🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KAR KA GUJENI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Na Aisha A Yabo*🌺
fulani 🌸
*Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#http://www.Facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot
_wa d'anan sune shafukan mu da zaku ziyarta Dan samun k'ayatattun littafanmu_
*5 to 10*
Allah ne kawai ya kaita gida lafiya da k'yar ta iya saita kanta bayan ta ajiyi motar a gurin da aka tanada dan ajiye mota ta shiga cikin gidan zauni ta tarar da Aunty da 'yan aikinsu suna kallo falon k'asa
murmushi tayi cikin k'ok'arin boye damuwarta tace "Aunty kallo kuke"?
"uhm Bety su Ma'u dai ke kallo nikam hankalina na gunki ya mai jikin"?
sai yanzu ma ta tuna da abun da ya fitar da ita har ta had'u da azzalumin da yayi mata a bun da ba a tab'a yimata ba a rayuwarta
nisawa tayi kafin tace "Alhamdulillah yaji sauk'i su DADY fa"? Aunty tace "basu dawo ba dama zullumina kenan tun d'azun Alhamdulillah gashi har kin dawo cikinsu ba wanda ya dawo"
"OK bari na shiga ciki" tana tafiya take amsa gaisuwar su Ma'u tana shiga d'akinta Alwala tayi ta gabatar da sallah magrib bata bar gurin ba sai da tayi isha'i
ba yanda Aunty batayi da ita ba taci abinci tak'i ce sai Holandia kawai ta d'an sha
"Aunty tace "wai me ya sami fuskarki ne tayi haushi idanunki duk sunyi ja"? cikin kawar da kai tace "bakomai Aunty kawai na tausayawa Meenat ne Abban ta bai da lafiya sosai"
"Ayya Allah ya bashi lafiya" ta fad'a ba dan ta amince da maganar Bety ba.
da dare ma sai sarkin b'araye ne ya saceta barce ne tayi ciki da mafarkin Al'amin yana marinta harda duka. wannan kenan
Al'amin suna shiga gida Inna da take tan kad'an garin da zasuyi tuwo tace "A'a Babana ya naga kun dawo miye ya b'ata maku kaya haka"?
Cikin furzar da numfashi yace "wallahi Inna wata 'yar iskar yarinya ce tayi mana haka" Lawal ne ya bawa Inna labarin Abunda ya faru
ai kuwa ta hau bakinta fad'a take masa "haba Babana meyasa zaka dake ta nifa bana son zafin zuciyarnan naka haba ace mutum bshi da wani abu sai zafin zuciya ko namiji ne ka ce kasakar masa k'awanji ballatana macci ni dai wallahi banji dad'i ba
dan Allah kasanyawa zuciyarka salama haba!" ganin yanda ta d'au zafi yasa ya sassauta murya yace "Dan Allah Inna kiyi hak'uri nima ban san ya akayi na mare ta hakan ba raina ne ya b'ace kiyi hak'uri kinji Innata"?
ya k'arasa maganar yana mai d'aura kansa a kafad'anta shafa sumar Kansa tayi cikin muryar da ke nuna ta sauko tace "bakomai Babana ni dai fatana ka rage zafin rannan kaji"?
"to Inna Insha Allahu kiyi mun adu'a" "inayi Babana Allah dai yayi maku Albarka"
"Amin" ya fad'a tare da mik'ewa d'akinsa ya nufa bayan sun shiga Al'amin yaciri kayan ya sanya jallabiya bak'a duk da rigar ta d'anji jiki hakan bai hana kyansa fitowa ba tamkar balarabi kasancewar fari ne
d'ura kayan yayi kan kujera yayi kwanciyarsa kan 'yar k'aramar katefarsa Lawal ya dube shi da mamaki yace "ya zaka kwanta ko kafasa tafiyan"?
"mts eh nafasa kaje kawai" daga haka bai saki cewa komai ba ya rufi idanunsa
Lawal kad'a kai kawai yayi ya ficewarsa ba tare da ya saki cewa komai ba.
ga baki d'aya ranar Al'amin baiyi barccin kirki ba kukanta ya tsaya masa a rai haushin kansa ya keji "meyasa ya mareta?"
haka dai yayi barccin ba cikin natsuwa ba.
*BAYAN KWANA BIYU*
tana kwanci ajikin Yaya saif tana danni danni waya Yaya Saif yace "wai Bety yaushi ne makarantar ku zasu janyi yajin aikin"?
"cikin ya tsinar fuska tace Yaya nima ban sani ba wallahi" "Bety wallahi dan kin nacewa makarantar nanne kawai amma ni a India naso kicigaba da karatunki kika k'i"
"uhm ni dai nafi son nan" "aifa nikuwa naga ranar da zaki gama makarantar da wannan shigen yajin nasu na tsiya"
murmushi tayi tare da saurin canza maganar "Yaya Dady yace jibe zakuje Sudan ka karb'omun turare da lalle gun 'yar tsuhuwa" ( kakarsu)
"au ke bazaki bane"? "eh Yaya saboda ko yaushi zasu iya janyi yajin aikin"
ba dan komai ta dujewa tafiyan ba sai dan Farhan sarkin nacenta k'arar da wayarta keyi ne ya katsi firar tasu ganin Meenat ce yasa ta tashi zauni ta d'aga kiran cikin fara'a
"oh Meenat ba kiyi fushi ba"?
"kema kinsan ko banyi fushi ba zanji haushi"
"nasani kiyi hak'uri dan Allah wallahi su biyu ina shirya zuwa sai uzuri ya gitta amma kina raina ya jikin Abba"?
"da sauk'i amma fa ban d'auke maki zuwa ba"
cikin murmushi tare da duban gefin Yaya Saif taga ya tashi baya falon hakan ya mata dad'i tace karki damu jibe Insha Allahu zanzo"
sun jima suna fira kafin daga bisani sukayi sallama
ranar laraba a hanyarsu ta dawowa daga filin jirgi rakiyarsu DADY tacewa drv su wuce Hayin ma'azu
sanda suka isa dai dai kwanar da zata sadata da gidansu Meenat tace "suyi pakebg"
ba musu suka bi Umurninta cikin takun k'asaita ta fito iscod d'inta ne a bayanta sun kai su goma
Al'amin ne zauni a kantin Lawal suna fira akan idonsu motoce biyar sukayi Pakeng ganin wacce tafito cikin mortar ba k'aramin d'agawa Lawal hankali yayi ba musamman da yaga gurinsu suke nufuwa
nan taki yaji yawun bakinsa ya k'afe jikinsa ya fara rawa cikin sark'ewar murya Lawal yace
"shikenan Al'amin zafin kanka ya janyo mana masifa ka duba yarinyar nan tazo mana da k'attan samudawa wayyo Allah na shikenan nasani k'arshinmu yazo
b'abb'alamu zasuyi tuni fitsari ya fara zubu masa k'afafunsa sai karkarwa suke
uban gayyan ko ajiknsa kallonta yake fuskarsa murtuk'i hankalinsa kwanci ko d'ar baiji ba jira yake yaga da wacce tazo ashiryi yaki da duk yan da tazo masa.
_mai k'aunar ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KAR KA GUJENI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Na Aisha A Yabo*🌺
fulani🌸
*Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#http://www.fascbook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot
*10 to 15*
Sanda ta k'araso gurin kallo d'aya tamasa ta d'auke kanta domin ba zata manta fuskarsa ba wani irin firgici da bugun zuciya take ji jin take tamkar a lokacin ya ke marinta sam mantawa tayi da zata sayawa mara lafiya kayan dubiya da bazata tsaya gurin wannan azzalumin ba runtse idanunta tayi kafin daga bisani ta bud'esu cikin k'arfin hali da k'ok'arin boye yanayin da tashiga ta dubi Lawal da yake cikin kantin yanata had'a uban gumi tace
"dan Allah ina son drinks" cikin rawar murya yace "w..w..a.ni iri kikeso"?
"uhm koma wani irine" "to to k'wara nawa"? "katan hud'u"
"ranki ya dad'i katan biyu ne yayi saura"
"OK ba damuwa kawo sai ka had'oda sweet da biskit"
nan take ya had'a mata iscod d'in suka d'auka inda tabiya shi kud'insa tabar gurin cikin tsananin bugun zuciya.
bayan tafiyarta Lawal ya fito yana sharci gumi tare da sauki ajiyar zuciya "wai Allah ya somu alk'ur'an har nafara hangoni a mak'abarta"
Al'amin da ke kallonsa duk yanda yaso had'i dariyar da ke tasu masa kasawa yayi ai kuwa dariya yake sosai da tafara k'ular da Lawal
"kaifa d'an iskane miye zaka wani sani gaba kana dariya kamar kaga sabon kamu"?
ganin Al'amin ya k'icewa da shi komai sai dariya yake yana nuna shi hakan yasa ya kai dubansa gurin da Al'amin ke nuni Wandon sa yayi shakaf ko ba afad'a ba yasan fitsari ne wannan ya wuce akirashi da gume
shafa kansa yayi ciki da kunya yama rasa me zaiyi cikin dariya Al'amin yace "wallahi Lawal tsoronka yayi yawa haba kamar macci yanzu miye abun tsoro a wad'annan mutanan"?
harararsa Lawal yayi kafin yace lallaikam d'an rainin hankali agunka ne ba komai ba wad'annan bani ba ko kai sarkin cika bakin idan ka shiga hannunsa wallahi komai ba zaka iya ba, da kake cewa tsoro kamar macci yo idan maza suna guri ai banbancinmu da macci k'alilanne"
cikin k'ok'arin had'i dariyar yace "haba wa ni d'in wallahi kaima kasan wasa kake ko sunfi wad'annan masu kama da dodanni nafi k'arfinsu kawai malam kazama namiji kuma wallahi maza kaje kaciri k'azantar nan"
ya k'arasa magar yana harararsa mts Lawal yayi tsaki tare da barin gurin ya nufi gida dan sauya kayan jikinsa
wani yaro ne yazo wucewa Al'amin ya k'wala masa kira "faruk' zunan" da sauri faruk' ya k'arasa yana fad'in gani yaya"
yauwa maza d'auki butar nan a kwai tsintsiya a bayan k'ofa shiga cikin zakaga inda ruwa ya zuba ka k'ara ruwan kashare sosai kaji"?
yaron ya amsa da to cikin k'ank'anin lokace ya gyara wajan da taimakun Al'amin" faruk' zai wuce yaga waya ak'asa yace "lah yaya ka yarda wayarka" ya fad'a bayan ya d'auko wayar
Al'amin ya karb'a cikin mamaki dan shi dai wayarsa gata a hannunsa Lawal kuwa wayarsa ba irin wannan bace
yana duba scrm d'in wayar yaga hoton bety ya cika scrm d'in ko shakka bayayi wayar 'yar gidan Lawal ce hakanan ya tsinci kansa da shiga ma'adanar ajiyi hotona yana kallon hotonan ta ne da sukafi yawa
wani irin yanayi mai wuyar fassarawa da bazai iya tantanci ko na miye ba ya kejin yana ratsa zuciyarsa da jinin jikinsa, tura hotonan yayi a wayarsa tare da sa numbarsa cikin wayarta yayi fulashin d'in wayarsa sannan ya kuma wayarta ya goge tasa, ya bawa faruk' wayar yace "ungu maza ka shiga layinmu duk inda kaga motoce sun tsaya ka tsaya anan idan kaga wata zata shiga mota ka bata ka fad'amata inda tayar"
bayan tafiyar faruk'u ya fara jin haushin kansa miye zaiyi da numberta ko hotonanta shi baima San dalilin da yasa ya d'auka ba mts yayi tsaki kafin ya mayar da wayar aljihunsa.
da murna Meenat ta tarota sai rawar jiki take sai da takaita guri Ummi suka gaisa tare da tambayr mai jiki Ummi tace "yaji sauk'i ai har yafita yau"
"Masha Allahu Allah ya k'ara sauk'i" "amin 'yar nan sannu da k'ok'ari mun gode sosai" tafita tabarsu Meenat tace "ban zaci zaki gani gidannan ba"
"haba Meenat me kika mai dani zuwana fa biyu gidanan" dariya Meenat tayi kafin tace "hakane fa mutuniyar k'wak'awalwarki naja"
"uhm ke dai ki kasani" sunjima suna fira kafin tayi masu sallama bayan tsarabar da tayi , masu harda dubu goma tabawa Ummi sai godeya suke mata,
har mota Meenat ta rakota faruk'a da yake gefi a tsayi yazo da sauri yace "Aunty ga wayarki kin yar a k'ofar kantin Yaya Lawal"
cikin sauri ta karb'a tana fad'in "oh na gode sosai kinga halina ko sam ban kula ba gurin na bashi kud'i nasan nayar da wayar"
Meenat tace "anci sa'a raboce baki yar a idon b'ata gariba"
"wallahi kuwa" tabawa faruk' dubu d'aya yak'i karb'a ya bar gun da gudunsa hakanan sai taji yarun ya burgeta har take tambayar Meenat sunansa
"faruk' kenan d'an k'anwar Inna Haulatu ne amma a gurin Inna yaki babansa ya rasu tun yana wata biyu"
wani irin tausayi da k'aunar yaron taji ya shigeta farat d'aya tace da Meenat "Insha Allahu zan saki zuwa ki kaini gidansu"
"to sarkin tausayi sai na ganki ta fad'a tana dariya Bety murmushi kawai tayi tashiga mota. *wannan kenan*
_mai k'aunar ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KAR KA GUJENI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Na Aisha
A Yabo*🌺
fulani🌸
*Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#http://www.Facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*15 to 20*
An janyi yajin aiki sun koma makaranta sun cigaba da karatunsu hankali kwanci da dare daga k'arfe 8:00 ya sayyadi yana zuwa yayi mata karatu zuwa 9:00 suke tashi.
*WACE CE BETY?*
asalin sunanta Aisha 'yan asalin Sudan ne mahaifinta Alhaji sufiyan da mahaifiyarta safna dukansu 'yan famili d'aya ne sun kasance 'ya'ya ga Baffa Hamid da Baffa Ahmad wanda suke uwa d'aya uba d'aya,
Baffa Hamid yaransa hud'u Sumayya ce babba sai sufiyan Asiya auta Alk'asim,
Baffa Ahmad yaransa biyu Muhammad Safna,
Sufiyan da Safna suka had'a kansu inda iyayansu sukayi farin ciki cikin k'ank'anin lokace akayi aurensu watansu d'aya a sudan suka tattaru suka dawo nagiria kasancewar anan yake kasuwanci
Kaduna garin gwamna anan ya sauka da amaryarsa Unguwar kinkinau anan ya tambatsa had'add'in gidansa naji da gani ban san ya zan kwatanta iya had'uwar gidan ba naira dai ta kuka,
rayuwar gidan gwanin sha'awa suna matuk'ar tattalin juna soyayya sukewa juna har karasa wa yafi son d'an Uwansa Abokinsa Alhj ma'azu mak'ota ne gida d'aya ne tsakaninsu shi ya samu masa 'yan aiki acikin 'yan aikin a kwai Abu Amma tun zuwanta safna ke kiranta da cikakkin sunanta Zainab
tana matuk'ar son zainab saboda na tsuwarta hakan yasa ta janyota jiki tamkar k'anwarta,
shekararsu biyu da aure Allah ya albakaci su da samun k'aruwar kyakyawan babynsu Zo kuga murna tun daren suna 'yan Sudan suka cika gida ranar suna a kasawa Baby Saifullah kusan rainunsa duk Zainab ce banci kad'ai ke rabasu yanada shekara ukku Zainab tayi Aure da Isa drvn DADy Anan cikin gidan Akwai b'angarin da ba kuwa nan suka zauna inda Momy Safna tayiwa Zainab komai da ya kamata Uwa tayiwa 'yarta daga Zainab har iyayanta adu'an gamawa da duniya lafiya da sakamako mafi tsoka a gurin Ubangiji sukewa Momy da Dady domin duk wani gata sun mata shi.
aurenta bai hanata zuwa b'angarin Momy ba da mijinta ya fita tare da Dady zataje gun Momy sai sun dawo sannan ta koma b'angarinta.
Saifullah nada shekara goma har sun ciri rai da saki haihuwa sai gashi Allah ya bata wani cikin wai zo kuga murna gun su Momy da Saif tun kafin a haihu babu ne kawai basu saya ba
saif duk suka fita da yaga kayan wasa sai yace asayawa Babynsu idan sweet ko bisket aka saya masa sai ya dinga kukan sai ansayawa Baby haka dai suke nuna so da tattalin baby tun bai fito duniya ba.
wata tara da kwana goma cif da k'arfe goma na dare Allah ya sauketa lafiya a cikin gidanta tasamu 'yarta kyakyawa kamarta sak ba abun da tabari na momynta.
ranar suna aka rad'a mata Aisha Humaira suna kiranta da ( *BETY D'IYATA A YAREN HINDU*)
HUM mai karatu fad'ar irin so da gatan da akewa Bety Alk'alamina yayi kad'an ya kawo maku kullum zaka ganta goyi a bayan Zainab sai idan za tasha mamma ko baci ke rabasu idan Saif ya dawo makaranta kacukan lokacinsa nata ne,
lokacin da takai shekara d'ai da wata bakwai Zainab tayi yayenta shak'uwarsu da Zainab ba zai kwatantu ba ko Momy da Dady bata yarda dasu idan tana hannunta Saif kad'ai take yarda dashi.
*BAYAN SHEKARA HUD'U*
ranar asabar ba boko Saif ne da Bety b'angarin Zainab sai wasansu suke yana mata doki sai b'angala dariya take Uncle Isa da Aunty (haka Saif ke kiransu)suka fito Uncle yace to 'yan gidan Aunty ku tashi muje ya fad'a yana rik'o hannun Saif Aunty ta d'auki Bety suka nufi gurin su Momy
sun tarar da ita shirya su kawai take jira Momy ta mik'i tare da fad'in "yauwa dama Ku nake jira Bety zo muje"
Bety ta mak'i kafad'a alamar bazata ba Momy tayi murmushi kafin tace "daman nasan ba zuwa zakiyi ba waya isa ya rabaki da Auntynki" ta kalli Saif tana fad'in "d'an gidan Momy zo muyi tafiyanmu"
cikin b'ata fuska kamar zaiyi kuka yace nima Momy bazani ba tunda Bety ba zata ba" rik'i baki Momy tayi kafin tace "iyye wato haka zamuyi ko Saif shikenan nayi tafiyata"
ta d'auki jikka tana fad'in "Zainab zamu tafi ga yaranki nan ki kula dasu da gidan kiyi ta hak'uri da yarintarsu
"to Momy Allah ya tsare ya dawo daku lafiya" ta rakata har mota tayiwa yaranta kiss sannan ta shiga mota Uncle yaja suka kama hanyar Abuja bikin 'yar Abokin Dady Alhji ma'azu wanda ya koma Abuja da zama Dady yana legos daga can zai wuce gurin d'aurin Auren.
ga ba d'ya tun tafiyarsu Momy Zainab take junta wani iri jikinta takeji tamkar ba nata ba, su Momy ko minti talatin da barin Kaduna basuyi ba Sukayi hatsari da taimakun mutane da wani bawan Allah da yazo wucewa yaga abun da ya faru ya sasu motarsa da wusu mutane Ukku suka nufi kaduna dan kaisu Asibiti.
ko Kaduna basu kaiba Uncle yace ga garinku hankalin mutanin ya matuk'ar tashi Momy cikin tsananin jin jiki tace dan Allah kukira mun mijina ga numbersa tafad'a masu number cikin jin azaba anyita kiran wayarsa bai d'auka ba har suka shiga Kaduna wanda zuwa lokacin Momy tafita hayacinta suna isa asibiti aka wuce imagns da ita.
_mai k'aunarku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KAR KA GUJENI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Na Aisha A Yabo*🌺
fulani🌸
*Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#http://www.Facebook.com/Pml_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*20 to 25*
Ana shiga da ita ta fara kalmar Shahada tana idarwa numfashinta ya d'auke Doctor ya duba ta yana gama dubata yaja mayafi ya rufeta kafin ya kalli wa d'an da suka kawota yace "sai dai kuyi hak'uri Allah ya karb'i Abarsa"
*Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" suke ta furtawa kafin mai motar yace "yanzu ya zamuyi ma sada mamattan ga iyalansu"?
"ranka ya dad'e me zai hana asake kiran number da baiwar Allah ta bayar" cewar d'aya daga cikinsu
"hakane bari na sake gwada kira Allah yasa wannan karan ya d'aga" ya fad'a cikin jimami.
Dady fitowarsa kenan daga wurin meeting da wasu turawa akan wani kamfani da yake so ayi masa gini anan legos harya sayi fili, duk wani iri yake jinsa ga wani irin sanyi da yake ji cikin wannan yanayin wayarsa ta dinga k'ara alamar neman agaji kasa d'aga kiran yayi sai cewa PA d'ine da yake tattara faels ya d'aga kiran
sanda PA yaji bayanin da aka masa hankalinsa ya matuk'ar d'agawa cikin sassauta murya yanda Dady bazaiji shi ba ya kwatanta masu gidan Dady tare da sheda masu basu gari amma yanzu zasu biyu hanya
bayan ya gama waya ya dawo kusa da Dady yace "yallab'ai dama hajiya ce takira tace suna asibiti Bety bata da lafiya" aransa yace "gara na fad'a masa haka yafi da dai gundarin zancen" cikin tashin hankali Dady ya mik'e yana fad'in "me yasa meta me yake damunta!?"
cikin tsananin tausayin uban gidansa yace yallab'ai abun da tafad'a kenan"
"maza ka kira K'asim ya shirya mana tafiya Kaduna yanzunan" cikin ladabi yace "to yallab'ai".
lokacin da sukayi duk abun da ya kamata suyi sannan aka basu gawawakin sukayi gida dasu
uhm fad'an irin tashin hankalin da wannan familin suka shiga alk'alamina ba zai iya ba iyakar tashin hankali sun shiga
Dady abun kamar hauka ya zame masa Aunty sai da ta kwanta asibiti.
bayan adu'ar sati Umminsu Safna taso ta d'auki Bety da Saif Dady yak'i bazai iya rabuwa da yaransa ba
Umminsa tace "kai da ba zama kake ba taya za abarma yara dole kayi hak'uri kabarsu hannunmu ko ka tattara ka koma Sudan"
"Ummi kuyi hak'uri narasa Safna bazan iya juran rashin su Saifullah ba Zainab tana tare damu nasani zata kula dasu" ya k'arasa maganar cikin zubar hawaye
Baffan Dady yace "in banda abunka Zainab d'in zatai ta zama ne batayi Aure ba ko kuma zata cigaba da zama gidannan daga kai sai ita"?
cikin sauri Zainab da take gefi tana kuka wacce rashi biyu ya dake ta miji da Uwar d'aki tagari tace
"Baffa dan Allah karku tafi dasu wallahi zan iya kula dasu har iyakar rayuwata bazan iya jure rashin su AISHA ba"! ta fad'a cikin kuka kamar numfashin ta zai d'auke
dukansu sukayi shiru kafin daga bisani sukace shikenan suje an sallame su bayan fitar su Dady
iyayan da yayyinsu sukayi wata maganar da duk k'wak'wata nakasa jiyo me suke fad'a daganan taro ya tashi washe gari 'yan Sudan suka wuce aka bar Ummin Dady tare dasu Aunty.
saif tun yana fitinar akaishi gun Momy ayita lallashi yau da gobe har ya daina Bety kuwa Sam bata san me ke faruwa ba.
*bayan Wata biyar*
Baffan Dady dana Safna yayyansu sukazo bayan sun huta Baffa yace
"Sufiyan ba komai ne yasa nazo tare da Baffanka da kuma 'yan Uwanka ba sai kan maganar Yaranka idan har kana Son abarma su to dole zaka amince da zancen mu idan baka amince ba to lalle zamu d'auke Su Aisha"
ba tare da tunanin komai ba yace "Baffa ko miye ne nayi maku alk'awarin zanyi matuk'ar bai sab'awa addini ba" ya fad'a cikin ladabi
Murmushi Yaya Sumayya tace "Sufiyan ba komai bane face ka amince da Auren Zainab saboda zamanku hakan ba zaiyu ba sannan munyi tunanin dukanku ba kwason rabuwa da yaranku wannan yasa akayi shawarar had'aku aure"
zuciyarsa ce ta dinga bugawa da sauri da sauri nan take yayi sharkaf da gumi ya zaiyi ya riga ya d'aure kansa wani b'angari kuma yana buk'atar yaransa
ba tare da dogon nazari ba kawai ya amince yana furtawa ya bar falon inda ya barsu suka cigaba da tattaunawa dan kuwa sun yaba da halin Zainab da yanda take kula da yaran kamar d'iyan cikinta.
washe gari da Abban Zainab ya zo daga k'auyensu da yake cikin zariya lokacin da Abban Zainab ya fad'a mata maganar Auren hankalinta ya matuk'ar tashi
kamar ta d'aura hannu aka taita rusa ihu take ji "ya ma za ayi ta aure uban gidanta mijin Momyn da tamata dukkan halaci gaskiya Abba bazan iya ba"!
"ba komai Zainab bazan maki dole ba amma dai ki sani kakannin yarannan zasu karb'esu zamu tafi dake gida"
shiru tayi tana kuka "wayyo ni Zainab ya zanyi? bazan iya rayuwa ba kuba banda mafita bayan na amince Momy kiyi hak'uri ki yafeni dole tasa amincewa"!
ranar Juma'a bayan an sauko sallah Juma'a dubban al'umma suka shidi d'auren Dady da Aunty sai fatan Allah ya bada zaman lafiyada zuri'a d'ayyaba.
iyaye da 'yan uwa sun masu nasiha sosai kafin suyi masu sallama akabar ango da amarya sai yaransu.
da dare Dady na hango d'akin amarya wanda tuni ankawota b'angarinsu bayan ancanza komai na gidan da d'akunan duk cikin umurnin iyayansa
ina ganin ya shiga da guduna nabi bayansa dan kar ayi bani sai dai kash ina zuwa na tarar harya kullo k'ofa na manna kaina ga k'ofa ko zan jiyo sai dai kash komai banji ba nabar gurin kamar zanyi kuka☹
tunda Saif yaji Autynsu ta Aure Dady ya tsaneta baya shiga lamarinta sam bata damuwa da wulak'anci da gorin da yake mata ita dai lallab'ashi take wannan dalilin ne ya kawo rashin jituwa tsakaninsu Dady yana sane amma bai tab'a damuwa ba yana matuk'ar son yaransa shiyasa yake lallab'asu yanda suke so.
Saif yana kammala sakandiri Dady ya kaishe INDIA gidan Uncle Muhammad (yayan Momy Safna acan yake aiki yayi Aure acan yana zaune Mumbai)
acan yayi Digiri har masters d'insa lokaci lokaci yana kawo masu ziyara ko suje masa.
Bety an girma anzama 'yan mata kyakkyawa ce ajin farko tana da diri da gashi dai dai gwargwadu wankan tarwad'a sak larabawan Sudan tana da kyan hali da Yakana duk da kasancewarta 'yar gidan masu hali gaba da baya ga gata da ya sata a gaba hakan baisa ta wulak'anta talakawa ba ko wad'anda suke k'ark'ashinsu
tana da tausayi da taimako ga yawan fara'a duk suffa da halin Momynta ba wanda tabari shagwab'ab'iya ce tak'ar she zan iya cewa shagwab'a ajininta taki
sab'anin Yaya Saif yana da masifar ji da kai bai d'auki talaka abakin komaiba bayan su nemi taimako a gunsa ya d'auka ya basu halin Dady sak.
lokace lokace sukan je Sudan har Aunty idan sun kwana2 su dawo Bety bata san ba Aunty ce ta haifeta ba sai bayan da ta gama sakandiri Saif ya fad'a mata tare da nuna mata hotonan Momynsu ranar kam tasha kuka da k'yar Aunty ta lallasheta
sai dai wannan baisa ta sauyawa Aunty fuska ba saima k'aunarta da takejin ta fiye da da.
tayi saukar alk'ur'ani mai girma a islamiyarsu da ke unguwar har tafara karatun littafan addini k'awarta d'aya tun furamari Zainab Alk' asim tana matuk'ar ji da zee saboda sunan Auntyn ta.
tana shekarar farko a A.B.U anan suka had'u da Meenat duk da kasancewarta d'iyar talakawa basa wulak'anta ta jininsu ya had'u sosai suna taimakunta sosai akan harkar karatun ta.
har zuwa wannan lokacin da Bety take da shekara goma sha takwas Yaya Saif baiyi aure ba anyi fad'a anyi nasiha har angaji anzuba masa ido dan acewarsa har yanzu baiga matar aure ba.
daga Dady har Yaya Saif duk basa yawan zama agida yau sune waccan k'asar gobe sune a wacan k'asar yana da kamfanuni da yawa acikin jahuhin nageria har k'asashin turai yana da gidajan mai sosai a nageria *WANNAN KENAN*
*CIGABAN LABARI*
_kuyi hak'uri da wannan banda lafiya Insha Allahu idan nasamu sauk'i zanyi maku tpyng anjima ko gobe ina baran Adu'a_
_mai k'aunar ku_
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌹🌹🌹🌹🌹
*KAR KA GUJENI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Na Aisha a yabo*🌺
Fulani🌸
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*
*GAREKI ZHARA MUHAMMAD SURBAJO MAGANAR GASKIYA BANSO NASHIGA CIKIN MAGANARKI BA DOMIN DUK WANDA YAYI NAGARI KANSA SAI DAI KIN FAD'I WATA KALMA DA BAZAN IYA SHIRU BA. KINCE YANDA AKE FAD'AN SURBAJO KO ANNABI S.A.W BA AFAD'A HAKA GASKIYA WANNAN KUSKURE NI KI GYARA FURUCINKI ANNABI S.A.W YA WUCE KO SANNAN YA WUCE KWATANCIN MAI KWATANCIN SHI SONSA DA AN BATARSA DUK BUGUN NUMFASHI NE DA GUDANYAR JINE YA WUCI MISALI DAN HAKA DAINA KWATANTA KANKI DA SHI TSAYA IYA KE DA MASU YI DAKE DA FATAN ZAKI FAHIMCE NI KI DINGA SANIN INDA FURUCINKI ZAI TSAYA.*
_Wannan shafin na sadaukar da she ga duk maccen da take samun matsala da 'ya'yan mijinta sunyi aure ma baza su barki ki huta ba sai sun wanko k'afa daga gidan mijinsu sunzo taya uwarsu kishi Ubangiji Allah ya k'ara maku hak'uri da jureya yayi maku sakayya ta alkhairi_
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
_Wannan su ne shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya baku ikon zuwa amen_
*25 to 30*
Kwanci taki tana chatin fira take acikin GRP d'in Aisha A Yabo suna calanji da Zainab KT taji sak'o ya shigo hakan yasa ta fita GRP dan ta d'auka Zee ce ba k'uwar number ta gani tana shiga ta fara karanta sak'on
" _Aslm barka da dare ma abociya kyau da sanyin hali tun ranar da na fara ganinki Zuciyata ta abka acikin k'aurki k'auna Marar misiltuwa ga d'an bawan Allah da k'ok'on baransa ki karb'e ni ba danne ba sai dan Asalin soyayya_ *ANNABI MUHAMMAD S.A.W*
_mijinki Insha Allah mai k'aunar ki A.A_"
ta mai maita sak'on ba adadi ba wai dan ba a saba turo mata sak'wanni irin wad'anan ba Aa hakanan kawai take jin wannan daban da na kowa ita dariya ma ya bata wai mijinta ba ko dad'in ji
kashi data tayi tare da ajiye wayar tayi kwanciyarta adu'an kwanciya barcci tayi ba awani jima ba sarkin b'araye yayi awun gaba da ita.
kusan sati biyu kenan kullum A.A sai ya turo mata sak'wanni na safi daban na rana daban na dare daban tun bata damuwa har tazo ta fara jin kalamansa na mata tasiri a zuciyarta
sak'wannin sa sun zamo masu d'ebi mata kewa da faranta ranta.
yau kwana ukku kenan bai turo mata sak'o ko d'aya ba ga ba d'aya bata cikin natsuwarta har Aunty ta ganu damuwarta
suna zauni da yamma Aunty tace "Bety mi ya ke damunki ya nayinki duk ya canza"?
murmushi tayi tare da kwantuwa jikin Aunty kafin tace "lah Aunty ba komai fa kawai karatu ne"
"uhm um Betyna ban yarda ba fad'amun gaskiy"
"da gaski fa nake Aunty ba abun da ke damuna"
tabar maganar ba Dan ta yarda ba dan tasan halin Bety da zurfin ciki idan zasu kwana ba zata fad'a mata ba zata bita da adu'a Allah ya yaye mata damuwarta.
yau gajiyi ta dawo makaranta wanka kawai tayi tabi lafiyar gadu dama tana hutun sallah
kid'an wayarta ce ya tashe ta barcci sai da tashiga ban d'aki tayi burush sannan tafito ta duba wayar sak'onni ne har hud'u duk na A.A duk cikin sak'onnin na k'arshin yafi sauran tsaya mata a zuciya ga abun da ke ciki
_naso najurewa nisanta kaina da k'aunarki saboda sanin nisan tazara da ke tsakanina da ke sai dai Zuciyata ta kasa juran hurun da nake mata, bazan b'oye maki ba ni d'in talaka ne marar wadata sai dai Alhamdulillah ni mai wadatar zuci ne, ina maki Soyayyar gaskiya bana kallon komai naki bayan tsantsar k'auna ki bani dama na gabatar da kaina gareki"._
kwanciya tayi rairan tare da lumshi idanunta "A.A nima zan so na ganka kariga ka saci Zuciyata da tsadaddin kalamanka sai dai lokacin had'uwarmu baiyi ba"
tajima kwanci tana tunanin A.A kafin ta tashi d'akin Aunty tanufa ta tarar tana karatun k'ur'ani zama tayi kusa da ita bayan takai aya sukayi adu'a tare
bayan Aunty ta ajiyi k'ur'ani ta dubeta fuskarta d'auki da murmushi tace "Bety na antashi barcin shigata biyu d'akinki"
"wallahi yau gajiyi nadawo shiyasa Auty yunwa nakeji me aka dafa a gidannan"?
"tuwo mukayi" ta fad'a tana linki hijab d'int b'ata fuska tayi kamar zatayi kuka tace " ni dai Aunty gaskiya kisan yanda zakiyi dani yunwa nakeji kuma bazan iya cin tuwo ba"
rik'o hannunta Aunty tayi tana dariya tace "da wasa fa nake maki jalof d'in kuskus nayi sai farfeson ragon ruwa"
ajiyar zuciya tayi kafin tace "yawwa Aunty yanzu naji zance" tabar d'akin da gudunta Aunty ta nufi kitchen.
tana gama d'ibar abinci a plet tabi Aunty kitchen tana ci suna fira da Aunty da ladidi Aunty tace
"Bety ki daina biyiwa Yayanki ke macci ce Aure zakiyi ba kisan wani irin miji zaki aure ba mai kud'i ne ko akasin haka shiyasa nake so ki kuyawa kanki cin ko wani irin cima"
"Aunty ya zanyi Allah bazan iya cin tuwo ko wani kala ne ba kuma ko baya da kud'i ai muna da Dady ga Yayana ga Auntyna ai bamu da matsala"
"uhm Bety yarinta na damunki an fad'a maki namijin kirki zai zauna iyayan matarsa na d'aukar nauyinsa garama ki sauya tunani run wuri"
ladidi tace "uwar d'akina gaskiya Aunty ke fad'a maki duk namijin da bai da zuciyar nema sai dai jiran abashi hak'ik'a ba mijin Aure bane"
cikin sanyin jiki tace "to zanyi k'ok'arin koya" daga haka bata saki cewa komaiba tabar kitchen d'in su Aunty suka cigaba da tattaunawa.
ranar asabar k'arfe ukku na yamma tayiwa Aunty Sallama tanufi Unguwar ma'azu.
bata wani jima gurin Meenat ba tace "kefa zuwa nayi ki kaini gidansu Faruk' "
cikin mamaki tace "wai dama baki manta ba"?
ta hararita cikin wasa kafin tace "ga zahiri nan kin gani ni Dan Allah tashi muje kiraka ni"
ta fad'a tana mik'ewa tsayi tare da gyara mayafinta
Meenat ta d'auko hijab tasa suna fituwa tsakar gida ta kalli Inna da take zaune cikin rumfa tana sak'ar rigunan sanyi (sana'arta kenan)
tace "Inna zan raka Bety"
"to sai kin dawo Aisha ki gaida iyayan naki"
"zasuji Inna"
suna fituwa k'ofar gida Meenat tace "ina kuka ajiye mota"?
"ni kad'ai nazo mota na ajiyeta farkon layinnan saboda ruwa sun kwanta ahanya"
suna zuwa k'ofar gidan tace "to ga gida nan ni zan koma"
"ban gani zaki koma ba na d'auka tare zamu shiga"
"kiyi hak'uri aiki zanyi kije kawai sai mun had'u makaranta" tabar gurin da sauri
Bety tabita da kallo ciki da mamaki bata wani tsaurarawa kanta tunanin dalilin k'in shigar Meenat ba ta fad'a gidan bakinta d'auki da sallama
Lawal ne zaune akan tabarma yana cin kwad'un k'anzo da zogala Al'amin na gefe yana koyawa Faruk' karatunsa na islamiya
Inna ta amsa mata sallamar cikin fara'a tace "maraba shigo Lawal da yakai loma bakinsa dai dai nan idonsa ya fad'a kanta ai kuwa ya k'ware sai tare idanunsa sun firfito sunyi jajir sabo da wahala da tsoro.
_na gode sosai da adu'anku gare ni_
_mai k'aunar ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
fulani
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌹🌹🌹🌹🌹
*KAR KA GUJENI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha a yabo*🌺
Fulani🌸
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
_Wannan su ne shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya baku ikon zuwa amen_
*30 to 35*
Inna tayi saurin mik'ewa ta d'ebu ruwa a randa ta kawu masa "sannu ga ruwa kasha ko zai lafama"
hannunsa na rawa ya karb'i ruwan yana sha cikin ikon Allah taren ya lafa masa Al'amin ya dube shi cikin tausayi yace "sannu Kaine baka cin abu a hankali cin abincin ma sai kasa garaji aciki"
shi dai Lawal komai baice ba sai kallon Bety dan iyakar gaskiyarsa tsoraci yaki
Al'amin ya kai dubansa inda Lawal ke kallo sai da Zuciyarsa ta bada dum! "me ya kawota gidansu? kenan ganinta yasa Lawal kwarewa mts Lawal akwai kayan tak'aice shegin tsoro wallahi ko wata macci albarka"
mts tsaki ya sakiyi fuskarsa tamau sam ba annuri ya cigaba da yiwa faruk' karatu
Inna tace "oh 'yar albarka yi hak'uri na barki tsayi ina zuwa bari na d'auko tabarma"
Bety da ga bad'aya jikinta yayi sanyi ganin marar tausayinan a inda bata tsammani ba duk sai taji dama bata shigo ba
Murmushin da bai kai ciki ba tayi kafin tace "lah Inna ba komai wallahi nanma yayi" ta fad'a tare da janyo kujerar tsugguni da ke ajiye gefin Inna ta zauna
cikin ladabi ta gaishe da Inna, Inna ta amsa cikin fara'a kafin tace "sai dai ban sheda fuskar ba"
"hakane gaskiya dama ranar ne nashigo unguwar nan na yarda wayana a kantin wannan ta nuna Lawal kafin tacigaba da fad'in
shine Faruk' ya kawoman gaskiya naji dad'in haka wannan yasa nayi alk'awarin idan nasaki dawowa zanzo mu gaisa"
cikin jin dad'i Inna tace "Allah sarki sannu da k'ok'ari mun gode sosai"
ta kallo Faruk' tace "Faruk' baza ka gaida Aunty ba"?
tasowa yayi cikin fara'a da ladabi yace "ina wuni Aunty"
"lafiya k'alau Faruk' ya karatu"
"Alhamdulillah" yana fad'a ya koma gurin Al'amin tashi yayi ya shige d'akinsa yana fad'in Faruk' bari sai da dare sai mucigaba"
"to Yaya"
itama mik'ewa tayi tana fad'in "Inna na tafi sai na saki shiguwa"
to "har kin tashi gashi ko sunanki baki fad'an ba"
murmushi tayi kafin tace "sunana Aisha Humaira amma amfi kirana da Bety"
"to Humaira mun gode ki gaida gida"
"zasuji" tafad' tana rik'o hannun Faruk' suna zuwa mota tabashi kayan k'walama da tasayo masa yak'i karb'a
sai da tab'ata rai kafin tace "idan nabaka abu ka daina cewa bazaka karb'a ba kaji"?
"to amma Inna za tayi fad'a"
"Aa baza tayi ba ungu maza kaje"
karb'a yayi yana godeya sai da yaga tafiyanta sannan ya shiga gida.
Bety na fita Inna ta harare Lawal cikin fad'a tace "kaima kazama irinsa ko? ina laifin wanda ya so naka sabi da Allah uhm
kai kazuba mata k'walak'walan idanunka kamar zasu zazzago k'asa amma ko uhm bakace da ita ba
shikuma ya wani d'aure fuska ya tashi ya shige d'aki yana ya tsinar fuska kamar yaga kashi"
Lawal da ya kasa natsuwa da maganar Bety gani yake kamar da wata manufa a alak'arta da Faruk'
ganin fad'an Inna bazai k'are ba cikin kwantar da kai yaci
"Inna kiyi hak'uri ni wallahi duk a tsoraci naki itace fa yarinyar da nake fad'a maki Al'amin ya mara ranar da zamuje gidan kawu salmanu daganinta 'yar masu kud'i ce ina tsoron karta ce d'aukar fansa za tayi ta hanyar Faruk' "
Al'amin da fitowarsa kenan yace "waye ya fad'ama kawai tunaninka ne haka amma ba wani d'aukan fansa"
cikin harara Lawal yace "itace ta fad'ama hakan"?
"bata fad'an ba amma kasan abun da na karanta ko"?
Inna za tayi magana yayi saurin zaunawa kusa da ita ya rik'o hannunta cikin lallashi yace "Dan Allah Inna kiyi hak'uri Allah tun ranar da abun ya faru nayi nadama yanzun ma kunyar abun da na mata ne yasa na shige d'aki batare da na mata magana na"
cikin fushi tace "ba zan yarda kayi nadama ba har sai ka bata hak'uri"
"Inna idan dai hak'uri ne na maki alk'awarin duk inda na ganta zan bata hak'uri ni dai karkiyi fushi dani"
"shikenan Allah yayi maku Albarka"
"amin Inna nagode" Faruk' na shiguwa da Maya Inna ta hau fad'an me ya karb'a shi dai hak'uri ya shiga bata shima Yaya Al'amin yayi masa fad'an kar ya koma karb'an duk abun da ta bashi ko wani ya bashi".
tun bata tura masa amsa har tazo ta fara tura masa sak'o sukanyi waya lokaci lokaci cikin k'ank'nin lokaci sukayi shak'uwa ta ban mamaki sai dai har zuwa wannan lokacin basu tab'a had'uwa ba.
yau ma kwanci taki kan kujera suna waya "Aishana me yasa duk lokacin da zan maki maganar ga batar da kaina gidanku kike k'i?"
cikin shagwab'ab'iyar muryarta tace "nifa bak'i nayi ba"
"to naji ko baza su bawa talaka aurenki ba"?
"haba sam ba haka bane"
ajiyar Zuciya yayi kafin yace "Aishana ina so ki bani dama na gabatar da kaina gidanku amma kafinnan ya kamata kisanni kisan waye ni"
shiru tayi tana nazari kafin tace "shikenan ba damuwa duk sanda ka tashi zuwa ina maraba"
cikin farin ciki yace "yawwa Aishana gobe da yamma zan zo sai dai ina tsoron kiganni mummuna ki *GUJE NI*"
"kenan baka yarda da son da nakema aganina soyayyar gaskiya ba ta duban komai kyau kud'i ko wani muk'ami,
soyayyar da nakema ta wuci na *GUJE KA*aduk yanda kaki ina Sonka *KARKA GUJE NI* Duk rintsi"
"Aishana na yarda da k'aunarki gareni ina Sonki burina ki kasance matata uwar 'ya'yana ke d'in rayuwata ce bazan iya guje maki ba duk rintsi"
sun jima suna waya cikin nuna tsantsar k'auna wa junansu suna gama waya taji an fara kiran sallah azahar alwala taje tayi bayan ta idar da sallah ta saki shiryawa ta nufi gidansu Faruk' bayan ta fad'awa Aunty.
zuwa yanzu sunyi sabo sosai da Inna tana jinta har cikin ranta jinta take tamkar Momynta.
haka Inna tana Son Bety tun zuwanta na biyu ta bata hak'uri kan abun da Al'amin ya mata ta nunawa Inna ba komai ya riga ya wuce.
sai dai duk zuwan da take basa had'uwa da Al'amin sai dai wani lokacin ta kanga Lawal a cikin kantinsa ko gidan Inna su gaisa.
tana zuwa ta tarar Inna nawa wata kitso zama tayi kusa da Inna tana fad'in
"lah Inna Ashe kin iya kitso"?
murmushi Inna tayi kafin tace "na iya Humaira yanzu like tafe"?
"eh wallahi Inna nayi kewarki kwana2 makaranta ta hanani zuwa na ganki ina Faruk' d'ina"?
cikin kulawa tace "nima kullum sai nata jajin rashin ganinki Faruk' yaje gidan Abbansa sai jibi zai dawo"
duk sai taji ba dad'i matar da akewa kitso tace "Inna ina kika samu 'ya kyakyawa haka"?
dariya Inna tayi kafin tace 'yata ce"
"gaskiya inawa k'anena kaminta"
"babbar magana to gaki gata idan zata so shi"
Inna ta fad'a tana dariya "diyar Inna ki so shi ai ko shima kyakyawa ne kamarki"
"Uhm" kawai tace tabar gurin d'akin tai shigewarta ta kwanta kan gadon Inna mai rumfa da ke matuk'ar burgeta ga d'akin a tsabtaci.
_mai k'aunar ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌹🌹🌹🌹🌹
*KAR KA GUJENI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha a yabo*🌺
Fulani🌸
® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
_Wannan su ne shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya baku ikon zuwa amen_
*INA MATUK'AR GODEYA DA JIN DAD'IN ADU'AN KU GARENI FNS ALHMDLH NA SAMU SAUKI NAGODE ALLAH YA BAR K'AUNA*
*35 to 40*
Sun jima suna fira bayan tafiyar wacce akaiwa kitso sai k'arfe biyar na yamma tayiwa Inna sallama.
daga gidan Inna Supermarket ta wuce dalema ake malali dan canne gurin sayayyarta
bayan ta fito an samata kayanta a bayan mota har zata shiga mota wata mata tana bara
matar ba zata haura shekar 30 ba tazo da yara d'ayan a goye d'aya a hannunta
Bety ta kalleta cikin tausiyi tace "ke kuwa baiwar Allah me yasa da sauran k'arfin ki da k'urciyarki zaki na yawon bara ga yara k'anana"?
cikin karyar da kai ta fara magana kamar za tayi kuka tace "hajiya nima ba a son raina nake baran nan ba
ni d'in na tasu marainiya ba uwa ba uba ina gun k'anin babana na tashi cikin wahala da k'unci ga talauce ga tsangwama matar kawuna da yaranta
a haka dai Allah ya kawo man mijin aure bayan aurenmu muna son junanmu matsalar talauce a haka dai muke rayuwa cikin rashi da rashin taimakon dangi
kwatsam k'addara tasame mu Allah yayiwa mijina rasuwa sanadin ciwon ciki na dare d'aya ya barni da yara goma wad'annan 'yan biyun tun suna wata takwas Babansu ya rasu rashin mataimaki ya sani shiga sana'ar bara"
ta k'arasa maganar cikin kuka Bety ma hawaye ne suke zarya a fuskarta
shiga motar tayi cikin tsananin tausayi baiwar Allah tace "shiga mota na kaiki gida"
cikin d'an firgi ce matar tace "anya hjy ayi haka"?
"karki damu ki shigo ba zan cuta maki ba Allah yaga zuciyata taimakonki nake so nayi"
haka matar ta kwatanta mata gidanta da yake ba wani nisa da gurin,
ganin yanayin gidan kad'ai zai tabbatar ma da masu gidan suna cikin k'agin talauci,
kud'i masu yawa ta d'auko cikin jakka "ga wannan ki rik'i kafin gobe Insha Allahu zan dawo"
matar ta karb'a cikin rawar jiki sai godiya taketa zubawa kamar harda 'yar kwalla,
ita dai Bety bata tsaya jin godiyar ba tai shigewarta mota tare da yiwa motar key tabar unguwar ciki da tausayin matar.
sanda ta shiga ta nunawa yaranta Alkhairin da suka samu sunata murna da shewa Bety Albarka ko da babbar 'yarta Nafisa 'yar shekara 13 ta k'irga kud'in dubu hamsin ne nan fa murna ta karu kowa sai fad'an abun da za asaya mai yake.
sai da tayi wanka sannan ta shiga d'akin Aunty itama fituwarta kenan daga gurin wanka
zama tayi kan gado tana fad'in "wash Aunty na gaji wallahi"
"da ki kayi me"? tayi mata tambayar tana saka rigar barci
"Uhm Aunty ko driving ai aiki ne"
ta harareta cikin wasa tace "gun raggaye ba kuma ai ke kika sa kanki tunda da drvnki kikace ke zakiyi"
cikin turo baki irin na shagwaba tace "nifa Aunty ba komai kesa nace ni zanyi drvn ba zugar isct d'innan ke ban haushi wallahi"
Auty ta zauna kusa da ita tana fad'in to Bety ya zakiyi kin dai San halin yayanki duk randa ya ganu bayan makaranta kina zuwa wani gun ban san yanda zamu kwashe ba musamman ne tawa sai tafi zafi kin sani"
cikin sanyi tace "ayya Aunty kiyi hak'uri ba fa wani gurin nake zuwa ba"
"to naji ina kike zuwa kwana biyun nan? gashi yau kinyi dare abun da baki sabayi ba
ina tsoron idan Betyna ba wasu k'awayen kika samu ba suke son sauya halinki ba"
d'ura kanta tayi akan kafad'ar Aunty cikin murmushi tace
"wayyo Auntyna Betynki nan yanda kika santa tarbiyar da kika d'aurani akai ba abun da ya sauya
dama shigowar nan da nayi na fad'amaki sai gashi kin mun magana"
anan tabata labarin had'uwarsu da su Inna har abun da ya faru yau ta k'ara da cewa
"Aunty ina son na taimaki su Inna Amma komai na basu basa karb'a sai dai tace dani k'aunar da nake masu ta wadatar dasu
ina so nasa Faruk makaranta saboda zuwan da nake na fahimci baya zuwa boko ina so *Salfanamoh college* dake Unguwarnan
Amma ban san ta yanda zan tunkari Inna ba ina tsoron karta ce Aa"
ta k'arasa maganar kamar zatayi kuka
Aunty ta rungume ta cikin farin ciki tace "Betyna 'yar Albarka ba inda kika bar Momy gurin kyan hali wannan yasa nake alfahari dake"
nan take ta bata shawarar yanda za ta taimake su Inna ba tare da samun wata matsala ba
tabar d'akin cike da jin dad'in shawarar Aunty.
washe gari da yamma Babbar mota ce cike da kayan masurufi tayi parking daidai kantin Lawal
driver ne tare da macci d'aya suka fito motar kai tsayi kantin suka nufa kamar yanda Bety ta umurce su
Lawal kad'ai suka tarar Sallama sukai masa bayan sun gaisa drvn yace
"sunana Muhusin wannan da muke tare sunanta hajara mun zo k'ark'ashin gwamnati ne muna bin unguwanni muna raba kayan abinci da abun da ya sawwak'a
har dai yau Allah ya kawomu wannan Unguwar ko zaka taimaka kayi mana jagora gurin rarraba kayan"?
cikin fara'a yace haba me kuwa zai hana sannunku da zuwa"
cikin taimakon Lawal suka dinga rarraba buhun shinkafa da carton d'in taliya da man gyad'a da manja da dubu goma wajan gida goma sha biyar suka samu har gidansu Meenat
duk gidan da aka sallama idan mai gidan bayanan sai hajara ta shiga tabawa matar gida
Muhusin yace "Abokina baka nunan gidan naku ba"
ya fad'a yana murmushi shima Lawal murmushi yayi kafin yace Ayya gidan namu yana da d'an nisa da nan amma ga gidansu
Aminina nan kusa da dama yanzu nake shirin magana"
"OK ba damuwa suka ciri buhun shinkafa biyu taliya carton biyu mai ma biyu biyu da ✉ dubu hamsin ne aciki
yace "ga naka" ya karb'a yanata godiya gidansu Al'amin komai hud'u hud'u tare da dubu d'ari hud'u wai zo kuga murna Addu'a kam da albarka sun shata agun Inna da mutan Unguwa.
Bety da kanta taje gidansu baiwar Allah ta kaimata kayan abinci da kud'i masu yawa har kuka sai da tayi tana shimata albarka da kyawawan addu'oi.
haka ta koma gida cike da farin cikin sauke nauyin da take ganin ya hau kanta.
cikin mayar da zancen kiran Dady ya shigo wayarta cikin murna ta d'aga kiran
"DADY I MISS YOU yaushe zaka dawo Yaya ma ya tafi yayi zamansa"
ta k'arasa maganar kamar za tayi kuka
murmushi Dady yayi kafin yace "nima ina k'ewar ki sosai cikin satinnan Insha Allah zan dawo kuna dai lafiya ko"?
"lafiya K'alau Daddy idan kadawo akwai labari mai dad'i da zan baka"
"Uhm Betyna fad'amun yanzu harna k'agara naji"
cikin shagwab'a tace "Aa Dady sai kadawu zan fad'ama kaji Dadyna"
sun jima suna fira kafin yace "Bety naga kinciri kud'i masu yawa
mi kikayi da kud'i da yawa haka"?
"Ayya Dady kayi hak'uri inaso na fad'ama mantawa nayi" nan tayi masa bayanin abun da tayi dasu sai dai bata nuna masa tana zuwa gunsu Inna ba,
"kin kyauta Allah yayi maki Albarka amma dai ki kularmun da kanki bana son kina huld'a dasu tsakaninki da talaka taimako"
"to Dady" ta fad'a cikin sanyin jiki sun d'an tab'a fira kafin daga bisani sukayi sallama.
Al'amin dawowar sa kenan daga gurin sana'arsa ya ga kayayyaki a k:ofar Inna
ya k'arasa d'akin Inna bakinsa d'auki da tambayoyi Faruk kawai ya tarar yana shan fura
"Faruk ina Inna"?
"Yaya sannu da zuwa Inna tashiga ban d'aki"
"OK kayi Alwala kafin na fito wanka muwuce masallaci"
da ganan yawuce d'akinsa.
a hanyarsu ta dawowa daga masallaci Lawal yake baiwa Al'amin labarin alkhairin da suka samu yau
Al'amin ya dubi Lawal cikin mamaki yace "yanzu kai me ka fahimta?
kyautarka tafi ta sauran mutan Unguwa tamu ta shafi ta kowa kai dole akwai ayar tambaya acikin al'amarinnan" ???
"mtsw kaifa wallahi kana da matsala to miye aciki kowa rabonsa yake ci kawai malam kaciri komai aranka Allah ne ya kawo mana d'auki dan haka mugode masa mu kuma godewa wanda yayi mana wannan taimakon"
"Uhm shikenan tunda kace hakan" da ganan sukayi salama Lawal ya wuce gida Shima ya shige gida.
Yana cin abinci suna mayar da zancin da Inna "Al'amin nace tunda Allah yasa ansamu kud'i me zai hana asa Faruk makaranta"?
"Inna maganar makarantar Faruk tana raina dama k'udirina idan nayi kwasar adashe na zan saka shi kuma wannan satin Insaha Allahu zan karb'a"
"duk da hakan tunda Allah yasa ansamu asashi d'in idan ka karb'o adashen sai ka had'a da wad'annan kayi jarin kanka"
cikin sauri yace "amma Inn... saurin katsi shi tayi ta hanyar d'aga masa hannu bana son musu kayi yanda nace"
numfasawa kafin yace to Inna Allah ya saka da alkhairi" da ganan ya wanki hannunsa da bakinsa yasha ruwa sannan yace "Inna zan d'an fita amma ba jimawa zanyi ba"
"Allah ya tsari"
"amin Inna".
Bety tariga ta gama shirin tarba bak'onta tun sanda ya kirata ta masa kwatancin gidansu
tana son ta fad'awa Aunty sai dai tana jin kunya
tana cikin tunanin yakira yana fad'amata ya k'arasu Bintu ta Kira tace ta shigo dashi d'akin bak'i
bayan fitar Bintu tasa hijab tanufi d'akin Aunty cikin jin kunya taiwa Aunty bayani
Aunty tayi shiru tana kallon Bety kafin daga bisani tayi Murmushi tace "Betyna kice na fara shiri nayi suruki"
Bety tabar d'akin da gudu tana dariya.
sanda ta k'arasa d'akin yana zaune kan d'aya daga cikin kujerun da aka k'awata parlour'n yana latsi latsin waya
sallamarta ne yasa ya d'ago fuskarsa ciki da annuri
sanda idanunta suka sauka kan fuskarsa ba k'aramin firgita tayi ba
nunasa tayi tana fad'in "d..d..a..m..a..n k...kk.aini"?
tana fad'i tare da juyawa zata bar palour'n saurin shan gabanta yayi tare da durk'usawa kan guiwowinsa ya had'i hannayen sa guri d'aya
ya fara magana cikin marairaice wa "Aisha na zan iya juran dukkan hukuncin da zakimun ciki kuwa harda rama abun da namaki
Amma Dan Allah Dan darajar Annabi S.A.W Aisha na *KAR KI GUJENI*"
ya k'arasa maganar kamar zaiyi kuka.
*TURK'ASHI! MASU KARATU KU BIYUNI DAN JIN YANDA ZATA KAYA TSAKANINSU SHIN WAYE WANNAN A.A? ZATA HAK'URA KOKUWA?*
_MAI K'AUNAR KU_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸 Fulani🌸🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌹🌹🌹🌹🌹
*KAR KA GUJENI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha a yabo*🌺
Fulani🌸
® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
_Wannan su ne shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya baku ikon zuwa amen_
*INA MATUK'AR GODEYA DA JIN DAD'IN ADU'AN KU GARENI FNS ALHMDLH NA SAMU SAUKI NAGODE ALLAH YA BAR K'AUNA*
*40 to 50*
Zaunawa tayi gabansa cikin d'aure fuska tace "sai fa na rama marin da akamun ihin" ta fad'a tana turo baki
cikin sauri yace "eh na yarda idan har ramawar zaisa ki hak'ura bisimillah"
kawar da kanta gefi tayi tana murmushi kafin tace "ya zanyi dole na hak'ura domin hannuna bazai iya kaiwa ga fuskarka ba da niyar mari"
cikin farin ciki yace Aishana da gaski kin hak'ura ba zaki *gujeni ba*?"
girgiza kanta tayi tana dariya k'asa k'asa ajiyar zuciya yayi tare da yin dariya marar sauti
"Aishana da kin gujeni wallahi da ban san ya zanyi da rayuwata ba ke d'in wani b'angarice ga rayuwata
Sonki yayiwa Zuciyata mamaya lungu da sak'o na Zuciyata zallar k'aunarki ne ke yawo ajinin jikina
Aishana zaki Aure talaka mai sana'ar kafinta"?
k'asa tayi da kanta ji tayi gabaki d'aya kwarjinsa ya cika palon wata irin kunyarsa takeji wannan yasa takasa cewa dashi komai
ya marairaici fuska kafin yace "Dan Allah kice wani abu tun kan na zautu Aishana"
"Ina sonka fiyi da tunanin mai tunani bazan iya rayuwa ba farin cikina ba Al'amin ka kasance farin cikina kaid'in rayuwata ne duk rintsi *KAR KA GUJENI*Al'amin"
kallonta yake cikin tsananin shauk'i kalamanta sun faranta ransa
cikin jin kunya tace "ka zauna a k'asa"
"barni anan d'in zaman yamun dad'i"
cikin shagwab'a tace "Uhm um ni dai ban yarda ba muje ga kujera ka zauna kaji"
ta k'arasa maganar kamar zatayi kuka cikin sauri yace "Aa basai kinmun kuka ba muje"
bayan ya zauna ta zuba masa kunun aya a kup ta bashi cikin ladabi ya karb'a yana murmushi
zata zubo masa abinci yace "Aa Alhamdulillah wannan ya ishini nagode"
ta shagwab'i fuska zatayi magana yayi saurin taran hanzarinta "kimun uzuri Aishana sai da naci abinci kafin nazo nan"
"to me yasa zakaci bayan kasan zaka zo nan ni dai karka koma"
"shikenan Aishana bazan koma ba kin hak'ura"?
yayi maganar yana mai zubamata idanunsa cikin salon kallonsa dake k'ara mata sonsa
"Uhm ai bana fushi da kai yasu Inna da Faruk da Lawal"
"dukansu suna lafiya"
sunjima suna fira har goma tayi basu kula ba haka masoyan suka rabu ba son ransu ba.
ad'an k'ank'anin lokaci masoyan sukayi wata irin shak'uwa dukansu burinsu su kasance a inuwa d'aya.
tana makaranta Dady ya dawo sai d'uki take ta koma gida harsu Meenat na mata tsiya
suna fitowa Zee ta shiga motarta tana Bety tace "KD zakiyi hutun k'arshan maku kenan"?
"eh kin San na fad'amaku zamuyi bikin Sister d'ina kano gobe da safi zamu tafi"
"oh na manta agaida momy"
"tab Allah nima ba zaku barni ba bari na d'auko kayana mutafi" cewar Meenat
Zee tace "kinga Ku tafi tare da Beety kunfi kusa sauri naki"
daganan sukayi sallama da Zee tawuce.
a hanya Beety take tunanin yanda zatayi "ba zata iya cewa da Meenat d'ai daga cikin Driver ya kaita gida ba
hakanan tana jin nauyin su had'u da Al'amin ko wani nashi musamman yanzu kullum Al'amin sai yamata k'urrafin tadaina zuwa gurin Inna
Inna sai jajan rashin ganinta take itakam kunya takeji ba zata iya zuwa ba"
sanda suka isa Unguwar Sun tarar da samari k'ofar kantin Lawal sunata cafta Al'amun na daga gefi yana latsi latsin waya
3kwata ne jikinsa bulu sai teshat fara mai k'aramin hannu gashin kansa da yake a nad'aid'ayi sai shik'i yake
ya mata kyau sosai mts! tsakin da tajini ya sata saurin jiyuwa tana kallon Meenat da mamaki
"ke kuma ke dawa"? cikin nuna takaicin abun da zata fad'a tace "acikin samarin can kin kula da wani
wanda yayi shigar 'yan iska mai 3kwata da farar teshat"?
cikin tsananin bugun Zuciya tace "eh amma miye daga ganin mutum zakice dashi d'an iska"?
cikin yatsinar fuska tace "saboda na tsaneshi iyayanmu maza aminan junani sunyi alwashin had'amu Aure
wai dan yana d'an rainin hankali d'an iska aranar da ya fara zuwa gurina bud'an bakinsa wai shifa ba sona yake ba kawai zaiwa mahaifinsa biyayya
dan nid'in Sam ba kalar maccin da yake so bace"
ta k'arasa maganar tana k'wafa
cikin k'ok'arin b'oye tashin hankalin da take ciki tace "to ke kina Sonsa kenan"?
"wa! hud'ijjam kema dai kamar bakisan wacece Meenat ba aini talaka komai kyansa baya cikin tsarina
shiyasa anan taki na mayar masa da raddi nace dashi daina ganin kyanka zai rud'ani kud'i sune kyau agurina tsana kuma wacce nakema ta zarta wacce kakemun Dan haka Umma ta gaida Aysha
in tak'aice maki labari na haukace masu bana so Abbana ya dage dole sai anyi ganin nak'i na kwantar da hankali yasa babansa yace
tunda bana so a hak'ura kar azo ayi matsaluli su kunnu kai da k'yar Abban ya yarda aka fasa"
"gaskiya Meenat bakya kyutawa miye aibun talaka idan dai yana da kyan hali Meenat dugon burinki yayi yawa ki dinga sassautawa rayuwarki"
dariya Meenat tayi kafin tace "Bety ba zaki gani illa da ciyon da ke k'unshi acikin talauci ba
saboda kin tasu cikin arzik'i gaba da baya dan haka duk abunda zance ba zaki gane ba"
"uhm ba wani nan kawai ki sauya tunani Meenat"
"um kinga bara na wuce dan ko zamu shekara ina maki bayani ba zaki gane ba"
ta fad'a tare da bud'i k'ofar motar da dama sunjima da yin pakeng bayan ta fitone take cewa "ba zaki Shigaba"?
"Aa sai dai wani lokacin ki gaida su Umma"
"tom zasuji sai nazo karb'an tsaraban Dady"
cikin Murmushi Meenat tace "muna maraba daganan sukayi sallama.
ko da suka zo wycewa su Lawal ne kawai Al'amin baya gurin.
tana shiga gida suka had'u da Aunty Palo hannunta rik'i da plet anyanka kayan furut
ta rungume Aunty ta baya cikin murna tace "Aunty ina Dadyna"?
cikin dariya Aunty tace "oh Bety tunda Dady ya dawo shikenan ko gaisuwa ba zamu samu ba"?
dawowa tayi gabanta tarik'i kunni cikin marairaicewa tace "yi hak'uri Auntyna ai ban isa ba na k'usa naga Dadyna"
"yana d'akinsa da gudu tabar gurin ta haura Sama
a hankali ta bud'i k'ofa tsayi ta tarar dashi yana waya yaba k'ofa baya
da sauri taje ta rungumeshi tana "Oyo yo Dady" cikin sauri ya katsi kiran
ya jiyu da ita gabansa cikin farin cikin ganin 'yar tasa yace "Betyna haka kika k'ara girma da kyau wai me Auntynki ke baki kike k'ara hawa kamar farashin mai"?
turo baki tayi cikin shagwab'a tace "Dady nifa har rama nayi saboda kewarku"
"kai 'yar gidan Dady anya kuwa"?
"Allah Dady"
ta fad'a dai dai sanda suka zauna bakin gado
Dady yace ya makaranta kina dai maida hankali ko"
"eh Dady"
"to karatunki na arabikfa"?
"inayi Yasayyadi kwana2 baizo ba Babansa aka kwantar asibiti amma ina betan karatun"
"ayya Allah ya bashi lafiya"
"amin Dady ina tsarabana"
hancinta yaja yana fad'in bakinki baya mantawa da tsaraba
na sayo amma sai anbani labarin da akamun alk'awari"
dariya tayi kafin tace "Dady zan fad'ama amma ba yanzu ba"
"shikenan nima tsarabar ba yanzu ba"
janyi jikinta tayi ta koma gefe tana bubbuga k'afa ta fara "Aa Dady ni ni yanzu za aban"
janyota yayi jikinsa cikin lallashi yace "shikenan yi shiru zan baki amma dai ki tuna girman Alk'awari"
murmushi tayi cikin jin kunya tace "zan fad'ama Dady amma sai ka rufi idonka"
"tom na yarda" ya rufe Idanunsa yana murmushi
taje dai dai kunninsa ta rad'a masa "Dady dama zan fad'ama kayi suruki" tana gama fad'a tabar d'akin da gudu
da sauri Dady ya bud'i idonsa Wanda tuni murmushin da ke fuskarsa ya b'ace
wayarsa ya d'auka ya kira Aunty ba ad'auki dogon lokaci tashigo d'akin
ko gaisuwarta bai tsaya amsawa ba yace "da saninki Humaira ta fara Soyayya"?
cikin sanyin jiki tace "Aa sai dai ranar da ya fara zuwa nima nasani"
cikin b'acin rai yace "wato itace amanar da nabar maki ko?
to wallahi ki gaggauta walwali wannan al'amarin tun kan rayuka su b'ace kin San alk'awarin da aka k'wulla tun shekarun baya ke baki isa kisa na warwareshi ba"
zatayi magana yayi saurin katseta ta hanyar d'aga mata hannu cikin tsawa yace b'acemun da gani bana buk'atar jin komai daga gareki lallai kiyi abun da nace"!
cikin sauri tabar d'akin tana Shari hawaye.
wayar Yaya Saif yakira bai jira ya gama gaisuwar da yake ba yace "duk abun da kake Saifullah kabarshi ina so gobe na ganka Nageria"
ya katsi kiran ba tare da ya saurari tambayar da Yaya Saif ke jihu masa ba.
_mai k'aunar Ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌹🌹🌹🌹🌹
*KAR KA GUJENI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha a yabo*🌺
Fulani🌸
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
_Wannan su ne shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya baku ikon zuwa amen_
*HAR ABADA KEWARKI BAZATA TAB'A GUSHEWA BA IDANUNA BA ZASU DAINA ZUBAR HAWAYEN RASHINKI BAZAI TAB'A ZAMA SABO GAREMU BA UWA MA BADA MAMA UWAR KUWA hjy ZAHRA A. YABO ALLAH UBANGIJI YAJIK'ANKI DA RAHAMA YA HASKAKA K'ABARINKI DA DUKKAN NI'IMUMI ALLAH UBANGIJI YA DAWWAMAR DAKE A FADAR ANNABI MUHAMMAD S.A.W*
*50 to 60*
Bety tana zuwa d'aki wanka tayi tana cikin shiri wayarta ta fara ringing
tana dubawa taga Al'amin cikin farin ciki ta d'aga kiran tare da yimasa sallama cikin 'yar siririyar muryarta
bayan sun gaisa yace "Aishana kin kyauta kin shigo unguwarmu inata murna zanga sanyin idaniyana koda naje gida bake ba 'yan rakiyanki"
rik'e baki tayi tana murmushi tace "lah Yayana wa ya fad'ama nazo"?
"au kin d'auka bazan gane motanku ba"?
"oh kayi hak'uri Allah inajin kunyar Inna kuma k'awata na kawo inata sauri nazo naga Dady kasan na fad'ama ya dawo yau da safe"
"sun dawo lafiya"?
"lafiya k'alau kasan miye harfa na fad'a masa maganarka"
"da gaske Aishana"?
"Allah Yayana na fad'amasa"
cikin farin ciki yace "gaskiya Aishana naji dad'i gobe Insha Allahu zanzo na gaida Dady"
"tom Allah ya nuna mana" haka masoyan suka cigaba da firarsu sun jima kafin nan sukayi sallama.
Tana shan Ice craem Aunty ta shigo d'akin yanayin da taga Aunty ta firgita cikin sauri tace "Aunty me ya sameki afuska naga tayi kumburi idanunki sunyi ja kamar kinyi kuka"?
zama tayi kusa da Bety kafin tace "na d'an bugi fuskana ne a k'ofa Bety inaso ki bani hankalinki nan muyi magana"
ta fad'a cikin tsurawa Bety ido cikin sanyin jiki da fad'uwar gaba tace "to Aunty"
"Bety kin sani mahaifinki na tsananin Sonki haka ya nuna maki gata fiyi da tunani mai tunanin tun tashinki baki tab'a neman abu kin rasa ba
da zarar kin nuna kina son abu ko baki furta ba da hanzari zai maki duk abun da zai b'ata maki rai yana gudunsa
burinsa ko yaushe ya ganki cikin farin ciki shin Aisha da akwai abun da zai nema a gunki ki k'iyi masa"?
zuwa lokacin Bety jikinta duk yayi sanyi bugun zuciyarta sai k'aruwa yake tanaji kamar wani abu marar dad'i ke shirin faruwa da ita,
sai da Aunty ta sake maimaita mata tambayar cikin sanyin murya tace "Aa Aunty babu"
ta bata amsar a tak'aici
ajiyar zuciya Aunty tayi kafin tace "Aisha tun kina da shekara bakwai mahaifinki da amininsa Alhaji ma'azu sunyi alk'awarin had'aku Aure da d'ansa fa'iz wanda yanzu haka yana singapor a can yayi karatunsa yake kuma aiki babban likitan zuciya ne
anasa ran dawowarsa jibi kuma dama shi akejira ya dawo ayi bikin ku
ina rok'onki da kiyi hak'uri ki cire Al'amin a zuciyarki kiyiwa mahaifinki biyayya ki amince da zab'insa"
ta k'arasa maganar tana mai kallon wani gefen
ban san taya zan kwatanta iya tashin hankalin da Bety ta tsinci kanta ba
cikin muryar kuka tace "amma Aunty me yasa baku fad'an da wuri ba? har sai da zuciyata tafara son wani sannan za azo man da zancin wani anmun adalci kenan?"
Aunty ta dafa kafad'anta cikin tsananin tausayinta tace kiyi hak'uri Dadynki ne ya hana afad'a maki ya kuma hana Fa'iz zuwa saboda baya son ki had'a karatunki da soyayya"
"uhm tom Aunty zanyi yanda kuke so"
daga haka bata sake cewa komai ba tayi kwanciyarta taba Aunty baya
ganin tayita magana Betyn tak'i tace da ita komai yasa tabar d'akin cikin tsananin tausayin Bety.
ranar kam Bety duk nacin barcci hak'ura yayi yabarta tunaninta "me zata fad'awa Al'amin ya zai d'auketa marar cika Alk'awari mak'aryaciya??
ya zata rayu da wanin Al'amin? ya Allah gani gareka ya Allah ka kawo man mafita Alfarmar Annabi S.A.W"
ganin kukan bazai fisheta ba yasa taje ta d'auro Alwala ta fuskanci gabas tana fad'awa mai kowa mai kukanta.
washe gari sai sha biyun rana ta farko saboda rashin barccin da bata samu tayi ba sai da tayi wanka ta shirya cikin Pakistan duk da batayi kwalliya ba hakan bai hana kyanta fitowa ba,
wayarta ta d'auko bayan ta kwanta kiran Al'amin ta tarar ba adadi sai sak'on da ya turo nmata
_Slm Aishana da_ _fatan kin tashi lafiya_
_Aishana ina kika_ _shiga inata kiran_ _wayarki bakya_ _d'agawa?_
_Aishana ban san_ _meyasa ba tun jiya_ _naketa jin fad'uwan_ _gaba har zuwa yau_ _d'innan sai k'aruwa yake_
_ina cikin damuwa sosai Dan girman_ Allah da ma'aiki S.A.W ki d'aga kirana _ko zanji sanyi a raina_"
_mijinki Insha Allahu_
tana gama karantawa ta cusa kanta cikin filo tana kuka fad'e take "Yayana kayi hak'uri ban gujeka dan ina k'inka ba sai dan ba yanda zanyi"
tana haka Aunty tashigo cikin sauri ta k'arasa gurinta tallabota tayi jikinta tace "Bety kukanne har yanzu
Dan Allah kiyi hak'uri ki daina sawa kanki damuwa adu'a itace abunda yafi ya kuma kamata awannan lokacin ba wai kuka ko damuwa ba "
da lallashi da ban baki akasamu tayi shiru ta d'anci abinci kad'an suna haka Yaya Saif ya shigo d'akin
Aunty ta gaishe shi ya amsa ba yabo ba fallasa fita tayi d'akin
Yaya Saif ya zauna bakin gado ta fad'a jikinsa tana kuka bayanta ya dinga shafa cikin sigar lallashi yace
"fad'amun damuwarki k'anwata idan bakya Son Fa'iz fad'amun baki da wanda yafi ne duk duniyarnan nima banda wacci tafeki
matuk'ar bakya Sonsa ba zaki Aureshi ba bazan bari farin cikinki ya sub'uce saboda wani ba"
cikin kukan farin cikin samun mafita tace "Yaya nifa bana Sonsa ban tab'a ganinsa ba ban san ya kalarsa yaki ba kawai ace shi zan aure
kumani koma nasan sa banayi inada wanda nake So idan narasa shi shi komai zai iya faruwa dani"
cikin damuwa yace fad'amun waye shi wanda kike so k'anwata zanyi iyakar k'ok'arina wajan ganin Dady ya amince da zab'inki"
sake rungumeshi tayi cikin farin ciki tayi masa bayanin Al'amin ai bata k'arasa ba ya tureta jikinsa
cikin b'acin rai yace Aisha ashe baki da hankali saboda talaka fak'iri kike k'in zab'in Dady to wallahi bara kiji ko kinso ko kink'i sai kin aure Fa'iz wawuyar banza kawai"
sosai ya shiga yimata fad'a kamar zai daketa
shigowar Dadyni yasa shi yin shiru
Dady yace "Saifullah miye haka? kaida na turo ka lallasheta sai ka hau yimata fad'a"
cikin huci yace "Dady waifa Wanda take so kafinta ne fak'iri"
maganar ta daki Dady haka ya daure yace "shikenan naji jeka"
bayan fitar Yaya Saif Dady yaje gurin da take tanata kuka ya janyota jikinsa
cikin lallashi yace "kukan ya isa haka Betyna idan bakya Sonsa bazan maki dole ba gara naji kunya gun Abokina da nadinga ganinki cikin damuwa"
tausayin mahaifinta taji "tun tashinta burinsa ya ganta cikin farin ciki me zai hana itama ta faranta ransa
Al'amin ina sonka Kaine farin cikina sai dai bazan bari sonka ya rufen ido ba na kasa yiwa mahaifina biyayyyaba
d'agowa tayi cikin murmushin k'arfin hali tace "Dadyna na amince zan aure Fa'iz"
"Aa Bety bar maganarsa na janye Burina na ganki cikin farin ciki"
dariya tayi kafin tace Dady da gaske nake zab'inka shine farin cikina"
"kin tabbata" ya fad'a cikin jin dad'i
"eh Dady na amince"
"Allah yayi maki Albarka Betyna" haka yabar d'akin cikin farin ciki.
_mai k'auna r ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸Fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌹🌹🌹🌹🌹
*KAR KA GUJENI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha a yabo*🌺
Fulani🌸
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
_Wannan su ne shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya baku ikon zuwa amen_
_na sadaukar da wannan shafin kacukan ga 'YAN Uwana jinin jikina A Yabo Famili_
_Ina Alfahari daku 'YAN REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS Acigaba da gashi suya sai........
UP
UP
UP
*60 to 70*
Al'amin wunin ranar tamkar marar lafiya ya zama ko agurin sana'arsa bai iya aikin komaiba sai alfarma ya rok'a agun Uban gidansa
zaije gida kansa na masa ciyo bai hana shi ba saima adu'a Allah ya bashi lafiya da ya rakashi da ita.
yana zuwa gida wanka yayi yasa k'ananan kaya bayan ya gama shiryawa ya saki d'auko wayarsa a aljihun wandon da ya ciri numberta ya kira akashe
kwanciya yayi akan 'yar katefarsa ya rufe fuskarsa da tafukan hannunsa
"ya salam Aishana Allah yasa lafiya bakya d'aga kirana kin kashe waya me ke faruwa"?
tunawa yayi da jiya da dare sunyi waya take fad'amasa ta fad'awa Dady maganarsa hakan yasa ya zabura zauni
cikin damuwa yake furta *"INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN*
kardai Dady bai amince da maganar ba lallai dole ni yaje gidansu yau yaji abunda ke faruwa ya Ilahi Ubangiji Allah yasa tunanina karya zama gaskiya
ya zanyi da rayuwata idan narasaki Aishana ke ce farin cikina ke d'in rayuwata ce"
haka ya zauna yanata sabbatu kamar wanda ya zautu sai da akayi kiran magarib sannan yaje ya d'auro alwala yana fitowa ya samu Inna bakin rijiya tana Alwala
cikin mamaki Inna tace "Al'amin dama kana gidannan? akazo nemanka nace baka nan"
"ayya Inna koda nadawo kina band'aki kuma kaina ne yake ciyo shiyasa na kwanta"
cikin tausayinsa tace "sannu Allah ya sawwak'a kasha magani"?
"eh nasha ya ma daina yanzu"
"to Allah ya k'aro sauk'i"
"amin Inna zan tafi masallace idan anyi isha zanje wani gurin amma ba jimawa zanyi ba"
"kaida ba kada lafiya kuma ina zaka kayi hak'uri har Allah ya kaimu gobe"
"Inna naji sauk'i fa kuma ba jimawa zanyi ba"
"to Allah ya tsare sai kadawo"
"amin Inna".
"Bety dauri kici abinci ko kad'anne"
"Aunty ba zan iya ba ruwan Lipton kawai zansha"
"haba Bety yaufa tun safe bakici komaiba taya mutum zai zauna da yunwa salon wani cutan yazo ya shigeki uhm Dan Allah kiyi hak'uri
kisawa zuciyarki salama mafe akasari abun da kakeso ba shine yake zama alkhairi agunka ba
ki nemi zab'in Allah tsakanin abunda kikeso da wanda mahaifinki ke so yafi wannan damuwar da zata iya janyo maki wani ciyon"
janyo hannan Aunty tayi ta d'ura ak'irjinta saitin zuciyarta cikin muryarta da ta disashe saboda kuka tace "Aunty kinji yanda nakeji azuciyata?
nasani mutuwa zanyi Al'amin rayuwata ne Allah ne ya jarbce ni da son sa ban san taya zan iya cireshi araina ba"
Aunty kamar zatayi kuka dan tausayin Bety tace "Allah zaki rok'a Bety shi zai ciremaki"
"Aunty bazan iya d'aga hannuna na rok'i acire mun son Al'amin ba tamkar nayi sabo' ne"
Aunty ta zuba mata idanu tana kallonta aranta ji take "inama tana da iko inama tana da halin sawa ko hanawa hak'ik'a da tahana aurennan da tabawa Bety zab'inta farin cikinta
sai dai bata da wannan fawan Adu'a ce nata"
da k'yar tasamu ta d'anci Indomen da akayi mata jalof da busashin kefe.
bayan ta idar da sallah taje tayi wanka tasa kayan barcci d'aukar wayarta tayi tana son kiran Al'amin tana son jin muryrsa
sai dai gani take gara tun yanzu ta sabawa kanta rashinsa tasani yanzu duk inda yaki yana cikin damuwa rashin d'aga kiransa da tayi
wasu hawaye masu zafe suka dinga zarya afuskarta.
_______________________________
d'an acab'a ne ya sauke shi dai dai k'ofar gidansu Bety bayan ya sallami d'an acab'a ya k'wankwasa k'ofar gabansa sai dakan ukku ukku yake
Maigadi ne ya bud'i k'ofa yana fad'in "waye ne"?
cikin fara'a yace "Baba nine"
"au Aminu kaine"?
(sun saba da Baba zuwan da yake gun Bety)
fitowa Baba yayi kafin yace "Aminu kayi hak'uri yau da safe masu gidan sunce kar akoma bar bari ka shiga
kayi hak'uri dan Allah barinka zai iya janyowa narasa aikin da ni da iyalaina muka dugara da shi"
ba k'aramin kad'uwa Al'amin yayi ba wani irin jiri yaji wanda yasa shi saurin dafa bangon gidan idansa rufe yace
"bakomai Baba nagodi" cikin tausayi Baba yace "yaro sai hak'uri dama soyayya da 'ya'yan masu kud'i ai ta gadi
haka
k'warya tabi k'warya ne inko ta hau akushi ba muriya 'yar mai kud'i sai d'an uwanta mai kud'i talaka ai sai talaka
karambani ne kesa talaka shiga gonar da ba tasa ba"
zuwa wannan lokacin maganganun Baba k'ara k'ona masa zuciya suke har bai san sanda ya d'agawa Baba murya ba "shikenan naji tunda ka isar da sak'onka jeka abunka!"
Baba ya shige tare da rufe k'ofa yana magana k'asa k'asa da nakasa jiyo me yake fad'a.
abun hawa ya samu yanufi gida
Inna da Lawal suna zaune suna fira Faruk na gefensu yayi barcci Al'amin ya shigo yana dafa bango
Inna ta mik'e tsayi tana fad'in "Subuhanalillah Al'amin ba dai ciyon ba"?
cikin k'arfin hali yace "Inna jiri ne kawai nakeji"
"ayya sannu" tafad'a kamar zatayi kuka dan tausayin tilun d'anta
da taimakon Lawal ya k'arasa d'aki kwanciya yayi sai sannu su Inna kemasa
Lawal yace "ko zamuje asibiti"?
"bari kawai Lawal zai daina zuwa anjima"
ba yanda Inna batayi dashi ba yaci abinci yak'i yace da ita ak'ushi yaki duk da kuwa tun safe rabunsa da abinci
ranar kam agidan Lawal ya kwana dan ya kula Al'amin najin jiki.
_____________________________
acikin kwana biyunnan ta rame ga damuwa ga rashin cin abinci ko ina bata zuwa Yaya Saif ya karb'e wayarta makarantar ma ya hana
bayan aure zata cigaba da karatun tana so ko su d'aya ne taji muryar Al'amin sai dai babu hali.
yau gidan sai girki girki ake saboda Fa'iz yau zaizo Dady yakirata yayita lallashinta duk sai ya bata tausayi
ta d'aukarwa kanta Alk'awarin zata jure bazata wulak'anta shi ba ko Dan ta faranta ran Dady.
zauni suki a Palon bak'i shikam dama ya santa dan duk yazo gida sai yazo ya ganta yana mat'ar sonta
itama tana ganin sa ta gane shi dan wani lokacin yana zuwa gun Yaya Saif ba laifi kyakyawa ne Hutu da jin dad'i sun ratsa shi
sai dai kash ya makaru dan kuwa Al'amin yariga ya gama mamaye ciki da wajan zuciyarta
firar tasu bawani armashi shi kad'ai ke zancin iya kacinta uhm um um bai kawu komai aransa ba tunaninsa kunya ce yasa takasa sakewa dashi
haka dai ya k'araci surutunsa yayi mata sallama tare da d'inbin Alkhairi.
ansa ranar biki wata d'aya kowani b'angari shiri ake tayi.
___________________________
tana d'akinta kwanci k'irjinta ke ciyo sai dai ko Aunty tak'i ta fad'awa tana cikin wannan halin Zee da Meenat suka shigo mik'ewa tayi cikin farin cikin ganinsu
tace "Zee Meenat sannunku da zuwa yau manyan bak'i muke dasu agidannan"
lokaci d'aya suka hararita kafin Zee tace "kin kyauta Bety kin daina zuwa makaranta kin kashi waya"
karyar da kai tayi cikin sanyi tace "ayya kuyi hak'uri wayarce ta fad'i dama kuma ina so zanje gurinku sai gashi Allah ya kawu mun Ku har gida"
anan tabasu labarin aurenta da za ayi shine dalilin barinta makaranta (sai dai tab'oye masu bata so da kuma labari
Al'amin tadaice dasu had'in tun tana k'arama ne Dan Bety akwai zurfin ciki)
aifa nan suka hau yimata tsiya kafin saga bisani Meenat tace "gaskiya Bety zamuyi kewarki"
cikin damuwa Zee tace "bari ke dai wallahi har nafara jina wani iri"
haka dai sukaita jimaminsu sai yamma sosai suka bar gidan da alk'awarin zasu sake dawowa dan dan shiryi shiryin biki.
____________________________
yau saura sati biyu biki gobe ne zasu wuce Sudan a can za ayi komai har d'auren Aure daga can akai amarya gidanta da ke Singapur tare dasu Zee da Meenat za aje. (Oh wa yaga Meenat ak'asar waje lol😜)
idan kuga yanda Bety ta koma abun zai baka tausayi tarame tayi sanyi sosai ko yaushe zaka sameta tayi shiru tana tunani Aunty na iya k'ok'arinta wajan lallashinta d kwantar mata da hankali,
(Allah sarki rabuwa da masoyi ba dad'i😭)
Zuciyarta yau tak'i tank'wasuwa da abunda take muradi so take taga Al'amin suyi bankwana hakan yasa ta shirya ta fito ba tare da tabari Aunty taganta ba
masu tsarunta na ganin fituwarta suka tasu tace "Ku tafi kawai bana buk'atar rakiya ba nisa zanyi ba"
ta d'auki sabuwar motar ta da Yaya Saif yasaya mata tabar gidan ciki da tunanin ya Al'amn zai d'auki maganar aurenta da waninsa?
"Al'amin na kula ba ciyo ne kad'ai matsalar ka ba kana da wata damuwa ak'asan zuciyarka da kake b'oye mun
ka fad'amun damuwarka idan bazan iya yimaka maganinta ba sai nama adu'a yafi kabar Abu aranka yana cinka
baka da Uwar da tafine ni yafi cancanta da ka fad'awa damuwarka bai kamata ka b'oyemun damuwarka ba d'ana"
Inna da ke zauni gefinsa tafd'a kamar zatayi kuka
Al'amin ya tashi zauni da kyar dan kuwa yana jin jiki yayi sati akwanci ko ina bai iya zuwa masallace kawai yake zuwa
yaje asibiti antabbatar masa da jininsa ne ya hau ya rage yawan tunanin idan ba haka ba ciyon gaba zaiyi Wanda hakan zai iya janyo masa matsala
damuwa kam yanzu ya fara tunda ya rasa Aishansa dukkan farin cikinsa natsuwarsa sun tafi ,
d'aura kansa yayi akafad'an Inna cikin damuwa ya baiwa Inna Labarin Soyayyarsa da Bety da kuma abunda ya faru na hanashi ganinta da rashin samunta awaya.
Inna harda k'wallarta saoda tsananin tausayin d'anta cikin tausayi tace "ayya d'ana dan dai nasan lamari na soyayya Allah ne kesawa bawa
kuma nasan halinka baka da kwad'ayi da son abun hannun wani da nace me ya kaika fad'awa soyayya da 'yar masu kud'i
hak'ik'a nasani Aisha bata da girman kai da k'yamar talaka kamar wasu masu kud'in da kasame ta da nayi matuk'ar farin ciki ina yaba hankalinta
nasihar da zanyi maka shine kayi hak'uri ka rungumi k'addara mafi akasari abunda mutum keso ba shine alkhairi gareshe ba
kacigaba da adu'a idan matarka ce ko duk duniyar nan zasu taru suk'ika wallahi sai ka aure ta idan kuma ba matarka bace ko duk duniyar nan zasu taru su so ka ba zaka aureta ba dan haka damuwa da tunanin ba naka bane mik'awa Ubangiji lamarinka kai masa kukan ka zai sharema *Bijahi Rasulullahi S.A.W*"
nasiha sosai tamasa tare da kwantar masa da hankali aikuwa sai yaji damuwarsa ta ragu wata natsuwa ta saukar masa
rungumeta yayi yana fad'in "nagode Innata Allah ya barmun ke Insha Allahu zanyi amfani da nasiharki"
murmushi tayi tana shafa kansa tace "naji dad'i Allah yayima Albarka bari na tashi naje gidan kawunka dubashi kwana2 bai da lafiya ciyonka ya hanani zuwa dubashi
tunda naga da sauk'i zanje amma bazan jima ba"
"sai kin dawo ki gaishe shi da jiki" ya fad'a yana mai kwanciya.
lokacin da tabar layinsu Yaya Saif ya kunnu kan motarsa ya ganta abun ya bashi mamaki "na zata kuma ita kad'ai?"
ba tare da wani dugon tunani ba ya juya motarsa yabi bayanta Fa'iz da ke zauni a gefensa yace "ya dai abokina ina zamu kuma"?
"zaka gani" ya bashi amsa a tak'aici.
a k'ofar gidan tayi pakeng ta zauna tana tunanin yanda zatayi taso ta sameshi kantin Lawal sai dai kash kantin a rufe yaki bata da ta da ya wuci ta shiga gidan duk kuwa da kunyar Inna da takeji.
da Sallama ta shiga gidan sai dai shiru kamar ba kowa k'ofar Inna ta kalla arufe alamar batanan ta mai da dubanta ga k'ofar 'Al'amin alamar yana nan
Sallama tayi tare da fad'awa d'akin fitowarsa wanka kenan k'aramin tawul ne d'aure a jikinsa yana zauni abakin katefa yana shafa mai
Fa'iz yace "Malam kace dani Amaryata kagani shikenan ka ajiye ni anan idan tafito sai mutafi gurin photon a motarta kai sai kayi tafiyanka"
Yaya Saif bai ce dashi komai ba sai ma fitowa mortar da yayi yanufi gidan da yaga tashiga hakanan zuciyarsa ke bashi gurin d'an iskan yaronnan tazo
Fa'iz ya fito yana fad'in "Saif wai lafiya ya zaka shiga gidan mutane"?
ganin yak'i kulashi yasa yace "lallai ba lafiya ba bari yabi shi yaga meke faruwa"
kai tsayi k'ofar d'akin da yaga takalminta ya shiga
sanda Idanunta na fad'a Kansa da sauri ta runtsi idanunta ta juya da sauri zata bar d'akin cikin rawar murya tace "don Allah kayi hakuri"
jin tayi karo da mutum yasa tayi sauri bud'i idanunta suka fad'a cikin na Yaya Saif da yake k'ok'arin shigowa ai kawai sai ta koma ciki da gudunta ta b'oye bayan Al'amin tana k'walla ihu
cikin sauri Al'amin ya idea zura jallabiyar da shigowar Bety yasa yayi saurin janyota dama tana ajiye agefinsa
arud'i ya rik'ota yana tambayarta "Aishana me ya faru"?
jikinta sai rawa yake takasa cewa dashi komai sai k'ofa take kallo hakan yasa ya kalli k'ofan ya gansu atsayi sai huci suke Saif ya nufusu afusaci.
_mai k'aunar Ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌹🌹🌹🌹🌹
*KAR KA GUJENI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha a yabo*🌺
Fulani🌸
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
_Wannan su ne shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya baku ikon zuwa amen_
*70 to 80*
Yana zuwa ya d'aga hannunsa zai mare shi Al'amin yayi saurin rik'e hannun cikin d'aure fuska yace "awani dalili zaka mareni"?
Yaya Saif ya fito da ido cikin mamaki da takaici yace "lallai har kana da bakin magana naganka da k'anwata kace awani dalili"?
sakin hannun yayi tare da yin murmushi kafin yace "nasani duk da ba saninka nayi ba kamarku kad'ai ta tabbatar mun da kai waye agurinta
amma atunanina banma laifin da har zai kai ga duka ba amma idan na b'atawa Yayanmu rai ina neman afuwa"
ya k'arasa maganar yana mai had'a hannayinsa guri d'aya 🙏🏻
takaici ya rufe Yaya Saif cikin d'aga murya yace "kai d'an iska talaka da kai ka isa kace zaka fad'an magana naga k'anwata ad'akin ka kace awani dalili zan dake ka?
kai ga d'an iska mai lalata 'ya'yan mutane to bara kaji k'anwata tafi k'arfinka
tawuci ajinka idanma kwad'ayi ne da son abun duniya yasaka cusa kanka inda Allah bai kai ka ba to tun wuri kaiwa kanka nasiha
kafita hanyar k'anwata idan ba haka ba wallahi tallahi ba kaiba kaf danginka kajanyo masu masifa"!
"Uhm gaskiya ne ni talaka ne amma ba mai zuciyar kwad'ayi ba ba kuma mai nakasassar zuciya ba k'anwarka naganta ina so
soyayya ta gaskiya ba dan na lalata mata rayuwa ba dan ba halina bane ba kuma zan fara kan abunda nakewa k'auna ta fisabilillahi ba
dan haka wannan tunaninka ne kawai ban sota dan kud'inku ba, ban kuma b'oye mata ba tayarda dani ahakan ta soni
dan haka maganganunka bazasu sa na daina sonta ba ko na *GUJETA* sai dai idan ita da kanta tace bata yi dani
dole zan barta ba dan naso ba, sannan kai baka isa kamun abunda Allah bai nufi ya sameni ko dangina ba"
cike da takaici Yaya Saif ya nufi bayan Al'amin zai janyota tayi saurin ja baya tana fad'in "dan Allah Yaya kayi hak'uri kaje yanzu zandawo wallahi magana kawai zamuyi"
ta k'arasa maganar cikin kuka "Wallahi Bety idan bakizo muntafi ba ranki zai b'aci zan b'abb'allaki fa dan kinga muna lallab'aki shine zaki nemi ki rainamu
akan wannan d'an iskan talakan ko"?
"wayyo Yaya pls kadaina zaginsa miye laifinsa dan Allah dan kawai ya soni shine laifinsa miye banbancin talaka da mai kud'i duk fa d'aya ne agun Allah sai wanda yafi bautamasa shine ya zarce talakan ko mai kud'i
kadaina wannan Yaya sam ba kyau kuma ni ba komai ya kawuni nan ba gobe zamu bar k'asar bankwana kawai fa nazo muyi
dan Allah Yaya kabarni muyi magana dan Allah"
a fusace ya kaiwa bakinta bugu Al'amin yayi saurin janyota jikinsa hakan yasa bai sameta ba
cikin sanyi Al'amin yace "kayi hak'uri zata bika ba sai ka daketa ba"
yana gama fad'a ya rik'o hannunta suka fito d'akin sai da suka kai k'ofar gida yace "ina motar taki"?
ta nuna masa da d'aya hannun sai da ta zauna yace "Aishana kiyi hak'uri kije gida anjima k'arfe biyar na yamma zanzo amma sai dai ki fito
saboda naje mai gadinku yace ance karya kuma barin na shiga gashi kuma ba asamun wayarki meyasa"?
kallonsa tayi kafin ta sunkuyar da kanta cikin muryar kuka tace "Yaya ya k'wace wayar kuma au......
tsawar da Yaya Saif yayi matane ya hanata k'arasa maganar "Wallahi Bety idan baki bar gurinnan ba ranki zai b'ace zansa a hallakar da wannan d'an iskan da yake hure maki kunne"!
da sauri ta rufe k'ofa tare da yimata key tabar Unguwar tana kuka kamar ranta zai fita.
"na dawo gareka ba dai kai d'an iska ba gaka talaka sai fad'in rai da nuna isa zaka san ka tabka babban kuskure shiga gonar da ba taka ba"
yabar gurin afusace ya shiga motarsa suka bar Unguwar Fa'iz da tun faruwan al'amarin ya kasa cewa komai tsabar takaici da kishi sun rufeshi
"dama rufeshi sukayi yarinya bashi take soba tana da wanda take so har d'akinsa take zuwa lallai ai ko autar mata ce ya barta
dan atsarinsa bayada burin auren macen da bata sonsa dan baiga ribar hakanba da aurensa ma sai tadinga huld'a da saurayin kai ina ba zaiyu ba dole ne ma nasan abunyi"
Saif ya d'an kalleshi kafin ya maida hankalinsa ga hanya yace "Fa'iz ka kwantar da hankalinka kar wannan ya tayarma da hankali Bety bata isa tak'i aurenka ba
shikuma wannan d'an iskan yau zansa ayi masa hankali sai yayi nadamar da ko wani yaga zaiyi soyayya da 'yar masu kud'i zai hana"!
Fa'iz murmushi yayi cikin takaice yace "Saif kenan meye laifinsa itafa takai kanta gurinsa bashi ba dan haka idan dai dan nine karkayi masa komai dan Allah"
daga haka ba wanda ya saki cewa komai har suka isa gida kowa da kalar nazarin da yake.
Aunty ta shiga d'akin Bety da plate d'in abinci a hannunta ta tarar bata nan ajiyewa tayi tare da zama kan kujera tana jiranta dan azaton ta tana band'aki
jin shirun yayi yawa yasa tayi tunanin lek'awa band'akin taga ko lafiya
_
tana turawa taga wayam ba kowa lamarin ya tsorata ta
ko ina na gidan ta duba bata ganta ba hakan yasa ta fito harabar gidan ta tambayi ma aikatan aka tabbatar mata da anga fitarta.
haka ta koma d'akinta ta zauna tana tunanin inda Bety taje tana cikin jimamin Dady ya dawo har zai wuce d'akinsa ya fasa ya nufi d'akin Bety ya tarar bata nan hakan yasa yayi sashin Aunty
da sallamarsa ya shiga Aunty ta mik'i tsayi tai masa sannu da zuwa cikin ladabi
"ina Bety? naje d'akinta batanan"
cikin fad'uwar gaba tace "ta d'an fita nan amma ba jimawa zatayi ba "
ya fara magana cikin fad'a "saboda me zaki barta ta tafita bayan kinsan na hanata fita"
"kayi hak'uri wajan zainab taje"
fau yafice ba tare da ya saki cewa da ita komaiba
ajiyar zuciya tayi aranta tace "gara haka da dai tace dashi batasan fitarta ba bari zatayi zuwa anjima tagani idan bata dawo da wuri ba sannan tasan abunyi"
maganar Dady tajiyo sama sama yasata fitowa taga me ke faruwa
Dady yana fitowa Babban Palo ya had'u da Bety ta shigo da gudu tana kuka cikin sauri ya rik'ota suka zauna kan kujera yana tambayarta
"Bety lafiya kedawa waye ya tab'amun ke"?
lafewa tayi jikinsa tana cigaba da kukanta batari da tace dashi komai ba
hakan ya d'aga masa hankali matuk'a Allah yasa 'yar tasa ba gamu tayi ba
fitowar Aunty yayi dai dai da shiguwar su Yaya Saif
da sauri Dady yace "yawwa Saif zo ka tambayar mun ita abunda ke damunta tak'i tamun magana sai kuka take"
zama yayi kafin yace Dady k'yaleta kukan rainin hankali ni kawai take agidan saurayinta naganta dan na kurota shine take wannan kukan"
nan ya basu labrin abunda ya faru Dady ransa ya matuk'ar b'ace zuciyarsa ta rufe har baisan sanda ya rufeta da duka ba da k'yar Aunty da Fa'iz suka k'waceta hannunsa fad'a yake sosai
"Aisha kincuceni kinci amanata tarbiyar da naginaki da ita kenan zuwa d'akin saurayi"!?
Bety da take jikin Aunty tana kuka tunda tae da wayonta Dady bai tab'a dukanta ba kai ita bata tab'a sanin zafin duka ko fad'a ba sai akan wannan auren
sai dai maganganun Dady sunfi komai d'aga mata han Kali wanda yasata yin da nasanin biyewa zuciyarta zuwa gurin Al'amin
duk da tasani bada wata mummunan manufa taje ba kamar yanda suke zato amma taya zata fahimtar dasu?
maganar Fa'iz ce ta dawo da ita daga tunanin da take
"Dady ina Neman alfarma dan Allah dan Annabi kayi hak'uri kabarta ta aure wanda take so idan dai dan nine wallahi na hak'ura kuma zanyiwa abbana bayani zai fahimta
karka zargi Bety da komai kuskurenta d'aya zuwa d'akinsa da tayi bayan wannan bana tunanin da wani abu kayi hak'uri Dady ka fahimceni kakuma gafarce ni idan na b'atama rai"
daga haka bai saki cewa komaiba ya sunkuyar da Kansa k'asa saboda irin kallon da Dadyn ke masa.
_tofa shin Dady zai amince kokuwa?🤔 to kudai biyu 'yar mutan yabo Dan jin yanda zata kasance_
_mai k'aunar Ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌹🌹🌹🌹🌹
*KAR KA GUJENI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha a yabo*🌺
Fulani🌸
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
_Wannan su ne shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya baku ikon zuwa amen_
*80 to 90*
Gyaran murya Dady yayi kafin yace "ba zanga laifinka ba Fa'iz ba kuma zan tilastama ba zanyi magana da Abbanka"
ya juyo da kallonsa ga Bety cikin fad'a yace "kin kyauta Aisha kin nuna ban isa dake ba ban isa nasaki ko na hanaki ba shikenan sai ki turoman yaron yau inaso na ganshi
Saif kabata wayarta"
"haba Dady karka biyewa Bety yarinya ce sam bata san inda yake mata ciwo ba"
"Saif kayi abunda nace" cikin tashin hankali Bety ta matsa kusa dashi cikin muryar da taci kuka tace "Dady kayi hak'uri kamun rai wallahi banje da wata manufa ba ko dan nak'iyin biyayya gareka ba dan Allah Dady kayafe mun wallahi zan aur... tsawar da ya daka mata ne yasata had'iye sauran maganar batare da ta shirya hakan ba
"bana buk'atar wata magana kiyi abunda nace idan ba haka ba wallahi kinji na rantse zan bada ke sadaka ga kowaye"
da ganan ya tashi ya nufi d'akinsa yana fad'in "Zainab ki sameni d'aki"
Fa'iz mik'ewa yayi yabar falon cikin damuwa ya sani zaiji jiki na rashin Bety sai dai hakan da yayi shine dai dai ba zai iya aurenta ya kasance gangan jikinta ne kad'ai atare dashi Zuciyarta na gun wani ba zaiyu ba.
Aunty ta wuce d'akin Dady cikin fad'uwar gaba da tunanin me zai faru?.
Yaya Saif ya kai mata rank'washi aka wanda yasa tasaki k'ara cikin jin haushin ta yace "kika kuskura kika nacewa auren fak'irinnan Allah dagani har Dady Zamu ciri hannunmu acikin al'amurranki banza marar tunani yana talaka me yaci me ya baki
kirasa abun so sai talaka wanda idan ya samu na yau da k'yar tunananin inda zai samu na gobe zaiyi"
fad'a sosai yayi mata kafin yaje ya d'auko mata wayar ya jefa mata ajiki yabar falon yanata meta
ita dai komai bata iya cewa dashi ba sai kukanta take oh dama ya lafiyar kura ballatana an tab'ota
tarik'e wayar tana tunanin mafita "takira Al'amin kokuwa? idan kuma tak'i kiransa Dady zai had'ata da kowa ma kai gara kawai takirashi da dai ahad'ata da wanin kuma wai sadaka tab"!
haka dai ta zauna tana sak'awa da warwarewa.
ahankali Aunty ta tura k'ofa yana tsayi abakin window ya goya hannayansa abaya yaba k'ofa baya
ahankali ya fara magana ba tare da ya jiyo ba "Zainab abun da kika mun kin kyauta kenan? da saninki Bety taje d'akin sauraye sannan nazo na tambayeki kimun k'arya idan 'yar da kika Haifa ce zakiyi mata irin wannan tarbiyar amanar da na barmaki kenan"?
cikin rawar murya Aunty tace kayi hak'uri kuskurena d'aya da na b'oyema gaskiyar magana Amma wallahi tallahi ban San fitar Bety ba nima dubawa nayi naga batanan
ban kuma b'oyema dan wata manufa ba sai dan gudun karkayi fad'a amma kasan bazan tab'a cewa da Bety taje wani gun da zai iya zama illa ga rayuwarta ba
banci amana ba ba kuma zan tab'a ciba kasani"
jiyowa yayi suna fuskantar juna kafin yace "bazan tab'a yarda da wani zancinki ba domin tun farko kin tabbatar mun da saninki ta fita
kin karya Alk'awarin da mukayiwa juna
ina so ayau d'innan ki bar gidannan na *SAKE KI SAKI D'AYA*duk da kin b'ata mun rai hakan ba zaisa na manta alkhairan da kikayiwa yarana ba"
janyo wata 'yar akwati k'arama mai kyau ya mik'o mata "ga wannan kirak'i k'adarurin da ke ciki zasu ishiki komai awannan rayuwar"
murmushin takaici tayi kafin tace "karik'i kayanka bana buk'ata amma kasani ni ban karya alk'awari ba kaine ka karya alk'awari idan ka manta bara na tuna ma"
*BARI MU D'AN WAIWAYA BAYA KAD'AN*
zauni take kan gado fuskarta lullub'e da mayafi kuka take sosai tana tunani taya zata zauna da Uban gidanta kuma mijin Momy wacce tarik'eta tamkar 'yar da ta Haifa,
shigowarsa ce tasa ta saurin sauka daga kan gado ta sunkuya cikin girmamawa tace dashi "sannu da zuwa"
"yawwa" ya amsa bayan ya zauna gefen gado ya d'an kalleta kafin yayi gyaran murya yace
"Zainab ina so ki bani hankalinki nan muyi magana ta fahimta kinji"?
gyara zamanta tayi kan kafet cikin natsuwa tace "eh yallab'ai"
"kiyi hak'uri da maganar da zan fad'amaki magana ta gaskiya bazan iya zama dake amatsayin mata ba,
ina maki kallon kamar yanda marigayiya tanemi na d'auke ki d'iya har yanzu ahakan na d'auke ki,
na amince wa aurenki saboda ina so na rayu da yarana kema nasan saboda ba kyaso arabaku kika amince,
wannan yasa na yanki hukuncin zamu zauna da juna kamar da ba tare da kowa ya sani ba,
duk lokacin da kikaso rabuwa da yaran ashiryi naki da na sallameki yaya kin amince"?
yayi mata tambayar yana mai zuba mata idanu
ko kad'an bataji haushin maganarsa ba dan tasan gaskiya ne ya fad'a hakan yayi mata dad'i hannunta tasa tana mai share hawayen dake ta zarya afuskarta
batare da dogun nazari ba tace "ba komai na amince amma ina so kamun alfarmar barina gidannan har sai ranar da Bety tayi aure aranar nayi alk'awarin zan barku"
cikin mamaki yace Zainab shekararki 15 Bety shekararta hud'u da 'yan watanne amma kike maganar zaki zauna ba tare da abokin rayuwa ba tsawun wannan shekarun"?
"karka damu zan iya ai shiyasa na nemi hakan saboda ban san wace irin mata zaka aure ba kar tazo ta k'untata masu aranar da Momy zata rasu kafin su tafi tabar mun amanar su Aisha ya zama dole na rik'i wannan amanar duk rintsi" ta k'arasa maganar cikin shishshik'a kuka
ganin ta dage yasa ya bar maganar yayi mata saida safe
bayan fitarsa tayi shirin kwanciya hankalinta kwanci duk wani damuwa da zullumi ya gushe azuciyarta taso ta d'auko Bety su kwana tare sai dai gudun tambayarta dalili yasa dole ta hak'ura tayi barccin ta ita kad'ai.
kwanci yake tunani ya hanashi sakat anya yayiwa yarinyarnan adalci amma ya zaiyi dole ne yayi wannan hukuncin Allah yagani baya jin sonta ba kuma zai iya cin amanar marigayiya ba ta d'auki Zainab tamkar 'yar cikinta hakan yasa shima yake d'aukarta a wannan matsayin har gobe bazai iya rayuwar aure da ita ba haka dai yayita tunani har barcci yayi awun gaba da shi.
tana matuk'ar kyautatawa su Bety k'auna ce take nuna masu tamkar ita ta haifesu Saif ne kawai ke d'an bata matsala rashin kunya da tsiwar da yake mata yana damunta amma sam bata biye masa tsakani da Allah take sonsu.
tana yawan ciyon Mara musamman lokacin al'adarta haka take daurewa har tayi taji sauk'i batare da tabari kowa nagidan ya sani ba ko yaushe cikin azumi take
tsakanin ta da Dady kowa gaisuwa ne sai girkin da take masa idan yana gari ko yaushe zaka ganta cikin hijabi.
iyaye da 'yan uwa kuwa tun suna damuwa da rashin haihuwarta har aka hak'ura aka dage da adu'a sai dai suna matuk'ar tausayinta aganinsu gara shi yana da biyu itace dai ko d'aya bata da
wannan yasa sanda yajewa iyayansa da zancin zai k'ara aure suka hanashi saboda suna son Zainab suna tausayin rashin haihuwarta file ya hak'ura ba dan ya so ba.
*bayan shekara ukku*
Dady ya k'ara aure ba tare da Zainab da iyayansu sun sani ba 'yar nan Kaduna ce suna zaune a malali yaransu hud'u
Farhan Safna da taci sunan Momyn Bety ana kiranta da (Ilham) sai Zainab da taci sunan Aunty ana kiranta (Ihsan) sai auta Isma'il ko yaushe Mamy na damun Dady ya kaisu gun danginsa kodan yaransu da kuma halin rayuwa
duk san da tamai maganar hak'uri yake bata zai kaisu sudai k'ara hak'uri. wannan kenan.
*ci gaban labari*
"ina fatan ka tuna dan haka ban karya alk'awari ba kaine dai ka karya alk'awari"
daga haka bata sake cewa komai ba tabar d'akin.
Bety da take zaune a inda Aunty ta barta cikin damuwa tama rasa tunanin yi shin farin cikin samun Al'amin zatayi ko bak'in ciki saboda Al'amarin ya zo mata ba yanda taso ba, ba kuma yanda ta zata ba
tana cikin wannan yanayin ne taga fitowar Aunty a hargitsi ta nufi d'akinta hakan ya matuk'ar d'aga mata hankali tashi tayi da sauri tabi bayan Aunty.
_mai k'aunar Ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌹🌹🌹🌹🌹
*KAR KA GUJENI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha a yabo*🌺
Fulani🌸
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
_Wannan su ne shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya baku ikon zuwa amen_
*80 to 90*
Gyaran murya Dady yayi kafin yace "ba zanga laifinka ba Fa'iz ba kuma zan tilastama ba zanyi magana da Abbanka"
ya juyo da kallonsa ga Bety cikin fad'a yace "kin kyauta Aisha kin nuna ban isa dake ba ban isa nasaki ko na hanaki ba shikenan sai ki turoman yaron yau inaso na ganshi
Saif kabata wayarta"
"haba Dady karka biyewa Bety yarinya ce sam bata san inda yake mata ciwo ba"
"Saif kayi abunda nace" cikin tashin hankali Bety ta matsa kusa dashi cikin muryar da taci kuka tace "Dady kayi hak'uri kamun rai wallahi banje da wata manufa ba ko dan nak'iyin biyayya gareka ba dan Allah Dady kayafe mun wallahi zan aur... tsawar da ya daka mata ne yasata had'iye sauran maganar batare da ta shirya hakan ba
"bana buk'atar wata magana kiyi abunda nace idan ba haka ba wallahi kinji na rantse zan bada ke sadaka ga kowaye"
da ganan ya tashi ya nufi d'akinsa yana fad'in "Zainab ki sameni d'aki"
Fa'iz mik'ewa yayi yabar falon cikin damuwa ya sani zaiji jiki na rashin Bety sai dai hakan da yayi shine dai dai ba zai iya aurenta ya kasance gangan jikinta ne kad'ai atare dashi Zuciyarta na gun wani ba zaiyu ba.
Aunty ta wuce d'akin Dady cikin fad'uwar gaba da tunanin me zai faru?.
Yaya Saif ya kai mata rank'washi aka wanda yasa tasaki k'ara cikin jin haushin ta yace "kika kuskura kika nacewa auren fak'irinnan Allah dagani har Dady Zamu ciri hannunmu acikin al'amurranki banza marar tunani yana talaka me yaci me ya baki
kirasa abun so sai talaka wanda idan ya samu na yau da k'yar tunananin inda zai samu na gobe zaiyi"
fad'a sosai yayi mata kafin yaje ya d'auko mata wayar ya jefa mata ajiki yabar falon yanata meta
ita dai komai bata iya cewa dashi ba sai kukanta take oh dama ya lafiyar kura ballatana an tab'ota
tarik'e wayar tana tunanin mafita "takira Al'amin kokuwa? idan kuma tak'i kiransa Dady zai had'ata da kowa ma kai gara kawai takirashi da dai ahad'ata da wanin kuma wai sadaka tab"!
haka dai ta zauna tana sak'awa da warwarewa.
ahankali Aunty ta tura k'ofa yana tsayi abakin window ya goya hannayansa abaya yaba k'ofa baya
ahankali ya fara magana ba tare da ya jiyo ba "Zainab abun da kika mun kin kyauta kenan? da saninki Bety taje d'akin sauraye sannan nazo na tambayeki kimun k'arya idan 'yar da kika Haifa ce zakiyi mata irin wannan tarbiyar amanar da na barmaki kenan"?
cikin rawar murya Aunty tace kayi hak'uri kuskurena d'aya da na b'oyema gaskiyar magana Amma wallahi tallahi ban San fitar Bety ba nima dubawa nayi naga batanan
ban kuma b'oyema dan wata manufa ba sai dan gudun karkayi fad'a amma kasan bazan tab'a cewa da Bety taje wani gun da zai iya zama illa ga rayuwarta ba
banci amana ba ba kuma zan tab'a ciba kasani"
jiyowa yayi suna fuskantar juna kafin yace "bazan tab'a yarda da wani zancinki ba domin tun farko kin tabbatar mun da saninki ta fita
kin karya Alk'awarin da mukayiwa juna
ina so ayau d'innan ki bar gidannan na *SAKE KI SAKI D'AYA*duk da kin b'ata mun rai hakan ba zaisa na manta alkhairan da kikayiwa yarana ba"
janyo wata 'yar akwati k'arama mai kyau ya mik'o mata "ga wannan kirak'i k'adarurin da ke ciki zasu ishiki komai awannan rayuwar"
murmushin takaici tayi kafin tace "karik'i kayanka bana buk'ata amma kasani ni ban karya alk'awari ba kaine ka karya alk'awari idan ka manta bara na tuna ma"
*BARI MU D'AN WAIWAYA BAYA KAD'AN*
zauni take kan gado fuskarta lullub'e da mayafi kuka take sosai tana tunani taya zata zauna da Uban gidanta kuma mijin Momy wacce tarik'eta tamkar 'yar da ta Haifa,
shigowarsa ce tasa ta saurin sauka daga kan gado ta sunkuya cikin girmamawa tace dashi "sannu da zuwa"
"yawwa" ya amsa bayan ya zauna gefen gado ya d'an kalleta kafin yayi gyaran murya yace
"Zainab ina so ki bani hankalinki nan muyi magana ta fahimta kinji"?
gyara zamanta tayi kan kafet cikin natsuwa tace "eh yallab'ai"
"kiyi hak'uri da maganar da zan fad'amaki magana ta gaskiya bazan iya zama dake amatsayin mata ba,
ina maki kallon kamar yanda marigayiya tanemi na d'auke ki d'iya har yanzu ahakan na d'auke ki,
na amince wa aurenki saboda ina so na rayu da yarana kema nasan saboda ba kyaso arabaku kika amince,
wannan yasa na yanki hukuncin zamu zauna da juna kamar da ba tare da kowa ya sani ba,
duk lokacin da kikaso rabuwa da yaran ashiryi naki da na sallameki yaya kin amince"?
yayi mata tambayar yana mai zuba mata idanu
ko kad'an bataji haushin maganarsa ba dan tasan gaskiya ne ya fad'a hakan yayi mata dad'i hannunta tasa tana mai share hawayen dake ta zarya afuskarta
batare da dogun nazari ba tace "ba komai na amince amma ina so kamun alfarmar barina gidannan har sai ranar da Bety tayi aure aranar nayi alk'awarin zan barku"
cikin mamaki yace Zainab shekararki 15 Bety shekararta hud'u da 'yan watanne amma kike maganar zaki zauna ba tare da abokin rayuwa ba tsawun wannan shekarun"?
"karka damu zan iya ai shiyasa na nemi hakan saboda ban san wace irin mata zaka aure ba kar tazo ta k'untata masu aranar da Momy zata rasu kafin su tafi tabar mun amanar su Aisha ya zama dole na rik'i wannan amanar duk rintsi" ta k'arasa maganar cikin shishshik'a kuka
ganin ta dage yasa ya bar maganar yayi mata saida safe
bayan fitarsa tayi shirin kwanciya hankalinta kwanci duk wani damuwa da zullumi ya gushe azuciyarta taso ta d'auko Bety su kwana tare sai dai gudun tambayarta dalili yasa dole ta hak'ura tayi barccin ta ita kad'ai.
kwanci yake tunani ya hanashi sakat anya yayiwa yarinyarnan adalci amma ya zaiyi dole ne yayi wannan hukuncin Allah yagani baya jin sonta ba kuma zai iya cin amanar marigayiya ba ta d'auki Zainab tamkar 'yar cikinta hakan yasa shima yake d'aukarta a wannan matsayin har gobe bazai iya rayuwar aure da ita ba haka dai yayita tunani har barcci yayi awun gaba da shi.
tana matuk'ar kyautatawa su Bety k'auna ce take nuna masu tamkar ita ta haifesu Saif ne kawai ke d'an bata matsala rashin kunya da tsiwar da yake mata yana damunta amma sam bata biye masa tsakani da Allah take sonsu.
tana yawan ciyon Mara musamman lokacin al'adarta haka take daurewa har tayi taji sauk'i batare da tabari kowa nagidan ya sani ba ko yaushe cikin azumi take
tsakanin ta da Dady kowa gaisuwa ne sai girkin da take masa idan yana gari ko yaushe zaka ganta cikin hijabi.
iyaye da 'yan uwa kuwa tun suna damuwa da rashin haihuwarta har aka hak'ura aka dage da adu'a sai dai suna matuk'ar tausayinta aganinsu gara shi yana da biyu itace dai ko d'aya bata da
wannan yasa sanda yajewa iyayansa da zancin zai k'ara aure suka hanashi saboda suna son Zainab suna tausayin rashin haihuwarta file ya hak'ura ba dan ya so ba.
*bayan shekara ukku*
Dady ya k'ara aure ba tare da Zainab da iyayansu sun sani ba 'yar nan Kaduna ce suna zaune a malali yaransu hud'u
Farhan Safna da taci sunan Momyn Bety ana kiranta da (Ilham) sai Zainab da taci sunan Aunty ana kiranta (Ihsan) sai auta Isma'il ko yaushe Mamy na damun Dady ya kaisu gun danginsa kodan yaransu da kuma halin rayuwa
duk san da tamai maganar hak'uri yake bata zai kaisu sudai k'ara hak'uri. wannan kenan.
*ci gaban labari*
"ina fatan ka tuna dan haka ban karya alk'awari ba kaine dai ka karya alk'awari"
daga haka bata sake cewa komai ba tabar d'akin.
Bety da take zaune a inda Aunty ta barta cikin damuwa tama rasa tunanin yi shin farin cikin samun Al'amin zatayi ko bak'in ciki saboda Al'amarin ya zo mata ba yanda taso ba, ba kuma yanda ta zata ba
tana cikin wannan yanayin ne taga fitowar Aunty a hargitsi ta nufi d'akinta hakan ya matuk'ar d'aga mata hankali tashi tayi da sauri tabi bayan Aunty.
_mai k'aunar Ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KARKA GUJENI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *na Aisha a yabo*🌺
*Fulani*🌸
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
_Wannan sune shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya baku ikon zuwa amen_
*90 to 100*
Gurin wadrobe ta tatarar da Aunty tana fito da kayanta cikin sauri ta k'arasa gurinta tana fad'in "Aunty lafiya naga kina had'a kaya"?
"lafiya k'alau Bety" ta bata amsa ba tare da ta juyo ba "dan Allah Aunty fad'amun me kefaruwa yanayin ki kad'ai ya tabbatar mu da ba lafiya ba"
rik'o hannunta Aunty tayi suka zauna bakin gado ta fara magana cikin muryar da ko yaushe zata iya fara kuka
"Bety banji dad'in abun da kikayi ba Allah ya gani banmaki irin wannan tarbiyar ba meyasa zaki biyewa zuciyarki kije gun saurayi"?
cikin kuka tace "Aunty koda kowa zaik'i yarda dani ban zaci kema zaki k'i amincewa dani ba wallahi summa tallahi banje gun Yaya Al'amin da wata manufa ba,
kawai naje ne dan nayi masa sallama na kuma fad'a masa abunda ke faruwa dan kar yaji awani gurin ya kalleni amatsayin mayaudariya"
"ni bance banyarda dake ba amma meyasa kafin kije baki nemi shawarana ba sannan ga waya me yahana ki ki kirashi"?
"Aunty kinfa san ank'wace mun waya taya zan kirashi sai dai kuskure na rashin fad'a maki da banyi ba kiyi hak'uri dan Allah Aunty"
ajiyar zuciya Aunty tayi kafin tace "shikenan koma dai miye yariga da ya faru sai dai akiyayi gaba"
"Insha Allahu Aunty ya zanyi kibawa Dady hak'uri nifa bance bazan aure zab'insa ba"
"uhm Bety kinfa san halin Dadynki kaifi d'aya ne tunda ya yanki wannan hukuncin ba makawa kika k'i kowa ma zai iya had'aki dashi
ko auren ki da Fa'iz da kiga ya hak'ura dan dai shine yace ya hak'ura dan haka shawarar da zan baki ki turo Al'amin d'in"
kad'a kai tayi ciki da gamsuwa sai dai aranta tarasa farin ciki zatayi ko bak'in ciki
"Aunty meyasa kike had'a kayanki"?
Aunty ta kawar da kanta gefe cikin rawar murya tace "Bety Dadynki ya *Saki ni*saboda yana ganin na gaza gurin tarbiyarki"
Bety ta rungumi Aunty tare da fashewa da wani irin kuka cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shigesu ni Aisha ya zanyi?
Aunty dukan alkhairan da kekamun kin soni kin bani kulawar da uwa ke baiwar 'yarta tun ban san kaina ba har zuwa wannan lokacin
na rasa sakayyar da zan maki sai na zamo silar mutuwar Aurenki
wayyo Aunty ki yafemun zanje nabawa Dady hak'uri ya janye *Sakin*"!
ta mik'e da sauri zata bar d'akin Aunty ta janyo ta jikinta
"kiyi hak'uri Bety baki da laifi aciki dama ko hakan bai faru ba lokacin barina gidannan yayi"
da mamaki Bety ta d'ago fuskarta tana kallon Aunty kafin tace "Aunty kamarya lokacin barinki gidannan yayi"?
murmushi Aunty tayi wanda yafi kuka ciwo kafin tace "eh ina nufin Allah ya k'addarta rabuwar mu kuma lokace yayi dan haka karki damu"
"Aa Aunty kiyi hak'uri dan Allah zan bawa Dady hak'uri dan Allah"
da k'yar Aunty ta lallasheta tabar maganar inda ta k'ara k'arfafa mata gwiuwa da ta aure Al'amin shine miji mafe Alkhairi da tajima tana mata adu'a tasamu,
tana kuka tana taya Aunty had'a kayanta
lokacin da Aunty zata fita Bety d'akinta tashige tana kuka kamar ranta zai fita kacokan ta d'aura laifin sakin Aunty akanta.
bayan tafiyan su Bety d'akinsa ya koma ya kwanta zuciyarsa ba dad'i adu'a yake tayi Allah yasa kar wani abu ya sami Aishan sa
dan yaga yayanta yana da zafin rai wani b'angare na zuciyarsa yana ciki da zullumi da tambayar ina zata tafe da take cewa bankwana tazo masa
haka yawuni cikin damuwa Allah Allah yake ayi la'asar ya tafe gurinta dan jin me kefaruwa.
Dady da tun fitar Aunty d'akin ya koma ya zauna kan kujera yana jin ba dad'i azuciyarsa lallai hukuncin da yayiwa Zainab ba dai dai bane bai kyauta ba bai mata adalci ba haka yayita tariyu zamansu da ita ko yaushe cikin kyautata masu take
dai dai da rana d'aya bai tab'a sauki hak'inta ko d'aya da yake kansa da ya shafe zaman takewar aure ba
kansa yaji yana masa wani irin ciwo kamar zai rabu biyu haka ya janyo wayarsa ya kira Dadyn Fa'iz
bayan sun gaisa Dadyn Fa'iz yace "Alhajin Allah yanzu nake shirin kiranka sai gashi ka kirani"
"hakane dama gami da maganar Fa'iz da Bety ne"
Dadyn Fa'iz yayi saurin katse shi yace "Fa'iz ya fad'amun komai karka damu muyi fatan Allah yasa hakanne mafe Alkhairi
dama can ba matarsa bace mutum kuma baya auren matar da ba tasa ba amintarmu tana nan basu suka had'amu ba ba kuma zasu rabamu ba"
cikin jin dad'i Dady yace "gaskiya naji dad'i sosai da ka fahimceni Allah yasa hakan yafi alkhairi"
daganan suka d'ura wata firar kafin daga bisani sukayi sallama.
Aunty tana fitowa ta d'auki motarta ta d'au hanyar zariya zuciyarta a cunkushi
sanda ta isa gida Mahaifiyarta ta tare ta da murna sai dai yanayin da taga Aunty yasa jikinta yayi sanyi bayan sun gaisa Inna tace "Abu anya zuwannan na lafiya ne"?
Aunty tasa hannynta tana share hawayen da suka zubu mata cikin kuka Taiwan Inna bayanin sakin da Dady yayi mata da dalilin Sakin sai dai ta b'oye mata gaskiyar zaman da sukayi da Dady
Inna ta dinga tafa hannu tana "LA ilaha illallahu Mahammadu Rasulullahi S. A.W ni Fad'ima naga Rasulu yanzu sabida Allah da Ma'aiki Alhaji bai saki ki da k'urciya ba sai yanzu da girma yazo ya kuma ga k'asa yarufe idon Mahaifinki
akan laifin da 'yarsa tayi bake ba zai huce kanki ai shikenan Allah ba azzalumin bawa bane ki kwantar da hankalinki karki sawa kanki damuwa Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairi
tashi kije kiyi Sallah la'asar kizo kici abinci"
Aunty ta tashi ta nufi tsakar gida tana fad'in "Inna inasu Abulkhairi"
"suna iskamiya anjima kad'an zaki gansu".
zaune take akan darduma ta idar da Sallah la'asar tayi kuka harta godewa Allah shiguwar Dady ne yasa ta saurin d'ago kanta tana duban k'ofa
zama yayi kan kujera fuskarsa sam ba annuri cikin tsoro tace "barka da wuni Dady"
"kiramun saurayin naki" yayi mata magana ba tare da ya amsa gaisuwarta ba
cikin kuka tace Dan Allah Dady kayi hak'..
katseta yayi cikin fad'a yace "zaki kirashi kokuwa sai na b'abb'allaki"?
cikin rawar jiki ta mik'i ta d'auko wayarta da ke ajiye kan madubi cikin sa'a tana kira number ta shiga mik'awa Dady wayar tayi ta rakub'e gefe tana 'yan Matan hawayenta.
Al'amin da fitowarsa kenan daga masallaci yaga kiran Aisha abun ya bashi mamaki d'azun ta fad'a masa yayanta ya kwace wayarta to miye zai kirashi ko cin mutunce zai masa na d'azun bai ishe shi ba lallai kuwa idan hakane zaiyi da nasanin kiransa
da wannan tunanin ya d'aga kiran amsa Sallamar da Dady yayi masa yayi cikin ladabi dan jin muryar babban mutum
Dady yace "kana magana da Mahaifin Aisha idan har da gaske kake inaso nan da k'arfe biyar naganka tare da waliyanka koda minti d'aya ka k'ara akai zan d'aura da wani"
bai jira amsar Al'amin ba ya katsi wayar tare da cillamata wayar yana fad'in "kin dai ji abunda nace idan ya k'ara minti d'aya ko waye zan d'aura aurenki da shi"
kifa kanta tayi akan gado tana kuka mai cin rai da danasanin biyewa zuciyarta zuwa gun Al'amin gashi Dady yak'i fahimtarta
"Dady ina son Al'amin amma banso na aure shi ba da son ranka ba Dady"
ringing d'in wayarta ne ya katse mata tunani tana dubawa taga Al'amin d'aga kiran tayi sai dai ta kasa magana sai shishik'ar kuka take
hakan ya matuk'ar d'aga masa hankali "Aisha na dan Allah ki taimake ni kiyi hak'uri ki daina kukannan fad'amun me ya faru"?
cikin kuka ta masa bayanin abunda ya faru tun sanda akayi maganar auransu da Fa'iz da dalilinta na zuwa gurinsa har zuwa abunda ya faru bayan dawowarta
"Innalillahi wa inna iIaihi raji'un Aishana kin aminci nazo adaura dani idan na rasaki komai ma zai iya samuna"
kad'a kai tayi kamar tana gabansa tace "na amince Al'amin"
da zumud'i yace "nagode Aishana sai munzo" daganan ya kashi wayar
gida ya shiga Faruk ya tarar da shirin islamiya "Faruk me kakeyi har yanzu baka tafe islamiya ba"?
"yaya harfa naje wani malamin mu ne yarasu yau akace baza azauna ba sai bayan kwana ukku"
"ayya Allah ya jik'ansa da rahama da dukan musulmi amin ina Inna"
"bayan tafiyanka masallace mijin Aunty uwaliya yazo ya d'auketa"
cikin tashin hankali yace ina zasu" Faruk da ya tsorata da yanda yayansa yamai magana cikin tsoro yace "Aunty Uwaliya ce aka kwantar asibiti shine akazo akai Inna "
Al'amin ya rik'i Kansa yana fad'in "ya Salam yanzu ya zanyi? Allah ka kawuman mafita" agogon da ke mak'ali a hannunsa ya duba 4:40 nan take idanunsa suka kad'a sukayi jajir ya zaiyi Inna bata nan ba zaiyu yaje yayi gaban Kansa ba
ba tare da yardarta ba wani tunani me yazo masa hakan yasa da sauri ya d'auko wayarsa aljihu ya lalubu number mijin Aunty Uwaliya ya kira sai dai kash wayarsa arufe wannan Karan kam ba Kansa ba har zuciyarsa ji yake tamkar and'ura masa garwashin wuta akai.
_mai k'aunar ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KAR KA GUJE NI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌸
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*K'anwata Hafsat musa Indon k'auye ina tayaki murnar kammala littafinki SAMU DA RASHI ALLAH UBANGIJI ya k'ara basira da lfyar idanu*
*100 to 105*
Rik'e kansa yayi tare da lumshi idanunsa yana tunanin mafita idan yace zaije unguwar su Aunty Uwaliya ya tambayi asibitin da suke zai canyi lokacinsa
zuciyarsa ta bashi shawarar ya sake gwada kiran mijin Aunty ko zai samu cikin sa'a yana kira ta shiga ba ajima ba mijin Aunty Uwaliya ya d'auka
bayan sun gaisa da tambayar mai jiki ya nemi da ya bashi Inna
bayan sun gaisa Inna tace "Al'amin kazo ka tarar bana nan ko"?
"eh wallahi Inna ya jikin nata"?
"da sauk'i ya naji muryarka wani iri ko jikin ne"?
shafa sumar kansa yayi kafin yace "Aa Inna naji sauk'i dama mahaifin Aisha ne ya kirani"
"to Allah yasa lafiya me yace ma"?
nan yayi mata bayanin duk yanda sukayi da Dady
Inna ta d'anyi jim kafin tace "Al'amin ba zank'i auren ka da Aisha ba sai dai ina tsoron kar wani abu zaima ya biyu ta hakan dan kaje amma in banda haka a ina aka tab'a irin wannan auren"?
"indai wannan ne karki damu kanki Inna Insha Allahu ba abunda zai faru sai alkhairi"
"uhm" ajiyar zuciya tayi kafin tace "kana ganin zaka iya Al'amin yarinyar nanfa 'yar Hutu ce masu kud'ine akwai nisan ta zara a tsakaninmu da ita mu talakawa ne"
"Inna ai Aishan duk tasan da ko ne waye ta aminta dani dan Allah kisa mana albarka karki ce Aa"
"uhm shikenan Allah ya sanya Albarka kaje ka fad'awa Baffanka da Malam (mahaifin Meenat)
ka d'aga katefa akwai kud'i sai kayi amfani dasu"
da murnarsa yace "nagode Inna sai dai kin manta na fad'a maki jiya da dare Lawal ya karb'o man adashina zanyi amfani dasu nagode" daga haka sukayi sallama.
Lawal ya kira ko gaisawa basuyi ba yayi masa bayani da mamaki Lawal yace "Al'amin waci Betyn wai"?
"kaga had'iye duk tambayar ka daga baya zaka iyayi yanzu ba lokaci"
"OK ganinan dama zanzo gurin ka"
yayi sa'a Baffa na tare da Malam a k'ofar gidan Baffa suna fira dama mak'wabta ne basu da nisa yayi masu bayani atak'aici"
da Mamaki Baffa yace "ikon Allah wannan wani irin Aure ne Al'amin ba mu kosan da kana neman yarinya ba sai kawai kazo mana da maganar aure sai kace auren 'yar tsana ba binciki ba komai"?
Al'amin da ya kejin kamar ya rusa ihu saboda tambayuyin da Baffa kemasa wanda ganinsa duk b'ata lokacine yace
"kuyi hak'uri Baffa dama ina niyar nazo nafad'a maku to sai aka samu 'yar matsala"
Baffa zaiyi magana Malam da ya kula da duba agogon da Al'amin keyi ga damuwa tattari da fuskarsa yace
"kaga tashi mutafi babu cikakken lokaci tun da yaran sun fahimci juna ai shikenan magana ta k'are"
"to muje mu samu abun hawa sai muje gidan" Lawal ne yazo da motar yayansa ya kwashisu suwa gidansu Bety.
Dady ya karb'esu cikin rashin walwala suka gaisa Baffa ya nemi alfarmar ad'an basu lokace akimtsa sannan ayi d'aurin auren
Dady yace "yaron naka baima bayani bane ayau d'innan nayi niyar zan aurar da ita idan kun shirya to idan baku shirya ba sai kuyi gaba na bawa wani"
malam yace ba komai Allah ya sanya Alkhairi ashiryi muki"
ba tare da b'ata lokaci ba aka d'aura auren Al'amin da Aisha akan sadaki dubu biyar kamar yanda Dady ya yanka masu
ana idar da d'aura auren Dady yasa Yaya Saif ya kira Bety
lokacin da ya shiga d'akinta ya tarar da ita zauni tayi tagumi tana ganinsa tayi saurin tashi tsayi tana kallonsa zuciyarta na bugawa fat fat fat kamar zata faso k'irjinta ta fito saboda tsoro
tab'e bake yayi kafin yace "ba dai kin nacewa talakan can ba to hankalinki ya kwanta an d'aura maku auren
amma kisani ko a hanya kika ganni kika ce kin sanni ballatana ki wanko k'afanki kizo gidannan Wallahi Allah sai na b'abb'alaki"!
jin an d'aura auren ta da Al'amin sai ta tsinci kanta cikin wani yanayi da takasa gane ko miye farin ciki ko akasin sa
ganin tamasa tsayi batace dashi komai ba sai ya fusata wato ga d'an iska yana mata magana tamasa shiru
hakan yasa ya fizgota da k'arfi yayi hanya Palon bak'i da ita kira take "wayyo Yaya ka sakarmun hannu wallahi da zafe wayyo Yaya hannuna zai karye"!
ina sam bai kulata ba ballatana ya tausaya mata ya sassauta rik'on da yayi mata
suna zuwa yayi cille da ita gaban Al'amin k'iris ya rage ya gwara kanta ga hannun kujera
Al'amin kallonta yake ciki da tausayi yau da wani ne ba yayanta ba da sai ya karkarya masa hannu
lumshi idanunsa yayi zuciyarsa na masa k'ona kukanta yana d'aga masa hankali
maganar da yaji Dady nayi yasa shi saurin bud'i idanunsa yana kallon Dady
"Aisha ga zab'in naki nan na baki sai dai ina so daga yanzu kiciri ne ko wani da ya shafe ni daga rayuwaki
karki kuskura ki tako gidannan da sunan yaji ko k'ara ziyararma mun yafe
sai ki tashi ku tafe gatanan zaku iya tafiya"
cikin tsananin kuka ta rarrafa zuwa gurin da Dady yake kafin takai Yaya Saif yayi mata tsawa "zaki tashi ku tafe ko sai na b'abb'allaki"?
ganin tak'i tashi yayu kanta Dady yace "Saifullah k'yaleta ke Aisha maza tashi Ku wuce ko na k'yaleki da shi"!
yayi mata maganar atsawaci su Malam da sukayi shiru suna mamakin wannan al'amarin me yayi zafi haka
Malam yace "kuyi hak'uri abun bai kai na duka ba kai Al'amin rik'ota mutafi Alhaji mun tafi Allah ya huci zuciyarku"
haka Al'amin yarik'ota suka shiga mota kamar ranta zai fita.
har cikin d'akin Inna suka rakata tare da k'ara lallashinta kan tayi hak'uri idan an kwana biyu zasu je da Kansu su bawa mahaifinta hak'uri da wannan Alk'awarin sukayi masu sallama
Lawal yace "mutumin nima zan fita sai na dawo anjima"
"aha nagode sai najika"
Lawal na fita Al'amin ya rungumita yana bubbuga bayanta ahankali ya fara magana cikin lallashi
"Aishana kiyi hak'uri ki daina kukan nan yana d'aga mun hankali Insha Allahu Dady zai hak'ura yanzu yana cikin fushi idan an kwana biyu zamuje mu bashi hak'uri kinji Aishana"?
Bety da tunda tajita a faffad'an k'irjinsa kukanta ya d'auke cak sai ajiyar zuciya take yanzun ma takasa cewa dashi kumai sai sake lafewa da tayi tana shak'akar k'amshin jikinsa.
*kuyi hak'uri da wannan Insha Allahu gobe zanyi maku tpyng ngde*
_mai k'aunar Ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KAR KA GUJE NI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌸
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*105 to 1010*
Daina kukan nata yayi masa dad'i kiran sallah yaji anfara yasa ya d'agota yana kallon fuskarta cike da k'auna yace
"Aishana bara naje nayi alwala na wuce masallaci" kallonsa tayi kamar zatayi magana kuma sai tayi k'asa da kanta
fuskarsa ya had'a da nata har suna shak'ar numfashin juna cikin muryar k'asa k'asa yace "meyasa zaki fasa fad'ar maganarki fad'amun abunda ke ranki"
lumshi idanunta tayi cikin jin kunya tace "inasu Inna"?
murmushi yayi kafin yace "Inna tana asibiti wata sister d'inmu ce bata da lafiya Faruk kuma ban san ina yaje ba"
"yanzu idan ka tafi ni kad'ai zan zauna"? tayi magana kamar zatayi kuka
hancinta ya lakata yana fad'in "oh Aishan tawa matsoraciya ce ashe to tashi muyi alwala sai na mana jam'i tun lokaci bai tafi ba".
bayan sallah isha suna zauni k'ofar d'akin Inna kwanci take ajikinsa yana wasa da hannunta ya kira Inna bayan sun gaisa da tambayar mai jiki ta nemi ya bata Aisha
cikin jin kunya ta karb'i wayar zata tashi yayi saurin saki rungumeta kallonsa tayi cikin k'auna kafin tayi k'asa da idanunta
ta fara magana ahankali "ina wuni Inna"
"lafiya k'alau Humaira ya bak'unta"?
"Uhm ya mai jiki"?
"da sauk'i haihuwa ce har yanzu shiru ai da tuni na dawo gida,
Al'amin ya fad'a mun abun da ke faruwa kiyi hak'uri haka Allah ya k'addarta bawa kuma bai isa ya kaucewa k'addararsa ba"
sosai tayi mata nasiha kafin daga bisani sukayi sallama tabawa Al'amin bayan sunyi sai da safe
ya d'ago fuskarta yasa hannu yana share mata hawayen da keta zarya afuskarta cikin damuwa yace
"Aishana kukan ya isa haka kinji"
girgiza kai tayi kafin tace "Yaya Al'amin kaga yanda aurenmu ya zo dan Allah karik'e amana *KAR KA GUJE NI* duk rintsi"
hannunsa ya had'a da nata kafin yace "har abada Aishana bazan tab'a guje maki ba ke d'in farin cikina ce rayuwata
guje maki yana nufin rasa farin cikina rasa rayuwata bazan tab'a cin amanarki ba yanda kika zab'e ni Insha Allahu bazan baki kunya ba"
"nagode Yaya Al'amim Allah ya shige mana gaba"
"amin ya zamuyi kinga har yanzu Faruk bai dawo ba ina so na fita ba jimawa zayi ba"
Sallamar Lawal sukaji yasa Bety saurin janyi jikinta aranta tana hamdala harga Allah tsoron zama take ita kad'ai cikin gida ba kowa gashi ba NEPA
Lawal ya mik'a masa hannu sukayi musabaha sannan ya juya kan Bety yace "amarsu ta ango wato keda abokina haka kuka mun akabarni da tsoro da fad'uwar gaba Ku kuma kuna gefi kuna soyayyar ku"
Bety Sunkuyar da kanta tayi cikin mayafi takasa cewa dashi komai Al'amin yayi murmushi kafin yace "kamanta baka fad'i d'ayan ba harda fits...
Lawal yayi sauri katse shi "kaifa d'an rainin wayau ne bayan laifin da kamun harda sharri zaka mun"
"to idan sharri ne kabarni na fad'amata mana"
"o o nak'i ai awuci wurin kawai amma alk'ur'an kun d'au alhakina da yawa"
dariya sukayi kafin daga bisan Lawal ya basu ledar da ya shigo da ita da kula yace "gashi ni zan wuce sai da safenku Faruk kuma yana gidanmu"
har k'ofar gida Al'amin ya rakashi yana masa godiya.
bayan ya dawu yace "Aishana tashi muje d'aki sanyi ya fara sauka"
d'akinsa ya kaita ko ina tsab tsab tamkar ba d'akin saurayi ba sai k'amshi ke tashi
fita yayi zuwa d'akin Inna ya d'auko Plat da cop sannan ya koma d'akinsa ya zuba mata sinasin d'aya Plat d'in ya zuba gasashiyar kaza
ya tura mata gabanta "oya canye"
fito da ido tayi cikin shagwaba tace "haba duk ni kad'ai ina zan iya ni bana ma jin yunwa"
harararta yayi sannan yace "kema kin san wasa kike"
kafin tace wani abu har ya matsu ya d'auketa ya d'aurata kan cinyarsa da lallashi da ban baki ya samu taci abinci sai da ya tabbatar ta k'oshi sannan ya k'yaleta ruwan wanka ya kaimata
yace taje tayi wanka bayan ta shiga shima yaci abincin tana fitowa ya bata rigar barci cikin kayan da Lawal ya shigo dasu
shima wankan ya shiga ya barta tana shiryawa
rigar iya karta gwaiwa k'aramin hannu take dashi bayan tasa ta d'aura Zane sannan tasa hijab
zama tayi kan katifa tayi tagumi tana jin kewar Aunty da Dady koda wasa bata tab'a kawu wa aranta watarana zata samu matsala mai girma da Dady Yaya Saif
da zaisa su nisanta Kansu da ita suyi fushi da ita haka ya Allah ka sassauta zukatan su Dady su daina fushi dani
lumshi idanunta tayi ba tare da ta damu da hawayen da ke bin fuskarta ba
Al'amin da fitowarsa kenan ganin yanayin da take ciki duk sai yaji ba dad'i cikin sanyin jiki ya shirya cikin kayan barcci sannan ya rufe masu k'ofa
har ya zauna kusa da ita bata sani ba sai da taji ana cire mata hijab ta jiyo firgici ganin shine yasa ta ajiyar zuciya
ta turo baki cikin shagwaba tace "o o kabar mun hijab d'ina sanyi nakeji"
"o o nik'i idan sanyi kikeji inada abun lullub'a" ya kwai kwaye muryarta ta b'oye fuskarta cikin hijab tana murmushi
da wayau da lallami ya cire mata hijab da zani ya barta da rigar barcci ya sata k'irjinsa ta lafe tamar 'yar baby ba ajima ba barcci yayi awun gaba dasu cikin yanayi mai dad'i.
washe gari sunayin sallah asuba ta koma barcci kafin ta tashi har ya gyara gida ya had'a masu abun kari zai shiga wanka ta farka zaunawa yayi kusa da ita yana kallonta cikin k'auna
yace "sannu Aishana kin tashi"?
zamewa tayi daga kan katefa zata gaishe shi yayi sauri janyota ta fad'a jikinshi kunninta ya lalubu ya kai bakinsa yana hura mata iska ahankali
tsikar jikinta taji tana tashi tsam jin halshansa na yawu cikin kunninta cikin wani irin salo yasa jikinta ya fara disko lol😜
sai da yagama kashe mata jiki sannan ya k'yaleta ya kai fuskarsu ya had'i guri d'aya yana gugan hancinsa da nata yace
"Aishana ina sonki tsakanin jiya zuwa ban san ya zan kwatanta maki irin farin cikin da nake ciki ba duk da aurenmu yazo awani yanayi,
ina matuk'ar godewa Allah da ya bani ke da narasa ki ban san wani yanayi zan shigaba Aishana *KAR KI GUJE NI*duk rintsi"
rungumeshi tayi cikin shauk'i tace Al'amin d'ina farin cikina bazan tab'a guje maka ba har abada fatana na rayu dakai ba anan duniya kad'aiba har Aljanna fiddausi"
cikin jin dad'i yace "Allah ya amsa mana tashi muje muyi wanka"
k'waci jikin ta tayi tashige cikin zanin da suka rufa dashi tana dariya k'asa k'asa tace "o o nidai idan kafito zanyi"
binta yayi yana k'ok'arin k'waci zanin tak'i ai kuwa ya hau yimata chakulkuli ba shiri ta sakar masa zanin tana dariya d'aukarta yayi suka shiga wanka sai b'oye fuskarta take ak'irjinsa saboda kunya.
bayan sun fito ya bud'i jikka kayansa ya d'auko mata wata duguwar Riga bak'a mai kyau ya bata ta karb'a fuskarta d'auki da mamaki
murmushi yayi kafin yace "kina mamakin me ya had'ani da kayan mata ko?" bai jira amsarta ba yaci gaba da Magana "matar yayan Lawal ke sayar dasu ranar munje gidan nagansu sun mun kyau na saya maki guda ukku ina fatan sun maki"
da fara'a tace "sosaima nagode Allah ya k'ara bud'i"
bayan sun gama karyawa yace "Aishana zan fita amma ba dad'ewa zanyi ba"
"to yaushi Inna zata dawo"?
"na manta na fad'a maki d'azun kina barcci munyi waya da ita tana gaisheki da yamma zata dawo"
"an haihu ne"?
"eh da asuba aka haihu ansamu 'ya macci"
"Allah yaraya"
"amin karki damu ba dad'ewa zanyi ba kinji"?
cikin k'arfin hali tace "Allah ya tsari ya dawo da kai lafiya"
cikin jin dad'i yace "amin Aishana ki kularmun da kanki sai nadawo".
bai jima da fita ba Inna tadawo da farin ciki Bety ta tarbuta "Inna Sannu da zuwa"
"yawwa Humaira ya zaman kad'aice"?
Murmushi tayi batace komai ba sai bud'e d'akin Inna da tayi
Inna tace "ba zama zanyi ba bari na watsa ruwa tukunna ko naji dad'in jikina"
"to Inna bara na kai maki ruwa"
"Aa barshi nagode"
"Haba Aa Inna ki bari na kai maki"
duk yanda Inna taso hanata tak'i sai da tad'ibi ruwa takaimata Inna tashiga wanka tana tasa mata albarka.
12:30Pm Al'amin suka dawo tare da Lawal da kaya nik'i nik'i yara sun shigo da wasu kayan lokacin Bety tana kwanci jikin Inna suna fira
shiguwarsu ne yasa ta tashi tana masu sannu da zuwa tare da karb'ar kayan dake hannun Al'amin
wanda yake ta kallonta cikin k'auna da farin cikin yanda ya tarar da ita da mahaifiyarsa
bayan ta ajiye kayan ta d'auko ta barma ta shimfid'a masu sannan ta d'ebu ruwan randar Inna ta kawo masu
"sannu Aishana yayi magana ahankali yanda ita kad'ai za taji
murmushi tamasa tare da komawa gurin Inna ta zauna
bayan sun gaisa da Inna yake nuna mata sayayyar da yayu kayan abinci ne da kayan kitchen da risho
sai akwati d'aya da take mak'il da sutara da kayan kwalliya dai dai k'arfin talaka yaba Inna wata leda atamfa da les ne aciki ya saya mata
Inna sosai ta yaba tana ta samasu albarka.
Lawal bai jima ba yayi masu sallama bayan sunsa kayan d'aki
Al'amin ma d'aki ya shiga Inna ta kalli Bety da take wasa da zoben hannunta tace "Humaira tashi kibi mijinki"
"to" tace cikin jin kunya ta wuce d'aki tana zuwa ta tarar dashi kwanci ya rufe fuskarsa da tafukan hannunsa
tana zuwa ta kwanta ak'irjinshi rungumeta yayi cikin shauk'i yace"ai na d'auka bazaki zo ba"
hannuta takai fuskarsa tana wasa da sajan fuskarsa da ya kwanta tace "ai ban isa ba sannu da k'ok'ari nagode sosai Ubangiji Allah ya saka da Alkhairi Allah ya k'ara bud'i"
"amin Aishana nagode da kika yaba"
tashi zatayi yasaki rungumeta yana fad'in "ina zaki"?
"zan kawuma abinci ne"?
"Inna tayi girki ne"?
"Aa Faruk ne ya kawu daga gidansu Yaya Lawal"
"Allah sarki angode kinga ina can inata tunanin na barki da yunwa Allah Allah nake mu dawo gida na dafa maki ko Indome Allah ya saka masu da Alkhairi"
"Amin".
da daddare ma sai da Inna ta kurata da k'yar ta tafi dan harga Allah tana jin kunyar Inna
tun adaren take ta yimasa kukan Dady da Aunty da k'yar ya lallasheta da Alk'awarin gobe za suje.
washe gari bayan sunyi sallah ta fito ta gaida Inna sannan ta taya Inna suka gyara gidan duk da Inna ta hanata amma tak'i
ita ta had'a masu abun kari wainar k'wai ta masu sannan ta dafa masu ruwan te sai da ta kaiwa Inna da Faruk nasu sannan ta kai nasu d'aki
tana ajiyewa ya janyota jikinsa yana mammatsa mata jikinta sai sannu yake mata cikin tausayi ganin tayi aikin da bata Saba ba.
ba halin ya taimaka mata tunda Inna na nan ko afuska bata nuna masa tagaji ba haka sukayi karin kumallo cikin tattalin juna
banyan sunyi wanna sun shirya ya fita ita ta zauna gurin Inna.
bayan sallah isha ya aro mashin d'in Lawal ya d'auketa suka nufi gidansu Bety koda ya fad'awa Inna inda zasu bata hana ba sai adu'an da taraka su da ita.
abunda suka tarar ya matuk'ar d'aga masu hankali.
_mai k'aunar Ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KAR KA GUJE NI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌸
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*LALE MARHABABIKI YA IBNATEE Ubangij Allah ya raya mana ke bisa sunna*
*FNS ina mai baku hak'uri na jina shiru da kukayi sabgogeni suka mun yawa amun afuwa*
*1020 to 1030*
Jikinta ya fara rawa tana so ta k'waci kanta sai dai gangan jikinta sunk'i su bata had'in kai sak'onni ya shiga aika mata
Al'amin jikinsa ne ya fara shock d'aurata yayi kan katefa ya mirgina kanta inda yayi mata rumfa da faffad'an k'irjinsa
nan ya shiga aika mata sak'onnin soyayya ga baki d'aya sun fita hayyacinsu sun jima a cikin yanayi na shauk'i
kafin daga bisani ya mirgina gefe yana maida numfashi idanunsa a lumshe
Bety ta runtsi idanunta tana jinta wani iri d'aya gefen wata irin kunyar Al'amin takeji
hannunsa ya kai ahankali ya janyota jikinsa ya rungumeta yana sauki ajiyar zuciya
d'ago fuskarta yayi yana so su had'a ido tak'i yarda sai b'oye fuskarta take ak'irjinsa dariya yayi marar sauti kafin yace
"Aishana ba dai kunyata kikeji ba amma ba laifinki bane laifina ne da nabarki da ita zanyi k'ok'ari nacire maki ita"
komai takasa iya cewa da shi sai murmushin da takeyi.
da dare bayan sun shige barcci ya umurceta da ta yo alwala cikin sanyin jiki tace "ina da Alwala kumafa nayi sallah"
murmushi yayi kafin yace "eh nasani"
bata sake cewa dashi komai ba nan ya jasu jam'i sukayi nafila cikin kuyarwar Ma'aiki S.A.W ga dukan sababbin ma'aurta ya jima sosai yana masu adu'a bayan sun shafa yayi mata tambayoyi gami da addini Alhamdulillah tabashi amsa dai dai baiyi wani mamaki ba sanin yanda take da sun ibada kuma tana koyawa Faruk karatunsa,
bayan sun gama cin gasasshiyar kaza da madara mai sanyi sunkayo burush Al'amin ya shiga wanka
Bety da dama tun bayan magrib tayi wanka k'ara shafi jikinta da turaruka tayi sannan ta d'auko rigar barcci marar nauyi tasaka ta d'auko zumbulilin hijab tasaka
kwanciya tayi rub da ciki tare da lumshe idanu zuciyarta
sai lugude take yau kam wannan rawar jikin da Habibi keyi tasan yau sai yanda Allah yayi da ita
yana fitowa ban d'aki idanunsa suka sauka kanta ganin hijab d'in da tasaka sai ta bashi dariya murmushi kawai yayi ya cigaba da shirinsa,
hawowa yayi kan katefa ya d'ura rabin jikinsa abayanta yana lek'in fuskarta cikin muryarsa mai dad'i yace
"Aishana wannan hijab d'infa bakya jin zafi?"
cikin shagwab'a tace "eh ni zafi nake j... au sanyi zance"
ta k'arasa maganar tana rufe baki da hannunta
dariya yayi yaja hancinta kafin yace "shikenan ai kin riga kin fad'i gaskiya"
cikin dabara yaciri hijab d'in yana tsokanarta da wasanni su Bety fa ido ya fara raina fata lo😜
ni dai daganan na rufu masu k'ofa dan kar idona ya ganemun abunda yafi k'arfin ganinsu.
tun adaren ya taimaka mata ta zauna cikin ruwan zafe sai kuka da shagwab'a take masa shikuwa ya biye mata sai lallab'ata yake da samata albarka
bayan sunyi wanka ya sauya masu zanin gado sannan suka kwanta rungume take ak'irjinsa tamkar zai maidata ciki wani irin sonta yake k'ara huda zuciyarsa da jinin jikinsa sai k'ara godewa Allah yake da ya mallaka masa Bety amatsayin matarsa
duk da azabar da tasha hakan baisa ta tsani Habibinta ba saima soyayyarsa da take k'araji da farin ciki yanda take ta samun Albarka da kalaman soyayya masu tsada daga gun Habibi.
tun k'arfe hud'u ya tashi ahankali ya zame jikinsa dan karya tasheta zanin gado ya wanki ya shanya a k'ofar toilet sannan yayo wanka tare da d'auro alwala
bayan yayi nafila ya zauna yana karatun k'ur'ani sai da akayi kiran farko sannan ya tasheta.
bayan sunyi sallah asuba ta kwanta akan darduma tayi filo da cinyoyinsa cikin kulawa da k'auna yace "sannu Aishana barccini" idanunta alumshi ta girgiza masa kai
gyara mata kwanciya yayi ajikinsa yana lallab'ata har tayi barcci.
bayan ya gama lazaminsa ya kwantar da ita kan katefa sannan yafita
d'aki ya tarar da Inna bayan sun gaisa take tambayarsa Bety cikin jin kunya yace "ai bata da lafiya ne shiyasa bata fito ba"
"ayya Allah ya bata lafiya"
"amin Inna bara naje nai mana abun karin kumallu"
"haba Al'amim barshi kawai nayi ji ka kula da matar ka"
zaiyi magana tace "bana son musu" tashi yayi yabar d'akin cikin jin kunya yana susa kansa ko bata fad'a ba yasan Inna taganu abunda yafar.
yana zuwa ya kwanta tare da janyota jikinsa ba ajima ba barcci yayi awun gaba dashi.
zaman nasu gwanin sha'awa soyayya aminci da girmamawa ne atsakaninsu rashin aikinsa bai hana suka rasa cima mai kyau ba cikin taimakon Inna da Aboki nagari Lawal
bayan wata d'aya yasamu aikin gini ta hanyar wani mak'wacinsa duk da aikin mai wahalane haka ya jure saboda Inna da Bety
ko sati biyu da fara aikin baiyi ba aka koreshi duk akan maganar farko hankalinsa ya matuk'ar tashi shikam waye wannan me yamasa yake masa bita da k'ulli?
tambayar da yayi ta yiwa kansa kenan yarasa mai bashi amsa.
sau biyar yana neman aikin hannu sai yasamu har yafara mura sai akure shi
haka yau ya dawo gida ransa ajaguli sanadin kurarsa da akayi wajan 'yan walda da duka baifi sati d'aya da samun aikin ba
yau ya fita da zummar yasamu 'yan canjin ya kai Inna asibiti da jiya ta wuni da zazzab'i mai zafi yau dai ko da ya barta da sauk'i
sai dai ya fita da k'udirin idan ya dawo ya kaita asibiti sai ga wannan bak'in cikin ya sameshi duk da nisan da suke dashi daga gurin 'yan walda zuwa Unguwarsu haka ya taku sayyada zuwa gida
dan dama d'are ya tashi dasu canjin cefanin da yayo masu da zai tafi ya hau acab'a.
haka ya k'arasu gida agajiyi gashi ya kwasu k'ishin ruwa dan yau ana tsuga rana agarin Kaduna
abun da ya gani k'ofar gidan ya matuk'ar d'aga masa hankali jikinsa yayi sanyi har ya kasa d'aga k'afansa daga gurin da yake tsayi.
*FNS kuyi hak'uri da wannan nayi bak'i shiyasa ban samu nayi maku da yawa ba*
_mai k'aunar ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KAR KA GUJE NI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌸
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*1030 to 1040*
Tun bayan fitarsa jikin Inna ya tashi Bety tana gefenta cikin damuwa sai sannu take mata
cikin jin jiki Inna ta rik'e hannun Bety tace "Aisha kiyi hak'uri da sauyin rayuwar da kika sami kanki ki rik'i mijinki karki barshi duk runtsi Aminullah maraya ne baida Uwa bai da Uba"
cikin firgici Bety tace "Inna kefa wacece agareshi"!?
Murmushin k'arfin hali tayi kafin tace "Karki tashi hankalinki Aisha nima mahaifiyarsa ce amm...
tarin da ya tarnik'ita ne ya hanata k'arasa maganar ta sai sannu take mata cikin sark'ewar murya tace "Allah yayi maku albarka ya albakaci aurenku da zuri'a mai albarka"
daganan ta fara Kalmar shahada Bety da take tallabi da ita taji Inna duk ta saki ga wani irin nauyi da taji ta mata
kuka tafashi dashi itakam duk a tunaninta zafin ciwo ne yasa Inna bata ko iya motsa jikinta
ahankali ta zame jikinta ta kwantar da Inna akan shimfid'a tana tunanin yanda zatayi wa zata kira?
tana haka sai ga matar Baffa Baba Furaira tazo cikin mamaki Baba Furaira tace "Aisha lafiya kike kuka ina Innar Al'amin"?
cikin Kuka Bety tace "tana d'aki kwanci bata da lafiya sosai kuma gashi Yaya bayanan"
"Subahanalillah muje d'akin tun yaushe ne bata da lafi... kasa k'arasawa maganar tayi lokacin da idanunta ya kai inda Inna take kwanci
cikin sauri ta k'arasa bakinta d'auki da salati bayan ta duba Inna da kyau sai ta hau " *Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un* shikenan Inna antafi gidan gaskiya"
"iye Baba mutuwa fa kike nufi"!!
Bety tayi maganar da k'arfi
jin Baba na kuka ta kasa bata amsa yasa ta sulali k'asa tana wani irin kuka gwanin tausayi.
Baba takira Baffa ta waya ba ajima ba sai gashi yazo cikin tashin hankali anta kiran wayar Al'amin bai d'aga ba abun da basu sani ba ya manta wayar gida shima kawu ba ajima ba yazo
cikin d'an k'ank'anin lokaci aka shiryata da taimakun mak'wabta.
sanda Al'amin ya k'arasu k'ofar gida yaga jama'a wasu suna tsaitsaye wasu na alwala
wannan yasa yaji ya kasa d'aga k'afansa zuciyarsa ta tsinki Kawu ne ya hangoshi ya tahu gurinsa "sannu Al'amin ka dawu"?
cikin rawar murya yace "Kawu me ke faruwa"?
rik'o hannunsa Baffa da ya k'arasu yayi yana fad'in "mushiga ciki Al'amin"
haka ya dinga bin Kawu har cikin gidan inda yaga mata zazzauni masu kuka nayi masu tagumi nayi
har d'akin Inna cikin tausayawa Kawu yace "Al'amin sai dai mu d'au hak'uri da dangana mukumayi imani da duk abun da Allah yayi shine dai dai
*KULLI NAFSIN ZA IKATUL MAUT* dukan mai rai zai d'and'ani zafin mutuwa"
sai da yayi masa nasiha sosai kafin ya sanar da shi Rasuwar Inna
fad'ar irin tashin hankalin da Al'amin ya shiga bakina ko alk'alamina ba zasu iya ba.
wunin ranar zukata ba dad'i Bety ranar sam batasa Al'amin a idonta ba sai dare
tana kwance d'akinsu haryanzu kuka take idanunta duk sunyi hushi kanta na mata ciyo yau komai ta kasa sawa cikinta dukuwa da lallashi da banbaki da su Baba sukai mata
bak'aramin jin mutuwar Inna tayi ba tana jinta tamkar mahaifiyarta
sam bataji shigowarsa ba sai jin hannunsa tayi abayanta cikin sauri ta tashi fad'awa tayi jikinsa tana k'ara fashewa da kuka
rungomota yayi shima yana zubar hawaye da k'yar ya iya had'iye kukansa ya fara magana ahankali cikin lallashi yace "yi hak'uri Aishana kukan ya isa haka adu'a Inna take buk'ata agurinmu kukan bashi da amfani"
da kyar ya samu ya lallasheta ta daina kukan tashi tayi ta d'auko filaks d'in ruwan zafe da kayan tea wanda duk suna cikin sayayyar da yayo masu jiya
tea ta had'a masa mai kauri ta matsa kusa da shi ta nufi bakinsa da Cop d'in "Habibi nasan bakaci komai ba kasha tean sai na kawuma abinci"
rik'i hannunta da take rik'i da tean yayi ya kai bakinta yana fad'in "nasani kema ba komai kika ci ba"
haka suka ciyar da Kansu sai da suka k'oshi sannan suka kwanta barcci yak'i d'aukar su sai tunani da kowaninsu keyi alwala suka je suka yi suka fuskanci Ubangiji dan nemawa Inna da dukan musulmi rahama agun Mahaliccinmu.
*BAYAN WATA D'AYA*
ahankali suka fara sabawa da rashin Inna Faruk ya koma gun Mahaifinsa duk da Al'amin yaso abarmasu shi uban yak'i
sosai yanayin rayuwar ya sauya masu abincin da zasu ci yana neman gagararsu ya rasa aikinyi wannan na matuk'ar d'aga masa hankali ba kansa yakeji ba Bety
yana matuk'ar tausaya mata yanda tasaba rayuwar jin dad'i da hutu bata san babu ba abunda da tafi k'arfinsa
yau shine yafi k'arfinta.
Bety tun tana wahala na rashin irin cimar da tasaba har yazame mata jiki dai dai da rana d'aya bata tab'a nuna masa gazawarta ba sai zallar k'auna da tausayi da take nuna masa hakan ya k'ara k'aunarta da k'ima azuciyar Al'amin.
kwanci yaki daga shi sai vets da wando 3kwata ya rufe idanunsa tunani yake ina zai samu wa Bety abunda zatayi kari yau ko kwabo bai tashi dashi ba
har ta zauna dab dashi bai sani ba hannunta takai fuskarsa tana shafa sajen da yake kwanci afuskarsa gwanin sha'awa cikin damuwa tace
"Habibi nasani ba barcci kake ba bana son ina ganinka cikin damuwa da tunani Allah baya d'aurawa bawansa abunda yafi k'arfinsa
dukkan d'an adam da kalar jarabawarsa mu tamu jarabawar kenan muyi fatan mu cinyeta muyita rok'on Ubangiji da kaimasa kukanmu,
nasan damuwarka bazai wucini ba har kullum ina fad'ama ina tare da kai da dad'i da babu banda damuwa idan har ina da ita to naganka cikin damuwa"
janyota jikinsa yayi ya rungometa yana jin wutar k'aunarta na k'ara ruruwa azuciyarsa cikin tsantsar k'aunarta yace "Aishana har kullum ina godewa Ubangiji da ya mallaka mun ke a matsayin matata hak'ik'a kin kasance macce tagari irin wacce Annabi S.A.W ya kwad'aitar damu da mu aura,
kinzamu mun macce tagari idan ina cikin damuwa kallonki kad'ai ya kan gusarmun da damuwata kikan sakani farin ciki da murmushinki kin bani dukan soyayyarki cikin gaskiya da amana,
Aishana banda bakin yi maki godeya Ubangiji Allah yayi maki Albarka Allah yasa ki zamu Uwar 'ya'yana kikasan ce matata har a Aljanna Fiddausi ki kasance shugabar matana na Aljanna"
cikin tsantsar farin ciki ta amsa da "amin mijina farin cikina abun alfaharina"
sallama sukaji anayi k'ofar gidan Bety tace "Habibina kamar muryar su Baffa"
"eh nima kamar shi naji d'auko mun rigana"
"to" ta fad'a tare da tashi tsayi bayan ta d'auko tasa masa yayi mata kiss a goshi sannan ya fita.
"ah Baffa kawu sannunku da zuwa ku shigo daga ciki kun tsaya awaje"
"haba bakomai nan d'inma yayi ya iyalin naka"?
"lafiya k'alau bari na d'au ko maku shimfid'a" komawa yayi cikin gida ya d'auko masu tabarma bayan sun zauna suka saki gaisawa Kawu yace
"to Aminullah bakomai ne ya kawumu gurinka ba sai maganar gidannan da kake ciki sanin kanka ne gida ya zama na magada kuma Inna bata da magadan da suka wuce ni da kuma Baffa gashinan zauni
saboda bata bar d'a ko d'aya ba, mune 'yan Uwanta kuma shak'ik'anta ko ba haka ba Baffa"?
Baffa ya gyara zamansa kafin yace "sosai kuwa sanin kanka ne bayan alak'a ta musulunci da rainunka da tayi tun kana d'an k'ank'ani bayan wannan ba wata alak'a ta 'yan uwan taka ko zumunci,
to atak'aici dai muna buk'atar gida mun Baka nan da kwana biyu rak ka tashi kabamu gida muna kuma fatan zaka mana kyakyawar fahimta"
Al'amin da tunda suka fara maganar kansa yaki aduni zuciyarsa na masa suya idanunsa har sun sauya kala d'aguwa yayi ya kallesu cikin girmamawa yace "to Kawu Baffa na fahimce ku Insha Allahu zanyi k'ok'ari na baku gidan cikin lokace nagode sosai"
"yawwa d'an albarka ai mune da godeya da ka fahimce mu"
daganan sukai masa sallama suka wuce suka barshi zauni cikin tashin hankali da rashin madafa.
_mai k'aunar Ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
Fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KAR KA GUJE NI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌸
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*HAK'IK'A BA ABUN DA ZAKA SO KAYI FARIN CIKI FACE RASULU S.A.W SON SANE HAK'IK'ANIN K'AINA BEGENSA NE HAK'IK'ANIN SHAUK'I ALLAH YA BARMU DA K'AUNAR MA'AIKI S.A.W DARE DA RANA ZAFI DA SANYI AKOWANI YANAYI AKOWANI LOKACI DUK BUGUN NUMGASHI DUK GUDANYAN JINI.DANGE ANNABIN DAI*
*140 to 150*
Ya jima zaune yana sak'a da warwara sai dai ya rasa mafita haka ya tashi ya nad'e tabarma ya shiga cikin gida.
tana kwance tana game da wayarsa taga ya shigo jikinsa asanyaye da saure ta ajiye wayar ta mik'e tsaye tana tambayarsa "Habibi lafiya na ganka haka me ya faru"?
rik'e hannunta yayi suka zauna kan kujera d'aura kansa yayi kan kafad'arta ya lumshi idanunsa hannunta ta d'aura kansa tana wasa da sumar kansa
ba tare da tace dashi komai ba ya jima ahaka ganin yak'i
yayi magana yasa cikin sanyin murya tace "Habibina kasani adamuwa fa wai me ke faruwa ko wani ne bashi da lafya ko mutuwa akayi"?
ajiyar zuciya yayi kafin yace ba ko d'aya Aishana zan fita ki tayani addu'a kinji karki damu"
ya k'arasa maganar yana murmushi dan kawar mata da damuwar da yagani kwance afuskarta
taimasa Allah ya tsare ya bada sa'a ba dan ta gamsu da ba komain ba.
bayan layinsu yaje shagon Sani ya sayar da wayarsa zatayi dubu d'are Yayan Lawal ya saya masu iri d'aya dawowarsa Dubai amma yanzu da k'yar yasamu aka saya dubu talatin yana karb'ar kud'in yaje yayi masu sayayyar abinci dai dai k'arfinsa
ya bawa Walid mak'wabcinsu ya kai masa gida daganan ya hau acab'a zuwa kasuwar barci har bakin gurin da Kawu yake sana'arsa aka ajiyeshi.
bayan sun gaisa cikin rashin sakin fuska Kawu yace "Aminu lafiya dai ko"?
gyara tsuguninsa yayi kafin yace "lafiya k'alau Kawu dama alfarma nazo nema gurin....
cikin sauri Kawu ya katseshi ta hanyar d'aga masa hannu "kaga Aminu idan dai kan maganar gida ne karka ma suma dan ba zaiyu mu barma ba baka da gadonsa ba zumunci atsakaninmu sai taimkon da marigayiya tama ihin"
cikin jan numfashi yace "hakane Kawu nasani ba wai ina nufin zaku barmun kyauta bane Aa zaku mun alfarma ne kubani haya ne har zuwa sanda Allah zai hore mun sai na tashi"
Kawu ya d'anyi jim kafin yace "to naji zamuyi shawara ko me kenan zan neme ka"
"nagode sosai Kawu" daganan sukayi sallama.
tasha ya nufa ya dingayin dako da zarar motar matafiya ta tsaya zai zo ya d'auki kayansu zuwa gurin ababin hawa ko bakin titi har idan lokacin Sallah yayi jam'i baya wuce shi sai yamma lik'is yanufi gida.
gajiyi ya isa gida yana zuwa ya fad'a kan katifa yana "wash Allah"
kallonsa tayi cikin tausayawa tace "Sannu Habibina"
lumshi idanunsa yayi kafin yace "yawwa Aishana ya gidan"?
"lafiya k'alau Habibi" ruwan randar Inna masu sanyi ta d'ebomai sannan ta kawo masa abinci
tashi zauni yayi yana fad'in sannu Aishana Allah yayi maki albarka"
"amin Habibi" kallonsa ta dingayi yanda yake cin abin cin gwanin tausayi
bayan ya gama ci ta kai masa ruwan wanka.
bayan Sallah Isha yana kwance tana masa tausa tace "Habibi amma yau tunda kafita bakaci komai ba ko"?
murmushi marar sauti yayi kafin yace "me kika gani Aishana"?
"yanayin ka ya nuna mun hakan"
mirginawa yayi yana kallonta yace hasashen ki ne kawai"
"Hum Habib... "kiyarda dani" ajiyar zuciya tayi kafin tace "Habibina munga kayan abinci mungode Ubangiji Allah ya k'ara bud'i da lafiya"
"amin Aishana" yayi maganar yana mai janyota jikinsa bakinsa yakai cikin bakinta ya dinga aika mata sak'wannin soyayya duk k'ok'arinsa na kawar da dukan wata tambayar da yasan zata iya yimasa daganan aka fad'a sunnar Ma'aiki S.A.W. wannan kenan
*kuyi hak'uri da wannan banda lafiya I love you all FNS*
_mai k'aunar Ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
Fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KAR KA GUJE NI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌸
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*Soyayya wacce ba juya baya ba danasani ba kaicu sai tsantsar farin ciki da annashuwa samun natsuwa itace Soyayyar Annabi MUHAMMAD S.A.W dangi mu saki kowa mukama Annabi da iyalan gidansa da jikukinsa dangi Annabin dai*
*150 to160*
Washe gari da wuri ya shirya ya bar gida gurin wani Abokinsa yaje ya koyi sa'a ya tarar dashi yana wankin mashin d'insa bayan sun gaisa yace
"Al'amin ya garin kwana biyu ka b'uya daga kai har Lawal" Al'amin dake jingina jikinsa da kusurwar gidan yasa hannun shi d'aya cikin aljihu
yayi murmushi kafin yace "wallahi lafiya k'alau Alhamdulillah Lawal yayi tafiya shiyasa kadaina ganinsa"
"au kardai kace mun tafiyar sa Abuja ta tabbata"
"eh wallahi Amma dai bazai jima ba zai dawu"
"bai samu aikin bane"?
"yasamu akwai abun da zaizo yayi sai ya koma ga ba d'aya"
"Allah sarki gaskiya namasa murna Allah ya taimaka muma Allah yasamu a danshin sa"
"Amin summa amin Sagir nazo ne na tambaye ka ko zaka mun hanyar da zan samu Mashin na dingayin acaba"?
"ah sosai ma kuwa akwai wani da naji yana neman wanda zai dinga yi masa haya da mashin saboda wanda ke masa bayada gaskiya wannan yasa ya karb'i mashin d'in idan dai har zaka iya baka da matsala"
cikin farin ciki yace "ai dan zan iya na nema nagode sosai Sagir"
"haba Al'amin ba komai ai ana tare"
sun d'an tab'a hira kafin sukayi Sallama da juna.
da ganan yaje gurin 'yan buga bugansa sai magarib ya dawo gida kai tsayi masallaci ya nufa sai da akayi Isha sannan ya shiga gida.
Bety tun fitarsa take kwanci sam bata jin dad'in jikinta kwana biyu haka take wuni da zazzab'e da tashin zuciya
haka take jure wa ta gyara gidan idan
da akwai abun da zata girka tayi komai cikin dauriya take yinsa
yauma hakan tayi sai dai yau wahalce ta wuni komai takasa ci ko k'amshin abincin bata so haka tayi girkin tana amai
da k'yar taga ta gama sannan tayi wanka ta shirya cikin k'ananan kayan da Lawal ya sayo mata ita da Al'amin (Allah ka had'amu da Abokai na gari)
tana jin Sallamarsa tafito da gudunta tana zuwa ta fad'a jikinsa shima da murnar sa ya rungumeta yana kiss d'inta.
bayan sun natsu yayi wanka yaci abinci yake fad'a mata ya samu mashin gobe da safe zai fara fita kamar yanda Sagir yakira ya fad'a masa
sosai tai murna da Adu'an Allah ya sanya Alkhairi da albarka aciki.
su Kawu sun amince zasu bashi haya amma da alk'awarin zai dinga biyan kud'in haya cikin lokaci.
acikin d'an k'ank'anin lokaci abubuwa suka sauya musu sosai Allah ya san yawa sana'ar albarka.
Bety yau ta tashi da ciyon kai sosai ko d'aga kan bata iyayi hankalin shi ya matuk'ar tashi haka yaje yasamu adai daita sukai asibiti
bayan tambayoyi da aune aune aka tabbatar da tana da juna biyu
wai zo kuga murna gun Al'amin kamar ba gobe sai Hamdala yakewa Ubangiji magani suka rubuta mata sannan suka sallameta.
soyayya ce da tsantsar kulawa Bety take samu gun Al'amin wanda zata iya cewa ba maccen da takaita sa'ar miji.
watansa d'aya da fara acab'a mai mashin ya karb'i abunsa tare da bashi hak'uri anmasa barazana ne shiyasa ya karb'e ba dan baya jin dad'in aikinsa ba.
ranar haka ya dawo gida zuciyarsa ba dad'i sai dai sam bai bari Bety ta fahimci halin da yake ciki.
washe gari ya kwaso wankenta da nashi ya zauna yanayi kamar yanda yasaba tunda tazo ko pant d'inta bata tab'a wanke wa ba, shi ke wanke mata duk yanda tayi nacin ya barta tayi hanata yakeyi
tana zauni kan kujera tsugune ta d'aura kanta a kafad'arsa tace "Habibi yau bazaka fita bane ka d'auko wanke"?
"uhm yau ina so na zauna da iyalina idan kuma Aishana bata buk'atana to sai nasan gurin zuwa"
ya k'arasa maganar cikin tsokana dariya marar sauti tayi kafin tace "lallaima ai ni bank'i muyita zama tare karka fita ko ina har Illah Masha Allah ba"
matsi rigar da ya wanke yayi ya ajiye cikin wani bokiti kafin yace "Aishana matata Uwar 'ya'yana in banda abunki idan ban fita ba me zamuci da kuma me zamuyi d'awainiyar kanmu da na yaranmu idan Allah ya kawomana"?
far tayi da idanunta kafin tace "Soyayya zata ishemu komai"
kallonta yayi cikin shauk'i yace "Allah Aishana"
"Allah kuwa Habibina"
"nayarda Aishana Allah ya barmu tare har a Aljanna fiddausi"
"Amin Habibina Mijina Uban 'ya'yana".
rashin aikinyi yasa Al'amin ya koma ma buga bugarsa har watarana ya yanki shawarar zai fara sana'ar sai da gwanjo ya nemi shawarar Bety ta k'arfafa masa gwaiwa
ya had'a 'yan kud'ad'ansa yayi jari dasu alhamdulillah Allah ya san yawa sana'ar Albarka.
cikinta nada wata bakwai abubuwa suka fara ja baya yanzu sam babu ciniki watarana haka zai dawo gida ba cinikin ko sisi
bangarin abinci kuwa watarana sukan samu su dafa sau d'aya awaini shinkafa fara da mai ko ya sayo masu dawa ko masara suyi tuwo tun bata iya ci har tasaba.
wani lokacin da kyar yake samun kud'in da zai sayo mata abincin da zatace baya ta kansa idan dai taci to falillahi
dai dai da rana d'aya bata tab'a nuna gazawarta ga sauyin rayuwar da ta tsinci kanta ba hakan ya kan matuk'ar k'ara masa soyayyarta da tausayinta aransa.
kwana ukku kenan yanda ya fita haka yake dawowa ko taro bai samun ba
sai dai ya ciyo bashin garin kwaki da k'ule ayi kwad'o
kantin Hamisu ya shiga bayan sun gaisa yace "Malam Hamisu dan Allah adai k'ara hak'uri damu abani shinkafa gwangwani d'ayaya da mai na naira hamsin Insha Allahu zanyi k'ok'ari na kawoma kud'inka gaba d'aya"
cikin rashin walwala wanda aka kira da Malam Hamisu yace "gaskiya kayi hak'uri Al'amin bashinnan yafa yi yawa naira dubu nake binka kusan sati biyu kuma yanzu kazo na dad'ama wani
Aa gaskiya da sake inama laifin ace ka rage bashin ne amma baka rage ba kace na k'arama idan dai ba so kake ka karyani ba mu taru mu zama d'aya"
Al'amin cikin damuwa yace "dan Allah Malam Hamisu kayi hak'uri wallahi ina nan ina k'ok'ari naga kud'in sun samu na biyaka kud'in ka amma ba fatana na b'atama jari ba kataimaka mun dan Allah"
"aifa sai kayi" ya joya kan wacce tun zuwan Al'amin take tsayi yace "yi hak'uri baiwar Allah me za abaki"
Murmushi tayi kafin tace "ayya bakomai su Malam Al'amin talaucin naku har ya kai ga cin bashin abinci
Allah sarki Bety wallahi har tabani tausayi ko da yaki ai ita tajawa kanta tana cikin gatanta ta fita ta zab'i tsiya
bayan talauci ga rashin asali waya sanima ko shig...
afusaci ya d'aga mata hannu cikin b'acin rai yace "ya isa haka Meenat wai nikam me natare maki ne arayuwa?
kike neman tozartani aduk inda kika ganni bana shiga lamarinki meyasa kike neman shigarmun rayuwa
na rok'iki dan Allah kifita rayuwata da ta iyalina tun baki kaini bango ba"!
cikin shewa tace "ahayye nanayi dama talaka marar asali yana da wani katab'us ne ai wallahi ba abunda ka isa kamun matsiyaci kawai"!
hannu ya d'aga zai mareta ko me yagani sai ya fasa kawai ya juya yabar kantin ba tare da ya kula tijarar da Meenat take masa ba
mai kantin sai hak'uri yake bata da k'yar yasamu tabar kantin.
daga lokacin unguwar ta d'auka Al'amin shegeni baya da asali ba damar ya fita sai a hau nuninsa ana zagensa
yayi kukan zuci yayi na fili harya godewa Allah.
Bety sam batada labarin abunda ke faruwa kasancewar ba fita take ba ko yaushe tana gida Al'amin kuma bai fad'a mata ba
sai dai damuwar da take gani a fuskarsa ta alak'anta ta da rashin sana'ar yine da rashin madafa shiyasa ko yaushe take k'ok'arin kwantar masa da hankali.
tana zaune tsakar gida tana gyaran k'umbar hannunta wata yarinya tashigo "salamu ailaikum wai ance ana wa mai gidannan sallama"
"bayanan ya fita kice waye ne"
"to" yarinya tafita da gudu sai gata ta dawo "yace Lawal ne"
da murnarta tace "ji kice da shi ya shigo"
hijab d'inta da me sarkafi a k'aure ta janyo tana sawa ya shigo da sallamarsa
kujera ya janyo ya zauna suka gaisa cikin girmamawa tace "Yaya Lawal saukar yaushe"?
"Wallahi yanzunnan ko gida banje ba nan na fara zuwa"
"ayya sannu andawo lafiya"?
"lafiya k'alau wai me yasami wayar Al'amin inata nemansa bana samusa"?
"ai wayar ce ta lalace shiyasa"
"ayya to ni zan wuce gida amma anjima zan dawo dan Allah idan ya dawo kice dashi ya jirani"
"to Insha Allahu zan fad'a masa ko ruwa ban kawoma ba Yaya Lawal bari ba kawoma"
"haba karki damu ba komai nagode".
bai jima da fita ba Al'amin ya dawo da gudunta taje gurinsa ta fad'a k'irjinsa rungumeta yayi cikin kulawa tace
"Aishana bakya jin magana ko"?
cikin shagwab'a tace "uhm Habibi me nayi na rashin ji"?
fuskarta ya d'ago suna kallon juna yace ba na hanaki gudu ba ko kin manta yanzu ba ke kad'ai bace"
ya k'arasa maganar yana shafar cikinta b'oye fuskarta tayi cikin k'irjinsa tana murmushi
zaiyi magana yaji ana sallama cikin sanyin jiki ya janyeta tare da yimata kiss a goshi yace da ita yana zuwa bayan ya mik'a mata ledar da ya shigo da ita.
kamar yanda ya zata d'in hakane Baffa ne tare da Kawu "ah Baffa sannunku da zuwa"
"kaga rik'i gaisuwarka ba ma buk'ata kasani ka sab'a alk'awari wata biyu kenan Baka biya kud'in haya ba Dan haka yanzu ba sai anjima ko gobe ba ka tattara inaka inaka kabar gidannan"
durk'usawa yayi cikin muryar Lamar zaiyi kuka ya fara rok'onsu da suyi masa lamuni zuwa sati biyu zai biya su kud'insu
amma fir sukak'i haka ya koma cikin gida zuciyarsa a cunkushi
_Mai k'aunar Ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
Fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KAR KA GUJE NI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌸
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*WA ZAI SO UBA YA K'YALE D'IYA INA BAZAIYU BA SOYAYYA BATA CIKA SAI KASO UBA DA 'YAY'YANSA SAYYADA 'YAR SAYYADI SHUGUBA 'YAR SHUGABA SAYYADA FAD'IMATU ZAHRA BINTU RASULULLAHI S.A W AMUNCE MUN KI YARDA DANI 'YAR MUTAN YABO WALLAHI BANDA ABUN K'AUNA BAYAN ABANKI K'AUNAR SA CE TASA NAKE SON FAD'IMA, BAKI DA ZUCIYA BAZA SU IYA MISALIN TSANTSAR K'AUNAR DA TAKE MUKU BA KI YARDA DANI KISAN DA ZAMANA HAR KULLUM INA TA K'OFARKI SAYYADA INA MAULA NA SANI KYAUTA HALINKI NE GADON KI NE, BA KWA JEKA KADAWO ANAN TAKE KO KE BADA KYAUTA, ZAUNA DA LAFIYA SHALE LE TA ANNABI TAKAWARKI LAFIYA 'YAR SAYYADA SHUGABAR MATA NANA KHADIJA SANNU SANNU JIKA GA SAYYADI ABDULLAH DA AMINA*
*NA GAIDA MAHAIFIYAR HASAN DA HUSAIN LAMUNCE MUN KI RIK'E HANNUNA DA HANNUNKI MAI* *ALBARKA KI KAINE HAR GURIN MAHAIFIN KI DAFA KAINA KI SANYA MUN ALBARKA DA BAKIN DA BAI TAB'A SAB'O BA, IDAN KIN* *YARDA DANI NASA NI ALLAH DA MA'AIKI ZASU YARDA DANI, ALLAH KA K'ARA NARKAR DAMU DA ZUKATAN MU DA RUHINMU DA GANGAN* *JIKINMU ACIKIN SOYAYYAR ANNABI MUHAMMAD S.A.W DA SAYYADA FAD'IMA DA IYALAN GIDANSA DA* *JEKUKINSA SHEHU AHMAD TIJJANI DA SHEHU IBRAHEEM INYES, HAK'IK'A* *KUNE GATANA SHURAFA'U DA* *BAZARKU NAKE RAWA* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃
*150 to 160*
Zaune take ganin yanayin da ya shigo yasa ta saurin tashi tsaye arud'i tana tambayarsa "Habibi lafiya?"
murmushin k'arfin hali yayi kafin yace mata "bakomai Aishana"
ya fad'a yana mai zaunar da ita shima gefenta ya zauna yace "Aishana kin san abaya na fad'a maki yanda mukayi da su kawu ko"?
cikin k'aguwa tace "eh na tuna"
"to yanzu sunzo suna buk'atar na basu gida saboda rashin biyansu kud'i har karo biyu kiyi hak'uri Aishana na kasa rik'eki yanda ya kamata muhallin da zan suka ki yau yana neman ya gagare ne"
ya k'arasa maganar yana mai zubar hawaye
hannun shi ta rik'e cikin nata tana murzawa ahankali ta fara maga cikin natsuwa tace "ka daina fad'an hakan habibi Ubangiji ya sani nima kuma na sani baka gaza da komai ba gurin kula da hakk'ina ta ko wani b'angare
kana iya k'ok'arin ka jarabawa ce da bawa bai isa ya kauce mata ba dan haka karka damu ina tare da kai akowani yanayi
fatana Ubangiji Allah ya bamu ikon canye jarabawar Allah ya kawo mana d'auki alfarmar Annabi S.A.W"
rungometa yayi cikin tsantsar farin ciki yace "nagode Aishana Allah yayi maki albarka Allah ya faranta maki fiye da yanda kika faranta mun"
"amin Habibina yanzu ya zamuyi"?
"tafiya zamuyi Aishana sai dai zaki jira na je na dawo"
"to Allah yasa su d'aga ma k'afa har ka dawo d'in"
"amin"
ya fad'a yana mai tashi tsaye har ya kai k'ofa tace "lah Habibi namanta na fad'a ma Yaya Lawal ya dawo har ya zo bai tarar da kai ba"
cikin farin ciki yace "yaushe yazo"?
"bai jima da fita ba ka dawo amma yace mun zai dawo"
"Allah sarki Lawal zanyi k'ok'ari idan komai ya daidaita na nemeshi"
daga nan ya fice d'aki yana jin wani abun aransa.
yana fita ya tarar da su kawu suna ganinsa Baffa yace "ya naga ka fito ka kad'ai"?
"kuyi hak'uri Baffa a yau d'innan zan bar gidan amma kumun alfarma naje na samu wani gurin sai nazo na tafi da iyalina"
"uhm raina mana hankali dai kake so kayi wani gurin kake da shi"?
"Aa ba zan rainawa iyayena hankali ba gaskiya ne banda wani gurin amma ba a rasa na Allah a ko ina"
"kai dai kasani duk inda zaka ba abun da ya shafe mu ayanzu dai muke buk'atar gida ba sai anjima ba ihen"
Lawal da tun fitowar Al'amin yazo sai dai sam hankalin su bai kai kan shi ba yace "Ku daina tada jijiyoyin wuya Kawu Baffa yanzu zai bar maku gidan
kuma Allah ba azzalumin bawa bane dan kunga k'asa ta rufe idon Inna shine kuke neman Ku tozarta amanar ta
uhm idan dai duniya ce wallahi kuje ta ishi kowa Riga da wando"
daga haka bai safe cewa komai ba ya fad'a gidan yana k'wala sallama
yabar su kawu cirko cirko suna mazurai shima Al'amin bai ce da su komai ba ya bi bayan amininsa.
"Bety Bety kina ina"
cikin sauri ta fito ban d'aki tana fad'in "Yaya Lawal lafiya"?
"lafiyar kenan fito da kayanku mu tafi"
za tayi magana idanunta suka kai kan Al'amin da ya keyi mata alamar tabi umurnin Lawal
kayan sawar su kad'ai suka d'auka sai wata 'yar ma dai daiceyar jaka da Al'amin ya d'auka
har suka shiga motar Lawal magana bata had'asu ba Lawal sai hirarsa yake da Bety
murmushi Al'amin yayi kafin yace "wai mutumin laifin me nayi ake ta shamun k'amshi haka"?
Lawal ya sakar masa harara kafin yace "oho shafa kaji"
dariya Bety tayi kafin tace "ni dai idan laifi mukayi muna bada hak'uri ayi mana afuwa"
"uhm K'yale ni da shi Bety wai duk yanda muki da Al'amin yana cikin wani yanayi da ya kamata ace na sani ya b'oye mun sai dai naji abakin wasu
agurin su Sageer nake jin komai sai gashi ina zuwa ba tarar da su Kawu na masa tijara
kuma da banzo ba shikenan sai dai na shafa naji ba kwanan hakan ya kyauta kenan"?
"Aa gaskiya amma kayi hak'uri"
Al'amin ya karb'e kayi hak'uri Lawal bana so ne na d'aga maka hankali shiyasa na b'oye ma halin da nake ciki"
"hum Al'amin ai babban tashin hankalina nazo na tarar ba kanan ban kuma san inda zan gan ka ba"
"kayi hak'uri ni dai"
"to idan banyi ba dukan ka zanyi"
"idan dai har dukan nawa zai sa ka daina fushi dani ina maraba" yayi maganar yana dariya
nan take aminan suka ware suna hira cikin nishad'i basu jima ba suka isa Malali kai tsayi ya nufi wasu tagwayen gidaje masu kyau da tsari komai iri d'aya
gidan da ke hannun dama yayi hon mai gadi ya bud'e masu k'ofa
bayan yayi pakeng suka fito ya fito da key cikin aljihu ya bud'e masu k'ofa da mamaki suka bishi bayan shi
gida ne mai kyau dai dai misali komai cikin tsari yanayin sa tamkar gidan turawa sai da ya nuna masu ko ina na gidan
farkon shiga babban falo ne sai d'akuna ukku kowani da toilet acikin bedrooms komai wait
babban falon yana set biyu komai na falon yana da ash an bolec reid labulayen ma da tayes duk kala d'aya ne sai kayan kallo irin ba zamani
sai kitchen shima dai dai gwargwadu an k'awata shi da kayan zamani
bayan sun dawo falo Lawal yace "Al'amin ya kaga gidan"?
cikin murmushi yace "gida kam masha Allah yayi kyau gwanin sha'awa"
"alhamdulillah ga key gidan ka ne halat malak kamar yanda ka sane mun yiwa juna alk'awari idan Allah ya hore muna zamuyi tagwayen gidaje zamu zauna guri d'aya za muyi aure rana d'aya
Allah ya cika mana d'aya burin na zama guri d'aya aure ne dai bai nufa muyi tare ba saboda naka rabon yafi nawa zafe"
ya k'arasa maganar cikin tsokana kafin yaci gaba da magana "kuma kamar yanda Yaya ya sama mun aiki a Abuja kaima ina farin cikin shaida maka ya d'auke ka aiki a Sabon kamfaninsa da ya bud'a a garinnan amatsayin manaja
da zai kira ka ya fad'ama ni na hana nace zan zo da kaina na fad'ama Dan na karb'i goron albishir"
daga Al'amin har Baty suman zaune sukayi sun zubawa Lawal idanu ba tare da sun iya cewa da shi komai ba.
*kuyi hak'uri da wannan Muna hidima ne*
_mai k'aunar Ku_
🌺 *Aisha A yabo*🌺
FulaniHy🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KAR KA GUJE NI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌸
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*Jikukin Annabi S.A.W yau gani gaban Ku nayi durk'usu Ku sanya mun Albarka Ku yarda dane Ku Kaine gaban Kakan Ku yasan dani acikin masoyan sa ta hak'ik'a. wallahi shaihanai 'ya'yan Nana fad'ima asoku adace da samun rabo mai d'aurewa har gaban Ubangiji ak'iku atab'e tabewa har ga Ubangiji na gaishe Ku shurafa'u.*
*Allah ya k'ara mana soyayya da kusance*
*160 to 170*
Al'amin tsabar farin ciki rungume Lawal yayi kawai sai ya fashe da kuka "haba mutumin miye haka dan Allah ka daina kukannan bana so"
cikin muryar kuka Al'amin yace Lawal ban da bakin yi maku godeya tun muna yara kuke taimako na Yaya bai banbanta ni da kai ba komai yama yana mun,
Ubangiji Allah ya saka maku da mafificin alkhairin da kuka mun Allah ya biya ku da gidan aljanna fiddausi alfarmar Annabi S.A.W"
cikin sanyin jiki da jinjina aminta irin ta Lawal da Habibin ta tace "amin summa amin Yaya Lawal muna godeya sosai Ubangiji Allah ya faranta maku fiye da yanda kuka faranta mana,
Alhamdulillah Allah mun gode ma"
cikin murmushi Lawal yace "amin na gode da addu'oin ku ni zan tafi gida sai mun had'u anjima"
Al'amin yace "ai ba zaka barni ba tare zamu fita"
"Aa ni baza ka bini ba haka kawai kasa Bety tace nazo na d'auke mata miji kaga har ta fara harara na"
rufe fuskarta tayi tana dariya tace "lah Yaya Lawal yaushe akayi haka"
"yanzu mana"
ya fad'a yana dariya Al'amin yace "Lawal Allah ya shirye ka ni kasan ma me na tuna"
"Aa sai kafad'a" "hahahahaha ranar da wani yaga motoce sabo da tsabar tsoro sai da ya sake..
Key d'in mota Lawal ya jefa masa yana dariya yace "wallahi zan sab'a ma Al'amin"
yana maganar tare da tashi tsaye "madam na gudu tunda mijinki ya kure ne"
haka suka bar gidan suna raha
bayan fitarsu ta sake gyara gidan duk da bai da wani datti sannan ta duba kitchen taga akwai kayan abinci sai ta dafa masu jalof d'in kuskus da busasshin kefe bayan ta kammala girkin tayi wanka ta shirya cikin dogowar Riga ta atamfa
ta zauna falo tana kallon tashar larabawa.
da dare ya d'auke ta suka je gidan Yaya suka masa godeya matarsa sai meta take masa sai yau yaga damar kawo masu matar shi dai hak'uri kawai yake bata.
Alhamdulillahi cikin k'ank'anin lokace rayuwa ta sauya masu ya fara aikinsa cikin gaskiya da rik'on amana
zamansu da Baty k'auna ce da tsantsar kulawa tuni ta fara zuwa awo ta hanyar shawarar wata mak'wamciyar ta
wacce sukayi sabo sanadin ya ranta kwanan su ukku da dawowa Unguwar ta raku Al'amin har bakin get har zata shige sai budurwar wacce bazata wuce shekara goma sha shidda ba tayi mata sallama
Bety ta amsa cikin fara'a budurwar tace "Sunana Ilham kinga gidanmu can gaban gidanku amma tun jiya na ganki kin raku mijinki naji kin tsaya mun arai har na fad'awa Ummyna amma dai baku jima da dawowa ba ko"?
cikin Murmushi tace "Allah sarki sannu Ilham eh bamu jima da dawowa Unguwar ba"
"haba nikam nace sababbin dawowa ne"
"wallahi kuwa munyi tsaye awaje bisimillah shigo daga ciki"
"Aa nagode ina sauri zamuje d'auko Dady kinga yayana can yana ta mun hon dama ganinki ne yasa na tsayar da su sai na shigo" ta fad'a tana mai barin gurin da gudu
daga ranar Ilham tana zuwa wajan ta har ranar Ummyn su tazo da dare suka gaisa shak'uwa mai k'arfe ya shiga tsakanin Bety da su Ilham.
*Ina labarin Dady*
bayan tafiyar Bety duk sai yaji gidan ya masa fad'e zuciyarsa ta masa nauye wannan yasa ya yanki shawarar barin gidan gaba d'aya yakira Yaya Saif ya bashi umurnin ya sallame dukan ma aikatan gidan da kud'ad'e masu yawa.
da safe suka rufe gida Yaya Saif da Dady suka nufi Sudan sai lokacin iyaye da 'yan uwa sukaji abun da ya faru aikuwa Dady yasha fad'a kamar zasu dake shi
Baffa yace "ilimin ka da girman ka basu amfane ka da komai ba tunda har ka biyewa rud'un duniya
ka guje 'yar ka da matar ka saboda abun duniya miye illar talaka uhm? sam ba irin tarbiyar da muka d'aura ka akai ba"!
ya k'arasa maganar afusace yayansu yace "ai sai mu shirya gobe mu tafe ka kaimu gidan yaron dan baza ayi wannan haukan damu ba sannan ayi bekon ita Zainab d'in"
cikin muryar nadama yace "kuyi hak'uri na yanki hukunce cikin fushi ban san yaron ba ban San daga ina yazo ba"
ga baki d'aya d'akin ya d'au Innalillahi wa inna ilaihi raji'un
cikin tashin hankali hajyarsa ta tasu ta kifa masa mari tana magana cikin kuka "amma anyi shashan yaro yanzu ka d'au marainiyar yarinya ka bawa wanda baka San ko waye ba,
baka san daga ina ya fito ba to wallahi duk inda zakaje ka nemomun jika sai ka nemota ba ruwana"!
Dady yayi k'asa da kansa yana jij zafe azuciyar sa sanadin biyewa zuciya yau ya kai shi ga nadama, ya sanya mahaifiyarsa kuka
cikin fushi Yaya Saif yace "wai sai fad'a kuke da tada jijiyoyin wuya shi Dady miye laifinsa ai itace mai laifin ita tace taji ta gani ba shikenan ba"
"uwar ka nace uwarka shashan banza wato da kai aka had'a bake aka cutawa 'yar uwarka ko to kun kyauta"
ranar kam daga Dady har Yaya Saif basuji da dad'i ba gurin famili
washe gari Baffan Dady dana Momy Safna da Babban ya'yansa sukak'i shigo jirgi zuwa nageria Yaya Saif kuwa run adaren yayi tafiyansa ba Wanda yasan ina yaje ba kuma wanda ya nemeshi.
hotal suka sauka sai da sukayi sallah la'ar sukayi wanka sukaci abinci sannan suka nufi zariya cikin angayar Motocen Dady
kyakyawar tarba suka samu gun Inna kamar ba abunda ya faru bayan sun natsu d'akin Abban Aunty aka sauke su sannan aka kira k'anin mahaifinta
bayan sun sake gaisawa Abbun Safna yayi gyaran murya kafin yace "to Malam ba komai ne ya kawo mu ba sai dan mu bada hak'uri akan rashin hankalin da yaron mu yayi
adubi girman Allah ayi hak'uri wallahi bamu da masaniya akan d'anyen hukuncin da ya yanke ayi hak'uri ta koma d'akinta"
Malam Kawu yace "maganar gaskiya da shi kad'ai yazo gidannan ko kallo ba zai ishe ni ba albarka cinku ne yasa na zo maganar komawar yarinya kuma yana gurinta idan ta amince LA ba asa"
ke Zainab ina kiki ne"?
"na'am Kawu" ta amsa daga d'akin Inna
bayan ta shigo tasamu gefe ta zauna Dady ya d'ago ya kalleta wani irin abu yaji ya suke zuciyarsa tamkar kibiya da bazai iya tantanci ko miye ba
maganar Kawu ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin da ya fad'a
"ke Zainab iyayan mijinki sunzo bada hak'uri da Neman ki komawa d'ansu me kika gani zaki koma koku Aa"?
Dady tuni ya jik'i shakaf da gumi wani irin tashin hankali da bai tab'a ji ba arayuwarsa ne ya ziyar ce shi shin idan Zainab ta fallasa asirin zamansu wani hukucin zai fuskanta agurin iyayansa?
_mai k'aunar ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
Fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KAR KA GUJE NI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌸
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*Tabbata ttar soyayya itace ka so masoyan Wanda kake so Sahabbai Masoya Annabi S.A.W Soyayyar Ku gare ta daban ce zuciya da baki baza su kwatan ta tsantsar k'auna ta gare Ku ba daku nayi rik'o daku nake kamun k'afa Ku kaini har gaban Annabi Muhammad S.A.W*
*Ina yinku irin sosai d'innan 'yan Aisha A Yabo Hausa Nvl&Aisha A Yabo Lvly true FNS*
*170 to 180*
Sai da Kawu ya sake mai maita maganar sannan ta fara magana cikin girmamawa tace "Kuyi hak'uri Kawu Baffa abar zan cin komawa ko hakan bata faru ba dama zaman nawa na d'an lokace ne"
Baffa yace "Zainab me yasa zaki ce haka mun sani ba akyauta maki ba amma duk da haka muna mai baki hak'uri Insha Allahu hakan bazai sake faruwa ba"
"Baffa kuyi hak'uri wallahi bank'i maganar ka ba amma dama can hakan zai faru abisa alk'awari da yarjejeniyar da mukayi da Dadynsu Bety kuma gashi nan a tambaye shi"
dukansu da ke d'aken suka mayar da kallonsu kan shi Yaya yace "Sufyan fad'a mana abun da ke faruwa"
Dady k'asa yayi da kansa cikin muryar rud'u yace "Yaya ba komai kawai shirmin ta ne"
Kawu ya hau kanta da fad'a "Zainab bana son shashance da yawo da hankali idan komawan ne ba zakiyi ba sai ki fad'a ba wai sai kin mana yawo da hankali ba"!
ganin yana son d'aure ta da dawo da laifin kanta taga gara kawai ta fad'a
cikin nafsuwa ta walware masu irin zaman da sukayi da Alk'awarin da sukayi har kawu dalilin saken da yayi mata
ai gaba d'aya d'akin ya d'au salati masu Innalillahi nayi
cikin tsananin b'acin rai Baffa yace "Sufyan ka kyauta Allah ya saka ma da Alkhairi kayi duk abun da ya dace"
ya juya kan Kawu da ya daskare ya kasa cewa komai saboda tsabar takaici da b'acin rai
"Malam Dan Allah ayi hak'uri bamu da masaniya akan komai hak'ik'a Zainab tayi k'urciya da ta fad'a tun farko da hakan bai faru ba
Zainab ban San me zance ba amma nasani ko ban fad'a ba Allah zai yi maki sakayya"
Uhm ajiyar zuciya kawu yayi kafin yace "ai Sufyan bai da laifi mutumin da ya fad'a maki gaskiyar baya sonki to name zaki nace kice sai kin raini yaransa ko ke kika haife su
ai kya hak'ura ki barsu ballatana ba dangin iya ba na baba kin cotawa kanki abanza
kai kuma mun barka da Rabbul Izzati ya mana sakayya"!
ya bar d'akin afusace Zainab itama bayansa tabi jiki ba k'wari su Baffa suka bar gidan dan basu da kalamin magana.
awashi gari suka wuce Sudan ba tare da sun kula ban hak'urin da Dady ke basu ba.
Iyayen sa da 'yan uwa sunyi bak'in cikin jin wannan labarin kowa fushi yake da shi yayi zuwa ban hak'uri har ya godewa Allah ba Wanda me kula shi.
ya dawo gidansa da ke malali gurin iyalinsa idan dai ba tafiya yayi ba yana tare da su sai dai ya rame yayi duhu damuwa ta masa yawa ga fushin da iyayan sa keyi da shi ga wani irin son Zainab da ke d'awainiya da shi
zai iya cewa a rayuwarsa bai tab'a son macce yanda yake son Aunty ba
ko yaushe cikin zarya zariya yake amma ko sau d'aya ba abari ya ganta ba
yau da yamma ya shiga zariya sai da ya biya masallaci yayi sallah la'asar sannan ya k'arasa gidan
yana zuwa kawu na fitowa gidan ai kuwa ya murtiki fuska kamar yaga kashi da sauri Dady ya fito mota durk'usawa yayi har k'asa "Barka da yamma kawu"
cikin tsawa Kawu yace "rik'i gaisuwarka bana buk'uta na kuma godewa Allah da ya kawo ka ina nan
duk zaryar da kake inada labari ina so daga rana ta yau karna koma ganin k'afanka ak'ofar gidannan in dai Zainab ce ko bayan raina ban yafe ba idan ta komawa auren ka
sannan idan dai gida dan yana naka zaisa kana mana zarya to zasu tashi subar ma tsiyar ka"!
fau ya wuce afusace yabar Dady durk'ushi agurin ba tare da ya saurari maganar da Dadyn keyi ba
hawaye nagani suna zarya afuskar Dady turk'ashi Lallai wani abun sai so ba ruwansa da tsofa ko yarinta.
*kuyi hak'uri da wannan FNS INA Buk'atar addu'an Ku banda lafiya*
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
Fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KAR KA GUJE NI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌸
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*TAKAWAR KA LAFIYA SAYYIDUL WUJUDI GATAN KOWA ALFAHARIN KOWA GARKUWAR KOWA K'AUNAR KA DA'IMAN BA GUDU BA JA DA BAYA ZUCIYA DA JINI KAUNAR KA SUKE BURINA NA KASANCE DA KAI DUNIYA DA LAHIRA SOYAYYAR KA TABI JINI DA JIKI BABU MASAK'AR TSINKI DA'IMAN SAI ANNABI* *MUHAMMAD S.A.W* RAINA *FANSA NE GARE KA YA NABIYU RAHAMATI*
*DANGI ANNABIN DAI!!!*😍😍😍
*180 to 190*
Haka ya mik'i tsaye jiki ba k'wari baiyi zuciya ba ya nufi cikin gidan yana ta k'wala sallama
ya d'an jima yana sallama sai can ya jiyo muryar Inna tana amsa sallamar
"amin alaika salam waye ne"?
tayi tambayar dai dai sanda ta k'arasu surun tana ganinsa ta b'ata fuska tana fad'in "lafiya"?
sunkuyawa yayi gabanta yana fad'in "Inna mun wuni lafiya"?
"lafiya ya akayi ne"? ta amsa gaisuwar atak'aici
cikin k'ara k'ask'antar da murya yace "dan girman Allah da Ma'aiki Inna ayi hak'uri hak'ik'a Inna nasani abun da nayi ban kyauta ba
kuma wallahi nayi nadama Dan Allah kuyi hak'uri Zainab ta koma d'akinta"
cikin sanyin jiki Inna tace
"bakomai yawuce ai dama bawa bai isa ya kwaucewa k'addararsa ba
Dan haka mun yafe ma amma zan cin komawar Zainab ba ahannuna take ba tana gunta da kawun ta ni bazan ja da ikon Allah ba"
"nagode Inna Allah ya saka maki da Alkhairi"
"amin ba komai ka shiga d'aki bara na turo Zainab d'in"
"nagode Allah ya k'ara girma".
Inna ta shiga cikin gida d'akin da Aunty take ta nufa tana zaune tana duba littafin addu'oi
jin shigowar Inna yasa ta ajiye littafin gefenta cikin murmushi tace "Inna sannu"
"yawwa Zainab Alhaji ne yazo yana son ganinki"
b'ata fuska tayi kafin tace " wanne Alhaji Inna "?
"ah Baban su Bety ki tashi kije ni bazan maki dole ba amma kisani kowani bawa da k'addararsa Allah yarubata sai hakan ta faru bawa bai isa ya canza ba,
sannan idan Alhaji na da laifi to kema da naki laifin ya fad'a maki gaskiyar abun da ke zuciyarsa kin nace zaki zauna saboda yara
wanda banga dalilin cutawa kanki akan yaransa ba dan haka kiyi hak'uri kije ban kuma ce ki wulak'anta sa ba
domin gudun aikin da nasani dan baki san abun da zai faru agaba ba"
cikin sanyin jiki tace "to Inna".
dama da hijab ajikinta d'akin da yake ta nufa
bayan sun gaisa ya fara bata hak'uri cikin sauri tace "nifa ban rik'e ka da komaiba wallahi na yafema"
ajiyar zuciya yayi kafin yace "nagode Auntyn yara ina Neman wata alfarma da ki amince mun amaida auren mu"
cikin murmushi tace "kayi hak'uri bazan iya koma wa auren ka ba kawai mubarwa Allah zab'e,
ya wajan Bety tana lafiya"?
ta d'auko zancin Bety dan takawar da zancin
"Uhm bana ce tana lafiya ko akasin hakan ba saboda banda labarinta ban san gidan mijin nata ba
amma ina nan ina bin cike har Allah yasa adace"
sosai lamarin ya tab'a zuciyarta addu'a sosai tayi akan Allah ya bayyana ta
daga haka ta mik'i zata wuce yaciru kud'i ya bata tak'i karb'a tayi shigewarta gida.
haka yabar gidan jiki ba k'wari.
a cikin wata ukku da fitowarta gidan Dady Allah ya kawo mata miji Malamin islamiya yana da mata da yara hud'u
ko wata basuyi da had'uwa ba akayi auren su suna zauni lafiya da maigidanta da abokiyar zamanta.
lokacin da Dady yasamu labarin Auren Aunty yanki jiki yayi ya fad'i asumi iscs d'insa ne suka kai shi asibiti
sannan suka kira gida suka fad'a cikin tashin hankali Ummy da iyalanta suka k'arasu asibiti sun tarar yana barcci sai dai kallo d'aya zaka masa ka fahimci yana jin jiki
office d'in Dr d'insu ta nufa bayan sun gaisa tace "Dr me yake damun Mijina"?
"gaskiya hajiya damuwa ta yiwa Alhaji yawa da har ya haifar masa da ciyon zuciya
dan haka shawarar da zan baki kuyi k'ok'arin guji duk abunda zai b'ata masa rai ko sanya shi damuwa
hakan zai sa maganin da muka d'urashi akai suyi tasiri akansa cikin yardar Ubangiji
dan gaskiya idan yaci gaba da sa damuwa aransa komai zai iya faruwa"
godeya ta masa tare da tabbacin za su kula haka ta komawa d'akin da yake
yaran suna ganinta sukak'i fara tambayarta "Ummy me yake samun Dady"?
"kuyi masa add'u'a kunji"?
"to Allah ya bashi lafiya"
"amin".
kwanansa hud'u aka sallame shi bayan yayi wanka yaci abinci Ummy ta kora yaran
bayan fitarsu cikin hikima take tambayar sa abunda ke damunsa da har ya janyo masa ciyon zuciya
nan take ya bata labarin abunda ya faru abaya
kallonsa tayi cikin wani yanayi kafin tace "gaskiya Alhaji baka kyauta ba kuma wallahi ko nice bazan dawo maka ba
kama godewa Allah da Ta yafe ma da abun yafi haka
kuma nikam ina buk'atar ka kaini gurn dangin ka saboda yarana da kuma abun da gaba zata haifar"!
tana gama fad'a ta mik'e tsaye zata fita yayi saurin rik'o hannunta cikin damuwa yace
"haba Ummyn yara kar ki juyan baya alokacin da nake buk'atar tallafin ki
hak'ik'a nayi matuk'ar nadama akan abun da na aikata kuma Insha Allahu acikin satinnan zan shirya mana tafiya Sudan"
komawa tayi ta zauna tayi cikin tausayin sa tace "shikenan Allah ya nuna mana ka daure kaciri damuwa k'addara ce bawa bai isa ya kauce mata ba sai dai k'arfin addu'a yasa ta zowa mutum da sauk'i
ka nem gafarar Ubangiji da neman sassauce agurin sa"
haka ta zauna tana kwantar masa da hankali da lallab'ashi.
acikin satin suka nufi Sudan gidansa da ke Sudan suka sauka sai da suka huta sukaci abincin da 'yan aiki suka girka masu
sannan suka nufi gidan iyayansa yaran sai murna suke zasu ga kakannin su da sauran familin Dady
Ummy kuwa damuwa ce fal aranta da tunanin waci irin tarba zata samu a gun sarakanta?
Dady ma kusan tunaninsa d'aya da Ummy ya zasu karb'i zancin shikam yasan mai laifuka ne agun iyayansa da familinsa addu'a d'ai yake Allah yasa komai yazo masa da sauk'i.
_Mai k'aunar Ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
Fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KAR KA GUJE NI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌸
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*Son Annabi ne mafita Mustapha Babban Bango d'aha rik'e ni Dan nasamu rabauta babba k'aunar ka nake dare da rana Begen ka nake ya khairil khanzillah shugaba aso ka aji dad'i ak'ika akasan ce cikin k'unci wallahi komaina naka ne ya Habibullah ya Shafi'ullah Allah k'ara kusan tamu da narkar damu acikin Ma'aiki S.A.W* *DANGI ANNABIN DAI*!!!😍😍😍😍
*200*
Lokacin da suka isa Baffa baya nan sai Hajiyar sa ganin shi da bak'in fuska yasa ta tare su da fara'a sai dai zuciyarta fal da mamakin
yaran da taga suna matuk'ar kama da Dady tambayoyi ne aranta amma haka dole ta hak'ura tasa aka gabatar masu da abinci
basu wani ci da yawa ba saboda a k'oshi suki
cikin ladabi yace "Hajiya Baffa na gari nata neman wayarsa bata shiga"?
"eh yana gari nasan yanzu yana hanyar dawowa gida"
ko rufi baki batayi ba Baffa yayi sallama d'akin bayan yasa mu guri ya zauna Hajiya tamasa sannu da zuwa
ya amsa yana kallon yaran da mamaki yace "Ikon Allah wad'annan yarafa masu kama da yaran gidannan"?
"uhm nima mamakin da nake yi kenan tare suki da Sufyan"
da sauri ya kai duban sa gun Dady wanda sam bai kula da shi ba sai yanzu Dady yace "Baffah mun same ku lafiya"?
"lafiya" Baffa ya amsa masa atak'aici Ummy tazo gabansa cikin ladabi ta gaishe shi ya amsa mata da sakin fuska suma yaran haka suka gaishe shi
bayan sun gama gaisawa Dady yasa 'yar aikinsu ta shiga dasu Ummy d'akin bak'i
bayan fitarsu Dady ya fara basu hak'uri sannan yayi masu bayanin aurensa da yaran da suka samu
nisawa Baffa yayi kafin yace "bazan ja da Ikon Allah ba, ba kuma zank'i karb'arsu ba amma kasani baka kyauta ba kanuna wa duniya mu iyayanka ba abakin komai muki ba
tunda har zaka iya aure tsawon wannan shekarun ba tare da sanin mu ba
ka cutawa Zainab ka danni hakk'inta akan wani dalili marar tushe ka godewa Allah da bata shiga wani hali na aikata zina ta silarka ba"
fad'a sosai Baffa da Hajiya sukayi masa kafin daga bisani suka yafe masa.
ko kafin kace me maganar ta yad'u cikin famili kowa sai jinjina lamarin yake sai dai hakan bai hana su nunawa Ummy da yaran ta soyayya da kulawa ba.
Yaya Saif yana Mumbai yaji labarin aikuwa 'yan ransa yayi dubu ya b'ace wannan yasa yayi fushi da Dady da kowa na gida
har suka dawo Nageria baizo ba sai da Dady yayi da gaski da nuna b'acin ransa sannan yazo cikin ikon Allah yana ganin 'yan Uwansa yaji k'aunarsu ba kad'an ba
Dady da sauran 'yan Uwa sai addu'a suke akan Allah ya bayyana masu Bety.
Al'amin Alhamdulillah likkafa taci gaba ko wata da fara aiki baiyi ba Yaya ya saya masa Mota bud'i ya samu hankalinsu akwanci
basu da damuwa sai fatan Allah ya sauke Bety lafiya
sai damuwar da take ransa wanda ko Bety baya barin ta fahimta rashin sanin iyayensa da familinsa wannan na matuk'ar damunsa ko yaushe yana addu'a akan Allah ya bayyana masa familinsa
abunda bai sani ba babu ranar da zata fito har ta fad'i Bety bata yi addu'a akan Allah ya bayyana dangin Habibinta ba.
yau kam ta tashi jikin sai ahankali ko karin kumallo da kyar ta iya had'a masa bayan fitarsa ta koma ta kwanta
har zuwa azahar bata gyara gidan ba batayi girki ba sallah ma da kyar ta iya yinta
tana zaune kan darduma tana salatin Annabi S.A.W taji shigowar mai gidan
yana k'wala mata kira "Aishana Ashana"
"Na'am Habibi ganinan zuwa" tayi maganar tana mai mik'ewa tsaye falon ta nufa tsaye ta tarar da shi ransa b'ace aikuwa yana ganinta ya hau fad'a
"miye haka Aishana yanda na fita nabar gidannan haka na dawo na tarar da shi ba shara"!
cikin kwantar da murya tace "kayi hak'uri Habibi wallahi tun fitar ka ina kwanci banda lafiya shiyasa amma yanzu zan gyara kayi hak'uri kaji"
ta k'arasa maganar ciki lallami
"me yasa baki fad'an ba kafin na fita ko ki kirani awaya"?
"kayi hak'uri nayi kuskure bazan sake ba da yardar Allah"
janyota jikinsa yayi cikin kulawa yace "ya jikin"?
"da sauk'i"
"Allah ya k'ara sauk'i zauna bara na gyara gidan kinci abinci"?
cikin shagwaba tace tun fitarka komai fa banyi ba"
"ayya sannu idan kinji baki da lafiya ki daina yin shiru idan ba haka ba zamu b'ata"
kanta ta kad'a alamar to
cikin d'an k'ank'anin lokaci ya gyara gidan ko ina yayi fis sannan ya girka masu farar shinkafa tunda dama tana da Soyayyar miya
sai da sukaci abinci sannan sukayi wanka
suna zaune a falo kwanci take ajikinsa shikuma yana kall idanunta suna lumshi ciyon mara take ji can taji tana jin fitsari
ta tashi ahankali zata wuce ya kalleta yana fad'in "me nine Aishana"?
"zan shiga ban d'aki ne"
"OK"
tana shiga ciyo yace salamu alaikum durk'usu tayi tana nishin wahala
Al'amin jin shirun nata yayi yawa yasa shi bin bayanta yana zuwa kukan Baby ya fad'a kunninsa arud'i ya fad'a ban d'aki yana kiran
"Aishana haihuwa kikayi"?
cikin murmushin k'arfin hali ta gyad'a masa kai tana fad'in "wayata na kan firij kakira Ummy"
da sauri ya fita yana fad'in "to to sannu"
yana kiran Ummy ya fad'a mata ai ba awani jima ba ta zo gidan d'akinsa ya koma dan yana matuk'ar jin nauyin Ummy
cikin d'an k'ank'anin lokaci Ummy ta gyara Baby da Uwar Baby ta wanki kayan ta gyara ban d'aki tare da Fishe ko ina da turare ko ina sai k'amshi yake
tei mai kaure ta had'awa mai jego ta kai mata d'aki
"Sannu d'iyata ungu wannan maza shanye"
karb'a tayi cikin jin kunya tace "nagode Ummy Allah ya saka maki da mafificin Alkhairin sa"
"Amin ba komai ai d'a na kowa ne ina jinki kamar yanda nakejin su Ihsan karki damu kinji"
d'aukar jaririya tana fad'in "Sannu d'iyata barakallah masha Allah wannan girma na kishiyata ai kam kinyi fama"
Bety dai kumai ta kasa cewa sai murmushi take Ummy tace "bara na tafi gida Dadyn Ku na hanya yau zai dawo"
"Allah ya dawo da shi lafiya"
"Amin inawa Baban Beby barka"
"to Ummy zai ji Insha Allahu"
yana jin fitar Ummy ya shigo d'akin yana zuwa ya rungometa cikin tsananin farin ciki yace
"sannu Aishana Allah yayi maki Albarka Allah ya faranta maki fiye da yanda kika faranta mun"
"amin" ta amsa cikin jin dad'i d'aukar Babyn yayi yana mata addu'a sosai sai kallonta yake ciki da k'auna
su Ilham suka shigo gidan suna hayaniyar murna basu ko jira an amsa sallamar su ba suka fad'a d'akin
"lah Yaya yi hak'uri ba musan kana nan ba"
dariya yayi kafin tace "karku damu 'yan k'annena Ku k'arasu ga 'yar taku"
har rigin rigin ake wajan d'aukar Babyn "Woww Aunty kyakyawa har tafiki"
"kai Ihisan Ilham Ku fad'i dai gaskiya Ku ciri son kai" cewar Bety
"Allah da gaski Aunty"
haka dai Al'amin ya fita ya barsu suna ta murna
ba ajima ba Autan Ummy ya kawo mata abinci da farfesun naman rago.
kwana ukku da haihuwa Lawal ya dira garin da abun arzik'insa ko shi akaiwa haihuwar muranar da ya nuna sai haka.
daga Al'amin har Bety basu da bakin yiwa su Lawal da su Ummy godeya sai dai kawai suyi masu addu'a
domin sun tsaya masu akan komai sun zame masu iyaye 'yan uwa.
ranar suna aka rad'awa Baby sunan 'yar shugaban Halitta Fad'ima shugabar mata (Allah ya k'aramana soyayya da kusance amin)
ana kiranta da (sajida)
ko yaushe tana gurin Ummy sosai suke k'aunar Baby Dady son da yakewa sajida har mamaki yake baiwa Ummy indai yana gidan zaisa ad'auko ta
yayi ta yi mata wasa idan ya fita ko yayi tafiya tsarabar ta dabance.
Ranar asabar Al'amin yana gida kwanci yaki kan kafet ya d'aura Sajida 'yar wata hud'u akan cikinsa yana mata wasa
sai dariya take Bety na kitchen tana masu girkin rana taji yana kiranta da sauri ta fito kitchenn hannunta rik'i da Pleat d'in da ta yanka masa furut ajiyewa tayi gefensa tana fad'in
"yi hak'uri Habibi na tsaya sauki miya ne"
"OK ungu Sajida ki d'utata a fu naji tana nishi k'ila kashi zatayi karta mun ajiki"
karb'arta tayi kafin tace "idan tayi ma ba sai kaji yanda nakeji ba"
"Aa ai ku dama aikin ku ne bana mu ba"
ya fad'a yana dariya
"him lalle haka zaka ce ko"?
bata jira amsar sa ba ta fita tsakar gida ta d'urata a fo aikwa kamar jira take tana azata ta fara sai da tajira tagama sannan ta wanke mata da sabulu ta dawo falo
ta tarar autan Ummy yazo suna fira da Al'amin
"Aa Auta yau Kaine agidan mu aini fushi nake da kai"
"ayya Aunty kiyi hak'uri muna jarabawa ne shiyasa kika daina ganini"
"oh to ya jarabawa ana dai maoda hankali ga karatu ko"?
"eh Alhamdulillah"
"Allah ya taimaka"
"amin Aunty"
ya amsa yana mai karb'ar Sajida da taketa mik'o masa hannu
Al'amin yace "Auta Dady yana gari"?
"eh jiya sukak'i dawo da babban yayanmu amma naji yace yau da yamma zaiyi wata tafiyar"
"to Aishana ya kamata da anyi Sallah azahar muje mu gaida Dady tun bai bar gari ba"
"eh wallahi duk sanda zamuje bayanan"
"Auta kafad'awa Dady muna nan shifowa kaji"?
"to Yaya sai kunzo mun tafi"
bayan fitarsa ta kwanta k'irjinsa tana fad'in "Habibi tun safe nakjin fad'uwar gaba"
rungometa yayi kafin yace "ki dinga fad'an Innalillahi wa Inna Ilaihi raji'un da Hasbunallahu wa ni'imal wakeel,
Insha Allahu zaki daina ji kinji Indona"
dukan wasa ta kaima sa ak'irji cikin shagwab'a tace "um um ni bana son sunan nan fa"
"um um ni kuma ina so ya za ayi"?
yayi maganar cikin kwaikwayun muryarta.
Bety da sallamarta ta shiga Falon gidan tana sakin labulen tayi turus sakamakun abunda idanunta suka gane mata
kamar wacce akayiwa shoken ta jiyo da gudu tana kuka ta wuce Al'amin da ke tsaye bakin get yana jiran isu cikin rud'u yabi bayanta yana
"Aishana Aishana Aishana ki tsaya nace mineni"!?
_Mai k'aunar Ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
Fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KAR KA GUJE NI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌸
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*Burina addu'ata shine na kasan ce da Annabi Muhammad S.A.W a lokacin da nake numfashi dare da rana ya RASULULLAHI S.A.W kasance akusa dani alokacin da za azari raina ina kallon ka kana mun Murmushin ka mai d'aukar hankali har raina ya d'auke ba tare da nasani ba Ya SHAFI'ULLAH kasa hannunka mai tsalki da Albarka acikin Ruwan wanka na su kasance suna k'amshi daga cikin k'amshinka kasance dani Ya HABIBULLAH Acikin k'abari karkabari amun tambayoyi Dan wallahi ban San komai ba sai tsantsar k'aunarka Ya KHAIRAL KHANZILLAH kasance dani a ranar tashin k'iyama ranar da ba mai ceto sai kai ranar da kowa yake takansa ranar da Iyaye za suce basu San d'ansu ba d'a zai ce bai san iyayensa ba yarda dani na kasance a inuwar ka adamanka ya Aba Zahra Ameen!* *DANGI ANNABUN DAI*!!😍😍😍😍😍
210
Auta na zuwa ya tarar da Dady suna magana da Yaya Saif afalo
yace Dady "Abban Sajida yace na fad'ama idan anyi azahar zasu zo gaishe ka"
da fara'a Dady yace "Allah ya kaimu da zan fita amma zan jira kawo man amaryar tawa"
Ummy da take fitowa tace "nifa gaskiya zan fara kishi idan dai kana gari baka da lokacina sai na wannan k'uwailar"
dariya Dady yayi kafin yace "ai kuwa aiki ya same ki mai rabani da My Sajida ai sai Allah ki d'au na Annabawa kawai"
"lallaima Alhaji aikuwa zan dinga tare k'ofa naga ta inda zata shigo"
Yaya Saif yace "ina kuka samu Baby mai kyau haka"?
yayi maganar yana karb'arta hannun Dady
"wallahi nan mak'otanmu suki muna mutunci da Babar yarinyar" cewar Ummy Yaya Saif ya zubawa Yarinyar idanu cikin wata irin k'auna
yace "gata da shiga rai inama zasu bani ita"
yayi maganar cikin nuna da gaske yake dukansu dariya sukayi kafin Ummy tace "in banda abunka kaida ba mata kake da ita ba taya zasu baka 'ya"?
"ai Ummy ko ne zan iya kula da ita ba saida mata ba"
"uhm haka dai kake gani kadaiyi k'ok'ari ka samu mana sirika zaman ya isa hakanan idan kuma so kake sai Farhan yayi aure yabar ka shikenan
har ya haihu yaransa su fara kiranka Uncle na soro"
dariya yayi kafin yace "O o Dady zanyi Insha Allahu amma nafi so sai anga Bety"
"to Allah ya bayyana mana ita"
cewar Ummy "amin" suka amsa gaba d'aya.
bayan Sallah azahar duk suna zaune ababban falo har su Ilham anata fira Ihsan na kwance jikin Yaya Saif tana masa shagwab'an sai ya saya mata sabuwar laptop
tana tuna masa Bety yanayin su shagwabar su duk d'aya shiyasa yake ji da ita
Sajida na Hannun Dady yana mata wasa
Yaya Saif yace "Ihsan kin fiya fitina ba kuna da ita ba"
cikin turo baki tace "to ai Yaya ta tsufa pls ka sauya mun"
"to naji anjima zan saya maki"
ihu tayi tana tsallin murna Ummy za tayi magana Sallamar Bety taji hakan ya hanata maganar ta amsa Sallamar cikin fara'a
daga Dady har Saif jin muryar yasa sukayi saurin kallon k'ofa cikin ikon Allah tana shigowa idanunta suka fad'a Kansu
da sauri Dady da Yaya Saif suka mik'e tsaye cikin had'a baki suka kira sunanta "Bety"!
juyawa tayi tabar falon da sauri tana kuka.
da mamaki su Ilham ke kallon su Dady Ummy tace "kun santa ne"?
ina basu kula da tambayar da Ummy take masu ba suka bi bayanta
suna fitowa su Bety na shigewa gida.
Al'amin ya rufe k'ofa sannan yabi bayanta kwanci ya tarar da ita kan gado tana kuka
hawa kan gadon yayi ya rungumeta cikin damuwa yace
"wai mi yafaru ne agidan wani ne bashi da lafiya ko mutuwa akayi"?
girgiza kanta tayi tana mai ci gaba da kuka "ko wani abu ya samu Sajida"?
nanma girgiza kanta tayi tambayar duniya yayi mata amma tak'i magana
ransa ne ya b'ace ya janyeta jikinsa cikin fad'a yace
"zaki daina kukannan ki fad'amun abun da ke faruwa ko sai na b'ata maki rai"!
fad'awa jikinsa tayi cikin shisshik'a tace "ashe dama Dady yana da wata mata harda yara nice basasu shiyasa ya fita harkana
saboda ni tawa Uwar bata raye harda Yaya Saif yafi sonsu dani"!
da mamaki ya d'ago fuskarta yana kallo kafin yace "da gaske su Dady kika gani"?
"eh wallahi su nagani"
"to in banda abinki daga ganinsu sai kice gidan sa ne kika sani ko gidan abokinsa ne yazo"
"uhm Habibi duk yanda kaki da Yaya Lawal zaizo gidannan baka nan yayi d'are d'are falonka tare damu"?
cikin sanyin jiki yace "Aa amma dai baki da tabbaci kuma ko hakanne zaiyu da yaranta ya aureta"
mayar da kanta tayi k'irjinsa ba tare da ta sake cewa komaiba
jin ana bugun k'ofa yasa yayi yunk'urin tashi yaje ya bud'e
tarik'e shi "Allah ba inda zaka nasan sune suje yanda basa buk'ata ta nima bana buk'atarsu Habibi ka ishini rayuwa da 'yata suje na TSA.....
da sauri ya rufi bakinta cikin lallashi yace "haba Aishana meyasa kike haka iyaye sun wuci wasa ko mai sukai maki dole kiyi hak'uri tunda suka amsa sunan su na iyaye
sannan kina tunanin rashinsu a tare da ke yana mun dad'i ne?
kice baki sani ba ko yaushe ina zuwa tsohun gidanku ina away ko sun dawo bana samunsu
dan haka kisani wallahi nayi matuk'ar farin ciki da ganin su Dady
kima daina fad'an bazan bud'e masu ba ko basu zo ba ni zanje"
tashi tsaye tayi cikin fushi tace "to shikenan idan dai har zaka nemesu nikuma zan barma gidan yau Kaje na barma su kai da kake da buk'atarsu"!
da sauri ya tashi tsaye yana kallonta cikin mamaki yace "Aisha ni kikewa gorin iyaye ni kikecewa tunda ni nake da buk'atarsu
kenan nida band iyaye ni nake buk'atarsu ko? nagode kije kiyi duk abunda kikaga dama iyayanki ne ba nawa ba"!
yayi maganar cikin tsananin b'acin ran da bata tab'a ganinsa ciki ba
yayi hanyar k'ofa zai wuce tayo sauri shan gabansa cikin tashin hankali tarik'ishi tace "wallahi Habibi ba nufina kenanba taya zanma gorin iyaye wallah...
tureta gefe yayi ya fita d'akin ba tare da yaji sauran maganarba d'aura hannunta tayi aka kamar zatayi ihu kafin ta mik'e tabi bayansa da gudu tana zuwa yana kullu k'ofa
k'wank'wasa k'ofar ta dingayi tana kuka tana kiran sunansa amma Sam yak'i kulata
a can k'ofar gida ma sunk'i hak'ura da bugun k'ofa da sauri tanufi k'ofar gidan aranta tana fad'in zata bud'e masu ko Dan ta faranta ran Habibi
tana bud'ewa tayi ido hud'u da Dady kawai sai ta fad'a jikinsa tana kuka
bubbuga bayanta yadinga yi shima kamar zaiyi kuka yace "ya isa haka Bety daina kukan kinji ina maigidan naki"?
muryar Al'amin taji yana "sannunku da zuwa Dady Ku shigo daga ciki"
bayan sun zazzauna a falo harsu Ummy da Ilham
Dady ya fara magana "kiyi hak'uri Bety ki yafe mun nayi nadama sosai akan abunda na maki"
sake shigewa jikinsa tayi kafin tace bakomai Dady nima kayafe mun rashin biyay... da sauri ya katseta
" ni baki mun komaiba Bety ni ne namaki naso naja da ikon Allah nagodewa Allah da yabarni da raina har naganu kuskure na hak'ik'a da ko rabun Sajida zai iya kashe ni"
ya jiyo da kallonsa ga Al'amin "zo nan d'ana"
Al'amin ya matsa kusa da Dady, Dady ya rik'o hannunsa "kayafe min kaji d'ana"
cikin murmushin da ke nuna jin dad'insa yace "bakomai Dady ban rik'ika da komaiba"
"nagode Allah yayi maku albarka Farhan Ihsan Ilham Auta ga Yayarku da nake fad'a maku Ummy ga 'yarki"
tasuwa sukayi suka Rungume juna cikin k'auna ta 'yan Uwan juna
"Ummy tace ikon Allah Ashe k'aunar da sukewa juna ta jini ce"
cikin sanyin jiki Yaya Saif yace "k'anwata ki yafewa yayanki mai tarin laifuka k'anena kaima ina mai neman ya fiyarka ni ne na dinga bibiyar duk wajan da kake Sana'a inasa ana koranka haka nazo na saye gidan da kake zaune nasa suka kureka
duk tunanina idan Bety taji wahala da rashin kula zata sa ka saketa duk sai naga ashe ba haka bane soyayya ta gaskiya ce atsakaninku
sosai nayi nadama nata neman inda kuka koma ban gane ba suma su Kawu da natambaye su cewa sukayi basu sani ba
a lokacin Allah ya jarrabce ni da son wata yarinya 'yar talakawa ce sosai anan k'auyen Zariya motata ta Lalace a hanya ita kuma zata tallan nono
wallahi gani d'aya namata Allah ya jarrabtan da sonta so mai zafi namata magana tak'i kulani sai 'yan uwanta suka kwatanta mun k'auyensu da gidansu
wallahi maganar da nake maku daga yarinyar har mahaifanta sunk'i su kulani duk sintirin da nake agarin nasani alhakinku ne ke bibiyata"
zai durk'usa gabansu Al'amin yayi sauri rik'eshi yana fad'in "haba Yaya dan Allah kadaina wallahi ban rik'eka ba ko abaya na yafema kuma Insha Allahu zan tayaka da Addu'a idan da Alkhairi Allah yasa matarka ce"
sosai yaji farin ciki har baisan sanda ya rungume Al'amin ba yana fad'in "amin nagode d'an uwana"
Bety ta tasu ta rungumeshi cikin farin ciki ranar kam sun idar da wunin cikin farin ciki.
da dare kowa ya nufi makwancinsa Bety tsayi wanka ta shirya cikin kayan bacci wanda zan iya cewa dasu da babu duk d'aya
ta d'auke 'yarsu tanufi d'akin mai gidan zaune ta sameshi kan gado yayi tagumi hannunsa biyu da alama yayi nisa cikin tunani
kwantar da Sajida tayi kan gadonta sai baccinta take
zuwa tayi ta rungumeshi tare da fashewa da kuka cikin kuka tace "dan Allah Habibi kayi hak'uri ka yafe mun wallahi abun da kake zato Sam ba haka nake nufi ba har abada bana fatn wannan ranar tazo
kahimce ni Habibi Dan girman Allah da Manzon Allah S.A.W mijina ka yafe mun"
Rungumeta yayi kafin yace "na fahimceki Aishana baki mun komaiba zuciya ce bata da k'ashi Dan haka karki dam yawuci
ina taya junanmu murnar sake kasancewa acikin famili"
"nagode Habibi" daganan takai bakinta cikin nasa tana kiss d'insa kamar jira yake shima ya cab'e daganan fa labari ya fara sauyawa ganin haka yasa nagudu na rufu masu k'ofa.
*Bayan sati biyu*
Dady ne da Yaya Saif sai Al'amin zaune ad'akin Dady suna fira gwanin sha'awa
Dady yace "Al'amin ya kamata ka kaini gun iyayanka mu San juna tunda mun zama d'aya"
shiru yayi tare sunkuyar da kansa hankalinsa ya matuk'ar tashi da wannan tambayar ta Dady
dafa kafad'arsa Dady yayi kafin yace "d'ana fad'amun damuwarka karkaji komai ne mahaifinka ne karka b'oye mun damuwarka"
ajiyar zuciya yayi kafin yace "jamar yanda Inna ta bani labari bayan na zama saurayi tace ta tsince ni ne wata ranar juma'a
ta dawo daga tafiya da rana antattafi masallaci ba jama'a taganni a hanya inata kuka lokacin bazan wuci shekara ukku zuwa hud'u ba
da ta tambaye ni sunana nayi shiru sai Abbu Mami da Dada nake ta kira
tace na nuna mata gidanmu ban bata amsa ba
ta tambaye 'yan tsirarun mutanen da ke wucewa suma basu sanni ba suke cewa
haka ta tafi dani gida mijinta na dawowa ta fad'a masa shima yayi binciki bai samu wanda ya sanni ba
haka sukaci gaba da rik'ona tamkar d'an cikinsu dama yaransu biyu sun rasu tun suna yara,
sun tsayi mun akan karatuna saga islamiya har boko cikin taimakun Yayan aminina Lawal da abotarmu ta d'auko asali tun muna yara unguwarmu d'aya muna son juna sosai
komai tare mukeyi,
inada sekara ishirin Baba yarasu haka Inna taci gaba da d'awainiya dani har Allah ya karb'i Rayuwarta" daganan yayi shiru yana mai zubar da hawaye
" *Alhamdulillah*" naji Dady na furtawa kafin yacigaba da magana "Saifullah wallahi shine tun ranar da naganka kamanninka suka tsayamun arai
zarge ya shiga zuciyata
kai ne d'ana d'an Yayanmu da ya b'ace tun yana k'arami kunzo ganin d'an uwanka Saifullah saboda iyayanka basu samun damar zuwa sunansa ba sai bayan suna suka zo
kafito ba tare da sanin kowa ba munta nemanka tundaga k'afafan watsa labarai har wajan hukuma amma ba labarinka haka suka bar garinnan zuciya ba dad'i
kamanninka da mahaifinka Sak wannan yasa ka tsayamun arai ikon Allah ranar da nabaka auren Bety Sam ban kula da hakanba saboda banma kallon tsab ba"
wai mai karatu kwatanta irin farin cikin da Al'amin zai tsinci Kansa hum baki ko alk'alamina baza su iya kawu maku irin farin cikin Al'amin da su Dady suke ciki ba.
_mai k'aunar Ku_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
Fulani🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KAR KA GUJE NI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
🌸fulani🌸
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*Ya Allah yarda mu so Manzon Allah S.A.W Ya Allah yarda mu nutsi nutsewa wacce babu tsinkaya aciki sai tsantsar so da k'aunar Annabi S.A.W mu narki zuciya da jini ruhi da gangar jiki duk acikin Son Annabi domin sonsa ne mafita k'aunarsa ce tsera begensa ne dacewa Annabi yarda dani Kasan dani acikin masoya yarda na zamu mafi kusa da kai ahannun daman ka ya Aba Fad'ima* *amin*🙏🏻 *dangi Annabin dai* !!😍😍😍
*END END*
*ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH*
Rungumi juna sukayi dukansu ukkun suna masu zubar da hawayen farin ciki
Yaya Saif yace ikon Allah "wallahi Dady sai da ka fad'a naga kamanninsa da Uncle d'in India pls Dady ni zanwa su Uncle albishir"
"Aa ai bazan fad'awa kowa ba sai dai su ganmu dashi d'ana maza tashi kuje kuyi shiri da bizarmu tasamu zamu India gurin su Yaya daganan sai muwuce Sudan gurin kakanninka da sauran dangi
Saif kuje ayi duk abunda ya dace gami da tafiyarmu"
"to Dady angama tashi mutafi Yayana dukda dai na baka Bety ni ya kamata kacewa Yaya"
"Haba k'anena ai kamakaru dole dai ni zaka cewa Yaya ko ba haka ba Dady"?
Al'amin yayi maganar cikin fara'a "Dady Yace "sosai Son dole yace Yaya dan Shekara hud'u ba wasa ba"
haka suka bar gurin Dady cikin farin ciki ak'ofa suka had'u da Ummy zata shiga d'akin tace "Aa ina zuwa haka sai farin ciki kuke ko ta samu ne"?
Rungumeta Saif yayi kafin yace "sosaima Ummy ke dai shiga Dady zai fad'a maki mun tafi"
"abincin fa"?
Al'amin yace "Ummy sai mun dawo dai" suka bar wajan da sauri
ta kad'a kai sannan ta fad'a d'akin tana fad'in "Alhaji wai me kabawa yarana ne suke ta murna haka"?
nan ya bata labari sosai tayi farin ciki da tayashi murna.
suna fita gidan Al'amin suka shiga tun daga waje yake kwala mata kira hakan yasa da sauri ta fito ban d'aki tana fad'in
"Habibi wannan kirafa lafiya"?
tana zuwa ya d'agata sama yana juyi da ita sai da ya gaji dan kansa ya direta kan gado ya rungometa yana fad'in "Albishirinki"
Bety da take ta kallonsa tana mamakin wannan farin ciki da take gani afuskarsa tace "goro"
"nasamu iyayena da 'yan uwana"
fito da ido tayi cikin sauri tace "dan Manzon Allah"
"S.A.W wallahi kuwa ashe Aishana bayan k'auna ta aure da nake maki har k'auna ta jini ce ajikna shiyasa nake jin sonki fiye da tunanin mai tunani"
"Habibi kasani aduhu yimun bayani yanda zan gane"
nan take ya bata labari ihun murna ta saki "Wayyo Allah Allah na Allah nagode ma da ka nuna mun wannan babbar ranar"
" *Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah*" suka furta atare sun jima d'aki suna farin ciki kafin ya tuna ya bar Saif a falo
da sauri ya mik'i "Aishana na manta Saif na falo yana jirana zamu fita"
sai da suka gaisa da Saif da taya juna murna Sannan suka fita ita kuma ta rufe gida ta nufi wajan Dady.
Dady yasa Al'amin ya kaishi gurin Yayan Lawal yayi masa godeya Sosai tare da addu'a Allah ya biya shi da mafificin alkhairinsa.
Lawal farin cikin da yayi na samun iyayan Al'amin baya misiltuwa yace dole dashi za aje yaga mahaifan amininsa dan haka tare Dady ya shirya masu tafiya
cikin Sati na biyu komai na tafiya ya kankama ranar talata suka nufi Legos daga can suka hau jirgi sai India shigar safe sukayi shatar tx sukayi har unguwar da Uncle Muhammad yaki zaune (yayan momy Safna
bayan sun shiga gidan shiru kamar ba kowa Dady ya kira sa da waya bayan ya d'aga kiran Dady yace "Yaya gamu fa acikin gidanka sai dai kamar ba kowa"
cikin farin ciki yace "haba Masha Allah gamu fitowa duk suna barcci ne gamu nan sannun Ku da zuwa"
ba ajima ba Abbu da Mami suka fito Al'amin yana ganinsu yaji kamar yaje ya rungumesu wata irin k'aunar su ce yaji tana ratsa jini da zuciya
muryar maminsa ya tsinkayu tana maraba da k'aramin mai gida zuwa ba sanarwa"
"wallahi kuwa mun sameku lafiya"?
"lafiya k'alau Ummyn yara sannunku da hanya"
"yawwa Aunty Yaya mun sameku lafiya"
Uncle yace "Masha Allah Ashe anga Bety shine baka kira ka fad'amun ba"
"ayi hak'uri Yaya na bari ne sai munzo shiyasa"
nanfa aka shiga gaishe gaishe Bety taje jikin Uncle ta kwanta a kafad'arsa takai bakinta dai dai kunninsa cikin rad'a
tace "Uncle kalli wanda ke gefen Dady sosai"
shafa kanta yayi kafin yace "Me nine"? yayi tambayar dai dai sanda idanunsa suka fad'a kan Al'amin da shima shi yake kallo firgici ya mik'e tsaye
"Sufyan waye wannan Maminsu kalli wani ikon Allah"!
itama Mami kallonsa take ciki da firgici Dady yayi Murmushi kafin yace Alhamdulillah Yaya Ku kwantar da hankalinku wannan da kuke gani ba kowa bane face d'anmu da ya b'ata a shekarun baya wato *ABDULHAKEEM*
nanfa aka shiga maida zance Rungumeshi sukayi suna mai godeya ga Ubangiji
da yanuna masu d'ansu da har sun ciri tsammani auta Salma ta fito tana hamma da Alama barcci ta tasu
ganin su Bery da Ilham yasa tazo da sauri ta fad'a jikinsu tana "Oyo yo" Mami tace "Salma ga yayanku *Hakeem* da ya b'ata
da sauri taje ta fad'a jikinsa tana ihun murna
nanfa gidan ya kacame da murna baki har baka Sajida 'yar dangi har na rasa wa yafi sonta tsakanin iyaye da kakanni.
nan aka kira 'yan uwansa biyu da ke aure Mumbai Fatima da Ruk'ayya duka k'anninsa ne cikin dare suka isu ranar kam kwana hira akayi.
satinsu d'aya suka nufi Sudan Al'amin ko nace *ABDULHAKEEM* yaga soyayya da gata agun iyaye da dangi Lawal sai mamaki yake Ashe haka amininsa yake da gata ji yanda shi Kansa ake nuna masa k'auna da kulawa duk saboda *Hakeem* Allah da iko yaki
walima akayi Sudan saboda murnar ganu d'ansu nda akayi sadaka sosai ga mabuk'ata
uhm abu dai sai sambarka.
asati na biyu Dady dasu Lawal suka shirya dawowa Nageria su *Hakeem* da iyayansa zasu wuce India Abbu yace ba zai iya nisa da su ba.
*Bayan shekara d'aya*
Bety tana kwanci jikin *Hakeem* cikin shagwab'a tace "Habibi yaushe zamu je Nageria? ina so naje "
"Aishana kinfiya son yawo me zakiyi a can duka duka yaushe muka dawo naga dai su Dady basu jima da kumawa ba 'yan matan Ummy sunzo mana Hutu yau satinsu ukku da komawa"
"uhm um Habibi ka manta Auntyn Zariya ta haihu ina so naje suna Dan Allah Habibi karka ce Aa"
"kiyi hak'uri da sunannan ga bikin Saif da Lawal saura wata d'aya kuma duk a Kd za ayi idan angama sai kije
Zariya kimata kwana biyu kinji 'yar k'anwata"
ya k'arasa maganar cikin lallashi murmushi tayi kafin tace "na hak'ura Habibi Allah ya nuna mana"
"amin ya kamata ki bani baby hakanan tunda dai Mami ta k'wace mana Sajida"
yana maganar tare da shafa mararta
"wasa kasa shiyasa babyn baizo ba"
"iye haka kika ce aikuwa zaki sani daga yau zan ciri wasa aikin zan dingayi tuk'uru ba dare ba rana"
cikin dariya tace "o o bafa haka nake nufi ba"
"koma ya kike nufi za kiyi bayani ne yarinya"
kiran wayarsa ce ta katsi hirar tashi tayi taje ta d'auko masa wayar number Nageria ce sai dai ba suna
yana karb'a yayi tsaki tare da katsi kiran da mamaki tace "meyasa Habibi kasani ko wani na gida ne"?
"wata ce ke yawan damuna"
"iye wata"?
tayi tambayar firgici zaunar da ita yayi kusa da shi yace "miye na d'aga hankali dan Allah ki kwantar da hankalinki
bafa wata bace face Meenat ban san waye ya bata number na ba yau sati d'aya kenan tana damuna da kira
wai hak'uri take bani kuma dan Allah ita ta amince zata aure ni nayi hak'uri"
cikin sanyin jiki tace "to me kace mata"?
"kema kinsani ko ak'afa aka d'ura mun ita zan cire na yar bare kuma da hankalina ta manta duk tijarar da tamun da wacce ta maki ne
ai da bazatayi gigin kirana ba tas na mata na kuma fad'a mata ko kyautar ta akabani banayi akai kasuwa
kuma tun daga ranar ban sake d'aga kiranta ba amma tak'i zuciya ta k'yaleni sai kirana take da nambube barkatai da na d'aga naji muryarta zan katsi kiran"
kwantar da kanta tayi a k'irjinsa cikin sanyi tace "Habibi dan Allah *KAR KA GUJE NI* saboda wata"
gashin kanta da yasha gyara ya dinga wasa da shi kafin yace "bana fatan zuwan wannan ranar Aishana har abada bazan tab'a guje maki ba mun zama anta da jini
ke kad'ai kin ishe ni rayuwa banda burin zama da macci fiyi da d'aya ballatana ma har na d'auko wacce zata sa na guje ki
sai dai ban san ikon Allah ba idan yayi zan zauna da maccin da tafi d'aya banda ja sai dai nai addu'an kar Allah ya had'ani da wacce zata rabani da farin cikina
Meenat kowa ko ahanya bana fatan had'uwarmu ballatana aure Insha Allahu"
sai da ya tabbatar ta natsu sannan yayi mata sallama zai je ya lek'a kamfaninsu.
ranar litinin suka dira Kaduna agidansu da ke malali suka sauka wanda Dady yasa ank'ara gyara masu sosai har kayan d'akin an sauya mata
ko hutawa basuyi ba suka fara shirye shiryen biki Yaya Saif da Halima 'yar kauye wacce da k'yar ya ciyo kanta ta karb'i soyayyarsa
Lawal kuwa 'yar gida za ayi Salma k'anwar Al'amin au na manta Hakeem
duk gidan Dady za ayi komai.
bayan an gama biki ankai amare gida jansu Lawal anan Malali gidan da dai kuka sani sai dai ank'ara masa girma da gyara kamar na Hakeem wanda Abbu ne ya saye filin da ke kusa dasu yasa aka k'ara fad'in gidajan aminan da k'ayata shi.
Saif kuwa abuja aka kai amarya Dan acan aka tanbatsa masa gida naji da gani 'yan k'auyen su Halima sun koma gida da santin gidan Halima.
bayan kwana biyu da gama biki
ta had'a kayanta sai Zariya da abubuwab arzik'in da Dady da Saif da kuma Hakeem suka bayar akawu mata sosai Aunty tayi murnar ganin 'yartata
Bety kamar ta had'iye d'an Aunty Muhsin d'an watanni.
kwananta biyu ta dawo KD sai shirin kumawa India suke tana kitchen tana aikin abinci tajiyo sallama
fitowa tayi tana amsa sallama ganin Zee yasa ta buga tsalle suka rungume juna
sai da suka natsu Bety tace "ashe dama zan sake ganinki Zee"?
harararta tayi kafin tace "ban sani ba 'yar rainin wayo wai Bety kin san inda naki amma kikasa nemana"
langwabar da kai gefe tayi kafin tace "ayya Zee ba haka bane had'uwata da Meenat ne baimun dad'i ba shiyasa nazata ko ke hakan zata faru wannan yasa ban nemeki ba
amma wallahi kina raina"
"me 'yar iskar ta maki hala"?
nan ta kwashi yanda sukayi har bibiyar Hakeem da ta dingayi ta bata labari
"him Meenat ai bazanyi mamaki ba dan zata iya tunda kwad'ayayya ce nifa tub bayan barinki makaranta alak'armu tayi nisa dama danki nake tare da ita saboda tafiya kwad'aye da ruk'o kice baki gani halinta
sai da ta nuna maki amma ai tayi butulci kuma kanta tayiwa
Dan shekaranjiya nakejin labarin tayi aure sai dai ta had'u da wanda ya fita
yazo yana ta mata k'arya motoci da naira duka kwanansu goma da had'uwa akayi auren ba binciki ba komai iyayan suka biye mata in fad'a maki Ashe wankin mota ne sana'arsa
yanzu satinsu biyu da aure matsaluli sun kunnu kai Fa'iza khamees sabuwar k'awarta ke fad'amun da muka had'u wajan salon agunta ma nasamu adris d'inki tace kun had'u wajan bikin su Yaya Saif"
"oh lallai kuwa mun had'u da ita dan tace matar Yaya Saif 'yan uwansu ne na can k'auye
wallahi Meenat taban tausayi Allah ya kawu mata mafita"
"ke mubar zancin kwad'aye da dugon buri ya janyo mata ina 'yata"?
"tana gun Ummy ygd ya bayan rabuwa"
"wallahi sai alkhairi"
"bara na kawu maki ruwa na barki sai zuba muke"
bayan ta kawu mata abunsha da danbun nama tace "bisimillah kafin na k'arasa giriki wai Zee aure fa"?
"Wata biyar da aure na harda d'an yaron cikina"
"Wow gaskiya na maki murna Allah ya raba lafiya"
"amin"
da yamma *Hakeem* ya dawo yasamu bak'uwarsu sosai suka gaisa da 'yar fira kafin ya shige d'akinsa.
sai dare Mijinta Alk'asim yazo d'aukarta suka rabu da alk'awarin zasu kawu masu ziyara kafin su koma India inda mazajan sukayi musayar number.
Bety na hango tana turo ciki tafiya da k'yar *Hakeem* yana zaune kan kujera yana wani binciki a laptop d'insa zama tayi kusa da shi tare da mik'o masa madarar da ke cikin cop karb'a yayi yace "nagode maman biyu"
harara ta kaimasa cikin turo baki tace "tab d'ayanma ya akaji da ita bare biyu kama daina mun fata"
dariya yayi kafin yace "hum haba madam nasan wannan himman da na bayar ya wuci d'aya sai biyu kima shirya rainun 'yan biyu"
duk ta kaimasa cikin shagwaba kamar zatayi kuka da k'yar ya rik'i hannunta tare da rungometa ta baya yana dariya yace "yi hak'uri na daina amma kinsan me
bank'i kibani yara ukku ukku ba ina son yara da yawa Aishana"
"nima Habibina Allah ya kawu mana masu Albarka"
"amin Aishana k'anwata matata uwar 'ya'yana farin cikin rayuwata"
"I love you Yaya *HAKEEM* hasken rayuwata"
"I love you too Aishana"
*Alhamdulillah anan na kawu k'arshin littafina mai suna KAR KA GUJE NI kuskuren da nayi ciki Allah ka yafe mun Masoyana aduk Inda kuke ina alfahari daku ina k'aunarku k'auna irin sosai d'innan*
*ina alfahari daku 'yan Uwana jinin jikina A Yabo Famili*
*ina alfahari da ku 'yan REAL PML Allah ya k'ara had'a kanmu amin*
daga marubuciyar
*AMAL*
*MUKULA 'YAN MATAN ZAMANI*
*KAR KA GUJENI*
sai kun sake jina awani sabon Littafi na mai Suna
*MA AURATA*
Insha Allah
?
_mai k'aunar Ku har kullum_
🌺 *Aisha A Yabo*🌺
Fulani _Visitwww. Nafiunafson@mywapblogs.com_
Download Karka Gujeni Littafi Na Daya Complete
0 Comments
Thank you for this comment