*_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
__________________________
*_Kai jama'a yau dai kun Sani typing dole saboda munafurcin y'an bani Na iya, wannan karon kuma kurasa k'ullin da zakuyi sai akan Uwa da 'Diya?, nikam yau koda mamana (mamu gee) kwaikwayar RAINA KAMA tayi to wlhy birgeni zatayi, ai baiwace ma wani yayi Abu kabishi daki-daki kana kwaikwayo. Irin wannan shirmen naku baya cikin kan Bily, ba mamu gee ba koda watace aka jingina da hakan bazanji komaiba wlhy, sannanma nifa abinda yabani mamaki a writeup d'in da mamana tayi bata ambaci sunan RAINA KAMA ba aciki ko wani littafi daban, to tayaya y'an bani Na iya da tsugunne-tsugunne su anasu writeup d'in suka saka sunan RAINA KAMA? (Wlhy halin wasu daga cikin writers namu ko kad'an bashida k'yau, neman sunane kokuwa son asanine niban saniba🤦🏻♀)._*
_Reader's kuma da naku, sometimes bakunanku basuda linzami, irin wannan abubuwan kune ke fara tsirarsu saisuzo kuma su buwayeku, Ku ke karanta RAINA KAMA DA TARAYYA Ku kusan banbancin abinda ke cikin kowanne, amma dayake Ku irin wannan dama shine farin cikinku saikuyita k'irk'irar abinda dolene daga k'arshe saiya zama rikici, to nikam zan sanar muku, awanan karon sai had'in naku baiyiba, Dan MAMU GEE DA BILYN ABDUL duk Abu d'ayane, daga tarayya har Raina kama buks d'inmu ne, mu muke rubuta abunmu, babu wata munafukar writer ko reader da mukayi shawara da ita kafin mu d'aura alk'alaminmu a takarda, masu had'a husuma kuma sai kusha fetur Ku had'iyi ashana kuyi bombing d'in kanku, ina dai shikenan ko?🙅🏻_.
*Daga k'arshe inamai muku nasiha da kuji tsoron ALLAH, wlhy bashin naira 10 kacal yana hana bawa kwanciyar kabari, karo tsakanin rago da rago kawai akwai hisabi tsakaninsu, aranar kiyama bayan an tsaya hisabi duk Wanda kasani koya sanka saika Ganshi kakuma ganeshi, bawai kaitsaye za tantanceka akaika wuta ko aljanna ba, wlhy sai an tsidaka, ancire hak'in mutane a kanka, ka zagi wane babu hak'k'insa, ka harari wane, kama wane zind'e, ka cinye kud'in wane, ka had'a fad'a tsakanin wane, ka 6ata sunan wane, ka cuci makwafcin, ka...ka...ka...da yawan gaske, duk wani cin amana ko zalunci dakama wani inhar bai yafe makaba a wannan ranar sai an cire masa hak'insa a cikin ayyukanka, (Dan sune kad'ai guzirinka) komai tarin aikin alkairin daka tara inhar kanada irin wad'annan bashishshikan d'aya bayan d'aya sai an zaresu daga gareka, koda dabba da kafiri ka zalunta kuwa, idan dama bakada komai, sai ayita kwashe nasu zunubai ana lafta maka, sai angama tas, kabiya an biyaka saikuma a gwada ayyukanka a kan mizani, miyarage kuma? Saika koma gefe jiran sakamako. Wlhy y'an uwa babu babban tashin hankali irin kar6ar sakamako, a wannan lokacin uba baya gane d'ansa, y'a bata gane uwarta, miji baya gane matarsa saboda tsantsar tashin hankalin da ake ciki, da wane hannu xaka amsa, ina ne zaizama mazauni Na dindindin, duk baka saniba, haba y'ar uwata, kinada wannan babban aiki a gabanki amma kika shagala wajen had'a husuma irin ta social media wadda bansanki ba, baki sanniba, maybe ma har Abadan bazamu ta6a sanin junanmu ba, muji tsoron ALLAH wlhy, yakamata irin wannan abubuwan su tsaya hakanan, daga ni har mamana badan Neman suna mukeba, domin Isar da sak'o mukeyi a cikin tarayya da raina kama, burinmu kuma ko mutum d'aya ya amfanu da manufarmu ya wadatar, bawai tarin masu karantawa ba, ni miyasa babu Wanda yata6a tarata yacemin tarayya copy d'in raina kama ne? to Ku kama kanku please, kodan tsoron ALLAH.*
_My Sweet mah-mah mamu gee wannan page d'in sadaukarwane a gareki, kiyi yadda kikeso dashi nabaki, ALLAH yabarmu tare, I love you irin trillions d'innan, kisamun albarka nakuma zama gagara badau😁😘._
Bilyn Abdull & Mamu gee RAINA KAMA ne mu, sannan munyi TARAYYA NE akan Isar da sak'o mai muhimmanci, mabiyanmu Na gaskiya a KAFTA kawai⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀😂👍🏻.
HARUN da GALADIMA kuma Ku KAFTA naku wasan🤣🤣🤣🤸🏻♀🤸🏻♀✍🏻😜.
__________________________
~Book 3~ 👉🏻1⃣➖2⃣
...............Saida suka fara tafiya sai Harun yafara jin tamkar k'amshin turaren Galadima yakeji, mamaki ya kamasa, ya kalli gaban motar yana fad'in “lawwali nikam kaji minakeji kuwa? k'amshin Sameer fa”.
Murmushi Galadima yayi, baice komaiba sai “Uhmm”.
Hakan yakuma d'aure kan Harun, kamar zai sake magana saiya fasa, ya d'auki wayarsa domin son kira yaji ina Galadima, yasan Abu dolene ke fiddashi da daddare daga masarauta, amma sai kira ya shigo a wayarsa, k'aramin tsaki yayi Dan ba'a ko'ina yake d'aga wayaba, ya yarda da lawwali drivern babansa waziri amma bakomai yake barin ya saniba, ganinfa an damesa da kiran saiya d'aga. Da sauri ya janye wayar a kunnensa yana lek'o kansa gaban motar danya tabbatar. shin ina tunaninsa ya tafi dahar ya iya gaza banbance lawwali da Sameer?.
yace “Sameer!”.
Galadima dake tuk'insa hankali kwance yana kuma sauraren wayar Harun ta abinda yasa akunne, saboda ya saita duk wayar dazata shiga ta Fita a war Harun saiya shigo wayarsa shima kota fita yace, “Uhmyim”.
A tsorace Harun yakoma baya ya bigi seat da k'arfi, babu abinda zuciyarsa keyi sai dukan 100-100, wayarsa ya jawo jiki Na rawa yafara k'ok'arin kiran wani.
Galadima yay murmushi, cike da izzar k'asaita yace, “bar wahal da kanka my dear friend, duk wata waya dazaka kira a yanzu wayata zata shiga”.
Harun yay jifa da wayarsa a kujera jiki yana rawa, batare da wani tunaniba ya mik'e kawai ya shak'e Galadima, da hannu d'aya Galadima yake driving, hannu d'aya kuma yana k'ok'arin kare kansa daga shak'ar da Harun ya masa.
Da k'yar yasamu ya gangara gefen titi, yasaka hannunsa d'aya ya bigi gefen cikin Harun daya samu damar shak'esa da k'yau, Dan numfashin sa harya fara fita afisge.
Dukan cikinsa da Galadima yayi yasakashi sakinsa da sauri, Galadima ya juya yakuma naushin bakin Harun saiga jini, dama bai gama dawowa hayyacinsa ba daga dukan cikinsa da yayi.
Harun ya fad'a saman kujera yana rik'e ciki da shafar hancinsa dayaji yana yoyo, kallon hannunsa yayi saiyaga jini, ya zaro ido cikin matuk'ar mamakin shi Sameer ya fasama baki, yo ko danbe zasuyi ai babu abin zai d'auka a jikinsa, (Dan shima Harun d'infa ba bayaba).
Galadima daketa huci ya dafe sitiyari da kife kansa ya kuma tada motar a harzuk'e ya fara tafiya cikin tsananin gudu.
Cikin hakki da fidda numfashi a wahalce Harun yace “Sameer n..n..ni ka daka? harda fidda jini?”.
Banza Galadima yamasa yacigaba da tuk'insa, Harun ya kuma yunk'urawa zai tashi amma saiya kasa, saboda ba k'aramin duka Galadima ya masa a gefen cikiba, wajen ya k'ulle, dole ya koma ya kwanta yana cije baki da matse ido, hannunsa rik'e da wajen har yanzu.
Suna isa inda ya nufa yay horn, saiga Nuren da kansa yazo ya bud'e masa k'ofa, a fusace ya shiga gidan, shi Nuren ma har yana tsorata.
Yana tsaida motar ko kashewa baiyiba yabud'e ya fito a harzuk'e, inda Harun yake ya bud'e ya jawoshi, yakuma kai masa naushi, shima ya kai masa dukda azabarda cikinsa ke masa.
Nuren da Muftahu sun iso wajen a hanzarce, Dan ganin danbe Na Neman hark'ewa tsakanin aminai guda biyu, Nuren yaja Harun, shikuma Muftahu Galadima.
“Waishin mikukeyi ne haka brother? Da girmanku da ajinku kuke danbe? danbe fa? Wannan wane irin kuma abin kunyane? Lallai da y'an jarida zasu samu labari gobe dasunci kasuwa sosai.....”
Hankad'a Muftahu Galadima yayi baya, yay taga-taga zai fad'i, bai kuma kallon ko wanne a cikinsuba ya nuna Harun da d'an yatsa, “Mara kwakwalwa kawai, kafin ni ka kasheni ninan zan kasheka daga kai har munafikin ubanka, dak'ik'i kawai”. yana gama fad'ar haka yabar wajen zuwa cikin gida, taku yake kamar wani bajimi ya fito za6en sarauniyar k'yau.
Daga Nuren har Muftahu da kallon mamaki suka bisa, shi kansa Harun maganar Galadima tasakashi girgiza, kardai guy d'innan yana sane da wanene ni tun tuni amma ya k'yaleni? da k'arfi ya fisge shima daga jikin Nuren yana kaima Muftahu duka, “Munafiki dakai zan fara”.
Saurin kare kansa Muftahu yayi, Nuren yakuma yunk'urin rik'e Harun, danshifa abin yafara d'aure kansa, kowa yasan Harun aminin Galadima ne Na kusa, yau kuma miya had'osu haka? harda zancen kisa? Galadima yanada matuk'ar zuciya, idan ransa ya 6aci babu ubanda ke gane kansa....
Fad'a dai Neman komawa yay ga Muftahu, saida su Ameer sukazo suka rirrik'e Harun, cak suka d'aukesa yana fisge-fisge da fad'ama Muftahu magana suka shiga dashi ciki.
Nuren ya kalli Muftahu dake murmushi yana gyaran kwalar rigarsa.
“Amma mike faruwa kuma haka? Yau Sameer ne ke fad'a da Harun?”.
Muftahu ya dafa kafad'ar Nuren, “'Dan uwa akwai abinda baka Sani bane, amma Na tabbatar yanzu zama sanshi”. Yana gama fad'ar haka yayi gaba abinsa, shima da kallon Nuren ya bisa, kenan shima yasan dalilin fad'an nasu ashe? jiki a sanyaye ya nufi wajen motar ya kashe sannan ya nufi gidan shima, a yanzu kam lamarin wanan case yafara rud'ar dashi, dan yanda Sameer keta abubuwa a tsakaninnan basuyi kama da nasa zarginba shi.
Galadima Na kwance cikin kujera doguwa, tunda ya shigo anan yazufe, duk yanda zuciyarsa taso 6aci sai kalaman Munaya su danne su (mata kunga amfanin hikimar zance ga mazajenmu ko), zantuttukanta suka shiga dawo masa a rai daki-daki, tabbas a yanzu ba fushinsa bane abin buk'ata, jarumtar hak'uri ce, kamar yanda ta fad'a idan kwallo ta 6ata ba daina wasa akeyiba, wata kwallon ake d'auka ayi da ita, cikin lumshe ido ya ciji lips nashi yana wani miskilin murmushi.
Daga Muftahu har Nuren dai ido suka zuba masa, ga Harun da aka saka a wani d'aki aka kulle sai bugun k'ofa yake yana fad'ar magana masu zafi akan Galadima.
Mik'ewa Galadima yayi yana gyara rigarsa, ya kalli su Muftahu yana cire safar hannunsa, “bara naje gida”.
Abinda kawai ya fad'a kenan yay ficewarsa.
Tamkar sokaye haka suka bishi da kallo, yana fitowa ya iske sarkin mota a waje yana jiransa (Ashe dama ya biyo bayansu) da hanzari ya bud'e masa motar ya shiga, Galadima ya zauna yana sauke ajiyar zuciya a cikin kujera. Har suka Isa masarauta babu Wanda ya iya tankawa.
Sarkin mota nayin parking baima jira an bud'e masaba ya bud'e da kansa ya fice, hadimai masu tsaron sashen Na masa barka da zuwa amma ko kallo basu isheshiba.
Kai tsaye sashen Munaya ya nufa, babuko sallama balle Neman iso ya danna kai cikin d'akin. Laraba da samba da yara duk sunyi barci, Munaya kam takasa hakan, sai safa da marwa takeyi tun d'azun, taje d'akin Galadima yafi sau 7 amma bai dawoba, hankalinta a tashe yake da tunanin ina yaje a darennan? shida idon mak'iya kullum a kansa yake, dama kad'an suke nema ta cuta masa?.....
Cak tunaninta ya tsaya lokacin da taji anyi sama da ita, zata fasa ihu yace, “yima mutane shiru”.
A hankali yayi maganar, Dan haka ta had'iye ihunta cikin sauri da mamakin abinda yayi, yana fitowa falonta ya ajiyeta yaja hannunta zuwa sashensa.
Babu abinda zuciyarta takeyi sai dukan 50-50, miye yashiga kansa haka wai?. Basu tsaya a falo ba sai bedroom d'insa, dama tun a hanya ya fara cire jacket d'insa, suna shigowa yana ida cirewar, yay wurgi da ita a tsakar d'akin yakuma d'aukar Munaya suka fad'a saman gado.
Tsoronsa yakuma shigarta lokacin dataji ya sakata jikinsa ya matseta, kaikace zai maidata a cikine.
Cikin matse baki da sakin k'aramar k'ara tace, “wai minene haka yalla6ai?”.
“shiiii!!”. Yafad'a yana d'ora yatsansa d'aya akan bakinta, batada za6in daya wuce tayi shirun, sai zuciyarsa dake wani irin bugu da k'arfi, hannunta ta saka a saitin zuciyar tana karanto addu'a.
Duk abinda takeyi yana jinta, hawaye masu zafi suna kwarara masa a ido, saidai tacan gefene shiyyasa Munaya bata saniba, tsawon lokaci muna a haka, har zuciyarsa tafara dai-daita bugawa, takoma normal, sai ajiyar zuciya da k'ok'arin dai-daitar numfashi kawai yakeyi, a haka barci ya kwasheshi, saida nabari barcin yayi nisa sannan nazare jikinna cikin dabara da k'yar nabarshi, Dan Dana motsa saiya k'ara k'ank'ameni, da k'yar dai Na kwaci kaina Na maye masa gurbina da filo, cikeda tausayawa nake kallonsa ina hawaye, a haka Na cire masa takalman k'afarsa, naja bargo Na lullu6a masa, addu'ar barci nayi Na tofa masa, gudun karna ta6ashi ya farka na tofa d'in, Na kashe wutar d'akin nabar da barci kawai na fice ina share sauran kwalla. 'Dakin da Sauban yake kwance na kwankwasa, yataso cikin mayen barci ya bud'e, ganina yasashi watstsakewa babu shiri, “Aunty gimbiya lafiya kuwa?”.
“lafiya lau Yaa Sauban, cazan dama kaje d'akin Abban su Amaturrahman ka kwanta tare dashi, naga kamar bayajin dad'i, ba'asan mi dare zaiyiba”.
Kansa ya jinjina yace, “to aunty”.
Tunda na koma d'aki sai damuwa ta katantaneni, na dad'e ban barciba, daga k'arshema saida na saka karatun Qur'an da k'ara kad'an sannan barci ya saceni batare da na shiryaba.
*_Washe gari_*
Tunda asuba kasa hak'uri nayi na nufi d'akinsa.
Mamaki da kunya suka kamani, Dan ganinsa ragal ya fito wanka, gashi d'aure yake da towel, Sauban yafita saishi kad'ai.
Da sauri na juya da nufin komawa amma sai naji an rik'o hannuna, kasa juyawa nayi, yamatso dani ya saka a jikinsa, laimar ruwan da k'amshin sabulun sai suka sakani lumshe ido, ya d'ora hannunsa d'aya bisa cikina ya rik'e hannuna da d'aya, kansa a dokin wuyana yace, “Thanks matar Contract”.
Kamar bazanyi magana ba sai dai nayi, Dan karna barta ta kasheni, nace, “Tausayinsu Abie ya sakani, kaji mijin Contract”.
Murmushi yayi mai sauti yana shinshinar dokin wuyana, hannu na saka na ture kansa ina fad'in “ka dinga kula fa”.
Ya kuma maida hancinsa a wajen, cikin tura hannunsa a rigata yace, “Nida sadakina gwaggo tsiwa”.
Ban tanka masaba na fisge jikina, shima saiya barni yana wani bina da ido cikin k'ank'ancesu da miskilin murmushi. Saida naje bakin k'ofa na tsinkayi muryarsa yana fad'in “Kinzo kawai kin karyamin alwala”.
Babu shiri na juya Na kallesa, amma saiya basar tamkar bashine yayi maganarba, yama juya ya nufi hanyar bathroom.
Kwafa nayi na ida ficewa.
Bayan Galadima yakuma d'auro alwala ya fito saiya iske tea a mug da da cake a k'aramin bowl, ya d'anyi luuu da ido tamkar zai lumshe saikuma ya bud'e yana murmushi da shafar kansa. jallabiya ya saka yay salla a d'aki, bayan ya idar yazauna yasha tea d'in, dama jiya baici komaiba ya fita, yunwa yakeji, koda ya kammala saiya fice abinsa.
Sashen mai martaba ya nufa hadimai nata zubewa suna kwasar gaisuwa, sukan samu amsa iya kan la66a da d'aga hannu, da haka harya Isa.
Saida jakadiya tamasa iso sannan ya shiga, a k'aramin falon mai martaba dayake hutawa idan baya buk'atar ganin kowa har matarsa ya iskeshi, yayi mamaki kwarai, dan inhar mai martaba ya shiga falonnan kofa mama Fulani sai dai tayi hak'uri da ganinsa.
Yana kishingid'e saman tattausar darduma da aka k'awata da kilisa ta asalin sarakuna masuji da tsantsar mulki, ga tumtum da sauran kayan k'awa, an saka na'urar dake d'umama d'aki kad'an saboda yanayin sanyin safiya musamman na wannan lokacin da bazara take kunno kai.
Da hannu mai martaba yayma Galadima nuni da kusa dashi, Galadima yaje ya zauna yana tankwashe kafafu, cikin girmamawa ya risinar da kai yana fad'in “barka da asuba Abba”.
Mai martaba ya jinjina kai yana lumshe ido da amsa cikin fad'in, “barka dai yarona, ina d'iya ta da abokaina da amarya?”.
Murmushi Galadima yayi, kansa a k'asa yace, “duk suna lafiya Abba”.
“Masha ALLAH, yaya jikin naka to?”.
“Na warke ai Ranka ya dad'e”.
“To Alhmdllh, haka akeso ai, Yaya maganar tafiyar ita mai d'akin naka? duk da dai abin yazo da tsoratarwa yakamata a ayi yanda kowa yakeyi Sameer, ALLAH shine mai tsarewa, kuma zai tsaresu, domin ransu a hannunsa yake, idan an hanata zuwa an tauye hak'inta, zakuma ta iya ganin hakan kamar ita danba wata baceba, nagama shirya komai yau za'amata rakkiya kamar yadda akema kowacce mace dake aure a masarautarnan”.
Cikin had'iye yawu da wani Abu daya tokare mak'oahinsa yace, “to Abba, ALLAH yasa hakan shine mafi alkairi, nima zuwa yamma zan koma India, akwai abubuwan da zanyi na kwanaki biyu zuwa uku zan dawo”.
Mai martaba yay murmushinsu irin na manya, cikin jinjina kai ya ajiye k'aramin mug d'in hannunsa mai k'yau yana fad'in “ALLAH ya taimaka, Maybe kana dawowa nima zanje insha ALLAH”.
Galadima yace, “ALLAH ya kaimu”.
Daga nan sund'an cigaba da ta6a hira, a haka jakadiya ta shigo nemawa matawalle iso, yabada izinin a shigo dashi. bayan shigowarsa da yin gaisuwa sai suka d'ora hirar su uku gwanin sha'awa da birgewa. da Wanbai yazo gaida Sarki jakadiya ta sanar masa ai Galadima da matawalle suna ciki, shi komawa yay wai yafasa gaisuwar, jakadiya ta ta6e baki tana 6azgar goro da fad'in “kaikuma kasani gwandararren banza, kai koma y'ar k'autarnan ta jinin girma ba iyawa kaiba, dakasha kanu da sirrika a wajena wlhy”. duk a hankali take maganar yanda kowa bazai jitaba🤣.
Saida gari yay tangaran da haske sannan Galadima da matawalle suka fito, suka bar Sarki zaiyi shirin zuwa fada.
Koda Galadima ya dawo sashensa wajensu Munaya ya nufa, saboda jiyo kukan yaransa.
Ya iske Ashe wanka ake musu, Munaya kuma tana wankan itama, sai Samha da Sauban keta faman jijjigarsu a kafad'a, Abdurrahman kuma yana hannun laraba tana masa wanka. duk gaidashi suka shigayi, ya amsa musu cikin jinjina kai da lumshe ido, baki kam ko motsi bai yiba. Samha ta kawo masa Amaturrahman dake hannunta, bai d'auketa ba, ya dai shafa kumatun yarinyar yana murmushi, sai tayi shiru tana kallonsa kaikace tasan wanene.
Murmushinsa ya fad'ad'a yana jan d'an hancinta.
Samha tace, “Uncle Sam ALLAH Amaturrahman tafi su Abdurraheem wayo, shiyyasa nafi ji da ita”.
Murmushi yakumayi, ya shafi muskar Samha itama tareda d'an bubbugawa, hakan ya sakata fahimtar yau babu y'an maganar a kusa. Saima ya juya yay ficewarsa abinsa daga d'akin.
d'akinsa ya koma ya sake wanka da shirin fita cikin wani d'anyen boyal fari tas, anmasa surfani da golden color sai walk'iya yake da d'aukar idanu, takalmansa na ainahin masu sarauta half cover da lankwasarsu a gaba suma fari da kwalliyar Golden d'in, ya matsa gaban Mirror yana kallon kansa da d'aura a gogo, ganin komai dai-dai ya d'auki turarensa ya fesa kala-kala sannan ya zuba wayoyinsa a aljihu da d'aukar links d'in hannun rigar yafice yana k'ok'arin sakawa.
Da Sauban sukaci karo, yabisa da kallon birgewa, kai manyan kaya na matuk'ar k'awata k'yawun dirin yayansa, kuma sai akayi sa'a yana masifar sonsu, Dan ko'a India yakan sakasu fiyeda k'ananum kaya ko suit.
Zungurinsa galadima yayi yana fad'in “baka sanni bane?”.
Ajiyar zuciya Sauban ya sauke, yana sosa k'eya, “Yaa Sam please one pic.. Mana”.
Galadima ya hararesa zai cigaba da tafiya, da sauri Sauban yakuma had'e hannanyen sa alamar rok'o.
Galadima yay guntun tsaki, “kaiwai shin mikake da hotone? kullum baka gajiya da tarasu”. ya k'are maganar yana d'an dafe goshi.
Shidai Sauban ya marairaice, babu yanda Galadima ya iya dole ya yarda yamasa hoton, harda zuwa sukayi tare. Shidai Galadima ya girgiza kai kawai ya nufi sashen Munaya.
Ya isketa taci gayunta cikin doguwar riga ta popul d'in material, tayi d'as da ita, bazaka ta6a kallonta kace itace da yara uku ba, tana zaune tana bama Abdurraheem nono, sauran kuma suna hannun Samha, laraba tafita..
Zama yay kusada Munaya ya kar6i sauran yaran a hannun Samha, ya d'an rankwafa kan Munaya yana kama hannun Abduraheem data cire a nono ta gyara rigarta, da sauri ta d'ago tana kallonsa da mamakin koya manta Samha na d'akin dazai wani shige mata, shima kallonta yayi yana d'age gira d'aya fuska babu walwala.
Hakan kam saiya bama Samha damar yimusu hoto jiki na rawa, Dan ba k'aramin bada kala sukayiba😘.
Hasken camera d'in ya saka su d'agowa duk suka kalleta, wani ta sake k'yastawa ta fita da gudu.
Munaya ta saka hannu tana toshe bakinta saboda dariyar dake Neman kufce mata, shikam kwafa yay yana fad'in “zan kamaki ne Dan k'aniyarki, yara duk sunbi sun rainani”.
Dariyar Munaya ta fito Dan takasa rik'eta, hararta yayi dukda dariyar tata tamasa k'yau, yad'an rankwasheta akai, “kece kika sakasu ko? dama ai Sauban shima titsiyeni yayi”.
Daina dariyar tayi ta turo baki gaba tana tsafa inda ya rankwasheta, “yoni mizanyi da wani hotonka malam”.
“waya Sani ko sokike ki mallakeni”.
Baya Munaya tayi tana kallonsa, ya wani basar tamkar bashine yay maganarba, ya hauma yaransa wasa dukda basusan mima yakeyiba.
Dan gwarar da Abdurraheem tayi gefensa tana mik'ewa, “Humm, ko inason mallaka bazan mallaki abinda bai minba”.
Yi yay tamkar bai jita ba, yabama yaransa gaba d'aya hankalinsa.
Munaya taji haushin k'in kulatan da yayi, yakai mintuna 30 a d'akin kafin yay kissing kumatunsu ya ajiyesu. inda Munaya take tsaye jikin mirror tana kallonsu ya nufa ta d'auke kanta tana maidawa gefe.
Gabanta ya tsaya daf har tanajin hucin numfashinsa, hannunsa duka cikin aljihun rigar boyal d'insa 3Quarter, “Na dawo gareki, idan kin Isa maimaita abinda kika fad'a”.
Tasan halinsa da makomar maimaicin, shiyyasa ta ta6e baki tana cewa, “aini ba'a sakani abinda ban niyaba”.
Bakinsa ya ta6e yana murmushin gefen baki, “matsoraciya kawai”. yafad'a yana juyawa zai fita, saida yaje bakin k'ofa sannan ya kalli agogonsa, “kuzama a shiri, dana dawo....”. Bai k'arasa ba yay ficewarsa.
Da mamaki Munaya tace “daka dawo? To daka dawo za'yi mi?”. Batada mai bata amsa dan haka ta share ta koma kusada yaran.
Da hanzari Su sarkin Mota suka mik'e, aka bud'e masa mota ya shiga, sashen da aunty Mimi take suka fara zuwa, ya shiga Dan yasan tana nan tanajin haushinsa akan fitar jiya.
Aiko a falo ya isketa zaune a dining tana breakfast, hadimanta nata kaikawon gyara 6angaren, dining d'in ya nufa yaja kujera ya zauna, idonsa a kanta, ta shareshi tamkar batasan dashiba, shima baice uffanba ya d'auki spoon ya saka a plate d'in da take cin Arish, harararsa tayi, shima ya rama yana ta6e baki da basarwa ya cigaba da cin Arish d'in hankali kwance.
Kallonsa ta tsaya yi kawai da mamaki, takai hannu ta daki damtsen hannunsa, shafa wajen yayi yana bud'e baki, saikuma ya kwa6e fuska alamar shagwa6a.
Dariya Aunty Mimi tayi tana sake dukansa da fad'in “kadai girma rigimamme”.
Yay Murmushi tareda kwantar da kansa gefen kafad'arta, a hankali yace, “kin daina fushin dani to? kinsanfa babbar ya uwa”.
Murmushi tayi itama, ta shafa kansa tana fad'in “bazan iya fushi da kaiba ai my k'ani”.
Yace, “Nagode Auntyna”. yafad'a yana tashi zaune sosai.
Mug d'in tea d'in hannun ta ta mik'a masa, ya girgiza kansa.
Tace, “miyasa?”.
Iska yad'an furzo daga bakinsa, yace, “K'anwarki tamin d'ura tunda asuba Dan mugunta”.
Aunty Mimi tayi dariya, “'Dan rainin wayo, inama laifin daka samu mai maka d'urar, kama tunamin, Yaya maganar tafiyarta gida?”.
Saida ya rage fara'a sannan yace, “mungama magana da mai martaba” ya kalli agogonsa da cigaba da fad'in “yanzu zand'anje wani waje, insha ALLAH zuwa 2 to 3 zan dawo, basai yamma bane?”.
“To Alhmdllh, naji dad'i da mai martaba yasa baki, dan da wannan taurin kan naka bazaisa ka saurari kowaba”.
Mik'ewa yay yana ta6e baki, tareda cewa nayi nan, saina dawo, kudai zama cikin shiri jirgin 7:30pm zamubi”.
“ALLAH ya tsare ya bada sa'a”.
“Amin” ya amsa yana ficewa.
Aunty Mimi tayi murmushi da binsa da kallo, tana tausayin k'aninta da gwagwarmayar rayuwa ta zauna jiransa tunkan yazo duniya, ALLAH dai ya kawo iyakar komai dan shima yasamu kwanciyar hankali.
Nace, “amin aunty Mimi mu😘👍🏻”.
*******************
Koda Galadima ta fita waya ya kira, Wanda suke wayar ya tabbatar masa k'arfe 11:00 dai-dai Alhaji Shehu Darma zaibar gidansa.
Galadima yay murmushi, sannan ya kalli sarkin mota.
“Baseer!”
Sarkin mota ya amsa da “na'am Ranka ya dad'e”.
Kwantar da kansa yay jikin seat d'in yana cewa “Zamu banbanta tafiya dasu, dan haka a plaza zamu kar6i mota hannun Saleem, da ita zamu samu Shehu, itace irin motar dazai shiga”.
Cikin mamaki Sarkin mota yace, “Amma ranka ya dad'e ta Yaya? Kasanfa yanada bodyguards kuma masu had'ari”.
Murmushi Galadima yay yana d'agowa, yace, “Duk had'arinsu Muhammad Sameer Saifudden yafisu, kaidai yi abinda nace”.
Da to kawai sarkin mota ya amsa cikeda girmamawa................✍🏻
😨🙆🏽Galadima ma yazama kidnapper, readers saiku kiyaye⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀🤣.
_Masu nemo picture's d'in mutane suna cewa wane da wane canta matse muku, nidai banyi cover d'in RAINA KAMA ba, sannan ban fad'i kamannin mutum ko guda d'aya a buk d'inaba balle mutum yace na siffanta da Wanda kuke yawo dashi, naga wasu suna fad'ar duk maganar datazo bakinsu akan hoton babu taunawa, Ku kama kanku bansan rainin hankalinnan, yafara isata hakanan kuma, bazai yuwu kulum ina asarar data da lokacina ba sannan kuzauna kuna yankama mutane magana batare da kun duba cancantar fitarta ba, please ya Isa haka, ya isa Wanda bazai iyaba babu lali babu tilas, idan kungama wannan kunga batakai mukuba saikuma Ku tsokalo wannan, shin wane irin rayuwane hakan dan girman ALLAH🤦🏻♀, salon cikin Luke d'auka ko k'alk'yalin duniya?, bazaku ta6a magana akan Abu mai muhimmanci da amfaniba sai Mara amfani._
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭
*_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
~BOOK 3~ 👉🏻3⃣ & 4⃣
................Suna Isa plaza Saleem ya fito, dan yana ganinsu ne ta CCTV, Galadima yay k'asa da glass 6angaren da yake, idonsa akan Saleem dake fitowa, ya k'araso yana rissinawa da gaisheshi, hannu kawai ya d'aga masa, Saleem ya mik'a masa key d'in motar yana fad'in “gashi ranka ya dad'e”.
Kansa ya girgiza masa, sannan ya bud'e baki yana fad'in “ai Kaine da kanka zakaja motar, mu zamu bika a bayane”.
Da “to” Saleem ya amsa, ya juya ga motar ya shiga.
Haka suka tafi su Galadima a gaba Saleem nabin bayansu, suna tafiya Galadima nayin waya har suka isa inda aikai musu kwatance, wajen wata ma'aikatane, motocine birjik a wajen, alamun sunada yawa a ciki, daga d'an nesa suka tsaya, kusan mintuna biyar saiga wani dattijo ya fito tsakanin motocin jikinsa na rawa, harya k'araso wajen motar su Galadima idonsa akansa yake, ta window ya lek'o, amma sai Galadima yay masa nuni daya zagaya ya shigo.
Ya zauna a d'arare yana gaishe da Galadima, cikin y'ar sakin fuska Galadima ya gyara zama yana kallonsa, “Baba Rabilu ka kwantar da hankalin, insha ALLAH zaka ku6ta kuma zaka samu y'ancinka, ni namaka wannan alk'awarin, bazaka ta6a taimakona nabari ka wulak'anta ba insha ALLAH, a hankali iyalanka da duk wani dake tare dakai zai fahimci baka mutuba, yanzu mi sukeyi cikin nan d'in?”.
Baba Rabilu ya had'iye yawu, muryarsa na rawa yace, “Ranka ya dad'e ban saniba wlhy, amma abinda na fahimta shine lallai sunfara farga dakai, dan naji jiya mai wani a cikinsu yana waya wai kaima lokaci yayi dazasu maka irinna mahaifinka, dan kana neman zamewa rayuwarsu barazana”.
Murmushi Galadima yayi, yana cije lips, “karka damu baba Rabilu, wannan ai a hannun Ubangiji yake, yanzu dai ga mota nan ankawo, saika kar6a, zakayi gaba, mukuma zamu bika a baya da y'ar tazara, inason kafinma su d'auki hanya komai zai wakana, su Ameer a shirye suke suma”.
“shikenan ranka ya dad'e, ALLAH dai yabamu nasara, kaikuma yabaka kwarin gwiwa da k'arfin zuciyar abinda ka faro, ka ruguza rundunar wad'annan azzaluman da kullum cikin zaluntar bayin ALLAH suke ba a saniba, wasu kuma sunsani tsoronsune ya hanasu magana ko d'aga murya.....”. ya k'are maganar cikin sharar hawaye’.
Shiru kawai Galadima yayi yana kallonsa, shima zuciyarsa sai suya da k'una takeyi, saidai yanata ambatar sunan ALLAH kodan neman sassaunci, ajiyar zuciya ya sauke da furzar da huci, yace “shikenan muje ko, dan zamu iya rasa damarmu”.
Jin jina kai Baba Rabilu Yayi, ya fita yana rufo k'ofar, hawayen da suka cikama Galadima idone ya sakashi d'aukar glasses d'insa ya saka yana had'iye abinda ya toshe mak'oshinsa, yagaji hakanan, buk'atarsa yanzu kawai k'arshen al'amarinnan yazo kowa ya huta, shima ya gina rayuwarsa data y'ay'ansa cikin salama.
Sun isa k'ofar gidan Alhaji Shehu Darma, amma baba Rabilu ya tsayane nesa da gidan, sai motar su Galadima Ce ta k'arasa har gate.
Mai gadi yasan Galadima, dukda bawani zuwa gidan yakeba sosai, dan haka babu wani bincik'e-bincike ya barsa ya shiga.
Gidane babba na alfarma, Wanda kallo d'aya zaka masa kasan lallai an kashe dukiya ta musamman.
Galadima yana zaune a mota bai fitoba, sarkin mota ya fita domin nema masa iso, mintuna dabasu wuce 3 ba saiga P.A d'in Alhaji Darma tare da Sarkin mota, shine ya bud'e ma Galadima mota ya fito yana mai masa barka da zuwa.
Yay masa iso har cikin gida falon Alhaji Darma na saukar bak'i masu muhimmanci. Zamansa babu jimawa aka cika masa gaba da kayan ciye-ciye, kai kace jiranshi suke, motsi Galadima bai yiba balle ya nuna alamar zaici, saima latsa wayarsa kawai yakeyi hankalinsa kwance, ga iskar AC na ratsa ga66ansa, kamar daga sama yaji ance “laaah Kaine a gidanmu yau?”.
Da farko sharewa yay yak'i koda motsawa, mikuma ya tuna saiya d'ago a nutse ya zuba k'yawawan idonsa a kanta, gabansa yad'an fad'i, wannan ai yarinyar da suka ta6a had'uwane a jirgi, sannan itace suka kuma had'uwa a airport har yayma Munaya Abu dantaji haushi, to mitakeyi ana........?
Tunaninsa ya kuma katsewa lokacin da ta tafa hannayenta guda biyu a saitin fuskarsa, firgigit ya dawo hayyacinsa, amma saiya basar kawai ya maida kansa ga wayarsa yana cigaba da danne-danne.
Tana niyyar yin magana saiga Alhaji Shehu ya shigo, Galadima yakuma saita camera d'in wayarsa danya ga yanayin da Alhaji Darma zai shiga idan ya gansu.
Ilai kuwa da mamaki ya kalli yarinyar, ya bud'e baki kamar zaiyi masifa saikuma ya had'iye yana fad'in “kekuma waya kawoki nan Rumaisa?”.
Dariya tayi cikin nuna ita ta6ararriyace zata fara zaro zance ya harareta, sannan ya nuna mata k'ofa da hannu, “wannan ai iskancine, ya za'ayi daga yin bak'o kiwanizo ki tsaya masa akai, kedai uwarki tagama lalataki, ta6ararki tayi yawa w.......”
Katseshi Galadima yay da fad'in Afuwa Alhaji, maybe itama uzurintane ya kawota”.
“Shikenan Sameer, amma abunne babu dad'i ai”.
“babu komai”. Galadima ya fad'a cikin lumshe ido.
Gaisuwa sukayi da tambayar juna Ahali, Alhaji Darma yace, “ina Haneefa? had'uwa tayi wahala, siyasa ta 6oyemu, tunda kunk'i bani dai”.
Murmushi kawai Galadima yay baice komaiba.
Alhaji Darma daduk yakasa nutsuwa da wannan zuwa na Galadima ya mik'e yana fad'in “kad'anci wani Abu Sameer, ina zuwa dan ALLAH”.
Galadima ya jinjina kai kawai, Alhaji Darma na fita ya murmusa, bodyguards biyu da suka shigo tare dashi d'aya ya fita, d'ayan harzai fice saiya dawo baya kad'an, wani Abu ya ajiyema Galadima ya fice shima da sauri.
d'auka Galadima yay ya saka a aljihu, sannan yamik'e alamun shirin tafiya, hakan ya nuna dama can abinda yazo nema kenan. A tsaye Alhaji Darma ya iskeshi, cikin mamaki yace, “Sameer yana ganka a tsayene?”.
Cikin murmushin dole Galadima yace babu komai Alhaji, zan wucene, dama hanyace ta biyo damu, shine nace bara na shigo mu gaisa an dad'e ba'a had'uba”.
“Aiko ka k'yauta, ALLAH dai ya saka da alkairi, ai kafi Haneefa da saitazo k'asar sau nawa bata tuna damuba”.
Nanma dai murmusawa Galadima yayi kawai.
Har harabar gidan Alhaji Darma ya rako Galadima, saida yaga ya shiga mota sannan hankalinsa ya kwanta, ya sauke ajiyar zuciya yana goge zufar fuskarsa data wuya.
Sarkin mota yay murmushi, “Ranka ya dad'e yanzu kam komai ya kammala, d'an shegiyarnan shima yazo hannu”.
Galadima baice komaiba sai ciza lips kawai da yayi. Guri suka kuma samu suka tsaya, duk motsin shiga da fitar gidan akan idon sune, suna nan zaune har Motocin Darma suka fito, suna fara tafiya baba Rabilu ya take musu baya, su Galadima kuma suka fara binsu nesa-nesa, can tafiya tad'an fara Nisan daba mai yawaba wani go slow Mara dalili ya tsayar dasu, Ameer daya zama mai bada hannu a yau a hanya data rabu biyu cikin hikima ya nuna motar da Alhaji Darma yake ciki yana sanarma driver d'in ya fito ya duba tayarsa.
driver dake shirin fad'ama Ameer bak'ar magana Alhaji Darma yamasa tsawa akan ya fita ya duba mana, jikinsa na rawa ya fita, shikuma Alhaji Darma ya maida kansa ga duba newspaper d'in hannunsa.
Da Sauri Baba Rabilu ya fito daga motar da yake ya maye gurbin driver Alhaji Darma, akuma time d'in Ameer yabasu hanya, shikuma wancan Driver yana can sagare da baki wai yana duba tayar mota, ganin motar tayi gaba sai yashiga k'ok'arin binta, Ameer ya dakatar dashi da fad'in anfa matsarne saboda ta tare hanya, bagasu a wannan hannunba inda zakaji dad'in dubawa”.
Tsaki driver yayi yanama Ameer kallon banza, ya matsa ga Motar dake a fake ya shiga yana k'ananun magana, “wlhy Alhaji yaronnan k'arya yakeyi, irin y'an iskan yarannan nema fa masu shan kwayarsu suyi mankas suzo sunama mutane dabanci a titi, yakamata ad'au mataki akan irinsu”.
Shiru dai yaji Alhaji bai amsaba. daga nan shima sai yayi shiru, duk zatonsa ko Alhaji baya buk'atar magana ne.
A can kuwa tuni baba Rabilu yayi ciki da Alhaji Darma, dan harya d'auki hanya Su Galadima na binsa a baya, Alhaji dai baisan wainar da ake toyawa ba, hankalinsa nakan jarida🤣😜.
Su kuma can sun d'anyi nisa da tafiya Driver dai yaga yanata surutu Alhaji ko tari bai yiba, saiya waigo yana kallon bayan, babu shiri ya taka birki da masifar k'arfi, jikake k'uuuuuu!!!! Gabbbb! Ya bigi motar gabansa, mota saita fara katantanwa a titi, nanfa mutane suka tsaya kallon abin al'ajabi, sauran motocin Alhaji Darma ma duk suka tsaya. Da k'yar dai wannan mota ta tsaya, jama'a suka zaro driver da k'yar, nan mutane na kaya-kaya akaisa asibiyi karya mutu tunda yana numfashi, sukuma bodyguards d'in Darma hange-hangen ina za'a ganoshi shima suke, saidai alama ta nuna motar mutum 1 nema a cikinta.
Tofa babbar magana, an dai d'auki driver da gaggawa zuwa asibiti, yayinda bodyguards suka shiga jaje sukuma. Kafin kacemi gari yafara d'auka ta silar social media, saikuma y'an sanda.
Jin mota ta tsaya Alhaji shehu ya d'aga kai danya tambayi ko lafiya? yasan dai ko quarter d'in inda suka nufa basuyiba, to miye na tsayawar?.
Baki bud'e yace, kai Antoni miye haka? gidan uwarwa ka kawoni nan kuma?”.
Baba Rabilu ya lek'o da kansa yana Murmushi, “Aboki aiba Antoni baneba”.
A matuk'ar firgice Alhaji Darma ya jefar da jaridar hannunsa, jikinsa na rawa da taune harshe yace Alhaji Rabeelu? Dama baka mutuba?”.
“Mutuwa ai sai kwana ya k'are abokina, ganidai yau kam harda tuk'aka”.
Cikin matuk'ar tsawa yace, “Karya kake munafuki, wlhy ka mutu saidai idan fatalwa kayimin, dafa hannunsa na kasheka shekaru 19 kenan?. Toko fatalwarka Ce yanzu itama zan kuma kasheta”. ‘yay maganar yana waige-waigen neman makami, amma babu.
Baba Rabilu ya bud'e motar ya fita yana dariya, bud'e ma Alhaji Darma k'ofar shima yana fad'in “maza fito ka kuma kashe fatalwata.....”
Aiko a harzuk'e ya fito, saida kuma wata rikitarce takuma kamashi ganin Galadima tsaye a jikin motar dake kusada wadda yake, ya hard'e hannuwansa a k'irji yayi wata tsayuwa mai sunam firgita mak'iyi. baya Alhaji Darma yay taga-taga zai fad'i ya dai samu ya dafe mota jikinsa na tsuma, cikin rawar murya yake nuna Galadima da hannu yana fad'in “S...S..Sameer! ba yanzu muke tare dakaiba a gidana?”.
Galadima yay wani murmushin gefen baki yana gyara tsayuwa, eyeglasses d'in idonsa ya cire sannan yasa handkerchief ya goge fuskarsa, glasses d'in da handkerchief ya maida cikin aljihu, cikin d'age gira yace, “Nine kuwa tabbas SD, dan yau kaiba mai wancan sunan dana Sani bane a gaba na........”.
Katseshi Alhaji Darma yayi, “kai Sameer! Kardai ka yarda da zancen wannan fatalwar?, wlhy fa Fatalwane, shekararsa 19 da mutuwa, karka yarda da munafuncinsa, kafa tuna nid'in wanene a wajenku, ta ya za'ayi na iya cutar daku? Ka yarda dani domin ALLAH”.
murmushi Galadima yakuma saki, ya taka a hankali zuwa gabansa, yatsansa d'aya ya saka yana shafar girarsa, yace “SD aishi mugu dama bashida kama, bakasan yanzu babu kasuwancin dayafi yad'uwa a duniyaba sama da cin amanar juna, kuma na jikinka ke maka. Waynot ka Adana kalamanka ko zasu maka amfani nan gaba k'ad'an”. Yay Salute nashi yana ra6ashi ya wuce zuwa cikin gidan.
“Sameer! Sameer!! ka saurareni mana”. Alhaji Darma keta fad'a kamar zai had'iye harshensa.
Ko sau d'aya Galadima bai juyoba yay ciki abinsa.
Wannan damar Alhaji Darma yay amfani da ita wajen harin baba Rabilu, amma sai su Ameer suka zagayeshi, cikin mamaki ya kalli Ameer d'in, danya ganesa sarai.
Ameer ya d'aga kafad'a yana ta6e baki alamar bashida matsala😂.................✍🏻
🤦🏻♀yau dai typing d'in rowa nayi muku, gaba d'aya banajin yin typing d'in, kuyi manage kawai⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀.
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻_*
*_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
~BOOK 3~ 👉🏻5⃣ & 6⃣
...............Galadima ya shigo murmushi d'auke a fuskarsa, dattijon dake zaune a falon ya d'ago ido yana kallonsa shima fuskarsa d'auke da murmushin, k'arawa Galadima yayi garesa, ya zauna kusa dashi yana fad'in “Baffina kanata jirana ko?”.
Kafad'arsa dattijon ya dafa, yace “karka damu d'an baffinsa, nasan aiki mai muhimmanci ne ya tsaidaka. ya k'ok'ari?”.
“Alhmdllh baffi, munata fama”.
“ALLAH ya dafa mana, yanzu ina shi Darma?”.
“Gashi a waje tareda ma'aikata, zamu jira zuwan Sir Isa ne, dan asan miya kamata, bazai yuwu mu had'ashi da su Harun ba”.
“Uhm hakan shine dai-dai kam, amma yakamata suma bayanansu kagama tattarasu waje d'aya ka kawomin, kasan abubuwa zasu cud'e mana a tsakaninnan, dan fatana insha ALLAH wannan shine case Na k'arshe dazan fuskanta a rayuwar aikina, shekara 1 kacal ya ragemin cika talatin a matsayin lauya, insha ALLAH kuma zan cikasune bisa alk'awarin gurfanar da dukkan mai hannu akan mai martaba”.
Murmushi Galadima yay, idonsa cike da kwalla, ya had'iye Abu mai d'aci yana fad'in “ALLAH ya cika maka wannan buri baffi, lallai ina alfahari dakai amatsayin uba, Kaine ka nunamin hanya alokacin da k'ofa ta rufe min, Kaine ka tsallakar dani a lokacin da gada ta karye ina tsaka da tafiya, ga kuma gagarumin hadad'i mai cike da tarnak'in iska ya taso, badan kaid'in ba da jajircewarka da yanzu ruwan daya zuba ya shafe da tarihina dana ahalina, da ace wani zai saurari labarina saiya d'auka labarin film ne ko novel, ni karan kaina nakanyi zaman yin tunanin anya akwai mai irin rayuwata a k'asarnan? Dan mafi yawa a tatsuniyoyi da hikayoyi akejinsa, saikuma abin mamaki ga nawa a zahiri, a yankin k'asar hausa, yanki mai tsananin ruk'on addini da Al'ada, yanki mai mutunta ahali da zuminci, inhar a shekaru 26 baya za'a iya samun masu irin ayyukan su tanderu lallai akwai abin tsoro kenan a k'arni nagaba da y'ay'anmu zasu mu'amulanta, Baffi da ace d'an Adam Na iya za6ama kansa rayuwa da banzo cikin ahalin jinin sarauta ba, amma Alhmdllh, ina godiya da Ubangiji daya halicceni yakuma San cancantar fitowa daga cikinsu.......”. kukane ya sark'e Galadima, Baffi ya mik'a masa handkerchief yana girgiza masa kai alamar kar yayi.
Murmushin takaici Galadima yayi, sannan ya kar6a handkerchief d'in ya tsane k'ananun hawayensa.
Baffi yace, “Muhammad Sameer akwai labarai da tarihin mutanen da yafi naka sark'ak'iya da hargitsi wlhy, sometimes abinda mukan gani a films ko hikayoyin marubuta akwaishi azahiri, saidai inhar bai faru akanka ba ko waninka saikaga tamkar k'anzon kuregene, kasan su mutane sunfi amfani da abinda suka gani da ido wato zahiri, ko suka San Wanda ya Sani wato tabbaci, a shekarun da nayi INA aiki nahad'u da cases da dama masu sark'ak'iya da ban tsoro, nakuma halarci kotuna da Dama domin ganin wasu cases d'in, idan ka samu wani case kai kanka saika ringa kokwanton anya kuwa wannan da gaske ya faru d'in? Amma daka tsananta bincikema saikaga abinda yafi Na farko mamaki, lallai a ranar gobe kiyama wasu zasu kasance cikin bayi masu tsananin kunyata agaban Ubangiji, Dan wata shari'a Ubangijine kawai mai iya mata, mu kammu acikin lauyoyi da alk'alai hummmm”. Baffi ya d'an bubbuga kafad'ar Galadima yana murmushi cikin takaici.
Bai samu damar k'arasa magana ba akayi sallama, izinin shigowa ya bada, wani matashin dattijo da shekarunsa bazasu gaza 45 ba ya shigo, baikai girman baffi ba, sannan ya girmi Galadima sosai.
Mik'ewa Galadima yayi yay salute nashi, dattijo ya murmusa yana kama hannun Galadima ya zaunar da fad'in “ni da kai adai bincika mai sarama wani”.
Baffi yay dariya, “kudai kuka Sani da gardamarku wacce kullum bata k'arewa inhar kun had'u”.
Bak'o mai amsa Sir Isa yace, “wai Yaya naga alhaji Rabilu zaune a waje suna sa'insa da banzan can?”.
Nanma dai baffi ne Yakuma darawa, yace, “duk cikin aikine, dukkan wata magana dazai takalesa ya fad'a ai itama hujjace, kasanfa halin Alhaji Rabilu ai, shiyyasa nace masa da irin aikinku ya dace ba siyasa ba”.
Sir Isa da yay dariya shima, yayinda Galadima ke murmushi, “Ai yalla6ai yanzu ma aikin dayake mana bashi da banbanci damu d'in, danya bamu damar sanin abinda tsawon shekaru muketa wahala da kaikawon sani”.
“Wannan gaskiyane kam Isa, yanzu Yaya za'ayi da Darma kenan?”.
Sir Isa ya gyara zamansa, yana saka d'an yatsa a baki alamar tunani, zuwa can yace, “inaga kam saidai mu nema wajen ajiyesa ko yalla6ai ya Adana mana shi, dan yakamata saimun kammala tattara komai a hannunmu bayan yalla6ai Galadiman mu ya dunk'ule kifaye a ragaya, idan sun mik'a wuya shima sai a sakashi a ayari ko?”.
Baffi yace, “shawararka tayi kam, inaga yanzu abinda kasaba za'ayi, dan aiki da ilimi yafi aiki da agogo, kaike 6oyewa, kuma kaine akesa kanemo 6oyayye”.
Murmushi Galadima ya sakeyi baice komaiba sai jinjina kai. Duk d'insu basu damuba, dan sunsan halinsa Na rashin son hayaniya tuni, ayanzuma suna d'an ganin canji fiye da shekarun baya, shiyyasa suka fara zargin ko (Hikimar matace take aiki?) Dan kad'an daga aikin mace ta tada gari, kuma kad'an daga aikin ta ta gyarashi.
Sund'an tattauna har baba Rabilu shima ya shigo, wayar dayay recoding d'in dukkan musayar yawunsa da SD yabasu, babu Wanda baimasa jinjina ba, Galadima ya d'ora da musu godiyar hidimar da sukeyi a kansa tsawon lokaci.
Suka amsa da cewar lallai mahaifinsa ya cancanci sumasa fiyema da hakan, dan yataka rawar gani shima a tasu rayuwar.
Lokacin da suka fito abinda yabani mamaki shine su Ameer duk salute nasu sukayi suna k'amewa.
Galadima basarwa yay, sai Sir Isa ne yay musu inkiyar su sauke hannayensu, baffi yay murmushi yana kallon Galadima dayak'i kallon kowa ta gefen ido.
Sarkin mota dai yasha jinin jikinsa, musamman Basarwar da yaga Galadima yayi.
SD dake zaune ya zuba tagumi yana kallonsu kawai ya janye hannunsa, cikin jinjina kai yace, “lallai duniya tana cike da abin tsoro, wai Isa kana nufin kaima wani abune a k'asarnan? Kai kuma babban munafuki Brr Usman Audu Tsanyawa! Ba kaine da kanka kaje kasamemu da albishir d'in ajiye aikiba? Ashe wannan k'aramin kwaron d'an cikinku kukema aiki?........”
A tsawace Ameer ya katseshi, tareda d'aga hannu zai makeshi amma sai Galadima ya d'aga masa hannu.
Sir Isa ne yay wata y'ar dariya yana matsawa ga Darma, yace, “Idan banda abunga Alhaji shehu kowama irin kune mai tsukakken tunani? Ai abin kallo bai k'are makaba saima nan gaba kad'an, kasan ita mota hanyarta kwaltace, birji ma idan tasamu bitake, balle dagwalon ruwa mai kayan datti, shikam jirgi miye gamisa da wannan? ko d'aga a tashi hanyar babu duk wad'annan, kaga kenan aikwai matuk'ar tazarar banbanci a tsakaninsu, kallon idoma tattancewa yake basai an shiga gasar tabbatarwa ba, kaikuma ai taka ta k'are, sauran shekaru sai a prison d'in dajin SAMBISA zaka idasu”.
Dariya SD yayi, ya mik'e tsaye yana fad'in “iyaka dai Ku kaini police station, ina mai muku alwashin kwana d'aya bazanyiba a can, daga can a mik'amu Court, alk'alinma namune masu k'ananun basira, yanzu haka nasan sak'ona ya Isa ga y'an uwana, kafinma Ku kaini station d'in reshe ya juye da mujiya, dan dolene a kamaku da alhakin kamani kunga martabar wasu saita zube, mulkin da akema mutane homa da buri babushi kenan”.
Murmushi Galadima yayi, dan yasan dashi yake, yad'an ta6e bakinsa yana cigaba da latsa waya hankalinsa kwance, Sir Isa da baffi da baba Rabilu, su Ameer duk kallon Galadima sukayi, don suji amsar dazai bada, amma saiya basar tamkarma baijiba.
Saida ya kammala abinda yakeyi yay kiran Nuren suka kammala magana sannan ya kalli SD yana murmushi, “Wannan lissafin naka fa ya birgeni Alhaji shehu, saidai albishir d'in dazan maka nima shine, duk wani kira dazakayi ko ayi maka to zai shigo wayatane, yanzu haka driver d'inka yayi had'ari, rashin ganinka a motar kuma zantuka sun baje kowacce kafar yad'a labarai, Na tabbata dukkan labaran rana kaine shafin farko, hakama jaridun gobe masu fita, labarin nemanka da ta Yaya ka 6ata? Shine babban labari, sukuma abokan naka hakan zai tada hankalinsu, saisu fara zargin ko dai d'an tsohon Sarkine Galadima Sameer da wannan aiki?, dole kuma sufara bincike, bayan sun haukata y'an sanda wajen nemanka, daga haka kaga nikuma saina cigaba da samun hujjoji........🤦🏻 kai zaka samin ciwon kai wlhy”. Galadima ya karashe maganar da bud'e mota ya shige abinsa.
Su Ameer duk suka shiga k'yark'yala dariya, saboda yanda Darma ya mugun shiga rud'ani da sakin baki yana bin Galadima da kallo harya shige mota.
basu tsagaitaba saida Sir Isa ya tsaidasu ta hanyar d'aga musu hannu, yace, “Alahaji Shehu yadai? Kaji irin aikin masu basira ko? Kai! Kai! Harna tausaya muku lallai. Ameer! Kubi yalla6ai Galadima dashi, shikeda masaukinsa”.
Angama ranka ya dad'e. Suka fad'a suna salute nashi.
🤦🏻♀lallai nimafa yau nashiga ciwonkan Galadima, shin wane laujene cikin nad'i kuma dabamu saniba haka? Nadai fahimci Su Ameer ba y'an iskan matasa bane, kamarma jami'an tsarone?🙆🏽. To Aunty Salama fa? Data kawosu a cakwakiyar. Masu karatu, kumuje zuwa dai, nasan komai yana gab da bayyana lallai kam.☹⛹🏻♀⛹🏻♀.
__________________________
Galadima dai kam plaza suka koma, yayinda Nuren ya tari su Ameer a hanya suka bashi SD.
Acikin Plaza Galadima yad'anyi zagaye-zagaye, saida ya tabbatar da komai dai-dai a wajen ma'aikatan sannan ya fito suka d'auki hanyar masarauta.
*****************
Bayan fitar Galadima Aunty Mimi sashen su Munaya ta nufa, ta isketa har yanzu tana juya kalaman Galadima dabata fahimtaba.
Bayan sun gaisa tabata Umarnin ta shirya dan za'a kaita sashen manyan gidan ta gaishesu da bangajiya sannan suga yara, inhar zaki tafi wanka bayan kwana d'aya da suna haka akeyi a masarautar, to amma su nasu Munaya yazo da Matsala, tunda gashi sai bayan kwanaki hud'u da suna zasu tafi, matan Sarkine kawai basa zuwa gida wanka.
Kuyangi biyu sukaima Munaya shiri, itadai wannan lamari Na d'aure kanta, haka kawai da girmanka ace komai sai anmaka, dolene mai mulki yake kallon talaka ba komaiba, sauk'inta ma bakomaine Galadima ke bada fuskar ayi mataba, yama hana hadiman masarautar sakewa a sashensa gaba d'aya, sai iya wad'anda ya aminta dasu kawai.
Yaukam tasha kallon kanta a mirror, hakan yakuma tabbatar mata da tuna mata agidanfa SARAUTA take, a kuma matsayin matar mutum mai girman rawani da matsayi a Masarautan.
(Kusan dai mutuniyar taku da jan aji😉, ai saita kuma tsumewa tana basarwa🤣).
Suma yaran an musu shirin dake nuna lallai Ubansu waninine a wannan masarauta, sannan suma ababen tattaline ga wannan kujera kwara 1 tal dakowa ke mutuwa da rayuwa a kanta a masarautar gagara badau☹.
Sun sami rakkiyar kuyangi da Aunty Mimi, kowane sashe saida suka zagayashi amma a mota, an farane da fada.
Yau itace ranar farko da Munaya ta shiga Fadar sarkin ta, yaukam taga abin mamaki, musalta yanda wannan fada ta k'awatu ai 6ata lokacine kawai, ammafa lallai komai yaji, ga Sarki hakimce bisa garagarsa cikin kwarjini irinna mutuntakar mulki, sarkinmu kenan kuma sirikinna ta wani fannini, daga ni sai aunty Mimi da kuyangi ukune muka shiga, kowanne d'auke da yaro d'aya a hannu.
Fada cike take mak'il anata fadanci, Su Wanbai da talba duk ana ciki, hakimai da masu manyan muk'amai Na masarauta da wajen masarauta duk an hallara, kasancewar shine zaman farko Na wannan makon, kuma ana saka ran zuwan Governor ne da zaizoma mai martaba jajen abinda ya faru Na 6atan y'an uku, dan labarine daya zagaye kowacce kafa ta yad'a labarai da socia media Na k'asar nan, (kunsan dai abin manya duk k'ank'antarsa saiya fita, balle wannan da yazamo mai girma).
Bayan Munaya da aunty Mimi sun zauna a k'asan lallausar darduma can gefe suka kwashi gaisuwa, dogarai suka amsa da yawun Sarki, sannan suka kuma gaisheda fadawa.
Daga nanan aka amshi su Abdurrahman, y'an majalissar Sarki sukaita d'auka d'ai-d'ai suna saka musu albarka, da addu'ar fatan alkairi.
Bayan fitowarsu sai sashin iyalan mai martaba, yau ma dai gimbiya zulfa bata fasa nunama Munaya da yaranta soyayyaba, daga Munaya har aunty Mimi basu San komaiba, dan haka sukaji dad'i da sakin jikinsu fiye da sauran matan sarki.
Daga nanan sai sashen Mama Fulani, (kaga manya, Sarautar gagara badau a hannunku take, mama fulaninmu ta mutunci🤸🏻♀😂, ga irin naku manyan mata👍🏻)
To kunsan dai mutuniyar taku, yauma dai cikin izzar mulkinta suka isketa, ita dama Aunty Mimi babu ruwanta, tana mata yanda takeso, shiyyasa babu y'ar habaici ko bak'ar magana tsakaninsu kamar Galadima, hakanne yasaka munaya samun tsira daga samun nata rabon, amma mama Fulani bata d'auki yaro ko d'aya ba, a hannun kuyangin ta gansu tana ta6e baki.
Daga Munaya dai har aunty Mimi babu Wanda yay ko tari, to balle kuyangi dasuka zama takalmin takawarta, basu jimaba suka fito, haka sukaita zuwa sashe-sashe, basu sami Kansu ba saida suka Shiga ko ina .
Sun dawo kusanda awanni biyu aka gama loda kayansu a mota Samha da Sauban suka shige gaba aka kai gidansu Munaya. Ita kuma sai zuwa yamma za'a mata rakiya.
************
Gidansu Munaya dai tunda kaya suka isa aka tsaya kallon-kallo, daga Sauban kam har Samha babu Wanda yamusu kallon arzik'i, yo sunaji da hayak'in girma dana mulki, innarsu Munaya da Munubiya da tuni tana gida kawai suka kula, harda sakin jiki dasu sukaita hira, sunmayi zamansu anan sai ankawo Munaya zasu koma.
Nanfa matan gidan suka fara k'ananun magana, saidai babu mai yunk'urin d'aga murya saboda tsaro🤣.
Oho innarsu Munu ma batasan sunayiba, balle Munubiya da yanzu saita ma gadama suke ganinta, ko yaushe tana d'akinsu, da anyi magana tace jego, dukda gasu Fiddausi a gidan duk suna wankan suma, Fauziyyace kan shigo susha hirarsu ta zuminci, amma sauran saidai idan an had'u a gaisa, kowa uwarsa Na kitsa masa munafurci a d'aki (🤦🏻♀gaskiya iyaye mata munada gyara babba ta wannan fannin, inhar zaka rayu gidan yawa sai kayi gamo da irin wad'annan matsalolin kuwa, ALLAH ya ganar damu baki d'aya dai).
******************
Su gadima Na shigowa masarauta ana kiran salla, hakanne ya sakasu yada zango a massalaci, saida aka idar sannan suka k'arasa sashensa, Duk agajiye yake, d'akinsa daret ya nufa, yashiga zame kayansa tun a falonsa, yana shiga ciki k'arasawa kawai yayi yashige bayi.
Ya dad'e aciki kafin ya fito, baiko cire rigar wankanba yasha wani Magani ya kwanta, dan kansa ciwo yake masa. Cikin mintuna k'alilan barci yay gaba dashi.
Munaya batasan ya dawoba, d'okin zuwa gida ya hanata barcin ranarma ita, sai yawan duba lokaci takeyi😂👍🏻.
*_3:35pm_* Galadima ya tashi, saboda kiran wayarsa da akayi, idonsa a lumahe ya d'aga, a haka suka gaisa da Momma, ya tambayi Abie tace barci yakeyi, sunyi wayar kusan mintuna 15 haryaso makara fita sallar la'asar.
Bayan yadawoma papi ya kira suka tattauna, sannan yakuma sabon shiri cikin Orange d'in yadi anmasa kwalliyar bak'i kad'an, yayi k'yau sosai, sai tashin k'amshi yakeyi, saidai fusakar kam babu alamun yasan miye dariya.
A haka ya iso sashen Munaya, babu kowa daga ita sai yaranta da Khaleel dake barci a gefensu, itako wayama take latsawa, da alama game takeyi Kodai wani Abu.
Sallamarsa ciki-ciki da k'amshin turarensa ya sakata d'ago ido suka kalli juna, yawani Basar yana shan k'amshi, hakanne yasaka Munaya sake kama kanta, ta gaisheshi, sau d'aya ya amsa ya zauna a bakin gadon yana shafa kan yaran d'ai-d'ai harda Khaleel.
Handbag d'inta da mayafi dake ajiye alamar lokaci take jira kawai ya kalla, baki ya ta6e ya d'auke kai.
Key d'in mota guda biyu ya fiddo a aljihu ya jefa min akan cinya.
Ni harma Na tsorata na kalli keys d'in sannan Na d'ago na kallesa.
d'auke Kansa yay daga inda nake, cike da k'asaitarnan tasa yace, bak'in kibama Abba, d'ayan kuma ki ajiye a wajenki, motar tana can, saboda ko wani abu yataso musamman kai yara asibiti sai wani ya kaiki cikin yayyenki, ki kulamin da yara, kuskure d'aya kikayi a kansu zand'au mataki mai tsaurine, duk abinda zuciyarki batayi na'am dashiba ki gaggauta kirana na sani, ki kula da Abdurraheem sosai, banda barinsa yana dogon kuka saboda doctor ya sanar mana yana d'auke da ciwon......”.
Saikuma yay shiru yana furzar da iskar bakinsa.
Masifar tsura masa ido nayi zuciyata Na bugu tamkar zata fad'o dan tsoro, sai tsuma nakeyi, babu shiri na taso na dawo inda yake, durk'ushewa nayi gabansa tamkar mai neman gafara, “Yalla6ai ciwon mi? Please ka k'arasa fad'an dan ALLAH”.
lumshe idanunsa yayi yana cizar lips, “Ba abin tada hankali baneba ai, domin ALLAH daya d'ora mana yafimu sanin hikimar hakan, bagashi ni nakai lokacin da Magauta basuyi tunaniba”.
Maganganunsa ya nuna minta cewar Abduraheem Na d'auke da Ciwon zuciya? kenan shima yayo gadon mahaifinsa?”.
Matsowa nayi na fad'a jikinsa na sanya kuka, bashida za6i saina kar6ata shima ya rungumeni cikin yima Ubangiji tasbihin Neman dauriya da kar6ar jarabawa a duk yanda tazo. Bai hanani kukanba saida nayi mai isarta sannan na share hawayenna. d'agowa nayi daga jikinsa zan tashi amma saiya hanani hakan, cikin kunnenna yace, “Baki da kunya gaskiya, ban ta6a ganin uwa mara kawaici akan y'ay'an fariba saike”.
Kunyace ta kamani, na 6oye kaina a jikinsa ina murmushi.
Galadima ma murmushin yake yana shafa bayanta.
Sun dad'e a haka sannan na tashi daga jikin nasa gudun kar khalel ya farka ya ganmu a haka, shima ya fahimceni, dan haka bai hanani ba.
Yace, “Addu'arki yake buk'ata da taka tsantsan, dukda ba wayonmune zai hana Ubangiji ikonsa ba idan yaso, sai yakai watanni 6 zai fara ganin doctor insha ALLAH, ya mik'a mamin ATM d'insa, ga wannan dukdai abinda yataso saiki cira, amma a bimin kud'i a sannu ni talakane mai yawan buk'atu, ga Abdurraheem ya k'aru shima, to idan bawa bai nema kud'iba ai yagama shiga uku a wannan zamanin daba kowa ya damu da damuwarka ba, inadai kuma gargad'inki ki kula min da yara, yau zamu koma India, amma kwanaki uku zanyi insha ALLAH na dawo”.
Nace, “ALLAH yabashi lafiya da dukkan al'ummar ANNABI, nagode sosai, saidai kuma inason kawai idan na tafi shi.......”
Hannu ya d'aga min, “karki damu nasan maganar Aurenmu ne, kamar yanda na alk'awarin inhar komai ya fito kan shekara zamu rabu, inkuma ba a samu yanda akesoba shekara biyu inakan Sani, sauran bayani kibani lokaci zuwa kammala abinda ke gabana OK?”. ‘yay maganar yana kallonna’.
Kaina kawai na d'aga masa ina had'iye abinda ya tokare mak'oshinna.
Bai sake cewa komaiba ya mik'e yana kallon agogon hannunsa bak'i, “ku fito”. yafad'a yana ficewarsa.
Da kallo kawai nabisa idonna yana cika da k'wallan dabasan na minene ba.
**************
Munaya tasamu rakkiyar wasu daga masarautar, bisaga jagorancin Galadima da suke zaune a mota d'aya, daga ita har shi babu Wanda ya tankama wani koya kalli wani, shi tundama suka fito latse-latsen System yakeyi hankalinsa kwance, itama ta basar gefe tana kallon waje dukda glass d'in mai duhune.
Sun Isa k'ofar gidan k'arfe 5:24pm, bayan su Aunty Mimi sun fita duk suka shige cikin gidan tareda Kuyangi.
Munaya tayi yunk'urin fita amma sai taji motar a kulle, Sarkin Mota ta kalla sai taga harya fice, ta dawo da kallonta ga Galadima daketa aikinsa tamkar ya manta a mota yake.
Shareshi nayi kamar nima bazanyi magana ba kamar yanda ya basar, amma saina kasa, na kuma kallonsa murya a sanyaye nace, “ka bud'emin mana, miye ma'anar zaman namu? Wanima saiya zargi wani Abu ai?”.
Banza yay mani tamkar bazai tankaba, kusan mintuna biyu sannan yace, “idan sun zarga laifine? Naga Sadaki na biya”.
“Hummm”. Munaya ta fad'a kawai tana d'auke kai.
Saida ya gama shan k'amshinsa sannan ya ajiye lap-top d'in gaban motar yana matsoni. da mamaki na kallesa, “yalla6ai lafiya?”.
“ita ta kawo haka”. ‘yafad'a yana wani ciccijewa da jawoni jikinsa’.
Tamkar zan tsala kuka haka naji, dan naji zafi, mukaima juna kallon ido cikin ido, idona da kwalla tafara taruwa sai wani marmar yakeyi, matso da fuskarta yay sosai, cikin magana rad'a yace, “kin fara kewata ne?”.
Baya naja da kaina ina tura baki da yamutse fuska, amma sai hannunsa daya sa ya tokareni ya dakatar dani daga matsawar, yakuma matsowa gaf, numfashin junanslmu na sauka a fusakar juna, a hankali yafara hura min iskar bakinsa saman ido, babu shiri na lumshesu, hawayen da suka taru suka zubo, sai kawai ya shiga sumbata ta.
Tuni nabashi had'inkai babu wani gardama, saida yay yanda yakeso da ni sannan kowa yakoma gefe, wata y'ar k'aramar souvenir bag ya d'ora mani a cinya, sannan ya cire luck d'in motar, saida naja wasu Seconds nasamu dai-daita sannan ta bud'e na fice rik'eda bag d'in daya bani, ban yarda nasake koda kallonsa ba.
Shima harta fice bai kuma kallon nata ba.
Jiki a sanyaye nashiga gidan, matan gidanmu duk suna falon innarmu gaida bak'i, ina shiga muka rungume juna nida Munubiya muna hawayen da ita Munubiya tana tayani ne, nikuma bansan dalilin yinsuba🤣.
Kowa dai da kallon mamaki ya bimu kawai.
Su Aunty Mimi basu dad'eba sosai suka tafi, anbar laraba anan zata zauna damu.
Samha da khaleel harda kukansu.
**************
Bayan komawar su Galadima masarautane yakejin wai ba'aga Harun ba, k'ala bai tofa ba balle nuna alamun damuwa ko jimama.
Saima shirinsa Na tafiya ya fara hankali kwance, yaje yayma mai martaba sallama. Suka wuce airport abinsu, dan jirgin 7:30pm zasubi.............✍🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻_*
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*
*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BOOK 3_* 👉🏻7⃣➖8⃣
..................Momma tayi farin cikin dawowar yaranta da jikoki, hakama Abie, wanda su Galadima sukai matuk'ar rikicewa da murnar ganin cigaban jikinsa, babu wanda baiyi hawayen farin cikiba, nanfa su Samha suka shiga nunama Momma da Abie hotunan yara da Munaya, Abie dake murmushi ya kalli Galadima da shima yake zaune ya hard'e hannaye a k'irji yana kallonsu da Murmushin, da ido Abie yamasa magana ya matso gareshi.
Galadima ya tashi daga inda yake ya matsa kusada gadon, Aunty Mimi tabashi kujera ya zauna, hannunsa ya saka cikin na Abie yana d'an matsa masa, ada komi zakayi awani sashe Na jikinsa bayajin komai, koda zakaita dukansane bazaijiba, amma wannan hannun da aka samu canji da k'afarsa d'aya yanzu ko Yaya aka ta6asu saiyaji, yanda Galadima yake matsa masa hannun a hankali sai yakeji tamkar tausa, yad'an lumshe idonsa cikin jin dad'i yace, “ALLAH yay muku albarka gaba d'aya Muh'd Sameer, Na taya kaina farin cikin samun jikoki a tsatsona biyu, nakuma tayaka murna da samun y'ay'a a karo Na farko, bazan 6oye makaba ina k'aunar matarka, ina jinta a jikina tamkar kud'innan, tun randa Na fara ganinta ALLAH ya samin k'aunarta amatsayin d'iya, ina fatan ALLAH ya cigaba da saka albarka a cikin aurenku, ALLAH ya d'orar dashi har mutuwa”.
Babu abinda zuciyar Galadima take sai lugude, auren dake gab da tsinkewa akema wannan doguwar addu'ar? Shikam yaga ta Kans.......
Girgiza hannunsa Abie yay ganin ya fad'a duniyar tunani, ya sauke ajiyar zuciya yana murmushin yak'e da fad'in Amin akan la66a.
Sun jima a haka Abie nata masa hira, kunsan dai halin mutumin naku, saidai yayta zuba murmushi, inda ya dace ya bada amsa kuma ya bayar, sun dad'e a asibitin kafin su koma gida, amma su aunty Mimi sun riga Galadima tafiya, danshi saida yaje Asibitin su namasu ciyon zuciya yaga likitansa, saboda a tsakaninnan dauriya kawai yakeyi, amma bayajin dad'in jikinsa. Duk wani abinda ya kamata Doctor Subash yamasa, Yakuma k'ara masa da Shawarwari.
Lokacin daya iso gida har Samha ta gyara masa samansa da taimakon Sauban, ko ina yayi fes, dama suna sauka asibiti suka wuce, saboda d'okin son ganin jikin Abie.
Ya fara zame kayansa idonsa bisa Sofa, ya lumshe ido yana cizar lips d'insa, bai kuma kallon sofar ba ya shige bayi, acanma dai bata sauya zaniba, dukkan abinda Munaya ta ajiye Na amfaninta irin Na mata idonsa Na wajen, haka dai yay wankan ya fito yana goge fuskarsa, sallar zuhur yafara gabatarwa sannan yadawo bakin gado ya zauna, wayarsa ya had'a, ya maida dukkan layikansa Na k'asar aciki.
Knocking k'ofa da akayine ya sakashi kallon k'ofar, batare daya tankaba ya d'auke kai, aka kuma knocking, gutun tsaki yayi kafin yabada izinin shigowa.
Samha ce d'auke da babban tire, kallo d'aya tamasa ta d'auke kai saboda ganin yanda ya d'aure. itadai ta ajiye ta lalla6a ta fice abinta. Yaja wasu adadin mintuna kafin ya mik'e zuwa wajen abincin, bubbud'ewa kawai yayi, yad'an ta6e baki yana rufewa, sai yama fice daga d'akin gaba d'aya zuwa d'akinsa na sirri.
Komai yana nan yanda yabar kayansa, sai y'ar k'urar daba'a rasaba, amma dukda haka saiyaji yana k'yank'yamin d'akin, fita yay ya sauka k'asa, babu kowa a falon, da alama kowannensu gajiya ta kadashi, tsayawa yay yana tunanin wama zai tado? idonsa ya tsaya d'akin Sauban, can ya nufa, Sauban na kwance a gado yana danna lap-top Galadima ya Shiga da sallama ciki-ciki, tashi yay zaune da sauri, “Yaya Sam lafiya dai?”.
“Shi wancan d'akin laifin mi yamuku dabaku gyarashi ba?”.
Sauban ya marairaice kalar tausayi “ALLAH yaa Sam bayana ciwo, duk mun gajine”.
Hararsa yayi, yana masa nuni da k'ofa, ya juya yay ficewarsa.
Sauban yad'an tura baki yana sakkowa a gadon kamar zaiyi kuka, cik'in k'unk'uni yace, “shi Yaa Sam d'inna yanda yake aiki kamar wani ingi baya gajiya ya d'auka kowama haka yake”.
Sanda ya fito har Galadima ya koma sama, shima hawan yay yanata kunkuninsa, a falo ya iskeshi zaune ya zubama wata kujera ido, baiyi maganaba ya shige d'akin, saida ya Shiga sannan ya Sanya dariya, dan ya kula kujerar da Munaya ke yawan zamace Galadima yakema kallon har hanji😂.
Tsaf ya gyara ko'ina sannan ya fito, yanzu kam a kwance ya iskesa ido a lumshe, yace, “yaya Everything is done”.
Hannu kawai ya d'aga masa, Sauban ya wuce abinsa, saida ya sauka ya juya ya kalli benen yana fad'i “Chiii yaa Sam He is too stubborn wlhy”.
Aunty Mimi dake bayansa bai saniba tai dariya, “kadage ya jika dai, kasan ko kurar wasa saita fika gata agidannan”.
Juyowa Sauban yay ya kalli aunty Mimi yana dariya shima, “Aunty babba ai lamarin boss ne sai addu'a” ya matso kusa da ita yana rage murya alamar gulma, “kinsan mineme kuwa?”.
Kanta ta girgiza masa.
Yacigaba da fad'in “Wlhy Ku taimakemu Ku amso masa matarsa da wuri, dan yafara rikid'ewa zai koma asalin Muhammad Sameer d'insa saboda kewarta”.
Idanu Aunty Mimi ta zaro waje, cikin sakin baki da tafa hannaye tace, “Sauban! Yaushe ka fara sanya masa ido?”.
Dariya Sauban ya tuntsure da ita ya shafa kansa yana fad'in “Aunty jeki sama kisha kallo mana”. ya shige d'akinsa yana cigaba da dariyarsa.
Itama dariyar tayi, a fili tace, “Munaya kin biyamu wlhy, ALLAH ya bamu ikon miki halacci kema fiye da wanda kikai mana”.
Nane, “amin waunti mimi😄”.
)*()*()*()*()*()*()*()*()*()*()*(
To yau dai ga Munaya ga Munubiya a gida, gaban innarsu, ga y'an k'annensu, abin sha'awar harda k'arin y'ay'ansu, ita kanta Innarsu kallo d'aya zai tabbatar maka da farin cikin datake a ciki, badan aureba mixai rabata da y'an y'ay'anta masu tausayinta.
Ranar dai haka muka kusan kwana hira da labaran yaushe gamo, kota yaranma bamayi sai laraba ce da innarmu kemana magana akan mu shayar dasu.
Washe garima mun tashi cikin farin cikin kasancewa da juna, aka dama mana kunun kanwa mai rai da lafiya, yanata k'amshin kayan yaji, ga k'osai mai dad'i a gefe, munacin kayanmu muna hira, Fauziyya ta shigo itama tsaf da ita, jegon ya kar6eta sosai, rungume juna mukayi ni da ita cikin kewa, itama ta zauna muka cigaba da karin kumallon tare, anan take bamu labarin wahalar datasha wajen haihuwa, yanzu hakama ita ba'a mata wankan jegon, saboda jininta yak'i sauka, sosai Muka tausaya mata, da fatan samun lafiya a gareta, nace muma ai munsha wahalar, nabasu labarin nak'udar kwana uku danasha kafin mu taho Nigeria, Munubiya harda hawayenta, dukda itama tasha tata azabar.
Inna dai da Laraba najinsu daga tsohon d'akin su Munayar suna musu dariya, sunsha hirarsu har d'agawar hantsi, saida aka aiko kiran Fauziyya yaronta Na kuka sannan tamik'e ta tafi.
A sannan ne Innaro ta shigo gidan, dama kullum takanzo taga masu jegon, d'akin kowa ta shiga taga sauran, Dan ita Safara'u ma takusa komawa, tunda itace ta fara haihuwa itada Haleematu.
Ni da Munubiya muka gaida Innaro, amsa muna tayi babu yabo babu fallasa, hakkane ya sakani shareta nacigaba da latsa wayar Munubiya da ke hannuna.
Innarmu ta fito daga d'aki d'auke da Abdurraheem daya farka yana kuka.
Innaro ta wani bud'e baki da rik'e ha6a tana kalon innarmu, cikin tafa hannaye tace, “O ni Marwanatu, yanzu nan Ai'sha jikan farinne kike mamuk'a haka tamkar wani autanki?”.
Kallon juna Mukayi ni da Munubiya, sannan muka kalli innaro, ganin Innarmu ta tsaya sororo alamar tad'anji kunya sai Munubiya ta mik'e, inda take taje ta amsa Abdurraheem d'in.
“la'ilahailllahu..”. Innaro tafad'a cikin mik'ewa a zabure alamar mamaki, tace, “A lallai duniya tazo k'arshe, ke kinmafi uwar taku ashe? Dagani babu tambaya nasan Munaya ce wannan, fetsararriya anzo a d'ora daga inda aka tsaya kenan?”.
Murmushi nayi, Na kar6i Abdurraheem da Munubiya ta d'oramin a cinya, saida Na fara shayar dashi sannan Na kalli innaro, nace, “Innaro inhar kin shirya d'orawa daga inda kika tsaya muje zuwa mana, indai bazaki canjaba Munaya ma har abada zabata canjaba, miye laifin Innarmu danta d'akkoshi yana kuka?, rawa kika tarar tana masa ko wata tsiya? Yo nagama kema haka kikaita ma mutane kuka saikinje jiyyar abbanmu India, halan kema kunyar d'an farince.......”.
Bankai k'arshen zancenba innaro ta d'ora hannu bisa ka ta aza mana kuka. Ni da Munubiya muka kuwa kwashe da dariya abinmu, a haka abbanmu ya shigo ya samemu, Innarmu tanata bama innaro hak'uri tak'i saurarenta.
Girgiza kai kawai Abba yayi, Dan akan idonsa komi ya faru, hannu ya d'agama Innarmu alamar ta barta, zata fara magana ya girgiza mata kai. Shiru tayi takoma gefe, innaro saita k'ara k'arfin kukanta wanda harya fara jawo hankalin matan gidanmu, saidai babu damar zuwa kallon kwaf tunda a d'akine.
Hannun innaro Abba ya kama ya zaunar da ita, cikin kwantar da harshe yace, “haba dai inna, yanzu dan ALLAH abinda akayi yarannan Na k'anana yanzuma shi za'a sake azaman dazasuyi Na wata 1 kacal dawasu kwanaki? Haba inna, minene Dan yaro yayi kuka Ai'sha ta d'akkoshi? Inna ina dad'i irin wad'annan abubuwan haka?”.
Share hawaye innaro tayi, tace, “to naji Auwalu, indai nice bazan sake magana akan y'ay'anka da matarka ba....”.
“da yafi”. Nafad'a ina murgud'a baki.
Hararata Abba da Innarmu sukayi, Abba ya rik'e hannun innaro da sauri saboda k'ok'arin tashi da takeyi, “kiyi hak'uri Dan ALLAH inna, niba haka nake nufiba, da ni da abinda Na mallaka ai duk mallakinkine, nafad'a ne dan kawai a zauna lafiya yarannan sugama wanka kowa takoma gidan mijinta cikin salama, tunda kinga dai da yaran d'akinnan ne kawai irin wannan sa6anin ke shiga, yanzufa kika fito d'akin can kina tsokanar yarinyar Haleematu, mizaisa anan kuma hakan bazata kasanceba?”.
“shikenan naji”. Abinda innaro tace kenan kawai ta mik'e ta fice.
Abba ya bita da kallon kawai cike da takaici.
Gaidashi mukayi, ya amsa yana had'iye 6acin ransa, ya tambayemu ya yara?, duk shiru mukayi muka kasa amsashi saboda kunya.
Murmushi yayi, ya kar6i Abdurraheem daya gama shan nono, bayan Innarmu yabi d'akinta d'auke da yaron, dan tunda yamata magana tabar falon ta shige d'akinta.
Zaune ya isketa a bakin gado tayi tagumi tana hawaye.
Ya zauna kusada ita rungume da Abdurraheem, shiru yay yana kallonta, kusan mintuna biyu ya kwantar da yaron a bayansu yamatsa jikinta sosai yana kwantota jikinsa, “kiyi hak'uri Ai'sha, a halin inna babu wanda baki saniba yanzu, tunkan kizama mata a gareni kinsan wannan, to mizaisa hakan yasakaki kuka a yanzu? wani abin nata harda tsufa yanzu, amma kiyi hak'uri dan ALLAH”.
“Ni ba kuka nakeyi saboda abinda inna takeminba, ina kukane saboda rashin jituwar da kullum take k'ara tasiri tsakaninta da yarannan, duk yanda naso hana girmamar irin wad'annan abubuwa n abun ya gagara, bai kamata ace laifina yana shafar jikokinta ba, jinintane fa su, idan ni tace banda asali sukuma ai itace asalinsu ko? wlhy Abbansu banason wad'annan abubuwan, wani lokacin zuciyata takan gaza d'auka”.
“kiyi hak'uri, insha ALLAH komai mai wucewane, yakamata kuma zuwa yanzu kufad'a mana Ku su wanene? Kodan yaranki, dangin mahaifiya sunada matuk'ar tasiri a rayuwar yaro, banason zuwa nan gaba su zargi abinda ba haka yakeba, kodan gudun suma y'ay'ansu su taso suyi musu irin wannan tambayar”.
Murmushin takaici inna tayi, ta d'ago daga jikinsa tana share hawayenta, suduka kallon Abdurraheem daketa motse-motse da k'afafu yana dungurin bayansu sukayi, Abba yay murmushi yana shafa kansa, sannan ya kalli inna yana fad'in “Ai'sha kodan wad'annan yaran, dolene watan watarana sai tarihinsu ya shafi tsokaci dangane da usilin mahaifiya, dukda nawa za'a kawo saifa naki ya taka rawar gani shima”.
Inna tayi murmushi itama tana shafar kumatun Abdurraheem d'in, ta mik'e tsaye tana cewa “karka damu, a bani lokaci, da izinin ALLAH saisun taka tushena da k'afafunsu”.
Abba ya d'auki Abdurraheem ya rungume yana fad'in “ALLAH ya tabbatar”.
Mukan bamusan wainar da ake toyawaba, muna falo yara suna Neman haukatamu da kukansu, dukfa barci suke, amma Meena Na tashi kamar jira suma duk suka tashi masu kawunan kwakwar.😏
Haushi ya isheni nakusa make Amaturrahman datafi kowa daddagewa, saida Munubiya ta rik'e hannuna, “Sweetheart wai baki da hankaline? Uwarmi zaki daka ananne?”.
Cikin tura baki nace, “yo Sweetheart haukatamu zasuyine?”.
Daga inna har Abba dake fitowa baki suka gumtse suna dariya, “A lallai akwai aiki babba a gaban mata ashe?”. Inna tafad'a tana kallon Abba.
Murmushi yayi shima yace, “babba kuwa Ai'sha”. Sai sukayi dariya.
Hakanne yasakamu farga dasu, muka juyo muna kallonsu kowa fuska a tur6une, saboda haushin da yaran suka bamu.
%%%%%%%%%%%%%%%%
Bayan kammala gyara da Sauban yayi, Galadima ya mik'e zuwa cikin d'akin, zama yay ya kunna dukkan Computers d'in d'akin, saida komai ya dai-daita sannan yafara aikinsa cike da kwarewa, har lokacin sallar la'asar yana a d'akin, shiko gajiyar zaman jirginma bata damesa ba, bedroom d'insa ya dawo yay salla sannan ya sauka k'asa, Samha yabama Umarnin abinda yake buk'ata ya dawo yacigaba da aikinsa.
Mintuna kad'an sai gata takawo masa. takan shiga shauk'i idan taga Uncle Sam yana sarrafa Computers d'innan, saitaji tamkar yafi kowa ilimin sarrafa Computer a duniya, amma tasan dole sai ansamu wanda suka fishi, badan karya maketa ba data tsaya taita kallonsa kawai.
Shi baimasan tanayiba, hankalinsa nakan aikinsa gaba d'aya, dukda kansa daya fara ciwo kad'an-kad'an burinsa yakai inda yake hari.
Saida duhun magriba ya gabato sannan yasamu kansa, yanzu ma a d'akin yay sallar magrib, ya zauna karatun Qur'an har time d'in isha'i yayi. Yana idarwa ya d'ora da shafa'i da wutiri, saboda barcin dake damunsa, soyake ya kwanta da wuri, duk abinda yakeyi kafin barci saida yay k'ok'arin kammalashi da k'yar sannan ya kwanta, dukda tunani da kewar yaransa Na neman 6atar da barcin nashi haka yayta yak'i da shi har barcin yaci Galadima akan tunanin.
Samha tazo kawo masa dinner ta iske yanata barci cikin bargo, yama kashe hasken d'akin saina fitilar gefen gadon kawai itakuma haske kad'anne. Ajiye abincin tayi, dukda mawuyacine ya tashi domin cinsa, musamman da saida yamma yamaci d'azun..
(((+)))★(((+)))★(((+)))
Yau kwananmu biyu kenan da dawowa gida, nayi waya dasu Samha duka amma banda uban gayya Galadima, bai nemini ba nima ban nemeshiba, Momma kam kullum sau biyu take kira muyi video call itada Abie, safe da yamma duk takan kirani.
Muna kwance a gado ni da Munubiya, sai kuma mak'e murya takeyi suna waya itada yaa Marwan, koni dake kusa da ita ba komai nakejiba, nayi murmushin takaici ina juya kwanciyata zuwa d'ayan 6arin, danma Na daina jinta gaba d'aya, wata kwalla ta tararmin a ido, ba bak'in cikin kasancewar y'ar uwata a farin cikin nakeba, a', tausayin kainane ya kamani, maybe ita kad'aice zata koma gidan nata mijin banda ni, Na kalli yaranmu da laraba keta musu shirin barci, Aiyaan da Aryaan nata jagwalgwalasu, saurin d'auke k'ananun kwallar dake Neman zubomin nayi.
Ni dai har barci ya d'aukeni bansan lokacin da Munubiya tagama wayarnanba, ban farkaba saida yaran suka farka da kuka, yanzu sabon iskancin da suka tsiro dashi kenan su duka 5 d'in, wato kukan dare, da zarar 2am tayi tamkar an kad'a musu k'ararrarwar tashine, haka zasuyita kuka har sai asubahi ta gabato sukeyin shiru, da zarar asuba tayi saisu hau barci, ko wankan safe za'a musu sai an tashesu, daganan wani sabon barcin suke d'orawa, haka zasu yini barci, sai dare yayi suce basusan zancenba.
ALLAH yau tamkar namusu kuka haka naji, dama ga haushin Ubansu dana kwanta dashi, ficewata nayi daga d'akin nakoma falo Na kwanta, nabar Innarmu da Munubiya da laraba dasu.
🤣ho Munaya kad'anma kenan🤭.
////....//////.....//////....////
A kwanaki biyunnan gaba d'aya Galadima cikin kai kawo yayisu, bashi Company bashi wajejen daduk yake Business, bashi Asibiti wajen Abie, yanason ya killace komai wajen wad'anda zasu iya kula masa da Amana, saboda baisan iya adadin lokacin da zai d'auka a Nigeria ba wannan lokacin, inma zai shigo india bazai dinga wuce kwanaki biyuba zai barta, shima dan yadinga zagayo iyayensa ne.
Har y'ar rama yayi saboda tsabar komawa busy, ga kewar yaransa (niko nace kodai harda uwar yaran🤣🥴).
Momma kawai tasan halin da ake ciki, amma koda wasa basa sanarma Abie komai dangane da hakan, yakanyi dai mamakin komawar Galadima busy a wanan dawowar, dan ko asibiti yaje baya zaman 30minutes yake fitowa. Abie dai ya kasa hak'uri ya tambayi Momma, saita cemasa wani aikine zasuyi a Nigeria gameda Company d'insu, kuma shi aka d'ora akan aikin, shiyyasa yakeson tattara komai wajen mutanansa nanan.
Abie yace, “to ALLAH ya taimaka, yabada nasara fiye da wanda ake tsammani”.
Momma taji dad'in wannan addu'ar, dan haka ta amsa da “Amin” cike da fara'a.
A kwana Na uku Galadima bai samu damar tafiyarba dai, saboda bai kammala uzirorinsa ba, dole ma zai k'ara koda kwana biyune.
Sauban harda rawa dan dad'i, dan shifa bason zaman masarautar nan tasu yakeba🤥.
Yauma a gajiye ya dawo gidan, kallo d'aya zaka masa ka fahimci hakan ko a yanayin tafiyarsane da fuskarsa datai cinkus babu walwala, hannu kawai ya d'agama su Samha dake falo suna gaidashi, harya 6acema ganinsu daga hawan benan idonsu Na kansa, tausayinsa ya kamasu, shidai yana shiga tun a falo yafara zame green jacket d'in dake saman kayansa, ya k'arasa cikin bedroom d'in yana jefa rigar saman sofa da furzar da huci, freight ya bud'e ya d'auki ruwa, batareda kofiba yahau shan kayansa, tas ya shanyeshi ya jefar da robar yana had'iye wanda ke gumtse a bakinsa, sannan ya k'arasa bakin gadon ya zauna ya dafe kansa, tsawon mintuna uku yana a haka shiru, har wayarsa tafara wringing amma bai kulaba, saida aka kira kusan sau uku sanannan yama kalli wayar yana k'aramin tsaki, kamar bazai d'agaba amma saiya d'auki wayar tana gab da tsinkewa, kafin yay picking call d'in ta tsinke. Kiransa yayi dan Nuren ne.
Bugu d'aya Nuren ya d'aga, bayan sun gaisa yake sanar masa yarinyar minister ce batada lafiya, kuma ya lura yarinyar kamar tanada Asthma ma ne.
“Asthma? to miye ya tada ciwon nata? naga dai ba wani Abu dazai iya shafar tashin ciwon nata a gidan?”.
“hakane Brother, wlhy muma bamusan daliliba”.
“Toni yanzu daka kirani mizan muku ina nan?, kufita ku nema mata magani mana”.
“Muftahu ya tafi, dama na gaya maka ne ka Sani kawai”.
“okay. ALLAH yabata lafiya to. Ya maganar Harun?”.
“Sunan sun baza cigiyarsa gidajen redio shida Alhaji Darma, kaga yanda kuwa suka gama rikicewa, da farko sunce yayi Accident shida driver d'insa amma anrasa inda yake shi, to inaga ko driver n ya dawo hayyacinsa ne ya sanar musu shikad'ai yay Accident d'in oho, jiya dai saiga wata sanarwar suna fad'in anyi Garkuwa da shine tunkan accident d'in, amma har yanzu ba'a nemi kud'in fansaba, dan kidnappers d'in basuce komaiba”.
Galadima yay murmushin gefen baki yana susar gashin girarsa a hankali, yad'an cije lips yana fad'in “toko zaku saka kud'ine marayu su sami na abinci da kud'in makaranta”.
Dariya Nuren ya kwashe dashi, yace, “dan ALLAH da gaske kake brother”.
Kwanciya Galadima yayi yana fad'in, “kai d'an air wasa nakeyi”.
Nuren yay kwafa, “wlhy da ace gaske kakeyi Kansan ALLAH saina k'ure dukiyarsa sannan, nakuma rud'asu da cewar ya fad'amin wani sirri, idan basu biyaba zan tona”.
“ALLAH ya shiryeka to”. Galadima yafad'a yana kuma tashi zaune.
“Amin”. Nuren ya amsa.
“Wai anya kuwa zaka shigo yau d'in?”.
“No, maybe ma sai nanda kwana biyu ko uku, bangama hidimomina ba, kudai kuci gaba da kulawa...”.
K'it ya yanke wayar batareda jiran abinda Nuren zai ceba.
Takalminsa ya cire da kayan ya shiga wanka, yad'an jima sannan yafito d'aure da towel ya yafo wani a jikinsa, ya zauna saman sofa yana d'aukar wayarsa, number d'inta ya lalubo, sai kuma ya kasa kira ya kurama number ido kawai, tun randa suka iso hakanne ke faruwa, saiya d'auki wayar kamar zai kira saiya fasa, gashi yanason jin Yaya yaransa da jikin Abdurraheem, ya danna kiran yana cizar lips d'in nasa daya zame masa jiki🙄😏.
_______________
Muna zaune a d'akin mu ni da Ayusher, Feena da sukazo, tirene a tsakkiyarmu munacin d'an wake da Maman yaa Hameed tayi yau dan aikintane, wayata na hannun Feena tana kallon pictures kiran ya shigo, kallona tayi ta kalli wayar ta kwashe da dariya tana mik'omin.
Muduka kallonta mukayi da mamaki, na kar6i wayar ina fad'in, “kekam kokin fara zarewane?”.
Bata bani amsaba, saima dariyarta take cigaba dayi, na kalli wayar nima, a dai-dai nan kiran ya tsinke, sunan mai kiranne ya d'auki hankalina, *_“Rabin raina!”_* na fad'a a saman lips, ni dai banyi saving number kowa hakaba, yanzu na fahimci abinda yabama Feena dariya kenan.
Daga can Galadima yay tsaki, yana jefar da wayar ya mik'e zuwa gaban mirror, saidai kuma zuciyarsa takasa hak'ura, sukda haushin kansa da yakeji na kiranta da yayi, to amma ai dan yaransama yayi, shine zatak'i d'aga masa waya? zuciyarsa tace idan kuma bata kusafa? Kokuma yaran ne suka d'auke mata hankali da kuka.
Iska ya furzo daga bakinsa, dan tuna hakan zata iya yuwuwa kuma, saiya mik'e ya d'auki wayar, lallai yau Munaya takafa tarihi a rayuwarsa, ko Momma idan yay mata kira d'aya bata d'agaba yakan hak'ura saita kirashi, inhar baya mantaba baita6a kiran mutum a jere sau biyu ba a rayuwarsa. kiranta ya kumayi yana wani ciccijewa fuska a murtuke, kai kace tana gabansa ne.
Har yanzu ina cikin mamakin ina na samo sunan? kiran yakuma shigowa, yayinda feena take gayama su Munubiya abinda ta gani, tashinai daga wajen ina d'aga kiran saboda hayaniyarsu.
Koda na d'aga sai akak'i magana, nima sai nayi shiru, ganin abin bana k'are bane nace, “Idan babu buk'atar magana ai banga dalilin kiraba”.
Daga can Galadima yay murmushi yana shafa sajensa da kallon kansa a mirror, a ransa yace anan da hali dai.
Har zan yanke sai akayi gyaran murya, tun a sannan na gane shine, na zaro ido cike da mamakin waye yaymin saving number haka? Lallai ko rantsuwa nayi babu kaffara, Samha ko Sauban.
Galadima ya katseta da fad'in, “wannan tarbiyyar zaki bama yarana kenan na rashin iya gaida na gaba dasu?”.
Dukda Naji haushin maganarsa amma naji kunya, nace, “To ba shiru kayiba kaima”.
“naji to mai bakin tsiwa, gaisheni”.
Nakula abin nasa harda tsokana, dan hakan nace, “ina kwana?”.
Yace, “A 9ja ko?”.
Tunawa nayi time d'inmu fa ba d'ayaba, sai nace “Ina yini”.
Ya amsa da “lafiya. Ina abin cikin kwan?”.
Kamar bazan amsaba saidai nace, “waye mai wannan sunan?”.
Galadima ya murmusa yana cija lips, “karki damu kwanaki kad'an zakiji wasu ukun ko biyu a jikinki, daga nan saiki tuna mai sunan”.
Da sauri nace, “can gasu gada, idanma hakan tafaru to sai dai ga masoyina mai zuwa, wanda yadamu dani, ina maka albishir nasamu mijin aure”.
Murmushi Galadima yakeyi yana shafa kansa, yace, “Ayya natayaki murna gaskiya, sai dai shifa mijin ina tayashi jajen rashin iya za6e”.
Wani haushine ya kamani, na yanke wayar ina tsaki.
Dariya sosai ta kama Galadima, ya ajiye wayar yana fad'in “kujimin yarinya, ke kika kawo zance, miye kuma najin haushin?”.
Ta6e baki yayi ya tashi zuwa gaban wardrobe yay shirin barci hankalinsa kwance.
_____________
Tunda na yanke wayar sainaji kuka na Neman tahomin, amma na daure na danne abina, komawa nayi cikin d'akin na haye gado, Ayusher tamin magana akan nazo muci gaba dacin abincin amma nace na k'oshi, lallashina sukaitayi itada Feena, nak'i saurarensu, Munubiya kam uffan bata ceminba, hasalima ko kallon inda nake k'inyi tayi, dukda nasha jinin jikina akan haushina takeji saina shareta nima.
Har dare muna tare dasu Ayusher, sai bayan isha'i Yaa Marwan yazo d'aukarsu, nafita kawo masa ruwa saboda na freight d'inmu ya cika sanyi, yace kuma bazaisha mai sanyiba, koda na dawo saina tarar basa nan shi da Munubiya, Ayusher tace, yace nakai masa d'akinmu.
Ban kawo komai a rainaba na nufi d'akin cikin karsashina, saida naje tsakkiya sannan idona yay mugun gani, daga Munubiya har yaa Marwan da suka farga da shigowata suka d'ago kowanne ya zubamin harara.
Babu shiru na dangwarar da ruwan a wajen nima ina murgud'a baki na fice abina............✍🏻
🤣Ya Marwan kamin dai-dai kaida Munubiya🤨 su o'e sai a canja hali, dan duniya saida kud'i lahira kuwa sai da hali🤸🏻♀, ko ya kukace my Guys😂😜?.
*_Duk wanda yamin magana PC shekaran jiya yaga babu reply yamin afuwa, wayar tawace hawan madara ya kamata, sai kawai ta goge komai, shiyyasa nai zuciya jiya naki muku typing, dan nayi ya goge😢_*
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*
*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BOOK 3_* 👉🏻9⃣➖🔟
..............Kwana biyu Galadima ya k'ara suka dawo Nigeria shi da Sauban, burinsa a yanzu ya fuskanci abinda ke gabansa da iyakar k'arfinsa da basirarsa, bai shiga masarauta ba saida ya had'u da baffi yabashi wasu takardu.
Dole yay barcin wasu awoyi domin samun nutsuwar gajiyar tafiya, sannan yay shirin fitowa, ya lek'a sashen mai martaba dansu gaisa saiya tarar yanada bak'o, jakadiya sarkin gulma ta gutsiri goronta tana kallon Galadima, “Ranka ya dad'e ai takawa yana tare da bak'one, bak'on kuma Na lura Wanda ba'ason sanin dami yazone, dan kullum ganawar sema k'unshe yakeyi da takawa”.
Shiru yamata tamkar bai jiba, danshi mutumne da baya shiga abinda bai shafeshiba, kowa yasan haka a masarautar, shiyyasa Duk makircin masarauta bazaki ta6a samun wani ya sakoshiba, kokuma kawo masa gulmar wani.
Ganin haka itama jakadiya sai taja bakinta tayi shiru.
Galadima ya mik'e yana kallon agogon hannunsa, “Bara naje, zan dawo anjima”. ba tare da ya kalleta ba yay maganar yay kuma ficewarsa.
Da kallon ta bishi tana cigaba da 6allar goronta, tace, “wannan murd'ad'd'en da ace zai saurara dana bashi sirrika da yawa wlhy, amma ina, maganama ta kud'ice a garesa, ka huta wlhy, wai gurgu ya za6i zaman waje d'aya😏”.
😂😂🤭
_______________________★
Kwance yake jikin seat d'in mota idonsa a lumshe, duk yanda yaso ture zancen jakadiya a ransa karyay tasiri ya gaza hakan, sai kaikawo zancen ke masa, tabbas bak'o mai muhimmanci ne kawai zai iya ganawa da mai martaba har cikin turakarsa, to mike faruwa ne haka?, bashida amsa dan haka ya cije lips d'insa, tafiyar tasu yau dagashi sai sarkin mota, ya hana dogaransa binsa, gidan da su Nuren suke ya isa, dukda shi Nuren ma baya nan yaje gida saboda kiran gaggawa da papi yamasa, Muftahu kam dole kullum a Masarauta yake kwana, saida taka tsantsan ma yake zuwa gidan da rana, saboda rashin ganin Harun yanzu motsin kowa lura akeyi dashi. Su Ameer ne suka bud'e musu k'ofa Sarkin mota ya shiga, yanayin parking suka bud'ema Galadima ya fito, cike da girmamawa suka gaisheshi, ya amsa musu da d'an sakin fuska, sannan ya tambayesu Yaya aiki?.
Da Alhmdllh suka amsa. Har cikin falon sukai masa rakkiya, babu kowa cikinsa, amma ko ina k'al yake a gyare, ga k'amshi mai dad'i yana tashi.
Yayi zama yakai Na 10minutes saiga baba Rabilu shida wani dattijo da zai iya girmarsa kad'an, kokuma wahalace ta girmamawa tsufan nashi oho.
shidai Galadima kallon mutumin yake tamkar ya sanshi, amma ya manta a ina.
Zama sukayi, cikin girmama juna suka gaisa, sukaima Galadima barka da dawowa, da d'an guntun murmushi ya amsa, har yanzu dai idonsa akan dattijonnan.
Lura da hakan da baba Rabilu yayi saiya murmusa, yace, “Ranka ya dad'e ka shaidashi ne?”.
Galadima ya hard'e k'afafunsa yana murmushi, yace, “baba rabilu inadai masa kallon Sani kam”.
Baba Rabilu yay k'aramar dariya yana kallon dattijon dake durk'ushe a k'asa shima yana Murmushi, sannan ya dawo da kallonsa kan Galadima yace, “Zaka sansa Ranka ya dad'e, amma gaskiya kana tare da k'uruciya lokacin, Sunansa Badi, mahaifinsa shine mai kula da dawakan Sarki a wancan lokacin”.
Da sauri Galadima ya sauke k'afafunsa daya hard'e, cikin tsantsar mamaki yace, “Baba Rabilu kana nufin wannan Badi ne?”.
Dattijo ya risinar da kansa k'asa alamar girmamawa ga Galadima. Yace, “Nine ranka ya dad'e”.
Rasama abinda Galadima zaice yayi. Sai bakinsane ke motsawa alamun yanason maganar amma ya kasa. Sai ido daya tsurama Badi cikeda tunosa a lokacin da shi yake d'an shekara 5 kacal a duniya, dukda bazai yuwu ya iya tuna komaiba, amma tabbas yasan fuskarsa, yasan kuma shine mai kulawa da barga ta dokunan masarautarsu shi da iyayensa, a lokacin inhar baiyi k'aryaba Badi bazai wuce shekaru 33 ko 35 ba. Amma yau gashi zaune gabansa furfura da girman tsufa duk sun bayyana a garesa......
Sallamar Muftahu ce ta katse tunanin galadima, Muftahu ya zauna suka gaisawa da Baba Rabilu, sannan ya gaida galadima, idonsa dai nakan Badi shima.
da k'yar Galadima ya amsama Muftahu gaisuwarsa.
Badi dakema muftahu kallon sani ya gaisheshi cike da girmamawa (Dan ALLAH yayisa mutum mai yawan rik'o).
Muftahu dai kasa hak'uri yayi, ya kalli baba Rabilu yana neman amsa.
Murmushi baba Rabilu yayi, ya gyara zamansa yana fad'in, “Yalla6ai baka ganesa bane?”.
Muftahu yace, “Banma ta6a ganinsa ba alhaji”.
Badi ya kalli Muftahu sannan yay k'asa da kai. Yace, “Nikuwa kaga Na ganeka yalla6ai, dan bazan manta sanda kukan rako Yarima ba idan za'a fita da shi bakin ruwa shan iska, ka kan nace sai a doki d'aya zaku tafi kai da sauran abokan nashi”.
Murmushi Muftahu yayi, ya kalli Galadima dayay shiru yana kallon Badi kawai, yasan yana tuna bayane, kuma akwai tambayoyi fal ransa sai dai ya kasa furtawa, janye idonsa yayi ya maida ga Badi, yace, “Amma Badi minene ya faru da kai harka bar masarauta? dan bazan iya tuna wani abuba a wad'ancan shekarun namu, yanzu kuma daga ina kake?”.
Zama Badi ya gyara. Yace, “lallai labarine mai tsawo da Nisan zango, amma a tak'aice dai abinda zan iya cewa shine.....”.
_“Bayan kwanciyar mai martaba adalin sarkinmu jinyar da ba'asan mafarinta ba da wata biyu kacal ranar wata lahadi da tashin hantsi munje kasuwa ni da mahaifina mun sayo abincin dokuna mun dawo, muna tsaka da sauke kaya a barga saiga wani mutum a tsakkiyar harawar dokunan cikin a kori kurar da muke zubo kayan kenan, dagani har mahaifiyata da mahaifina mun razana matuk'a, harma k'anwata taso tayi ihu amma mahaifiyarmu ta toshe bakinta saboda rok'on da mutumin kema babanmu akan muyi shiru Dan ALLAH, a razane matuk'a mutumin yake dan ko ina Na jikinsa mazari yake, yace a taimaka masa da ruwa yasha zaimana bayani, iya mahaifiyarmu ta nufi d'akunanmu dake cikin bargar dagacan gefe ta d'ebo masa ruwa a randa cikin kwanon sha ta kawo masa, babana ya taimaka masa ya fito daga akori kurar, ya zauna bisa buhun harawar da muka fara saukewa, ruwan ya kar6a ya kafa kai saida ya shanye kusan rabi sannan ya ajiye yana musu godiya, wani Abu irinna d'aukar hoto (camera) ya fiddo a cikin aljihunsa ya mik'ama mahaifina cikin yin magana da k'yar. yace____”.
_“Sarkin Barga ga wannan abun, nasan zakayi mamakin miyasa Na bakashi, to banida wajen daya dace Na damk'ashi sai wajenka a kaf masarautarnan, Dan kaine hanyata mai sauk'i, akan wannan abun aka biyoni za'a kashe, shine ALLAH yabani ikon shiga motarku, dan nashigo tacikin kasuwa domin tsira da raina shine Na ganku, karka bama kowa camera d'innan sai d'an Sarki, Yarima Sameer, kokuma d'iyarsa, gimbiya Haneefa, ko matarsa uwargidansa wadda ta haifi su Yarima d'in, harda wad'annan takardunma, nasan ni tawa ta k'are Dan babu makawa saisun kasheni, Dan ALLAH ka tabbatar cikin mutane ukunnan ka bama wani, nasan yarima bashida wayon dazai fahimci minene, amma idan ka nuna masa yabama mahaifiyarsa zai bata, dukkan abinda ya faru da mai martaba yana acikin wannan Camera d'in, ni zan koma, Dan banason wani ya fahimci nama shigo masarautar nan balle har asan Na gana daku”._
“duk yanda mahaifana sukaso tsaida mutuminnan sun gaza, dan ya tabbatar mana dolene yabar masarautar a lokacin, saboda akwai munafukan da sukasan abinda yafaru da Mai martaba. Sai dai kuma abinda bamu saniba shine, Ashe dukkan abinda ya faru akan idon waziri ne, dan haka a wannan dare yabiyo sahun abinda mutumin yabada, mahaifana Na barci ya tashesu akan su bashi, sukace basusan mi zasu bashiba, shine ya kashe mahaifiyarmu wai dan baba yaji tsoro yabashi, dukda baba ya razana hakan baisa ya bashiba, ya yarda d'in gwamma a kasheshi shima da dai yabada , daga k'arshe shima ya kasheshi, k'arar da mahaifina yayi sai dukkan dokuna suma suka d'au haniniya. Hakanne ya sakani farkawa a rud'e Na fito daga d'akina, ina sako k'afata a d'akin mahaifana, Waziri Na cakama baba k'arfe a mak'oshi,, babana ya rik'e mak'ogwaronsa da hannu, yaringa min nuni da d'ayan hannun alamar Na gudu karnayi magana kuma, Na fahimci haka saboda ni baba yabama ajiyar abin d'aukar hoton da takardun, inhar iyayena zasu iya jurar mutuwa akan su bashi ni mezai hana na bi umarnin baba na gudu da abun, ko takan iyalaina banbiba na gudu ta hanya mafi sirri dana Sani, lokacin dana fito zan gudu waziri ya farga dani, hakanne ya sakashi biyo bayana, ganin bazai cinmini ba saiya saka dogarai masu tsaron k'ofa akan su bini wai na kashe iyayena zan gudu. Na rasa Inda zan dosa da wad'annan kaya saboda na tabbata ana bina a baya, saboda mun had'a ido da waziri, na shiga cikin jeji sosai, dan a wancan lokacin gari bai gama dunk'ulewa waje d'ayaba irin haka, Masarautar gagara badau ba tsakkiyar gari takeba kamar yanzu, dabarar hawa bishiyace tazomin dan haka na hau itaciyar wani Kalgo dake kusada k'oramar da mukan raka Yarima hutawa, har dogarannan da waziri ya saka su biyoni suka iso wajen domin nemana, ALLAH bai basu ikon ganinaba, saima suka wuce ni, lokacin sanyine sannan, nasha sanyi dan na wahala, sosai na fita hayyacina, abin mamaki da asubahi sainaji hayaniya a kusa dani, ido na bud'e da k'yar saboda tsantsar jigatar da nayi da muku-mukun sanyin wannan lokacin, wannan bawan ALLAHn nagani tare da Wanda yazo masarauta ya bamu abin d'aukar hoto (ya nuna baba Rabilu), hakanne ya sakani jin dad'i na sakko a nufin maida masa abinsa, nakuma sanar masa dalilin abin d'aukar hoton an kashemin iyayena, sai dai ina sakkowa wasu mutane na isowa wajen a mota guda biyu, yunk'urin guduwa mukayi mu duka ukun dukda su saima lokacin suka farga da ni a wajen, sun sami damar kama Wanda ya bama mahaifana abin d'aukar hoton, saboda kamar yaji ciwo a k'afa bazai iya guduwa ba, shine ya ringa fad'a mana mu gudu karmu sake mu basu abinnan. Iya k'arfinmu muka ringa gudu a lokacin Ranka ya dad'e, nashiga tashin hankali ganin rana tsaka masifa tazo ta haye mini ba tare dana san farkonta ba, gashi na rasa iyayena, na baro iyalina da k'anwata, bansan halin da suke cikiba, na samu damar shiga wani k'auye, Anan ne nasamu taimakon wani tsoho makaho, dan shine yabani mafaka ta tsawon shekaru 4, makahon tsohonnan yana zaune ne da matarsa amma ita tana gani, lokacin da jama'ar gari suka farga dani a gidan sai sukaje suka sanarma mai unguwar yankin, shikuma ya sanarma dagaci, har gida akazo aka tafi dani wani babban k'auyen dake kusa dasu inda dagacin yake akamin tambayoyi nida tsohonnan makaho, koda aka tambayi baba makaho saiya sanar musu ni d'an y'ar uwarsane, nazo ne na koyi sana'a na koma garinmu, dagaci yarigada ya yarda da baba makaho shiyyasa ya amince, aka kuma barni nacigaba da zama a k'auyen, tundaga wannan lokacin nasamu saken zama k'auyen gamji, ban sake waiwayar masarauta ba har tsawon shekaru hud'un nan. Saida ALLAH yayma baba makaho rasuwa sannan, matarsa gudun kar naci gadonsa shine tace yakamata na koma gida hakanan, ban mata musuba na had'o y'an kayana da abinda na samu a k'auyen da wad'annan takardu da abin d'aukar hoto nabaro k'auyen ina kuka saboda sabo. Sai dai abinda ban saniba Ashe anata bibiyata har lokacin, tun a hanyata ta shigowa gari wasu mutane suka farmin, na zubda komai nawa amma banda akwatin dana zubo abin d'aukar hoto d'innan da takarda, a cikin wannan gudu sai Ubangiji ya had'ani da wani bawan ALLAH akan besfa, ya bigeni, naji mummunan ciwo dan alamomin fitar rai sun bayyana agareni, cikin magana da k'yar, na mik'a masa akwatin ina rok'onsa dan ALLAH ya kar6i akwatinnan, ya Isar da shi masarauta amma yarima Sameer ko gimbiya Haneefa zai bamawa, ko mahaifiyarsu, bayansu karya bama kowa, idan bai samu damar badawa a yanzuba yabari sainan gaba inhar Yarima Sameer yay girman mallakar hankalinsa, zai iya kwatama kansa y'anci saiya bashi, na rok'esa karya ci amanata dan ALLAH, na aminta da shine shiyyasa na bashi....., da Sauri ya amsamin da insha ALLAH bazaici amanataba dan shima yana aikin jaridane, iya abinda naji kenan Daganan na suma a wajen, ban sake sanin komiba kuma, sai farkawa nai na ganni tare da wani maharbi jikinsa duk ciwuka, shine yaci gaba da kulawa dani tsawon lokacin ina jiyya, ban ta6a fad'amai ni waneneba, baikuma ta6a tambayata ba har shekaru sukaja, ganin girma ya kamashi sosai ya rok'eni na sanar masa daga ina na fito?, dan karya bar duniya da kokwanto a ransa, banyi nauyin bakiba na sanar masa komai. Yasha mamaki kwarai da gaske, dan suma labarin ciwon Sarki yaje musu, harma da nad'a k'aninsa da akayi ya maye gurbinsa. Shine yabani shawarar fara bibiyar masarauta kozan samu wani labari akan ahalina da jikin mai martaba, daga lokacinne nafara 6adda bamin shiga masarauta, na fahimci k'anwata ta auri wani bawa, matata ALLAH yamata rasuwa wajen haihuwar cikin dana barta dashi, d'an yayata data rasu itama ta bari shine k'anwata tacigaba da rik'o, a yanzu haka shine Wanda yazama direbanka Ranka ya dad'e, wannan shine abinda nasani ALLAH ya k'yautata rayuwarka, ya d'aukaki darajarka da mulkin masarautar gagara badau.”
Daga Muftahu har Galadima ajiyar zuciya suka sauke, kowanne yana jinjina lamarin a zuciyarsa, shi dama baba Rabilu ya fad'a masa kafinsuzo, kafin Galadima ko Muftahu su sami damar magana baba Rabilu ya fara fad'in “Lallai kamar yanda na sanarmaka randa nazo gareka ranka yadad'e d'an uwanane shi wannan daya bada camera d'in, da ni da shi duk aikinmu d'ayane, bayan yakai wannan camera ga mahaifin Badi, gidana ya zarto, amma saiya iske ban dawoba sai iyalina kawai, yabar musu sak'on wasik'a da address d'in inda zan sameshi, wato k'oramar bakin gari inda shi Badi ya gammu, inayin sallar asubahi kuwa na nufi wannan wajen dan ya rubutamin Cewar yana cikin mawuyacin hali, yana tsaka da fad'amin abinda ke faruwa saiga wad'annan mugaye sun biyomu, bansan a ina sukaji muna canba, na gudu ne a tunanina shima Habu ya gudu, Ashe sun kamashi, saida na fara jiyo sautin muryarsa dake amsa kuwwar karmu tsaya mu gudu, badan nasoba na gudu nabar Habu a hannunsu, wasu a cikinsu sun cigaba da bina, amma wani mai lambu ya taimakeni ya 6oyeni, kwanana biyu a cikin lambun, saida mukaga komai ya d'an natsa sannan na fito Na koma gida, duk tunanina ai basu ganniba, shiyyasa nacigaba da y'an hidindimuna domin 6adda kama, a 6oye kuma na shiga binciken wanda Habu ya bama Camera d'in, dan ya gayamin tana masarauta wajen mai kula da barga, Labarin mutuwarsu tazomin shida matarsa a bisa bincikena, saidai a masarauta ance d'ansu Badi shine ya kashesu, Sam ban aminceba, wannan ya sakani Neman Badi domin na kar6i camera d'in hannunsa, inada tabbacin shine Habu ya sanarmin cewa gashi can alokacin da mutanen nan suka iso, saidai kallo d'aya namasa muka fara gudun tsira, daga nan kowa ya kama tsaginsa. Dole na ajiye aikina saboda tsaro, na kawo rigar siyasa na sanya dan nema ma kaina girma, shekarata 6 a rigar siyasa akayi yunk'urin kasheni, ba kowa bane da wannan aikin face Alhaji Shehu Adamu Darma, har gidana ya saka aka satoni, nayi mamakin ganinsa, dan jam'iyyarmu d'aya, wani sa6ani bai ta6a shiga tsakaninmu ba, dan haka na nemi dalilin sanin miyasa zaisa a d'akkoni cikin iyalina? bayan mu y'an jam'iyya d'ayane. Ya kwashe da dariya yana nunani da fad'in lallai Alhaji Rabilu fanisau bakada hankaki, a tunaninka dukkan 6addamin da zakayi bazamu ganoka ba? yanzu dai dukma ba wannanba, ina camera?. Nace wace camera kuma? Wani wawan duka yaronsa yamin, na dafe wajen saboda azaba, Darma yakuma cemin ina camera d'in da Habu idris ya bani? nanma na sanarmasa ban saniba, wannan ne yasakashi kar6ar k'arfe ya kwad'amin a kai saboda haushi, daga nan na fad'i a wajen, ashesu duk sun d'auka a lokacin dukna mutu, shiyyasa suka jefar dani gefen hanya suka tafi, wani bawan ALLAH ne ya d'aukeni yakai asibiti, abinda yasa su Darma basuji labarina ba wanann mutum ba d'an nan yankinmu baneba, fataucine ya kawoshi, daya d'aukeni kuma saiya bar nahiyar wannan yanki dani gaba d'aya, nayi jiyyar shekaru biyu, kafin na dawo dai-dai, duniya sukta d'auka na mutu, saida na d'au shekaru bakwai banzo wannan yankinba, dan bawan ALLAHn nan yazo har nan ya kwashe iyalaina ya kaimin, bayan yamusu bayanin dazasu fahimta, bayan shekaru bakwai nakanzo nad'anyi bincikena na koma cikin 6adda kamanni, a wannan yanayinne na farga da Badi, ban sanshiba gaskiya, amma ganin yanayinsa tamkar mai lek'en asiri shine na fara bibiyarsa harna fahimci wanene shi, hakama waziri da d'ansa, na lura kullum cikin bin diddigin yalla6ai Galadima suke suma, nima wannan abun shine abinda na sani, kunji dalilin Darma na kirana Fatalwa”.
Galadima da Muftahu sunyi shiru cike da tsabagen rud'ani da al'ajabi, da k'yar Galadima ya iya bud'e baki cikin muryar tsananin damuwa yace, “waishin minene a cikin camera d'in nan? Yanzu kuma wanene ke rik'e da ita?”.
Baba Rabilu yace, “Duk wannan muke son sani ranka ya dad'e, yanzu haka muna kan neman wanda badi yabama wannan Camera, dan na sanar masa har yanzu batazo gareka ba”.
Galadima ya sauke ajiyar zuciya yana cije lips, idonsa yayi jazur, ya kalli Muftahu sannan ya kalli Badi dake zaune kansa a duk'e, “Badi yanzu idan ka gansa zaka iya ganesa kenan?”.
“insha ALLAH ranka ya dad'e zan iya, saidai idan har ya mutune, bakuma ma fatan hakan”.
Shiru dukansu sukayi kowa na nazari, Galadima sai ajiyar zuciya kawai yake saukewa, shi kad'ai yasan mi yakeji, ya kalli Muftahu yana fad'in “Sarkin mota ya shigo, dan nasan baisan matsayin Badi a wajensa ba”.
Muftahu ya amsa da “to ranka ya dad'e”.
Cikin y'an mintuna saiga Sarkin mota tare da Muftahu sun shigo, a k'asa ya durk'usa yana musu sannu, Galadima ya kallesa yana nuna masa Badi, “kasan wannan?”.
Badi da Sarkin mota suka kalli juna, a lokacin ne Muftahu da Galadima sukaga kamannin su, saidai shi Badi tsufa ya 6oyesa kad'an.
Ganin sun shagala da kallon juna kowa yakasa magana sai baba Rabilu ya katsesu da fad'in “Badi kamasa bayani mana”.
Dattijo badi ya kamo hannun Sarkin mota kusa da shi, yana zubda hawaye yace, “matso gareni Yunusa, nine babanka yayan mahaifiyarka, Badi ya rungume Sarkin mota suka fashe da kuka, a haka yake bashi labarin alak'arsu. Saida kwalla ta cika idon Galadima, hakanne ya sakashi tashi ya fice daga falon, Muftahu da tausayinsu ya kamashi shima ya bi Galadima da hanzari.
A tsaye ya iskeshi ya tsurama flowers d'in da akama gidan ado dasu ido, hannayensa biyu duk cikin aljihu, gaba d'aya bugun zuciyarsa ya fara canjawa, sai had'iye yawu yake da k'yar, wayarsa ya zaro daga aljihu, rasa wanda zai kira yayi, sai bin numbers d'in yake da idanu yana canki canka, ya tsansa dai ya sauka kan number Munaya.........
**************************
Fitowata daga wankan yamma kenan Munubiya ta shiga, yau kwana biyu duk zuciyata babu dad'i, hakannan na tsinci kaina cikin 6acin rai, harzan fara shafa mai Aryaan ya shigo d'auke da Abdurrahman yana kuka, dole na ajiye man na kar6esa, na ta6a jikinsa da har yanzu zafin zazza6in daya yini da shi bai saukaba, saboda tunda asuba ya farka da kuka cibiyarsa na ciwo, kashinsa harya canja kala, saida innaro tazo tabashi magani sannan muka samu nutsuwa, daga nan kuma sai zazza6i, shine har yanzu nake d'an jin jikin nasa da zafi kad'an, nono na saka masa a baki kozai kama, dan duk yinin yau bai shaba, na sauke ajiyar zuciya ganin ya kar6a, ina shafa kansa idona na kallon fuskarsa data fara rikid'ewa zuwa kamannin mahaifinsa wayata ta shiga Ring, d'auke idona nayi daga kan Abdurrahman na maida ga wayar, nayi mamakin ganin yalla6ai, danna canja sunan tun a waccan ranar, na daiyi picking a d'arare na saka a kunne. yau dai banjira k'orafinsa ba nace, “Ina yini”.
A yanda ya amsa min sallamar da gaisuwar saida gabana ya fad'i har na cire ma Abdurrahman nono ban saniba, aikam ya fashe da kuka.
Hakkane yakuma rikita Galadima daga can, yace, “miya faru? Waye ke kuka?”.
K'aramin tsaki naja, nace, “Abdurrahman ne, wai dama ka dawo?”.
Bai amsa min na k'arshen ba saina farkon, yace, “mi'akai masa?”.
“Babu komai, bayajin dad'ine kawai”.
Lips d'insa ya cije yana fad'in “yanzu zanzo gidan”. Bai jira cewar Munaya ba ya yanke kiran.
Sororo nayi ina kallon wayar, kai kace zan ganosa a wajen ne, Munubiya data fito ta katseni da fad'in “mikike kallo haka? ga ruwan nono kin bari yana zuba a jikin yaro”.
Ajiyar zuciya na sauke, sannan na gyara ina kwantar da Abdurrahman d'in dayay shiru.
Munubiya dai takuma tambayata, fad'a mata zuwan Galadima nayi, tace, “oh shine kikema wannan mamakin ko miye?”.
'Dan hararta nayi, amma bance komaiba, itama ta ta6e baki tana kamo hannuna ta zauna a stool d'in Mirror. Wai sai tamin kwalliya.
Da faro k'in yarda nayi, saida naga ta 6ata rai sannan na hak'ura dai tamin inata tura baki gaba.....................✍🏻
*_ALLAH Sarki, wlhy harna fara missing d'inku, waya tamana tsiya😢, yanzuma da wayar Oga nayi typing, koba komai Comments naku na sakani nishad'i, I Miss you so much all😔😘😘😘❤❤_*
Insha ALLAH vary soon zan dawo gareku😂.
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻_*
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*
*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BOOK 3_* 👉🏻1⃣1⃣➖1⃣2⃣
.............Mintuna basufi 20 da gama kwalliyar ba saigasu Aiyaan sun shigo dad'an gudunsu, Munaya na cikin d'aki tak'i fitowa, wai kunyar su inna suganta da kwalliya takeyi.
Inna ta dakama su Aryaan tsawa saboda batason wannan gudun.
Nutsuwa duk sukayi.
Tace, “Gudun mi kukeyine?”.
Y'ar rige-rigen fad'a suka fara, kowa yana ture d'an uwansa akan shine zai fara fad'a, ana cikin haka Yaa Anas yay sallama.
Hayaniyar su Aiyaan ta hana aji, sai laraba ce ta farga dashi, shine Yakuma yimasu Aiyaan tsawa suka nutsu, kowa ya zauna gefe yana tura baki.
Yaa Anas ya gaishe da laraba da innarsu munaya, Munubiya ma ta gaisheshi, ya Amshi Ameen dake hannun inna yana fad'in “inna Yalla6ai Galadima ne fa agidan namu, gashi kuma duk su Abba basa nan, shine nace ko'a kawoshi nan ne”.
Inna tace, “A'a Anas, ai ba'ayi hakaba, bara na d'akko makullin d'akin Abbanku saika bud'e masa nan ya shiga”.
Anas yace, “to inna”.
Laraba dake taya Munubiya shirya su Amaturrahman tayi murmushi, a ranta tana yaba yawan karamci na ahalin Munaya, mutanene masu dattako da sanin darajar d'an Adam, shiyyasa kullum take kuma taya Galadima murna da samun tsatson wannan mutane.......
Tunaninta ya katse lokacin da inna tadawo da key ta bama Anas, Ameen ta kar6a a hannunsa shikuma ya fice.
Munubiya tace, “innarmu ajiye wannan ki k'arasa sama Abdurraheem kayan Dan ALLAH, sainaje na had'ama Abbansu abincin, nasan yanzu yayi”.
Inna ta harareta, “kai nifa kunma maidani Nanny d'inku, nizan ke muku hidimar y'ay'ane?”.
“please mana innarmu, basune masu kawo miki kaza kina ciba sannan kin tsufa”.
Laraba tayi dariya tana fad'in “Gaskiyarki kuwa Maman 2, ALLAH dai yaja da rai”.
Inna tace, “iya kema biyema shirmennan nata zakiyi?”.
Laraba takuma darawa tanama Abbdurrahman rawa.
Itadai Munubiya ta fice tabarsu, laraba na bama inna amsa.
Duk ina jiyosu daga d'aki, haka kawai sainakejin wani iri, yanzu dole ta gaban su Innarmu zanbi natafi wajensa? Na kalli kaina a mirror kunya ta kuma kamani, dukda Simple kwalliya Munubiya tamin nayi k'yau, dan d'aurin kaina ya zauna dak'yau, fuskata ta kuma nutsuwa, har rantsuwa tamin inhar na canja wani Abu saitayi 2weeks batamin maganaba, nasan kad'an kenan daga abinda Munu... Zata iya, shiyyasa dole na hak'ura na bari.....
Shigowar Munubiya yasani waigawa na kalleta, ta harareni tana matsowa tamin kallon tsaf, nasan sotake taga mina goge kona canja, ganin komai yana yanda tayishi saita kuma d'aukar soson hoda ta gyara, ta d'akko turare tana kuma fesamin, hannunta nai saurin rik'ewa ina 6ata fuska, “Wai Sweetheart bazaki barshi haka bane? Turaren nan har hawa kaifa yake, Ni wlhy kunyarma fita nakeyi”.
Munubiya ta fisge hannunta tana dariya da fad'in “to kibi ta k'ark'ashin k'asa kawai mana, kuma wlhy ki nutsu, idan yauma tsiwar zaki masa saiki bada himma, anacewa mutum Idan ya haihu yana hankali kedai bakiyiba, saima rashinsa kika k'aro, malama muje yana jiranki”.
Yanda kukasan na make Munubiya haka naji, amma saina k'yaleta, nima nasan ta hanyar da zanbi na rama, gyalen data samin a kafad'a nabi da kallo.
nace, “haba Munu, amma wannan d'an gyalen Dan ALLAH?”.
“Okay, wajen surukinki zakine? ALLAH ki kiyayeni”.
Baki na murgud'a mata.
Tace, “oho dai, kije kimasa kidawo ta cinyayyen lips, danba barinki zaiyiba”.
Juyawa nayi na kalleta, amma saita d'auke kai tamkar bama itace tayi maganarba. Nayi kwafa kawai muka fito.
ALLAH ya soni babu kowa a falo sai su Aiyaan, hakkane ya sakani sauke ajiyar zuciya nad'an saki jikina.
Gwaggon Haleematu dake kaikawo a kitchen da tsakar gida saboda itace ta kar6i girki tabimu da kallo, gulma nacin ranta, daga ni har Munubiya d'auke kai mukayi tamkar bamu gantaba, muka shige falon Abba da takalman Galadima heif cover milk ke a k'ofar.
K'amshin turarensa yafara amsa mana sallama, na shak'a na lumshe ido.
Hankalinsa nakan yaransa da duk suke jikinsa, yana sanye cikin milk d'in shadda harda hular zanna bukar itama milk da d'an kwalliyar Brown kad'an, sosai yamin k'yau amma saina d'auke kai tamkar banma gansa ba.
Munubiya tace, “To Abban 3 gatanan nakawo maka”.
Murmushi yayi, idonsa sanye cikin farin eyeglasses, cikin muryarnan tasa mai kama da anmasa dole yace, “Thanks you Auntynmu”.
Murmushi itama Munubiya tayi, ta jinjina masa kai ta juya zata fita, har takai k'ofa ya katseta da fad'in “Su twins rowarsu akemin?”.
Hannu ta saka ta dafe bakinta, saikuma ta janye tana cewa, “A'a Abban 3 zasuzo su gaida abbansu insha ALLAH”.
Baice komaiba sai murmushi daya sakeyi.
Ta harareni sannan ta fice, Nina ramawa nayi.
Koda Munubiya ta fice saiya kuma maida hankalinsa ga yaran ya shareni, abin yabani haushi, jinaima kamar na fice abina, amma na danne zuciyata na matsa gabansa. Wajen tiren abincin na durk'usa, na d'auki jug d'in zo6on na zuba a k'aramin cup, d'agowar da zanyi na kamashi yana kallona, amma saiya basar, baki na tura kad'an, na mik'a masa cup d'in.
Bai kar6aba, sai wani bina da kallo yake tundaga sama har k'asa, a raina nace rainin wayo.
Idonsa ya janye daga kaina, ya fara kwantar da yaran d'ai-d'ai a gefensa, saboda a doguwan kujera yake.
Saida ya gama nakuma mik'a masa cup d'in, hannuna ya had'a da kofin ya rik'e, na d'ago ido muka kalli juna, duksai na daburce, danya cire eyeglasses d'in, kamar mai koyan magana na had'o kalmomin gaisuwar da gyar.
Nace, “i...na..yini”.
Wani Munafukin murmushi yayi yana lumshe idanu, ya kuma bud'esu a kaina yana d'age girarsa d'aya da cizar lips, a hankali ya furta “ke matsoraciya Ce, miye na rikitar daga kallo uhmyim?”.
Idanuna nad'an juya nace, “Tab badai niba”.
Ya ta6e baki kad'an, idonsa akan hannunmu dake had'e waje d'aya akan kofin.
Nima saina kalli hannun, cikin sanyin muryar dabansan nayiba nace, “da sanyi fa”.
“Really?”.
Shiru nayi ban amsashiba, ya zame kofin a hankali, sannan ya koma jikin kujerar ya kwanta yana hard'e k'afafu.
6oyayyar ajiyar zuciya na sauke, bansan miyasa inhar Galadima zai kasance kusa dani daf irin haka koya kafeni da ido nake rikicewa ba, haka kawai sainaji jikina yana tsuma...
Yay wani luuu da idanu saboda ajiyar zuciyar da tayi, zo6on ya kai bakinsa ya kur6a kad'an, dad'insa ya sakashi lumshe idanu ya had'iye.
Da hannu yamin nuni da kujera, tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki na mik'e, harzan bar wajen naje ta nesa dashi saiya rik'o hannuna. Juyawa nai na kallesa, ya nunamin kujerar kusa dashi da ido cikin tsare gida.
Banida za6in daya wuce bin umarninsa, na zauna tamkar mai shirin guduwa da ance ar.
Zo6on yakuma sha yana kallona, kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru.
Ganin haka sai nace, “yaya jikin Abie? dasu Momma?”.
Yaji dad'in ganin ta damu da ahalinsa, ya ajiye kofin yana gyara zama, yace, “jikin Abie Alhmdllh munata k'ara ganin haske, duk since na gaidaki dak'yau”.
Nace, “ina amsawa”.
Daganan mukai shiru, kowa yana tattaunawa da zuciyarsa, Idan ka gammu saika d'auka wasu saurayi da budurwane, irin had'uwar farko d'innan😂.
Abimda na fahimta dai kamar yana tattare da damuwa ma, nad'an kallesa ta gefen ido, idonsa nakan yaransa, nace, “Abinci fa?”.
Maido da kallonsa yay gareni, yad'an yamutsa fuska yana girgiza kai.
Kallonsa nayi, cikin marairaicewar da bansan nayiba nace, “please mana yalla6ai, yanzu haka bakaci komaiba ka fito gida”.
Wani Abu dabaisan miyeba yaji ya tsarga cikin kansa har zuwa tafin k'afa, idonsa k'yam akan Munaya ko k'yaftawa bayayi, itama gareta hakanne, ta zuba masa ido batare da ta shirya hakanba, sai tsantsar tausayinsa dayake hangowa cikin idanunta, hannunta ya kamo cikin nasa, yana fad'in “kinaso naci?”.
A sanyaye na jinjina masa kai alamar eh.
Murmushin gefen baki yayi, ya matsa hannunta kad'an, “indai kinason naci akwai sharad'i”.
Batareda nasan mi bakina ya fad'aba nace, “kafad'a kona miye na amince”.
Kansa ya jinjina yana janye hannunsa, ya gyara zamansa yana fuskantata sosai, akan la66a ya furta, “saidai idan zaki bani da kanki”.
Babu shiri na waro manyan idanuna ina dafe baki alamar mamaki, ya had'e fuska yana ta6e baki da kwantar da kansa jikin kujerar. Yace, “Ashe ba sokike nacinba, kuma yunwa nakeji”.
Harga ALLAH inason yaci, dan na fahimci yanada buk'atar abincin, amma yana azabtar da kansa saboda bai yarda yaci na kowaba amasarautarsu, idan kuma ya fito inhar ba birnin gayu yajeba bazai ta6a cin komaiba inba ruwa ba harya koma gida kuwa...
Na sauke ajiyar zuciya, idona cikeda kwalla nace “to amma...”
Idonsa ya bud'e ya d'agamin hannu, amma baice komaiba.
Nima ban sake yunk'urin cewa wani abunba, na sakko daga kujerar na durk'usa a k'asa ina bud'e kulolin.
Mamaki ya kamani, dan ganin masa, a ina Munubiya ta samo masa haka? A lokacin da tasan zaizo yayi k'arancin da har za'ayi Masa. ganin babu mai amsamin tambayar na zuba hud'u a plate d'in, na d'ago ido na kallesa, Ashe shima ni yake kallo, idanu ya lumshe alamun ya Isa. Nima saina jinjina kai, kwanon da zansa miya na d'akko, amma saiya rik'e hannuna yana girgiza kai, na kalli plate d'in masar sannan na d'ago Na kallesa, ya kad'amin kai.
Fahimtar mi yake nufi da nayi saina zuba miyar gefen masar, sannan na mik'e da nufin komawa inda na taso, tiren abincin ya janye gefe, ya jawo center teble d'in a gabansa sosai.
Kallon teble d'in nayi shima na kallesa, saiya d'auke idonsa, a yanda ya janyo teble d'in inhar na zauna dolene k'afafunmu suke gogar juna, amma ya zanyi tunda na d'auki alk'awari.
Zama nayi, na d'ora plate d'in saman cinyata, na d'ebo masar da spoon na nufi bakinsa, baki ya ta6e yana girgiza kai.
Na dafe kaina irin naga ta kaina d'innan, na kallesa a marairaice, “yalla6ai to ya kakeso nayi please?, kaifa kace zakaci”.
Da d'an yatsa ya nuna hannuna. Cikin mamaki nace, “da hannu?”.
Yanda tai maganar tana zaro ido saiya so bashi dariya, amma ya had'iye kayarsa.
“O ni Munaya naga ta kaina”. Nafad'a a hankali.
A ransa yace zadai ki gani yarinya.
Dole na mik'e nakuma wanko hannuna a bayin falon Abba, na dawo, gyalena na zame dole na shinfid'a masa saman cinya gudun karna 6ata masa kaya, na fara d'ibar masar kamar yanda yake buk'ata na nufi bakinsa, saida ya kama hannuna sannan ya k'arasa dashi cikin bakin, ALLAH sai da tsigar jikina ta tashi, amma na daure nakuma d'ibowa, haka naita bashi har ya cinye, na bashi nama ya girgiza kai, alama namasa a k'ara?. Da d'an yatsa ya nunamin wai d'aya, bud'e kular nayi na d'auka, sauran miyar plate d'in ta isa, zan gutsura ya rik'e hannuna, a mamakina sainaga ya d'an ja hannun rigarsa sama ya saka hannu a plate d'in, idanu na waro da bud'e baki Dan mamaki, sai kawai naji hannunsa cikin bakina ya sakamin masa, ya d'agamin gira d'aya damin alamar inci, tamkar sokuwa haka na shiga taunawa, harna had'iye idonsa nakan bakina, saida ya rage saura lauma d'aya ya dakata da bani, na ida d'aukar laumar k'arshen na saka masa nima, ina niyyar tashi na wanke hannu ya maidani zaune, hannun dana bashi ya kamo yana sud'ewa, salon dayake lashe miyar saiya haifarmin da kasala, na rumtse idona harya gama sannan ya sakarmin hannu. Nima saina kama nasan na tsotse sannan na mik'e, ina toilet zan wanke hannuna zan d'ibo shima nakawo ya wanke sai na jishi a bayana, juyowa nayi na kallesa, ya mik'amin hannunsa. Bance komaiba na kama na wanke masa, na zuba masa ruwa ya kuskure bakinsa. Nidai gaba d'aya mamaki dukya nemi halakani.
Koda muka fito ina niyyar komawa inda na fara zama sai naji an fisgoni, jikinsa na fad'a, bance komaiba dukda naji zafi. Shima baice uffanba.
Lallai akwai abinda ke damunsa da gaske, hannuna na d'ora a kan k'irjinsa saitin zuciyarsa, ya bud'e ido sosai yana kallon hannun nawa, cikin aro jarumta nace, “Autan Momma mike damunka wai?”.
Murmushin dabai shiryaba ya saki, ya kalleni ido cikin ido yana fad'in, “kin rainani ALLAH kuwa, wannan autan bazai bar bakinkiba dai ko?”.
Murmushi nayi mai sauti, har hak'orana na bayyana, na had'e hannayena a waje d'aya alamar ban hak'uri, cikin langa6e kai nace, “tuba nake to na tsakkiya nefa kai ashe”.
Rankwashi yamin a kai, na dafe wajen dukda d'ankwali yasa banji zafiba sosai, amma na 6ata fuska ina k'ak'alo hawayen k'arya.
Gira d'aya ya d'age yana kallona alamar yadai?.
Na tura baki gaba ina fad'in, “da zafifa”.
Murmushi yayi yana kauda idonsa yana kallon yaransa.
Na yunk'ura da nufin sauka a jikina amma ya rik'eni, ba tare da ya kalleniba yace, “yakamata kisan kin girma”.
Bakin na kuma tunzurawa nace, “hu'im ina nan a babyna wlhy”.
Shi kansa baisan k'aramar dariya ta kufce masaba, ya d'an dara yana girgiza kai da kallona.
Ganin ya fara sakin jikinsa saina kuma cewa “Please yalla6ai bakada lafiya ne?”.
Tafin Hannunsa ya sanya saman kumatuna, a hankali tamkar mai rad'a yace, “mikika gani?”.
Na d'an kuma kwantar da murya ina janye idona daga cikin nasa, “Ba komai, kawai yanayinka ne ya nuna”.
Baice komaiba ya matso da fuskarsa gab da tawa ya had'e bakinmu, dukda na tsorata kar wani ya shigo ya gammu haka na barsa, yayi yanda yake so inhar hakan zai kauda damuwar dake ransa, nidai fatana na cika alk'awarin dana d'aukarma Momma a duk sanda na gansa cikin damuwa.
Saida ya gaji da kansa sannan ya bari tareda rungumeni yana sauke ajiyar zuciya, muryarsa can k'asan mak'oshi yace, “haka kike son ganina”.
Kaina na girgiza masa, ya d'agoni da sauri yana kallona, yace, “to yaya?”.
Murmushi nayi nafad'a k'irjinsa ina 6oye fuskata saboda kunya, shima saiya saka hannuwansa ya zagayeni yana murmushin, a hakanla ya furta “Thanks”.
Bance komaiba, amma naji dad'i daya godemin.
Kiran wayarsa da akayi ya sakani tashi daga jikinsa, zan tashi gaba d'aya ya rik'eni, a haka yay picking call d'in, na fahimci da papi yake waya, dukda kakansa ne yanda yake magana cikeda tsantsar girmamawa saiya birgeni, *_Mai dawakai_* danaji yana ambata da bayanin d'ansa mai suna Badi ne yaja hankali na, tsaf na fahinci zancen dukda bansan mafariba, yakuma yanke maganar bai k'arasaba yana fad'ama papi sai yazo zasu k'arasa zancen.
Yanke wayar yayi yana huremin ido saboda kallonsa dana keyi, tunda ya fara wayar.
K'asa nayi da kaina dan naji kunya ya kamani ina kallonsa, ya ajiye wayar yana fad'in “Zamukai Abdurrahman asibiti ne?”.
Kaina na girgiza masa. nace, “A'a aiya warke bama sai an kaisa ba”.
Yace, “Okay”. Idonsa akan yaran, Abdurraheem ya fara motse-motsen tashi, sauka nayi a jikinsa nakoma gaban kujerar na durk'usa ina d'an bubbuga bayansa, dan banason ya tashi, inhar ya tashi saiyasha nono, sauran kuma suma duk tashi zasuyi, bada nono a gaban Galadima shine abinda nake gudu ni kuma.
Shikam tsura musu ido yayi cikeda sha'awa daga ita har yaran, ya d'auki wayarsa yamusu hoto batare da ta saniba.
Saida naga ya koma barci sannan Na dawo kujerar dana fara zama, shima zamansa yagyara yana kallona, magana yakeson yi amma yanata juyata a zuciya, nidai bance dashi komaiba, saida ya gama k'asaitarsa da basarwa sannan yace, “Abba fa?”.
Nace, “yayi tafiya yau kwana biyu”.
“zuwa ina kenan?”.
“wlhy ban saniba, amma miya faru?”.
Kansa ya girgizamin alamar babu komai, yad'an furzar da huci yana kallona agogon hannunsa. “Shikenan ni zan wuce, zan iya dawowa a kowane lokaci inhar Abba ya dawo”.
Kaina na jinjina masa, ya mik'e, nima saina mik'e ina fad'in “yaa Sauban fa?”.
Bai tankaminba saida ya duk'a yayma yaransa kisses a kumatu sannan ya d'an kalleni ya d'auke kansa, “Tare muka dawo, amma zai wuce masarautar su papi gobe, dan a can zai zauna harya gama”.
“ALLAH ya bada nasara”. Nafad'a ina sauke ajiyar zuciya.
A kan la66a ya amsa da amin.
Harya kusa nufar k'ofa nace, “bakace komai game da maganarmu bafa”.
Cak ya tsaya amma bai juyoba, a haka yace “wace magar?”.
Wani yawu na had'iye da k'yar ina fad'in, “Maganar rabuwa, nifa gaskiya bazan komaba”.
Saida yaja kusan seconds 20 kafin ya juyo yana fuskantata, kallon da yakemin yasani janye idona daga kallonsa, cikeda k'asaitarsa yatako ya dawo inda nake tsaye, hannayensa ya cusa cikin aljihu yay matuk'ar d'aure fuska, cikin izzarsa yace, “wai nikam miyasa kikeda naci?”.
Nima fuskar na tamke. Nace, “Neman y'ancina nake, tun farko a wannan tubalin ka gina auren, mizaisa kuma lokacin rugujeshi yayi bazakayi hakanba?”.
Lips d'insa ya ciza yana kallona da k'ank'ance idanu, cikin salon Basarwar tasa yace, “So what idan nine na gina a haka d'in? Kinsan dai bazaki ajiyemin yara ba koda abinda kikeson ya kasance, dan yarana bazasu sha madaraba bayan sunada abinci”.
“Humm” na fad'a cikin takaici. na gyara tsayuwa idona na cikowa da kwalla, “Yalla6ai karka manta a randa na kwana biyu gidanka da bakiknka ka tabbatar min baka zalunci? daga ni har kai mun amince cikin yarannan ya zone cikin k'addarar dabamu shiryama zuwanta ba, to mizaisa kuma zuwansu duniya yazama salon tauye hak'k'ina? Na amintane da aurenka domin warware k'ullun da akaimin da wanda yake kan mahaifina, bawai dan bansan y'ancin kainaba ko darajata, idan har nice a matsayin Amaturrahman zakaso wani ya aureni a matsayin auren shekara d'aya ko biyu domin cikar wani burinsa ya rabu dani?, addininmu da al'adarmu duk basu koyar damu hakaba, anayin aurene domin ibada, saboda bautar ALLAH ne, sannan ana ginashine bisa tausayi da rahama, inhar zuciyarka bazatayi dad'iba a matsayinka na mahaifin Amaturrahman idan hakan ace akanta ta kasance, to ya kake tunanin randa nawa mahaifin yasan gaskiyar matsayin nawa auren zaiji?, tunda nataso nake d'and'anar zafi da d'aci na zamantakewar rayuwar gidan yawa, taya zanso saka rayuwata a walagigin kila wa kala, na shigo wannan yak'inne domin neman y'ancin kai badan ribantuwa da ganima ba, amma lokacin dana wayi gari da abinda ban shiryamawa ba a cikin jikina haka na hak'ura na kar6a da hannu biyu saboda k'ok'arin cinye jarabawa, miyasa kakeson yin wasa da rayuwatane wai? Duk motsi dai yaranka! Yaranka! Karka manta nimafa y'ar wasuce, kamar yanda kakeji haka suma sukeji akaina, inason nima nayi aure na zauna tamkar kowacce mace a gidan mijinta, na fidda hak'insa da ALLAH ya wajabta min, shima ya fidda min nawa da ALLAH ya wajabta masa......”.
Hannu ya d'agamin alamar ya isheshi haka, yakuma matsowa gabana cikeda izza yace, “mikikeso yanzun?”.
Nace, “sanin matsayin aurena, inhar yaranka ne zan muku sadakar shayarwa na wata shida na yayesu nayi aurena da mijin dazai soni ya k'aunaceni domin ALLAH”.
Bakinsa ya ta6e yana cije lips, jijiyoyin kansa duksun mimmk'e saboda 6acin rai, cikin takaici yace, “Yarinya har abada babu shegen namijin daya Isa na k'etara gona shima ya k'etarata, koda kuwa wannan gonar ta jinginace, ko ayanzu nabar duniya wani yayi hakan ban yafeba, duk gonar dana ra6a tawace ni kad'ai koda banyi noma a cikinta ba, wannan yazama first and last da zaki kuma kawomin irin wannan maganar, kodan kinga ina k'yaleki ne shiyyasa kike d'aukata wani sauna kiringa min zancen wani banza can daban, Munaya karki yarda na nuna miki a salin true color d'ina wlhy, ina kuma gargad'arki a karo na k'arshe”. ‘ya k'are maganar da bugamin yatsunsa biyu saitin fuska ya fice abinsa’.
Baki na ta6e ina bin inda yabi da harara, sannan na saka gyalena na goge hawayen dake zarya a kumatuna nai kwafa na fice abina nima nabar yaran.
**************************
Tunda ya fito Muftahu ke binsa da kallo, harya bud'e mota ya shiga baiko kalli Muftahun ba shi.
Dama shine ya kawoshi, amma yana ajiyeshi ya koma saboda wani aiki daya bashi, dawowarsa kenan yana k'ok'arin kiransa yace zai shigo su gaisa da Munaya shine yafito a fusace.
Baice dashi uffanba ya bud'e motar shima ya shiga ya tada suka tafi, saida sukayi nisa da tafiya sannan Muftahu yace, “Ranka ya dad'e wai mike faruwane?”.
Shiru yamasa yak'i tankawa, shima Muftahu sai yaja bakinsa ya kulle ya cigaba tuk'insa.
Sai jera tagwayen tsaki yakeyi, Muftahu ya kuma kallonsa sannan ya maida hankali ga tuk'insa, ya kuma rik'e sitiyarin yana fad'in “ALLAH ya huci zuciyarka ranka ya dad'e, idan kana ganin bazaka juri zuwanba kace ta dawo mana kawai”.
Cikin jan wani tsakin yace, “inhar taci gaba damin zancen wani wawa lallai zan datse harshenta wataran”.
6oyayyan murmushi Muftahu yayi, a zuciyarsa yana jero hamdala wa ubangiji, dan babu abinda yake hange tattare da galadima sai tsantsar kishin matarsa, dukda baisan miya had'asuba yaji dad'in hakan, koba komai yanzu ya fita daga damuwa da fargabar rabuwar wannan auren. cikin son kuma fahimtar wani Abu yace, “to amma ranka ya dad'e yazamuyi idan lokacin rabuwarku yayi kenan? Kasanfa alk'awarin da mukai mata”.
“Oho! Maka”. Galadima ya fad'a cikin tsananin fusata.
Da k'yar Muftahu ya iya had'iye dariyarsa, bai sake cewa komaiba har suka isa gidan baffi, dan karya mazgeshi a banza. Muftahu ya fita domin nema masa ison shiga ciki, a lokacinne yasamu yay dariyarsa mai isarsa, lallai Galadima akwai kishi, tashin hankali, irin wannan ajiyar zuciya haka.
***************************
Tunda na shiga Munubiya take bina da kallo, ta ce, “ina yaran?”.
“Suna can”. ‘nafad'a ina shigewata ciki’.
K'ala bata sake cewaba tafita abinta.
Har dare ina fushi, nak'i kula kowa, innarmu yitai kamarma batasan inayiba, dukda batasan mike damunaba, Munubiya ma shareni tayi, sai laraba Ce ke tambayata kodai banajin dad'ine?, nace a'a.
__________________________
Saida Muftahu ya raka Galadima har falon Baffi sannan yace zaije ya dawo kafin su gama.
kansa kawai ya d'aga masa amma bai tankaba.
Fitar Muftahu babu dad'ewa baffi ya fito shima, zama yay idonsa akan Galadima, dan ganinsa cikin damuwa, “d'an baffi miya farune haka?”.
Galadima yafara k'ok'arin saita kansa cikin k'ak'aro murmushi yace, “Babu komai Baffi”.
Duk da bai gamsu ba saiya k'yaleshi, dan maybe ba huruminsa baneba, yace “Alhaji Rabilu yakai maka bak'o ko?”.
“Eh d'azunnan muka rabu dasu, abindama ya kawoni kenan, dan ina ganin insha ALLAH mun sami dukkan bakin zaren, zan fara aikina kawai”.
Murmushi baffi yayi yana gyara zamansa, yace, “eh to ansami bakin zare kuma ba'a samuba, dan yanzu binciko Wanda Camera d'in take hannunsa shine babban aikin dake gabanmu, dan itace babbar hujjarmu bayan d'unbin hujjoji da muke dasu a k'asa”.
Galadima ya sauke ajiyar zuciya yana jinjina kai, “hakane Baffi, amma akwai dai wasu y'an bayanai danake dasu a hannu yanzu haka, sai dai banida tabbacin dai-dai ne? Kokuwa akasin haka, amma kama SD da mukayi shine zai fito da gaskiyar hasashen nawa”.
“To shikenan, ALLAH yasa muji alkairi”.
“Amin, saidai ni a bayanin Baba Rabilu akwai abinda har yanzu yakemin rawa a zuciya”.
“tofa, minene kenan?”.
“Maganar siyasa dayacemin ya shiga a wancan shekarun, bayan kuma lokacin mulkin sojane, kenan wace siyasa sukayi?”.
Baffi yay murmushi, “wato abinda na fuskanta anan shine, yasako kalmar siyasa ne domin mu mufasa sauran bak'in da kanmu, amma tabbas a wancan lokacin babu wata jam'iyyar siyasa, wayema ya Isa d'aga murya akan mulkine? Saidai bincikena ya nuna Dalilin kafa Group nasu tanderu yanada nasaba da son kafa mulkin farar hula, wato sunason mulki yabar hannun sojoji kenan, saidai a 6oye sukeyin dukkan abinsu, har suka ringa jawo ra'ayin mutane mabanbanta a cikin tafiyar tasu, abinda na kasa fahimta nima shine, shin sunjawo Alhaji Rabilu ne dansu tabbatar Camera na hannunsa? Kokuwa shine yakai kansa garesu domin lek'en asiri? Dole cikin biyunnan a samu d'aya, kodan yunk'urin kasheshi da suka saka Darma yayi”.
Galadima dayay shiru yana fassara zancen Baffi dak'i-daki ya shiga jinjina kansa alamar gamsuwa da bayaninsa, zuwa can yace, “Baffi ka bani kwanaki biyu zanyi bincike insha ALLAH, dan zan tattauna da SD da kuma Harun, sannan akwai yaron da aka saka yay aikin da aka buga a jaridarnan, shima inason yazo hannuna insha ALLAH ”.
“ALLAH ya cigaba da dafa maka, Yakuma tsareka da dukkan sharri, lallai ka ringa kulawa, dan yanzu dukkan wata hanya da zasubi domin cuta maka sun tanadeta, karka d'auka suma basa bibiyar lamarinka kamar yanda kake bibiyar nasu, dan ranar naga Alhaji Abdul- Naseer da wani masanin Computer, saidai shi bai ganniba, nasha jinin jikina kwarai da gaske, amma nikam inamason tambayarka, minene alak'ar Surukinka da senator halluru ne?”.
“kamar dai abokinsa ne baffi”.
“Ok! Ok! To lallai ka sanar masa ya lura, dan Senator Halluru yaronsu tanderune, za'a iya bi ta hanyar surukinka a 6ata mana aiki, tunda sun san akwai alak'a tsakanin kai da shi”.
“wannan gaskiyane Baffi”.
Sun cigaba da tattaunawa akan matsalolin da ayanzu zasu fuskanta, baffi na kuma bama Galadima dabaru a shara'ance Wanda bazai aikata abinda shima zai rufta ba.
Sai dare ya koma masarauta, yinin yau gaba d'aya a tsaye yayisa, shiyyasa duk jikinsa ciwo yake masa, yanayin zirga-zirga amma ba irin wannanba mai cikeda cajin kwakwalwa da rikitar tunani. Ga maganganun Munaya dake cin ransa, ya tabbata duk gaskiya ta fad'a, hakan datake yana kuma tabbatar masa da tasan darajar kanta, inda watace shiru zatayi sai yanda yaso yi da ita, duk kuma abinda zai mata koda Mara k'yaune zata shanye saboda kasancewarsa d'an wani, amma duk da kasantuwarta mace kuma wadda take k'ark'ashin mulkinsu ALLAH bai sakama zuciyarta tsoro ko kwad'ayi ba, itadai kullum burinta shine asan darajarta da kimar ahalinta, sa6anin y'an matan yanzu da duniyar Ce kawai burinsu da son ganinta a tafin hannunsu, auren mai kud'i ko mulki, mai k'yau ajin farko, na nunama k'awaye da yin alfahari a duniya, yasan darajarta kona iyayenta wannan ba matsalarta bace, yanada addini ko kula da addinin shiyya Sani, son gaskiya yake mata ko albarkatun jikinta yakeso batada matsala, ya zube a kujera yana sauke tagwayen numfashi.
Sauban dake zaune yana kallo yakuma kallonsa, yayansu na bashi tausayi, saidai shi taurinkai da rashin yarda da kowansa ke had'ashi dashi, amma ta wani fannin yakan kalli hakan a matsayin gaskiyarsa, dan massarautar tasuce abar tsoro, ba kowane abin yardaba, yanda zaka tantance na kirkin shine mai wahalar kuma.
*********************
Na kasa hak'uri da danne maganganun Galadima, hakanne ya sakani yanke shawarar tambayar Munubiya kota Sani, saida mukai shirin barci dukda sharenin da takeyi nadai danne nawa Fushin na zauna kusa da ita tana shayar da Meenat data tashi. Kan yarinyar na shafa sannan nace “Munubiya in tambayeki mana please?”.
Kamar bazata kulaniba sai kuma ta kalleni. Tace, “Ina saurarenki”.
Ajiyar zuciya nayi ina gyara zamana, nace, “dan ALLAH idan namiji yace gonarsa mi yake nufi?”.
Jimm tayi alamar tunani, ta kwantar da meenat tana fad'in “Matarsa”.
Da mamaki na kalleta, yayinda wani sanyi ya ratsa raina, amma na danne.......
Ta katseni da fad'in “Munaya ki fito fili ki sanarmin abinda ke faruwa, kinsan banason kwana-kwana, sirrinki keda mijinkine kawai a rayuwa bazanso saniba, domin ALLAH ya haramta bud'e wannan, saikuma yankin sirrinsa na rayuwa Wanda yarda da matarsane kawai zaisa ya fad'a mata, shima wannan kirik'e masashi, amma Munaya na fuskanci har yanzu babu dai-daito tsakaninki da mijinki, duk da kin sanarmin da manufar aurenku nazata darajar zuri'ar data shigo tsakkiyarku zai kawo muku sasanci Ku manta da wani auren Contract, duk da na fahimci mijinki jinin mulki na yawo a jikinsa, danne Abu a rai da basar dashi tamkar jinin jikinsa yake, kekam nasan halinki mutumce maison a damu da ita, sannan a nuna mata komai a aikace da furucin baki, kema danaki jinkan Wanda bansan gidan uwarwa kika samoshiba, amma mike wakana a duniyar aurenki? Mikuma kuke shiryawa keda surukarki?”.
Shiru nayi nakasa magana, dan banso fitar da wannan sirrinba har zuwa lokacin da Momma ta bani, duk da nima rashin sanarma y'ar uwata yana damuna, dan bamu ta6a 6oyema juna wani abuba, ko akan aurena daga baya kasa daurewa nayi na sanarmata, duk da na 6oye matanne saboda gargad'in da baba mai kanwa yamin......
Kwanciyarta tayi tana cewa, “idan kinga bazaki iya fad'aba kibar abinki arai yayta cinki, daga k'arshe idan kika rufta auren ya tsinke kekika Sani, kinsandai minene wannan gidan da irin mutanenen cikinsa, dama kullum burunsu kenan”.
Idona cike da kwalla na kamo hannunta, “kiyi hak'uri sweetheart tashi muyi magana”.
Munubiya taiyi kamar ta shareta saikuma ta tashi tana share mata hawayen dake bin fuskarta.
Ta gyara zamanta tana fad'in “wato Munubiya.................🤫✍🏻
Kumuje zuwa page nagaba my guys😉🤩.
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu👏🏻😭_*
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*
*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BOOK 3_* 👉🏻 1⃣3⃣
..............“Wato Munubiya abinda yasa kikaga inata 6oye miki shine, bansan manufar mahaifiyarsa ba kai tsaye, nidai bayan tabani tarihin masarautarsu takuma rok'eni nabama Galadima gudunmawa wajen saka idanu akan motsin kowa dazai mu'amulanceni, abinda ta lura shi yafi maida hankalinsane ga mak'iyan waje, gani yake kamar a masarautarsu babu mai iya cutar dashi. tace min Galadima bashi da yarda ko kad'an, sannan mutumne mai zama akan ra'ayin kansa, tankwarashi sai ita da baya iya bijirema umarninta”.
“Na damu kwarai da gaske Munu.. Dan rayuwa da irin mai wannan halin yanada wahala, musamman mutum mara yarda, wlhy nadad'e a gidannan bai bar zargin an turoni Na cutar dashi bane, saida Momma tafara koyamin dabarun zama dashi, tace nadaina jin tsoronsa, inhar yafad'amin magana Na daurema zuciyata Na dinga maida masa murtani, a tak'aice dai nake masa tsiwa. A lokacin da taimin wannan maganar abin yaban mamaki, Yaya uwa za tace aringama d'anta rashin kunya ko rashin raga masa?, kema kinsan bawai bazan iya baneba, amma yanamun matuk'ar kwarjini, bansan kuma miyasaba nakejin shakkarsa a zuciyata, har gobe idan yamin Abu zan maida masa murtani wlhy saina dage saboda tsoro. Saida zamanmu yad'an fara nisane Na fahimci abinda take nufi, inda bana nuna masa banida tsoroba zansha wahalar zama dashi, sannan bazai ta6a aminta dani ba ya saki jikinsa, zaita d'aukatane a y'ar lek'en asiri, Dan babu abinda ya tsana irin karinga masa Abu kana nuna tsantsar biyya da kwantar masa dakai, shi a wajensa kazo cutar dashine kawai. Maganar zuwana wanka itace tadage akan sainazo, sannan tace duk zuwan da zaiyi wajena Na nuna masa cewar. nifa bazan koma gidansa ba, dan bazan iya da hallayarsa ba, tadai nunamin dukkan dabarun dazanbi Na dinga zungurinsa da zancen, to ni wlhy ban fahimci manufartaba, tunda nasan babuma Wanda yasan mafarin ginin auren namu, daga ni sai shi, saikuma ke dana sanarmawa. yau kuma namasa zancen rabuwarne da nuna masa zan shayar dasu Abdurraheem ne Na wata shida nayi aurena nima, shinefa yahau kaina da bala'insa, wai babu wawan daya Isa shi ya k'etara gona wani yako ra6eta, koda kuwa ace gonar ta jinginace, inkuma hakan ta faru kobaya numfashi bai yafeba”.
Munubiya ta zaro ido waje Dan mamaki, saikuma ta tuntsure da dariya harda rik'e ciki, galala nayi ina kallonta, danni banga abin dariya ananba.
Saida tayi mai isarta sannan ta zauna dak'yau tana fad'in “yi hak'uri sweetheart, wlhy mijinkine yabani dariya, amma anya kuwa mahaifiyarsa batasan manufar aurenkuba?”.
“Ta ina zata Sani Munu.., shidai wlhy nasan bazai fad'aba, Dan nakula yanada masifar zurfin ciki, balle yasan abinda yay bamai k'yau bane, tunda a al'adarmu da addininmu hakan ba tsarinmu bane, nadad'e ban iya fahimtar matsalarsaba, saikuma naita tambayarsa yamin banza, sai daga bayane naringa Neman dabarun samo kansa harya sanarmin da damuwarsa”.
“Eh bank'i ta takiba, amma a ganina koshi bai fad'a mataba kina ganin Muftahu bazai fad'aba? Nifa tun pills daya zuba muku nafara zargin anya bada k'yak'yk'awar niyya yayi hakaba?”.
“Kai Munu.. ALLAH bana tunanin haka, gani nake kawai itama da tata manufar, Dan batason halayyarsa ta shiru-shiru d'innan da k'untata kansa dayake akan yawan damuwa kodan ciwonsa, Dan tace min ciwonsa Na yawan motsawa a baya saboda yawan shiga damuwa da yakeyi, gashi bazai yarda kowa yasan matsalarsa ba saboda tsatstsauran ra'ayinsa, itakuma bataso Dan abaya yanda kikaga Sauban k'animsa da faran-faran haka shima yake, amma tunda ya fahimci miya kwantar da mahaifinsa saiya canja musu gaba d'aya, maganar ma saiya gadama idan kayi yake amsaka, abinda Na lura yanzu kuma wannan abun yarigada yazame masa jiki gaskiya”.
“dukna fahimceki Munaya, amma abinda Na lura kamar wata alak'a mai k'arfi da kusanci takeson ginawa tsakaninki dashi, Dan babu wata uwa dazatasa matar d'anta ta ringa ma yaronta rashinkunya, itakuwa tasan halin d'anta ciki dabai, tanada dabarun dazata d'oraki domin shi su k'ayatar dashi harya ringa kallonki a matsayin mata ba auren wucin gadiba, dukkan maganganun daya fad'a miki d'azun wlhy Na mutumne mai nuna tsantsar kishi, ALLAH ma yasoki dabakizo da kumburarriyar fuskaba wlhy”. ta k'are maganar da sanya dariya.
Harara Na zuba mata ina fad'in “nikuma kamar wata sokuwa saina zauna ya dakeni, danma gaskiya shiba mutum bane mai yawan saurin hannu, saidai k'asaita da shariyar tsiya, kaita magana yayi tamkar bai jikaba”.
“Yo Sweetheart ai mulkin kenan ko, wannan shine ake kira sarautar, idan bashida wannan izzar da k'asaita lallai baicika jinin basarakeba, shi nashi ai da sauk'i tunda yasan darajar d'an Adam. Amma lallai ki godema ALLAH da samun suruka irin wannan, to amma ke kina sonsa yanzu?”.
Harararta nayi, nazame Na kwanta batareda Na bata amsaba, ta d'akamin duka a cinya tana fad'in “Munafuka kema sonshi kike, wannan jan ajin naku dukshi ke cutarku, shi mulki ya hanashi ya fad'a, ke shegen jan aji yahanaki ki nuna masa, basai kuyitayiba har yaranku su taso su ganku a haka”.
Baki Na murgud'a mata ina Sosa wajen data dokenin, Dan naji zafi, cikin harara nace, “ai ba a haifi namijin dazan fara furta masa ina sonshiba koda ace son nasa zai halakanine, k duk taurin kai da miskilancin Yaa Marwan ince saida yace yana sonki sannan kika amsa masa?, saini kikeson Na zubar da tawa darajar, salonma ya d'auka kwad'ayine ya sakani hakan, zai ru6e kuwa inhar jira yake sainace Sameer ina sonka, bank'i idan naga zan iya nabika ta wata hanyarba, amma shida yace auren Contract shine zai dawo ya gyara kuskuren da yayi da kansa, shiyyasa nake son canja masa tunaninsa ta hanyar tunatar dashi yasan mace tanada daraja, ba'a sakata lokacin da akaso sannan ayi tunanin cirewa lokacin da akai niyya, wadda batasan darajar kanta bace zata amince da hakan, nikuma bana cikinsu danba Auren kwad'ayi nayiba”.
Munubiya tayi dariya tana jinjinamin, “yayi k'yau gimbiya matar Sarkinmu mai jiran gado, wlhy kin burgeni dan wannan shine kima, amma dai a sassautama galadimanmu, Dan naga alama shimafa ya zurma fad'arce kawai mai wahala a harshensa, amma mizai hana mubi wasu dabarun Dan bud'e bakinsa”.
“babu wasu dabaru dazamubi sweetheart, Dan nidai bazanbi ta hanyar talla da jikina ba a gareshi danya soni, randa Na tsufafa? K'yawun jikin ya 6ata ko Na nakasa?, bazanbi ta yaudaraba ko wani kwarkwasa, randa yaga wadda yakeso tsakaninsa da ALLAH fa? komai zan masa bazai birgeshiba, Dan soyayya ta gaskiya daban take, baruwanta da k'yau ko k'yale-k'yale, zandai iya k'yautatama zuciyarsa domin dukkan zuciya tanason mai k'yautata mata, amma son gaskiya nakeson mijina yamin, bana k'yalek'yalen duniyaba, ko tsufa ya kamani bazai bar sonaba, ko nakasa ta kamani bazai bar sonaba, ko babu dukiya tattare dashi bazan gujesa ba, idan ciwo ya kamani koya kamashi zamu tattali juna saoda tausayi da rahamar dake cikin Auren da soyyar gaskiya da mukema juna, ko kishiya yatashimin nasan son gaskiya yakemin bazan ta6a saka kaina a matsananciyar damuwa ba tunda inada yak'ini akan son gaskiya yakemin, bazai ta6a tozartaniba, sannan ban Isa hanashi yaso matarsa ba Dan ni yana sona, nafison amin komai tsakani da ALLAH bada yaudaraba kema kinsani, Dan haka muyitayi inhar bai gajiba nima bazan gazaba”.
“Duk mace haka yakamata tasan darajar kanta, takumayi abinda mijinta zai sota son gaskiya Munaya, wannan k'arancin soyayyar ta gaskiya da Muke fuskanta ayanzu shineke yawan ruguje rayuwar aure, mafi yawan mazan sukanso macene domin wata halitta ta jikinta, dasun sami nutsuwa dake kuma shikenan haskenki ya dusashe a idanunsu, wasu kuma Matan mai dukiya ne hangensu ko k'yau, da zarar mijin yazo babu saikiga wuta ta tashi, kokuma bashi dashi dama duk k'aryane, dakinje bakiga abinda kika aureshi danshiba babu sauran zaman lafiya kuma, gaskiya muna cikin matsala yanda taron biki yake a wannan zamanin kawai ya Isa ruguza dukkan albarkar aure, amma ni dazakiji ta tawa tunda shima yana sonki kubar wannan 6oyewar mana”.
“Munu, idanfa bai canjaba nima bazan canjaba, bakinsa daya furta shi nakeso ya gyara da kansa”.
“lallai to sai kiyita 6oyewar, idan ya nemi kasheku duk zaku fiddoshine kowama yaji, ai nama godema ALLAH da Muftahu dan ta silarsa ALLAH yamuku dabaibayi da yarannan, Ubangiji sarkin hikima kenan, naga Wanda zai iya barma wani ai”.
Banza namata nayi kwanciyata, harma barci 6arawo ya saceni. Munubiya ta d'auki wayar munaya tana murmushi, tayi abinda zatayi ta ajiye mata abarta itama ta kwanta.
★★★★
Galadima daketa juye-juye a gado abin duniya dukya ishesa saijan tagwayen tsaki yakeyi ya kalli wayarsa datayi alamar shigowar sak'o, harzai share dai saiya kasa, dan numbers d'in cikin wayar duk masu muhimmancine.
Jawo wayar yayi ya danna ta kawo haske, hoton y'an uku ya bayyana a screen d'in, saida yad'an ja wasu Seconds yana kallon yaransa sannan ya bud'e massage d'in, ganin wadda ta turo sak'on sai mamaki ya kamashi, Munayar da inhar bashine ya kirataba bata ta6a d'aukar waya ta kirashiba ita, amma yau itace harda message? Dukda baiyi tunamin samun mai dad'iba haka yabud'e dai, yasan bai wuce maganar data damu mutane da itaba...
_Ina fatan ka koma gida cikin aminci da farinciki? Yaranka namaka fatan alkairi da addu'ar samun k'yak'yk'yawar Nutsuwa mai tarin hak'uri._
ya dad'e idonsa akan wayar yana kuma bitar sak'on, baisan murmushi ya su6uce masaba, watoma yaransa ba itaba?, kai jan ajin yarinyarnan yayi yawa, da ace agidan sarauta ta fito lallai bayi da hadimai sunga takansu, ya ajiye wayar yana gyara kwanciya, jiyay zuciyarsa tayi sakayau, dandanan barci ya d'aukesa, dama video call yayi dasu Momma, dan tun bayan daya sauka bai kuma kiransu ba saboda yau ya yini busy, ga tunani sunma kansa yawa, Munaya tagama saitashi yad'an samu nutsuwa amma shine takuma hargitsoshi da abinda zuciyarsa bazata iya d'aukaba.
..............
*_Washe gari_*
Munaya dai batasan minene ya faruba, dan Munubiya goge sak'on tayi bayan ta tura, da safe kuma ko alamar tayi wani Abu bata nunama Munaya ba.
Wajen tashin hantsi saiga Aunty Salamah tazo, cikin farin ciki duk muka mak'alk'ale mata, ta rik'e baki tana fad'in “oh ni, ALLAH yabani y'ay'an da basu San sun girmaba”.
Innarmu tace, “wlhy kuwa salama, baki moreba kam”.
Laraba dai tanata musu dariya.
Kayan gyaran jiki Na musamman Aunty salamah ta kawo musu, takuma bisu da gargad'in wlhy kowa tazage tayi, harda rok'on laraba ta saka musu idanu Dan ALLAH.
Gaba d'aya yau a gidan tama yini, hakanne ya d'aukema Munaya damuwar data tashi da ita.
★★★★★★*★★★★★★
Tunda yadawo salla ya koma barci, saboda jiya bai wani samu yin isasheba, wajen 10 ya farka, brush kawai yayi yazo ya zauna yana hada wasu takardu, sosai aikin ya d'auke hankalinsa saboda muhimmancinsa, sauban datun d'azun yay shirin tafiya yagaji da jiran fitowar Galadima Dan haka yazo yaymasa knocking, Dan yanason biyawa wajen Munaya kafin ya wuce.
Galadima dake zaune bakin gado ya baje takardu yana kuma rubutu a jikin wasu ya d'aga kai ya kalli Computer d'in dake hasko masa dukkan CCTV camera's d'in sashen nasa, ganin Sauban ne sai ya d'auke idonsa yace ya shigo.
Zama sauban yayi saman stool d'in mirror ya gaida Galadima, hankalinsa nakan aikin dayake ya amsa. yace, “Dama katashi?”.
“Wlhy Yaya tun d'azun Na tashi, naga baka fito baneba gashi inason kafin Na wuce nabiya Na gaida Aunty gimbiya naga my Triplet's kuma”.
Galadima baice komaiba, sai had'e takardun gabansa daya shigayi, Sauban yamatso bakin gadon yana tayashi, saida suka gama tsaf, ya shiryasu cikin wani k'aramar briefcase sannan ya kalli Sauban dake zaune, “Mik'omin System d'incan”.
Sauban yad'an marairaice fuska cikin tausayawa. Yace, “haba yaa Sam kad'an huta mana”.
Da mamaki Galadima yace, “to idan Na huta kaine zakamin aiki?”.
Girgiza kai Sauban yay alamar a'a. Ya tashi ya d'ako masa.
Kar6a Galadima yay yana girgiza kansa saboda ganin yanda Sauban keta 6ata fusaka, a zuciyarsa yace bazaka fahimtaba yaro.
Batare da sake kallonsa ba yace, “yanzu mikake buk'ata kenan?”.
“yaa Sam kud'in wajenafa basuda yawa”.
“Humm” Galadima ya fad'a hankalinsa akan aikinsa. yace, “Aikai dama baku iya tausayin kud'iba kai da Samha, mutum yarasa uwar mi kuke saya? Kaje zan turo maka, Dan yanzu kama nima buk'atar kud'in nakeyi, gashi sunyi cak, nasan kuma daga inno har papi idan suna dashi baka zasuyi”.
“shikenan yaya, amma Dan ALLAH ko kad'anne”.
“ka duba cikin kayan dana cire, maybe ka samu”.
“yauwa Yaa Sam d'inmu. ALLAH ya k'ara girma”.
Galadima Dai baice komaiba, ya kwaso kud'in duka yana fad'in “na kwashe duka?”.
Kai kawai Galadima ya d'aga masa.
Sauban yazo ya rungume Galadima ta baya yana godiya, sannan ya sakesa. Murmushi Galadima yayi yana fad'in “ALLAH ya gyaraka Sauban”.
“Amin yayana”. Sauban ya fad'a cikin dariya.
Sunyi sallama ya tafi akan cewa shima saiya zo, yakuma gaida su papi.
*****************
Munaya taji dad'in ganin Sauban, sund'an ta6a hira sannan yamata sallama ya tafi tana shaida masa ya gaida mata su inno da k'yau, har k'ofar gida ta rakoshi, dukda dai bata fitoba iyakarta jikin gate, saida yashiga mota sannan ta koma ciki, tanamai jin k'aunar ahalin Galadima har cikin ranta.
************\/**********
Galadima na shirin fita kira ya shigo wayarsa, saida yagama d'aura belt d'in da yakeyi sannan ya matsa gaban gadon ya d'auki wayar, a dai-dai lokacin kiran ya kuma shigowa, ganin Sir Isa saiya d'aga.
Ko gaisuwa basuyiba yace, “yalla6ai kaga kuwa aika-aikar da ake neman mana?”.
“Aika-aika kuma? Tami?”.
“Tabbas ansaka wani yamaka kutse cikin Computer, Nazatama kagani?”.
Gaban Galadima ne ya fad'i babu shiri ya yanke wayar, system d'insa ya jawo ya zauna bakin gadon, “innalillahi...” Yashiga ambata zufa Na tsatstsafo masa saboda abinda yagani Na shirin faruwa, ya manta daya gama aiki bai saka security a matakin farkoba, saurin sakawa yayi, dukda yasan babu tabbacin zai iya dakatarwa ahakan kawai da yayi, ya ajiye lap-top d'in yana mik'ewa da hanzari, sauri d'aukar rigarsa yayi ya saka, yana saka bottoms d'in a tsananin hanzarce, haka dai ya k'arasa shirin a gaggauce, ya d'auki abinda zai d'auka yafito, babu gaisuwar Wanda ya amsa, hannu kawai ya d'aga musu yanufi mota yashige da kansa yaja ya fice daga masarautar, Wanda yatafi kiran Sarkin Mota duka iso tare, duk mamaki ya kamasu, yau Galadima da kansa yaja mota, anya kuwa lafiya?.
Ganin wannan bazai musuba sarkin mota ya shiga mota shima ya bishi.
Yana tuk'i suna waya da Vijay abokin aikinsa Na India, a haka ya iso gidansa dake bayan gari, kusan lokaci d'aya suka Isa da sarkin mota, ganin Galadima zai fita ya bud'e gate da kansa, shi saiya kashe motar dayake ciki da sauri ya fito yazo ya bud'e masa ya shige, bai bisaba, tunda Alhmdllh yaga dai inda yazo, maybe kuma baya buk'atar kowa a wajene shiyyasa ya buk'aci tahowa shi kad'ai.
Wani d'aki dake cikin bedroom d'in gidan ya bud'e ya Shiga, bazaka ta6a tunanin akwaima d'aki a wajenba, da y'ar k'ura a d'akin, amma hakan bai damu Galadima ba a yau, k'yallen da aka rufe kujeru da Computers d'in d'akin yashiga yayewa, da sauri ya fito zuwa can bayan d'akunan, yad'anyi ajiyar zuciya saboda ganin Gen... d'in gidan akwai fetur, dayake yad'an zazzo gidan kwannan, tadawa yay ya kuma komawa cikin gidan, ya kunna komai sannan ya zauna a kujera, medical eyeglasses ya saka, idonnan yayi jazur saboda 6acin rai, duk jijiyoyin kansa sun mimmk'e, hakama gashin jikinsa, kallon farko zai tabbatar maka ran maza ya 6aci. Koma a yanda yake sarrafa Computers d'in.
Abinda ke kunnensa kawai naga ya danna yanayin kwatancen d'akin da za'a sameshi.
Mintuna 3 tsakani saiga Sir Isa da Baffi sun shigo, saikuma ga Sauban Wanda harsun d'auki hanya Muftahu ya kirashi akan ya dawo, dole ya dawo masarauta, shine suka fito shida Muftahun.
Sir Isa da Sauban duk zama sukayi, Galadima Na Sanar musu abinda zasuyi.
“Gaskiya shegene guy d'innan yalla6ai, wlhy yasan Computer, kagafa yana Neman lalata mana dukkan security d'inmu.......”. ‘hankali tashe sir isa yake magana.
Sauban kam har kwalla ta cika masa ido.
Galadima baice komaiba, aikinsa yake iya iyawar k'arfin zuciya dana k'wanji.
Sai Baffine yad'an bubbuga kafad'ar Sauban yana fad'in “ka kwantar da hankalinka Sauban, insha ALLAH bazasuci nasaraba, kacigaba dayin komai a nutse kaidai”.
Sauban ya kad'a kansa yana share hawaye.
Galadima dayay zufa sharkaf ya kalli Sir Isa, yarigada yaci k'arfinmu kafin muzo, k'ofa ukuce kacal ya rage masa bud'ewa yasamu dukkan komai, abinda zamuyi mu bud'e masa sauran kawai, bayan yashiga ciki insha ALLAH inada wata dabara”.
Muftahu yace, “Amma Ranka ya dad'e hakan riskine gaskiya, idan kuma shi yanada plans akan hakan fa?”.
“Gaskiya ka fad'a Muftahu, amma hakan shine kawai hanya mai sauk'i da zamubi, inhar muka bari harya bud'e da kansa lallai zai lalata komaine, Dan wannan shine shirinsu”. Sir Isa ne mai maganar.
Galadima ya danna abin kunnensa yana fad'in “Vijay mubashi dama kawai, a lokacin daya shiga kaikuma ka tabbatar da ka zuk'e dukkan nasa shirin, ga wata akwatinan dayake yawo da ita a bayan handle d'in Computer d'insa, karka ta6ata Dan makircine ya shirya a cikinta, munayin kuskuren ta6awa labari zaisha Banban. Alex yay gaggawar had'amin sabbin Securitys muga kozasu ja hankalinsa can, ga hoton yaranan zan d'ora masa, dasu zaiyi amfani, dan dolene mu kauda masa hankali, yasan mi yakeyi sosai”.
“Ok! Ok! muje zuwa kawai” vijey ya amsa a hanzarce.
Da sauri Galadima ya maida kallonsa ga Sauban yana fad'in “dakaje duk ka d'auki su Amaturrahman ne?”.
“Eh yaya dukna d'aukesu”.
“A lokaci d'aya ko daban-daban?”.
Na d'aukesu lokaci d'aya, nakuma d'auki kowa shi kad'ai”.
“Alhmdllh taso nan”.
Tashi Sauban yayi ya matsa inda Galadima yake, wani glass Galadima ya tura masa, yace, “'Dora duka hannayenka anan mugani”.
'Dorawa Sauban yayi, bayan ya ta6a wani farin Abu da Baffi ya bashi, shatin hannun yaran suka bayyana, dayake yayi musu wasa sosai, amma kuma hakan bazai gamsarba.
Daga can Alex yace bazaiyiba, dole akawo yaran. Shima Galadima ya tabbatar bazaiyinba, sai hankalinsa ya kuma tashi, yaran sunyi k'ank'atar daza'a fito dasu daga gida.
Muftahu yace, “Ranka ya dad'e bara kawai naje Na kawosu inaga zaifi sauk'i”.
Baffi yace, “hakan shine kawai dai-dai sai dai bakai yakamata kajeba, a kira mahaifiyarsu tabama Wanda zai iya 6adda bamanni wajen kawosu, kuringa tunawa sumafa idonsu nakan kowane motsinmu a yanzu, shiyyasa tun a jiya naima Sameer hannunka mai sanda akan hakan”.
Galadima daya zubama Computers d'in ido kawai yana kallon 6arnar da ake shirin masa. Ya mik'e tsaye yana fad'in “Muftahu ka kira mai taxi d'innan yaje inda yata6a ajiyeta za'a kawo masa yaran”. fitowa yay daga d'akin yana k'ok'arin neman number Munaya ya kira.
Bugu biyu Munubiya da wayar ke hannunta ta d'aga, tana mannama Munaya wayar a kunne, bai amsa sallamarta ba yace, “Yanzunnan ki bama Innaro da laraba su Abdurraheem, sufito bakin layinku akwai mai taxi zai d'akkosu”.
Cike da mamaki Munaya tace, “yalla6ai ban ganeba?”.
A tsawace yace, “basai kinganeba, Dalla malama kibasu karki 6atamim lokaci”.
Sosai Munaya ta tsorata da tsawar tasa, kad'an yarage wayar ta su6uce mata ta daiyi azamar rik'ota, batada za6in daya wuce bin Umarninsa, dukda hankalinta bai kwantaba da hakan. Yanda yace ayi haka tayi, innaro da laraba Na fitowa suka samu mai taxi yana jiransu.
Cikin mintuna k'alilan suka iso, Muftahu da Sauban sukazo suka kar6i yaran, akabar su innaro a mota zasu jira.
Akan wani Abu akad'an d'orasu, da hotonsu ya fota a Computer d'in sai'a ciresu, sud'uka duk aka d'ad'd'orasu, sannan su Muftahu suka maidasu wajensu innaro aka koma dasu. Sudai duk mamaki ya cikasu akan miya faru? Basuda mai basu amsar wannan lamari.
Bayan su Galadima sun turama su Alex hotunan yaran sai duk suka koma gefe suka zubama Computers d'in ido, sauran lamari sunbarma ubangiji. Suna kallo wancen ya shige inda yakeso, bayan sun bashi dukkan dama, tashin hankalin Galadima shine, mutumin lalata komansa yakesonyi bawai d'auka ba, idan da ace d'aukace hakan mai sauk'ine, k'iris yarage wancan ya cinmusu, Galadima ya lumshe idonsa zuciyarsa Na k'una yana ambaton sunayen ALLAH, abinda ya d'auki tsawon shekaru yana tanadinsu ga wani banza zai gogesu cikin seconds, hakan ya tabbatar masa da Harun ne yabada wani yanki Na sirrinsa, saboda yasan abubuwa da yawa akan aiyukansa, sauban ma k'asa yay dakai yana hawaye, shikenan dukkan hujjojinsu da suke ganin zaisa su samu a hukunta masu laifi suntafi, baffi da sir Isa da Muftahu ma duk jikinsu yayi sanyi, kowa sai zuciyarsa Ce ke bugawa......
Sauban yace, “Yaa Sam!”.
Galadima ya tashi zaune sosai yana bud'e ido da kallon Sauban, batareda ya amsaba.
Sauban yace, “yaa Sam mizai hana mu gwada dabaran kashe Computers d'insu, kaga seconds 30 kawai yarage ya cimma burinsa”.
Ajiyar zuciya Galadima ya sauke, murya a sark'e yace, “Sauban abinda ya rage mana yayi kad'an wajen yin hakan, kuma zamu iya kuskuren da komai zai goge d'in da kanmu, kubarsa kawai yayi yanda yakeso......”
Katseshi baffi yay da sauri, “Sameer mu gwad'a d'in kawai, maybe a samu dacewa”.
Badan Galadima yayi tunanin samun nasaraba yatashi zaune jiki a sanyaye yana dannawa, Sauban yakuma fad'in “yaya Please kayi da yak'ini, saura 20 seconds fa”.
Tamkar Sauban yayima Galadima allura ne, yafara komai cikin hanzari, yayinda sir Isa ke taimaka masa.
Muftahu da Baffi dai y'an kallone, Dan basusan komai dangane da wannan harkarba.
Saura second 1 ya rage Galadima yasamu damar kashe Computers d'insu dana wad'ancan.
Suda ke murnar samun nasara duk sai sukayi tsit, su Galadima kuma Sauban ya sanya ihu.
Hararsa Galadima yayi, yayinda su Baffi sukai dariya.
Dukda suna addu'ar samun nasara hankalinsu bai kwantaba, Dan sai an kunna Computers d'in zuwa wanu lokaci, idan an tabbatar da samun nasara sannan.
***************
Hankalim Munaya bai kwantaba saida taga su innaro sun dawo k'alau, babu kunya taita d'aukar yaran tana jujjuyawa wai kozataga wani abinda aka musu, saidai kuma bataga komaiba.
***************************
Baffi ya kalli Galadima dayay shiru ido a lumshe, yace, “Sameer dolenefa komai yazo k'arshe yau, kabi ta hanyar da katsara domin zuwansu hannu gaba d'aya, daga baya saimu cigaba da Neman camera, dan Na tabbata bazasu hak'ura ba, shiyyasa tun a jiya Na sanarmaka”.
Galadima ya jinjina kansa batare da ya bud'e idoba yace insha ALLAH komai yazo k'arshe Baffi, safiyar gobe zaku tashi dajin yanda ta kasance, Nuren yana hanyar dawowa. Zamu tafi matakin k'arshe yau”.
Atare suka had'a baki wajen addu'ar ALLAH ya bada nasara.
Galadima ya amsa akan la66a da amin...............✍🏻
Lallai gobe da kallon kenan. Galadima manmu ka cika musu aiki kawai🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀.
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏼
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*
*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
_________________________
_Masoyan RAINA KAMA... Alkairin ALLAH yakai gareku aduk inda kuke❤❤❤❤, bilyn Abdull nayinku fiye da yanda kukeyinta._
*TASKAR LITTATAFAN HAUSA*😘👌🏻
*ZAUREN HASKE*😘
*KUNDIN HASKE*😘
*RAINA KAMA FANS CLUB* GROUP 1,2,3,4,5 duka Na gaisheku, Wanda Na bud'e da Wanda masoya suka bud'e, inayinku over wlhy, I love you irin Trillion's d'inan fa🤸🏻♀😘.
*ZUREN BIEBIE ISA*😘👌🏻
*NICE N COOL NOVELS*😘
*PHARTY NOVELS*😘
*HUGUMA CONVERSETION*😘
*RANO NOVELS* 😘
*MANSHAT NOVELS*😘
*XUMUNTA NOVELS*😘
_Aradun ALLAH kunada matuk'ar yawa, gashi bana kusa balle naita jeroku babu gajiyawa, ina missing naku gaba d'aya, irin babu dad'i d'innan😔😂._
I love you all irin manya-manya d'innan😘😘😘😘😘😘😘🤸🏻♀👌🏻
__________________________
*_BOOK 3_* 👉🏻1⃣4⃣
.................Duk da dai sumbar komai a halin k'ila wa k'ala haka kowa yafito jiki a sanyaye, Baffi da Sir Isa suka wuce, Galadima ma kallon Sauban yayi daya zuba uban tagumi, yad'an murmusa yana fad'in “Haba autan Momma, miye kuma Na damuwar haka? katashi kuwuce kawai kar yamma tayi”.
Shagwa6e fuska Sauban yayi yana kallon yayansa, yace, “please Yaa Sam kabarni sai gobe saina wuce insha ALLAH”.
Galadima yay shiru alamar tunani, saikuma ya girgiza kansa, “uhm-uhm Sauban ka wuce yau, Dan gobennan akwai riski”.
Kamar Sauban ya tambaya dai amma yay shiru, yasan halinsa mawuyacine ya sanar masa. Dan haka saiya amsa da to kawai. Badan yasoba yaymusu sallama shima driver dazai kaisa yad'aukesa suka tafi.
Ajiyar zuciya Galadima ya sauke, zuciyarsa Na k'una da tsantsar damuwa.
tausayinsa ya kama Muftahu dake zaune shima yayi shiru damuwa da tausayin d'an uwan nasa fal ransa.
★★★★★★
Gaba d'aya zuciyar Munaya takasa sukuni gameda yanda taji muryar Galadima, tunda kuma aka maido yaran saita kasa zaune ta kasa tsaye, Munubiya dai da innarsu duk suna hankalce da ita, kamar Munu zata shareta saidai tamata magana.
“Nikam aganina da wannan zagaye-zagayen da kiketayi Sweetheart ai gara ki kirashi kisan damuwarsa, koma ladan kwantar masa da hankali k'yasamu”.
Munaya dake kwance akan gado ta kifa meenal saman cikinta datai barci ta kalli Munubiya, amma sai munu ta basar tamkarma ba ita tayi maganarba. Ajiyar zuciya Munaya ta sauke, yayinda Munubiya ta tashi tamayi ficewarta daga d'akin duka, harta fice Munaya nabinta da kallo, saida tabar ganinta sannan ta janye idonta a k'ofar tana cigaba da shafa bayan meenal.
Shawarar Zuciyarta dake cigaba da k'arfafa mata shawarar y'ar uwarta ta addabeta da k'awato mata Galadima a damuwa, da alk'awarin dataima Mahaifiyarsa. Kasa daurewa tayi saboda tausayin ahalinsa dashi kansa daya kamata, ta jawo wayar tana lalubo number sa, dukda k'irjinta Na dukan gama-goma Na tsoron tsawar daya mata d'azu da yanda suka rabu jiya. Haka dai ta dake tayi dialing number sa.
Galadima suna zaune cikin halin shiru da Neman mafita a zukata shida Muftahu kira ya shigo wayarsa, sharewa yay tamkarma bai jiba, ganin zata tsinke muftahu ya taso yay picking da sauri ganin *My Mata* yasan dai Munaya Ce, a kunne ya saka masa, Galadima ya bud'e jajayen idonsa ya kallesa, Muftahu yamasa alamar please da fuska.
Baice komaiba ya kar6a wayar yana maida idanunsa ya lumshe, Muftahu kuma ya fice abinsa.
Munaya tayi shiru takasa magana, kamar yanda shima yak'i cewa k'ala, sai sautin ajiyar zuciyarsa take jiyowa kad'an-kad'an, daurewa tayi tace, “Assalamu alaika”.
Dukda yasan itace saida yaji sanyi a ransa, Dan ita kad'aice kemasa haka a waya ya jure, saida ya d'auki wasu seconds kafin ya amsa sallamar.
Yanda ya amsa sallamar kawai ta tabbatar akwai matsala, Cikin aro jarumta tace, “Ranka ya dad'e barci kakeyi?”.
Yad'an murmusa, a zuciyarsa yace yarinyarnan a kwai wayo, “Uhm-uhm”. ‘yafad'a a sanyaye’.
Ganin tafara samun dama saita kuma saita muryarta tace, “'Dan gatan Abie, to mikakeyi ne haka? naji muryar taka can k'asa”.
Zamewa Galadima yayi ya kwanta cikin kujerar, yanzunma tamkar bazai amsaba, saida ya gama basarwarsa sannan yace, “k mikikeyi?”.
Munaya tayi murmushi mai sauti har yana jiyowa, ta shafa kan Meenal tana fad'in “kwance kawai nake ina tunanin rayuwa da abinda ta k'unsa, harma da Wanda ke gudana a cikinta”.
Yace, “Humm kamar mikenan?”.
“Kanason ji?”.
Ya kuma cewa “Uhm”.
“humm yalla6ai nakula duk yanda bawa yakai da samun komai Na rayuwa saikaga wata damuwa ko tawaya mai kutse acikin al'amuransa, bana manta maganar nan taka da kata6a fad'amin wani lokacin murmushin da jama'a kanyi iyakarsa fuskane, amma zuciyarsu sune kad'ai sukasan sirinta, lallai wannan gaskiyane, amma kasan mike birgeni da k'aramin k'warin gwiwa a rayuwata koda ace Na tsinci kaina a fagen sanyin jiki?”.
Galadima yace, “uhm-uhm”.
Munaya ta sauke wata sassanyar ajiyar zuciya da Galadima yajita har cikin ransa, yayinda wani Abu ya tsarga masa ta cikin kai har zuwa yatsan k'afa, ya gyara kwanciyarsa yana jiran jin mizatace.
“Komai girman fad'uwa inhar da yak'inin HAK'URI dana k'arfin ZUCIYA to lallai akwai tagomashin sirrin samun NASARA, hak'uri da juriya basa ta6a zama fad'uwa, inhar kaga bawa yayi hak'uri babu kuma NASARA a ciki to lallai hak'un nasa kad'anne, sometimes gaggawa aikin shaid'anne, saikuma ansha wahala ake shan dad'i, abinda kawai muke kasa fahimta shine riba akan sameta ne a muhalli biyu, walau a duniya kokuwa a lahira, duk wadda bawa ya samu sunanta nasara, amma kowa yafi fata da samun ta duniya, saidai ta lahira ita yakamata mufi d'oki da addu'ar samu, meybe tazame mana tsani Na zuwa inda bamuyi zatoba, hikimar Ubangijice yabaka nasarar anan kokuma a can, Dan babu yanda za'ayi a zalunceka mai kowa da komai sarkin Rahma da jink'ai ya bari, bai yarda da zalunciba, yakuma haramtashi agaremu mu bayinsa”.
Wasu k'ananun hawaye suka gangara ta gefen idon Galadima, fuskarsa d'auke da murmushi, yayinda kalaman munaya ke tasiri adukan magudanar jininsa da zuciya, wata nutsuwa ta musamman daya rasa tashiga ratsashi da bashi k'arfin gwiwa, a hankali yace, “ke y'ar baiwace matar Contract”.
Dukda maganar k'arshe ta sosa zuciyarta saita murmusa, cikin kuma kwantar da murya tace, “Ni a suwa Mijin contract ”.
Ya d'an dara batare daya shiryaba. Yace, “one-one kenan?”.
Munaya tayi dariya tana fad'in “nidai bada manufa na fad'aba”.
“Fad'i gaskiya dai yalla6iya tsiwa”.
“Gara mai tsiwa da miskili, koba komai akansan muna waje ai saboda tsiwarmu”.
Galadima ya kuma Murmusawa. Yace, “ki kiyayi randa zan kamaki ALLAH”.
Itama dariyar tayi. Tace, “yalla6ai ka fad'i wani Abu nabaka k'yauta mana”.
Yay d'an jimm tunanin mikenan?, saikuma yayi ajiyar zuciya yace, “mikenan?”.
Cikin wani salo Munaya tace, “R. Ita kawai nakeson ji a harshenka”.
Lallai yarinyarnan taga gadon barcinsa wlhy, yay maganar a zuciya fuskarsa na k'awatuwa da murmushi. yace, “Okay, kibari sai ina gabanki”.
“Tab, Indai ba yanzuba na fasa”.
“uhmyim, miye na karayar hajiyar tsiwa?”.
“Aiba karaya nayiba, lokacin kawai kabari ya wuce, ni karmafa yarannan suma su gadoka”.
“Dai-dai kenan ai y'ammata, kokin manta k'yan d'a ya gaji ubansa”.
“Humm Alfahari kenan, ita uwa an rainata”.
Dariya tabashi, amma ya daure baiyiba. Yace, “keda kike gudunsu mizaisa su gadoki?”.
Munaya ta d'an ta6e baki, cikin juya idanu tamkar tana gabansa tace, “yanzu kana ina?”.
Murmusawa yayi saboda basar da maganar da tayi. Yace, “kinason ganinane?”.
“A'a, son sani kawai nake”.
“Humm, naje tad'i to”.
Shiru munaya tayi, sai kuma ta d'an dara, “Yalla6ai kasan wani Abu kuwa?”.
“Saikin fad'a”.
Cikin danne dariya tace, “irinku kwantai kukeyifa, sai anyima y'ammata tallarku asamo mai taimakonku ta aura, kaima nasan saisu takawa sunmaka haka.....”. Sai yaji kitt, ta yanke wayar.
Wani k'asaitaccen murmushi ya saki yana shafa kumatunsa, ya d'ora wayar saman cikin sa yana fad'in “lallai yarinyarnan kin girma, zaki tabbatar nayi kwantai kuwa”.
Daga canma Munaya dariya taketa k'yalk'yatawa, harta tada Meenal, Mununiya datun d'azun take kallonta ta bayan labule bata saniba tayi murmushin jin dad'i itama tana share hawaye, tanason y'ar uwarta sosai, sannan wayonta da iya mu'amullarta na birgeta, tabbas Munaya tanada tsiwa, amma tanada wayo, inhar zaka takurata bazata ta6a raga makaba, amma tanada tausayi dason ganin farincikin wani koda ita zata rasa nata farincikine, gakuma son girma uwa gyambo, tanason komi zaka mata ka nuna muhimmancinta a gareka, a fili tace, “ALLAH yakawo farinciki mai d'orewa a ratuwarki kema y'ar uwata”.
Amin munu😘☺.
★★★★★★★★
Tunda Muftahu ya shigo yakebin Galadima da kallon mamaki, ganin yasake yanata fara'a tamkar ba shine a matsananciyar damuwa yanzunba, ya zauna zuciyarsa na addu'ar samun mace tagari, dan lallai *MATAN KWARAI RABIN ADDINI ce*.
Galadima ya hararesa yana tashi zaune, “malam lafiya ka k'uramin ido?”.
Dariya Muftahu yayi sosai, yace, “to miye na tsarguwar ranka ya dad'e, wlhy kuna sha'aninku kaida gimbiyarka, yanzu nan harta saukeka daga hawa saman da kayi”.
Filo Galadima ya jefama Muftahu, shikuma ya cafe yana dariya.
Galadima ma murmushin yayi yana danna kiran Sauban. Dan yasan har yanzu yanacan cikin damuwa. Hasashen nasa kuwa yayi dai-dai, Dan har yanzu muryarsa a cinkushe take. Amma jin ta Galadima a sake sai farinciki ya kamashi, cike da zumud'i yace, “yaya an dace ne?”.
Murmushi Galadima yayi mai sauti, yace, “muna fatan hakan autan Momma”.
Alhmdllh Sauban yashiga jerowa, saiya saki jikinsa kuma harda tsokanar Galadima yana dariyar k'eta.
Galadima dai murmushi yakeyi yana girgiza kai, ya yanke wayar zuciyarsa na addu'ar ALLAH ya saka farinciki a zuciyar Munaya fiye da yanda ta sakasu. Massage ya tura mata sannan ya kalli Muftahu yana gyara zama.
Munaya na kwance har yanzu takasa fita, tunda tasamu Meenal ta koma barci saita lumshe ido tana dulmiya duniyar nazari, shigowar sak'one ya sata bud'e ido ta jawo wayar. Ganin Galadima ne saita mik'e zaune babu shiri, sak'on ta bud'e.
_“Kin yaudareni da zance banko tambayi yaya jinin jikina sukeba yalla6iya, to ki shafamin kansu._
*_ALLAH ya sanya farinciki a rayuwarki fiye da yanda kika Sani_*.
Wasu hawayen farinciki suka gangaro a kumatun Munaya, bata ta6a tunanin shirmen datake masa yanayin tasiri a zuciyarsa ba, Dan bai ta6a nuna mataba, a fili ta furta “ALLAH na gode maka dana zama sanadin saka wani bawa naka farinciki a lokacin jarabawar damuwa ta lullu6e jinsa da ganinsa da zuciyarsa”.
Amin munaya, muma Ya ALLAH kabamu ikon bama bayinka muminai gudunmawar farinciki mai amfani koyaya ne, amma bata hanyar sa6onka ba ko take k'a'idar daka shinfid'a mana, amin👏🏻😭.
*************************
Muftahu da Galadima suka fito, yauma bai zauna bayaba duk yanda Muftahu yaso hakan, dama yay masa maganar zama bayan hararsa yayi, dole yaja bakinsa yay shiru yana murmushi.
Wani wajen cin abinci Muftahu ya tsaya, ya kalli Galadima dake kwance jikin seat ya lumshe ido yace, “ranka ya dad'e Dan ALLAH ina zuwa”.
Kai Galadima ya jinjina masa kawai batareda ya bud'e idoba, Muftahu ya fita, mintuna 15 saigashi ya dawo hannunsa d'auke da ledoji, ya bud'e seat d'in baya ya ajiye, sannan yadawo mazaunin driver yana maba Galadima hak'urin jira.
Baice dashi komaiba, Dan tuni yama lula wata duniyar.
Gidan gonar Nuren suka nufa, inda su Harun suke a ajiye, a falo suka yada zango, ko ina k'al yake a tsaftace ga k'amshi, cikin masu kula da gidan gonar ya shigo d'auke da wankakkun y'ay'an itatuwa masu k'yau, zubewa yay yana kuma kwasar gaisuwa, Muftahu ne kawai ya amsa, Galadima hannu ya d'aga masa.
Muftahu ya bud'e abinda ya siyo yana fad'in “Ranka ya dad'e mizakaci?”.
Cikin d'an ta6e baki ya girgiza masa kai alamar bazaici komaiba.
“Okay, to bara na kira Gimbiya meybe ita ta saka kaci”.
Bud'e ido yayi yana zubama Muftahu harara, shikuma ya fuske tamkar bai ganiba.
Saida Muftahu yasha fama kafin Galadima ya yarda yad'anci abinci, rabima duk fura da kayan itatuwan ne yasha. Sunkai 1hour da shigowa ya buk'aci ganin Harun da SD.
Sun fara shiga d'akin da harun yake, bayan Muftahu ya saka key ya bud'e matsawa yay yabama Galadima hanya yafara shiga, takun takalmansa ya saka Harun dake zaune bakin gadon d'akin kansa a duk'e d'agowa, kallon ido cikin ido sukaima juna, Galadima ya janye nasa cike da basarwa yana wani miskilin murmushi mai k'ona zuciyar mak'iyi.
Harun ma janye idanunsa yayi yanajan tsaki, Muftahu kuma ya ta6e baki yana gyarama Galadima kujerar zama.
Galadima ya zauna idonsa akan harun, hannunsa ya mik'a ya kar6i lap-top d'insa dake wajen Muftahu, ya d'orata bisa cinya sannan ya janye idonsa ga harun dayak'i sake kallonsa, lap-top d'in yafara dannawa cikeda kwarewa, cikin seconds dabasufi 10 ba ya d'ora lap-top d'in saman stool d'in da Muftahu ya sake ajiyewa, sannan yay playing abinda ya kunna yana hard'e hannaye a k'irji da zubama Harun ido.
Harun har yayi tamkar zai share sai dai ya kalla lap-top d'in, Wato shine a ranar sunan y'an uku gab da za'a sace yaran shida d'aya daga cikin kidnapers d'in.
“Bibo inaso Ku tabbatar da kun kwashe yaran, karku kar6i wad'anda suke hannun k'annen matarsa, Dan na bogine, baby dolls ne aka sakama kaya irin na yaran domin kauda hankali, Sameer yanada wayo fiye da yanda kuke tsammani, Dan haka kuyi komai cikin kulawa da taka tsantsan, dai-dai lokacin da wutar hotel d'innan zata d'auke, zan kwashe yaran insha ALLAH, harsai nabar cikin hotel d'in ni da ku sannan za'a kunna, ina fata ka fahimta”.
“Eh na fahimta ranka ya dad'e, namaka alk'awarin ko y'ay'an sarkine bana Galadima ba yau saisun kwana a alahira”.
“No, banason su mutu yanzu, sai shi ubansu ya d'and'ana d'acin rashinsu, yana gab da mutuwa sai a kawo masa gawarsu, daganan shima kaga ai sai tafiya shida wannan tatsitsiyar matar tasa y'ar bayi”.
“Okey nagane boss”.
Mamaki ya kama Harun har Muftahu. Zuciyar Harun tamkar zata fad'o waje dan mamaki, ya akai Galadima ya d'auki wannan video d'in, bayan dukkan CCTV cameras d'in dake hotel d'in saida suka saye mai kula dasu na hotel d'in aka tsayar dasu daga aiki........
Murmushin da galadima yayine ya katse tunanin Harun , cikin lumshe idanu da kad'a kai ya gyara zamansa, cikeda izza yace, “Abin mamaki ko? haka nake ni dama, kullum cikin bada mamaki, tabbas 6oyen dakai masa bazai yuwu muganiba, saidai kamanta da koda ace banida hanyar ganin naka idan ubangiji bai k'addaro ruhi na kona y'ay'ana ko matata zai salwanta a hannunka ba babu yanda ka iya, kana tunanin duhu da tsayar da cctv d'in hotel d'in zai baka dukkan dama ko? To kayi kuskure dan Muhammad Sameer kansa cctv ne, eyeglasses d'in dake idona komai duhun waje shi zai haskokane, dan camera d'in jikinsa tana tareda komai, kasan miyasa nabaka damar d'aukar yaran? Saboda hakan yana cikin k'addararsu, nakuma barka dasune danna kafa maka tarkon neman hujja da tabbatar da abinda Muftahu ya sanarmin”.
Muftahu ya d'age gira saboda kallon tsana da Harun ke masa.
Murmushi Galadima ya kumayi yana cigaba da fad'in “ka kira matata tatsitsiyar yarinya y'ar bayi ko? Saikuma abin mamaki ita wannan y'ar bayin, tatsitsiyar ce ta zame maka RAINA KAMA, dan lallai gashi zakaga GAYYA. itace ta haskomin kai a cikin madubin fik'irarta tunkan Muftahu ya sanarmin, takuma koyamin yanda zan fahimci makircinka da nagartar Muftahu, tabbas na yaba ma basirarka Harun, kanada basira k'warai da gaske, tunda kasan kanka kake a jikina kana cin dunduniyata, ni matsayin aboki d'an uwa mafi kusanci nake kallonka, kamar yanda mahaifina yarink'a kallon mahaifinka, ashe kud'in duk kaskane a garemu, nayi imani da cewar lallai ku jarabawane a garemu, kamar yanda k'addarar auren Munaya tazamema rayuwata alkairi, a kullum cikin aibanta Muftahu da bak'antashi kake a gareni, ashe kaine bak'in ba shiba, mimuka muku ni da mahaifinane haka da zafi? Nawa suka biyaku kuke cutar damu.............?”.
“Sameer!!”. Harun ya kirayi sunan galadima cikin fushi, ya mik'e tsaye sunama juna kallon ido cikin ido shida galadima, cikin matsannan ciyar tsanar juna.
“Kabar alfahari magen matarka tamaka bajinta, shawarama zan baka ka janyeta cikin wannan hargitsin, danko ubanta daya shiga a had'ari yake balle ita karan kad'a miya, wlhy Sameer ban ta6a k'aunarka ba, bakuma zan ta6aba har abadan, domin tsakanina dakai BASHIN GABANE, dan haka banida lokacinka yanzu har sai Camera ta dawo hannunmu, bar ganina anan a rufe, akwai mai sarrafa dukkan tunanina a waje, yarage naka kanemi hanyar kare Surukinka kafin aikinmu yazo kansa...”.
A fusace Galadima ya mik'e shima yana dunk'ule hannu, amma sai Nuren daya shigo yanzu ya rik'eshi, “relax my brother, kainefa ka ta6a fad'amin ba'a maidama abokin gaba murtani da murtani, sannan ba'a bashi damar sanin sirrin yak'i sai an had'u a filin daga”.
Galadima ya saki hannunsa daya dunk'ule da bakinsa daya cije, yatsunsa ya kad'a suka bad'a k'ara d'as! 'Das! Sannan ya zagaya hannunsa a wuya alamar I will kill you.
Cikin d'aga murya Harun yace, “d'an halak ka fasa Sameer!”.
Daga Nuren har Muftahu da Galadima babu Wanda ya amsa masa, a falo suka tsaya, Galadima ya Nufi d'akin da SD yake batare da yace uffanba,
Nanma dai Muftahu ya bud'e masa, ya shiga cikin tsananin fusatar da Harun ya sakashi. zauna suka iske Alhaji Darma cikin kujera yana duba jarida, kaikace a d'akinsa yake.
Galadima ya taune lips nashi tamkar zai hudasu da hak'ori, zuciyarsa Na k'una, lallai sai Harun da ubansa sun k'are rayuwarsu a jail inhar yana numfashi, dan barin irinsu a duniya had'arine babba, musamman a gida irinna sarauta.........
Nuren ya katse masa tunani ta hanyar yima SD magana.
cikin ta6e baki Alhhaji Darma ya kalli Galadima yana wani murmushin mugunta, ya ajiye jaridar hannunsa tare da hard'e k'afa.
A bakin gadon Galadima ya zauna, ya kalli Alhaji Darma, sosai Darma ya tsorata da rinannun idanun Galadima, amma saiya dake.
Galadima daya lura da rikitar Darma ya murmusa, cikeda k'asaita ya d'age girarsa, “Alhaji Shehu kenan, angaya maka mutum yakanci bashi ya kwana lafiya, duk wata jarumta da zaka aro kasama ranka tuni nagama bitar karatu a kanta, karigada ka shigo ramin damusa iya gudunka babu wajen 6uya, bama duk wannan ba, minene had'inka da surukina? Sanann minene yasa kuka kashe mijin y'ar uwata? Dan ko tantama banayi da hannunka a cikin kisanshi!!”. Galadima ya k'are maganar cikin matsanancin tsawar data rikita Alhaji Darma.
Dukya rud'e yarasa ina zai kama, cikin in ina yace, “Ni sharri zakaimin bansan komai akan mutuwarsa ba”.
Galadima yay dariya, saikuma ya gimtse fuska. Yace, “Okay, babu hannunka amma kake tursasa yarinyarsa Samha ta dinga d'akko maka sirrikana tana kawo mata? Kullum kana ma yarinya barazana da mutuwa ko? Alhaji shehu aini tun ranarda mijin aunty Mimi zai koma ga ALLAH naga idonsa ya tsaya cak akanka lokacin da numfashinsa ke bankwana da duniya na d'ora alamar tambaya a kanka, sai kuma yanda kake kaffa-kaffa da Samha a gaban mutane, yayinda itakuma take a d'arare dakai, dukkan wayar dakake mata kana sakata sato maka sirrina INA kan sani, dan nine da kaina nake ajiye mata tagani danta tura maka batareda ita kanta ta saniba, shiyyasa na jata jikina fiye da kowa a gidanmu, duk abinda Sameer zaiyi cikin ilimi yakeyinsa Darma, koda yake bamuzo wannan matakinba, miye had'inka da surikina?”.
Alhaji Darma dake a rikice saboda tsoro da tashin hankalin zantukan Galadima ya had'iye yawu da k'yar yana fad'in, “B..babu ruwanka da abinda ke tsakanina dashi kuma”.
“Hummm". Galadima ya fad'a cikin cije lips, wayarsa ya d'akko ya kunna wani recording daya nad'a a wayar Darma ranar da suka kamoshi kafin su d'akkoshi.
Waya yake da wani cikin tsananin fusata, “Boss wai miyasa bazamu aika shegenan barzahu ba idan yak'i bamu Camera d'innan? Tunda munada hanyar da zamubi mu kar6a d'in, Nibansan miyasa kuke cewa abishi mataki-mataki ba, kasanfa y'arshi yaronan Sameer take aure, yanada hanya mai sauk'i dazai bashi camera d'innan, shi wancan banzan Alhaji Halluru babu tsiyar da y'ay'ansa zasuma mutane, kullum sai tsarin banza yake mana”.
“Karka damu Alhaji shehu, mu bashi damar k'arshe daya buk'ata, tunda ya tabbatar mana a wannan karon zai kar6o camera d'in ta hanyar matan y'ay'ansa, yana son takara, yakuma San inhar burinmu bai cigaba shida takarar Governor saidai kallo”.
“shikenan boss, bara naje ance nayi bak'o”.
“Ok ngd”.
Galadima ya gimtse recording d'in dai-dai nan yana murmushi da kallon Alhaji Darma dake tsuma dukan jikinsa na 6ari.
Cikin d'age gira Galadima yace, “wannan ma ba matsalata bace? Kasanfa shikad'ai ya isheni hujjar gurfanar dakai gaban K'uliya, shikenan babu girma babu mulkin da ake mana Homa da tak'ama dashi right? ”.
Mi Nuren zaiyi kuwa inba Bushewa da dariya ba, dan yatuna Alhaji Shehu ne yafad'ama Galadima maganarnan randa suka kamoshi.
Cikin Fusata Darma yake kallon Muftahu da Nuren dake dariya, ya mik'e tsaye yana nunasu da yatsa, “y'an samari lokacin dariyarku baiyiba, dan camera d'in da kuke farfagandar nema tana gab da zuwa hannunmu, kunga kuwa ai kune abin dariya”. Ya k'are maganar da kwashewa da dariya.
Dukda furucinsa ya daki zuciyar Galadima bai nunaba, saiya mik'e yana murmushi da kallon Darma. Yace, “lallai kaine ka cancanci ayima dariya, indai camera ce tadad'e da zuwa hannuna”.
Yana gama fad'a ya fice, su Nuren suka kuma sanya dariya, dukda yanayin Galadima ya tabbatar musu akwai matsala. Sunama Alhaji Darma dariya suka fice abinsu daga d'akin.
A falo suka iske Galadima yanata safa da marwa cikin tsantsar damuwa, sai danna waya yake yana sakawa a kunne alamar Neman wani tak'i shiga.
Cikin sassarfa duk suka k'araso garesa suna tambayar lafiya?.
Bai tanka musuba, saboda Munaya ta d'aga wayarsa, “Abba ya dawo kuwa?”. abinda kawai yace mata kenan.
A tsorace tace, “Miya farune?”.
Tsawar data rikitata ya daka mata, “ya ina tambayarki kina tambayata?”.
Cikin in ina tace, “Kayi hak'uri, bai dawoba”.
“ya salam” yafad'a cikin dafe kai. yace, “Kinyi waya dashi? Ko kinji wani yayi waya dashi?”.
“A'a gaskiya, Jiya da safe dai nayi waya dashi nida Munubiya, amma yau ko innarmu banji sunyi wayaba.......”
Cikin katseta yace “kinga maza bincikamin waye yay wayar k'arshe dashi a gidanku, sannan kuma awa nawa dayin wayar”.
“Okay” munaya tafad'a tana yanke wayar.
Shima wata Number yashiga nema yana fad'in “Lallai akwai matsala, tunda kukaji Harun da Alhaji Shehu sun fad'a to sunsan misuka shiryama Abba, gashi nabaza su Ameer sumin wani aikin...” ya k'are maganar da saka wayar a kunne saboda daddy ya kira.
Bayan sun gaisa ya tambayesa ko sunyi waya da Abba a yau?.
Daddy yace, “eh da asuba yakirashi akan zai dawo yau”.
Galadima yace, “Alhmdllh Dady wace number ce?”.
Dady yace bara Na turo maka.
Koda Galadima ya yanke wayar saiya kira baba k'arami shima, shima ya tabbatar masa sunyi waya da Abba bayan fitowa salla, Dan wannan al'adarsu Ce ko a ina wani cikinsu yake saisunyi gaisuwar safe da bankwanan kwanciya barci, sannan idan wani cikinsu yayi tafiya zai kira y'an uwansa yayin dazai kamo hanya.
Hankalin su Nuren ma duk a tashe yake, balle uban gayya Galadima.............✍🏻
🙆🏽Turk'ashi, ana wata ga wata kuma🤦🏻♀.
Lallai yaukam tura na shirin kaiwa bango🤦🏻♀.
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻_*
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*
*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
__________________________
*_Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya Ubangijin Al'arshi kama mahaifin takwara (Bily s Fari) rahama, ka yalwata kabarinsa da Ni'ima, ALLAH ka yafe masa, harda iyayenmu😭👏🏻_*.
_Takwara ALLAH ya k'ara mana hak'urin rashinsu, muma ALLAH yasa randa zaka d'auki ranmu muna cikin masu imani da tsoronka, da soyayyay Manzonmu ANNABI MUHAMMADU S.A.W._😭😭👏🏻
____________________________
*_BOOK 3_* 👉🏻1⃣5⃣
.................Duk da Munaya a rikice take haka tayi jarumtar danne zuciyarta, cikin hikima ta dinga bin jama'ar gidan d'ai-d'ai tana tambayar wad'anda tasan Abba zai iya kira kai tsaye, amma kowa yakance tun daren jiya basuyi wayaba, hankalinta a tashe ta sulale gidan innaro ba'a saniba, itama dai tace tun bayan sallar asuba bai sake kiranta ba. Munaya tafito jikinta sai rawa yake, kiran Galadima tayi, lokacin yana waya, tamkar zata fasa kuka ta cire wayar daga kunnen ta, tana niyyar sake kiranshi saigashi ya kirata.
Da sauri ta d'aga.
Yace, “yauwa Yayi waya da wani?”.
Muryarta na zuga alamar tahowar kuka tace, “A'a, innaro kawai ya kira bayan sallar asubahi, amma yau koda su innarmu baiyi wayaba”. ta k'are maganar hawaye na gangarowa a kumatunta.
Galadima ya furzar da huci daga can, a hankali yace, “Munaya”.
Muryarta na zuga ta amsa tana share hawayen da bakin hijjab.
Had'iye abinda ya tsaya masa a mak'oshi yayi da k'yar, muryarsa takuma komawa can k'asan mak'oshi, cikin sigar lallashin da Munaya bata ta6a sanin galadima ya iyaba yace, “insha ALLAH babu abinda zai faru da Abba, kiyi mana addu'a, sanan karki sanarma kowa wani Abu har inna, wayarki tazama kusa dake, Dan zan dunga kiranki idan buk'atar hakan ta taso”.
Munaya takuma goge hawayen dasuka gaza tsayawa, cikin had'iye kukan tace, “ALLAH yabaku nasara, ya tsareku da tsarewarsa”.
“Amin ngd”. Galadima ya fad'a yana yanke wayar.
A bakin fanfo Munaya ta tsaya ta wanke fuskarta, akuma lokacinne Zarah da Siyama suka shigo kusan lokaci d'aya.
d'agowa nayi Na kallesu ina k'ak'aro murmushin da musu sannu da zuwa. Saidai ayanda suka amsamin cikin sanyin jiki saina tsorata, nabaro bakin fanfon da hanzari zuwa garesu ina fad'in “Kai lafiyarku kuwa?”.
Duk d'insu murmushi suka k'ak'alo, Siyama tace, “babu komai fa sis...”.
Dukda ban yardaba haka nayi murmushi, sannan Na kar6i yaransu duk biyu Na rik'e ina yaba Girman da sukayi, saikace tagwaye.
Daga Siyama har Zarah basuce dani Uffanba duk suka shige, kowa tanufi d'akin Uwarta. Duk binsu nayi da kallo, saida suka shige Na sauke ajiyar ziciya nima Na nufi sashenmu Ina tunanin mike faruwa? Dan alamu sun nuna akwai dai wani Abu a k'asa.
Saidai bankai ga Shiga d'akinmu ba mamansu Yaa hameed ta tareni ta kar6i yarinyar Zarah. Ban musaba Na bata tundai ALLAH yasa Nima Na Haifa balle ace, na shige falonmu da d'an Siyama nima.
Bayan Galadima sun gama waya da Munaya, number da daddy ya turo masa ya duba, ganin wadda yake da itace saiya gwada kira, switch up, ya ciza lips yana kallonsu Nuren da suma duk suka zuba masa idanu.
Muftahu yace, “Ranka ya dad'e mu sanarda y'an sanda mana?”.
Murmuahi takaici Galadima tayi, ya girgiza kansa yana fad'in “Hakan zai 6ata aikinmu, duk indama yake a safiyar yaune suka sameshi, akwai zoben dake hannunsa zamu iya bibiyarsa tanan, saidai matsalar d'aya dole sai wayarsa Na aiki, gashi number sa kuma switch up”.
Nuren yace, “to mizai hana mu bincika kozamu samu daga inda Number tabar aiki”.
Da sauri Galadima yace, “yes, yes Nuren, shawara mai k'yau.....”
Shiru yay yakasa k'arasawa, saboda tuno da matsalar da Computers nasu suke ciki kuma, ya dafe kansa.
Daga Muftahu har Nuren duksun fahimceshi, zuwacan kuma miya tuna saiya mik'e da hanzari zuwa cikin d'akin, babu dad'ewa yafito dawani k'aramin abu a hannunsa, lap-top yajawo ya manna a jiki, ya had'a da waya ya Shiga sarrafata cike da kwarewa.
Zuwa can yad'ago yana kallon su Muftahu da tura musu lap-top d'in gabansu, yana sanar dasu titin da wayarsa ta daina aiki.
Cikin takaici yace, “Sunriga da sun tsara komai, mubarma tunanin plan A, muje zuwa plan B kawai”.
Cikin mamaki duk suka kallesa alamar miye plan B d'i?.
Lips d'insa yad'an ciza yana d'age gira d'aya da buga yatsan saman bakinsa, Yace “maida hankalinmu a nemansa shine target d'insu Na farko wajen janye ra'ayinmu, plan d'inmu mukuma anan shine bazasu ta6a kasheshi ba inhar bai basu Camera d'inba, a yanda Na lura kuma yanada taurin kai shima, bazai ta6a basuba ko fad'a musu inda take. Sunada damar yin amfani da surukan senator halluru wajen turasu gida su nema musu camera d'in, kodai ta hanyar musu barazana da mutuwa, kokuma akan aurensu, ko kashe mahaifinsu, kodai wani Abu daban, shiyyasa dolene mumaida matsalarsa cikin plan B d'in”.
Duksun gamsu, dukda sufa har yanzu yak'i sanar musu miyake shiryawa a plan B d'in.
Cikin damuwa Nuren yace, “Amma nasan zasu wahalar dashi”.
Galadima baice komaiba dan shikad'ai yasan azabar da zuciyarsa kemasa, bayason ya nuna karayarsane saboda karsuma su Muftahu su karaya, sannan koda sanyin jiki yanemi tasiri gareshi sai kalaman Munaya su masa allura, inhar yarinya k'arama kamarta zata iya tasirantuwa da abinda ta fad'a, mizai hana shima ya samu jarumta cikin tagomashin fik'irarta.
Mik'ewa yay tsaye yana tattara kayansa da fad'in “Bara Na wuce, sai kunji yadda zata kaya kawai”.
Basu barshi yatafi shikad'aiba, saida sukai masa rakkiya har masarauta, koda ya shige sashensa saiya kulle kansa, domin yin shiri.
Hummm,🤸🏻♀shirya da k'yau Galadiman mu.
★★★★★★★★★★★
Abinda ya faru da Abba shine, bayan yagama kammala shirinsa domin baro inda sukaje shida S... halluru daya jashi domin masa rakkiyar tafiyar kwanaki biyu kacal.
Lafiya lau suka shiga mota zasu taho, amma sai shi S... Halluru ya dakata da cewar Abba yayo gaba, shi anmasa kiran gaggawa, bai kuma kamata ace ya tsaidashiba shi, tunda ya sanarma iyalansa yau zai dawo.
Da farko Abba kamar zaice suzauna kawai harya gama, saikuma tunanin yariga da ya sanarma su innaro zai dawo ya fad'o masa, shiyyasa kawai yataho, basuyi wani nisa da tafiya ba driver ya tsaya wai motar Na d'aukar zafi, ALLAH Sarki Abba, sai shima ya fita domin taimaka masa, suna tsaka da duba motarne garadan samari hud'u suka fito daga ma6oyarsu sukai ma Abba d'aukar amarya. Duk yanda yaso kare kansa ya gaza.
Driver da dama duk cikin shiri yayi haka saiya hau tsallen k'arya cikin pretending yana ihun azo a taimakesu, (🤦🏻♀bayan yasan baza'a samu kowaba a wajen tunda jejine☹).
Abba mutumne mai dagiya akan ra'ayinsa, hakan yasa duk yanda sukaso yabasu had'inkai akan zancen Camera yak'i, yama dage shi baisan Cameran da ake magana a kaiba, kuma dayaso basun tun lokacin da ake bibiyarsa da dukiya mai tsoka daya bada, amma basuda kud'in dayakai darajar camera d'in, sannan inda zai bada kodan barazana da rayuwarsa da sukasa aikaitayi tunba yanzuba daya bada, amma yasan ruhinsa Na hannun Wanda ya halicceshi, shine kuma mai kar6a aduk lokacin da yaso, inma sun kasheshi dama kwanansa ya k'arene, Dan haka subar wahalar da Kansu kawaima.
Wannan maganar Ce ta fusatasu, wani ya daki Abba a baki harya fashe, dukda yaji zafi saiyayi murmuahi kawai yana kauda kai gefe.
Wanda sukasa yamusu aikin lalata documents d'in Galadima Na cikin Computers ne ya ankarar dasu zoben hannun Abba akwai wata kimiya a cikinsa, wannan ne ya sakasu cire zoben daga yatsansa, shi Abba saima yanzune yasan manufar zoben, yay murmushi, Dan hakan ya tabbatar masa cewar Galadima yasan wani Abu game dashi.
Duk yanda suka ringa k'ok'arin yima Galadima mugunta a sirrinsa Na Computer Abba Na kallonsu, hankalinsa kuma a tashe yake, amma jarumin namijineshi mai iya sarrafa kai aduk yanayin daya kasance, ko'a fuska bai nuna musu yana tare da damuwar abinda sukeyinba, saida Galadima ya kashe komai nasune Abba ya sauke 6oyayyar ajiyar zuciya, dukda yasan hakan ba shine nasaraba.
Wanda suka saka aiki mai suna William yashiga rud'anin abinda Galadima yayi, Dan da farko yanata cika baki babu wani d'an African daya isa ja dashi a fannin ilimin Computer, bak'ak'en fatar ai a wajen su suke koyan komai, ta Yaya kuma zasu fisu Sani?.
wad'annan kalamai nasa sun Sosa zuciyar Abba da sakashi cikin takaici, shiyyasa yayta jerama Galadima addu'ar samun nasara a zuciya.
Yayinda sukuma wad'anda akema aiki suke kuma hurama William kai da kwanzartashi (ko kishin Kansu basayi😏, a zageku da kuma k'ask'antar daku kuna yabon mai ganinku marasa daraja🤦🏻♀, wata dai bahaguwar rayuwa sai bak'in fata😏🙄.
Dak'ilesu da Galadima yayi ta hanyar kashe komai ya fusatasu suda William d'in, suna kuma kunna Computers d'in komai naciki ya goge, wannan Abu ya rikita William matuk'a, gashidai yagama proud d'in shi kwarone kuma bak'in fata d'an Africa ya masa kwaf d'aya, dukkan fushinsu saiya dawo kan Abba.
Ana cikin haka saiga Alhaji halluru da sauran tawagar y'an group d'in, wad'anda sai yanzune suka samu k'arasowa, da farko Abba ya zata Alhaji Halluru taimakonsa yazoyi, saida yaji suna masa izgilanci sannan ya fahimci komai, cikin tsantsar mamaki yace, “Alhaji Halliru da kanka?”.
Ta6e baki Alhaji Halluru yayi, yace, “zaka bani takarar Governor ne?”.
Abba yay murmushin takaici yana fad'in “Tir da kai Halluru, wannan ai jahilcine, ALLAH shikad'aine ke bada mulki ga Wanda yaso, akuma lokacin dayaso,, yanzu kana nufin duk shekarun daka d'auka a jikina kai dama da manufa kake tare dani?”.
Alhaji Halluru ya kuma ta6e baki yana murmushin mugunta, yace, “Alhaji Auwal kenan, ai bama zaka tabbatar da hakanba sai y'ay'anka da kansu sun d'akko min camera sun kawo, sannan mukuma kasheka a gabansu babu yanda zasuyi, yanzu haka suna gida, zuwa anjima kad'an kuma camera zatazo garemu”.
Zufa ta fara karyoma Abba a dukkan sassan jikinsa, danjin za'ayi amfani da gudan jininsa wajen tarwatsa abinda yad'au shekaru yana rik'ewa amana, k'ala baice da Alhaji Halluru ba, su kuma sai kiraye-kirayen waya suke Na had'ama Galadima tarko.🤦🏻♀
Abba ba tausayin kansa yakejiba, tausayin Galadima yakeji matuk'ar tik'ewa, Dan ganin rai kusan 15 kowa k'iyayyarsa akansa take da muguntarsa...
★★★★★★★★★★
Tunda Galadima ya shigo bai zaunaba, saida yagama had'a komai dazai buk'ata, yabama sarkin mota yakai cikin motar dazaiyi amfani da ita, alwala yay yafita salla massalacin masarautar, bai yarda sun had'u da Sarki ba, yay fitowarsa, koda ya dawo saiyasha magani ya kwanta, kaikace bashida wata matsalane, babu dad'ewa kuwa barci yay gaba dashi.
Bai tashiba saida aka kira sallar la'asar, nanma massalacin yaje, bayan ya dawo yay kiran Momma ta video call, duk suna asibitin hardasu Samha, d'aya bayan d'aya ya gaisa da kowa, Samha harda kukanta tanason zuwa Nigeria, ita missing nasu takeyi sosai. Galadima yace a'a ba yanzu ba, tashi tai tabar gaban lap-top d'in tana kuka, Galadima ya girgiza kai kawai.
Yasha hirarsa da Abie sosai, saboda Alhamdullah jikinsa saidai godiyar ALLAH, dama ciwo keshiga farat d'aya, sauk'i kam sai a hankaki. Addu'a kuma takobin muminice ako yaushe.
Bayan ya gama waya dasu Momma Sir Isa ya kirashi, ya tabbatar masa da komaifa is done, Dan ansami kowanne acikinsu, yanzu haka wasu sunma iso.
Galadima yay murmushi yana shafa fuskarsa. Yace, “Nama canja shawara, zamu canja gidan da zamu ajiyesu da, yanzu akwai wani gida annan kusada plaza d'ina, nagama magana da Saleem komai yayi ready, Ameer duk yakaisu can, insha ALLAH ana idar da sallar Isha'i zan fito”.
Sir Isa yace, hakan yayi, dan acikin yaran nasuma za'a iya samun munafukai, tunda duk sunsan gidan daza'a ajiyesun, yanzu kuwa shi Ameer kad'ai zaisan da wannan.
Galadima ya kira Munaya, dama tun d'azun kiran nashi take jira, ta d'aga tana shigewa cikin bayin d'akinsu Dan kar wani yaji.
Galadima yace, “haryanzu kukan?”.
“a'a” ta fad'a cikin share hawaye.
Yad'an murmusa kawai yana fad'in, “Akwai bak'in da sukazo gidanku?”.
“A'a babu Wanda yazo, sai Siyama da Zarah”.
Galadima yay murmushin gefen baki yana cigaba da danna lap-top, hasashensa yazama gaskiya kenan, gyaran murya yad'anyi kad'an yana fad'in, “kina jina?”.
Munaya tace, “eh”.
“Ki saka ido akan d'akin Abba, motsin kowa yazama akan idonki koda cikin matansane, ko yayyenki maza, Dan za'a iya yin amfani da kowa, inda da dama ma key d'in d'akin yazama a hannunki”.
Munaya tayi d'an jimm alamar tunani, zuwa can tace, “babu damuwa, zan gwada hakan insha ALLAH, amma kunji labarin Abban?”.
“Karki damu, insha ALLAH Abba zai dawo gida, addu'a muke buk'ata”.
Munaya ta jinjina masa kai tamkar tana ganinsa, ta share hawayenta dake zubowa.
Yana yanke wayar nafito, cikin dabara nashiga d'akin innarmu, key d'in d'akin Abba Na d'akko, dukda nasan kowama yana dashi cikin matansa, fitowa nayi naje cikin dabara da sauri-sauri Na saka key d'in cikin k'ofa d'in, cikin addu'ar Neman nasarar kozai karye a ciki, amma ko gezo baiyiba, hannuna sai azabar zogi yake, danma nayi amfani da wani abin sarrafa k'arfene, cirewa nayi nakoma ciki kozan samo wani k'aramin k'arfe dazai iya Shiga, saida nasha wahala nanma sosai kafin Na samo, gashi duk a tsorace nake kar wani ya fahimci abinda nakeyi, cikin kafar makullin Na turashi, Alhmdllh nasamu ya shige, nagwada saka key amma yak'i Shiga, nasan babu yanda za'ayi wani key ya sake shiga wajen harsai mai gyara yazo, tunda kuma Abba bayanan ai babu buk'atar hakan, Dan duk wanda zai buk'aci shiga yanzu lallai akwai manufa. Dukda haka saida nasamo kwad'o nakuma sakawa sannan hankalina yad'an kwanta.
**************************
*_9:00pm_*
Fitowarsa kenan daga wanka baiko tsaya shafa mai ba ya hau shiri cikin wandon da riga k'ananu, fuskarnan babu alamar walwala tattare dashi, komai yana yinsane cikin karsashin fushi da damuwa, ya kammala tsaf yad'an saka turare.
A k'ofar sashensa ya iske Nuren yana jiransa, sauran Hadeemansa dabasuyi barciba suka shiga masa barka da fitowa, kansa kawai ya d'aga musu, d'aya daga ciki ya bud'e masa bayan motar, amma sai bai shigaba ya d'aga masa hannu ya bud'e gaba da kansa ya Shiga, Nuren yay murmushi kawai, yasan yau mazan a wuya suke.
Shiga yay shima mazaunin driver yaja suka fice.
Gidane matsakaici sabo, dagani ko dad'ewa da gama gininsa ba'ayiba, saidai anzuba komai Na amfanin gida, ahaka suke buk'atar badashi haya. Dan haka da saleem yanemi hayar suka bashi kai tsaye.
Suna isowa Muftahu ma ya iso d'auke da su Harun, Alhj Darma, Farhat d'iyar Minister sai mal. Saminu driver Alhaji balala, kusan shima yana hannunsu har yanzun.
Ameer ya mik'e da Sauri yana salute d'in Galadima, hararsa yayi, Ameer yay murmushi yana yin k'asa da kansa. Cikin girmamawa yace, “Ranka ya dad'e wad'annan sune phones d'in yaran da tarkacen kayamsu”.
Jinjina kai Galadima yayi, hannunsa duk biyu goye a bayansa yana zagaya table d'in da aka zube wayoyi, da lap-tops, iPad's dukna wad'anda aka kawo d'in, ya kalli Ameer cikeda k'asaitarnan tasa yace, “Suna INA?”.
“Duk suna sama ranka ya dad'e, Dan inaga yakamata kazauna acan, danka ke ganin motsin kowa daga waje, dukda ansaka cctv a ko ina na wajen”.
Galadima ya kad'a kai alamar gamsuwa da bayanin Ameer.
Cikin takunsa na izza da lafiya ya nufi saman benen dake gidan, Muftahu da Nuren suka kalli Ameer cikin neman k'arin bayani, murmushi yamusu, yana tattare wayoyin yabi bayan Galadima dasu.
A k'aramin falon k'asan ya iskeshi tsaye yanabin komai da kallo, Ameer yace, “ranka ya dad'e yazamuyi da wad'annan phones d'in nasu?”.
Galadima yad'an ciza lips yana kallon Ameer, yace, “inasu Nuren d'in?”.
“Suna k'asa”.
Galadima baice komaiba, hakan da yayi ya saka Ameer fahimta su shigo kenan, saiya ajiye abin hannunsa ya sauka k'asan Dan kiransu.
Saleem yafito daga wani d'aki ya taso k'eyar wani matashin Saurayi k'yak'yk'yawa, daka gansa kasan hutu yagama ratsashi, kallo d'aya Galadima yamasa ya d'auke kansa, Saleem yaja kujerar dining d'aya ya zaunar dashi, sannan yasaka igiyar daya d'auka ya d'auresa jikin kujerar, saurayin sai zaginsa yakeyi, amma Saleem ko kulashi baiyiba, saida yagama tsaf sannan ya kalli Galadima, wata alama yamasa da ido.
Sai kawai naga Saleem ya d'auke saurayi da wani shegen mari, Wanda yasaka su Nuren dake shigowa jan birki suna kallon Saleem, bakin saurayi bai mutuba, Dan haka Saleem yakuma zuba masa wani har hancinsa Na fashewa, azaba ta sakashi kama bakinsa yay shiru yana huci da had'iye hawaye.
Galadima ya ta6e baki yana d'age kafad'a. Alamar sudai suka sani.
Haka Saleem yayta fiddosu d'aya bayan d'aya harsu 7, maza 5 mata 2, sai Farhat cikon ta takwas, amma su matan babu wacce aka d'aure, mazanma idan har bakayi gardama ba ba'a ta6asu.
Saleem yagama jerasu reras gaban Galadima daya d'ora k'afa d'aya kan d'aya cikin kujera yana danna lap-top hankali kwance.
Muftahu da Nuren dai sunyi mutuwar zaune, basu ta6a tunanin Galadima zaibi wannan hanyarba, gashi yak'i basu wata fuska dazasu masa magana ko tambaya.
Saleem da Ameer suka kamo Harun shima aka d'aureshi a gefe ba cikin yaranba, shi baima cikin hayyacinsa, Dan su Nuren saida suka shak'a masa Abu, Alhj Darma da m. Saminu ne kawai ba'a d'aureba, suma dai aka kawosu gabansa aka zube.
Galadima ya d'ago yana kallon su Muftahu dasuka Gaza barin kallonsa, cikin ta6e baki yace, “kallonfa?”.
Ajiyar zuciya suka saki a tare, Nuren yace, “Brother mufa bamu fahimtaba”.
Lips yad'an ciza yana ta6e baki da fad'in “Duk wannan dalla-dalla d'in da akai muku?”.
Shiru sukayi Dan inhar a fahimtarsuce dai yau sunzama Kidnappers Na gaskiya kenan🤭😂.
Galadima yace, “Well, Ku ajiye zancen fahimta gefe, kuduba phones d'in su Wanda babu charge a saka, Dan zuwa safiya duk za a fara aiki dasu, daganan mai buk'atar barci yaje ya kwanta kawai, sauran aiki sai safiyar gobe”.
Babu Wanda ya iya cewa komai, dan sunsan dai Galadima bazai sakasu a had'ariba saboda son zuciya, Ameer ya fidda Chargers suka saka dukkan wayoyi ajikin caji, Dan akwai wuta.
A wannan daren Galadima ya tura sak'o ga dukkan iyayen yaran, lokacin duk sunbar wajen Abba sun koma gida, anbarsa da garadan samarinnan akan sai washe gari, Dan sun tsarama su Zarah duk yanda zasuyi.
Babbar magana, Alhaji Mansur habibu Uba yana shirin kwanciya barci wayarsa tayi tsuwar shigowar sak'o, sharewa yayi, hakan kuma saiya saka matarsa a zargi, tatashi zata d'auki wayar ya hana, saita kuma tsarguwa, a zarginta wata shegiyarce ta turo masa, ganin ta fusata saiya bud'e sak'on.
Babu shiri ya dirgo daga gadon a tsorace yana tambayarta ina nerh-nerh take?.
Da mamaki race, “batace ta sanar maka zataje wajen Rahma ta kwanaba?”.
A rikice yace, “Rahmar ubanwa, maza kiramin ita yanzunnan su Abubakar suje su d'akkota”..
Bata fahimci inda ya dosaba, amma rikicewarsa saiya sakata d'aukar waya ta kira nerh-nerh d'iyarsu, wayar na Shiga amma ank'i d'agawa, cikin tsantsar tashin hankali ta sanar masa, ya daka mata tsawa yana fad'i “ki kira Rahma d'in ko wani d'an gidansu mana!!”.
Maida akalar kiran tayi kan Rahma, itama dai ank'i a d'aga, bataso kiran Hajiya yalwa ba, dan atunaninta kota kwanta, amma dole ta kiratan.
Hajiya yalwa Na zaune kusada mijinta Alhaji Abdul-Naseer Nafi'u kiran ya shigo, tayi mamakin Kiran, Dan hajia Marya bata kiranta a irin wannan time d'in, saitayi tunanin ko takasa hak'urine da rashin nerh-nerh abinka ga auta. Cikin raha tayi picking tana nunama mijinta wayar da baki, yay y'ar dariyarsu ta manya yana kuma kishingid'a da zubama matar tashi idanu.
Tambayar da Hajiya Marya tama hajiya yalwa ce ta rikitata, ta mik'e zumbur tana fad'in “bara Na duba to, Dan wajen 3pm suncemin zasuje zaga gari, amma 7 zasu dawo gida, to wlhy bak'i mukayi suka d'auke hankalina nikuma ban nemi ganinsuba, tunda ina tunanin sundawo suna sashen Rahma”.
Duk kiranda Alhaji Abdul-Naseer kema hajiya yalwa batajishiba, hakan ya sakashi biyota.
Kusan atare suka iso sashen Rahma d'iyarsu, y'an aikinta guda biyu Na zaune a falonta sunata gyangyad'i, kai kace sashen wata mai aurene ba budurwa y'ar 17years ba, Dan itace autarsu suma.
Hajiya yalwa ta dakama masu aikin tsawa tana tambayarsu ina su Rahma?.
A rikice sukace suma dawowarta suke jira tun d'azun (Dan sunsan inhar ta iske sunyi barci zasu yabama aya zak'inta, maybe ma yazama sanadin barin aikinsu).
Alhaji Abdul-Naseer yana k'ok'arin gwada kiran Rahma shima irin sak'on Alhaji Mansur ya shigo masa.
Ai sai suka kuma rikicewa, Ashe sak'o dukya jema sauran abokansu, dan dannan suka Shiga kiran juna kowa yana tabbatarwa d'an uwansa Galadima ya d'auke masa d'a ko y'a.
A wannan Daren suka sanarma police, gidajennan 11 babu Wanda ya rintsa barci, dukda yaran 8 ne a hannun Galadima, biyu basuda sauran yara a gabansu, duk sunyi aure, Galadima kuma yakafa musu nasu tarkon ne daban, biyu kuma a ciki bamasu ta6a haihuwa ba, biyar sun mutu yace bashida matsala da matacce, shi wannan saisunje babbar Court ALLAH zaimusu nasu hisabin. Sauran yaransu irinsu Alh halliru kuma yace nasu mai sauk'ine tunda manyansa suna hannunsa.
Tun a wannan daren manyan police suka Shiga Neman ina Galadima yake, tunda kai tsaye yasaka sunansa a sak'on messages d'in daya turama iyayen yaran.
Galadima yarigada ya tsara komai yanda ya dace, duk wata waya dazata fita a wayarsu saiya ganta yakumayi recoding d'in maganar, wannan yasa duk abinda suka fad'ama police yaji, murmushi kawai yaytayi, yayinda su Nuren sudai hankalinsu bai wani kwantaba, dukda sunji dad'in rikicewar da mak'iyar Galadima sukayi.
Abinka ga manya, tun a labaran 12am Na daren ranar aka fara saka maganar, labari yafara shiga kunnuwan wad'anda basuyi barciba.
Ciki kuwa harda y'an masarautar gagara badau.
Hankalin mai martaba ya tashi, a Daren ya aika jakadiya data rako matarsa turakarsa kiran Galadima, danya kira wayarsa switch up.
Lokacin da jakadiya taje sark'in k'ofa ya tabbatar mata Galadima ya fita tun farkon dare.
Komawa jakadiya tayi ta sanarma mai martaba, aiko yakuma shiga tashin hankali, minene haka Sameer dayake kallo mai nutsuwa da hankali ya aikata?.
Yana cikin wannan damuwa Waziri ya kirashi, ya tabbatarmasa Sameer ya turo masa sak'o shima Harun yana hannunsa.
Zuface ta shiga jik'a mai martaba, yanzunan duk jajen da akeyi Na 6atan Harun d'an waziri dama Sameer yasani amma yay kunnen uwar shegu da kowa, hazbinallahu wa ni'imal wakil, shikam baya fata wannan mummunan labarin yaje kunnen 'Dan uwansa dake kwance cikin halin matsananciyar jiyya (kunsanfa har yanzu babu Wanda yasan samun sauk'i da Abie yakeyi, bayan ahalinsa dasu papi) a gagara badau babu Wanda yasani.
Su Galadima duk suna ganin abinda ke faruwa a TV suma, amma ko'a kwalar rigarsa, damuwa d'aya kecin ransa halinda Abban Munaya ya tsinci kansa a ciki, amma sauran matsalolin dama dukya dad'e da shirya abinsa, komi zai biyo baya dama zuciyarsa ta shirya d'auka.
Yau dai kam kusan a zaune suka kwana, abin tausayi saiga Galadima da kwannan kujera, aiko yasha wahala, Dan tashi yayi jikinsa Na matuk'ar masa ciwo, d'akin da aka saka masa kayansa yashiga, yasamu yay wanka sannan yayo alwala sukayi salla a jam'i, Dan har yaran duk kwancesu akayi, wad'anda kuma basayi suna zaune daga gefe.
Galadima yace Ameer yaje da y'ammatan su had'a musu breakfast, cikin cika umarni yatasasu gaba suka fice, saidai kuma Farhat ce kawai ta iya girkin a cikinsu, gashi tanada Asthma, bakomai take iya sakewa wajen yiba, haka dai Ameer ya saka Nerh-nerh da Rahma suka taimaka mata da Abu mai sauk'i, dayake a tsorace suke, komai aka saka su yi sukeyi, sunga zuk'ek'iyar bindiga ahannun Ameer yo🤭😂.
Koda aka kawo abincin dukda tashin k'amshi da yakeyi Galadima cayay bazai ciba, sudai su Muftahu kam ci sukayi, shikuwa yak'are dacin cake da tea, Wanda dama da kayayyakinsa yazo caf (Galadima fa da shirin zama yazo🤣 fans).
Tun'a daren jiya gidan da su Galadima suke aka zagayeshi da y'an sanda, yasan kuma da hakan Dan CCTV Na nuna masa komai, amma saiyayi tamkar baima San da zuwansuba.
Harun dai yak'i ci shima, hasalima sai yankama Galadima magana yake, wai inhar ya isa shid'in shegene ya kwanceshi mana, Ashe shid'in matsoracine ma, Dan ba'a sake d'aure kowaba bayan sunyi salla saishi Harun d'in daya nemi yin gardamar k'in nutsuwa waje d'aya.
Ko inda yake Galadima bai kallaba.
Nuren yay gyaran murya, duk suka maida attentions d'insu garesa. Yace, “inhar kun shirya bamu had'inkai kowa zai fita a gidannan lafiya babu ko kwarzane a jikinsa, Dan bamuda matsala daku, da iyayenku mukeyi, Wanda yaza6i kuma tafiya barzahu babu shiri saiya nuna jarumtarsa ko rashin kunya, wannan wawanma ya isheku izna”. Yay maganar yana nuna Harun daketa bige-bige yana kumfar baki masifa.
Duk suka amsa da zasu bada had'inkai.
Yau dai Darma kam shima yashiga hankalinsa, Dan yaga lamarin yafi k'arfinsa.
Galadima ya d'auki k'aramar wata waya dake kusa dashi yafara dannawa yana shan tea d'insa hankali kwance, yayinda k'afarsa ke hard'e d'aya kan d'aya.
Munaya ya kira, wadda itama batayi isashen barciba, gashi suna a yanayin rashin tsarki balle ta duk'ufa gayama ubangiji itama, amma dukda hakan bata fasaba, zuwa dare kuma kowa ya ankara da rashin dawowar Abba akwai matsala, dan around 7:30pm Baba k'arami ya dawo gida, babu dad'ewa kuma saiga Dady shima, dawowarsu yasaka kowa Sanin mi ake ciki, innaro ce kawai aka hana kowa ya sanar mata.
Babu Wanda yay barcin kwanciyar hankali a gidan su Munaya, saidai yaran k'anana dabasu San dawan garinba, irinsu Inna ma ai akan sallaya suka kwana suna gayama ALLAH kukansu😭.
Basuda wuta a daren jiya, shiyyasa basuga abinda yake faruwaba, rashin kwanciyar hankali ya hana a kunna musu gen..., Gasu Abdurraheem kwana sukayi kuka.🤦🏻♀
Cikin sanyin jiki Munaya ta d'aga kiran, muryarta ta dushe saboda kuka, ahaka ta gaisheshi.
Ya amsa a sanyaye shima yana tambayar yaranshi, tace, barci sukeyi.
Cikin lumshe ido yace, “karki damu daduk abinda zaki gani, sannan karki kirani, dan duk kiran dazakiyi nasan baizama lallai nikad'aine zan jishiba, zan dinga kiranki dakaina insha ALLAH. Please take care of yourself”. Kitt ya yanke wayar batare da yajira cewarta ba.
Kanta ta cusa cikin k'afafu ta fashe da kuka, yayinda Munubiya ma ke gefenta tana nata da shayar da Ameen daya tashi barci.
Galadima kuwa yana yanke wayar ya mik'e cikin takun izza da k'asaita ya k'arasa gaban Harun da bakinsa yakasa yin shiru.
Izzarsa da k'asaitarsa Na burge matasan samarin nan, hakan yasa duk suka bishi da idanu har y'ammatan, ga fuska a cakud'e babu alamar yasan minenema dariya.
Gaban Harun ya tsaya hannayensa duka a cikin aljihun wandonsa, babu Wanda yakula da lokacinda Galadima yaciro hannunsa d'aya a aljihu, saidai k'arar mazgar Harun dayayi abaki sukaji kawai, kafin Harun ya farfad'o Galadima yakuma k'ara masa ta d'ayan gefen.
Sannan ya d'an risuno yanama bakinsa alamar zip da yatsunsa biyu🤐, Harun yamasa shiru kenan🤣.
Kutt, gaskiyafa Harun ya mazgu babu k'arya🤭🤣.
Amma d'an bala'in naku bakinsa bai mutuba, bayan ya farfad'o daga azabar dukan saiya cigaba da magana cikin haki da huci.
Sharesa Galadima yayi yakoma ya zauna dan fuskantar abinda ke a gabansa, a fusace ya d'auki k'aramar bindigar daya fiddo yanzu yafara Harbin inda Harun yake, ta saitin k'afafunsa. Rikicewa kowa yayi, Harun yashiga mutsu-mutsu da k'afafu yanasan d'agewa Dan kar Harbin ya sameshi.
K'aramin d'an iska Ashe kanajin tsoron mutuwa🤣?.
Wannan harbi ya kid'ima police d'in dake a wajen gidan, akuma dai-dai lokacinne manyansu suna iso suma, kuma duk sunji harbin.............✍🏻
Humm babbar magana, komiye shirin Galadima Na zama kidnapper?.🤦🏻♀
Wane ahiri kuma su Zarah sukazo dashi gida🙆🏽?.
Sannan wane shiri Galadima yake akan ku6tar Abba? tunda yace plan B😔☹.
Ina baba mai kanwa? Wane taimako zaibamu shima😭.
Kumuje zuwa my guys karku k'osa dai, sannu-sannu bata hana zuwa, saidai a dad'e ba'a zoba😏🐢.
*_ALLAH ya gafartama mahaifanmu_*😭👏
🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*
*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BOOK 3_* 👉🏻1⃣6⃣
.................Jin tsayuwar motoci ya saka Ameer lek'awa ta window, juyowa yay ya kalli Galadima, “Ranka ya dad'e y'an sandane”.
Baki Galadima ya ta6e, ya share tamkarma baijiba, yana cigaba da bud'e wasu file daya fiddo a briefcase. Saida yaja kusan 1 minute sannan ya mik'ama Nuren dake kusa dashi wasu files, ya zaro takarda kuma yay rubutun dabai Gaza layi biyarba ya mik'ama Ameer da wata k'amar waya a kwali.
Kar6a Ameer yazo yayi, batareda Galadima yayi magana ba ya nuna masa window.
Muftahu daya fahimta yace, “Ameer ka jefa musu takardan da wayan”.
Ameer ya amsa da to, yanufi window d'in, cikin dabara ya jefa kwalin da takardar.
Wani d'ansanda dayaga tahowarsu yay saurin zuwa kusada window d'in, ALLAH yabashi nasarar cafewa.
D.p.o dake tsaye tare da sauran police ana shawarar yanda za'a shiga gidan ya kaimawa.
Yay salute nasu kafin ya Isar da sak'on dukda yasan duk sunga daga ina kayan suka fito, d.p.o ya gyara tsayuwarsa yana fad'in “bud'e kwalin mu gani”.
Bud'ewa yayi, yaciro wayar yana cewa, “wayace sir”.
Cikin ta6e baki d.p.o ya jinjina kansa, yace, “takardar fa?”.
Itama bud'ewa yayi, yafara karanto abinda ke jiki, wanda Galadima ya rubuta da harshen nasara.
*_Kamar yanda suka fad'a Muhammad Sameer ba d'an ta'adda baneba, inhar zakubi yanda nace lallai yarannan zasu fita lafiya, idan kuma har kuka nuna k'arfin iko, zanta jeho muku gawarsu d'aya bayan d'aya ta saman benenan, ga wayanan, idan kuna buk'atar magana koni ina buk'ata ta wadatar, Dan kar wani yay gigin cewa zai shigo. Idan nayi ba dai-daiba a gafarceni👏🏻_*
Daga d.p.o har jama'ar dake kusa dashi duk ajiyar zuciya suka sauke, ya jinjina kai yana cije bakin mamaki, cikin sauke numfashi yace, “saimu bishi yanda yakeso mugani, idan munga zai mana wasa da hankali sai a d'auki mataki, C.. babangida a zagaye gidan”.
“Ok sir”. C babangida ya amsa yana salute nashi.
Dandanan suka warware wani blue d'in zare suka zagaye gidan dashi, mutanen anguwa dasuka fara fahimta harsun fara taruwa kallo, harma wad'anda sukaji a labaran sunfara gangarowa anguwar damin ganema idonsu.
Duk abinda ke faruwa Galadima Na zaune k'afa d'aya kan d'aya yana kallo ta CCTV, sai famar buga pen yake saman la66ansa a hankali, suma dai su Muftahu dasu Harun suna kallon komai.
Kujera aka kawoma d.p.o ya zauna, dayake da sauran safiya babu maganar neman runfa ko umbrella.
Wayar d.p.o ya kar6a da kansa, dan case ne Na manya IG da kansa yakirashi, yakuma abbatar masa shima yana nan zuwa.
Shiru d.p.o yay yana bincikar wayar da Galadima ya aiko da ita, babu komai a cikinta sai Number guda d'aya, baice komaiba yaciro wayarsa yayma IG bayanin komai.
Daga can IG yafara fad'a, wai tayaya zasu saurareshi, bayan d'an ta addane, duk Wanda zai iya kidnapping aiko d'an ta'addane, kawai su nuna masa k'arfin iko wajen ku6tar da yaran.
Shidai d.p.o ya kwantar da murya cikin sigar lallashi yace, “Nidai Sir da ace za'abi ta tawa daminbishi a hankali, maybe akwai sak'on da yakeson isarwa, karfa mu manta shima d'an manyan mutanene, shikansa akwai sarauta mai daraja a kansa, ai mai martaba bazai ta6a jin dad'iba shima, tunda ya buk'aci dama mu bashi, idan munga batai manaba saimu d'auki mataki”.
IG yace, “shikenan, Ku kirashi muji miyake buk'ata, nima a had'a dukkan maganar da zakuyi dani naji komai, dukda munama hanyar isowa yanzunan”.
Cikeda farin ciki d.p.o yace, “ok sir”.
Duk kayan aikin dasuke buk'ata suma sun tanadesu, yayinda y'an jarida suka fara isowa wajen.
Shima C.P ma saigashi ya iso, duk suka k'ame wajen salute nashi har d.p.o.
Ya amsa musu cikin jinjina kai, sannan ya buk'aci jin mi'ake ciki?.
Bayani d.p.o d'in yamasa, shima ya gamsu da shawarar abi komai a sannu d'in.
Galadima ya murmusa yana lumshe idanunsa yana sauke ajiyar zuciya. Saboda dukkan wayar da d.p.o yay da IG a kunensa ne.
Sudai su Nuren sunyi jugum-jugum Dan son ganin minene shirin Galadima waine?, da har yaza6i fiddo kansa wa duniya a matsayin mai laifi?.
Kiran da C.P yayi da kansane ya shigo wayar Galadima bud'e ido yayi yana kallon su ta CCTV, sannan yay picking call d'in, shiru yay yak'i magana, saida C.P ya fara masa sallama sannan ya amsa.
C.P yace, “Ranka ya dad'e barka da safiya”.
Baki Galadima ya ta6e, ya amsa da “Barka dai”.
Gyara zama C.P yay yana kallon saman gidan, duk su Galadima suna ganinsa, yace, “Ranka ya dad'e muna saurarenka, ka fad'i buk'atar taka, inhar batafi k'arfinmu ba za'a biya maka insha ALLAH ”.
“Humm” Galadima ya fad'a yana mik'ewa tsaye, duka hannunsa Na zube cikin aljihu, dayake yana amsa call d'in ne da abin da ke kunnen sa.
Falon ya shiga zagayewa cikin takunnan nasa na k'asaita da izza, saikace namijin tantabara yana gwada gasar tafiya a gaban matarsa😜🤣.
Suko sai binsa da kallo suke tamkar wani magiji.
A hankali yace, “Buk'atata ta farko shine iyayen yarannan su fiddo Alhaji Auwal fharuk, idan sunyi haka lallai zakuji manufata kai tsaye batare dana ja muku raiba, Dan nima ina buk'atar hutu”.
C.P ya shiga jinjina kansa kawai yana sauraren Galadima da dukkan sauran police d'in dasuma sukeda alhakin jin komai ta hanyar abinda suka saka a kunne.
Bai k'ara komaiba ya yanke wayar, Yakoma mazauninsa ya zauna yana kallon yaran dasuma dukshi suke kallo, d'an murmusawa yayi yana d'aukar ruwan daya ajiye, saida ya bud'e murfin ya mik'ama Wanda yake kusa dashi.
Shima yay murmushi yana girgiza kai da fad'in “A'a ranka ya dad'e, Na gode”.
Galadima ya mik'ama sauran suma, amma duk sai sukace A'a, murmushi yayi yasaka kayansa a Baki yasha, yana kallon Harun daya zuba masa ido, rabi yasha ya mik'ama Harun sauran, amma saiya kauda kansa gefe, Galadima ya ta6e baki yana d'aga kafad'a alamar kaika Sani.
Sauran ruwan ya ajiye yana kuma kallon yaran, da hannu yakuma yima Na farko alamar yaya sunansa?.
Bai fahimtaba Dan haka ya kalli Na kusa dashi, sannan yakuma kallon Galadima yana nuna kansa da fad'in “Sunana wai?”.
Galadima ya jinjina kai yana lumshe idanu.
“Sunana Ahmad Bana bb gana".
Galadima ya had'e yatsansa babba da manuniya👌🏻 alamar nice name.
Ahmad yace, “Thanks you sir”.
Na kusa dashi Galadima ya sake nunawa, shikuma yace, “Ahakam Balala”.
Shima jinjina Galadima ya masa, nakusa dashi kuma Gebirel Timothy, sai Nerh-nerh Bilkisu Mansur, Rahma Abdul-naseer, Yassar Mamman, Sulaiman sager sulaiman, Marcel Miracle.
Cikin murmushi Galadima yace, “Duk sunan y'an gayune daku”.
Gaba d'aya suka sanya dariya, banda Harun da Alhaji Darma, Harun yasan Galadima sosai, dama yanada tsokana idan yaso hakan, koda kai zakayi dariyar shi ya fuske kuwa.
Galadima Yakuma fad'in “Duk kun kammala Secondary schools ne?”.
Duk suka amsa da eh, kowa yashiga fad'a masa matsayin karatunsa da abinda suke karanta, dukda ba magana yakeba murmushinsa Na sakasu farin ciki.....
.............★
A can kuwa waje, police nata k'ullawa da kwancewa da jiran isowar IG, Dan yace su jirayi zuwansa.
Dukda Galadima yana hira da yaran hankalinsa nakan saurarensu ta abinda ke kunnensa.
Babu dad'ewa saiga IG ya iso, kar6ar wayar yayi da kansa bayan sungama salute nashi ya zauna, ya kuma kiran Galadima da kansa.
Galadima yay picking amma sai yak'i magana yanzunma, hakanne yasaka IG yin magana cikin takaici da fusata, “Kai bamason rainin hankali, kafad'i abinda kawai kakeso duka amaka kabasu yaransu”.
K'ala Galadima bai ceba ya yanke wayar.
Mamaki ya kama IG, C.P yace, “Sir dadai anyi hak'uri an musu magana kawai suma aji mizasu ce”.
Cikin matuk'ar takaici IG ya dangwarar da wayar yana huci da cire hular kansa, da hannu yayma C.P umarnin a kirasun.
Da Sauri Aka danna kiran wayar d'aya daga cikin su, dama duksun tattarune a waje d'aya, Dan haka ya saka Hans free duk sunaji.
C.P da kansa ya sanar musu buk'atar Galadima, kallon kallo aka dungayi, kowa ya kasa magana, Shidai C.P ya yanke wayar yana fad'in “nanda mintuna 10 zasu kira”.
Suna ganin C.P ya yanke wayar suka hau cecekuce da fad'in yaronan yagama raina musu hankali, kaza-kaza dai, wasu suna bada goyon bayan abadashi sai abi tawata hanyar a kar6i camera d'in saboda suna matuk'ar k'aunar yaransu, wasu kuma sunce kar'a sakeshi, Dan haka tamkar tonon sililine agaresu. Sundai kasa samun matsaya har 10minute's ta cika C.P ya sake kira. Ba'a samu Wanda ya iya d'agawaba harta yanke.......
(**************************)
Zuwa yanzu gidan su Munaya sunsan halin da'ake ciki game da Galadima dakuma maganar fitowar Abba, Dan y'an jarida nata yad'a komai live a gidajen redio da TV, ga masu d'auka a waya y'an gani da ido dasukazo suka kafa suka kuma tsare.
Kuka dai Munaya Na shansa, tayi wujigi-wujigi, miji da Uba duk suna cikin matsala, da k'yar inna ta bata tea tasha da kanta, yaranma sai an mata dole take shayar dasu, ta lafe jikin innarsu tanata hawaye daga ita har Munubiya, yaran sai innaro dasu mama rabi'a da sukazo gidan Tun farar safiya ke kula dasu.
A can gefe kuma Zarah da Siyama NATA zagayen d'akin Abba Dan son samun damar shigewa su d'auki camera🤦🏻♀.
**************************
Alhaji Hallurune yabasu shawarar su d'auka kawai suce su k'arya ake musu Alhaji Auwal baya hannunsu.
Wannan shawarar sukabi, da Kansu suka kira C.P suka shaida masa. Sharri Galadima ke musu.
Galadima dakejin komai yayi murmushi kawai yana cizar lips. Laptop d'insa ya janyo yafara danne-danne.
Daga can C.P ya yanke wayar yana Neman izinin IG domin kiran Galadima shima.
IG ya bada izini zuciyarsa Na sakejin zafin Galadima da rainin wayonsa.
Saida ta kusa tsinkewa sannan Galadima yay picking, C.P ya sanar dashi amsar da suka bada.
Cikin murmushi mai sauti da har su C.P sukeji Galadima yace, “ga za6i biyunan, kodai su fad'i inda yake, kokuma su sakoshi, kokuma shi yasaki video d'in yanda suka saceshi”.
Jikin C.P fa kansa yafara sanyi, Dan yafara hango k'amshin gaskiyar Galadima.
Bindiga Galadima ya nuna Alhaji Darma da ita, yamasa alamar ya matso gabansa, jikin Alhaji Darma Na rawa ya matso, waya ya mik'a masa, sannan ya danna kiran su C.P yana fad'in a had'ashi dasu yanzunan.
Kallon IG C.P yayi, alamar neman izini, IG ya bada damar hakan. Dan danan aka had'a Galadima da su, bindigar hannunsa ya d'ora saman kan Ahmad, maimakon Alhaji Darma, jikin Ahmad yafara rawa, tuni yafara kuka saboda tsoro, tsawa Suka dakama Galadima daga can.
Ahmad daketa mazari ya sanya kuka yana fad'in “Dady please and please kubashi abinda yakeso Dan ALLAH, wlhy zai kasheni, wayyo daddy I love you so much”.
Tuni Alhaji Bana ya rikice jin muryar d'ansa, Galadima ya cire bindigar daga kan Ahmad ya harbata gefe, k'arar ta tsorata su Ahamad suka rikice da ihu.
Rud'ewa su Alhaji Bana sukayi, Dan azatonsu Galadima ya kashe Ahmad ne, su kansa su IG dake waje duk sun tsorata da tunanin ko Galadima ya harbi wanine a cikinsu.
Galadima yace, “idan Baku shirya sakinshiba zan kashe Na gaba kuma”.
A tare suka hau ihu kowa yana rige-rigen fad'in zasu saki Abba.
Galadima ya ta6e baki yana gimtse kiran.
Alhaji Bana dai ya suma tuni, saboda tunanin an kashe masa d'a. Saidai suka zuba masa ruwa ya farfad'o, kuka rurus yashiga musu yana kiran sunan Ahmad d'insa, Yakuma rikicewa lokacinda Hajiya Fannah Maman Ahmad ta kirashi. Kasa d'agawa yayi.......
****
Galadima yay kiran su IG yana fad'in “inhar suka nakasa Abba ko kawoshi da wani mummunan raune abakin ran d'aya daga cikin y'ay'ansu, Dan haka a matsayinsu Na police su gargad'esu.
*********
Antura Police inda suka kwatanta aje a d'akko Abbansu Munaya.
A inda aka d'aukeshi suka iskeshi ajiye cikin mota a sume, haka suka d'akkoshi suka taho, kai tsaye asibiti aka wuce dashi domin duba lafiyarsa, dukda babu wani ciwo a jikinsa Na alamar duka sai fashewar baki da kumburin da fuskarta tayi shima bada wani yawa can sosaiba.
Galadima sunga komai a TV saboda nunawar da akeyi, hawayen da suka taho masa ya had'iye da k'yar yana sunkuyar dakai danma kar wani cikin yaran kosu Muftahu su fahimci wani Abu, saidai tuni Nuren and Muftahu da Harun sun fahimceshi, Dan sunsa halayyarsa duka, yana da tausayi ainun.
Ran Harun A 6ace yake akan bada Abba dasu Alhaji Mansur sukayi, zuciyarsa sai tafarfasa takeyi, gashi kuma a d'aure.
Galadima ya mik'e yana bada izinin kowa yaje yay alwala time d'in salla yayi.
Idan kuma anyi salla su Farhat su shiga kitchen nema musu abinci.
Wannan adalci Na Galadima yanata tasiri a zukatan yaran, harsu gebiral.
Duk yanda Galadima yace haka sukayi, har Harun dake d'aure saida aka kwanceshi bisa tsayawar Ameer kansa da bindiga yay alwala.
Koda su IG suka nemi yin magana da Galadima saiya jefa musu takardar yana sanar musu time d'in salla yayi, bazai sake saurarensuba sai yayi salla..
Dole sukabi yanda yakeso, suma kuma ya tunatar dasu abinda suka manta.
.............................★
Bayan idar da salla da gama girkin su Farhat aka kawo abincin kowa ya d'ebi iya buk'atarsa, yanzuma Galadima bai Ciba, kwanciyarsama yayi cikin kujera ya lumshe ido.
Harun dai anji wahala anci yanzu🤣😜.
.............................★
Tuni mazan gidan su Munaya suka d'unguma zuwa asibitin Dan duba halin da Abba yake ciki, matan dai da yaran an barsu a gida, sai innaro kawai data Dage sai taje aka tafi da ita.
.............................★
Buk'ata ta biyu da Galadima ya kawo bayan idar da salla itace a tura jami'an tsaro suje subama iyalan Abba tsaro a gidansa, hakama a asibiti.
Babu musu IG yasaka C.P, shikuma CP yabama D.P.O Umarni, dandanan aka sanar da station d'in yankin su Munaya, aka kuma k'ara dawasu police d'in harda mata da zasu shiga cikin gida.
Munaya taji dad'in hakan da Galadima yayi, Dan a tsorace tale dama.
Dole kuma Zarah da Siyama suka nutsu, Dan Munaya k'ofar Abba taja zugar y'an uwanta suka shimfid'a tabarma sukayi zaman jugum-jugum d'in a can.🤨👍🏻.
************************
A masarautar gagara badau kam babu abinda kakeji Na tashi sai k'ananun magana. Bayi da kuyangi, dogarai da y'an gidan, manya da yara, kowane hadimi burinsa yafara kaima sashen dayake gulma, sunyi gungu-gungu suna tayi, sai anga wani babba zai wuce saikiga an watse.
Mai martaba ya kira papi, dukda yasan shima yaga komai, bayan sun gaisa a mutunce irin gaisuwar d'a da uba, suka shiga tattauna abinda ke faruwa, papi yace, ya kirashi amma wayarsa a kashe, yakira Nuren ma shima waya a kashe, Dan yasan lallai a tare suke shuka wannan tsiyar.
Mai martaba yace, “To amma Abba kaga kuma yanzu ga surukin namu sun fiddo kamar yanda ya buk'ata. Ina ganin akwai wani Abu da Sameer keson ankarar da jama'a Wanda mu bamu San dashiba, nasan halin yaronnan yanada k'yawawan halaye ababen koyi......”.
Cikeda 6acin rai papi ya katse mai martaba, “Jalaludden komai k'yawun halin Muhammad a yanzu ba kowane zai gansu koya yarda dasuba, dukda inaji ajikina bawai ganganci ya sakashi yin hakanba, dama yanada hujja, amma miyakai Na kisa?, a labarai sun nuna ya kashe yaron Alhaji Bana, shin wannan halin mutanen kwaraine? Wannan hanyar dayabi fa bazata ta6a 6ullewa da shiba sai 6ata masa suna damu kanmu, daga fitowar maganarnan zuwa yanzu nasamu kira babu adadi”.
Mai martaba yace, “kayi hak'uri Abba. Insha ALLAH zan shirya naje wajen zuwa anjima kad'an”.
“Shikenan. Idan naga nima abin yayi tsamari zan taho”.
Sallama sukayi kowa yana jimami akan lamarin.
Tunda labari yakaima mama Fulani tashiga tafa hannu tana sallallami da fad'in “A lallai zai iya zai aika, yo wannan yaron mai ido a tsakar goshi, fitinanne zai 6atama masarautarmu suna akan wani banzan talakan surukinsa, akuwa yanda ya kashe d'an mutane shima kasheshi za'ayi, idan munan ya rainamu yanzu kam ya d'ebo ruwan dafa kansa, fand'ararre kawai gagararre”.
Haka taita k'ananan magana da jifan Galadima da munana.
Oho shi baimasan tanayiba☹😏.
********************
A asibiti likitoci sun Shiga bama Abba taimakon gaggawa, Dan ba'asan minene ya sumar da shiba, tunda babu wani alamar duka ko harbi ko makamancin wannan a jikinsa..
**************
Suma police sun buk'aci Galadima ya basu gawar Ahmad.
Murmushi yay yana kallon Ahmad d'in dake zaune yana shan ruwa saboda tsoratar dayayi sosai ta harbin da Galadima yayi, har yanzu yakasa sakin jikinsa, salla ma da sukayi a d'arare yayita, yazata da gaske shid'in aka harba, saida Galadima yayma Saleem nunin abashi ruwa, Saleem yakawo ma Ahmad ruwa, a lokacinne ya farga da Ashe yanada rai bai mutuba🤣😜.
Ya kar6i ruwa kuwa jiki Na rawa ya shiga kwankwad'a idonsa akan Galadima dake masa murmushi, yana bama su IG amsa da fad'in “karku damu yalla6ai. Inada freight d'in dazan dunga saka gawarsu anan, bayan aiki ya kammala saisu d'auki y'ay'ansu sumusu sutura, idan kuma sunyi abinda nakeso kaga magana ta k'are, gawar Ahmad kawai ce a k'asa dai yanzun, sai idan ank'imin yanda nakesone za'a samu fiye da hakan dai”.
C.P ya jinjina kai yana gyara tsayuwa, idonsa nakan ginin, yace, “to miye buk'atarka ta gaba yanzu?, tunda gashi an maka ta farko ai”.
“Eh tabbas anmin, dukda dai ankawoshi ba'yanda Na soba”.
“amma ranka ya dad'e suma ai ankashe musu yaro d'aya”.
Gira Galadima ya shafa da d'an yatsa yana ta6e baki, “ito dakuma wannan Dan wannan fa, yanzu dai inaga buk'atata tagaba shine ku kama mutanen nan guda 11 dazan lissafo”.
“Muna saurarenka, dawa-dawa?”.
Ajiyar zuciya Galadima ya sauke, cikin Nisawa ya gyara zamansa yana d'aukar takardar dake gabansa ya shiga lissafosu. “Alhaji Balala, Alhaji Bana baba gana, Alhaji Abdul-Naseer Nafi'u, William Solomon, Hajiya A'i Barnawa, Alhaji Sageer Sulaima Sulaiman, madam Victoria, Mansur Habibu Abu, Josaya bamma, Alhaji Mamman k'afur, Alhaji Halliru garba”.
Kallon kallo aka tsayayi tsakanin IG da sauran police, sai C.P ne yasamu k'arfin halin cewa “amma to Ranka ya dad'e akan wane dalili? Kasan dai bazai yuwu muje kama mutane babu dalilin komai damuka saniba”.
Wani muskilin murmushi Galadima yayi, ya kwantar da kansa jikin kujera yana lumshe ido da cije lips, “Dalilin ai a fili yake yalla6ai namu, bisa dalilin Samun Alhaji Auwal Fharuk a hannunsu mana, dan yakamata asan dalilin samunshi a hannunsu, miya musu? Mi suke nema a wajensa? Baniba nasan dukan jama'ar garima abinda sukeson ji kenan, kunsan dai bazan ajiye ayukan gabana da jiyyar mahaifina nazo Nigeria Na zauna Ina kama yaran mutane saboda rashin aikinyiba ai, aimin kokuma nakuma aika yaronsu biyu barzahu yanzunnan!!”. Galadima ya k'are maganar cikin tsawa da matsanancin fushi.
Tsawarsa saida ta kad'a hanjin yaran, hatta da Harun dasu Muftahu saida suka rumtse ido, suma haka police d'in dake sauraren Galadima.
IG ya mik'e daga zaunen dayake yashiga safa da marwa Na mamakin wannan lamari, sukan ai ansakasu a tsaka mai wuya, cikin tsakkiyar fad'an manya. C.P ya kira suka koma gefe suna tattaunawa.
............................★
A can kuwa hankalin su Alhaji Sageer ya kuma k'ololuwar tashi, Alhaji Mamman yace, “lallai yaronnan anyi tsinanne, dama wannan ranar Na ringa gudu tun boss nada rai (tanderu yake nufi), amma wasunmu sukace yaron bai Isa mana komaiba, gashinan rana tsaka yana Neman zame mana RAINA KAMA....”
“Yama zama ai, Dan gayya kawai muka fara gani yanzun”. ‘Hajia A'i ta fad'a a tsorace’.
Duk sun kasa zama waje d'aya, Miracle yace, “yanzu nan da mutuncinmu za'ace wai y'an sanda su kamamu a k'asarnan?, lallai yaronnan yataro March wlhy”.
“Kokuma mune muka taro March d'inba”. Alhaji Bana dayake cikin kukan mutuwar d'ansa yafad'a yana share hawayen.
...............................★
IG sun yanke shwarar bin umarnin Galadima kawai, kodan tseratar da yaran, yad'anyi magana da manyan dake kusa dashi dukda shine Oga kwata-kwata, kowadai yabada goyon bayan a kamasun kawai.
Dan haka IG da kansa yay kiransu, Yakuma basu dama a girmamame akan sukai Kansu kawai station d'in dake kusa dasu, kodan rayukan yaransu, daga baya za'asan abunyi insha ALLAH”.
Galadima dake saurarensu a zuciyarsa yace, abinyi kuma ai saidai a prison.
Duk sunk'i amincewa, wasunsuma sai bak'ak'en magana suke fad'a.
waya Galadima ya jawo yana daddannawa, sannan yayma Marcel nuni yazo, Dan yaji babansa yafi kowa zak'ewa, jikin Marcel sai 6ari yakeyi, ahaka ya rarrafo gaban Galadima.
Galadima yace, “'Dauka wayarka anan”.
Jikin Marcel na rawa ya d'auka.
“Kira daddynka”.
Dandanan yay kiransa, bugu d'aya kuwa ya d'auka shima jiki yana 6ari, duk suma sukayi tsitt suna jiran mizaice.
Galadima ya d'orama Marcel binduga a tsakkiyar kai, ya juya idanunsa alamar yay magana.
Marcel ya sanya kuka saboda tsoro. Rikicewa daddynsa yayi yana tambayar mi aka masa? Badai yay musu komaiba ba ko?.....
Katseshi Galadima yayi da fad'in “Zandai yimasa, Dan kaima yanzu d'anka zai wuce Inda Na Alhaji Bana yatafi”.
“kai kai dakata please ka dakata, nidai Na yarda zan mik'a wuya, karka ta6amin yaro kaji Na rok'eka”.
Cire bindigar Galadima yay yana maida kunamar da fad'in “shawara mai k'yau, lallai kanason d'ankan nan, ka tambayi abokanka, Wanda bazai mik'a wuyanba saiya fad'a yanzun nan”.
“karka ta6a mana yara please, duk zamu mik'a wuya”.
Galadima ya tuntsire da dariyar da wanima zai iya rantsewa bai ta6a ganin yayiba, yace, OK, good dattijan k'asa, saina jiku acan”.
🤣🤣ana shagali a Nigeria yau kam🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀ amma Nigeria novel ba tamuba😜.
Su Alhaji balala dai kam sun mik'a wuya, da Kansu suka kai Kansu police station mafi kusa, daga can suma d'aukesu zuwa inda IG yace.
Galadima yay hamdala ga ubangiji dukda bawai komai yagama kammaluwa bane, amma lallai an d'akko hanya.
Ya bada Umarnin tashi suyi sallar La'asar, kafin a dawo a cigaba da gashi😜.
....................................★
Bayan sun idar da salla C.P ya kira Galadima, suka shaida masa su Alhaji Bana suna hannunsu yanzu haka.
Galadima dake tsaye yace, “Alhmdllh, zuwa safiyar gobe kuma sai a kai case d'inmu Court, Dan inason komai yafarune cikin gaggawa ya k'are, bana son jan jiki a aiki”.
C.P ya kalli IG Dan jiran amsa.
Kai IG ya jinjina masa alamar za'ayi hakan.
C.P ya shaidama Galadima amsar IG.
Galadima yace, shikenan, shi yatashi daga aiki, saikuma safiyar gobe.
C.P zaiyi magana I.G ya dakatar dashi alamar ya barsa kawai.
Ta6e baki Galadima yayi yana yanke wayar, ya maida kallonsa gasu Muftahu da duk suna maidashi television, gira d'aya ya d'age musu, sukuma sukai masa jinjina👍🏻.
Kauda idonsa yayi ya maida ga yaran, yace, “yaya akwai mai buk'atar wanka ko barci?”.
Gaba d'aya suka amsa da duk suna buk'ata.
Kallon Ameer da Saleem yayi yabada Umarni da ido.
..............................★
'D'aya bayan d'aya suka dinga kaisu suna wanka, duk Wanda yagama sai abashi lemo, batare daya San miye acikiba saiya shanye, daga sha ko mintuna 3 basa k'arawa suke 6ingirewa barci🤣.
🤣🤣ho Galadiman mu kasan takan tsiya, Zuma kenan, ga zak'i ga harbi🤸🏻♀, kaga Na Munaya baban triplets, bada kanka a sare kaje gida kacema su mama Fulani an k'illesa👌🏻😜😂.
Da akazo kan Harun k'in tankawa yayi, Dan haka Galadima yace su barshi kawai, amma harsu Malam Saminu da Alhaji Darma su Farhat duk sunma Kansu gyad'ar dogo sunje sun mik'e zasu huta.
Nuren ya kalli Galadima cike da tausayi yace, “Brother kaima kad'anje ka huta mana”.
Murmushin gefen baki Galadima yayi, yajawo lap-top gabansa yana girgizama Nuren kai alamar a'a.................✍🏻
*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu_*😭👏🏻
_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*
*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
___________________
*_Na gaisheku, gaisuwa irinta musamman d'innan. Makaranta buk d'in RAINA KAMA dake JAMI'AR KUST dake WUDIL, alkairin ALLAH yakai agareku, ALLAH ya yalwataku da ilimi mai tarin albarka damu baki d'aya._*
Ina inyinku irin Trillion's d'innan my guys🤸🏻♀😘😘😘😘❤❤.
____________________
*_BOOK 3_* 👉🏻1⃣7⃣
...................Abin surutu lallai ya samu, mak'iyan Galadima kuwa duk sun kasance a tsorace, Dan ba kowane ya fahimci inda shirinsa ya dosaba, hakama a cikin masoyan nasa, wasu suna ganin daidainsa wasu kuskurensa, kowa da irin fahimtar dai da yayma lamarin.
Yauma dai haka suka kwana zagaye da police.
Amma su IG duk sun tafi, d.p.o ne kawai tare da tawagarsa, kamar kuma yanda ya buk'ata sunakan tattara case d'in zuwa Court.
6angaren su Baffi kuwa lauyan Abie dukkan shirye-shiryen shiga Court suma suna akanyi. Dan dukkan shirin Galadima yasan dashi tsaf, hakan yasa koda yagani baiyi mamakiba, kisan Ahmad daine da akace yayi yabashi mamaki, dukda zuciyarsa bata aminta Galadima zai iya kashe yaro ko d'ayaba. Amma lallai hakan ya sakashi a rud'ani, harma ya kira sir Isa sukayi maganar. Sir Isa yace shima yagani a labarai amma gaskiya bai yardaba, akwai dai abinda duk basu saniba, Dan Galadima bazai aikata hakanba.
Da wannan maganar ne Baffi yad'an samu Nutsuwa yacigaba da tattara bayannsa daduk abinda zasu kafa hujja dashi a court.
Duk abinda ke faruwa Momma tasan komai. Dan Galadima ya sanar mata, baya kuma 6oye mata dukkan shirinsa akan wannan case d'in dama, amma sai tayi lup tamkar batasan anaiba, koda labari yazo musu saita taya su Aunty Mimi rud'ewar itama, harda pretending d'in kukanta tana Neman number Galadima, amma sai tak'i wucewa.
Daga Baffi har mai martaba babu Wanda ya kirata akan batun, duk a nufinsu Na 6oyemata kar hankalinta ya tashi balle Na mahaifinsa dake kwance yana fama da kansa.
Amma saiga kira daga mama Fulani, tafad'ama Momma maganar daduk yazo bakinta ta 6atanci akan Galadima, itadai momma cikanki batace da itaba, har tayi ta gama ta yanke wayar.
Saiga gimbiya Zulfah ma ta kira Momma, itakam ai harda kukan makirci irinna y'an duniya. Itama dai tayi kid'anta tayi rawarta Momma Na saurarenta.
Koda ta Yanke wayar saita kira munaya. Taita kwantar mata da hankali da lallashinta akan ta kwantar da hankalinta. Insha ALLAH komai zaizo k'arshe, kowace rayuwa takan tafine da jarabawa. Babu wani rai dazai rayu cikin farinciki da samun yanda yakeso 100%, dolene kowacce rayuwa akwai NATA k'alubale, nakowa kuma akwai ta hanyar dayake fuskantar nashi.
Sosai Munaya ta gamsu da nasihar momma hakannema yad'an samu mata nutsuwa tad'an rintsa a wannan dare.
.................................★
*_WASHE GARI_*
Nasara ta farko da aka wayi GARI da ita shine farfad'owar Abba cikin hankalinsa, saidai har lokacin baya sanin Wanda yake a tare dashi, hakanne yasaka likitocin fad'in a k'ara masa lokaci yasamu isashen hutu.
Ahalinsa sunsamu Kansu a farinciki ainun, hakama masoyansa, shikansa Galadima Yakuma samun kwarin gwiwa da karsashi akan aikinsa.
An kuma shigar da case d'in Court kamar yanda Galadima ya buk'ata, abinka da lamarin manya har antsaida washe gari a matsayin ranar da za'a zauna Court d'in.
Yinin ranar zubur Galadima baiyi magana da police ko d'ayaba, koda sun buk'aci magana dashi saiya had'asu da Muftahu ko Nuren. Daga k'arshe dai dolensu suna k'yaleshi.
★★★★★★★★
*_⚖RANAR SHIGA COURT_*⚖
Yau ta kasance ranar zaman court, shari'ar su Galadima Ce kuma farko da za'a fara saurara a court d'in, lallai wannan shari'a ta manyace, Dan court d'in ta cika da manyan k'asa wad'anda sunfi kud'i wahalar gani, amma yau gasu available, y'an jaridar ma manya-manya aka bari, k'ananun suna awaje sunyi tururuwa domin rajin nemawa d'an uwansu hak'insa wato Alhaji Auwal fharuk dayake a asibiti har yanzu cikin halin ni y'asu.
Mukuwa talakawan gari y'an jiran jin yazata kaya mu sai dai gani a tv☹.
Yo Wayaba asibi laya ubanta ba malam ba😬, ai ko babama da babansa aradu🤕.
*_Court_* d'in tayi tsit babu abinda kakeji sai gudun fankoki da tarin manya jefi-jefi, dan babu alamun fara'a a fuskar kowa.
Daga masarauta dai k'anin mai martaba ne yazo wato Garkuwa Hayatudden Abubakar, sai wasu daga tawagar y'an majalissar Sarki, harda waziri dayazo bisa tirsasawar mai martaba.
Daga masarautar su Papi kuwa yarima mai jiran gado mahaifin su Nuren wato Wambai Abubakar Abdul-fatah Wanda yagaji sunan kakansu Galadima marigayi Abubakar kenan. Saikuma wasu daga jiga-jigan masarautar suma.
Fitowar alk'alin alk'alai Othman Ibraheem gwannu tasaka dukkan jama'ar Court d'in mik'ewa domin girmamawa a garesa, (dan shima Alk'ali baba uban su babane shima🤭😝).
Saida ya zauna sannan yabada izinin kowa ya zauna, Court d'in tayi tsit kowa ya Zubama alk'ali dake karanta takardar k'arar hankali kwance ido, kusan mintuna 3 ya d'ago yanabin Court d'in da jama'ar cikinta da kallo ta cikin eyeglasses nashi daya jawo k'asan ido, d'auke idonsa ya ya maida ga Lauyoyi dake zaune suna jiran kule, suce cas.
Gyaran murya yayi yana maida idonsa ga takardar da fad'in “Ina wad'anda suke k'arar da kuma wad'anda akai k'ara? Idan kuma Lauyoyine to na masu k'ara da wad'anda ake k'ara suna inane?”.
A tare Baffi suka mik'e shida abokan aikinsa su uku, cikin girmamawa ga alk'ali ya risinar dakai yana mik'a gaisuwa da fad'in “yamai girma mai shari'a sunana Barrister Usman Audu Tsanyawa, nine lauya mai kare Wanda yake k'ara, tare dani akwai Yohan Emanuel, da Bilkisa Ibraheem Musa (kutu melesi su bilyn Abdul anzama lauyoyin novel🤸🏻♀😎🤣😜).
Bilkisu da yohan suka risina alamar girmamawa.
Alk'ali ya jinjina kai alamar gamsuwa, su Baffi suka zaune, lauyan wad'anda ake k'ara shima ya mik'e, ya rissina tamkar yanda Baffi yayi, sannan yace, “ya mai girma mai shari'a sunana Barrister Adam Sadiq Adam, nine lauya mai kare wad'anda ake k'ara, tare dani akwai Barrister Aliyu Sa'adu yaro”.
Barrister Aliyu ma ya mik'a gaisuwa ga alk'ali sannan suka zauna.
Alk'ali yabama Baffi damar tashi domin yin magana.
ALLAH Sarki dattijon kwarai kenan, masu wahalar samu cikin k'asa a halin yanzu, ya gyara hularsu ta lauyeyi dake Kansa, tare da farin eyeglasses d'insa dan rayuwa taja, ijiya duk sun raunana, ya kalli jama'ar cikin Court d'in sannan ya dawo da kallonsa ga alk'ali, yace, “yamai girma mai shari'a! Kamar yanda kowa yasani Muhammad Sameer Saifuddin Abubakar (Galadima) shine yake Neman son sanin miya saka wad'annan mutanen 11 yin gamayya wajen kama surukinsa harsu wahal dashi? Bayan kuma shikeda alak'a dasu bawai surukinsa ba?”.
Kai Alk'ali ya jinjina, cikin sauke numfashi yace, “Lauyan wanda ake k'ara gareka”.
Barrister Adam Sadiq Adam ya mik'e shima yana fitowa fili, yayinda Baffi Yakoma ma zauninsa ya zauna, Brr Adam Sadiq Adam yace, “yamai girma mai shari'a wace irin tambayace ke fitowa daga bakin lauyan mai k'ara? Ai sune yakamata ayima tambayar minene dalilin shi Galadima Na kama yaran wad'annan mutane 11 yayi Garkuwa dasu yau tsawon kwana biyu? harma da kisan wani a cikin su.........
A hanzarce Baffi ya d'aga hannu sama yana mik'e da fad'in “yamai shari'a tambaya akaima lauyan mai k'ara, amsa kuma yakamata ya bamu baya sakko tashi tambayarba”.
Hannu Alk'ali ya d'agama Brr Adam Sadiq Adam, yace, “Brr Adam ka gyara, amsa muke buk'ata, kanada dama kaima kayi taka tambayar daga baya”.
Brr Adam Sadiq Adam ya risinar dakai alamun ban hak'uri sannan ya gyara tsayuwarsa yana fad'in “Yamai girma mai shari'a akwai abinda ke hannun Alhaji Auwal Fharuk Wanda mallakin su wad'annan mutane 11 ne, shine sukeda buk'atar kar6a”.
Baffi yamik'e yana fad'in “yamai girma mai shari'a ko zamu iya sanin minene wannan Abu da suke tuhumar Alhaji Auwal Fharuk akansa, dahar suka kasa mik'ashi ga sharia domin kar6a har sai sunbi ta hanyar nuna k'arfin ikonsu?”.
Brr Adam Sadiq Adam yay shiru yakasa cewa uffan, dan ganin tun a tashin farko yana shirin zurmawa.
Ganin yak'i cewa komai Baffi ya kuma cewa “ya mai girma mai shari'a idan baza'a samu amsaba ina buk'atar d'aya daga cikin y'an wad'annan tawaga domin ya amsamin tambayata idan shi Barrister bai saniba”.
Alk'ali ya jinjina kai yana bada Umarnin tasowar d'aya daga cikin su Alhaji Mansur.
Dukfa abinnan dake faruwa Galadima yana kallon komai kai tsaye ta Computer, danshi baizo Court d'inba, babu damar hakan, yana fitowa a gidan police kamashi zasuyi, wannan yasa tukan zaman Shari'a Alk'ali yabada wannan damar ta had'a video call d'in da Galadima zai iya ganin komai da za'ayi kamar yanda IG ya buk'ata bisa umarnin shi Galadima d'in, kamar yanda ya shard'anta ko amasa hakan koya jeho gawar yaro d'aya ko yarinya. Hakan yasa sukai masa babu gardama.
Alhaji Abdul-Naseer dake farkone ya taso, ya shiga inda aka tanada domin buk'atar hakan, ya fad'i sunansa da matsayinsa, sannan Alk'ali yabama Baffi damar masa tambayar.
Baffi ya k'arasa jikin katakon d'aya shiga tsakaninsa da Alhaji Abdul-Naseer, idonsa a kansa yace, “Alhaji Abdul-Naseer, nasan kana d'aya daga cikin y'an wad'annan tawaga, shin kozaka iya amsa mana tambayar da lauyanku ya kasa?”.
Murmushin Alhaji Abdul-Naseer yayi, cikin kwarin gwiwa yace, “Brr Usman, a ganina wannan sirrinmu ne, koma mi muke buk'ata a hannun Alhaji Auwal Fharuk mukeda alak'a dashi ai ba kowaba ko?”.
Baffi yashiga jinjina kai yana murmushi, yayi taku d'aya biyu saikuma ya juyo ga Alhaji Abdul-Naseer, yace, “lallai wannan gaskiyane Alhaji Abdul saidai kuma dalilin sanin Court yanada alak'a da samo Alhaji Auwal Fharuk a hannunku, wanda ta silar kama y'ay'anku da surukinsa yayine kowa yasan hakan, saikuma gashi shi wannan bawan ALLAH Alhaji Auwal Fharuk a jiya daya farfad'o dukda baya cikin hayyacinsa, amma yana ambatar sunan Alhaji Halluru da jaddada lallai koda zaku kasheshi bazai bada wannan camera ba, domin shekarunma da kuka d'auka kuna ma rayuwarsa barazana bai bakuba balle kuma yanzu da lokacin Isar da ita ga Wanda akace ya Isar yayi, kenan Alhaji Auwal Fharuk k'arya yayi?”.
Da sauri Brr Adam Sadiq Adam ya mik'e yana fad'in “ya mai shari'a wannan ai tamkar titsiyene Brr kema Wanda ake zargi, dan babu yanda za'ai la'akari da mutumin da baya cikin hankalinsa kamar yanda ya fad'a.....”.
Shima Baffi azamar dakatar dashi yayi, yace, “yamai girma mai shari'a Barrister Adam bashida hurumin yanke hukunci akan yanayin Alhaji Auwal, sai ya bari bayanin likitoci ya tabatar mana hakan”.
Alk'ali yay gyaran Murya da buk'atar ganin likitan dake kula da Alhaji Auwal Fharuk (Abba).
Cikin mintuna 3 saiga doctor ya shigo.
An sakashi d'ayan wajen, ya fad'i sunansa da aikinsa, sannan Alk'ali yace, “kaine likitan da ke duba lafiyar Alhaji Auwal Fharuk? ”.
“eh nine yamai shari'a”.
Alk'ali yace, “kozamu iya sanin wani Abu dangane da jikin Alhaji Auwal Fharuk? ”.
“kwarai kuwa ya mai shari'a, an kawo mana Alhaji Auwal Fharuk cikin hali irinna suma, amma babu wani alamar duka ko harbi a jikinsa, saidai bincikenmu ya nuna an shak'a masa wani Abu. Daya saka numfashinsa Nisan zango, sai ajiyane bisa hukuncin ubangiji ya farfad'o, wad'annan kalamai sune abinda ya farka dasu a bakinsa, kuma kwakwalwarsa ras take, abinda aka shak'a masanne kawai bai sakesaba har yanzun, danma yanada jini mai k'arfine”.
Cikin wad'anda suke zaune ma'aikatan Court d'in d'aya yaje ya kar6i wayar doctor da yay recording ya kaima alk'ali.
Alk'ali ya kunna recording ya saurara, ya ajiye wayar gefe da sallamar doctor cikeda gamsuwar abinda yaji. Sannan shima yabada Umarnin sanin ita camera ta micece?.
Baffi yakuma mik'ewa tsaye yana gyara k'atuwar rigarsa, yace, “ya mai shari'a, ita wannan Camera da wad'annan gamayyar mutane suke farautar rayuwar Alhaji Auwal Fharuk a kanta tanada alak'a da Muhammad Sameer Saifuddin Galadima ne, itace kuma musabbabin d'aukar yaran wad'annan mutane 11 dayayi yake tsare dasu a gida mai labba 67 dake anguwar tudun na ALLAH a tsakiyar binni, damin camera dai k'unshe take da abinda ya faru da tsohon Sarki dake jiyya a India, wato Mai martaba Saifuddin Abubakar tsawon shekaru 26 kenan ba'asan wad'anda suka aikata masa abinda ya kaisa da jiyyarba”.
Turk'ashi, kallon kallo kenan, to lallai shine aka shigayi a wannan Court, nanfa k'ananun magana suka fara tashi tsakanin manya, Court ta harmutse da hayaniya babu maijin zancen wani, saida alk'ali ya tsawatar sannan akayi tsit.
Inda kuma a gefe tsantsar rud'ani da rikita ta mamaye su Alhaji Balala, ko kad'an basuyi zaton shigowar wannan maganar da wuri ba cikin shari'ar, shima kansa lauyansu haka, tunda wawantar dasu Galadima yayi akan Shari'ar ta shafi d'aukar Alhaji Auwal Fharuk ne da farko.
Alk'ali da shima kansa ya shiga wani yanayi ya buk'aci ganin Muhammad Sameer a Court.
Baffi ya kuma mik'ewa yana fad'in “ya mai shari'a, ai Muhammad Sameer Saifuddin Galadima bashida ikon zuwa court a yanzu, domin kuwa yana can tsare da yaran wad'annan mutane 11 ne, kuma yana fitowa y'an sanda zasuyi ram da shine a matsayin mai laifi babbama kuwa, dan yanzu akwai laifin garkuwa da yara d'in a kansa, saidai munada hanya sassauk'a ta had'a wannan adalar kotu da Galadima kai tsaye”.
Alk'ali ya bada damar hakan.
Dandanan kuwa aka had'a Galadima da kotu, Wanda dama shi tuni yana ganin duk abinda sukeyi, sunedai basa ganinsa.
Galadima dake zaune a falon gidan da yake tsare dasu harun ya mik'e tsaye domin girmamawa ga alk'ali, sannan ya gabatar da sunansa kamar haka, “ya mai shari'a sunana Muhammad Sameer Saifuddin Abubakar, ma'aikaci a hukumar bincike ta DSS”.
Wani sabon kallon kallon aka koma, Wanda yaja hankalin mutane fiyema dana d'azun, hattada y'an masarautar gagara badau basusan da wannan aiki Na Galadima ba.
Alk'ali ya kuma tsawatarwa, sannan ya maida hankalinsa ga Galadima yana fad'in “To Muhammad Sameer minene alak'arka da iyayen yaran dakake rik'e dasu, danmu ka rikita mana tunani, da farko kallon Criminal muke maka, saikuma gashi sunanka yafito a d'aya daga cikin manyan hukumominmu Na tsaro masu muhimmanci?”.
Murmushi Galadima yayi yana gyara tsayuwa, ya hard'e hannayensa a k'irji yana sauke numfashi da cije lips, yace, “ya mai shari'a wannan labarine mai tsawo, amma tabbas abinda lauyana ya fad'a shine gaskiyar zance, Camera dake hannun Alhaji Auwal Fharuk itace babbar alak'ar dake tsakanina dasu, wadda nad'au tsawon shekaru akan nemanta, sai a shekararnan ne cikin watanni shida nasamu labarin inda take dukda banida tabbacin ita d'ince, bansan mike cikin camera d'inba, amma su Alhaji Balala duk sun Sani, tunda har suka iya salwantar da rayuka da yawa akanta, shi kansa Wanda suka hara a yanzu ALLAH ne kawai yasaka yanada tsawon rai, amma da tuni sun kasheshin, ni kaina rayuwata tasha hare-hare iri-iri harda jariran yarana da aka sace kwanaki 7 kacal da zuwansu duniya”.
Alk'ali da yay shiru yana sauraren Galadima yaja dogon numfashi yana ta faman jinjina kai tamkar k'adangare yaga abinci mai manja😱🤭.
Yace, “lallai wannan Court tana buk'atar jin cikakken bayani daga Muhammad Sameer Saifuddin, dan haka ta d'aga wannan k'ara zuwa nan da kwanaki uku masu zuwa, kotu tana bama y'an sanda Umarnin subar Muhammad Sameer Saifuddin ya fito daga wannan gida a ranar da Court zatayi zama Na gaba batare da koda masa hararaba, sannan kuma kotu ta bada Umarnin a cigaba da tsare su wad'annan mutane guda 11, likitoci kuma su cigaba da bama Alhaji Auwal Fharuk kulawa ta musamman dan shima kotu Na buk'atar ganinsa a zama Na gaba saboda son sanin mike cikin camera d'in”. Alk'ali ya buga gudumarsa yana mik'ewa.
Gaba d'aya kowa ya mik'e har alk'ali ya shige.
Galadima yay wani k'asaitaccen murmushi yana zaunawa cikin kujera bayan shigewar alk'ali.
Muftahu, Nuren, dasu Harun dake zaune gefe suma suna kallon komai tun farkon Shari'ar duk sunyi mutuwar zaune tun lokacin da Galadima yafad'i kasancewarsa cikin hukumar C.I.D.
Ameer ne kawai yay murmushi yana k'amewa da salute d'in Galadima.
Shima baki sake su Nuren suka bishi da kallo suna nunashi alamar dama yasani shi?.
Murmushi yay musu har hak'oransa Na bayyana ya had'e hannayensa waje d'aya alamar tuba a garesu.
★.....................................★
Yau kam Galadima wani farin ciki Na musamman ya tsinci kansa a ciki, ya shige d'akin da yake matsayin nasa a yanzu ya fad'a gadon yana rungume filo idonsa Na zirar da hawaye, ko a haka aka tsaya lallai yaci nasara, dan ya nunama su Alhaji Abdul-Naseer d'an zaki ya girma.
Wayarsa dake saman gadon a can gefe yasa hannu ya janyo, ya kunnata, massages ne sukaita shigowa a jere-jere kamar jira, bai bud'e ko wanneba ya shiga binciko number Munaya, ya dad'e yana kallon Number amma ya kasa dialing, yaja wasu seconds kafin yatsansa ya sauka akan number ya danna kawai.
Munaya Na zaune a falo tare da su Ayusher da kullum sai sunzo, d'an kunne ne ya shige cikin jikin Amaturrahman yanata cin jikinta basu saniba, sai yau da an ta6a fuskarta koyaya saita fashe da kuka, Munaya tarasa mike damun yarinya, dukta rikice ita kanta, saida laraba tace ta bata nono, tana kwantar da ita ta wajen kunnen sai takuma d'ad'ewa da kukan da Munaya ke jinsa har cikin jini, d'agota tayi tana duba wajen, Laraba tace, “Anya ba kunenta ke ciwoba?”.
Munubiya dake kusada Munaya ta amshi Amaturrahman ta kifata a cinyarta tana dubawa, sai taga d'an kunne ne ya shige Ashe duk bayan kunnen yayi ruwa, tsoro ya kama Munubiya, cikin zaro ido waje tace, “innalillahi, d'an kunne natacin kunen yarinya bamu saniba”. Da an fara k'ok'arin ciremata saita kuma fashewa da kuka tana mimmik'ewa, gwaggo safiya data shigo yanzu saboda jiya ta iso akan abinda ya faru da Abba, ta k'araso cikin falon tana fad'in “mike faruwane?”.
Bayani feena tai mata, gwaggo safiyya ta kar6i Amaturrahman tana cewar asamo mata ruwan d'umi da k'aramin handkerchief.
Ana cikin hakane Galadima yayi kiran Munaya, tashitai tabar wajen tana had'iye kukan dake shirin taho mata saboda tausayin yarinyar.
'Dakinsu ta shiga, ta fad'a saman gadonsu ta kwanta tana amsa wayar.
A hankali Galadima ya sauke ajiyar zuciya yana gyara kwanciya. Murya can k'asan mak'oshi yace, “babu fad'a miya kawo gaba yalla6iya?”.
Murmushi Munaya tayi tana share hawayenta. Tace, “Kodai Kaine za'aima wannan tambayar?”.
Jimm yayi saboda jin muryarta ba ayanda yasaniba. yace, “mike faruwa kike kuka?”.
Mamaki ya kama Munaya, ta Yayama ya gane kukan take, cikin k'ok'arin kare kai tace, “ba kuka nakeba yalla6ai, ina yini”.
bai amsa gaisuwarta ba yace, “kina wasa da sanin danai miki ko?”. Yay maganar cikin d'an kausasa murya.
Munaya sai bataji dad'iba, tace “kayi hak'uri, dama Amaturrahman ce d'an kunne ya shigema a jiki taketa kuka, amma gashi can suna cire mata d'an kunnen”.
Babu shiri Galadima ya tashi zaune yana fad'in “k ya akayi har d'an kunne ya ringa cin jikinta baki saniba? Anya kuwa kinason yarannan Munaya?”.
Wani haushine ya kamata, tama rasa mizata Ce masa.
Shima bai jira amsartaba yace, “maza ki tashi kuje asibiti a dubamin yarinya, karkuce zakuyi gangancin cire mata a gida wata matsalar ta biyo baya”.
“Uhumm”. Kawai Munaya tace ta yanke wayar.
Ta jefar da wayar gefe tana hawaye, shi kawai yaransane damuwarsa, harma zaice yafita sonsune dazai dinga jifanta da bata sonsu kulum-kullum, itafa wannan Abu yafara kaita bango wlhy.
A can kuwa shima Galadima duk sai yaji ya damu, jiyake tamkar yay tsuntsuwa yafita yakai yarinyarsa asibiti da kansa, amma babu damar hakan.
Ya dad'e jikin window tsaye yana kallon mutane daketa zirga-zirga a anguwa da police d'in dake zagaye da gidan har yanzu.
Fita munaya tayi dan ganin ko ancire?, ta iske an cire ana gasa kunnen, Amaturrahman taci kuka harta koma ajiyar zuciya, Gwaggo Safiyya tace, “zoki zauna kibata tasha sai'a k'arasa gasawar”.
Zuwa Munaya tayi ta zauna tana kar6ar Amaturrahman.
K'in k'ar6ar nono tayi, sai ajiyar zuciya taketayi, Laraba tace, “yaranan zuciya irinta Magajin gari suke da ita, yanzu inba sa'a ba bazatashaba”.
Dariya su Ayusher sukayi.
Dak'yar dai Munaya ta turama Amaturrahman nono abaki ta kar6a. Akad'an kuma gasa kunnen dayay uwar huda naman wajen yafita sosai, k'ofar tazama babba.
Munaya dake kallonta tasaka hannu tana goge mata zufar data taru mata a goshi, saikace wata babba.
Galadima yanata kiran Munaya yaji kosun tafi asibitin amma bata d'agaba, dayake ta bar wayar a d'akinsu.
Saida Ayusher taje d'akin ta gano, ta d'akko da sauri ta kawo mata tana saka mata a kunne.
Maganarsa kawai munaya taji yana fad'an ina ta ajiye wayar.
Ajiyar zuciya ta sauke tabashi hak'uri kawai, dan bata buk'atar jan maganar.
Yace, “kunje asibitin?”.
Munaya tace, “An cire mata ai, babu wata matsala tunda bai ta6a cikiba”.
Ca yay ta d'auka hoton wajen ta turo masa yagani, kamar tace bazatayiba sai kawai ta cire wayar ta katse kiran, hoton wajen ta d'auka ta tura masa”.
Tausayin yarinya ya kamashi ganin yanda wajen yay cinye sosai, Yakuma kiran Munaya yana jaddada mata karta sake akuma sakamata wani d'an kunne.
To kawai ta amsa masa dashi dan a zauna lafiya.
..............................★
Tun daga ranar Munaya bata sake jin Galadima ba, saboda yayi busy da yawa akan shirye-shiryen shari'ar dake gabansu, dan fatanshi wannan zaman yazama zama Na k'arshe insha ALLAH.
Alhmdllh jikin Abba anata samun haske sosai, dan sauk'i yana samuwa iya gwargwadon iko.
*_RANAR DA ZA'A KOMA KOTU_*................✍🏻
Hummm😬
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻_*
_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*
*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BOOK 3_* 👉🏻1⃣8⃣
.................Yauma dai kotun ba'a cewa komai, wad'anda ma basuzo zaman farkoba yau sunzo, Dan su sir Isa duk suna wajen da muk'arabansa, hakama tawagarsu Tanderu, Dan suma lauyansu a cewarsa yau yazo da sabon shiri, ranarma an mamesa ne kawai.
Galadima yagama shirinsa tsaf cikin wani lallausan yadi sky blue dayasha d'inkin boda, Dan rigar iyakarta Rabin cinyarsa, kayan sunmasa k'yau matuk'a, danya fito ainahinsa Na jinin Hausa Fulani, ya Mirza hularsa sky blue itama, fuskarnan tayi fayau Dan hardasu gyaran fuska yayi abinsa, danma ya tabbatarma mak'iya yana cikin farinciki fiye da zatonsu, yana cikin saka sock's Nuren ya lek'o yana fad'in “Brother ka hanzartafa mun makara”.
“umhum” kawai yace masa yacigaba da saka kayansa a tsanake kamar yanda yafara, danshi komai saurin dazaiyi akan Abu to anutse zaiyi abinnan, ganin haka sai kawai Nuren ya ida shigowa, ya durk'usa gabansa yana kama k'afar daya sakama sock's d'in ya saka masa takalmi.
Baki Galadima ya tsa6e yana cewa, “kaifa shegen gaggawane dakai wlhy, ni bansan INA kuka kwaso halinnanba, haka Momma da Aunty Mimi suke, komai kunfison mutum yanayi kamar wani mazari”.
Nuren ya sanya dariya yana saka masa d'aya takalmin, yace, “to sokake muke Abu kamar marasa laka a jiki? Munaya dai kam tana fama...”
Hararsa yayi, hakanne ya hana Nuren k'arasawa, Galadima daya wani tsaresa da ido yace, “Tana fama da k'aniyarka”.
Nuren ya mik'e yana fad'in “oho maka dai, mu ka fito su sarkin mota tuni sukazo”.
Mik'ewa yay ya d'auki turarensa Na kullum a bag d'in daya had'o kaya ya fesa, k'amshin ya gauraye ko ina, waya d'aya ya zura a aljihu ya fito.
Su Ahakam duk shagala sukayi da kallonsa, a ransu suna matuk'ar yaba tsarinsa, komai nasa abin birgewane, kamar yanda ya saba haka yabasu hannu da kansa sukayi musabaha dukda suna nok'ewa alamar jin kunya da girmamawa a gareshi, shikam babu ruwansa, inhar bakasan halinsa bane dolene tashin farko ka jefeshi da kalmar girman kai.
Su Farhat ma suka gaisheshi cikin risinawa, wani miskilin murmushi yamusu yana d'aga musu hannu kawai, ya kalli Saleem tare da masa nuni yabama kowa kayansa.
Saleem ya amsa da cewar “ok boss”.
Bag d'in da wayoyinsu ke ciki ya d'akko, amma sai sukace sukam ya barsu, Dan inhar ba'a yanke hukunci ba zasu dawo su cigaba da zama dasu, Dan zama da Galadima akwai dad'i, kuma ko an yanke hukuncima masarauta zasu bishi.
Shi dariyama abin ya bashi, hakanne yasakashi bubbuga kafad'ar Yassar dake kusa dashi yana sakin murmushin da har hakwaransa ke bayyana, ya wucesu yana sauka daga benen cikin takunsa Na birgewa.
Suma duk binsa sukayi a baya, komai nasa Saleem ya tattaroshi, dan bazai sake dawowa gidanba koda ba'a yanke hukunci ba kuwa.
Harun dai anyi laushi matuk'a, dan maganarma yanzu ba iyayin mai k'arfi yakeba, saboda saiya gadama yakecin abinci, babu kuma mai sakashi dole yaci.
Cikar k'ofar gidan tabama Galadima mamaki matuk'a, yakuma d'aure fuska tamkar bai ta6a dariya ba, musamman yanda duk aka zubo masa ido, a Bayama an kallesa balle yanzu da yayi abun kallon, y'an sanda da dogaransa da suka zo d'aukarsa tun d'azun sai k'ok'arin hana y'an jarida dakeson zuwa ga Galadima sukeyi, amma suna k'ok'arin kutsowa.
Tsaye Galadima yayi ya zuba dukkan hannayensa a aljihu, saida yaga shigarsu Rahma mota dasu alhaji darma sannan yanufi inda sarkin mota ya bud'e masa, y'an jaridar daketa masa tambaya ko kallo basu isheshiba ya shige mota abinsa, yayinda Muftahu ya zauna gefensa, Nuren Na a gaba.
Mortar y'an sanda Na a gabansu da Bayansu, a haka akayi tafiyar.
Sauran y'an sandan da aka bari suka shiga gidan domin d'akko gawar Ahmad, amma sun bincika lungu da sak'o babuma alamar an cutar da wani, sai harbi guda d'aya daya shiga jikin bango, (shima Wanda Galadima yayine sanda ya tsoratasu da cewar ya kashe Ahmad), basu samu komaiba dazai nuna Galadima d'an ta'addane, sai suka fito suna kulle gidan, amma basu tafiba harsai kotu tabada damar hakan.
............................★
Sun Isa Court d'in, inda Galadima da Nuren da Muftahu ne kawai suka Shiga, yaran dasu Alhaji Darma an kaisu wani d'akine kusada wajen.
Takun takalman Galadima dake tafiya cikin tsantsar izza da nuna jinin mulki ya saka dukkan jama'ar kotun zuba masa idanu, shikam ya had'e fuska tamkar hadarin gabas Na tsakkiyar ogusta dabaya d'aga k'afar zubar ruwa, kallon kowa bayayi, gashi ya toshe idanu da Google eyeglasses d'insa da babu mai kallon kwayar idonsa.
A kujerar farko irin wadda su Alhaji Mamman ke zaune shima aka nuna masa shida Nuren da Muftahu.
Wani zama yayi dake tabbatarma da mak'iya shid'infa sarakine, gaba da baya kuma.
Hakan ya k'ona zuciyar su Alhaji balala matuk'a, amma babu yanda zasuyi.
Zaman Galadima babu jimawa saiga alk'ali ya fito, kowa ya mik'e domin girmamawa, saida ya zauna sannan duk aka zauna.
Kotun tayi shiru kowa ya zubama alk'ali idanu, yagama dube-duben ta kardun gabansa sannan ya d'ago ido yana kallon jama'a, yace, “Yau shari'ar zata tafine kai tsaye batare da shigar lauyoyi Na kowanne 6angare a tsakiyaba, Dan haka muna buk'atar Wanda yay k'ara, da wad'anda ake k'ara a gaban kotu”.
A hargitse su alhaji Sageer suke kallon kallo, hakama lauyansu dukya shiga rud'ani, saboda mugun shirin dayayo yau akumace ba haka za'ayiba.
Shikam Galadima wani mugun murmushi yayi yana kallonsu Alhaji mansur d'in damusu wata inkiya da yatsu biyu alamar a kafta, sannan ya mik'e.
Dole suma duk suka mik'e inda aka buk'aci ganinsu, dukda wajen yamusu kad'anma.
Alk'ali ya kalli galadima. Yace, “kaine Wanda kai k'ara, Dan haka munason jin shin minene mafarin wannan takun sak'a kai tsaye?”.
Murmushi galadima yayi, ya cire eyeglasses d'in idonsa ya saka cikin aljihu, tareda zaro handkerchief ya goge fuskarsa, yasa hannayensa biyu ya dafe katakon gabansa yana jifan waziri mahaifin Harun dawani mugun kallon daya hargitsa y'an cikinsa da tunaninsa, hakanne yasaka mutane kallon waziri suma, duk sai yaji ya muzanta.
Galadima ya ta6e baki yana janye idonsa dad'an cije lips, cikin k'asaitacciyar muryarsa yace, “ya mai shari'a labarina mai tsawone kwarai da gaske, sannan cike yake da abubuwan ban mamaki da takaici masu tarin hargitsi, duk da nasan kowa yasan sunana amma zan sake maimaitawa, sunana Muhammad Sameer Saifuddin Abubakar, gidan sarauta Na fito, mahaifina shine tsohon Sarki da k'addarar ciwo ta kwantar tsawon wasu shekaru, amma lallai da sanadi, wannan kuma sanadin shine Na d'auki tsawon shekaru tundaga tasowata har zuwa yau ina nema. tun daga lokacin dana mallaki hankalin kaina nasan minene matsalar mahaifina natashi da burin d'aukar fansa, sai dai kuma tayaya? Wannan shine yayta wahalar da Muhammad Sameer a tsawon shekaru”. Galadima ya k'are maganar idonsa Na ciko da hawaye, yay murmushin takaici yana jinjina kansa da had'iye hawayen.
Hakanne yasaka jikin wasu fara yin sanyi, musamman wad'anda suka k'ullaceshi da farko.
Galadima ya cigaba da fad'in, “Ban taso maraya ba, amma nayi rayuwa irinta marayun, ALLAH shine gatana saikuma mahaifiyata da kakana da suka tsaya tsayin daka wajen tsayamin nazama jarumi wajen sanin wahalhalun rayuwa Na yau da kullum, duk Sana'a mai wahala kad'ance banyitaba a k'asar daba tawaba, gakuma gefe ana gwagwarmayar Neman ilimi, ga burin son sanin suwaye suka durk'usarmin da mahaifi?, ban cutar da kaina wajen nutsuwa Na fahimci rayuwa ba, hakama nabama karatuna muhimmanci saboda k'aunarsa da nakeyi, duk da banida burin yin aiki a k'ark'ashin kowa, Alhamdllh yanzu haka inada Company Na had'aka da duk shekarar duniya yake fidda wayoyin Hannu da computers dakan zagaya cikin duniya, ina alfahar da samun cikar burina sosai, Na dad'e ina bulayin Neman hanyar bincike akan abinda yafaru da Abie na, alokacin mutum d'ayane zuwa biyu ke bani gudun mawa, wato lauyan mahaifina, baffina Barrister Usman Audu, sai kakana Sarki Abdul-fatah. Ganin inata wahala sanan babu wani haske a cikin lamarin sai suka bani shawarar mizai hana a nemamin aiki k'ark'ashin wata hukumar tsaro, da farko ban aminceba, Dan irin wad'annan ayyukan basa wani birgeni, hasalima haushin masu yinsa nakeyi, Dan sun gaza binciko Wanda ya cutarmin da Abie na. A tashin farko dana nuna banaso Papi da Baffi sun k'yaleni, basu sake min magana ba, sai wata rana kwatsam wani Abu yafaru anan Nigeria, wasu y'an ta'adda sukayi mummunar 6arna a sirrin gwamnati, k'ark'ashin hukumar DSS. wannan 6arna ta rikita Nigeria sosai a lokacin, shekaru 10 kenan inhar ban mantaba, a lokacin nagama bautar k'asata anan Nigeria ina shirin komawa india, bansan ya akayi sukasan nasan Computer ba, har masarauta akazo aka rok'i mai martaba akan Na taimakesu. Da farko kam naso bijirewa amma babu abinda iyayena zasuce nayishi banyiba inhar bai sa6a shari'a ba, nasanma bazasu sakani wannanba, bisa umarnin mai martaba Na amince da gwadawa idan zan iya, haka akaje dani headquarters d'insu, tun hawan Computers d'in danai a tashin farko Na gane da had'in kan waaunsu aka kwashi bayanan, sannan masu kula da Computers d'in sunada buk'atar k'arin ilimi ma gaba d'aya. Cikin sauk'i Na d'akko bayanan da aka d'auka Na dawo musu dashi, sannan nasaka musu securitys masu tsaurin gaske daba wani mahaluki dazai kuma musu irin wannan kutsen. Ni ban d'auki abinda nayi matsayin komaiba, amma agaresu sun girmamashi, sunkuma biyoni har gida da rok'on kasancewa a cikinsu amma nak'i Sam, nama tattara Na koma India, Ashe sunata bibiyata ta wajen kakana, to shima dama yana burin nayi aikin, Dan haka yabasu goyon baya, sannan yaje har India ya sameni da batun, ya nunamin ta wannan hanyarne kawai zan iya binciko abinda ya faru da mahaifina cikin sauk'i, hakama Baffi ya fad'amin a lokacin, Na zauna nayi nazari dakuma samun kwarin gwiwa daga Mahaifiyata. Rana d'aya sai nima naji yakamata Na amince, Dan haka Na amince, tundaga lokacin nashiga cikin hukumar CID nima, saidai ina musu aikine cikin sirri, a hukumarma ba kowa yasan daniba, tunda ni komai ta computer nake gudanar dashi. Sir Isa Maharazu shine ya taimaka min wajen binciko file Na binciken case d'in mahaifina, Wanda tun kusan shekaru 8 mai kula da case d'in ya rasu, Wanda kuma suke ta fannin y'an sanda suma sukayi shiru, daganan aka ajiye case d'in gefe kawai. Tun a file d'in nafara cin karo da sunayen wasu daga cikinsu Alhaji Lawan tanderu. Nasha mamaki kwarai da gaske amma sai banyi wani yunk'uriba, ina wata shida da aiki wani yaso min kutse a cikin Computer, ta silarsa nagano uban gidansa, har zuwa Kansu Marigayi Alhaji Labaran kachia. Tundagafa wannan lokacin saina tsananta bincike da kwakwalwa dakuma tannin aiki, bisa taimakon sir Isa, mun baza yara cikinsu Tanderu batare da sunsaniba, kullum kuma cikin bin diddigin motsinsu suke. Kwatsam sai Tanderu ya rasu sanadin had'in mota, babu jimawa shima Alhaji Labaran khacia ALLAH yamasa rasuwa sanadin rashin lafiya. daga nan saina d'an dakatama gaba d'aya da wani bincike Na koma gefa Na zuba musu ido kawai.
Saida Na d'auki kusan shekaru biyu ban sake wani yunk'uriba sai kwatsam muka wayi gari mijin Yayata Haneefa yayi had'arin Mota, saidai kuma a ranar ne aka turomin massage daya nuna accident d'in nashi akwai saka hannu a ciki, dayake bai rasuba a lokacin sai a asibiti bayan awanni uku da kaisa, Alhaji shehu Darma abokinsa ne Na kut da k'ut sannan d'an uwansa, Dan haka yana tare damu a wajen, saina matsanta akan tambayarsa kozai fad'amin akan miya faru dashi kafin had'arin? Bai iya cemin komaiba sai murmushin k'arfin hali da yayi yana kallon Alhaji shehu har numfashinsa ya k'are, wannan kallo ya tsayamin a rai sosai, Dan nagaza mantawa dashi, abinda Yakuma k'arfafa min zargin Alhaji shehu shine Aunty Mimi Na fita daga takaba sai Yace yanason aurenta, nine Na hana, nama tattarata gaba d'aya itada y'ay'anta Na maidasu india, dukda dangin mahaifin yaran sunso d'aukarsu suma. Dama can lokaci-lokaci Alhaji shehu yakanbi mijin Aunty Mimi suje duba Abie, dan haka ko bayan rasuwarsa bai daina zuwaba, abinda na fara fahimta shine Samha d'iyar marigayi tana tsoron Alhaji shehu, amma shi yana tsananin nuna mata kulawa dayin kaffa-kaffa da ita a gaban mutane. Wannan ma yasa na kuma saka ido a kansa, abinda Na fara karo dashi shine Alhaji shehu yana tursasa Samha ta hanyar mata barazana akan ta d'akko masa wasu sirrikana”. Galadima ya murmusa cikin takaici yana gyara tsayuwa da goge fuskarsa da handkerchief. Yaciga da fad'in,
“Tunda Na fahimci hakan saina jata a jikina, nakuma dinga ajiye mata dukkan abinda yasaka ta d'akko, itako data gani saita tura masa saboda tsoron barazanar da yake mata. Suma sauran Na cigaba da bibiyarsu suda ayyukansu, so banida matsala da sauran mugayen halayyarsu, nidai kawai wadda ta had'amu nakeson Sani, Dan Na gano sun gana da mahaifina ana gobe abinda ya sameshi zai sameshi, kuma yafito daga d'akin tattaunawar ransa a 6ace. Batanci da akaimin a shekara d'aya data wuce cikin jaridar manuniya shine mafarin yalwatur haske a matsalolina, dukda Na fahimci ankai tsawon shekaru ana bibiyar dukkan al'amurana, kuma inhar Nazo k'asarnan kullum cikin bibiyata ake, domin rufe bakin mak'iyana Na auri wadda sukaso sakawa a matsalar dabatajiba bata ganiba, wadda a yanzu Alhmdllh itace uwar y'ay'ana, nasan hakan ya girgizasu a lokacin kwarai da gaske, adalilin zama da ita nama fahimci abinda ban fahimtaba da farko, Dan da Duk zargina ko da itane aka had'a kai wajen Neman 6atamin suna, amma sainaga dukba haka baneba, ya mai shari'a Alhaji Auwal Fharuk sai shine surikina mahaifin matata, kuma anyi yink'urin kasheshi watanni kusan 7 da suka shige, saidai ALLAH ya k'addara yanada sauran kwanaki a gaba, bisa dalilin yun k'urin kisansa ne kuma Na fara karo da alak'ar case d'in mahaifina dashi, hakan kuma tafaru bisa sanadin matata, data dinga zak'ulomin wasu masu alak'a da mahaifinta kuma Na jikinsu tanderu, irinsu Mamman k'afur, Alhaji Halluru, saikuma daga baya ga SD, wato Alhaji shehu Darma, Wanda shine aka saka yake bibiyar Alhaji Auwal Fharuk yana masa barazana, satar yarana da akayi a ranar sunansu ta kawo bayyanar aminina d'an uwana cikin case d'in mahaifina daban ta6a tunanin kasantuwarsa a cikiba, wato Harun d'an gidan waziri, shine wazirin mahaifina shine kuma wazirin Sarki Na yanzu, ina cikin rud'anin Hakan saikuma ga Alhaji Rabilu ya bayyana a gareni shida Badi d'a ga mai dokuna a masarautarmu, Wanda tun ina k'arami Na sanshi, amma daga baya ya 6ata 6at. Bayanan wad'annan bayin ALLAH da bincikena Na had'a suka tabbatar min da zargina akan wad'annan mutanen, nasan abune mai wahalar gaske samunsu cikin sauk'i da fahimtata da duniya zatayi akan zargin danake musu, shiyyasa naza6i yin Garkuwa da yaransu bisa tursasasu tilas sufad'i abinda ke ransu da Wanda suka aikata. Dukkan Wanda ya shigo cikin labarin nan nawa akwaishi a wajennan, mijin yayatane kawai bayada rai sai mahaifan Badi, dakuma wasu daga cikinsu da sukabar duniya, Dan haka ina rok'on wannan kotu data nemo dukkan Wanda Na ambata domin jin ta bakinsa”.
Alk'ali ai yama kasa magana, sai kad'a kai kawai yake mamaki da al'ajabi Na cinsa, yayinda kotu tayi tsit kowa yana k'ullawa da kwancewa da tausayin Galadima, irinsu Alhaji Halluru kam ai cikine ya d'uri ruwa, sunsan dai tasu tagama k'arewa kam, Dan yau ranar bankad'a Ce da walle-walle.
Alk'ali yad'anyi rubuce-rubucensa sannan ya buk'aci ganin Badi da Alhaji Rabilu, Galadima kuma yaje ya zauna.
Alhaji Rabilu da Badi sun bayyana a gaban kotu, hakan ya kuma hargitsa hanjin cikin Waziri, yana mamakin dama Badi bai mutuba? Amma su hak'ilu sukazo sukace ya mutu a wancan lokacin, dan agabansu mai besfa ya kad'eshi, innalillahi ya shiga ambata a zuciyarsa, sai zufa ke jik'eshi, sauk'insa ma akwai malun-malun da rawani a jikinsa, Abba Hayatudden kallonsa kawai yake da tsantsar tsana da mamakinsa.
Duk yanda Badi da Alhaji Rabilu sukaima Galadima bayani haka suka maimaita a gaban kotu, wasu harda hawayen tausayinsu suke matsewa, Alk'ali yace, a kawo Alhaji Auwal Fharuk Dan Badi yaga idan shine yabama camera.
An kawo Abba, Wanda Alhmdllh jikinsa yayi sauk'i sosai, saidai abinda ba'a rasaba Na k'arfi, kallo d'aya Badi yayma Abba ya ganeshi Dan bai canja masaba sai canjin girma irinnan shekaru, hakama Abba ya gane Badi sarai Dan shima d'in bai canja masanba, aiko suka rungume juna kowa yana hawaye, Abba yana fad'in “Bawan ALLAH Dama baka mutuba a waccan ranar?”.
Shima Badi cikin kuka yace, “ban mutuba, sai daga baya ne Na farfad'o a wajen”.
Alk'ali ya ankarar dasu cewa a kotu suke, kotu kuma Na buk'ar jin bayani daga bakin Abba, ta Yaya Camera ta dawo hannunsa?.
Abba ya dai-daita tsayuwarsa sannan ya gabatar da kansa ga kotu, ya d'ora da fad'in “shekaru 22 kenan da suka shud'e wannan camera take a hannuna ranka ya dad'e, nakuma sametane ta hanyar kad'e wannan bawan ALLAH danayi da abin hawana a wancan lokacin, saboda ya shigo hanya yana matsanancin gudun dabansan mafariba sai yanzu danaji a ya fad'a a gaban kotu. bayan na bigeshi numfashinsa Na Nuna alamar bankwana da gangar jikinsa ya d'auki wannan camera yabani acikin akwati da sunan amana, yakuma ambatamin sunan wad'anda zanba kamar yanda yafad'a, daganan numfashinsa ya tsaya cak da aiki, ina cikin k'ok'arin taimakonsa saiga wasu mutane da gudu da makamai sun dosoni, tsoro naji, Dan inada tabbacin shima sune suka biyoshi, saboda son isar da amanar daya bani inaji ina gani badan nasoba Na tsallakesa Na gudu, Dan nasandai zasu iya kwatar abinda yabani d'in. tunda camera d'in nan ta dawo hannuna ban sake barci mai dad'iba, kullum burina da tunanina tayaya zan Isar da amanarta Na huta, tsawon shekaru ban ta6a fuskantar wani k'alubale akanta ba, Dan ko iyalina babu Wanda yasan da zamanta a hannuna, matata tasha tambayata idan taganni cikin damuwa amma banta6a fad'a mataba, kwatsam cikin laluben Wanda zan bamawa sai Marigayi Alhaji Abdul-hakeem Uba tsohon Governor d'inmu ya fad'omin, Dan ganin yana auren d'iyar tsohon Sarki wadda tana d'aya daga cikin wad'anda akace nabamawa, to lallai anan Alhaji shehu SD yasan Camera Na hannuna, Dan tabbas yaji zancen da mukayi da Alhaji Abdul-hakeem d'in ta hanyar la6ewa, aranar da mukayi zan bama Alhaji Abdul-hakeem camera ya damk'ata ga matarsa sai aka samu akasi wani aiki ya tasomin Na manta ban fito da camera ba, amma mun had'u da shi marigayi Alhaji Abdul-hakeem Na bashi hak'uri da sanar masa uzirina, shikuma SD a tunaninsu nabama Alhaji Abdul-Hakeem wannan camera, shine suka hari rayuwarsa da nufin kar6a kafin ya kaima matarsa, inaga daga baya da suka fahimci babu Camera d'in a hannunsa shine suka juyo kaina. Sunta matsama rayuwata da barazana iri-iri, kiran waya da sauransu, duk number da suka kirani da ita gobe bada ita zasu kirani ba, hakkane ya sakani ware sim card guda kawai dansu, babu Wanda ya sanni dashi, sai matata Dana saka number cikin wayarta batare da itama tasan hakanba, nayi hakanne saboda watarana koda ALLAH yabasu nasarar kasheni d'in. A lokacin da akaima yarana 6atanci da Galadima lallai hankalina ya tashi matuk'a, amma daga baya danayi nazari saina gano maybe su SD ne suka aikata hakan domin 6atamin suna, hukuncin ALLAH kuma saigashi mai martaba Sarki jalaludden da mai martaba Sarki Abdul-fatah sunzo nemawa d'ansu Galadima auren yarinyata da abin yafaru akanta, dukda a 6adda kama sukazomin ni sarai Na ganesu, amma ko y'an uwana ban sanarmawaba, abinda yabani k'arfin gwiwar aurar musu da yarinyata shine Isar da amanar hannuna cikin sauk'i, saikuma aminin mahaifina Baba mai kanwa yace nabasu, Dan shine kawai yasan da zaman Camera a hannuna, shima bani Na sanar masaba, bankuma San a ina yajiba. A randa za'akai y'ata gidan mijinta a ranar Na saka wannan camera da takarda cikin wani kwali Na sakashi a kayanta batare da tasaniba, bansaniba kota gani? Dan cikin gifts d'inta data samu a hannun abokan mijinta ranar dinner d'in auranta Na sakashi, nabama d'an uwantane Abdul-Hameed babban d'ana yabata batare da shima ya san minene a ciki ba. Hikimata anan idan tagani tabama mijinta batare da kace Na ceba. SD bashikad'ai ke bibiyar rayuwata ba, Dan akwai masu sakashi yazomin da farashin kud'i masu tsoka akan camera d'in amma nayi kunnen uwar shegu dasu, hakanne yasakasu k'ok'arin salwantar da rayuwata wai tunda Na hanasu camera, nasan sunajin tsorone saboda Na kusantu da Galadima a lokacin, zan kuma iya bashi camera d'in, saidai abinda basu ma saniba tuni Camera d'in tabar hannuna. Alhaji Halluru abokinane Dan school mate d'inane, ada babu wata alak'a mai k'arfin tsakanina dashi, amma daga baya sai yayta Jana a jikinsa, ban fahimci manufarsaba dagashi har Alhaji Mamman, Dan da zuciya d'aya ni nake zaune dasu. Sai wannan karon da suka tabbatarmin da zulwa jahainin fuskarsu, sannan suka tursasa y'ay'ana biyu Dana d'auka nabama y'ay'ana Alhaji Halluru aure saboda yarda wai su d'akko musu camera a d'akina kosu kashesu dani dakuma iyayensu mata, sun razanasu da cewar sun dasa bomb a gidana, agabana duk suka sanar musu a waya. Abinda yasa ban damuba nasan k'arya suke, sannan Camera d'inma bata gidan, duk k'ok'arin lalatama Galadima sirrika da sukayi agabana sukayishi, amma ALLAH baibasu nasaraba, jin asirinsu zai Toni ta hanyar Garkuwa da y'ay'ansu da Galadima yayi shine suka shak'amin abinda ban saniba, daganan ban kuma Sanin ina kaina yakeba sai a asibiti yamai shari'a”.
Wannan bayanima Na Abba ya girgiza zukata sosai. Dan har alk'ali kasa motsawa yayi, saidai yaja kusan mintuna biyu sannan ya sauke ajiyar zuciya mai k'arfi. Ya buk'aci a kawo masa camera nanda awa 2 kacal. Anbar lokacin a matsayin hutun kotu.
Babu Wanda yaso matsawa konan da can, kowa burinsa dai camera ta iso aga mita k'unsa.
Galadima ya kira Munaya, yace ta shirya ga Sarkin motanan zasuzo da Nuren su kaita masarauta ta duba cikin gifts d'inta Na Aure data samu Abba yace camera Na ciki.
Dayake a labarai an nuna takuma gani, sai kuka dama takeyi da mamakin miyasama bata duba gifts d'in auren nataba tun wancan lokacin? Koda yake bata dad'eba a Nigeria suka wuce India, itakam a dukkan zaman da suka d'an tayi idan sun dawo bata sake bi takan gifts d'inba, to kawai tace masa ya yanke wayar, Dan yanzu babban burinsa kawai a tabbatar camera d'in tana wajen nata.
Tana gama shiryawa sarkin mota yazo da Nuren dakuma police, bata d'auka yaro ko d'ayaba tafito suka tafi masarauta.
Sun iske masarautar tsit, tamkar anyi sharar mutane, kowa Na sashensa abinda ke faruwa yama zukatansu murus, hannu kawai take iya d'agama hadiman sashen nasu dake gaisheta, basu damuba, dansunsan tana cikin wani yanayine.
Sashen nasu yayi y'ar k'ura, saboda kwana uku babu kowa a ciki, Munaya kanta tsaye bedroom d'inta ta shige kawai, ta bud'e wardrobe nata tashiga fiddo gifts d'in aurenta data tara gefe, tareda Na haihuwar su Abdurraheem. d'ai-d'ai taita farkesu, idan taga bashi bane ko bud'awa batayi take jefawa saman gado, tasha wahala matuk'a kafin ta gano akwatin da idonta ya ta6a tozali dashi a d'akin Abba itada Munubiya, rungume akwatin tayi ta fashe da kuka maiban tausayi, ana haka kiran Galadima ya shigo wayarta, share hawayenta tayi ta d'aga.
A d'arare yace, “kin hanshi?”.
Cikin dariya da kuka ta amsa masa da eh ta gansa, shima murmusawa yayi, yace, “maza Ku tahoto, mintuna 46 suka rage a lokacin da alk'ali ya bada, sonake kawai a kammala shari'arnan a yau”.
Munaya ta amsa da “to gamunan.................✍🏻
*_“insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu, koma mike cikin camera d'in dai zamu gani, nima Na k'osa nagani a wuce wajen😬🤦🏻♀”_*.
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*
*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BOOK 3_* 👉🏻1⃣9⃣
.................Su Munaya sunyo nisa da tafiya danja ta tsaidasu, kamar daga sama suka fara jin harbi, y'an tsirarun mutane dake bisa titin suka fara guduwa, dan titin wajen baicika yawan mutaneba, kasancewar wajen tamkar sabuwar anguwane kuma gefen gari kad'an, itace hanya mai sauk'i da zata iya kaisu da wuri shiyyasa suka biyo.....
Batakai k'arshen tunanintaba taji wani azababben zafi a damtsen hannunta, ko kad'an bataji k'arar wannan harbinba (dam inhar harbi zai shiga jikin mutum aishi bazaiji k'arar bindiga ba) kallon inda akayo Harbin Munaya tayi, glass d'in ya huda ga wani garjejen k'ato yayo wajen motar, a kid'ime ta kalli sarkin mota da hankalinsa shima yake a tashe, sai zufa yake yana waige-waigen ganin yanda police d'in suka fita sunason basu kariya.
Cikin k'arfin hali Munaya race, “Sarkin mota, ka kar6i Camera d'in nan ka hanzarta kaita kotu, ya tabbatar min lokacin buk'atarta tayi, karka sanar masa komai harsai shari'arnan ta kammala dan ALALH, inason burinsa yacika koda ace zan rasa raina a yau, please karka damu sarkin mota jeka, maza jeka kar Mara imaninnan ya k'ara so.
Badan sarkin mota yasoba ya kar6a ya fice da sauri cikin dabara, saboda Munaya tabashi tausayi, ga harbi ta samu, amma bata kanta takeba ta cikar burin mijinta takeyi.
Fitar sarkin mota tayo dai-dai da isowar garjejen k'atonan, ya bud'e murfin motar yana fisgo Munaya waje, fad'owa tayi kanta ya bugu da kwalta sai jini kawai, tuni numfashinta yafara fita da k'yar, dishi-dishi take hango wani Na dukan Nuren da bakin bindiga yana k'ok'arin kare kansa da kiran sunanta yana mik'o hannu, amma ina, sun riga sunci k'arfinsa, idanunta suka lumshe a hankali, yayinda wasu hawaye masu zafi suka gangara ta gefen kumatun data fad'in, fuskarta d'auke da murmushin k'arfin hali.
Nuren daketa kwala mata kira a rikice yana mik'o hannu, dukda dukansa da ake, ya zube a k'asa yana fashewa da kuka maiban tausayi da ambatar “please Munaya karki tafi kibarmin d'an uwa, ke wani yankin farin cikinsace mai matuk'ar girma ple......
Shima baikai k'arshenba ya sulale k'asa saboda dukansa da sukayi a kai.
Wani dake bincika camera d'in a motar ya juyo a fusace yana fad'in “babu camera d'in fa boss”.
A rud'e Boss d'in dake tsaye gaban Munaya ya taka hannunta da mugun takalminsa yayo wajen, ko motsi kuwa batayiba alamar ruhinta yabar gangar jikinta.
Ture yaron nasa yayi yafara lalube da kansa, hankalinsa yakai gaban motar. yace, “Ina driver!!? ”.
Yanda yay maganar a rikice ya saka yaran rikicewa suka hau waige-waige, sarkin mota dayay nisa a gudu yana jiyo ihun ogan, saiya k'ara k'aimi.
Wani yace, “gashi can zai gudu da camera d'in ”.
Tuni suka rufoma sarkin mota baya a guje, shima yacigaba da gudu iya k'arfinsa. Cikin amincin ALLAH saiga wani mai mashin tamkar an jehoshi, ya tsaya yana fad'in “maza hau muje”.
Sarkin mota ya haye, mashind'in nabarin wajen suna k'arasowa, Dutsuna suka d'auka suka dinga jifansu sarkin mota suna binsu da gudu, amma ALLAH bai basu nasaraba. Hardai ubangijin sammai ya kaisu court lafiya.
Sai lokacin Na lura Ashe Ahmad ne yaron Alhaji Bana, ya kalli sarkin mota yana fad'in “Maza kakai, yanzu haka ita kawai ake jira, kasa nutsuwa a ranka kar boss ya fahimta balle yakasa nutsuwa a shari'ar shima, yanzu haka suma police zasuje su taimakesu, muma can zamu tafi da sauran y'an uwana”.
Kai sarkin mota ya jinjina, ya k'arasa gaban k'ofar kotu yay knocking yana share hawaye da tausayin Galadima. Anzo an bud'e masa aka shiga dashi, dama camera d'in kawai ake jira.
A can kuwa suma saiga Police an k'aro, wad'anda suke tare dasu Munaya su 6 ne kawai dama, gashi bawani isassun kayan aikine dasuba, bindugun hannunsu babu mai bullet, sun daki d'aya yasuma, d'aya kuma yasamu ya sulale domin kira yasanarma ogansu abinda ke faruwa, yayinda biyu suka gudu, biyune kawai a wajen, sukuma sunyi musu yawa y'an ta'addan.
Isowar police d'in ta saka wasu a cikinsu yunk'urin guduwa, saidai ina, ALLAH yakan ara maka rana, randa kuma zai kamaka babu hanyar ku6ta, dukansu ram akayi dasu, dukda wasu sunso yin gardama, duk aka zubasu a mota, yayinda Ahmad yasake dawowa shi da Yassar tareda Ambulance, suma su Munaya da Nuren aka kwashesu😭.
...............................★
Tunda Galadima yaga sarkin mota ya kawo camera hankalinsa bai kwantaba, dakuma yaso had'a ido da Sarkin mota shi saiya kauda nashi, yak'i yarda su had'a idon.......
Maganar Alk'ali ta katsema Galadima tunaninsa, yayinda yake bada Umarnin a bud'e camera d'in, takardune aciki guda uku, d'aya abbane ya rubutata yanama Galadima bayanin yanda akai camera tazo hannunsa, d'aya kuma sunayen dukkan wad'anda ke bibiyar sa akan camera d'in ne, d'aya kuma wadda mutumin farko d'an uwan baba Rabilu daya bada camera d'in ne ya rubuta ce.
Ita kad'ai alk'ali yabada umarnin karantawa, yayinda masana keta k'ok'arin saita camera da TV dake kotu suma, Wanda Galadima ne ke k'ara sanar musu dukkan dabarun daya kamata suyi daga inda yake tsaye.
Abinda takarda ta k'unsa shine.....
*_Assalamu alaikum_*
_Sunana Habu, wannan takarda ina fatan ta iso agareku, ko yarima, ko gimbiya ko matar Sarki mahaifiyar su yarima, Ku duba wannan camera d'in, duk yanda aka k'ulla faruwar ciwon mai martaba da wad'anda suka kulla suna a ciki, nidai nasan tawa ta k'are, dan tunda suka ganni ina d'oukar sirrinsu saisun kasheni, wata uku kenan ina 6oye-6oye, yaudai Na yanke shawarar fito fili Na baku koda hakan yana nufin zan mutu, dama can kwanana sun k'arene, koma basu nayi saisun kasheni, ballema bazan ta6a basu d'inba, ALLAH yabama mai martaba lafiya da tsawon kwana mai amfani, yakuma baku ikon hukunta wad'annan tsinannun masu jinin Fir'auna a jiki, wad'anda mulkine da tara duniya kawai a gabansu ba al'ummar k'asarsuba, duk yanda zakuyi karkubar la'anannnun nan yin mulkin al'umma, subasu cancanci zama shuwagabanniba._
*_Bisalam_*.
Kotufa tayi tsitt, ko tarin wani bakaji sai k'arar fanka, yayinda zufa tagama jik'e su Alhaji balala sharkaf, kallo d'aya zakai musu ka fahimci ruwafa ya k'arema d'an kada.
Alk'ali baice komaiba, jira kawai yake camera ta daidaita ajikin TV kowa yagani, matsalar camera Ce irin ta da, shiyyasa take bada wahala, da k'yar dai cikin amincin ALLAH ta kawo, tofa, saidai kalar da take nunawa White and black, ga wani rawa-rawa da takeyi saboda ba nutse aka d'aukaba, kuma da alama ana yayyafine.
Dagani wajen wani ke6antaccen wajene daba kowa ya isa shigaba, shikansa d'an jarida habu kota Yaya yayi hakan? ALLAH kad'ai ya Sani saishi, gashi bashida rai balle mu Sani.
Mutanene da ak'alla sunkai 20 a wajen.
Alhaji balala, Alhaji Mansur, Alhaji Lawan tanferu, Alhaji Bana, Alhaji Abdul-Naseer, Alhaji Labaran khacia, Timothy, Hajia A'i, Victoria, Miracle, Alhaji Sageer, William, Josaya bamma, Kabiru Ibarheem, Alhaji Mamman, Waziri, Sai wani Sarki daba wani k'arfin ikone dashiba, yama rasu tuni, tun ciwon Abie babu dad'ewa, sai Mahaifin Gimbiya Zulfah uwargidan Sarki, shima sarkine mai fad'a aji, Sai mahaifin Mama Fulani😱, sauran Biyun turawane.
Duk suna zaune kowanne da kwalbar coca-cola a gabansa (sannan shinsa sai manya🤣).
Alhaji Lawan tanderune ya mik'e yafara jawabi kamar haka.
_Masu girma saraki dake wannan waje, da bak'inmu (turawa) sai abokaina shak'ik'ai ina muku sallama gaba d'aya_
Duk suka amsa a tare. yaci gaba da fad'in,
_Muduka nan mun tarune akan mak'iyinmu guda d'aya, Wanda ya tare mana gabas ya tare mana yamma, hakama kudu da arewa, mun bishi ta lallami akan yabamu goyon bayan cikar burinmu amma yak'i, yana wulak'antamu saboda yaga ALLAH yabashi k'arfin iko da izzar mulki a hannu, a daren jiya mun yanke shawarar kasheshine kowa ya huta, amma yanzu mun fasa hakan, zamuyi masa abinda saiya gwammaci yazama gawa, dan zai rayune shiba mutumba Shiba butun butumiba, ahaka naman jikinsa zai ringa ru6ewa sashe-sashe, mukuma zuwa sannan mulkinnan dai dayake ganin bazai dafa mana muyiba ya dawo hannunmu, dan mungaji da mulkin soja hakannan, gashin kanmu muke buk'atar ci koya kukace?”_
Hannu suka d'aga suna fad'in eh hakane hakane.
Alhaji Lawan tanderu yayi dariya yana gyara babbar rigarsa, ya d'akko wani ruwa a kwalba yana nuna musu, _“kunga wannan itace gubar ruwan allurar da za'ai masa, ita cikin mintuna biyu zuwa biyar take fara tasiri koba haka kaceba Mike?”._
Cikin turawa biyu dake tare dasu d'aya ya gyad'a kai yana murmushin mugunta.
Gaba d'aya suka sanya tafi, raf! Raf! Raf!, saikuma suka koma tafawa da musabaha a junansu (irin sun samu cikar burinsu d'innan).
Tanderu yacigaba da magana bakinsa a washe.
_“Wannan aiki ba kowane zai mana shiba sai wazirinsa, Munaso da asubahin yau kamasa wannan allura dakagani, inamai tabbatar maka inhar ya Idar da sallar to bazai shiga gida da kansaba”_.
Waziri mahaifin Harun ya kar6a yana washe baki tamkar gonar auduga, da fad'in “lallai nafi kowa farin ciki da samun wannan dama, domin kobabu komai zanyi maganin mak'iyina da kaina, daga yanzu sainaga da bakin dazai kuma cin zarafina da jifana da kalaman banida hali, toshi mai halin saiya cigaba da shukashi muda bamu dashi muyita girba munakaiwa gidanmu munaci....”.
Gaba d'aya suka kwashe da dariya suna tafawa, a Na wannan dariyane Alhaji Bana idonsa yakai ga camera, alamun yaga habu kenan, ajiye k'aramin kofin silver dake hannunsa ya zuba coc yayi yana mik'ewa zumbur.
Sauran suka fara tambayarsa mike faruwa?, tuni habu daya farga dasu ya shek'a da gudu. Daga nan ba'a sake nuno kowaba, sai gudu da habu yakeyi da hakkinsa, Camera d'in Na wani shuw-shuw harma aka bar ganin komai.
Kwakwkwaran Motsi kowa ya kasayi acikin Court d'in, Galadima ya duk'ar dakai yana kallon k'asa hawaye Na zirara suna d'iga, hakama Abba Hayatuddin kuka yake saboda tausayin d'an uwansa da takaicin waziri daya kasa zama kusa dashi yanzun, ga takaicin wai harda kakansu Wanda ya haifi mahaifiyarsu, shin shikuma miye matsalarsa da d'an uwansa ne? Kenanma mama Fulani mahaifiyarsu itama tasan komai? Innalillahi wa inna'ilaihiraji'un, wannan wace iriyar masifacene hakan?.
Alk'ali daya buga gudumarsa a sanyaye ya katse tunanin mutane da yawa dake cikin kotun, cikin sauke nannauyan numfashi yace, “yanzu babu tanderu a duniya, shin ko akwai mai wakiltar wannan group a yanzu?”.
Su Alhaji balala da duk jikinsu yay lak'war kunya da nadama duk sun lullu6esu sukayi tsitt.
A fusace cikin daka tsawa Alk'ali yace, “waishin! Ba'a jini bane?!!”.
Jiki Na rawa Josaya bamma ya mik'e, tsufa sosai ya kamashi, danma akwai jin dad'i tattare dashi, ko a wancan lokacin dagani ya girmi tanderun ma gaba d'aya.
Wani cikin ma'aikatan kotun yaje inda alk'ali yake suna magana k'us-k'us, komi yake fad'a masa oho, nagadai alk'ali yayi alamar a kawosu, wancan ya sakko, shikuma alk'ali ya maida hankalinsa ga Josaya bamma dake k'ok'arin shiga inda ake buk'atar ganinsa.
Josaya Yaje inda ake tsayawa ya tsaya, Alk'ali ya kallesa cike da tsantsar tsana yace, “kotu tanason jin shin minene kuka nema ga adalin Sarki mai gaskiya da son ayi gaskiya irin Sarki Saifudden yak'i baku goyon baya har kuka nakasashi?”.
Josaya bamma ya gyara tsayuwa kansa a duk'e saboda kunya. Yace, “Ya mai Shari'a, mu mun kasance y'an k'ungiya d'aya masu burin kafa gwamnatin farar hula a wacan lokacin, mafi yawa acikinmu tare mukayi karatu a landan, tunkuma munacan wannan shine babban burinmu, dan haka koda muka dawo najeriya muna kan wannan buri, duk da mulkin soja shike gudana a k'asar tamu, kuma babu wani mahaluki daya Isa yin koda kwakwkwaran tarine, da farko mun fara janyo wasu mutane da yawa suka shigo jikinmu, sannan muka farabin sarakunan gargajiya Na kudanci da arewaci dan samun had'inkai, wasu sun amince mana, wasu kuma sun nuna babu ruwansu, Sarki Saifudden yana sahun farko Na manya-manyan sarakunan gargajiya da akeji dasu da girmama maganarsu a arewaci, munada yak'inin inhar ya bamu goyon baya mun gama samun abinda mukeso, wannan yasa muka fara binsa ta k'ark'ashin k'asa, wato su Mike sukaje ga wazirinsa suka gana da samun manya-manyan sirrika a wajensa, sunje da kwanaki biyu muma sai muka tunkari Sarki Saifudden bisa jagirancin Waziri. Cikin lalama da rok'o muka fahimtar dashi manufarmu, amma saiya fusata, yakuma jamana gargad'i karya kuma ganin koda masu kama damune a masarautarsa, kuma lallai shi da kansa zai nemi shugaban k'asa mai mulkin wancan karon ya sanar masa manufarmu, munta k'ok'arin fahimtar dashi amma yak'i saurarenmu, daga k'arshema saiya koremu daga masarautarsa, wannan shine dalilinmu Na shirya cewar zamu kasheshi, amma daga baya saisu Mike suka kawo mana shawarar masa allurar poison, bamusan ya akayi wannan d'an jarida ya San da shirinmuba harya biyomu inda muka ke6e dan tattaunawa, munta bibiyar rayuwar d'an jarida amma bamu sameshiba, marigayi tanderu ya k'arfafa mana gwiwa akan karmu fasa yin shirinmu, waziri zai kula da motsin kowa a masarautar, a ranar Waziri yatafi da wannan allurar guba, dakuma asubahin washe gari yacika mana aiki, bamu sakejin labarin d'an jarida ba saida Sarki Saifudden yacika watanni uku da fara jiyyasa, saigashi cikin yaranmu wani ya samoshi, sun bishi dansu kasheshi amma saiya 6oyema ganinsu, Ashe yabi motar mai dawakai ne daya gani akasuwa yazo sayen abincin dawakai. Wani bawane yaga wannan d'an jarida tareda mai dawakai a barga, shikuma bawan yana d'aya daga cikin wad'anda waziri ya baza a masarautar domin saka ido, dan yasan komai Daren dad'ewa d'an jaridarnan saiya so kawo camera d'in a masarautar, a lokacin yasaka ancigaba da bin d'an jarida, yakuma k'yale su mai dawakai har zuwa dare yaje garesu. Camera dai tacigaba da walagigi, har muka samun kashe d'an jarida, a lokacin bamusan Alhaji Rabilu munafuki bane yasan komai, har yazo ya shiga jikin mu da cewar yazo shiga tafiyarmune, Ashe munafuki yasan komai, dan bamuga fuskarsa ba lokacin damukaje fadamar bayan gari, shi Badi shikad'ai muka gane tunda dama waziri ya sanar mana. Muncigaba da Neman Badi har tsawon shekaru 4 amma ko labarinsa babu, saidaga baya cikin shekara ta biyarne muka samu labarinsa a wani k'auye, munta bibiyar rayuwarsa daki-daki, har randa yabaro k'auyen muka cigaba da binsa, lokacin daya farga damu shine ya gudu Alhaji Auwal Fharuk ya bigeshi da besfa, lokacin da yaranmu sukazo shi Alhaji Auwal Fharuk saiya gudu, dan haka basuga fuskarsa ba, shikuma Badi ya suma, a tunaninsu ya mutu, suka daddike gawarsa suka dawo suka sanar mana babu camera d'in a hannunsa, sannan kuma ya mutu, amma suna k'yautata zaton yabama wani kafin zuwansu, kilama mai besfa d'in daya bigeshine, bamu hak'uraba, mun cigaba da lalube dukda bamusan wanene ba, ana cikin hakane kuma muka samu damar kar6ar mulki, burinmu ya cika, Alhaji Labaran Khacia yazama shugaban k'asa kamar yanda muka tsara, dan dukya fimu arzik'i a lokacin, saidai kuma yana shekara biyu kacal da hawa mulki Alhaji Lawan tanderu ya rasu sakamakon had'in mota, shugabanci k'ungiya yadawo hannuna, Tanderu bai dad'e da rasuwa ba shima Alhaji Labaran yakwanta jiyya, kwanansa baifi 6 ba ya mutu shima, lallai wad'annan rashin sun girgizamu matuk'a, har yanzu kuma mun kasa mantawa. Tun daga wancan lokacin duk Wanda zaiyi shugabanci a k'asarnan da taimakonmu yake yinsa, kuskuren da mukayi shine mantawa da Sarki Saifudden nada d'a namiji, kuma komai Nisan lokacin zai iya Girman da zaibi ba'asin ciwon mahaifinsa, gaba d'aya sai hankalinmu ya k'arkata ga son samun Camera kawai, a tunaninmu damun sameta dukkan magana ta k'are. Har lokacin da muka fahimci Alhaji Rabilu shima munafukinmu ne, shine muka titsiyeshi akan camera, amma yace bai saniba, Alhaji Shehu ya d'auki mataki a kansa, dan dukkan Wanda yasan da zancen camera burinmu mu kaudashi kawai magana ta k'are, Bamu farga da yarima Sameer ba sai lokacin da ya fara bibiyarmu, Ashe a time d'in shi C.I.D nema, mukuma duk bamu saniba, da taimakon d'an waziri Harun muka samu bayanan sirrin Documents d'in shi yarima Sameer, dan haka Kabiru Ibraheem da shima masanin Computer ne ya shiga yimasa kutse, dan munason musan shin yarima Sameer yana sane da mune? Inhar yana sane damu mukaudashi shima. Saidai kuma yaron ya wuce da dukkan tunaninmu, yanda muke bashi wahala haka shima yayta bamu wahalar, aka cigaba da yak'in sunk'uri, kowa baya ganin kowa kenan, kwatsam saiga Alhaji Shehu Darma yazo mana da labarin Camera fa Na hannun Alhaji Auwal Fharuk, wannan yasa muka koma bobiyarsa, mun masa tayin dukiya mai yawa sau babu adadi amma yak'i saurarenmu, munma rayuwarsa barazana nanma a banza, daga k'arshe muka nemi kasheshi shima, amma ya tsira bai mutuba, Yarima Sameer ma ya d'aukeshi zuwa India, dukda a India d'inma bawai mun barsa bane, canma musha bibiyarsa da barazana, amma taurin kansa yahanashi bamu har zuwa yau d'inan, munsha kaima rayuwar Sameer hari shima ta 6angarori da dama amma yana shallakewa cikin tsarewar Ubangiji, wannan shine abinda ya faru yamai shari'a”.
Babu abinda kakeji a kotunnan sai sauke ajiyar zuciyar jama'a, alk'ali yace yaje ya zauna.
Yad'anyi rubuce-rubucensa sannan yace “kotu tana buk'atar son ganin Waziri a gabanta”.
Waziri Munafuki, saikace an tsamo 6era a ruwa haka yafito yana wani kakkange fusaka, shima inda kowa ke tsayuwa yaje ya tsaya, bayan ya fad'i sunansa Alk'ali ya jeho masa tambaya.
“humm Waziri, kotu zataso sanin minene ya had'aka da Sarki Saifudden da zafi haka? Harka za6i cutar dashi wajen had'akar wasu bare can?”.
Waziri yakuma k'asa da kansa, murya a raunane yace, “maganar gaskiya son zuciyane kawai ba wani abuba, danshi mai martaba ya kasance mutum mai zama akan ra'ayinsa, sannan mai gaskiya da sauk'in hali, nikuma nacika tsugunne-tsugunnen rashin gaskiya, sannan inada sonkai, komai nafison a masarautar gagara badau a fifitani saman kowa, akuma girmamani, wannan halin nawa nason handame komai Na mutane yasaka kullum Sarki kemin nasiha dason gyara halayyata, nikuma nak'i saurarensa, saina kallon hakan danake matsayin cin zarafina yakeyi a kullum, lokacin dana fara ganin take-taken Sarki nason tu6eni sai hankalina ya tashi, nafara Neman mafita, (kusan dai ita sarautar waziri ba gadonta akeba a k'asar Hausa) ina cikin fad'i tashine Neman mafitane wad'annan turawa biyu su Mike sukazo min da tayin mak'udan kud'i da wasu alk'awura, bisa sharad'in sonjin sirrin masarautar gagara badau, babu wani 6oye-6oye Na sanar musu komai, karaf sai'a kunnen wani dogari amintacce ga Sarki, shine yaje ya sanar masa komai, Sarki yakirani har turakarsa ya titsiyeni, yaci mutuncina iyakar iyawarsa, wannan Abu shine ya fusatani, naje Na samu su tanderu muka had'e, dan aganina Sarki ya tozartani a masarauta, tunda gashi yana niyar tu6eni kamar yanda ya fad'amin, nikuma aganina kafin ya tu6eni ya tozartani gara ni nahad'a kai da wad'anda zamu tu6eshi, wannan dalilinne yasakani basu had'inkai, akuma washe garin dana amso allurarna da asuba muna salla, anyi sujudar farko ta sallar asubahi Na kafa masa allurar a cinya Na tsiyaye ruwan kafin a d'ago, amma Sarki dukda nasan yaji zafi, yakumasan cutar dashi akeyi baiko motsaba, saida aka idar da sallar dashi, anayin sallama ya juyo muka had'a ido, baisamu damar min maganaba ya yanke jiki ya fad'i, tun daga wannan lokacin yakoma shida gawa banbancinsu kad'annane, to dama shima wazirin Sarki Abdul-Fatah kuma d'an uwansa shima da nashi shiri akan Sarki Saifudden, dan yanajin haushin ba jikokinsa y'ay'an y'arsa gimbiya Marawuyane (mama Fulani) zasuyi mulkiba, dan lokacin su zaharadeen sunyi had'arin jirgi sun mutu, to burinsa kullum ya durk'usar da Sarki Saifudden jikansa Jalaludden ya gaji mulki, wai tunda gimbiya Kahdija matar Sarki Abdul-fatah ta gaje musu masarauta, shima dolene d'iyarsa mama Fulani ta gaje ta gagara badau, wannan ya sakashi shigowa cikin tawagarmu dasu tanderu, Sarki Saifudden Na kwanciya jinya kuwa aka d'ora Jalaludden bisa karaga a matsayin mai ruk'on kwarya, bisa alk'awarin zan cigaba da wazircinsa, sannan kuma sarautar waziri tazama din din din, y'ay'ana ma zasu iya gadona, shiyyasa lokacin da aka sanarmin ga camera a hannun mai dawakai nayi azamar son kar6a, amma yamin gardama, nikuma Na kashesu shida matarsa dan karsu tonamin asiri, nakuma saka yara subimin d'ansa daya gudu da camera, a masarauta kuma nace Badi da kansa ya kashe iyayensa. Maganar gaskiya mama Fulani batasan mahaifinta yayi wannan shirinba, danya ta6a tuntu6arta da batun kashe Sarki Saifudden amma tace Sam bata aminceba, bazata ta6a kisan kaiba, shiyyasa bai ta6a sanar mata yanda akayiba, shikansa Sarki Jalaludden baisan komaiba, dan yana masifar son d'an uwansa, bayason abinda zai ta6ashi, shiyyasa nikuma Na dinga kwantar masa dakai dan karma ya fahimci wani Abu, nasaka d'ana Harun yake bibiyar mana dukkan motsin Sameer. Wannan shine dalilina yamai shari'a”.
Alk'ali yace, “toshi mahaifin gimbiya zulfa uwargidan Sarki na yanzu minene ya kawo shi a ciki? tunda dai yanzu bashida k'arfin da zaizo kotu ya bamu amsa saboda girma ya kamashi sosai, nakuma San Kasan komai shima a kansa?”.
Waziri ya gyara tsayuwa yana jinjina kai, yace, “shima dai shirinsa bai wuce akan mijin y'arsa yayi sarautar ba, wato Sarki Jalaludden Na yanzu kagadai dolene jikokinsa su gaji sarautar anan gaba, sannan kuma yanajin haushin sarki Saifudden d'in, dan shi yaso ya auri d'iyarsa zulfa amma sai Marigayi Sarki Abubakar ya had'ashi da d'iyar Amininsa gimbiya Zaitun, bayan rasuwarta ma Yakuma masa tayin wata y'ar tashi amma sai aka maye gurbin gimbiya Zaitun da gimbiya Zeenah, shi burinsa dai ya nuna inhar ank'i aurama Sarki mai sarauta y'arsa to jikokinsa koda tsiya saisunyi sarautar gagara badau d'in, lallai wannan dai shine dalilinsa shima”.
Babbar magana, wai dukdai akan mulki kayan duniya aketa wannan k'ulla-k'ulla, Wanda gashi yanzu a cikinsu wasuma sunbar duniyar baki d'aya, wannan wace iriyar masiface haka?.
Alk'ali ma kasa magana yayi, saida yad'au ruwa yasha tukunna, Galadima kam ai babu mai iya tantance halin dayake ciki, ya kwantar da kansa jikin kujera yasaka handkerchief ya lullu6e fuskarsa gaba d'aya.
Alk'ali yace, “Lallai a gaisheku, Ku yanzu dan girman ALLAH bakuji kunyar kankuba? Kamarku manyan mutane da k'asa ke alfahari daku da girmamaku Ashe ru6a66une a bad'ini, maciya amanar k'asa, lallai barin irinku ma ai had'arine wa duniya baki d'aya, dan duk abinda aka nema Na wulak'anta k'asarku zaku iya mik'awa domin cikar burinku, kune masu 6ata shugabanni Na kwarai masu k'yak'yk'yawar zuciya, ALLAH ya cigaba da tona mana asirin irinku a k'asarmu”.
Gaba daya Kotu ta amsa da Amin!!!,
Alk'ali yay k'asa da kansa yana bincike a k'aton books d'in gabansa kusan hud'u, kotu tayi tsitt kowa ya zuba masa ido, ya d'auki tsawon lokaci yana rubuce-rubuce kusan 30minute's sannan ya d'ago yana cire eyeglasses d'in idonsa, yasaka handkerchief ya goge fuskarsa sanan ya goge eyeglasses d'inma ya maida a idonsa yana kuma gyara zama dayin gyaran murya. Yace, “Bisa ga hujjoji da bayanan da suka fita a bakin wad'anda ake zargi kai tsaye, wannan kotu mai adalci ta yankema wad'annan mutane 20 da sukayi gamayya wajen ciwon Sarki Saifudden hukunci d'aurin rai da rai a gidan kaso, saboda kisa da suka dinga sakawa a nayi bayan laifinda suka aikata”.
Kotu ta d'auki sowa gaba d'aya, saida alk'ali ya tsawatar ta hanyar buga gudumarsa, kowa yay tsitt.
Alk'ali yacigaba da fad'in “Wazirin Sarki kuwa hukuncinsa shine kisa ta hanyar rataya, sakamakon kisan mai dokuna da matarsa, Hakama Alhaji Shehu darma, d'aurin rai da rai da horo mai tsanani saboda bada had'in kai wajen kisan d'an Uwansa Alhaji Abdul-Hakeem uba, dakuma tsiyatakun da suka dinga sakashi yanayi. Akwai yaransu dake hannu bisa laifi daban-daban da suka sanyasu, suma dai d'aurin rai da rai ne akansu, Irinsu Alhaji Halluru, Timothy da sauran su shekaru 30-30 ne hukuncinsu, da horo mai tsanani, dukansu babu maganar beli, dolene saisun rayu a gidan kaso. Sannan wannan kotu ta wanke Muhammad Sameer Saifudden bisa zargin ta'addancin Garkuwa da yara da yayi, dan bai ta6a kowaba a cikinsu, dagashi har tawagarsa da suka bashi gudunmawa kotu ta wankesu tas. Akwai d'angidan Waziri mai Suna Harun, kotu ta yanke masa zaman kaso Na shekaru goma bisa ga cin dunduniya Muhammad Sameer daya dingayi wajen sato bayanansa, ina fatan kowa yasamu hukunci dai-dai da abinda ya aikata, kuma duniya ta gamsu da hukuncin da muka yanke?”.
Kotu ta d'auki sowar gamsuwa da ALLAH wadai da halin irinsu waziri dasu Darma. Kowa tur yakeyi da halin masu.
Alk'ali ya buga gudumarsa alamar kotu ta tashi, daganan kowa ya mik'e saida ya shige sannan aka kacame da hayaniya, harda masu kaima su Alhaji Halluru duka, ana musu ihu, saima da aka fidosu mutane sukaita jifansu da duwatsu, sai y'an sanda suka dinga karesu har aka zubasu a mota, wasunsuna kuka sukeyi rurus dan ganin iyalansu ko damuwama basuyiba, wasu a cikin yaransu ai ko'a kwalar rigarsu, k'alilanne a cikinsu suka damu.
Galadima har kowa yafita a kotun shi yakasa motsi, saida Abba Hayatudden da baffi da Abban munaya sukazo kansa, baffi ya cire Handkerchief d'in daya lullu6e fuskarsa saisukaga ashema a sume yake?, rikicewa sukayi, aka samo ruwa Abba Hayatudden ya shafa masa a fuska ya kawo numfashi.
Zabura yayi, saida Abba Hayatudden ya rungumesa, jinsa a jikin k'anin mahaifinsa saiya saki wani irin kuka maiban tausayi, daga Abba har Baffi suma idonsu yacika da kwalla, Abba Hayatudden yashiga shafa bayan Galadima alamar allashi. Kusan mintuna uku ya d'ago da hanzarinsa yana fad'in “Abba Munaya da Nuren, lallai ban yarda darashin zuwansu kawo camera ba, alamun sarkin mota sun nuna akwai wani abu”.
Da sauri baffi ya fita Neman sarkin mota, a waje ya iskeshi tsaye yana jiran fitowar Galadima.
Baffi ya tambayesa miya faru, bai 6oye masaba ya sanar dashi komai, hankalin Baffi a tashe yakoma ciki yace su fito suje, hakkanne ya tada hankalin Galadima da tabbatar da lallai akwai matsala.
A rikice suka shige mota, ko kallon y'an jarida dakeson jin bayani a bakinsu basuyiba, balle bi takan jama'a dake jiran su fito sumusu jaje....................✍🏻
*_Lallai K'arshen munafuki dama duk inda yake jin kunya, duk yanda kakai ga k'ulla kuttun sharri watan watarana saikaga k'arshenka, a duniya ne kokuwa a lahira, babu abinda ke dawwama sai ALLAH, Idan khairan ka shuka lallai saika girba khairan, idan kuma sharranne shima saika girbe abinka, duk danne Gaskiya da k'arya zatai wlhy watan watarana sai gaskiya tadawo sama k'arya ta koma k'asanta, kwanaki 99 ne suke zama Na masheranci, 1 tak kuma suzama namai gaskiya da k'yak'yk'yawar zuciya, d'ayarnan kuma saikaga yazo maka da nasarorin daka rasa shekaru aru-aru, duk nisan jifa k'asa zai fad'o, gashi dai yau su Harun sunzama a k'asa, k'asanma cikin matuk'ar k'ask'anci, musamman ma iyayensu._*
_Ya rabbi ka tsaremu ka tsare mana zukatanmu, ka hanamu cutar da wani koda da fatar bakice, ko'a social media bana fatan kwana da hak'in wani ko hassadar wani, idan nabar duniya wace amsa zanbama ubangiji akan d'aukar zunibin wandama banta6a ganiba a zahiri😭, ya ALLAH ka gafartamana muda iyayenmu da dukkan musulmai baki d'aya, ALLAH ka rabamu dacin hak'k'in kowa koda kwayar zarrane😭😭👏🏻._
_Kumuje zuwa asibiti, danjin wane hali Munaya take ciki itada Nuren kuma?.😔_
*_Nagode sosai da addu'oinku gareni, da mahaifina, ALLAH ya bada ladan zuminci Yakuma kar6a mana baki d'aya, bansan yazan nuna godiyata ga masoyanaba, saidai nace kuma ALLAH ya biya muku buk'atunku, kaini har mak'iyinama ALLAH ya biya masa buk'atarsa ta alkairi, dan saida mak'iyi duniya ke dad'in zama🤸🏻♀🤸🏻♀, idan babusu tamkar miyace lami babu gishiri da magi🤨😝😂.🤸🏻♀🤸🏻♀
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*
*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
________________________
*_K'atotuwar gaisuwa a gareku my sweet friends_*
_Shamsiyya Yahaya D/Z, Farida Muh'd gadanya (y'ar farida😝), Umma Yahaya /D/Z, Sadiya Abdullahi S.A, Hadiza 'Dayyabu Fama, Bahijja Musa Tyw, Hadiza yakubu Tyw, Fatima 'Dayyabu Fama, Hadiza isyaku Gurun, Hadiza Umar fama, Ummi Sani Tyw, Fa'iza Zakari Tyw, Sadiya Sulaiman SS, Hauwa'u Muhammad Nsw, Nafisa Ibrahim G/mutun 1 (I miss you y'ar gidan baban😅) Rabi'a Lawan Tyw (ho y'ar kwana🤣) Ruk'ayya Muhammad Tyw, Zainab Ado Tyw, Zakiyya Liti Tyw, Sadiya Lawan Fama, Bariya Salisu yashe, Umayya Yusuf R/gado, Zahariyya idris R/gado, Naja'atu Rabi'u R/gado, Zuwaira Abdullahi k/giwa, Nafisa kabir Tuge, Shamsiyya Kabeer Tuge, Zainab Adam Bichi, Amina Rabi'u N/iya, Ummi k/giwa, Maryam Tasi'u Tyw (ALLAH ya gafarta miki, ya raya abinda kika bari😭)._
*Aradun ALLAH yawane daku, wasuma sunansu ya 6acemin😔, I miss you all. Kai duk wadda ma yay GGASS D/ZABUWA ina mik'o gaisuwar fatan alkairi a gareshi, Musamman ma y'an 2010 Graduation boko and Arabic, Alkairin ALLAH yakai gareku baki d'aya. Bilkisa Ibarheem Musa (Bil-Gur) kai malam basheer lamba ya iya sa suna🤣, Na gaisheku irin trillions d'inan wlhy, nasan kunata missing tuwon Malam kabiru da koko mai saka barci, ga fatan wake mai kwari (nama a wancan lokacin🤣😜) Yaya kwad'on tuwo da shayi mai kauri🤸🏻♀, kai duniya, komai Na rayuwa labari, INA missing d'an sirri d'ebo ruwa wlhy😔😂.*
_________________________
*_BOOK 3_* 👉🏻2⃣0⃣
.................Galadima ganima yake kamar Sarkin mota baya Sauri, amma baiyi maganaba, zuciyarsa tamafi motar gudu, dan bugawa take da sauri-sauri tamkar zata fito.
Suna isowa bai saurari an bud'e masaba ya bud'e da kansa yay cikin asibitin, dayake k'aramin asibitin ne, na kud'i su Ahmad suka kaisu, da sauri Nurses d'in dake reception suka masa sannu, tare da gaisheshi, dan 6atancin da aka musu Shida sh Munaya a wancan lokacin yakuma sakawa wad'anda basu sanshiba ma suka sanshi, ga kuma abinda ya faru a kwanakinnan.
Uffan baice da suba yay gaba abinshi, cikin takunnan nasa Na k'asaita da izza, Wanda a yanzu yak'ara armashi da 6acin rai.
Su Ahmad da suka hango tahowarsa duk suka mik'e a tare suma suka nufosa, kallon mamaki yake binsu dashi, suma duksun lura da hakan.
Gebiral yace, “Uncle!”.
Kallonsa Galadima yayi idonsa sakaye cikin eyeglasses daya 6oye jajayen idonsa, kafin wani ya sake rmagana a cikinsu doctor ya iso wajen, duk hankalin su suka maida ga doctor d'in suna tambayar ya jikin Aunty?.
Doctor yace, “ku kwantar da hankalinku, insha ALLAH komai zai zama normal, Ranka ya dad'e barka da zuwa”.
Hannu kawai Galadima ya iya d'aga masa, a lokacinne suma su Abba Hayatudden suka k'araso wajen.
A hankali Galadima ya bud'e baki yace, “Ina matata da d'an uwana?”.
Cikin girmamawa Doctor yace, “Ranka ya dad'e inason magana dakai idan babu damuwa”.
Kamar Galadima bazaiyi maganaba saikuma ya gyara tsayuwa yana fad'in “Inason ganinsu tukunna”.
Doctor yay jimm baice komaiba.
Hakanne ya d'arsa tashin hankali a zukatan kowa Na wajen, Galadima ya yunk'uro zaiyi magana doctor yay saurin taresa ta hanyar fad'in “Amma ranka ya dad'e namijin kawai, dan gaskiya ita ba'ason ayi wani kwakwkwaran motsi a kusa da itane”.
Kowa Na wajen ajiyar zuciya ya sauke, danjin sunada rai, Galadima daya kasa koda motsi doctor ya kuma kalla, zaiyi magana ya d'aga masa hannu alamar baison jin komai.
Abba Hayatudden da Baffi da sukasan halinsa idan yana cikin damuwa suka kalli doctor, baffi yace, “doctor yakamata ko shi kad'aine ya ganta, mu saimu duba Nuridden d'in”.
A sanyaye doctor ya gyad'a kai, dan inda sonsamune babu mai shigar.
Nurse ya had'a su da ita takaisu inda Nuren yake, amma kar ayi hayaniyar dazai farka, dan ana buk'atar yasamu barci sosai.
Doctor kuma yayma Galadima jagora da kansa, amma a k'ofar d'akin suka cire takalmansu, dagasu sai sock's d'in k'afarsu suka shiga.
'Dakine madaidaicine da gad'o d'aya, asibitin sunada Kayan aiki babu laifi, tamkar an zarema Galadima lakar jiki haka yake takawa cikin sand'a, doctor ya nuna masa kujera guda d'aya dake kusa da gadon, idonsa a kanta tunda suka shigo, harya zauba yakasa janyewa, tana kwance sam6al a gadon tamkar wata gawa, kanta nad'e da bandeji alamar taji ciwo akan, dan har fuskarta tanuna saboda kumburi da tayi, alik'a mata oxygen a hanci Wanda da alamar shike taimakawa numfaahinta fita, ya maida kallonsa ga damtsen hannunta da shima yake anad'e, sannan kuma tafin hannunta ma haka, wasu hawaye masu zafi suka gangaro tacikin eyeglasses d'in idonsa daya hana ganin tahowarsu tun daga cikin idon.
Ya kalli doctor da shima yake tsaye kansa duk'e a k'asa alamun damuwa, baice komaiba ya mik'e ya fito abinsa, doctor ya biyoshi a baya shima da hanzari.
Da hannu yamasa alamar ya kaisa inda Nuren yake.
Nanma shine yamasa jagora, duk inda suka gitta idanun mutane akansa, oho baimasan sunayiba, abinda ya dameshi shine gabansa.
Su Abba Hayatudden suna d'akin har yanzu, shigowarsu Galadima ya sakasu juyowa suna kallonsa gaba d'aya, ya k'araso gaban gadon idonsa akan Nuren dake barci shima, saidai shi babu bandeji ko d'aya a jikinsa, dan baiji rauniba, dukansa da sukayi a kai ne ya sakashi suma, anama zuwa asibitin babu dad'ewa ya farfad'o, shine sukai masa allurar barci da saka masa k'arin ruwa danya huta, sanda zai farka ya farka da k'arfi a jikinsa..
Galadima ya durk'usa a gaban gadon ya kamo hannun Nuren cikin nasa, yana k'aunar Nuren sosai har cikin ransa, danshi mutumne simple, idan yamaka wani abun bazaka ta6a cewa shi jinin sarauta baneba, ko kad'an bashida damuwa a rayuwarsa, tunba yanzuba Nuren yake bama rayuwarsa gudunmawa, baita6a k'osawa ko gundura da halinsaba, balle yace masa bazaiyiba, saidai inhar abin baida tsarine zai bashi shawaran a canja kokuma ayi haka ko haka..........
Wayarsa datai ring ce ta katse tunaninsa, yad'an karkata yana cirota a aljihun wandon yadinsa, ring d'in daya sakama papi shi kad'aine ya sakashi fahimtar waye, ya mik'e daga gaban gadon yana picking call d'in, saida ya fice a d'akin gaba d'aya sannan ya amsa sallamar da papi yamasa cikeda girmamawa da tsantsar damuwa.
Daga can ajiyar zuciya papi yayi, dan baiyi zaton samun Galadima cikin k'oshin lafiya hakaba, cikin tausasa Murya papi yace, “Muhammad kana inane?”.
Shiru galadima yayi, kamar bazai iya maganaba, saikuma ya bud'e baki da k'yar yace, “papi asibiti”.
“Asibiti kuma? Wanene babu lafiya?”.
Kasa danne kukan daya taho masa yayi, ya fice daga cikin asibitin da sauri, mota ya bud'e ya shiga, ya kife kansa a sitiyari ya fashema papi da kuka mai tsima rai da 6argon jiki, gaba d'aya jikin papi yay sanyi lakwas, saima ya kasa magana shima, yay shiru kawai yana sauraren jarumin jikansa mai yawan hak'uri da juriya akan abu, saida yay kusan mintuna biyu yanayi, papi ya tabbatar nauyin da zuciyar galadima tayi ta ragu sai yay gyaran murya, cikin tausasa harshe yace, “Muhammad Sameer mike faruwane? Kokuwa kukan farin cikin cikar burine?”.
Da k'yar Galadima ya iya bud'e baki yace, “papi yanzunan duk abinda suka aikata a gareni tsawon shekaru bai ishesuba? Saisunyi yunk'urin kashemin d'an uwana da matata? Papi minayi musu da zaifi haka? Miye laifin mahaifina danyak'i goyama k'arya da cin amana baya? Miye laifinsa danya zama shugaba? Bayan hakan ba shirinsa bane tsarin ALLAH ne? Miyasa suka manta babu abinda ke dawwama sai ALLAH, papi inhar matata ko d'an uwana suka rasa ransu wlhy bazan hak'uraba, saina kashesu da hannuna nima s........”
Dakatar dashi papi yay ta hanyar kiran sunansa.
Galadima ya amsa masa da k'yar.
“Kayi hak'uri Muhammad kaji, ALLAH yana tare da masu hak'uri, Hayatudden ya sanarmin komai, ALLAH yabasu lafiya, ba shari'ar duniya bace kawai shari'a, akwai babba wadda babban alk'ali zaima kowa, koba komai ALLAH ya kunyatasu tun a duniya, kowa yasan misuka aikata, kuma ka dak'ilesu suda masu burin aikata irin nasu, ka ringa tunawa akwai tonon asirin dayafi wannan, harma abinda yafi wannan da suka aikata akwai babbar kotu mai cikeda d'unbin jama'a da babban alk'ali a gaba, banason kabar wannan abin yayma zuciyarka tasiri haryakai ga kadaka k'asa, sannan karna kumajin kayi kuka, ka kwantar da hankalinka muci gaba da musu addu'a, insha ALLAH gobe zan shigo garin”.
Gyad'a kai Galadima yayi tamkar yana gabansa, papi yakuma kwantar masa da hankali da nasiha mai ratsa jiki, saida ya tabbatar hankalinsa ya kwanta sannan ya barsa....
Ya jingina da kujerar yanamai lumshe idanu, wata nutsuwa ta musamman Na ratsa jinin jikinsa da zuciyarsa, knocking glass d'in da akayi ya sakashi bud'e idanu a hankali, ganin sarkin motane saiya sauke glass d'in k'asa, cikin girmamawa sarkin mota ya mik'o masa gorar ruwa.
Bai musaba ya kar6a yana gyad'a masa kai alamar ya gode.
Sosai yasha ruwan kuwa, wata nutsuwa takuma saukar masa, ya kuma d'aukar kamar 5minutes ya fito daga motar, ya koma cikin asibitin, yanson ganawa da doctor d'in, idan yaji bai gamsu da aikinsaba dolene yasan mai yuwuwa.
Yana shigowa su Ahmad suka k'araso gareshi suna gaidashi da jajanta masa.
Cikin k'arfin hali yace, “baku tafi gida bane?”.
Sarkin mota dake tsaye kusa dasu yace, “Ranka ya dad'e ai Ahmad shine ya taimakeni nakawo camera d'in kotu d'azun”.
Da mamaki Galadima ya kalli Ahmad yana nunashi da d'an yatsa alamar kaid'in?.
Murmushi Ahmad yayi yana gyara tsayuwa. yace, “Uncle bayan fitowa daga kotune za'a hutunnan sai naji wani yaron su Abbana yana waya akan atare su Aunty a kar6a Camera d'in, dan basa buk'atar ta k'araso Court d'in, to hakan danaji shine Na k'arasa garesa Na bigi cikinsa akan zancen”.
“nake cemasa zamuje ni da su Ahakam muma a kwato Camera d'in damu, so hakan dayaji saiya d'auka da gaske tare nake dasu, shine yabani key d'in mashin. Ina ajiye driver d'inka, sai mukazo asibiti ni da Yassar muka sanarma da Uncle d'ina, shine ya bimu da Ambulance har wajen da abun ya faru muka d'akkosu”.
Galadima ya kamo hannun Ahmad ya rungumesa, yayma su Yassar dake kallonsu alamar suma suzo, cike da farin ciki suma duk sukazo jikinsa.
__________________________
Hankalin mai martaba a matuk'ar tashe yake, jin wai dan kawai yayi mulki wasu suka bada gudunmawa domin durk'usar da d'an uwansa, “hazbinallahu wa ni'imal wakil” wannan wace iriyar masiface hakan?.
Sai safa da marwa yakeyi a bedroom d'insa, idanunsa Na kwarar da hawayen tausayin d'an uwansa da Galadima, ALLAH Sarki mahaifiyarsa, yadad'e yana zarginta akan ciwon d'an uwansa, Ashe babu hannunta a ciki, son zuciyar mahaifinta ne, Wanda a yanzu haka tsufa ya kamashi sosai. Waya ya d'auka ya kira Abba hayatuddeen danyaji wane hali d'an d'an uwansa yake cikine? Dan yayi tsumayen shigowarsu masarautar amma yaji shiru.
Bugu biyu Abba Hayatudden ya d'aga. Mai martaba ya tambayeshi suna inane?.
Abba hayatudden ya amsa masa da vewar gasu a cikin asibiti, Dan mutanen su Alhaji Mansur sun saka an tare matar galadima a hanya itada Nuridden yayin kawo Camera Court.
Kasa magana mai martaba yayi, saboda jin kuma wani sabon zaluncin, Wanda suka aikata baya baima ishesuba kenan.
Abba Hayatudden ma bai kuma cewa komaiba saboda yasan ran yayan nasa ya 6aci.
Mama Fulani kanta yau cikin damuwa take, bata ta6a tunanin mahaifinta zai iya aikata hakanba, dukda tsantsar son datake da burin y'ay'anta suyi mulki bazataso duk'usar da Saifudden akan hakanba, shekaru 26 bawan ALLAH Na kwance yana jiyya tamkar gawa, banbancinsa da gawar fitar numfashi, wannan wane irin son zuciyane su jinin sarauta sukeyi? Shikenan saboda sarauta sai aita halaka juna? “Ni Marawuyya wannan wane irin burine mai cutar da imani.......”
Lallai zato zunubine koda ya zama gaskiya😢, kiyi hak'uri mama Fulani munata zarginki Ashe ba haka bane🤔🤦🏻♀.
.............................★
A gidansu Munaya ma hankalinsu a matuk'ar tashe yake, gasu Abdurraheem nata kuka, dan tunda Munaya tabar gidan suke kuka, kukansu ya tada hankalin Munubiya dasu Inna sosai, lokacin da aka harbi Munaya bak'aramar fad'uwa gaban Munubiya tayiba, ta mik'e a zabure tana dafe k'irji, number Munaya tashiga nema, dan taji a jikinta wani mummunan abu ya faru da y'ar uwarta.
Lokacin da labarin abinda ya faru da Munayar ya iso garesu mafi yawan jama'ar gidan saida suka koka, Dady kuma ya hana kowa zuwa asibitin, saisu mazan kawai sukai shirin zuwa, gashi basusan wane asibitin bane.
__________________________
Iyalan su waziri hankalinsu a matuk'ar tashe yake, hakama su Alhaji Sageer, ga duniya tanata ALLAH wadai dasu, gaba d'aya yau kowacce kafar yad'a labarai da social media maganar kenan, su kansu sauran manyan kowa ya shiga hankalinsa, dan lamarin yayi matuk'ar girgozasu, suna yabama basirar Galadima matuk'a, gashi yabi ta hanyar da babu Wanda yata6a zaton zata 6ille masa yayi nasara, inhar za'a iya samun irinsa a yau, to lallai wataran za'a samo Wanda ya fisa ma.
....................★
Yanda masarautar su Galadima take a harmutse gameda wannan lamari haka tasu papi ma ta gama harmutsewa, dan lamarin ba'a cewa komai, cin amanar da waziransu sukayi yayi matuk'ar girgiza masarautun, bakajin komai sai gutsiri tsomar bayi da dogarai, harma da manyan gidan ba'a barsu a bayaba.
Tashin hankalin da papi da inno suke ciki ba'a magana, ga Sauban ya tasasu gaba yanata kukan son zuwa yaga halin da Munaya da Nuren suke ciki, harma da yayansa.
Dukda an hana fad'ama Su Momma amma saida labarin yakai musu, aranar aka nemama Aunty Mimi ticket d'in tahowa Nigeria, Samha nata kuka itada Khaleel zasu biyota, amma bata sauraresuba, dan hankalinta a matuk'ar tashe yake.
............................★
Doctor da kansa ya fito yayma Galadima iso cikin office nashi, bayan sun zauna doctor ya kalli Galadima cikin alamun damuwa, yace, “ranka ya dad'e da farko dai ina mai baka hak'uri akan zaluncinsu mijin y'ar uwata, ALLAH yay maka babban samako da sayya agaresu”.
Murmuahi kawai Galadima yayi amma baice komaiba.
Doctor ya kuma gyara zama yana fad'in “Alhmdllh jikin namijin babu wata babbar matsala, yanzuma mun saka masa alurar barcine cikin ruwan danya huta sosai yasamu nutsuwa, daya farka Normal zaku gansa. Ita kuma akwai harbi da akai mata a hannu, amma Alhadullh mun samu nasarar cire harsashin, tafin hannunta kuma shima anji mata ciwo, dan yatsunta Na tsakkiyama duk sun samu karaya, amma shima an gyarashi, maganar gaskiya ranka ya dad'e bazan 6oye makaba, tasamu buguwa akai, dan ALLAH ne ya tak'aita batasamu wata babbar Matsala a brain ba, saidai ahalin yanzu dukkan wani motsi mai k'arar sauti bama buk'atarsa kusa da ita, insha ALLAH inhar za'a kiyaye cikin kwanaki kad'an komai zai iya dai-daita, takuma dawo normal kamarma komai bai faruba, zamu bata dukkan kulawar daya dace da izinin Ubangiji. daganan har kwanaki uku zuwa hud'u zata kasance a halin barci, dan hakanne kawai zai girmama nutsuwar da muke buk'atar ta samu d'in, kai kad'aine kuma zaka ringa shiga d'akin”.
Galadima ya lumshe idonsa tausayin Munaya da yaransu Na kuma mamaye jinin jikinsa da kowanne ga6a, da k'yar ya iya bud'e baki yace, “Doctor! Kana ganin zaku bata dukkan kulawa?. Sannan tanada yara jinjirai, yaya kenan za'ayi?”.
Insha ALLAH ALLAH ranka ya dad'e, dan munada kayan aiki a asibitin mu, dakuma kwararrun likitocin da zasu iya aiki a kowacce k'asa, maganar yara inaga inhar akwai mai kulawa dasu acigaba da basu madara har ALLAH yasa ta farfad'o, saboda mu yanzu matsalarmu kawai shine motsin dazai iya farkar da ita ko wanda zaiyi tasiri cikin brain nata”.
Gyad'a kai kawai Galadima yayi, yabama doctor hannu sukayi musabaha, daganan ya fito.
Kuma ficewa yayi daga cikin asibitin, Sarkin mota yay saurin biyo bayansa, da hannu yamasa alamar yashiga mota suje.
Dukda sarkin mota baisan inda suka nufaba haka ya amsa cikin girmamawa.
Saida suka fara tafiya ya sanar masa inda zasuje.
yana nufi gidansu Munaya dan yaga halin da yaransa suke ciki.
Munubiya da kanta ta fito masa dasu itada Ayusher, tausayin su ya kamashi matuk'a, musamman ma Munubiya, dan tayi wujiga-wujiga.
Cikin k'arfin hali yace, “kiyi hak'uri Sister, muyi musu addu'a ita kad'ai suke buk'ata a wajenmu, yanzu yaza'ayi dasu Amaturrahman? Dan nakula kamarma yunwa sukeji?”. ‘yay maganar yana kallon yaran da sukayi barcin wahala bayan sun gama shan kuka’.
Share hawaye Munubiya tayi. tace, “Yakamata a nemo musu madara, idan kuma Na shayar dasu to shikenan”.
Galadima ya jinjina kansa yana fad'in “Bamusan hikimar da ALLAH ya 6oyeba a gaba, karmuyi ganganci, bara kawai a nemo madarar, dan dolene su kwana anan, ita ba'ason mata hayaniya yanzun, maybe ma harnan da wasu kwanaki, saboda ta bugu a kanta, kuskuren kwakwkwaran motsi zai iya shafar brain nata”.
Munubiya takuma fashewa da kukan tausayin y'ar uwarta, hakama Ayusher, shi kansa Galadima dauriya kawai yakeyi, danma ya 6oye idanunsa cikin eyeglasses shiyyasa basa ganin nasa tsantsar damuwar.
Muftahu ya kira ya sanar masa a samoma su Abdurraheem Madarar da zasu ringa sha.
Daga nan gidan yabaro akan cewar Muftahu zai kawo, yakuma rok'esu akan Abdurraheem, dan ba'ason yacika yawan kuka.
A gurguje please😏😜
___________________________
*BAYAN KWANAKI UKU*
A kwanaki ukunnan fad'ar tashin hankalin da bayin ALLAH suke ciki 6ata lokacine, musamman ma Galadima da har wata uwar rama yayi lokaci d'aya, hakama Munubiya da innarsu, Nuren dai ya farka tun washe garin faruwar lamarin, kuma jikinsa Alhmdllh yanata murmurewa, saidai tausayin d'an uwansa daya addabi ransa.
Ko abinci Galadima bayasonci, sai Aunty Mimi ta turkesa tana bashi abaki, shima baifi yay lauma biyarba yace ya k'oshi. tayi-tayi kuma ya kafe, garama idan tea ne, shima sai an had'a da lallashi, babu abinda ke addabar ransa irin damuwar Munaya da yaransa, sukansu duksun rame, danma suna samun tsantsar kulawane ta kowanne fanni.
Papi yazo ya dubasu, hakama su mom da iyayen su Nuren d'in da y'an uwansa, mai martaba ma da daddare yazo cikin 6adda kama ya dubasu.
Mama Fulani ma kullum saitazo, a matan Sarki gimbiya Zulfah Ce kawai batazoba, Dan kunyama ta hanata walwala gaba d'aya a masarautar, Mai martaba kuwa ya hanata hanyar ganinsa gaba d'aya itada y'ay'anta, sai matawalle kawai daya nuna damuwa akan abinda kakansu da mahaifiyarsu suka bada gudunmawa wajen aikatawa wan mahaifinsa, sanan yay ALLAH wadai akan son zuciyarsu, koda yaushe yana tare da Galadima da Muftahu a asibitin, da wata buk'ata ta taso kafin Galadima yayi shi yayita.
A koda yaushe Momma cikin kira take taji yaya jikinsu Munaya, koda wasa ba'a sanarma Abie komaiba, Dan ana ganin cigaba da haske game da jikinsa sosai, ba'a fatan wani abinda zai maido da hannun agogo baya game da ciwon nasa.
Addu'oi kam sosai aka duk'ufa yinsu game da Munaya, wadda har yanzu Galadima ne kawai keda alhakin shiga ya dubata, shima sau d'aya a rana kawai, yau dai duk ake saka ran farkowarta, Dan an dakata damata dukkan wata allura dake sakata barci, saidai kuma har dare babu wani bayani.
Zasu tayar da hankalinsu doctor yace suyi hak'uri, maybe zuwa dare ko safiyar gobe ta farka d'in, danba a sume takeba, barcine kawai da sune suka sakata ta hanyar mata allurar.
Badan hankalin nasu ya kwantaba sukai shirun, har lokacin barinsu asibitin yayi babu wani bayani game da farkawar tata.
*Washe gari*.
Duk dai yanda akaso farkawar Munaya a ranar sai a washe garine ALLAH ya amince da hakan, Alhmdllh anci nasarar farkawar tata yanda ake buk'ata, saidai ciwukan jikinta a halin yanzu.
Saida doctors suka gama dukkan kai kawonsu naganin komai ya ida daidaita sannan aka bama Galadima damar shiga.
Tamkar mai sand'a haka ya shiga d'akin, tana kwance amma idonta biyu, sai dai a lumshe suke, an kuma cire mata bandejin da aka zagaye mata fuska, sai kad'an aka bari inda ciwon yake.
Durk'usawa yay a gaban gadon, ya kamo hannunta Na haggu dakeda lafiya ya saka nashi ciki, a hankali ta bud'e idanunta saboda jin tattausan hannunsa cikin nata, ga k'amshin turarensa daya mamaye d'akin Wanda ya tabbatar mata da shid'inne, tana shak'a a hankali.
Idonta ta saka cikin nasa, kowanne yakasa koda kwakwkwaran motsi tsawon mintuna 2, a hankali Galadima ya bud'e baki tamkar mai rad'a ko gudun wani ya jisu yace, “Munaayaa I love you, I really love you, I love you more and more my Heartbeat..”
Lumshe idanu Munaya tayi, wasu hawaye suka gangaro daga cikin idanu zuwa gefen kunnuwanta, zuciyarta sai wani irin bugawa take da sauri-sauri, ta kuma damk'e hannunsa cikin nata tana maijin tsigar jikinta Na tashi, jininta sai yamutsawa yake a kowanne 6angare. Kuma bud'e idon tayi a kansa, suka sakarma juna lallausan murmushi ga hawaye Na zuba a idonta har yanzu, shima kwalla sun tarar masa a cikin ido sun saka idon wani k'yalli Na musamman daya kuma sakama munaya wata kasala da tsantsar k'aunarsa, ya lumshe idanunsa alamar tabbatar da abinda ya fad'a mata har cikin ransane ba iya fatar bakiba.
Itama hawayen ta kuma matsowa, ta bud'e baki da k'yar tana cigaba da kwararo hawaye. Tace, “i love you too yalla6ai, I love you so much...”. ‘takai k'arshen maganar wani kukan Na kwace mata.
Hannunta dake rik'e cikin nasa ya sumbata yanamai jin farin ciki, yace, “ki kasance dani Munaya, ki kasance dani har k'arshen rayuwata, ke Katanga tace, haskena ce, farinciki nace, duniyata ce, duk duniya kece mace ta farko bayan mahaifiyata da y'ar uwata danakema so Na musamman, please karki barni uwar y'ay'ana, karki gujeni komai rintsi, nima namiki alk'awarin kasantuwar mu tare har k'arshen numfashi, ki rayu dani, ki mutu dani bugun zuciyata, kamar yanda nima burina kenan a gareki tsawon lokaci”.
Lallai yau daba'a halin ciwo takeba har rawa sai tayi, Wanda bata ta6a tsammani ko tunanin zaisotaba shine yake furta wad'annan dad'ad'an kalamin agareta, shine yake rok'onta ta kasance dashi har k'arshen rayuwarsa?, shine yake kiranta katangarsa?, harskensa, bugun zuciyarsa? Koda a yau tabar duniya ta ribantu da nasarorin masu yawan da wahalar k'ididdiga wajen lissafi.
Galadima dake share mata hawaye da hannayensa ya duk'a ya manna mata kiss a goshi da saman la66a.
Ta kuma bud'e idonta da suke jajur akansa, murmushi suka kuma sakarma juna, ya girgiza mata kansa alamar tabar kukan, idanunta ta lumshe alamar amsawa.
Shikam ya tsura mata idanu ko k'yaftawa bayayi, y'ar ramar da tayi saiya k'ara mata k'yau da k'uruciya, ya shafa k'ananun kitson dake kanta ta kuma bud'e ido tana kallonsa.
Cikin d'age gira d'aya yace, “baki tambayi ina yaraba?”.
Lallausan murmushi ta kuma sakar masa, ta kwanto hannunsa dake sark'e da nata saitin bakinta ta sumbata, sannan ta d'orasa a saman k'irjinta.
Tausayinta ya kamashi sosai, domin jikinta akwai zafi har yanzu, ga abincinsu sunyi matuk'ar cika, Wanda zazza6in nata yanada nasaba da rashinsu gareta, dukda akwai Na zafin ciwo.
Hakan da tayi shima saiya fahimci mitake nufi, kuma duk'owa yay ya sumbaci goshinta, zaiyi magana doctor ya shigo.
Shiru Galadima yay ya juyo yana kallonsa, itama Munaya daga kwancen take kallon doctor ta k'asan ido.
Doctor dake gulma da zuciyarsa yana fad'in lallai ya yarda, duk sarautar Sarki a gaban matarsa bawane, matarce ke zama sarauniya..... (Ga naku Matan kwarai sarakin duniya👍🏻👌🏻😜)
Galadima ya katse tunaninsa ta hanyar buga yatsunsa biyu suka bada sautin d'as-d'as.
Doctor ya dawo hayyacinsa a kunyace. Yace, “sorry ranka ya dad'e, dama Nurse zata goge mata jikine da kuma gasa mata, Dan tasamu sauk'in nauyin da yay mata”.
Murmusawa Galadima yay, ya zare hannunsa daga cikin Na Munaya yana mik'ewa tsaye, hannayensa ya hard'e a k'irji yana kallon doctor da fad'in “Doctor da raina zan bar wasu ganarmin sirrina? Ku kawo kayan buk'ata kawai”.
Doctor daya fahimci Inda zancen Galadima ya nufa saiya murmusa yana cewa “Afuwan ranka ya dad'e”.
Hannu kawai Galadima ya d'aga masa, ya juyo suka had'a ido da Munaya ya d'aga mata gira da cizar lips d'insa.
Baki ta tunzuro masa tana yamutse fuska.
Ya d'aga kafad'a da ta6e baki alamar bashida matsala🤷🏿♂🤣.
Nurses biyu suka shigo da dukkan abinda ake buk'ata, Galadima Na tsaye ko kallon inda suke baiyiba, idonsa nakan matarsa k'yam, sukam sai satar kallonsa sukeyi, suka ajiye suna fad'in “Gashi Ranka ya dad'e”.
hannu kawai ya d'aga musu amma ko tari baiyiba.
Fita saukai cikin takaici, dan sunso yayi musu magana koda sau d'aya ne.
Takawa yay a hankali jikin k'ofar ya Mirza key, sannan ya dawo yana cire link d'in hannun rigar farar shaddarsa da tattarewa zuwa sama.
Suka had'a ido da Munaya tai azamar janyewa cike da kunya.
Murmushin gefen baki yayi yana zama bakin gadon kusa da k'ugumta.
Bottoms d'in jikin green d'in rigar asibitin yafara cirewa a hankali, itadai kunya ta hanata bud'e ido, gashi ya tsareta da idanu, Dan tanajin yanda idanunsa ke yawo cikin jininta, salon daya koma wajen cire bottoms d'in ya sakata dafe hannunsa da hannun haggunta, ta bud'e ido tana kwa6e fuska.
Gira ya d'aga mata, da wani mata salo da kwayar ido.
Babu shiri ta maida idonta ta rufe ruf, tsigar jikinta Na tashi.
A haka dai aka gama cire rigar, yaja bedsheet d'in da ake lullu6a mata a k'afafu ya rufa mata a jiki, sannan ya kuma gyara hannun rigarsa yana tsoma madaidaicin towel d'in cikin ruwan d'umin dake a boket, ya matsa dukda akwai d'an zafi ruwan haka yafara danna mata jiki dashi.
Tanajin zafi, amma kuma tanajin dad'in d'umin ruwan sosai, k'in yarda tayi su had'a ido har aka gama, ya d'auki wani d'an kwalba da mai ke ciki tamkar zaitun, karantawa yay yaga amfaninsa sannan ya zuba a tafin hannunsa yana murzawa, kumajin tattausan hannunsa daya had'u da sul6in mai tayi a k'afafunta, tad'an kuma bud'e ido tana kallonsa. Ganin ba ita yake kalloba saita shagala da kallonsa, babban mutum mai daraja jinin mulki yau shine ke mata hidima irin haka, itako badan kar ace tayi alfahari ba da cika baki da yawa da tace ta more fiye da kowacce mace (🙄nidai fa bandani, reader's Ku kun yarda harda Ku🤷🏻♀)?.
Sosai tafara jin dad'in tausar, Dan da salon nutsuwa yake mata, tuni tafara lumshe idanu, hardai barcin yaci galaba a kanta. Sai dai saukar numfashinta yaji a hankali.
Ya kalleta yana murmushi da lumshe idanu, bai bartaba saida ya tabbatar barcin yayi nisa, cikin dabara ya canja mata rigar da suka sakko a kayan domin canji. Ya duk'o ya sumbaci goshinta da bakinta yanajan bedsheets d'in sosai ya kuma lullu6a mata.
Kayan ya maida gefe, ya koma saman kujerar dake gefem gadon ya zauna ya zuba mata idanu, kai kace yaune ya fara ganinta, ya dad'e a haka kafin ya d'auka wayarsa yana dannawa.
A haka Nurses d'in suka masa Knocking, izinin shigowa yabasu, amma sai suka murd'a k'ofar a rufe.
K'aramin tsaki yaja yana muk'ewa, shi yama manta ya rufe. Bud'ewa yay yadawo ya zauna yana d'ora k'afa d'aga kan d'aya da kuma d'aure fuska.
Tuni Nurses d'in suka shiga hankalinsu, cikin risinawa d'aya tamasa bayanin zasu canjama Munaya bandejin jikinta ne.
Batareda ya kallesuba yace, “kuyi a hankali, Dan barci takeyi, idan kuma kunsan zata iya farkawa kubarsa saita tashi ”.
Kallon juna suka, kowacce tad'an ta6e baki, d'ayar tace, “insha ALLAHU bazata tashiba ranka ya dad'e”.
Nanma Kansa kawai ya jinjina musu yacigaba da latsa wayarsa.
Haka sukai wannan aiki a gabansa Dan yak'i fita, data motsa ya zuba musu uwar harara mai rikita hanjin ciki.
Dolensu suka bita a sannu har suka samu kammalawa lafiya, kowacce ta fice a tsorace.............✍🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*
*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BOOK 3_* 👉🏻2⃣1⃣
.................Kusan mintuna 7 da fitar Nurses d'in doctor yay Knocking, Galadima ya amsa ba tare da ya ajiye wayarba, doctor ya shigo abinsa, Nurse d'aya da sukai akin d'azun Na biye dashi.
Galadima ya d'ago yana kallonsu fuska babu walwala, Dan shifa yafara gajiya da wannan shigi da ficin, amma baice komaiba.
Doctor daya d'an tsargu yace, “Afuwan ranka ya dad'e, dama ina ganin yakamata tafara cin abincine, Dan ruwan da muke saka matane dama yake taimaka mata, to yanzu kuma zata fara shan magunguna insha ALLAH”.
Galadima yad'an sauke numfashi yana fad'in “ok, to amma yaranfa? za'a iya kawosu yanzu?”.
“eh to, sunkai nawa?”.
Yatsu uku Galadima ya d'agama doctor, dukda yayi mamaki saiya danne abinsa, musamman dayaga munayar y'ar k'arama da ita. yace, “Ranka ya dad'e dadai and'an k'ara mana lokaci koda kwana biyune, har yanzu zancen danake maka ba'ason abinda zai cika mata hayaniya a kai”.
Jinjina kai Galadima yayi kawai, alamar gamsuwa.
Daganan Doctor yay d'an dube-dubensa ya bama Galadima Drugs d'in Munayar akan Nurse zata dinga zuwa tana bata kullum.
Doctor Na fita shima ya ajiye wayarsa kusa da ita ya fito, d'akin da Nuren yake ya shiga, yana zaune Aunty Mimi Na bashi abinci a baki, Galadima yad'an hararesa yana fad'in “k'aton banza kacika shagwa6a”.
“Uhmyim” Nuren ya fad'a yana ta6e baki da rama Harar da Galadima ya masa.
Ita dai aunty Mimi murmushi kawai take da wannan rigima tasu dabata k'arewa, dama can inhar Nuren da Galadima Na waje sai kayi dariya, Dan kafin su rabu sai anyi kusan fad'a goma.
Galadima yace, “Ya jikin?”.
“Aini kam Alhmdllh, yanzu kawai maganar gaskiya amin aure, inda Na mutufa shikenan, kukan kwana uku zakuyi a wuce wajen, amma in mat......”
Hannu Galadima yakai zai bige bakinsa, yay saurin duk'ewa, Aunty Mimi ta sanya dariya, Galadima kuwa kwafa yay yana kallon Aunty Mimi, “oh ALLAH, maimakon kimasa fad'a dariyama kike masa? Wannan yaron wlhy fitsararrene, idan kunk'i masa aurenan zai iya zuwa yayi baku saniba ma”.
Nuren ya gyara zama yana hararsa, “Yo angaya maka ni irinkane, soyyaya Na cin zuciyata k'asaita ta hanani fad'e, Malam mufa dama munsan komai, munzuba idone muga yanda wasan zai k'are”.
Murmushin da Galadima bai niyyar yibane ya su6uce masa, ya mik'e da fad'in, “Duk iskancin da kamin ninaso, tunda nine nazo dubaka, idan nakuma zuwa d'akinnan kace ba sunanka Nureddin ba”.
“Ahaf, yo dama sunana Sameer ne?”.
Galadima bai kulashiba, ya kalli aunty Mimi daketa musu dariya, “Auntyna yakamata a sanarma gidansu ta farka, naga har yanzu babu Wanda ya iso”.
Murmushi Aunty Mimi ta masa, ta ajiye plate d'in datake bama Nuren Abinci tana cewa, “babu damuwa, mu barsu har zuwa yammar, tunda kaga har yau basu bada damar a shigaba”.
“Ok, hakan yayi”.
Harzai fice aunty Mimi tai saurin cewa “Abincinfa?”.
Kansa ya girgiza mata yay ficewarsa.
Nuren dake murmushi ya kalli Aunty Mimi yana fad'in “Auntynmu soyayya nacin Guy d'inan yak'i fahimta”.
Dariya tayi “Nuren kenan, ingaya maka sarai yasan yana sonta, shegen son girma da miskilancine kecinsa, amma ai naga alamar yanzu an wuce wajan”.
“A haba? Aunty da gaske?”.
“kwarai ma kuwa Nureddin”.
Hannu yabata suka tafa, yanajin wani sanyi a ransa, da sakama Muftahu albarka a zuciyarsa, danya zama aboki kuma d'an uwa Na k'warai.
Fitowar Galadima yaci karo dasu Yassar, ya fad'ad'a murmushinsa, shima yaran sun shiga ransa sosai, k'arasowa sukai gareshi, cikin girmamawa duk suka gaisheshi, ya amsa da kulawa.
“ku bakwa gajiya da yawo?”.
Soshe-soshen kunya suka farayi, Marcel yace, “ai daga gida muke, munzo muk'ara ganin jikin Aunty da Uncle ne”.
Galadima yad'an murmusa yana tura hannayensa duka a aljihu, cikin d'an lumshe ido yace, “kushiga to kugansa”.
“Uncle! Auntynfa? Ta farka itama?”. ‘Ahakam ne mai maganar’
Galadima ya jinjina kai. Yace, “ta farka Ahakam, amma tana barcine”.
Gaba d'ayansu farin cikine ya bayyana a fuskokinsu, kai kace y'ar uwarsuce ta jini, da wannan farin cikin suka shiga d'akin da Nuren yake, shikuma yakoma inda Munaya take murmushi d'auke a fuskarsa.
Dad'an hanzarinsa ya k'arasa gareta, ganin ta farka, zama yay a kujerar suna kallon juna, murya a sanyaye yace, “Kin tashi?”.
Da idanu ta amsashi.
Ya shafa kanta yana fad'in “Sannu, yanzu ina ke miki ciwo?”.
Fuska ta d'an yatsine, ta nuna masa hannunta da kanta.
Cikin tausayawa Yakuma mata sorry, sannan yace, “mizaki ci?”.
Kanta ta girgiza masa alamar babu komai.
Ya d'an 6ata fuska yana fad'in “Ban yarda ba, kinga kuwa yanda kika rame?”.
Murmusawa tayi, itama ta masa alamar wai ya rame shima.
Baki yad'an ta6e, amma baice komaiba ya d'auka wayarsa dake kusa da ita yay kiran Muftahu akan abinda za'a kawoma Munayar kozata d'anci.
Itadai kallonsa kawai takeyi. Ya yanke wayar yana kallonta shima da d'age mata gira d'aya alamar kallonfa?.
Dukda taji kunya saita yamutse fuska irin miye abin kallon anan.
Galadima yay wani miskilin murmushi cikin murya k'asa-k'asa yace, “Really?”.
Ta lumshe idonta alamun tabbabatarwa.
“zaki maimaitamin idan kin warke yarinya”. Yay maganar da wata siga harda cije lips.
Munaya ta kauda idonta tamkarma bata fahimci ina ya dosa ba.
A ranardai haka kowa ya yini cikin farincikin farfad'owar Munaya, gashi anbarsun sunshi sun gagganta, saidai anata musu gargad'in banda hayaniya, tausayin ta duk ya kamasu. Innaro harda hawayenta, aka saka bakin Zane ana sharewa da jemasu Alhaji balala ALLAH ya isa, harda cewa sai an koma kotu an sake sabuwar shari'a an kar6oma jikarta hak'inta.
Shi Galadima ma abin dariya ya bashi matuk'a, yadai had'iye yana duk'ar da kai baiyiba, wannan tsohuwa akwai abin dariya wlhy.
Munubiya kam rungumeta tayi taita hawaye, itama Munayar nayin nata.
★★★★★★***★★★★★★
Bayan kwana hud'u da farfad'owar Munaya jikinta yayi k'yau Alhmdllh, Dan tana samun kulawa ta kowanne 6angare, ciwukan jikinta ne kawai basu gama warkewaba.
Aunty Mimi da Laraba na a d'akin, Dan kowa ya tafi, suna zaune d'auke da su Abdurraheem da ake kawowa su yini yanzu, sai dare a koma dasu.
Munaya tana zaune ne a gadon datake jiyya an saka mata filo ta jingina, abincin da aka zuba mata taketa faman jujjuya cokali a cikinsa, tasaba kullum Galadima ke bata abincin, gashi yau tun safe da'aka kirashi ya fita bai sake dawowa asibitinba har yanzu, dukta damu, da taji motsin tahowa za'a shigo d'akin saita zata shine, sai anshigo taga bashi bane sai haushi ya kamata, Munubiya data fahimceta tsaf taita gumtse dariya har suka tafi, su Aunty Mimi hankalinsu gaba d'aya yanaga yaran, basusan mitakeyiba.
Turo k'ofar da akayi ya sakasu kallon k'ofar gaba d'aya, dan k'amshin turarensa yafara musu sallama kafin shigowarsa, wayace manne a kunnensa yana magana a hankali, hannunsa d'aya cikin wandon aljihun Ash color d'in shaddarsa daketa maik'o, Munaya daketa sauke k'ananun ajiyar zuciya tunda taji k'amshinsa tad'an saci kallonsa, shima idonsa a kanta, gira ya d'aga mata, tai saurin janye idonta tana tura baki kad'an.
Murmushi yayi ya zauna a bakin gadon kusada k'afafunta yana cigaba da wayarsa, yayinda yakema Amaturrahman da aka kwantar kusada ita wasa, yaran sund'an fara wayo, Dan idanuwa k'yar suyita kalle-kalle, kwanakinnan da suka dawo shan nono sunyi y'an k'u6ul-ku6ul dasu abin sha'awa.
Munaya dai tafara tura abincin da k'yar, sai wani faman had'e rai takeyi, shidai Galadima dariya na cinsa a rai amma baiyiba, saidai ya saci kallonta ya maida idonsa ga Amaturrahman data rik'e d'an yatsansa gam daya saka a d'an hannunta, kaikace tasan minene.
Sudai Su aunty Mimi da laraba suna cigaba da hirarsu, Dan laraba na bata labarin halinda su Abdurrahman suka shiga a kwanakin da Munaya bata farfad'oba ne.
Galadima ya ajiye wayar yana d'aukar Amaturrahman da fad'in, “O my lil princess I miss you”. Ya k'are maganar da sumbatar kumatunta, sannan ya juyo suka gaisa dasu aunty Mimi dake kallonsa shida babyn tashi abin sha'awa.
Cikin tsokana aunty Mimi tace, “Ai dama shirin kiranka nake danna kula my k'anwa bazataci abincin nanba sai kana kusa”.
Galadima ya juya yana kallon Munaya data waro ido tanajan mayafi ta rude fuska Dan kunya, dama aunty Mimi suna kula da ita kenan, itakam taga idi.
Galadima yace, “A lallai Aunty Mimi da gaskiyarki fa, kamarma kuka tayi?”.
“kad'an dai ya rage tayishi my k'ani, tun d'azun ina lura da ita, rabin hankalinta naga k'ofa”.
Laraba da Galadima sukayi dariya, ya kuma kallon Munaya data kasa d'ago kai ta kallesu.
Galadima ya had'iye dariyar dake Neman kufce masa, ya ajiye Amaturrahman d'in yana matsowa kusa da ita, Murya k'asa-k'asa yanda su Aunty Mimi bazasujiba yace, “Any problems my Princess?”.
Munaya ta saci kallon su Aunty mimi, ganin basa ganinta saita tura masa baki kad'an tana matso k'ananun hawaye.
“O my God”. ‘ya fad'a a hankali yana d'ora tattausan hannunsa saman nata, cikin wani salon daya saka tsigar jikinta tashi ya kar6ar spoon d'in. Babu shiri ta sakar masa.
Yakuma k'asa da murya yana d'ebo abincin da fad'in, “nifa kibarmin shagwa6arnan kokuma humm”. ‘ya k'are maganar da ciza lips yana jifanta da wani kallon mai cike da sirrika’.
Waro idanu Munaya tayi tana kallonsa baki bud'e. Abincin ya zuba mata yana kashe mata ido d'aya.
Kunya ta kamata, Dan wlhy Galadima bashida kunya ko kad'an, kad'an daga aikinsa ya aikata duk abinda yazo masa a rai d'in, danta San halin kayanta sarai.
bata k'ara yarda sun had'a idoba har yagama bata abincin, ya d'akko d'an Basket d'in da drugs d'inta ke ciki yana dubawa.
Aunty Mimi data kasa hak'uri ta mik'e tana tawa, “Oh ni Haneefa, dama abinda ya hanaki cin abincin kenan da gaske dai tun d'azu kiketa cuna baki my k'anwa”.
Munaya tai saurin jan d'an gyalen dake yane bisa kanta ta rufe fuska saboda kunya dataji, Aunty Mimi ma akwai iya 6aro zance, kuma ta Fiske abinta.
Laraba tayi y'ar dariya itama tana bin bayan Aunty Mimi suka fice, itakam dai birgeta sukeyi sosai, komai nasu a nutse.
Galadima dake binsu da murmushi ya juyo da kallonsa ga Munaya yana fad'in, “Saiki bud'e fuskar, dama haka kikeso su fita a barki daga ke sai mijinki ko?”.
Babu shiri Munaya ta janye mayafin tana d'an hararsa da kwa6e fuska tamkar zati kuka.
Ya ta6e baki da d'aukar ruwa ya zuba a cup yana mik'a mata, kauda kanta tayi gefe kamar bata ganshiba.
Mik'ewa yay ya koma kusada ita sosai yana sakata jikinsa, “Haba dai yalla6iyan yalla6ai miye na fushin to?”.
Munaya ta ture fuskarsa tana fad'in “Ni babu ruwana dakai, ka koma inda ka fito”.
Yace, “Oh God Babie na sorry kinji, wani babban uzirine ya rik'eni, yanzu dai ga maganin kisha, sai amin hukuncin laifina”.
Munaya ta matso hawaye sannan ta bud'e bakin ya zuba mata maganin ya bata ruwan tashanye, yakuma zuba wani, ahakadai tagama sha.
Dawowa yay tagabanta ya zauna yana murmushi, “Dad'ina dake shagwa6a, amin murmushin mana”.
Kauda kai Munaya tayi gefe murmushi na kufce mata.
Galadima ya dawo da fuskarta suna kallon juna, cikin k'ank'ance idanu yace, “ko kefa sweedy na, kindai hak'ura ko?”.
Kaita jinjina masa tana wani far da ido.
Hannunta mai lafiyar ya sumbata, yace, “Thanks My Queen, Saura wanka ko?”.
Munaya tai k'asa dakai saboda kunya, danta zata ya manta da maganar wankan da Doctor yace tafarayi yau indai zata iya. Murmushi Galadima yayi, dan kunyar tata na sakashi a shauk'i.
Kanta a duk'e tace, “Nidai kabarni zan iyayifa da kaina wlhy”.
Baice uffanba ya mik'e zuwa k'ofar ya saka key, yazo yawuce cikin bayin dake a d'akin. A sace ta bishi da kallo harya shige, ta lumshe idonta wani farinciki nabin sassan jikinta.
tsaf bayin yake, dan kullum cikin gyaranshi ake, hakama kayan ammafani irinsu boket, buta da sauransu komai need yake, ruwa ya saka danya d'anyi zafi dayake akwai wuta, ya fito yabarshi.
Har yanzu idon munaya a rufe suke.
Saukar Numfashin Galadima da k'amshin turarensa kawai taji a kan fuskarta, ta bud'e ido da sauri, Ashe yana gab da ita, motsawar datayi saiyazama kawai fuskarsu ta manne da juna, hakan yabashi damar aikata yanda yaso cikin sauk'i.
Batada za6in daya wuce mik'a masa ragama gaba d'aya, danya cancanci abindama yafi haka a gareta.
Tsawon mintuna biyu ya d'ago suna kallon juna, kasa daurewa Munaya tayi ta rufe idonta, yay murmushi gefen baki yana hura mata iska a saman idon.
Dole na bud'e idona nakuma sakasu cikin nasa, a hankali ya furta “I love you so much my Munaah”.
Murmushi na masa mai kashe ga66an jiki, na matsa kad'an ina bashi Sumba a kumatu, lumshe idonsa yayi yana sauke wani nannauyan numfashi, ya d'ora kaina a k'irjinsa, daddad'an k'amshin turarensa ya shige hancina, nima na lumshe idanu ina shak'a da godema ALLAH. muduka nutsuwa ta musamman ta sauka a zuciyoyinmu. Wayata datai ring ce ya sani d'agowa daga jikinsa na zauna sosai ina kauda fuska saboda kunyarsa.
Ganin Samha Ce na d'aga wayar cikeda farin ciki.
Galadima mik'ewa yay shima ya lek'a ruwan daya saka, ganin yayi zafi saiya kashe ya juye, surkawa yay, saida yaji yayi dai-dai sannan ya fito yana cire bottoms d'in rigar shaddarsa, hankalin Munaya baya garesa, shiyyasa batasan miyakeyiba, sai ji kawai tayi an amshe wayar tareda yin sama da ita. Da farko ma tsorata tayi, zata saka masa ihu yay saurin cemata “Shiiiii!!”.
Ajiyar zuciya na sauke na kallesa, ya kashemin ido d'aya. Murmusawa nayi ina janye idona daga kallonsa, dan naga lamarin nasa na Neman fin k'arfina, koya manta a ina muke oho? harda su cire rigafa.
Nidai wannan wanka anyisane kawai dan banida yanda zanyi, dan dana nema yin gardama saiya had'e fuska yana hararata, dole nabarsa yayi yanda yakeso, ya d'auramin towel ya kamo hannuna muka fito, Muduka Kallon Amaturrahman mukai daketa wutsil-wutsil da k'afafu.
Na zauna a bakin gadon shikuma ya jawo kujera ya zauna yana rik'o hannuna mai ciwo, fara'ar dake a fuskarsa dukta d'auke, alamar ransa yana 6aci inhar ya tuna tushen ciwon.
Cikin son kauda masa damuwarsa nayi murmushi ina d'ora hannuna mai lafiya saman nashi dake rik'e da mai ciwon, d'ago ido yay muka kalli juna, nad'an juya idanuna ina fad'in “yafi k'yau a haka ko?”.
Hararata yayi kawai baice komaiba.
Nayi k'aramar dariya.
Yiyay tamkar zai matsa hannun nai azamar janyewa ina d'ane gadon gaba d'aya dayin y'ar k'arar tsorata, kad'an yarage na haye Amaturrahman.
Murmushi yayi har hak'oransa na bayyana. yace, “ga tsoro ga tsiwa”.
Nace, “naji dai ba komai”.
Bai kuma cewa komaiba, sai murmusawa da yay, da kansa ya shafamin mai ya canjamin riga, dukda kakkauda fuskan kunya danaitayi, shikam ko a jikinsa, kai tsaye yake lamarinsa kuma hankali kwance.
A gurguje please😏😜.
*********************
Satina Uku a Asibitin aka sallameni, jikina kam sai godiyar ALLAH, dan na warke sarai, saidai y'ar ramar danayi, dakuma ciwon kai dake yawan addabata inhar waje yacika hayaniya.
Tunda na dawo sai kuma kewar Galadima ta tasoni gaba, su Fauziyya nata shirin komawa gidajensu, sainaji inama harda mu🤭.
Tunda na fito asibiti Aunty Salamah takuma k'aumi wajen bamu kulawa, musamman ma ni, dan ita Munubiya ina asibiti akaita mata nata.
Tunda aka sallami Munaya daga asibiti ta koma gida sai yaji zaman k'asarma dukya gunduresa, ganin zai saka kansa a damuwa saiya had'a inasa-inasa yabar k'asar, itama Munaya rana tsaka yazo mata da zancen komawar.
Addu'ar fatan alkairi kawai tamasa, da kuma sak'on magungunan Abie, a ranar yaso shiga su gaisa da baba mai kanwa, amma sai akaje wai bayanan, d'ansa yaje kaisa wani k'auye nan kusa gaisuwar Mutuwa da akayi.
............................★
Su momma sunyi farin cikin dawowarsa garesu cikin k'oshin lafiya, sai dai y'ar ramar da yayi.
Shima wani matsanancin farin cikine ya kamashi ganin jikin Abie ya k'ara k'yau, yanzu har mitsa hanunsa yakeyi sosai, ga doguwar hira da akanyi dashi batareda ya k'osa ba, ranar sunsha hira sosai, har saida doctor d'in Abie yace subarshi ya huta sannan Galadima ya tafi gida shi da Momma, ranar Aunty Mimi aka bari wajen Abie tunda ita tasan komai.
Sabuwar hira Momma da Galadima suka kuma dasawa a gida, dukkan abinda yafaru yabata labari dallah-dallah, dukda Aunty Mimi tabata dama, Momma harda hawayen jin dad'i, ta rungume Galadima tana saka masa albarka shida matarsa da yaransu.
Babu kunya ya ringa amsawa cikin tsantsar farin ciki.
Yanzu kam koba komai hankalinsa ya kwanta, ya maida hankalinsa ga dukkan aikinsa da sana'oinsa da suke samun kud'in shiga akan jiyyar mahaifinsa.
Shiri yake a gaggauce saboda kiran da Doctor d'in Abie yamasa tun a daren jiya akan yanason ganinsa yau da sassafe.
Yayi k'yau cikin Orange d'in Suit, sai k'amshinsa yake mai dad'i, cikeda salon birgewa yake sakkowa daga steps d'in benen yana waya, bayin daketa aikace-aikacen k'imtsa falon duk suka zube suna gaisheshi.
Hannu kawai ya d'aga musu ya nufi hanyar fita a hanzarce yana cigaba da wayarsa, ya d'ora briefcase d'insa saman motar yasa key ya bud'e, bag d'in yafara ajiyewa gefen mai zaman banza sannan ya dawo ya bud'e ya shiga mazaunin driver ya tada motar ya fice.
“Muftahu kabari zamuyi magana daga baya dai kawai”.
Daga can Muftahu ya amsa da to babu damuwa.
Ajiye wayar Galadima yay ya maida hankalinsa ga tuk'insa, yayinda sashen zuciyarsa ke tunano masa hirarsa da Munaya ta daren jiya, kwana biyunnan idan yamata maganar dawowarta saitai ta masa yawo da hankali, yarasa dad'inmi zaman can d'in yake mata? Ai wankan jegon ya isa haka, shima yana buk'atar zama da iyalansa koya samu nutsuwa tamkar kowanne magidanci, k'aramar tsaki yaja yana furzo isaka daga bakinsa, mata kenan, wataran su baka zuma, wataran su caja maka kai.
Da wannan tunanin ya k'arasa asibitin, wayarsa kawai ya d'auka ya fita a motar, kai tsaye Office d'in Doctor Ajay ya nufa, yay Knocking aka bashi izinin shiga, (Abu Na CCTV suna kallon shige da ficin kowa) Doctor Ajay ya fad'ad'a murmushi sa yana mik'ewa, hannu suka bama juna cikin Musabaha suna gaisawa, Doctor ya nunama Galadima wajen zama.
Bayan sun zauna Doctor daketa faman murmushi yace, “Sameer wani abun farin ciki ne nasamo a daren jiya, shiyyasa nakasa sukune saida Na kiraka a daren domin buk'atar ganinka”.
Galadima dai kallonsa yake baice komaiba.
Dr Ajay yaci gaba da fad'in, “Wato wani Doctor ne mai suna Dr Erfan Fahad Sajaad, d'an k'abilar Kashmir ne, Likita ne babban masani ta fannin irin matsalolin su Abie, yanzu haka yana k'asar England akan wani aiki, nakai watanni 6 inason ganinsa akan matsalar Abie amma ban samu damaba, saboda matuk'ar Busy dayake, sai a daren jiya nasamu magana dashi, bakaji farin cikin dana samu kaina a cikiba, dan mun tattauna sosai akan matsalar Abie, yanzu haka yabamu date d'in dazamu sameshi can Kashmir a asibitinsa”.
Alhmdllh Galadima yaketa ambata a zuciyarsa tunda Dr Ajay yafara bayaninsa, cikeda farin ciki yace, “Doctor lallai nayi farin ciki da wannan albiahir naka sosai, ka wuce matsayin likita kawai a garemu saidai d'an uwa”.
Murmushi Dr Ajay yayi, suka rungume juna shida Galadima kowa yanajin dad'i a ransa.
Galadima ya fito d'auke da wannan farin ciki sukaci karo da Akash a hanya.
Akash yace daddyn Triplets kenan, kwana biyu ka 6uya?.
Hannu Galadima ya bashi yana fad'ad'a murmushinsa, yace, “Sorry my friend ka ganni dai yawo kamar ruwan sama, idan bani anan aganni acan, ya aikin?”.
“Gashi munata fama, ya naka?”.
Galadima yace, “Alhmdllh”.
“Wai sai yaushe zaka dawo mana da Mummyn triplets ne? ga bikina yanata matsowa, bafa zan muku alfarma ba”.
Murmushi Galadima yayi, ya dafa kafad'arsa yana fad'in “kwantar da hankalinka, ai babu yanda za'ai bikinka babu mu a wajen”.
Aksha yace, “Ato kun wanke kanku, daga ina ka fito haka cikin farin ciki?”.
Bayanin komai Galadima yayma Akash, dan baya 6oye masa komai gameda ciwon Abie.
Shima ya nuna tsantsar farin cikinsa kuwa, kafin suyi sallama kowa ya nufi inda zaije.
Waya yaciro yana lalubo number Munaya................✍🏻
*_Zan iya cewa yanzu zaku dinga rashin ganina, wlhy ammana haihuwar da tilas saina kasance a wajen a kullum, amma inhar Na samu time zaku dinga ganin posting, dan yauma banyi tunanin zanyiba, amma saigashi ALLAH yabani iko bayan dawowata daga asibiti, nima kaina Na k'agara nagama Na huta kuma Ku huta🤦🏻♀, I love you all😘😘😘😘❤🤝🏻_*
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
Download Raina Kama Littafi Na Uku
0 Comments
Thank you for this comment