Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU(YAYA HAYAT)
(ADMIN OF ADMINS)
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)
WHATSAPP NO:
09030159301
[6/24, 20:38] Washa: *SILAR KAYAN SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘👘👘Ko
*A SHORT STORY*
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽
_Wannan d’an gajeran labarin nayi shine dan murnar zagayowar sallah da kuma halin da muke ciki a yanzu, da fatan za a d’au darasi a cikin d’an wannan labari_.
_Barka da sallah to all my fans_
_Allah ya maimaita mana ya kuma k’arbi ibadun mu_.
_Na sadaukar da wannan littafin ga duk wani masoya na a duk inda suke, Allah ya bar mu tare_
1-5
Zaune take akan wata ‘yar tabarma, hannun ta akan fuskar ta, da alama wani tunani take yi.
Mahaifiyar tace ta fito daga ban d’aki rike da buta a hannun ta, bin ta tayi da ido tana nazarin ta kafin ta kira suna ta ‘Husna!
Kiran sunan ta da mahaifiyar ta tayi shi ya katse mata tunanin da take yi.
Shiru ne ya ratsa gurin kafin mahaifiyarta ta d’akko kujera ta zaman tsakar gida da ta zauna kusa da ita "Husna wai tunanin me kike yi ne? kin fi son ki d’aura ma kan ki wata lalurar, ga azumi da ake yi, maimako ki kaiwa Allah kuka kukan ki, kin san wannan watan gara’basa ne na amsar rok’on bayin Allah, ina ganin in ki ka kaima Allah kukan ki yafi miki akan wannan tagumin da kika yi".
Wata nannauyar ajiyar zuciya tayi kana ta kalli Mahaifiyar ta tace "Mama, ba komai ne ke damu na ba sai in na duba yanzu muna cikin goman k’arshe na azumi, banda kayan da zanyi fitar sallah , sai wani yadi da Baba ya d’inka min kuma tuntuni nasan anyi yayin shi, kin san k’awaye na in suka ganni dariya za su min, gashi wannan sallar ma har gidan k’awayena na group nake so na je, ran sallah ba ki ga yadda kowa yake turo hoton shi ba, ni me zan tura, yanzu group d’in mu na Kainuwa Writers nasan tun ran sallah har a gama sallah da sauran group d’in da nake, zaki ga kowa na turo kayan da ya d’inka masu tsada, ni me zan tura? Ni dai bazan iya d’aukar hoto da kayan da Baba ya siyo min ba, kowa na gani yasan mai arha ne.
Tun da ta fara maganar mahaifiyarta ta bi ta da idanu, lallai sai yanzu ta k’ara yadda Husna tayi nisa akan buri da kallon na sama da ita, irin haka ne mutum zai iya jefa kanshi a wani hali saboda ya burge mutane, abin da yafi shine ta ci gaba da mata nasiha, ta hakan ne za ta jawo hankalin ta akan son burge mutane da take so tayi.
Cikin lallashi tace "Husna, kowa da kike gani a rayuwar nan baya wuce rabon shi, ki daina d’aukar buri da hangen wasu, ‘yan yatsun kowa fa ba d’aya bane, ko naki in kika duba zaki ga wani yafi wani tsawo bare kuma arzik’i, kina d’aura ma kanki abin da yafi k’arfin ki bayan kinsan ke ba ‘yar kowa ba ce, hasalima Mahaifin kin san gyaran mashin yake yi da mota, sai d’an abin da ya samo yake kawowa a sarrafa, mun dai gode Allah tun da muna cikin rufin asirin Allah, muna samun na cin yau da gobe, tun da dai har Baban ku ya miki kala d’aya ki hak’ura dashi, ni in Allah ya hore min an ba ni biyan bashin da nake bi, sai in d’inka miki, sannan shawarar da zan baki in da hali ki hak’ura da wannan yanar gizon dan har dashi yake dad’a sa miki buri, ki zauna a iya matsayin ki".
Maimakon nasihar da mahaifiyar ta tayi mata ya sanyayar mata da jiki, sai ma wani k’arin buri da ta k’ara ci ma alwashi alamar ba gudu ba ja da baya kenan.
Ci gaba tayi da cewa "Mama, har yau ba ki gane abin da nake so ki fahimta ba, yanzu rayuwa tazo da ci gaba, ko ba ka dashi kana k’ok’arin yin kaya masu kyau da tsada dan kar a raina ka a cikin mutane, kuma ni a yanzu yadda na sa ba da chat d’in nan ba iya daina wa zanyi ba, dan a ciki ne nake k’ara sanin mai duniya take ciki, kina gani ita kanta wayar Salim na tilasta ma wa ya siya min saboda ba na so a raina ni a cikin mutane, yanzu kuma kayan sallah ya gagara sai wani takalmi da jaka da gyale kawai ya siyo min, yana fad’a min wannan sallar ba wani ciniki, kuma a haka yake so mu yi aure, ai wallahi da sake kuma ni yaushe zan sa lissafi da kayan da kika ce za ki k’ara min, bayan kin san mutane da taurin bashi kamar sun sha nonon uwar su, ba lallai su biya ki da wuri ba" ta k’arasa maganar alamar ranta ya k’ara ‘baci.
Cikin fad’a Mamar ta tace "yanzu Husna duk abin da Salim yake miki baki gode ba, ki na ganin yaron shago ne amma hak’a yake k’ok’arin ya faranta miki, maimakon ki yaba mishi sai ma kushewa da kike yi, ki dai dinga gode ma Allah sai ya k’ara miki".
"Mama!" Husna ta kira sunan mahaifiyar ta.
Ido ta zura mata ba tare ta amsa mata ba, tana jiran jin mai ‘yar ta za ta fad’a mata.
"Ina ganin zan kai jinginar waya ta a bani kud’in in sai kayan sallah, in Allah ya kaimu bayan sallar sai in san yadda zan yi in samu kud’i in kai a bani waya ta".
Tsaki mamar ta taja kana ta mik’e tace "sai kiyi duk yadda kike so, ni kinga tafiya ta, Allah ya shirye ki".
Tana tafiya Husna ta fara zubar da hawaye saboda yaddda ba ta so ta kunyata a lokacin sallah.
*Ko ya za a k’are da kayan sallar Husna?*
[6/24, 20:38] Washa: *SILAR KAYAN SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘👘👘
*A SHORT STORY*
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽
6-10
Husna ba ta san iya tsawon lokacin da ta d’auka a gurin ba ta na neman mafita amma ba ta samu ba, jin kiran sallar da aka yi ne yasa ta mik’e ta d’auki buta ta nufi band’aki.
Yau ko aikin da take taya mahaifiyar ta ba ta fito tayi ba, ita a dole fushi take yi da mutan gidan akan kayan sallah.
Sanin halin ta da Mama tayi in tana fushi shi yasa ba ta neme ta ba, sai k’anwar Husna mai suna Fatima, ita ta taya mahaifiyar su aiki.
Ko da aka sha ruwa bata fito ta d’auki kayan shan ruwan ta ba, sai Mama ce ta ba d’ayar k’anwar su Amatullah abincin ta kai mata, dan tasan ba zuwa za tayi ta k’ar’ba ba.
San da ta shiga d’akin su da sallama a lokacin Husna ta sauke hannun ta daga rok’on Allah da take yi akan Allah ya kawo mata yadda za ta fita kunyar mutane, ya kawo mata hanya mafi sauk’i ta samu tayi kayan sallah.
Ajiye mata tayi tace "Anty Husna ga abincin nan in ji Mama".
Shiru ta mata kamar ba taji mai tace ba, ganin haka ne yasa Amatullah ta juya ta fita daga d’akin.
Wani gajeran tsaki tayi san da taci karo da kunun tsamiya da k’osai da aka soya, ido ta zuba ma k’osan wanda bai fi k’waya biyar ba a ‘yar roba.
Nan ta tuno da kalan kalan abincin da ake turo wa a groups, tun kafin kaci sai ka ji miyon ka ya tsinke bare a ce ka kai abincin baki, Allah kad’ai yasan dad’in da abincin zai yi, yanzu ita tsakani da Allah mai k’osai biyar zai mata a cikin ta, tana ganin ko d’an yaye aka ajiye ma k’osan sai ya cinye har ya nemi k’ari bare ita santaleliyar budurwa.
"Allah ka wa kowa arziki" ta furta a fili.
A hankali ta d’auki k’osan ta fara ci tare da kunun tsamiyar tana sha, lokaci zuwa lokaci tana jan d’an k’aramin tsaki.
Bayan ta gama shan ruwan ne ta mik’e ta nufi d’akin Baban su dan yi mishi sannu da shan ruwa.
Sallama tayi ta samu guri ta zauna akan ‘yar ledar dake shinfid’e a d’akin.
Amsa mata sallamar yayi ya bi ta da ido ganin kamar bata cikin kuzari.
"Sannu da shan ruwa Baba".
"Yawwa sannu Husna".
Ci gaba yayi da cewa "Husna me yake damun ki na ga yanayin ki ya canza?" ya tambaye ta.
Cikin sanyin murya tace "Baba ba na jin dad’in jiki na ne".
"Allah ya baki lafiya, jeki ki huta ki sha magani, in kika yi sallar isha’i da nafila sai ki kwanta, yau sai ki huta ba sai kin je tarawihi ba".
"Toh!" ta amsa a gajarce.
‘Dakin Mama ta shiga ta mata sannu da shan ruwa kafin ta mik’e ta bar d’akin, Mama kuwa tun da ta masa mata ba ta k’ara bi ta kanta ba.
Koma wa d’aki tayi ta bud’e datar wayar ta, messages ne suka dinga shigowa cikin wayar ta, a wani group mai suna Tauraruwar Mace group ta tsaya wanda Maryam Ahmad Paki ta bud’e dan k’aruwar matan aure da ‘yan mata.
Hotuna ne birjik na style d’in d’inki kala - kala aka turo kama daga atamfa, material, lace, kimono, shadda da sauran kayayyaki.
Wasu style ne suka d’auki hankalin ta, nan taji burin ta ya sake dawowa sabo fil, nan ta k’ara d’aukar burin samun kaya don yin wannan style d’in.
Haka taci gaba da kallon style d’in da ake ta turowa har aka kira isha’i.
Fatima ce ta shigo d’akin da sallamar ta.
A ciki - ciki ta amsa mata wanda in ba ka kasa kunnen ka kayi ba, ba lallai ba ne ka ji me tace.
"Anty Husna ki zo mu je tarawihi, an kira salla".
Husna wadda har yanzu ba ta huce daga fushin da take yi ba akan kayan sallah, ta watsa mata wani banzan kallo kafin ta d’aura da cewa "kin san ai ni kurma ce, banji kiran sallah ba sai yanzu da kika zo ki ka fad’a min, to yau ba zani ba, ki kama hanyar ki ke da Amatullah kuyi tafiyar ku"
Cikin sanyin murya Fatima tace "Anty Husna da kin daure kin zo mun je, kin ga goman k’arshe muke, da anje ne zaki ga ba mu d’au wani lokaci ba mun dawo, kuma kin san an fi so a goman k’arshen nan mutum yafi yin ibada a wannan lokacin".
Wata irin harara ta mata kana tace "Allahu akbar! Malama, kinsan ni ba ibadar nake yi ba bare in san har a goman k’arshe ake, sai ke da kike taya limaman jan sallar sannan kika san goman k’arshe ake, naga ladan in naje ni za a ba, bawai za a raba mana ni dake ba, in kuma ke kike rabon ladan saboda ban je ba dan Allah kar ki raba dani".
"Allah ya baki hak’uri in akwai abin da na fad’a miki wanda ba mai ki dad’i ba" Fatima ta fad’a
"Da Allah ‘bace min daga nan".
Juyawa tayi tana jinjina fad’an Husna, ita ba ta ga abin zafi ba a maganar da ta mata.
Bayan Sallar tarawihi ne Salim yazo gidan su Husana.
Wayar shi ya d’akko yayi dialing d’in numbar ta, sai da tayi ringin kusan uku kafin ta d’auka.
"Assalamu alaikum" ya fad’a cikin lallausar muryar shi.
"wa alaikumus salam" ta amsa kamar wanda akayi ma dole.
"ina k’ofar gida".
Ba ta amsa mai ba, sai ma kashe wayar da tayi.
Sai da ta d’auki kusan minti goma kafin ta fito fuskar nan a tamke.
Tun da ta fito ya sakar mata wani tsadadden murmushi har ta k’araso in da yake.
Dakalin dake kusa da gidan su ta nemi guri ta zauna, yayin da Salim yay a sakko daga kan tsohuwar kan frajen d’in shi ya zauna kusa da ita.
Sama – sama ta gaishe shi kafin ta tamke bakin ta tayi shiru.
Nazarin ta ya yi kamar akwai abin da yake damun ta, ganin haka yasa yace "Husna lfy na ganki haka?"
Sai da ta mishi wani kallo mai had’e da harara sannan tace "mai ka gani?".
"gani nayi yau kamar ba kya jin yin magana" ya fad’a yana murmushi.
"kasan yau da gobe sai Allah" ta bashi amsa a tak’aice.
Ganin kamar yau fad’a take ji yasa ya mik’a mata wata ‘yar farar leda.
Amsa tayi don ganin abin dake ciki.
Fashion d’in d’an kunne ta gani mai had’e da sark’a, a cikin ledar har da wani turaren fesa wa mai suna "Heart break".
Wani k’aramin tsaki tayi saboda tasan fashion d’in da ya kawo mata ba wani mai tsada bane, gwara ma turaren tasan zai d’an yi tsada, ita da take ganin fashion a waya kamar a jikin mutum aka yi, shine zai tashi ya siyo mata wannan sark’ar wadda in ba ayi wasa ba, k’yalk’yalin ta fita zai yi, ita ba ma wannan ba, a yanzu tafi buk’atar kayan sawa akan wannan tarkacen da ya kawo mata.
Jikin Salim ne yayi sanyi ganin yadda Husna ke ta’be fuska kamar ba ta yaba da kyautar da yayi mata ba.
"Husna kiyi manage dashi ba yawa, kinsan yanayin garin yanzu sai addu’a".
"Ai na ga alama kam" ta fad’a da gatse.
Shiru yayi bai tanka mata ba, sai ma mik’ewa da yayi da niyar tafiya.
Kallon ta yayi yace "Husna bari in tafi in je gida in sha ruwa, ina so in je tafsir ne".
Ganin ba ta bashi amsa ba yasa ya fara tafiya.
"Salim" ta kira sunan shi cikin taushin murya.
Tsayawa yayi da tafiya ba tare da ya amsa mata ba.
K’arasowa tayi kusa dashi tayi tace "Salim ina kayan da muka yi dakai zaka siyo min".
Mamaki ne ya kama shi da wannan maganar da Husna ta mishi amma sai bai nuna ba yace "Ki yi hak’uri Husna, kud’in ne ba su kai in siyo miki kaya ba, shi yasa na siyo miki sark’a da turare, ki yi hak’uri in na samu kud’i zan siyo miki"
"Sai yaushe kenan" ta tambaye shi cikin masifa.
"In dai Allah ya kawo, ko gobe ne sai in siya miki".
Salim ka ga dai ba hali bane rok’o, amma tun da ka ga na k’arya ‘yancina na rok’e ka kasan ba yadda zanyi ne, amma na ga kai kamar b aka d’auki magana ta da mahimmanci ba, in ba za ka samu siya min bane in sani tun da ai kasan goman k’arshe muke, dan ma ina da tela na a hannu, in kuma ka fi so in kunyata a cikin mutane shi kenan, sai mutane su min dariya da hujjah, da kake maganar sarka da d’an kunne su kad’ai zan sa in fita ba tare da na sa sababbun kaya ba".
Wannan maganganun ne yasa Salim ya hassala saboda shi a ganin shi yana iya k’ok’arin shi amma ita Husna ba ta gani, shi dai abin da Allah ya hore mishi kawai zai yi, ba zai d’aura ma kanshi wani nauyi ba.
"Husna, ni dai ban a yin abin da yafi k’arfi na, kin san ni ba wani mai k’arfi bane, amma sai ki dinga d’aura min buk’atun da suka fi k’arfi na, kamar dai yadda nace in na samu kud’i zan siya miki, idan kuma ban samu ba sai dai kiyi hak’uri, kuma ni abin da yake bani mamaki dake shine yadda a da nasan ki, baki da takura wa mutum akan ya miki abu, sai gashi yanzu kin koyi wasu halaye wanda ban san ki dasu ba, plsss Husna ki gyara".
Cikin masifa tace "Au gori za ka min dan kana min abu, dad’in abin dai ba rok’on ka nake yi ba, in banda wannan ma ta kama, ai ba zan tambayeka ba, ka ganni nan, ban a son a raina ni a cikin mutane, sabida hakan zan iya yin komai dan in ga na fita kunyar mutane".
Cikin fad’a ya fara magana yace "gaskiya Husna ya kamata ki canza, wannan halin bai dace dake ba, ci gaba da irin wannan halayen zai iya sa mu dinga samun sa’bani".
Jikin tane yayi sanyi da maganganun da ya fad’a mata, tasan yana son ta, ita ma tana son shi, abin da yake ‘bata mata rai dashi shine gazawar shi gurin fitar da ita kunya, ba za ta yi saurin ajiye makaman ta ba har sai ya fitar da ita kunya.
Haka dai suka rabu kowa rai a ‘bace.
*SILAR KAYAN SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘👘👘
*A SHORT STORY*
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽
11-15
Tun da Husna ta koma cikin d’akin su ta rasa sukuni, dubarar da tayi na nuna ‘bacin ranta ga Salim bai yi amfani ba tun da bai sa ya amsa cewa zai kawo mata kayan sallar ba, sai ma cewa da yake yi wai in Allah ya hore mai a yadda yake cewa ne ba ciniki za ta tsaya jiran shi, idan ba tayi wasa ba har sai a gama sallar bai daina ce mata ba ciniki ba, ita yanzu ma in ban da dad’in ‘bacin rai baa bin da ta dawo dashi, haushin ta yanzu akan abu biyu ne, rashin amsa kawo mata kayan sallar da bai yi ba, ga kuma maganganun da ya fad’a mata masu ciwo.
Duk son da take mai za ta iya ajiye shi gefe su dinga samun sa’bani in dai ba zai dinga fitar da ita kunyar mutane ba, yanzu ma kenan idan suka yi aure haka zai dinga ce mata ba ciniki, gaskiya da sake wai an ba wa mai kaza kai.
Shawarar dake kai kawo a ranta shine ta kai jinginar waya in yaso daga baya tasan hanyar da zata bi ta samu kud’i ta amso wayar ta, amma a yadda take ji da wayar nan ba za ta iya kai jinginar ta ba.
Amatullah ce da Fatima suka shigo d’akin da sallamar su.
Amsa musu sallamar tayi ta kau da kanta taci gaba da neman mafitar ta.
Kowannen su tarin tambayoyi ne a zuciyar su game da halin da Husna ke ciki, saboda tsoron fad’an ta yasa cikin su an rasa mai tambayar ta.
Haka suka kwanta suka bar Husna a zaune ita kad’ai.
Duk wata hanya da take ganin in ta bi za ta samu kud’i sai ta ga ba mai sauk’in bi ba ce, da haka ta kwanta ba ta samu mafita ba.
Cikin dare taji ana tashin ta dbaa bacci.
Da magagin bacci ta bud’e idon ta dan ba ta kwanta da wuri ba.
Fatima ta gani a tsaye da hijabin ta wanda ke nuni da ita ta tashe ta.
Wata irin harara take sakar ma Fatima a lokaci d’aya tana dad’a lumshe ido saboda baccin da bai gama sakin ta ba.
"Wai miye kike tashi na ina cikin yin bacci na" Husna na fad’a.
Da ladabi Fatima tace "Gani nayi lokacin Tahajjud yayi za mu tafi shine naga ba ki tashi ba, na tashe ki".
"Gaskiya kam kin kyauta, amma kuyi tafiyar ku ba za ni ba".
Ido kawai Fatima ta tsura mata, ta rasa me yake damun yayar ta, tun jiya take neman fad’a da mutane, hakan ba zai hana ta lallashe ta su tafi Tahajjud d’in nan ba, yadda azumin nan ya zo k’arshe, ko wani mutum yana dad’a nema lada ne a wajen Allah da gafarar sa, amma ita sai da azumin yazo k’arshe za ta fare janyewa daga jikin ta daga ibada.
"Anty Husna ki daure ki zo muje, ko a gida kika ce za ki yi ba zai kai tsayuwar da zaki yi a masallaci ba, yanzu yanda kike jin baccin nan, muna tafiya zaki koma bacci ne, idan ko ki ka zo muka tafi massalacin zaki ga kin daina jin baccin da kike yi, kuma ina ganin abin da yasa kike jin baccin rashin kwanciyar ki da wuri shi ya janyo miki haka, bari in jira ki kije kiyo alwalar".
Cikin fad’a Husna tace "Wai ke Fatima wace irin mutum ce, ke kin fi kowa ibada ne da za ki dinga takura min, tun da kin tashe ni to nagode kin yi aikin lada, ni kuma nace ba za ni ba, a gida zanyi nawa, to miye damuwar ki da sai kin tilasta min mun tafi masallaci, ko zuwa massalaci ne kad’ai ake amsan buk’atun mutane, ba a amsa a gida, to ki fita harka ta in ba haka ba sai in sauke miki haushin da nake ji a kanki".
Itama wannan lokacin ran Fatima ne ya fara ‘baci da abin da Husna take mata, daga ta mata magana sai ta juya ta dinga zazzaga mata masifa, ko dan taga tana mata biyayya a matsayin ta na yayar ta shi yasa take amfani da wannan damar tana fad’a mat aba dad’i.
"Ki yi hak’uri Anty Husna, nima ban daddara da abin da kika min ba ne jiya na Tarawihi na dawo na k’ara miki magana akan Tahajjud, tun da naga daga tunatarwa sai ya zama laifi, bari in yi tafiya ta, ki yi bacci lafiya".
Cikin k’unar zuciya Husna ta diro daga gadon tana nuna Fatima da yatsa tace "ke Fatima kar ki nemi ki zage ni, naga alamar kin fara raina ni, yanzu sai in ci miki mutunci, ko jikin ki ya fad’a miki".
Ganin abin da Husna take yi na nufin kad’an take jira ta ci mata mutunci, gwara tayi tafiyar ta tun da ba za taje masallacin ba, in tayi ai kanta tayi ma wa.
Tafiya ta fara yi ba tare da tayi magana ba, sai da takai bakin k’ofa sannan ta juyo tace ‘ki yi ke kad’ai Anty Husna, ni kin ga tafiya ta massalacin tun da ba zaki ba’ ta fad’a da alamar tsokana.
Ai kuwa da gudu Husna ta biyo ta, ita kuma Fatima ta wuce d’akin Mamar su da gudu.
Band’aki Husna ta shiga ta kama ruwa, kana ta fito ta d’aura Alwala.
D’aki ta shiga ta shimfid’a sallaya ta tada sallah, ta d’au lokaci tana nafilfili, bayan ta idar da sallah ne ta d’aga hannun ta sama tana rok’on Allah ya biya mata buk’atun ta, rabin addu’ar ta akan Allah ya ba wa kowa arziki, ya cire su daga halin babu da suke ciki, sannan ta rok’i Allah akan ya kawo mata hanyar da zata samu wanda zai siyan mata kayan da zata yi fitar sallah ko ya sa ta samu wata hanya da zata samu wanda zai ba ta kud’i ta siya kayan.
Bayan ta gama addu’ar ne ta rufe da salatin annabi ta shafa.
Gado ta koma takwanta taci gaba da baccin ta.
San da aka tashe ta sahur taji zuciyar ta d’an yi sanyi, dan haka ta je d’akin Maman su aka yi sahur da ita.
Mamar su ma tayi mamakin sakkowar ta amma bata nuna mata ba.
Washe gari da ita aka yi ayyukan gida kamar ba ita ba, da alama ta fara sakkowa.
Bayan ta gama ayyukanta ne taje ta juya ruan da ta d’aura akan wuta ta shiga band’aki tashek’o wanka.
Gaban d’an madubin d’akin su da ta samu carpenter ya had’a mata ta yada zango.
A kujerar madubin ta zauna dan yin kwalliya.
Sai da ta gama shafe-shafenta sannan ta d’akko ‘yar jakar kit d’inta na Make-up ta bud’e ta fara ciro kayan kwalliyar.
Ni da nake la’be a bakin k’ofar d’akin nasha mamakin ganin kayan dake cikin d’an kit d’in, kayan make-up kama daga foundatioin na kwalba na classic, powder kamfanin Tara, jambakin ta ma kamfanin classic, set up brush, bronzer, primer, setting powder, kai da duk wasu kayan make- up ne a ciki.
Mamaki ne ya kama ni ganin kayan dan nasan masu tsada ne.
Anan na k’ara jinjina lamarin Husna, na yarda ita ta daban ce, ko ni Maryam Ahmad Paki ba ni da irin wannan kayan.
A raina nace ina ma nima zan samu in had’a wannan kayan make-up da na fara yi wa mutane kwalliya.
Nasan young writers irin su Ummy Ontop, Ummy Abdoul, Pretty, Hauwee love, Mufida Mu’azu, Memcy Ata, Jamila Sama’ila, Noor za su zo in musu kwalliyar.
Nasan su ma matan auren ba yadda za suyi ba, suma sai sun ce in musu kamar su Fauxia Mb, Mrs Makama, Mrs Mansoor, Mrs Adam, Batul Adam Jatko, Hauwa Saudiyya, Maman Rufaida da sauran ‘yan Kainuwa writers.
Fans d’ina kuwa Casual make-up zan musu irin su Tawerh, Xarah Auwal, Nafisa Khaleed, Hussaina, Hauwa Rani, Fadeela, Maimuna, Fatima Arkilla, Badiyya Kano, Saudat, Maejeeddarh Othman, Fannata ta Annabi (Zinder), Hussaina Paki, Zinatu gatari, Meeynarh, Asiya Paki, Meeynah, Maryam Ibrahim Kusada da sauran fans da ban ambata ba saboda yawan ku.
Kuma su Maman Walida, Auta Mama, Sakina Ilyas, Mom Affan zan muku bridal make-up dan ina so ku dawo amarya.
Husna sai da ta shafe mintina sama da ishirin tana kwalliya.
San da ta gama kwalliyar ne ta mik’e taje ta tafi ta bud’e akwatin ta wanda take zuba gogaggun kaya.
Wasu had’ad’d’un material riga da skirt ta d’ak’ko ta saka, kana ta d’akko gogaggen hijabin ta wanda ya shiga da kalar kayan ta saka.
Gaban madubi ta wuce ta d’auki turare mara k’arfi ta fesa.
Ni kaina a lokacin Husna ta min kyau gaskiya, ba laifi tana da na ta kyan, shi yasa take son yi k’walisa.
D’akin Mamar su ta shiga ta mata sallama.
Ba ta yada zango a ko ina ba sai a wani Massalaci dake can gaba da layin su.
Tafsir na mata ake yi a cikin masallacin a watan Ramadan, da an gama Tafsir d’in a lokacin,sai a kira sallar azahar.
Sai da aka shafe tsawon awa biyu sannan aka tashi daga Tafsir d’in.
Tafiyar ta take yi cikin natsuwa kamar ba ta son taka k’asa wanda in b aka san yanayin tafiyar ta haka take sai kace yanga take yi
Wata tsaleleliyar mota ce k’irar Maybach mai launin bak’i ta taka burki a gaban ta.
Wani had’ad’d’en saurayi ne matashi ya fito daga motar yana sanye da k’ananun kaya a jikin sa.
Rainin hankalin da wannan saurayin yayi na taka mata burki ya k’ona mata rai, duk fad’in hanya bai mishi ba, sai yazo a gaban ta zai tsaya, tayi niyar tsayawa ta fad’a masa bak’ak’en maganganu, tana ganin kamar ‘bata lokaci ne, hakan yasa ta fara tafiya ba tare da tayi maganar ba.
"Beauty" abin da taji wannan matashin saurayin ya kira ta dashi.
Ba ta tsaya ba taci gaba tafiya dan a ganin ta ba girma tsaya kula saurayi a titi.
"Dan girman Allah ki tsaya" saurayin ya sake fad’a.
Cak ta ja ta tsaya ba tare da ta juyo ba.
*SILAR KAYAN SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘👘👘
*A SHORT STORY*
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽
16-20
Ganin ta tsaya yasa cikin takun shin a k’asaita ya zo inda take.
Wani sansanyar murmushi ya saki kana yace "Sorry Beauty na tsayar dake akan hanya ko? nasan class d’in ki ya wuce haka, nima ba yadda nayi ne don ba nasan ki kufce min, tun da kika tawo na ke bin ki saboda na had’u da sanyin idaniya ta". ya fad’a yana murmushi.
Ita duk wannan surutun da yake yi damun ta yake yi saboda ba ta saba tsayawa da namiji akan hanya.
"Plsss ina sauri ne, na ga kamar ba ka da abin fad’a" ta fad’a cikin d’aure fuska.
"Ni ko ke da abin fad’a Beauty, tun san da naga tahowar ki naji na kamu da son ki, shi yasa ma na dinga bin ki dan in fallasa miki abin dake raina, ina fatan za ki amshi k’ok’on bara ta ki bani matsuguni a zuciyar ki, ina ta miki surutu ban fad’a miki suna na ba, suna na Khalid, in ban takura miki ba pls zan iya sanin sunan ki".
Ta gefen ido Husna ta kalle shi, hak’ik’a matashin saurayin na da kyau ba laifi, a yanayin shi da motar shi ya nuna cewa yana tashe da kud’i, sannan yanayin shi ya nuna irin ‘yan bokon nan da idon su yake a bud’e, duk wannan nazarin tayi shine a cikin ‘yan mintina.
Ba ta ji wani son shi a ranta ba duk irin namijin da take kwad’ayin samu kenan amma ba za tayi saurin nuna mishi haka ba saboda kar tayi biyu babu, gwara ta amince dashi ko ba komai zai mata amfani a wasu lokutan idan hakan taso, bare yanzu da take cikin buk’atar neman taimako na yadda zata samu kayan sallah.
Yalwataccen murmushi ta sakar mai kana tace "Suna na Asma’u Auwal, amma an fi kira na da Husna". Ta fad’a cikin yangar ta.
"Nice name Husna, zan iya samun numban ki".
Wani d’an tunani tayi kafin ta fad’a mishi numbar.
Yanzu Beauty kin amince da tayin soyayya ta? Khalid ya tambaye ta.
Ganin in tayi saurin amsa masa kamar ta zubar da class d’in ta ne, dan haka tace mai sai sun had’u ta waya.
Ya nemi da ya kai ta gida amma tak’i, ganin haka yasa yace ta kwatanta mishi gidan su da sunan layin, nan ta fad’a mishi.
Ba su rabu ba sai da ya sa mata numban shi sannan suka rabu.
Husna tun san da ta koma gida ta tsinci kanta cikin farin ciki, gani take yi ta samu mai fitar da ita kunya, had’uwar ta da Khalid tasan wani tsani ne da za ta dinga amfani da shi wajen maida ita fitacciyar mace a gurin jama’a.
Da yamma tana zaune ta kunna data d’in ta taga Khalid ya mata sallama kasancewar tayi saving d’in numbar shi.
In da ya d’auki hoton ne yaja hankalin ta saboda wani had’ad’d’en gida ne na zamani wanda ya gaji da had’uwa, kai da gani ba sai an fad’a maka ba kasan kud’in yayi kuka a wajen k’awata ginin gidan bare a je ga alatun dake cikin gidan.
Ya zama dole ta yarda da soyayyar Khalid dan zai fi mata amfani wajen share mata hawayen ta akan Salim da yake mata kukan ba ciniki, tasan so d’aye ta riga ta ba Salim, amma hakan ba zai hana ta ajiye shi a gefe ba.
"Hello Beauty" Khalid ya turo mata
Reply ta tura mishi da "Hi Khalid".
"Ya kike ya hutu" ya sake tambayar ta.
A ranta tace wani hutu mutum na fama da abinci kala d’aya, kan a sauya sai an ji a jiki, za ka tambaye ni hutu, hutu ai sai ku da kuka kwanta a cikin daula.
Saboda kar ta ba da kanta sai ta tura mishi reply da "Normal ya aiki".
"Aiki alhamdulillah".
Haka dai suka ci gaba da hira, ya mata alk’awarin akan gobe in ya samu time zai zo gidan su.
Dad’i ne ya kamata saboda tasan ba zai zo haka ba, tasan zai iya had’o mata da kayan sallar tun da yasan a goman k’arshe ake.
_Ni ko readers na ce ku ji ni da Husna, daga mutum yace zai zo har ta yanke zai zo mata da kaya, lallai Husna ba k’aramin d’aura wa kanta buri tayi ba_
Da daddare bayan taje tarawihi ta dawo aka aiko Salim na kiran ta, sai da ta gama ‘bata lokaci sannan ta fito.
Yau ma kamar jiya, tun da ta gaishe shi ta kama bakinta ta rufe, sanin fushin da take yi yasa bai damu ba, yasan da kanta za ta sakko.
Cikin tsokana ya ce "Ran gimbiya ya dad’e".
A ranta kuwa cewa tayi "Ko zai dad’e ba a cikin wannan k’uncin da nake ciki ban a talauci, kullum mutum yana tunanin hanyar da zai fitar da kan shi kud’i".
Jin shirun da tayi ne yasa ya k’ara cewa "Gimbiya ta ko sai na siya maganar ne, naga yanzu magana ma wahala take miki".
"ya ka ke?" ta tambaye shi a tak’aice.
"lafiya lau Husna" ya amsa da murmushi a fuskar sa.
"Ya ibada" ya sake tambayar ta.
"Alhamdulillah".
"Ya shirye-shiryen sallah".
Gani tayi kamar da gayya ya tambaye ta, wani shirye-shirye za ta yi bayan har yau ba ta ganta da kaya kala uko ko hud’u ba, kuma yasan da haka amma yake tambayar ta.
Yatsina fuska tayi kana tace "Masu shirye-shiryen nayi, amma wasu sai dai su gani da ido da fatan ayi sallar lafiya tun da ya bar su da lafiyar su amma ba wai dan suna da abin yin sallar ba".
Yasan magana ta fad’a mishi a fakaici don yaji haushi, ba zai biye mata ba, yaga alamar neman abin da za su samu sa’bani take yi, shi dai fatan shi Allah ya yaye mata wannan halin da ta d’aura ma kanta, dan ba k’aramin matsala ba ce bare ga ‘ya mace.
Haka ya ci gaba da jan ta da hira ba armashi, rabin hirar duk bak’ar maganar take fad’a mai a habaice.
Bai wani dad’e ba ya mata sallama ya tafi.
San da ta koma gida ne ta bud’e data ta shiga groups tana ganin latest kayan da aka sake turowa na siyarwa kama da kayan sawa, side bags, fashion jewelries, takalma, gyaluluwa da sauran su.
A cikin group d’in da ta shiga ba wanda ya kaita tambayar kud’in kayan kamar za ta siya.
Wanda suke siyar wa a group d’in haka suka dinga fad’a mata kud’in kayyakin.
_Ni ko nace ta samu ma ta samu k’arin kala d’aya ko mai arha ne da tambayar kud’in kayan da take yi_.
Tana cikin chat d’in ne taga sak’on Khalid ya shigo, sun d’an yi hira ta ga ya sauka, ba a dad’e ba ya sake hawa, katin waya taga ya turo mata na dubu biyar.
Dad’in da tajin a wannan kyautar katin ba ya misaltuwa a gurin ta, tasan za ta toshe wata kafar, ya wuce ta ajiye dubu d’aya a cikin wayar ta dan siyan data da kiran waya, sauran dubun hud’un sai ta kaima masu saida katin waya su siya, ko za su karyar da katin kad’an ne, wannan kyautar ma kenan tun kan yazo kenan, ina ga yazo, Allah kad’ai yasan yadda zai jik’a ta da kud’i.
Jerin godiya haka ta dinga mishi, nuna mata yayi wannan ai ba komai ba ne dan ya mata ‘yar k’aramar kyauta za tai tayi mishi wannan godiyar.
Kaji harkar girma in ji Husna.
Haka suka rabu a chat yana k’ara jaddada mata yadda yake jin ta a zuciyar shi.
Washe gari bayan an tashi daga tafsir ne ta biya ta gidan su k’awar ta Bilkisu.
Bilkisu iyayen ta masu kud’i ne dan mahaifin ta d’an gwal ne, Husna sun had’u da Bilkisu ne wajen gyaran gashi, anan suka yi ta hira har suka saba, san da za su rabu ne suka yi exchanging d’in numba, daganan suka ci gaba da zumunci a waya har takai kowa yasan gidan kowa kuma suna ziyartar junan su, kasancewar su Bilkisu masu kud’i hakan bai sa tana k’yamatar Husna bad an bas u dashi, in ba kasan asalin Bilkisu, ba laillai ka ce suna da kud’i ba saboda ba ta da girman kai kamar na wasu ‘ya’yan masu kud’i da suke yi in iyayen su na da kud’i suna kallon kowa banza ne a gurin su in dai bai da kud’i.
Tsakanin gidan su Husna da Bilkisu ba wani nisa dan layi ne y araba su.
Wannan shine ainihin k’awance Husna da Bilkisu.
San da ta isa gidan ta samu su Hajiyar su Bilkisu a falo tana kallon tauraren d’an adam.
Bayan sun gaisa ne Hajiya ta shaida mata Bilkisu na d’akin ta.
Lokacin da ta shiga d’akin k’amshi ne kawai ke tashi na musamman, a lokaci d’aya kuma A.C ke aiki, ita kuwa Bilkisu kwance take akan lafiyayen gadon ta wanda ya gaji da had’uwa tana bacci.
Dukan wasa Husna ta mata tana dariya, da sauri Bilkisu ta tashi dan ta tsorata.
Ganin Husna ce yasa ta mata hararar wasa tace "Ai nasan ba wanda zai min haka ina bacci sai ke daman, mutuniyas daga ina haka".
"Daga tafsir nake shine na biyo, na ga kwana biyu kin guje ni" Husna ta fad’a da alamar wasa.
Sakkowa Bilkisu tayi daga kan gado ta shiga band’akin dake cikin d’akin ta, d’aurayo bakin ta tayi da fuskar ta kana tazo ta zauna kusa da Husna.
Husna ce tace "Kina jin dad’in ki, yanzu da ranar nan kike bacci".
"Wallahi gajiya nayi da zaman, kuma na ga abin da zanyi shine nazo na kwanta bacci ya d’auke ni".
"Ai kin ji dad’in ki Bilkisu, ko ni na samu wannan A.C in na kwanta ban san lokacin da zan tashi ba, sai dai a zo a tashe ni, amma kai kuna had’e a d’aki d’aya da k’annen ka, hayaninyar su ma ba za ta barka kayi barcin arziki ba".
"Kai Husna, za ki fara halin naki ko, ki dinga dai gode ma Allah dan kin fi wasu, amma ke kullum cikin k’orafi kike, kuma wani yawa gare ku da har Fatima da Amatullahi za su hana ki barci, na ga ba wani hayaniya gare su ba, kuma Junior na ga ba wani rigima gare shi ba".
Yatsina fuska Husna tayi kana tace "Ni n ace miki ban gode ma Allah, ke dai kawai ayi sha’ani dan yanzu nasan za ki fara cika ni da wa’azin ki".
Dariya kawai Bilkisu tayi tana jinjina halin Husna na hange da kallan na sama da ita.
Canza hirar Bilkisu tayi da cewa "To ya shirye-shiryen sallah".
"Yana gurin ku, ke da aka miki komai, amma ni ina wani shirye-shirye ta ‘bangare na ina fama da Kala d’aya, in samu ma Salim ya k’ara min ya gagara, sai wasu tarkacen d’an kunne da sark’a ya kawo min, sai takalmi da jaka, yanzu akan kayan sallar nan har fad’a muka yi dashi amma ba ta canza zani ba".
Bin ta kawai da kalloBilkisu take yi, tasan kad’an kenan daga halin Husna ne in dai akan buri da ta d’aura ma kanta.
"Wai miye kika tsura min ido" Husna ta fad’a tana hararar ta.
Girgiza kai Bilkisu tayi tace "Kin san ba ki kyauta ba, shi yasa za ki fake da na tsura miki ido, yanzu abin da kika yi kin kyauta kenan Husna, duk yadda Baba da Salim suke miki k’ok’ari amma ba kya gani, kullum cikin yi miki nasiha nake yi amma sam kunnen ki ba ya d’auka, yana da kyau ki dinga gode ma Allah sai ya k’ara miki, ki dinga rok’on Allah akan Allah ya biya Baba da Salim, sai ki ga Allah na kawo hanyar da za su dinga miki irin kayan da kike so dan ni nasan suna iya k’ok’arin su, ke ce dai ba kya gode musu".
"Yayi Alarammiya, ai bansan wa’azin naki yakai haka ba, da na daina zuwa Tafsir in dinga zuwa nan dan na ga ba k’aramin iya wa’azi zaki yi ba" Husna ta fad’a.
Dariya Bilkisu tayi tace "Allah baki hakuri Husna, ki barni a d’aliba ta".
Mik’ewa Husna tayi da niyar tafiya wai ita tayi fushi.
Da sauri Bilkisu ta rik’o hannun ta tana ba ta hak’uri akan ta zauna.
Husna ce tace "Ai gwara in tafi, nag a yau wa’azin naki ya tashi ne".
"To ya hak’uri, zauna in d’akko miki kayan sallah na ki gani"
Husna na jin haka ta nemi guri ta zauna kamar wadda aka ce za a mata kyautar kayan sallah.
_To nima dai bari in je in d’akko Zainab lawyer da Sadiya lawan da muk kasha k’wark’watar idon mu, amma ni ba ruwa na dan kar kusa rai kuma Bilkisu zata ba Husna kuma kuce a baku_.
*SILAR KAYAN SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘👘👘
*A SHORT STORY*
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽
21-25
Wasu tsadaddun kaya Bilikisu ta ciro daga wardrope, Husna tun da ta ga Bilkisu ta d’akko kayan take bin ta da ido.
Ajiye mata kayan tayi akan gado kana ta nemi guri ta zauna.
Rasa wanda za ta fara d’auka ta gani tayi don duk kayan sun burge ta.
Hannun ta ne yakai kan atamfa da aka mata d’inkin riga da skirt, rigar an yi mata ado da wasu bit, hakan ya k’ara fito da atamfar.
Wani cotless kalar brown ta d’aga wanda aka ma d’inkin doguwa riga.
Bayan ta ajiye atamfar ne ta d’auki wani tsadadden lace kalar milk mai background kalar light brown, d’inkin an mishi d’inkin buba da zani.
Tana ajiyewa ta d’auki wani had’ad’d’en material kalar purple wanda aka watsa ma stone a jikin rigar, hakan sai ya k’ara ma d’inkin kyau, skirt d’in kuma aka mata yankan six pieces.
Takalmi ta gani gani kamfanin AMEIGO mai matsakaicin tsaho kalar brown da Jaka ita ma kalar brown da gyale kala biyu kamfanin R&S kalar brown mai adon duwatsu a jikin gyalen, sai wani d’an flat shoe mai tsada kalar milk da gyale shima kalar milk.
Ba ta gama rud’ewa ba sai da taga wasu kaya a irin farar ledan nan da ake sa kaya irin na amare, cire su tayi dan ganin ma idon ta.
Wani irin yadi ne kamar kalan yadin maza haka yake, kai da gani kasan masu tsada ne, yadin kalar Peach, a jikin yadin sai a ka mishi wani zane da kalar light brown, maroon, yellow da orange a ji, yadin ba k’aramin tafiya yayi da Husna ba, gashi an mata wata had’ad’d’iyar doguwar riga.
Wannan karan kasa daurewa tayi sai da ta ma Bilkisu magana ta ce "Bilkisu wai dan Allah wannan yadin irin na maza ne da na sani ne, ko kuma haka yake".
Bilkisu ce ta ba ta amsa da cewa "Wannan yadin haka ake yin shi kamar irin na maza amma wannan na mata ne, wannan jakar da takalmin da gyalen da kike gani, Samir ne ya kawo min" sai a nan idon ta yakai kan gyalen da ta gani da takalmi kamfanin Vinci shima kalar peach, gyalen ma kalar peach, komai dai perfect da wasu d’an kunne masu kyau.
Kallon Bilkisu tayi ta ce "yanzu duk wannan yadin da takalmin da jakan da gyale duk Smair ne ya kawo miki, kin ga inda ake kaya nan ba irin na Salim ba kamar wanda kaje maula ya d’auka ya baka".
Ci gaba tayi da da cewa "Gaskiya Bilkisu ke ba ki da wata matsala in dai ta fannin jin dad’in rayuwa ne, duk wanda ya samu irin wannan kayayyakin me zai nema kuma a fannin jin dad’in rayuwa, ai sai dai ya nemi fatan gamawa da duniya lafiya, mu ma Allah yasa mu a danshin ku".
Bilkisu rasa bakin magana tayi dan ita lamarin Husna yafi k’arfin ta, yanzun nan ta gama mata fad’a akan irin wannan halin da take yi na nuna rashin godiya ga Allah da hangen wanda yafi ta wadata amma ba ta d’auka ba, ba za ta gaji da fad’a mata gaskiya ba, Allah ne ya had’a su da ita kuma ita a yadda suke yanzu d’aukar ta take kamar ‘yar uwarta.
Bilkisu ce ta nisa ta ce "Husna gaskiyar dai da ba kya so in fad’a miki ita, zanci gaba da fad’a miki ko da ba za ki so ba, Allah (S.W.A) yace a cikin Alkur’ani mai girma "kuma a lokacin da Ubangijin ku ya sanar, ‘lallai ne idan kun gode, hak’ik’a, ina k’ara muku, kuma lallai ne idan kun kafirta, hak’ik’a azaba ta, tabbas, mai tsanani ce", Husna gode wa Allah a duk wani hali da kake ciki wani ginshik’i ne na samun nasara a rayuwa, Allha na iya jarabtar kowane bawa ta hanyan da yaso, idan ka yi hak’uri sai ki ga kin ci ribar hak’uri ta hanyar hawa tsanin da ba ki ta’ba zata ba, ki samu duk abin da kike so, a lokacin ma mantawa za ki yi da kin ta’ba shiga wata rayuwa ta babu, ni dai nasan Salim yana iya k’ok’arin shi akan ki, ke ce dai ba kya ganin haka".
Ta’be baki Husna tayi kana ta ce "Wai ke Bilkisu ke kad’ai kika fi kowa sanin Allah ne, ba da ma in fad’i magana sai ki kama min wa’azi, ce miki aka yi ban gode ma Allah, ko akwai inda aka haramta in ka ga abu ya maka ka yaba, da kike ta damu na Salim yana k’ok’ari, ni dai ban gani ba, nasan in dai azumi ya kama, kowani saurayi yana k’ok’arin yi wa budurwar shi Ramadan basket, amma shi bai yi min ba, sai Dabino da ya siyo min mai uban yawa ya kawo min, da yake yaga shi wannan bai da tsada shine ya siyo min, ko ce mai aka yi Dabino nafi buk’ata ban san mai ba, gashi sallah tazo yayi tunanin tun da bai min Ramadan basket ba ya daure ya siya min kaya masu d’an tsada, bai yi wannan tunanin ba, sai Jaka da takalmi da wasu ‘yan kunne ya had’a ni dasu, ko an ce mai ni k’aramar yarinya ce, in ma yana duba dan mu talakawa ne yasa yake min haka to ni na wuce wannan class d’in, a ce mutum yayi ta fake wa da bayi dashi dan kar yayi wani abun arzik’in, ko a kanshi a ka yanke ma babu cibiya sai hakam ni fa bari in fad’a miki Bilkisu, nasan ina son Salim sosai, amma gaskiya ina ganin tafiyar mu ba za ta tafi dashi ba, dan ba zan yarda in jefa kaina a wani taskun rayuwa ban da wanda nake ciki a yanzu a gidan mu, babu wanda bai son wadata".
Murmushi Bilkisu tayi ta ce "Babu inda aka ce in ka ga abu kar ka yaba, Allah ya baki hak’uri, nasan nasiha da nake miki wataran zata yi miki amfani, ki sani ba inda hange yake kai mutum sai kogin danasani, za kuma ki gane Salim na miki k’ok’ari duk da bashi ne dashi ba amma ke ba kya ganin haka, ni dai kullum ina taya ki addu’ar Allah ya ganar da ke".
Cikin masifa Husna tace "Da yake a ‘bata nake, ai dole ki ce Allah ya ganar da ni, ba dama mutum ya fad’a ra’ayin shi sai a bi a canza mishi maganar shi, dole ki yi ta kare Salim tunda ke su Momi da Dadi da Samir sun miki gata, sun gwangwaje ki da kayan sallah, ni ai dole ki ce min haka".
Haka Humaira taci gaba da fad’an ta, Bilkisu na jin ta amma ba ta tanka mat aba dan tasan in fad’an ta ya tashi abin ba sauk’i.
Jin Bilkisu ba ta biye mata ba yasa ta kama bakin ta tayi shiru.
Tashi Bilkisu tayi ta nufi wardrope ta bud’e, wasu had’ad’d’en materials ta d’akko kala biyu, kala ne ya banbanta su amma komai iri d’aya ne.
Husna dai sai kallon kayan take yi da ido ba tare da tayi magana ba.
Bilkisu ce ta dafa kafad’ar ta tace "Husna cikin wannan kayan, wanne ne yafi miki kyau".
Ai kamar an had’a Husna da aiki, sai kallon kayan take yi, ta rasa za’ban wanda za tace ya fi mata kyau.
_Ni da Mrs Adam marubuciyar ‘Yar Hutu da nace ta rako ni d’aukar rahoton Husna, ita ce naga tana k’ok’arin shiga cikin d’akin, da na tambaye ta mai zata yi, shine take ce min wai za taje ta taya Husna za’be ne, tunda ta ga ta rasa wanda za ta za’ba_.
_Da k’ar na samu ta fasa zuwa don nima ina gudun masifar Husna_.
Ganin ta rasa wanda za ta za’ba, sai kawai ta nuna mai kalar maroon d’in.
Bilkisu ce ta ce "Kin tabbata wannan yafi miki kyau".
Gyad’a kai Husna tayi alamar "Eh".
Bilkisu ta ce "Tun da kin ce yafi miki kyau, ki d’auka".
Kallon mamaki kawai Husna take bin Bilkisu dashi, gani take yi kamar ba’a take yi mata.
Dariya Bilkisu tayi ta ce "Miye kike kallo na, ko ba kya so ne".
Da sauri Husna ta ce "Wai dagaske kike yi ko wasa kike min".
"Au kin d’auka wasa nake yi, to bari in kwashe kaya na" Bilkisu ta fad’a cikin wasa.
Ai Husna najin haka tayi saurin cafkar kayan tana dariya, ganin yadda Husnan tayi yasa itama dariya.
_Ko ni da Mrs Adam sai da muka yi dariya_
Cikin jin dad’i Husna ta ce "Bilkisu ban san da wacce kalma zan miki godiya ba, kin fitar dani jin kunyar mutane, hak’ik’a ke k’awa ce da ba a cika samun irin ku ba, ba abin da zance miki sai dai Allah ya saka miki da alkhairi".
"Ba komai Husa, miye amfanin zaman tare in ba ka taimaki wanda ku ke tare ba, Dadi ne ya bani kud’i na siya mana".
"In Dadi yazo pls ki mishi godiya, Allah ya k’ara arzik’i da jin dad’i".
"Amin Husna, kema Allah zai kawo lokacin da zaki dinga bayar wa".
"Allah ya amsa bakin ki Bilkisu".
"Amin Husna".
Gurin Momi ta raka ta dan yi mata sallama, haka tayi ta zuba ma Momi godiya kamar ita ce ta mata kyauta.
Sallama ta ma Momi yayin da Husna ta rako ta har kusa da layin su, suna tafiya suna hira.
A hirar ne Husna take fad’a ma Bilkisu tayi sabon saurayi kuma da alama yana da kud’i.
Ita dai Bilkisu ba ta nuna wani farin cikin ta ba, dan har ga Allah Salim yafi kwanta mata a rai akan shi saurayin da ta ce tayi duk da ba ta ganshi ba, dan Salim mutum ne nagari, wanda ya iya mu’amala da mutane, gashi yana da sakin fuska da wasa da mutane, ita kanta Bilkisu ta rasa me yake damun Husna dan tasan tana son Salim amma yanzu taga alamar so take yi ta ajiye shi gefe duk kuma saboda hangen na sama da ta d’aura ma kanta, Allah dai ya gyara mata halin ta.
_Mu da muke bayan su muka amsa da amin, dan nima hali Husna yana ba ni mamaki_.
Sallama suka yi a daidai kwanar da za ta shigar da Husna layin su, kana kowa ya nufi gida.
_Bin Bilkisu na fara yi, Mrs Adam ce ta min magana akan ina zan koma, mu da za mu bi Husna sai kuma in kama bin Bilkisu, fad’a mata nayi akan zan je nima in rok’i Bilkisu ta sa Dadi ya siyan ma Zainab Lawyer da Sadiya Lawan irin material d’in da aka ba ma Husna suma da sun zo su zo, amma basu sami zuwa ba, da k’yar Mrs Adam ta hana ni bin Bilkisu muka bi Husna a baya_
Husna na shiga gida ta dinga k’walla wa Mamar su kira "Mama! Mama!.
Jin kiran da Husna ke mata ne yasa ta fito da sauri tana d’aura d’ankwali.
Tsayawa tayi tana kallon ta dan ba ta ga wani abu da ya faru da take mata wannan irin kiran ba.
"Lafiya kike min wannan kiran".
Bakin Husna kuwa da ya kasa rufuwa saboda farin ciki ta ce "Mama dan ba ki san kiran da na ke miki ba, shi yasa kike min fad’a".
"To me ya faru".
Mamar su Husna ta fad’a tana jiran bayanin da Husna za ta mata.
Dariya Husna tayi kana ta ce "Mama yau nayi gamdakatar da babbar kyauta a gidan su Bilkisu, ashe alheri ne yake kira na shi yasa na biya bayan an tashi daga tafsir".
"Wace irin kyauta kuma aka miki" Mama ta fad’a cikin k’osawa.
Ciro material d’in tayi daga cikin bak’ar leda ta mik’a wa Maman su.
"Mama kin ga kyautar da Dadin su Bilkisu ya min, yanzu tsakani da Allah Mama ya za ayi ba zaka yi buri ba, ki kalli irin wannan tsadaddan Material d’in, ko a ido ma ki ka kalla kin san mai tsada ne ba irin wanda Baba ya siyo min ba kamar na tatar koko".
Maman kasa magana tayi dan tasan lamarin Husna sai dai addu’a, ba irin fad’an da ba ta mata da nasiha amma ba ta d’auka, har ga Allah taji dad’in wannan kyautar da aka ma Husna, ko ba komai za su sami sauk’in k’orafin da take damun su dashi.
Mik’a mata material d’in tayi tace "Gaskiya kayan yayi kyau, Allah ya saka musu da alkhairi".
Cikin sauri Husna ta amsa da "Amin Mama".
"Kin ga yanzu sai in kai ma Muri tela ya min irin sytle d’in da aka turo a waya, ko Mama".
"Haka ne Husna, Amma kin san ai ba ki da kud’in d’inki".
"Ke dai Mama tun da na ce zan kai d’inki, ai kin san zamu warware da Murin kafin ya gama d’inkin, nasan yanzu ma sai dai in biya kud’in express…".
Katse ta Mama tayi da cewa "Amma dai Salim za ki matsa ma wa ya biya miki ba, kina dai kallon hidimar da ya miki kwanan nan, kar abin ya zama rashin hankali".
Dariya Husna tayi ta ce "Kaji Mama wai kar in matsa ma Salim, yaushe zan sa Salim a lissafin wanda zai biya min kud’in d’inki, mutumin da kullum bai da wani aiki sai kiran babu ko ba ciniki, wani Khalid na had’u dashi, yau zai zo, nasan zan samu kud’in d’inki a gurin shi, har katin waya ya turo min na dubu biyar, yanzu kin ga tun da na samu an amshi katin a shago duk da an rage min kud’in katin, yanzu dashi zan je in ba Murin advance".
Mama ce ta nisa kafin ta ce "Husna, kiyi ma kanki fad’a, kar son abin duniya da burgewa ya ja miki ki sa kan ki a wani halin, ni dai nafi so ki tsaya ma Salim, yaro mai hankali, shine zaki fara jawo wani kuma".
"yanzu Mama ba kya min sha’awar mai kud’i, kin fi so in ta zama a talauci, kowa fa son ci gaba yake yi, bazan tsaya ma saurayi d’aya ba alhalin ba wani kud’i gare shi ba, gwara ka sirka da mai kud’i, ko banza zai biya maka buk’atun ka".
Suna cikin maganar ne su Fatima da Amatullah suka shigo gidan.
Sak’on da Mama ta aike su suka bata, a nan ne Fatima ta hango material d’in dake hanun Husna.
Da fara’ar ta tace "Anty Husna ina kika samo wannan material d’in".
Kallon rainin hankali ta mata kan ta ce "Ke ina kike zaton zan samu wannan material d’in da ya wuce gidan su Bilkisu, ku da ba ku da k’awa mai kud’i ba sai kuyi ta zama kuna kwasar takaici ba, kun ga yanzu ai kwa zauna da kala d’ayan da Baba ya d’inka muku".
Jin yadda Husna ta canza zancen yasa ta ce "Anty Husna daga tambaya, sai cibi ya zama k’ari, to Allah ya baki hak’uri, ni kin ga tafiya ta" tana gama fad’ar haka tayi shigewar ta d’akin su.
Amatullah kuwa da take bin Husna da kallon takaici ta ce "Anty Husna wannan abubuwan da kike yi bai kamata ba, arzik’i da talauci na Allah ne, Baba na iya yin k’ok’arin shi akan mu, amma ke kullum ba kya nuna godiyar ki akan haka, sai aikin kushewa, mu mun gode da kala d’ayan da Baba ya mana, wasu ma kala d’ayan suke nema ba su samu ba…".
Husna ce ta katse ta cikin fad’a ta ce "Wai Amatullah ni kike fad’a ma wannan maganganun, ko Fatima ba ta fad’a min haka ba sai ke, wai ke kin girma ko, za ki min rashin kunya, to ki fita harka ta in ba haka ba sai jikin ki yayi tsami a banza".
Itama cikin tsiwa Amatullah ta fara magana dan itama ba baya ba ce idan aka ta’ba ta, a cikin su Fatima ta fi su hak’uri "Dan na fad’i gaskiya sai ki dake ni, ki ce na miki rashin kunya, ashe ba dad’i kenan yanzu ki ke kushe abin da Baba ya mana kenan".
Tashi Husna tayi da niyar dukan Amatullah, Mama ce ta ja ma Husna kunne akan kar ta kuskura ta daki Amatullah tun da ita ce ba ta da gaskiya, haka ma tayi ma Amatullah fad’a akan rashin kunyar da ta ma Husna.
Ran Husna ne ya ‘baci da Mama ta hana ta dukan Amatullah, amma ko ba yau ba za ta gane kuren ta.
Bayan Amatullah ta shiga d’aki ne Mama ta kalli Husna ta ce "Ai ita duniya fad’i gare ta, kayi ne ayi maka, yanzu nan ki ka gama fad’a ma Baban ku magana akan ya siyo miki material kamar abin tatar koko, sai gashi an samu k’anwar k’anwar ki tana fad’a miki magana, ko wannan kad’ai ya ishe ki darasi".
Mama na gama fad’ar haka ta tafi d’akin ta.
**SILAR KAYAN SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘👘👘
*A SHORT STORY*
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽
*Wannan Shafin naki ne kyauta Mrs Adam (Marubuciyar Auren kisan wuta) kyauta*
*Ina mik’a sak’on gaisuwa ta gare ki*
*Ana tare har kullum*
31-35
Kallon tuhuma Salim yaci gaba da bin ta dashi, hakan yasa ta sha jinin jikin ta.
A hankali ta k’araso inda yake zaune akan frajen d’in shi.
"Sannu da zuwa Salim, an sha ruwa lafiya".
Bai amsa mata gaisuwar da ta mishi ba sai ma jafa mata tambaya da yayi.
"Husna, ni da kike gani ina da kishi akan abin da nake so, zan iya jurar duk abin da za ki min amma ban da yin min yawo da hankali, ina so ki fad’a min meke tsakanin ki da wancan mai motan da ya fara zuwa gurin ki, dan zuciya ta ba ta yardarm min da cewa wai mutunci kuke yi ba, in ma mutuncin ku ke yi ina ganin bai da wani amfani dan ba maharramin ki bane da zai dinga zuwa a mota kuna shiga ciki ba, hakan zai sa zuciya ta a wani hali…".
Da sauri na katse shi da cewa "Kenan zargin mu ka ke yi kenan".
"Ni ba zargin ku nake yi ba, ki fad’a min alak’ar ku zuciya ta za ta fi samun kwanciyar hankali".
Tausayin Salim ne ya kama ta, tasan Salim na son ta, tun da ta ga ya nuna ‘bacin ranshi to abin ya dame shi ne.
"Salim zan fad’a maka abin da ke tsakani na da Khalid, mun had’u da Khalid a hanyata ta dawo wa gida, shine ya tsayar dani, bayan na tsaya ne yake fad’a min yana so na, kaga kuwa duk wanda yace yana son ka ya gama maka komai, gani na da kake yi dashi ba hakan yana nufin wai ina son shi bane, kawai kasan ita budurwa haka take da farin jinin samari, ina ganin kar wannan ya d’aga maka hankali, dan kai nake so".
Takaici ne yakama shi da jin wannan bayanin da Husna take mai, yasan Husna na son shi amma son abin duniya ba zai bari ta nuna mishi hakan ba, a gurin shi ba zai iya jurar ganin ta da wani ba da sunan saurayin ta dan son da yake mata ba zai iya fasalta shi ba a zuciyar shi, ya kamata ya nuna mata ‘bacin ranshi dan ta haka ne kawai zai sa Husna ta rabu da wanda yake zuwa gurin ta.
Cikin d’aurewar fuska ya ce "Husna in dai har kina so na da gaske to ya kamata ki kiyaye abin da ba na so, Husna ban a son muna yawan samun sa’bani dake akan abin da bai kai ya kawo ba, plss ki rabu dashi mu maida hankalin mu akan soyayyar mu".
Jikin ta ne yayi sanyi dan tasan Salim ba komai ba ne yake ‘bata mishi rai, za tayi k’ok’arin ganin ta canza ma Khalid time d’in zuwa dan kiyaye had’uwar su da Salim, amma maganar ta rabu da Khalid bai taso ba, ta lura kamar Salim yafi so ta zauna a halin da suke ciki na talauci, kowa a rayuwar nan ci gaba yake so dan samun walwala a rayuwar shi, komai yanzu yana tafiya ne da wadata, in dai kana da ita to duk wata alfarma zaka same ta, dan me ko za ta guji arzik’i alhalin yana tunkarar ta.
Salim ne ya katse mata shirun da cewa "Husna na ji kin yi shiru ba ki ce komai ba".
Cikin sanyin murya ta ce "Zan kiyaye Salim insha Allah".
Murmushi mai k’ayatarwa ya sakar mata alamar jin dad’i kana ya ce "Na gode lovely Husna".
Ita ma murmushin ta maida mishi.
Hira suka ci gaba da yi kana da zai tafi ya mik’a mata leda suka yi sallama ya tafi.
Tana shiga d’aki ta ajiye kayan ta tafi ta zubo abinci.
Tuno da ledar da Salim ya bata ta tashi ta d’akko dan ganin abin da ke ciki.
Murmushin jin dad’i tayi ganin abin da ke cikin ledar.
Naman rago ne gasasshe da fantar gwangwani biyu da gorar ruwa faro guda biyu.
A ranta tana k’ara jin son Salim, matsalar shi d’aya ce ba ta wuce talauci ba, in ban da wannan bai da wata matsala, fatan ta Allah yasa yayi arzik’i, ta hakan ne za su fin jin dad’i wajen gudanar da soyayyar su.
Naman ta zuba akan abinci ta fara ci kana ta d’auki gwangwanin fanta guda d’aya ta bud’e ta sha.
Ranar haka Husna ta kwana cikin farin ciki.
WANENE SALIM?
Salim Usman d’a ne ga Malam Usman mai manja, sana’ar mahaifin shi kenan siyar da manja, Salim matashi ne d’an kimanin shekaru 28 zuwa 29.
Su Salim suna zaune ne a Dorayi.
Mahaifin shi ba wani mai k’arfi ba ne, suna dai cikin rufin asirin Allah kasancewar mahaifin su akwai shi da zuciyar nema, su biyar ne a gurin iyayen su, yayar shi Zaliha tayi aure, Salim ne ke bi mata, bayan shi sai k’annen shi guda uku, Rahmatu, Kabiru sai auta Fadila.
Gidan su Salim suna da natsuwa da girmama nag aba dasu, hakan yasa mutane ke sha’awar halayen su.
Salim matashi ne da ya tashi da neman na kanshi kasancewar ganin shine babba a maza a gidan su, shi yasa yake jajircewa ganin ya taimaki mahaifin su, ya yi karatun shi a nan Bayero University inda ya karanci Computer engineering.
Rashin wanda zai samar mai aiki yasa ya fad’a kasuwa dan tallafar kanshi da ‘yan uwan shi.
Salim yaron shago ne a wani shago na saida takalma dake Kasuwar kwari.
Sun had’u da Husna ne a lokacin da ta matsa ma Baban su ya ba ta kud’i ta sai takalmi, sanin halin ta na hange yasa ya tara kud’in ya bata taje ta siyo.
Anan suka had’u da Salim, tun da ya ganta yaji ya kamu da son ta, hakan yasa ya tambaye ta unguwar su ta kwantata mishi.
Bayan an tashi daga kasuwa ne da daddare sai ga Salim yazo, bayan ta fito ne ya bayyana mata abin da ke ran shi, ta nemi alfarmar ya d’an ba ta lokaci, bai mata musu ba, sun rabu akan in an kwana biyu zai dawo yaji amsar shi kana ya mata sallama ya tafi.
bayan kwana biyu sai ga Salim ya dawo gidan su Husna, sun d’an ta’ba hira ne ya tambaye ta akan amsar shi, ganin kamun kan Salim da natsuwar shi da ta lura da yana dashi yasa taji ya kwanta mata a rai, nan ta sanar dashi ta amince da soyayyar shi.
Tun daga wannan lokacin suka k’ulla soyayya mai burgewa, sai da suka yi nisa a soyaya ya fahimci halin Husna na rashin godiya, buri, hange, son burgewa.
Iyayen Salim sun zo sun nemar ma Salim izini gurin mahaifin Husna, sannan sun kawo kud’in na gani ina so, sa rana kawai ya rage.
Wannan halayen na Husna ne yasa suke samun sa’bani akai.
Yana k’ok’arin ganin ya mata ihsani daidai k’arfin shi, amma Husna ba ta yabawa saboda hangen na sama da ita da ta d’aura ma kanta.
Salim yana da hak’uri, ba kowane lokaci ba ne kake ganin ‘bacin rai a fuskar shi, sai dai in yayi fushi abin ba kyau, kasancewar hausawa na cewa mai hak’uri bai iya fushi ba idan aka ‘bata mai.
Salim na hak’uri da kau da kan shi akan duk abin da Husna za ta mishi, sai dai yana ganin had’a soyayyar shi da wani ne ba zai iya jurewa ba saboda shi mutum ne mai kishi.
Wannan shine labarin Salim.
Ranaku na ta wuce wa yayin da mutane ke ta bankwana da azumi da ya fara tattara kayan shi, sai kuma ga masu yawan rai idan suna da rabon ganin na wata shekarar.
Yau ta kasance ranar jajibarin sallah, ranar da kowa ke ta shirye-shiryen sallah tare da bankwana da azumi.
Kowa idan ka duba a ranar yana cikin aiki ne inda za ka samu kasuwa ta cika da mutane, shagunan teloli sun cika, wasu sun tafi yin gyaran gashi, zanen lalle, maza kuma sun tafi aski da sauran su.
Gidajen mutane kuwa in banda k’amshin soye-soye ba abin da ke tashi, ya danganta da iya k’arfin mutum.
A gidan su Husna kuwa Baban su ne ya kawo musu kaji biyu da d’an kayan yin cin-cin, sai cefane da yayi wanda za a d’an sauya abinci saboda zuwan sallah.
Duk wannan aikin da ake yi, Husna tunanin ta ya tafi ne akan d’inkin ta na gurin Muri, gashi ba ta ga alamar samun wasu kayan ba, Khalid tasa ran zai kawo mata amma shiru.
Zai yi wuya yazo ba tare da ya rik’o wani abu da zai kawo mata, sai duk abubuwan da yake kawo mata bashi tafi buk’ata ba, kayan da za ta yi fitar sallar shi yafi damun ta.
Tana ganin ba girman ta ba ne a ce ta k’ask’antar da kanta ta rok’e shi kayan sallah, ya kamata a matsayin shin a wayayye ya san da hakan tun da yasan ba wani kud’i gare su ba.
Fatima ce ta kalle ta tace "Anty Husna lafiya na ga kin yi shiru".
"Ba komai" ta amsa mata a tak’aice.
"Gani nayi kamar akwai abin da yake damun ki".
Dama a sama take, dan haka ta ce "Wai ke Fatima ina ruwan ki da ni ne, na ga kin sa min ido, duk abin da nake yi akan idon ki, idan nayi shiru me ya ruwan ki, ko so ki ke in bud’e baki in ta yin surutu kamar famfo".
Gigirza kai kawai Fatima tayi kana ta ce "Allah ya baki hak’uri, ban san tambayar zai zama laifi ba".
Harara ta watsa mata kana ta saki wani dogon tsaki.
Ajiye wuk’ar da take yanka cin-cin da ita tayi ta tafi d’aki.
Bin ta da kallo Fatima tayi har ta shige d’aki, tana mamakin halin yayar ta ta da take abubuwa kamar mai iska.
Husna tana shiga d’aki ta zura hijab, Jakarta ta bud’e ta d’auki wallet d’in ta kana ta fito d’akin.
Kitchen ta wuce inda Mamar su ke soya kajin da Baban su ya kawo, Anisa kuma ke soya cin-cin.
"Mama" Husna ta fad’a.
"Ya aka yi ne Husna, ina zaki ne nag a kin sa hijab bayan aiki kuke yi".
"Mama aikin da bai da yawa, Fatima za ta k’arasa".
"To yanzu ina zaki?".
Mamar su ta tambaye ta.
Amsa mata tayi da cewa "Shagon Muri zani in amso d’in ki na da na basi, anjima ban da lokaci, zan je a min gyaran gashi da zanen lalle".
"Me yasa tun da wuri ba ki fad’a ranar da za ki amso d’inkin ba, sai da lokaci ya k’ure, ki bari Baban ku ya dawo ko za a samu kud’in d’inkin, kin ga nib a kud’i a guri na da na baki kin amso".
Kallon Maman su tayi kana ta ce "Ke ma dai Mama kin san ba bani zai yi ba, cewa zai yi bai da kud’i ya yi cefane dasu, akwai kud’i a hannu na zan amso…".
Cikin sauri Mamar su ta katse ta da cewa ‘Ina kika samo kud’i, ke da ba sana’a ki ke yi ba".
"Khalid ne ya bani" ta amsa mata a tak’aice.
Cikin takaici Maman su ta ce "Yanzu Husna ba za ki daina wannan halin na ki ba, sau nawa nake nuna miki akan amsar kayan saurayi, hakan da kike yi zai zubar miki da mutunci ne, abin da yasa kika ga ban a miki fad’a in Salim ya miki kyauta saboda na yaba da halin shi, kuma kin ga da maganar aure a tsakanin ku, amma shi wannan da yake zuwa gurin ki da mota hankali na ba ya kwanta dashi ba ne, ya kamata ki yi wa kan ki fad’a".
"Mama ni fa ba rok’on shi nayi ba, shi ya ga damar bani, kin ga kuwa bazan k’i amsa ba, an ce shaid’an ne ke maida hanun kyauta baya, gwara in ci rabo na, da nayi aure shi kenan".
Maman su ba tace mata komai ba saboda takaicin ta da ya k’ara kama ta.
"Mama sai na dawo" tana gama fad’ar haka ta fita daga gidan.
Shagon Muri Tela ta wuce inda ta tarar da shagon shike da mutane.
Guri ta nema ta zauna yayin da Muri ke ci gaba da fasa mata kai.
D’inkin ya d’akko ya mik’a mata.
Ganin yadda d’inkin yayi mata kyau kamar yadda take so ya sa ta saki murmushi na farin ciki.
Cikon kud’in shi ta bashi kana ta mishi sallama ta tafi.
Tana dawowa ta shiga d’aki ta gwada d’inkin, kayan ya zauna a jikin ta, haka ta fito tana nuna musu d’inkin.
Su kansu su Fatima sun yaba d’inkin, hakan yasa ta k’ara jin dad’i.
Zuwa tayi ta shire kayan ta adana su a akwati.
Wajen bayan sallar azahar ne ta fito da niyar tafiya gyaran gashi.
Had’uwa suka yi da Baban su inda take sanar dashi za ta gyaran gashi ne.
Kud’i ya ciro aljihun shi ya bata yace ta raba da su Fatima da Amatullah suma su je a musu gyaran gashin.
Amsar kud’in tayi ta mishi godiya ta wuce d’akin Maman su inda ta tarar da su Fatima da Amatullah.
Kud’in ta basu akan su raba in ji Baban sun a gyaran gashi da zanen lalle, ita a ganin ta ko mutum d’aya aka ba ma dubu d’ayan ta mishi kad’an a ce yayi gyaran gashi da dayis, shi yasa ta hak’ura ta bar musu kud’in.
San da ta isa gurin saloon d’in cike yake da mutane, kasancewar ita customer ce yasa mai shagon ta ce ta zauna za ta mata.
Ba a d’au wani lokaci ba aka fara mata zanen lallan, bayan an gama ne aka fara gyara mata gashi.
Khalid ne ya kira ta a waya a lokacin da ake mata gyaran gashi.
"Assalamu alaikum".
"Wa’alaikumus salam" ya amsa mata.
"Kina gida ne?" ya tambaye ta.
"Ba na gida, ina wajen Saloon".
"Ok in an gama miki ki kira ni zan zo in d’auke ki, sai ki kwatanta min gurin".
"In an gama min zan kira ka" tana gana fad’ar haka suka yi sallama.
Ana gama mata ta d’auki wayarta ta kira shi ta fad’a mishi an gama mata gyaran gashi.
Bai d’auki wani lokaci ba, ya bi kwatancen da ta mishi har ya zo shagon saloon d’in.
Kiran ta yayi akan ta fito su tafi.
Tana fitowa ta bud’e d’ayan gefen ta zauna ta hakimce.
Kallon da ke bayyana wani sirri ya jefa mata kana yace "Beauty an gama miki gyaran ko? nasan ba k’aramin kyau zai yi ba kasancewar ke d’in mai kyau ce".
Yadda a kullum Khalid ke yaba mata yasa taji ya kwanta min a rai, ya iya dad’ad’an kalamen da zai kwantar ma da budurwa hankali.
Ido shi ne ya sauka akan hannu ta da yasha zanen lalle, da sauri ya kamo hannun ta yana ganin zanen da aka ma ta, hakan da ta gani ne yasa tayi saurin k’wace hannu ta.
Wayancewa yayi da cewa "Sorry Beauty, kyan lallen ne ya rud’a ni har yasa na ta’ba miki hannu, gaskiya dole ne in biya kud’in wannan gyaran dan nasan ni aka yi ma wa" ya k’arasa maganar yana sakar min mayaudarin murmushi.
Murmushi kawai tayi ba ta ce mishi komai ba.
Haka suka ci gaba da tafiya muna hira mai k’ayatarwa, ta tabbatar had’uwa ta da Khalil alkhairi ne ta yadda yake k’ok’arin faranta mata.
Tun a hanya ta ke tunanin fad’a mishi matsala ta na rashin kayan sallah, sai wata zuciyar ta hana ta akan in tayi haka ta zubar da class d’in ta.
Da haka suka k’arasa gida ya sauke ta ba tare da ta fad’a mishi matsalar ta ba.
Tun da ta koma gida take tunanin mafita ganin gobe sallah amma kaya kala d’aya ta ke dashi, dan ba ta sa na Baban su a lissafi.
Mafitar d’aya zuciyarta ta samo mata shine ta ajin ta a gefe ta fad’a ma Khalil halin da take ciki, tasan shi kad’ai ne zai share mata hawayen ta.
Da wannan shawarar ta samu ta d’akko wayarta ta kira shi ta fad’a mishi ta na neman shi da daddare.
Ya mata alk’awarin zuwa in dai ya samu lokaci.
Wayar da suka yi da Khalid ne yasa ta samu sassauci a halin da take ciki na damuwar kayan sallar da ta sa ma kanta.
Da daddare sai ga Khalid ya kira ta ya sanar da ita zuwan shi.
Kwalliya tayi ta same shi a cikin mota, sanyayyar k’amshin turaren ta da na Khalid ne ya had’e ya ba da wani irin k’amshi mai dad’i.
Kunna musu Ac yayi kafin ya d’aura da cewa "Gimbiya Husna barka da fitowa".
"yawwa Barka dai, ansha ruwa lafiya?".
"lafiya lau, yasu Fatima da su Mama?".
"Suna nan lafiya lau, yasu Momi".
"Tana tanan lafiya, ta ce ma in gaishe ki".
Murmushi tay kana ta d’aura da cewa "Ina amsawa, in ka koma ka ce ina gaishe ta".
"Zan fad’a mata".
Kallon ta yayi da cewa "Azumi ya zo k’arshe, Allah yasa muna da rabon ganin na wata shekarar, Allah ya amsa ibadun mu".
"Amin ya Allah".
"Gani na amsa kira Beauty, na ji kina nema na".
Shiru tayi kamar wacce ke tunani, ita kanta tana tunanin ta hanyar da za ta bi ta fad’a mishi dalilin kiranshi da tayi.
"Why silent Husna" Khalid ya fad’a.
Wannan ita ce damar da ya kamata tayi amfani da ita, maganar kunya ba ta taso ba in dai za ta samu ya mata kayan sallah.
"Daman akan kayan sallah ne, tela bai d’inka min kayan da na kai mai ba, kala d’aya ya d’inka min, gashi kuma gobe ne sallah".
Dariya yayi wacce ta k’ara k’awata fuskar shi ya ce "Tela bai kyauta ma Beauty ba, ni kaina na so in siyo miki kaya, sai nayi tunanin ba lallai ne ki amsa ba idan na kawo, naji kin ce ana miki fad’a idan na miki kyauta, anyway gobe in Allah ya kaimu in an sakko sallar idi zan zo mu je a siya kayan, yanzu dare yayi nasan a gida za a miki magana idan muka je yanzu".
Dad’i ne ya kama Husna da har hakan ya kasa ‘boyuwa a fuskar ta, godiya ta fara mishi tun kan goben tayi.
Shi kuwa tunanin abubuwa da yawa yake kissamawa a ranshi, yana ganin komai na tafiya mishi yadda yake so.
Da haka suka yi sallama dashi akan sai gobe zai zo su tafi.
Tun da ta koma gida ta sake aka ci gaba da hira da ita, a yanzu ji take yi ba ta da wata sauran damuwa.
Washegari ta kasance ranar Sallah, ranar da take zuwa ta musamman ga mutane, kowa ka gani a rananr cikin farin ciki yake, idan kayi duba ga mutane za ka ga sun sanya sababbin kaya, kowa yayi wanka yasa sababbun kayan, sababbun takalma, Gayle, Jaka, hula da sauran su, Za Ka ga mutane na haramar tafiya zuwa idi, a gidaje kuwa za ku ga ana dafe-dafen abinci, wasu na had’a wa da yin snacks ko drinks ga masu hali yayin da in an gama abincin za a aika mak’ota da gidan ‘yan uwa, a ranar za ka ga ana ziyartar ‘yan uwa na nesa da na kusa.
Duk wannan shagalin na kasancewa ne ga wanda Allah ya bashi ikon gani.
Sallah kenan, mai yawan baya, ta tafi ta bar wawa da bashi in ji hausawa.
*(Ni ko ‘yar mutan Paki na ce Allah ka maimaita mana ka kuma amsa ibadun mu)*
Husna ma a ranar cikin farin ciki take, tun bayan da suka gama yin aikin su ta dawo d’aki ta kunna waya.
Sak’on barka da sallah aka dinga turo mata tana amsa wa mutane cikin nishad’i, duba Dp d’in wanda suka sa kayan sallah take kallo tana comment akai, haka ta shiga groups ta gama yaba kwalliyar mutane ana hira kafin ta sauka daga online.
Wanka taje tayi ta d'akko material d'in da Husna ta ba ta tasa, tana jiran zuwan Khalid.
Wajajen misalin k’arfe uku Khalid ya kira Husna ya fad’a mata ta fito su tafi.
Da sauri ta tashi ta shirya ta tsantsara kwalliya irin ta ‘yan matan da suke ji da kan su, kai idan ba ka san asalin Husna ba, zaka iya cewa ‘yar wata attajiri ce ce saboda yadda ta iya d’aukan wanka, ga kaya yadda suke amsar jikin ta, sannan ba laifi tana da nata iya kyan da za ta iya jawo hankalin samari.
Sai a lokacin ta fara tunanin hanyar da za ta bi ta fad’a a gida cewa za su fita da Khalid.
Wata dubara ce ta fad’o mata, hakan yasa ta nufi d’akin Baban su ta sanar dashi za ta gidan su Bilkisu taje ta dawo.
Jin gidan su Bilkisu za ta yasa ya ce ta je, tare da ba da sak’on gaisuwa ga iyayen Bilkisun.
D’akin Mamar su taje ta sanar da ita kana ta fito tana taku d’ai-d’ai har ta iso in da motar take.
Tana shiga ya ja motar suka tafi yayin da ya sa musu cool music.
Husna saboda yadda wak’ar ke mata dad’i yasa take lumshe ido jefi-jefi, Khalid na lura da ita.
A wani had’ad’d’en boutique yayi parking.
Fitowa suka yi suka shiga boutique d’in, mutanen gurin ne suka dinga gaishe da Khalid kasancewar customer su ne.
Kaya ya dinga jidar ma Husna kama kaya ready made, dogayan riguna dasauran kayayyaki, ita abin har mamaki yake ba ta kamar bai san ciwon kud’in ba, sai da ta mishi magana akan kayan sun isa sannan ya daina d’ibar kayan, kud’i ya biya su suka tafi.
Husna ba tasan da wani baki za ta ma Khalid godiya ba, ya mata abin da yasa ta farin ciki.
A gida ya sauke ta tare da mik’a mata ledar da suka yi siyayya, san da zai tafi ne ya mik’a mata kud’in da ya mata alk’awari na gyaran gashi, sannan ya k’ara mik’a mata wasu kud’in yace ta raba ma su Amatullah, yace in ya k’ara dawowa zai bata barka da sallah.
Sallama ya mata ya tafi kana ta nufi cikin gida.
Tana shiga cikin gidan su ta ga su Mamar su da Baban su da su Fatima a zaune a tabarma suna cin abinci, jikin ta ne ya mata sanyi saboda ba taso ta same su a tsakar gida ba, yanzu suna ganin ta da leda zasu tambaye ta wa ya ba ta in ta ce musu Bilkisu ce ba za su yarda ba saboda yawan kayan, In kuma ta ce musu Khaleed ne ya ba ta za su mata fad’a akan me yasa ta amsa ko su ce kayan yayi yawa ta maida mishi.
Mamar su ce ta katse mata tunanin da take yi tace "Lafiya kika tsaya kika k’i shigowa kin tsaya kina bin mu da kallo ko sallama ba ki mana ba".
Sallama tayi ta k’araso inda suke zaune ta musu sannu da gida.
Amsa mata suka yi tare da tambayar ta har ta dawo, ta amsa musu da eh.
Baban su ne yabi ledar da kallo da alama ledar irin ta shago ce idan kayi siyayya ake zuba maka kayan a ciki.
Kallon ta yayi kana yace "Husna wannan ledar da na ganki da ita fa".
Cikin daburcewa ta ce "Eh…am …Baban su Husna… ne ya… bani".
Kowa bin ta yayi da kallo, saboda yadda take magana za kasan ba gaskiya a maganar ta.
Kallon tuhuma Baban su ya mata kana yace "Mu ga ledar".
Mik’a mishi ledar nayi ina jiran jin me zai ce min, na lura kamar ba su yarda da maganar da na fad’a musu ba.
Kallon yawan kayan da ke ciki yayi kana ya juyo da kallon shi gare ni ya ce "Husna ban yarda da maganar ki ba, nasan Baban su Bilkisu zai iya baki kayan amma ba mai yawa haka ba, wannan kayan kana gani kasan shago aka je aka siye su saboda ga tambarin shago na gani".
Ganin ba ta da wata sauran dubara tun da k’arya ta ba ta amsu ba, gwara ta fito ta fad’a musu duk kuwa da fad’an da za su mata.
"Daman Khalid ne ya kawo min".
"Kina nufin wannan mai zuwa a motan?" ya k’arasa maganar da tambayar ta.
"Eh shi Baba" ta bashi amsa a tak’aice.
Ran Baban su Husna ne ya ‘baci saboda a gaji da halin Husna, yayi iya
k’ok’arin shi dan ganin ya inganta tarbiyar ta amma ita kullum hanyar rushewa take yi, ya sha dukan ta da yi mata nasiha akan kai kanta inda Allah bai kai ta ba amma ba ta d’auka.
Cikin fushi ya ce "Husna ke ce babba, amma sai k’annen ki suka fi ki hankali da natsuwa, ke kad’ai ce me irin wannan halin na hange, na zuba miki ido ne akan shi wannan mai zuwa gurin ki a mota in ga iya gudun ruwar ki amma na ga ke ba ki san haka ba, kin san kina da wanda za ki aura amma shine yanzu za ki fara tsayawa da wani dan ki ci kud’in shi, ni da kike gani ina tsayawa inda Allah ya ajiye ni, ba na kallon na sama dani, ina koyi da fad’ar manzon Allah (S.A.W) inda wani mutum ya tambayi manzon Allah (S.A.W) yace *ya Manzon Allah, me zanyi mutane su so ni?, sai manzon Allah (S.A.W) yace mishi ka guji abin hannun mutane, mutane za su so ka*, kin ga wannan hadisin da shi nake koyi shi yasa kika ga ina zaune da kowa lafiya, mahaifiyar ki ma ba ruwan ta da kallon na sama da ita, duk abin da na samu na kawo godiya take yi ta amsa, ga ‘yan uwan ki ma sunyi irin halin mu, amma ke ban san in da ki ka koya wannan mummunan halin ba, tun da abin naki ya zama haka zan ma Salim magana ya turo iyayen shi a sa ranar auren ku, zan fad’a mishi kar ya matsa ma kan shi, duk abin da yake dashi ya kawo, ba zan zuba miki ido ba kina abin da kike so ana ganin kamar ban miki fad’a, A wannan lokacin da muke ciki, duk wanda kika ga yana miki kyauta mai yawa yana da manufar shi a kanki ne, ba kowa ne yanzu yake maka kyauta saboda Allah ba, duk da ba duka ba ne aka taru aka zama d’aya, har yanzu akwai na Allah, ya kamata ki yi wa kanki fad’a akan abin da kike yi".
Ci gaba yayi da cewa "In ba kina son ranki ya ‘baci ba ki maida mishi kayan shi in ya dawo" yana gama fad’ar haka ya tashi ya shiga d’akin shi.
Wani abu ne ya tsaya mata a zuciyar ta, ya za ayi a ce ta maida uban wannan tsadaddun kayan bayan tana ganin kud’in da ya biya, shawarar da zuciyarta ta ba ta shine ta ‘boye kayan, in an kwana biyu a hankali sai ta dinga d’akko kala d’aya ko biyu ta ce Salim ne tasa ya siya mata irin su, ga wani k’arin ‘bacin rai shine sai yanzu da aka ga ta fara zama big girl Baban su zai fito mata da maganar aure, tana ganin aure ba a wannan shekarar za tayi shi ba, sai taci rabon ta, za ta ma Salim magana akan in Baban su ya mishi magana akan bikin su yace a k’ara mishi lokaci dan ba yanzu ta shirya yin aure ba.
Mamar su ce ta kalle ta tace "Husna halin ki daban ne, na lura duk abin da ake fad’a miki ba kya d’auka, kin d’akko wani hali kin d’aura ma kanki wanda ba zai kai ki ko ina ba, kin dai ji abin da Baban ku yace in saurayin naki yazo ki maida mishi kayan shi".
Turo bakin ta tayi ita a dole an ‘bata mata, ta d’auki kayanta ta shiga d’aki.
A ranta kuwa ta k’udurta ba za ta maida ma Khalil kayan shi ba.
Amatullah ta ba kud’i ta siyo mata carton d’in faro da drinks saboda fita kunya idan tayi bak’i.
Su ma ta ajiye musu na gida wanda za su yi amfani dashi.
Da yamma Bilkisu tazo suka sha hirar su, sai da aka kusa kiran sallar magrib sannan ta musu sallama.
Raka ta tayi inda take sanar da ita za ta kawo mata Khalid gobe su gaisa, amsa mata tayi da sai sun zo, nan suka rabu Husna ta koma gida.
Da daddare Salim yazo suka yi wa juna barka da sallah, da zai tafi ne ya bata barka da sallah ya tafi.
Washegari Husna dubarar ta ce ta k’are, ba ta da kayan da za tasa a ranar tun da ta riga tasa wanda Bilkisu ta d’inka mata, dama shi kad’ai gare ta.
Tashi tayi ta nufi d’akin Maman su dake kwance a d’akin ta.
Guri ta samu ta zauna, ta canza fuskar ta zuwa ta tausayi.
"Mama" Husna ta kira sunan ta.
"Na’am Husna" Mamar ta amsa mata.
"Dama jiya ne da Khalid yazo na maida mishi kayan shi ya k’i amsa, yace ko ya amsa bai san me zai yi dasu ba, yace min zai kiyaye tun da gidan mu ba sa so ya min kyauta, ba yadda banyi dashi ba amma yak’i amsa, yanzu kayan su na d’aki, kin ga ajiye kayan bai da amfani dan an ce ba kyau kayi ta ajiyar kaya, Maman dan Allah kuyi hak’uri in sa".
Jin wannan bayanin da Husna ta mata yasa ta yarda da maganar ta, tun da an maida mishi yak’i amsa ya kamata a bar ta tasa tun da ajiyewar bai da amfani.
"Ki je ki sa tun da kin ce yak’i amsa, tun da ajiyewar ma bai da amfani, amma daga yanzu ki kiyaye da amsar abin hannun shi, in Baban ku ya shigo zan mishi bayani".
Dad’i ne ya kama ta ganin k’aryar da tayi ta amsu, dan haka tace "Na gode Mama, zan kiyaye".
Tashi tayi ta shiga d’aki ta tsantsara kwalliya kamar wacce za ta gidan biki, casual make-up tayi wanda ya fito da kyan ta.
Cikin kayan da Khalid ya siyan mata ta d’auki wata doguwar riga mai adon duwatsu a jiki tasa, kayan ya mata kyau kasancewar jikin ta yana amsar ko wani irin kaya.
Wayarta ta d’auka ta dinga d’aukar selfie, style kala-kala ta dinga yi irin na ‘yan mata masu yayi.
Tana gama d’aukar hoton ta dinga watsa wa a social media, sai comment ake yi, hakan yasa kan ta ya k’ara girma jin yadda ake fad’an tayi kyau, ita kuma sai reply ta ke musu da ta gode, haka ta d’au lokaci tana chat kafin daga baya ta sauka daga online.
Khalid ya kira wayar ta akan ta shirya, zai zo su fita outing da ita.
Tun da Khalid ya kira ta take jiran zuwan shi, dan dama tana son zuwa irin wajen shak’atawa, tasan had’uwar ta da Khalid zai sa ta k’ara wayewa, mutane su dinga kallon ta a babbar yarinya.
Kiran shi tayi akan in yazo kar ya shigo layin su, ya tsaya a farkon layin su, za tazo ta same shi.
D’akin Baban su taje ta nemi izinin shi akan za ta gidan k’awar ta, gargad’in ta yayi akan kar ta dad’e in ta je.
Dawowa d’aki tayi tana zaman jiran shi, can sai gashi ya kira ta akan ya k’araso tazo ta same shi a inda tace ya tsaya.
Kasancewar daman tayi kwalliya yasa ba ta sake yin wata kwalliyar ba, powder kawai ta shafa da d’an jan baki, ta d’akko turare ta fesa, sannan ta d’akko takalmin da Salim ya siyo mata tasa.
D’akin Mamar su ta shiga ta fad’a mata za ta fita ta tambai Baban su.
A hankali ta dinga tafiya, salon tafiyar ta kamar mai yanga, a haka har ta k’arsa inda motar Khalid d’in take.
Bud’e motar tayi ta shiga ya ja motar suka tafi.
Wak’ar Bob Marley ce ke tashi a hankali.
Kallon ta yake yana isar mata da sak’o da irin kallon nashi, ganin kallon yayi yawa yasa tace "Khalid wannan kallon fa".
Dariya yayi kana yace "Beauty you a special, komai naki mai kyau ne, duk abin da kika sa kyau yake miki, irin wannan kwalliyar taki ta na sa in k’ara son ki, kayan sun miki kyau sosai".
Abin da yasa ta ke jin dad’in kasancewar ta da Khalid shine yadda a ko wane lokaci yake yaba mata, hakan yasa take mutunta shi.
Cikin salon ta tace "Na gode" ta fad’a a hankali.
Suna cikin tafiyar ne ya kamo hannun ta, d’aura fukskar ta alamar ba ta son abin da ya mata, lura da hakan da yayi ne yasa ya sakar mata hannu yana murmushi.
Wani tsadadden gurin shak’atawa ya kaisu, gurin da ganin shi kasan na ‘ya’an manya ne.
Parking yayi a gurin da ake ajiya motoci kana suka nufi wani guri na musamman.
Gurin siyar da kayan k’walama kama daga Snacks da drinks da abinci suka tsaya.
Sai da ya siyan musu abin da za su ci kana suka nemi k’ebantaccen guri suka zauna.
Hira suke yi mai
k’ayatarwa a tsakanin su.
Tsadaddun kalamai yake furta ma Husna na irin son da yake mata da tabbatar mata da zai iya mata komai saboda irin son da yake mata.
Haka suka ci gaba da zama a gurin suna hirar su cikin nishad’i, a cikin hirar ne ya kalli Husna da mayaudarin kallon shi yace "Husna ina ganin mun zama d’aya da bai kamata ki yi tunanin zan iya cutar dake ba".
"Ya za ayi kace haka Khalid, nasan kai masoyi na ne ba za ka cutar dani ba".
"To in har kin yarda bazan cutar dake ba, me yasa in na rik’e miki hannu kike k’wacewa?".
Shiru tayi kamar ba ta ji tambayar da ya mata ba.
"Kin ga kenan zargi na ya tabbata, kina nufin zan iya cutar dake kenan…".
Katse shi tayi da cewa "Ba haka ba ne Khalid, abin da yasa ka ga ina k’wace hannu na saboda na ga kamar bai kamata ba, kasan shi kad’an yake jira ya rinjayi mutum, kayi hak’uri in hakan da nake yi yana ‘bata maka rai".
K’asaitaccen murmushi yayi kana yace "Ba komai Husna, bazan iya fushi dake ba, amma ina so ki sani ni mutum ne mai son yin social life, ina tafiya ne da zamani, ya kamata ki fahimci hakan ba wai ki dinga yin abubuwa kamar ba ki waye ba, alhalin ana kallon ki an san kan ki ba a duhu yake ba".
Shiru tayi tana tunanin abin da Khalid ya fad’a mata, ko da take son yin rayuwar jin dad’i ba ta son yin abin da mutuncin ta zai zube, za ta samu ta lalla’ba shi ta bashi hak’uri dan ba ta son yayi fushi da ita, hakan zai sa ya iya rabuwa da ita, ba za taso hakan ta kasance ba ganin yadda yake kasha mata kud’i, idan tayi duba da kud’in da yake kashe mata tun daga san da suka had’u har zuwa yau.
Kallon shi tayi da irin kallon da yake so tace "kayi hak’uri Khalid, zan kiyaye".
Yalwataccen murmushi ya mata yace "Ba komai".
Haka suka ci gaba da hira kafin su mik’e da niyar tafiya.
Siyayya ya mata a gurin na kayan ciye-ciye da drinks kana suka shiga mota suka tafi.
Suna cikin tafiyar ne ta ce mai za su biya gidan su Bilkisu, fad’a mishi sunan layin tayi, suna zuwa layin ta nuna mishi gidan.
Ba ta shiga gidan ba ta kira ta a waya ta sanar da ita suna k’ofar gidan su.
Fito wa tayi cikin shigar alfarma ta k’araso inda suke.
Fitowa suka yi daga motar, Bilkisu ta gaishe da Khalid ya amsa mata cikin sakin fuska.
Husna ce ta gabatar mata da Khalid, sannan ta gabatar da Bilkisu gurin Khalid.
Sun d’an yi hira cikin mutunci duk da Bilkisu ba ta wani saki fuskar ta ba, dan ita hankalin ta yafi kwanciya da Salim.
Da za su tafi ne ya ba Bilkisu kyautar kud’i a matsayin barka da sallah, k’in amsa tayi tace ta gode ta musu sallama ta shige gida, sanin ba amsa za tayi ba yasa Husna ta amsa ta bi ta cikin gidan ta nuna ‘bacin rai akan k’in amsan da tayi, ganin ranta ya ‘baci ne yasa Bikisu ta amsa ta mata godiya.
Tana fitowa ta fad’a mishi ta amsa, shiga tayi suka nufi layin su, cewa tayi ya sauke ta ba sai ya k’arasa da ita gida ba.
Nan ta mishi godiya suka rabu.
Tun daga ranar, Husna sai ta nemi izini gurin iyayen ta akan za ta gidan k’awayen ta yawon sallah, sai Khalid ya zo farkon layin su ya d’auke ta ya kaita gidan k’awayen ta ko su je wani gurin na shak’atawa, shi yasa Husna taji dad’in wannan sallar saboda tazo mata a yadda take so.
Sabon salon da Khalid ya fito mata dashi shine bayan rik’e mata hannu da yake yi sai ya fara ta’ba ta, ga fingering da yake yi da hanun ta, akan shi suke samun sa’bani saboda ta nuna mishi ba ta so, hakan yasa rage abin da yake mata.
Bilkisu ma ta zo gidan su Husna, ta nuna mata kayan da Khalid ya kawo mata da irin kyautar da yake mata duk ta fad’a mata.
Bilkisu ma ta mata fad’a akan ta rage amsar kayan shi, kyautar da yake yi mata tayi kyau.
Nan ma sai da suka hau sama da Husna akan wai ta lura daman ba son tarayyar su da Khalid take yi ba.
Haka suka rabu Husna na ta k’orafin ta ga Bilkisu.
San da Salim yazo take fad’a mishi in mahaifin ta ya neme shi da ya turo iayen shi a sa ranar auren su ya ce a k’ara mishi lokaci, ya tambae ta dalilin ta nayin haka, ta kawo mishi wasu uzururruka wanda bai gamsu dasu ba, yasa a ranshi zai jawo hankalin ta a hankali har ta amince ya turo.
Haka kuwa aka yi, san da Mahaifin Husna ya same shi akan ya turo iyayen shi ayi maganar sa rana a nemi izinin a d’an k’ara mishi lokaci, Baban su Husna ya amince mai da hakan.
Had’uwar Khalid da Husna yasa ta k’ara wayewa, yana kai ta gun shak’atawa lokaci-lokaci in baida aiki.
A kyautar da ya mata har da waya ya canza mata k’irar infinix hot 5 mai tsada, hakan yasa Husna ta k’ara d’aukar kan ta a mai tsada.
Duk iya yadda Salim ya nuna ‘bacin ran shi akan tarayyar su da Khalid hakan bai sa ta rabu dashi ba, ganin yadda suke yawan samun sa’bani da ita yasa ya rage zuwa gurin ta zance.
Yau ta kasance ranar lahadi, Khalid bai da abin yi, shi yasa ya kira Husna akan ta shirya za su fita.
San da yazo kiran ta yayi ta fito suka tafi, yau ma gurin shak’atawa yakai ta kana suka shiga mota.
A yadda ta zata daga gun shak’atawar gida zai kai ta, sai ta ga akasin haka.
Zoo road taga sun nufa, kallon shi tayi ta tambaye shi gun wa za su a unguwar.
Sanar da ita yayi gidan shi za su zai d’au wani abu ne.
Ba ta ce mishi komai ba, amma fuskarta ta nuna ba taso zuwa gidan ba.
Parking yayi a wani madaidaicin gida mai ban sha’awa, horn yayi mai gadi yazo ya bud’e musu.
Gidan ya k’awatu da shuke-shuke wanda hakan ya k’ara ma gidan kyau.
Fito wa suka yi ya fara tafiya yayin da Husna ke bin shi a baya.
Bud’e musu kofar yayi suka shiga.
Kallon fallon tayi yadda ya k’awatu da kayan alatu irin na zamani, gaskiya falon ya mata kyau.
Guri ta nema ta zauna ta na k’ara bin falon da kallo.
Wata hanya ya bi ya shiga wani d’aki, sai da ya d’an d’auki lokaci a ciki kana ya fito ya kalle ta ya ce "Sorry Husna na barki ke kad’ai ko, yanzu zan zo mu tafi".
Murmushin yak’e kawai tayi dan zuciyar ta ba ta yarda da biyo shi da tayi ba.
"Plss Khalid ka d’an yi sauri, ka ga kar a min fad’a a gida, ga kuma yamma ta fara yi".
Wani k’asaitaccen murmushi yayi ya ce "Yanzu nan kuwa Beauty zan zo mu tafi, bari in d’an kawo miki drinks ki sha, kar Beauty ta ce na mata rowa".
Murmushi ita ma ta maida mishi ba bare da tace komai ba.
Kitchen ya nufa ya d’akko fanta da coke ta gora, bud’e gorar fantar ya yi, wani kwayar magani ya zuba a ciki ya girgiza ka na ya rufe ya d’akko glass cup d’in ya dawo falo.
Ajiye mata yayi akan center table ya zauna.
Coke ya d’auka ya fara sha, ganin Husna ba ta d’auka ta sha ba yasa ya ce "Husna ki sha mana, kina abu kamar bak’uwa, ko da yake nag a hankalin ki ayi gida, bari in zo mu tafi".
Dan Khalid ya ga kamar da wani abu idan ba ta sha ba, shi yasa ta bud’e fantar ta tsiyaya a cup ta fara sha.
Sai da tasha rabin cup sannan ta ajiye kofin.
Tun da Khalid yaga tasha ya tashi ya shiga d’aki.
Bayan wasu ‘yan mintuna Husna ta ji jikin ta ya saki, d’akin na juya mata, ga wani irin bacci ne yake fisgar ta, hakan yasa ta jingina da kujera.
Sai da aka d’au kusan mintuna 10 Khalid ya fito falon, ganin Husna tayi nisa a baccin ta yasa ya saki wani mayaudarin murmushi.
Hannun ta ya kama ya ga ba ta motsa ba, hakan yasa ya d’auke ta yai bedroom da ita.
Kayan jikin shi ya cire kana ya hau gadon ya fara cire ma Husna kayan jikin ta.
Duk wannan abin da Khalid ke yi Husna ba ta motsa ba, da alama maganin da yasa mata mai k’arfi ne.
*Ni da nake la’be ta bayan slicing window ina kallon duk abin da Khalid ke yi yasa na fara tunanin me zai ma Husna?*
*Nasan kuma readers tambayar da ke ranku kenan*
*SILAR KAYAN SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘👘👘
*A SHORT STORY*
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽
Maryamahmadpaki.blogspot.com
Facebook: Kainuwa Writers Association
36-40
Bayan ya cire mata kayan jikin ta ne ya tsaya yana kallon kyakkawar surar ta, jikin da ya dad’e yana marmari, yau ga dama ya samu da zai cika burin shi, wata irin sha’awar Husna ce ta mishi dabaibaiyi.
Ba tare da ‘bata lokaci ba ya fara aika mata sak’onni a sassan jikin ta a ko ina, haka Khalid ya ci gaba da sarrafa Husna yanda yake so ba tare da yaji tausayin ta ba, haka Khalid ya ci gaba da abin da ranshi yake so da Husna har sai da ya cika burin shi na amsar budurcin Husna.
Khalid a lokacin da ya keta ma Husna mutuncin ta hakan yai daidai da wani matsanancin zafi da taji a k’asan ta wanda yasa ta farka wa daga nannauyan barcin da ya d’auke ta.
Wata irin k’ara ta saki lokacin da ta ji wani zafi ya ziyarce ta a k’asan ta.
Bud’e idon da tayi ne ta ganta ba kaya yasa tayi saurin janyo wani bargo ta rufe jikin ta dashi.
D’akin ta bi da kallo kafin ta juyo da kallon ta ga Khalid dake zaune a kan gadon.
Shi kuwa Khalid in ban da murmushi ba abin da yake yi saboda yadda ya zama shine namiji na farko da ya san ta a ‘ya mace, gashi kuma irin kalar matan da yake so yana mu’amala dasu ne.
A hankali ta tashi ta zauna yayin da zafin da take ji ya ci gaba da ziyartar ta.
Wani irin kuka ta fashe dashi mai ban tausayi ga duk wani mai saurare.
Cikin kuka ta kalli Khalid ta ce "Khalid me ya kawo ni d’akin ka, ka fad’a min me ka min".
Ba tare da damuwa ba Khalid ya ce "Cool down Husna, I will explain to you".
Cikin tsawa Husna ta k’ara cewa "Khalid ka min bayanin abin da ka min na ce".
Shi kanshi ya tsorata da halin da Husna ta shiga, gashi tausayin ta ya kama shi ganin shine wanda ya fara sanin ta a ‘ya mace.
A hankali ya fara da cewa "Husna am sorry how i treat you, i don’t mean to hurt you, am sorry to say, na yi making love dake ne".
Husna na jin wannan bayanin da Khalid ya mata ta tabbatar da zargin da take yi na Khalid yayi disvergin d’in ta.
Birgima ta fara yi akan gadon har ta gangaro k’asa taci gaba dayi, a lokaci guda kuwa wani irin kuka mai tsuma rai take yi.
Ba abin da take cewa sai "Wayyo Allah na, Na ga ta kaina, Khalid me nayi maka da za ka min sakayya da mummunan sakamako irin wannan, Allah ka saka min, Allah ka bi min hakk’i na akan abin da Khalid ya min na keta min mutunci na da yayi".
Kalamen da Husna ke fad’a akan shi ne ya ‘bata mishi rai, yana ganin wannan rainin hankali ne gurin Husna za ta mishi, dan haka cikin ‘bacin rai ya kalle ta ya watsa mata wani kallo kafin ya d’aura da cewa "Husna akan me za ki dinga min wannan addu’ar, saboda kawai nayi making love dake kike min wannan shouting d’in, Ina ganin kin waye ashe ke bagidajiya ce ban sani ba, daman ba ki san me duniya ke ciki ban a wayewa, yanzu baki san akwai irin wannan affairs d’in ba tsakanin Saurayi da budurwa".
Cikin muryar ta da ta fara dusashewa saboda kukan da tayi ta ce "Akan me Khalid za ka aikata min haka, dama duk son da ka ke ik’irarin kana min na k’arya ne".
Wani irin mayaudarin murmushi Khalid ya yi kana ya kalli Husna ya ce " Husna sai yanzu na tabbatar da ba ki da wayau, yanzu ba ki san do me i do you ake yi ba tsakanin saurayi da budurwa, wanda hausawa su ke ce ma *ban gishiri in ba ka manda*, abin nufi shine kina nufin duk hidimar da na miki ta tashi a banza ba tare da nima na ci ribar hidimar da na miki ba".
Jin wannan maganar da Khalid ya fad’a ma ta yasa tayi saurin tsayar da kallon ta tana bin shi da kallon mamakin abin da ya fad’a mata.
Fahimtar hakan da yayi ne yasa ya ci gaba da cewa "Husna duk wani saurayi da kika ga yana wa budurwar shi hidima ko yana kashe mata kud’i da ya wuce misali to yana da nufin shi akan yarinyar, ba wai na ce miki haka wasu mazan su ke ba, ni da ki ke gani zan iya kashe ma mace ko nawa ne in dai nima za ta dinga sa ni nishad’i, in yanzu na ce ki yi lissafin abin da na kashe miki tun azumi zuwa kayan sallar da na miki nasan na had’a ki da aiki saboda yawan kud’in, boutique d’in da na kai ki na siya miki kayan sallah ko shi kad’ai ya isa misali, ban da sauran hidimar da na miki da sallah har zuwa wucewar sallah, Husna ni da ki ke gani zan iya kashe ma budurwa ko nawa ne in dai za ta dinga faranta min, in har za ki ci gaba da bani had’in kai, ni kuma zan kasha miki ko nawa ne" ya k’arasa maganar yana sakar min shu’umin munrmushi.
Tun da Khalid ya fara wannan maganar hawaye ne ke zubo mata daga ido, maganganun da Baban su ya fad’a mata lokacin da yake mata fad’a akan kayan da Khalid ya kawo mata ta amsa, su suke mata yawo kamar yanzu yake fad’a mata inda ya ce mata "A wannan lokacin da muke ciki, duk wanda kika ga yana miki kyauta mai yawa yana da manufar shi a kan ki ne, ba kowa ne yanzu yake maka kyauta saboda Allah ba, duk da ba duka aka taru aka zama d’aya ba, akwai na Allah yar yanzu, ya kamata ki yi ma kan ki fad’a akan abin da ki ke yi" tana gama tunano wannan nasihar da Baban su ya mata ta k’ara fashewa da wani kukan mai tattare da danasani.
"Me yasa ba ta d’auki nasihar da Baban su ya mata ba, da wadda Maman su take nuna mata illar amsan kayan Khalid da take yi, Me yasa ba ta d’auki fad’an da Bilkisu take mata akan hidimar da Khalid yake mata ta yi yawa, Me yasa lokacin da Salim ya nuna mata fushin shi akan ta rabu da Khalid me yasa ba ta hak’ura dashi, Me yasa lokacin da Fatima da Amatullah ke mata nasiha ba ta d’auka ba, maimakon haka ma sai tayi ta musu fad’a, Me yasa ba ta hak’ura da abin da Baban su da Salim suke mata ba, sai ma kushewa da take yi, Me yasa ba ta tsaya akan mai son ta da gaskiya wanda kowa ke mata sha’awar shi kuma ita ma take son shi".
"Me yasa san da kowa ke mata fad’a akan halin ta na son burge mutane, da hangen na sama da ita, da rashin zama a inda Allah ya ajiye ta bata yi karatun ta natsu ba, sai a yanzu da lokacin da ya k’ure mata ta gano illar abin da halin ta ya jawo mata na rasa mutuncin ta na ‘ya mace wanda ba zai ta’ba dawowa ba".
A fahimtar bayanin da Khalid ya mata ta fahimci cewa *SILAR KAYAN SALLAH* shi ya jawo mata rasa mutuncin ta na har abada wanda ba za ta daina kuka ba akan abin da Khalid ya mata.
Duk wannan danasanin ta riga tayi shi ne a lokacin da ya k’ure mata, sai dai tana ganin a yanzun ma tana da damar da za ta gyara halin ta duk da martabar da take tak’ama dashi na ‘ya mace ya riga ya zube.
Lokaci d’aya taji wani tsanar Khalid ya kama ta, dama can ba wai ta kamu da son shi ba ne, tana ganin abubuwan da yake mata a matsayin kyauta yasa take ganin mutuncin shi, ba za ta ta’ba mantawa da tabon da Khalid ya dasa mata a zuciyar ta ba.
Murmushin takaici tayi ta watsa mishi wani irin kallo kana ta ce "Khalid a yanzu na k’ara fahimtar inda rayuwa take, A dalilin had’uwa dakai Khalid yasa na shiga wata makaranta wanda na d’auki darussa da dama a cikin ta, na fahimci ba kowa ne yake maka kyauta saboda Allah ba sai dan ya samu ya cin ma burin shi, ni kaina nasan har da laifi na da na tsinci kaina a halin da nake ciki a yanzu, sai dai Khalid ka min abin da ba zan ta’ba mantawa har k’arshen rayuwa ta ba, ba abin da zan ce maka tsakani na da kai sai dai in ce Allah ya min sakayya akan abin da ka min, na bar ka da Allah".
Tana gama fad’ar haka ta k’ara sautin kukan da take yi, kukan da tayi ne yasa idon ta ya k’ak’ance ya canza kala zuwa ja.
A hankali ta tashi dan yadda take jin jikin ta na mata ciwo da rashin k’arfin da take ji a jikin ta, ga zazza’bin da yake so ya kama ta ba ta jin za ta iya motsa jikin ta yadda ya kamata.
Kayanta ta d’auka tana sawa yayin da taci gaba da kukan da take yi.
Shi kuwa Khalid duk wannan maganar da Husna ta fad’a mishi bai d’au hakan da wani abu ba, yana ganin taimakekeniya ne tsakanin shi da ita, sun yi trade by barter ne, ya mata kyauta da take so ta ji dad’in hakan da ya mata, shi kuma yayi amfani da jikin ta wajen samun natsuwa shi ma yaji dad’i.
Tana gama sa kayanta ta fara tafiya a hankali saboda yadda take jin jikinta ta fito falo.
Khalid ne ya biyo bayan ta da ruwa a glass cup da magani a hannun shi.
Samun ta yayi ta rataya Jakarta ta fara tafiya.
Bin ta yayi ya kira sunan ta "Beauty".
Kamar ba da ita yake yi ba, sai ma tafiyar ta da ta ci gaba da yi.
Ganin hakan ne yasa yayi sauri ya sha gaban ta, cikin lallashi ya ce "Plsss Husna ki tsaya ki sha magani ki yi wanka, in dai kika fita a haka kika tafi gida za a iya fahimtar halin da kike ciki, wannan abin da na miki ba nayi ba ne dan in cutar dake, ya kamata ki gane yanzu zamani ya canza, bai kamata ki sa kanki a wannan halin ba na damuwa ba".
A yanzu ne ta k’ara fahimtar Khalid irin mazan nan ne masu ‘bata ‘yan mata ta hanyar kashe musu kud’i.
Duk da tana da buk’atar yin wankan da shan magani ko ta samu sauk’i a jikin ta amma hakan ba zai sa ta k’ara wani lokaci a wannan bak’in gidan ba, gani take yi gara kowa ya fahimci halin da take ciki akan ta tsaya ta sha maganin da Khalid ya kawo mata.
Gani take yi in ta tsaya mishi wata maganar kamar k’ara wani bak’in cikin za ta k’ara haddasa ma kanta.
Tafiya taci gaba da yi ba tare da tace mai komai ba.
K’ara biyo ta yayi a karo na biyu ya mik’o mata kofin yana lallashin ta.
Amsar kofin tayi ta watsa mishi ruwan da ke cikin kofin kana ta wurgar da kofin ya fashe.
Fita tayi daga gidan ta fara tafiya kasancewar ba abin hawa a unguwar da Khalid su ke ganin yadda garin ya fara duhu, sai da ta d’an yi tafiya sannan ta tari keke- napep ta hau.
WANENE KHALID?
Khalid Bashir d’a ne ga Alhaji Bashir da Hajiya Maimunatu, haifaffen garin kano ne, Mahaifin shi d’an kasuwa ne da yake yin kasuwancin ci tsakanin gida Nigeria da k’asashen waje, mahaifin Khalid shahararre ne a ‘bangaren kasuwanci.
Khalid ya taso cikin gata saboda shi kad’ai iyayen shi suka haifa, iyayen shi sun mishi gatan da ya janyo rugujewar tarbiyar shi, a na haka suka tura shi karatu k’asar waje Maleshia dan yin degree d’in shi akan Banking & Finance.
A can tarbiyyar shi ta k’ara ta’bar’barewa kasancewar abokan da ya had’u dasu, duk da Khalid irin masu baiwar nan ne da ake ce ma sharp learner hakan yasa bai samu matsala ba ta ‘bangaren karatun shi, sai neman ‘yan mata in har ya k’yasa, zai kashe ma budurwa ko nawa ne, daga baya sai ya cin ma burin shi ta hanyar keta mata mutuncin ta, da wannan Khalid ya k’ware har ya gama karatun shi ya dawo gida Nigeria yaci gaba daga inda ya tsaya.
Yanzu haka yana aiki a wani Babban private company, shine Accountant a kamfanin, haka kuma shi yake jan ragamar kasuwancin mahaifin san a nan gida Nigeria.
Tun san da yaga Husna yaji ta kwanta mishi a ranshi, irin ‘yan matan da yake da yake so yana mu’amala dasu, hakan yasa ya biyo ta ya mata magana har ya samu ta kwatanta mishi gidan su, da wannan damar ya samu ya dinga mata kyauta har ya samu abin da yake so a jikin ta.
Ci gaban labarin
Layin su Bilkisu ta ce ya sauke ta, dan tasan in dai ta je gida a wannan halin, za a iya fahimtar halin da take ciki.
Tana sauka ta k’arasa gidan su Bilkisu ta shiga.
San da ta shiga falon su Bilkisun ba kowa sai mai aikin su, tambayar ta tayi ina Bilkisu take, ta fad’a mata tana d’akin ta.
Hakan yasa ta wuce d’akin Bilkisu.
Tana shiga d’akin ta fad’a kan gado ta k’ara fashewa da wani kukan wanda yayi daidai da fitowar Bilkisu daga toilet d’in dake cikin d’akin.
Da sauri ta k’araso gurin da Husna ke kwance ta fara girgiza ta tana cewa "Husna lafiya na ganki da wannan lokacin kina kuka".
Maimakon ta ba Bilkisu amsa sai ma wani kuka da ta k’ara fashewa dashi.
Hakan ya k’ara d’aga ma Bilkisu hankali.
Cikin lallashi Bilkisu ta ce "Pls Husna for the sake of Allah ki daina kukan nan haka, pls ki fad’a min abin da ya sameki ki ke kuka, nima kin ga hankali na ya tashi".
Cikin dashewar murya ta ce "Bikilkisu ki taimake ni, ke kad’ai ce za ki iya rufa min asiri".
Jin wannan maganar da Husna take yi yasa Bilkisu ta fara hawaye duk da ba ta san me yake damun Husnan ba, yanayin ta da ta gani ne tasan tana cikin wani hali.
Cikin rawar murya ta ce "How can I help you Husna bayan ba ki fad’a min abin da yake samun ki ba, dan Allah Husna in har kin yarda dani ki fad’a min what’s wrong with you".
Rawar jikin da ta ga Husna nayi ne yasa ta fahimci kamar ba ta da lafiya.
Hannunta tasa ta ‘taba jikin Husna wanda taji ya rufe da zafi alamar zazza’bi ne ya rufe ta.
"Me ya same ki Husna, na ji zazza’bi ne a jikin ki?" Bikisu ta tambaye ta.
"Ban da lafiya Bilkisu, ki taimake ni da paracetamol in sha" Husna ta fad’a cikin rawar murya.
Da sauri Bilkisu ta tafi first aid box ta d’akko paracetamol da ruwa a kofi ta nufo inda Husna take kwance tana faman rawar sanyi.
K’arasowa tayi ta zauna akan gadon, filo ta d’akko ta jingina mata a jikin gadon.
Tashi tayi ta jingina da gadon tana maida numfashi a hankali alamar zazza’bin ya mata mugun kamu.
Maganin da ruwa ta mik’a mata ta amsa tasha.
Bilkisu kuwa tarin tambayoyi ne suka cushe mata game da halin da Husan ke ciki.
"Sannu Husna, Allah ya baki lafiya" Bilkisu ta fad’a cikin tausaya wa.
"Amin" ta amsa a tak’aice.
Tashi tayi taje ta d’ebo mata abinci ta kawo mata.
Duk yadda Bikisu ta matsa mata akan taci abincin kasa ci tayi saboda halin da take ciki, ba yadda Bilkisu ba tayi ba amma tace ta k’oshi ba za ta iya ci ba.
Haka Bilkisu ta tashi ta k’ara had’o mata kakkauran shayi wanda yasha madara da milo a ciki.
Ba irin lallashin da Bilkisu ba ta yi ma Husna akan tasha shayin ba amma shima tace ta k’oshi, ganin yadda Bikisu ta d’aure fuska ne alamar tayi fushi yasa ta amshi shayin, ko da ta fara shan shayi ji tayi kamar tana shan magani saboda yadda bakin ta ya mata d’aci, kad’an tasha ta ajiye sauran ta jingina da filon.
Kallon Bilkisu tayi ganin yadda ta zuba mata ido tana nazarin ta, kallon da take mata na nuna alamar tambayoyi ne a ranta.
"Bilkisu ki taimaka min da ruwan zafi zan yi wanka ne" Husna ta fad’a a hankali.
"Akwai ruwa a water heater, bari in tarar miki" Bilkisu ta fad’a tana nufar toilet d’in.
Dawowa tayi ta sanar da ita ta had’a mata ruwan.
A hankali Husna ta tashi ta cire kayan jikinta ta d’aura tawul a jikin ta, ta d’auki hijab d’in ta tasa ta nufi band’akin.
San da ta shiga cikin ruwan ne taji wani azababben zafi ya ziyarce ta wanda yasa ta sakin ‘yar k’aramar k’ara.
Da k’yar ta samu ta zauna a cikin ruwan duk da azabar da take sha.
Bayan ta d’aki mintuna a cikin ruwan ne ta canza wani ruwan tayi wanka, sai da ta gama wankan ne tayi wankan tsarki ta d’auro alwala ta fito kasancewar taji har an shiga sallah a wasu masallatan.
Fitowar ta daga band’akin yayi daidai da shafa addu’ar da tayi bayan ta idar da sallar Bilkisu tayi, a hankali ta fara tahowa ta zauna a kan gadon.
Bilkisu kuwa tun da Husna ta fito daga band’aki take bin ta da kallo, gani tayi tafiyarta ta canza, gashi a hankali take tafiya kamar wacce taji ciwo.
"Husna me ya same ki na ga tafiyar ki ta canza, ko ciwo kika ji?" Bilkisu ta tambaye ta.
Jin wannan tambayar da Bikisu ta mata ya k’ara ta da mata da tabon dake cikin zuciyar ta, hawaye ne ya fara gangaro wa daga idanun ta.
Bilkisu kuwa wacce tun zuwan Husna ta rasa kwanciyar hankalin ta, saboda ba ta san me yake damun Husnan ba.
Cikin lallashi Bilkisu ta ce "Husna dan Allah ki daina wannan kukan, kin ga yanda idanun ki suka koma kuwa, tuntuni nake tambayar ki abin da ya ke damun ki, ni kaina na rasa natsuwa ta saboda halin da kike ciki".
Wata ajiyar zuciya Husna ta sauke kana ta kalli Bilkisu ta ce "Zan fad’a miki abin da ke damu na Bilkisu saboda nasan ke me rufa min asiri ce, na yarda dake, bari in yi sallah sai in fad’a miki, sai dai yanzu ki taimaka min da wani zanin in yi sallah dan bazan iya yin sallah da nawa ba".
Tashi Bilkisu tayi ta d’akko mata wata doguwar riga ta ba ta tasaka ta tada sallah.
A daddafe ta idar da sallar tayi addu’o’inta ta jingina da jikin gadon.
Kallon Bilkisu tayi ganin yadda ita ma yanayin ta ya canza, hakan yasa ta k’ara yadda da Bilkisu amininyar arzik’i wacce za ta iya rufa mata sirrin ta.
"Bilkisu na d’aga miki hankali ko, ki yi hak’uri, yau wata mummunar k’addara ce ta hau kaina wacce ba za ta ta’ba ‘bace min ba…".
Da sauri Bilkisu ta katse ta da cewa "Wannan wace irin k’addara ce haka Husna da tasa ki a wannan halin".
"Bilkisu dan Allah ki rufa min asiri, na yarda dake ne shi yasa ko gidan mu ban je ba na taho nan dan nasan ba za ki ci amana ta ba".
"In Allah ya yarda bazan baki kunya ba Husna, mun riga mun zama ‘yan uwa".
A hankali Husna ta da’ura da cewa "Husna a yau Khalid ya min abin da ba zan manta ba, a yau ya amsar min abin da yake da matuk’ar mahimmanci a gare ni a matsayina na ‘ya mace, a yau ya raba ni da k’imata ta ‘ya mace, a yau ya bar min tabon da ba zai warke ba, a yau ya barni da zargin da duk namijin da ya aure ni zai dinga min kenan, a yau ne kuma ya k’ara fahimtar dani abin da mutane ke nuna min ban d’auka ba sai a yau na d’auka".
Ci gaba tayi da cewa "Bilkisu kin san me ya min?".
Girgiza kai kawai Bilkisu tayi saboda ta k’osa Husna ta fad’a mata abin da Khalid d’in ya mata da yasa ta a wannan halin.
Gauron numfashi Husna tayi kana ta ce " Ba komai ya min ba illah fyad’e".
Da sauri Bilkisu ta d’ago ta kalle ta dan ta gasgata maganar da taji Husna ta fad’a mata.
Kallon tuhuma ta bi ta dashi amma ba tace mata komai ba.
Fahimtar hakan da Husna tayi ne yasa ta nisa kana ta ci gaba da cewa "Nasan za ki yi zargin ko da had’in kaina hakan ya faru, ke kanki Bilkisu shaida ce akan yadda nake tsare kaina, yayi amfani da dubarar shi ne ya kai ni gidan shi bayan mun dawo daga outing akan cewa zai je ya d’auki wani abu ne, bayan mun je ya kawo min fanta ya bani nasha, tun daga wannan fantar da nashi ban k’ara sanin halin da nake ciki ba sai da mai aukuwa ta auku, Bilkisu Khalid ya cuce ni".
Ta k’ara fashe wa da wani kukan, domin ji take yi kamar yanzu abin ya faru.
Cikin kuka taci gaba da cewa "Khalid ya raba ni da abin da zan yi tunk’aho dashi a gidan miji na, nasan ban da sauran wata daraja ga duk namijin da yasan abin da ya same ni, nasan ba komai ya ja min haka ba sai rashin godiyar Allah da ba nayi akan duk abin da ya min, da rashin tsayawa in duba ni wacece, da son burge mutane da kuma hangen na sama dani duk shi ya jawo min domin shi kanshi Khalid d’in ya fad’a min abin da yasa ya aikata min haka, yace trade by barter muka yi ni dashi, ya min kyauta masu tsada, shima ya amshi abu mai tsada a jiki na, ya nunar min da cewa kud’in da ya kashe min tun daga azumi ba zai lissafu ba bare a je ga Kayan sallar da ya min, haka ya fahimtar dani dalilin k’ara shiga na wannan halin shine *SILAR KAYAN SALLAH* shi ya k’ara jawo min fad’a wa wannan halin da nake ciki, Bilkisu me yasa lokacin da kuke fahimtar dani akan gode ma Allah ban fahimta ba, Me yasa ban yi koyi da kyawawan halayen ki ba, na tabbata in Baban mu da Maman mu su ka san halin da nake ciki sai sun yi tur da hali na, saboda sun sha nuna min illar abin da hali na zai janyo min in dai ban gyara halaye na ba, gashi yanzu ina yin danasani wacce ba ta da amfani dan ba za ta goge min bak’in cikin da nake ciki a yanzu ba, ina ma baya za ta dawo na gyara kuskure na" ta k’arasa maganar cikin kuka.
Ita kanta Bikisu sai da hawaye suka fara zubo mata na tausayin halin da Husna take ciki.
San da ta fad’a mata Khalid ya mata fyad’e ta ga laifin ta saboda tana sha ko da had’in kanta ne hakan ya faru, amma a bayanin da ta mata ta fahimci ba ta da laifi.
"Ki daina wannan kukan da kike yi Husna, ba shi zai miki maganin matsalar ki ba, addu’a ita ce mafita a gare ki, ki sani komai muk’addari ne ya riga kuma ya faru, sai dai a kiyaye gaba, ki d’auki hakan a matsayin jarrabawar ki, kin ga irin abin da ake guje miki kenan Husna, ba ko wane namiji ba ne a yanzu zai maka kyauta mai yawa ka amsa ko da ansa ranar ku dashi saboda yaddda mutanen cikin ta suka ‘baci ki ke ganin kamar muna takura miki, na sha fad’a miki akan ki dinga gode ma abin da Salim yake miki saboda yana iyakar k’ok’arin shi wajen ganin ya kyautata miki da abin da yake dashi, amma ke ba kya ganin haka, yanzu ma lokaci bai k’ure miki ba Husna, za ki iya gyara kuskuren ki shine ta hanyar watsi da wannan halayen ki, sannan ki rik’e Salim hannu bibbiyu dan shine yake miki so na tsakani da Allah, sannan ki dinga ma Baba da Mama godiya akan dukkan abin da suka miki, ina ganin in kika yi hakan ba ki da sauran wata matsala".
Cikin kuka Husna ta ce "Ki na ganin Salim zai iya aura na a haka, in ya aure ni mai zan ce mai a lokacin da tuhume ni".
"Kar ki damu Husna, Salim zai aure ki a ko wane hali kika tsinci kan ki, sai dai zai yi kishin ki kasancewar yana son ki, abin da nake so dake Husna shine ki bar wannan maganar daga ni sai ke, ko su Mama kar ki fad’a ma wa saboda ba za su fahimce ki ba, hakan ma zai iya sa su d’aura laifi a kan ki tun da sun sha yi miki fad’a akan Khalid ko su yi fushi dake, babu wani iyayen da za su ji irin abin da ya same ki su samu kwanciyar hankali, ko shi Salim kar ki fad’a mishi yanzu, ki bari in Allah ya nufa kun yi auren sai ki fad’a mishi komai, yanzu in ki ka fad’a mai zai iya fushi dake ko ya d’aura laifin akan ki".
Wannan shawarar da Bilkisu ta bata taji dad’in ta, za kuma tayi k’ok’arin ganin tayi amfani da shawarar da ta ba ta.
"Na gode Bilkisu, insha Allahu zan yi amfani da abin da kika fad’a min".
"Ba komai Husna, matsalar ki matsala ta ce, Allah dai ya k’ara mana ikon rik’e amanar junan mu, ya kuma k’ara mana fahimtar juna da aminci".
"Amin Bilkisu".
Husna ce ta tashi daga kan daddumar ta zauna a kan gado ta kalli Bilkisu tace "Zan tafi Bilkisu, na gode da taimakon ki, Allah ya saka miki da alkhairi".
"Amin Husna, amma ina ganin ba za ki iya tafiya a halin da kike ciki ba, kin ga tafiyar ki ma ta canza, duk inda kika fita kallon ki za a dinga yi, ki dinga amfani da ruwan zafi kina tsarki dashi, za ki samu relief, bari in fad’a ma Momi zan raka ki gida ba ki da lafiya, sai in sa Driver ya kaimu" tana gama fad’ar haka ta fita daga d’akin.
Ba ta wani jima ba ta dawo ta sa hijab ta ce Husna ta fito su tafi driver zai kaisu gida.
San da suka isa gidan, sai da gaban Husna ya fad’i, gani take yi kamar kowa zai gane abin da ya same ta.
Su na shiga gidan, d’akinsu Husna suka wuce kasancewar ba kowa a tsakar gidan.
Bilkisu ce ta umarce Husna da ta kwanta ta huta, za taje ta fad’a ma Maman su Husnan akan ba ta da lafiya ne shi yasa ba ta dawo da wuri ba.
D’akin Maman su Husnan ta wuce, bayan sun gaisa ne take shaida mata rashin lafiyar Husna.
Tare suka fito daga d’akin suka nufi d’akin Husna, samun ta suka yi har tayi barci.
Nan Bilkisu ta yi ma Maman su Husna sallama ta tafi.
Sai bayan sallar isha’i sannan Husna ta farka daga baccin da take yi, har yanzu tana jin kin ta bai koma mata daidai ba.
Tashi tayi ta je tayi sallah kana ta dawo d’akin su ta zauna, yayin da abin da Khalid ya mata ya k’ara dawo mata sabo a ranta.
Su Fatima da Amatullah ne suka dinga tambayar ta akan me yake damun ta, amma tak’i musu bayani, sai ma kukan ta da taci gaba da yi.
Kukan ta da Maman su taji ne yasa ta shigo d’akin ta nemi guri ta zauna.
Cikin kulawa ta kalle ta tace "Husna sannu ya jikin, kukan me ki ke yi?".
Ji take yi kamar ta fad’a ma Maman su halin da take ciki, sai dai idan ta tuna hukuncin da za ta fuskanta a gurin su sai taji gwara ta danne abin da yake damun ta, tasan in har Maman su ta ji wannan labarin to ita ma sai ta shiga halin damuwa da tunani, hakan yasa ta ga gara ta bar zancen daga ita sai Bilkisu, tasan za ta rufa mata asiri.
"Wai Husna ba da ke nake magana ba ne ki ka zauna kina kuka, na tambaye ki abin da yake damun ki kuma kin tsaya kina tunani".
"Ba komai Mama" ta fad’a cikin k’ok’arin ‘boye abin da yake damun ta.
"Haka kawai mutum zai zauna yana kuka ne ba tare da wani dalili ba, in jikin ne ba sai ki fad’a a siyo miki magani ba, amma da girman ki kin zauna gaban k’annen ki kin tasa su a gaba kina kuka, suma za ki sa su a wani halin ganin kukan da kike yi, yanzu ina ne yake miki ciwo" Mamar su ta tambaye ta.
Rasa in da za ta ce yake mata ciwo, dan haka ta ce "Kaina ne yake min ciwo yanzu, d’azun ma na sha magani a gidan su Bilkisu".
*Wai yaushe ki ka fara ciwon ne, na ga lafiya kika fita daga gidan nan".
"Tun da na je gidan su Bilkisu na fara jin zazza’bi ya kama ni da ciwon kai, daga baya kuma zazza’bin sai ya rufe ni a gidan har sai da na kwanta, da na sha magani Bilkisu ta rako ni".
Mamar su ta ce "Ba zai wuce typhoid ko malaria ba, zuwa gobe in zazza’bin bai sauka ba sai ki je asibiti, Allah ya baki lafiya, Amatullah zo ki amsar mata paracetamol, idan ta ci abinci sai ta sha maganin".
Bayan fitar su ne Fatima ta ga Husna ta ci gaba da kukan, duk d’aukar ta ko zafin ciwon ne ke damun ta, dan haka cikin tausayawa ta ce "Sannu Anty Husna, Allah baki lafiya, ki daina kukan".
Share hawayen ta tayi kana ta ce "Na gode Fatima".
Amatullah ce ta shigo da abincin da ruwa a hannun ta, ajiyewa tayi a gaban Husna.
Kad’an taci abincin saboda yadda bakin ta ba ya mata taste kana ta d’auki maganin tasha.
Baban su ma ya zo ya duba jikin ta.
Ranar dai haka Husna tayi kwanan k’unci da danasani mara iyaka.
Washegari ba laifi Husna ta ji k’arfin jikin ta, sai dai zazza’bin da bai gama sakin ta ba.
Tana d’aki ta ji sallamar Bilkisu suna gaisawa da Mamar su.
Bayan sun gama gaisawa ne ta shigo d’akin su Husna rik’e da food flask a hannun ta.
Murmushi ta sakar ma Husna lokacin da ta gan ta a zaune akan gado.
K’arasowa tayi ta zauna kusa da Husnan tana tambayar ta ya jikin ta.
Ta amsa mata da ta samu sauk’i.
"Ina su Fatima ne na gan ki ke kad’ai a d’aki" Bilkisu ta tambaye ta.
"Sun tafi makaranta" Husna ta ba ta amsa.
Bilkisu ce ta tashi ta tafi ta d’akko plate da cokali ta zuba ma Husna farfesun kayan cikin da tazo dashi.
Duk da k’amshin da farfesun ke yi, ta kasa shan farfesun yadda ya kamata saboda rashin dad’in da bakin ta yake mata.
Sai da Bilkisu ta matsa mata sannan tasha mai yawa.
Bilkisu ce ta kalle ta tace "Husna ki shirya mu tafi asibiti, na riga na fad’a ma Mama cewa za mu je asibiti dake, tace za mu iya zuwa, Driver na waje yana jiran mu".
Tashi tayi ta d’akko Hijab d’in ta tasaka suka tafi asibitin.
Wani private hospital suka je aka duba Husna.
Likitan da ta dubata ta rubuta mata magungunan da za tayi amfani dasu da kuma shawarwarin yadda za ta kula da kanta, likitan ta fad’a mata nan da d’an lokaci za ta daina jin zafin da take ji.
Sai da suka biya gurin siyar da magani, Bilkisu ta biya kud’in maganin aka basu maganin suka dawo gida.
Husna haka ta dinga ma Bilkisu godiya akan taimakon ta da take yi, Bilkisu ta fad’a mata ba godiya a tsakanin su, sun riga sun zama d’aya.
Mamar su Husna ma ta mata godiya akan hidimar da tayi da Husna.
Sallama suka yi ta tafi gida akan sai ta kira ta a waya.
Husna ta bi shawarar likitan da ta ba ta wajen kula da kanta.
Tun daga wannan lokacin Husna ta canza salon rayuwar ta, magana ba damun ta tayi ba, ta dawo shiru-shiru, duk abin da aka bata za ta amsa tayi godiya, ta ajiye burin ta da hange a gefe.
Su kansu ‘yan gidan su sun yi mamakin canzawar halayen ta lokaci guda har suka zo suka daina mamaki, hakan yasa iyayen ta da k’annen ta farin ciki da wannan Sabon halin da Husna tazo dashi.
Yanzu ba ta da wata sauran matsala tsakanin ta da iyayen ta da kuma k’annen ta.
A lissafin da tayi, yau rabon Salim da zuwa gidan su tun fad’an da suka yi akan Khalid yayi fushi ya daina zuwa, a lokacin hakan ba wani damun ta yayi ba, ganin wani lokacin yana kiran ta a waya, sai a yanzu da ya d’auki kusan wata d’aya bai zo ba, gashi kiranta da yake yi jefi-jefi, hakan ya k’ara d’aga mata hankali, tasan ko da can tana son Salim, abin da yasa take ajiye shi a gefe shine yadda ba kowane lokaci ne yake mata abin da take so ba.
Yanzu ma kiran shi tayi, cikin sa’a numbar ta shiga.
Murna ce ta kama ta ganin numbar ta shiga.
"Assalamu alaikum" Salim ya fad’a.
"Wa’alaikumus Salam, Ina wuni Salim".
"Lafiya lau, ya mutanen gida" Salim ya tambaye ta.
"Suna nan lafiya" Husna ta bashi amsa.
"Ya kasuwa" Husna ta fad’a.
"Kasuwa Alhamdulillah" Salim ya amsa mata.
Shiru ne ya ratsa a tsakanin su kafin Husna ta ce "Salim kwana biyu, ka guje ni".
"Ni ban guje ki ba Husna, ba ina kiran ki a waya ba".
"Kana kira na jefi-jefi ba, yanzu rabon ka da zuwan gidan mu yau tsawon wata guda kenan, pls in laifi na maka ka yafe min, bazan juri rashin ka ba" Husna ta fad’a cikin damuwa.
Mamaki ne ya kama shi, wai Husna ce ke rok’on shi yazo gidan su har da bashi hak’uri.
"Kayi shiru Salim".
"Ai abin ne da mamaki Husna, ko da yake a bar zancen, amma kema kin san dalilin daina zuwa na akan wannan wanda yake zuwa gurin ki ne wanda ki ke ganin na takura miki akan shi, Husna bazan juri ganin ki dashi ba, shi yasa na k’aurace miki".
Tasan ba kowa yake nufi ba illah Khalid, da yasan yadda ta tsani Khalid da bai mata zancen shi ba.
"In dai akan Khalid ka ke fushi to kayi hak’uri, mun rabu dashi rabuwa ta har abada".
Duk da yaji dad’in maganar ta, sai bai nuna ba, yasan halin Husna, za ta iya yuwawa dan taga kwana biyu bai zo ba, shine take so ya zo, alhalin ba ta rabu da Khalid d’in ba.
"In na samu lokaci zan zo, ki gaida mutanen gida" yana gama fad’ar haka ya katse wayar.
Hawaye ne ya fara zubo mata, tasan in har Salim ya rabu da ita za ta iya shiga wani hali ban da wanda Khalid ya je fa ta a ciki, tana ganin za ta iya jure duk wani abin da Salim zai mata in har zai ci gaba da son ta.
Tun ran da suka yi waya da Salim take sa ran ganin shi, amma shiru, hakan ya d’aga mata hankali, gani take yi ko Salim rabuwa yake so yayi da ita.
Bilkisu ta kira akan in ta samu lokaci ta na neman ta.
Kwana d’aya da yin wayar su da Bilkisu sai ga ta tazo.
Nan ta warware mata halin da suke ciki tsakanin ta da Salim, rok’onta ta dinga yi akan ta kira Salim ta bashi hak’uri.
Tausayin Husna ne ya kama Bilkisu, tasan a yazu wanda zai kwantar mata da hankali take buk’ata, ita shaida ce akan Husna tana son Salim, halin ta ne ya rinjayi son da take ma Salim d’in, shi yasa ba kowa ba ne zai fahimci irin son da take ma Salim d’in.
Wayarta ta d’auka ta kira Salim d’in, ba ta dad’e tana ringing ba ya d’auka.
Sun gaisa cikin mutunci kana Bilkisu ta fara bashi hak’uri akan abin da Husna take mishi, ta nunar mishi da yanzu Husna ta gano laifin ta.
Ya amsa mata da yana nan zuwa, dama ya daina zuwa ne saboda yana so Husna ta gano laifin ta, amma yanzu shi komai ya wuce.
Nan suka yi sallama da Salim d’in.
Bayan ta gama wayar ne ta ci gaba da yi ma Husna nasiha akan ta rik’e Salim hannu bibbiyu.
Da haka suka yi sallama da Bilkisu inda ta raka ta har wajen layin su.
Kwanab biyu da yin wayar su da Bilkisu, sai ga Salim yazo da daddare.
Kiran ta yayi a waya ya sanar da ita zuwan shi.
Murna a gurin Husna ba a magana, sai a yanzu ta k’ara tabbatar wa da tayi kewar Salim d’in.
Make-up tayi na d’aukar hankali kana ta fito ta sami Salim inda yake zaune akan wani dandamali dake kusa da gidan su.
Tun da ta zauna take sakar mishi tsadadden murmushi.
Hakan yasa shima ya dinga maida mata martanin murmushin da take mai.
Gaishe shi tayi ya amsa mata da yalwataccen murmushi a fuskar shi.
"Kin yi kyau Asma’u" Salim ya fad’a yana ci gaba da kallon ta.
Rausayar da idon ta tayi cikin na ta salon kana ta ce "Na gode Salim".
Hira suka ci gaba dayi mai nuna tsantsar son da suke yi ma junan su.
A yau sun yi hira irin ta masoya da suka dad’e ba su yi ba, kowa ya amayar da sirrin zuciyar shi, hirar tasu tayi armashi.
San da zai tafi, Husna ji take yi kamar kar ya tafi, shima hakan take a gurin shi Salim d’in, ji yake yi kamar kar ya tafi saboda bai gaji da ganin ta ba da jin dad’in kalamenta, a wuri guda ga wata kulawa ta musamman da ta bashi.
Da haka suka yi sallama da juna ba dan kowa ya gaji da ganin d’an uwan shi ba.
Tun daga wannan ranar Husna ta dawo da soyayyar da take ma Salim sabuwa, yanzu ba wani shamaki a soyayyar su.
Salim ma yana jin dad’in yadda yanzu suke gudanar da soyayyar su ba tare da sun samu sa’bani ba.
Tun Salim na mamakin canzawar halayen Husna, har ya daina mamaki, ganin duk abin da ya mata komai k’ank’antar shi sai dai tayi godiya, duk wani abu da ba ya so game da ita duk ta daina, wannan abun da Husna tayi ne yasa ya k’ara jin wani son ta a ranshi.
Dama abun da yake had’a su fad’a kenan da kuma wannan saurayin da tayi mai mota, tun da yanzu duk ta rabu dasu, yana ganin babu wata sauran matsala a tsakanin su.
Da wannan ne soyayyar su ta ci gaba da gudana cikin kwanciyar hankali.
Yanzu abin da yake damun ta shine yadda Salim bai k’ara mata maganar turo iyayen shi akan sa ranar auren su ba, tasan laifin ta ne a wannan ‘bangaren, dan ita ce ta mishi iyaka da wannan maganar, saboda haka ita ya kamata ta mishi maganar ta amince ya turo ayi maganar auren su.
Salim na zuwa da daddare ta mishi albishir d’in cewa ta amince akan ya turo a sa musu ranar auren su, wannan maganar da Husna ta fad’a mishi ya sa yayi murna da wannan maganar, farin cikin shi kasa ‘boyuwa yayi, ya tabbatar mata da zai samu iyayen shi da wannan maganar, dama abin da yake jira daga gare ta kenan, tun da ta amince yana ganin ba wata ragowar magana da ta rage.
Husna tsintar kanta tayi cikin farin ciki saboda tana ganin ta kusa zama mallakin Salim da zarar an sa ranar bikin su, idan ta tuno da abin da Khalid ya mata sai taji jikin ta yayi sanyi saboda tasan Salim yana kishin ta, idan yasan abin da ya same ta ba ta san wani hukunci zai yanke mata ba, fatan ta Allah yasa komai yazo mata da sauk’i a ko wane hukunci Salim zai mata.
Salim yana koma wa gida ya samu iyayen shi da wannan maganar da suka yi da Husna.
Iyayen shi sun nuna farin cikin da jin wannan labarin, saboda haka ne Baban su Salim d’in ya fad’a mishi da ya sanar da Baban su Husna nan da sati d’aya suna nan zuwa a sa ranar bikin su.
Washe gari da Salim ya koma gidan su Husna ya samu Baban su Husna akan iyayen shi suna nan zuwa nan da sati d’aya akan maganar bikin su.
Mahaifin Husna ma ya nuna farin cikin shi da haka.
Bayan sati d’aya sai ga iyayen Salim sun zo gidan su Husna akan maganar bikin su, wan baban su Husna da wani abokin Baban su da Baban su suka tarbi iyayen Salim.
Bayan an gaisa ne iyayen Salim suka gabatar da abin da ya kawo su na nemar wa Salim auren Husna
.
An tsayar da ranar bikin su nan da wata bakwai.
Tun san da aka tsayar da bikin Baban su Husna ya fara tanajin shi na kayan d’aki da sauran shirye-shirye na bikin, Mamar su Husna ita ma tana na ta fad’i tashin dan ganin ta fitar da ‘yar ta kunya.
‘Yan uwan Baban su da suma sun yi nasu k’ok’arin gurin kawo gudunmawar su na bikin.
Ta ‘bangaren k’arashe ya rage mai a shirye-shiryen shi kasancewar tun kan a sa ranar ya fara tanajin shi da ya danganci bikin.
Ogan shi na kasuwa ya bashi gudunmawar shi da ‘yan uwa sun yi nasu k’ok’arin.
Ko ta wani ‘bangare suna nasu iya k’ok’arin dan ganin an fita kunya ta hanyar yin daidai k’arfin su ba tare da sun takura kan su ba.
Biki na ta matso wa yayin da fargaba ke ta d’awainiya da Husna, duk da tana farin ciki da wannan auren da za tayi da Salim, sai dai ta wani ‘bangaren idan ta tuno halin da za ta tsinci kan ta a ranar da Salim yasan ta rasa budurcin ta ta kan shiga damuwa, wani lokacin ji ta ke yi kamar ta fito ta fad’a mai abin da ya faru sai ta fasa, tasan yadda yake kishin ta zai iya fasa auren ta duk da son da yake mata.
Bilkisu ma ta kawo mata magunguna na gyaran jiki ta ce in ji Mamar su, Mamar su Husnan ma ta siyan mata magungunan.
Haka take shan su duk da tasan magungunan basu za su hana Salim ya gane ita ba cikakkiyar budurwa ba ce.
Idan ta tuno wani posting da ta gani a wani group inda wata mata take cewa "Duk wanda aka yi disvirgin d’in shi ba yadda za a yi ya dawo virgin duk kuwa dubarar da za ayi wajen d’inke gurin ko wasu dubarun" jikin ta sai ya k’ara sanyi.
Haka lokaci ya ci gaba da tafiya inda biki ya rage saura sati d’aya a lokacin ne kuma ‘yan uwan Salim suka kawo akwati uku da kit, gaskiya yayi k’ok’ari wajen zuba kaya masu tsada.
A yanzu yadda Husna ke ji ko da akwati d’aya ya kaeo mata ba za ta nuna jin haushin ta ba, dan ta ga illar rashin godiya ga Allah da ya haifar mata.
Dadin su Bilkisu ya ba da kud’i aka kawo ma Baban su Bilkisu yayin da Momin su ta ba da kayan turarruka na gyaran jiki da na d’aki masu kyau ta ba da a kawo ma Husna, Samir ma saurayin Bilkisu sai da ya ba da gift a kawo mata.
Ba abin da Husna za tace ma Bilkisu sai godiya, ta mata abin da ko da a ce ciki d’aya suka fito iya abin da za ta mata kenan, ba za ta manta da karamcin Bilkisu gare ta ba.
Ganin yadda wani lokacin Husna ke zama ta dinga tunani yasa Maman su Husna da su Fatima su ke tambayar ta ko lafiya, idan suka mata tambayar sai taji kamar ta fito ta fad’a musu abin da yake damun ta, sai dai idan tayi duba da halin da za su shiga sai taji gwara ta bar matsalar a cikin ta tun da ita jawo ma kanta.
Abokan Salim sun zo sun ba da kud’in da za ayi hidimar biki.
An ma Husna jeren kayan ta a unguwar Dorayi charanci inda Salim ya kama haya.
Ana gobe bikin ne Husna tayi walimar ta a gidan su Bilkisu.
Washegari aka d’aura auren Asmau (Husna) Nuhu Da Salim Usman a k’ofar gidan su.
Tun da aka d’aura auren Husna ke kuka, mutane na d’aukan kukan rabuwa da gida take yi, a ‘bangaren Husna kuwa kukan abu biyu take yi, na rabuwa da gida da kuma fargabar halin da Salim zai same ta.
Bilksu ce ta ja ta gefe tana tambayar ta kukan da take yi.
"Husna wai kukan me ki ke yi, yau ranar farin ciki ce a gare ki, bai kamata ki maida ranar farin cikin ki zuwa kuka ba" Bilkisu ta fad’a cikin kulawa.
Cikin kukan Husna take ce mata "Bilkisu ke kad’ai ce ki ka san k’addarar ta same ni, kin san dole ne in yi kuka na tunanin yanda zama na zai kasance idan har Salim yasan abin da Khalid ya min".
Ita kanta Bikisu tana tausaya ma Husna halin da take ciki tun san da abin da ya same ta tsakanin ta da Khalid, sai dai ita k’addara ba ka kauce mata in dai ta tunkaro ka.
Cikin tausayawa Bilkisu ta ce "Ki yi hak’uri ki yi shiru Husna, tun da an riga an d’aura muku aure ina ganin komai zai zo da sauk’i, shawarar da zan baki shine nasan sai Salim ya tuhume ki akan abin da ya same ki, ina so ki fad’a mishi gaskiya, sai Allah ya d’aura ki akan Salim d’in ya hak’ura da hukuncin da yayi niyar yanke miki sakamakon fad’ar gaskiyar da kika yi duk da zai shiga wani, ba yadda za ayi miji ya tarad da matar shi wani ya riga shi kasancewa da ita, dole ne yaji haushin haka, bare Salim da yake miki son gaskiya, insha Allahu komai zai zo da sauk’i, sannan shawarar da zan baki a k’arshe shine ki yi hak’uri da duk abin da zai miki, daga baya zai sakko".
Taji dad’in shawarwarin da Bilkisu ta ba ta, hakan yasa ta saki murmushi a lokaci d’aya ta daina kukan da take yi, sai hawaye ne yake zuba a idon ta.
Ci gaba tayi da cewa "Yanzu mu je ki wanke fuskar ki sai ki shafa powder, kar Salim ya ganki ya tuhume ni me yasa amaryar shi kuka".
Dariya suka yi suka koma cikin gidan suka ci gaba da gudanar da shagalin bikin.
Da daddare aka kai Husna gurin Baban su da Maman su suka mata nasiha akan zaman aure tare da mata fatan alkhairi.
Haka suka rabu da iyayen ta tana kukan rabuwa dasu.
D’orayi charanci nan aka kai Husna, a nan ne Salim ya kama haya.
Gida ne daidai da amarya, ciki da falo ne a had’e, idan ka fito akwai extran d’aki guda d’aya, sai kitchen a kusa da d’akin, a can gefe kuma band’aki ne.
Bayan ‘yan kai amarya sun ga d’aki suka fara watsewa kasancewar an riga an mata jere hakan yasa ba za a kwana ba, su Amatullah da Fatima da za su tafi haka Husna tasha kuka, su kan su sai da suka yi kuka.
Shi yasa aka ce sabo ake ma kuka.
Bilkisu ce kad’ai ta rage tana jiran zuwan Salim yazo ta kira driver ya kaita gida.
Bilkisu ce tasa Husna ta tashi ta sake wanka tayi make-up had’e, turarurruka kuwa ba a magana da Husna tayi amfani dasu.
Bilk’isu ta ci gaba da k’arfafa mata gwiwa akan ta cire tsoron da ke ranta, insha Allah komai zai zo da sauki.
A haka har Salim yazo da wani abokin shi Kabir suka siya baki aka yi wasa aka yi dariya tare da add’o’i akan Allah ya basu zaman lafiya kana Bilkisu ta kira Driver gidan su yazo ya d’auke ta.
Da za ta tafi sai da Husna ta k’ara sa wani kukan, tasan yanzu ba ta da sauran wata dubara da ta rage mata tun da yanzu ita da Salim kad’ai za a bari.
Ita ka ta Bilkisu sai da tayi kukan a lokacin dan tasan me kukan Husnan yake nufi.
Sai da Salim yazo ya rik’e ta sannan ta saki Bilkisu, shi kanshi bai yi mamaki ba saboda yasan yadda suka shak’u dole ne hakan za ta kasance.
Sallama Bilkisu ta musu ta tafi suna ma su kewar junar su.
Rik’o hannun ta yayi suka zauna a tsakiyar falon, nan ya bud’e musu naman da ya tawo dashi da fresh milk.
Husna kad’an ta ci ta koma gefe, duk yadda Salim yaso taci da yawa ba taci ba, sai ma ce mishi da tayi ta k’oshi ne.
Bayan ya gama cin naman ne yaje ya ajiye sauran a frij kana ya d’aro alwala ya dawo d’’akin ya tarad da Husna a zaune in da ya bar ta.
Umartar ta yayi da taje tayi alwala, ba ta musa mishi ba ta tashi ta je ta d’auro alwala.
Sallah raka’a biyu suka yi, bayan sun idar da sallar ne Salim ya kama kanta ya dinga jero addu’o’i akan Allah ya basu zaman lafiya.
Kallon ta yayi cikin so da K’auna ya ce "Husna ki je ki canza kayan ki sai kwanta, na ga kamar kin gaji".
Cikin sanyin jikin ta masa masa da "Toh".
D’aukar night gown d’inta tayi ta fita daga d’akin ta koma d’ayan d’akin ta canza shigar ta zuwa night gown yayin da ta d’aura hijab a saman kayan.
Dawowa tayi ta zauna a falo ta ci gaba da karanta wasik’ar jaki.
Shirun da yaji ba ta dawo bane yasa ya fito daga uwar d’aka, ganin ta yayi a falo tana zaune.
Murmushi yayi ya zo ya zauna kusa da ita kana ya ce "Husna ya za ki zo ki zauna a nan, ki shiga d’aki ki kwanta, na ga yau kin k’i sakin jikin ki, ko sai na biya ne, nasan amarya komai nata mai tsada ne".
Gaban ta ne kad’ai yake fad’uwa, ita kad’ai tasan halin da take ciki a yanzu.
Murmushin yak’e kawai tayi ta tashi ta tafi d’akin ta zauna akan gadon.
Shi Salim abin dariya ma ya bashi ganin yadda Husnan tak’i kwanciya kamar wacce za a kama, hakan da Salim ya gani ya fahimci rashin sabo ne yasa ta kasa sakewa ta kwanta, Shi yasa ya fita falo, in yaso in tayi bacci sai ya dawo d’akin ya kwanta.
Kasancewar gajiyar biki yasa a zaunen ta fara gyangyad’i har ya kai ta ga kwanciya.
Nan bacci ya d’auke ta ba tare da ta sani ba.
Shigowar shi d’akin ne ya ga har tayi bacci, kashe bulb d’in d’akin yayi yah au gadon ya kwanta.
K’amshin turaren da Husna ta sa a jikin ta ne yake fisgarshi har ya kasa controlling d’in kanshi.
Janyo ta jikin shi yayi yana ci gaba da shak’ar turaren mai sanyin k’amshi.
Nan Salim ya ga ba zai iya daurewa ba ya fara isar da sak’on shi ga Husna, hijab d’in jikin ta ya cire mata, ganin yadda aka yarfa mata k’ananun kitso ya k’ara d’aukar hankalin shi kasancewar ta mai gashi.
Shafa kitson ya fara yi a hankali kana daga bisani ya canza zuwa wani gurin.
Haka hannun shi ya dinga yawo a jikin Husna.
Husna cikin bacci taji ana shafa ta, hakan yasa tayi saurin bud’e ido, ganin Salim ya fara nisa bai san in da kanshi yake ba yasa ta fara bashi hak’uri, jikin ta kuwa in banda rawa ba abin da yake yi, ganin Salim bai da alamar tsayawa yasa ta fashe da wani irin kukan da yasa dole Salim ya dawo cikin hankalin shi.
Tausayin ta ne ya kama shi, yasan duk da rashin sabo yasa ta kasa sakin jikin ta.
Lallashin ta ya dinga yi har ya samu ta yi shiru ta daina kuka, amma jikin ta bai daina rawa ba.
Jikin shi ya janyo ta ya fad’a mata kalamai masu dad’i.
A hakali yake mata magana a kunne "Sorry Husna, cool down, ba abin da zan miki, ki yi baccin ki kin ji".
Da haka ya samu ta koma bacci yayin da shima baccin yayi awon gaba dashi.
*(Hmmmm Readers, yau fa ake yin ta, ga dai Salim ga Husna, ma ji yadda za ta kaya tsakanin su*.
*Sai dai nima Husna ta ba ni tausayi, halayen ta ya jawo mata ta fad’a wannan halin da take ciki wanda a dalilin abin da ya same ta yasa tayi watsi da wannan halayen na ta, amma duk da haka ba ta daina danasani ba*.
*K’alubalen ku masu irin halin Husna*.
*(Allah ka shirya mu baki d’aya)*
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU(YAYA HAYAT)
(ADMIN OF ADMINS)
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)
WHATSAPP NO:
09030159301
Download Silar Kayan Sallah Littafi Na Daya From Page 1 To 40
0 Comments
Thank you for this comment