🅰ⓂAKIRCI NA💦

Na Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele
Part 1

Bismillahir-rahmanurrahim
07038260028



Tafiya take Cikin yanga da jan ajii.
Tana rangaji ha'de da karka'da jikinta
Kallo 'daya xaka mata kagane makirace game Sa ido

Ha'dad'diyace tako ta'ina
Farace soll doguwa me matsakarcin jiki da yalayalan gashin kai me tsawo da sheqi ha'de da laushi
Tanada dogun hanki da 'dan madai daicin baki
Haka fuskarta doguwace me kyawun gaske.
Tanada hq da breast masu 'daukan hankali
Gaskiyane Amina MEENAT taha'du

Tana tafiyan ne tana tunanin yanda xusu Kaya da surukar Anisa qawarta
Matace mafa'daciya me mugunsa ido
Duk wanda yaje gun Anisa toh daga ranar baxai qara xuwaba dan qiri qiri xatace maka karka qara xuwa mata gun sirika
Kuma bawani da'dewa auran nasu yayiba kwata kwata wata 'dayane 
Toh itadai  baby MEENAT bata samu halartar xuwa bikinba. Shine yau takira Anisan tagaya mata
Nan take Anisa tafara murna
Tana cewa Wlhi baby surukar nan tahanani sukuni
Baby tace barni sainaxo

Da sallama tashiga gidan
Da gudu Anisa tafitoh ta rungumeta tana mecewa
Saiyanxu.
kedai bari natsaya kar6a miki turarene gun Aunty Rahama gaskiya ya ha'du tafa'da taname miqa mata
Cikin sauri Anisa  ta'amshe tace nagode qawata Allah yabarmin ke
Baby Tace AmEEn yanxu dai bani naci tace mefah
Kaxar amarcin da kukaci kuka rage
Anisa Tace ammake akwai 'yar iska yau wata 'daya da kwanaki  da aurena sainata ajiyar kaxar daran farko
Idan baki ajiyeba kitashi kigasa min idan kinqi naje nayi dakaina Amma kisa kika bari nashiga kitchen 'dinki sunanki sorry
Anisa tace tab bara naje bagasa miki nasan sharrinki sarai.....
Bab bab bab
sukaji anbanko kofar
Anisa nasan yin masifah kawai taga uwar mijintace
Da sauri baby MEENAT tadurqusa tace Amincin Allah ya tabbata agareki ya mahaifiyarmu
Washare baki inna tayi tace nidaku ko 'Yar albarka
Murmushi baby tayi. Sai inna takalli Anisa tace irin wa'dannan qawayan yakamata kidinga qawance dasu ba 'yan iskaba
Itadai Anisa batayi magana ba inna tafita.
Tanafita baby takoma kujera tace amma anyi banxar sirika anan
Anisa tace Gaskiya qawata kinha'da

Tace amakirci na xan'iya Komai ba boka ba malam xan dafah sirikar nan taki


Anisa tace ke sirikata tahucce makircinki Wlhi
Baby MEENAT Tace ban kasance sirikarta bane shiyaki fa'din haka
Anisa tayi Murmushi tace nasani Komai xaki iya danke makirace Amma fa'damin yanda Xanyi da ita dan Wlhi tafara damuna
Tace kinsan mexaki. Anisa ta girgixa kai
Tace duk wanda yaxo gunki yana sallama to kira'damai cewa yaje yafara gaida ita Cikin matuqar ladabi
Tace ko
MEENAT taya tsina fuska tace sawasa Wlhi saikinyi mamakin yanda baxata qara koran miki kowaba Tace aiko xangwada....
Wayar MEENAT tafara ringing
Cikin yanga ta'dau wayan
Tace me martaba sarkin samari Amincin Allah ya tabbata agareka
Acan 6angaran Yace
Nidake tauraruwa me dushashe hasken mata idan tashiga cikinsu
Murmushi baby MEENAT tayi Tace ina fatan aiki bai wahalarmin dakaiba Yace koda yayi yunqurin wahalar dani daxaran natunoki nakan tsinki Kaina Cikin qarfi da warewa
Tace gud my luv Allah yabarni dakai Cikin aminci Yace AmEEn farin cikina inasan kifitoh naganki dan ina kofar gidanku
Tace kash
Meyasa qafata tacutar dani wajan rinjayata tafiya gidan Anisa
Yace idan nagane xancanki kinasan cemin bakya gida
Tace wayyo nashiga uku baxanga masoyinaba Yace naso ganinki MEENAT tace tun'daxu xuciyata takemin xafi saboda rashin ganinka dabatayiba da safe
Gashi yanxu kaxo batare daxata gankaba Yace no kirarrashan min ita dace mata xamu ha'du da dare Tace OK kadawo lafiya  Allah ya temaka Yace nagode.
Ta'ajiye wayan
Anisa Tace da"alama da Ahmad kikayi waya
Tace eh dashine Anisa Tace tabbas xaiyi dacan mata yasameki Tace kedai bari Wlhi soyayyar Ahmad tashigeni kamar yanda tawa tashige shi
Anisa tace aikowa nagano hakan tuni
Tace waima acikin satinnan xaigayama dad "dinshi aturo da maganar aurena dashi. Anisa tace ya kamata kam Amma ina jiye miki sharrin mahaifiyarsa Momy kilishi....



MEENAT tata6e baki tace wai mesa kowa yake tsoran wannan baiwar Allah
Anisa Tace dole aji tsoranta idan kinmanta sharrinta ni barina tunatar dake

Momy kilishi take
Mata tabiyu ga Alhaji barau meji da lera
Duk acikin matanshi itace gwanarsa itace mejuya gidan meyanda taso
Dukkan abinda takeso shi akeyi
Sunha'dakai da uwar gidan suna bin yawan malamai da bokaye. Saboda dukiyarshi ita ka'daice agabansu
Kwatsam ranar yayo musu kishiya Zainab 'yaramar yarinya 'Yar shekara goma Sha hu'du
Kekanki kinsan wane irin xama take agidan na wiya da xalinci
Duk da akwai 'yan aiki agidan itace take aikin gidan
Yarinyace Amma kinga inda suke neman lalata mata rayuwa
Alhaji barau yana da yara 10
Shidda na Uwar gida momy Hauwa. Hu'du na Momy kilishi
Hassana da usaina da Rahamat Aisha Najib kamal
Sune yara ga Momy Hauwa Uwar gida
Ahmad da Anwar Bashir Yusra
Sune yara ga  Momy kilishi
Dukkansu basajin magana koka'dan yaran gidan

Kinsani manyanmu a unguwar sun tabbatar da hakurin Alhaji barau me hakurine 
Hakan yasa Momy kilishi da Momy Hauwa suke cutar dashi

Bangama amfanin baki wannan labarinba tunda gida biyu ne tsakanin gidanku da nasu.

MEENAT tace aikowa dai.
dan saidai naqara miki sani akan rayuwar gidan. Sannan ni ban damuba tunda inasan 'danta ba boka ba ko Uwar boka takebi tacigaba dabi ni'dinnan xangyara mata xama Wlhi
Anisa tace futunarki nada yawa MEENAT gaki da Masoya mexaisa kijefah kanki amasifa kinaji kina gani
Tace ke kikaga masifar ni soyayyar 'danta tarufemin ido 
Anisa tagyara xama Tace kin manta taja miki kunne akan kifita mata aharkar 'da kotaci mutuncinki
Tace natuna tunda agabanku tafa'da Amma bacin haka Wlhi na manta
Anisa tace niii ban mantaba danna tsorata da ita

MEENAT tayi Murmushi tace saini Amina MEENAT yarinya 'Yar shekara goma sha shidda. 'Yar gadan gidansu sannan kuma futunanniya agidan
bawanda nakejin tsoro
Wlhi Amakirci na saina koyama Momy kilishi hankali
Anisa tayi dariya tace kinyima kanki kirari Amma kinmanta da dodanki na gidanku
MEENAT tawaro ido


Tace kinji inda gabana ya fa'di
Anisa Tace kobaki fa'daba yanayinki ya nuna
Tace ya Aliyu meyasa nakejin ba'il tsoranka Wlhi da gaske Anisa ana kiran sunansa gabana yake fa'duwa
Anisa tace kinga bara naje na gasa miki kaxarki dan hirarmu bata qarewa
Tace nina qoshima tunda kika ambaci ya Aliyu
Dariya Anisa tayi tace aibaki isaba
Gaskine Allah yamiki mugun kamu akan ya Aliyu

'Daukar jakarta MEENAT tayi  tace kinga tafiyata
Anisa ta6atarai tace meyasa xakimin haka tace kiyi hakuri Anisa Wlhi hankalina ya tashi sam namanta yau xaizo Wlhi sanda kikayi xancansa natuna yanxu
Anisa tace hmm kedai jeki lamari idan nashine toko rasa nutsuwarki kike
Tace xaki iya fa'dan koma miye dan abaiyane yake Kinsan halinsa sarai dan ya xaneni akan yadawo baisa meni ba bawani abu bane nidai kinga tafiyata
Dama Anisa tasan lamarin MEENAT indai akan ya Aliyu
Dan haka tarakota tama inna sallama harda ajiye mata ku'di. Tayita murna dasa mata albarka
Anisa tace banga ranar daxaki canja bah
Tace namefah tace motocinki uku Amma Sam bakya hawansu kinfi ganema tafiyar qafah
Tace tafimin da'dine dan idan danni kayi mota to anyi nabanxa
Tace naga alama
Nan MEENAT tatafi

Taxo dai-dai da kofar gidansu taga sirikinta wato baban Ahmad
Wanda koyaushe kicin kallanta yake tun tanajin kunyarshi hartadena dan talura ila haka halinsa yake na kallan mutane

Cikin ladabi tagai dashi ya'amsa mata kamar yanda yasaba wato Cikin farin ciki da annushuwa da kulawa
Tashige gidansu

Da yah Aminu taci karo Yace ke daga ina haka tace daga gidan Anisa Yace toga kayananan kiwanke min. taturo baki gaba tare da fara yarfe hannu kamar yanda tasaba
Tace nifah nagaji ya Aminu Wlhi da qafa naje na dawo kumama ga "yan wanki
Yace kenakesan kiwanke min
Tayi kamar xatayi kuka Yace jeki dan Allah karkimin halinki (kuka) shigiye me san jikin tsiya
Da sauri tahucce shi
Tana shiga falo taga Sadiya da SafiYYA suna kallo tace baku da aiki sai kallo kunajin ana kiran sallar azahar Amma kukayi biris da kiran Allah
Tashi sukayi atare batare da sunci komaiba dan sunsan gaskiya tafa'da
Amma banda haka dasunci ubanta dan Cikin rashin kunya tamusu xancan

Da taga haka itama tashige toilet tayo alwala tayi sallarta
Sannan taje gun momynta wato mahaifiya ga ya Aliyu
Tace baki da'deba tace ya Aliyu natuna Yace yau xaidawo
Momynta tace eh har sunje 'dauko shi......
Mahaifiyarta wacce suke kira da mamah CE tashigo 'dakin tace ke badake sukaje 'dauko yayan nakiba
Tace eh gidan Anisa naje
Tace shine dan munafunci kika dawo da wuri dankar yaci qaniyarki ko.
Dariya momynta tayi tace eh kai kinsanmu da tsoro tace aiko dai
Nan MEENAT tafita dan taga kamar magana xasuyi...



Direct 'dakin ya Aliyu  tayi tasamu SafiYYA da Sadiya suna ta gyara
Tata6e baki tace hmm idanma kunyi wannan bashixai hanashi canja muku halinsaba
Cikin fusata SafiYYA Tace to'ina ruwanki
Tace waime namikine SafiYYA naga kina bina da mugun kallo

Tace wato harkin manta yanda kika ha'dani da Salim ko.
Cikin dariya tace am sorry my sis 
Sadiya ta galla mata harara tace nikuma wane munafuncinne yasaki gayama mamah cewa Yusuf Yace xaituro iyayansa
Tace farin ciki mana
Tace yanxu inkuma bai turobafah
MEENAT tata6e baki tace mutuncinshi ya xube tace dama haka kikeso ko Tace kwarai. Dan bana sanki dashi tace waike wacce irin maiyace da'inkinqi abu kowama sai yaqishi
Tace dan Allah Aunty Sadiya kifuta daga harkar 'dan iskannan Wlhi kokifita aharkarshi ko na gayama ya Aliyu halinshi
Tace haba qanwata xan rabu dashi plx mubar xancan
SafiYYA tace ni Wlhi damuwata shine taha'dani da Salim
Sadiya tace metacene
Tace fa'da mishi tayi wai bashi ka'dai yake xuwa guna ba..
Xarab MEENAT takar6e maganar dace qarya nayi
Kinsa ankar6i sadakinsa Amma hakan bai hanaki kula wasu maxan ba shiyasa nagayamai dan hakan bai dace bah
Tace aikin kyauta
Sadiya tace anya MEENAT baxata iya kashe aure ba.
SafiYYA Tace hmm koda kunkai shakara 'dari akwana 'Daya xata kashe muku auranku adai makircinta Sadiya tace toh Allah ya kyauta
MEENAT xatayi magana sukaji shigowar motoci. Gabanta yayanke yafa'di.
Da'alama ya Aliyu ne da shegiyar matarsa
Itakam bataso xuwansuba

Tace nashiga uku ya Aliyu ne
Tagudu suka fita itako takasa ko motsi

Suna xaune afalo bayan sunci sunsha
kowa Na musu  barka da xuwa
Cikin farin Cikin ganinsu.
Abban shi Yace naji da'din xuwanka Aliyu da fatan kadawo kenan Yace xandai dawo kwata kwata ada'damin afuwa
Abban MEENAT Yace to Allah yayi jagora
Kowa Yace AmEEn.
Su Abba suka bar falan
Lubbah matar Aliyu wacce suke kira da Aunty tace shine ku... Tanunasu Sadiya
Bakuxo 'daukarmu bah
SafiYYA tace mun tsaya aikine tace OK.
Tashi ALIYU yayi Yace dafatan kungyara shashinmu
sukace  tas yake yayah Yace gud
Har yakai kofah yajuyo
Ina baby
Sadiya tace tanacan Yace can ina Tace shashinku.
Fita yayi baiqara magana bah

Lubba tata6e baki tarasa dalilin da yasa ALIYU yadamu da yarinyar.
Batasan lokacin da tajah tsakiba
Danma Momy da mamah sunbar gun
SafiYYA Tace Aunty lafiya Tace lau


Suwaye su ga asalinsu
Alhaji Isa wane ga Alhaji musu
Uwarsu 'daya ubansu 'daya
Iyayansu sun rasu tunsuna qanana. Agun kawunsu suka tashi
Dasuka girma ne ya danqa musu dukiyarsu me tarin yawa
Shine fah sukayi aure
Sana'ar kasu wanci suke 
Alhaji Isa ya auri Zainab wacce MEENAT ke kiranta momyna
Tanada yara uku
Aliyu da Hamisu da SafiYYa.
Alhaji Musa ko yaranshi hu'du
Aminu Sadiya Amina MEENAT sai 'Yar autarsu Jamila wacce MEENAT taba shakara 'daya

Suna garin kono ne da xama a nasarawa

Aliyu shine babba agidan yana xama aqasar waje inda yagama karatunshi suka riqeshi akan yay musu aiki nawani lokaci
Yabiko ra'ayinsu.
Doctor ne tafanni da dama.


Hamisu yana aiki a first bank.
Yayinda Aminu ya taka matsayin loya

Akalla ALIYU xaikai 33 years aduniya
Matarsa Lubba Allah yayi xai auretane Amma badan sungina soyayyar axo aganiba
Farace sol me kyau tana matuqar san ALIYU baka'dan ba
Kuma tanajin shakkarsa danshi bayasan raini
Kuma irin wasan rainin hankalinnan na mata da miji babu tsakanin ALIYU da Lubba

Baqamin tsanar MEENAT tayi ba
Kuma daxa'a tambayeta baxatace ga kwakkwaran daliliba

ALIYU ya ha'du iyakar ha"duwa kalarshi me 'daukar hankali
Fatarshi me bala'in kyauce
Ita ba faraba kuma baqaba
Amma xaki kirashi dajan mutun
Komai nashi anutse yakeyi
Yanada xafi sannan yanada kwarjini
(Nidai Rahamat nasan ALIYU kat ne)
Yana San  tsafta da qamshi ga koma miye
Ababin mace kowa
ALIYU yanasan shagwa6a da iya girki da soyayya

Yayi iya bida mace dan ya karanci soyayya yanada kyauta
Amma baya 'daukar raini koka'dan
Duk gidan sunajin shakkarsa da tsoransa
Amma na MEENAT dabanne
Tana ba'in tsoransa
Takasance futunanniya duk abinda takeyi akace bari MEENAT baxata bariba. Amma da xaran ankira ALIYU toko anan xata bari taqara da gudu

Dan acewarta tace shi mugune
Baya barinta tasakata tawala koka'dan kuskure ka'dan tayi dukane
Sam baya raga mata

Saidai akwai wani abu dayake faruwa tsakanin ALIYU da MEENAT
Duk wani abu wanda ALIYU yasiya toko idan MEENAT tayi ido hu'du dashi Wlhi saita 6atashi
Koya lalace ko ya 6aci
Kuma bawai MEENAT tanayi da niyar ta6atamai bane aa.
Kaddarar ALIYU kenan Komai yasiya MEENAT takai hannu saita 6atamai
Sam baita6a nuna damuwarshi akan hakan ba.

Sannan yana siya musu suturo masu kyau da kece raini
Qaryane ALIYU yakawoma MEENAT kaya tasaka bai mata kyauba
Haka duk wani Kaya da iyayan xasu siya musu susaka baxai ta6a yima MEENAT kyau ba kamar yanda idan ALIYU yakawo mata nashi

Duk da muguntar da ALIYU yakema MEENAT in jita da fa'da.
Baqaramin shagwa6ata yakeba. Dan duk abinda takeso shiyake mata ammafah idan tayi lefi aka kawo mishi qara baqaramin 'kaniyarta yake ciba


Sannan MEENAT tanada saurayi Ahmad wanda take bala'in sanshi da kaunarshi
Saidai Amma kash
Sam Ahmad yaudarar MEENAT yake. Danshi burinshi ya kusan ceta kawai yarabu da ita.

Yagaya mata xai fa'dama iyayanshi suturo gidansu dan maganar aure duk qaryane yaudara ne 
Amma yasaka aranshi burinshi xaicika akanta Cikin satinnan

Duk gidansu MEENAT bawanda baisan da soyayyar MEENAT da Ahmad ba.
Amma agidansu Ahmad  bawanda yasan da soyayyarsu sai mahaifiyarshi wacce tatsani MEENAT dan acewar bokanta Yace mata xata bata matsala akan duk wani shirinsu da sukeyi agidan.
Nan tace ina bata yarda MEENAT taxama sirika agareta ba


MEENAT tanada samari da dama Amma kasan cewar tarbiyar gidansu yasaka take rabuwa dasu
Musamman idan ALIYU yaganta da samari baqaramin wahala takeci ahannunahi bah
Tanada qawaye hu'du Anisa Salmah Ameera Nusaiba

Ayanxu tana s:s 3 a skull
Yayinda tasauke qur'ani
Tanada ilimin addini sosai dan tafi Bashi mahimmanci fiye dana boko

MEENAT bata wasa da sallah koka'dan
Sannan akwaita da kuratun qur'ani da asubayi da yamma da kuma dare
Sannan akwaita da tashiyin sallar dare
Sam bata wasa da neman lahirarta

Saidai anyi rashin sa'a tanada San waqa musamman ma idan UMMAR M SHARIFF ne ya rera da Nura m inuwa
Dama sauran mawaqa na hausa Usaini danko Adamu Hasan nagudu
Duk waqar mawaqin da MEENAT taji to dama tasan waye dan tayi ilimi a karantar muryoyinsu.
💎💎🅰ⓂAKIRCI NA💦
Mundawo labari
Direct ALIYU shashinsu yayi inda suke sauka idan sunxo
Aiko yaga MEENAT nan tsaye. Tanaganin shi tace sannu da xuwa yayah 
Yace yauwa mekikeyi Tace um ba komai....
Hamisu da Aminu ne suka shigo da Kaya niqi niqi.
Suna ajiyewa Aminu yace sannu da xuwa ya ALIYU
Xaiyi magana Hamisu ma Yace sannu da xuwa
Yace yauwa da fatan nasa meku lafiya sukace qalau Wlhi
Yace gud
Nan duka fita ibo sauran

MEENAT ta kalleshe yaqara kyau sosai ba abinda yake tsaya mata arai kamar 'kamshinsa

Harara ya galla mata nan tayi niyar ficewa Yace ha'damin ruwa
 toilet tayi tana cewa aranta aiki yasameta saikace baida mata
Ciki ciki bayan kulle kofar taja tsaki
Nandai taha'damai
Tafito bata ganshiba tafice

A farfajiyar gidan sukaci karo ita da Lubba
Kamar baxata kulataba Tace sannu  da xuwa Aunty kinxo lafiya
Ko kallanta batayiba tahucce
MEENAT tayi kwafah Tace Xan koya miki hankali

Cikin Takaici tashiga falo. Momy da tafito daga kitchin taga ranta 6ace tace autata dake haka take kiranta Tace lafiya Tace momyna Wlhi bansan me nayima Aunty Lubba bah tatsaneni
Murmushi irin nasu na manya tayi tace rabu da ita kinji kishine yake damunta
Tace tohni ina ruwana da ita saboda karna fita daga harkarta yayah yadaken akan ban mata ladabi bah
Momy tace to xan mata magana
Jin muryar Mamah kawai mukayi tace  kidena biyema mata qarya take mata
Momy tace ai MEENAT bata qarya kuma kinsan halin sirikar taki badama
Shuru mamah tayi
Itama Momy bata jira cewarta ba taja MEENAT sukayi gefanta dan tasan 'yar tsamar dake tsakaninsu itadai  batajin tsanar Lubba haka batajin sonta aranta kadaran kadaham dan talura tanada San girma kai
Xancan Momy kenan axuci


Misalin qarfe 8:30 MEENAT CE keta feshe jikinta da turare tayi kyau sosai cikin riga da siket na atamfah 'dinkin yaxauna ajikinta dai-dai.
Takafah 'dauri me 'daukar hankali

Taqarema kanta kallo ba shakka bata muqatar ace ta ha'du dan (ni Rahamat na shaida hakan)
Murmushi tayi....
Wayanta tafara ringing nan tada'dayin Murmushi dan ganin Ahmad ne
Bata 'daukaba tace kanada futuna yanxu dai xanfito kaganni hankalinka ya kwanta

SafiYYA Tace lalle gwano bayajin warin jikinshi
Banda haka harkece xakice wani yanada futuna

Tace kanki akeji ta'dau gyalanta har takai kofa Sadiya tace  Allah ya ha'daki da ya Aliyu Tace duk da gabana yafa'di Amma xuciyata bata karaya wajan san ganin masoyina bah tafice
SafiYYA takalli Sadiya itama kallan nata tayi Tace Lalle soyayyar Ahmad tama MEENAT mugun kamu. Sadiya Tace aikam


Bayan tagayama Momy da mamah Ahmad na kiranta tafito kenan taci karo da ALIYU
Duk da gabanta yafa'di Amma hakan bai hanata lumshe ido ba.
Saboda da'din sanyayyan turaranshi.
Ta6a fuskarta yayi tayi saurin bu'de ido danjin wani xirrrrrrr dataji
 yaqare mata kallo Yace xuwa ina cikin daran nan........



Cikin in ina Tace xan kar6i abine Yace baby Tace Allah yayah
Wuccewa yayi Yace minti biyu nabaki
Cikin sauri tace toh tayi gaba dan batayi tunanin xaibarta tajeba
Aminci Allah ya tabbata agareka me Martaba sarkin samari MEENAT tafa'da tana lumshe ido wanda hakan yakusa sa nutsuwar Ahmad tarwatsewa Yace nidake tauraruwa me dushashe hasken mata
Gaskiya xuciyata tayi sanyi daganin masoyana  
Yace xuciyata tafi taki xu'kuwa taganki
Murmushi tayi take indai tafannin maganar soyayyace ba'acin galaba akanka
Yace. Duk ranar da kikaci galaba akaina toko nasan sanda kikemin ya xarce nawa. Tace ranar naxuwa
Allah ya kawota AmEEn ya babbi
Yace Wlhi kinyi kyau fiye da kwalliyar kowace mace
Tace kawo kunnanka ingaya maka wani abu Yace nasan xancan naki karki fa'da Tace toh inajinki Yace xakicene karmu rabu
Tace Ina mamakin yanda xuciyata da taka takesan xama abu 'daya yace fatana kenan kullun taxama abu 'daya

Tace Allah yasa
Yace AmEEn
Yauwa inaneman amin cewarki akan wani abu. Kuma ina Addu'ar Allah yasa ki amince dan xuciyata ma ban take baxaki aminceba.

Tace no inajinki fa'di Yace sonake gobe kirakani gidan wani abukina. Dan matarshi kullun gori takemin akan naqi kawo mata ke....


Tata6e baki tace sainayi tunani yace kuma dan Allah karki tambaya tace idan na tambaya kasan babarina Xa'ayiba Yace Hakka Amma ina rokwan xuciyata data amince tace karka damu
Gyara xama yayi yace wato MEENAT aduk lokacin danake taredake xuciyata cika take da farin ciki

Tace hmm meyasa mahaifiyarka bata sona Yace tanasanki mana MEENAT mekika gani tace kwanaki tajamin kunne akanka kumani naga ban aikata mata wani abu na Allah wadai ba
Gashi xuciyata tacika da santa taqarashe xancan jikinta asanyaye

Duk da Ahmad manufane aranshi Amma yaji da'din yanda tace tana san momynshi
Yace karki damu idan kika xama mata agareni xata soki fiye da tunaninki

Tace Allah yasa toh
Ya ALIYU na jirana dan minti biyu yaban
Yace OK dan Allah ki'    amincemin goben
Murmushi tayi tace
Na amince
Da sauri Yace qarfe nawa tace xuwa 2 ko
Yace OK
Allah ya barminke nutsuwata tace AmEEn farin Cikina tafa'da tamai shigewa gida

Afalo taga ALIYU da mamah Suna magana
Ya galla mata muguwar harara. Itadai tashige 'dakinsu tunda baiyi mata maganaba

SafiYYA tace Amakirci kingama siye xuciyar Ahmad ne da wuri haka
Tace Yah ALIYU ne yasamin gaba. Ni Wlhi banso xuwansuba
Dariya Sadiya tayi tace niko nayi murna da xuwanshi dan xai setaki yanda ya kamata

Tace ta Allah duk ba takuba
SafiYYA Tace Ku kutsaya kuji
Sadiya dasan gulma Tace Mene
Tace idan kunha'du da Aunty gobe koqare mata kallo cikine da ita. Sadiya tace xamuga iyayi tace aiko kinsanta ko da iyayin da girman kai tsiya

Tsaki MEENAT taja tace nina tsaneta Wlhi kamar yanda tatsaneni bana santa.
SafiYYA tace aike bansan meyasaka kuka tsani junaba
Tace Wlhi wata rana saina nuna mata kalata


Dariya Sadiya tayi Tace tab kudai nunama juna kalolinku kina ganinta kinga  idanta ajuye yake da makirci
MEENAT tata6e baki batayi magana bah
Salim saurayin SafiYYA yakirata.

Washe gari bayan sunkarya taje tagaida ALIYU
Yace jiya kedawa kika tsaya da dare. Gabanta ya fa'di tace Ahamad ne
Cikin takaici Lubba tace toh hony menene dan ta tsaya da wani ya watsa mata mugun kallo ba shiri tasaita nutsuwarta tayi shuru.

Falle MEENAT yayi da mari yace ban hanaki tsayuwa da maxaba. Tayi shuru dan marin ya shigyeta
Yace yarinya dake wai harkinsan ki tsaya da saurayi kina wani cemishi xuciyarki tayi sanyi da ganinsa
Ta'dago ta kalleshi
Yace muna fuka tashi kibarmin nan ko nakaryaki
Har tana tuntu6e wajan barin  falan
Lubba tajah tsaki tace tokai ina ruwanka
Tashi yayi yace Lubba xan...
 saurin barin gun tayi

Shiryawa MEENAT tayi  dan xuwa skull Cikin gogaggan inifun 'dinta me tsafta
Tana tuna Marin da tasha

Direbanta ya 'dauketa  dan Su Sadiya sungama secondary tuni. Suna UJE



sunfito tarane Salmah kecema MEENAT naganki wani iri tace kedai bari
Wannan 'dan takurannan ne  yadawo mugu
Tace badai ya Aliyu ba dace hmmm inbashiba waye me takuramin
Nusaiba Tace saifashi
Ameera Tace yauwa ina wannan guy 'din da muka ha'du dashi ranar kingane shi
MEENAT Tace aa tace kyakkyawannan me qamshin touch me Tace yah naganeshi. 'Dan shaye shaye ko
Tace yana shaye shaye ne
Tace nima Salmah ce taban labarinsa
Tace me dai sanyi haka
Salmah tace sanyin minafunci ba shidai
Tace Anya shine
Tsaki Salmah taja tace oho

Nusaiba tace kedai banxace inxaba mutane labari saikinta  wani jama mutane rai 

MEENAT tace miye Tace kullun saiyaxo gidanmu akan inmishi kwatancen gidanku Amma sanin halinki yasani kasa bashi cikakkiyar amsa

Salmah tace indai shine xamu ganshi ahanya
MEENAT Tace aiko xan jamasa kunne akan yarabu dani.  xuciyata Ahmad ne kawai acikinta


Nusaiba tace gaskiya Ahmad yayi dacanki MEENAT
Tace kamar yanda isma'il yayi dace dake ba
Dariya tayi tace qarfin soyayyarmu baikai takuba....
Lokacin komawarsu ajine yayi shiyahana cigaban hirar tasu


Dasuka tashine
Dake dama direban MEENAT kawota kawai yake dan tace yadena xuwa 'daukarta saboda soyayyarta da tafiyar qafah

Sunyanko kwanar layinsu Ameera kenan sukaci karo da wannan saurayin
Yace  MEENAT ina gaisuwa tashareshi
Yadinga binsu Amma ko kallanshi MEENAT batayiba

Ahaka har suka iso layinsu baidena binsuba
Nusaiba da Salmah suka shige gidajansu dake makwaftaka danasu MEENAT

Yace dan Allah kitsaya farin Cikina tace wai mexan maka
Yace sunana Nawas
Dan Allah karkice baki sona Wlhi sanki da qaunarki sunhanani samun nushuwa. Plx kisoni.

Tace Wlhi baxan soka ba Nawas. Yace meyasa Tace ance shaye shaye kakeyi da yima yaran mutane fay'de
Yace Wlhi xandena shaye shaye kuma baxan miki fay'deba
Tace dan Allah karabu dani banasanka akwai Wanda nakeso yake sona plx

Yace Wlhi tallahi baxan barkiba inasanki ina qaunarki kishirya kema kinkusa fa'damin

Tsaki tajah tashige gida
Nawas ko Murmushi yayi yashafa kansa.
Idan naci da kalamai suna aiki akan Masoya toh Wlhi saina tusa miki sona

MEENAT nashiga gidan taga wata fitinanniyar mota wacce ta'dau hankalinta ba 'danka'danba.
Gyefe guda kuma taga wani ha'dad'dan mashin
Kwarai yabata sha'awar tatuqa dan haka tacire hijab 'dinta ta'ajiye ha'de da jakarta gyefe ta'dane kan mashin 'din

 MEENAT da karfin hali Nafarko batasan kona waye ba nabiyu bata iya mashin ba

To ya'abin xaikasance

Can kuma kome tatuna saita sauka daga kan mashin 'din ta'dau jakarta tana cewa
Bara naci abinci nafijin da'din tuqin

Tanashiga falo taga Ya ALIYU
Nan ta gaidashi yabita da kallo
Tasan ganinta da yayi da hijabi ahannu ne yasashi binta da kallan

Suna dining suna cin abinci dasu Sadiya
Taji ALIYU nace ma Su Momy
Motar danasa abokina ya kawomin taxofah
Cikin murna mamah da Momy sukace toh masha Allah tana ina
Yace tana waje

Suka fita dan gani hardasu SafiYYA
MEENAT ko saka riga da wando tayi tafito.
Direct wajan mashin 'din nan tayi
Kowa yabita da kallo tako 'dane abinta Cikin sa'a mashin din ya kunnu
Aiko tafara tafiya dana dariya

Momy Tace kisauka karkiji ciwo tace toh bari in'dan 'dana
Mamah tace Allah yasa ki6ata mishi kuha'du.

Ga ALIYU ko tunda MEENAT tahau mashin din yasan wani abu xai'iya faruwa
Aiko birki ya kufce mata

Tadinga tafiya batsayawa
Gashi kuma setin motar ALIYU mashin 'din yanufa
Nan tahau ihu atemaketa
Kowa tsoro ya kamashi  dan ganin ba'abinda xaihana mashin 'din nan gwaruwa da motar ALIYU

Aiko jikake fas tafashe mishi futular motar har talotse
Kowa rufe ido yayi.

Ahankali ta tasauka takalle shi tafashe da  kuka.
Tace Dan Allah kayi hakuri..


Ko kallanta baiyiba.
Momy tace anya ba saukar qur'ani xa'ama MEENAT ba. Mamah tace ni yanxu abin natama yafara ban tsoro
Takalli MEENAT tace
Duk abinda ya kasance na yayanki ne saikin batamai hankalinki yake kwanciya ko
Tayi kif kif da ido...

Aminu ne yashigo idanshi ya sauka akan mashin din daya ajiye dama ba nashi bane
Yace kai😳 dan ganin da yayi ya lotse

Karab Sadiya tace Wlhi aikin MEENAT ne
Yace xako kici  qaniyarki Wlhi
Yafara kici-kicin cire bell
Duk da yaga motar ALIYU yanda tayi Amma Sam bai damuba dan yasan dama tasaba jaxamai asara akan Komai

Ganin da tayi da gaske dukanta xaiyi shiyasa  tashigye bayan Momy Yace ko bayan Su Abbah kikaje ba'abinda xaihanani dukanki
Da sauri kuma taje bayan ALIYU taqan qameshi
Cikin fusata yabiyota....
ALIYU ya 'dakatar dashi
Yace dan Allah yayah kabari nadaketa Yace barni da ita jeka
Badan yasoba yabargun

Momy da mamah dasu SafiYYA ma suka bargun

Ahankali MEENAT tasaki ALIYU tana shirin fecewa da gudu......
Yace kika kuskura kikayi taku 'daya ranki xai6aci. Cak tatsaya Tace dan Allah.....
Yakatseta da cewa muje

Tana gaba yana bayanta tiryan tiryan har tashige falansa
Ta xauna tace dan soyayyarka da Allah da Annabi yayah kayi hakuri
Xama yayi akujerar datake fuskantarta
Yace baby idan banyi hakuriba mexanyi

Meyasa baby
Duk abinda naxo dashi saikin 6atamin
Cikin shagwa6a tace Wlhi ban sani ba kaji narantse Wlhi bana sanin yanda abun yake faruwa
Yace gud kin kyauta. Taqara marai rai cewa tace Kahakura.
Harara yasakar mata tayi saurin sunkwai da kanta....

Lubba CE tashigo tana cewa honey badai motar da kace xa'akawo maka bace talotse haka
Yace itace
Agarin yaya Yace bansani bah
Tata6e baki da gallama MEENAT harara



Aiko MEENAT tarama batare da ALIYU yaganta ba
 tace wakike harara Tace niban harareki ba😚

ALIYU yace sweetheart barnan  Tace Amma....
Yace bakijiba kenan
Batayi musu ba tabar gun tana aikama ma MEENAT wata hararar

Tashi yayi ya'dau wayarshi da ke'din motarsa yafice. Ganin haka yasa tatashi itama tafice
Takalli motar data 6atata yanxu tabbas ta bugu

Tana xuwa 'dakinsu kiran Ahmad yashigo wayanta
Ta'dauka da cewa ina gaida 'dan autan maxaje
Yace nikuma ina gaida nur hasken mata.
Tace toh ya'akayi mijin MEENAT
Yace ina waje ina jiranki dan nasan har kingaji da jirana tunda yanxu kusan 3:30pm.
Tace subuhanallah
Yace kinmanta fitan ko Tace eh. kuma gashi.....
Yace gashi me tace lokacin sallah yayi kasan banxan fitaba har sainayi Yace hakane sayyada
Tace toh yanxu bari nayi sai muje ko. Dan nasan kaima yin xakayi.
Yace Hakkane Autata

Sadiya Tace ina xaku tace gun wata amaryar abokinsa
SafiYYA tace idan mukaga dama yanxu mu wargaxa miki shiri Wlhi

Da sauri tafara basu hakuri akan surufa mata asiri dan Allah
Sadiya Tace xamu rufa miki asiri baxamu tona ba. Amma da shara'din zakibarni da Yusuf muwala dan ya kintsu
SafiYYA tace kuma inkinga Salim xaki bashi tabbacin wasa kike mishi ranar

Tace duk naji xanyi yanda kukeso

Wanka tayi tafeshe jikinta da sanyayyan turaranta
Tayi sallah ha'de da karatun qur'ani

Taje takarka'de kai taxabgawa mamah da Momy qarya wai tun jiya aka kwantar da Babar Ameera a asibiti batajin da'di
Har suna cewa Allah yabata lafiya tagaisheta dakyau xasuxo dubata tace toh.


Tun daga nesa tahan goshi yana mata Murmushi
Itama Cikin murmushin tashige motarsa. Baiyi magana bah yaja motar.

Wani gida mekyau taga sunxo zoo rot Amma duk dakyen gidan ba megadi
Yace bari nashiga nabo'de get 'din saina shiga da motar ko
Tace muda xamu tafi yanxu kawai kabarta anan Yace OK
Nan suka fito



Suka shiga gidan tana mamakin yanda yaxaro key yabu'de falan
Tace basa nanne yace no qaqidarsu ne idan kai nagidane ambaka ixinin kabu'dewa da key basai katsaya kwankwa sawaba
Tace oho shine suka baka key 'din kaima Yace eh

Balefi yanda waje yake dakyau hakama ciki yake

Yace bari ya shiga  yayi musu magana
Tabishi da kallo kawai dan tafara yin wani  tunanin

Har tsawan minti goma bai fitoba
Can saigashi da drink da plate me 'dauke da cincin aciki  ahannunsa yana Murmushi yabata Tace naqoshi fah
Yaxaro ido Yace dan Allah kisha gatanan xuwa baxataji da'diba.

Hmmm
Xuciya 'daya MEENAT takar6a tasha
Yana janta da hira can taji wani nauyi kamar an'dora mata kaya akanta nanko bacci yafara kamata
Ta 6ingire

Dariya Ahmad yakece da ita Yace yau burina xai cika akanki MEENAT
Baccinnan daya 'daukeki xaikai awa uku kan yasakeki kan lokacin nayi abinda Xanyi nagana

Nan yacire kayan shi dagashi sai gajeran wando da singilet
Yana quqarin cire mata nata ne tabu'de ido Yace hakuri xakiyi MEENAT shekarata biyu inajiran wannan ranar taxo min akanki.
Toyau dama tasamu xanyi amfani dake

Cinkin rashin qarfin jiki tahanka'deshi
Yasaki dariya Yace baxaki iya komaiba Wlhi
Yada'da cakumota.....
qoqari tayi taha'da qarfinta gabaki 'daya cikin shammatarsa ta'dauki wannan fulet 'din tamaka masa akai
Aiko nan yayi saurin saketa da kwalla qara dan jinine ya 6allemai  saiko jiri daya fara ibanshi



Nan yaxube sumamme
Ahankali ta'dau jakarta da wayanta tana tafiya tana layi. Dan kallo 'daya xaka mata kagane 'Yar mayece danganin yanda take tafiya

Hartafita daga gidan tadinga tafiya
Ananne baccin yaci qarfinta Amma takasa tsayawa waje 'daya

Basaiga Nawas ba  yaxo kar6ar wasu takaddu gun wani abokinsa 
Kawai yaga MEENAT Cikin wannan hali yayi farking Cikin sauri yafito
Yace yadai MEENAT
Ta'dan kalleshi tace bacci..
Yace bacci... 'Dagamai kai tayi
Nan yakama hannunta yakaita motarshi Yana mamakin dama MEENAT ma tana shaye shaye
Yatada motar saikuma yafara tunanin yakaita gidansu ko yakaita gidan shi tasamu nutsuwa
Nan yabi shawarar xuciyarshi yakaita gidanshi. Wanda yake hutawa da 'yan matansa

Lokacin baccin yaci qarfinta 
Shinema ya kinkimeta yakaita falan  nashi


Ya xauna kawai ya xuba mata ido
Shidai yana matuqar San MEENAT yana addu'ar Allah yasa taxama mata agareshi


MEENAT ko saikusan bayan isha tafarfa'do

Shuru tayi tana naxarin 'dakin. Juyawar daxatayi tayi ido hu'du da Nawas
Yace sannu ko
Shuru tamai Amma taqi 'dauke idanta akanshi

Yace wata kwaya kikasha
Nan tatashi xumbur Tace meyakawoni nan yaba labarin yanda yaganta

Nan tahau tunanin abunda yafaru
Tafashe da kuka tace yacuceni
Nawas yace wanene
Takalleshi
Tace inasan kakaini gida yanxu 
Ba musu Yace toh muje
Ta'dau Jakarta da wayanta. Shinema ya rufa mata gyalanta
Suka shige motar...
Yajata



Suna tafiyanne Nawas Yace ashe kemah kina shaye shaye.
Tace hmmm banayi Yace Amma naganki Cikin maye.
Cikin qosawa da xancan nasa Tace kwayar bacci wata qawata tasamin a drink Yace Amma ko bata kyautaba. Tace barni dashi dan wlhi sainaci bura ubansa.
Yace suhanallahi. waye haka
tajah tsaki tace qawar tawa Yace shine kika kirata da namiji.
Ta gallamai harara dacewa tambayarka ta'ishenifah koba'a mantuwane
Yace Allah yahuci xuciyarki gimbiyata
Bata kulashiba

Ya parka motar tashi kofar gidansu. Tafito abinta xata shige gidan nasu Yace gimbiya tah.
Tace inajinka Yace gobe inxo. Tace aa
Tashige

Gabantane yafa'di dan saiyanxu tatuna mexatace dan tasan xa'a tambayeta daran da takai. Tajah tsakin baqin ciki tashiga falon duk sunanan

Mamah tace saiyanxu. Tace natsaya......
SafiYYA tayi saurin cewa kuntsaya hira ko.
Tayi saurin cewa eh
Tashige bet room 'dinsu. Dan ganin mugun kallan da ALIYU yake jifanta dashi

Alwala ta'dauro tayi sallar magriba da isha'i
Tayi addu'ointa da karatun Qur'ani
Sannanfah tahau kuka Ashe dama haka namiji yake
Duk irin sanda take nuna masa Ashe shi manufarsa dabance akanta
Tashi tayi tafara safah da marwah a'dakin
Jitayi ta tsaneshi tsana metsanani

Abaiyane tace narantse da Allah saina baqantama rayuwarka Ahmad. Saikayi dana sanin yaudarata arayuwarka.
Tabbas makircina xaifara akan mahaifinka......
Tana fa'din haka tashige wanka. Bayan tafito tashafa turarukanta tasaka kayan baccinta. tabi lafiyar gado ko abinci bata nemaba.



Koda su sadiya suka shigo bayanda basuyi da MEENAT tamusu maganar gidan amarya ba Amma taqi kulasu.
SafiYYA tace lafiya dai. Sadiya Tace wayasan mata.
SafiYYA Tace baxakiyi magana bah. Tsaki Sadiya tajah tace iskancin natane ya motsa dallah barta 'yar iska.
Suka gyara kansu suka kwanta suna 'dan hirarrakinsu
Duk MEENAT najinsu


Washe gari a hanyarsu tadawowa daga skull
Salmah tace yauwa MEENAT meya sami Ahmad akai naganshi da safe kai afashe duk idanshi yafa'da.
Tace oho nima bansaniba
Nusaiba Tace kamar yaya baki saniba. Tajah tsaki batace komai ba
Ameera tace anya kinji Wanda aka ambata.....
Takatseta da cewa
Ina Ahmad
Da mamaki har suna ha'da baki wajan cewa shiiii
Tace niyanxu ba budurwarshi bace natsaneshi ko maganarshi banaso plx karku qaramin maganarsa. Idan nasami wani gwanin masoyina xansanar daku
Meya ha'daku. Salmah tace
Tace kawai yanxu bana sanshi shine kawai
Nusaiba tace da dalili Wlhi
Ameera tace kodai kinganshi da watane
Dasauri tace eh nikuma banasan yaudara
Tace yanxu haka ba budurwarshi bace
Tace komah miye tashi canyasani
Salmah tace Amma ko kenaki kishin na musammanne
Tace aiko

Jefar da jakarta tayi
Taje dining tafara cin abinci
Tana cikin cine SafiYYA tace yanxu Yah ALIYU yashigo nemanki
Tace menayi kuma tace ina xansani bayan kinsan basai kinyi abuba yake nemanki
Shuru tayi har takammala
Tayi wanka da canja Kaya tayi shashinsu

Tana shiga falan sukayi ido hu'du da Lubba
Takauda kanta tace naxo gun yayah ne tace baki iya gaisuwa bane
Tace saikin koya min
Cikin mamakin rashin kunyan da yau takesan mata Tace baxan koya miki bah dan gaida nagaba agida ake koya wajan manya da'alama bakiga anayiba.
Murmushi MEENAT tayi
Taleqa ko'ina bata hango ALIYU bah
Sannan Tace mata
Eh kam agida ake  koya.
Gwarani gaisuwace ban'iyaba
Amma ke kwata kwata bakiyi dacan tarbiya ba iyayanki basu karantu tafannin karatun mahammadiya ba.
Shiyasa kike furta xancan 'yan jahiliya Wlhi kije kikoyo tarbiya ko xaki iya furta kalma maikyau.

Cikin fusata Lubba tatashi tafalleta da mari
Aiko MEENAT ta'da hannu xata rama taji motsin ruwa a bet room "din ALIYU Cikin toilet
Tasauke hannunta tace Wlhi xanrama marinnan Amma sai yayah yafita.

Tace ni Lubba xaki mara.
Kokulata MEENAT batayiba tashige 'dakin ALIYU.

Har kusan minti goma baifito daga toilet din ba tafara gajiya da xaman
Can tahango laptop 'dinsa

Aiko tajanyota tahauyimai danne danne.
Ita dai aniyarta game take nemah.
Amma kash
Ta'asa tamishi dan magana suke akan wani business wanda yakesan fa'dawa ciki.
Yakai kusan wata uku yana neman sani akan business 'din  wanda saiyau yasami yanda yakeso
Yace aturo mishi pix "din kayan da bayanan da yakeso
Toh shigarshi toilet akaturo miki
Gashi MEENAT ta6ata Komai Sam laptop 'din taqi gaba taqi baya
Cikin tsoro tarufe laptop din
ta'ajiye inda tagani  kenan yafito.

Tayi kif kif da ido narashin gaskiya.
Yace me kikamin baby Tace Allah Wlhi narantse maka banyi komaiba
Ya qura mata ido tare da 'dan dube dubensa  baiga dai komaiba.

Cikin tsoran karya ankare tace wai kaje nemana
Yace dama inasan kishirya xamu koma jibi.
Inasan namiki siyayya
Duk da atsorace take hakan bai hanata  tadaka tsalleba Tace inshirya yanxu Yace eh harxata futa Yace xonan. taje ahankali
Yakama fuskarta Yace wakikama lefi ya mareki Tace hmm amm Kawai na.....
Yace Jeki kawai
Tafice da sauri tana murnar xasu koma.
Dan dama sati 'daya sukeyi
To wannan karanma basukaiba
Murna take xataci karanta ba babbaka. bataga Lubba afalanba tafice abinta

Shiko ALIYU zama yayi yajanyo laptop dinsa. Me xaigani 6arnar MEENAT
Yaxare ido Yace
Innalillahi baby......


Dafe kansa yayi yana naxarin MEENAT
Yayi shuru
Can ya tashi ya kintsa kansa. Tare da 'daukar wayoyinsa da key 'din motarsa yafito
Afalo yaga Lubba
Tace my d kafito
Yace eh xanje supermarket yima Su baby siyayya kinada wani abunda kikesone
Tace no
Amma tare xuje  ko Yace no nida baby xamu
Tata6e baki tace toh muje tare Yace bance ba.
Yana fa'din haka yafito xuwa falonsu mamah

MEENAT ko harta manta da 6arnar data masa  tashirya tsaf da ita. Cikin doguwar riga baqa me ratsin jaaa
Tayi kyau sosai
Zainab qanwarta tace ga yayah can Yana jiran Ki
Tace toh
Nan tafita tanama SafiYYA gwalo wai wannan karan da ita ka'dai Ya ALIYU xaije siyayyar.

Afalo ko taganshi suna 'dan magana da mamah. Sam bai kalleta bah. Yace
Taje mota tajirashi
Tafita tana cewa aranta kadai kusa tafiya inhuta.

Sanda tashiga motarne bayan ta'dan nutsu tatuna da 6arnar da tamasa gabanta yafa'di
Can kuma tace qila bai ganiba da yabini da harara kan ya 'dau.....
Saiji kawai tayi ya shigo motar .

Suna fitowa waje taga dadyn Ahmad.
Aiko tabishi tawani sirrin kallo.
Ya washare baki yana kallanta. Sam ALIYU bai luraba
Tacije baki ganin sunyi nisa. Ta'dan kalli ALIYU ka'dan
Aiko suka ha'da ido ya gallah mata harara
Yace uban wa Yace kita6amin laptop
Me makwan tabashi amsa
Sai tafashe mai da kuka
Bai mata magana ba sanda yayi faking a harabar supermarket 'din
Yace Wlhi ko kimin shuru kona fasa bakinki yanxu
Ai kamar anyi ruwa ancinye MEENAT tayi shitttt



Yaqara 6alla mata harara. Tace kayi hakuri Wlhi baxan.....
Yace furucin kenan kullun baby
Baki gajiya da Wlhi baxan qara bah
Nikenan duk abinda nakeso saidai nayi hakuri dashi inhar kika ta6a
Tace Wlhi baxan qaraba
Yace yayi kyau muje
Haka suka shiga ta'ibi abinda takeso. Da ibamma su  sadiya.

Sunfito ne taqara ganin dadyn Ahmad
Abin ya bata mamaki. Haka yadinga kallanta itama tana kallansa
ALIYU ya daka mata tsawa da cewa tsayuwar me take
Nan taseta nutsuwarta tashige mota tana tunanin Ashe sun'dau lokaci  suna kallan juna


ALIYU nayin parking Yace Wlhi baby idan naqara ganinki da wani kina ta'di saina karyaki.
Watanni shidda xanyi wannan karan nadawo
Dan haka kikulamin da kanki
Takalleshi
Ya 6allah mata harara Tace toh
Ta'ibi kayan da fita
Yajuya motar yaqara ficewa
Tace ko ina kuma xai qara xuwa oho
Nan tashiga ta'ajiye kayan afalo da sauri tayi gun Lubba
Bataga ganta afaloba  dan haka tayi hanyar kitchen
Nan taganta tana Wanke hannu
Aiko cikin san'da taqarasa da shammatarta tadallah mata mari
Mamaki yakama Lubba tatsaya kawai tana kallanta
Tace dama nagaya miki saina rama Marin da kikamin
Bana yafe abinda nafurta
Tajuya xata fita
Cikin xafin nama Lubba tayi yun'kurin cafkota
Amma ina MEENAT ta ankare da hakan
Nan tafalle da gudu
Aiko Lubba bata fasa bintaba
Dan MEENAT na gudu tana binta
Har sukaje 'dakin Momy
Dan MEENAT batayi gigin xuwa 'dakin mamah ba dan tasan ranta 6aci xaiyi

Momy tace lafiya
Lubba tace bata da kunya Wlhi  Momy mari nafa tayi
Da sauri Momy takalli MEENAT Tace mari
Tace Wlhi ba gaskiya bane Momy cewa fatayi wal ban iya gaisuwa.....
Momy takatseta da cewa bata hakuri kawai
Ko musu MEENAT batayi bah. Takalli Lubba tace yi hakuri
Kwafah Lubba tayi tafice


Misalin qarfe biyar na yamma
Tana xaune ita da Nusaiba nusa jin waqar m shariff
Kallo 'daya xakama MEENAT kagane tana Cikin farin ciki

Qanin Salmah yashogo Yace mata taje
Tace inji wah Yace Ahmad.....
Ai MEENAT batasan lokacin data miqe xumbur bah. Ta'dau gyalanta ganin tatashi da sauri shiyasa Nusaiba tabi bayanta

Suna ko fitowa taganshi tsaye har'de da hannu
Yace kimin afuwa dan Allah MEENAT akan abinda yafaru tsautsayine da sharrin she'dan
Tace koh
Yace yah
Tace Amma banta6a ganin 'dan iska kamarkaba
Yace habah MEENAT tauraruwar mata
Nur me haskake mata
Juyawa tayi xata tafi yakamo gyalanta
Aiko tajuyo tatsinka mishi wani lafiyayyan mari
Tace natsaneka Ahmad bana sanka bana kaunarka
Wlhi bana san kallan mummunar fuskarka idan kaqara kuskuran ta6a gyalena
Wlhi merabani dakai sai Allah
Mayaudari 'dan iska fasiqi
Tana gama fa'din haka taja mugun tsaki tayi shigewarta gida tabarshi baki saki

Nusaiba data gama jin komai
Tace gaskiya MEENAT kirage kishi
Tace Wlhi ba kishi bane yasani mishi haka
Hasalima niban ganshi da mace bah kamar yanda Nace muku.
Tace tome ya ha'daku kikamai wannan wulaqancin
Tace kawai share dan tunowa mah qara 6atamin rai xaiyi
Shuru nusaiba tayi kawai tarabu da ita.

💦💎💦
Yau murna kawai MEENAT takeyi dan  yanxu haka tafiya ALIYU xaiyi shida matarsa Lubba America inda yake aiki
Su Momy da mamah sai fatan alkairi suke masa dasu Abbah
Hamisu ne da Aminu xasumai rakiya
Yakama hannun MEENAT cikin qasa qasa da murya yanda bawanda xaijishi sai'ita Yace sai murna kikeko Tace aa Yace toh Inasan kimana  rakiya
Tace toh
Lubba tashige motar Hamisu tana cika tana batse tare da jifan MEENAT da mugun kallo
Meenat ko ta6e baki tayi tashige motar Aminu dan nan shima ALIYU ya shiga
Suka tafi airport

Bayan sunkaine Aminu yafice daga motar da alama wayan shi yakesan amsawa

ALIYU Yakama hannunta. Taji zirrrrr Yace baby tace na'am Yace kitemaken karki kula maxa tace Allah baxan kula kowa bah
Yace Wlhi naji labari Xanyi mummunan sa6a miki
Tace baxan kula kowa ba Allah
Yace gud my luvly baby
Kasan cewar gilashin motar me duhune
Ya kama fuskarta yayi mata kiss agoshi. Ta lumshe ido
 Hakan bai masa ba sanda ya'dan mata abaki sannan ya saketa
Tabu'de idanta tace Allah yadawo daku lafiya
Yace tnx. yafita
Kasa fita tayi
Tayi lub amotar
Ahaka har Aminu yashigo motar Yace karkimin bacci amota a'dauka satoki nayi
Ta bu'de idanta ahankali
Tace tafiya xamuyi Yace da xama xamuyi
Shuru tayi ahaka harsuka iso gida

Tahango dadyn Ahmad yana xaune yana karanta jarida
Tace ya Aminu saukeni anan basai kashiga gida bah  hakako ya tsaya tafita yashige abinsa



Direct wajanshi tanufa ya fara Murmushi
Har qasa tadurkusa tagaidashi tana wani fari da ido
Yace Aminatu
Tayi Murmushi cikin sanyin murya da shagwa6a tace
Dady nifa sunana MEENAT......
Saura ka'dan jaridar hannunshi tafa'di dan ya rikice da kirsarta
Yace to to to MEENAT
Tarausayar da kai tace bara nashiga gida dadyna  dama natsaya gaida Kaine.
Yace baxaki tsaya mu'danyi hiraba
Tayi Murmushin samun nasara
Tace dadyna
saidai da daddare dan yanxu karatu xanyi
Yace yauwa MEENAT kishirya kar6ata kinji
Tatashi dawani irin juyi ha'de da yarfe hannu Tace toh
Yace qarfe nawa kikesan naxo. Tayi fari da ido tace bayan isha'i
Yace gud MEENAT.
Tatafi tana tafiyar ahankali harta shige gida

Tana xuwa room 'dinsu wayanta nayin ringing.
Tsaki tajah dan ganin Ahmad ne. Taqi 'dauka.
Can yaqara kira
Tayi Murmushi tace nahucce babinka Ahmad. mahaifinka shine dai dai dani
Haka yadinga kiranta taqi 'dauka
Qarshema kashe wayan tayi


Dareko nayi bayan sallar isha"i saiga xainab qanwarta wai taje awaje
Dama tagama shirinta tsaf da ita. Sai xuba qamshi take. Bakintako sai qamshin kanunfari yake
Taje tagayama Su Momy ankirata sannan tafito.
Yana Cikin mota ya'dan haska wayanshi dan taganshi.  Nanko taganshi taje tashige motar
Tace barka da dare dadyna
Yace barka MEENAT
Tayi shuru
Abinka da babban mutun Yace
Wato MEENAT tunkina da shekara goma Sha biyu Allah ya jarrabeni da qaunarki.
Ina sanki ina qaunarki kitemaken ki aureni
Tayi shuru tana wasa da zoban hannunta
Yace kinyi shuru
Tace hmm toh yaxanyi da soyayyar kamal Yace wanene haka Tace wani saurayinane me sona sosai kuma nima inasanshi
Yace Wlhi duk duniya ba wanda ya kaini sanki kitemaken Ki amince nasameki cikin watannan  agidana
Takalleshi da shagwa6e fuska tace nidai um uhmm
Yace dan Allah dan Annabi tace toh toh sainayi tunani
Yace toh yaushe Tace nanda sati 2
Yawaro ido sati biyu Tace eh
Yace kinasan akaini asibiti ne tace aa Yace toh inbakyaso kibani amsa gobe kuma idan kikace baki sona mutuwa Xanyi
Batasan lokacin da takalleshi da fashewa da dariya bah Yace Allah
Tace toh xanje sai goban dan bacci nakeji. Yace toh Amaryata abani number dan nakira idingajin lafiyarki
Nan Ta bashi  da shigewa gida



Bayan tayi shirin kwanciyane
Sadiya tace 'daxo tafiyanki rakiyar ya ALIYU  Anisa qawarki taxo 
Tace kash naso ganinta Wlhi
SafiYYA tace aigobe xataxo wai
Tace saifah wai
Dan mijin tannan dagani kulle xaiyi
Dariya Sadiya tayi tace har kintunomin da yah ALIYU da Aunty
Ita gasan yawo shikuma takura
SafiYYA Tace hmmm aishiyasa yake disfulata.
Sadiya Tace danma yana santa shiyasa ahakan yake raga mata
Gaban MEENAT yafa'di
Kuma bawani abu bane ya fa'dar mata da gabanba kamar yanda Sadiya tace danma Yana Santa...
Tajah tsaki da cewa plx dan Allah kubar hirarnan banaso
SafiYYA Tace dan anta6o dodonki
Sadiya tace shareta Wlhi baxamu bariba

Daukar wayanta tayi daje 'dakin Momynta. Bata ganta bah dan tana 'dakin Abbah
Tahaye gado....
Wayanta tayi qara Ahmad ne
Ta'dauka da cewa lafiya kake damuna
Yace haba MEENAT
Na'dauka idan nayi kuskure akanki xakimin afuwa dan akwai qauna metsanani a tsakaninmu
Tajah tsaki
Tace nalura kai 'dan rainin hankaline Amma bari namaka kat yau.
Na tsaneka.
Wlhi banasan kaganinka
Qaunar da kake magana Wlhi Ahmad tajuye tsana
Namaka alqawari daga Kaina baxaka qarayin yaudara bah
Wlhi idan kaga yaudara guduwa xakayi dan saina cusa maka tsoranta
Kuma maganata taqarshe dakai shine idan kaqara kirana xanmaka xagin dahar kamutu baxaka ta6a mantawaba.
Idanko kayi saken da katareni ahanya hmmmm
Takatse wayan nashi dan taga wani number na kiranta ta'dauka
Da sallama
Nawas Yace ran gimbiya ya da'de tace ha'de da naka
Yace kinyi mamaki ko
Tace aikowa dai
Yace Ameera ce taban number tace nasani
Yace Ki aminta dani mugina soyayya da qauna kixoma uwar 'ya'yana


Tayi Murmushi wanda saida yaji sautinshi Tace banasan na yaudareka. dan ina da wanda nakeso....
Yayi saurin katseta da cewa naji Amma kibani dama intusa sona axuciyarki dan Allah
Tace Nawas
Yace na'am Tace kanada naci Yace Wlhi bakiga komai anacina bama
Indai akankine haka xandameki da nacin harsai kin xama tawa
Tace nabaka dama Nawas. Allah ya tashemu lafiya bacci nakeji.
Cikin murna Yace I luv u nagode
Tace luv u 2
Takashe wayan

Har tagyara kwanciya
Kiran wayan ALIYU yashigo
hakka kawai gabanta yafa'di
Ta'dauka Yace my baby...
Wani zirrrrrr taji. Cikin kasala tace na'am
Yace dawa kike waya tun'daxo tace da Salmah ne fah
Yace baby
Tace Allah yayah
Yace banyarda dakeba
Tace toga inba Momy kaji gaskiya
Yace no Amma Wlhi kikula da kanki Tace toh
Saiya kashe wayan
Ajiyar xuciya tajah
Tace dakace naba Momy yaxanyi


Washe gari bayan tadawo daga skull dadyn Ahmad yakirata awaya yana tambayarta yadai Tace ta'amince yaxamo miji agareta.
Baqamin murna yayiba yadinga samata albarka
Yace ina waje inasan ganinki yanxu.
Cikin shagwa6a tace nidai saigobe Yace haba Amaryata tace toh ganinan Yace yauwa farin cikina

Murmushi tayi wato shidai namiji baya tsufah indai tafannin macene


Tofah😳
Soyayya me xafi tashiga tsanin MEENAT da dadyn Ahmad
Inda MEENAT take rikitashi da salanta
Ga Nawas ko
Shima soyayya take dashi sosai

Duk abinda yake faruwa Ahmad bai saniba bare "yan gidansu 
Haka gidansu MEENAT mah
Dan sirrin tatciyar soyayya sukeyi ita da dadyn Ahmad


Toyau tadawo daga skull agajiye
Cikin farin Cikin yau sungama SS:3
Saijiran sakamako

Bayan tayi wanka da cin abinci
Su Abbah suka kirata. Taje
Abban ALIYU Yace Alhaji barau yamana maganar kin yarda dashi xaki Aure shi   hakane
Shuru tayi


Yaqara maimaita xancan  tace eh Abbah
Abbanta Yace kinasan shi kenan tace eh
Yace to madallah
Yanxu yau xamu kar6i sadakinki. Kuma bawani jinkiri xa'ayi bah wajan saka bikin. Tayi shuru
Yace jeki Allah yamiki albarka Tace AmEEn
Tatashi tafita
Abban ALIYU Yace ikwan Allah yanxu Alhaji barau takeso Abbanta Yace eh ai abin yaban mamaki
Saidai sha'anin 'dan yau


Itako tana xuwa 'dakinsu tajuyema Su SafiYYA Komai
Mamaki da al'ajabi ya kamasu. SafiYYA Tace Amma ke 'yar iskace cikakkiya
Sadiya tacafke da cewa
Kiso 'daa kiso uba me kike nufi
Tace plx karku xargeni dan Allah
Sukace toh fa'da mana meyake faruwa.
Nan takwashe yaudarar da Ahmad yamata tafa"da musu

Da al'ajabi kam. Lamarinki da Ahmad
Amma nayi mamakin yaudarar da yayi miki duk san da kike masa
SafiYYA ce  mai wannan furucin

Sadiya taja numfashi Tace Amma dakin mishi afuwa kinfasa auran Ubansa 
Tace Wlhi saina aure shi......
Wani xaxxafan mari ne taji wanda yayi awan gabah da xancanta
Tayi saurin kallan wanda yabata marin Ashe  mamah ce
Tace dan ubanki a'ina kika ta6a ganin budurwa tayi soyayya da "da tadawo kuma tayi da ubansa
Tace Wlhi mamah ko kasheni xakiyi ni dady nakeso
Kuma Wlhi inbaku bani shiba mutuwa Xanyi
Tace kimutu mana
Ina tsoran miki shiga gidansa dan makiran matansa sunfi qarfinki
Baxai ta6a yuhuwa Ki auresa bah nagaya miki
Aiko tafashe da kuka tace nidai inasansa
Momy da tace toyi shuru Autata kamar kin auri Alhaji barau kingama
Tajuya da kallanta kan mamah tace addu'a xamu mata kawai
Dane mam mata tsari akan dukkan kowane sharri kuma mah kinsanta da ibada da addu'a Allah xai kare mana ita
Mamah Tace toh Allah ya shige mana gaba tace AmEEn
Suka fitah

Sadiya tace anya MEENAT ba addu'a yayi miki bah
Tace kome yayi nidai shinake soh
SafiYYA tace harna farajin tausayinki agidan Wlhi
Tace toh kidena. Badai sun dogara da boka da Malam ba
Toh ni da Allah subuhanahu wata'ala na dogara


Koda MEENAT taha'du da qawayanta Salmah Nusaiba Ameera
Nan tafa'da musu Auranta da dadyn Ahmad
Xaro ido sukayi
Ameera tace ke MEENAT kiraba kanki da auran sah

Muje xuwa



Tace tab aikin makara ina sanshi
Nusaiba tace babbar magana shin da hankalinki xaki shiga gidan kurkuku
Tace kwarai
Salmah taja numfashi tace Lalle tunaninki ya gushe Wlhi
Kiso 'da da uba
Tace tosaime wai akaina akafarane
Sukace aa. Munadai jiye miki makircin matansa ne
Murmushi tayi ta girgixa Kai da cewa
🅰ⓂAKIRCI NA xanbi dasu yanda yadace.
Namuku alqawarin saina baku mamaki
Hmmm


Anisa ce tadafa MEENAT tace menakeji wai
Tace abinda kunnanki  suka jiye miki xan auri Alhaji barau mahaifin Ahmad
Xama anisa tayi tace bala'i
Inatabbatar miki wata rana saikin jefa kanki Cikin bala'i Tace ina addu'a Allah kuma xaikareni da yardarsa
Plx kudena tsorata da Matansan  nan dan Allah
Anisa xatayi magana Tace plx mubar xancan ya sirikarki
Tace tananan da halinta Amma ta'dan rage dana bi xancanki
Tace bana gaya miki bah
Kuma kidage da mata ladabi da biyayya da kirsar da kikasan inkinbi kina samun kanta
Anisa tagyara xama tace lamarinki MEENAT naban mamaki. Naga baki karance karance sai tsabar jin waqar UMMAR M SHARIFF Amma Kinsan kiss da makirci kala kala
Tayi dariya Tace Anisa kenan ai abin ba daganan yakeba.
Daga kwakwalwane
Kinga naji mijinki yaja miki kunne akan karki da'de dan haka ya kamata kitashi kitafi badan nakoreki ba
Tace Ashe la6e kika tsaya yimin a soyayyata
Tace aa
kinsan dai wayarki 'yar tonan asirice ya kamata kirage volume 'dinta dan inda ni kishiyarkice dana da'de da kwashe kalmominki na soyayyarki na ha'da danawa inkwace miki miji
Tace tab😳.
aiko rage volume ya kamani tafa'da tana me miqewa 
Nan tama Su mamah sallama MEENAT tarakata tatafi
MEENAT tadawo.
Tana xama ya ALIYU yakita
Tarasa dalilin dayasa gabanta yake fa'duwa idan ya kirata
A'da'dare ta'dauka

Yace baby gabana yana bafuwa akanki me yake faruwa  Cikin in ina tace hm am Bakomai yayah Yace kin tabbata Tace eh
Yace fa'damin
Cikin tsagwa6a tace toh mene
Yace kina tunanina 
tace eh sosai mah
Yace har wajan ba bacci

Tace eh
Kuma Allah yayah nayi missing 'din muryarka
Yace toh naji kikula da kanki tace toh
Nan ya kashe wayan
Taja ajiyar xuciya
Da gaske ne MEENAT batajin da'din  muryar kowa saina yayanta ALIYU
Haka duk duniya bawanda takejin wani yanayi akansa kamar shi
Idan taganshi jikinta mutuwa yakeyi
Barinma idan yakai hannunshi jikinta. Ya rungume  Jitake kamar su dauwama ahaka

Bayan Alhaji barau yakawo sadakin MEENAT kwata kwata biki wata 'daya aka saka
Inda kuma hankalinta yatashi dan Nawas yadameta da soyayyarshi
Ta tabbatar da San gaskiya yake mata
Ashe yana dah mata wai ita Suwaiba

Kamar yau SafiYYA da Sadiya suna wajan shan iska gidan agefe. Yayinda da MEENAT da Nawas suma suke gefe axaune suna hira ita dashi
Yace Wlhi MEENAT sanki yana wahalar dani tace Nawas kenan karage sona dan ankawo sadakina
Yayi Murmushi yace wasa kenan
Tace Allah Yace banyarda ba plx kideba fa'damin mummunar magana irin wannan
Tace Allah ya hucci xuciyar 'dan Autan maxaje Amma bana mah jama"a qarya dan konayi sainadawo nafa'di gaskiya
Ya ALIYU ne ka'dai nakema qarya
Yace naji mubar xancan Ganin da gaske bawai ya yarda bane yasa tayi shuru da bakinta tana cewa aranta kaji a salansa

Tafiyarshi da minti biyar saiga
Wata mata tashigo gidan
Direct gunsu SafiYYA tayi cikin fusata
Tanuna Sadiya da yatsa Tace inaja miki kunne akan kifita daga harkar mijina koki fa'da kicin masifah da bala'i 'yar iska kawai karuwa kije kinemi sauri mana Amma kyaxo kinememin miji.
SafiYYA tatashi Cikin jin xafin kalmominta Tace ke kuma 'yar gidan uban wacece
Xatayi magana aiko saijin saukar Mari taji
Cikin mamaki tajuya dan taga wanda yamata wannan marin.
MEENAT CE tabata Marin tace kekin'isa kin'isa kishigo gidanmu kixagi yayata harda cemata karuwa gaki kalar karuwai jahila dabbah
Ina shawartarki kibar gidannan tunkan inxaneki
Ta'daga hannu xata mareta  SafiYYA tariqe hannun tace karki soma munada 'yancin mudakaki
Tsaki MEENAT tajah Tace dakin barki tajaxama kanta bala'i
Momy tafito danjin hayaniya tace lafiya
Sadiya takwashe Komai tagaya mata
Tace baiwar Allah kiyi hakuri xata rabu da mijin naki
Tace dako tama kanta gata dan Wlhi ni Suwaiba ba 'yar iskar da ta'isa tashigomin gida
Tadawo da kallanta kan MEENAT. Kekuma karki xaci marin da kikamin kinyishi abanxa Wlhi saikinyi nadama dan tunda nataso da wayona banta6a shan mari hakaba  Wlhi xaki gane kuskuranki
Dariya MEENAT tayi Tace koh
Ba shakka Amma xanso ganin wannan ranar. Nikuma namiki alqawarin kafin.....
Sanin halin MEENAT yasa Momy tayi saurin rufe bakinta tace tafi abinki xata rabu da mijinki
Kwafah tayi xata tafi
SafiYYA tasha gabanta tace saikin gaya mana wane wawa ne mijinki
Saiyanxu tayi dariya tace wawane kam tunda nida yayarki muna san shi kinga ni ina Auran wawan haka kuma  yayarki takama wawan saboda rashin mashin shini
Sunansa Nawas dan idan ke baki sanshiba ita tasanshi
Sadiya takalli SafiYYA
SafiYYA takalli MEENAT
SafiYYA tasheqe da dariya tace keda ita kundace. Gaki masifaffiya kuma wacce kikaxo gunta tafiki bala'i
Suwaiba Tace bata isa tafini bala'i ba
MEENAT tace kasan cewar nida yayata muna kama shiyasa tasha marinki
Amma nice MEENAT budurwar Nawas
Da sauri Suwaiba takalleta tace eh tambas biri yayi kama da mutun Wlhi ba'abinda xai hanaki yin nadama akan soyayyata. Lefi biyu gareki aguna nabarku lafiya tafita furrr

Momy data xama 'yar kallo Tace Allah ya kyauta tashige abinta


MEENAT tadafah SafiYYA tace gaskiya matannan tarainani Amma xannuna mata kuskuranta duk rannan da muka ha'du
Sadiya tace watarana saina 6allaki Wlhi idan har baki dena jamin masifaba
Da axagin mutanan naki natsaya Amma yanxu har takaiga amfara dukana
Tace kiya kuri banso kikayi kama dani bah
tajah tsaki tashige ciki wayar Nawas MEENAT takira
Cikin makirci tace Ashe dama baka gama tsayawa agidan kaba Amma kake neman qarin aure
Yace ban fahimci me kike nufiba.
Tace baxan iya auranka bah. Saboda jakar matarka
Taxo har gidanmu bayan tafiyarka tayimin garga'di harda kiran Aunty Sadiya  karuwa
Saidai nima bam bartaba dan nafa'da mata magana
Kasani daga yau bani bakai.
Kaje kaxama cikakken namiji wanda xai'iya da gidansa
qila kasamu wata tasoka kamarni.
Tana gama fa'din haka takashe wayan gabaki 'daya

SafiYYA tace yadai
Tayi Murmushi tace narabu dashi badan matarsa ko tsoranta ba aa
Saidan dama neman yanda xanrabu dashi nake.
'Dan dukanta SafiYYA tayi Tace sai kuma ga dama tasamu.
Tace Wlhi kuwa cikin sauqi. Tace Amma fah har nafara jin tausayinshi dan nalura yana matuqar sanki tace eh yana sona dan soh Amma kidena tausayin shi dan dadyn Ahmad yamishi nisa
Tace hmm nidai bana sanki dashi
Tace wata rana xakiso
Suka shige ciki
Tana niyar shiga wanka saiga Zainab tashigo da gudu tace Aunty MEENAT ya Nawas nakira
Tace kice masa bananan nafita
Nan tafice tagayamai da rashin jin da'di yatafi
MEENAT da taji tashin motarshi tace Allah sarki Allah yabaka wacce tafini

Yau saura sati 'daya bikin MEENAT da dadyn Ahmad
Kuma har yanxu gidansu Ahmad basu saniba
Haka Ya ALIYU baisani ba dan MEENAT taje gunsu Abbah tace dan Allah kar'a gaya mishi sukace danme Tace ai yaja mata kunne akan karta kula kowa
Sanin halin 'yar tsamar da suke ita dashi yasa Su cewa shikenan in anyi afa'da masa


Tafiya suke Cikin yanga da jin gayu  MEENAT da Ameera da Nusaiba dan xuwa gidan Anisa
MEENAT tace kunsan ya ALIYU. Bai saniba Nusaiba tace aiko xaki sani Tace a'ina
Bayan ina gidan mijina.
Ameera tace kumafah
Ganin sun'iso gidan MEENAT Tace inmunshiga muma matarnan ladabifah
Sukace ke karki damemu
nan suka shiga gidan.

Aiko da inna sukaci karo takafah tatsare
Nan suka durqusan suka gaidata
Tafara fara'a tana kallan MEENAT tace angaisheku yaran kirki
Suka shege shashin Anisa

Tsallan murna tadaka daganinsu Cikin murna Tace kunyimin baxata
MEENAT tace ai baxata tukunna mah dan bikina saura sati 'daya
Cikin mamaki da tsoro Tace dan Allah
Nusaiba tace Wlhi  dagaske
Tace dawa Ameera Tace Alhaji barau mahaifin Ahmad
Tace innalillahi Ashe haryanxu xancan nanan
Ameera tace aisai abinda yayi gabama
Tace Allah ya kyauta miki MEENAT dan Wlhi Sam hankalina bai kwanta akan auranki dashi bah
Tace toh naji mubar xancan......
Inna CE tashigo da waina da miyar tantakqashi ahannunta direct gun MEENAT tayi Tace 'Yar albarka gashi ciki
Da murna sosai da jin da'di takar6a tace sannu Allah yasa  tafice
Nusaiba Tace yaushe kika saba da matarnan Tace hmm ha'din Allah Ameera Tace saifa ha'din Allah
Anisa tace Ni mamaki yahanani magana
Dariya MEENAT tayi Tace toh yabarki kiyi
Nan suka ta6a hira sosai
Suka bata ankon  MEENAT da sweet 'dinta
MEENAT Tace banajin Xanyi wani abu banda walimah saboda kasan cewarshi Babban mutum
Anisa tace hmm aifah sai haka dan holewa da tsowo bacin raine
Cikin Takaici MEENAT tatashi da 'daukar jakarta tace nalura so kike ki6atamin rai akan mijina kinga tafiyata. Nusaiba Tace xaidai xama mijin naki
Ameera tace tsayamu mana. Bata tsayaba tafice tanayima inna sallamah




Da sauri suka biyota Anisa nacewa koxaki mutu saina fa'di gaskiya

Ahanyarsu ne Ameera tace tambayar ya maganar Nawas
MEENAT tata6e baki tace nabarshi mana
Nan takwashe yanda sukayi tafa'da musu
Taqara dacecwa Wlhi bakuga yanda yake sintiri agidanmu bah. Amma Sam bana futa
Sukace dadyn Ahmad yamishi karantsaye
Tace aikowa dai

Cikin qaddara saiko suka ha'du da Nawas 'din
Yace dan Allah MEENAT kiyi hakuri naja Mata kunne baxata sakeba
Kicin rashin sanin abinda xatace mishi tace gaskiya xuciyata bata hucce bah kabari intahucce xanne meka
Yace naji Amma kidinga 'daukar wayata Tace saina huce fah
Yace haba MEENAT
Tace toh
Yashige motarsa yana kallanta
Bayan yayi nisane tace saidai kayi hakuri masoyina
Tsaki Ameera tajah. Nusaiba Tace Allah sarki Wlhi yaban tausayi



Yau aka 'daura Auran Alhaji barau da Amina MEENAT akan sadaki dubu sittin
Kayan lefe akwati seti 'daya da sauransu
Komai anyishi Cikin tsari

 Saidai tashin hankali yafaru lokacin 'yan uwan MEENAT suka shiga gidansu Ahmad shashin dadynsa dan zubama MEENAT Kaya matan biyu sukace basusan da xancanba
Xance yaje kunnan dadyn Ahmad Yace shiyace musu saiyi aure sukace aisun 'dauka xolayace dan cikin wasa yagaya musu kuma dada 'dewa
Yace aise suyi hakuri
Shuru sukayi tare da mamakin  baxatar da yayi musu

Ahmad ko dayaji dadyn shi MEENAT ta Aura baqaramin tashin hankali yashigaba
Yace axuciyarshi Lalle wannan 'yar iskar yarinyar  tacika makira


Amarya tasha qamshi har tagaji
Jikinnan yayi lu6o lu6o kamar na jinjiraye
Ba'a maganar kyau dan tahucce gun tako ta'ina




8:00pm
Misalin qarfe takwas har lokacin gidansu MEENAT cike yake da mutane
Su Sadiya sai shirin kai Amarya MEENAT suke.



Anisa tace yau tsoho xaihau saban gado
Nusaiba tace kinmanta yanada Amarya bata wani da'deba Tace ke share wannan sunace dan makiran matansa sun 6atata sun hanata sakewa Sam taxama abin tsusayi.
Salmah Tace hmm aigidannan baiyiba.
Toh gashinan dai xa'akai musu me makircin xamani dai dai dasu
Dariya Ameera tayi tace mudaiga tafiya fatan alkairidai gareki MEENAT.
Tanajinsu tayi shuru dan ganin miss call 'din Ya ALIYU data gani
Tana qoqarin kiransa
Kiranshi yashigo
Gabanta yayi mummunan fa'duwa tadai 'dauka a 'da'dare
Yace baby....
Tayin saurin katseshi da cewa Wlhi yayah auran dole sukamin Allah nabi umarninka ban kula kowaba kayi hakuri taqarashe maganar da fashewa da kuka
Cikin rikicewa Yace what😳
Me kikesan cewa
Tace un am
An 'daura Auranki dawani kome Tace Allah yayah nibance musu ina sanshi bah....
Katse wayan yayi
Tasauke ajiyar xuciya Amma hankalinta 'dan tashe yake akan yayan nata
Galala SafiYYA Sadiya Ameera Nusaiba Salmah sukayi dajin qaryar da MEENAT taxuqama Ya ALIYU

SafiYYA tace kinada munafunci. Saiki gaya mana waye yamiki Auran dole
Tace hmm dan Allah kubarni


Nasiya sosai Momy da mamah dasu Abbah sukama MEENAT
Nan aka shiga da ita gidan Alhaji barau da addu'oi


Direct 'dikin Uwar gida Momy Hauwa sukayi
Nan takar6esu da 'dan sakin fuskarta Amma kallo 'daya xaka mata kagane bata tare da nutsuwarta
Nan suka danqa mata amanarta tace Allah yatayamu riqo

Sukayi shashin  momy kilishi wato mahaifitar Ahmad
Wani mugun kallo tawatsa musu
Sam basu nuna sun ganiba suka danqa amanar MEENAT agareta itama
Tajah tsaki da bar musu gun
Haka sukayi shashin Zainab
Itakam da murnarta tataresu duk da qaramar yarinyace ba lefi tayi aikin manya
Nanma suka gabatar mata da MEENAT amatsayin 'yar uwarta
Sannan sukayi shashin MEENAT
Bashakka ya ha'du sosai
Dan anxuba mata dukiya
Nan suka qara mata nasiya suka tafi
Yarage qawayanta Su Ameera
Tacire gyalan kanta
Anisa Tace toh nidai mijina Yana waje Yana jirana. Ina miki fatan alkairi.
Tace kixauna mukwana
Tace shikuma yakwana dawa
Tace shegiya uwar 'yansan maxa jeki karki 6atamai rai
Tace nibanta6a ganin 'Yar iskar Amarya wacce bakinta yakasa mutuwa irinki bah
Tace Naji jeki.
Futa tayi tana cewa dena korata xan tafi Amma kisani xaki nemeni
Su Salmah sukace toh muma xamu tafi
Allah yabuko hakurin xama
Tace kugaida gida
Cikin mamaki sukace Lalle MEENAT ba'irin mutsaya 'dinnan nakewa da nuna damuwa tace eh
Sukace xakiji wuji wuji xaki nememo 'yar iska
Tace idan naji nanemekun

Tabiyarsu baifi da minti biyuba
Saiga Zainab tashigo gunta.
Yace naxo gaya mishi wani abune
Tace inajinki
Zainab tagyara tace karki bari dady ya kusanceki yau dan xaki shiga bala'i
Tace dalili
Tace idan ya kusance yau ba shakka xakiyi mummunan mafarki akan Momy Hausa da Momy kilishi
Tace wannan shine dalilin daxaisa najama kanna fushin Allah na da tsinuwar mala'iku
Zainab taca hmmm
Kigane man.
Wlhi haka kawai naji sanki araina banasan kicucu ne
MEENAT tajah tsaki tace nagane man
kishi ne yake damunki baxanbi umarninki ba ba kishiyar dana ta6aganin tacema kishiyarta tanasanta saike dan munafunci fitanmun daga 'daki
Cikin mutuqar jiki Zainab tafita

Shuru MEENAT tayi tafa'da tunani
Amma dagaske tahango gaskiya a idan Zainab sedai baxata sake da ita yanxu ba.....

Alhaji barau yakatse mata tunaninta da shigowar da yayi
Yace Amaryata tayi shuru
Kosai nasai baki
Tace hum umm aikawucce gun
Ya matso kusa da ita sosai Yace sanyinki da qamshinki ha'de da shagw6arki suna sani nisha'di
Tayi Murmushi

Yaqara cewa nayi farincinkin kasan cewarki mata gareni
Tace haka nima nayi murnar samun nagartaccan miji kamarka
Yace gud Amaryata
Batare da 6ata lokaciba tashi kiyo alwala muyi sallah
Tace inada alwala
Yace tashi muyi toh
Tace nayifah sallah Yace wannan tagodiya ga Allah ce dayasa muka xama ma'aurata
Tashi tayi sukayi
Bayan sun idarne Yakama kanta yayi mata addu'a da tambayarta yanda ake sarki taba shi amsa fiye da tunaninsa dan ya hango ilimi atattare da ita
To sai me Kuma
Ya'dauko kaxar daya shigo da ita da madara yajera a gabanta
Amma yayi yayi taci taqi
Yace konavaki abakine.
Ta'daga mai kai alamar eh
Kusantota yayi sosai yadinga bata tanaci shima tana bashi ahaka harsuka gaba
Yace bari naje 'dakina nayi wanka dan kyafi ganina dakyau ko
Tace dadyna kenan
Aiko bakayi wanka bah idan kashiga cikin maxaje da mataye haskesu kake dan kyau irin naka
Washere baki yayi cikin jin da'di yafita
Itama tashi tayi tayo wankan da saka kayan bacci masu kyau.

Tana Gaban madubine bayan tashafe jikinta da turare. juyo wannan daxatayi  saitaga momy kilishi ta6ullo daga jikin bango tace
Ke qaramar yarinya mara kunya
Kisani Wlhi kika bari Alhaji ya kusanceki toh taki taqare ina shawartarki daki nemi takardarki yanxu ahannunsa.....

Wata dariya taji kuma anshe da ita ta gefanta. Tajuya danganin me dariyar Momy Hauwa ce itama ta6ullo daga bangon
Tace Wlhi Aminatu kafin ki6ata quruciyarki toh kanemi takaddarki gun Alhaji
6at 6at. suka 6ace

Dafe kai MEENAT tayi tace innalillahi tabbas nashigo sabuwar rayuwa


Tasauke hannunta daga kannata Cikin sauri takoma toilet taqara yin alwala tayi sallah raka'a biyu tare da roqon Allah daya mata maganin mugayan bayinsa
Tashafah addu'arta tare da qara feshe jikinta da turare
Tahaye gado abinta
Haye warta da minti biyu saiga dadyn yashigo da kayan bacci ajikinsa
Yahaye gadan yajanyota jikinsa
Nanfa yafara sarrafata tana xillewa
Can tafashe mai da kuka Amma Sam bai saurara mata ba
Yafara harka da ita tasaki wani firgitaccan qara
Dan yakawar mata da budurcinta

(Afurgice ALIYU ya bu'de idanshi dayake rufe gabanshi yayi mummunar fa'duwa. Abaiyane Yace My baby...
Lubba tabu'de idanta tace naji kamar ka ambaci baby Yace yes wani abune
Cikin takaici tace aa. Tamaida kanta qerjinsa tana naxarin meyasa mijin nata yadamu da lamarin MEENAT )

Shiko dady ihu da sunbatu yaketa yima MEENAT Amma inaaaaam
MEENAT tasume
Yayinda shisam baisani bah
Dan sai kai harka yake da sambatun da'di

Sanda yasamu nutsuwane ya lura da aika aikar da yayi
Nan ya sureta sai toilet.
Jinta cikin ruwa ne ya farfa'do da ita daga suman
Taqan qameshi da samai kuka
Nan ya dinga sakata Cikin ruwa yana gasata Yana canja mata
Ahaka tadaure har tayi wankan tsarki
Yadawo da ita gado

Tace inasan karatu yanxu
Cikin lallashi yace karatun me ayanxu Tace karatun qur'ani
Yace toh bari na'dauko miki
Shuru tamai yafice
Ta lumshe ido dan wani xaxxa6ine yakesan kamata
Yakawo mata Qur'anin harda carbi
Cikin xaxxaqar murya ta karanta TABARA
Dayin Ayatulkursiyu qafah hamsin dan bata manta garga'din Su Momy kilishi bah.
Bayan tagama ta kalleshi Ashe xubah mata ido kawai yayi Yana kallanta
Tace dadyna Yace na'am Amaryata
Tace yakamata kayi sallah kafin ka kwanta
Kamar wani 'danta
Yatashi yashige toilet yayi alwalar yayi sallar duk tana cikin bargo tana kallansa har yadawo gadan ya rumgumeta
Yace Wlhi Amina ke kina 'daya daga Cikin matan SHU'ARA

Hakan take inji Rahamat

Shuru tamai yaqara da cewa Wlhi banta6a samun nutsowa da kwanciyar hankali yayin saduwa kamar yauwa bah
Naqara sanki Amaryata ina kaunarki zanxama tamkar yaranki idan kikamin ladabi da abinda nakeso
Qara lafewa tayi ajikinsa tace ladabi agareka farillane agareni fatana shine xuciyarka tacika da qaunata da soyayyata
Yace kinsamu kinsamu Wlhi MEENAT.
Bacci me da'di da rahamane ya'daukesu

Acikin baccinne taji kamar amarki anata surutai a Cikin 'dakin nata
Tabu'de idanta Amma bataga kowaba
Can taji ance banfa banta.
Wata siririyar murya taji tace toh nima haka mukoma mugaya musu ba kowa sai Alhaji
Sai kuma taji 'dakin na jijjiga
Aiko nan tafara karanta addu'a saitaji kamar anyi ruwa an'dauke

Qarfe hu'du tatashi kasancewar tasaba tashi hakan
Amma saitaji gabanta namata xugi da xafi
Ahankali tafara jan hancinsa
Yabu'de ido Yace Amaryata tace lukacin sallar farko ya gabatoh Amma nakasa tashi
Da sauri yatashi ya rungimeta Yace aikina ya wahalar dake da yawa ko
Shuru tamai
Yakaita toilet ananne  taqara gasa jikinta taji 'dan dama dama
Atare sukayo alwala
Sukayi lafula harsanda aka kira asubahi yatafi masallaci.
Bayan ta'idar da sallar dakoma bacci
Ahaka yadawo yaganta tana bacci  Yace Aminatu kinyi Allah ya barminke da xumarki

7:00am
Bakwai dai dai nasafiyar
Momy Hauwa da Momy kilishi suka fara doka masu kofah
A'dan furgice MEENAT tafarka
Shima tashi yayi da mamakin waye haka
Yabu'de kofar
Da Momy kilishi yafara cin ido ba gaisuwa tace
Saitafito tama mutane kayan kari
Yawaro ido Yace wah😳
Momy Hauwa tace ita Amaryar taka man
Yace ba 'yan aikine
Cikin takaici momy kilishi tace  daga kanta kafara tambayar 'yan aiki ko haka Zainab tayi
Yace saidai kuyi hakuri dan batajin da'di



Cikin farin Cikin ko aikinsu ne yaci har suna ha'da baki wajan cewa meyasa meta
Xaiyi magana...
Sai kawai sukaji maganarta tana gaidasu
Ganinta garau dasukayinne yasaka suka kasa amsawa
Momy kilishi tace saiki fito kima mutane kayan kari aikinji Komai tace toh

Suna ke6ewa Momy kilishi tace ke anya yarinyar nan bata taki wani abuba
Momy Hauwa taja nunfashi tace akwai abinda tataka
Kuma ina ganin dan bamuyi nisa atsafin bane shiyasa
Tace aishiyasa nace miki muje gun boka nakan dutse Kinsan aikinshi nan takene
Momy hauwa Tace Amma ai tsafi yafi bokanci mu'dan dakata dai
Tace Hauwa kinada taurin Kai karki manta   baifi kwana uku da shigarmu tsafinnan bah bamusan kan abinba Tace aixamu sani mubarshi mudai gani Tace aishikenan

Dady ko rungumar MEENAT yayi yace am sorry Amaryata Tace Bakomai
Yace xaki iya 'dagamai kai tayi

Cikin sauri tayi wanka tasaka Riga da siket na atamfa tayi mata kyau sosai
Dadynne yanuna mata kitchen 'din ananma taga Zainab tana fere dankali
Suka gaida juna
MEENAT Tace kiyi hakuri da abinda namiki jiya Tace lah Bakomai
Shuru MEENAT tayi tana qarema kitchen 'din kallo da tunanin ta'ina xata fara ha'da break 'din batasan kan Komai ba
Zainab tace lafiya Tace bansan kan yanda kukeba
Tace karki damu zannuna miki Komai
Tace nako gode
Ruwan shayi suka ha'da da soyayyan dankali ha'de da farfesun kaji
Zainab tace danke nayi farfesun tunjiya dan nasan baxaki iya aikin dukka ba Tace nagode
Haka suka jera komai a dining  Cikin nutsuwa
Yaran suka gaisheta kamar yanda suka gaida zainab
Itadai tayi shashinta dan xaxxa6ine yake damunta

Bayan sungama breakfast 'dinne yaran da manyan kowa Yakama gabansa dan neman ilimi sai dadyn ya gabatar musu da MEENAT amatsayin 'Yar uwarsu  wacce xata musu ladabi da biyayyah
 Ayatsine suka amshi xancan nashi

Kwanan MEENAT uku kenan
Amma bata qara ganinsu Momy kilishi bah saidai batayi yunqurin barin addu'o'intaba
Gashi tafahimci dadyn nata Yana da takura da yawa tawajan saduwa
Gashi bataso Sam
Allah Allah take kwana bakwai 'din yacika yabarta tahuta da futunarsa
Batasan  dalilin da yasa Sam tatsani ya kusan cetaba.



3 week MEENAT taqara fahimtar Komai agidan. Yaran gidan basu da kunya Sam
Amma saikin shiga harkarsu
A'iya saka idanta tagano Su Momy basa sallah kwata kwata

Mutuminta ko Ahmad hararace tsakaninsu
Dan akwai ranar da Yace mata 'yar iska karuwa
Tace ni matar ubanka CE idan kakirani da 'yar iska kaga nidashi muke iskancin kenan karuwa ko daka kirani akaruwancin ubanka yaganni yaso
Tundaga ranar baiqara shiga harkar taba

Sam dady baya ma Zainab adalci dan baya kwana da ita ran girkinta
Gashi tatayin aiki kamar jaka kuma yana gani baita6ayin magana bah
Dama ita MEENAT tasaukema kanta girki da aikin gidan dan baxata iyaba
Dan satinta 'daya agidan dan makirci tayi wani girki mara da'di wanda ko dabba akaba saidai takauda kai dan baxata iya ciba
Sukayi magana tace ita bata iya girki bah
Hakka suka sauke mata girki dan dole
Toh aikima bayinsa takeba saidai Zainab 'din Amma tana'dan yin ka'dan

To yau suna xaune wajan shaqatawar gidan girkin MEENAT ne
MEENAT ke tamvayarta meyasa takeyin aiki haka bata dawani lokacin kanta
Tace toh yaxatayi tunfarkwan zuwanta Hakka Su Momy kilishi suka koyar da ita
MEENAT tace kuma da'alama bawani naki dayasan irin rayuqar da kike agidan nan tace eh wasu sunsani wasu basu sani bah
Tace toh Allah ya kyauta

Gyara xama Zainab tayi tace MEENAT inasan fa'da miki wani zance Amma ina tsoro Tace fa'di kanki tsaye karkiji Komai
Tace naji Su Momy sunasan binne wani asiri akanki da kuma Dady
Danya tsaneki kamar yanda ya tsaneni
Kuma suhanashi kusantarki tare da inkinsami ciki yadinga xubewa

Tace taya akayi kikasan hakan tace karki manta jikin window nah nabet room 'dina yana jikin  'dakin Momy kilishi Wlhi duk abinda suke kullawa inajinsu
Harta wani tsafi da sukaje suka shiga kwanaki  Wlhi majisu
Sam yanxu ni bandamesu bah Amma ke kindamesu

Qarema Zainab kallo MEENAT tayi Tace Amma Kinsan da haka kika kasa nemamma kanki 'yanci
Tace nifah banta6a gayama kowa maganarsu bah saike kuma bani da abinyi saiji da sauraran yanda sukayi dani

Tace kidage da addu'a ba abinda yafi qarfinta
Xanbaki addu'o'i sosai Sannan kikiyaye sallarki kidena wasa da'ita
Tace toh


Tace toh yanxu a'ina xasu binne asirin Tace a'dakinki Naji sunce wai inkin fita
Tace a'ina xasu sami keey
Yace suna dashi ai Tace bayan na'dakina suna da wani Tace eh kai
Jan numfashi tayi tace toh ai duk tays ne Tace hmm sunada Wanda yake xuwa ya fasa musu kuma atake yamayar da sabo kamar ba'a fasaba  Tace duk ya'ayi kikasan wannan
Tace tab ai 'dai 'daikune tayass 'din Dady na'dakinshi Wanda basuyi binne binne bah
Dan yawanci akan idona suke
shuru MEENAT tayi can tace toh insha Allah idan addu'a namagani baxata barsu sushiga shashina ba bare 'dakina
Zainab Tace Allah yasa
💎💎
Tana xaune kanta na cinyar dadyn nata
Yace Wlhi MEENAT ina matuqar sanki kinyi tako ta'ina
Tace nima haka Dadyna ina sanka fiye da tunanin me tunani
Yace nagode kici gaba da sona
Tashi tayi taqura mishi ido Yace daga Gani wannan kallan naki bana lafiya bane
Cikin makirci Tace kwarai Dadyna kawai wata matsala
Yace tamefah
Tace bakayima Zainab adalci Dady
Sannan duk abinda yashafeta banxatar dashi kake
Yace yaxanyi Aminatu Wlhi inasan kyautata mata. Amma daxaran naje kofar 'dakinta sainaji natsaneta bana santa gashi nakasa rabuwa da ita tahuta nima. indena 'daukar xunufi
Tace kadage da ibada da addu'a Dady inaji ajikina kawai matsala
Yace gaskiyane Aminatu bana maida hankali a ibadata sosai kamar da Sannan addu'o'i basu dameni bah.
Yaqashe maganar Cikin sanyi da damuwa
Tace toh kadage dan she'dan nasayin galaba akanka
Yace toh nagode da tunatar dani da kikayi.
Tayi Murmushi
Yace duk randa nake wajanki ina samun nutsuwa da kwanciyar hankali Tace nima idan ina tare dakai banasan kamatsa daga gareni koka'dan
Cikin farin ciki yafara Neman hakkinsa
Nennefah ran MEENAT ya 6aci dan tatsani ya kusanceta
bata nuna mishi ba
Amma tatabbatar ma kanta Lalle wata rana xata nunamai bataso


Su Momy ne saka kasa hakuri har MEENAT tafita anguwa su saka asirinsu
Dan haka yanxu suna durkushe gaban bokansu sunkoromai bayanin MEENAT
Yasheqe da dariya Yace batasan ya kusanceta Sam dan bai'iyabi da ita yanda takeso ba. Amma duk yanda kukakai da tsafinku da bokanci ina tabbatar muku baxai dena kusantar taba
Dan ita'din tana 'daya daga Cikin mataye masu da'din aurataiya
Tanada ni'ima sosai mesaka duk Wanda ya kusan ceta qara qaunarta sune matan da ake kira shu'ara ba macan da xata kaisu ni'ima da da'di duk maganin ko da xatasha
Sauke ajiyar xuciya sukayi atare. Sukace toh yanxu baxa'a iya xuqe ni'imar tatabah
Yace Ku bari ingaya muku gaskiya yarinyar akwai tsari ajikinta bata wasa da sallah Sannan bata barin jikinta ba tsarki
Tanada addu'ar da takeyi wanda duk tsafinku da bokancinmu baxasuyi tasiri akanta bah
Saidai akwai mafuta 'daya idan tana al'ada ga wannan maganin kuxuba musu a abinci taci yaci idan hakan tafaru  xai tsane kuma xaisaketa atake
Ammfah idan shiyaci ita bataciba xaiqara Santa da qaunarta
Idan kuma ita taci shibaici bah
Ku tabbata ku xaku fita.
Dan xaku ha'du da makircinta kala kala Sa annan baxai ta6a ganin aibin abunda xatayi bah kuma Santa nanan daram axuciyarshi.
Sukace bamu boka bama fa'duwa akan Komai
Yace angama nan yabasu suka 6ace saigasu a 'dakin Momy kilishi

mmy hauwa tace yaxa'ayi yarinyar nan taci maganin nan kinga lokacin datake girkima baci take bah. Toyanxu yaxamuyi
Tace habama mana kiyi tunani saka mata baxai xu da matsala bah tacin shine matsala danta Alhaji ko kinsan wannan ahannu yake
Tace kumafah

Daga wanka MEENAT tafito tana share jikinta tasaka rigarta da wando sunmatsata sai qamshi take
Tafitoh falo tasaka waqar mutuminta Umar m shariff tana bi tana ka'da kai dan da'di taxauna tajawo abincinta Wanda gamawarta kenan tashiga wanka tahauci abinta
Sanda tayi qat sannan tatashi dan kai kayan kitchen...
Wayanta tayi qara Dadynta tagani
 tata6e baki da cewa mexakamin bayan ba girkina bane  tadai 'dauka Yace kixo Amaryata ina 'dakina. TOH Tace takashe wayan

Bayan takai kayan kitchen direct gunshi tayi Yace kawai dama nakirakine inganki dan inyi baccin farin ciki cikin yanayin shagwa6arta Tace kanada neman magana Dady salan Momyn Aisha taganni ko
Yace toh miye inta ganki xoma in rungume ki konaji da'di tamale kafa'da alamar aa yace hmm yunwa nakeji tace yanxu magana cin abinci Yace mekikaci tace sakwarace da miyar egoshi
Yace gud
Xubamin nawa abincin  saikitafi.
Haka tabu'de abincin nashi shinkafah da miyace da farfesun kayan ciki
Yace kai baxan cibah
Jeki kikawomin sakwarar taki Tace saidai nabaka ta zainab dan dama tare namana yace yauwa kawomin
Haka takawo mishi yaci yakoshi
Yace anya nata6a koshi irin nayau kowa tashi tayi tana Murmushi xatayi magana Saiga Momy Hauwa
Kallo 'daya MEENAT tamata taji ayau tatsaneta
Ga Momy Hauwa ko
Gabanta ne yayi mummunar fa'duwa dan ganin baici abincin dasukasa maganin wajan bokanba
Gashi sunsama MEENAT taci shibaici bah
Kodai na MEENAT 'dinne sukaci tare dan tatabbatar sai takalli MEENAT tace abincinki kukaci dare ko


Tace Abincinki kukaci tare ko
Kamar baxata amsa mata bah dan wani haushintan da taji haka kawai tata6e baki Tace eh nacinye nawa wani nakawo mishi
Yanxu tatabbatar baici me maganin bah
Cikin jin haushin MEENAT 'din kamar ta tsinka mata mari tace dan iskanci inkawo mishi abincin shine kika kawo mishi naki

Dama MEENAT kamar jira take ta'dage baki tace shiyace yanasan nakawo mishi nawa baxaici naki ba lefine danna kawo mishi

Cikin mamakinta Momy Hauwa tace rashin kunya xakimin.
Kindai san na'aifeki
Tsaki MEENAT tajah Tace  toh dan kin haifi wa 'yanda suka fini shekaru ni kika aifah.....
Momy kilishi ce tashigo tace yafara aiki akanta Hauwa munshiga uku dama sanda yafa'da
Tamaida kallanta ga Dady
Tace kana gani baxaka mata magana bah Alhaji
Bu'dar bakinshi saicewa yayi metayi
Ba'abinda tayi kudai bakusan axauna lafiya. Nalura tunda yarinyar nan taxo gidan nan kukabi kuka tsaneta nibanasan tashin hankali
 Sake baki sukayi dan ganin yanda yau Alhaji yake mayar musu da magana
Mmy Hauwa ce tayi qarfin halin cewa kasanko me kake cewa
Cikin qarfin hali dajin Isa MEENAT tace nifah sunfara damuna Dady
Da sauri mmy kilishi tace dan ubanki girkinkine daxakice munda meki kajimin 'yar iska yarinya
Cikin sauri Dady Yace kuje dan Allah banasan damuwa wayace kushigo Wlhi kukasa ran yarinyar nan ya6aci Wlhi sai naku 6aci 
MEENAT taturo baki tace kaja mata kunne karta qara xagina dan ina ganin mutuncinta taqarashe xancan da niyar fita daga 'dakin
Aiko da sauri Dady yatashi Yace dan Allah Aminatu karki tafi ta'dan juyo tace toh mexanyi mah bayan ba girkina bane
Yace mu'danyi hira mana. Tace um um ha'de da maqale kafa'da.
Raina ya6aci tunda taxagen xanxo maka Cikin mafarkinka.
Yace toh Amaryata ki kwana lafiya tafice abinta
😳😳
Waro ido su momy sukayi cikin tashin hankali
Mmy Hauwa tace meyake shirin faruwa
Ya 6alla mata harara Cikin 6acin rai Yace kufita tunkan raina ya6aci
Ganin da gaske  Cikin 6acin rai yafa'di kalmar shiyasa  suka fita ransu 6ace



Tun daga nanar MEENAT  tasaka Su Momy agaba da rashin kunya da futsara da makircin ta kala kala da sharri Amma sai sunshiga harkarta
Dady ko Sam baya ganin lefinta dan asirce asircansu yafara sakeshi

Tun yaran basa gane rashin kunyar da rashin mutuncin da MEENAT takema iyayan nasu harsuka fara ganewa aiko maqaramin tsanar MEENAT sukayi bah
Dan akwai ranar da suka tsareta wai saisun xaneta sunata xaginta
Itako takira Dadyn nata awayarta taqi magana yadinga jin xagin da suke mata.
Aiko sai ganinshi sukayi ya cicci qaniyarsu da jamusu kunne akan karsu qara mata kallan banxa bare maganar banxa inko suka kuskura hakan tafaru Wlhi shida sune

Gashi Su Momyn sunsata agaba da tsafinsu da asiri kala kala
Sam bata isa takwanta bah saisuta tsoratar da ita addu'arta ce take kwatanta agunsu
Danba qaramin tsoratata suke bah. Gashi takasa fa'dama kowa duk dako Su Sadiya suna 'dan xuwa mata dasu Ameera Amma takasa fa'da musu


Anacikin haka ranar Momy kilishi batanan tatafi bikin wata 'Yar qanwarta da duk yaran gidan mata banda maxan da basanan
Yarage daga Momy Hauwa sai Zainab da MEENAT dama girkin tane ita MEENAT 'din

Ta zaga ko ina bataga Zainab ba kawai saitayi shashin Momy Hauwa duk da bawajan xuwan Zainab 'din bane Amma tayi tubanin ko tananan

 bataga kowa afalan ba  dan haka tayi shahadar shiga bet room 'din
Aiko tayi mugun gani dan ganin momy Hauwan tayi tana tsafi da kiran sunanta dana Dady
Cikin furgici da tashin hankali xuciyarta nadukan uku uku tadawo da baya ahankali
Da sauri takoma shashinta gabanta nafa'duwa
Atake takira Dadyn nata Yace yadai Amaryata gani acikin layi nadawo qara shan xumarki kinsan bana gajiya dake tace kayi sauri Dady kaga wani abu
Tana fa'din haka takashe wayan da saurin xuwa bakin get dan kar yashigo da mota Momy Hauwa taji qarar shigoqarshi takatse aikin tsafin nata

Aiko ko minti 'daya batayi da tsayuwa abakin get 'dinba sai gashi Yace lafiya tace xomuje kagani
Aiko yabita dungul dungul har falan Momy Hauwa tanunamai betroom 'din alamar ya shiga. Aiko yasa kai
Mexai gani
Ganin Momy Hauwa yayi tsirara da ratsin jan qelle akanta da kwarya agabanta fuskarta arufe tanata surkulle da kiran sunanshi dana MEENAT

Toshida ba qaramin yaro bane dan nan take ya gano me takeyi Jiri yaji yana ibarsa ahankali yadawo falan hannunshi dafe akanshi
Yayinda MEENAT take gefen kofah tana fa'di aranta yau taki taqare Uwar Gida



Shuru yayi hankalinsa tashe
Yace innalillahi
MEENAT Tace ai in gayama itada Momyn Ahmad suke yin irin wannan abun kullun suta kiran sunan mu nidakai shine yau naji kamar tana kuka shine nakiraka dan kaduba ko dai lafiya dankar nashiga tamin masifah
Yace kikace kullun sukeyi tace Wlhi ranar mah a 'dakinka sukayi katambayi Zainab.
Yace kinshiga 'dakin 'daxune tace eh nashiga naganta  tsirara
ai inxasu kullun haka sukeyi shine yau naji tana kuka nakiraka

Yace subhanallah innalillahi
Cikin makirci tace wani abune Dady inadai tadena kukan kuma ina ba Komai Yace da matsa........
Bai qarasa ba kawai sukaga ta6ullo daga bango batasan mah sunanan ba
Agigice ta6ace

Duk da MEENAT tasaba da yanda suke 6ullo mata Amma yau
Saitayi yunkurin rugawa aguje Dady ya cafkota tacallah qara da qanqanmeshi Tace wayyo Dady Momyn Aisha ta6ullo abango wayyo
yayi saurin rufe bakinta  yace Ki nutsu ba'abinda xata miki kinji
Nan tafara sauke ajiyar xuciyar qarya
Can saiga Momy Hauwan tafito kamar yanda take fuskarta a'daure Tace me kukaxo yimin a'daki
Cikin mamakin tah Dady Yace abinda kuka da'de kuna aikatawa mukaxu gani
Tayi shuru tanabin MEENAT dake jikin Dadyn da mugun kallo

Yace tirr da halinku Hauwa  Ashe keda kilishi abinda kukeyi kenan mekuke nema wanda bana muku
Yaruwata kuke nemah
Tayi shuru
To Wlhi baxan iya xama da matsafah bah
Agigice MEENAT tace tsafi Dady
Baikulata bah
Yaci gaba da cewa kije Hauwa nasakeki saki uku kedah 'Yar uwarki kubarmin gida

Tace saime Amma saikayi nadama daganin abinda xaifaru da makirar yarinyar nan tanuna MEENAT
Yace ai yanxu ba'abinda xaiqara tasiri akaina akan tsafinku tunda nagani da idona muxuba nidaku ne matsafan banxa
Nan ta6ace 6at

MEENAT tafashe da kuka tace Dady xasu kasheni. tsafi fah kace
Cikin damuwa Yace ba'abinda xasu miki kiyi shuru
Yanxu tashi muje gun wani me maganina yabamu natsari ina Zainab tace ban ganta ba Yace muje mudubata

Ashe Zainab na toilet tana wanka
Sunsameta tasaka Kaya kenan Yace sutafi tare
Nan sukabar gidan xuciyar Zainab da tunanin lafiya ina kuma xasu




Zainab kasa hakuri tayi har sanda tatambayi MEENAT ina xasu
Nan MEENAT takwashe Komai tagaya Mata
Qura mata ido Zainab tayi Amma batayi magana.
MEENAT talura da magana abakinta tayi saurin yimata sigina tayi Murmushi.

Gun malamin nashi sukaje ko
Dady yakoro mishi bayani
Yafahimci komai Amma Yace sai anje dashi gidan dan afutar da kayan tsafin nasu
Dady Yace toh aise muje yanxu
Yace ya kamata kam

Afarfajiyar gidan sukaga Momy kilishi da yaran gidan  fuskannan tata a'daure cikin fusata Dady Yace meyadawo dake gidana ko bata gaya miki na miki saki uku bane kema tace tagayamin
Naxone nagaya ma wlhi sai burinmu yacika akanka
Yace me kuke nema danine tace duciyarka
Yace idan itace kuke nema ai xan iya mallaka muku basai kun jefah kanku amasifaba
Tajah tsaki ta 6ace
Nan yaran suka dare da ihu cikiko harda manyan

Dady ya daka musu tsawa da cewa toh susani iyayansu matsafane dan susani
Cikin mamaki da tsoro sukace tsafi
Yace eh

Nan malam yadinga xaqulo kayan tsafinsu
Da asirce asircen da yake gidan
Nacikin tayesne 'dinne Yace sai anfasa
Atake Dady yasaka aka farfasa
Duk akacire
Maganin tsari sosai malam yabasu
Da addu'o'I

***
Duk yanda Su Momy sukaso yin tsafinsu akan MEENAT da Dady abin ya faskara
Yanxuma suna xaune Momy Hauwa tace Wlhi kilishi tunda yarinyan nan taci galaba akanmu Wlhi saitabar gidannan Momy kilishi tace hmm yarinya qarama ta gagaremu
xataci ubanta ko

Muje xuwa



Ayau Ya ALIYU suka duro Nigeria shida Lubba tiqi tiqi da cikinta Wanda baxai bai hucce sati 'daya ta'aihu bah
Aminu da Hamisu ne sukaje tarosu

Tun amota suke cewa
Kai Amma yayah kaqara kyau sosai
Yayi Murmushi
Aminu Yace Amma yayah wannan karan  banga farin cikinka na dawowah bah ina fatandai lafiya 
Yace qalau Bakomai

Koda sukaxo gida murna wajan Mamah  da Momy Su Abbah abin ba'a cewa Komai
ALIYU yakalli Hamisu Yace ina fatan angyara wancan gidan
Hamisu yayi saurin cewa eh
Mamah tace aa badai yau agidanka xaku kwana bah
Ga shashinku nanan gidan angyara muku kodai yau kadawo da San xama acanne
Yayi Murmushi Yace eh toh ina Sadiya da xainab auta
SafiYYA tace tana gun Yusuf saurayinta xainab ko tanagun MEE...
Yace inasan idan tadawo keda ita kufidda maxajen da kukeso dan yanxu kungirma
Tasunkuyar dakai
Momy tace kamarko kasan xancan da Abban Ku yagamayi jiya kenan akansu ga qanwarsu tana xamanta lafi......
Bai bari taqarasa bah ya miqe da cewa
Bara muje can akwai Kaya amota nakune
Mamah Tace toh madallah
Yace ina ganin saigobe zan dawo
Tace aikam kahuta gajiya Amma anan Lubba zata xaunako Yace yanda kikace mamah
Tace taxauna anan kawai dan Cikin nan nata inaganin fitarshi xaiyi wuya yahucce kwana uku
Murmushi yayi yafita Lubba tabishi da kallo tana naxarinshi Sam baiso dawowar wannan karan bah

MEENAT ko tana bet room dinta tana bacci
SafiYYA tazo ta'daka mata duka
A'dan furgice tatashi
Tace saiki tashi Ya ALIYU yadawo .....

Gaban MEENAT yafa'di ras ras
Tace nashiga uku
SafiYYA Tace namefah bayan yanxu agidanki kike Tace hmmm yanxu Yana gidane Tace aa yatafi gidanshi Aunty Lubba CE agida
Tace xaidawo Tace wai sai gobe
Dafe kai tayi Tace Wlhi gabanane yayi mummunar fa'duwa dan ambatan sunanshi da kikayi
Tace hmm tsoran shine haryanxu bai barki bah
Kinga ko yanda yaqara kyau
Waima Yana wani business acan. Wlhi Ya ALIYU yayi fah......
Wayanta ce tayi qara nan tatashi tana cewa Salim yaxo saikin shigo
Tace saigobe xanxu in gaisheshi Tace toh

Shuru MEENAT tayi dan haka kawai taji hankalinta yatashi da xuwansa nawannan karan

Tofah

Washe gari MEENAT tagama shirinta tsaf dan xuwa gidansu
Zainab tashigo falan nata
Tace harkin gama shirin Tace eh Wlhi banajin da'di Sam gashi gabana saifa'duwa yake
Tace Allah yasa alkairine
Tace kamarya Tace fa'duwan gaban da kikeji Tace Ai AmEEn
Dama kikar6i girkina yau Tace tab Dady baxai yarda ba kinsan yanda yakeji dake
MEENAT tata6e baki xatayi magana Saiga Dadyn yashigo falan
Zainab tatashi tafita
Ya kalli MEENAT Yace  ina buqatarki nefah kafin kifita
Sarai tasan me yake nufi Amma dake tatsani kusantarta da yakeyi Tace
Toh menene Dady
Yakama qugunta Yace cewa nayi ina buqatarki
Ta6atarai kamar zatayi kuka
Tace nifah Dady....
Yayi saurin katseta da cewa
Wai meyake damunki ne MEENAT
Kina axabtar dani bakyasan indinga samun kwanciyan hankali dake meyasa
Inasanki dan Allah kiji tausayina kibani hakkina yau dan Allah
Taturo baki gaba tana tana yarfe hannu tace toh saina dawo
Da sauri Yace kin'dau alqawari Tace eh
Yace kice yau ango nake
Fari tamai da ido tare dawani shigemai jiki tana kai bakinta  wiyanshi
Tuna yafara nisha da qam qameta
Yace subhanallah
Ganin datayi yafara tafiya jos dan rikicewa
Shiyasa tayi saurin yakice kanta tayi kofah tanamai Murmushi da cewa saina dawo dadyna
Jiyayi ranshi ya6aci kamar yajawota daqarfi yabiya buqatarsa

Itako hartakai shashin Zainab Tace nabar Dady afalo plx inyafita kyakulle min 'dakin ga keey
Tace toh kigaidamin da YA ALIYUN
Tace toh tafice

Tunda takai kofar gidansu taji qamshin turaran  ALIYU na kusantota talumshe ido tare dajin fa'duqar gabah

Aiko taganshi a farfajiyar gidan shida mamah da momy su SafiYYA na gaisheshi da'alama xuwanshi kenan 

Tagaida su Momy
Sannan tagaida shi kokallanta baiyiba saima cema mamah da yayi
Inajin kwana 3 xanyi inkoma
Cikin nuna 6acikin rai tace wai meyasa kakemana hakane  iye
Muna buqatarka sosai muma
Sannan kuma inasan kafasa tafiyan harsai matarka ta aihu komai yalafah
Yace mamah........
Tace ALIYU
Yace toh shikenan nabi umarninki
Dai dai nan Zainab autarsu tafito tanacin ayaba
Ganin ALIYU datayi ya sakata yar da 6awon ayaban
Ta rungumeshi Yace my qanwa ya akayi tace lpy yayah Yace gud......
MEENAT taqara cewa sannu da dawowa yayah
Fakar idan kowa yayi ya 6alla mata harara
Sannan yace yauwa
Sauke ajiyar xuciya tayi sannan tayi hanyar shiga falo

Aiko Cikin rashin sa'a tataka 6awon ayaban da Zainab auta tayar
Aiko sai tatafi xata fa'di
Taqwallah ihu

Saijinta tayi jikin Ya ALIYU
Haka kowa yayi mamakin wane irin sauri Ya ALIYU yayi wajan tarota dan akwai taxara tsakaninsu

Itako qam qameshi tayi dan tatsorata daganin fa'duwar da xatayi
Suka ha'da ido
Yagallah mata harara da saurin saketa
Momy tace yau dakinkai qasa dakin karye
Mamah Tace aikowa
SafiYYA da sadiya ko dariya sukayi wai data fa'din sunga 6arkewa da kukanta dansun kwan biyu basu gani ba

Duk sukayi falon momy banda ALIYU dayayi shashin mamah wajan motarsa

Sauke numfashi MEENAT tayi lokacin data xauna abakin gado
Tarasa dalilin da yasa idan jikinta dana Ya ALIYU yaha'du takejin wani shocking tundaga kanta harkasa
Gashi batajin hakan ga Dadyn nata

Bama wannan bah ayau tahango tsanarta a idan ALIYU
Tabbas akwai lefin da tamasa. Tome tayi. Tatambayi kanta
Shuru tayi tana tunani kuma hankalinta tashe
Can ta'dura hannu aka Tace nashiga uku
Dan tunowa da tayi ashefah yamata garga'din karta kula maxa takula da kanta
Kuma lukacin da akayi auranta da Dady koda tacemai auran dole aka mata baice mata Komai bah

Tabbas ba shakka wannan shine lefinta gareshi batabi umarninsa bah
Ya salam
Yaxanyi daKai yayanah Wlhi banasan 6acin ranka banasan katsaneni
MEENAT tafa'di hakan abaiyane

Yayinda SafiYYA Tace wanene kuma meyasa meki kikace kinshiga uku
Tace nama yayah lefi. Sadiya Tace naga alama dan nahango 6acin ranki a idansa
Gabanta yafa'di Ashe ba ita ka'dai taga hakan ba.

Tashi tayi tafice xuwa shashin mamah dan taga nan yashiga




Ba kowa afalan hakan yasa taduba duk 'dakunan ba kowa tace aranta nanfah naga yayo
Can tayi tunanin xuwa shashinsu
Nan tamesu afalo
Kan Lubba na cinyarshi
Yayinda yake shafa Cikinta Cikin annushuwa da farin ciki suna hira
Gefe guda kuma yana ta6a laptop 'dinsa
Innalillahi tafa'di hakan Cikin ranta
Danjin wani mummunan 6acin rai daya xiyarceta nan take
Batasan daliliba saiji tayi taqara tsanar Lubba

Shiko ALIYU yaganta yiyayi kamar baiganta ba yaci gabah da ba matarsa kulawa
Lubba ta6ata rai kamar xata fashe
Tace menene kokinxo ne kimin tashin kunya
MEENAT ta 6allah mata hararah Tace bagunki nazoba
Tashi lubbah tayi tace dagaske kenan rashin kunyar xakimin
 toh gunwa kikaxo
Tace gun yayanah
ALIYU ya gallah mata harara takawar da fuskarta
Lubba xatayi magana
Yace plx jeki 'dakin mamah sweety
Tashi tayi Cikin 6acin rai tafita harda hanka'de MEENAT

Kamar MEENAT xata rama tatuna ka'dan da akin Ya ALIYU ya falleta da mari shiyasa tarabu da ita

Cikin nutsuwa taqarasa gareshi tadurkusa idanshi nakan laptop 'dinshi yana danne danne

Tace dan Allah dan Annabi yayah kayi hakuri kayafemin Wlhi Ni bance inasan auran nan bah. Na hango tsanata afuskarka yayah kamin rai kayi hakuri dan Allah
Bai kalleta ba bare tasaran zaice wani abu
Aiko ta6arkemai da kuka
ya rintse ido  tare da ture laptop 'din tashi ya kalleta Cikin Takaici Yace plx dan Allah tashi kifita karkisamin ciwon kai.

Me makwan tafitan saita xauna taqara fashewa da kuka sosai. Tace nidai kayi hakuri

Yace Wlhi baby tsanarki yanxu nasoma
Baxama kitabbatar da natsaneki bah sai kinbari wannan mummunan 'dan iskan tsowan yayi miki ciki
Anan xaki tabbatar da cewa natsaneki

Gabanta yafa'di
Tace Wlhi yayah.......
Ya katse wajan daka mata tsawa Yace get out
Cikin tsoro tatashi tana kuka sosai amma taqi tafiya
Cikin takaicinta yatashi ya falleta da mari Yace Wlhi Xan karyaki inbaki fittaba
Aiko dagudu tayi kofah tana kuka mecin rai
Ta'dan juyo takalleshi aiko suka ha'da ido taji wani shock
Ya 6allah mata harara
Har tana tuntu6e wajan ficcewa

Xama yayi ya jingina jikin kujerar ya  rumtse idansa
Abai yane yace come back 2me my baby

Itako dagudu taje tafa'da cinyar Momy tana kuka
Tace waya ta6amin ke Autata tace yaxanyi Momy ya tsaneni
Baya sona yanxu banasan 6acin ranshi ya tabbata akaina
Tace wah
Tace yayah
Tace haba bai tsaneki bah qilah kinmishi lefine Tace tu Momy kice yayi hakuri



Tace to xance Amma saikin dena kukannan 
Tace  nadena
Haka MEENAT tayi wuninnan bata tare da walwala
Taso taqara ganin ALIYU tada'da roqarshi Amma basu ha'duba
Haka tatafi gida da tunani barkatai


Misalin qarfe 8:30pm nadare tana xaune tana shafe shafan Humranta.
Saiga Dady yashigo hankalinsa tashe  kuma fuskar nan tashi a'daure tamau bawasa

'Dago da fuskarta tayi Ganin waye yashigo mata haka
Ganin shi yasaka taqaqalo Murmushi......

Baxato taji ya falleta da mari ya kumayi
Xaiyi na uku tayi saurin jada baya
Cikin mummunan 6acin rai Yace Ashe dama ke 'yar iskace malalaciya munafuka maxinaciya .

Quramai ido kawai tayi
Aiko hakan yaqara fusatashi.
Ya wurga mata hotuna kusan guda 3
Yace kije nasakeki saki uku
Wlhi natsane
Dama narageki MEENAT
Kullun sainaxo miki da buqatata Amma saiki hanani hakkina
Ashe kinacan kina rabama mazinata kan nakin atiti
To kije nasakeki saki uku
Allah ya isa tsakanina dake
Yana fa'din haka ya fice

Yayinda takwashe hotunan tana kallo
Innalillahi Tace
Dan ganin hotunanta da wani qatan jirgegen gardi
shi tsirara ma yale itacedai da'dan tawul ajikinta
Kuma abin mamaki acikin bet room 'dinta aka'dau hotan
Dan gashinan akan gadanta
'Daya tadafa mai qirji 'daya kuma ya rungumota 'dayan ko
An'daukane lokacin da tafito daga wanka

Jirine taji Yana ina ibanta taxauna gefan gado tana naxari
Tabbas me hankaline xaigane ha'da hotunan akayi
Tadafe kai hawaye yaxubu mata

Tashi tayi tagyara kanta tare da'daukar gyalanta tayafah taxira takalminta da 'daukar wayanta
Tayi shashinsa
Ganinsa tayi yana kuka Tace Allah sarki Dadyna maqiyammu sunci galabah akanmu naganin sunraba mu
Amma Wlhi banta aikata xina arayuwata bah
Nasan nan gaba xaka fahimci gaskiya. nabarka lafita .
tafice daga falon tayi shashin Zainab

Afalo taganta. Tana kallo Tace toh Zainab yaudai nabar gidan nan har'abada inasanki 'yar uwata Sannan ina rokwanki da Allah kikula da Dady kibashi kulawa da farinci ciki karki bari wata tashigo rayuwarku tawargaxa muku farin Cikin Ku
Tace banfahimci me kike nufiba
Tace Dady ya sakeni saki uku
Abisa wannan sharrin da aka 'dauremin
Tafa'da tanamai miqa mata hotunan
Afurgice takar6e tana gani tace sharrine sharrine wlhi sharrine
Meyasa dady yayanke hukunci batare da tunani ba kuma da aiki da hankaliba
Meyasa yamanta alkairinki yayi amfani da ganin wasu ya tabbatar da gaskiyarsu toyasani in bakya gidannan wlhi bana cikinsa
Taqarashe maganar hawaye naxubar mata.

Kama hannunta MEENAT tayi suka zauna Tace inasan kisani Zainab qarshen zamana dashine yaxo
Kuma ba abinda zakimin kifaranta min kamar kitabbata har abada Cikin gidannan
Idan kinasona dagaske toh kiriqe Dady da kyau kibashi kulawa fiye da kowane Abu naki
Kisoshi kinji
Tace kina nufin yanxu nika'dai Xanyi rayuwa agidan nan
Tace kwarai danke yafi cancanta daki xauna
Kinga kuna shiri da yaran gidannan kuma tun tafiyar iyayansu kika samu 'yanci xaman auranki
Nixan tafi tatashi hartakai kofah Zainab taxo da gudu ta rungumeta Cikin kuka Tace  kimin alqawarin baxaki ta6a rabuwa daniba
Runtse ido MEENAT tayi hawayan tausayin Zainab yakamata
Tabbas taji qaunarta aranta Tace namiki alqawarin baxan ta6a rabuwa dakeba
Tace nagode
Amma tsaya kigani
Nan take Zainab ta'dauko ashana ta qone hotunan kaf Tace ganinsu dafine baxan jure kidinga kallansuba
Murmushi MEENAT tayi
Duk xancan dasukeyi akunnan Dadyn Ahmad ya runtse tabba yanxu yaji wani iri akan batun
Nan MEENAT tafice tashiga gidansu


Kowa Yana falan Momy idan kacire Lubba datake 'dakin mamah tana bacci.
MEENAT tashinga falan da sallama hankalinta tashe ALIYU yaqura mata ido Yana naxarinta
Yayinda Momy da mamah suka tashi afurgice sukace lafiya.
Tace Dadyn Ahmad ne ya sakeni saki uku

Kowa yamiqe Cikin tsoro da mamaki banda ALIYU
Momy Tace mekikamai Tace ban masa komaiba kawai yadawo ne yanxu afugice da'alamun baya Cikin hankalinsa yamin sakin
Mamah Tace qarya kike
Tace to atambaye shi
Momy taxo tarungumeta sukayi bet room 'dinta

Mamah takalli ALIYU Tace Sam banyarda da xancan yarinyar nan bah
Yace ajetoh atambaye shi inaga hakan zaifi

Su Abbah shuru. Sukayi
Can Abbanta Yace tab saki lokaci 'daya atake
Abban Ya ALIYU Yace muje gunshin muji ya abin yake
Nan suka fita
Ya ALIYU mah yafice



Su Sadiya suka shige bet room 'din Momyn suka  zauna gefan MEENAT
Momy tace kinqi fa'damin gaskiya ko
Tace da gaske abinda yafaru kenan
Tunowa dasu Momy kilishi da Momy tayi shiyasata cewa.
Tabbas xai'iya komai Cikin rashin nutsowarshi dan Komai xasu iya


Koda su Abbah suka sami Dadyn Ahmad da batunda MEENAT tace nakawai yashigone yasaketa
Bai qaryatata bah Yace Hakkane
Saiyanxu yasan ya tabka babban kuskure
Dan Allah suyafemai
Abban yasa Bakomai nan sukayi xancansu na manya suka dawo gida suka tabbatarma da mamah da Momy xancan MEENAT gaskitane


Shiko Dadyn Ahmad yafa'di hakane
Dan yana sanyin tunani da naxarin abun
Shin MEENAT ta aikata hakan ko bata aikataba
Bashi da wannan amsar saidai ya roqi Allah ya baiyana mishi gaskiya

Washe gari akaje aka kwashe kayan MEENAT

sati 2 da batun sakin MEENAT kowa yaji
ALIYU ko Sam yaqi yarda suha'du da MEENAT komiye dalili

Yanxu haka MEENAT CE tare da Anisa da Salmah
Anisa Tace kingani ko waya gaya miki barno gabas take .
Tace Allah ne yayi rabuwata da shi bawai makircin matansa bah

Dariya Salmah tayi  Tace da'dina dake MEENAT rainin hankali kedai jeki da burin kunyarki Su Momy kilishi Sunci galaba akanki
MEENAT tata6e baki tace kansuci aini nafara cin galabar akansu





Anisa tace kuma fah Amma ya akayi sakin yafaru
MEENAT tata6e baki Tace hmm makirci da sharri.....
Shigowar su Ameera da Nusaiba ne suka katse mata zancan
Ameera Tace sainaji labari me da'di wai Dadyn Ahmad yayi saki
MEENAT taharareta
Aiwannan abun da'dine Wlhi
Bandake inake ina tsoho me 'ya'ya
Anyako kina kallan kanki amadubi MEENAT
 kinsan da cewar ke mekyauce
Nusaiba CE mafa'din hakan

Anisa Tace inafah tasani gaskiya nayi farin Cikin fitowarki
Haka suka dinga yin maganar Cikin tsokanarta
Itako shuru tamusu

Qarfe tara nadare Lubba ta haifu 'danta namiji kyakkyawa mekama da babansa ALIYU
Karkuxo kuga murna gun mutannan wannan gida
To dama anata sakaran ganin aihuwar tun satin da ya hucce bataxo bah
Kuma duk binciken da ALIYU yayi lafiyarta kalau yake Gani h
Toh yaudai Allah yayi Lubba tahaife
Farin ciki gun ALIYU ba'a magana.
💧💧💧
💃🏻haka akayi suna cikin farin ciki da samun alkairi 💃🏻


Lubba takalli ALIYU Tace yaushe xamu koma
Yace da jegwan xantafi dake tace tome Menene
Yace innaaa dama inada amaryane sai intafi da ita. Gaskiya dole inqara Aure dan xama da mata 'daya Wlhi matsala ne
Tace hmmm kaima kasan wasa kake dan Wlhi nika'daice matarka agidan duniya dama lahira
Yace koh
Tace kwarai
Mubar xancan plx yaushe xamu tafi
Yace sai baby tagama iddarta
Cikin baqin ciki Tace toh wai kai inaruwanka da ita ne
Ya watsa mata wani kallo nantake takawai da fuskarta daga kallansa
Yace sweetheart Wlhi kiso baby
Dan ba wacce nake bala'in so acikin qannena kamarta
Tashi tayi dan Takaici tabar gun
Shiko yaja 'dansa Yana kallansa
**********



Jiya MEENAT tafita daga iddarta
Kuma yayi dai-dai Da yaune walimar Ameera dan bikinta yaxo

Toh Su MEENAT ankwana biyu ba'ayi make-up ba
Dan haka yau wani wanka tayi me furgita duk Wanda yaci karo da ita
Tayi kyau sosai
( dannima Rahamat nashaida hakan)
Wata jar atamface me ratsin fulawa baqaqe
Rigace da siket 'dinkin yayi kyau sosai ya kar6i jikinta abinka da farar mace nan tahaska

Tafeshe jikinta da turare......
Wayanta tafara ringing Ameera tagani
Abaiyane Tace shegiyar amarya ganinan
Sannan ta'dauka nantake Ameera tafara cewa kefa 'Yar iskace tun safe akejiranki bakixo bah
Gashi yanxu lokacin walimar ma saikinyi iskanci Tace yihaku qawata ganinan Kinsan baki kaini 'daukin san in fittaba kokinmanta kusan 4 mont da kwanaki ina kunshe agida Tace kumafah plx dai kixo yanxu Tace insha Allah
Nan ta'dau jakanta da da gyale
Tafito falo SafiYYA Tace wow gaskiya kinyi kyau tace hmm nagode Sadiya ma Tace wannan kyau haka
Tayi Murmushi tayigunsu Momy
Sukansu sunyaba kwalliyar tata sukasa Mata albarka tafito
Aharabar gidan taci karo da Ya ALIYU


Tace sannu yayah. yace yauwa
Yana qare mata kallo
Yace inaxaki. Gabanta yafa'di. Amms Cikin marairai cewa Tace walimar Ameera.
Yace baby baxakiba
Tace what 😳
Ya 6allah mata harara da cewa
cewa nayi baxaki.....
Bata bari ya qarasa bah tafashemai da kuka Tace dan Allah yaya kabarni Ameera ce suna jira na. Yace dubi shigarki kinasan  tafiyane maxa nakallanki baxaki bah
Kibu'de bayan mota akwai kayanki aciki
Yana fa'din haka yashige shashinsa ya barta nan tsaye

Da sauri tabu'de motar akwati 'dayane
Amma yayi nauyi daqer ta'iya fito dashi tajah har cikin falan Momy ta'ajiye tana maida numfashi
Sadiya Tace baki tafiba. SafiYYA tayi dariya Tace baki ganta da kuka bah qila yayah ya hanata xuwane
Aiko kamar jira take tafashe da kuka tayi gunsu Mamah
Momy tace lafiya Autata.
 yayane ya hanani xuwa
Tawaro ido Tace bikin Ameeran ya hanaki xuwa
 Ta'daga
Momy Tace saikinje Yana inane
Yana shashinsu
Tace jeki kiramin shi
Da sauri tatashi tayi shishin nasu
lubba ce afalon Tace naxo gun yayane kokallanta batayi bah
Ganin hakan yasa MEENAT shigewa bet room 'dinshi
Wasu takaddu ne yake 'dauka
Ya kalleta da wani kallo Wanda yasa nantake jikinta ya mutu yalura da hakan danta kasa fa'din Komai
Sanda ya gama 'daukar takaddun yasaka gefanta
Yakama fuskarta taji wani xiiirrr
Ya manna mata kiss agoshi talumshe idanta
Yace me xanmiki kuma. Cikin wahalalliyar rawar murya tace Momy... Momy ce me kiranka
Yace hmmm kinkai qarata ko
Ta bu'de idanta sosai da cewa aa
Yace kinasan xuwa. Tace eh
Jeki canja kaya kisaka duguwar riga da hijab kixo nasauke Ki
Waro ido tayi tace duguwar riga yayah
Yakai bakinsa setin kunanta Yace ranki xai 6aci idan bakisa bah
Toh Tace dan yanda ya kusantota ka'dan yarage ya rungumeta
Yasaketa da sauri ko tafita falo
Lubba ta watsa Mata harara
Bata ramaba taficce

Sauri sauri gudu gudu tacanja kwaliyar da kayannata
Data kalli akannata amadubi ranta ya6aci dan ganin  batayi kyau kamar yanda tasoba
Tafito falo fuska a'daure
Su kansu Su Momy dasu Sadiya sunyi mamakin canja kwalliyar tata
Momy Tace ya dahaka
Tace hmm yayane wai incanja ninatafi
Sukabita da kallo

Amotar shi taganshi tashiga ya jata
Sanda sukaxo kofar gidan ya qare mata kallo Yace kinyi kyau my baby
Turo baki tayi kamar xatayi kuka Amma takasa magana
Ya 'daga mata gira alamar yanasan tayi maganar
Tace Ni Ni Ni banyi kyau bah nafi kyau 'daxo taqarashe maganar kamar xata fashe da kuka
Yakama hannunta ahankali yake murxashi
Taji xiirrrr. xiirrrr yana shiganta
Hakan baimasa bah sanda ya kama fuskarta direct yakai bakinshi kan nata ya manna mata kiss
Yace shagwa6arki baby tana birgeni
Lunnnnn jikinta yasaki
Yasakar mata hannun da cewa awa 'daya nabaki kidawo gida
Cikin wata siririyar murya Tace toh da saurin futa daga motar
 har xai tafi tamatso kusa da ginashin da yake tace dama dama um am
Duk taburkice takasa fa'din abinda xatace saima juyawa datayi tashige gidansu Ameera tala6e ajikin get

Shikoma ganin tashiga gidan yasa yajah motarshi

Sanda ta tabbatar ya'danyi nisa. Saita kira wayansa ya 'dauka
Yace tunda yanxu bakya ganina saiki gayamin miye Tace dama xance kagoge bakinka da jambaki agun Yace wanda kika shafamin
Hmmmmm Tace
Tana fa'dan haka takashe wayan
Shiko Murmushi yayi ganin dagaske yashafe janbakin kamar shi ya shafah


Itako saiji tayi andafata tawaiga afurgice dan tatsorata
Salmah tace kinada iskanci MEENAT kinsan yanxu muke cewa bara mutafi
Tace kumin afuwa gani naxo Ya ALIYU ne ya tsaidani
Tace gaskiya Ya ALIYUN nan yakoma dan yanasan daqilemu.
Karo nafarko kenan da MEENAT taji aranta bataso ya koma qasar waje
Tace wannan karan banaso ya koma Sam
Dariya Salmah tayi Tace wasa kenan atunanina har abada baxakiso xamanshi dakuba
Tace awannan Karan ban san koma warshi da gaske
Tace qila yadena takura mikine shiyasaki fa'din haka
Ciki sukayi tana cewa xaidai dena

Ameera ta 6alla Mata harara Tace Aida baki xoba Tace abu me sauqi aisai inkoma. Tace kikoma man. Tayi Murmushi Tace nayi lefi ayafemin Tace anyafe miki Amma da shara'din gobe nida kene xamu xauna jiran mutane bawai ke ajiyaraki ba
Tace naji insha Allah
Nusaiba tace Allah gobe kika mana haka nidakene
Tace toh munafuka.....
Bata qarasa bah
Momyn Ameera tashigo Tace momyna Tace na'am MEENAT badai yanxu kika xoba Tace Allah Momy ya ALIYU ne ya tsaidani ina wuni
Tace lafiya lau ammafah gobe kixo da wuri tace toh
Momy ta'ajiye drinks 'din data shigo dashi tafice

Ahaka sukaje walimar da tatara mutane
Komai anyishi Cikin nutsuwa
Wa'axikam anshashi sosai
Sai wajan 7 akatashi sanda suka sauke MEENAT agida Sannan tatunafah Ya ALIYU awa 'daya yabata
Allah yasa bata ganshi afarfajiya bah Amma tabbas yadawo dan taga motarshi
Momy Tace saiyanxu Tace eh yanxu aka tashi
Mamah Tace yanxu yayanki yake tambayarki Nace baki dawoba idan kinhuta saikije
Gabanta yafa'di tace toh
Wanka tayi taci abinci dama tana al'ada bata tsaya komaiba tabi lafiyar gado tana cewa baxanje nasha mari bah Wlhi

Canko tayi nisa abacci taji wayanta na ringing takalli agoga 10:30 da rabi
Da sauri ta'dau wayan ganin ALIYU ne
Tace hello Yace my baby inasan ganinki yanxu. Tace dan Allah yayah kayi hakuri Wlhi bansan nawucce awa 'dayan bah 
Yace Oooo xakixone kosaikin cikani da surutu
Xumbur tatashi tace ganinan. Yakashe wayan
Nan tasa hijabi taje
Abin Baqin ciki tanasaka kai da sallama taga kan Lubba akan cinyarshi da alama bacci tayi
Rai 6ace taxauna ahannun kujera tana cewa gani yayah
Ya yauwa my baby naganki xaki iya komawa dama ganinki kawai nakesanyi
Takalle da sauri ya'daga mata gira alamar eh
Tamaida kallan nata ga fuskar Lubba
Nan ranta yaqara 6aci akan me xata saka kanta akan cinyan yarshi tafa'di hakan axuciyarta
(Tohfah😳 kuji MEENAT da qarfin hali saikace ba mijinta bah)
Nan tatashi kamar xata fashe dan takaici hartakai kofah Yace baby
Ko waiwayowa batayi bah tafice
Yayi Murmushi

Tsaki taja tahaye gado. SafiYYA Tace lpy Tace hmmm kedai bari.
Sadiya Tace 'daxo kinyi bacci iyayensu Yusuf da Salim sukaxo sunkawo sadaki da Komai
Cikin dariya da murna tatashi Tace da gaske SafiYYA eh man
Tace kai Amma naji da'di yanxu ansaka rana. Sadiya Tace eh wata takwas.
Ya salam Allah yasa ayidamu
Suka AmEEn
Wannan yasa xuciyar MEENAT sakewa har suka dinga hira

Can kuma saiga kiran ALIYU yashigo kamar baxata 'dauka ba saikuma ta'dauka
Hhhhjjjjjj


Yace menene my baby lefin menayi
Taturo baki kamar yana gun Tace Bakomai Yace kintabbata Tace eh
Yace toh kiyi bacci mecike da mafarkina kinji tace toh
Ya kashe wayan
Sadiya Tace waye namu tace Ya ALIYU ne

Da gaske sanda MEENAT tayi mafarkin ALIYU
Hakanko ya harfar mata da mutuwar jiki dan da safe kallo 'daya xaka mata katabbatar dacewa jikinta amace yake


Kunsan 1:00pm
Tashirya dan xuwa gidansu Ameera
Tayi kyau sosai Amma tasaka gyalanta ajaka Sannan tasaka hijab tana cewa aranta inkasan wata aibakasan wataba
Xainab CE tashigo Tace Aunty MEENAT Ya ALIYU nakira
Tace Yana ina.
Yana 'dakin shi tace toh aunty Lubba nanan Tace aitun 'daxu tafita wai taje gidan Aunty maryam qawarta yau Auranta tace ok
Har xainab takai kofah tajuyo Tace Amma kinyi kyau sosai kamar yanda ya ALIYU yayi kyau saidai  kicire hijabin
Tayi Murmushi da cewa toh naji.
Haka taje tamasu Momy sallama tayi gunsa

Yana falon Yana danna waya tashigo
Ya qura mata ido har sanda taxauna
Yace kinyi kyau my baby
Kallansa tayi sosai shima yamata kyau Cikin qananan kaya gaskiya ya ALIYU kyakkyawane naqarshe kuma yasan sirrin wanka....
Hure mata ido yayi Yace yau kika fara ganina
Kunya takamata tayi qasa dakai
Tashi yayi yashiga bet room 'dinsa
Ganin haka yasa MEENAT 'daukar wayansa tafaramai danne danne
Can wata number ta'dau hankalinta
Inda taga yasa Aisha my luv
Gabanta yafa'di ras (ko miye dalili)
Hakan baisa ta'ajiye wayan bah
Tacigaba da bincikenta.
Can waya tatsaya cak taqi Komai
Gabanta yaqara fa'diwa kardai ta6atamai
Aiko saiga waya ta'dauke
MEENAT tayi tayi waya takawo Amma taqi kawowa
Hartasata acaji Amma bata kawoba......

Fitowar ALIYU ne yasata saurin 6oye wayan abayanta tawaro ido
Ya qura mata ido da cewa ban wayata
Tagirgixa mai kai alamar aa....



Ya 6allah mata harara
Yaqaraso daf da ita
Yace bani nace
Taqara girgiza mai kai daja da baya
Yace  baki da bakin maganane
Cikin tsoro da  shagwa6a Tace dan Allah dan Annabi kayi hakuri yayah Wlhi bansan ya'akayi ba.
Taqarashe maganar kamar xatayi kuka
Ya 'dan lumshe idanshi ka'dan Yace toh naji bani.
Taqara girgixamai kai
Shuru yayi na'dan wani lokaci yana kallanta. Itako sai qif qif da ido take
Can ya 'dauki jakarta yaciro mata gyalan nan nata data 6oye
Nan tasaki baki tana mamakin ya akayi yayi tunanin ta6oye gyalanta
Tana tsayan ya cire mata hijab 'din jikinta Yana kallan kwalliyar tata
Ya manna mata kiss agoshi Yace my baby kinyi kyau sosai so sweet
Tace kaima haka yayah
Yaxira hannunshi bayanta yaxare wayar shi
Yace kin6ata ko
Tayi shuru
Xaiqara magana tayi niyar arcewa tagudu
Yakama hannunta Yace kin6atamin baby
Nayi tunanin yanxu kindena 6atamin Abu Ashe abun nanan

Marairai cewa tayi xatamai kuka Yace Wlhi randa raina ya6aci akan hakan kitabbata saina karyaki
Tace Allah baxan qara bah
Yace toh muje  kirakani wani gu
Tawaro ido da cewa gidansu Ameera xanifah yayah
Yace baxaki bah
Tace dan......
Yace Wlhi baxakibah
Xatayi magana
Yajah hannunta har xuwa gun motarshi tashiga yajasu


Sunyi nisa da tafiya MEENAT takalleshi qasa qasa tace yanxu yayah baxani bah
Shuru yamata. Itama bataqara magana bah  harsukai wani wajan shaqatawa
Abinda yabata mamaki shine yanda taqa anke6e wanigu da decorations mekyau
Duk mutanan gun daka gansu xaka basu wannan sunan
masoya amare
Kowane Namiji da matarsa
Kallo 'daya xaka musu kagane sunjiqu da ilimi da wayewa kuma masu gidan rana ne
Su gomane biyar mata biryar maza
Sai ALIYU da MEENAT
Na shabiyun su
MEENAT tace aranta anya ba abokan Ya ALIYU bane

Haka suka fito daga motar suka tsaya jingine da jikin motar

ALIYU ya kalli MEENAT Yace baby kinga wa'yancan mutanan Tace eh
Yace duk Abokanaye nane da matarsu
Tace Amma sunyi kyau sosai
Yafara shafah jefan fuskarta talumshe ido yace naha'da miki birthday ne nacikarki 19 years bawanda yasani agida my baby
Da sauri tabu'de idan nata taxubamai
Cikin murna tarungume shi da qam qameshi
Tace wayyo da'di yayah naji da'di I luv u
Cikin sanyin murya Yace me2my baby
Yakama hannunta suka qarasagun tana manne dashi sam taqi barin jikinta da nashi
nan abokansa suka saka tafi taf taf taf

Wani Yace Amma wannan tafi qarfin qanwa dan tafi cancanta da Masoyiya
Shuru ALIYU yamishi har suka xauna takwantoh da kanta akafa'darshi
Shikuma yasaka hannunshi ya tarota
Yace wato 'yan Uwa wannan itace my baby MEENAT wacce kukejin labarinta aguna
Inasanta sosai fiye da tunanin metunani
Wani Yace hmm munda'de munajin karatun nan naka
Murmushi ALIYU yayi
Yace Mubarak aigwara na maimaita
Yace ai inbaka maimaitaba atambayeka

Yakai bakinsa setin kunnan MEENAT Yace toh  baby gaki garesu
Ahankali taraba jikinta danashi tagaidasu dukka
Sannan taqara da cewa nagode da tayani murnar wannan ranah Allah ya barku da yayana Cikin aminci
Sukace AmEEn dan sunyaba da hankalinta
Nan suka yanka cake 'din ita da ALIYU
Tabashi shima yabata
Abin ya birge kowa agun dan baqaramin dacewa da juna ALIYU da MEENAT sukayi bah har wani abokin ALIYUN yakasa hakuri Yace wannan dai Amaryarmu ce
ALIYU ya kalleta Yace wai haka my baby
Tayi saurin 6aye kanta agirjinsa
Yayi Murmushi suko dariya sukayi sukace wannan 'yar luv ce fah
Yace nagaya muku wannan qanwace Amma karku damu Amarya naxuwa...



Gaban MEENAT yafa'di akan me zaice amarya naxuwa
Haka sukaji ka'de  ka'de da ciye ciye da shaye shaye
Da raba abubuwa atsakanisu
Baqamin ku'di Ya ALIYU ya kasheba
Inji MEENAT da fa'da aranta

Haka kowa yakama  haryar gida dajin da'din wannan 🆒 birthday

Saura ka'dan su'iso gida
MEENAT Tace yayah naji da'di sosai Allah yabarmin kai
Ya watsa mata wani kallo
Wanda yasata saurin sunkwai dakai
Baxato taji yatsaya da motar
Yace kiss me my baby.
Ba musu tamatsa tamishi agoshi Tace kaji abinda nakeji
Ya gargixa matakai
Yarinta yasata cewa idan da nice kamin inajin xirrr tundaga Kaina harqasa idan kamin
Yace koh
Tace eh
Cigaba da tafiya yayi
Tace yauwa yayah wacece Aisha my luv awayanka nagani
Yace wata Auntynki ce tabiyu
Nantake ranta ya 6aci tayi shuru 'dif kamar anyi ruwa an'dauke
Yace yadai
 cikin jin haushi Tace qalau
Yayi Murmushi
Dai dai nan suka iso gida yana faking tayi yunkurin ficcewa
Yace kee
Tatsaya cak batare da takalleshi bah
Yakamota ya rungumeta Yace menayi kuma baby
Tayi shuru
Can tace toh meyasa xaka qara aure Yace ina buqatar hakanne tace banaso yayah dan Allah karka qara Yace meyasa Tace Aunty Lubba ta'isheka
Yace bata isheni bah
Baxatoh yaji tasamai kuka sosai
Cikin rikicewa ya'dagota yana gogemata hawaye Yace naji baxanyi bah shikenan
Ta'gamai kai
Yakai minti uku yana rarrashinta sannan tafita tashige falan Momy

Yayi shuru
Can yace akwai aiki agabana lubba baby Aisha
Baisan lukacin da yace bala'i 😳

Itako MEENAT fa'dawa gadan Momy tayi tafashe da kuka tace nashiga uku meyake shirin faruwa
Son ya ALIYU yakamani kokuma me sanshi nake shiyasa nake kishinsa meyasa
Kai inaga baso bane
Can kuma taqara fashewa da kuka



Can wata xuciyar ta daka mata tsawa da cewa
Lalle baki da hankali Ya ALIYU xaki so. Maxaki 6atar da wannan tunanin tunkai wani yajiki dan basan shi kikebah kawai bakya sone ya qara Auran.
Hakan yasa MEENAT tayi saurin kawar da tunanin kosan yayanta ALIYU take


Fushi sosai Ameera tayi MEENAT Amma dake MEENAT 'din nada baki nan tawanke kanta agunta
Yanxuma tana hanyar dawowa daga gidan Ameeran ne itada Salmah
Taha'du da Nawas Yace sainaji da'dad'dan labari kinfitoh
Tace qaddara tasani fitowa ya matarka
Yace tananan qalau
Tace madallah
Yace dan Allah kiqara bani dama akaro nabiyu
Tace hmm kaga yanxu agajiye nake kuma darene kusan 8:Pm kabarni nashiga gida nanda kwana uku saikaxo.....
ALIYU ne dallesu da futular motarshi sunko ha'da ido da MEENAT ya gallah mata mugun kallo
Daidai nan megadinsu yagama bu'de get 'din  yashige ciki
Salmah Tace MEENAT nayi gida tashige gidansu
Jikin MEENAT narawa tace saina ganka Nawas tashige Ciki

Aiko tanasa kai taganshi jingine ajikin motarsa
Yace xonan
Ahankali take tafiya hartaje gunsa
Baxato ya falleta da mari kyawawa biyu
Tagigice dajin marin hakan yasata fashewa da kuka
Yace narantse da Allah baby naqara ganinki da wani nalahira saiya fiki jin da'di
Yana fa'din haka ya bargun zuwa shashin mamah
Cikin kuka tabi bayansa

Duk suna falan harda Lubba
Momy tace meyasa meki Autata
Zatayi magana ya 6allah mata garara
Saitayi shuru
Mamah Tace bakiga tare suka shigoba qila wani lefi tayimai
Momy ta6atarai  tace wai meyasa kake takurama yarinyar nanne
Yace hmm Momy barni da ita
Tace idan naqifah
Yayi murmushi ganin tahau yace kiyi hakuri toh
Mamah tace kyalesu ALIYU naji waixaka tafi gobe
Da sauri MEENAT takalleshi anyi sa'a shima kallanta yayi
Yace eh mamah baxan wucce  sati biyu bah xandawo kwata kwata .Tace yauwa Allah yamaka albarka naji da'di sosai Yace AmEEn
Momy tace lubba tanasan kutafi tare
Yace no momy taxauna kawai
Tace toke kinji
Cikin rashin jin 'da'di Lubba Tace naji Momy

Washe gari ko ALIYU yagama shirinshi tsaf Hamisu da Aminu ne xasu kaishi kamar yanda suka saba
Kowa yana mishi fatan alkairi
Ya kalli Momy Yace ina baby ne
Tace tanacan 'daki waikanta na mata ciwo
Su Abbah sukace ashsha tasha magani dai ko Tace eh nabata

Shiga ciki Aliyu yayi
Yaganta kwance idanta biyu Yace my baby yadai
Tace banaso katafi yayah Yace aidaga wannan xuwan shikenan babyana
Ya'dagata
Narkemai tayi tace xaka dinga kirana Yace sosaima
Yanxu dai baki kiss lokaci natafiya
Haka tamai agoshi yamata shima Yace kikulamin dakanki baby
Tace insha Allah
Ya'dan rugumeta ka'dan yace inasanki
Tace nima haka Allah yakareka yayah ya kuma dawomin dakai lafiya
Lakuce mata hanci yayi sukayi dariya lokaci 'daya
Yafice
Tayi shuru. Ahaka tayi tashin motarsu
Wato ya ALIYU yatafi
Aiko saita sulale takwanta tana tunani.......




Meyasa bataso tafiyan shi nawannan karanba.
Meyasa takejin haushin Aunty Lubba
Meyasa takesan tajita ajikinsa manneda shi
Meyasa take tunaninsa takesan jin muryarsa
Meyasa takesan ya kasance tare da ita

Wannan shine tunanin da MEENAT takeyi

Yana sauka yakirata Tace yayah dan Allah kadawo da wuri Yace Naji fatana kilulamin da kanki
Tace insha Allah
Yace banda kula samarifah Tace toh
Yace bani kiss
Tayimai

Yau antashi da 'dan sanyi garin dan haka tunsafe datayi  shigar sanyi bata cire kayanba
Nawas yakirata taje
Yace wato MEENAT kedai tadabance Tace mekagani Yace gani nayi kayan sanyine ajikinki Amma ba qaramin kyau kikayiba.
Tace nagode
Yace ina muka tsaya da xancanmu Tace kabari idan yayana yadawo Ya ALIYU saikuyi magana
Cikin murna Yace banta6a jin da'di irin nayau bah Allah yadawo dashi lafiya nasan baxan samu matsala dashi ba
Tace ko Yace yah

Haka kullun Nawas yake xuwa susha hira San ransu shi da ita

Lubba ko da MEENAT kullun Cikin fa'da suke tun Momy namusu magana har tahakura tasaka musu ido

Kamar yau
Sadiya da SafiYYA sunje shopping
Momy mah batanan
Daga Lubba sai mamah da Lubba

Lubba na xaune wajan shaqatawar gidan ita da qawarta Mimi suna maganar maxajansu
Yayinda MEENAT kegefe tana karatun Qur'an
Lubba Tace wata shegiyace tasani agabah wai ita Aisha tabi tafine ni shegiyace duk makircina tafini
San ALIYU take sosai kuma shima baqamin santa yakeba.
Da sauri MEENAT takalleta kuma hankalinta ya karkata kan hirar tasu
Mimi Tace tab bakici ubanta bane Wlhi
Tace hmmm shegiyace batada ubu tananan gun yayarta dannayi bincike akanta sosai
Kuma Wlhi bakiga yanda nake jamata kunne akansa bah
Abin Takaici waishi tausayinta yakeji
Mimi takama baki Tace au waike har hiranta kukeyi dashi
Lubba tata6e baki Tace hmm aitadole ne tunda idan yakai dare Nace ina yaje saiyace gun Aisha..
Idan nafara masifah saiya maidani "yar iska ko qala baxai cemin bah
Mimi tayi dariyar Takaici tace tab banta6a sanin ke wawiyace ba saiyau
Banda haka ai Wlhi danice sainaje gidansu nana'da mata 'dankaran duka dayima yayar tata xagin cinmutunci da kashedi
Tace hmm Mimi kenan Amma baxanqi tataki bah.
Tace yauwa yanxu yaushe xamu shirya Komai
Tace kan masoyin nata yadawo

MEENAT najinsu tayi shuru wato wannan dai Aisha da Yace mata Auntynta tabiyu itace yanxu Su Lubba suke magana akanta
Tab jitayi dama suyi shirin da ita
Sai kuma tajah tsaki tana cewa aranta inama ruwanta da xata damu.

Tsakin datayi sai Lubba  taxata ko da ita takeyi dan haka saitace
Wakikema tsaki
MEENAT tamata kallan raini Tace dawanda ya tsargu
Mimi Tace Amma yarinyar nan bata da kunya ina qanwar ALIYU ce
Tace bar 'yar iska qanwarshi CE inadai dai da iskancinta
MEENAT takalli Mimi Tace banda kunyar kisam min taki mekunya
Mimi tawaro ido tace ke karki kuskura kimin rashin kunya danni tsinannan duka xanmiki Wlhi
Tace ko
Tace aikinji
MEENAT tata6e baki Tace dako kinyi kuskuran dahar kimutu baxaki mantaba
Dan medukan wannan fatar tawa saiya shirya.
Mimi xatayi magana Lubba Tace kinga qawata shareta tunda takemin rashin kunyar natabbata baxataji tsoran yimiki ba plx karki xama ita tashi muje part 'dina
MEENAT taja tsaki Tace dayafi muku
Haka suka ficce Mimi nakwafah
MEENAT tagalla mata harara

To iri irin wa'dannan abubuwan susuke faruwa tsakinin Lubba da MEENAT Sam basa jituwa


Yau tun safe Lubba  Momy mamah suketa 'dan shirye shiryan tarban ALIYU dan yau xai dawo
MEENAT ko Allah Allah take taji diranshi
Dama da ita xa'aje taranshi Amma tana shiga wanka Su Hamisu suka tafi.
Ranta ko ya6aci sosai
Tasaka wata shaddarta ALIYU ne yasiya mata
Mekalan ruwan ganye riga da siket dama kanta yasha gyara Amma batayi kitsoba
Tana Cikin kwalliyane  taji qamshinsa yabigeta
Subhalallah
Nan take taji wani sanyi yashigeta Amma takasa juyawa
Yaqaraso ya saqala fuskarshi akan wiyanta.
Saurin rintse ido tayi
Yace my baby gaye haka. Fa'damin wakikama
Tayi shuru....
Ko ba'ayi murnar ganina bane inkoma yanxu
Tayi saurin bu'de idanta. Aiko suka ha'da ido tajikin madubin
Yamanna mata kiss awiyan. Nan tsagar jikinta yatashi yarrrrr
Taqer ta'iya cewa nayi farin ciki da xuwanka yayah
Ya zare fuskarshi daga wiyanta  ya tsaya yana qare mata kallo Yace kinyi kyau sosai my baby
Plx tashi inganki dakyau kona qara samun nusha'di axuciyata
Tatashi tajuyo tana kallanshi yayi mata kyau sosai Cikin qananan kayanshi hakan yasa talumshe ido tabu'de alokaci 'daya
Yaware mata hannunshi. Da sauri tarungumeshi Yace nayi missing 'dinki my baby. Kifa'damin yakikaji da kika ganni
Cikin su6utar baki ko yarinta da sanyin murya Tace tunda katafi najishiga tunaninka yayah bansan dalili bah Hakka kawai natsinta kaina dasan inkasance dakai akoyaushe
Yace ranar xataxo my baby yanxu dai kibani abinda kika dafamin dan naki xanfaraci
Yafa'di hakan yanamai xareta daga jikinsa
Tace ban yima komaiba yayah dan ganin mamah da Momy suna shiryama kalolin abubuwa
Ga Aunty Lubba itama sai shiryama take 
Amma fa'damin mekakeso namaka yanxu
Ya qura mata ido Sannan yakai hannunshi kan fuskarta Yana shafawa Yace yanxu kuma ya hucce baby.
Ta6ata rai Yace karki 6atamin kwalliyarki plx  dan nasan ni akama ko
Ta'daga mai alamar eh Yace gud naji da'di sosai bara naje gun Auntynki tunkai ranta ya6aci
Tace danme fah Yace dan kinasan shiga gonarta.
Yana fa'din haka yafita
Yayinda ita kuma taxauna jagwab agefan gado tana tunanin  meyake nufi da tanasan shiga gonar Aunty Lubba
Ganin takasa gano Amsar shiyasa tawatsar da xancan

🅰ⓂAKIRCI NA💦
Mu ha'du a part 2
Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele
07038260028




Download A Makirci Nah Littafi Na Daya Complete HausaNovel