga inda kike zaune ko inzo in saukeki?"

 Da sauri ta cire hannunta daga jikin Taura ta sauko daga kan desk din, wani kazamin kallo ya mata yace " fita fa? Zaki iyayi ko sai na jaki daga nan har waje?"

 Kallan Taura tai tace "MyT?"

  Taura ya kalleta ya dake yace "ke karki kara cemin wani urT agidan uban wa na zama naki?"

 Juyowa tai jiki a sanyaye ta fara takowa, kusa dashi tazo ta tsaya tana kallansa, tare da dan girgiza kirjinta.

  Tsaki yai yana kallanta yace "kina tunani wai kin cika mace a hakan?"

 Tace "mene?"

Bai bata amsa ba yace "kinsan wani suna ake kiran mata irinku?"

 Tace "mene?"

Nan ma bai bata amsa ba yace "kinsan a wani jere nake sa mata irinku?"

 Haushi ya kamata tace "mene?"
Yace "Trash! Get out."

  Idanunta ne suka firfito fuskarta ta nuna tsananin bacin rai ta kalleshi tace "mene?"

 Yace "bakyajin turanci?"

 Kallansa ta sakeyi cikin wani yanayi na tsananin bacin rai, cikin mumunan bacin rai ta fito.

  A waje taga Sageer a tsaye a jikin kofa, kallansa tai yai dariya har tayi gaba yace "ke Trash kin manta jakarki."

 Yafada tare da kallan jakarta dake kan desk.

 Dawowa tai ko kunya ta dauka ta fita da sauri.


 Sageer ya bita da kallon mugunta, ya kalli Hassan yace "kai Yaya baka zafafa ba?"

 Hassan yace "kaima ka zafaffa ai wai ke Trash...."

 Abba ne ya hade fuska yana kallansu yace " wato dai kune masu kula dani ko? Sai a fadamin wanene ma ya samar daku?"

 Hassan ya kalli Sageer, da sauri Sageer ya juya kai yace "Abba na manta inada appointment" dariya suka saka a tare hardashi Abban, Abba yace "amma yanzu ai bazata sake dawowa ba ko? Sageer yace "inta dawoma tana da mai maganinta....

  Suka kara yin dariya.....

 Abba yace kuyi alwala muje masallaci sallar la'asar tare.

  Hassan ya kalleshi, Abba yace "let us try kaji?"

 Ya daga kai alamar to.

 Haka suka yi alwala suka zauna a office din Abba macema Sageer ya daure ya fara aiki anan, Hassan na taya Abba har la'asar ta karasa, Abba ya kalli Hassan yace "muje?"

Atare suka fito su uku abin sha'awa, basuga motar Zaliha ba agun da alama ta bar gun.

 Masallacin suka nufa, tsayawa yai yana kallan yanda mutane ke ta shiga ciki, ya kalli Abba.

 Abba yasa hannu ya riko hannunsa sannan ya riko hannun Sageer yace "gamunan mu uku, ka cire komai a ranka kawai kasa a ranka gun bautawa Allah zaka, sannan gamu a kusa dakai."

 Hassan yai murmushi suka nufi masallacin, daurewa kawai yake dan zuciyarsa sai bugawa take da sauri da sauri.


  A bakin kofar suka tsaya sukai addu'a sannan suka shiga.

  Haka suka shiga, suna shiga ciki suka hau jam'i a tsakiya suka sakashi, liman yaja sallah.

  Suna idarwa Abba ya kalleshi, wasu zafaffan kwalla ne suka shiga neman zubomai a lokacin daya daga hannu yana rokon Allah, yaushe rabo? Addu'a ya shiga yi har bai san sanda hawaye ya zubo mai ba.

 Sageer ma sai daya zubo da kwalla saboda tsananin tausayi.

  Ya dade yanata addu'oi kafin su fito, dan sukan shi suka tsaya jira, dukansu sai tausayinsa yakeyi.

^**********

Dady ne ya kalli kofar gidan, kwanansa biyu kenan yana zuwa yana komawa dan shifa gaskiya ya kasa sa kafa cikin gidan, ko dai wayau zaiyi ya fara zuwa gidan da Goggo take? Ita yasan mai sauki ce inyaso sai tazo nan da kanta ta basu hakuri.....


  Juyawa yai da motar kamar zai koma sai ga motarsu Abba.

  Kallansu yai sun shiga ciki, sun hada ido da Hassan amma sai ya dauke kai, da kallan takaici ya bishi yace "wannan dan iskan yaran....."

 Suna shiga shima ya shiga da motarsa.

  Su Abba na fitowa shima ya fito da sauri yace "Ranka ya dade!"

 Abba ya juyo ya kalleshi, murmushi yai yace "Ah Alhaji kai ne?"

 Dady ya matso yana kallan Sageer da Hassan da sukai kamar basu ganshi ba.

  Hassan ya kalleshi bayan ya karaso yace "Ina wuni?"

 Dady ya washe baki yace "Hassan an wuni lafiya?"


  Hassan yace "lafiya."

 Ya wuce ciki, Sageer ma yace "Ina Wuni?"

 Nan ma yace "malam Sageer ko?"

 Sageer yace "eh."

 Ciki yai Abba yace "bismillah!"

 Nan suka shiga ciki...........


  Falonsa ya kaishi ya zauna sai wani washe baki yakeyi, yana cewa "wlh na dade inasan nazo."

 Abba ya kalleshi baice komai ba.....

 Shiru sukai dan Abba kam shikanshi haushinshi yakeji, ai koda laifin su Inna da Mumy to tabbas laifinsa yafi yawa, dan a matsayin sa na uba, miji abinda ya aikata shi kansa yayi alawadar dashi, tun ma daga auran mahaifiyar Jalila zuwa zaman da sukai......

 Dady ya kalli Abba jiki a sanyaye yace "Ranka ya dade nace........"


  Abba ya kalleshi, Dady yanda yaga ya kalleshi ya daure yadanyi shiru......



**********

 Hassan na shiga ya kalli kitchen, Ameera ce ta fito rike da kofi tana shan abu, tana ganinshi ta matso tace "Yaya."

 Kallanta yai yace "baki tafi islamiya ba?"

Tace "ai yau alhamis."

 Yace "okay."
Ya wuce sama, da sauri ta koma kitchen ta taba Jalila tace "Aunty mai sanyin ya dawo...."

 Jalila ta juyo ta taka kafarta, Ameera ta saki yar kara   Jalila tace "bari na fadamai wai mai sanyi."


  Ameera tace "wayyo Allah na ki rufamun asiri."

 Jalila tana dariya ta fito, da sauri ta hau sama tana murmushi, ina yaje dazu?

 Tana shiga ta taraddashi yana cire kaya, da sauri ta juya baya tana cewa "yaya ashe ka dawo."

  Yana cire kayan amma kallanta yakeyi, yace "nemana kike?"

 Juyowa tai ta manta sam da abinda yakeyi tace " naga......."

 Ganin ya cire rigar tasa gaba daya tai sauri sake juyawa, murmushi yai yana kallanta, Jalila menene tsakaninki da Sageer? Me ya faru a baya? Anya ya dace nama Sageer haka?

 Tambayoyin da yakeji kamar ya yimata kenan, ta juyo ita kuka da sauri tace "Yaya kasan me?"

  Kallanta yai, ta kara kallan jikinsa da sauri ta sa hannu ta rufe fuskarta.

  Murmushi yai sannan yace "ki hadiye maganarku tunda kunyata kikeyi, in kuma so kike in matso to."

 Tace "ka matso ina?"

 Takowa yai yazo inda take, idanu ta bude da sauri, ya sa hannu ya lankayo cikinta yace " haka kikeso?"


 Idanu ta zaro tana kallansa tace "yaya wlh ni......."

  Shiru yai yanayin fuskarsa ne ya dan canza, murmushi yai sannan ya saketa yace "Mahaifinki fa yazo."

 Tace "yaushe?"

 Yace " yanzu ya shigo, da alama yazo ganin yar sa ne."

 Tace "hmm yadai zo abinda yazo yi, ko an turoshi."

 Hassan ya kalleta kamar zaiyi magana sai ya fasa, cikin toilet ya shiga ya rifo kofar.

 Da kallo ta bishi tare da yin ajiyar zuciya.....
Itakam batasan ya akai take tsananin san ganinta da Hassan haka ba, lalai yanzu ta fahimci kaunarshi ta fara yin nisa a ranta.

 Dolene ta je gun Goggo ta fada mata dan itakam yanzu tanajin Hassan har ranta...........


 

#OneLuv💕
*_🗯JALILAH!!🗯_*

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on wattpad : *Ayusher Mohd*


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

_Wannan shafin sadaukarwa ce gareku yan Sparkling Son Sorians💖 ina godiya da kaunar da kukema min da littafin nan💕Luv u all....._
 

*60*


 Juyowa tai ta fito daga dakin fuskarta dauke da murmushi.

 Shikuwa Hassan a toilet ruwa mai dumi ya sakar ma kansa yana ta zuba a jikinsa, Jalilah! Sageer! Wani irin so Sageer yakema JalilahA? Wani irin so Jalila takema Sageer? Abinda yaketamai yawo kenan a kwakwalwar kansa, duk yanda ruwan ke zuba a jikinshi baiyi tunanin lafiyarsa Wba.
I jm.  J
  Ya dade a haka kafin ya saba jikinsa ya fito, ya zura doguwar riga jallabiya ya zauna akan kujera yana tunane tunane.

 Jalia kam tana sauka Ummy ta fito daga falon cxAbban nc, kallanta tai tace “kun gaisa Wn

 Tace “da wa?”
Ummy tace “mahaifin.......”
Yanayin fuskarta ne ya canza wanda yasa Ummy kallanta tace “ki shiga yana ciki.”  Jalila tace to sannan ta nufi ciki.

 Abba kuwa a falo ya hade fuska yana sauraren Dady dakemai zancen banza, ya cika yayi fam.

 Dady kuwa tsabar hauka baima kula ba ya dauka fahimtarsa Abba yakeyi.

 Ya kara kallan Abba yace “ gaba daya haka rayuwata take a cikin wannan gidan nasu, komai sai abinda suka tsara, basu dauke da girma ba duk kuwa da nine mahaifin yaran.”

 Ya kara neman marairaicewa zai kara wani rainin hankalin Ummy ta shigo falon dauke da ruwa da juice.
Wannan dalilin ne yasa ta yin shiru, tana kallan yanayin Abba ta fahimci baya jin dadin hirar, sai tai sa’a kuwa tana fitowa sai ga Jalila.


 Dady ya kalleshi ya sake marairaicewa yace “a koda yaushe sai sun yanke hukunci nake sani, sannan ban isa na kawo nawa uzurin........”


Sallamar Jalila ce ta katseshi, haushi ya kara kamashi.

 Abba kam yana ganin Jalila ya mike tsaye yace “bari na barku ku tattauna.
 Dady ya mike da sauri yana cewa “Danka ya dade......”
Ai Abba bai jira cigabansa ba yai waje, yana fita yaja wani dogon tsaki ya kalli Ummy yace “wlh dabadan mahaifin Jalila bane da wlh mutumun nan...” sai kuma yai kwafa.

 Ummy tai daria tace “ni ina kallanka nasan ha labari.”
Ya kalli kofar yace “mutum na kara banzatar da kansa da wulakanta kansa saboda abin duniya?

 Dady kallan Jalila yai bayan ta shigo ta tsugunnadaga can bakin kofa.

 Yace “Jalila! Ya da zama daga nan? Nine fa mahaifinki, yanzu in wani ya shigo ya ganmu ai dauka zaiyi wani abin nake miki, taso dan Allah.”

 Kallan mamaki tamai, sannan ta mike ta taso, zaka tai daga gefensa kadan matso da jikinsa inda take, yace “Jalilah!”

 Dagowa tai ta kalleshi sannan ta gaisheshi, ya amsa fuska a sake kamar wanda akayima wani gagarumin albishir, Dady ya kara sakin fuska yace “ya jikin Goggon taki?”

 Kallansa ta sakeyi tace “da sauki.”

 Yace “Jalilah!”
Ta kalleshi sai dai fuskarta ba a sake ba, tace “naam”

Yace “Jalila ni mahaifinki ne wanda nine na haifeki, nafi kowa sanin zafinki da darajarki, koda duk mutanen duniya zasu kike wallahi ni bazan taba gudarki ba.”

 Jalila batasan sanda ta juyo ta kalleshi ba cikin mamaki take kallansa.

  Dady yace “ki dainamin kallan tantama sai dai nidin da gaske nine na haifeki, jinin jikinki daga jikina yake, amma nikam Jalilah kinji wani abu na harkar company dinmu a nan gidan?”

 Yanzu kam zargin da take ta gama tabbatarma kanta, ta daure tace “kamar name kenan?”

 Dady ko kunya yace “ dama inata tunani ne ko da yanda za’ai tunda dai yanzu kudin sirikanki ne gaba daya yanzu yake tafiya da company din me zai hana ki taimaka ki sanar dasu a bani company din, ni nafi kowa sanin darajarsa, lokacin kankani zan maida musu kudin su, na tabbatar bazan taba basu kunya ba.”

  Jalila kallan mamaki kawai takemai, baijira tama kaiwa kwakwalwarta amsar da zata fadamai ba taji yace “Jalila har zuciyata banasan rabuwa da mahaifiyarki, in har suka takura sai na bar musu gidan kawai, muzo muyi rayuwarmu daga ni sai mahaifiyarki, sai ke inkinzo.”

  Jalila yanzu kam ta kai matuka gun tunzura wato itace kuka mai dadin hawa kenan itada mahaifiyarta, shiyasa yazo mata da wannan zancen?


 Ta kalleshi ta tuno kalaman Hassan tace “Dama ko da wasa nasan wallahi Dady bazaka taba zuwa saboda ni ba, ko goggo.”

 Ya kalleta yace “bangane ba?”

 Tace “yanzu Dady wani mahaifine zaiyiwa matarsa haka? Wani mahaifine zai nemi saida yar sa amma daga baya ya dawo ya nemi kara saida nasa mutunci?”

  Cikin tsananin bacin rai yace “Jalilah? Bakida hankali? Ni kike..........” sai kuma ya canza tone din maganarsa yace “Nine na haifeki ba wani ba, nine jininki.”

 Hawaye ne ya zubo mata tace “jini? Dady sai yanzu kasan jini? Sanda ni da mahaifiyata muke kuntata muke neman tallafinka, Dady kana ina? Kana ina lokacin da.........”

 Hawayene yacikarfinta, ta kasa karasawa, Dady ya turzuko yace “bakin ciki kikemin? Bakin ciki kikeyi zaki taimakeni?”

 Jalila ta kalleshi cikin takaici tace “bakin ciki kamar ya?”

 Yace “inba bakin ciki ki...........”

 Bakin ciki take maka, ko dole ne dan ka haifeta sai ya zama dolene duk wani abu daka zarta mata sai ta bishi?”

  Juyowa yai da sauri, saboda muryar dayaji, a tsorace ya mike tsaye ya kalleshi.

 Hassan wanda har ya zauna yai tunanin kamar ya dace yazo ya gaida shi, yana tsaye Dady ya fara mata zancen karshe da amsar data bashi, dan dama yana fitowa daga wanka riga ya zura kawai ya sauko.


 Dady ya kalleshi yace “Hassan ba.......”
Hassan yai saurin cewa “bansan me ka ke nema a gunta ba, na dauka bayan neman saida ita dakai bakada idan neman wani abu daga gunta, amma yanzu na gane duk ba haka bane, tun farko zuciyarka dama ba komai a ciki sai tsantsar san kai, in ba kanka ba banaji akwai abinda kakeso a ciki.”

  Dady ya fara kokarin yin magana, Hassan ya matso ya kama hannun Jalila yabar falon da ita.

 Dady ya tsaya sakato, cikin kunar rai.


 Hassan kam janta kawau yakeyi, ya matse mata hannu har sai da suka shiga daki, ransa ya gama baci ya kalleta yace “sau nawa zance ki zama mai confidence?”

  Kanta ta karkatar tana kallansa, a hankali ta saki murmushi tare dacewa “ Kasan dazu harda hawaye na? Amma kana zuwa falon naji sun dauke.”

 Kallanta ya sakeyi fuskarsa a hade yace “ ina tambayarki abu daban kina ban wata amsar.”

 Tace “Yaya, me yasa inkaga ana wulakantani baka iyayin shirun? Ko wanene kuwa?”

  Kallanta yai kamar zaiyi magana sai ya saketa, juyawa yai zai fita ma daga dakin.

 Da sauri ta riko hannunsa daya saketa dashi, tsayawa yai sai dai bai juyoba tace “Yaya.”

 Juyowa yai yanzu ya kalleta idanunsa sunyi jaa, Jalila ya zanyi da kaunarki? Menene tsakaninki da Sageer?

Kallansa tai tace “me kake tunani?”

 Kallanta yai sannan ya girgiza kansa alamar a’a, zame hannunsa yai ya juya ciki me makon ya fita, jitai yace “yau munje masallaci da Abba.”

 Cikin tsananin zumudi ta matso kusa dashi, shi kuma baisani ba ya juyo tare da takowa, bugar kirjinsa tai tsayawa sukai a haka, a hankali ta dago ta kalleshi, idanunta sun canza.

 Shima kallanta yai cikin wani yanayi, murmushi ta sakar mai sannan tace “dan Allah? Tayaya?”

  Idanu kawai ya kura mata kafin yace “tare da Abba da Sageer.”

 Cikin jin dadi batasan sanda tasa hannu ta zagayo dashi ta cikinsa ba ta rungumeshi, tace “naji dadi yaya Alhamdulila.”
Wani abu ne ya shiga ratsashi kafin yace “Jalilah?”

Yanda ya kira sunan nata ne yasa gabanta faduwa.
 yace “menene ya faru tsakaninki da Sageer a baya?”

 Gabanta ne ya fadi da sauri ta sakeshi tare da kallansa, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri.

 Tace “naam?”

 Kallanta yai yana shirin yin magana...........


 #OneLuv💕
*_🗯JALILAH!!🗯_*

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on wattpad : *Ayusher Mohd*


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

_Ga taku na musamman 'yan JALILAH NOVEL, D QUEEN BEE & AYUSHER FANS CLUB._
_Wannan shafin sadaukarwace gareku gaba daya, ina godiya sosai da kauna💕OneLuv_



*61*


  Kallansa tai cikin tsananin tsoro idanunta suka firfito cikin tsananin mamaki, daurewa tai tace "Yaya......."

 Kallanta yai bakinsa na san magana amma ya kasa, idanu kawai ya kura mata, sai dai shikam a gunsa yaga rashin gaskiya karara a bayanne a fuskarta, murmushi yai wanda gaba daya inka shakeshi bazai ce ya iya irinshi ba, sannan bazaice ma yasan manufarsa ba.

  Juyawa yai kawai ya koma hanyar waje, Jalila kam gaba daya ta kasa furta komai, saboda tambayar tazo mata a ba zata, sannan bata taba tunanin zai mata irinta ba.

  Kallan kofar tai wacce ya rufota, saukowa kasa yai Ummy na kokarin yimai magana taga ya fita da sauri, ina zaije da magrib din nan?

  Jalila kam tafi minti goma sha biyar a tsaye ta kasa motsawa daga gun, kafin haushin kanta ya kamata. Me yasa batace mai komai ba? To me zatace? Da munyi soyayya amma aka kwaceni daga gunshi akamin auran dole?

  To me zata ce? Hanyar kofa ta nufa da sauri ta fito daga dakin, saukowa kasa tai da sauri, sai dai baya kasa.

 Fitowa waje tai nan ma bataga motarsa ba, jiki a sanyaye ta kalli inda yake ajiye mota, sannan ta juyo ciki.

 Ameera ce wace ke rike da cup da spoon tana juya cornflakes din data hado ta kalleta tace "Matar Yaya daga ina?"

  Jalila ta kalleta tare da yimata yake kawai ta nemi hanyar sama, Ummy ce tace "Jalila?"

 Juyowa tai ta kalli Ummy wace itama take fitowa daga kitchen tace "ashe Mahaifinki ya tafi?ai bansani ba."

 Jalila tace "nima bansan ya tafiba Ummy."

 Kallan mamaki ta mata "wani abun ya faru ne? Naga Hassan ma ya fita."

 Jalila tace "bakomai Ummy."

 Ummy ta kalli Ameera tace "in zakici abu ki zauna banasan cin abincin nan naki a tsaye."

 Ameera ta koma ta zauna, Jalila kuwa tahau sama.

  Ummy ta bita da kallo tare da fatan Allah yasa ba wani abun bane.

 Jalila kuwa tana komawa ta zauna a falo tana jiransa, ganin ta kasa zaman yasa ta dauko wayarta ta sauko da sauri, dakin Ameera ta shiga.

 Ameera wacce shigowarta kenan tana kokarin yin alwala ta kalleta tace "Yaya Jalila lafiya?"

 Jalila ta matso ta dau wayar Ameera ta mika mata, Ameera cikin mamaki take kallanta, Jalila tace dan kira Yayanki.

 Cikin mamaki Ameera tace "ni? In kirashi ince mai me?"

  Jalila tace "ki dai ki kirashi."
Ameera ta amsa tana cewa "yaji yayi ne?"

  Jalila tace "abinda yafi yaji ne. Tunda kin taba gani namiji da gidansa yayi yaji."

 Ameera tai dariya tana dialing tace "kece dai baki taba gani ba amma yanzu maza ma yi suke."
 Jalila ta harareta tace "wallahi Ameera nikam kina ban mamaki, bansan a ina kika san komai haka ba, yarinya kafin ki tafasa kina neman konewa."

  Ameera tai dariya tace "nasan komai wlh, pratical ne......."
Jin alamun kamar an dauka yasa tai gum tare da cewa "hello!" Ta fada tana kallan Jalila.

 Jin ba magana yasa ta kalleta, sannan ta kalli wayar.

 Cikin mamaki tace "banaji."

 Jalila tai shiru kafin ta amshi wayar tasa a kunnenta, tace "Hello!"
 Tana magana aka kashe wayar, kallan Ameera tai ta amshi wayar ta sa number ta juya ta fita.

 Ameera na san magana amma ba dama, saboda ta fahimci sabani suka dan samu.
Jalila na fitowa ta koma sama ta zauna a bakin gado rike da waya a hannu.

 Ta zarfafa cikin tunani taji wayarta na kara, da sauri ta dauka ko kallan mai number batai ba tai sallama.

 Goggo tace "Jalila!"

 Cikin mamaki ta kalli number sannan tace "Goggo? Number wanene?"

 Goggo tace "tawa ce, yanzun nan aka aikon da ita."

 Tace "wane?"
Tace "ai ke zan tambaya,tunda haka akacemin gashi daga Jalilah, na dauka ma number ce baki sani ba."

 Jalila tace "bansani ba wlh,amma nasan bai wuce inji Ummy."

 Tace "kila to, ya gidan naku?"
Tace "lafiya kalau inatasan nima nazo."

 Goggo tace "a'a banasan yawon zuwan nan ba dadi, ke dai ki zauna a gidanki cikin iyalanki, ni muna zaune da Lantana lafiya anan, komai muna dashi, a koda yaushe sai dai in muku addu'a dake da mutanen nan na arziki."

  Jalila tai murmushi sanda ta tuno Hassan a ranta tace Goggo ina cikin wani hali.

Amma a fili tace "to Goggona."


 Nan sukai yar fira kadan kafin suyi sallama, Kara kallan wayar tai tana tunani, idanunta ta rufe sannan ta mike tai alwalar magrib tai sallah ta kara dauko wayarta, yanzu kam kiranshi tai sai dai bai dauka ba harta katse.

  Shi kuwa Hassan tunda ya fita yake tafiya a mota, yayi tafiya mai tsawo kafin ya ja gefen titi yai parking? Kansa ya kwantar akan kujera ya rufe idanunsa, da wani irin zama zasuyi? Ya tabbatar akan wata alaka a tsakaninsu mai karfi, yanda ta razana, idanunta ta ya tuno da yanayin da ta shiga a lokacin, kenan har yanzu tanasan Sageer?


 Idanunsa ya runtse cikin wani irin hali, yana ganin kiranta bai dauka ba har ta gaji ta daina.

 Ummy daga kasa taga ba Jalila gashi har lokacin cin abincin dare yayi, Ameera ta aiko akan ta kirata, lokacin tana kwance akan sallaya, Ameera ta turo kofa tana lekowa tare dayin sallama a hankali, Jalila ta kalleta tana ganin ita kadaice ta shigo.

 Ameera tace "ki sauko muci abinci, yaya fa?"

 Jalila tace "nakoshi, sai dai bari sauko na daukomai nashi."

 Ameera tace "kinsan sai dana bude kofar na shiga tunanin in yaya na nan fa?"
Hmm kawai Jalilah tace batace komai ba, ta mike suka sauko w AUmmy tace "bai dawo ba?"
Tace "eh Ummy inaji ya tsaya a wani gun ne bari na daukar mai."

 Ummy ta dauka su biyun take nufi, shiyasa batace komai ba.

 Kitchen ta shiga ta zuba mai sannan ta dau tiren ta fito, tana shigowa falon Sageer da Ameera na fitowa daga daki, da alama kiransa taje yi.

  Gaisheshi kawai tai ta wuce sama tareda yima Ummy sai da safe.

 Ta hau sama, abincin kawai ta ajiye tai sallar isha'i sannan ta dauko qur'ani inda ya koya mata jiya ta biya sannan ta dawo farko, ta dade tanayi kafin ta rufe qur'anin tadan kishingida tai akan sallaya, bacci ne ya dauketa.

 Sai can wajen karfe 11 ya dawo, yana shiga ya shiga toilet ya fito ya kwanta.

 Juyi ya shiga yi, hankalinsa bai kwanta da kwanciyar datai a kasa ba, gashi ba bargo, duk yanda yaso yai bacci ya kasa.

 Mikewa kawai yai yadau bargo ya rufa mata ya koma ya kwanta.

 Da asuba yana sallah yau ko karatun bai koya mata ba taga ya juya ya kwanta.

 Dama tashin ma sai data farka taganshi kawai yana sallah.

 Tace "Yaya ba....."
Yanda ya kwanta yasata yin shiru dan bashida alamar sauraranta.
Tama rasa me zatace, haka ta gaji ta kwanta.
Tana tashi taga baya dakin.

 Gaba daya hankalinta ya kara tashi, ta fito falo ta zauna idanunta suka ciciko, batasan ta damu da Hassan ba kamar yanzu, gaba daya kin kulatan dayai na kwana dayan nan jitake kamar tayi hauka, me yasa Yaya bazai bari tayi magana ba?

  Shikam gaba daya bayasan yaji wani abu daga gunta, tsoro yake kar tacemai Sageer takeso ba shiba, dan bayaji zuciyarsa zata dauki wannan hukuncin, a yanzu bayaji zai iya rayuwa ba Jalilah, to in itama bazata iya rayuwa ba Sageer bafa? Ko shi yace bazai iya rayuwa ba ita fa? Wannan dalili yasa yake tsoron jin abinda zai fito daga bakinta.

  Wajen karfe 8 ta farka, da sauri ta bude dakin sai dai ba shi ba alamarsa, abincin daren ta kalla, ta bude kulolin, gaba daya ba alamar ma ya bude shi.

  Kawai zama tai a kasa tasa kanta a cikin cinyoyinta, samun kanta kawai da sa kuka, yanzu inyace yabarma Sageer ita fa? Dan ta kula gaba daya ba wanda yake damuwa da ra'ayinta dukansu tunanin junansu kawai sukeyi.

  Haka ta sauko da abincin, tai sa'a Ummy ma sun fita da Abba, tana fitowa Sageer ya sanar da ita, Ummy ta riga hartayi abincin safe, komawa tai sama kawai ta kwanta dan bazata ma iya cin abincin ba, tai wanka tasa atamfa riga da skirt kawai ta murza mai da turare ta kwanta.

  Wayarta na hannunta jefi jefi tana kokarin kiran Hassan.

 Sai wajen rana ta sauko tai abinci kawai tasa a kula ta koma sama.
Yauma bai dawo ba sai data kwanta barci, ya dade a tsaye yana kallanta, sannan ya kalli abincinsa data ajiye masa, zuciyarsa na tsoron jin labarin nan, jiyake bazata iya daukan abinda zata ji ba.

  Bargo ya dauka kamar jiya ya luluba mata, sannan ya kashe wutar dakin ya taho kamar zai wuceta sai kuma ya dauko pillow yazo yadagata ya sa mata sannan ya mike zai tashi.

 Hannu tasa da sauri dan taji alamunsa ta rikoshi, idanu ta bude da sauri.

 Kallanta yai sannan yace "ba bacci kike ba?"

  Tace "bacci nake yanzu na farka."

 Hannunta ya dan zare zai mike, da sauri ta kara rikoshi, bai kalleta ba sai dai ba damar tashi.

 Cikin sanyin murya tace " Yaya haka zamu zauna? Kafin na farka ka fita sannan kafin ka dawo nayi bacci?"

 Kallanta yai kamar zaiyi magana sai ya fasa, tace "Yaya ka tambayeni dan Allah duk wani abu da kake sanji, ni kuma na baka amsa, wannan abin ba shine mafita ba."

 Hannunsa ya zare yamike tsaye, Jalila ta mike tsaye da sauri tare da rungumeshi ta baya.

 Tsayawa yai sai dai zuciyarsa na harbawa da sauri da sauri, tace "yaya dan Allah."

 Kasa daurewa yai kawai ya juyo ya rungumeta tsam ajikinsa, can yace "Jalila zuciyata ta kasa daukar abinda take zargi, na kasa samun nutsuwa, ina tunanin kamar na tauyekine da abinda kikeso....."

 Kai ta shiga girgizawa da sauri da sauri, kafin tace " ko kadan Yaya, bazan musa ma akan da ba amma banda yanzu."

  Dagowa yai ya kalleta, yace "Inke hakan ne shi......."
Daga kafarta tai ta kara rungumeshi tace "Yaya......."

 Bakinta taji a cikin nashi, wani yanayi ya shiga mata wanda ita kanta batasan sanda ta shiga maidamai ba, jitai kafafuwanta sun kasa daukarta, hannu yasa ya dagata gaba daya ya kaita kan gado, sun dade suna sumbatar juna kafin ya saketa kadan, yana wani irin numfashi yace "Jalilah banaso na zama mai tauye miki hakki........"

 A hankali ta lumshe ido hawaye suka taru mata ta sumbaci bakinsa, sannan tace "yaya da ne, shikansa yaya Sageer din ya hakura, sannan duk cikin rashin sani ne, please ka........"

  Kara hade bakinsa yai da nata, yanzu kam ya kasa controlling din kansa, a hankali ya shiga zare mata rigar jikinta.

  Idanunta kawai ta rufe tana tunanin yaushe ta zama haka? Wai ita ke kara mikama namiji kanta?
 Kafin ta gama lissafi ya gama zare kayan jikinta a hankali ya kara maida bakinsa cikin nata..........

 (Ban kula ba najini a kasa timmmm wai ashe dadin soyayya ne yasa Hassan ya hankadoni waje da kafarsa sai ji nai ansa lock a kofar.


  Nace hmm asha love kafiya)



#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


  (_D home of expert and perfect writer's_💡)


  _Ga kyautar shafi kyauta gareku 'yan Zauren Biebie, Word of Hausa Novel, Haske Fans, Kundin Haske, Pherty Novel godiya gareku mai dumbin yawa 🥰Luv u💕



  *62*


 Dagota yai ya kara rungumeta a jikinshi wani sanyi na ratsashi, kanta nakan kirjinsa idanunta a lumshe suke, a hankali yace "Jalilah!"

  Cikin sanyin murya tace "Naam"
Yace "Nagode kwaraia da gaske da kika shigo rayuwata, a koda yaushe yanzu ina godema Allah daya kawomin ke, kin canzamin komai na rayuwata wanda ban taba tunanin zai canzu ba."

  Kanta tadan gyara sannan tace "Yaya kaine kake tunanin nice na canzaka amma a zahirin gaskiya ba haka bane." Yace "menene to."

  Ta dago ta kalleshi sannan ta nunashi da yatsa tace "kaine ka canza kanka da kanka, ni dai na taimaka maka ne."

  Jitai ya sumbaci bakinta, da sauri tasa kanta akan kafadarsa saboda kunya, yace "ya zafin gun? Ya ragu?"

  Bata kalleshi ba tace "kadan."

 Yace "ansha raki."
Cikin shagwaba tace "haka ne raki? Wallahi nayi dauriya......"

 "Wayyo yaya......."
hannu tasa da sauri ta toshe mai baku dan ta fahimci abinda tai dazu yakesan ya maimaita, kallanta yai yana dariya.

 Ta saki bakin nasa tace "yaya nidai ka daina."
Yace "zan daina amma mai za'a bani?"
Tace "me za'a baka kamar ya?"

 "Yanzu bakisan ba'a aikin banza ba? Indai kinaso na daina sai......." ya nuna kuncinsa wai saita sumbata.

 Tace "ni fa kunya nakeji."
Yace "ansha kunyar karya, dazu wanene ya fara rungume......."
Da sauri ta sumbaci kuncin nasa dan tasan yanzu zai fara.

 Tana sumbata ta kule cikin jikinsa, yace "da alama dai wannan jikin ana sanshi dayawa, naga kamar baza'a iya sakeshi ba."

 Sa hannu tai ta dan ture jikin nasa, ya jawota ya maida ita yana dariya, tace "wlh yaya kaima...."

 Yace "zaki iya tashi kiyi wanka ko ni na zo muyi tare?"
Da sauri ta kalleshi tace "muyi tare? A'a zan iya."

 Ya kalleta yace "fara to dan na tabbatar zaki iya."

  Kallansa tai sannan ta fara neman mikewa, guntae dariyarsa yai dayaga yanda take dan dingisawa, sai data kusa zuwa toilet sannan ta juyo, ya mata alama da ya taso? Da sauri ta girgiza kai alamar a'a
 Ta shige tare da rufe kofa.

  Wanka tai da ruwan zafi sannan tai wankan tsari ta fito.
 Yana ganin ta fito ya taso yazo kusa da ita, tambayarta yai ya jikin? Batace komai ba sai shagwabe fuska datai, kallan kan gadon tai har ya canza bedsheets din, dan dama Hassan bashida wannan girman kan, ko sanda bashida lafiya.

 Hannunta ya rike tace "zan iya fa."
Ya saketa sannan ya shiga toilet shima, sai daya fito ya kalleta tana kan kujera a zaune, yau ma towel dinshi a kasa ya daura, yau kam sai taga ta rage kunyar kallansa, sannan ko ita datai wanka towel ta fito dashi sai dai ta yafa wani a samanta.

  Kallanta yai yaga tana kallansa yace "ya ya? Yanzun ma so ake akwanta?"
 Yanda yai maganar ta gane me yake nufi da sauri ta dauke idanunta, sai daya sa riga jalabiya sannan ya matso yace "let's pray."
Tace "nayi isha'i ai."
Yace "na godiya ga Allah."
Bata musa ba ta mike da kyar, hannunsa ya miko mata ta rikeshi suka karasa, sallah sukai raka'a biyu, ya danyi addu'oi sannan ya kalleta, mikewa yai kawai yazo kusa da ita, tana neman yimai magana sai jitai ya dagata, kan gado ya ajiyeta sannan ya zubo musu abinci a plate, yasa spoon daya.

  Kusa da ita yazo ya zauna ya fara ci, kallansa tai tace "yaya nimafa yunwa nakeji."
Yace "au ai ma dauka ke bakyajin yunwa."

 Hade fuska tadanyi, ganitai ya debo a cokali ya miko mata, baki tadan turo tana neman yin magana.
Sumbatar bakinta yai ta kalleshi da sauri, yace "bude"
Bakin ta bude tana kallansa, haka ya dinga ci yana bata, bayan sun gama ne ya zauna kusa da ita tare da kwantar da ita kan kafadarsa, ya rufe musu kafa da bargo sannan ya sa hannunsa cikin naga, shiru sukai na wasu mintina kafin taji yace " bacci?"

 Tace "a'a kawai tunanin rayuwa nakeyi."

 Shiru sukadanyi kafin yace "mene daga ciki kike tunani?"
"Hmmm yanda kawai rayuwa ta juyamin."

Ya dan kwantar da kansa a saman nata yace "yaushe kika san Sageer kanina ne?"

  Ta dago ta kalleshi tace " sanda yazo gidanmu kawo sako."
 Yace "ya kukai?"

 Tace "kawai fa kasan me? Na fito inata yan kunkunina wai ina zuwa falo naga Uncle? Mamaki ya kamani, shima yana ganina..........."
Yanda Hassan ke kallanta ne yasa tai shiru, sannan tai dariya tace "bacci nakeji."
Da sauri ta kwanta ta lulube kanta da bargo.


 Shiru yai kafin yace Sageer am really sorry.

 Ya dade a zaune hartai bacci kafin shima ya kalli agoggo karfe 2 saura, yaye bargon yai yana kallanta tanata baccinta kafin ya sunkuyo ya sumbaci goshinta, sannan ya kwanta ya jawota jikinsa.

  Yau kam zai iya cewa bai tabayin bacci mai dadi kamar nayau ba, dan sallar asuba ma makara sukai.
 Sai karfe bakwai na safe ta farka, tana kwance a daga gefe da alama garin dadin bacci ne har ta matsa daga kusa dashi, juyowa tai ta kalleshi, batasan sanda murmushi ya bayyana a fuskarta ba, juyowa tai ta kalli agoggo, karfe bakwai? Badai yaya ganin tanata bacci bane yasa bai tashe ta ba?

 Mikewa tai sam ta manta da jikinta, tana mikewa da karfi taji azaba, da sauri ta koma ta zauna, sannan ta sauka a hankali, tana bude toilet ya bude idanunsa, yana ganin yanayin gari ya kalli agoggo da sauri.

 Istigfari ya hau yi kafin ya mike, tana fitowa ya shiga, mamaki ne ya kamata, yau yaya ne ya makara? Daren jiya ta tuno, kunya ya kamata, da sauri ta shimfida sallaya tana neman tada sallah.

 Gani tai har ya fito, ya mata alama data matso nan ta matsa bayansa kadan ya tada sallah sukai, sai daya mata dori sannan suka kwanta, bacci ne ya kwashesu tana kwance akan jikinsa.........


  ************

  Ummy ce ta kalli agoggo karfe 11? Lafiya? Gashi sai ita kadai, yau juma'a Ameera na skul, Sageer da Abba sun fita tare, tana san ta dubasu amma tana ganin rashin dacewar hakan, a zaune take tsuru ta zubama sama ido tana addu'a akan Allah yasa lafiya, taji wayarta na kara.

 Jawota tai tare da dagawa tace "Aunty Nana in kwana?"

 "Wato tunda Ameera ta dawo bakida niyyar kira ko?"

 Ummy tace "kiyi hakuri wlh inata san kira abubuwane duk suka chabe min."
"Hmm akwai abinda zai chabe miki banda damuwar yaran can, gaba daya komai na rayuwarki kin dorashi akansa, sam bama kya damuwa da wanda ya dace ki damu dashi."

 Tace "zaki fara ko? Wai meyasa kike haka ne? Da Sageer da Hassan ai duk 'ya'yanane kuma 'ya'yanki   me yasa kike haka ne?"
Aunty Nana tace " hmm haka zaki bar Sageer din ba aure?"

 "Wai yaushe ma Sageer ya girma ne? Duka duka yaushe ya gama service? A bari ya zauna mana?"

 Aunty Nana cikin dan zafi tace "sai ki bari inya taufa sai kimai....."

 "Allah ya baki hakuri, ni narasa me yasa kike haka wlh."

 Aunty Nana tai karamin tsaki, Ummy tace " Ina Hajiya Aina'u ta gujemu."

 "Aina'u nanan, dazun nan ma taje skul dubo result."

Ummy tace "to Allah ya taimak ya kuma bada sa'a."

  Tace "Ameen."
Sun danyi hira kadan kafin suyi sallama.


*********

 A sama kuwa sai karfe 11 da rabi Jalila ta bude ido, tsananin mamaki yasa ta kara murza idanunta tare da kallan agoggo.
 Inda Hassan ke kwance ta kalla, a zaune ta ganshi rike da littafi, cikin mamaki tace "yaya ya zaka barni nai ta bacci haka?"

 Kallanta yai tare da ajiye littafin kan cinyarsa yace " ban fahimta ba? Baccin ne bakyasan na barki kiyi?"

 Ta kalli agoggo sannan ta kara kallanshi tace "Yanzu me zancema Ummy? Kalli fa agoggo?"

  Agoggon ya kalla sannan yace "dan kin kai 11:30 kina bacci menene damuwar Ummy?"

  Ganin kamar ma bashida niyyar ganewa tace "nikam yau bansan ya zanyi ba." Tafada tana kokarin sauka.

  Kallanta yai tana dan dingisa kafa, dariyarsa ya gumtse sannan yace "me zakice ma Ummy in taga tafiyarki?"

 Gabanta ne ya fadi, ta kalleshi da sauri, tace "yaya nashiga uku? Ya zanyi? Yau nikam na gama yawo."

  Kara matse dariyarsa yai sannan yace "kawai ki kwanta sai nace bakyajin dadi.

  Karasowa tai kusa dashi tace "gaskiya kam, yaya ka taimaka kacemata ina zazzabi."

 Yace "karya fa kenan?"

 Kallan mamaki tamai tace "yaya kaifa ka fara cewa, sannan ai ba karya bane tunda dai da gaske banajin dadin."

  Da sauri yasa hannu saman goshinta yace "daga ina ne yake miki ciwo? Nuna min?"

  Kara shagwabewa tai kamar mai neman yin kuka tace "haba yaya!"

 Dariya yadanyi sannan yace "ki kwanta bari na sauka kasa."

 Kwanciya tai tana cewa "yauwa Yaya."

 Fuska ya hade yace "me zakimin in zan sauka na kai sakonki?"

 Tace "kamar ya kenan?"
Yace "aikena zakiyi naga, to me zaki biyani?"

  Tace "oh ni yaya, yanzu kuma me kakeso?"

 Yace "banasan sunan yayan nan, na rasa me yasa kika kama suna kamar ke kika rada min, komai yaya bayan ni ba yayanki bane."

  Ya mike ya fita, kasa ya sauko Ummy na zaune tana kallo, sai dai idanunta ne kawai ke kan Tv din amma batasan me ake ba, hankalinta nakan su Hassan.

 Hassan taga yana saukowa, daurewa tai kamar bata damuba ta kara kallan Tv din da kyau kamar bataganshi ba.

 Harsai da ya kusa saukowa sannan tace "Hassan!"

 Murmushi ya mata ya matso kusa da ita yace "Ummyna an tashi lafiya?"

 Tace "lafiya kalau yarona, ina Jalila? Ko tana bacci?" 
 Yace "a'a."

 Kallansa tai kamar zata sake tambaya, yanda tafa yayi gefe da kansa ne yasa tace "ga breakfast dinku can sai ka daukarmuku."

 Yace "tam."

Kitchen din kawai ya shiga ya dauko musu tiren abincin sannan ya hau sama, yana ajiye wa ya dauko na daren ya sauko dashi.

 Ummy tai murmushin jin dadi, tace "Hassan, Abbanka yace ka shirya anjima zaizo shiga Sageer kuje sallar juma'a in kuma bai gama abinda yake ba zai kiraka a waya kaje sai ku tafi."

 Yace "To Ummy."

Haryadanyi gaba sai kuma yace "yarinyar nan fa?"

Tace "kwana biyu kenan banga kiranta ba."

 Yai murmushi sannan ya juya ya tafi.


 *********

 Dady cikin bacin rai ya kalli Mumy yace "wai menene hakan?"

 Kara kwantowa jikinsa tai tace "menene? Ranka ne a bace?"

 Daurewa yai yace "a'a kawai banajin dadi ne."

 Hannunta ta zaro daga cikin rigarsa tace " meke damunka?"
Yace "menene ma bazai damen ba? Gaba daya ba wanda yake ganina da daraja? Yaran nan bakiga yanda yaci mutunci na ba? Ita kanta yarinyar ba mutunci na take gani ba, Harta employees din company dinmu ba mutunci na suke gani ba."

 Jiki a sanyaye ta kalleshi tace " ko inma transfer na share dina na company?

 Ya kalleta yace "so kike Inna ta kara tsanata?"

Tace "ba sai ta sani ba, sai muyi a tsakaninmu."

 Jawota yai jikinsa yace "banaso inzama silar samun matsala tsakaninki da mahaifiyarki."

 Kwanciya tai a jikinsa tace "karka damu da wannan."


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

_Where are u my beloved Wattpadians? A word can't express how much u means to me, when ever i feel down, ur comments always cheers me up.........💕💕💕💕Luv U All💕💕💕



*63*

  Yana shiga daki ya kalleta, tana dukunkune cikin bargo wai a dole kar Ummy ta shigo.

 Hassan ya matso kusa da ita yace "Amarya tashi ku gaisa da Ummy."

 Kara dukunkunewa tai tana dagamai hannu alamar tanasan magana, guntse dariyarsa yai ya matso kusa da ita gaf da fuskarta.
 Tana juyowa ta ganshi gaf da ita, idanu ta kifta tare da hadiyar yawu tace "Yaya me ka cema Ummy?"

 Yace "kamar me kenan kike san ji?"

 Cikin rada ta sake cewa "ba tare kuke ba?"
Yace "ni da wa kenan?"

  Labanta tadan ciza kamar zatai kuka tace "Yayah Please."

 Baki yadan tabe sannan ya koma kan kujera yace "Ummy wai ki tafi batasan magan........."
Ai bai karasa ba ta yaye da sauri tana cewa "Ummy wallahi ba......."

 Ganin ba kowa yasa ta hadiye maganarta, kallansa tai cikin mamaki, gani tai bashida niyyar kallanta, waya yake danna wa.

 Jitai kamar tasa kuka, lalai yayan nan, wato dama rashin lafiya ce ta rikeshi zolaya da tsokana ce fal cikinsa?

Gaba daya ma kamar baisan tanayi ba, haushi ya isheta ta koma ta kwanta.

 Dariyarsa ya guntse sannan ya kalleta, yace "Amarya yaushe zaki bani abinci ne? So nake na shirya kafin sallar azahar."

 Juyowa tai bangaren da yake, ta hade fuska wai a dole tayi fishi ta kalleshi.

 Kallanta yai yace "Allah daga na irga yan mintina ba'a ban abinci ba bazanci ba."

 Mamaki ya kamata tace "da gaske sai ka ki ci?"

 Yace "Ko zamu gwada?"

 Batasan sanda tai dariya ba, shima dariyar yai kadan a ransa yace "u smiled."

  Amma a fili ido kawai ya kura mata yana kallo, yana san yarinyar nan har baisan wani irin so yake mata ba, ko dan a rayuwarsa bai taba zama da wata mace bane daga Ummy sai ita? Dan Ameera ma saboda matsalarsa basu samu sun shaku ba.

  Jalila ta kwantar da kanta tana kallansa, batasan me yasa ba, tanasan taga murmushi a fuskarsa.

  Ganin yanda take kallansa ne yasa ya ajiye wayar ya mike a hankali yazo inda take, tsayawa yai yana kallanta kafin yace "Kallan fa?"

 Tace " kawai mamaki nakeyi ne."

 Yace "mamaki na ko?"
Kai ta daga alamar eh, yace "in zan zuba mana abinci me za'a biyani dashi?"

 Tace "kamar ya?"

 Yace " dazu ma nace a daina cemin yaya kuma har yanzu an kasa dainawa, karfa biyan bashi ya miki yawa."

  Tace "a'a ni bari na zuba da kaina, me yai zafi?"

 Ta fada tana neman mikewa, hannu yasa ya maidata yana murmushi yace "just joking, amma na yanzu."

  Bargon ya yaye ya miko mata hannu, kallansa tai ya mata alama data kama hannunsa, nan tasa hannu ta rikeshi, a hankali ya taimaka mata ta sauka, gun da suke cin abinci ya karasa da ita sannan ya zaunar, shima ya zauna.

  Kular ta bude, plantain ne aka soya aka dora soyayyan wainar kwai a sama, dayan kular kuma anyi potato ball, sai farfesun naman rago.

 Zubawa tai a plate, sannan ta matso mus da plate din tsakiya, kallanta kawai yakeyi har ta gama sannan yai bismillah ya fara ci.
Itama ta fara ci, sunyi shiru suna cin abinci sai dai kallon juna da sukeyi jefi jefi, in suka hada ido kuma sai su saki murmushi a tare.

  Ya kalleta yace "kin samo sunan da zaki fada min?"
Tace "wlh ni yaya......"
Kallan daya mata ne yasa tai shiru tana cewa "oh ni..."

Jitai yace "me kike cema Sageer?"

Kallansa tai kawai tasa dariya, tace "oh ni, shi fa uncle din mu ne dama haka muke cemai."

 Bai kara magana ba ya cigaba da cin abincinsa, sai dai yanzu ya daina kallanta.

 Har suka gama cin abinci, ya mike yace "bari nai wanka."

 Ta daga kai alamar to, ya wuce toilet.

 Murmushi ta bishi dashi sannan ta hada kwanukan, mikewa tai ta gyara gadon sannan ta dan kara kimtsa dakin, kofar ya turo hangota yai tana gyara gun kujera tare da maida littafin dayai amfani dashi, a hankali ya tako inda take, ita kuma jin motsin kofa yasa tace "yaya ka fito?"

 Sam batai tunanin yazo inda take ba, ta sukunya tana ajiye littafin taji ya sanya hannayensa ya zagayo cikinta, tsayawa tai cak dan batai zaton jinsa haka ba, a hankali ta juyo ta kalleshi sumbatar bakinta yai kadan sannan yace " kinasan kari ne?"

  Tace "karin me?"
Kara sumbatarta yai yace "yanzu fa?"

Kallansa tai kamar zatai magana sai kuma tai dariya, ya matso saitin kunnenta yace "Jalila bansan meke damuna ba?"

 Dagowa tai, ya juyo da ita saitinsa, tace " bakajin dadi ne?"

 Yace "ko kadan kawai sai nake jina kamar ba ni ba."
Tace "jikin naka ne?"
Ya zare hannunsa daga kugunta ya sa akan fuskarta yace "ko kadan kawai dai haka nakejina, da alama shekarun dana samu a dukunkune sune nakesan na fanshe."

  Murmushi tai har hakoranta suka fito tace " haka ake so ka fanshe duka, tun daga yarintar ka data rike zuwa yanzu....."

  Yanda yake kallanta ne yasa tai kasa da idanunta tana murmushi gaba daya yaya yasa tana neman cire kunyarta.

  Saketa yai yace  "kin tabbatar zaki jure ko?"

  Tace "zan jure."

  Juyawa yai yana sa kaya, ta juya tare da zama kan kujera, shadda ya dauko sabuwa, cikin wanda Abba ke yawan dinkamai baya sawa, duk sanda Abba zai dinkama Sageer manyan kaya sai ya dinka masa, sannan dama ko kananan ma shi yake siyo masa.

  Yayi kyau kamar ba shi ba, ya dauko hula ya saka, ya karasa gaban madubi ya sa turare tare da sa agoggo, Jalila ta zuba mai ido ta cikin madubi, kallanta yai tai saurin dauke idanta, takalmi ya dauko yazo kusa da ita, hannu yasa ya dau wayarsa tare da nuna mata sannan ya dau key yai hanyar waje.

  Sai dayaje kofa yace "na tafi."

 Wani lallausan murmushi ta sakar mai sannan ta daga kai alamar to, ya fita tare da turo kofar, idanu ta lumshe tana tuno daren jiya, lalai itakam bata taba kawo wannan yanayin ba, kwanciya tai kan kujerar tare da lumshe idanunta.

  Knocking din data jine yasa ta bude idanunta, tare da kokarin mekewa, Ummy ce ta turo kofar tana cewa "ba sai kin taso ba Jalila."

 Ganin Ummy ce yasa cikin hanzari ta mike tana neman tahowa gunta, azabar dataji ne saboda saurin datai yasa tadan tsaya sannan tadan cigaba da takowa a hankali.

 Ummy tana kallanta ta fahimci lalai danta ya girma, tana karasowa kusa da Jalila kawai ta rungume Jalila.

  Cikin mamaki Jalila tai tsuru tana san sanin meke faruwa, Ummy tace "Allah ya miki albarka ya kareki daga sharri duk wani wanda yake nemanki da sharri, ya sa aljanna ta zama itace makomarki, ta sa ki gama da duniya lafiya."


 Jalila a hankali tace "Ameen."

 Ummy ta saketa sannan ta jawo hannunta suka zauna a bakin gado, tace "kin dan shiga ruwan zafi ne?"

 Cikin rashin fahimta tace "ruwan zafi?"

  Tace "zaki iya saukowa? Muje kasa?"

 Jalila tace "eh."

 Ummy tace "dauko kayan da zaki saka sai muje kasa."

 Mikewa tai ta bude drawer kawai kayan dake sama tasa hannu ta jawo, Ummy tai murmushi tace "Jalila atamfar ya dinkinta yake?"

 Tace "wlh ban sani ba Ummy, na daiga shine a sama."

 Ummy ta mike tazo ta bude kayan, maidasu tai ta cigaba da dubawa, sai datazo kan wani material mai masifar kyau, jikinsa kamar lace yake sai dai ba kafe bane, ita tasiyoshi da kanta sanda ake hada lefe.

  Budeshi tai taga dinkin kuwa yayi kyau riga da skirt ne.

 Ta ajiye sannan tace "muje?"

 Jalila tace to, Ummy tace "dauko inners."

 Kunya ta kama Jalila ta zaro ta cusashi tsakiyar kaya, Ummy tace "mu tafi to."

 Nan suka sauko Ummy na rike da hannunta.

 Da yake toilet din sama bashida bath hub kawai gun shower ne aka killaceshi shi yasa ta sauko da ita.

 Dakin Ameera ta kaita sannan ta shiga toilet ta kunna ruwan zafi, sannan ta toshe makwararar ta fito, zama tai kusa da Jalila wacce ita gaba daya ta kasa gane me Ummy ke nufi, ba dai tasan wani abun ya faru ba? Ko da yake bata fada ba ta ya zata sani?

(Nace uhm yaro man kaza🤣)

  Fita Ummy tai bata dade ba ta shigo rike da kofi, na baza ido ina san ganin menene a ciki, mikama Jalila tai tace "sha."

 Jalila ba musu ta amsa ta kafa kai ta shanye, sannan ta mikama Ummy kofin, Ummy ta kalleta tace "Munyi waya da Goggonki tace "tanaso tadan je kauye taga gida."

 Jalila tace "jiya munyi waya amma bata fadamun ba."

 Ummy tai dan dariya kafin tace "batasan ne kece sai kin bita."

 Jalila tace "Amma Ummy ba tare ya kamata muje ba?"

 Tace "tunda dai ita kadai take san zuwa yanzu sai ki barta taje inyaso ke daga baya sai kije ko da Hassan ne ko kuma ku koma tare."

 Jalila ta daga kai alamar to, sannan tace "yaushe zata?"

 Ummy tace "gobe da safe, nasa Sageer ya tura Mamman driver da mota sai suje tare."

 Jalila tace "to Ummy Allah ya kaimu, mungode sosai."

  Ummy tace "muma mun gode, ta shiga toilet, sai dataga ruwan yayi kusan rabi sannan ta kashe ta taba ruwan, jun zafi sosai yasa ta kunna na sanyi.

 Sai data tabbatar komai yayi sannan ta fito ta kalleta tace "ki shiga cikin ruwan ko zuwa minti 20 ne zakiji dadi inkin fito."

 Yanzu kam Jalila ta fara fahimta, da sauri ta sunkuyar da kai cikin kunya, Ummy ta juya ta fita.

  Jalila kunya ta rufeta da kyar ta mike a shiga.


 Yanda Ummy tace tayi haka tayi.

  Ta dade a ciki kafin ta cire tai wanka.

 Taji dadin jikinta sosai, kaya ta saka ta shafa mai da powder sai turare kawai ta fito falo.


  ****************



 Zaliha ce ta shiga wurgi da kayan dake cikin wardrobe dinta tana wani irin ihu, Auntyn ta ta matso tana cewa "Zaliha menene hakan wai? Tunda kika dawo daga kano gaba daya kin koma kamar wata wacce bata cikin hayyacinta, wani abun ya faru ne wai?

 Kayan kawai take zubarwa tana ihu, ganin abin yaki karewa yasa ta matso kusa da ita ta rike hannayenta, ta girgizata tace "Zaliha wai meke damunki? Gaba daya kin canza, ko abincin kirki ba ci kike ba, wai menene ke faruwa? Kin ki fadamin sai ihu kawai kike."


  Ture Aunty nata tai ta fada kan gado tace "me? In amince duk abinda nakeso zan samu? Kinsan me aka kirani dashi? Ko bacci nakeyi in na tuno abinda akamin sai dai na farka, ko abinci nasa abakina ina tunowa sai naji bazan ita taunawa ba."

 Tace "to me aka kiraki dashi?"

 Kara watso wasu kayan tai wanda suka rage a ciki ta sa wani ihu na bakin ciki......
 Mamaki da tsoro ne suka hanata magana, tana kallan yanda take ihu daga baya ta tsugunna kawai tasa kuka.........

**********

 Yana isa yai parking ya fito da sauri dan ganin motarsu na kokarin fita, wayarsa ya dauko da sauri ya kira number Abba, Abba ya daga yana kallan Sageer.

 Hassan yace "Abba gani nazo, naga kamar zaku fita."

  Ya kalli Sageer ya fadamai, nan Sageer ya juya kan motar, a tsaye suka ganshi, suna karasowa kawai ya shiga bayan motar.

 Abba yace "motar taka fa?"
Yace "in mun dawo sai in biyoka sai na dauka, ko na turo mamman."

 Abba yace "okay, dan daga masallaci gida zamy muyi lunch."

Sageer ne ya juyo ya kalleshi yace "Yaya barka da isowa."

 Hassan ya kalleshi cikin tsantsar kulawa yace "ya? Ko na anshi tukin ne?"

 Sageer yai dariya yace "yaya ka manta? Na rigaka fa iya mota, kai da sai da daga tasa ka gaji da zaman daki kasa Mamman ya koya ma."

 Hassan ya harareshi yace "amma dai daga nan har......"

 Abba yai dariya yace "ba wani har..... shi dai mutun tunda an wuceshi shine yake neman waskewa."

 Hassan yace "bakomai tunda hademin kai za'ai zan sanar ma Ummy na nima."

 Sageer yai dariya yace "wai yaya wallahi Allah ne kawai ya tsare da katon Mama Boy za'ai."

 A tare suka sa dariya da Abba, Abba yana cewa "sosai ma."

 Hassan yace "to duk kowa ya gama nima zan fanshe."

 Haka sukai ta yan tsokana kana ganinsu kaga mutanen dake cikin tsantsar farin ciki, bazaka taba tunanin wani ba dan wani bane a cikinsu.....


(Ni kaina da badan Hassan ya sanar ma Jalila ba ko da wasa ban taba kawo hakan ba.....)


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

_Gaisuwa gareku yan Maryam Salisu Maidala, Hausa Novels Room, Unity Girls 2011, Mamu Novella da Billy Giro Novel...._


*64*

 Yanda ake ta shiga cikin masallacin ga wasu sunata sa sallaya a waje, wasu akan tabarma, wasu kuwa ma a haka suke tsayawa, anata huduba,Hassan ya kurawa mutanen ido zuciyarsa na wani irin bugawa, Abba ya sa hannu ya riko hannunsa, sannan ya kallu Sageer yace "muje?"
 Sageer ya daga kai tare da cewa "Yaya yau sai mu rubuta ta cikin tarihi."

 Hassan yai murmushin yake, haka Abba ya rikeshi, Sageer na rike da babbar sallayarsu, masallacin ya cika dan haka daga baya ya shimfida musu sallayar, Hassan zuciyarsa na ta sake rauni, yana neman yafiya gun Allah akan rashin ziyarta dakinsa dayai na shekaru haka masu tsayin gaske.

 Haka suka je suka zauna sunajin huduba, a hankali wasu zafafan kwalla suka gangaroma Hassan, dan a iya tsawon hankalinsa zaice bai taba jin huduba haka ba sai dai dayake yanajin na saudiya a waya amma bai taba ji zahiri haka ba, Abba ma ji yai gaba daya jikinsa yayi sanyi, hannu Sageer ya sa ya dafa kafadar Hassan.
 Hassan ya kalleshi cikin wani yanayi na jin dadi da tausayawa, ji yai ya fara yi masa addu'a a ransa "Allah ka kare wannan yaran, ka biyamai bukatunsa na alkairi, ka kareshi daga sharrin masu sharri, ka bashi mace ta gari wacce zata so shi ta kuma kaunaceshi fiye da tunanin mai tunani."

 Ganin yanda yake kallansa yasa Sageer yace "yaya."

 Hassan ya maida kansa kasa kawai baice komai ba, har lokacin sallah yai sukai sallah sannan suka shiga mota.

 Abba yace "yanzu mu wuce gida? Ko da wani abun?"

 Hassan ya kalli Sageer yace "kanada abinyi? Ni dai gidan nan nafi san zuwa."

  Abba yace "gida kafisan zuwa ko gun matarka?"

 Hassan ya kalli Sageer, shikam dariya yai yace "da alama Abba ka gano yaya, dan na kula ya gama matowa."

  Ganin yanda Sageer yai ne yasashi yin murmushi kadan yace "Abba ba haka kakeso ba dama?"

 Da sauri Abba yace "ka gama magana dan kuwa hakan shine buri na."

 Nan Hassan ya tada mota dan dama yanzu shi ya karbi tukin, Yace "Sageer kai fa? Har yanzu ba labari?"

 Abba yace "ni kaina na matsu inji labari, ya? Haryanzu dai?? Gashi har zaka fara aiki."

 Sageer yace "in nayi auren ina zan sata?"

 Da sauri Hassan yace "Sama, dan ni......."
Yanda Abba ke kallansa ne yasa yai shiru tare da waskewa yace "ni sai in barma saman."

 Dukansu sun gane me yake nufi, Sageer yace "ayi haka kuwa?? Ba gwara ni in fita ba ko kusa ne sai na nema?"

 Da sauri Hassan yace "a'a kaga kaine karami kana......."

 Dariyar da suka samai ne yasa yai shiru tare da cewa "ya akai?"

 Abba yace "wato kafisan kaganku ku biyu?"

 Hassan yai gum tare da cigaba da tukinsa, Abba ya mai nuni da fruit suka tsaya suka siya.

 A cikin gida yai parking, suka fito.


**********


 Jalila kuwa bayan ta fito Ummy ta kaida ita daki ta sata ta shafa janbaki da kuma kwalli, tana sawa kusa ta fito das, Ummy tace "ko ke fa? Ki dinga yin wannan simple makeup din amma ba daga mai sai powder ba."

 Jalila tace to a kunyace, Ummy ta fito tana cewa "Jalila fito ki tayani mu karasa, nan Jalila ta fito da sauri dankwalin na saman kanta, haka suka karasa girki dan dama Ummy tayi kusan rabi, suna jerawa a dinning Ameera ta dawo, tsalle tai tana kallan Jalila tace "gaskiya ne Matar Yaya irin wannan kashe kala?"

 Jalila ta maka mata harara tace "to hajiyar sa ido."

 Ameera ta ajiye jaka da hijab ta matso kusa da Ummy ta gaisheta da gida sannan ta gaida Jalila da gida tace "amma an samu matsala da daurin dankwali."

 Jalila ta matso kusa da ita tace "ai anan matsalar take."

 Ameera ta sa hannu ta rikota tace "Ummy muna zuwa."

 Jalila ta tirje tace "bari mu karasa jerawa, ko?"

 Ameera ta saketa sannan itama ta fara neman tayasu, Ummy tace "dama kin barshi dan ana gama ci zakiyi wanke wanke, sannan kiyi abincin dare."

 Kallan Ummy tai da sauri tace "duk ni kadai?"
 Ummy tace "ko dani za'ayi?"

 Ameera tace "a'a!"

 Jalila tasa dariya dan yanda tace a'a abin dariya.

 Suna gamawa taja hannun Jalila sukai daki, zata fara yi mata Jalila tace "tsaya ayi a hankali dan na koya."

 Ameera tace to, nan ta fara mata a hankali tana gani, suka gama aka sake warewa aka sakeyi, Ameera tace "yauwa Matar Yaya yanzu kinfi kyau."

 Jalila tai murmushi tace "Allah yasa na iya daurin da kaina."

 Ameera tace "ai ba wuya zaki iya."

 Nan ta kara sa dan sosan hoda ta gyara fuskarta, jin magana a falo yasa ta kalli Ameera da sauri.

 Ameera tace "Mai Sanyinki ya dawo."

 Jalila ta mintsineta tace "wallahi zan fadamai sunan da kike cemai."

 Ameera tace "na tuba ayi hakuri."

 Nan Jalila tai dariya, Ameera ce ta cire kaya ta sa wasu tana cewa "ba wanka dan wallahi sanyi nakeji."

 Jalila tace "ni dai sa mu fita tare dan kunya nake."

  Ameera ta sa riga yar kanti doguwa zuwa gwiwa sannan tasa wando pencil tasa mayafi, ta kalli Jalila tace "ya kamata muje kema mu samo miki kayan....."

 Ta wani kanne ido, Jalila ta zuba mata ido can tace "wai ni Ameera a gidan wa kika san komai haka? Gaba daya nikam mamaki kike bani."

 Ameera tai dariya tana sa turare tace "lalai Aunty Jalila ai mu nan.... a dai bar maganar kawai kar aji kunya amma idanun nan sun san komai."

 Jalila tace "to kuwa na kusa fadawa Ummy ko in fadama Yaya."

  Ameera tace "rufamin asiri wallahi wata kawa nai a islamiya ita ke fadamin komai, har littatafai take karanta mana."

 Jalila tace "ba karatu kuke ba kenan?"

 Ameera tai shiru kafin tace "munayi."
Jalila tace "Hmm..."

 Da sauri Ameera tazo kusa da ita tace "Ni kaina nasan abinda muke bai daceba, kafin ma ki fada Allah na daina, dan na tabbatar Ummy inta sani zataji ba dadi dan ta yarda dani."

 Jalila tace "to dan Allah adaina."

 Nan suka fito tare.


*******

A falo kuwa Hassan suna shigowa ya wuce sama dan ya dauka tana can, yana shiga yaga bata ciki, juyowa yai ya fito sai daya fito falo ya tsaya yace "yanzu in na sauka bazasu fahimci abinda nazo nema ba?"

 Nan ya zauna a falo na wasu yan mintina kafin ya sauko, Ummy na ganinsa ya sauko tace "Hassan ka sauko?"

 Ya matso yana cewa "eh Ummy nadan shiga toilet ne."

 Tace "ya kaji yau? Dakaje masallaci?"

 Kusa da ita ya zauna yace "Ummy dadi, sosai."

  Tai murmushi tace Alhamdulila, muje muci abinci."

 Nan suka nufi dinning.
Abba da Sageer na zaune suna magana, suka karasa, Abba yace "ah mama boy an karaso?"

 Hassan yace "Ummy kinji Abba abinda yake cewa"

Ummy ta kalli Abba tace " gaskiya adaina tsokanarmin yaro, haka kawai mutum da matarsa muna sa ran baby kusa amma........."

 Kallan da Hassan ya mata ne yasa tace "Hmm me ma nake cewa?"

 Dariya sukasa dukansu banda Hassan wanda yama rasa me zaiyi, Ummy tace "zauna kaji Hassan dina."

 Hassan ya zauna yana cewa "Ummy na kula kema."

 Tace "a'a ni ai wasa kawai nake ma.

 Fitowar dasu Jalila sukai ne yasa ya kalli gun, dan yanajin motsi yasa tasa ce ta fito, baimayi tunanin Ameera ba dan ya dauka bata dawo ba, sannan yama manta dasu Ummy agun.

 Zuba mata ido yai, wanda itama ta kalleshi, ganin yanda yake kallanta yasa kunya ta kamata, ta sauke idanunta kasa.

 Sageer ne ya tabashi yace "Yaya ka manta muna falon ne?"

 Juyowa yai ya kallesu yace "waccan yarinyar nake kallo, badai yau bataje makaranta ba?"

 Sageer yace "taje mana sun dai tashi ne."
Fcd
Ya kalli Sageer kamar gaske yace "da wuri haka?"

 Yace "ka manta friday ne? Ai da wuri suke tashi."

 Yace "oh! Lalai."

 Yaja baki yai shiru.



 Su Jalila ne suka karaso Ummy tace "Jalila zauna kusa da mijinki, Ameera ke dawo kusa da Sageer."

 Jalila ta dan kalleshi sannan taja kujera a kunyace ta zauna, itakam da kyar gaskiya ta iyacin abinci a haka? Dan ma ta yafa mayafi a kasan kafadarta.


Ameera ta karaso ta gaida kowa, ita ma Jalila ta gaishesu, Hassan kam kallanta kawai yai bai ce komai ba.

 Abba ne ya fara zuba abinci kafin kowa ya zuba, Hassan bai kara kallanta ba sai dai gaba daya so yake a dan tashi su hau sama kawai ya dan jawota jikinsa ya rungume.

  Haka kowa ya zuba itakam dan kadan ta zuba a plate dinta, Hassan dayazo zubawa ya jawo plate dinta ya kara mata, a hankali cikin maganar rada yace "ko kinfisan ci da ni?"

 Kallansa tai sannan tai kasa dakai, tura mata plate dinta yai sannan ya zuba nashi ya ajiye.

  Duk abinda sukeyi kowa na kallansu amma ba wanda ya bari aka  gane, a hankali take cin abinci, har ya kusa cinye nashi bata wanici dayawa ba, Hassan ya karkato kadan yace "in ba so kike na baki a gun nan ba kiyi gaggawar ci."

 Tace "inafa ci?"
Yace "to ko na taimaka miki kici sosai?"

 Da sauri tace "zanci."

 Murmushi yai sannan ya juyo, Sageer? Abinda ya fado mai kenan da sauri ya kalleshi, gani yai hankalinsa ma baya kansu, magana suke da Ameera.

 Gaskiya shikam yana tunanin barin gidan nan, ko saboda Sageer kamar bai mai adalci ba, gwara ace suna dan nesa ko yaya ne.


 Abba ne bayan sun gama suna shan fruit din da suka kawo a falo, Jalila da Ameera na zaune a gefe, ya kalli Hassan sannan ya kalli Ummy yace " jiya inata wani tunani."

 Tace name kenan?

 Yace " akan karatun Hassan, kinsan yanda kasarmu take, yanzu in Hassan zai nemi level 1 duk abin baxai mai dadi ba saboda shekarunsa, shiyasa nake tunanin mu nemarmusu kasar arab haka suje can shi da matarsa suyi karatunsu a tare."

  Hassan ne ya kalli Abba yace"Abba wata kasar?"
Yace "Eh mana ai gwara a nema tun yanzu kafin karfina ya tafi, yanzu ga Sageer kaga inka dawo kuka hadu ku biyu hankalina zaifi kwanciya nima sai na ajiye aikina na huta."

 Ummy tace "kace jiya bakai bacci ba kanata tsare tsare?"

 Yai dariya yace "kudaije kuyi shawara ku gani dakai da matar taka."

 Hassan yace to, yanasan barin gida amma ba wata kasar ba.


 Mikewa yai ya hau sama, Jalila ta bishi da kallo, Ummy ce tace "La Jalila kinga baisha abarbarnan ba, dauka ki kaimai."

 Tace to sannan ta mike tazo ta dauka tahau sama.

 A hankali tasa hannu ta murda kofar tare da sallama, Hassan na zaune a bakin gado ta shigo, drawer dake gefen gadon da yake ta ajiye sannan ta zauna kusa dashi tace "Ummy tace na kawo......"

 Jawota yai ya rungumeta tare da sakin numfashi, a hankali yace "ya jikin?"

Tace "da sauki."

  Saketa yai sannan yasa hannu ya jawota kan cinyarsa tare da sakala hannunsa ta cikinta, kansa ya zuro ta kafadarta ya dan kwantar kadan yace "Jalila me kike tunani akan maganar Abba?"

 Tace "Kaine zakai tunanin abinda kaga ya dace, ni ko me ka yanke yayi a guna."

 Hannu yasa ya juyo da fuskarta saitinsa a hankali ya sumbaci bakinta yace "kinyi kyau wanda har ji nai kamar na jawoki jikina."

 Idanunta ta dago ta kalleshi tace " ya bakai ba?"

 Yace " oh kumafa haka ne, ya akai banyi ba?"

 Tace "ah haba nima ai wasa nake."

 Yace "wasa? Nikam ba wasa nake ba, next time ki bini bashi."

 Idanu ta zaro tace "da gaske sai kayi?"
Yace "ah ba matata bace?"

 Kallan mamaki tamai tace "agaban su Ummyn? Su Abba?"

 Yace "Uhm Hmm....."
Baki ta saki tana kallansa, nashi bakin yakai ya sumbaceta kallansa tai.
Yace "me? In kara ne?"

 Tace "kai yaya."

 Fuska ya hade yace "wai ne menene hadinki da sunan nan?"

 Tace "wai to meyasa bakaso?"
Yace "ah ni yayanki ne? A yaushe na zama yayanki?"

 Tace "to ba duk haka aka cema ba?"
Yace "inji wa?Ummy Hassan take cemin haka ma Abba, Sageer da Ameera ne ke cemin haka."

 Tace "to ni me zance ma inba haka ba?"

 Yace "oho amma nidai banasann sunan."

 Kallansa tai ta sakarmai wani murmushi tace "to ya...."
Sai kuma tai gum...


(Nace samun gu su Hassan🤔)

#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


  (_D home of expert and perfect writer's_💡)


*65*


  Idanu ya kafeta dashi, tace "to ni wlh...."
Katseta yai yace "shikenan fadi abinda ya miki nima zan fadi abinda yamin."

Ya dagata daga jikinsa ya mike, da sauri ta sa hannu ta rikoshi, kallanta yai fuskarsa a sake yace "menene?"
Tace "haushi kaji?"
Yace "ko kadan, banasan ne na takura miki akan abinda bakyaso."
Tace "baka fahimceni bane yaya bawai banaso bane."
 Sai kuka tai shiru tana kunyar tace batasan me zatace mai ba.

  Kallanta yai yace " mubi komai a hankali, gaba dayanmu a new to this, kar muyi rushing, let's take it slowly.
Kinji?"
Yai tambayar yana kallanta, kafin yace "it look like kamar ni nake rushing dinmu."

 A hankali tana kallansa tace "a'a yaya, ko kadan ba haka bane."

 Ya daga kai alamar fahimta, kafin ya dan rungumeta na wasu sakan ni sannan ya saketa ya nufi toilet.

  Zama tai tare da yin ajiyar zuciya, ta sa hannu akanta tare da cewa "duhun kai baiyi ba wlh, ni yanzu sunan ma dazan cemai kadai bansani ba?"

  Kwanciya tai rigingine tare da sa hannunta a saman goshinta tace "Goggo na!"

 Hassan kuwa yana fitowa ya shafa mai a hannunsa ya sa turare, kallanta yai itama ta kalleshi sannan ta mike zaune, yace "kin gaji ko? Naga kunsha girki."

 Tace "a'a bayan duk Ummy ce tai sama da rabi."

 Ya matso tare da daukan agoggonsa daya cire daya shigo yana sawa yace "Ki sha abarbar."

 Tace "Ummy ce tace na kawo ma fa?"
Yace "itama Ummy wasa takeyi tasan abarba bata dameni ba inasha amma ba sosai ba tun ina yaro."

 Cikin mamaki take tunanin to meyasa Ummy tace ta kawo mai?
Kallanta yai yace "nasa a dauko mun motata inaji yanzu ta iso, ko zamu ki gaida goggo?"

 Da sauri tace "da gaske?"
Yace "eh, naji zatai tafiya gwara kije kafin ta tafi."

 Tace "bayan ko fadamin batai ba."

 Wayarsa ya dauka yace "to tunda bazaki ba bari ni naje."

 Da sauri ta mike tace "zani zani."

 Murmushi yai tare da yin gaba.

  ***************


 A zabure Inna tace "me kace?"

 Dady yai murmushi tare da ajiye mata takarda yace "Yanzun nan muka dawo daga gun lawyer 'yarki tamin transfer na shares dinta, shine nace bari na sanar dake karkiji a gari kiji ba dadi."

 Hannunta ne ya shiga rawa ta na kokarin daukan takardar, Dady yasa hannu ya dago mata tare da mika mata saitinta yace "gashi! Shiyasa yanzu nake tunanin kamar zan iya kwatar matsayin da aka hanani, dan yanzu na fiki shares a company din balle in na hada dana Safeena da Sultan, tunda jininane su, ni an hanani saboda ni ba jininki bane yanzu fa?"

  Inna kam takardar kawai take kallo ga kalamansa na ratsata, kanta ne yadau wani irin zafi sai gani nai tayi baya luuu.....
  Dady ya mike tsaye a tsorace tare da kwallawa Mumy kira, ya boye takardar a aljihu, gabansa na wani faduwa saboda tsoro karyaje ya zama ajalinta.

 Mumy wacce ke kwance akan kujera tunda suka dawo ta mike da sauri a zabure ta hawo sama.

 Ganin Inna a kwance yasa ta kwalla kara tare da kallansa tace "mu kaita asibiti, in wani abu ya samu Inna banaji zan iya rayuwa...Nashiga ukuna."

 Da sauri ya kinkimeta sukai kasa, a rikice suke dukansu, a mota ya sata suka ja sukai gaba.

 A cikin asibitin Standard suka tsaya, Mumy rungume da Inna sai kuka take kamar ranta zai fita.

 Suna shiga aka amsheta, nan likitae dake aiki a lokacin ta shiga duba halin da Inna ke ciki.

 Sai da suka dade dan har Mumy tayi kuka harta gaji kafin su fito.

  Kallan Mumy wacce tana ganin likitan ta fito ta taso da sauri, tace "Doctor menene ya faru da Innata?"

 Murmushi ta mata tare da dafa kafadarta tace "ki shiga tana ciki, in kin gama ki sameni a office zanga wasu patient ne."

 Da sauri ta shiga ciki, Dady ya bi bayanta.

 Inna na kwance tana bacci, ansa mata abu a hancinta, Mumy ta zauna tare da rike hannunta tana hawaye.

 Wayarta da tun suna mota taketa kara ta kalla, zaro ta tai a jaka tare da duba mai kiran.
Number Safeena ce a hankali ta daga tare da cewa "Safeena!"

 Kuka kawai taji ansa mata, hankali a tashe tace "Safeena? Menene hakan?"

 Safeena cikin kuka take cewa "Mumy ki taimakeni, dan Allah ki zo ki daukeni daga garin nan ko kice in taho."

 Hankali tashe tace "Safeena menene hakan? Ke da kika tafi karatu?"

 Tana kuka tace "gaba daya ni banajin dadin komai a garin nan, ban iya komai ba, dan komai yi min ake anan, ni ba kawaye ba kowa baya sona, gaba daya komai yamin zafi, wallahi ni karatun ma ba gane shi nake ba, Mumy ki taimaka ki ce na taho inba haka ba Allah zakuyi dana sani."

 Cikin tsananin tashin hankali ta mike tsaye tace "Safeena! Karkiyi komai na rokeki da Allah, naji koma menene ni zan dauki laifin ki shirya ki sai ticket ki taho, koma menene ayi daga baya."

 Safeena tasa kuka tace "nagode Mumy!"

 Kafin Mumy ta sake magana harta kashe, Dady ne yasa hannu ya rikota yace "menene ke faruwa? Me makwan ki lalasheta sai kice ta taho?"

 Tace "to ya zanyi? Cewa tai wallahi zamuyi dana sani, intai abinda bai kamata ba fa?"

 Yace "ke bakisan birgar yara ba? Bakisan halinsu ba kenan? Tayi ne dan dama ki tsorata."

 Tace "Dadyn Yasmeen in kuma ba hakan bane ba fa?"

 Yace " amma yarinya akaita wata kasar ki sa ta dawo? Kudin da aka kashe fa?"

 Mamaki ya kamata tace "kudi? Mu daina musu anan, Inna na kwance, amma nikam ya akai Inna ma ta shiga wannan halin?"

 Shiru yai kafin ya jawota jikinsa ya rungume yace "ina lekawa na ganta a haka, bakisan tashin hankalin dana shiga ba."

 Hawaye ne ya zuba mata tace "nagode ma Allah ma dayasa ka shiga da bansan ya zamuyi ba."

Dady ya kalli Inna tare da runtse ido.....


************

 Yana gaba tana binshi a baya suka fara sauko wa, harya kai steps na hudu tace "yaya? Me zakacema su Ummy?"
Yace "ke zakiyi musu bayani ai."

 Ta saki baki zatai magana taga har ya yi nisa, da sauri ta sauko.

Suna falo a zaune anata hira, Ameera ta zake sai labari take basu.

 Sageer sai dariya yakeyi.

 Suka sauko, Ummy ta kallesu tace "za'a fita ne?"

Yace "eh Ummy dama...."

 Bata jira ya cigaba ba tace "a dawo lafiya."

 Yace "sai mum dawo."

 Sageer yace "Yaya ba neman Ameera tai rakiya?"

 Harararsa yai yace "yau ba islamiya ne?"

 Tace "yau fa friday yaya..."

 Yace "oh ba'azuwa yau?"

 Tace "eh!"
 Ya juya ya fita, Jalila kanta a kasa tace "Ummy!"

 Ummy tace "a dawo lafiya Jalila"


Ameera tai dariya, fitowa tai ta taddashi a gun Mamman da alama makullin ya ansa sannan suna magana.

 Yana ganin ta karaso ya bude motar da key din hannunsa sannan suka cigaba da magana.

 Itakam shiga tai ta zauna tare da kallansa yana magana, ta tabbatar da dane gaisuwa ma dakyar zata hadasu.

 Can ya taho itakam ta saki jiki tana kallansa, sai dataga yazo jikin motar ta sauke idanunta da sauri.

  Bude motar yai ya shiga tare da kallanta ya kunna motar suka fita.

 Sun danyi shiru kadan kafin yace "Kinsan wata rana da kika taho cikin ruwa, kina kuka?"

 Tace "ni? Yaushe?"
Yace "ranan dana fara ganinki amma ke baki ganni ba."

 Kallansa tai da sauri tace "kaine dama wannan dan......"
Sai kuma tai gum, sai kuma tasa dariya tace "dama kaine?"

 Ya kalleta sannan yace "kinsan nasan kin zageni a lokacin?"

  Tace "ni?"
Yace "sosai dan na ganki a adaidaita ma kina harare harare, da yan maganganu."

  Kallansa tai tace "inalilahi..."
Ya kalleta kawai tare da mai dakai kan titi yace "ban taba tunanin mara kunyar nan itace wacce ake nemamin ba."

 Tace "Allah inada kunya."

 Yace "ai da nake nufi, dan haka na daukeki, sai dai in aka duba abin nine na miki ba daidai ba, ta ya ina ganinki cikin wannan halin amma nai ignoring dinki sannan naji haushi dan kin hararen?"

 Ta kalleshi tace "nima ai ban kyauta ba, menene nawa nasan wanda ban sani ba ya taimaka min?"

 Yace "kuma fa haka ne."

 Dariya tai tace "lalai yaya ba kara?"
Yace "karar kenan, fadar gaskiya."

Ita kanta mamakin yanda suke hira tai har suka isa kwanar gidan, wani shago ya tsaya yace suje sudan siyo mata abinda zata kai kauye, Jalila tace "kamar me?"
Yace "ina na sani?"

 Tace "nima wlh ban sani ba kaga ban taba zuwa ba."

 Yace "to kawai mu bata kudin gobe in zasu tafi sa biya ita da Mamman su siya."

Tace to.
Nan suka ja mota.

  A kofar gidan sukai parking, matsowa yai gaf da ita, ta zaro ido tana kallansa cikin mamakin me yake shirin yi da yamma nan, gari da haske? Jitai yace "kin manta spots din nan?"

 Kallansa tai tace "name??"
Yace "ko ayi sai a tuno?"

 Da sauri tasa hannu tadan tureshi kadan tana dariya tace "ba ruwana."

Yace "au baki manta ba ashe neman magana ne."

 Da sauri ta bude kofa tana dariya, ta shige ciki.

 Goggo na ta kara karfafa kafarta tana ta yawo a tsakar gida, lantana na falo ana ta kallo ana yanka alayahu, Jalila ta budo kofa.

 Goggo cikin mamaki ta kalleta tace "Jalila!"

 Da gudu Jalila ta karasa ta rungumeta, tace "Goggona!"

 Goggo ta shafa bayanta tace "haryanzu ba'a girma ba?"

 Jalila ta kara kankameta tace "shine zakiyi tafiya ba rakiya."

 Hassan daya shigo ya tsaya yana kallanta, Goggo tace "Hassan sai kayi hakuri wannan matar taka inta samu gu akwai sakalci da shagwaba."

 Da sauri Jalila ta dago, ta kalleshi, dan batasan ya shigo ba.

 Sake Goggo tai cikin kunya ta boye a bayanta.

 Hassan ya karaso ciki, Goggo tace "muje falo."

 Lantana tanaji alamu ta dauke kwanan alaiyahun ta shige kitchen.

 Hassan ya shiga yana murmushi, Jalila na rike ta baya da rigar goggo.

 Da zata zauna tasa hannu ta ture hannunta tace "to ai abarni na zauna ko?"

 Jalila ta saketa tare da zama a kusa da ita.

 Hassan ya kalleta yace "ikon Allah! Malama a barta ta sake mana."

 Jalila ta noke kafada alamar a'a dariya ma ta bashi ya kalli Goggo sannan ya gaisheta ta amsa tana cewa "ai kanada aiki, dan wannan in ta samu guri...."

 A ransa yace ai haka nake so.
Amma a fili kawai murmushi yai yace "tafiya kuma tazo."
Tace "wallahi, ai in ba zuwa nai ba hankalina bazai kwanta duka ba."

 Yace "Hakane, Allah yasa a taradda alkairi."
Tace "Ameen."

 Nan ta tambayi su Ummy da mutanen gidan, suka danyi hira, Jalila na makale da goggo.

 Goggo ta kalleta tace "tashi ki taya lantana ayi sauri a gama abinci yaci."

 Ta mike tai kitchen.

 Basu dawo ba sai da sukai sallar magrib, da zasu tafi yaba Jalila kudi ta kai mata, da kyar Goggo ta amsa tanata cewa ai Ummy ta bata wasu, taira godiya kamar ranta zai fita.

 Tana mamakin wadan nan mutane da halinsu, lalai haihuwa ta biya mata, ko a mafarki bata taba kawo kanta cikin wannan halin ba......


  #OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


*66*

  A hanya hannunta ya jawo ya rike yana tuki da daya hannun, shiru tai kawai tana tunanin yanda taji haushin mutumin nan sanda ruwa ya daketa, lalai inkaga mutum ka kalleshi, ikon Allah baya karewa a rayuwarnan.

 Kallanta yai yace “me kike tunani?”

 Tace “kawai!”
Yace “ni sai yaushe za’a fara mannemin kamar yanda akema Goggo?”

 Ta kalleshi sannan ta sunkuyar dakai tace “manne mata nake?”

 Yace “umm, gashi ni kuma abin birgeni yakeyi, a taimaka a faramin irin shi.”

 Dariya tai tana kallanshi tace “lalai yaya! Nikam bansan ya nakeyi ba.”

 Hade fuska yai tare da sakin ajiyar zuciya yace “ya zanyi? Da alama sai na jira.”

 Tace “sai ka jira me?”
Kallanta yai tare da kara hade fuska yace “ ya na iya?”

  Shiru suka danyi har sukai tafiya mai dan nisa kafin yace “Jalila haryanzu bakiyi tunanin komai akan maganar Abba ba?” Yai maganar yana murza hannunta.”

 Ta kalleshi cikin kulawa tace “ko kara kawoshi a raina ma banyi ba, ai na fada ma duk yanda kace haka za’ayi.”

 Iska yadan furzar kadan yace “ina san mubar gida mu zauna mu biyu amma bana sha’awar barin kasata, sannan banasan tafiya nabar family na.”


 Shiru tadanyi kafin tace “ka duba kaga abinda ya dace, ni duk abinda ka yanke daidai ne a gurina.”

  Kallanta yadanyi kafin ya karkatar dakan mota kan layinsu, yace “ nagode Jalila, na tabattar akan dukan lamurana yanzu am not alone.”

 Murmushi tamai tare da saukar da idanta kasa.

 Cikin gidan suka shiga yai parking din motarsa tare da kashe ta, kallanta yai yace “muje ko?”
Tace “hannuna...”
Yace “au.”

 Sannan ya saketa, kallansa tai tace “na dauka yanzun ma cemin za’ai, kin tabbatar ba ke kike san na rikeki ba?”

 Tai maganar yanda yake magana, girman idanunsa yadan rage yace “haka nakeyi?”

 Tace “eh mana.”
Yace “sakemin naga?”

 Tai gyaran murya kadan tace “kin tabbatar ba ke kike san........”
Bakinta ya sumbata tai saurin zaro ido tare da kallansa, sannan ta waiwaiga wajen window, yace “ya akai? Kunya kike?”

 Tace “yaya? In wani ya ganmu fa?”
Yace “hmm to menene a ciki? Mukai a wajen gidan goggo ma bare cikin gida?”

  Da sauri tasa hannu ta toshe ma baki tace “oh ni Habiba!”

 Kafadarsa ya daga alamar ko a jikinsa kafin ya nunamata bakinsa da hannu.

 Sakarmai baki tai ta turo bakinta tace “yaya dan Allah ka daina zancen wajen gidan Goggon nan tun kafin mu fada a inda za’aji.”

 Yace “ahh ta ya za’ace indaina zancen rana datake special a gurina?”

 Idanu ta kuramai kamar zatai kuka yace “kinaso na daina?”
Da sauri ta daga kai alamar eh.

 Yace “tam sai kin min abu goma wanda nace inaso.”

 Tace “abu goma?”
Yace “eh! A duk lokacin danacemiki inasan abu sannan na hade hannayena haka to dole kimin, kin yarda.”

 Dariya tai kafin tace “lalai yaya tun daga yarintarka kakesan fanshewa, wannan fa abin yara ne.”

 Yace “sosai, ai dama na fada miki ki shirya, kuka kika ce kin shirya.”

 Tace “to naji.”

Bude mota yai ya fito yana Murmushi, itama ta bude ta fito tana murmushi.

 Ba kowa a falo da alama kowa yana daki, sama kawai ya wuce ita kuma tai dakin Ameera.

 Kanta tasa a jikin kofar tace “Ameera!”

 Ameera ta taso ta bude da sauri tace “matar yaya an dawo daga hotel din?”

 Tace “hotel? Nan mukace zamu dama?”

 Ta dan daga mata gira tace “ai na gano.”

 Jalila ta daka mata duka tace “wallahi ke yar duniya ce, uban hotel mukaje ba hotel ba.”

 Ameera tasa dariya tace “wasa nake miki wallahi, kawai so nake naga na tsokaneki.”

  Jalila ta harareta tace “su Ummy fa?”

 Tace “sun tafi daki, ya Sageer ma haka, abincin ku na kitchen.”


 Jalila tace “ai mun koshi amma bansan ko Yaya zai kara ba.”

 Ta juya tace “sai da safe.”

 Ta hau sama.

 Hassan ya cire riga kenan tana turo kofa, kallansa tai da sauri ta nemi fita daga dakin.

 Da sauri yace “Amarya ina zaki?”

 Ta juyo tace “ na manta akwai abincin mu ne a kasa.”

 Takowa yai inda take kawai ya maida kofar ya rufe sannan yasa hannu ya rikota.

 Tace “Yaya....Abinci....”
Yace “ai kinsan a koshe muke ko?”

 Tace “hmm na dauka...”
 Saketa yai sannan ya koma ya dauko yar shara sharar shirt ya saka sannan yasa wando three quarter bata taba ganin ya kwanta a haka ba dan da doguwar riga jalabiya yake kwanciya.

 Kallansa tai kallan mamaki, yace “ya akai? Kyau na miki?”

 Tace “nagane...” sai kuma tai shiru, yace “da can ma dan karki takura ne yasa nakesa jalabiya amma dama haka nake kwanciya ta.”

 Jalila tace “yanzu fa?”

 Takowa yai kusa da ita, tadan yi baya kadan yace “yanzu na san mun zama daya ba maganar takura.”

 Kallansa tai kawai tai yake sannan ta zauna akan kujera.

 Yace “ ina kinyi sallah a gidan Goggo?”
Tace “eh!”
Yace “to ki taho mu kwanta dan bacci nake ji.”

 Tace “ zan danyi tilawa ne tukunna.”

 Yace “okay to ki shirya ki matso sai muyi tare, ta kalleshi kafin tace “to.”


 Yaka ta shige cikin mayafi ta canza kaya cikin dabara sannan ta shiga toilet, pant dinta ta wanke ta shanya sannan tasa wanda ta shigo dashi daga falo.
Bazata manta ba a makaranta Zahra take bata labari haka taga yayarta nayi in tazo gida ko a gidanta.

 (Mata ba wai sai kince ke bazaki iya wanka ba in dare yayi ba, ko kice inkinyi wanka ma miji zai saki ki sake wani, ko baki yi wanka ba at least change ur pant, wannan abu nada mahimmanci, Please karki sa pant tun safe har washegari yanada babbar illa.)


  Jalila na fitowa ta dauko qur’ani sannan ta matso kusa da gadon ta hau, sai data biyamai yamata gyara inda ya dace sannan ta rufe qur’anin ta ajiye.

 Jawota yai jikinsa suka kwanta, luff tai a jikinsa tanajin duminsa, a hankali taji yace “zan daure.”

 Dagowa tai ta kalleshi tace “da me kenan?”

  Kwanciyarsa ya gyara yace “ba komai.”

 Yanda yai maganar yasa ta murmusa.

 Yace “dariya kikai?”

 Dagowa tai ta kalleshi tace “ni? Yaushe kenan?”

  Da sauri ta maida kanta jikinsa tare da jan bargo.

 Shima rufa bargon yai har kansu yana cewa “inji da kunene acemin ba’ai ba?”

 Dariya tasa tace “da gaske fa Yaya ba abinda nai......”

 (Jinai suna dariya nace hmm bari nai nan kafin Hassan ya fara tunanin wani abu har ya makoni......)
  **************


 Mumy sam ta kasa bacci daga ya dauketa take farkawa, balle dataga Inna taki farkawa, abinda likita tace mata take tunowa.

 “Fatima sai dai addu’a, da yardar Allah mun samu numfashinta ya dawo sai dai bamuda ikon sawa ta bude idanunta, sai dai mu dage da addu’a sannan a kula da ita sosai, kar a dinga hayaniya a inda take, da alama wani abu mai tsananin mamaki ya faru da ita ne har yasa ta shiga shock haka.”

 Mumy ta kalli Dr hankali a tashe tace “ba wani abu da ya faru da ita.”

 Dr tace “ bazai yiwu ba, dan alama ce ta taji wani abu wanda ya girgizata har ya santa cikin wannan halin, karfa ki manta bawai faduwa tai ba ko kuma dama batada lafiya ne.”

 Mumy tai shiru tana kallan Inna, a hankali ta goge hawayenta.

 Jitai an dafata ta baya, juyowa tai ta kalleshi hawaye suka zubo mata.

 Dady ya tsugunna tare da rungumota jikinsa, yana shafa bayanta alamar lalashi.

 Itakam kuka kawai takeyi.

  Washe gari suna zaune a asibiti wajen karfr hudu na yamma, Sultan ne ya fara shigowa.

 Ajiye basket din da suka kawo kato dauke da kuloli kala kala yai sannan yace “Mumy!”

 Kallansa tai tace “Sultan Yasmeen fa?”

 Yace “tana tare da Dady.”

 Bude kofar da akai ne yasa ta kalli kofar.

 Safeena ce ta shigo da gudu ta karaso ta rungumeta kam, atare suka sa kuka, tare da kankame juna.

  Mumy ta dagota tace “Safeena? Jiya fa mukai waya.”

 Tace “Mumy dama na riga ma na sai ticket lokaci, da bakice na taho ba da wani gun zanyi.”

 Mumy tasa hannu akan fuskarta tace “ya naga kin rame?”

 Safeena ta share kwallarta tace “Mumy ya jikin Inna?”

 Tace “gatanan sai addu’a Safeena na ma rasa ya zanyi.”

 Sultan dake tsaye ya juya kansa saboda hawayenn da suka zubomai......

 
  **************


  Ihun da ake yi ana bin motar da gudu ne yasa na ruga da gudu nima dan ganin meke faruwa, kauye ne sosai dan haryanzu mota ba shiga take kauyen ba sai da dalili, dan basuda mutane masu mota.

 Goggo ta kurama kauyen ido itakam bataga wani canji ba da aka samu, yana nan kamar yanda ta barshi, duk tsawon shekarun nan kuwa.

 Tuno rayuwar datai a kauyen mara galihu ne yasa ta yin shiru tana bin yaran dake bin motar da kallo.

 Ita da kanta ta dinga nuna layin, har suka je.

 Katon gida ne na gaske amma fa ba katon da kuke zato ba, kato na yawa nake nufi.

 Duk wanda zaiyi aure a cikin gidan yake zama.

 Mata gasunan kacha kacha, yara kusa kamar kaje wani taron.

 Ganin mota ta tsaya a kofar gidan wasu da ke cikin masu bin motar wadanda suka kasance a gidan suke suka kwalkwala da gudu gidan dan sanar musu.

 Kankace me sai ga mata manya ana leka katanga dan ganin abinda ke faruwa, yara maza kuwa har sun gangara gona da gudu wasu sunyi majalisa dan kiran iyayensu maza dan suzo suga abinda ke faruwa a garin nasu.

 Abba mota ya bada makekiya mai masifar kyau motar da ko a birni inkaga mutum da ita to fa lalai ya isa ne, shikansa Abba ba hawanta yakeyi sosai sai inza’ai abu mahimmi yake hawanta.


  Goggo ta kalli matan dake ta lekowa ta katanga duk bata sansu ha sai guda biyu wandanda suka kasance matan yayanta maza ne.

 Mamman ya juyo yace “nan ne ko?”

 Tace “eh nan ne, sannu da kokari mungode fa.”

 Yace “karki damu Hajiya, ki shiga kiyi abinda zakiyi a nutse inyaso da yamma sai mu koma.”

 Tace “har yamma? Kai kuma fa?”

 Yace “karki damu dani, zan gangara garin misau na samu abinci naci na jira ku, in kun gama sai ki kirani.”

 Tace “to, ta mikamai wayar tace “ samana lambarka ko?”

 Ya amsa ya saka, yai saving sannan ya nuna mata taba Lanta tace Lantana ki kalla yanda ko na kasa ganewa zaki nunamin, tace “to.”

 Ta amsa ta gani sannan ta bata.



*************

 Baki a sake ya tsaya yana kallan titi, me ya gani yanzu? Anya kuwa ba gizo idanunsa suke masa ba? Yanzun nan Yasmeen ke damunsa akan ice cream sun fito shiyana tunanin yanda zaiyi ya kwaci matsayin da yakeso a company dinsu, ya tsaya a gun bada hannu kawai yaga daga gefensa wata katuwar mota.

 Kallan motar yai saboda kyan datamai, daidai lokacin da aka dan zuge glass din baya kadan, hakan kuma yayi daidai da bada hannun da akai, sai dai ana zuge glass din nan ya hango wata mace kai kama da Goggo, bai kara kare mata kallo ba motar tai gaba.

 Kansa ya girgiza da sauri tare da cewa “lalai na fara haukacewa.”

 Yasmeen tasa kuka kallanta yai yace “menene kuma?”

 Ice cream dinta daya zube ta nunamai tana kuka tare da bua kafa, haushi ya kamashi yace “dan ya zube shine zaki dinga kuka haka?”

 Ganin yanda yake mata fada abinda bai taba yi ba yasa ta sa kuka sosai.

 Yanda yaga ana kallansa ne yasa yai saurin daukanta yana cewa “sry muje a siyo wani, shikenan?”

 Kwanciya tai a jikinsa tare da ajiyar zuciya.

 A ransa yace “yara duk an batasu da sakalci.”

(Nace kuma🤔?)



 #OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


*67*


  Dady yana tuki yana tunani harya isa asibitin, Mumy na zaune akan kujera kusa da Safeena tanata tambayarta rayuwar datai,  jefi jefi Mumy na share hawayenta dan tausayin yarta, tace "kiyi hakuri Safeena, ni a guna gata muka miki, sai dai daga baya na gane ba gata muka miki ba."


 Safeena tana kuka tace "yanzu Mumy ina Jalilan?"

 Mumy ta kalleta tare dayin ajiyar zuciya na takaici tace "Jalila tafi karfin mu, tafi karfinki, yanzu tana wani matsayin da muke neman alfarma da taimako a gurin ta."

Safeena cikin mamaki tace "ban gane ba Mumy?"

 Shigowar Dady ne ya hana mumy bada amsa, Yasmeen ta rugo gun Safeena da gudu tare da fadawa jikinta, Safeena ta kankameta tana hawaye.

 Dady ta kalla sannan ta mike tazo kusa dashi ta rungume shi tana kuka.

  A hankali ya dagata sannan yace "Saukar yaushe?"

 Tace "dazu na iso shine akace su Mumy nanan muka taho da Sultan."

 Ya kalli Mumy sannan yace "ya mai jikin?"

 Kai kawai ta girgiza alamar ba labari.
Ya kalli Safeena yace "ki huta zanje na dawo."

 Ya janyeta ya fita waje, yana fita ya tsaya a jikin katangar dakin yai shiru, ba dai yanzu opportunity bane ya bude mai bai sani ba? Kila Allah ne ya dubi zuciyarsa da yanda yai musu wahala ko shiyasa Allah ya kwantar da ita dan ya samu abinda yake so? Lalai yanzu kam ya gama sanin Allah ne yake sanshi da rahama.
 Da sauri ya dau waya ya kira babban board director na company dinsu.

 Yana dagawa yace "Abakar ne."

 Cikin mamaki yace "Abubakar kana lfy?"

 "Lfy kalau dama kira nai na fadama Hajiya ba lfy she is unconscious."

 Fuskarsa dauke da mamaki yace "Subhanallah garin ya ya?"
 Cikin muryar damuwa yace " wlh sai Allah, muna asibiti."

 Yace "ba kanta, gashi munada meeting jibi monday."

 Yace "bansan nima ya za'ai ba."
"Tunda kaine sirikinta sannan next in line ai kawai sai kai kazo."

 Yace "ta inaxan zo, kamar bai kamata ba."
"Bai kamata ba kamar ya? Dama Hajiya ai ta girma akan running din company yaci ace tun yaushe tayi resigning, sai mun ganka."

 Kafin Dady yai magana ya kashe.

 Dady yai dariya yace "ikon Allah! Cikin sauki haka?"

Ya sake wata dariyar, hada ido suke da wata nurse sai ya wayance ya fito daga asibitin.


   **********


Goggo ta shiga cikin gida ta zauna, matar babban yayansu sai kallannta takeyi.

 Goggo ta kalleta tace "Yaya an wuni lafiya?"
Cikin mamaki tace "Hajiya ai ban gane bane."

 Goggo tace "nice Laraban Meero (haka aka dinga kiranta lokacin tana yarinta)"

 Idanu ta zaro cikin mamaki tace "inalilahi wa ina ilaihi raji'un, kece?"

 Nan fa ta matso ragowar matan suka baza ido, dayar matar yayan nata ma ta taho da sauri.

 Maza da suka iso daga gona kowa ya shiga mamakin jin wacece.

 Goggo ta kallesu bayan sun gaisa tace "Innata fa?"

Nan akai shiru kowa na kallan dan uwansa.


 Jikin Goggo a sanyaye tace "batada rai?"

 Babban yayansu yace "ta rasu shekara biyar da suka wuce, har ta mutu sunanki ne a bakinta."

 Goggo idanunta ya ciciko, tace "Baffa fa?"

 Sukace yana kwance ba lafiya yafi shekara yana fama da ciwon ko waje baya fita."

  Goggo ta kallesu nan aka shiga yi mata introducing din kowa, nan ta Nuna musu tsarabar data kawo, mamaki ne ya kamasu, ganin buhun shinkafa kwalin taliya biyu da macroni, katan din sabulun wanka guda biyar, katan din omo guda hudu, katan din sabulun wanki guda biyu, ga jarkar mangyada irin katan nan.


 Nan fa aka shiga godiya da ban hakuri akan abinda aka mata, haka akai ta bata labarin yanda mahaifiyarta tai rashinta.

 Goggo ta share kwallarta kafin ta shiga gun mahaifinta.

 Shikam harda kukansa wajen neman yafiya agunta, yayi dana sani kara kuka ma yai a lokacin data ajiye kudi dayawa a gabansa, sannan ta fito tare da neman a rakata gidansu Abakar saboda mahaifinsa.

  Sa albarka agun Baffa har ta bar dakin, mahaifin Abakar yasha kuka daya ganta, yai ta neman yafiya shima a gunsu, ta ajiye mai kudin data kawo da katan din omo da sabulun wanka tai sallama ta fito.

 Bata wani zaga gari ba saboda kafarta, sai dai dakansu mutane sukaita zuwa da wanda ya santa da wanda baisanta ba, kowa yanajin tazo kawai sai dai kaga yazo.

Haka tai ta rabasu an kudi har ta samo ta baro garin....

Zuciyarta cike da tausayi da alfahari da yanda rayuwa ta juya musu....


***********



  Yanda taga yana bacci hankali a kwance yasa ta zuba mai ido tana kallo, ko da wasa bata taba kawo rayuwarta nan gurin ba.

  Idanunta na kansa sam batasan murmushi takeyi ba, jitai ance "zan iya bude ido?"

 Mamaki ne ya kamata da sauri ta dauke ido daga kansa tare da neman dankwalinta.

 Ya bude idanunsa tare da sa hannunsa ta ratsinta ya sa kansa a kasan bayanta yace " angama kallan nawa?"

 Tace "wai ba bacci kake ba?"

  Tai maganar tana dan juyowa kadan saboda rukun daya mata har jikinta takeji.

  Fuskarsa ya dago kamar me sanyin bacci yace " kina tashi na tashi, kawai banasan farkawa ne."

 Murmushi tai tace "ga alama nan, idanka ya nuna."

 Matsowa yai yasa kansa akan cinyarta yana kallanta yace "idan kara kadan?"

 Yanda yai maganar ne yasata murmushi tace "a nan?"

 Kai ya daga tare da rufe ido yace "kinga sai ki kalleni da kyau ba takura."


 Tace "ni fa ba kallanka nai........"

 Fuskarta ya nuna da yatsarsa ba tare da ya bude ido ba, tace "kasa fa?"

 Bai bude ido ba yace "yau Saturday kowa na gida, Ameera ma nanan."

 Tace "to........"

  Juyowa yai yasa kansa a cikinta wanda ya hanata magana, jitai har numfashinta sai daya amsa.

  Ta kalleshi idanunsa sun firfito a hankali tai murmushi.

  Hannuntantasa a cikin kansa tana mamakin rayuwa yanda ta juya musu daga ita har shi.

 Kamar yasan me take tunani, dan ita ta daukama ya fara bacci sai taji yace " Jalila!"

 A hankali tace "Naam!"
Yace "mu bar kasar nan."

 Fuskarta dauke da mamaki tace "mubar kasar nan?"

 Juyowa yai saitinta yace "Uhmm, I really want to see us alone."

 Tace "nan ma ai mu kadai ne."

 Sai kuma can tace "kana  nufin ka yanke hukunci?"

 Idanu ya lumshe mata alamar eh sannan yace "yanzun nan!"

 Tace "yanzu ka yanke?"

 Yace "Umm haka kawai naga barin mu nan shikadai ne zaisa mu kebe, kinga kafin mu dawo sai na fadawa Abba a nemo mana gida."

 Dariya ya bata, pillow din data daura hannunta akai shita dauka ta sa a saman fuskarsa tana dariya tace " gaskiya yaya ba kunya a harkarka, saboda haka kawai kake san tafiya?"

 Pillow din ya turo yasa hannunsa a saman wuyanta ya jawota daf dashi yace "bakya tausayina Jalila?"

 Tace "Tausayin me kuma?"

 Ya kara marairaice fuska yace "bakya tausayawa zuciyar dake san ganinsa manne da matarsa?"

 Tana dariya tace "mene?"

 Yace "nikam tafiya zamuyi, Allah yasa kafin mu dawo Sageer yayi aure ya tare saman."

 Jalila tana dariya tace "wato shi ya zauna kai ka gudu ko?"
Yace "a'a shima yadan dana kadan sai mu gudu dukanmu."

  Jalila ta girgiza kai tana dariya tace "ni dai gaskiya so nake na sauka kasa Allah kunya nakeji aga ban sauko ba."

 Ya daga ta tare da hade fuska ya koma ya kwanta akan pillow.

 Hannu tasa ta taboshi tace "fishi kai?"

 Ya kalleta yace "abani cin hanci na fita ko kuma inje in nemi izinin zama da matata."

  Jalila tai dariya tace "kace me?"

 Yace "mu gwada mu gani?"

 Da sauri ta sumbaci kuncinsa tace "inje?"

 Kai ya daga mata yana murmushi.

 Ta kalleshi sannan ta fita.


Tana rufe kofa ta kalli dakin sannan ta murmusa tace "Yayah!"

 Sannan ta sauka.

 Kunya ta kamata dataga Ameera da Ummy sun gama aikin breakfast harsuna jerawa akan dinning cikin kunya ta karasa tace "Ummy ina kwana?"

 Ummy tace "Jalila kin fito? Ai da kinyi zamanki ma Ameera anjima zata kaimuku abincinku."

 Jalila da sauri ta amshi kayan hannun Ummy tace "a'a Ummy."

 Ameera ta guntse dariyarta.

 Jalila ta shiga maka mata harara......

 Bata dade da fita ba ya mike daga kan gadon ya gyara sannan ya dau wayarsa ya sauko.

 Tana kokarin hawa sama ta kirashi sai gashi.

 Ummy ya gaida tana amsawa Abba ya fito daga daki ya gaisheshi.


 Sageer ma ya matso suka gaisa yana cewa "jiya nikam bansan sanda ka dawo ba."

 Hassan ya harareshi sannan yace "Ummy nikam a sama zanyi breakfast."

 Da sauri Jalila ta kalleshi.

 Ya dauke idanunsa yana kallan Abba wanda ke cewa "gaskiya ne, a basu abincinsu in yaso juma'a sa dinga saukowa."

 Ummy tace "kuma hakan yafi ko saboda ma Jalila bazata sake anan ba."

 Hassan ya kalli Jalila yaga yanda tai tsuru tana kallansa.

 Dariya ya kamashi ya guntse ya kalli Sageer yace "Malam gauro aci abinci lafiya."

 Sageer yai dariya yace "gauron ma ya kusa yin zuciya ya kama nasa."


 Hassan yai sama yana dariya.

 Ameera ta kalli Jalila tace "Aunty Jalila ga naku nan dama Allah yaso Ummy ta ware muku."

 Ta matso kusa da Kunnenta tace "oh su yaya ba kunya."

 Jalila tasa kafa ta taka ta.


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


*68*


 Tana ajiye tiren abincin ya sa hannu ya jawota ta fada jikinsa, kallansa tai tace "Yaya?"

 Yace "me? Bakiso na fadi haka ba?"

 Tace "taya zakace haka bayan kasan yanda su Ummy kijin dadin cin abinci dakai?"

 Ajiyar zuciya yai mai sauti yace " nikaina ba haka naso ba, to amma ya zanyi? Na kasa jurewa."

 Tace "ka kasa jure me?"

 Jawota yai ya kara rungumeta yace "nafisan na jimu shiru."

 Dagowa tai ta kalleshi tace "yaya? Nikuma tsoro nake ai."

 Yace "tsoron me?"

 Tace "naji ance duk ma'aurata farkon aure ne kawai miji ke nuna musu so, amma da zarar sun shekara daya, biyu zuwa uku zai canza mata, wani maganar mutunci ma ba samu zatai ba."

 Yanda yake jinjina kai yana tabe baki ne yasa tace " Da gaske haka ake cewa."

 Ya karkata kai yace "ohhh haka ne kenan?"

 Tace "mene?"
Yace "ban taba ji ba amma yanzu da kika fada da alama na fahimta."

 Kallansa tai a tsorace tace "me ka fahimta?"

 Dagata yai daga jikinsa ya zauna gaban abincin da ta kawo, ya nuna mata tare da cewa "matso muci abinci, yunwa nake ji."

 Kallansa tai jikinta duk yai sanyi, a hankali ta matso ta zauna tace "Yaya bakace komai ba."

 Yace "me kikeso nace?"

 Tace "Hmm abinda ke ranka."
Yace "bakomai a raina."

 Kallansa tai tace "bakomai?"
Yace "sosai, saboda labarin rayuwar wasu can daban kika bani wanda banida hadi dasu."

 Tace "yaya Goggo....."
Yace "Jalila?"

 Yanda ya kirata ne yasa tace "naam."
Yace "ya sunana?"
Tace "Ya..."
Yace "ba wannan ba ya sunana?"
Tace "Hassan?"
 Yace "gud, mahaifinki fa?"
"Abubakar."

 Yace "toh, banaso a rayuwata dake ki dinga hadashi da rayuwar wasu da kikaji ko kika gani, koda kuwa rayuwar mahaifinki ce, ni nine, sannan ke kice, bansan mace ba, ban taba magana mai tsayi da wata mace ba bayan mahaifiyata, ko Ameera kina ganin yanda muke magana, ke kadai na sani, so Please inaso ki daukeni a yanda na daukeki, nasan haryanzu baki saki jiki dani ba wanda nasan a hankali ni zan canza wannan, amma banaso ki dinga sako rayuwar wasu a cikin tamu.
 Bazan miki alkawarin rashin canzawa ba ko wani abu makamancin haka, i am a human being wanda baisan ke zai faru dashi anjima ba bare gobe, amma i will try my best to love and protect you."


 Kallansa kawai takeyi batasan kwalla ta tarun mata a ido ba, sai jitai ta gangaro mata, kai ta jinjina tana sharewa tace "nagode yaya, insha Allah bazan sake ba, sannan nima zanyi kokarin cire duk wata kunya dake damuna, sannan nima i will try my best to love and protect you."

  Murmushi yai sannan ya miko mata hannu, itama mikomai nata hannun tai ya jawota kusa dashi, yasa kansa akan kafadarta yace "Baby yunwa, yunwa nakeji."
 Murmushi tai cikin kunya tace "yanzu zakaci abinci."

 Zuba musu tai a plate, chips ne da soyayyan kwan sai farfesun kaza.

  Fork ta mikamai, kai ya girgiza mata alamar a'a tace "kace yunwa kakeji?"

 Yace "sosai ma." Ya karasa yana rike ciki.

 Tace "to naga kaki amsa kuma?"

 Yace "hannuna ciwo." Tace "hannu? Garin ya ya?" Yanda tai maganar a rikice ta kara matsowa tana duba hannunsa ne yasashi yin wani lalausan murmushi.


  Ahhhhhhh abinda taji ya fada kenan, kallansa tai rike da hannunsa tace "Ahhhhh?"
 Ya daga kai yana kara bude baki, wato shine ya sa hakalinta ya tashi? Tace "ok, ta sa fork ta debo tace Ahhh

 Bude bakin yai tare da rufe ido, jin shiru ne yasa ya bude idansa ya kalleta.

 Gani yai tana cin abincinta tana kallansa tana danne dariyarta.

 Ya kura mata ido, tace "ohh ashe fa hannun Yaya na ciwo ko?"

 Ya kara hade rai yana harararta, tace sorry na mantane yanzu ahhhh

 Fizge fork din hannunta yai yace "banaso."


 Murmushi tai sannan ta sa hanunsa cikin nata tace "bakaso?"

 Yanda tai maganar tare da langwabar dakai ne yasa ta kashe mai jiki, ita kanta batasan me ya sameta take wannan sakalcin ba, ko d yake dama can Jalila sakaliyace agun Goggonta.

 Yace "inaso."
 Yanda yai maganarne ya bata dariya ta maze tace "to In baka?"

 Ganin kamar zolayarsa take tasa ya zare hannunsa yace "nama daina cin abincin tare, a samun nawa."

 Ya juya baya tare da jan tiren gabansa.

 Dariya tai sannan ta kwantar da kanta a bayansa tace "dani yaya?"

  Idanu ya runtse dan bazai iya jurewa ba, juyowa yai ya kalleta yace "Jalila? Wato kin gama sanin lago na da alama."

 Tai dariya tace "Allah yanzu zan baka Ahhh."

 Bude bakin yai fuskarsa a daure ta samai tana dariya.

 Kare hade rai yai yana taunawa.


************


 Wani irin ihu ya saki a cikin motarsa na tsantsan farinciki, dan sai da ya zoge duka glass din motar sannan ya saki ihun tare da cewa "Kai Chairman Abubakar."

 Idanu ya lumshe can ya hango sunansa a rubuce a jikin kofar office dinsa ansa *Chairman Abubakar*

 Dariya ya saki tare da cewa "kai mutumin."
 Tunowa yai yanda members na board din suka aminta dashi da kuma yimai alkawarin bashi matsayin Inna a jibi, zasuje company din da kansu suyi convincing din directors na cikin company din."
 Wata muguwar dariya ya saki yace "kai ba sauki, kamar na janyo jibin nan haka nake ji.

Kamar ya kamata na nemi gida, dan na tabbatar matarnan tana farkawa zata nemi korata daga gidanta tunda company din na kwace.

 Can kuma yace "to in ta koreni yar ta fa? Jikokinta fa?"

 Dariya yai na jin dadi tare da cewa Ranka ya dade
Ina zaka?

 Dariya yai sannan ya tada mota, mai makon yaje asibiti kamar yanda ya kamata kawai ya wuce gida ya shiga daki ya kwanta yana latsa waya cikin nishadi mara misaltuwa.


**************


  Cikin takaici ta wanka mata mari tace "Zaliha ba kiji me nace miki bane?"

 Kallanta tai shekeke tare da sa hannunta akan kuncinta tace "shine kika mareni?"

Tace "na mareki din, dan ina yayarki sai akace duk abinda kikeso a duniya sai na miki?"

 Zaliha ta kumburo fuska tace "magana daya ce na miki in har kina so in cigaba da samo miki alhazawa muna amshe kudinsu, ki tabbatar kin kamomin akalar Babban yaran Taura, dan sai na kwanta dashi na nuna masa ya kwanta da trash sannan hankalina zai dawo jikina, ba sai lalai na aureshi ba."


 Aunty haushi ya kara kamata tace "dalla ni rufemin baki da zancen yaran nan, sai ki dinga wani nunawa kamar fansa zaki dauka akansa alhalin ni na fahimci so kike kawai ki ganki dashi, kudi nawa kikasa muka kashe akan yaran nan da mahaifinsa? Duk abinda muka tara kinsa ya kare a shirmen banza, maza nawa ne ke sanki? Dolene sai shi? Ko dolene sai ubansa?"


 Ihu tasa mata tare da cillar da pillow din dake kan kujera kasa tace "ni dai sai shi, na kuma fada miki."

 Hannu tasa ta kara kifa mata wani marin tace "duk kinsa kudina ya kare akan yaran can da ubansa, bazan iya ba, ki tattara ki koma gida inyaso sai in dauko Sariha ta zo ta zauna, dama ita ta fiki san ta taho sannan na tabbatar ita bazata dinga bijeremin ba."

 Ta juya tai gaba rai a bace, ihu Zaliha ta saka cikin wani irin murya tace "Aunty Aunty!"

 Tanajinta ta rufo kofar falon ta fita.

"Inkoma kasarmu? A ta ina? Kasar da bakomai a cikinta sai wahala? Ni?"


(Hala ni😏)


**************

 Yanda motar gabansa ta taka burki ne yasa shima ya taka, a tsorace ya dago ya kalli motar dake gaban nasa, ganin ya fita yasashi shima ya fito daga motarsa ya nufi gaban motar.


 Yarinyace wacce da kadan tafi Ameera kana kallan yanda gwiwarta ke jiki da gwiwar hannunta zakasan bige ta akai tadan fadi, kokarin mikewa ta shiga yi saboda yanda zanin jikinta ya kwaye, ga mutane harsun fara taruwa.

 Juyawa yai zai koma mota yaji muryar mai motar na cewa "ungo! Dan ma tabbatar saboda ki samu kudi kika fadomin kan titi haka, ba tin yau ba dama mukasan irinku."

 Juyowa yai cikin mamaki ya kalli mutumin sannan ya kalli yarinyar, wacce ko kallansa batai ba kafarta kawai take dingisawa tana neman wucewa.

  Ya sha gabanta yace "ungo tun kafin ki ha kin masifa, ko?"

 Juyowa tai ta kalleshi, kamar zatai magana sai suka hada ido, rike da hannun mutumin wanda yake rike da dubu daya yai.

 Ya kalleta sannan ya kalleshi yace "in zakai wulakanci sai kayi dakyau, sannan ita data fado dan ta samu kudi kana tunanin 1000 ya isheta?"


 Ranta ya kara baci ta kalleshi sannan ta fara tafiyarta, itakam yau da alama batai addu'a ba ta fito daga gida...


 Murya a zafafe yace "kai kuma waye?"

 Nunamai motarsa yai sannan ya nuna kansa alamar mai motar ne.

***********

#Oneluv💕
🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


*70*



 Mumy tai zuru tana bin Inna da kallo, me Inna take nufi da abinda ya faru a dan kankanin lokacin nan?
 Shiru tai tana kallanta waya rike a hannunta, ganin hankalinta ya kasa kwanciya yasa kawai ta kara kiran Dady, har ta katse ba'a dauka ba ta sake kira, yanzun ma sai data kusa katsewa aka daga.

 Hankali a tashe tace "Dadyn Yasmeen, ina ka shiga inata 

 Shiru yai bai amsa mata ba, tace "kana ina? Dan Allah inkana gida kazo, Inna ce yanzu....."

 Katseta yai cikin fada yace "me zaki cemin a cikin daren nan? Wai bakiga agoggo bane? Me yasa ne wai bazaku bar mutum yai bacci hankali a kwance bane?"

 Tsananin mamaki ne ya kamata tace "Bakajin dadi ne?"

Dan karamin tsaki yai yace " koma ina jin dadi ko banaji inaso a sararamin haka nan, akan me za'a dinga damuna da kira ba gaira ba dalili?"
 Tace "bangane mai kake........"

 Jin kamar ma an riga an katse wayar ne yasa tace "Hello? Hello Dadyn Yas..."
Kallan wayar tai taga kuwa an riga an katse ta tsananin mamaki ne ya kamata, tace "lafiyarsa kalau kuwa? Ko stress ne?"

 Shiru tai tana kallan Inna, kafin ta kamo hannunta cikin tausayawa tace "Inna dan Allah ki bude idanunki, gaba daya kaina ya daure."

 Anan ta dan kwantar da kanta har safiya tai, sallah tai sannan ta gyarama Yasmeen kwanciya ta dau wayar Inna ta kira Sani.

 Yana ganin kiran ko gama ringing din farko baiyi ba ya daga tare da cewa "Hajiya? Lafiya kuwa inata kira wayarki a kashe."

 Mumy tace "Sani ina kwana? Fatima ce."

 Yanayin maganarsa ne ya canza yace "Ina kwana ranki ya dade."
 Tace "me kake neman Inna ka fada mata?"

Yace "a'a bakomai, bata kusa ne?"

 Mumy tace "tana kusa sai dai bazata iya ko magana ba, menene? Ka sanar dani."

 Yai shiru tare da jan numfashi kafin yace " Hajiya muna cikin matsala, dan tabbas yau akwai gagarumar matsala dazata afku a company dinmu."

 Gabanta ne ya fadi kila hakan ne yasa hankalin mijinta ya tashi, jiki a sanyaye tace "meke faruwa?"

 Yai shiru kafin yace "Hajiya ina tsoron sanar dake domin abin ya shafeki."

"Ni kuma? Ta yaya? Ni yanzu kiranka nai akan Inna ta bani sallahu gunka, ban fahimci kuma abin ya shafeni ba."

 Shiru yai har saida ta sakemai magana sannan yace "Hajiya mijinki....."

  Sai kuma yai shiru, tace "Abubakar? Me ya sameshi?"

 Yace "ba wani abin bane ya sameshi."
Ajiyar zuciya tai dan hankalinta yadan kwanta tace "to menene?"

 Iska yadan firzar kadan kafin yace "Kwace matsayin Hajiya zaiyi a gobe dan har ya zauna da Board members."

 Cikin rashin fahimta tace "ban gane kwace matsayin Inna ba, ta yaya? A kuma wani dalili? Bayan dama matsayin nashine nan gaba?"

Yai shiru kafin yace "Ranki ya dade ki taimaka ki duba abinda yake a lulube da bargo, ki daina kallan abinda zuciyarki kesan gani, please ki duba reality."

Tace "bangane ba."

Cikin takaici yace "in bakiyi wasa ba san da kikema mijinki shine dalilin da zai halaka komai na rayuwarki, bakisan wanene mijinki ba, mutum ne dabaisan komai ba sai kansa, masan komai game dashi saboda Hajiya tasa inyi following dinsa dan ganin me yake aikatawa."

 Cikin tashin hankali tace "ni kasa na rasa me ma kake nufi da kalamanka."

Yace "ba sai kin gane ba a wannan lokacin, saboda munacin crisis din da muke bukatar mafita cikin gaggawa, Anjima karfe 10 za'a sauke Inna daga matsayinta a bashi, bawai bashin bane matsala shi din ne matsala, dolene kizo ki kwace company din da mahaifinki da mahaifiyarki suka sha wahala gun ginashi."

 Hawaye ne ya cika a idanunta fal, tace "yanzu me ya kamata muyi? Sai dai inaji kamar ina betraying din mijina akan san zuciyata."

 Ya runtse ido yace "dan Allah na rokeki da Allah ki tashi daga baccin da kikeyi, ki duba sosai kiga wanene ke betraying din wani tsakanin ke dashi, sannan ki duba mahaifiyarki da mahaifinki."

   Mumy tai shiru kafin tace "yanzu me ya kamata muyi?"

Yace "dolene a cikin dayan biyu mu zabi daya, ko dai kiyi amfani da shares dinki ki ja ra'ayin directors din, ko kuma mu nemi wanda yai investing a company din ya baki matsayin."

 Shiru tai tana tunani kafin tace "plan din farko ama cireshi dan na riga na bashi shares dina, plan na biyu kuma da matsala saboda investors din gidan mijin yarsa ne."

Inalilahi wa ina ilaihi raji'un Sani ya hau fada kafin yace "ki taimaka ki hadani da Hajiya muyi magana ma tabbatar ita zatasan yanda za'ai."

 Mumy ta share kwallarta tace "Inna tana asibiti ba lafiya."

 Sani ya runtse ido yace "shikenan magana ta kare,haka Allah yai, ya jikin nata?"

 Mumy tace "gatanan dai a kwance."

 Yace "shikenan sai nazo dubata, da alama ba sai nake company din bama."

 Mumy tai shiru hakan yasa yace "sai anjima."
Ya kashe wayar, Mumy ta dafa kanta dake sarawa, agoggo ta kalla karfe bakwai da rabi na safe, wayar Abubakar ta sake kira, bayan tayi kira biyu ma sai ma taji an kashe wayar gaba daya, shiru tai tana kallan wayar sannan ta kalli Inna, tunowa ta dingayi da kalaman Inna daya bayan daya tun kafin auranta da Abubakar yanda ta dinga neman hanata suna fada akan itafa sai shi, to itakam ai haryanzu tana sansa kuma ta tabbatar akwai wani misunderstanding ne a tsankaninsu dan Abubakar bazai mata haka ba, da kwacewa yakesan yi da ai tuntuni halayensa dake boye sun fito.

 Lalai ko saboda Inna tasan ba hakan bane gaskiya dolene ta binciko gaskiyar al'amari ko kuma kila dai da akwai wani abun.
 Sai dai ta ina? Taya zai nemi taje gidansu Jalila?

Inna ta kalla wace ke kwance, yanda mahaifiyarta da mahaifinta suke kaunar company din yanda sukasha wahala gun kula dashi.


  Idanu ta runtse tana tunani, hawaye ne suka sake zubo mata, kukan Yasmeen ne ya dawo da ita hankalinta, mikewa tai da sauri tazo ta dauketa tace "Yasmeen ganinan."

 Yasmeen ta rungumeta sannan ta fara neman komawa bacci.

 Tana komawa Mumy ta kwantar da ita sannan tadau waya ta kira Safeena, tana dagawa tace "Mumy lafiya da safan nan?"
Mumy tace "dubamin ko Dadynku na nan."

Nan ta mike tai dakinsu wayar na kunnenta tana cewa "Mumy nikam meke damun Dady wai?"

Tace "me kika gani?"

Tace jiya sai barbaza takardu yake a daki na shiga kamar yana neman wani abun, sannan da na fito kai plate kitchen najishi yana waya yana cewa "nagode yallabai bazan manta da hallacin da akamin ba, kn dai na zama chairman i will definitely fulfil your wishes."

 Cikin tsananin mamaki Mumy tace "meyake nema?"

 Safeena tace "bansani ba."
Ta karasa maganar tana knocking, jin ba amsa yasa ta tura kofar dakin, bakowa a ciki tace "Mumy ya fita."

 Mumy tace "shikenan kidanzo asibiti inasan fita ne."
Tace "okay bari nai wanka dan naga har ma angama break din da za'a kawo."

 Mumy ta kashe wayar tare dayin shiru tana tunani, me yake nema? Sannan wanene yallabai?

 Ganin batada mafita yasa ta mike tana zarya a tsakiyar dakin.
 Safeena na shigowa ta zari mayafinta tace mata ina zuwa.

 Fita tai ta hau motar da aka kawo Safeena dan daka drivern ya shigo duba Inna, tace mai gidan Jalila.

************

  Hannunsa yasa a cikin kasan rigarta tasa hannu ta rike hannunsa tare da cewa "Yayah?"
Yace "wai abin haryanzu bai wuce ba?"

Tace "menene bai wuce ba?"
Yace "gashinan gaba daya sai wani mazewa kikeyi, kindai san na fiki iya hade fuska ko?"

Ta kalleshi tare da cewa "nifa ba hade fuska nake ba."
"Ohh tafiya ne bakyasan yi dani ko me?"

 Tace "Allah ba haka bane Yaya kawai dai bansan yanda zan sauka kasa bane, nasan yanzu Abba ya fadawa Ummy."

 Yace "ikon Allah! To sai me? Ai ko bai fadaba ni zan fadamata."

 Cikin shagwaba tace "haba yaya?"

 Yace "to naji bazan fadaba, Abban ya fada mata shikenan?"
Ta kalleshi kamar zatai kuka, da alama Yaya bazai gane ba, agoggo ta kalla tace "oh ya kamata na sauka kasa fa."

 Ta fada tana neman saukar da kafarta daga kan gado, Yaya ya jawota tare da cewa "yanzun ma fitar za'ai a barni?"

 Cikin zolaya tace "ko zamu tare? Sai ka tayani?"
 Ganin yanda ya tsaya yana kallanta yasa tai dariya tare da rufamai bargo ta mikomai littafi tace "malam mai karatu ai karatu dayawa."

 Ta mike ta fita tana dariya, Yaya kam birgeshi tai, gani nai ya mike ya zura doguwar riga kawai ya sauka.

 Jalila kam sam batai tunanin zai kawo wani abun a ransa ba, kitchen ta nufa, yau kam tai sa'a Ummy bata fito ba, dadi ne ya kamata ta wuce kitchen tare da tunanin abinda za'ai breakfast dashi.

 Jan nama ta dauko ta shiga wankewa, sannan ta fara yanka albasa tana dan kankane ido.

 Jin hannu ta bayanta yasa gabanta ya fadi, a tsorace ta juyo yanda ya riketa yasa tana juyowa ta juyo daf daf da fuskarshi, sumbatarta yai yace "na sauko, da me zan tayaki?"

 Kallan kofa tai sannan ta kalleshi cikin mamaki tana kokarin zamewa tace "Yaya!"

 Yace "da me zan tayaki?"

 Tace "tayani? Yaya in wani ya ganmu fa?" Ta fada tana dan zamewa, yace "ohoo naga ke kika ce na sauko?"

 Baki ta bude tace "wasa fa nake maka kaima ka sani."
Yace "wasa? To ya akai ban sani ba? Sannan banaji kema kincemin wasan nan kikeyi."

 Baki ta bude tana kallansa tace "lalai yaya, me zance in su Ummy suka ganka anan?"

 Yace "me zakice kuwa? Kawai mijinki ne yake taimaka miki."

 Dariya tasa tace "a haka sauki fada."
Yace "a can din ma sauki zai.....yi"

 Yai maganar yana kara jawota, tace "Yaya Allah kar Ummy ta fito."

 Sumbatar wuyanta yai yace " wasa wasa da ke matsoraciya ce."
 Tace "naji, nayi surrender, ayi hakuri, hanuna a sama."

 Ta fada tana daga hannayenta.

 Murmushi yai sannan ya saketa tare da bude fridge, sannan ya rufe yace "yanzu a haka zan tafi?"

 Tace "hmm dan Allah yaya jeka ko falo ne,wallahi bansan ya zanyi ba in wani ya ganmu anan."

 Baki ya tabe sannan yace "za'asan an koreni wallahi."

 Ya juyo tare da hade fuska.
Da sauri tace "yaya?"
Tsayawa yai fuska a hade, ta matso ta dan daga kafafunta ta sumbaci kuncinsa, tace "sorry!"

 Kallanta yai fuska a hade yace "wannan karan wannan bai isa ba."

 Ya fita, kallansa tai tana murmushi har batasan tasa wuka a kusa da bakinta ba sai dataji warin albasa sosai yasa tai saurin sauke hannunta tana dariya.

 Yaya ma yana fita yadan harari kitchen din sannan yace "chance din ramawa ya samu."

 Yana kokarin bakin falon Sageer na fitowa, kallansa yai yace "Yaya? Daga ina?"

 Yace "hmm na fito gaida Ummy ne naga batanan."

 Sageer Yace "oh wallahi da sassafe suka fita itada Abba, sunje Bauchi, ka duba wayarka har text ta maka kai da Jalila."

 Yace "Bauchi? Wani abun ya faru ne?"

 Yace "wallahi ban sani ba, inaji dai zasu je gun dangin Baffanane, sannan kila akwai abin aiki da ya kaisu daga nan."

 Hassan yace "Shine baka bisu ba?"

 Sageer yace "kasan halinsu, in Ummy taje sai sun mata gori, gwara ni naje daga baya."

 Hassan ya jinjina kai yace "Hakan yayi, kace kai kadai ne a gidan kenan?"

 Yace "hmm amma nima anjiman nan zan fita zanje office din Abba akwai abinda ya sani."

 Hassan a ransa yace "kenan sai mu kadai?"
Amma a fili yace "hakan yayi, ya kamata ka dinga fita ko ka samoma Ummy wata surikar tunda dai kaga ni tafiya zanyi."

 Sageer yai dariya yace "kar ka damu an kusa."

 Hassan yace "haba? Ka gano wata ne?"
Sageer ya matso sai tin kunnensa yace "na gano amma bansan ko inada chance ba."

 Hassan yasa dariya zaiyi magana sukaji ana knocking din kofa.
 Sageer ya karasa ya bude.

 Mumy ce tsaye a gun, Sageer ya kalli Hassan sannan ya kalleta.

 Ganin haka yasa Hassan din matsowa.

 Kallan mamaki ya mata kafin yace "Bismillah."

 Mumy ta shigo jiki a sanyaye.

  Abinda takeyi hakan ya dace kuwa? Anya kuwa ta kyautama Abubakar?

  Zama tai a kasa sannan ta kalli Hassann da Sageer.

 Hassan ya kalleta yace "lafiya?"

  Kallansa tai sannan ta hada hannayenta biyu tace "Hassan ku taimaki Inna ta da ni kaina da kuma Mijina, ku duba girman Allah. Bawai abinda muka aikata ba ku taimaki rayuwarmu."

 Yanda take magana da karfi yasa Jalila lekowa.

 Ganin Mumy yasa ta tsaya tana kallanta, Hassan ya kalleta sannan ya kalli inda Jalila take, Sageer ka ya kalleshi.



#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


*71*

 Mumy ta kalli Hassan idanunta sun ciciko, idanunta duk sun koma kalar tausayi, ta kara daga hannunta alamar tsananin neman taimako, tama kasa magana sai hannunta kawai datake ta murzawa.
  Hassan kam Jalila ya kafa ma ido yana kallanta, wacce tai tsuru tana bin Mumy da kallo.

 Sageer ne ya kalleshi yanda yaga yana kallan Jalila ne yasa yace “Yaya?”

 Hassan ya kalli Sageer sannan ya kalli Mumy, daurewa yai yace “meke faruwa?”

 Mumy ta kara kallansa idanta duk ya canza zuwa tausayi, kallan inda Jalila take tai a hankali tace “Jalilah?”

 Jalila wacce gabanta ke ta dukan uku uku tana tsoron kar ace wani ya mutu, tsoron matsowa takeyi, Mumy ta kara cewa “Jalila!”

 A hankali Jalila ta fara takowa zuwa inda take, tana tafe gabanta na wani irin faduwa, kusa da Hassan ta matso ta tsaya a hankali itama tace “Mumy menene?”

 Mumy ta kalleta tace “Jalila ki rokarmana mijinki da mahaifinsa su taimaka su dakatar da mahaifinki.”

 Cikin rashin fahimta ta kalleta tace “dakatar dashi kamar ya?”

 Nan mumy ta kwashe abinda ke faruwa ta sanar musu sannan ta dora da cewa “bawai hanashi company din nakesan yi ba, dan ni a gurina yafi kowa dacewa daya mulki company din, sai dai ina tsananin tsoron kar san zuciya ya jefashi cikin wani halin, sannan bansan me yake kitsimawa a ransa ba, ance yanata duba takarda a gida, da farko ban kawo komai a raina ba sai dai bayan na taho ina hanya na fahimci me yake nema, takardun gidan da muke ciki yake nema, dan dama tun shekara uku da suka wuce nasa aka canza sunan gidan daga sunana zuwa nashi, saboda na kwantar mai da hankali, kenan korar mu zaiyi daga gidan, ni duk na rasa me Abubakar yake kitsimawa a kwakwalwarsa.”

  Hassan wanda ko kadan baiyi mamaki ba yace “yanzu halayen mijinki kike sanar mana anan? Ko kuma halin da kuke ciki ke dashi?ni na kasa fahimta.”

  Mumy tace “Hassan ka dubi girman Allah ka taimaka mana, na tabbatar in wani abu ya samu company din Inna wallahi mutuwa zatai.”
 Yace “Rai a hannun Allah yake, in lokacinta yayi banaji ke ko ni mun isa mu dakatar dashi.”

 Ya fada tare da juyawa ya wuce sama.

 Mumy ta bishi da kallo kafin ta matso kusa da Jalila, hannunta ta riko tace “Jalila?”

 Jalila ta kalleta, idanunta sun ciciko itama, Mumy tace “Jalila na san bamu kyauta miki ba ko kadan, ke da mahaifiyarki, mun wulakantaku daidai wulakanci, sai dai inaso ki dubeni ta fuskar fahimta bawai dan ke akayima ba, a’a ki dubeni a matsayinki na mace, ya zakiyi idan wanda kike masifar so rana daya yazo miki da mace sannan da tsohon ciki? Ya zakiyi in mijin da kike masifarso ya nemi ku barsu su zauna a muhallinki? Ya zakiyi in kikaga mijin naki baisan darajarsu ba, basu isheshi kallo ba bare ya nuna damuwarsu akansu?”


  Jalila tai shiru tana kallanta, Mumy tashare kwallarta tace “Nasani bazaki fahimceni ba, na kuma san ban kyauta muku ba daga ke har Goggonki ko da Abakar bai nuna damuwarshi akanku ba ni kuma baikamata na maidaku kamar masu aiki ba, sai dai Jalila ki dubeni a matsayin ba kowa ba, dan Allag ki ceshi mai neman bukata, Jalila Inna tana cikin wani mawuyacin hali.”

 Jalila tai shiru tama rasa me zatace muryar Sageer taji yace “ Please in kin gama ki fita.”

 Shima ya wuce ciki dan shikam gani yake ko kadan basu cancanci a taimaka musu ba.

 Mumy ta kalli Jalila ta kamo hannunta tace “Jalila!”

 Jalila ta daure tace “Mumy zan shiga ciki.” Ta karasa tana dan zare hannunta.

 Jalila ta juya zata tafi,muryar mumy taji “Safeena ta dawo.”

 Cikin mamaki Jalila ta juyo ta kalleta tace “ta dawo daga Abujan?”
Mumy ta girgiza kai tace “ba abuja taje ba, fita da ita abroad mukai karatu sai dai alhakinki ne inaga yasa gashi ta dawo ba karatun ba kuma jin dadin, ta fita a banza mun kashe kudi a banza sannan me makon ta dawo cikin farinciki ta dawo cikin kunci.”

 Jalila tai shiru tana kallan Mumy, kafin Mumy tace “kinga yanda rayuwa take Jalila, a da bamu daukeki a komai ba, yar mu kawai muka sani yanzu gashi kece a matsayin komai, ki duba darajar da Allah ya baki, ki rokarmana Sirikinki da mijinki su taimaka mana.”

  Jalila tai shiru, sai dai ya zatayi? Ko da ace naman jikinta suka dinga yanka, yan uwanta ne, duk duniya batada kamar Safeena, Sultan da Yasmeen, dan jini ba wasa bane.

 Yanda Mumy ke kara rokarta ne yasa tace “bari na mai magana, sai dai ko da wasa Mumy karkisa ran zasuyi abinda kikeso, ni dai zan yi iya nawa ne, ba kuma dan kowa zanyi ba sai dan Allah da darajar yan uwantaka.”

 Mumy ta hau gyada kai tana cewa “nagode Jalila, nagode.”

 Jalila ta shiga kitchen ta rage gas sosai sannan ta fito tai sama, Mumy ta bita da kallo, rayuwa kenan, wai su da sunyi tunanin cutar da ita sukai, sun killace tasu, sai gashi ashe daukakata sukai, hawaye ne ya kara taruwar mata sai yanzu hankalinta kadan kadan yake kai mata manufar Abakar, yanzu kam ta fara tantama ma in har yana santa.

  Jalila ce ta tura kofar dakin, yanna zaune yana latsa waya ta shigo, kusa da kafarsa ta zauna dan yadan jasu sama.

  Sa kanta tai saman gwiwoyinsa, ta dan karkato da kanta gefen da wayar take tace “Yaya! Shine ka gudu ka barni?”

  Kallanta yai tare da ajiye wayar yace “Bansan me zance miki bane, shiyasa na taho.”

 Ta dan rufe baki kadan kafin tace “me zaka cemin kamar me?”
Yace “mahaifinki ne, me zance?”

  Kanta ta kwantar akan gwiwar tasa kafin tace “mahaifina ne sai dai tunda nake dashi Yaya ban taba zama dashi munyi maganar mutunci ba, duk maganar da zata fito daga bakinsa zakaji san zuciya ne da tsantsan san kai.”

  Hassan yai shiru yana mata kallan tausayi, murmushi tai kafin tace “ sai dai Yaya duk yanda naso na gane na kasa fahimta.”

 Ya mata kallan rashin fahimta, tace “wani irin uba ne Dady? Yaya duk yanda naso na kasa gane wa.”

  Fuskarsa ya sa ko kusa da tata, yace “wanda baisan baiwar da Allah ya mai ba?”

  Tace “baiwa?”
Kiss ya mata yace “baiwar yarinya kamarki mana.”

 Idanu ta kankance tana kallansa kafin tace “ahh yaya.”

 Murmushi yai kafin yace “yau kinsan mu biyu ne a gidan nan?”

 Murmushi tai sannan tace “kafin mu zama mu biyu kadan taimakamin kadan.”

 Name? Tayaki breakfast din zanyi? Ya fada yana dan kamo gefen cikinta.

 Dariya tasa tace “kai Yaya!”

 Yace “ba su bane?”

 Tace “ka taimakeni kar Dady zuciyarshi tai nisan da bazata taba waiwaye ba.”
Yace “kamar ya?”

  Tace “banaso mahaifina idanunsa ya rufe, ina tsoron halin da zai afka, baya tunanin komai sai kansa, shiyasa nakeso a dakatar dashi haka daga kan san kansa da yakeyi, ya fahimci yanada responsibility’s da kuma abinda yafi shikansa daraja.”

  Yace “yanzu me kikeso ayi a tsayar dashi?”

Tace “dan Allah ka taimaki Mumy, hakkinsu ne company din nan, mahaifinta da mahaifiyarta sune sukasha wahala gun ginashi, taya Dady zai zo lokaci daya ya nemi kwacewa? Bayan na tabbatar da yayi hakuri Mumy yanda take sanshi da kanta ma zata bashi, kaga alama ce ta san zuciyata da tsantsar burin rayuwa ne yake damunsa, wanda ya rufemai ido daga taimakon da aka mai, yake ganin kamar komai ya cancanta ne shiyasa ake mai?”

  Hassan ya sa hannunsa yaja kumatunta kamar wata baby sannan yace “ohhh wannan babyn da alama ta mike tsaye.”

 Bai saki kumcin nata ba ta shiga kokarin magana tana cewa “Yaya Please!”

  Dariya yai yanda tai maganar yace “to ni kinsan bansan kan harkar ba, ta ina zan taimaka miki?”
Tace “ muje mumy sai tama bayani, lokaci yana kurewa.”

 Yace “Hmm umm.” Cikin shagwaba yai tasa dariya tace “da alama in an gama wannan zan kara nema amin abin nan.”

 Fuska ya hade yace “haka kawai ina murna zamu zauna mu biyu yanzu kuma kinzo da wani zance daban?”

 Tace “sry yaya.”


 Ajiyar zuciya yai sannan yai gaba.

  Da kallo ta bishi sannan tai murmushi, bin bayansa tai.

 Kasa suka sauko Mumy nata amsa waya tanata magana da Sani.

 Tana ganinsu ta kashe wayar tare da gyara zama.

 Hassan ya sauko kofar Sageer ya nufa tare da yima knocking.
Sageer da ya bude kofar ya kalleshi.

 Hassan yace mai “Sageer dan fito plx.”

 Fitowa yai tare da rufe kofar.

 Jalila kam na saukowa kitchen ta nufa kawai ta cigaba da harkarta.

 Duk da hankalinta nakan abinda ke faruwa a falo sai dai ta sa wa ranta abu daya, duk abinda Hassan ya yanke kawai yayi, dan bazata tilastamai akan abinda bayaso ba.

 Mumy ce ta kalli Hassan wanda yacemata “fado abinda kikeso ayi muji.”

 Nan Mumy tamai bayani kamar yanda Sani ya mata, tace “duk yanzu kudin dake running a company din 80% kudin Mahaifinku ne, hakan yasa kuna da hujjar kwatar company din kuba wanda kukeso in har bamu biyaku kudin da kuke bin mu ba.”

 Sageer yace “amma contract din ai kamar lokacin biyan nada tsayi.”

 Tace “eh, sai dai nunawa zamuyi kamar abin yazo.”

 Hassan yace “nuna wa zamuyi? Har a yaushe muka zama mu?”

 Mumy tace “bada wani abun na fada ba, kuyi hakuri dan Allah.”

 Hassan ya kalleta sannan yace “na kasa fahimtar wani abu, in an amshi company daga hannun mijinki wa kikeso a ba?”

 Tace “ni kaina bawai so nake ba, saboda koda wasa ban taba burin mulkar company din nan ba, ni kaina shi nakeso aba sai dai bata wannan hanyar ba.”

 Hassan ya mata wani kallo dan shikam ya dai jitane.

 Yace “Sageer ya kake gani?”

 Sageer yace “bari na kira Abba muyi discussing.”
Ya fada tareda mikewa.
Ganin za’a barsu su biyu yasa ya mike ya shiga kitchen.

 Ta banyanta ya tsaya tana soya yankanken kayan miya akan frying pan.

  Tana ganinshi ta juyo tana kallanshi.

 Karasowa yai ya sa hannunsa ya zagayo da ita ta cikinta ya kwantar da kansa a kafadarta yace “kallanfa?”

 Tace “ya kukai?”

 Yace “kawai dai.”

 Murmushi tai kafin tace “Thanks alot Yaya.”

 Yace “banasan wani thanks kawai zanbi bashi ne dan sai an biyani.”

 Murmushi ta sakeyi tace “da alama bashin nan nawa karuwa yakeyi dayawa.”

 Sumbatar wuyanta yai yace “da alama zamu dan barki a gida ke kadai na dan wata awa daya.”

 Kai ta daga alamar gamsuwa ba tare da ta tambayeshi ba.

 Saketa yai sannan ya wuce sama, wanka yai yasa kananan kaya sannan ya sauko, Sageer ya tarar a falon Abba yana rike d wasu takardu yana kuma waya.

  Yana ganin Hassan yamai alama dayazo, nan sukai magana su biyu kafin su fito falo.

 A tare suka fita, Mumy ta shiga motarta suma suka shiga motar Sageer.

 Suna shiga Hassan yace “haka Abba yace?”

 Sageer ya shiga yimai bayani, Hassan ya jinjina kai alamar gamsuwa yace “shikenan.”


*************

 Ba wani kato bane main branch din nasu, sai dai dayake ajiyar kayan abinci sukeyi daga baya akwai wani tangamemen fili da akai gini inda ake aikin a ciki.

  Sani na ganinta ya taso da sauridan dama yana zaune a waje yana jiranta, tanna karasowa ya matso da sauri yace “sun shiga cikin meeting din kamar minti 5 da suka wuce.”


 Mumy ta matso ta sanarma Hassan.

 Dakin babban taro na hadaka suka nufa, suna zuwa Sani yasa aka bude dakin.

  A lokacin kuwa Dady ne tsaye yana bada speech dinsa na yanda company dinsu wai ke cikin matsalar da suke san akawo mafita dan a kwatota daga ciki, Babban director din yace “Bravo! Gaskiya duk company din nan ba wanda yake sanshi da kula dashi kamar kai, shiyasa nazo da babban shawara akan sauke Hajiya wacce girma ya kamata yasa take neglecting din aiyukanta, a baka kai sirikinta wanda ka sadaukar da komai naka akan company din mu.”


  Muryar Sani sukaji yace “Investors din da suka taimaki company dinmu sunzo.”

  Kowa kallan su ya juyo yai, Mumy ta zubama Dady ido wanda gaba daya shima idanunsa na kanta.

  Hassan ya matso inda Dady yake yace “will you please get down?”

 Dady ya kalleshi zuciyarsa gaba daya ta rage bugawa yanda ya kamata, Hassan ya kalli Sageer yamai alama dakai akan ya matso.

 Sageer ya kalli Dady wanda yake saukowa kamar wanda bashida ragowar laka a jikinsa.


 Sageer ya fara bayani kamar yanda Abba yamai.
Takarda ya zaro ya daga sama yace “wannan shine contract din da mukai da company dinku akan za’a biyamu 50% na kudinmu a kwana uku da suka wuce.
 A cikin wannan contract din munyi bayani time da kuma kudin da za’a fara biyanmu.
 Sai dai jiya mun nemi Chaiwoman din company din me makon ta bamu sai ma taki daukan wayarmu, wannan dalilin ne yasa muka sauko kasan contract din wanda yace “in har ba’a biyamu kudin mu akan lokaci ba rabin company din zai dawo namu.”


 Nan fa kowa ya fara kananan maganganu, Sageer ya kallesu yace “ saboda haka daga rana tayau zan zama nine shugaban company din nan har zuwa ranar da za’a biyamu kudin mu.”


  Nan fa guri ya kachame da kananan maganganu.


  Hassan kam abin ya birgeshi wani irin dadi yakeji a ransa, lalai ilimi rahama ne.

 Hannu ya daga ya yima Sageer jinjina.

 Dady kam ji yai gaba daya wata muguwar zufa na ketomai ta ko ina.

 Wani daga cikinsu ne yace “ta ina zamu yarda da abinda ke faruwa?”

  Sageer yace “da farko ga signing din Chairwoman din nan sannan ga yartanan zatai duba, dan tana nan akai komai, sannan zan miko muku ku gani kuma.”

 Mumy wacce gaba daya dana sani ya gama kamata, jikinta duk ya gama yin sanyi, meke faruwa? Itakam ai ba haka sukai ba, ta dauka ko ita zasu barikon kwarya kafin ta samu Dady ya dawo hankalinsa, ya kamar take ganin anyi amfani dasu?


Haka tace ai komai daya fada daidai ne sannan aka mikama kowa ma ya gani, nan fa ba yanda suka iya aka ba Sageer kujerar shigabanci ya zauna akai.


  Dady kam gaba daya ya koma mutum mara amfani dan jiyai ma dakin kamar ba kowa a ciki ba kuma abinda ake cewa a ciki.

 Sai zafi da kirjinsa yakeyi......


 Mumy kallansa kawai takeyi......


Sageer ya kalli Hassan sukai murmushi, Sageer ne ya tuno kalaman Abba dayace akwai tsuhuwar contract din da suka farayi dama time din da akasa kenan, to shi bai yaga ta ba shine yasa Sageer ya nemo, Abba yace da Jalila tayi nisa a karatu da ita zai sa aba wannan matsayin ko dan mahaifinta ya hankalta.


 
#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


*72*


  Gaba daya haka kowa ya fito daga dakin taron zuciyarsa a cunkushe da wannan al'amari.
 Ya rage daga Hassan, Sageer, Mumy, Dady sai Sani ne kadai a ciki.

  Mumy ta kalli Hassan tace "amma nikam ai ba haka mukai daku ba."

 Hassan ya mata wani kallo yace "ke wacece da zaki tsara mana abinda kikeso muyi? Na dauka farincikinki kawai a kwace company din ne daga gun wannan, ba kuma naji kinada wani iko na samu ko hanamu."


 Dady zuciyarsa takai makura dan dama daurewa kawai yakeyi, jin kalaman Hassann ya kara tunzuro shi, matsowa kawai yai naga ya daga hannu kamar zai gaurawa Mumy mari, sai kuma ya sauke hannunsa yana hucci, kamar wani kumurci sannan ya bugawa Hassan wani banzan kallo.

 Hassan kam ganin yanda yake kallansa yake muzurai yasa shi yin wata dariya tare da cewa "bani na kar zomon ba, sannan ni na taba ganin wannan karfin halin?"

 Cikin tsananin fada yace "karfin hali? Karfin hali fa kace, ka san wace irin rayuwa nai har na kawo wannan ranar?" Yadanyi kara cikin karaji yace "who are u? Da har ka isa ka wargazamin abinda nake shiri shekara da shekaru?"

 Baa mumy taja saboda tsoron da Dady yake bata, Hassan ya hade fuska yace "rayuwar dakai? Wani ne ya saka? Kai fa ka sa kanka, sannan kai tambayar who am i? Nine wanda har karshen rayuwata indai har inada dama bazan taba barinka ka saci abinda ba naka ba."

  "Sata? Sata nai? Uban waye yacce haka ake sata?"

 Yace "To sanar dani in ba sata ba menene? Tsabar san zuciya ka wulakanta iyayenka, matarka, yarka, sannan yanzu kake neman ka sace abinda dayan matar da 'ya'yanka ke da shi."

 Cikin tsananin zafin rai ya matso ya sa hannu da karfi ya hankade Hassan, baya yai saura kadan ya fadi ya rike teburin dake gun.

 Dady yayo kanshi cikin fada yace "uban waye ya baka damar shiga rayuwata? Uban waye?"

 Yanda yake yi ne yasa Hassan ya kura mai ido yana kallan ikon Allah, gaba daya ma mutanen dake gun ma kowa kallan mamaki yake mai, Mumy kam hawaye ne kawai ke zubo mata, cikin masifa yake kallan Hassan yace "Uban waye nace? Duk duniya duk wanda ya kuskura yace zai hanani abinda nasa gaba wallahi zan iya mai abinda ni kaina ban san zan iya ba."

 Mamaki ne ya kara kama Hassan yace "ya zamuyi?"

"Dame?" Dady ya fada a harzuke, Hassan yace "dan banaji zan dakata daga nan, har kasa na fara zakuwa naga mai zaka iya aikatawa."

  Cikin tsananin zafin rai da bakin ciki, Dady yakai hannu ya naushi Hassan, wanda sai da ya fasa mai gefen bakinsa, ya daga hannu zai kara Sageer ya rikeshi, Dady ya juyo cikin tsananin masifa yace "menene hakan?"

 Hassan ya mike ya goge bakinsa, yace "ya zamuyi yanzu kuma?"

Dady ya mai wani kallo, Hassan yace "Sageer baka tunanin ya kamata a koreshi daga aiki?"

 Sageer yace "ai ba sai ka bata bakinka ba Yaya, Zakai resigning ne ka fita da martabar ka ko kuma kafisan mu koreka?"

  Dady yace "mene?"

 Sageer yace "ba dai kana tunanin duk wannan bugun dakai a banza kayi shi ba? Sai dai fa kayi hakuri dan duk na dau video ina jiran naji uzurinka dayasa ka naushi investors din ku."

  Dady ya zaro ido ya kalli Hassan gani yai Hassan ya mai wani murmushi sannan ya matso ya danyi ajiyar zuciya yace "in zaka saida shares dinka na company in gari yama zafi ka kawo Jalila zata siya."


  Hassan yai gaba ya barshi a gun, cikin takaicin hali irin nasa, Sageer yace "sai naga resignation letter gobe a sabon office dina." Ya juya ya fita.

 Dady ya saki wani irin ihu wanda ya kara razana Mumy.

 Sani ma juyawa yai ya fita dan shikam hankalinsa ya kasa jawomai cikaken abinda ke faruwa.

  Dady ya matso kusa da Mumy ya daga hannu ya sharara mata mari, ya kara daga hannu ya sake mata wani sannan ya nunata da yatsa yace "ke har kin isa ki sa wannan dan iskan yaran yacimin mutunci?"

  Kallansa tai tana hawaye tace "Dear."e

 Da yatsa ya kara nunata yace "don't you dare call my name like that."
 Ya matso kusa da ita sosai yace "ni kika ci amana saboda bakyasan na zama wani abun ko? Na miki saki daya."

 Kawai taga ya juya ya fita, gaba daya jitai kanta na wani irin juyawa dan ta kasa tantance takamaimai meke faruwa.
Batasan yawan mintinan da ta kwashe a tsaye ba kamar mara numfashi.
 Yanda wayarta ke ta zuba kara ne yasa ta farga, daga wayar tai ba tare data dubama wanda ya kira ta ba.
 "Mumy ki zo gida yanzu." Muryar Sultan taji a rikice yana fadar haka.

 Da sauri ta fito ta fada mota sukai gida, wasu gardawa ta gani a cikin harabar gidan, gefe kuma Sultan ne a tsaye.

 Tana zuwa ta karasa gunsu tace "lafiya?"

 Turo mu akai akan ku tattara kayanku ku bar gidan nan.

 Cikin mamaki tace "mu bar gidan kamar ya kenan?"

  Yace "ko ku bar gidan gaba daya ko kuma yace ku koma boys quaters."

  Yanzu kam ta gane wanene ya turo su, waya ta daga ta kirashi.

 Kamar bazai daga ba sai taji ya daga, cikin mamaki tace "Abakar me kake nufi akan munar gidan da mahaifina ya gina?"

 Yace "kema kiji in aka kwacema abinda yake naka ya kakeji."

 Tace "ni menene naka dana kwata?"

  Tambaya kike?
Tace "badai company dinmu kakeso kace ba?"

 Yace "ko ma menene magana ta kare, ke kika bani gidan nan da kanki sai kisan inda dare ya miki."

 Tace "zan san inda dare yamin amma 'ya'yanka fa?"

 "'Ya'ya? Ki tabbatar kin kwashesu."

  Hawayenta dake zubowa ne ya karo, tace "nikam Abakar tunda nake dakai ka taba min so na tsakani da Allah kuwa?"

  "So? Wasan yara kika koma yi kuma?"

 Mumy ta toshe bakinta saboda kuka na neman cin karfinta, kawai kashe wayar tai ta kalli Sultan tace "wuce kaje gidan Kawu, ni zan koma asibiti."

 Yace "wai mumy meke faruwa ne?"

 Tace "jeka in na dawo mayi magana."

 Shiru yai kamar ya sake magana sai kuma yace "to."


 Tana ganin ya fita kawai ta tsuguna tasa kuka, ba kowa a wajen sai ita dan mutanen ma sun tafi, itakam me tayi? Laifin me tayi da rana daya rayuwa ta juya mata haka? Hakkin bayin Allah da kukaitaci.
Kuka ta sake sawa, ta dade tana kuka kafin ta mike ta tafi asibiti.


  Safeena na ganinta ta taso tace "Mumy menene?"

 Mumy hawaye ne yazubo mata tace "Safeena ya zamuyi?"

 Hankalin Safeena ne ya tashi tace "menene?"

  Nan mumy ta kwashe komai ta fada mata tana kuka, sam basu san kafin su fara labarin Inna ta farfado ba.


  Kuka sosai sukeyi itada Safeena, Safeena tana kuka tana cewa "yanzu Mumy haka Dady ya mana? Kema Mumy kamar baki da wayau kina ganin yanda ya banzatar da abinda ya haifa duk rashin mutuncin mutun ko duk mutuncinsa indai har bai daraja abinda Allah ya bashi ba banaji zuciyarshi a tsarkake take, kina ganin duk abinda za'ama Jalila bai taba sa baki ba, bai kuma taba nuna damuwa ba, tunda kikaga haka ai kema kinsan Dady ba mutumin kwarai bane."

 Mumy tana kuka tace "duk laifinane Safeena, Inna tasha nunamin gaskiya amma banaji, yanzu gashinan ai."

Yanda Inna ke yi ne yasa suka juya inda take da sauri, hankalin Mumy ya tashi tace "Safeena kira likita."

 Da gudu ta fita, Mumy ta kamo hannunta kawai ta sa kuka.

  Inna ta fizge abin hancinta cikin wani irin murya tace "Fatima!"

 Mumy ta dago da sauri tana kuka, Inna tace "ki daina kuka, ni nasan tawa tazo karshe, ke nakeji Fatima bansan wace rayuwa zakiyi ba."

 Mumy tana kuka tana girgiza kai tana cewa "Inna ki daina fadar haka."

 Inna ta girgiza kai cikin tsananin ban tausayi tace " ki duba kasan katifa ta akwai key na safe dina akwai takardun gida dana siya kwanaki can da suka wuce, kisa Sani ya kaiku gidan.

 Fatima kiyi hakuri duk nice na cuceki, duk nice na dauraki akan rayuwar da kikeyi, san kaina da sanki yasa bana tunanin komai, Fatima bansan ya zakuyi ba, shares dina basuda yawa sai dai nasan zasu rage muku na cin abinci.

 Yanda numfashinta ke kara sama ne yasa hankalin Mumy ya kara tashi, Inna tace "karkima Abakar magana, kar kuma ki nemi kwatar gidan, ki barshi rayuwa ce,  gashinan nima na gani dayawa sun gani shima kuma zai gani, sai dai ki taimakeni da abu daya.

 Mumy ta kara runtse ido hawaye na kara zubo mata "Jalila! Da Mamanta!"

  Idanunta ne suka shiga lumshewa tace "Fatima ki nemarmin yafiyar........."

  Yanda ta kara birkicewa ne abu na ta zubowa daga bakinta ne yasa ta kasa magana, Dr ne ta shigo da sauri ta matso kusa da Inna.

   Kafin ta yi wani abu har rai yayi halinsa.
Wani irin kuka Mumy ta saka, Safeena ma ta sa kuka abin tausayi.


 ***********


  Abubakar kam yana zaune a dakin hotel din daya kama, idanunsa sunyi jaa in ya tuna abinda aka mai sai yajii zuciyarsa na kara tafasa, Fatima? Sai kaga ya naushi gefen da yake zaune, can ma sai gani nai ya mike a zuciye ya nude window kawai yana kallan waje.

  Bai taba tunanin wani abu zai kawo mai cikas ba a wannan lokacin, ihu ya saka tare da cizar lebe.


************

Goggo kam hankalinta ya kwanta dan yanzu kam taje taga yan uwanta data dade tana kewa, sun dan dade suna waya da yayanta wanda ta amshi numbersa sukai ta gaisawa da yan uwa suka mata ban gajiya sannan ta kashe, wai yanzu itace yan uwanta ke nuna mata kauna haka? Lalai duniya juye juye.


***********


  Suna shiga mota Sageer yace "Yaya wannan mutumin kansa daya kuwa?"

  Hassan yace "kansa daya kawai tsabar greediness ne ke damunsa."

  Sageer yai tsaki yace "ji fa abinda ya maka?"

 Murmushi yai yace "kar ka damu ba komai, sannan dan Allah mu bar abin nan mu biyu."

  Sageer yai dan tsaki sannan ya cigaba da tukinsa.

 Suna isa gida ya kalleshi ya mai alamar zip da bakinsa.

 Sageer ya bishi da kallo, shikam da sauri ya shiga ciki, Sageer kam juya kan mota yai ya fita dan dama akwai abinda zaiyi.

 Hassan na shiga ya wuce kitchen da sauri, ba kowa a ciki, da alama harta kammala yanda yaga har kitchen din ta gama gyarawa, juyowa yai ya wuce sama.

 Kallan kanta tai a madubi tace "kai inaa.... bazan iya sa kayan nan da Ameera ta ban ba."

 Rigace iya gwiwa, ba dogon wando, tace dama taban wando ne kila dana saka.

 Ta juya jikin wardrobe tana neman cirewa ya turo kofar dakin.

  Ta manta kayan dake jikinta, gani tai ya taho inda take da sauri, yana karasowa ya rungumeta tsam a jikinsa.
  Shiru tai a hankali yace "Baby wannan shigar fa?"

  Tunowa tai, ta kasa cewa komai, dagota yai ya kalleta daga sama har kasa, kunya tasa ta juya baya da sauri, kara juyo da ita ya rungumeta yace "saura kadan fa na fadi."

 Kallansa tai tace "kai Yaya."

 Sumbatarta yai zaiyi magana sai ya fasa yanda yaga ta kura mai ido.

 Yace "menene?"

 A hankali takai hannunta gefen bakinsa tace "me ya faru?"

  Hannunta yadan ture yace "ba wani abun bane ina sauri ne ban kula ba na danji."

  Idanunsa ta kalla sai dai ta rasa me yasa bata yarda ba.


 Kamar zatai magana sai kuma ta fasa, gani yai idanunta sun fara cicikowa yace "Menene kuma?"

  Ta fara kokarin shanye kwallar tace "ba saboda fitar dakai bane wani yama haka? Ko dad......"
Kara jawota yai ya rungume yace "ki bani abinci, yunwa nake ji."

  Shiru tai cikin rada  yace "mu biyu ne a gidan, na dauka Sageer zai shigo sai naga ya juya, kinga yau sai mu....."

 Sai ya kara matsowa kusa da kunneta yace "sai a biyani bashina duka."

 Dagowa tai ta kalleshi, kamar zatai magana kuma sai yaga tayi murmushi tace "ka dainajin yunwar ne?"

 Cikin shagwaba yace "ina fa? Ai ni yau a nan ma za'a bani indai anaso inci." Ya fada yana nuna bakinsa.

 Dariya tai, ya ja hannunta suka nufi kasa.


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


*74*


 Haka ya jawo hannunta har kasa, dinning ya nufa ya zauna akan kujera yace "anan."

 Kai ta daga alamar to sannan ta nufi kitchen, tana zuba abinci tana tunanin abinda ya faru har aka bigemai baki dan kana gani kasan ba faduwa bane.

  Haka ta zuba ta nufi dinning, tana ajiye wa ya dagata ya daurata akan saman dinning din inda yake, kallansa tai tana dariya tace "karfa nai barna, inya fashe fa yaji nauyi."

 Baki ya bude alamar mamaki yace "kuma fa haka ne, kar muje muji abu ya fashe ba shiri."

 Fuska ta hade tace "yanzu ni har katuwa ce dazan fasa wannan table din?" Ta fada tana bubuga table din."

 Ya dan canza fuska yace "kuma fa haka ne, taya ma za'ace babyna guda zata karya wannan katan abin? Wai waye ma ya fada?"

 Ido ta kafeshi dashi, waige waige ya shiga yi yace "ni wai waye ya fara maganar nan?"


  Serving spoon ta mikamai tace "zubama da kanka."

  Kwanciya yai a kan cinyarta yace "ni kam in ba'a ban abinci ba nan da minti biyar Allah inaji za'a samu matsala."

  Dayake rigar karama ce daya kwanta sai ya zama kasansa kadan rigar ta tsaya, hannu yasa ta cikin cinyoyinta da sauri tace "zan zuba wallahi, ni wallahi tsoron zama anan nake, in wani ya shigo fa?

 Dauke kansa yai daga cinyarta yana dariya yace "in suka ganmu kinga sai suyi gaggawar bamu namu muhallin."

Jalila ta kalleshi cikin mamaki tace "lalai yaya." Ta karasa da dariya tare da fara zubamai abincin.

 Shiru yai yana tunanin mahaifinta, Jalila ta kalleshi tace "Yayah!"
 Kallanta yai yace "yah?"

 Tace "me kake tunani?"
"Me kika gani?"

 Tace "bakomai."

 Fork ta mikamai, ya kalleta sannan ya dan shagwabe yace "ni faduwar danai dazu ma kamar na bige hannuna."

 Murmushi tai sannan tace "ba sai kayi pretending ba." Ta karasa tana debo abincin.

 Murmushi yai sannan ya shiga karba, yaci sosai sannan yasha tea, kwantar da kansa ya sake yi a cinyarta tace "yaya....."

 Jitai cikin sanyin murya yace "Jalilah?"

 A hankali tace "Naam."
"Ki dinga ma mahaifinki addu'a yayi nisan da sai dai a kwatoshi da addu'a, da fatan nemar masa shiriya agurin mahalicci."

  Jalila tai shiru tana kallansa, dago da kansa yai amma kan na kan cinyarta yace "bawai wani abun bane, kawai dai ina tunani addu'arku ita yafi bukata. Ya karasa da murmushi wai dan ya nuna mata bakomai.

  Yanda take kallansa ne yasa yace "ba wani abun bane kawai dai........"

 Katseshi tai tace "shi yama haka ko?" Ta fada tana taba gefen bakinsa."

 "Oh wai akan me babban mutum zai daki kamar ni? Ni ba dan yaro ba nima?"

 Jalila tace "abinda Mumy ta fada hakan ne ko?"
"Name kenan?"
Na Dady zai kwace musu company dinsu da gidansu?"

 Kai kawai ya juyar ya kara kwanciya yace "bansani ba."

  Hannu tasa ta dagoshi tace "Yayah?"

 Yanda ya kalleta yasa ta sakeshi tana murmushi tace "hakan ne , yanzu ya kukai?"

 Yace "mun samu an kwace company din daga gunsa yana gunmu yanzu sai dai bansan maganar gidansu ba."


  Jalila ta fara neman hadiye kwallarta tace "Yaya ta ina dan Adam zaiyi haka? Taya mutum zaiyi haka? Kuma mutum din ma wanda yake mahaifi? Miji?........"
Hawayenta ne suka nemi fitowa yasa ta shiga motsa baki tana neman hadiye kukanta.

  Hassan ya jawota kan cinyarsa yana kallanta, kallansa tai sannan ta sunkuyar da kanta hawaye suka fara zubo mata.

 Yace "to ke yanzu kukan me kike a takaice? Ke kikai? Shifa yai sannan a yanda mahaifinki ya nuna kamar ba wanda ya isa ya....."
Sai kuma yai shiru, hawayenta ta shiga sharewa suna sake zubowa tace "ni da wani ido zan kalli mutanen gidan nan? Da wani ido zan kalli wadanda suke jinina?"
Hassan ya jawota jikinsa yana lalashi, yace "mubar kasar nan a dan kwanakin nan, naga alama in ba barin kasar nan mukai ba bazan daina ganin kina kuka akai akai haka ba."

  Dagowa tai ta kalleshi, yace "ni kila zan dan saki kuka amma kadan, dan haka." Ya fada yana nuna tsagun karamar dan yatsansa.

 Jalila tace "ashedai zaka sani kaima."
Yace "kardai inyi karya ne ai.


 Murmushi tai sannan ta kalli gefenta da wayarta ke ta kara.

 Ganin sabuwar number yasa "ta daga jiki a sanyaye."
 Jalilah? Cikin mamaki tace "Safeenah"

 Safeena tana abin kuka tace "Jalila Allah yayima Inna rasuwa."

 Gaban Jalila ne ya fadi, ta mike tsaye daga jikinshi jikinta duk ya fara rawa tace "Inalilahi wa Ina Ilaihi Raji'un, yaushe?"

 Safeena tana kuka tace "dazun nan, yanzu muna hanyar kaita gida ne za'a mata wanka."

 Jalila hawaye ne ya zubo mata tace "bari nima ganinan zuwa."

 Safeena tace "Gidan kawu zamu kaita, acan za'ayi zaman makoki, dan Dady ya koremu."


 Jalila jitai kanta yayi dum kafin tace "ya koreku kamar ya?"

 Safeena tana kuka tace " sai kinzo."
Dan batasan me zatace ba acikin wannan yanayin, gaba daya Jalila ta juyo tace "Yaya? Inna ta rasu."

 Hassan wanda tundayaji yanda take magana jikinshi ya bashi Inna ce ya matso ya rike hannunta wanda keta rawa yace " Jalilah?"

 Kallansa tai tana zare ido tace "yaya ina Dady yake?"
Yace "wallahi bansani ba, menene?"

 Tace "Yaya meke damun Dady? Taya zai kori mutane daga gidansu?"

 Hassan yace " bangane kora ba?"

 Tace "nima bansani ba amma kome ya faru wannan abinda dan adam ya kamata ya aikata ne? Gidansu ne fa?"


 Ta fada a rikice, Hassan yace "yanzu kizo muje in kaiki gidan gaisuwa komai ya biyo daga baya, sannan mutanen nan sumafa sun cutar dake."

 Hawaye ya sake zubo mata tace "sun cutar dani amma ba kamar shi wanda ya haifeni ba, ya banzatar dani da mahaifiyata duk abinda ya faru damu ba ruwansa........."

 Rungumentan dayai ne yasa tai shiru, yace "ya isa haka nan, ki kira Goggo ki sanar mata sai mu biyo mu dauketa."

  Ta daga kai alamat to.


 Nan ta kira ta sanar mata, Hankalin Goggo ya tsahi tsantsa dan gaba daya ma kasa magana tai, Jalila ta koma ta shirya suka fito suka shiga mota, gaba daya haryanzu hankalinta ya kasa kwanciya dajin abubuwan nan biyu.


Gidan Goggo suka wuce suka daukota suka fito, Hassan yace "kamar ya kamata asai wani abun ko?"

 Jalila tace "abu kamar me?"

 Yace "bari na tambayi Abba."

  Shiru tai ya kira Abba sukai magana, itakam sai cewa take "Goggo nikam dama Inna batada lfy ne? Ni gaba daya na kasa gane abinda ke........"

 Tabota da Hassan yai ne yasa ta kalleshi, magana yai mara sauti yace "Karki kauce hanya."

 Shiru tai itakam gaba daya....
Goggo kam dama tundaga gaisuwa batasake magana ba, gaba daya mutuwar tazo mata a ba zata.



**********

  Kallan kansa yai a madubi "me ya kawoshi nan?"

 Hannu yasa yana shafa kirjinsa yace "Sageer da alama ziyara zaka gidan Aunty Nana."

  Wata zuciyar tace "kaine kake zuwa gidan haka kawai?"

 Can yai sauri ya kara cewa "ai yanzu haka na koma."

  Kallan layin da yake yai yace "ai dubata zanyi a musulunci kuma ziyarar mara lafiya akwai lada mai yawan gaske."

  Kara tada motar yai yana dan hango gidan shikam yaje yace me?
 Inaa bada shi ba, gaba yai kadan ya juya kan motar, yana neman yin gaba mai adaidaiti na parking, fitowa tai daga ciki sanye da kayan makaranta na health school, kudi ta mikamai ta juya, hartayi gaba sai kuma ta tsaya ta juyo ta kalli motar, girman idanta ta rage dan ganin mutumin dake ciki.


 Kunya ta kara kama Sageer ya daure ya fito tare da dan daga mata hannu kadan, yana yake.

 Maimuna ta dan fara takowa shima yana takowa, sai da suka matso kusa da juna sannan tace "Ina yini?"

 Yadan sosa keya kadan yace "lafiya, nazo wucewa ne sai na hango gidanku, naji kamar ya kamata na tambayi jikinki."

  Kallansa tai dan taga sanda ake juya motar tana hanya, tace "na gane shine kake neman juyawa?"

 Yace "hmm daga bayane nai tunani kamar kuma na tafi, kar kiji abin banbarakwai."

 Murmushi tai tace "yanzu fa?"

 "Yanzu kam tunda naga kingani naga kuma kamar dai kamar dai."

  Tace "to yanzu nagode zance?"

 "Ba nagode kadai ba kinga saboda kar asani tunani dawowa inaji number kawai za'a bani yanda zan kira."

  Batai mamaki ba, dan yanda fuskarsa take da idanunsa yasa ta fahimceshi, tadai gane ta baya yakesan biyo mata.

  Murmushi tai kafin ta mikamai hannunta, wayarsa yamika mata yana murmushi.

  Amsa tai ta saka mai, nan suka danyi hira kadan kafin ta shiga ciki.

 Tana shiga ya washe baki yace "ahhh Malam Sageer da alama kaima......"

*************


  Kayan abincin da ake ta shigowa dashi ne yasa mutanen dake zaune suka mike suna cewa "daga ina??"

  Jalila ce ta shigo itada Goggo bayan masu ajiye abincin sun ajiye, Safeena na hango Jalila ta mike da gudu tazo ta rungumeta tare da fashewa da kuka....

 Itama Jalila hawaye ne ya zubo mata, Yasmeen dake kwance jikin Mumy ce itama ta mike da gudu ta taho gun Jalila.

 Hawaye ne ya kara zuboma Mumy aranta tsantsar nadama ce fal, Goggo Safeena ta kalla tana kuka tace "Goggo sannu da zuwa." Dan da bata ganeta ba saboda canzawar datai.

 Mumy ta mike tacema "Goggo tazo ta zauna."

 Mutanen gun kuwa mamakin kayan da aka shigo dashi da kuma sunan Jalilah da suka jine yasa kuwa ya kunshe gulmar dake ransa, dan tabbas sunsan sunan wasu kuma sunsanta.

  (Balle dama a wannan lokacin da gidan mutuwa ya zama gidan gulma, gidan sa ido, gidan hira da gidan cika ciki, mutuwa kuma anbarma wanda akayima)


********

Tsaki yai tare da cillar da wayar kan gado dayaga sakon Safeena akan cewa Inna ta rasu, a fili yace "Ankarama kasa nauyi."


  Ya kwanta kawai tare da neman yin bacci.

Sai dai duk yanda yaso yai baccin nan ya kasa, daga ya kwanta sai ya farka a razane, mikewa yai ya dara bankan ruwa, tare da komawa kan kujera ya zauna......



#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


_Am sry nayi mistake a gun sa number, 73 ya kamata na saka sai na saka 74🤦🏼‍♀, yanzu wannan shafin dame zan kirashi🙇🏻‍♀?_

*74*

Su Jalila sun dan dade a gidan dan Hassan fita yai ya barsu a ciki, Safeena na zaune kusa da Jalila, can wajen sallar azahar Mumy ta nemi Goggo data shigo tai sallah, Goggo ta mike ta nufi dakin da Mumy tai.

 Tana shiga Mumy ta zube a gabanta Goggo cikin mamaki take kallanta tace "Fatima menene hakan?"

 Mumy ta kara sa kuka tare da riko hannun Goggo kuka kawai takeyi tama rasa ta ina zata fara.

 Goggo ta sa hannu ta dagota sannan ta kalleta tace "duk mai rai mamacine, muma wata rana sai labari, Inna a wannan lokacin addu'a kawai take nema."

 Mumy ta share kwallarta tana kallanta tace "Nama rasa ta ina zan fara, dan Allah ku yafe mana, ba dan mu ba bakuma dan halinmu ba sai dan darajar ma'aikin daya hallicemu, ku yafe mana ku yafema Inna, mun wulakantaku, mun maidaku kamar bayin mu, bama tunanin komai sai kanmu, yanzu ga yanda rayuwata mana, mijin da nake tunanin yana kaunata yanzu na gane ba komai a ransa sai san kansa, mahaifiyar dake tsananin kaunata ta tafi farat daya, dan Allah ki yafemin ki yafema Inna....."

 Kuka take sosai, Jalila wacce ganin su Goggo sun tafi yin sallah yasata mikewa itama dan tayi, Safeena ma ta mike tace "muje tare."  Sun shigo sukaji kalaman Mumy, Jalila ta runtse ido hawaye suka zubo mata, itakam Safeena gun Mumy ta tafi ta sa kuka itama.

  Jalila ta matso sannan ta kalli Goggo, wacce itama hawayen takeyi.

 Mumy ta kalli Jalila tace "Jalila ki yafe mana dan Allah."

 Safina ta dawo kusa da Jalila tana kuka, rungumeta Jalila tai itama tana kuka tace "ya isa haka nan, duk wani abu na rayuwa mai wucewane, sannan tunda dai har kunsan baku kyautamana ba kunyi dana sanin haka, ni na yafe muku har Inna, tunda a yanzu in har ma na nemi kin yafe muku to lalai hakan na nuna ban gode ma Allah akan ni'imar daya bani bane, ban godemai akan canjin dana samu ba, bangode mai akan mutanen daya hadani dasu bane."

  Goggo ta dafata tare da cewa "hakane Jalila, a koda yaushe na kasance mai alfahari da ke a matsayin 'yata, nima na yafe muku, sai dai mu nemi yafiyar Allah gaba dayan mu."


  Haka sukai alwala sukai sallah, Mumy sai bama Goggo labarin yanda abin yadamu inna farat daya da kuma abinda Abubakar ya musu.

 Goggo kam batai wani mamaki ba, banda dai gidan daya kwace musu, amma itakam ai tana mamakin yanda idanun Mumy suke rufe ruf akan Abakar.

  Goggo tace "bai kyautaba sannan kuma bai kamata a barshi ba, wannan fa fashi ne, kema kinyi laifi maida sunanshi dakikai.

 Mumy tai murmushi tace "bakomai mun bar mai gidan, dan ko Inna cewa tai mu barmai, ita rayuwa haka take, wanda kake tunanin yana sanka a lokaci guda sai ka fahimci ba sanka yake ba, wanda kuma kake tunanin baya sanka sai daga baya xaka fahimci shine jego na rayuwarka."


 Sai yamma lis suka fito daga gidan, Hassan yazo daukansu, tare sukazo da Abba da Ummy a tasu motar suka musu gaisuwa suka fito.


  Gaba daya idanun Mumy ya canza, duk tabi ta yashe a lokaci daya, mutane kuwa kowa sai tambayar inda Dady yake sukeyi, itakam batasan me zatace musu ba, Safeena ce ma ta daure tace musu bayanan kuma wayar sa tun jiya a kashe take shiyasa ma har a wannan lokacin baisani ba.


 **********


  Goggo suka fara ajiye wa sannan suka nufi gida, gaba daya Jalila ko magana bata iyayi, tayi shiru kawai tana tunanin rayuwa, hannunsa yasa ya riko hannunta, juyowa tai ta kalleshi a hankali tai murmushi.
 Yace "tunanin me kike?"

Tace "rayuwa kawai, yanda ta juya mana."

  Ya dan murza hannunta kafin yace " ya isa haka nan ni dai na gaji da ganin hawayen nan."

 Kallansa tai sannan tace "na daina."

  Yana kokarin shiga gidan kawai sukaga anzo gaban motar aka tsaya, saura kiris ya buge wanda ke tsayen, wani irin burki yaja tare da rintse idanunsa.

 A zabure Hassan yai parking dan yayi tsananin tsorata, kansa yasa a jikin sityarin motar, Jalila ma idanu ta rufe da sauri tare da sa kanta a kasa.


  Knocking din glass din motar inda yake a zaune aka shiga yi, a hankali ya dago tare da addu'a, kallan glass din motar tasa yai, sannan ya zuge tareda kallan gun.


  Matar daya gani ne yasa shi yin mamaki, yace "baiwar Allah lafiya? Taya zaki doro gaban mota in tsautsayi ya ratsa fa?
 Kallansa tai sannan tace "Hassan nice."

 Hassan nice? Ya maimaita yana kallanta, Jalila ce ta kalleta tace "ke wa?" Batasan sanda tai tambayar ba saboda mamaki.

  Zaliha ta kalleshi tace "Zaliha."

 Zaliha? A ina na sanki?

 Jalila ta kafeshi da ido, da sauri yace "a gidan ubanwa na sanki? Yau naji ikon Allah."

 Tace "Hassan dan Allah ka taimakeni, dan Allah ka taimaka ka min magana da Taura."

 Cewa Tauran datai ne yasahi kallanta yace "wai Trash ce?"

  Kallansa tai tace "Hassan?"

 Kallanta ya sakeyi yace "me kike anan gidan?"

 Ya fada yana kallan kayan jikinta, yace "kece wai haka?"

  Tace "Hassan ka taimakeni dan Allah."

 Hade fuska yai yace "wallahi in baki barnan ba zansa a kulleki."

 Ya fada tare da jan motarsa yai ciki, kuka tasa sannan ta juya tana tafe tana hawaye, itakam tayi dana sanin yanda ta dauki rayuwa, yanzu gashi kudin abincin dazataci ma wahala yake mata, ama bar maganar gurin kwana, gaba daya samarinta sun gujeta, dukansu tunda sukaga batada gata, kowa nema yake yai amfani da ita yaki biyanta, wani ma dayai amfani da ita korota yai wai yanzu gaba daya bayajin komai, to yanzu batada mai bata kayayyakin datake cutar maza dasu.

 Hawayenta ta share tare da cigaba da tafiya.....


 Suna shiga cikin gida Jalila ta kalleshi sannan ta hade fuska tana neman fita daga motar, dariya yasa tare da riko hannunta yace "Hajiya ya zaki tafi ba tare da Alhaji ba?"

 Tace "wai wacece haka da har tasan sunanka?"

 Yace "wa? Wai Trash?"

 Ta kalleshi, yace "au kishi kike da abin zuba shara?"

 Tace " wai wacece?" Yanzu kam ta saki fuska dan ta tabbatar ba abin mutunci ne ke tsakaninsu ba.

 Hassan yace mata "itace wacce ta nemi ruguzamana gida."

 Jalila tace "wannan yarinya? Amma ya akai ka santa?"

 Nan ya sanar da ita abinda ya faru wanda bata sani ba, cikin mamaki tace "macen dake ji da kanta haka itace ta koma haka?"

 Ya daga kafada alamar rashin damuwa yace "duniyar kenan, mutum yayi dakyau ma ya yakare bare irinsu? Wanda burinsu su ruguza farin cikin iyalan dake zaune cikin farin ciki?"


 Jalila ta jinjina kai cikin mamaki tace " Allah yasa mu gama da duniya lafiya."

 Hassan ya jawota jikinsa yace "wai sa gaske kishi kika fara daga ganin mace?"

 Ta dan turo baki tace "a iya sanina bakasan wata mace ba kaga in naga kasan wata ai dole nai tunanin abu daban."

 Yai murmushi ya dan matso saitin kunnenta yace "ya zamuyi?"
Tace "dame?" A tsorace ta tambaya.

 Ya kara nanikota yace "dan banida niyyar sanin wata mace bayan ke."

 Wani faffadan murmushi ta sake sannan tace "kai yaya?"

 Dariya yai sannan ya saketa yace "kin dauka wani abin zan fada?"

 Tace "eh mana." Ta fada tana dariya.

 Ido ya kura mata, tsayawa tai da dariyar tace "ya akai?"

 Yace "inaso naga kina dariya Babyna."

 Kallansa tai sannan tai murmushi, ya dan shagwabe yace "Ahhh! Ina murna za'a barmu mu biyu ashe......."

 Hannu tasa ta rufe mai baki tace "zaka fara ko?"

 Yace "gaskiya ni mu tafi gidan Abba."

 "Muje muyi me?"

 Yatsa ya nuna mata alamar 2 ta harareshi ta dan ture hannunsa tace "gaskiya yaya bakada dama."

 Ya sako kansa kusa da ita yace "yanzu muna shiga nasan su Ummy zasu iso, ahhh nasan kila Ameera da Sageer ma suna ciki."

 Ta kalleshi tana dariya tace "ni su Ummy basu dawo ba?"

 Yace "eh zasu biya gidan Aunty Nana ne."

 Tace "ayya, muma haryanzu bamuje ba, sai randa muka dauko Ameera shikuma bamu shiga ba."


 Yace " hmm ni duk ba wannan bane a gabana yanzu burina mu tafi inda zamu zauna mu shana."


 Dariyarta ta guntse tace "sai kaje kai kadai ni ina nan."
Ta fada tare da saurin fita tana dariya.


 Biyota yai tana shiga ciki ya jawo hannunta yace "me kika ce?"

 Tace "bance komai bafa."

 Yace "mu shiga daga ciki sai a sanar min."

 Dariya tasa tana cewa "dagaske..........."

 Kallan gefensa yai cikin falon, Sageer ne zaune shida Ameera sun saki baki suna kallan ikon Allah.

 Da sauri Jalila ta dan matsa tana sinne kai, Hassan ya kalleta tare da dauke kai yace "muje?"

 Ta kalleshi ta gefen ido tana nuna mai su Ameera, yace "muje sama ki kara fadamun."

 Tace "ni hira zamuyi da Ameera."

 Hassan yace "zakije ko na sungumeki?"

 Kallansa tai da sauri tace "Yaya??"

 Yace "Sageer da Ameera hira kuke?"

 Sageer yace "eh."

 Hassan yace "banaji kuna kallan nan bangaren ko?"

 Sageer yasa dariya yace "sai ma mubar falon."

 Hassan yace "kinji, muje?"

 Da sauri tasa gudu tai sama tana dariya......

 Matsowa yai kusa dasu Sageer yace "sry fa kasan ni."

 Sageer yace "hmmm ai ba sai an bamu hakuri ba, mun sama idan mu labule."

 Hassan ya kalli Ameera yace "ke kuma fa? Gulma ko?"

 Tace "a'a nazari nake a raina."

 Ya juya yai gaba, yana hawa suka sa dariya......



#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


_Gaisuwa tare da sakon godiya gareku Mom Farhan, Haske da Meela Adeel wanna shafin naku ne 🥰🥰🥰🥰Much Luv

 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Tuba nake jiyaan jini dif kamar wutar nepa🙈
*75*


  Tana shiga daki ta jingina da jikin kofa tana maida ajiyar zuciya, itakam Hassan nema yake ya maidata mara kunya.

  Jin an murda kofar yasa ta kalli jikin kofar inda take a jingine, yace "wallahi ko a bude ko kuma in na shigo in wahalar da mutum."

 Jalila tace "menene wahalar?"

 Yace "Ayya wallahi in na irga uku ba'a budemin ba? Hmm ban masan ta ina zan fara ba."

Guntse dariyar ta tai tace "nima sai na kira Ummy."

Yace "wacce Ummyn? Ai kema kinsan Ummy tawa ce, ko kwace akesan min ne dama ban sani ba."

 "Zan faea irgawa fa, kuma ko wacce number na kira tana dauke da babban bashi wanda kiss kadai bazai biyashi ba."

  Daga kofar tai ta shige can cikin dakin, yana shigowa ya bita da inda tai, da sauri ta haye gado tare da saukowa daya bangaren, tana kokarin nufa kofar yai gudu ya rufe kofar sannan ya fizgota suka fadi kan carpet.

 Wani irin dan kara yai tare da cewa "shikenan an karyani."

 Dagowa tai da sauri gabanta na faduwa, ta lleahi idanunta sun firfito.
Cikin tsananin tsoro tace " Yaya? Ina ne? Nashiga ukuna."

 Hannunsa ya langwabar yace "nan ne, nikam kamar kashin gun ma ya karye."

  Gabanta ne ya kara faduwa a tsorace ta kalleshi sannan ta shiga taba hannnun, tsabar tsoro sai ma taji kamar ya karye din, tana tabawa yana cewa "wash Allah na...."

 Jalila ta kar rikicewa tace "Yaya tashi muje asibiti, nashiga ukuna."

 Idanunta duk sun canza, yadan karkace kai irin abin zafin nan yace "Jalila kaini na kwanta kawai ba sai naje asibiti ba."

 "Yaya kargun yai tsami gobe azo kasha wahala."

 Yadan kara raunane fuska yace "yanzu insu Ummy sukaji kin karya musu d'a mai zasu ce? Ki bari gobe sai mu fita ba tare da kowa ya sani ba."

  Jalila tai shiru tana tunani, yace " kinsan dai in Ummy taji kin karya mata d'a akwai karamin matsala ko?"

 Jalila tai shiru tana tunanin yanda Ummy ke san Hassan, yawo ta hadiya sannan ta kalleshi.

  Yace "kaini na kwanta bakomai insha Allah."

 Jalila idanunta sukai raurau gaba daya itakam batasan ma ya zatai ba, yace "ni nace ki kaini na kwanta ba wani abun."

 Jalila ta dagashi yanata wani wash, ta kwantar dashi.

 Yace "dan bani ruwa nasha."

 Da sauri ta juya ta dauko mai ruwa a fridge ta matso ta bashi, yace "bazan iya mikewa ba."

 Da sauri ta ajiye ruwan ta shiga kokarin dan jinginar  da shi, sannan ta miko mai ruwan ya amsa da dayan hannun ya fara kokarin yanda zaiyi ya bude, da sauri ta amsa ta bude mai sannan ta mikamai, amsa yai da hagu yasha.

 Yana gamawa ya mika mata jarkar ta amsa, yace "bari na kwanta dan buguwar tasamin ciwon kai, idanunta suka kara raunana tace "yaya Allah muje asibiti naba su Ummy hakuri."

 Yace "karki damu Baby, Kinga Ummy tanada hakuri tana kuma da sanyi sai dai bata kyale wanda ya tabani ko kadan, kinga mubar maganarnan."

 Jalila ta kalleshi sannan tace "to."

 Gyaramai kwanciya tai sannan ta zauna a gefenshi, tare da rike mai dayan hannun.

  Yace " banfa ci abinci ba tun na safen nan ga yanzu har an kusa magrib."
 Tace "bari naje kasa na zuboma nasan tunda Ameera ta dawo tayi girki."

 Ya daga kai kamar wanda baya magana, tace "sannu." Sannan ta mike ta fita, tana fita yai dariya yace "ahh baby nah." Ya jawo pillow ya rungume.


  **********

 Kallansa yai kafin yace "kana nufin bazaka bani kudina ba kenan ko me? Ni na kasa fahimtar inda ka dosa ne."
Wani mugun murmushi yai yace "wai kai da a haukarka kana tunani ni zan bi wadanda muka rabama kudi ince su dawo dashi ne ko me?"

 Cikin zafin rai Dady yace "dama ba sun amshi kudin bane dan su bani mukami? To tunda bai samu ba basai su dawo dashi ba?"

 Wata dariya yasa mai wanda ya kara kular da Dady yace "stop dreaming Abakar, dama nine na damu mu baka wannan mukamin ko saboda nima na samu abinda nake so, ko da dan haukarka da karamin tunani ka dauka 'yan board din ne suka amince a kawo ka a baka matsayin nan?"

 Kallan mamaki Dady yakemai kafin yace "ba hakan bane?"

 Director din yasa dariyar mugunta yace "ah haba? Abinda ka dauka kenan? Saboda na basu kudinka na lalabasu ne yasa kaga suna daga wuya akan a baka mulkin nan, kudin daka raba musu ne yasa suka bi bayanka bba wani abun ba."

 Dady ya matso a zuciye ya cakumeshi yace "ni zaka wulakanta? Kasan ko ni wanene?"

  Cikin karfi ya fincikeshi hakan yasa dady ya fadi kasa, board director din ya nunashi da yatsa yace "kai wanene? Mtsw ni zaka maida karamin mutum? Ko ni nace ma ka kwaso kudi dayawa? Ni dai nasan cema nai kawai ka kawo kudi a basu, ko nace ma ga yawon kudin da zaka ciro? Shashashan banza kawai, har kai ka isa ka maidani karamin mutum? Ashe da babban kuskure na kusa tafkawa.

 Yai tsaki sannan ya koma cikin gida, Dady ya mike da kyar ya shiga mota yai shiru, can ya dauko wayarsa ya duba dan yaga balance dinshi.

 Dubu dari shida ya gani kwata kwata, dan dama miliyan bakwai ne dashi a ciki, wai saboda ya birgesu sai yabada miliyan shida wai a raba musu dan su zabeshi, sannan ya kama katan hotel inda yake ciki, tsaki yai kafin ya sa hannunsa a saman kansa, yanzu gashi ance dole ya kawo takardar ajiye aikinsa gobe, nausan sityarin motar yai kafin yai wata ajiyar zuciya, tun farko ya riga ya bata kansa agaban mijin Jalila yazu gashinan hanyar daya bi bata billemai ba.

  Kwafa yai kafin yaja mota yai gaba, hotel dinsa ya shiga ya wuce ya kwanta yana lissafi, can ya dau waya ya kira Jalila, dolene ya kira ta ya lallabata ta samu tasa mijinta ko aikinsa ne a barshi dashi in har baza'a bashi matsayinsa ba.

  Hassan na kwance yana jiranta ta kawo mai abinci yaji wayarta na kara, ganin number ne yasa ya ko daukan wayar, kiran bai dade da katsewa ba ta turo kofar, da sauri ya gyara kwanciyarsa.

 Ta shigo ta ajiye abincin ta matso inda yake, tace "yaya tashi kaci abincin."
Kallanta yai tare da kara ragwancewa yace "Jalila hannuna kamar zai cire."

 A tsorace tace "nikam yaya ka taimakamin muje asibiti zanba Ummy hakuri."

 Yace "dagani naci abinci."

 Dagashi tai sannan ta kalleshi rike da spoon din, dan a hannun dama ne ta ina zaici?
 Kallanta yai sannan ya bude bakinsa, haka ta debo zata samai wayarta tai kara, kallan wayar tai sannan tasamai sannan ta matso gefensa tasa hannu ta dauko wayar, dauka tai tare da yin sallama.

Jalila! Sunanta da aka kirane yasa gabanta faduwa dan ta gane mai muryar, dady yace "Jalila magana zamuyi in kina kusa da mijinki dan Allah kidan matsa."

 Jalila ta kalli Hassan wanda shima kallanta yakeyi, tace "me zakacemin da har sai na matsa?"

 Dady yace "Jalila wai yaushe kika zama mai musu ne? Nine mahaifinki wanda fa duk duniya baki da kamarshi."


 Shiru tai sannan ta ajiye abincin a side bed sannan tamike, Hassan kam bai mata magana ba yana kallo ta fita falo ta rufo kofar.

  Jalila tace "inajinka yanzu ba kowa, Dady yadan ja numfashi yace "Jalila tunani nakeyi, mai zai hana in
dawo da mahaifiyarki? Na tabbatar ke kanki babban burinki ne hakan, yanzu tunda nasamu gurin zamazan kula da ita yandaya dace, ke kanki kinsan bawai santa bane banayi, ba dai yanda zanyi ne."


 Jalila tai Shiru tanajin wannan sabon salon wulakancin, cikin takaici taji Yana cewa "Jalila kinsan abinda mijinki yamin kuwa? Kinsan wulakancin da sukamin shida kaninsa? Amatsayina na mahaifinki ai banaji ko mai nai ya kamata yaran nan yaci mutuncina, sai dai bayansa zanyi nima nasan ban kyauta ba dana nausheshi, dan Allag Jalila ki bashi hakuri kinji? Ni mahaifinkine ya kamata yasan darajata kinji?"


Bakin Hassan ta tuno a ranar dama jikinta ya bata Dady ne sai dai batasan zargi shiyasa.

  Dady zaiyi magana tace "kaje gaisuwar Inna?"

 Yace "wani gaisuwa bayan na rabu da matar sannan ko kin manta ne? Yanzu nake miki zancen komo da mamanki."

 Jalila cikin takaici tace "Dan Allah dady kai wani irin mutum ne? Wanda zuciyarsa da kansa kawai ya sani? Taya mutum magidanci mai iyalai kamarka za'ace bakasan komai ba sai kanka? Baka tausayin mu? Baka tunanin yanda muke kallanka?
In har ni da Goggo bazaka faranta mana ba taya za'ace wadanda ka moresu a iya tsawon rayuwarkasuma bazakaji tausayinsu ka faranta musu ba?  Wannan wani irin tsabar san kai ne?
Sannan maganar Goggo ma ka dainata dan alama ce ta kaidinba mutumin da zai iya rike wani bane, kanka kawai zaka iya rikewa, sai ka cigaba da zama kai kadai har karshen rayuwarka dauke da alhakin 'ya'yanka wadanda Allah ya daura maka hakkinsu, sannan magana ta karshe, Karkayi tunanin Goggo har yanzu a wacce ka sani ne,  yanzu tanada gatan da ya wuce tunaninka, dan tanada gidan zama sannan bata rasa komai na duniya ba, insha Allahu kuma Allah zai bata wani mijin ta aura, hakan yasa dama nake neman taimako a gurinka akan in da auranka a kanta ka taimaka ka sauwake mata, ko dan........."

 "Jalila ni Abubakar kike fadawa haka? Har yaushe aka haifeki da zaki nemi yimin wa'azi?"

Jalila ta maida numfashi tace "ba wa'azi nake ma ba rokonka nake."

 Roko? A banza? Inhar kinasan na saki mahaifiyarki sai kin sa mijinki ya barmin aikina ya kuma barmin company din dana sha wahala gun kula dashi."


 Mamaki ya kara kama Jalila idanunta suka ciciko cikin takaici tace "Dady yaushe ka zama haka? Nasan dama can kanada san kanka sai dai bansan abin naka yakai haka ba? Dady wace irin rayuwa ka daura kanka a ciki?"

 Dady yai shiru, Jalila tana kuka tace "ka manta wahalar dakaba baiwar Allahn nan? Kasa ta rabu da iyayenta, ta rabu da 'yan uwanta, sannan kai baka bata farin ciki ba sai kunzuga mata dakai, yar data haifa baka taba tausaya mata ba, baka taba nuna mata ko kula da ita kamar yanda Uba ya kamata ya kula da dansa ba, dan Allah dady a tsawon rayuwarka mai ka taba yima baiwar Allahn nan? Wannan wani irin san.........."

 Kukan daya kubce mata ne yasa ta kasa magana, dady yai shiru shikansa yanzu jikinsa yayi sanyi dajin kalamanta, da sauri ya kashe wayar sannan ya kwanta rigingine a kan gado.

 Hassan na jin kukanta, sai dai baisan me zai ce mata ba, bakin cikin mahaifi ne wanda ba wanda ya isa cire mata shi.

  Idanu kawai ya runtse yanajin kukan har ransa, mikewa tai ta bude kofar tana share hawayenta, kusa dashi tazo kawai ta rungumeshi tsam, shafa mata baya ya shiga yi, ta dago ta kalleshi tace "bari nasa abincin a microwave nasan yanzu duk ya huce."

 Kai kawai ya daga mata ta dau abincin ta fita dan dama a plate kawai ta zubo mai.


 Tana sauka su Ummy na shigowa ta musu sannu da zuwa sannan tai kitchen, Ummy ta kalli Abba tace "Jalila akwai sansanyan hali, yanzu kaga wai matar data mutu fa tayima kuka haka idanta ya canza haka?!

 Abba yace "matar data wahalar da ita, gaskiya mu gode Allah."

  Nan sukai ciki suna hirarta, komawa tai sama ta taraddashi a zaune yanda tabarshi, kusa dashi taje ta zauna tace "tunanin me kake?"

 Yace "ba komai." Amma a ransa yace a satin nan zamu muyi visa.

 Haka ta zauna ta bashi abincin har ya koshi, ta bashi ruwa yasha, zata mike ya riko rigarta, kallansa tai yace "wanka nake sanyi."

 Cikin mamaki tace "yanzun? Ya zamuyi?"

 Yace " ya zakiyi kuwa tunda ke kika jimin ciwo kika karyani, haka nan zaki zo kimin."
 Idanunta taxaro tace " ni?"

 Yace "sosai."

 Haka ta taimaka mai ya cire kaya yasa towel itakam duk kunya ta isheta, sai rokonshi take ya bari yayi wankan gobe amma yaki, haka ta jashi sukai toilet.

 Bayata juya saboda kunya shikam ya sa hannu ya jawota cikin bath hub din, kallansa tai da sauri zatai magana ya saki shower gaba daya ta jike, kallansa tai sannan ta kalli hannun daya riketa dashi tace "Yaya?" Ta fada tana kallan hannunsa.

  Zata sake magana ya jawota tare da kai bakinshi cikin nata.........



^**********


  Ganin magrib ta kawo kai yasa Mumy ta kalli wayarta sannan ta kira Safeena.

 Da sauri Safeena ta daga tace "Mumy ina hanyya"

 Ahankali Mumy tace "kin dauko takardun?"

 Tace "eh Mumy sa'a nai Dady bayanan."

Mumy ta kashe wayar tare da jinginar dakanta jikin kujera.

 Matar kawunta ce ta kalleta tace "Fatima ki taimaka kisa abinci abakinki."

 Mumy ta girgiza kai alamar a'a sannan tace "karki damu dani, ko nasa abincin ma banaji zan iya taunawa."


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

*76*


 Safeena na shigowa ta shige daki, Mumy ta mike ta bita.

 Hijab dinta ta cire sannan ta mikama Mumy katuwar enveloped din dake boye a hijab dinta, Mumy ta amsa sannan ta bude, kamar yanda Inna ta fada takardar gida ne da kuma fili, sai kuma takardar bankinta wanda ke dauke da kudi da dan dama, sannan sai takardun shares dinta na company dinta.”

  Kurama takardun ido tai wasu zafaffan hawaye na zubo mata, kuka ne ya kwace mata tanayi tanA cewa Inna ki yafemin...”

 Safeena ce ta rungumeta Itama tana kuka, sun dade a haka kafin Mumy tace “in anyi uku ma sanar ma Sultan abinda ake ciki.”

 Safeena tace “ai Mumy inaji ma yasan abinda ke faruwa, nasan dai bai san duka ba amma na tabbatar yasan rabi daga ciki, dan ko tambaya ta dady baiyi ba.”

  Mumy tai shiru kafin ta share hawayenta tace “Rayuwa ce, nasan mun cuci su Jalila amma ko da wasa banida hakkin mahainfinku, dda zuciya daya nake zaune dashi....”

 Safeena ta share nata kwallar tace “Mumy dan Allah ki daina kuka hakanan, sannan kisa tawakalli a ranki.”

 Mumy tai shiru tana kallanta, kafin tace “Safeena ban taba tunanin wannan abin bazai shafeki haka ba, ban taba tunanin kece zaki zama mai lalashina ba.”

 Safeena tace “Mumy baki san halin dana shiga ba bayan tafiyata, da yanda gaba daya rayuwata ta nemi hargitsewa a lokaci daya, na tabbatar addu’arki ce ta kareni, tun a lokacin na shiga hankalina ganin irin abubuwan dake neman faruwa dani.”

 Mumy ta jawota jikinta tace “Safeena nagode sosai, Allah shine ke shiryar da bawansa na tabbatar da irin tarbiya da nuna komai dole ne ki samu da muka nuna miki shi kikai amfani dashi, da yanzu bansan abinda zai faru ba, Allah mungode ma.”

Haka suka kwana cikin wani irin yanayi da su kadai sukasan irinshi, dan Mumy kam bata ko rintsa ba, dan tana matukar san Abakar, ta kuma yarda dashi dari bisa dari...


***********


  Yau kwana goma sha hudu kenan da mutuwar Inna, zuwan Jalila uku gidan gaisuwa, a duk sanda zata je kuma sai Hassan ya hada kayan abinci sun kai, sau biyu sukaje da Goggo dayan kuwa ita kadai taje, wanda shine yau ranar bakwai, su Mumy sun shirya dan yau zasu koma can gidan,  dan dama itace tadanyi rashin lafiya shiyasa basu koma da wuri ba, jiya tasa Sultan yaje ya ga gidan shida Driver dinsu wanda sun san yanzu suna tattarawa zasu sallameshi, ga gidan da nisa sosai ga kuma jarabawar Sultan ta matso, jarabawar karshe waec, Mumy tai shiru tana tunani, Jalila ta kalli Sultan tace “yakai minti nawa daga can zuwa makarantar taku?”

 Sultan yace “tab gidan fa a can wajen gaba da gida dubu yake, wasu sababbin gidaje agun.”

 Cikin mamaki Jalila tace “kai!”

 Safeena ta kalleta tace “da nisa sosai ko?”

 Jalila tace “nima bansan gun ba nadai taba wucewa sai dai gaskiya da nisa sosai.”

 Sultan yai ajiyar zuciya yana cijen lebensa yanda ya saba in ransa ya baci.

 Mumy tace “sai dai ka hakura da jarabawar, dan kaga kawunka tafiya zasuyi, dan dama mutuwar goggo ce ta tsayar dasu, ga kuma itama datai rashin lafiya, sannan a yanda suke nuna mana suma yanzu kamar sun gaji da zamanmu ne, kaga ban isa in kara daura musu wani nauyin ba.”


  Jalila ta kalli Yasmeen dake jikinta a kishingede sannan ta kalli Mumy, tace “ko zai zauna a gidan Goggo?”

  Gaba daya kallanta sukai, Jalila tai murmushi tace “ban tambayeta ba sai dai nasan Goggo bazata taba hanashi ba, mai zai hana ya zauna a can inyaso sai mu nemarmai keken hawa kawai ya dinga zuwa?”

  Idanun Mumy ne suka ciciko, tai shiru tana kallan Jalila, Sultan ma kallanta yake kafin yace “Akan me zaki taimakamin Jalila?”

 Tace “ban gane ba?”

 Muryarsa ta fara rawa yace “kin manta cin kashin da  aka miki a gidan mu? Kin manta wahalar da Mumy, Inna, Dady da wannan Safeenar suka miki? Taya zaki........”

  Kunnenta ta toshe tace “ya isheni haka nan, oh ni Sultan yaushe ka fara magana haka? Sannan kome ya faru ai dane, sannan ka manta kai wanene a gareni?”

  Mumy batasan hawaye sun zubo mata ba sai da Safeena ta kamo hannunta, Mumy ta share kwallarta tace “Jalila nagode, ko ince Mun gode, kin nuna mana yanda ake saka sharri da alkairi, butulci da hallaci, mungode.....”

 Jalila tai murmushi tace “bari na kira Goggo na sanar mata inyaso sai mu fara kaishi kafin kuwuce.”

  Mumy tace “Jalila dan Allah wata alfarma.”

 Kallanta tai tace “tame?”

 Mumy tace “ki taimaka kima mahaifinki magana munaso mu kwashi kayan sawar mu.”

 Tace “Safeena ta kirashi ta fadamai ko ke mana, ai kayanku ne dole ya baku.”

 Mumy tai murmushin takaici tace “tun shekaran jiya muke kiranshi bai dauka ba.”

 Jalila ta mike tare da yin sallama saboda muryar Goggo dataji, tace “Goggona!”

 Ta fada tare dayin ciki, bayan ta gaisheta ne ta sanar da ita abinda ke faruwa, Goggo ta tausaya musu kafin tace menene a ciki, yazo ya zauna ai duk daya ne.”

 Jalila tace “Lanta ga?”

 Goggo tace “dama tare muke kwana da ita, shimfida takeyi a kasa, nace ta hau kan gado mu kwanta taki wai ita tafi san kwanciyar kasa, dama dakin a rufe kawai yake.”

 Jalila tace “shikenan ma.”
Sun danyi hira kadan kafin suyi sallama, harzata fita daga dakin sai ta kira wayar Dady, yana ganin numberta ne ya dauka da sauri yace “Jalila.”

 Tace “Dady kana ina?”

 Yace “ba gaisuwa bakomai haba Jalila?”

 Ta daure tace “Ina wuni?”

Yace “lafiya ina gida, ya akai?”

Tace “zamuzo dasu Mumy su debi kayansu ne dama shine nake so naji inda kake.”

 Yai tsaki yace “sabodasu kika kirani? Wai Jalila baki da wayau ne? Kin manta mai mutanen nan suka miki?”

 Tace “sai munzo, kawai ta kashe, tare da zama akan gado tana rike da wayar.”

 Mikewa tai sannan tace musu ta fadamai, sannan Goggo ta amince, murna agun Mumy kamar me, Sultan kam shiru kawai yai yana kallanta, duniya kenan.

  Text tama Hassan tace “Yayana ka dawo?”

 Da yake dama ajiye tayai akan zai leka gun Abba ya dawo, ganin reply tai akan saura 2mins ya iso.

 Murmushi tai sannan ta kalli Mumy tace “Mumy nima tafiya zamuyi da Yaya.”

 Cikin mamaki Mumy ta kalleta alamar rashin fahimta, Safeena cikin zumudi tace “ina zaku? Umara?”

 Jalila tace “a’a zamu tafi Qatar ne munyi visa shekaranjiya amma bata fito ba tukunna.”

  Mumy jiki a sanyaye tace “me zakuje yi?”

 Tace “karatu zamu.”

 Sultan yace “haba? Kai congrats, kun samu admission ne?”

 Tace “wlh a’a tukunna, mun dai cike, sai dai dama zamu samu, ko muna can zata fito.”

  Safeena tai shiru tana kallanta yanzu fa da itace take wannan rayuwar?”

 Jalila tai murmushi tace “bansan sanda zamu tafi ba, amma daga visa ta fito nasan ba jira.”

 Mumy ta jinjina kai tace “masha Allah, Allah ya bada sa’a, ya karo ci gaba.”

 Jalila tace “ameen...”
Sakon Hassan ne ya shigo, “Baby am back, ko nazo na kinkimoki?”

 Murmushi tai bayan ta gama karantawa sannan tace “Mumy muje.”

 Mumy ta mike suma suka mike suka fito, motarsa suka mufa itada Safeena da Yasmeen, Mumy kuma ta shiga motar su itada Sultan.

Tana shiga ta baza tagumi.

 Jalila kam tana shiga ya kalleta sam bai kula da Safeena ba yadaiga Yasmeen a hannunta ya wani saki murmushi zaiyi magana tai saurin nunamai baya da idanta, Safeena yaga ta shigo sannan ta gaisheshi, Hassan ya kalleta ya amsa, sannan ya kalli Jalila ya dan matso saboda abin na cinsa yace “kiyi maza nima ki gaifarmin yar baby.”

  Harararsa tadanyi tace “zaka fara ko?”

 Gyara zama yai tare da gyaran murya sannan yace “me zan fara?”

 Jalila tace “Yasmeen ga Uncle.”

 Yasmeen tace “ Uncle ina wuni?”

 Hassan yadan ja kumatunta yace “Yasmeen ko?”

 Kai ta daga tana murmushi, ya mika mata hannu yace “nice to meet u.”

 Hannu ta mikamai dan ta fahimci gaisawa zasuyi, tana dariya.

  Hassan ya kalleta yace “yanzu ina zamuyi Ranki ya dade?”

 Murmushi tai kafin tace“zamu fara zuwa gidan Mumy ne ta debo kaya sai mukai Sultan gidan Goggo mu wuce gida.”

 Ya kalleta yace “To angama Hajiya.”

 Dariya tasa tace “Yaya?”

 Yace “ me? Ohhh na manta ashefa ba’a zama Hajiyar ba tukunna, to ko mu fara zuwa Hajj ki zama Hajiya kafin mu tafi Qatar din?”

 Tace “Nayi recording zan fadawa Ummy.”

 Safeena tai shiru tana kallansu abin sha’awa, jitai idanunta na neman tara ruwa, da sauri ta maida idanunta jikin window tana kallan titi.

 Yasmeen kuwa sai zolayarta yake tana dariya, Safeena kuwa tundaga gaisuwa bai kara ce mata komai ba, har suka isa gidan.

  Dady na falo suka shigo,  Jalila ce ta fara shiga rike da Yasmeen.

  Mikewa tsaye yai yana kallanta, zaiyi magana yaga Mumy ta shigo itada Safeena.

 Komawa yai ya zauna yai shiru, Jalila ta kalli gidan gaba daya ya canza a dan wannan lokacin, shikanshi dadyn duk ya wani canza, Mumy ta zuba mai ido ya kalli Yasmeen datazo gunsa da gudu ta rungumeshi, har a jikinsa sai dayaji yace “Yasmeen ya gida?”

 Tace “Dady ina kaje? Baka siyomin ice cream ba?”

 Ya dagata yana murmushi, shigowar Hassan da Sultan ne yasashi sauketa, yana kallan Hassan.

 Hassan ya kalleshi sannan yace “Barka dai.”

 Dady ya hade fuska yace “Barka dai? Wace gaisuwa ce hakan?”

 Hassan ya kalli Jalila ba tare da ya kara mai magans ba yace “kuyi sauri ina mota.”

 Ya fada tare da juyawa.

 Dady ya bishi da kallan takaici, ba yanda baiyi ba akan Sageer ya barshi ya cigaba da aikinsa amma yaki, ya kuma tabbatar wannam mara mutuncin ne ya hana.

 Shiga su Mumy sukai, Safeena gaisheshi kawai tai ta wuce, Sultan kam ko kallanshi baiyi ba ya wuce dakinsa, Dady ya kalleshi dan duk a yaransa yafi san Sultan.

  Mumy ta shiga dakinsu, gaba daya dakin yai kacha kacha, Dady ne ya shigo ciki ya kalleta yace “yanzu ina zaku koma?”

 Tace “ko ina zamu koma ai ba kada ta cewa tunda ka koremu daga gidan da yake halak dinmu.”

 Dady yace “ku kwashe kayanku duka dan saida gidan zanyi.”

 Cikin mamaki ta kalleshi tace “siyarwa?”

 Yace “sosai, ina zan kai katan gida haka?”

Haushi ya kamata tace “dan Allah Abakar ka sanar dani menene ribarka na abinda kake aikatawa?”

 Yai shiru yana kallanta tace “yanzu ka tabbatar min ilimi bai ratsa kaba, sannan ka tabbatarmun kai bagidaje ne, na dauka daka wulakantamu zan ganka kana rayuwa yanda ya kamata, sai dai menene hakan? Kalleka, kalli gidanka? Sannan siyarwa zakai?”

 Zaiyi magana tace “basai kace komai ba, tunda har mahaifiyata ta mutu baka tako ka min gaisuwa ba, ai a tunani na ko zaman kiyayya mukai dakai kaminn gaisuwar mutuwar mahaifiyata balle, ni ai yanzu ka nunamin tabbas ko da wasa baka taba sona ba.”

 Ta share kwallarta tana cigaba da kwashe kayanta, zuru yai ya tsaya yana kallanta fitowa tai zata dakin Safeena dan tattara kayan Yasmeen, har ta wuceshi ta tsaya tace “Ahh Sultan zai zauna a gidan Goggo saboda makarantarsa, naga kamar ya kamata ka sani.”

 Ta juya zata tafi, da sauri ya fizgota yace “Goggon har gida gareta?”

 Tace “eh sirikanta sun siya mata.”

 Yace “me?”

 Tace “sakeni dan Allah.”

 Yace “amma shi Sultan din bazai zauna anan ba har ya gama?”

 Tace “ya zauna a ina? Gidan mutumin da bai kaunarsa bai kaunar mahaifiyarsa? Ta ina ma zai zauna a wannan gidan?”

 Dady ya fara hucci, fizge hannunta tai ta fita, Dady yai shiru gaba daya yama rasa abinyi.


******

 Jalila kuwa tana ganin sun shiga kwaso kaya ta fito inda Hassan yake, tace “Yaya muje kaga dakinmu.”

 Fitowa yai ya riko hannunta yace “ahh yau zanga muhallin Baby.”

 Tai murmushi tace “Yaya daka dan sake hannuna kar a ganmu.”

 Yace “to wai ni in an ganmu menene a ciki? Ahhh dana sani London nace a nemarmana dan su nasan ko me kai ba ruwann wani dakai ko a ina ne.”

 Jalila tace “Lalai, wato kai abu ma kake so ka dingayi a ko ina? Oh ni yays ba kunya sam.”

 Zaiyi magana tace “Yaya zaka saima Sultan keke?”

 Yace “keke?”

 Ta kalleshi tace “eh, a gidan Goggo zai zauna saboda exams.”

 Yace “ban gane ba.”
Nan ta fadamai yanda sukai, hannu yasa ya shafi kanta ta baya yace “ahh baby na u are sooo kind....”

 Tace “kai yaya....”

 Tana tura kofar dan dakin yai shiru yana bin dakin da kallo, gaba daya jikinsa yayi sanyi.
Ganin yanda yake bin dakin da kalli yasa ta matso ta rungumeshi ta baya tare da kwantar da kanta a bayansa....


#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

*77*


  Hannu yasa ya juyo da ita saitinsa sannan ya rike hannunta, janta yai zuwa katifar dakin, kwantawa yai sannan ya miko mata hannu, murmushi ta sakar masa sannan ta kwanta kusa dashi itama, jawota yai ya rungume ta ajikinsa sannan ya shafa bayanta yace "Yau na kwanta a inda Baby take kwanciya shekara da shekaru."

  Jalila ta dago da fuskarta ta kalleshi tace " katifarka duk tayi kura ka kwanta."

  Yace "katifar da kika sha kwanciya akai ko me tai ai banaji zan kasa kwanciya."

 Jalila ta kankance ido tana kallansa, yace "wannan kallan fa? Ko kin dauka karya nake?"

 Tace "ah haba wani karya kuma kawai dai ina tunanin da Yayan nan lafiyarsa kalau, yan mata nawa zaiso kafin ni? yan mata nawa ne zasu soshi kafin ni?"

 Yatsa yasa ya dungure mata kai yace "wadannan tunanikan naki sai nadau mataki babba akansu."

 Tai dariya zatai magana yace "badai a kasan ranki kina farin ciki da rashin lafiyar danai ba ko?"

 Da sauri tace "ni? Inji wa?"

  Hannunta ya riko ya matse yace "fadamin gaskiya....:"

 Dariya ta dinga kyalkyalawa saboda yanda ya mata rikon tana cewa "yaya wallahi da zafi...."

  Ganin yanda take dariya sosai yasashi a wani farin ciki, can yace "Jalila."

 Ta kalleshi bayan ta daina dariyar, yace "Shigowata dakin nan sai na fara tunanin kamar ban kyauta miki ba, zan daukeki daga inda zakiga Goggonki saboda wasu burika nawa, nasan ci gaba da karatu da kuma san kadaicewa."

 Kallansa kawai takeyi fuskarta dauke da murmushi, kara kwantar da kanta tai a jikinta tace "ka manta me nace ma tun farko?"

 Yai shiru yana saurarenta, tace "ko ka manta nacema duk abinda ka tsara daidai ne a gurina?"

Ta dago ta kalleshi sannan tace "Goggo ma dinga yin waya, sannan kaima ai is not easy ka rabu da su Ummy da su Abba."

  Shiru yai kafin yace "nifa kinsan me na miki?"

 Tace a'a yace " course daya na cike mana fa ni dake."

 Dariyarta ta kunshe tace "shiyasa a sanda Abba ke tambayata wani course nakeso kaketa shashantar da zancen?"

  Hassan yai dariya yace "eh mana, nafiso mu shiga tare mu fito tare, sannan kinga in muka tashi aiki muyi a company din Abba a tare."

  Jalila tace "Hmm wannan wayan yayi."

 Yace "ai dama yayi sosai ma."

 Jalila tai dariya kawai......

Su Mumy na gama hada kaya suka fito suka shiga motarsu, ita kuma da Hassan sukadau Sultan, Hassan yaba Mumy kudi suka fito, dady na tsaye zuru yana kallansu, Yasmeen sai kuka take ita gun Dady takeso.

 Shikam Dady haushi ne ya isheshi har dakin Sultan ya shiga dan suyi magana amma Sultan yaki kulashi.
 Haka ya fito rai a bace.

  Mumy kam shiru tai kawai a cikin mota gaba daya ta kasa ko furta kalma daya, itakam Safeena kanta ta kwantar akan kujera kawai.


**************

 Sun isa gidan Goggo, Sultan ya tsaya a jikin kofar shiga falon, Hassan ya sa hannu a kafadarsa ya jashi ciki, Goggo tana ganinsu ta mike cikin jin dadi, Jalila kam da sauri aka wuce aka fada jikin Goggo.

 Goggo tasa hannu ta tureta tace "ko kunya ma bakyaji mutum inya girma ai yasan ya girma."

Ta koma gefe tare da turo baki, Goggo ta kalli Hassan tace "Yasu Ummy?"

 Yace "suna lafiya."

 Ta kalli Sultan wanda yai shiru a tsaye, tace "Sultan! Ba magana?"

 Ya tsugunna kansa na kasa yace "Goggo ina wuni?"

 Tai dariya tace "Haba Sultan menene hakan? Kamar wanda baka sanmu ba?"

Yai shiru kansa a kasa.
Sun danyi hira kadan kafin su taso su tafi......

***********


  Takardar gidan ya mika musu tare da sa hannu akan takardar shaida sannan suka bashi check na kudin gidan, kallan check din dake dauke da kudi zunzurutu har million 30, gidan ya kara daraja ne saboda akwai furnitures, wani irin dadi ne ya kamashi, dan shikam gani yake ya cucesu ne, ya danne farincikinshi yace "kamar yaushe zaku dawo?"

 Mutumin ya kalleshi yace "eh, muna sa ran gobe dan dama iyalaina zasu baro garin Abuja ne su dawo nan."

 Dady ya jinjina kai yace "bakomai ni yau zan tashi, nagode sosai."

 Sukai musabaha sannan suka fito, dady cikin murna yai daki dan dama ya gama tattara kayansa, sannan ya koma ciki, wani irin ihu naji ya saki na farin ciki sannan ya kara gyara kayansa kawai ya jawo ya lodasu a mota ya ja ya fita.


 Hotel kawai ya wuce ya kama katan daki suit room, ya kwanta cikin jin dadi, ya fara tunanin menene zai fi mai? Business zai fara ko kawai ya fita yawon shakatawa? Inya dawo ragowar ya nemi gida karami.

  Haka yai ta sake sake marasa ma'ana, har wani bacci mai dadi yai gaba dashi.


  Washegari yana tashi kawai ya fita yaci abinci ya siyo kayan makulashe ya dawo ya kwanta saboda yana san gobe yaje ya ciro kudin nan yasa a account dinsa.

  Ba abinda yakeyi sai dai yaci yasha ya kwanta kawai ya kunna waka yana ji.
Rayuwa ta masa dadi.


****

Yau da safe yana sallar asuba ya kasa komawa bacci saboda zumudin zuwa bank, wanka yai kawai yasa kaya ya zauna akan kujera yana kirgen lokaci, ganin lokacin baya sauri ma yasa ya fito daga hotel din ya shiga mota yaje gaban banki ya tsaya.

 Karfe takwas nayi yana ganin anfara hidima yai wuf ya shige ciki.

  Sama yahau sannan yaje inda ya kamata ya mika check dinsa tare da sa hannu a aljihu irin babban alhajin nan.

 Kallan check din yai ya dinga juyashi kafin ya kalleshi yai kafin yace "Alhaj wannan check din waya baka shi?"

 Yai murmushi saboda ya fahimci kudin ne ya tsorata su.

 Yace "Menene na tambayar abinda bai dameka ba, yi sauri ka bani inaso nai transfer dinsu bank dina ne."

  Mutumin yai shiru kafin ya fito daga inda yake yace "ina zuwa."

 Bai fi minti 10 da fitaba sai gashi ya dawo shida wani, nan dayan ya kalli Dady yace "Alhaji ina ka samu wannan check din?"

 Ran dady yadan baci yace "kunsan ko ni wanene kukemin wannan tambayar banzan?"

 Mutumin ya kara sanyaya murya yace "ba haka bane, wannan takardar ta check ba namu bane, anyi amfani da irin namu ne anyi jabu, dan idan ka daga shi sama shida namu zakaga ba iri daya bane, sannan ko karfin takardar ma ba iri daya bane."


Dady cikin rashin fahimta yace "me kuke nufi kenan a takaici? Kunaso kucemin ba zaku bani kudi na bane ko kuma me?"

 Yace "bawai zancen zamu baka ko zamu hanaka bane, zancen an cuceka an baka abu jabu mukeyi."

  Cikin tashin Dady yace "an cuceni kamar ya?"
 Yace "am sorry to say amma mu ba abinda zamu iya maka, sai dai ka koma gun wanda ya baka ka nemi ya baka wani ko kuma ya maka transfer."


  Yana neman sake magana dayan ya dafashi alamar yai shiru dan ya kula Dady kamar ya gama hasala, Dady yai shiru kafin ya fito da sauri daga cikin bank din, da sauri ya fada mota sannan ya wuce gidan.

  Gani yai anata sauke kaya da sauri ya karasa gun mutumin dake tsaye yana bada umarni, da gudu ya karasa inda yake yace "Malam dan Allah ina mai gidan nan?"

 Mutumin cikin mamaki ya tureshi tare da cewa "Meye hakan?"

 Dady a rikice yace "dan Allah mai gidan nan nake nema."

 Yace "nine mai gidan kai waye?"

 Dady hankali a tashe yace "bakai ba wanda na saidawa gidan shekaranjiya."


 Mutumin ya tureshi da karfi har Dady ya fadi a kasa yace "kai dalla bansan hauka jiyan nan nasai gida million 50 yau kuma kazo kana tambayata maganar banza?"

 Da karfi ya kira mai gadinsa yace "ya fitarmai da wannan mutumin daga gidansa.

 Mai gadin ya kalleshi yace "zaka fita ko na fitar dakai?"

 Dady ya mike kamar wanda zai fadi ya fita, yana fita gate ya zauna a bakin gate din..........


*******

#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

*78*


  Dady yai tsutsuru a waje har baisan sanda lokaci yai ta tafiya haka ba, mikewa yai jin cikinshi na wani irin karar yunwa, motarsa ya shiga ya zauna idanunsa sun firfito, tada motar yai ya wuce hotel din da yake ciki, yana shiga ya wuce cikin toilet ya sakarma kansa ruwa ruwa na zuba yana tunanin abinda ke faruwa, yanzu wannan uban zuzurutun kudin ya wuce kenan ko me? Gidansa fa?

 Jiyai kansa yayi dumm da karfi ya saki wata irin kara na takaici ya daki bango da hannunsa, sam bai kula da jinin dake ta zubo mai ba, hucci kawai yakeyi kamar wani kumurci.

  Haka ya fito yasa doguwar riga ya bude window yana kallan gari, gaba daya kansa ya rufe yama rasa ta ina zai fara yin tunani, ga wata uwar yunwa da yakeji, mikewa yai ya dau jakarsa ya fita reception.

  Gun masu aiki a hotel din ya nufa yace "yanaso a bashi karamin daki da toilet sai a bashi ragowar kudinsa."

 Nan sukacemai ai bazai yiwu ba tunda dai dama na kwana hudu ya biya kuma yanzu yayi biyu bayanda zasuyi, bakin ciki ya kara mamayeshi gashi dama ragowar na account din ya kwashe ya biya saboda yana ganin yanzu kudi sunzo masa.

  Ya baza tagumi a cikin reception yaji ance "dunoyar tama zafi ne?"

 Juyowa yai ya kalleta, yarinyace wacce batafi shekara 30 ba tasha gayu nagaske, Dady ya kalleta sannan ya juya yana kallan wani gun.

  Kallansa tai sannan tace "kudi kake nema?"
 Idanu ya kura mata baice komai ba, tace "ka biyoni zan baka."

 Ta fada tare da ajige key din dakinta a kusa dashi sannan ta mike, ta dan matso kadan tace "1day 500k, deal?"

  Dady da sauri ya dago ya kalleta, kashenmai ido tai sannan ta mike tai ciki.

 Dady ya bita da kalli sannan ya dauki key din ya mike tare da jan jakarsa, haryakai hannunsa zai murda dakin ya tuno Jalila, Safeena, Sultan da Yasmeen.

  Da sauri ya saki kofar sannan ya fara ja baya baya, yana san kudi na fitar hankali dan shi burinshi kenan ya zama babba wanda ba wanda ya isa ya rainashi, sai dai duk a cikin san kudinsa banda ta hanyar zina, in yaransa suka ganshi fa?"

 Da sauri ya juya yai waje tare da yarda makullin( ina duniya zaki damu? Ace wai yanzu mace itace ke neman namiji kuma ita ke biyanshi saboda rashin hakuri da san kai da san zuciya? Allah ya mana tsari ameen)

Dady ya koma cikin dakin nan wanda yanzu gaba daya haushi yake bashi......

 Haka ya gama kwanansa ya fito daga hotel din, ina zai je? Shi ba abokai ba ba wasu yan uwa ba, haka yaje ya nemi karamin hotel ya kara biyan wani kudin ya shiga, yanzu kam gaba daya ba komai a account dinsa sai dubu talatin, wanda haka yake zara yana siyan abinci.

 Gaba daya a dan kankanin lokacin nan har Dady ya canza.

 Duk yanda ya kira Jalila kuwa bata dauka dan itakam tasan magana daya ce tsakaninsu, itakuma bazata taba taimaka mai ya kara lalacewa ba.

******

  Yanda aka bude kofar kitchen din ne yasa Ummy da Jalila suka juya da sauri dan ganin meke faruwa, Hassan kam idanunsa sun rufe da farinciki, kusa da Ummy yazo ya rike hannunta yace "Ummy na ta fito."

 Tace "Visa din?"
 Da sauri ya daga kai yana dariya ya kalli Jalila wacce ta juya da sauri tare da cigaba da wanke wanken da takeyi.

  Ummy ta mintsine hannunsa tace "Shine kake murna haka gaba daya kamar dama ka gaji da mu?"

 Kansa yadan sosa yana dariya yace "kema Ummyna kinsan ba haka bane, murna kawai nake dai abinda ake nema an samu ba wani abu ba."

 Tace "ba wani nan, bayan ga fuskarka nan ta nuna min a fili."

 Yai dariya yace "dagaske?" Ya fada yana shafa fuskarsa, Ummy ta girgiza kai tace "oh ashe ni kadai ce nake tunanin rashinku."

 Ta juya itama tana karasa abinda takeyi.

 Hassan ya matso yace "Kai Ummy na."

Tace "Ah bari na dauko wayata." Ta juya ta fita.

 Hassan na gani ta rufe kofa ya matso ya rungume Jalila yana dariya.

 Tace "Oh ni yaya, dan Allah ka daina farin cikin nan haka nan, kar Ummy taji ba dadi."

  Yace " to wai ni yazanyi na daina? Nikam ki gama wannan aikin kizo mu fara hada kaya."

 Jalila ta dan tureshi tace "ni dai kar Unmy ta shigo."

 Ya saketa yace "ni yau ma zan sai ticket dan jibi sai tafiya, gobe na kaiki gidan Goggo sallama."

 Baki ta bude tana kallansa tace "oh ni yaya."

 Yace "harna fadawa Abba ma nasan yanzu shima ya fadama Ummy, kallan mamaki kawai takemai, shikam juyawa yai ya fita.

  Haka kuwa tana fitowa taji a bakin Ummy wai jibi zasu tafi, haka ya sata a daki sukahau hada kaya, itakam duk kunya ta isheta.

 Washegari ya kaita gidab Goggo acan ta wuni, sunsha hira da Sultan, Goggo itakanta tayi mamakin wannan tafiyar da wuri haka, rasa mai zatace tai kawai sai dariya tai.

 Ya sallami Goggo kudi mai kauri dan yasan Ummy da Abba zasu dinga kula dasu, sai dai shima yana san yai wani abin.

  Wajen magrib yazo ya dauketa ya kaita gidan Mumy wai tanasan tayima su Safeena sallama.

  Gida ne karami amma agunsu wadanda suka taso daga katan guri, dakuna biyu ne da falo da kitchen.

 Mumy na ganin Jalila ga saki fara'a cikin jin dadi, Safeena ma tana toilet tanajin Mumy na kira. Sunan Jalila tai sauri ta fito tana murna, Jalila na zaune kusa da Mumy, Yasmeen na zaune a cinyarta tana bude alawoyin da Jalila ta bata, Safeena ta taho da sauri, ta rungumeta.

 Mumy tace "nikam har abin yazo haka?"

 Tace "wallahi gashi har mun kusa tafiya."

 Jalila ta kalli Safeena tace "kin fara neman skul ne?"

 Tace "wallahi maganar da muke da Mumy kenan kullum amma jiya na dameta ta kira Sani yace sai nayi Jamb.

 Jalila tace "haka ne amma wacce kikeso?"

 Tace "F.U.D."

 Jalila tace "Allah ya taimaka ya bada Sa'a."

 Tace "Ameen."

 Jalila ta kalli kasan carpet wanda da alama Yasmeen abinci ta gama ci, shinkafa da wanke sukai damai da yaji, Jalila ta kurama kasan ido tana tuno lokacin da agida ake sata yin abinci kusan kala uku, kuma ko za'ai me basa cin mai da yaji sai anyi miya da nama kachha kacha.

 Kallan Mumy tai tace "Mumy ya kuke da kayan abinci?"

 Tace "kudin da Hassan ya bamu muke cancanawa kafin mu samu a saida filin Da Inna tabarmin, sannan tanada wasu kudi a bank, sai dai su sai anyi cike ciken takardu kafin a bamu."

  Jalila tace "To Allah ya taimaka, amma Mumy tunda kinyi karatu ba gwara ki fara aiki ba ko a company din Inna ne? Inkika fara kamar abin zai kara sauki."

 Cikin mamaki ta kalli Jalila tace "Oh ya akai wannan tunanin baizo min ba?"

 Jalila tai dariya, Mumy tace "aikam zanyima Kanin Hassan magana, sannan ai inama da Shares din Inna."

 Jalila ta kura mata ido tana kallo, shiyasa Dady ke cutanta sam bata tsayawa tai tunani  mai zurfi.

 Jalila ta kalleta tace "bari na baki numbersa sai ki kirashi."

 Sundanyi hira kafin Hassan ya kirata ya sanar da ita dawowarsa, fitowa tai ta shiga mota, a hanya tana bashi labarin yanda sukai.

 Ya riko hannunta yace "Umm wannan babyn daga inna aka samota ne haka?"

 Tai dariya tace "daga ina kuwa?"

 Yai dariya zaiyi magana wayarta ta shiga kara, kallan wayar tai sannan ta katseta ta kalleshi, yace "shine?"

 Tace "eh."

 Yace "bakya tunanin ya kamata kiu hadu kafin ki tafi?"

  Ta kalle tace "Ai ni Dady bansan....."
Ya katseta yace "ko me zai miki, ai sallama kika mai, muje gidan ko yayane kuyi sallama mahaifine."

 Jalila tai shiru batace komai ba, a kofar gidan suka tsaya saboda sunata yima mai gadin alama amma bai ko kallesu ba.

  Sai da sukai parkin ya matso yace "Daga ina?"
 Hassan ya kalleshi wato har mai gadi ya canza?

 Yace "kayima mai gidan magana kace Jalila nasan magana dashi."

 Kamar bazaije ba sai kuma ya shiga, bai jima ba sai gashi ya dawo, ya sanar dasu cewa bai san wata Jalila ba.

 Ran Jalila ya baci ta kalli Hassan idanuta suna neman tara ruwa tace "Yaya!"

 Hassan ya kalli gidan sannan ya tada mota, Jalila ta kwantar da kanta a jikin window, kiran daya kara shigo mata ne yasa ta kalli wayar sannan ta kalli Hassan, ran Hassan ya baci, bai santa ba amma yasan numberta? Haushi ya kamashi ya daga wayar rai a bace, kafin Dady yace wani abu Hassan yace "baka santa ba taya kasan number ta? Inhar baka santa ba bai kamata kasan numberta ba."


 Kan Dady ya fahimci abinda yake nufi har Hassan ya kashe wayar, ya kasheta ma gaba daya cikin bacin rai.

 Haka suka shiga gida, Su Ummy dukansu na zaune a falo suka shigo.


  Jalila na shiga ta gaishesu da gida, Abba yace "Jalila an gaji ko?"

 Tak dariya tare da maida kai kasa, yace "ya zakiyi, wannan mijin naki ya zafaffa sai kin bar kasar da wuri? Kamar wanda ake korarsa."

 Hassan ya kalli Abba yace "Abba kaifa ka karfafamin gwiwa akan na tafi da wuri."

 Ummy ta kalli Abba da sauri tace "dama kaine?"

 Da sauri yace "ni a ina? Gani fa nai hakan yakeso sai nadan sa baki kadan dan kadan fa nabi bayan hakan."

Hassan yace "kadan? Abba kaifa ka......."

 Abba ya harareshi tare damai alamar yai shiru.

 Hassan yana dariya yace "Ummy na!"

 Sageer yace "Ummy karki wani yarda da dadin bakin yaya, matarsa kawai ya sani."

 Kunya ta kama Jalila tai kasa dakai, Amira tace "kaima Yaya Sageer ya kamata ka motsa, kaga in Aunty Jalila ta tafi gidan zaiyi shiru gwara ka kawo wata."

 Sageer yai dariya tare da kallan Hassan, Hassan yace "me? Badai haryanzu baka fadama ko Abba ba?"

 Sageer ya sinar dakai yana dariya, Abba yace "Sageer ni aka munafirta?"

 Sageer da sauri yace "wallahi ba haka bane Abba inataso muyi maganar, kasan yanzu aikin ha karu shiyasa."

 Haka akai ta tsokana Ummy na hira tana kuma kukulla abubuwan data shiryama Jalila wanda zata tagi dashi.

*********

Dady kam gaba daya yau ta karemai dan kudin daya biya na hotel din ya kare kuma bashida wani, shiyasa yake ta neman Jalila akan ta taimaka mai, cikin lota ya fito ya shiga yana ta nemanta jin ma wayar a kashe daga baya yasa ya cilar da wayar tasa cikin takaici.

  Kwanciya yai a cikin motar sannan ya dauko wayarsa yana duba sunaye ko akwai wanda zai iya kira, sai dai kaf wayarsa ba wasu mutane, daga su Mumy sai 'ya'yanta sai Jalila, sai number Inna sai kuma harkokinsu na business.

Bakinsa ya ciza cikin bakin ciki yace "duk kun lalatamin rayuwa, na dage ina muku bauta amma karshe ku hanani abinda na dace dashi? Gyara kwanciyarsa yai tare da kallan cikin motar, wai shine ke kwana a mota? Lalai dole ya nemo mafita, zaije ya samu Jalila gobe har kasa zai tsugunna ya nemi yafiyar Hassan da Mahaifinsa, ya tabbatar intaga halin da yake ciki zata tausaya masa.


**********

Hannu yasa ya jawota yace "me kuma kikeyi?"

 Tace "bakomai, so nake kawai na karasa hada kayan nan."

 Yace "Yanzu ina toilet wani abu ya fadomin, anya Dadynki bai saida gidan nan ba?"

 Tace "ah haba? Ya saidashi ya koma ina? Sannan gidanda ba nashi ba? Taya zai saida musu abinda ba nashi ba?"

 Hassan ya ajiyaf zuciya yace "kuma haka ne."

 Tace "Bansan dai mai ke damunsa ba, na kasa gane dalilin kiran nawa."

 Hassan yai shiru shima yana tunani.


  Bayan sun kwanta wajen karfe shadaya hankalinsa ya kasa kwanciya, mikewa yai ya dau wayar Jalila ya fito falo.

 Kunnata yai sannan ya kira wayar Dady, Ringing uku ya dauka da sauri yace "Jalila?"

 Hassan cikin mamaki yace "dazu da mukazo gidanka me yasa ka kore mu?"

 Jin murtar Hassan yasa yadan yi dum....
Sai dai jin kalamansa yasa yace "gidana???"



#OneLove💕
🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*

_Gareku duk mai kaunar littafin nan, ina tsananin godiya akan yanda kuka nuna kaunarku ga littafin nam, nagode kwarai da gaske🥰🥰OneLuv💕_


 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

*78*

Dady yai shiru har saida Hassan yace "dazu."

 Dady ya hadiye wani abu na bakin ciki yama kasa magana.

 Hassan yace "kana ina?" Dan ya fahimci da matsala.

 Dady yace "inzo ne?"

 Hassan yace "eh in zaka iya, sai na sameka a waje."

 Da sauri dady yace "to."

 Mamaki ya kama Hassan ya bi wayar da kallo kafin yakoma ya zauna yai shiru yana tunanin rashin adalcin da akama Jalila da mahaifiyarta, da rashin adalcin dayama Mumy da 'ya'yanta.

 Wayarce tai ringing kamar zata katse kafin ya daga, Muryar dady taji akan wai yana waje.

 Hassan ya sauko a hankali ya fita waje.

 Dady na tsaye a wajen gate, yana ganin Hassan ya taho da sauri, Hassan ya bishi da kalli duk ya wani mole ya canza, kayan jikinsa duk sunyi datti.

Dady ya matso da sauri yace "Ina wuni?"

 Cikin mamaki Hassan ya kalleshi yace "Ina wuni?"

 Dady ya kalleshi sannan yadan sosa kai yace "Hassan ina Jalilan?"

  Hassan ya hade fuska tamau yace "menene dalilin korarmu dakai da mukaje gidanka?"

 Dady ha kalleshi jiki a sanyaye sannan yace "Gidan ba nawa bane yanzu."

 Hassan ya kalleshi wato tunaninsa ya tabbata, Dady yace "wasu mugaye na hadu dasu suka kwace gidan ba tare da na samu kudina ba."

 Hassan ya cigaba da kallansa, Dady ya riko hannunsa yace "Hassan ka taimakeni, wallahi yanzu inda zansa hakarkari na ma bani dashi, Hassan kai mijin 'yatane kantaimaka ka bani ko gida ne inda zan zauna."

 Hassan ya bishi da kallo yace "in baka gida? Nidin cema akai gidajen rabarwa gareni?"

 Dady yace "nasan na batama dayawa nayima abubuwa kala kala nasan ma gaba daya rayuwata bana kyautawa, sai dai na tuba ka duba ka taimakeni."

 Hassan ya zare hannunsa daga nashi yace " da kai a tunaninka hakkin mutanen daka take ka gakesu ne a banza? Ko ka dauka duk abinda kai Allah bazai hukuntaka ba?"

 Dady baki na rawa yace "nasan ban kyauta ba."

 Hassan yace "zanshiga bacci nakeji dan inada abinyi gobe, harya juya sai kuma ya juyo yasa hannu a aljihu ya zaro wallet dinsa dubu biyar ne a ciki, ya zara ya mikamai, Dady ya amsa satoto yana kallansa, kafin ya tattara abin fada har Hassan ya shige ciki.

  Daki ya shiga, ya kwanta kusa da Jalila tare da sa hannu akan fuskarta a hankali yace "am sry Jalila, sai dai ina tunanin barin duniya ta dan gara mahaifinki shine zaisa yasan rayuwa yasan kuma abinda ya aikata bamai kyau bane, kiyi hakuri zan daukeki ba tare da kinsan halin da yake ciki ba, duk lokacin da kika sani zan nemi yafiyarki akan kin taimaka masa danai."

A hankali ya sumbaci bakinta sannan ya kwanta yana kallanta.


********

 Dady kam kasa motsawa yai daga kofar gidan, yana tsaye satoto ruke da kudi a hannu, sai dayaji sanyi na busashi sosai sannan ya koma mota ya ja yai gaba gaba daya kansa ya kulle.

 Sukam su Jalila washegari suka shirya tsaf, Ummy ta biya itada Abba, Mamman na jansu suka je suka dauko Goggo suka tafi airport.

 Sageer kuma da Ameera a gaba Hassan da Jalila a baya, Hassan nata tsokanar Sageer akan budurwarsa, Hassan yace "in bikin yazo ma zo muyi sati daya."

 Sageer yace "indai sati ne banaso."

 Hassan yana dariya yace "to kwana 10."

 Jalila tace "a'a sati biyu dai ya kamata."

 Sageer yace "yauwa matar yaya kaga inda ake min kara."

 Ameera tasa dariya tace "Gaskiya yaya sati biyu dai."

 Ya kalleta yace "wai ni ina Aina'u ne? Sam ta buya"

 Ameera tace "Yaya kaida ka gujeta?"

 Yace "ba gujeta kamar ya?" 

 Ta juyo tace "badai yaya bakasani na?"

 Jalila ya kalla wacce itama kallansa take, da sauri yasa hannu ya buge kan Ameera yace "to yanzu waya kawo wannan zancen daga tambayarta?"

 Ameera tasa dariya tace "Ai naji haushi me makin yaya Sageer ya dan yi mata hucce shine shima ya nemo a waje."

 Sageer yace "wa? Ni?"

 Haka sukaita zolaya har suka isa airport.

 Jalila kam abin kamar mafarki haka take ganninshi wai yau itace zata hau jirgi zuwa wata kasar, abinda takeji a labari.

 Goggo ma tayi shiru tana tunanin rayuwa, suna tsaye ne sai ga wani yazo ta gaban Abba, Abba ya kalleshi sannan ya mika mai hannu tare da sakin fuska. Yace "Ghali?"

 Wanda ya kira da Ghali ta washe baki yace "kasan tundaga nesa nake kallanka ina zargin ko ba kai bane."

 Ghali ya kalli Ummy yace "Hajiya shekaru masu yawa."

 Ta kalli Abba tace "wai Dr Ghali naka?"

 Yace "nine Hajiya."

 Ya kalli Hassan da Sagir yace "'yan biyun ne?"

 Ummy tace "eh, ikon Allah."

 Ta kalli Hassan tace "kaga wanda yai treating din Yaya (mahaifiyar Hassan) kafin ta rasu."

 Hassan ya gaisheshi, su sageer suma suka gaisheshi, Goggo ce ta gaisheshi itama, ya kalleta yace "ka kara aureni?"

 Yace "a'a mahaifiyar matar dana ce."

 Yace Allah sarki, sun danyi hira kafin sudan ware gefe suna kara tattaunawa, Su Hassan da Jalila kuma suka shiga ciki inda zasu kai kayansu.

 Ghali ya kalli inda Goggo take yace "Diabetes's n da ita?"

 Abba yace "wa? Ya fada yana kallan gun, ganin Goggo yasa yace "eh wallahi."

 Ghali yace "ayya da hawan jini kuma kenan?"

 Abba yace "gaskiya ne likita."

 Dariya yai kafin Dady yace "ya matarka? Da yaranka?"

 Yace "mai dakina Allah ya mata rasuwa shekara biyu da suka wuce yarana kuma sunata karatu, yanzu ma babban ne zai koma makaranta a saudia yakeyi."



 Abba yace "Wayyo Allah ya jikanta banji ba ai."

 Sannan ya cigaba "Allah ya taimaka kace shi acan yake?

Yace wallahi.
Abba yace "....Ah to ko zaka kula da patient?"

Ghali yasa dariya dan ya gane sannan yace "batada aurene?"

 Abba yace "tanadashi kuma batadashi."

 Cikin mamaki yace "kamar ya?"

 Abba yace zan baka labari inmunje gida, dan su Hassan na tafiya gidana zaka musha hira, itama can zata kaga sai ka kara ganinta dakyau."

 Ghali yai dariya.

Idanun Jalila gaba daya sun canza, ganin sun fito yin sallama zasu shiga ciki, tana zuwa ta rungume Ummy kawai tasa kuka, Ummy ma idanunta duk suka ciciko, ta shiga shafa bayanta alamar lalashi, Jalila ta dago ta dawo gun Goggo ta rungumeta taba kuka, Goggo kam sai da hawaye suka zubo mata, ta sharesu tare da yi mata addu'a, shikam Hassan yana tsaye gun Abba da Sageer suna magana, kafin Goggo ta dagota tace
 "Jalila akara hakuri, karkice akoda yaushe dan mijinki nasanki zan dinga miki duk abinda kikeso, karkizama mai takura masa akan sankanki, sannan ki dinga jin maganar sa, yanzu shine uba, aboki sannan mijinki, kiyi kokafi kyautata masa akoda yaushe."

 Jalila ta daga kai tana hawaye, Goggo ta kalli Hassan wanda kentsaye yana jinsu tace "Hassan ga Jalila nan, kawai abinda zance kenan."

 Ya kalleta tare da yin murmushi yace "nagane Goggo insha Allah bazan sata kuka mai yawa ba."

 Ummy ta makamai harara tace "zaka sata kenan kake cewa?"

 Yai dariya yace "eh amma kadan dan haka..." ya fada yana nuna dan karamin yatsansa.

 Goggo tai dariya tace "nayarda Hassan."

 Jalila ta kalleta sannan ta kalli Ummy tace "Ummy kinjisu?"


 Ummy tace "karki damu yana samin ke kuka zanzo in daukeki."

 Dariya sukai su dukansu, nan sukama Abba sallama, idanun Jalila ne suka fara neman kara cikowa.

 Hassan ya kamo hannunta, da sauri ta kalleshi, yace "in bakyasan na rikike wallahi ki hadiye hawayen nan."

 Da sauri ta zare hannunta tare da kokarin hadiye kukanta.

 Ya guntse dariyarsa,nan suka karayin sallama da Abba suka wuce ciki.

(Nace a sauka lafiya🕊)


***********

 Ghali ne ya kalli Abba yace "inalilahi, ita kuma haka tata kaddarar take?lalai taga bakincikin rayuwa."

 Abba yace "ai abin ba'a cewa komai."

 Fuskarsa ya shafa sannan yace "amma wannan kwai dan iska, menene laifina dazai wulakantaa haka? Mace kamar ta haka?"

 Abba yai shiru cikin takaici.

Yace "to ya shi ya saketa ne?"

 Abba ya kalleshi yana dariya yace "kana so ne?"

 Yace "naga kai kace in kula da patient ya kake neman canza shawara?"

 Abba yai dariya yace "kabar komai a hanuna ni kaina babban burinane maga matarnan na cikin farinciki."

 Haka sukai ta hirar Goggo har dare yaja, Ghali yace zai wuce gida.

*********


  Zaune yake a kofar gidan sanyi sai ratsashi yakeyi, yanata kiran number Jalila bata shiga, sanyi sai kara kadashi yakeyi ga azabar yunwa dake damunsa, tun safiyar jiya har yau bai ci abinci ba, hasken daya dalleshi ne yasa ya rufe fuskarsa, tsayar da motar yai maimakon ya shiga gidan, ya fito sannan ya kunna fitilar wayarsa yana  haska shi.

  Dady ya mike da sauri yana neman yin gaba.

 Abakar? Abinda ya fada kenan, gaban Dady ya fadi dan yanzu ya gane Abba ne, kasa juyowa yai saboda tsananin kunyar yanda kayan jikinsa da yanda duk ya canza yake.

 Abba da sauri ya karaso ya jawoshi, Dady ya juyo tare da yake baki yace "Taura!"

 Abba cikin tsananin mamaki yake kallansa yace "menene hakan?"
 Ya fada yana kallan jikinsa, Dady ya dan zare hannunsa yace "bakomai."

 Abba yace "daga ina kake haka?"

"Daga ina ma zance? Dama zuwa nai ko zanga Jalila inata kiranta bansameta ba."

 Abba yace "Jalila ai bata kasar ita da mijinta."
  Da sauri Dady ya kalleshi yace "batanan?"

 "Suna Kuwait, amma kai meya faru naganka haka? Kwanaki inata nemanka har gidanka naje akacr kum tashi."

 Yai shiru yana kallan Abba, Abba yace "Abakar?"

 Dady ya kalleshi, idanunsa suka canza yace "dama inasan ganin Jalila ne ta bani dan wasu kudi wanda zan koma kauyen mu dan na gaji da kwana a masallaci ko karkashin gada."

 Abba cikin mamaki yace "bangane ba?"

 Nan Dady ya sanar dashi abinda ke faruwa, Abba yai shiru yana kallansa kafin yace "Abakar kaga yanda rayuwa take ko? Shiyasa akesan mutum yayi dakyau, yanzu gashinan bakada wani wanda zaka nemi taimako agunsa, bakada wanda zai ji tausayinka, kanada 'ya'ya amma ka banzatar dasu, yanzu meka mora a duniyar nan?"

 Dady cikin raunaniyar murya yace "nikam ai banga wani abun dana mora ba...." hawaye suka zobo masa yai saurin gogewa.

 Abba ya kalleshi yace "menene matsayin mahaifiyar Jalila a gurinka?"

 Kallan Abba yai yace " nikaina ban sani ba."

 Abba yamai wani kallo yace "kai kana tunanin da hakkin ta kadai ma zai barka? Ka saketa ne ko me?"

 Dady yace "nikaina bansan halin kaina ba, amma ni tun farko ban dauketa a matsayin mata ba."

 Abba ya runtsr ido cikin wani irin kunar rai yace "yanzu ba aurenta kenan a kanka?"

 Dady da sauri ya kalli Abba, yace "ko akwai?"
Dady yace "bangane nufinka bane."

 Abba yace "in ba auranka akanta ka bata takardarta ta nemi miji ta aura, saboda wannan abinda kake yi ba karamar tauye mata hakkin rayuwa kakeyi ba, ayanzu ma danaji baka dauketa a matsayin mata ba, in na sanar da ita auranku ya rabu sai dai nafisan ka rubuta saboda abinda zai iya faruwa nan gaba."

  Dady yace "amma ni.:......."

 Abba ya katseshi "akwai sauran cin zarafi ne dakake kokarin yi mata?"

 Dady yai shiru yana tuno irin wulakancin dayama Goggo, Abba yace "akwai mai santa inhar kanaso wani ya gyara abinda ka bata sai ka rubuta min yanzu ka bani."

 Dady ya kara goge kwallar data zubomai sannan yace "to zan rubuta yanzu, dan na tabbatarban camcanci zama mijinta ba."

 Abba ya wuce mota Dady ya biyoshi, paper ya dauko da biro ya mikamai, Dady ya rubuta saki daya yaba Abba.

 Gaba daya sai ya kara ba Abba tausayi, Abba ya koma cikin mota yana tunanin ya taimaka mai ne? Sai dai in ya tuno abubuwa marasa kyau da Dady ya aikata sai yaji inaa bazai iya ba gwara ya kara sanin duniya ta garashi tukunna, wallet dinsa ya dauko ya duba ciki, dubu takwas ne a ciki, yasa hannu a aljihunsa yaji dubu biyu ya mikamai yace "gashi kai kudin mota sannan ka nemi na abinci."

 Dady ya fara godiya, Abba ya shige ciki da sauri.

 Yana parking ya fito jiki a sanyaye..........


#OneLove💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*

🥰🥰

*80*

*************

Bayan wata takwas.

Jalila ce ta turo kofar falon, tana shigowa ta zube a kasan carpet din falon ta kwanta.

  Hassan na kitchen yana jinta ya fito falo yana cewa "Hajiya an dawo?"

Harararsa tai tace "wallahi daga yanzu na daina yarda da wannan wayan ace wai ni kadai xan dinga zuwa siyayya."

 Kusa da inda take kwance yazo ya kwanta shima yace "kefa kikace ayi game, wanda ya zabi zuwa siyayya shizai dinga zuwa cefani."
Tace "amma ai wayau kamin, kasan wanda ka rubuta hakan, tunda kana dauka ka zabi abinda kake so."

Juyowa yai ya kalleta tare da jawota kafadarsa yace "baby ba wayau, ya zakiyi? Tunda kin zaba ai ba yanda zakiyi."

 Ta turo baki tace "ni gaskiya a sake."

 Yace "inaaa ban yarda ba."

 Tace "Allah ga yunwa, na dawo daga makaranta ansani wucewa cefani."
Ya dan bubugata alamar lalashi yace "karki damu wannan ur Hubby ya shirya miki sai dai kawai kici."
 Da sauri ta kalleshi tace "Allah?"

 Ya mike yana daga mata gira alamar yes, da sauri ta bishi kitchen ta bude tukunya tana murna, hade ran datai ta juyo ta kalleshi ne yasashi yin dariya yace "Surprise!"

 Kallan Indomien dake cikin tukunyar tai tace "Yaya Allah ni nagaji dacin indomie."

 Yace "ah haba? Ta kalleshi tace "nisaidai kamin dan wake."

 Dan wake? Tayaya akeyi? Badani ba."

 Tace "Allah yau inbanci ba banaji zan iya bacci."

 Yace"baban magana, sai ki dafa mana muci."

 Nanta shigayindan wake, sai dai tana gamawa sunzo ci ta kasa, da sauri ta mike tai toilet ta shiga kela amai, Hassan cikin mamaki ya kalleta tare da dafa goshinga yace "Baby stress ne ya miki yawa? "

 Ta kalleshi tace "bakai bane ka sani?"

 Mikar da ita yai yace "muje gari ki duba wani abin kichi."

 Ta kalleshi kamar zatai magana sannan sai yaga kuma ta tsaya, yace "ya akai?"

 Kallansa tai tace "Yaya yaushe rabon nai period?"

 Yace "period? Na manta, badai shi bane? Ahh nikam gaskiya....."

 Yanda yaga tana irge da hannunta ne yasa ya kalleta yace "oh gaskiyarki fa kin dade bakiyi ba."

 Ta kalleshi tare da saurin rikimai hannu tace "muna ta fama da skul ga murnar zani nigeria bikin Ya Sageer next month inaji shiyasa sam ban kula ba."

 Yace "da matsala ne?"

 Tace "a'a sai dai inaji......"
Sai kuma tai shiru, yace "me?"
Ta kalleshi ta nunamai yatsa guda biyu, yace "baby?"

 Tace "maybe."

 Da sauri ya sureta sama yana wani irin farinciki, Jalila ta hade rai tace "yaya murna ma kakeyi? Karatu na fa?"

 Ya sauketa yace "menene aciki? Sai muje mu taho da ko Amira tunda ta gama secondary tazo ta zauna mana."

 Ta kalleshi cikin gamsuwa tace "amma saifa munje anyi test karka sa rai dayawa."

 Hannunta ya rike kawai yanata tsalle kamar wani yaro, dariya kawai ya shiga bata.....

 ************

 Yanda aketa shirye shirye a gidan ne zai kayatar dakai, Goggo da Ummy na kitchen suna ta shirya abinci kala kala, Ameera da Aina'u suna gefe suna aiki suma, Goggo ta kalli Ummy tace "Oh na tabbatar jiya Jalila batai bacci ba."

 Ummy tai dariya tace "inafa zatai zata zo taga na gida, malam Hassan dai na tabbatar ya shari baccinsa."

 Goggo tai dariya, Ummy ta kalleta tace "Dr dai yau zai bar mana ke ki kwana ko?"

Goggo tai dariya tace " bazan bar Nabila da Muftahu ba a gidan, shima cemin yai in kwanab amma nikam badani za'ai wannan abin kunyar ba, anjiman nan zan koma, suna zuwa zamu tafi."

Ummy tai dariya tace "ya labarin su Mumy kuwa?"

 Goggo tace "suna nan, ai kun gama musu komai, tunda kukace su dawo gidan danake ciki inyaso su sa dayan haya."

 Ummy tai murmushi tace "kinsan da ke naso a dinga ba ma rabin kudin hayar dazasu dinga samu, sai dai ke yanzu kinyi gaba, tunda Allah ya dagaki."
 Goggo tai murmushi tare da cewa "Ummy Dr ba karamin kyautatamin yakeyi ba, 'ya'yansa ma basida hayaniya, sai godiyar Allah, duk abinda nakeso kafin ma in nema yamin, sannan kinga akwai gidansa na haya da ya barmin, mezan nema nikuwa yanzu a duniyarnan, inba kuma san zuciya nake neman bi ba?"
 Ummy ta jinjina kai tace "Alhamdulila ala kulli hal, hakurinki me ya biya miki, Allah ya dubi zuciyarki ne."

 Goggo tai dariya sannan tace "Ai duk haduwata da ku shine ya ja min haka, daga ni har Jalila,/ shiyasa akoda yaushe nake gode ma Allah daya hadanu daku."

 A tare sukai murmushi.

 Lantana ce ta shigo da kaya da sauri ta ajiye tamatso gun Goggo tace "Goggo gashi, kiranki akai."

 Goggo ta amsa tare da fitowa daga kitchen din dan tasan Dr ne.

*************

  Juye yake akan gado yana ta zuba waya sam bai kula yazo karshen gadon ba, Maimuna tace "nikam kunya nake ji."

 Yace "Kunya ko? Ki jira......."

 Dim ya tiko daga kan gadon, Maimuna tasa dariya, yace "wayyo Allah na." Dan kam Sageer yaji zafin faduwar, budar kofar Ameera tai dauke da kayan guga, kallansa tai a kasa yana shoshe soshe, dariya ta saka ganin alamar waya yakeyi tace "Yaya anji jiki, ka fito za'a tafi airport."

 Ta ajiye kayan ta fita.

******^^^*

Ya dage sosai yanata wanke dakin, sai daya gama tass ya fita sosai sannan ya maida katifar ya shifida ya zauna akai tare dasa kansa a cikin cinyoyinsa yana tunanin rayuwa, tunda ya dawo kauyen nasu mahaifinsa ke kwance ba lafiya, haka ya shiga jinyarsa, baya iya komai sannan komai a kwance yakeyi, haka yai ta kula dashi har Allah ya dau ransa a daren jiya.

  Gaba daya rayuwa tamai zafi, yai shiru yanzu shikam baisan ina zai nufa ba dan yan uwansa duk ba wanda yake sanshi, kowa kyararsa yakeyi, yau ya samu ma su barshi ya zauna a waje gun amsar gaisuwa sun hana sun koroshi ciki.

 Jakarsa ya dauka dan baiga amfani zamansa ba, dan dama sun sanar dashi mai tarar mai fada wato mahaifinsu ya rasu ya tattara nasa ya nasa ya bar musu gida.

  Haka ya fito yana neman zama a tabirmar yayansa yasa kafa agun yace "malam kama gabanka."

 Dady ya fito daga kauyen gaba daya abin duniya ya dameshi, balle waccen watan daya wuce yana garin Goggo tazo itada mijinta, haka tazo da kaya kala kala taita rabawa, yanaji zatazo gidansu yabar gidan, haka ta kawo kaya dayawa, haka ya tsaya ta bayan gari yana lekensu.

(Ranar kam ko ni sai da dady yaban tausayi.....lol)

  ***********

Gida ya cika sosai anata hira da dariya abin gwanin ban sha'awa kana ganinsu kaga mutanen dake cikin farinciki.

 Jalila na kankame da Goggonta, Ummy ta kalli Hassan yace "nikam Hassan sai naga Jalila ta rame, ko Goggo?"

 Goggo ta kalleta tace "bangani ba nikam."

 Hassan yai dariya yace "wato Ummy so kike kice banaba 'yarki abinci ko?"

 Ummy ta kalli Jalila tace "Jalila? Anya ana kila dake kuwa?"

 Jalila tai dariya tana kallan Hassan, yana kallanta yace "da alama zuciya zatai kafin Sageer yai aure tana so ta maidani babba saboda kar a rainani."

  Ummy tace "babba? Oh Hassan kaikam dai......"

 Sai kuma ta tsaya tare da kallansa da sauri tace "Jalila ciki ne da ita?"

 Da sauri Jalila ta kalleshi tana mai alamar yai shoru.

 Ya kalli Abba yace "Abba ya ka gani na kusa zama baba fa."

  Nan fa murna ta karu, Sageer yace "gaskiya ne yaya."

 Hassan yai dariya yace "ya? A ina zaka zaunane?"

 Yace kasan layin nan, muka samu gida."

 Hassan yasa dariya tare da dafashi ya matso kusa dashi yace "wato ni kakesan yima wayau ko? Inyi ta zama anan kenan ko?"

  Sageer shima cikin rada yace "ai naji fadanka ne."

 A tare sukai dariya Abba yace "ai da kun daina rada dan nikam ina jinku."

 Dariya sukai su duka.......

 Jalila ce ta kalli Goggo bayan sun shiga dakin Ameera tace "Goggo kinganki kuwa?"

 Goggo ta harareta tace "bansan gulma fa, bari na kira Dr yanata san ku gaisa."

 Tai murmushi tace " Goggo ya labarin Dady?"

 Goggo ta kalleta tace "ina zan sani?"

Jalila tai shiru kafin tace "Yaran sa fa? Duk kuna zaune lafiya?"

 Goggo tace "sosai Jalila, har mamaki nakeyi, a farkon auranmu basu saki jiki dani ba saboda ziga na yan uwan mahaifiyarsu, amma daga baya abin kam har mamaki yake bani."

 Jalila tai murmushin jin dadi tace "ai gashinan na gani a jikinki."

  Haka sukai ta yan hira kafin su fito dan Goggo zata koma gida sai kuma wani satin in za'ai bikin Sageer.

  *********

#OneLove💕
🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*

_Last Page😘_

An daura auran Sageer da Maimuna sun tare a gidansu dake karshen layin su Ummy, gidan ba babba bane sosai sai dai ya tsaru iya tsaruwa.

  Ansha shagali kala kala,  amarya ta tare a gidanta.

 Mumy kam dasu Safeena komawa sukai 'Yan kallo dan yanda Goggo da Jalila suka saje a cikin manyan masu kudi, gaba daya ji sukai bikin yafi karfinsu.

********

  Har ta wuce ta layin a cikin adaidaita sahu ta dawo daga dan karamin aikin data samu a company din inna, dan bayan rasuwar inna daga filin da Inna ta bar musu da shares din duk kudin sun kare, saboda batsan yanda zata juya su ba, sai da Allah ya taimaketa da Goggo zatai aure Ummy ta tausaya musu, yanzu kam suna cancanawa dan aikin ba wani babba bane dan bata san abubuwa dayawa ba, tadaiyi karatun ne.

  Tsaida mai adaidaitar tai ta fita da sauri, yana zaune a bakin masallaci yana alwala, daga dan nesa kadan ta kura mai ido,meya sameshi? Dab taga duk ya canza, juyawa tai ta tsaya idanunta duk sun ciciko, taku uku tai taji ance "Fatima!"

 Tsayawa tai cak ta kasa juyawa, yace "ashe dagaske kece? Nayi zatan gizo kika min."

 Yanzu kam ta daure ta juyo ta kalleshi, ido suka kurama juna ta daure ta dauke idanunta dan inta tuno abinda ya mata ji take ta tsaneshi gaba daya, juyawa tai kawai ta fara tafiya.

 Da gudu yazo yasha gabanta yace "Fatima!"

 Karabin dayar hanyar tai tawuce, tai sa'a mai adaidaita ya taho tagun kawai ta tsayar da sauri ta shige.

Shima a hanzarce yaga wani awai ya tsayar yace "dan bimin adaidaitarcan dan Allah."

Nan ya bi bayan su, da yake dama ta kusa zuwa gida bata dade ba ta sauka, zata biya kudi kawai taganshi ya fito, batai mamaki ba sai dai tayi saurin bada kudin da neman juyawa, Yasmeen ce ta leko ta gate din tana ganin itace ta taho da gudu tana murna.

 Mumy ta rumgumeta tace "wayace adinga lekowa."

Zata bata amsa ta hango Dady, Yasmeen ta kalleshi cikin mamaki tace "Dady?"

 Dan kwanakin ba kadan ba, Dady wanda idanunsa suka ciciko ya tako a hankali ya bude hannayensa, rugawa tai da gudu inda yake ta rungumeshi tace "Dady sai yau ka dawo daga tafiyar? Ta fada tana kuka."

 Gaba daya jikinsa ne yai sanyi hawaye suka zubomai, kenan shi da daya koresu ina yake sa ran su zauna? Mikewa yai ya dauketa yace "Yasmeen angirma."
Sannan ya kalli Mumy wacce ta wuce ciki, Tsayawa yai yana kallan gate din gidan, Yasmeen tace "dady muje."

 Haka suka shiga cikin gidan Safeena na shara sai ga Mumy tana shigowa ta wuce daki, Safeena zatai magana ta hango dady da Yasmeen.
 Gaba daya yanayin fuskarta ne ya canza, Dady ya kalleta yacee "Safeena?"

 Dakyar ya lalabata ta shiga ta kiramai Sultan wanda yana fitowa yaga shine ya koma ciki yasa key.

 Mumy ma dakyar Safeena tasata ta fito, Dady kam tana fitowa ya sulale ya tsugunna a gabanta, kallansa tai da sauri, Safeena ma ta kalleshi tace "Dady!"

  Idanunsa na zubar da hawaye yace "ki yafemin Fatima, ita kadai ce kalmar dazan iya fada miki."

 Mumy tai shiru tana kallan yanda yake zubar da hawaye.

  Kallansa tai tace "ka tashi mayi maganar."

 Yace "ban isa tashi ba harsai kin yafemin."

 Mumy tai shiru tana kallansa, tace "gidan ka fa? Naga ka koma haka?"

 Nan ya sanar da ita yanda aka kwacemai gidan da komawarsa kauye."

 Tausayinsa ne ya kamata dan tana masifar sanshi, abinda ya mata ne yasa ta tsaneshi.

 Tai shiru kafin tace "ta yafemai."

 Dady yace "nagode."
Na dawo daga baya lokacin da Sultan ya huce."

 Ya mike zai tafi, kasa jurewa tai tace " a ina kake kwana?"

 Juyowa yai ya kalleta yace "inda ya samu, masallaci ko..." sai kuma yai shiru ganin Safeena na kallansa cikin tausayawa.

 Mumy ta juya baya tace "inzaka iya sai ka dinga kwana a falo, kafin ka samu abinyi, sannan in rana tayi sai ka fita.

 Kallanta yai kamar yace a'a saboda kunya sai dai inyace ina zai zauna? Yana shirin magana yaga ta shige ciki.

 Idanunsa ya runtse dan yasan bai kyauta ba a rayuwarsa.

  ***********

  Yana fitowa daga gidan yaje ya dauko jakarsa sannan ya wuce gidansu Jalila, dan har ya fito zai taho dazu Safeena ta biyoshi gate, ya tsaya yana kallanta, kafin yace "Safeena ki yafemin dan gaba dayanku na cutar daku."

Nine silar dayasa duk abinda ya faru daku ya faru.

 Tace "bakomai Dady dukanmu munyi laifi,
sannan bamu bane ya kamata ka fara neman yafiya a gunsu ba, Goggo da Jalila ya kamata ka fara nema."

 Yace "Safeena na sani sai dai bansan inda zan samesu ba, ita Jalila ance batanan...."

 Da sauri ta katseshi tace "ta dawo, ana bikin kanin mijinta."

 Da sauri Dady yace "haba? Bari naje."

 Bai jira mai zata ce ba yai waje da sauri, Safeena tai murmushi tace ban fadama Goggo tayi aure ba.

*********

 Mika tai tare da yin juye, Hassan ta gani tsaye a kanta.

 Idanu ta zare sannan ta mike tace "Yaya?"

 Rufto da kansa yai kanta ya sumbaci bakinta, yace "Hajiya Baby kin farka?"

 Tace "Yaya yaushe ka tashi? Naga ina rigakafa tashi."

 Ya kalleta sannan ya danna wayarsa hasken agoggo ya bayyana, da sauri ta mike zaune tace "11? Inalilahi  da alama bana cikin hayacina, ko yaya?ko duk gajiyar bikin ne?

  Ya zauna kusa da ita tare da dan sa kansa kadan saman cikinta yace "ya zakiyi? Twins sun sa kin makara?"

 Hannu tasa tadan ture kansa daga cikinta tace "yaya da gaske Twins ne?"

 Yai ajiyar zuciya yace " maganar gaskiya Jalila banaso na tsorata kine amma 'yan uku ma likita yace zaki haifa, ya gano wani daga nan, wani anan sannan wani a kwance tanan." Ya fada yana wani taba cikinta.

  Gabanta ne ya fadi tace "yan uku?"

 Yace "eh shiyasa banasan ki sani dan nasan hankalinki tashi zaiyi, kinga Amira kadai mana kadan sai mun hada da Aina'u."

Kallansa tai ta hade rai tace "abinda yafi Aina'u."

 Yadan saki fuska yace "yanzu Jalila ya zamuyi? Ga karatu?"

 Idanunta ne suka fara rau rau, dariya ya sa harda kyakyatawa yana nunata, tana ganin haka tasan tsokanarsa ce ta motsa.

 Kafa tasa ta tureshi daga kan hadon ya fadi a kasa, amma duk da haka dariya yake, ta hade rai tace "Allah zan rama."

 Yace "a yaushe kenan? Bayan kullum haka ake cewa?"

 Ta turo baki, yace "tashi kiyi wanka Baba Ghali zaizo gaida 'yarsa."

 Da sauri tace "haba?"
Yace "kin manta Goggo ta fada miki yau zasu zo dashi? Dasu Nabila? Kafin mums muje?"

 Tace "inalilahi nikam naga ta kaina wallahi na manta."

 Ta mike da sauri tai toilet ya bita da kallo yana
Murmushi.

 Tana shiryawa yana taimaka mata tasa kaya da sauri dan tana fitowa daga wanka akace sun iso

 Nan suka fito mayafinta a hannu.

  Neman gudu takeyi gun sauka daga kan steps, Hassan yasa hannu ya rik kugunta, kallansa tai tace "yaya karfa suga mun dade."

 Yace "gwara suga laifina na basu hhskuri akan kijin asara."

 Dariya tai sannan ta sauko a hankali.

 Nabila na zaune yarinya yar shekara 12, tana ganin Jalila ta saki fuska dan sun hadu a biki.

 Dr na ganinta yace "masha Allah ana ganinki anganta."

 Ummy tace "ah haba? Anya ba san kai kuwa?"

 Dr yace "inafa sankai? Sai dai inkece kike sanyi."

 Abba yai dariya, nan ta karasa kusa da Ummy ta tsugunna ta gaishesu, fuska a sake ya amsa sannan ta gaida Goggo, dasu Ummy da Abba.

  Nabila ta dawo kusa da ita ta zauna.

 Hira suke sosai har lokacin yingirki yai, Jalila, Amira suka shiga kitchen Nabila ma tabi bayan Jalila dan ko ina Jalila tai binta take.
Bayan sun gama cin abinci akai sallah sannan aka karasa wani hira.

 Can yanma wajen magrib suka fito dan tafiya, dukansu suka fita harabar gidan ana karayin hira.

 Mai gadi ne yazo ya sanar dasu zuwan Dady.

 Jalila naji gabanta ya fadi,Hassan ta kalla da sauri.

 Hassan yace "abarshi ya shigo.
Yana shigowa ya tsaya turus, ganin mutane, sai daiduk da haka ya gano Jalila.

Cire kunyarsa yai ya nufosu.

 Dr ya kalli Goggo yace "shine baban nata?"

 Tace "eh."

 Dady ya karaso jiki a sanyaye, hannu ya mika musu suka gaisa dukansu, sai dayazo kan Dr sannan ma yaga Goggo ce ashe dan da sam bai gaje taba.

 Dr yace "barka da haduwarmu, nine mahaifin Jalila na yanzu, mijin mamanta kenan."

Dady ya kalli Goggo yaga yanda ta canza, ya kalli motar da suke jin gine agun dan alama ce ta motarsa ce.

Jiki a sanyaye ya kalli Jalila da Goggo, kamar zaiyi magana sai sukaga yasa gwiwowinsa a kasa, da sauri Hassan yaje ya sa hannu ya dagashi.

 Dady ya kasa magana kawai sai kuka..........

Gaba daya tausayinsa ya kamasu, dan kam Dady yaga rayuwa adan lokacin nan.

  Idanun Jalila ne suma suka ciciko.

 Gaba daya Dady yama kasa magana kawai sai kuka.........

**********

Gidan ya cika sosai anata shirye shirye, Jalila na zaune a daki tayi rau rau da ido kamar zatai kuka, Hassan yace "wai da zafi sosai?"

 Tace "nidai wallahi da zafi."

 Bude kofar da akai bayan an kwankwasa ne yasa Hassan juyowa.

 Goggo ta kalleshi tace "Hassan jeka gidan Sadiq ankai muku abincinku can."

 Yace "Goggo har gidan Sadiq cin abincin? In tafi in barta?"

 Mumy tace "ai kuwa dai tafiya zakai, dan na kula Jalila neman raki takeyi dan taga yau ka dawo, ai sanda tana nakudar bata dinga zabga mana raki haka ba, amma yau dan ta ganka shine takesan fanshewa, dama ai suna na mata ne, kaje kaci abincin amarya."

 Jalila ya kalla wacce ta shagwave, haka ya fita.

Goggo tana zuwa ta dungurema Jalila goshi tace "ko kunya? Shayarwar akema raki haka?"

 Jalila ta turo baki, tace sai fa yau yazo?

 Basu san Ummy tazo ba sai ji sukai tace "abarta tai abinta wayace kar ya dawo da wuri? Wai shi a sole yanajin haushin na daukota da cikinta yakai wata tara? Itama ku barta ta fanshe."

 Mumy tace "dama dai Ummy ke shagwabata."

 Sukasa dariya, Safeena ce ta shigo da kaya tace "gashi inji Wata tace dole dole wannan za'a sama jariri."

 Ummy ta girgiza kai tace "Aunty Nana kenan, sam ba dama."

 Nan Ummy ta dauki yaran wanda yake jin yunwa tace "Jalila bashi yasha asamai kaya."
 Dan nasan mijin nan naki dakyar zai bari ki kara sati biyu anan.

 Sukasa dariya.

Ameera ce ta shigo da flask na ruwan zafi ta ajiye kusa da Jalila.

 Jalila ta daga mata gira, Ameera ta hade fuska tace "bamu shirya ba."

 Jalila ta jawota tace "badai ruwana in naji kina lalabashi a waya cikin dare.

 Ummy tace " gulmar ce?"

 Jalila tai dariya......

A kasa kuwa falon Abba, dady na zaune daga dan gefe yana ta kallan yanda aketa hira tsakanin Dr da Abba.

 Shikam sai dai hmm ko um um shiyanzu rayuwarsa ta fiye mai, dan yanzu Hassan ne ya budemau dan shago yake business dan dama ya iya kasuwanci, Alhamdulila kuma abin na tafiya yanda ya kamata, sannan Jalila ta shiryasu da Mumy.

 Suna zaune a gidan da Inna ta zauna, sai dai yanzu rayuwarsu tafi tada, gashidai ba kudi kamar da sai dai akwai fahimtar juna, Sultan da Safeena suna ta karatunsu........

Allah ya bamu ikon kuka da zuciyoyinmu, ya bamu ikon fin karfinta akan abinda take aiyana mana mara kyau, ya bamu ikon jure rashi, ya kuma bamu ikon yadda da kaddara a duk sanda tazo mana.......

Ameen
Suma
Ameen.......

Alhamdulila!!!

Ina godiya ga Allah subhanahu wata ala daya bani ikon kammala littafin nan lafiya, abubuwa dayawa sun faru a dan lokacin da nake rubuta littafin nan, sai dai muce Alhamdulila ala kulli hal.....

 Abinda na fada na kuskure Allah ka yafemin, wanda na fada daidai kuma Allah ya sa muyi amfani dashi.

  Allah ka kare mu daga sharrin duk wani wanda yake nufinmu da sharri, ka nisan tamu dashi, ka hadamu da duk mai nemanmu da alkair👏🏻

Ina godiya gareku masoyana, na gode sosai da hakurin da kuke dani, nakinyin typing da wuri, yin delay agun responding din text dinku da sauransu, nikaina ba asan raina bane.

 Love u all🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰

Download Jalila Littafi Na Daya Complete