💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
1to5
Sorry my fans najin banci gaba dayi muku posting ba hakan ya faru ne sakamakon rashin lafiya da nayi gashi yanzu na fara daka farko thx
Bismillahir rahmanir rahiim, godiya ta tabbata ga Allah wanda ya sake bani dama na rubuta wani littafi, Allah ya bani ikon gamawa lafiya,
KIRA GA MASU CANZA MIN NOVEL
Duk wanda ya kara canza min novel koya cire suna na ban yafe ba, Allah ya isa,
Tana zaune a cikin daya daka cikin jerun manya manyan kujerun falon wanda ya sha ado da kayan more rayuwa, idonta na kan tv, tana kallon tashar channel, amma gaba daya tunaninta baya wajan, inka ganta zaka rantse hankalinta na kan Jin sauraran news din da akeyi ne, gaba daya Kiran da kanwarta ta Mata a waya taji tana kuka shine ya d'aga Mata hankali, toh maiya sameta data ki fada Mata, tace sai tazo, ta danyi ajiyan zuciya tare da fadin nasan dai tatsuniyar gizo bata wuce koki, bari tazo inji koma miye.
Hauwa ta shigo cikin falon gidan tana kuka, ganin haka yasa hajiya salma ta tashi tana fadin Hauwa maiya faru haka? Tun dazu kinsa na kasa sukuni, Hauwa bata kulata ba sai kukan ta da taci gaba dayi, ganin haka hajiya salma yasa ta zauna ta gefenta tare da fadin Hauwa miye amfanin wannan kukan, kina ganin shine zaiyi miki maganin matsalanki?
Lokaci daya ta kurama hajiya salma ido, kaman mai son gano wani abu, tace salma anya ni dake uwarmu daya kuwa? Hajiya salma da mamaki tace Hauwa mai kike fada haka, anya kina cikin hayyacinki kuwa, karfa ki manta uwarmu daya uban mu daya, dan mai yasa zaki dinga tantama, bayan kin san mu biyu ma suka mallaka iyayenmu,
Hauwa dai kallonta kawai take, lokaci daya tace salma mai yasa bakya son nima inji dadi irin yanda kike ji, mai yasa bakya son ganin farin ciki na, mai yasa ba zaki sa nima na zama tauraruwa wajan mijina ba, kaman yanda kike a wajan mijinki, indai ko ciki daya muka fito zaki soni da wannan abubuwan, salma tace Hauwa bani da wani buri a kullum shine inga farin cikin ki, wlh Hauwa ina shiga damuwa fiye da yanda kike zato duk ranan da naji kin samu matsala da mijinki ko kuma na tuna irin rayuwar da kuke yi, bakin ciki na daya shine babu abun da zan iyayi a kai, sai dai in tayaki da Addu'a duk da kema kina da naki laifin..... Dan Allah niba wannan nake son jiba salma, nidai kawai ki hadani da malaminki yamin aiki ko zan dace, "Salma tace Hauwa wani irin malami kuma, Hauwa ta Mata kallon rainin wayau tare da furta in baki gane ba ina nufin bokan ki wanda ya mallake miki mahmud baya ganin kowa sai ke," Salma tace amma Hauwa kin ban mamaki wlh ke har zaki iya furta min wannan maganan, bayan kinfi kowa sanin koni wacece, wlh Hauwa ban taba zuwa wajan boka ba ko wani malami ba... Dan Allah ya isa haka nifa ba yarinya bace yanzu nasan komai, kuma wannan maganan da kike fada kin San ko mahaukaci bazai kama ba balle ni da hankali na, duk matar da mahmud ya aura saita bar miki gidan nan, sannan duk abunda kika cemai shi zai miki, sannan kice wai bakya bin malami, kima daina wani boye2 domin nasan komai, tana fadin haka ta tashi tare dayin tsaki ni zan wuce in kinki hadani da malamin zan nemo wani, tayi fuuuuu ta fita cikin fushi, salma ta girgiza kai cikin takaici yanzu itama Hauwa ta yarda ina bin boka, tace wai mai yasa ake samun irin wannan matsalan ne musamman a kasar hausa, indai miji zai nuna miki so toh za'a ce kin mallake shi, amma idan yau za'aga Kuna fada zaki ji bamai cewa komai sai dai ma a sami masu muku dariya, na rasa mai yasa Mata da yawa suka yarda da bin boka ba, wanda a dan nazarin da nayi, duk mace mai bin boka bata cikin kwanciyan hankali domin kullum tana cikin fargaba kar abun data kulla ya warware, na rasa mai yasa mutane ke zargina akan ina bin malamai ba, shin laifi ne dan mahmud yaso ni a matsayina na matarshi? Tayi dan shuru domin bata da amsa kuma bata damai bata, ganin tunanin bashi da amfani yasa tayi kitchen dan daura dinner,
Ya fito daka office, yana irin tafiyar nan tashi na kasaita, gefe kuma masu bashi tsaro ne suke biye dashi, yazo zai shiga mota sukai ido biyu dashi wanda wajan kwana biyu kenan yana ganinta, kaman zai Mata magana saiya share kuma, ya shige motar security ya rufe, sannan suka wuce tunanin yarinyar daya gani yake tayi wanda yau shine rana na biyu daya taba ganinta, tabbas yarinyar nan akwai abun da take nema, daka gani tana neman taimako, har suka shiga gida ya fito yayi ciki, wani kamshin turare ya bigi hancin shi, ta fito da sauri cikin English wear tayi hugging dinshi lokaci daya duk yaji ya manta da damuwar shi, salma tana da kyau wanda duk wani namiji zaiso ya mallake ta, uwa uba ga biyayya sai yasa mahmud baya ganin ko wace mace sai ita, duk da irin miskilanci irin nashi inka ganshi wajan salma da yanda yake mata sai kayi mamaki, ya kuma janyo ta tare da kara rungumeta yana Jin kamshin jikinta wanda ako da yaushe yake son ji, salati sukaji tare da tafi duka suka waiga dan Jin muryan hajiya binta maman mahmud, fuskanta babu alaman wasa ta kalli Salma wanda tayi kasa dakai gabanta na fadi dan tasan yau akwai rigima domin zuwan hajiya binta gidan ba alkairi bane, cikin sanyin murya ta gaidata amma bata amsa ba, ta kalli mahmud tace dole ka like mata bayan sihirin data maka harda karuwanci, toh wlh bari kaji indai nice uwarka kuma nono na kasha inaso ka kara aure koh naga jikana domin na gaji da jira,wannan karan ma sai nasa anyi min Addu'a sosai domin a barka da wacce zaka aura karta kuma koranta, kuma wlh wata uku na baka indai ya wuce haka zaka ga fushi na, tana gama fadin haka tayi waje, gaba daya jikin mahmud yayi sanyi tare da tausaya ma Salma ya rasa mai yasa zuri'anshi suka tsaneta sunbi sun damu akan bata haiyuwa wanda ni nasan na Allah ne kuma komai lokaci ne, Salma duk da irin tashin hankalin data shiga, ganin mijin nata yayi shuru yasa ta matsa gareshi tare da hura mishi kunne, yayi firgit ya kalleta ta sakar mai murmushi tare da fadin baby ba tunani zaka tsaya yiba yanzu kazo mu zauna musan miye mafuta kafin nan da wata daya ka nemo min kanwata nasan hajiya za tayi farin ciki, nima hakan zaisa inji dadi, yace salma bani da wacce nake so Sai ke wlh salma bazan iya auren wata mace ba, domin nasan bazan iyayin adalci ba, domin ke daban ce a cikin rayuwa na, tabbas tasan mahmud na santa itama tana sonshi tana bala'in kishin shi, amma dole ta daure tayi hakuri a wannan karon ma ya kara aure, duk da tasan abune mai wuya ya dade da matar, lokaci daya taji wani azababban kishi.
Hajiya binta rai bace ta shiga gida, taga zaliha a falo zaune da alama ta dade da zuwa,kanwar hajiya binta ce, tace a'ah zaliha yaushe kika zo tace tun dazu, ina kika je da wannan yamman haka, tace gidan mahmud mana, yaro matarshi duk ta shanye shi baya ganin kowa sai ita, zaliha tayi murmushi domin an tabo Mata inda yake Mata kaikayi, tace aini hajiya wlh da zaki dauki shawara na da anyi yar gida shida fauziya hala ma itace keda rabo dashi, nan hajiya binta ta washe baki tace aiko kin kawo shawara amma fah kin San wannan matar tashi a tsaye take dan muma sai mun tashi tsaye, zaliha tace kar ki damu ni zanyi maganinta yanzu dai saiki fada mishi dan nasan bazai miki musu ba tace babu damuwa, zaliha tayi wani murmushi wanda ita kadai tasan na miye.......
Maryam obam😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
6to10
Washe gari da safe salma tana kitchen tana hada breakfast mahmud ya shigo daka shi sai gajeran wando da singlet a jikin shi, kasan cewan yau sati babu office duk ranan da yake gida tare suke girki suna yi suna fira cikin so da kauna har suka kammala suna cikin yin breakfast wayan shi yayi kara ya duba yaga Hajiya a screen din wayar cikin ladabi ya dauka tare da gaida ta, ta gefenta ta amsa cikin fara'a, tace anjima kazo ina son ganin ka, ya amsa da toh insha Allah zanzo bada dadewa ba, ta kashe wayan, salma wacce tayi shuru ko ba'a fada ba tasan mamnshi ce, suka hada ido ta sakar mishi murmushi yace Mata Hajiya nason gani na bari inzo inje tace gaskiya ya kamata kaje kaji ko miye, mahmud yana matukar son salma yanda take nuna ma yan uwanshi kulawa duk dasu basa ganin hakan komai tayi a wajansu bata iya ba, amma bata taba nuna gazawa wajan yi musu hidima duk da Halin da suke nuna Mata, mahmud yayi daki baiyi 30 minutes ba ya fito cikin kananan kaya wanda ya kara fito mishi da kyawunshi, salma tace anya ba zance zaka ba kuwa yayi dariya tare da fadin haba dai ina da kamarki a gida ai babu ni babu zuwa zance ke kadai kin isheni tayi dan murmushi tare da fadin Hajiya na jiranka gwara ka tafi yace hakane bari inje in dawo ya fita.....
Mahmud yana bayan motar driver yana janshi sunzo wajan traffic suka tsaya tazo ta wajan motarshi tana fadin sadaka fisabillillahi, ganin fuskanta yasa yayi saurin saukar da glass din motar amma lokacin traffic ya basu alaman su wuce driver yaja motar sukai gaba, har suka karasa gidan Hajiya yana tunanin yarinyar wanda baiga dacewan ace tana bara ba, tsayuwan motar da yaji yasan sun karaso ya fito cikin tafiya irin ta wanda yaji naira, masu aikin gidan suna ta gaidashi cikin girmamawa suna Jin dadin ganin shi domin indai yazo gidan to ranan suna shan kyauta, kai tsaye falo ya nufa yako ci Sa'a hajiyan na falo nan ya zauna yana gaidata ta amsa cikin fara'a, suka dan taba fira na tsakanin d'a da uwa, tayi gyaran murya tace abun da yasa na kiraka na yanke wani hukunci duk da ba yardan ka nake nema ba, yace Hajiya ai duk abun da kika yanke nasan bazai cutar dani ba, tayi dan murmushi tare da fadin na maka Mata lokaci daya yaji zufa ta keto mai kuma wannan karon na gida ne, fauziya na zaba ma, nan yaji gabanshi ya fad'i yace Hajiya Wace fauziya? Tace wacce ka sani mana yar uwarka, ji yayi komai nashi ya tsaya, yace Hajiya da an zabo min wata amm....... Dakata malam wato a zabo maka wata bare wacce matar ka zata koreta koh toh wlh baka isa ba, koh kaki koh kaso saika auri fauziya, yai kasa dakai tare da fadin Hajiya kiyi hakuri Allah yasa hakan shine alkairi tace amin cikin fushi, tabbas an cuceshi domin fauziya ba irin tsarinshi bace bata da tarbiya uwa uba bata da kamun kai ga shegen sangarta da rashin kunya babu mai fada Mata taji, shi baima cika shiri da ita ba, ganin tunanin bashi da amfani yasa yama Hajiya sallama ya wuce......
Tunda mahmud ya koma gida salma taga yana yinshi tasan akwai abun daya faru, tamai Sannu da zuwa ta koma kitchen ta kammala hada lunch, kai tsaye bedroom dinsu tayi ta ganshi a kwance yayi shuru yana tunani, tace dear lafiya kuwa naga kayi shuru haka, yayi dan gajeran tsaki tare da fadin lafiya babyna, ta kafeshi da ido tace kar muyi haka dear nafi kowa sanin ka, in kana farin ciki na sani haka in kana da damuwa na sani, yayi shuru can yace salma dazu da naje gidan Hajiya tayi min maganan aure, nan taji wani iri amma saita dake, tace kai dear shine kake damuwa, yace babyna Kin San ko wacece kuwa? Ta girgiza kai alaman a'a yace fauziya ce fah wacce Hajiya tace zan aura, nan taji dus domin tafi kowa sanin waye fauziya, wani kishi ya taso Mata amma saita dake, tace dear aiko abu yayi kyau kaga tuwo na mai na, kaga da auran wanda baka sani ba gwara wanda ka sani, kallon salma kawai yake domin yasan dama hakan zai faru, sai yasa a kullum yake son salma tare da tausaya Mata, duk abun daya kawo za tayi na'am dashi duk munin abun indai bai saba ma addini ba, ya dan janyo ta jikin shi tare da fadin Allah yayi miki Albarka, tayi murmushi tare da fadin muje kaci abinci, yace no ki kawo min nan tace ok sir, tayi waje, tana shiga kitchen ta saki kuka mai zafi tare da wani zafin kishi daya taso Mata, yanzu mahmud fauziya xai aura wani abu ya taso mata a wuya........ Hmmm anya salma zata iya jurewa kuwa?????
Maryam obam😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
10to15
MASOYA KUYI HAKURI NAJI NA SHURU YANZU INSHA ALLAH NA DAWO ZANCI GABA NA DAN DAKATA NE SABODA RASUWAN MAHAIFINA ALLAH YAJI QANSHI YASA YA HUTA, WA INDA SUKA KIRANI SUKAI MIN TA'AZIYA DA WANDA SUKA ZO DA WA INDA SUKAI MIN MESSAGES INA MIKA GODIYA TA A GAREKU ALLAH YABAR ZUMUNCI👏👏
Wannan page din naki ne kawata ta rai da rai habiba s Ali👌👌
Salma taci kukanta lokaci daya ta share hawayen tare da wanke fuskanta dan kar mahmud ya gane tayi kuka, ta gama hada mai kayan abincin ta dauka ta nufi dakin dashi kallo daya yayi mata ya gane tayi kuka dan idanta ya dan sauya kala duk sai yaji babu dadi ta kuma bashi tausayi inda badan karya saba ma mahaifiyarshi ba toh wlh daya fasa auren fauziya dan baya kaunar ganin bacin ran salma ko abun da zai daga mata hankali, bayan ta ajiye abincin ta koma gefe ta zauna tashi yayi yaje kusa da ita yayi hugging nata tare da mata magana cikin kunne salma mai yasa kikayi kuka kin san bana San ranki na baci dan Allah ki daina sama kanki damuwa please my dear kinji tayi dan murmushi tare da fadin waya cema nasa ma kaina damuwa ka daina tunanin haka babyna ina farin ciki yanda baka misali yayi dan murmushi tare da kara janyota jikin shi.....
Hajiya zaliha na zaune a tsakar gida tana gyara shinkafar tuwo fauziya ta shigo tana sanye da riga da wando na yan kanti duk sun matse ta, ga wani kitso da tasha na attachment ta yafa wani siririn gyale waita rufe gashin amma gaba daya rabin gashin a waje yake,tace Amma yau tuwo kuma za kiyi daka shugowa na nayi Karo da tuwo, hajiya zaliha tace wai ina kikaje baki dawo gida ba tun jiya sai yanzu nayi ta kiranki baya shiga, fauziya ta dan tabe baki tare da fadin daka dawo wana har kin fara jeromin tambayoyi ko zama banyi ba ta daure fuska ganin haka hajiya zaliha tace kiyi hakuri y'ata hankalina ne ya tashi da ban ganki ba wlh, ta dan ya matse fuska tare da fadin gidan kawata na kwana sai yasa ban dawo ba, hjy zaliha ta washe baki tare da fadin yar albarka mai kashin Arziki albishirinki tace goro, ta mika mata hannu fauziya ta xaro dari biyar ta bata, tace wlh yayi kadan ai dubu goma zaki ban sai kiji albishir mai dadi, fauziya tace ni banda kudi in zaki fada ki fadamin in kuma ba zaki fada ba kinga bani kudina, hjy zaliha tayi dariya tace shikenan bari in fada miki na shawo miki matsalanki binta ta yarda mahmud ya aureki tsalle fauziya tayi tare da fadin Amma ban San wasa fah, tace wlh y'ata dagaske nake nan fauziya ta tashi tana rangada bud'a tare da rawa ta zaro dubu ishirin taba maman tace ga kyautar albishir Amma ya akai ta yarda haka cikin sauki, hjy zaliha tace ni wasa ce wajan wani boka naje yaban wani turare yace indai zani gidan insa komai nace mata zata yarda, fauziya tace amma ina tsoran ta canza ra'ayi kin san yar uwarki din nan sai a hankula, hjy zaliha tace wane ita indai akwai bokaye kuma ina da rai ai Sai kin auri mahmud wlh munci daula mun barta suka saki shewa cikin jin dadi duniya tasu,
Hajiya zaliha tana sa kaya fauziya tace ina zaki kuma kike ta sauri tace wajan malam mana inje inji yanzu miye abun yi dan kin San dole sai mun san yanda mukayi muka rabashi da wannan matar tashi dan yana bala'in tsoran ta, itama kin San a tsaye take sai munyi dagaske karta bata mata shirin mu sai yasa gwara ma ayi abun da wuri fauziya tace nima ai banga ta zama ba, tare zamu hjy zaliha ta saki dariya tace yauwa yar gari gwara muje in kina da wata matsalan saiki fada mai ma ya miki magani, suka fita.
Sun isa gidan boka yau sunyi sa' a babu kowa a wajan, nan suka zauna a kasan carpet din dake falon, hjy zaliha tace kaga likita mai bada maganin ko wani ciwo, mai yaye ma mutum damuwa wanda ya bika ya more wanda ya bijire maka yana cikin wahala, wa'iyazubillah Allah yasa mu dace, ya saki dariya wanda tun shigowansu idonshi nakan fauziya yace wannan fah, zaliha tace y'ata ce, wanda na baka labari ya lashe baki tare da fadin toh toh barka yan mata naji duk matsalanki, yanzu mai kikeso ai miki, tace ina so a mallake min mahmud sai abun dana ce ya soni kaman zaiyi hauka, yaji ya tsani matarshi, sai kuma mahaifiyarshi ita inaso a mallake min ita, boka ya fara dariya ya fara duba kasa lokaci daya ya daure fuska gaba daya muninshi ya fito, ya kalli fauziya yace kina da aiki a gabanki domin mallakan mahmud abune mai wuya dan matarshi tana yawan tsayuwan dare shima yana yi, tace toh yanzu miye abunyi yace abu daya ne shine Zan sa ayi auran da wuri in kin shiga gidan sai muga ko zamu iya mallake shi, ga wannan ki dinga amfani dashi kullum ta amsa turare ne sannan ya bata wani laya yace tasa a jikinta ta daure ta amsa tare da fadin to, yace karta taba kwance layan sai anyi bikin yace suje gida zasu ga abun mamaki suka bashi kudi suka wuce......
Fauziya tace anya wannan bokan ya iya aiki kuwa? Hjy zaliha tace tabdi ai bana tantama akan aikin sa wlh, suna firan har suka je gida suna isa kofar gida suka ga mota ko ba'a fada ba sun San hjy binta ce, cikin sauri suka shiga gidan, suka ganta zaune kan kujera a tsakar gida, hjy zaliha tace a'ah yaushe kika zo badai kin dade ba tace a'a ban dade da zuwa ba, fauziya ta gaidata ta amsa cikin fara'a tace nazo miyi maganan bikin nan ne tun da kika zo na jiki shuru hjy zaliha cikin jin dadi tace aida kirana ma kikayi, fauziya cikin murna tace gskiya wannan bokan ya iya aiki......... Hmmmm
Maryam obam😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
15to20
Hajiya zaliha tace tashi muje d'aki mana muyi maganan a ciki, hajiya binta bata musa ba, ta tashi sukai d'aki, fauziya kuma ta shige ciki wai ita a dole kunya, hajiya binta tace su fauziya manya yanzu an fara yar buya kenan, suka saki dariya ita da hjy zaliha, nan hjy binta tace toh yanzu nidai nazo inji ne kun shirya dai koh dan nan da sati daya nake so ayi a wuce wajan, nan hjy zaliha ta dafe kirji tace sati daya, ni yanzu ina naga kudi, da zanyi siyayya, hjy binta tace haba zaliha siyayyan mai zaki yi, bana bukatan kisai koda tsintsiya ne, komai zansa mahmud yayi, tace anya ayi haka kuwa, hjy binta tace to miye a ciki aiko bashi Zai aureta ya kamata yayi mata kayan d'aki nan hjy zaliha ta hau godiya Amma na ciki na ciki, hjy binta ta zaro yan dubu daya2 bandir daya dubu dari kenan tace ga wannan ki fara hidima dashi kafin a kawo abunda za'a dafa ma yan biki, ta amsa tana washe baki cikin jin dadi tace Allah ya saka da alkairi, inba naka ba waye xaima haka, ta fada tare da kallon hjy binta wanda taji dadin godiyar data mata,.
Hajiya binta tana ta shirye shiryen biki ba tare da mahmud yasan tana yiba, ta hada akwati cikin kwana biyu ansa kaya masu tsadan gaske, an kuma kai gidan su hjy zaliha, murna wajan fauziya ba'a magana zata zama matar mahmud zata kece sa'a wajan kawayenta, har tana ganin irin takun da zata dinga yi a gidan, sai dai ko da yaushe ta tuna da salma sai taji gabanta ya fadi dan tasan irin son da mahmud yake mata, sai dai itama ta dau alwashi indai akwai bokaye a gari da malaman tsubbu to tabbas sai tasa mahmud ya sota fiye da irin sonda yake ma salma wannan kenan.
Salma tana kitchen tana hadama mahmud dinner kafin ya dawo daka office, taji kaman muryan hajiya binta nan ta fito da sauri tana fadin sannu da zuwa mama, ko kallo bata isheta ba balle tama san tana magana ta nemi waje ta zauna, tana sakar mata harara cikin tsana, ganin tayi banza da ita ta tashi tayi kitchen ta hado mata kayan motsa baki, bayan ta ajiye tace keee zo nan ki dauke wannan abun daka nan, wa kika kawo ma wa an gaya miki shiya kawo ni, wato nima inci ki mallake ni koh, toh wlh ni nafi karfin bokan ki wlh kije ki sake shiri, salma ta dauka tare da cewa kiyi hakuri mama, tace kaya ne ta bita da harara, yarinya kin shanye min yaro baya ganin kowa sai ke, wlh dubun ki ya kusa cika, a dai2 nan mahmud yayi sallama ya shigo yace a'ah mama yau kece a gidan, tace eh nice mana tunda kai an hanaka zuwa bah, yace haba mama waye zai hanani zuwa wajanki, tace matarka mana wacce ta shanye ka baka ganin kowa sai ita, yace mama kiyi hakuri wlh ba haka salma take ba yarinya ce mai biyayya sai....... Dakata malam bashi ya kawo niba, banzo kuma dan inji hakan ba, abun daya kawo ni shine in fada maka ran Friday daurin aurenka da fauziya nan salma take kitchen wani xazzafan hawaye na xuba mata a ido, koya zata zauna da fauziya a gidan nan a matsayin kishiya tirkashi ada ma ya aka kaya balle itama yanzu ta zama matar mahmud, mahmud din shima cikin rawan murya yace mama Friday kuma ai ya kamata a fadamin da wuri inyi shiri, tace karka damu na gama komai gobe za'a kawo kaya asa a kusa da d'akin matarka dan kar a riga cutanta, yace mama d'aki nane nan sai dai asa ana kasa tace wlh baka isa ba sai dai ita waccan mayyar ta dawo kasa amma ba yata ba, wato tun yanzu ka fara nunamin za kayi rashin adalci ko wlh ka shiga hankalinka, tun wuri yace to mama kiyi hakuri yanda kikace hakan za'ayi tace shine zaman lafiya, tace ni Zan wuce saika fara shiri kuma anjima ka shirya kaje gidan su fauziya din dan kaji mai take bukata, yace toh, ta tashi tare da fadin saura kuma kaki zuwa, yace zanje insha Allah, ta fita yabi bayanta dan ya rakata,
Bayan ya dawo yaga salma a falo wanda ya tabbata taji abun daya faru, duk sai yaji babu dadi, ta sakar mishi murmushi tare da fadin sannu da zuwa bbyna, tace lafiya kuwa yau naga jarumin nawa kaman yana fushi, ta matsa kusa dashi tare da hugging dinshi tace plz kayi mun murmushi ko zanji dadi, ban san ganinka cikin wannan halin, my one, yayi dan murmushi tare da kara matseta a jikinshi tace naji duk abunda mama tace karka damu matar mutum kabarinshi kuma ina murna zan sami yar uwa, yace salma ke yar aljanna ce, tayi dariya nan ta shiga gaya mishi kalamai masu dadi taja hannunshi sukai toilet nan ta taya shi yayi wanka, sannan ya shirya cikin manyan kaya wanda ta xaba mai, ta kalleshi tace kayi kyau my, muje kaci abinci, bai musa ba suka nufi dinning, tuwan shinkafa ne miyan agusi yaji dry fish da ganda ga kuma nama, yaci ya koshi, har aka kira Isha'i Bayan ya dawo tace toh my sai ka nufi wajan kanwata dan ka ganta sannan in kaje ka gaida min da ita, wani irin kallo yake ma salma wanda itama da kanta sai da tayi mamaki......
Maryam obam😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
20to25
Yace kina tunanin zani wajan tane? Tace ban fahimta ba my, yace salma bazan iya zuwa wajan fauziya ba, tayi rau2 da ido tace haba babyna Mai kake fada haka, kar ka manta dazu kama hajiya alkawari kuma ni ban sanka da karya alkawari ba, kuma in baka jeba nima bazan ji dadi ba, sannan ita fauziya din zata ji wani iri, plz my muje in raka ka mota ka tafi, yayi hugging dinta tare da gadin "I love you salma u r my happiness, tayi dan murmushi tare da fadin I love you too my, ta danja baya daka rikon daya mata tace saika dawo, ya fita tare da fadin OK, tabi hanyar da yabi ya fita da kallo idonta ya ciko da kwalla mai zafi yanzu mahmud tad'i xaije wajan wata macen wanda zata shigo a matsayin kishiya ta, lokaci daya ta cire abun a ranta tare da fadin Allah kaban juriya da hakuri.
Fauziya anci kwalliya tayi kyau sosai dan itama fauziya ba'a baya ba wajan kyau sai dai masu iya magana sunce kyan hali yafi kyan sura da fuska, babu amfanin kyau indai babu tarbiya, tana ta sakin tsaki hjy zaliha dake gefe tana fadin ki kara hakuri fauziya Zai zo, ni dai ina fatan kinyi amfani da wannan turaran koh, tace eh nayi sai yasa kika ga ina ta wannan takaicin karya ki zuwa, hjy zaliha tace bari in kira binta inji kafin ta dau waya Sai ko gashi yayi sallama ya shigo cikin murna fauziya ta tashi tayi waje da sauri tace lah mahmud harka iso wlh tun daxu nake jiranka, mu koma motarka mana, yayi tsaki cikin takaici wai fauziya ce matar da Zai aura kai Allah yai wadan naka ya lallace, bai kulata ba yayi d'akin hjy zaliha data bude kunne taji abunda yake faruwa, ya shiga da sallama ta amsa cikin fara'a tare da fadin sannu da zuwa, ya gaida ta, ta amsa tare da fadin ya iyalin yace suna lafiya tace in gaidaku, fauziya data kumbura ta leko tare da fadin bama amsawa, tayi tsaki, hjy zaliha tace kee kina da hankali kuwa fauziya anya kanki daya, ta turo baki tana yan kun kune, ganin haka ya zaro kudi wanda baisan ko nawa bane yace ga wannan ni zan koma, hjy zaliha ta washe baki tare da fadin harda dawainiya to mun gode dan Allah kayi hakuri da halin wannan yarinyar kasan yarinya ce, yace babu komai ya fita, ganin ya fita tabi bayanshi da sauri amma yana shiga mota yace driver yaja suka wuce, nan ta kuma cika lallai mahmud saina tashi tsaye sosai a kanka wlh sai kayi dana sani ta shiga gida tana kuka, hjy zaliha ta shiga tambaya lafiya kike kuka, tace ni mahmud zai wulakanta, nan hjy zaliha tace toh ai kema da naki in banda abunki keda ba sonki yake ba maiya kai kiyi mishi rashin kunya, ai Sai ki bari sai mun sameshi a hannu kafin kiyi mai komai kuma kin san koda mun mallake shi dole sai kin hada da biyayya kafin aikin zaiyi tasiri, fauziya ta tabe baki tace badai ni ba sai dai shi yamin wlh,ta tashi ni na fita sai gobe zan dawo tace toh a dawo lafiya.
Mahmud yana mota yana bakin cikin wannan auren da ake son yi mishi, shi baiki kara auren ba amma wacce aka bashi ne yake ganin ba'ayi mishi adalci ba, gashi kuma auren zumunci yayi dan tsaki tare da fadin Allah ka zaba min mafi alkairi.
Biki ya rage saura kwana biyu, amarya tana ta shan magani kala2, dan so take ta nuna ma mahmud itama ba'a baya ba, kawayenta sun cika gidansu komai naci dana sha hjy binta ta bayar da kwangila ana kai musu, har wanda xa'aci ran daurin aure, fauziya sai cika take tana batsewa cikin kawayenta, yayin da suke ganin tayi sa'a babba domin samun namiji kaman mahmud ba abu bane mai sauki yaro mai tashe ga naira kaf garin babu wanda bai san shiba, bama garin ba kawai kaf kasan zance babu inda sunan shi bai jeba, yayin da wasu daka cikin kawayen fauziya din suke ganin mahmud bai dace da ita ba, dan yafi karfinta, sun dai ja baki sunyi shuru suna dan gwalan Arziki.
Mahmud yama salma akwati set 12 yace na fitan biki ta amsa tana ta godiya tare da mai addu'a, nan tace yama amarya itama dai koh dan tasan halin kayanta, yace a'a mama ta mata, nan salma tace bata yarda ba shima ya kamata yayi yakai nashi, yace na mama ya isa babu abun da zai kuma yi, tace toh shikenan ni Zan dauki 6 ka kai mata 6, kima daina bata bakin ki dan babu abunda zaki dauka wallahi duka amarya xa'a kaima nan duka suka waiga salma tace sannu da zuwa mama tace dallah yimin shuru makira kai kuma sannu shanyayye ka kyauta wannan shine adalcin to wlh baka isa ba duka za'a kaima fauziya yace haba mama ita salma fah ta daka mai tsawa kai mahmud ka shiga hankalinka wlh tun kafin inci maka mutunci, naga wuyanka yayi kauri ina fada kana fada toh baka isa ba nice mai iko dakai kuma yanzu xan nuna maka ikon, ina so ka saki salma indai nice na haifeka...........
Maryam Obam😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
25to30
Faduwa yayi kasa da gwiwowin shi, yana hawaye kaman wani karamin yaro wanda bai ma san yana yiba, salma koh gaba daya komai nata ya tsaya ko miyau ta kasa hadiye wa saboda firgita da kalaman hjy binta, ta kalli mahmud cikin fushi tace bada kai nake ba, amma ganin halin da dan nata ya shiga yasa taji wani iri domin duk duniya bata da kaman shi, kuma ita da kanta tasan yana mata biyayya, tabbas idan ta matsa mishi zai iya shiga wani hali, ta kalli salma ji take kaman ta kasheta dan haushi yarinyar nan na rasa wani kalan asiri tama mahmud da baya ganin kowa sai ita, mahmud dinne ya katse mata tunani da fadin mama zanyi duk abunda kika ce, bana fata Allah ya nuna min ranan da zanyi miki gardama a rayuwa na, tabbas salma itace macen da nake so kuma nake son in rayu da ita, rabuwa na da ita kaman barazana ne da rayuwa na, wlh indai na rabu da salma zan iya shiga cikin wani Hali, hjy binta tasan tabbas abunda ya fada hakan ne dan tasan akan wannan makiran salman zai iya shiga ko wani hali, tace dakata mahmud naji wannan karan zan hakura amma ka sani duk ranan daka nuna ma fauziya rashin adalci akan salma saika rabu da ita wlh kaji na rantse, tun yanzu ya kamata kasa son fauziya ma a ranka, in banda abun yaro wake Kin nashi yaso bare, fauziya yar uwarka ce inma abu zakayi sai nata yafi yawa saboda yan uwantaka, Amma kai naga baka san haka ba toh tun yanzu ka dai daita sahun ka, kar inji kar ingani maza ka kwashe akwatin ka kaima fauziya yanzu ya amsa da toh tare da fadin ngd mama, tace ni xan tafi, salma tace ki gaida gida mama, ta sakar mata harara tare da fadin idan ina magana da d'ana ki daina sa baki, salma taja baki ta tsuke tare dayin kasa dakai, tayi tsaki ta fita, shima ya bita,
Nan salma ta saki kukan da take boyewa tare da fadin wannan wani irin rayuwa ne, dan mijina ya nuna min so sai dangin shi su tsaneni shin laifi ne dan ya soni a matsayina na matarshi, na rasa mai yasa suke cemin na shanye shi, ladabi da biyayya ya zama shine tsafi, ni da ko hanyar zuwa gun boka ban sani ba, mai ya hadani da tsafi, jin motsin kaman mahmud yana shigowa yasa tayi sauri ta goge hawayen amma lokaci ya Kure dan ya ganta, ta sakar mishi murmushi tare da fadin har ta wuce? Ya kafa mata ido tare da fadin salma kukan mai kikeyi? Tace babu komai dear, yace kar kimin karya ban sanki da hakan ba, kiyi hakuri salma nasan abunda mama take miki ne yake...... Tayi sauri ta toshe mai baki tare da fadin dear mai kake fada haka, mama ta isa tace komai a kaina kuma ta isa tamin ko wani irin abu dan a matsayin uwa nake kallon ta, kaga mahaifiya tana da ikon tayi ma yaranta fada babu mai cewa komai kuma, wani irin son salma yaji yana shigarshi, tabbas salma samun mace mai irin halinki sai an tona, tayi dan murmushi tare da fadin tashi muje in tayaka diban kayan nan ka kaima kanwata, ya janyota jikin shi tare da fadin nop ki zauna zansa a diba a kai, nan suka shiga faranta ma juna rai.
WAI WAYE MAHMUD
mahmud El-hassan ya taso cikin gata, kasan cewan shine d'a guda daya wajan iyayenshi duk wanda mahaifiyarshi ta haifa sai su koma, shine kawai ya rayu, babu wani abu daya nema ya rasa, mahaifinshi tsohon minister ne na agriculture, sai da yayi shekara takwas akai, sannan aka canza wani ya koma kasuwanci ya tara dukiya wanda shi kanshi bai san adadinta ba, ya rasu a lokacin mahmud yana shekara ishirin da uku a duniya, yayi dan gajeran jinya, gaba daya komai na dukiyar shi ya koma hannun mahmud da mahaifiyarshi, wanda suka sa wasu suna kula da wasu aikin kasuwancin mahmud ya koma company din kera motoci wanda yake garin Abuja, lokaci kadan mahmud yayi suna kaman mahaifinshi, ya hadu da salma a garin katsina lokacin yaje bikin wani abokin shi, nan suka kulla soyayya abun daya burgeshi da ita, kunyanta da addininta dan a lokacin daya fara nuna yana sonta tace yaje ya fara ganin iyayenta kafin ya fara mata magana, aiko anan yace ya sami matar aure, kafin yabar katsina sai da yaje gidansu salma ya gabatar da kanshi kuma iyayenta mutanan kirki ne, mahaifin salma yana da rufin asiri, ya yaba da hankalin mahmud sosai yayi na'am dashi yace ya bashi izini in sun dai daita to shikenan nan mahmud yayi godiya ya bashi kudi yaki ansa yace bazai amsa ba, baya son haka, babu yanda mahmud baiyi ba yaki amsa, tun daka lokacin mahmud ya fara zaryan zuwa katsina wajan salma har mahaifiyarshi tace wai mai yake yawan zuwa yi katsina ne, nan ya sosa keya yace wajan salma, tace wacece salma kuma? Nan ya bata labari tace waye babanta yace sunanshi alh Muhammad, yana da mata daya yara biyu salma da hauwa, nan hajiya binta tace miye aikin shi? Yace yana dai da rufin asiri tsohon ma'aikacin gwamnati ne, ta tabe baki tare da fadin wannan maganar ka barta mahmud ka nemi dai dai kai kaji, abun da mahaifiyarshi ta fada bai mishi dadi ba, domin ita ta nuna yar masu kudi take so ba tarbiya ba, yace mama salma tana da tarbiya sai yasa nake sonta, ta nuna mai Sam yabar maganan, ganin taki na'am yaje ya sami wani yayanta wanda suke uba daya ya fada mishi nan yazo ya mata nasiha akan taji tsoran Allah Arziki da talauci duk na Allah koh ita lokacin da mijinta ya aureta suna da Arziki ne, babu shiri tace babu komai suyi duk abun daya dace, kaf yan gidansu hajiya binta suna tsoran haruna shine babba, yayin da gaba daya dangin ta suke girmamata dan tana da kudi shine kawai yake gaya mata magana ya zauna lafiya, mahaifinsu matanshi uku, jamila tana da yara uku, haruna shamsu, rabi, sai aysha itace ta biyu , tana da diya daya fatima binta,sai larai itace ta uku tana da yara biyu zaliha, habiba
Lokacin da mahmud ya dawo ta mishi tatas tace sai kaje ka aureta tunda har karata ka kai, nan ya fara bata hakuri da rarrashi tace babu komai nan akayi komai aka daura aure amma ba tare dason hajiya binta ba, kawai dai tayi shuru ne dan ta faranta ma danta,wani katon gida ya gyara da yake maitama a nan suka tare, salma tana da hakuri dangin mahmud sun sha zuwa suyi ta mata habaici da zage2 musamman hjy raliya da yarta fauziya, suna yine kawai dan su faranta ma hjy binta,yayin da zaliha babu komai zuciyarta sai...tsanan hajiya binta dan tana da Arziki wanda take ganin ita ta dace dashi....
Maryam obam😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
30to35
Tun farkon aurensu salma take fuskantan matsala wajan dangin mahmud, gashi baban abun tashin hankali shine yau shekaran salma uku da aure amma shuru babu haiyuwa, nan hjy binta tace Sam bazai yiwu ba, mahmud ya zama dole ya kara aure domin tana son ganin jikoki, bazai yiwu kaita zama da juya ba, badan ranshi yaso ba ya amince dan yabi umarnin mahaifiyarshi dan baya so ya saba mata, Amma shi a nashi ra'ayin baya sha'awan tara mata shi salman shi ta isheshi kawai,amma babu yanda ya iya matsalanshi kawai yanda zai gayama salma zai kara aure yake damunshi dan baya San bacin ranta, kaman yanda bata san nashi, duk wani abu da zaisa shi farin ciki shi take so, bata san bacin ranshi sai yasa shima yake gujema abun da zaisa ta bacin rai ko zargi duk da yasan ba halinta bane tana da hakuri,amma babu yanda zaiyi dole ya fad'a mata dan yafi so taji abakinshi akan taji a wajan wasu, ya yanke yau Zai fada mata.
A lokacin da mahmud yaje gida, salma ta tarbeshi kaman yanda ta saba,yaci abinci suna fira amma gaba daya yana tunanin yanda za'ayi ya fada mata, haka dai ya daure yayi na maza ya sanar da ita, amma abun da yayi zata sai bai gani bah, tace alhamdulillah Allah ya sanya alkairi yasa abokiyar zama ce ya baka ikon yi mana adalci, ya amsa da ameen tare da kara son salma, haka aka shirya biki hjy binta ta nemo mai wata yarinyar mai suna bilkisu yar masu kudin gaske anyi biki an kashe naira, amarya ta tare cikin gidanta, suna zaman lafiya ita da salma abun su, tun lokacin da hjy zaliha tazo gidan taga irin yanda suke zama ta kitsa ma bilkisu abubuwa iri2 aiko Tun daka ranan ta canza ta fara yima salma bakaken magana da zagi salma bata taba kulata ba, sai dai ma tace bilkisu mai na miki naga kin canza dan Allah in laifi nayi ya kamata ki fadamin ta daga hannu ta mari salma dallah yimin shuru munafuka, jin muryan mahmud sukai yana fadin bilkisu kije na sakeki saki uku, da sauri salma ta juya tana fadin innalillahi wa inna'ilahira jiun, mahmud wannan wani irin abune haka mai tama zaka mata wannan hukuncin, yace salma bazan zauna da macen da zata ci mutuncin kiba, domin ke nake so bazan bari a wulakanta min ke ba, harga Allah salma bata ji dadin sakin da mahmud yama bilkisu ba, a lokacin da hjy binta ta samu labari tazo tama salma ta tas tace kuma wlh aure nan da sati biyu zai kara, aiko hakan akayi aka aura mishi wata shima dai akan salma din suka kara rabuwa tun daka lokacin suke fadin salma ta mallake shi, tana koran duk wanda ya aura, wannan kenan
MUN DAWO KAN LABARIN
yau aka daura aure, Mutane sun taru domin hjy binta tayi gayya sosai, ango dai kwata2 baya cikin nishad'i, zai iya cewa yau itace ranan bakin cika a rayuwanshi domin an daura mishi mara tarbiya shi yama rasa mai yasa mama ta yarda ta bashi fauziya ba,
Ita kuma gefen amarya tana cikin farin ciki, yau itace matar mahmud abun da take ta burin samu shekara da shekaru yau ya zama nata, ta lumshe ido tare da fadin yau zan nuna maka nawa fagen soyayyar, yau zaka sha zumata, ji take kaman azo a tafi da ita yanzu, ta tashi ta dauko maganin da boka ya bata tayi matsi dashi, tayi murmushi tare da tuna abun da bokan ya fada mata indai ki kai amfani da wannan maganin ya sadu dake toh daka ranan sai yanda kikayi da mahmud, domin duk macen daya sadu da ita zai jita kaman dusa, tace salma saina rabaki da mahmud har abada domin nawa neshi.
Salma anci kwalliya sosai tayi kyau, tasa wani tsadaddan material wanda mahmud ya kuma siyo mata tasa da bikin, gefen ta kuma kanwarta ce hauwa, wanda tazo taya ta zama har a kawo amarya ta wuce, suna dan fira jefi2 hauwa tace niko salma mai yasa kika bar mahmud ya kara aure bayan nasan ba zaki barta ta zauna ba, salma tace hauwa mai kike nufi? Tace naga duk wanda mahmud ya aura kin koresu itama nasan wannan ba barinta za kiyi ba, salma tayi murmushin takaici tace hauwa kenan, kina bani mamaki wlh, tace name ai gaskiya ne abun da yake a zahiri mahmud fah akan ki zai iya komai inba wani abu kika mai ba toh mai yasa zai dinga miki haka, salma tace bana tsafi bana shirka, bana makirci, hauwa tayi dariya tare da fadin toh sai me? Tace KISSA hauwa ta kafeta da ido tare da kuma nanata kalman da salma ta fada kissa, tace ya ake ita kissan hala naki na daban ne, tace a'a kaman na kowa ne, hauwa tace toh koya min mana nima inji ko zan gamsu ita kikeyi, salma tace zan fada miki nan gaba hauwa tace dan Allah ki fadamin yanzu dan na matsu inji, tace na miki alkawari dakai na zanzo gidan ki in fada miki, hauwa tace toh shi kenan, nasan bakya karya alkawari ai, sukayi dariya a dai2 nan mahmud ya shigo salma ta tashi da sauri tare da fadin wlcm my dear dana iya guda da nama, yayi dan murmushi yace toh Ina binki bashi tayi dariya dan ta fahimci abun da yake nufi yayi gefenshi itama ta bishi anan suka bar hauwa tana shs'awar irin rayuwar su, sai dai salma taki fada mata sirrin yayin da ita nata mijin suke yawan samun matsala wannan kenan
Anzo daukan amarya an jera motoci masu tsadan gaske, nan fauziya ta tashi cikin murna da zumudi, aka fita, kai tsaye aka wuce da ita gidan ta, suna shiga suka fara guda da habaice2 suna fadin an kawo wacce zata haifa mana y'ay'a Allah ya rabamu da juya sai ci ana zubarwa, salma dai tana d'aki bata fito ba,.
Hjy binta ta kira mahmud taja mishi kunne akan idan ya saki fauziya toh wlh saiya saki salma itama, dan wannan karan bazan dauka ba, gwara ma ka dawo hankalinka tun wuri yace insha Allah hakan ma bazai faru ba, tace toh saika tashi kaje dan fauziya tana jiranka dare kuma yana yi ya amsa da to, ya wuce.
Yan kawo amarya sun wuce aka bar amarya ta tashi ta fad'a bayi tayi wanka tasa wata rigan bacci wanda dashi ma gwara babu, ta zauna tana jiran mahmud ya dawo, lokacin daya dawo taji shigowanshi nan ta koma ta zauna, shi kuma kai tsaye dakin salma ya wuce, nan ya zauna yana ta faman yi mata kalaman soyayya, tace ka tashi kaje d'akin lanwata tana can tana jiranka, yace korata kikeyi salma? Tace a'a inaso ka zama mai adalci ne kuma kasan yau ranan tane ranan dako wace mace take buri kaga bai kamata mu shiga hakkin taba, fauziya jin ya dade bai shigo bah ta fusata tare da fadin yama raina min wayau ta tashi ta fita tana huci tayi d'akin salma....
Maryam Obam😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
35to40
A dai2 lokacin ya fito daka dakin, nan sukai Karo, salma na bayan shi, kallo daya ya mata cikin tsana yace ke wace irin mara hankali ce, zaki fito haka bayan kin san bake daya bace a gidan, salma gaba daya ji tayi ta dauke wuta dan wani azabban kishi ne ya dauketa, wanda yasa idonta ya canza amma saita daure tace dear sai da safe ta rufe kofarta, dan bazata iya ganin wannan takaicin ba, kuka ta sake mai karfi, gaba daya xuciyarta tafarfasa yake, daka ta rufe idonta sai taga fauziya da mahmud ranan barci gagaranta yayi duk yanda taso ta dake ta cire abun amma ta kasa, da dai taga haka ta tashi ta dauko al'qur'an, tana fara karantawa nan ta danji dama2.
Mahmud tunda sukai d'aki shida fauziya ya kasa sukuni dan bai yarda da yanayin salma ba, dan yaga kaman ta dan shiga damuwa, yayin da amarya ta kame a gefe ta daura kafa daya kan daya tana girgizawa amma abun mamaki shi gogan ko kallo bata isheshi ba, ta saki tsaki tare da fadin wannan fah inna biye tashi babu abunda zai faru yau, zai sa inyi asaran magani gashi boka yace sau daya yake bama mutum shi, ta tashi ta nufi mahmud din wanda yake zaune kan kujera yana danna laptop, ta zauna ta gefen kujeran tare da rufe laptop din, ta fara magana tana kashe mai ido haba mahmud dare fah yayi kasan kuma Ina jiranka ya kamata kazo mu kwanta, gaba daya mamaki ya hanashi magana dan bai taba xaton haka ba, tasa hannunta cikin riganshi, yayi sauri ya tashi tare da fadin tir da halinki duk wata mace mai mutunci indai tayi aure aka kawo ta duk rashin kunyanta bata neman namiji sai dai shi ya nemeta, amma ke dubeki wai amarya kenan babu kunya babu komai, ta tabe baki tare da fadin toh miye aciki kuma miye abun jin kunya,ina bukatar ka, dan me bazan nuna ba, kallon tsana da mamaki yake mata, yace lallai sai yanzu na yarda da baki da kunya kuma baki santa ba, inba karuwa ba babu wacce za tayi abun da kikayi a daren farkon ta, dan haka yanzu ni kin samin tantama sai anyi miki test kafin in kulaki, cikin fushi tace mai kake nufi kana nufin ni yar iska ce? Yace waya sani abu a duhu, zama tayi tana hawaye ta rasa abunyi tana tunanin shirinta zai rushe lokaci daya ta kuma tashi tace toh naji na kuma yarda in kace baka yarda dani ba, zaka iya amfani da condom, dan ina bukatar ka, yace fauziya am sorry bazan taba kiba har sai anyi test ya tashi ya koma kan gadon ya kwanta abinshi, ranan tayi kukan bakin ciki tare da daukan alwashi sai ta rama duk abun da mahmud ya mata tare da fadin kai da kanka zaka nemeni, a lokacin zan wulakanta ka zan nuna maka aikin boka, itama dai ranan juyi tayi2 bacci yaki zuwa,
Washe gari tunda mahmud ya nufi masallaci da asuba, bayan an idar da sallah ya nufi dakin salma, ya ganta akan dadduma, nan ta gaidashi ya amsa cikin fara'a yayin da ita kuma take jin kishi dan tana ganin komai ya faru yanzu, ta tashi ta dauki dadduman ta ninke, mahmud yazo yayi hugging dinta yace dear mai yake faruwa, tayi murmurshi tace babu komai, babyna ya kamata ka koma dakin amarya tunda mun gaisa, yace salma korana kikeyi koh? Ta zaro ido tare da fadin ni na isa in kori king dina, wanda duk duniya babu abunda nake son inga ina gani kaman ka, kaine kake sani farin ciki kaine rayuwa na, bana so kona minti daya kayi nesa dani, yace mai yasa toh yanzu kike korana? Tace dear ina sonka banso ka tashi cikin maza marasa adalci indai bazan daura ka akan hanya ba ai bana sonka ta karashe maganan cikin sanyin murya, yayi murmurshi tare dajin dadin kalamanta salma kina sani farin ciki sai yasa koda ina fushi ke daya ce zaki iya sani dariya da nishad'i ya bata fake a saman goshinta tare da fadin ngd dear sannan ya fita, bayan ya koma dakin fauziya ya sameta kwance yanda ya barta, ya girgiza kai ya fara tashin ta, tace mai nene? Yace kinyi sallah ta amsa da eh nayi, amma badan tayi ba dan dai kawai kar yasa ta tashi daka baccin ta.
Salma bayan mahmud yabar dakinta kitchen ta nufa dan ta hada breakfast, cikin lokaci kadan ta gama ta jera a dinning sannan ta koma dakinta, tayi wanka ta shirya cikin wani atamfa dinkin riga da skirt ya mata kyau sosai, ta koma parlor ta zauna dan jiransu su sauko, wajan 10 mahmud ya fito yace dear kinyi kyau mahmud a kullum salma kara kyau take mai, yazo ya zauna kusa da ita tare da kafeta da ido, tayi dariya tace my lafiya? Yace ina kallon halali na ne, tayi dariya tare da tashi zata bar wajan ya janyota ta fado jikinshi, ta fara mai magana kaman mai rad'a tace dear bafa mu kad'ai bane yace sai akayi ya, tayi shuru ba tare data bashi amsa ba, tace muje kayi breakfast ina sister na? Ya gane tana so ne ya saketa daka rikon daya mata dan ya fahimci bata so fauziya ta fito ta gansu a haka, yayi murmurshi tare da fadin tana d'aki, tace go and call her, yace kyaleta zata fito da kanta, tace dear itafa bakuwa ce bata riga ta saba ba, plx ka kirata yace ok my lovely wife, bari in kirata tayi murmurshi ya tashi ya nufi sama, Jim kadan sai gasu shida ita, tasa jallabiya, ko kallo salma bata isheta ba, ta nemi waje ta zauna, salma tace morning sister, kaman ba zata amsa ba, komai ta tuna kuma tace antashi lafiya? Salma tace lafiya qalau, ta tabe baki, salma ta hadama mahmud abinci sannan ta xuba nata, tace sister bismillah kar in xuba miki inyi miki kauro, fauziya cikin isa tace ai dama an saba tunda gida babu, mahmud yace aifa kam yanzu ne naga an shigo gari tunda kin fara neman kudi, ta daure fuska, mahmud yasan ta gaya ma salma magana ne shi kuma, ya bata amsa dai2 da ita, har suka kammala fauziya bata ce komai ba, sai mahmud da salma wanda suke fira jefi2, mahmud yace bari inje office yanzu Zan dawo akwai masu jirana, salma tace ok saika dawo take care, ya tsaya yau daka nan zaki min sallama, tayi dan murmurshi ta tashi ganin ta Mike fauziya itama ta tashi tana huci salma sukai waje mahmud ya wuce, tana shiga falo fauziya ta tareta tace naga kina wani rawan kai toh bari kiji kinga duk wannan abun da yake miki ni nace ya miki dan kar kice ya canza miki dan ya kawo ni, amma da kinga yanda yaban wuya jiya da kin tausaya min yace min baki da dadi kaman dusa kike, salma tayi dariya tace eh toh kin san indai namiji yaji dadin mace bazai barta ba ya fita koda wa yake jiranshi musamman a ranan daya fara saninta, ni nasan da hakan kuma sai yasa nace ya kara aure inda ban yarda ba aida bai auroki ba, so kuma maganan kice ya dinga kulani plx daka yau kice karya kara kulani indai ki kai hakan xan San dagaske ke Zuma ce tana fadin haka ta wuce tabar fauziya da bakin ciki, xan nuna miki ni Zuma ce kuma na isa nan bada dadewa ba.....
Maryam Obam😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
40to45
Salma d'aki tayi abunta dan bata son dangin fauziya din suxo su sameta a falo, tana ko yin d'aki bata dade da shiga ba taji shewa da gud'a tare da habaice2 abun ko a jikinta ta kwanta abunta, ta fara bacci taji kaman mutum a kusa da ita, tayi sauri ta farka sukai ido biyu ya sakar mata murmushi tare da fadin wannan irin razanar fah? Ta kasa magana dan ta tsorata dan ita a zaton ta tasa key a dakin kuma ba tayi zaton mahmud din bane, saida ya janyota jikin shi, sannan tayi ajiyan zuciya, shima da kanshi yasan a tsorace take da zaman dan ya shigo yaji irin zage2 dasu fauziya sukeyi suna ganin shi sukai shuru, ta katse mai tunani da fadin yanzu ka dawo? Yace eh ban dade da shugowa ba, tayi murmushi tare da fadin wlcm, ban san zaka dawo yanzu bah gashi ban daura lunch ba am so sorry bari inje inma, yace no barshi na siyo mana gashi nan, ta kalleshi da mamaki tace siyo abinci kuma? Yace nasan yau gidan mutane zasu zo sai yasa nace bari in kawo, tayi dan murmushi tare da sauka a kan gadon ta dauko ledan fried rice ne da garden salad, sai kuma kaza, ta dauko musu drinks cikin fridge din dake dakin, nan suka ci suka koshi..
Su fauziya ana falo ita da kawayenta da yan uwanta, suna cin abinci yayin da ita fauziya din bata abincin take ba, wata daka cikin kawarta mai suna jamila suna kiranta da jamcy, kana ganinta kasan yar bariki ce wacce ta goge a harkan ansha mai fatar nan tayi jawur, tace fauzy ke yanzu a nan zaki zauna kina ganin yayi sama tun daxu ke an barki a nan, fauzy data qumu da bakin ciki ta tabe baki tace jamcy to mai kikeso inyi nan jamcy ta saki dariya tace lallai fauzy, ashe za kiyi sanyi dama akwai abun da xai sa kiyi shuru, tabdi amma kin ban mamaki ina zafin naki? Ina rigiman ki? Fauzy tace jamcy kin san mahmud shine namijin da nake so, ke kin san yanda akayi na shigo komai sai na bishi a hankali kin san dan rainin wayau babu abun daya hada ni dashi jiya sai bakaken maganganu, wai bazai taba niba, sai anyi min test, jamcy tace toh fah mai yake nufi? Fauziya tace abun da kike tunani, jamcy tace toh gskiya sai kinyi dagaske inba haka ba zaki zama yar kallo, dan wannan matar tashi ba'a zaune itama take ba, dan yanda yake sonta ai yayi yawa, wlh gwara ki farka kisan abunyi da ita, fauziya tace karki damu ni yanzu matsalata daya yanda zani wajan malam yaban wani abun, jamcy tace toh gskiya kema kin san wannan abune mai wuya, keda kike amarya ai babu hanyar fita, fauziya tayi dan gajeran tsaki tace ina zuwa tayi sama, kai tsaye dakinta ta shiga ta dauki waya ta kira mamanta, hjy zaliha ta dauka cikin fara'a nan fauziya tasa mata kuka tace lafiya fauziya mai aka miki? Nan ta zayyane ma mamanta abunda ya faru, tace yanzu ma daya shugo yana dakinta Tun dazu, koda ya shigo ko magana bai min ba, yayi wajan matarshi, nan hjy zaliha tace kiyi shuru fauziya karki damu yanzu zan fita zani wajan malam komai ya faru zaki jini, kar ki kara xubar da hawayenki a banza, dan kuka ba naki bane, tace mama kisan duk yanda xa'ayi aban abunda xan mallaki mahmud, sannan a rabashi da salma, hjy zaliha tace an gama bari inje yanzu banso mutane su shigo suji abunda ke faruwa, sai kin jini ta kashe wayan, ta yayibi gyale ta fita.
Kawayen amarya sai wajan karfe goma suka bar gidan, mahmud shida salma suna tare sai dai yaje sallah ya dawo, duk yanda yaso ya sadu da salma taki yarda dan ta nuna mishi bai kamata ba, in sukai haka zasu shiga hakkin fauziya, ganin kaman ya danyi fushi abun da bata saba gani ba a tare dashi, tace dear plx kar kayi fushi dani wlh fushin ka a kaina ba alkairi bane, ya dan juya mata baya, ta juyo ta gabanshi tana hawaye gaba daya ya rude tare da riko ta, cikin tashin hankali yace salma mai yasa ki hawaye, tace ba kai bane, cikin shagwaba, yace sorry my baby, ki daina plz bana so, bana son abun da zai saki bacin rai, tace nima haka yau naga abun da baka taba yi min ba, kayi fushi dani, ban hanaka kaina da gangan ba sai dai gudun kar insa kayi zalinci domin Allah zai kama ka, tunda bani bace dakai, zamu shiga hakkin fauxiya tunda bata yarda kayi hakan ba, kaga gwara muyi hakuri, yayi murmushi tare da fadin na fahimceki salma kuma na gane, bakya taba yin kuskure komai kina yine akan abun da addini ya tsara, ngd ma Allah daya bani ke, tayi dariya cikin jin dadi tare da fadin ngd ina koda yaushe ina godiya da Allah ya bani kai a matsayin miji, domin duk wata mace irin mijin da take son samu kenan, yace waya fada miki? tayi dariya tace abun da yake zahiri ne ai, tace dear ka tashi ka tafi dare yayi dan naji shuru da alama babu kowa, bai musa ba ya tashi ya fita kai tsaye dakin fauxiya din ya nufa, ya ganta a zaune tana waya jin motsin shi yasa tayi sauri ta kashe, kallo daya ya mata ya kauda kai gefe ta tashi cikin isa da gadara tace sai yanzu ta barka kazo, bai kulata ba hakan ya mata xafi, tace anje ana cin amana ta toh wlh baka isa ba yau sai an ban hakki na wlh dan ban san abunda kake nufi dani ba, namiji ya koma mijin tace, yace ki koma ki nemo tarbiya da yanda ake magana da miji, domin mace mai tarbiya ba xatayi abun da kikeyi ba, tace naji bani da tarbiya din, nidai abu daya na sani kaban hakki na, ganin bazai iya da ita ba yasa yayi banza da ita ya kwanta abunshi, nan ta zauna tana ta fadin magana bai tankata ba, haka dai itama ta gaji ta kwanta.
Tunda ya fita sallah sa asuba, ta tashi ta dauki waya ta doka ma mamanta kira, ringing daya ta dauka, fauziya tace wai ina kika shiga tun jiya inata kiranki baya shiga,, tace kedai bari, tunda na fita sai wajan daya na dawo, fauziya tace an dace? Tace eh an dace amma da sharadi, tace name? Yaban na wanda zaki sami mahmud zai fara kulaki Amma yace bazai yi wani tasiri ba har sai kinje da kanki zai baki wanda zaki mallake shi gaba daya, yaji baya ganin kowa sai ke, tayi dariya cikin jin dadi tace an gama yanzu yaushe xan sami wanda ya baki tace anjima zan zo dakai na in kawo miki tace toh sai kinzo amma kixo da wuri tace babu komai,
Wajan karfe goma koh saiga hjy zaliha taxo gidan, a lokacin salma tana falo, ta shigo da sallama salma ta amsa, tare da gaisheta ko kallo bata isheta ba, tayi sama dakin fauziya, tayi nocking fauziya ta bude ganin mamanta yasa ta saki dariya cikin jin dadi domin yau zata sami cikan burinta, bayan ta shigo ta zauna tace ina mahmud din tace baya nan ya fita, nan ta fito da maganin ta bata turare ne, tace kiyi amfani dashi ki tunkare shi zaki sha mamaki, tace mama Kin tabbata xaiyi aiki tace sai yasa yace ki gwada in yayi kije da kanki tace shikenan, tace mai kuka dafa ne dan ban karya ba, tace tashi muje kitchen din muga mai waccan mayyar ta dafa, nan suka fita salma na nan yanda ta barta daxu, hjy zaliha tace samun waje an tura min y'a d'aki ke kin fito falo kina kallo, koh ke ga mai gida, toh bari kiji kin kusa b..... Lokaci daya kuma tayi shuru tare dayin tsaki, ganin haka salma tayi d'aki, nan hjy zaliha aka zauna a dinning aka bude ciki ana kwasan abinci, sai wajan biyu tabar gidan,.
Fauziya tana ta jiran mahmud ya dawo taji shuru to wai yau ina yaje ne banji motsin shiba? Wajan 8 taji an bude gate ta leka ta window taga shine ya dawo da sauri tasa turaran da aka bata, ta zauna dan ya shigo, amma taji shuru tace nasan yana dakin waccan shegiyar, ta tashi tayi dakin basa nan, nan tayi falo tagansu mahmud ya daure fuska dan yana yin shigan da tayi night gown ne sai wani da tasa a sama ana ganin jikinta, yace ke wai yaushe xakiyi hnkali ne, bata ce komai ba sai daura hannunta da tayi akan kirjinshi gaba daya ya fita hayyacin shi, ya riko hannunta yana shin shinawa ta kara makale shi, tace dear yaushe ka shigo yace tun dazu tace tashi muje d'aki kai nake jira, ya tashi tare dayin hugging dinta, salma wani irin jiri ta fara gani dakyar ta iya tafiya d'aki fauxiya tace kadan kika gani, mahmud gaba daya ya fita hayyacinshi baya ganin komai sai fauziya.
Maryam Obam😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
45to50
Salma tunda ta shiga d'aki take ta aikin kuka, domin babu abun da yafi wannan wulakanci kenan abun da fauziya ta fadamin gaskiya ne, lokaci daya idonta yayi jaa, tace dama akwai ranan da mahmud zaiyi min haka? Na shiga uku da nasan wannan ranan zata zo dana roki Allah ya dauki rayuwa ta, haka ta zauna taita tunani kala2 lokaci daya zazzbi mai zafi ya rufeta, ga ac a kunne amma babu daman ta tashi ta kashe dan ba zata iya tashi ba, domin yanda take jin jikinta ga kirjinta yana mata ciwo sosai,
Mahmud da fauziya ansha soyayya sosai, yau fauziya ana cikin nishadi, domin ta sami abunda take so, ta tabbata zata mallake mahmud yanzu tunda magani yayi aiki yanzu, yanzu abu daya take fargaba In mahmud ya farka, domin tunda ya gama abunda zaiyi da ita wani bacci mai nauyi ya dauke shi,ta dan tabe baki tare da fadin inma ka farka aikin gama ya riga ya gama, domin na sami abunda nake so, kuma daka yanzu dole ka dinga biya min bukata na,
Mahmud sai wajan 4 na dare ya tashi, gaba daya yaji jikinshi ya mishi nauyi, kaman yayi wani aiki mai wuya, ga kan shi dake ta faman ciwo sosai,sai kallon dakin yake kaman wanda bai san dakin ba,ga fauziya a gefe dake ta bacci, lokaci daya ya fara tuna abunda ya faru nan yayi salati tare da fadin salma, ya tashi da sauri, yayi waje, kai tsaye dakin ta ya nufa, ya bude kofan ya jishi a bude, bai gnta kan gadon dakin ba, nan yaji gabanshi ya fadi, tare da fadin ina salma taje, ya hangota gefen gado a kasa ta kudun dune, da sauri ya nufi wajan, ya fara fadin salma, ya kamo ta, ji yayi gaba daya jikinta zafi sosai, ya rude ya rasa mai ya kamata yayi, lokaci daya ya dauketa cak yayi waje da ita, yaje dakin security din gidan yana Kiran driver dinshi da karfi cikin rudewa, nan fauziya itama ta farka, ta leka ta window taga salma a hnnunshi ya riketa tayi tsaki tace wahalalle, ta koma ta kwanta abunta, driver din ya fito tare da sauran security din cikin tsoro, yace budemin kofa muje asibiti nan yaje da sauri ya bude motor ya shigar da ita suka fita, zuwa asibiti, kai tsaye emergency aka kaita domin ko numfashi bata yi, da kyau, mahmud gaba daya ya kasa zama, sai kaiwa da komowa yake, har aka kira sallah asuba yaje yayi sallah ya dawo amma shuru.
Sai wajan 8 Dr ya fito yace mahmud ya sameshi office, a tare suka tafi, nan yace ya zauna, bayan ya zauna yace Dr maike damunta? Dr yace jininta ne yahau sosai, dole sai ta rage damuwa inba haka ba Zai iya taba abunda yake cikinta, mahmud yace Dr abunda yake cikinta? Yace yes, yace kana nufin salma nada ciki?? Yace yes harna wata biyu da sati daya, nan mahmud ya fara kwalla tare da fadin Dr are you serious? Yace kwarai dagaske, nan ya daga hannu yana ma Allah godiya, yace Dr yanzu yaushe zata farka? Dr yace gaskiya ban sani ba, munyi iya kokarin mu sauran sai a barma Allah, yace zan iya ganin ta? Yace yes amma banda hayaniya, nan mahmud ya tashi yayi emergency din, ya bude kofar ya shiga, ya ganta a kwance tana bacci numfashinta ya koma normal ba kaman yanda takeyi sanda ya kawo taba, gaba daya tausayinta ya kamashi, wani irin sonta yake kara shigarshi tare da kosawa ta farka taji good news, lokaci daya yasa hannu a aljihu dan ya ciro phone dinshi amma yaji wayam, yayi dan tsaki daya tuna bai dauko ba, nan yayi waje wajan driver ya amshi phone dinshi, ya kira hjy binta, ta dauka cikin muryan bacci tace ya akayi dan tasan no din driver din mahmud ne, amma sai taji muryan mahmud, tace lafiya kuwa? Yace lafiya mama ya gaidata sannan yace salma ce bata da lafiya tun wajan 4 muka zo asibiti, ta tabe baki tace nasha ko wani abune ya faru, toh Allah ya kyauta, baiji dadin kalaman mmn nashi ba, amma babu yanda ya iya, kaman karya fada mata abun da yake son fada, yace mama salma nada ciki, tace what, tare da tashi daka kan gado, tace mahmud mai ka fadamin yanzu?? Kace salma nada me?? Yace ciki, tace waya fada maka? Yace Dr ya fadamin yace na wata biyu da sati daya, nan tace Alhamdulillah Allah ya raba lafiya, ta kashe wayan nan ta zauna tayi shuru tana nanata maganan ciki? Kai anya kuwa kodai wasa yake min? Lokaci daya kuma tayi murmushi tare da godema Allah duk da bata son salma, tana son taga d'anta shima ya haifa ace itama ga jikanta, nan ta dauki waya ta kira hjy zaliha ta fada mata abun da yake faruwa, gaba daya hjy zaliha ta dauke wuta, ta dai daure tace kai naji dadi shima hakan ta fada ne dan taga hjy binta din na murna, tana kashe wayan ta doka ma fauziya waya, bata dauka ba ta kara kira, ta dauka cikin muryan bacci tace wai miye wannan Kiran dasassafe haka, hjy zaliha tace au ke bacci ma kikeyi nan taba mmn labarin abunda ya faru jiya, tare da cewa yanzu tana asibiti ma kishi ya tashi ta saki dariya, hjy zaliha tace lallai ke kina nan baki San maike faruwa ba, salma tana da ciki bata san lokacin data saki ashar ba inji uban wa? Hjy zaliha tace yanzu binta take fadamin mahmud wai ya fada mata, fauziya tace ai banga ta zama ba, ki shirya gani nan zuwa yanzu domin wlh bazan bar salma ta haihu da mahmud ba.......
Maryam Obam😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
50to55
Tana kashe wayan tasa wata doguwar riga, ta dauki gyale, ta fita, tuki take amma gaba daya bata cikin haiyacinta, kai tsaye gidansu tayi, tana shiga tace mmnta taxo su wuce wajan malam, itama ta zira hijab suka nufi wajan malaminsu, sun tarar da Mutane a wajan sai da suka bi layi har yazo kansu suka shiga, yana ganin fauziya ya fara Washe baki, nan suka zauna, yace ya zaku zo ku biyu bayan nace ita daya zata xo? Nan hjy zaliha tace akwai matsala ne sai yasa ka gammu tare, ya daure fuska sannan yace tafita ta basu waje da fauziya zaiyi magana, nan ta tashi tayi waje tana fadin tuba nake, ya kalli fauziya yace ya akayi?? Tace maganin daka bani yayi aiki amma makirar matarshi na rasa mai tamai baya ganin kowa sai ita, yanzu ma tana asibiti ance tana dauke da juna biyu, yayi dariya tare da fadin yanzu mai know kikeso ayi mata? Tace a xubar da cikin domin indai ta haiyu na shiga uku komai nata ne, sannan asa ya tsaneta, inaso asashi ya soni kaman ranshi, na zama komai nace dashi za'ayi aiki a gidan, yace an gama ya taso yazo kusa da ita yana mata murmushi ganin haka yasa ta tamke fuska tare da fadin ya haka kuma? Yayi dariya warin bakin shi ya doketa, yace ta hakan ne kawai Zan baki abunda kikeso, tace bazan iya wannan abun dakai ba ka fadi ko nawa ne Zan baka, yace bana son kudi keee in kin yarda to, in baki yarda ba tashi ki tafi haushi ya kashe ki, nan ta zauna tayi shuru, can tace ta yarda, ya saki dariya nan suka fara aikata zina saboda neman abun duniya Allah ya tsare mana imanin mu, taji jiki sosai yayin da mlm shi kuma abun yamai dadi, nan ya bata magani yace tayi hayaki dashi, sannan ya bata wani turare yace ta feshe duka gidan dashi indai salma ta shaka toh cikin zai zube, sannan ya bata wani kwalli yace tasa indai sukai ido biyu da mahmud toh babu shi babu salma, yace wannan kwallin kar ki kuskura koda da rana daya kiki sawa duk ranan da kika yi fashi toh komai Zai baci, tace toh inya kare fah? Yayi dariya yace bazai kare ba, kullum zaki ganshi a cike, nan tayi godiya ta tashi dakyar ta fara tafiya dan taji jiki, har taxo wajan kofa ya kirata yace duk ranan sati ki dinga zuwa tace toh ta fita tana tsaki, nan taga mmnta tace suje, bayan sun fita tace ya kukayi tace yaban magani tace dakyau kar dai kiyi wasa gaskiya tace hauka nake inyi wasa tabdi da haka har suka karasa gidansu ta sauke mmnta sannan ta wuce gida, har yanzu mahmud bai dawo ba,
Salma har yanzu bata farka ba, mahmud gaba daya ya kasa sukuni, hankalinshi a tashe yake, ya tambayi Dr yakai sau goma yaushe zata farka amsa dai daya yake bashi, bai sani ba amma koda yaushe zata iya tashi, sai wajan karfe uku na rana ta bude ido tare dayin salati mahmud dake gefen gadon bai san ta farka ba dan a hankula tayi salatin, ta hango mahmud a gefenta lokaci daya abun daya faru ya fara dawo mata nan ta saki kuka tare da tambaya maiya faru dani, mahmud yayi sauri ya tashi dan yaji sheshekan kukanta, yace salma dan Allah kibar kuka, ya kamota tare da rungumeta yace salma dan Allah kiyi hakuri nasan na miki laifi babba wlh salma nima na rasa mai yasa nayi haka ji nayi kaman ana turani, am......, tace mahmud badan haka nake kuka ba komai kayi ai matarka ce, ina kuka ne kawai dana ganni a nan ban san maiya faru dani ba, kalamanta yasa gaba daya jikinshi yayi sanyi tare da kara tausaya mata, ya tabbata abun daya faru jiya shiya sata cikin wannan halin amma gudun karta sashi damuwa tace ba abun bane yake damunta, nan ya tashi yace bari ina zuwa, bai dade ba ya dawo tare da driver dasu flaks da kayan tea, nan ya hada mata ya bata tasha, tana sha gaba daya ta amayar dashi a jikinshi, babu abunda yake fada sai sannu, harta gama sannan ya tashi yayi toilet da ita, ya wanke mata jikinta,ya kalleta yace tana da number din hauwa a kai tace eh, ta bashi yasa a phone din driver ya kirata ya fada mata halin da suke ciki, yace ta kawo ma salma kaya, tace toh, nan ya kura mata ido yana kallonta yana murmushi, tasa hannu ta rufe kirjinta, abun ya bashi dariya yace yau ni akema haka, ta dan saki dariya tace naga kallon yayi yawa ne, yace albishirinki tace goro, yace salma Allah ya anshi addu'ar mu, saimu kara gode mai, cikin kosawa taji abun daya faru tace ina jinka, nan yace salma kina da......... Nocking suka ji, yace waye nan yaji muryan hauwa, ya bude tare da amsan kayan ya rufe kofan, yasa mata kayan jallabiya ce, tace ina da me?? Ya matsa kusa da kunnenta yace kina da ciki, lokaci daya wani hawaye ya xubo mata tare dayi ma Allah godiya, yau itace dauke da ciki,
Fauziya tunda ta shiga gidan ta feshe shi da turaran da boka ya bata, jiran dawowan salma kawai take, tayi dan dariya badai ki haiyu anan ba wlh domin ni ya kamata ace na haiyu da mahmud bake ba, tabdi wlh zan iya aikata komai akan inga babu cikin nan.
Dr yazo yaga jikin salma da sauki, yace zasu iya tafiya gida, amma karta dinga d'aga hankalinta, nan ya rubuta mata magani sannan suka wuce, saida suka fara ajiye hauwa kafin suka nufi gida, bayan sun shiga falo nan taji jiri yana neman dauketa tayi sauri ta rike mahmud dan yanda take ganin dishi2 shi kuma gaba daya ya rikice yana fadin salma salma, amma gaba daya bata san yana yiba, fauziya dake d'aki taji maganan shi ta fito da sauri ganin halin da salma ke ciki yasa ta saki dariya tare da fadin ciki sai dai kiga anayi badai ke ki dauka ba, ganin wani ruwa yayi yana xuba daka kafarta da sauri ya dauketa ya kuma fita da ita suka koma asibiti, nan fauziya ta saki shewa burinta ya cika..
Maryam obam😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
55to60
Driver gudu yake amma mahmud gani yake kaman baya tafiya, gaba daya ya tsorata da yana yin salma, suna isa asibitin aka kuma yin emergency da ita, nan Dr ya shiga ya fara dubata mahmud sai kaiwa da komowa yake, Dr ya dauki wajan 30mnt kafin ya fito, ya kalli mahmud yace saika godema Allah yanzu ta dawo haiyacinta, yace Dr cikin fah?? Hope babu abunda ya sameshi?? Dr yace eh babu abunda ya sami cikin sai dai tana bukatar bed rest, inba haka ba cikin zai iya fita, nan yayi ma Dr godiya sannan ya nufi d'akin da aka canza mata, ya sameta a kwance ga wata nurse tana gefenta, bayan ya shiga nurse din ta fita, ta sakar mishi murmushi, ya kamo hannunta tare da fadin ya jikin naki? Tace da sauki, yace kiyi hakuri babyna yana baki wahala koh? Yanda yayi maganan abun ya bata dariya, nan ya zauna tare da ita har wajan 10 tace yaje gida, ya mata wani irin kallo yace in tafi in barki dawa? Tace nurse zata dinga kula dani, yace a'a babu inda zani ina tare dake, tayi murmushi tace plz dear ka tafi kaga babu wani abu dake damuna, na warke kawai hutu nake bukata, yace shikenan amma sai dai in kira hauwa taxo ta kwana dake ban yarda ki kwana da nurse kawai ba, tayi dariya tace toh shikenan,
Kai tsaye gidan hauwa din suka nufa, dama ya kirata ya fada mata zasu zo su dauketa tace babu komai mijinta yana lagos ta fada mishi, bayan sun dauketa yace bari suje gida ta dauko ma salma kaya sai driver ya dawo da ita, hakan koh akayi sunje gidan babu kowa a falo hauwa taje d'akin salma ta kwaso mata kayan sawa da sauran abunda take bukata ciki harda wayarta, sannan suka koma asibiti ita da driver, driver ya taya ta diban kayan sukai ciki dashi sannan ya wuce, hauwa ta kalli salma tace wannan abun kaman wani almara kin tafi lafiya kuma kin dawo jiki babu dadi, salma tayi dariya tace ikon Allah kenan babu yanda bazai iya ba, jarabawa ne, hauwa tace hakane Allah dai ya sauke ki lafiya ta amsa da amin, da hauwa da nurse suka kwana da salma komai take so sai dai a mata basa bari tana wani motsi mai karfi domin har yanzu ruwan nan yana fita.
Mahmud kwanciya yayi a falo, can ya tuna da wayoyinshi a dakin fauziya yayi tsaki sannan ya tashi ya nufi d'akin, tana nan daka ita sai wata riga na bacci iya cinyanta, suka hada ido ta sakar mishi murmushi, lokaci daya yaji komai nashi ya tsaya, shima ya mayar mata da martani, ganin haka yasa taji dadi domin abunda take so ta samu magani yayi aiki, matsawa yayi kusa da ita yayi hugging dinta, gaba daya ya gigice, ji yayi kaman ana tsungulinshi nan suka shiga soyayya, tun daka lokacin gaba daya yaji fauziya ta shiga ranshi har yake ganin ta fiye mishi salma, amma wani gefen na zuciyanshi na karyata hakan, washe gari har wajan 12 suna ta bacci abunsu gaba daya fauziya ta kashe wayanshi,.
Salma ta tambayi hauwa mahmud yazo kuwa dan itama tasha bacci, tace a'a bai zo ba, abun ya bata mamaki tace anya lafiya kuwa? Har karfe daya tayi bai shigo ba, tace bani wayana in kirashi ta kira a kashe, tace anya lafiya, wayanshi a kashe mahmud kuma baya kashe waya, duk ta rude, tace hauwa dan Allah ko zaki gida kiji koh lafiya, tace salma ki kwantar da hankalinki dan Allah, ki kira driver dinshi kiji, nan ta doka ma driver kira, ya dauka tare da gaidata ta amsa tare da fadin oga fa Kuna tare ne? Yace yana cikin gida dazu na shiga naji shuru bai fito ba dan ko sallan asuba yau banga ya fito ba, sai madam tace min yana bacci yace wai ya gaji yana son ya huta, nan salma taji gabanta ya fadi ta kashe wayan, ta kalli hauwa tace hauwa ki kira min Dr ya sallameni, hauwa tace akan wani dalili salma? Tace hauwa barin fauziya da mahmud hatsari ne ki duba fah har yanzu bai zo ba kuma ko waya baiyi ba yaji ya jikina, na kira ance yana bacci wai ya gaji, hauwa tayi shuru tare da tausaya ma yar uwarta tace toh ko Kin je gidan mai zaki yi, ba gwara ki zauna a nan ba ki sami lafiya, tace hauwa baki San wacece fauziya ba, fauziya makira ce wlh ina tsoran makircinta, hauwa tayi dan murmushi tace salma kenan, har akwai macen da zata baki tsoro keda ake jin tsoranki kin mallake miji, ganin hauwa ba zata fahimce taba yasa tayi shuru, gaba daya ranan mahmud bai zo asibitin ba, hankalin salma yayi mugun tashi, ta tashi daka kan gadon nurse tace madam lafiya ina zaki ko toilet zaki shiga, tace mata eh, nan ta taya ta sauka a hankula sannan ta shiga toilet din, tayi alwala, taxo ta zauna tana sallah tana kuka tana rokan Allah ya kare mata mijinta tun wajan biyu ta fara sai da takai wajan uku tana yi, data sallame, nurse din tace madam sannu gaskiya kina burgeni yanda bakya wasa da sallah salma tayi dan murmushi, ta tashi ta koma gado ta taimakon nurse din ta kwanta tana ta Istigfari, bacci barawo yayi gaba da ita.
Mahmud harga Allah ya manta da salma, gaba daya baya ganin kowa sai fauziya ta hanashi fita ko nan da can, salma ta kira ta kira amma sai dai fauziya taita danna mata busy, harta hjy binta itama ta kirashi amma fauziya taki bari ya gani balle ya dauka, ta zauna dashi daka tace kaza yace mata toh an gama,
Yau satin salma daya a asibiti, babu mahmud babu dalilinshi, koda yaushe salma na gayama Allah kukanta, cikin ikon Allah wannan ruwan ya daina zuba, duk ta rame, hjy binta tazo asibiti da kanta ta sami salma a zaune ita da hauwa, ta mata tatas tace kin shanye min d'a inna kirashi baya dauka baya zuwa waje na, to wlh baki isa ba, babu abunda salma take sai kuka, nan hauwa tace hjy kiyi hakuri wlh itama rabonta da mahmud yau wajan kwana bakwai kenan, nan hjy binta tayi shuru, can tace karyan banza muna fukai wlh zanyi maganinki, ta fita fuuuu, tana mota tana tunani ko dai gaskiya aka fada mata domin inta kira fauziya itama bata dauka, sai rannan data dauka tace tana gidansu ta tambaye ta mahmud fa tace yana gida, da haka har driver ya karasa da ita gida, mahmud ko ya koma saniyar tatsa dan fauziya ansan kudi take a hannunshi kaman hauka, har gida ta gani tace tana so ya bata kudin ta siya,
Yau salma ta cika kwana goma sha daya a asibiti, Dr ya bata sallama, yace ta dinga kiyaye wa, tace toh, ta kira wayan mahmud a kashe nan tace suje su hau taxi, hauwa ta fita ta samo mai taxi suka kwashe kayansu suka sa a ciki, kai tsaye gidan suka nufa, babu kowa a falo, har yanzu tana jin kalan abun da taji ranan data shigo falon, tana ta furta innalillahi wa inna'ilahira jiun......
Maryam obam😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
60to65
Har suka haura sama sai data shiga dakinta taji dai2, nan hauwa tace bari inje in hada miki wani abu kici, tace toh, nan ta sauka tayi kitchen, bayan hauwa ta fita salma ta zauna tana kuka tare da tambayan kanta mai tama mahmud, wata zuciyar tace baki masa komai ba, aikin fauziya ne, nan tayi sauri ta kawar da tunanin dan bata son ta gasganta abunda zuciyarta take fada mata,lokaci daya ta share hawayenta tare da fadin koma mai nene addu'a shine magani,
Mahmud ya shigo gida dan yau ya fita suna da meeting, yaji motsi a kitchen ga kamshi dake tashi, nan yayi kitchen din amma sai yaga ba fauziya bace, yace hauwa, yaushe kika zo? Ranta a bace tace dazu, tace salma fa? Tace tana d'aki, nan yayi sama, har hauwa ta gama ta dauka takai mata farfesun kayan ciki ne, da teba miyan ogbono, tace tashi kici, salma ta tashi tare da daukan kayan cikin ta fara ci, tace kaman Kin san abunda nake so inci gashi yayi yaji, hauwa tayi dariya tace mai ciki an bani da kwadayi yanzu wannan ne yayi yaji, tace eh sosai yajin yamin dadi, nan suka fara fira can hauwa tace mahmud ya shigo kuwa? Tayi shuru tare da kallon hauwa taci gaba da cewa dazu ya shigo kitchen nace kina d'aki, salma ta 'kago murmushi tace eh ya shigo yace min bari ya dawo, shuru tayi tare da tunanin toh mai yasa mahmud bai zoba bayan ta fada mai ina d'aki, ganin shurun yayi yawa hauwa tace bari inzo in wuce gida, salma tace kai mai yakon ki bari in dan kara warkewa tace ai kin warke yau gida zani, nan ta tashi ta dauki kayanta tace toh sai min yi waya, Allah ya kara sauki ta fita,
Mahmud yazo zai shiga d'akin salma suka hadu da fauziya tasha wannan kwallin nata, ta fara mai fari da ido, gaba daya ya rikice ya bita, duk da zuciyanshi nason ganin salma din amma ya kasa shiga ya rasa mai yasa, fauziya tabbas ta tsorata da dawowan salma, domin tunda suka dawo ta gansu ta window din d'akin ta, amma abu daya take jin dadi inta tuna cikin salma ya xube, tace yanzu inna bari ta haiyu ta sami namiji aina bani komai ya koma wajanta, tayi dan murmushi tace akan kudi zan iya komai wlh, .
Har gari ya waye mahmud bai zo wajan salma ba, abun ya dameta sosai amma babu abunda take sai addu'a dan daran jiya batayi bacci ba, sallah take tayi, Sai wajan asuba ta samu tayi bacci, shima mahmud din yana son zuwa wajanta amma ya kasa ya rasa dalili, sun fito suna breakfast shida fauziya amma gaba daya hankalinshi na wajan kofar salma yana son yaga koh zata fito ya ganta, fauziya ta lura da hakan, tace lallai zan dauki mataki gaskiya kafin abu ya lalace, ta kalleshi tace ya kamata yau kaje gidan mama ka gaidata yace toh an gama bari in gama sai inje, hakan koh akayi yana fita, itama ta fita, gidan malaminta tayi babu kowa dan haka kai tsaye ta shiga, fuskanta a daure ta zauna yace lafiya kuwa? Tace ina lafiya abu yana so ya lallace, yace ina zuwa nan ya buga kasa, yace kai karya ne ya kuma bugawa, ya hargitsa tare da fadin ya zaku min haka wannan karya ne, ya hargitsa yakai sau biyar yana fadin karya ne, tace wai mai yake faruwa ne, yace cikin bai zube ba, tace what kar ka raina min wayau mana, kana nufin duk aikin da kayi baiyi ba, toh wlh da sake kullum kasa ina ta faman zuwa duk sati kana tabani da wannan kazamin jikin naka amma kace cikin bai zube ba, ya daka mata tsawa cikin murya mai karfi lokaci daya tayi shuru yace ke yarinya karki fadamin maganan banza wannan cikin ko mai zaki a kanshi bazai fita ba, in kika matsa zaki iya rasa rayuwarki, kuma daka yau karki kara zuwa nan inko kika sake zuwa saina sa aljanu sun illata min ke tunda baki da kunya baki San mutunci ba, duk rashin kunyan fauziya ta tsorata musamman yanda taga kwayar idonshi ya canza daka fari zuwa jaaa, yace fita kiban waje da sauri ta tashi tayi waje kirjinta na dukan uku3,
Mahmud bai dade da fita ba, ya dawo, domin babu abunda yake son ya gani kaman salma, dan ko gidan mama din bai jeba, yana dawowa kai tsaye d'akin salma yayi ya ganta a zaune tana kwalla, lokaci daya yaji jikinshi yayi sanyi, ya kira sunanta cikin sanyin murya, salma, tayi sauri ta waigo sukai ido biyu gaba daya yaji kaman an cire mai wani abu, ya nufeta tare da tsugunnawa a gabanta yana fadin salma nayi miki laifin da ban San da wani kalma Zan baki hakuri ba, dan Allah salma ki yafe min wlh ni kaina ban San abunda yake damuna ba, kwana biyu da suka wuce kullum na kasance cikin kasala, wanda bana iya aikata komai, dan Allah ki yafe min, tayi sauri ta toshe mai baki tare da fadin miye haka, dan Allah ka tashi daka wannan tsugunnan kana sani ina jin wani iri, yace salma bazan tashi ba har sai kin yafe min, tayi dan murmushi tare da fadin baka min komai ba inma kamin na yafe maka, nayi ma kaina alkawari bazan taba yin fushi dakai ba, yayi murmushi tare da tashi yayi hugging dinta, yace Zan iya magana da babyna ta d'aga mai gira alaman eh, yasa kunnenshi akan cikinta yana fadin baby hi, how are you, hope you are ok, talk to dady my baby say hi to dady, dariya salma ta saki, ya taso yana kallon ta cikin so da kauna ganin kallon da yake mata yasa ta rufe fuska yayi murmushi nan suka shiga farantawa juna rai,
Fauziya tana fita, ta kira hjy zaliha tana kuka tana fada mata abun daya faru tace rabu da dan iskan, kina ina yanzu muje wajan wani malamin gari da yawa tace ki fito bakin titi zanzo in daukeki mu tafi, tace toh nan ta yayibi gyale ta fito, kai tsaye gidan wani mlm suka je, inda yake zaune a wani daji saida suka ajiye mota sukai tafiya mai nisa a kafa, bayan sun karasa babu abunda kake ji sai kukan tsintsaye fauziya tace nifa tsoro nake ji, hjy zaliha tace karki damu babu abunda xai faru, suna tsaye bokan ya bullo, fauziya ta rike hannun mmnta, ya saki dariya yace ya akayi, hjy zaliha zata fara magana yace dakata nasan maiya kawo ku, ya kwashe da dariya yace wannan cikin bazai fita ba,tace toh yanzu miye abun yi? Babu wani hanya? Ya kwashe da dariya yace hanya daya ne shine ki bar maganan wannan cikin, ki nuna kina so komai zai miki zan baki wani abu da zaki dinga murzawa komai kika tambaya zai baki, tace toh nan ya bata wani abu kaman gyad'a guda daya amma yana da dan girma suka wuce, ranan sunyi sunturi gidajan malamai amma ance cikin bazai fita ba sai gidan wani boka da suka je shine yace cikin zai fita amma aikin da xa'a mata akwai tsada tace babu damuwa ko nawa ne zan biya, nan yace zata bada 3 million, tace yanzu babu a hannuna amma gobe zan kawo, nan suka tashi suka wuce da nufin gobe zasu dawo.. Hmmm muje zuwa dan jin ko fauziya za tayi nasara.
Maryam Obam 😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
65to70
Sai wajan 9 fauziya ta dawo gida, kai tsaye tayi dakinta bata ga mahmud a ciki ba, nan ta kirashi a waya bai dauka ba, tayi shuru tana dan nazari kar dai ace wannan dan iskan ya lallata komai, dana shiga uku, ta kuma doka mai kira yasa mata busy, tace na shiga uku wlh ya bata komai ni yake kashe ma waya, kai tsaye tayi dakin salma tana bugawa, mahmud yazo ya bude cikin bacin rai yace wai ke mahaukaciyar inace? Tace dole ka fadi haka, dama kana nan shine na kiraka kaki daukan waya ko, toh wlh ni nafi karfin wulakanci sai dai kama waccan mara zuciyar, yace keee kisan abunda zaki dinga fadamin inba haka ba wlh ranki zai baci, tace ya baci din mana babu abunda ka isa kamin wlh, yace haka kika fada koh? Tace eh yace ok kije gidanku saina neme ki, ta saki dariya wlh babu inda zani baka isa ba wlh, ai gidan nan na shigo kenan sai dai kai ka fita ka barshi wlh,kuma ina nan kaida kanka zaka kawo kanka yayi murmushi tare da tsaki ya koma dakin salma yasa key ya barta tana ta hauka, salma gaba daya ta tsorata dan bata san tashin hankali ko kadan, ya kalleta yayi murmushi tare da fadin dear ya naga kin canza? Tace dan Allah ka tafi wajenta wlh ban san rigima plx, ya daure fuska, ganin haka yasa tace kayi hakuri ban fadi haka dan in bata maka rai ba, yace toh karki karamin maganan inje wajanta, tace insha Allah babyna, salma gaba daya ta tsorata da kalaman fauziya, tace dole in kara dagewa da addu'a,
Fauziya tana yin d'aki ta kira hjy binta ta fada mata abunda mahmud ya mata da wanda yayi da wanda baiyi ba duk ta fada mata, dama tana fushi dashi yaki zuwa wajanta wajan sati daya kenan, tace kiyi hakuri gobe zanzo gidan da safe tace toh sai kinzo tana kuka,ranan fauziya bacci gagaranta yayi ta kosa gobe yayi taje wajan mlm a xubar da cikin salma.
Hjy binta karfe bakwai ta dira gidan mahmud, lokacin basu tashi daka bacci bama dan sai da suka kai asuba suna sallah kafin suka kwanta, fauziya ta fito ta rungumeta tana kuka, tace yi shuru ina mahmud din? Tace yana dakinta basu fito ba, ta haura sama ta fara buga dakin tana Kiran sunan shi, yayi sauri ya farka, yace salma ta canza kaya da sauri dan rigan bacci ne a jikinta tayi sauri tasa jallabiya, sannan ya bude kofar kai tsaye dakin ta shiga tana sakar mishi harara, tace sannu shanyayye, ta kalli salma tace kin shanye min d'a baya ganin kowa sai ke, kin raba ni dashi kwata2 baya zuwa wajena yanzu harta office Kin hanashi zuwa toh wlh baki isa ba, daraja daya kika ci shine kina dauke da jikana a jikin ki da yau wlh baki kwana a gidan nan ba, mahmud yace dan Allah mama kiyi hakuri wlh ba laifin salm...... Dallah yimin shuru karka cemin komai ai dama ita bata laifi, kai da ita Kuna ta wulakanta min y'a toh wlh ka fita daka ido na, gwara ka dawo cikin hayyacinka wlh, tun kafin inyi mugun saba maka, kazo ka makale mata kun bar min y'a ko oho, duk ta rame sai zalintan ta kake wlh mahmud Zan saba maka indai kaci gaba da haka, ta fita fuuuu yabi bayanta yana bata hakuri kun San tsakanin d'a da uwa, tace babu komai fauziya tana nan ta labe tana jin abunda suke fada, tace ya jikin salma din? Yaji dadin tambayan da tayi cikin jin dadi yace da sauki, tace kar dai ka bari ta dinga abubuwa Mai wahala tunda baiyi kwari ba, yace toh mama na gode, ta wuce, Fauziya dake labe tace kambu wlh da sake wato itama tana son cikin dukanku zanyi maganin ku wlh, hjy binta bata dade da fita ba itama fauziya ta fita,
Mahmud a ranan salma tace ya kamata yaje office dan ya kwana biyu a gida, bai musa ba yace babu damuwa, yace baya son inya fita tace za tayi wani abu da kanta ta zauna kar baby dina ya samu matsala, tayi murmushi tace shikenan babu damuwa sai ka dawo, ya bata fake sannan ya fita,
Fauziya taje banki ta cire kudi, ta nufi wajan mlm yau ko biya ma mamanta ba tayi ba, ta wuce ita daya, bayan taje ta bashi kudin yace ta koma gida nan da sati daya cikin zai xube cikin murna ta wuce, ba tayi gida ba wajan mamanta tayi, ta sameta tana kallo, ganin fauziya din yasa ta Washe baki tace Tun daxu inata jiranki amma shuru, fauziya tace ai har naje ma daka can nake, tace kaji yar albarka, yanzu ya akayi tace yace nan da sati daya zai xube, hjy zaliha ta washe baki tace yauwa kinga inya xube kowa ya huta, ke naji ma har yanzu shuru ta tabe baki tare da fadin bari in wuce gida, ta fita.
Salma bayan mahmud ya fita, tayi dariya tare da fadin bari inje in daura mishi abinci tunda naji sauki inna biye mishi babu abunda zan dinga yi, gwara inyi in sami lada, tayi kitchen ta daura abinci, fauziya ta dawo taji kamshi na tashi kai tsaye tayi kitchen din tace munafuka dama kece, salma tayi banza da ita nan ta matsa kusa da ita takai mata duka a ciki nan ta fadi tana wash Allah innalillahi wa inna'ilahira jiun, ganin haka yasa tabar kitchen din tana fadin kadan kika gani,
Mahmud tunda ya fita yaji gaba daya hankalinshi bai kwanta ba, ya dawo gida Tun daka waje yake jin kauri da sauri ya shiga gidan, yaga hayaki a kitchen yana fitowa da sauri yayi kitchen din ya fara tari ya kashe gas din yaga salma a Kwance nan ya kuma rudewa ya dauketa yai waje da ita, driver ya shiga suka kama hanyar asibiti yana ta fadin yi sauri driver yana ta gudu, tazo zata tsallaka yayin dashi kuma ya kasa tsayar da motar ya bigeta, nan mahmud ya saki Salati, jini gaba daya jikinta, nan matar da suke tare ta saki ihu mahmud yazo yace ta shigo suje asibiti, dakyar ta yarda ta shiga sukai asibiti dukan su emergency akayi dasu, yayin da yarinyar ko numfashi ba tayi ita kuma salma gaba daya ta fita hayyacinta.
Maryam Obam😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
70to75
Mahmud ya shiga cikin tashin hankali, har rama yayi na lokaci daya fuskan shi tayi fayau, hada kanshi yayi da bango yayin da zuciyarshi take bugawa, gefe daya kuma ga matar da suka bigema yarinya tana ta faman ihu sun kashe Mata y'a,yayin da driver kuma gaba daya komai nashi ya tsaya dan yana tsoran kar ace yarinyar ta rasu, gaba daya suna cikin tashin hankali, dukansu suna son suga Dr ya fito ya musu bayani,.
Fauziya tunda ta bige salma tayi d'aki take a tsorace yanxu idan wani abu ya sameta fa? Tace ni na aikata mata hakan nasan Mahmud bazai barni ba, nan ta fito tayi kitchen din amma babu salma babu dalilinta, kai tsaye dakinta tayi shima dai bata ciki, nan ta kuma tsorata tayi waje, tana tambayan security salma ta fita ne? Suka ce eh oga ya dauketa kaman a sume take nasan dai asibiti Suka tafi, nan tayi gida da sauri tare da fadin na shiga uku, nan tayi d'aki ta dauko key din mota tama rasa ina zata sai yawo take a titi, daka karshe ta yanke bari taje gidan hjy binta, nan ta nufa bayan tayi parking ta fito tana kuka, nan hjy binta ta fara tambaya lafiya kuwa Fauziya mai ya faru? Nan ta fara shargo mata karya salma ce tana ta nemana da kokawa naki kulata ganin haka shine tazo zata janyo ni shine ta zame ta sume, ni yanxu ina tsoran ta farfado ta kullamin sheri wajan Mahmud, tace ni na tureta, nan hjy binta ta kumbura tare da fadin wato tana bakin cikin wannan cikin koh tana so ya xube dama naga take takenta bason cikin take ba wlh, nasan magani tayi tasha dan karta dauka yanzu Allah ya kamata ya bata shine take son ta zubar min da jika toh wlh idan cikin nan ya zube wlh saina sa an daure min ita harda iyayenta kaji yarinyar banza mara mutunci, tashi muje asibitin.
Dr dai shuru har yanzu bai fito bah, Mahmud dai yana nan a tsaye tun dazu ya kasa zama, wani gefen kuma yana tunanin mai yasa salma taki Jin magana na nace kartayi komai amma taki ji, yanzu gashi taja ma kanta matsala wani hawaye ya xuba a idonshi ya furta a hankali salma ina sonki, I can't live without you, mai yasa kika ki jin magana na why salma??? Jin an taba shi yasa ya waigo hjy binta ce cikin bacin rai amma ganin tilon dan nata na hawaye yasa gaba daya jikinta yayi sanyi, tasa hannu ta share mai tare da kamo shi ta zaunar dashi lokaci daya yasa kanshi a kafadanta yana kuka kaman karamin yaro, nan hjy binta ta tsorata, Fauziya kuma babu abunda zuciyarta keyi sai bugu, hjy binta tace Mahmud mai ya sami salma din? Tace har yanzu Dr bai fito bah mama ina tsoran kar in rasa salma ina sonta, hjy binta tace haba Mahmud kaji ance ma zata mutu ne? Ka daina wannan maganan kaji, yace mama wlh a cikin wani yanayi muka zo asibitin nan, ina cikin tashin hankali, nan taita bashi baki tare da mishi nasiha, ita kuma babu abunda take sai Allah yasa kar cikin ya zube domin tana bala'in son cikin, matar dake gefe itama ta zabga tagumi tana jiran taji lafiyar yar tata,
Wasa2 sai da Dr yayi kusan awa biyu kafin ya fito, gaba daya Suka tashi badda Fauziya da tsoro ya dameta, Mahmud yace Dr ya jikinta? Dr yace muje office nan duka Suka bishi harda driver, bayan Dr ya zauna ya kalli Mahmud yace gaskiya you are very lucky, matarka na abubuwa wanda basu dace damai ciki ba, sai dana fada maka karta dinga yin abu mai wuya amma Ka barta tana yi, hjy binta ta katse shi da fadin yanzu maiya sami cikin? Yace cikin na nan, sai dai kuyi mata addu'a ta haiyu lafiya, hjy binta tayi ajiyar zuciya tare da furta alhamdulillah, Fauziya jin haka taji kaman ta shake hjy binta dan takaici dan taga yanda take wani zakewa akan cikin, Mahmud yace Dr yarinyar nan fah? Hjy binta Tace wace yarinyar nan ya bata labari Dr yace eh munyi iya kokarinmu sai kuyi addu'a domin har yanzu bata farka ba, nan matar nan ta saki kuka tare da fadin nashiga uku sun kasheta, hjy binta Tace haba baiwar Allah ki daina fadin haka miye amfanin kukan addu'a xaki mata, ta kalli Dr Tace zamu iya shiga yace eh, nan sukai emergency din, salma tana kwance amma idonta biyu tana kallon sealing, yayinda yarinyar ita kuma ansa mata oxygen, saman kanta ansa plaster da kafanta na hagu, alaman ciwo taji a wajan, Mahmud wajan salma ya nufa, ya kira sunanta a hankali tare da rike mata hannu, hawaye ya zuba a idonta, yace ya jikin? Ta amsa cikin sanyin murya dasauki, nan ta hango Fauziya da hjy binta gabanta ya fadi, hjy binta ta matso tare da fadin kinci sa'a cikin bai xube ba da wlh sai kinje freezing keda iyayenki Mahmud yace haba mama bakya ganin halinda take ciki, tace yimin shuru, kana nan tana maidaka wawa baka San abunda kake ba, taso ta zubar da cikin ne Allah ya nuna mata iyakar ta, nan salma ta saki kuka, tace kaji makira koh, ai baki kuka ba sai kinyi kuskure kin zubar da cikin nan sannan zaki kuka, tayi tsaki ta fita Fauziya ma tabi bayanta, nan Mahmud ya zauna yana ta bata hakuri tare da fada mata wata rana sai labari, ta kara hakuri akan duk abunda mama zata mata, tayi dan murmurshi tare da fadin nasha fada maka, komai mama tamin babu komai mahaifiyata ce, ta isa tamin komai, yayi murmurshi yace nagode salma Allah ya saka miki da alkairi, nan ya tashi yaje kan yarinyar nan yana dubata yana fadama salma abunda ya faru lokaci daya yayi shuru tare da kara kurama fuskan yarinyar ido yana tuna inda ya Santa, salma dake kwance gaba daya idonta na kanshi tana mmkin irin kallon da yake ma yarinyar gashi yana mata magana yayi shuru, lokaci daya yayi murmushi, ya dago kai sai a sannan ya tuna salma na wajan kuma yaga tana kallon shi.......
Maryam Obam😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
75to80
Suka hada ido da salma yace salma nasan wannan yarinyar, tace a ina?? Yace tana yawan zuwa office dina kwanaki daka baya na daina ganinta, tunda na ganta naji kaman tana naiman taimako Amma Allah baisa na taba tsayawa naji mai take nema ba, salma tace Allah sarki komai ai sai Allah ya nufa, Allah ya bata lafiya sai kaji matsalanta inna taimakawa ne a taimaka mata, ya amsa da ameen, nan ya kira driver yace ya kwantar da hankalinshi insha Allah zata tashi babu abunda zai sameta, driver yayi ajiyan zuciya tare da fadin Allah yasa oga hankalina ya tashi sosai ban taba bige ko kaza ba amma na fara da buge mutum, Mahmud yace idan Allah yasa abu zai faru babu mai hanashi, dan haka kayi imani da hakan, yace hakane oga ngd, nan Mahmud ya zaro kudi ya bashi yace ya siyo musu abinci, ya amsa cikin ladabi ya fita,
Mahmud yana tare da salma har driver ya dawo yarinyar bata farka ba, Mahmud ya cire nasu da drinks, sannan yace ya dauka yaba ma matar nan itama, nan ya amsa da to ya fita, Mahmud ya bude fried rice ne, da kaza rabi a ciki, da garden salad, nan ya fara ba salma tana ci harta kochi, sannan shima ya samu yaci, bayan ya Gama ya kalleta yace salma ta amsa da na'am, yace mai yasa kika shiga kitchen bayan nace kar kiyi aikin komai? Tace kayi hakuri Mahmud bayan ka fita ne, nace bari inje inma abinci dan naji jikina da sauki kuma na gaji da zama waje daya, ina cikin aikin.... Tayi shuru yace inaji tace ban San maiya faru ba kuma sai dai na ganni a nan, shuru yayi yana kallonta kaman yana son gano wani abu, can yace salma dan Allah daka yau koda mun koma gida ban son ki kara yin wani abu da kanki, inaso kimin alkawari, Tayi shuru tana kallonshi, tace insha Allah bazan kara yiba, har sai na warke sosai, yace no koda kin warke bana son kiyi komai har sai kin haiyu, ban San matsala, tayi dariya tare da fadin shikenan koda yaushe ni mai bin umarninka ce, yayi murnushi tare taba mata hanci, jin motsin yarinyar nan yasa sukai saurin waigawa da sauri, Mahmud yayi wajanta da sauri ya danna wani abu ja, ko minti biyu ba'ayi ba saiga Dr ya shigo dasauri, nan ya fara dubata ganin numfashinta ya koma normal aka cire mata oxygen din, Dr yace mata ya jikin tace da sauki cikin sanyin murya, yace inane yake miki ciwo? Ta nuna mai kanta, yace kiyi hakuri a hankali zai daina, ya kalli Mahmud yace jikin da sauki sai dai ciwon da taji shine yake damunta, nan Mahmud ya godema Allah ganin ta tashi kuma ance jikin da sauki, Dr yasa a fitar dasu daka emergency asa su cikin wani daki, salma tace a kaisu na mutum biyu ita da yarinyar kar a raba su, hakan koh akayi, lokacin da aka fito dasu za'a kaisu dakin driver da mmn yarinyar suka taso a tsorace ganin yarinyar idonta bude tana dago hannu tana mika ma mmnta yasa driver yaji dadi tare dayi ma Allah godiya, tana rike da hannun mmn sukai dakin, nan mmn ta saki kuka tana fadin ya jikin naki? Ta amsa dasauki, tasa hannu tana share mata hawaye tare da fadin aina warke kin sha naki maganin? Ta amsa da eh nasha, salma taji sun bata tausayi, tace mama kiyi hakuri Dr yace babu komai dake damunta yanzu ciwon jikinta ne kawai, shima insha Allah zai warke da wuri, matar da waigo tana kallon salma tace Allah yasa hakan ita daya gareni sai yasa na shiga damuwa ina tsoran in rasa ta, sai a sannan Mahmud yayi magana yace insha Allah babu abunda zai sameta,
Kwanan su hudu aka sallame su, a dan kwanakin da sukayi salma ta fahimci matar kaman tana da wani ciwo, tana yawan shan magani, in bata shaba yarinyar zatai ta mata magana tasha, gashi bata San shiga cikin dakin wanda ako da yaushe zaka ganta a waje, sai anyi dakyar zata shigo ta rakube wajan gadon yarta, suna hada kaya salma tace mama yanzu dai sai kuxo muje gidan mu, idan kuka kimtsa sai a kaiku gida, nan matar tace a'a babu inda zasu sun gode, saida mahmud ya shigo ta fada mai sannan yayi mata magana shine ta yarda, driver ya dibi matar ya fara tafiya dasu sannan ya dawo ya kwashi su salma, dakin baki driver ya kaisu, koda su salma suka je gida fauxiya bata nan, nan Mahmud ya bada kudi a kawo musu abinci, ba'a dade ba driver ya kawo, ya bashi na matar yace ya kai mata sannan yayi sama dana hannunshi, ya tarar salma bata dakin ya daiji kanshi sabulu a nan ya gane tana toilet, ya xauna bai dade ba ta fito, ido ya kura mata yana kallonta, tayi murmushi tace wannan kallon fah, dariya yayi ya tashi ya kamo ta sannan ya xaunar da ita akan kujeran dake dakin, yace bana hanaki yin komai ba, tace mai nayi yanzu tare da xare ido, yace wa yace kije ki wanka da kanki? Tayi dariya mai sauti tare da fadin ai wannan ba aiki bane, yace to daka yau shima bana so kina yi, ni zan dinga miki, Ta kalleshe suka hada ido, tayi sauri tayi kasa da kanta tana dariya, nan ya tashi ya dauko ledan abincin ya bude sakwara ne da miyan egusi, yaji ganda da dry fish, ga wani kamshi dake tashi, dayan ledan kuma farfesun kayan ciki ne, kafin ya gama budewa harta dauki sakwaran Ta fara ci, dariya yayi tare da fadin babyna yasa bakya wasa da abinci itama dariyar tayi taci gaba daci, har Ta koshi sannan ta ajiye, yaje ya dibo mata ruwa a wani bowl ta wanke hannu, ta kalleshi tace yasu mama suma an kai musu? yace eh tace bari inje in duba su, yace a'a ki zauna ki huta anjima sai kije bata musa ba ta zauna nan ya xauna da ita yana ta bata kulawa har bacci ya dauketa, sannan ya fita.
Salma sai wajan 4 ta tashi, alwala tayi, sannan tayi sallah, kai tsaye dakin baki tayi taga kofar a bude ta shiga, taga matar da yarta, suna zaune akan kujera sunyi wanka sun sa kayan data basu, da fara'a tace sannunku suka amsa da yauwa nan salma ta tambayi yarinyar miye sunanki mmnki taki fadamin yarinyar tayi dariya tace ai bata fada, tace sunana salamatu, salma tayi dariya tace lah sunan mu daya, yarinyar tace to yanzu xaki sa mamana ta fara jin kunyan ki, salma taci dariya, salma ta kalli mmn da tayi shuru tana musu dariya, tace mama a wani anguwa kuke? Nan tayi shuru, yarinyar tace bamu da gida duk inda muka samu anan muke kwana, salma tace kaman ya? Mmn tace ke ban San surutu, yarinyar tayi shuru salma tayi dan murmushi tare da fadin mm yanzu dai saiku xauna a nan idan ta gama warware sai ku tafi bata musa ba tace babu komai, jin muryan Mahmud yasa ta tashi ta fita dan taji security na mishi sannu da zuwa, ta fito tana mishi murmushi da sauri ya karaso wajanta yayi hugging dinta sannan sukai ciki, a falo suka xauna nan take fada mishi abunda ya faru, shuru yayi na wani lokaci kafin yace inaga mu basu kudi su wuce, salma tace a'a ina so in san ko su waye su, ina son ka taimaka musu, yace salma idan na basu kudi aiya isa, no need ki san kosu su waye, tace dear plz wlh suna ban tausayi kar ka hanani in san labarin su, plz yace owk Allah ya taimaka, fauxiya ta shigo falon babu sallama sai sakin tsakin da tayi tare da fadin mayya, kwadayi dai mabudin wahala, Mahmud cikin fushi yace ke wace irin mara tunani ce, tace eh bani dashi sai waccan yar iskan data dauko cikin wani tace naka ne,yace keee fauxiya kije na sakeki saki daya kuma ki jira takardan kotu akan shegenta min d'a, tace wlh ba........ Kafin ta karasa magana suka ji muryan hjy binta tana fadin dakyau ya waiga cikin tsoro.......
Maryam obam😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
80to85
Harta karasa shigowa falon, bai kuma cewa komai ba sai kllonta da yake yi, yayin da falon ya cika da sautin kukan fauziya, hjy binta zama tayi akan kujera, sai a sannan Mahmud ya iya furta kalman mama, ta daga mai hannu alaman yayi shuru, tace naji komai bana bukatan wani magana, yanzu dai kafin wani bayani ka dawo da matarka, ganin ynda ta daure fuska babu alaman wasa a ciki, yasa yace na dawo da ita, jin haka fauziya dake kukan munafurci ta matsa kusa da hjy binta tana fadin wlh mama nasan nan gaba zai kara saki na, indai akan waccan matar tashi ne, ta nuna salma da gaba daya komai nata ya tsaya cak, sai a sannan hjy binta ta kalli salma, tace mlm ki zauna kin wani tsaya ki kam, salma tayi sauri ta zauna, nan hjy binta ta kalli fauziya dake faman sharara kuka, tace fauziya naji abun daya faru tun daka farko, nayi mamakin da wannan kalman ya fito daka bakin ki, a yau inda bani da wani halaka dake dasai nasa an hukunta ki, domin bazan bari aci zarafin jika naba, ina so daka yau ki sani akan wannan yaron zan iya sabama kowa dan haka ki kiyaye karki kuma aikata wannan kuskuren dan bazan dauka ba, fauziya da mamaki ya cika ta, ta amsa da toh, amma cikin zuciyarta fadi take wlh sai nayi maganinki basai kinga abun da za'a haifa ba, balle ki kirashi jika ba, nan da kwana biyu cikin zai zube sai inga ta tsiya,
Hjy binta ta katse mata tunani da fadin saura ke nazo ne in miki kashedi, salma ta dago dakai cikin tsoro tare da fargaban mai zata fad'a, tace naga take takenki bakya son wannan cikin sai yasa kike wasa dashi, wlh kinji na rantse miki indai wani abu ya sami wannan cikin saina sa an hukunta ki, taci gaba da fadin nasa an kawo masu aiki wanda zasu dinga yi muku abinci, saura kuma ki koresu, indai kikai hakan saina saba miki, daka yau zasu fara abinci a gidan nan har sai kin haiyu, in yaso kyayi duk abinda kika ga dama, salma cikin sanyin murya tace nagode mama, hjy binta tace daina godemin badan ke nayi ba, tace ku bamu waje, nan ita da fauziya suka tashi ko wacce tayi dakinta,
Ta kalli Mahmud wanda gaba daya ya shiga cikin wani hali, sai taga kaman ya rame, lokaci daya taji ya bata tausayi ta tashi ta dawo kujeran da yake, ta kira sunanshi, ya amsa cikin taushin murya, tace banji dadin abun da kayi ba, duk da itama bata kyauta ba, bai kamata ka saketa ba, yar uwarka ce, ko kana so ka bata mana zumunci ne? Yayi saurin cewa a'a mama abubuwan fauziya ne sunyi yawa rashin mutuncin yau daban na gobe daban, tace kayi hakuri kaji, bana so in kara jin ka furta kalman saki a bakin ka, kaima gashi yanzu za'a fara maka haiyuwa ko kana so kaima aima naka ne? Yace mama Allah ne shaida na, bana sakin mace ba tare da hujja ba, tace koma miye daka yau bana so, ka kara hakuri akan komai kaji, yace insha Allah, nan suka dan taba fira na d'a da uwa, sannan ta tashi ta wuce,
Fauziya tana shiga d'aki ta dauki waya ta kira mamanta, tana fad'a mata abunda ya faru, hjy zaliha, tace lallai binta, dole in sake daukan mataki akanta, wato ita idonta ya rufe akan zata sami jika koh, shine har take fad'a miki magana a gaban wannan yar iskan, kar ki damu zan dau mataki, fauziya tace ni yanzu gaba daya ma ya daina zuwa d'aki na, gaba daya ya tare a wajanta, hjy zaliha tace kar ki damu kwanan nan zai dawo wajanki bari cikin ya zube, ai yau saura kwana biyu sati dayan ya cika, kinga in cikin ya zube a nan sai musan yanda za muyi mu xuga binta akan da gangan ta zubar, na tabbata sai tasa an mata wulakanci, daka karshe tasa Mahmud ya saketa, kinga ya dawo naki ke daya sai ynda kika ce, nan fauziya ta saki shewa cikin jin dadi tace kai mama sai yasa nake sonki wlh, hyj zaliha tayi dariya tace zan iya yi miki komai ai dan inga kina farin ciki,.
Wasa2 har sati dayan ya wuce sati biyu, amma cikin na nan, fauziya ta shiga damuwa sosai kullum salma kaman ana kara mata lafiya, ga wani abun bakin ciki hjy binta tana yawan zuwa duba salma, taga ya take ciki, hjy binta ta sauko akan tsanar da tama salma,suna da gida a zone2 wani katon gida, ta sami labarin gidan ya zama na fauziya, ga wani gidan gonan su inda ake had'a su drinks kala2 dasu kaji kifi da sauransu shima ya zama mallakinta ga wasu gida da take dasu guda biyu, a cikin Abuja, nan ta kira Mahmud ta tambaye shi akan mai zaisa yaba fauziya gida da gidan gona bai fad'a mata ba, nn yace wlh bashi ya bata ba, ta kira fauziya tace ya akai ya zama nata, budan bakinta tace ki tambayi danki mana, abun ya bata mamaki, gashi taji labari wajan mutane da dama akan halayen fauziya na bin malamai nan Hjy binta taji ta fitar mata a rai, tace insha Allah zan kara dagewa da addu'a, tun daka lokacin ta fara sakema salma domin ta gano itace mai son danta tsakani da Allah,
Fauziya taje wajan boka akan har yanzu cikin bai zube ba, nan yace mata ai cikin bazai taba fita ba, amma abu daya xa'a mata yaron zaizo bada rai ba, yace inta yarda toh, tace ta amince, yace toh duk sati za'a dinga yima aljanu ynka suna shan jini, a kalla zaki dinga kashe million 5 duk sati, tace babu komai indai za'a kashe dan yaxo bada rai ba, ni burina kawai yaron ya mutu tunda ni har yanzu bani da ciki yama daina kulani, boka ya kwashe da dariya domin yaga zai tatseta yace ki tashi kije sai na jiki, ta tashi ta tafi, boka ya kuma kwashewa da dariya tare da fadin mahaukaciya ni na isa in kashe mutum ne, ko in zubar da ciki, nima sa'a ne inna fada abu ya faru, amma wannan banyi sa'a ba, sai ki kawo kudi inta ci.
Salma taja yarinyar matar nan jikinta inda yarinyar take fad'a mata bara xuka zo Abuja, ita da mamanta wanda take dauke da breast cancer sai a sannan salma ta lura inta shiga dakin tana jin wani wari duk saita dauka ciki ne yasa take ji, yarinyar tace babanta ya rasu wajan shekara biyar kenan dangin shi suka cinye dan abun daya bari, ga cuta na damun mamana anyi na hausa abun ya warke ashe ya lafa ne, daka baya ya kuma tashi anyi na hausan yaki yi, dole muka je asibiti akace sai an yanke nonan, ta yarda aka yanke gashi dayan kuma ya kama, wanda wannan karan taki yarda a yanke, sai dai magani da take tasha, gashi bamu damai bamu sai dai muyi bara mu sami na abinci, wata wacce muke bara ta bata shawaran muzo Abuja zamu iya samun wanda zai dauki nauyinta a dubata a babban asibiti hala ta warke, shine abun daya kawo mu Abuja, muna bara duk inda muka ga kango sai mu kwana abun mu, wata rana na sami labarin mijinki akan yana taimaka ma mutane, wata wacce muke bara ta rakani office dinshi nan muka zauna muna ta jira amma shuru bai fito ba, muka wuce wata rana na kuma komawa ni daya a nan naga ya fito zai shiga mota shida masu bashi kulawa, gaba daya saina kasa zuwa wajanshi, haka naita zuwa amma bana iya yi mishi magana daka karshe masu gadin wajan suka ce kar in kuma zuwa, shine bamu sake haduwa ba saida na ganshi asibiti driver dinshi ya bigeni, salma ta tausaya masu sosai, ta dau alkawarin zata sa Mahmud ya taimake su.
Maryam Obam 😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
85to90
Salma tama Mahmud bayani akan yarinyar da mmnta, shima ya tausaya yace zai sa a kaita asibiti koh Allah zai sa a dace, salma taji dadi tare dayi mai godiya, yayi murmushi yace sai ki fada mata su shirya gobe sai a kaita, nan salma tace toh tare da tashi ya bita da kallo yana murmushi ganin yanda ta tashi tana nishi, ganin yana murmushi yasa ta bishi da ido tare da fadin lafiya? Dariya ya saki mai kara yace babu komai, ta dan bata fuska tace akwai mana ka fadamin plz, tashi yayi yaxo kusa da kunnanta yace I love you, murmushi tayi cikin Jin dadi tace I love you too my dearest husband, sannan ta fita.
Salma ta shiga dakin da sallama, salamatu ta amsa tare da fadin sannu aunty yanzu nake son inzo wajanki inji koh kina son wani abu, salma tayi dariya tare da fadin ina mama? Tace tana bayi, nan salma ta zauna suna ta fira da takwaranta, har mmn ta fito daka bayi, salma tace sannu mm nan tayi murmushi tare da fadin yauwa ya jikin naki? Salma tace da sauki, nan taci gaba da magana gobe da safe zaki shirya zaku asibiti Dr ya duba ki, mmn ta kalli salma da mamaki ya akai tasan bata da lafiya, ko dai taji warin da takeyi ne, salma ta katseta da fadin salma ta fadamin komai, insha Allah zaki warke kuma za'a dace da yardan Allah, mmn tace ngd Allah ya saka da alkairi, da ana samun irinku masu taimako da talaka yaji dadi, Allah ya kara arxiki salma ta amsa da ameen, salamatu tace aunty Allah ya saka miki da gidan aljanna, ina son mmn ita daya ta rage min, ita nake gani inji dadi, ciwon yana damunta sosai, bani da wani Jin dadi, kullum ina kwana da fargaba, Amma a yau zanyi bacci cikin Jin dadi, salma idonta ya ciko da kwalla tace takwara ta insha Allah komai zai wuce babu abunda zai sameta kici gaba da addu'a, sun dan taba fira sannan ta tashi ta nufi gefensu,
Fauxiya gaba daya, ta shiga damuwa komai tayi baya yi, gashi tana ta kashe kudi, harta gidajan da take dashi ta saida, dan dai kawai taga ta sami Mahmud, sannan abun dake cikin salma yaxo bada rai ba, indai taje wajan boka ko nawa yace zata bashi dan dai taga ta sami biyan bukata, Amma kullum kaman ana kara sama Mahmud tsanarta, ga hjy binta itama yanzu ta dawo wajan salma, komai tasa ayi a kanta shima yaki aiki, Amma duk da haka Fauxiya bata saduda ba, ita da mahaifiyarta.
Washe gari da safe, kaman yanda Mahmud yace za'a kai su asibiti, hakan ko akayi, salma tace ya bari suje tare yace a'a baya son tana fita kar wani abu ya sami baby dinshi haka ta hakura, driver ya kaisu Mahmud yace ya tsaya ya musu komai, hakan ko akayi, sunje Dr ya dubata, yaga dayan wajan da aka yanke, sai kuma dayan daya kama, yace dole sai an miki aiki ta wajan gefen breast dinta akwai wani bkin abu daya fito, shima yace za'a yanke shi, tace Dr Idan aka cire zan warke kuwa? Yace insha Allah, nan tace toh ta yarda, yace taxo jibi a mata aikin nan suka tashi suka fita, ita dai salamatu gaba daya hankalinta bai kwanta da wannan aikin ba, sun dawo sunma salma bayani, ta fadama Mahmud ya bama driver kudi yace ya biya komai da komai, kafin jibi din,matar gaba daya ta shiga cikin damuwa, tun da suka dawo babu abunda take sai tagumi da hawaye, salamatu itama ta shiga damuwa, tana ta rarrashi amma sai tace ina ganin kaman bazan tashi ba, yarinyar ta tashi da sauri tana kuka tayi gefen su salma, a nan ta ganta ita da Mahmud a falo, salma ganin yanda ta shigo cikin tashin hankali tana kuka, yasa tace salma lafiya kuwa? Maiya faru? Tace mama,... Ta kasa magana nan salma tace maiya sameta? Mahmud yace muje mu gani, suka fita sukai dakin suka ganta tana ta kuka , salma ta matsa kusa da ita tace mm maiya faru wani abu aka miki? Tayi dan murmushi tace babu ko daya ina ganin kaman wannan ciwon nawa bazan tashi ba, ina tausaya ma yarinyar nan ban san wani hali zata shiga ba, bata da kowa sai ni, salma tace mama ki daina fadin haka cuta fah ba mutuwa bane, tayi murmushi tace hakane ta kama hannun salma tace dan Allah kimin alkawari koda na mutu ban tashi ba ki rike min yarinyar nan,har zuwa sanda za tayi aure, salma ta waiga ta kalli Mahmud ya daga mata kai alaman eh, tace nayi miki alkawari zan riketa amana, balle ma insha Allah zaki tashi, tace ngd Allah ya saka miki da alkairi, salma wani kwalla ya zubo mata ta amsa da ameen, salamatu babu abunda take sai kuka, salma ta rarrasheta tare da fada mata cuta ba mutuwa bane, tayi hakuri,
Kaman yanda Dr yace su koma, haka suka shirya suka tafi, wannan karan harda salma, an kaita dakin theater, nan Dr uku suka shiga, salamatu gaba daya jikinta yayi snyi tana tuna abunda ta fad'a mata jiya, da daddare ko bayan raina inaso ki zauna da wannan baiwar Allah bisa amana ki dauketa tamkar ciki daya kuka fito, sannan ki rike maraicin ki dan Allah kar ki manta ko ke wacece, salma ce ta katse ta tare da dafa ta, tace kiyi hakuri insha Allah zata tashi, Dr sunyi wajan 3hr kafin suka fito ko wanne a sanyaye, salamatu tana ganinsu ta tashi da sauri tana tambaya ya jikin mmnta? Duka suka mata shuru, har salma ta karaso tace Dr ya jikin nata da fatan anyi a sa'a, daya daka cikin Dr din yace hajiya sai dai kuyi hakuri Allah ya mata rasuwa, salamatu ta saki ihu tare da fadiwa kasa sumamma, nan aka dauketa akai emergency da ita, aka bata taimakon gaggawa cikin ikon Allah ta farfado, salma na kusa da ita tace aunty dagaske mmna ta rasu bazan sake ganinta ba, nan salma ta rike mata hannu tana fadin kiyi hakuri duk mai rai mamaci ne, muma lokaci muke jira, yanzu kibar wannan kukan addu'a take bukata, tace aunty ban taba zata mmna zata rasu yanzu ba, mai yasa ni mutuwa bata daukeni ba, salma ta toshe mata baki tare da fadin kar kiyi sabo, salamatu Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, ki mata addu'a Allah ya gafarta mata, a dai2 nan Mahmud ya shigo, gaba daya yarinyar ta bashi tausayi, ya mata gaisuwa tare da mata nasiha daka karshe yace bari su tafi dan a mata sutura, nan salamatu ta sauko tace su wuce tare, taga mahaifiyarta na karshe, hakan ko akayi Dr yace zata iya tafiya, gidan hjy binta suka nufa ga mutane sun taru, an mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya duk wanda yaga salamatu saiya tausaya mata, musamman salma da aka bama amanarta itace yanzu uwa a gareta, saida akai uku suka koma gidansu, Fauxiya ko lekowa ba tayi ba, bayan sun koma aka gyarama salamatu wani daki a gefen su salma, kullum zaka ganta tayi shuru tana tunani salma intaga haka taita mata nasiha,
Cikin salma ya kai wata7 Mahmud kullum inya fita yaga kayan yara saiya siya na mata dana maza, salma inya kawo kayan tayi ta dariya, Fauxiya gaba daya ta fita hayyacinta domin yanzu komai nata ya kare malamanta duk sun cinye kudin, amma duk da haka bata saduda ba, tana ganin za tayi nasara dan ta rasa wannan inta kara mallake Mahmud zata sami wanda ya fishi,. Yayin da salamatu take zama tare da Salma,wata rana suna fira salma take ce mata wai salamatu kina da saurayi kuwa, tayi dan murmushi tace a'a aunty bani da kowa, ni bama na sha'awan saurayi domin maza basu da kirki, amma ke kinyi dace, inda zan sami irin namiji mai halin mijinki dana more, salma tayi shuru tana kallonta, har salamatu ta lura da shurun yayi yawa, sai taji wani iri akan maganan data mata, tace aunty kiyi hakuri inna bata miki rai, salma tayi dariya tace zaki auri mijina......? Cikin zabura salamatu ta dago tana kallonta.......
Maryam Obam😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
90to95
Girgiza mata kai ta fara yi, alaman a'a, salma tace takwara dagaske nake miki, ba wasa ba, sai a sannan salamatu ta sami daman magana tace aunty dan Allah kar ki karamin wannan maganan abune da bazai yiwu ba, bazan iya auran mijinki ba, ko a mafarki balle a zahiri, salma tace kina nufin bakya son shi?? Tace bawai bana son shiba, kodan taimakon da kuka min dole in soshi , balle ma akwai soyayya na musulunci, salma tace toh miye a aibun aurenshi bayan kince kina son namiji mai irin halinshi, salamatu tace haka ne, samun namiji irin shi sai an tona, amma bazan iya auranshi ba dan aunty kinyi katangar karfe a tsakani ko hauka nakeyi bazan taba auran mijin da kika aura ba, salma tace kenan ni bani da ikon in miki zabi? Shuru tayi tana hawaye tace aunty kina dashi, kece uwata kece ubana, kina da iko dani amma..... Ta dakatar da ita tare da fadin tunda ina da iko bana son in kuma ji kince bakya so, ta daga mata kai alaman toh, ta sannan ta tashi dasauri tabar wajan, salma ta bita da ido tare da tausaya mata, tace salamatu wannan shine gatan da zan miki amana abune mai wuya, na amsa amanarki, ban san mijin da zaki kawo ba, inma nace zan xaba miki ban San ya halinshi yake ba, Amma nawa mijin nasan koshi waye, nasan halinshi, nasan bazai cutar dake ba, auran Mahmud shi zaisa in sami kwanciyan hankali muna tare, jin an taba ta tayi firgit ta waiga taga Mahmud ne, ya hura mata ido tare da fadin tunanin mai kikeyi haka? Murmushi tayi tare da fadin yaushe ka shigo? Yace tun dazu nayi wajan 5mnt akanki Amma baki sani ba, kina ta tunani, lafiya kuwa? Tayi Murmushi tare da fadin lafiya dear muje kayi dinner, kai tsaye danning suka nufa, ta tashi zata zuba mai abinci yace ta zauna zai sa dakanshi, dariya tayi tare da zama ya zuba a plate ya dawo kusa da ita, yana bata shima yana ci, har suka koshi, fauziya ce ta shigo cikin fushi sukai ido hudu da Mahmud ga salma a jikinshi tana ta faman yi mishi shagwaba, haushin nata ya kuma karuwa taje ta janyo salma ta tureta salma ta saki kara, Allah yaso akan kujera ta fadi, nan Mahmud ya tashi ya wanke ta damari tare da fadin ke mahaukaciyar inace, tace ta gidanku wannan tso...... Kafin ta karasa ya kuma kwasheta da mari, yace kije na sakeki saki uku, mara tarbiya, ta cakume shi tana fadin wlh baka isa ba, yau ko ni ko kai saina kashe ka sannan in kashe wancan yar iskan da abunda yake cikinta, hjy binta data shigo da kaya niki2 na baby ta kawo ma salma, tazo taji ana rigima ana za'a kashe mata d'a da jika nan ta kira police, suka shigo gidan tace ku kama min ita, fauziya da mamaki tace wlh baki isa ba, ai zan fito sai na kashe ku wlh, nan police suka tasa keyarta sukai gaba da ita, salma gaba daya ta shiga cikin tashin hankali hjy binta ta matsa kusa da ita, tana fadin sannu y'ata bata dai taba kiba ko? Kafin salma tayi magana nan Mahmud ya fara bata labarin farkon abunda ya faru, hjy binta tayi Shuru tare da fadin kayi hakuri duk ni naja maka, na tsani matarka haka kawai ba tare da tamin komai ba,, inata matsa maka kayi aure, gashi na baka yar'uwarka tana kirarin zata kashe mu, hjy binta harda hawaye, tace ma salma dan Allah ki yafe min duk abunda na miki, salma tace mm baki min komai ba, kefa mahaifiyata ce,, komai kika min kin isa ne, ban taba rikeki a raina ba, hjy binta cikin kuka tace ngd Allah ya miki albarka ya saukeki lafiya, salma ta amsa da ameen, Mahmud yau yana cikin farin ciki ya rabu da fauziya zai zauna daka shi sai matarshi, suna ta fira, hjy binta tace ina yar amananki? salma tace tana daki, hjy binta tace Allah sarki, bari inzo in wuce dare yayi, ga kaya can dazu na amso su, nace bari in kawo shine naji wannan bala'in, kayan baby ne masu tsadan gaske, ta tashi, suka rakata har mota sannan suka dawo,yanxu gida ya dawo na salma sunsha love ranan ita da Mahmud duk da ta nuna Mai bai kamata ya saki fauziya har saki uku ba,
Washe gari da safe, suna breakfast, salma ta kalli Mahmud tace ya kamata kaje kasa a saki fauziya, ya bata fuska tare da fadin dan Allah salma kar ki karamin maganan fauziya a nan, tace shikenan bazan kara ba, kayi hakuri plz, yayi Murmushi yace matar da take ikirarin kashe ki, shine har kike tausaya mata, dole sai an hukunta ta, salma dai Shuru Tayi, amma inda za'a nata da an barta da hlinta an saketa, zata hadu da dai2 ita, Indai duniya ce wanda bai zoba ma tana jiranshi balle wanda yake cikinta, Mahmud ya katseta da fadin yau kina da zuwa hspt ki tashi muje, tace toh ta kira salamatu suka fita, bayan ya kaisu asibitin yace bari yaje ya dawo Kafin su gama, tace toh, kai tsaye gidansu yayi nan yaga hjy zaliha tana ta bama hjy binta hakuri akan a saki fauziya, hjy binta tayi banza da ita, ganin Mahmud yasa ta fara fadin dan Allah dana kayi hakuri kasa a saketa, hjy binta tace ai babu ruwanshi a wannan maganan, bai isa yayi komai ba sai yanda nace, hjy zaliha cikin fushi tace shikenan in baki sa an saketa ta dadi ba, zaki sa a saketa ta wuya, ta fita fuuuuu, hjy binta tace ina jiranki, Mahmud ya gaidata ta amsa sannan ya zauna, yace mm ni a nawa ganin da ansa an saketa ko dan xumuncin dake tsakani, hjy binta tace hakane amma ba yanzu ba sai naga abunda zaliha za tayi, yace kar ki biye mata bacin rai yasa ta fadi haka, nan Mahmud ya shawo kanta ta yarda, sannan ta dauki waya ta kira police ta bada umarnin a saketa,Mahmud yace bari ya koma hspt yabar salma acan, tace ita daya dan mai zaka barta, yace ita da wannan yarinyar ne, tace oho toh maza ka koma hala sun gama, ya tashi ya fita.
Fauziya gidansu tayi, hjy zaliha tana falo a zaune, taganta tace fauziya ya akai kika fito, tace haka kawai suka ce inzo in wuce Kuma gidan iyayena zani, kar ince zani gidan Mahmud, hjy zaliha tace bari zanyi maganin su wlh, duk da ya sakeki sai na wulakanta hjy binta ita da danta wlh, fauziya tace ko ke baki haka ba ni sai nayi, matsala ta daya shine banda kudi a hannu ina ganin gidan nan zamu sa a kasuwa, hjy zaliha tace toh ina zamu zauna? Tace haya zamu kama a hankali na siya mana wani amma yanzu ina bukatar kudi, hjy zaliha tace ai kiyi duk abunda ya dace, akwai wani boka a maiduguri dana sami labarinshi ance wlh inya maka aiki Kafin ya karye sai anyi dagaske, fauziya tace toh sai muje can yanzu ki kira dillali ki fada mai gidan nan a kasuwa yake, hjy zaliha tace an gama,
Mahmud suna daki shida salma, ta kalleshi tace dear, ya amsa da na'am, tayi Shuru na wani lokaci, yace ya naji kinyi Shuru inaji, tace inaso kamin wani Abu guda daya, yace salma koma guda dari ne zan miki Indai kina so, tayi Murmushi tare da fadin kayi alkawari yace yes nayi, tace toh dama ina so ne ka auri salamatu, tashi yayi tare da fadin what????...........
Maryam obam😘💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
95to100
Lokaci daya yayi murmushi tare da fadin, wannan wani irin wasa ne salma? Kar ki mata we are not in April fah, balle kice kina fooling dina ne, itama murmushin tayi tare da fadin dear am serious, ba wasa nake ba, ina so ka aur......... Daga mata hannu yayi alaman tayi shuru ya tamke fuska, yace salma daka yau bana son ki karamin wannan maganan indai baso kike kiga fushi naba, tashi tayi tazo kusa dashi tana hawaye tare da rike mai hannu, ganin tana hawaye yasa yaji wani iri, tace dear kayi hakuri ban fadi haka dan in bata maka raiba, ban kuma fadi hakan ba sai da nayi tunani sosai akai, kuma kar ka manta kamin alkawari komai na fada zakamin, yace look salma bawai inaso ayi ta wannan maganan ba, ki bari zan duba mata miji wanda zai aureta kinji, tace Idan ka duba mata miji, shin mai kalan halinka ne? Koh kuma zai iya riketa kaman yanda kai zaka iya,? Yace shuru yayi yana kallonta, Lokaci daya yace salma bari kiji koda ba iri na bane karki manta akwai wanda suka fini, kiyi hakuri kibar wannan maganan plz, shuru tayi tare da matsawa daka kusa dashi ta juya baya tana kuka mai kara kadan, tace wannan ne Karo na farko dana taba nuna ina son abu kaki min, gaba daya jikinshi yayi sanyi, taci gaba da cewa wanda ko a mafarki bazan taba yarda zaka ki abun dani nake so ba, matsowa yayi kusa da ita tare da janyota jikinshi yace salma mai yasa kike son in aureta? Tace Mahmud yarinyar nan amana aka bani ita, kuma ta isa aure, bata da saurayi tace tana son namiji mai hali mai kyau, ni kuma nasan nawa mijin yana da hali mai kyau, sai yasa naga ya dace kai ka aureta, ance imanin dayanku baya cika har sai yaso ma dan'uwanshi abunda yaso ma kansa,Mahmud kai nake so kuma nake ganin nayi dacen miji, dan mai zaisa inki so ka aureta tunda nasan halinka, tace dan Allah ka yarda hakan zai sani farin ciki, yayi shuru har na wajan minti hudu, babu abunda yake kara a dakin sai sautin kukan salma, yayinda yake ji har cikin zuciyarshi, yace shikenan tun da haka kika ce na amince, amma ki sani bazan aureta ba har sai an nemo dangin ta, cikin murmushi tace kar ka damu wannan mai sauki ne, tace ngd Mahmud Allah ya barmu tare ya baka ikon yi mana adalci,.
Fauziya sun saida gidansu, a ranan da aka biya kudin sukai maiduguri wajan sabon boka, Fauziya ji take kaman mota baya sauri, dan ta kosa ta ganta a gabanshi dan tana ganin Idan taje duk wani matsalanta ya tafi kenan, gudu suke zubawa, karan harbi sukaji an fasa musu taya nan motar ta fadi ta fara kundun bala ta tsaya ta cikin daji, har ta tsaya, yan fashin suka karasa motar tana kife da yake suna da yawa sun kai su goma sha biyar, suka fara kokarin daga motar, cikin ikon Allah suka daga ta, yayinda duk yan motan sunji jiki wasu kuma sun mutu, ciki harda Fauziya wanda ta rasu hjy zaliha kuma kafanta daya ya karye ga harshenta ya datse, driver dinma ya rasu da wanda suke gaba, bai fi mutum uku suka rayu ba, nan yan fashin suka dibe duka kayan motar, suka wuce, hjy zaliha ganin fauxiya bata motsi ta tabbatar ta rasu, gashi ita babu daman magana babu baki harshe ya datse da karfe ga karaya a kafa kuka take kaman zararra tana takaici, namiji daya sai mata biyu suka rayu suma duk sunji jiki sai hjy zaliha, nan namijin ya fita dakyar yana tsayar da mota amma kowa yki tsayawa sai wani mai motar albasa ya tsaya, nan ya mishi bayani abun daya faru yana ta salati yace ina sauran? Yace suna ciki, nan yace bari ya karasa gaba kadan akwai gari sai a sanar da sarki, hakan Koh akayi aka kira sarki da mutan gari, da yan sanda aka kwashe wa inda suka mutu, aka kira tashar motar aka sanar domin su kira yan uwansu ita dai fauxiya anan aka birne ta, yayin da wasu yan uwansu sun zo an tafi dagawarsu, hjy zaliha kuma an daure mata kafa, hmm rayuwa kenan hausawa na cewa in zaka gina ramin mugunta gina shi gajere wata kila kai zaka fad'a,hjy zaliha tana gidan mai gari, babu abunda take sai kuka tare da nadama tana fadin na cuceki fauxiya na bata ki dabin malamai kin mutu akan turban, matan maigari in suka ga tana kukan suyi ta tausaya mata,
Hjy binta da Mahmud yayi maganan auren taki yarda tace sam bata amince ba, akan me zai kara aure yama rasa wacce zai aura sai wannan yarinyar da ba'a san kowa nata ba, gwara ka zauna da salma ita daya yafi maka, yace mama salma ce ta matsa min akan in aureta, nan hjy binta tace bana son wasa, ya fad'a mata komai nan tayi shuru tare da fadin lallai salma wannan abun da take shirin yi ban taba gani ba, gaskiya tana da xuciya mai kyau, amma baka san dangin yarinyar ba, yace eh salma tasa anyi bincike akwai wani yayan babanta yace babu komai shiya amince, yanzu turawa kawai za'ayi da komai a daura, tace toh Allah ya tabbatar da alkairi ya amsa da ameen,
Yau salma ta tashi da mugun ciwon mara, saiya tashi ya lafa, Mahmud yana lura da ita, yace suje asibiti taki, sai da kyar da taga ciwon na karuwa, suna zuwa asibiti akace haiyuwa ne, nan aka kaita labour room, Mahmud ya kira hjy binta da hauwa, kusan a tare suka zo, asibitin, salamtu tare dasu salma suka zo, kowa yana rokan Allah ya sauketa lafiya, cikin ikon Allah bata wuce 30mnt ba ta haifo yan uku, maza biyu mace daya, waiyo Allah zo kuga murna wajan Mahmud da hajiya binta, abun ba'a magana, a ranan suka dawo gida basu kwana ba, Mahmud sai kashe kudi yake komai ya bayar yace a siyo shima ya siyo da kanshi, salma tace tana son ran suna a daura auren Mahmud, bata fada mishi ba, ta fadama hjy binta aiko hakan akayi ta tura mutane aka tafi ba tare da sanin Mahmud din ba, balle salamtu ita da bata san komai ba, an kashe naira kaman babu gobe, mazan ansa sunan mahaifin Mahmud el-hassan suna nickname nashi farhan, sai dayan kuma sunan baban salma Muhammad, nickname dinshi anan, sai macen kuma sunan Hjy binta fatima nickname dinta zarah, anci suna an watse har yan daurin aure sun dawo an daura, dama salma ta kira mai lalle ana gobe suna ta musu, kayan dakin fauxiya gaba daya an kwashe akasa sabo, tace salamtu taje tayi wanka ta bata kaya tasa, ta amsa tayi wankan sannan tasa ta fito, ta kaita dakin fauxiya tace ta zauna tana zuwa, Mahmud dake dakinta yana kallon yaranshi yana dariya, tazo itama tayi dariyan tare da kama hannunshi tace suje ya gani, bai musa ba yabi bayanta yaga tayi dakin fauziya din, ganin salamtu a ciki yasa abun ya bashi mamaki, itama kanta salamatu sai da taji faduwan gaba, salma tayi murmushi tare da fadin yau ka zama mijin salamatu itama ta zama matarka an daura muku aure yau, yace salma miye haka, nan ta fada mishi yanda akayi shuru yayi yana kallonta, salamatu kuma kuka takeyi, salma ta kama hannun Mahmud tare da zaunar dashi akan kujeran da salamatu take tace Allah ya baku zaman lafiya sannan ta fita, tana zuwa daki ta fashe da kuka tare da bakin kishi da taji yana taso mata, Lokaci daya ta share hawayen tare da koran shedan ta matsa kusa da yaranta tana kallonsu tana dariya tare da godema Allah,
BAYAN WASU SHEKAR
salma ta kara zama babban mace, ga naira tana juyawa sosai, yanzu tana da yara biyar, ta kara haifan yara biyu maza duka, aka sa musu yusuf da Ibrahim, yayinda salamatu kuma take da yara biyu, mace daya namiji daya, zainab da usman, salma ta kara mallake zuciyar Mahmud da kissa irin nata, ga wani irin girma da salamatu take bata, sai abun da salma tace akeyi a gidan, komai na Mahmud yaso yasa sunanta tace a'a yasa na yaranshi, hakan kuma akayi, hjy zaliha itama Allah ya mata rasuwa bayan tayi jinya mai tsawo taji jiki sosai tare dayin dana sani keya ce,
Hauwa tazo gidan salma ita da yaranta su uku, suna ta fira da salma, hauwa tace wai salma har yau baki fadamin irin naki kissan ba, tayi dariya tace bari in fadamiki ba wasu abu bane masu Wuya kema kin sani sai dai kikiyi, hauwa tace inaji, salma tace hauwa da farko mace ta fara sanin waye mijin ta, tasan miye halinshi, tasan miye yake so miye baya so, babban abu shine kisa ma kanki hakuri, domin shi namiji a koda yaushe yana daukan kanshi sarki matarshi kuma baiwa, yana so Idan ya miki abu duk da shine da laifi ki bashi hakuri ki nuna kece da laifin bashi ba, sannan kuma duk wani hanya da zai sa ke kiyi mishi laifi karki bita, sannan Idan namiji yana fushi kar ki kai mai wata bukata naki kiyi hakuri har sai ya sakko koda kuwa bukatar babba ce, ki ajiyeta a gefe kisan yanda zaki rarrashe shi ya sauko, kar kice ke bai dameki ba tunda a waje aka bata mai rai kema bari ki kara mai wani toh kinga in kikai haka kinja ma kanki matsala, sannan karki dinga yima miji wasa da abinci koda kuwa kina fushi dashi kiyi mishi abinci dan namiji ya tsana yazo gida ya tarar ba'a mai abinci ba, wannan abun zai iya ja muku mugun matsala, sannan ki zama mai tattali da dukiyar miji, sannan Idan yace yana son abu ki nuna kin fishi so indai bai sabama addini ba, kaman ni a lokacin da yace zai kara aure mahaifiyarshi ta matsa mai, nace na amince banyi wani hayaniya ba, kinga a lokacin ji nayi kaman zanyi hauka dan tsabar kishi amma na daure na hakura, inda na tada hankalina na mishi hauka duk da yana sona sai yaji wani kala hala son ya ragu yazo ya fara gayamin magana shikenan na xubar da kimana wani namijin ma saiya sake ka, in kuma ka sami mai surutu saiya fadama amaryan haukn da kikeyi kinga tun kafin ta shigo ta raina ki, shima kin xubar da kimarki a wajanshi, amma da nayi hakuri kinga komai ya wuce, harta fauziya da aka daura mishi wani irin asiri ne ba tayi ba, amma da yake Allah yasan bani da hakki, sai abunta ya koma mata, mata da yawa inda zasu duba zasu ga asiri wlh baya aiki biyayya da iya kissa shike sa namiji ya soki, in kuma Allah ya jarabta mutum asirin yayi kwana arba'in ne fah ya karye, in Allah ya dauki ranki kina wannan aikin mai zaki cema Allah, sannan ko su bokayen zasu ce asiri baya yi sai da biyayya, Idan kikayi tunani tunda sunce haka sai ki duba dan me toh zan kashe kudina a banza, sai kiyi biyayyan kawai ki gani, hauwa tace wlh salma haka ne kinyi gaskiya, amma mai yasa kika karama Mahmud aure toh? Tayi murmushi tace hauwa duniyar guda nawa ce, mata da yawa sun sa bakin kishi akan kishiya inda zaki tara mata dari kice wai akan mai yasa suke kishi da kishiyoyinsu wlh dakyar ki sami guda goma wacce Zata ce ga dalili, kuma fah kar ki manta duniyar ba zama muka zo yiba, zamu mutu mu barta in kin hana mijinki aure Idan kika mutu zaki hanashi yine, ba zaki hanashi ba, gashi kin bata duniyar ki wajan malamai lahirar kuma kije bata samu ba, yanzu dana hada Mahmud da salamatu ba karamin kara daukaka nayi aranshi ba, haka itama yarinyar tana bani girma sosai mai yafi wannan dadi mijinka duk inda ya zauna yace ke yar aljanna ce, ya dinga labarin alherin ki a ko ina, salma tayi shuru tare da cewa kin san wani abu hauwa? Ta girgiza kai alaman a'a? Tace wannan abun da nayi shine kissa wacce babu bokan da zai baki ita, yanzu sai ki fadamin tsakanin KISSA KO MAKIRCI, Wanne yafi, hauwa tace KISSA nima na koya zanje inyi dan in gyara rayuwar gida na suka sa dariya tare da tafawa.... To nima dai anan zan tsaya..
ALHAMDULILLAH
INA MIKA GODIYA GA MASOYA NA, WANDA DA BAZARKU NAKE RAWA ALLAH YABAR KAUNA MASU YIMIN MSG SUNA CEWA BANA REPLY KUYI HAKURI INSHA ALLAH ZAN DUBA SAKON KU ZAN BAKU AMSA NGD
GODIYA TA MUSSAMMAN GA
hajiya nafisa
Amina aliyu
Nana fiddausy
Kawata hibbat
Hassan atk
Ina godiya gareku akan karfafa min giwa da kukeyi 👍
MASU SON MAGANA DANI SU NEMENI TA EMAIL DINA KAMAR HAKA: MARYAMALHASSAN206@GMAIL.COM
LOVE YOU OL MY FANS😘😘😘
maryam obam😃
Download Kissa Ko Makirci Littafi Na Daya Complete
0 Comments
Thank you for this comment