Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Arewa hausa novels
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)
WHATSAPP NO:
+2347039625239
MEYE DALILINKA 💞 1
Bismillahir Rahman Rahim
Haj Munnira ta tsaya ta karewa dakin kallo cikin
takaici komai a hargitse gado kamar yara biyar
ke kwana, filo daya a kasa da kayan bacci sai
ledojin sweet dana capri sonne. Gefe kuma
wardrobe shima a bude duk an hargitsa har
wasu kayan sun fado kasa. A takaice dai dakin
tamkar yayi sati baa gyara shi ba. Me zan mata
ne idan ta dawo abinda take ta tambayar kanta
kenan. Can dai ta kwalawa Inno kira Inno
yaushe rabon da a share dakin nan? Inno tana
raba idanu tace Hajiya yau ne kawai ban share
ba kuma zan gyara shi tas kafin ta dawo har
bandakin duk zan wanke.
Hajiya Munnira tace ni ba dalilin da yasa na
tambayeki ba kenan jiya ba tare muka gyara ba
dake har na shirya mata wardrobe? Haka yake
Hajiya ta bada amsa. Hajiya tace to wallahi idan
ta dawo kika nemi hanani dukanta zamu saba
dake na fada miki tun wuri. Tana gama magana
ta fita. Nan da nan Inno ta hau kwashe kaya
zata fara gyara.
Da gudu ta shigo tayi jefa da school bag dinta a
kasa, lunch box ma ya bi shi sai takalmi wanda
ta rinka cilla kafafunta sai da suka fita da
kansu. Na kafar hagun yana fita sai a kan fuskar
Haj Munnira. Ai tana ganin haka tayi saurin
durkusawa kasa tace Assalamu alaikum
Ummana na dawo na sameki lafiya? Ko kulata
batayi ba don in da sabo to ta saba da halin
Khairi na bada hakuri da nutsuwa idan tasan
bata da gaskiya wayar rediyo ta ciro tayi kan
tilon yar tata. Tsoron duka ne da Khairi kamar
me don haka iyakar muryarta ta bude tana ihu.
Ummana kiyi hakuri kada ki dokeni wallahi na
dena jifa da takalmina. Inno ta fito da sauri
Hajiya kiyi hakuri. Ya mukayi dake Inno? Ta
tambayeta cikin fushi sannan ta cigaba. Yarinya
ita kadai ta rinka caja min kai. Ke ba namiji ba
Khairi amma gara wasu mazan da ke. Dakinki
kamar filin dambe ga kazantar tsiya. To daga
yau babu me sake yi miki shara ko wankin toilet
da gyaran kaya kuma kullum sai na tabbatar kin
gyara zaki fita makaranta. Khairi ta kalli Umman
tata tace na dena Umma daga yau Allah kuwa.
Ni tashi ki bani wuri. Tana tafiya Umma ta lura
hijab dinta ya yage ta baya tace Khairi me ya
sami hijab din? Umma kusa ce a seat dina ina
tashi ji kike kyeeeet. Inno abin dariya ya bata
ita kuwa Umma bata jira ta rufe bakinta ba ta bi
ta tace sai dan banzan baki kamar reza zo nan
ta sake daga wayar zata dake ta.
Yi hakuri Anti taji an fada daga bakin kofa. Da
gudu Khairi taje ta rungume shi. Umma tace ai
yau ko zaka ari baki Ahmad sai ta zane yarinyar
nan. Khairi wadda tuni ta fara hawaye ta
kankame shi Uncle Ahmad don Allah ka bata
hakuri. Dan murmushi yayi wanda ya kawata
kyakkyawar fuskarsa yace Anti Munnira kiyi
hakuri kinga yarinya ce idan ta girma zata dena.
Umma tace kayya dai ai ba alama ta maida
kallon ta ga Khairi tace idan kika girma a haka
bana jin zaki sami mijin aure.
Subhanallahi Inno tayi saurin fada tace haba
Hajiya kada kiyi wa yar tawa baki mana. Umma
ta tabe baki ta zauna bakin kujera tace yo yar
shekara tara tana wannan abin ai ban ga ranar
girman ta ba. Ahmad shima zaman yayi yace ni
ina sonta Anti so bata da matsalar miji. Ya
kama hannun Khairi kinsan bana son kazanta
ko? Eh ta bashi amsa. To daga yau kada ki bari
na sake jin zancen rashin tsaftarki. Tayi
murmushi har gibinta ya fito. Ai na dena daga
yau Uncle Ahmad. Tashi tayi taje ta cire uniform
dinta sai dai kafin ta kai dakin yana kallonta
tasa hannun damanta a hanci ta share hannun a
rigarta. Wayar hannun Umma ya karba ya bita
yana cewa ashe ni zan fara zaneki tana gudu.
Umma dariya tayi tace wai! Gaskiya Ahmad kayi
sa'ar mata.
Batul Mamman
💕 MEYE DALILINKA 💞 2
Filo ta jawo ta dora kanta ta cigaba da karanta
wasikar jaki. Gadon duk books ne da handouts
ko ta ina amma yau ma tunanin Uncle Ahmad ta
tashi dashi ta kasa mayarda hankali tayi karatu
gashi test gareta gobe.
Kausar ce ta shigo dakin ta daka wa Khairi doka
a cinya ba shiri ta tashi zaune tana murza wurin.
Tace to muguwa me nayi miki. Kausar ta zauna
kan gadon tace tun dazu nake sallama baki
amsa ba kina ta juyi kamar waina. Nasan bazai
wuce tunanin Uncle Ahmad ba. Har kin manta
muna da test gobe ko? Ni karatu nazo muyi
malama tashi ko na kara miki ta sake daga
hannu.
Wani hoto ta nunawa Kausar din wanda Uncle
din ya turo mata ta whatsapp. Shi da yaransa
ne Iman da Sadiq a bakin ruwa. Komai hassadar
mutum dole ya yaba domin duk sunyi kyau.
Kausar ta ajiye wayar a gefe tace Khairi har
yaushe zakiyi ta son wanda bai san kinayi ba?
For God's sake he is married with two kids.
Murmushin yake Khairi tayi tace Allah Kausar
ban damu na zama ta hudu a gidansa ba. Ni
tunda yace wa Umma shine mijina nake gina
rayuwata dashi. Tun bansan so ba har na sani
duk akansa. Kausar ta tabe baki to zan cigaba
da taya ki addua idan ya dawo kasar hankalinsa
ya dawo kanki. Allah Ya amsa Khairi tace
sannan suka fara karatu.
********************
A falo ta hadu da Malam yana ta rubuce rubuce
ga Qur'ani da sahihul muslim a gabansa yana
kokarin hada khudbar juma'a ya turo glasses
dinsa can karshen hanci. Tsugunawa tayi ta tura
masa shi ciki sannan tace Malam ya aiki? Lafiya
kalau ya bata amsa yana murmushi Ummulkhair
kin mayar dani kakanki ko? Tace to idan babu
kaka ai da uba ake yi. Ajiye biron hannunsa yayi
yace tun jiya nake aikawa kizo kina wasan buya
dani. Keya ta sosa to ai nasan dalilin kiran.
Umma wadda ta shigo falon lokacin tace to
sarkin zance meye dalilin. Shiru tayi ta sunkuyar
da kanta kasa Malam yace zauna ayi maganar a
gabanki Munnira.
Ya ce to a ajiye wasa a gefe Ummulkhair ina
zancen miji ya kwana? Na baki dama ki fitar da
miji amma abin mamaki duk yadda ake zuwa
samuna akan maganarki har yau babu wanda
kika amince dashi. Umma tace to ai Malam
irinsu Khairi ba'a basu wannan damar ko cikin
almajiranka kawai ka bawa daya. Almajiri kuna
Umma? Khairi ta fada tana zaro idanu sannan
tacewa Malam ya kara mat lokaci. Ni dai ba
haka naso don a yadda na tsara kina gama
secondary zan aurar dake amma tunda hakan
bai samu ba gaskiya bana son ki cika shekara
23 a gabana. Alh Mahe yazo dazu kina
makaranta akan maganarki da dansa Tahir kuma
na amince. Gabanta ne yayi mummunan faduwa
********************
Kuka take a daki Inno tana ta bata hakuri Khairi
tace Inno ta yaya zan fada musu Uncle Ahmad
nake so? Inno ta cigaba da share mata hawaye
kiyi hakuri 'yata da yardar Allah komai zai zo da
sauki. Yau kwana hudu da maganar nan amma
baki da aiki sai kuka? Ina baki shawara da kada
ki taba bijirewa Malam domin sabawa mahaifi
ba karamin hatsari gareshi ba.
A daidai wannan lokacin Dr Ahmad ke saukowa
daga jirgi shi da matarsa Mufida da yaransa
guda biyu bayan shekaru uku da yaje yayi wani
course a kasar Singapore.
Taku Batul Mamman ce
💕 MEYE DALILINKA 💞 3
Ko da wasa babu wanda ta bari ya san sirrin
dake boye a ranta daga Inno sai aminiyarta
Kausar Mukhtar wadda makota suke tun suna
yara. Tare suka yi secondary sai kuma suka
nemi course daya a jami'ar Bayero. Khairi da
Kausar wadanda kawayensu ke kira da 2K basa
boyewa juna komai. Tsayinsu kusan daya
sannan dukkansu suna da matsakaicin haske.
Khairi akwai kyau kuma akwai fara'a idan ka
cire lokutan da take tunanin Uncle Ahmad da
wuya ka ganta fuskar nan babu murmushi. Da
kuruciya dai anyi fitina yanzu da ake ji da 'yan
matanci kuwa nutsuwa ta danzo musamman da
take 'yar daya taga cikin malaman da ake ji
dasu a kano Dr Abdallah Saraki. Sai dai ba'a
raba ta da tsokana da tara shirgi a dakinta.
Ummulkhairi Abdallah Saraki.
Ta gama kukanta na yamma yau saura na darw
kamar yadda ta tsarawa kanta kullum tunda
Malam yayi mata zancen Tahir. Idar da sallar
ishan takeda wuya Inno ta shigo dakin da sauri
har tana tuntube da takalman da Khairi ta cire a
bakin kofar daki. Albishirinki 'yata ta fada tana
wangale baki. Goro Inno ta amsa mata a
sanyaye. Inno tace tunda naga kamar ban
burgeki ba to kije falon Malam ana kira.
Dammm taji gabanta ya fadi. Har tasa hijab
wanda ya dace da kayan jikinta sai ta fasa ta
jawo wani a kayan wanki ya gama yamutsewa
ga manjan wainar filawar da suka ci ita da
Kausar a gidan Lami makociyarsu. Tasa ta fita
idan Tahir ne tasan dole ya ce ya fasa. Yau
kazanta zata yi mata rana ta fada a ranta tana
murmushin mugunta.
Qamshi ne mai dadi ya bugi hancin Khairi tana
daga labule suka hada ido. Yarrr taji a jikinta
kamar wuta ta ja ta. Ta bude baki galala tana
kallosa...wallahi ya kara kyau da haduwa ta
fada a ranta. A zahiri kuwa ta kasa magana
tana karasa shigowa ya mike kamar an mintsine
shi. Kada ki karaso wurin nan ya fada yana
mata wani irin kallo. Umma ma cewa tayi Khairi
meye wannan? Sai a lokacin ta kula da umman
ta. Tace Umma me kika gani? Uncle Ahmad yayi
tsaki ni duk na zata zanzo naga kina ji da gayu
kin girma ashe kina nan a Khairin kazanta.
Subhanallahi ta fada sannan ta koma ciki da
gudu. Ba komai bane illah hijab din korar Tahir
da ta saka sai dai tana dawowa falon Umma
tace ya tafi gida domin dare yayi dazu jirginsu
ya sauka.
Da wani kukan ta koma daki tana share kwalla
taga bakuwar number na kiranta. Tana dauka
bayan tayi sallama taji muryar dake sanyaya
mata zuciya. Khairi ya kira sunanta (kai sunan
ma daban yake a bakin Uncle ta fada a zuci).
Naam Uncle shine ka tafi kafin na dawo ko? To
ai kece kanwata ina ta dokin surprising dinki
shiyasa ban fada miki ma zamu dawo ba kawai
sai na ganki kamar anyi wasan kura dake.
Murmushi tayi ai na zata Tahir din da Malam
yace zai aura min ne yazo. Yanzu dai a bar
maganar hijab mai datti don yanzu na zama yar
gayu. Ina Anti Mufida da su Sadiq? Lafiya kalau
suke ya bata amsa. Gobe kizo ku hadu dasu
Umaima ku taya Mufida gyaran gida zan turo
azo daukarki da safe nasan sunday ne ba
school.
Ranar Khairi bacci mai dadi tayi harda mafarki
ta haifawa Uncle Ahmad yan biyu. Gari na
wayewa ta kira Kausar a waya ta bata
kyakkyawan labari. Suna ta shirmen murna
domin kuwa dai ba'asan suna yi ba. Kafin
takwas na safe ta gama shiryawa taje ta gaishe
da itayenta. Malam ya kalli Umma yace yau
lafiya kuwa Ummulkhair take? Ina wucewa naji
tana share dakinta. Umma tace ai tun jiya
Ahmad yace zai turo a dauketa shine take ta
doki.
Abincin ma da kyar taci tana ta kallon agogo shi
kuwa driver din gidan Alh Aliyu wanda wan
mahaifin Khairi ne baizo ba sai 9:30. Kafin yazo
kuwa ta kira Umaima da Ummi yafi a kirga su
gane mata ko ya taho. Hijab dinta yau light blue
ne kamar atampar jikinta. Ba wata kwalliya sosai
tayi ba tunda Malam bazai yarda da hakan ba
amma ta tabbatar tayi fes yadda Uncle zaiji
dadi.
4rm Batul Mamman
💕 MEYE DALILINKA 💞 4
Gidan Baba Aliyu ya wuce da ita suka dauki
Umaima suka wuce sabon gidan Uncle Ahmad a
unguwar 'yan kaba. Mufida tayi farinciki da
ganin su tare suka hadu da kannenta suka share
gidan tunda kafin su dawo an riga an gama
jeren komai.
Baba Aliyu shine babba a gidansu, Malam ke
binsa sai Hashim wanda ya gamu da lalurar
paralysis sakamakon fadowa da yayi daga bene
shekaru 35 da suka wuce. Baba babban dan
kasuwa ne yana da mata biyu da Hajiya Karima
wadda ake kira Hajiya shekararsu 5 da aure
sannan ta haifi Ahmad daga shi bata sake
haihuwa ba. Sai Hajiya Zainab wadda ya aura
daga baya ta haifi Amina, Rahma, Umaima da
Hashim. Suna kiranta da Momi. Suna zaune ne
tare da matar babansu Yakumbo. Ita bata taba
haihuwa ba amma ko da iyayensu suka rasu ta
kula dasu sosai musamman Baba Karami wato
Hashim wanda ya gamu da lalura. Haj Zainab
amaryar Baba 'yar kanwar Yakumbo ce.
********************
Khairi tana yiwa Umma tsifa Inno ta shigo cike
da fara'a tace Hajiya yanzu mai gadi yace na
sanar ana sallama da 'yata. Shiru tayi kamar
bata ji me akace ba sai da Umma tace Khairi
bazaki tashi bane? To sakar min kaina ta fada
tana kokarin daura dankwalinta. Tashi Khairi rayi
taje ta dauko hijab ta saka. Tana dawowa falon
Umma tace kije falon bakin Malam ki same shi.
Tahir ne wanda an sanar dake babansa ya yi
magana.
Sallama tayi ta shiga falon hannunta da tray
wanda ke dauke da juice, ruwa da meat pie.
Bayan ta ajiye masa a kan centre table ta sami
kujera can nesa da shi ta zauna ta hade fuska
ita kada ma ya kawo mata wargi. Yanayin Khairi
dariya ya bawa Tahir amma sai ya gintse yace
mun wuni lafiya? Lafiya ta bashi amsa a dakile.
Haka suka zauna suna kallon kallo. Tahir yana
karanta wata journal da ya gani a kan kujera ita
kuwa Khairi waya ta dauko tana dannawa.
Kusan mintuna 15 suna haka daya gaji da shirun
ya ajiye jaridar ya dubeta. Ina fata Malam ya
sanar dake dalilin zuwana. Gyada kai tayi kamar
kadangare, a ransa yace lallai ina da aiki. Ya
cigaba da magana kamar yadda aka sanar dake
suna na Tahir, ina aiki da Nigerian airways ni
pilot ne. Ina da yayye uku da kanne biyar. Ina
fata wannan ya isheki for now, uhm kawai tace.
Ganin bata da niyyar magana yasa shi mikewa
har ya kusa bakin kofa yace oh ni wane laifi na
yiwa Alhaji ya rasa matar da zai nema min
aurenta sai bebiya. Kafin ta bashi amsa har ya
fice.
*******************
Kwanan Tahir hudu da zuwa Khairi ko zancensa
bata so taji anyi a gidansu. Kausar kuwa ta
sami abinyi kullum sai ta tsokane ta. Ta kusa
gama karatun da take na bayan sallar isha Indo
jikar Inno ta leko tace Umma tace kizo inji
Tahir.
Ai tuni ta kara karatun, bayan kamar minti goma
Umma da kanta tazo cikin fada tace bana son
wulakanci Khairi, ganin karatun dai take yi tayi
wata 'yar dariya tace haba Khairi ai ko ban fada
miki ba kinsan karatunki babu lada don kuwa
babu niyya ki tashi tun ranki bai baci ba. Yace
sallama yazo yi miki zaiyi tafiya yau. Ko da ta
dago kanta idonta cike yake da hawaye. Ta
yaya zata fahimtar da iyayenta akwai wanda ta
riga ta mallakawa zuciyarta?
Batul Mamman💖
💕 MEYE DALILINKA 💞 5
Saroro Umma ta tsaya tana kallonta. Khairi ko
dai aljanun ne dake da gaske? Daga magana sai
hawaye, to daure kije ki dawo kizo muyi magana
kinji 'yar Umma. Share hawayen tayi ta fita
Umma ta bita da ido. Bari Malam ya dawo dole
asan abin yi.
Yauma sallama tayi a hankali ta shiga falon. A
tsaye ta tarad da shi yana sanye da kayansa na
matukan jirgi. Sunyi masa kyau don sai yau ma
ta kalle shi sosai. Dogo ne sosai don yafi Uncle
Ahmad tsayi,kalar fari ne amma har yafi Uncle
din nata kai kila ma zabiya ne ban kula ba.
Gashi yana da kyau amma dai Uncle ya fi shi.
Duk wannan zancen zuci Khairi take shi kuwa
Captain Tahir kallonta kawai yake. Ko ba komai
tana da kyau kuma 'yar Malamin da yake
matukar jindadin tafsirinsa ce. Littafin aljihunsa
ya dauko mai suna Sign Language ya dan duba
wani page sai yayi mata alama da hannu. Dariya
ce ta kwace mata ganin yadda ya dage yana ta
motsa hannuwansa. Sai da ta gama tace idan
ka gama excercise din ka fada min. Shima
dariyar yayi yace ai na zata bebiyar gaske ce.
Kafin ta sake magana Uncle Ahmad ya daga
labulen falon ya shigo da sallamarsa rike da
ledoji biyu a hannunsa. Gaban Khairi har faduwa
yayi da ta ganshi tayi saurin mikewa tsoronta
kada ganin Tahir yasa kara lalata chance din ya
gabatar mata da soyayyarsa. Su biyun sun mika
wa juna hannu sun gaisa Uncle yace Khairi shine
baki fada min zanyi inlaw ba. Ya juya ga Tahir
gaskiya nayi murna dana ganka Allah Ya
tabbatar da alkhairi sai kayi a hankali kanwar
tawa akwai kiriniya bata san ta girma ba. Tahir
mikewa yayi yace to babban yaya ni zan gudu
dama a hanya nake idan Allah Ya dawo damu
lafiya zan nemeka. Allah Ya tsare ya fada
sannan yace ni sunana Ahmad shi kuma yace
Tahir.
Tare suka fita daga falon Khairi ta koma ta
zauna tana tunane tunane har Uncle ya dawo.
Ga tsarabarki ta Singapore ya fada yana mika
mata ledojin hannunsa. Ko dago kai bata yi ba
sai alamar sheshshekar kuka yaji. Khairi me ya
sameki ko kukan rabuwa da masoyi kike yi?
Kamar ya kara zugata ta sake bare baki tana
kukan ta mike ta fita daga falon yana kiranta
bata amsa ba.
Su Umma ma haka ta wuce su. Uncle Ahmad na
fitowa Inno tace masa lafiya? Nima daga na fita
raka bakonta ta dawo na tarar tana kuka. Kila
ko don zai tafi ne. Inno ta girgiza kai anya
kuwa? Yau ne fa zuwansa na biyu, akwai abinda
ke damun yarinyar nan. Umma wadda ita kanta
abin ya fara damunta tace ka fara tambayarta
Ahmad idan abin ya faskara zan sanar da
Malam.
*******************
Tun ranar da ya ga wannan kukan Ahmad ya
rasa sukuni. It is so unlike Khairi ta bar abu a
ranta har ya sata kuka. Duk cikin kannensa yafi
shaquwa da ita kuma bata boye masa komai
amma wannan karon yayi yayi taki magana.
Bayan ya gama ganin last patient dinsa na yau
ya yanke shawarar ya sami Malam suyi magana
idan bata son Tahir abar zancen. Bazai iya jure
rashin walwalar Khairi ba.
Kausar tana ta ban baki da rarrashin kawarta
tace Kausar son Uncle ya zame min cuta.
Zuciyata kamar zata fashe nake ji tunda ya
dawo abin ya karu. Ko kinsan yanzu har waya
suke da Tahir tunda ya dawo daga tafiyar da
yayi kwanaki sun dinke kamar wasu abokan da
suka dade. Kausar gama kwasar tuwon da take
tace to Khairi idan abin nan bazaki iya hakura
ba why not ki sanar da uncle Ahmad din. Kai
bazan iya ba idan har bai fahimta don kansa ba
shikenan.
*******************
Kwance yake yana kallon kyakkyawan hatonta a
wayarsa. Hakika Jalilah taci amanarsa. Ita din
mai kyau ce kuma tasan tana da kyan. Sati uku
ya rage ayi bikinsu Yayanta yazo har gida ya
dawo musu da kudinsu da kayan lefe wai ta
fasa. Ya jima yana maimaita abinnan a ransa
yaje gidansu kuma taki fitowa. Sati ukun na cika
yaji sanarwar aurenta a kafafen yada labarai da
Senator Bukar Danbuba. Wannan dalilin yasa ya
tsorata da lamarin mata domin iyakar so Jalilah
ta nuna masa na shekara ukun da suka yi tare.
Shiyasa ya dena neman kowacce mace sai
yanzu da Alhajinsu ya nemar masa Khairi. Sai
dai yarinyar ta zame masa kamar karatun littafin
da baa ganewa. Abu daya ya sani shine tun
ranar da ya fara zuwa ta shiga ransa
Batul Mamman💖
💕 MEYE DALILINKA 💞 6
Khairi ta duka tana kokarin turawa Malam
glasses dinsa Umma ta kallesu tace ni cikinku
bansan wanda yafi wani ba, kullum ka turo glass
gaba zata mayar maka ciki amma baka fasa
turowa. Ke kuma kinsan ko kin tura masa ciki
gobe ma zai kara amma ba kya gajiya. khairi ta
zauna kusa da Malam tace aini ina jin dadin
turawar shima Malam yace inayi ne kawai don
jin dadin Ummulkhairi na. Suna cikin dariya suka
ji sallamar Uncle Ahmad da Mufida tare da
yaransu.
A take taji jikinta ya fara rawa. Ina zata kai son
Uncle? Yanzu abin har ya kai tayi loosing
composure dinta idan yana kusa?
Sun gaisa da kowa sai dai ta kula da yadda
Mufida ta dan daure fuska amma bata kawo
komai a ranta ba don tasan ba soyayya take da
Uncle ba. Uncle da Malam sun koma daya falon
inda Uncle Ahmad ke yi masa bayanin abinda ya
kawo shi. Murmushi malam yayi irin na manya
yace to Ahmad mai kanwa munyi magana da
kanwar taka sai tace min ranar haka nan ta
tashi da bacin rai. Na fada mata ta rinka azkar
safe da yamma. Ya cigaba da cewa Ummulkhairi
ta gama girman da zata yi a gida kuma nasan
iyaka abinda Allah Ya hore mana mun bata
tarbiya abinda ya rage kawai aure ne. Ina fata
Tahir ya zama mijinta. Ahmad ya gamsu da
maganar Malam kuma a yadda ya fahimci Tahir
yana ganin kamar mutumin kirki ne.
********************
Ajin tun daga waje ake jin hayaniya kasancewar
babu malami. Kausar ta dubi Khairi tace 'yar
uwa wata shawara zan baki game da maganar
Uncle don na lura har yau baki da nutsuwa. Kina
istikhara kuwa? Ji wata irin tambaya khairi ta
fada to ke yanzu idan nace bana yi ai anyi
asarar kudin tara. Kausar tayi murmushi ai
nasan kina yi amma da wuya idan ba kina yi ne
kawai don samin abinda kike so ba ba domin
neman zabin Allah ba tunda kin dade da
yankewa kanki wanda kike so. Shiru tayi alamar
tunani sannan tace gaskiya ne Kausar amma
daga yau zan canza niyya. Banda niyya ina
ganin shima Uncle ki koyi dena shiga sabgarsa
da yawa kamar wayar da kuke yi kullum da
yawan fara'a kamar gonar auduga idan kin
ganshi. Khairi tace tohh wani sirrin ne kuma da
hakan. Eh ta bata amsa sannan ki dan bawa
Captain chance kiga ikon Allah.
Ta karbi shawarar kausar yanzu ba ta kiran
Uncle a waya kamar da idan ya kira ma sai taki
dauka. Amma hakan ba karamin punishment ta
dauke shi ba. Shi kanshi Uncle Ahmad abin ya
fara isarsa. Ko haduwa suka yi ta dena rawar
kan da take yi.
Tana zaune da Tahir a waje saboda zafi gashi
injin gidan yaki kamawa. Yauma ta kasa sakin
jiki sosai amma dai tana amsa shi idan yayi
magana. Wayarta ya dauka wadda ke kan wani
karamin table da ta ajiye masa lemo. Amma dai
kasan daukan kayan mutane ba da izini ba babu
kyau ko? Eh ya bata amsa tare da cigaba da
kokarin kiran wayarsa da tata domin ya sami
number dinta. To ai sai ka ajiye min tunda ka
sani wannan karon cikin fushi take maganar.
Karkari dai ki kirani barawo kuma ba kaina farau
ba. Murmushin da yake yi ne ya bata haushi
tace me kake nufi? Hmmm Khairi kenan i love
your eyes idan kika kalli mutum sai yaji kamar
ya gudu dake. Ganin yana neman canja topic
din ta tashi zata koma ciki yace barauniya....cak
ta tsaya sai kuma ta waigo kafin tayi magana
yayi yar dariya barauniyar zuciyata ina zaki ba
sallama.
Bata iya yin fadan data yi niyya ba sai ta shige
gida. Yana tashi shima gidan ya nufa sai dai a
hanya wayarsa tayi ta ringing. Yana parking a
cikin gidansu ya duba yana da 13 missed calls.
Kira yayi don bai gane nunber din ba.
Hello yaji an fada ana daga wayar.. ko cikin
bacci dole ya gane muryar nan duk da ya
shekara biyu bai ji ta ba. Katse wayar yayi tare
da dafe kirji. Meye dalilin da yasa Jalilah take
kiransa a yanzu?
Batul Mamman💖
💕 MEYE DALILINKA 💞 7
Yau kuma me ya faru kika shigo da fushi 'yata?
Khairi ta kalli Inno idanunta cike da hawaye
tace Inno ko sau daya Uncle bai taba kallo na da
wata manufa ba bayan kanwarsa da ya daukeni.
Kada ki manta na fada miki ki bin iyaye wajibi
ne idan kika bi su zaki ga amfanin yin hakan
'yata. Ki daure ki bawa Tahir din dama kiga
abinda Allah Ya tsara miki. Share hawaye tayi
da dankwalinta Inno in Allah Ya yarda zanyi
kokari na cire Uncle a raina. Zan koyawa
zuciyata son zabin Malam. Ni dai ki taya ni
addua.
Yana shirin kwanciya ya sake jin waya ta shigo
ko da ya duba number din da Jalilah ta kira shi
da ita ce dazu. Wannan karon ya dauka yayi
sallama.
Tahir nice Jalilah. Ta fada cikin siririyar muryar
jan hankali.
Lafiya kike kirana a daren nan?
Lafiyar kenan my one and only. Shiru tayi tana
jiran amsar shi.
Yaushe rabon da yaji muryarta balle ma ta
ambace shi da wannan sunan. Disconnecting din
call din yayi ya kashe wayar gaba daya. Me
Jalilah ke nema tare dashi bayan irin cin fuskar
da suka yi masa?
********************
Gidan Baba Aliyu Umma da Khairi suka nufa
kafin azahar bayan Hajiya ta kira su bayan
asuba ta sanar dasu haihuwar Rahma. Yakumbo
ta gani tana yiwa baby wanka tace to yar
tsohuwa ki wanke ta da kyau dai kuma kada ki
fesa mata goro. Hajiya dake ta fama da Rahma
taci abinci tace to yar nema daga shigowarki
zaki fara ko. Da kin kyale ni da ita Karimatu in
gama da 'yar ta ta in buge bakin. Wa zai buge
miki baki khairi taji ana fada daga bakin kofa.
Tana juyawa suka hada ido bata bashi amsa ba
sai ta gaishe shi ta mike zata fita. Au yau bakya
son na tare miki fadan ne? Ya tambayeta sai dai
bata bashi amsa ba tace bari naje wurin Baba
Hashim mu gaisa. Kallonta kawai yayi gaba
daya Khairi ta canja masa ya rasa dalili amma
ko kadan abin baya masa dadi.
Dariya suke ita da Umaima suna zaune gaban
wheel chair din Baba Hashim yana basu labari.
Duk basu kula da tsayuwarsa a wurin ba sai da
ya danyi knocking kofar yace Baba Hashim wane
labari kake basu ne ba'a hada damu ba? Shigo
Ahmad ya fada yana murmushi. Labarin kiriniyar
ka nake basu. Ai mun sami na tsokana ko
Khairi? Umaima ta tambayeta ita kuwa kokarin
tashi take tace ina zuwa zanyi waya ne.
Idan wasa ne ya soma yin yawa. Uncle Ahmad
ya fara gajiya da yadda Khairi take share shi. ko
a waya amsar maganarsa bata wuce eh ko a'a
wanda ko kadan ba haka suka saba ba.
******************
Toilet ta shiga tayi kuka mai isarta sannan tayi
alwala ta diga maganin ciwon ido mai sa ido
yayi haske. Ba tun yau take amfani dashi ba
indai tayi kukan Uncle sai ta diga. Khairi kenan
Rashin kula shi ba karamin damunta yake ba sai
dai tasan hakuri ya zame mata dole. Kamar ba
ita ba ta fito ta shiga dakin Momi tayi sallah.
******************
Shi kan shi bai sani ba amma bayan mintuna
kadan yake dauko waya ya duba ko text dinta
ya shigo. Sau uku kenan yana mata text yau na
tsokana ta share. Wai ni wayar wa kake jira ne
Abban Iman? Tun dazu kake abu daya. Abu daya
kamar me fa Mufida. Kallon ka raina min hankali
tayi mishi kafin ta bashi amsa kallon wayarka
mana. Its nothing to worry about bani ruwa mai
sanyi dai. Ita tasan akwai abinda ke damunsa
amma idan bazai fada ba zata jira.
Batul Mamman 💖
💕 MEYE DALILINKA 💞 8
Sati biyu kenan da khairi ta fara ja da baya da
Uncle Ahmad kuma ta daure tana kula Captain
sai dai ta rasa sukuni da walwala kamar yadda
ta saba. Wannan abu kuwa babu wanda baya
damu a gidansu. Babbar matsalarta yanzu bata
wuce zafi da kirjinta yake yawan yi sai taji
kamar zuciyarta zata cika mata kirji. Babu
wanda ta iya sanarwa wannan hali da take ciki
iyaka ta dage da yawan addua.
Ba irin wayar da Jalilah bata yiwa Tahir amma
yaki saurararta daga karshe tayi masa text
wanda a ciki take ta sanar dashi aurenta ya
mutu tana so su dawo da soyayyarsu. Ji rainin
hankali..tamkar ta aikawa dutse haka ya share
zancen.
Iyaye sun gama magana an yanke shawarar yin
bikin khairi bayan babbar sallah lokacin Tahir zai
dauki hutunsa na shekara. Yana jindadin yadda
khairi take bashi hadin kai suyi hira wadda bata
wuce zancen makaranta, kausar da uncle
Ahmad. Bai taba kawo komai a ransa ba sai dai
ya fahimci kamar tana cikin damuwa wadda
bata so a sani.
*****************
Ina kuma zaka je daga dawowarka Abban Iman?
Wani kallo yayi mata bai amsa ba ya cigaba da
saka safa a kafarsa. Abban Iman magana fa
nake yi maka 'yan kwanakin nan na kasa gane
kanka idan anyi magana kace ba komai. Tashi
yayi ya dauki keys dinsa ya fita ya barta tsaye
saroro. Shirun nasa shi yafi bata tsoro don a
yadda take da Ahmad bata magana biyu baiyi
abinda take so ba. Idan ma wata yar isakar ke
neman daga mata hankali to wallahi tayi kadan.
Dole ta koma wurin Mai Dafai ya bata wani
sirrin malakar. Ahmad baya cikin mazan da
mace zata sameshi taso rabuwa dashi.
A hanya yana ta sake sake a zuciyarsa.
Damuwarsa bata wuce ta Khairi da yadda ta
canza masa lokaci guda.
Khairi ki fada min gaskiya ko baki son aurena
ne? Wani murmushi tayi wanda ya kara haska
kyawunta wa ya fada maka Captain? Kefa kin
saba amsa tambaya da wata tambayar. To ai
kaine kamar wani lauya ka cika tambaya baka
san ance wala ta jassasu ba. Tana magana tana
yar dariya sai dai Tahir ba yaro bane yasan
dariya kuma ya san yake. Lemo ta zuba a cup
zata mika masa Indo da Uncle Ahmad suka
shigo falon. Sakin cup din tayi ba shiri da jin
muryarsa yana sallama. Duk su ukun kanta suka
yi suna tambayar ko bata ji ciwo ba don ya
tarwatse ko ta ina.
Allah Captain babu abinda ya same ni ta duka
tana matse kasan skirt dinta. Abin ya bawa
Ahmad mamaki kamar bata ganshi ba taki
amsawa yana magana. Tahir ya lura da abinda
tayi sai ya mika masa hannu suka gaisa.
Mikewa tayi bari na gyara jikina na dawo. No ba
sai kin dawo ba Ummulkhairi zan tafi kinga tara
tayi. Wani murmushin tayi to kana tsoron dare
ne? Gidan uncle fa yafi naku nisa amma kaga
yanzu yazo. Ahmad kaji kanwarka ko wato
gidanmu ne banda ita. Ganin yadda suke wasa
yasa yaji ransa ya kara baci. Da shi kadai khairi
ya kamata tayi wasa irin haka. Kuji karfin hali.
Wato ko kunyata ba kwa ji ko. Tahir yana dariya
yace tuba muke yi Uncle. Sai da safe Khairi.
Yana fita ta kama hanya zata fita daidai lokacin
da Indo ta dawo da tsintsiya da tsumma zata
gyara wurin da khairi tayi bari. Ke ina zaki ya
tambaya fuskarsa babu fara'a. Da yasan yadda
ta kidime da ganinsa da bai tsayar da ita ba.
Batul Mamman 💖
💕 MEYE DALIINKA 💞 9
Yanayin da taga fuskarsa ya bata tsoro don da
gani ransa a bace yake. Indo ya jira ta gama
sharar da take bayan ta fita a hankali ya rinka
tafiya ita kuwa yana matsowa tana kara tsorata.
Sai da yazo daf da ita sannan ya tsaya yace
Khairi wai menene matsalarki ne these days i
dont understand you. Bakinta na rawa ba...ba
kkkomai Uncle. Sami wuri ki zauna, ba musu ta
koma ta zauna. Kada ki bata lokacinki wurin yi
min karya irin yadda kike min kwanakin nan
nasan akwai wani abu. Kanta a kasa don ba
zata jure kallon da yake mata ba. Babu komai
da gaske kawai yanzu ina dan jin kunyarka ne.
Kin manta nine ma sirikinki Alh Mahe, malama
ki saurare ni da kyau Allah idan na sake kiranki
kika ki dauka ranki sai ya baci...kuma the next
time kika yi pretending baki ganni ba..hmmm
kada ki sake kawai. Yana gama magana ya fice
ba ko sallama.
Da gudu ta tafi dakinta tana shiga tayi jifa da
hijab da dankwalinta ta kwanta tana kuka.
Yanzu haka Uncle Ahmad zai rinka yin abinda
zai kara daukan hankalinta amma yana nuna
halin ko in kula a kanta. Wani irin tari ne ya
sarke ta tana cikin kukan tasa dankwalinta ta
rufe baki sai dai tana cirewa ba karamin razana
tayi ba domin kuwa jini ta gani a jikin dankwalin.
*******************
Mufida zaune a gaban Mal Mai Dafa'i ta fada
masa duk matsalolinta da mijinta yace kada ki
damu ga wannan kwalli da hodar da zarar kin yi
amfani dasu kun hada ido to an gama magana.
Tana ta washe baki ta mika hannu zata karba
ya noke tare da mika mata daya hannun nasa.
Haba ranki ya dade ai sai naji kafin alkalami a
tukunna. Da sauri ta bashi kudin ta mike , a
ranta kuwa tayi kwafa tace dani kake zancen
Ahmad.
Yaya Kausar wai ki zo inji wani Tahir. Tahir
kuma ta maimaita cike da mamaki. Ni yace ka
kirawo Hassan? Eh ya gyada kai. To kace ina
zuwa kuma ka gaishe da mamanku. Neman izini
tayi a wurin mahaifiyarta sannan tace ya shigo.
A farfajiyar gidan ta ajiye musu kujeru yazo ya
zauna. Nasan zaki yi mamakin ganina duk da
bamu taba haduwa ba ko. Haka ne ta amsa da
'yar fara'arta. Yanayinsa ya nuna alamun
damuwa yace Kausar nine Tahir din da zai auri
kawarki Allah baiyi mun hadu ba sai yau. Nan
da nan ta mike Allah sarki ai ban gane ba...ina
fata lafiya dai ko? Lafiya kalau in sha Allah. Ya
nuna mata kujera dawo ki zauna magana nazo
muyi akan Khairi. Jin haka ta dan sha jinin
jikinta, ita kanta ta san khairi ta canja yan
kwanakin da suka gabata.
Canjin da Uncle Ahmad yace yana son gani
daga gareta ya gagara domin kuwa Khairi yanzu
yawncin kullum bata jindadi daga zazzabi sai
ciwon kai. Malam ya shiga damuwa kwarai
itama Umman khairi abin ya isheta domin gidan
ya zama shiru ba hayaniyarta. Suna zaune a
falo zasu yi karatun asuba da Malam ya turo
glasses dinsa gaba sai dai sabanin yadda ta
saba yau Khairi kwantar da kanta tayi a jikin
kujera bata da niyyar tashi. Malam da Umma sai
kallon kallo.
Batul Mamman 💖
💕 MEYE DALILINKA 💞 10
Kasa karatun tayi ta tashi ta koma daki. Ba
komai take gudu ba face tarin da ya taho mata
kada su ga jini su tsorata. Ita kadai tasan yadda
take ji a jikinta. Su Malam da ta baro a falo
kuwa hankalinsu ya tashi. Gari na karasa
wayewa Malam ya kira yayansa ya sanar dashi
halin da ake ciki.
Uncle Ahmad yana ta sauri ya shirya saboda
yana son fara biyawa ta sabon asbitin hadin
gwiwa da suke shirin budewa shi da abokinsa
wayarsa tayi kara. Momi ce ta sanar dashi Baba
yana nemansa idan har bashi da patient da safe
yazo yanzu. Yana ajiye wayar ya fita da sauri ko
breakfast baiyi ba. Mufida tasha takaici domin
maganin dubu ashirin zuba masa a abincin.
********************
Mamakin ganin Malam yayi a gidan da safe
haka sai Baba Hashim da Yakumbo. Malam ya
zayyana musu halin da Khairi ke ciki hankalin
Uncle ba karamin tashi yayi ba. Kowa a wurin
yana fadin irin canjin da ya gani a tare da ita.
Baba ya dubi Ahmad yace to kaine babba wanda
idan babu mu dole kasa ido kan kannenka kuma
gaka likita dole kayi wani abu a kai. Kansa a
kasa yace in Allah Ya yarda zanyi iya kokarina.
Kuma tunda kun shaku sosai kayi kokarin sanin
ko wata matsala gareta inji Yakumbo.
'Ya'yan Alh Mahe ne suka zo duba Khairi domin
Tahir ya sanar dasu bata jindadi. Wata kanwarsa
tace antinmu anya ba ciwon tafiyar yaya kike yi
ba. Duk suka yi dariya cikin karfin hali tace ai
duk inda yake tare muke banda abinki. Haka
suka tafi suna ta yabonta.
Daga wurin aiki gidan Malam uncle Ahmad ya
wuce. Ya gaisa da Umma da take kitchen tace
masa Khairi tana falo. Kamshinsa mai dadi ne
ya fara dokan hancinta ta yunkura ta tashi
zaune Uncle dina sannu da zuwa. Yauwa
kanwata ya amsa mata a sanyaye. Khairi kin
rame ji idanunki a loko. To kada dai kace min
mujiya don ita ce mai ido a loko. Yana dariya
yace ai fa ke din nan da bakinki. Ko ciwon karya
kike yi ne duk kin wani tayar mana da hankali.
Tsayuwar da yayi a gabanta yasa duk jikinta
yayi sanyi shi kuwa wani irin kallo yake yi mata.
Yadda yake ji game da kanwar tasa yau daban
ne,yana tausayinta sanan yana tsoron rabuwa da
ita. Rashin kula shi da take yi yasa ya kara
sanin cewa Khairi is an important part of his
life.
Uncle ka zauna mana ta fada kanta a
sunkuye.kujerar da ke kallonta ya zauna. Khairi
kafin ayi zancen asibiti don Allah ki fada min
abinda ke damunki. Hawaye taji yana taruwa a
idanunta sai ta kasa bashi amsa. Kinsan yadda
muka damu da ke gaba daya amma cikin
kankanin lokaci kin canja ga rama kamar ana
tsotse ki. Murmushin da tayi sai da yasa zuciyar
Ahmad bugawa da karfi...God Khairi is so
beautiful. A zahiri kuwa cewa yayi ko aure ne
baki so ko Tahir din? Babu ko daya Uncle
malaria ce ta sani a gaba. Duk kin zama
makaryaciya ya fada yana kallon ta ido cikin ido
tana kokarin kawar da kanta yace Khairi...wani
iri taji har tafin kafarta. Ki kalle ni da kyau ki
rantse baki da matsala...
Kafin ta bashi amsa tari ya sarke ta ga hawayen
da take kokarin mayarwa. Uncle Ahmad tashi
yayi da sauri ya dauko mata tissue yana cewa
wanke ni zaki yi da virus din mura ko? Yana
mika mata tissue din tayi wani tari mai karfi sai
jini ya watso masa a gaban riga. Ita kuwa Khairi
faduwa kasa tayi a sume.
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun shine abinda ya
fada da karfi har Umma, Inno da Indo suka shigo
falon da sauri.
Batul Mamman💖
💕 MEYE DALILINKA 💞 11
Ganin halin da Khairi ke ciki Umma ta soma
kuka ina zan sa kaina ni Munnira ta koma ga
Uncle Ahmad don Allah kayi wani abu ita kadai
gareni. Yadda suke ta kuka yasa shima ya dada
rudewa. Daukarta yayi ya fita Indo tayi saurin
bude masa mota yasa ta a ciki. Umma ta shiga
gaba kan Khairi a cinyar inno suka nufi asibiti.
Tun kafin su isa ya kira wani abokinsa ya
kwatanta masa halin da take ciki domin a tanadi
kayan da ake bukata kafin su iso. Umma a gefe
daya ta kira Malam sai da taji shiru bai dauka
ba ta tuna yau alhamis yana yin karatu a
masallacin Mus'ab ibn Umair a nan unguwarsu.
Driver dinsa ta kira Lado ta sanar dashi idan
Malam ya fito ya fada masa.
Ko da isarsu asibitin sake daukarta yayi abokan
aikinsa suka yi masa jagora zuwa dakin da zai
kaita. Yana dora ta akan gado sai ta fara aman
jini idan tayi yunkurin aman sai kirjinta ya amsa.
Haka Uncle ya rirrike ta tana amai tana hawaye
duk kayansa sun baci sai dai ba ta su yake.
Yana daga zaune bakin gadon ya rike ta yana
bada command kamar wani soja. Daya ga kamar
ta fara fita hayyacinta sai ya fara marin
fuskarta da sauri Khairi stay with me, wani gumi
ke karyo masa hasbunallahu wa ni'imal wakil
open your eyes please. Karshen maganar dai da
kuka ya kare ta. Dr Maina ne yaja hannunsa da
kyar ya fitar dashi daga dakin. Tamkar karamin
yaro haka ya zauna a kofar dakin yana kuka.
Umma na ganin haka ta fadi a sume. Ana
kokarin dauke ta Malam da iyalan gidan Baba
Aliyu suka shigo.
********************
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un shine kawai ake
fada. Inno ce ta iya yi musu bayanin abinda ya
faru domin Uncle Ahmad kai kawai ya rike yana
zubar da hawaye saboda baya tunanin Khairi
zata tashi. Bayan an sami kanta Umma ma ta
farfado Malam da Baba suka tafi office din Dr
Maina. A can suka tarar da Ahmad fuskarsa duk
ta nuna alamun damuwa.
Baba ya sake kallon likitan cikin fushi wai
nufinka karamar yarinya kamar Ummulkhairi ita
ce da hawan jini da ciwon zuciya? Dr Maina ya
dubi Uncle yace Dr Saraki ai na nuna maka
dukkan binciken da mukayi. Malam yace to ni ba
wannan ba ku fada min meye abin yi. Ina ganin
ina maganin da aka bata ya sake ta sai mu
tambayeta menene problem dinta. Me ta sa a
ranta har ta kamu da wannan ciwon cewar
Baba. Uncle Ahmad yace zan tambayeta Malam.
Ku daure ku tafi gida a kawo abubuwan da zata
bukata da mai kwana daya. Nima ba tafiya zanyi
ba.
Batul Mamman 💖
💕 MEYE DALILINKA 💞 12
sai da ta kwana uku ta dan fara dawowa
hayyacinta. Duk yadda ake ta rarrashinta ta fadi
matsalarta abu yaci tura domin kuwa cewa take
babu komai. Ai da kunya tace tana son wani da
namiji da bakinta. Musamman Uncle wanda bata
taba ganin alamun zai mata son aure ba.
Kausar suna ta fada da mai adaidaitan da ya
kawo ta asibiti saboda bata da chanji sai ta
hango shi yana fitowa daga mota. Kaf idanunsu
suka hadu sai kallon kallo. Ko me ta tuna tayi
saurin dauki ido tare da cewa a'uzubillah. Tun
kafin karaso kamshinsa yayi masa iso yana
zuwa dubu daya ya mikawa mai dan sahun yace
mata muje ko. Ko sauraron godiyar mai dan
sahun baiyi ba. Itama dai godiyar tayi masa tare
da gaishe shi. Kafin su shiga wayarsa tayi
ringing ya dauka yana magana da kyar. A ranta
kausar tace idan namiji yasan ya hadu
wulakancinsa karuwa yake. Jalilah na fada miki
ki dena kirana kuma idan kika sake zuwa
gidanmu zan sa kannena suyi miki duka. Kausar
dai dariya ma take yi. Yana gamawa ya harareta
ku mata kun iya rainin wayo.
Khairi yaya jikin naki? Dan murmushi tayi sai
idanu da suka fada ga rama. Kausar tace ai
baka ganta ba lokacin da bata gane waye a
kanta. To dadin abin dai banyi surutai irin naki
ba...ina jinki kina cewa khairi kada ki mutu ki
barni wayyo yar uwata. Lallai kin warke amma
ba don kina gadon asibiti ba dundu zan miki. Ai
dama ki saba min mugunta. Shi dai Tahir abin
dariya ya bashi to ko zaku kara ne nayi refree.
Uncle Ahmad ne shigo dakin da sallamarsa. Yayi
mata kyau sosai har taji zafi a zuciyarta sai tayi
shiru ta dena magana shi kuwa ido ya zuba
mata kamar ya manta da mutane a dakin. Tahir
da Kausar suka hada ido irin kallon you see
what I told you din nan.
Sun dan taba hira wadda Khairi tayi shiru. Tahir
yace doctor ina son ganinka idan ka gama.
Khairi wadda tun dazu bata kula kowa ba tace
gulma zaku fara? Sai a lokacin Uncle yayi
murmushi fuskarsa ta kara yin kyau. Khairina ta
fara dawowa kenan. Ya maida dubansa ga Tahir
muje ko Captain.
********************
Kafin Dr Ahmad ya rufe kofar office din Kausar
ta shigo ya kalleta da mamaki a fuskarsa Tahir
yace ai maganar da ita zaayi. Bayan duk sun
zauna Ahmad yace kun barni a suspense fa don
Allah me ya faru. Tahir ne ya soma magana tare
da fada masa irin yanayin dayake ganin khairi
tun farkon zuwansa ya lura tana da damuwa.
Dalilin haka yasa ya nemi kausar wadda da kyar
ya shawo kanta ta fada masa matsalar khairin.
A takaice dai doctor Khairi is in love with
someone else. What??? Kausar da gaske kike yi.
Eh Uncle ta bashi amsa. Wannan abu tun muna
yara ya fara har yanzu kuma mutumin bai ma
sani ba. Ko kadan zancen bai masa dadi ba.
Yanzu khairi wani take so....to waye ma wannan
mutumin karshe dai wani kishi mai tsanani yaji
ya turnuke shi ya kasa magana. Tahir wanda
yake lura da abinda yake yi yayi murmushi ashe
dai Khairi ba son maso wani takeyi ba. Yace
kada ka damu dan uwa ai sanin irin matsalar
tata zai kawo saukin lamarin. Sai ka dage wurin
jin ko waye take so din. Kausar kallon shi tayi
da mamaki don a yadda sukayi shawara zasu
fada masa ko waye. Ni dai zan sami Alhajinmu
nayi masa bayani na janye daga maganar auren.
A waje yace kausar kinga na canja plan ko? Na
kula kamar yana sonta ne shima gara mu bari
suyi resolving din issue din da kansu. Mungode
sosai Captain domin badon kayi hakan ba
bazamu taba iya fada ba. Ba komai Kausar sai
dai tunda kin hanani kawarki sai ki nemo min
wata matar.
Ahmad ya rike kansa wanda ke masa
matsanancin ciwo. Waye yasa khairi wannan
ciwon, ina ma dai ace.....Khairi bazan iya jure
rashinki ba ya fada a sarari
Batul Mamman💖
💕 MEYE DALILINKA 💞 13
Bayani Ahmad yayi musu game da abinda Tahir
ya fada musu. Malam yayi matukar mamaki
domin ko da wasa bai taba ganin alama ba, uwa
uba kuma shi a yadda ya santa ko saurar
samari bata yi. Baba dai cewa yayi a bita a
hankali kuma su fara tambayarta kafin a yanke
hukunci.
Babban yaya aka barwa aikin tambayar kanwar
tasa sai dai abin yaci tura domin kuwa kuka
take saka masa idan ya tambayeta. Shi dai yana
son ta sami lafiya amma tsakani da Allah yana
tararrabin wa zata ce. Wasa wasa sai da tayi
sati a asibitin. Duk iyaye da lallami da rarrashi
anyi anyi taki magana sai kuka. Ga ciwo yana
neman dawowa sabo. Inno abin duk ya ishe ta
kullum ita da kausar suna aikin bata shawara
tace ita bata yafe ba ma duk wanda ya fada a
cikinsu. Tahir dama bai taba nuna mata ya sani
ba.
Sai da ta tabbatar babu kowa a bakin motar sai
shi kadai yana jiran dreban sa ya idar da sallah
Inno taje bakin motar ta durkusa har kasa. Baba
Aliyu yace haba haba don Allah tashi yana
magana yana waige waige. Ya zaki durkusa min
haka bayan ko ba'a fada ba nasan kin girmeni
ko so kike babban Malam ya fara min waazi? ya
kare zancen da murmushi. Inno ta mike ta
sunkuyar da kai kasa. Ranka ya dade akan
maganar ummalhairu ne. Ina jinki Inno ya fada
hankalinsa na gareta. Alhaji tun yarinyar nan
bata san kanta ba take son shi har girmanta.
Saboda shi wallahi bata fita fira da wasu mazan
gashi bai ma san tana yi ba tana fadin haka sai
kuka. Baba yace bangane ba waye shi din. Ta
face hanci yallabai Amadu nake nufi na wurinka.
Wani irin farinciki ne ya saukar masa a zuciya
har fuskarsa ta nuna. Ahmad kika ce fa? Kin
tabbata? Alhaji wallahi bazan maka karya ba.
Bandir din 'yan dari biyu ya dauko daga
aljihunsa ya bata. Murmushi tayi irin nasu na
tsofaffi Alhaji bani da burin da ya wuce naga
auren Ummalhairu da Amadu shine kawai abinda
zaka bani tukwici.
Bai taba zata haka abin zai kasance ba. Sai dai
yayi murna mara misaltuwa. Alhaji Aliyu yana
son kannensa sosai. A dalilin su ya hakura da
jami'a a shekararsa ta biyu don kudin da yake
samu bazai isa ya ciyar da gidansu kuma duka
suje makaranta ba. Dr Abdallah 'ya daya gareshi
idan dansa ya aura yasan ya gama hada kan
'ya'yansu tunda Hashim lalura tasa ko auren
baiyi ba. Karshe sai ya yanke shawarar bazai
fadawa kowa ba sai ya sami hanyar bullowa
lamarin.
******************
Ahmad zaune a dakin mahaifinsa ya sunkuyar da
kai kasa ga mahaifiyarsa a gefe. Kalon agogo
yake yi domin kuwa yabar khairi jikin babu dadi
sauri yake ya koma. Baba yayi gyaran murya
yace Ahmad idan na baka umarni za ka bi? Baba
bana fatan Allah Ya nuna min ranar da zan
ketare maganarka. Alhamdulillah yace sannan
ya dubi Haj Karima duk abinda muka zanta da
Inno ke kadai na fadawa saboda na aminta da
cewa kema bazaki bijire min ba, Ahmad ko
kasan cewa kanwarka ciwon nan da take yi
dalilinka ne. Da sauri ya dago kansa...ni kuma
Baba ya fada cikin rudewa. Eh Ahmad kai. Dazu
Inno tayi min gamsashen bayani ashe ka taba
cewa kaine mijinta tun tana karama. To tasa
abin a ranta ta kuma girma da sonka. Ikon Allah
haka kawai yake fada a ransa. Ko shiyasa ya
zama restless akan lamarinta? Lallai kuwa idan
haka ne zai share mata hawaye domin ko ba
komai a cikin kannensa daban khairi take. Baba
ya katse masa tunani da cewa ina son kayi min
alkawarin zaka aure ta kuma bazaka taba
wulakanta min 'ya ba. Kafin ya bada amsa
Hajiya tace Alhaji ina ganin abinda yafi shine
kace kai ka hada auren kawai kasan mu mata
da gutsiri tsoma ko da wasa wata zata iya fada
mata magana nan gaba. Ahmad ya kalli
mahaifiyarsa Hajiya akwai tunani. Baba ma yaji
dadin shawararta..yace kaga jiya Abdullahi ya
tafi madina taron malamai na sati uku daga nan
zaiyi umra kafin ya dawo. nasan shima ciwon
yarinyar nan ya tsorata shi fada ne kawai baya
yi. Idan ya dawo zamu yanke lokacin aurenku da
su Kawu Hadi.
******************
Kausar da Inno sun sami Umma a barandar
asibitin sunyi mata bayanin komai. Suna haka
Baba ya kira yayi mata zancen tare da sanar da
ita cewa kada ta fadawa Malam wannan aikinsa
ne idan ya dawo. Ya sanar da ita ne domin yana
son a samin kan Khairi kafin ya dawo. ita Hajiya
tace bama zata nuna tasan komai ba kada
Umman taji babu dadi shiyasa ita bata kira
ba.Kaji manya masu tunani.
Batul Mamman💖
💕 MEYE DALILINKA 💞 14
Uncle Ahmad gida ya wuce ya tarar yaransa
sunyi bacci a falo ya dauke su ya kai daki.
Mufida wai meyasa kike son barin yaran nan a
falo su kadai? Gashi har sunyi bacci. A fusace
ta juyu zata bashi sai taji tsoron kada ranshi ya
baci yaki kwana da ita ta sake asarar maganin
mallakar da Mai Dafa'i ya bata ta shafa a kirji
da mara. Abban Iman nasan kanwarka tana
kwance a asibiti amma hakan ba yana nufin ka
dena dawowa da wuri ba ko ka dena cin abinci.
Rungumota yayi amma hankalinsa yana wurin
khairi. fuskarta ya shafa yi hakuri Mufida
kinsan dole hankalina ya tashi ita kadai Malam
ya mallaka kuma idan zaki tuna ko kafin
aurenmu mun shaku sosai. Itama sakin fuska
tayi tana kokarin su hada ido yayi arba da
kwallin data sa. Sai dai hakan bata samu ba
domin sakinta yayi tare da bata hakuri. Mufida
wanka zanyi na koma asibiti jikin khairi babu
dadi na barta dazu. Kai wannan yarinya ko
jaraba tana asibitin ma ta hana ruwa gudu.. gara
a aurar da ita kowa ya huta.
Bakin wando da maroon din shirt ya saka sunyi
masa kyau sosai. Sai turare yana fesawa yana
dan humming din wata waka. Mufida ta harare
shi ni wannan abin da kake yi sai na zata zance
zaka ba wurin patient ba. Dariya yayi don baya
so suyi fada kada ta bata masa lokaci. Daren
yau na Khairina ne ya fada a ransa.
Yana tuki cike da farinciki kamar wani sabon
shigar soyayya. Shima abin mamaki yake bashi.
Fada suke da Inno akan cin abinci Uncle Ahmad
yayi sallama sai da suka masa izini ya shiga.
Tare da wata nurse suka shigo dakin ta gaishe
shi kanta yana kallon plate din abincin. Inno
allura zan mata har biyu ina fata taci abinci.
Yana maganar ne cikin zolaya inno tace bata ci
ba ai rigimar da muke yi kenan kafin ka shigo.
Nurse din ya sallama dama yana sane wurin yin
rounds dinsa yabar dakinta ya zama na karshe.
Kujerar gaban gadon ya jawo kusa da kafafunta
ya zauna sannan ya kalli inno nifa zance nazo
Inno gaskiya ki bamu wuri. Eyye dan nan lallai
yaran zamani ba kunya. Ita kanta khairi ji tayi
kamar gadon ya tsage ta shige. Lafiyar Uncle
kuwa?
Inno na fita ya dauke plate din daga cinyart.
Bude bakin in baki a baki kinji khairina. Kallonsa
take galala ikon Allah. Dan zare mata ido yayi
da gaske nake fa. Ni zan iya ci da kaina....shima
kwaikwayon muryarta yayi ya maimaita abin da
ta ce har tayi dariya gaskiya Uncle da kai mace
ne saboda muryarka zaka rasa miji. Wai!!!
Garmaho kenan. Ganin yadda har ta sake tana
dariya ya sanyaya zuciyar Ahmad. Khairi will
never sieze to amaze him. Matso da fuskarsa
yayi kusa da tata. Tell me something khairina..
ina jinka ta bashi amsa sai dai cikinta har
kadawa yake don tsoro. Gaba daya nauyinsa
yake ji bare ya matso kusa da ita gani take ya
kara girma. Katse mata tunani yayi bakya son
muryar tawa ne? Ina so mana, tana fada taji
kunya sai tayi saurin rufe fuskarta. Shi kanshi
dadi yaji a ransa bude fuskar ki ci abinci akwai
allura da zan miki. A ina ta tambaya a tsorace.
Yau ba tsoron allurar bane kadai harda tsoron
wanda zaiyi domin kullum nurse ke yi mata.
Indai kin cinye duka zan kira Sister Shukriya tayi
miki. Ai kuwa tana da kirki Uncle zan cinye.
Tana ci suna hira abin gwanin shaawa shine
nima har nayi addua Allah Ya kara mana so,
kauna, tausayi, mutuntawa, da girmamawa tare
da dunbin romanciyya tsakanin mu da mazan
mu. Amin
ta cinye abincin tas sannan Uncle Ahmad yace
to Khairina sai da safe na korar miki inno ko. Ai
nasan zan sha mita. Sai da safe kanwata ya
fada yana bude kofa...sai da safe Uncle dina.
Yaushe rabon da ta kira shi da wannan sunan?
Yana fita Inno ta shigo da nurse yau khairi ko
ihun allura bata yi ba. Bayan ta fita ne Khairi
cike da nishadi tace Inno yau Uncle Ahmad ya
canja min sosai. Ai naga kina ta faraa kamar kin
tsinci hakori amma tuntuni baki kula bane haka
yake miki tunda kika fara ciwon nan har kuka fa
yayi. Da gaske? Zan miki wasa ne 'yata. Ki
cigaba da addua kila bukatar ki ce zata biya.
Dama ta samu an cire mata drip saboda haka
alwala ta dauro ta yi nafila tare da kara addua
indai akwai alkhairi Ya Allah Kasa Uncle Ahmad
ya zama mijina.
Batul Mamman💖
💕 MEYE DALILINKA 💞 15
Tun daga lokacin da Uncle Ahmad ya fara nuna
kulawarsa ga Khairi. Kulawa irin ta soyayya
sauki ya fara samuwa sosai dama ciwon nasa
ne. Umman khairi dai farincikinta baya
misaltuwa domin tilon yarta ta sami lafiya.
Alh Aliyu duk da ya hana a sanar da Malam
halin da ake ciki amma har gida yaje ya sami
Alh Mahe akan maganar Tahir. Hakika duk
mutum mai halin kirki ya kan dace da abokin
kwarai. Alh Mahe yace kada ka damu Alhaji
kafin yayi magana da Ahmad din ma sai da ya
sanar dani halin da ake ciki. Idan Malam ya
dawo shima nasan zai fahimta. Allah Ya yi
mana jagora.
Tun safe suke baki kasancewar yau asabar
babu aiki masu zuwa dubiya sun karu. Ganin har
wurin takwas na dare da baki Uncle Ahmad yazo
da kanshi ya sallami kowa domin a cewarsa
Khairi na bukatar hutu sosai. Umma da Indo ne
karshen tafiya yaje rakasu mota. Yana dawowa
ya tarar khairi tayi bacci. Abin ya daure masa
kai. Inno ba yanzu na fita tana hira ba ya kika
bari tayi bacci bata sha magani ba. Kasan dai
bata son maganin nan na dare kullum ta sha sai
tayi kakarin amai, wai wari yake yi. Murmushi
yayi don yasan sarai idonta biyu. To tunda bata
so ai akwai allurarsa sai nayi mata. Yana fita ta
mike ta gyara kwanciya harda rufa har kanta
duk da zafin da akeyi saboda hadarin da ke
haduwa. Inno dai dariya take yi. Ko da ya dawo
ta fara gumi a karkashin bargo yace kinga ban
sami karamin syringe ba sai wannan babban shi
kuma allurarsa akwai girma. Kallonta yake yi
yana magana don sai mutsu mutsu take daga
cikin bargon....hmmm yarinya zafi zai koro ki ya
fada a ransa. Inno sai kin dan danne min ita fa
don allurar nan idan aka yiwa mutum yana
dadewa bai motsa ba. Jin hannun Inno yasa ta
bude kanta ba shiri shi kuwa ya dage sai yayi.
Kuka ta sa masa da rokon yayi hakuri zata sha.
Komai na khairi shaawa yake bashi. Har yanzu
dai zancen soyayya bai hada su ba amma kana
ganinsu tare zaka gane akwai wata a kasa.
Malam yayi matukar farinciki yadda yake jin
muryar khairi a waya. Umma ta fada masa an
kusa sallamarta ma.
******************
Dakinta yasha gyara don yau Umma da kanta ta
gyara shi ta fitar da kayan wanki sannan ta
gyara mata wardrobe. Gida yana ta kamshi
kamar wata amarya zata tare. Gidan Baba aka
fara kaita ta gaishe da yakumbo da baba
Hashim wanda ya damu kwarai da ciwonta sai
dai sau biyu aka kaishi dubuta. Daga nan kuwa
gida suka wuce Umma baki har kunne. Ashe dai
tana ji da khairin ta ta. Wanka tayi tasa wata
dogowar rigar atampa tayi kwalliya kausar tace
khairi irin wannan ado kamar ba daga gadon
asibiti kika taso ba. Dariya sukayi harda tafawa
sai wayar khairi tayi ringing tana dauka ya fara
fada. Ina kika shiga ina ta waya baki dauka ba?
Duk kin daga min hankali. Yi hakuri Uncle dina
ta bashi amsa a sanyaye. Na shiga wanka ne
kuma dana fito ban duba wayar ba.
Jin yanayin maganarta yasa baiji dadi ba ko ya
bata mata rai. Khairina ba fada nake miki ba
kinji ko. Naji tsoro ne ko wani abu ya same ki.
Murmushi tayi har yaji sautinsa wanda hakan
yayi masa dadi. I am already missing you here.
Na saba ganinki kullum kwanakin nan. Shiru tayi
tana sauraronsa. Khairin Ahmad kina ji na?
Wayyo dadi har wani juyi tayi a kan gado.
Kausar tana gefe tana kallon ikon Allah. Ina
jinka Uncle dina ta bashi amsa.
Ki shirya yau zanzo zance na gaske after
magrib.
Zance kuma Uncle?
Eh ko zaki hanani ganin mata ta ne?
Wace matar ta tambayeshi cike da murna.
Ummulkhair Abdallah Saraki
Batul Mamman💖
💕 MEYE DALILINKA💞 16
Tana ajiye wayar ta rungumo kausar nagode da
adduarki yar uwa. Allah Ya saka da alkhairi.
Ture ta tayi tace duk nasan saboda uncle
Ahmad ne kike wani tarairaya ta. Dariya tayi
kafin ta zauna bakin gado. Ki fada min gaskiya
tsakani da Allah baki da hannu a lamarin nan?
Ni Allah Ya isan ma da nayi idan kika fada na
yafe fa. Yadda take magana yasa kausar yin
murmushi sannan ta fada mata duk yadda
sukayi da Tahir da Uncle din nata. Karshe tace
mata Allah Khairi shima yana sonki don baki ga
fuskarsa ba lokacin da Captain yace masa kina
da wanda kike so. Da kina ganiyar ciwonki kuwa
ai yadda ya rinka yi ko Umma albarka. Ke dai
mu dage da addua a kodayaushe. Khairi dai bata
tsaya jin karshen maganar kausar ba ta daga
gira daya wato Captain ta wani ja sunan yadda
kausar tayi. Lah wallahi kada ki fassara ni. Me
kika ji nace har kin tsargu kamar mara gaskiya.
Khairi ki kiyaye ni fa. Ganin kausar ta yo kanta
yasa ta mike itama zata gudu idan naki fa...
Umma tana daga falo tana jin hayaniyarsu.
Zuciyarta fes ta Inno Allah Ya biyaki. Ji yau
kadai da khairi ta dawo gidan nan har ta cika
min kunne. Ai Hajiya idan da rabo sai kiga ta
cika miki gida da yara nan gaba.
******************
Uncle Ahmad ya cika alkawari domin kuwa a
masallacin kusa da gidansu khairi yayi sallar
Isha sannan ya kira ta a waya. Ya sanar da ita
zuwansa. A falo ta makale saboda Umma tana
kallon news. Yana ta kira tana rejecting calls
din. Umma kuwa tana lura da ita idan bazaki
tashi ba nima bazan baki wuri ki sami damar fita
ba zan ga karshen gulma. Gajiya yayi ya shigo
falon bayan an amsa masa sallama. Gaban
Umma yaje ya zauna. Anti Munnira barka da
yamma. Mun wuni lafiya Ahmad? Ya zirga zirgar
ku, Allah Ya kara zumunci Ya saka da alkhairi.
Amin ya bata amsa. Khairi ko kallonsa taki yi
duk yadda yaso su hada ido. Umma har ta fara
jin kunya ganin haka ta tashi ta tafi daki.
To ai sai ki tashi tunda nayi miki hanya ko a nan
zamu yi hirar? Kunya ce ta kamata. Yanzu sai ta
bishi falon baki...anya zata iya kuwa. Ganin
bata da niyyar tashi yasa ya miki 5mins na baki
idan baki zo ba zan tafi.
A hankali ta shiga falon kamar wadda zaa kama.
Yana daga zaune yana dariya ashe dai kina son
mijinki. Mayafin jikinta tasa ta rufe fuska a haka
taje ta zauna.
Kin dena magana ne khairi na. A'a ta bashi
amsa cike da kunya. bazan hanaki jin kunya ba
yanzu khairi amma very soon zanyi maganinta.
Janye mayafin tayi ayi maganinta fa kace
Uncle? Babu inda za ta. Hmm..... akwai ranar da
zan kashe bakin nan. Mu kashe na juna dai
...tana fada kuma sai ta tuna da wa take
magana ba shiri ta mike Uncle sai da safe..
Shima tashin yayi ina zaki kike wani sauri? Sai
kin fada min yadda zamu kashe bakin juna. Da
gudu ta fice zuciyarta tana bugawa da sauri.
Shima Ahmad ta barshi cikin wani irin yanayi
mara misaltuwa.
Gidan su Khairi yau an tashi da gyara da girke
girke Malam yana hanya. Kwananta uku da
dawowa daga asibiti. Cike da doki ya shigo
gidan Khairi ta kankame shi tana ta murna. Yayi
mata addua tare da bata guzurin zamzam da
yayi mata. Da murna ta shiga daki ta kira Uncle
tana sanar dashi dawowar Malam. Ita kuwa
Umma tsabar murna bayan ya gama cin abinci
tace Malam albishirinka. Goro fari Munnira yana
magana cike da nishadi. Ba dole ba khairinsu ta
warke. Tace to bani tukwici don nasan sai ka fi
Alhaji murnar abinda zan sanar da kai. Allah
Yayi miki albarka uwargidana. Amin ta amsa
sannan ta bashi labarin khairi da Uncle Ahmad.
Tunda ta fara gabansa ke faduwa ai kuwa
abinda yake tsoron ji ta fada. Ummulkhair da
Ahmad. Tana gama bayani ya mike a sanyaye
Munnira...naam Malam ta amsa masa cikin
jindadi. Mikewa yayi idanunsa fal da hawaye
yace kiyi hakuri amma ko na mutu kiyi min
alkawarin Ahmad ba zai taba auren Ummulkhair
ba.
Batul Mamman💖
💕 MEYE DALILINKA 💞 17
A tsorace ta miki har wayar da ke kan cinyarta
ta fadi ta tarwatse. Malam meye dalilinka na
fadar wannan maganar. Bai iya bata amsa ba
don bashi da bakin magana. Dakinsa ya shiga ya
rufo kofar. Haj Munnira ta shiga tashin hankali
saboda sabanin reaction din da tayi tsammani ta
gani a tare da shi. Ko dai Ahmad yana da wani
mugun hali ne da basu sani ba?
Shi kuwa Dr Abdallah ko da ya shiga daki alwala
ya dauro yazo ya fara nafila wadda bai san
adadinta ba. Yana yi yana kuka tare da
tsananta addua ga Allah SWT kada ya nuna
masa wannan bakar rana da Ahmad zai auri
Khairi.
Ita kuwa khairi da bata san abinda ke faruwa ba
baccinta tayi mai dadi domin kuwa sun dade sun
hira da uncle Ahmad a waya. A nasa bangaren
bayan yaje gida ya tarar Mufida tana wanka.
Cire kayansa yayi daga shi sai singlet da
gajeren wando ya zauna a kan gadon yana jira
ta fito shima yayi. Tunawa yayi wani abokinsa
ya bashi gift din pack din necktie bai sami
damar dubawa ba sai ya tashi ya bude wardrobe
dinsa yana nema bai san inda Mufida ta ajiye
ba. Garin dube dubensa yaga wata bakar leda a
bangaren kayanta. yana budewa wata takarda ta
fado sai ga wasu kananan kwalabe da kulle
kulle a leda. Tattatawa yayi zai mayar mata don
ya zata irin kayan matan nan ne da take sha ya
dai yi mata fadan ta tabbatar ta san me take
sha saboda lafiyarta ma. Haka nan ya bude
takaddar ya fara karantawa domin rubutunta ne
a jiki yana yar dariya...
1. Farin kulli hodar fuska idan miji ya gani komai
kika tambaya zaki samu
2. Kwalba mai jan ruwa na shafawa a goshi,
mara da kirji miji yaji tsoronki
3. Kwallin mallaka a saka lokacin kwanciya
bacci
Dama ga zafin gari amma wani gumi ta fara yi.
Ita kuwa mufida me na rage ta dashi take
neman fadawa shirka. Ko da ta fito bai nuna ya
gani ba yaje yayi wanka ko mai bai shafa ba yaji
ta rungume shi harda riko fuskarsa da
hannayenta don su hada ido. Shi kuwa sai
nokewa yake yana karanta Ayatul kursiyy. Ranar
dai bai yadda anyi abinda take so ba don yana
tsoron wanda ake shafawa mara kada ya hadu
dashi ya fara tsoronta. Baccin karya yayi kafin
na gasken ya zo tare da yanke shawarar fadawa
Malam don ya bashi shawarar abinda ya kamata
yayi.
******************
Malam bai sami kansa ba sai bayan isha ya tafi
gidan yayansa. Alhaji Aliyu yace ai nasan kana
samun labari zaka zo. Baba Hashim da yake
gefe yace ai yaran nan sun gama mana komai.
Allah Ya tabbatar da alkhairi. Amin, amin Baba
ya amsa. Malam ya tattaro courage dinsa yace
amma Yaya ka manta da maganar yaron wurin
Alh Mahe? Yar dariya yayi nasan zaka ce ana
neman aure cikin neman wani ko? To kwantar
da hankalinka har gida naje na sameshi kai
shima Tahir din da kansa yace ya janye. Ba
haka Malam yaso ji ba amma yasan idan ya bari
aka yi auren nan Allah bazai barshi ba. Saboda
haka ya dake yace Yaya ni dai gaskiya kayi
hakuri kuma na baka damar nemawa khairi miji
amma banda Ahmad.
Yayi kusan minti biyar a bakin kofar yana
sallama basu amsa ba shiyasa bai shiga ba
amma maganar Malam wadda ba karamin
razana shi tayi ba yasa ya saki kwalaben asirin
mufida har suka waigo suka ganshi.
Batul Mamman💖
💕 MEYE DALILINKA💞 18
Yayi yayi amma ya rasa me zai ce karshe dai
shigowa yayi ya zauna. Baba yace Abdullahi
fada min me yake faruwa. Ahmad yayi maka
laifi ne ko akwai halinsa na sabon Allah da
bamu sani ba. Fuskar Ahmad kawai yake kallo a
ransa yana cewa ka yafe min Ahmad. Ganin
yayi shiru abin ya fara batawa Baba rai yace
muna sauraronka kayi shiru. Baba Hashim yace
Ahmad tun kafin abu yayi nisa ka fada mana
gaskiya domin naga baban naka baya son yin
magana kada ya fadi sirrinka. Kana kallon shi
kasan a rude yake. Wallahi baba Hashim bansan
me nayi ba. Malam yayi ajiyar zuciya babu
abinda kayi kada ma ka zaigi kanka auren ne
kawai bana son ayi na zumunci. Allah Ya baku
wasu ku aura. Baba ya dago kai cikin bacin rai
yace Ahmad bamu wuri. A sanyaye ya fita ya
koma dakin mahaifiyarsa. Tana ganin yanayinsa
tasan ba lafiya ta fita ta kira Momi da yakumbo
suka shiga falon tare.
Ni Ahmad baiyi min komai ba amma Yaya kayi
hakuri auren nan wallahi baza ayi shi ba. Yana
fadin haka ya fita.
Yauma rufe kansa yayi a daki Umma ta rasa
yadda zata yi gashi bata so khairi tasan abinda
ke faruwa. Waya ya dauko ya kira Baba malam
mahaifin Umma yana magana yana kuka ya
sanar dashi halin da ake ciki. Ka taimaka kasa
baki kada muyi abinda Allah zaiyi fushi damu
amma kafi kowa sanin dalilin da yasa bazan bari
ayi auren nan ba. Baba Malam yace ka kwantar
da hankalinka ranar juma'a in sha Allah zan zo
kanon. Amma kafin nan kada ka bari ayi auren
kaji ko Abdallah. To Malam ya amsa masa cikin
kuka.
Haj Karima da su Yakumbo kowa kansa a daure.
A daki ta tsare Ahmad lallai ya fada mata
abinda yayi wa Malam. Karshe tace ko dai kana
da cutar nan ne ka boye mana. Wace cuta kuma
Hajiya ya tambayeta a razane. Kanjamau mana.
Haba hajiya wallahi bani da ita. To ba komai
nasan babanku bazaiyi shiru da maganar nan
ba. Ni dai babu komai a tsakaninmu na fada da
zai sa yaki jinina amma da safe zan kira
Munnira naji ko tasan dalili.
Khairi tana dafa indomie zata ci ta tafi
makaranta ta ji muryar Umma tana cewa wallahi
haj karima nima yadda kika ji maganar nan haka
naji ta. Ko kinsan yanzu ko dakinsa baya bari na
shiga da sassafe yake fita sai khairin ma tayi
bacci yake dawowa. Ni tsoro na daya kada taji
cewa mahaifinta ne baya so ta auri Ahmad. Kirji
ta dafe sakamakon wani zafi da taji zuciyarta
tana yi.
Batul Mamman💖
💕MEYE DALILINKA💞 19
Da gudu ta ta shigo falon Umma na ganinta tayi
saurin katse wayar. Khairi tace Ummana me ya
faru? Meyasa Malam baya son auren tana
magana hawaye suna wanke mata fuska. Umma
bata da amsa ta fara rarrashinta duka duka
yaushw ta fito daga asibiti malam zai janyo
musu tashin hankali.
A kasa ta zauna tana ta kuka Umma na bata
baki sai ga indo ta shigo daga baya da gudu ta
nufi kitchen saboda kaurin indomie din da khairi
ta dora. Daki ta koma ta dauko waya ta kira
Uncle Ahmad tana kuka yana jin yanayinta
yasan abinda ya faru yace khairina kina ji na?
Da kyar ta iya amsawa. Bana so ciwonki ya kara
tashi kiyi hakuri ki dena kuka Baba zai masa
magana. Ni kaina bansan ma abinda nayi masa
bane but dont nasan Allah zai mana magani.
Makaranta dai tasha ruwa haka tayi ta jiran
Malam sai can dare ya dawo. Jugum jugum ta
gansu ita da Umma yace me ya faru Munnira?
Dole kace me ya faru mana kana neman kashe
min 'ya da fada take maganar don kokarinta yaji
haushi ya fadi dalili kowa ya sani. Bai kula ta
ba ya dubi khairi yau ko sannu da zuwa bata yi
masa ba yace Ummulkhairi...ta dago fuskarta
idanunta sunyi ja kamar gauta kiyi hakuri ki cire
Ahmad a ranki. Bai ma jira ta amsa ba ya shige
daki. A dakin umma ta kwana tana ta aikin
kuka.
***************
Ahmad bai taba shiga tashin hankali ba kamar
yanzu da yake ganin zai rasa khairi da gaske.
Baba da su Yakumbo sunyi iya yinsu amma ya
dage kan bazaayi auren ba. Gashi uwa uba yaki
fadin dalilinsa.
Zuwa yanzu duk 'yan gidan sun san abinda ke
faruwa Mufida tayi murna sosai jin malam yaki
yarda. Wato da don munafurci babu wanda ya
fada mata zancen auren, maganinsu kenan.
Kawu Hadi wanda shi kadai ya rage a kannen
babansu Malam shima har ya gaji da magana.
Malam yace sai dai suyi hakuri shima ba a son
ransa bane.
Yana kwance a daki yau kwanansa biyu baije
aiki ba don bashi da nutsuwa da kwanciyar
hankali. Mufida bata gabansa tun ranar da yaga
kulle kullenta. Waya ya dauko ya kira ta
Khairina...kana jin muryarsa abin tausayi.
Naam Uncle Ahmad sai kawai ta fashe da kuka.
Tamkar tana watsa masa ruwan zafi haka yake
jin kukanta. Ki yarda dani Khairi bazan taba bari
a raba mu ba indai ba auren namu zai zama
hatsari bane a rayuwarki.
Bata ce komai ba sai shesshekar kuka...kiyi min
magana mana. Uncle kada ka bari a rabamu
tana fada muryarta na rawa.
I won't, I promise
Bayan ya ajiye wayar text yayi mata
( I Love you Ummulkhairi ina fata you feel the
same way about me.)
Text dinsa dai kuka ya kara mata tana cikin yi
kirjinta ya fara bugawa numfashi yana sama
sama. A haka Inno tazo ta ganta ta yi saurin
kiran Umma. Kuka ta saka tana wargaza
magungunan khairin ta rasa wanda zata bata. A
haka Malam ya shigo hankali a tashe zai daga
khairi ,Umma ta daga masa hannu tana kuka
dakata Abdullahi kada ka taba min 'ya. Ba so
kake ta mutu ba kowa ya huta ai gara ta mutun.
Amma wallahi kaji na rantse maka idan na rasa
'yata na gama aurenka. Ana maka kallon malami
a waje amma ni yanzu nasan cewa ina tare da
mutum mara tsoron Allah. Shi kanshi idan ka
kalle shi sai ka tausayawa yanayin da yake ciki.
Munnira kada kiyi sabo saboda fushi. To Dr
Abdullahi Saraki sai ka fada min MEYE
DALILINKA na hana auren khairi da Ahmad ta
fada tana rike kugu kana ganinta kasan bata
cikin hayyacinta sosai.
Batul Mamman💖
💕MEYE DALILINKA💞 20
Shima magungunan ya rinka dubawa da ya rasa
yadda zai yi waya ya ciro da aljihunsa ya kira
uncle Ahmad. Cikin bacci ya dauka jin muryar
malam yasa ya ce me ya faru don wayar malam
a daren nan yasan ba lafiya. Khairi ce ciwonta
ya rashi ya bashi amsa a gigice.
Doguwar riga ya dora akan kayan baccinsa gaba
a baya ya suri keys din mota ya fita. A kan gado
ya ganta kamar ta suma. Allurai yi mata har uku
sannan yasa mata drip. Umma kallon malam
take kirikiri yace bai yadda da aure ba amma da
yaga babu yadda zaiyi ai ya kira shi ya ceci ran
'yar sa.
A falon gidan ya kwana da asuba Malam yazo
ya tashe shi. Tare suka je masallaci yana son
tambayar Malam amma yayi masa kwarjini.
malam dai bai ce komai ba har suka koma gida.
Ya sake shiga tana kan abin sallah. Fita yayi
bayan ta idar ta zo falo ta same shi. Ya
tambayeta ya take ji tace masa da sauki daga
nan ta koma daki domin malam yana zaune
yana kallon su. Bayan yaje gida yayi wanka
gidansu ya tafi ya yi saa Baba bai fita ba. Ya
sanar dashi abinda ya sami khairi Baba yace
Ahmad kayi hakuri bana son tashin hankali da
Abdullahi amma kasa a ranka zanyi maganin
abin da yardar Allah.
Gwaggo baki ga halin da khairi take ciki ba
kamar baya tausayinta. Ni ba don ina tsoron
Baba Malam ba wallahi gida zan taho. Gwaggo
mahaifiyar Munnira tace kul na sake jin zancen
tahowa kiyi hakuri babanki yana hanyar kanon
ma. Umma ta share hawaye me zaiyi a kano
kuma? Akan maganar auren ne dai, Allah Yayi
miki albarka. Tana ajiye wayar itama hawayen
take yi tana tausayin 'yarta. Lallai yau kila asiri
zai tuno me zasu fadawa Munnira bayan sun
san komai.
Ana idar da sallar Juma'a Alh Aliyu ya matsa
kusa da liman ya sanar dashi akwai daurin aure
suyi hakuri abin yazo a haka. Liman yayi
sanarwa ta loudspeaker saboda haka wasu daga
cikin mutanen suka tsaya. Ya dubi Baba Hashim
ya ajiye masa kudi a kan cinyarsa yace kaine
waliyin Ahmad yace to yana cike da mamaki
wato shirun da Alh Aliyu yayi ba na wasa bane
ashe . A take a nan yayiwa khairi walicci aka
daura aurenta da Ahmad akan sadaki dubu
hamsin mutane suka shaida.
Text ya turawa kaninsa yana sanar dashi daurin
auren kuma yazo yana jiransa a gida. Shima
Ahmad text din ya gani murna da farinciki suka
rufe shi.
Gumi ne ya rinka karyo wa malam yana ta salati
Umma ta dauki wayar tana karanta text din ta
rangada guda tace Allah Ya saka wa Yaya da
alkhairi. Dakin khairi ta shiga ta same tana
karatu. Khairi ki gode Allah yanzu Baba ya
daura muku aure da Ahmad. Tana kai karshen
aya ta rungume umma tana kuka. Suna tsaye a
haka sai jin muryar Malam suka yi yace su fito
zasu tafi gidan Baba.
Umma ko a jikinta domin dai bukata ta biya.
Yana parking din mota a kofar gidan sai umma
ta lura da kaninta Umar shima yana gyara
parking yace mata tare suke da Baba Malam
yanzu ya shiga ciki. Khairi har kasa ta durkusa
tana gaishe shi tace kawu umar ina su ibty da
zainab. Suna nan kalau ya bata amsa kafin
itama ta bi bayan iyayenta.
Baba Malam ne zaune kan kujera sai iyalan
gidan Baba dana malam tare da Kawu Hadi. A
yara kuwa daga Uncle Ahmad sai khairi. Bayan
sun gaggaisa Baba ya nuna mamakinsa na ganin
babban Malamin a gidansa wato Shiek Hamza
Samaru daya daga cikin malaman da kasa ke ji
da su.
Baba Malam yace naji dadi sosai Aliyu yadda
kake kokarin habbaka zumunci tsakaninka da
'yan uwanka. Hakika abinda kayi yau na kokarin
ceton rayuwar 'yar kaninka aikin lada ne babba
sai dai akwai kuskure a yin hakan. Umma wadda
dama ganin baban nata a gidan itama yasa
tasha jinin jikinta ta fara tsorata. Ya mayar da
kallonsa ga Malam, yace Abdallah ranar wanka
ba'a boyon cibi.
Malam gumi yake ga jikinsa har tsuma yake yau
sirrin boye zai fito fili. Ji yayi bakinsa gaba daya
babu yawu idanunsa sunyi ja saboda firgici.
Yakumbo tace yi magana mana ka barmu da
zulumi.
Hmmm yayi ajiyar zuciya kafin yace kuyi hakuri
amma Ahmad...............................
.........shirunsa ya kara tada musu hankali.
Ahmad.....dana ne ya karasa da kuka.
Batul Mamman💖
💕 MEYE DALILINKA💞 21
INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN kowa
abinda yake fada kenan. Lokaci guda tsanin
rudani ya shiga tsakanin 'yan uwan. Haj Karima
ta kadu sosai da kyar ta iya mikewa tana nuna
Malam kamar zata yi magana sai dai kafin ta
iya takawa ta fadi kasa a sume. Nan da nan
hankali ya koma gareta. Umma tace Malam
wallahi na gama auren nan. Ka sake ni gidanmu
zan tafi. Tana magana kamar mai sumbatu sai
da Baba Malam ya daka mata tsawa. Ta koma
ta zauna tana kuka. A wannan lokacin kuwa
Ahmad ji yayi inama ya mutu ya huta ga tashin
hankali ga hajiyansa a kwance. Khairi kuwa
kirjinta ta dafe idanunta babu ko digon
hawaye....ashe kuka ma rahma ne. Baba kuwa
kallon kowa yake dai dai zuciyarsa na sake
sake.
Baba Malam da Kawunsu Baba da kyar suka
shawo kan jamaar wurin aka yi shiru. Haj karima
tana tashi ta dubi Malam tace Abdullahi ba sai
kayi min sharri ba don baka son auren nan...ta
juya ga Ahmad idan ka haifu cikin uwa da uba
ka saki yarinyar nan a yau, a yanzu saki uku. Shi
kam jikinsa babu kwari ko kadan bashi da
sauran katabus bai iya cewa komai ba. Dattijan
suka ce kowa ya saurara Baba Malam yayi
gyaran murya. Nasan kowa a nan ya shiga cikin
rudani da tashin hankali amma yana da kyau ku
saurari uzurin Abdallah kafin a yanke hukunci.
Malam dai kuka yake yau din da yayi ta gudu for
the past 36years tazo ta cimmasa.
Yaya idan ka tuna shekarunku hudu da Hajiya
baku haihu ba. A lokacin dukkanmu gida daya
muke tare da ku. Muna karatu ni da Hashim
kana kasuwancinka.
(Tana jin haka tasan karshenta wannan
maganar dalilin makircin da ta kulla ne shekarun
baya)
Malam ya cigaba da bayani to wata rana na
dawo gida ina cin abinci sai ta shigo falon da
zobo ta zuba min itama ta sha. Daga nan na
farka na ganni a dakinta kan gadonta. Tana
daya gefen a kwance....kuka yaci karfinsa. Sai
da ya numfasa ya cigaba. Har na fita bata sani
ba. Kuma a ranar ne hashim ya fado daga bene.
Bayan wata uku ka sanar dani tana da ciki
wannan dalilin ne yasa na koma zaria har na
hadu da Baba Malam. Yasan komai don ban
boye masa ba.
Bayansa ya kwaye musu shatin bulala ne ya dai
yi fading baa gani sosai. Zuwa nayi aka yi min
bulala dari a matsayin kaffara. Wannan shine
dalilin da yasa nake da yakinin Ahmad dana ne.
Wallahi Abdullahi kayi karya haka take fada cikin
gunjin kuka. Baba haki ya fara Malam yayi
yunkurin kamashi ya mike ya doke masa hannu.
Uncle Ahmad ne ya fitar dashi da kyar ya sa shi
a mota domin falon tamkar kurkuku kowa yake
jinsa. Umma ta kama hannun Khairi fuuuu ta
tashi suka fita. Ita dai khairi binta kawai take yi
idanunta a bude amma bata ganin inda take
takawa. Sai da suka fito Umma ta suma kuka
ina suka nufa? Ita dai bazata koma gidan Malam
ba. Ace wai Ahmad wan khairi ne uba daya???
Shiru taji daga bayanta tana juyawa don taji
shiru khairi ba magana sai taga jini ke fita daga
bakinta. Ihu ta kwala don ta shiga tashin
hankali. Da gudu Malam ya fito ya ciccibe ta ya
dora a kan kafadarsa yasa ta a mota sai asibiti.
Batul Mamman💖
💕MEYE DALILINKA💞 22
Kwana biyar kenan ana faman abu daya, kokarin
ceto rayuwar Baba wanda jininsa yayi mugun
hawa da Khairi mai fama da ciwon zuciya.
Kausar kullum tana asibitin amma khairi bata
gaya mata ainihin abinda ke faruwa ba domin
wannan sirrin gidansu ne. Tahir ma yazo dubiya
rabonsa da duk su biyun tun ranar da ya sanar
da Uncle Ahmad zancen khairi na da wanda take
so.
Kausar ina kyautata zaton akwai matsala a tare
da friend dinki. Ina fata ba hanata auren aka yi
ba. Ya gyara tsayuwa kuma naga kusan
dukkansu kowa yana tattare da damuwa. Kausar
tace to Captain nima haka na gani mu taya su
addua dai. Haka ne ya bata amsa. Sai kuma
yace kina ganin ya dace na tafi na barki kina
jiran abin hawa? Ah haba kada ka damu ai basa
wuya. No ya fada yana girgiza kai. Kizo na ajiye
ki. Kememe taki yarda karshe dai kudin mota
ya bata yace idan bata karba ba zai hana kowa
daukarta. Yana wurin ta sami taxi ya biya kudin
tare da kashedin kada a dauki kowa.
Khairi ta fara samun sauki sai dai har yanzu
jinin Alh Aliyu yaki sauka. Baya kaunar Malam
ya shiga dakinsa da sunan dubiya. Ita kanta
khairin girman babanta ya sauka a idonta. Abin
duniya yayi masa yawa gashi ko sau daya
Umma taki sauraron sa. A corridor din asibitin
ya hadu da hajiya Karima ta dawo daga raka
'yan uwanta. Niyarsa ya wuce don bashi da idon
kallonta tace Abdullahi....yau ba malam
din...tsayawa yayi cike da fargaba. Idanunta fal
hawaye kayi min tabo wanda baya taba bacewa
ka sheganta min da daya da Allah Ya bani.. ka
cutar min da rayuwa. Ajiyar zuciya yayi ki sani
da mutumci na bazan so na jawowa kaina
mummunar matsala irin wannan ba. Sai dai idan
na bari akayi auren yaran azabar da zan gamu
da ita mai radadi ce. Duk abinda nayi na yi shi
ne domin mu rabauta a wurin Allah. Ta sa
mayafi ta goge hawayenta ba komai Allah zai
mana sakayya jira nake Alhaji ya sami sauki ayi
gwajin jini amma duk da haka ka bata min
suna. Har ta shige yana jin sautin
kukanta...shima hawaye ya share da hannunsa.
Duk abinda yayi yasan saboda tsoron Allah ne.
(Tana labe tana sauraronsu ita ma ta rasa
farinciki tunda aka fara maganar nan. Wai da
wane bakin zata tona gaskiyar da ta binne
tsahon shekarun nan?)
Yau aka sallami Khairi suna shirin fita ta kalli
Ummanta. Umma ina muka nufa? Zaria zamu je
idan Baba Malam ya hana mu zama ina da
gidan haya a ja'in sai na sallame su mu koma.
Yakumbo ce ta shigo bayan sun gaisa tace
Mannira ku shigo dakin Alhaji mana ina son
ganin ku.
A raku be suke a dakin wannan ya kalli wannan.
Tun ranar da abin ya faru sai yau ta ganshi sati
biyu kenan. Uncle Ahmad ya rame sosai.
Hajiyansa tana kan tabarma ita da Momi sai
Malam dake tsaye bayan wheelchair din Baba
hashim. Baba dake kan gado juya musu baya
yayi.
Yakumbo tace to Alhamdulillah tunda duk mun
taru a nan. Lokaci yayi da zan fadi sirron boye.
Baba yayi saurin.juyuwa a tsorace yace
Yakumbo kada dai kice ni ko daya daga cikin
kannena ma ba mu da uba.
Dariyar da tayi mai cike da nuna takaici ce da
damuwa. Aliyu, Abdallah, Hashim kowanne tana
kiran sunansa tana kallonsa. Ku yafe min abinda
nayi muku amma hakika Ahmadu ba danka bane
Abdallah. Aliyu ne ubansa. Wata irin ajiyar
zuciya Uncle Ahmad ya saki. Haj Karima kuwa
cewa tayi uhmm kunji ko? Ai na fada muku
wallahi dannan dan aure ne.
'Yar tsohuwa tasa kuka ta fayyace musu
gaskiyar abinda ya faru shekaru 36 da suka
wuce.
Nima nace ku biyo ni don jin wannan labari
Taku Batul Mamman
💕 MEYE DALILINKA💞 23
AINIHIN ABINDA YA FARU SHEKARU 36 DA
SUKA WUCE
Mahaifinsu sunan sa Ahmadu amma jamaa sunfi
kiransa da Saraki. Sana'ar dinki yake yi wadda
ya koya wa 'ya'yansa Aliyu da Abdallah domin
lokacin Hashim yana karami. Bayan rasuwar
mahaifiyarsu ne ya auri Yakumbo Larai. Ta rike
su da gaskiya kuma ita Allah bai bata haihuwa
ba. Aliyu yana aji biyar a sakandire baban nasu
ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya. Ko da aka
raba gado sai ya kasance Yakumbo bata da rabo
a cikin gidan, gasu maza sun fara tasawa basa
son a rabasu tsakanin gidajen yan uwan babarsu
ko babansu. Dalilin haka suka roki Yakumbo
kuma akayi sa'a ta amince ta cigaba da zama
dasu. Da dadi ba dadi haka suka cigaba da
zama, itama tana dan sanaar sayar da kayan
kamshi kamar su citta da kaninfari. Aliyu da
Abdallah kuwa sun cigaba da dinki.
Lokacin da Aliyu zai shiga aji biyu a jamia
Abdallah yake bukatar kudin jarabawar gaba da
sakandire. Kudin hannunsu kuma mutum daya
zai isa har ma da ciko.
Aliyu na zaune gaban Yakumbo yake fada mata
yaje wurin Kawu Hadi amma kudin basu samu
ba. Nima nasa akuya ta a kasuwa Ali har yau
ba'a siya ba ta fada tana share hawaye. Ni
shawara gareni idan zaka yarda. Ina jinki ya
bata amsa. Da kanka kake cewa Abdullahi akwai
kwakwalwa ga hadda a kan nan nasa. Mu shaida
ne kullum na daya yake yi. Ka daure a biya
masa idan yaso ina sayar da akuyar da dan
kudin dinkinku sai ka biya. Mutmushi yayi haba
Yakumbo bazan taba musa miki ba. Allah Yasa
kada ya bamu kunya ni zan hakura in jira.
Abdallah yayi jarabawa kuma cikin ikon Allah
sakamakonsa yayi kyau sosai zai sami gurbin
karatu a jamiar bayero ta kano. Zuwa wannan
lokacin Aliyu yayi nisa a kasuwanci ya ma bar
zancen makaranta. Kokarinsa duk bai wuce
kanen nasa su sami ilimi ba. Bayan shekara
daya ya auri Karima 'yar makotansu. Kuma daga
lokacin ne suka fara samun sabani da Yakumbo.
Ita a ganinta ta sha wahalarsu dole tafi Karima
jindadi a gidan duk da cewa babu abinda aka
rage ta dashi.
Shekaru hudu kenan babu haihuwa Yakumbo
kullum gori da bakar magana. Sai dai Aliyu yayi
ta bata hakuri a daki domin yace bazai iya sa in
sa da Yakumbo ba. A dalilinsu taki kara aure
duk da bata rasa manema ba.
Abdallah ya samu nasarar gama karatunsa na
jamia inda ya zakara a wannan shekarar na
daliban da suka karanci Mass Communication.
Karatun ya dace dashi saboda akwai shi da baki
ga iya tsara zance. Yana jiran a kirasu bautar
kasa ne tsautsayin ya faru.
Yakumbo ta jima tana bawa Aliyu shawarar ya
auri Abu 'yar kaninta saboda zuwa lokacin arziki
ya karu gareshi har mota ya siya ya kuma
sayawa Abdalla vespa. Kullum korafinta ai
karima bata haihuwa shi kuwa Abdallah idan yaji
haka ranar zai wuni nasiha ga 'yar tsohuwa.
Hakan yasa ta fara tsanarsa saboda yana shigar
wa Karima fadan da ba nasa ba.
Basiru dan autansu ta samu suka yi shawarar
yadda za'a kori Karima da Abdallah gaba daya
daga gidan. Abdallah ya dawo daga shago
saboda har yanzu basu tafi bautar kasa ba yaje
ya dauko abincinsa ya zauna a falo yana ci.
Ah ah malam Audu yunwa ta koro ka ne? Ta
tambaya tan a kokarin zaunawa. Ke dai bari
babbar yaya meye a jug din ne? Zobo ne ta
bashi amsa. Shine ko ki dan sammin. Zuba
masa tayi yana sha yace sukari bai ji ba. To
shazumamu sarkin zaki ni kadan nasa saboda
yayanka da Hashim basa son zaki da yawa. Ni
ko oho kenan.
Tana bayan kofa tana saurarensu.
Jim kadan Karima ta fara gyangyandi, Abdallah
yace shima cikin muryar me kama da ta maye ki
shiga daki mana. Da kyar ta mike ta tafi. Ba'a
jima ba shima ya fara baccin.
Dariya tayi sannan ta fita ta kirawo kanin nata.
Sun sha wahala kafin su ka iya kaishi dakin
suka kwantar dashi a kan gadon. Yaya bari kiga
na cire masa riga. Itama ki cire mata dankwali.
Haka suka aiwatar kafin su fita tace ai in Allah
Ya yarda sai ya auri Abu. Haka kawai ya ajiye
juya a gida ga kudi ya fara samuwa wata
sakarai tana ci. Tana gama magana ta juya
kawai ta ga Hashim wanda yake SS3 a lokacin
yana masu wani irin kallo.
Batul Mamman💖
💕 MEYE DALILINKA💞 24
Gaishe su yayi ya wuce dakinsa domin ya cire
uniform sai dai yana ta mamakin me suke yi ita
da kaninta a sama bayan nasu bangaren a kasa
ne.
Wani irin ciwon kai ne ya kama shi kamar kansa
zai fashe ya farka a razane. Kansa ne ya yuye
domin bai ma gane a ina yake ba. A hankali ya
fara tuna me yayi karshe kafin ya ganshi anan.
Ganin jikinsa babu riga ga Karima a gefe ba
karamin razana shi yayi ba. Me suka yi? Garin
yaya ya biyota daki? Innalillahi wa inna ilaihi
rajiun. Yana ganin ta fara motsi yayi saurin fita
daga dakin. Kasa ya sauka ya shiga wanka don
kansa yayi clearing. Wani irin yanayi ya tsinci
kansa saboda bai san me ya faru ba a dakin.
Haka ya zauna har laasar ga matsanancin ciwon
kai.
A tsakar gida Yakumbo ta ganshi yana alwala.
Saboda tsabar gigita da tayi ruwan da ke
bakinta har kware ta yayi. Garin yaya ya farka
da wuri bayan maganin da ta zuba a zobon
wanda zai sa su bacci har na awa biyar ne.
Gashi Aliyu ya kusa dawowa. Ita kuma bata isa
tace ta gansu ba. Dama niyarta Aliyu ya dawo
daga kasuwa da laasar idanunsa su gane masa.
Fakar ido tayi ta koma saman tana neman inda
ta jefar da ledar maganin wadda ta yar cikin
sauri don kitchen din karima a sama yake. Motsi
taji a bayanta tana juyuwa ta sake ganin hashim
ai kawai sai ta kwalla kara wai ga gizogizo nan
don tasan akansa Hashim ya taba suma saboda
yana tsoronsa a kokarinsa na guduwa yayi
missing step ya fado daga benen.
Ita tayi haka ne don ya dena binta shi kuma
yadda yaga tana sanda ne yasa ya bi bayanta. A
sume ta sauko ta sameshi ta fara ihu.
Gidan nasu ya hadu da tashin hankali a lokacin
da likitoci suka tabbatar musu da cewa bazai iya
kara motsa wata gaba a jikinsa ba banda kansa.
Yakumbo tayi nadama mara misaltuwa. Garin
son zuciya ta cutar da dan maraya. Wannan
tashin hankalin yasa Abdallah mantawa da
abinda ya faru sai dai bayan wata uku Aliyu cike
da farinciki ya sanar dashi karima na da ciki.
Wannan dalilin yasa da posting dinsu ya fito ya
tafi kaduna sai da yayi shekara guda bai dawo
ba. Shi niyarsa ma ya tafi kenan don bazai iya
cigaba da ganin karima da abinda zata haifa ba.
A garin kaduna an tura shi wata makaranta a
zaria bautar kasa wadda take kusa da
masallacin da Baba Malam mahaifin Munnira
yake koyarwa. Kullum bayan magariba ake
karatun. Wata rana ana karanta suratul Nur yaji
irin hukuncin da Allah Ya tanadar wa mazinata.
Ranar yayi kuka sosai bayan sunyi isha ya tari
Malam a hanya ya sanar dashi yana da matsalar
da zaiso su tattauna a kai.
Washegari yaje gidan malam din kamar yadda
sukayi alkawari ya sanar dashi halin da yake
ciki. Malam yayi masa nasiha yace ai ba da
gangan kayi ba kaje ka yawaita istigfari. Yace
to Malam maganar haddi fa? Idan baayi min ba
bazan taba samun kwanciyar hankali ba ko da
ita ce ajalina. Ba yadda Baba Malam baiyi ba ya
dage sai an yi. Anyi masa bulala dari tunda da
bakinsa yace ya aikata.
Baba Malam ya tausaya masa sosai ya bashi
daki a gidansa ya sanar da matarsa komai
domin mace ce ta kwarai me rikon sirri. Da
kansa yayi jinyar Abdallag har ya warke kuma a
nan ne ya nuna shaawarsa ta son juya akalar
kartunsa ga addini. Yayi karatu sosai tare da
Baba Malam har aka gama bautar kasa ya kara
lokaci. Da malam yaga bashi da niyyar komawa
gida yayi masa nasiha sosai. A dole ya koma
'yan uwansa bayan doguwar mita suka hakura.
Bayan wasu shekaru ne lokacin da Munnira ta
gama secondary Baba Malam ya bashi aurenta
saboda ya yaba da hankalinsa kuma yaga bashi
da niyyar aure sai karatu.
A lokacin ne kuma Aliyu da kansa ya nemi auren
Abu wato haj zainab ko muce Momi matarsa ta
biyu. Yakumbo ta dada tsorata da lamarin Allah.
Wato zafin nema baya kawo samu. Gashi da
kansa ya nemi auren. Ta kira Basiru ta roke shi
da su binne maganar abinda ya faru zata cigaba
da kulawa da hashim har mutuwarta. Kuma ba
zata taba tona wannan abin ba tunda basu sani
ba. Sannan ta gargade shi da kada ya bari
baban Abu ya sani domin shi mafadaci ne akan
abinda yake gaskiya ita ma yayarsa tsoronsa
take ji.
Batul Mamman 💖
💕 MEYE DALILIKA💞 25
Ko da Yakumbo ta gama bada nata labarin
shima Malam ya fadi abinda ya faru a zaria.
Dakin sai sautin kuka da salati ake ji. Har kasa
Yakumbo ta tsuguna neman gafara. Baba ya
sauko daga kan gadonsa yace ta tashi. Ai ni
Yakumbo tunda dai ta tabbata Ahmad dana ne
wallahi na yafe miki sai dai wadanda kika yiwa
laifi suna da yawa. Komawa tayi gaban Baba
Hashim wanda yake ta zubar da hawaye ka yafe
min dana, ka yafe min. Ita ma kukan take yace
Allah Ya yafe mana baki daya....ya tuna yadda
ko sau daya bata taba nuna kyama ko gazawa
akansa ba duk da tsufanta.
Momi ta kalli Yakumbo yanzu duk a kaina kika
kusa tarwatsa gidan nan? Nata kukan yafi na
kowa bata taba tsammanin wannan badakalar ta
shafe ta ba. Ita dai Yakumbo kuka take yi duk
wanda ke wurin dole ya tausayawa tsohuwar.
Kafin su fita daga dakin kowa ya yafewa dan
uwansa. Malam ya kira mahaifin Umma ya
sanar dashi komai.....ikon Allah yafi karfin wasa
Abdallah, hakika Allah Yaso cire maka wannan
tunanin na ka aikata zina shiyasa Ya hada
zukatan yaran nan don gaskiya tayi halinta.
Allah Ya kara mana imani.
Khairi da Ummanta gida suka wuce tare da
Malam. Umma kamar ta ari baki wurin bashi
hakuri ranar. Sai da suka kebe yace Munnira
ban taba jin haushinki ba duk abinda kika yi
akan gaskiya ne.
Bayan kwana biyu Baba ya matsa a sallame shi
daga asibiti saboda yana son ayi ayi bikin
Ahmad da khairinsa.
Bayan ya kai babansa gida, gidansu khairi ya
taho. Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka
ta shigo falon. Shiru shiru babu mai niyar
magana rabon da su hadu tun ranar da aka fasa
kwai a gidan Baba. Ita carpet ma take ta kallo
yau. Bata ankara ba taji shi a kusa da ita. Tana
dago fuska suka hada ido...gaba dayansu sunji
wani irin yanayi a tare dasu. Tayi kokarin
matsawa yasa hannu ya riko ta gaba daya ji tayi
kamar bata taba shiga yanayin farinciki kamar
wannan ba. Bata ki su zauna a haka ba sai
kuma ta tuna kada ta bada mata...uncle ka sake
ni. Daya hannun yasa yana shafa fuskarta....
aure ni da ke mutu ka raba kinji ko. Ganin bai
fahimce ta ba tace ba haka nake nufi ba. Daga
gira yayi yana kallonta me kike nufi? In bari ki
zauna kina kallon kasa kamar baki da abin kallo.
Kafin ta bashi amsa wanda ita duk a rike ce
take saboda yadda yake zagaye fuskarta da dan
yatsan sa yace kin rame sosai khairi na. Bana
son motsatstsiyar mace. Lallai ma nice
motsatstsiyar? To ni kuma bana son
kajamemmen miji. Dukkansu dariya suka yi.
Sannan ya hada goshinsa da nata a hankali yace
mata I love you Ummulkhair... khairin Uncle
Ahmad. Dadi ne ya ratsa zuciyarta. Tayi saurin
tashi ta gudu sai wayarsa ta fara ringing. Yana
dubawa sunan Mufida ya gani.
Batul Mamman💖
💕MEYE DALILINKA💞 26
Yana dauka ta fara masifa. Na kira Umaima
tace tun dazu ka mayar da Baba gida...ina ka
tsaya? Ta tambayeshi cikin bacin rai. Bata jira
ya bata amsa ba tace ina jiranka maza ka dawo
gida. To kawai ya ce ya ajiye wayar domin shi
mamaki yake yadda ta sami kwarin gwiwar ya
masa magana a haka. Can ya tuna maiko-
maikon daya gani a goshinta da kirjinta a daren
jiya. Dariya ce ta kubuce masa daya gane kayan
mallaka da juya miji akayi amfani dasu shine
take gwadawa yau,Allah Yasa khairi ta fice ma
yayi mai isarsa. Shegiya to ta Allah ba taki ba
ina karanta Ayatul kursiyy har wani surkullen
banza zai kamani.
Daga kofar falo Sadiq ya rugo da gudu ya
rungume shi. Yana shirin daukarsa ya kula gaba
daya hannuwansa da bakinsa harma da gaban
rigarsa duk sun baci da miya. Da fada ya shiga
gida Mufida tana zaune tana kallo ta galla masa
harara. Dama jira nake ka dawo ka wanke
masa....ga wurin da yaci abincin ma duk ya bata
min ka goge don Atine mai aiki bata nan.
Kallonta yayi shekeke sai kuma ya tuna yanzu
fa tana tunanin aikin bokanta yayi. Daukan yaron
yayi yayi masa wanka ma gaba daya sannan
yazo ya gyara wurin. Ranar mufida sai faraa da
farinciki. Uncle Ahmad kuma sai dariyar
mugunta idan ya faki idonta. Yaro bai san wuta
ba sai ya taka...ranar da zan damke ki a
hannuna zaki wahala ya fada a ransa.
Sati biyu aka sa bikin Khairi sai dai sam Baba
yaki yarda yace shi akwai shirye shiryen da
zaiyi. Malam ya dube shi haba Yaya wane shiri
kuma ya rage ai kawai a kaita dakinta. To nuna
min iko zaka yi kuma Baba ya tambaya. Allah
Ya baka hakuri ya bada amsa. Yana gyara karin
hularsa yace ai nasan zaka ce baka son bidia
sai dai kada ka manta bikin aure yana da
bambanci da taron mutuwa kuma dole mu
gayyaci mutane su taya mu murna. After all we
have been through Abdallah dole muyi abinda
ran kowa zaiyi dadi. Baba Hashim yace duk
abinda ya faru da khairi ai baza mu kaita daki
ba kamar ladan noma ko yakumbo. Haka ne ta
bashi amsa a hankali. Har yau ta kasa sakin jiki
da su kamar da.
Mahaifiyar Kausar ita ce ta dauki nauyim gyaran
amarya ciki da waje domin mutuniyar nijar ce
kuma sana'arta kenan. Hatta turaren wuta na
gida duk ita ce take yi. Kwanaki uku kawai da
fara gyaran jiki Khairi ta soma canjawa ga wani
kamshi da take yi. Abincin da take ci ma ita
take bata don a cewarta khairi ta rame saboda
ciwo ita kuwa bata son ganin mace a tsamure
kamar kudin guzuri. Tana zaune kan kujera
umman kausar ta sa mata kaskon turaren jiki ta
lullube ta da katon bargo wayar kausar ta fara
ringing sai ta katse. Haka take ta yi da an kira
sai tayi rejecting khairi kuwa ta sa ta a gaba da
kyar ta fada mata wai Tahir ne yake yawan
kiranta a waya. Khairi tayi murmushi to meyasa
bakya son dauka ko don ina wurin ne? Lah
wallahi ko baki nan bana dauka. Khairi tace to
kinsan wulakanci ba halin mu bane. Kika sani
ma ko ya fada ne...eyye eyye Kausar ta captain
tahir. Nan suka fara aikinsu na cacar baki kamar
kananan yara.
Umma ta zage da shirin aurar da tilon yarta su
inno ma baa barsu a baya ba. Mufida dai ta
cigaba da sa maigida aiki yana biye mata. Ko
sau daya taba ce ya fasa auren ba don tasan ko
a wurin danginsa bata isa ba. A cewarta zata yi
maganin ta idan ta iso.
Batul Mamman💖
💕MEYE DALILINKA💞 27
Anyi biki na gani na fada sannan kuma ayi abin
a tsaftace kamar yadda Malam yaso. Babu
kwadon maza da mata ayi ta rawar rashin kunya
ko kaga budurwa ta tafe kamar sanda wani
lokacin harda masu aure a wurin biki babu
mayafi sai gwaggwaro. Ayi dinkin nan riga ta
matse duk kayan kirjin su rinka neman fitowa ta
sama. Wani katon banza ya kalle ki a bati
siddan. Wallahi mu kiyaye mata mu saya wa
kawunanmu mutumci.
Ranar asabar za'a kai amarya tasa wani farin
material me adon lemon green flowers.
Takalminta da 'yar karamar jaka harda katon
mayafin da ta lullube jikinta duk lemon green ne.
Kamshi take me dadi Anti Rumana da Anti
Sadiya kannen ummanta su suka shirya ta.
Wata matar wan umman kuwa da suke kira
Umma Zainab mouth freshner ta bata kafin ta
fito daga daki tace ki fesa yaji kamshi mu ma
iyayenki duk a haka muke gyara tsufanmu.
Kunya ce ta kama Khairi. Ranar sun sha kuka
ita da Ummanta dakyar aka raba su.
Gidan Baba aka kaita yayi mata nasiha. Ana
shirin tafiya yace ai Malam ya sanar dashi a bar
mijinta yazo ya dauketa saboda haka kowa ta je
ganin daki daga baya. Momi dai sai mita don ta
gama shirin kai amarya tunda Umma da Hajiya
duk babu su. Ko da Uncle Ahmad ya iso da
abokinsa daya Baba har waje ya rako su jikin
wata sabuwar mota kirar honda silver colour mai
kyau. ya kama hannun Khairi ya sa mata makulli
a hanunta...cike da mamaki ta dago kanta yace
Ummulkhairi wannan kyautar ki ce fatana ku
zauna lafiya da dan uwanki. Sai ka daure ka
koya mata don ba taka bace yace da Uncle
Ahmad. Godiya suka yi masa yace maza maza
ku tafi dare na kara yi. Ahmad ka bar motarka a
nan gobe Hashim karami sai ya kawo maka ku
tafi a wannan.
Tana kuka baba ya bude kofa da kansa ya
zaunar da ita a ciki suka tafi. Kusan mintuna
biyar yana tuki sai sautin kukan khair ake ji. Can
sai taji shima kamar yana kukan ta dago kai
murya duk ta dakushe saboda kuka Uncle lafiya?
Shiru yayi ya cigaba da abinda yake yi.
Hankalinta ya fara tashi....uncle dina me ta
faru? Kwaikwayon muryarta yayi yace Khairina
ce bata so na. Bude idanunta tayi wadanda suka
yi ja tace wallahi ban fada ba, waye ya gaya
maka. Ganin ta rude yasa shi yin dariya ashe
kukan gulma kike yi ana turo ki kina wani
makalewa. Kin bashi amsa tayi wai ita tayi
fushi. Haka yayi ta tsokanarta har suka iso
gidan.
Ta kofar kitchen ya shiga da ita sannan ya wuce
da ita part dinta. Ita dai bata tambayeshi dalili
ba shi kuwa yayi haka ne saboda Mufida da
kawayenta da suke babban falon gidan wanda
take sada mutum da dukkan parts din gidan.
Suna zaman jiran kwakwaf.
Tun daga falo take jin kamshi lallai su kausar da
umaima sunyi aiki. Tana shirin zama ya kama
hannunta suka shiga daki. Wani guntun zazzabi
taji ya kama ta lokacin da ya rufe kofar...wai
itace a daki daya da Uncle dinta. A darare ta
zauna a bakin gado ta sake jan mayafi ta rufe
fuska. Hmm wai ko wacce amarya don gulma
sai tayi ta rufe rufe da an kwana biyu ta fi ruwa
iya gudu. Sarai ta fahimce shi amma sai tayi
shiru. Hula da rigarsa ya cire daga shi sai dogon
wando da singlet ya dawo gabanta ya zauna.
Tun dazu kamshinta ke tada masa hankali
amma yanzu da ya zauna gabanta abin karuwa
yayi....da kyar yace khairina yau ya akayi baki
da amsar bayarwa idan nayi magana? Ko har an
zo ranar da zan kashe bakin aku ne....tsit ya
sake ji sai ya mike ya shiga toilet. Alwala ya
dauro ya fito yace itama taje ta yi.
Bayan sunyi sallah ne ya dafa tsakiyar kant yayi
addua sannan yayi musu doguwar addua da
fatan zaman lafiya. Kazar amarci ta al'adar
bahaushe ya kawo mata da lemo, ruwa tare da
shawarma don yasan tana son ta. yau dai khairi
jiki ba kwari kadan ta ci bayan ya matsa mata.
Tashi yayi bayan sun gama yace zaije ya rufe
gida tana iya yin wanka kafin ya dawo.
Ko da ya shiga falon mufida ya tarar da
kawayenta biyu suna ta shewa. Tayi mamakin
ganinsa sai kuma tace ko an fasa kawota ne
munji shiru tun dazu...tafawa kawayen suka yi.
Shi bai ma taba ganinsu ba kila a gidan boka
suka hadu ya fada a zuci. Ku tashi ku tafi zan
rufe kofa dare yayi. Kai!!! Mufida tace daga
zaune. Kawayen nawa kake kora to babu mai
fita sai an kawo wannan ragowar asibitin. Tsawa
ya daka musu yace idan basu fita ba zai kira
maigadi yayi waje dasu. mikewa tayi cike da
mamaki . Yau ita yake wa haka kuma a gaban
wadanda ta gama cika baki a gabansu. Suna
fita ya rufe kofar gidansa sannan yace mata sai
da safe. Kafin tayi magana yayi gaba.
A bakin gadon ya sake ganinta ya wuce ya
shiga toilet yayi wanka. Ko da ya fito daga shi
sai tawul a kugunsa ya tarar ta juya baya tana
ninke mayafi. Niyyarta ta kwanta baccin karya
kafin ya fito. Tsayawa yayi yana kare mata kallo
ta baya. Riga da skirt din duk sun matse ta ga
gashinta da ya fito ta dankwalunta ya kwanta
wurin kafadunta. Ji tayi kawai yayi hugging
dinta ta baya...nan da nan jiki ya fara rawa. A
ya dawo da kansa daidai kunnenta yayi mata
rada a kunne. Zaki yi wankan ne ko nayi miki ya
fada bata ma iya bashi amsa ba domin ji tayi
yana mata kiss a wuyanta. Duk isakar dakin ita
zafi take ji. Juyu da ita yayi ya sake jawota
jikinsa ya sake yi....Khairina shiru ba amsa. To
ta ina ma zata yi magana bayan yau uncle din
nata ya sauya gaba daya. Shi kuwa kasa hakura
yayi ji yayi idan bai rike ta ba bazai iya shirin
bacci ba. Da kyar ya sake ta ya koma ya shafa
mai a jikinsa....a sace ta rinka kallonsa har ya
gama ya sa kayan bacci itama ya miko mata
wasu riga da wando. Bari na saka miki tunda ke
baki iya tattalin miji ba. Ba shafa min mai babu
saka min kaya . Sai yanzu tayi magana tace
kamar wani baby? Bata ma san maganar ta fito
ba. Karbar kayan hannunta yayi yace idan na
bazaki min kamar baby ba ni zan miki. Nan suka
fara kokawa ya dage shi zai cire mata kaya ya
sa mata kayan bacci.
Suna haka suka ji wani irin bugun kofa kamar
zaa ballata.
Batul Mamman💖
💕 MEYE DALILINKA💞 28
Bugun aka sake yi kamar maiyi na da tabin
hankali. Fita Uncle Ahmad yayi yaje ya bude
kofar ita kuwa khairi tana cikin daki. Yana
murda mukulli ta banko kofar dakin. Don
wulakanci sai ka dawo dakin nan ka zauna idan
ba'a kawo amaryar ba sai ka hakura. Yana
kallonta fuskar nan tasha hoda har ta so tayi
yawa ga uban kwalli ido rambajau. Lallai mufida
ta dage da son juya miji. Daga daki Khairi na
jiyo maganganun da take ita mamaki ne ya
kamata dama haka Anti mufida take. Lallai zata
koya mata hankali don ko bata auren Uncle
bazata jure matarsa taci mutumcinsa ba a
matsayinsa na yayanta.
Mufida ki koma dakinki khairi na ciki. Me ka ce?
To ta ina ta shigo wannan karon cikin ido take
kallonsa. Tare muke Mallam baya son taron kai
amarya ya bata amsa. Ganin ya kalli fuskarta da
idonta yasa tace kaga Abban Iman nifa ban
yarda ka kwana a dakin nan ba ka wuce kawai
mu tafi. Yana kokarin magana tace dakata bana
son jin komai kawai ka wuce. Khairi dai abin
duniya ne ya isheta lallai uncle ya bari ake
masa haka. Muje kawai yace da ita Khairi tayi
saurin fitowa daidai lokacin da yake jan hannun
mufida. Wani azababben kishi ne ya kama ta
suna fita ta kama kofar dakin ta kulle ta ciki. Ta
fada gado tana kuka.
Dakinsa ya wuce da ita don baya son tashin
yaransa a dakinta sannan baya son yin hayaniya
gaban khairinsa saboda bata da ishasshiyar
lafiya. suna shiga yace ke ni kike wa tsawa
saboda baki da kunya? Ko kina zaton ban san
abinda kike yi ba? Wallahi idan kika sake kokarin
maimaita abinda kika yi yanzu sai na fasa miki
jiki. Shashashar banza da iliminki da wayonki kin
mayar da kanki mahaukaciya. Ganin yadda ya
rufe ido yana mata fada yasa tayi shiru har ya
gama fadansa ya fita. Da sake wallahi
damanasan zaa rina kishi da yar malam . wato
itama tazo da shirinta.
Ko da ya koma sai ya shiga falon nata ya kulle
kofa ya kama kofar daki yaji a rufe. Murmushi
yayi wato tayi fushi tun yanzu kenan. Khairina
please ki bude kofar. Tana daga kan gado ta
share hawaye anki din....tohhh rashin kunya
kika fara kema? Shiru yaji tayi. Idan baki bude
ba zan koma wurin mufida. Sai ka dawo ta bashi
amsa amma a zuciyart tana tsoron kada ya tafin
da gaske. To ki taso ki kulle kofar falon sai da
safe. Tasowa tayi ta dauki mayafinta ta yafa
kan rigar baccin da ta saka ta dawo bakin kofar
da sabon kukanta. Yanzu maimakon ka bani
hakuri sai ka koma? Ashe fushin karya kike ma
tunda har kin karaya ya bata amsa. Sweet
dreams kinji khairina. Alamar an bude kofa an
rufe taji hasken fitilar da take hangowa ya bace.
Cike da takaici ta bude kofar daki da gaske ka
tafi take magana cikin muryar kuka tana shafa
bango don bata san inda makunnin filar yake ba.
Lallai ma sai na fadawa Umma gobe ta sake
fada. Ji ta yi an daga ta gaba daya ya shiga
dakin ya ajiye kan gado.
Kulle kofar dakin yayi tare da kashe fitila ya
dawo ya kwanta tare da jawota jikinsa. Me zaki
fadawa Umman? Uhmmm tace a hankali. Baki ji
me nace ba zo na maimaita miki. Kwacewa tayi
ta koma gefen gado ka koma wurin anti mufida.
Allah Ya baki hakuri khairina yace tare da sake
janyota jikinsa. A haka suka yi bacci. Kamshin
da take yana dada tada masa hankali sai dai
yasan yadda take rai a bace ta wani kankame
jiki gara ya barta ta huta.
Batul Mamman💖
💕 MEYE DALILIKA 💞29
Har yadawo daga masallaci tana bacci. Ji tayi
ana ja mata yatsun kafa ba shiri ta tashi tana
dariya don ita ana taba mata kafa ji take kamar
cakulkuli ne. To shashashar madina daga taba
kafa ya fada yana zama kan gadon. kinyi sallah
kuwa? Saurin mikewa tayi tace a'a meyasa baka
tashe ni ba ta fada tana tabe baki. Har dundu
nayi miki ashe haka kike da nauyin bacci. To
daga yau da ruwan sanyi zan rinka tashinki.
Wucewa tayi toilet tayi alwala bayan ta idar da
sallah ta jira ya kammala karatun Qur'an ta
gaishe shi. Kin amsawa yayi sai da ya ajiye
Qur'anin yace wa ya fada miki haka ake gaishe
da miji. To ya zan gaisheka Uncle? Lips dinsa ya
nuna mata tayi kamar bata gane ba. Bushewa
yayi ne kake son na miko maka mai. Kin manta
tsagewa yayi ki miko allura da zare. Biyota yayi
tayi saurin shiga toilet ta rufe.
Bayan ta fito daga wanka ta tarar baya dakin.
Riga da skirt ta saka na atampa dinkin yayi
mata kyau. Turare da humra kuwa sunyi aiki.
Tana fitowa falonta ya shigo shima yayi wankan
yana ta kamshi. Fito muyi breakfast yace tare
da komawa. Biyo bayanshi tayi. Tana shiga
babban falon taji an rikota ta baya. Anti Khairi
wai kin zama maman mu kema? Iman ce yar
shekara hudu me sunan hajiyar uncle. Na zama
ta amsa mata sannan ta daga ta sama yadda ta
saba yi mata. Sadiq ne ya taho yana cewa nima
nima. Shima daga shi tayi yana ta dariya. Uncle
Ahmad yana kan kujera yana musu dariya. Suna
haka Mufida ta fito da tray a hannunta. Khairi
tace Anti Mufida ina kwana....wace irin anti
kuma ana zaune kalau? Idan ni antinki ce ai
bazaki aure min miji ba. Shiru khairi tayi bata ba
ta amsa ba. Mufida ta dubi mijinta ina fata ba
zuwa kayi da ita ku ci abinci ba don wallahi
bazanyi mata girki ba Kura da shan duka gardi
da kwashe kudi. Uncle Ahmad yace Khairina
muje dakina akwai kayan tea.
Bayan sun gama ya kira mufida a waya. Sai da
ta fi 20minutes kafin ta zo ran Uncle duk ya
gama baci. Khairi tana ta kallon yanayin
fuskarsa ranta yana sosuwa. Ita tasan har ga
Allah bata zo da niyar fitina ba gidan amma tana
ganin zata saitawa Mufida zama indai ta nemi
batawa mijinta rai. Banko kofar tayi ta shigo ta
sami wuri ta zauna tana ta kumburi fuskar nan
tasha hoda. A ransa Uncle yace narambada
wannan boka ya cuceni. To dama magana zanyi
muku game da yadda nake son tafiyar da
gidana. Bana son rigima ko tashin hankali
saboda haka ku kiyaye....abu na biyu kowa nayi
mata kitchn dinta duk me girki ita zata dafa
abincin duka gida. Ga store nan duk abinda babu
magana zaku yi. sannan zaku rinka raba kwana
bibbiyu bayan an gama kwanaki bakwai na
farko. Idan da mai tambaya sai tayi. Mufida
mikewa tayi kayi ka gama rawar kafarka akan
wannan yarinyar da ta rasa miji. Wani takaici ne
ya kama khairi tana ganin Uncle Ahmad ya tashi
da niyar fada sai kawai ta ja hannub rigarta
daya zip dinta ya bude ta baya ta tashi ta tafi
gabansa. Uncle dina zuge min zip dinnan please.
Yadda take maganar yasa yayi murmushi ya
tashi. Ai da gudu Mufida ta fita tana kuka.
Iskancin har a gabana Allah Ya isa.
Batul Mamman💖
💕MEYE DALILINKA💞 30
Tana fita suna jiwo muryarta tana ta fada. Ina
kokarin daidaita matsala kina karawa ko
Khairina...ashe kin iya rigima. Don Allah kada ki
biye mata kema kila kiyi abinda ya fi nata idan
kika ji zanyi aure. Yana magana yana jan
hancinta.
Karar mota suka ji yayi saurin sakin khairi tare
da lekawa waje ta window. Mufida ce taja mota
ta fita da yaranta a ciki. Yadda ya juyo ransa a
bace ya nuna khairi wallahi duk yarinyar da ta yi
min yaji sai dai iyayenta su kawota. Ba 'yar da
zanyi biko. Yadda yake fada sai ka ce khairi ce
tayi laifi. Ficewa tayi daga dakin itama rai a
bace.
Ranar haka ta wuni sukuku shi kuwa Uncle ko
dakinta baije ba. Ko da wasa bai taba tunanin
rabuwa da mufida ba saboda yana sonta amma
ya rasa waye ya bata gurguwar shawara har ta
fara neman hanyar bata. Mukullinsa ya dauka
shima ya fita daga gidan. Har ya kusa kwana ta
tuna baiyi wa khairi adalci ba. Dawowa yayi ya
tarar tana toilet. Duk yadda ya buga taki
budewa. Dakin Mufida ya koma ya nemo yan
tarkacen mallakar da take amfani dasu ya nufi
gidan Malam.
Girgiza kai Malam ya rinka yi da yaji bayanin
Ahmad. To ka kira ta a waya kaji inda ta tafi
ne? A'a malam amma nasan gida zata je. Wayar
babanta Malam ya kira ya tabbatar da zuwanta.
Ai nima kiranka nake shirin yi ka rigani. Daga
anyi mata kishiya sai yaji. Abinda nake so ka
kyale ta har sai tayi sati taji uwar da ake ji a
gidan sai muyi maganar. Malam yace ai bazaayi
haka ba ni ina da karatu ne yau na kusa makara
amma gobe in Allah Ya yarda zanzo mu
tattauna. Godiya yayi masa sosai. Bayan ya
ajiye wayar ya sanar da mahaifiyarta. Itama ko
kadan bata goyi bayanta ba.
Khairi dai ana fushi da angon saboda haka da
ya dawo bayan laasar ta hade masa fuska.
Dariya yayi Khairina kinyi fushi ne...ko dago kai
bata yi ba tana daddana waya a kan kujera.
Zama yayi ya kwashe kafafunta ya dora kan
cinyarsa. Tana jin haka ta fara murmushi sai
kuma ta dake kada tayi saurin sauka. Tafiyar
tsotsa ya fara mata sai dariya tana kokarin
kwacewa. Rungume ta yayi yana mata magana
a kunne. Kiyi hakuri kinji khairina. Bata bashi
amsa ba jin yadda yake shafa mata baya. Can
taji yace nifa yunwa nake ji. Ta tura baki bayan
baka bani komai naci ba ka fita. Da sauri ya
tashi tun safe haka kika zà una. Don Allah kiyi
hakuri. Bari na dafa miki indomie da kaina sai
na hada miki gas cooker dinki ta baya. Ganin ya
rikice tace kai dai wasa nake. Naga zaka min
horon yunwa ne shine na hada ai ba wuya. Ga
naka abincin can amma ba nama don ban gani
ba. Kissing din goshinta yayi duk da haka kiyi
hakuri.
Daren ranar kuwa anyi kwanan farinciki tsakanin
ma'auratan. Khairin Uncle har Allah Ya isa tayi
masa karshe tace masa mugu saboda ganin
yadda ta wahala yayi mata allurar bacci. Da
taimakonsa ta tashi ya cika mata bucket da
ruwan zafi tayi wanka. Sai da tayi sallah ta
shirya tsaf ya dawo dakin. Tana ganinsa jiki ya
fara rawa. Dariya yayi harda hawaye ta
mugunta. Haka kike da tsoro dama...harararsa
tayi kai amma kinyi kyau kamar a sake. Sai
hawaye ya gani sharrr. Ikon Allah na auro mai
arhar hawaye. Rarrashi ya zauna yi bayan tayi
shiru yace yanzu khairina jiya fa kin min Allah
Ya isa. Bude idanu tayi ni din? Kwarai kuwa
harda kirana mugu. Gaskiya bani bace ta fada
tana dariya. Ni har ina tunanin irin rakin da zaki
yi lokacin haihuwa.
💕MEYE DALILINKA💞 31
Bai bari tayi komai ba ranar duk. Da kansa ya
sama musu abinda za su ci. Yana dawowa daga
sallar laasar yace mata zaije wurin Malam. Ta
so binshi yace idan ba so take ayi musu fada ba
su bari ko sati ta cika.
Har bakin kofa ta rako shi yana rike da
hannunta. Sai ka dawo Uncle dina kada ka
dade...kashe mata ido yayi akwai abinda zaki
bani ne ko salon na dawo a bini da Allah Ya isa.
Hannuwanta biyu tasa ta rufe ido cike da kunya
ta koma ciki da gudu.
Kana ganinshi kasan yana tare da nishadi. Yana
zuwa bayan ya gaisa da mutan gidan Malam
yace ya tashi su tafi gidan su Mufida. Bata rai
yayi ni fa har rantsuwa nayi bazan taba zuwa
biko ba duk ranar da tayi yaji. Murmushi Malam
yayi ai ba biko zamu ba. Ina son muje iyayenta
su san abinda take yi ne domin suyi mata fada.
Idan aka kyale ta zata cigaba da shirka ne. Ni fa
shiyasa naji na ma gaji da zama da ita Malam.
Tunda har take iya zuwa wurin bokaye ko yan
tsibbu. Ai tasan hakan ba karamin sabo bane.
Eh lallai zaka ce haka mana tunda ka kwashi
budurwa. Kunya ce ta kama shi jin malam ya
fadi haka. Suna shiga motar Ahmad, malam
yace ban aminci ko Yaya yasan maganar nan ba
balle Ummulkhair. Shi rike sirri yana da kyau
kuma rufin asirin matarka rufin asirinka ne.
Hotoro suka nufa gidansu Mufida. Mahaifinta ne
zaune da Uncle Ahmad da Dr Abdallah. Sun
gaisa cikin girmama juna sannan suka fara
abinda ya kawo su. Mufida aka kirawo tare da
mahaifiyarta wadda ta shigo ne don ta gaisa da
Malam. Tana shirin fita yace ai gara ta zauna.
Malam yace me akayi miki kika dawo gida
Mufida? Rainin wayo tace a ranta kamar ba yar
cikinsa ya turo mata suyi sharing miji ba. A
zahiri kuwa cewa tayi babu komai. Ashe baki
san cewa duk matar da take fita ba tare da
izinin mijinta ba duk taku daya a wuta take
yinsa ba. (To yan uwana mata masu tambayar
fita daya suyi biye biye ko ayi satar unguwa.
Don Allah mu kiyaye domin haramun ne).
Da bata bada amsa ba sai ya fiddo ledar da
Uncle ya kawo mishi. Tana gani ta razana sosai
Malam ya hade fuska yana mata magana a
matsayinsa na malami ba uban miji ba. Kuka ta
fara yi iyayenta basu gane me yake faruwa ba
sai da uncle yayi musu bayani. Kuma ta fara
amfani dasu ne kafin ma zancen aurensa ya
tashi. Mahaifiyarta ce ta rinka dukanta yanzu
zubar min da mutumci zaki yi mufida? Ashe ban
miki tarbiyar arziki ba. Tana magana tana kuka.
Babanta duk kunya ta kamashi. Shi dai Ahmad
baice komai ba.
Babanta ya dago kai Mufida wa ya koya miki
zuwa gidan boka? Baki san sallarki ta kwanaki
arbain bazasu karbu ba banda shirka ta yadda
da su. Cikin kuka tace wallahi Baba ba boka
bane. Malami ne shima sunansa Mai Dafa'i.
Sunansa mai uwarki dai inji mamanta. Malam
yace haba hajiya ya zaki zage ta. Huci kawai
take yi don takaici so tayi a barta ta jibgi yar
banza. Cikin kuka ta kwatanta gidansa a wata
unguwa. Dabara ta fadowa malam yace ai
kawarki da kuke zuwa tare ce ta tona miki asiri.
Ta kalle shi tana sharar hawaye kuma fa wallahi
malam ita ce ta dage sai munje. Lallai Laraba
ta cuceni. Yace to ya kamata kusani akwai
bambanci tsakanin boka da malam. Duk wanda
zai zauna yana bugun kasa ko a baki dogon
carbi ace ki kama daya duk ba hanyar Allah
bace. Yanzu an baki hoda da kwalli ki mallake
miji to daga mallakar sai me. Karshe bazaki
taba jin dadin zaman ba tunda kinsan ba don
Allah yake miki ba kuma tun daga kabari a fara
azabtar da mutum kafin aje lahira. Suna amfani
ne da son duniyarku sai su kira kansu malamai
a wurin irinku masu sauran imanin da basa son
zuwa wurin boka.
Mufida tayi shiru maganar ta shigeta ta bawa
iyayenta da mijinta hakuri. Malam yace ta shirya
yaranta ta koma gida tunda ba sakinta mijinta
yayi ba.
Tana fita Malam yace da Ahmad ka nemi
laraban nan ko wace kayi mata nasiha idan bata
ji ba ka hanata shiga gidanka. Baban Mufida
yace au baka santa ba dama. Wayo kawai nayi
mata nasan dole kaita aka yi.
Tunda ta koma gidan Uncle Ahmad ake zaman
lafiya. Rayuwarsu abin shaawa. Lokacin da
khairi ta sami ciki Uncle Ahmad ya ga shagwaba
iri iri. Mufida tana biye mata suna tsula tsiya
son ransu.
Tun safe take jin ciwo kadan kadan tana
daurewa. Suna falo Mufida tace anya Khairi ko
abin yazo ne. Khairi tace a'a saura sati uku fa.
Cikin dare kuwa ciwo yasa ta farka daga bacci
ta dumawa Uncle dundu ya tashi ba shiri. Kai
khairina me ya faru. Jin tana numfashi da kyar
yayi saurin tashi ya kunna fitila. Cikinta ta nuna
masa yace yana zuwa ya tafi ya dauko
handgloves zai dubata sai mamaki ya kamashi
ganin har kai ya fara fitowa. A daki su kadai ya
taimaka mata ta haifo masa santaleliyar
budurwa. Sai da ya yanke cibi ya jira mahaifa ta
fito sannan yaje ya taso mufida. Tana ganin jini
jikinta ya fara rawa na shiga uku Abban Iman
meye wannan? Wani kuka taji baby tana sanar
da zuwanta. Ai bata tsaya daukan baby ba ta
tafi neman ruwan zafi. Ta wanke baby tas tasa
mata kaya. Itama khairi tayi wanka mufida ta
hada mata tea mai zafi tasha. Sai da asuba
suka rinka buga waya Umma da kyar ta jira
takwas na safe tayi. Malam yana ta mata tsiya
yar fari ce fa. Tace ai yau duk mai iyawa ya
kirani mara kunya amma sai na je.
Khairi na kwance a daki ya shiga. Khairin Uncle
a zama mama. Tayi dariya dama jira nake kazo.
To gani wani cikin zan miki ne...an gaya maka
ina tsoro ne ....yanzu dai kaga banyi raki ba
kyauta zaka bani. Kin manta naci dundu a baya.
Kinsa ina tafiya kamar tare mukayi nakudar.
Rungume matarsa yayi Allah Yayi miki albarka. I
love you...love you too uncle dina. Nan suka yi
shawarar sunan baby da zaa sawa baby.
Suna ta boye boye sai ranar suna kowa yaji
sunan yarinya Hawwa amma zasu kirata Jiddah
saboda sunan Yakumbo ne. Ita kam Yakumbo
har kuka tayi yaran da taso bata tsakanin
iyayensu ne suka yi mata wannan karar.
Jiddah na bacci Uncle ya fara mintsinin khairi
tana juyuwa yace Khairina tashi ayi sabon baby
please. Yadda yayi maganar yasa tayi dariya
yana fara kissing dinta Jiddah ta tsala ihu. Duk
suka juyo suna lalubenta don har an kashe
fitila.....
To daga nan zamuyi sallama da iyalan Dr
Ahmad Aliyu Saraki. Sai muce Allah Ya bawa
kowace mace mijin kwarai Ya zaunar damu lfy
da mazanmu Ya bamu zuria dayyiba.
Taku Batul Mamman💖
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Arewa hausa novels
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)
WHATSAPP NO:
+2347039625239
Download Maye Dalilinka Littafi Na Daya Complete
0 Comments
Thank you for this comment