[4/22, 2:13 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!._*
👉ğŸ»1âƒ?
*Matsanan cigar* hayaniyar dake tashi agidan ce taja hankalina, cikeda bak'in ciki natashi daga barcin safen dana koma, fitinar gidanmu dabance data kowane family House dana Sani kona ta6a jin labarinsa a rayuwata, haka gidan namu yake kullum tamkar kasuwar 'yan danbe, daga matan gidan zuwa 'yan mata da yara tamkar muna ganin hanjin juna, saika rantse badaga tsatso d'aya muka fitoba.
Kururuwar danaji maman Safara'u ta kurma yasani kuma jan dogon tsaki, sai kuma najiyo muryar gwaggon haleema Na fad'in â€Å“kai amma wannan lamari baiyi dad'iba, kekuwa maman biyu ya kamata ki canja wannan halin naki, dan tabbas inba wani abu kikayiba babu yanda za'ayi yaronan Sadeequ yadage shi cikinsu *MUNAYA* yakeso, duka yaushe aka gama maganar nan akan shafi'u amma shine zaki koma kan Sadeequ kuma yanzu?â€?.
gaba nane ya fad'i, cikin zaro idanu waje nace, â€Å“ashema mu akanmu fitinar take yau?â€?. yink'urin sakko nake daga gadon Munubiya tashigo tana share kwalla, binta nayi da kallo harta fad'a saman gadon ta kwanta rufda ciki tareda fashewa da kuka mai ban tausayi. Hakan Yakuma tabbatar min lallai mud'inne dai ake hargowar akanmu. a fusace Na dirgo daga gadon na nufi k'ofar fita, (ko kad'an banida hak'uri, musamman akan cin zarafin mahaifiyarmu da akeyi agidan lokuta da dama idan irin hakan ta taso), taku biyu nayi naji an damk'oni, najiyo cikin masifa dan nasan Munubiya ce.
â€Å“wlhy ki sakeni kafin nafara huce haushina akanki munu! yau saina gyarama kowacce 'yar iskar mata zama agidannan dan kutu.....
Bankai ga k'arasawa ba Munubiya tai saurin rufe bakina da tafin hannunta.
Kici-kicin kwacewa nafarayi amma nakasa, dan bak'aramin ruk'o taminba, raina yak'ara 6aci ainun danjin irin rashin kunyar da Safara'u ke zubama innarmu a tsakar gida, bansan na wancakalar da Munubiya gefe ba nafice da gudu.
Babu Wanda yaga fitowata sai dai saukar sautin marin dana zubama Safara'u a farar fuskarta sukaji.
Hakan yaja gidan yay tsit na wucin gadi, sai kuma hayaniya takuma 6allewa, Safara'u da mamarsu sukayo kaina danufin duka....
Tsawar da baba k'arami ya bugace tasaka kowa dakatawa tsakanin ni dasu, hakama matan gidan sai suka fara jan k'afafu danufin barin wajen.
A tsawace yace, â€Å“kar wadda tabar wajen!!â€?.
Tsitt kakeji gidan yayi, tamkar bashi bane d'azun ya cakud'e da hayaniya tamkar ana biki ko suna.
Jarabar gidanmu ba bak'on Abu bane a anguwarmu, danta rigada tazama tamkar ajininmu take (yo ajininmu mana zance) tunda kullumne babu fashi sai anyi hayaniya, kodai matan gidan kokuma mu 'ya'yan gidan. Babu mai d'agama wani k'afa koda na second d'ayane kuwa, yanzun zakaji gidan shiru, anjima k'ad'an kaji an doka gangar shaid'an, musamman ma fad'an yara dayafi komai saurin had'a fad'an matan gidan da a kulum, a rana sai ayi fad'a biyar akan yara kawai, innarmu ce kawai da Maman Fauziyya keda k'ok'arin K'aucewa irin wannan fitintunun dasuka zama tamkar shan ruwa acikin gidanmu.
Baba k'arami yafara fad'a tamkar zai ari baki, inda yake shiga bata nan yake fitaba, kowa yayi tsit yana saurarensa, (saboda kasancewar masifaffe shima) sai da yayi mai isarsa sannan yajuya yafita yana fad'in nida Safara'u mu sameshi falonsa. harda iyayenmu mata.
Duk abinnan da akeyi innarmu na kicin tana had'a Karin kumallon safe, kuma kalma d'aya bata tofaba a zancen nasu, datasan ma zan fito bazata barniba nima.
A falon baba jafaru yanemi jin ba'asin tushen fitinar, cikin d'aga muryar da hargowa maman Safara'u tafara fad'in â€Å“Alhaji wlhy kashiga tsakanina da maman biyu a gidannan, idanfa tanama sauran matan gidannan Yanda taske so, suna barinta nibazan bartaba, tasanni tasan waye ubana ehe, kum.......
Hannu yay saurin d'aga mata, â€Å“kinga Suwaiba nifa ba wannan ne yasani kiranku ba, sonake naji minene ya kawo hayaniyar?â€?.
Cikin jin haushin an tareta tace, â€Å“Alhaji akan yaronnan Sadeequ ne, kowa yasan wajen Safara'u yake zuwa a unguwarnan, amma jiya da yamma sai ya aiko kiran Munaya, dayake ALLAH yatashi tonon asirinsu sabida bayaune na farko ba sai d'an Aiken ya kwatsa maganar a tsakar gida, babu dai Wanda yace komai, dan azatonmu ba Sadeeq d'in Safara'u baneba, goshin magriba saiga Safara'u tashigo tana kuka. Na tsareta da tambaya da k'yar tacemin cikinsu 'yan biyu tagani da Sadeeq a zauren gidan Malam halilu suna hira da dariya, kuma hardama mata gwalo akayi. Saboda na gaskata zancenta na sake aiken Rahma taganomin da idonta, harma taji Sadeeq d'in nafad'in ai koma miza'ayi bazai auri Safara'u ba, cikin wad'an nan munafukan yaran daba ganesu akeba zai aura, saboda darene yasani d'inne maganar a raina har safiyar yau d'inan, amma wlhy Alhaji da k'yar na iya barci nida Safara'u jiya.
â€Å“hummmâ€? kawai nafad'a ina dafe kaina, saboda jin Yanda aka canja maganar.
Babak'arami ya kalleni yace, â€Å“Munubiya ce ko Munaya?â€? (dan basa ganemu saboda tsananin kamata da hassana ta).
Zuciyata cikeda bak'in ciki nace, â€Å“Baba Munaya ceâ€?.
â€Å“yauwa Munaya, ina 'yar uwarki?â€?.
â€Å“Tana ciki babaâ€?.
Baba ya kalli Safara'u daketa matse kwallan munafurci tun d'azun yace, â€Å“k! Safara'u tashi kiramin Munubiya â€?.
Batareda ta amsaba tatashi tafita, mintuna kad'an saigata sun dawo tareda Munubiya datasha kuka idanu sukayi luhu-luhu. tsaki naja a raina ina hararta ta gefen ido, rashin jarumtar ta na bani haushi, ta cika hak'uri da sanyin hali tamkar innarmu.......
Maganar baba ce tadawo dani daga tunanin dana tafi. nad'ago ina kallonsa saboda kiran sunana dayayi, muryar a dake na amsa da â€Å“na'am babaâ€?. kallonsa ya maida kan Safara'u yana fad'in â€Å“wacece acikinsu kika gani tareda Saddik'un?â€?.
Binmu da kallo Safara'u tayi, cikin matse kwalla tace, â€Å“baba niba ganesu nakeba, sai sun banbanta min Kansu sannanâ€?.
Baice komaiba dan shima yasan da hakan, (ta hallaya ne kawai kowa ke banbantamu agidan, hatta da innarmu kuwa). Baba yabimu da kallo alamar son sanin wacece acikinmu.
Da sauri Munubiya tace, â€Å“baba niceâ€?.
Nima na kar6e da fad'in â€Å“baba k'arya takeyi nice jiya Sadeeq ya aiko kira, kuma babu wata alak'a dake tsakaninmu, hasalima ya kirani ne akan Safara'un, sune dai suka maida zancen hakaâ€?.
Daga Safara'u har mamanta harara suka ballamin, babu ragi nima na rama kuwa.
Baba ne yakatsemu da fad'in â€Å“miya faru to Munaya?â€?.
Janye idona nayi daga Kansu na maida gareshi, kaina ak'asa Nace,
â€Å“baba ya kirani ne yana tambayata minene abinda Safara'u tafiso a rayuwarta, dan yanason yabata gift na birthday d'inta, kuma soyake yayi mata bazata. shinefa nake lissafa masa muna dariya saboda ina cewa ya had'o mata da gyad'a soyayya dan ita mayyarta ce, a dai-dai lokacinne kuma na hangota zata shigo gida, nifa dama tsokana namata gwalon, Ashe ita ta d'aukeshi wani Abu. Kuma wlhy Rahma k'arya takeyi, lokacin data fito tareda yaa Hameed ta ganni yana bani kayansa nakai masa ciki shi zai shiga masallaci salla. Wannan shinefa abinda yafaru, shine suke cewa nakwace mata Sadeeq, har ana cin zarafin innarmu da farar safiyar nanâ€?.
Ajiyar zuciya innarmu ta sauke a hankali, taji dad'i daba abinda suke zargin baneba.
Wata uwar harara baba jafaru ya watsama maman Safara'u, â€Å“kai Suwaiba kedai ALLAH ya gyaraki, dan ALLAH kuringa bincike akan Abu idan yara sun fad'a muku, tokinji dai abinda yafaru, kekuma Safara'u dayake bakida tarbiyya har bakinki yana iyama Ai'sha rashin kunya ko, ki tabbatar saina saka Abdulhameed yacimin ubanku keda Rahama yau a gidannan. Ai'sha kiyi hak'uri dan ALLAH â€?.
Innarmu ta yink'ura zata mik'e tana fad'in babu komai babansu, ALLAH ya kauda fitinar gaba�.
â€Å“Aminâ€? muka fad'a muma muna mik'ewa mukabi innarmu a baya.
Koda muka fito, sai matan gidan suka zubo mana ido suna kallo tamkar yau suka fara ganinmu, a raina nace munafukai, haka zaku k'are.
Ran innarmu ya6aci matuk'a a wannan karon, amma kasancewarta mutum mai hak'uri da shanye damuwa sai bata nunaba.
Nida Munubiya kam kasa shanye 6acin ranmu mukayi, munsan koma wace irin wulak'antawa za ai mana agidan *KAKARMU* ce taja mana, itace tabada kowacce iriyar k'ofar tozartamu, idan kaga abubuwan da ake mana saika d'auka ba jinin gidan baneba, tunda muka taso a haka muka tsinci kanmu, hakama mahaifiyarmu a wannan halin muka risketa tana fuskantar k'ask'anci da wulak'anci daga Kakarmu da matan Abban mu, harma da matan k'annensa, bamuda 'yanci irin na 'ya'ya, mahaifiyarmu batada kima irinta matar gida (Uwargida), hakan yasamo asaline dalilin................âœğŸ?
ğŸ‘ğŸ»
Tofa masu karatu dalilin mi? Dani daku duk muna buk'atar jin wannan dalili a bakin MUNAYA!, saiku kasance dani danjin Yanda wannan labari mai d'unbin harmutsi da tsalle-tsalle zai kaya, miye manufarsa? ina kuma ya dosa?.
Amsa d'aya zan iya baku.👇ğŸ»
*_LABARIN MAI TSAWONE_*
saikun kasance dani a hankali zancigaba da warware muku lauje cikin nad'i.
ALLAH yasa zaku bani had'in kai, tabbatarwata shine yanda zaku kar6i wannan labarin.
Dan haka kumuje zuwağŸ¥ÂºÃ¢Å“ğŸ¼Ã¢Å“ğŸ¼
Zamu cigaba Monday insha ALLAH, wannan d'and'anone.
Sannan wannan karon zandinga typing ne Monday to Friday kawai insha ALLAH, kunga banda weekend kenanğŸ˜Å .
One luv🥰
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmuğŸ˜ÄŸÅ¸‘ğŸ»._*
[4/22, 2:13 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
👉ğŸ»3âƒ?
.........Fad'a sosai innarmu tamin akan Marin Safara'u danayi, sannan ta d'ora da nasiha kamar yanda tasaba, wani kam yashiga kunnena, wani kuwa tabaya yabi, dan harga ALLAH Na daina zama kowa yana taka mana mahaifiya a gidan.
Innarmu tace, â€Å“ku shirya gobe idan ALLAH ya kaimu Ku tafi gidan mamanku Rabi'a Ku k'arasa hutunku, banason zamanku a gidan nan tunda fitina yake kawowaâ€?.
A sanyaye Munubiya ta amsa da â€Å“to innarmuâ€?.
Amma ni saina tunzuro baki gaba ina k'unk'uni, dan banason tafiya ko ina, canma saboda d'an mama Rabi'a d'inne Marwan, ko kad'an bama shiri dashi, saboda masifarsa. â€Å“kai innarmu, yanzu dan ALLAH saboda wasu can bazamu mik'e kafa yanda mukeso ba agidanmu, duka fa hutun sati biyu ne kacal, amma saimunje wani waje?, ni wlhy inkika barni babu mai k'ara mana koda kallon banza a gidannan, harma innaro bazan bartaba.........â€?
Maficin danaga innarmu tajawo yasani tashi da sauri nabar gurin, Na tabbata shirin bugamin takeyi. Munubiya ta saka dariya tana kallona, â€Å“ke ga rashin arzik'i ga tsoron tsiya, dukan maficin kikema wannan gudun?â€?.
Harara Na balla mata, â€Å“yo k'ya fad'i haka mana tunda ba jikinki baneba, tsoro kam kinsan waye matsoraci acikinmu aiâ€?.
Munubiya ta ta6e baki â€Å“naji dai, koma mizaki ce kije kiyita cewa, inama kayana dakika saka jiya? na wanke, dan dasu zanjeâ€?.
Wayar innarmu Na d'auka ina dannawa, batareda na bata amsaba Na nuna mata laundry basket d'inmu.
Innarmu tace, â€Å“to Aljanar waya ajiyemin kafin ki k'ararmin kud'in ciki, ina taki?â€?.
â€Å“kai innarmu, please mana, zan kira Ayusher nefa nasanar mata muna zuwa gobe, ALLAH wayata babu ko nera aciki Munu ta cinye min jiyaâ€?.
â€Å“kiji tsoron ALLAH munaya, Nina cinye mini kud'in waya? bake kika kira Balkisu ba da kanki?â€?.
â€Å“to dana kirata sai nace kuyita surutu har kud'ina ya k'areâ€?
innarmu Na shirin yin magana muka jiyo kururuwar kukan Safara'u da Rahama. dariya Na k'yalk'yale da ita, ina fad'in â€Å“o, ALLAH ga yaa hameed can yana gwajin kwanji a jikin gayuâ€?.
Harara innarmu ta ballamin, saikuma tamik'e tana shirin fita, nasan kar6arsu zataje, nai saurin fad'in â€Å“kai innarmu, kid'an barsu su lallasu manaâ€?.
Dakk'uwa ta watsomin tareda fad'in â€Å“K'aniyarki Munayaâ€?.
Dagani har Munubiya dariya muka sanya harda tafawa kuwa.
Ba'a rufa mintuna 3 da fitar innarmu ba muka fara jiyo hargowar Maman safara'u (dama ita bata magana a hankali) Yaa hameed takema masifa akan dukansu safara'u dayakeyi, maman su yaa hameed babu hak'uri, itama tafito suka fara cacar baki, yaa hameed kam ficewarsa yayi bayan innarmu ta kwaci su Rahama a hannunsa da k'yar. kafin kace mi gidan yakuma kaurewa.
Munubiya tace, â€Å“kai jama'a ko breakfast ba'ayi agidanba har antafi wrestling zagaye na biyuâ€?.
Na fad'a saman gado ina Dariya, danni mamaki 'yan gidanmu nakeyi da bala'insu. wayar Innarmu tayi ringing, da Sauri Na duba sainaga Abbanmu ne, cikeda d'oki Na amsa tareda masa sallama sannan Na gaidashi.
Yace, â€Å“Munubiya ina maman takune?â€?.
â€Å“Abba ba munu bace, nicefaâ€?.
â€Å“to to munaya ce? hayaniyar mi nakeji haka agidanne Munaya?â€?.
K'yafta min ido da zungurina Munubiya tashiga yi wai karna fad'a masa (dayake a Hans free nasaka wayar, tana jin komai) amma saina harareta da murgud'a baki nace, â€Å“Abba Mama Ce da maman safara'u suke fad'aâ€?.
Tsaki yaja da fad'in â€Å“ALLAH ya shiryesu to, ina maman taku ne?â€?.
â€Å“Amin Abba, Innarmu tana can wajen rabon fad'an aiâ€?.
â€Å“shike Nan, idan tashigo kice takirani muyi maganaâ€?.
â€Å“to Abba byeâ€?.
Yace, â€Å“ok dear byeâ€?. Sannan ya yanke wayar.
Ina yanke wayar Munubiya ta kaimin bugu, Na kauce ina dariya â€Å“yo da bakina a hanani fad'ar gaskiyaâ€?.
â€Å“ba hanaki akayiba, amma kinsan idan Allura ta tono garma mune tushen fad'an ai, kinkuma san halin Abba da d'aukar zafi kamar baba k'aramiâ€?.
â€Å“tab, ta k'are musu dai suda suka takalo wlhy, jarababbu dangin masifaâ€?.
â€Å“kina ciki kenan tunda kema dangin kine aiâ€?.
Dariya muka Sanya nida munubiya.
*washe gari*
Tafiyar mu gidan mama Rabi bai yuwuba, saboda dawowar Abbanmu, da innarmu ta sanar masa a waya zamuje can muk'arasa Hutu sai yace a'a muyi hak'uri mu zauna, Dan akwai bak'in da zaiyi a k'arshen sati (weekend), kuma yanason dukkan yaran mukasance muna nan.
Innarmu tace shikenan.
Wannan dalilinne ya hanamu tafiya Hutu, dama ni ba so nakeba, Munubiya ce keta zakwad'in tafiyar.
Yau ta kasance alhamis, tunda safe muka tashi da himmar wanki nida Munubiya, ina sharar sashenmu Munubiya na fidda kayan wankin, yayinda Aryan da Aiyan keta tara mana ruwa daga fanfo zuwa banbu.
Ina gama sharar na wanke hannuna na k'arasa bakin fanfo inda Munubiya ke k'ok'arin jik'a kayan. zama nayi bisa d'an dakali da akayi wajen saboda irin hakan, wanki ko wanke-wanke da sauransu, waya nake latsawa ina nemo mana wak'a, dan muji dad'in wankin, maganar aunty khaleesa kawai mukji a kanmu tana fad'in,
â€Å“k! Munaya tashi kije ki gyaramin d'akinmu, akwai wani zanina nan ki d'akkosa ku wankeminâ€?.
Banza namata ban d'agoba, sai Munubiya ce tace, â€Å“to aunty khaleesaâ€?.
Shirun danayi ina kuma tamke fuska yasata gane nice munaya, Dan haka ta kalli Munubiya dahar tatafi, â€Å“k Munubiya!... dawo, bakece zakiyiba, k! Dan uwarku Munaya tashi kije kiminâ€?.
Da sauri Munubiya tace, "Aunty khaleesa ai nice munaya, waccan Munubiya ce�.
Hararta tayi, â€Å“mai dani 'yar iska to, ko kina tunanin ban ganeku nima d'in?â€?.
Banyi niyyar d'agowa ba, amma jin abinda tafad'a yasani sakin guntun murmushi, nasan k'arya takeyi tace tana ganemu kai tsaye, yanzu ma dan kawai na nunu halin nawane shiyyasa tagane nice, kawai tafad'ane dai, mai da kaina nayi nacigaba da abinda nakeyi.......
Wata ashar ta lailayo ta makamin, tareda zaburowa tamkar zata dakeni, dai dai nan sallamar innaro ta karad'e tsakar gidan. mu duka kallonta mukayi, nikam kallo d'aya namata na d'auke kaina, (dan nikam natsani kakarnan tamu) Munubiya da aunty khaleesa suka gaidata, nikam a d'age nace â€Å“ina kwanaâ€?.
â€Å“kin yima uwarki Ai'sha dan Ubankiâ€?, cewar innaro ta na nunani da d'anyatsanta manuniya👉ğŸ», tacigaba da fad'in â€Å“ni zakima gaisuwa a haka? kamar wata sa'ar uwarki?, aiko Aisha da ubanki basu isa sumin gaisuwa hakaba balle ke haihuwar yanzunâ€?.
Baki na la6e, ba tareda na kalleta ba natashi nahau wankin, Munubiya kuma tawuce danta gyarama su aunty khaleesa d'akinsu. abinda nayi na nuna halin ko in kula saiya kuma tunzura innaro, ta fara hayagaga da matse kwalla wai naci zarafinta.
Wannan yasaka matan gidanmu da yara fara fitowa d'ai-d'ai suna kallonmu (dan al'adar gidanmu ce hakan, da anji kaya-kaya kowa zaiyo waje yaganema idonsa abinda ke faruwa).
Dady ya k'araso da sauri yana fad'in â€Å“Inna miya farune haka da kuka? Keda waye?â€?.
â€Å“wannan shed'aniyar yarinyar manaâ€? tayi maganar tana nunani â€Å“waini yarinyar nan zataima d'ibar albarka saboda uwarsu kullum tana aibantani a gurinsu, shiyyasa duk sun rainani....â€?
Baki bud'e nake kallon innaro da sherinta. wlhy wannan tsohuwar bazataga Annabi ba........
Maganar Dady ta dawo dani daga mamakin innaro. Yace, â€Å“Munaya ce ko Munubiya? miya farune keda inna?â€?.
Dady yanada sauk'i, ba kamar Abbanmu da baba k'arami ba sun fishi zafi.
Nace, â€Å“dady Munaya ce. wlhy babu abinda namata, kawaifa daga shigowarta duk muka gaidata, shine kawai ta hau zagina wai ban gaidata da k'yauba.......â€?
â€Å“amma ai gaisuwar rashin tarbiya kikai mataâ€?. ‘cewar Aunty khaleesaâ€?.
Dady zaiyi magana Aunty Ramlah tace, â€Å“wlhy Dady ba haka bane, duk abinda yafaru akan idona yafaru, dan nafito zan d'iba ruwa a fanfoâ€?.
Dakuwa Innaro ta mata, â€Å“kinci uwarki hadiza, kema ashe munafukace ban saniba, to ko hadizar ta haifama Ai'sha ne ke?â€?.
Fakar idon Dady aunty Ramlah tayi ta dallama innaro harara, sannan tace, â€Å“yo daga fad'ar gaskiya, nidai wlhy Dady abinda nagani nakuma ji kenanâ€?.
Girgiza kai Dady yayi, sannan yace, â€Å“kiyi hak'uri Inna, Munaya tayi kuskure amma bazata sakeba. Munaya zoki bata hak'uriâ€?.
Ban musaba nazo har gabanta nace tayi hak'uri, bata amsamin ba, saima hararata datayi kawai. nima saina bar wajen nakoma kan wankina.
Dady Yakama hannun innaro suka shiga falonsa, matan gidanmu duk suka bar wajen, basuso wasan yak'are a nanba, sunso ace cin mutuncin innaro yasauka har kan innarmu.
Innarmu dake tsaye daga k'ofar falonta tanajiyo abinda ke faruwa dukda katanga ta shiga tsakiya, ta girgiza kai kawai tana komawa ciki da fad'in ALLAH ya k'yauta.
Ina wanki ina zubda hawaye, sosai raina ya sosu yau akan abinda Innaro tamin, dukda bawai yaune karon farko da hakan ya faruba, sai dai na yau yamin zafi ainun, har inaji natsani zaman gidanmu, a fili na furta ALLAH kabamu miji muyi aurenmu mubar gidannan�.
Munubiya dabansan tazo wajenba naji ta amsa da Amin sweetheart, wlhy koni yanzu addu'ar danake mana kenan, sai dai banason mutafi mubar innarmu a wannan halin dasu Aryaan�.
â€Å“hakane Munu..., karki damu, insha ALLAH munayin aure d'auke innarmu zamuyi ko Abbah ya yarda kobai yardaba wlhy!!â€?. ‘ta k'arashe maganar a harzuk'eâ€?.
Murmushi Munubiya tayi, dan tasan ran 'yar uwar tata yakai k'ololuwar 6aci.
Har muka gama wankin innaro na gidan bata tafiba, bamusan uwarmi takeyiba. dayake girkin gwaggon Haleema nema ranar. ina tsaye a bayan flowers d'in d'akinmu ina goge glass d'in windows naga Abdul yafito d'aukeda tire an jera sabbin kuloli akai, nasan Abbanmu baya gari, dan haka nace, â€Å“Abdul wazaka kaima abinci haka?â€?.
Yace, â€Å“Aunty zan kaima innaro tana falon dadyâ€?.
Kai na jinjina masa kawai nace jeka, cigaba nayi da aikina ina fad'in â€Å“shidai munafurci ai dodone, maishi yakeciâ€?.
Koda na koma ciki sai nake bama Munubiya labari, innarmu dake bayanmu bamu saniba tace, â€Å“to ina ruwankine wai Munaya?, nifa banason gutsiri tsoma wlhy, wai sai yaushene zaku daina jamin fitina a gidanan ne?â€?.
A sanyaye mukace kiyi hak'uri innarmu�.
Batace komaiba tashige d'akinta, muduka da kallon tausayi muka bita, dukda tasan ita ake tauyema hak'i amma bata ta6a nuna itace mara laifi, kullum ta amince itace a k'asan kamar yanda kowa ke kallonta agidan.
★★★★�
Washe gari Abbah yadawo da yamma, duk munyi murnar ganinsa, shima kuma hakan take a garesa.
Sai da daddare suka tara iyayenmu mata meeting shida Dady da baba k'arami.
Abbanmu yay gyaran murya sannan yace, â€Å“dama wani abune yasaka muka taraku, maganace akan yaranmu mata, Ramlah da khaleesa da Rahaima da Hauwa'u kowa yasan sun fida mazajen aure harma an tsaida bikinsu nanda bayan sallaâ€?.
Duk suka amsa da eh.
â€Å“yauwa to Alhmdllh, yanzu munada sauran yara 'yan mata agidanan ak'alla su 8, kuma duk kusan Kansu d'ayane, dukda su Ramlah sun girmemusu, to wani uzirine yataso na tilas zamu had'awa auren wasunsu danasu khaleesa. shin ko akwai wad'anda a cikinsu sukeda tsayayye? domin a fiddasu?â€?.
Da sauri maman safara'u tace, â€Å“Safara'u nadashi, dan harma yanason turo iyayensa, amma nace ta dakatar dashi sai angama na yayyensuâ€?.
â€Å“to Alhmdllhi, sai kuma wa?â€?.
Umma Ruk'ayya ma tace, â€Å“Fiddausi tanada tsayayye itamaâ€?.
â€Å“masha ALLAH, to bayansu fa?â€?.
â€Å“mamansu yaa hameed tace, â€Å“ai inaga sukenan kam Abban Hameedâ€?.
â€Å“yanzu su 6 kenan suka rage? to dama Alhaji halliru d'an majalissar datta6ai, nasan duk kunsan abokinane shak'ik'i? to shine yanemi alfarmar nemama 'ya'yansa maza biyu auren biyu daga cikin 'ya'yana, d'aya d'ansane na cikinsa, d'aya kuma d'an yayarsane tarasu tabari yacigaba da rik'onsa. to harga ALLAH nasan yaransa sunada tarbiyya dan haka na amince, amma dukda haka saida nasake dogon bincike akan yaran saboda yaron yanzu ka haifeshine baka haifi halinsa ba, to Alhmdllh suma basuda wata matsala, dan haka mun yanke magana dashi akan suzo saisu za6a acikinsu, wannan shine dalilin dayasa muka taraku kenanâ€?.
Hummm yaufa anzo da Sabon al'amari a gidan namu, nanafa iyayenmu mata suka hau tsugunne-tsugunne, kowa burinta ace d'iyarta aka za6a, harma da iyayensu safara'u dakeda mijin a hannu, ganin sunji gidan maik'one kowacce tafara k'ok'arin gani da fatan 'yarta ta kasance acikin gidan, aiko sai shirye-shirye kowa keyi a asirce, aka fara gyara 'ya'ya.
Mudai a 6angarenmu babu abinda innarmu kemana, hasalima inda taji maganar anan ta barta, komu bata sanarma ba, sai abakin Fauziyya mukejin komai.
Yanda ake shirye-shiryen bak'i takowanne 6angare saika d'auka 'ya'ya. Shugaban k'asane zasuzo, ni abinma mamaki yabani dan kowanne d'aki da nasu shirin, dayake kowane d'aki akwai budurwa d'aya, mu 8ne, su shida kowanne d'aki 1 kenan, saimu mu biyu a d'akinmu, 'ya'yan abbanmu mu 4 kenan, na baba k'arami 2 na Dady 2, gashi biyu za'a za6a acikinmu amma saika d'auka mu duka za'a za6a saboda shirye-shiryen da iyayenmu keyi.
Ranar Asabar (Saturday) kenan takama zasuzo, dan haka muduka 'yan Matan 8 baba k'arami yace muhad'u muyi girkin tarbarsu.
Ni Munaya, Munubiya, Safara'u, Fauziyya, Haleematu, Fiddausi, Zarah, Siyama.
A kitchen d'in 6angarenmu muke girkin, dukda dai iyayenmu sun d'an saka mana hannu wajen tsara kalolin abincin daya dace a tanada. Ni abunma haushi yabani, yanda naga 'yan uwana NATA rawar kai, sai wani k'alk'ale-k'alk'ale akema abinci da drinks na gargajiya damuka had'a.
A raina nace Kodai sune iyayen cin tsiya, ai bazasuci ko quarter d'in abincinnan ba, wannanma ai almabazzaranci ne wlhy, mutun biyu kawai amma anmusu abinci wajen kala 6, banda kuma kayan ciye-ciye irinsu snakes da nau'in nama da aka sarrafa zuwa daban-daban. haka dai muka gama aka kai falon baba k'arami aka shirya, sannan kowa takoma 6angarensu danta kimtsa........âœğŸ?
Anan ne za'ayi kece rainin👌ğŸ»ÄŸÅ¸˜„ğŸƒğŸ»Ã¢€Ã¢™€
Guys kumuje zuwa😉ğŸ‘ğŸ»
One luv🥰🥰
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*ğŸ‘ğŸ»ÄŸÅ¸˜
[4/22, 2:13 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
_Ban yarda wani yaymin amfani da labarin nanba tako wace irin hanya, idan hakan tafaru ban yafeba gsky, ALLAH yabani ikon fad'ar abinda zai amfanar dani da Ku, ya tsare harshena daga fad'ar abinda zai cutar damu baki d'aya._
*_ALLAH ka gafartama mahaifina da dukkan sauran musulmai dasuka kwanta dama, kabama marasa lafiyarmu lafiyağŸ‘ğŸ»._*
👉ğŸ»2âƒ?
...........Zan iya ce muku fitinar gidanmu ta farone daga tushe, dan kuwa ginannen abune tun zamanin k'uruciyar iyayenmu...
Malam Faruku shine kakanmu, matarsa d'aya Marwa'natu (Innaro), 'ya'ya hud'u suka Haifa a duniya, maza uku mace 1. Auwal, Hameesu, Saffiya, Jafaru.
ALLAH yayi Innaro mace mai mugun son abin duniya, arayuwarta tanason ace komai daga gareta aka fara ganinsa, kokuma wajen 'ya'yanta, sun tsayama 'ya'yansu duk sunyi karatun addini dana boko, sai dai Safiya iyakarta primary aka mata aure. Sukuma mazan duk sunkai matakin babar makaranta (jami'a). wannan yasaka Innaro d'aukar burin duniya ta d'ora akan 'ya'yan, harma matan dazasu aura.
Auwal shine yafara kammala karatunsa, dan haka Malam faruku mahaifinsu yace ya fiddo matar Aure.
Bai wani tsaya Jan rai ba ya gabatar da Ai'sha amatsayin wadda yakeso.
Kai tsaye innaro tace sam bata aminceba, d'anta bazai auri d'iyar buzayeba kuma 'Yar iska, Auwal yayi lallashin yayi rok'on akan fahimtar da ita sonda sukema juna shi da Ai'sha, amma Sam tak'i saurarensa balle ta fahimcesa.
Da farko Malam faruku yasaka musu ido, azatonsa innaro zata sakko cikin sauk'i, amma ganin yanda ta kafe akan bakanta saiya sanya baki da tambayarta dalilin k'in amincewar.
Kai tsaye tace batason su Ai'shar ne, Dan ba'asan asalin suba, sannan kuma 'Yar iskace, shima kuma yasani ai. cikin hikima Malam yaso fahimtar da ita halin k'addara kowa da irin tasa, itama Aishar bayin kanta bane ba, amma tak'i saurarensa shima. ganin abin zai tasamma rashin mutumci yace to aure tsakanin Auwalu da Ai'sha kamar anyi an gama. A wannan lokacin ba k'aramin birkicewa innaro tayi musuba, amma Malam faruku yace tayi tagama, dan hujjarta batada muhimmancin dazai haramta auren Auwal da Ai'sha. babu 6ata lokaci kuma aka fara shirin bikin.
*Wacece Ai'sha?*
Ai'sha d'iyace gawasu buzaye 'yan k'asar Niger wad'anda k'addarar rayuwa ta jawosu zuwa k'asar Nigeria, su biyu kacal iyayensu suka Haifa, Aisha itace babba, sai k'anwarta Rabi'atu, wurjanjan suka shigo k'asar Nigeria, sun fara rayuwane awata tashar mota, inda anan tsautsayi ya fad'ama Ai'sha wani mara imani yamata fyad'e anan cikin tasha da daddare, randa abin yafaru Malam faruku yaje tashar zai bada sak'o akaima wani d'an uwansa dake garin Maiduguri, ya taras anata cecekuce atashar, yayinda Ai'sha da iyayenta ke rungume da d'iyarsu sunata kuka da kururuwa.
Malam faruku yatambayi abinda ke faruwa daga wajen mutanen dasuka zagayesu suna kallo, babu 6ata lokaci matashin saurayi yafad'a masa komai.
Hankalin Malam faruku yayi matuk'ar tashi, danshi mutumne mai kishin al'umma, anan ya d'auki Ai'sha da iyayenta suka nufi asibiti, saboda jinin daketa zuba daga jikinta (Dan bazata wuce 15 ba sannan), duk wata kulawar da yakamata anbama Ai'sha a asibitin, har tsawon kwanaki hud'u tasamu lafiya sarai, kamarma komai bai faruba, sai dai tabo Na zuciya da aka bar mata itada iyayenta. tun suna zaman asibiti Malam faruku ya fiskanci iyayen Aisha basuda wajen zama, dan haka yak'udiri niyyar taimakonsu.
Akwai wani d'aki k'arami ciki da falo dake gidansa, saiya zagaye musu shi da Katanga yamasa gyara.
Tunda aka fara aikin innaro ta tada hankalinta, duk zatonta aure zai k'ara, ganin tana neman tara masa k'asa ya zaunar da ita yamata bayani dallah-dallah, maimakon ta kwantar da hankalinta tunda ba kishiyar bace saima takuma tadashi, tace bazata zauna da iyayen Aisha ba.
Malam faruku yace bata isaba, Dan gidansane babu mai hanashi ajiye Wanda yakeso akuma lokacin dayaso.
Dole badan innaro tasoba su maman Aisha suka zauna agidan, sai dai ko kad'an basajin dad'in zama da ita, kullum gori da cin mutunci take musu, su Aisha kam basuda sakat awajenta, saita koma sakasu aiki tamkar boyi-boyinta. Malam faruku ne ya koyama mahaifin su Aisha sana'a, har shima yasamu rufin asirin rik'e iyalensa dai-dai gwargwado, amma ko kama k'afar Malam faruku baiyiba, lokuta da fama ma shine ke taimakonsa dawasu abubuwan Na rayuwa, musamman d'inkin sitturar su Aisha da wasu matsaloli Na yau da kullum dasukan taso. tun zuwansu gidan Auwal yafara k'aunar Aisha, duk da mahaifinsu ya Sanar musu da komai akan k'addarar da ta fad'ama Aishan kuwa, shekararsu biyu suna soyayya, tun Aisha Na d'ari-d'ari dashi saboda tsoron abinda aka aikata mata har tazo tasaki jikinta dashi, sai dai babu Wanda yasan suna soyayyar sai Rabi'a k'anwarta.
Ana haka kuma Auwal yazo da zancen Aisha zai aura.
To haka dai akayi auren Auwal da Aisha badan innaro tasoba.
Wannan kuma yasakata d'aukar Karen tsana ta d'orama Aisha, kullum cikin zagi da cin mutuncin Aisha take, sosai tazamar mata Uwar miji mai kishi da sarakuwa, ga gorin datake mata akan ita 'Yar iskace, babu wani fyad'e da'aka mata, taje tayi iskancinta an fake da fyad'e an dawo an lik'ema d'anta da asiri, tujara dai iri-iri dai ta innaro.
Aisha tanada hak'uri, ko kad'an abinda innaro kemata bai hanata girmamata ba da bata matsayi irinna uwa, amma innaro bata gani.
Watan aurensu 7 kacal innaro ta samoma Auwal wata yarinya mai suna Mero, mero d'iyace ga wani matashin d'an kasuwa, tun alokacinma ana lissafashi a masu kud'in yankin balle yanzu daya zama shahararre, Auwal bayason Mairo, amma dolensa ya aura saboda innaro tace zata tsine masa.
Shigowar Mairo Yakuma k'untata Aisha a gidan, dan tunkan ta shigo innaro tagama 6ata sunan Aisha dana iyayenta awajensu mairo, shigowar mairo da wata 1 kacal kuma tasamu ciki, wannan fa yakuma k'ara ta6ar6arewar al'amura, gashi sannan ALLAH ya yalwatama Auwal d'in babu laifi, harma yasayi wasu filaye uku shida 'yan uwansa anan cikin anguwar kusada su innaro, amma ba'a ginaba, dan babu kud'in ginin lokacin.
A wannan lokacinne kuma k'addara ta afkama iyayen Aisha, ranar wata alhamis da daddare aka maka ruwa Na tashin hankali, Wanda yay sanadin fad'awar d'akin dasuke ciki suka rasu.
Aisha da Rabi'a sunshiga matuk'ar tashin hankali, hakama Malam faruku, innaro kam ko'a jikinta.
Rasuwar iyayen Aisha yasaka rabi'a k'anwarta dawowa hannunta da zama, akuma lokacinne Hameesu shima yace Rabi'a yakeso da aure. tashin farko innaro ta taka masa birki da kukarin zata tsine masa kuwa. dole yabar maganar auren Rabi'ar yasamo wata Ruk'ayya ya aura.
A lokacinne Mairo ta haihu namiji, zokaga murna wajen innaro da mairo, Malam ma yayi murna, hakama Aisha, dukda innaro tace Na munafurcine. ranar suna yaro yaci Abdulhameed, koda wasa mairo bata ta6a yarda Aisha ta d'auki hameed ba, dan innaro tahana, Auwal yayi fad'an shida Malam harsun gaji.
Rayuwa tacigaba da tafiya tsawon shekaru, zuwa sannan su Auwal sun had'a hannu sun gina filinsu, kowa da 6angarensa, gidanmu yafara yawaita da 'ya'ya, dan matar Hameesu ma ta haihu Namiji Shafi'u, hakama matan gidanmu sun k'aru, dan jafaru ma yayi aure, hakama Hameesu yak'ara aure shima, ga iyayenmu sun kuma bunk'asa, dansu wuce buk'atun yau da gobe, dai-dai gwargwado akwai rufin asiri agaresu, alokacin kuma sai Auwal yakuma auro ta uku, auren iyayenmu yakoma tamkar gasa wajen za6o 'ya'yan manya, dan kuwa Aisha ce kawai d'iyan talakawa acikinsu, tana zaunene kawai da k'arfin ALLAH dakuma Na Malam faruku, saikuma soyayyar mijinta Auwal, amma da dan ta innaro ne da tuni Auwal ya saketa.
Akwaima randa fada ya had'a mairo da Aisha akan Rabi'a ta doki hameed saboda yamata rashin kunya, dukan da mairo taima Rabi'a saiya sa Aisha kasa hak'uri a ranar ta tanka mata, nankuwa mairo tafara zuba mata gori da cin zarafi, da innaro tazo danjin ba'asin rigimar saitace dole Auwal yasaki Aisha, dukda kuma mairo ce mai laifi, Auwal yayta magiya amma innaro tace yaza6a ko ita ko Aishan, babu yanda zaiyi yasaki Aisha saki d'aya alokacin. Hankalin Aisha yatashi matuk'a, dan batasan inda zasu dosaba, tunda basuda kowa a Nigeria, ga innaro tsaye akanta tace atake saita bar mata gidan d'a.
ALLAH ya tak'aita abunne dai-dai sanda Aisha ke fitowa rik'eda hannun Rabi'a kuma saiga Malam faruku yadawo daga kasuwa, nanfa ya tambayi ba'asi, Aisha tasanar masa komai, maidata yayi gidan, yakuma saka Auwal ya maida aurensu atake awajen, sannan ya tabbatar masa ko bayan babu ransa yasake sakin Aysha bai yafeba, kuma inhar innaro tasake sakashi ya saketa itama abakin aurenta.
Wannan shine dalilin dayasa auren Aisha da Auwal bai sake rawaba. rayuwa kuma tacigaba da shurawa. Matan gidanmu 7.
Auwal matansa uku, Aisha (innarmu) Mairo (mama) Sadiya (gwaggon haleema)
Hameesu nada biyu, Ruk'ayya (umma) Hadiza (momy)
Jafaru Nada biyu shima, Suwaiba (maman safara'u) Hafsatu (maman Fauziyya).
Kowacce ta haihu acikinsu, amma banda Aisha, wadda saida sukayi shekara 20 da aure itada Auwal sannan ALLAH yabata ciki, zokiga murna wajen Auwal da ahalinsa, saidai banda matan gidanmu da innaro, dan aganinsu duk sunfi Aisha matsayi, (maman fauziyya) Ce kawai babu ruwanta, dan suna d'asawa da Aisha sosai, ita kad'aice bata raina innarmu ba, dan Yaya ma take cemata.
Babu irin wahalar da Aisha batasha agidanba acikin shekarunan, kullum cikin mata gorin haihuwa dana talauci ake, harma dana batada asali, tundaga kishiyoyinta har matan k'annen mijinta basu raga mataba, kowacce jitake ina wuta tasaka innarmu a gidan, dama ga d'aurin gidi daga innaro suna samu. innarmu bata cemusu komai, saidai tashiga d'aki tasha kukanta, 'ya'yan maman fauziyya ne kad'ai ke shigowa d'akinta, amma sauran duk an hanasu, gashi ta aurar da Rabi'a tuni, itama harta haihu uku ma.
to saikuma ga Aisha da ciki rana tsaka, bayan tagama fidda ran haihuwarma gaba d'ayanta. cikin ikon ALLAH cikinta yakai haihuwa, ranar data haihu saiga 'yan biyu k'yawawa kamarta duk mata, A zahiri matan gidanmu suna k'untatama innarmu ne saboda yanda innaro tagama 6ata Aisha awajensu, a bad'ini kuma suna k'in Aishane saboda tafisu k'yau da komaima Na halittar jiki, (dan cikakkiyar buzuwa Ce) mai k'yawu Na asali, dirarriyar macece doguwa, fara tas, gashin kai, idanu da komai ALLAH yabatasu. Sa6anin su daba haka sukeba. cikin ikon ALLAH kuma saigashi ta haifo 'ya'yanta masu tsananin kama da ita.
Hassana (Munubiya) da Hussaina (Munaya) wad'anda suke matuk'ar kama da juna, kamar Munaya da Munubiya ta 6aci matuk'a, ko Aisha saitayi da gaske take banbancesu, saida suka fara girmanema ake d'an banbantasu tawajen halayya shima ba kowaba, amma Aisha ita tana ganesu kai tsaye a sanan.
Munubiya tanada hak'uri tamkar Aisha, duk wahalar dasukesha wajen yaran gidan bata iya ramawa, saidai tasha kukanta tashare hawaye. sa6anin Munaya da take fitinanniya, bata bari a cuceta, koda anfi k'arfinta saitabi tawata hanyar tarama kuwa, wannan yasaka matan gidan da yara sukafi tsanarta, sai dai kuma basa iya banbancesu itada Munubiya, sometimes Munaya takanyi laifi akama Munubiya a daka, itakuma Munubiya bazata ta6a fad'in ba itaceba.
Ganin hakan yasaka Aisha yima Munubiya shaida saboda aringa banbantasu, amma Munaya Na k'yalla ido tagani sai itama tayima kanta irin ta Munubiya komai da komai, idan sau dubu akama Munubiya shaida ajiki Munaya ma zataje taima kanta, hakama Munubiya takanyi idan anyima munaya, hakan yasa Aisha ta hak'ura kawai harma suka Shiga makaranta, nanma rikicin Munaya bai k'areba, dan saima abinda yay gaba, tajawo fad'a akama Munubiya adaka, hakan kuma bazaisa gobe ta fasaba.
Shekarar su goma Aisha takuma haihuwar 'yan biyu duk maza, Aryaan da Aiyyaan, tundaga lokacin kuma bata sakeba.
Sai dai Munaya da Munubiya suna matuk'ar k'aunar junansu over abinma har saiya Baka mamaki, sannan suna k'aunar mahaifiyarsu da k'annensu, Munaya ce kan shiga idan ana cin zarafin mamansu, amma ita Munubiya saidai taita kuka.
Yanzu haka zancen danake muku shekarunmu 19 nida Munubiya, muna matakin farko a jami'a, munzama 'yan mata, k'yawunmu da tsananin kamarmu da innarmu yasake fitowa, mun fita daban a gidanmu, dan mukad'aine kamarmu daban, Ayyan da Aryan ma duk Abbanmu suka kwaso, wannan yasaka suke kama da 'yan gidanmu.
Tabbas bamajin dad'in zaman gidanmu, saboda k'unci da hantara damuke fuskanta muda mahaifiyarmu awajen Innaro da matan gidan, harma dawasu yaran gidan 'yan uwanmu, amma wasu muna shiri dasu sosai, musamman ma mazan yayyenmu manya, dansu babu ruwansu da gutsiri tsomar cikin gidan.
Gidanmu gidane tamkar gidan hayar daya had'a k'abilu daban-daban saboda yawan rikici, kullum cikin fad'a muke, ba iyayenba ba yaranba, kai kace muna ganin hanjin junane.
Gwargwadon iko akwai hali a gidanmu, dan iyayenmu sun rik'e gidanmu sosai da buk'atinmu, dukda yawa da ALLAH yabamu, bamu rasa ci da sha ba da situra, hakama matsalolin karatunmu, dan kai tsaye zance gidanmu gidan 'yan bokone, kullum cikin gasa da juna ake, burin kowa ace shine gaba, batun ilimin addinima kam Alhmdllh, dan tsaye iyayenmu suke akanmu, har gobe yaa hameed bai daina zama gaban malamai ba balle mu 'yan baya-baya. ak'alla yaran gidanmu munkai mu 43 kuma.
ALLAH yayma Malam jafaru kakanmu rasuwa shekara biyu kenan, innaro Ce dai tana nan daram, al'amuranta sai abinda yay gaba, dan har gobe bata k'aunar innarmu, kuma bata daina cin zarafinta ba agaban kowa da mata gorin rashin dangi.
Hakan yasa kullum cikin buri da k'udirin binciko dangin Innarmu nake, ko itama zata samu 'yancin kanta kamar kowa😢.
Wannan shine labarin gidanmu, sai ahankali zaku cigaba da fuskantar ainahin halayen jama'ar gidanmu da aiyukansu, harma da sunayensuğŸ˜Å .............âœğŸ?
To masu karatu, sai nace yanzufa za'a fara, saiku kasance dani danjin labarin *_RAINA KAMA.... kaga gayya_* dan akwai babban al'amari a gaba, bawai gidan su Munaya kawai labarin ya shafaba, akwai wani lauje cikin Nad'i daga d'ayan 6angaren labarin Na Raina kama.....😉 suga gayya bağŸ‘ğŸ»ÄŸÅ¸˜„.
One luv🥰
*_ALLAH ka gafartama IyayenmuğŸ˜ÄŸÅ¸‘ğŸ»_*
[4/22, 2:13 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
👉ğŸ»4âƒ?
.......Daga ni har Munubiya babu wata kwalliya damukayi, hasalima ni ko mai k'in shafawa nayi, danayo wankanma sainayi kwanciyata na hau barci. sai wajen 1 munubiya ta tadani wai sun iso, dama lokacin duk fashin salla muke nida munu.... (zakusha mamaki idan nace muku dai-dai da prioud yakanzo mana rana d'aya nida hassana ta, kuma musami tsarki tare), tashinai ina yatsine fuska, dan naji haushin tadanin datayi, toilet nashiga domin kimtsa jikina, sama-sama nadinga jiyo maganar Ikram tana fad'in â€Å“Aunty wai innaro tace kuzoâ€?.
Cikeda mamaki munubiya ta amsa da to. nima abin yabani mamaki, dan haka nafito da Sauri, â€Å“wai Munubiya minake jiyowa ina toilet? â€?.
Maganarta d'auke da mamaki tace, â€Å“wai innaro ke kiranmuâ€?.
â€Å“ni da ke? kokuma mu duka?â€?.
â€Å“wlhy ban saniba munaya, sai dai munje d'in maganiâ€?.
Innarmu tashigo d'akin tana cewa â€Å“waishin Baku naji innaro ta aiko kira bane?â€?.
Muka amsa da â€Å“eh innarmu, muneâ€?.
â€Å“to mi kuke jira, kuwuce kutafi manaâ€?.
Babu Wanda yay magana acikinmu muka fita muna mamakin wannan kira Na innaro.
Tun a k'ofar falon baba k'arami mukaga wasu k'yawawan takalma, ga wani k'amshi yacika wajen, wicewa mukayi batareda mun shigaba, dukda mun hango Zarah da Siyama da Fiddausi natahowa cikin matsanancin gayu, saika rantse fita zasuyi wani gagarumin biki.
A k'ofar gidama munci karo da motoci uku duk bak'ak'e wulik, sai dai ta tsakiyar tafi k'yau da d'aukar hankali, garadan samarine majiya k'arfi kusan su 7 tsaitsaye ajikin motocin, duk suna sanye da bak'ak'en suit, daka gansu kasan babu sauk'i, hakan yasa muka fahimci bodyguards d'in bak'inne.
Gida biyu ne tsakanin gidan innaro da gidanmu, dan haka muka Isa da wuri. a tsakar gida muka isketa tana shanyar lawashin albasa. muka gaidata.
Yanda ta saba haka ta amsa mana, amma tace mushiga ciki tana zuwa.
Kusan mintuna 40 muna falon innaro zaune, amma bata shigoba, hakan yasakani tunanin tabas akwai wani lauje cikin nad'i a kiran namu, tashi nayi nalek'a tsakar gidan ta window, amma bata nan. â€Å“Munubiya kinsan Innaro bata gidanan kuwa?â€?.
Cikeda mamaki tad'ago tana kallona, â€Å“kamarya bata nan?â€?.
â€Å“Munu... Wlhy ko rantsuwa nayi babu kaffara aciki, akwai dalilin kawomu nanâ€?.
A sanyaye Munubiya tace, â€Å“karki damu Sweetheart, ko mai suke nufi ALLAH ya fisu, dama naga mamansu ya hameed tafito d'azu bayan mungama girki, ai d'an hakkin daka raina shike tsolema ido, *_RAINA KAMA KAGA GAYYAFA_* inji masu iya magana.
Hakane dear.
Daga nan muka zauna shiru kowa da abinda take tunani, har barci ya sace Munubiya, nukuma nahau chart kawai.
A gidanmu kuwa su Siyama ne suka fara Isa falon, tundaga k'ofar falon daddad'an k'amshin turaren bak'in yafara rikitasu, sun shiga da sallama, yayinda sukuma bak'in suka amsa.
Gaskiya masha ALLAH dan kuwa matasan samarine k'yawawa masu aji da gayu, suna kama da juna, hakan zai tabbatar maka da cewa jininsu d'aya. sunci ado cikin wasu rantsatstsun shaddoji gizna, sai maik'o sukeyi, d'aya yafi d'aya sakin fuska.
Su Siyama sun gaidasu cikin shauk'i da zumud'in fatan kowaccensu ta kasance abar za6i.
Sun amsa musu cikeda jan aji da nazartar su, ahaka Fauziyya da Safara'u da Haleematu suka shigo suma, suma dai gaidasun sukayi. Fauziyya da Zarah ne kawai sukayi hankalin tashi su zuba musu ruwa da lemo, sannan suka musu bismillar abinci.
Mai d'an yawan fara'ar ne yamusu godiya, sannan yace, â€Å“to ya sunan k'annen namune?â€?.
Cikeda yanga kowacce tafara gabatar da kanta agaresu, yayinda sukuma suka maida hankali sosai wajen nazartarsu, bayan sun gama suma suka gabatar musu da kansun.
â€Å“Ni sunan Sulaiman, brother d'ina kuma Sa'eed, munji dad'i kwarai da gaske Na tarbar damuka samu daga garekuâ€?.
Murmushi duk sukayi suna nuna farin cikinsu suma, sund'an ta6a hira.
Babu Wanda yadamu da rashin ganinmu acikinsu sai Fauziyya, iyayenmu kuma basusan babumu ba, dansu suna falon Abbanmu suna hira.
Kusan awa d'aya sannan duk suka fito suka barsu dan sud'anci abinci.
Suna fita Sa'eed ya kalli Sulaiman a yatsine, â€Å“my man nida yaran nan nakula sunada rawar kai, garama mai farin kayannan naga kamar tafisu nutsuwa (Fauziyya)â€?.
â€Å“wlhy gskyarka bro... Amma Kasan dolenefa mucika umarnin dad, tunda yayi rantsuwa akan dolene muza6a acikinsu, kai wlhy mun jama kanmu, ni dama tun maganar farko da dad yamana Na maida hankali naza6o da duk hakan bata faruba gareniâ€?.
Cikin ta6e baki Sa'eed yace, â€Å“wannan kuma kaika Sani malam. amma basuma 8 akace manaba?â€?.
â€Å“eh hakane, amma kamanta ance biyu acikinsu sunada samariâ€?.
A nanma bakin Sa'eed Yakuma ta6ewa. sun d'anci abinda aka ajiye musu, sannan su Abba suka shigo suka gaisa, cikeda girmamawa suka gaida su Abba, hakan yayima Dady da baba k'arami dad'i, sun kuma tabbatarwa yaran sunada tarbiyya, dama basa kokwanto akan zance yayan Nasu.
An musu rakkiya duka Sassan gidanmu, sun Haida iyayenmu mata. ganinsu Yakuma rud'ar da iyayenmu, kowacce addau'arta ALLAH yasa d'iyarta aka za6a, yo wad'annan zuk'a-zuk'an samari haka, ga kud'i ga ilimi, kowacce saida suka ajiye mata kud'i suke fitowa, har innarmu ma.
Tun aiko kiranmu Innarmu taji ajikinta da biyu aka turamu can, amma baiwar ALLAH hakan bai dametaba, tasan dai wata bata aurar mijin wani, dan haka ko'a fuska bata nunama wani bama cikin wad'anda suka je wajen bak'inba.
Saida Innaro takusa awa d'aya sannan tashigo gidan, yinai tamkar ban gantaba, Munubiya kam tanata barcinta, itama sai bata kulaniba tashige bedroom d'inta.
Shigarta baifi da mintuna 3 ba mukajiyo sallama a k'ofar d'akin, nice Na amsa, Basheer yafara shigowa, sai kuma Sulaiman da Sa'eed, irin k'amshin damukaji a k'ofar d'akin baba karami yasani d'agowa dan jinsa anan, hakan ya tabbatar min da sune sukazo gaida Innaro.
Tunda suka shigo idonsu ya sauka a kanmu, sun kasa d'auke kai daga kallonmu.
Cikeda jan aji nace, â€Å“ina yininkuâ€?.
Duk suka amsa da â€Å“lafiya big girlâ€?.
Basheer yace, â€Å“kai Aunty dama kuna nan Ku?â€?.
Kallonsa nayi nace, â€Å“eh, ana nemanmu ne?â€?.
â€Å“a'a, amma dai ba'asan badaku akaje wajen bak'ibaâ€?.
Hararsa nayi, saboda sanin halin shegen surutunsa, â€Å“malam kaje ka kira musu Innaro ka zauna kana zubama mutane shegen surutu uwa akuâ€?.
Baki ya zum6ura sannan yanufi bedroom d'in Innaro.
Wanda tunda suka shigo yakasa d'auke kai daga kallona, saima zama dayayi kujeraf dake kallona yace, â€Å“ok dan bakwa buk'atar ganinmu kuka gudonan kenan? Sai kuma gashi ALLAH ya kawomu mun ganku, dama ance rabon kwad'o...... koko my man?â€?.
Murmushi Sulaiman yayi, yace â€Å“hakane wlhy bro, hakanma dasukayi yamana dai-daiâ€?.
Magan ganinmu yasaka Munubiya tashi, Sulaiman yace, â€Å“sleeping beauty kin tashi?â€?.
d'an waro idanu Munubiya tayi, sai kuma ta kalleni dan neman k'arin bayani.
Innaro takatsemu da fad'in â€Å“toku kuna ganin bak'i basai Ku tashi Ku basu wajebaâ€?.
â€Å“cikin tsokana Sulaiman yace, â€Å“a'a Granny idan sun tashi wazamu kalla? Sun gudo wajenki dan karmu gansu kuma sai gashi ALLAH ya kawomu har gidaâ€?.
Ba k'aramin k'ona ran innaro maganar tayiba (dama an kawomu nanne dankar bak'in su gammu balle su za6emu, amma kuma sai gashi sun gammu anan d'in. Anyi gudun gara kenan.....🤣ğŸ™Å ).
Bamu tsaya sauraren abinda innaro zata ceba mukayi fitowarmu zuwa gida.
Su Sa'eed sun gaida innaro, anan take tambayarsu kosun za6a acikin wad'anda sukaje gaishesu acan gidanmu.
Sa'eed yace, â€Å“eh mun za6a Granny, amma wad'annan dasuka fita yanzuâ€?.
Caraf innaro tace, â€Å“ai wad'annan anmusu miji shiyyasa su basujeba, sai dai cikin wad'ancanâ€?.
Bahaka sukasoba, amma yazasuyi, sai dai har sukabar gidan basu sanar da wa suka za6aba.
Koda muka sanarma innarmu cewa tayi babu ko mai, karma hakan ya damemu.
★★★★★★★★
Har tsawon kwana 5 babu wata magana data fito akan suwa bak'in suka za6a, su Abba basuce da kowa komaiba.
Hankalin iyayenmu mata duk atashe yake, kowa takasa kunne taji wacece aka za6a, sai dai babu mai iya tunkarar iyayenmu maza da zancen, dan duk ba suga fuskar hakanba.
Satinsu guda da zuwa saiga bak'i sunzo wai an kawo kud'in aure.
Hankalin iyayenmu fa yakuma tashi, dan ganinsu wani munafurcin akayi shiyyasa aketa k'unbiya-k'unbiya. Nanfa suka shiga 'yan tsugunne-tsugunne Na gulma irinta gidan yawa.
Kwana biyu dayin haka su Abba suka sanar da cewa nida Munubiya sukace sun za6a.
Innaro ce tafara k'aryatawa, sannan tace, Sam bata aminceba, ina jikokin talakawa 'ya'yan bak'in haure suka kai matsayin auren 'ya'yan babban mutun irin sanata halliru, ai k'aryane sannan munafuncine, agabanta su Sa'eed sukace Zarah da Siyama suka za6a. (Zarah k'anwar ya hameed Ce, babanmu d'aya, Siyama kuwa d'iyar momy Hadiza Ce d'iyar dady).
Jin wannan zance yasa kowa ya fahimci akwai munafunci a lamarin, kowa yasan yanda mamansu ya hameed suke da momy Hadiza a gidan, kansu had'e yake. aikam matan gidanmu suka harzuk'a sunata yada magana, harma abin yaso yazama fad'a, innarmu ce batace komaiba, ita cewama Abbanmu tayi dan ALLAH amaida zancen auren kansu Siyamar tunda innaro tace dama su suka za6a.
Banza abbanmu yamata dan yasan innaro tayi hakanne danta k'untatama innarmu, amma tabbas dabakin su Sulaiman sukace 'yan biyunnan suka za6a, shin sai yaushene inna zata bar muzgunama Aisha da munanata a gidannan?, shekara kusan Arba'in ana Abu guda babu sassauci, tunda yake baita6a ganin rana d'aya da innarmu tama innaro koda kallon banzaba bare rashin kunya, sa6anin sauran matan gidan da basa kunyar ya6a mata magana koda ta habaicine.
Kwana kusan hud'u ana d'auki ba dad'i akan wannan zance, saboda akawo k'arshen maganar sai Abbanmu yace su Sa'eed suzo su nuna wad'anda suka za6a da kansu.
Hummm bamusan miya faruba, (konace mi innaro dasu momy hadiza suka k'ulla ba) munga dai sunta murnar zuwansu Sa'eed d'in, sai rawarkan had'a abincin tarbarsu sukeyi, dan ranar su biyu kacal sukayi, kuma abin mamaki wannan karon agidan innaro aka saukesu.
Bayan isowarsu dakamar mintuna 20 sunci abinci sai akace duk muje gidan innaro.
Su Haleematu duk sun rigamu tafiya, mune k'arshen zuwa muda Fauziyya, saidai muna shiga gidan Innaro ta samu mukabi ta k'ofar kitchen nida Munubiya kawai, Fauziyya kuma aka barta tashiga ta falo.
Yanda sukaita zumud'in kallonmu wancan karon a yau ba haka bane, gaba d'aya hankalinsu Na kan Siyama da zahra, abin ya bamu mamaki har sauran 'yan uwanmu.
Tunda mukaga haka duksai muka fice muka koma gida, su Haleematu harda kukansu, mukanmu zukatanmu sun sosu, dan harga ALLAH Sa'eed ya kwantamin arai.
Wanan lamari saida yajawo gagarumin fad'a agidanmu irinma wanda ba'a ta6a yiba, dan saida takai matan gidanmu da 'Yar tone-tone asirinsu yanda suke kulle-k'ulle wani lokaci akan innarmu da junansu.
Sosai ranar saida ran kowa ya 6aci, amma mamansu yaa Hameed da momy Hadiza su wasai sukejin kansu, koba komai sune a sama suke gani, 'ya'yansu zasuje gidan Hutu.
Abbanmu yasamu innarmu yayta bata hak'uri, dan tabbas yanada tabbacin akwai lauje cikin nad'i akan lamarin, tunda su Sa'eed da kansune suka Samar masa za6insu, amma gashi a wannan karon since su siyama ne ba 'yan biyu ba.
ALLAH sarki innarmu sarkin hak'uri, cewa tayi babu komai, dama can su Siyamar ne matansu, Dan haka tunran gini tun ran Zane, suma sauran ALLAH yabasu Na kwarai.
Sosai Abba yak'ara jin jinama hak'uri da tawakkali irin Na matar tasa, abin sonsa, wadda yakejin har duniya ta tashi k'aunarta dabance a ransa, yana sonta harma baisan yanda zai fassaraba, kullum cikin mata k'yak'yk'yawar addu'a yake akan ribar hak'urin datakeyi da kowa agidan har mahaifiyarsa. yana ganin Kimar Aisha sosai da girmanta, tunda suke babu rana d'aya dazaice gawani abun aibu data aikata masa, sai dai abinda ba'a rasaba saboda zomu zauna zomu sa6a, balle shekara kusan 40 ba wasabace.
★★★★★★�
An tsaida bikin Siyama da Zarah dai-dai danasu aunty Hauwa'u, komai kuma ankawo, saura lefe da sadaki kawai.
Ahaka muka koma makaranta inata yak'in fidda Sa'eed daga raina, ALLAH ma ya taimakeni dama bawai yashiga irin cancikin nan baneba.
******
Yau lectures d'in safe garemu, dan haka mukayi shiri da wuri nida Munubiya, a tsaitsaye mukasha kunun da innarmu ta dama mana, Dan yau girkin mamansu ya Hameed ne, idan bata gadama ba sai takai 8 bata kammala ba, har yara saisun makara,
Aiyaan yashigo d'auke da lunch boxs nasu yana tura baki gaba. â€Å“kai kuma lafiya kake cuno baki uwa na agwagwa?â€?.
6ata fuska yakuma yi tamkar zai fasa kuka, ya zube lunch boxs d'in saman kujera â€Å“Aunty ba mama bace tace wai yau batayi abincin dazamuje dashi makaranta ba, hakama fa jiya abincin dare ta d'umama ta zuba mana, amma damukaje school saigashi a kulan Haneep Indomi ne da kwaiâ€?.
Aryaan ya kar6e da cewar â€Å“ALLAH kuma aunty namu tsami yayi kafinma muci, haka mukadawo da yunwaâ€?.
tausayi yaran suka bani, Munubiya tace, â€Å“kuyi hak'uri kunji 2 d'in inna, watarana sai labari aiâ€?.
Kansu suka jinjina mata sukace â€Å“to auntyâ€?.
innarmu tana jinmu amma uffan bataceba.
Fita nayi batareda nacema kowa komaiba, wani shago dake can k'asan layinmu naje, nasiyo musu yoghurt da cake k'ananu, nahad'o musu da biscuits.
A harabar gidan Na iskesu harsun fito, sauran yaran sunata shiga school bos d'insu da ake kaisu makaranta. School bag d'insu nabud'e Na saka ma kowa nasa, sannan nace ayi karatu da k'yau kunji babys d'inmu�.
Cikeda jin dad'i suka amsa min da fad'in â€Å“to auntynmuâ€?.
Kumatunsu Na sumbata sannan na taimaka musu suka shiga motar suma.
Ina shigowa munubiya tamik'e tana fad'in â€Å“wai ina kikaje? kinsanfa jarababben lecturer d'inanne zai shigar mana yauâ€?.
â€Å“sorry sweetheart tashi mujeâ€?.
Dubu 1 innarmu tamik'o mana, kar6a mukai muna mata godiya, muka fito tana binmu da addu'oin fatan alkairi.
Mun lek'ama su Siyama, kowacce sai tace batada lectures d'in safe, fauziyya da Feedausi ce kawai muka tafi, dansu duk department d'inmu d'ayane..........âœğŸ?
One luv🥰🥰
*_ALLAH ka gafartama iyayrnmuğŸ‘ğŸ»ÄŸÅ¸˜_*
[4/22, 2:13 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
👉ğŸ»5âƒ?
...........Wajen 4pm muka fito daga cikin makaranta, mu 6 ne yanzu, sa6anin d'azu damukazo mu hud'u, bayan tahowarmu Safara'u da Haleematu suka taho suma, duk da mun rigasu gama lectures sai muka jirasu suka fito muka rankayo tare domin tafiya gida, bamu samu school bos ba, dan haka muka da6o sayyadarmu har zuwa babban gate, muna tsaitsaye abakin titi, tareda wasu daga cikin tsirarun d'alibai irinmu, tundaga nesa muka hango tahowar motocin da uban gudu, saika d'auka sukad'aine akan titin saboda gudun dasuke tsulawa tamkar zasu tashi sama. duk baya muka matsa, dan tabbas wad'annan suka sameka babu abinda zai hanasu takeka su wuce batareda sun damuba.
Tamkar wucewar iska haka suka dinga gittamu, jikake shuuuu!! shuuu!! shuuu!!.
Furicin wani mayshin saurayi dake jingine jikin motarsa yazo d'aukar wasu 'yan mata biyu dake gefenmu 'yan matan sunada jin kan masifa, ko'a makarantar bakowa sukema maganaba, department d'inmu d'aya dasu amma ko kallo basu isheniba, dan ko sallama bata ta6a had'ani dasuba..
Saurayin yabi motocin da kallo yana fad'in â€Å“tab ashe *_GALADIMA!_* yashigo gari kenan?â€?.
â€Å“Da gaske yaa Usman?â€?. ‘d'aya acikin 'yan Matan tafad'a cikin matuk'ar zumud'iâ€?.
Yace, â€Å“da gaske mana baby, baga motocinsa kuna ganin sun wucebaâ€?.
Dan danan suka shiga murna, kai kace an musu albishir da aljanna ne.
Baki na ta6e inajan k'aramin tsaki. Fiddausi tace, â€Å“to waye shi galadima d'in?â€?.
â€Å“oho musuâ€?, ‘cewar Munubiyaâ€?.
Budurwar dake tsaye d'ayan gefenmu itada saurayinta suna jiran abin hawa suma tace, â€Å“Galadima d'an Sarki kenan, *Yarima Sameer!â€?*.
â€Å“humm lallai kuce manyane, shiyyasa suke gudun da kosunbi takan talaka babu abinda za'ayiâ€?. ‘cikeda 6acin rai nake maganarâ€?.
Dariya su siyama sukayi suna fad'in â€Å“toke ina ruwanki?, k'asarfa tasuce, sai yanda sukayi da ita, tsakaninmu dasu saidai mu hangesu cikin mota ko ranar hawan sallaâ€?.
Dogon tsaki nakuma ja tareda kauda kaina daga garesu na maida hankalina wajen tare wata taxi dake gabatomu.
A motama firar dasu Haleematu sukaitayi kenan, ta Galadima ne ko uwarmi ne ma Na manta. nidai uffan ban kuma tofawaba, hasalima haushi hirar tasu takoma bani, dan mai taxi d'in yasaki baki sai wani basu labarin Galadima d'in yakeyi dakuma kwarzan tashi, earphone na jayo a cikin lady's bag d'ina na manna a kunne danma nabar jinsu gaba d'aya.
Saida muka iso gida sannan Fauziyya dake kusa dani ta zungureni, d'agowa nayi Na kalleta sainaga duk sun fice, bance komaiba nafito nima.
Mun iske innarmu bata nan, saisu Aiyaan kawai zaune a falo suna kallo, shigowarmu yasasu tasowa da gudu suna mana oyoyo, muma mun taryesu da murnarmu, Munubiya tace, â€Å“Aryaan miyasa baku cire Uniform ba kukayi wanka?â€?.
â€Å“yo aunty mun dawo munga Innarmu bata nananeâ€?.
Nace â€Å“innarmu bata nan? to ina taje?â€?.
â€Å“muma bamu saniba aunty, munje kuma kitchen bamuga abinci ba, kuma yunwa mukejiâ€?.
Munubiya tace, â€Å“ya salam, kujira ina zuwaâ€?.
Fita tayi, babu dad'ewa sai gata tadawo cikin damuwa, ina cirema su Aryaan Uniform, Na kalleta ina fad'in â€Å“mike faruwa Munu...? Ina abincinne?â€?.
Kwallar idonta ta share, ta zauna bisa kujera sannan tace, â€Å“naje mama tace wai innarmu ta d'auka abinci tatafi dashi hospital, dan haka shine rabonmuâ€?.
Raina a 6ace na mik'e zan fita, da sauri munubiya ta ruk'oni, â€Å“please Munaya, kibarta kawai, yakamata mu kira innarmu muji waye a hospital? Inaga wannan yafi komai muhimmanci nake gani akan abinda mamar tamanaâ€?.
â€Å“Haba Munubiya, wannan wane irin rashin mutunci ne, wai mi Matan gidannan suke tak'ama dashine? Idan suna tak'ama da Ubanninsu muma ai nan gidan Ubanmune ko, yanzu ace yarannan kamar su Aryaan su dawo school tun 3 amma ahanasu abinci, wannan wane irin zaluncine? Kisakeni kawai naje naci kutumar uban matarnan munubiya, wlhy sai dai yau Abba yace nabar masa gidansaâ€?.
â€Å“A'a munaya, duk hakama bata tasoba, idan hankali ya6ata hankali ke nemosa, bai kamata mutaru muzama d'ayaba mu da su. bara kawai naje kicin d'in Na dafa mana wani abun mai sauk'i, kiyi hak'uri dan ALLAH, kinga innarmu bazataji dad'iba idan tatarar da faruwar hakanâ€?.
Badan raina yaso ba Na hak'ura, saman kujera nakoma Na zauna ina huci, nikad'ai nasan minakeji a zuciyata.
Munubiya tafita dan nema mana abinda zamuci, nikuma Na d'auki waya domin Kiran innarmu naji abinda tajeyi asibiti.
Harta katse bata d'agaba, nakuma kira akaro Na biyu sannan ta d'auka, gaisheta nayi da tambayar mitajeyi asibiti?.
Daga can tace min Nafisar mama Rabi'a Ce jikinta ya motsa yanzu hakama jini ake buk'ata amma an Gaza samu, gashi yaa marwan dayakan bata jinin baya nan yayi tafiya shida Abbansu.
Hankalina a tashe nace â€Å“innarmu ganinan zuwa yanzunnan insha ALLAH, kuna general hospital ne?â€?.
â€Å“eh muna nanâ€?.
â€Å“ok insha ALLAHU ganina zuwaâ€?.
'Dakinmu nashiga da Sauri nad'an watsa ruwa a tsaitsaye saboda naji dad'in jikina, komai ban tsaya shafawaba Na zira doguwar Riga jallabiya Na fice da hanzari. A k'ofar fita falo naci karo da munubiya d'auke da babban faranti tazubo spaghetti tanata turiri.
namatsa baya da Sauri INA fad'in sorry, munubiya bara naje asibitin wajensu innarmu, wai jikin feena ne ya motsa kuma ana buk'atar jini, gashi yaa marwan sunyi tafiya da abbaâ€?. Munubiya tace, â€Å“toko Na juye mana abincin a kula mu tafi gaba d'aya?â€?.
Nace, â€Å“a'a munu... Ki zauna dasu Aiyaan bara naje ni kad'ai, baikamata mubar wajen ba kowabaâ€?.
â€Å“to shikenan, yanda akayi ki ta6oni awaya, amma in kunkai dare zakuganmu muma, abincinfa?â€?.
â€Å“humm munu bar abincinnan, banida wata nutsuwar cinsa, saina dawoâ€?.
Ban jira amsarta ba nafice. ALLAH ya taimakeni INA fita nasamu napep. Mintuna kad'an muka isa hospital d'in, kud'insa na biyashi nashige da hanzari ina k'ok'arin kiran innarmu.
Babu dad'ewa kuwa ta d'aga, nace mata gani acikin asibitin. Kwatance tamin na inda aka kwantar dasu 6angaren masu sikila.
A rikice na iske innarmu da mama Rabi'a, saboda jikin feena ya motsa mata sosai a wannan karon.
Nace, â€Å“mama yanzu mi ake cikine?â€?.
â€Å“Rashin jininne matsala yanzu Munaya, sunce kuma anemoshi da gaggawa, to dama can jinin Fadeel baya yimata shiyyasama ko gwadasa ba ayiba, Marwan dake bata kuma sunyi tafiya da abbansuâ€?.
â€Å“mama ina zuwa, bani takardar da suka bakuâ€?.
Mik'omin tayi nafita da saurina. dukna rikice inata kai kawo dan ganin ansami jinin, amma har magriba ta rufa ba a samuba, saboda jinin feena yanada wuyar samu, ana cikin kiraye-kirayen sallar isha'i saiga Ayusher ta iso itama, dama an barta a gidane saboda babu kowa, to takasa hak'uri tabiyo sahu, da ita muka cigaba da shiga da fita, saida aka fito sallar isha'i ALLAH yasa aka dace da samun leda 1, saura 1, dama biyu suke buk'ata. ana cikin d'aura mata saiga Munubiya ita dasu Aryaan da kulolin abinci.
Koda aka gama sakawa sai muka koma Neman d'ayar ledar data rage, yanzu harda munubiya muke tare.
Muna a lab d'inne muna shawarar ko a d'iba namu jinin idan zaiyi babu damuwa. Takun takalman damuka jiyo yasamu juyawa harda likitan da maganarsa takatse bisa k'ok'arin bamu amsa dayakeyi. wani ni'imtaccen k'amshine ya iso hancinanmu tunkan mamallakin turarenma yakai ga isowa inda muke. d'auke kaina nayi na maida ga mai d'ibar jinin.
Likitan naga yafara gyara kujera yana fad'in â€Å“dama yalla6ai ya shigo gari yau? Ni nama manta yaune ranar dayake bada jiniâ€?.
Bai samu mai bashi amsaba a cikinmu har tawagar Wanda yakira yalla6ai suka iso wajen.
Munubiya da Ayusher suka matsa gefe saboda wata uwar tsawa da masu take masa baya suka daka mana, nikam koma motsawa banyiba bare nasan ALLAH yayi ruwansu awajen, saima baki dana ta6e na d'auke kaina daga saitin dasuke.
Bulala d'aya daga masu jajayen rigunan ya d'aga da nufin zubamun.
â€Å“Wanda suke kira Yalla6ai dake zaune a kujerar da doctor ya ajiye masa ya d'agamasa hannu da Sauri, alamar karya dakeniâ€?.
Cikeda girmamawa yace, â€Å“angama zaki s.........â€?.
Hannu Yakuma d'aga masa alamar baya buk'atar kirarin.
Baki nakuma ta6ewa sannan na ra6a ta gefensu nafice, banga fuskar Yalla6ai d'in nasuba, saboda ya juyamin bayane ni, sananan shima tunda yashigo bai kalli kowaba a lab d'in, yanata aikin danna wayarsa, kuma baiyi magana ba, ko doctor da Norse's d'in da suka gaidashi hannu kawai ya d'aga musu, kuma ko d'agowa baiyiba yanata aikin danna waya kai kace zai danno hanyar zuwa aljannane aciki.
Waje na dawo nayi zamana ina cigaba da game a waya, su Munubuya dai suna cikin, bansan uwarmi suka tsaya yiba awajen.
Kusan mintuna 40 saigasu sunfito, takun takalmansu kawai naji, amma ban d'agoba, sai k'amshin turarensa daya cika illahirin wajen, saikuma gaisuwar da mutane keta faman zubewa sunayi masa, ko sau d'aya banji ya amsaba.
Tsaki naja inamaijin haushin wannan mutumin, to wayema shine? dayakema mutane wannan jinkan., motsooww aikin banza kawai.
Tabbas yaji tsakin da akayi, hakanne yasakashi d'ago k'yawawan idanunsa yakai duba saitin Inda yajiyo tsakin, akan *munaya* dake zaune bisa kujerun dake Jere awajen ya sauke su, sai dai baya ganin fuskanta sosai, saboda ta duk'ar da kai tana danna waya, kuma gyalen jallabiyarta yarufe mata Rabin fuska, ita kad'aice zatayi wani motsi awajen suji, dan tafi kusanci da Inda suke tsaye.
Janye idanunsa yayi kawai daga gareta, yay saurin d'agama bayin dake k'ok'arin tafowa gareni hannu. Cikin Wata tattausar murya mai aji dake cike da k'asaitar masu isa najiyo yana fad'in â€Å“Bayta kawaiâ€?.
Cikeda girmamawa bawan yace, â€Å“ya shugaba tsaki tayi faâ€?.
Shiru yay kamar bazai tankaba, saikuma najiyo yace, â€Å“kasan dawa take?â€?.
Bawan girgiza kai yayi alamar a'a.
Bai sake cewa komaiba yay gaba suka bishi a baya.
'Dago ido nai nabi bayansu da kallo, sainaga sun nufi 6angaren mata masu haihuwa.
janye idona nayi ina fad'in â€Å“kadaiji dashi Malam, kana fama da Girman kai kamar wani Sarki? Abinma dariya ko (R) bai iyaba, wai baytaâ€?.
Dai dai nan su Ayusher suka iso cikeda farinci, hannunsu d'auke da ledar jinin
Cikeda jin haushi nace, â€Å“wai uwarmi kuka tsaya yi acikin lab d'inne?â€?.
â€Å“Uwarmu ta godeâ€?. â€? cewar Ayusherâ€?.
Munubiya kuma tace, â€Å“zaman namu aiko yayi amfani, tunda gashi mun samo sauran jinin koâ€?.
Na kallesu da mamaki, â€Å“ina kuka samo jinin kuma to?â€?.
â€Å“Galadima ya bayarâ€?.
Cikin ta6e baki nace, â€Å“miye kuma Galadima? A inama kukaga wani Galadima kome ma kukace?â€?.
â€Å“wanda yashigo muna cikifa, ai Galadima ne (Yareema Sameer d'an sarki)â€?.
Ido na waro waje, â€Å“wai kuna nufin wannan mai shegen girman kai d'in dama shine Galadiman? kenan munu.... shine yawucemu d'azu munfito makaranta?â€?.
â€Å“kwarai kuwa sweetheart shine, kuma wlhy bashida Girman kai kamar yanda kike zato ko Sis.. Ayusher? â€?.
â€Å“Wlhy kuwa hakane Munu..., ashe duk k'arshen ko wane wata saiyazo asibitinan yabada jininsa gamasu buk'ata, gashi jinin nasa mai irin wahalar samu d'inanne irinna feena, kai mutuminnan yayi wlhy, Sarauta ba karya baceba, danyau naga tsantsar sarauta da mulki da k'asaita ajikin Galadima, yanzu haka zai zagayane yaduba marasa lafiyaâ€?.
Harara na ballama Ayusher daketa zabga surutu uwa aku, na warce jinin daga hannun munubiya ina fad'in â€Å“idan kun gama shirmen kwa tahoâ€?.
Kallo suka bini dashi, Ayusher tace, â€Å“Anya yarinyarnan batada aljanu?, ke kowama bai mikiba?, yanzu nan duk had'uwar Galadima Munaya tana nufin bai burgeta ba kenan?â€?.
Dariya Munubiya tayi, sis... Ayusher har yanzu baki gama fahimtar Munaya ba na lura, kyagama abinda yafi haka indai daga wajentane. Yanzu hakama tunda kikaji tace haka ko sau d'aya bata kalleshiba wlhy bare tasanma kalarsa. kinga muje kinji.
â€Å“humm aiko wlhy inabata kalleshiba anyi babu ita kuwa, ruwa ta shata kuma, yo kobabu komai aina bada koda labarine nace nata6a ganinsa ido da ido koâ€?. ‘cewar Ayusherâ€?.
Dariya kawai Munubiya tayi, taja hannunta suka tafi.
Sanda suka iso harma an fara k'ok'arin sakama feena jinin, dama wancan yak'are.
Duk muna zaune a k'ofar d'akin bisa kujerun wajen, Aryaan da Aiyaan duk suna jikin mama Rabi'a barci ya d'aukesu, fadeel na kusada innarmu yanacin abincin dasu Munubiya suka kawo, zama nayi kusada fadeel d'in na saka hannu nad'au cokalin dayake cin abincin ina fad'in bro... nimafa yunwarnan nakeji, rabona da abinci tun kusan 1 danaci a kafteriya na makaranta�.
Kallona yayi yana cewa â€Å“sannu da k'ok'ari sis...., shiyyasa gakinan tsula guda bak'ya gaba bakya baya keda munu....â€?.
Cokalin nakai zan kwala masa a kai ya kauce yana dariya, nima dariyar nayi na d'auki kular abincin na k'ara mana.
Muna cikin ci Ayusher ma tamatso tace zataci, munci mun k'oshi sannan muka gyara wajen, mama da innarmu ma sukaci, dan zuwa yanzu duk mun sami 'Yar nutsuwa.
Kusan 10pm saiga Abbanmu shida baba k'arami, duk muka gaidasu suka tambayi mai jiki, innarmu da mama Rabi'a suka amasa musu da sauk'i.
Har d'akin suka shiga, suka duba feena daketa barcinta, sannan sukace muzo mu tafi gida, za'a bar innarmu da mama Rabi'a su kwana.
Saida safe mukai musu muka fito, Fadeel ya d'akko Aryaan, baba k'arami ya d'akko Aiyaan.
Saida muka fara sauke Ayusher da Fadeel gida sannan mukuma muka wuce.
Mun tarar gidan tsitt alamun duk anyi barci, saidai masu wayar dare da samari irinsu aunty Ramla, saikuma masu charts.
Abbanmu da baba k'arami suka d'auki su Aiyaan, har d'akinsu suka kaisu sannan suka fita.
Muma shirin barci mukayi muka kwanta cikeda kewar Innarmu, muna kwanciya muka kirasu da k'arajin mai jikin sannan muka tafi duniyar barci muma, dagani har Munubiya babu mai wani saurayin da zamu 6ata lokaci wajen yin hirar dare...............âœğŸ?
Kumuje zuwa my guys🤩ğŸ‘ğŸ»
Gobe idan ALLAH ya kaimu baza kujiniba, inada wani d'an uziri, sai Monday idan ALLAH ya kaimu kuma.
https://chat.whatsapp.com/K1qwmMusX7ILDLATGSvfHJ
*_RAINA KAMA........ FANS CLUB_*
_Duk Wanda yasan yana karanta wannan buk d'in ya garzaya yanemi link Na RAINA KAMA FANS CLUB, a wannan gidan kawai zan dinga posting a halin yanzun, awannan karon bazan turama kowa buk ta PC ba, narigada nayi rantsuwa. Amma annan zaka iya samu da faro, sannan inhar ba'a tattaunawa akan novel d'in zanyi waje da mutum babu ruwana, kuma kar a turomin kowanne novels acikinsa Dan ALLAH, inba hakaba zan fidda mutum ko Yaya nake dashi🙅ğŸ», nabud'e gidanne saboda anan kawai zan dinga posting yanzu, sai wasu groups dabasu wuce 3 ba._
Ina fata zaku bani had'in kai please, inba hakaba ALLAH zai koma Na kud'ine saboda tsaro ba tsorobağŸ˜ÄŸÅ¸¤£
One luv🥰🥰
*_ALLAH ka gafartama iyayenmuğŸ‘ğŸ»ÄŸÅ¸˜_*
[4/22, 2:14 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
_____________
*_ASSALAMU ALAIKUM_*
_Jiya da daddare akaita kirana mutane Na tanbayata Yaya jiki, tun ban fahimci maganarba hardai nafara tsarguwa nayi tambaya. Dan sai kira kan kira ake jeramin, wata take sanar dani taga wani posting ne yana yawo wai za'amin CS. babu shiri nabud'e data naga mike faruwa, group d'in farko dana bud'e sainaci karo da wannan posting d'in mutane nata comments, nabud'e nabiyu ma hakan dai._
*_Assalamualaikum Alaikum,Dan Allah kuyiwa billyn Abdul(ma rubuciyan RAINA KAMA. Adua'baby ya mutu a cikin ta zaa cire Mata Shi yanzu_*
_sai daga baya nakejin Bily galadanci ce batada lfyar, amma wata ta maida zancen haka saboda sunan namu yazo d'aya, to ALLAH yabata lfy itama._
_sannan ina shawartar jama'a Dan ALLAH kuringa nutsuwa wajen tantance Abu kafin Ku yad'ashi, domin wadda tayi wancan write up d'in ta zaunane ta tsara nata son zuciyar, wadda tayi posting d'in farko akan ciwon Bily galadanci sunan Bily tasaka ba nawaba, itakuma ta canja nata tsarin tashiga ya d'awa, ALLAH ya shiryar damu, yakuma bama marasa lfyarmu lafiya._
*banyi niyar posting ba yau, amma ganin wancan write up d'in yana cigaba da yad'uwa yasani dole yi Dan na warware muku zancen.*
______________________________
👉ğŸ»6âƒ?
.......Bamusan abinda yafaruba, mukaji 'yan gidanmu suna k'ananun magana da safe, wai girkin jiya na dare da mamansu yaa hameed tayi sai asararsa akayi, girkin yay d'anye yak'i dahuwa, kuma a gas tayi girkin bare ace iccen yabata matsala, gashi kuma normal gas d'in yake aiki.
Muna cikin yima su Aiyaan shirin school muka fara jiyo hayaniya, sai da muka gama musu shirin sannan muka fito, cirko-cirko muka iske 'yan gidanmu, yayinda mamansu yaa hameed keta zabga masifa. tana fad'ama abbanmu wai mune muka mata kwari shiyyasa jiya abinci yay mata d'anye danta hanamu abinci, kuma gashi yanzuma tasaka doya amai tak'i soyuwa.
Ni dariyama taso bani wlhy, wai mune muka mata kwari, to miye kwarinne ma datake magana a kai? danni bamma sanshiba.....
Maganar Abbanmu ta katsemin tunanina.
� 'Yan biyuna kuzo nan naji kunji�.
K'arasowa mukayi kusada abbanmu harsu Aiyaan, ya kallemu cikeda kulawa, â€Å“haba 'yan albarka mike faruwa haka?â€?.
Cikeda rashin fahimta nace, â€Å“Abba a ina?â€?.
â€Å“haba twins d'in Abba, bakuji mi mamanku take fad'aba? abinci yamata d'anye jiya da yauâ€?.
â€Å“amma Abba Dan abinci yayi d'anye kuma sai ace mune? Kagafa jiya munama asibiti bamuci abincin dareba agida, darana ma mama hanamu tayi tace innarmu tatafi da kasonmu asibiti, haka muka dawo muka iske su Aryaan sunajin yunwa, sai Munubiya Ce tamana girki, kuma tayi takai mana wani asibitin, ni wlhy Abba bammasan wani kwari dasuke maganaba akai, wannan ai canfine, tunkuma zamanin da aka barsaâ€?.
â€Å“canfin uwarki, kujimin munafukar yarinya, inbakune kukayi muguntarba uwarwaye yayi, to wlhy ahir d'inku, ba 'yan biyu ba ko 'yan gomane ni ubanku zanci a gidannan.......â€?
Afusace Abba yace, â€Å“to ai gani, saikizo kici ko, ai gaskiyama yarinyarnan tafad'a, wannan canfine kawai, dan abinci yayi d'anye saikuma a fassarashi dawani Abu daban, haba Dan ALLAH, saikace wata mara ilimin addini? Karna sake jin wannan maganar, inba hakaba rankowa zai 6acine a gidannanâ€?.
Yana gama fad'a yabar wajen. muma ganin haka muka tasa su Aiyaan gaba muka koma 6angarenmu. duk da nakasa fassara mi mama ke fad'i hakan yamun dad'i, koba komai dai ai ALLAH yamana sakayya da hanamu abinci datayi muda wad'anan k'ananun yaran da basu da alhakin kowa.
Yanzuma munubiya Ce ta dafo mana indomi mukaci, sanan ta zubama su Aiyaan a kulolinsu Na makaranta, suna tafiya muma mukayi shirin tafiya School.
Bamu tsaya jiran sauranba mukayi gaba saboda zamu biya ta asibiti, kuma munsan acikinsu babu mai binmu, harmun fita saiga Fauziyya tabiyomu, itama zataje taduba feena d'in.
Alhmdllh munma tarar an sallamesu sunata shirin tafiya gida, mukaima feena sannu, ta amsa tana fara'a da tambayarmu ya makaranta?. mukace gatanan zamu tafi.
Bamufi mintuna 30 ba muka fito, Fadeel ya d'aukesu, mukuma muka wuce school.
A mota Munubiya take bama Fauziyya labarin ganin Galadima damukayi jiya a asibiti, ko sau d'aya ban saka musu bakiba har muka sauka.
★★★★�
A wannan karon har mamansu yaa hameed tagama girkinta Na kwana biyu asarar abinci akaitayi, Dan kullum d'anye yake mata. hakan yasa taita sakin habaici agidan itada muk'arrabanta irinsu momy hadiza,.
Maman Fauziyya ta sanar ma innarmu komai tun randa taje duba feena agidan mama Rabi'a, Dan haka Innarmu tayi kunnen uwar shegu dasu, tamkarma batasan da ita sukeba balle ta nuna tama fahimci zancen nasu.
Innaro ma tazo tayi tata tsiyar San rai, tabi duk ta zagemu dacin mutuncin innarmu, koma fitowa innarmu hanamu yi tayi, har Innaro tagama tafice. Matan gida najin dad'i.
★★★★★★
Haka rayuwar tacigaba da tafiya, yau da gobe kayan ALLAH har gashi azumi ya rage saura kwanaki uku kacal a fara, Dan haka musulmai NATA shirin tarbar wannan wata mai tarin albarka da falala.
Kasuwanni sun cushe saboda yawan hada-hada, duk da 'yan kasuwa sunyi taiyar tasu ta k'arama abinci kud'i, maimakon su sassauto bayin ALLAH su sami sauk'i (ALLAH ka shirya 'yan kasuwarmu subar wannan hali dai).
A 6angaren gidanmu ma iyayenmu maza duk sunyi shirin, Dan dukkan wani abun buk'ata an tanadeshi, sai abinda ba'a rasaba dazai iya lalacewa idan an ajiye, wannan anbarsa yayunmu maza su ringayo cefanensa kullum kamar yanda aka saba.
Itama Innaro an ajiye mata dukkan abinda zata buk'ata, dukda kullum daga gidanmu ake kaimata abinci, safe yamma da dare, kuma dolene kowane 6angare sai sunkai nasu.
Muma a 6angarnmu munyi dukkan namu shirin, dukda abin zai had'e mana da zuwa makaranta, hakan yasa nake tausaya mana, gashi ana tsula rana mai zafi kuma.
Alhmdllh yau ta kasance Alhamis, kuma yaune ake saka ran ganin wata atashi da azumi washe garin juma'a.
Har zuwa 9pm kunnen kowa naga redio da talabijin, jira kawai Muke muji sanarwa daga sarkin musulmai. sai wajen 9:30pm sanan aka Sanar da ganin wata, duk wani Muslim yana cikeda d'okin fara azumin watan Ramadan da zamu Shiga goma ta marmari (inji hausawa😂).
Tun alokacin duk muka d'auki niyya, kasancewar girkin innarmu ne tayi shirin tafiya d'akin Abbanmu, muma tace mu kashe TV muje mu kwanta kar atadamu da asuba kuma muzo muna k'unk'uni.
Badan mun soba muka kashe mukaje mukai shirin barci muka kwanta da addu'ar abakunanmu.
Aiko da asuba dak'yar innarmu ta iya tashinmu mukai sahur, tea kawai muka shama, dama mu bama sahur da abinci nida munubiya, garama ita wani lokacin takan had'a da kunu ko fura.
Bamu kwantaba saida akayi sallar asubahi, still kwanciya muka kumayi, sai 8 innarmu ta tadamu, kasancewar yau saima 10 mukeda lecture, kuma zamu fito 12 ne.
Tunkan aje da nisa azumin yafara garani, dak'yar Na daure aka kammala lecture muka fito, amma badan Na fahimci komaiba nidai yau.
Su Munubiya sai dariya suke mini wai Raguwa, nidai ban kulasuba, Burina kawai naga mun Isa gida Na kwanta.
Tunda muka dawo school nazube a falo k'asan carpet, ban sake Sanin duniyar danake cikiba saida munubiya ta tadani nayi salla, Ashe harsu Aryaan sun sako masallacima inata barci, sallarma dak'yar nayita atsaye, INA kammalawa nakuma kwanciya.
â€Å“oh ni Aisha, wai Munaya mikikeson maida kankine? yanzu azumin kikema langa6e haka? saikace yau kika fara azumi a rayuwarki?â€?.
â€Å“ALLAH innarmu bazaki ganeba, nidai ALLAH yasa akira salla da wuriâ€?.
Munubiya dasu Aiyaan suka sakamin dariya. â€Å“Aunty yanzufa k'arfe 2 ma, sauran kusan awa 5 dawani Abu asha ruwaâ€?. ‘Aryaan yafad'a yana dariyaâ€?.
Harara Na Dalla masa INA fad'in â€Å“ALLAH inbaka rife wannan bakin naka mai gajerarrun hak'oraba zaka dakune, Dan k'aniyarka kaiba yanzu kagama lodama cikinka abinciba?â€?.
Aunty nimafa Dan innarmu bata tadamu baneba kawai, amma insha ALLAHU gobe zamuyi ko Aiyaan?�.
cikin zumud'i Aiyaan yace, â€Å“eh mana, muma zamuyi broâ€?.
â€Å“kuma wlhy yaro bai Isa karyashiba, garama karku d'aukaâ€?.
Munubiya tamik'e tana dariya, â€Å“imm innarmu bara kiga naje nafara rage aikin, miza'ayi?â€?.
â€Å“ki fere doya kafin Na fito, Munaya tashi maza kuje, kekuma ki gyara kayan miyaâ€?.
â€Å“wayyo innarmu ki tausaya min manaâ€?.
â€Å“mukuma mu kashe kanmu tunda bama azumin ko?â€?. ‘cikeda gatse tayi maganarâ€?.
â€Å“a'a innarmu, bara naje kodaga zaune sainayiâ€?.
â€Å“kimayi daga kwance, raguwar banza kawai, ai mijinki yashiga uku, wataran sai yadawo aiki baki gama abincibaâ€?.
Baki Na tura gaba sannan nafita.
Mun rage aiki sosai kafin la'asar, sai bayan sallar la'asar d'in 'yan Matan gidanmu suka shishshigo kitchen d'in kamar yanda aka saba, dama duk shekara gaba d'aya muke had'uwa a kitchen d'in 6angarenmu ayi abincin bud'a Baki, saidai saboda munada yawa akanyi time table saboda a rarrabu kowa da ranar da Zai taya mai aikin ranar.
Da yake aikin yawane dandanan muka kammala kafin 6, a can tsakar gida aka shinfid'a manyan tabarmi bayan an tsaftace wajen, duk azumi gaba d'aya muke had'uwa asha ruwa dama anan, kafin matar ya hameed ta rasu har itama anan suke zuwa suyi bud'a Baki.
Bayan mun had'u mun gama shirya komai kowa yanufi 6angarensu ya watsa ruwa kafin akira salla, dolene kaga jama'ar gidanmu aranar mu burgeka, babu fad'a babu hantarar juna, (yo kowa azumi yagama cin k'aniyarsa🤣ğŸ¤Âª).
Kasan cewar babu wuta ya kamal yazuba fetur a Gen... Ya tada, kowa yayi wanka saiyayi shirinsa da alwala yadawo tsakar gida ana jiran kiran salla, yara dabasuyi azumi baneba suketa shargallensu a tsakar gidan.
Yanda na zube a tabarman tamkar mara kashi yasaka yaa Shafi'u fad'in â€Å“kai kekam anyi raguwar yarinya wlhy, nasan dai Munaya Ce, Dan Munubiya tafiki jarumtaâ€?.
Dariya wad'anda ke wajen sukayi, yaa Naseer yace, â€Å“gaskiya mijinki yaga banu, yo idan yayi wasa dai bazai dinga cin abincin bud'a bakiba a gidansaâ€?.
Cikin dariya Aunty Hauwa'u ke fad'in â€Å“sai ya d'auka mata 'Yar aiki aiâ€?.
Caraf maman Safara'u ta amshe zance... â€Å“yo basai idan mai halin d'aukar 'Yar aikin bane, ana fama da masarar tuwo da shinkafa a jajibo mai aiki?â€?.
Gurin tsit yayi kamar ruwa ya cinyemu, da alama kowa baiji dad'in furucin Na maman safara'u ba, sai mamansu yaa hameed ce tayi dariya itada momy Hadiza.
Ganin abin zai koma cin zarafin juna sai maman fauziyya ta d'ako wani zance, daga nan aka koma hirar d'inkin salla. babu dad'ewa ma aka kira sallar magriba, cikeda d'oki kowa yafara k'ok'arin cin dabino. tab aini kam bandani, tuni Na d'ebi ruwa mai sanyi nafara sha, Dan shine babban burina. a gida mukayi jam'i, baba k'arami yajamana limanci. da ganan kuma kowa ya maida hankalinsa wajen bud'a baki, harda su hajiya innaro😕, tayi kane-kane ita masu gidan 'ya'yağŸ˜, koda wasa dagamu har innarmu babu Wanda yashiga sabgarta gudun gwalasa, har aka gama lafiya muka gabatar da sallar isha'i da asham. daga nan aka d'an ta6a hira kowa yahad'a kan 'ya'yansa zuwa 6angarensa.
haka muka cigaba da gudanar da ibadar azumin watan ramadan, tun ina ragwan taka harna fara daurewa, an gama goman farko aka shiga ta biyu (goma ta wuyağŸ™Å ).
Gaskiya nad'an wahaltu a tsakanin, ga makaranta ga aikin gidanmu dabaya k'arewa, ko wanke-wankema ya isheka, dukda had'uwa akeyi anayi kuwa.
Azumi yana 13 aka kawo kayan sallarmu, an bajesu tsakar gida kowa ya za6a, kala uku-uku ne dama duk shekara, atanfa, shadda, les, saikuma iyayenmu mata su k'ara mana gwargwadon abinda ALLAH ya hore musu.
Munada telolinnmu masu mana d'inki iya 'yan gidanmu kawai, shiyyasa bamuda matsala. Washe gari kuwa sukazo suka gwadamu, kowa aka saka sunansa ajikin kayansa da style d'in data za6a.
Innarmu ma sun saya mana itada mama Rabi'a, dan tunma kan azumi an kammala mana d'unkunanmu mudasu feena, (innarmu tana business itada mama Rabi'a) shiyyasa duk wani abun kwalliya Na 'yan mata bama rasashi, duk da dai 'yan gidanmu suna mana d'agawar sun fimu komai, saboda danginsu masu kud'ine, suna ganin kayansu sunfi namu tsada. hakan baita6a damunmu ba, dan aganina duk sutura sunanta sutura, yawan kud'in nawani bai d'ad'ani da k'asaba, to barema Munubiya da babu ruwanta.
Ana cikin haka muka shiga goman k'arshe Na azumi (goma ta d'okin sallahğŸ¤ÂªÄŸÅ¸˜‚).
Ranar wata weekend yayyanmu maza suka kwashemu domin za6o takalma da sauran tarkace Na kwalliya, dama duk ankai yaran suma kowa ya za6o, mu matasan 'yan matan muka rage dakuma yayyenmu su Aunty khaleesa.
Plaza ce babba mai k'yau da burgewa, kayansu Na manyane, amma yayyenmu dayake sunaso mufito suka kaimu can, sa6anin da da ake kaimu kasuwa kamar sauran yaran, su aunty khaleesa ne kawai ake kawowa nan saboda sune manyan 'yan mata, to yanzu muma mun shigo layi💃ğŸ».
Sosai muka rikice da tsarin wajen, takalmane 'yan waje wad'anda duk inda kayi taku sai an kalleka ansan kagama Isa. Harda bags, kayan makeup, turarurruka da dogayen ruguna irinsu Arabia's gowns, gyalilla da kayan 'yan kunne, kananun Maya Na garari Na mata da maza, kai inaga babu abinda zakazo Baja sameshi awannan PLAZA d'inba kam�.
Lallai an narka dukiya a wannan waje, ko plazan wanene? oho. munga dai sunan plaza d'in *BIRNIN GAYU!!*
â€Å“Lallai kuwa taci sunanta birnin gayuâ€?. â€? cewar Anty Ramlahâ€?.
Haleematu tace, â€Å“wlhy wannan ace plaza d'in mijinace to bazan maimaita kaya sau uku ba, hakama waya duk wata za a dinga canjaminâ€?.
Dariya tabamu, dan haka muka shiga darawa kuwa. kowa yad'auki abunda yakeso gwargwadon iko, yayyanmu suka biya da kud'in dasu Abba suka basu, sannan suka cika mana danasu kud'in, kowa yafito cikin farin ciki muna jera musu godiya, mun d'auki picture's sosai awajen kuwa. muna tafiya a mota nake cewa yaa Anas dan ALLAH wai Plaza d'in waye wannan?�.
â€Å“ai plaza d'in ta babban kwaroce k'anwata, plaza d'in *GALADIMA* ceâ€?.
shiru nai kamar banjishiba, danjin sunan wanda ya ambata, inada tabbacin kuma wannan mai girman kan tsiyar yake nufi kenan, yayinda 'yan uwana suka rud'e da firar galadiman.
d'an tsaki naja nace, â€Å“ashema Na mai shegen girman kai d'innan neâ€?.
Kusan atare sukace ke a ina kika sanshi? dahar kikasan yanada girman kai�.
Shiru namusu, sai Munubiya ce tashiga basu labarinsa da had'uwar damukayi a asibiti da shi, aikam duk sai sukabi suka rikice, harda masu fatan yazame musu mijin aure.
bansan miyasa duk hirar tasu ta k'untataniba, tabani haushi, saina maida hankalina ga kallace-kallacen jama'ar daketa kai kawo akan titi.
Har mukaje gida suna hirar Galadima sudasu yaa hameed dake basu labarin halayen kirki Na Galadima d'in, wai kuma bashida girman kai kamar yanda Na fad'a, kawai dai dan ban fahimcesa bane nima.
Nidai jinsu kawai nakeyi, amma badan Na yarda baida girman kai ba, tunda da idona Nagani ba labari aka baniba.ğŸ˜ehe
Innarmu tayi mamakin wad'annan kanya, dan haka takasa hak'uri, har 6angaren samarin gidanmu taje tamusu godiya da fad'an d'awainiyar tayi yawa ai, ga hidimar biki Na tunkarosu.
Sunji dad'i sosai akan hakan da innarmu tayi, koba dad'i kowa yayi aikairi yanaso anuna jindad'i kuma amasa godiya.
Sukace tayi hak'uri, ai k'annensu ne, idan basu mana ba wazai mana, da samari suzo suna mana hidima su lalata mana rayuwa ai garasu sumana su kare mutuncinmu.
Sosai innarmu ma taji dad'in furicinsu, dan hakan ya nuna cewa su basu d'auki halayen iyayensu mataba Na raba d'aya biyu.
Salla nata gabatomu, yayinda aka fara 'yan kimtse-kimtse Na shirin bikin sallar, masallatai nata rufe tafseer, hakama gidajen redio dana talabijin..............âœğŸ?
*Kusaka yayan mahaifiyata a addu'arku, ALLAH yamasa rasuwa ranar alhamisğŸ˜ÄŸÅ¸‘ğŸ», ALLAH ya gafarta masa, ya raya abinda yabari.*
_Bansan makaranta Raina kama.... kunada yawa hakaba wlhy, nazata ki rabin group bazaku kaiba🙆ğŸ», gashi yacika wasu basu sami wajeba kuma._
Na gaisheku k'yauta, ina fatan duk kuna cikin k'oshin lafiya kuda iyalankuğŸ¤ÄŸÅ¸»ÄŸÅ¸˜Å ?.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*.ğŸ‘ğŸ»ÄŸÅ¸˜
[4/22, 2:14 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
👉ğŸ»7âƒ?
.......Yau ake saka ran ganin wata, dan haka kowane gida zaka iya jiyo kamshin miya dana nama, harma da kayan snacks.
Muma agidanmu kusan hakanne ta kasance, dan kowanne 6angare sunata hidimarsu, yau ko bud'a baki bakowa yasamu zaman yinsa ba.
Muma muna namu 6angare muna taya innarmu ayyukanta, dayake kowa yana miyarsane, da safe ahad'u ayi tuwo da masa da shinkafa, haka muke had'a kalolin abinci iri-iri saboda yawan jama'a da gidanmu kan tara a ranar salla, abokan yayunmu maza, abokan su abbanmu dawasu dangin iyayenmu mata.
Har wajen 10 munata aiki, sai kuma a lokacinne mukaji ana sanar da ganin wata.
Nannafa yara suka shiga murna gobe salla, Muma kanmu manyan murnar mukeyi. badan mun kammala aikiba muka kwanta.
Washe gari tun kiran sallar farko aka tadamu muka fara aiki, sai wajen 7am muka samu kanmu, a gurguje muka fara wanka da shirin tafiya idi, duk shekara dama 'yan gidanmu a masallacin da sarki yake salla muma mukeyi.
A gurguje duk mukaita fitowa saboda horn da yayyenmu suketa mana, yara an d'urasu a school bos d'insu Na makaranta, yayinda mukuma muka rarrabu a motar yayinmu datasu Abba dasuka bayar, tunda bakowa keda motarna acikin yayyen namu.
Dagani har Munubiya cikin shigarmu muke iri d'aya tamkar yanda muka saba a koda yaushe, dai-dai da kwalliyama iri d'ayace a fuskarmu, komai namu mukayishi iri d'ayane, wannan yasaka ake gaza banbancemu akoda yaushe.
Mun Isa filin idi, inda muka taddashi dank'am da jama'a maza da mata, wasu harda iyalansu, kamar yanda muma muka taho baki d'aya harsu innarmu, mu mata muna 6angaren mata, yayinda mazan sukayi nasu 6angare.
Khud'ubar da aka gabatar tazamo mana mai ratsa jiki da 6argo, Malam yayita cikin tsantsar larabci, yayinda wani malamin ya fassara acikin harshen Hausa, saboda marasa jin larabcin irinsu o eğŸ™Å .
Daga nan aka gudanar da sallar idi kamar yanda addini ya koyar.
Had'a kan yaran muka shigayi gudin karsuyi wani waje, sai dai hakan bata samuba, dan annemi Kamal da Haneep an rasa, nannafa muka shiga bulayin nemansu, duk mun rikice, gashi baba k'arami da Abbah sai fad'a suke wai sakacinmu ne.
Tamkar zan kifa haka nake tafiya da sassarfa ina kalle-kalle. ban ankaraba naji naci karo da Abu, tunkan inkai idona kansa k'amshin turarensa yabigi hancina. da sauri na ware manyan idanuna bisa kamilalliyar fuskarsa dake d'aure babu alamar yasan miyema dariya, janye idona nayi cikin fargaba da fad'awa kogin tunani, inban mantaba irin wannan k'amshin naji a asibiti wajen Wanda aka kira galadima a wacan ranar da feena batada lafiya.
Cikin yanayin tantama Na maida idona nad'an saci kallonsa...
Tsaye yake kyam tamkar dutshin da aka dasa waje d'aya, idonsa akan wayarsa dake k'asa a tarwatse, Wanda inada tabbacin karon damukacine yasaka wayar fad'uwa.
A rikice nace â€Å“ya Salamâ€? tareda duk'usawa nafara harhad'a wayar.
A hankali ya durk'usa kamar yanda nima nayi, ya d'ora hannunsa akan wayar dana ke k'ok'arin sakama battery ya zareta daga cikin hannuna. bugun zuciyata yak'aru saboda tsoro gashi yak'i cewa uffan, nasan nice da laifi, kafin Na ankara ya sake d'oramin wayar bisa hannuna yamik'e yabar wajen.
Sororo nabisa da kallon mamaki da al'ajabi, sanye yake cikin farar shadda k'al, wando da riga harda malun-malun, ya murza hularnan da ake kira Minister bak'a a kansa, takalminsa da agogonsa duk bak'ak'e, duk da bawani k'are masa kallo nayiba fuska da fuska nasan tabbas yayi k'yau, kayan sun maidashi wani babban mutum. Ajiyar zuciya Na sauke saboda ya 6acema ganina, nabi wayar daya barni da ita a hannu da kallo, tomi yake nufi da hakan?.
Banida mai bani amsa, dan haka nacigaba da had'a wayar, sai alokacin Na lura da sim card d'insa dake kan wayar yacire d'azun lokacin daya kar6a kenan.
Jujjuya wayar nashigayi cikin tafin hannuna, wayace mai azabar k'yau ga k'amshin turarensa ya manne jikin wayar tamkar itama ana fesa matane. 'Yar tsagewane tayi kad'an daga gefe, amma daga hakan ni banga wata matsalaba, kenan yana nufin koyaya waya ta tsage a hannunsa tatashi aiki a garesa?. Nanma babu mai bani amsata. Cikin mak'oshi Na furta to wanene wannan d'in shikuma?�.
â€Å“Galadima!â€?. ‘naji wata murya tafad'a abayanaâ€?.
Cikin hanzari najuyon dan inga mai bani amsar tawa. wayam naga babu kowa, sai alamar gittawar mutum mai jajayen kaya.
Goshina Na dafe inamai runtse idanuna, cikeda mamaki nace, â€Å“kenan shine wanda yabama feena jini? Galadima!â€?.
Nafad'a cikin bud'e idanuna inabin inda yabi da kallo tamkar zan sake ganinsa, a hankali nakuma furta _â€Å“Galadima!â€_.
â€Å“galadima kuma?â€?.
Najiyo muryar Safara'u a bayana, da sauri a cusa wayar cikin hijjabina Na mik'e, kallonta nayi cikin basarwa nace, â€Å“ya angansu neâ€?.
Tace â€Å“eh mana an gansu tun d'azun, saikuma aka koma nemanki, miya faru naji kina kiran sunan galadima?â€?.
d'an guntun tsaki naja â€Å“naji wasu 'yan matane suna fad'in wai INA zasuga Galadima, tunda ance yazo sallar idi. shine nikuma nake maimaita sunan Galadiman saboda takaicinsuâ€?.
Dariya Safara'u tayi, ke 'Yar uwa karkiga laifinsu wlhy, koni zan sameshi saina bar Sadeeq wlhy, yanzu fa Nima ake nunaminshi, dama haka yahad'u? Wayyo ALLAH yau naga tsantsar gwanzartakar sarauta ajikin bawan ALLAH nan, tafiyarsama kawai abin kalloce, inaga kuma yayi magana?, kai ALLAH yakai damo ga harawa...... kedai kawai........
Baki kawai Na ta6e, batareda nagamajin k'arshen zancen nataba nayi gaba abuna da mamakinta a raina, wai zata iya Barin sadeeq?, saikace ba'akan sadeeq d'in bane akaso cin zarafina da innarmu, amma yanzu saboda taga Wanda ya fishi bakinta yake furta haka.
Da gudu Safara'u tabiyoni. Kusan a tare muka k'arasa Inda motarmu ta tsaya, yaa hameed yafara zagina akan INA kuma naje Na tsaya?, hak'uri nabashi muka Shiga mota kawai, dan nasan shima d'in masifafene kamar su abbanmu.
Amotar ana fira amma ni tunanina yanakan had'uwarmu da Galadima ta yau, ga mamakin wayarsa daya bari yatafi a hannuna batareda yace min uffanba, kai wannan Bawa yanaji da k'asaita da mulki.
Har muka Isa gida bakina bai iya furta komaiba acikin hirar tasu. Mun tatar su innarmu ma harsun huta su, yara kan summa fara cin abinci.
Ban zauna faloba kamar yanda munubiya tayi, saina zarce bedroom d'inmu Na 6oye wayar sannan nacire hijjab d'ina nashiga bathroom Na wanke hannuna gudun kar wani yaji k'amshin turaren saina dawo falon.
Tuni gidanmu ya kacame da hayaniya, munubiya tazubo mana masa da fankasu zamu faraci Ayusher da Feena suka shigo da gudu, juna muka rungume muna murnar ganinsu, Yaa Fadeel & yaa Marwan suma suka shigo, sai mama Rabi'a dake take musu baya tana rik'e da hannun Ahmad.
Nan muma muka kacame da farin cikin ganin 'yan uwanmu wad'anda bamuda kamarsu, innarmu ta baje mana abinci da kayayyaki da dama dansu duk ta tanadesu, sai makwafta dasuke gaisawar arzik'i suma duk tabada ankakkai musu.
Bamusan hidimar da kowa keyi anasa 6angarenba, mudai namu muka sani.
Ayusher takawo bakinta saitin kunnena, ahankali ta rad'amin sweet sis.... Wlhy k'amshin turaren Galadima kikeyi, kinsan har abada bazan mance k'amshi nan ba�.
Cikin dakiya Na d'ago kai Na kalleta tareda balla mata harara, â€Å“Ayusher wlhy ki kiyayeni, a'a k'amshin turaren sarki kikaji bana Galadima ba k'arewaâ€?.
dariya ta sanya harda rik'e ciki, nikuma Na tashi Na canja waje ina mamakin Ayusher mai gani har hanji, duk dawanke hannuna danayi sosai amma ace wai har yanzun anajin k'amshin turaren?, kai shikam wannan dawane mayen turare yake aiki haka?�.
Wajen 12 muka fito domin zuwa kallon sarki dazai wice yima governor barka da salla.
A wannan karan tafiyarmu daban data 'yan gidanmu, dan mafi yawancinsu duk sun fice gidajen kakanninsu, tacan masu ra'ayin zuwan suma zasuje.
Mukuwa mudasu yaa marwan muka tafi.
Acikin gari duk inda ka kalla jama'a ne keta kai kawo, musamman yara da 'yanmata da samari, kowa yaci kwalliya ta kece raini da garari (yo dama ai ance ba'a za6ar budurwa ran salla, saboda duk k'azantar mutum ranar saika sameshi cikin tsafta da gayu😂).
Dukda akwai rana hakan bai hanamu jeruwaba domin kallon wucewar mai martaba sarkinmu da jama'arsa.
Masu busa algaita da kid'an taushine suka fara wucewa, sai kuma ga tawagar sarki Na biye.
tawagar saiki Na wucewa sai ta Galadima, kamar yanda mukaji wasu gungun samari Na fad'ar cewa ga Galadima nan.
Kowa yasan dama tsarin haka yake, daga sarki sai shi.
'Daga idanuna nayin donson sake ganinsa a karo na biyu. yanzu kam ya canja shigarsa zuwa milk coulor d'in janfa da wando Na lallausan yadi, Wanda aka k'awatashi da d'inkin surfani Na ainahin gidan masu sarauta, ya d'ora Brown Na alk'yabba mai kwalliyar Milk Color, hakama rawaninsa daya zagaye fuskarsa ya kasance milk ne, takalmansa heir cover masu lankwasa daga gaba irinna sarauta, sukuma Brown. yanzun kam fuskarsa d'auke take da k'asaitaccen murmushi mai kama da anmasa dole, hannunsa d'aya dayake d'agama mutane yana d'aureda farin agogon azurfa, sai zabba biyu a yatsunsa Na tsakkiya Wanda nake k'yautata zaton azurfane suma.
Nanfa su Ayusher suka fara d'aukarsa hotonsa a wayoyinsu.
Tsaki naja ina hararsu, â€Å“mtsoww wahalallu kawai, dama kanku kuka d'auka yafi Ku k'are wajen d'ura hotunan Wanda baisanma da zamankuba a wayarkuâ€?.
Kafin cikin su Ayusher wata tabani amsa, wasu 'yan mata dake kusadamu d'aya ta kar6e da fad'in â€Å“k 'yan mata kama kanki, kodai kema son nasa ne yakaiki ga kishinsa?â€?.
Wata wawuyar harara Na buga mata, â€Å“kekuma shasha waya sako bakinki?, kajimin ballagaza kawai, uwarmiye abin so a jikinsa dahar ya isa ayi kishinsa? Ke dai dabakisan inda ke miki k'aik'ayiba ita dakon wahala, dan nakula ke amatanma suffar mata maza ALLAH yayiki....â€?
Gaba d'aya suka taso min da masifa tamkar zasu cinyeni d'anya itada k'awayenta..
Yaa marwan dake zaune saman mota a bayanmu duk yana saurarenmu yad'ago kai ya kalleni, yasan tabas Munaya ce, baya buk'atar k'arin bayani kuma ko tambayar wacece ita, tunda Na nuna halin nawa, yace, â€Å“K munaya zoki shige motaâ€?.
Nasan halinsa sarai baya wasa damu, cikin tunzura baki gaba nazo nashige motar Na zauna, amma saina bar k'ofar abud'e k'afafuna awaje, banida buk'atar cigaba da kallon kuma, dan haka nabud'e data nashiga chart kawai ina cika ina batsewa masifa nacin raina, gashi kuma an hanani amayar da'ita,. sai antayama yaa Marwan harara nakeyi ta gefen ido baima San inayiba, gaba d'ayama sainaji dama banzo kallon hawanba.
Koda muka bar nan ba gida muka komaba, yawo yaa Marwan yaytayi damu gidajen dangin babansu, bamune muka dawo gidaba sai magriba, kowa yayi ti6is da gajiya.
Mun tarar innarmu da mama Rabi'a sunata shan hirarsu ta zuminci.
Sai kusan 10 suka bar gidan.
★★★★
Washe gari muma agidansu mama Rabu'a muka yini har innarmu, koda yakema fitarmu mukayi nida Munubiya, Feena, Ayusher, mukabar su mama agida dasu Aryaan.
Yauma mun zaga gari sosai, dan Ayusher takira mana wani saurayinta yazo ya kwashemu, yauma munje munga hawan sarki da la'asar, saidai yau babu Galadima a tawagar, hakan bai dameniba, dan nama manta da lamarinsa ni.
Kwanaki kusan biyar zuwa 7 munashan shagalin salla, munsha yawo tamkar bamuda mafad'i mudasu Ayusher, sai Fauziyya dakan bimu wani lokacin idan basu fitaba da mamarsu suma.
'Yan matan gidanmu kowa sabgar gabansa yayi, rana d'ayane muka fita gaba d'aya domin gaida danginsu Abbanmu da Innaro takafa ta tsare akan sai munje wai su Anty Ramla sunyo musu sallamar aure.
Kwanaki 10 cif dagama bikin salla muka koma makaranta.
Haka rayuwa tacigaba da shud'ayawa, yayinda 'yan gidanmu keta shirin bikin 'ya'yansu, shiri akeyi babu kama hannun yaro, kowa burinsa ace 'ya'yan d'akinsa sune Star's, kuma sunfi kowa komai.
Sati uku kacal bikin yarage, an kawo lefe daga gidan senator halliru, akwatina 24, siyama 12 Zarah 12.
Humm ai ranar munsha kallo Na al'ajabi wajen mamansu yaa Hameed da momy Hadiza, habaici da gugar zana da burga, kowa yashashi, har dai abin yak'ure mamansu haleematu da maman Safara'u suka tanka musu, kafin kice mi gida yagama kacamewa da hayaniya, kowa yana ya6ama kowa magana, saida suka gama cin zarafin junansu sannan sukayi shiru bisa tsawatarwar baba k'arami, dayake yana gida a lokacin.
An bar maganarne kawai amma badan ta k'areba, mudai a 6angarenmu ma innarmu hana kowa fitowa tayi, dayake weekend ne.
Suma sauran duk an kawo nasu lefan, Aunty Rahaima, Ramlah, Hauwa'u sai aunty khaleesa, suma dai Alhmdllh, komai sai dai mak'iyi, duk da basukai nasu siyama ba gaskiya. a wannan karonma dai saida akayi 'yan gulmace-gulmace a gidanmu, amma basu bari tafito sarariba.
Suma su yaa Hameed aka kai nasu lefan gidajen matan dazasu aura shida Ya shafi'u da yaa Nasser. suma iyayenmu sunyi k'ok'ari wajen had'a musu lefen girma, ankai kuma kowa Na sambarka.
Tun bayan gama kai lefe gidanmu yakuma d'inkewa da k'us-k'us na gutsiri tsomar gidan yawa, kowa yana gulmar kowa akan aga wace rawa zaka taka, su 5 masu aurar da 'ya'yan.
Mamansu yaa hameed zata aurar da 3, yaa hameed, aunty khaleesa da Zarah.
Sai maman Haleematu zata aurar da aunty Hauwa'u.
Sai Momy Hadiza zata aurar da Siyama da aunty Raihan.
Mama Ruk'ayya kuma zata aurar da yaa Shafi'u da yaa Naseer.
Maman Safara'u kuma Aunty Ramlah.
Innarmu da maman Fauziyya ne kawai bazasu aurar da kowa ba, dan haka suka zama 'yan kallo, sai idan mazajensu sun saka su acikin shawarane.............âœğŸ?
*_Ya Rabbi ka gafarta iyayenmuğŸ˜ÄŸÅ¸‘ğŸ»_*
[4/22, 2:14 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
_________________________
_Happy marriage life *SANNA S MATAZU* ALLAH ya sanya alkairi da albarka a wannan aure, yabaku zaman lafiya na har Abadan da zuria d'ayyiba, bad'i muzo cin rangam💃ğŸ»ÄŸÅ¸’ƒğŸ»ÄŸÅ¸’ƒğŸ»ÄŸÅ¸’ƒğŸ»ÄŸÅ¸˜„👌ğŸ»._
__________________________
👉ğŸ»8âƒ?
.......Hidimar biki ta kankama gadan-gadan, dan har bak'in nesa sun fara isowa, a ranar alhamis aka gudanar da sister's and brother's day Wanda mune k'annensu muka shirya musu da yayinmu maza. da farko a tsakar gidan innaro aka shirya, saboda su Abba bazasu barmu mu saka kid'aba a gidanmu, gashi mun gayyato k'awayenmu ne, sai abokan su yaa Nasser danasu Anas. daga baya kuma sai muka canja shawara saboda samun wani fili damukayi can k'asan layinmu, filin a zagaye yake da katanga an saka gate. Tunda safe suka fara shirye-shiryen gyara wajen, kasancewar sai 4pm za'a fara, mudai makaranta muka tafi nida fauziyya da Munubiya, dan munada lectures, amma sauran duk k'in zuwa sukayi, barema su Siyama amare.
Around 3pm muka dawo gida, yauma kam da alama wasu bak'in sun iso, dan gidan Yakuma cika da yara da 'Yar hayaniya.
Mun tarrar innarmu tana d'akin abbanmu, dan haka mukayi wanka muka fara shirin tafiya wajen taron, ko abinci bamu nemaba, dagani har munubiya mun iya makeup, kasancewar mama Rabi'a tasakamu wajen koya muda Ayusher lokacin damuka gama secondary, a d'an tsakanin kafin fitowar results d'inmu, taga damuyi zaman banza gamma muje mukoya wata 'Yar sana'ar, tunda bamusan inda rayuwa zata kaimuba. Ko gama shiryawa bamuyiba Rahma tashigo kiranmu inji su Aunty Rahaima, dan mune zamu musu kwalliya.
Mun tarar dasu duk sunyi wanka dama mu suke jira, zaman musu kwalliyar mukayi, ni nafarama Aunty Hauwa'u, yayinda Munubiya takema aunty Ramlah.
Kiran Ayusher yashigo wayar munu...., ta d'aga tana fad'in â€Å“kin isone?â€?.
Bansan mitace mataba daga can, naji tace, â€Å“kizo muna 6angaren su Aunty Ramlahâ€?.
Babu dad'ewa saiga Ayusher itama, ta gaggada su Aunty's d'in, sannan muma tabamu hannu muka gaggaisa cikina musabaha.
â€Å“lah dear nifa harna fidda ran zakizo ALLAHâ€?.
Ayusher tace â€Å“kibari kawai, wancan jarabbaben ne yasakani aiki, tuwo mama tayi da rana, kinsan kuma bayaci shi, shinefa ya tsareni wai saina masa sakwara, harfa nayi shirin tahowaâ€?.
â€Å“uhm ai lamarin yaa marwan saishi, matarsa dai taga banu wlhy, shi anya ma yata6a budurwa kuwa?â€?.
Dariya duk muka sanya a d'akin, aunty Hauwa'u tace, â€Å“ai marwan akwai miskilanci wlhy shima, nifa zan iya cewa mun ta6a magana dashi kuwa?â€?.
Ayusher tace, â€Å“yo aunty ai wannan kowama haka yake masa, komu muka gaidashi sai yaso yake amsawa, kullum mama cikin masa fad'a take amma abanza wlhy?â€?.
Nann dai hira Yakoma kan yaa Marwan da mutane masu muskilanci irinsa, Munubiya ce mai kareshi, (dama ita suna d'an d'asawa, nice dai kamar muna ganin hanjin juna dashi danma ina tsoronsa ).
Kasan cewar mu uku ne sai kwalliyar tai sauri, dan danan muka kammala, nida munubiya mukayi tamu muma, simple makeup mukayi, amma komai iri d'aya, dama haka mukeyi, komai namu kullmun iri d'ayane.
Munyi k'yau, 6angarenmu muka koma mukayi shiri cikin blue d'in skirt da pink d'in Riga kamar yanda aka tsara sai veil shima blue.
Na jujjuya ina kallon kaina a mirror, â€Å“kai jama'a nikam bazan iya fita hakaba gaskiyaâ€?.
Ayusher dake kwance tana danna wata tad'ago ta kalleni, â€Å“kai amma kuma wlhy kayan sun miki k'yau, kinganki kuwa? dan ALLAH ki barsu, kiyi rolling veil naki kawaiâ€?.
â€Å“kai ba munaya kad'aibafa, nima bazan iyaba, after dress zan d'ora wlhyâ€?.
Dariya Ayusher tayi, ta tashi zaune tana ajiye wayar, â€Å“waiku miyasa k'auyawane sister's, naga a ke6antaccen waje za'ayi?â€?.
â€Å“amma kuma dai ai akwai maza kema kin saniâ€?.
â€Å“to alaranmiya, Ku saka, amma kafin Ku saka d'in nidai kuzo miyi hotunaâ€?.
Gaskiya koni nasan munyi k'yau, kasancewar mud'in fararene, kalolin duk sai suka kar6i jikinmu blue & pink. Wanda bai saniba saiya ce mu 'yan uku ne har Ayusher, dan muna matuk'ar kama da juna, sai dai Ayusher tafimu haske da d'an jiki.
Sai da mukad'anyi hotuna sannan muka fito. Innarmu tace kunyi k'yau, amma dan ALLAH kar inji wani yayi abinda za'ace gashi-gashi, Ku kama kanku da mutuncinku kunga dai acikin anguwane, idon kowa akanku yake�.
Mukace to innarmu insha ALLAH. mun fita tana binmu da addu'a.
A k'afa muka taka har wajen taron, tunkan mu k'arasa muke jiyo tashin kid'a. wajen dank'am yake da 'yanmata da samari, k'awayen amare da namu muma, sai 'yan uwa kuma da abokan su yaa Nasser, dama shi ya Hameed bai gayyaci kowaba, yace ya bar mana mu k'anne (shidama ba auren farko bane).
Tunda muka shigo akai mana caa da idanu, wasu tsantsar kamarmu ce tajawo hankalinsu kanmu, wasukuma burgesu mukayi, wasu kuma gulmarmu sukeyi da zaginmu, to dama shi taro ya gaji hakan, ballemu da ake ganinmu k'ask'antattu agidanmu, kamar kowama yafimu komai.
Amare suma duk sunyi k'yau cikin tasu shigar ta Riga da wando pink gaba d'aya, sai suka d'aure k'ugunsu da blue d'in belt, suka d'aura jacket blue.
Snacks ne kawai akad'anci a wajen da drinks, sai pictures da'aka d'auka da video, 'yan mata sunata casar rawarsu da samari, mudai muna daga gefe zaune muna shan kallo. mun rarraba gifts d'in damuka tanada, bawani Abu bane masu tsada. silifas d'in wankane sai brush, MacLean, soson wanka da sabulu d'ad'd'aya aciki, gifts d'in nan mun shiryashine kawai dan tsokana dama. gabda magriba taro yatashi lfy, kowa ya kama gabansa. muma gida muka koma.
★★★★�
Washe garima saida mukaje makaranta, sai dai 11:30 muka fito lecture, ALLAH ya taimakemu muka samu taxi da wuri.
Sanda muka dawo har 'yan jere sun dawo, kowa dangin mamarsa sukaje jerensa, shiyyasa mukaji tsitt babu gutsiri tsoma.
Muna dawowa ko wanka bamu tsaya yiba mukaci abinci muka tafi shagon auntynmu data koyar damu makeup domin yin k'unshi da saloons.
Cikin farin ciki ta tarbemu, dan mun rabu da ita cikin mutunci bayan mun iya aiki, Aunty salamah batada damuwa, inkaga tana maka fad'a to baka fahimtar abinda take koyar dakai ne, kwazon damuka nuna alokacin yasa takeji damu over. Tana kiranmu 'yan ukun ta.
K'unshi aka mana mai k'yau da gyaran kai, (dan d'aurema k'arya gindi irinnan aunty salamah harda mana gyaran jikiğŸ˜Å , wai tanaso muma musamo mazajen aureğŸ™Ë†).
Kowa ya gammu yasan munyi k'yau sosai.
Amakare mukaje gida, dan mun tarar amare nata jiranmu mu musu kwalliya, 'yan gidanmu harsun fara k'ananun magana, wai wulak'ancine yasa muka fita ai, kuma muna kallon lokaci yana k'urewa mukak'i dawowa. hakan da innarmu taji yasata kiranmu tana mana fad'a, hak'uri muka bata dacewa gamunan a hanya.
Masifa mukaitayi nida Ayusher, munubiya na bamu hak'uri, wlhy badan innarmu ba da bazanyi kwalliyar nanba yau.
Babu zancen mu huta muka hau musu kwalliyar. aikam ranar k'in fita wajen kamun nayi da akayi a tsakar gidanmu, kwanciyata nayi, innarmu taitamin fad'a kuwa.😕
Washe garin asabar d'aurin aure, dakam gidanmu yacika tab, 6angarenmu dai da sauk'in mutane, sai mama Rabi'a kawai da matan abokan Abbanmu.
K'arfe goma aka d'auro auren yaa Hameed da amaryarsa, sai yaa Nasser shima da yaa Shafi'u.
Na 'yan matan kuwa sai k'arfe 1:30pm. K'ofar gidanmu yacika dank'am da jama'a ta ko'ina, 'yan siyasa tawagar senator halliru da abokan su Sa'eed, hakama mijin aunty Rahaima d'an siyasane, dan haka harda governor a mahalarta taron d'aurin auren.
Har aka gama d'aura aurarrakin ina d'akinmu kwance, ko wanka banyiba, garama munubiya da Feena da Ayusher su duk sunyi, amma suna d'akin basu fitaba, sai balkisu k'awarmu da itama tazo mana.
Hira suketayi, nikam dai ina kwance kaina namin ciwo.
Gidanmu babu masaka tsinke, tako ina jama'ane, amare ansha k'yau, su siyama baki har k'anne an auri 'ya'yan sanata, hakama iyayensu sai burga sukeyi, ranar munga gasar dressing wajen iyayenmu mata kam, kowacce so take ace itace uwar amarya datafi kowa fita.
Innarmu kam babu ruwanta, shiga d'aya tayi ta atanfar da Abbanmu yamusu Na fitar biki, sai da yamma ta canja da less.
Aranar kowaccensu tayi yini. Baza'a kai amareba sai washe gari, saboda anason agudanar da dinner waje d'aya, amma an kawo nasu yaa Shafi'u sudai.
Yau d'inma dai mune muka musu kwalliyar su dukansu, kafin k'arfe 8pm afara kwasar mutane zuwa wajen daza'a gudanar da dinner d'in.
Gurin yayi k'yau sosai, yayinda aka shirya ma amare da anguna hi table.
Sai dai kuma wata sabuwa, ba duk angunan bane suka halarci wajen dinner d'in, nan fa aka fara 'yan gulmace-gulmace tsakanin dangin iyayenmu mata, tuni labari harya kai kunnuwan iyayenmu mata dasuke zaune a gida.
Amaren da babu angunansu sunsha kuka, wad'anda kuma dama sukasan angunan nasu ustazaine bazasu zoba basu damuba.
Haka dai aka gudanar da dinner d'in zukatan wasu babu dad'i, tunkan agama ma wasu sukaita tafiya gida abinsu. K'arfe 11 aka tashi.
A wajen dinner kam nayo saurayi mai suna Fu'aad, hakama munubiya da Ayusher dun sunyi, Fu'aad k'yak'yk'yawa dashi masha ALLAH, duk da dai bawani sake masa nayiba ya burgeni.
Su Ayusher sunata tsokanata, nidai ban kula suba.
Washe gari da safe kuwa saida abin yazama fad'a, wai ankama wasu suna gulma akan rashin zuwan sauran anguna, kuma dangin momy Hadiza ne, aikam sosai aka zuba rikici, har saida abbanmu ya tsawatar.
Aranar aka shirya kai amare, dole sai dai a rarrabu, tun la'asar aka fara kawo motoci, baba k'aramine yabada shawarar ahad'a tafiyar kawai gaba d'aya, su aunty Hauwa'u suma su siyama rakiya, sannan suma haka.
Haka kuwa yayima wasu iyayenmu mata dad'i, dan kobabu komai saji yanda gidan kowacce ya kasance.
mun fara kai su Siyama da Zarah, wad'anda babu alamun kuka a idanunsu, gidajensu jere da juna, sunyi k'yau masha ALLAH, kayan gado dai duksu Abba sukayi, kuma kud'insu d'aya, saidai kowa da za6insa, kayan kitchen ne kowa uwarsa tayi da sauran tarkace, ananne kowa ya ware ido dan aga kwazon uwar mutum, nidai agareni babu makusa, gidansu Zarah duk yayi.
Mun ajiyesu tareda k'awayensu, mukuma muka tafi kai sauran.
Daga Nan sai gidan aunty Rahaima, itama masha ALLAHU wlhy, saidai mak'iyi, gidanta yayi k'yau, sai dai tanada kishiya.
Saikuma gidan aunty khaleesa, itama dai d'in zamm zamm wlhy, daga nan sai aunty Ramlah, wlhy itama yayi d'as, itama tanada kishiya. Aunty Hauwa'u ce k'arshe dan itace babba, itama gidanta yayi k'yau sosai.
Nidai aganina babu wadda mahaifiyarta batayi k'ok'ari ba wlhy, amma hakan bai hana sauran gumtso gulmarmakiba aka taho da ita.
Kasancewar duk babu Inda muka zauna aka taho gida da wuri, harzamu wuce Fu'aad daya d'akkomu yace bari yashiga Birnin gayu plaza damu.
Nace a'a muwuce gida kawai, kar aga kowa yadawo mu bandamu, gashi lokacin har 8:30pm ya wuce.
Ayusher ce tace indai bazamu dad'eba ashiga, saimuce muna gidajen su siyama mu, mun zauna jiran anguna.
Kamar dai nace a'a amma nayi shiru, saboda naji munubiya da feena suma sun bada goyon bayan mu Shiga, sannan Fu'aad yace bazamu dad'eba.
Ya kalleni murya k'asa-k'asa yace, â€Å“ginbiya bakice komaiba?â€?.
Murya a sanyaye nace, â€Å“indai bazamu wuce 1hour ba mujeâ€?.
â€Å“insha ALLAHU my luv bazama mu kaibaâ€?.
A kasalance Na d'aga masa kai saboda agajiye make ti6is.
Haka yashiga wajen nidai zuciyata Na dukan uku-uku daban San Na miyeba.
Munshiga cikin plaza d'in, bansan takamaimai miyasa Fu'aad yace mushigo wajenba, tunda dai bawani abin ci ake saidawa a wajenba.
Mun shiga 6angaren kayan kwalliya, yace kowa yaza6i abinda yakeso.
Nidai nace masa a'a mun Gode.
6ata fuska yayi yana hararata, ya maida kallonsa gasu munubiya dake tsaye â€Å“please dan ALLAH karku biye mata, kuje Ku d'aukaâ€?.
Badan suma sunasoba suka amsa da to.
Ya kalleni yana fad'in â€Å“mujeto ni na d'ebar mikiâ€?. bance masa komaiba nabi bayansa ganin kamar yayi fushi, wayarsa aka kira, ya zaro daga aljihu, saida yad'an saci kallona yaga hankalina baya kansa sannan ya d'aga, murya k'asa-k'asa tamkar mai gulma yace, â€Å“nagama aikinaâ€?.
Dawowa yayi wajena bayan ya katse wayar, da kansa yake za6ar mini duk abinda yadace.
Su munubiya ma sunacan suna d'auka, kamar ance munubiya ta bar wajen saita zagaya tabaya, a dai-dai wannan lokacinne shikuma yake tunkarowa shida wasu matasan samari guda biyu, da alama yana zagayene kowani abun daban. tafiya yake cikeda nutsuwa da sarauta, sai sautin takunsa dakakeji, tunkan su iso gareta k'amshin turarensa ya iso.
Waige-waige munubiya tafara, tanason tuno mai wannan k'amshin. bata ankaraba saijinta tayi tatafi suuuu santsi ya kwasheta.
Shi mutumne mai yawan tausayi da taimako, da sauri yayo kanta kafin taje k'asan, Dan yasan fad'uwarta a wajen babban had'arine, yakai hannu zai rik'eta itakuma ALLAH yabata ikon dafe wasu tarin baskets dake wajen. Cikin runtse ido da sauke ajiyar zuciya ta furta â€Å“Alhmdllhâ€?.
Janyewa yayi daga rankwatowar dayay kanta tamkar zai rungumeta, batareda yace uffanba yafar wajen.
Muduka akan idonmu komai ya faru, wad'anda suke tare dashine sukaima munubiya sannu, mukuma muka k'araso da sauri gareta muna tanbayarta babudai wata damuwa ko?.
â€Å“babu komai Alhmdllhâ€?. ‘tafad'a tana gyara tsayuwartaâ€?.
Nace, â€Å“kunga kuzo mu tafi hakanan, wlhy inajin tsoron agane bama gidansu siyamaâ€?.
Duk suka amsa da gsky mu tafi, da k'yar muka yarda mukaje wajen biyan kud'in. yabiya sannan muka tafi.
ALLAH ya taimakemu ba'a mana fad'aba.
Duk cikinmu babu Wanda yakuma maida hankali akan abinda yafaru a birnin gayu plaza, saidai abin yakasa barin raina, kamar zuciyata tana cikin fargaba, amma bansan ta miyeba, ita kanta Munubiya wani sukuku nake ganinta, bandai tanbayeta ba Na share.
Washe gari Monday, muka tashi da shirin makaranta, saida muka gama gyara gidan tsaf sannan muka tafi harsu Ayusher, dayake lectures d'inmu Na yau sai 1:30pm ne. yauma sauran 'yan uwanmu bakowa yaje school d'inba ma har fauziyya.
Tun muna tsaye abakin titi muna jiran taxi naga wasu tsirarun mutane nabinmu da kallo. ban kawo komai arainaba muka samu taxi.
Driver ma yana tuk'i yana kallonmu ta madubi, sainaga kuma ya kalli takardar dake saman cinyarsa. d'an fara tsarguwa nayi, amma saina dake ina zaton irin dirobobin nanne masu shegen kallon tsiya.
Da muka sauka cikin makaranta ma bata sauya zaniba, kallonmu akeyi har ana nunamu, wasu da jaridu a hannu wasu kuma waya.
Munubiya tace, â€Å“Manaya bakiga abinda ke faruwaba tundaga fitowarmu gida zuwa nan ne?â€?.
â€Å“nagani wlhy Munubiya, bansan miyakawo wannan kallon k'urilla d'inba, dama bakiga kallon da direban can yake manaba ni da ke harya saukemu, ko sanda muke sallama dasu Ayusher idonsa Na kanmu kyam kuma yana kallon wata jarida dake cinyarsaâ€?.
Muduka kallon jikin junanmu mukeyi, babu wanda shigarsa tazama aibu acikinmu, sannan bama tareda wani abin kallo,
Hannun juna muka kama muka cigaba da tafiya cikin tsantseni da nazartar kallonda 'yan uwanmu d'alibai suke mana.
Tunda muka shigo cikin class sai duk aka zubo mana idanu, kuma anata k'us-k'us. yanzu kam hankalinmu yatashi sosai, wai mike faruwane? saikace yau mutane suka fara ganinmu? shin yaune muka fara shigowa makaranta?.
Bamu da mai bamu amsar tanbayarmu, muka nufi Bilkisu dake zaune itama tazubo mana idanu, ga jarida agabanta, kamar yanda muka gani wajen sauran 'yan department d'inmu, wasu narik'e da jaridu wasu wayoyi, sunyi group group kuma suna k'us-k'us.
Da sauri Na k'arasa zan d'auki jaridar gaban Bilkisu amma saitayi saurin d'aukewa............âœğŸ?
Babbar magana, shin mike faruwane? kallonmi jama'a kema su Munubiya? Sannan mi ake kallo a jikin jaridar da wayoyin kuma?🤦ğŸ»Ã¢€Ã¢™€.
Nasan masu karatu ma wannan amsar suke son sani🤔
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*ğŸ˜ÄŸÅ¸‘ğŸ»
[4/22, 2:14 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
👉ğŸ»9âƒ?
.......K'yaleta nayi najuya sit d'in bayanmu Na fusge ta hannun wani guy, rubutun farko dage jikin jaridar a shafin farko na tsirama idanu.
*_BABBAR MAGANA, GALADIMA SAMEER RUNGUME DA MATASHIYAR BUDURWA A PLAZA 'DINSA SUNA SUMBATAR JUNA!!_*
sai kuma hoton dake k'asan rubutun shima har kala biyu, Na farko abinda yafarune na fad'uwar Munubiya a birnin gayu plaza, har Galadima yay yink'urin taimakonta amma tadafe baskets ko ta6ata ma baikai gayiba, amma abin mamaki da al'ajabi a hoton galadima ya rungume munubiya ne bakinsa akan nata.
Hoto nabiyu kuma ni da shi ne afilin idi lokacin damukayi karo har wayarsa ta fad'i, ko kad'an bai ta6aniba, ko waya daya kar6a a hannuna hannuna danashi basu had'uba, amma anan an nuna hoton yana rik'e da hannuna duka biyu muna kallon juna.
â€Å“Innalillahiâ€? nafara maimaita jikina har yana rawa, gawata uwar jufa data fara jik'a sassan jikina, lallai dolene duk inda muka gitta abimu da kallo.
Ju yowa nayi na kallo munubiya dake tsaye a bayana, itakam hawayema takeyi.
Jikina a sanyaye nakama hannuta muka fita daga cikin hall d'in, kallon da ake Manama ayanzu yafi na d'azun, Dan labarin sai kuma yad'uwa yakeyi yanzun.
Muna fitowa muka samu taxi sai gida.
Tunda muka sauka naga wasu gungun samarin dake layinmu a majalissarsu sun zubo mana idanu gaba d'aya, tuni zuciyata tafara tsitstsinkewa, kenan labarin harya iso nan?. Dagani har Munubiya jamukai muka tsaya, saboda ganin dukkan ahalin gidanmu tsaye cirko-cirko a tsakar gida, hardasu yaa hameed anguna, ga bak'i dabasu gama tafiyaba, innarmu kwance akan tabarma maman fauziyya namata fifita, ga Abbanmu kusada ita tsugunne yana shafa mata ruwa.
Jaridar dake hannun baba k'arami mukabi da kallo, bansan sanda wani kuka yatahominba nima, sa6anin da munubiya kawai keyin kukan.
Da gudu mukayi kan innarmu, amma sai yaa hameed ya daka mana tsawa, â€Å“karku sake Ku ta6ata wlhy, idan bahakaba jikinku kuwa saiya fad'a mukuâ€?.
Babu shiri mukaja burki, amma sai muka durk'ushe ak'asa muka fashe da kuka.
Innro tace, â€Å“kwayi kuka kuwa munafukai, ahiyyasa ai ANNABI yace a auri mace tagari, Dan 'ya'ya susami uwa tagari, yo wannan aimu ba sabon abu baneba agaremu, tunda dama halin uwarku kenan, itama saida tagama tambad'arta a titi aka k'ak'abama d'anaâ€?.
Rintse idanu nayi saboda yanda maganganun innaro ke sukar zuciyata. Dady yakatseta da fad'in â€Å“dan ALLAH inna kiyi hak'uri kibar maganarnanâ€?.
â€Å“hameesu barni nafad'i gaskiya, wannan abin kunya har ina, wai jikokinane yau aka buga ajikin jarida namiji rungume da d'ayarsu a titiâ€? ta face hanci tana share hawaye da bakin zani, â€Å“ALLAH ya wadaran irin wannan rayuwa taku kuda uwarku, kun jawo mana abunkunya, yanzu dawane ido duniya zata cigaba da kallonmuâ€? feeet, takuma fyace majinaâ€?.
Mudai ni da munubiya muna durk'ushe rungume da juna Luna rairai kuka maiban tausayi dacin zuciya, yayinda 'yan gidanmu da sauran 'yan biki suketa k'us-k'us a tsakaninsu.
Isowar likita yasa aka kama innarmu aka maida falon Abba, a sank'ame take tamkar gawa....
�.�.�.�.�.�.�.�.�.�.�.�.�.�
*_GAGARA BADAU PLACE_*
Shirye-shiryen komawa India yakeyi hankalinsa kwance, Dan yau zai koma ga mahaifansa da 'yan uwansa dake can, jirgin k'arfe 8pm zaibi.
Yana gama had'a 'yan abubuwan dazai iya buk'ata yadawo falo ya zauna, sanye yake cikin farare k'al d'in kayan Adidas na training, dogon wando da Riga mai dogon hannu, yasaki hular abaya, kayan sun masa k'yau sosai.
Kallo d'aya yayma abincin dake kan center table d'in ya d'auke kansa, cikin k'asaitacciyar muryarsa mai cikeda isar masu mulki naji ya furta â€Å“Saykin k'ofaâ€?.
Kai kace anmasa dolene saiyayi maganar.
Da hanzari sarkin k'ofa yashigo falon, ya zube a k'asa â€Å“barka da hutawa ya shugabanaâ€?.
Kansa kawai ya jinjina, sannan yace, â€Å“waye yakawo abinci nan ne?â€?.
â€Å“ya shugabana bansan daga ainahin wane 6angare bane, amma bayin dasuka kawo daga 6angaren sarauniya Zulfah neâ€?.
Baice komaiba ya d'aga masa hannu alamun yatafi.
Sai da yad'an rissinar da kansa alamar girmamawa sannan yamik'e, dokace agareshi shi bayason kirarin da akema 'yan gidan sarautar. dan haka basa yimasa shi, Saboda gudun 6acin ransa.
zamewa yayi yay kwanciyarsa akan doguwar kujerar ya lumshe idanunsa batareda yabi takan abincinba.
Sallamar sarkin k'ofa tasakashi bud'e idanunsa akansa, ya amsa sallamar bisa la66ansa, sarkin k'ofa yazube agabansa, cikeda girmamawa yace, â€Å“ya shugabana yalla6ai Muftahu yace amasa iso garekaâ€?.
Alama yamasa akan yabada izinin ya shigo.
Fita sarkin k'ofa yayi. babu dad'ewa saiga Muftahu yashigo da sallama, Galadima yabud'e idonsa yana kallonsa tareda amsawa.
Zama yayi kujerar dake kallon Galadima, yace, â€Å“yalla6ai barka da hantsiâ€?.
Murmushi Galadima yayi, ya tashi zaune sosai yana fad'in â€Å“my man daga ina haka naganka ayikice? bakaje aikibane?â€?.
Ajiyar zuciya Muftahu ya sauke, yacije le6ensa na k'asa yana mik'ama Galadima jaridar dake hannunasa, â€Å“nafita wlhy sainaci karo da wannan jaridar data fito a safiyar yauâ€?.
Cikin halin ko inkula Galadima yace, â€Å“Miye had'ina da jayidan to?â€?.
â€Å“Kayi hak'uri ka kar6a ka dubaâ€?.
A shafin farko yay karo da abinda yasakashi sake kallon Muftahu, kai Muftahu ya d'aga masa alamar yacigaba.
*_ANYI WALK'IYA...., GALADIMA DA AIKA-AIKA A FILIN IDI_*
cikin hanzari yabud'e shafin farko, nankuma an saka.
*_BABBAR MAGANA, GALADIMA SAMEER RUNGUME DA MATASHIYAR BUDURWA A PLAZA 'DINSA SUNA SUMBATAR JUNA!!_*
sai hoton farko dana biyu, wad'anda suka d'aure kansa, danshi gaba d'ayama ya manta daduk abinda yafaru, tundaga na birnin gayu plaza harna filin idi d'in. d'agowa yay yakalli Muftahu sannan ya maida kallonsa ga dogon rubutun da akai akan sharhin hotunan. bazai iya karanta rubutun ahakaba, saiya fara waige-waigen neman medical glasses d'insa.
Fahimtar haka da Muftahu yayi yace, â€Å“ina yake in d'auka maka?â€?.
Da hannu ya nuna bedroom d'insa ba tare da yace komai ba.
Mik'ewa Muftahu yayi yanufi bedroom d'in, babu dad'ewa saigashi yadawo, ya mik'a masa sannan yakoma inda yake da ya zauna yana fad'in â€Å“ko ka kawo na karanta makaâ€?.
Nanma baice uffanba yamik'a masa jaridar, kansa ya maida jikin kujerar ya jingina ya lumshe idanunsa.
Tiryan-tiryan Muftahu yafara karanto k'aryar da aka jera jikin jaridar, ko sau d'aya bai motsaba, amma yana saurarensa.
Muftahu yagama cikin sauke ajiyar zuciya, Amma tabbas wannan wata k'ullaliyace, ai ba abinda yafaru kenanba jiya a birnin gayu, ni nama rasa mizan cema wannan gidan jaridar wlhy�.
Galadima ya bud'e idonsa dake a lumshe, ya kad'a yay jajur saboda 6acin rai, akan Muftahu ya saukesu batareda yace komaiba, tuno abinda yafaru a filin idi yayi kusan sati 4 kenan, tabbas sunyi karo da yarinya, wadda ayanzu haka ko fuskarta bazai iya tunawaba, dan ko'a waccan ranar kallo d'aya yamata, a jiya kuma ko ta6a yarinyar baiyiba ALLAH ya kareta daga fad'uwar dazatayi. jinjina kansa yayi cikeda 6acin rai da mamaki.
Muryarsa a sark'e yace, â€Å“Muftahu imason bayanai akan yayannan najikin jayiday su dukaâ€?.
â€Å“ok yalla6ai, amma ai yarinya d'ayace duba kaganiâ€?.
Kar6ar jaridar yayi yakuma kallon hotunan, tabbas duk yarinya d'ayace, wannan ya sake tabbatar masa da an shirya masa hakanne.
Mik'ewa yayi yazari mukullin mota batareda yace ma Muftahu komaiba, ganin haka shima Muftahu saiya mik'e yabi bayansa.
Cikin sauri dogaren dake binsa inhar zai fita suka taso gareshi, amma saiya d'aga musu hannu.
yana k'ok'arin bud'e motarne Jakadiyya ta iso inda yake...
Cikin rissinawa tace, â€Å“barka da hantsi galadimaâ€?.
Bai iya amsa mataba, sai hannu daya d'aga mata kawai.
Kuma rissinawa tayi tace, â€Å“Galadima takawane yabani izinin in kirayekaâ€?.
Kallonta yayi zaiyi magana saikuma yay shiru ya maida motar yarufe tareda cillama Muftahu dake bayansa kyes d'in.
Muftahu ya cafe.
Komawa yayi 6angarensa yashiga wanka, kusan mintina 40 sannan yafito sanye da bathrobe fara k'al, bai wani d'au dogon lokaciba yay shiri cikin k'ananun kaya, yayi k'yau sosai, ya feshe jikinsa da turarensa masu matuk'ar k'amshi.
Wayarsa ce tashiga ringing, baibi takantaba yacigaba da hidimarsa, dama tun yana bathroom yakejin ana kiransa.
ta baya yabi inda bayi bazasu isheshi da gaisuwa gaisuwa d'innanba, dayake sarki yana gida, yau ana hutun zaman fada saboda tunawa da abinda yafaru da tsohon sarki (mahaifin Galadima Sameer) duk ranar litinin tana zama ranar daba'a zaman fadane...
�.�.�.�.�.�.�.�.�.�
Kowa ya ganmu yasan muna cikin rud'ani, da k'yar aka samu innarmu ta farfad'o, sai dai an hanamu mushiga mu ganta.
Gidanmu kam abin nema yasamu, hakama cikin anguwa, saboda yad'uwar labarin a social Media.
Muna zaune a falo duk mun zabga uban tagumi dagani har munubiya, idanunmu duksun kunbura saboda kuka, Ni ba abinda yafaru a jaridar ne yafi damunaba, halin da mahaifiyarmu ke ciki shine babbar matsalata, bamuda kamarta duk duniya, bazanso wani Abu ya sameta asanadinmu ba, bayan bak'incikin datake k'unsa agidanmu kuma.
Kamar anjeho mama Rabi'a itada ya Marwan suka shigo falon. mun tsorata kwarai da gaske, cikin daka tsawa mama Rabi'a take tambayarmu innarmu.
Hakanne ya tabbatar mana da suma labarin yaje musu. munubiya ce tabata amsa cikin kuka, sannan tace â€Å“wlhy mama sharrine, ba abinda yafaruba kenan n......â€?.
Saukar marin datajine yasakata rufe bakinta 6am, kafin na tantance mai Marin nima naji saukar nawa.
Ko kad'an yaa Marwan baiji tausayinmu ba, saida yamana lik'is da duka, dak'yar Dady ya kar6emu a hannunsa, amma baba k'arami da Abbanmu casukai yama k'ara mana.
'Yan gidanmu duk sunfito cirko-cirko a tsakar gida, kowa na tofa albarkacin bakinsa, gashi akwai sauran 'yan biki dabasu gama tafiyaba.
Iyayenmu da yayinmu duksun taru akanmu, ana tambayarmu wacece daga cikinmu.
Kafin Munubiya tayi magana nayi saurin cewa â€Å“kuyi hak'uri iyayena, nice munaya a gaba d'aya hotunan, wlhy kuma tsautsayine, amma ba ainahin abinda yafaruba kenanâ€?.
Munubiya zatayi magana nayi sarin rik'e hannunta alamar kartace komai, â€Å“karki d'aurama kanki abinda ba laifinkiba Munubiya, nice Munaya na aikata....â€?
Itama cikin kuka tace â€Å“wlhy bake baceba, nice, wlhy niceâ€?.
Nima nace â€Å“wlhy niceâ€?.. ....
Tsawa Abbanmu yadaka mana, atare mukayi shiru yace â€Å“nasan dama Munaya kece, Munubiya bazata aikata wad'annan abubuwan ba, dukda kema d'in nayarda da tarbiyyar dana baki, amma bansan miya kaiki ga aikata hakanba, shiyyasa ranar idi mukaita nemanki, Ashe kinacan kina d'akko mana magana, tunda aure kikeso zan miki, nabaki nanda sati 2 kacal, inbaki kawomin mijiba zan had'aki dadu Wanda nayi niyaâ€?.
Yana gama fad'ar haka yatashi ya fice, baba k'arami ma ficewarsa yayi.
Wani kuka mai tsuma rai muka kuma fashewa da shi, musamman ma ni danasan nasaka kaina a tarko, amma hakan shine dai-dai, bazan amince naga 'Yar uwata cikin bak'in cikiba, insha ALLAH koma minene zan jureshi, muniya tanada hak'urin dazai iya cutar da ita akan wannan lamarin, gashi baba yafurta in ban fiddo da mijiba zai auramin Wanda yaso, to idan hakan ta kasance kan Munubiya wane hali kuke tunanin zata shiga? Musamna dabamusan gidan dazamu iya fad'awaba tunda nasan abinda Abba yafad'a tabbataccene, dan shi baya magana biyu.
Dady ne yashiga lallashinmu, tareda mana nasiha da nuna mana illar abinda muka aikata, musaman ma ni. ya Marwan kam sai antayamin harara yakeyi shida yaa hameed.
Yinin yau kam kuka muncishi harmun godema ALLAH, mu duka kwance muke rijif da zazza6i, har akayi isha'i bamu kumajin motsin kowaba, mukuma muna d'aki kwance mu duka k'udundune a bargo.
Su Aryaan sunacan nanuk'e da innarmu dake 6angaren Abbanmu har yanzun, dan haka 6angarenmu saiya kasance tsitt. a ranar dai haka muka kwana babu lafiya nida Munubiya, babu mai iya taimakon wani acikinmu, ga yunwa ga damuwa ga ciwo.
Zuwa asubahi ko salla kasa gashi muyita mukayi, dan k'arfinmu yagama k'arewa...ğŸ˜
�.�.�.�.�.�.�.�.�.�.�
Ya isa sassan mai martaba, bayan masu tsaron k'ofa sun gama kwasar gaisuwa suka masa iso.
Izinin shiga mai martaba yabashi.
Falone k'aton gaske, Wanda nikaina banmasan yanda zan musalta k'yansa da girmansaba, ga kujeru rukuni-rukuni, ko ina yagama d'umamewa da sanyin AC, gawani k'amshi na musamman.
daga can gefe na hango mai martaba kishingid'e bisa wani lallausan carpet da aka k'awata da tarin tum-tum, gabansa tirene dake d'auke da jug na glass cikeda zo6o, sai wani k'aramin kwano na tangaram Wanda bansan miye acikiba, saikuma k'aramar butar shayi awani tiren daban, da mug guda d'aya.
Fuskarsa d'aure take tamau alamar yana cikin 6acin rai, ga jarida a hannunsa.
Cikeda girmamawa Galadima ya zauna a gefen dardumar, ya tankwashe k'afafunsa sannan ya risina yana fad'in â€Å“barka da rana ranka ya dad'eâ€?.
Mai martaba bai amsaba, sai ma cilla masa jaridar hannunsa dayayi.
Galadima yabi jaridar da kallo batareda ya d'aukaba.
â€Å“ka d'auka ka duba mana, dan inason sanin gaskiyar zancenâ€?.
Kan galadima a k'asa yace, â€Å“takawa nima yanzu Muftahu yakawo min nagani, nama fito zanje ga gidan jayidayne kiyanka ya isomin, amma wlhy Abba ba gaskiya baneba, ka.......â€?
Da sauri mai martaba ya d'aga masa hannu cikin 6acin rai â€Å“mi kakeson fad'amin? kana nufin zasu buga abinda baka aikata bane? ai sunsan gidan daka fito, haka kawai bazasu maka sharri ba kodan gudun abinda zaije ya dawo. Sameer yanzun nan da mutuncinmu kaje ka aikata wannan son zuciyar domin ka 6atama wannan masarautar suna? Lallai kacika d'an halak, kuma kayi dai-dai, tabbas ka kafa tarihin dawani bai ta6a yin irinsaba a wannan masarautar, Dama Ashe kabud'e waccan plaza d'inne domin son zuciyarka? Yanzu da ace lafiyar Yaya k'alau wane irin hali kake tunanin zai tsinci kansa? Ina ganinka shiru-shiru Ashe kaid'in shaid'anineâ€?.
Runtse idanu Galadima yayi zuciyarsa na k'una da kalaman mai martaba k'anin mahaifin nasa, amma yagaza furta komai, sai idanunsa daketa k'are rinewa zuwa jajazur.
Har mai martaba yak'araci fad'ansa yagama Galadima bai iya furta komaiba, kansa ak'asa ko motsi baiyiba.
â€Å“katashi kabani waje, k'arfe 8:30pm akwai meeting, saika jira hukunci daga mama Fulani â€?.
Rissinar da kai Galadima yayi yace, â€Å“ALLAH ya huci zuciyayka, na bayka lafiyaâ€?.
Banza mai martaba yay masa, yatashi yafice shikuma cikin k'unar zuciya.
Yana fita wayarsa ta fara ringing, ransa adagule yacirota da nufin kashewa gaba d'aya, saiyaga *_My dear Momma_* rintse idanunsa yayi ransa nakuma suya, yasan tabbas labari ya Isa gareta kenan, wannan wace irin masiface, mahaifiyarsa dake wata k'asa har ankirata an Sanar mata, ko halin datake ciki baza'a kallaba?. Kasa d'aga wayar yayi harta tsinke.
Tabbas duk Wanda yake gidan jaridarnan saiyayi Dana sanin saninsa arayuwa.
Kiran Momma ne yakuma shigowa, yanzuma bai d'agaba harya k'arasa sashinsa.
Sai da ya zauna sannan yafara k'ok'arin nemanta cikin suyar zuciya data ruhi...............âœğŸ?
To masu karatu, ko wanene da wannan aika-aikar? tabbas yau Munaya tabani matuk'ar tausayi daga ita har munubiya, kai harma Galadima.🤦ğŸ»Ã¢€Ã¢™€
Kumuje zuwa danjin Yaya kuma zata kasance🙆ğŸ»?.
Yanzufa aka fara wasan👌ğŸ»Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€ÄŸÅ¸¤¾ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€
*_YA ALLAH ka gafartama iyayenmuğŸ˜ÄŸÅ¸‘ğŸ»_*
[4/22, 2:14 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
👉ğŸ»ÄŸÅ¸”Ÿ
.......Maman Fauziyya ce taga shirun yayi yawa narashin gittawarmu ta aiko Kamal yagani muna nan, dan ita azatonta ko mama Rabi'a tawuce damu gidanta ne.
Da gudu yakoma ya sanar mata gamucan babu lafiya a d'akinmu.
ai bata tsaya jin k'arshen zancenba ta garzayo, halin data iskemu aciki itama hankalinta yakai k'ololuwar tashi, takira baba k'arami a waya tana Sanar masa, duk da haushinmu dayakeji hakan bai hanashi shiga tashin hankaliba shima. atare suka shigo da dady, shima abbanmu sai gashi yashigo.
Duk kuma jikinsu sai yayi sanyi, aganinsu yakamata su sauraremu ajiyan, amma duk da haka babu iyayen dazasuga wannan abun hankalinsu bai tsashiba, garashi d'an manyan mutanene, nashi mai sauk'ine, amma mune awahale.
Haka aka kira doctor yaduba mu, yace damuwace ta haddasa mana zazza6in, sai kuma yunwa.
Da k'yar maman fauziyya ta taimaka mana mukayi wanka da ruwa mai d'umi, sannan mukayi sallar asubahi. tea ma dak'yar muka shashi sannan mukasha magani, still kwanciya muka k'arayi, nan barci ya kwashemu.
Dadyne ya kalli 'yan uwansa, cikin damuwa yace, â€Å“yaya Auwal yanzu bazamuyi wani yunk'urin bincike akan lamarinnan ba? ni dai sainake ganin kamar yarannan bazasu aikata hakaba, tsawon shekaru muna tare dasu, bamu ta6a jin makamancin abinan ba daga garesu, sainake ganin bai kamata mu yanke hunci ba akan abinda bamuda tabbas kuma cikin fushiâ€?.
â€Å“Hameesu karka goyi bayansu akan wannan lamarin, babu yanda za'ayi abuga labarinan alhalin bai faruba, kaduba fa shi yaron d'ane ga Sarki, shinema Galadima, kodan tsoron abinda zaije yadawo ai nasan gidan jaridarnan saji tsoron buga labarinâ€?.
â€Å“hakane yaya, amma baka ganin mak'iyanshi zasu iya amfani da wannan damar domin 6ata sunansa? maybe kuma su yaranmu tsautsayine ya gitta akansuâ€?.
â€Å“maganarka gaskiyane Jafaru, nima wlhy hakan nake tunani, amma yakamata mujira muji daga gidan Sarki, Dan inhar Dan 6ata sunan yaron akayi nasan bazasu k'yaleba, kuma zasu nememuâ€?.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke yace, â€Å“nidai koma minene gsky aure yakamata ayima Munaya, Dan nikam banta6a cin karo da abinda ya rud'ar daniba irin wannan, mahaifiyar yarannan wlhy batayi barciba jiya, kwana tayi kuka, kuna ganin dai irin cin zarafin da inna tadinga mata jiya a tsakar gida gaban kowa, shin minene laifin A'isha akan wannan lamarin? zata aiki su Munubiya ne akan suje su aikata hakan?â€?.
â€Å“kayi hak'uri yaya, lamarin inna sai hak'uri, kasan dai halinta aiâ€?.
Haka sukaita tattauna yanda zasu 6ulloma lamarin.
�.�.�.�.�.�.�.�.�.�.�.�
Jiki a sanyaye ya danna kiran Momma, bugu biyu ta d'aga, cikin girmamawa ya gaidata, ta amsa itama cikeda kulawa kamar yanda ta saba. hakanne yad'an sakashi jin sanyi a zuciya, ya sauke ajiyar zuciya yana fad'in â€Å“Momma ya jikin Abie?â€?.
â€Å“Alhmdllh Moh'd. wani mummunan labari yanzu Ummu Erfaan takirani take sanarmin?, sai kuma ga mama Fulani ma takira tanata fad'a. yanzu kuma Sauban ya nunamin wasu pictures wai an turo masaneâ€?.
Rintse idanunsa yayi cikin k'unar zuciya, murya a sark'e yace, â€Å“Momma nima haka kawai naganiâ€?.
â€Å“ban gane kaima haka kaganiba Moh'd, kagayamin gaskiya please, wannan ba k'aramin Abu bane bafaâ€?.
Da k'arfi ya cije lips d'insa tamkar zai hudashi da hak'ori, cikin wata murya dake nuna k'ololuwar 6acin ransa yace, â€Å“Momma wlhy bansan komaiba, yanay idi tabbas munyi kayo da wata yayinya hay wayata tafad'i ta fashe, jiya kuma yayinya takusan fad'uwa a plaza nayi yink'uyin taimakon ta saima ALLAH yasa bata fad'iba, kuma ko ta6a banyiba, shine kawai yau gidan jayiday nan suka maida pictures d'in haka faâ€?.
Ajiyar zuciya Momma ta sauke, (dan tarigada tasan halin d'an NATA, duk da ba'a shaidar d'an yau musamman idan yabar gaban idonka) â€Å“Muh'd tabbas wannan k'ulline, amma kuma yarinya d'ayace aiâ€?.
â€Å“haka nagani nima Mommaâ€?.
â€Å“yanzu mi sarki yace?â€?.
â€Å“Momma wlhy maganay babu dad'inji, hayma sun shiyya meeting a kainaâ€?.
â€Å“Humm Muh'd wannan maganace mai girma, kuma tabbas domin 6ata sunanka ne da namu akayi, akwai kuma dalilinsu nayin hakan, ita wannan yarinyar kodai da saninta kokuma an shigo da itane saboda cikar manufarsuâ€?.
â€Å“Momma su waye to?â€?.
â€Å“Masusan ganin bayanmu mana, sun biyo wannan hanyarne domin dak'ileka da ragema kaifiâ€?.
Wani naushi ya kaima k'aramin teble d'in gabansa na glass, nan take ya tarwatse. bai damu da ciwon dayajiba, cikin k'araji yace, â€Å“tabbas kafin suga bayana nizanga nasu!!! rayuwar mahaifina bazata salwanta abanzaba!! Saina wulak'anta dukkan masu hannu aciki kosu waye su wlhy billahi Momma! numfashina fansa akan mahaifina!!â€?.
Dole Momma tacire wayar daga kunnenta saboda yanda Galadima ke magana cikin matsananciyar tsawa.
Saman kujera ya wurga wayar, batareda ya katse kiranba, afusace yafito daga 6angaren nasa, tsawa ya dakama dogaransa.
Gaba d'ayansu cikin rawar jiki suka nufi motocin da ke fake a wajen, ko jira abud'e masa baiyiba yabud'e yashiga.
Hankalinsu a tashe yake daganin yanayin shugaban nasu, sunsan tabbas ran 'yan maza ya 6aci yau, Dan kowa yasan rashin son hayaniya irinta Galadima a masarautar nan.
Saida suka fito daga masarautar a d'arare sarkin mota yace, â€Å“ranka ya dad'e ina muka dosa?â€?.
Tamkar bazai tankaba, sai kuma can afusace yace, â€Å“plaza!â€?.
â€Å“angama Ranka ya dad'e, ALLAH ya huci zuciyarka ya shugabanaâ€?.
Banza yamasa bai tanka masaba, sai huci yakeyi yanna karkad'a k'afafu da taunar lips, idonsa yayi zajur saboda masifar 6acin rai.
A plaza ma tunda yashigo kowa ya fahimci yanda cikin 6acin rai, Dan ko kallon masu gaisheshi bayayi, mutane masu siyayya sai kallonshi sukeyi, dama wasu gulmace takawosu dansu k'ara ganema idonsu akan labarin da ayau yazaga ko'ina da ina. kai tsaye wani Office yashiga.
Cikin hanzari Wanda yake a office d'in yamik'e domin kwasar gaisuwa, sai dai yanayin ogan NASA yayi masifar rikitashi.
Bai saurari gaisuwarba yace, â€Å“inason ganin abinda yafayu a CCTV tundaga safiyay jiya hay dayeâ€?.
Jiki Na rawa guy d'in yace â€Å“angama ranka ya dad'eâ€?.
Kujera ya jawoma Galadima ya zauna, sannan yagyra zaman computers d'in wajen sosai, tariyo wa yafarayi cikin nutsuwa, saida yadawo Sunday morning 6pm sannan ya saki, tundaga bud'e plaza har zuwa masu share-share da goge-goge dasukayi aikinsu, har lokacin da masu sayayya suka fara Shiga da fita a plaza d'in, har an wuce yace â€Å“dawo baya kad'anâ€?.
A slowly yadawo bayan kad'an, har zuwa kan wasu samari biyu d'aya sanye da jallabiya d'ayan wandon Jeans da farar t-shirt.
â€Å“kayo zooming d'in yayannan dake tsaye sunan waige-waigeâ€?.
Zooming d'insu yayi, sannan yasanya play yanna tafiya a slow.
Samarin sunata 'yan kalle-kallene, saikuma zuwa can d'aya yasaka waya a kunne yana magana da kallon cctv camera d'in dake hasko tsakkiyar plaza d'in Inda motoci ke Parking, saikuma ya janye idonsa ya maida kan motocin dakeJere a wajen. da ganin Kasan yana maganane, Dan d'ayan dasuke tare yanata gyad'a Kansa alamar gamsuwa da abinda d'an uwansa yake fad'a.
Galadima Na zaune shiru, idonsa nakan computers d'in yana nazarin gayun har aka wuce Kansu, baice uffanba yacigaba da kallon shigi da ficin jama har zuwa 8:11pm, daga nan Computer tayi d'iff.
Da Sauri Galadima ya kalli sarayin â€Å“mi yake fayuwane?â€?.
â€Å“Ranka ya dad'e wlhy nima ban saniba, amma bara Na dubaâ€?.
Danne danne saurayin yafara da 'yan dube-dube, babu wata matsala daga nan.
Kallon Galadima yayi yace â€Å“ranka ya dad'e babu wata Matsala daga nan, sai dai Idan daga cameras d'inneâ€?.
A tsawace yace â€Å“bangane mikake nufi daga cameyas d'inne ba!? Kenan hay shigowata jiya babu kenan!? kuma kana zaune a office amma bakayi complain ba tun ajiyan? mika aikata!!? mi suka baka ne domin tozarta ni!!? nace nawa suka baka Saleem!!!!?â€?.
Kusan duk Wanda ke cikin plaza d'inan a yau yaji wannan hargagin Na Galadima.
Jikin matashin saurayin ne yafara rawa, ya zube a k'asa gaban Galadima saboda tsabar tsoratar dayayi da yanayinsa, tunda yake aiki a k'ark'ashinsa baita6a ganinsa cikin wannan yanayin irin Na yau d'inna ba, duk da labarin abinda yafaru yazo kunanensu, sunkuma ganin a jarida da social media baiyi zaton lamarin zaiyi zafi hakaba.
â€Å“wlhy yalla6ai babu Wanda yakeda abinda zai sayeni na cutar dakai, Kaine ka ceci rayuwata daga garari, ka tallafi maraicina a lokacin da nake Neman lalacewa saboda rashin matallafi, kazama gatana nida mahaifiyata da k'annena, mizaisa nabiyema rud'in wasu akan 6ata maka suna....â€?
â€Å“ya Isa haka!!â€?. ‘galadima yafad'a cikin tsawaâ€?.
Gaba d'aya Galadima ya birkice musu a plaza, yasa securitys d'in wajen da dogaransa sun kori dukkan masu sayya dake ciki, ya tartare ma'aikatan wajen a d'aya, ya tabbatar musu da in har munafukan cikinsu da aka had'a baki dasu basu fidda kansuba gaba d'aya sai sunyi dana sanin saninsa.
Kaf d'insu sun rud'e, sai rantse-rantse da k'ok'arin kare Kansu sukeyi, amma yak'i saurarensu, ganin zasu kuma dagula masa lissafi saiya basu suspension kawai aka rufe plaza d'in baki d'aya.
Motocinsa Na k'ok'arin barin wajen motar Muftahu tashigo.
Muftahu ya faka motarsa waje d'aya suka fito shida Harun, (shima Harun abokin Galadima ne makusanci, Dan zan iya cewama yafi sanin sirrin Galadima fiye da kowa a abokansa gaba d'aya, shi d'an waziri ne).
Tunkan su k'araso Galadima ya sauke glass d'in motar da kansa. kallo d'aya sukai masa duk suka tsorata, Dan basu ta6a ganinsa a irin wannan 6acin ranba, baice uffanba, sai nuni daya musu akan su shigo motar.
Basu musaba suka bud'e suka shiga, Muftahu a gaba, Harun yashiga baya kusada Galadima.
Bayan gaisuwa dasukayi garesa babu Wanda Yakuma cewa komai, Dan ko gaisuwar bai amsa musuba, hannu kawai ya d'aga musu.
Sun hau titi sarkin mota yace â€Å“Ranka ya dad'e ina muka dosa?â€?. ‘cikin girmamawa da taka tsantsan yay maganarâ€?.
Murya a shak'e yace â€Å“gidan Jayidayâ€?.
Sarkin mota bai fahimtaba, amma yana tsoron tanbaya, murya k'asa-k'asa ya tambayi Muftahu �.
Murmushi kawai Muftahu yayi yana girgiza kai, shiya shiga yima sarkin mota kwatance har suka Isa.....
�.�.�.�.�.�.�.�.�.�
Muna tsaka da barci saboda allurar da doctor yamana Innaro tafad'o d'akin, babu ko tausayi tashiga tashinmu cikin d'ad'd'aka mana duka a baya da cinyoyinmu.
Dagani har Munubiya a firgice muka tashi zaune.
â€Å“kutashi munafukai, Ashe abin ba a iya runguma da kama hannu ya tsayaba harda ciki kuka kwaso mana?, tsinannun gayyar tsiya, wlhy dagaku har uwarku yau saikin bar gidanan, a yau d'inan idan ubanku bai saki uwarkuba kun tattara kun tafi saina tsine masa albarka, yazo yaza6a ko Ku ko ni yau agidanan. sai kuma tafashe dakuka, takama bakin zaninta datayo lullu6i tana sharar hawaye, â€Å“kai ni dai Malam ya cutar dani akan had'a wannan aure da d'iyar marasa asali, ai gashinan ta Haifa mana bala'i da masifa, shikuma yatafi yabarni da kunyata, Malam kacuceni katafi kabar mana baya da k'ura. Wlhy yau sai A'isha tabar gidanan itada gayyar tsiyar 'ya'yanta, natsaneku daduk wandama zai soki A'isha, natsaneku wlhy, takuma fashewa da kuka.
Tuni matan gidanmu kowa yafito, wasu harsun shigo falonmu, wasu kuma Na daga k'ofar d'aki, harda tsirarin 'yan biki da sukak'i tafiya domin tsayawa kallon kwaf.
Cikin matan gidanmu ne wata taje tasanarma innaro wai bamuda lafiya munata amai duk abinda mukaci, anakiran likita ya dubamu yace duk munada ciki wata uku-uku.
Ni da Munubiya mun had'e kai muna kuka mai tsuma rai saboda tozarcin da innaro kemana muda mahaifiyarmu agaban bainar jama'a.
Dady da Abba k'aramine suka shigo sunama innaro magana akan bafa haka zancen yakeba, babu Wanda yace munada ciki.
Hayayyak'o musu tayi tana zaginsu, wai k'aryane suna kare Innarmu ne, aida likitan bai fad'aba baza'aje a sanar mata ba.
Cikin 6acin rai baba k'arami yace, â€Å“inna waye yaje yafad'a miki wannan maganar to?â€?.
â€Å“cikin matan gidanan mana, kuma daga bakin wadda nasan bazataimin k'aryabaâ€?.
Ran Dady ma a wannan karon ya 6aci, afusace yace, â€Å“inna wacece acikinsu? Wace 'Yar isakar mataceâ€?.
Nanafa matan gidanan mu suka shiga raba idanu akan juna.
Innaro tace â€Å“karka kuma zaginta, idaba ayiba bazatace anyinba, kuma koma wacece bazan fad'aba, idan kuma ni kake zagi sainaji?â€?.
â€Å“ALLAH ya huci zuciyarki inna, ni yaza'ayi Na zagekiâ€?.
â€Å“kai dai kasani sakaraiâ€?.
Duk abinda ke faruwa Abbanmu da Innarmu Na saurare daga d'akinsa amma acikinsu babu Wanda yayi yunk'urin fitowa.
Kayanmu innaro tafara kwasa tana watsowa waje, wai saimun bar gidan.
â€Å“Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, wannan wane irin tashin hankaline?â€?. ‘innarmu tafad'a cikin matsanancin kukaâ€?.
Rungumeta Abbanmu yayi shima yana k'ok'arin maida kwallar data cika masa idanu.
Ganin abin yana Neman wuce gona da iri baba k'arami yafita da hanzari, wani tsoho dake can k'asan layinmu yaje ya d'akko, tsohon abokin Malam faruku ne na k'ut da k'ut, shika d'aine zai iya takama Innaro burki kuma.
Aiko hakance ta kasance, tunda yashigo yay magana Innaro ta dakata da abinda takeyi tana huci da fidda numfashi.
Tsoho Malam Labaran yace, â€Å“haba innar jafaru, da hankalinki da girmanki kike aikata wannan abin Na yara a gaban sirikanki da 'ya'yanki da jikokinki? Shin babu mai fad'a miki kijine wai kekam?â€?.
Cikin sassauta murya tace, â€Å“malam mai kanwa nasan bakasan ainahin abinda yafaru bane kaima, amma wlhy da dakanka zakace Auwalu yasaki marar asalinnan sukama gabansu itada 'ya'yanta am.....â€?
Hannu ya d'aga mata, yagyara tsayuwarsa jikin sandarsa dake taimaka masa tafiya, naji komai innar jafaru, amma wannan hanyar da kuka biyo ba wai itace mai 6illewa ba, bincike yakamata ayi domin asan gaskiyar lamarin. dan haka zoki wuce gida, zuwa gobe zamu tattauna akan lamarin sannan kowa ya nutsu, mukuma jira abinda zai fito daga can gidan Sarkin�.
Badan innaro tasoba tafice, hakama matan gidanan mu basuso wasan yak'are iya nanba, sunso a yau Innarmu tabar gidan da saki, sannan mukuma mahaifinmu ya koremu. Kowa taja k'afa takoma d'akinta cikeda takaici da addu'ar ALLAH yasa daga gidan sarkin suma su d'auki mummunan mataki akanmu.....
Maman fauziyya Ce kawai ta nuna damuwarta akan lamarin
�.�.�.�.�.�.�.�.�.�.�
Su Galadima ma sun isa gidan jaridar *Manuniya* tun sanarwar isowarsa ta kad'a hantar cikin ma'aikatan wajen, musamman wad'anda basuda laifi akan lamarin, tirsasu akayi.
Shi kansa manaja d'in wajen a kid'ime yake, dukya rikice yarasa matsugunni har Galadima da gayyarsa suka iso office d'in bisa jagorancin sakatare d'insa.
K'asa yazube kawai yana kwasar gaisuwa wajen Galadima, ko kallo bai ishi Galadima ba, cikin daka tsawa yafara magana...........âœğŸ?
Tofa masu karatu, ko manajan jaridar MANUNIYA zai amsa laifinsa? Kokuwa zai fad'i wad'anda suka sanyashine inba laifinsa bane shima? to koma dai shima da had'in bakinsa?. Wane mataki masarautar su Galadima kuke ganin zata d'auka akansa? Shin ina ma maganganun Momma suka dosa ne? Miya faru da mahaifin Galadima har suka koma k'asar India da zama?.😕
Kumuje zuwa my guys danjin yanda zata kaya. da amsoshin d'unbin tambayoyinkun nan.⛹ğŸ»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€ÄŸÅ¸¤¾ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€
_Naga mutane basa fahimtar yaren yarima😂, yarima later R ne baidashi, bawai tsamin bakine dashiba fa, kun gane, naga wasu kamar suna zaton tsamin bakine dashi🤣._
_Ngd da comments d'inku, kuna sakani farin ciki sosai, kuyi hak'uri da rashin amsawa ta, kunada d'unbin yawane wallahiğŸ˜Å 🥰🥰🥰🥰. I love you wujiga-wijiga allğŸ˜Ã¢Å“‹ÄŸÅ¸?._
*_Ya ALLAH ka gafarta ma iyayenmu_*ğŸ˜ÄŸÅ¸‘ğŸ»[4/22, 2:14 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
__________________________
*_Naga idi🙆ğŸ», Galadima fa ba tsamin baki bane dashi, Ku fahimta😂, bashida (R) ne, amma gashinan nayi gyara, ina fatan yanzu zakuna fahimtarsa🤣._*
_______________________________
👉ğŸ»1âƒ?1âƒ?
.........Ba manager kawaiba, hatta da sauran jama'ar dake gidan jaridar saida suka tsorata da tsawar Galadima, su Muftahu ma tsorone ya kamasu, sunsan irin wannan matsanancin fushin gareshi babbar matsala ce ga lafiyarsa.
Aikam sai gashi ya dafe kansa, saboda yay wani mugun sara masa, da sauri Harun yajawo kujera ya kamashi ya zaunar, har yanzu dafe yake da kan nasa.
Muftahu ya furzar da hucin, matsalar da suke gudun ta d'akko hanyar faruwa kenan. kallon manaja dake durk'ushe har yanzun yayi,
yace â€Å“tashi ka zaunaâ€?.
Mik'ewa manaja yayi jiki Na rawa yakoma saman kujera, Muftahu da Harun ma suka zazzauna.
Cikin tsare gida Harun yace, â€Å“manager ka nutsu, kabamu had'inkai wajan fad'ar gaskiya, inba hakaba wlhy zakayi nadama ne, ba kaiba hatta da ahalinka saisunyi nadamar kasancewarka acikinsuâ€?.
Manaja yashare guntun kwallar dasuka taru masa a idanu, a nutse yafara fad'in â€Å“ai tunkan jaridar jiya tafita nake acikin nadama, nayi dana Sanin kasancewata ma'aikacin jaridar da aka ci zarafin d'an Wanda yay tushen kasan cewata a wannan matsayin danake, da ace remote d'in rayuwata a hannuna yake, dana tariyo bayana jiya bata shigo rayuwata ba, amma Na.....â€?
Muftahu ya katseshi cikin d'aga masa hannu â€Å“kaga manager, ba rayuwarka mukazo saniba, munason ka fad'a mana waye yasaka wannan aikin? nawa suka biyaka kamusu shi?â€?.
â€Å“wlhy tallahi yalla6ai basu biyani komaiba, kaga wacan jakar sune suka ajiye min ita, amma ko bud'eta banyiba. kuma babu wani ma'aikaci daya buga labarinan agidan jaridar nan da hannunsa. sune da Kansu adaren jiya sukayi komai, bayan sun had'emu waje guda da bindugu, kuma sunzo nannane dukansu fuska arufe, wlhy ko fuskar mutum d'aya bamu ganiba, yanzu haka sun kwashe muhimman documents dake ma'aikatar nan sun tafi dasu. kuma sunsan da zuwan yalla6ai gurinnan yau, Dan komai sunyishine a tsare kamar yanda mukaji suna hira a tsakaninsuâ€? manaja ya fashe da kuka, sannan yacigaba da fad'in â€Å“saboda sunsan zakuzo nan yau, sunje gidana tun adaren jiya, sun kwashemin iyali da mahaifiyata, yanzu haka suna wajensu, sun tabbatar min inhar wani magana yafito abakina abakin ran matata da yarana hud'u da mahaifiyata sai k'anwata. wlhy ina cikin masifa, yau anan Na kwana, nakasa fita waje saboda banason jin 6atancin da jama'a suka gani a wannan safiyar akan yalla6ai. Wlhy Na rantse muku bansan komaibaâ€?.
Tunda manaja yafara magana kowa yay tsit, Galadima bai d'agoba saida yaji manaja ya ambaci iyalansa Na wajen wad'anda suka aikata aika-aikar. Idonsa yakad'a yayi jazur, sosai manaja ya tsorata da idanun Galadima, haryana tunani a zuciyarsa anya Galadima shi kad'aine, bashida aljanu kuwa?.
Komai Galadima bai ceba, ya tashi dafe dakai yafice daga office d'in, ma'aikatan wajen sai zubewa suke suna kwasar gaisuwa, amma kallon kowa baiyiba yafice.
Dogaransa suna ganinsa suka mik'e da Sauri, Mota suka bud'e masa yashiga, suma su Muftahu suka fito da hanzari.
�.�.�.�.�.�.�.�.�.�.�.�
Tun daga fitar innaro sai gidan yay tsit, kowa ya kama gabansa zuwa d'akinsa, a can suka cigaba da gulmace-gulmacensu suda bak'insu.
Niko da Munubiya muka shiga raira sabon kuka, munubiya ta kamo hannuna ta rik'e anata.
â€Å“Munaya dan girman ALLAH kibarni Na kar6i hukuncin laifina, nice Na aikata bakeba, miyasa zaki cema iyayenmu kece? kibari nafad'a musu gaskiya please â€?.
â€Å“A'a Munubiya, wannan laifin nawane, karki manta ta sanadina abinnan yafaru, da ace Fu'aad bai kaimu plaza d'innanba da hakan bata faruba wlhy, munubiya farincikina fansane agareki, har abada bazan iya juriyar ganinki cikin k'unciba, Dan Girman ALLAH koda da wasa kar wani agidannan yaji banice Na aikata abunnanba koda kuwa innarmu Ce, namiki alk'awarin zan jure duk wata fitina dazata taso, zankira Fu'aad yafito muyi aure, duk da naso ace rana d'aya aurenmu zai kasance, amma haka ALLAH ya k'addara manaâ€?.
rungume juna mukayi muka kuma fashewa da kuka, cikin shashshekar kuka Munubiya ke fad'in â€Å“mi mukaima Wanda ya k'ulla mana wannan sharrin? mi muka tare masa agidan duniyarnan Munaya?â€?.
â€Å“ban saniba Munubiya, bansan waneneba? Amma nafi zargin gidan wannan jaridar, aganinsu sun sami babban labari, bara su buga suyi suna, Sun zaluncemu Munubiya, sun yad'a labarin abinda ba haka faruwarsa ta kasanceba, Galadima ko ta6aki baiyiba amma suka saka har yana kissing d'inki, wane irin zaluncine wannan? wlhy nima bai ta6a niba da mukayi karo a filin idi, amma ki duba hannunsa rik'e da nawa ajaridar, Munubiya banga laifin iyayenmu ba, kowanne mahaifa bazasu so ganin wannan mummunan abinba, kuma ko zamu kwana rantsuwa bakowa zai amince damu ba, INA tausayama innarmu, ada Yaya muka k'are ma a gidannan bare yanzu?, munubiya innarmu innarmu, banason innarmu tashiga mummunan hali akanmu, yazamuyi innarmu ta fahimcemu, koda ace kowa bai yarda damu ba inason innarmu fahimcemu munubiya.....â€?
â€Å“Na fahimceku 'ya'yana, tabbas nashiga tashin hankali da ganin hotonku a jarida, kuma a yanayin da kowace uwa ba zataso ganin 'ya'yanta a wanna halinba, kuma ace bazata shiga fiyeda yanayin Dana fad'aba, sai dai ni ba abinda naganine yasakani cikin rud'ani irin haka ba harna yanke jiki na fad'i, cin zarafin innaro ne.
'ya'yana nasan bazaku aikata koda makamancin hakanba, dan naji ajikina sharri akai muku.....�
Da gudu suka sakko a gadon sukazo suka fad'a jikin innarsu suka cigaba da raira kuka harda ita kanta innar, saida sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru.
Duk suka nutsu suka mata bayanin komai, har Munaya ta d'akko wayar da Galadima ya barta da ita a filin idi ta nuna musu.
Nanna INA ta kuma fahimtar akwai 6oyayyen al'amarin abinda basu saniba akan lamarin, kuma tafi zargin k'ullin Anma Galadima ne kawai, 'ya'yanta k'addara Ce ta sakasu cikin sark'ak'iyar, itadai Addu'arta ALLAH ya fiddashi da 'ya'yanta baki d'aya, saitaji yabata matuk'ar tausayima.
Suna cikin haka saiga mama Rabi'a dasu Ayusher, nanma aka kuma zaman warware zance, mama Rabi'a da inna suka kuma fahimtar komai yanda yake.
Nasiha suka Shiga yima 'ya'yan Nasu mai ratsa jiki, sannan suka nuna musu illar biyema samari batareda wani dogon tunaniba, duk sai jikin su Munaya yayi sanyi, sun fahimci bin Fu'aad dasukayi plaza shine yazama babban kuskurensu.
Sun nemi gafarar iyayen nasu akan hakan dasuka aikata, daganan suka Shiga tattauna maganar Auren munaya da Abba yakafe akan nanda sati biyu.
Sun Yanke shawara akan akira Fu'aad, inhar da gaske yakeyi to saiya fito kawai.
Akan wannan shawarrar suka zauna gaba d'aya.
★★.★★.★★.★★.★★
Har suka Isa cikin masarautar Galadima baiko motsaba, yana tangad'i da layi yashige 6angarensa, daga Muftahu har Harun babu Wanda yayi yunk'urin binsa.
Tunda yaje yazube saman 3seater bai sake sanin inda kansa yakeba saboda matsanancin ciwon kai dake damunsa, da k'yar ya iya gabatar da sallar magrib da isha'i a lokaci d'aya, a saman abin sallar ya kwanta rigingine dafe da goshi, yana kwance shiba mai barciba shiba ido biyuba.
8:30pm dukkan mai ruwa da tsaki a meeting d'in ya hallara, hatta da sarki gaba d'aya, sai dai kuma babu Galadima babu dalilinsa har mama Fulani tafito.
(Babbar magana 😨) na fad'a a raina, saboda ganin tsantsar mulki da isa ajikin hamshak'iyar tsohuwa dazata iya kaiwa shekaru 77 a duniya, sai dai tsantsar hutu da gayu ya 6oye ziryan d'in tsufan nata, gata da k'aramin jiki kuma, daka ganta haka bafulatanar asali.
Tunda ta fito kowa a falon yamik'e tsaye saboda girmamawa a gareta, amma banda sarki, ya risinar da kansane kawai alamun girmamawa ga mahaifiyar tasa.
Saman kujera 2seater ta zauna cikeda izzar mulki, (saikace itace sarkin🤦ğŸ»Ã¢€Ã¢™€) sai da ta gamaima kowa dake falon kallon tsaf sannan takuma kamewa, cikeda k'asaita tace, â€Å“Shi yana ina? Ko raini. Hankalin nasane ya hanashi zuwa?â€?.
Kowa dake wajen yasan galadima take nufi, babu wanda ya iya cewa komai sai wani matashin saurayi dazasu iya zama sa'annin juna da galadima, ya gyara zamansa yana wani 6ata rai shima, â€Å“Granny kinsan halinsa aii, ba ganin kowa da gashi yakeba a masarautar nan mtsowwâ€?.
Mama Fulani ta turo hanci ga bada, cikeda fushi ta bada umarnin a kira mata jakadiya.
babu dad'ewa saiga jakadiya tashigo, k'asa ta zube tamkar zatayi mata sujuda tafara fad'in â€Å“ALLAH yaja zamaninki ranki ya dad'e, kinga taki kinga tawasu, fatanmu kiga tawasun wasuma, Sarautar gagara badau a hannunki take, domin kaida kaya ai duk mallakar wuyane, duk mai shirin ganin barcinki ya tabbata shima bazaiyi nasaba, kece k'i gudu samaza gudu, jaruma mai dad'and'en tarihi, kin ajiye tarihin da babu wanda yake dashi a masarautar nan, koda kuwa mai martaba gagara badaune, ALLAH ya tsare gabanki ya tsare bayanki, mace mai kamar maza, mazanma a tafin k'afafunki suke ya uwar gijiyataâ€?.
Sosai kirarin jakadiya yayima mama Fulani dad'i, takuma kishingid'a a kujerar, cikeda izza tace, â€Å“inason ganin Galadima yanzunanâ€?.
Angama damusa k'i sabo, cika umarninki wajabtaccene a gareni 'Yar sarki, matar sairi kuma mamar sarki, wata ran kakar sarki, ki huta lafiya babbar giwa�.
Fita jakadiya tayi.
Ta isa 6angaren galadima, inda sarkin k'ofa yashiga domin yimata iso, halin daya isake shugaban nasa ya razanashi, amma haka yadake ya isar da sak'on jakadiya.
Da k'yar galadima yay masa nuni akan yabarta tashigo.
Babu dad'ewa saiga jakadiya, ta rusina cikin girmamawa ta gaisheshi, bata damu da rashin amsawar tashiba ta isar da sak'on mama Fulani. hannu kawai ya iya d'aga mata.
Kusan mintuna 7 da fitar jakadiya yamik'e dafe da kansa dayakejin tamkar zai fad'o k'asa, jiyay falon na juya masa, ya dafe bango da gyar kusan 2munute sannan yad'an lafa, haka yafito yana d'an tangad'i, wajen mota yanufa, dan bazai iya zuwa sashen mama Fulani da k'afaba, saboda akwai tazara sosai a tsakaninsu.
Da sauri sarkin mota yataso ya bud'e masa, shima shiga yayi mazaunin driver, sauran dogaranma suka shishshiga mota.
Da k'yar galadima yafurta â€Å“sashen mama Fulani zamuje, sauran su zaunaâ€?.
cikin girmamawa sarkin mota ya amsa, sannan ya sanarma sauran dogaran.
dukkan jama'ar dake falon idanu suka zuboma Galadima daya shigo dafe da kansa, baima kowa magana ba yasamu can gefe ya zauna, har yanzu hanunsa na saman kansa, muryarsa a shak'e yace, â€Å“barkanku da dareâ€?.
Hakan yayi masifar k'ona ran mama Fulani, saboda ma ya rainata tare zai gaidata da kowa? kuma bazaizo gaban taba ma yabata girmanta?.
A falonma wasu sun amsa wasu basu amsa mishiba, shi baima San sunayiba, ta kansa kawai yakeyi.
Cikeda izza mama Fulani tace, â€Å“to isashe, gaisuwar ma saina rok'a ko yayaâ€?.
Dukda halin dayake ciki bai hanashi sakin guntun murmushiba, ya janye hannunsa daga goshinsa, idanunsa dasuke matuk'ar jajur yad'ago ya kalleta, ba mama Fulani niba kowama a falon ya firgita daganin idanunsa, hakan ya tabbatar musu da bashida lfy kenan.
Ahankali Yakuma furta â€Å“bagykanki da hutawaâ€?.
â€Å“ALLAH yarabamu da bak'in haliâ€? . ‘mama Fulani tafad'a batareda ta amsa gaisuwar baâ€?.
Baice uffanba ya maida kansa ya duk'ar, tareda kuma tallafe goshin yana ta6e baki.
Idanun Ummu Hasheem yacika da kwalla saboda tausayin Galadima, ko kad'an batasan bashida lafiya ba, dukda d'azun ta aika bayinta su duba matashi suka tarar yafita.
Mama Fulani kam baki ta k'ya6e tareda kuma hard'ewa a kujera, takai dubanta ga wani dake gefenta, Matawalle! ahad'amin video call da Zeenah yanzunan�.
â€Å“angama ranki ya dad'eâ€? Dan danan yahad'a video call bayan yakira wata number, wata kamilalliyar matace ta bayyana ajikin System d'in, tana sanye cikin shigar kamala, kallo d'aya namata Na hango kamannin Galadima tartare da ita, dukda kamar tafisa haske, hakkane ya tabbatar min da Momma ce.
Cikin girmamawa ta gaida mama Fulani, ita kuma ta amsa cikeda k'asaita sannan tafara magana kamar haka.
â€Å“nasan kowa yasan miya taramu anan wajen?, bana buk'atar maimaita wannan shed'ancin a harshena, wanda kuma ya aikata yasan kansa, Dan haka hukunci biyune, yanada za6i aciki. Na farko tozarcin da yayama masarautarnan da zubar mana mutunci mun haramta masa auren kowacce yarinya data fito daga kowacce masarauta, na biyu ya gaggauta fidda matar aure acikin shekararnan kafin yaje yayma wata ciki a waje akawo mana d'an tsakar gida a masarauta, kokuma mu muza6a masa acikin bayin gidannan, hukunci na farko babu sasauci acikinsa kuma babu canji, Na biyu yanada za6i nemowa komu nema masa. Wannan shine tabbataccen hukuncin kotun fulani. Idan akwai mai abun fad'a sainaji?â€?.
Kowa ya girgiza kai alamun a'a, wasu hukuncin bai musu dad'iba, wasuko yamusu fiye da zaton mai karatu.
A hankali Galadima ya yunk'ura yatashi batareda yacema kowa uffanba yanufi hanyar fita.
â€Å“to fand'ararre, daka tafi ba'a gama magana ba ai uwarka zataji, mara mutunci mai bak'in haliâ€?.
Juyowa Galadima yayi ya kalli mama Fulani, wani k'asaitaccen murmushi ya sakar mata sannan yay salute nata yafice abinsa�.
Mafi yawansu saida suka zaro idanun mamakinsa, dama Kowa yasan galadima baya tsoron mama Fulani a masarautar, duk masifarta saima yagadama yake amsata, gaisheta kam saiya zo k'asar yatafi ma bata ganshiba. Iya kacinta tayi masifarta da sababi ta hak'ura, babu yanda ta iya dashi.
Murmushi kawai shima sarki yayi baice komaiba.
Mama Fulani kam kasa koda motsi tayi a kujerar saboda abin kunyar da galadima yayi mata gaban kowa, ta tsani shed'anin yaronnan mai ido a tsaitsaye dabaya shakkar kowa. Kwafa tayi sannan tatashi tabar falon tana tafiya cikeda mulki da izza.
Gaba d'aya suke fad'in ALLAH ya huci zuciyar sarauniyar sarakuna.
Duk abinda ke faruwa Momma naji kuma tana gani, amma dayake Galadima yana bayan laptop d'in bataga miyayiba, hasalima bataji ko sau d'aya yayi magana ba, hakanne ya tada hankalinta, mama Fulani Na barin wajen ta katse call d'in, waya ta d'auka takira number Galadima, amma harta tainke bai d'agaba.
Kira Na biyu ta sakeyi, hakan yay dai-dai da shigowar Galadima falon dafe da kansa.
Da k'yar ya iya d'aga wayar, muryarsa a shak'e yace, â€Å“Momma zan kigyaki anjimaâ€? bai jira cewarta ba ya yanke wayar.
Hankalin Momma yakuma tashi, tasan ransa yakai k'ololuwar 6aci, da sauri ta danna kiran Harun, yana d'agawa ko gaisuwar dayake mata bata amsaba tace, â€Å“Harun maza jeka duba min Moh'd yanzunanâ€?.
Yanda yaji Momma Na magana shima kansa saiya kid'ime.....
�.�.�.�.�.�.�.�.�.�
Ayusher tafita tasiyo min credit domin kiran Fu'aad.
Jikina a sanyaye nagama loda katin, tunani nakeyi shin Fu'aad zai kar6eni bayan yaji abinda yafaru a jiya zuwa yau? tunda komai akan idonsa yafaru. Na dad'e ina juya wayar a hannu kafin Nayi dialing d'in Number d'insa d'in, harta tsinke bai d'agaba, ban damuba Na sake kiransa da tunanin ko baya kusa da wayarne.
Bugun farko kuwa ya d'aga wayar...........âœğŸ?
Humm masu karatu, mi kuke tunanin zai faru tsakanin Munaya da Fu'aad a waya, zai kar6eta kokuwa sa6anin haka?.
Yaya zata kasance ga Galadima kuma?.
Wannan amsar tana a page 12 da zaizo muku ranar MondayğŸ˜Æ’👌ğŸ».
Barkanku da juma'a.
Musha weekend lafiyağŸ¤ÄŸÅ¸»ÄŸÅ¸¥°ÄŸÅ¸¥°.
Team *_INNARO & MAMA FULANI_*🥴🥴⛹ğŸ»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€.
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu._*ğŸ˜ÄŸÅ¸‘ğŸ»
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
👉1�2�
.......Murya a sanyaye Munaya tace, â€Å“Assalamu alaikaâ€?.
â€Å“wa'alaikissalamâ€?. ‘wata murya ta amsa sa6anin Fu'aadâ€?.
â€Å“Uhhm 'yar uwa please, ko ina mai wayar dan ALLAH?â€?.
â€Å“Mai wayar kuma? ai nice mai wayarâ€?.
Wani iri munaya taji a zuciyarta, suka kalli juna itada Munubiya dan a Hans free tasaka wayar. alama munubiya tamata akan tayi magana. kai Munaya ta jinjina mata, sannan tace, â€Å“ayya 'yar uwa sorry dan ALLAH, wlhy wanine yabani number d'innan mai suna Fu'aadâ€?.
â€Å“Fu'aad!â€?. ‘yarinyar ta maimaita daga canâ€?, saikuma tace â€Å“to gaskiya 'yar uwa yabaki wrong Number, ni sunana Afnan, ina Katsina state neâ€?.
Wasu hawaye masu zafi suka zubo a kumatun Munaya, â€Å“shikenan ngd sis..., kiyi hak'uriâ€?.
â€Å“no babu damuwaâ€?.
Bayan Munaya ta katse wayar ta dafe kai tana hawaye, daga Ayusher har Munubiya basa Neman k'arin bayani, tunda sunji komai, Munubiya ta share hawayenta tana murmushin takaici, â€Å“kibarshi karki sake kiranshi, nasan shine yabama yarinyar nan wayar akan tace wrong number ne, ya ALLAH ka kawo mana sauk'i a wannan lamari daiâ€?.
Tsaki Ayusher taja, ta kamo hannun Munaya â€Å“sweet sis..., please wannan karya zama abinda zai ta6a zuciyarki, ki d'auki hakan matsayin ba komaiba, kuma hakan da Fu'aad yayi yasani kuma tabbatar da zargin danake a kansa, ku duba yanda yazage saimunje birnin gayu plaza aranarâ€?.
Gaba d'ayansu zuba mata ido sukayi cikin wani yanayi.
Feena dake kwance tatashi zaune, â€Å“humm aini wlhy tunda zancen jaridar nan yafito zargina yana kan Fu'aad ne, Na barine akirashi dama danna sake tabbatarwaâ€?.
Munubiya tace, â€Å“sisters nifa duk Na kasan fahimtar zancennan naku fa, zargi babu k'yau ai, miye ribarsa idan ya aikata hakan? dukama yaushe muka San juna dazai yi hakan a garemu? yarasa kuma dawa zai mana hakan sai galadima?â€?.
Zama Ayusher ta gyara, tafara musu bayani dalla-dalla. â€Å“tad'ora da fad'in kinsani ko saboda galadiman yayi?â€?.
â€Å“to amma Dan zaima Galadima mu miye Na had'awa damu kuma?â€?.
â€Å“wannan amasar tana wajen Fu'aad sister â€?.
Hankalin Munaya yatashi ainun, itafa ko kad'an bata ta6a kawo Fu'aad acikin wad'anda take zargiba, amma maganar Ayusher tasata dogon nazari yanzu, duk da dai bawai tama yarda baneba kwata-kwata..
★★★★★★★★★★
Lokacin da harun ya iso sashen Galadima bai wani jira isoba yashiga, kwance ya iskeshi bisa 3seaters sam6al, hannunsa d'aya dafe da k'irji, d'aya dafe da kansa.
Da sassarfa ya k'arasa gabansa â€Å“Sameer lafiya kuwa?â€?.
Da hannu Galadima yamasa nuni da k'irjinsa da Kansa.
â€Å“ya salam, Sameer! Shiyyasa naketa cemaka kacire abunnan a ranka, kafasan matsalarka batason yawan takura da tunaniâ€?. Wayarsa dake ringing ya Ciro a aljihu, Momma Ce ke kiransa.
Cikeda girmamawa ya amsa sallamar data masa, sannan naji yace, â€Å“wlhy Momma bashida lfy, kuma k'irjinsa yake complain akaiâ€?.
â€Å“ok Momma â€?.
Yana yanke wayar sai yayi kiran Dr Jalal.
â€Å“Jaalal please kana gida kuwa?â€?.
Bansan wace amsa ya bashi ba daga can, naji dai yace, â€Å“please kazo kaduba Galadimaâ€?.
Babu dad'ewa saiga Dr Jaalal, damuwa sosai Nagano a fuskarshi saboda ganin halin da Galadima yake ciki.
Harun ya taimaka masa suka kaishi bedroom, sannan yamasa allurar barci.
Babu dad'ewa kuwa barcin ya kwasheshi.
Su duka ajiyar zuciya suka sauke, Dr jaalal yama harun sallama yatafi.
Yana fita Muftahu Na shigowa, gaisawa sukayi da Harun, sannan ya tambayi jikin Galadima d'in.
Harun ya amsa masa Cesar da sauk'i.
Anan sashen Galadima suka kwana, sai dai kowanne acikinsu da dalilin kwannan nasa.
*_Washe gari_*
Alhmdllh Galadima yatashi jikinsa da d'an sauk'i, yakuma ji dad'in ganin Harun da Muftahu a tare dashi. bai iya zuwa masallaciba sai a d'aki yayi salla.
Yana zaune akan sallayar yana azkar su Muftahu suka shigo, zama sukayi bisa Sofa suna jiran yak'arasa azkar d'in nasa.
Bayan ya k'arasa ya juyo garesu, hannu ya mik'a musu sukayi musabaha, suka tamyashi jikinsa.
Yace da sauk'i Alhmddlh, sannan yace, â€Å“Muftahu inason ticket, dan yau zan wuce India, ina buk'atar ganin doctor d'inaâ€?.
â€Å“ok babu damuwa, bara na bincika idan akwai jirgi mai zuwa India daretâ€?.
Harun yamik'e yana fad'in â€Å“bara ahad'a maka ruwan wanka toâ€?.
Kai ya d'agama harun, ya maida idonsa ya lumshe tareda jingina da Waldrop.
Muftahu dake latsa waya yad'ago ya kallesa, â€Å“babu jirgin dazai tashi a yau, sai gobe 1:30pmâ€?.
Batareda ya bud'e idonsa ba yace, â€Å“bincika min ta Abuja ko legos. dan bazan iya kuma kwana a k'asar nanba yau, ina buk'atar ganin lilitaâ€?.
Kai Muftahu ya jinjina ya cigaba da latse-latsensa a wayar, kusan mintuna 4 sannan yad'ago, â€Å“an samu, amma zai biya Abu-Dhabi ya sauke Passenger's, daga nan zasuyi hutun kamar na 1hourâ€?.
Idomsa a lumshen yace â€Å“yaushe zai tashi daga Nan?â€?.
�12pm, yanzu na saya maka ticket d'in zuwa Abuja, jirgin zai tashi 8am ne�.
â€Å“Ok bara na shirya toâ€?.
Harun dake tsaye yana saurarensu yace â€Å“bara naje Na watsa ruwa nimaâ€?.
Shima Muftahu mik'ewa yayi suka fita tare.
Galadima yashiga bathroom, kusan mintunansa 40 sannan ya fito, dauriya kawai yakeyi, amma shi kad'ai yasan irin suyar da zuciyarsa ke masa. tsaf ya shirya cikin Suit blue, rigarshi ta ciki Orange, yayi k'yau sosai, yana zaune bakin gado yana saka takalminsa Muftahu yashigo da sallama.
d'ago idanunsa yayi akan Muftahu, sannan yatashi tsaye yana gyara belt nashi, â€Å“ya maganar binciko yarinyar nan?â€?.
â€Å“Nagama komai, inason kasami nutsuwane sai muyi maganar damanâ€?.
Galadima dake gyara 'yar sumarsa da bawani yatarata da uban yawa bane yace â€Å“ok, katura min komai zan duba, sannan inason kaje kuyi magana da commisshiner of police akan iyalan Manager d'innanâ€?.
â€Å“ok yalla6ai angama insha ALLAHâ€?.
Sallamar Harun suka amsa gaba d'aya, ya zauna kan sofa sannan yace â€Å“amma yakamata ma'aikatan plaza su koma aikinsu, naga jama'a kamar suna fassara abin dawani Abu daban kumaâ€?.
Murmushin gefen baki galadima yayi, ya ajiye Cumb d'in hannunsa yajiyo yana kallonsa â€Å“aini yanzun kuma babu kuma ta sigar dabaza'a fassara ni ba, inaga akan mace kawai yarage jaridu su buga duniya ta ganni, so sukoma aikin su kawaiâ€?.
Daga Harun har Muftahu kallonsa suke cike da tausayawa. Muftahu yace wannan d'inma kansu sukai mawa, kuma ALLAH bazai barsuba�.
â€Å“insha ALLAHUâ€?. ‘cewar Harunâ€?.
Galadima baice komaiba, sai d'an kimtse kimtsen da ba'a rasabane ya k'arasa, su Harun kam suka fice suka bashi waje.
Baifi mintuna 10 ba yafito suka fice, bayan yatsaya da bayinsa na mintuna biyar, bansan miya fad'a musuba, naga dai sunata faman godiya damasa addu'a.
Aka bud'e masa mota yashiga, duk wanda yake k'ark'ashimsa saikaga fuskarsa ta canja alamun baya son tafiyar tasa.
Kai tsaye fada suka nufa, bayan motocin sun tsaya aka bud'e masa yafito.
Shi kad'ai yashiga fadan, cike take da dukkan masu ruwa da tsaki anata fadanci.
Saida ya gaida sarki, sannan ya zauna mazauninsa kusada sarkin, sauran fadawan suka gaidashi cikin girmamawa, shima ya amsa cikeda mutuntawa.
â€Å“ya adalin sarkinmu yau zan koma inda na fito, saboda inason ganin likitanaâ€?.
Murmushi sarki yayi, sannan ya gyad'a kai bare da yayi maganaba.
Da sauri Dogarawa suka d'auka da fad'in Sarki yajika Galadima, Yakuma amsa, yana maka addu'ar sauka lfy kuma.
â€Å“ina godiya da wannan alfarmaâ€?. ‘galadima yafad'a cikin rissinar da kai alamun girmamawaâ€?.
Sarki yad'an gyara zamansa, ahankali ya furta â€Å“ka gaidamin da d'an uwana da gimbiya Zeenah, insha ALLAH nima nextweek ina nan zuwaâ€?.
â€Å“ina godiya ranka shi dad'e, insha ALLAH d'an uwanka zaijiâ€?.
â€Å“gyad'a kai kawai sarki yayiâ€?.
â€Å“An gaisheka galasima, ALLAH ya tsare gabanka da bayanka, ALLAH ya kaika lafiya yabama adalin tsohon sarki lafiya, Alkairin ALLAH da ni'ima sukai a garesa, gaba dai gaba dai Galadima mai jiran gado, d'an sarki jikan sarakuna k.....â€?.
Hannu ya d'aga musu alamar ya Isa.
Ya risinar da Kansa domin girmamawa ga fada sannan yamik'e suna jera masa addu'oi, yayinda shikuma yake amsawa asaman la66ansa.
Bai shiga sashen kowaba yay tafiyarsa, suna isa filin jirgi ko 20 minutes basuyiba jirgin su yatashi zuwa Abuja.
Muftahu da Harun da dogaransa suka dawo cikeda kewarsa.
Koda ya isa Abuja hotel yanufa kai tsaye, yakama d'aki danya huta, akwai kusan 3hours nan gaba kafin jirginsu ya tashi. Rigar suit d'insa yacire tareda tie d'in, sannan ya zame wandon da rigar cikin ya kwanta dagashi sai boxer da vest.
Juyi kawai yakeyi agadon, Dan barci yakasa d'aukarsa, abinda yafaru a kwanaki biyunnan yakasa barin zuciyarsa, yarasa wane irin hasashe zaiyi ga masu aikata masa hakan... Ringing d'in da phone nasa tayine yasakashi bud'e idanunsa, wayar yajawo yana kallon mai kiran. *_Sweet papi_* yagani ajikin wayar, yay saurin d'agawa kafin ta tsike.
Cikeda girmamawa tamkar yana a gabansa ya rissinar da kansa bayan yatashi zaune, â€Å“Barka da hantsi ranka ya dad'eâ€?.
Daga can aka amsa â€Å“da yauwa Muhammad, ina fata kana lfy?â€?.
â€Å“Alhmdllh ranka ya dad'eâ€?.
â€Å“To masha ALLAH, dama mamanka Ce takirani takemin wasu bayani, duk da kafin kiran nata dama naga zantukan dake yawo a jaridu da yanar gizo, zuciyata bata yarda zaka aikata hakanba Muhammad, amma inason sanin gaskiyar zancen?â€?.
â€Å“wlhy ranka ya dad'e sunyi hakanne kawai domin 6atamin suna, amma ainahin abunda yafaru shine.............â€?
Nan Galadima ya zayyane masa komai.
Murmushi mai sauti tsohon yayi, har Galadima Na jiyosa, sannan yace, â€Å“hummm! to yanzu kai kana wace nahiya ne?â€?.
â€Å“Ina Abuja zan koma India, saboda jikina yana Neman motsawaâ€?.
â€Å“to to, hakanma dakayi dai-daine, amma a kwantar da hankali, komai mai wucewane, komai kaga yafaru da d'an Adam rubutaccene a littafinsa, dama ita rayuwa tana tafiyane da k'addara, yanzu zan isa fada, bayan kasamu nutsuwa idan kaje zamuyi magana, duk da watak'ilma nashigo ganin mahaifin naka k'arshen watannanâ€?.
â€Å“to shikenan, ngd sosai, ALLAH yak'ara tsahon rai da lafiya mai amfaniâ€?.
â€Å“amin ya rabbi Muhammadâ€? cikin tsokana tsohon yace â€Å“kaga d'annema, duk kabi ka susuce akan k'aramin Abu, kazo Na sanmaka jarumtata manaâ€?.
Dariya Galadima yayai (karon farko danaga yayi dariyağŸ™Å 😂) cikin tausasa harshe yace â€Å“haba dai, ai sai dai Na sammaka tawa, nifa sabon jinine, ta ina mai shekaru 80+ zai fi mai 29 jarumta?â€?.
Daga canma Sarki dariya yayi, cikeda k'aunar jikan nasa, â€Å“uhmyim tunda kace haka idan kazo saimu gwada kwanji aiâ€?.
â€Å“hhh tom kafad'ama inno ta tsumaka sosai, inba hakaba zatayi takabaâ€?.
â€Å“ja'irin gora zan kamakane ai, ALLAH ya tsare hanya, ka gaida iyayen nakaâ€?.
â€Å“zasuji ranka ya dad'e, a gaidamin inno, tayi hak'uri wannan karon ban shigo naci tuwon taba, nazo k'asarne da uzurori dayawa, gashima banyi ko d'ayabaâ€?.
â€Å“zataji insha ALLAHU, babu komai, adage dai da addu'a watarana sai labari, *zakaran da ALLAH ya nufa da cara, ko ana mazuru ana shaho sai yayi jikana kaji*.
Murmushi Galadima yayi dan jin maganar kakan nasa, sukayi sallama cikeda k'aunar juna�.
Ajiye wayar yayi yakoma ya kwanta fuskarsa d'auke da murmushi, yana k'aunar kakansa (mahaifin Momma) saboda shima yana nuna masa k'auna da kulawa, akan la66ansa ya furata â€Å“ALLAH ya k'aramaka tsawon rai my sweet papiâ€?.
Amin Galadima.
⛹ğŸ»Ã¢€Ã¢™€bara nalek'o su munaya.
★★★★*★★�*★★★★
Bansan yanda zan musalta muku irin bak'in cikin danakeba a yau, tundaga kiran Fu'aad zuwa yanzu zuciyata sai suya takemin, banida wata walwala, sai dai ina dannewa kodan kwanciyar hankalin innarmu da 'Yar uwata Munubiya, dama tun randa abunnan ya faru bamu sake fita koda tsakar gidaba dagani har 'yar uwata, abinci sai dai innarmu kosu Aryaan su kar6o mana.
Habaici dai da gugar zana muna shanshi acikin gidanmu, innarmu bata cemusu uffan, nikuma mai maida murtanin damuwa ta hanani iya cewa komai, 'yan biki dai zuwa yau kowa yakama gabansa, yanzu dagamu sai mune agidan.
Sauk'inmu d'aya tun ranar innaro bata sake shigowa gidanba, inaga baba mai kanwa yahanata.
Babu Wanda yay mana maganar komawa makaranta, muma kuma bamuyi yunk'urin zuwanba, kullum dai innarmu NATA k'ok'arin ganin munkwantar da hankalinmu, a koda yaushe cikin mana nasiha take dayimana kwatance da rayuwarta itada mama Rabi'a, takan Nuna mana muhimmancin hak'uri da amfanin yinsa, koda baka ci ribarsa anan gidan duniyaba zakaci ribarsa a lahira inda kowa ke rububin tara ayyukan alkairi.
Alhmdllh muma mun fara rage damuwar kodan ganin farin cikinta, Abu d'ayane kecin zukatanmu shine maganar fidda miji da Abbamu yace nayi acikin sati biyu kacal, gashi kuma babu wani tsayayye a hannu.
Duk mun rame mun zuge nida munubiya, dama gamunan bawani aukin kirkiba, ahaka muka cinye satin da abin yafaru.
Yau ta kasance lahadi, wasu a yaran gidanmu sunata shirin ziyartar gidajen amare, kaf sa'aninmu 'yan matan gidan sunyi shirinsu, Fauziyya, Fiddausi, Safara'u, Haleematu, amma ban da mu, Dan kogaya mana mu shirya ba'ayiba, saima Fauziyya Ce data tashigo da safe gaida innarmu take sanar damu wai mushirya zamuje gidajen amare.
Dagani har Munubiya bamuce da ita komaiba, sai 'yar dariya damukayi.
Koda suka gama shirinsu basu nememu ba, sai Fauziyya Ce tashigo danta mana magana akan mufito.
Turus tayi Dan ganinmu babu wani shiri, hasalima muna falo zaunene, Munubiya ta kwantar da kanta bisa cinyata ina kwance mata kai, innarmu kuma Na zaune gefe suna waya da mama Rabi'a, sai Aiyaan da Aryaan daketa faman buga game.
Hira mukeyi da Munubiya akan wasu write-ups datake dubawa a Instagram da akayi akan maganarmu da galadima, cikin damuwa take karanta writeup d'in, shiyyasa bamuga shigiwar Fauziyya ba saida tayi magana...
â€Å“wai sisters kuna nufin ma ko shiryawa bakuyiba?â€?.
Gaba d'aya muka kalleta, nayi murmushi ina fad'i â€Å“kiyi hak'uri Fauziyya, kutafi kawai, har yanzu fita bata kamacemu ba, dan abubuwa basu gama daidaitaba tukunnaâ€?.
Cikeda damuwa ta gyad'a kai, jiki a sanyaye tace â€Å“shikenan saimun dawoâ€?.
â€Å“ok to Ku gaida mana amareâ€?.
Kanta ta jinjina nanama tana ficewa.
Munubiya tace, â€Å“ALLAH Sarki Fauziyya, itadai tana sonmuâ€?.
Nad'an murmusa ina taje mata Wanda Na tsefe, â€Å“Munu.... nima ina k'aunar Fauziyya wlhy itada mamansu, sune kad'ai suke sonmu agidannan, Na tabbata wannan fitar dama ba'a sota damuba, itace kawai taketa k'ok'arin taga munje d'inâ€?.
â€Å“wlhy hakane sweetheart â€?. ‘cewar Munubiyaâ€?.
Innarmu dai tanata waya, Dan haka batace mana komaiba.....
★★★★★★★★�
Lokaci na gabatowa yay shiri yabar hotel d'in, zuwansa airport babu dad'ewa jirginsu yad'aga, sun tsaya a Dubai Abu-dhabi sukayi hutun 1hour sannan suka nufi India.
Tunkan jirginsu ya sauka Sauban da Samha sukazo d'aukarsa.
Dan haka yana fara taka matakalar jirgin suka hangosa, cikeda jin dad'i suka nufo gareshi.
Duk da fuskarsa babu walwala hakan bai hanasu nuna farincikin ganinsa ba, shima dai yayi farin cikin ganinsu, duk da kwanaki 4 kacal kenan da barinsa k'asar.
Sauban ya kar6i bag d'in hannunsa yana fad'in yaya welcome�.
Kansa ya shafa yana lumshe ido alamun amsawa.
Samha ma tace â€Å“Wellcom back Uncle Samâ€?.
Ahankali ya furta Thanks you dear, ya school?�.
â€Å“Alhmdllh Uncle, ya kabaro Nigeria? â€?.
Murmushi kawai yayi batareda ya amsa mata ba, yasan surutun Samha bamai k'arewa bane, yana amsa wannan wata zata jeho masa.
Sauban ya bud'e masa back seat ya zauna, sannan yarufe shi yakoma mazaunin driver, Samha Na gefensa.
Idonsa ya lumshe ya maida Kansa ya jingina da kujera.
Wani madaidaici Gida suka isa, Wanda baza'a kirashi k'aramiba, sannan ba k'ato baneba, sai dai muce tsaka tsaki.
Samha ce tafita da kanta tabud'e gate d'in, Wanda ana ganin komai dake farfajiyar gidan ta jikinsa daga waje. Sauban ya ida shiga da motar, kusada wasu motoci uku yay parking, Samha data k'araso tabud'ema Galadima yafita.
Kusan atare suka shiga falon gidan, yana gaba suna baya.
Masha ALLAH nafad'a saboda ganin tsaruwar falon, sai dai shiru gidan alamun babu kowa a ciki.
Ya zube bisa rukunin kujerun farko dasuka kasance golden color and white. Isaka yad'an turo daga bakinsa sannan ya kalli Sauban dake shirin zama shima.
â€Å“yanaji gidan shiru? inasu Momma ne?â€?.
â€Å“duk suna hospital, har jakadiya ma, zamu tafi d'akko kanema Aunty Mimi tatafi itama, dama ita kad'aice agidan saboda mu muna school â€?.
â€Å“Ok, ya jikin Abie?â€?.
â€Å“hummm da sauk'i yayaâ€?.
â€Å“mik'ewa yayi yana guntun murmushi, tunda yafara girma yafahimci mahaifinsa Na kwance yakejin idan antanbaya Momma jikin Abie tana cewa da sauk'i, amma shi shekaru kusan 25 Abie Na kwance amma shifa baiga wannan sauk'inba, kawai suna dai fad'ane, sauk'i d'ayane zai iya cewa yagani shine magana da idanu da Abie keyi kawai.
Da wannan tunanin ya haye steps d'in benen, yana tafiya yana sasaauta tied d'in wuyansa. ahaka harya k'arasa d'akinsa.
Komai needs kamar yanda ya barsa, (kullum ne babu fashi sai Samha ta gyara d'akin) Komai a d'akin fari ne, sai golden dasuka kasance d'ai-d'ai. d'akin yayi k'yau sosai, sai tashin k'amshin turarensa daya manne yakeyi, gakuma na air fresheners, saiya had'u yana bada wani ni'im taccen k'amshi. kayansa yashiga cirewa d'ai-d'ai yana sagewa jikin hanger. wanka yashiga sannan ya gabatar da sallan data riskeshi a hanya .........
★★*★★*★★*★★*★★
Da daddare muna zaune munacin tuwo saiga kiran Abba yashigo wayar innarmu, tana d'agawa yace ta turo masa mu.
To kawai tace ya yanke wayar.
Kallonmu tayi ad'an sanyaye, tace â€Å“idan kun gama cin abincin kuje abbanku Na kiraâ€?.
Daga ni har Munubiya sai da gabanmu yafad'i, jiki a sanyaye muka amsa da â€Å“to innamuâ€?.
Kasa cigaba Dacin abincin mukayi, dole muka ajiye kawai mukaje muka wanko hannu..................âœğŸ?
🤔ko wane kira kuma Abba yakema su Munaya😕?.
Barkanmu da dawowa✋ğŸ?, ina fata duk kuna cikin k'oshin lafiya?😄ğŸ¤ÄŸÅ¸».
To gashinan Na k'ara yawan page Masu k'orafi😄⛹ğŸ»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€
*_ya ALLAH ka gafartama iyayenmu_*ğŸ‘ğŸ»ÄŸÅ¸˜
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
👉ğŸ»1âƒ?3âƒ?
.......Mun d'anji sanyi a ranmu, ganin kiran bamu kad'ai baneba, hardasu Safara'u Ashe, waje muka samu muka zauna, sannan muka gaidasu.
Fiddausi kad'ai ake jira, itama babu jimawa sai gata ta shigo da sallama, duk muka amsa, ta gaida su Abba.
Falon yay tsit Na mintuna biyu, sannan Abbanmu yay gyaran murya, kallonmu yake mu duka cikin nazari, ganin muduka mun hallara yace â€Å“mun kiraku nan ne saboda dalilin abinda yafaru kwanan nan, hankalina yakasa kwanciya da zamanku a gabanmu, mun yanke shawara nida 'yan uwana zamu aurar daku duka kawai, kowace saita cigaba da karatunta a d'akinta, muma hakan zai sama mana kwanciyar hankali. dan haka kowacce saita sami mai zuwa wajenta ta sanar masa munason ganin magabatansa inhar da gaske yakeyiâ€?.
gaba d'aya muka amsa da to abba kanmu ak'asa.
Wasunmu murna suke da hakan, amma banda ni da Munubiya, dan bamuda wasu tsayayyu a hannu, bawai samarinne bamu dasuba, a'a wad'anda zamu kawo amatsayin Na aurene matsalarmu.
Maganar Dady ce ta katsemin tunani, danaji yana fad'in su sutashi suje, amma ni Na tsaya.
Haka suka fice suka barni, duk tsoro yakuma cika zuciyata. bayan fitarsu baba k'arami yanuna min gabansu alamar Na matso.
Tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki haka natashi Na isa gabansu, na zauna kaina ak'asa.
Baba k'arami yace â€Å“Munaya!â€?.
Muryata Na rawa Na amsa da â€Å“na'am babaâ€?.
Ya gyara zamansa sosai, â€Å“Munaya na sanki bak'ya k'arya, kifad'a min tsakaninki da ALLAH miye had'inki da Galadima?â€?.
Gabanane yafad'i daaam!, nai k'ok'arin had'iye kukan daya taho mini â€Å“wlhy Baba banida had'in komai dashi, hasalima ban ta6a saninsaba sai awajen hawan sallah, shima ba ganin fuskarsa na ta6a yiba, sai kuma randa mukai karo dashi a filin idi ina neman su kamal, kuma wlhy aranar hak'uri kawai nabashi, koma amsamin baiyiba yatafi, ni banma san shibane alokacinâ€?.
â€Å“amma miyasa aka buga hotonku kuna cikin plaza d'insa?â€?.
â€Å“Dady kuyi hak'uri, tabbas nasan munyi laifi anan, amma Ku yafemin, dan nasan da bamuje plaza d'inba a daren da k'ila hakan bai faruba, amma wlhy abinda yafaru shine...................., cikin nutsuwa ta zayyane musu komai, saidai batace Munubiya ce zata fad'inba, tace itace.
Koda basuga ainahin abin da idonsu ba sai zukatansu sukayi sanyi, baba k'arami yace â€Å“to ALLAH ya k'yauta, wannan akwai wani Abu daban dabamu saniba acikin lamarin, ALLAH ya warware komai cikin sauk'iâ€?.
Duk mukace amin.
Dady yace, â€Å“Munaya! bisa hak'uri damukaita bama yaya kin sami sassauci akan sati 2 daya ce ki fidda miji, yanzu saiki nutsu ki kawo kamar sauran 'yan uwanki, insha ALLAH bayan babbar salla zamu aurar daku gaba d'aya kawai, ALLAH yayi muku albarka kinji, kucigaba da kare mutuncinku, sannan Ku koma zuwa makaranta tunda abin ya lafaâ€?.
Kai na gyad'a sannan nayi godiya.
Na iske innarmu da Munubiya jigum-jigum a falo suna jiran dawowata, nasami waje na zauna jikina a sanyaye.
Innarmu tace, â€Å“miya faru kuma?â€?.
Guntun murmushi nayi INA share kwallar data zubomin, â€Å“babu komai innarmu, sun tanbayeni gaskiyar abinda yafaru ne, sannan since sun janye maganar sati biyu nafiddo miji da sukace nayi. nima za'a had'a danawa zuwa bayan salla kamar su Munubiya, kuma since mukoma makarantaâ€?..
Daga Munubiya har innarmu ajiyar zuciya suka sauke, â€Å“to Alhmdllhi, ALLAH yabaku mazaje na gariâ€?. ‘cewar innarmuâ€?.
A zukatanmu muka amsa mata da amin.
Washe gari.
Mukayi shirin zuwa makaranta, gudun abinda zaije yadawo sai muka saka nik'af dagani har Munubiya kamar yanda innarmu tabamu shawara muyi.
Alhmdllh tunda muka fita bamuci karo da abinda ya Sosa zuciyarmu ba, saboda fuskokinmu arufe suke.
A ajima babu Wanda ya shaidamu sai Bilkeesu, nanma dai munyi mun fito lafiya babu wata damuwa. amma saboda a d'ar-d'ar Muke bamu wani sakeba, ana fitowa lectures muka nufi gida.
Haka muka cigaba da zuwa makaranta kulum fuska arufe, ko cikin anguwa za'a aikemu saimun saka nik'af, dan yanzu fuskokinmu sunrigada sun zama sannanun fuskoki....
★★★★★★★★★★
Yana gama kimtsawa yafice, ko abincin da Samha ta shirya nasa bai sauraraba, kai tsaye yanufi Hospital d'i. da Abie ke jinya.
da jakadiya yafara cin karo tana rik'e da Khaleel a hannu, khaleel yakwace yataho da gudu yana fad'in â€Å“Uncle oyoyoâ€?.
Hannayensa ya bud'e masa yafad'a jikinsa, ya shafa kan yaron yana fad'in â€Å“my boy ykk?â€?.
â€Å“lafiya Uncle Sam... yaushe kadawo?â€?.
Murmushi Galadima yayi, yad'an ja kumatun khaleel â€Å“to maganatu yau na dawoâ€?.
Dariya yaron yayi, zai sake joho wata maganar Galadima ya d'ora yatsansa akan bakin yaron alamun yayi shiru. Shirun kuwa khaleel yayi dan yasan halin Uncle Sam.. saraii.
Jakadiya ta rissina tana gaidashi, amsawa yayi fuskarsa da 'Yar fara'a, ya tambayeta ya jikin Abie.
â€Å“jiki Alhmdllh ranka ya dad'eâ€?.
Kansa kawai ya jinjina mata yay gaba rik'e da hannun Khalel.
Da sallama ya shigo d'akin da Abie ke jinya, d'akine babba kamar Bana asibitiba, daka gani Kasan anyisane saboda manyan mutane irinsu, Momma na zauna akujerar gaban gadon da Abie ke kwance, gadon Kansa bawai ainahin gado bane na asibiti, duk wasu na'urori ne ajikinsa, da alama sune suke taimakama jikin Abie d'in, k'umba Momma ke yanke masa.
Aunty Mimi na zaune bisa kujerun da aka shirya a gefe tamkar falo, System Ce agabanta tana danne-danne.
Sallamar Galadima yasata d'agowa tana murmushi, â€Å“My k'ani oyoyoâ€? tafad'a tana ture system d'in daga cinyarta.
Murmushi yamata shima, cikin maganarnan tasa ta k'asaita maikama da anmasa tilas yace â€Å“my dear aunty barkankiâ€?.
Hannu tasa tad'an bigi damtsen hannunsa, cikin wasa tace barka zakace ba bagyka ba�.
Shafa Inda tad'an bigesan yakeyi yanda 6ata fuska kamar wani k'aramin yaro, â€Å“ALLAH akwai zafi aunty Mimi, wai har yanzu ban girma da buguba awajenki?â€?.
â€Å“tab ai da sauranka, sai randa kayi aure zan dainaâ€?.
Bakinsa ya ta6e yak'arasa inda Momma take yana fad'in, â€Å“aiko k'yadad'e baki barinba kenanâ€?.
Momma dake murmushi saboda drama d'in tasu ta kalli Abie da shima fuskarsa take a washe alamun yayi farinciki da ganin d'an nasa.
Gabansa yaje ya durk'usa, saitin Face d'insa, ya saka hannunsa cikin NASA fuskarsa d'auke da murmushi yace, â€Å“my Abie barka da ranaâ€?.
Da idanu Abie ya amsa masa, dan sune bakin maganar yanzu.
Yakuma masa magana da ido alamar yaka barosu?.
Murmushi Galadima yayi na takaici, sannan yace, â€Å“mai martaba na gaidaka, shima zaizo nextweekâ€?.
Farin cikine Yakuma fad'ad'a a fuskar Abie, dasu sukasan yanayinsa, sukad'ai zasu iya fahimtar farin cikinsa ko damuwarsa, musamman ma Momma.
Momma dake kallonsu tayi murmushi, Galadima ya maida kallonsa gareta, â€Å“Momma na yana sameku?â€?.
â€Å“Alhmdllh Muh'd, yaka barosu?â€?.
Baki yad'an ta6e sannan yace â€Å“lfy lau, ya jikin Abie?â€?.
â€Å“jiki Alhmdllhi, dan randa ka tafi yatsun hannun damarsa sund'an motsaâ€?.
Da Sauri Galadima yace â€Å“da gaske Momma?â€? yay maganarne yana kallon hannun Abie d'in, sannan cikeda farin cikin ya sumbaci hannun yana fad'in Alhmdllh ala kulli halin, ALLAH yabaka lafiya my sweet Abieâ€?.
Lumshe idanu Abie yayi farinciki na k'ara fad'ad'a a face nashi, aunty Mimi da momma da jakadiya suna kallonsu cikeda tausayi suka amsa da amin. khalel yata6a kafad'arsa, juyowa yayi yana kallonsa. yaron yakai hannu yana sharema Galadima hawayen dasuke kwance a kumatunsa. galadima yajawosa ya rungume yana sumbatar kan yaron, fuskarsa d'auke da murmushi.
★★�
Yau mune k'arshen tafiya school, saboda lectures d'in yamma ne damu, Fauziyya kuma batada lafiya bazatajeba.
Kasancewar abubuwa sun kuma lafawa yau sai bamu saka nik'af ba, amma yana rik'e a hannunmu idan mun shiga cshool zamu saka.
Mun fito bakin titi muna jiran taxi ko napep saiga wata bak'ar mota wulik ta faka agabanmu, dagani har Munubiya d'auke kanmu mukayi gefe.
Mai motar ya sauke glass d'in yana kallonmu, sallama yayi mana, Munubiya ta amsa, nikam koma kallo bai isheniba.
Ganin haka saiya bud'e motar yafito, matashin saurayine bak'i k'yak'yk'yawa mai yawan fara'a. Yace, â€Å“haba 'yan mata, babu fad'a miya kawo gabaâ€?.
Cikeda tsiwa nace â€Å“sai aka cemaka mu 'yan matane? to matan aureneâ€?.
Murmushi yayi, sannan ya gyara tsayuwarsa, â€Å“dear hakan ma dakikayi yakuma tabbatar min da Bahaka banebaâ€?.
d'an hararsa nayi na d'auke kaina, danni yanzu maza duk haushi suke bani wlhy.
Dariya yayi, â€Å“oh sweety karkisa na sume mikifa a titinnanâ€?.
Ganin yana neman shiga hancinmu yasani jan hannun Munubiya muka bar wajen, k'yalemu yayi Yakoma mota ya zauna. har muka sami abin hawa yana kallonmu. haka yayta bin mai napep d'in har k'ofar makaranta, daga nan kuma bamusan ya akayiba mudai muka shige.
Kwana biyu da faruwar haka muna wanki a tsakar gida saiga ya Anas yashigo, ya kallemu yana murmushi, twins cikinku waye mai saurayi mai bak'ar mota?�.
Mu duka kallonsa mukayi, gwaggon Haleema da maman safara'u dake aiki a tsakar gidan suma duk suka kallemu.
Da sauri Munubiya tace â€Å“munaya Ce yaa Anasâ€?.
â€Å“kije to yana jiranki a k'ofar gidaâ€?.
harara na dallama Munubiya â€Å“wlhy Munubiya k'arya dai babu k'yauâ€?.
Dariya tayi tacigaba da wankinta, â€Å“kitashi kije kina 6ata masa lokaciâ€?.
Hijjab na d'auka nafita danufin zuwa na sauke masa masifa na dawo.
Gwaggon Haleematu da maman Safara'u suka bini da kallo cikin wani yanayi. oho ni bammasan sunayiba.
Jingine da motarsa na gansa, sanye yake da shadda ruwan zuma, harda hula, sa6anin ranar damuka gansa da k'ananun kaya, kwarjini yamin nakasa masa masifar danayi niyya, namasa sallama sannan nace â€Å“miya kawoka k'ofar gidanmu? waya nuna maka ma?â€?.
Yad'an murmusa, â€Å“miyake kawo saurayi gidansu budurwa?â€?.
â€Å“oho makaâ€? Nafad'a cikin kauda kai gefe.
â€Å“kimga baby sorry, mu ajiye wannan drama d'in, ni bada wasa Nazo nanba, tun randa na ganku keda 'yar uwarki kuka rikatani, nasa a raina duk wadda ALLAH yabani cikinku tamin, bansami kwanciyar hankaliba saida na binciko gidanku, sunana Haidar Mustaphaâ€?.
Shiru nayi ban tanka masaba.
Yay murmushi yana matsowa kusa dani, â€Å“please mana baby, kimin magana?â€?.
Da k'yar ya sami na amsashi sannan nima nafad'a masa nawa sunan. abinda na fuskanta da haidar shi mutumne mai sauk'in kai, sannan ko kad'an banga alamun yaudara ba tattare dashi.
Cikin kwanaki kad'an mungama sabawa da haidar, sabawa maiban mamaki, wadda nikaina har mamakin kaina nakeyi wlhy.
Alokacinne kuma yaa Marwan shima ya nuna yanason Munubiya, wayyo zokuga farin ciki wajen iyayenmu, tamkar su zuba ruwa a k'asa susha dan dad'i.
Wannan Abu fa ya bak'anta ran 'yan gidanmu, sunso ace munyi kwantai, har agama sakama 'ya'yansu rana mu babu mazaje a hannu, amma ALLAH ya fisu ai.
Kud'in Munubiya aka fara kawowa gidanmu, daga nan saina Safara'u. nima saiga iyayen Haidar sunzo, ranar har kukan dad'i mukayi muda innarmu, duk wani masoyinmu zai tayamu murna akan wannan al'amari, dan ba'a ta6a tunanin zamu iya samun mazaje da wuri ba saboda abinda yafaru.
Sauran 'yan uwanmu ma duk ankawo kud'ad'en aurensu, dandanan aka tsaida ranar aure, watanni uku kacal, bayan salla babba da wata biyu.
Zuwa yanzu kam hankalinmu ya kwanta, sai dai matsaloli na gidanmu da basa k'arewa, saikuma abinda yafaru tsakaninmu da Galadima, wani lokacin mukan fuskanci tozarci daga wasu jama'a idan mun fita, tunma muna zama muyi kuka har zukatanmu suka fara dakewa.
Galadima kam bamu sake koda jin d'uriyar saba, hakama Fu'aad, tunima Haidar ya mantar dani wani Fu'aad gaba d'aya.
Ahaka babbar Salla tafara gabatowa. Masu shiri natayi, nikam dai babu mu aciki, dagani har Munubiya munyi alk'awarin babu inda zamuje sai gidan mama Rabi'a........
Munshiga bikin salla lafiya, inda iyayenmu sukayi layya kamar yanda kowacce shekara suka saba, itama innaro anmata, babu inda mukaje wannan karon, su Safara'u dai ansha yawo, ranar suyar nama kuma saiga dukkanin amare sunzo yawon salla, abin tamkar had'in baki, kowaccensu tayi 6ul-6ul da ita, harma damasu tsarabar ciki.
Kowacce jinta take a sama, mijinta yafi na kowa, iyayensu kam anata baza hak'wara da tink'aho ana zuba mana habaici.
Babu Wanda ya tanka musu acikinmu, dan innarmu ta hana.
wajen Ayusher mukejin wai babu Galadima a hawan salla wannan karon, hakan bai dameniba, danni baya gabana, nama manta dawani Galadima can.
Bayan gama bikin salla da kwanaki uku saiga wani tashin hankali.
Iyayen Haidar sunzo wai abasu kayansu sun fasa, ance musu ni 'Yar iskace.
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Yau munga tashin hankali muda innarmu, kuka da hawaye innarmu keyi itada mama Rabi'a, haka aka had'a kayansu aka basu.
Innaro tashigo tafara tata tsiya babuji babu gani, sai zuba cin mutunci takeyi ga innarmu, 'yan gidanmu natajin dad'i, jisuke kamar anmusu gafara da fasa aurennan nawa, aganinsu yaza'ayi 'ya'yansu suna auren masu kud'i nima na auri mai kud'i, ai bazai yuwuba..
Cikin kuka nakira Haidar ina tanbayarsa miyasa zaimin haka, yasan tun farko ba sona yakeba miyasa yazo gidanmu har iyayensa suka shiga.
â€Å“k dalla malama yimin shiru, ni mahaukacine zan auri yarinyar da aka buga hotonta jikin jarida wani na kissing d'inta, ok da an 6oyemin za'a bani sauran wani Ashe ked'in karuwar Galadima ce, to ALLAH ya toni asirinku dagake har iyayen naki, ko a hanya muka had'u karki kuma nuna kin sanni maâ€?.
Baki na bud'e da nufin maida masa murtani ya yanke wayar, nayi saurin kuma kira amma sai najita arufe.
Kuka na fashe dashi, bansan miya faruba sai dai najini ak'asa kawai.
Cikeda tashin hankali Munubiya tayo kaina tana kuka da girgizani.
Dandanan d'akin yacika dasu Dady, babu alamar rai atare dani, hakan yasa aka d'aukeni da gaggawa sai asibiti.........
★★★★�
A 6angaren Galadima kuwa wasu ayyukane suka d'auke hankalinsa, gaba d'aya yayi busy saboda kamfaninsu na k'ok'arin fidda wata waya sabuwar k'ira.
Abinda ya faru kuwa a Nigeria ya watsar dashi gefe, saboda gargad'in da doctor d'insa yamasa akan yarage yawan damuwa, saboda ciwonsa yana k'ok'arin tashi.
Haka yadage yacire komai d'in, amma har yanzu yasaka amasa aikin bincike ta k'ark'ashin k'asa, sannan iyalan manager sun ku6uta suma, yabar Nigeria da sati biyu suka sakosu.
Gaba d'aya ya ajiye duk wani abinda yashafi Nigeria a gefe, ko bikin salla bai hakarta ba, sannan zuwan dayankan yi duk karshen wata ma ya daina, Momma batace dashi komaiba akan k'in zuwan nasa.
Dan lokacin da mai martaba (mahaifin momma) yazo sun tattauna sosai akan abinda yafaru, shine yace Galadima yad'an tsahirta da zuwa Nigeria nawani lokaci, idan komai ya lafa sai acigaba da bincike, dan wad'anda suka aikata sumafa baza suyi barciba, yanzu idonsu abud'e yake akan komai, amma idan anyi burus dasu komai ya lafa sai a d'auki mataki. Wannan yasa bai sake zuwaba, gameda business d'insa nacan kuwa Harun yana tsaye akan komai.
Fitowarsa kenan daga office zaije gida yad'an kimtsa sannan yaje asibi, wayarsa tashi ruri, zarota yayi daga aljihu ya duba, ganin Muftahu a kan layi saiya maida wayar cikin aljihu kawai batare da ya amsaba.
Hannu yabama beejay abokin aikinsa sukayi sallama akan saikuma gobe. yana k'ok'arin shiga motar kiran yakuma shigowa, shiga yayi ya zauna sannan ya d'aga, suka gaisa da Muftahu, ya tambayesa jikin Abie.
Shikuma ya amsa da Alhmdllh.
Muftahu yace, â€Å“ALLAH yasa ban takuraka ba? Inason muyi magana ne damaâ€?.
Kwantar da kansa yayi jikin kujera ya lumshe idanunsa, cikeda k'asaita ya furta â€Å“ina saurarenkaâ€?.
Daga can Muftahu yay murmushi, sannan yace â€Å“dama akan yarannan ne, d'aya daga cikinsu an fasa aurenta, wai Wanda zai auretan yace yafasa sabo...da sa... sa.... yakasa fad'a saboda maganar tamasa nauyi abakiâ€?
Galadina yace â€Å“kafad'a mana, kasanfa bana son kwana-kwana a magana niâ€?.
â€Å“wlhy maganarce babu dad'in ji, ca yayfa wai ita karuwarka ce, yanzu haka yarinyar tana asibitimaâ€?.
Da k'arfi ya cije lips d'insa, zuciyarsa na suya, saikuma ya saki guntun murmushin takaci, yatashi zaune yana bud'e idonsa, â€Å“humm Muftahu waye shi yaron dazata aura d'in?â€?.
â€Å“wlhy ban saniba nimaâ€?.
â€Å“o right karka damu, zanyi tunani akan lamarin, ni bamma duba bayanai daka turomin akan yarinyarba fa, abubuwa sunmun yawane wlhy. amma masu bibiyar tata basuga wani abunda ya shafi waccan maganarba?â€?.
â€Å“Gaskiya basuga wani abuba sa6anin tunaninmu, ammafa bama yarinya d'aya bace ba, twins ne, kaduba bayanan kaganiâ€?.
â€Å“ok sai munyi magana kenanâ€?.
Bayan sunyi sallama yay shiru yana tunani a ransa, da gani kasan ransa a6ace yake, ya furzar da huci daga bakinsa sannan ya tada motar yatafi. idonsa yayi jajir saboda bak'in ciki, yanzun har takai wani yafasa auren wata akansa? waye yamasa wannan abin? miya masa ne da zafi haka ya tozartashi? wlhy yayi alk'awarin duk Wanda keda hannu akan wannan tozarcin da akai masa bazai d'aga masa k'afaba, dolene yayi dana sanin saninsa.
Da wannan tunanin ya k'arasa gida.
Babu kowa a gidan sai jakadiya, su Sauban suna makaranta, Aunty Mimi da Momma kuma suna asibiti, jakadiya ta rissina tana gaidashi, hannu kawai ya iya d'aga mata ya haye sama.
Binsa tayi da kallon tausayi, hakan da yayi mata ya nuna ransa a 6ace yake, danshi mutum ne mai girmama nagaba dashi, dukda tana a k'ark'ashinsu bai ta6a wulak'antata ba, wannan tarbiyar mahaifiyarsu ce kuma.
Koda yashiga rigarsa kawai yacire ya zauna a bakin gado, medical glasses d'insa yasaka sannan yajawo System yabud'e, Emailil na Muftahu ya shiga.
Dukkan bayanai da tarihin su Munaya ne awajen.
Gaba d'aya ya nutsu ga abinda yake karantawar, shi mamakima abin yabashi, sukuma wane irin gida wad'annan yaran suka fito haka? Wani abun yakan bashi dariya (sai dai yakanyi dariyar ne a zuciyarsa), wani kuma haushi, tsaf yagama karanta tarihin yaran masu kama da juna.
Ya mik'e yana zagaye d'akin da tunanin miye mafita, har yanzu zuciyarsa bata bar karanta masa da hannun wad'an yaran aka masa wannan abunba, sai dai shi kansa yana tambayar kanasa mizaisa su aikata? miye kuma ribarsu bayan suma hardasu aka tozarta?. yanzu kuma zuciyarsa na masa wani tunani daban bayan yaji tarihinsu.
Zuciyarsa na cigaba da tunzurashi akan yayi amfani da damar k'arshe wajen bincikensa, tunda yabi dukkanin sauran bai samu wani bakin zareba.
To amma kuma wannan ai ba tarbiyyar Malam bahaushe baceba, daga baya kuma idan komai yafitofa? wane kallo kuma za'a masa?, shinma zata iya fahimtarsa kuwa? dan irin wannan abun yakan farune a labaran films ko Novels, to amma wannan ce damarsa ta k'arshe ai kawai, dolene ya jefi tsuntsu biyu da dutsi d'aya kenan?.............âœğŸ?
Tirk'ashi, Nikam dai nakasa fahimtar wannan cirkud'ad'd'en tunanin na Galadima�, fan's koku kun fahimta Ku fassara mana🤔?.
*_Ya ALLAH ka gafartama iyayenmuğŸ˜ÄŸÅ¸‘ğŸ»_*
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
👉ğŸ»1âƒ?4âƒ?
.......An kai ruwa rana kafin asamu na farfad'o, ina farfad'owa kuma sukamin allurar barci domin nasamu Hutu.
Sai a lokacin hankalin iyayena yad'an kwanta.
Baba k'arami da yagama birkicewa akan shifa bazai yardaba, saiya maka iyayen Haidar a kotu. wannan wane irin tozarcine haka? sunzo sun kar6i kayansu, anbasu batareda anduba wulak'ancin dasukayiba, shine kuma dan rashin mutunci shi Haidar d'in zai jamusu 'yarsu ta salwanta, to shifa bazai aminceba.
Hak'uri Dady da Abbanmu suketa bashi suna tausarsa akan yayi hak'uri, su d'auki hakan matsayin k'addara kawai, indai mijine ALLAH zai bani wani ai. k'ilama shid'in ba alkairi baneba agareni dama.
Innarmu dai tun tana kukan zuci harya fara fitowa fili, mama Rabi'a nata tausarta.
'Yan gidanmu babu Wanda ya biyomu sai maman fauziyya, har innaro k'in zuwa tayi.
Ban farfad'oba sai gabanin magriba, lokacin su Abba na shirin tafiya masallaci, na bud'e idona ahankali, da innarmu na fara tozali, sai mama Rabi'a da maman Fauziyya a gefenta, Munubiya na gefen gadon danake kwance rik'e da hannuna ta kifa kanta ajikina alamar barci ya saceta ahaka.
Nan komai yashiga dawomin sabo a zuciya, fashewa nai da kuka mai tsuma rai, cikin dasashiyar murya nace â€Å“shikenan innarmu, shima na rasashi, Haidar yatafi, yakuma ce har abada bazai ta6a dawowa gareniba, mi muka musu suka za6i mana wannan sharrin dabazai ta6a barin rayuwarmu ba? yarigada yazame mana tabo a tarihinmu, ya ALLAH ka gaggauta saka mana akan duk mai hannu akan buga jaridarnan, wlhy Haidar ban aikataba, sharri sukaimin, dan ALLAH karka barni, ina sonka wlhy, sosai nake sonka, dan ALLAH mama Rabi'a kuce masa sharrine, ban aikataba, Munubiya dan ALLAH karkubar haidar yatafi, ina sonsa wlhy.......â€?.
Kuka Munubiya takeyi sosai, dan tunda na fara magana ta farka, dama barcin nata bawani nisa yayiba. Innarmu kam tashi tayi tafita tana share hawaye, maman Fauziyya na rik'e dani tana lallashi. Mama Rabi'a ma kuka takeyi saboda ganin 'Yar uwarta Na kuka.
A haka su Abba suka shigo suka samemu inata wannan sambatu, da rok'on akiramin Haidar, dan wani masifar sonsa nakeji a lokacin, fiyema da son Dana masa muna tare.
Duk saida nabama su Abba tausayi, Dady ya zauna akujera tareda rik'e hannuna.
â€Å“Munaya ya isa haka kinji, kiyi hak'uri, ki yarda da k'addara, dama can ALLAH ya rubuta shid'in ba mijinki baneba, insha ALLAHU mijinki nanan zuwa soon. Ubangiji nason bayinsa masu hak'uri, wata rana komai zai zama labari tamkar ba'ayiba kinjiâ€?.
Ahankali na fara sassauta kukan danakeyi, ina sauraren lallashin Dady, sai ajiyar zuciya danakanyi lokaci-lokaci.
Bayan doctor yazo ya dubani yace abani abinci nasha magani, sunaso nakuma samun isashen barci danna samu na kuma hutawa. Saboda jinina yahau gaskiya.
Hankalin su baba k'arami yakuma tashi, ace 'Yar k'aramar yarinya dani amma da hawan jini, (ALLAH yay gaggawar sakamin akan duk mai hannu akan wannan tushen matsalar).
Da k'yar aka samu nasha shayi, nasha magani barci yakuma kwasheni.
Sai kusan 10pm su Abba suka tafi gida, akabar Mama Rabi'a da Munubiya zasu kwana dani.
***°â€¢Ã¢€¢Ã‚?***°â€¢Ã¢€¢Ã¢€¢Ã‚?***°â€¢Ã¢€¢Ã‚?***
Yana shirin fita asibitin sai ga Momma tadawo gida, tun yana sakkowa daga benen ya hangota zaune afalo itada jakadiya, da alama magana sukeyi.
Takun takalmansa da k'amshin turarensa yasasu juyowa suka kalleshi gaba d'aya, ya k'araso cikin falon cikeda takunsa na asalin jinin sarauta cikakke. Kujerar gefen Momma ya zauna yana fad'in â€Å“Momma yaushe kika shigone?â€?.
Idonta akan d'an nata tana nazartar yanayinsa tace, â€Å“ban dad'e da shigowa ba, nama zata barci kakeyi ai? danJakadiya tacemin tuni kana gidaâ€?.
Guntun tsaki yayi yana lumshe ido, tare da kuma jingina kansa jikin kujerar, ahaka yace, â€Å“wlhy kuwa Momma, nad'an tsaya wani aikine acikiâ€?.
Idanu ta tsira masa domin hango damuwa k'arara a fuskarsa. â€Å“Muh'd mike faruwane? mike damunka?â€?.
Idanunsa da har yanzu suke da sauran ja ya bud'e, yasaki murmushin gefen baki, â€Å“babu komai Momma, mikika ganine?â€?.
â€Å“bakaso dai nasani kawai Muh'dâ€?.
Yad'an narke face alamar shagwa6a, â€Å“please Momma ki yarda dani manaâ€?.
Girgiza kai kawai tayi tana murmushi, â€Å“to na yarda dakai. yanzu sai ina?â€?.
â€Å“dama zanje hospital ne, dan inaga zanje Goa gobe idan ALLAH ya kaimu, maybe kuma na kwanamaâ€?.
â€Å“ok. ALLAH ya kaimu to, dama muna magane da jakadiya akan akawo wasu sabbin bayin, kaga aikin yanama su Samha yawa a gidannan Muh'd, gakuma makaranta, idan suka fita kaima ka fita sai gidan yay shiru, gashi mukuma muna Asibitiâ€?.
6ata fuska yayi yana gyara zamansa, â€Å“Amma kuma Momma bakwa tunanin a kuma samun matsalar datafi ta baya? kiduba kiga dad'ewar da mukayi da wad'ancan, amma hakan bai hanasu munafuntar mubaâ€?.
â€Å“Humm Muh'd kenan, wancan karonma bawai dabararmu bace ta tsaremu, muyi hak'uri akawo koda guda 20ne, maza 10 mata 10â€?.
â€Å“kai Momma, amma har 20 ma?, ina laifin 5 kawai, idan sukayi yawa gidanan hayaniya zaiyi yawaneâ€?.
â€Å“wane irin 5 kuma Muh'd?, yanzu badan laluraba data kawomu nan ta ajiyeba konan da can ka isa matsawa batareda bayi ko dogaraiba, sha'anin gidan sarauta sai hak'uri, wlhy tunda aka kwashe bayinan gidan saiyayi wani iri, tamkar bana masu sarauta ba, yanzu haka kullum k'orafin Mimi kenan adawo da bayin gidananâ€?.
â€Å“momma kenan saboda Aunty Mimi za'a maidosu?â€?.
â€Å“kusan haka to, saboda ita saboda buk'atunmu muma koâ€?.
â€Å“shikenan, sai a dawo damasu min hidima idan naje ko?â€?.
â€Å“a'a baza'ayi hakaba, idan an kwasosu kaikuma idan kaje kuma fa? wad'ancan munriga da mun yardaba da amarsu, idan mun maidosu nan kafin mu samu masu amanarsu zamusha wahala,, amma idan nan aka kawo mana wasun zamu saka ido sosai akan su yanzu ai?â€?.
Kai kawai ya gyad'a mata batare da yace uffanba. saikuma zuwa can yace â€Å“inaga nima next week zanje Nigeria â€?.
â€Å“Nigeria kuma Muh'd? mizakayi?â€?.
â€Å“murmushin gefen baki yayi yana kallonta, kwantar da hankalinki Momma, 3days kawai zanyi na dawo, wani d'an aikine zai kaini, ko masarauta bazasu San najeba ma Dan ba a can zan saukabaâ€?.
â€Å“Amma Muh'd baka kudin abinda zaije ya dawo? kuma kana ganin zaka iya Shiga Nigeria kafito batareda kowa yasani a masarautarku ba?â€?.
â€Å“kimin addu'a Momma, insha ALLAHU lafiya lau d'anki zanje ya dawo kinji, kuma zanyi taka tsantsan d'in yanda bazasu San najeba insha ALLAHUâ€?.
Murmushi Momma tayi, tace â€Å“to shikenan, ALLAH yabada nasara akan abinda za'aje, yakuma tsare mana kai. amma nikam Muh'd yamagar yarinyar nan da aka muku 6atancinnan tare?â€?.
â€Å“ban saniba Momma, dan ni ba saninta nayiba faâ€?.
â€Å“amma dai gaskiya ba a k'yautaba, yarinyarnan dukda anazargin da had'in kanta yakamata anemi iyayenta ai, amma ba ayi burus da lamarinta ba, kuma wannan aikin Kaine yakamata kayishi tunkan kabaro k'asar alokacinâ€?.
â€Å“Nima nayi tunanin hakan daga baya Momma, amma wlhy a time d'in hankalinane yatashi sosai, sai dai karki damu, a wannan karon zansa amin bincike akantaâ€?.
â€Å“hakan yafi kam gaskiya, bara na kimtsa saimu wuce k'ila kafin mu tafi su Sauban sun dawo. antafi d'akko Khaleel kuwa?â€?.
â€Å“ai da sauran time Momma, kuma nifa yanzu nace aringa kawoshi a school bos, dan kinga mu ba kullum Muke gidaba, ga khumar har yanzu bai dawoba, inaga jikin mahaifiyar tasa yayi tsanani shimaâ€?.
â€Å“kama tunamin wlhy Muh'd, yakamata koda kaida Sauban ne kuje Ku dubata, wannan shine adalci da zakama Wanda yake k'ark'ashinka idan wani Abu yasamu rayuwarsaâ€?.
â€Å“Hakane wlhy Momma, zamuje insha ALLAH, miye ma sunan k'auyen nasune?â€?.
â€Å“nikam nad'an manta, amma bari zan tanbayi jakadiya kota rik'eâ€?.
â€Å“ok tom shikenanâ€?.
Tunda Momma ta shige saiya maida Kansa ya kwantar jikin kujerar, yacigaba da tunaninsa datum d'azun yake cin zuciyarsa da ruhinsa. baya buk'atar shawara da kowa akan wannan maganar gsky. to amma koya fad'ama Harun?. kai a'a, inma fad'arne Muftahu yakamata ya sani, tunda shine ya d'ora akan aikin, kuma shi kad'ai yasan komai akan yaran, to amma ba komai ne Na sirrinsa Muftahu ya saniba ai. (zuciyarsa tace, to ai wannan baikai girman sauran sirrikanka ba, kuma abune daza'ayi Na k'ank'anin lokaci yawuce, tunda ka yanke shekara d'aya ne ko biyu), iska ya furzo daga bakinsa yad'an dafe kansa dayakejin yana Neman fara masa ciwo.....
★★★★�
Washe gari natashi da d'an sauk'i, sai dai har yanzu hawayen sun kasa barin fuskata nida 'yar uwata Munubiya. mama rabi'a ce keta lallashinmu da mana nasiha, ahaka su Ayusher sukazo kawo mana break fast itada Feena, ya Marwan ya kawosu.
Daga gidanmu kam ko ruwan zafi babu Wanda yakawo har kusan 10, sai kuma ga Fauziyya itada Jameela k'anwarta, sukace inji mamansu, tace ayi hak'uri Mubarak ne shima babu lafiya.
Mukace mun gode ya jikin Mubarak d'in?.
Fauziyya tace, â€Å“da sauk'i, tare suke da maman tasu, sunacan zasuga likitaâ€?.
Anan su Fauziyya suka zauna ana hira dayake weekend ne babu school, kusan hirar duk akan abinda haidar yayine shida iyayensa, dagani har munubiya bamu saka musu baki, ni hirarma k'onamin zuciya takeyi.
Yaa marwan dake zaune a gefe yanata latsa waya tamkar baya jinmu yamik'e, kallon Munubiya yayi yace â€Å“zo manaâ€?.
Saida yafita sannan ta mik'e tabi bayansa, su Ayusher suka sanya dariya suna fad'in soyayya ruwan Zuma.
Nidai bance komaiba, saibin 'Yar uwata da kallon tausayin zama da wannan mai shegen miskilancin nayi. zama da irinsu yaa marwan sai mai hak'uri wlhy.
A ranar da daddare aka sallameni muka koma gida, sai dai 'yan gidanmu maman Fauziyya ce kawai tazo, amma ko innaro batazoba. sai bayan an sallamemu su Dady sukaji babu Wanda tazo dubani. kuma Maman fauziyya Ce kawai me kai mana abinci, dukda ba ranar aikinta bane haka take dafa mana su fauziyya sukai.
Aiko ranar sunga tsantsar bala'i, dan su Abba birkice musu sukayi suduka ukun, har Dady da ake gani mai hak'uri. ita kanta innaro saida tasha jinin jikinta ga 'ya'yan nata.
Nacigaba da samun kulawa wajen innarmu da 'Yar uwata Munubiya, duk hanyar dazasubi Dan samamin farin ciki ita sukebi, burinsu kawai suga Na manta komai, hakama iyayena maza, sai yazama kowa tausayina yakeyi acikinsu, yayunmu mazama babu laifi, suna nunamin kulawa dai-dai gwargwado.
Ahaka nafara rage wasu damuwoyin.
Satina d'aya kenan da dawowa daga asibiti, duk na k'ara ramewa Na fige, hakama Munubiya, saika d'auka tare muka kwanta ciwon.
Ahaka muka tak'ark'ara muka koma makaranta, ayanzu kam maganar gsky bana fahimtar karatu, saboda damuwace tsatstsage da zuciyata, nasanma nida aure kuma har abada, kowa yafito haka za'a sokeshi ya janye, ita dai 'Yar uwata Munubiya ALLAH ya taimaketa na gidane yace yana sonta, itama nasan da yanzu an soki lamarin, musamman daba banbancemu jama'a sukeyiba. Nagodema ALLAH da abinnan bai shafi rayuwar Munubiya taba sarkin hak'uri, tabbas danafi haka shiga tashin hankali, bansan yanda zan musalta muku k'aunar danakema 'Yar uwataba, ina sonta fiyeda zaton mai tunani, wlhy zan iya fansar da raina awajen kare nata, kamar yanda nasan itama zata iya yin hakan agareni.
Yau ta kasance juma'a, dagani har Munubiya bamuje makarantaba, saboda tatashi da ciwonkai, tun muna primary idan d'aya bai da lafiya d'ayan bazaije school ba, komin zare idon ko dukanmu da za'ai kuwa, wannan abinne yazame mana jiki har girmanmu gashinan.
Bayan nagama gyaran 6angarenmu innarmu tace Na shirya naje nakaima wata k'awarta sak'o.
Badan nasoba Na kar6i sak'onnan natafi, saboda banajin dad'in tafiya nikad'ai arayuwata, tunda nataso nayi wayo ko ina zamuje sai nida Munubiya ne, mawuyacine kiga d'ayanmu tafita batare da d'ayaba.
Tafiya nake tamkar zan fasa kuka, gani nake kowa nikad'ai yake kallo, sanye nake da jallabiya bak'a datasha adon honey color d'in duwatsu, Na nad'a Veil ruwan zuma shima, haka ma takalmana masu d'an tudu ruwan Zuma, sai lady's bag d'ina, ahankali nake tafiyar cikeda takuruwa, ahaka nazo bakin titi domin samin abin hawa.
Banfi tsayuwar 15minutes ba saiga taxi, ganin babu kowa a taxi d'ina kamar karna shiga, amma sainayi addu'a kawai nashiga, gudun karnazo nayi sakin Na hannu kamun na guje.
Munyi nisa da tafiya naga mai taxi d'inan yak'i d'aukar kowa, gashi anata tsaidashi, kumani bance masa drop na d'aukaba gaba d'aya.
Cikin dakiyar zuciya nace â€Å“bawan ALLAH miyasa bazaka tsaya ka d'auki mutaneba? bayan kuma gashinan anata tsaidakaâ€?.
Ta madubi ya kalleni yana murmushi, sorry hajiya, kekad'ai aka bani izinin d'auka ai�.
Da mamaki nace â€Å“kamar ya?â€?.
Dariya yad'anyi sannan yace â€Å“karki damu da wannan, ina muka dosa yanzun dai?â€?.
Yawu mai kauri na had'iye da k'yar sannan na fad'a masa inda zamuje.
Har k'ofar gidan ya ajiyeni, nabashi kud'i kuma yak'i kar6a, haryaja motar yabar wajen ina binsa da kallon mamaki, na sauke ajiyar zuciya nidai ina hamdala ga ALLAH dayasa na sauka lafiya.
A fili nace â€Å“k'ilama aljanineâ€?. saikuma nace â€Å“wayyo ALLAH ya tsareni da hawa motar aljanuâ€?.
Da wannan tunanin nashiga gidan, tun a soro nake kwad'a sallama.
Daga ciki najiyo ana amsamin, tace shigo mana baiwar ALLAH.
Shiga nayi inda ake amsamin sallamar, dattijuwar macece da zasuyi sa'anni da innarmu, ba yaune karon farko dana fara zuwa gidanba, tun muna k'anana muke zuwa yawon da innarmu ko idan munzo suna ko biki, (inna lami k'awar innarmu ce, a anguwarmu take, tun zuwansu innarmu gidansu innaro suka k'ulla k'awance da inna lami d'iyar makwaftan su innaro. harkuma yanzu akwai zuminci mai k'arfi a tsakaninsu).
â€Å“a'a a'a lalale marhabin da d'iyata, Munubiya ce ko munaya?â€?.
Fuskata d'auke da murmuahi nace â€Å“inna munaya ce, munu.... tana gida bata jin dad'iâ€?.
â€Å“Ayya ALLAH ya sauwak'a yabata lafiya, ya Ai'shar dasu Aryaan?â€?.
â€Å“lafiya lau take, tacema na gaisheku. ga wannan tace na kawo mikiâ€?.
â€Å“to madallah, ina amsawa. ngd sosai kuwaâ€?.
Murmushi nayi kawai bance komaiba, sai zuwa can nace â€Å“Ameera batanan? naji gidan shiruâ€?.
â€Å“wlhy Ameera tafita d'azunnan gidan Mariya, amma nasan duk inda take tana hanyar gida yanzuâ€?.
â€Å“ALLAH sarki, to a gaida min ita idan tadawo ni bara na tafiâ€?.
â€Å“haba dai Munaya, daga zuwa kice zaki tafi?, Dan ALLAH ki zauna yanzu zakiga Ameeran tadawo aii. bara kiga nasa miki ko kallone kisamu abokin hiraâ€?.
Badan nasoba na zauna har ameera ta dawo, sosai tayi murna da ganina, dayake munsan juna, school d'aya mukayi a secondary, kuma ajinmu d'aya, nan muka zauna mukasha hirarmu, har ta soya mana wainar fulawa mukaci muka k'oshi abinmu.
Ban bar gidanba sai bayan an sakko masallaci, har titi ta rakoni, da k'yar muka samu taxi kasancewar anguwar tasu tad'an shiga lungu abin hawan yana wahala.
Saida muka hau titi na fad'ama driver inda zamuje.
'Yar dariya yayi yana fad'in â€Å“aina sani hajiyaâ€?.
Cikin fad'uwar gaba nad'ago na kalleshi, Dan naji kamar muryar driver n d'azun, ido na zazzaro waje da dafe k'irji dan ganin shine kuwa.
Na ware baki zan maka ihu ya jehomin farin Handkerchief a fuska. luuuu nayi da baya na kwanta a kujerar, tun ina ganinsa dishi-dishi har na daina gaba d'aya................âœğŸ?
Tofa jama'a ana wata ga wata wanene yasa a kwamushe Munaya🙆ğŸ»ÄŸÅ¸˜?.
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmuğŸ‘ğŸ»ÄŸÅ¸˜_*
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
👉ğŸ»1âƒ?5âƒ?
.......Tunda yafara tafiya bai tsaya ko inaba sai a wata sabuwar anguwa, shiru anguwar take babu yawan hayaniya, dan gidajenma tsilli-tsilli suke tamkar rugar Fulani, wani gida dakecan nesa da sauran gidajen yanufa, gidane babba mai k'aton bak'in gate, yay horn sau biyu akazo aka bud'e masa. a babbar harabar gidan yay parking, yana cikin motar bai fitoba har kusan 10 minutes bayan yagama waya yace ya iso.
Idanu na zaro waje saboda ganin Muftahu yafito daga wata k'ofa yanufo motar, gaba d'aya mamaki yahanani kwakwkwaran motsi harya k'araso.
Mai taxi yafito ya risina ya gaidashi, sannan yace nagama aikina Oga.
Murmushi Muftahu yayi, sannan ya lek'a Munaya dake barci kashir6an ta glass, janye kansa yayi sannan ya zaro wayarsa daga aljihu yay kiran wani.
â€Å“Umh yalla6ai akwai 'Yar matsala fa, dan barci takeyi sosai, kona d'akkotaâ€?.
Da sauri yace â€Å“No ina zuwa, amma wannan driver dayay aikin yabar wajen, dan bana buk'atar ya ganniâ€?.
Murmuahi Muftahu yayi, tare da fad'in â€Å“angama ranka ya dad'eâ€?.
Muftahu ya sallami drivern daya kawo Munaya, yace zai kirashi ya maidata zuwa anjima, yaje yabar motar anan.
â€Å“babu damuwa Oga, saina jikaâ€?.
Bayan tafiyar driver Galadima yafito, dama duk yana kallon abinda ke faruwa ta window.
Taku yake cikin tsantsar nuna jinin mulki dake yawo ajikinsa, ga wata izza ta zamowarsa cikakken namiji mai isashshiyar lafiya. fusakarnan babu walwala kamar kullum, ahaka ya k'araso wajen motar, Muftahu ya bud'e masa murfin inda Munaya ke kwance tana kwasar barcinta.
Kallonta yayi na tsayin mintuna uku, sannan ya janye idonsa ya rankwafo da kansa cikin motar, saida yad'an cije lips d'insa sannan yasaka hannayensa biyu ya tallafota ahankali ya fito da ita, tamkar 'Yar baby haka ya d'akkota acikin hannayensa, sai wani kuma d'aure fuska yakeyi yana kauda kai, kaikace anmasa dolene ya d'auketa.
Hannu Muftahu yasaka yatoshe bakinsa saboda dariyar dake Neman kwace masa.
Wai yau Galadima gudane d'auke da mace a hannu, mutumin da ko kallon mata bai cika yiba, inkaga yana walwala ko dariya wa mace to Momma ce ko aunty Mimi.
Jakarta ya d'auka shima yabi bayansa.
Ya iske harya shinfid'eta a doguwar kujerar dake falon, yana gyara hannun rigarsa daya nannad'e yana jan k'aramin tsaki, ganin Muftahu na murmushi saiya kuma had'e fuska, Muftahu ya ajiye bag d'in yana had'iye dariyar da k'yar saboda gudun yin laifi.
Hannu yamik'ama Muftahu.
Muftahu yabashi handkerchief d'in daya zaro a aljihu, rankwafowa yayi kanta ya d'ora Handkerchief d'in bisa hancinta, tsayin minti 2 ya janye.
Tari tafarayi, saikuma ta fara k'ok'arin bud'e idanunta tana lumshewa, Muftahu ya mik'o masa gorar ruwa mai d'an sanyi.
Cikin hannunsa ya tsiyaya kad'an ya shafa mata a fuska, ahankali ta fara bud'e idanun ta, shikuma yaja da baya yakoma ya zauna bisa kujerar mai zaman mutum d'aya.
d'ora k'afa yayi d'aya kan d'aya ya jingina kansa jikin kujerar ya lumshe idanu, saika rantse idonsa arufe suke, amma ya zubasune akan Munaya dake ta mutsu-mutsun tashi zaune.
Da k'yar ta iya tashi ta samu ta jingina da kujerar tana k'arema falon kallo, yayinda hawaye ke zirara a kumatunta.
Ruwa Muftahu ya mik'a mata, babu musu ta kar6a dan wata kishirwa takeji, tunda tafara shan ruwan bata ajiyeba saida ta shanye tas, nan wata zufa tafara karyo mata kuma.
Mik'ewa Muftahu yayi yak'ara gudun AC n.
Ahankali zufar tafara tsanewa, saikuma tad'anji k'arfin jikinta, Muryarta na rawa alamun kuka tace, â€Å“Please Ku suwaye? miyasa kuka kawoni nan? dan ALLAH kuyi hak'uri karku cutar dani, karku lalatamin rayuwa dan girman ALLAH, Ku tausayama mahaifiyata, damuwar damuke ciki kad'ai ta ishemu, wlhy daku keta mutuncina gwamma Ku kasheni yafimin sauk'iâ€?.
Daga Muftahu har uban gayyar kallonta kawai sukeyi, ita ko kad'anma bata gane Galadima ba, saboda yayi sama da fuskarsa.
Muftahu ne yace â€Å“ki kwantar da hankalinki, kuma ba abinda yasa muka d'akkokiba kenanâ€?.
â€Å“to miyasa kuka d'akkoni? bawan ALLAH, mina muku?â€?.
Muftahu ya juya ya kalli Galadima, amma saiyaga ko motsawa baiyiba, bashima da niyyar tanka musu.
Itama Munaya saita maida kallon nata ga Galadima, a kuma lokacinne yad'ago kansa zai gyara zama.
Wata razananniyar k'ara Munaya tasaki saboda tsorata, da Sauri Galadima ya toshe kunnensa, shima tsawar ya Daka mata wadda tasakata nutsuwar dole.
â€Å“k!!! Dalla karki ciremana dodon kunni!!!!â€?.
Dole Munaya tayi shiru jikinta na 6ari da k'yarma.
Yaja wani wawan tsaki, tare da janye hannayensa daga kunnensa yana harara Munaya. â€Å“k wace irin shashashace ne?â€?.
Sukda halin da take ciki saida ta watsa masa harara, amma bata iya cewa komaiba.
Hannu yakai tamkar zai maketa saikuma ya FASA, komi yatuna oho.
Komawa yayi inda yataso ya zauna, ya maida k'afafunsa yay crossing d'insu.
Shi dai Muftahu yana kallonsu yakasa cewa komai, bakajin motsin komai saina shashshekar kukan Munaya Dana k'arar AC.
Cikin kuka tace â€Å“minamaka kasa aka kawoni nanan? ko sokake kakuma jamin wani sabon 6atancin bayan Wanda yafaru abaya? wane Abu na tare maka waishin aduniyarnan dan ALLAH bawan ALLAH?â€?. takuma rushewa da kuka mai tsuma rai.
Bakinsa ya ta6e a zuciyarsa yake fad'in daganin yarinyarnan akwai tsiwa dai, saikuma uban tsoro kamar farar kura. banza yamata, azahiri idonsa a lumshe suke, amma kuma abad'ini yana kallon Munaya ne, kukanta Neman saka masa ciwon kai yakeyi, dan haka yay maganar cikeda izza da mulki.
â€Å“kinutsu muyi abinda ya kawomu, inba hakaba zaki kwana anan gidan neâ€?.
Da Sauri Munaya ta share hawayenta, â€Å“indai kukane na daina wlhy, kayi hak'uri ka sanarmin, dan ALLAH ka maidani gida kafin hankalin innarmu ya tashiâ€?. tak'are maganar da share hawaye.
Dariya taso bashi amma saiya gimtse, saikace ba itace tagama tsiwa ba yanzun.
Muftahu dai kasa hak'uri yayi saida yad'an dara, Galadima ya balla masa harara, hakanne yasashi yin shiru ya had'iye dariyar.
â€Å“kin shirya tafiya kenan?â€?. ‘galadima yafad'a tamkar an masa dole sai yayi maganarâ€?.
Munaya tace, â€Å“wlhy na shirya ranka ya dad'eâ€?.
Yace â€Å“good girlâ€? yana ta6e baki.
â€Å“ki fad'amin waye yasaki aikin nan?â€?.
Cikeda rashin fahimta Munaya tace, â€Å“wane aikin?â€?.
Shiru Galadima yayi bai tanka ba, sai Muftahu ne yaymata bayani dalla-dalla akan abinda yafaru a plaza kwanakin baya�.
Cikeda k'unar zuciya Munaya tace â€Å“ni babu Wanda yasakani, saima tozarci da hakan ya jawo mana muda mahaifiyarmu, bansan komaiba, amma tunda al amarinan yafaru muka kuma tsintar kanmu a k'unci, kullum da irin abin kuka dazamu gani agidanmu, yanzu haka akan waccan abin maganar aurena sau biyu tana lalacewa, yanzu haka satina guda kenan da baro asibiti saboda tashin hankalin dana shiga a dalilin fasa aurena da cin zarafi dana fuskanta daga Wanda yafasa aurena nawa, wlhy Ku yarda dani bansan komaibaâ€?.
Muftahu ya juya yana kallon Galadima da idonsa ke a rufe, amma yana sauraren Munayar.
Kusan mintuna 3 sannan ya bud'e idonsa, akan Munaya ya zubasu, bazata iya jurar kallon kwayar idonsa ba dan haka tayi azamar janye nata, shima janye nasa yayi ya gyara zamansa. â€Å“kince babu hannunki? amma miya kaiki plaza a wannan time d'in daya kamata duk yarinyar kwarai tana gidansu?â€?.
â€Å“Muna bikine, bayan munkai amare mun dawo sai fu'aad yamatsa akan saimun shiga, ba dan nasoba nayarda, kuma bani kad'ai baceba, harda 'yan uwana su ukuâ€?.
â€Å“waye shi Fu'aad d'in?â€?.
â€Å“Saurayinane, awajen bikin muka had'u dashiâ€?.
da sauri Galadima yace â€Å“miye kamaninsa? kuma ya kukayi dashi bayan abin ya faru?â€?.
A nutse Munaya tabasu labarin komai, sannan ta zano musu kamannin Fu'aad dalla-dalla, danma bawani kallon tsaf tamasa ba a cikin kwana biyun.
Muftahu yace â€Å“kozamu iya samun Horton shi Fu'aad d'in?â€?.
â€Å“banida hotonsa, dan bai yarda munyi ko photo d'aya ba awajen bikin, amma zamu iya samu a video d'in da akayi maybe awajen dinner? â€?.
â€Å“galadima yace â€Å“a ina zamu CD d'in yanzu?â€?.
â€Å“gaskiya wannan shine mai wahala, dan bansan taka maimai cikin angunan waye yasaka ayibaâ€?.
Galadima ya cije lips d'insa da k'arfi, sai kace zai hudasune.
Kusan mintuna 3 kowa baice komaiba, sai can munaya tace â€Å“kunji na fad'a muku gaskiya, Ku maidani kafin afara nemanaâ€?.
â€Å“zamu maidaki bisa sharad'i guda d'ayaâ€?. ‘cewar Muftahu â€?.
â€Å“wane sharad'ine?â€?. ‘Munaya ta tambayaâ€?.
â€Å“Sharad'in shine zakuyi auren 1year keda Galadimaâ€?.
Cikin zaro idanu waje munaya tace â€Å“kamar ya? ban fahim cekaba fa?â€?.
â€Å“ina nufin Auren yarjejeniya zakuyi na shekara 1 ko 2, ta wannan hanyarne kawai zamu iya kamo bakin zaren, sannan kekuma zaki sama ma iyayenki kwanciyar hankali, nanda kafin adadin da aka d'ibama auren yacika kinga komai ya wuce, saiya sakeki kiyi idda ki sami Wanda kikeso sannan kuje gida a d'aura miki aure dashi, Galadima ma zai iya sawa har auren a d'aura muku, daga baya sai kuje ya warwarema iyayenki komai, yakika gani?â€?.
â€Å“tabd'i, wannan wace irin maganace saikace labarin Novels ko films? to tayayama za'ayi hakan yafaru? bayan nama sanarma iyayena banida wata alak'a dashiâ€?.
Murmuahi Muftahu yayi, yace â€Å“dan wannan duk mai sauk'ine, kedai amincewarki kawai muke nemaâ€?.
â€Å“amma dai kun maidani wawuya wlhy, to ban aminceba, gara na dawwama banyi aureba aiâ€?.
Baki Muftahu ya bud'e zai k'ara magana Galadima ya d'aga masa hannu alamar yayi shiru ya barta.
â€Å“kinga tashi kije kawai, amma wannan maganar tazama iyamu ukunnan, idan najita awani waje saina zubar miki da hanjin ciki waje, duk shawarar dakika Yanke da zuciyarki zaki iya nemanmu daga nan zuwa kwana biyu kawaiâ€?.
Da sauri Munaya tazaro idanu waje tana kallon Galadima.
Harara ya zuba mata yace â€Å“karki cinyeniâ€?.
Baki ta zun6ura gaba tana k'unk'uni, bayajin mitake fad'a, sai motsin la66anta kawai yake gani.
Sai da aka rufemin iso sannan aka baro gidan dani, bankuma kwanceba saida motar ta tsaya, Wanda yake tare dani yacire k'yallen sannan yace na fita.
Ko kallonsa banyiba saboda tsoro nafice amotar da sassarfa.
Gudu-gudu sauri-sauri na Isa gidanmu, mutane sai kallona sukeyi, ALLAH ma yasoni babu kowa a tsakar gida, inaga matan gidan duk sun shige sallar magriba yaran kuma basu dawo daga islamiyya ba.
A 6angarenmu ma innarmu na d'akinta, hakanne yabani damar shigewa d'akinmu wuff, na iske Munubiya na barci itama, na sauke ajiyar zuciya mai k'arfi ganin ALLAH ya tsareni babu Wanda ya ganni, kayana nacire daketa kamshin turaren Galadima, bayi nashige nida kayan, nayi wanka sannan suma na wankesu na shanya a bathroom d'in.
Harna fito Munubiya bata tashiba, nayi sallar magriba sannan nafito wajen innarmu.
Da mamaki take kallona, â€Å“yoni har ina shirin kiranki naji lfy baki dawoba had dare yarufa?â€?.
Zama nayi ina murmushin yak'e, dan abinda yafaru tsakanina dasu Galadima d'anzu ya min kane-kane a zuciya. ganin abin nakeyi kamar a mafarki. â€Å“ayya innarmu ai tun d'azun nashigo, lokacin kina salla, harfa nayi wanka ma nad'an huta. tace tana gidaki, yaya jikin Munubiya?â€?.
Jikinta Alhmdllh, tad'an watsa ruwa takoma ta kwanta bayan taci d'an abinci�.
To Almdllh, ALLAH yak'ara afuwa.
Amin innarmu ta amsamin, daganan muka koma hirar gidan Inna lami.
Munkai tsawon lokaci afalon muna hira da innarmu, sai dai nifa bama fahimtar hirar nakeba, dan fili kawai nakeson samu nayin tunanin maganar su galadima.
★★★★
Tun bayan tafiyar Munaya Galadima yakoma kan doguwar kujerar yay kwanciyarsa tamkar mai barci.
Muftahu dake kallonsa yace, â€Å“Amma miyasa kace ta tafi? batareda ta bamu gamsashshiyar amsa ba kuma?â€?.
Shiru Galadima bai amsaba tsawon mintuna uku, sai zuwa can yabud'e idonsa yana kallon Muftahu, baki yad'an ta6e â€Å“karka damu kanka, tama yarda, amsa ce kawai bata bamuba, itama kuma zata bayarne, tuni naga yardarta cikin kwayar idonta, akwai abinda take shakku akansa shiyyasa tak'i amsa manaâ€?.
Kai Muftahu ya jinjina kawai, yasan tunda Galadima yafad'i haka to hakanne kuwa, amma sai yace â€Å“to amma bamu bata koda number ba, tayaya zata sanar damu amincewar tata kenan?â€?.
Murmushi kawai Galadima yayi baice komaiba.
Hakanne ya tabbatarma Muftahu murmushin Galadima shine amsar tambayarsa. Daga nan bai sake cemasa komaiba shima.
Falon yay tsit.
★★★★
Gaba d'aya a kwanaki biyunan banida wani sukuni, tunanin maganar yak'i barin zuciyata, a kowacce dak'ik'a zuciyata tunzurani takeyi akan Na amince kawai, dan banida wata mafita sai wannan, ni kaina inason sanin Wanda ya aikata mana wannan abun, sannan bana fata sauran 'yan uwana suyi aure su barni a gidannan, hakan ba k'aramin tozarci zai zamarminba, ga Munubiya tadage akan innarmu ta sanarma Abba itama ad'aga bikinta har saina samu miji nima ahad'a ni da ita, na nuna mata 6acin raina akan maganar amma abanza, tanuna Sam ita tana a kan bakanta, nikuma harga ALLAH ba zanso hakan ta kasanceba.
Ita kanta innarmu nakula danne zuciyata kawai takeyi akan fasa aurena, amma tana cikin matsananciyar damuwa.
Yanzu yazanyi kenan? Na amince ko karna amince? gashi ya gargad'eni akan kadda Na nemi shawarar kowa, ni kaina nama kasa sanarma koda Munubiya, kuma kullum cikin tanbayata take mike damuna? duk da ita zatonta akan maganar Haidar ne har yanzu nake cikin damuwar.
Yau dai kwanaki biyu kenan da faruwar abin, har yanzu kuma nakasa tsayawa a matsaya d'aya.
Kusan tashin hantsi muna tsakar gida a baranda muduka 'yan matan gidan, kowa da hidimar dayakeyi, sai wasu daga cikin k'annenmu dake wasa agefenmu, iyayenmu kuma Na daga can k'arshen barandar suma kowa da hidimarta, innarmu ce kawai babu tana gidan mama Rabi'a taje duba feena da jikinta yad'an motsa.
Tsayuwar mota mukaji a k'ofar gida, yara suka tafi da gudu dansuga wanene? azatonsu cikin su Dady ne.
Mintuna baifi 10 ba saigasu suna shigowa da ledoji, saikuma ga Zarah tashigo cikin kwalliyar kece raini, tana taku d'ai-d'ai, daka ganta kaga mai yaron ciki, cikeda muran muka hau mata sannu dazuwa, itako saiwani ciccijewa take tana kuma Jan kai, ita adole matar manya.
Abin kallo bai k'areba saida mamansu yaa Hameed ta iso da d'an gudu ta rungume Zarah a jikinta, duk mukai galala muna kallon wannan sabon salo.
â€Å“masha ALLAHU Zarah sarkin haske, kinganki kuwa, da anganki anga matar manya yarinyata, kai ai aure Ni'ima ce babba, duk wacce ALLAH yabama 'yarta miji matan gidannan ta godema ALLAH, Dan wlhy yana sontaâ€?.
Caraf Momy Hadiza ta kar6e da fad'in â€Å“wlhy kuwa Yaya, ai babu babban bak'inciki irin kanada gandamemiyar budurwa a d'aki tayi kwantai takasa auruwa, aimu sai godiyar ubangiji wlhy, babu ta inda ni'ima bata saukar manaba, Zarah zoki zauna ki huta kinji 'yar albarkaâ€?.
Maman safara'u da gwaggon haleema da maman su Fiddausi suka kwashe da dariya.
Kowa yasan damu ake wannan gugar zanar, amma sai mukayi murmushi kawai bamuce komaiba, maman fauziyya ma batace komaiba, nama godema ALLAH da innarmu bata nan balle ranta ya 6aci.
Tsam namik'e nabar wajen zuciyata Na suya, Na danne kukan dake shirin tahomin...
Maman Safara'u tace, â€Å“to yanzu ke bazaki iya danne zuciyarki ba saikin nuna hasaadarki a filin ALLAH?, to Ashe ranar auren 'yan uwanki mutuwa kuwa zakiyi?, dan kina gani za'a d'auke kowacce abarki agidan.
Wani k'arfine yazomin a zuciyata, Na had'iye kukana, najuyo ina kallonta ido cikin ido, wani murmushin takaici nasaki, sannan nace â€Å“maman Safara'u ke uwace agareni, sannan innarmu takoya mana tarbiyyar girmama kowacce mace agidannan, badan hakaba dana fad'a miki maganar dabazaki ta6a mantawaba, kuma ba hassadar tasani tashiba kamar yanda tunaninki yabaki, natashine Na d'aukama Zarah ruwansha, naga tashawo rana kuma babu Wanda yayi yink'urin bataâ€?.
Ina gama fad'ar haka nabar wajen. tsit banji kowa yasake maganar ba, bansan miyasa ba, maganar tawace tasakasu yin shiru kokuwa oho.
Ina shiga falonmu Na fashe da kuka, anzo ga6ar da kawai zan amince da buk'atar Galadima, insha ALLAHU aranar datake fad'ar za'a tafi abarni, aranar nima zanbar gidan, Na gwammace nayi auren shekara d'ayan nafito.
Tunanin tawace hanya zanbi Na fad'ar musu Na amince na farayi, dan basu bani number ko wata hanyaba dazan iya nemansu, gashi kuma bazan iya gane gidan dasuka kainiba.
Tunawa dawata farar takarda nayi, wadda nagani a bag d'in dana fita da ita a ranar, kuma nasan ni bani Na ajiyeba.
Da Sauri Na d'auki bag d'in na zazage, saiga takardar tafad'o, na d'auka na bud'e, Number wayace ajiki kawai.
Jikina har rawa takeyi na d'auki wayata na kwafe number, sai kuma nakasa kira, na fara zagaye d'akin.
Motsi naji kamar na tafiya, da Sauri na shige bathroom d'inmu dan nasan Munubiya ce.
fanfo na kunna yanda zata d'auka wanka nakeyi.
Sha warar tura massage kawai na yanke. dan haka na rubuta
*_â€Å“na amince inhar bazai zama ka wulak'anta rayuwa tabaâ€?._*
Haka kawai natura masa na cire kayana nafara wankan gaskiya...........âœğŸ?
⛹ğŸ»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€time d'in wasa yafara.🤸ğŸ»Ã¢€Ã¢™€
*_Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu_*ğŸ‘ğŸ»ÄŸÅ¸˜
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
👉ğŸ»1âƒ?6âƒ?
.......Zaune yake cikin wata runfar bunu dake harabar gidan, dagashi sai wando 3quarter da t-shirt mara nauyi, k'afafunsa hard'e saman table dake tsakkiyar kujerarun, an yisane da ainahin siminti kamar kujerun, sai dai anmusu ado da katifa a sama wadda inma bakayi kallon tsaf ba zaka d'auka na katakone.
Laptop ce ajiye asaman cinyarsa, yayinda idanunsa ke sakeye cikin siririn farin medical glasses d'insa Wanda har kana iya hango fafaren k'wayoyin idonsa aciki.
Gaba d'ayan hankalinsa naga aikin dayakeyi a laptop d'in, lokaci-lokaci yakan d'auki fresh milk na hollandia dake a cikin kofin glass ya kur6a ya ajiye. d'an k'aran da wayarsa tayi yasashi waigowa ya kalli wayar, saikuma ya d'auke kansa ya maida ga system d'in. Saida yagama duk abinda yakeyi sannan ya ajiye laptop d'in bisa table ya sauke k'afarsa d'aya k'asa.
Ruwa ya d'auka yasha sosai sanann ya ajiye ya d'akko wayar da sak'o yashigo d'azun yana k'ok'arin dubawa. sabuwar number ce, dan haka yabud'e cike da mamakin waye?.
*_na amince inhar bazai zama zaka wulak'anta rayuwata ba._*
Shiru yayi yana nazarin massege d'in, dan yakasa fahimta India ya dosa, Yakuma maimaita karantawa har sau biyu, ana ukunne yarinyar shekaran jiya tafad'o masa arai.
Murmushin gefen baki yasaki, tareda d'age girarsa d'aya yana ta6e baki da fad'in â€Å“iyimm!. kingama Jan ajin kenan? Well dama nasan zaki amince aiâ€?.
Wayar ya ajiye gefen table d'in, yazame ya kwanta a kujerar idonsa na kallon rufin bunun, yanzu dai yarinya ta amince, amma tayaya zai tunkari ahalinsa kuma da wannan batun? Mai martaba mahaifin Momma ne matsalar farko, saikuma k'anin mahaifinsa Sarki, Momma bashida matsala da ita inhar papi ya amince, yad'an cije lips d'insa yana lumshe idanu, dole yay gaggawar nemo mafita, dan bak'aramin aiki baneba agabansa, musamman daya zam duniya tagama saninsa da yarinyar a yanayin da bai dace da d'iyan bahausheba musulmi.
Ya sauke ajiyar zuciya mai k'arfi, kafin yaja kuma siririn tsaki.
Zumbur yamik'e saboda wani tunanin daya zo masa a zuciya. waya ya d'auka ya lalubo wata number da aka rubuta my second Momy. kusan mintuna biyu yana kallon number d'in batare da yayi dailing ba, saikuma ya danna cikeda jimami.
Ringing uku aka d'aga daga can.
bayan yayi sallama aka amsa daga can tace â€Å“a'a yarona dama kana k'asar?â€?.
Murmushi yayi tamkar yana gabanta, yad'an zame ya kwanta jikin kujerar yana shafa kansa. â€Å“Sorry my mom, wlhy 2days kawai da shigowata, kuma babu ma Wanda yasan nazo, wani d'an aikine ya kawoniâ€?.
Dariya tayi daga can, cikin tsokana tace â€Å“yo dama ai kai kullum cikin aiki kake katafilaâ€?.
â€Å“oh my mom sunan dakika samin kenan? to nagodeâ€?.
â€Å“ai shine yadace dakai, yaka baromin 'Yar uwa da jikin yayana?â€?.
â€Å“Everything Alhmdllh mom. wlhy nakiraki muyi wata muhimmiyar maganane, ALLAH yasa ke kad'aice?â€?.
â€Å“ni kad'aice yarona, inama bedroom kwancene, miya faru?â€?.
â€Å“uhmmm mom inason nayi a...â€? saikuma yay shiru yakasa k'arasawa.
â€Å“ina jinka manaâ€?.
â€Å“ai mom maganarce bansan yanda zaki fahimceta ba, amma zancene inason nayi auren â€?.
Zumbur tamik'e zaune, saboda jin maganar tayi tamkar daga sama, dan bata ta6a jin makamanciyar wannan maganar daga bakin Galadima Sameer d'in ba, hasalima bata ta6a jin ance yanada budurwa ba, kullum cikin yimasa maganar aure suke yana basarwa da cewa akwai sauran time, shiyyasa koda maganar jaridar nan tafito kai tsaye ta k'aryata zancen. â€Å“yarona wasa ko gaske dan ALLAH?â€?.
murmushi mai sauti ya saki tareda ajiyar zuciya, har yanzu hannunsa na yawo bisa Kansa yana shafawa â€Å“mom da gaske nakeyi, aiban ta6a kawo miki irin wannan maganar baâ€?.
â€Å“hakane, to 'Yar wace masarautace ka samo mana?â€?.
Sai da yad'an ta6e bakisa sannan yace â€Å“no mom, babu kowacce masarautaâ€?.
â€Å“tofa, d'iyar waye to?â€?.
â€Å“ba 'Yar kowa baceba mom, yarinyar Nance dai da aka mana 6atanci tareâ€?.
â€Å“Sameer ban gane mikake nufiba? kana haukane? Koma kafara shaye-shaye bamu saniba?â€?.
tashi yayi zaune sosai, ya d'auki ruwa yad'ansha, â€Å“ban fara shan komaiba mom, inason ki fahimceni da k'yau, dan kece ta farko Dana fara sanarma maganar, sannan kinsan Ku ukune kuka iya Sanin damuwata kai tsaye aduk duniyarnan. nasan zuciyarki zata kawo miki abubuwa dayawa akan maganarnan, to duk ba haka baneba...............â€?.
Anutse ya zayyane mata tarihin su Munaya, har zuwa maganar aurenta data lalace, yad'ora da fad'in mom banason nazama silar tawatsewar rayuwar yarinyar da bata jiba bata ganiba, ki fahimta mana, inason na bibiyeta ta hanyar auren Nata kozan sami wasu evidence akan case d'inan�.
Ajiyar zuciya mom ta sauke daga can, â€Å“to na fahimceka, amma ni mikakeso nayi yanzun?â€?.
â€Å“yauwa momyna, sonake kisamu inno da mai martaba da maganar, amma kinuna kamar kece kikayi tunanin su Sani na auri yarinyarâ€?.
â€Å“iyim nagane, kenan dai yazamto kamar kaid'in bakasan komaiba?â€?.
â€Å“yes my mom, kin fahimceni dai-daiâ€?.
Murmushi tayi, â€Å“ok babu damuwa, kamayi sa'a zanje gidan anjima dama na duba inno datayi muraâ€?.
â€Å“wayyo 'Yar tsohuwarnan, karfa ta wuce bataga 'ya'yanabaâ€?.
â€Å“k'aniyarka Sameer, aiko zan fasa kenanâ€?.
â€Å“no please, sorry mom, nabari, ALLAH ya k'arama ginbiya inno lafiyaâ€?.
â€Å“zan kamakane fitsararreâ€?.
Dariya yayi yana kissing d'in wayar sannan ya yanke kiran Yana cigaba da murmushi, yasan inhar inno da papi suka amince komai yagama yuwuwa, dan ko masarautarsu dolene kowa ya amince.
★★★★
d'aure nafito da zani ina goge ruwan goshina, Munubiya data zubamin ido tace â€Å“kuka kikayi ko sweetheart? â€?.
â€Å“lah a'a wlhy, aini basukai namusu kuka ba wlhy Sweetheart, dan haka kima share batunsu. nifa kitsoma nakeson muje wlhy, kaina yagama yin datti har d'an tsami-tsami yakeyiâ€?.
â€Å“kice kawai kin zama k'azama baby?â€?.
janbaki na d'auka na wurga mata, tai saurin cafewa tana dariya. nima dariyar nayi ina fad'in â€Å“kin tsira yanzu, amma next time bazan barkibaâ€?.
â€Å“hhhh idan na zauna ko? kinga shirya kawai muje wajen aunty Salamah mu wanke kai, daga can saimu biya muga jikin feena ma ko?â€?.
â€Å“ok, hakan yayiâ€?.
Shirina nayi cikin zani da Riga na wata oxblood d'in atanfa da ratsin milk, nakawo milk hijjab na saka batareda na d'aura d'an kwaliba, itama Munubiya irin kayan nawa ta canja. tsaf muka fito damu, saida Munubiya takira Innarmu ta sanar mata sannan muka tafi.
Mun tarar duk sunbar tsakar gidan, kowacce tashige 6angarenta, 6angaren su fauziyya muka lek'a domin sanarma mamarsu zamu fita.
bamu wani jimaba muka fito muka tafi.
Tunma a layinmu muka sami napep. har k'ofar shagon Aunty salamah ya saukemu..
Kamar yanda ta saba haka tamana tarba ta mutunci da d'oki. muma hakan ne daga garemu, dan muna k'aunar auntynmu data koya mana aiki, tace �'yan ukuna ina hasaanar to?�.
Dariya mukayi, dan munsan Ayusher take nufi, mukace bama tasan mun tahoba amma daga nan gidansu muka nufa.
An wanke mana kai, sannan mukayi kitso bawani mai yawaba, aunty ce tace dole sai ammana kunshi ko kad'anne, dole badan mun soba aka mana Jan lalli sai bak'i daya zamo kad'an, bamu baro shagonba sai bayan la'asar, dan mund'an taya aunty aiki.
Kai tsaye gidansu Ayusher muka nufa, mun iskesu gaba d'aya afalo suna hira, Ayusher na tacema Feena tafarnuwa dazafa sha. yayinda innarmu da mama Rabi'a ke zaune kusada juna suna hira k'asa-k'asa. Aiyaan Ahmad da Aryaan kam hankalinsu nakan wasa a can gefe.
Yaa fadeel ne yafara fad'in â€Å“oyoyo 'yan biyunmuâ€?.
Dariya mukayi, sannan muka k'arasa cikin falon, bayan mun gaida iyayenmu muka gaida yaa Fadeel, sannan mukaima Feena ya jiki, ta amsa tana murmushi.
Ayusher daketa antaya mana harara Na kalla, â€Å“kekuma lafiya kike wani hararmu?â€?.
Harar takuma watsa mana tana mik'ama Feena kofin tafarnuwa, â€Å“ban saniba 'yan rainin hankali, tun k'arfe nawa kukace zaku taho amma sai yanzu?â€?.
Munubiya tatashi taje inda take ta rungumeta, sorry habibati, wlhy mun biya shagon aunty ne munyi kitso, saikuma ta tsaremu wai sai munyi k'unshi, tamace a gaidaki�.
â€Å“kai shine baku kirani mun jeba? wlhy nima kan nan nawa yana buk'atar kitso, tana lafiyaâ€?.
Namik'e ina fad'in â€Å“Sumul- sumul, mukuka dafa? ALLAH yunwa nakeji?â€?.
Cikin tsokana mama Rabi'a tace â€Å“tuwoâ€?.
Na tunzuro baki gaba, kai mama wai keda innarmu kullum tuwo bakwa gajiya?�.
â€Å“yo yaza'ayi mu gaji tunda shi mukaci muka girma, kajimin ja'iran yara, wai kukam bakuda mak'iyi sai tuwone?â€?.
yaa Fadeel yace â€Å“yo k'aton ciki yake saka mutane, ina daliliâ€?.
Dakuwa innarmu tamasa, â€Å“gidanku Fadeel, mu miyasa bamuyi k'aton cikinba?â€?.
Feena tace â€Å“ALLAH innarmu gaskiya yaa Fadeel yafad'a faâ€?.
â€Å“lallai Nafeesa, kema ina ganinki salo-salo Ashe k'yalleceâ€?.
Dariya muka sanya gaba d'aya, akuma wannan lokacinne yaa Marwan yashigo da sallama.
Su Aiyaan sukaje da gudu suka taryoshi da amsar kayan hannunsa.
Waje yasamu ya zauna yana gaida su innarmu, muma muka gaidashi.
Ayusher datasan dokarsa ta yana shigowa a kawo masa ruwa ta kalli Munubiya, sis.... Please kibama yaa Marwan ruwa, ni nariga da na ta6a tafarnuwa�.
Kamar munubiya bazata tashiba saikuma tamik'e saboda harara daya antaya mata, shi zatonsa ma nice, dan yasan Munu.... Akwai sauk'in kai.
Mama da innarmu kam hirarsu suketa zubawa kamar basusan mi mukeyi ba.
Babu dad'ewa saiga Munu... da k'aramin tire tazubo ruwa mai sanyi a jug, ajewa tayi a gabansa, ta durk'usa ta tsiyaya masa tabasa, sai da suka had'a ido ta janye nata da Sauri, alokacin ya fahimci Munubiya Ce, yana gama shan ruwan yadire kofin yana mik'ewa, â€Å“ki kawomin abinci d'akiâ€?. ‘yafad'a yana yin gaba abinsaâ€?.
Tad'an bishi da kallo sannan tamik'e takoma kitchen d'in.
Kallon juna mukayi nida Ayusher muna d'aga gira, yaa Fadeel daya gammu shima saiya saka dariya, k'asa-k'asa yanda su inna bazasuji ba yace â€Å“muma ALLAH kabamu masu sonmoâ€?.
Muma ahankali mukace amin nida Ayusher.
Feena tace â€Å“ALLAH ya shiryeku, dama yajiku wlhyâ€?.
Yaa Fadeel yace â€Å“saidai su susha duka, nikam ai bani dokuwaâ€?.
Nanma dariyar mukayi.
Da sallama tashiga d'akin, yana zaune bakin gado dagashi sai vest da dogon wandon kayansa bai cireba, wayace a hannunsa yake latsawa, ta dire tiren abincin a gefe sannan ta janyo k'aramin table d'in gefe gabansa, abincin ta zuba masa, har sannan bai kalleta ba, saida tagama zata tashi yace â€Å“wato k saima ance kibani ruwa ko?â€?.
Shiru Munu... tamasa, Dan batasan mizata ceba, yad'ago idanunsa irin nata (dan duk 'ya'yan mama Rabi'a kama muke da juna, saboda ita suka biyo, idan kacire Feena dake kama da babansu) yana kallonta, itadai kanta ak'asa tana wasa da zoben hannunta.
â€Å“baki jina ne?â€?.
Ahankali tace â€Å“kayi hak'uri toâ€?.
Shiru yamata bai tankaba, yaja abincinsa yafaraci anutse, baice ta tashiba itakuma bata tashinba, gashi bawata hira sukeyiba, ita tunaninma yanda zatayi zaman aure da yaa Marwan takeyi, Yaya za'ayi rayuwa tayi dad'i Dan ALLAH?.........
maganarsace tasaka ta d'ago ido tad'an kallesa, shima idonsa Na kanta. ta janye nata idanun.
Yakuma fad'in â€Å“nace yaushe zakije kiga gidanki?â€?.
Saitaji maganar wata iri, wai gidanta, gidansa dai, muryarta a sanyaye tace ai basai najeba�.
Yace â€Å“ko?â€?.
Kai ta d'aga masa alamar eh.
Yad'anyi wani munafukin murmuahi, Sanan yamik'e yanufi hanyar bathroom yana fad'in â€Å“ki shirya jibi zanzo na d'aukeki da yammaâ€?.
Bai jira amsarta ba yashige abinsa. tadad'e zaune tana kallon k'ofar toilet d'in, tamkar nanne zata ganoshi, saida taji motsin kamar zai fito sannan tamik'e da sauri ta kwashe kwanikan ta fice.
Bamu bar gidanba sai bayan sallar isha'i, yaa Marwan da kansa ya kaimu har gida.
_____________________________
Yana kwance a falon gidan daya zama mafakarsa, waya suke da momma akan yaushe zai koma? dan doctors d'in Abie nason ganinsa.
â€Å“maybe ma gibe ki ganni Momma dan nagama abinda ya kawoniâ€?.
â€Å“shikenan babu damuwa, amma kana ganin a masarautar ku babu Wanda yasan kazo?â€?.
â€Å“babu Wanda yasani momma, hatta da Harun, sai Muftahu kawaiâ€?.
Cikeda mamaki tace â€Å“Muftahu kuma?â€?.
â€Å“eh Momma miya faru?â€?.
Tayi d'an jim sannan tace â€Å“babu komai, amma ka dinga kula dai Muh'dâ€?.
Shima yad'anyi shiru yana nazarin maganarta, sai kuma yace â€Å“ok Momma insha ALLAHâ€?.
Yana ajiye wayar kuwa saiga Muftahu ya shigo, kallonsa Galadima yayi.
Muftahu dake shirin zama yace â€Å“yalla6ai barka da ranaâ€?.
â€Å“ykk?â€?.‘cewar galadimaâ€?.
â€Å“wlhy Alhmdllh, dama akan yarinyarne, kagafa har yanzu bamuji daga gareta baâ€?.
Murmushin gefen baki Galadima yayi, sannan yabud'o massage d'in da Munaya ta turo masa yamik'ama Muftahu wayar.
Babu musu Muftahu ya kar6a, saida ya gama karantawa sannan ya d'ago yana kallon Galadima fuskarsa washe da murmushi, â€Å“Alhmdllh yalla6ai ta amsa Ashe?â€?.
Kallonsa kawai Galadima yakeyi cikeda nazarinsa, yana mamakin yanda Muftahu ke d'okantuwa da wannan maganar auren, tunda yabashi damar binciken su Munaya bai barsa ya hutaba, haka kawai sai zuciyarsa ta d'arsa masa wani Abu, musamman idan yay dubi da yanda Muftahu ya nuna tsantsar farincikinsa dayace zai auri yarinyar na shekara 1. to koma dai miye, zai sanya masa idanu.
Muftahu yace, â€Å“yalla6ai to yanzu ya za'ayi dasu mai martaba ne?â€?.
Galadima dake latsa d'ayar wayarsa yace, â€Å“no, karka damu da wannan, zan k'arasa komai kawaiâ€?.
Kamar Muftahu baiso hakanba, amma saiyayi murmushin yake, â€Å“shikenan ALLAH ya tabbatar da alkairi, yasa ayi damuâ€?.
d'ago ido Galadima yayi ya kallesa, â€Å“to miye kuma na wannan doguwar Addu'ar? Saikace wani auren gaskiya?â€?.
â€Å“Hakane kuma yalla6ai, sorryâ€?.
Shiru Galadima bai amsaba. falon ya d'auki shiru kowa da tunaninsa.
★★★★
Harda safe inata yawan duba wayata kozanga replay daga Galadima amma shiru, hardai munubiya tace â€Å“wai miye bini-bini saiki duba waya?â€?.
Kallonta nayi ina k'ak'alo murmushin yak'e nace â€Å“babu komai faâ€?.
Badan ta yardaba ta k'yaleni, cigaba mukayi da aikin da innarmu ta samu.
Aryaan yashigo yana kuka, muduka mukace miya faru kaikuma?.
Cikin kukan yace â€Å“ba Abdul bane ya dakeni, wai dan Zainab ta zubamin ruwa na ramaâ€?.
Nace â€Å“ina Abdul d'in?â€?.
â€Å“Suna wajen fanfoâ€?. ‘cewar Aiyaan daya shigo yanzunâ€?. â€Å“Auntynmu kuma wlhy sosai yabama Aryaan mari a fuska, sannan ya halbeshi ga k'afarsa har yafad'iâ€?.
Da hanzari nafice daga sashenmu, na iske Abdul da sauran yaran gidanmu a bakin fanfo suna wasa da ruwa, rankwashin Abdul nayi tareda murd'e kunnensa, â€Å“mi Aryaan yamaka ka dakesa dan k'aniyarka?â€?.
Hannuna yadafe saboda zafin dayaji na murd'ar kunnen, cikeda tsiwa yace â€Å“yoba Zainab ya daka ba danta watsa masa ruwa bata ganibaâ€?.
K'eyarsa na mangara, â€Å“to ina ruwanka, Zainab d'in ba k'anwarsa baceba? kokuwa dan kai mama d'aya ta haifeku? daga yau kasake dukan wani acikinsu saboda yadaki Zainab ko Fahad saina lallasaka agidannan, masu shegen 'yan ubancin tsiya, iyayenku duksun 6ataku da k'in 'yan uwanku jininkuâ€?. nak'are maganar dakuma rank'washinsa.
Aikam ya daddage ya kwantsama kuka, kaikace wani uban bugu namasa.
Kamar jira gwaggon haleematu keyi tafito tana tambayarsa miya faru?.
Fad'a mata yayi waina mareshi da murd'a masa kunnen saboda ya daki Aryaan, harda cewa na zageta.
Hummm tamkar dama kad'an take jira damu, har k'ofar d'akinmu taje tana zazzaga masifa da zagina.
Innarmu tafito tana tambayar miya faru? dan ita bama tasan an bigi Aryaan d'in ba.
Maimakon tama innarmu bayani saita koma kanta da cin mutunci, kamar innarmu tayi shiru amma yau saita kasa.
Ta kalli Goggon haleema tana murmushi, Sadiya bakinki yasan mizai fad'a, inba hakaba zan baki mamaki agidannan wlhy, bakinki ya tsaya iya maganar yara, idan kika kuskura iyayena suka kuma shiga a furicinki zakiyi nadamar sanina�.
Innarmu nagama fad'a tashigewarta.
Galala gwaggon haleematu da duk matan gidanmu sukayi da mamaki, duk kuma sai shakkar innarmu ya shigesu, Ashe akwai ranar dazata iya maidama wani murtani acikin gidan?.
Murmushi nasaki, sannan nabama Munubiya dake kusadani hannu muka tafa, nace â€Å“ho innarmu, kina aljanna ina binki da addu'a, haka nakesonki agidannan, kiringa watsema kowa aniyaâ€?. naja hannun Munu.... muma muka shige ciki.
Abbanmu dake kallon komai ta window d'akinsa yasaki murmushi yana girgiza kai, yasan gaba d'aya halayen Munaya nashine, yarinyar batada tsoro, amma yau Ai'sha ta birgeshi datama Sadiya haka, koba komai tasaka musu shakkarta azukatansu.
Aikan kowa jiki babu kwari taja k'afarta tashige d'aki tana gulma da zuciyarta.
Gwaggon Haleema kam ai saida Nusaiba taja hannunta sannan ta iya d'aga k'afarta.
Koda muka Shiga sai innarmu tahau mana fad'a akan dukan Abdul d'in da nayi, hak'uri kawai na bata danni yau raina fes, innarmu tafara maida murtani.😅
★★★★�
Da k'yar ya iya bud'e idonsa ya janyo wayarsa dake ringing, batare da ya dubaba ya amsa yasaka a kunne.
â€Å“Assalamu alaika Muhammad kana lafiya?â€?..
Zaram ya mik'e zaune tareda watstsayewar dole saboda jin muryar mai martaba mahaifin Momma papi.........âœğŸ?
To ko mai martaba zai amince da auren Munaya? duk da baisan kai tsaye auren yarjejeniya baneba🤔?.
Karku manta Amincewar mai martaba itace ta kowa.
Muje zuwa my guys⛹ğŸ»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*ğŸ˜ÄŸÅ¸¤Å¡ÄŸÅ¸»Ã¢Å“‹ÄŸÅ¸?
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
👉ğŸ»1âƒ?8âƒ?
..........A Asibiti gado suka bani, sunata fad'an yanda jinina ya hau sama, su mamakima suke yi 'yar k'aramar yarinya dani amma inada hawanjini, shin miyayi zafi haka?.
Su Abba dai kasa cewa komai sukayi, dan su kansu abin na yata6a zuciyarsu.
Wannan karonma Mama Rabi'a da Munubiya ne suka kwana a wajena, washe gari da yamma saiga 'yan gidanmu wai sunzo dubani, bamuyi mamakiba Dan munsan ba domin ALLAH sukazoba, kawai sunzo ganin kwafne.
Duk suncika d'akin da surutu akan wai suna mamakin miya samin hawan jini?. daga mama Rabi'a har Munubiya babu wanda yabasu amsa.
Doctor ne yashigo yace sud'an ragu wasu su fita baranda dan ALLAH, duk fita sukayi harda mama Rabi'a aka barmu iya mu yaran kawai, dansu Fiddausi duk hadasu akazo.
Ina daga kwance kan gado ina sauraren hirar dasukeyi, wai safara'u da Halimatu ne sukaje gidan su Siyama tai tamusu yatsina da d'aukar kai, saikace ba 'yan uwanta ba, mijinta yadawo sukayi shigewarsu suka barsu afalo har yamma sannan suka fito, mai makon tabasu hak'uri sai cewa tayi wai dama basu tafiba🤣.
Wannan abun daya faru shine yajawo rigima a gidanmu jiya da daddare, har saida su Abba suka tsawatar.
Murmushi kawai nayi Na gyara kwanciyata, a zuciyata ina fad'in maganinku ai, baku masu dangiba..........gabana yafad'i, saboda jin tamkar k'amshin turarensa. da sauri Na d'ago kai saboda jin su Fauziyya ma sunyi tsit daga surutun dasukeyi suna kallon bayanmu.
Wani yaam naji a raina domin ganin Galadima da tawagar dogaransa, sai wani dake gefensa amma ba muftahu bane, (Harun ne). Sanye cikin k'ananun kaya wad'anda suka fidda ainahin k'irarsa ta cikakken namiji, fuskarnan kamar kullum babu walwala.
Mu 4 ne kawai a d'akin, dan haka yana tsaye a gadon farko da alama tanbayoyi yakema matar dake jiyya a gadon. gani nai yasaki wani guntun murmushin gefen baki sannan ya kalli harun, bansan miya cemasaba nagadai yabaro wajen yana tunkaro gado Na biyu.
A hankali Na lumshe idanuna wani Abu Na tsikarar zuciyata mai kama da tsoro da rud'ani.
Sauran 'yan uwana kam sun zuba masa idanu tamkar zasu cinyesa, kowacce takasa furta komai a fili saida a zuciyarta take tattaunawa da yaba Galadima d'in.
Annanma yayi kusan mintuna hud'u sannan ya tunkaro gadon takusa damu, dan nice ta k'arshe. duk da akusa damu yake banajin miyake fad'a, saidai motsin la66ansa kawai nake gani, tabbas Galadima naji da Girman kai da mulki, kallo d'aya zaka masa ka tabbatar da tsantsar sarauta da mulki dake yawo a jinin jikinsa....... tunda naga yanufo inda nake sai kawai narufe idanuna gaba d'aya.
Su Munubiya duk suka risina suna gaidashi.
Hannu kawai ya d'aga musu yamatso jikin gadon danake.
Tsantsar mamakine ya bayyana a fuskarsa, yad'anyi kamar zai nunani da hannu saiya kuma fasa, su safara'u kam duk sun zubo mana idanu suga yanda za'a kwashe.
Munubiya ce cikin k'arfin hali tace â€Å“Munaya ki tashi ana miki magana faâ€?. daka ganta kasan a tsorace take maganar.
Shima juyowa yayi ya kalli Munubiyar domin jin kuma Muryata, maganar Muftahu ta fad'o masa arai dayace yaran twins ne, kuma ba'a iya banbancesu.
Suma Kansu dogaran NASA da Harun duk sunyi tsuru suna kallonmu, domin babu wanda baiga jaridarba a wancan lokacin.
Maganar sace tasaka kowa maida hankali a kansa, nidai har yanzun idona arufe suke, cikin basarwa da nuna halin ko in kula yace, â€Å“ya jiki?â€?. tamkar bayaso haka yayi maganar.
Nima cikin dakiya da shariyar kamar yanda yamin nabud'e idona nace â€Å“Alhmdllhâ€?.
Kamar yanda yake tambayar kowa nima haka ya tambayeni miye matsalata?.
Na d'a6e baki sannan nace â€Å“masassaraâ€?.
Harun ya kalla, danshi baima fahimci minake nufiba.
Murmushi harun yayi, danya fahimci bai ganeba, cikin gyara tsayuwa yace â€Å“tana nufin feverâ€?.
Caraf fiddausi tace, â€Å“ranka yadad'e k'arya take hawan jinineâ€?.
Juyowa yayi ya kalli fiddausin da fararen idanunsa wad'anda suka nemi zautata, bai Ce komaiba ya janye ya maida kan Munubiya, â€Å“Sister naga drugs d'innan?â€?. yafad'a kamar anmasa dole.
Ko kad'an Munubiya bataji maiya fad'aba, dan a saman la66ansa yayi maganar, tana shirin sake tambayarsa d'aya daga cikin dogaran ya maimaita mata a tsawace.
Nikaina saida Na bud'e ido saboda tsawar, Na bankama dogarin harara ina magana k'asa-k'asa yan da babu mai jina, kajimin shegen dogari, dan tace batajiba zakawani daka mata tsawa?, shi mizaisa bazai bud'e baki yayi magana yanda kowa zaijiba? Mutum sai azabar Girman kai mtsoww, koma R bai iyaba.
Duk maganar danake la66ana ne kawai ke motsawa, shikuma idon nasa nakan la66ana, dukda duba kwalin drugs dayakeyi, tsaf ya karanci duk maganar danakeyi. yayi wani munafukin guntun murmushi yana mik'ama Munubiya magungunan.
Juyawa yayi yama Harun magana, sannan ya juyo ya kalleni yana fad'in â€Å“ALLAH yak'ara lafiyaâ€?.
Harara Na zuba masa batare da tunanin zai ganiba, amma sai caraf muka had'a idanu.
Janye idanunsa yayi a kaina yajuya yabar wajen yana cije lips d'insa da mamakin yarinyar nan da batada tsoro.
su Safara'u Na zuba masa godiya, duk da zukatansu Na mamakin yanda yanuna tamkarma bai sanmu ba.
Ko kallonsu baiyiba ya d'aga musu hannu, sukuma sunyine dama danya tanka musu.
Harun ya tambayi Munubiya wane doctor ne ke dubani?.
Ta Sanar masa.
Addu'a yaymin sannan yabar wajen shima.
Lumshe idanuna nayi zuciyata Na kaikawo, yanda Galadima yayi, saiya kuma tabbatar min da mafarki dai nayi kenan, bawai gaba da gaba ba yace muyi Auren Contract ba kenan.
Innalillhi, mike shirin faruwa danine ni Hussaina, hawayen dasuke neman zubomin nai k'ok'arin had'iyewa, Munubiya kanta tashiga kogin mamakin yanda Galadima yay tamkar ma komai baita6a faruwaba, shin kodai shi baiga abinda yafaru a jaridar baneba?....
Batada mai bata amsa, su safara'u ma magana suketayi k'asa-k'asa a tsakaninsu, alokacinne kuma matan gidanmu suka shigo.
Mamansu yaa hameed take tambayar wai wananan bashine Galadima ba na jikin jaridar nan?.
â€Å“wlhy shine kuwa mamaâ€?. cewar Fiddausi.
Haleematu ta kar6e da fad'in â€Å“mama kinga yanda ya nuna kuwa? tamkar ma bai gane su twins ba balle ya nuna yama San abinda yafaru a bayabaya tsakaninsuâ€?.
Murmushin mugunta mamansu ya hameed tayi, â€Å“yo ai dama saboda irin haka ake cewa Ku kare mutuncin kanku, danshi namiji komi yayi adone, sannan shi d'an manyan mutanene, ko kallonsa da abin babu mai sakeyi, amma Ku gashi har ana fasa aure, kamun kai dai dad'i gareshi ai dama, kum.......â€?
Shigowar doctor tasaka maman su yaa hameed yin shiru, korarsu yayi gaba d'aya, yace subarni Na huta.
Basuso hakanba, dan shirya cin zarafinmu maman yaa hameed tayi.
Daganan gida suka wuce suna 'yan gulmace-gumacensu da dariyar mugunta.
★★★★�
Galadima kuwa yana gama zagaye-zagayensa a asibitin na duba marasa lafiya gida suka wuce.
Bayanin doctor yabashi mamaki, wai wannan 'yar yarinyar keda hawan jini, itako miyayi zafi haka a rayuwarta�. wani sashi na zuciyarsa yabasa amsa da (6atancin da akai muku).
Lips d'insa ya cije yana jan dogon tsaki, shikad'ai yasan burin daya d'auka akan dukkan Wanda yasamu da hannu a wannan lamarin.
Sun biya birnin gayu plaza yaga komai yana tafiya dai-dai, daga nan suka koma masarauta.
★★★★
Nima a ranar da daddare aka sallamoni, nadawo gida nacigaba da shan Magani, yayinda biki keta gaba towa kuma.
Har yanzu innarmu tana cikin damuwa dani kaina akan zancen aurena daba asan taka maimai angoba.
Zancen galadima kuwa ai tini na shareshi, dan nabarsa amatsayin mafarki nayi, musamman kuma dana bincika banga number wayan daya baniba, a wayata kuma tun randa na tura masa massege na gogeta dama gudun kar wani yagani.
Yanda 'yan gidanmu suketa rawar kai akan bikin saran 'yan uwanmu innarmu batayi, bazama ka ta6a d'auka itama zata aurar da 'ya'ya har biyu baneba.
Mama Rabi'a ce ke tsaye akan komai, sai aunty salamah datazo da magunguna ta d'id'd'irka mana, mu bamusan namiye ba, takumace mudinga sha, saikuma had'ad'd'en sabulun wanka da mai data had'a mana, ga wasu turare masu sirrin k'amshi, takuma gargad'emu daga yanzu muna saka hijjab duk inda zamuje da nik'af, domin fatarmu tasami nutsuwa kar rana ta maidamu gidan jiya.
Ni dai dagani har munubiya da to kawai muke binta, kuma duk abinda tace muyi munayinsa.
Abbanmu yakira mama Rabi'a yabata wasu kud'i akan tak'ara amana siyayyar kayan kitchen da 'yan uwa keyi, tunda ita innarmu bawasu dangi ne da itaba dazasu tara mata.
Sosai tamasa godiya, sanan tasanarma innarmu, ko babu komai taji dad'i, harma tamasa godiya itama.
Tafiya mama Rabi'a tayi da k'ud'in, washe gari suka Shiga kasuwa itada inna lami, kaya masu k'yau suka sissiya mana dai-dai gwargwadon k'arfinmu. aka adanasu gidan inna lami duka.
*_kwanci tashi_*
Babu wahala wajen ubangiji, yau gashi abinda kowa yake jira yazo, domin kuwa ankawo lefen Haleematu, gaskiya angonta yayi k'ok'ari, akwati 5 abinta, kuma kaya masha ALLAH, sai-dai hakan bai hana 'yan gidanmu gulmaba, washe gari kuma aka kawo kayan Safara'u da Fiddausi.
Suma dai kam saidai mak'iyi, amma jikin maman safara'u yayi sanyi, dan gaskiya kayan sauran duk sunfi nata. Itama dai akwati biyarne, amma kayan cikine basukai na sauranba.
Again washe gari saiga na Fauziyya da Munubiya, mama Rabi'a tasan komai dake wakana a gidanmu, dan haka suka dage sukaima Munubiya lefe na 'Yar gata, wlhy ba fariyaba lefenta yafi na kowa, ranar har kukan dad'i nayi, domin banyi zaton hakanba. itama dai fauziyya angonta yayi k'ok'ari gaskiya.
Tuni hassadar matan gidanmu tafito fili suka fara yada habaici wai an aro kaya anzo ana musu burga, da anyi aure sai ake maidawa d'ai-d'ai.
Dagamu har innarmu babu Wanda ya tanka musu, dan munsan yau dai mune aciki sune a kwana🤣🥴.
Rashin kawo nawa lefen kuwa ko a kwalar rigata bai dameniba, dan bama sanin mijin nayiba balle nadamu dawani lefen banza. saima Munubiya ce harda kukanta rurus akan wai saidai araba mana kayanta mu biyu.
Nifa dariyama tabani wlhy.
Ganin ni babu lefe yasaka su baba k'arami siyomin kaya masu k'yau na fitar biki har kala 10, aka d'inka min, sai takalma da bags da veils masu k'yau suma.
Habaici dai kam munshashi wa su innaro da matan gidanmu, danma ita innaro gwaggo Safiyya na hanata ne, da bamu san tijarar dazata zubarba a ranar kam.
A haka aka shiga satin biki, mu bamu wani gayyaci k'awayeba, daga Bilkisu sai su Ayusher, ashe Ayusher ta buga invitation na k'awaye suka raba itada Bilkisu bamu saniba.
Abin mamaki ranar kamu sai ganin k'awayenmu mukayi harna secondary.
munji dad'in hakan sosai kuwa.
A ranar kamun saiga wasu mata hud'u sunzo wai dangin miji nane, su mama Rabi'a sukayi musu tarba ta mutunci, ba a nuna musu komaiba kuma, dukda a yanayin shigar talauci da sukazo, saidai zund'e da gulma irinta 'yan biki. Matan gidanmu kam komai ya kaimusu dai-dai, sai dariya da yada magana a kaikaice sukeyi. Da aka kaisu su gaisa da innaro taita musu yatsine-yatsine, harda tanbayarsu waisu garinsu ba'a lefene? dabasu kawoma jikartaba?.
Basuce komaiba sai murmushi kawai da sukayi.
Washe gari kuma akayi k'unshi, mudai namu aunty Salamah ce tamana, tana tsaye akan komai namu tamkar yayarmu ciki d'aya.
A ranar kuma akaje a kaima sauran amaren jere, harda Munubiya, amma ni banda ni, tunda ba'asan ina za'aje ayiba.
Aranarma Munubiya tayi kuka, nidai ina k'ok'arin danne zuciyata, saboda nabama innarmu kwarin gwuywa karta tada hankalinta.
Aiko Alhmdllh ta dake tamkar komai baya damunta, tashige cikin abokan arzik'inta sunata harkoki. kowanne 6angare yacika da dangin matan gidanmu, abin tamkar fariya, namu 6angarenne kawai keda sauk'in jama'a, hakama gidan innaro yacika da danginta da dangin kakanmu.
Tunda aunty Salamah tagama yimana k'unshi da gyaran kai dana jiki sai muka nufo hanyar gida, saboda yaa marwan yazo neman Munubiya harsau biyu, sai kiran wayarta yake yana masifa saboda tare yake da abokansa. hakan yasa muka taho gida.
Gashi Yau zamuyi sister's and brother's day, duk da dai saima da yamma.
★★★★�
Galadima dake zaune a makeken falon Ummu hasheem, yanata bin jerin akwatinan da kallo, ga wasu daga 'yan uwansa zazzaune sunata kuma kimtsa kayan, aunty Mimi ta kalleshi, â€Å“kunga zanma mantafa, my k'ani ina kayan dana baka kayo gaba dasune?â€?.
Yatsine fusaka yad'anyi yana gyara zamansa, â€Å“nifa nama manta inda suke, shiyyasa nace bazan d'akkoba aiâ€?.
Wata uwar harara ta watsa masa tace, â€Å“lallai bakada kai yaro, bar ganin matarka za'a kaimawa, suka 6ata biyana zakayi eheâ€?
Murmushin gefen baki yasaki yana lumshe idanu, cikeda k'asaitarsa yace, â€Å“Samha! jeki bedroom d'ina ki duba, maybe suna canâ€?.
â€Å“bama kada tabbas kenan?â€? cewar mom.
Bud'e idanunsa yayi yana murmushi, â€Å“no mom insha ALLAH sunama can. ni yanzu kam kun sallameni natashi natafi? dan zansa aje a d'auko su Akash a airport â€?.
Ummu Hasheem tace â€Å“kaje kawai, dama dan kaga kayanne, tunda kuma kace komai yayi ai shikenanâ€?.
Mik'ewa yayi yana fad'in â€Å“thanks you Ummu, nabarku lafiyaâ€?.
Tunda yasamu yay escape sai ya sauke ajiyar zuciya, shi dariyama suke bashi dagasu har su papi, su Dan basu san auren shekara d'aya bane dabasu dinga wannan rawar k'afarba, sun wani zauna sun had'a uban kayan lefe, yad'an ta6e bakinsa kawai yana nufar sashensa.
Komai na gidan sarauta mai tsarine, dan haka kai lefen MUNAYA da suke shirin yima a tsare akayisa, (papi ne yace Subari sai yau ana gobe d'aurin aure sai akai, tunda gidan su munaya basusan kosu su wayeba).
An tsara iya wad'anda zasu kai lefenne.
Bayan an gama zuba akwatunan a wata farar mota mai k'yau sabuwa dal aka rufe, driver ne kawai zai shiga cikin motar.
Sai kuma motoci 6 da aka zaba wad'an da zasu kai lefen.
Motar farko dogaraine, ta biyu kuma kuyangi ne, sai guda biyu 'yan cikin gidansu Galadima ne su hud'u, ko wacce mota mutum biyu, sauran biyun kuma 'yan 6angaren masarautar su Momma, suma su hud'u, kowacce mota biyu. sai Samha datasa kuka saitaje taga matar Uncle Sam.
Aunty mimi harta korata da zare mata idanu saiga Galadima motocin na niyar tashi.
Da kansa yabud'e mata gaban motar da aka saka akwatinan yace tashiga nan, idan taje ta gaida masa matarsa.
Cikeda d'oki tace zataji Uncle Sam, bazaka bada komai akai mataba.
Kansa yad'an dafe dan yakula Samha na neman k'uresa, shikuma yafad'a mata maganarne domin yanason agaban jama'a yadinga yana tsantsar k'aunar Munaya, a bad'ini kuma suna zaman aurensu na contract, shiyyasa ko lefennan baiji tsadar kud'in saba yabud'e bakin aljihu aka zuba kaya masu azabar k'yau, gakuma kud'in da Mai martaba yabada shima, dakuma sauran k'annen mahaifinsa.
Hannu yasaka a aljihunsa yana duba kozai samu wani Abu, amma babu komai sai wata chocolates guda biyu, wadda ya d'akkota ne zaiba khaleel d'azun yama manta, mik'ama Samha yayi yace â€Å“gashi kibataâ€?.
Da dariya samha ta kar6a tace â€Å“Uncle ta gode toâ€?.
Kansa kawai ya jinjina mata ya shirin barin wajen.
motocin suna fita daga masarautar saiya sauke ajiyar zuciya kawai.
★★★★
Gidanmu ya cakud'e da hayaniyar da akasan gidan kowanne biki da ita, bare mu daya kasance har auren mutum 6, dukda sai gobene d'aurin aure kuwa, yara sunata wasansu da tsalle-tsalle.
A jere motocin suka shigo cikin anguwar, jama'a sai binsu da kallo sukeyi, dai-dai k'ofar gidanmu driver daya san gidan yay parking.
Babu Wanda yay mamaki a 'yan kawo lefe, domin kuwa dama labari ya karad'e masarautar cewar Galadima'yar talakawa zai aura.
Dogarawa da kuyangi suka fara fitowa, sannan suka bud'e motor da akwatina suka suka fara fitarwa. Nanfa jama'ar anguwa sukayi cirko-cirko suna kallon ikon ALLAH dan ganin akwatinan da aketa fitarwa daga mota.
Batare da neman isoba Kuyangin suka fara kwasar akwatinan suna shiga dasu gidanmu..............âœğŸ?
😂😂😂
Team innaro kufito mu caskale yauğŸ™Å 🤸ğŸ»Ã¢€Ã¢™€
⛹ğŸ»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€
Asha weekend lafiya😅✋ğŸ?
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmuğŸ‘ğŸ»ÄŸÅ¸˜_*
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
👉ğŸ»1âƒ?7âƒ?
.........Cikeda girmamawa yace, â€Å“Ranka ya dad'e barka da dare?â€?.
â€Å“barkan ka dai Muhammad. dama kashigo k'asar kenan?â€?.
Gabansa yad'an fad'i, danshifa yama manta mai martaba baisan yazo k'asarba, dakiyar dole ya aro yace, â€Å“wlhy kuwa nashigo d'azun yin wani aiki, amma gobema idan ALLAH ya kaimu zan komaâ€?.
â€Å“tofa, gobe gobe? kuma gashi inason ganinka a gobenâ€?.
d'an jimm yayi, irin tamkar baisan komaiba, cikeda shakku yace, â€Å“ranka ya dad'e lafiya dai ko?â€?.
â€Å“lafiya k'alau, wata muhimmiyar magana nakeson muyineâ€?.
â€Å“to shikenan, zanshigo insha ALLAH â€?.
â€Å“to madalla saina gankaâ€?.
Dafe kai Galadima yayi yana mamakin kansa, anya kuwa baima kansa d'aurin gorobo? koda yake idanfa yayi hak'uri shekara 1 ne ko 2 kacal, inma komai yafito kafin cikar shekarar zai sawwak'a matane, yad'an murmusa sannan yakoma ya kwanta abinsa cikeda tunani barkatai.
★★★★�
Rashin reply d'in Galadima ya dameni, haka dai naita danne zuciyata dankar innarmu da Munubiya su fahimta, nacigaba da harkokina tamkar banida wata damuwa a zuciya, saima sallar dare damuka fara dagewa da tashi nida Munubiya, gakuma azumin damuka tashi dashi yau litinin.
Duk da innarmu ta fahimci inada damuwa batacemin uffanba, saidai tausayina na damun zuciyarta, tana dannewane kawai.
Munubiya kam tsaf tagama fahimta ta, amma itama saita nuna bata fahimci komaiba, taje tasamu innarmu da maganar son a d'aga bikinta again.
â€Å“munubiya ba wannan yakamata muyiba, addu'a yakamata muyima 'Yar uwarki, idan da rabo saikiga ALLAH ya kawo mata miji a cikin watanni 2nan dasuka rage kinji. nima nasan tana acikin damuwa, amma tana dannewa a zuciyarta saboda farin cikinmu. addu'ar dazamu mata itace tsantsar k'aunarta a garemuâ€?.
â€Å“shikenan innarmu, insha ALLAH zamu kuma dagewa da fad'ama ALLAH, itama ALLAH ya kawo mata ta hanyar da batayi zatoba, ya sakanka mata fiyeda sadaukarwar datayi, innarmu nasan sadaukarwar da 'Yar uwata tayine yasakata a wannan halin, ta sadaukar da farincikinta saboda ni, mizanyi na biyata nikamâ€?.
Murmushi innarmu tayi, tace, â€Å“addu'aâ€?.
★★★★�
Washe gari yatashi ya shirin tafiya masarautar su Momma, Harun yakira yace ya nema masa ticket.
Cikeda mamaki Harun yace, â€Å“yaushe kashigo k'asar Galadima?â€?.
K'aramin tsaki yaja, dan shifa yama manta Harun baisan da zuwansa ba, Link d'in hannun rigar milk d'in shaddarsa yake k'okarin sakawa, cikeda dakiya yace, â€Å“jiya nazo da daddare, kuma inagama yau zan komaâ€?.
â€Å“tofa, amma baka cikin masarauta?â€?.
â€Å“no a hotel Na saukaâ€?.
â€Å“ok barato a nema ticket d'in, sai muzo mu d'aukekaâ€?.
â€Å“karka damu harun, banason kowa yasan nazoma, muhad'u dakai kawai a airport â€?.
Koda suka yanke wayar sai yaja tsaki, gaba d'aya yakoma mak'aryaci, abinda yatsana arayuwarsa fiye da komai kenan (k'arya) amma sai gashi shi yana zundumata, â€Å“Astagafurullhâ€? yashiga maimaitawa a zuciyarsa.
Tsaf yafito cikin shadda milk color (nakula yana k'aunar milk) d'inkin rigar 3quarter, harda su hula, yayi k'yau sosai, yafito ainahin sa na cikakken bahaushe kuma basarake, ya fesa turaraensa Na kullum, komai nasa dayazo dashi ya had'a a waje d'aya. sannan yakashe kayan wutar bedroom d'in.
Afalo ya iske Muftahu zaune yana jiransa, yad'anyi mamaki amma sai bai nunaba, yabashi hannu suka gaisa.
Muftahu yace, â€Å“zaka dawo ta nan kenan?â€?..
Kai Galadima yad'aga alamar a'a, sannan yanufi kayan wutar falon yafara kashewa. saida yagama komai sannan ya kalli Muftahu alamar suje.
Murmushi kawai Muftahu yayi, danya lura yau miskilawanne aka.
Sun isa airport, lokacin shima harun harya je, mamakine ya kama harun Dan ganin Galadima tare da Muftahu, shima yanzu yana mamakin yanda Muftahu ke kuma kusanta kanshi da Galadima, baice komaiba yabashi hannu suka gaisa kamar yanda yabama Galadima.
Harun yanason suyi magana da Galadima amma ga Muftahu a wajen, sai kawai yashare akan sayi a waya kawai.
Basu wani dad'e a airport d'inba jirgin su Galadima yatashi.
★★★★
Yau hankalin kowa a tashe yake agidanmu saboda gwaggo Safiyya da aka kawo batada lafiya, dayake ba'anan kusa damu take aureba, tanacan wani gari daban, tun lokacin bikinsu yaa Hameed tamasu Abba complain akan batajin dad'i, amma kunsan maza darashin d'aukar Abu serious, sai basu maida hankalinsuba.
Ita kuma kunya tahanata kuma musu maganar, har aka gama biki ta tafi, ashe baiwar ALLAH ciwo nata cin jikinta babu Wanda yasani, tun tanayi a tsitsaye har takai ga kwanciya, yaranta sun kaita asibiti amma basuga wani canjiba, hakanne yasa suka maidota gida, Dan aganinsu dai su Abba sunfi mahaifinsu k'arfi.
Aiko suna isowa babu 6ata lokaci aka wuce da ita asibiti.
Dan danan aka fara bata taimakon gaggawa.
Muda innarmu ne kawai da innaro a asibitin, amma matan gidanmu babu wace tabimu, kusan mudasu baba k'arami muketa shiga da fita a asibitin dan ganin komai ya dai-daita.
Kusan yamma saigasu Safara'u lokacin ma gwaggo Safiyya tana barci, yaranta duksunyi jigum-jigum da innaro saboda tashin hankalin dasuke ciki.
Har dare ba'abar kowa yashiga wajen taba, sai su Dady kawai, ganin dare yayi akace mu muje gida kawai.
Haka muka tafi akabar innaro da aunty habiba d'iyar gwaggo safiyyar ta uku, itama tayi aure amma tafito, yanzu zawarci takeyi. saikuma yaa Anas da aka barmusu saboda ko wani Abu zai taso.
★★�
Tunda yafito daga jirgi ya hango tawagar masarautar kakannin nasa, yasan tarbarsa sukazoyi, inhar zaishigo haka sukeyo gayyar tarbarsa, saikace wani bak'o daban, gefe yayi da fuskarsa dankarsu gansa, sashen motocin da akan d'auka drop ya nufa, duk manyan motocine da aka tanada dama domin irinsu, d'aya yabud'e da Kansa yashige da sauri, alamar yayma driver d'in suje.
Tacikin glass yake kallonsu yana murmushi, yanda suketa d'aga kai nason hangosa, suna fita daga airport d'in ya kwantar da kansa ajikin seat ya lumshe idanunsa yana tunanin wane hukunci mai martaba zai yanke akan maganar, shin ya amincene? Kokuwa?.
Driver yace, â€Å“oga ina muka nufa?â€?.
Bai bud'e idonsaba kuma bai d'agoba, yace â€Å“gidan sarkiâ€?.
Ta madubi driver n ya kallesa, â€Å“yalla6ai ko kaine ma dai akazo tarba daga masarauta?â€?.
Murmushi kawai yayi batareda yace komaiba.
Jin bai amsaba sai driver yakama bakinsa ya tauke shima.
Ganin shine yasa dogarai suka bari aka shigar dashi har cikin masarauta, tunda yafito bayi da hadimai keta zubewa suna kwasar gaisuwa, hannu kawai yake d'aga musu, fuskarsa ad'an sake take, bai d'aureba baikumayi murmushi ko dariya ba kai tsaye.
Tuni an kar6i kayansa an nufi sashin inno dasu, shikuma yanufi fada, Dan yasan yanzu Sarki suna fadanci.
Cike fadar take da 'yan majalissar Sarki anata fadanci, bayan an masa iso yashiga da sallama, nanfa dogarai suka fara zuba masa kirari.
Hannu kawai ya d'aga musu ya rissina yana mik'a gaisuwa ga Sarki.
Sarki da fuskarsa tacika da fara'ar ganin jikan nasa ya amsa cikin lumshe idanu.
Nan dogarai suka d'au da fad'in â€Å“sarki ya amsa maka sarkin gagara badau na gobe, an gaida magajin sarki, galadiman gagara badau, ALLAH yabaka zamani irinna sarki gagara badau.
Galadima Yakuma rissinawa ya mik'a gaisuwa ga 'yan majissar sarki, suma cikeda fara'a suka amsa, kowa yasan irin tsantsar k'aunar da sarki kema jikan nasa a masarautar.
Atake anan sarki ya sallami kowa, fadanci yatashi saikuma gobe idan ALLAH ya kaimu, yau yanada ganawa ta musamman da jikansa.
Haka kowa yatashi yana musu addu'ar kasancewa cikin aminci.
Tareda Galadima sarki yashiga cikin gidansa, hannunsa Na rik'e da Na Galadima, ba sabon Abu bane hakan a masarautar, duk Wanda yakwana yatashi acikinta yasan matsayin Galadima azukatan masu masarautar.
Akatafaren falon sarki suka yada zango, babu dad'ewa da shigowarsu saiga jakadiya da kuyangi uku, kowanne d'aukeda babban tire, bayan sun dire komai suka zube suna kwasar gaisuwa wa sarki, sannan suka gaida Galadima.
Jakadiya ma ta rissina ta gaida Galadima damasa barka da zuwa masarautarsu.
Bayan fitarsu Galadima yakuma risainawa a girmame ya gaida sarki kakansa.
Cike da murmushi sarki ya amsa yana kamo hannunsa, â€Å“Muhammad Sameer! kana lafiyaâ€?.
â€Å“Alhmdllh ranka ya dad'eâ€?.
â€Å“Masha ALLAH, ya kabaromin Zeenah ta da jikin babanka da 'yan uwanka kuma su Haneefa?â€?.
â€Å“Momma lafiyarta lau, hakama jikin Abie Alhmdllh, suma su aunty mimin hakaâ€?.
â€Å“to Alhmdllhi, ALLAH yacigaba da jagorantar lamuranku ya albarkaci rayuwarku ta gobe da jibin jibimaâ€?.
Murmushi Galadima yayi yana amsawa da amin.
Sarki da Galadima tare sukaci abinci, (tun yana k'arami dama idan yazo gidan hakance ke faruwa tsakaninsu) Sunci sun k'oshi sukayi hamdala ga ALLAH.
babu wani 6ata lokaci sarki yashiga masa bayanin kiran nasa akan maganar da Fateema (mom) tazo masa da itane jiya, shima ya zauna yayi nazari yagane hakan shine dai-dai, Galadima ya auri Munaya.
tur6une fuska Galadima yayi tamkar baisan komaiba, yace â€Å“ranka yadad'e ka gafarceni, ammafa ni bata minba aiâ€?.
Sarki yay murmushinsu Na manyan k'asaitattun masu ji da mulki, â€Å“basai tayi makaba Muhammad, domin sanda Na aurama babanka Zeenah itama bai mataba, amma saboda biyayya dakuma tausayin d'iyar 'Yar uwarta ta amince tamin biyayya, to kaima hakan nakeso gareka, ka amsamin da to kawai saimu zauna lafiya, kasan magana biyu ba halina baceba koâ€?.
Jinjina kai Galadima yayi yana kuma tankwashe k'afarsa, cikeda girmamawa yace â€Å“ALLAH ya huci zuciyarka ranka ya dad'e, Na amince da za6inka, ALLAH yabani ikon rik'ewaâ€?.
Cike da tsantsar farinciki Mai martaba ya rik'o hannun Galadima, â€Å“Muhammad ALLAH shiyi maka albarka, ya tsareka dadukkan sharri, ALLAH yabama mahaifinka lafiya kajiâ€?.
â€Å“amin ranka ya dad'e, ngd sosai â€?.
Daga nan hira suka cigaba dayi cikin tsantsar soyayya da k'aunar juna, kowanne yanajin d'an uwansa sosaih a ransa.
Kusan atare suka yini, inno tun tana zuba idon shigowar Galadima harta hak'ura. Galadima bai shigo wajenta ba sai bayan sallar magriba.
Tundaga k'ofar sashenta hadimai keta kwasar gaisuwa, tuni labarin tahowarsa ta iske inno, hakan yasa ta k'imtsa da k'yau, ta sallami bayinta masu mata hidima.
Fuskarsa d'auke da k'ayataccen murmushi ya k'araso falon, bai zauna ko inaba sai jikin kakarsa, oh my sweet inno I miss you so much wlhy�.
Kunnensa tad'anja kad'an, cikeda tsokana tace â€Å“miskili kafi mahaukaci ban haushi, aini harna fara shirin yo bikonka daga turakar mai martabaâ€?.
Yayi 'Yar dariya yana fad'in â€Å“tuba nake ginbiyar papiâ€?.
â€Å“ja'irin kaya, bazaka canjaba dai? ya kabaro iyayen naka da 'yan uwanka?â€?.
â€Å“kowa lafiya lau ranki ya dad'eâ€?.
â€Å“to Alhmdllhi â€?.
Nanma hirarce ta 6alle tsakanin kaka da jikanta, kan mace me nanma an cika masa gaba da kayan itatuwa, shikuma yana zubama inno shagwa6ar daya saba tana biye masa.
Masu jiran Galadima kuwa a airport saida sukaga kowa yagama fita ajirgi babushi sannan wani dogari yakira sarkin fada yake sanar dashi sufa basuga Galadima ba.
Sarkin fada yace â€Å“yo kunacan kuna shashanci yaza'ayi Ku gansa, shi harma sun shige cikin gida da sarki â€?.
'yan uwansa ya sanarmawa suka tattaro suka dawo masarautar.🤣
Dole a nan masarautar ya kwana, washe gari ya zagaya duka sashen sauran matan sarki ya gaidasu a mutunce. suma dai sunmasa tarbar mutunci kamar yanda suka saba, duk da dai taciki Na ciki. Sannan sai sassan iyayensa yayun momma da k'annenta, dukda dai bako ina yashigaba.
Yanzunma tare sukayi karin kumallo da maimartaba, sannan suka fita fada tare, da Galadima akayi fadanci yau, yana gefen adalin kakansa.
Washe gari da safe ya tattara inasa-inasa ya cane India, yabar tsofin da kewarsa, shima yatafi yana kewarsu.
********
Gwaggo Safiyya tacigaba da samun kulawa sosai, dukda dai tanad'an jin jiki, kullum matan gidanmu sukanzo sau d'aya, muma dai makaranta tasa bama yini a asibitin, amma kullum da safe mukanzo mu kuma dawo da yamma.
Matan gidanmu kam jarabar innaro tasakasu k'ok'arin zuwa kullum, dan tace wlhy duk Wanda bata zuwa saitayi Dana sanin saninta.
Wannan furuci ya d'an tsoratasu, dan kowa agidan yasan wacece innaro, idan kaga mutuncinku ya d'ore to kana cinna mata 'yan canji ta k'ark'ashin k'asaneğŸ™Å , amma kana hanata gobe bazai hana ta karta maka rashin m ba🤣. (Ho innaro mu ta mutunci🤸ğŸ»Ã¢€Ã¢™€, ina yinki over ginbiyar Malam farukuğŸ˜Å“ğŸ™Å )
⛹ğŸ»Ã¢€Ã¢™€
Abin yafara tsoratani ganin har sati 1 dayin maganarmu dasu Galadima amma babuko labarinsu, tun ina saran yau gobe har na daina lissafin ma, ganin zan saka kaina a damuwa nacirema zancen a raina gaba d'aya, domin Na gama fahimtar maganar Galadima da abokinsa k'aryace, maybe ma mafarki nayi naketa shirmena kawai.
A tsaitsaye damuwa tafara ramar dani a tsaye, sai idanuwa da dogon hanci.
Tun ina daurewa har Abu yaso yaci tura, ciwon kai Dana k'irji suka fara zama abokaina.
Ranar data kama sati biyu cif saiga bak'i su Abba sunyi, babu Wanda yasan daga ina suke, kuma su Abba basuma kowa bayanin komaiba dangane da bak'in. saida sukayi kwanaki uku da zuwa sannan naji wai wanine yakawo kud'in aurena yana son abama d'ansa.
Lamarin yabama kowa mamaki, nanfa 'yan gidanmu suka hau dariyar mugunta wai kwantai dai ya tabbata kenan.
Gugar zanar dasuke tayine ya fusata innarmu, tasakama Abba kuka akan bata aminceba, yaza'ayi su d'auki aurena subama mutumin dabasu saniba, idan su sun gaji dani itafa tanason kayarta.
Lallashi duniya Abba yayi dan innarmu ta fahimta amma Sam tak'i saurararsa, wannan ne karon farko da yaga tsantsar fushinta.
Yarasa yazai mata, dan shima lamarin Na damunsa, yarasa minene yasakashi amincewa yabada auren d'iyartasa ga mutanen?, shi dai kawai tsohon yamasa kwarjinine wlhy, dan jiyay ko kad'an bazai iya musa masaba. dukda talakawane kamarsa, harma yana ganin yafisu abubuwa da yawa.
Lamarifa yayi tsamari a d'an tsakaninnan a gidanmu, dan innarmu takasa kwantar da hankalinta, hakama abbanmu, yayinda 'yan gidanmu sukejin Dad'i kamar su had'a fati.
Nikuwa uwar gayya ai ba'a magana ma, nakira number Galadima yafi sau 200 amma tak'i shiga ko sau d'aya, lokaci guda nagama fita hayyacina, 'Yar uwata kanta dukta lalace kamar itace cikin matsalar.
Innaro kam ciwon gwaggo Safiyya ne ya d'auke hankalinta, duk da dai su Abba sun mata bayanin kawo kud'in nawa, amma cikin halin ko in kula tace su basu kawai, idan sun barni agidan kuwa najawo musu abin kunyar dayafi nabaya, harma tashafi sauran kannena suk'i auruwa tamkar ni.
Wannan furuci ya Sosa zuciyar abbanmu, amma saiya danne saboda girman mahaifiya.
An sallamo gwaggo Safiyya da kwana biyu jikina ya birkice nima, dole aka kwasheni aka kai asibiti.....
*********
A 6angaren sarki kuwa bayan tafiyar Galadima da kansa yazo masarautar gagara badau, an masa tarba ta girmamawa domin shid'in babban abokine ga kakansu Galadima wato (marigayi sarki Abubakar na lll).
Mama Fulani kanta in kunga yanda take girmama sarki (Abdul'fatah idris) saikusha mamaki Ku d'auka ba itace mai ji da kanta d'innanba da tsantsar nuna sarauta(gaba da gabanta yo🥴).
Sarki bai 6ata lokaciba ya sanar musu abinda yazo dashi, ganin tsantsar farinciki nayi ga mafi yawan jama'ar gidan, dan hukuncin sarki Abdul'fatah yamusu dai-dai, koba komai an k'ask'antar da Galadima d'in, Wanda yadace ace an sama masa d'iyar wani mashahurin sarki ya aura, kodan sarautar da ake da yak'inin shine yakama ta ya gada.
Murmushi papi yayi, saboda ganin farinciki zancensa a fuskokin wasunsu, yasan tabbas dawata manufa suke wannan farinciki, amma hakan bai damesa ba, domin shi da k'yak'yk'yawar niyya yayi. maganar sarauta kuwa sune suke ganin bazai iyaba saida wata d'iyar babban sarki, amma shi yanada yak'inin ko d'iyar shugaban talakawan duniya koda baiwace agidan Galadima ya aura sarauta ta ALLAH Ce.
Daga baya ya tsara musu yanda yakeso Neman auren ya kasance, bawai zasuje musu da rigar mulki baneba, yanason suje amatsayin talakawa domin ganin tarbar dazasu samu daga iyayen yarinyar, daganan zai gwada yak'inin tarbiyar gidan da mutuncin iyayenta.
A masarautar sarki ya kwana, washe gari sukayi shigar talakawa shida sarki jalaludden k'anin mahaifin Galadima, sai wazirin papi dana sarki, saikuma k'annen mahaifin Galadima biyu sannan aka sami tsohuwar mota suka tafi aciki bisa jagorancin wani dogari da sarki yasa yamasa binciken gidansu munaya.
Abinda basuyi zatoba shi suka samu, domin tarba ta mutunci da girmamawa suka samu dagasu Abba, duk da suna kallonsu talakawa fitik harma da yak'inin sun fisu komai.
Hakan ya burge sarki Absul'fatah (papi) shi kansa sarki jalaludden lamarin ya masa dad'i. Sun bada kud'in gaisuwar farko data biyu naira subu 30 kacal.
Sai bayan tafiyarsu sannan su Abba sukaita mamakin kansu anya mutanen bada wani siddabaru sukazo musuba? Yazama ayi basu sansuba amma suzo su kar6i auren 'yarsu? sukuma su basu babu musu kamar sun gaji da ita. (Niko nace kwarjinin sarauta suka muku abbağŸ˜Å“😂).
Can kuma dasu sarki suka tafi sunata yabawa suma, sarki Absul'fatah dad'i dukya gama cikasa, lallai Galadima yasamu tsatson daya dad'e yana masa fata da addu'ar samu.
Momma koda papi yakira yamata bayanin bataji komaiba, saima addu'a data masa da kuma nuna farin cikinta akan lamarin, koba komai zataga auren Galadiman ta, amma saida tayi hawaye data tuna za ayi auren Galadima babu mahaifinsa, kamar yanda akayi na Haneefa (Aunty Mimi).
Data sanarma Abie saiya fad'ad'a murmuahinsa, yayinda hawaye ke zirara ta gefen idanunsa, ALLAH sarki iko da falala, tun yaronsa na shekara 5 a duniya yake a wannan halin, gashi har zaiyi aure, yagodema ALLAH da wannan jarabawa shikam.
A satin papi yaje India ma da kansa, yaduba jikin Abie dakuma maganar auren Galadima dayayi musu, nanma saida Abie yay hawaye, amma sarki Absul'fatah yayta masa nasihar yawan hak'uri da kar6ar k'addara, ya nuna masa sunada yak'inin zaici ribar can.
Abie yana son surukinsa kuma aminin mahaifinsa sosai, dan duk lokacin dazaizo dubashi da irin salon nasihar dazai masa wadda zai k'ara tasirantar da imani a zuciyarsa.
Galadima kuwa sai wani basarwa yakeyi irin shifa abin bai d'ad'ashi da k'asaba, kuma bayason abin, aurenma dole za ai masa, haka yaytaima Abie korafi yana shagwa6a.
Murmushi Abie yay tayi yana lallaahinsa da idanun.
Cikin tsokana sauban dake d'ayan gefen Abie shima yace â€Å“yaa Sam to kawai ni abani kana, kaga na huta da zuwa tad'i k'ofar gidan kowaâ€?.
Wata uwar harara Galadima ya maka masa, wadda tasaka Momma da auty Mimi da samha da jakadiya dariya, shi kansa Abie murmushine ya fad'ad'a afuskarsa.............âœğŸ?
Wannan shine yafaru 6angaren Galadima munaya bata saniba.
Guys kuje zuwa kawai, k'ila zuwa dare kujini da bonus⛹ğŸ»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€
ALLAH yabama munaya lafiya.
Barka da juma'a.😄✋ğŸ?
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*ğŸ˜ÄŸÅ¸‘ğŸ»
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ğŸ»_*
👉ğŸ»1âƒ?9âƒ?
.......Kallone ya koma sama yayinda kuyangin suka shigo cikin gidanmu, na d'akima tuni sun fara rige-rigen fitowa, baba k'arami da fitowarsa kenan daga sashensa yak'araso ga kuyangin, domin tambayarsu daga ina haka?.
Baiwa d'ayace tabashi amsa da fad'in basu kad'ai bane, masuyin bayanin suna waje.
Fita yayi sukuma suka ajiye kayan gefe suka kuma fitowa domin kwaso sauran.
Muna falo a zaune inna lami ta tsaremu sai mun sha romon wani nama da aka dafa k'anana, sai yatsine fuska mukeyi saboda rashin dad'in naman. shigowar Ahmad da Aryaan da gudu yasa mama Rabi'a tambayarsu lafiya?.
Ahmad yace â€Å“mama wlhy bak'ine da akwatina da yawa suka shigoâ€?.
Gaba d'aya muka zuba masa idanu, kafin wani yay masa tambaya a cikinmu mukajiyo sallamar baba k'arami.
Innarmu ce tamik'e domin fitowa, ganinsa da manyan mutane cikin alk'yabbu yasata fad'in â€Å“baba k'arami bak'i mukayi?â€?.
Cikin washe baki yace, â€Å“wlhy kuwa maman biyu â€?.
Itama murmushine shinfid'e a face nata, tabasu hanya suka shigo falon, duk suka zazzauna.
Muduka muka durk'usa muka gaisasu, yayinda suka kuma gaisa dasu innarmu cikin mutunci.
Fita baba k'arami yayi yasa yaa Anas ya kunna Gen..... dayake babu nepa. Shikuma yakuma fita da hanzari domin nemawa wad'annan bak'i masu bazata kayan tarba, bayan yakira Dady da Abba ya Sanar musu.
Kaf matan gidanmu suka shigo, kowa yanason jin daga ina kuma.
Mukam d'akinmu muka koma muda su Ayusher muna hasashen bak'i daga ina haka? da gani dai kasan jinin sarautane, ko kad'an ban kawo Galadima a rainaba ma, dan narigada Na shafe labarinsa ni.
Suna cikin gaggaisawa da matan gidanmu saiga innaro tashigo, kai kace an wurgotane. baki tarik'e tana fad'in â€Å“o ni Marwanatu, manyan bak'i irin wad'annan surasa gurin sauka sai 6angaren Ai'sha? kuko bayin ALLAH daga ina haka? â€?.
Su aunty Mimi basu fahimci zancen taba, dan haka duk sai sukayi d'an murmushi, matan gidanmu kuwa kowacce tayi k'asa da kai dariyar mugunta Na cinta, Innarmu dai bata tankaba, hakama mama Rabi'a, sai inna lami ce tace, â€Å“yo inna in banda abinki waka hana rana fita idan lokacin fitar tata yayi?â€?.
Kallonta innaro tayi zatayi magana baba k'arami yashigo da sallama, su Yaa Anas na biye dashi da kayan ciye-ciye nik'i-nik'i, bayan sun ajiye suka gaishesu cikeda girmamawa suka fita.
Zama baba k'arami yayi suka sake gaisawa, sannan yace, â€Å“kufayi hak'uri, mukam duk kun sakamu a duhu wlhyâ€?.
K'asaitaccen murmushi aunty Mimi tayi, domin dama papi yamata bayani akan komai na 6oye musu dasukayi. ta gyara zamanta sosai â€Å“Alhaji daga masarauta muke, munkuma zo kawo kayan k'anwatane Gimbiya munayaâ€?.
Kusan kowa dake falon saida ya waro idanu waje, domin jin furicin aunty Mimi, wasuma zuciyar tasu kad'an tarage tayo tsalle waje.
Aunty Mimi bata damu da yanayin nasuba tacigaba da fad'in â€Å“kuyi hak'uri fa, nasan nakuma sanyaku a wani duhun, mai martaba sarki Abdul'fatah da maimartaba sarki Jalaludden Abubakar, sune sukazo Neman auren yarinyar Ku Munaya wa d'ansu Galadima Muhammad Sameer Saifuddeen Abubakar, sun 6oye muku kansune saboda wani dalili, amma sun aikomu da sak'on ban hak'uri a gareku, yanzu dai mun kawo kayan lefen Munaya ne gasunanâ€?.
Jin jina kai kawai baba k'arami ke iyayi, bakinsa yakasa rufuwa saboda d'unbin farinciki da al'ajabin dake dank'are a zuciyarsa, yanzu nan daman manyan sarakunane agabansu a wancan karon sukazo Neman auren d'iyansu, lallai sun godema ALLAH dabasu aikata wani Abu Mara k'yauba agaresu, lallai ya yarda kwarjinin mulkine yasakasu mik'a Auren d'iyarsu ga mutanen dabasu saniba.
Ai su madam innaro sai aka zauna k'asa babu nauyi, muryarta har zuga take tace â€Å“ranki ya dad'e wai gaskene saboda ALLAH?, kokuwa wasa kikeyi?â€?.
Murmushi aunty Mimi tayi, sannan ta kalli su Ummu hasheem da suma suketa murmushi, kallonta ta maido akan innaro, â€Å“hajiya kaka mizaisa muzo muyi muku wasa irin wannan akan magana mai muhimmanci irin ta aure, tabbas maganar nan gaskiyace, munama fata gobe idan ALLAH ya kaimu iyanzu Munaya tazama d'aya daga cikin zuri'ar masarautar gagara badauâ€?.
Innarmu da mama Rabi'a juna suka rungume suka fashe da kuka, yayinda innaro tamik'e ta callara gud'ar data jawo hankalin tawagar jama'ar 'yan biki, sai kawai tashiga taka rawa.
Dariya sosai tamaba su aunty Mimi, shi Kansa baba k'arami dariyar yayi yana girgiza Kansa da mamakin innar tasu mai kayan arzik'i Dana tsiya.
Matan gidanmu kam ba'a magana, kowacce tayi d'if takasa koda kwakwkwaran motsi, kowaccensu jitake tamkarma tafasa ihu take a nan.
Muryar gwaggon halimatu na rawa tace â€Å“wai da gasken dai Munayar gidan sarauta zatayi aure?â€?.
â€Å“kwarai kuwaâ€?. ‘innaro tafad'a tana mata wani kallo, â€Å“jikata sai gidan sarauta, masu bak'in cikin kuma sai a maceâ€?.
Lallai maganar innaro tadaki zukatan dukkan matan gidanmu, Sanin halin innaro da baba k'arami yayi saiyace duk afita abama bak'i waje susha koda ruwane.
Jiki babu kwari sukaita Jan k'afa suna fita Su da danginsu 'yan biki da gud'ar innaro tajawosu shigowa. bak'in cikin kuwa k'arara a fuskokin wasunsu, maman su yaa hameed tayi taga-taga zata fad'i saida aka taryota.
Gwaggo Safiyya tace â€Å“lallai jama'ar gidannan yau ake *RAINA KAMA KAGA GAYYAFA* duk Wanda kake Kallon bai kaiba to tabbas watan watarana shine zai kereka, babu ruwan arzik'i da mugun gashi, Wanda yace shine to tabbas bashi banebaâ€?.
Su Ayusher suka shigo suna gumtsa mana, kallonsu kawai nakeyi amma badan na gaskataba, munubiya ta rungumeni ta fashe da kukan dad'i, kallonta kawai nakeyi nakasa koda motsi, to murnar Auren shekara d'aya zanyi? Kokuwa murnar Ashe galadimane mijin nawa? bawani can da ban ba kamar yanda muketa hasashe?.
Ban iya ta6uka komaiba wata k'yak'yk'yawar budurwa tashigo, daka ganta kaga wadda Hutu yagama ratsawa, babu shakka zamu iya zama sa'anin juna da ita, fuskarta d'auke da murmushi tace, â€Å“to ina amaryar Uncle Sam d'in?â€?.
Feena ta nuna ni da hannu itama tana murmushi.
Gadon ta hayo batareda jiran abata iziniba, ta mik'amin Chocolates guda biyu tana kuma fad'ad'a murmushin nata.
Cikin mamaki muryata a sanyaye na girgiza mata kai nace â€Å“yar uwa namiye?â€?.
Hannuna takamo tasakamin tana 'yar dariya, â€Å“inji Uncle Sam yace nabama matarsa, sunana Samha, d'iyar yayar Uncle Sam â€?.
Duk da mamakin daya cika zuciyata, hakan bai hani mata murmushiba, nace â€Å“nagode Samhaâ€?.
Tad'an langa6e kai alamar itad'in shagwa66iyace tace , â€Å“zan dai fad'ama Uncle Sam kin gode, lallai Uncle ya iya za6en k'yak'yk'yawar sarauniyar gagara badau mai jiran gado insha ALLAHUâ€?.
dariya su Bilkisu sukayi, nidai nakasa cewa komai, sai d'an murmushi danayi.
Ta dafa munubiya takuma fad'in inason twins sisters arayuwata, dan ALLAH nima kuna sona?�.
Yanzun kam kasa daurewa nayi, nima saida na dara kamar yanda su munubiya ke dariyar, nakula ko kad'an Samha batada girman kai irinna 'ya'yan sarauta, sannan tanada surutu gaskiya�.
Cikin shagwa6a ta langa6e kai gefe, â€Å“ALLAH da gaske nake kubarmin dariya, ina addu'ar ALLAH yasa nanda wata 9 aunty ki Haifa mana twins mumaâ€?.
Amin su Ayusher suka amsa atare.
Matsowa tayi kusa dani tafara mana hotuna, nidai nakasa ma magana, lallai Samha akwai rawar kai, ta tubure da shagwa6a wai sainayi murmushi kamar yanda munubiya tayi, tanason taje tabama Galadima tagani kozai iya banbancemu. Babu yanda na iya dole na murmusa akayi, sannan mukayi gaba d'aya.
Bata bar d'akinba saida mama Rabi'a tashigo kiranta zasu tafi, aikam kamar tayi kuka, dan bataso tafiyarba, sai dai tace anjima zasuzo wajen brothers and sister's event.
Har k'ofar gida su Ayusher suka mata rakkiya, dan lokacin su aunty Mimi harsun fita, sunso ganina amma sukayi shiru kar aga kamar dawata manufa sukayi hakan, sun hak'ura tunda dai insha ALLAH gobe ina cikinsu.
Basuci komaiba dai a kayan da'aka jibge musu sai ruwa, dan haka baba k'arami yasaka aka bisu dashi mota, yace inhar ba wai bazasu iya cin cimar tamu bane to dan ALLAH suje dashi koda bazasuci ba su bada.
Godiya sukayi, suna mai yaba halaccin wannan gida mai cikeda karamci, dukda dai sunkula akwai lauje cikin nad'i gameda wannan family d'in, musamman yanda wasu suka kasa 6oye hassadarsu, aunty Mimi ta murmusa a zuciyarta tana fad'in Ashe ba masarautar mu kawai baceba keda irin wannan kitimurmurar ta family.
Mukulin farar motar da aka zubo akwatinan suka dank'ama baba k'arami sukace ta amaryace.
ai yanzu kam rasa abin fad'a baba k'arami yayi, yak'agara 'yan uwansa su dawo suga wad'annan tarin baiwa da hikimar ubangiji da yayma d'iyarsu, wadda akulum ake ganin mahaifiyar yaran a k'ask'ance acikin gidan, sai gashi tazama *RAINA KAMA.....*
Bak'i na tafiya gwaggo Safiyya tasaka aka baje manyan tabarmi a tsakar gida, aka fiddo akwatinan domin kowa yagani, makwafta duk sun shigo suma kam dan kar ayi babusu.
Gaba d'aya gidan yacike da shewa da hayaniya, tun anama irga kayan har aka bari, saibi da idanu, 'yan bak'in ciki kam sun kume waje guda, sai kukan zuci, wasuma kasa daurewa sukayi suka bar wajen.
Kasancewar su Ayusher duk suna can nashige toilet d'inmu nashiga raira kuka, nifa bammasan yanda zan fasalta muku yanda nakejiba wlhy.
★★★★
A 6angaren sister's d'ina kam su Safara'u harda kukansu, fauziyya ce kawai ta nuna farincikinta, dan har d'aki tashigo ta rungumeni tana ALLAH ya sanya alkairi.
maganar tashin hankali ga jama'ar gidanmu ba'a magana, sunma rasa yanda zasu masalta lamarinma, maman yaa hameed data kasa hak'uri saita saka masifa da zage-zage wai ai munafurcine su abbanmu suka shirya, wannan zancen k'aryane akwai magana a k'asa, 'yan koranta ma irinsu momy Hadiza suna tayata.
Nanfa gidan ya hargitse da hayaniya, kowa da abinda yake tofawa, innaro dai Abu biyune ya dameta, farinciki dakuma damuwar abinda tayita ma innarmu shekara da shekaru, yau kuma gashi ALLAH ya d'aga darajarta, ita dawanne ido kuma zata kalli Ai'sha.
Babu Wanda ya tanka a 6angaren innarmu, saima farinciki dasu mama Rabi'a ketayi abinsu, inna lami kuwa da aunty salamah sunata callara gud'a dawasu acikin matan anguwarmu, hakanne yakuma harzuk'a su maman Safada'u, suka murje idanu sunata zuba tsiya, danginsu na tayasu.
Innarmu dai tana daga cikin d'aki abinta, sai zuba murmushi take tana sharar hawayen dad'i, yau kokad'an rashin mutuncin 'yan gidanmu bai 6ata rantaba, saima wani farin ciki dasuke sakata.
🤣🤣
Maganar sisters and brothers event kam ai bai yuwuba yau, dan gidanmu gaba d'aya a harmutse yake, ga 'yan anguwa sunata turuwar zuwa ganin kaya harda mota.
Nikam ma zazza6ine yagama rufeni tunda nagama kukan, duk wannan kacaniya da akeyi ina cikin bargo k'udundune, su munubiya kam sunacan tsakar gida sun kasa sun tsare akan kayan gudun masu suruf bahanağŸ˜Å“🤣.
Da k'yar aka tartare kayan aka kaisu falon baba k'arami kasancewar magriba ta gabato, sai bayan isha'i su Abba da Dady suka gani, ranar Abbanmu shima saida yayi kukan dad'i, ALLAH Sarki Ai'sha, nagodema ALLAH da wannan babban al'amari yashigomin ta 6angaren tsatsonki, kema yanzu k'ya samu 'yancin kanki agidan mijinki, 'ya'yanki zasu samu 'yanci a gidan mahaifinsu, dama akance ka yarda da k'addara kakuma godema ALLAH a yayin da ya jarabceka, Ashe sharrin da akama d'iyarsa zai zame mata alkairine, sun had'ata da babban mutum domin 6atanci agareta dashi kansa Ashe zai zama sanadin alkairi a rayuwar yaranne, dan yasan inba dan wannan abin yafaruba ina Galadima zai ga munaya har iyayensa sunema masa aurrenta? hikimar ubangiji yawane da ita, yakan jarabeka domin kankare zunibinka, kokuma danya d'aga darajarka ta inda bakayi zato ko tsammaniba.
★★★★★★
Labarin tarbar mutunci dasuka samu tuni ya karad'e masarautar, wasu kam dariyama abin yabasu, ina wata tarba dazasu samu ga talakawa fak'irai. suna dai fad'ane dan kar amusu dariya.
Mama Fulani koda labarin yaje kunnenta saita ta6e baki tana murmushi k'asaita, Wanda ita kad'ai tasan fassarar kayanta.
Tsaf yagama shiryawa zaije sashen da aka sauke abokansa a cikin masarautar, dan babu damar saukesu a 6angarensa, saboda angama masa gyara tsaf amarya kawai ake jira, su aunty Mimi ma dasuka kai lefe sun Sanar da amaryarsu kawai suke buk'ata, basai su Abba sun wahalar da kansuba wajen kaita da komai. Wannan dalilin yasaka aka yanke shawarar k'arama munubiya kayan munayar kawai, da safe za'aje a kuma jera mata su a gidanta😄.
Cikin takunsa na kasancewar cikakken namiji mai tashen k'uruciya ga jinin mulki dake yawo ajikinsa yafito, waya ce manne a kunnensa, yayinda d'ayan hannunsa ke cikin aljihun jeans d'insa, bayi da hadiman gidan sai zubewa sukeyi suna kwasar gaisuwa, kansa kawai yake d'aga musu yayinda yake cigaba da wayarsa da Momma wadda tana India ita batazoba.
Samha tak'araso gareshi a hanzarce, â€Å“Uncle ka tsaya mana please â€?. ‘tayi maganar a shagwa6e saboda ganin ya basar da ita tamkar baima gantabaâ€?.
d'an juyowa yayi ya kalleta sannan ya d'auke idonsa yana cigaba da Murmushin sa na k'asaita saboda addu'ar da Momma ke jero musu ta zaman lafiya da samun albarka ta har abada acikin auren daza'a d'aura a gobe. jiyake tamkar yace Momma ta dainama auren shekara d'ayannan addu'a irin haka, shifa harma tausayi suke bashi yanda suke nuna farin ciki da zumud'insu akan auren, musamman idan ya kalli yanda masarautar tagama cika tab da dangi takowanne 6angare, ga tawagar wasu masarautu dasukayo gaba tun yau, hakama 'yan siyasa ba'a magana, dan ba k'aramar gayya papi da Sarki sukaima wannan aurenba, kasancewar shine jika namiji na farko dazaiyi aure a masarautar, Wanda kuma kowa ke saka ran shine magajin sarautar masarautar.
Ita dai Samha tana tsaye tana kallonsa harya kammala wayar da Momma ya kashe.
Had'e fuskarsa yayi yana hararta, â€Å“to maganatu miya faru kuma? kike kwalan kira tundaga wata uwa duniya?, wai sai yaushene zakiyi hankali Samha?â€?.
Baki ta tunziro gaba, idonta harya cika da gwalla â€Å“amma dai Uncle aina fara yin hankalin ko, kumafa wani Abu Nazo na nuna maka, naje Sashenka wannan sarkin k'ofar yawanice kana wajen mai martabaâ€?.
Kansa kawai ya girgiza yana kallonta, saida takai aya sannan yace â€Å“to aini inada abunyi, yanzuma ba wai sauraren naki zan zauna yiba, dan nan ba India bane, ba'a ganina available ko yaushe OK?â€?.
Harya juya zai tafi tarik'o hannunsa tana daddaga k'afafu idonta na zubar da hawaye.
Kansa ya dafe domin sanin fitinar Samha, tace,
â€Å“please Uncle Sam 2munutes toâ€?.
Juyowa yayi tamkar zai maketa, saikuma komi ya tuna ya fasa, d'an cije lips d'insa yayi yana hararta, â€Å“ke wai wace irin fitinanniyace ne?, Uwarmi to zaki fad'amin?â€?.
Dariya tayi tana share hawayenta dan ganin tasami nasara, wayarta ta daddana sannan ta mik'a masa.
Nanma Harar tata yayi kafin ya kar6a, itace yagani a photo da 'yammata biyu masu kama d'aya, kamarma yarinyar dasuke shirin auren contract, harya yatsina fusaka zaice suwaye? saikuma yatuna. d'an murmushi basarwa ya saki kafin ya kalli Samha da ta tsaresa da idanu. â€Å“Uncle ina aunty Munaya anan? â€?.
Wayar yamik'a mata yay gaba abinsa yana fad'in titsiye zakimin ma kenan? an fad'a miki bazan ganeta baneba?�.
Baki ta turo tana k'unk'uni, â€Å“waikai Uncle Sam bazaka ta6a canjawa baneba? kai kenan kullum sai jan ajin tsiya, shiyya sama ALLAH yayoka jinin sarauta wlhy, Aunty Munaya kin bani da wannan mijin naki mai k'asaitar tsiya, aiko wlhy tunda kace haka saina had'a maka mugunta gobe a wajen dinner â€?.
Ta tuntsire da dariya saboda tuno mizata shirya masa.
★★★★�
*Rana bata k'arya........*⛹ğŸ»Ã¢€Ã¢™€
Yau mun wayi gari safiyar d'aurin aure, gida yakuma d'inkewa da jama'ar dukda d'aurin Auren na Azhar ne bayan sakkowa masallacin juma'a.
Tun jiya banida lafiya, amma na hana su Ayusher fad'ama kowa, sai Magani suka samo min nasha, itama dai Munubiya duk sukuku take, babu abinda ke damummu sai jimamin rabuwa da juna, dan itama kusan zazza6inne ma ta kwana dashi, sai dai dayake nawa ya had'a da damuwa saina fita nuna jin jiki.
Jama'ar gidanmu dai a harmutse suka kwana, wasuma ko barcin basu sami damar yiba saboda ciwon hasada dake cin zukatansu, gashi gida d'inke da jama'ar babu damar matsawa koda nan da canne sai an gane, bare sufita neman mafitar tarwatsa Auren, waddama suke d'an samin tallafinta kwad'ayinta yasaka canja shek'a (innaro🤣), dan jiya da suke zuba tijara shigowa tayi tamisu tas, harma tana Neman tone musu asiri gaban tawagar 'yan biki, badan gwaggo Safiyya ta lalla6a taba ba'asan inda jarabar innaro zata tsayaba kam.
Ko karyawa ban iya tashi nayiba bare aje maganar wanka, ina kwance cikin bargo sai shar6ar kuka nakeyi babu wanda yasani.
Ahaka gwaggo Safiyya tashigo kiranmu nida Munubiya, da k'yar su Ameera suka samu natashi zaune ina tangad'i, gaba d'aya nayi wujiga-wujiga dani, da taimakon Munubiya dake rik'e da hannuna muka iso gidan innaro inda su Abba suke jiranmu.
Gaba d'ayanmu ne amaren aka had'a, abin mamaki saiga innaro ta kamani ta zaunar tanamin sannu, harda lallashina wai na kwantar da hankalina.
Kowa zuba mana idanu kuwa yayi, su Fiddausi sai jan tsaki suke a zukatansu sunajin wata tsanar innaro aransu.
Itakam bama tasan sunayiba, sai nannan takeyi damu nida Munubiya.
Nasiha mai ratsa jiki da 6argo sukai mana sosai, muhimmancin aure da hak'uri, biyya da tsoron ALLAH, kare hak'in miji da k'yautatama danginsa da iyayensa, k'arfafa zaman lafiya a tsakani da rik'e sirrin miji, banda biyema k'awayen banza sukaika su baroka, musamman ma da dukanmu zamu cigaba da zuwa makaranta.
Gaba d'ayanmu kowa hawaye yakeyi, musamman mani danakejin tausayin kaina dana iyayena dabasu San auren shekara d'aya nake shirin yiba nadawo garesu.
Munci kuka sannan aka sallamomu, tunda muka dawo sai aunty salamah ta saka mu agaba dole mukayi wanka, da k'yar muka amince aka mana simple kwalliya, muka saka dakakken leshin da mama Rabi'a tasa aka d'inka mana cikin kayan biki dasuka mana itada innarmu, less d'in blue ne da fararen bet ajikinsa, sai aka nad'a mana d'an kwalima blue, munyi k'yau harma bansan yazan musalta ba, nan su Ayusher suka hau zuba mana pictures. lokacin 12 tama wuce, masallacin anguwarmu daza'a d'aura auren yagama cika dank'am da jama'a, dayake bashida nisa da k'ofar gidanmu.
Cikin gidanmu kam ai ba'a magana, dan babu masaka tsinke, sai hayaniya kakeji wani bayajin zancen wani, rabin hirar jama'a kuwa duk akan zancen lefe nane da Wanda zan aura, wad'anda suka gani suna bama wad'anda basu ganiba labari.
Su siyama dai koma ganinsu ba ayi, dan suna taya iyayensu kishi da hassada, aunty Ramla da aunty Raihana sai aunty Hauwa'u ne kawai suka shigo sukaima innarmu murna har d'akinmu, amma aunty khaleesa ko k'eyarta bamu ganiba, kuma tunda safe tazo gidan daga ita har zarah, matar yaa hameed ma mama hanata zuwa tayi, dukda tanaso tazo tama innarmu murna amma surukarta takasa ta tsare, gashi bama dad'in zaman 6angaren takejiba, saboda 'yan ubanci na dangin miji da aketa nuna mata, itama matar yaa Naseer tashigo, dan har picture mukayi da ita, amma matar yaa Shafi'u ma bata shigoba.
Hakan duk bai dameniba, dan ni yanzu basune agabana ba, damuwata tarkon dana saka kaina na auren contract shike cazan tunani a halin yanzun, Wanda ko munubiya nakasa sanarma gaskiya lamarin.
*_1:30pm_*
Masallacin yagama cika taban mamaki, tuni tawagar gidan Sarki sun iso tun bayan gama sallar juma'a, d'aurin aurene daya tara manyan mutane ta dalilin gidan sarauta, manyan sarakunan k'asarnan da 'yan siyasa, governors senators attajirai na gida dana k'etare, talakawan gari da tawagar iyaye da dangin sauran angunan, abokan su abbanmu danasu yayunmu, abokan anguna da abokan arzik'i, dangin iyayenmu mata danasu abbanmu, kowa ya hallara, bakajin komai sai kad'e-kad'e da bushe bushe irinna gidan sarauta. president da Kansa ya iso wannan waje bisa gayyatar papi, bansan yanda zan musalta muku irin cikarda anguwarmu tayiba aranar, bama zaka iya gane taka maimai inane ake d'aurin aurenba. Su Kansu masarautar su Galadima sunsha mamaki, basuyi zaton auren Na Galadima zai tara jama'a manyan mutane hakaba, dubi da yanda ba d'iyar wata hamshak'iyar masarautar zai auraba. basu San abin ba anan yakeba wai *d'uwawu yafi fuska k'yawun gani*ğŸ™Å 🤥ğŸ˜Å“😂 inji masu iya magana......................âœğŸ?
Amin afuwa, mu had'u tomorrow danjin yanda d'aurin aurenba zai kaya⛹ğŸ»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€Ã¢›¹ÄŸÅ¸»Ã¢€Ã¢™€.
Barkanmu da dawowa😄✋ğŸ»ÄŸÅ¸¤ÄŸÅ¸?
*_ya ALLAH ma gafartama iyayenmu_*ğŸ˜ÄŸÅ¸‘ğŸ»[4/30, 7:45 PM] Sis Naja Atuh: *_Typing?_*
*_HASKE WRITERS ASSO...?_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_?RAINA KAMA......!!?_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce??_*
??2?1?
.......Har safiyar yau jikina sai k'amshin turaren Galadima yakeyi, feena dake kwance kusa dani tace, ¡°Mrs Galadima! k'amshin nan nakufa yayi over¡±.
Harara Na dalla mata, tareda kai mata bugu ta kauce tana dariya, Bilkeesu ma dariyar takeyi, ta jawo wayarta tana fad'in ¡°jama'a kunma tunamin, bara na duba comments d'in jama'a akan pictures d'in jiya¡±.
Zumbur natashi zaune ina kallon Bilkeesu, ¡°Bilkeesu kinada kai kuwa? yanzu nan hotunanmu kika mik'ama duniya?¡±.
Da sauri Ameera tace, ¡°to miye aciki, ai gamma mak'iya masu yad'a hotunan wancan 6atacin har 6utiyarsu Na rawa sugani yanzu kin zama halalinsa, ai wlhy jiya kusan kwana nayi karanta comments d'in jama'a akan pictures d'in, idanma mu bamu turaba wlhy abokansa sun yad'a a kowacce kafar yanar gizo, kuma yarinya harma a news wlhy an nuna, idanma baki saniba live aka nuna komai awasu gidajen tv¡±.
Hannu na d'ora aka kawai nafashe da kuka saboda bak'inciki, nace ¡°dan ALLAH harda abinda yaymin?¡±.
¡°sosaima kuwa¡±. ¡®cewar Ameera¡¯.
Kukana yakuma k'arfi sukuma suka saka dariya harda rik'e ciki sukeyi, nikam wlhy kukan gaske nakeyi basu saniba.
Munubiya ce ta fahimci hakan, saita rungumeni tana k'ok'arin rik'e dariyarta data kasa rik'uwa.
Ahaka aunty salamah tashigo tasamemu, ¡°kai lafiyarku kuna dariya kuma ita tana kuka?.¡±
Labari suka bata, ita kanta dariyar tayi, ¡°yo miye abin kuka anan, koba komai ai ya nunama duniya yana k'aunarki, 'yan bak'in ciki kuma yasaka musu ciwon zuciya¡±.
Kallonta nayi ina shar6ar hawaye, ¡°yanzu nan aunty salamah kema haka zakice? mutum yamin wannan iskancin a bazama duniya sannan kuringa d'aukarsa abin kirki? yanzu dan ALLAH idan su Abba suka ganifa? tunda ance harma gidajen TV aka nuna¡±.
¡°kajimin yarinya, yo ina kuma ruwan su Abba, mijinki nefa yanzun, to ai su inna ma duk sun gani agida, haka suma su abban¡±.
Zumbur nayo tsalle tsakar d'akin hannuna bisa kai nace ¡°galadima ka kasheni wlhy, ka cuceni ALLAH ya isana¡±.
Dariyarsu k'aruwa tayi, suka shiga yi harda hawaye. yanda kukasan Na bibbigesu haka nakeji.
Aikam yinin ranar ban yarda Na had'a ido da kowaba agidanmu, har lokacin da innarmu suka kiramu sukai mana fad'a itada mama Rabi'a da inna lami.
Munci kuka tamkar zamu k'arar da hawayenmu.
Zuwa la'asar fa anfara shirin kaimu gidajenmu, saifa lokacin hankalina dana Munubiya yakuma tashi sosai, domin abinda ake gudun yazo (rabuwa?, sabo turken wawa).
Muna d'aki nida munubiya kowa zazza6i ya rufeta, yayinda iyayenmu keta k'imtse-kimtse, ita kanta innarmu jikinta yayi sanyi lakwas, saboda ganin abinfa da gaske ake, tafiyar zamuyi mu barta.
Suma sauran amaren kowacce Na d'akin uwarta, wasunsu kam ko'a jikinsu, hankalinu kwance Dan d'okin auren sukeyi su.
Anayin sallar magriba inna lami tazo tasakamu mukayi wanka, ana shiryamu muna kuka, bayan mun saka atanfa iri d'aya da aka bamu da gyale aunty Salamah tafara zazzage mana turarurruka ajiki.
Duk wasu tarkace an had'a manashi kowa a handbag d'insa, sannan aka tarkatamu dukkan mu amaren zuwa falon Abbanmu, dukkan iyayenmu mata suma suka shigo, harda innaro da gwaggo Safiyya.
Nasiha aka shiga mana mai ratsa jiki, mukam sai shar6ar kuka mukeyi mu dukanmu, hakama iyayenmu mata bakowa ya iya yimana nasihar ba. tun ana mana fad'an naji ana rad'e rad'in isowar wasu daga cikin angunan, wani kukan bak'in cikine Yakuma tahomin saboda tuna ni nawa Auren nanda shekara 1 ya k'are.
Rungume innarmu mukayi yayinda akace mufito masu d'aukar amare duk sun iso.
Innarmu Itama kukan takeyi, da gyar aka ciremu daga jikinta, an fara fita dasu fiddausi saboda motocin d'aukarsu duk sungama isowa, nice dai basu isoba.
Suna kuka da komai aka fita dasu, yayinda dangin iyayensu mata kowa tabi tawagar mortar tasu amaryar, danginsu abbanmu kuwa rarrabuwa sukayi, domin su sami zuwa kowanne 6angare suma.
Motocinsu Na fita daga anguwar na gayyar abokan Galadima suka shigo, mitocine a Jere kuma masu yawa, abokan yaa marwan ma dama su suke jira, dan ance dole sai Munubiya tamin rakkiya sannan tunda nice k'arama.
Bushe-bushen algaita yafara tashi anguwar tamu, dukda darene hakan bai hanasu busa kayarsu ba, hakan ya tabbatarma da 'yan anguwa tawagar gidan sarauta sun iso kenan.
Mata hud'u sun shigo gidanmu tareda kuyangi, Alk'yabba mai azabar k'yau da suka kawo aka sakamin, sannan aunty salamah takuma fesheni da tirare dagani har Munubiya.
Da k'yar aka 6an6aremu daga jikin innarmu, tana kuka munayi, haka aka fita damu k'ofar gida wajen motoci.
Motar datafi kowace tsari da k'yau aka sakamu nida munubiya, sannan inna lami da gwaggo Safiyya suka zauna a gefenmu.
Kuka muke rik'e da hannun juna, har aka Isa damu cikin masarauta.
Mom itace zaune a matsayin Momma uwar Ango kenan, Dan haka aka kaini sashenda take tareda dangin Momma.
Tarba ta mutunci aka mana, irin wadda kowad'anne iyaye suka kai 'yarsu gidan wani aka mata wannan tarbar hankalinsu zai kwanta sosai.
Su inna lami basu wani dad'eba suka fara mik'ewa, saboda suna son mik'a Munubiya itama.
K'ak'a rak'a k'aka, yanzufa akeyinta, danni da Munubiya mun rik'e hannun juna gamma munk'i saki, anyi lallashin da ban magana amma munk'i, da k'yar aka rabamu muna kuka tamkar ranmu zai Fifa. mun burge jama'a da basu tausayi sosai, sai hotuna ake zuba mana kuwa a wayoyi, (yo gidanne kwanyar da lantarki ko ina??).
Mom tasakani a jikinta tana lallashina da bani hak'uri, bayan fitarsu aka kaini wani d'aki, har lokacin ina shashshekar kuka, su Ayusher duk suna tare dani, basubi Munubiya ba, dan sunsan ita yau yaa Marwan zai shiga daga ciki???.
Har lokacin mom Na tare dani, zazza6ine mai zafi yarufeni kuwa, amma dukda haka saiga wata mata wai tazo shiryani, Ashe za'ayi Mother's event ne acikin gidan dakuma wanu Abu dasuke kira wai tarbar amarya a masarautar.
Babu yanda zanyi, haka Na zauna tamin kwalliya Na shirya cikin less lemon green, aka sakamin alk'yabba mai k'yau itama, yanzuma har hular aka sakamin, Dan haka fuskata arufe take, saina sami damar yin kukana hankali a kwance.
Mom da kanta tazo ta kama hannuna muka fita, yayinda kuyangi ke binmu abaya.
Filine aka k'awata da haske, anmasa decoration da kayan sarauta Na kwalliyar gida, anutse kowa yake zaune, babu wata hayaniya sosai, (abinka da lamarin manya to?).
Yaukam Galadima cikin ainahin basarakensa yafito, domin komai Na jikinsa Na sarautane, yasha alk'yabba kalar tawa, sai dai tasa ta maza ce, hard'e yake a zaune bisa wata kujera 2sita, wlhy wanda baima saniba saiya d'auka sarkinne gaba bad'aya, yaci mur fuskarnan d'inke, yasha rawani abin zak'k'yau kamar nabama (gwaurayen group d'ina shi????¡Ã¢).
Gefensa mom ta zaunar dani, tunda aka shigi wajen dani suka d'auki tafi, fuskata a rufe take, ba kallon kowa nakeba, saima hawaye dake cigaba da zirara har yanzun.
Mom tad'an ja hancin Galadima ya murmusa, sannan takamo hannuna tasaka cikin nashi tabar wajen.
K'amshin turarena da nasa ya had'e yabada wani kalar k'amshin Na musamman.
Dukda kukana a hankali nakeyi mara sauti hakan bai hanashi jin ajiyar zuciyar danake saukewa ba, yad'an matsa hannuna dake cikin nasa amma baiyi magana ba, nima sai bance komaiba nacigaba da kukana.
An fara gudanar da addu'oin fatan alkairi da zaman lafiya agaremu, sannan akamin barka da zuwa cikin wannan masarauta mai d'unbin tarihi, Mom takar6a tayi jawabi irina uwar kwarai mai tarin mutunci da kamala. aka shiga tafa mata, saboda taburge kowa.
Hakama aunty Mimi tayi jawabi mai birgewa, sannan mama Fulani tafito cikin tsantsar izzarta da k'asaita tayi welcoming d'ina a wannan family, hakama matan Sarki, saikuma k'annen galadima mata da yayunsa, yayun momma da k'annenta, komai yana tafiyane cikin nutsuwa, nidai ba ganin kowa nakeba, amma ina sarrarensu, har lokacin kuma hannuna yana cikin Na Galadima, yakan d'an murzashi time to time.
Duk Na k'agara a tashi wlhy, dan jikina yayi masifar zafi saboda zazza6i, shikansa Galadima yanajin zafin a hannuna, ganin kamarma ina rawar sanyi saiya kwantoni jikinsa.
Ban musaba, saboda babu abinda nake buk'ata a lokacin kamar kwanciya, ga barci ga ciwo da gajiya.
Bayan angama jawabai da k'yaututtuka da kowa kan bani wad'anda aketa zuwa ana jibgewa a gabanmu aka fara gudanar da liyafar cin abinci kamar yanda komai yake a tsari, sai abinda kakeso za'a kawo maka.
Muma ankawo fruits salad da gasashen kaza da snacks sai drinks da wani abinci dabansan miyeba an ajiye agabanmu.
Da hannu Galadima yayi kiran aunty Mimi, ta k'araso inda muke.
¡°my k'ani lafiya dai? Ko abincin bai matabane?¡±.
¡°no aunty bama abinci baneba, batada lafiya fa, ta6a jikinta kiji¡±.
Hannu aunty Mimi tasaka a wuyana, tausayi nabata saboda zafin da jikina ya d'auka, ¡°to yaza'ayi yanzu? ko tad'an k'ara hak'uri kad'an tunda naga ankusa tashi, kasan halin mama Fulani, kuna tashi yanzu zata d'aukeshi wani Abu daban, dama wannan d'an kwantar da itan dakayi ajikinka inaji tana maganar bakada kunya wai¡±.
Guntun tsaki yaja yace ¡°canta matse mata, indan tagadama tacika masarautarnan da surutu, nanda minti 30 inba'a gamaba zamu tashi kawai¡±.
¡°karka damu zama'a gama insha ALLAH¡±.
duk maganar dasukeyi ina jinsu, sai naji tausayin kaina ya kamani, domin nafahimci nanma akwai mai irin halin innaro kenan. Wasu hawaye suka silalomin a kumatu, sauk'i nama auren 1year ne Na kama gabana.
Daga ni har shi babu Wanda yaci wani Abu har aka tashi a taron, lokacin 12pm, yanzuma mom ce takama hannuna muka koma 6angaren da aka fara kaini, muna shiga kwanciya nayi, bayan mom tasakani cire alk'yabbar jikina, duk kunya ta rufeni, ganin haka yasata ajiyemin kayan barci masu kauri ta fita, a hanzarce na shirya na saka hijjab sannan na kwanta, saida ta kintaci time sannan suka shigo itada aunty Mimi da Galadima sai wani ba'indiye, Ashe abokinsa ne dayazo biki, kuma doctor ne.
Galadima ya zauna a bakin gadon kusada kaina, dayake na juya musu bayane, bargon Dana rufa har fuskata yad'an janye, Idan Akash yay tambaya saishi ya d'an rankwafo Dan yaji amsar da zan bada, saiya maimaita masa abinda na fad'a.
Bayan gama tambayoyin Akash yace damuwa ce da gajiya kawai, ya rubuta maganin daza'a sayo min, (duk cikin harshen ingilishi suke maganar).
Kar6a Galadima yayi ya d'auki waya yakira Harun, sunan maganin ya Sanar masa sannan ya yanke wayar, mintuna 10 saiga Samha takawo maganin.
Ya kalli mom yace, ¡°amma bataci abinciba ai¡±.
Kallon Samha mom yayi, tace ¡°taje ta had'o min tea.
Samha na kawowa duk sai suka fice suka barni dagani sai shi, shima Akash fita yayi.
Bargon jikina ya yaye gaba d'aya, muryarsa a dake yace ¡°tashi kisha¡±.
Shiru na masa, hakkane yasakashi kausasa muryarsa, ¡°wai bak'ya jinane?¡±.
Yun k'urawa nayi na tashi da k'yar, kad'an na saci kallonsa, harya cice kayansa na d'azu, yana sanye da dogon bak'in wando da T-shirt mai gajeren hannu, gefen wandon anmasa zane layi 2 da farin zare. fuskarshi babu walwala kamar kulum.
Mug d'in tea n ya mik'omin bayan na gyara zamana na jingina da gado, ALLAH ma ya soni sanye nake da hijjab.
Kar6a nayi dan nima nasan harda yunwa ke cina, inaga rabona dawani abincin kirki tun ana jibi d'aurin aurenmu, (ranar kamu).
Nasha rabin cup d'in na mik'a masa, bai kar6aba yashiga hararata, cikeda k'asaitarsa yace ¡°cup d'in kawai nake buk'atar gani, kina 6atamin lokaci zanje na kwantane¡±.
Tamkar na makeshi haka naji, na harareshi nima a k'asan ido, muryata na rawa nace ¡°wlhy na k'oshi, zanyi amaine¡±.
Bai tanka minba kuma bai k'ar6i mug d'inba, hakan ya nunamin dole dai saina shaye kenan, haka na rumtse idanu na shanye na mik'a masa mug d'in.
Kar6a yayi ya ajiye saman table glass d'in dake gabansa, sannan yad'auki magungunan ya 6alla min, bana tsoron Magani sai allura, dan haka babu musu na kar6a nasha tareda ruwan daya bani a cup.
Ina gamawa na zame na kwanta, mik'ewa yayi yaja bargon ya lullu6a min sannan ya fice batareda ya tanka minba.
Babu dad'ewa barci ya kwasheni, bamma San su Ayusher sun shigo sun kwantaba suma. da yake gadon babbane duk sai ya d'aukemu.
Washe gari natashi dad'an sauk'i, sai dai kewar munubiya data innarmu, harma data gayyar tsiyar 'yan gidanmu, sauk'i nama d'aya ina ganin su Feena.
Break fast mai rai da lafiya aka kawo mana, su Ameera sai zuba santi sukeyi, nidai uffan bance da suba, nad'an tsakura kad'an na turo, maganin jiya na d'auka nasha na safe, dan har lokacin kaina na ciwo kad'an-kad'an, babu dad'ewa barci yay awon gaba dani.
Ban farkaba sai 12, shima tadani akayi, wai za'ayi ko hawan mi, nidai wannan bidi'a ta isheni hakanan wlhy.
Shiri akamin yanzuma cikin farin less, sanan aka samin alk'yabba, yanzun ma fuskar tawa a rufe take.
Gaskiya gidan sarauta akwai girma, dan shimafa dole akirasa da suna wani gari guda kam.
A mota aka sakamu zuwa inda za'a gudanar da hawan, dukda kuwa acikin gidanne fa, nida Samha ne kawai a mortar, tana ta zubamin surutu har muka isa.
Wata daban santa bace ta fitar dani daga motar, tana rik'e da hannuna har gurin da aka tanada domin zamana, yanzun fuskata a bud'e take, ba'a sakamin hular alk'yabba d'inba, dan muna zama awajen matar data fidoni ta ciremin, sai dai kunya tasani kasa kallon kowa, duk tsiwata inada tsananin kunya da rashin son zama wajen da mutane suka cika yawa.
Aunty Mimi ce a gefena na haggu.
Ban iya kallonba saida ta min magana tana kamo hannuna, dole babu yanda na iya na kallesu, su Galadima ne a saman dokuna shida samari kusan biyar duk da irin shigarsa ta sarauta, dokunan suna a tsaitsaye, da alama umarni suke jiran abasu, dan kamar gasace zasuyi.
Caraf muka had'a ido dashi, murmushin gefen baki ya sakarmin, cikeda mamaki na janye idona daga kallonsa.
Ana busa wani k'aho kowa yabama dokinsa k'aimi suka rera da gudu, nanfa hankalin kowa yakoma kansu ana zufa tafi, babu wata hayaniya dan bawani yawane damuba, kusan ma wajen duk 'yan matane sai abokan Galadima dasuke son ganin al'adar dabasu saniba. Saikuma yayunsa mata irinsu aunty Mimi, amma babu manya kamar su mom awajen.
Ni ban saniba Ashe wannan tafiya saisun zagaye masarautar su dawo, Wanda yafara zuwa shine na d'aya.
Muna nan kusan mintuna 30 saigasu aguje suna tada k'ura, ko ganin fuskarsu ma ba'ayi sosai bare kagane wanene a gaba.
Jinai kawai ansaki tafi kowa na ambatar Galadima! Galadima!!, wai Ashe shine yafara isowa. ya diro akan dokin yana murmushi da goge hannunasa da handkerchief d'insa daya zaro aljihu, sannan yagoge fuskarsa.
Ruwa wani dogari ya mik'a masa, ya d'auka daga saman tired'in da aka d'oro yabud'e Goran, batareda ya saka kofiba ya hau shan kayansa, tas ya shanye ya jefar da robar, suma sauran duk ruwan suke sha.
Daga nan hotuna akayi, sannan yazo har inda muke ya kama hannuna, wai Ashe nima yanzu dole saina hau dokin, ahakane zamuje sashe-sashe, dan kowa yanacan yafito waje yana jiran zuwanmu.
Banta6a hawa dokiba sai yau, dan haka jikina yakama rawa. Muryarsa can k'asan mak'oshi yace ¡°k bak'auya ki nutsu¡±.
Maganarsa saida tabani haushi amma ya zanyi, da taimakonsa na hau dokin bayan dogarai sun baza rigunansu yanda baza'a ga hawa naba.
Saida na hau da k'yau sannan shima yaje ya hau nasa, kuyangine a gabanmu suna zuba flowers, a bayanmu kuma dogarai, gefe da gefenmu ma dogaraine, wasu suna busa algaita wasu suna kid'an taushi, sai gayyar abokansa biye damu abaya dasu Ayusher da 'yammatan masarautar.
Ahaka muka dinga zuwa sashe -sashe inda duk sun firfito, duk muna akan dokin bamu saukaba, sai dai mukan risina alamar gaisuwa. fuskata kuma tana abud'e yanzun kowa Na ganina, saida muka zagaye ko ina a masarautar sannan aka maidani wajensu mom. Lokacin la'asar tayi.
Dukna damu saboda kiran munubiya danaketa yi wayar akashe, tsakin danakeyine ya saka Ayusher tambayata, na fad'a mata.
Dariya tayi, ¡°yo banda abunki ina zakiji munubiya kuwa, yaa marwan nacan nashan amarci kema kin sani ai, kema zuwa gobe wazai kiraki ya samu, Galadima nacan yana kwa.....¡±.
Filo na d'auka Na jefa mata a fusaka, suka sanyamin dariya kuwa.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Nasha kuka yayin tafiyarsu Ayusher, inaji ina gani suka tafi suka barni nikad'ai cikin wad'anda ban saniba.
Tun magriba aka shiryani tsaf cikin wata tattausar atanfa, sannan aka d'oramin alk'yabba, wlhy nagaji da saka alk'yabba r nan, saboda nauyi sukemin, har mamaki nakeyi yanda su basu damuba.
Zan iya cemuku nidai yau wanka akamin da turare dan kowane lungu da sak'o na jikina saida yasha ruwan turare, ruwan danayi wanka dashi kansa na musamman ne, nayi k'yau harna gaji.
An fiddoni aka sakani cikin mota, sannan aka nufi sashen Galadima dani. Dukda nasan auren Contract nayi, hakan bai hana zuciyata luguden dakaba, tunda bamuyi wata yarjejeniya dashiba ta zaman da zamuyi, addu'a natayi a zuciyata ina tunano innarmu da munubiyata da kewarta ta gallabeni, jinake tamkar mun shekara 5 bamuga junaba, bamu ta6a yini ba'a tareba, saigashi yau munyi kwana da yinima, ko'a waya bamuji muryar junaba.
Duk da fuskata a rufe take hakan bai hanani shaida 6angaren Galadima ya had'uba, dan k'amshinsa ma da banne.
Muryar wata na tsinkayo a cikinsu tana fad'in wai falon Galadima za'a kaini, gabana yakuma fad'uwa.
Nidai naji mun iso inda turaren Galadima yafi ko ina yawa, inaga nanne falon nasa, gawani lallausan Abu danake takawa a k'afata, sun zaunar dani akan wani laushin dayafi Wanda nake takawar, sannan sukayi addu'a suka fice.
Tunda suka fita ban iya d'ago kainaba, dukda falon tsitt yake alamar babu kowa cikinsa, sai k'arar AC kawai da ni'im taccen k'amshin dake tashi, a falon, sai TV dake magana can k'asa an rage k'arar sosai, hawayen danaketa rik'ewa tun d'azun suka shiga ziraro min a kumatu. a hankali nakejin takun takalmi na tunkaro falon.........??
Muhad'u tomorrow idan munkai da rai da lafiya, yau kaina namin ciyo kuyi manage da wannan please???¡Ã¢.
Ko Galadima zai angwance oho mar??.
???¡Ã¢???¡Ã¢
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu???_*
[4/30, 7:45 PM] Sis Naja Atuh: *_Typing?_*
*_HASKE WRITERS ASSO...?_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_?RAINA KAMA......!!?_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce??_*
??2?2?
..........Takun takalminsa yana bada sautine dai-dai da kowacce dak'ik'a na bugawar zuciyata, gaba d'aya saina nemi jarumtata na rasa, musamman da firarsu a Ayusher tashiga dawomin a zuciya.
Zuciyata tashiga tsitstsinkewa, saikace ba Munaya mai tsiwarnan ba da rashin barin kota kwana, kululu cikina yabada sauti lokacin da aka murd'a handle d'in k'ofar. kamshinsa ne ya buso min har cikin hancina.
Shikam cak yatsaya yana kallona da mamaki, yasan wannan aikin aunty Mimi ne ko mom, yakuma tamke face saboda tsaro ba tsoroba?.
Oho ni bamma san yanayiba, nima tawa ta isheni a zuciya, dan wani tsoronsa ALLAH ya dasamin lokaci d'aya. kusan mintuna 2 yana a tsaye tamkar bak'on falon, yayinda k'amshin turarena ke dukan hancinsa, yau da ace auren soyayya yayi da wadda yakeso, babu abinda zai hanasa sauke nauyin daya damesa tsawon shekaru. a hankali yacigaba da takowa har cikin falon, ya zauna a kujera mai zaman mutum biyu cikeda izza, k'afarsa d'aya a kan d'aya yana wani kallona a k'asan idanu, shiru kakeji tamkar bama a cikin falon.......
Muryata a sanyaye nace ¡°ina yini¡±.
tamkar bazai amsaba, saikuma yace ¡°lafiya¡±.
Daga nan kowa yay shiru.
Knocking d'in k'ofar da akayine yasakashi sauke 6oyayyar ajiyar zuciya, cikin muryarsa mai kama da anmasa dole ya tambayi wanene?.
Cikeda girmamawa sarkin k'ofar yace, ¡°nime ranka ya dad'e, dama an kawo sak'one¡±.
Kansa ya jingina da kujera, sannan yace ¡°su shigo¡±.
Kuyangi kusan biyarne suka shiga falon da sallama, duk muka amsa akan la66a, suka dire kayan hannunsu sannan suka zube suna kwasar gaisuwa agaremu, hannu kawai ya d'aga musu, nidai koma motsi banyiba, dan nima kunyama nakeji idan naga sun durk'usa suna gaidani, danfa wasuma sun girmeni sosai wlhy, wasuma sun haifeni, kai sarauta dabance gaskiya, al'amuransu sunada wahalar gaske, nidai harma yanzu ban fahim ci komaiba wlhy.
Bayan fitarsu da kusan mintuna 4 naji alamar mik'ewarsa, yanzu ma baice dani uffan ba yashige wani d'aki danake k'yautata zaton bedroom d'in sane a wajen.
Guntun tsaki naja, a raina nace ALLAH ka rabamu da girman kai dai wlhy.
Ban damu da cire hular alk'yabba d'inba, dan sanyin Ac yasa ban takura ba, sai zamana dana gyara sosai yanda zanji dad'i da k'yau a saman lallausar kujerar, duk da har yanzun a tsoracen nake kuwa. dan wannan d'an jinkan yafi k'arfina, zai iya amfani da k'arfinsa ya cutamin batareda yayi la'akari da matsayin auren namuba.
Shikam yana shiga d'akin nasa yafara k'ok'arin cire bottom d'in rigarsa, idon sane ya sauka akan gadonsa dake lailaye da zanin gado blue, dan komai nasa na nan white and blue ne, sa6anin na India dasuke White and Golden, kuma matsawa yayi sosai saboda ganin farin k'yalle dake saman bedsheets d'in.
Tsaki yaja yana fad'in ¡°waisu wad'annan mi suke nufi da shinfid'amin wannan farin abun a saman gado? samazo su d'auki kayansu yanda suka ajiye, motsww¡±. Yakuma jan tsaki sannan ya shige bathroom.
Acanma yana wankan yana jera tagwayen tsoki, bai wani dad'eba yafito sanye da bathrobe milk, hannunsa rik'eda k'aramin towel yana goge fuskarsa zuwa kansa.
Bai shafa maiba, wando yasaka da t-shirt duk milk color marasa nauyi, da alama yayi shirin barci kenan, ya d'auki turarensa na barci mai sanyin k'amshin ya faffeshe jikinsa, sannan ya saka silifas bak'ak'e a k'afarsa yakuma fitowa..
Kallona yayi da mamaki ganin ko fuskarta na kasa bud'ewa, ya ta6e baki da cije lips nashi saman ya zauna bisa tattausan carpet d'in tsakkiyar falon inda kuyangin suka ajiye kayan d'azun.
Tankwashe kafafunsa yayi yashiga bud'e kwanikan domin duba abinda ke ciki. ¡°halan kekam bak'ya jin zafi?¡±.
Yayi maganar yana zuba fruits salad a k'aramin bowl na tangaran mai k'yau.
Shiru nayi tamkar ban jishiba, shima saiya shareni yaja bowl d'in gabansa yafara sha a hankali tamkar bayaso.
Duk abinda yakeyi ina kallonsa ta k'asan ido, saboda kaina Dana jingina da kujera.
Kusan mintuna 5 yana shan fruits salad d'in tamkar wani k'aramin yaro, dan ko Rabin Wanda yazuba baiyiba, araina nace abincinma sai an masa sarauta kenan.
Idanunsa ya d'ago yana kallona, ¡°k wai bakijin ana Miki maganane? bazaki bud'e face nakiba?¡±.
Saida naja kusan seconds 20 sannan na janye hular alk'yabba d'in.
Janye idonsa yayi yacigaba da shan kayansa, nikuwa saima na zame na kwanta a kujera, dama 3setter ce, idanuna na maida na lumshe saboda ciwon da kaina yakeyi kad'an-kad'an, ga kewar innarmu da munubiya dasu Aryaan na damuna, ga wannan auren na fargaba na addabar zuciyata.
Dukda yaga kwanciyar danayi bai tankaba, ya kammala shan fruits salad d'in yamik'e, saman kujera yakoma ya zauna, ya d'auki wayarsa yana latsawa, saikuma ya ajiye ya d'auki remote ya canja tasha zuwa labarai.
Haka muka zauna tamkar kurame, shi yana kallon labarai yayinda nikuma barci 6arawo ya saceni batareda na shirya ba, to gajiya na nuk'urk'usata.
Shi duk bai farga barci nakeba harya kammala kallon labaransa ya kashe tvn, kallona yayi da nufin min magana saiyaga kamarma nayi barci a haka.
Yay d'an jim yana tunanin tayaya zai tasheni, danshi soyake ya shige yayi shafa'i da wutiri ya kwanta, a ganinsa kuma bai kamata ya barni a wajenba.
Matsowa yayi kusada kujerar, ya d'an bubbuga hannun kujerar, dama barcin nawa baiyi nisaba, na bud'e idanuna dasukayi d'an jaa a hankali, saboda barcin dana fara.
¡°tashi muje ki kwanta¡±.
Gabana ya fad'i, amma saina yunk'ura da k'yar natashi zaune.
Ganin ya nufi k'ofar futa sainaji d'an sanyi, tashi nayi nabi bayansa muka fita, bakowa falon alamun duk suntafi makwanci. Wani falon muka shiga daban kuma, gaskiya shima ya had'u, komai na cikinsa lemon green ne da milk, sai tashin k'amshin turaren wuta da air fresheners masu dad'i yake. bai tsaya ananba yay gaba, nidai ina binsa abaya kawai, munshiga k'aton bedroom tamkar nasa, saidaifa aganina nasan yafi had'uwa duk da ban ganiba, nanma komai lemon green ne acikinsa, sai labuloli milk kamar falon, shima yanata tashin k'amshin.
Juyowa yayi ya kalleni ¡°nan shine d'akinki¡±. ¡®yayi maganar tamkar an masa tilas¡¯.
Uffan bance masaba, sai d'aga masa kai nayi alamar naji, shima bai sake cewa komaiba ya fice abinsa.
d'akin na shiga bi da kallo, yamin k'yau sosai, na cire alk'yabba jikina ina sauke numfashi, sanan na cire sark'a da 'yankunne da bangles d'in duk na zube saman madubi. Suma kayan na hau cirewa dan bazan iya barci da suba, sai kuma na shiga tunanin inda zan samu kayan barci? tunda lefena suna gidanmu ba'a kawoba, akwatin da'a kawoni dashi kuma jiya ban Ganshi a d'akinba, zuciyatace tabani shawarar duba wardrobe d'in dake d'akin, banyi musuba naje na bud'e, a mamakina saina ganta da kaya, sai dai duk k'ananune, kayan barcinma babu na mutunci, tamkar zan fasa kuka haka naji, da k'yar nasamu wasu Riga da wando masu sauk'in fidda tsiraici, duk da suma d'in dai sai a slow.
Gadon na hau amma saina kasa barci, kewar 'Yar uwata yadawomin sabuwa, na tashi zaune na fashe da kuka.
Ina zaune ina kukana sai kawai naga mutum yashigo min da sallama ciki-ciki.
Da Sauri na jawo gyalen dana ajiye gefe na yafama jikina, plate d'in hannunsa ya ajiye a table d'in dake jikin gadon, dan harya kwanta yatuna banci komaiba, gani yayi bai dace ya barni da yunwa ba, danni bak'uwace yanzu a gidan, dole sai an bani zanci.
Tamkar bazai tankaba saikuma ya kalleni, ¡°mike faruwa kike kuka?¡±.
Wasu kwallanne masu zafi suka sake kwararomin, na sharesu da gefen gyalena nace, ¡°wlhy ni tsoro nakeji, ban ta6a kwana ni kad'aiba, dan ALLAH ka kiramin Samha ta tayani¡±.
Shiru yay ya tsaya kawai yana kallona, azuciyarsa yace kajifa wannan yarinyar dawani batu, kawai saina tafi kiran Samha ta tayata kwana?. guntun tsoki yaja, Wanda yasakani d'agowa na kallesa. Ya cije lips d'insa sannan ya juyo yakuma kallona ¡°mikike nufi da bazaki iya kwana ke kad'aiba? kin san dai babu wanda yasan manufar aurenmu, daga ni sai ke sai muftahu, dolene ki koya ma kanki iya kwana ke kad'ai d'in, sannan inason kisanfa dolene ki dinga canja behavior naki agaban mutane, domin su agaresu aurene mukayi kamar kowa, sannan ta wannan hanyarne kawai zamu iya samun wani avoidance a kan case d'inan, nasan kinada wayo dan haka saiki bud'e idanunki dan kema zaki iya zama security d'in kanki da kanki, game da zaman gidannan kam za'a samu mai koyar dake komai, dan komai a tsare yake, sauran bayani zamuyishi daga baya, kisa a ranki zaman da zamuyi dake zamane na taimakon juna irinna abota, bayan aiki ya kammala zan baki sakinki kamar yanda nayi alk'awari¡±.
Duk da hawayen dake neman zubo mini haka na had'iyesu, cikin aro jarumta nace, ¡°insha ALLAH komai zai tafi yanda yakamata, kuma zaka sameni mai tsare gaskiya da amana, ALLAH yabamu nasara, ina fata da lokaci yacika komai ya bayyana zaka cika alk'awarin sakina?¡±.
Batare da ya kalleniba yace, ¡°zaki sameni mai cike alk'awari insha ALLAH koda ace bamu cika shekararba komai ya bayyana zan sakeki, idan kuma ashekara 1 bamu samu yanda Muke soba zamuyi 2 ne kamar yanda nafad'a miki tun farko, amma inama addu'ar kafin shekara komai yazama done OK?, ga abinci nan kici, kiyi addu'a ki kwanta, zakiyi barci insha ALLAH¡±.
Batareda ya jira cewata ba yay ficewarsa, kusan mintuna biyu idona na kallon k'ofar, saikace zanga dawowarsane, mamaki yabani sosai, dama yana magana mai yawa irin haka? Kuma cikin kwantar da murya. na sauke ajiyar zuciya tareda bud'e plate d'in daya ajiye, gasashen namane mai rai da lafiya, yawu nane ya tsinke, gashi dama inajin yunwa, na mik'e na bud'e fright d'in dana gani ad'akin, ruwane kawai aciki aka zuba, guda d'aya na d'auka na dawo saman gadon na zauna, inacin naman ina hawaye, gaba d'aya kewar 'yan uwana ta gallabeni, musamman Munubiya, waya na d'auka na kuma gwada kiranta, amma still akashe, wasu hawaye masu zafi suka kuma kwararowa a kumatuna, naman na ture gefe naciga da kukana, saida nayi mai isata sannan natashi nashiga toilet d'in d'akin na wanko fuskata da bakina na d'auro alwala, a fright d'in na saka naman da sauran ruwan na kwanta kamar yanda yabani shawara, addu'ar barci nayi sannan narufe ido. tunani yace salamu alaikum, haka naita juye-juye a gadon, barci 6arawo bai saceni ba sai around 3. daga nan ban sake sanin inda nakeba saida naji ana bubbuga gefen filon danake kwance.
Da k'yar na bud'e idanuna dasuka kumbura saboda kuka da rashin isashen barci. Galadima ne tsaye a kaina, sanye cikin jallabiya ruwan hanta, tamasa k'yau dukda kallon fisha na masa.
Agogon d'akin ya kalla sannan ya juya zai fita yana fad'in ¡°kitashi kiyi salla¡±.
Da k'yar na iya sauka, dan jikina duk ciwo yakemin, ga barci danake masifar ji. daurewa nayi nafara wanka da ruwa mai d'an zafi sannan nayo alwala nafito, salla na gabatar ta asuba nayi addu'oina sannan namik'e na koma gadon, dan danan barci ya kuma kwasheni.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
A gidanmu bayan kwashemu dukkan amare washe gari 'yan biki suka fara kama gabansu, sai makusanta ne kawai aka bari.
Lokacin da su Ayusher suka koma sun iske innaro na zuba tijara a tsakar gida, wai an munafunceta ba ace ta fitoba lokacin da akazo d'aukata, dama tasan innarmu bak'in ciki take mata karta dangwali arzik'i, to kuwa ita k'adangaren bakin tuluce, babu yanda aka iya da ita, duk wani makirci da innarmu zata shirya mana akan karmu taimaka mata dolene tanan matsayin uwar ubanmu.
'Yan gidanmu fa abin nema yasamu, saifa aka hau dariyar gatsa-gatsa suda sauran bak'in su.
Innarmu kam murmushi kawai tayi, zuwa yanzun ita ta wuce k'aramar yarinya, dama sarai tasan bawai nadamar gaskiya innaro tayiba, kawai dai wani abu dake a ranta kawai. Ko lek'owa batayi tsakar gidanba, barema tanuna tasan da ita takeyi.
Shigowar su Ayusher da kaya nik'i-nik'i na biki da mom tabasu yasa innaro waryar leda d'aya tana fad'in munafukai, Ashe kune aka tura domin Ku tattaro komai, to ALLAH ya fiku, kafin mai biri yaga mai gona mai gona yaga biri¡±.
Ayusher zatayi magana mama Rabi'a ta hanata, haka suka shige da sauran kayan suna k'unk'uni.
Innaro na bud'ewa taga duk drinks ne aciki saita biyo bayansu, ledar ta dangwarar a k'ofar falon tana kunfar baki, ¡°bazansha kayan ruwan ba kayan fitsari, yanzu-yanzu a canjamin kokuma na kwashe komai babu yanda za ayi dani dangin tsiya dangin rashin asali, kai ALLAH yarabamu da bak'ar zuciya mai cike da nunkufurci dai wlhy¡±.
Babu wanda ya tanka mata, Mama Rabi'a ta bud'e komai ta d'iba mata, tanuna ledar datafi kowacce girma da mama Rabi'a bata bud'eba, ¡°to uwar iya, ita waccan ledar miye aciki?¡±.
Da sauri Bilkeesu ta d'auke tana murgud'a baki, ¡°wlhy babu mai baki wannan, domin a lissafe suke, kuma mu aka bamawa bawaniba, zannuwane¡±.
¡°to 'Yar karoro, kekuma asuwa gand'oki muje biki? Aiba uban wani ya Haifa min Auwalun ba daya haifi munaya, saiki bari sai ALLAH yabaki farin jinin auren koda kansilan anguwarkune sannan kimana iyayi, kujimin bak'ar banza kawai¡±.
Baki Bilkeesu ta ta6e, suka ja ledar itada feena suka shige tsohon d'akinmu, yayinda su Ayusher da Ameera suka take musu baya.
Daga mama Rabi'a har innarmu babu wanda ya dakatar dasu.
Aiko sai innaro ta saka kuka wai su Ayusher sun zageta agaban innarmu batace komaiba.
Duk abinda ke faruwa 'yan gidanmu na tsaye cirko-cirko suna dariya.
Yaa Hameed daya shigo gidanne yazo har inda innaro ke tsaye a k'ofar fallon innarmu yana tambayarta lafiya?.
Cikin kuka da shar6e majina ta kora masa bayani, Kansa kawai ya girgiza, danshi lamarin innaro baya burgesa. Da lallashinsa tahak'ura tafita yarakata har gidanta da ledar da mama Rabi'a ta zuba mata kayan bikin.
Acanma zage-zage taitayi tana aibanta innarmu, kunya dukta ishi gwaggo Safiyya ga sauran 'yan biki suna saurarenta, gwaggo Safiyya fitowa tayi ta baro gidan, gidanmu tashigo tazo tana bama innarmu hak'uri.
Murmushi innarmu tayi, tace, ¡°wlhy babu komai gwaggonsu, ai inna nima mahaifiya tace, mizaisa dantamin Abu yazama ya 6atamin rai, ai ta Isa danine shiyyasa¡±.
Innarmu ta bama gwaggo Safiyya tausayi, tana k'ara jinjina hak'urin innarmu a ranta, tabbas da acikin sauran matan gidanne da innaro ta magantu, dan ba raga mata zasuyiba, danma suna Shankar mazajen gidan su Abbanmu.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯**?¡Ã£?¡Ã£?¡Ã£?**¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Su Munubiya amaryar yaa marwan, ?baiwar ALLAH taban tausayi, dan kallo d'aya namata nasan yaa Marwan ya ajiye muskilamci ya kashe arna?.
Duk takuma zama wata silent, tana kwance a falonta dayayi k'yau da tsari, hannunta dafe da kanta, idonta arufe tamkar nai barci, tunanin innarsu da kewar 'Yar uwarta ya gallabeta, gashi tun shekaran jiya yaa Marwan ya kar6e phone nata ya kashe, tayi rok'on duniya yabata takira Munaya da innarsu amma k'ememe ya hana, yadai kira mata innar sun gaisa jiya da daddare, amma munaya yace ba yanzun ba. hawayene suka ziraro ta gefen idonta.
Tun d'azun yashigo yake kanta tsaye bata saniba, tsigunnawa yayi saitin fuskarta yafara share mata hawayen, da sauri ta bud'e idonta, ganinsa yasata tashi zaune tana k'ak'aro murmushi damasa sannu da zuwa.
Bai amsaba, sai zama dayayi kusada ita yajawota jikinsa ya rungume, ¡°haba my baby yanzu kukannan bazai k'areba? ko har yanzu wajen yana ciwonne nasake had'a miki ruwan zafin ki shiga?¡±.
Kanta ta girgiza masa tana kuma matso hawaye, murya na rawa tace ¡°ina kewar Munaya¡±.
Tausayi ta bashi, tareda mamakin tsantsar k'aunar da sukema juna itada 'Yar uwar tagwaicinta, shikuma wlhy bayason kiran Munayar ne saboda karsu shiga hak'in Galadima, amma yanzu kam bashida mafita, yakai dubansa ga agogon falon, 11:49am, maybe zuwa yanzu sun tashi, wayarsa ya d'auka ya lalubo number Munaya yafara kira. cikin sa'a kuwa sai gata tashiga.
Mik'ama Munubiya yayi, cike da d'oki ta kar6a tana murmushi tana hawaye, shi saima abin yaso bashi dariya.
Ina cikin barci naji ringin d'in wayata, da k'yar na lalubota batareda na dubaba nayi picking kawai, a kunne na kara cikin muryar barci nayi sallama.
Daga can Munubiya ta amsa mani.
Ai zumbur namik'e zaune danjin muryar gudan jinina, ¡°Sweetheart kece? Wlhy I Miss u so much ¡±. ¡®nafad'a ina share hawayen dasuka ziraromin¡¯.
Itama Munubiya hawayen takeyi, muryarta na zuga tace ¡°miss u 2 sweetheart, I love you I love you for ever¡±. sai kawai ta rushe da kuka tareda fad'awa jikin yaa Marwan dake kallonta tana rera kukanta.
Hannu yasaka yana bubbuga bayanta yana murmushi, yayinda nima naketa maimaita mata kalmar I love you ina kuka.
Wayar yaa marwan ya kar6a, muryarsa kawai naji yana fad'in ¡°to kukan ya Isa haka kema, kar Galadima yagani ya d'auka munyi miki wani abune, sai anjima idan kin nutsu masake kiranki¡±.
d'if ya yanke, batareda yajira amsa taba.
Sai kawai nakuma ruahewa da kuka na fad'a saman filoluwan da suke zube a saman gadon.
Galadima dake tsaye bakin k'ofar yazo dubani saboda dangin mom da zasuzo mana sallama, saiya koma da baya bai bari na gansaba, zuciyarsa tana masa tunanin dawa nake waya? har nake jera masa kalaman I love u?.
Ya d'an ta6e bakinsa, tareda kauda tunanin a zuciyarsa, to shi inama ruwansa, kwana nawane zai bani takardata na kama gabana.
Falonsa yakoma ya zauna yana jan tsakin Aiken mama Fulani na d'azun data tuna.
Yakuma jan tsakin yana gyara zamansa, dolene ya takama tsohuwarnan birki da wuri, inba hakaba tana neman Shiga masa hanci.
Abinda yafaru d'azunne da safe kusan around 7:30, yadawo daga masallaci bayan yaje ya tadani yadawo d'akinsa, zaune yake a doguwar kujera a falonsa yana azkar kamar yanda yasaba a kowacce Safiya ta duniya. sarkin k'ofane yamasa knocking.
¡°waye?¡± yayi tambayar batareda ya bud'e idanunsa dasuke a rufe ba.
Sarkin k'ofar ya amsa da ¡°nine ranka ya dad'e, dama Amintacciyar kuyangar Fulani Ce ke Neman iso¡±.
Saida yaja guntun tsuka sannan yace tashigo.
Babu dad'ewa saigata kuwa, saida tayi sallama a k'ofar yabata izinin Shiga sannan ta shigo, risinawa tayi (dan ya hanata durk'usa masa saboda ta manyanta sosai) tana fad'in ¡°barka da Safiya ranka ya dad'e¡±.
Idonsa yabud'e a kanta yace ¡°kin tashi lafiya¡±.
¡°lafiya lau ranka ya dad'e, dama Fulani ce tace azo a d'auki yankin jiya¡±.
Bai fahimceta ba, dan haka yace ¡°miyene hakan?¡±.
¡°ka gafarceni ranka ya dad'e, yankin farin k'yallen mutuntaka da aka shinfid'a a gadonka jiya¡±.
Bakinsa ya ta6e, ya maida kansa ya jingina tareda maida idonsa yanda suke, kusan minti 1 harma ta fidda ran zai amsa, saitaji yace ¡°kije kawai, zan kawo mata da kaina¡±.
Idanu tad'an zaro waje saboda mamakin zancensa, amma babu yanda ta iya, kowa a masarautar yasan murd'ad'd'en hali irinna Galadima, saidai akwaishi da kirki da yawan k'yauta. ta risinar da kai, ¡°na barka lafiya ranka ya dad'e, afito lafiya¡±.
Uffan baice mataba harta fice tarufo k'ofar.
Azkar d'insa yacigaba dayi batareda ya maida hankaliba.
Mom ce takirasa a waya, bayan ya gaidata cikin mutunci ta sanar masa gasunan zuwa sashensa suyi sallama, dan jirgin 1pm zasubi ya maidasu tasu masarauta.
Wannan dalilinne yasakashi zuwa Sanar min, amma saiya Tatar ina Waya da fad'in I love you ina kuka kuma, shine yajuya batareda yayi maganaba.
Kamar na sani natashi na gyara gadon fes, nad'anyi shara dukda babu wani datti, toilet nashige nayo wanka.
Ina tsaka da shiri najiwo sallamar da wata murya ketayi tun d'azun, a gurguje na shirya naje na bud'e k'ofar.
Yarane matasa a durk'ushe can gefe a falona, sai wad'anda suka d'an girme musu su biyu.
Ina fitowa suka zube suna gaidani, abinda baka saba ganiba to, duk sai kunya ta kamani, nace ¡°please Ku tashi minene ya faru?¡±.
¡°d'aya acikinsu tace ¡° gimbiya ranki ya dad'e, ki gafarcemu mune masu miki hidima. ni sunana Alawiyya nice mai gyara miki makwancinki kawai da shiryaki, sukuma wad'annan zasu cigaba da sauran hidimominki, irinsu gyaran falo, girki, wanki, baki labari, da sauransu¡±.
Babbar jaka uba, shirinma sai anmin kamar wata 'Yar baby, nidai naga idi gaskiya, wannan wace iriyar rayuwacw haka?.
¡°ranki ya dad'a zamu iya fara aikinmu?¡±. Alawuyya takuma maimaitawa a aladabce.
Kafin nabata amsa muka jiyo gyaran murya a abayanmu. dandanan naga sun juya suna kwasar gaisuwa, jikinsu har 6ari yakeyi.
Hannu kawai ya d'aga musu, kafin yabud'e baki da k'yar yace, ¡°miya faru ne?¡±.
Alawuyya takuma rissinar dakai tace, ¡°ranka ya dad'e mune masuma gimbiya hidima¡±.
Shiru tamkar bazai amsaba, yad'an yamutsa fusaka yana gyara tsayuwa ¡°wanene ya turoku?¡±.
¡°ranka ya dad'e mama fulani ne¡±.
Baice komaiba ya ra6a ta gefena zai wuce ciki, harya kusa shiga sannan yace, ¡°zaku iya tafiya zan nemeku¡±.
Atare suke fad'in godiya muke ranka yadad'e, ALLAH ya kiyayeka, yatsare bayanka da gabanka.
To tunima yariga yashige, nikam tausayi suke bani wannan abun dasukeyi, nace ¡°please kutashi kuje kawai¡±.
¡°to ranki ya dad'e, godiya mukeyi........
Nidai juyawa nayi nashiga d'akin nima, dan banason wannan kirarin wlhy.................??
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*???
[4/30, 7:46 PM] Sis Naja Atuh: *_Typing?_*
*_HASKE WRITERS ASSO...?_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_?RAINA KAMA......!!?_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce??_*
_____________________________
_Wannan page d'in na sadaukar dashi agareki Hafsat writer d'in *HAFEEZ* na gode sosai, ALLAH yabar zuminci, Bilyn Abdull na yinki irin sosai d'inan dear?????._
______________________________
??2?3?
..............A saman sofa na iskeshi zaune, ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana waya. Idanu ya d'ago yad'an kalleni ya janye.
kunyace takamani saboda babu ko gyale ajikina, gashi kayan sket da rigane, kamar munafuka haka nawuce inda akwatina yake da aka kawo da safe, nima farkawa nayi kawai na gansa a d'akin.
Gyale na d'auka na yafa, sannan naje bakin gadon na zauna ina sauraren wayar dayakeyi, abinda na fara lura da halayensa shine, shi mutumne marason hayaniya, komai nasa zaka sameshi a nutse yakeyi, yanzu haka a d'aki d'aya muke zaune, amma ba komai nakeji ba a maganar dayakeyi, ga jan aji tamkar wani mace, jinin mulki dake yawo a jikinsa ne ke k'ara masa k'asaita da izza.......
Gyaran muryar da yayce yasakani d'agowa na kalleshi, idonsa a kaina, Dan haka muka had'a idanu, kowa janye nasa yayi cikeda basarwa.
Saina samu kaina da cemasa ¡°ina kwana¡±.
Saida yaja wasu seconds sannan yace, ¡°kin tashi lafiya?¡±.
¡°Alhmdllh¡± kawai nace masa nayi shiru.
Shiru mukayi babu Wanda yasake magana, yanata aikin latsa wayarsa, nikam ina satar kallonsa da mamakin wannan halayya tashi, shi koma takura bayayi? ina dad'i dan ALLAH kai kenan kullum baki 6am?.
Kusan mintuna 5 muna a haka, bakajin komai a d'akin sai k'arar AC, ni dukma sanyin ya isheni. batareda ya d'agoba yace ¡°mikike buk'ata akawo miki break fast?¡±.
ALLAH shi k'yauta, nafad'a a raina kafin nace, ¡°ko miyema¡±.
Idanunsa ya d'ago yana kallona, baice komaiba ya janye ya mada ga wayar. sai kuma yasaka a kunne, ¡°mom ki basu su kawo abincin ta tashi¡±.
Bansan mitace masaba daga can, naga dai yayi murmushin gefen baki tareda yanke wayar.
Ya kalleni yana gyara zamansa, tareda kuma shan mur alamun maganar da zaiyi important ce, ¡°ki kimtsa su mom zasu iya shigowa a kowanne time, dan zuwa anjima zasu tafi, duk yanda dai zaki nuna musu wani Abu yashiga tsakanina dake kiyi, dan banason su tafi dawani zargi a ransu OK?¡±.
Duk da na fahimci inda zancensa ya dosa, hakan bai hanani yimasa kallo mamakiba, nace, ¡°kamar ya ban ganeba fa ni¡±.
Shima kallon mamakin yamin, kamar zaiyi magana saiya fasa kuma, yad'an furzo huci a bakinsa kafin ya cije lips nashi da d'an k'arfi. tsaye yamike yana zuba wayoyinsa cikin aljihun ash d'in wandonsa, sannan yafara tafiya, sai da yakusan fita sannan yace, ¡°ki nuna musu tamkar wata mu'amullar aure tashiga tsakaninmu, wannan shine kawai mafita, idan kin gama kizo kiyi breakfast¡±. ficewarsa ya ida yi.
Yayinda nikuma na sauke ajiyar zuciya, danni maganganun nasa duk sunzomin a cirkud'e, to mom d'in nasa ba'a gidan takeba kome? Sannan kuma ai mu yakamata muje mu gaisheta bawai ita tazoba aganina, mi hakan ke nufi?. banida mai bani amsata, dan haka namik'e a gadon ina sauke numfashi, inason kiran Munubiya amma ina tsoron yaa marwan. wayar innarmu nakira, amma a kashe, idona yacika da k'walla, murya na rawa nace ¡°wayyo innarmu I miss u wlhy¡±.
jinake tamkar nayi tsintsuwa naganni a gida, dama ashe akwai randa zatazo na kwana Na tashi ba'a gidanmu tareda munubiya taba? gaskiya masu cewa aure da dad'i basuda kai wlhy, dan ALLAH ina wani dad'i anan?.
Da Sauri Na goge hawayena saboda jin maganar Samha a kaina, jikinta a sanyaye ta zauna kusada ni, nima saina yunk'ura natashi zaune ina murmushi da share sauran hawayen fuskata.
¡°Samha yaushe kika shigo¡±.
Kanta ta langa6e gefe cikin damuwa tace, ¡°Aunty yanzu na shigo, miya sakaki kuka? ko Uncle Sam.... ne?¡±.
Murmushi namata, danni dariya wannan shagwa6ar tata ke bani, ko kad'an bata d'aukar kanta ta girma, ¡°A'a Samha, ba shi baneba, ina kika shigene haka?¡±.
¡°ina nan, tun d'azun naso zuwa Amma mummy ta hanani, yanzu ma tare muke dasu mom, suna falo kisaka Al'k'yabba muje¡±.
Kallon jikina nayi, nace ¡°bara dai na saka hijjab, ALLAH Alk'yabba d'inan nauyi takemin¡±.
Dariya Samha tayi, ¡°lallai aunty ai Indai kina gidannan dole saikin sakata, sai dai indan kun taho india, yanzu mafa dole ki saka¡±.
Badan nasoba na d'akko Samha ta tayani sakawa, sannan muka fita bayan nafesa turarrurruka na masu dad'in k'amshi.
A zatona suna falona, ashe suna nashi, Samha na rik'e da hannuna tamkar wata 'yar jagora har sashensa, Wanda sai yanzune nake d'an kallon wasu abubuwan, dukda face d'ina arufe take da hular alk'yabba. Sallama mukayi a k'ofar falon akabamu izinin shiga, gabana na dukan tara-tara muka shiga, duk zatona irin sunada yawa d'innanne, saina gansu su 5 kawai, kuma duk manyane, mom kawai na gane acikinsu, sauran ban sansuba, saikuma shi boss d'in yana zaune a kujerar mai zaman mutum d'aya kamar ma yana wayane. ban zauna akujera ba sai a k'asa, mom tayi saurin fad'in ¡°a'a d'iyata tashi ki zauna saman kujera mana¡±. kaina na girgiza muryata a raunane nace ¡°a'a nanma ya isa¡± sannan a ladabce na gaishesu. cikeda fara'a da sha'awa suka amsa, shi kansa uban gayyar saida ya kalleni, yaji dad'in girmamawar dana bama k'annen mahaifiyarsa.
Samha ta gwargwad'ama mom magana a kunne, wai ta iskeni ina kuka. murmushi kawai mom tayi, tasan kukan bai wuce na shiga kwaryar manyaba, ga d'an nasu dagani jarumine (aikam mom ragone tunda ba abinda kike tunanin bane??).
Kallon Galadima tayi dake harar Samha, ¡°gulmammiya mikike fad'a? tashi kibar falon nan¡±.
Tashi tayi tana tunzura baki, ¡°wlhy Uncle Sam ni Vance wani abuba, Mom dan ALLAH wani Abu nace?¡±.
Murmushi mom tayi, tace ¡°a'a bakice komaiba¡±.
Batareda ya kalleta ba yace, ¡°naji, tunda kin rakosu wuce ki tafi¡±.
Fita tayi tana daddaga k'afafu, yaja guntun tsuka, yayinda su mom suke mata dariya da tsokana irinta kakanni, nidai kaina na k'asa nima ina murmushin rigimar 'ya da Uba, duk dama har yanzu bansan yasukeba, naji dai tana Uncle kawai.
Bayan fitar Samha d'aya acikin matan ta kalleni, d'iyarmu cire hular kisha iska kinji, mu nan duk iyayenki ne, daina jin kunyarmu.
Babu yanda na iya, dole na zame hular Alk'yabba d'in, amma kaina na duk'e sosai yanda bazasuga fuskataba, nasiha mai ratsa jiki da 6argo suka Shiga mana daga ni har harshi, duk jikinmu sai yayi sanyi k'alau, nikam kukama nakeyi, Dan dama kad'an nake jira a ta6ani na fashe. sun dad'e sosai sannan suka ajiye min k'yaututtuka suka tafi harda shi domin musu rakkiya.
Bayan fitarsu saina shiga rera sabon kuka, saida nayi mai isata sannan natashi da nufin tafiya nawa d'akin, kallon falon nashiga yi, masha ALLAH, komai yayi a falonnan, kujerun Navy blue ne, sai labuloli da Carpet sun kasance Silver da kwalliyar k'ananun flowers blue, babu wani tarkace sosai, wani hotonsa ne yay masifar d'aukar hankalina, gaskiya hoton ya d'auku, yana sanye cikin kayan sarauta akan dokin dashima yasha kwalliya, murmushin dake d'auke a face nashi shine Yakuma k'awata tsarin hoto, ga hoton irin k'aton nanne kamar kamasa magana ya amsa maka.
Na juya na kalli d'ayan dake bangon kudu, shikam sanye yake cikin farin wando k'al da farar riga itama, ya tsuke k'ugunsa da bak'in belt, takalmansa da hularsa duk bak'ake, yana awani k'aton filine daya k'awatu da korayen ciyayi, hannunsa rik'e da wani k'arfe ga k'aramar boll a gabansa, nan ma fuskarsa washe da murmushi, har hakwaransa sun fito waje, a raina nace dama d'an wasan Golf?? ne? kokuwa yasaka kayanne kawai?.?
Da sauri na juyo jin motsi a bayana, sai kunya ta kamani ganinsa tsaye hard'e da hannayensa a k'irji yana kallona, gudun karya zaci kallon hoton nake sainayi saurin cewa ¡°dama kana buga Golf? ¡±.
Murmushin gefen baki yayi, yatako a hankali ya zauna a kujerar dake kallon hoton, shima idonsa na kan hoton, ya d'ora k'afarsa d'aya kan d'aya....
Jin yayi shiru yasani juyowa na kalleshi, a tunanina kobai ji baneba, ido muka had'a, kowa ya janye cikeda basarwa, saiya lumshe nasa tareda jingina da kujerar, tamkar anmasa dole yace ¡°kinason wasanne?¡±.
Nace, ¡°kusan haka, duk da bansan kan wasanba har yanzun¡±.
Murmushi naga yayi kawai amma baice komaiba.
Nima saiban sake cewa komanba na juya zan fita. idanu ya bud'e yabini da kallo harna fice.
Yana mamakin yanda bata da tsoro, zai iya cewa itace yarinya ta farko budurwa dakan iya masa magana kanta tsaye bada wani shakkuba atare da ita.
Tabbas a wannan fagen ya yaba mata, domin takafa tarihin da manyan 'yan mata masuji da mulki da Kansu suka kasayi, akwai 'ya'yan sarakuna da yawa dakesonsa amma sukan kasa fad'a masa, sunsha shan alwashi akansa amma da zarar sun had'u dashi sai alwashin nasu ya gudu, hakama 'ya'yan manyan attajirai, kuma baisan abinda yasa sukejin shakkar tasaba, shidai kawai abinda yasani baya sakar musu fuska, to ita wannan tatsitsiyar yarinyar koda fuskar tasa takai hadarin gabas murtukewa bata Shankar masa magana, ya cige lips nashi yana ta6e bakinsa wanda shiyasan dalilin yin hakan.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Mama Fulani tagama cika tayi fam da rainin wayon Galadima, ba'a ta6a angon dayay abinda Galadima yayiba a masarautar, duk randa ango zai shiga d'akin amarya za'a kai farin k'yallen dasuke kira (yankin mutuntaka) a shinfid'a agado, washe gari za'a aika a d'ako domin kowa yaga mutuncin da yarinyar takawo, sannan dolene kuma kakawota da safe ta gaida matan Sarki da Sarki kafin yafita fada, saikuma sauran jama'ar gida wad'anda suka kasance iyaye.
Amma saboda rashin mutuncin fand'ararren yaron can anje d'aukar k'yallen yace zai kawo da Kansu saboda shine shugaban marasa kunya na duniya, ta aika bayi masu hidima damata CID ya korosu wai zai nemesu, gashi ana neman k'arfe uku na yamma amma har yanzu baizo gaisuwa ba shida matarsa, sai bayintane ke sanar mata sunga yarako dangin uwarsa lokacin dazasu tafi, amma ita tunda yazi bikinnan bama ta sakashi a idonta ba sai ranar da akayi Mother's and tarbar amarya event ta gansa awajen. yaron nanfa yana shigar mata hanci da yawa fa, bari taga iya gudun ruwansa da k'arshen wutsiyar iskancinsa, ai ko ubansa bai Isa mata abinda gagararren yaronnan ke mata ba a gidannan.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Shi baima San tanayiba, Dan tun bayan fitar Munaya daga sashensa yatashi zuwa masallaci sallar azhur, ana idarwa ko yarda su had'u da Sarki baiyiba ya shiga gida, shigewarsa yay bedroom, yayi kwanciyarsa domin yasamu yad'an huta, jikinsa duk ciwo yake masa, saboda ainan-ainan na al'adar biki, dukda yasan ko Rabin hidimar da harun yayi shi baiyiba, saima ka rantse Harun shine angon wlhy.
Bai wani dad'e da kwanciyar ba barci ya kwasheshi hankalinsa kwance.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
A gidanmu ma dai bak'i kowa yakama gabansa, an barsu daga su sai su, da daddare Abba yace ashirya da safe kowacce abita da akwatunanta, shi baiga dalilin ajiya ba.
Duk sun amsa da to, amma kowacce burinta ace da ita aka kai nawa, Dan sunason suyo kallon kwaf, basu gamsu da labarin da 'yan kai amarya suka fad'aba akan gidana Dana munubiya, su a tunaninsu ma an aurenine domin a maisheni baiwa, yaushe nakai matsayin da har d'an Sarki guda mai sarautar Galadima zai gani yace yanaso, bayan lungu da sak'on hotunan mun gama zagaye duniya ni da shi.
K'ilama da gaske yagama lalatani d'in.
Haka dai sukaita gutsiri tsomarsu da kushe irinta masu hassada, duk da wasu abubuwan suna dawo kunnen innarmu batako damuba, ita dai babu abinda zatace ma ALLAH sai godiya, tunda 'ya'yanta kowanne yasamu matsugunni, yanzu saita maida hankalinta ga ibadar ALLAH da tarbiyar yaranta biyu maza dasuka rage, sune basu gajiba indai tozarcine.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Zuwa la'asar mama Fulani tafara k'ananun magana akan rashin nuna shaidar Munaya takawo budurcinta, dakuma rashin fitowarsu gaida mutane.
ALLAH Sarki Aunty Mimi sai abin ya dameta ganin yanda aketa k'ananun magana a masarautar, hakkane yasata nufar sashen Galadima, babu zancen jiran a mata iso, sarkin k'ofa yabata hanyar tashiga.
Tun'a falon farko daya raba sashina da nasa tace bayinta su jirata.
Babu kowa a falonsa, Dan haka ta zauna tad'au waya ta kirasa, dan batasan halin dayake acikiba, baikuma kamata tashiga kai tsayeba, balle yanzu yanada mata.
Fitowarsa kenan daga wanka saboda tashin dayayi a makare baisamu sallar la'asar ba, sai anan d'aki yayita sannan yashiga wanka. Wayar ya kalla yayinda yake goge ruwan fuskarsa, ganin aunty Mimi yasashi picking call d'in, saiya saka a Hans free yana cigaba da hidimarsa.
¡°my aunty kin 6uya fa¡±.
¡°na 6uya ko ka 6uya my k'ani, gani zaune ai a falonka¡±.
¡°kai haba dai? to bani kamar 5minutes na shirya nafito¡±.
¡°ok babu damuwa¡±.
Bai wani dad'eba yafito sanye cikin farin boyal mai shara-shara, yayi k'au sosai, sai zabga k'amshin turarensa yakeyi na koyaushe. daga shi har Aunty Mimi suka sakarma juna murmushi, ya zauna kujerar dake kallonta yana fad'in ¡°sweet aunty na ni kad'ai¡±.
¡°anya kuwa yanzu bamu raba da Munaya ba my k'ani?¡±.
Murmushi yayi wadda har hak'waransa na bayyana, ya d'ora k'afafunsa d'aya kan d'aya yana gyara zama, ¡°in haka kikeso my Aunty saiku raba ai¡±.
dariya tayi tace, ¡°nama bar mata. wai kasan mike faruwa a gidannan kuwa?¡±.
¡°A'a saikin fad'a¡±.
¡°tun kafin tafiyar su mom aka fara k'ananun magana a masarautar nan, wai anzo kar6ar yankin mutuntaka ka hana¡±.
¡°mtsoww!¡± yaja tsaki yana jingina da kujerar da lumshe idanunsa, ¡°Aunty Mimi dan ALLAH karki biyema wannan jahilcin kema¡± yabud'e idonsa akanta, ransa a d'an 6ace yacigaba da fad'in ¡°kawai da Wanda yakai sanin sirrinka da Wanda ma baikaiba wai duk sai sun sani?, a wace ayar alkur'ani ko hadisi akace dan ka tare da matarka a daren farko sai duniya ta sani?. ita mai aiko a d'auki k'yallen ince agaban kowa na gidannan lokacin da abunnan yafaru take fad'in bakinta bazai iya maimaita k'azantar danayiba?, to kuma tunda tariga da tasan nayi k'azantar abaya miye na aiko da wani k'yallen banza da wofi? wlhy fa suka kaini k'arshe zan shuka rashin mutunci kinji na rantse¡±.
Shiru Aunty Mimi tayi tana kallonsa, tasan ransa yakai k'ololuwar 6aci, dan Galadima yanada hak'uri sosai, gudun kar matsala ta biyo saboda ciwonsa saita kwantar da murya, ¡°haba my k'ani kwantar da hankalinka mana, ai abun bana 6acin rai baneba kaji, haba my habibi¡±.
¡°Aunty Mimi nagaji ne wlhy, rashin mutuncin masarautar nan yafara isata, nifa komai zan iya kawoshi karshe a wannan karon¡±.
Tasowa tayi ta zauna kujerar gefensa, ta kama hannunsa ¡°please cool down mana my man, kaci gaba da hak'uri tamkar yanda kakeyi abaya, ALLAH yana tare da masu hak'uri, Momma bazataji dad'in wani Abu yabiyo bayaba, hakama Abie duk da yana a kwance zuciyarsa zatayi kunci, kansu ai sukema wa, yanzu ina k'yallen? ¡±.
Iska ya furzar daga bakinsa, sannan ya nuna mata bedroom d'insa da hannu.
Tashi tayi tashiga, a saman sofa taga k'yallen dan haka ta d'akko ta fito. zama takuma yi a kusa da shi, ¡°my K'ani ina zamu samu syringe?¡±.
Idonsa yabud'e ya kalleta, ¡°syringe kuma? mizakiyi dashi?¡±.
¡°Sameer duk abinda zamuyi mu kare mutuncin mahaifanmu da lafiyarka muyishi mu zauna lafiya. yanzu dai kasa wani ya kawo mana¡±.
Baice komaiba yajawo wayarsa yakira Muftahu, buk'atarsa ya fad'a masa sannan ya yanke wayar batareda yajira cewar Muftahun ba.
Wata hirar Aunty Mimi ta d'akko masa, tun yana basar da ita, har ya fara tanka ta, daga nan suka cigaba da hira.
Knocking d'in k'ofar akayi, Galadima yace, ¡°waye¡±.
Sarkin k'ofa yace, ¡°ranka ya dad'e yalla6ai Muftahu ne yazo yace amasa iso¡±.
¡°kace ya shigo¡±.
Da sallama Muftahu ya shigo, ya rissina ya gaida Aunty Mimi sannan yabama Galadima hannu suka gaisa cikin musabaha.
Ledar hannunsa ya mik'ama Galadima, ¡°no kabama aunty mimi¡±.
Aunty Mimi ta kar6a ta fiddo da Syringe ta 6are daga ledar, had'awa tayi tare da Allurar sannan ta janyo charger ta d'aure tsintsiyar hannunta, Galadima da Muftahu dai kallonta sukeyi, allurar zata tsira Galadima ya rik'e ¡°mizakiyi hakane Aunty Mimi?¡±.
¡°Sameer! wannan itace kawai mafita, kabari kawai na d'iba a saka musu, da safe saika basu¡±.
lips d'insa ya cije da k'arfi, yashiga kwance charger data d'aure hannunta, ¡°ki barsa zan saka musu nawa, yanzu ma koda an saka zai bushene, dan yayi wuri ai¡±.
¡°karfa kazo ka shukani¡±.
¡°karki damu zanyi, kema kin sani ai, tunda na amsa to zanyin¡±.
Mik'ewa tayi tana fad'in ¡°shikenan to, bara na duba k'anwata itama¡±.
Kansa kawai ya jinjina mata, yayinda muftahu yamata sallama ta fice.
¡°wai mike faruwa? ranka ya dad'e¡±.
Tsaki Galadima yaja, yay shiru kusan minti 2, har Muftahu ya yanke tsammani da samun amsa. labarin komai yabashi.
Shima Muftahu tsuka yaja, ¡°wai dan ALLAH yaushe za'a daina jahillar al'adarnan a masarautar nan? abinda ba addini ya wajabtaba sun kama sun rik'e, kuma duk matsalar tsohuwar nan ce wlhy, masarautu nawa ne suka daina wannan abun, amma mu takafa ta tsare, ALLAH lokacin da akayi na Uncle Hayatudden, kunya abinnan yabani saboda shi kawai nata6a gani, sashe-sashefa haka akaita nuniyar abinnan a masarautar nan wlhy¡±.
Wani mugun tsuka Galadima yaja saboda haushi da abin yakuma bashi, fitarma da yay niya saiyaji yafasa.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Ni bansan mike faruwa ba ma, ina d'aki kwance duk kewa da kad'aici sun gallabeni, ga wayata babu caji saboda na manto cajan a gida.
Nayi zurfi a tunani naji ana sallama. firgigit nayi sannan na amsa, hijjab d'ina najawo na saka, ina k'ok'arin tashi tashigo. da Sauri na mik'e ina mata sannu da zuwa, dan nariga da na shaidata itace aunty Mimi. rissinawa nayi na gaidata, ta amsa cikeda fara'a sannan ta zauna. mik'ewa nayi na nufi freight domin bata ruwan amma saita dakatar dani ta hanyar kamo hannuna.
¡°no k'anwata barshi kinji, yi zaman ki, ya zaman kad'aici da bak'unta?¡±.
Kaina a k'asa nayi murmushi kawai, sannan nace ¡°Alhmdllh aunty¡±.
¡°masha ALLAHU k'anwata, babu dai wata matsala ko?¡±.
Kai na na d'aga mata alamar babu, daga nan mukayi shiru saboda rashin sabo.
Zuwa can nace, ¡°ina Samha?, tun d'azu tace zata dawo amma har yanzu?¡±.
Murmushi tayi, tace, ¡°sun fitane itada Sauban tun d'azun, amma nasan suna hanyar dawowa kam¡±.
¡°Ayya ALLAH ya dawo dasu lafiya¡±.
Ta amsa da amin tana mik'ewa. har falona namata rakiya, inajin dad'in yanda take nuna tana sona.
*******
A can kuwa bayan Muftahu yafito daga wajen Galadima sai yayi murmushi, tabbas yasamu hanyar dazata zame masa tsanin *CIKAR BURINSA*, da wannan kawai zai iya cin galaba akan Galadima.
Da wannan tunanin ya hau mota yabar masarautar gaba d'aya.
Mikake k'ullawa ne Muftahu??
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Bayan sallar isha'i ina zaune ina karatun Alkur'ani Galadima ya shigo, ban daina ba saida na kai aya sannan, na d'ago domin gaidashi sainaga idonsa a kai na.
Janyewa nayi nace ¡°barka da dare¡±.
Bai amsaba cewa kawai yayi ¡°tashi ki shirya zamuje gaisuwa cikin gida¡±.
Nima sai ban amsa shiba namik'e kawai na maida Alkur'anin inda na gansa. tashi yayi yafita danya bani damar shiryawa. banja wani lokacin mai tsayiba nafito cikin Alk'yabba, tsaye na iskeshi a falona, batareda yace uffanba yafara k'ok'arin fita, nima sai nabi bayansa batareda na tanka d'inba.................??
?mun tafi sashen mama Fulani, maison jin yanda zata kaya saiya biyoni.
???¡Ã¢???¡Ã¢???¡Ã¢
Barka da juma'a???
*_YA ALLAHA KA GAFARTAMA IYAYENMU_*???
[4/30, 7:46 PM] Sis Naja Atuh: *_Typing?_*
*_HASKE WRITERS ASSO...?_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_?RAINA KAMA......!!?_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce??_*
??2?5?
..........Bugu biyu ta d'auka, jinayi tamkar anmin bishara da aljanna dan dad'i, lokacin danaji muryar innarmu tayi sallama cikin sanyinta sai kawai na Sanya mata kuka.
Ita kuma daga can batasan wayeba, a sanyaye tace ¡°baiwar ALLAH ko bawan ALLAH lafiya kuwa?¡±.
Murmushi nayi, gakuma hawaye na kwaranya, nace ¡°innarmu nice fa¡±.
Cikeda d'okantuwa tace, ¡°Munaya kece? ya kuke?¡±.
Murmushi nayi mai sauti, nace ¡°innarmu ina yini? inasu Aryaan? Wlhy ina missing d'inku innarmu, ALLAH kamar na dawo gida¡±. na k'are maganar da sakin kuka.
Kallon juna sukayi da Abbanmu, da yake girkin tane tana d'akinsa, sukama juna murmushi, Abba yace, ¡°haba dai munaya ta jaruma ce da kuka haka? Ina aka ta6a kai mutum gidan miji yayi sha'awar dawowa gida inbada yawoba?¡±.
¡°wayyo Abbanmu I miss u so much kaima wlhy¡±.
Dariya suka sanyamin shida innarmu, Abba yace, ¡°yo ga sakaran yarinya, miyeto na kukan hakan? Yaya mijin naki da jama'ar gidan?¡±.
¡°komai lafiya lau Abba, sai kewarku, musamman ma Munubiya, ALLAH ina kewarta Abba, dan ALLAH kace ya kaini na ganta¡±.
Yanzu kam dai su Abba sosai sukemin dariya, saikuma suka shiga tsokanata, tun ina kukan harna ware nima ina dariya, munyi hira sosai, kafin Abba yace ¡°saida safe hakanan, karda ki k'are masa kud'in, ki gaidashi¡±.
Cikeda farinciki namusu sallama, da cewa zankirama gobe.
Na yanke wayar ina murmushi, Munubiya na kira itama, cikin sa'a tashiga kuwa. tana kwance jikin yaa Marwan yana d'an rage zafisa?, wayar tafara ring, shine yamik'o mata, ta amsa tana kallon number, irin Special number d'in Nance, wadda zaka ganta a tsare. (?bara na Baku, amma banda matan aure 07000000000?)???¡Ã¢???¡Ã¢.
Saida ta kalli yaa marwan ya d'aga mata kai alamar tayi picking sannan ta d'aga.
Muryar Munaya dataji yasata mik'ewa zaune zumbur cikeda d'oki.
Kowa yay kewar d'an uwansa, dan haka ko gaisuwa bamu tsaya yiba muka shiga fad'ama juna yanda mukai missing. muka 6alle hira kamar zamu ga juna tacikin wayar..
Mun d'au tsawon lokaci munayi kafin yaa Marwan yasamu dole yin sallama, wayar ya kar6a ya jawo matarsa ya rungume, zatayi magana ya d'ora yatsansa a bakinta alamar tayi shiru tareda yanke wayar ko sallamar arzik'i bamuyiba.
Inajin sukur-sukur d'insu ta wayar, dan haka na tuntsure da dariya ina fad'in oni su yaa marwan Ashe dai ashe?....??.
Number Fauziyya na gwada itama akashe, nace lallai amarci yayi dad'i kenan?, itama Ayusher na kira number busy, 'Yar tara, nasan tanacan itada khamees ana soyewa.
Feena ma wayarta Switch up, nad'anyi tsok'i na ajiye wayar Na tashi domin yin shirin barci, dan yau ina cikin farin ciki, tunda naji muryar families d'ina.
Tun bayan fitar Munaya kam Galadima yafara jin canji a jikinsa, a hankali yakejin wani feelings na bijiro masa, kamar wasa abufa yafara tsamari, tun yana basarwa har mamaki yafara kamashi, shin wai mike faruwa ne dashi haka? bazaice baya sha'awa ba, yanayi sosai, dan wani time d'inma saiyasha tablets, ko allurar kwantar da sha'awan, amma baita6a jin irin na yauba, k'arfin sha'awarsa yasashi katange kansa daga dukkan abinda zai iya zurmasa ga halaka har yazama hanyar tsanin aikata zina. duk da jiya yad'ansha wahala saboda abinda yafaru tsakaninsa da yarinyar can duk da shi yayine badan yaji wani abuba, amma Abu yaso zamar masa Matsala a yinin gaba d'aya, sai dai tunda yaje yay allura sai nutsuwa tazo masa.
Dauriyarsa ce take Neman zuwa k'arshe, sai kawai jikinsa yafara rawa, da bin bango yashiga bedroom d'insa, drowan gefen gadomsa yabud'e yad'iba drugs kusan uku ya watsa a baki, ruwa ya d'auka frigate ya korasu suka wuce.
Humm abanza wai man kare, maimakon yaji sauk'i saima abin ya k'aru. yadawo falo saman doguwar kujera Yakuma kwanciya bayan ya kashe AC n gaba d'aya, Dan k'ara dulmiyar dashi yakeyi.
Nima d'in agareni kusan hakane, kad'an-kad'an nafara jin tsigar jikina Na tashi.
Kamar wasa ina wanka sai Abu yafara shan kaina, abinda bansan ma'anarsa ba yafara bin jinin jikina da 6argo, na lumshe idona ina hango abunda yafaru tsakani na d'azun da Galadima, duk dani wahala ma nasha, wani feelings na tashin hankali yafara bijiromin, idanuna harsun sauya kamanni, da k'yar nayi wanka nafito, ko towel d'in ban cireba na saka hijjab Na d'au wayarsa Na fita, koda nayi sallama a k'ofar falonsa banji ya amsa ba, nayi har sau uku shiru kakeji, shikam yana kwance yana jina, amma bakinsa yakasa koda motsawa barema ya amsa min, saima muryata dake sakashin jin wani zirrr, duk sanda nayi sallamar sautin muryata na motsawa da tsigar jikinsa ne, gaba d'aya gashin jikinsa ya tashi.
Jin shirun yayi yawa natura k'ofar kawai Na Shiga abuna, azatona ko barci ya d'aukesa kokuma bai jiniba.
Ganinsa kwance saman doguwar kujera yasa gabana d'an fad'i, gawani iri dana kuma ji jikina yayi, dagashi sai boxer da vest, hannunsa d'aya dafe da mararsa, d'ayan kuma dafe da kansa, kauda kaina nayi daga kallonsa saboda tsorata da ganinsa a ainahinsa, gaskiya ba k'aramin namiji bane guy d'innan, duk kunya ta isheni, ban ta6a ganin namiji ba a haka, yo samarin gidanmu basa zama haka. duk tunanina barci yakeyi, na ajiye wayar saman cikinsa a hankali, kamar yanda naga d'ayar a ajiye, caraf ya rik'e hannuna da hannunsa daya dafe kansa, tsoro yakamani lokacin daya bud'e idonsa yana kallona, jazur idon yake abin tsoro. Muryarsa a matuk'ar sanyin daban ta6a Sanin yana da shiba yace ¡°mi zakiyi?¡±. idanu na nad'an waro waje cikin tsarguwa nace, ¡°mi zanyi kuma? wayarkace fa na ajiye maka¡±. ajiyar zuciya yad'an sauke, ya zuba min idanu batareda yasakimin hannunba. Gaba d'aya jikina yakuma rikicemin, jima nake tamkar Na fad'a kansa saboda abinda nakeji, ganin karna aikata abinda zanzo ina nadama saina zare hannuna dad'an k'arfi, jikinshi babu kuzarin kirki, danhaka yasaki hannun kawai, nikuma na juya nafice daga d'akin da saurina.
Lips d'insa ya cije da matuk'ar k'arfi kamar zai huda, Yakuma dafe mararsa datayi tamkar zata fashe masa, kai bazai iya daurewaba, domin zai iya mutuwa wlhy, ganin yarinyarnan kuma Yakuma birkita tunaninsa. idonsa yarigada yarufe, ya manta matsayin Auren Nasu, duk da gargad'in da wani sashen zuciyarsa yake masa akan alk'awarin daya d'auka, burinsa kawai ya sauke wannan nauyin kozai samu nutsuwa, da k'yar yamik'e ya fice zuwa d'akina.
Nikam INA zuwa na zube saman gado bayan Na zare hijjab d'in, dagani sai towel, marata data d'aure tamkar zata fashe na rik'e da hannu biyu Ina hawaye, wai wannan wace iriyar masiface ne?, nashiga uku ni Munaya, mike shirin faruwa dani ne?..
¡°innalillahi¡± kawai nake iya karantawa saboda tashin hankali, jikina harwani rawa yakeyi, ko kad'an bansan Galadima ya shigo d'akinba, dan nafad'a wata duniya ta daban, babu zato kawai naji mutum yafad'o jikina yana sauke numfashi wani na k'orar wani, wata wawiyar runguma yamin tareda matseni ajikinsa gam, kai kace cikinsa zai maidani.
Humm maimakon na turesa sai nima nakuma k'ank'amesa, banyi k'asa a guywaba wajen maida masa murtani abinda yakemin..
Daga ni harshi kowa yafita hankalinsa, dan idonmu yarufe bamusan mi Muke aikatawa bama.
Hankalina bai nemi dawowa ba saida naji Galadima na neman kasheni, duk da inajin lokacin dayake jero addu'a amma ban dawo dai-daiba, nayi nisan da banajin kira kam, saida mai gayya mai aiki ke shirin faruwane na farga.
Ina yayi Nisan da bazaiji kiranaba balle kuka da magiyata akan karya cutar dani, yatuna alk'awarin daya d'auka please, baimasan inayiba, duka, cizo, yakushi, babu kalar da ban masa ba, amma bawan ALLAH nan saida yamin biji-biji, dukkan fushinsa na shekarun baya saida ya fanshe a wannan daren.
Nayi kuka harma ba'a jin sautin fitarsa, a jama'ar gidanmu kuwa ai mutum d'ai-d'aine ban kiraba, duk tsanar innaro danayi ranar saida nakirata ta taimakeni (?Munaya anga idi?).
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯*¡Ã¯*¡Ã¯*¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
A can kuwa muftahu Na fita sukaci karo da Harun, kallon-kallo akama juna, cikeda tsantsar mamaki Harun yace, ¡°wai Muftahu mikake shiryawa ne?¡±.
Kallon rainin hankali muftahun yamasa, yagyara tsayuwarsa yana wani murmushin da bakowa zai iya fassara Shiba, ¡°ban fahimci tambayar takaba, amma mikake nufi?¡±.
Harun ya d'an hararesa, ¡°Muftahu karka rainamin wayo, tabbas nasan ni da kai duk abokan Galadima ne, bayan zumunta dake a tsakaninmu, amma shige masan dakake fiye da kowa a wannan tsakanin yana bani mamaki¡±.
Muftahu ya ta6e baki yana wani basarwa, kafin ya kalli Harun a wani yanayi, ¡°Harun kana sakamin idone kenan a al'amurana? humm bazance ka bariba to, kacigaba, ni da kai d'an halak ka fasa, idan kaga dama ka kunna wutar jefani bayan kaga abinda zanyin, wannan ba damuwata baceba, inar Na cimma burina right?¡±.
yana gama fad'ar haka yabar wajen kawai. Yayinda Harun yabishi da kallo kawai tamkar wani soko, a zuciyarsa yana tunanin mi Muftahu ke shiryawa ne akan Galadima? tun kwanaki yakeson fargar da Galadima illar kusanta Muftahu a jikinsa, amma abin kamar wani tsafi, da Zarar sun ke6ance da Galadima to saikaga Muftahu a wajen, saikace mai gani har hanji, kenan yakamata yasake shiri akan Muftahu?.
Da wannan tunanin shima yashige mota yabar gidan, saikuma Galadima ya fad'o ransa, waya ya d'auka ya kirashi, amma saiyaji Number busy, hakanne yad'an sakashi nutsuwa, a tunaninsa ko Galadima yana wayane dasu Momma. (A time d'in Munaya Na waya da phone d'in Galadima).
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯*¡°*¡°¡Ã¯¡±*¡±*¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Yanda ta tashi a firgice haka shima ya tashi, jikinsa ya jawota ya rungume saboda waige-waige da takeyi tana kwala kiran sunan MUNAYA!.
jinta a jikinsa saita d'an sami nutsuwa, cikin kuka tace, ¡°yaa marwan mike faruwa da 'yar uwata ne?, nayi mafarkinta cikin mawuyacin hali tana kuka da kiran sunana Nazo Na ceceta¡±.
¡°sorry baby, ki kwantar da hankalinki mafarki ai ba gaskiya baneba, maybe shaid'anune kawai suka taswuranta hakan a gareki, amma ba d'anzun kuka gama wayaba? kofa awa 5 ma ba'ayiba da gama wayar taku?¡±.
¡°hakane yaa marwan, amma acikin awa 3 wani Abu bazai iya faruwa ba? ka kiramin ita please naji?¡±.
¡°no kiyi hak'uri, dare yayi gaskiya, babu yanda za'ayi mu kirata a wannan time d'in, k'arfe 1 fa ta wuce, 2 ma saura, karkuma ki manta tanada miji itama yanzu. Muyi addu'a ALLAH yasa alkairine, da safe saiki kirata ko?¡±.
Cikin share kwalla ta d'aga masa kanta, a hankali ya kwantar da ita a jikinsa bayan shima ya kwanta, yad'an furzo huci kafin yakai hannu yana shafa kanta tareda sumbatar goshinta yacigaba da bubbuga bayanta a hankali, kowa yana yin adu'a, ahaka barci ya kwashesu, duk da sun dad'e basu koma ba, musamman ma Munubiya da mafarkin yak'i barin ranta, Dan takasa yadda Munaya Na cikin k'oshin lafiya gaskiya, ka wai dai dan batada yanda zatayine ta hak'ura.
*****¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯*¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯****
Hawaye kawai nake iya zirarwa, amma kwakwkwaran numfashi bana iyawa saboda jigata, zan iya danganta abinda Galadima yayimin da fyad'e, dan baya cikin hayyacinsa ko kad'an, kamar yanda nima nawa ya gushe daga farko nabashi gudunmawa. (Nasan duk mai hankali ya k'iyasta a yanda Galadima ya zomin zai tabbatar dolene na jigata d'in?).
Tunda yasamu nutsuwa yana gefena a kwance kawai, a hankali memory d'in brain nasa ke tariyo masa abinda ya aikata tamkar a mafarki, ya bud'e idonsa da hanzari akaina, domin kuma gaskata abinda yafarun, shin da gaskene ya aikata? ¡°innalilahi¡± yashiga maimaitawa dan ganina kwance a gefensa ina hawaye, daganin yanda nake a kwancen ina fidda numfashi d'ai-d'ai kasan nagama jigata, yabi d'akin da kallo cikin tsantsar takaici, yaushema shikam yazo d'akinnan? ¡°Hasbinallahu wa ni'imal wakil. mike faruwa danine ni Sameer? wace k'addarace kuma ta kutsoma rayuwata? yanzu nan ni Muhammad Sameer ne da wannan d'anyan aikin? miya samu tunanina haka?.......¡±
Tunaninsa ya tsaya cak lokacin daya jiyo dasashshiyar muryata ina kiran innarmu da Munubiya, muryata a raunane, runtse idanunsa yayi tareda mik'ewa zaune da k'yar, dan jikinsa gaba d'aya yayi week, ga wani masifaffen ciwo da kansa keyi. da k'yar ya iya kuma bud'e idanunsa a kaina, babu shiri yakuma runtsewa saboda tsorata da ganin yanda yamin, hawaye kawai yaji suna neman zubowa a face nashi saboda shi mutum ne mai tausayi, bayason yaga ancutar dawani bare kuma shi da Kansa ya aikata, jarumtar had'iyesu yayi tareda kuma bud'ewa, yazubama fuskata ido batareda ya iya cemin uffanba, yama rasa ta inane zai fara shikam, mizai fad'amin kuma a yanzu Na yarda dashi? mizai cemin shikuwa?.
Innarmu dana sake ambata murya a sark'e yasakashi saurin kallona, baisan yarik'o hannuna ba ya rumtse anasa, la66ansa sai motsawa suke amma yagaza yin magana, shi yanzu ma baisan wane irin taimako zai baniba, bai ta6a irin hirarnan dawani abokiba balle yace yasan ya zaiyi, bai ta6a aikata zinaba, zai iya rantsuwa da Ubangijin daya haliccesa bai ta6a ta6a jikin wadda ba muharramarsa ba, sai ita Munayar daya d'auketa randa yasa a sato masa ita. Kuma ko muharramar tasa bazai wuce yarik'e hannun taba shima ba kowaba wlhy, inhar kacire Samha Momma Aunty Mimi ko Mom, sukad'aine mata Muharramsa da zaice yanada shak'uwa ta musamman dasu, amma shi ko yaran masarautar nan bama kowacce zai iya ambatarta da sunanta dai-daiba.....
Rashin ya cika da tashin hankali, kukan danakeyine yasakashi waigen phone nashi, baiga komaiba, tunawa yayi ba d'akinsa baneba nan, ya saki hannuna ya sakko agadon bayan ya suturta jikinsa, jikinsa gaba d'aya ya mutu, ahaka da sand'a yakai falonsa, wayarsa dake a saman kujera ya d'auka, to inama zai dosa shikam? wazai kira akan wannan abin kunyar daya aikata? tunanin bincike a network ne ya fad'o masa a rai, maybe yasamu bakin zaren, Google yashiga yay d'an rubutu yahau Searching, amamakinsa kam saigashi sun bashi, saiya kuma wata tambayar, nanma yasamu amsa dai-dai, ¡°Alhmdllh¡± yafad'a yana mik'ewa rik'e da wayar.
Inda yabarni ya iskeni, Toilet yawuce kai tsaye, yayinda nabishi da kallon tsana, nikad'ai nasan minakeji akansa, ayanda nakeji ko wuk'a aka bani zan iya fidda masa hanji waje, tabbas yanzu nakuma yarda banida wayo, yanda tun farko Na yarda da maganar wai auren yarjejeniya mukayi da Wanda yafi k'arfin ajina da matsayina, inma banda wauta irin tawa tayaya mutum kamar Galadima zai nemi kulla aure dani?, Na manta namiji zai iya komai domin cikar burinsa, k'ilama *AUREN 'DAN'DANE* yayi dani, ai sainaji wani kuka ya tokaremin mak'oshi, har ina neman shid'ewa.
Kamar yanda yaga sunsa ya had'a ruwa mai zafi-zafi, sannan yafito, ficewa yakumayi, babu dad'ewa sosai yadawo yakuma shigewa toilet d'in, ni dai idonama Na rufe gaba d'aya, dan bana k'aunar ganinsa.
Jinai kawai an kama hannuna ana k'ok'arin tadani zaune, wata azaba naji har cikin kwalwar kaina, saina fashe dawani marayan kuka Wanda yasakashi saurin sakina nakoma Na kwanta.
Runtse idonsa yayi saboda jin addu'ar danake jero masa ta neman sakayya ga ALLAH tsakanina dashi, wani bai ta6a masa makaman ciyar addu'ar nanba, amma gashi matarsa ta sunnah tana masa, duk da yasan hak'in sane ya k'ar6a agareta hakan bai hanashi jin bak'in cikiba, dan aganinsa inada hujjar masa addu'ar da tafi wannan muni, tunda Bahaka mukayi dashiba.
Cikin tsantsar damuwa ya d'aukeni zuwa bayin, yayinda nikuma nake kuka ina fad'in ya saukeni, duk da a hankali nake maganar yana jina.
Ba k'aramin daga mukayi dashiba wajen taimakona, harda cizonsa nayi a damtsen hannunasa, aiko yacizu wlhy, dan hakwarana saida suka huda lallausar fatarsa, (to dama ba wahala tasaniba fatar) amma a mamakina sainaga ko gezau baiyiba, kuma Na tabbata yaji zafin cizonnan, saidai bansan dalilinsa Na daurewaba, da k'yar ya samu nayi wankan tsarki kuwa, dan saida yakusa makeni ma dan haushi sannan nayi, harya dawo dani d'akin ban daina jera masa ALLAH ya isaba a fili da kiransa mugu azzalumi.
Duk da kalamaina suna sukar zuciyarsa haka yadake yanuna tamkarma baya jina.
Bashida maganin dasuka rubuta akan matsalata, sai dai yanada Wanda zai iya taimaka min kafin zuwa Safiya ya nemo wancan.
Haka yakawo min maganin da tea wai nasha, harara kawai Na zuba masa Na maida kaina Na kwanta batareda nako motsaba balle yayi zaton zan tashi.
Shima baice komaiba yakamani ya tayar, hannunsa da k'irjinsa nashiga bugu, ina kuma kaimasa cizo, amma k'arfin ba d'ayaba, bai barniba saida ya tadani, sannan ya wani ci uban Magani fusakarsa amatuk'ar murtuke, yace ¡°kinsan ALLAH koki kar6a kokuma....humm¡±.
Yanda yay maganar kuma sai tsoro ya kamani, Na watsa masa harara kafin nabud'e bakin, da kansa yabani shayin, sannan yabani magani. mugun Ashe harda Na barci, cikin mintuna k'alilan barci yay awon gaba dani.
Sai lokacin ya samu damar sauke ajiyar zuciyarsa tareda dafe kansa dake tsananin sara masa. Duk yanda yaso yayi tunanin ya akayi hakan tafaru yakasa, saboda matsanancin ciwon da kansa kemasa, dole yamik'e zuwa d'akinsa, shima ruwan mai zafi yay wanka dashi sannan ya tsarkake jikinsa ya fito, Magani yasha ya haye gado ya kwanta shima, yasan bazan farkaba a nan kusa.
Maganin barcin da shima yashane yasaka barci suresa shima.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯(())¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Tun daga shigar Muftahu wajen Galadima har zuwa sanda ya zuba Abu cikin milk d'in Galadima lokacin daya Shiga bedroom d'insa d'aukar Abu suna kallo, har ya girgiza ya ajiye kwalin da sauri inda ya d'auka, fitowar Galadima zamansa da files d'in daya bama Muftahu Na masu buk'atar taimako a asibiti da aka kawo masa zai biya, har shigowar Munaya falon Galadima da fitar Muftahu, zamanta da kar6ar wayarsa zuwa fitarta itama, yanda Galadima yafara fita hayyacinsa har dawowar Munaya sashen takawo masa wayarsa, fitarta dakuma bin bayanta dayayi, hankalinsu ne yad'an tashi ganin yadad'e bai dawoba, gakuma a yanayin daya fita.
Hakanne yasaka aka turo wasu mata biyu da kayan fruits wai sukawoma Galadima domin suyi CID d'in yana ina?.
Sai dai sarkin k'ofa kuma yace saiya musu iso, kamar yasani saiya rufe k'ofar ta ciki sannan yanufi sashen Galadima d'in, yayi sallama tafi sau 15 amma babu amsa, ya tabbata da yana kusa daya amsa, komawa yayi yace musu ai yamayi barci, su koma dashi kawai, babu magiyar dabasu masaba yak'i bud'e musu, dan yarigada yasan komai Na kitumurmurar gidan, sannan yasan Galadima bayacin abincin kowa a masarautar, ko ankawo su yake bamawa, idan kaga yaci abincin dawani yadafa a masarautar to tabbas aunty Mimi tana k'asar, sunzo tare kotazo ta iskeshi. dan haka yahanasu shiga, harma yad'an tsargu da tunanin kawai wani Abu a k'asa ganin sun jajurce dason shigar.
Ransu a 6ace sukabar wajen, inda aka aikisu suka koma, sun Isar da abinda yafaru.
Hakan kuma yakuma tada hankalin masu Aiken nasu, domin an ruguza musu plan d'insu kenan...........??
?hummmm.????¡Ã¢???¡Ã¢???¡Ã¢
_ko Yaya za'a kwashe tsakanin Galadima da Munaya da safe kuma??, Munaya team amin afuwa???ku kora da wanan??????????._
??
*_Masu karatu nasan kowa yamatsu yasan tarihin masarautar su Galadima, insha ALLAH zakuji, inason muzo ga6ar daya kamata kuji d'inne insha ALLAH, saura k'iris???._*
Barkanmu da dawowa???.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*?[4/30, 7:46 PM] Sis Naja Atuh: *_Typing?_*
*_HASKE WRITERS ASSO...?_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_?RAINA KAMA......!!?_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce??_*
??2?6?
..........Da kuka na farka, duk da naji dad'in jikinna kuwa, dan banajin azabar kamar jiya, tashi nayi zuwa toilet danna d'auro alwala, na tuna labarin da wata k'awarmu ta ta6a bamu akan yanda taita ciwon jiki, saida mijinta yata mata ruwan zafi a ranar, ruwan mai d'an zafi na had'a na shiga ciki, nasha zafi kuma naji dad'i, amma inajina kamar ba a dai-daiba maganar gaskiya, haka dai nasamu nayi sallar asubahi, ina tsaka da sallar yashigo da nufin tadani, ganin na tashi ma saiya juya yafice abinsa zuwa masallaci shima.
Koda na idar kwanciya nayi saman abin sallar nacigaba da kuka na, ina kuma tunano abinda yafaru a jiya tamkar a films ko novels ko mafarki, babu abinda zuciyata keyi sai tsinemar, a yau d'inan dolene saiya bani Sakina natafi gidanmu, nafasa auren Contract d'in ma, da dai na zauna da mugunnan gwamma nakoma gidanmu nacigaba da rayuwa dasu innaro yafimin....
Tun d'azun yana tsaye a kaina, tausayina yakamashi, dan yasan shine silar kukan mawa, bayason zalunci ko kad'an, amma saigashi shine da aikatawa kuma, zama yayi a bakin gadon, cikin muryar nan tasa mai kama da anmasa tilas yace ¡°tashi zaune muyi magana¡±.
¡°baza na masa, a zuciyata nace bazan tashiba mugu kawai, bakada abinda zaka fad'amin na yarda, azzalumi, dama abinda ka shiryawa rayuwata kenan? Dan kaganni d'iyar talakawa banida k'arfin gogayya da kai, tabbas nayi kuskuren yadda da Wanda shikansa ma bai gama yadda da kansaba, ALLAH ya Isa wlhy tunda ka ketamin mutunci har abada bazan yafe makaba, kullum cikin sallata saina sakoka da neman sakkaya ga mahaliccina akan zalincin dakami.........
A fili kuma nace, ¡°kagama zalintata kazo kanamin mazurai da mulki, ank'i tashin¡±. a hankali nake maganar banyi tunanin yana jinaba, sai tsawa kawai naji ya dakamin
¡°k!!!!!¡±.
Yafad'a cikin daka tsawa, Ashe tunda nafara maganar ya rumtse idanu saboda yanda Kalmar zaluncin suke sukarsa a zicciya, ban ta6a ganinsa a wannan yanayinba, a cikin fad'a yace, ¡°Niba azzalumi baneba, zina nayi dakene!? dazaki dunga aibantani damun duk furucin dayazo bakinki? to bara na tuna miki idan kin manta, SADAKI na biya na auroki! tun jiya kike fad'an magana amma na shareki, ni sa'an kine? wlhy idan bakiyi wasaba zan koya miki hankali! danaso muyi magana ki saurareni mana kiji mizance?.........¡±
Zumbur namik'e zaune, duk da azabar da k'asana kemin, na kallesa ido cikin ido ina zubda kwalla nace, ¡°bakada abin fad'a shiyyasa bazan saurarekaba, bar ganina 'Yar talaka bana d'aukar raini wlhy, mina maka ne? miye had'ina da kai kaketa bibiyar rayuwata da bala'i, tunda na had'u da kai ban kuma samun nishad'iba, wlhy bazan yafe makab.......
Jikake bamm! ya make bakina da bayan hannunsa, cikin zazzaromin ido yace bazaki nutsuba Ashe?¡±.
Naji zafi sosai, dan haka nafashe dawani marayan kuka mai ban tausayi, ga wani bala'in tsoronsa daya kuma shigata, maganar ma a tsorace dama nayita, Dan tsabar bala'i na hango cikin idonsa Dana kallesa.
Kansa ya dafe da hannu, jiyake tamkar ya tariyo jiya a rayuwarsa ya goge dukkanin abinda yafaru
Ganin bazan sauraresan ba da gaske saiya tashi ya fice yabarmin d'akin.
Nakuma 6arkewa da kuka.
Koda yafita a falona ya zauna, ya dafe kansa daya koma masa ciwo k'asa-k'asa yau, tunaninsa yafara komawa baya daga jiya zuwa yau, shin miya sakashi wannan matsananciyar sha'awar ne wai? dan bai ta6a jin makamancin feelings irin na jiya ba, da sauri yamik'e yanufi sashensa, a falo ya tsaya, ya d'auki kwalin hollandia fresh milk d'in jiya yana dubawa, shi dai yasan shine last abu daya sha a jiya, to kenan koma miye daga cikinsa yake?. to amma ai ba yaune yafara shan fresh milk ba a gidannan balle yace kuma shine. kwalin ya ajiye yakuma dafe kansa, gaba d'aya tunaninsa ya kulle, dama shi indai yana cikin 6acinrai to komai nasa birkicewa yakeyi, dolene saiya kwantar da hankalinsa zai iya kamo bakin zaren. a kujerar Yakoma ya kwanta, ko azkar yakasayi yau, babu dad'ewa barci yakuma kwasheshi anan.
Itama Munaya daga kuka barci yay awon gaba da ita a wajen.
Har Samha suka kawo abinci duk barci suka Tatar sunayi, tasan halin Uncle Sam shiyasa bata tadasu ba, kad'an daga aikinsa ya mammaketa a safiyarnan.
Su duka sai wajajen 12 suka farka, kowanne yatashi da damuwarsa.
Tunda nayi takun farko nakuma tabbatar da akwai matsala, dan ruwan zafin da yaymin jiya kad'ai ya isa na daina jin zafinnan irin haka, balle kuma nima nayima kaina da safennan, amma maimakon k'asana yabar zafin saima zugi yake k'arawa, gashi idan nashiga ruwan, zafi nakeji sosai.
Yanda nake takawar ina hawayene yabashi mamaki, dan aganinsa yakamata nasamu sukuni saboda yanda yamin jiya. bansan yashigoba, maganarsa kawai naji..
¡°Wai mike faruwane? Ko dai kinji ciwone?¡±.
Wata uwar harara dataso bashi dariya na zuba masa, amma saiya danne baiyiba, takowa yayi har inda nake yakama hannuna na fisge, ya d'aure fuska shima yana hararata, ¡°k! Wlhy kinutsu kafin na canja miki kamanni¡±.
¡°yo kammani na yaushe kuma zaka canja min? bayan Wanda ka canja min yanzu? dama haka kake? a fuska kamar babu ruwanka amma sai zalunci taf zuciyarka¡±.
Idonsa ya runtse dan bayason Kalmar zaluncin nan danake jifansa dashi, jinai kawai an fusgoni an zaunar a bakin gadon, nakuwa fashe da kuka ina fad'in ¡°wayyo zafi, munubiya Azalumin nan zai kashe miki ni¡±.
Ko kallona baiyiba yafice, ina nan ina kuka saigashi yadawo da wayarsa a hannu, ya zauna saman sofa batareda ya kalleninba, bashida mafita saita kiran Akash, dan yanason sanin minene matsalar datake sakani wannan kukan da complain d'in zafin, yasan koya tambayeni ba fad'a masa zanyiba..
Da turanci suka gaisa, amma da zaiyi tambayar saiya canja harshe zuwa yaren daban saniba.
Akash yace saidai idan ciwo taji, dan bai kamata ace tana Complain zafi irin haka ba, zataji ciwo kam amma bawai yanda yake nuna masa yanzun ba.
Galadima ya gyara zamansa sosai yace ¡°to ai na sanar maka fyad'e akama yarinyar fa¡±.
Akash yace ¡°zata iya kai shekara nawa yarinyar?¡±.
'Dago ido yayi ya kalleni kafin ya janye yana fad'in ¡°Maybe 19years ko 20 kawai¡±.
¡°ai bama yarinya baceba can sosai, inaga taji ciwone gaskiya, yakamata doctor ya dubata gudun samun matsala, amma kabada gudunmawa a hukunta Wanda yay abunnan my man, please ka kwatarma yarinyar hak'k'inta wajen azzalumin nan¡±.
lips d'insa kawai ya cije maganar Akash na sukar zuciyarsa, da Akash yasan shine yay aika-aikar dabai ce hakaba. sallama sukayi ya yanke wayar, saikuma yafara tunanin doctor d'in dazai nemo ya dubani, dan bashida damar fita dani a gidan yanzun.
Can doctor Hafsat ta fad'o masa a rai, ita kad'ai zai iya aminta tasan matsalarsa, dan ya yarda da ita sosai, yasan zata masa k'yak'yk'yawar fahimta.
Kiranta yayi bayan sun gaisa cikin mutunci ya fad'a mata matsalar ta yanda zai iya, dukda ya 6oye mata wacece keda matsalar ta fahimcesa, d'an murmushi kawai tayi tana girgiza kai da tausayin yarinyarnan data shiga hannun Galadima, duk abinda zata buk'ata tagama had'ashi sannan ta fito, matsalar gidansu data Sani yasakata yin shiri tamkar ba doctor ba.
Shiru d'akin yayi, sai kukana dayake fita a hankali, shikam ya zubamin idanu yana kallona k'asan ido, zaune yake k'afa d'aya akan d'aya, ya jingina da kujera, saika rantse idonsa a rufe yake, amma yana kallonane ahaka.
Bayan doctor Hafsat tazo k'ofar fada saita kirashi, dan baza'a barta kai tsaye tashigaba.
Ina kallonsa ya fice bayan ya yanke wayar daban San dawa yakeyinta ba.
Kusan mintun 20 saigasu sunshigo dawata mace, ba yarinya baceba can gaskiya, zasu iya zama sa'anni da Galadima d'in, dan haka na tashi zaune na gaidata cikin girmamawa.
Ita kuma ta amsa cikeda fara'a.
Kallon Galadima tayi dayake tsaye yana kallonmu, ¡°ranka ya dad'a kozaka bamu wajene¡±.
Murmushi yad'anyi yana fad'in babu damuwa.
Yana fita matar ta zauna kusa dani a bakin gadon, fuskarta d'auke da murmushi tace, ¡°sunana doctor Hafsat Abu, friend d'in Galadima ce tun a primary school¡±.
Murmushi nayi mata na yak'e kawai.
Takuma gyara zamanta tana kallona, please dear karkiji nauyina, ki fad'amin matsalarki kai tsaye, dan ba'a wasa da wannan matsalar, takan zama babban Abu anan gaba ga d'iya mace¡±.
Kai na jinjina mata ina hawaye, sannan nace ¡°inajin zafin wajen sosai¡±.
¡°ok kozaki iya kwanciya nagani¡±.
Ido na waro waje a tsorace, sai kuma nayi k'asa da kaina saboda kunya.
Tayi murmushi tana kama hannuna, ¡°karkiji kunya akan lafiyarki dear, please ki daure kinji¡±.
Kai kawai na gyad'a mata sannan na kwanta, babu yanda zanyi dole na yarda ta duba, kanta kawai ta girgiza da mamakin Galadima, saikace Wanda ya kusanceni da k'arfin tuwo?, ai wannan kam da wani doctor d'inne saiya yima Galadima fad'ama wlhy, dan ko kad'an bai bini a hankaliba, amma ciwon daya jimin bazai zama mai cutarwa ba insha ALLAH.
da kanta yanzu ta had'amin ruwan zafi tazuba wasu magani, sannan ta taimakamin har zuwa bayin ta nunamin yanda zanyi. ban cutar da kainaba na nutsu nayi komai yanda tace, dukda inajin zafi kuwa, bayan nafito saina sameta zaune ta gyara gadon tsaf, gakuma abinci a ajiye, da alama Galadima ne ya kawo, tsareni tayi da lallashi naci abincin ma yanzun, sannan tabani magunguna nasha, ta kalleni da murmushi, ¡°ALLAH yak'ara lafiya gimbiyarmu, indai zaki cigaba da kulawa kamar yanda na nuna miki insha ALLAH nan da 2days zaki dawo normal, ga drugs d'inan saikina sha, shima wannan cream d'in kina matsi dashi awajen a koda yaushe¡±.
Kaina na jinjina mata sannan nace ¡° nagode Aunty¡±.
Sallama tamin tafice.
A falo ta iske Galadima, bayan tamasa bayanin yanda yakamata a kula dani saita kallesa cikin tsokana, ¡°ranka ya dad'e kafayi 6arna gaskiya, Shifa wajenan ba a nuna masa k'arfi, please a kiyaye¡±.
Murmushi kawai yayi baice mata komaiba.
rakiya yamata tareda mata alkairi sannan yadawo.
A kwancen data barni ya iskeni, zama yayi gefen gadon yad'an kalleni ya janye idonsa ¡°yaya kikeji yanzun?¡±.
Baki na turo masa, amma ban tankaba. shima bai damu da amsawar tawaba, ya basar kawai ya d'akko wata maganar.
¡°nasan babu abinda zan fad'a ki yarda dani tabbas, sai dai zankuma maimaita miki SAMEER BAYA ZALUNCI, koda wasa ban ta6a kawo zan aikata hakan agarekiba har kibar k'ark'ashin kulawata, bansan miya shiga kainaba a jiya¡±.
Kallonsa nayi ina hawaye da takaicin maganarsa, nace ¡°bakasan miya Shiga kankaba ka d'auki fresh milk kabani? bayan kasan mika zuba¡±.
Shima kansa ya d'ago yana kallona, cikeda k'asaitarsa yace ¡°ban fahinceki ba, mikike nufi? dan ina son na kusance ki sainayi amfani da wani abu? da hakan naso daret zanzo gareki tunda nasan nabiya sadaki ai, tunda ba tsoranki zanjiba ko?¡±.
¡°dama ai bazaka fahimceni ba tunda Kasan ka aikata ai, kuma ai alk'awarin zama tamkar abokai kamin ba irin wannan ba¡±, na had'e hannuna alamar roko?? ina kuka nace ¡°dan girman ALLAH ina rok'onka kabani Sakina a yau natafi gidanmu, wlhy nafasa auren Contract d'in, koma waye yayi abun ni na yafe masama, kawai ka sallameni¡±.
Yama rasa mizai cemin shi, ajiyar zuciya yad'an sauke, kafin ya cije lips nashi, ¡°shikenan, zan miki yanda kikeso, amma kibari ki warke, bai kamata ki koma gida ahakaba¡±. ¡®yana gama fad'ar haka yatashi yafice batareda yaji amsa taba.
Duk da naso yabani sakina a yau, amma zanyi hak'uri na warke d'in kwana nawane.
******
Yinin yau haka mukayishi duk zukatanmu babu dad'i, Galadima kam ai ciwon mara saiya nemi dawo masa sabo, jiyayi kawai yana sake buk'atar kasancewa dani, haka yayta dannewa har zuwa dare, dan bazai kuma yarda yin gangancin nanba. ganin yana neman mutuwa yay shiri a gaggauce yafito domin zuwa hospital.
Tunda yafito suke zubewa gaisheshi, hannuna kawai yake iya d'aga musu, dan kallo d'aya zaka masa ka tabbatar yanada damuwa, da sauri sarkin mota yazo yabud'e masa ya shiga, suma dogaran dakan bisa idan zai fita sai duk suka taso.
Tundaga fitarsu gidan Muftahu na kallonsu, yad'an murmusa kawai abinsa. (?wlhy Reader's suka kamaka zaka gane bakada wayo?)
Shi kad'ai yasan azabar dayakeji a jikinsa, yana kwance cikin kujerar ne sai faman cije lips yakeyi.
Tunkan sarkin mota ya tambayama ya sanar masa asibitin da zasuje.
Sarkin mota ya amsa cike da girmamawa da tausayin shugabansa, dama shi tunda yaga yafito ya fahimci akwai matsala.
Tun amota yakira wata number yana tambayarsa ko yana asibiti?. Dr Jalal ya amsa da eh yana nan.
Yanke wayar yayi kawai baisake cewa komaiba. Dr jalal yabi wayar da kallo yana mamakin Galadima da halinsa, kiransa yakuma yi shi dan bai fahimci inda maganar tasa ta dosaba. sai dai harta yanke bai d'aukaba, yana k'ok'arin sake kira yaji ana Knocking d'in k'ofar.
Amsawa yay da yes tareda izinin shigowa.
Wani dogari ya bud'ema Galadima k'ofar yashiga, da hanzari Dr Jalal yamik'e yana murmushi da masa welcome.
Hannu kawai ya iya d'aga masa ya zauna kujerar gaban decks d'in.
Shima Dr jalal saiya zauna, ¡°ranka ya dad'e lafiya dai ko?¡±.
Saida yaja wasu Seconds sannan yafara ma Dr jalal bayanin damuwarsa, ya sanar masa mararsa namasa ciwo tun jiya, kuma ada bata masa kamar hakan.
Shiru Dr jalal yay yana nazarin maganar tasa, saida yakai aya sannan yace ¡°ranka yadad'e kokasha pills ne?¡±.
Kallonsa Galadima yayi, ¡°pills kuma? wane irin tambaya kakemin haka?¡±.
¡°afuwa ranka ya dad'e, matsalar taka tayi kama da wanda yasha tablet ne, mikaci na k'arshe jiya?¡±.
cikeda nazarin maganar Jalal yace ¡°fresh milk ne last abinda nasha jiya da daddare¡±.
¡°to amma bayan shi kafara jin matsalar?¡±.
¡°kusan haka gaskiya¡±.
Dr jalal dai shiru yayi, dan ya tabbatar wannan aikin desire tablets ne, amma koya fad'a dawuya Galadima ya yarda, sai kawai yashare ya had'a masa drugs da injection yamasa, yace yad'an kwanta na kamar 20 minutes a office d'in. bai musa masaba ya shiga inda jalal kan huta idan yaso, saiya kwanta kawai, dan shima bazai iya tafiyarba, d'akin ma da taimakon jalal d'in yashigo.
Ni bansan hidimar da akeyiba, dan rabona dashi tun bayan munyi maganar saki, abinci ma tun Wanda doctor tabanine a cikina, sai kusan 8 Samha takawo min kayan fruits dawani Abu mai dad'i daban san mineneba?.
Ta zauna mund'anyi hira kafin tafice. a bakin ta nakejin wai jibi Friday zasu koma India.
Na danci abinda takawo nasha magani nayi kwanciyata cikeda kewar 'Yar uwata dana kanyi akowanne dare.
Galadima kam bai dawo ba sai kusan 1pm, yana shigowa sashensa yawuce yay shirin barci ya kwanta, Alhmdllh zuwa yanzu yaji k'arfin jikinsa, sai dai zuciyarsa nata cud'a masa tunanin ina yasamo pills? dan shima yafara yarda da maganar jalal, musamman idan ya tuno furucin Munaya na d'azun da safe.
To kenan wani ya zuba masa bai saniba? to amma wazai zarga shikam? duk wad'anda suka shigo wajensa a jiya amintattun sane, Sauban, Samha, Harun, Muftahu, duk sun shigo wajensa a jiya, amma Muftahu shine last shigowa, shiru yay yana nazari, can kuma saiya cije lips d'insa ya lumshe idanu yana shafa gurin Dana cijesa.
A haka barci ya kwasheshi.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Munubiya tashiga damuwa sosai akan rashin jina a waya, takira number ta yafi sau goma amma switch up, gashi yaa Marwan ya hanata kiran number dana kirasu a ranar, yace wai number Galadima ce bai kamata su damesa ba.
Haka taci kukanta a yinin ranar, saikace mara lafiya haka ta yini, zuwan su Ayusher ne ma yad'an sanyaya ranta har suka janye mata hankali da yawan tunani, a ranar gidan suka yini cir, sunsha hira da labarina, kowacce tana missing d'ina.
Sunce suna son zuwa amma an hanasu, wai gidan danake ba gidan da ake zuwa any how bane ba, babu yanda suka iya haka suka hak'ura.
*********
A gidanmu ma yau sukayi niyyar kawo min akwatinana da abinda ba'a rasaba, amma ankira wayata akashe, wannan yasa Abba yace abarni akaima su fauziyya nasu. ni daga baya idan an sameni akai min nawa d'in.
Duk inda akaje da innaro ake zuwa, kowacce ta taima gidanta kallon kwaf kenan, sotake taga gidan wacce tafi acikin sauran 'yan uwana.
ALLAH ya taimaki munubiya lokacin dasukaje gidanta yaa Marwan yana gidan, hakama su Ayusher.
Fita yayi yasiyo musu abubuwa yakawo, sannan suka zuba musu girkin da sukayi, babu ko kunya suka mik'e kafafu suka ci abinsu, to dama gidan Fauziyya ne kawai suka samu sukaci abinci, su Safara'u kam casukai basu fara girkiba, dan ita haleematu ma ruwa wannan bata basuba, banda innarmu akaje, dayake kowacce idan za'aje gidan 'yarta banda ita ake zuwa.
Zasu taho kuma yaa Marwan yabasu kud'in mota, dukda kuwa a mortar Dady yaa Anas ya kaisu.
Tunda suka dawo gida aka shiga labarin yanda aka iske gidan kowa, nanfa wad'anda gidan 'ya'yansu ba'a samu wani abun kuzo aganiba sai suka fusata, kunsan dai halin jama'ar gidan namu?, wannan Abu saida yakawo rikici, fad'a sosai sukasha abinsu, itadai innarmu k'ala bata ceba, saima ta maida hankalinta ga girkin dare datakeyi, ga innaro sai habaici takeyi, saida gwaggo Safiyya tazo da k'yar ta lalla6ata tafita.
Matan anguwa makwafta kam sun masa kunne suna saurare da kwasar dariya, dan lamarin gidanmu yazama kamar na 'yan wasan kwaikwayo.
Duk tsiyar dasukeyi dady yana gidan yana jinsu, amma ko lek'owa bai yiba, danshi bashida hayaniya ko kad'an, balle daya fahimci abin yashafi 'yan bani na iya d'in gidan ne, dariya kawai yayi yace ALLAH ya k'yauta. kad'anma kenan ai, bakuga komaiba tunda yanzu kuka fara aurarwar, kuma har yanzu da sauran 6ur6ushin amarci ga yaran harsu Aunty khaleesa kam dake cikin watanni na hud'u da auren.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Alhmdllh yanzu kam naji dad'in jikina, dan ko ciwonma banaji, sai shirye-shiyen kayana nakeyi dan yau nakeson tuna masa batun sakina, tun shekaran jiya rabona da ganinsa, harma na d'auka baya gidan sai d'azun da safe Samha take cemin ai tare suka fita itada Uncle Sam da Sauban birnin gayu da asibiti zagayen marasa lafiya, sune har Asibitin mahaukata, tace duk atsorace take ALLAH yasa kartayi mafarki.
Ni dariya ma tabani yanda take bani labarin kamar a firgice take.
Komai nagama had'ashi tsaf, Galadima kawai nake jira, amma abin haushin har kusan 4pm babu labarinsa, gani nayi zan zauna jiran gawon shanu, dan haka na mik'e zuwa sashensa.
Nayi sallama yafi 7 amma babu amsa, sai kawai natura na shiga, a zatona rainin wayonsane da mulkin ya motsa, babu kowa a falon sai wani k'amshi dake tashi na musamman, ko ina kuma need a gyare,, a yanda naga yanayin falon kamar babu kowa a sashen gaskiya, dan komai akashe yake har AC, dawuya kuma yana nan kaga AC n sa a kashe, duk da haka saina d'an zauna ina k'arema ko ina kallo, kai kace yau nafara shigowa, hotunansa da bana gajiya da kallo naketa kallo yanzun ma, idona nacikin zageye-zagaye saina hango wani k'aramin frame na photo, bana ganin mutanen jiki sosai dan haka namik'e tsaye, ga hoton na isa, yana a kusurwar d'akinne ta gabas, saman wani d'an katako da aka k'awata wajen, bayan foton akwai flower babba mai k'yau, sai aka jigina hoton jikin flower d'in.
K'yak'yk'yawan mutum ne ajiki Wanda kallo d'aya zaka masa ka hango tsantsar kamaninsa da Galadima, saikuma mace a gefensa itama masha ALLAH, Galadima kuma yana satar kamanninsa da ita, musamman idonsa ha6arsa dawasu abubuwa, saikuma wadda nake k'yautatama zaton aunty Mimi Ce kusada matar, shima namijin ina tunanin Galadima ne, yana cinyar mutumin, bazai wuce 5 to 6 years ba a picture d'in, Anty Mimi kuma bata wuce 10 ba, sai tsohon ciki ajikin matar, dukda ban saniba sainayi tunanin iyayensane, duk cikin kayan sarauta suke.
Samha ta fad'amin iyayensa suna india, Abbansa bashida lafiya, ban wani tambayeta komaiba, iyanan naji kawai.
Hoton na maida na ijiye ina murmushi, sun birgeni gaskiya sosai, flower d'in nabi da kallo, itama tamin k'au, gawani k'amshi mai dad'i datakeyi, kuma nalura da dare kamar tana wuta haka. Hannuna na kai na ta6a ganye d'aya ajiki, sainaji Ashe ta roba Ce ma, mamaki ya kamani, banyi zaton ta roba bace wlhy, dan tayi k'yau.
Har zan bar wajen, kamar ance na d'aga kaina saman p.o.p d'in ta jikin kusurwar sainaga tamkar CCTV camera, amma bakowa zai iya fahimtar hakanba, domin ansata cikin tsantsar kulawa, gabanane yafad'i, nayi azamar kauda idona tamkar ba ita nake kalloba, saina d'an gyara zaman flower d'in kawai nabar wajen zuciyata na tsitstsinkewa, toshi miye nawani saka CCTV camera a falonsa?, komawa nayi na zauna, zuciyata nawasu tunane-tunane daban.
Sai lokacin tunanin koma bayanan yazomin, abinda Nagano ya hanani lek'a bedroom d'insa, dan nasan zai iya ganin komai ta CCTV camera d'insa.
Sai kawai natashi na fice nakoma nawa d'akin.............??
Hum masu karatu kuna zaton Galadima bai fahimci Muftahu namasa zagon k'asaba kuwa??. kuduba yanda ya shashantar da binciken ya akayi yasha desire tabs a fresh milk?.
To koma dai miye kumuje zuwa, ai masu iya magana kance *Karshen alewa k'asa*???.
Humm ya kuke ganin sakin da Munaya ta nema? Shin zata samu? kokuwa zai bita bazai bayarba??.
Kumuje zuwa dai a page nagaba my guys????¡Ã¢???¡Ã¢???¡Ã¢
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*???
[4/30, 7:46 PM] Sis Naja Atuh: *_Typing?_*
*_HASKE WRITERS ASSO...?_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_?RAINA KAMA......!!?_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce??_*
??2?4?
............ Tunda muka fito masu hidimar sashensa suketa zubewa suna gaishemu, hannu kawai yake d'aga musu, nikam ma ba amsawa nakeba.
Wata mota aka bud'e mana muka shiga, mamaki ya kamani, shin ba'a cikin gidan bane?. banida mai bani amsa dan haka nayi gum.
Duk da darene muna ganin bayi dake yawo tsilli-tsilli, ga ko'ina kwanyar da haske, a k'ofar wani sashi ya tsaya da motar.
Kallona ya juyo yayi, cikin muryar nan tasa ta k'asaita yace, ¡°basai na fad'a mikiba, kinsan yanda ya kamata ace kowa ya ganmu, nan sashen kakarmu ne mai suna mama Fulani ¡±.
Kai na na gyad'a masa, sannan muka fito saboda anbud'e mana dama tuni.
Tunda muka fito ake kwasar gaisuwa, nikam sai binsu da kallon tausayi nakeyi, su shikenan a bautama wasu zasu k'are, basu da wani 'yancin Kansu......
Tunanina ya kakare, lokacin danaji tattausan hannunsa cikin nawa, kowannen mu saida yaji shock, nad'an rumtse idanuna, yayinda shikuma ya cije lips.
Saida aka mana iso sannan muka shiga. kata faren falone na alfarma, iyakar k'yau da tsaruwa yayi, saikace ba falon tsohuwa ba, ga k'amshin turare na musamman na tashi,.
Bafulatanar tsohuwace mai jikin fulanin asali, dankuwa akwai k'yawu iya k'yawu, tabbas wannan a zamanin k'uruciya anyi asalin k'yak'yk'awa, sai dai gajarta tamata tsiya kam??.
A kishin gid'e take, yayinda hadimai ke zagaye da ita, kowanne da aikin dayakeyi. Shigowar mu tasakasu kowa tasaki tanemi hanyar fita kamar yanda tabasu umarni. Bai saki hannuna ba har muka k'arisa gabanta, yayinda ita kuma idonta ke akan hannayenmu dake sark'e dana juna ko k'yaftawa batayi.
Saida ya taimaka min na zauna bisa tattausan carpet d'in dake falon, gaf da mama Fulani kad'an, sannan shima ya zauna kusa dani.
¡°Ranki ya dad'e barka da hutawa¡±. Nima sai bayi saurin gaisheta.
Cikeda izza da tak'ama ta d'ago idanu tana kallonmu, a raina nace (ga wadda tafi Galadima izza ashe, ko dai itace sarkin??)..
Kamarma bazata amsaba, saikuma naga ta gyara zamanta, idonta a kaina tana k'aremin kallo, ¡°sai yanzu ka gadamar zuwa gaida mutanen saboda giyar amarci na kwasarka?¡±.
Wani k'asaitaccen murmushi Galadima yasaki, Wanda ban ta6a Sanin ya iya shiba, ¡°kusan haka ranki ya dad'e, kinsan masu iya magana kance amarya kota buzuzu? ce d'okinta akeyi, bare ni kuma mai wannan dirarriyar macen doguwa k'yak'yk'yawa abun buk'atar kowanne namiji¡±.
Idanu na zaro domin mamakin maganarsa, kakarsa yake fad'ama hakan?. maganarta Ce yaja hankalina itama........
Saida ta yamutsa fuska tana guntun murmushi, duk da maganar Galadima ta daki zuciyarta kwarai da gaske, ta kalleni da k'yau, ¡°to ke dirarriyar mace abinda mijin naki yafad'a gaskiyane kuwa? dan mu bamu gani a k'asa ba¡±.
Gabana yashiga fad'uwa, dan bansan mizan Ce mataba, 6oyayyiyar ajiyar zuciya na sauke saboda jin Galadima na bata amsa, dukda kuma amsar tashi itama tazomin a rud'ani.
¡°to ranki ya dad'e miye amfanin gani a k'asan?, tunda nida ALLAH ya halattama ganin naga kayana¡±.
Yanzu kam a kufule tace, ¡°a titi ko?¡±.
Ya murmusa yana kallona, ¡°tunda Nina gani ai babu damuwa ranki ya dad'e, koda a titinne kuwa, bawai dole bane saike kin gani a gida ba¡±.
Rasama mizata cemasa tayi, sai can tace inbanga na matarka ba ai naga na Uwarka da yayar uwarka ko?¡±.
¡°well hakanefa ranki ya dad'e, amma nasan kafin kiga nasu, kema anga naki, so banga laifin hakanba ai¡±.
Kutt, tsantsar 6acin rai na hanga a fuskar mama Fulani kuwa, nidai kam sun d'aure kai na da wannan zantuka nasu masu kama da gugar zana, wannan dai baza'a kirashi wasan jika da kaka ba, dan baimayi kama da wasanba, nataso gidanmu na yawa da tun ina k'aramata nagama sanin miye habaici miye gugar zana ko shagu6e. tabbas naji a raina akwai lauje cikin nad'i gameda wannan masarautar, dan tundaga zuwana zuwa yanzu naci karo da abubuwan mamaki bila adadin, ashe ba'a rabu da bukarba an haifi habu kenan, nabaro guguwar gidanmu na fad'a tarnak'in gidan sarauta mai wahalar zama, ni dai ALLAH ka taimakeni komai yafita filima kafin shekara d'ayarnan na kama gabana, bazan iya da kitimurmurar wannan gidan sarautar ba gaskiya.
Mun mata sallama muka fito tana jifan Galadima da kalmar ¡°fand'arrare mara mutunci, wlhy zanyi maganin kane, amma zan kira uwar taka naji idan itace ta baka wannan sak'on kabani¡±.
Baice uffanba sai murmushi daya saki yakamani na tashi, munje bakin k'ofar zamu fita yajuyo yana kallonta, salute nata yayi sannan yace, ¡°da safe za'a kawo miki jinin budurcin matata OK?¡±.
Gaba nane yafad'i, da mamakin yanda yay furucin babu ko kunya bare shakka. nidai kam narasa yanda zan fassara wannan lamari, har muka shiga motar ina juya zantuttukansu a raina.
Mun isa sashen dayafi kowanne sashe girma a gidan, sannan ya had'u iya had'uwa shima, Hadimai sunfi yawa anan fiye da ko ina, anan d'inma dai gaisuwar ce aketa mana.
Mun isa wani k'ofar mai azabar k'yau, matar dake zaune a k'aramin falon farko ta rissinar da kanta tana fad'in ¡°lale marhabin da Galadima, Gimbiya barkanki da zuwa fadar masarautar gagara badau¡±.
Murmushi nayi na jinjina mata kai, amma gogan naku fuska a d'inke yace ¡°Amana iso ga mai martaba idan bai kwantaba jakadiya¡±.
¡°angama ranka ya dad'e, 6auna mai tafiyar k'asaita, bajimin zaki sa d'auka sa yak'i, magajin masarautar gagara badau........
Hannu ya d'aga mata alamar ya isheshi haka..
Ruf tarufe bakinta sannan tashige wata k'ofar, kusan mintuna 5 saigata yafito tana fad'in mu shigo.
Jama'a karkuce nayi k'auyanci, tabbas ni Munaya yau naga daular duniya, dolene sarakuna suringa tunanin kamarma bazasu mutuba, yo irin wannan daular inbakayi yak'i da shaid'anba ai bautar ALLAH ma saika bari, dole suke halaka juna akan sarauta kam lallai.
Wanda nakeda tabbacin shine sarki yana kishingid'e a kilisarsa, idonsa bisa TV yana kallon labarai, sai wata hamshak'iyar mace dake cikin ado na kece raini da alfarma zaune a gefensa, koba a fad'a makaba kasan matar sarkice.
Yanzu ma har gabansu muka isa hannun na cikin nasa, dukda mutsu-mutsun kwata danakeyi yak'i saki, saima k'ara damk'ewa da yayi, nesa dasu k'ad'an muka zauna, cikeda girmama Galadima yace ¡°barka da dare Abba?¡±.
Murmushi sarki yayi, yace, ¡°Galadima sai yanzu ake ganinka?¡±.
Murmushi yayi yana shafa gefen wuya alamar jin kunya, ya kalli matar yace ¡°barka da hutawa ranki ya dad'e¡±.
Fuskarta d'auke da fara'a ta amsa masa..
Nima na rissina na gaidasu cikin tsantsar ladabi.
Sun kar6amin fiye da yanda nayi zato, matar tamik'amin hannu alamar na matso gareta, banyi musuba na matsa, hannuna takama tana murmushi, ¡°yaya bak'unta gimbiyarmu?¡±.
Muryata a kunyace na amsa da ¡°Alhmdllh ranki ya dad'e¡±.
Murmushi sarki dake kallonmu yayi, ya maida kallonsa ga Galadima da shima idonsa na kanmu. ¡°yarona babu dai wata matsala ko? ¡±.
¡°Alhmdllh Abba babu komai¡±.
¡°to Alhmdllh ai haka muke fata mu dama, ALLAH yayi muku albarka, yabamu zaman lafiya na har abada da zuri'a d'ayyiba, wadda musulunci da Muslims zasu alfahari da ita............¡± Nan yashiga mana nasiha mai ratsa jiki da 6argo, har lokacin hannuna na rik'e ga matar sarki, wadda k'amshin turarenta kemin dad'i sosai a hanci.
Mun dad'e anan, dan sai kusan 9pm muka fito, tare da gagarumar k'yauta ta mukullin mota da sarki ya bani, matar kuma tace zata aikomin da tata insha ALLAH.
daga ni har Galadima munyi godiya sannan muka fito, sai juya keys d'in nake ahannu inajin wani makahon dad'i, wai nice da mota har biyu, yanzu Abbana da Dady sun samu kenan, saura baba k'arami, dan nikam babu abinda zanyi dasu, iyayena zan baiwa.
Daga nan munje 6angaren sauran Matan sarki, sai kuma na k'annen babansu Galadima d'in, mune har sashen da aunty Mimi ta sauka,, k'yaututtuka dai nasamesu sosai, harda masu sark'ok'i da sauransu, mun dad'e annan fiyema da ko ina, dan har 12 muna can, sunata hira tsakaninsu, danni dai ban iya cewa komai, sai sun sakoni ne nakanyi murmushi, musamman Sauban sarkin tsokana da Samha sarkin surutu, galadima kam ba komai yake tankasuba, shida aunty Mimi ke maganarsu jefi-jefi, khaleel ma sanda mukaje yayi barci. saida aunty Mimi tace mutashi muje sannan muka dawo namu 6angaren.
Sai da yarakani har d'akina sannan ya juya yafita batareda yace uffanba.
Binsa kawai nayi da kallo ina sauke ajiyar zuciya. Ni ban ta6a ganin murd'ad'd'en mutum irin wannan mutuminan ba, wlhy miskili yafishi dad'in zama, danshi na lura ba muskili baneba, tsabar jin kai ne kwai ke d'awainiya dashi.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Shikam har yayi shirin barci yagama yay shafa'i da wutiri maganar Mama Fulani na caccakar masa rai, ya murmusa kawai saboda takaici, ya zauna saman kujera d'akin, Syringe d'in d'azu ya d'akko da k'yallen yana jujjuyawa a hannu, wani sashe na zuciyarsa na cewa kawai yayi dabaran Aunty Mimi, wata kuma nacewa kar yayi tunda ba addini baneba, koma Dan ya k'ular da zuciyar mama Fulani, to amma kuma ita yarinyar za ana kallonta wani iri ai kuma a masarautar, harma sudunga tunanin ta zubar da mutuncinta a wajene kamar yanda mama Fulani tace, gara yayi kawai dabarar Dan fatansa harsu rabu baya son wani abu na family d'insa ya shafeta. Wannan shawarar da zuciyarsa ta yanke masa yasashi jawo charger ya d'aure hannunsa, jijiya ta bayyana, ya rintse idonsa yayinda ya tsira allurar, cikin cije lips yaja jinin kad'an sannan ya zare ya danne da auduga yanajan tsaki, charger d'in ya kwance yay wurgi da ita saikace itace tamasa laifin??.
d'aukar gyallen yayi ya yamutsashi da hannu duk yayi Squeezing sosai sannan ya matse jinin ajikinsa yad'an yayyarfa bayan yazuba shi awaje d'aya da yawa. sai wani yamutse fuska yakeyi tamkar yaga kashi, kokuma jinin ba daga jikinsa yafito ba. ya ajiyeshi gefe sannan yamik'e yafito, a duzben d'in falo ya saka syringe d'in da kad'ar yakoma ciki, saida ya wanke hannunsa sannan ya haye gadonsa ya kwanta yana wani 6ata rai.
Nima can bayan na kammala hidimata kwanciyar nayi cikeda kewar 'Yar uwata, yauma nadad'e banyi barciba, sai daga baya ya saceni.
Washe gari bansan miya faruba naji busar algaita na tashi a k'ofar sashenmu, yayinda aketa cillara gud'e-gud'e dake tashi, ina niyar fitowa domin ganin abinda ke faruwa Galadima yashigo da d'an hanzarinsa, hannunsa d'auke da k'aramin tire da kofin shayi akai. ¡°hau gado ki kwanta¡± yay maganar yana ajiye kofin a table d'in gaban gadon.
¡°miya farune?¡±. na tambaya cikin binsa da kallo.
¡°ok zauna tambayata har su shigo ciki, oya malama ki hau¡±.
Nidai duk mamaki ya isheni, kamar wadda aka make haka na hau gadon na zauna, kallon face d'ina yayi yaga babu wata alamar dawani zaiga nashiga wani hali, dolene ya canja yanayina kenan idan har yanason ya tsira daga kwakwaf d'in wannan shirmen kafin su shigo.
Kawai sainaga ya hayo gadon shima, kuma kaina yayo gadan-gadan, na bud'e baki da nufin tambayarsa dalili, kawai naji bakinsa cikin nawa. tsorone ya kamani da fargaba, sai kawai nahau dukan bayansa da k'ok'arin turesa, haka dama yakeso, yazam nayi yunk'urin kwatar kaina har nad'an jigata yanda kowa zai d'auka wahalar daren jiyanne. kuma rikicewa nayi saboda wasa daya fara da wasu 6angare na jikina,, so kawai nake na kwaci kaina awajensa, tun ina iya yunk'urin turesa harna kasa, dama nima nasan ganganne na iya da wannan basamuden mutumin?? (munaya tafad'a ba niba????¡Ã¢).
Sai da yaga nayi lakwas ina hawayene kawai na daina tureshi sannan ya d'agani yana sauke numfashi, nikam saina kuma fashewa da sabon kuka, (kai jama'a Galadima akwai bariki??) yanajin takun isowar su Fulani da kirarin kuyanginta sai yayi saurin jan bargo ya rufamin zuwa cikina, yawani kwantar da murya yana fad'in ¡°please my jannat kiyi hak'uri hakanan, kukan ya isa kinji, tun daren jiya kike Abu d'aya, haka ai kowacce mace tayi sannan tazama uwa, ALLAH dai yayi miki albarka, kifad'amin wace kauta kikeso saboda tukuycin budurcinki daki kawomin har gidana¡±.
Idanu nad'an zaro saboda tsorata, mi wannan gayen yake nufi? wai ko dai Galadima yana shaye-shayene ban saniba, abunda yazo yamin daban sannan yakuma d'akkomin wani zancen daban.........
Gyaran muryar da akayice yasamu waigawa ni da shi, kakarsa ce ta jiya a atsaye dawasu mutane biyu, gabana ya fad'i da matsananciyar kunyar su, Dan inada tabbacin sunji ko sunga abinda yamin, ko dai saboda su yake wannan abun? da sauri naja bargon na rufe fuskata saboda kunya.
Yayinda shikuma ya kalli mama Fulani yana wani susar gefen wuya kamar gaske, ¡°o ranki ya dad'e kune? bar kanku da zuwa Ku shigo mana, saima Ku tayani lallashi ai¡±.
Matannan buyu gud'a suka callara a tare, yayinda mama Fulani ta kafama Galadima idanu, alamun tuhuma. kansa ya d'ago shima suka kalli juna ya sakar mata wani lallausan murmushi, kafin ya janye idonsa ya maida a kaina danake k'udundune cikin bargo.
d'aya cikin matan ta rissinar da kanta, cikin girmamawa tace, ¡°Ranka ya dad'e ko zaka bamu waje mu k'imtsa ta?¡±.
Kallonta yayi, fuskarsa d'auke da murmushin Dana sakama suna na rainin hankali, cike da k'asaitarsa yace, ¡°na hutasheku jakadiya, danni tun a daren jiya na gyara matata¡±.
Mama Fulani dake kallonsa a zuciyarta tace amma dai yaronnan d'an rainin wayone wlhy, gaba d'aya ya shirya komansa dai-dai ta yanda babu wanda koda ta k'aryata zai yarda da ita, Dan tabbas tasan duk k'arya yakeyi gameda wannan k'yallen, gashi lungu da sak'o na gidan angama nuna k'yallen, saboda ma ya raina mata wayo ba 6angarenta aka kaiba, sashen matan sarki ya aika da k'yallen, zancennan ma da akeyi ita bataga k'yallen ba har yanzun, Dan ba'a kai mataba, kowa ya d'auka daga sashenta ya fito, tunda ita ake fara kaimawa tagani sannan Matan sarki.
Had'a ido sukayi da Galadima, bakin ya ta6e mata, tareda d'age gira sannan yasaki murmushin Dake k'ular da mama Fulani aduk lokacin da yayisa.
Ta had'iye wani yawun bak'in ciki tareda kauda kanta gefe, su jakadiya kam tuni sun yi nisa wajen kar6o k'yaututtukan da kuyangin kowane sashe ke kawowa daga Matan gidan da iyaye, duk abama Munaya.
Dole mama Fulani ta k'arasa gaban gadon tasakama munaya turare da Sanya mata albarka tamkar yanda al'adar gidan ta tanadar, sannan takama hannunta ta saka mata bangles na goal masu k'yau da d'aukar idanu. Ta shafa kan munaya tana murmushin yak'e. sannan tadawo gaban Galadima shima takama hannunsa ta d'aura masa agogon Azurfa mai k'yau.
Salute nata yayi yana fad'in thanks my sweet Granny ¡±.
Uffan batace masaba tajuya tafice daga d'akin. yayinda su jakadiya suka take mata baya.
Suna fita ya sauke ajiyar zuciya tareda dafe kansa yana jan tsaki, nima kaina na bud'e amma nakasa tashi saboda kunyarsa data dabaibayeni.
Kusan mintuna 5 muna a haka, ni inata hawaye da jamasa ALLAH ya isa a zuciya, ga la66ana sai zugi sukemin saboda Sumbata d'inma na mugunta yamin. shikam yana dafe da kansa har yanzun yana sauraren kukan danake rairawa.
Zamansa ya gyara ya juyo yana kallona, fuskarsa a matuk'ar d'aure yace ¡°tashi ki zauna muyi magana¡±.
Yanda yay maganar yasani tashi zaune batare da na musaba.
Yad'an kalleni ya janye idonsa sannan ya mik'amin Handkerchief d'insa daketa tashin k'amshi alamar na goge hawayena. Kamar bazan kar6aba dai saikuma na kar6a na goge fuskata.
Nanma shiru mukai nawasu mintuna da basufi 2 ba, nakula magana yakeson min amma yanata mulmulata a zuciya saboda jin kai, kuma d'agowa yayi ya kalleni saikuma yay gyaran murya kad'an, ¡°em kiyi hak'uri, bamuda wata mafita sai wannan, munada wata kidahumar al'adane a masarautarnan, dolene randa katare da matarka sai kowa yasani ta hanyar ganin jini ajikin k'yallen da aka shinfid'a muku a gado. mukuma namu auren yasha banban dana saura, banida niyyar zalintarki na maidaki bazawara sannan na sakeki, inason idan mun rabu duk mijin daya aureki yasameki cikin mutuncinki, shiyyasa bazan aikata abinda suke buk'atar ba. ajiya anta surutu saboda bamu bada wannan shaidar ba, shiyyasa a Daren jiya nayi wata dabarar daban, fitowata kenan daga wanka najiyo busar algaita da gud'a alamun k'yallen yagama zaga masarautar, shiyyasa nayi azamar d'akko coffee d'in da aka had'amin zansha nanufo nan dashi, Dan Muftahu yakirani ya sanarmin zafa azo har sashena domin sanyamiki albarka da k'yaututtuka dakika samu saboda kin kawo mutuncinki, yanayin dana ganki nasan zasu gane shirina, shine dalilin yimiki wannan abun dan fidda zuciyarsu daga zargi, karki d'auka nayi mikine da niyya koki kalleni cikin mutane masu sa6a alk'awari¡±.
yana gama fad'a yamik'e zai yafice, nidai kaina ak'asa jinake tamkar namasa masifa amma kwarjininsa ya hanani, saida yaje bakin k'ofar zai fita sannan ya kuma furta ¡°kiyi hak'uri, Sameer baya zalunci¡±. ya ida ficewarsa kawai.
Duk da na yarda da abinda ya fad'a, hakan bai hanani rushewa da sabon kuka ba, nace mugu kawai ALLAH ya isana wlhy, na shafa la66ana da da haryanzu zugi sukemin suda k'irjina wlhy, dan tsabar mugunta shine yama tsaya iya bakin amma harda wani wajen, ALLAH ya isana nidai.
??kujifa, mutum da sadakinsa Munaya ke kiransa da mugu da jamasa ALLAH ya isa?, yau munga auren Contract readers????¡Ã¢???¡Ã¢.
Tunda abunnan yafaru bamu sake had'uwa da shiba a ranar da yinin washe gari , kullum dai Samha kan kawomin abinci tareda kuyangin Aunty Mimi.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Bayan sallar isha'i damuwa da rashin jin innarmu da Munubiya ya gallabi zuciyata, jinai bazan iya daurewa ba, dan haka na yanke shawarar zuwa na rok'esa ya aramin charger kona samu nayi charge wayata, duk da ma banida isashen credit aciki. na d'au turare nad'an fesa kad'an sannan nazura dogon hijjabi nafita zuciyata na d'ar-d'ar.
Na dad'e k'ofar falon tsaye ina tunanin yanda zan shiga, daurewa nayi nai Knocking, wata murya naji ta amsa sa6anin tasa, akace ¡°waye?¡±.
Saida gabana yad'an fad'i, cikin rumtse idanu nace ¡°nice¡±.
Galadima dake kwance cikin kujera idonsa a lumshe yana sauraren Muftahu yabud'e idonsa da sauri.
Shikam muftahu cewa yayi ¡°bismillah ranki ya dad'e, ki shigo¡±.
Na tura k'ofar ahankali na shigo da wata sabuwar sallamar, Muftahu ne kawai ya amsa cikin washe baki, (yayinda k'asan zuciyarsa ke wata iriyar murna ganin shirinsa zai tafi dai-dai kenan). Galadima kam idanu kawai ya zubamin cikeda mamakin miya kawoni?.
Gaisawa mukayi da Muftahu cikin mutunci. saiya mik'e yana fad'in ¡°ranka ya dad'e nikam na wuce, zuwa Safiya zamu k'arasa maganar kawai¡±.
Kansa kawai ya d'agama Muftahu n.
Muftahu ya kalleni yace ¡°gimbiya mu kwana lafiya¡±.
Na murmusa sannan na amsa da ¡°to ALLAH ya tashemu lafiya¡±.
Koda Muftahu yafita sainayi tsaye nakasa magana ganin ya zubamin idanu, ganin banida niyyar magana saiya nunamin kujera alamar na zauna. shima yana tashi zaune sosai.
Ban musaba na zauna.
¡°miya faru?¡±. ¡®yafad'a yana zuba Hollandia fresh milk a glass cup d'in gabansa¡±.
d'agowa nayi nad'an kallesa, dai-dai yasaka kofin a bakinsa zai sha, janye idanuna nayi ina kuma had'e fuska. aransa yace kai wannan yarinya akwai jan ajin tsiya.
Saida naja wasu seconds sannan nace charger zaka aramin please, nabaro tawa a gida, gashi inason waya da munubiya da innarmu.
Crossing kafarsa yayi yana cigaba da shan free milk nashi tamkar bai jini ba, harna fidda tsammanin zai tanka min, sainaji yace, ¡°ina wayar?¡±. yay maganar da mik'omin hannu alamar na bashi
Mik'ewa nayi na kai masa wayar ina tunanin mizaiyi da ita?.
Koda ya kar6a saiya mik'omin cup d'in hannunsa bayan yak'ara fresh milk d'in a ciki.
Na girgiza masa kai alamar na k'oshi.
wani kallo ya watsamin daya sani kar6ar dole. nadawo mazaunina na zauna, inata rik'on cup d'in amma nakasa sha, haka kawai naji hankalina bai kwanta da fresh milk d'in ba, bawai zargin yazuba wani Abu nakeba, haka kawai dai banjin sha.
Shikuma ya basar dani yanata juya wayar kawai a hannusa, basan miyake kalloba ajikinta.
Kallona yayi yace, ¡°kin rik'e Number su?¡±.
¡°eh¡± nafad'a batareda na kallesa ba.
Wayarsa ya d'auka guda d'aya ya had'omin da tawan ya mik'omin, ¡°kije kuyi wayar kawai, da safe sai a nemo miki charger d'in¡±.
Na tashi naje na kar6o tareda cewa ¡°nagode¡± najuya nafice da cup d'in fresh milk d'in a hannu na.
Bina yayi da kallo harna fice, ya sauke ajiyar zuciyata kafin ya cije lips nashi domin jin mararsa tad'an rik'e masa kad'an.
Koda naje d'akina saina kasa ajiye fresh milk d'in, haka kawai naji kuma sha'awar nasha, nako d'aga cup d'in na shanye tas sannan na zauna ina juya wayar tasa datamin k'yau, saina tuno wayarsa daya barmin ranar idi, na ta6e bakina kawai nafara saka number innarmu..............??
Hummm mi zai biyo baya bayan shan fresh milk kuma?. da zuwan muftahu?.?
Wannan amsar sai ranar Monday?. naso yimuku wannan weekend d'in amma munada biki gsky.???
*_hhhh naji k'orafinku sister's, ammafa ko pages biyu nakeyi ba isarku zaiyiba?, wlhy bama nida time d'in yin typing 2pages a rana, saboda inada aure, akwai nauye-nauye a kaina nima, masu kuma so nagama kafin azumi suma ina basu hak'uri, bazai yuwu nagama kafin azuminba, dan azumin kad'an ya rage, kuma banason datse labarin nan kamar yanda nayi a SIYASA KO KABILANCI, zanbi a hankali na gama, wlhy nafiku son nagama nima Na huta, Dan dana fara buk zai fara cizona a zuciya nima, so kawai nake naga nagama?, karku manta ko tarihin masarautar su Galadima sameer har yanzu bamu saniba, Dan haka zamuyi, iya inda muka tsaya saimu cigaba bayan salla idan ALLAH ya kaimu da rai da lafiya, Dan kamar yaune ai.???._*
Ngd sosai da soyayyar dakuke nunama buk d'innan, ina sonku nima har cikin raina, ina fata zaku fahimceni???.
???????
???¡Ã¢
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu???_*
[4/30, 7:46 PM] Sis Naja Atuh: *_Typing?_*
*_HASKE WRITERS ASSO...?_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_?RAINA KAMA......!!?_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce??_*
??2?5?
..........Bugu biyu ta d'auka, jinayi tamkar anmin bishara da aljanna dan dad'i, lokacin danaji muryar innarmu tayi sallama cikin sanyinta sai kawai na Sanya mata kuka.
Ita kuma daga can batasan wayeba, a sanyaye tace ¡°baiwar ALLAH ko bawan ALLAH lafiya kuwa?¡±.
Murmushi nayi, gakuma hawaye na kwaranya, nace ¡°innarmu nice fa¡±.
Cikeda d'okantuwa tace, ¡°Munaya kece? ya kuke?¡±.
Murmushi nayi mai sauti, nace ¡°innarmu ina yini? inasu Aryaan? Wlhy ina missing d'inku innarmu, ALLAH kamar na dawo gida¡±. na k'are maganar da sakin kuka.
Kallon juna sukayi da Abbanmu, da yake girkin tane tana d'akinsa, sukama juna murmushi, Abba yace, ¡°haba dai munaya ta jaruma ce da kuka haka? Ina aka ta6a kai mutum gidan miji yayi sha'awar dawowa gida inbada yawoba?¡±.
¡°wayyo Abbanmu I miss u so much kaima wlhy¡±.
Dariya suka sanyamin shida innarmu, Abba yace, ¡°yo ga sakaran yarinya, miyeto na kukan hakan? Yaya mijin naki da jama'ar gidan?¡±.
¡°komai lafiya lau Abba, sai kewarku, musamman ma Munubiya, ALLAH ina kewarta Abba, dan ALLAH kace ya kaini na ganta¡±.
Yanzu kam dai su Abba sosai sukemin dariya, saikuma suka shiga tsokanata, tun ina kukan harna ware nima ina dariya, munyi hira sosai, kafin Abba yace ¡°saida safe hakanan, karda ki k'are masa kud'in, ki gaidashi¡±.
Cikeda farinciki namusu sallama, da cewa zankirama gobe.
Na yanke wayar ina murmushi, Munubiya na kira itama, cikin sa'a tashiga kuwa. tana kwance jikin yaa Marwan yana d'an rage zafisa?, wayar tafara ring, shine yamik'o mata, ta amsa tana kallon number, irin Special number d'in Nance, wadda zaka ganta a tsare. (?bara na Baku, amma banda matan aure 07000000000?)???¡Ã¢???¡Ã¢.
Saida ta kalli yaa marwan ya d'aga mata kai alamar tayi picking sannan ta d'aga.
Muryar Munaya dataji yasata mik'ewa zaune zumbur cikeda d'oki.
Kowa yay kewar d'an uwansa, dan haka ko gaisuwa bamu tsaya yiba muka shiga fad'ama juna yanda mukai missing. muka 6alle hira kamar zamu ga juna tacikin wayar..
Mun d'au tsawon lokaci munayi kafin yaa Marwan yasamu dole yin sallama, wayar ya kar6a ya jawo matarsa ya rungume, zatayi magana ya d'ora yatsansa a bakinta alamar tayi shiru tareda yanke wayar ko sallamar arzik'i bamuyiba.
Inajin sukur-sukur d'insu ta wayar, dan haka na tuntsure da dariya ina fad'in oni su yaa marwan Ashe dai ashe?....??.
Number Fauziyya na gwada itama akashe, nace lallai amarci yayi dad'i kenan?, itama Ayusher na kira number busy, 'Yar tara, nasan tanacan itada khamees ana soyewa.
Feena ma wayarta Switch up, nad'anyi tsok'i na ajiye wayar Na tashi domin yin shirin barci, dan yau ina cikin farin ciki, tunda naji muryar families d'ina.
Tun bayan fitar Munaya kam Galadima yafara jin canji a jikinsa, a hankali yakejin wani feelings na bijiro masa, kamar wasa abufa yafara tsamari, tun yana basarwa har mamaki yafara kamashi, shin wai mike faruwa ne dashi haka? bazaice baya sha'awa ba, yanayi sosai, dan wani time d'inma saiyasha tablets, ko allurar kwantar da sha'awan, amma baita6a jin irin na yauba, k'arfin sha'awarsa yasashi katange kansa daga dukkan abinda zai iya zurmasa ga halaka har yazama hanyar tsanin aikata zina. duk da jiya yad'ansha wahala saboda abinda yafaru tsakaninsa da yarinyar can duk da shi yayine badan yaji wani abuba, amma Abu yaso zamar masa Matsala a yinin gaba d'aya, sai dai tunda yaje yay allura sai nutsuwa tazo masa.
Dauriyarsa ce take Neman zuwa k'arshe, sai kawai jikinsa yafara rawa, da bin bango yashiga bedroom d'insa, drowan gefen gadomsa yabud'e yad'iba drugs kusan uku ya watsa a baki, ruwa ya d'auka frigate ya korasu suka wuce.
Humm abanza wai man kare, maimakon yaji sauk'i saima abin ya k'aru. yadawo falo saman doguwar kujera Yakuma kwanciya bayan ya kashe AC n gaba d'aya, Dan k'ara dulmiyar dashi yakeyi.
Nima d'in agareni kusan hakane, kad'an-kad'an nafara jin tsigar jikina Na tashi.
Kamar wasa ina wanka sai Abu yafara shan kaina, abinda bansan ma'anarsa ba yafara bin jinin jikina da 6argo, na lumshe idona ina hango abunda yafaru tsakani na d'azun da Galadima, duk dani wahala ma nasha, wani feelings na tashin hankali yafara bijiromin, idanuna harsun sauya kamanni, da k'yar nayi wanka nafito, ko towel d'in ban cireba na saka hijjab Na d'au wayarsa Na fita, koda nayi sallama a k'ofar falonsa banji ya amsa ba, nayi har sau uku shiru kakeji, shikam yana kwance yana jina, amma bakinsa yakasa koda motsawa barema ya amsa min, saima muryata dake sakashin jin wani zirrr, duk sanda nayi sallamar sautin muryata na motsawa da tsigar jikinsa ne, gaba d'aya gashin jikinsa ya tashi.
Jin shirun yayi yawa natura k'ofar kawai Na Shiga abuna, azatona ko barci ya d'aukesa kokuma bai jiniba.
Ganinsa kwance saman doguwar kujera yasa gabana d'an fad'i, gawani iri dana kuma ji jikina yayi, dagashi sai boxer da vest, hannunsa d'aya dafe da mararsa, d'ayan kuma dafe da kansa, kauda kaina nayi daga kallonsa saboda tsorata da ganinsa a ainahinsa, gaskiya ba k'aramin namiji bane guy d'innan, duk kunya ta isheni, ban ta6a ganin namiji ba a haka, yo samarin gidanmu basa zama haka. duk tunanina barci yakeyi, na ajiye wayar saman cikinsa a hankali, kamar yanda naga d'ayar a ajiye, caraf ya rik'e hannuna da hannunsa daya dafe kansa, tsoro yakamani lokacin daya bud'e idonsa yana kallona, jazur idon yake abin tsoro. Muryarsa a matuk'ar sanyin daban ta6a Sanin yana da shiba yace ¡°mi zakiyi?¡±. idanu na nad'an waro waje cikin tsarguwa nace, ¡°mi zanyi kuma? wayarkace fa na ajiye maka¡±. ajiyar zuciya yad'an sauke, ya zuba min idanu batareda yasakimin hannunba. Gaba d'aya jikina yakuma rikicemin, jima nake tamkar Na fad'a kansa saboda abinda nakeji, ganin karna aikata abinda zanzo ina nadama saina zare hannuna dad'an k'arfi, jikinshi babu kuzarin kirki, danhaka yasaki hannun kawai, nikuma na juya nafice daga d'akin da saurina.
Lips d'insa ya cije da matuk'ar k'arfi kamar zai huda, Yakuma dafe mararsa datayi tamkar zata fashe masa, kai bazai iya daurewaba, domin zai iya mutuwa wlhy, ganin yarinyarnan kuma Yakuma birkita tunaninsa. idonsa yarigada yarufe, ya manta matsayin Auren Nasu, duk da gargad'in da wani sashen zuciyarsa yake masa akan alk'awarin daya d'auka, burinsa kawai ya sauke wannan nauyin kozai samu nutsuwa, da k'yar yamik'e ya fice zuwa d'akina.
Nikam INA zuwa na zube saman gado bayan Na zare hijjab d'in, dagani sai towel, marata data d'aure tamkar zata fashe na rik'e da hannu biyu Ina hawaye, wai wannan wace iriyar masiface ne?, nashiga uku ni Munaya, mike shirin faruwa dani ne?..
¡°innalillahi¡± kawai nake iya karantawa saboda tashin hankali, jikina harwani rawa yakeyi, ko kad'an bansan Galadima ya shigo d'akinba, dan nafad'a wata duniya ta daban, babu zato kawai naji mutum yafad'o jikina yana sauke numfashi wani na k'orar wani, wata wawiyar runguma yamin tareda matseni ajikinsa gam, kai kace cikinsa zai maidani.
Humm maimakon na turesa sai nima nakuma k'ank'amesa, banyi k'asa a guywaba wajen maida masa murtani abinda yakemin..
Daga ni harshi kowa yafita hankalinsa, dan idonmu yarufe bamusan mi Muke aikatawa bama.
Hankalina bai nemi dawowa ba saida naji Galadima na neman kasheni, duk da inajin lokacin dayake jero addu'a amma ban dawo dai-daiba, nayi nisan da banajin kira kam, saida mai gayya mai aiki ke shirin faruwane na farga.
Ina yayi Nisan da bazaiji kiranaba balle kuka da magiyata akan karya cutar dani, yatuna alk'awarin daya d'auka please, baimasan inayiba, duka, cizo, yakushi, babu kalar da ban masa ba, amma bawan ALLAH nan saida yamin biji-biji, dukkan fushinsa na shekarun baya saida ya fanshe a wannan daren.
Nayi kuka harma ba'a jin sautin fitarsa, a jama'ar gidanmu kuwa ai mutum d'ai-d'aine ban kiraba, duk tsanar innaro danayi ranar saida nakirata ta taimakeni (?Munaya anga idi?).
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯*¡Ã¯*¡Ã¯*¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
A can kuwa muftahu Na fita sukaci karo da Harun, kallon-kallo akama juna, cikeda tsantsar mamaki Harun yace, ¡°wai Muftahu mikake shiryawa ne?¡±.
Kallon rainin hankali muftahun yamasa, yagyara tsayuwarsa yana wani murmushin da bakowa zai iya fassara Shiba, ¡°ban fahimci tambayar takaba, amma mikake nufi?¡±.
Harun ya d'an hararesa, ¡°Muftahu karka rainamin wayo, tabbas nasan ni da kai duk abokan Galadima ne, bayan zumunta dake a tsakaninmu, amma shige masan dakake fiye da kowa a wannan tsakanin yana bani mamaki¡±.
Muftahu ya ta6e baki yana wani basarwa, kafin ya kalli Harun a wani yanayi, ¡°Harun kana sakamin idone kenan a al'amurana? humm bazance ka bariba to, kacigaba, ni da kai d'an halak ka fasa, idan kaga dama ka kunna wutar jefani bayan kaga abinda zanyin, wannan ba damuwata baceba, inar Na cimma burina right?¡±.
yana gama fad'ar haka yabar wajen kawai. Yayinda Harun yabishi da kallo kawai tamkar wani soko, a zuciyarsa yana tunanin mi Muftahu ke shiryawa ne akan Galadima? tun kwanaki yakeson fargar da Galadima illar kusanta Muftahu a jikinsa, amma abin kamar wani tsafi, da Zarar sun ke6ance da Galadima to saikaga Muftahu a wajen, saikace mai gani har hanji, kenan yakamata yasake shiri akan Muftahu?.
Da wannan tunanin shima yashige mota yabar gidan, saikuma Galadima ya fad'o ransa, waya ya d'auka ya kirashi, amma saiyaji Number busy, hakanne yad'an sakashi nutsuwa, a tunaninsa ko Galadima yana wayane dasu Momma. (A time d'in Munaya Na waya da phone d'in Galadima).
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯*¡°*¡°¡Ã¯¡±*¡±*¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Yanda ta tashi a firgice haka shima ya tashi, jikinsa ya jawota ya rungume saboda waige-waige da takeyi tana kwala kiran sunan MUNAYA!.
jinta a jikinsa saita d'an sami nutsuwa, cikin kuka tace, ¡°yaa marwan mike faruwa da 'yar uwata ne?, nayi mafarkinta cikin mawuyacin hali tana kuka da kiran sunana Nazo Na ceceta¡±.
¡°sorry baby, ki kwantar da hankalinki mafarki ai ba gaskiya baneba, maybe shaid'anune kawai suka taswuranta hakan a gareki, amma ba d'anzun kuka gama wayaba? kofa awa 5 ma ba'ayiba da gama wayar taku?¡±.
¡°hakane yaa marwan, amma acikin awa 3 wani Abu bazai iya faruwa ba? ka kiramin ita please naji?¡±.
¡°no kiyi hak'uri, dare yayi gaskiya, babu yanda za'ayi mu kirata a wannan time d'in, k'arfe 1 fa ta wuce, 2 ma saura, karkuma ki manta tanada miji itama yanzu. Muyi addu'a ALLAH yasa alkairine, da safe saiki kirata ko?¡±.
Cikin share kwalla ta d'aga masa kanta, a hankali ya kwantar da ita a jikinsa bayan shima ya kwanta, yad'an furzo huci kafin yakai hannu yana shafa kanta tareda sumbatar goshinta yacigaba da bubbuga bayanta a hankali, kowa yana yin adu'a, ahaka barci ya kwashesu, duk da sun dad'e basu koma ba, musamman ma Munubiya da mafarkin yak'i barin ranta, Dan takasa yadda Munaya Na cikin k'oshin lafiya gaskiya, ka wai dai dan batada yanda zatayine ta hak'ura.
*****¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯*¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯****
Hawaye kawai nake iya zirarwa, amma kwakwkwaran numfashi bana iyawa saboda jigata, zan iya danganta abinda Galadima yayimin da fyad'e, dan baya cikin hayyacinsa ko kad'an, kamar yanda nima nawa ya gushe daga farko nabashi gudunmawa. (Nasan duk mai hankali ya k'iyasta a yanda Galadima ya zomin zai tabbatar dolene na jigata d'in?).
Tunda yasamu nutsuwa yana gefena a kwance kawai, a hankali memory d'in brain nasa ke tariyo masa abinda ya aikata tamkar a mafarki, ya bud'e idonsa da hanzari akaina, domin kuma gaskata abinda yafarun, shin da gaskene ya aikata? ¡°innalilahi¡± yashiga maimaitawa dan ganina kwance a gefensa ina hawaye, daganin yanda nake a kwancen ina fidda numfashi d'ai-d'ai kasan nagama jigata, yabi d'akin da kallo cikin tsantsar takaici, yaushema shikam yazo d'akinnan? ¡°Hasbinallahu wa ni'imal wakil. mike faruwa danine ni Sameer? wace k'addarace kuma ta kutsoma rayuwata? yanzu nan ni Muhammad Sameer ne da wannan d'anyan aikin? miya samu tunanina haka?.......¡±
Tunaninsa ya tsaya cak lokacin daya jiyo dasashshiyar muryata ina kiran innarmu da Munubiya, muryata a raunane, runtse idanunsa yayi tareda mik'ewa zaune da k'yar, dan jikinsa gaba d'aya yayi week, ga wani masifaffen ciwo da kansa keyi. da k'yar ya iya kuma bud'e idanunsa a kaina, babu shiri yakuma runtsewa saboda tsorata da ganin yanda yamin, hawaye kawai yaji suna neman zubowa a face nashi saboda shi mutum ne mai tausayi, bayason yaga ancutar dawani bare kuma shi da Kansa ya aikata, jarumtar had'iyesu yayi tareda kuma bud'ewa, yazubama fuskata ido batareda ya iya cemin uffanba, yama rasa ta inane zai fara shikam, mizai fad'amin kuma a yanzu Na yarda dashi? mizai cemin shikuwa?.
Innarmu dana sake ambata murya a sark'e yasakashi saurin kallona, baisan yarik'o hannuna ba ya rumtse anasa, la66ansa sai motsawa suke amma yagaza yin magana, shi yanzu ma baisan wane irin taimako zai baniba, bai ta6a irin hirarnan dawani abokiba balle yace yasan ya zaiyi, bai ta6a aikata zinaba, zai iya rantsuwa da Ubangijin daya haliccesa bai ta6a ta6a jikin wadda ba muharramarsa ba, sai ita Munayar daya d'auketa randa yasa a sato masa ita. Kuma ko muharramar tasa bazai wuce yarik'e hannun taba shima ba kowaba wlhy, inhar kacire Samha Momma Aunty Mimi ko Mom, sukad'aine mata Muharramsa da zaice yanada shak'uwa ta musamman dasu, amma shi ko yaran masarautar nan bama kowacce zai iya ambatarta da sunanta dai-daiba.....
Rashin ya cika da tashin hankali, kukan danakeyine yasakashi waigen phone nashi, baiga komaiba, tunawa yayi ba d'akinsa baneba nan, ya saki hannuna ya sakko agadon bayan ya suturta jikinsa, jikinsa gaba d'aya ya mutu, ahaka da sand'a yakai falonsa, wayarsa dake a saman kujera ya d'auka, to inama zai dosa shikam? wazai kira akan wannan abin kunyar daya aikata? tunanin bincike a network ne ya fad'o masa a rai, maybe yasamu bakin zaren, Google yashiga yay d'an rubutu yahau Searching, amamakinsa kam saigashi sun bashi, saiya kuma wata tambayar, nanma yasamu amsa dai-dai, ¡°Alhmdllh¡± yafad'a yana mik'ewa rik'e da wayar.
Inda yabarni ya iskeni, Toilet yawuce kai tsaye, yayinda nabishi da kallon tsana, nikad'ai nasan minakeji akansa, ayanda nakeji ko wuk'a aka bani zan iya fidda masa hanji waje, tabbas yanzu nakuma yarda banida wayo, yanda tun farko Na yarda da maganar wai auren yarjejeniya mukayi da Wanda yafi k'arfin ajina da matsayina, inma banda wauta irin tawa tayaya mutum kamar Galadima zai nemi kulla aure dani?, Na manta namiji zai iya komai domin cikar burinsa, k'ilama *AUREN 'DAN'DANE* yayi dani, ai sainaji wani kuka ya tokaremin mak'oshi, har ina neman shid'ewa.
Kamar yanda yaga sunsa ya had'a ruwa mai zafi-zafi, sannan yafito, ficewa yakumayi, babu dad'ewa sosai yadawo yakuma shigewa toilet d'in, ni dai idonama Na rufe gaba d'aya, dan bana k'aunar ganinsa.
Jinai kawai an kama hannuna ana k'ok'arin tadani zaune, wata azaba naji har cikin kwalwar kaina, saina fashe dawani marayan kuka Wanda yasakashi saurin sakina nakoma Na kwanta.
Runtse idonsa yayi saboda jin addu'ar danake jero masa ta neman sakayya ga ALLAH tsakanina dashi, wani bai ta6a masa makaman ciyar addu'ar nanba, amma gashi matarsa ta sunnah tana masa, duk da yasan hak'in sane ya k'ar6a agareta hakan bai hanashi jin bak'in cikiba, dan aganinsa inada hujjar masa addu'ar da tafi wannan muni, tunda Bahaka mukayi dashiba.
Cikin tsantsar damuwa ya d'aukeni zuwa bayin, yayinda nikuma nake kuka ina fad'in ya saukeni, duk da a hankali nake maganar yana jina.
Ba k'aramin daga mukayi dashiba wajen taimakona, harda cizonsa nayi a damtsen hannunasa, aiko yacizu wlhy, dan hakwarana saida suka huda lallausar fatarsa, (to dama ba wahala tasaniba fatar) amma a mamakina sainaga ko gezau baiyiba, kuma Na tabbata yaji zafin cizonnan, saidai bansan dalilinsa Na daurewaba, da k'yar ya samu nayi wankan tsarki kuwa, dan saida yakusa makeni ma dan haushi sannan nayi, harya dawo dani d'akin ban daina jera masa ALLAH ya isaba a fili da kiransa mugu azzalumi.
Duk da kalamaina suna sukar zuciyarsa haka yadake yanuna tamkarma baya jina.
Bashida maganin dasuka rubuta akan matsalata, sai dai yanada Wanda zai iya taimaka min kafin zuwa Safiya ya nemo wancan.
Haka yakawo min maganin da tea wai nasha, harara kawai Na zuba masa Na maida kaina Na kwanta batareda nako motsaba balle yayi zaton zan tashi.
Shima baice komaiba yakamani ya tayar, hannunsa da k'irjinsa nashiga bugu, ina kuma kaimasa cizo, amma k'arfin ba d'ayaba, bai barniba saida ya tadani, sannan ya wani ci uban Magani fusakarsa amatuk'ar murtuke, yace ¡°kinsan ALLAH koki kar6a kokuma....humm¡±.
Yanda yay maganar kuma sai tsoro ya kamani, Na watsa masa harara kafin nabud'e bakin, da kansa yabani shayin, sannan yabani magani. mugun Ashe harda Na barci, cikin mintuna k'alilan barci yay awon gaba dani.
Sai lokacin ya samu damar sauke ajiyar zuciyarsa tareda dafe kansa dake tsananin sara masa. Duk yanda yaso yayi tunanin ya akayi hakan tafaru yakasa, saboda matsanancin ciwon da kansa kemasa, dole yamik'e zuwa d'akinsa, shima ruwan mai zafi yay wanka dashi sannan ya tsarkake jikinsa ya fito, Magani yasha ya haye gado ya kwanta shima, yasan bazan farkaba a nan kusa.
Maganin barcin da shima yashane yasaka barci suresa shima.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯(())¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Tun daga shigar Muftahu wajen Galadima har zuwa sanda ya zuba Abu cikin milk d'in Galadima lokacin daya Shiga bedroom d'insa d'aukar Abu suna kallo, har ya girgiza ya ajiye kwalin da sauri inda ya d'auka, fitowar Galadima zamansa da files d'in daya bama Muftahu Na masu buk'atar taimako a asibiti da aka kawo masa zai biya, har shigowar Munaya falon Galadima da fitar Muftahu, zamanta da kar6ar wayarsa zuwa fitarta itama, yanda Galadima yafara fita hayyacinsa har dawowar Munaya sashen takawo masa wayarsa, fitarta dakuma bin bayanta dayayi, hankalinsu ne yad'an tashi ganin yadad'e bai dawoba, gakuma a yanayin daya fita.
Hakanne yasaka aka turo wasu mata biyu da kayan fruits wai sukawoma Galadima domin suyi CID d'in yana ina?.
Sai dai sarkin k'ofa kuma yace saiya musu iso, kamar yasani saiya rufe k'ofar ta ciki sannan yanufi sashen Galadima d'in, yayi sallama tafi sau 15 amma babu amsa, ya tabbata da yana kusa daya amsa, komawa yayi yace musu ai yamayi barci, su koma dashi kawai, babu magiyar dabasu masaba yak'i bud'e musu, dan yarigada yasan komai Na kitumurmurar gidan, sannan yasan Galadima bayacin abincin kowa a masarautar, ko ankawo su yake bamawa, idan kaga yaci abincin dawani yadafa a masarautar to tabbas aunty Mimi tana k'asar, sunzo tare kotazo ta iskeshi. dan haka yahanasu shiga, harma yad'an tsargu da tunanin kawai wani Abu a k'asa ganin sun jajurce dason shigar.
Ransu a 6ace sukabar wajen, inda aka aikisu suka koma, sun Isar da abinda yafaru.
Hakan kuma yakuma tada hankalin masu Aiken nasu, domin an ruguza musu plan d'insu kenan...........??
?hummmm.????¡Ã¢???¡Ã¢???¡Ã¢
_ko Yaya za'a kwashe tsakanin Galadima da Munaya da safe kuma??, Munaya team amin afuwa???ku kora da wanan??????????._
??
*_Masu karatu nasan kowa yamatsu yasan tarihin masarautar su Galadima, insha ALLAH zakuji, inason muzo ga6ar daya kamata kuji d'inne insha ALLAH, saura k'iris???._*
Barkanmu da dawowa???.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*?
[4/30, 7:46 PM] Sis Naja Atuh: *_Typing?_*
*_HASKE WRITERS ASSO...?_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_?RAINA KAMA......!!?_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce??_*
??2?6?
..........Da kuka na farka, duk da naji dad'in jikinna kuwa, dan banajin azabar kamar jiya, tashi nayi zuwa toilet danna d'auro alwala, na tuna labarin da wata k'awarmu ta ta6a bamu akan yanda taita ciwon jiki, saida mijinta yata mata ruwan zafi a ranar, ruwan mai d'an zafi na had'a na shiga ciki, nasha zafi kuma naji dad'i, amma inajina kamar ba a dai-daiba maganar gaskiya, haka dai nasamu nayi sallar asubahi, ina tsaka da sallar yashigo da nufin tadani, ganin na tashi ma saiya juya yafice abinsa zuwa masallaci shima.
Koda na idar kwanciya nayi saman abin sallar nacigaba da kuka na, ina kuma tunano abinda yafaru a jiya tamkar a films ko novels ko mafarki, babu abinda zuciyata keyi sai tsinemar, a yau d'inan dolene saiya bani Sakina natafi gidanmu, nafasa auren Contract d'in ma, da dai na zauna da mugunnan gwamma nakoma gidanmu nacigaba da rayuwa dasu innaro yafimin....
Tun d'azun yana tsaye a kaina, tausayina yakamashi, dan yasan shine silar kukan mawa, bayason zalunci ko kad'an, amma saigashi shine da aikatawa kuma, zama yayi a bakin gadon, cikin muryar nan tasa mai kama da anmasa tilas yace ¡°tashi zaune muyi magana¡±.
¡°baza na masa, a zuciyata nace bazan tashiba mugu kawai, bakada abinda zaka fad'amin na yarda, azzalumi, dama abinda ka shiryawa rayuwata kenan? Dan kaganni d'iyar talakawa banida k'arfin gogayya da kai, tabbas nayi kuskuren yadda da Wanda shikansa ma bai gama yadda da kansaba, ALLAH ya Isa wlhy tunda ka ketamin mutunci har abada bazan yafe makaba, kullum cikin sallata saina sakoka da neman sakkaya ga mahaliccina akan zalincin dakami.........
A fili kuma nace, ¡°kagama zalintata kazo kanamin mazurai da mulki, ank'i tashin¡±. a hankali nake maganar banyi tunanin yana jinaba, sai tsawa kawai naji ya dakamin
¡°k!!!!!¡±.
Yafad'a cikin daka tsawa, Ashe tunda nafara maganar ya rumtse idanu saboda yanda Kalmar zaluncin suke sukarsa a zicciya, ban ta6a ganinsa a wannan yanayinba, a cikin fad'a yace, ¡°Niba azzalumi baneba, zina nayi dakene!? dazaki dunga aibantani damun duk furucin dayazo bakinki? to bara na tuna miki idan kin manta, SADAKI na biya na auroki! tun jiya kike fad'an magana amma na shareki, ni sa'an kine? wlhy idan bakiyi wasaba zan koya miki hankali! danaso muyi magana ki saurareni mana kiji mizance?.........¡±
Zumbur namik'e zaune, duk da azabar da k'asana kemin, na kallesa ido cikin ido ina zubda kwalla nace, ¡°bakada abin fad'a shiyyasa bazan saurarekaba, bar ganina 'Yar talaka bana d'aukar raini wlhy, mina maka ne? miye had'ina da kai kaketa bibiyar rayuwata da bala'i, tunda na had'u da kai ban kuma samun nishad'iba, wlhy bazan yafe makab.......
Jikake bamm! ya make bakina da bayan hannunsa, cikin zazzaromin ido yace bazaki nutsuba Ashe?¡±.
Naji zafi sosai, dan haka nafashe dawani marayan kuka mai ban tausayi, ga wani bala'in tsoronsa daya kuma shigata, maganar ma a tsorace dama nayita, Dan tsabar bala'i na hango cikin idonsa Dana kallesa.
Kansa ya dafe da hannu, jiyake tamkar ya tariyo jiya a rayuwarsa ya goge dukkanin abinda yafaru
Ganin bazan sauraresan ba da gaske saiya tashi ya fice yabarmin d'akin.
Nakuma 6arkewa da kuka.
Koda yafita a falona ya zauna, ya dafe kansa daya koma masa ciwo k'asa-k'asa yau, tunaninsa yafara komawa baya daga jiya zuwa yau, shin miya sakashi wannan matsananciyar sha'awar ne wai? dan bai ta6a jin makamancin feelings irin na jiya ba, da sauri yamik'e yanufi sashensa, a falo ya tsaya, ya d'auki kwalin hollandia fresh milk d'in jiya yana dubawa, shi dai yasan shine last abu daya sha a jiya, to kenan koma miye daga cikinsa yake?. to amma ai ba yaune yafara shan fresh milk ba a gidannan balle yace kuma shine. kwalin ya ajiye yakuma dafe kansa, gaba d'aya tunaninsa ya kulle, dama shi indai yana cikin 6acinrai to komai nasa birkicewa yakeyi, dolene saiya kwantar da hankalinsa zai iya kamo bakin zaren. a kujerar Yakoma ya kwanta, ko azkar yakasayi yau, babu dad'ewa barci yakuma kwasheshi anan.
Itama Munaya daga kuka barci yay awon gaba da ita a wajen.
Har Samha suka kawo abinci duk barci suka Tatar sunayi, tasan halin Uncle Sam shiyasa bata tadasu ba, kad'an daga aikinsa ya mammaketa a safiyarnan.
Su duka sai wajajen 12 suka farka, kowanne yatashi da damuwarsa.
Tunda nayi takun farko nakuma tabbatar da akwai matsala, dan ruwan zafin da yaymin jiya kad'ai ya isa na daina jin zafinnan irin haka, balle kuma nima nayima kaina da safennan, amma maimakon k'asana yabar zafin saima zugi yake k'arawa, gashi idan nashiga ruwan, zafi nakeji sosai.
Yanda nake takawar ina hawayene yabashi mamaki, dan aganinsa yakamata nasamu sukuni saboda yanda yamin jiya. bansan yashigoba, maganarsa kawai naji..
¡°Wai mike faruwane? Ko dai kinji ciwone?¡±.
Wata uwar harara dataso bashi dariya na zuba masa, amma saiya danne baiyiba, takowa yayi har inda nake yakama hannuna na fisge, ya d'aure fuska shima yana hararata, ¡°k! Wlhy kinutsu kafin na canja miki kamanni¡±.
¡°yo kammani na yaushe kuma zaka canja min? bayan Wanda ka canja min yanzu? dama haka kake? a fuska kamar babu ruwanka amma sai zalunci taf zuciyarka¡±.
Idonsa ya runtse dan bayason Kalmar zaluncin nan danake jifansa dashi, jinai kawai an fusgoni an zaunar a bakin gadon, nakuwa fashe da kuka ina fad'in ¡°wayyo zafi, munubiya Azalumin nan zai kashe miki ni¡±.
Ko kallona baiyiba yafice, ina nan ina kuka saigashi yadawo da wayarsa a hannu, ya zauna saman sofa batareda ya kalleninba, bashida mafita saita kiran Akash, dan yanason sanin minene matsalar datake sakani wannan kukan da complain d'in zafin, yasan koya tambayeni ba fad'a masa zanyiba..
Da turanci suka gaisa, amma da zaiyi tambayar saiya canja harshe zuwa yaren daban saniba.
Akash yace saidai idan ciwo taji, dan bai kamata ace tana Complain zafi irin haka ba, zataji ciwo kam amma bawai yanda yake nuna masa yanzun ba.
Galadima ya gyara zamansa sosai yace ¡°to ai na sanar maka fyad'e akama yarinyar fa¡±.
Akash yace ¡°zata iya kai shekara nawa yarinyar?¡±.
'Dago ido yayi ya kalleni kafin ya janye yana fad'in ¡°Maybe 19years ko 20 kawai¡±.
¡°ai bama yarinya baceba can sosai, inaga taji ciwone gaskiya, yakamata doctor ya dubata gudun samun matsala, amma kabada gudunmawa a hukunta Wanda yay abunnan my man, please ka kwatarma yarinyar hak'k'inta wajen azzalumin nan¡±.
lips d'insa kawai ya cije maganar Akash na sukar zuciyarsa, da Akash yasan shine yay aika-aikar dabai ce hakaba. sallama sukayi ya yanke wayar, saikuma yafara tunanin doctor d'in dazai nemo ya dubani, dan bashida damar fita dani a gidan yanzun.
Can doctor Hafsat ta fad'o masa a rai, ita kad'ai zai iya aminta tasan matsalarsa, dan ya yarda da ita sosai, yasan zata masa k'yak'yk'yawar fahimta.
Kiranta yayi bayan sun gaisa cikin mutunci ya fad'a mata matsalar ta yanda zai iya, dukda ya 6oye mata wacece keda matsalar ta fahimcesa, d'an murmushi kawai tayi tana girgiza kai da tausayin yarinyarnan data shiga hannun Galadima, duk abinda zata buk'ata tagama had'ashi sannan ta fito, matsalar gidansu data Sani yasakata yin shiri tamkar ba doctor ba.
Shiru d'akin yayi, sai kukana dayake fita a hankali, shikam ya zubamin idanu yana kallona k'asan ido, zaune yake k'afa d'aya akan d'aya, ya jingina da kujera, saika rantse idonsa a rufe yake, amma yana kallonane ahaka.
Bayan doctor Hafsat tazo k'ofar fada saita kirashi, dan baza'a barta kai tsaye tashigaba.
Ina kallonsa ya fice bayan ya yanke wayar daban San dawa yakeyinta ba.
Kusan mintun 20 saigasu sunshigo dawata mace, ba yarinya baceba can gaskiya, zasu iya zama sa'anni da Galadima d'in, dan haka na tashi zaune na gaidata cikin girmamawa.
Ita kuma ta amsa cikeda fara'a.
Kallon Galadima tayi dayake tsaye yana kallonmu, ¡°ranka ya dad'a kozaka bamu wajene¡±.
Murmushi yad'anyi yana fad'in babu damuwa.
Yana fita matar ta zauna kusa dani a bakin gadon, fuskarta d'auke da murmushi tace, ¡°sunana doctor Hafsat Abu, friend d'in Galadima ce tun a primary school¡±.
Murmushi nayi mata na yak'e kawai.
Takuma gyara zamanta tana kallona, please dear karkiji nauyina, ki fad'amin matsalarki kai tsaye, dan ba'a wasa da wannan matsalar, takan zama babban Abu anan gaba ga d'iya mace¡±.
Kai na jinjina mata ina hawaye, sannan nace ¡°inajin zafin wajen sosai¡±.
¡°ok kozaki iya kwanciya nagani¡±.
Ido na waro waje a tsorace, sai kuma nayi k'asa da kaina saboda kunya.
Tayi murmushi tana kama hannuna, ¡°karkiji kunya akan lafiyarki dear, please ki daure kinji¡±.
Kai kawai na gyad'a mata sannan na kwanta, babu yanda zanyi dole na yarda ta duba, kanta kawai ta girgiza da mamakin Galadima, saikace Wanda ya kusanceni da k'arfin tuwo?, ai wannan kam da wani doctor d'inne saiya yima Galadima fad'ama wlhy, dan ko kad'an bai bini a hankaliba, amma ciwon daya jimin bazai zama mai cutarwa ba insha ALLAH.
da kanta yanzu ta had'amin ruwan zafi tazuba wasu magani, sannan ta taimakamin har zuwa bayin ta nunamin yanda zanyi. ban cutar da kainaba na nutsu nayi komai yanda tace, dukda inajin zafi kuwa, bayan nafito saina sameta zaune ta gyara gadon tsaf, gakuma abinci a ajiye, da alama Galadima ne ya kawo, tsareni tayi da lallashi naci abincin ma yanzun, sannan tabani magunguna nasha, ta kalleni da murmushi, ¡°ALLAH yak'ara lafiya gimbiyarmu, indai zaki cigaba da kulawa kamar yanda na nuna miki insha ALLAH nan da 2days zaki dawo normal, ga drugs d'inan saikina sha, shima wannan cream d'in kina matsi dashi awajen a koda yaushe¡±.
Kaina na jinjina mata sannan nace ¡° nagode Aunty¡±.
Sallama tamin tafice.
A falo ta iske Galadima, bayan tamasa bayanin yanda yakamata a kula dani saita kallesa cikin tsokana, ¡°ranka ya dad'e kafayi 6arna gaskiya, Shifa wajenan ba a nuna masa k'arfi, please a kiyaye¡±.
Murmushi kawai yayi baice mata komaiba.
rakiya yamata tareda mata alkairi sannan yadawo.
A kwancen data barni ya iskeni, zama yayi gefen gadon yad'an kalleni ya janye idonsa ¡°yaya kikeji yanzun?¡±.
Baki na turo masa, amma ban tankaba. shima bai damu da amsawar tawaba, ya basar kawai ya d'akko wata maganar.
¡°nasan babu abinda zan fad'a ki yarda dani tabbas, sai dai zankuma maimaita miki SAMEER BAYA ZALUNCI, koda wasa ban ta6a kawo zan aikata hakan agarekiba har kibar k'ark'ashin kulawata, bansan miya shiga kainaba a jiya¡±.
Kallonsa nayi ina hawaye da takaicin maganarsa, nace ¡°bakasan miya Shiga kankaba ka d'auki fresh milk kabani? bayan kasan mika zuba¡±.
Shima kansa ya d'ago yana kallona, cikeda k'asaitarsa yace ¡°ban fahinceki ba, mikike nufi? dan ina son na kusance ki sainayi amfani da wani abu? da hakan naso daret zanzo gareki tunda nasan nabiya sadaki ai, tunda ba tsoranki zanjiba ko?¡±.
¡°dama ai bazaka fahimceni ba tunda Kasan ka aikata ai, kuma ai alk'awarin zama tamkar abokai kamin ba irin wannan ba¡±, na had'e hannuna alamar roko?? ina kuka nace ¡°dan girman ALLAH ina rok'onka kabani Sakina a yau natafi gidanmu, wlhy nafasa auren Contract d'in, koma waye yayi abun ni na yafe masama, kawai ka sallameni¡±.
Yama rasa mizai cemin shi, ajiyar zuciya yad'an sauke, kafin ya cije lips nashi, ¡°shikenan, zan miki yanda kikeso, amma kibari ki warke, bai kamata ki koma gida ahakaba¡±. ¡®yana gama fad'ar haka yatashi yafice batareda yaji amsa taba.
Duk da naso yabani sakina a yau, amma zanyi hak'uri na warke d'in kwana nawane.
******
Yinin yau haka mukayishi duk zukatanmu babu dad'i, Galadima kam ai ciwon mara saiya nemi dawo masa sabo, jiyayi kawai yana sake buk'atar kasancewa dani, haka yayta dannewa har zuwa dare, dan bazai kuma yarda yin gangancin nanba. ganin yana neman mutuwa yay shiri a gaggauce yafito domin zuwa hospital.
Tunda yafito suke zubewa gaisheshi, hannuna kawai yake iya d'aga musu, dan kallo d'aya zaka masa ka tabbatar yanada damuwa, da sauri sarkin mota yazo yabud'e masa ya shiga, suma dogaran dakan bisa idan zai fita sai duk suka taso.
Tundaga fitarsu gidan Muftahu na kallonsu, yad'an murmusa kawai abinsa. (?wlhy Reader's suka kamaka zaka gane bakada wayo?)
Shi kad'ai yasan azabar dayakeji a jikinsa, yana kwance cikin kujerar ne sai faman cije lips yakeyi.
Tunkan sarkin mota ya tambayama ya sanar masa asibitin da zasuje.
Sarkin mota ya amsa cike da girmamawa da tausayin shugabansa, dama shi tunda yaga yafito ya fahimci akwai matsala.
Tun amota yakira wata number yana tambayarsa ko yana asibiti?. Dr Jalal ya amsa da eh yana nan.
Yanke wayar yayi kawai baisake cewa komaiba. Dr jalal yabi wayar da kallo yana mamakin Galadima da halinsa, kiransa yakuma yi shi dan bai fahimci inda maganar tasa ta dosaba. sai dai harta yanke bai d'aukaba, yana k'ok'arin sake kira yaji ana Knocking d'in k'ofar.
Amsawa yay da yes tareda izinin shigowa.
Wani dogari ya bud'ema Galadima k'ofar yashiga, da hanzari Dr Jalal yamik'e yana murmushi da masa welcome.
Hannu kawai ya iya d'aga masa ya zauna kujerar gaban decks d'in.
Shima Dr jalal saiya zauna, ¡°ranka ya dad'e lafiya dai ko?¡±.
Saida yaja wasu Seconds sannan yafara ma Dr jalal bayanin damuwarsa, ya sanar masa mararsa namasa ciwo tun jiya, kuma ada bata masa kamar hakan.
Shiru Dr jalal yay yana nazarin maganar tasa, saida yakai aya sannan yace ¡°ranka yadad'e kokasha pills ne?¡±.
Kallonsa Galadima yayi, ¡°pills kuma? wane irin tambaya kakemin haka?¡±.
¡°afuwa ranka ya dad'e, matsalar taka tayi kama da wanda yasha tablet ne, mikaci na k'arshe jiya?¡±.
cikeda nazarin maganar Jalal yace ¡°fresh milk ne last abinda nasha jiya da daddare¡±.
¡°to amma bayan shi kafara jin matsalar?¡±.
¡°kusan haka gaskiya¡±.
Dr jalal dai shiru yayi, dan ya tabbatar wannan aikin desire tablets ne, amma koya fad'a dawuya Galadima ya yarda, sai kawai yashare ya had'a masa drugs da injection yamasa, yace yad'an kwanta na kamar 20 minutes a office d'in. bai musa masaba ya shiga inda jalal kan huta idan yaso, saiya kwanta kawai, dan shima bazai iya tafiyarba, d'akin ma da taimakon jalal d'in yashigo.
Ni bansan hidimar da akeyiba, dan rabona dashi tun bayan munyi maganar saki, abinci ma tun Wanda doctor tabanine a cikina, sai kusan 8 Samha takawo min kayan fruits dawani Abu mai dad'i daban san mineneba?.
Ta zauna mund'anyi hira kafin tafice. a bakin ta nakejin wai jibi Friday zasu koma India.
Na danci abinda takawo nasha magani nayi kwanciyata cikeda kewar 'Yar uwata dana kanyi akowanne dare.
Galadima kam bai dawo ba sai kusan 1pm, yana shigowa sashensa yawuce yay shirin barci ya kwanta, Alhmdllh zuwa yanzu yaji k'arfin jikinsa, sai dai zuciyarsa nata cud'a masa tunanin ina yasamo pills? dan shima yafara yarda da maganar jalal, musamman idan ya tuno furucin Munaya na d'azun da safe.
To kenan wani ya zuba masa bai saniba? to amma wazai zarga shikam? duk wad'anda suka shigo wajensa a jiya amintattun sane, Sauban, Samha, Harun, Muftahu, duk sun shigo wajensa a jiya, amma Muftahu shine last shigowa, shiru yay yana nazari, can kuma saiya cije lips d'insa ya lumshe idanu yana shafa gurin Dana cijesa.
A haka barci ya kwasheshi.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Munubiya tashiga damuwa sosai akan rashin jina a waya, takira number ta yafi sau goma amma switch up, gashi yaa Marwan ya hanata kiran number dana kirasu a ranar, yace wai number Galadima ce bai kamata su damesa ba.
Haka taci kukanta a yinin ranar, saikace mara lafiya haka ta yini, zuwan su Ayusher ne ma yad'an sanyaya ranta har suka janye mata hankali da yawan tunani, a ranar gidan suka yini cir, sunsha hira da labarina, kowacce tana missing d'ina.
Sunce suna son zuwa amma an hanasu, wai gidan danake ba gidan da ake zuwa any how bane ba, babu yanda suka iya haka suka hak'ura.
*********
A gidanmu ma yau sukayi niyyar kawo min akwatinana da abinda ba'a rasaba, amma ankira wayata akashe, wannan yasa Abba yace abarni akaima su fauziyya nasu. ni daga baya idan an sameni akai min nawa d'in.
Duk inda akaje da innaro ake zuwa, kowacce ta taima gidanta kallon kwaf kenan, sotake taga gidan wacce tafi acikin sauran 'yan uwana.
ALLAH ya taimaki munubiya lokacin dasukaje gidanta yaa Marwan yana gidan, hakama su Ayusher.
Fita yayi yasiyo musu abubuwa yakawo, sannan suka zuba musu girkin da sukayi, babu ko kunya suka mik'e kafafu suka ci abinsu, to dama gidan Fauziyya ne kawai suka samu sukaci abinci, su Safara'u kam casukai basu fara girkiba, dan ita haleematu ma ruwa wannan bata basuba, banda innarmu akaje, dayake kowacce idan za'aje gidan 'yarta banda ita ake zuwa.
Zasu taho kuma yaa Marwan yabasu kud'in mota, dukda kuwa a mortar Dady yaa Anas ya kaisu.
Tunda suka dawo gida aka shiga labarin yanda aka iske gidan kowa, nanfa wad'anda gidan 'ya'yansu ba'a samu wani abun kuzo aganiba sai suka fusata, kunsan dai halin jama'ar gidan namu?, wannan Abu saida yakawo rikici, fad'a sosai sukasha abinsu, itadai innarmu k'ala bata ceba, saima ta maida hankalinta ga girkin dare datakeyi, ga innaro sai habaici takeyi, saida gwaggo Safiyya tazo da k'yar ta lalla6ata tafita.
Matan anguwa makwafta kam sun masa kunne suna saurare da kwasar dariya, dan lamarin gidanmu yazama kamar na 'yan wasan kwaikwayo.
Duk tsiyar dasukeyi dady yana gidan yana jinsu, amma ko lek'owa bai yiba, danshi bashida hayaniya ko kad'an, balle daya fahimci abin yashafi 'yan bani na iya d'in gidan ne, dariya kawai yayi yace ALLAH ya k'yauta. kad'anma kenan ai, bakuga komaiba tunda yanzu kuka fara aurarwar, kuma har yanzu da sauran 6ur6ushin amarci ga yaran harsu Aunty khaleesa kam dake cikin watanni na hud'u da auren.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Alhmdllh yanzu kam naji dad'in jikina, dan ko ciwonma banaji, sai shirye-shiyen kayana nakeyi dan yau nakeson tuna masa batun sakina, tun shekaran jiya rabona da ganinsa, harma na d'auka baya gidan sai d'azun da safe Samha take cemin ai tare suka fita itada Uncle Sam da Sauban birnin gayu da asibiti zagayen marasa lafiya, sune har Asibitin mahaukata, tace duk atsorace take ALLAH yasa kartayi mafarki.
Ni dariya ma tabani yanda take bani labarin kamar a firgice take.
Komai nagama had'ashi tsaf, Galadima kawai nake jira, amma abin haushin har kusan 4pm babu labarinsa, gani nayi zan zauna jiran gawon shanu, dan haka na mik'e zuwa sashensa.
Nayi sallama yafi 7 amma babu amsa, sai kawai natura na shiga, a zatona rainin wayonsane da mulkin ya motsa, babu kowa a falon sai wani k'amshi dake tashi na musamman, ko ina kuma need a gyare,, a yanda naga yanayin falon kamar babu kowa a sashen gaskiya, dan komai akashe yake har AC, dawuya kuma yana nan kaga AC n sa a kashe, duk da haka saina d'an zauna ina k'arema ko ina kallo, kai kace yau nafara shigowa, hotunansa da bana gajiya da kallo naketa kallo yanzun ma, idona nacikin zageye-zagaye saina hango wani k'aramin frame na photo, bana ganin mutanen jiki sosai dan haka namik'e tsaye, ga hoton na isa, yana a kusurwar d'akinne ta gabas, saman wani d'an katako da aka k'awata wajen, bayan foton akwai flower babba mai k'yau, sai aka jigina hoton jikin flower d'in.
K'yak'yk'yawan mutum ne ajiki Wanda kallo d'aya zaka masa ka hango tsantsar kamaninsa da Galadima, saikuma mace a gefensa itama masha ALLAH, Galadima kuma yana satar kamanninsa da ita, musamman idonsa ha6arsa dawasu abubuwa, saikuma wadda nake k'yautatama zaton aunty Mimi Ce kusada matar, shima namijin ina tunanin Galadima ne, yana cinyar mutumin, bazai wuce 5 to 6 years ba a picture d'in, Anty Mimi kuma bata wuce 10 ba, sai tsohon ciki ajikin matar, dukda ban saniba sainayi tunanin iyayensane, duk cikin kayan sarauta suke.
Samha ta fad'amin iyayensa suna india, Abbansa bashida lafiya, ban wani tambayeta komaiba, iyanan naji kawai.
Hoton na maida na ijiye ina murmushi, sun birgeni gaskiya sosai, flower d'in nabi da kallo, itama tamin k'au, gawani k'amshi mai dad'i datakeyi, kuma nalura da dare kamar tana wuta haka. Hannuna na kai na ta6a ganye d'aya ajiki, sainaji Ashe ta roba Ce ma, mamaki ya kamani, banyi zaton ta roba bace wlhy, dan tayi k'yau.
Har zan bar wajen, kamar ance na d'aga kaina saman p.o.p d'in ta jikin kusurwar sainaga tamkar CCTV camera, amma bakowa zai iya fahimtar hakanba, domin ansata cikin tsantsar kulawa, gabanane yafad'i, nayi azamar kauda idona tamkar ba ita nake kalloba, saina d'an gyara zaman flower d'in kawai nabar wajen zuciyata na tsitstsinkewa, toshi miye nawani saka CCTV camera a falonsa?, komawa nayi na zauna, zuciyata nawasu tunane-tunane daban.
Sai lokacin tunanin koma bayanan yazomin, abinda Nagano ya hanani lek'a bedroom d'insa, dan nasan zai iya ganin komai ta CCTV camera d'insa.
Sai kawai natashi na fice nakoma nawa d'akin.............??
Hum masu karatu kuna zaton Galadima bai fahimci Muftahu namasa zagon k'asaba kuwa??. kuduba yanda ya shashantar da binciken ya akayi yasha desire tabs a fresh milk?.
To koma dai miye kumuje zuwa, ai masu iya magana kance *Karshen alewa k'asa*???.
Humm ya kuke ganin sakin da Munaya ta nema? Shin zata samu? kokuwa zai bita bazai bayarba??.
Kumuje zuwa dai a page nagaba my guys????¡Ã¢???¡Ã¢???¡Ã¢
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*???[5/1, 4:25 PM] ? M B A ?: *_Typing?_*
*_HASKE WRITERS ASSO...?_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_?RAINA KAMA......!!?_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce??_*
??2?7?
...........A gajiye yadawo gidan, daga masarautar su papi yake, dan shine yamasa kiran gaggawa a daren jiya, yau tunda safe ya tafi, dan jirgin 7am yasamu, shine sai yanzu yake dawowa.
Saman kujera ya zube yana furzo iska, sarkin mota daya biyoshi dawasu kaya ya ajiye, yana niyyar fita yajiyo maganar Galadima d'in. tsayawa yayi yajuyo yana kallonsa.
idonsa a rufe yace, ¡°kunnamin AC ¡±.
¡°to ranka ya dad'e¡±. sarkin mota yafad'a yana risinar da kai alamun girmamawa.
Ya dad'e zaune a wajen idonsa a rufe, jin ana kiran salla a masallacin masarautar yasashi mik'ewa da k'yar yanufi bedroom d'insa. makunnar fitilar ya laluba, haske ya gauraye d'akin, komai normal kamar yanda yabarsa. anutse yafara zame sky blue d'in shaddar jikinsa. wanka yashiga, bai 6ata lokaci sosai ba yafito, jikinsa ya goge tsaf yajawo jallabiya fara tas mai dogon hannu yasaka, tamasa k'yau sosai, yad'an fesa turare yafita da hanzari jin za'a tada sallar magrib.
Nagaji da jiransa har zuwa magrib, bansan hawaye sun fara bin kumatuna ba, ahaka nayi sallar magrib, nayi alk'awarin ko yanzu yazo yabani sakina a gidanmu zan kwana, bayan na idar yau ko doguwar addu'a banyiba nadawo kan sofa na zauna tareda rabga tagumi na zubama akwatina idanu.
A wannan yanayin yashigo ya sameni, cikeda mamaki yake bin akwatin gabana da kallo, shi yama manta dawani maganar saki da mukayi.
Ban San ya shigoba saida yad'an bubbuga hanun sofa d'in, firgigit nayi ina kallonsa, bansan murmushi ya su6uce minba da ambatar Alhmdllh.
Idonsa ya janye a kaina ya zauna bakin gadon ¡°lafiya na ganki da trolley?¡±. Yay maganar cikin kuma d'aure face.
Nikam ban damu da yanayin nasaba na rashin walwala, dan narigada na fara sabawa ma da hakan, nad'an murmusa ina ta6e baki, nace ¡°kayan tafiya gida na had'a¡±.
Yi yay tamkar bai jiniba ma, ya zaro wayarsa dake ring yana kallo, a mamakina sai naga yayi murmushin gefen baki tareda saka wayar a kunne. ¡°Amincin ALLAH ya tabbata a gareki my Momma¡±.
¡°tare dakai Muh'd d'ina, yakuke? Ina d'iyata?¡±.
Murmushin yakuma yi tareda satar kallona, yace, ¡°gata a gefena Momma, Yaya jikin Abie?¡±.
¡°jiki Alhmdllh wlhy, yaushe zaku tahone? kun barmu mu kad'ai nida jakadiya¡±.
¡°kai Momma duk kuyangin gidanann kice kuna cikin kad'aici?¡±.
¡°to Muh'd ai d'a dabanne a zuciyar iyaye, musamman ma mu damuka k'agara muga sabuwar d'iyarmu¡±.
Bakinsa yad'an ta6e yana murmushi, ¡°karki damu Momma zaku ganta wataran, amma su aunty Mimi ai inaga gobe zasu taho jirgin darema suka samu¡±.
¡°haka tacemin, amma kufa to? dan banjiKu a lissafin masu tahowaba?¡±.
¡°nima insha ALLAH zan biyo bayansu bada dad'ewa ba Momma, dan nayi missing d'inku, bazan iya gama hutuna ananba gaskiya¡±.
¡°ita kuma d'iyar tawafa?¡±.
¡°nan zan barta mana Momma, duk k'arshen wata zanzo na ganta kamar yanda na saba¡±.
¡°lallaikam, to yanzu dai saika nemi tickets kafin Safiya, gobe idan ALLAH ya kaimu kutaho dasu Haneefa domin takawa yaga d'iyarsa, idan kun k'are hutun tare anan zuwa k'arshen watan saika maidatan¡±.
Tunda tafara maganar gabansa yafad'i, yawani marairaice murya tamkar yana a gabanta, ¡°please Momma wannan shawaran kumafa? dan ALLAH karkice haka ba yanzu ba sai nan gabafa zatazo?¡±.
¡°to nidai nagama magana Muh'd, za6i kuma yarage naka ai, bani ita mu gaisa time d'in gogema takawa jiki yayi zan shige¡±.
Ransa a 6ace yamik'omin wayar, banyi magana ba na kar6a dan naji yana Momma ai nasan mahaifiyarsa ce. gakuma yanda yaketa kwantar da murya irinna ladabi da shagwa6a.
Cikin nutsuwa da tsantsar girmamawa na gaisheta, daga can ta amsa min cikeda kulawa, bayanin daya firgitani naji tanamin, na waro idanu waje cikin tashin hankali, amma sai na kasa musa mata, na shiga amsawa da to cikin rawar murya.
Duk da AC d'akin zufa nakeyi, nida ke shirin fecewa gidanmu yau da takardar saki amma shine ake rok'ona nayi shiri gobe zamuje India, na taresu ni Munaya, ban kuma fahimtar dukkan sauran zantukan nataba, sai maganar k'arshe naji datace nabashi wayar.
Murya na rawa namata godiya da Addu'ar samun lafiya ga abban su Galadima, taji dad'i sosai kuwa, dan har sautin murmushinta ina jiyowa, hannuna har rawa yakeyi namik'a masa wayar, yana kwance idonsa a lumshe, damuwace a fuskasa karara, muryata na rawa nace, ¡°gashi tace abaka¡±.
Batare da yabud'e idonba ya kar6a, a kunne yasaka wayar, cikin kwantar da murya yace ¡°haba sweet Momma na a sassautamin mana¡±.
Murmushi kawai tayi daga can, tace ¡°ai iya sassaucin dazan maka kenan Muh'd, gobe idan ALLAH ya kaimu ka kaita gidansu tama iyayenta sallama da 'yar uwar tagwaicinta¡±.
¡°amma Momma..... ¡±
¡°kasan banason maida magana baya ko? kayi yanda nace kawai¡±.
Shiru yay bai iya cewa komaiba harta yanke wayar gaba d'aya.
Ransa a6ace ya tashi zaune, wayar Harun ya kira, yana d'agawa ko gaisuwar bai amsaba yace, ¡°Harun inason tickets guda biyu na India¡±.
¡°lafiya dai ko Galadima?¡±.
¡°Normal¡± kawai yace ya yanke wayar.
Harun ya girgiza kai, dan yaji alamar ransa a 6ace yake.
Mintuna basu wuce 5 ba yakirashi yace an samu naka, sai dai ita kuma batada passport ai, dolene da safe sai Anje anyo, amma na darene jirgin.
¡°yayi¡± kawai yace nanma yay shiru.
Harun nason masa wata tambayar amma babu dama, sai kawai ya yanke wayar.
Nidai ina dafe da kai abin duniya dukya isheni, shikenan an ruguza min plan d'ina.
Tashi yay yafice batareda ya kuma ko kallona ba, ban damuba, dan nima tawa ta isheni, yana fita hawayen bak'in ciki suka zubomin a fuska, ban samu damar sharewa ba na zame na kwanta a sofar.
Yana fita sashen mai martaba yaje, bayan jakadiya tamasa iso yashiga, gaidashi yayi cikin saisaita yanayinsa kafin yamasa bayanin zai koma India gobe, saboda kiran gaggawa daya samu daga doctors d'in Abie.
Fatan alkairi mai martaba yamasa, kafin ya tambayesa maganar nikuma fa.
Kansa a k'asa yace, ¡°ranka ya dad'e da ita zamu tafi, idan komai ya dai-daita saina maidota¡±.
¡°to shine nan, hakan yayi ai¡± nasiha sosai mai martaba yayi masa, tareda jan doguwar addu'a wa jikin Abie, ya dad'e a can sannan yafito.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
d'ayar wayarsa daya manta a kan gadona tashiga ring, ban d'auka ba harta tsinke, aka kuma kira ta yanke, saga nan ba'a sake kiranba, tunanin kiran Munubiya ne ya zomin, Dan haka na tashi zaune ina share hawayen fuskata na d'auki wayar nasaka number, Dan na haddace ta akai, harta tsinke bata d'agaba, saida na sake kira sannan tad'aga.
Acikin rashin sanin wanene tayi sallama a d'arare, amsawa nayi ina jan ajiyar zuciya, cikeda d'oki tace, ¡°Sweetheart kece? ykk?¡±.
¡°lafiya lau munu...., ke kad'aice a gidan dan ALLAH¡±.
¡°eh nikad'aice yaa marwan bai dawo masallaciba. miya farune?¡±.
¡°magana zamuyi Munu.... amma kiyi hak'uri da 6oye miki da nayi tun farkon matsalar, banason ki tashi hankalinkine shiyyasa¡± tun daga farkon maganar aurenmu da Galadima a randa suka saceni har zuwa yau ban 6oye mata komaiba, inayi ina kuka, itama daga can kukan takeyi harda shashsheka.
Cikin Jan aziyar zuciya tace, ¡°Naso nafahimci wani Abu tunkan aurenmu, amma ganin bakicemin komaiba na share, banga laifinki ba na aminta da auren yarjejeniyar kamar yanda ya buk'ata, domin kowaye a irin matsayinki abinda zaiyi kenan inhar yana tausayin iyayensa. Abu d'ayane gaskiya sai naga kamar bazai aikataba¡±.
¡°mikenan?¡±.
¡°Saka miki desire tabs dakikace, kiduba yanda kikace yadamu sosai, Munaya kofa saka mikin yayi babu laifi, tunda hakinsane, sadaki yabiya ya aureki, inma banda wautarki koda auren Contract d'inne kukayi ai ba'a fatar sakin ko. atunaninki innarmu wane tashin hankali zata shiga idan ance aurenki ya mutu cikin kwanaki 5 kawai da arenmu, ni yanzun shawarar dazan baki ki kwantar da hankalinki kuje India d'in, ki duba mahaifinsa, saikiga tarbar da parent nasa zasu miki, daga nan samu san mafita, idan sakin zaki nema kinga saiku rabu, idan kuma zaki iya zama da shine shikenan, saimuyita addu'ar ALLAH ya dasa masa sonki a zuciya¡±.
¡°Humm, Munubiya kenan, kinga kuwa tashin hankalin danake ganowa a masarautarsun nan, wlhy akwai babban lauje cikin nad'ifa, bazan iya wannan rayuwarba gaskiya, dan tanada wahalar gaske, shi kansa ba ta6a sona zaiyiba, dan tun farko dawata manufa ya aureni ai¡±.
Murmushi Munubiya tayi mai sauti, tace ¡°amma ke kina sonshi?¡±.
¡°ALLAH ya kiyaye, ni wlhy bana sonsa, kuma ban tunanin zansoshi ko anan gaba¡±.
Dariya Munubiya tayi, harda kwantawa a gado, cikin dariyar take fad'in ¡°to badai asan maci tuwoba sai miya ta k'are, kika sanima kona samu baby's d'ina a jiyan¡±.
Kwafa nayi kawai, nace can dai a bakinki, kedai mukema fatan ALLAH yasa mun samu, ki shirya min kayan dad'i gobefa zanzo kinji Sweetheart ¡±.
¡°karki damu habibati, a gaidamun Galadima ango¡±. tayi maganar cikeda tsokana.
Aiko sai Munaya ta saka mata kuka.
Dariya ta tuk'e Munubiya tayanke wayar tana mamakin yanda Munaya tayi sanyi, dawuya Munaya kaga ta zauna yima Abu kuka, koyafi k'arfinta tanada jimirin wahala, lallai Galadima baije da wasaba ashe.??
Koda tayi sallar isha'i saida ta saka 'Yar uwarta a addu'a, fatanta wannan auren ko igiya d'aya karta samu rauni barema akai ga saki. ta d'au alk'awarin cigaba da sakata a addu'a a kowacce sallarta.
Nima ina ajiye wayar tashi nayi nayo alwala nayi sallar isha'i d'in.
Kallon hotuna na zauna yi awayarsa, duk kusan ma bawasu pictures bane na azo agani, daga hoton wayoyin salula sai na kamar kayan waya Daba a had'aba da computers, mamaki ya kamani, saikace mai k'era waya?, nidai gajiya ma nayi na ajiye wayar, har barci ya kwasheni ban kuma jin labarin Galadima ba.
Shikam tunda yabaro wajen mai martaba suka fita shida sarkin mota, birnin gayu plaza yaje, yayi wasu 'yan abubuwa sannan ya gana da ma'aikatan wajen. Sai kusan around 11 ya dawo gidan, ko sashena bai kallaba ya shige d'akinsa, abinda duk zai buk'ata yad'an harhad'a, yakira Wanda zai kira awaya akan wasu harkokinsa sannan yay shirin barci ya kwanta..
Washe gari da asuba ko tadani bai zoba kamar jiya, ALLAH yasama nariga da na saba da tashi sallar tun a gidan mu, dan haka akan lokacin na tashi nayi kayana. barci nakuma komawa, ban tashiba sai 9am.
Wanka nafarayi, ina tsaka da shafa mai yashigo da sallama ciki-ciki, na zawo hijjab da sauri na saka.
Bakinsa ya ta6e yana kauda kai gefe. ¡°ki shirya zamu fita¡±. ya juya ya fita.
Da kallo na bishi ina girgiza kai, oh ni, saikace anmasa dole sai yayi maganar?.
Dukda bansan inda zamuba saina d'okantu da fitar, kobabu komai nasha iska ai, danni gidannan jinsa nake tamkar wata duniya daban ba duniyarmu ta mutaneba, yo komaifa gidan akwaishi, makaranta ne asibiti k'aramine, wajen wasan yarane, babufa yanda zaka fita waje inba doleba, musammamn ma mu matan aure, garama mazan da masu fita karatu kuma.
Shiri nayi cikin zani da Riga na atanfa, sunmin kau sosai, danni fa saima naga kamar fatata tawani d'an murje hakannan?..
A falona na iskesa zaune, muka had'a ido kowa ya janye nasa cikeda basarwa, saida yagama k'asaitarsa da mulki sannan yatashi, sanye yake cikin milk d'in shadda datasha ainahin aikin masu sarauta, takalmansa ma hakanne, sai fidda k'amshin turarensa mai narkar da mutane yakeyi, sajennann ya kwanta luf bisa face nashi, hular na hannunsa bai sakaba.
Gaba yayi nabisa abaya ina takuna d'ai-d'ai, takalmana masu sauk'in tsini sai bada sautin kwas-kwas sukeyi.
Mun tarar da motocin dazamu fita dasu a shirye guda 3, an wankesu sai d'aukar idanu sukeyi, gaisuwar da hadiman gidan suke mana muketa kar6awa, nikam banason abunnan wlhy, amma shi ko'a jikinsa.
Bud'e mana motar akayi muka shiga, nida shi muna baya, sai sarkin mota agaba, yayinda mota biyun kuma dogarai suka shiga.
Babu Wanda yay magana tunda muka fita, nidai kawai kallon hanya nakeyi da mamakin ina muka dosa?, mun Isa immigration office Ashe passport za'amin, abinka da manya, cikin 1hour aka kammala min komai. Bamu bar office d'inba saida harun yazo ya kar6i passport d'in domin nema min visa, daga nan muka fito.
wani dad'ine ya rufeni danaga mun doshi hanyar gidan mu, shi kansa ya hango farin cikin dake shinfid'e a face d'ina, ya janye idonsa daga kallona ya maida kan kallon mutanen anguwar daketa hada-hadarsu hankali kwance.
A dai-dai k'ofar gidanmu motocin suka paka, da hanzari na nemi 6alle murfin zan fita.
Caraf ya damk'e hannuna, juyowa nayi ina kallonsa tamkar zanyi kuka, idonsa a lumshe yake tamkar ma baisan miyayiba.
¡°dan ALLAH ka sakar min hannu naje¡±. ¡®nayi maganar tamkar zanyi kuka¡¯.
Banza yamin, saida yamula dan kamsa sannan yabud'e idonsa a kaina yana hararata, ¡°ki nutsufa, ko an fad'a miki haka akeyi?¡±.
Baki na tunzuro gaba.
Ya janye idonsa daga kallona yana kuma matse hannuna cikin nasa.
Ni ban saniba Ashe wai dole sai an nema masa ison shiga gidan namu, sarkin mota dai tuni yafita dama.
'Yan anguwarmu sunyi cirko-cirko suna kallon motocin, jira kawai suke suga Wanda zai fito aciki, dukda sunga masu jajayen riguna a tsaitsaye, alamar daga masarauta ne.
Muna a haka saiga yaa hameed yafito daga cikin gidanmu dad'an hanzarinsa, inaga yazo gaidasune, dan kullum Safiya duk sai sunzo shidasu yaa Shafi'u.
Jikin motar damuke ya k'araso, sarkin k'ofa yay knocking d'in glass d'in 6angaren Galadima. duk da yasan yana kallonsu shi.
Sauke glass d'in yayi a hankali, sannan yama sarkin k'ofa nuni daya bud'esa, har yanzu hannuna yana cikin nasa kuma. Ya d'auki hularsa ya saka.
Cikeda fara'a Yaa Hameed yake masa barka da zuwa, sai lokacin ya saki hannuna, sannan yazura k'afarsa d'aya yafito, nima dogari d'aya yazagayo da sauri yabud'emin, na fito, handbag d'in hannuna dogarin ya kar6a yana zubomin kirari.
Kallofa Yakoma sama ga 'yan anguwarmu, kowa sai kallona yake yana fad'in ashe munaya Ce, kai masha ALLAH, kugafa auren sati d'aya harta canja kamanni, lallai sarauta dad'i.
Inda yaa Hameed da Galadima suke na zagayo, suna rik'e da hannun juna sunyi musabaha, fuskar yaa Hameed a washe, yayinda ta Galadima ke d'ukeda wani munafukin murmushi.
Cikin murna nace ¡°yaa Hameed I miss u¡±.
¡°miss u too Darling sister. bismilla ranka ya dad'e kumuje ciki to¡±.
Atare muka shiga ciki, ina gaba suna bina a baya shida yaa Hameed.
Matan gidanmu kowacce na mak'ale jikin window d'inta tanason ganin Galadima, yayinda Aryaan da Aiyaan suka shek'o da gudu kaina, ganin haka suma sauran yaran sai suka shek'o, duk na tarbesu cikeda farinciki da kewa.
Ni nama manta dawani Galadima muke tare, Ashe shi yanata kallonmu cikeda sha'awa.
yaa Hameed yamasa jagora zuwa falon Dady.
Nikam ai d'akin Innarmu sha, tareda gayyar 'yan tarbata.
A zaune na iske innarmu tana ninke kayan su Aryaan, da alama wankewa tayi, sai tausayinta ya kamani, yanzufa kowanne aiki dole itace zatakeyi, babu mai tayata, jikinta na fad'a ina hawaye.
Itakam tace ¡°kajimin ja'irar yarinya, to miye abin kukan kuma? wai nikam yaushe kika lalace da sauri kuka haka Munaya?¡±.
¡°innarmu kewarku cefa wlhy¡±. nashiga gaidata, cikeda farincikin yanda na koma a kwana 6 kacal take amsamin, sai jero hamdala take a zuciyarta.
Zainab k'anwar Fauziyya tashigo d'auke da tire an d'oro zo6o da ruwa akai.
¡°inyee, kaga su zee anzama 'yan matafa, kace bad'i sai aure kenan?¡±.
Fuskarta ta rufe tana fad'in kai Aunty kibari please, innarmu kice ta daina¡±.
Innarmu dariya take mana itakam, saiga Rahma itama tashigo, saiga Ameenatu da Khadija ma, lallai bad'ima Ashe zamu aurar da yawa, a kwana ki 6 d'innan sainaga yaran duk sunmin girma a ido. Nasha mamakin su na zuwa gaisheni, dan bansa akaba nikam, araina nace ko jama'ar gidanmu dun fara canja haline dai?.
Muna haka saiga innaro tamkar an jehota, kowa ido ya zuba mata, dan shigowa tayi tana masifar wai bamu fara shiga gidan taba nida Galadima.
Na kalleta a d'age ina ta6e baki, ¡°yo banda abinki innaro ai sai nafara ganin Uwata, dan banida kamarta kaf duniya¡±.
Ha6a tarik'e tana kallona ¡°eh lallai kam, yo ai Dama ke halin uwarki gareki, ba mutuncine dakeba, ballan tana yanzun kuma ido yak'ara fetsarewa ansan komai na aure¡±.
Zan maida mata murtani innarmu ta harareni, shiru nayi na k'yaleta badan nasoba.
Shima Galadima yana falon Dady yasamu tarbar mutunci daga maman Fauziyya, dan matan gidanmu babu wadda ta aika masa dako ruwa, yaji dad'in tarbar daya samu kuwa, musamman yanda su Abba suka nuna masa tamkar d'ansu, baiyi dubi da sarautar dake kansaba ya duk'a har k'asa yakwashi gaisuwa wajen iyayena uku.
Hakan yamusu dad'i, domin ya mutuntasu, kuma sun kuma tabbatarwa shid'in mai tarbiyyane.
Anan yamusu bayanin munzo musu sallama ne zamu tafi India.
Fatan alkairi su abbanmu sukai mana da k'yak'k'yawar addu'a, daga nan sukad'an ta6a hira dashi, dukda yana nonnok'ewa saboda kunya irin ta jinin hausa Fulani.
Nikam can innarmu ta iza k'eyata nashiga kowanne d'aki na gaidasu, sai kallon k'urulla suke bina dashi, anason ganin wata makusa a jikina, amma sai basuganiba kuwa, komai sai sambarka. Aikam bak'in ciki tamkar ya karsu, kowa hassada nacin zuciyarsu (kai jama'a ALLAH yarabamu da cutar hassada komai k'ank'artatta???)
Na dad'e d'akin maman Fauziyya sosai, dan acanma naci abinda tad'an girka mana mara nauyi, yaa Hameed yazo ya d'auki na Galadima da kansa.
Sashenmu na dawo inatama innarmu shagwa6a, duk nabi na nanik'e mata, dukda tureni datakeyi. Nashiga tsohon d'akinmu harda kukana, komai nanan yanda yake, harma dawasu 'yan tarkacenmu daba a gama badawa ba, haka kawai bamu mutuba d'akinmu Yakoma kango, anan na d'akko cajata da wayar Galadima daya barmin a filin idi, sai wad'ansu 'yan abubuwa danake buk'ata.
Na fito ina tambayar innarmu waye ya d'auki wani hotonmu dake saman mirror nida Munaya?, tacemin maybe Ameeran inna lami Ce ko Bilkisu, dan taji suna rigima akan d'aukar Horton.
Shigowar Galadima da yaa Hameed tasaka innarmu yin shiru, nikam ban daina daddaga k'afa k'asaba ina k'unk'unin miyasa tabari suka d'auka?.
Galadima dake k'ok'arin zama yad'ago ido yad'an kalleni sannan ya janye.
Yaa Hameed ne yace kekuma lafiya?.
Fad'a masa nayi tamkar zanyi kuka, yace ¡°to kuka zakiyi?¡±.
¡°ALLAH yaa Hameed inason hotonfa¡±.
¡°ai saiki hak'ura yanzun tunda sun d'auka ko?¡±.
Innarmu da Galadima dai gaisuwa sukeyi, babu Wanda ya tanka mani. shi saima mamakin ta6arar danakeyi yake a zuciyarsa.
Nikam bansan yana yiba.
Sosai yaji innarmu ta burgesa, yakula ko kad'an ba halinta nabiyoba, dan ita tanada sanyi, dagani batada hayaniya, amma nikam ai sai addu'a.
Yad'an jima anan dukda ba hira sukeba, kowa kunya na cinsa, a raina nace dama yanda kunya guy d'inan ashe?.
Alkairi mai yawa ya ajiyema innarmu, dawata leda da yaa Hameed yabiyosa da ita, sannan yafita innarmu na saka masa albarka yana amsawa cikeda jin dad'i, jinta yake tamkar Momma d'insa.
Daga nan saida yashiga kowanne d'aki, sannan yaa Hameed ya rakashi gidan innaro.
Abba ne yashigo yana fad'in a tattaro lefena muwuce da kayanmu.
Na marairaice fuska nace Abba abarsu anan, kagaba tafiya zamuyi can d'in babu kowa.
¡°a'a Munaya bazai yuwuba, idan mun ajiyesu anan mizamuyi dasu?, kitafi da kayanki, duk randa dai kuka dawo suna d'akinki ai.
Badan nasoba na amince, amma naje wajen kayan ina fitar da wasu, ni saima yau naga lefen, gaskiya su Galadima sun zuba kud'i a wajennan.
Duk matan gidanmu atanfofi na fidda musu, maman fauziyya kam guda biyu, sannan yaran gidanmu 'yan matan yanzu kowa nafidda masa wani abun, su Aryaan ma dukda mazane kowa na fidda masa abinda zai iya amfani dashi.
Sai su Ayusher da inna lami da Ameera, Bilkeesu ma da nata, hakama mama rabia, na ware akwati guda na lodama Munubiya kaya sosai aciki, aunty salamah ma da nata, sai gwaggo Safiyya da yaranta mata, itama innaro jarabatu na fidda mata, su Abbanmu ne dai narasa mizan basu aciki.
Innarmu na kira tagani, ta kalleni tana fad'in ¡°munaya bazasuga an kwashe kayanba?¡±.
¡°a'a wlhy innarmu bazasu ganiba, kowafa da sashensa a gidan, kuma babu mai shiga harkar wani, idan na barsu mizanyi dasu? Kayan sunmin yawa ai¡±.
¡°to shikenan, ALLAH ya saka da alkairi¡±.
Na amsa da ameen ina fad'in ¡°ganaku nan keda su Aiyaan innarmu¡±.
¡°a'a ni bazan d'auki komaiba, bakiga yama kawomin abuba, ga kud'i dama bansan ko nawa bane¡±.
Kuka na Sanya mata akan saita kar6a, babu yanda ta iya ta amsa, amma saida tarage. Sai dai tana fita na maida mata harda k'arima.
Zainab Ce ta kaima kowa nasa, kowacce rai babu dad'i ta amsa, sotayi ace daga 'ya'yantane wannan abun arzik'in yafito bawai innarmu ba, (basusan shi Ubangiji babu ruwansaba, yakan azurta Wanda yaso Yakuma k'ask'antar da Wanda yaso a lokacin dayaso).
Babu wadda tazo godiya sai maman fauziyya, nace ¡°oho dai, aikin banza wai talaka ya girmi sarki???¡Ã¢¡±.
Banyi maganar su d'auki motarba, dan sonake nasami cikon d'ayar nabasu su duka ukun.
Nima naje na gaida innaro, dasu Abbanmu, naje gidan innaro lokacin su Galadima harsun fito,, na iske Ashe gwaggo Safiyya tama koma jiya, sai d'iyarta Habiba datake zawarci aka bari anan.
Munsha hira da ita, tanata yaba k'yan da nayi.
Innaro kam dukda jana datake ajiki sai basar da ita nakeyi, amma hakan bai hanata yaba Galadima ba, catake wai na more miji, nafi kowa morewa a gidanmu.
Nidai banda ta6e mata baki da bak'ar magana babu abinda nakeyi, bata damuba saboda neman gindin zama take ajikina.
Bamu baro gidanmu ba sai gab daza'a shiga sallar juma'a, an taho da motata da lefena, duk kayan daza'a bana mutane kuma na barsu a can, harna Munubiya.
Su Abba sunsha alkairi awajen Galadima Ashe, hakama matan gidanmu d'akin kowacce daya shiga saida ya ajiye alkairi, sunata kukan zuci da fad'in inama-inama 'ya'yansu ne a wannan daular??.
Zamu shiga motane ina sharar kwalla baba k'arami yace namusu godiya wajen Galadima, kaina kawai na iya d'aga masa.
Innarmu bayan tafiyarmu har 'yan kwalla tayi, matan gidanmu kam duk haushinta sukeji, idan kacire maman fauziyya.
Daga nan gidan Munubiya muka nufa, amma anan bai shigaba, yace naje zuwa anjima zai dawo mutafi, dan yanzu zaije sallar juma'a.
Kai na kawai na d'aga masa, nafita bayan dogari d'aya yabud'emin k'ofa, basu bar gate d'inba saida sukaga na shige ciki, ya maida kansa jikin kujera ya kwantar tareda lumshe ido, abinda yafaru a gidanmu kawai yake tariyowa, yakula family nawama sai a hankali dai. Sunada shigen irin halallayyar family d'insa.
Nikam da gudu nashiga ina kwala kiran sunan Munubiya, itama yafito aguje muka rungume juna, sai muka fashe da kuka kawai, ALLAH ma ya somu yaa Marwan yarigada yafita masallaci.................??
*_Masoya bansan yanda zan nuna muku tsantsar farin cikinaba, amma tabbas inajin dad'in Comments naku, kuyi hak'uri da rashin amsawata d'ai-d'ai, kunmin yawane wlhy, ga massages na PC, idan kuma nagama typing d'inan kaina d'aukar zafi yake, ko son ta6a waya banayi wlhy, naga wasu suna d'auka kamar wulak'ancine rashin amsawar, wlhy ba haka bane, kumin afuwa da uzuri please & please, duk da nasan bazan iya k'yautatama kowa acikinku yanda yakamata ba, dole wani yaga gazawata koyayane tawani fannin?._*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu???_*
[5/2, 2:22 PM] ? M B A ?: *_Typing?_*
*_HASKE WRITERS ASSO...?_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_?RAINA KAMA......!!?_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce??_*
??2?8?
...........Bansan yanda zan musalta muku farin cikin damuka tsinci kanmuba nida 'yar uwata Munubiya, abin kawai ba'a magana.
Duk da bata yarda zan zo d'inba amma bata fasa tanadar min duk abinda tasan inasoba, tarasa inda zata sakani dan dad'i, gaskiya gidan munu yayi k'yau sosai, gashi an cika ko ina da kaya, kasancewar harda nawa aka had'a mata, muna yin salla muka 6arke da hirar yaushe gamo, a haka yaa marwan yazo ya samemu, yaukam abin mamaki naga fara'a a fuskarsa, nace lallai aure yayi citta kenan, yanda yake bama Munubiya kulawa sai abin ya birgeni, kamar Na lashesu kuwa Dan dad'i. Haka muka yini muna tad'i har lokacin sallar la'asar yafita salla.
A lokacinne aunty Salamah tazo gidan, Ashe Munubiya ce takirata ta fad'a mata zamu tafi India yau da daddare, mun tarbeta da murna sosai, yayinda ita kuma taketa yaba wai munyi k'yau. mukaita rufe fuska alamar kunya.
Shawarwari taita bamu akan rayuwar aure da yanda zamu tattali mazanmu, babu ko kunya take 6aro mana komai, sai mune muketa sunkuy da kai, itakam ko a jikinta, ta rarraba mana wasu buks da ke d'auke da abubuwa masu amfani dazasu bada gudunmawa a zaman takewar aure, nidai bawai na d'auki nawa da muhimmanci baneba.
Wajen 5 tatafi, tafiyarta babu dad'ewa saiga Galadima da yaa marwan sun shigo, Ashe wai ya dad'e a k'ofar gida zaune, ya kira yaa marwan yace baya gida amma gashinan zuwa.
Shine yajirashi amota harya iso suka shigo tare. Sun gaisa da Munubiya a mutunce, ta shirya musu abinci, da yace yagode sauri yakeyi, amma munu ta marairaice wai yaza'ayi mijin 'Yar uwarta yak'i cin abincin gidanta, in baimasa baneba ta sake masa.
Murmushi yayi ya zauna yaci kad'an, yayinda mukuma muka shiga d'aki dan mu basu waje suci abincin, d'an kuskus d'inmu mukayi muma, takuma kwantar min da hankali akan auren nawa da wasu 'yan shawarwari, da nunamin fushinta akan abinda nace nama Galadima d'in, ta nunamin wannan ba tarbiyyar da iyayenmu suka bamu baneba, gaskiya karna sake irin haka, kuma nabashi hak'uri akan hakan, nace ¡°to amma tayaya zan basa hakurin?¡±.
'Yar takarda ta d'auka tayi rubutun tabani wai nabashi.
Na kar6ane kawai badan ina tunanin zan bayar d'inba, duk da nasiharta ta shigine gaskiya, kuma nima tun a ranar nayi nadamar ce masa azzalumin gaskiya, Duk da nasan a cikin fushine Nima Na fad'a, Dan nashiga rud'ani sosai akan abinda yayimin daban zataba.
tabani kayan da aunty salamah takawo a Leda, batareda na dubaba na amsa.
Itama k'yauta mai tsoka yamata sannan muka fito, nida ita kowa yana sharar kwalla, bamason rabuwa da juna, amma yazamuyi? aure ya rabamu.
Daga nan gz yaa marwan muka nufa gaida mama rabi'a, namayi mamakin yanda yasanta, nankam tare muka shiga, su Ayusher suka rukunkumeni cikin tsantsar farinciki da kewa.
Bamu dad'e sosaiba itama ya ajiye mata alkairi muka fito, su Feena ma yabasu kud'i wai su sai kayan kwalliya, hakama Ahmad, yaa Fadeel dai mun tarar baya nan, yakoma inda yake bautar k'asa.
Nanma saida nayi kuka dazamu taho.
Saida muka shiga mota ina sharar hawaye sannan ya kalleni cikeda k'asaita yana ta6e baki, ¡°ke wai bak'ya tsoron hawayenki su k'are ne?¡±.
Bance masa komaiba nacigaba da kukana, shima saiya shareni.
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯***¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Koda muka isa Masarauta bamu wuce sashenmu kai tsaye ba, wasu 6angarorin gidan mukaje mukai musu sallama, harda sashen mama Fulani, yauma dai babu magana mai dad'i tsakaninta da Galadima, nifa lamarin nasu na d'aure kaina gaskiya.
Mai martaba kam munsha addu'a a wajensa, sannan muka fito.
Mun shiga sashenmu ana kiran sallar magriba, zan shige yace ¡°kiyi azamar shirya kayanki trolley d'aya, karki wani kwashi kaya dayawa¡±.
Da to kawai na amsa nayi shigewata ciki.
*_7:30pm_* Muka bar masarautar, nida shi da Samha motarmu d'aya, muna baya tana gaba.
d'ayar motar kuma Sauban da aunty Mimi da khaleel ne aciki.
Mun sami rakkiyar Harun da Muftahu sai wasu k'alilan daga masarautar.
Tom nidai ba k'auyace a airport, dan banta6a shiga jirgiba, amma kunsan mutuniyar taku da Jan aji,? saina Fiske abina nima inajan citta tamkar wadda ta saba.
Duk abinda yadace ayi anyi mana, musamman ma ni danake sabuwar fita k'asar, harun yad'an sha cukuniya a kaina tunda rana.
9pm dai-dai jirginmu ya shilla a gajimare???.
Lokacin da akace asaka belt ban sakaba, sai shine ya jawo yasakamin batareda yace uffanba, yana jikin window nikuma ina gefensa, sai bayan mu khaleel da Samha, can baya kuma aunty Mimi da Sauban.
Ina lafe jikin kujera, yayinda shima yake kwance ya jingina bayansa, wani English novel ne a hannunsa yana karantawa, dama tun amota yake rik'e da kayansa.
Da akazo tambayarmu mi muke buk'ata Coffee kawai yace yacigaba da karatunsa, nima ta tambayeni saina girgiza mata kai alamar bana buk'atar komai.
Janye book d'in yayi yana kallona, saikuma ya janye ya maida kanta, harta bar wajen ya kirata, yace takawo min abinda su Samha sukace sunaso.
Bance komaiba nidai, shima saiya cigaba da karatunsa.
(*************)
Alhmdllh mun sauka kasar India, k'asar da nake gani a films, abin mamaki sainaga dogarawa ne sukazo tarbarmu, saikuma Akash dawani danaji Galadima yakira da beejay.
Bamu 6ata lokaciba mukabar airport d'in, a nawa tunanin sainaga rayuwar tasu kamar dai tamuce gaskiya, saidai banbancin sutura zuwa wasu mu'amullat haka, mutane sunata hidimarsu da kai kawo hankali kwance.
Masha ALLAH na fad'a yayinda muka isa gidan danake k'yautata zaton nasu Galadima ne. gidan kam yamin k'yau gaskiya, su beejay basu shigaba suna saukemu suka juya, mune muka Shiga hannuna aunty Mimi tarik'e, yayinda su Samha suke agaba.
Galadima kam mun barsa a harabar gidan yana waya.
Ai kaina bai gama kwancewa ba saida muka shiga falon gidan, hummm manyan k'asarmu sunajin dad'insu gaskiya, yo kanada irin wannan gidan a k'asar daba takaba to k'asarka kumafa?.
A falo muka zube bayi suka Shiga hidima damu, muna zaune a wajen Galadima yashigo, shima zaman yayi ya aza k'afa d'aya bisa d'aya, Sauban yazuba ruwa a cup yabashi, kar6a yay yana fad'in ¡°thanks¡±.
Ya kalli baiwar datake shirya abinci daga can gefenmu, ¡°k zonan¡±.
Da sairi ta ajiye spoons d'in hannunta tanufo inda muke, agabansa ta zube tace ¡°gani ranka ya dad'e¡±.
¡°kisamu wata ta tayaki Ku gyara d'akin can nakusada Samha yanzun nan¡±.
¡°angama ranka ya dad'e¡±. tayi maganar cikeda tdantsar ladabi.
Aunty Mimi Na najinsa batace uffanba. Shigowar momma tasaka khaleel tashi da gudu yaje ya tarbota, itama Samha zuwata ta kwakwameta, tunkan ma afad'amin nagane mahaifiyarsu Galadima ce, koda yanda fuskar kowannensu ta washe da farincikin ganin juna.
Hankalinta Na kaina tana murmushi da fad'in ¡°oyoyo d'iyata¡±.
Zamowa nayi daga kujerar na durk'usa har k'asa ina gaisheta, ta k'araso inda nake ta kama hannuna ta tadani nakoma saman kujerar, ¡°zauna kinji, sannunku da zuwa, kinsha hanya ko?¡±.
Murmushi nayi ina duk'ar da kaina.
Galadima yace ¡°wai Momma dan ALLAH duk baki ganmu baneba?¡±.
Kallonsa tayi cikin Hararar wasa, tace, ¡°yo naganku bata taku nakeba¡±.
Su aunty Mimi dariya suka Sanya, yayinda Galadima yad'an 6ata rai yana fad'in ¡°da tsohuwar Zuma dai ake Magani Momma¡±.
¡°a fad'arka ba, amma sabuwa ma aitafi aiki da dad'i¡±.
Nidai murmushi nakeyi, Dan wasan nasu ya burgeni, inason ganin family haka cikin farinciki, gaskiya sai sunfi jin dad'in zaman nan fiyema da masarautar sun can.
Gaishe-gaishe aka shigayi, kowa yana k'ok'arin bama Momma labarin yanda biki ya kasance, sai dad'i takeji da sanya albarka, nidai nida Galadima babu mai cewa komai.
Mik'ewa Galadima yayi, ¡°bara nad'an watsa ruwa Momma¡±.
¡°to afito lafiya Muh'd¡±. ta kalleni nima, ¡°d'iyata tashi kibi mijinki kiyi wanka kuzo ga abinci¡±.
Harya fara tafiya saiya tsaya, juyiwa yayi yana mata magana a yaren daban saniba.
Ta galla masa harara da masa dak'uwa, itama bansan mitace masaba. naga dai ya tura baki yaci gaba da tafiyarsa. ita kuma tace natashi naje.
(Wai ashe cayay mata ai yasa a gyaramin d'akin da zan zauna, shine tamasa dak'uwa tana cewa d'akin safa?, shi idan ance Araba mana d'aki saiya amince?, to tare zamu zauna, shine yakuma cewa ammafa d'akinsa ai ba kowa ke shigaba, tace tasani aii, muje nima sirrinsace ai, shinefa ya tura baki gaba).
Kamar an maken k'afafu haka nabisa abaya muna taka steps d'in benen, har muka isa k'aramin falo mai k'yau, komai farine a wajen, TV ce kawai takasance bak'a.
Falon yad'anyi k'ura alamun ba'a gyaraba (babu mai aikin dake hawa samansa, gashi kuma sunyi tafiya suduka, Momma kuma batada time d'in gyara masa d'aki).
Guntun tsaki yaja yana yamutsa fuska, d'an zaman danayi dashi na fuskanci bayason k'azanta komin k'ank'antar datti yata yamutse fuka kenan, bamu tsaya ananba muka shiga bedroom d'in bayan yabud'e, mayataccen k'amshinsa yana manne da d'akin, sai dai nan d'inma yayi k'ura, waya yazaro yayi kira, ashe Samha yakira, yace ¡°k zoki gyaramin d'aki¡±.
Bai jira cewarta ba ya yanke wayar.
Bance masa uffanba nima nataka nawucesa, bina yayi da kallo dan yaga ina zanje?.
Zanin gadon na yaye duka, nacire rigar filaluwan tareda rumfar da akama gadon, shidai kallona kawai yakeyi, yana tsaye jingine da bango (baiyi tunanin zance zan gyaraba).
Knocking d'in da akayine yabada izinin shigowa, Samha ce d'auke da kayan tsintsiya, ta zubesu a k'asa tana fad'in ¡°aunty kibarsa zan gyara¡±.
Kaina na girgiza nace ¡°barshi Samha, nunamin kawai yanda zanyi, kije kema ki huta¡±.
Nunamin komai tayi, har inda bedsheets suke, tafice a d'arare da zaton Galadima zai hanata yace takoma ta gyara.
Amma saitaji baice komaiba, yama kauda kansa gefe kamar baisan munayiba.
Bathroom nashiga, nazage sosai na tsaftaceshi, Dana k'urarce kawai, duk abinda zaisa toilet k'amshi da tsafta nasakashi, saida naganshi need sannan nafito, ban iskeshi a d'akinba, Dan haka hankali kwance Nagyara bedroom d'inma nagama, nasaka kamshi sosai. falon nafito danufi gyarawa, sainaga Samha harta gama itama tana saka air fresheners masu dad'in k'amshi, da turaren wuta irin namu na gargajiya.
Sannu da aiki namata, itama tamin, Galadima yafito daga wata k'ofa yawucemu batareda ya tankaba, bedroom d'in yakoma.
Kallon Samha nayi nace, ¡°saura wannan d'akin daya fito cikin ko?¡±.
¡°ai Aunty wannan d'akin dakansa yake gyarawa, babu mai shigarsa duk gidannan inba Momma da Mummy na da shiba¡±.
Cikin mamaki nace ¡°miya sa to?¡±.
¡°d'akin sirrinsa ne aunty¡±.
Ban fahimci maganarba, bankuma tambayeta ba, ta tattara kayan damukayi amfani dasu tafice tana fad'in ¡°aunty bara naje nayi wanka, dama wankan zanyi yakirani¡±.
Kaina kawai na iya d'aga mata, saman kujerar na zauna shiru ina nazarin maganarta, miye kuma ma'anar d'akin sirri? nashiga k'ololuwar nazari banyi zaton time yawuce hakaba, k'afata yad'an shura, nad'ago idona ad'an firgice na kallesa, haryayi wankan yana sanye cikin jajayen kaya na Adidas, sun masa k'yau sosai.
Juyawa yay zai sauka k'asa yana fad'in ¡°kitashi kije kiyi wanka¡±.
Bai jira cewata ba ya sauka.
Nima saina tashi nayi yanda yace, d'akinsa sosai ya had'u gaskiya, harma bansan Yaya zan fasalta mukuba, nasan farin Abu namai tsaftane, lallai yanada tsafta, daga bedroom parlour zuwa bathroom nashi komai farine, bedroom d'inne kawai keda d'an sirkin Golden kad'an-kad'an shima.
Nidai ina wanka da d'unbin tunani, haka kawai naji kwad'ayin son Shiga d'akin sirrin nasa.
Koda na fito saina saka zani da riga na atanfa, ban shafa komaiba na d'auki turarensa na saka saboda neman magana?. ina tsaka da saka turaren Samha tashigo kirana.
Ajiyewa nayi na d'auki gyale nabi bayanta.
Falon k'asa muka sakko, inda aka shirya abincin saman wata lallausar darduma, duk suna a zaune har Momma, kusada Galadima daketa cin abincinsa ko kallon mutane bayayi Aunty Mimi ta nunamin wai na zauna.
Kamar nafasa kuka haka naji, Sauban dake gefen haggunsa yace, ¡°auntynmu har yanzu amarcin bai k'are bane? kin shige d'aki kinyi bulum¡±.
Murmushi kawai nayi na k'asa ce masa komai, dan yabani kunya gaskiya, nakula kuma yanada yawan tsokana, aunty Mimi kam dariya tayi, yayinda Samha tarufe baki tanayin tata.
Momma tamasa dak'uwa, ¡°o kai Sauban ALLAH ya shiryeka, kowama bazaka d'agama k'afaba?¡±.
Dariya ya kumayi yana satar kallon Galadima dayay tamkar baya wajen, yace ¡°to ai gaskiya nafad'a Momma. dan ALLAH aunty ba haka bane?¡±.
¡°gaskiyarka fa Sauban¡±. Aunty Mimi ta fad'a tana dariya.
Momma tace ¡°barsu kinji my daughter, ci abincinki¡±.
Kai na jinjina mata cikeda kunya.
Galadima dai har yanzu baice k'alaba, baima d'ago ya kallemu ba.
Haka muka ci abincin nidai duk a takure nake, kamar yanda yafara cin abinci haka yarigamu kammalawa, tashi yay yabar wajen, yakoma can saman wasu kujeru guda biyu ya zauna, laptop d'in dake saman table d'in wajen ya d'auka ya kunna, da alama shiya ajiye kayansa.
Bayan mun gama duk muka mik'e, kowa ya hau shirin zuwa asibiti duba Abie, time d'in barcin sane shiyyasa ma Momma tasamu tataho, jakadiya kawai aka bari a wajen, itama a waje, da yake in time d'in barcinsa yayi kowa fitowa yake daga d'akin a barsa shi kad'ai.
Galadima saboda aikin da yakeyi yace muyi gaba shima zai taho.
Momma tace ¡°to matarka ta zauna ta jiraka, mudai mun tafi¡±.
Kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru, cigaba yayi da aikinsa harsuka fice, jinai kamar nace nidai zan bisu kawai. Amma na makaro, dan harma sun fice abinsu.
Ganinai tsayuwa ta isheni, shikuma d'an latsin baice na zauna ba, sai kawai naje na zauna d'ayar kujerar dake kallon tasa, nima na d'ora k'afa d'aya kan d'aya tamkar yanda yayi. nayi gefe da kaina cikin basarwa.
Daina danna System d'in yayi, ya d'ago idanu yana kallona, yayinda yake Murza hannunsa na haggu daya d'ora guywar a hannun kujera hannun yana sama, yinai tamkarma bansan yana kallona ba kwata-kwata.
cije lips d'insa yayi kad'an, ya janye idonsa ya maida ga system d'in, aransa yana mamakin izzar yarinyarnan, tabbas data fito gidan sarauta da anga mulkin tsiya.
Falon shiru babu kowa, tunda kuyangin suka gama hidimarsu duk suka koma 6angarensu dake can baya.
Kusan mintuna 40 yagama abinda yakeyi, laptop d'in ya kashe sannan ya mik'e, batare da ya kalleni ba yace ¡°muje¡±.
Saida na d'an ja wasu seconds sannan na mik'e, saidama ya juyo ya kalleni, dan har yakai k'ofar fita.
Gyalena na maida saman kai nabiyo bayansa, a k'ofa na iskeshi tsaye, na fito shikuma ya daddana wasu madannai agefen k'ofar, Ashe wai security yasaka.
Ranar farko danaga yayi tuk'i da kansa, dogarin dasuke gate suka bud'e mana muka fice.
Tunda muka tafi ba Wanda yayma wani magana, shi yanata deriving d'insa nikam ina kalle-kalle abuna, mun Isa katafaren asibiti mai k'yawun gaske, inma badan sunanba da saika d'auka wani wajen shak'atawa ne, asibitin ya had'u gaskiya, har ciki muka shiga bayan security sun mana 'yan tambayoyi dakuma gaisawa da sukayi, naga alamar sun sanshi sosai, amma duk da haka saida akai searching d'inmu.
Abin ya birgeni gaskiya, inda aka tanada domin parking ya tsaya, ya kashe motar sannan muka fito kusan a atare, bai tafiba saida na zagayo, muka jera zuwa ciki, yanata gaisuwa da jama'a, ina mamakin yanda ya iya yarurrukansu, nikam dai saidai da turanci nake gaishesu, kuma ba kowaba.
Mun fara zuwa office d'in wani doctor, suka d'an tattauna akan cigaban da aka samu na jikin Abie, mun gaisa dashi yaymana murnar aure, murmushi kawai nayi, sai Galadima ne ya amsa masa.
Daga nan muka shiga d'akin da Abie yake jiyya, iyalansa su aunty Mimi duk suna zagaye dashi, nidai a raina danaga d'akin nace oni kamar ba Asibitiba?.
Tunda muka shigo fuskar dattijon dake kwance a gadon ta fad'ad'a da murmushi, kallo d'aya namasa naga kamanninsa dana hoton d'akin Galadima na Nigeria.
Gabansa muka k'arasa, Galadima ya durk'usa yarik'o hannunsa, nima saina durk'usa ina gaidashi da Hausa.
Momma ce tazo ta kamani na tashi, cikin wani yanayi tace, ¡°d'iyata ai Abban naku baya iya magana kinji¡±.
Da sauri na kallesa, ya sakarmin murmushi, sai kawai na mayar masa hawaye nabin kumatuna domin tausayi, duk kallona sukeyi sukam, harda Galadima.
Kuma zamewa nayi na durk'usa a gaban gadon, cikin rawar murya nafara jera masa addu'ar samun sauk'i wajen ubangiji. duk suna amsamin da amin.
Murmushi yakasa barin face d'in dattijon, Wanda k'aunata take shigarsa har zuciyarsa, Momma takuma d'agoni a karo na biyu ta rungume tana lallashina.
Galadima ya had'iye hawayen dake Neman zubo masa shima, yafara gaida Abie dake murmushi, da ido ya nuna masani wai ya lallasheni mana.
Sai Galadima yayi murmushin jin kunya yana susar k'eya.
Murmushi Abie yayi sosai, har hakwaransa na bayyana.
Ban ta6a jin tausayin Galadima ba sai yau, dama haka suke cikin tashin hankali? Lallai dan ba'aga dariya a fuskarsa ba ba laifi baneba, nama yabama k'ok'arinsa yanda yake zirga-zirga tsakanin Nigeria da nan d'in.
Ahaka akaita firar dani bana fahimta, danshi Abie da idanu yake maganar.
Bamu baro asibitinba sai dare sosai, a can mukayi salloli dacin abinci.
Mun taho muka baro Momma a can, jakadiya ma ta biyomu, dama Momma kad'ai ke kwana a wajensa, shima ba kullumba, dan wasu ranakun basa bari a kwana dashi, a sati sau uku take kwana a wajensa.
**********
Tunda muka baro asibitin tsohonnan ketamin yawo a zuciya da ruhi, sai cud'awa nake da kwancewa, inason jin labarin masarautar su Galadima gaskiya.
Yanzun ma iza k'eyarmu aunty Mimi tayi muka wuce d'akinsa, muna zuwa bathroom yashiga, kusan mintina 25 saigashi yafito, da Alama wanka yayi, harya sauyo kayan barci aciki, dama da abinsa yashiga.
Nima tashi nayi nashiga da nawa masu kauri a hannu. Wankan nayi da shirin barci, sannan nasako hijjab na fito.
Saman gado na iskeshi yawani barbaje a tsakiya, alamar baya buk'atar wani ya hau.
Na ta6e bakina, a raina nace koma bakayi hakaba ai bazan ta6a had'a makwanci da kaiba, aikin banza kawai, naja tsaki a zuciyata.
Saman sofar d'akin na hau na kwanta, inata tunanin Abie da ma tsalarsa.
Kasa daurewa nayi, na kallesa nace, ¡° wai miye matsalar Abie (kamar yanda naji suna fad'a)¡±.
Shiru yamin, harma na zata yayi barci, sai can yacemin ¡°ciwone dai kawai¡±. daga haka yaja bakinsa yay shiru.
Nima shirin nayi, dan bakuma nida abin fad'a, musamman yanda yabani amsar.
Nidai zan iya cewa barcina na daren ranar rabi da rabine, kewar 'yan uwana da bak'unta, gakuma matsalar babansu Galadima data k'asa Barin zuciyata.
Da asuba narigashi tashima, na fito toilet bayan gama d'aura alwala na iskeshi zaune bakin gado dafe da kai, k'ala bance masaba nad'au abin salla na shinfid'a, tashi yayi ya shiga bayin yana Jan tsaki a zuciyarsa, Shifa wlhy dukya takura, yasaba zamansa shikad'ai a d'akinsa, yanzu duk anzo an cika masa?.
Haryaje k'ofar toilet d'in yadawo baya, doguwar riga ya d'auka ya shige, saida yay wanka da brush sannan yayo alwala yafito sanye cikin jallabiya blue.
Turare yad'an fesa sannan ya d'au key d'in mota yafita, Ashe inda yake zuwa sallan can gaban gidanne, kuma daga sallar asuba yake wucewa asibiti ya kar6i Momma tataho gida itakuma, duk ranar weekend haka yakeyi, yanzu kuwa yana cikin hutune.
Da yake ina sallah yafita, banyi zaton yafita kenanba, bayan na idar saina d'an kwanta, maganar d'akin sirrinsa ce taita cin zuciyata, namik'e nafita, saida na lek'a falon k'asa naga babu kowa sannan nadawo, cikin tantama na murd'a k'ofar d'akin, sai naga ta bud'e, banyi zaton hakaba gaskiya, musamman danaji an kira d'akin dana sirri. (bakisan ya manta bane bai rufeba Munaya? dan harda security a d'akin).
'Dakin k'aramine bashida wani girma, gaba d'aya bangon d'akin zagaye yake da hotuna, sai Computers guda hud'u da kuje d'aya gabanta akwai deck's babba, wanda duk Computers d'in akansa suke, sai pens da yawa cikin wani d'an Abu, gefe kuma k'aramar loka Ce ta glass cikeda takardu, gakuma tarin wasu takardun kashi-kashi da akayi kamar files a seman decks d'in, matsawa nayi jikin bangon nafara kallon picture's d'in, hotunan mutanene daban-daban, harda wasu manya dana Sani a TV, mafi yawa yayi rubutu a k'asan kowanne photo, bana fahimtar rubutun gaskiya, danhaka nacigaba da kallon picture's d'in kawai, harda na mama Fulani,?
?
Kutu melesi hotona fa jama'a a d'akin sirri, naga idi, nakaranta rubuntun k'asan yafi sau goma ban fahimci komaiba, saiwasu lissafi-lissafi kamar mai rubutun Mathematics?.
Na Muftahu nagani a k'arshe, abinfa ya d'aure minkai, mu kuma ni da amininsa Muftahu miya kawomu d'akin sirri???.
Agogon d'akin na kalla naga 7am tayi, da sauri nafita gudun karya zo ya sameni.
Na rufe k'ofar a hankali nakoma bedroom d'insa, ajiyar zuciyata na sauke ganin bai dawoba.
Zama nayi na zabga tagumi ina tunanin ma'anar wad'ancan pictures d'in dana gani, danma a tsorace nake, ban nutsu tsaf naganiba???¡Ã¢.
Ban sauka k'asaba saida 9am tayi agogon k'asar, na iske su Samha suna breakfast, harda Momma, na durk'usa har k'asa na gaidasu itada aunty Mimi, cikeda fara'a suka amsa.
Momma tace ¡°ai nayi zaton barci kike, shiyyasa na hana a tadoki¡±.
Cikeda kunya nace ¡°a'a na tashi tun d'azun¡±.
Aunty Mimi ta zaunar dani kusada ita, Sauban ya had'omin komai na breakfast d'in.
Yanzun ma a kunyace naci abincin, kunyata na burge Momma sosai.
Bayan mun kammalane Momma ta kama hannuna muka shiga d'akin ta, a bakin gado ta zaunar dani itama ta zauna, anutse ta kira sunana.
Hakan yasani maida hankalina a kanta nima dan nakula magana mai muhimmanci zamuyi da ita............??
*_tofa, mi Momma zata fad'ama Munaya kuma?._*?
*_Ya ALLAH ka gafartama Iyayenmu???_*
[5/3, 4:28 PM] ? M B A ?: *_Typing?_*
*_HASKE WRITERS ASSO...?_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_?RAINA KAMA......!!?_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce??_*
??2?9?
...........¡°Munaya taimakona nakeson kiyi akan mijinki¡±.
'Dagowa nayi na kalleta cikin tsantsar mamaki, saina sinne kaina alamar jin kunyar ta, nace ¡°Umarni zaki bami Momma, domin ke mahaifiyatace¡±.
Murmushin jin dad'i tayi kamfin takamo hannuna cikin nata, ¡°Alhmdllh Munaya, nagode da wannan karamci naki, yanzu nakuma aminta Muh'd yasamu irin macen danake musu addu'a shida d'an uwansa, ALLAH yayi miki albarka. nasan dukkanin yanda aurenku ya gudana¡±.
Gabana yafad'i, a raina nace badai Na yarjejeniyar ba?.......maganarta ta katsemin tunanin.
¡°Mahaifina Sarki Abdul'fatah shine yasakashi aurenki saboda abinda yafaru daku, Wanda nasan k'addarar Muh'd ce kawai tashigo dake cikin lamarin. Kafin nafara neman alfarmar zan fara baki tarihin masarautar su Muh'd, da dalilin zamanmu wannan k'asar daba tamuba tsawon shekara 24 kenan¡±.
Kaina na jin jina mata, nace ¡°to Momma¡±.
Zamanta ta gyara sosai yanda zataji dad'in fad'ar abinda ke a bakinta.
*_MASARAUTAR GAGARA BADAU A WASU SHEKARU DASUKA SHU'DE?_*
Masarautar gagara badau masarautace mai d'unbin tarihi, da mulkinta ya gudana hannun sarakuna masu yawa, a hasashen masana masarautar sarakuna a k'ala 51 ne suka mulketa harda Sarki na yanzu, wato *Sarki jalaludden Abubakar*.
Sunan masarautar awani shud'ad'd'en lokaci ba *gagara badau* ake kirantaba.
Tasamo sunan gagara badaune dalilin wani Sarki daya mulki masarautar a zamani mai shud'ewa.
Abaya mulkin masarautar basai ka mutuba yake barin hannunka, a'a, da zarar anyi yak'i kayi sakakin da aka ci masarautar tom dolenefa kayi murabus a nad'a wani kuma. kuma bawai cikin 'ya'yankaba, saidai asamo wani hazik'i a masarautar a nad'ashi sarautar.
Tom alokacin Sarki Hameesu Alasan sai aka kawowa masarautar wani gagarumin hari dayaso girgizata. Sarki Hameesu yanada wani d'a da ake kira da suna *Barde* amma asalin sunansa shine Salisu. lokacin da aka kawo musu harinnan ba'a cikin shiri sukeba, amma haka Salisu barde yay saurin had'a mayak'a suka tunkari wannan runduna, bak'aramin gumurzu akashaba, sojojin masarautar Sarki Hameesu duk sun salwanta, amma hakan bai tsorata Salisu ba, yacigaba da bata kashi shida wasu 'yan tsirarun mayak'a, ALLAH mai iko saigasu sunci wannan runduna data kawo musu hari.
Wannan nasara da Salisu yasamuce tasaka babansa Sarki hameesu sauka a kujerarsa aka nad'a salisu. tundaga ranar takoma *_MASARAUTAR GAGARA BADAU_* abin nufi annan salisu barde yazama gagara badau.
Bayan Sarki Salisu gagara badau sarakuna kusan goma sunyi mulki kafin Sarki *_ABUBAKAR_* kakansu Muh'd kenan, mahaifin su takawa.
Shima ya gaji sarautarne a hannun mahaifinsa Yusufa.
Rana d'aya aka nad'a Abubakar Sarki shida amininsa d'an sarkin kan karofi yarima Abdul'fatah, mahaifin Abubakar Yusufu abokine ga Sarki idres na ll, dan haka rana d'aya suka yanke shawarar yin murabus suka nad'a 'ya'yansu.
Sannan aka d'aura musu aure kuma a ranar da matan da su Sarki Yusufu & Idres suka za6a musu.
Gimbiya Marawuyya (mama Fulani) d'iyace ga waziri Sama'ila k'anin Sarki idris, a masarautar Idrees kenan, Sarki idres bashida d'iya mace, dan haka ya d'auki mama Fulani d'iyar k'aninsa yabama Abubakar d'an Sarki Yusufu a masarautar gagara badau, shikuma Sarki Yusufu ya d'auki Khadeeja (inno) yabama Abdul'fatah d'an Sarki idres.
To Ashe ita gimbiya Marayuyya (mama fulani) tana masifar son yarima Abdul'fatah ne, kuma yasani, amma ya nuna mata shi dama gimbiya Khadija (inno) k'anwar abokinsa Abubakar yakeso.
Tun daga lokacin gimbiya Marayuyya (mama Fulani) ta tsani Khadija (inno), ko wani Abu yahad'a masarautunsu bata mata magana, sai zagi da habaici.
Sukuma iyaye basusan gimbiya Marayuyya nason yarima Abdul'fatah ba, sukayi wannan had'in aure. (Iyayen mama Fulani ma sunso ta Auri yarima Abdul'fatah d'in domin sarauta ta dawo tasu)
Gidan sarauta idan an shata layi babu mai k'etarashi, dan haka gimbiya Marayuyya da iyayen ta dolen suka hak'ura da auren yarima Abubakar (tunda acanma suna saka ran gadar sarautar) haka aka kawota gagara badau. ita kuma Khadija (inno) aka kaita masarautar su Mama fulani.
Kusan atare duk suka haihu, saidai Khadija (inno) namiji ta Haifa, yayinda Marayuyya (mama Fulani) ta Haifa mace.
Duk da ba masarauta d'aya sukeba hakan yasaka mama Fulani bak'in ciki, dan aganinta inno taje zata gaje musu masarauta, ita kuma bata samu damar gaje tasuba. A haihuwa ta biyu kuma sai inno ta Haifa mace, mama Fulani kuma ta Haifa namiji. Alokacin kuma duk mazajen nasu suka k'ara aure, daga Sarki Abubakar har Sarki Abdul'fatah. kamar atsare haka sukaita kuma aure har suka cika mata hurhud'u.
A masarautar gagara badau Mama Fulani na zuba mulkinta a masarautar, yanda kasan itace sarkin, dayake shi Sarki Abubakar yanada hak'uri da sauk'in kai.
Humm matan Sarki Abubakar duk basu haihuba, sai mama Fulani keta zubo 'ya'ya. Saikuma amaryar Sarki ta uku ta Haifa d'anta namiji, kusan tare da mama Fulani a haihuwa ta hud'u, duk da mama Fulani itace da manyan 'ya'ya mace 1 maza 2 hakan bai hanata shiga tashin hankaliba, saita shiga tsangwamar gimbiya bagobura da aibanta d'anta *Saifudden*, wani lokacin har shegantashi tayi, saida Sarki Abdul'fatah yazo har masarautar ya taka mata birki sannan.
Mama Fulani tasaka sauran matan Sarki Abubakar sun juyama gimbiya bagobura baya gaba d'aya, batada sakewa ko kad'an acikin gidan. Sarki Abubakar yasan komai dake faruwa a gidansa, amma saiyayi tamkar bai ganiba, bakuma Dan mama Fulani tafi k'arfinsa baneba, yadai zuba mata idanu kawai yaga iya gudun ruwanta.
Ahaka yaran suka taso, gimbiya bagobura ma bata sake haihuwa ba, sai mama Fulani ce takuma biyu, mace 1 da autanta namiji Hayatudden.
Saifudden da jalaludden sun tashine tamkar tagwaye, dukda Saifudden ya girmi jalaludden d'in dakusan 1? kuwa. danma mama Fulani na hana jalaludden sakewa da Saifudden ne. Kokuma Kamaludden da Shamsudeen suyita dukan Saifudden idan sun gansa tareda jalaludden d'in.
Ahaka Saifudden yatashi cikinsu a tsangwame har suka girma suka zama manya.
Saikuma wani Abu tashin hankali ya samu, a time d'in da mama Fulani ke ganin sarauta zata dawo wajen 'ya'yanta sai ubangiji ya nuna mata ikonsa.
Dan kuwa Shamsudeen da kamaludden sai sukayi had'arin jirgi zasuje umara duk suka rasu.
A time d'in a marine kawai ba a saka mama Fulani ba, amma hauka tuburan tafara a masarautar gagara badau. Saida aka had'a da addu'a sannan talafa, saita kullaci gimbiya bagobura, wai ita tama 'ya'yanta asiri suka mutu domin d'anta Saifudden yagaji sarauta.
Gimbiya bagobura zata tada hankalinta Sarki Abubakar yace tama kwantar da hankalinta.
Bayan mutuwar su Kamaludden babu dad'ewa aka had'a auren gimbiya Zakiyya d'iyar Sarki Abdul'fatah da Saifudden aure, shikuma lokacin Jalaludden da Rafi'atu d'iyar wani Sarki.
Aikam sai mama Fulani ta hau bala'i wai munafunci aka shirya. Babu Wanda yabi takanta akasha biki.
Gimbiya Zakiyya da gimbiya Rafi'atu kusan atare suka haihu a time d'in, gimbiya Zakkiya ta Haifa d'iyarta mace, saidai tana haihuwarta ko ganinta batayiba takoma ga ALLAH?.
Wannan shine silar aurena dana Saifudden.
Dan bayan rasuwar yayata gimbiya Zakiyya da kwana 7 aka d'aura min aure da yarima Saifudden, domin nacigaba da rainon abinda tabari.
Banason Yarima Saifudden, domin ina masa kallon *Mijin yayata* amma banida yanda zanyi, dole na aminta da auren domin yima iyayena biyyaya.
Nasha wahalar zama dashi, saboda shi hankalinsa yana kan yayata ne marigayiya, silar soyayyar danake nunama Habeefa (aunty Mimi) d'iyar da gimbiya Zakiyya tabarine ya siyamin soyayyar yarima Saifudden, a hankali har shak'uwa tafara shiga tsakanina dashi. Soyayar dayakema 'Yar uwata saita dawo kaina.
Sai daifa inashan wahalar mama Fulani, duk da kuwa itad'in (Gwaggona ce) tana amsa sunan k'anwar mahaifina, amma k'iyayyar datakema mahaifiyarmu gimbiya Khadija (inno) saita shafemu, duk da abaya tana ik'irarin son mahaifinmu Sarki Abdul'fatah kuwa. Kamar yanda yayata gimbiya Zakiyya tasha wahalarta a gidan nima hakane, saima tawa taso fin ta 'Yar uwata, bansan dalilintaba, wai Ashe dan ina tsananin kama da inno ne?.
¡°Ina fata dai kina fahimtata Munaya¡± ¡®Momma tayi maganar tana kallona dana rabga tagumi inajin cakwakiyar masarauta.
Kaina na jinjina mata cikin damuwa.
Saitayi murmushi tacigaba da fad'in.
Mama Fulani taso d'iayarta ta farko gimbiya Mansura ta auri yayanmu yarima Abubakar, Wanda babanmu Sarki Abdul'fatah yayma amininsa takwara.
To saikuma hakan bata faruba, dan ita tata dabarar itada iyayenta, idan Yayana Yarima Abubakar ya auri gimbiya Mansura sarauta takoma hannunsu kenan, tunda yarima Abubakar shine magajin masarautar mu, kinga ai d'ansa ne zai gajesa kenan, idan tahad'a auren kuwa yazama jikanatane da masarautar nan gaba.
To saikuma tsarin nata bai yuwuba, saima nida yayata mukazo masarautar gagara badau tushen mahaifiyarmu mukayi kane-kane, gashi kowa yana Saran Saifudden shine zai gaji masarautar gagara badau alokacin, tunda manyan 'ya'yan Sarki Abubakar sun rasu, Saifudden kuma shine babba namiji a lokacin.
Shiyyasa takuma d'aukar karantsana ta d'aura mana muda gimbiya bagobura.
Bayan haihuwar Haneefa babu dad'ewa gimbiya bagobura ta rasu, rasuwar data gigita yarima Saifudden kenan da Sarki Abubakar har ma da jama'ar masarautar gagara badau, amma banda mama Fulani da sauran matan Sarki, dansu hakanma dad'i yamusu.
Sanadin rasuwar gimbiya bagobura Sarki Abubakar ya kwanta ciwo, sai yayi murabus yace a d'aura d'ansa Saifudden a madadinsa.
Wannan Abu yama kowa dad'i a masarautar, amma banda mama Fulani dakejin tamkar tamutu dan bak'in ciki.
Saidai batada yanda ta iya, tanaji tana gani yarima Saifudden yazama Sarkin masarautar gagara badau.
Alokacinne kuma akace dole ya k'ara aure, dan Sarki baya zama da mace d'aya, gashi kuma ni ban haihuba har lokacin.
A rana d'aya aka d'aurama Sarki Saifudden aure da mata biyu. Nanfa mama Fulani tashiga jansu ajiki wai dan a kuntatamin, tana kuma koya musu yanda zasu kuntatama shi Kansa Saifudden d'in.
Sarki Saifudden nada shekara 9 a karagar mulki ALLAH yayma Sarki Abubakar rasuwa, mutuwarnan ta girgiza mahaifinmu Sarki Abdul'fatah sosai, dan saida aka had'a masa a addu'a.
Tun daga wannan lokacin masarautar gagara badau takoma hannun mama Fulani, dan sai yanda tace tanaso Sarki Saifudden zaiyi, dayake shi mutumne mai sanyin hali, baya ta6a sa6a mata.
Duk da haka wannan bai ishetaba, hattada yanda za'a gudanar da mulki saita tsara.
Har lokacin amaren Sarki Saifudden babu wacce ta haihu.
Cikin ikon ALLAH sai gani da ciki, babu kitumurmurar daba aima cikinnan nawaba d'anya zube amma ALLAH ya k'addara mijinki *Muhammad Sameer* saiyazo duniya.
Lokacin Dana haihu shekarar haneef 10 cif a duniya.
Muhammad shine jika namiji na farko da aka fara haihuwa a masarautar gagara badau, dan kuwa matar Jalaludden ma mata taketa haihuwa.
Daga nan nima ban sakeba saida Muhammad yacika shekara hud'u, yanda Saifudden yasha tsangwamar mama Fulani haka Muhammad ma yashata tun yana yaro.
Shima Sameer hak'urin mahaifinsa Saifudden ya gado sosai, dan ko abu aka masa saidai yayi kukansa ya goge hawaye, koni bazai sanarmawa ba, saidai in wata baiwa tagani ko Haneefa (aunty Mimi) su sanarnin.
Da *Ciwon zuciya* na haifi Sameer, dan haka kullum cikin kaffa-kaffa muke dashi saboda gudun samun matsala ga lafiyarsa, da yawa jama'ar gidan sukan masa abune wai dan zuciyarsa ta buga? ya mutu. sun manta rayuwa da mutuwa duk Na ALLAH ne.
Da sauri na kallo momma.
Ta d'aga min kai tana murmushin takaici, ¡°hakane d'iyata, kullum burinsu kenan akan Muhammad tun yana yaro..
Ranar wata litinin da asuba Sarki Saifudden yafita sallar asubahi sai kawo manashi akayi cikin gida, wai yafad'i ana tsaka da sallah.
A lokacin kafafunsa ne kawai basa aiki, amma sauran jikinsa yana motsawa.
Nice naita wahalar jinyarsa, ga cikina yafara tsufa, sai jakadiya ke taimakona, amma sauran matan Sarki ko'a jikinsu.
A hankali ciwo yacigaba da girmama a jikin takawa, tun ana kafa har yadawo duka jiki, idonsane kurum ke aiki a lokacin.
A asibitin garinan muke jiyyarsa a time d'in, a asirce batareda jama'ar gari sun saniba.
Acikin wannan tashin hankalin na haihu Namiji, shine Abubakar (Sauban).
Nidai lokacin kawai ina rainon Sauban ne, amma rabi duk Haneefa ce (aunty Mimi) yayinda kulawar Sameer takoma hannun k'anwata Zaituna (mom), autarmu kenan, dan dole aka dawo da ita wajena tana taimakamin.
Na haifi Sauban babu dad'ewa aka maida sarautar Saifudden akan Jalaludden d'an gidan mama Fulani, saikuma lokacin jama'ar gari suka San Sarki Saifudden bashida lafiya ma.
Ko kad'an ban damuba, danni ta lafiyar mijina nakeyi ma.
A lokacin anta kananun magana akan zargin mama Fulani dawasu kuma manyan attajirai, dan akwai wani zaman sirri da sarki Saifudden yayi dawasu attajiran k'asar ana jibi abin zai sameshi, kuma anga yafito ransa a 6ace daga tattaunawar, alamar sun buk'aci wani Abu ya hanasu kenan. suma angansu ran nasu A 6acen. Nikam bamma maida hankali akan wannanba, mahaifina Sarki Abdul'fatah shine kawai tsaye akan ciwon Saifudden, saini kuma da jakadiya.
Masarautar kuwa ai duniya sabuwa. Matan Sarki Saifudden ma duk sun kama gabansu, sunce bazasu iyaba.
Shekararmu d'aya a asibiti babu wani canji, saima jikinsa dake neman fara ru6ewa saboda komai sai an masa. Baya iya d'aga koda d'an yatsane. (Tun farko likitocinmu na nan sun Sanar damu an masa allurar gubane, kuma guba mai had'ari, dan babu makarinta, itakuma tana sakar da jijiyoyin jikine su daina aiki gaba d'aya, wannan yasaka jikin Sarki Saifudden ya sandare?.
Wani amintaccen likitanmune yabada shawarar mu maidashi India dansu sunada kwararrun likitoci, kuma zaifi samun kulawa da tsaro a can.
Wannan shine silar dawowarmu wannan k'asa, da cuku-cukun mahaifina Sarki Abdul'fatah, dan komai namu mukam ya k'are, duk abinda Sarki Saifudden kedashi yagama k'arewa a neman Magani.
Tunda muka dawo India kuwa Sarki Saifudden yafara samun kulawa ta musamman, saidaifa maganar ta kud'ine. Wasu sarakuna da yawa sun bamu gudunmawa, wasuma suna akan bamu.
Sanin Zara bata barin dami, gashi kullum cikin buk'atar kud'i muke sai mahaifina yakafa wasu sana'oi da sauran kud'enmu, tanan muke samun kud'in shiga. Karatun Muh'd da Haneefa kuma Mahaifiana ke d'aukar nauyi..
Tundaga primary har jami'a anan Sameer yayi karatunsa.
Kiyayyar Saifudden kuma ga mama Fulani saita dawo jlkan Muh'd gaba d'aya, kokad'an bata k'aunar ganinsa, kullum tsakaninta dashi sai aibantawa da jifansa da kalamai masu had'ari ga yaro.
Tunda Muh'd yafara sanin Kansa, yaga halin da mahaifinsa yake saiya fara canjawa daga mai hakuri zuwa mai zafi.
Ga ciwonsa kuma, duk yabi yayta kuntata zuciyarsa akan ciwon mahaifinsa da burin d'aukar fansa.
Muh'd mai fara'a da barkwanci yakoma mutum marason magana da azabar rashin d'aukar raini, duk da hakurinsa nanan bai dainaba, dan zakata masa Abu ya shareka kamar bai ganiba, sai randa yazo k'arshene zaka gane kurenka a wajensa.
Mahaifina Sarki Abdul'fatah shine yamatsa tun Muh'd na secondary school dole idan akayi Hutu yazo najeria, dan acewarsa tahakane kawai zai fahimci sarautar gidansu.
Muh'd ya karanci Engineering ne, dama tun yana yaro kingansa kullum cikin son had'a Abu yake, shine tsinka wayar fitila tsinka ta redio ya had'a wani abun, tunma ina masa fad'a harna bari kawai. Ashe abincinsa awajen yake. Yanzu haka sunada Company na had'a wayoyi? da Computers??, da sauran kayayyaki dai. Sannan yana wasu business domin dai muke samun kud'ad'en kulawa da mahaifisa da sauran matsalolinmu, dan babu mai kulawa damu a masarautar gagara badau sai Sarki Jalaludden.
Wani zuwa da Muh'd yayi Nigeria shine aka bashi sarautar *Galadima*, galadima Sarautace mai k'arfin gaske, dan sai d'a mafi soyuwa ga Sarki ko k'ani ake bamawa. Kuma akance batada banbanci da sarautar waziri, dan duk abinda waziri zaiyi Galadima ma zai iyayinsa. Akwai ma wasu abubuwan da daga Sarki sai Galadima kan yisu a fada.
Da da farko nace ya mayar musu amma sai mahaifina yace a'a, ai hakan da sukayi dai-daine.
Sharrin kuwa dakika sun masa, har tsautsayi ya jefaki a ciki, sunyine dan hankalinsa ya tashi, har takai zuciyarsa ta buga ya mutu sun huta.
Dan ayanzu ne suke ganin sunfa *kashe macijine basu sare kansaba* Galadima yazamar musu *RAINA KAMA.....*, basuyi tunanin zaikai tsawon rai hakaba, saboda Ciwo mai had'ari dake a tare dashi.
Shikuma Muh'd yafi karkata hankalinsa ga jama'ar wajene sukama mahaifisa haka, koda akwai jama'ar masarautar gagara badau to kalilanne, kuma mama Fulani kawai yake zargi.
Nikuma ba ita kad'ai nake zargiba, amma yakasa fahimtata gaba d'aya har kawo yanzun kuwa. Dagashi har Haneefa sunfi zargin jama'ar waje, don mutananen masarautar suna 6oye musu ainahin fuskarsu ta zalunci, mama Fulani ce kawai tata take a bayyane.
Wannan yasaka tun sharrin da akai muku nasaka amin bincike a kanki, Alhmdllh ban samu wata matsalaba a tarihinki,, daga nan na dukufa addu'a da neman za6in ALLAH.
bamma kai ga furtama kowa matsalata ba sai mahaifina Sarki Abdul'fatah (papi) yace Muh'd saiya aureki.
Nasan ba sonsa kikeba, amma ina rok'on ubangiji da yasa wataran kuso junanku, kinada tarbiyya da wayon da zaki iya canjamin Muh'd, dan banason hallayarsa ta yanzu, nafi son nake ganin walwala atare dashi a ko yaushe, ki taimakeni ki shiga rayuwarsa sosai, dan ke macece, sai kin fishi zama cikin jama'ar masarautarsu, zakuma ki fishi fahimtar halayyarsu, sannan kidinga bashi shawara akan abinda yadace dashi. Inaji a jikina zaki iya canjamin Muh'd, saboda kinada hankali. gudun kar wani yasakama zuciyarki tunani daban yasaka nace yakawoki da wuri, domin kisan yanda zaki rayu a masarautar, kafin kutafi insha ALLAH komai Na zamantakewar masarauta za'a koyar dake kinji¡±.
Kaina Na gyad'a mata, sannan a sanyaye nace ¡°Momma namiki alk'awarin zai taimakesa akan matsalarnan, kuma zan bama rayuwarsa gudun mawa insha ALLAH, Sai dai Abu d'aya ne ban ganeba¡±.
¡°miye baki ganeba d'iyata?¡±.
¡°Abokinsa Muftahu, shima a masarautar yake?¡±.
Murmushi Momma tayi, tace ¡°daga Muftahu har Harun duk 'yan masarautar ne, Muftahu kakanni suka had'a dasu Muhammad, da kakan Muftahu da Sarki Abubakar kakansu Muh'd uwarsu d'aya ubansu d'aya, shikuma Harun d'an waziri ne na yanzu, kuma shima wazirin haifaffen gidanne, saidai inason sanin ko wani Abu kika gani tareda wani acikinsu?¡±.
Kaina Na girgiza alamar A'a.
Momma ta sauke ajiyar zuciya, ¡°Munaya saikin dage kinji, domin Na had'aki da aiki mai wahalar gaske, mai kuma sark'akiya, musanman akan halayyar Muh'd, dan bai yarda da kowaba dakike ganinsa nan, koyaya Abu ya had'aku sai yayi zargin turoka akayi garesa, kuma zaka Shiga jerin wad'an da yake tuhuma. amma kekad'aice mafi kusanci da Muh'd yanzu, zakifi kowa sanin matsalarsa da wuri, saikuma kin fimu fuskantar tunaninsa, danni kinga jinyar mahaifinsa tasa banwani zauna dasu irin sosai d'innanba, yanzu haka kafin nasan matsalarsa 'Yar uwata Zaitun (mom) tasani ko Haneefa (aunty Mimi), garama Sauban.
Nace ¡°shikenan Momma ki tayamu da addu'a kawai¡±.
¡°insha ALLAH muna kan yimuku kullum, ALLAH yayimuku albarka, ya albarkaci aurenku da dukkan rayuwarku da abinda zaku haifa¡±.
Ban iya amsawa ba, kaina Na k'asa nikam, ko azuciya ma ban amsaba, dan nayi alk'awarin zai taimakesa kamar yanda ta buk'ata. Amma ina gamawa zan nemi sakina, koda nanda shekaru 2 ne kuwa, amma gaskiya Na tausayama Galadima, dan nakula yana cikin tsakkiyar mak'iyane masu fuska biyu. abinda kuma nalura da Momma bata ganeba shine Galadima bawai bai yarda 'yan gidansu nada saka hannu akan ciwon babansa bane, baya dai nunawane kawai, sai dai bansan dalilinsaba.
CCTV camera d'in dana gani a d'akinsace tadawomin a rai, maybe ya sakatane domin sanin masu shiga da fita koda bayanan.
Haka Na kusan yini cikin damuwa da tausayinsa, dan duk saiya bani tausayi wlhy. shiyyasa zaka gansa kullum shiru-shiru, gaskiya 6angaren hak'uri Na yarda yanada hak'uri kam.
***********
Yau saida yamma mukaje muka duba Abie, mun iske Galadima baya asibitin, dama tun da rana yazo gida yay wanka yakuma fita.
Har dare muna a asibitin, saida Galadima yazo muka taho tare, ina gaba ni da shi da khaleel dake barci a cinyata, yayinda sauban da aunty Mimi da Samha ke baya.
Maganar da samha ta fad'amin d'azun a asibiti ta dawomin a rai, Ashe mahaifinsu ya rasu suma shekara 2 kenan, itace d'iyar Aunty Mimi ta farko, sai Hakim da suka rasu tareda babansu, saikuma khaleel auta. Suma a Nigeria da suke zaune, bayan rasuwar mahaifin nasune suka dawo nan india, duk da dangin mahaifinsu sunso kar6arsu papi yahana, babansu tsohon Governor ne shima, mutuwar tasa kuma akwai lauje cikin nad'i shima, dan ya tsananta akan binciken ciwon surukinsa Abie sosai, shiyyasama ake zargin an kasheshine saboda wani Abu daya gani.
Har muka Isa gida bansan hirar dasukeba a baya, dan shima Galadima baya cewa uffan.
Shine ya kar6i khaleel a hannuna, ya sa6ashi a kafad'a muka shiga ciki, har d'akinsa ya kaisa. ni lokacinma harna haye saman..........??
Barkanku da juma'a.
Zanyi last page gobe idan ALLAH ya kaimu da rai da lafiya???¡Ã¢???¡Ã¢.
Network yanata min iskanci tun jiya shiyyasa kuka jini shiru?
*_YA ALLAH ka gafartama iyayenmu_*???
[5/4, 1:09 PM] ? M B A ?: *_Typing?_*
*_HASKE WRITERS ASSO...?_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_?RAINA KAMA......!!?_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce??_*
??3?0?
..................Da sallama ciki-ciki ya shigo, nayi saurin maida zip d'in rigata sama nafasa cirewa, a sace ya kalleni yawuce bakin gadon ya zaune tareda dafe kansa.
Kallonsa nayi Na kauda idona nima, kusan mintuna 3 kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa. d'agowa yayi yakuma kallona, kamar an masa dole yake maganar cikeda k'asaita, ¡°k! Wai bazakima Momma magana ba kikoma d'akinki?¡±.
Kamar bazanyi maganaba saikuma nayi batare da Na kallesaba, ¡°inaga kaine yakamata kamata maganar ai, dan nima zanfi son haka, duk nabi Na takura zama da Namiji d'aki d'aya¡±.
Banza yamin bai sake tankawa ba, saima yamik'e yana jan k'aramin tsaki, nikam Na ta6e baki a zuciyata ina fad'in ka iya fad'ar R kafin kamin mazurai.
Baima san ina yiba, yaje wajen wardrobe d'insa ya d'auki kayan barci yanufi bathroom.
Murmushi kawai nayi, danni rayuwar mutuminnan mamaki take bani, ina dad'i kabi ka k'untata kanka irin haka? baka hira da kowa, baka dariya, shifa ko kallo inba labaraiba ban ta6a ganin yanayiba, hakama wak'a banta6a jin yana jiba, koranar dana duba wayarsa karatun Qur'an kawai nagani da Tafseer. nakai dubana gawata 'Yar kanta dakecan gefe a bedroom d'in nasa, mafi yawanci littatafan addini ne awajen, sai English Novels. (To yayi karatun addinine? tunda naji Momma tace anan India ya girma?). Wata zuciya tacemin su India basuda musulmai ne?. ¡°hakane kumafa¡± nafad'a a fili ina mik'ewa.
Ganinaima bara nacire kayana kafin yafito, daya fito saina shiga nima.
Har ga ALLAH banyi tunanin fitowarsa ba yanzun, dan haka hankalina kwance na zuge zip d'in rigar, na cireta gaba d'aya, shima sket d'in nayi k'asa dashi yafad'i k'asa.
Juyowarnan da zanyi da nufin d'aukar towel dana ajiye saman akwatina sai kawai naga mutum tsaye a k'ofar bathroom, hannunsa rik'eda k'aramin towel yayi tsaye yana kallona.
Bansan Na kwalla k'araba wlhy, Na rarumi towel d'in nayi saurin kare jikina, ALLAH ma yaso k'ofar a rufe take, dan dawuya su Aunty Mimi sujini.
K'arata tadawo dashi daga sumar tsayen dayayi, yawani kauda kansa cikeda basarwa yana ta6e baki, saikuma yaja guntun tsaki yaje bakin gadon ya zauna yana cigaba da goge fuskarsa, dan har yayi shirin barcinsa a ciki.
Jinayi tamkar na makesa, d'an rainin hankali yagama kalleni zai wani miskile fuska asfa baiga abin kalloba. hijjabin sallata na janyo Na saka, sannan nawuce bayi ina hararsa.
Ina shiga yamik'e yana wani munafukin murmushi, abin salla ya shinfid'a ya kabbara shafa'i da wutiri.
Nadad'e abayin nak'i fitowa, saida nabar jin motsinsa duka sannan Na fito, dayake nayi shirina a bayin nima, nazata ya kwanta, amma saina iskeshi zaune a kujerar dake gefen kantar littatafan nan ya bud'e laptop yana danne-danne, gefensa kofine yanata turiri, da alama coffee ne aciki.
Yad'an juyamin baya kad'an, dan haka cikin sand'a Na rufe k'ofar, nakuma tako a hankali har zuwa wajen sofa Na kwanta, duk zatona baya ganina, Ashe yana kallon duk abinda nakeyi ta gefen idonsa.
A ransa yace munafunci. cigaba yay da aikinsa hankaki kwance, bai bar wajenba har kusan 1:30pm, maimakon ya kwanta sainaga yashiga bayi ya d'auro alwala.
Nima har time d'in barci yakasa d'aukata, maganar Momma tanata min yawo a zuciyata, tunanin ta inda zan taimaki Galadima kawai nakeyi.
Ina kallonsa ya kabbara salla. saida yay kusan raka'a 6 yanayi yana sallamewa, daganan ya d'auki alku'ani yafara karatu k'asa-k'asa.
Masha ALLAH nafad'a a raina, danjin yanda muryarsa ke fita cikin karatun littafi mai tsarki, gashi yana fidda kowane harafi cikin tsantseni da kwarewa. Tun ina saurarensa har wani barci mai dad'i ya saceni, bansan lokacin daya kammala ba yazo ya kwanta.
Muduka makara mukayi sallar asuba yau, dan haka shima yau a gida yayi.
Bayan ya idar waya ya d'auka naga yayi kira.
Bayan an d'aga daga can sukayi gaisuwa, jin ya tambayi ya Nigeria Na gane da 'yan can yake wayar. yacigaba da fad'in.
¡°Nuren naga ka turomin hotonsa, shin a inane yake haka?¡±.
Bansan mi akace masaba daga can, naga dai yayi kwafa, sai yace ¡°ya maganar Minister? dan nagansa wajen d'urin aurena, ban kuma yi zaton zai zoba¡±.
Canma aka kuma yin wata maganar.
Zamansa yagyara, yakuma jingina da bangon, dayake yana kan abin salla har yanzun. ¡°kayi k'ok'ari Nuren, yanzu abinda nakeso dakai shine, akwai yarinyarsa d'inan datake karatu a nan jami'ar Abuja, inason a sacemin ita k'arshen watannan, yanzu ka saka ana bibiyarmin komai nata, Shikuma Alhaji Balala driver n sa zaku d'aukemin, dan bincikena ya ganomin shekarunsa 30 dawani Abu yana masa aiki, kuma randa su Alhaji balala sukayi zama da Abie shine ya kaisa masarautar mu, inada tabbacin zai San wani Abu koda kad'anne, kuyi aikinku da kulawa Nuren, banason asami matsala kamar wancan time d'in, gobe kashiga birnin gayu plaza kuyi zama Na musamman da Saleem akan maganar CCTV camera data daina aiki randa abinnan ya faru, ni naso Na zauna dashi, amma kaga Momma tamatsa akan dawowata¡±.
bayan nacan yagama magana.
Yace ¡°ok babu damuwa, zan turo maka number yarinyar, saiku bibiyeta tanan. sai anjima, ka gaidamin Mom d'ina¡±.
Koda ya ajiye wayar saiya koma gado ya kwanta abinsa, nikam ina zaune sai cud'awa da kwancewa nakeyi, ban fahimci wayar tasaba gaba d'aya, shin wanene kuma NUREN!? shikuma miye alak'arsa da Galadima kuma?.
Tabbas aikina bazai yuwuba saina San wanene NUREN, wane kuma aiki yakema Galadima a sirrence, su waye wad'annan mutanen biyu daya ambata Minister da Alhaji balala? suna cikin wancan case d'in Na Abie ne? kokuwa tasu dabance?.
Kwanciya ta na juya yanda zanji dad'in tunanin da k'yau, saikuma naga ai ba sanin waye Nuren bane matsalata yanzu, kamata yayi nafara sanin shi kansa Galadima d'in da rayuwarsa, na tuna maganar Momma da tece ¡°shi mutumne dabashi da yadda¡±. Mutum mara yarda kuwa yanada wuyar sha'ani, kad'an na juyo na kallesa, idonsa a rufe yake, amma ban yarda barci yakeba, na janye idona nima na maida lumshe, barcine mai nauyi ya kwasheni, harya fita bamma saniba inata barci, babu kuma Wanda yazo ya tadani.
Sai around 11:30 na tashi, wani masifar ciwo kaina yakemin, haka dai na tak'ark'ara nayi wanka, nagyara d'akin sannan na sako k'asa, gidan shiru tamkar babu kowa, sai television daketa aiki, zama nayi bisa kujera dafe da kaina.
¡°ranki ya dad'e lafiya dai?¡±.
Bud'e idona nayi a hankali, sai naga jakadiya ce, namata murmushi tareda yunk'urin tashi zaune, ¡°wlhy kaina ke ciwo jakadiya, halanma ke kad'aice ma a gidan?¡±.
¡°subahanalla, sannu ranki ya dad'e, bara na samo miki abinci saikisha magani, eh ni kad'aice ranki ya dad'e su Sauban sun tafi makaranta. Gimbiya Mimi kuma tana asibiti itama, taga kina barcine shiyyasa tahana a tadaki¡±.
Nace ¡°ALLAH sarki¡±.
Wucewa tayi zuwa kitchen, babu dad'ewa saigata tadawo da tire, a gabana ta ajiye tana fad'in ¡°gashi ranki ya dad'e, kici saikisha magani kafin Magajin gari yadawo saikuje asibiti¡±.
Kallonta nayi da mamaki, ¡°jakadiya waye magajin gari kuma?¡±.
Tayi 'Yar dariya, ¡°ranki ya dad'e ina nufin mai gidanki, ai magajin gari nake cemasa¡±.
Murmushi nayi ina girgiza kai kawai, na had'a tea nasha, sannan nasha maganin, anan falon na kuma kwantawa, barci yakuma kwasheni.
Jakadiya na zaune tana gadina.
Da sallama ya shigo, jakadiya ta amsa tareda mik'ewa da sauri ta kar6i kayan hannunsa tana masa sannu da zuwa, yad'an saki fuska yana amsawa. d'aya acikin kujerun ya zauna, sai lokacin idonsa ya sauka kaina.....
maganar da jakadiya take masa ce yasakashi janye ido daga kaina ya maida kanta.
¡°ranka ya dad'e akai kayan samane?¡±.
¡°no jakadiya kibari zan hau dasu, ai sunmiki nauyi, ita wannan mike damunta tayi barci anan?¡±. ¡®yay maganar yana maido idonsa kaina¡¯.
¡°kanta ke ciwo ranka ya dad'e, amma tasha magani ma, shine barcin ya kwashe a wajen¡±.
Ido yad'an tsuramin, kafin ya cije lips d'insa kad'an.
Jakadiya tajuya zuwa kitchen, babu dad'ewa tadawo da ruwa ta ajiye masa.
Sannu yamata sannan yad'auka yana sha, itakuma tabar wajen.
Kofin da yasha ruwan ya ajiye, ya maida kansa jikin kujerar ya jingina kansa, tareda maida k'afarsa d'aya kan d'aya, lumshe idonsa yayi, ta k'asan ido yake kallona, tsawon lokaci yana a haka, yayinda nikuma nake barci bansan yana yibama.
Kamar an tasheni saina bud'e idona a hankali, dashi na fara tozali, dan haka namik'e zaune da sauri, tareda warware d'an kwalina na yafa, dan gown d'in material ce a jikina, gashi irin mai santsinan, kuma rigar takamani sosai, a raina nace dukma yagama kalleni, wama yasan tun yaushe yake anan?.
Duk abinda nakeyi yana kallona, sometimes yarinyar nan takan bashi dariya, a d'an zaman dayayi da ita yalura tanada kunya, saidai batason raini, bakuma tada tsoro ko kad'an, ganin ina Neman mik'ewa saiya bud'e idonsa.
Harna fara tafiya saina juyo, danjin kamar ana kallona. idonsa a kaina, amma saiya wani basar tareda janyewa.
Kaina kawai na girgiza, harzan cigaba da tafiya saina tuna nemanfa kusanci nake dashi domin cika alk'awarin Momma da zanyi, baya na dawo nakoma na zauna, muryata a sanyaye nace, ¡°sannu da dawowa¡±.
Sosai na bashi mamaki, dan haka ya kalleni da k'yau, kamar zaiyi magana saikuma ya fasa, kusan minti 1 dawasu Second's sannan yace ¡°mike damunki kika kwanta anan?¡±.
¡°kainane ke ciwo amma yama daina¡±. maganar dayayice tabani mamaki.
Mik'ewa yayi yana fad'in ¡°ba gulma tasaki k'inyin barci jiyaba, dole ai kitashi da ciwon kai¡±.
Galala nabishi da kallo, kai wannan guy d'in yafara bani tsoro, dama yasan banyi barciba jiya kenan? Anya guy d'innan baya gani har hanji?? nabishi da kallo yayinda yake taka step d'in benen cikeda izza, hanunsa d'aukeda ledojin daya kwashe a falon, saida ya 6acema ganina sannan na sauke ajiyar zuciya.
¡Ã¯*¡Ã¯*¡Ã¯*¡Ã¯*¡Ã¯*¡Ã¯*¡Ã¯
*_Nigeria_*
Tun bayan zuwanmu sallama da tafiyarmu 'yan gidanmu sai suka dainama innarmu magana, musamman yanda sukaga anata fita da abubuwan dana bari a baiwa mutane, innarmu ko'a kwalar rigarta itakam, bata damu da rashin mata maganar dasukeba, harkokin gabanta kawai takeyi hankali kwance.
Innaro kam kud'in da Galadima yabata suka sakata d'agama innarmu k'afa, ko gaidata tayi cikin salama take amsa mata, a jiya harda siyoma su Aryaan sllifas, wai taganine a hanya sun mata k'yau ta siya musu, murmushi kawai innarmu tayi damata godiya ta kar6a.
Wannan k'yauta tasaka mamansu yaa Hameed kasa hak'uri taita sakin habaici, daga nan sauran matan gidanmu suka d'auka suma, innarmu saita saka karatun alkur'ani ma a waya tashige d'aki tarufe kanta.
Har sukaci suka tsire dan kansu sukayi shiru.
Kusan k'arfe hud'u na gamma saiga Zarah wujiga-wujiga tashigo gidan, ga ciki yafito masha ALLAH, Innarmu dake tsakar gida tana wankin kwanuka tayi saurin cewa ¡°zarah lafiya?¡±.
Jikin innamu tafad'a ta fashe da kuka, ¡°innarsu 2 ki taimakeni zai kasheni, wlhy bani na d'auka masa kud'iba, narantse da ALLAH........¡±
Tuni 'yan gidanmu duk sun fito, danjin kururuwar Zarah, mamansu yaa hameed tazo ta janyeta daga jikin innarmu, ¡°k mahaukaciyar inace dabazaki nutsu kisan wazaki fad'ama matsalarki bane?¡±..
Oho ita Zarah ba wannan bane matsalarta a yanzun, takuma fad'awa jikin mamansun tana kuka da rantsuwar ba ita ta d'auki kud'iba.
Ganin tana neman yage musu zani a kasuwa sai mamansu tajata suka shige d'aki.
Wata dariyar gatsatsa maman Safara'u tayi, tareda ta6e baki tana kallon Gwaggon Haleematu dake k'usa da ita ¡°to anfara da bismillah kenan? Wata 6 an koro yarinya da duka?......
Caraf Momy Hadiza ta k'ar6e ¡°yo mai kashi a gindi ai baya toshe hanci yace makwafcinsa na wari, kidai iya bakinki tunda kema kinkai gidan wani¡±.
¡°can a bakinki, nakai kuwa, kuma tawa zama daram babu yaji balle nik'a gari, tunda ba auren hange-hange da tauye hak'in wasu namata ba, ai bama saikin zak'eba, munsan mai kaza a aljihu dama baya jimirin Asss!, indai nice kinga tafiyata, kiyi da wani ba niba¡±.
Tamkar Momy Hadiza zata daki maman Safara'u haka ta hayayyak'o mata, wannan hayaniya ce tafara jawo kunnen makwafta gidanmu, saiga innaro tamkar an jehota, ta shiga tambayar ba'asin hayaniyar, dansu Abbanmu duk suna wajen aiki.
Duk shiru sukai mata, sai innarmu Ce da maman Fauziyya suke fad'a mata abinda yafaru.
d'akin mamansu yaa hameed tashige domin jiyo ba'asin dawowar Zarah n.
Itadai innarmu jikinta duk yayi sanyi, wannan zamanin ko aurar da yaranka mata kayi tsugunne bata k'are makaba, dan sai ALLAH yabasu mazaje na garin dazasu iya hak'urin zama da juna, aurene tunkan ayisa zakaga angama kwashe masa albarka wajen buruka da bidi'oin biki, ga iyaye yanzu gaba d'aya hankalinsu Yakoma ga d'irkama 'ya'yansu kayan mata kawai ba koya musu dabarun zaman aurenba, sun manta kayan mata basu kad'ai bane ma'aurata ke buk'ata a zaman aure, sudai sukan kawo wata nutsuwane da kuma dank'o cikin rayuwar auren, gaba d'aya yanzu zakiga gidajen auren Malam bahaushe sun canja, wuyarta dai akai yarinya miji ya kauda mata budurcine, wata biyu yayi yawa kwarnafinsa ya kwanta saiya fara Neman makusarta, gakuma yaran basuda wata dabara dazatasa su taka tsantsan ga zamantakewar, har yakai an sami sassaucin cin zarafi daga mazajen nasu, to an nuna musu kayan mata sune kawai jigon aure da hangar mallakar mijin kansa, to ALLAH ka zaunar mana dasu lafiya dai agidajensu.
Nace amin innarmu???
¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯¡Ã¯
Kusan minti 10 da shigarsa saina tashi nabi bayansa, waya nakeson ya aramin nayi kiran su innarmu Susan mun sauka lafiya.
Saida nai sallama yabani izinin shiga sannan, saman sofa na iskeshi zaune yana latsa waya, da alama waya yagama ko zaiyi.
Zama nayi a kujerar da yake karatu takusa da kanta, na kwantar da murya cikin sigar ladab nace ¡°yalla6ai ka aramin waya dan ALLAH nayi kiran innarmu da Munubiya¡±.
Biris yay dani, sai zuwa can yad'ago ido ya kalleni, ya motsa baki zaiyi magana amma jin kai ya hanashi, saiyay shiru kuma yacigaba da latsa wayar, saida yamula dan kansa sannan yajawo ledar daya shigo da ita, wata k'aramar pink d'in souvenirs bag yamik'o min batareda yace uffanba.
Tasowa nayi zuwa gabansa zan kar6a, hanun bag d'in k'aramine, dan haka hanunmu ya had'u waje d'aya, ni da shi kowa saida yaji shock, yay saurin janye hannunsa, yayinda bag d'in tayi k'asa zata fad'i yay saurin kuma k'ok'arin tarewa kamar yanda nima nakawo hannun hagguna da sauri. Sai kawai na damk'e hannunsa kanmu ya gwaru waje d'aya.
Kowanne dafe kansa yayi da sauri, yayinda hanun damarsa dana hagguna suke tallafe da juna mun tare bag d'in karta fad'i.
Na kallesa tamkar zanyi kuka, dan wlhy naji zafi, kansa kamar kwakwa?.
Hararata yayi yana fad'in ¡°k wane irin kaine dake haka?¡±.
Haushi saiya kamani, shi baiga nasaba sai nawa, na matso kwallar dasuka cikamin idona, cikin turo baki nace ¡°kana niyyar fasan kai, shine zaka maida abun kaina?¡±.
Hanunsa daya dafe kai yasaka ya d'an bugi bakina, ¡°k kinma rainani wlhy¡±.
K'asa na durk'ushe kawai nasaki masa kuka. ya waro ido da mamaki yana kallona, wannan d'an abin dayamin shine na kuka? yarinyar nan akwai rainin hankali fa¡±.
Ganin abin nawa azimunne saiya mik'e tsaye, tareda d'iremin wayarsa bisa cinyata ya shige bathroom.
Yana shiga nama bayansa gwalo, dama duk cikin takune, sonake kawai nagano lagwansa. goshina nad'an shafa dan gaskiya naji zafi, saima naji wajen kamar yafara kumbura.
Ban tashi a wajen ba nashiga loda numbar innarmu, amma tak'i shiga, saina saka ta Munubiya, itama tak'i tafiya, nad'an ja tsuka, ina kuma shafa goshin, kamar wasa wajen sai rad'ad'i yakemin, ina cikin mulmulawa da matse baki yafito, kallona yad'anyi kamar zai basar saikuma ya kasa, ya k'arasa jikin wardrobe d'insa yana bud'ewa, ¡°har yanzu goshin zafi yake?¡±.
Kamar zanyi kuka nace, ¡°eh wlhy ¡±.
Daina abinda yakeyi yayi yajuyo yana kallona, saikuma ya maida drowan yarufe yanufe inda nake zaune. A gabana ya d'urk'usa, k'amshin sabulun wankan ya daki hancina, hannunsa na haggu ya d'aura bisa kaina, ya d'aura na damar akan goshina, sanyin damshin ruwan da taushin hannunsa suka ratsa goshina, a hankali yafara mulmula goshin, nafara matse baki ina rik'e hannunsa, dan wlhy akwai zafi, ¡°please kabarsa dan ALLAH, wlhy akwai zafi fa¡±, bai saurareniba, duk rik'e masa hannun danake saida ya mulmulamin sosai sannan yamik'e yana hararata da ta6e baki, ¡°halan kekam kina jaririya ba'a miki wankan jegoba?¡±.
Baki na tunzuro masa, nace ¡°ka kira innarmu ka tambayeta mana, ni ina zan sani¡±.
Batareda ya shiryaba ya murmusa yana barin wajen. Kayansa ya d'auka yakoma bayi danya sanya.
Nikuma saina mik'e nakoma kan sofa d'in ina bud'e bag d'in d'azun. kwalin wayane mai k'yau, wani dad'i ya kamani, amma saboda jan aji saina maida na ajiye gefena, nacigaba da danna kiran su innarmu.
A haka yafito ya sameni, yana sanye cikin Brown d'in wando da Navy blue t-shirts mai gajeren hannu, ya tsuke k'ugunsa, bai kalleniba yawuce wajen wani kwando mai k'yau da aka zuba sandunan wasan Golf a ciki?, guda biyu ya ciro, sannan ya tako inda nake yana fad'in ¡°bani wayata idan kin gama¡±.
Fuska na marairaice nace ¡°ALLAH kagani bamma yiba, tak'i shigama¡±.
Wayar ya kar6a ya duma number, bakinsa ya d'an ta6e ¡°k bak'auyar inace dazaki kira number a haka? ko nan k'asarkice?¡±.
Tunawa nai da saina saka + ashe, nace ¡°oh namanta saina saka + wlhy¡±.
Aljihu ya saka wayar, ¡°saiki bari sai wani time d'in kuma, yanzu sauri nake ana jirana¡±.
Da sauri nace ¡°zan bika please, wlhy gidan shiru babu dad'i¡±.
Yana fesa turare yace, ¡°ba yauba, baga jakadiya nan a gidanba, yanzu kuma Khumar zai d'akko khaleel a school ai¡±.
Shiru nayi bance komaiba, saiya juyo ya kalleni, ganin na kwa6e fuska cikin damuwa saikuma yaji wani iri, juyawa yayi yagara kwalar rigarsa, kafin yaje drowan gefen gadonsa ya d'akko wasu album na pictures har hud'u, saman cinyata ya ajiye batareda yace uffanba, yakwashi sandunansa yakama hanyar fita, batareda ya juyoba yace ¡°wad'annan kayan nakine ki duba¡±.
Kafin nabasa amsa harya fice abinsa.
Kaina na girgiza ina ta6e baki, a fili nace, ¡°Alaramma mara R ALLAH ya gyarakama Momma kai dai¡±. (Kifad'a a gabansa mana yarinya. ??).
_______________,,___________,,,______
Da sauri mamansu yaa Hameed ta kwa6e bakin Zarah alamar tayi shiru, saboda shigowar innaro, innaro bata kulaba, dan haka ta zauna a kujerar falon idonta akan Zarah, ganin yanda duk jikinta shatin duka, ¡°kekauwa zara'u miya sameki haka? Ga ciki?¡±.
Harara mamansu yaa hameed taketa zubama Zarah, amma ina bata kulaba, ta share kwallar fuskarta tana fad'in ¡°innaro wai kud'i ya ajiye a gidan jiya, shinefa yaduba yau bai ganiba, ina kitchen yashigo yana tambayata wai kona canja musu wajene? shine nace bammasan yashigo da kud'i gidan ba bare harna canja musu waje, ko rufe baki bai bari nayiba ya fallamin mari, nikuma naji zafi namasa ALLAH ya Isa, shinefa kawai yacire belt d'in jikinsa yahau buguna, wlhy da k'yar nagudo na fito, nasan idan nashiga gidan Siyama zai iya bina har can, tunda gidan d'an uwansane, dak'yar nasamu napep a anguwar nataho gida¡±.
Innaro tarik'e ha6a tana fad'in ¡°oh ni marwanatu jikar Falalu, yanzu shi Sa'eedunne yamiki haka da hankalinsa? toke kin tabbata baki d'aukar masa kud'iba?¡±.
¡°wlhy innaro ban d'auka ba, kinji na rantse miki, shi dama halinsane haka?, indai ransa ya6aci ko kika masa kuskure sai dai kawai kiji mari, wlhy zuwana gidannan tun bankai satiba yake marina idan namasa Abu, yaune harda duka, gashi ko kad'an bashida hak'uri, Abu kad'an yagani saiyayi tsogumi, idan kuma kin masa na kirki bazai yaba mikiba, dawuya kimabasa Abu sau 10 bai kushe 8 a cikiba, 2 kuma bawai zai nuna yaji dad'i baneba?¡±.
¡°kai amma wannan yaro anyi wulak'antaccen yaro, yoshi dama dukan mata yake akasa nabashi jikata? Bari su Auwalun suzo, koti zansa su kaishi, sai an kwatar miki hak'inki,¡±.
¡°nidai babu wani court k innaro, kawai akirasa amasa bayani a sasantamu nakoma d'akina, inason mijina wlhy¡±.
¡°enyeee! A lallai zara'u kinkai kuwa, nikike fad'ama kina son mijinki? to dan ubanki auwalu saiku tashi ki koma yanzu, idan yagadama anjima akiramu jana'izar gawarki¡±. fuuu tafito tana sababi, kayaya tunta da maimaita maganar da Zarah tafad'a mata yasaka 'yan gidanmu fahimta komai, wasu dad'i har tsakar kansu, (yo dama gidanmu kowa bawani son d'an uwansa yakeba, salon munafurcine kawai da bariki na tsoffin mata).
'Daki Momy Hadiza tashige takira Siyama danjin k'arin bayani, anan Siyaman ke sanar mata wai dama ba wannan ne karon farko da Sa'eed d'in yay Complain Zarah na d'auka masa kud'i ba¡±.
Momy Hadiza ta rabga salati tana fad'in ¡°k 'yarnan da gaske?¡±.
¡°wlhy kuwa Momy, yanzu haka ma gashi anan gidanmu suna maganar da Sulaiman¡±.
¡°to ALLAH ya k'yauta, ni dama auren ya mutu ki zauna daga ke saike, danni bama na k'aunar wannan had'in gambizar family d'in, komai yaro yamaka ido nakai¡±.
¡°yo nifa Momy wlhy yanzu haka bama magana da Zarah, daga ranar mun had'u da ita a gidan sunan Hanan k'anwarsu, toni shine ya kaini da kansa, itakuma Ashe bashi yakawitaba, shine ta tambayeni miyasa ban biya mata mun taho tareba? Nace mata ai shine yakawoni, itama nazata Sa'eed d'inne zai kawota, shinefa taketa faman fushi da gaba dani¡±.
¡°eye, kice tafara miki hassada kawai saboda taga mijinki tafi kulawa dake? to wlhy bance ki d'aga mata k'afaba, karma kituna da ubanki da ubanta ciki d'aya suka fito¡±.
¡°insha ALLAHU Momy bazan raga mataba¡±.
¡°yauwa 'yar albarka. Yanzu yamaganar kud'in damukayi ranar? kinsan fa bikin nata tahowa?¡±.
¡°zan aiko miki Momy, wai Momy da gaske Munaya bata Nigeria? ¡±.
Tsaki Momy Hadiza taja, cikin bak'in ciki tace ¡°haka dai iyayenta sukace, mudai bamuda tabbas tunda ba'a gabanmu jirgin yatashiba, anzo dai mana sallamar munafunci itada wannan miskilallen mijin nata¡±.
¡°aikam Momy indai da sunzo d'in to da gaskefa sun tafin, dan Sulaiman yacemin yaga Galadima a airport shekaranjiya da sister d'inan watawa, shikuma yaje raka babansune zaiyi tafiya¡±.
¡°suyita tafiyar mana, kema dan sakaraice ai, yo mi mijin nata yafi naki? Amma kod'an Honeymoon d'in nan da ake zuwa ke kin kasa sakashi ya kaiki¡±.
¡°lallai momyn nan, shikenan tunda laifina kike gani, nidai zan kiraki anjima, yanzu jirana suke nakai musu abinci¡±. ¡®bata jira cewarta ba ta yanke wayar¡¯.
Takaici yakuma kama Momy Hadiza, saitaja tsaki, amma saboda munafurci saita nufi d'akin mamansu yaa Hameed jiyo abinda ya maido Zarah gida. (Fuska biyu??).
*******************
Hotunan na ajiye nafara bud'e wayar, woow irinfa wayarsa ce komai da komai, saidai tawa pink ce, gakuma extra condom na wayar har kala uku, kai gsky wayar tayi babu k'arya, layin dana gani a ciki na d'auka na saka sannan na jona charge saboda d'oki, sauran ledojin nahau bud'ewa, duk kayan sawane k'ananu marasa nauyi, kuma bamasu fidda tairaiciba, zan iya sakasu gaban kowa, a raina nace Ashe Galadima yanada kirki haka?, saida nagama had'a kayan waje d'aya sannan na haye gadonsa da yaune karon farko zan haushi, nawani 6ararraje ina kallon hotunan, wasu hotunan abin dariya wlhy, dan wasu yana yarone k'arami, wani a makaranta, wani awajen wasan yara, wani a masarautarsu, wani tareda mom, wani da aunty mimi da sauban, duk inda suke da Abie saida nayi kuka, dan abie duk yana kwancene, k'alilanne yakeda lafiya sannan. wasu kam ya zube wayoyi yanata had'e-had'en abubuwa na wasan yara?.
Kallon hotunan ne suka d'aukemin hankali har wani lokaci dasu Sauban suka dawo, bamma san sun dawoba saida Samha tahawo saman.
Zama tayi tanamin bayanin wasu mutanen jikin hotunan muna dariya, bamu sakkoba saida Sauban ya hawo yakiramu.
******
Sai bayan isha'i suka dawo shida aunty mimi.
Ina d'aki zaune har sannan ina kallon pictures d'in ya shigo, d'ago kaina nayi na kalleshi tareda amsa masa sallamar. Namasa sannu da zuwa.
Ciki-ciki ya amsa yana zubewa bakin gadon, d'an kwanciya yayi kusan minti 10 kafin yamik'e yashiga bathroom, kusan 1hour sannan yafito maybe su yalla6ai an sauke nauyine (??).
Yau saida na jirasa harya idar da shafa'i da wutirinsa, dan magana nakeson muyi, ganin ya idar ya zauna latsa wayane nace ¡°dan ALLAH yalla6ai in tambayeka?¡±.
Batareda ya d'agoba yace ¡°uhmm¡±.
Zamana na gyara cikin nutsuwa nace, ¡°shin tunda Abie yafara jiyya anta6a masa maganin gargajiya ko amaida hankali ga addu'oi haka?¡±.
Yanzun kam d'ago ido yayi ya kalleni, dama tunda nafara maganar ya dakata daga latsa wayar.
¡°lips d'insa yad'an cije, kamar zaiyi magana saikuma yay shiru.
Nace ¡°kayi hak'uri idan nashiga hurumin daba nawaba¡±.
Nanma shiru yamin, saida yaja wasu mintuna kafin ya ajiye wayar yagyara zamansa, cikin alamun bak'in ciki yace, ¡°duk an gwada masa, saidai gaskiya bakamar yanda aka maida hankali gana asibitinba, saboda anriga da an sanar mana Allurar gubace aka masa, amma muna k'ok'arin sakashi a sallalolinmu na farilla dana nafila. Kullum addu'oinmu akansa yake¡±.
Ajiyar zuciya na sauke, nace ¡°ALLAH yabashi lafiya, yakawo mana iyaka, yakuma bashi ikon cinye jarabawar nan¡±.
¡°amin yafad'a a la66ansa¡±.
Dagani harshi babu Wanda yasake magana har muka kwanta, saidai yauma banyi isashen barciba, inata cud'awa da kwancewa, har gabannin asubahi kafin barcin ya saceni..................??
_To Alhmddlh my sweet fans, zamu dakata anan kenan, saikuma ALLAH yakaimu bayan salla darai da lafiya, zanbar wannan a matsayin *RAINA KAMA..... PART ONE* yanda zamu tafi a tsare kawai, basai mundawo ba kuma mushiga tunanin inama aka tsaya? Ina kuma za'a tashi, a *RAINA KAMA PART TWO* zamuga yanda Munaya zata taimaki Galadima kamar yanda Momma ta buk'ata, shin zai bata had'in kaima Kuwa? domin kunji Momma dai tace bashida yarda? ya matsayin auren Zarah? Muftahu yaya zata kasance idan Galadima ya cafkoshi? shin Munaya tanada wani fikra ne game da ciwon Abie?. wannan amsoshin duk suna cikin *RAINA KAMA PART TWO* da zaizo bayan sallah insha ALLAHU my guys, one Luv?????????_
_tabbas banida bakin godiya a gareku, saboda addu'oi da mahaifina ke samu agareku, Comments naku suna matuk'ar sakani a farinciki sosai, ngd ALLAH yabar zuminci, duk inda masoyin wannan buk yake yasaka aransa yana can k'ark'ashin zuciyar Bilyn Abdull.???????????????????._
_ga azumi zamu shiga, 'yan uwana dan ALLAH mu maida hankalinmu ga ibada, sadaka da k'autatama marasa k'arfi, marayu,, k'autata mu'amullarmu da jama'a dayin amfani da abinda malamai zasu fad'akar damu, karya zam kullum muna wahalar zuwa tafseer amma bamu d'aukar komai, da bayan salla yawuce munkuma koma kan munanan ayukanmu, karmu manta irin wannan watan saikuma mai rabon gani, sau 1 tak yake zuwa mana akowacce shekara, wani yawuce agaresa kenan har Abadan, zata iya yuwuwa nice ma?, zata iya yuwa kece 'Yar uwa???, zata iya yuwa kaine d'an uwa???. dan ALLAH mu gyara please & please, muyi amfani da damarmu kafin ta kufce mana, (kullu nafsin za'ikatul maut, kowane rai saiya d'and'ani mutuwa, ubangiji bai turo maka date d'in da rundunar mala'iku zasuzo d'aukar rayin nakaba,? mutuwa bata kwankwasa k'ofa, batada wata alamar yanda zatazo ta riskeka, kana tafiya ne, ko kana barci, ko kana salla, ko zaune, ko kana hira, ko kana aikata wani sa6o, ko kana wani abin alkairi?, ya ALLAH ka d'auki ruhinmu muna masu imani agareka da tsoranka, ALLAH ka gafarta mana, kamana maganin abinda muka Sani da wandama bamu saniba._
_ina rok'on dukkan Wanda na 6atamawa a yayin wannan rubutun ko kafin shima dan ALLAH Ya gafarceni, nidai na yafema kowa._???
*_duk masoyina na gaskiya Dan ALLAH inason yasakani a ddu'arsa ta cikin azuminnan koda sau d'ayane, idan munada Rabon haihuwa adunaya nida mijina ALLAH ka azurtamu da samu masu albarka cikin sauk'i da rahamar ubangijin talikai, idan ba alkairi bace agaremu ALLAH kasamana hak'uri da juriyar azuciyata???, ALLAH kayaye mana dukkan damuwarmu baki d'aya._*???
Dan ALLAH ko sau 1 yane kar'a manta dani???
Amin afuwa zan rage groups saboda yawan groups d'in suna cimin data wlhy, idan nayi sub na wata d'aya ko sati bata yimin take k'arewa??.
Ngd sosai, ALLAH yabar zuminci, ALLAH yasa munada rabon sake had'uwa a bayan salla, ALLAH ka kar6i ibadunmu baki d'aya. yabamu juriya da hak'urin ibadar dake tunkaromu nanda kwana 1??.
Happy Ramadan Advance??????????
Binyn Ku Ce dai??
Writer??
*Abdul-maleek bobo!!*
*Auren k'addara ko biyayya!?*
*Ban saketa ba!!*
*Ciki da gaskiya...!!*
*Karayar arzeek'i!!*
*k'anwar uwace ko kishiyar uwa!?*
*Kukan krciya...!!*
*Ni da Aminiyata!!*
*Nawaff!!*
*Rashin Sani!!*
*Raina kama.....!!*
*Sabon Al-amaree!!*
*Sanadin bikin salla!!*
*Siyasa ko k'abilanci!?*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*???
Download Raina Kama Littafi Na Daya Complete
0 Comments
Thank you for this comment