[03/12 23:02] Meela Adeel: *GUMIN HALAK...*馃挵3

*Batul Mamman*馃挅




Jirgin safe Alh Sule Chanji ya biyo yana ta tararrabin me zai tarar a gidan. Da shigarsa ko sama bai hau ba yaje dakinsa ya huta yayi wurgi da jakarsa da babbar riga ya sake ficewa. Baya ya zaga dakin BB yana kwala masa kira rai a bace.

Haj Mara tana ji ta fito da sauri don tasan zuciya irin ta mijinta. Kafin ta karaso ya banka kofar dakin BB yana bacci yaji wani mugun bugu domin kuwa da kafa mahaifinsa ya haure shi a ciki.

"Tashi mutumin banza wanda bai san inda ke masa ciwo ba. Yanzu Babawo har kayi girma da wayon danne mace ka gwada mata karfi? Lalacewar taka har ta wuce ace kana bin mata sai dai ace kana yiwa mata fyade? Ni kuwa me na rageka dashi? Tarbiyya ko ilimin boko dana addini"

Tuni BB ya koma bayan Haj Mara yana rike da cikinsa da ya kulle saboda harbin da ya sha. Alh Sule bai hakura ba ya sake yowa kansa tayi saurin tarewa.

"Haba, haba Alhaji! Kashe min yaro zakayi akan wata mai aiki"

Dariyar takaici yayi dama ita akan 'ya'yanta musamman BB kowa bai isa ba.

"Dole kice haka mana tunda ita mai aikin uwarta ba nakuda tayi ta haifeta ba. Nuna tayi a bishiya suka tsinkota ga dukkan alamu" ya fada tare da juyawa zai fita sai kuma ya dakata "ki sameni a mota muje asibitin na dubata. Idan taji sauki har gidansu zamuje kuma wallahi ko kunki ko kunsu Babawo sai ya aureta"

Haj Mara ta tafa hannu alamun dama na fada dinnan "Ahaf ai na sani, to ka makaro don tun jiya na mayar da ita kauyensu"

A harzuke ya juyo zuciyarsa na tafarfasa.
"Kika yi me?"

"Nace tana gidansu. Haba ka shigo babu neman karin bayani duk zaka hatgitsa mana gida. Abin nan duk rashin fahimta ne"

Tsayuwarsa ya gyara yana kallon yadda take wani kare danta kada  yayi yunkurin dukansa
"To fahimtar dani"

"A dakin nan na ganta kwance shine nayi zaton wani abu ne ya sameta. Sai da na bincika ashe sata tazo yi masa shi kuma sarkin zuciya yayi mata duka. To ni bazan iya zama da barauniya ba shine na mayar da ita"

Daga bayanta BB ne yake dariyar shakiyanci jin mahaifiyarsa tana gilla karya. Alh Sule yayi murmushi mai ciwo
"Kinga dan naki ma dariya yake miki saboda yaji kina sakin kwai a gabansa. Kukanki  lokacin da kika kirani ya isheni hujjar da zance yanzu  karya kike yi. Ki gama kwana-kwanar kizo muje garin nasu. Idan mun dawo sai kiyi min bayanin dalilinki na fita ba da izinina ba"

"Alhaji!"

Bai saurareta ba ya fita ta bi bayansa da sauri. A bakin bene ta same shi zai hau sama

"Ko aurena ne zai mutu bazan taba kaika garinsu Mawadda ba. Na riga na bata kudi har dubu ashirin ga kayayyakin sawa. Magana ta riga ta mutu sai dai a kiyayi gaba kawai"

Rasa abin cewa yayi. Wai dubu ashirin. Ko dubu dari biyu ta basu ai bazai zama fansa ga mutumcin 'yarsu da aka zubar ba. Ransa ya kai kololuwar baci har ya rasa matakin dauka. Yasan Mara bata da kirki amma baiyi zaton harda rashin hankali da tunani ba.

"Ni dai na aurar da yarana mata duka ban taba jin wani labari mara dadi game da mutumcinsu ba. Har izuwa yanzu Allah bai taba bani ikon yin lalata da 'yar kowa ba. To Alhamdulillah. Ke da danki ku jira sakamako. Shi sharri dan sakone. Idan ka aike shi ya isar da sako sai ya dawo gareka. Ki rubuta ki ajiye lokaci shi zaiyi muku alkalanci ke da shi da yarinyar da kuka cuta" daga haka ya haye sama abinsa sai karar kofa taji garam.

Tsaki tayi ko a jikinta. Tunda dai ya bar maganar aje a haka.

"Alkhairi zamu gani har duniya ta tashi mugun fatanka bazai bimu ba"

Babawo kuma aure zata masa  kafin ya sake sakata a tsaka mai wuya.
******

*Asalin Mawadda*

Mal Fatihu Wali dan kauyen Tariwa ne ta cikin karamar hukumar Bebeji a jihar Kano. Sana'arsa dinkin hula wadda wani dan kasuwa a Kwari yake zuwa sara lokaci zuwa lokaci. Sai kuma 'yan garin wani zubin. Idan babu cinikin hular yakan taba noma da kiwo.

Auren saurayi da budurwa sukayi da Haule. Suna zamansu lafiya Allah Ya azurtasu da 'ya'ya mata har hudu ya dauki soyayya ya dorawa iyalinsa.

Wata rana kanwar mahaifinsa taje ta sami baban nashi da kuka tana rokon ya taimaketa yasa Fatihu ya auri babbar 'yarta Sa'ade. Koda ya tambayi dalili ashe wani ne daga dangin babanta yake neman aurenta iyayen suka hana saboda marainiya ce ba idon uba kuma a cewarsu babarta tana da farar kafa don suna aure komai nasa yaja baya ciki kuwa harda lafiya da tayi masa karanci har tayi ajalinsa.

"Yaya Wali yarinyar nan bana shekararta daidai har goma sha tara. Habaici babu irin wanda ba'ayi min. Shine naga nima ba 'yan uwa na rasa ba. Don Allah kasa baki Fatihu ya aureta tunda sauran duk ta girme musu shine dai zai dubi zumunci ya taimaki 'yar uwarsa"

Mal Wali yayi shiru yana nazari. Baya son shiga sabgar gidajen 'ya'ya saboda rike girmansa. Sai dai ganin hawayen 'yar uwarsa ya taba masa zuciya. Haka ya kwantar mata da hankali sannan ya umarci Fatihu da aurenta. An kai ruwa rana dai saboda shi Fatihu baya son matsawa matarsa tunda suna zaman lafiya. Ita kuma Sa'ade har yanzu Balarabe take so dan wan mahaifinta duk da rashin mutumcin da ake yiwa mamanta.

Haka dai akayi auren. Tsakaninta da Yaya akwai girmamawa sosai amma fa bata ragawa Fatihu ko kadan da farko. Abu na Allah zama yai zama sai gashi sun dinke tamkar tsofaffin masoya. Ba jimawa sai ciki nan fa soyayya ta karu. Ta haihu lafiya aka sakawa yarinya suna Mawadda.

Wata rana a lokacin Mawadda tana da shekara daya da rabi kawar Sa'ade tazo daga Misau inda take aure. Suna hira take cewa "Oh Sa'ade kamar ba ke bace mai cewa idan aka aura miki Fatihu sai kinyi ajalinsa in bai sakeki ba"

Sa'ade tayi murmushi tana cigaba da yiwa Mawadda tsifa "ke dai bari...."

Iya abinda Fatihu yaji kenan ya juya da ledar hannunsa mai cike da magwaro da aka bashi ladan aikin lodi da sukayi a gonar wani. Ganin Sa'ade ce da girki shine ya kawo ta raba yaji wannan mummunan kalami.

Baiwar Allah Sa'ade ta cigaba da cewa kawarta "....kullum nayi sallah sai nayiwa Iya addu'a saboda ita tayi sanadin hadani da Malam. Ina son shi..." ta rufe ido da tafukan hannayenta wai ita kunya.

Dariya sukayi su biyun harda tafawa suna ta yabon mazajensu.

Fatihu kuwa bakinciki kamar ya kashe shi. Ashe duk zaman nan da son da yake mata ita kashe shi take son yi kila ta komawa tsohon saurayinta wanda akace yaki aure har yau saboda ita. Tsabar takaici har kuka yayi.

Da yamma ya dawo Sa'ade ta tashi ta dauko masa ruwa don bata ma san ya shigo dazu ba. Kwanon shan ya tankwabe a hannunta ya mika mata hannu.

"Kwanto min 'yata ki tafi gida na sakeki saki uku"

Gabanta ne ya yanke ya fadi ta dafe kirji sai kuka
"Malam me nayi maka haka da zafi?"

"Kinfi kowa sani. Kafin ki kasheni dai gara na sawwake miki kije ki auri wanda kike so"

Ta ma rasa gane kan zancen shi kuwa ya hauta da fadan ta fice masa daga gida kuma ta bashi 'yarsa. Bayani taso yi masa don duk yadda akayi yaji hirarta da kawarta ta dazu amma yaki saurara. Yaya tana ta bashi hakuri ya daka mata tsawa itama. Haka Sa'ade ta durkusa tana ta ban hakuri amma bakin  alkalami ya bushe. Maganganun da ya rinka fada mata cikin bacin rai yasa ta kwance goyon ta dangwarar masa da Mawadda a kasa. Yarinya ta hau kuka ko kallonta batayi ba saboda zuciya ta fice. Yaya ta dauketa zata bita yace idan ta fita kada ta dawo.

Gidansu kawarta ta ta fara zuwa tana kuka ta sanar da ita yadda sukayi. Ta tausaya mata tare da yin tir da bakinta da ya tado zancen. Daga nan suka wuce gidansu Fatihu suka sanar da iyayensa. Rayuka dai sun baci ranar musamman nasa. Balle da akayi masa bayanin karshen maganar gashi yayi hukunci cikin fushi.

Da kyar aka shawo kan Sa'ade ta karbi 'yarta don tayi fushi sosai da abinda yayi mata. Bayan ta yayeta aka mayarwa Yaya ita ta rike hannu bibbiyu. Mawadda ce take kiranta Ade shine sunan a hankali ya bita.

Sai bayan shekara uku da mutuwar aurenta sannan ta sake aure da tsohon saurayinta dai Balarabe. Iya bata so ba kamar yadda iyayensa basa so don ko auren fari baiyi ba sai dai ya kafa naci. Kano ya kai matarsa inda yake aikin walda.

Da farko kamar abin arziki suke zaune kalau. Daga baya ta gane mijin nata maketaci ne. Dan kudinsa a cikinsa yake karewa. Yaci banza yaci hofi. Shine teburin mai shayi shine gaban tukubar tsire. Iyalinsa kuwa kullum suna fama da garau-garau.

Da wahala ta ishi Ade sai ta fara kitso. Kan kace kwabo unguwa ansan da zamanta tana samun 'yan canjinta. Ganin ta soma samun sukuni wanda shi a wautar Balarabe mace tayi ta kwantar da kai gaban miji yana hura hanci shine aure. Sai cewa yayi mata na cika masa gida. Kitson nata sai ya koma bin gidajen mutane nan ma yace ta fiye yawo ga yaransu ba kulawa sosai. Ta hakura ta koma wankau yace danshi ya soma kama gidansa kada sanyi yayi musu illa. Surfe da dakan su yaji yace karar daka tana saka masa ciwon kai. Tuni hakurinta ya kare tace dole ta fita nema ko don yaran suyi karatu. Rigimar yau daban ta gobe daban har dai auren ya mutu shine ta fara aikatau. Shi kuma sai yanzu yake ta neman shiri a mayar da auren taki
******

Wurin shadaya ta gama aikinta na safe har tayi wanka tana shafa mai taji 'yar wayarta na kara. Ta dauko kafin ta dauka duk da rashin boko yau da gobe ta gane sunan Baban Mawadda a wayarta saboda da ita Mawadda take kira su gaisa. Zuwanta Bebeji gidan surukanta kuma kawunta kwanaki da akayiwa autanta kaciya har Tariwa taje aka sanar da ita Mawadda tana Kaduna aiki. Bata ji haushi ba don tasan ba kiyayya bace tasa aka turata. Duka 'ya'yan Yaya dake dakin aure sunyi kafin a aurar dasu. Yadda tasan zafin nema bata so 'yarta ta zama mai matacciyar zuciya ba. Indai zata sami gidan mutanen kirki babu matsala. Aikin da sukeyi ba kwadayi ke kaisu ba sai neman halak kuma kowa da inda Allah Ya rubuta masa abincinsa. Yanzu da taga wayar a zatonta Mawadda ta koma gida ne tunda biki ya gabato.

Da sallama ta dauka sai taji muryar dan uwanta tsohon masoyinta Fatihu. Gaishe shi tayi ya amsa muryarsa a karye alamun damuwa.

"Sa'ade do Allah idan zai yiwu kizo gida cikin satin nan"

Zuciyarta ta harba a take hankalinta ya tashi tasan ba lafiya ba.
"Ita wannan din ina take?" Ta fada a sanyaye.

Sarai ya gane wa take nufi tunda bata fadin sunan Mawadda. Kallonta yayi dukunkune a jikin Yaya tana ta rawar dari. Asibiti zasu je dama saboda zazzabin tun jiya yaki sauka ga sambatu tanayi ko yaya taji sauti mai dan kara ta rinka buge-buge kenan tana neman agaji.

"Bata da lafiya ne yanzu ma asibiti zamu je." Ya amsa a raunane.

Mawadda daga kwance da ta fuskanci da wa ake wayar cikin kuka ta fara cewa "Ade kiyi min addu'a ji nake kamar zai biyoni. Kamar mutuwa zanyi"

Da sauri Baba ya bar dakin sai dai Ade ta riga taji. Kuka ta saka masa tana rokonsa ya fada mata wane irin ciwo ne yace sai tazo. Bai bari ma ta gama magana ba ya katse kiran shima damuwa da bakinciki suna kara baibaye shi.

Ade kuwa da kuka ta fita daga dakinsu hankalinta a tashe sosai. Cikin gidan ta nufa 'yan uwanta masu aiki sunata tambayar ko lafiya ta kasa amsawa. Tana shiga falo tayi sa'a Sakina ta fito cin abinci. Har gaban tebur din taje ta durkusa daga gefe tana sharar kwalla.

"Umman Abbati don Allah ina son tafiya gida. Yanzu baban Mawadda ya kirani bata da lafiya sosai" kuka ne ma yaci karfinta ta kasa bayanin yadda taji muryarta.

Cikin halin ko in kula Sakina tace "Tohhh wace Mawadda kuma?"

Tsabar tashin hankali yau har sunan 'yar ta fada ashe.
" 'Yata da nace miki zatayi aure jiya"

Dariya sosai Sakina tayi tana kada kai ta mike tsaye tana salati "Amma Ade kin raina min hankali. Jiya wato don nace kwana shida na baki na zuwa bikin shine zaki ce bata da lafiya. Nufinki na barki ki tafi ni da ganinki sai an gama biki sai kiji dadin cewa jinya kika tsaya ko"

Ade ta bude baki tana kallonta kafin ta daure tace "idan baki yarda ba ga wayar ki duba da kansa ya kirani duk da bama waya. Yarinyar nan cewa take nayi mata addu'a mutu....wai mutuwa zatayi" sai sautin kukanta ya karu.

Kankance ido Sakina tayi ga masu aikin gidan suna saurarensu.
"Nafi karfin ki kawo min shirme irin wannan na yarda. Idan lokacin da na baki ne yayi kadan kije zan kara miki ya koma kwana goma ince ko ya isa"

Kan Ade har sarawa yake ba don fargabar halin da 'yarta ke ciki ba yanzu sai tsabar wulakancin uwardakinta. Wai shin duk abinda ya shafi rayuwar masu aiki ba shi da mahimmanci? Su ba mutane bane kamar kowa. Basu isa su kawo uzuri ba sai a nemi bin diddigi saboda kawai an rainasu? Da wata mai fada ajin ce tana kawo uzurinta za'a karba kila har a bita garin nasu don neman suna. Iyakar bacin rai tana jinsa a wannan lokacin.

" 'Yata ta cikina zan yiwa sharrin ciwo don ina son zuwa gida? Ba ni na kawo kaina ba har sai nayi haka idan tafiya nake son yi?"

"To wa ya sani ne? Ku maganarku ai ba abar yarda bace. Daga magana dake jiya yau zance ya sauya"

Juyawa tayi zata koma daki ta hada kayanta ta tafi Sakina ta dakatar da ita.

"Idan kika tafi kada ki dawo don a satin nan zan nemi wata"

Ade ta share hawaye "To Allah Ya baki daidai dake. Idan nayi miki wani abu saboda yanayi na zaman tare ki yafe min. Na barku lafiya."

Fita tayi Sakina tana jin kamar tace ta dawo amma har ranta gani take kawai karya take yi. Sai da ta tattaro kamai nata ta dawo falon tayi sa'a tana nan

Tace "Albashina nazo karba na watan nan zan wuce"

Sakina ta tafa hannu "wannan kuma kinyi kadan wata bai kare ba"

Ba tsoro a zuciyar Ade bare kara tunda tayi a baya ansa kafa an shure.
"Yau kwananmu goma sha tara da karbar wancan albashin. Na iya kwanakin da nayi aiki zaki bani"

Mai shararsu Sakina ta nuna da yatsa tace ya kira mata sikuriti tana ganin Ade abin nata harda wulakanci kuma.

Jakarta ta gyarawa zama dama sauran manyan suna bakin kofa guda biyu "basai an kirasu ba zan tafi. Amma ina so ki sani ba kullum ake kwana a gado ba. Zabin Allah ne ya kawoki nan ba iyawarki ko dabara ba. Hakkina kuma ki rike zan karba ranar da baki da kudin biyana."

Tana kaiwa nan ta fita sauran masu aiki suna biye da ita wasu na bata hakuri wasu na mata fatan alkhairi. Godiya tayi musu ta sabi kayanta tayi waje.

Har ta isa tasha tana mamakin hali na wasu masu kudin. Indai haka kudi yake sa zuciya ta bushe daga tausayin na kasa bata fatan samun wannan arzikin. Arziki irin wanda zai sa wani ko wata ta tafi da ita a rai kwatankwacin yadda ta tafi da Sakina tana mai jin zafi tare da neman sakayyar Allah akan yanayin zaman da sukayi.
******

Lokaci yana ta tafiya har uku da rabi kanin Baba da yake da akori kura ta daukar itace bai iso ba. Gudun tonon silili Baban ya nemi alfarmar ya kaisu asibiti yace dama yana hanyar zuwa garin yau. To gashi nan shiru har yanzu. Shima yana can ashe duk ya damu sai dai babu yadda ya iya yana jiran cikon kudinsa daga wurin wanda ya kaiwa iccen. Da kudin zaisa mai a tsohuwar akori kurarsa sannan ya hadowa iyalinsa cefane. Tun safe yake gidan ance maigidan bai tashi daga bacci  ba shine fa yake ta jira. Daga karshe hakuri ya kira dan uwansa ya bashi saboda bashi da halin tahowa a ranar. Ya kuma san tunda Mal Fatihu ya nemi alfarma lallai ciwon Mawadda ba na wasa bane.

Tun kafin ya gama bayani Baba yaji idonsa yana neman tara kwalla. Daga zuwan Mawadda zuwa yanzu kwana biyu kacal bai san adadin hawayen da ya zubar ba. Bakincikin halin da suka tsinci kansu yake yi saboda talauci. Yau da shi wani ne da tuni 'yarsa tana asibiti ana bata kyakkyawar kulawa shi kuma yana can ofishin 'yan sanda tare da dan iskan da yayi mata fyade fada sai inda karfinsa ya kare. Yanzu kuwa samun lafiyarta kadai ne a gabansa. Tsoronsa bai wuce firgicin da take yawan shiga ba da sambatu.

Har kofar gidansa achaba ya ajiye Ade da kayanta niki-niki. Tana ta adduar samunsu basu riga sunje asibiti ba. Kafin ta gama sauka Baba ya fito yana ganinta gabansa ya fadi. Baiyi zaton zata zo yau ba. Yanzu me zaice mata? Jikinta a sabule ganin yanayinsa itama ta tambaye shi ko sunje asibitin.

Har wani kwarjini tayi masa na dole da kyar ya iya cewa mota ce babu. Ainihin abinda ya hana samuwar motar garesu dama bai wuce yana gudun fita titi nemanta ba. Yasan duk wanda ya ga ya kawo mota kofar gidansa zai sha tambayoyi. Kauye kuma da bin kwaf baza'a dade ba yasan gaskiya zata fito a tsangwami 'yarsa.

Dan acaban Ade ta roka akan zata biya shi ya samo musu mota a bakin titi. A ranta tana cewa abinda zai hana Malam zuwa neman mota da kansa saboda lafiyar 'yarsa ba kadan bane.

Shi ya tayata daukar kayan ta shige gaba na dukan uku-uku. Tana sallama Mawadda ta fito tsakar gidan kamar an wurgota ta rungume Ade. Yau dai babu kunyar 'yar fari saboda yadda ta ganta ta fige fuskar nan kamar ba tata ba don ma ta fara sabewa.

Yaya ta fito suka gaisa a mutumce tana shimfida mata tarbarma don yaran duk sun tafi makarantar allo. Yaya kunya ta kamata rashin sanin me zata fadawa Ade. Ita kaddarar sai akan 'yar amana ta fada duniya zaginta zatayi kawai ace sakaci ne don ba 'yarta bace. Nata yaran babu wadda tayi aiki a gida irin wannan sai 'yar kishiya.

Ade tana ta rarrashin Mawadda tana kuma son tambayar me yake damunta amma ta kula daga Malam har Yaya babu wanda yake son mata bayani. Ba jimawa Baba ya shigo yace su fito mota tazo.

Duka su ukun suka fito dama Yaya ta fadawa sauran yaran idan sun dawo gidan babu kowa su tafi gidan kakaninsu. Tashin motar sai yayi daidai da zuwan Dahiru da leda a hannunsa ta kayan dubiya. Ya tabbatar su Baba ne a motar hankalinsa duk ya tashi ko jikin Mawadda ne. Yayi sa'a dan acabar bai tafi ba ya tambayeshi ina zasu je yace yaji kamar suna cewa asibitin Bebeji.

Bai tsaya wata-wata ba ya koma gida ya sanar da iyayensa. Inna har tausayi ya bata don tasan irin so da shakuwar dake tsakaninsa da Mawadda. Abinda zai baka mamaki shine duk son da suke yiwa juna idan an zauna hirar fa bata wuce yaya mutan gida, ya karatu lokacin tana zuwa makarantar allo da ta dare, ya aikin gonar da yake yi da 'yan buga bugarsa tsakanin Tariwa da Bebeji. Daga nan sai dai idan an hada ido yayi murmushi ita kuma ta sunkuyar da kai.

Baffansa yace "nifa nayi zargin da matsala don yau sau uku ina ganinsa a kofar gida kana ganinsa kasan bashi da nutsuwa. Amma kinsan Fatihu da kawaici sai ya kasa fadamin. Ban ga ta zama ba sun fita da la'asar sakaliya akwai matsala kila jikin Mawadda ne ba dadi sosai."

Inna tace "Baffa nima zani. Kuma kasan dole Dahiru ya bimu. Akwai kudi a jikinka dai koda zasu nema ko?"

Dan murmushi Baffa yayi. Inna akwai zurfin tunani da son taimako.  Tasan yafi Mal Fatihu wadata shiyasa take masa inkiyi ya fita da kudi. Musamman ma da abin ya hada da surukarta.

Dahiru ne ya samo musu mota ba jimawa suka bi bayansu Baba. Kafin wani lokaci magana ta fara yawo ai an ga iyalin Mal Fatihu da na Mal Isiyaku duk sun shiga mota sun bar gari da yamma.

Su Baba na zuwa asibiti sunyi sa'a likitan da zaiyi aiki har dare yana nan. Ade dai hakuri yazo wuya da taji likitan yana tambayar me ya sameta Baba yana cewa ita da Yaya su fita.

Ranta a mugun bace ta soma fada "Wai yaya kuke min haka ne? Tun a hanya nake ta magana duka ku ka ki amsawa ita sai hawaye kamar wata mai lalurar ciwon kuka. Na hakura na daure kuma yanzu a nan dinma dabara zakuyi min ko me?"

Mawadda ta dago da take jikin Yaya "Ke me ya sameki?"

Likita yace tayi hakuri suyi aikinsu. Ba don taso ba suka fita ita da Yaya suka barsu da wata Nos mace. Kallon Yaya tayi tana goge hawaye da gefen mayafi ta sake harzuka sai dai ta danne. Yaya mutum ce a wurinta harda kari. Ita kuwa bata manta karamci komai kankantarsa.

Daga cikin dakin duba mara lafiyar taji Baba hankali a tashe yana cewa " 'yan sanda kuma likita? Yanzu bazaka taimaka mata ba sai na nemo 'yan sanda sai kace wadda tayi sata ko kisan kai. Ita fa aka cuta"

Tuni Ade ta banka kai cikin dakin tana huci ko kallon Baba batayi ba "Likita me yace ya sami yarinyar nan?"

Mawadda taja mayafinta ta rufa har ka tana daga kwance an sakaya wurin da labule saboda bakinciki da kunya yayin da Likitan cike da alhinin yadda zata dauki maganar don ga dukkan alamu mahaifiyarta ce yace "fyade akayi mata"


"ME???" Ta fada da karfi wanda ya janyo hankalinsu Baffa, Inna, Dahiru da Yaya wadda mamakin ganinsu ya kasheta a tsaye duk suka nufi kofar dakin duba marasa lafiyar.

Nos da take tare da likitan kuma ita ta duba Mawaddan ta dafa Ade ta zaunar da ita "kiyi hakuri alamu sun nuna fyade akayi mata wanda yayi sanadiyar ji mata mummunan rauni"

"Mun shiga uku" cewar Inna hakan ya janyo hankalin su Baba zuwa bakin kofar dakin.
[03/12 23:02] Meela Adeel: *GUMIN HALAK...*馃挵2

*Batul Mamman*馃挅



Baban Mawadda yana shiga cikin gidansa ya samesu a tsakar gida kan tabarma inda suka zauna tun shigowarta da Haj Mara. Yanzu tare take da kannenta suna ta hayaniya su kadai domin ita kanta kunshe yake cikin hijab kamar yadda aka bata umarni tun a hanya. Idanunta kawai ake gani tana ta rarrabasu tana bin kowa daidai. Kai ya girgiza yana murmushi a tunaninsa 'yan shiru-shirun ne a kusa. Maimakon ya kirata sai ya je har inda take ya dora hannunsa a kafadarta tare da yin gyaran murya. Ba karamin tsoro bane yakamata hantar cikinta ta kada ta saki kara iya karfinta ga zuciyarta tana matsanancin bugu. Hakan yasa kannenta darewa a tsorace suna kallonta.

Yaya dake wurin girki tana gyara wuta don tasan yau babu mai tayata aiki sun ga 'yar uwarsu ta hango fuskarta a kumbure saboda hijabin ya zame lokacin da ta tsorata. Da sauri ta sake janshi ta boye fuskar tana inda-inda rashin sanin me zata ce ya bata tsoro, to ashe shima Baba ya ga fuskar. Zuciyarsa a take tayi nauyi da sake-saken me ya sami 'yar tasa.

Yaya baro wurin girkin tayi ta sallami duka yaran da fadan basuyi sallar la'asar ba har babansu ya dawo daga masallaci. Haka suka tafi suna ta kananan maganganu da hasashen ko yayar tasu tayi gamo ne a birni. Baba kuma hanyar waje ya kama zai fita Yaya ta tsayar dashi.

"Malam ina kuma zaka je ko baka kula da fuskar Mawadda bane?"

Jiki a sanyaye yace mata yanzu zai dawo. Waje ya koma tun daga soro Dahiru yaji sautin tafiya yayi saurin gyara tsayuwarsa a zatonsa Mawadda ce. Ganin Baba ya sake fitowa yayi saurin tsugunawa yana dan tsintar tsakuwa kansa a duke.

Baba ya kakalo murmushin dole "Tashi Dahiru, ai cewa nayi bari na fito da kaina kada a barka a tsaye kannen suna sallah. Wato ina shiga na sameta ba yadda take zazzabi ya rufeta."

"Assha, Subhanallahi.." cewar Dahiru damuwa karara a fuskarsa ma'abociyar fara'a da murmushi.

Baba ya cigaba da karyar dole saboda rashin sanin ainihin abinda ya sami Mawadda "kasan ita ba mai son doguwar tafiya bace a mota, inajin zaman ne duk ya saka mata zazzabin"

Shi Dahiru kunya ce ta lullube shi da takaicin kansa na zuwa tadi daga saukarta a garin ko hutawa batayi ba. Ashe ma ba lafiya take ba.

"Baba Allah Ya bata lafiya. Ina dubata da jiki. Ko zuwa gobe idan taji dama sai nazo dubiya"

Daga haka ya tashi ya tafi Baba ya juya cikin sauri. Wannan karon ba kowa a tsakar gidan. Daga kofar dakinsa ya hango takalman Mawadda ya karasa da sassarfa.

Yana daga labulen ya samesu jigum ita da Yaya. Yaya ta rafka tagumi ita kuma tana kuka mara sauti.

"Me tace miki ya sameta? Hatsari sukayi a hanya?"

"Ko daya Malam, jira nayi ka dawo don nayi juyin duniya taki magana"

Wannan abu da mamaki yake. Yarinya wata bakwai bata gida ta dawo babu farinciki sai fuska a kumbure.

"Mawadda me ya sameki?" cewar Baba

Ko dagowa batayi ba sai kukanta da ya tsananta. Ga tsoron fadin gaskiya ga azabar ciwo.

"Kina da wasu da suka cancanci sanin halin da kike ciki?"

Ganin taki kulasu ran Yaya ya baci. Dama can ita mace ce mai zafi sai dai akwai kirki da sanin ya kamata. Hijabin tasa hannu ta cire ta karfin tsiya sai ga shatin belt kwance a wuyanta da hannu. Lebbanta kuwa na saman tsakiyarsa yayi ja alamun jini ya taru na kasa kuma girmansa yayi ukun yadda yake a da. Batun kumatu kuwa sai a lokacin suka gane ba karamin kumburi sukayi. Da yake kuma tana da haske daidai gwargwado shiyasa tabban suka nuna sosai.

Jikin Baba yayi mugun sanyi wannan kam ko ba'a fada ba kowa yasan duka ne. Yaya kuwa kuka ta fashe dashi ta rungume Mawadda.

"Sai da nace kar kije ko kadan hankalina bai kwanta da tafiyar ba" Yaya ta fada cikin kuka

Wurin minti ashirin kafin kukan ya tsagaita. Zuwa lokacin ma zazzabi yayi mugun kama Mawadda jikinta sai bari yake tana rawar sanyi. Hankali a tashe Yaya ta fita taje ta kira sauran 'yan matan suka tayata dora ruwa a babbar tukunya. Suna tambayarta lafiya tace yayarsu ce bata jindadi faduwa tayi a can gidan aikin nata.

Baba da kansa ya fita ya tafi kemis neman panadol. Da ya dawo tana bandaki tana wanka. Duk yadda Yaya taso taje ta gasa mata jiki taki yarda. Sai dai bata sani ba tun a lokacin Yayan take kula da tafiyarta da ta sauya.
*****

Dahiru yana komawa gida Inna ta tsare shi da tambayar yaya akayi ya dawo da wuri ko kunyar magana yasa shi dawowa. Murmushi yayi tace

"Wannan gulma ana so ana kaiwa kasuwa. Kana jin ta dawo ka diba a guje kamar gaske"

"Inna bata da lafiya ko haduwa bamuyi ba. Ashe zazzabi ne ya rufeta saboda zaman mota" yayi maganar a sanyaye cike da damuwa.

Nan da nan Inna ta rude. Yadda danta yake son Mawadda haka take kaunar yarinyar saboda nutsuwarta da tarbiya. An shaidi gidan Mal Fatihu da tarbiya duk da yawancin yaransa mata ne. Yaya akwai kokari da jajircewa.

Zakara babba mai rai da lafiya Inna tasa Danlami ya kama ya yanka mata. Yana zaune yana aikin figa sai tura baki yake yau an hanashi zuwa kwallo. Yana gamawa Inna tasa aka jajjaga mata kayan miya ta hada da kayan kamshi harda daddawarta mai kyau tayi farfesu mai dadi. Kai da kafa kawai ta cire a ciki aka bawa Danlami da Ummiyo mai bi masa suka lasa. Sauran kuwa maigidanta ta aiki Dahiru ya sanarwa a bakin kasuwa zata je dubiya idan anyi magariba.
*****

Inna da Dahiru suka tafi yace zai jirata a kiyos din wani abokinsa kada ya sake zuwa a ga rashin hakurinsa kuma.

Tunda Mawadda tayi wanka take kwance iyayenta sai kai kawo suke gashi taki magana balle cin abinci. Sallamar Inna yadda ta kada mata hanji haka ta kadawa su Yaya. Basa so kowa ya ganta a wannan yanayin har sai sun san abinda yake faruwa. Inda Allah Ya taimakesu babu wuta saboda haka bata ganta ba sosai. Da tayi yunkurin tashi ma Innar da kanta tace ta kwanta har tana basu shawarar idan zazzabin bai sauka ba da safe su kaita asibiti. Haka suka taba hira sama-sama ta kawo farfesun nan tace a bata. A mutumce sukayi sallama ta fito.

Fitarta tayi daidai da sauke ajiyar zuciyar Yaya. Rai a dan bace ta soma yiwa Mawadda fadan sai ta fadi me ya sameta. Wannan karon ma kukan ta soma sai ta kyaleta saboda yara.

Wuri karfe taran dare ta tashi zata zaga bayi Yaya ta kuma ganin tana tafiya kamar mai dingishi tana karkace kafa. Tsoro ne sosai ya kamata ta dai kama bakinta. Sai dai sam ranar ta kasa bacci. Baba yana kula da yadda take ta juyi cikin dare sai ta danyi tsaki ko ajiyar zuciya. Can dai da abin ya isheta ta tashi da sanda ta fita. Lokacin daya saura na dare.

Dakin yaran taje ta leka ta taga ta jiyo alamun kukan Mawadda. Dakin da suke ajiye kwanuka da tarkace taje ta dauko wuka ta dawo. A hankali ta shiga ta tabota. Yanzu ma zabura tayi kafin tayi ihu Yaya ta haskata da 'yar fitilar da batir din yayi sanyi ba haske sosai.

"Tashi muje dakina ki kwanta nan zaki takura"

"Yaya ki barni a nan tsoro zanji ni kadai"

"Zan tayaki kwanan tashi mu tafi"

Ba musu ta tashi suna shiga Yaya ta tura kyauren ta hade rai sosai tare da daga wukar yadda Mawadda zata gani.

"Tambayarki zanyi kuma kika sake kika min kuka sai na lahira ya fiki jindadi kin sanni sarai. Me ya sameki???"

Kuka zata fara bakinta ya soma rawa Yaya ta dora yatsanta akan baki "wallahi Mawadda zanci mutumcinki idan kika min karya. Ki bude baki ki fada min uban me kike boyewa? Sata kika yi a gidan suka miki duka ko kuwa?" Har ranta bata son fadin abinda take zargi.

Ta yaya zata fada bayan kashedin da akayi mata? Banda ita duka gidan fa Haj Mara tace zata sa a harbe.

Wukar Yaya ta dago "ko ki fada min ko na yankaki a dakin nan babu wanda ya isa ya kwaceki....kin bude bakin nan ko sai jikinki ya fara jini?"

A raunane Mawadda ta durkushe a kasa "tace harbemu duka harda ku zata sa ayi idan na fada"

"Ita wa kenan?"

"Hajiyan da ta kawoni dazu wadda nake yiwa aiki"

Jikin Yaya duka yayi sanyi hannunta yana rawa ta riko Mawadda.
"Babu wanda ya isa ya cutar da wani sai Allah Yaso. Ki fada min me ya faru"

Kuka mai sauti Mawadda ta soma da kyar ta iya cewa "BB ne"

"Wa kika ce?"

"Dan Hajiyar ne, shine...shine.." kuka ya hanata cigaba

Yaya tuni zarginta ya kara tabbata. Wukar ta yar tayi kan Mawadda ta kwantar da ita tare da janye zanin jikinta. Abinda idonta ya gani yasa tayi baya a gigice tana salati. Tana kaiwa jikin bango ta sulale a kasa kawai sai ta fashe da kuka.

Mawadda ta rarrafo ta fada kanta itama tana yi.

"Yaya wallahi fin karfi yayi min...ya zaneni, ya fasa min baki sannan....kuma nayi ta rokon Hajiyar ta maidoni gida tunda ya fara bina taki. Ciwon da nake ji Yaya gara na mutu na huta"

Yaya bata iya cewa komai ba sai kukan da take bilhakki.

Mal Fatihu wanda tun fitar Yaya ya taso shima musamman da yaga ta dauko wuka yana jingine a jikin kofar dakin  yaji jiri na dibarsa bayan ya gama jin komai. Duk tunaninsa bai taba hasashen zai ji wannan bakin labari ba.

Kofar dakin ya dan buga a hankali "Haule bude min kofar nan"

Da saurinta ta tashi ta bude yana shigowa ta nuna masa Mawadda wadda ta gama tsurewa saboda yanayin fuskarsa duk da rashin wadatar haske babu annuri.

"Malam fyade akayi mata...mun shiga uku Malam....na gani da idona wallahi aikin karfi ne da ganin wannan rashin imani"

Hannun 'yarsa ya kama ya tayar da ita tsaye.
"Ki dubi girman Allah ki fada min gaskiya karfi aka saka miki ko kwadayi ne yasa kika kai kanki?"

Tana kuka ta rinka basu labarin abinda BB yayi mata.  Ba komai bakinta ya iya maimaitawa ba tana kuka iyayenta suna yi.

Baba yana rike da ita ya share mata hawaye "Allah Ya isanmu Mawadda, Allah zai bi mana hakkinmu zaiyi miki sakayya kinji"

A fusace Yaya ta mike tana kuke ido "Malam kada kace min a iya nan zaka bar maganar nan? Shegiyar mata don rashin kunya ta shigo har gidan nan tace wai tafiya ce ta kamasu. Mu zata wulakanta saboda suna da arziki. Yanzu mutumcin 'yar tamu da aka kwata ta karfi shine aka fanshe shi a dubu ashirin din da ta bayar dazu. Kudinsu na banza to Yasin bazamu lamunta ba"

Baba yace tayi a hankali dare ne fa "banda abinki me zaki iya yi musu? Ya riga ya cucemu sai dai mu barsu da Allah"

"Shikenan mu talakawa ba mutane bane Malam? Hawayenmu ruwane? Bakinciki, damuwa da ciwonmu duka ba ababen dubawa bane saboda bamu da kudi?" Yaya ta fada tana sake rushewa da kuka.

Daren ranar babu wanda ya rintsa cikinsu daga kuka sai kuka. Baba ne yayi karfin halin dauro alwala ya tayar da nafila domin neman sassauci.
******

Kwanuka ne jibge a gabanta tana wankewa ga rana ta take har ruwa idanunta suke yi. Kofi aka jeho ya sameta a tsakiyar baya sai da ta gantsare. A haka ma wai don na roba ne. Bata bukatar karin bayani tasan ko waye da wannan aikin. Duk gidan babu wanda ya rainata a matsayinta na mai aiki kamarsa.

"Ke Ade Umma tana kiranki tace kiyi sauri"

Fara'ar dole ta nemo ta yaba a fuskarta kafin ta bashi amsa.
"Abbati kace mata ina zuwa kaji, kuma don Allah ka dena jifa ka tuna na fada maka babu kyau" ta kare da sassauta murya. Indai zai kawo wani abu wurinta to sai dai ya jefa mata saboda baya son ta taba shi ma balle ta rabi jikinsa tunda dai sunanta mai aiki.

Ko kallonta baiyi ba da tayi maganar ya juya yana buga game a wayar babarsa. Gumi ne sharkaf a jikin Ade haka ta tashi ta dauraye hannunta sannan ta shiga cikin katon gidan ta kofar kitchen dake baya.

Sanyi ne mai ratsa jiki ya marabceta a falon matar gidan ta durkusa daga can gefe

Yaronta karami dan shekara uku da rabi ta nuna mata yana tsaye a jikin labule.

"Fa'iz ne yayi kashi kije kiyi masa tsarki. Idan kin gama ki gyara min wurin sosai kinsanni da jin wari. Kin karasa wanke wanken ne?"

Ade har tayi gaba tana kokarin daga dirkeken yaron mai uwar kiba tace saura kadan.

"Ni kuwa bana son nawa Ade gashi na kula kamar halinki ne. Kinsan sarai duk laraba sai kin wanke komai na kitchen saboda bana son ganin kwanukana da kura amma sai ki wuni abu daya" tana magana tana hade rai

Dan murmushi Ade tayi. A lalace tasan ko yaya zata baiwa matar nan shekara goma. Tasan ita ce a kasa dole ta bi ta amma wani wulakancin ko darajar shekaru ai a raga maka.

Wucewa tayi ta gabatar da aikin da aka sakata. Bayan ta gama ta koma wurin wanke-wanken a tsakar rana. Gida ne babba mai kyau don kuwa maigidan dan kwangila ne da ya shahara.  Uwardakinta Sakina  ce matarsa ta uku kuma kowace gidanta daban. 'Ya'yanta hudu duk maza shiyasa take fankama ita a dole ta kama gida saboda sauran yaransu maza bibbiyu ne.

Wurin ajiye motoci an kebe shi daban anyi rumfa. Haka wurin wasan yaran da ma wurin da maigidan yakan zauna shan iska a lambun gidan. Sai dai kash, wurin da Ade tafi wuni tana aikin wanke-wanke babu koda langa langa. Komai rana haka take yi, idan kuma ana ruwa ta koma ciki yana daukewa ta dawo, ba'a taba tunanin gyarawa ba tamkar ba mutum ke aiki a wurin ba. Uwardakin nata tamkar mai aljanu ko ruwa aka sha da kofi to ya zama kayan wanke wanke kuma. Ita gadara yaranta fitsara.

Sai da ta gama komai ta koma falon can inda aka ce ta rinka dakatawa saboda ba'a taka kafet indai ba maisharar cikin gidan ba ta durkusa.

"Dama akan maganar da na soma yi miki ce rannan na zuwa gida naga baki ce komai ba"

Tsaki Sakina ta buga ta ajiye remote din hannunta.
"Bala'i! wato na lura Ade ke fa da mayya ce idan kika kama mutum sai buzunsu. Kin tado maganar nan yafi sau biyar saboda bana son ji nake katseki amma kinki hakura. Ku wai baku da aiki sai son zuwa gida? Kwanaki kince kaciya akayiwa autanki na barki kinje har kwana biyu yanzu kuma kina son sake zuwa wani wurin..wane uzurin gareki kuma?"

Duk da ranta ya baci haka ta danne "Yarinyata ce bikinta ya matso watan cika ciki"

"Yarinyarki kuma? Yaranki duka ba maza bane su hudu kuma dai ai suna yawan zuwa gidan nan ganinki tunda suma a cikin Kanon suke"

"Ita babbar a kauyenmu take wurin nata mahaifin"

Sakina ta sake jan tsaki. Wannan abu yana matukar konawa Ade rai don bata son ayi mata tsaki amma ya ta iya.

"Gaskiya bana son yawo Ade idan aikin kika gaji dashi sai na nemi wata"

Hankali a tashe tace "Hajiya me ya kawo neman wata? Wallahi bikin 'yata ne baifi wata biyu ya rage ba. Shine nace bari na sanar dake da wuri don nasan ba kya son titsiye"

Shiru Sakina tayi tana tunanin muddin Ade ta tafi zasu wahala. Ita take wanke wanke da kula da yara. Mai shara namiji ne dama sai mai  girki wata bayerabiya duk rashin mutumcinta bata iya yi mata saboda tsoronta ma take ji. Matar bata daukar raini don da iliminta. Ade kuwa marainiyar wayonta ko waya zata kira sai ta bata ta roki ta nemo mata sunan da take son kira.

Da gangan tasha kunu "Ni dai bangane wani watan cika ciki ba. Bayan sallah da kusan sati biyar za'ayi bikin babban dan Alhaji kuma baki da yawa zasu sauka a gidana. Idan kin bincika watan bikin yar taki a na bature sai ki fada min. Satin bikin ki tafi talata ki dawo lahadi. Nasan halin mutanenmu uwar amarya bata wani abin kirki a bikin 'yarta akwai 'yan uwa da abokan arziki."

Ade tayi shiru tana tunani. Wato bikin dan Alhaji shine biki na 'yarta kuma ko oho. Dan kudin da take samu a gidan ba karamin tallafi yake mata ba. Ga yara hudu a gidan mijin data baro ga babbar a kauye tare da nata uban da aurensu ya dade da mutuwa. Bazata so rasa aikin nata ba shiyasa ta amince da sharadin Sakina ba don taso ba.

Murmushi tayi wai Mawaddanta ta isa aure. Da aikin nan ta hada ya kusa dubu dari da zata fito da tilon diyarta wadda kaddara ta rabasu.
*****

Gidan Mal Fatihu kuwa sun tashi da bakinciki da bacin rai. Mawadda a kwance take ba yadda take don jikinta har wata irin kyarma yake. Yau Yaya da kanta tayi mata wanka duk inda ta taba Mawadda sai tayi kara. Sai lokacin ta tabbatar da muguwar barnar da BB yayiwa diyarta. Har wani wari ciwon ya soma fitarwa saboda rashin kula da muninsa. Lokacin zabura Mawadda ta rinka yi tana sambatu sai kayi zaton wata mai haihuwa ce. Kuka sosai suka sha sannan ta fito da ita tana taku da kyar. Kannenta kuwa yadda suka dauka aljanu ne haka iyayen suka barsu.

Abu irin wannan babu mai son duniya ta sani shiyasa suke komai su kadai. Sunyi shirin tafiya asibitin karamar hukumarsu ruwa ya kece babu yadda zasuyi suka koma gida. Sannan ne kuma Yaya ta bawa Baba shawarar kiran Ade a matsayinta na mahaifiyar Mawadda.
[03/12 23:02] Meela Adeel: *FIKRA WRITERS ASSOCIATION*


 *GUMIN HALAK...*馃挵1

*Batul Mamman*馃挅

*Bismillahir Rahmanir Rahim*



Karar rufe kofar dakin Hajiya ta jiyo alamun ta gama shiri zata fita. Gabanta ne ya fadi saboda fargabar da ta dirar mata.

"Shikenan na banu na lalace" ta fada a fili cikinta yana wata irin yamutsewa saboda tashin hankali.

Tun shekaranjiya bata da lafiya ga matsanancin ciwon jiki amma ta kasa fadawa kowa. Hawaye ne ya shiga sintiri a kumatunta taji bazata iya karasa wanke tukunyar da ta fara ba ta ajiyeta a sink ta fito falon a gaggauce.

Baki na rawa kamar wani zai rigata tace "Haaaa....Haa..Hajiya...Hajiya yau ma fita zakiyi?"

Wani irin kalo Hajiyan ta bita dashi rai a bace tace
"Lallai Mawadda ni kike tambaya ko fita zanyi? Ni da ke wa yake zaman wani?"

Ko dukanta zata sake yi yau ma bazai hanata magana ba. Durkusawa tayi akan gwiwoyinta ta hada hannuwa tana kuka sosai.

"Don Allah Hajiya a kaini gida bani da lafiya"

Haj Mara ta sami wuri ta zauna tana mata kallon tuhuma.

"Ke! Tashi ki dauko min jakar kayanki maza-maza kafin na kirga uku kin dawo"

Da hanzari Mawadda ta tashi ta dauko jakar Ghana mustgo dinta harda sako hijabi ta fito da 'yar murnarta zata rabu da kaya.

Haj Mara tana zaune tana karkada kafa ta warce jakar ta zazzageta a kasa. Da kafarta wadda take sanye da takalmi ta rinka bankade mata kaya ta tabbatar babu wani abu a ciki da ba na Mawaddan ba sai tsirarun tsofaffin kayanta da ta bata tun farkon zuwanta Kaduna ta fara mata aiki.

Ita dai Mawadda tana daga gefe tana kallon ikon Allah. Kayan sawarta ne kamar kashi a kasa ake takewa da takalmi. Abin bai  ma bata mata rai ba tunda a ganinta burinta zai cika-zata bar gidan.

"Tattarasu ki mayar daki"

"Na'am" ta fada cikin zaro idanu.

Tsawa Haj Mara tayi mata wanda yasa ta fara kwasar kayan tana cusawa a jaka.

"Dama nayi zaton sata kika yi min shiyasa kike son tafiya gida na kuma ga ba hakan bane. Makota da kike shiga ne idan na aikeki aka zuga ki ko me?"

"A'a Hajiya bani da lafiya ne"

"Kinibabbabiya sai kiyi ta sunne kai irin na rikakkun munafukai. Wata gulmar ce zaki ce kina son tafiya ko shekara bakiyi ba. Ita mai kawokun duka duka yaushe tazo ta karbi kudin aikinki bakiyi zancen tafiya ba sai yau"

Ita dai bazata iya fadin dalili ba ko don tsira da rayuwarta amma a barta ta tafi kawai.

Ta cigaba da sababi "Dama haka kuke masu aikin nan da shegen kwadayi da rashin godiyar Allah. Sai kuzo da kunyi 'yan watanni an murmure ku fara hangen wani gidan. Ki bace min da gani kafin jikinki ya fada miki. Kuma ki tabbatar kin gama komai kamar yadda na fada miki tun daren jiya kafin na dawo. Banza jaka sai kiyi ta rarraba ido irin na mayu. To kurwata kur idan ma ita ce. Kudi dai ina aikawa iyayenki balle ace kyauta kike min"

Tunda ta fara magana Mawadda ko tari batayi ba sai zubar hawayenta da ya karu. Nadama ce fal a zuciyarta da mamanta ta dage bazatayi aikatau ba irin na sauran 'yan uwanta amma ita da Baban suka kafe wai a haka zata samo kudin da za'ayi mata kayan daki ga nauyin gidansu yayi masa yawa. Tabbas suna fama da talauci kuma gidansu babu maza sai yaran karshe biyu duk kananu bare su taimakawa Baban nasu. Sai gashi wata bakwai da zuwa ta gane tayi kuskure babba ma kuwa. Haj Mara masifaffiya ce ajin karshe ga rashin sanin darajar dan Adam. Duk da shekarunta sha bakwai amma yanayin rayuwa da wahalar kauye sai ka zata bata fi sha hudu ba. Idan tayi laifi duka Hajiyan keyi mata kamar wata kankanuwar yarinya ga zagi da gori har sun dena damunta ma. Duk wannan ba shi bane tashin hankalinta kamar dan Hajiyan da ya dawo daga turai BB wata daya da ya wuce. Dan duniya ne na bugawa a jarida ko irin kyamar nan ma baya mata ganinta 'yar kauye burinsa kawai ya bata mata rayuwa. Har alkawarin kama mata gida yayi da taki yarda shekaranjiya yaso gwada mata karfi suka sha dambe a dakinsa da aka shardanta mata gyarawa da kyar da sudin goshi ta kwaci kanta.

Jiya da Hajiyan ta wuni a gida ko bangaren bai shigo ba amma ta tabbatar tana fita zai dawo. Ta rasa yadda zatayi domin yace idan ta fada sharrin sata zaiyi mata yasa a kulleta a gidan yari. Da yake batayi karatu ba kuma babu wayewa shiyasa ta yarda da maganarsa ta kasa fada kuma tsoronsa yayi mata mugun kamu.

Tana wannan tunanin bata ma san Hajiyan ta fice ba haka ta dauki kayanta ta koma daki jiki a sanyaye.

Bayan ta ajiye ta dawo ta kama kofar falon ta rufe da sakata sannan ta saki dukkan labule tana fatan tsira daga sharrin BB sai ji tayi ana kokarin dagata ta baya. Wani irin razanannen ihu ta saki kafin ya gama fita daga bakinta ya toshe shi da hannu daya ya soma janta zuwa dakinta.

Suna shiga ya rufe kofar sannan ya dauko wata 'yar karamar wuka daga aljihunsa yana dora hannu akan labbansa. Ba shiri ta hadiye ihun da take shirin yi.

"Ka yiwa Allah ka rufa min asiri"

Katifarta ya dare ya kwanta yana mata wani irin kallo.

"Kinga malama ki saki ranki kici arziki. Duk yarinyar da tazo aiki birni dama ai abinda yake kawoku kenan. Kuji dadin zama ku fara neman mijin da zai ajiyeku a nan kada a koma kauye"

Cikin shesshekar kuka tace "ni anyi min baiko watan cika ciki za'ayi bikina"

"Me zakiyi da dan kauye keda kika dana birni? Nasan kina so gulma ce kawai kada nace miki 'yar hannu. Idan kika amince min fa aurenki zansa Hajiya ta nema min"

Jikinta sai tsuma yake tana kalle-kalle ko akwai wata mafitar bayan kofa. Bata manta irin kashedin Babanta kafin ta taho harda ikirarin sai ya yankata idan ta kwaso abin kunya duk don ya tsorata ta da sauya hali.

Shi kuwa BB wukarsa ya rinka karkada mata karshe ya bukaci tazo ta kwanta itama.

Ja da baya tayi dan hakurinsa tuni ya kare ya taso yayo kanta da wukar. Saduda tayi kawai tana kuka tace gara ya kasheta da ta amince ya bata mata rayuwa. Ganin idonta ya kekashe kawai ya jefar da wukar ya fincikota. Mari ya rinka tafka mata ta hagu ta dama ta ma rasa kuncin dafewa sai kukan da take yi kawai. A haka ya kaita kasa ya bita tana ihu tana rokonsa.

"Wayyo Allah, Baba ka taimakeni, Yaya za'a cutar miki da 'ya....."

Ihunta duk ya cika masa kunne ya zare dankwalinta tana shirin tashi ya danne mata ciki da gwiwar kafarsa sannan ya dangwarar mata da kai akan tiles din dakin ta koma bata iya motsi sosai. Bakinta yake kokarin daurewa tana cewa.

"Wuta balbal BB, wuta balbal bazan yafe maka ba ko kabarinka yana ci da wuta. Ko walakiri...."

Tana ji tana gani ya daure bakin ta samu ta sa kafa ta kai masa naushi a ciki har ya fada da baya. Wannan takaicin yasa shi zarar belt ya rinka tafkarta sai da yaji gunjin kukan ma bata iyawa sannan ya wurgata kan katifarta.

********
Haj Mara bata karasa gidan kanwarta da zata je ba duba maigidanta da ba lafiya kawai ta tuna yanayin fuskar Mawadda. Tsaki tayi don kawar da abin amma ya gagara. Kasa karasawa tayi duk da har ta shiga unguwar ta juya motar ta koma gida.

A wajen gate ta sami maigadinsu yana cin gyada. Ganinta da yayi yasa batayi horn ba ya bude mata kofar ta shige.

Iyakar rashin imani BB yayiwa Mawadda don jinta take yi kamar ba a duniya take ba shiyasa ko motsi ta kasa. Kwatanta ciwon da take ji ma bazai yiwu ba. Yana tashi yasa kafa ya haureta

"Banza arziki na binki kina gudu. Kuma wallahi na fada miki wani yaji zancen nan sai na farke miki ciki. Sannan ki fara shiri gida zan kama miki zamu fi sakewa don bana son takura"

Jin kofa da Haj Mara tayi a garkame yasa gabanta ya dan fadi. Sai tayi tunanin zagayawa ta baya ta shiga ta kitchen. Daidai tagar dakin Mawadda taji muryar BB hantar cikinta ta kada tayi saurin komawa ta kara kunne.

"Dalla malama ki tashi ki gyara jikinki kafin Hajiya ta dawo duk da dai nasanta da yin dare a waje idan Alhaji baya nan"

Haj Mara ta dafe kirji a tsorace tayi sa'a tagar ba a rufe take ba tasa hannu ta daga labulen. BB ta hango duke kan Mawadda yana kai mata mari "ke tashi mana ko wani sabon salon...."

"BABAWO!!!" Abinda Haj Mara ta iya fada kenan da karfi kafin ta soma gudu ta shiga gidan. Dakin Mawadda taje ta hau bugu tana cewa su bude. Bashi da zabin da ya wuce budewar saboda da ido kawai Mawadda ke binsa amma taki motsi balle ta tashi yana tsoron ko ta suma ne .

Bangaje shi Hajiya tayi ta shigo kamar zakanya tayi kan Mawadda ko kula da yanayinta batayi ba ta kwada mata mari.

"Karuwan kauye kunfi kowa iskanci. Ku shigo birni ku lalata magidanta da 'ya'yansu"

BB ne ya rike mata hannu zata sake dukanta "Hajiya bata motsi fa. Ba dai kin kashe musu 'ya ba. Ni dai babu ruwana da ranta na barta"

Sai a lokacin ta kula bakin Mawadda a daure yake ta yaye bargon ba shiri ta kawar da kai.
"Auzubillah Babawo ka jawo min masifa. Fyade kayiwa 'yar mutane?"

Mawaddan ya kalla wadda azaba taci karfinta tsoro ya kamashi kada ta mutu.
"To ai kece Hajiya nasan da cewa nayi ina son aurenta bazaki yarda ba"

Tashi tayi tana kuka tayi kansa da duka "fita dan ubanka....na shiga uku na."

Da kyar ta tallafi Mawadda ta dagata zaune ta ma rasa me ya kamata tayi mata kuma. Hannunta da kyar ya iya zaro waya a jakarta ta kira maigidanta Alh Sule Chanji. Yana can Lagos inda harkokin nasa suka fi karfi. Ko da ta fara masa bayani ba karamin tashin hankali ya shiga ba. Fada ya soma yi mata kamar ita tayi sannan yace a kai yarinyar asibiti yana nan tafe ranar laraba.

Haj Mara ta amsa har ta sakawa Mawadda kaya wata zuciyar ta kwabeta akan tonawa kanta da gidanta asiri. Dammara taci da mayafinta dankwali kuwa bata san inda ya fadi ba ta tafi dakinta ta debo ruwan zafi bokiti uku. Ita kadai take ta hawa da sauka bene BB ya fice ma bata san inda yayi ba. Haka ta zage ta soma yi mata wanka sai dai tana soma jin kwari a sanyaye tace zata iya.

Fita Hajiyan tayi tana ta kai kawo a dakin har Mawadda ta fito tana bin bango. Sai a lokacin ta tuna yadda ta rinka rokonta akan zuwa gida. Data sani ta barta da haka bai faru ba.

Ganin Hajiya a dakin yasa ta saki wani irin kuka mai shiga rai. Haj Mara ta riko hannunta zata zaunar da ita akan katifar ta zabura ta fice daga dakin da sauri. Ko zata mutu babu ita ba wannam bakin daki da ya kafa mummunan tarihi a rayuwarta balle kuma katifar.

A korido Hajiya ta ganta ta kama hannunta batare da tayi magana ba ta kaita nata dakin a sama. Daga cikin kayanta ta dauko mata doguwar riga wadda fadin ne kawai yayi mata yawa saboda Haj Mara ba tsayi gareta ba. Bayan nan ta bata shayi da maganin ciwon jiki tasha bisa tursasawa. Sai da ta dan nutsu Haj Mara ta soma magana.

"Mawadda kiyi hakuri akan abinda Babawo yayi miki kuma don Allah ki rufa maganar nan kada kowa yaji "

Batayi mamakin furucin Hajiyar ba saboda ta dade da gane mutane suna da son kai.

"Hajiya ki kaini asibiti don Allah" kuka ne ya taso mata mai karfi.

"Idan muka je asibiti kama Babawo za'ayi a kulle ki taimaka kiyi hakuri zan baki magani" Dole ta lallabata kada ta janyo musu bacin suna.
"nasan aure zakiyi kwanannan shiyasa zan baki kudi sosai saboda hidimar bikin naki. Kina samun sauki ko zuwa jibi ne zan mayar dake gida. Maganar nake so ta mutu kawai. Babawo shi kadai ne dana namiji kuma ya sami aiki a babban kamfani bana son abinda zai shafi mutumcinsa"

Yanzu kam tayi mamaki tunda son kai yasa an nuna mata ita nata mutumcin ba abin dubawa bane. Wani irin kallo tabi Hajiyar dashi musamman da taji tana waya da mijinta tana sanar dashi ai suna asibiti har an basu gado. Ransa duk a bace yace kada ta bari Babawo ya sake fita don har garinsu yarinyar sai sunje ta bishi da to kamar gaske.

Ranar Mawadda a dakin ta kwana da mugun zazzabi da ciwon kai bacci ma kasawa tayi. Ko yaya ta rufe ido Babawo take gani ga ciwo ko tafiya bata iyawa sai ta  dafa bango amma anki kaita asibiti.

Da safe data tashi fuskarta duk ta kumbura lebe yayi suntum saboda buguwa ashe ya fashe ta ciki. Hajiya da kanta tayi komai Mawadda tana jinsu da da BB tana masa fadan yana son bata musu suna. Haka ta wuni a daki tana kuka Hajiya na kawo mata abinci da panadol wai maganin rage ciwo ne.

Bayan kwana biyu ana gobe Alhaji zai dawo Hajiya ta shigo gidan da sassafe da kaya niki-niki cikin ghana must go biyu manya tasa Mawadda ta sakko daga sama da mayafinta.

Kayan ta nuna mata wai na yaranta ne mata biyu masu aure da na yaransu gashi nan ta kai gida tsaraba. Sai wata jaka ita kuma sababbin kaya ne atamfofi da shadda harda leshi wai tayi fitar biki. Sai kuma kudi dubu ashirin ta dora mata a hannu.

"Mawadda"

Idonta da baya rabo da hawaye yanzu ta dago tare da amsawa. Kana ganinta kasan a tsorace take gani take kamar BB zai shigo. A yanzu ko cokali ne ya fadi sai ta zabura. Ga tafiyarta gabadaya ta canja saboda ciwon da Hajiya taki kaita asibiti balle asan taimakon da ya kamata ayi mata.

Fuska a hade ta cigada da cewa "Yau zan mayar dake garinku. Wannan duk na baki ne ki kai gida magana kuma ta mutu. Wallahi duk ranar da wani naki yazo min da zancen abinda ya faru tsakaninki da Babawo zan sanar dasu bin maza kike yi shiyasa na gaji na dawo dake. Ke da duka garinku bana jin zaku iya rigima dani don bani da mutumci ke shaida ce. Ki kama bakinki sawunki a likkafa kiyi shiru kawai. Zan iya sawa azo har gida a harbeki da iyayenki kinsan kanina soja ne kin sha ganinsa a gidan nan da bindiga"

Zuciyar Mawadda ta tsinke da lamarin Hajiya sai tsoro da ya shigeta. Ita wa ma zata fadawa balle azo ayi yunkurin kashesu har gida. Don har ranta ta yarda Hajiyan zata iya. Ko a garinsu da aka taba yiwa wata irin haka kowa tsanarta yayi bata mantawa ga kyama ita da iyaye. Karshe ma dai barin garin sukayi cikin dare.

Haj Mara ta karance ta tsaf tasan ta dana mata dafi zata rufa musu asiri. Kawarta daya ta fadawa wadda ta bata shawarar ta tattara ta kaita gida kafin mijinta ya dawo don ba karamin aikinsa bane yace sai Babawo ya aureta.

Haka ta tashi suka fita tana ta kukan rashin sanin abinyi. Waye zai kwatar mata 'yanci? Yaya rayuwarta zata kasance? Shin laifi ne don mutum yazo neman halak da guminsa saboda talauci???

A hanya ma haka ta sakata ta rufe fuska da habar hijabin wai kada a gane me ya sameta. Idan an matsa mata da tambaya tace faduwa tayi. Bata ma iya tankawa ba saboda azabar ciwon kai da fargabar haduwa da iyayenta.
*******
Kauyen Tariwa-Bebeji LG

Zaune yake a karkashin katuwar bishiyar kukar da take kusan a tsakiyar gonar mahaifinsa yana shan farau-farau ya hango kaninsa Danlami a guje har yana tuntube da fatanya garin sauri.

"Assha Danlami meye haka kake gudu kamar kaga kura?" Cewar Dahiru bayan ya dangwarar da tasar hannunsa ya taimaka masa ya mike tsaye.

Sai da ya gama kade farar jamfarsa da ta rine zuwa ruwan kasa saboda wahala da gumi sannan ya dubi yayansa yana murmushi.

"Albishirinka, amma dai muyita da wajewa zaka bani aron wannan yadin naka ruwan kasa da ka dinka da sallah karama idan zamu je Kano dasu Samaila kallon hawa"

Dahiru ya girgiza
"Sannu shugaban 'yan son banza, cha nake tare akayi mana dinkin"

"Amma dai kala daban ne ka sani. Nawa dashi naje kallon da karamar sallah yanzu ma sai na sake zuwa dashi saboda nemawa kai raini"

Dahiru yasan halin kaninsa sosai. Tunda ya fara wannan rokon tabbas labari mai dadi ya kawo masa. Murmushi ne ya subuce masa da zuciyarsa ta harbo jirgin inda ya kwasa a guje har yana kifar da sauran farau-farau dinsa. Danlami a tsorace ya bishi shima don yayi zaton ko macizan da suka addabi gonar ne wani ya fito.

Sai da suka isa wurin mutane Dahiru ya dan nutsu sai farinciki bayyane a fuskarsa.

"Su Danlami sai a dau na damo wannan sallar ma da naka kayan zaka je kallo. Mawadda ce tazo ko ko ba haka ba?"

Danlami ya danyi sakato yana kallonsa kafin ya buga tsaki "yanzu fa sai ka nemi raina min wayo kace jikinka ne ya baka ko? Soyayya manya, to munji labarin Lela Majanu ma ehee. Kuma Qur'anin Allah sai ka bani ko yau na raka ka tadi muga tsiya"

Ko kula shi Dahiru bai sake yi ba ya kara sauri yana dokin ganin sahibarsa Mawadda. Sai dai kuma dole ya bada kayan idan ba haka ba baya jin akwai wanda ya isa ya hana Danlami rakashi tadi. Zuwa zaiyi yayi ta zuba karshe ko gaisuwar kirki bazasu sami damar yi ba. Gashi daga shi har ita ba masu magana bane sosai bare su kore shi. Ba karamin raina shi Danlami yayi ba duk da akwai mace tsakaninsu sai dai akwain shakuwa mai karfi tsakaninsu.

Suna isa gida Innarsu tace ko yunwa ce ta dawo dashi saboda bai karya ba ya fita gona sakamakon ruwan da aka kwana ana yi. Abincinsa tasa kanwarsa mai bin Danlami ta kawo masa ya daga hannu alamun ta barshi.

"Wanka zanyi na fita Inna idan na dawo sai naci"

"Da rana tsaka gagal Dahiru ina zuwa haka ka bari yamma tayi mana"

"Sahibar kokon zuciyarsa ce ta dawo" cewar Danlami yana buga masa harara har lokacin fushin kayan da baya tunanin samu yake ga sallah babba saura kwana goma sha biyar.

Inna ta hau fara'a yau tasan Dahiru zai kwana farinciki. Shi kuwa kunya tasa bai iya cewa komai ba ya shige ya watsa ruwa. Shirt da wando ya zaro a kasan akwati ya saka ya fito fes rike da kanbas din da babban wansu mai aikin kanikanci a cikin Kano ya kawo masa da zai zo.

Yana sakawa ya fito Inna ta washe baki jajayen hakoranta suka bayyana "ka gaishe min da 'yar tawa kaji ko"

"To Inna, ko zan dan sami turaren nan na Baffa ko feshi daya ne kiyi min dan Allah"

"Ai ba sai ka roka ba Danlami miko masa kuma idan ka fesa sai na hadaka da Baffan"

Yana kunkuni ya kawo masa sai dai shima yayan nasa ya burgeshi sosai don yayi kyau. Tare suka fito sai da yayi alkawarin bashi kayan sannan ya barshi ya tafi shi kadai.

Sai da ya kusa zuwa gidan don har yana hangoshi sai kuma kunya ta kamashi. Me zaice mata idan ta fito? Garin yaya ma baiyi tunanin bari ta dan huta ba. Yana tsaye yana ta tunanin har aka soma kiraye kirayen la'asar. Dayake da alwalarsa can gefen bishiyar da aka zagaye da duwatsu yaje sukayi sallah harda babanta wanda yace ya karaso mana zai tura a kirawota. Shi dai Dahiru kunya tasa yayi ta lankwasa kai yana murmushi.

Mal Fatihu yayi murmushi shima "kai da ita kowa kunya zanga wannan zama naku Dahiru. Yanzu dai idan ka koma gida ka sanar da Malam yazo muyi maganar bikin nan don bana jin zan bari ta koma birnin nan gaba daya. Gidan aikin nata sunce tafiya zasuyi na wata uku babu kowa a gidan, dama kuma lokacin ai ya matso  duka duka bana jin zai kai wata ukun ma a gaba"
[03/12 23:02] Meela Adeel: *GUMIN HALAK...*馃挵4

*Batul Mamman*馃挅



Kunya irin wadda basa jin sun taba ji a rayuwarsu ce ta saukarwa Baba da Yaya. Ade kuwa ko juyawa batayi ba ta yunkura zata kamo hannun Mawadda ta yanke jiki saura kadan ta fadi Baba yayi saurin tareta. A daddafe ta matsa jikin gadon duba marasa lafiyan sai kuka ya kwace mata. Kuka take bilhakki na tausayin Mawadda, na bakincikin yadda rayuwa take gara talaka sannan uwa uba ganin tamkar laifinsu ne ita da Baba da suka bar 'yarsu ta tafi aiki.

Shi dai Baffan Dahiru kunya yaji da suka biyo bayansu gashi sun samesu a wani yanayi da babu mai son a ritsa shi a cikinsa.

Likita ganin yadda jikkunansu suka yi sanyi yasa shi sake cewa suna bukatar dan sanda a gaggauta zuwa kiransu domin su sami damar bawa Mawadda kulawa.

Dahiru kallo daya ya yiwa Mawadda daga inda take rakube akan gadon ta rirrike karfen kamar ta shige cikin bango ya dauke kansa.  Zuciyarsa ke wani irin harbawa saboda yadda ya ga fuskarta. Wani daci ya soma ji a wuyansa yayi saurin juyawa zai bar wurin.

Inna duk ta rikice itama ta dakatar da shi "ina kuma zaka tafi?"

Bai kalleta ba sai kallon Baba da yayi "zan je kiran 'yan sandan ne"

Baba yayi saurin fitowa "muje dama tafiya zanyi yanzu"

Fita suka yi tare aka bar sauran da kallon kallo a gefe kuma uwa da 'ya suna kuka mai ban tausayi.

Tafiyar kurame ce tsakanin Baba da Dahiru har suka sami mashin biyu suka hau. Ofishin 'yan sanda mafi kusa suka sauka kowa tunani ya baibaye zuciyarsa.

Da suka shiga 'yan sanda biyu ne a wurin karbar korafi. Daya yana ta sakace hakora ya gama cin tsire dayan kuma gyangyadi yake yi akan wani benci. Sallamarsu ma basa su ji an amsa ba.

Baba ya matsa jikin kantar ya tsaya yana duban mai sakace "yallabai barka da yamma"

Suturar jikinsu kadai ta tabbatarwa jami'in tsaron cewa da wuya wani korafin kirki ya kawosu da ya wuce na satar su akuya ko rikicin iyakar gona. Duk su zo suyi ta damun mutane da yamman nan talauci yayi yawa kowa zuciya a sama. Bai amsa shi ba sai kai da ya gyada alamun yana sauraron shi.

Dan rissina kai yayi duk kuwa da cewa mutumin ko baiyi da dashi ba to lallai kaninsa ne na can baya ya dan rage sautin murya a kunyace ya soma magana
"daga asibiti muke mun kai yarinya ance sai mun zo da dan sanda za'a duba ta"

Tsinken ya ajiye sannan ya gyara zaman hularsa duk cikin nawa da nuna halin ko in kula da damuwar da ba tasu ba "to kai dattijo da baka san lalurar da sai anje damu da wadda ba sai munje ba?"

Dahiru zuciyarsa ta fara tafasa dama ya lafiyar kura ransa a bace yake tun dazu ga wannan mutumin yana musu magana a wulakance. Kafin yayi magana Baba ya cigaba

"Yarinyata ce aka yiwa fyade.." ya karashe kalmar a hankali saboda kunya.

"Babbar magana kai Nalado tashi wannan aikinka ne. Ka bisu asibitin bayan na gama daukar bayanansu."

Lalube ya soma yi a aljihu wai yana neman biro. Can dai ya tambayi wanda ya kira Nalado shima yace babu. Suna ta dibi-dibi duk su biyun wayar Dahiru ta soma kara. Ganin sunan mahaifinsa yasa shi tsorata ya kara a kunnensa da sauri.

"Dahiru kuyi sauri jikinta yayi mugun zafi har tana sambatu. Likitan ya taimaka zai saka mata ruwa"

Da yake waya ce techno mai dan karen kara Baba ya gama ji. Hankalinsa gabadaya ya tashi Dahiru ya tambayi dan sandan biro kadai ne babu yace eh babu ko kunya. Fita yayi yana gudu ya rasa wace hanya zai bi ya sami kantin da zai sayi biro. Daga can tsallake ya hango wani shago da ledojin ruwa, daga kafar da zaiyi takalminsa ya tsinke ya fadi fuska a kasa saboda da hanzari ya motsa. Ko kulawa baiyi ba ya tashi yana kade jikinsa zaiyi gaba wata mota fara kirar marsandi tazo tayi pakin a gefensa tare da buga hon. Abin mamaki sai ga 'yan sanda kusan bakwai sun fito daga cikin ofishin wanda tun dazu yake tsit sai mutum biyun da suka gani.

Duk wurin motar suka nufo DPO dinsu ya fito daga ciki. Yana kallon Dahiru yace wannan fa sai ga Bala wanda yace babu biro ya yo gaba da sauri.

"Yallabai yanzu zan dauki bayanansu. Case din fyade ne zamu je asibitin. Bawan Allah koma ciki muyi sauri"

Baba da Dahiru suka saki baki wato wulakancin da gangan aka yi musu ko don an ga basuyi kama da masu arziki ba.

Kamar yadda ta basu labari haka Baba ya labartawa Bala suka dunguma har Nalado suka bisu asibitin saboda ganin idon DPO da baya wasa da aiki.

Da isarsu ba bata lokaci aka gama abinda za'ayi suka shige da Mawadda wani dakin daban. Iyayen maza sunyi jigum matan na kuka. Inna kuwa hakuri kawai take basu lokaci-lokaci sai ta kallo Dahiru.  Sam ta kasa gane a wane hali yake ciki. Shi kadai yasan yadda yake ji a ransa sakamakon wannan tashin hankali.

Su sergent Bala suna jira a fito da ita idan zata iya magana tayi musu bayani sosai idan bazata iya ba su dawo washegari.

Kusan minti arba'in suka dauka kafin likitan da nos suka fito.

"Ina mahaifiyarta" cewar likitan yana binsu daya bayan daya.

Ade tayi saurin nuna Yaya duk da har kasan ranta a matse take taji me yasa ake neman mahaifiya.

Ajiyar zuciya likitan yayi "ki shiga wurinta ko zamu samu ta dena kukan nan don mutum daya nake bukata a dakin. Sannan gaskiya kunyi sakaci wannan abu ya wuce kwana uku ga dukkan alamu ciwo yana neman zame mata wani abu daban. Sauran bayani Baba muje nayi maka"

Yaya da Ade suna kallon juna kowacce na son tafiya wurin Mawadda. Inna tana kula dasu duk suka bata tausayi. Wannan bakar ranar kada Allah Ya nuna min ta fada a zuci.

Yaya da sanin ya kamata ta nemi wuri akan bencin da yake jingine da bango ta zauna "Sa'ade jeki ki rarrasar min ita tun jiya nake fama taki shiru"

Allah sarki dama a dofane take da sauri tayi gaba tana share hawaye.

Mawadda tana kwance tana hawaye taji an turo kofar dakin tana kara keyyyy ba karamin tsoro hakan ya bata ba. Tuna mata yayi da lokacin da BB ya shigar da ita dakinta na gidansu ya kulle. A firgice take gabadaya har Ade ta karasa gaban gadon.

"Ade..."

"Shhhh kukan ya isa haka."

"Gwara in mutu da wannan ..."

"Kada na sake jin kina zancen mutuwa. Shikenan kuma saboda Allah Ya dora miki jarabawa sai ki karaya lokaci guda? Tunda kukan bazai amfana mana komai ba ki daure babu abinda muke bukata yanzu sai samun lafiyarki"

Shiru tayi tana wata irin ajiyar zuciya mai karfi. Cikin dan kankanin lokaci bacci ya soma fizgarta kanta na cinyar Ade. Dama likitan ya sa anyi mata allurar bacci.

Ko minti goma bata cika ba ta tashi a gigice harda ture Ade don ta manta waye a gurin tayi waje. Allurar jikinta ta karin ruwa ta cizge harta ji mata ciwo ga jini yana diga. Mafarkin BB take yi yana kokarin danneta. Jikinta har tsuma yake yi lokacin da taci karo da Dahiru ya dawo daga siyo musu ruwan alwala saboda gabatowar magariba. Su Yaya duk sunyi kanta ana kokarin hanata fita.

A can ofishin likita ya yiwa yan sanda bayanin su dawo washegari saboda bata cikin hayyacinta sosai. Bayan fitarsu ya soma yiwa Baba fadan kai yara aikatau da suke yi.

Baba yayi murmushi mai ciwo yana da bayanai da yake son yiwa likitan akan matsalarsu amma yanzu ba muhallin hakan bane. Likita ya cigaba da yi masa bayanin cewa ciwukan jikinta sun basu dukkan wani taimako da ya dace. Babbar matsalar shine tabon da aka yiwa zuciyarta sai sunyi hakuri kuma sai an daure. Yanzu bazasu gane girman abin ba sai taji saukin ciwukan jikinta.

Suna wannan tattaunawar ne suka jiyo ihunta. Tare suka fito da sauri tana neman fita Dahiru ya saki ledojin hannunsa ya kamota. Jin namiji ya tabata ta sandare cikin murya mai ban tausayi tace
"ka rufa min asiri BB ni ba 'yar iska bace aure za'ayi min. Kayi hakuri don Allah"

Dahiru bai san lokacin da hawaye suka zubo masa ba a yayin da Ade da Yaya suka rikota suna ta koke koke. Baffa da Inna ma abin yayi matukar shigarsu suna kallo aka mayar da ita dakin.

Ba su suka sami kanta ba sai bayan isha da aka kara mata wata allurar da magunguna bacci mai mugun nauyi yayi awon gaba da ita. Sai a lokacin suka fara batun tafiya.

Baba yace Ade tazo su tafi don yasan zuwa yanzu Iya ta sami labarin zuwanta gari gashi bata je gida ba. Shima nasa iyayen dole zasu ji daga wurinta da kuma yara da suka tura musu daga makarantar allo  su zo su tada hankalin rashin sanin me yake faruwa.

Ba don taso ba sai don kara da kawaici ta bisu suka tafi.

Su Inna gida suka wuce da Dahiru yayin da Baba da Baffa suka tsaya yana yi masa bayanin yadda abin ya faru. Ade har tayi hanyar gidansu wanda iyayen Mal Fatihu da Iyarta suke ciki tare sai ta fasa. Gidan Mal Isiyaku ta wuce kai tsaye.

Ummiyo ce ta amsa mata sallama Inna ta zaga bayi. Tana fitowa tayi arba da Ade a tsakar gida tace ta shigo cikin rumfa. Dahiru yana bayansu duhu yasa basu ganshi ba. Zai shiga kawai ya ga Ade ta durkusa a kasa gaban Inna tana kuka sosai.

"Don darajar Al'Qur'ani da iyaye Innar Dahiru ki rufawa yarinyar nan asiri. Na sani maganar aure da Dahiru ko ba'a fada ba ta tashi kamar yadda nasan da wuya wani ya taba aurenta. Amma ki taimakeni ko don kada zaman garin nan ya gagaremu don Allah ki rufa mana asiri"

"Haba Sa'ade sai kace wata bare? Wannan magana nayi miki rantsuwar duk ranar da kika ji ta a waje to daga bakin wani ta fito ba ni ba. Bazan taba fadawa kowa an yiwa Mawadda fyade ba. Kinga ai bamu ma san takamaimai me ya faru ba"

Dahiru ja da baya yayi har wani jiri yake ji. Tausayi sosai Ade ta bashi. Motsin da yaji a bayansa yasa shi juyawa ko ma waye ya gudu kafin ya waigo.

Har Ade ta fito tana ta yi mata godiya. Ita dai Inna bata da niyar tozartasu amma taji dadin da kafin magana tayi nisa Ade ta gane cewa batun auren nan a barshi kawai.
****

Kusan tare Ade da Baba suka shiga gidan iyayen nasu. Iya tana daga dakin farko idan an shiga wani soro sai 'yan tumakinta. Daga soro na biyu kuma tsakar gidan iyayen Mal Fatihu ne wato wa ga Iya. Rashin jituwa da dangin miji bayan rasuwarsa yasa ta dawo gidan.

Suna sallama Innar Fatihu da Malam babansa da Iya suka taso suna tararsu da tambayoyi.

Malam yace "kun daga mana hankali yara tun dazu sun zo sun ce Mawadda ba lafiya. Tana ina yanzu? Yaushe ta dawo garin ma duka bamu da labari?"

Iya kuwa harara ta dokawa Ade "wani sabon salon kinibibin ne kika shigo garin nan sai a bakin jama'a naji wai kin fara biyawa gidan tsohon mijinki."

Baba na gaisheta kamar yadda ta saba tun rabuwarsa da Ade ta juya masa keya harda tura dankwali gaba.

Innar Fatihu ta tabe baki "ke kam zan ga lokacin da zaki girma, yaro na gaisheki kina juya keya abu duk a gwaguye"

Sanin cewa yanzu zasu fara rigima Malam ya tsawatar "bana son shirme, ance yarinya ba lafiya baku tambayi halin da take ciki ba sai rigimarku da bata karewa. Sa'ade ina kuka barota?"

Daga ita har Baba duka jikinsu a sabule ga idanunta a kumbure saboda kukan da bata san adadinsa ba a yau.

Baba ne yace duka su zauna magana mai mahimmanci zasu yi. Jin haka Iya ta kwala ihu harda zaman 'yan bori ta soma kuka haikan tana fyatar majina.

"Ni Tarasulu me zan gani, wayyo Allah mun shiga uku mun lalace."

Ade ta bata rai ganin wannan abu da mahaifiyarta take yi "Iya meye haka kuma don Allah?"

Sake fyace hanci tayi sannan ta dago "cha nake ta cika ne, na ga ke da Fatihun kamar kwai ya fashe muku a ciki gashi yace magana ce mai mahimmanci"

Malam ya girgiza kai cike da takaici.
"Fatihu ina jin ka kaji"

Kai a kasa Baba ya soma labarta musu abinda ya sami Mawadda. Kafin ya kai karshe Iya ta mike tana kumfar baka zani na neman faduwa tana kamo shi

"Qur'anin Allah Fatihu baku isa ba...tabdi yo ni na taba jin danyen aiki irin wannan ma. 'Ya'yan Haule sunje sunyi aikatau dinnan kowacce ta kai mutumci gidan miji sai tawa jikar saboda ka tsani uwarta. Idan ma wata manakisa kuka shirya ku kwance don billahillazi bazan yarda ba." Duk da fada take yi sai kuka kuma yaci karfinta. Ba karamin so take yiwa 'yan jikokinta ba musamman Mawadda abokiyar fadanta. Yarinya ba sawa ba fitarwa har haushi take bata. Ade ta riko hannunta suka zauna tana ta kuka da mita.

Malam da Innar Fatihu suma abin ya taba su. Shawara aka tsayar da safe zasu koma asibitin da kuma tsawatarwa cewa su iya bakinsu kafin magana ta fita don bazata yiwa kowa dadi ba cikinsu.

Iya ta mike tana gallawa Baba harara "da yake ba jikar da kuke son uwarta bace shine zaku ce sai da safe zaku je. To ni yanzu zan tafi. Ke kuma.." ta dungure kan Ade "kin kwaso jiki kin dawo gida har zaki iya bacci kin bar yarinya a wannan halin"

Innar Fatihu ta kada baki tace "Abin ko kara babu dadin abin nima jikata ce"

"Da nayi karar ba ga irinta nan ba. Ca nake 'ya'yan Haule har biyu a Habuja suka yi aikin. Daya a Jos dayar kuma a Fatakwal ina nan rahoto na zuwa gareni. Sai ni don an raina mu nan nan Kaduna fa aka kai min Mawadda. Ina Kano ina Kaduna banda wulakanci. Kuma ku kwana da shiri harda shi shegen gorar  ya taba min ita magana bata mutu ba. Idan ana yiwa 'ya'yan mutane fyade a binne magana a bar yarinya da bugun zuciya to Yasin ni sai mun shiga kotu. Yaro ko daga gidan Karuna ya fito zamu kara ai talauci ba hauka bane."

Har ta bar tsakar gidan ana jiyo sababinta. Ade ta tashi zata bita Malam ya hana. Da kansa yaje ya sameta tana laluben jaka wai zata tafi asibiti da shirin kwana. Harda bashi sallahun ya fadawa Fatihu matarsa komai dare zata dawo.

"Tarasulu bana jindadin irin wannan halaye naki ko kadan. Kiyi hakuri zuwa goben da wuri zamu tafi. Sa'ade da Fatihu duk 'ya'yana ne ko don kaddara ta rabasu sai mu kasa hakuri komai sai mun fassara shi da cewa da gangan akeyi. Ki rinka tauna magana kin girma fa."

Shiru yaji tayi ga mamakinsa ashe kuka take yi "yaya fyade ne fa? Yarinya kamar Mawadda mai zurfin ciki ta hadu da wannan bala'i ina zata saka kanta? Wallahi ko dan uban waye yaron nan bazan barshi ba. Allah Ya isa, Allah Ya kwashewa duk wani mara imani mai wulakanta da tozarta mutumcin mata yara da manya domin biyan bukatarsa"

Kukanta ya taba masa zuciya sosai. Su kadai suka rage a gidansu basu da kamar juna. Da kyar ya lallabata ta hakura zuwa wayewar gari. Sai dai babu wanda ya runtsa cikinsu kamar yadda a asibiti ma Yaya bata yi baccin ko da awa daya ba saboda yawan tashin da Mawadda take yi tana ihu.
*****

Tara na safe a asibitin tayi musu gabadaya. Yaya tana gaishe da Iya taki amsawa sai harare harare takeyi ita ba'ayi mata adalci ba.

Ganin Mawadda duk ta kare shi yafi daga mata hankali. Tana kuka tana surfawa BB tsinuwa da Allah Ya isa.

Duka zaman jiran likita suke yi sai ga sergent Bala da Nalado sun dawo. Ba jimawa Dahiru ya shigo ya gaishe da kowa na dakin.

Rabonsa da Mawadda tun ranar da zata tafi aiki sai jiya. Yau yana dago kai suka hada ido tayi saurin rufe nata hawaye na biyo baya. Me ya kawo shi inda take bayan yanzu bata da sauran daraja da kima? Ita din yanzu abar gudu ce da kyama ta tabbatar maganar aure tsakaninsu tuni tabi iska.

'Yan sanda sun nemi ta sanar dasu yadda abin ya faru sai dai idanun jama'a yasa ta kasa sai zubar hawaye. Idanunta har wani kwarmi suka yi saboda yini kuka. Ganin haka aka sallami kowa sai Babanta da Iya wadda ta dage babu inda zata je. Ita ta rike hannun Mawadda ta fada musu abinda baki zai iya fada. Iya tayi kuka har muryarta ta dashe. Kofar dakin ta dawo ta zayyane musu halin da Mawadda ta shiga a hannun BB. Duk wanda yake wurin yaji tausayinta sosai. Dahiru zuciyarsa kamar ta buga. Ji yake inama shi din wani ne da ko ya bar BB da rai sai yayi masa abinda idan ya ga mace ko da tunkiya ce sai ya canja hanya. Abu daya ya kudurcewa zuciyarsa shine aurensa da Mawadda babu fashi. Idan da yana sonta ne yanzu kaunarta da tausayinta sun taru sunyi masa yawa a zuci. A shirye yake ya fuskanci iyayensa da duk wanda zai nemi hana shi aurenta saboda yasan hakan shine daidai. Kasancewa da masoyi a lokacin da kaddara mara dadi ta same shi shine cikar soyayya.
[03/12 23:02] Meela Adeel: *GUMIN HALAK...*馃挵5

*Batul Mamman*馃挅


Bayan dan lokaci 'yan sandan suka fito. Sun bawa Baba shawara akan cewa idan yana bukatar maka BB a kotu sai yayi shiri sosai saboda shari'a yanzu sai da kudi. Sannan zasu zo da abokin aikinsu wanda zai dauki hotunan raunukan jikinta washegari saboda kafa shaida. Mutanen sun basu tausayi musamman Mawadda. Har hakuri suka bawa Baba wulakancin da suka yi masa a ofishinsu. Godiya yayi musu shima ya raka su sannan ya dawo dakin.

Iya tana rungume da Mawadda kamar za'a kwace mata ita. Da yake sun taho da abinci Innar Fatihu ta zuba mata kunun gyada fari kal yana ta kamshi amma taki karba.

Yaya tace "Inna haka muke ta fama taki cin komai. Jiya nayi fadan nayi nasihar amma duk a banza"

Nan fa suka shiga lallabata amma da aka matsa mata ma sai tasa musu kuka
"Ku barni yunwa ta kasheni na huta don Allah"

"Ahir na kuma jin wannan zance Mawadda. Kin taba ganin bawan da yafi karfin jarabta daga Allah?" Cewar Innar Fatihu

Iya ta tsuke baki
 "Ya haka ne, abin kiyi mata sannu-sannu sai fada saboda dai...."

Malam ne ya katseta "za'a sai da hali ne Ta Rasulu? To dai asibiti ne ba gida ba. Sai mu koma inda muka fito iyayenta suyi jinyarta"

Shiru tayi babu wanda ya sake cewa uffan kada Malam ya korasu gida.

Ade ta kurawa Dahiru ido yana tsaye daga gefen kofa. Tun da ya gaishe su bai sake cewa komai ba. Tana ta lura da yadda yake kallon Mawadda. Ita dai tasan batun aure babu amma ga dukkan alamu akwai dalilinsa na dawowa wurinta a yau. Cike da hikima irin na iyaye mata ta kafe Baba da ido har sai da jikinsa ya bashi tana kallonsa. Yana dagowa ta cilla idanunta bakin kofa nan ya gano me take nufi. Gajeren murmushi yayi ya riko hannun mahaifinsa yana cewa gara su fara jin nawa za'a cajesu kudin asibiti tun wuri. Malam yayi na'am da hakan suka tashi.

Bayan fitarsu kuma har lokacin Dahiru bai fita ba Ade ta dan tabo Yaya. Iya na gani ta hade rai
"Ke ni fa na lura sai wani shishshigewa Haule kike yi ko irin tsohon kishin nan baya dan motsa miki. To idan ma wata gulmar za'ayi muje ayi dani. Mawadda kwanta ina zuwa"

Yaya da Ade duka murmushi suka yi sanin halin Iya. Tana gani kuwa ta hau waka tana yadawa Yaya habaici
 "kishiyata idan sararki leke-leke, leka tukunya leka langa wata rana zaki sha ita ce a gadon baya...luba lubayye 'yan mata luba lubayye luba ta girma. Ehe idan mutum so yake ya shiga tsakanina da ahalina kurwarmu kur abadan wa tutur"

Kunya kamar Ade ta nutse a kasa. Duk da Yaya ta dade da sabawa da wannan habaici tun mutuwar auren Sa'ade amma bata jindadi duk ranar da Iya ta yaba mata magana. Musamman ma ga Dahiru a dakin.

Innar Fatihu abin ya kona mata rai ta bi bayansu tana ramawa Yaya. Ade ta dafe kai daga kokarin abin arziki rikici zai kaurewa tsofaffin. Kunya kuma bazata bari ta fadi gaskiya ba duk da ita Yayan ta ma fahimta.

Dakin yayi shiru sai sautin ajiyar zuciyar Mawadda. A hankali Dahiru ya soma takowa wurin gadon wani masifaffen tsoro ya ziyarci zuciyarta. Ita kadai a daki da namiji. Yanzu idan ya rufe kofa fa? Ina su Baba suka tafi? Wace hanya zata bi ta gudu kafin ya cutar da ita? Tunani barkatai ne suke yawo a kwakwalwarta sai dube-dube take yi ko zata ci karo da makamin da za ta kwala masa.

Ganin yadda ta rude ya sashi tsayuwa a inda yake sannan cikin muryar rarrashi ya kirata da sunan da ya sanya mata tun ranar da ya fara zuwa gidansu tadi.

"Mawaddatan wa Rahma"

Kamar an tsikareta a lokacin ta dawo hayyacinta ta soma neman nutsuwa. Ita kadai take ta nanatawa zuciyarta Dahiru ne. Dahirun da kika sani wanda zaku yi aure nan da 'yan watanni. Sai kuma ta girgiza kai, wane auren kina kwance a gadon asibiti anyi miki fy....

Kasa karasa tunanin tayi ta soma kuka. Yana lura da duk wani motsinta. Kukan ne ya sake taba shi.

"Assha, assha banyi zaton zuwana zai saka ki kuka ba. Kiyi hakuri bari na tafi"

Juyawarsa tasa ta jin wani iri a ranta. Shikenan BB ya rabata da masoyinta. Dahiru matashin da 'yan matan Tariwa suke rububi saboda ya maida hankali a karatun boko har turanci yana ji. Ranar da ya fara zuwa gidansu da maganar yana sonta har rawa tayi a daki ita kadai tsabar murna da samun abin da bata yi zato ba. Yanzu shikenan mafarkinta yazo karshe ba ma shi ba wani ma bazai so aurenta ba.

"Nagode jiya ma na ga kazo. Ka gaishe da su Inna. Kuma...kuma...uhmm Allah Ya baka mace tagari"

Girgiza kai yayi yana murmushi ganin yadda take kuka. A da sai yayi da gaske take iya yi masa magana. Wato yanzu a ganinta sunyi bankwana kenan.

"Ke kin fasa aurena ne ko fatan kishiya tagari kike yi tun kafin ayi bikin mu?"

Bata fahimce shi bata ta dan dago kai mayafin ya dan karkace har fuskar da yanzu kullum take lullubewa ta dan bayyana.

"Me kace?"

"Cewa nayi kin fasa aurena ne kike min addu'ar mata tagari?"

"To ai.." sai kuma ta sunkuyar da kanta. Ko ba'a fada ba ya kamata ya san cewa yanzu maganar aure ta tashi. Don ko shi yana so bata tunanin zata taba aure a rayuwarta.

Komai nata yanzu tausayi yake bashi. Minti daya tana magana, sai kuma tayi shiru ta hau tunani ita kadai sai dai a ga yanayin fuskarta na sauyawa ko tana girgiza kai.

"Kinga mu bar wannan magana ga kunun da aka zuba miki har ya huce baki sha ba."

"Na koshi" ta amsa a takaice.

"Kin taba ganin ciwo ya warke da yunwa?"

Bata son tsawaita magana dashi saboda duk da halin da take ciki har yanzu tana son sa. Rabuwarsu shine zai fi mata alkhairi. Ita duniyar ma gabadaya ta fice mata a rai.

"Su Iya ma na fada musu su kyaleni. Gara  yunwa da damuwa suyi ajalina ko na huta da wannan abin da nake ji a raina"

Kofin kunun ya mika mata taki karba sai ma kuka da ta soma mai cin rai.

Kamar zai ajiye sai ya juyo yana kallonta

"Mawaddatan wa Rahma!" Ya kirata idanunsa suna kwalla


"Idan kin manta bari na tuna miki. Da wanda ya cakawa kansa wuka, da wanda ya rataye kansa, da kuma mai shirin yiwa kansa horon yunwa da gangan duka idan suka mutu sunansu kafirai. Yanzu ke kin yarda rayuwarki ta kare a haka? Kin rayu cikin talauci, talaucin nan dai ya rabaki da inuwar mahaifanki ya kaiki inda wani bunsuru ya cutar da ke. Talaucin dai shine yasa kike kwance a wannan asibitin. Kofar dakin tana rawa kamar zata fadowa mutane ga taga babu ko kyalle. Sai an sallameki ki dawo gida da alakoron maleriya"

Bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba. Dahiru yayi dariya zuciyarsa tana samun nishadi daga fara'ar da ya ga tayi.

Saurin rufe fuskarta tayi yace "ko ke fa da kin takurawa kanki da kuka. Zancen gaskiya nake miki. Ace duk wahalar da kika sha a duniya kin zabi a lahirar ma...."

Da hannu ta dakatar dashi "naji bani kunun zan sha"

Dadi ya kama shi ya mika mata. Juyar da kanta tayi ga mayafi ta rufe kai ta kafa kai bata sauke kofin ba sai da ta shanye. Ashe ba karamar yunwa taji ba. Yana ganin ta shanye yace ta kawo ya kara mata. A kunyace ta mika kofin amma har ranta tana bukatar karin nan.

Yana cikin zuba mata su Iya suka dawo. Ganin Dahiru yana zuba kunu ta rike baki.

"Iko sai Rabbani, Dahiru daga jinya kuma sai ka nemi shanye kunun mara lafiya. Banda abinka ga tuwo sabo ne ma nayi mata yau da shi ka ci. Ita saboda yanayin jiki sai da abu ruwa-ruwa"

Wayyo kunya ba Dahirun ba, ba Mawaddan ba sannan ba iyayensu ba.

Ji yayi kamar ya saki kofin a kasa ya kwasa a guje. Yadda yayu tsamo ya bawa Mawadda tausayi.

Ade ta wayance "ke dai Iya ba kya rabo da zolaya abin harda suruki kuma"

Dahiru yana tsaye da kofi ya kasa karasa zubawa sai juya dan tsohon filas din kunun da kofin yake yi.

Iya ta isa gabansa kafin Innar Fatihu ta karasa. Karbar filas din tayi tana dan yin sama da kasa dashi ta auna yawan kunun

"Ya naji ba nauyi? Da bamu shigo ba sai ka shanye ko?"

Innar Fatihu taja tsaki "wai meye haka ne Ta Rasulu? Kinsa yaro ko motsin kirki ya kasa yi"

Duk sai ya basu tausayi musamman Mawadda. Tayi karfin halin cewa "Iya wallahi ni nasha karamin zaiyi"

"Ki bari dan Manzo" cewar Iya dadi ya kama ta. Ta dan dungure Dahiru "to kuma sai kayi shiru maimakom kayi min bayani? Kai da ita ashe zani ce ta tadda muje mu. Duk taron marasa magana ne"

Ganin yayi murmushi ne yana sosa keya yasa hankalin Ade da Yaya ya kwanta.

Iya ta sake cika kofin taf ta mikawa Mawadda "ungo"

Yamutsa fuska tayi tana satar kallon Dahiru "na koshi"

"Kin ma isa?" Har zata soma fada sai kuma ta hau dariya.

"Au, auho gulmammu, ashe da gangan kike kin cin abinci kina jiran na hanun masoyi. Oh ni Ta Rasulu kun gane min fitsarar yaran zamani. Ashe fitarmu dadi tayi muku."

Kan kace meye wannan Dahiru ya fice daga dakin Mawadda ta tura kanta a cinyar Iyan da ta zauna kusa da ita don kunya. Innar Fatihu duk abinta sai da ta dara. Ade kuwa kunya ta hana. Ita kuma Yaya tana tsoron tayi a watso mata maganar da zata yi mata ciwo.
******


Yana tsaye yana jiran abin hawa sai murmushi yake shi kadai saboda nasarar sanya Mawadda cikin nishadi da yayi. Da ya tuna tijarar da Iya tayi masa kuwa hannu ya dora a ka yana dariyar halin da ta jefa shi gaban Ade da Yaya.

Bai jima ba ya sami bus ya tafi gida. Rumfar Inna ya shiga jin taku ta taso daga kishingidar da tayi

"Ummiyo ina kika je tun dazu ina nemanki?"

"Inna ni ne" ya fada yana daga labulen ya shigo ya zauna sannan ya gaisheta.

Maimakon ta amsa ta bishi da kallon tuhuma "daga ina kake? Ina ka tafi da sanyin safiya ko karyawa baka yi ba?"

"Asibiti na koma kinsan jiya kafin mu taho dinnan jikin nata ba dadi"

Rai a bace ta daga yatsa tana karkada masa alamun gargadi
 "saurare ni da kyau Dahiru. Zamuyi magana mai bullewa da Baffanku amma kafin nan tun wuri ka cireta a ranka. Duk garin nan babu mai yarda dansa ya auri yarinyar da irin wannan kaddara ta sameta. To nima baza'ayi a gidana ba."

Duk da dama yayi zaton haka saboda maganar da yaji sunyi da Ade jiya amma baiji dadi ba. Sunkuyar da kansa yayi cikin tausasa harshe ya soma magana
"Inna kiyi hakuri kada kice na fasa aurenta. Kema gashi kin kira abin da kaddara ai ba kai kanta tayi ba tsautsayi ne"

Ta san za'a rina dama indai Dahiru ne sai ta tashi tsaye. Ana masa kallon shiru-shiru mai hakuri da iya zama da mutane amma a zahirin gaskiya mutum ne kaifi daya ga zafin zuciya idan ransa bai so abu ba. Idan tana so tayi nasarar raba shi da auren nadama sai ta bi a sannu.

"Shikenan ka jira mu tattauna dai kafin ka zartar da hukunci. Na fada maka ne domin ka fara dasawa zuciyarka hakuri tun yanzu."

Bai ce mata komai ba ya tashi ya fita. Yana son iyayensa kuma a shirye yake yayi musu biyayya amma fa sai inda karfinsa ya kare akan Mawadda. Abu daya ne yake masa yawo a rai shine yadda muke saurin manta alkhairin mutum da zarar kaddara mara dadi ta same shi mu guje shi. Wannan hali namu yana daga abin da yake cire mana tausayin juna. Mun mayar da kanmu mutanen da indai jifa ya wuce kansu to ya fada kan kowa ma bamu da damuwa.
******

Wani wawan duka ta sauke mata a cinya cike da al'ajabi tace
"Ke ki bari don Manzo!"

Ummiyo tayi saurin toshe bakin Rahane aminiyarta.
"To uwar karadi yi ihu kowa yaji"

Babar Rahane tana jiyo haka ta dawo bakin tagar dakin ta labe. Yo labe da leke a wurinsu ai ba komai bane. Balle kuma taji alamun gagarumin abu ne ya faru tsakanin Ummiyo da Rahanen don da ta shigo irin gaisuwar nan mike tayi mata ta wuce dakinsu Rahanen.

Mamaki sosai a fuskar Rahane baki na rawa tace "yanzu da gaske fyade aka yiwa Mawadda? Wallashi har ta bani tausai."

Babar Rahane ta ja numfashi a tsorace tare da dafe kirji tana kara kara kunne. Nan ta jiyo Ummiyo tana cewa
"Ki bar fadi mana Rahane kada a jiyo mu. Jiya Aden Mawadda har dakin Inna tazo ta roketa a rufe maganar. Da kyar na jira wayewar gari saboda na fada miki. Kuma fa Yayanmu Dahiru ya sani don ta bayansa ma na labe. Yanzu ban sani ba ko zai aureta"

"Allah Yasa kada yace ya fasa gashi kince ma tana asibiti baiwar Allah" cewar Rahane har da 'yar kwallarta saboda tausayin Mawadda.

"Don ba yayanki bane ki ke masa mugun fata? Ni dai gaskiya bana so ya aureta. Me zaiyi da 'yar iska. Rannan naji ance duk wacca aka yiwa irin haka ita ma shikenan ta zama irinsu. Kuma garin nan kinsan kowa gudunta zaiyi azo a tsani Yayanmu Dahiru. Ha'aan"

Babar Rahane tana jin haka ta janyo abin tatar koko daga igiyar shanya a zatonta mayafi ne. Makotansu ta shiga da sauri cikin dan kankanin lokaci ta labartawa matan gidan su hudu har da karin cewa Mawaddan tana asibiti an zubar mata da ciki.

Tuni gida ya dauka mata suka fara fita waje kowacce tana son kaiwa makusanciyarta labari.

Cikin abin da bai wuce awa biyu ba maganar nan tayi yawo fiye da zato. Mata da maza manya da yara da dama sun sani tunda safiya ce. Kusan ko ina zancen ake ta yi gashi a kowacce gaba labarin ya sami karin gishiri ya tashi daga fyade wasu sun kara da ciki wasu ma sun ce haihuwa tayi. Akwai wadanda suka dora da cewa dama tun tana garin ai kallonta kawai suke yi ana cewa tana da nutsuwa su kuwa sun san tana yawace-yawacenta ne kawai. Lokacin da Dahiru ya dawo ana ta binsa da kallo da yake bai kawo za'aji zancen ba ko kadan bai kula ba.

******

Ya fito da shirin tafiya gona saboda rashin samun lokaci tun ranar da Mawadda ta dawo gari bai gama cire kubewar da ya shuka ba wanda kusan duka gonar sun gama yado mai kyau. Idan ya cire Yayansa Bilya ne yake diba akwai masu kayan miya da suke karba a Kano. Sauran kuma Inna da Ummiyo suyi aikin busarwa da dakawa akai a sayar.

Sallama suka jiyo daga waje Inna ta amsa tace ana zuwa. Ummiyo ta shiga wanka bayan ta dawo ta sha fadan Inna. Danlami dama shi ba'a saka shi a lissafi dama.

Da fatanyarsa a kafada  Dahiru ya fita. Sakin fuska yayi ganin wani abokinsa Ali.

Hankali a tashe Ali yace "Dahiru ashe kuma abin da ya faru kenan. Ina shirin fita wata makociyarmu ta shigo take sanar da Fiddausi saboda ta san kawaye ne da Mawadda. Yanzu haka na fito na barta tana ta kuka."

Gaban Dahiru ya fadi da kyar ya iya cewa "me aka ce ya same ta?"

Sai kuma jikin Ali yayi sanyi a tunaninsa Dahiru bai sani ba
"To ina jin dai a gida basu sanar da kai ba saboda ansan za ka shiga damuwa. Mu bar zancen nan bari na wuce"

Tunani Dahiru ya soma na inda maganar ta fito kuma mutane nawa ne suka ji.

"Ali dakata mana ba ka fada min me kaji ba"

A dan tsorace Ali yace "ba a ji mutuwar sarki a bakina ba. Nasan su Baffa zasu sanar da kai. Sauri nake Dahiru sai mun hadu"

Bai jira cewarsa ba ya bar kofar gidan a gaggauce. Shi kuwa Dahiru sosai hankalinsa ya tashi. Balle da ya hango kanwar Inna wadda suke kira Yakumbo tana nufo gidan da sauri ita da babban danta Liti.

Tare suka shiga gidan bayan ya gaisheta tana binsa da kallon tausayawa. Sun gaisa da Inna ta dan bata rai.

"Yanzu saboda Allah magana irin wannan sai dai naji a waje? Ba don Liti ya fita siyo siga ba wani yayi masa jaje shikenan..."

Inna ta dakatar da ita itama nata gaban na faduwa "wace maganar?"

Yakumbo ta sake kallon Dahiru "zancen Mawadda mana ance anyi mata fyade wai harda ciki suna asibiti an zubar ne ko zata haihu ni ban ma gama gane zancen ba na fito"

Tafa hannuwa Inna ta soma tana sallallami "wane munafukin ne ya fito da maganar nan harda karya? Nasan dai su Haule bazasu dauki wuka su dabawa cikinsu ba. Sa'ade kuwa har dakina ta biyoni jiya tana rokon rufin asiri"

Yakumbo ta gyara zamanta "kice maganar dai gaskiya ne. Mu dai mun shiga uku duka-duka yaushe aka yiwa 'yar gidan Audu maikifi gashi zaman garin nan yazo ya gagaresu."

Inna dai har zufa ta soma yi saboda tashin hankali. Dahiru ya sami jikin bango ya jingina ransa na tafarfasa. Ummiyo tana fitowa da bokitin wanka a hannu taji Liti yana karin bayani.

"Wanda ya fada min yace wai a bakin kanwar Dahiru aka ji maganar shine duka kusan kowa a shiyarsu yaji. Ina jin haka nace to ko Ummiyo ce, ba tana kawance da yarinyar nan Rahane ba"

Da sauri Ummiyo ta lallaba ta koma bandakin tsoro ya cika ta. Amma Rahane ta cuceta yau ina zata saka kanta.

Hannu Inna ta dora a ka tana kiran ta shiga uku. Dahiru yayi fam yana cewa ina take. Suna wannan halin Inna tana yiwa Yakumbo bayanin ainihin me ya faru sai ga Baffa da Danlami.

Tun daga waje yake fada abin da ba halinsa ba yana kiran Inna. Ganin Yakumbo a gidan ya kara tabbatar masa da abin da yaji.

"Me yasa ku mata baku da hankali, babu rufin asiri sannan ba kwa tunani sam. Saboda Allah abu ya faru jiya amma har ya baza garin nan lokaci guda."

Hakuri Inna ta soma bashi yace tayi shiru kafin rai ya kara baci
"Ko inda zani ban karasa ba Danlami ya riskeni yana tambayata gaskiyar zancen da abokansa suke yi kan yarinyar Mal Fatihu. Ban gama al'ajabi ba Bilya da yake nesa ma ya kira yana tambayata. Wai kanwar matarsa ce ta kira 'yar uwar ta sanar da ita. Me yasa zaki yi min haka do Allah?" Ya kare fadan yana kallon Inna.

Duk jikinta yayi sanyi hakan ya kara konawa Dahiru rai. Wato Ummiyo ce jiya yaji motsinta shine kuma tana ji ana yiwa mahaifiyarsu fada tayi shiru.

Hanyar bandakin ya kalla sai ya ga sawu da danshi. Ta fito kenan ya fada a ransa. Baiyi wata wata ba ya fada bandakin Inna tana ya dakata sai gashi ya fito da Ummiyo da daurin zani har kirji da kuma wani da tayi lullubi dashi.

A gaban iyayen nasu ya soma sauke fushinsa a kanta inda ya fara dukanta kamar wanda aka aiko.

Baffa rabuwa yayi dasu zuciyarsa na kuna. Allah Ya sani baiyi niyyar cigaba da shirin auren Dahiru da Mawadda ba. Amma wannan rashin hankalin na Ummiyo ya janyo dole sai ya sake tunani.

Yakumbo da Inna suna ta fada amma Dahiru bai bar dukan Ummiyo ba. Da kyar Liti da Danlami suka kwaceta bayan ya tumurmusata a kasa. Tashi tayi da kyar tana kuka Baffa ya hauta da fada. Abu ya tarar mata ta rasa yadda zatayi sai hakuri take bayarwa.

Tsabar bacin rai yasa Dahiru ficewa daga gidan ya barsu da tunanin mafita don barna dai an riga anyi.

Sai can yamma ya dawo yana zuwa ya hau wanki. Kayansa masu dan dama-dama ya wanke Inna jiki duk a sabule saboda fushin Baffa tace ina zai je yake ta wanki da shiri.

"Kano zan tafi gobe wurin Yayanmu Bilya."

"Me zaka je yi Dahiru" Baffa ya tambaya.

"Kwanaki yace na sami gurbin karatu a BUK wanda ya nema min nace bana so noma zanyi. To gashi bukatarsa ta taso zan bincika idan har yanzu ban makara ba ina son inje."

"Ai gara kayi karatun kafin nan an kashe wannan gobarar ma" in ji Inna.

Girgiza kai Dahiru yayi "Inna ba zama zanje yi ba don ina dawowa idan ta fito daga asibiti nake so a daura auren sai na tafi da ita. Zan nemi aiki ko na karfi ne inayi saboda ciyar da ita da kuma karatun nawa"

Magana zata sake yi Baffa yace ya wuce abinsa Allah Ya kaimu goben.

A fusace ta juyo "Baffa yaya haka?"

"To gaya min yadda kike so ayi. Kina kallo na kasa fita saboda fargabar haduwata da Mal Fatihu saboda aika-aikar da 'yarki tayi. Kina jin ina da bakin fada masa an fasa auren yaran nan? Salon dan sauran mutumcin nawa ya karasa zubewa ko me"

Tashi tayi ta shige ciki rai a dagule. Ganin Ummiyo tayi rakube da kwaba ta mangareta kafin ta wuce "shegen surutun tsiya gashi nan zaki jawo mana jangwam haka kawai"
*****

Sai wajen taran dare Mal Fatihu suka dawo  da Yaya don tun la'asar su Innarsa suka dawo. An baro Ade da Iya a asibitin.

Yau ma sauran yaransu suna gidan kakaninsu.

Bilki, Hasiya, Nana da Jamila sune manyan 'ya'yan Yaya da ke dakunan mazajensu. Ga mamakin iyayen suna shiga gida suka samesu duka su hudun. Jamila ita ce sakuwar Mawadda kuma babbar aminiyarta don ba karamar shakuwa bace tsakaninsu. Sirrin da basa iya fadawa kowa a waje suna yi da juna. Da kuka ta tari Yaya tace tun la'asar suka zo dukkansu labari ya riskesu gashi sun je gidan Malam wato kakansu babu kowa. Kannensu kuma suna makaranta lokacin shiyasa basu san a wane asibitin aka kwantar da Mawadda ba.

Daga Yaya har Baba hankalinsu ba karamin tashi yayi ba. A ina suka ji har suka taho duka su hudun. Biyu ne ma a Tariwa wato Bilki da Jamila. Hasiya da Nana kauyukan da suke aure suna makotaka da Tariwan ne.

Zama suka yi Yaya ta basu labarin komai. Sunyi kuka kamar me suna takaicin dare yayi da a lokacin zasu tafi asibitin.

Kafin Baba ya tambayi inda suka ji wannan labari sai yaji sallama. Shi yanzu gabansa har faduwa yake yi idan yaji ana sallama dashi.

Haka nan ya tashi ya fita. Makocinsa ne da suka hada katanga. Musabaha suka fara yi sannan yace "Mal Fatihu haka ake zaman tare kuma abu irin wannan ya faru ba don gidan Mal Isiyaku ba ashe da bazan sani ba."

Wani irin sanyi ne ya soma ratsa Baba na tsananin shiga damuwa. Suna can asibiti ashe kowa ya gama sanin me suke boyewa. Kuma a rasa daga ina magana zata fito sai daga bangaren wanda yake tunanin ko yaya zasu rufa musu asiri. Shikenan tasu ta same su a garin nan. Basu da sauran mutumci kuma sai yadda hali ya yiwu.

A hankali ya iya cewa "kayi hakuri hankali na ne ba a kwance ba domin dawowata kenan ma gidan"

"Eh ai na kula shiyasa nayi saurin kiran sauran abokan arziki don duka fa mun damu. Wunin yau sur maza da mata zuwa muke ta yi gidan nan babu kowa."

"Mungode bari na shiga ciki kaina ke ciwo sosai" bai jira amsarsa ba ya koma ciki.

A nan ya sami Yaya tana kuka tana sanar dashi basu da sauran sirri an gama tozarta su a garin nan.

Da wannan damuwar gidan Baffa da na Baba suka kwana kowa da abin da ya dame shi.

Da safe da wuri suka shirya da su Bilki , masu goyo suka kintsa yaransu suka fita. Baba yaso ganawa da Baffa amma a yadda ransa ya baci yasan za'ayi batacciya ne kawai.

Fitar su Baba ke da wuya Baffa ya karaso gidan. Da ga waje wasu mutum biyu suka sanar dashi yanzu suka tafi bakin titi da iyalinsa zasu tafi asibiti. Abin duniya ya ishi Baffa ya juya gida jiki a sanyaye.

Nanatawa yake a ransa Ummiyo bata kyauta masa ba. Babu abin da ya kai kima da mutumci a wurin babba gashi ta zubar masa da nasa da kaikayin baki.

Bayan ya koma ba dadewa Dahiru ya shiga rumfarsa yi musu sallama shi da Inna. Idan ya sami yadda yake so baya sa ran wuce sati daya. Sun bi shi da addua da fatan alkhairi ya sabi jakarsa ta viva yayi waje.

*****
Su Baba sun isa asibiti suka samu 'yan sandan nan sun dawo kamar yadda suka yi alkawari. Mawadda na kuka Iya ta tursasata akan ta bude ciwukan jikinta kamar yadda mai hoton ya bukata domin a dauki shaida. Wannan wane irin tozarci ne BB ya janyo mata. Likitan da ya duba ta shine ya fadi wuraren da ya ga ciwo kamar shatin belt a bayanta, cinya da kuma fuskarta da bata gama daidaituwa ba. Da suka fita haka 'yan uwanta suka zagayeta suna ta koke-koke. A wannan halin Iya ta fice sadaf-sadaf ba tare da sun kula ba ta bi bayan Likitan.

Ko zama baiyi ba ta shigo tare da rufe kofa. A hankali cikin sigar rada ta soma magana tana kuma yi masa alama da kada ya daga murya shima.

"Dan nan ka fada min gaskiya ka tabbatar Mawadda ba wai haihuwa ce tayi ba fyade ne kawai"

"Me zai sa kiyi tunanin haihuwa tayi? Jikarki budurwa ce da tsautsayi ya afka mata"

Sake rage murya Iya tayi sannan ta fiddo zanin Mawadda da ta dauka da sunan za ta wanke "Likita ka taimaka ka duba min ita sosai. Tun jiya na kula idan ta jima a zaune ta tashi wurin sai yayi lema. Yau dai na dauki zanin sansana ka ji.."

Saurin kawar da kansa yayi ganin da gaske Iya tura masa zata yi a gaban fuskarsa.

Ko a jikinta yadda yayi ta sake juya zanin "nayi zaton haihuwa kadai ke kawo yoyon fitsari"

Ba arziki Likita ya tashi "yoyo kuma? Kai muje dai na sake dubawa"

Tare suka fita Iya tana biye dashi har dakin. Nos ya kira ya bukaci kowa ya fita da ga shi sai Mawadda da Nos din ya kalleta cike da tausayawa. Yarinya karama tana ta fuskantar matsaloli da kuruciya.

"Malama Mawadda dubaki zan sake yi"

Kukan nata ma ya kafe sai zafin zuciya. Tunda tazo ake bankada mata jiki ko ta ina. Wannan kadai ya isheta bakinciki. Ba musu ta kwanta inda yana daga gefe ya umarci Nos din da ta duba masa ita ko akwai danshi a tare da ita.

Gabanta ne ya fadi jin furucinsa. Tabbas kwana biyu bayan faruwar al'amarin nan gareta ta tsinci kanta da digar fitsari wanda bata iya rike shi idan yaso fita. Ko kwakkwaran motsi tayi sai taji alamunsa batare da kuma tana cikin matsuwar fitsarin ba. Tayi iya kokarinta wurin ganin tana rike shi kamar da amma abin yaci tura. Gashi bata sanar da kowa ba ta yaya aka gane?

Dubawar farko Nos din ta tabbatar masa da abin da suka zo nema. Hakan yayi matukar daure masa kai yayi 'yan rubuce-rubuce bayan Mawadda ta amsa tambayoyin da ya yi mata sannan ya fita.

Kusan awa uku a tsakani ya turo aka kira masa Baba. A lokacin dama suna sanar da su Iya maganar da ta bullo a gida kusan kowa ya san sirrin da suke boyewa a dalilin fitar maganar daga gidan Mal.Iskiyaku. Suna kuka suna bawa juna hakuri ya fita ya barsu.

Kasan babbar rigarsa yasa ya goge hawayen da yake barazanar zubo masa sannan ya shiga karamin ofishin likitan.

Waya ya ajiye ya dubi Baba cikin damuwa
"Baban Mawadda kayi hakuri da abin da zan fada maka"

Cikin Baba ya nemi kullewa a firgice. Me kuma ya faru yanzu.

"Ina jinka Likita"

"Bayan dan bincike da nayi da kuma amsoshin da Mawadda ta bani ina zargin ta kamu da lalurar rashin rike fitsari saboda raunin da jijiyoyinta suka samu har karfinsu ya ragu"

"Nufinka dai yoyon fitsari ta kamu dashi?"

"Eh... to! Ba na ce ba saboda abu ne da sai anyi dogon bincike da gwaje-gwaje. A takaice dai Baba yarinyar nan sai kun sauya mata asibiti. Ku kaita cikin Kano asibitin Malam Aminu Kano ko kuma asibitin Murtala. Mu nan bamu da kayan aiki sosai kuma rashin bata kulawa da wuri kan iya haifar mata da babbar matsala a gaba"

"To nagode" Baba ya iya cewa ya mike jiri na dibarsa. Banda fyade da ciwukan da aka ji mata saboda duka harda yoyon fitsari kuma. Ina zai saka kansa? Ina yake da kudin kaita asibiti a Kano?

Da wannan tunanin ya koma wurin iyalinsa. Bilki ce take tilastawa Mawadda cin abinci Iya tana basu labarin yadda suka yi akan kunu jiya da Dahiru.

" Idan taki ci ku aika a kirawo shi ku ga cin abinci da neman kari"

Dariya sauran sukayi ita kuwa sai murmushin kunya. Da Baba ya shigo kiran Yaya, Ade da kuma Iya yayi waje domin sanar dasu sakon likita.

Yaya da Ade suka soma salati Ade tana matsalar kwalla. Iya bata yi mamaki ba domin tayi zargin haka tun da ta kula da danshin take bari a wuri idan ta tashi.

"Ku koma ciki ba kuka zaku yi ba Allah zai kawo mana mafita" Baba yace yana juya musu baya saboda yadda zuciyarsa take neman gaza daukar wannan bakon lamari.

"A'a Fatihu gara mu san me muke ciki tun wuri tunda Likitan ma haka ya bada shawara. Ke Ade ina so ki saurareni da kyau. Gidan da kike aiki zaki samu ki koma ko gobe ne ki sanar da matar matsalar da ake ciki ko zasu ranta miki kudin ko da ba kyauta ba."

Tana maganar Ade ta soma girgiza kai "gaskiya bazani ba Iya"

Duka Iya ta kai mata a kafada "ji min sakarci fa. Kina so kice min kinfi karfin rokon taimako ne ko me? Indai baka dashi to ka yarda baka dashi din ka nema a wurin wanda ya fika. Kice rance ba kyauta ai dai bashi hanji ne a cikin kowa"

Hayaniyar yaran nasu ce ta fara yawa daga dakin Yaya sai ta fake da zata tsawatar musu ta basu wuri. Batah jiran karin bayani tasan suna bukatar kebewa don a shawarta yadda za'ayi.

Bayan ta shige Iya ta murmusa tana binta da kallo "Wallahi Fatihu matarka ba dai sanin ya kamata ba."

Yau wace rana Iya ta yabi Yaya.

Shiru yayi bai ce komai ba sai tunani da yake yi ta ina zai sami kudi shi ba wata kadara ba balle ya sayar.

Iya ta sami wuri akan wani benci ta zauna tana kallonsu duk hankalinsu a tashe.

"Duk wani so da zamu nunawa 'ya'ya fa ya bi bayan jajircewa wurin nema musu lafiya. Kyautatawar da muka yi muku da kuruciya ita take janyo jin kai tsakanin mu daku idan mun girma. Yanzu meye naki na cewa bazaki je ki ranci kudi a wurin matar da kike yiwa aiki ba? Mutum me da har yana da wani sauran jiji da kai ne idan bashi da kudin kulawa da dansa? Kwantar da kai ake yi gaban masu kudi idan kina son jindadin zama dasu"

Cikin kuka Ade ta labarta musu yadda suka rabu da Sakina. Hatta Baba ransa ya baci balle Iya. Sun jajantawa juna yadda masu kudi basu dauki hakkin talaka a bakin komai ba.

Rai a bace Iya tace "ko da nace ki kwantar da kai ba cewa nayi ki wulakanta kanki ba kina jina. Kwantar da kai daban, shi iyaka ki sawa ranki mutum ya fiki arziki babu ke babu girman kai a neman halak. Amma ban yarda kowa cikinku ya wulakanta kansa akan kudi ba. Kada kuje ana cin zarafinku kuna hadiyewa don wani abu da za'a baku mai karewa a duniya. Duk zafin talauci wuyarta ka mutu kana mumini magana ta kare. Hakkinki kuma ki bar musu muna nan dake ko ba a gaban idonki ba sai tayi nadamar abin da tayi miki"  Iyan kanta tana magana kuka na menan cin karfinta. Sai dai dattijuwa ce mai matukatar dauriya kuma a matsayinta na uwa garesu bata so ta karyar musu da zuciya.

Baba ta cewa ya koma gida akwai tumakinta uku da awaki biyar ya kama duka ya kai kasuwa.

"Ayi haka Iya gabadaya?" Yace a kunyace.

"Don kaniyarka ko ban haifi uwar Mawadda ba kai din ba dana bane? Ko matsayin nawa zaka nuna min eyee?"

Murmushi yayi yana bata hakuri. Ade ma tace kudaden da take tarawa na bikin Mawadda zata fito dasu idan yaso gobe da sassafe sai su wuce Kano.
*****

Da wuri Dahiru ya isa Kano saboda sammako da yayi. Rijiyar zaki ya nufa gidan Bilya. Da yake yasan da zuwansa dama yana gida yana jiransa. Abinci ya fara ci sannan suka zauna tattaunawa da dan uwan nasa.

Bilya ya nuna alhinin wannan al'amari bayan Dahiru ya gama bashi labari. Sannan suka koma batun gurbin karatu da ya samu.

"Kasan na fada maka yayan ubangidana na garejin mu ne ya sama maka adimishon din. To Alhamdulillahi jiya kana kira nayi maza naje na same shi. Munyi sa'a yace sai nan da sati biyar za'a fara zuwa karatu. Amma kafin nan akwai takardu da zan baka kaje ka cike su sai kasa suka hannu. Sauran bayani dai zaiyi maka tunda zamu je wurinsa"

Dadi ya kama Dahiru jin cewa bai makara ba. Bayan ya duba takardun da kudin da zai biya jikinsa yayi sanyi. Da gani wannan karatu za'aji jiki. Ga Bilya ba wani abin kirki gareshi ba shima ta kansa yake ga 'ya'ya biyu.

Ganin yayi shiru Bilya ya karbe takardun "kaga malam tunani ba naka bane. Tashi zaka yi muje wurin shi Oga Sani nayi masa maganar bamu da kudin karatunka sai ka nemi abin yi. Yace zai san yadda za'ayi idan ka zo"

A raunane Dahiru yace "Yayanmu Bilya ni kam me zan ce maka. Ka gama min komai nagode sosai"

"Me zaka ce kuwa da ya wuce idan an sami aikin ka rike amanar iyayen gidanka sannan kayi karatu sosai ka 'yan mana arzikin bokon a gaba. Kuma fa karatun injinniya yace ka samu saboda ya ga ka kware a lissafi. Baka ga dadin da naji ba" yayi maganar yana masa dariya.

Matar Bilya mai suna Furaira ta zo bayan Dahiru ya gama cin abinci tana masa tambayoyi kamar 'yar jarida game da Mawadda.

"Amma dai ka fasa aurenta ko?"

"In sha Allahu aure yana nan kamar yadda aka tsara tun farko"

"Kai kuwa me zaka yi da ita kamar dole"

"Ke!!! Ban fada miki ki rike bakinki akan maganar nan ba? Ina ruwanki idan yace zai aureta" Bilya ya daka mata tsawa.

Murguda baki tayi ta mike "gaskiya ce bakwa son fada masa. Allah na tuba wa ya sani ma ko 'yan ciwukan zamanin nan ta kwaso zai aura a hada shi da jafa'i"

Dahiru bai ce komai ba ya tashi ya saka takalmi. Yana jiyo hayaniyar Bilya da Furaira bayan ya bita dakin. Kaya ya chanja ya fito suka fita tare.

Garejin da Bilya yake aikin gyaran mota a bakin titin unguwar suka je. Sunyi rashin sa'a Oga Sani bai zo ba. Gefe Dahiru ya samu ya zauna yayin da Bilya ya sauya kaya zuwa kayan aiki ya shiga cikin abokan aikinsa kowa ya kama aikinsa.

Sai wurin karfe uku Oga Sani ya iso. Mutum ne na mutane mai faram-faram da jama'a da sanin hakkin na kasa dashi. Bisa wannan dalilin ne ma wata rana yaji Bilya yana fadawa wani abokin aikinsa burinsa Dahiru yayi karatu tunda yaci jarabawar shiga jami'a. Jin haka ya taimaka masa da kudi wanda da shi ne Bilya ya biya wa Dahiru yayi JAMB. Bai kuma tsaya haka ba ya kara da kaiwa yayansa da yake aiki a matsayin darakta a BUK din takardun gashi anyi sa'a ya sami  gurbin karatu zai karanta Computer Engineering.

Yana fitowa daga motarsa gaban Dahiru yaje yana murmushi "wannan dai ko ba'a fada ba nasan kaina kanin Bilya mayen honda"

Dahiru yayi 'yar dariya yana kallon Bilya da ya taho wurin "Yayanmu sunanka kenan ashe"

Oga Sani yace "ashe bai fada muku ba. To ai idan kazo wurin nan ba ka ce Mayen Honda ba da wuya a gane shi. Kunyi kama sosai amma dai ka dan fishi kyau"

Shi dai Bilya sai murmushi. Sallah suka yi Oga Sani ya daukesu a mota yace ya yiwa yayansa bayani ga dukkan alamu Dahiru zai sami aiki a gidansa.
*****

A can asibiti kuma sun gama hada kayansu an basu takarda da zasu nuna mai dauke da duk wani bayani dangane da Mawadda.

Kafin Baba ya dawo su ma sun taho tunda zaman babu amfani. Jin tana fama da lalurar rashin rike fitsari ba karamin dagawa 'yan uwanta hankali yayi ba. Haka suka tafi dai kowa rai babu dadi.

Daga bakin titi da suka sauka daga bus har zuwa gida idanu da kananun maganganu suna biye dasu. Mawadda rufe fuskarta tayi gabadaya saboda yadda ake binta da kallo. Duk bakin Iya bata ce komai ba saboda kunya. Iyalin Baffa ne suka sha zagi tas a wurinta na Dahiru ya ma fi na kowa bayan sun isa can gidansu Malam da Innar Fatihu. Lokacin duk sauran 'yan uwan Ade da na Baba kowa yana gidan.

Sun tausayawa Mawadda sosai yawancin matan harda kuka. Shirin tafiya Kano suka hau yi 'yan uwa kowa da ya mika  abinda Allah Ya hore masa a matsayin tasu gudummawa saboda basu san yaya zata kaya ba.
*****

Katon gida ne suka je a Sharada housing estate. Dahiru bakon birni sai bude baki yake bai taba ganin gida irin wannan ba.

Gida ne mai kyau ga filawoyi sun kawata shi. Can gefe kuma motoci ne wurin shida masu kyau da gani zasuyi tsada shine tunanin Dahiru.

A wajen maigadi Oga Sani ya barsu ya shiga ciki. Bai wani jima ba ya dawo ya kira su. Wata mata ce ta fito a daidai bakin kofa ta tsaya su kuma suna daga gefen matattakalar da za'a taka mai gudu shida ya isa inda take tsaye. Gaisheta suka yi a mutumce ta amsa tana faman yatsina.

"Sani wanne ne zaiyi aikin a cikinsu?"

Dahiru ya dan dago kai yayin da Oga Sani ya dafa kafadarsa "wannan ne sunansa Dahiru"

Kallonsa tayi ta dan tabe baki "Aikin share farfajiyar gidan nan da gyara flower zaka yi. Sai kuma duk asabar zaka rinka yi mana wanki nawa da na yaran gidan. Ranar lahadi ka goge ko babu wuta za'a tayar da inji. Idan aikin yayi maka albashinka dubu ashirin"

Tsabar murna Dahiru bai san lokacin da yace "ahirin???" ba.

Wata irin dariya suka ji an kwashe da ita daga bayansu. Yarinya ce budurwa ta fito daga cikin motar da take a kunne tun zuwansu taci ado sosai.

Dariya take har tana rankwafawa ta kalli Dahiru "yaya sunanka?"

"Dahiru" ya bata amsa a takaice.

Tana dariya tace "Sannu Dashiru"

"Dahiru ne sunan" ya gyara mata a zatonsa bata ji bane sosai.

"To Malam Dashiru mai ahirin" ta sake kyalkyalewa da dariya.

Ransa in yayi dubu to ya gama baci. Hatta Bilya shima fuskarsa ta sauya.

"Kawu Sani ina ka samo mana 'yan ahirin?"

Hade fuska yayi sosai "bana son wannan shirmen naki Qariba"

Mamanta ta bata rai itama jin anyi mata tsawa "kai fa Sani idan kazo gidan nan to yaran nan basu da sauran sukuni"

"Yara ko magidanta? Kin ajiye dika-dikan yara saboda boko kunyi yi musu aure. Kuma kina kallo nazo da bako tana yi masa dariya don rainin hankali"

"Bakon naka ba me aikin gidansu zai zama ba? Kai kudin yayi maka zaka iya?"

A sanyaye Dahiru yace eh. Ya ma isa yace bazai iya ba tashi daya dubu ashirin a wata me ya manta.

Sunyi sallama da matar bayan an daidaita zai fara zuwa ranar litinin nan da kwana hudu kenan. Batun karatunsa wanda Oga Sani ya fada mata tace zasu daidaita idan an fara karatun a tsara yadda zai rinka aikin.

Sun juya zasu tafi Qariba ta daga murya tace "Malam Dahiru me ahirin sai monday" dariya ta rinka yi har ta shige cikin gidan.

Oga Sani yace masa sai yayi hakuri sosai da yaran dan uwansa. Shi maigidan Dr. Auwal rikakken dan boko ne wanda yake taba kasuwancin sayar da motoci yayin da matarsa Dr. Tani likita ce tana da asibitinta mai zaman kansa. Yaransu hudu maza uku sai Qariba mace kuma ita ce ta uku. Sangarta ta wuce tunani da gata yaran sun tashi dashi shiyasa zama dasu sai an kai zuciya nesa.

[08/01 : *GUMIN HALAK...*💰6

*Batul Mamman*💖



"Baffa anya ba zanje gidansu Mawadda ba da kaina?" Cewar Inna tana kallonsa ya zurfafa a tunani.

Dan guntun tsaki yayi "kije kice kinzo bada hakuri saboda 'yarki bakinta bashi da linzami ko"

"To naga ka kasa komawa kuma ance sun dawo. Danlami yace tun daga bakin titi ake binsu da kallo nasan surutun ma sai anyi"

Takaici ne kawai yake cinsa a rai. Idan ya fita an rinka zundensa kenan ko shine Mal Fatihu sai haka. Wasu har cewa suke Dahiru ne ma yayi mata fyaden. Wasu kuma suna ganin bai kyauta ba sun tonawa surukansu asiri saboda tsautsayi ya fadawa yarinyar. Yanzu ta yaya zai dawo da mutumcinsa a gari? Tashi yayi ya zura takalmansa yayi waje Inna na kiransa bai ko saurareta ba ya fita.

Gidansu Mawadda yaje abin mamaki tun kafin yayi sallama gabansa ke faduwa saboda kunyar ganin Baba. Lallai baki shi ke yanka wuya. A da shine abin girmamawa ko ba komai ya girmi Baba a shekaru haka zalika ya fishi rufin asiri. Amma yanzu da yake ganin kansa mai laifi gareshi duk sai yaji ya muzanta.

Yayi sa'a Mal Fatihu ya dawo daga kasuwa inda ya sayar da dabbobin Iya tun magariba domin kuwa lokacin tara saura na dare ne.

Da Baba ya fito suka kalli juna sai wani nauyi ya sake lullube shi.

Da kyar ya iya bude baki yace "Mal Fatihu do Allah do Annabi kayi hakuri. Kuruciya da tsabagen surutu yasa Ummiyo wannan barambarama"

"Babu komai kada ka damu"

Yadda Baba ya amsa Baffa yasan ko kadan bai kai zuci ba to amma baya son jan zancen.

"Ga wannan ka rike saboda kulawa da ita." Kudi ya mikawa Mal.Fatihu har naira dubu biyar.

Shi kuwa ya noke hannu "idan domin abinda ya faru ne Mal Isiyaku ka dena damun kanka dama ko ba dade ko ba jima ai gaskiya zata fito"

Duk yadda Baffa yaso Baba yaki karbar kudin har sai da yace ko dai ya rike shi a rai ne. Jin haka yasa ya karba suka yi sallama.

Washegari Baba ne ya jagoranci tafiyarsu Kano tare da Mawadda da Yaya. Iya ba yadda batayi ba akan Ade ta bisu tace kada a ga rashin kawaicinta tunda Yayan ta tsaya tsayin daka akan lamarin. Idan sun je Baba zai kira ya sanar dasu halin da ake ciki. Idan da bukatar su tafi sai su bi bayansu.

Dubu talatin yasa a aljihu banda kudin mota. Kanwar Yaya da take aure a sallari wata unguwa cikin Kano ita ce zata shige musu gaba zuwa asibitin Malam Aminu Kano. Da isarsu gidanta suka fara wucewa. Mawadda tana ta dararewa a baya saboda ko yaya aka kalleta sai ta tsargu.

Gani take kamar ana ganinta ake gane abinda BB yayi mata. Uwa uba ta kara shiga takura saboda fitsarin nan. Duk wani motsi a sannu take yinsa sannan tana bakin kokarinta wurin ganin ta rike fitsarin. Da aka kawo musu abinci baifi loma biyar tayi ba shima don an matsa mata ne. Suna gamawa kuwa suka wuce asibitin kai tsaye.

Ita Barira a iya saninta layi ake bi idan anje asibiti a karbi kati. Saboda haka wurin ta kaisu gashi shadaya saura. Sun jima a kan layin da basu tantance na menene ba sai daga baya wani ya sanar dasu na karbar sakamakon gwaji ne ba na karbar ko bude fayil ba. Haka suka sake komawa su ka bi layin da aka nuna musu. Sun sha matukar wahala kafin suyi sa'ar bude kati amma saboda makara da suka yi aka ce bazasu ga likita ba a ranar sai washegari su tabbatar sunyi sammako.

Baba yaso su ga likita a yau saboda baya son takurawa Barira da maigidanta. Ita ce autar su Yaya bata fi shekarun Bilki ba. Bisa lalura suka kwana a gidan inda aka bawa Baba wani daki a soro.

Duk yadda suka yi ya sanar da Ade ita kuma ta fadawa su Malam. Da safe kuwa waahegari bakwai akan layi tayi musu. Suna nan har rana ta gama budewa suka karbi kati aka ce su bi layin ganin likita. Har wata ajiyar zuciya Baba yayi don murnar suna gab da samun abinda ya kawosu. Da yake ko karyawa basuyi ba suka fito yace su jira shi ya samo musu wani abin da zasu ci.

Ya dan sha wahala kafin ya sami wurin masu abinci don shi gabadaya kansa ma juyewa yayi ya kasa gane hanyar komawa inda ya baro su.

Zaman awa kusan biyu suka yi kafin a kirasu. Baba yace su shiga da Yaya zai jira su a waje. Takardun wancan asibitin da na 'yan sanda duka ya bata suka shiga.

Mawadda ta yiwa likitan bayani daidai gwargwado tana kuka. Shi tunda yake bai taba jin abu irin wannan ace daga fyade sai kasa rikon fitsari ba. Ya kira nos tazo ta duba masa jikinta har sai da tayi kwalla ganin yadda karamar yarinya irin wannan ta tsinci kanta a wannan yanayi. Ta yarda mutanen kauye akwai dauriya ba raki irin na 'yan matan birni.

Suna jiran su ji me zai ce ya daga waya ya kira. Da gani dai da na gaba dashi yake magana saboda yadda yake ta kwantar da kai tare da yin bayanin lalurar patient dinsa.

Dan dakatawa yayi yace "daga ina kuke?"

Yaya ta amsa masa "kauyen Tariwa"

Da ya gama yace suje daga waje zai kirasu akwai wadda zata zo ta duba ta.
*****

Dr Tani ta ajiye wayar ta gyara kwanciyarta tana tsaki. Maigidanta Dr Auwal yayi murmushi
"Ke da wa wannan tsakin haka?"

"Dr Yunus mana. Wai ya kasa gane kan wani case ne shine yake neman alfarmar nazo. Ni kuma yau bani ma da ra'ayin fita. Raina daya naje AKTH naje nawa asibitin."

"Idan bazai yiwu ba ko ajiye aikin AKTH din mana ki mayarda hankalinki ga naki."

"Ina jin haka za'ayi don na gaji. Yace mutanen daga kauye suke so nasan zasu iya jira ba tare da damuwa ba"

Gyara kwanciya tayi abinta duk da tasan dama ita zata karbi Dr Yunus din karfe daya. Bata jima ba ta koma bacci sai shabiyu da rabi ta farka. Shima zafi ne ya tasheta saboda an dauke wuta.

A tsanake take komai hankali kwance. Marasa lafiya indai sun damu da lafiyarsu ai dole su jira. Ba ita ta gama shiryawa ba sai wuraren biyu.

Cikin shigar da ta saba yi idan zata je asibiti ta sauko. Doguwar riga ce mai dogon hannu ta atamfa sai hijab dan madaidaici saboda dora labcoat.

Qareeba ce kadai a falon tana kallo.

""Mummy kin sauko" shine kalmar da ta fara fada mata a madadin gaisuwa.

"Eh, ina su Najib?"

"Basu tashi ba"

"Jeki ki taso min su bana son suna kaiwa rana basu yi breakfast ba" ta fada tana ajiye jakarta a gefen kujera.

Baki Qareeba ta soma turowa ta tashi ba don taso ba.

Dakunan yayyenta ta je Najib, Faisal da kuma kaninta Safwan. Da gunaguni suka iso falon Mummynsu tana cewa su ci abinci bata son suna zama da yunwa.

Abin da zai bada mamaki shine dukkaninsu sun bawa shekara ashirin baya. Safwan shekarunsa ashirin da uku. Shi da sauran duka shekaru bibbiyu ne a tsakaninsu. Dr. Tani ba karamin so take yi musu ba shiyasa tsabar gata yasa suka tashi su ba dolaye ba su ba shagwabbabu ba. Har gara Qareeba mace ce amma mazan idan suka yi wani abin tamkar a bugesu don takaici.

Zamanta tayi suna ta tabara da sokonci har suka gama cin abinci sannan ta tashi ta fita dreba ya kaita asibitin.
******

Yunwa, gajiya, kishi da bacci duka babu wanda su Mawadda basa ji. Gashi suna tattalin 'yan kudadensu saboda basu san yadda zata kaya musu ba.

Dan abin kunzugun da Ade tace ta rinka sakawa saboda danshin fitsari tuni ya gama jikewa ita kanta tasan idan ta mike za'a gani.

Yaya tana sallah a gefensu akan dankwalinta Mawadda ta dan matsa kusa da Baba. Duk yawan marasa lafiyan gurin duk sun kare sai su kadai.

"Baba ko zamu tafi gobe mu dawo" tayi maganar a hankali.

Cike da tausayawa ya kalleta "kiyi hakuri Mawadda tunda likitan yace akwai me zuwa dubaki. Nasan basu manta ba. Kinsan fa aiki yawa yake musu shiyasa kika ji shiru har yanzu"

So take ta fada masa ta soma jikewa amma kunya ta hana.

Wata mata ce ta shigo ganin Yaya tana sallah a wurin ta tabe baki.

"Babu wanda ya kai dan kauye kazanta. Ji wannan matar ta rasa wurin da zata shimfida dankwali tayi sallah sai nan da kowa yake wucewa."

Ba wasu manya bane masu maganar amma sunyi shiga ta alfarma da zata nuna ba kananun mutane bane.

Mawadda da Baba sunji ta amma duka sukayi shiru. Wadda aka nunawa yaya harda yin tsaki. Kamar hadin baki sai ga nurses da wasu likitoci uku sun fito suna gaisawa dasu. Ashe 'yar wani minista ce.

Sannan Dr Yunus ya hango su Mawadda wanda ya ma manta dasu gabadaya.

"Har yanzu kuna nan dama? Nayi zaton kun gama kun tafi tun dazu"

Baba ya danne bacin ransa. Su da babu wanda ya kulasu tun fitowarsu me zasu gama?
"Likitan da zata dubata bata iso bane?"

Dr Yunus ya dauko waya yana son sake kiran Dr. Tani amma kuma yana tsoron fadanta. Sai gashi yayi sa'a ta shigo lokacin uku da rabi tuni ta wuce ana neman hudu.

A mutumce suka gaisa da kowa musamman 'yar minista ana ta tambayarta yaya jiki sannan tace ina mara lafiyar da zata duba.

Fayil din Mawadda aka kai mata office sannan aka kirata.

Tana tashi kusan kowa a wurin ya ga yadda kujerar da ta zauna tayi naso alamun danshi. Ganin ana musu kallon wulakanci Yaya ta dauki dankwalinta ta tsiyaya pure water a wurin ta hau gogewa. Daga wannan ya yamutsa fuska sai masu kananun maganganu don me tasan tana da lalura zata zauna akan kujerar. Maganganun sun yiwa Yaya zafi ta dai gyara wurin ta bi bayan Mawadda da Baba zuwa ofishin likitar.

A nutse take gabatar da komai Baba duk haushi ya ishe shi. Sai da ta gama karanta duka bayanan wancan asibitin sannan ta dan kalli Baba.

"Yallabai a bamu wuri muyi aikinmu ko. Ko a gabanka zan dubata?"

Har dan rissinawa yayi mata saboda kawai ta kyautata duba masa Mawadda "yi hakuri ranki ya dade bari na dakata daga waje. Mawadda kiyi bayani sosai kinji ko"

Kai ta gyada masa ya rufo kofar. Dama a tsaye take saboda yanayin jikinta. Gadon da yake cikin ofishin Dr. Tani ta nuna mata tace ta kwanta.

Yaya dai tana gefe Dr. Tani ta tsaya a gaban Mawadda tana dubata. Yanayin da taganta yasa jikinta yayi matukar sanyi ba kadan ba. Wane dabba ne yayi mata wannan mugun aikin haka. Da kyar ta iya hadiyar yawu saboda tashin hankali. Musamman da taga ko yaya ta tabata sai ta runtse ido ko hawaye ya fito.

"Har yanzu wurin da ciwo ko?"

Kai ta gyada kawai zuciyarta tana kuna. Tasha tambayoyi sosai sannan tace ta sauko. Yaya ta kalla tace ta kirawo Baban yarinyar.

Da sauri ya suri silifas dinsa ya bi bayanta suka sami wuri suka zauna ita kuma Mawadda tana tsaye.

"Bawan Allah garin yaya kuka yi sake 'yarku ta sami kanta a wannan yanayin?"

Gajeren bayani yayi mata tace "a gaskiya lalurar yarinyar nan ba kasafai take faruwa ba idan anyi fyade. Amma kuma ana samu a daidaikun lokuta. Yawanci tsabar tashin hankali ke zaburar da mace idan haka ta sameta motsi kadan sai ya firgita ta har ta kasa rike fitsarin. Yanzu zan rubuta mata gwaje-gwaje da nake so ku samu kuyi zuwa gobe in sha Allah. Sai na ga sakamako zan san wane irin mataki ya kamata na dauka"

Baba ya rinka mata godiya tamkar ance Mawadda ta warke ta gama. Ta dakatar dashi.

"Zan bata gado saboda ciwon nan yana bukatar kulawa kada ya zame mata wani abu a gaba. Dadin dadawa ina bukatar sanya mata ido domin na gano wasu abubuwa da zasu taimaka wurin magance wannan matsalar ta fitsari."

Su Baba to kawai suke cewa ta kirawo wata ma'aikaciyarsu ta wakilta taje a bawa Mawadda gado a bangaren mata. Sannan a tabbatar anyi gwajin da ta rubuta a yau.

Cikin dan lokaci kadan an basu gadon a dakin can gefen taga. Kafin likitan ta iso haka taje ta yayyafawa jikinta ruwa tayi sallah saboda wucewar lokaci ga rashin kayan canjawa. Ganin haka Yaya ta karbi kudi a wurin Baba ta koma gidan Barira. Ta dauko musu kaya da zannuwa da kuma abin rufa da tabarma. Barira ta hada musu abinci suka koma tare.
******

Shirye shiryen fara karatu ya kankama a wurin Dahiru. Ya kira su Baffa ya fada musu aikin da ya samu duk sunyi murna. A nan kuma yake jin tahowar su Mawadda Kano. Duk da su ma su Baffan basu san me kuma yasa suka chanja asibiti ba amma ansan ba lafiya ne.

"Kana nan akan bakanka na aurenta har yanzu?" Baffa ya tambayeshi.

"In sha Allahu. Yanzu haka ma ina jiran Yayanmu Bilya ya dawo zamu fara duba gidajen haya"

"Dahiru ina jiye maka ga karatu, ga aiki sannan ka hada da aure. Auren ma irin wannan ba na dadin rai ba. Kada garin neman suna komai ya baci fa"

Murmushi yayi kamar Baffan na kallonsa "Baffa addua kawai zaku tayani da ita saboda ni dai don Allah nake son aurenta ba komai ba."

Bai kara cewa komai ba ya kashe wayar. Yasan yanzu kowa zaiyi kokarin cusa masa ra'ayin rabuwa da Mawadda. Sai dai ya shirya toshe kunnuwansa indai iyayensa suka saka masa albarka. Bai taba son wani yadda yake sonta ba. A halin yanzu yana ji a ransa tausayinta har yafi son da yake mata yawa. Bazai taba iya barinta ba saboda yanzu ne ma take bukatar kulawa da dukkan wani gata da shi ko wasu masu sonta zasu nuna mata.

Da yamma suka fita neman gida don yafi son ya samu da wuri.
******

Ranar lahadi washegarin da aka kwantar da Mawadda su Ade suka taho. Kafin isowarsu an kaita wurin gwaji inda aka debi fitsarinta da jini. Tun daga nan Baba ya fara sarewa da lamarin asibiti saboda kudin da yaji zai biya na wannan kawai. A haka ma wai don asibitin na gwamnati ne.

Da suka dawo ta samu dan bacci har su Ade suka iso bata sani ba. Sunyi sa'a karshen sati dama da wuri ake barin 'yan dubiya su shiga.

Tana cikin bacci ruwan hannunta ya kare Nos namiji ne a kusa aka kira shi yazo zai cire mata. Bude idon da zata yi ta ga namiji a kanta ta kwala ihu iyakar karfinta ta tashi a firgice.

"BB ka rufa min asiri kada ka cutar dani. Wayyo Allah Babana ka taimakeni"

A rude take gabadaya tana ta sambatu. Baba yana waje da kaninsa sai su Ade da Iya don Yaya ma ta tafi gidan Barira karo zannuwan da Mawadda zata rinka chanjawa.

Da kyar suka iya kamata idanunta akan Nos din tana kuka.
"Ade kada ku bari ya tabani wallahi akwai ciwo"

"Babu me tabaki kinji ki kwantar da hankalinki" ta amsa mata

"To kice ya fita"

Iya ta kalle shi da alamun roko. Shi tausayi ma yarinyar ta bashi ya  fita sai Nos mace ce tazo ta cire mata allurar don ta goce.

Wani baccin ne ya soma fizgarta ta kwanta a jikin Iya.

"Allah dai ya kwashewa wannan tsinannan yaro albarka. Dubi yadda yasa ta tarawa kanta 'yan kallo saboda yadda ta firgita. Allah Ya kaimu a sallameta ko zan sayar da gonata ta gado sai mun shiga kotu da yaron nan"

"Kayya dai Iya da kin bar maganar nan. Dame zamu tunkari shari'a da wadanda suka fimu. Sannan daga lokacin kowa zai san sirrinta duk inda ta zaga a nuna ta"

Wani tsaki Iya tayi mai kara sosai "amma kin bani mamaki. Wane sirri ne ya rage mata bayan a garin namu babu wanda bashi da labari yanzu. Kuma da kike batun za'a nunata an dade ba'a nuna ta ba. Iyaka ace ga wadda aka taba yiwa fyade ba wadda taje yawon ta zubar ba ko. Kai! Ni kam kuna bani mamaki abu mai girma kamar wannan ya faru ayi ta kubi-kubi dashi wai kada ya fito duniya ta sani"

"Yanzu Iya ba kya jin yadda rayuwar mata irinta take tagayyara?"

"Me zai hana ta tagayyara kuwa iyaye sai su rufe magana abar yarinya ita kadai tana fama da bakinciki. Yanzu da tayi shiru bamu sani ba haka zata rinka zabura muna banka mata hayaki ace mutanen boye ne. Kinga idan baza kiyi komai a kai ba ni ki barni. A ganina shirun da akeyi da rashin daukar mataki shine yake bada damar gobe ma a sake. Sannan yana daga abinda yake sa matan su ga kamar sune masu laifi ba matsiyatan da suka cutar dasu ba"

Shiru Ade tayi don ko kadan bata maraba da a kai maganar kotu a yiwa Mawadda tonon silili.

Sake kallon Iya tayi tana ta fada ta jinjina kai. Wannan karfin hali nata ga talauci ga rashin wayewa amma baya dakusar da ita akan niyyarta.

Suna nan zaune sai ga Baba ya shigo da Dahiru da Bilya. Ade na hango su ta dubi Iya.

"Don Allah kada ki ce musu komai"

Iya tayi guntun tsaki "ku kuka sani, mutane sunyi sanadiyar tona sirrin da kuke ta boyewa ya fito har akwai wani abu na mutuntawa tsakaninku kuma"

Da suka karaso sun gaisa dasu tare da tambayar mai jiki.

Ade zata amsa Iya tayi saurin katseta "jiki da saukin musulunci gata tana bacci. Raunukan zahiri dai suna ta warkewa amma kwarewa a tsegumi yasa an dasa mata wani tabon a kahon zuci. Uhmm ko da wane idon jama'ar gari zasu rinka kallon jikata kuma Allahu Ya'alamu"

Duka su biyun kai suka sunkuyar a kunyace don sun san dasu Iya take. Bilya ne ma ya iya bada hakuri sannan ya kara da cewa "muna nan muna neman gidan da zasu zauna ba a kauyen zai ajiyeta ba"

Tsananin farinciki a take ya kama Iya ta kalli Bilya ta koma tana kallon Dahiru.

"Kai yaro rantse, kace Allah Dahiru zai aureta"

Ledar lemo da ayaban da suka zo da ita Dahiru ya ajiye ya fice ganin su Baba duka shi suke kallo. Bayan fitarsa Bilya ya fada musu halin da ake ciki na dangane da samun gurbin karatu da aiki da zaiyi.

"Nifa shiyasa tun ranar da aka gabatar min dashi nace in anyi duniya dan Manzo Mawadda bata da miji bayan Dahiru. Zuri'ar gidanku ba daga nan ba ni shaida ce ra'ayil aini. Aure a wannan yanayin wallahi sai dan kwarai da ya haifu cikin uwa da uba."

Ade dai kasa cewa komai tayi Iya ta saka ta jin matsananciyar kunya. Amma anya iyayensu Dahiru sun sani kuwa? Shi kuwa Baba fita yayi yabi bayan Dahirun. A can gefe ya hango shi zaune. Ganin Baban yasa ya taso da sauri.

Kaunarsa ta sake shigar Baba ya yi masa murmushi "Dahiru nasan kai yaron kirki ne kuma ko gobe ka nuna kana son wata cikin kannen Mawadda zan baka. Amma ka hakura da ita, tata kaddarar kenan hakuri da aure"

Yana jin kunyar Baba gaskiya amma baya jindadin yadda kowa yake ganin rabuwa da ita shine alkhairi garesu.

"Baba don Allah ku sa mana albarka kawai. Na fadawa su Baffa kuma sun amince"

"Bazan so kaina ba Dahiru. Ko a yanzu ma mungode sosai da kulawa. Amma ka dauketa a matsayin kanwarka kawai. Idan ma saboda magana ta fito ne duka babu komai ko me za'ace za'a gaji a bari"

Magiya sosai Dahiru ya soma yi har ya bawa Baba tausayi. Amma don ya kara nuna masa illar auren duk kuwa da cewa ransa yana so ya sanar dashi dalilin zuwansu asibiti.

Dan nazari Dahiru ya soma har Baba yaji jikinsa ya kuma yi sanyi kada ya fasa da gasken sai kuma yaji yace "Baba haka zamuyi ta hakuri har ta sami lafiya amma aure in sha Allah ba za'a daga ba."

Kwalla ce ta taru a idon Baba. Ya sani wannan ba karamin abu bane. Ko dansa ne haka ta faru da wadda zai aura da wuya fa ya amince. Baya jin zai taba mantawa dashi ko auren bai yiwu ba yasan ya so 'yarsa kuma yaso rufa masa asiri.

"Nagode amma ka jira zamuyi magana da shi Mal Isiyaku kaji."

Bilya ne ya leko yace Mawadda ta tashi suka nufi hanyar dakin Dahiru yana rokon Baba akan su taimaka kada a fadawa iyayensa lalurar da ta kamu da ita yanzu. Baba ya ji shi ne kawai amma fada ya zama dole musamman yadda ya kara yarda da wuya ake boye abu a duniya. Bazai so a zargesu ba a gaba.

Tun shigowar Nos dinnan namiji har yanzu da Mawadda ta farka hankalinta bai gama kwanciya ba. Shiyasa su Dahiru basu wani dade ba suka tafi. Iya kuwa ta rinka mata fada akan ya kamata ta soma sakin jikinta da mutane.

Da yamma Dr. Tani ta shigo ta sake dubata. Sakamakon gwajin ta fadawa su Baba

"Sakamakon urinalysis da aka yi mata ya nuna bata kamu da wata kwayar cuta ba irin wadanda suke kama mafitsara. Saboda haka zan dorata akan magunguna sannan akwai abubuwan da nake bukatar ta kiyaye. Ku dan bamu wuri zanyi mata bayani"

Su Iya ne akan gaba wurin fita. Dr Tani ta kalli Mawadda tana dan murmushi. Yarinyar ta bata tausayi sosai har labarin abinda ya sameta ta bawa iyalinta.

"Kina jin saukin jikinki yanzu?"

"Eh" ta amsa murya can kasa.

"Abinda nake so dake shine na farko bana so kina zama da fitsarin nan duk da na kula ana chanja miki zani akai akai. Ga auduga nan za'a baki sai ki rinka sakawa ko da ya digo bazai taba miki kaya ba. Abu na biyu ina so duk lokacin da kika ji fitsari kiyi kokarin rikonsa na kamar minti biyar....ke security! kirawo min mahaifiyar yarinyar nan dai"

Yaya ce ta shigo Dr ta cigaba da bayanin yadda take so a kula da Mawadda. Idan taji fitsari su rinka dubawa da agogo sai bayan minti biyar da soma jinsa zuwa goma zata je tayi. Kuma ta dage sosai wurin rikonsa kada ya digo. Abu na biyu idan sun je tayi ta tabbatar ta gama sai ta sake dagewa ta kuma matso duk wanda yayi saura. Kada ta tashi sai ta tabbatar a karo na biyun ta sake yin wani komai kankantarsa. Tana so suyi haka na kwana uku domin horar da jijiyoyin wurin. Idan ta gamsu da cewa Mawadda tana yin yadda aka umarceta zasu sallameta sai ta dawo bayan sati daya a dubata amma dole zata cigaba da yin yadda tace din.

"Sai lamari ya baci ake yin aiki wanda bana fata muzo haka dake. Saboda haka ki dage sosai ki bi abubuwan da nace. Magunguna kuma za'a bawa babanta takarda ya siyo da wuri domin a fara amfani dasu."

Wasu cikin magungunan babu a pharmacy din asibitin aka kwatantawa Baba wani a waje. Ya samesu duka amma an kashe kudi kusan dubu hamsin. Yau ba don Iya da Ade ba da kila ko bara ce ta kama yayi zaiyi. Me za'ayi da talauci. Sai yayi huluna suyi sati yanzu ko tayawa ba'ayi balle kuma a saya. Gonar da yake dan nomawa yanzu amfanin da ake samu ba kamar da ba ita ma.

Da nannauyar zuciya ya koma ya kai magungunan. Suna ta fatan Allah Yasa a dace.

Abubuwan da Dr. Tani tace ta kula dasu na yanayin fitsari kuwa ta fara gwadawa iyayenta suna karfafa mata gwiwa.

******

Maigadi ne ya fito jin ana ta buga gate din. Yasan fuskar matar da ya gani duk da bai san sunanta ba amma yasan tana zuwa wurin Haj Mara.

Bude mata yayi suka gaisa ta tambayi Hajiyar yace tana ciki. Da sallama ta shiga. Da Haj Mara taji muryarta wani mugun tsoro ne ya kamata. Murmushi ta kakalo na dole gabanta na faduwa.

"Hajiya Gambo kece a gidan namu?"

Gambo dillaliyar masu aiki tayi dariya "ai ku ne hajiyoyi. Yaya gida da kujiba-kujibar yau da gobe? "

"Lafiya kalau"

Shiru Haj Mara bata sake magana ba tana jira taji me ya kawo Gambo. Ita kuma jira take Hajiyan ta turo mata Mawadda kamar yadda ta saba. Gajiya tayi da jiran tace

"Hajiya ina Mawadda ne? Yarinya na kawo nan Malali shine nace bari na leko mu gaisa."

Haj Mara ta hadiyi wani mugun yawu saboda yadda ta tsorata.

"Mawadda ai ta tsufa a gida"

"Ban fahimta ba"

"Rana daya kawai tasa min kuka tana son tafiya. Tun ina bata hakuri na gaji da kaina na mayar da ita"

Gambo tace "Mawaddan? Ni duk cikin yaran da nake kawowa ma ai tafi sauran hankali. Tasan cewa zan dawo na tafi da ita da kaina. Dama yau karfin zuwan nawa zanyi miki maganar bikinta ne da ya matso. Shine nace gara na fada ko zaki nemi wata. Ita idan nazo na kaita hutun sallah bazata dawo ba"

"Ni na hakura ma da masu aiki hakanan Gambo. Aikin nawa yake gida sai mu uku"

"Haba Hajiya da kanki"

"Ai dole, Gambo bazan boye miki ba Mawadda ta bani mamaki. Ta difga min sata ta ban mamaki shiyasa ta dage zata tafi"

Ran Gambo kuwa ya baci. Ta saba da ace ta kawo yarinya tayi sata amma batayi zaton haka daga Mawadda ba.

"Hajiya kada ki damu nawa ta satar miki? Wallahi da kaina zan dawo miki da kudinki don gidansu zani. Wannan sai su kashe min kasuwa azo ana ganin kamar hadin baki muke dasu"

BB yana kitchen yazo shan ruwa yaji Hajiyarsa tana karya don ta rufa masa asiri. Wata dariyar shakiyanci yayi ya fito falon.
"Hajiyata kenan, Allah Ya barmin ke muci karenmu ba babbaka"

Gambo ta bisu da kallo Haj Mara ta wayance tace ta bar maganar satar ita ta hakura.

Gambo na fita wayar Baba ta kira tunda tana da ita. Duk lokacin da tazo karbar kudin Mawadda da layin take kiransa ta hadasu su gaisa. Ko tasha bata karasa ba ya dauka ta soma fada masa abinda Haj Mara tace.

"Ince ko Kano zaki sauka idan kin taho."

"Eh dama gobe nayi niyar zuwa Tariwa din"

"To ki daure ki shigo asibitin Malam sai ki kirani"

Daga haka ya kashe wayar ya barta da mamaki. A tashar unguwa uku ta sauka ta wuce gidanta da niyar gobe zata je asibitin tunda dare yayi.
******

Haj Mara  tun zuwan Gambo hankalinta ya kasa kwanciya. Matar nan dai tasan gidanta. Idan ta dawo tare da iyayen Mawadda fa yaya zata yi?

Alh Sule har ya fuskanci tana cikin damuwa yayi kwafa.

"Tun ba'aje ko ina ba kin fara zurfafa a tunani akan barnar da yaron nan yake yi ko? To kadan ma kika gani. Ina me tabbatar miki idan bazaki kaini gidan iyayenta mu gyara lamarin nan ba to ki tanadi abin tarar hawaye nan gaba"

Ya gaji da magiya harda barazanar saki duka a banza tace bazata kaishi gidansu Mawadda ba.

Tsoron dawowar Gambo yasa ta dauki waya bayan ya fita daga dakin ta kira kawarta.

Saita muryarta tayi tamkar babu komai kafin ta soma magana da aka dauka
" 'yar boko matar dan boko"

Dr Tani tayi dariya
" 'yar kasuwa matar dan kasuwa jiya ina ta nemanki waya a kashe. Ya ya mutan gida"

Dan barkwanci da tsokanar juna suka taba irin na kawayen da suka tashi tare. Sai kuma Haj Mara ta tattaro nutsuwarta.

"Tani kwana biyu ina ta tunani nace bari dai na fada miki naji ra'ayinki. Cewa nayi me zai hana in turo Babawo yazo su daidaita da kanwarsa Qareeba?"

A zahirin gaskiya Dr. Tani bata da burin 'yarta tayi auren nesa saboda zaman su Haj Mara a Kaduna. To amma ta gaji da gorin dangin miji gashi Qareeban duk gayunta samari basa dadewa ta rasa dalili. Shekara ashirin da biyar gara tayi aure ko zata huta da surutu.

"Amma kinyi tunani mai kyau Marakisiyya na amince. Zanyi magana da Daddynsu sai na fada miki yadda muka yi"

Ajiyar zuciya Haj Mara tayi. Gara Babawo yayi aure kila zata sami saukin wannan bibiyar matan da yake yi.
******

Da kwatancen da Baba yake mata Gambo ta iso dakin da aka kwantar da Mawadda. Kafin tayi tambayar me suke a nan Yaya ta labarta mata komai. Idanunta jazur saboda kuka da takaicin rainin wayon da Haj Mara tayi mata jiya tace da zasu bata hadin kai da an kaisu kotu.

Iya tayi dariya "Allah nagode maKa na sami mai goya min baya. Mun yarda mun amince don ko wadannan basa so..." ta nuna su Baba "ni bazan yafe ba."

Sake kallon Mawadda tayi taji kamar ita ta jawo mata da bata tsananta bincike akan gidan ba. Ji yadda ya sabauta musu yarinya ta fada kumatu ba tsoka sai hakwara gayau da idanu.
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰7

*Batul Mamman*💖



Bayan Sati Daya


Aikin Dahiru a gidan Dr. Tani ya kankama kuma Alhamdulillah komai yana tafiya daidai. Matsalarsa daya ce a gidan Qareeba wadda ta zame masa tamkar horror. Ta matsa masa sosai duk wani motsinsa abin tsokana ne a wurinta. Ta kai ta kawo idan yaji muryarta gabansa har faduwa yake saboda bai san me zata ce masa ba.

Yau ta kama litinin dama tun jiya ya sanar cewa yana da uzurin da zai sa bazai sami damar zuwa da wuri ba. Asibitin makaranta suka je inda akayi masa gwaje-gwaje na sanin yanayin lafiyarsa kamar yadda makarantu suke bukata. Yana gamawa ya wuce wurin aikinsa ko gidan Bilya bai koma ba. Ga rana ga yunwa don bai ci komai ba ya fita.

Sanye yake da koriyar t-shirt da dogon wandonsa ruwan dorawa mai duhu sai farin canbas din da yake ji dashi. Yayi kyau abinsa daidai da kwalliyarsa.

Tunda ya fara aikin maigadi ya bashi shawarar ya ware kaya daya da zai rinka amfani dasu kada ya kashe suturunsa a bawa filawa ruwa da su shara. Kafin ya tafi jiya ya wanke su ya shanya a bayan gidan inda igiyoyin shanyar suke. Yana isowa hanyar bayan yayi domin dauko su.

Ta cikin falo Qareeba ta hango shi yana tafiya da sauri ta dawo bakin taga inda zata ganshi sosai.

Dariya yaji an saka ya dan cije lebe. Yau ya shiga uku kuma ko da me tazo.

Kayansa ne suka bata dariya yaji ta ce

"Ahirin irin wannan gayu haka. Gaskiya ka burge maza enyee."

Ta zuge labulen tana kallonsa sosai bayan ta bude tagar. Shi kuwa kamar ya kwadeta. Cigaba yayi da tafiya kawai sai ta fara masa waka harda tafi.

" Gayu, gayu Ahirin on top, gayu, gayu Dashiru on top"

Abin ya sosa masa rai fiye da zato saboda dariya akwai cin rai ga yunwa. Karasawa yayi ya kwaso kayansa tana ta shirmen wakarta. Sai da yazo daidai tagar zai wuce ya daga hannu ya yi mata dakuwa.

Zaro idanu tayi ta nuna kanta "Ni?"

Ya gyada kai tare da harararta ya wuce. Bai ko karasa gaban gidan ba yaji Dr. Tani tana kiransa. Hankali kwance ya nufi bakin kofar shiga gidan don a tunaninsa aiki zata saka shi. Yana tsaye a gefe ta fito. Ko gaisuwar da yake mata bata amsa ba ta soma fada.

"Dahiru har wuyanka yayi kaurin da za ka zagar min 'ya?".

Qareeba ya gani tana goge hawaye a gefenta ya dago kai fuskarsa na nuna mamaki.

"Hajiya ni din? Yanzu fa na shigo gidan."

A shagwabe Qareeba tana wani tale baki tace "Mummy ta window ya harareni yayi min haka..." ta yiwa Dr. Tani dakuwa yadda yayi.

Mummy tayi saurin rike mata hannun ganin ya bisu da kallon mamakin gaske yanzu.

Sai kuma ya koma kallon Qareeba "Assha Anti Qareeba kila dai baki kula bane sosai. Na hangoki ne ta taga shine na dago miki hannu"

"Mummy kinji wani wulakamcin wai Anti kamar wata babba"

"Abokiyar wasanka ce to da za ka daga mata hannu?" Dr. Tani ta fada a fusace.

Girgiza kai ya shiga yi "A'a Hajiya kiyi hakuri in sha Allahu zan kiyaye"

Tsaki tayi ta juya tana jan hannun Qareeba mai dagewa da gaske zaginta yayi. Bayan sun wuce ya kada kai yayi gaba yana mamakin jama'ar wannan gida. A haka fa ance masa Qareeban bautar kasa zata soma. Yayyenta sun gama don Najib har ya fara masters. Amma dukkansu wasu iri yake ganinsu saboda dabi'unsu.

A dakin Qareeba tana zaune a kan gado Dr. Tani tace "bana son wannan shisshigewa yaron nan da kike yi kinji ko. Kinsan sarai Sani da sauran dangin Daddynku basa kaunarku. Kila ma turo shi akayi sa ido shine  ke kuma da abin dariya baya yi miki wuya kin saka shi a gaba"
******

Karfe biyar a kofar bangaren da aka kwantar da Mawadda tayi masa. Tunda ya fara aikin sai yau ya sami damar komawa.

Kusan duka 'yan uwan Mawadda suna dakin idan ka cire Baba. Kanta ta kifa akan cinya tana kuka Innar Fatihu tana mata fada.

"Haba Mawadda ace mutum baya jin rarrashi ko kadan. Idan zaki karar da hawayenki fa babu wani abu da zai iya goge wannan abin. Ki rungumi kaddara kin kasa kullum sai koke-koke ki tayarwa kanki hankali muma ki tada mana"

"To, to, taji sai a barta haka." Cewar Iya tana rungume Mawadda a jikinta "kuma dole tayi kuka. Sati guda tana bakin kokarinta amma fitsarin nan yaki daukewa."

"Cuta dai aka sani da shiga farat daya amma sauki sai anyi hakuri. Wannan abin da kike yi mata Ta Rasulu ba soyayya bace"

Cacar baki suka yi ta yi 'ya'yansu da jikoki suna basu baki.

Dahiru ya matso a hankali yana kallon yadda mutanen da suke sauran gadajen suka kafesu da ido suna neman cika dakin da hayaniya.

Ai kuwa sai ga security tace gabadayansu su fita. Yaya ce ta lura da Dahiru tayi masa murmushi ya duka ya gaishesu.

"Zauna ku gaisa bari muje waje"

Ade ma murmushi tayi ta fita. Ita dai tana son yaron nan amma tana jiye musu lokacin da Baba zaiyi magana da Baffa. Abin da kamar wuya dai.

Sai da kowa ya fita ya matso tare da dafa bayan kujerar dake gafen gadon.

"Bazaki dago mu gaisa ba Mawaddan wa Rahma."

Wani sanyi taji a ranta sai kuma kunya ta sake jan mayafi tana kuma tura kanta cikin cinyoyinta.

"Yangar da kike yi min yanzu ko da bana jin kinyi irinta. Yanzu dai kin yini lafiya?"

A hankali ta dago "kai Yayanmu nice zan fara gaisheka fa"

"Kina wannan kukan me hada tsofaffi rigimar ne zan jira ki gaisheni?"

Shiru tayi tana son gyara zamanta amma tana kunyar ko yaya ta matsa kamar zai ga yadda wurin ya jike.

Shiru suka yi na dan lokaci can yace "kukan me kike yi ne?"

"Ba komai"

Yace "Ban isa a fada min ba kenan"

Da sauri ta dago "a'a"

Ya dan ja kujerar ya zauna "to ina jin ki"

Bagarar da zancen tayi tace "Ashe zaka fara karatu na tayaka murna"

"Murnar ba tamu bace mu biyu?" Ya tsareta da ido.

"Tamu ce mana harda duka 'yan Tariwa. Kowa yaji nasan zaiyi murna"

Tambayarta yayi yaushe za'a sallameta tace saura kwana biyu. Yayi alkawarin zuwa ranar suyi sallama.

"Kinsan yanzu na fara aiki babu damar kalula da na rakaki har gida. Zan cigaba da kokarin samar mana gida in Allah Yaso."

Jinsa kawai take don tasan ko me zata fada masa yanzu bazai fahimceta ba. Da zai tafi ya kawo dari biyar ya dora mata akan pillow. Tayi ta magiyar ya dauka yace idan tana rokonsa zasuyi rigima ne. Ba don yasa ba haka ya tafi ya barta.
******

Kwana biyu a tsakani aka sallameta. Dr. Tani ta bata magunguna sannan tayi gargadi sosai akan ta kula da wadannan abubuwa da ta sanar da ita ta kiyaye idan tana jin fitsarin.

Kalandar wayarta ta kalla sannan tace "nan da kwana shabakwai ku dawo. Zai kama sallah da sati biyu kenan. Akwai wani matakin da zamu dauka amma sai naga yadda wadannan suka karbeki"

Tasha godiya sosai sannan suka hada kayansu suka wuce. An bar Mawadda a gidan Malam saboda zata fi kusa da Ade don indai ta koma gidansu Ade da wuya taje.
*****

Anyi sallah babba lafiya. A bangaren Dahiru ya zage yana aiki sosai musamman ranar sallah da aka yanka katon sa da raguna uku. Sun aikatu sosai shi da maigadi wurin gyaran naman. Sai mata biyu da aka samo tare da ainihin kukun gidan suka hadu suka soya.

Ranar sai dare ya tafi. Yana bude gate Dr. Auwal yana shigowa. Suka gaisa ya wuce da ledar naman da aka bashi yana ta sauri ma kada yaje Furaira tayi bacci naman ya lalace tunda idan ba iyalin yayansa ba bashi da wanda zai bawa.

Dr. Auwal suna hira  da matarsa yake ce mata "na kula yaron nan Dahiru yana da kwazo kuma babu kyuya"

"Kai kuwa yaji kudi in maka ta Qareeba tace ahirin" tayi dariya.

Ido ya zaro "Dubu ashirin? Dubu ashirin za'a bashi?"

Dan turus tayi tana kallonsa "a'a fa Daddy maganar nan kai ka fadeta ranar da safe kace idan yazo ga abinda zan ce masa ni har inata mamaki ma"

Goshinsa ya shafa "gaskiya akwai matsala don wallahi subutar baki nayi. Ke a lokacin ai kya gyara min. Idan na bayar da yawa ya wuce dubu goma tunda nasan karatu zaiyi. Amma ke kin taba jin ana biyan dubu har ashirin a aikin shara banda abinki"

Cikin nuna rashin damuwa tace "ba wani damuwa bane. Idan wata ya kare sai a bashi abinda ya samu. Ga ci ga sha ko dubu biyar ka bashi ai ya gode"

Dr. Auwal ya dan fi matarsa sassauci duk da harka indai ta hada da fitar kudi sam baya kaunarta.
"Zan bashi takwas dai nasan ya riga yasa rai. Amma sai anyi min hakuri zuwa next month saboda harkar sallah duk nayi kaf. Daga shi har sauran kowa yayi hakuri wani watan sai na hada musu duka. Ai kin basu sadakar nama ko"

Ta amsa da cewar ta bayar kowa ya sami mai yawa ba laifi.

Hirarsu suka cigaba suna tsara yadda zata kasance nan da 'yan kwanaki da BB zai zo ganin Qareeba. A yadda abin yayi musu dadi saboda matsuwar da sukayi tayi aure basa so a dauki wani dogon lokaci.
*****

Can kuma Gambo mai kai masu aiki birni ta shige gaba tare dasu Baba akan kai karar BB. Fadi take dole ne su mutunta kawunansu idan suna so wani ya mutunta su. Aikin da suke yi kansa su wuni aikin ruwa, girki, wanke kashi da fitsarin yara da sauran ayyukan wahala da karfi amma abin da ake basu baya taka kara ya karya kuma a haka ma gani ake anyi musu gagarumar alfarma. Duk ranar da ta kuskure ta bangarensu masu gida basa musu da sauki. Kwandala aka nema aka rasa su ake fara zargi. Amma idan reshen ya juya aka cutar dasu sai dai ace suyi hakuri saboda su talakawa ne.

Ofishin 'yan sanda na Bebeji suka fara zuwa daga nan aka turasu Kano. Bayan daukar bayanan korafi daga bakin Baba suka tattara komai aka mika kotu don yanzu ana kokarin ganin an kawo karshen wannan mummunar al'ada ta fyade.

Cikin sati guda komai ya kammala aka aikawa BB da shammaci har gida da taimakon adireshinsu da Gambo ta bayar.

A tsakar gidan Malam an taru ana shawarar neman lauya da yadda za'a tara kudin.

Malam ya ce da Mawadda "amaryata sai kin daure sosai kamar yadda kika faro a baya. Duk wata tsangwama da surutun da ake yi miki na fada miki bazai fito miki a jiki ba. Da farko na dauki kai karar nan kamar daukar wuka mu dabawa cikinmu ne. To amma yanzu ina ganin lokaci yayi da zamu tashi tsaye mu dena rufawa masu laifi irin wannan asiri saboda gudun surutu"

Iya tayi shewa "dama can saboda shawarata ce shiyasa kuka yi ta runtse ido ana nuna muku hanya. Zance ya riga ya baza duniya tunda 'yan garin nan suka sani. To me kuma ya rage sama da a bi mata hakkinta. Shegen yaro bakin mugu babu abinda yafi kona min rai kamar uban dukan da yayi mata banda karfin da ya sa mata"

Kowa yana ta tofa albarkacin bakinsa banda Ade. Ita dai wannan tone-tone a bainar jama'a ranta baya so ko kadan.

*****
Abu kamar wasa Haj Mara tana shan fruit salad maigadi yayi sallama. Aikin gidan da tayi ta cika bakin zata iya ya gagara ta nemo wata tsohuwa tana mata.

Kwada mata kira tayi ta leka taji me yake bukata. Jim kadan ta dawo da takarda ta mika mata.

Tana kashingide hankali a kwance ta bude. Taken takardar kawai ta karanta hannunta ya soma rawa ta tashi a gigice tayi sama inda ta baro wayarta tana chaji.

Alh Sule ta kira yana China kwanansa uku da tafiya. A can dare ne tuni yayi bacci tayi ta kira shiru. Kuka take bilhakki ta karance takardar tsaf.
Ga gumi ga hawaye ta sake saukowa tayi bangaren BB tana kwala masa kira tun kafin ta isa. Wani mahaukacin bugu take yiwa kofar.

"Babawo bude min kofar nan mun shiga uku"


Tsaki yaja ya taso ya bude. Abubuwan da suke damunsa da yawa Hajiya kuma zata kara masa da damuwarta.

Bai lura da yanayin da take ba yace "Hajiya akwai matsala fa"

Ta daure fuska a zatonta yasan da sammancin.
"Kasan da matsalar ka ki gaya min da wuri sai da na gani yanzu"

"Ni dai kawai kiyi hakuri tunda kin sani yanzu a aura min ita. Wallahi kwanakin nam tunaninta baya barina ko baccin kirki nayi"

Haushi ya bata "kaga idan ba kashe wannan gobarar akayi ba babu abinda zaisa Dr. Tani ta baka auren 'yarta."

Ya wani hade gira "wai kin zata da wannan doluwar nake Qarira take ko wa. Nifa gaskiya bata yi min ba ko kadan. Shekaranjiyan ma da na zauna a gidan kawai don kada ranki ya baci ne. Maganar Mawadda nake miki, Hajiya sonta nake da aure"

Yadda maganarsa ta kona mata rai bata san lokacin da ta kwashe shi da mari ba. Yana rike da kumatun ta harzuka ta soma fada tare da jifansa da takardar.

"Idan ma kaje kayi shaye-shayenka ne ai baka manta yadda ake karatu ba ko. Shashashan banza"

Ko a jikinsa da ya karanta. Sai ma cewa yayi ta taimaka masa a kashe case din tun kafin aje kotu ta hanyar aura masa Mawadda.

Magana take son yi amma ta rasa abin cewa. Ta ga alama Babawo so yake ya kasheta da ranta. Fita tayi tana kuka ta koma dakinta tana sake gwada kiran Alh Sule amma shiru. Sai daga baya ta tuna lokacin ta  tura masa sakon text.

Da safe haka ta tashi sukuku. Da wa zatayi shawara kuma meye mafita? Sauran yaranta ta nema amma duka tayi musu karyar sharri Mawadda ta yiwa BB kamar yadda ta fadawa 'yan uwanta da na mijinta sai dai kadan cikinsu ne suka yarda saboda sun san waye BB. Dole ta yiwa tufkar hanci kafin mutumcinsu ya zube.

*****

Yau kwana biyar kenan Dahiru da sauran ma'aikatan gidan suna jiran albashi. Inna da kanta tazo gidan Bilya ta sanar dashi su Mawadda zasu shiga kotu. Ta kuma dage akan cewa indai suka shiga kotun nan to wajibi ya manta da wata maganar aure. Ita a ganinta ba gara ma surutun Ummiyo iyakarsa kauyensu ba. Amma yanzu kila har a In Da Ranka sai an fada.

Shima dai hankalinsa ya tashi baya maraba da wannan terere. Gashi bata da waya ko magana da sunyi. Albashinsa yake jira ya tafi gida ko kwana biyu ne yayi. Ya gama daidaitawa da wani mai shagon waya a kusa da garejin su Bilya ya sami 'yar karama second hand da zai kaiwa Mawadda. Ga gwanjo da zai saya saboda sun kusa fara lacca. Sannan ma dai nauyinsa dake wuyan Bilya da gorin da Furaira take yi masa yasa ya kuma matsuwa da kudin. A kalla ko cefane zai rage masa ya bashi wani abin.

Yana ta hamma Kuku ta fito da abincinsa da na maigadi. Sun dan taba barkwanci sannan Maigadin yace

"Ni kuwa baki ji komai game da albashinmu ba? Yarona aka koro daga makaranta kayansa sun lalace. Kinsan halin maza gwiwar duk ta fashe. Bana son bashi tunda wata ya riga ya kare nace ya zauna ayi albashi tukunna."

Mikawa Dahiru kwanukan tayi shima hankalinsa yana kan zancen.

"Shekaranjiya bayan bakon nan na Qareeba ya tafi naje na tambayi Hajiya saboda nima ina da bukatarsu. Shine tace wai muyi hakuri maigidan bashi da halin biyanmu yanzu saboda shidimar sallah da akayi, sai mu jira wani watan a hada mana duka"

Hankalin maigadi ya tashi  tsaye na Dahiru ya tashi sama. Abincin fice masa yayi daga rai ya rasa inda zaisa ransa yaji dadi. Ya dogara da kudin nan sosai. Bai gama fita daga wannan tashin hankalin ba Safwan ya leko yace masa ya shigo falo Mummy na kira.

A sanyaye ya tashi yabi bayansa. Hadadden falo ne da bai taba shiga irinsa ba.

"Daddy yace zaka je ganin gida karshen wata kunyi magana ko"

"Eh"

"Naji shiru baka tafi bane wani abin kake jira ko ka fasa?"

Ji yayi tambayar ma kamar wani rainin hankali.
"Dama albashi..."

Tayi dan murmshi "au ashe fa ban sanar daku ba. Albashi dai sai wani watan yanzu babu kudi. Sannan dubu takwas za'a baka"

Da sauri ya dago kai suka hada ido sai kuma ya sunkuyar da nasa. Dubu takwas din ma kudi ce kuma bai raina ba amma me zaisa su saka masa rai haka. Da dubu takwas anya zai iya rike Mawadda ga karatu? Ko dai ya sake neman wani aikin ne ya hada biyu?

Kallonsa tayi tsaf "kudin yayi kadan ne zaka fasa aikin?"

"A'a Allah Ya amfana. Gobe zan tafi in Allah Ya yarda." Tashi yayi kamar an zare masa laka ya fita ta bishi da dogon tsaki. Kasancewar kanin mijinta ne ya kawo shi yasa bata son shi ko kadan.
*****
Gari na wayewa ya gama shirinsa sai Tariwa. Abin takaici kudin mota ma Bilya ne ya bashi. Ganin Dahirun ya damu ya rinka bashi baki akan yayi hakuri neman halak da wuya. Haka nan ya kama hanya babu ko sisi sai kudin mota.

Iyayensa duk hakuri suka bashi akan rashin albashin. Allah Yaso shi ma baiyi gaggawar fada musu za'a bashi dubu ashirin ba da yaji kunya.

Rana na sanyi ya tafi gidan Mal Fatihu sai dai yayi rashin sa'a ba anan Mawadda take ba yanzu. Kaninta ne ya sanar dashi sannan yace ya jira Baba nason ganin shi.

"Mal Dahiru saukar yaushe? Ya ya Kano ya wurin aikin naka" Baba yace yana fitowa.

 Kamar kullum a kunyace ya duka suka gaisa.

Baba ya soma magana "Mal Dahiru kaji maganar zuwa kotu ko?"

"Eh Baba Allah Ya bamu sa'a"

"To amin, amma na dakatar da kai ne saboda munyi magana jiya da Baffanku. Alal hakika idan na baka Mawadda na cuceka. Sannan mutane da dama basu goyi bayan karar da muka shigar ba. To amma bani da niyar janyewa. Yarinya an rabata da farinciki ya kamata ko yaya a kwatar mata hakkinta ta hanyar ganin an hukunta yaron nan"

"Amma Baba zamu iya daukar lauya ne?"

Bayani yayi masa cewa kotu ta basu lauyan gwamnati da zai waklicesu saboda haka kudaden da zasu biya babu yawa sosai. Yanzu haka nan da kwana biyu za'a fara shari'a. Amma gobe zasu koma Kanon saboda likita da Mawadda za ta gani.

"Sauran magana nasan zakuyi da su Mal Isiyaku. Nagode sosai Allah Ya shi maka albarka. Mawadda tana tare da Sa'ade amma ba sai kaje ba. Ku fara magana a gida"

Gidan ya koma ya sami Inna ta tabbatar masa cewa Baffa yaje sunyi magana da Baba an soke zancen aure.

Ummiyo ce ta fito zata kwashe kwanukan da ta wanke yana ganinta ya hambareta da kafa "munafuka mai bakin reza"

Kifewa tayi a kasa ta soma kuka Inna ta taso "kada ka kashe min 'ya don an hanaka auren wata Mawadda."

Kwalla ce ta taru a idonsa "Inna da kanki kike kiranta wata Mawadda? To wallahi duk ku shirya bata da miji sai ni in sha Allahu. Ba dai ni zan zauna da ita ba."

Baffa da ya shigo lokacin yace "sannu Dahiru wata guda a birni shine zaka nuna mana kaima ka waye ko"

Matsawa yayi kusa dashi "Baffa don Allah kada ka hanani aurenta. Kaddara ce fa ba kai kanta tayi ba. Yanzu idan da akan Ummiyo ya faru zaku ji dadi manemin aurenta ya gujeta"

Inna ta buge masa baki "bakinka ya sari danyen kashi. Aure kuma sai dai idan zaka daurawa kanka"

Dakinsu ya shiga rai a bace baya so iyayensa su zama masu son kansu. Meye laifinta? Ko basu kula da irin dukan da tasha fuskarta duk ta chanja ba. Shikenan sai duk wani jindadinta ya yanke saboda anyi mata fin karfi.

Kwanansa daya ya tattara ya koma. Inna tace ala raka taki gona, yafi ruwa gudu idan yaso. Aure ne dai baza'ayi ba duk nacinsa.

Su Baba ma dai ranar suka tafi. Daga asibiti matan zasu kwana a gidan Barira shi kuma zai nemi wani abokinsa ya kwana wurinsa da safe su hadu a tafi kotu.
****

Haj Mara ta fita hayyacinta cikin kankanin lokaci kai kace ita ce ma BB din. Shi uban gayyar hankalinsa a kwance in ka cire nacin a aura masa Mawadda. 'Yan uwa duk ta nuna musu ba abin damuwa bane saboda tana da shaidu akan sharrin da aka kulla musu. Kowa dai yaja jiki tunda ba wai wani mutumci gareta ba. Daga ita sai 'ya'yanta suke ta fama.

Sun dauko lauya wanda ya cajesu kudi ba kadan ba. Ita duk wannan bai dameta ba ma kamar Alh Sule da ya zare hannunsa a ciki kuma yace bazai katse aikinsa ya dawo ba kasar ba.

Bisa ka'ida ba'a son yiwa lauya karya domin ya sami dabarun kare wanda yake wakilta. Lauyan nasu bai ha'incesu ba yace ta daure taje su sasanta dasu kafin a shiga kotu saboda idan aka kama danta da laifi kulle shi za'ayi sannan ana iya cinsa tara mai tsoka saboda dukan da ya yi mata. Sannan BB da kansa ya nuna masa yana son yarinyar. Ganin da yake masa kamar wani dan kwaya yaji tsoron kada ya bata komai a gaban alkali shiyasa ma yace taje su sasanta.

Tariwa suka tafi suka daki gurbi babu kowa a gidan nasu. A makota ne aka sanar dasu sun tafi Kano. Haka suka kama hanya tayi ta kiran Gambo domin jin inda zata samesu ko ta sani.

Gambo tayi dariyar mugunta don bata mata karyar da tayi mata ba ta fada mata suna asibitin Malam domin kuwa ba jimawa da ta baro su suna jiran Dr Tani. Kwantar da kai Haj Mara tayi Gambo kuwa ta kwatanta mata bangaren da suke.

Ba tare da shan wahala ba ta iso. Daga inda take hangosu ta hango mata biyu da namiji daya sai Mawadda a bakin wata kofa. Da gani tasan iyayenta ne ta shafa jakarta ta jiyo envelop din da ta sako dubu dari da zata basu a kashe maganar. Sai dai ko rabin tafiya batayi ba ta hango Dr Tani ta isa garesu harda dafa kafadar Mawadda. A take hanjin cikin Haj Mara kada ta juya da sauri.

Mota ta koma a gigice ta shiga ta cewa dreban su fita da sauri. Gabadaya kanta ya dau zafi ta kasa tunani.

Su Yaya kuwa rokon Dr. Tani sukayi da ta taimaka ta amince sun bada sunanta a matsayin shaida a kotu.

Dan nazari tayi ita bata son shiga sabgar mutanen to amma tana tausayin rayuwar yarinyar nan.
"Ba komai ai aikinmu ne. Duk lokacin da shari'a ta hado da aikinmu dole mu tsaya mu fadi abinda bincike ya nuna"

Su Ade sai godiya suke mata. Ciki ta shiga ta duba Mawadda tare da hadata da wasu magungunan.

Bayan fitarsu wayar Haj Mara ta shigo mata.

Cikin nishadi da shewa yadda ta saba tace "Bokan turai gani a Kano anjima zanzo gidanki yau nayi zuwan bazata"

Dr. Tani sai murna ko akan maganar auren ne. Qareeba ta kira tace idan batayi wanka ba maza ta shiga tayi amma kafin nan a hadata da Kuku. Umarnin gyaran gida da girki ta basu sannan ta tattara kayanta ta fito.

A gidan Haj Mara tayi la'asar suka zauna hira.

"Hmmm kinga yadda Babawo ya sakani a gaba kan kanwarsa kuwa? Baban ma duk ya damu so yake yayi ya kammala abinda ya kaishi China azo asa rana"

Wani mugun dadi Dr Tani taji ta kara fadada murmushinta "nima haka Qareeba take min, motsi kadan tace BB. Gara asa ranar kurkusa don naga sun fimu doki"

Dariyar shakiyanci suka yi suka tafa. Haj Mara ta lura ba karamin matsuwa aminiyar ta tayi da ayi bikin ba. A ranta tace ta sami makamin dafawa.

"Ya kamata muyi zama na musamman akan shirye-shiryen bikin. Yanzu ma fa in fada miki wai sammaci aka kawo mana har gida gobe zamu kotu"

"Ko... me?"

Haj Mara ta tabe baki "kar fa ki damu ba wani abin arziki bane da ya wuce sharrin 'yan aiki"

Ina zata ki damuwa ana batun kotu.

"Me ya faru?" Wannan karon muryarta ta soma sanyi

"Yarinya ce take min aiki kinsan halinsu da sun sami dama su fara bibiyar maza. Shine fa tayi wani saurayi mai shago ashe irin 'yan duniyan nan ne ina gida aka zo aka ce min anga mai aikina a dakinsa can bayanmu"

Kirji Dr Tani ta dafe "kinji halin yaran nan ko, kana zaman zamanka su janyo maka masifa"

Rangwadar da kai Haj Mara tayi "nima ai ta jaza min. Tana dawowa nayi mata duka kin sanni da zuciya ga raina ya baci. Kuma nace gida zan mayar da ita. Duk yadda ta bani haushi haka naje gidan yaranki da kaina nasa suka hado min kayayyakinsu na sawa da na yara na bata da dubu ashirin nace ta shirya washegari zan mayar da ita."

"Dama zaman me zata yi miki sai taje tayi ciki ta dorawa maigida ko dansa"

"Kamar ko kin sani"

Jikin Dr Tani ya hau rawa danginta da na Daddy kusan babu wanda bata sanarwa Qareeba tayi miji ba don su huta da gori. Mijin ma dan gidan Alh Sule Chanji.

Ganin ta tsorata Haj Mara tayi murmushi "ita ba ciki tayi ba fitar da nayi ne ta lallaba ta shiga dakina zata yi min sata Babawo ya ganta. Cikin fushi ya mammareta da safe muka kaita gida. Wai kawai bayan sallah sai ga sammaci ana zarginsa da yi mata fyade"

"Me???" Kanta taji yana sarawa. Idan makiyanta suka ji zancen nan ai ta banu.

"Ban fada miki don ki tada hankali ba domin ina da shaidu da zasu kareni. Babawo ban taba jin ya yabi wata mace ba balle ince fuska ta gani sai Qareeba. Alfarma daya nake nema kada babansu yaji zancen nan ku hanamu 'ya a gaba"

"Wa? Ni? yaya ma za'ayi na fadawa kowa. Ko shi bazaiji ba" ji tayi kamar ta saki ihu. Damarsu daya ta aurar da Qareeba tana neman subuce musu.

Haj Mara ta sami yadda take so ta cigaba "ai Mawadda da iyayenta sun dauko ruwan dafa kansu. Mistake dina bai wuce na rashin kula ba tun farko kila da na gano suna wani abu da saurayin nata da wuri"

Idanu a waje Dr. Tani tace "Mawadda kika ce?"

"Eh, kinji sunan wani iri ko" ta fada tana satar kallonta

"Patient dina ce indai wadda za'a shiga kotu gobe ne Mawadda Fatihu"

"Laaahhhhhh" Haj Mara ta saki baki ita a dole mamaki take "kinji wani abu kamar a fim"

Ran Dr. Tani ya baci matuka. Tasan kawarta bazata yi mata karya ba musamman ma da bata san ta sansu ba. Yadda ta matsu Qareeba tayi aure shine tana tausayinsu zasu kullawa yaron da yake son 'yarta sharri. Lallai zata shayar dasu mamaki. Kwafa tayi ta riko hannun Haj Mara wadda ta dukar da kai harda hawaye

"Tunda suka zo asibiti da gaske an mata fyade kenan zata dorawa Babawo"

"Babawo ba naki bane ke kadai Marakisiyya. Barni dasu kawai".
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰8

*Batul Mamman*💖



Fuska na nuni da alhini Dr Tani tace "ina Babawon yake yanzu?"

"Yana tare da wani abokinsa yace zai kwana a wurinsa. Nima akwai 'yar kanwar babana gidanta zan wuce yanzu" Haj Mara ta bata amsa muryarta har tana dan rawa kamar zatayi kuka.

"Haba ke kuwa Marakisiyya maimakon kuyi zamanku a nan, kada ki manta fa alaka mai karfi ke shirin shiga tsakaninmu banda ta kawance. Kiyi zamanki a nan. Shima ki kira shi ya taho ya kwana dakin 'yan uwansa. Ai mun zama daya"

Dadi ya baibaye Haj Mara. Batayi zaton abin zai zo da sauki kamar haka ba. Cigaba suka yi da tattauna yadda zasu bullowa su Mawadda a kotu washegari.
*****

Saukarsu kenan daga tasi suka ga gaban kotun cike da jama'a. Wasu 'yan kallo ne kawai wasu kuma 'yan jarida.

Cincirindonsu kadai ya sanyayarwa da Mawadda gwiwa ta daga hannu ta kamo Ade.
"Mu koma gida" tace a hankali wani siririn hawaye yana fita daga idanunta.

"Ki karfafi zuciyarki Mawadda. Idan kika sare tun yanzu to shari'ar nan bata da wani amfani. Ni dama nasan za'a rina tun jiya a rediyo da naji ana zancen fyade da ake yiwa 'yan aiki har aka bada misali da zaman kotun da za'ayi yau akan irin case din" Inji Basira kanwar Yaya.

Suna tsaye daga gefe wasu 'yan sanda biyu suka zo za'ayi musu jagora zuwa cikin kotun. Nan da nan 'yan jarida suka rufar musu domin sai sannan suka gane su waye. Tambayoyi ne ake ta jefa musu su dai suka samu suka shige da kyar fuskar Mawadda lullube da mayafi.

Kotu tayi shiru an gama sauraren shari'ar wasu kamar daga sama suka ji ance.

"Shari'a ta gaba da za'a saurara ita ce tsakanin Mawadda Fatihu da Babawo Sule Chanji inda ake tuhumar Malam Babawo dake zaune a gida mai lamba 190 Gambara cresent Kaduna da laifin yiwa Mawadda duka tare da fyade a ranar 14 ga watan Yuni 2010."

Hantar cikinta ce ta kada sosai da taji ance idan tana kusa ta taso.  Mikewa tayi tana ji a jikinta duk wani mai ido a wurin ita yake kallo. Tamkar ta shige cikin kasa ta rufe kanta haka taji a lokacin. Wurin da aka kebe domin tsayuwar wadanda shari'a ta shafa taje ta tsaya kanta a kasa. Alkali ya bukaci Babawo ya fito shima. A razane ta daga kai su ka hada ido. Zuciyarta ce ta dauki zafi saboda radadin da take ji da ta sake ganinsa ga Haj Mara itama a zaune hankalinsu duk su biyun a kwance.

Bayan shima ya tsaya lauyoyi suka gabatar da kawunansu gaban kotu.

"Sunana Barista Shafa'atu Aminu. Lauyan gwamnati mai kare mai korafi wato Mawadda Fatihu"
Cewar wata mace mai cike da nutsuwa da kamala.

Kujera ce ta danyi kara yayin da Barista Dalhatu Talba ya tashi ya gabatar da kansa a matsayin lauyan wanda ake tuhuma.

Alkali Dawud ya gyada kai sannan yace su fara tambayoyi da kawo shaidunsu.

Barista Shafa'atu ta taso ta matsu gaban zagayen inda Mawadda take tsaye

"Malama Mawadda ko zaki iya sanar da kotu abinda ya faru a ranar shahudu ga watan Yuni tsakaninki da Babawo?"

Shiru tayi gabanta na lugude, wuri yayi tsit ita kadai ake kallo da sauraro. Tunawa tayi da yadda Baba da Iya suka sakata a gaba da magiyar kada ta cuci kanta tayi shiru. Idan taji tsoro taki fadar gaskiya tamkar ta amince gobe Babawo ya sake yiwa wata yarinyar kwatankwacin abinda yayi mata ne.

Wani mugun yawu ta hadiya sannan ta soma bada labari harda yadda ya rinka bibiyarta kafin wannan rana. Da kyar ta iya kai karshen labarin saboda kukan da take yi mai taba zuciya. Mutane da dama a wurin wannan abu ya tabasu sosai. Sai da Alkali ya buga gudumarsa ya samu aka tsagaita da kananun surutan da suka soma tashi.

Barista Shafa'atu ta dan ja hanci alamun itama labari ya tabata sannan ta sake tambayarta game da Haj Mara. Shima duk yadda suka yi haka ta bada labari.

"My lord ina rokon wannan kotu mai adalci kamar yadda muka saurari bayani daga bakin Mawadda ta taimaka tayi mata adalci wurin hukunta Babawo da mahaifiyarsa daidai da laifinsu domin sunyi tarayya wurin cutar da ita" cewar Barista Shafa'atu.

Sai da yayi 'yan rubuce-rubuce sannan ya dubi Barista Dalhatu yace ko yana da tambaya da zai yiwa Mawadda ya amsa da eh.

Tun daga kallon da yake jifanta dashi tasan ba mutumin kirki bane. Wani kallo yake mata kasa-kasa irin na sai na gama dake.

"Kince Babawo ya dauki wani lokaci yana bibiyarki da son ki bashi hadin kai haka ne?"

"Eh"

"To amma me ya hana tun tsahon wannan lokacin ki sanar da mahaifiyarsa domin a yiwa tufkar hanci?"

Da sauri ta dago kai ta kalli Alkalin shi kuma yace ta amsa tambayar.

"Saboda....uhmmm dama saboda ina tsoron kada Hajiya ta dakeni ne"

"Uhmm Mawadda kenan, kina jin akwai uwar da zata daki wadda ta kawo karar danta yana neman keta mata haddi. A tunanina zata yi saurin kawo karshen matsalar ne ko don kada a wayi gari a rana irin ta yau"

Haj Mara daga inda take zaune tayi wani murmushin jindadi gamin Mawadda ta kasa bada amsa.

"Don baka santa bane na rantse duka na take yi ko yaya nayi laifi. Kuma tana sonsa shiyasa naji tsoron kada na fada tace karya nake"

"Ke kuma gaki jaruma zaki iya kwatar kanki ko ki jure duk wani hari da zai kawo miki"

Barista Shafa'atu ta mike da hanzari "objection my lord, Barista yana amfani da kalmoni domin cusa mata ra'ayin da ba nata ba"

"Objection sustained! Barista Dalhatu ka gyara kalamanka ko ka chanja tambayar" Alkali ya fada masa.

Dan sunkuyar da kai yayi "Nagode my lord. Idan kotu ta bani dama ina son yiwa wanda ake tuhuma tambayoyi"

Alkali ya bashi dama tare da umartar Mawadda ta koma ta zauna.

"Babawo Sule Chanji ko zamu iya jin takaitaccen tarihinka?" Ita ce tambayar da ya jefa masa.

Bai ko bude baki ba Barista Shafa'atu ta sake cewa objection wato bata amince da tambayar ba.

Baristar Dalhatu yayi saurin cewa "wannan tambayar tana da mahimmanci domin sanin wane ne Babawo kafin a tuhume shi da laifi irin wannan"

Alkali yace "objection over ruled, Barista ka cigaba da tambayarka"

Sai da ya bi Mawadda da kallo sannan ya fara basu labarin rayuwarsa da karatunsa da kuma dawowarsa wata hudu da suka wuce. Ya cigaba da sanar dasu cewa shi mutum ne mai mugun kyankyami  ko kofi mai aiki ta wanke baya iya amfani dashi sai ya sake wankewa. Shi a ka'idarsa ma babu wani abu da yake hada shi da masu aiki koda maigadi ne kuwa.

Yana gama jawabinsa Barista Dalhatu yace "My lord daga bayanan Babawo zamu iya gane cewa abu ne mai matukar wahala ace ya yiwa mai aikin gidansu fyade. Muna da shaidu da dama da zasu tabbatar mana da halayyar Babawo. Sannan kuma ita kanta Mawadda maganarta taci karo da korafinta. Ta nuna cewa ya dade yana binta kuma tasan manufarsa amma ta kasa sanar da kowa. Da wadannan dalilai nake rokon kotu da ta wanke Babawo domin kazafi ne kawai Mawadda tayi masa don cimma wata manufa tata"

Tasowa Barista Shafa'atu tayi bayan an bata izinin yiwa Babawo tambaya.

Duk motsinsa dazu tana kula da yadda yake bin Mawadda da kallo.

"Babawo kace kai mutum ne mai kyankyami sai dai ina so ka tuna girman rantsuwar da kayi a kotu farkon tsayuwarka a nan. Ka dubi wannan yarinyar da kyau zaka iya sake rantsuwa baka taba binta ka roki ta baka hadin kai ba?"

Kallon Mawadda yayi yana kokarin yi mata murmushi yaji ance

"Objection my lord, Babawo ya riga ya tabbatarwa kotu tsakaninsa da masu aikin gidansu. Idan an bani dama zan gabatar da shaidata ta farko"

Korafin Barista Dalhatu ya karbo Alkali Dawud ya umarci Barista Shafa'atu da ta chanja tambayarta. Komawa tayi ta zauna tana jiran shaidar da zasu kawo domin tasan me ya kamata tayi.

Mal Ramadan maigadi ne ya gurfana gaban kotu. Barista Dalhatu yayi masa tambaya ya kuma tabbatar musu da cewa Babawo baya shiga sabgarsu. Kai hatta mota idan ya goge masa in zai fita sai yasa hankici yake budeta wai akwai kwayoyin cuta a hannun maigadin. Aka tambayeshi game da Mawadda ya kallota da dan murmushin tausayawa a fuskarsa.

"Yarinya ce mai nutsuwa don gidan basu taba mai aiki irinta ba. Bata da hayaniya ko kadan shiyasa Na'ibi mai kiyos yake matukar sonta"

Maganganu ne suka fara tashi da kuma kallon kallo daga Mawadda zuwa Babawo da Maigadi.

Shi kuwa Barista Dalhatu dama sun shiryo abinsu ne. Abaibai suka dunkulewa Mal Ramadan bayanin shaidar da zai kawo kotu ana neman wanda yayi mata fyade ne. Tausayinta yaji amma baiyi zaton nema ake a dorawa wanda bashi da hakki laifi ba. Duk wata dabarar boye gaskiya ita Barista yayi amfani da ita ya ha'inci maigadin.

"Ko za ka iya sanar da kotu tsahon yaushe kake aiki a gidan Alh Sule." Ya yi masa tambayar yana murmushi don abu ya fara tafiya yadda yake so.

"Shekara biyar da kusan rabi"

"A iya zamanka ka taba ganin Babawo wato BB yana kula wata mai aiki mace fiye da alakar ubangida da hadiminsa?"

"Oga BB bashi da sakin fuska kuma gashi baya boye kyamarmu da yake yi"

Hankalin su Ade ya soma tashi da jin amsoshin nan suna ganin kamar ma an gama shari'ar sun sha kasa.

"Naji kayi maganar wani mai kiyos muna bukatar karin haske game da mu'amalarsa da Mawadda"

"Ehhhh to, Na'ibi ya jima yana sonta don yana yawan bani sako haka su kayan kwadayi kamar biskit yace na mika mata....to amm..."

Bai bashi damar karasawa ba yayi wata shu'umar dariya "My lord nasan zuwa yanzu kowa ya fara fahimtar inda shari'ar nan ta dosa. Mawadda bata da alaka da Babawo amma akwai wani abu tsakaninta da Na'ibi mai kiyos. Anya babu lauje cikin nadi a zaman nan kuwa? Anya ba wani ne yasa Mawadda kama sunan dan ubangidanta ba domin su samu su tatsi wani abu a jikin mutane masu mutumci kamar su Haj Mara ba"

Ran Barista Shafa'atu ya soma baci ga shari'a tana neman komawa hannun abokan hamayya sannan ita ko kadan Mawadda bata ambaci sunan wani mai kiyos ba. Kanta ya kulle ta rasa me zatayi. Tashi tayi ta nuna bata gamsu da furucin Barista Dalhatu ba domin yana neman karkata akalar shari'ar kan wani daban bayan kuma har yanzu ba'a wanke Babawo ba.

Alkali ya karbi korafinta sannan aka bukaci Haj Mara ta taso. Hankali kwance taje ta tsaya.

Ajiyar zuciya Barista Shafa'atu tayi tana kallonta. Shigar mutumci tayi harda hijab fuskarta fayau kalar tausayi.

"Haj Mara a ranar shahudu ga watan Yuni kin koma gida kin tarar da danki ya yiwa mai aikinku fyade bayan mugun duka da yayi mata. Ke kika taimakata ma tayi wanka sannan tsoron tonon asiri duk da raunukan dake jikinta kika ki kaita asibiti. Dadin dadawa kika dauketa kika mayar gida batare da yiwa iyayenta bayani ba"

"As....as...sal...salam...as..."sai kawai kuka ya kufce mata mai sauti da tsuma zuciya. Ta kwashi wurin minti biyu tana kuka tana goge hawaye.
"Ku gafarceni, assalam alaikum. Ni dai sunana Marakisiyya kuma nice mahaifiyar Babawo. Nayi mamaki matuka ranar da sammacin kotun nan ya iso garemu har gani na rinka yi ko anyi kuskure ne."

Ta kalli Mawadda idanunta jazur "Mawadda me nayi miki a duniya zakiyi min wannan sakayyar? Tabbas nasan ni mutum ce mai zafi bazan boye ba. Amma hakan bai hanani rungumar duk wata maiaiki ba saboda nasan da na kowa ne. Me muka yi miki Mawadda har kika rasa wanda zaki kai kotu sai ni? Ni bazan tonawa kaina asirin zaman da mukayi ba balle na kwashe ladana da baki. Idan kotu ta kamamu da laifi ayi mana duk hukuncin da ya dace." Ta kare a raunane.

Mutane sai tausayinta suke ji. Mace kamar wannan wadda ko ba'a fada ba zaka san cewa arziki ya zauna mata take yiwa yarinya karama kuka.

Da kyar aka iya rarrashinta ta bada nata jawabin kamar haka.
"Banyi niyar tozartaki ba Mawadda amma kin nuna min da gaske ne da ake cewa kayiwa mutum inuwa shi kuma ya kaika rana. Ya maigirma mai shari'a yarinyar nan satar da take min bazata kirgu ba ina kawar da kai. Da zata tafi iyayenta shaida ne ba karamin tanadi nayi mata ba. Yaron da ake magana a kai wato Na'ibi, kiyos gareshi kusa damu. Daga aike a hankali na fuskanci ko ban nema ba sai tayi kwalliya tace min akwai aike? Idan nace babu sai tace zata dan fita. Ban kawo komai a rai ba nake kyaleta. Sai kawai wata rana aka kawo min zancen an ganta a dakinsa. Nayi kuka nagode Allah. Sakacina shine rashin mayar da hankali da na fuskanci ta fiye yawo amma banyi mata zaton yawon banza ba. Wannan abin shine ya daga min hankali nace gara ta koma gida kada a haifi da mara ido. Tayi kukan tayi magiya duk a banza don bazan boye muku ba ranar har dukanta nayi. Na hukuntata kamar yadda zanyiwa 'yar cikina. Ina fita ne ta shigar min daki sata Babawo ya kamata shima zuciya ta kwashe shi ya mareta. Washegari na maidata gida bamu sake jin komai ba sai kararmu da aka kawo"

Mawadda kuka iyayenta kuka. Hatta Baba hawaye yake yi sosai.

Alkali Dawud yace idan suna da shaidar da zasu kawo ana bukata. Waige waige suka soma yi ba Dr Tani ba dalilinta. Wani mai kaya irin na masinja ne ya fadi uzurinta cewa ta taho aka kirata patient din da ta yiwa aiki tana zubar da jini. Wannan dalilin ya sanya aka dage sauraron karar sai bayan kwana goma sha biyu.

A sanyaye suka tashi kafin su fita Barista Shafa'atu ta hau Mawadda da fadan me yasa bata yi mata zancen Na'ibi ba. Su Iya suka tsaya sauraronta tana fada mata cewa da gaske ne ya nuna yana sonta amma da wuri ta sanar dashi aure zata yi. Kuma duk wata kyauta da yake bawa Ramadan maigadi ko tsinke bata taba karba ba. Game da zuwa kiyos dinsa tun da ta gane yana sonta ta gwammace ta tsallaka titi idan an aiketa. Dama yawanci siyan katin waya ne yake kaita. Kafin faruwar wannan abu gareta kuwa yafi wata bata ganinsa. Kiyos din ma ya koma shagon renting din finafinan hausa shi kuma bata san inda yayi ba.

"Wato sun nemo wanda baya nan bare ya kare kansa shine za'a dora masa laifin da baiji ba bai gani ba" Barista Shafa'atu ta fada tana rubutu.

Mawadda ta kalleta "wallahi babu karya a duk abinda na fada miki"

Murmushi tayi "na sani Mawadda kuma in sha Allah sai an kulle BB an bi miki hakkinki"

"Idan ba mu muka ci shari'ar ba ni za'a kulle kenan?" Yadda tayi maganar da raunin murya yasa Baba fita hankalinsa duk a tashe yake ya rasa me zaiyi ya samarwa 'yarsa farincikin rayuwa.

Fitarsa waje ke da wuya yaji wasu suna tattaunawa suna aibata 'yan kauye a matsayin kwadayayyu wadanda basa iya rike talaucinsu.

"Tsabagen son zuciya ke dibarsu su kwaso rida-ridan 'yan mata a kawosu birni aiki."

Wani yace "sai ta kwabe musu ayi ta dauki ba dadi"

"Idan basuyi haka ba ai basu amsa sunansu na 'yan kauye ba. Da anyi magana sai ace an turo yarinya tara kudin da za'a yi mata kayan daki."

Zuciya ta kwaso Mal Fatihu, ransa ya kai makurar baci ya karasa gaban wadannan mazan cikin daga murya wanda ya janyowa kansa taruwar 'yan jarida yace

 "Shi dan kauye ko talaka ba mutum bane? Meyasa idan dan birni ya nemi kudi ake jinjina masa idan dan kauye ya nema yake zama kwadayayye? Masu kudin da mutanen birnin me suke yi mana domin inganta rayuwa? Ko nan da Jigawa ban taba zuwa ba amma ina da tabbacin ko ina a fadin duniyar nan akwai masu kudi kuma akwai masu yi musu aiki talakawa kauyawa irinmu. Haka Allah Yaso kuma haka Ya tsara duniyar arzikin wani yana karkashin wani. Idan munyi bara kuce zukatanmu sun mutu idan mun nemi halak da guminmu ace mun kasa rike talauci. Wannan wane irin son kai ne da rashin adalci? Mune 'yan dako mune leburori mune masu kaskantacciyar sana'a amma duk ba'a gani. Talauci yasa yaro sa'an jikanka zai tsaya ka bude masa kofa ya shiga mota yana binka da harara. Mu maza mun nema a waje matanmu kuma su nema a cikin gidajen aure. Kuna da mata maaikata, suna bukatar masu tayasu raino, gyaran gida ko girki. Idan ba kaddara ta rabo mace da gidan mijinta ba ai dai bakwayi tsammanin matan aurenmu ne zasu baro nasu kananan yaran a kauye su fito aikatau ba. Dole yaran namu da suka kawo karfi zamu turo. Babu mai zurfafa tunani yaga cewa banda abinci muma fa muna rashin lafiya kamar 'yan birni waye zai bamu kudin asibiti, lalura da dama ta kudi tana taso mana. Kai da kake cewa muna turasu neman kudin kayan daki waye yace maka don muna kauye shikenan idan mun tashi sai mu aurar da 'ya mu kaita da tabarma? Haka al'adar bahaushe take waye yaki ya sami wani abu da zai taimaka masa yaji dadin rayuwarsa? Komai namu sai ya zama laifi saboda bamu da galihu. Mu yini muna muku aikin karfi ku sallamemu da dubu uku karshen wata har kuna ganin ba karamin karamci kuka yi mana ba. Yaranmu suna kauye da kokarinsu talauci yasa basa iya wuce sakandire idan sunyi sa'ar zana jarabawa. Ni Fatihu bazan boye ba kuma bazan fasa fada ba mu daku muna bukatar juna ne domin taimakekeniya ta rayuwa. A cikinmu da cikin kowacce sana'a akwai nagari akwai bata gari. 'Yata Mawadda da duk sauran masu zuwa aikatau ba kiyayya ko rashin sanin ciwon kai yasa muke turo muku su ba. Yanayi ne na kuncin rayuwa....Wallahil Azim bazan taba yafewa wannan yaro ba, babu wata riba da zamu tsinta don mun batawa dan wasu suna"

Kafin ya karashe maganar kuka ma yake yi sosai hawaye har gaban malun-malun dinsa ya jike. Masu daukar rahoto da 'yan kallo da dama sun zubar da kwalla. Haka zalika iyalansa da suke tsaye a bakin kofar kotun.

*****

Dahiru zaune gaban yayansa Bilya yana ta juya cokali cikin abinci.

"Kayi hakuri kada ka batawa su Baffa rai akan mace Dahiru komai mai wucewa ne"

"Na sani Yayanmu amma bazan taba iya cire Mawadda daga zuciyata ba. Yau aka fara shiga kotun ya dace ace ina tare dasu amma kaga banma san wace kotu bace"

Bilya yana tausayin kaninsa sosai amma Inna tayi masa gargadi mai karfi akan ya tsawatar masa da batun auren don bazata taba yarda ba duk runtsi.

Kasa cin abincin Dahiru yayi ya tashi ya fita wurin wani mai shayi a layin da suka saba zama. Ana ta hira ya zurfafa a tunani yaji muryar Baba a lokacin da yake maidawa wasu martani. Mai kawo rahoton yace hakika wannan mutumi ya nusar da mutane da dama abinda suka manta game da na kasa dasu a kowane matakin rayuwa. Komai talauci, rashin ilimi da wayewa mutum, mutum ne abin darajawa saboda haka zasu cigaba da bibiyar wannan shari'a da akeyi a kotu mai lamba biyar Court road domin jin yadda zata kaya.

Har kuka Dahiru yayi yana jin wannan labarai. Tashi yayi ya bar wurin da surutun jama'a ya ishe shi akan kukan me yake yi.

Washegari da sassafe yaje gidan aikinsa yayi shara da gyaran filawa ko sallama baiyi da kowa ba ya kama hanyar tasha. Yayi babbar sa'a su Mal Fatihu tun jiya suka koma Tariwa. Kai tsaye gidansa ya wuce sai ya tuna bata gidan ya kama hanyar gidan kakaninta.

Lokacin shadaya na safe yana tsaye yana jiran yaron da ya tura sai ga Baffa shima yazo. Da mamaki Baffa yace "Dahiru saukar yaushe?"

Gaishe shi yayi yaga bai amsa ba yace "isowata kenan"

"Shine ka fara zuwa nan? Ashe duk maganar da muke yi maka bayan kunnenka take bi. To billahillazi kaji na rantse ban lamunce maka auren yarinyar nan ba ka nemi wata. Garin nan kwana akayi ana zancen shigarsu kotu jiya shine nazo jajanta masa naje gidansa ance yana nan ashe rabon na ganka ne."

Kamar yayi kuka ya dan duka "Baffa don Allah kayi hakuri yanzu ne take bukata ta bai kamata na juya...."

"Dahiru kada ka bari na sauke maka bacin raina. Ka wuce muje jajen ma na fasa tunda shima ya kasa gane zuru da kawaici idan kazo maimakon yace ka dena zuwa aure tsakaninku bazai yiwu ba"

Duk yadda Dahiru ke rokon Baffansa haka ya saka shi a gaba suka tafi.

Mal Fatihu da ya dade a tsaye saboda yaron na cewa Dahiru ne ya kalli Mawadda da tayi shiru tana jiran taji ko za'a bata umarnin fita yace tayi hakuri a karo na karshe ta cire Dahiru daga ranta. Shima zai fita ya bashi baki ya bi maganar iyayensa. Kafin ya fito ne kunnuwansu suka jiye masa maganganun Mal Isiyaku. Wani irin zafi yaji a saitin zuciyarsa kamar ana daddaureta ya dafe kirjin ya koma ciki yana dafa bango.
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK..*💰10

*Batul Mamman*💖



Su Inna da sauri suka karasa inda Baba yake kwance ko motsi baya yi tamkar babu rai a jikinsa.

Mutane suka yi dafifi a wurin ko iskar kirki babu. Mawadda tana durkushe tana kuka ta soma kokarin daga kansa wani dan sanda  yace ta kyale shi kada wanda ya motsa shi. Waya ya shiga yi suka ji yana kwatanta inda suke da abinda ya faru.

Su Iya duk sun zagaye shi suna kuka Mawadda ta hango Haj Mara tana washe baki wasu mutane suna yi mata barka da arziki tana fada musu ai kudin tarar da alkali ya nema daga garesu ma sun yafe tunda gaskiya ta fito.

Yadda zuciyarta ke suya a lokacin duk wani tsoro ya fice mata. Tashi tayi da saurinta kada ta shige mota su tafi ta kutsa kai ta cikin mutanen ido a rufe ta samu ta damko hannunta.

"Ke meye haka?" Ta fada tana son kwacewa sai dai kusan janta Mawadda take yi tana son turjewa ta nuna hali amma tana tsoron kada ta bada kanta a gaban mutane.

Ba ita ta saketa ba sai da suka je inda Baba yake kwance Yaya tana masa firfita da mayafinta. Idanu jazur ta dubi Haj Mara cikin karaji tace

"Kinga hawayen da yake zuba daga idanun iyayena???"

Haj Mara ta tsorata da yadda Mawadda take dadinta daya suna fita ta danna BB a motar Dr Tani  tace zata biyo bayansu idan ta gana da iyayen Mawadda. Ba komai yasa tayi hakan ba sai tsoron kada ya tona musu asiri a bainar jama'a.

Bangazar kirjinta Mawadda tayi ta sake maimaita tambayar. Mutane suka soma darewa ana mata kallon mara hankali. 'Yan sandan da suke wurin suka fara matsowa ta dago idanu wanda kallo daya zaka yi mata idan ba ka jajirce ba kaji firgici ya ziyarceka.

Sassauta murya tayi tace "Na gani Mawadda, kinga ki kwantar da hankalinki komai zai wuce kinji ko"

Iyayenta ta rinka nuna mata  daya bayan daya hawaye yana bin kumatunta.

"Wannan hawayen nasu nake so ya zauna a ranki har abada Hajiya. Idan Babana ya mutu ne to shima ki samu wuri a zuciyarki ki ajiye saboda gaba"

Daga haka ta koma ta zauna a gefen Baba. Haj Mara ta kasa barin wurin sai mutane ne suke matsawa daga gareta. 'Yar wannan magana ta Mawadda tayi mugun tasiri a zuciyarta har tana ganin kamar har ta mutu fuskokin mutanen bazasu taba gogewa daga kwakwalwarta ba. 'Yan bani na iya tuni suka fara hasashen ko dai akwai wata a kasa ne.

Ba jimawa sai ga karar ambulance aka ajiyeta kusa da Baba. Cikin nutsuwa da kulawa suka dora shi akan gado akace mutum daya cikinsu ta shiga sauran su biyosu Aminu Kano bangaren emergency.

A gurguje suka fita suka tari adaidaita sahu yayin da Yaya ta bi Baba a cikin motar.
Lokacin da suka isa tana wajen reception tana bada bayanai kamar sunansa da shekaru. Shi kuma tuni likitoci sun amshe shi ana bashi taimakon gaggawa.

Duk wani abu da zasu yi na ceton ransa sunyi. Kusan awa biyu sannan aka tura shi dakin marasa lafiya idanu a rufe. Su Inna zuciya ta tsinke ganinsa a haka. Sai dai wata likita tace su kwantar da hankulansu in Allah Ya yarda zai tashi. Jininsa ne ya hau sosai ga dukkan alamu yana tattare da damuwar da tayi masa yawa.

Mawadda  na jin haka taji ta tsani kanta sosai tana ganin ita ce sila. Mahaifinsu talaka ne amma mutumin kwarai wanda rayuwar kauye bata hana shi zama uba mai barkwanci da iyalinsa ba.

A gefen gadon nasa duk suka taru sai daga baya suka fara tafiya yin sallah. Ya rage Yaya kawai a wurin Mawadda ta fita siyo musu ruwan sha ya bude ido a hankali.

Yaya tayi maza zata fita kiran likita kamar yadda suka bada umarni yace ta dawo ta gyara masa kwanciya yaji kamar ya karkace.

Tana ta ce masa sannu ta shiga kici-kicin daga shi ta kasa.

"Malam ai ka sakar min nauyi dan yunkara mana"

Gwadawa yayi yaji ya kasa sai ga Ade ta shigo. Yaya tace tazo ta tayata. Dan turus tayi tana kallonsa Yaya tayi murmushi

 "ni dai zo ki kama min jikin nasa yayi nauyi."

Tsohuwar kunya ce ta taso tazo ta kama sai dai duka sun kasa.

"Yaya Fatihu kaima baka motsawa"

Yaya tace "nima haka nace masa kafin ki shigo"

"Ku sakeni ragwaye" yace sannan ya dan yunkura amma kansa ne kawai ya motsa. Sake yunkurin yayi yaji da gaske bazai iya ba. Zuciyarsa ta buga da karfi don ya tsorata ya daure yace "Haule jeki ki kira min likita na kasa motsa ko ina banda wuyana"

Bai karasa ba ta fita a guje yayin da Ade ta soma kuka tazo tana cewa ya daure ya tashi. Likitan ya zo sai ga Iya da Inna tare da Mawadda. Gefe suka matsa ya dan dudduba shi sannan ya juyo yana fuskantarsu.

"Tun dazu da aka kawo shi munyi zargin haka amma bamu da tabbas sai yanzu da ya tashi. Kayi hakuri Malam ka sami shanyewar barin jiki"

"Innalliahi wa inna ilaihi raji'un" suka shiga fada wasu na salati. Kan kace kwabo sai kuka domin wannan abu ya dokesu ba kadan ba.

Likitan ya rinka basu hakuri sannan yace idan har zasu rinka kawo shi gashi ko bayan sallama to hakika bangaren hagunsa zai sami lafiya ko bai dawo daidai ba zaiji sauki.

Fita yayi ya barsu da jimami da kuka. Innar Fatihu ta kira kaninsa guda namiji da yake aikin dreba. Baya gari duk abinda akeyi a lokacin sunyi tafiya da ubangidansa tana kuka ta fada masa. Hankalinsa ya tashi ya kira mijin kanwarsu daya da yake da waya yace aje gidansu a sanar da Malam.

Kamar an tsikari Ade ta soma juye juye tana cewa ina 'yarinyar nan ne da ta farga Mawadda bata wurin. Kowa kuma sai lokacin ya lura Baba ya daure yace ta fita ta nemota.

Waje tayi kaf wurin reception din bata nan. Kofar shigowar ta kalla sannan ta fita, dubawar farko ta hangota tayi hanyar gate.

Kwala mata kira tayi iyakar karfinta amma Mawadda bata tsaya ba. Ganin tsayuwa bazata kai mata ba ta bita da sauri. Shima hakan baiyi ba don tafiya kawai take kai tsaya dole Ade tasa gudu tana kiranta. Tana zuwa gate Mawadda tayi gaba ta hau titi bata kallon gabanta. Kusan ma bata san me take yi ba da ya wuce kukan zuci na jin lalurar da ta kama mahaifinta.

Motoci ne suka taho suna ta horn da taka burki ganinta a tsakar titi. Wata mota ta taho da gudu mutumin sai taka burki yake abu yaki yi. Ade hannuwa ta dora a kanta kawai ta rufe ido tana kuka don ta saddakar sai an bigeta kawai.

Wani mugun burki mai motar ya sake ja tayoyin suka yi wata kara ya karkata motar ya daki jakin babangida. A fusace ya fito jibgege mutum yasha babbar riga yana zuwa ya dauketa da mari har biyu a inda tayi mutuwar tsaye.

"Baki da hankali ne zaki zo tsakiyar titi ki nemi jaza min masifa?"

Mutanen da suke wurin kowa ya tsorata aka soma zaginta wasu na cewa mahaukaciya ce kila. Kasa cewa komai tayi sai kalle kalle take yi kamar wadda ta tashi daga bacci. Ade ta taho ta kama hannunta tana bawa mutumin hakuri.

Yadda ya gansu cikin tsumma yasan babu abinda zai tsinta a tare dasu idan ma yaki hakura.

"Tunda babu abinda ya faru kuje kawai Allah Ya kiyaye gaba"

Tana ta yi masa godiya ta kama hannunta suka koma ciki. Kafin su karasa ta tsaya daidai jikin wata bishiya ta riko hannayen Mawadda.

"Kashe kanki zakiyi ki tona min asiri ko kuwa so kike muma mu mutu?"

Girgiza kai tayi tana hawaye "kinga yadda Baba ya koma saboda ni"

"Kaddara ce, idan kika kashe kanki ni dashi bazamj taba yafe miki ba kamar yadda Allah bazai yafe miki ba. Kiyi hakuri mu barwa Allah komai muna nan dake watarana mutanen nan sai sun dandani fiye da abinda suka yi mana"

Su biyun duk kuka suke suka koma ciki. Jikin Baba Mawadda ta fada tana kuka yana rarrashinta.
******

Karfe uku saura a kotun ta yiwa Dahiru sai dai ya tarar an gama shari'ar. Da tambaya wani ya sanar dashi yadda aka kare ransa ya baci ga tashin hankalin ance masa Baba ya fadi ba'a sani ba ko yana da rai ko babu.

Rashin sanin ina zai nufa daga nan ya koma gida ranar haka ya wuni ko makaranta bai samu yaje ba yana jira zuwa yamma ya kira Baffa a bawa Danlami suyi magana.

*****

*Bayan sati uku*

A daddafe Mal Fatihu yayi kwana tara a asibitin aka sallamosu.  Kudin kwanciya da na magunguna yana neman fin karfinsu dole suka nemi sallama da gaggawa. Cikin ikon Allah barin hagunsa ya mike kamar yadda likitoci suka sanar dasu sai dai nauyin bangaren daman da kuma rashin sabo yasa har yanzu sai ya dafa wani yake iya tafiyar kirki. Bangaren daman gabadaya ba kwari hannu da kafa duk sun shanye don ma an kaishi asibiti da wurwuri.

Kowa a gidan yanzu hidimarsa yake yi. Hatta manyan 'ya'yan suna zuwa kusan kullum. Ya kasa cire damuwa a ransa ganin Mawadda bata da aiki sai kuka. Makota baifi mutum uku bane maza da mata suka zo dubiya. Zantuka kawai ke yawo a gari cewa Mawadda ta gama yawonta ne a Kaduna tsoron kada asirinta ya tonu tunda biki ya gabato suka kirkiri wannan abu ita da iyayenta bayan ta dawo da cikin da suka zubar a asibitin Bebeji.  Wannan magana ita tafi kowacce karbuwa a garin shiyasa iyalin gidan suka zama abin kyama abin Allah wadai. Wani karin bakincikin shine da ake cewa sun so cin kudin mutanen da tayi aiki a gidansu ne amma bukata bata biya ba kunya da dogon buri irin na Mal Fatihu da kuma hakkin yaron da suka yiwa sharri ne suka kwantar dashi.

Kukan da iyalin gidan suka yi na zahiri da na zuci bazai kwatantu ba.
*****

"Ki dena kuka Jamila kina kara karyar min da zuciya"

Goyonta ta gyara sannan ta goge hawayen da ya zubo mata "Allah kadai Yasan halin da Baba zai shiga idan naje musu da maganar sakin nan"

Katuwar jakar bagco din da ta hado kayanta ya cicciba ya dora a kansa sannan ya duka ya dauki wata ghana mustgo suka fito daga dakin.

Mahaifiyarsa tana tsaye tana jiransu tace "gayyar na gayyaro dangin yawo a tafi inda aka fi wayo. Halisa kuma kina yayeta zanzo da kaina na karbeta kafin a koya mata mugun hali"

Jamila bata iya cewa komai ba ta fita mijinta na biye da ita da kaya niki-niki. Da kyar da sudin goshi ya lallaba mamansa ta barshi ya kai mata kayanta don tace ko kofar gidan ta sake zuwa Ja'e zata tsinewa. Yanzu ma da batun tsinuwar tasa ya saki matarsa duk kuwa da son da yake mata.

Cikin rana mai zafi suka isa gidan. Da kuka ta shiga gida su Yaya suka bita da kallo. Goyon ta kwance ta mikawa Mawadda wadda ta tashi tun shigowarta sannan tace tare da Ja'e suke.

Yana shigowa da kaya hankalin iyayen ya tashi sun san kwanan zancen. Hakuri yayi ta bawa su Baba da alkawarin yana komawa wurin aikin kafintansa a Dutse zai nemi gida ko daki daya ne ya dawo ya dauketa.

Gani yayi Mal.Fatihu yana hawaye shima ya fara yana dada bashi hakuri "don Allah kada ku bari tayi saurayi wallahi zan dawo komai dadewa. Ni na mayar da ita ma tun yanzu a gabanku"

Zuciyar Mawadda kamar ta fashe. Banda abubuwa da suke ta faruwa kuma harda kashewa yayarta aure.

Gashi dai ita ce aka cuta kuma itan dai ake kyama. Danginta sune suke ganin bakinciki da bacin rai duk akan abinda BB yayi mata. Jamila ta rungume suka shiga daki suna kuka ba mai rarrashin wata.

Bayan tafiyar Ja'e Baba ya kirasu yana musu nasiha akan ko bayan ransa su rike juna da zuciya daya kada suyi wasa da zumunci.

"Wannan abu da ya faru jarabawa ce ta imaninmu. Kuyi hakuri wata rana ko ina nan ko bana nan zaku ga farincikin rayuwa. Sakayya akan wadannan mutane ko a duniya ko lahira sai sun koka"

Zantukan Baba suka sake taba Mawadda tana cikin kuka kawai ta fadi a wurin. Hakan ya sake ruda gidan ba babba ba yaro kowa ido yayi ja suna zubar da hawaye. A haka Iya, Ade da Innar Fatihu suka samesu. Basu dade ba 'yan uwan Baba suka zo kowa dai basu baki yake akan hakuri da wannan iftila'i da ya fada musu.
*****

Zaune take tana danna remote tana chanja tasha wayarta tayi kara a karo na barkatai. Tsaki taja sannan ta dauka a wulakance.

"Likita bokan Turai"

Ajiyar zuciya Dr Tani tayi "haba Marakisiyya shiru-shiru sati uku kusan kullum sai nayi miki waya ba'a dauka. Qareeba ma tace Babawo baya kira baya amsa nata kiran. Me yake faruwa ne?" Ta fada cike da damuwa da fargabar ko sun fasa ne. Qareeba har wata rama ta soma saboda masoyi Man baya kiranta. Yanzu ma tana kusa da Mummynta ita ke kara takura mata akan kiran.

Haj Mara ta yamutsa fuska kafin kuma ta gyara murya ta soma tari.

"'Yar uwa ciwo ya sani gaba sai dai a kwantar a tayar. Daga  ni har Babawo ina muka ga karfin waya. Shi yake wuni dani tare da 'yan uwansa"

Hankalin Dr Tani in yayi dubu fa ya tashi "me yasa baki sa sun fada min ba? Ina Kano ina Kaduna da tuni nazo."

Ita fa Haj Mara gaskiya Qareeba ce bata so ko kadan. Yanayin maganarta na shagwaba da kuma shirme yarinyar ta fice mata a rai. Daurewa tayi tace mata ba sai tazo ba yau taji sauki sosai.

"Allah Ya kara sauki. Uhmm nace ba, wai yaushe su Alhaji zasu zo ayi maganar auren. Nasa Daddy ya sanar da 'yan uwansu da abokai don kada suji date bazata gara kowa ya zama cikin shiri."

Dariya Haj Mara tayi ta ganin wautar Dr Tani. Ita fa ba don ta santa ba sarai idan ance mata ta shiga aji tayi karatu na aikin lafiya sai ta karyata. Ba tantama 'ya'yanta  tsotso halinta suka yi a jikinta.

"Kada ki damu yana dawowa tare ma zamu zo yayi miki godiya sannan ayi magana sosai. Ya tsaya a Lagos ne zai jira kayansa su iso"

Dadi kamar ya kashe Dr Tani tana ta godiya kamar ta ari baki. Ita kuma Haj Mara sai lokacin aka tayar mata da bacin ranta. Alhaji yanzu ya fita harkarta ba waya ba text. Idan ta kira kullum cikin aiki yake baya sauraronta. Abinda bata sani ba shine sati biyu da suka wuce da ya dawo daga China ya wuce Birnin Kebbi inda aka daura aurensa da wata bazawara sakin wawa suna can Lagos ana cin amarci.
*****

Kwanaki na ta tafiya Dahiru ya fuskanci karatunsa sosai sannan yana kokari bangaren aikinsa don kada ya sami matsala a kore shi ya rasa abin tallafin kansa.

Ranar da akayi albashi yana jiran har na wancan watan amma dubu shabiyu Dr Tani ta bashi. Farinciki ya cika shi yana karba ya kirga ya ga babu dubu hudu a kai.

Dago kai yayi zai mata magana sai ya fasa. Itama daure fuska tayi

"Naji baka ce komai ba. Dubu hudu da ya hau kai nice na cire kudin sabulu. Na kula ashe kullum kayi mana wanki kana tsoma naka kayan a sauran ruwan kumfar. To wannan ba komai bane face ha'inci tunda ba haka mukayi da kai ba. Idan kana son wanki a gidan nan sai ka rinka siyo sabulunka da ruwa. Sannan igiyata ba wurin da zamu rinka hada shanya da mai wanki bane ina fata ka fahimta"

"Sosai" kawai yace ya juya yana jin wani irin bakinciki. Shi kadai yasan yadda yake maneji a makaranta amma wannan bai dameshi ba kamar halin karanta irin na masu gidan nan.

Dama lokacin tashinsa yayi tunda lahadi ce sai kawai ya fice. Wannan mutumin ya gani da yake zaton maigadi ne. Shima yana ganin Dahiru ya saki fuska yana murmushi. Gaishe shi yayi yana tambayarsa aiki

"Kwana biyu na dena ganinka a nan Baba har na fara tunanin ko ka dena aikin ne"

"Wani uzurin ne dai ya taso min. Ya karatun naka? Maigidan nan yace baka neme shi ba har yau"

Dahiru yayi dan murmushi "ni dai da ya barshi wallahi bana son zuwa ya ga kamar kuma maula nake. VC din BUK ne fa na gani a katin"

A take mutumin nan ya sake ji Dahiru ya kuma shiga ransa. Yana son yara masu kwazo sai yake tuna masa da kansa lokacin da ya fara karatu. A wannan lokacin har itace yayi domin biyan kudin makaranta tun daga firamare sai gashi ya zama tauraro mai haskawa a kauyensu. Mutane da dama basu san almajiranci ne ya kawo shi Kano ba yau shine shugaban jami'a ta gwamnatin tarayya a garin.

"Ka daure kaje don nayi masa zancen kaima dalibinsu ne yaji dadi sosai"

Dahiru yace "to amma yanzu nasan ya manta ni da yaya zan kwatanta masa kaina?"

"Kace Dahiru kawai zai gane. Shi ma sunan autansa Attahir kusan sa'anka ne."

Ba don yaso ba ya amince zai je ranar litinin. Hira suka cigaba Dahiru ya bashi dari biyu wai yasa masa albarka ya karbi albashinsa ne.  Da yaje gida ya yiwa Bilya korafin albashinsa da aka rage hakuri ya bashi tare da nuna masa masu aiki irin nasa da yawa albashinsu baya wuce dubu biyu. Shima tun farko saboda maigidan yasan zaiyi karatu ne suka saka masa albashi mai tsoka.

Ranar litinin kafin ya shiga lacca karfe biyu yaje ofishin VC. Daga suturar jikinsa sakataren ya fara masa kallon raini da dalilin zuwansa. Yayi sa'a ya tambayi sunansa ya fada. Yana shiga ciki ya fito ya nuna masa kofa.

"Bismillah"

Dahiru yayi godiya ya shiga. Mutumin da ya gani a zaune ne ya bashi mamaki sai kuma kunya da ya tuna dari biyun da ya bashi. Durkusawa yayi gwiwa kasa ya soma bashi hakuri kada ya kore shi.

Dariya ya rinka yi kafin yace ya tashi ya zauna.

"Yallabai Frofesa kayi hakuri kuskure ne wallahi"

Professor Abdulhadi Bature ya sake dariya "Dahiru tashi ka zauna magana zamuyi ta uba da dansa kaji ko. Yadda naga ka sake dani tun ranar yasa ban gyara maka zatonka na cewa ni maigadi bane. Akwai lemo a fridge dauko wanda kake so"

Tabdi yadda gabansa ke lugude idan ba gani yayi ya fita salin alin babu takardar kora ba yaushe zai iya shan wani lemo.

"Ko na dauko maka da kaina" yace yana masa dariya

Da gudu gudu Dahiru ya dauko wanda hannunsa ya fara kaiwa ya dawo ya zauna.

Daidaita fuskarsa yayi ba alamun wasa yace "Dahiru kada kaji tsoro alkhairi yasa na nemeka. Ina son yara masu kwazo da sanin yakamata. Yadda ka inganta rayuwarka da guminka yasa naji ka burgeni sosai. Ni bana son rago ba kuma nason yaron da zai kwanta yana jiran komai sai iyaye sunyi masa bayan hankali ya soma zuwar masa. Ga wannan ta Attahir ce amma ta kwana biyu. Ka fara amfani da ita kasan akan abinda kazo karanta. Computer engineering sai da laptop kuma nasan baka da ita. Wannan ita ce tukwicin dari biyun da ka bani"

Jakar laptop ya mikowa Dahiru wanda hawaye ya soma zubar masa. Sauka yayi daga kujerar yana ta godiya. Daga nan Prof Abdulhadi yace masa ya kusa sauka daga mukaminsa shiyasa yake gini zai dawo kusa dasu. Nasiha sosai yayi masa sannan yace duk sanda yake bukatar taimako ko shawara yaje gidansa na nan cikin BUK in sha Allah zai saurare shi.

Bayan ya tashi zai tafi ya tsayar dashi ya tambayeshi ko yana da wata matsala a yanzu. Dahiru baiyi kasa a gwiwa ba yace turanci ni yake bashi wahala yayi masa tsauri. Prof yace masa akwai English Academy a gwauron dutse ya nema ya shiga. Yana bukatar result din farko ya ga yayi kokari shi kuma yayi masa alkawarin kyakkyawan surprise kamar yadda yace yana dariya.

Ko kwabo bai bashi ba da zai tafi shima baisa a ka ba. Shi kuma Prof dalilinsa shine kada ya dora alakarsu akan kudi. Shi taimako daki daki ake bi domin samar da kyakkyawar alaka. Wani daga ka fara bashi kudi to fa duk inda yaji dugudugu wurinka zai kawo matsalarsa.

******

"Yasin bazamu yarda ba kawai asan wacce ake ciki"

Wani kaura ya cafe "ku barni na balbale gidan kawai a rage mugun iri kun gane ai"

"A'a mu dai ce kawai su bar garin nan. Idan ba haka ba sauran 'yan matan haka zasu rinka lalacewa a birni su dawo mu auri ragowar cuta"

Hayaniya ce sosai a kofar gidan Mal Fatihu. Samari da sanduna da gorori suna ta hargowa su dai kawai su bar garin. Kauyukan makota kowa zancen Mawadda akeyi ana bata mata suna. Su kuma sun gaji da zama dasu. Su kansu iyalin gidan abubuwa da dama idan suka je siya a yan kantunan dake kauyen sai a hanasu. Rayuwa tayi kunci garesu komai yayi tsanani.

Ana wannan rigimar Mal Isiyaku mahaifin Dahiru ya gansu. Kememe dama sun shatawa Dahiru layi akan zuwa gidan amma yadda yaga samari da yara suna wake wake ana jefa duwatsu a gidan ya tayar masa da hankali. Gidan maigari ya nufa kai tsaye ya sanar dashi. Ranar fadar maigarin hirar da aka dasa kenan.

Washegari Maigari da kansa yaje gidan Mal Fatihu saboda yasan bashi da lafiya. Shimfida akayi masa a karkashin bishiya matasa sukayi dafifi a wurin.

Kaninsa ne ya riko shi ya fito aka zaunar dashi akan tabarmar ya kwashi gaisuwa. Maigarin yasa aka kori matasan sannan ya soma magana.

"Mal Fatihu ina sake jajanta maka wannan hali da kuka sami kanku a ciki Allah Ya kiyaye gaba. Yaran garin nan sun bullo da sabuwar fitina wadda idan ban kawar da ita ba suna iya yin abinda bazai mana dadi ba. Sabili da haka ga mutane a wurin nan suna shaida nasan baka da wurin zuwa idan ka bar Tariwa. A cikin Kano unguwar Tunga ina da gida dan karami ne daki uku da bayangida. Wata shidan farko na amince ka zauna kyauta daga nan idan na shigo garin sai muyi maganar kudin haya. Ka amince?"

Kuka Mal Fatihu yake kamar yaro. Wannan wace irin masifa suka shiga. Ya koma Kano yayi me? A kauyen ma shi talaka ne sosai ina ga ya koma birni. Yanzu saboda kaddara ta fadawa yarsa shikenan sai a taru a koreshi daga mahaifarsa?

Maigari ga katse masa tunani "nasan kana cikin tashin hankali da damuwa amma ina tsoron abinda zaije ya dawo. Ka tafi da iyalinka idan kura ta lafa sai ku dawo. Zan gargadi yaran da iyayensu na baka sati guda"

Har Maigari ya tafi Mal Fatihu yana kuka ya ma kasa godiyar gida da aka bashi. Da taimakon kaninsa ya koma ciki ya sanar da iyalinsa. Ranar Malam babansa yazo gidan da kansa yace gara ma su tafin saboda yanzu ma meye marabarsu da basa nan kowa ya fita harkarsu.

Kuka dai baya karewa iyalin gidan. Haka suka hada kaya Mawadda tana jin kamar ta wayi gari taga komai mafarki ne ko kuma ta mutu ta huta.

*Sabon Shafi*
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰9

*Batul Mamman*💖



Kafin ya karasa ciki yayi kokarin saisaita kansa a soro sai dai kallo daya zaka yi masa kasan akwai abinda yake damunsa.

Innarsa ce ta fara tambayarsa ko Dahirun ya fada masa magana wadda batayi masa dadi bane. Murmushin dole ya kirkiro sannan yace

 "haba Inna kema kinsan yaron ba dai dattako ba kamar wanda ya tashi cikin tsofaffi irinku"

Jin har lokacin kirjin nasa ba dadi ya zauna sannan ya cigaba da cewa "yaso kwarai ya ga Mawadda nace ya dai yi hakuri ya nemi wata ita ma zamu yi ta bata baki ta karbi kaddararta"

"Hakane, amma gaskiya ban taba tsammanin haka daga gidan Mal Isiyaku ba" cewar Iya.

"Wani masoyin sai kana cikin yanayi kaka-ni-kayi dama kake sanin ainihin me ya aje a zuciyarsa game da kai. Allah Yasa hakan ne mafi alkhairi. Yaya Fatihu sai ka fadawa Yaya a tattaro komatsansu a mayar musu ko"
Ade ta fada kana ji kasan ranta a bace yake.

Shi dai Baba shiru yayi sai can ya tashi ya shige rumfar mahaifinsa ya nemi wuri zai kwanta.

Mawadda na zaune kamar an kafeta sai da ya tashi kuka ya taho mata ta mike tayi dakin Iya cikin sauri. Inda ta tashi Iyan ta kalla sai ga alamu na jini a jikin tabarmar.

Wata guda Iya tayi kai kace haihuwa ko amarya akayi a gidan. Innar Fatihu da Ade suka zabura suna kallonta ta murmusa sannan ta nuna musu wurin da Mawadda ta tashi.
"Allah Maji rokon bawanSa Yaga zuciyata da irin du'a'in da nake yi kada Ya jarabcemu da goya dan gaba da Fatiha. Ga shaida idona ya gani iftila'in Mawadda bai hada da ciki a dalilin fyaden nan ba"

Ade ta ma manta da abu makamancin wannan bata taba tunani ba akan zai iya yiwuwa fa ciki ya shiga. Wani sanyi itama taji ya ratsa zuciyarta tayi hamdala sannan ta bi bayan Mawadda tace mata ta gyara jikinta don ta lura tunani yayi mata yawa bata san dashi ba.

Innar Fatihu ta tashi ta shiga rumfar maigidanta wurinsa. Yana jingine da bango ya dafe kai yana aikin tunani.

"Fatihu fada min gaskiya ya kuka yi da yaron nan."

Jiki a sanyaye ya fada mata ta shiga tafa hannuwa.
"Amma sun bani mamaki sosai. Nasan ko nice da wuya na amince amma irin haka da sosa rai. Nagode Allah yarinyar nan ba da amincewar ta akayi ba da bansan yadda zamuyi da ranmu a garin nan ba"
******

A fusace Baffa yake ta doka sallama Inna ta saki rariyar da take tankade da sauri saboda tsoro.

"Menene?" ta fada tana mikewa sai kuma ta kula da Dahiru tasa fuskar tayi kalar tausayi harda guntun hawaye a idonsa.

"Kai kuma daga ina?"

"Ki jawa yaron nan kunne ina daf da nuna masa bacin rai mai tsanani. Ta yaya za'ayi naje nayiwa Mal Fatihu magana akan yarinyarsa mun gama yankewa a bar zancen aure danki ya rinka zagayawa ta baya. Wato ace gani mugun uba dana ya fini tausayi ko. To baka isa ba, in ba aure kake so nayi maka gobe goben nan ba kuma na soke karatu a Kanon ka shiga taitayinka"

Inna ta harari Dahiru sannan tace "kayi hakuri Baffa. Yanzu dai fada min me ya yi"

Cikin daga murya ya bata labari don ransa a bace yake. Inna kuwa hannu tasa ta tsinke Dahiru da mari. Tsabar mamaki ya hana shi kuka sai kallon iyayensa da yake yi wani iri. Ya kasa gano meye laifinsa don yace bazai guji masoyiyarsa a wannan lokacin da take bukatar karuwar masoya da masu nuna mata kulawa ba.

Muryar Inna ce ta dawo dashi daga tunaninsa "Dahiru kada kayi abinda zamuyi fushi da kai kana jina ko. An fada maka da ka muka yanke shawarar fasa auren naku? Wannan zamani na cututtuka idan ta shafa maka kanjamau waye da asara? Kuma muna nan galau bamu sani ba kila da ciki a jikinta a ganganda ayi aure a yaba maka dan jaraba"

Kwalla yaji ta taru a idonsa har yana zafi kamar yadda ransa ke yake yi. Ji yake kamar yasa ihu yayi musu bayanin da zasu gamsu. To amma iyaye da girmansu da darajar da Allah Ya basu bazai iya ba.

"Inna, Baffa kuyi hakuri don Allah. Auren nan idan anyi dama ina da niyar kaita ayi mata gwaje-gwaje sannan in taimaka mata yadda zata ji saukin bakincikin da yake ranta ne"

Baffa ya mike kamar ya rufe shi da duka "dan zaman naka a Kano ne yasa kake tunanin ka fimu wayo da sanin ya kamata? Idan baka yi hankali ba na fada maka karatun ma sai a hakura ka dawo gabanmu ka zauna...shashashan yaro ana ga yaki kana ga kura"

Inna tabe baki tayi "duk abin nan kila ma shiryowa tayi tazo ta fada kai kuma ka hau ka zauna. Idan karya take yi fa bariki ce ta kare mata shine ta dawo ayi auren ka rufa mata asiri fa"

Hawayensa ne ya sakko ya kalleta a sanyaye yace "Innaaaa!"

Jikinta ne yayi sanyi yayin da Baffa ya dauki bota ya shige bayan gida.

Abinci tayi masa tayi yace ya koshi kawai ya mike
 "zan koma a satin nan zamu fara shiga aji"

"Allah Ya bada sa'a Ya shi albarka. Ungo maza ka tashi ka tafi zan taushi mahaifinka kafin ka sake dawowa"

Zaninta ta dan kwance daga gefe ta hado masa dubu biyu da dari bakwai ta bashi. Karba yayi yasa a aljihu tare da godiya duk da fuskarsa babu annuri ko kadan.

Haka ya juya ko ruwa bai sha ba Inna tana ta masa addua har kofar gida. Yana jin ta koma ya dawo soronsu ya tsaya yaci kukansa sannan ya share ido. Yana son iyayensa amma  baiji dadin matakin nan da suka dauka ba sai dai zaiyi hakuri ya barwa Allah ikonSa.

*****

Haj Mara yau tayi bacci harda minshari tamkar an gama shari'ar an basu gaskiya. Juyi tayi akan makeken gadonta don jiya daga kotu gida suka wuto abinsu.

Wayarta ta janyo ta kira Alh Sule cikin isa da kasaita tace "da baka sa hannu ka nuna damuwarka akan danka ba me ya ci mu Alhaji? Na kira ne kawai nayi maka albishir da cewa kiris ya rage mu sami nasara mu baiwa marada kunya"

"Ni kike fadawa haka Marakisiyya?"

"Da 'yan hamayya nake wadanda basu damu da halin da 'ya'yansu suke ciki ba. Ko kana cikinsu ne?" Tayi masa tambayar rainin hankali tana 'yar dariya.

Murmushin takaici yayi "bana cikinsu gaskiya domin ni ina nan ina addu'a akan Allah Ya fitar min da dana idan yana da gaskiya idan kuma shi mai laifi ne Ya fitarwa wadanda aka zalunta hakkinsu"

Kafin ta ankare ta bashi amsa ya kashe wayar. Kallonta ta rinka yi rai na kuna tana ayyana yadda zata rama idan ya dawo.

Shima a nasa bangaren yana bakincikin yadda neman kudi yasa shi sakar mata ragamar gidan. Yayi babbar sa'a  sauran yaransu mata babu wata mai mugun hali ko ace miji ya kawo kararta. Ita Haj Mara din ma arzikinsa da ta ga yana ta habbaka ne yasa ta kara kwallafa rai akan tilon namijin nasu ta sangarta shi har ya kai matakin da tankwara shi zaiyi matukar wahala.

Mikewa tayi zata shiga wanka BB ya shigo dakin nata ba ko sallama yana muzurai.

"Babawo lafiyarka kuwa?"

"Ras nake Hajjaju mutan Makka da Madina. Wai yane....?"

Kasa cewa komai ma tayi jin yadda yake mata magana. Gashi kamar yasha wani abu. Da kyar ta iya cewa
"Me kake nema ne?"

"Ke muka yi magana kika ce min idan na fadi abinda kika sani yarinyar nan Mawadda kamar kin aura min ita kin gama ne kuma gashi har mun taho ko iyayenta baki nema ba"

"Bansan rashin hankalin naka ya kai nan ba. Ta yaya za'ayi nayi musu magana ba'a gama shari'a ba? Ka bari a kare komai mana ka ga iya gudun ruwana"

Hade rai yayi yana kunkuni "to ni dai kada ayi min solo don ba yarda zanyi ba na fada miki tun wuri."

Daga haka ya fita tayi saurin sakawa kofarta mukulli don tsoro ma ya bata.

*****

Dr Tani ta wuni a asibiti tana gyara duk wani report na Mawadda. Wadancan na gaskiyar ta sa wani masinja ya dauko mata ainihin file din ta bashi kudi sannan ta tura a jakarta. Nan ta zauna ta sake komai da taimakon masinjan ta buga sababbin takardu da suka dace da kwanan watan wadancan. Tana aikin tana tausayawa BB domin ba karamin abu bane ace anyiwa mutum sharrin fyade.

Wayarsu ta dazu da Haj Mara ta dada tayar mata da hankali inda tace mata ko ruwa baya iya sha zabgegen namiji kamarsa wai jiya har kuka yayi mata da suka dawo yana cewa rayuwarsa tazo karshe wace mace ce zata taba aurensa. Cikin lallashi Dr Tani tace ta bashi hakuri ta san duk wannan tashin hankalin nasa akan Qareeba ne kuma alkawari ne tayi masa kamar anyi aure an gama tsakaninsu.

Kwafa tayi a hankali tana jin tsanar su Mawadda. Tunda take ita dai tasan 'yarta ba mummuna bace gata fara amma samari basa wuce zuwa uku idan sun kai zuciya nesa suke zukewa a nemesu a rasa. 'Ya'yan nata duka sunki aurowa saboda yanayinsu. Ita kuma hakan bai taba damunta ba balle ta gane sokoncinsu yake hanasu aure. Murnar samun BB a matsayin suruki yasa komai aka fada mata take hawa ta zauna daram.

Sai da ta gama gyara komai ta tafi gida gabanin magariba.

Dahiru yana zaune a kan benci a kofar gidan ya nisa cikin tunani wani yaro da baifi shekara hudu ba ya taho kan titin gidajen wurin yana buga ball. Dr Tani ta taho ga duhu ya kawo kai saura kadan ta buge shi Dahiru ya tashi a guje ya dauke yaron har yana faduwa.

Kanta ta zuro ta taga tace masa "don tsabar wulakanci me ya hanaka dauke yaron tun da na karyo kwana?"

Batare da ya saki yaron ba yace "Hajiya kiyi hakuri"

Tsaki ta doka ta shige bayan maigadi ya bude mata gate.

Shi kuma Dahiru ya fuskanci yaron.
"Assha  ba dai kaji ciwo ba ko, daga ina kake?"

"Nan gidan" ya nuna wani gida da tun zuwansa ya kula aikin gininsa ake yi.

"Shine zaka fito kai kadai kana buga kwallo akan titi. To wuce muje ka shiga ciki kuma idan na sake ganin kafarka a wajen nan sai na yanketa."

Yaro yayi kwalkwal da idanu "da wuka ko reza?"

Dahiru ya dan murmusa. Shi tsorata yaron yayi niyar yi saboda ba karamin ganganci bane fitowar tasa "da almakashi zan yanke nasan yafi zafi. Idan zaka yi wasanka kayi a cikin gida banda titi kaji ko"

"Naji sakeni na tafi to.." yaro ya fada duk ya tsure.

"A'a sai na kaika har ciki nace a zaneka kana fita titi"

Wani mutum da yake jinsu daga gefen gate din gidan da ake aikin sanye da 'yar shara  ne ya fito yadda zasu ganshi sosai. Yaron ya ruga wurinsa shi kuma Dahiru yana ganin haka yayi zaton ko maigadin gidan ne.

"Baba don Allah a rinka kulawa da amana. Kaga da bana kusa yau da karshen aikinka yazo idan da tsautsayi"

Mutumin ya gimtse dariyarsa yace "Allah dannan me ya faru?"

Dahiru ya sanar dashi duk da cewa akan idonsa akayi komai. Shima da sauri ya biyo bayan jikan nasa sai dai kafin ya iso ya tsallaka titin.

"Zan kiyaye in sha Allahu. A nan kake ne?"

"Eh ina aiki a gidan can ne."

"Mu kuma aikin gini mukeyi a nan an kusa gamawa"

Addu'ar gamawa lafiya Dahiru yayi har ya juya zai tafi mutumin ya dakatar dashi suka je masallaci tare. Bayan sunyi sallah Dahiru yace zai shiga ya karbi abincinsa ya wuce gida. Mutumin yace to yana jiransa.

Ko da ya fito baiga yaron ba sai yayi zaton ko yana wurin ainihin masu gidan tunda ga dankareriyar mota an paka ta a wajen gate din. Da ya ga mutumin bai tafi ba sai yayi masa tayi abinci shi kuma yace ya koshi.

'Yar hira suka taba anan Dahiru yake ce masa gobe zai fara shiga aji daukar darasi
"Mu mun saba  karatunmu a kauye nan sai fargabar gobe nake yi zan hadu da 'yan gayun birni"

Mutumin nan yayi ta dariya. Dahiru kansa mamakin yadda ya sake dashi yake yi da yaga Isha na neman yi yace masa zai wuce gida ya sake goge rigarsa don kada 'yan birni su raina shi.

"Dannan kace 'yan mata zaka nema ba karatu ba"

Shiru Dahiru yayi yana tunanin Mawadda "ina da matar da zan aura a kauyenmu, karatu kawai zanyi na koma wurinta"

Yanayin maganarsa kadai ya nuna akwai babbar damuwa a tattare da shi. Mutumin ya sami kansa da tausayin Dahiru sosai. Gashi matashi don yace masa shekarunsa ashirin da biyar amma ba girman kai ga son cigaba yazo yana aiki domin yayi karatu. Kati ya ciro a aljihunsa ya mikawa Dahiru.

"Ga wannan inji Kakan Khalil yaron da ka taimakawa yace na baka ka neme shi"

"Kakansa ne mai gidan nan kenan"

"Eh"

Godiya yayi masa sosai da korafin baici abincinsa ba sannan ya tashi yayi gaba. Mutum ya bishi da kallo, da farko kudi yayi niyar bashi amma 'yar hirarsu tasa ya shiga ransa.

*****

A daddafe iyalin Mal Fatihu suka karasa kwanakin da kotu ta diba kafin a cigaba da zama. Tsagwama da bakaken maganganu kullum yi ake. Hatta 'ya'yansa masu aure su Bilki basu tsira ba. Makota suyi musu dangin mazajensu suyi. Abu ya taru ya cakude musu.

A wannan lokacin Mawadda ji tayi inama bata taba rayuwar duniya ba. Ko kuma da BB ya keta mata haddi dama harda ranta ya hada. Bakar rana guda daya ta zame musu bala'i ita da duk wani makusanci nata. Hatta Dahiru wasu sun fara yawo da zancen kila shine yake nemanta suke neman dorawa dan iyayen gidanta.

Abubuwa sai gasu nan babu dadi ko kadan. Kannenta ma yanzu ko kofar gida basa so a aikesu.

Da sassafe suka shirya suka tafi Kano saboda Baba yace baya jindadin yadda yake rara gefe yana takurawa mutane akan wurin kwana.

Shabiyu za'a fara sauraren tasu karar amma ko da suka isa wurin goma da rabi kotu ta cika da 'yan kallo da 'yan jarida.

Haj Mara a gidan aminyarta ta kwana shi Dr Auwal maigidan bai san wainar da ake tonawa ba. Matarsa dai ta fada masa zata je kotu shaida akan wata yarinya yace sai ta dawo.

Da hillata Haj Mara tasa BB ya amince yazo gidan. Qareeba duniya kamar an bata sweet-kamfo jinta take tafi kowa sai wani yauki akeyi.

Shi kuma BB komai yana yi ne kawai saboda biyan bukatarsa na samun Mawadda. Sun gama shiri zasu tafi kotu yana jingine da mota Qareeba tana tsaye a gefensa suna jiran fitowar iyayensu sai ga Dahiru zai wuce.

Sauri yake yi ya gama aikinsa Danlami ya tsegumta masa yau za'a sake zaman shari'ar su Mawadda da karfe shabiyu. Da yake mutum ne mai shige-shige kuma yana yawan zuwa Kano yawo yasan court road din ya kwatanta masa. A ka'idar karatunsa ma yana da aji yau hudu zuwa shida amma bai damu ba ko zai rasa indai zai ganta.

Qareeba ta kalle shi ya kwaso shara zai wuce tace "kai Ahirin meye haka baka ganin Man dina bazaka gaishe shi ba"

Dahiru yayi banza kamar baiji ba ta kuwa daga murya "Dashiru mai ahirin baka ji na ne? Tsaya nan dalla can ko na fadawa Mummyna"

BB ya dan daga ido ya kalleta sai yake baki take da suka hada ido "Man kaga wannan shine Dashiru din da nake fada maka yace ahirin....hehehe..." tayi dariya ita a dole 'yan mata zata burge masoyi.

Dahiru ganin zasu bata masa lokaci yace "barka dai Man"

Qareeba ta cika da haushi "me yasa kake min haka ne, ni kadai nake kiransa Man meye naka na fada. Kada kace min a kauyancinka baka san akwai sunaye da ake warewa na kiran wanda ake so ba"

BB duk ta ishe shi da hayaniya ya rasa me ya zaunar dasu Hajiyarsa a ciki. Ji yayi ta sake cewa

"Man kasan 'irinsu Ahirin basu san komai na love ba har tausayi suke bani ga auren wuri. Kai Dashiru  me kake kiran budurwarka ta kauye"

Har ransa tausayi ma take bashi saboda yana ganim yadda saurayin nata yake ta wani yatsina shi a dole ya hadu. Yasan idan baiyi yadda take so ba karshenta Mummynta ta hana shi fita idan ya nemi uzuri kafin lokacin laccarsa don har timetable dinsa tasa ya kawo mata.

Dan buga kafa ta soma na shagwaba tana kyabe baki "Man please mana kace ya fada maka muji muyi dariya"

BB ya tsani wannan suna na Man kamar ya bugeta ya dai maida hankalinsa ga Dahiru.

Shi kuma ganin haka yace "Qulqulatul qurabati nake kiranta. Zan iya tafiya ko"

Haba Qareeba dariya har da kaiwa kasa. Muryarta kuwa har bakin gate maigadi sai da ya jiyota. Dr. Tani suna doso wurin taji takaici ya rufeta har da kunyar idon Haj Mara. Ita kuwa nunawa tayi ba komai tunda bukatarta zata biya a kashe case ta tura danta wata kasar ta yakice Dr. Tani. Dan zamanta a gidan duk sun gundureta ita da 'ya'yan. Wai jiya gotai gotai dasu suka rinka fada lomar wa tafi girma ana cin abinci.

Dr Tani ta jefi Dahiru da kallon banza don tasan shi kadai ke kara kunna Qareeba tayi ta rashin hankali.

"Kai me kake a nan kamar mara aikin yi? Ka wuce yau nasan sai la'asar zaka shiga aji ga wanki can mun hada ka wankesu tas a goge zan bar sallahu a tada inji. Asabar ba sai kazo ba"

Uzurinsa ya gabatar mata yana da wurin zuwa ta haushi da fada harda cewa idan ba so yake ya bar aikin ba ya rufe mata baki. Duk bakincikinta dariyar da yasa Qareeba a gaban BB da babarsa.

Ba don yaso ba haka ya tafi yana jira su fita shima ya saci jiki ya fice.
*****

Lauyoyi sun gabatar da kawunansu sannan Alkali ya bukaci a cigaba. Wani matashi aka gabatar wanda yace shi abokin Na'ibi mai kiyos ne kuma shine ya ga Mawadda a dakinsa har ya sanar da Haj Mara.

Barista Shafa'atu tayi dariya "kuma kana ganinsu baka yi tunanin yin yekuwa jama'a suzo ka sami shaida ba ko ka kira wani da yasan Na'ibin sai uwardakin Mawadda ce kawai ta fado maka a rai?"

In-ina ya dan soma "saboda nasan zata dauki mataki ta hana ne"

"Ashe akwai alaka tsakaninka da Haj Marakisiyya kenan"

"Eh to....a'a babu kawai dai nasan a gidan Mawadda take kuma zata bata min aboki tunda da ba halinsa bane"

"Da gaskiyarka kuma. To zamu so ka kwatanta mana hanyar da ake bi daga gidan Hajiya Marakisiyya zuwa dakin Na'ibi" tayi maganar tana kallon Haj Mara wadda taji cikinta ya kulle.

Saurayin ya soma raba ido domin shi gaskiya ko Na'ibin bai taba gani ba hasali ma ba dan unguwar bane.

"Ni bansan gidan Hajiyar ba amma nasan dakin nasa"

"Kace kuma kasanta har kasan zata dauki mataki idan ka sanar da ita halin da mai aikinta take ciki"

"Objection my lord" cewar Barista Dalhatu. "Barista tana neman juya zancen shaidarmu. Babban abin nema shine ya gansu kuma yaje ya sanar da uwardakinta"

Alkali ya karbi korafinsa yace ta kiyaye. Jin haka tace zata gabatar da shaidarta wato Dr Tani.

Wata yar musabaha Dr Tani da Haj Mara suka yi sannan ta tashi taje ta tsaya. Iyayen Mawadda dukkansu da Mawadda suka zuba mata idanu.

"Dr Tani ko zaki iya fada mana meye aikinki da shekarunki a wannan sana'a"

Sunanta ta sake nanata musu da bayanin kanta a matsayin likita da ta kwashi shekaru ashirin  da uku tana aiki. Gashi har asibiti gareta wanda gwamnati ta bawa lasisin aiki.

Barista Shafa'atu tace "My lord munji wace ce Dr Tani saboda ina so kotu tayi duba da nazari mai kyau game da shaidun da zata kawo"

Alkali Dawud ya gyada kai ita kuma taci gaba.

"Doctor muna bukatar kiyi mana bayani game da halin da kika sami Mawadda ranar da tazo asibitinku"

"Tazo asibitin ne da lalura ta rashin iya rike fitsari sosai sannan tace anyi mata fyade ne shine dalilin wannan lalura"

Magana take babu wani alamu na damuwa kai tsaye kamar wadda tazo wurin a bisa tilastawa. Yanayinta kadai ya dagawa Barista Shafa'atu hankali sai dai ta cigaba da tambayarta.

"Idan na fahimceki kenan kina nufin fyade yakan iya janyo sakin jijiyoyin jikin mace har ta kasa rike fitsari hakane?"

"Gaskiya kamar yadda kowa ya sani yoyon fitsari ana samunsa ne ta dalilin haihuwa, tsufa ko infection wato idan kwayoyin cuta suka shiga mafitsara. Ni a tsahon lokacin da na dauka ina aiki ban taba jin ance fyade ya zama sanadin yoyon fitsari ba"

Barista Shafa'atu tun a lokacin ta gane inda Dr Tani ta dosa jikinta yayi matukar yin sanyi. Ta daure tace "amma ba yoyo take yi sosai ba tunda kadan kadan yake fita wannan ba alama bace dake nuni da cewa abinda ya janyo shi bai kai haihuwa ba?"

"Ga takardu na gwajin da muka yi mata mun tabbatar ba infection bane yake damunta. Sauran bayani kuma mun dogara ne da abinda ta fada da bakinta. Shawarata a nan shine idan da hali a sake bincikenta ko ta taba haihuwa ko yunkurin zubar da cikin da yayi kwari..."

Wani kukan kura Ade tayi ta taso daga inda take ta nufi Dr Tani take tsaye tana kuka sosai "Dafta amanarmu zaki ci? Nawa suka biyaki zaki yiwa 'yata kazafi irin wannan"

Durkushewa tayi a wurin tana kuka Alkali yace 'yan sanda suyi waje da ita ko ya hukunta ta saboda dakatar da shari'a batare da izini ba. Suna kokarin kamata Iya da Innar Fatihu suka taso suma suka rikota kowa cikinsu na kuka suka fitar da ita waje. Mawadda kamar ta hadiye zuciya ba kuka sai ajiyar zuciya.

Barista Shafa'atu tace ta gama tambayoyinta domin tun da fari yarda da itan yasa ta dada nanatawa kotu cewa likita ce da ya kamata a kama maganarta saboda dadewarta a aiki da kwazo.

Barista Dalhatu ya taso yazo gabanta kana ganinsa yana cike da nishadi.
"Dr Tani da kika duba Mawadda baki ga wata alama ba kenan dake nuni da cewa anyi mata fyade?"

Tunawa tayi da raunukan jikin Mawadda ta dan runtse ido. Ta tabbatar Haj Mara bazata yi mata karya ba amintarsu tun kuruciya. Idan an gama case din ya kamata iyayen Mawadda su tsareta ta fadi gaskiya waye yayi mata fyade.

"Abu daya na gani shine yarinyar ba budurwa bace"

Yaya sai kuka ta rike hannun Mawadda tana matsawa.

"My lord ina fata kotu taji bayani mai gamsarwa daga bakin shaidar da masu kawo kara suka kawo. Ta yiwu da gaske fyade aka yiwa Mawadda amma ba BB bane saboda  bayanin da suka yi shi da mahaifiyarsa da rashin wata shaida da zata karyata hakan. Haka zalika duk inda ake tunanin samun Na'ibi mai kiyos abu ya gagara mutane da dama sunce ko garinsu ba'a sani ba. Da wannan nake rokon kotu da ta taimaka ta yiwa Babawo Sule adalci" dan dukar da kai yayi ya koma ya zauna.

Alkali yace ko Barista Shafa'atu tana da karin bayani ta kalli Mawadda ta girgiza kai.

Ya duka yana kallon takardunsa yace ga hukuncin da kotu ta yanke bayan dan jawabi

"Duba da rashin kwararan shaidu daga bangaren masu korafi da kuma bayanan likita wannan kotu mai alfarma ta kori wannan kara, ta wanke Babawo Sule daga zargin da ake yi masa sannan ta ci Mawadda tarar naira dubu ashirin da biyar bisa dalilin bata masa suna. Wanda bai gamsu da wannan hukunci ba yana da damar daukaka kara."

 Yana gamawa ya buga gudumarsa ya mike sannan kowa ya tashi ya fita ta baya.

Yaya tayi tayi ta daga Mawadda daga wurin da take zaune ta kasa saboda mutuwar zaune da tayi. Barista ta matso kusa dasu

"Kuyi hakuri zamu iya daukaka kara sai mu karo shaidu. Kunga tun da farko bakuyi min bayanin asibitin Bebeji da ta fara kwanciya ba da tuni munje har can saboda karin shaida "

Mal Fatihu ya tashi yana murmushin da yafi kuka ciwo yace "Barista mungode a haka ma."

Zata sake magana ya je gaban Mawadda ya tayar da ita har lokacin murmushi yake yi mata "Ni nasan wa na haifa kinji ko, idan duniya zata taru ta nuna miki yatsa maganarki kadai zan dauka. Shari'a kuma mu barta haka zuwa lokacin da zamu taru a gaban Sarkin da Ya halicci kowa da komai"

Da haka ya samu ta tashi zuciyarta tana wani irin bugu da sauri da sauri. Suna fitowa waje aka yanyamesu da tambayoyi ga mutane kowa na fadin abinda yazo bakinsa.

Su Iya sun taso da sauri su tarar dasu Baba yana kare Mawadda daga 'yan jarida. Yaja hannunta suyi gaba kawai ya yanke jiki ya fadi ita kuma tayi kansa saboda rashin kwarin jikinta a wannan lokacin da kuma rikon da yayi mata ta kwala ihu  "BABA....!!!!"
[08/01 8:32 pm] : *GUMIN HALAK...*💰11

*Batul Mamman*💖



Yau su Mal.Fatihu zasu bar kauyensu, mahaifarsu kuma tushensu. Tuni sun gama hada kayansu da ba wani yawa garesu. Da wuri Yaya ta fita ta tafi sallama da 'yan uwanta wanda a gidanta suka yini a jiya.

Ade dasu Iya suka zo gidan domin tare zasu tafi har Innar Fatihu. Idan sun taimaka musu sun nutsu a gidan su dawo duk da Ade ma tasan zaman kauyen yanzu yafi karfinta. Aiki zata bazama nema ko don samun lafiyar Mawadda dake fama da digar fitsari har yanzu.

Kowa na can ana tarkata kaya Ade na zaune kan kujerar girki Baba yana daga kan tabarma yace mata

"Sa'ade ina fata zaki yafe min tura Mawadda aiki da nayi har hakan ta faru"

"Haba Yaya me ya kawo wannan zancen kuma? Ka barmu muji da bakincikin mutan garin nan na yanzu"

Gyara zama yaso yi hularsa ta fado. Dora masa ita Ade tayi akan hannunsa mai lafiya ya danyi murmushi

"Kinga fa naso shiga layin zaurawanki ashe ba rabo na koma rabin mutum"

Mawadda na fitowa daga daki taji abinda ya fada kunya ta kamata ta koma da sauri. Ade kuwa dariya tasa don ta kara kwantar masa da hankali tace  "ko zaka fito ne?"

Shima yayi dariya "rufa min asiri kada Iya ta cinyeni danye."

Iya na jinsu ashe da ga dakin da Mawadda ta koma. Murmushi tayi sannan hawaye ya sauko mata duk kuwa da dakiya irin ta ta.

"Ehem, ehemmmm....gafarar ku dai masu yi da mutane da rana tsaka. Muna jinku daga ciki ana shuka a idon makwarwa"

Ade mikewa tayi da sauri ta bar wurin don kunya shi kuma Baba ya dauki hularsa ya rufe fuska. Iya tayi 'yar dariya ta wucesu.

Sai da suka yi sallar azahar aka fara batun nemo mota daga bakin titi. Nan fa sai koke-koke yawanci daga 'ya'yansu ne ma saboda Baba yace bai yarda su biyosu a yau ba. Baya so suyi abinda suma nasu auren zai gurgunce irin na Jamila. Sun hakura tare da alkawarin zuwa kafin suyi sati. A haka Malam kakansu yazo ya riskesu an soma fita da kaya waje. Baba na ganinsa yaji kwalla ta taho masa.

"Meye hakan Fatihu a gaban 'ya'ya da jikoki" cewar tsohon mai halin dattako cike da dauriya. Ba karamin tashin hankali ya shiga ba sakamakon abubuwan da ke faruwa da iyalin dan nasa amma ya yarda jarabawa ce mai wucewa.

"Malam ka yafe min duk wani abu da na taba yi maka da gangan ko bisa kuskure."

Malam ya dafa masa kafada "Allah Ya baka lafiya Fatihu Yasa wannan tafiya ta zama tamkar budewar wani *sabon shafi* na rayuwarku. Bansan lokacin da zamu sake haduwa ba ni ga tsufa ga lalurar kafa da ido. Kai kuma ga yadda Allah Yayi da kai sannan Maigari yace yafi son ka bawa garin nan iska har abin ya lafa"

Nasiha yayi ta musu akan rike mutumcinsu idan sunje birni kada son abin duniya ya rudesu.
*****

Danlami ya shigo gidansu da sauri ya tari Inna a kofar dakin Baffa yana faman haki.

"Inna tafiyar fa tazo har an samo a kori kura sun fara lodin kayansu"

Juyawa tayi ta sanar da Baffa sai ta ga har ya fito shima. Kwanansa uku yana son zuwa yiwa su Mal Fatihu sallama amma tsananin kunya ya hana. Inna ce tace ya kamata su ajiye komai suje kada ayi rabuwa ba ta arziki ba. Rashin yardarsu da auren yaran suna ganin ko wasu ne da wuya su amince.

Mayafi ta sako Baffa yasa hula suka je gidan. An fito da Baba kenan za'a saka shi a mota. Mukullin sabon gidan nasu Maigari ya bawa kanin Mal Fatihu dreba shine zaiyi musu jagora an nuna masa gidan.

Baffa yana jin nauyi haka ya matsa jikin motar suka gaisa da Baba. Inna ma haka yayi suka gaisa dasu Yaya kowa yana kokarin boye abinda ke ransa. Idan ka cire 'yan uwa na jini su Inna ne kadai suka zo yi musu sallama. Inna ta kawo wani madaidaicin buhu da Danlami ya biyota dashi tace gashi ba yawa. Ledoji uku ne a cikinsa daya shinkafa, daya wake dayan kuma waken soya. Sun rabu su Bilki suna ta kuka a gefe ma Inna sai da tayi nata na tausayin wannan iyali.
******

*KANO TA DABO TUMBIN GIWA*


Sati biyu kenan da dawowarsu Kano. Gidan ba laifi yana da fadi fiye da tsammaninsu. Kuma banda dakuna uku na ciki akwai wani a soro shi aka barwa Marwanu da Saifullahi 'ya'ya biyu maza da Mal Fatihu yake dasu 'yan kasa da shekara shabiyar. Jamila, Mawadda da kanwarsu mai binta Rafi'a an basu daki daya su ma. Dayan kuma na Baba ne yayin da Ade dasu Iya suke cikin na Yaya.

Iya da Inna kwanansu biyar suka koma sai dai Malam ya matsa Iya ta dawo saboda hankalinsa bai kwanta ba. Ga bakunta ga maigida a kwance suna bukatar sa ido na babba. To dayake abubuwa da dama sun faru ko kadan da ta dawo babu wannan rigimar ta matsawa Yaya. Ita kanta tasan Yaya mai kaunar jininta ce shiyasa yanzu take kokarin rike girmanta. Ade kuma ta sami aiki gidan wani tsohon minista a rijiyar zaki da gudu ta karba don tasan banda 'ya'yanta da take biyawa kudin makaranta dole ta nemi kudi saboda Mawadda.

Wata rana suna zaune ana cin dumame Mawadda tace "Yaya wai bazamu fara sana'a bane?"

"Nima tunanin da nake kwana dashi kenan amma na rasa me zamuyi"

Jamila da take gwanar kitso tace anjima idan sun shiga gaisawa da sauran makotan da basu sami damar shigarwa ba zasu sanar dasu ana kitso a gidan.

Da wannan shawarar suka fita. Gidaje uku suka shiga. Dayan da yake da 'yar tazara dasu harda gate mai kyau dashi. Sun shiga sun sami matar tana hada garwashi a bayan gidan da danta ya kaisu. Gefe ga mace ta lullube da bargo fuskarta tayi yelo. Tana aikin suna gaisawa tace suyi hakuri bata shigo ba aikin amaryar nan ne ya tsayar da ita. Hankalin Mawadda kacokan yana gareta tana kallo ta zuba wani turare a kasko wurin ya bade da kamshi ta daga bargon ta tura kaskon sannan ta sake lullube yarinyar.

Mawadda ta kasa hakuri ta tambayeta me take yi haka.

Murmushi tayi "gyaran jiki ne na amare da matan aure ko kina so?"

A kunyace Mawadda tace a'a sai dai fa da kyar ta tashi suka bar gidan. Komai ta ga matar tayi burgeta yake. A kwaba wannan a kwaba wancan ance duk amarya za'a shafawa jikinta yayi kyau. Matar kanta mai suna Zahra ta kula da yadda Mawadda ke kallonta ita kuwa ba gajiyawa kome tayi sai tayi mata bayani.

Suna komawa gida Mawadda ta hau hirar gyaran jiki tana bawa su Yaya labari abinda ba halinta ba. Kowa yana mata dariya ko a jikinta.

Bayan kwana biyu Iya tace waken soyan da Innar Dahiru ta basu suyi awara dashi mana suci. Ai kuwa anyi awara Mawadda da Rafi'a suka tsiri jajjagen attaruhu da albasa suka soya yana ta kamshi suka ci dashi. Abu yayi musu dadi suka fara tunanin ko zasu fara awarar siyarwa. Kamar da wasa suka yi ta mai kyau da dadi maimakon yaji sai wannan jajjagen na attaruhu da albasa. Makota suka shiga suna sanarwar sun fara awara amma har dare ko kaza bata shigo saya ba. Allah Yasa ba yawa suka yi suka cinye abinsu.

Bayan wasu kwanaki Marwanu da Saifullahi suka ce sun gano masu kayan sayarwa a gefen titi a sake suyar awara zasu kai can. Batare da gajiyawa ba sukayi ta rabin kwano kada ta sake kwantai.

'Yar roba suka samu Mawadda ta yanka kabeji, tattasai da albasa kananu tace idan sun zubawa mutum sai su dan diba a watsa a kai.

'Yan samarin ba girman kai suka tafi shiru babu wanda ya tsaya siyan tasu. Haka sukayi ta yi har sau hudu. A karo na biyar Saifullahi zaman ya ishe shi sai ya soma waka yana cewa

"tamu ba irin tasu bace...awarmu ba irin tasu bace" haka nan ya kirkiri kayarsa yana yi Marwana ya hau buga cokali akan kwanon da ake zuba mahadin awarar. Mutane suna ta kallonsu wani mutum yace bari dai a bashi yaji irin tasu.

Da rawar jiki Marwanu ya zuba masa Saifullahi yana cewa "kasan shi yaji iska na kadawa sai ido mutum yazo ya kasa gane hanyar gida. Mu kuwa namu a soye yake ga gishiri ga mai tauraro, wani abin sai kaci dai"

Mutane suna ta dariya mutumin nan yaci ya hau santi. Kan kace kwabo an siyeta tas kowa yana cewa an ga sabon salo.

Awarsu uku da fita Yaya taji sallama.

"Oh ni Haule sai mu hakura da awarar nan kuma a nemi wata sana'ar. Kitson ma shiru babu wadda ta leko"

Baba yace tayi hakuri komai lokaci ne sai ga su Marwanu da kwanuka kwalam. Dadi ya kama mutan gidan kar ma Baba yaji labari. Yana zaune bashi da wani abu da zai iya domin tallafin gidansa.

A ranar suka fara tsarin yadda kasuwar awara zata cigaba. Cikin dan kankanin lokaci ta sami karbuwa har a cikin unguwa. Da rana tsaka sai mace taki girki a tura gidan awara a siyo. Kitson Jamila shima lokacin aka gane masa ya zamana gidan basa rasa abin batarwa.

Ana haka Zahra mai gyaran jiki tazo. Bayan 'yar hira dayake tana da mutumci take cewa Mawadda idan bata komai ta rinka zuwa tayata aiki don lokacin bukukuwa ya gabato saboda karshen shekara ne. Abu kamar wasa Mawadda ta fara don yanzu ta saki ranta ba kamar da ba. Matsalarta kuma ta ragu sosai yanzu sai idan tayi tari, zabura, ko wani aikin da zaisa jikinta motsawa ba shiri shine fitsarin yakan digo. Duk da haka kuma Ade tana dan tarin kudadenta idan anyi albashi ta kaiwa masu kemis ta siyo mata magani da kuma na Baba na hawan jini.
******

Karshen zangon farko na karatu yayi inda Dahiru yayu matukar dagewa ya sami G.P.A 2.34, ranar harda hawaye yayi saboda Prof yace masa so yake yayi kokari sosai sai gashi duk da babu darasin da zai sake maimaitawa amma bai sami yadda yaso ba. Rashin turancin nan da kuma rashin wadatar lokacin karatu yasa abubuwan nasa sai a hankali.

Yanzu sunyi sabo sosai da Baba Prof yana zuwa gidansa lokaci lokaci. Ranar da ya sanar dashi sakamakonsa duk kuwa da Prof Abdulhadi ya ma riga shi sani ya nuna masa farincikinsa sosai. Babu abinda ya bashi mamaki sai dauke masa nauyin kudin makaranta da yayi kamar yadda yayi masa alkawarin yi masa wani abun mamaki tun baya. Baffa da Bilya har gida suka je yi masa godiya yace da na kowa ne. Burinsa kawai Dahiru yayi karatu idan Allah Ya bashi iko shima ya zama inuwar da wani zai raba a gaba.

Har suka koma gida suna yabon kyaun hali irin na wannan bawan Allah. Ya hada Dahiru da dansa Attahir wanda shi yanzu yake shirin shiga jami'ar abota shiyasa zumuncinsu ya karu sosai.

******

"Kin sake magana da kawarki kuwa akan zancen yaran nan? Shirun yayi yawa" cewar Daddyn su Qareeba yana kallon Dr Tani fuska ba fara'a.

Tasan za'a rina yanzu kusan kullum sai ya tado zancen. Sun gama bazawa 'yan uwansu cewa biki ya matso komai lokaci guda za'ayi amma har yanzu wata kusan biyar ba amo ba labari. Sai ta jera sati tana kiran Haj Mara bata daukar wayar. Idan ta dauka a dakila take amsawa tana mata karyar aiki ne yake rike Babawo ita kuma tun zaman kotun nan lafiya tayi mata karanci.

Dr Tani dai ta shiga muguwar damuwa yayin da Qareeba soyayyar Babawo ta hanata sukuni.

A can Kaduna kuma Haj Mara ta rasa yadda zatayi don Alh Sule tun wannan tafiyar tasa China har yanzu bata sake saka shi a ido ba. Kamar kullum bashi da zancen da ya wuce zama ne baya yi sosai shiyasa taji shiru.

Tana zaune ta rafka tagumi bayan sun gama waya BB ya shigo yana tangadi. Tashi tayi hankali a tashe ta soma masa fada. Shima ya daga hannu yana nunata da yatsa yana fada cikin muryar maye.

"Hajjaju wal Makkatu ina matata Mawadda?

Tsaki taja "Babawo ka shiga taitayinka fa. An baka aiki kaki tafiya har sun cike gurbin da wani. Baka da abin yi sai kokarin lalata rayuwarka ko"

Ya zauna kamar kayan wanki a kujera "to kiyi min aure mana ki gani idan ban shiryu ba"

"Za ka auri Qareeba din ne? Dazu ma nayi ta ganin wayar Dr din ai"

"Dangin dolayen??? Gaskiya kin ma cuceni Hajjaju. Ai ni duniya babu wata mace a idona sai Mawadda. Duk sauran mata sunansu majajjawa"

Duka ta kai masa "dan ubanka harda ni?"

Ya dago yatsansa yana dariya "kece lamba one....hahahahhh"

'Yan uwansa mata tayi niyar kira to amma dukkansu ta kula wani zukewa suke daga gareta. Ga miji baya nan ji tayi komai ya soma kwance mata. Hanyar hawa sama ta nufa kakarin aman BB ya tsayar da ita. A nan kan tsadadden kafet dinta ya kwara abinsa ya damalmale ciki. Kamar tayi kuka amma babu wanda zata ce yazo ya gyara ko da dattijuwar dake mata aiki ce kada a sami na bada labari haka ta dawo tana gyarawa yana ta zage zage.

"Hajjaju ni dake nace kada ki sola ni akan maganar Mawadda ki ka ki. Ki nemo min ita miyi aure a ragargaji soyayya ko kuma wallahi na ragargazo miki ta'asa a gidan nan"

Dena abinda takeyi tayi tana kallonsa shima ya kafeta da ido. Shi fa banda tsoron shiga kurkuku da tuni a kotun nan ya fadi gaskiya.

Duk wani tunaninta ya kulle mafita daya ta hango idan ba haka ba yaron nan a gaba sai ya hanata shiga taro.
*****

*SHEKARA KWANA: 2018*


Wata macece mai cike da kamala da haiba ta shiga ofishin likita bayan an kira sunanta. Sanye take da doguwar rigar atampa ta daura dankwalinta ta yane kanta da mayafi mai kyau wanda ya dace da kayan. Ko kadan shigarta babu bayyana tsiraici don indai zata sa mayafi to fa sai wanda ta tabbatar ba shara-shara bane. Duk da ba kwalliya tayi ba da ta wuce kwalli, hoda da man lebe amma kallo daya zaka yi mata kasan cewa mace ce da tasan me take yi.

Da sallama ta shiga ofishin ta sami likitan zaune akan kujerar marasa lafiya yayin da yake nuna mata tasa da hannu nufinsa ta zauna.

Cogewa tayi a tsaye "Ni dai zan roki a canja min likita gaskiya idan haka zaka rinka yi min"

Mikewa yayi yana dariya ya koma mazauninsa "abin bai kai haka ba zo ki zauna ranki ya dade"

Zama tayi suka gaisa tayi masa bayanin yadda take ji yanzu kusan ta gama warkewa daga lalurarta ta rashin rikon fitsari. Ya ji dadi sosai yace zata yi wata batare da wani magani ba domin su tabbatar da samun lafiyarta.

"Alhamdulillah Mawadda wannan sauki daga Allah ne da kuma dagewarki wurin shan magunguna da yin kegel exercise yadda ya kamata. To sauki ya samu sai maganar aurenmu ko?" Ya daga mata gira.

Kai ta girgiza tana murmushi "kayi ka gama. Tare muke da Baba yana wurin karbar magani na barka lafiya"

"Mawadda meyasa kike min haka ne?" Ya fada a sanyaye.

Dan hade fuska tayi "saboda kasan komai game da ni Dr Imran. Babu wani dalili da zaisa kai ko wani yayi sha'awar aurena. Sannan....kasan burina na rayuwa har yau bai cika ba"

Cewa yayi zai kirata kawai don idan suka fara wannan muhawarar zancen baya taba karewa. Kafiya ce da ita sai kace irin mutanen farkon nan. Akwai ranar da ya zolaye ta ma yace da a wancan zamanin tazo irinsu ne suke yin riko da manyan gumaka a kasa chanja musu ra'ayi. Baya mantawa ranar ne ta fara sakin jiki dashi saboda dariyar da ya sakata sai dai gashi har sun bawa shekara baya babu wani cigaba.

Wurin Baba taje ya gama karbar magani da Saifullahi suka fito suka tafi.

Mawadda Fatihu kenan matashiya yar kimanin shekaru ashirin da biyar. Taga rayuwa ita da gabadaya ahalin gidansu a dalilin fyade da akayi mata a gidan da take aiki.

Bayan dawowarsu Kano sunyi ta fadi tashi har Allah Ya buda musu da taimakon Anti Zahra mai gyaran jiki. Matar nan ta riketa da zuciya daya ta koya mata sana'ar gyaran jiki sosai. Da ita take biyanta idan sunyi aiki daga baya cikin ikon Allah ta kware Anti Zahra tace lokaci yayi taci gashin kanta. Sannan ita sun dade da barin unguwar ta koma tudun yola da zama. Suna zumunci sosai har yanzu. A lalace a wata Mawadda bata sami kudi ba ta rike dubu talatin. Budi suka samu na ban mamaki da tasbihi ga Allah. Matan manya da 'yan uwa bata taba rainawa har kasuwarta ta bude haka.

Idan an zo gyaran jiki tana yi Rafi'a na lalle Jamila na kitso. Mal Fatihu sai son barka don kuwa 'ya'ya matan da bai taba rainawa ba sun zame masa babban arziki. Hatta 'yan uwansu na kauye su Nana suna cin arzikinsu.

Shekaru biyar baya Malam kakansu ya rasu amma bai bar duniya ba sai da ya mayarda auren Ade da Baba. Itama ta dena aikatau yanzu sun hada kai da Yaya awara suke yi fin kwano biyar a rana. Marwanu da Saifullahi sun koma makaranta almajirai ke jigilar fita da awara mai sauce da ta sami karbuwa sosai.

Kanen Mawadda na wurin Ade suma bata barsu ba tana tura musu kudin makaranta. Gabadaya ta sauya ta koma Mawadda cikakkiyar mace mara tsoro wadda burinta daya yanzu a duniya shine tayi ido hudu da Haj Mara da rabin ranta BB.

Innar Fatihu da Iya sun kara tsufa amma duka gida daya suke. Gidan Mal Fatihu na kauye sunyi kakara da Maigari ya karba suka yi masa ciko suna biyansa a hankali yanzu gidan Tunga ya zama nasu.

******

Tun kafin ya fito daga motar yara sun yanyameta suna ta shafawa ana kiran sunansa. Wata leda ya dauko a gefensa cike da kayan kwalama na yara ya bude motar ya fito. Kamshin turarensa da sanyin ne suka biyo bayansa. Rufe motar yayi ya shiga rarraba musu suna karba ana murna.

Daga cikin gida Innarsa tana jinsu ta soma fara'a tasan ya iso. Shima sauri yayi ya shiga gidan wasu matasa biyu suka biyo shi da akwatinsa da wata katuwar jaka.

Inna ta tashi tana tafi farincikinta baya buya "marhabin lale lale da mutanen ya ma sunan kasar...?"

Dahiru yayi 'yar dariya yana durkusawa a gabanta "Inna na sameku lafiya?"

"Lafiya lau Dahiru....oh ni Indo tafiyar wata biyu shine ka sake cika haka duk ka zama wani basamuden kato."

Ai kuwa ta saka shi dariya sosai. Muryarsa ma ta kara zama ta manya baka ce Dahiru saurayin Mawadda bane mai aikin kubewa a gona.

Baffa ne ya shigo suna tsaye Inna tana ta yiwa Dahiru  tsiya yace  ta barshi ya huta mana.

Bayan Isha suna hira da iyayensa Inna ta soma mitar rashin aurensa.

"Sai dai kaci banza kaci wofi aje iyali ya gagara" cewar Baffa

Bangaren da aka gyara masa da sunan zama da Mawadda ya kurawa ido yana tunani. Inna ma wurin ta kalla wanda Danlami ne daga baya ya ajiye matarsa kafin su koma cikin gari suma.

"To....to an tabo inda yake masa kaikayi ya lula duniyar tunani" Inna tace tana nunawa Baffa yanayinsa.

Tashi yayi bai kara magana ba ya shige dakin da ya sauka zuciyarsa duk babu dadi. Ina Mawadda take? Ina zai kara ganinta? Kuma a wane yanayi.

Bayan tashinsa Baffa yayi ajiyar zuciya. Tsahon shekarun nan basu taba sanar dashi Maigari ne ya basu gida ba saboda haka za'a iya gano inda suka koma. Hana karya lokacin rasuwar Malam  ance masa Mal Fatihu yazo jana'izar mahaifinsa amma ko kwana baiyi a kauyen ba. Shi kuma lokacin baya gari sunje Kano daurin auren 'yar Baba Prof ne.

Rayuwar Dahiru ta dade da sauyawa tun bayar hduwarsa da Prof Abdulhadi. Mutumin ya amsa sunansa mutum ta kowace  sigar kwatancen halin kwarai. Bayan ya daukarwa kansa biyan kudin makarantar Dahiru yakan taimaka masa da ihsani. Shi kuma Dahirun sai ya mayar da hankali sosai kada ya bashi kunya. Anyi sa'a kuwa sakamakonsa ya rinka kyau yana gama aji biyar ko bautar kasa bai tafi ba Prof ya samar masa tallafi wato scholarship aka tura shi Turkey karo ilimi. Yaje yayi masters  dinsa ya gama cikin shekara daya da rabi. Wannan kudi da ya samu dasu ne ya rinka taimakon iyayensa. Gidansu yanzu idan ka dade baka garin sai yayi maka wuyar gamewa. Yayi masa gyara dan gaske don ma Baffa ya dage bazasu bar garin ba.

Bilya shima likkafa taci gaba yana da nasa garejin har 'yar mota ya saya. Danlami kuma sana'ar busasshen kifi yake wanda yake zuwa kudu ya saro kala kala ya kawo. Yana nan da teburinsa har wuri biyu a kasuwar sabon gari. Ummiyo tayi aure harda yara uku. 'Yan uwanta maza sune gatanta don bata rasa komai.

Dawowar Dahiru kasar ke da wuya ya sami aiki a kamfanin Etisalat. Abu ne da ba zato ba tsammani wani abokin karatunsa ya takura masa suka cike form online. Ashe kawunsa wani babba ne a kamfanin sai gasu suna isowa ba jimawa aka basu offer shi yana Kano abokin nasa yana Lagos.

Haka Allah Yake abinSa Ya baka a lokacin da baka zato bare tsammani. Yanzu haka wani aiki aka tura shi Qatar na wata biyu shine ya dawo jiya ya wuto Kano yau.

Da tunani kala kala ya kwana washegari lahadi da yamma yace zai koma saboda baije ofishinsu ya yi reporting ba. Inna dai tunin aure tayi masa da barazanar idan baiyi wasa ba watarana zai dawo ya tarar da mace an auro masa.

Jikinsa duk ba kwari tun jiya ya kasa samun sukuni da tunanin ko zai kuma ganin Mawadda. Shatara ta arziki yayi musu kamar yadda ya saba ya fita.

Da isarsa Kano gidan Baba Prof ya wuce. Dattijon arziki yayi matukar farincikin ganin Dahiru. Shima murnar yake har ya dauke hankalinsa  daga damuwa da tunani.

Yana cin abinci suna hira Haj Mama matar Prof ta shigo.

"Tuzuru na daya...kodayake Attahir ya  yiwa kansa fada magana tayi nisa yanzu kai kadai ka rage mana"

Prof yayi dariya don zancen da suke kenan ta damu da rashin aurensa. Ta zauna sun taba hira ya bata tata tsarabar tayi ta sa masa albarka. Da ta fita Prof yake masa fadan yaushe rabonsa da gidan Dr Auwal.

Mukulli yasa yana sosa kai hade da murmushi.

Prof yace "irin haka ko ban fada ba kasan ba dadi ko kazo ka wuce gidansu ka shigo nan. Shekaru sun ja ko kuwa riko ka fara ban sani ba" ya kare yana dariyar rigimar da ta hado Dahiru da uwar dakinsa Dr Tani.

Zaman gidan dena yiwa Dahiru dadi yayi tun bayan da Haj Mara ta samu ta yanke alakar dake tsakaninsu ta hanyar tura BB Dubai wai ya karo karatu. Ba kunya ta sharawa Dr Tani karyar  babansa ne ya tura shi wai sai kura ta lafa akan case din Mawadda. A take Dr Tani ta nuna su a wurinsu babu komai ana iya auren ma a tura Qareeban. Son 'ya tayi aure yasa bata tunani yadda ya dace.

Qareeba bata da aiki sai koke-koke yayin da iyayen suka biye mata. Abu yayi gaba BB yafi shekara bai dawo ba. Tun suna bibiya har suka hakura. Albashin Dahiru tsabar kyashi yasa ta rage shi ya koma dubu biyar.

Haka yayi ta karatunsa har Prof ya gama cukucukun nema masa scholarship da admission. Sai da komai ya kankama yaje sanar da ita. Yana fada mata zaiyi tafiya bata tsaya taji me zaice ba ta tabe baki.

"An gaji da karyar bokon za'a koma gida kenan! Dama ido na zuba maka wai nan karatu kake kana mai shara da wanki ni ban taba jin ko alfarmar kudin registration ka roka ba. Ga kwadayi yana dawainiya da kai ka shigewa iyalin Prof Abdulhadi tun da suka dawo unguwar nan"

Takaici ya hana Dahiru magana suna haka Attahir ya shigo dama a bakin mota ya sameta. Hannu tasa ta yafito Attahir yazo ya gaisheta.

"Dama sanin hali na mutanenmu na kauye yasa nace kada yaron nan ya cuceku ya fake da mu wallahi iyakarsa shara da kuma wanki da guga. Idan ma wani abin yayi a gidanku kazo nemansa don yanzu haka ma zancen tafiya yake min to ka shaidawa iyayenka tun wuri maiaikinmu ne kawai"

Daga Dahirun har Attahir aka rasa me baki magana. Dama copy din admission letter dinsa Prof ya bayar yace ya bashi ya nuna musu.

Tun daga wannan ranar Dahiru bai sake shiga gidansu ba kuma duk zuwansa ko a hanya bai taba cin karo da wani dan gidan ba. Maigadin da ya sani ya dade da aka canza shi.

Alkawarin zuwa gidan yayi cikin sati a gaisa albarkan shekarun baya. Ya sami labarin duka mazan sunyi aure sai Hajiya Qareeba kadai ta rage. Duk abinda Dr Tani tayi dominta bukata bata biya ba.

Canja hirar yayi yace Prof yazo su ga sabuwar motarsa. Maimakon murna Haj Mama dai fadan aure ta sake dasawa wai bata ga amfanin kwalisa babu matar da za'a burge ba.
*****

Sati biyu kenan da Mawadda ta karbi sakamonta na makarantar yaki da jahilci da tayi. A daya bangaren kuma yau aka fara bikin Rafi'a.

Biki suka shirya daidai karfinsu na burgewa da kamun kai. Jamila ma ta dade da Ja'e ya mayar da ita da izinin babarsa yanzu gidan zai rage Mawadda kawai da 'yan maza.

Danlami sarkin shige shige ne Allah Ya kawowa katin daurin auren har kasuwa inda yake sana'arsa. Sai da ya nanata tambayar wanda ya bashi shima dan garinsu ne ya tabbatar masa da gaske kanwar Mawadda ce. Ranar da wuri ya tashi ya tafi ofishin Dahiru.

"Kai kuma daga ina haka kamar an jeho ka? Mutum da 'ya'ya biyu ya kasa girma"

Katin ya ajiye masa kafin ya mika hannu. Alkawari na yiwa kaina zan nemo maka Mawadda to ga katin auren kanwarta. Abu daya zaka bani ladan aiki shine ka ban mukullin motarka don Allah in zaga garin nan da iyalina muma mu kashe selfie.

Dahiru bai ce komai ba bayan karanta katin sai mukullin da ya jefa masa.

"Gobe da safe kafin na gama shiryawa ka dawo min da ita"

Danlami ya dauka yana ta murna yayi waje. Tabdi yau yasan Azima zata jidadi. Matarsa akwai saukin kai shiyasa yake son burgeta.

Dahiru kuma adaidaita sahu ya nema ya kaishi har layin gidan nasu ya tabbatar ba karya bane. Haka kawai yaji gabansa na faduwa wai cikin taron jama'ar dake waje ko cikin gidan nan Mawaddansa tana ciki.

Komawa yayi gidan da yake haya tare da wasu marasa auren na wurin aikinsu. Ranar yayi bacci mai dadi amma cike da zulumin ko tayi aure.

Washegari a daddafe ya kai karfe shida a office. Gida ya koma ya shirya yayi kyau sosai kamar ba Dahiru mai ahirin ba.

Su Mawadda ana ta shirin kai amarya suyi nan suyi can. Ba ita ba ba Rafi'a ba kowacce tayi kyau sosai. Jikinsu ya saba da gyara kowa na sha'awarsu.

Dahiru na zuwa ya tarar da motocin daukar amarya sai kawai ya shiga cikinsu yayi parking a karshe. Motarsa tafi ta kowa kyau da haduwa a wurin mata suka fara kokarin shiga. Lock ya saka kawai yana ta murmushi shi kadai ko a yaya zasu hadu da Mawadda.

Wata mai tsaurin ido cikin 'yan matan amarya ce taje ta fadawa Mawadda wani abokin ango yaki bude motarsa. Mayafi ta dora kan riga da skirt din jikinta ta ce bari ta duba idan angon yace wadda za'a saka amaryar a ciki baka ce kila mutumin amarya yake jira.

Yarinyar ta fada mata ruwan goro ce mai masifar kyau.

"Bari naje na gani idan bai daukeku ba da motarsa mai masifar kyau ko iyaye ya taimaka ya diba" ta fada tana murmushi tayi waje.
[08/01 8:32 pm] : *GUMIN HALAK...*💰12

*Batul Mamman*💖


Tana fitowa wata yarinya ta kwala mata kira "Anti Mawadda mai waccan motar yace a fada muku a tasa za'a dauki amarya"

Kallon motar tayi ta ga baka ce kamar yadda angon ya fada mata. Kamar ta juya sai ta hango motar da aka kai karar mai ita ga mata da yawa da basu sami tafiya ba kuma dangin ango suna ciki kowane lokaci zasu iya fitowa a tafi. Yanke shawarar rokarsa tayi don duk tunaninta cikin tawagar angon yake.

Sannu a hankali take takawa da takalminta mai tsini tayi kyau sosai.

Tun da ta doso motar Dahiru ya nemi nutsuwarsa ya rasa. Zuciyarsa kamar ta fito saboda halin da ya shiga na ganin macen da har yau bai taba son wata kwatankwacin yadda yake sonta ba. Matar da tunaninta bai taba barinsa ba tsahon shekara takwas da basa tare. Idonsa yaji yana masa zafi alamun taruwar kwalla ya shiga mika godiya ga Allah da rayuwar Mawadda bata tagayyara ba kamar yadda yayi ta jin tsoro. Kashe motar yayi ya kifa kansa akan sitiyari yana kokarin daidaita tunani da nutsuwarsa don a yadda yake ji a lokacin cikar kwanciyar hankalinsa shine ya rungumeta.

Ita kuma tana karasowa taji motar a kashe kuma da yake glass din tint ne bata iya ganinsa. Tagar mazaunin dreba ta matso sosai ta dan duka kafin ta girgiza kai tana murmushi a ranta tace ashe ma babu kowa shiyasa ba'a bude ba. Dahiru yana zaune yana kare mata kallo shi kadai yana murmushi ganin ta sake dukawa tana kallonsa wanda a zahiri fuskarta take kallo ta gilas din.

Sassanyan murmushi tayi kamar tasan ya shagala da kallonta ta gama turo bakinta da ya sha pink din janbaki kamar wadda zata dauki hoto sannan ta mike ta barshi da dariya a hankali. Juyawarta kenan zata koma yayi saurin budewa ya fito kada ta tafi baiyi mata magana ba.

Tsayawa tayi cak tana tunanin me motar nan ya gama da ita. Yanzu da ta dauko soson powder ta sake gogawa a fuskarta kamar yadda tayi niyya ai ya cuceta. Irin haka tunda ya iya yin shiru da farko ai da ya hakura gabadaya sai ta tafi ya fito.

Shiru ya wuce na wasu 'yan dakiku ita taki juyawa saboda yadda jikinta ya bata kallon ta ake yi shi kuma tsabar farinciki ya rasa me zaiyi. Daga kafa tayi zata yi tafiyarta kamar daga sama taji an ambaci sunan da mutum daya ke kiranta da wata murya daga can kasan makoshi har sai da tsigar jikinta ta tashi.

"Mawaddatan wa Rahma"

Mutuwar tsaye tayi jikinta ya soma rawa. Dahiru ya tako a hankali ya zagayo gabanta ya tsaya.

Anya zuciyarta za ta gaskata abinda idanunta suke gani kuwa. A hankali kamar mai tsoron kada ace karya ne abinda ke gabanta tace

"Yayanmu?....Yayanmu ne?? Yayanmu Dahiru???"

Kamar shi amma wannan yafi wancan komai sai dai bata jin akwai canjin da zaisa ta kasa gane fuskarsa duk kuwa da ya boyeta cikin kyakkyawan sagensa.

"Ashe dai zaki gane ni" ta sake jin muryarsa a karo na biyu.

Mamaki da farinciki ne suka lullubeta a lokaci guda. Ta bude baki tayi masa magana amma ko harafi daya ta kasa hadawa. Dahiru kuwa ganinta ya sauke masa duk wata sauran damuwar dake ransa.

Tabata taji anyi ta baya ta juya a firgice sai ta ga 'yar yayarta Bilki.
"Anti Iya tace kizo ki fitar da Anti Rafi'a ko tayi mata duka wai suna ta kuka ita da  Ade da Yaya sun hanata fitowa ga mutane na jira"

Sauran yayyen nasu duk suna gidan amarya ana karasa gyare gyaren da ba a rasa ba. Ita kadai ta rage sai su Iya da Innar Fatihu.

Yarinyar ta kama hannunta tana ja Dahiru yayi mata alama da hannu akan ta tafi.

Tamkar wadda iska zata dauka haka take jin jikinta ta soma tafiya kawai taji yace

"Kinyi aure?"

Ko da ta juyo ita yake kallo suka hada ido karo na farko bayan shekarun da suka yi basu hadu ba. Kai kawai ta iya girgizawa saboda ta kasa magana sai idanunta da ta kautar daga nasa.

"Alhamdulillah, amma kina da saurayi?"

Samari kai, ita manema aurenta yawa garesu amma tafi kowa sanin dalilin da ya hanata bawa kowa cikinsu dama. Dr Imran ne ya fado mata a rai sai ta gyada kai.

Yanayin fuskar Dahiru bai sauya ba duk da haka ya sake cewa "Iyaye sun shiga maganar?"

Wannan karon sai da ta murmusa kafin ta kuma girgiza kai.

"Wai, Allah Ya soni ina da sauran dama"

Wayarsa mai kyau da tsada ya miko mata ko bai fada ba tasan me yake nufi. Numbarta ta saka ta mika masa.

Tsayuwar wurin tayi mata wuya kuma tasan ana jiranta sai kawai ta kuma juyawa a karo na uku ya sake dakatar da ita ta hanyar cewa

"Mawaddatan wa Rahma...naji dadin sake ganinki. Sai na kira mu gaisa"

Sai lokacin ta tuna ko gaisawa basuyi ba. Tana juyawa ya shige mota ya dago mata hannu. Bata bar wurin ba sai da ya fita daga layin ta sauke ajiyar zuciya.

Har suka shiga mota a hanyarsu ta zuwa gidan amarya bata dawo daidai ba. Lokaci lokaci take sakin murmushi ko tayi ajiyar zuciya.

*****

Gidan Bilya ya wuce kana ganinsa zaka yi tunanin anyi masa albishir da kujerar Makka ne. Furaira matar Bilya ya gaisar ta dauke kai.

Yayi dariya don yasan dalilin fushin "matar Yaya kinsan babban wa uba ne matarsa kinga ta zama uwa. Fushin me kike yi dani kuma yau"

Ta kula wani nishadi ma yake yi tayi kwafa "nagode da wulakanci Dahiru. Wai kai kayi kudi kana nuna min iyakata"

"Assha me kuma ya kawo wannan maganar don Allah" ya fada murmushi na bayyana a fuskarsa mai nuni da rashin damuwa da fushin nata.

Hakan ya kara kular da ita "ba laifinka bane, laifina Hansa'u ne da ta dage sai kai. Tukwicin da ka ga ya dace ka bani kenan duk wahalar da muka yi da kai lokacin karatunka ka guji kanwata ko"

Hakuri ya bata don wannan rigimar kullum ya shigo sai anyi. Saboda shi kanwarta gidan ma ta dawo amma idan ka cire gaisuwa baya yarda wata hira ta hadasu. Ya tabbatar baya sonta bai ga dalilin sanya mata burin karya ba.

Tare da yayansa suka yi sallar magariba sannan yaci abinci ya tafi gida.

A daren yayi ta kiran Mawadda wayarta chaji ya kare kuma da ta dawo gida ta nemi chaja ta rasa. Haka nan taji babu dadi don tana tunanin da wuya idan Dahiru bazai nemeta ba. Yadda ta damu da rashin chajin har Ade sai da tayi magana tace ko akwai kiran wanda take jira ne. Wannan maganar ce tasa ta jin kunya ta hakura ganin an soma yi mata dan biki.
*****

Washegari ta kama lahadi Dahiru bazai je office ba. Baba Prof ne ya gayyace shi rakiyar daurin aure suna dawowa yace masa lallai ya wuce gidan Dr Auwal yau su gaisa da mutan gidan.

Bazai taba iya ketare maganar Prof ba shiyasa bayan ya kaishi gida ya tsaya. Horn yayi maigadi ya bude suka gaisa ya fada masa yazo wurin masu gidan ne. Maigadi ya ga babban mutum irin wannan ba wata-wata ya bude masa.

Shigarsa ke da wuya wata motar ta shigo. Matsawa yayi wurin mutumin da ya fito daga ciki ya mika masa hannu suka gaisa.

"Kamar nasan fuskar nan"

Dahiru yace "Safwan ko? Dahiru ne mai wanki da shara"

Idanu Safwan ya ware ya shiga zagaye Dahiru sannan ya saki ihu "Ahirin kaine? Tabdi, muje ciki"

Sun shiga korido da zai sada su da kofar falon Safwan ya rike masa hannu yana ta zuba surutu Dahiru ya tsaya daga bakin kofar.

"Ya haka muje mana"

"Ka shiga ka fara sanar dasu. Bai dace na shigo kai tsaye ba"

Safwan yace hakane ya shige da sauri yana ta mamakin ganinsa.

Dr. Tani tana yanke farce da nailcutter ya shigo ya zauna a gefenta.
"Mummyna..."

Dadin ganin autanta tayi yayi fes dashi ga uwar kiba yana ta hadawa.

"Ka ci abinci kuwa?" Ta tambaya don tasan matarsa da kyuyar girki ita kuma bata yarda danta ya wahala ba.

Kamar wani wawa irin maganar shagwababbu yace "Kai Mummy kema kinsan naci. Tun ranar da ki ka fada mata idan bata soya min chips da kwai yadda nake so zaki sa nayi mata kishiya ta canza. Yau ma shi tayi min da safe"

Dahiru yana jinsu ya girgigiza kai "ana jika har yanzu"

Kamar Safwan ya jiyo shi ya buga tsalle ya mike "Mummy albishirinki"

Murmushi tayi a zatonta ko jika zata samu "goro fari kal"

"Tare muke da Dahiru. Dahiru mai shara da wanki!"

Wani uban tsaki ta ja har zuciyar Dahiru.

"Me kuma ya kawo shi? Shi kadai ne ko an rakito iyali daga kauye a fake da zuwa gaishemu nan kuwa yawon maula ne"

Safwan ya kece da dariya "Hmmm baki ganshi bane tare muke yana bakin kofa bari na shigo dashi"

Rai a bace ta kai masa duka "kai meyasa kake abu kamar wawa ne. Ya zaka kawo min shi nan. Yana shigowa falon nan zai soma tashin warin rana kuma kasan Daddynku yana gida yanzu zai hau fada. Kace ya koma daga waje gani nan zuwa"

Ran Dahiru yayi bakikkirin. Da Allah bai daga shi ba yau baisan inda zaisa ransa ba wannan wulakanci. Wato kallon da masu kudi suke yiwa talakawa 'yan kauye kenan. Idan sun zo ba'a taba zaton alkhairi ya kawo su sai maula. Ficewa yayi ya koma mota abinsa kamar ya tafi sai wata zuciyar tace ya zauna. AC ya kunna ya rufe kansa ya dauko waya yana kallon numbar Mawadda. Kiranta yake son yi ta bashi dama yaje gidansu su gaisa yaji yadda rayuwarsu ta kasance.

Dr Tani tare da Safwan suka fito tana ta yatsina hanci. Idonta ne ya sauka akan motar tana cikin cewa ina Dahirun yake. Bata ankara ba ta ga wani mutum ya fito daga motar da ta dauke mata hankali. Kallonsa tayi daga sama har kasa babu abu mara tsada cikin suturarsa.

Yadi ne a jikinsa ruwan madara sai hula da takalmi ruwan toka. Kamshin turarensa har inda take tsaye.

Dahiru ya tako har kusa da ita ya duka "Hajiya barka da rana"

Wayyo dadi jiki na rawa tace "Safwan jeka ka taso Qareeba tayi bako"

Dariya ce ta kama Dahiru yadda yaga tana yi duk ta rude halinta bai chanja ba na son aurar da 'yarta . Ganin haka ta dan nutsu tana kallonsa. Sai ya wayance "Hajiya dadin ganinku ne kawai. Baki ganeni ba ko. Dahiru ne mai wanki"

"Laaaaaaaa" ta hangame baki cike da tsananin mamaki mara misaltuwa. Sai kuma ta sake kallonsa ta kalli motar "shine ka tsaya a waje Dahiru kamar wani bako kai da gidanku? Safwan ma dai wani lokacin ba ya aiki da tunani. Me zai sa ya barka a waje"

Ba don da kunnensa yaji ba kila da shikenan sai ya zata har zuciyarta hakan ne.

"Nan ma yayi Hajiya dama nace bari nazo mu gaisa ne zan wuce"

Dan shan kunu tayi "haba Dahiru ka shigo ku gaisa da Daddynku mana"

Mutum mai fuskoki ya fada a ransa. Bayanta ya bi duk ta gigice saboda yadda ta ganshi. Mai aiki ta kira tace maza a soya kaza a hado masa fruitsalad da juice mai sanyi. Ta nuna masa kujera tace ya zauna yace kasa ma yayi ya zauna a kan kafet.

"Dahiru shiru kuma shekara da shekaru ka manta damu" a matse take taji yadda akayi ya sami wannan cigaba amma ta daure kada ta nuna hali.

Gudu suka ji daga bene Qareeba da Safwan suna rige rigen saukowa. Daga ita sai riga da wando na bacci domin kuwa shigar Safwan ya tayar da ita sai hula da ta saka.

"Dashiru Ahirin!"

Ai kuwa sai da gabansa ya fadi saboda tunawa yayi da yadda take matsantawa rayuwarsa a baya.

Kusa dashi taje ta zauna tana ta tafa hannu.
"Ahirin kaine haka? Mummy kin gani"

Dr Tani tayi murmushi "na gani bari na taso Daddy yazo ku gaisa".

Tana tashi su Qareeba suka shiga bugawa 'yan uwansu waya wai ga Ahirin yazo ance mata da mota. Sai da ta leka ma ta ganewa idonta ta dawo tana ta damunsa. Shi kuwa kallo daya yayi mata tun saukkwarta ya sunkuyar da kai. Idan ba ballagaza ba ga kiba ta soma yi ta fito da kaya irin wannan duk motsinta jiki na rawa. Kuma a haka mahaifiyarta ta gani amma ko a jikinta.

Ba jimawa sai ga Daddy da Dr Tani. Shima ya nuna farincikin ganinsa har yake tambayarsa me yake yi yanzu. Kunnuwa Dr Tani a nbude taji yace yana aiki da kamfanin sadarwa na Etisalat.

Kasa daurewa tayi tace "amma kace mana zaka tafi munyi zaton kana kauye Qareeba kusan kullum sai tayi min zancenka"

Daddy ne ya take mata kafa don ya soma fahimtar daga nan ina ta dosa.

Dahiru yace "lokacin scholarship na samu na tafi Turkey masters"

"Wow! Ahirin Turkey fa kace. Can birnin Turkiya dai da na sani? Wowwww gaskiya big wowww ni Ghana Daddy ya turani ba rabon mu zauna wuri daya. Kasan nima can na nemi admission da farko" inji Safwan

Qareeba abu ya burgeta cewa take "tun haduwarmu ta farko nasan kai na daban ne. Shiyasa fa nake cewa Mummy ta dena maka wula...."

"Toh, toh, toh a tashi haka ku barshi ya sha iska" Daddy yace ganin za'a fara rashin hankali. Dr Tani tana kitchen ita ta karasa suyar kazar.

Ana kawowa ga su fruitsalad tray cike taf da kayan alatu na tarar bako Dahiru ya mike abinsa ko ruwa bai sha ba.

"Hajiya nagode amma cikina a cike yake"

Duk yadda taso yaki zama. Ba fariya yake son yi ba amma irin wulakancin da ya kunsa a zama dasu shi kadai ya sani. Kuma nata yafi masa ciwo tunda ita duk a cikin kyamar talaka ne. Yau daya komai ya chanja saboda ya zama wani.

Abin mamaki har waje ta rako shi tare da yaranta suna ta daga masa hannu ta ce ya rinka zuwa don Allah zumunci dadi ne dashi.
******

Tun asubar fari Haj Mara ta tashi ita da masu aikinta biyu ana ta gyaran gida Alhaji zai zo weekend. Ya sake samun budi fiye da shekarun baya yayi suna a Nigeria sosai ta fanin sana'arsa ta chanji.

Tsakaninsa da Haj Mara ba yabo ba fallasa. Kudi dai da sauran nauyin da yake kansa yana matukar kokarin saukewa amma fa sai yayi wata biyu bai zo Kaduna ba.  Gida daga ita sai masu aiki bata jindadi ko kadan tace zata dawo Lagos yaki amincewa. Wata rana tayi masa zuwan bazata a tunaninta kadagarun bariki yake ajiyewa ta ga babu kowa don ba zama yake sosai ba a nan din amaryarsa tana Abuja. Tafiye tafiye ne dai ta rasa gane ina  yake yawan zuwa kullum ka taba shi yace baya nan. Tayi fadan tayi mitar har ta gaji. Shi kuma yace idan tana son gida ya dawo daidai ta dawo da BB daga inda ta tura shi taki amincewa.

Anyi girke girke gida yasha turaren wuta taci ado ana jiran mijin da ta dade tana kewa kusan wata uku.

Tana zaune taji horn ta tashi ta koma dakinsa ta hada masa ruwan wanka tare da fesa airfreshner mai dadi. Bude kofar dakin tayi zata sauko kasa shi kuma ya shigo rike da hannun wata ga yara uku maza a bayansu.

Zaro idanu tayi ta ja da baya ta ga iya gudun ruwansu sai gani tayi ya taimakawa matar ta kwanta akan gadon da ta gyara da kanta ya rufa mata bargo.

Ya juyo "Hajiya ashe kina nan "

Yaran ya nunawa kofa yace su koma kasa su bar Mama tayi bacci yana zuwa. Babban cikinsu ya kama sauran biyu suka fita.

Haj Mara fa jin kanta take kamar ba ita ba. Me yake faruwa ko mafarki ne take yi?

Alh Sule ya katse mata tunani "Hajiya sauko kasa muyi magana"

"Kana son ganin haukana ne a gaban wadancan yaran ko me? Malam idan kana da abin fada ka fada min a nan kafin ka ga ba daidai ba"

Matar dake kwance akan gadon tayi juyi tare da mikewa a guje ta shige inda take tunanin bandaki ne tana kwara amai.

Bayanta Haj Mara ta bi "ni zaki yiwa bariki a cikin gidana? Kinsan a ina kike kuwa?Alhaji kalma daya nake son ji daga gareka indai ba ka fara shaye shaye bane wace 'yar....din ce wannan?"

"Matata ce" ya fada a takaice sannan ya wuce cikin bandakin yana yi mata sannu. Ruwan wankan ya taba yaji bai huce ba yace tayi wanka. Yana rufe kofar bandakin Haj Mara tana cakumar wuyansa.

"Wadancan shegun 'ya'yanka ne?"

Hannuwanta ya kama ya yarfar ya nunata da yatsa "jinina ne kada ki sake zagin kowa a nan. Ki wuce muje nace ina da magana dake"

Har wani haki take yi na tsananin bacin rai ta sauko nan ta sami 'ya'yanta mata zaune tare da yaran da Alh Sule ya shigo dasu.

Sun gaishe da mahaifinsu yana tambayar kowacce iyalinta sannan ya fara musu jawabi.

"Nasan zakuyi matukar mamaki idan nace muku yaran nan kannenku ne mahaifiyarsu tana sama mun taho bata jindadi. Kuyi hakuri da rashin sanar daku da nayi hakan ya biyo bayan fushin da nayi lokacin da Babawo ya yiwa yarinyar nan fyade ku kuma duka kuka biyewa mahaifiyarku akan marawa karya baya. Duk da haka nasan ban kyauta ba amma ina so don Allah ku bani hadin kai wurin ganin na hada iyalina yadda ya dace"

To su dinma sun dade da dawowa daga rakiyar Hajiyan tasu shiyasa suka bashi hakuri tare da nuna masa in sha Allahu zasu rike kannensu.

"Hajiya baki ce komai ba" ya waiga inda Haj Mara ta zauna sai dai babu ita babu alamunta.

Hayaniya suka ji daga sama ya tashi da sauri yace su jira yana zuwa.

Haj Mara tunda yace yayi auren nan ta koma dakin. Matar na fitowa daga bandaki ta daga hannu ta wanka mata mari sannan tace
"idan ma wani salon karuwancin ne ya hadaku kizo ki fita tun wuri. Nasan Alhaji bazai taba aure bai fada min ba don ban bashi wannan damar ba"

Murmushin gefen baki matar tayi tace "ashe?"
Sannan ta wuce ta zauna kan kujerar gaban madubi ta janyo man da hannunta ya fara tabawa ta soma shafawa.

Haj Mara ta daka mata tsawa "ba dake nake ba?"

"Bana son ihu kinga ba lafiya gareni ba"

"Eyyeeee sannu kwankwararriya ke nifa wanda ya ajiyeki ma bai isa ba"

Tashi tayi ta mikewa Haj Mara tsayinta "wanda ya ajiyeni ya isa kuma idan kika nemi tayar masa da hankali wallahi zan baki mamaki. Yanzu ma ra'ayin kaina ne naga ya dace yarana su san 'yan uwansu har ki ka ganmu. Kinyi sa'a laulayi ya sakani a gaba kuma bani da burin da ya wuce farantawa mijina da na nuna miki matsayinki a gidan nan"

Zuciya ce ta debi Haj Mara tana ihu ta kai mata duka irin na mahaukatan nan. Zata rama Alh Sule ya shigo kawai sai ta bage a kasa harda kwance tawul ta soma kuka.

Alhaji na zuwa ya ture Haj Mara ya janyo matarsa ya rungume.

"Sannu Yasmin babu inda ke miki ciwo? kwanta bari na dauko miki jakar kayanki."

Sakato Haj Mara tayi ganin wannan abu yarinyar da bata fi sa'ar 'yarta ta biyu ba ta wani lafe a jikinsa ga tawul dinta yana reto ya kusa faduwa sai karairaya take shi kuma duk ya gigice.

Yana juyowa marin Haj Mara yayi "idan wani abu ya sami cikin nan sai na bata miki rai. Wannan rashin hankalin na gaji da dauka. Duk da nima nasan da laifina akan kyaleki da na rinka yi amma ki sani wallahi baki fi karfina ba"

Bayan Yasmin ta shirya ya sake hadasu duka a falo. Haj Mara sai kukan zuci ta rasa me yake mata dadi.

"Kamar yadda ku ka sani shekaru takwas rabon Babawo da kasar nan. Hajiya ta tura shi kasar waje nayi nayi harda ku nasa ku tambayeta amma tana ganin kamar cutar da dan cikina nake son yi taki fada mana inda yake. To Alhamdulillah Allah Yasa nasa an nemo min shi ta hanyar binciken account din da kika rinka tura masa kudi. Duk abinda Babawo ya zama a yau sai muyi hakuri mu rungume shi tare da fatan shiriya"

Haj Mara na jin haka ta mike tsaye "yana ina?"

Zuwanta Dubai uku inda ta tura shi amma bata samunsa. Idan ta matsa masa da tambayar yana ina sai yace tafiya ce ta kama shi. Abinda bata sani ba shine ko wata shida baiyi a Dubai ba ya koma Italy.

Sai bayan kusan rabin awa BB ya iso gidan. Haj Mara ta manta da batun kishiya danta da take ta kewa take jira. Karar bude gate taji ta fito cikin sauri Alh Sule ya girgiza kai. Wannan makauniyar soyayyar da take yiwa danta ba gata bane gare shi ko kadan.

Motar bata gama tsayawa ba ya duro waje ya yo kan Hajiyar tasa yana ihun murna.

"Yooo, yooo Hajjaju meen.....see my Maama looking gorgeous"

"Na shiga uku" Haj Mara ta furta a hankali kwalla na sauko mata.

Wai yau Babawo da take mugun ji dashi ne haka sanye da wani mahaukacin jeans mai mugun fadi duk an gutsire kansa da kyar ya wuce gwiwa. Ga takalma kamar wanda zai shiga daji farauta manya manya. Rigar fara ce ta dame kwanjin da ya tara abin takaici da bakinciki yana sanye da sarkoki, dankunne ga gashi yayi kalba har kafada.
******

Kusan minti goma da zuwan Dahiru layin gidansu Mawadda yana ta tunanin kiranta zaiyi yace yazo ko kuwa ya tafi daga baya ya kira yace zai zo?

Can dai wata zuciyar tasa ya kirata. Gidan da sauran 'yan biki amma saboda gajiyar da suka yi tana daki a kwance kan gado. Yaya da Ade suna ware kayan gudunmawa saboda idan basu hadasu wuri daya ba wasu sai su salwanta gida na taro.

Tana jin waya tayi zumbur ta tashi zaune ta dauka tare da ficewa daga dakin ta koma kitchen.

Sallama tayi ya amsa mata sai kuma duk suka yi shiru sai bugun zuciyoyi.

"Ina cikin layinku fa. Zaki iya fitowa mu gaisa?" Ya katse shirun nasu.

Abin yazo mata a bazata sai kuma ta fara tunanin me zata ce a gida.

"Kunya nake ji Yayanmu"

Yayi 'yar dariya "nima haka Mawadda"

Suka sake yin shiru kamar wasu sabon shiga.
"Ina zuwa" taji yace sai ya kashe wayar.

Tunani ta fara me zaiyi ya kashe wayar sai ji tayi wani yaro yana cewa wai ana sallama da Baba inji Dahiru.

Gabanta ne ya fadi lokacin da Inna tace ace yana zuwa. Ita aka kira taje ta fadawa Baba ya fito yana cewa basuyi da kowa zai zo ba. Ita dai shiru tayi har ya fita. Yanzu jikinsa yayi lafiya sosai duk da shanyewar barin jikin amma yana zuwa gashi sosai yana iya tafiya da wasu abubuwan da kansa.

Daki Mawadda ta koma tana ta tunanin ya zata kasance.

Mal Fatihu yana fita Dahiru ya iso kofar gidan ya durkusa a gabansa. Har suka gaisa bai gane shi ba saboda kansa na kasa.

"Samari sai dai kuma ban waye ka ba"

Dahiru ya dago kai "Baba nine Da..."

"Dahiru? Laila ha illallahu kaine kuwa. Ikon Allah tashi tashi don Allah. Muje daga ciki"

Sosai mamaki ya kama Baba. Yana son Dahiru ko don yadda ya nuna soyayyarsa ga Mawadda a lokacin da ta rasa masoya.

Gyaran murya Baba yayi yana ce musu su gyara fa shi da bako ne. Ade ta kira Mawadda "yi sauri ki gyara dakin soro babanku yayi bako"

Dakin baya bukatar wani gyara saboda yau tun safe gyaran gida akeyi dama kujeru ne a ciki da dan tebur. Tana fita Baba ya shiga dashi yace ta kira su Iya su zo su ga bako.

Dahiru kunya ta rufe shi da ganin su Iya, Inna, Yaya da Ade. Dukkaninsu babu wanda ya nuna rashin jindadin ganinsa duk da yadda basu ji dadin irin rabuwar da akayi da iyayensa ba.
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰13

*Batul Mamman*💖

Baba yana ta cewa ya zauna akan kujera amma Dahiru sam ya kasa yana mai jin nauyinsu a matsayinsu na iyayen Mawadda da kuma mutanen da kanwarsa ta bada gudunmawa wurin tarwatsa abin da ya rage musu na farinciki.

Su kuwa kowa murmushi yake yi da sake ganinsa a lokacin da suka cire tsammani. Gashi alamu sun nuna ya samu sukunin rayuwa wannan ma kuma abin farinciki ne garesu.

Iya baki har kunne tace "Dahiru ka zama babban mutum iyali fa?"

Kai ya sake sunkuyarwa Yaya tana dariya tace "Ni Haule! shekarun nan basu sauya maka hali ba ashe. Wannan kunyar tana nan"

Dariya suka yi masa sai Iya ta hau kiran Mawadda wai ta zo su gaisa da Dahiru.

Faduwar gabanta ya tsananta ta fito sanye da hijab da bai karasa gwiwarta ba akan dogon skirt din dake jikinta. Daga bakin kofa ta rakube saboda falon ba wani girman kirki gareshi ba mutanen ciki sun cika shi. Ita kunya Dahiru kuma ganin idon su Baba a tare suka ce

"Ina wuni" ta fada da sassanyar muryarta shi kuma da tasa muryar mai amo daga can kasan makoshi.

Abinka da tsofaffi Innar Fatihu da Iya suka kalli juna suka murmusa.

Dariya su Baba suka yi ganin su biyun sunyi duru-duru sai aikin sunkuyar da kai. Shi Dahiru mamakin kansa ma yake yi saboda a zatonsa ya dade da dena jin kunya irin wannan ashe da gaskiya Yaya bata tafi ba. Tun a baya ya rasa wane irin tasiri ganin Mawadda yake yi masa wanda yake hana shi fadin duk wani zance da ya tsaro a gida zai fada mata. Ita kuma dama kunyarta ma da rashin magana bazasu bari tayi abin arziki ba.

Ade ce ta fara tashi ta sake tado zancen iyali.

 "Dahiru kayi zumunci mungode sosai. Ka gaishe da su Innarka don Allah. Kuma ina fata za ka kawo mana abokan namu ko kawaye mu gansu."

Gani yayi duk sun zuba mishi idanu yasa hannu ya rufe rabin fuskarsa yana kallon Mawadda da ido daya batare da sun gane ba

"Ade babu iyalin nan fa sai dai ku saka mu a addu'a"

Da sauri Mawadda ta dago kai don tsakani da Allah bata taba kawowa haka zai ce ba.

Baba ne ya fara yi masa fadan me ya zauna yi duk shekarun nan. Ya tabbatar dai ba ra'ayin su Mal Isiyaku bane.

Daya ban daya suka fice Mawadda ce akan gaba. Yaya ta kirata dakinta tace ta hada masa abin tabawa ta kai masa. Shiru bata motsa ba har Yayan ta tabata

"Ko baki so zuwan nasa bane?"

Kwalla taji ta taho mata ba shiri kuma mara dalili kawai ta fada jikin Yaya ta sa kuka. Nan da nan ta rikice ta zaunar da ita a bakin gado tare da sakaya kofar.

"Mawadda nasan zuwan Dahiru zai dawo miki da abubuwa da dama kamar yadda na tabbatar shima zai ji hakan. Amma ki barwa Allah komai tunda bamu ma san dalilin zuwan nasa ba yanzu. Goge idon maza ki tashi kada ya zargi komai"

Ajiyar zuciya kawai take saki ta tashi ta dauki tray din bayan Yaya ta hada da kanta. Sallama tayi sai da ya amsa ta shiga. Yana nan zaune a kasa har yanzu. Kusa dashi da ajiye tray din ta koma gefe da 'yar tazara tsakaninsu ta zauna a kasan itama.

Kayan cikin tray din ya kalla amma hankalinsa ya tafi ga muryarta da yaji alamun tana rawa  yace "cikin wadannan kayan akwai wanda ki ka yi da hannunki?"

"A'a" ta amsa a takaice kanta a kasa.

"To na koshi" ya fada yana dan tura shi gefe.

Ji tayi hankalinta ya dan tashi "ko babu abin da ka ke ci a ciki?"

"Ko daya. Kinga mu bar wannan maganar kukan me ki ka yi daga zuwana?"

Da sauri ta dago kanta za ta musa ya shiga kada mata kansa.
"Kinyi kuka Mawadda. Kuma nasan cewa nine silar zubar hawayenki"

Ai kamar yace hawaye ku fito idanunta suka cika da kwalla suka fara saukowa da duminsu.

"Assha Mawaddatan wa Rahma ko bakiyi kukan nan ba nasani cewa ban kyauta ba an rabani dake a lokacin da muka fi bukatar rarrashin juna. Su Baffa..."

Kuka take sosai amma hakan bai hanata dakatar dashi ba "Su Baffa akan gaskiyarsu suka rabamu"

"Duk da a lokacin babu abin da ki ka fi bukata daga duk wani mai sonki sama da ya kasance tare dake ba tare da kyama ko ganin laifi ba?" Magana yake cike da takaici da bakinciki. Yanayin muryarsa kadai zai fallasa ciwon da yake nukurkusar zuciyarsa wanda ya dade yana dannewa.

 Cikin wani irin yanayi mai ban tausayi tace "Yayanmu, ni kadai nasan menene a kasan zuciyata amma ina so ka sani ko kadan babu fushi da kai ko su Inna"

"Kenan ko yau na fito zaki aureni?" Ya jefa mata tambayar a bazata.

Murmushi tayi don son ta bagarar da zancen "ni bazan taba aure ba"

Ji yayi kamar ta zuba masa ruwan zafi maganar har kasan zuciyarsa ta daka "Mawadda zakiyi aure, zaki haihu, zakiyi farinciki kamar kowacce mace. Ke dai ki shirya don da gaske dawowa nayi na yaki duk samarinki a karo na biyu a sake sa mana rana."

Inama ace bata taba sanin wani Babawo ba kaddara ce kawai ta rabata da Dahiru yau da tafi kowa farinciki da kalamansa. Sai dai kaddara ta riga fata a yadda take jin kanta ta sani da matukar wahala ta iya rayuwar aure ko da kuwa iyaye da dangin mijin sun karbeta hannu bibbiyu. Wasu hawayen ta soma yi tun tana gogewa har ta kyalesu kawai tana shessheka yayin da Dahiru ya zuba mata idanu yana mai kara tsanar fasikin da yayi sanadiyar lalata mata rayuwa haka.

Sai da tayi mai isarta ta dago idanu duk sunyi ja kamar gauta. Dahiru yace ta taimaka ta sake masa magana da Baba amma ta dawo magana yake son yi masa a gabanta.

Gaba na faduwa ta tashi tana tsoron kada yayi wata maganar da ta shafi aure don bazata yarda a sake maimaita irin abinda ya faru baya ba. Tunda iyaye basa so magana ta kare.

Tare da Baba suka dawo yana zaune akan kujera su biyun a kasa. Dahiru ya soma bashi hakuri akan yadda abubuwa suka kasance a baya.

"Hanani auren Mawadda bai yi min ciwo kamar baza labarin da Ummiyo tayi ba. Nasan lokaci ya ja bazaku so ayi ta tada maganar ba amma tsahon shekarun nan babban burina bai wuce na ganka na roki gafararku ba. A dalilin fitar da maganar nan gashi an raboku da gida...." zuciyarsa tayi rauni sosai ya kasa karasa abinda yayi niyar fada.

Baba yayi murmushi irin na dattijan da suka san me suke yi.

"Dahiru ko da fitar maganar nan ko babu ka sani babu wani abu da zai hanamu tafiya saboda tun ran gini tun ran zane. Kuma banda abinka ma idan ka dubemu ka dubi kanka sai mu taro mu godewa Allah saboda a kowacce jarabawa ta rayuwa akwai alkhairi, ko dai mu fara girbarsa a duniya ko mu karbi sakamakonmu a lahira. Tabbas an cutar min da 'ya an bata mata rayuwa. Kai mu kanmu kamar yadda kake gani babu wanda al'amarin nan bai yiwa tabo ba. To amma me, a dalilin hakan ka fito neman ilimi don ka aureta ka tallafi rayuwarta ko ba haka ba?"

"Haka ne"

"Yau gaka ka taka wani matsayi wanda da hakan bata faru ba karshenta kunyi aure amma kila abincin da zaka bata ma sai an kai ruwa rana zai samu. Mu kuma da ko a kauyen kasan cewa ni talaka ne fitik yau gani a birni 'yan layin nan da yawa ma Alhaji suke kirana duk da banje ba" ya kare yana dariya.

Su ma murmushi suka yi wanda dama burinsa kenan. Nasiha mai ratsa jiki ya cigaba da yi musu akan hakuri da kaddara a kowane yanayi sannan ya tashi ya koma ciki. Yaya da Ade suka bishi daki suna son jin me Dahiru yace. Girgiza kai yayi yace mata duk halinku daya. Su kuwa suka matsa masa da tambaya ya samu ya kashe bakin nasu da yacewa Ade ta ajiye kunyar 'yar fari wannan abu har Innarsa sai ya fadawa. Ba shiri suka fita daga dakin suna kuskus kamar ba kishiyoyi ba.

A falon Dahiru ne ya mike tsaye yana gyara rigarsa. Itama Mawadda ta tashi ta matsa daga ciki ta bashi hanya ya fita ya tsaya daga gabanta ya dan daure fuska.

"Duk kin bata abin"

"Me na bata?" Ta tambaya da mamaki.

"Duk tsahon lokacin nan haduwarmu ta farko ta kare a koke-koke. Ni ba haka na tsara ba gaskiya."

"Haduwa ta biyu ce ko har ka manta da jiya kazo?" Tace masa.

"Yaushe zan manta bayan hatta kalar lipstick dinki na jiyan da kike ta turo min baki ta glass yana nan har yanzu a idona."

Kunya ta kamata ta dukar da kanta saboda kusancinsa da inda take tsaye.

Shi kuwa ko a jikinsa ya cigaba da magana yana kirgawa da yatsun hannunsa
 "Jiya ganinki kawai nayi. Yau neman yafiyarki nayi. Gobe zan so jin yadda rayuwa ta kasance miki. Jibi kuma idan mun sake haduwa sai mu gaisa in sha Allah"

Baki bude tace "yanzu gobe ma sai kazo?"

"Harda jibi in Allah Yaso"

Bai jira cewarta ba ya fita ta bi shi a baya sai dai iyakarta bakin kofar gidansu. Tana tsaya har ya isa ga motarsa ya shiga. Bayan ya daidaita ta yadda zai fita daga layin yayi mata horn tare da dago hannu sannan ya tafi.
*****

Haj Mara anci kuka an koshi. Babawo dan da ta kwallafa rai da duk wani burinta akansa shine ya koma haka.

Abinci yake ci hankali kwance yana yi mata hira don dakinta ta shiga dashi saboda ya zama abin kallo. 'Yan uwansa ma kallonsa suke yi balle kuma masu aiki. Karin bakincikinta Yasmin da take wurin ta gama ganinsa zata kara rainata. Gata tazo da 'ya'ya maza har uku kuma wai laulayi take yi. Kwafa tayi cike da takaici.

"Babawo yanzu ni ka kyauta min kenan saboda Allah?"

"Yo...yo ma Maama did I do anything to piss ya off?"

"Piss din u....," fasa zaginsa tayi ta sauke ajiyar zuciya "kaga Babawo yanzu wannan shigar rakwacham din da kayi kai ba dan daba ba, kai ba mafarauci ba sannan ba dan bori ba da me tayi kama? Gabadaya ka fita daga hayyacinka kamar wani kwancen hauka"

"To yi min baki in haukace" ya fada cikin fada-fada yana buga cokalin hannunsa cikin plate din sannan ya ture centre table din da ta jawo masa gabansa da karfi ya tashi tsaye.

Tsoro ya bata ta tashi itama kamar zata kamo shi ta mika hannuwa sai kuma ta mayar dasu.

"Yi hakuri ka zauna kaci abinci"

"Na koshi" ya amsa tare da fita abinsa.

Hawaye ne ya taho mata ta goge jiki a sanyaye.
******

Da daddare Alh Sule yaje dakin Haj Mara rike da hannun Babawo.

Tana zaune ta rafka tagumi abin duniya ya isheta. Ganinsu tare tayi saurin gyara yanayin fuskarta don bata so Alhajin yasan batayi farincikin ganin danta ba.

Wuri suka samu suka zauna sannan Alh Sule yace "Marakisiyya kinga illar yin gaban kanki da kika yi akan yaron nan ko? Yanzu wa gari ya waya daga ni har ke?"

Cikin masifa tace "Alhaji ai baka da asara ni kadai ta shafa. Kai da ka ajiye 'ya'ya maza har uku kila ga na hudu can a ciki da waccan dadiron taka"

Gajeren murmushi yayi "duk 'yan uwana maza sun shaida wannan aure sannab bata taba haihuwa dangina mata basu je suna ba. Ke kadai ce labari yazowa a kurarren lokaci"

Babawo ne ya tashi hade da buga hannuwa a cinyoyinsa yana kade wando "ni bara na kara gaba dama na dauka zaman nawa ne"

Kallon da Alhaji ya watsa masa ne yasa shi komawa ya zauna.

Fada Alh Sule ya fara yi masa akan barin inda Haj Mara ta kaishi ya wahalar dasu wurin nema. Sannan ya dawo fada akan irin rayuwar da ya daukarwa kansa mara bullewa. Daga karshe nasiha ya koma yi da bada shawara akan idan bai chanja hali ba akwai ranar da duniya zata yi masa tofin Allah tsine kafin aje lahira.

"Kazo mu cigaba da aiki tare ni girma ya kamani so nake na huta. Idan Allah Yasa ka gane aikin sosai ma kai za ka cigaba da shugabanci a wurin"

Ba kunya Haj Mara tana murmushi tace "yanzu kayi magana Alhaji. Dama kyan da ya gaji mahaifinsa, ko ba komai shine babba cikin 'ya'yanka maza ragamar komai kamata yayi ta dawo hannunsa. Kaga da ya fara aiki  sai ayi masa aure shikenan."

Tabe baki Alh Sule yayi yana girgiza kai "irinku ne mata wanda tun ranar aurenku kuke hasashen mutuwar miji a gaji dukiya. Allah shi kyauta wannan hali naki"

BB ya sake tashi don kansa har ya fara ciwo. Hayaniya idan ta wuce ta kida a gidan rawa to a kai kasuwa.

"Yo...yo Paapa ina da yarinyar da nake so magana kawai zakuyi da iyayenta"

"Alhamdulillahi kaji ma komai zai zo da sauki" cewar Haj Mara.

Shi kuma Alhaji ya fara tsoron ko cikin irin wadanda suka gama mu'amalarsu a titi ce ko wata baturiya.

Hade fuska BB yayi babu alamun wasa yace "Mawadda nake so Paapa. A nemo min ita nayi alkawarin riketa tsakani da Allah. Its a promise Paapa bazan karya ba" yana magana idanu na lumshewa.

Haj Mara tazo wuya a harzuke tace "Mawadda kuma??? Kai buhun ubanka Babawo. Kana da hankali kuwa?"

Alh Sule yayi dariya "kowa yayi zagi a kasuwa dai Marakiyya.." ya fita shima yabi bayan Babawo.

Yatsanta ta ciza don takaici. Wato da babanta Alh Sule yake saboda shine yayi sana'ar hatsi dan awo a kasuwa.

Kwanciya tayi tana ta juye-juye. Ace har yanzu Babawo bai manta da wata Mawadda ba. Ita ta dade da goge shafinsu ma a zuciyarta. Tsaki taja don da wuya idan bata yi aure ba yanzu. Yayi ya gama ya hakuri ya nemo 'yar mutumci a aura masa. Duk da tasan Alhaji yana dakinsa da matar da ya kawo hankalinta baya garesu yanzu. Burinta bai wuce kintsuwar BB ba.

A bangaren BB yana shiga daki fadawa yayi kan gadonsa yana tunani. Addu'a yake da fatan Mawadda batayi aure ba. Zai iya rantsuwa ya soma manta kamaninta sai dai ta zame masa kamar wani dafi a zuciya. Sonta yake ji a ransa burinsa kawai ya mallaketa a matsayin matar aure. Zaiyi kokarin mantar da ita duk wani bakinciki da ta kunsa a dalilinsa. Wani dan tunani yayi idan tayi aure fa.

"Kai inaaa ko tayi sai ta fito. Tawa ce ni kadai!" Ya fada yana jifa da filo daga kan gadon.

*****

Dahiru fa farincikinsa ya kasa boyuwa don duk wanda ya san shi dole ne ya gane cewa gabadaya yanayinsa ya chanja. Shigarsa gidan Bilya kenan ya samu Danlami da matarsa suna gidan su ma. Furaira na ganinsa ta kwalawa Hansa'u kira wai ta kawo masa abinci.

Gaisawa yayi da 'yan uwansa maza yayin da ya dauki yarinyar wajen Danlami ta bata wuce shekaru biyu ba yana mata wasa. Shi kuma Bilya ya fita waje amsa waya.

Hansa'u ta shigo fuskarta tasha kwalliya saboda tun dazu da ya kira Bilya yace zai zo itama yayarta ta sanar da ita ta shirya yau duk tsiyarsa sai sunyi zance. Yadda yake yiwa yarinyar hannunsa wasa ne ya bawa kowa mamaki. Ba wai mutum bane mai girman kai ko wani abu makamancin haka. Sai dai duk wasansa da yara baya dadewa zai mikawa iyayensu. Yau kuwa har dokin wuya ya yiwa Humaira mai sunan Innarsu.

Furaira ta kalli Hansa'u wadda ta shagala wurin kallonsa kamar wata tsohuwar mayya.

"Kin dai gani maigidan naki yana da son yara sai ki dage zubin farko ki watso masa 'yan biyu"

Danlami ya soma dariya "zubin farko kuma kamar kwasar adashi? Enjiniya ashe kun daidaita da Hansy baby bamu da labari"

Siddiqa matar Danlami ta watsa masa wata muguwar harara.

Kashe mata ido yayi "Maida wukar Hajiyata yau tsokana nake ji. Kinsan sabon kamu ga dukkan alamu an lasa masa tsohuwar zuma a inda yake"

Hansa'u ta hau harararsa balle da Dahiru yayi banza dasu duka sai murmushi da yake yi shi kadai. Hakan yasa su tunanin ko budurwa yayi.

Furaira taji haushi ta kalli Bilya shi da ba ruwansa.
"Lokaci yayi da zamu san a wane matsayi Dahiru ya ajiye min kanwa. Saboda shi ta dawo gidan nan kuma taki sauraron kowa amma kana kallo yake wulakanta ta. Idan yana tunanin saboda wani abin hannunsa ne ai ya san irin masu kudin da suke zuwa wurinta take kin fita."

"Kada in katse miki hanzari amma mai guri tazo duk wasu masu tabarma ko masu son shimfidawa sai su nade. Tauraruwar Yayanmu Dahiru ta dawo ga dukkan alamu da haskenta don Allah ki sararawa yarinyar nan ta fitar da wani cikin masoyanta" cewar Danlami.

Kowa zuba masa ido yayi banda Dahiru wanda ya shiga danna waya kamar baya wurin. Bashi da niyar wulakanta Hansa'u amma ya tabbatar da biyu Furaira ta nacewa son ayi auren. Sannan ko da can ba sonta yake ba.

 Furaira tabi Danlami da kallo kafin ta iya cewa "yarinyar nan da aka yiwa fyade kake nufi Danlami?"

Ya gyada kai shi kuwa Dahiru wannan kalma ta fyade ce ta kular dashi ya tashi ya fice ko sallama babu.

Rai a bace Furaira ta fita daga falon itama ta bar sauran cike da mamaki. Fitar Dahiru ta tabbatar da zancen Danlami. Wayar Inna ta kira tayi sa'ar samu kuwa ta sanar da ita ashe Dahiru yana tare da Mawadda duk tsahon lokacin nan shiyasa yaki aure. Harda karin cewa a bincike shi a tabbatar ba aurenta yayi ba bada sanin kowa ba.

Hankalin Inna ya tashi tasa yaron makotansu ya danno mata sunan Dahiru ya kira. Lokacin shigarsa gida kenan tace masa gobe komai dare idan ya taso daga wurin aiki yazo tana nemansa taji komai tsakaninsa da Mawadda daga wurin Furaira.

Baiyi mamaki ba sanin halin matar yayan nasa shima hakurin zama yake da ita. Ya dai kudurce niyar wannan karon ba gudu ba ja da baya. Duk wata soyayya da yake jin ta kwanta har ya kasa kula wasu matan ta dawo daga ganin Mawaddatan wa Rahama.

*****

Shirinsa na komawa gidansu Mawadda ya warware a dalilin kiran da Inna tayi masa. Shima kuma akwai maganar da yake son yi musu ita da Baffa. Izinin fita ya nema saboda baya son kwana idan yaje ya samu da kyar aka barshi ya tafi. Dashi akayi sallar azahar a Tariwa bayan yaci abinci ya zauna tare da iyayensa.

Baffa ne ya soma magana yace suna bukatar sanin gaskiya game da zancen da Furaira ta kawo jiya.

Dahiru ya warware musu komai tun daga katin auren Rafi'a da Danlami ya bashi zuwa yanzu harda sakon gaisuwar su Baba.

"Baffa na dade ina son muyi maganar su Baba daku Allah bai nufa ba sai yanzu. Ku iyayena ne kuma duk abinda kuka yi na hana aurena da Mawadda nasan kunyi saboda ni ne. To amma kada ku manta daku muka je asibiti likita ya tabbatar fyade ne. Ade tazo har gidan nan rokon rufin asiri Ummiyo ta tona. Daga wannan lokacin wane irin tozarci ne basu gani ba karshe harda kora daga garin nan. Baba barin jiki ya mutu Malam mai rasuwa kuma ga tsufa daga ranar da aka koresu bai kara haduwa da mahaifinsa ba sai jana'iza da yazo. Ku duba wannan al'amari babu wanda yafi karfin jarabawa irin wannan. Me zaisa don ta afka musu kowa ya juya musu baya? Wallahi har yau ana fyade kuma mace da danginta sune kadai suke fuskantar kalubale daga abinda bai zama laifinsu ba. Ina laifin wanda yake neman halak da guminsa Baffa? Maimakon a lokacin mu hada kai mu jajirce wurin kwato musu hakkinsu ta yadda gobe wani mai kudin zaiyi shayin yiwa 'yar aiki fyade sai aka juya musu baya. Wannan yana daga cikin dalilan da suke karawa duk wani mutum bata gari karfin gwiwa domin yasan indai yana da kudi idan yayi babu wanda ya isa dashi. Ko ban aureta ba a lokacin yaci ace mun tsayawa juna."

Yana magana Inna ta share hawaye tana kallon Baffa "ni dai na dade abinnan yana ci min rai amma kunya da tsoron yadda zaka dauki zancen yasa na kasa magana"

Shiru Baffa yayi kamar bazaice komai ba sannan ya nisa yace "Allah Yayi maka albarka Dahiru. Karshen mako kazo ka daukemu muje gidan Mal Fatihun"

Mamaki Dahiru yayi sosai yadda iyayensa suka yi saurin saukowa. Ya tsallake wannan saura kuma neman amincewar Mawadda ya sake tado da zancen aurensu.

Abinda bai sani ba shine duka iyayen nasa kowanne shi kadai ya dade da nadamar biyewa son zuciya akan abinda ya sami su Mal Fatihu amma sun kasa yiwa juna zancen. Batun yiwa 'yan aiki fyade wasu ma su dawo da ciki kuwa ko ba a garinsu ba suna ji sosai a makota amma har yanzu an rasa wani mataki da ya kamata a dauka domin dakile cutar da marasa karfi da akeyi.

Bayan la'asar ya sake daukar hanya cike da farinciki ya tafi. Zancen da suka yi da Inna a dakinta ya tuna yayi murmushi. Cewa tayi kada yayi gaggawar sake neman auren Mawadda har sai sunje sun fuskanci wace rayuwa tayi bayan rabuwarsu. Tado da zancen da tayi kawai yasa shi sanin cewa akwai yiwuwar amincewarsu kenan.

A gajiye sosai ya isa gida sai da yayi shirin kwanciya wurin karfe goma ya kira Mawadda.

Tana aikin hada turaren wuta saboda wasu amare biyu da zata fara yiwa gyaran jiki taji wayar. Hannunta ta goge ta dauka da sallama hade da faduwar gaba ganin mai kiran.

Amsawa yayi yana jin wata annashuwa tana ratsa shi.

"Da karfinki ki ka dawo naga alama"

Tayi 'yar dariyar da sautinta ya sake jefa shi cikin wani yanayi mai dadi "Karfi kamar wata 'yar dambe?"

Ajiyar zuciya taji ya saki har tsigar jikinta ta tashi "da gaske nake, ban san ta yaya zan kwatanta miki yadda nake ji game dake ba yanzu. Tunda na hadu dake shekaranjiya na kasa ganewa SO ne, KEWA ko duka biyun ne a tsakaninmu"

"Yayanmu!"

"Na'am"

"Kayi hakuri kada muje nan. Ni da kai yanzu wa ne da kanwarsa." Yadda tayi maganar mai ji zai fahimci akwai ciwo a tattare da ita wanda take kokarin dannewa.

Hakan ya taba zuciyar Dahiru sosai yasan tana kokarin boye damuwarta ne kawai don babu yadda zatayi "haka kika zabar mana? Mu koma wa da kanwa?"

Kai ta gyada kamar yana kallonta.

Yace "to naji amma idan mun tashi mu kara da zama abokan sirrin juna. Ke kanki kin sani abinda yake tsakaninmu mai girma ne. Kinga ina da abubuwa da dama da nake son baki labari Mawadda...Nace miki yau zan zo naji yadda rayuwarki ta kasance kema amma da ki ka ji shiru babu ko cigiya"

"To kayi hakuri"

Yasan akwai aiki a gabansa indai yana son ya dawo kamar da ko ma fi a wurinta yadda zata bada kai bori ya hau. Lallabata zaiyi a hankali ya sake cusa kansa. Ya iya hakurin shekaru takwas ma basu hadu ba bare yanzu.

Tambayarta yayi cikin sigar wasa "Gobe nazo?"

"Uhmm" ta iya cewa kawai. Saboda muryarsa idan yayi magana yanzu jinta take har ranta. Anya zata jurewa wata alaka tsakaninsu idan ba soyayya ba? Ita kanta tana mamakin yadda ya dawo cikin rayuwarta yake neman wargaza duk wani shiri da katanga da ta gina tsakaninta da maza.

"Nagode Kanwarmu Mawadda" ya fada a hankali yana jan kowane harafi.

Haka nan taji tana son yasan tayi ilimi itama yanzu shiyasa tayi masa sallama da turancin da ko lokacin da tayi firamare a garinsu yasan bata iya ba "Sweet dreams Yayanmu Dahiru"

Ai kuwa ba karamin dadi yaji ba da mamaki  sai da yayi da gaske ya iya cewa "mafarki na daya ne. Naki. Kuma yanzu kin hana tunda bai kamata wa yayi mafarkin kanwarsa ba. Amma duk da haka bari na kwanta da kyakkyawar addu'a kila nayi sa'ar ganin wadda zata zama matata don aure nake so wallahi"

"La ila ha illallahu" tace tana dariya kasa kasa sannan ta kashe wayar kafin ya sami damar sake magana.

Dariya yayi ya gyara kwanciyarsa "you can't escape easily adorable Mawadda".
******

Cikin bacci yaji waya ya farka. Shadaya da kusan rabi lokacin. Ko bai gaji ba yanayin aikinsa yasa ya koyi baccin wuri. Bai gane nambar ba amma ganin wayar ta katse an sake kiransa shiyasa ya dauka. Yana kara wayar a kunne yaji ance

"Ahirin..."

Takaici ne ya kama shi yaja siririn tsaki. Mutum daya ke kiransa da wannan sunan kuma muryarta yaji. Sai dai bai ga wani dalilin komai kankantarsa ba da zaisa ta kira shi a wannan lokacin.

Cikin zakuwa Qareeba ta sake cewa "Ahirin kana jina? Safwan ne nayi ta nema ya bani number dinka da ka bashi lokacin da kazo wayarsa a kashe sai yanzu na same shi"

"Naji, naji ya akayi?"

"Hmmmm dama magana ce nake so muyi idan da hali gobe sai kazo gida ko ni nazo office dinka. Duk wanda ka zaba is okay with me"

Me kuma take nema ya tambayi kansa. Kamar yaji shi ta sake cewa ya daure yazo. Baya son jan magana da ita kawai yace yaji sai ya taso daga office.
Babu sallama ya ajiye wayar ya juya abinsa ya kwanta.

Zuwa wayewar gari ya ma manta da wayar Qareeba harkokin gabansa kawai yake yi sai tunanin Mawadda da haduwar da zasuyi anjima.
*****

"Kin tabbatar da abinda ki ke fadi kuwa Qareeba?" Cewar Dr Tani cike da doki.

"Sosai Mummy zaki ganshi ma da kanki don yace yana tasowa daga office zai zo" Qareeba ta amsa tana dariya.

Dr Tani ta jinjina kai "Allah Sarki ashe shine rabon naki lokaci ne kawai baiyi ba. Dama ance matar mutum kabarinsa. Sai ki tashi a soma hada masa abinda zaici tunda daga office zai biyo"

Hannu Qareeba tasa ta rufe fuska wai ita kunya ta tashi tayi hanyar kitchen tana kiran mai aikinsu tazo ta tayata aiki.

Dr Tani kuwa zuciyarta fes tana murna da wannan sa'a da Qareeba tayi.

Dahiru na fitowa akan hanyarsa ta komawa gida yana tsaye wurin danja Qareeba tayi ta kiransa. Kallon wayar yayi sannan ya tuna jiya yace zaije. Agogo ya kalla yaga akwai sauran lokaci zai iya lekawa gidan nasu shap-shap ya koma ya shirya yaje wurin Mawadda. Yadda ya santa da naci idan baije ba kiransa zata yi tayi kamar yadda take masa da idan zata bashi aiki Abinda baya so kenan.

A falon Dr Auwal aka jera masa komai na tarar bako don Dr Tani tace dole a karrama shi yadda ya dace.

Qareeba ce a gaba yana biye da ita zuwa falon duk yabi ya takura saboda yadda yaga abin babba ne. Taci kwalliya sosai gashi yau shine har falon maigida.

A dofane ya zauna ya kasa sakin jiki. Sai da ta zuba masa lemo a kofi ta mika masa sannan ta zauna a kujerar kusa dashi. Haka ya rike kofin shi bai sha ba shi kuma bai ajiye ba yana jiran karin bayani.

Kusan minti biyar babu wanda yayi magana. Sai Qareeba ce tayi ta mata tace

"Baka ce komai ba?"

"To me zan ce ni da ki ka kirani"

Kai ta sukunyar tana wasa da yatsunta "kayi hakuri da jinkirin da aka samu na rashin fahimtarka da nayi a wancan lokacin."

Kansa ya shiga duhu ya kasa gane inda ta dosa yace "ban fahimceki ba."

"Ka tuna wata rana da na tambayeka me ka ke kiran masoyiyarka?"

Idan ma anyi haka gaskiya ya manta amma don a sallame shi da wuri yace ya tuna.

Murmushi tayi ta sake matsowa yadda zasu fuskanci juna da kyau.
"A lokacin abinda ka fada dariya ya bani. Kace wai kana kiranta Qulqulatil Qurabati. Sai bayan ka tafi rannan nayi dogon nazari ashe dani kake ban gane ba"

Da sauri Dahiru ya daga hannu "Dakata Anti Qareeba nifa na kasa fahimtarki"

Bayani tayi masa dalla-dalla kuwa. Bayan ta nutsu tayi tunani ta gane daga sunanta ne ya kirkiri wancan suna alamu na cewa yana sonta.

"Nasan a lokacin rashin kudi da wayewa yasa ka boye min soyayyarka. Amma yanzu tunda na fahimta na amince kuma Mummy is happy da hakan" tayi fari da ido tana sunkuyar da kai.

Wannan abu yafi gaban dariya a wurin Dahiru tausayi ma ta bashi. Banda shirme irin nata wane abu ta ga yayi da zai nuna yana sonta ko kuma duk tsabar son auren ne yasa kanta toshewa irin haka.

"Anti Qareeba..."

"Ka dena kirana Anti duk da nasan mu sa'anni ne kada ka damu kusan abinda yake tashe kenan yanzu auren sa'anni"

Gani yayi idan ya barta ta cigaba da wannan tunanin lallai ya cuceta. Gara kawai ya yiwa tufkar hanci tun ba'aje ko ina ba.
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰14

*Batul Mamman*💖



Nutsuwa yayi sosai ya fuskanceta  hannuwansa a hade kamar mai roko yace "don Allah idan daga ranar da muka fara haduwa zuwa yau nayi misleading dinki...uhmmm idan nayi wani abu da zai nuna miki ina sonki ne kiyi hakuri ba niyata ba kenan. Ina da..."

Katse shi tayi da sauri "kada kayi tunanin nafi karfin zama da kishiya, ko kadan wallahi. Ni bani da matsala kaima shaida ne. Matarka da yaranka duk zan zauna dasu da zuciya daya."

Girgiza kai yayi don ya fuskanci abin nata na gaske ne "Anti Qareeba!"

Idanuwanta ta ware a kansa "ni dai gaskiya bana son Antin nan"

"To Malama Qareeba ki tsaya ki gane me nake cewa. Ni Dahiru bani da mata amma ina da wadda nake so. Tsakanina da mutanen gidan nan ciki kuwa harda ke bai wuce mutuntawa ba albakacin zaman da nayi daku a baya"

Hawaye ne ya soma wanke mata fuska. Ita bata san ya shiga ranta haka ba sai da ta kula nema yake yace baya sonta.
"Dashiru kada kayi min haka...duk tsahon lokacin nan da banyi aure ba ban taba kai kaina ga namiji ba gudun irin haka. Yanzu ma ni na sani kana sona tsoron yadda iyayena zasu dauki maganar kake yi ko?"

Ikon Allah. Da Hausa yake mata magana amma kamar ma tana sane take kin gane me yake nufi.
"Kinga ki kalleni da kyau nine Dahiru mai shara da wankin gidanku na da"

Daidai lokacin Dr Tani ta iso kofar falon. Ta kasa hakuri so take ta ji da kunnenta don ta fara shirin gaske 'yarta tayi miji.

Hankalin Qareeba a tashe ta zamo daga kan kujerar da take kamar zatayi masa durkusu irin na me neman taimako.

"Ni mummuna ce ne?"

Tausayi ta soma bashi ya girgiza kai.

"To ko ina da wata nakasa da ban sani ba? Don Allah ka amince Mummyna ta dena kukan rashin aurena. Wallahi zan zauna da ko mata uku ne ni dai kawai ka amince. DAHIRU...SONKA NAKE YI"

Shiru yayi ya kasa magana yayin da Dr Tani ta toshe bakinta ta bar wurin don kada su ji kukan da take yi.

Sai da yaga ta dan sami nutsuwa ya soma yi mata magana "Anti"

Harara ta galla masa yayi dan murmushi "Malama Qareeba akwai girmamawa tsakaninmu bazan iya kiran sunanki haka nan ba. Kiyi hakuri Allah zai kawo miki naki mijin. Ni ina da wadda zan aura in sha Allah nan da lokaci kankani. Ina kara baki hakuri akan kuskuren da nayi bisa rashin sani har kika yi zaton soyayya ce. Allah Ya bamu alkhairi"

Kofin da ta bashi wanda ko kurba daya bai yiwa lemon ba ya ajiye ya fita tana ji tana gani. A wurin ta kife ta shiga rera kuka. Ta rasa menene aibunta da maza suke gudunta an rasa me tsayawa magana tayi nisan zuwa kunnen iyaye ma.

Yana fita ya shiga motarsa ya furzar da iska tare da nannauyan numfashi. Haka kawai da can banda wulakanci babu abinda yake hadasu da mutan gidan musamman Mummyn tasu. Qareeba kuwa kamar wadda aka kawowa abin debe kewa da sa nishadi. Duk wata sharar shirmenta akansa take saukewa. Shine kuma yau ya zama masoyi don rainin wayo. Fita yayi daga gidan rai a bace yana ayyanawa a ransa yayi zuwan karshe kenan. Gidan Prof Abdulhadi yaje yayi rashin sa'a fitarsa kenan. Sun dan taba hira da Hajiya Mama daga nan ya fita ya tafi gida sai yayi magariba yaje wurin Mawadda.

*****
Kusan minti goma da fitarsa sannan Qareeba ta fita idanu a kumbure. A falo ta hadu da mamanta ta yi saurin sakin fuska.

Dr Tani ta daure kamar bata ji komai ba tace "yaya kuka yi har ya tafi ne?"

Ta hadiyi yawu da kyar "eh Mummy daga zuwansa duk wahalar aikin da muka yi wai yana sauri." Tana magana hawaye na zuba tana gogewa da hannu "haushi naji shine harda kuka"

Idanun Dr Tani suka ciko da kwalla ganin 'yarta tana kokarin boye mata damuwarta. Ashe Qareebanta ta girma.

"Kiyi hakuri kila aiki ya masa yawa ne. Jeki ciki ki gyara fuskarki hawaye yasa kwalliyar duk ta cabe miki"

Tana tafiya Dr Tani ta goge nata hawayen. Wane irin bakin jini ne da Qareeba ace har mai wankinsu na da, wai Dahirun da ta raina shine yake da bakin cewa baya sonta.
*****

Ta dukufa tana murjewa amaryar dake gabanta dilka Ade ta shigo dakin da suke aikin ta sanar da ita Baba yace Dahiru yana jiranta an sauke shi a falon soro.

Sunansa kawai da taji yasa jikinta yin sanyi har ta kasa samun kuzarin yin aikin yadda ta faro.

Amaryar wadda ta kasance kawarta ta Islamiyar da suke zuwa a unguwar tace cikin mamaki "Mawadda dama akwai ranar da zanji ance ana kiranki? Lallai yau akwai labari don sai na fadawa 'yan ajinmu tun wuri ma na sanar dake kada a tsokaneki kice na kai gulma"

Dariyar dole tayi "to uwar son labari dan uwanmu ne"

"Mayar dani yarinyar goye dan uwan ne zai tsaya a wancan falon bai shigo ya gaishe da kowa ba?"

Mawadda ta cigaba da murje mata jikin sai dai gaskiya aikin nasu akwai saura sosai. Ita da kanwarta ne amaren kuma basu zo da wuri ba. Kanwar aka fara gamawa  har ta tafi yanzu nata baiyi nisa ba. Hannu tasa ta taya Mawadda ko fita abin baiyi ba ta dauko hijabinta ta saka. Duk yadda Mawadda tayi ta rokon ta zauna taki a cewarta taje ta saurari bakonta ita din ta gida ce gobe sai tazo da wuri tunda na sati zasu yi.

Bayan fitarta nuku-nuku Mawadda ta zauna yi har Baba da kansa ya sake magana yace taje mana. Ita gaskiya tana jin kunya don ta manta rabon da ta fita da sunan zance. Duk wanda yazo nemanta ba fita take yi ba dama Rafi'a ce mai zuwa sallamarsu.

Marwanu da Saifullahi duk basa gida yanzu. Daya yana ABU Zaria daya kuma yana Kazaure informatics da sai ta tura masa su kawai.

Ba wani shiri tayi ba ta dai gyara jikinta ta yafa mayafi ta tafi.

Innar Fatihu ta dubi Baba bayan fitarta "kada yaron nan fa yace zai sake dawowa neman aurenta a kuma komawa gidan jiya"

Iya tace "kuma na kula ita ma kanta tana son shi. Fatihu ko zaka dakatar dashi ne kada a sake fama mata tsohon ciwo a barmu da jinya"

"In sha Allah ni da kaina zanyi masa magana. Yanzu ma don naga bai dace bane daga zuwansa na dakatar dashi da gaggawa batare da sanin manufarsa ba. Ko menene ina tunanin zai sanar da ita a yau sai mu dauki matakin da ya dace"

Tausayinsu ne ya kama Ade don kuwa ta sani sarai kamar yadda Iya ta fada Mawadda har yanzu tana son Dahiru.

Daga bakin kofa yau ma ta zauna a kasa shi yana ciki akan kujera sai dai basu yiwa juna nisa sosai ba.

"Na fa jirgu Kanwarmu har na fara tunanin ko dai saurayi aka shanya ba yayan da yazo ganin kanwarsa ba" Dahiru yace yana mata murmushi.

Itama murmushin ta mayar masa "ai da saurayin ne karshenta sai dai ya gaji ya tafi gida"

Daga hannuwansa yayi "Allah Ya soni da aka yimin tayin zama yayan karfi da yaji na karba"

Wannan karon dariya Mawadda tayi sannan tace yayi hakuri yazo tana tsakar aiki ne. Ya nuna mata babu komai Yaya ta fada masa lokacin da ta kawo masa kayan ci da ke gabansa.

Mawadda ta kula ya sha kusan rabin jug din kunun ayar ta sake fuska "wato wanda na kawo rannan ne baka so shiyasa kaki shan komai"

"Kada ki fassara ni ranar ma kukan da na kula kinyi ne ya janyo. Yanzu kuwa da banci ba ai da na yiwa kaina. Wata awara naci mai dadi duk da bata dameni ba amma wannan gaskiya tayi dadi sosai"

"Kai dai Yayanmu santi kake yi. Baka san ko daga bakin titi idan kana neman gidan nan kace gidan awara za'a kawo ka ba? Tana cikin sana'ar da ta rikemu zuwa yanzu"

Kallonta yayi ita ce dai Mawaddansa amma ta chanja. Sai dai chanjin bai rage komai ba sai kara masa sonta a zuciyarsa.

"Yanzu ma aikin awarar ne ya hanaki fitowa da wuri?"

Gyara zama tayi kafin ta amsa masa "a'a ni sana'ata gyaran jiki. Idan ka tashi aure ka kawo min matarka nayi alkawarin yi mata kyauta"

Dagowa yayi sosai yace  "alkawari fa, Allah Ya kaimu ko wace amaryar kice tun yanzu nasan an 'yanta ni daga kudin gyaran jiki."

Dadi kawai take ji ganinsa da magana dashi a haka. Itama tunanin tasa sauyawar take yi. Ya zama dan gayu sosai banda kamshin turarensa da ya cika falon shigarsa ma kawai ta isa ta sanya mace ta soshi.

Tayi nisa a tunani taji ya kada mata yatsunsa har sun bada sauti tayi saurin dauke kanta daga gareshi.

Shi kuwa yace "irin wannan kallon sai kisa nayi tunanin promotion na samu, har na fara murna."

Kunya taji ta jawo mayafinta ta sake rufe fuska. Shi kuwa sai dariya yace "Allah kuwa haka kawai aje a sa min rai ina dalili. Yanzu dai fara bani labarin da nake kwadayin ji"

Kasa dago kai tayi maganarsa tasa mata jin nauyinsa "labarina kayan kuka ne da bakinciki kawai a ciki"

"Assha Kanwarmu a rinka godewa Allah dubi yadda rayuwa ta koma miki fa. Ni dai ina son ji. Idan anzo wurin kuka muyi tare idan na bakinciki ne mu rarrashi juna. So nake wannan gap din shekaru na tsakaninmu mu cike shi ta hanyar sanar da juna komai. Kada ki manta na roki alfarmar zama dan uwa abokin sirrinki ne"

Ji tayi bazata iya yi masa musu ba ta soma bashi labarin tun daga shigarsu kotu na farko har zuwa yanzu. Tayi kuka sosai kafin ta gama. Dahiru kuma jijiyoyin kansa suka dago saboda bacin rai.

"Kiyi hakuri Mawadda ban so haka ta faru dake bama tare ba" yace murya na rawa saboda yadda yake ji.

Dago kanta tayi wanda ta kifa akan cinyarta ta turo baki "ni ban yarda ba yanzu kace idan abin kuka yazo tare zamuyi"

Yasan wasa take so ta sako domin sassauta musu yanayin da suka shiga sai ya biye mata.
"Kada kiso jin kukana don muryata sai ta cika gidan nan ga rashin dadin sauraro"

"Ni kam tana min dadi" tace ba tare da ta kawo komai a ranta ba. Kallon da yayi mata ne yasa ta rufe baki sai kuma tace saura nashi labarin.

Tun farkon zuwansa Kano ya soma fada mata har yau da yaje gidansu Qareeba.

Sai ga Mawadda tana dariya kamar ba ita ta gama kuka ba.
"Yanzu Yayanmu mace tace tana sonka shine kake ja mata aji. Huhmm gaskiya ka koma kace ka amince kawai don ni tayi min"

Dahiru yasha kunu da gaske baya son zancen Qareeba.
"Ita ce nace miki tana kirana Ahirin ko Dashiru da farkon labarin ko baki gane ba?"

Ta kuma dariya "Ahirin na Qareeba yaushe zamu sha biki?"

Kula yayi zolayarsa kawai take yi shiyasa ya dena biye mata. Sun cigaba da tattauna abubuwa da dama yace  "amma likitan da taci amanarku a kotu baku sake binciken dalilinta ba?"

"Barta ta yiwa kanta ne. Kasan ranar Baba ya fadi muka taho asibiti shiyasa komai ya dakata"

Dahiru yace "naji dadi kinyi karatu yanzu Kanwarmu. Kinsan babban abinda ake cutarmu dashi bayan talauci shine rashin ilimi. Akwai abubuwa da dama da yakamata ace an kula dasu wancan lokacin. Kamar sanar da lauyan binciken farko na asibitin Bebeji, kawo wadancan 'yan sandan shaida da sauransu. Duk da haka kada ki damu hakkin da suka dauka bazai barsu ba"

Hawaye ne ya zubo mata tace "Yayanmu bazan taba yafe musu ba. Akwai ranar da abin ya ciyoni fa na kwana dashi a raina kawai sai gani a Kaduna"

Idanu ya zaro "me???"

Da sauri ta shiga girgiza hannunta tana kallon kofa "shhhhh babu wanda ya taba sani"

Yace "to wallahi fada min yadda abin ya faru ko na tona"

Wata harara ta doka masa wadda ta shiga ransa don yadda ta kada idanun ma burgeshi yayi "naji amma wallahi amanatul amana..."

"To  ya isa kada ki karasa bazan fada ba bare ta cini." Ya yamutsa fuska "kai Kanwarmu ashe baki girma ba har yanzu wai amanatul amana"

"Rigakafi nake yi don kada ka janyo min duka"

Shekara biyu kenan lokacin tana ganiyar mafarkin BB tun da barayi suka shiga makotansu akace sun kusa yiwa matar gidan fyade. Shikenan abu ya dawo mata sabo tana kwanciya take farkawa a firgice. Ranar da abin ya isheta zuciya ta raya mata wai taje Kaduna ta hadasu da 'yan sanda a koma kotu. Karyar makaranta tayi sai gata a tasha kamar wasa. Taje Kaduna ta fadi sunan unguwar amma ta kasa gane ko ina. Tana cikin yawon tambaya kamar wata mahaukaciya Baba ya kirata yace ta taho masa da maganinsa na hawan jini a lamco pharmacy. Sai lokacin ta dawo hayyacinta a gaggauce ta koma tasha. Ranar sai bayan magariba ta dawo gida ta zuga musu karyar dalilin rashin dawowa da wuri. Babu wanda ya tuhumeta tunda ansan ba yawo take ba.

Dahiru na jin labarin ya sake tausaya mata da sabon kuduri a ransa na tunanin dole ma ya aureta ya nuna mata soyayyar da zata gusar mata da tunanin wannan azzalumin mutumin.
******

BB ne ya fito daga dakin Alh Sule yana ta gunaguni don me zai ce masa sai yayi aski. Kunyar yanayin shigarsa yasa sun kasa tura shi ya gaishe da 'yan uwa ma.

Yana saukowa Yasmin ta fito daga kitchen da food flask ta yiwa yaranta girki. Haj Mara tace masu aikinta bazasu yi girki da ita ba. A nata bangaren hakan yafi mata don yadda ta kula ta sawa yaran nan ido ba abin mamaki bane ta nemi hallaka su. Anyi sa'a damuwarta gabadaya tana ga BB yanzu.

Yasmin ya hango ya taho inda take kusa da dinning table ko kula Haj Mara baiyi ba da take tambayarsa yaya sukayi da Alhaji.

"Matar Alhaji wai yaya kanen nawa suke kiranki ne ba dadi ina cewa matar Alhaji dinnan."

Yasmin tayi murmushi ganin Haj Mara ta bata rai "Mama suke kirana"

"To ai nima kawai sai nabi ayari. Ni dasu ai same to same ne...so ba wani abu kingane ai" yace yana yin gaba.

Ita kuwa kai ta gyada kawai. Bayan ya wuce Haj Mara ta tashi zata bi bayansa taji Yasmin tace "ta inda aka hau ta nan ake sauka"

Dawowa tayi ta tsaya a gabanta "me ki ke nufi"

"Nayi miki magana ne?"

Rai a bace dama neman wurin huce takaici take ta cakumi wuyan Yasmin din.
"Ki bar ganin na kyaleki idan na dawo gareki bazaki ji dadi ba. Kina tunanin kin shigo min gida ne don ki kwace komai nawa?"

Bude baki tayi zata rama taji Alh Sule ya fito sai ta soma kuka tana bawa Haj Mara hakuri. Harda cewa idan saboda zuwansu ne zasu koma Abuja nan ba da dadewa ba.

Alh Sule yana saukowa ya kamata da fada sosai da ja mata kunne babu ruwanta da iyalinsa.

Mamaki ne ya hanata magana kawai ta bi bayan BB tana hawayen zuci.
*****

Kwana biyu da zuwan Dahiru tun ranar Qareeba ta dena walwala a gidan. Dr Tani ta sami maigidanta tace lokaci yayi da zasu nema mata lafiya a ajiye boko a gefe.

"Neman lafiya wane iri?" Yace yana kallonta.

"Daddy na tabbatar Qareeba aljanu gareta irin masu hana auren nan. Idan ba haka ba wane dalili zaisa ta kai har yanzu babu aure babu mijin auren a hannu"

Bayan gajeren nazari ya amince da bukatarta don shima ya gaji da gorin 'yan uwa. Abokansa ma wasu sukan yi masa maganar tun yana bada amsa har yayi shiru.

Maigadinsu suka sanarwa saboda ustazu ne. Washegari sai gashi da malami aka zo aka rinka yi mata karatu harda hayaki. Malamin gudun kada ace baiyi komai ba ya zaro bulala zai fara lafta mata wai aljanun masu taurin kai ne. Tana ganin haka ta tashi a guje ta koma ciki.

Bayan 'yan kwanaki ta sami Dr Tani har daki tace ita dai tana son aure tunda Dahirun bai samu ba su taimaka su sama mata miji.

Ranar hankalin Dr Tani ba karamin tashi yayi ba don da kyar tayi bacci. A ina zata sami mai auren Qareeba? Bata son mijinta yaji wannan maganar sam domin a danginsa zai nema daga nan su sami na gori ace gwanjonta aka yi musu. Mutum daya gareta da ta rike kawa aminiya amma sun kwana biyu ko gaisuwar kirki bata shiga tsakaninsu ba. Duk da haka gani tayi gara ta sake gwada sa'arta a karo na karshe kafin a nemi wata mafitar.

Wayarta ta dauko ta jima tana sake-sake kafin ta danna kira.

Haj Mara tana zaune yau ko wanka ta kasa abin duniya ya isheta ta mika hannu ta dauki wayarta da take ruri. Sunan Dr Tani ta gani to itama damuwa ta isheta ta dauka da sauri ta gyara muryarta tayi sallama.

Dr Tani tana amsawa Haj Mara tayi wata shewa kamar bata san waye ba sai yanzu "Tani kece don Allah? Wayyo aminiyata shiru shiru na rasa nambarki ke kuma kin dena nemana"

Dr Tani taji dadi ashe dai Haj Mara bata ya da ita gabadaya ba rashin number ne amma sai ta dan dake.
"Haba Marakisiyya idan babu waya baki san gidana bane? "

Kamar zata yi kuka tace "na sani amma tun tafiyar Babawo naga kamar kinyi fushi dani. Kuma na fada miki Alhaji ne yace gara ya bar kasar kura ta lafa"

"Har shekara takwas? Ni mu bar wannan zancen dama kira nayi mu gaisa inji lafiyarku" ga dama ta samu na son jin yaya BB amma tana gudun kada ace yayi aure.

Kamar Haj Mara ta sani tace "ina 'yata kuwa Qareeba? Nasan yanzu kila tayi yara biyu ko uku. Ba rabonmu lokacin gashi shi yaki aure har yanzu"

Kankame wayar Dr Tani tayi dadi har kasan zuciyarta
"To ai nima har yau Qareeba dai tana nan in fada miki taki kowa. Nayi fadan nayi nasihar duk a banza. Wai tunda ta rasa BB na farko ta hakura da aure ke kiji"

Wata siririyar dariya Haj Mara tayi. Ta sani sarai Qareeba babu mashinshini ne tunda takan dan bibiyi me Dr Tani din take ciki. To amma dama ce ta karshe ta samu ta yiwa Babawo aure ko ya kintsu kamar kowa.
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰15

*Batul Mamman*💖



Tsohon kango ne wanda yaran unguwar da yake ciki ma tsoron yin dare suke a kusa dashi saboda 'yan daban da suka mayar dashi wurin sheke ayarsu. Daidai ballallen gate din BB ne zaune cikin daya daga cikin motocin Alh Sule yana yiwa shugaban 'yan daban bayani.

"An fada min kaima dan Kano ne ina tunanin nemanta bazai yi muku wahala ba"

Garwashi yace "to Yallabai ka bamu hoto da adireshi mana saboda rage wahala ko ya kace."

Sosa yamutsatstsen kansa yayi wanda yaki yarda ya aske har yau yace da yasan address din me zai kawo shi wurinsu ma. Gajeren tsaki yaja sannan yace.

"Sunanta Mawadda kauyensu yana cikin Kabeji a nan Kano"

Me Garwashi zaiyi in ba dariya ba "Kabeji kuma Ranka ya dade kwadon salak zaka yi hala?....hahahahhh zan taho maka da caras da gurji"

A fusace BB ya fito daga motar ya damki wuyansa. Yaran Garwashi suka soma tasowa ganin an kama ubangidansu. Shaka sosai BB yayi masa yana huci "ba wasa bane ya kawoni. Sati daya na baka ka nemo min inda take koda gidan miji ne zan baku 500k."

Jin haka Garwashi ya daga hannu ya dakatar da yaransa. BB ya ture shi har ya kusa fadowa ya dago kai a wahale "zamu duba amma duk da haka ka bamu wata inkiya mana yadda zamu jidadin yi maka aiki na dai fahimta garinsu a Bebeji yake ko"

Sai da ya shiga mota ya zauna sannan yace "anyi mata fyade shekara takwas da suka wuce har kotu an shiga amma basuyi nasara ba"

Zaro idanu Garwashi yayi "wane dan...."
Sai kuma yayi shiru ganin irin kallon da BB yake yi masa kafin ya bada musu kura yaja motar yayi gaba.

Yaransa da suke gefe suka marmatso yana rike da wuya yana jujjuya shi.

Na hannun damansa cikin yaran yace "Baaba ina tunanin shine fa yayi fyaden kaga ai yayi kalar eh yane. Kuma don rainin sense ya shake maka wuya a fadarka don yana takamar tsohonsa yana da maiko"

Cecekuce yaran suka soma suna nuna takaicin hanasu su far wa BB lokacin da ya shake shi.

"Ku barni dashi zamu nemo yarinyar nan duk inda take. Amma kwarankwatsa zamu nuna mata solidarity tunda 'yar uwa ce bakanuwa. Gayis (guys) mu ware gobe akwai trabilin gabanmu."

******

Mawadda na zaune gaban Baba daga gefen tabarma a tsakar gidansu. Yaya da Ade suna dakunansu haka ma Iya da Inna.

Kamar kullum nasiha da yabonta ya soma yi don baya gajiya wurin karfafa mata gwiwa akan hakuri da tawakkali.

"Ina alfahari dake sosai da yadda ki ka karbi kaddara bata sanya kin zama daga cikin mutane masu gazawa imaninsu yayi rauni ba. Ki cigaba da mika lamuranki ga Allah da sannu zakiyi ta girbar alkhairi kinji."

"In sha Allahu Baba"

"Bayan wannan Mawadda ina so kada kiji kunyata ki fada min gaskiya yaya kuka yi da Dahiru?"

Faduwar gaba taji hade da kunya a lokaci guda ta dukar da kanta sannan ta fada masa gaskiya wato maganar aure da Dahiru yayi mata sai dai bata fada masa yadda suka kare da ya zama yayanta kawai ba. Ta dai sanar dashi bata amince ba.

"Baba kada ka damu nima na san ba zanyi aure ba saboda bazan yaudari kaina ba" ta fada cikin dakakkiyar murya tana kokarin boye karayar da zuciyarta take neman yi.

Tausayinta Mal Fatihu yaji sosai "Allah ne Masani ko kina da rabon aure ko babu. Abinda nake so ki kiyaye dai bai wuce kada kisa Dahiru a zuciyarki ba. Kinga yadda abubuwa suka kasance a da bana jin yanzu zata sauya zani. Duk yadda na matsu inga kina dakinki kamar sauran 'yan uwanki bazan taba yarda kije inda ba'a bukatarki ba. Na shaida Dahiru mutum ne managarci amma aure Mawadda ba alaka bace tsakanin mata da miji kawai. Ta hada da iyaye da 'yan uwa makusanta. Duk inda kika samu matsala da daya daga ciki ko iyayen miji ko 'yan uwansa to ina mai tabbatar miki miji ko hadiyarki yake don kyautatawa sai jindadinki ya ragu musamman idan iyayensa ne."

Kasa daurewa tayi hawaye ya soma fita a idanunta "Baba zan kiyaye in Allah Ya yarda" tana kaiwa nan ta tashi ta bar wurin da sauri saboda kukan da ya taso mata. Bandaki ta shige ta rufe kofa ta shiga kuka har tsakar gidan Baba yana jiyo shesshekarta.

Shi kanshi ba don namiji bane babu abinda zai hana shi tayata kukan. Zuciyarsa ce tayi masa nauyi yana kara ganin laifinsa ne na turata aiki tun farko har haka ta faru.  Amma zasu cigaba da hakuri har Allah Ya kawo musu mafita.
*****

Washegari tana gama ayyukanta na gida asibiti ta tafi. Da yake da wuri taje bata dade sosai a layi ba.

Dr Imran ya gama jin duk wani bayani nata ya nuna mata file din gabansa.

"Duk wani bayani ko gwaji daga ranar da na fara dubaki har yanzu suna cikin nan. Ina fata kin rike duka bayannan da nayi miki game da ainihin abinda ya sameki har ya janyo miki lalurar?"

"Na gane Doctor. Nagode sosai" tace a hankali tana kokarin boye hawayenta. Tun maganarsu da Baba jiya haka ta tashi sukuku. Ba wai abin mamaki bane kuma itama kafin ya fada ta riga tasan da hakan. Sai dai yanzu tausayin rayuwarta take yi kawai. Bata taba hango rayuwarta zata zama haka ba. Tuni ta gama shiri da tsara rayuwarta da Dahiru a shekarun baya sai gashi Allah Ya zartar da ikonSa ta koma mai gyara amare wadda bata da ranar ganin nata auren.

Dr Imran tashi yayi ya dawo dayar kujerar marasa lafiyan wadda take kallonta ya zauna. Yana ganin yadda ta sake tura tata baya duk da cewa akwai tazara tsakaninsu tun farko. Ya sani irin haka yana daga cikin tsoron da yake bibiyarta har yanzu. A kokarinsa na taimaka mata ta rage ne yasa idan ta shiga office dinsa yake tilasta mata rufe kofa ko bata so don ta gane ba kowane namiji bane macuci. Tun tana zama tayi ta kallon kofa tana hawaye har ya samu ta dena kukan. Yanzu gashi ta yarda dashi zata zauna ba tare da tunanin komai ba.

"Mawadda."

"Na'am Doctor"

"A ka'ida yau ne last day da zan duba ki sai dai idan wata matsalar ta taso wadda bama fata."

Godiya tayi masa amma yadda ya gama karantarta na tsahon lokacin da take zuwa asibitinsu ya san tana da damuwa a ranta.

"Ko soyayyata ce tayi miki mugun kamu kike tunanin daga yau zamu rabu? Banyi niyar barinki ba yau ko kinki ko kinso zan zo gida neman izini wurin Baba"

Kai ta dago da sauri "don Allah kada kazo. Na fada maka bazanyi auren nan ba."

"Saboda wani banzan BB yake ko wa? Ki barshi haka duk inda yake sakayyar Allah zata kama shi" Ya fada ransa yana dan baci.

Kai ta girgiza tana soma kuka "ni dai kawai"

"Ke dai kawai me? Ko dai Dahiru ki ke jira?"

Dr Imran yasan labarin Mawadda domin kuwa bata boye masa komai ba bayan ya hillaceta da dabararsu ta likitoci a kokarin taimakonta. Duk duniya babu wanda take iya fadawa abubuwan da ba kowa ya sani ba bayan iyayenta sai shi.

Yanayin da yaga ta shiga yasa shi gane ko ma meye matsalarta da Dahirun a ciki. Rarrashi da shawara ya soma bata da kanta ta fada masa dawowar Dahiru cikin rayuwarta da kuma kudurinta na kin amince masa.

Dariya yayi ya shiga zolayarta "Akwai matsala kuwa don nima ba hakura zanyi ba. In fact kince na kara zage damtse mai rabo ya dauka. Wato ciwon soyayya zai tashi shine duk naga jikinki a mace yau kamar wata mara lafiya."

Sai da ya gama sawa ta saki ranta sannan yace ta yawaita addu'a da neman zabin Allah.

"Nasan kina son Dahirun nan Mawadda bazanyi muku katsalandan ba har sai naga yadda ta kasance. Ki sani dai ni masoyinki ne mai burin kyautata rayuwarki. Ina fata zumuncinmu ya dore ba wai kawai tsakanin likita da patient ba"

Taji dadin saurin fahimtarsa don bata jin zata juri fama da maza biyu akan abinda duka babu lallai su samu. Sun jima suna hira kafin wata nurse ta shigo tace ya bar mutane suna jira fa.

*****

Hira Dahiru da Attahir suke yi suna tsara bikin Attahir din da yake gabatowa nan da wata uku. 

Ango yana ta zumudi suna lissafin nawa za'a ware domin hada lefe da sauran abubuwa. Ga kama gida da yake son yi shima basu gama zabar unguwa ba.

Attahir ya nuna masa hoton wasu akwatuna masu kyau da yake son zaba cikinsu.

"Ba don ka tsaya ruwan ido ba kaga kamata yayi komai muyi tare. Akwatunan nan so nayi na saya mana iri daya amma kada a saya har su fita yayi baka tsayar da mata ba tuzurun Haj Mama"

Dahiru yayi dariya "yanzu ma ai komai taren muke yi. Mata kuma kasha kuruminka Haj Mama ta kusa dena yi min korafin rashin aure ana kirana tuzuru"

Dundu Attahir ya kai masa yana cewa yaci amanarsa tunda bai sanar dashi da wuri ba.  Labarin sake haduwa da Mawadda ya bashi domin kuwa amincinsu yasa ya sanar dashi rayuwarsa ta baya. Attahir na murna da wannan al'amari Dahiru ya sako zancen Anti Qareeba. Sunci dariya musamman Attahir wanda yaso kwarai ace yana wurin
"Da na wanke 'yar rainin wayo. Ni ka tabbata mamanta likita ce kuwa ba irin dafta dinnan da ake karawa gaban suna bace don ado?"

"Baka da kirki har asibiti gareta fa"

"To ai abin nasu ne ba ko kunya, gaskiya idan ka auri Qareeba sunan 'ya'yanka sorry. Tun wuri ma ka sani irin hadin zumuncin nan bazan yarda ba kada a cuceni a hada ni da jikoki 'yan ahirin"

Yana fada ya tashi a guje don Dahiru  bayansa ya bi suna dariya. Haj Mama tana shigowa taja tsaki tana girgiza kai.

"Allah nagode Maka. Kattin maza maimakon su kawo min yaransu in rinka jin hayaniyarsu ina bari bari shine da kansu suke cika min kunne. Kodayake gara kai Attahir, wani yana nan sai sayen kaya da takalma yana kwalliya."

Dahiru yayi dariya yasan dashi take. Iyalin gidan nan suna kaunarshi suna nuna masa soyayya tamkar jininsu. Attahir ne yayi mata albishir da an kusa gabatar mata da suruka ai kuwa ta washe fuska tana murna.

Bayan fitarta ya matsawa Dahiru ya kamata su je ya ganta ya kara wasa mata dan uwansa don tayi saurin amincewa.

Tagumi Qareeba ta rafka tana zaune daga ita sai zani da tayi dauri ya leko ta kasa sai wata vest da hannut daya ya sabule. Ko wanka bata yi ba tun safe. Rashin mijin nan fa yana damunta sosai.

Dr Tani ce ta shigo dakin rike da leda ta dora mata akan cinya.

"Qareeba bana son wannan damuwa da kika shiga 'yan kwanakin nan"

"Kiji Mummy fa na rasa mijin aure ya bazan damu ba? Dashiru ya gujeni saboda wulakancin da kika yi masa da." Ta kare da tura baki.

Bakin Dr Tani ta doke "shashasha karshenta ma Dashiru kika rinka kiransa a gabansa ba dole ya gujeki. Yanzu dai bude ledar nan ki duba"

Ihun murna ta saka bayan ta bude . Material ne mai matukar kyau da tsada. Kamar yarinyar da aka yiwa kyautar bazata tace
"Mummy nawa ne?"

Zama Dr Tani tayi sannan cikin murna itama tace "ki tashi kiyi wanka ki kai dinki. Next week sunday Babawo zai zo wurinki. Ya dawo kuma da maganar aure"

Sakin kayan tayi "Cabdi sai kace wata mara aji Mummy? Sai da ya gadamar dawowa za'ace yazo neman aure. To ni na wuce ajinsa wallahi Dashiru nake so ki fadawa Daddy kawai"

Ranta ya soma baci don Qareeba bata san yadda ta zubar da nata ajin bane saboda nema mata miji.
"Dahirun me, har nawa yake kuma me ya taka? Banda ma lalura shi har zai taba yin arzikin da zamu roki alfarma wurinsa ne?"

Har ranta Qareeba bata so ana fadin abu mara dadi ga Dashirunta yanzu. Daukan kayan tayi ba don taso ba ta ajiye akan gado ta shiga wanka.

Da ta shirya ta fito ma kana ganinta kasan an bata mata rai. Dr Tani bata son biye mata dama ina su ina Dahiru dan mutan Tariwa. Kawai dai taso amfani dashi ne lokacin da babu kowa. Ita ba wai kudin su Haj Mara ne ya dameta ba kamar son 'yarta tayi auren da zai bawa duka danginsu 'yan bani na iya mamaki. A yanzu ansa musu ido kamar su kadai suka fara haihuwar 'yar da ta rasa miji.
******

Yadda Attahir ya matsawa Dahiru dole ya kira Mawadda ya sanar da ita zai zo da dan uwansa su gaisa.

Tana kwance tana hutawa sanda ya kira. Taji dadin jin zaizo don kwana tayi tunaninsa da kuma tunanin maganarsu da Baba. Ya zama dole ta yaki zuciyarta ta dakatar da alakar da take tunanin zata kare a ciwon zuciya. Shawarar Dr Imran zata bi da yace ta yawaita addua amma duk da haka zata yi kokari wurin janye masa.

"Sai ana magana dake ki shiga tunani. Shirun na mene?" Dahiru ya fada don ya fara ganeta da yawan tunani yanzu.

Mikewa tayi kafin tace "tunanin saurayina, sai dai kazo zan baka labari yau zance naje"

Sai da ya fito daga falon ya iya amsawa yadda yaji wani bala'in kishi ya taso masa abin har mamaki ya bashi.

"Me kika ce?"

Muryarsa ta fahimtar da ita yadda yaji sai kuma ta soma karaya.
"Asibiti naje ba na fada maka ina zuwa checkup ba"

"Mawaddatan wa Rahma!"

"Na'am inji larabawa"

"Bana son wannan wasan don Allah da gaske zance kika je? Likita ne saurayin naki?" Yayi magana cikin cijewa.

Sosai ransa ya baci da kishin da ya rufe masa ido. Bai jira ta ansa masa ba ma ya nanata mata zuwansu yanzu ya kashe wayar.

Hannunsa yasa ya rike bakinsa da habarsa idanunsa suka kankance. Karshe ya koma ya dafe saman motar Attahir da hannuwansa biyu ya dukar da kansa yana kallon kasa.

Attahir da yaji bai dawo ba ya fito ya sameshi a haka. Kafadarsa ya dafa hakan yasa shi juyowa suna kallon juna.

"Me ya faru?" Attahir ya tambaya don kallo daya zaka yi masa ka gane baya cikin nutsuwa.

"Wai ni Mawadda zata cewa taje zance? Likitan da yake dubata saurayinta ne. Wallahi bazan iya sake rasata ba Attahir. Na sota sosai a baya amma yanzu ni bansan yadda zan kwatanta maka kaunar da nake mata ba. Ban taba son wata mace ba sai ita kaima shaida ne"

Motar Attahir ya bude suka shiga sannan ya kalli Dahiru "calm down bro, har ka manta rabonka da ita ne kake tunanin yanzu komai zai zo da sauki kamar ba'ayi ba?"

"Nayi zaton itama tana sona....na tabbatar ne ma. Baka ji yadda kalamanta suka tsaya min a rai ba"

Attahir ya jinjina kai "ashe haka kake da kishi Dahiru? Lallai Mawadda sai tayi a hankali"

Shiru kawai yayi Attahir yaja mota suka fita. Lokacin da yaji labarin anyi mata fyade abu daya ne a ransa wato aure. Sai dai yafi kowa sanin me ya jima yana dannewa har mutane suke masa kallon kamar mutum marasa damuwa a rai. Ko Mawadda baya son ta san yadda yake burin haduwa da mutumin da yayi mata fyade. Ko ranar da tace masa taje Kaduna da ya bagarar da zancen yayi ne kawai saboda yadda yaji abin zai fama masa tsohon ciwonsa. Soyayyarta da son sanyata cikin farinciki sune suke dakushe bacin ransa da kishin da yake damunsa game da kaddarar da ta sameta.

Suna fitowa daga gidan daidai lokacin Qareeba ma ta fito zata kai dinki. Dahiru ta hango jiki na rawa ta zuke glass ta soma kwala masa kira. Ganin bai ji ba yasa kawai tabi bayansu.

Attahir yana ta kwantarwa da Dahiru hankali kafin su tsaya a gidan mai ya sami nutsuwa sosai.

Ana zuba musu mai Attahir yana waje kusa da me zuban man yayin da Dahiru yake zaune ya kwantar da kansa jikin kujera hade da lumshe idanu.

"AHIRIN" Qareeba tace da karfi tana tsaye daga waje saitinsa.

A firgice ya bude ido yayi tozali da ita. Tsabar rudewa ma ya manta ina yake ya taso da karfi ya buge kansa. Dama gashi rai a bace abu ya tarar masa.

"Lahhhh Dashiru sannu kaji" tace da ya fito.

Attahir kawai ya gani a gefensu yana murmushi don tana cewa Ahirin ya zagayo ya kuma gane ko wacece.

Kin kulata Dahiru yayi Attahir yace "Anti Qareeba daga ina haka"

Habawa dadi kamar ta saka ihu ta rabe jikin mota ta rufe fuska da mayafi irin na jin kunyar nan. Dahiru kansa sai da yayi murmushi sannan yace.

"Mai kika zo sha kema?"

"A'a na fito zani wurin dinki ne na hango ku shine na tsaya mu gaisa" ta sake amsawa tana ta fari da idanu.

Attahir ya gimtse dariyarsa "ko dai dan uwana ya hure miki idon ne naga yana ta kadawa"

Dahiru ya watsa masa harara ita kuwa ta kuma sunkuyar da kai "Kai dai baka da kunya da alama. Dashiru ashe kana bawa 'yan uwanka labarina gashi har ya ganeni. Don Allah ka ajiye komai ka dawo su Mummy sun amince da soyayyarmu. Yaya sunanka ne?" Ta kalli Attahir.

Yayi dariya "Ni Attashir nake"

Sakin fuska tayi "sunanku kusan daya da My Man"

"Kut..." Dahiru yace tsabar mamaki wai my man, sai dai bai sami damar karawa ba Attahir ya sakar masa dundu a baya yana masa sannu wai ya kware. Shi kuma yana make tasa dariyar da tarin karya.

Duk ta rude "Man sannu wayyo me ya sameka haka? Attashir do something mana!"

Attahir dariya taci karfinsa Dahiru bakinciki ya turnuke shi zata tara musu mutane an fara kallonsu ya ma kasa magana sai biye masa da yayi yana duka bayan nasa.

Qareeba ranta ya baci da dariyar Attahir ta karbi purewater ta bawa Dahiru sannan tayi masa wani kallo da ya kara tunzuro dariyar tasa. Bakin gwargwado yake kokarin boyewa ta sake kallon Dahiru.

"Sannu Man ko zaka zo na mayar da kai gida. Bana jin hankalina zai kwanta idan na barka da wannan dan uwan naka. I am sorry to say amma kamar yana da matsalar brain ko?"

Yace cikin gatse  "haka kike gani?"

"Sosai kuwa , ka kware amma ya rinka dariya  haka. Kada ku rinka raina lalura inji Mummyna gara ku kaishi asibiti"

Dahiru ya kamo Attahir shima kamar yayi dariyar sai dai so yake kawai ta tafi "haka muke fama dashi amma gara ki tafi don daga dariyar nan abin nasa gaba zai kara. Jeki kawai zan kaishi gida"

A tsorace ta matsa gefe "akwai number din malamin da aka kira yayi min karatu kwanaki ko na baku? Ni dai an tabbatar bani da aljanu amma wannan...mtsw..akwai serious problem"

"Sai nazo zan karba" Dahiru yace ya danna Attahir a mota wanda dariya ta sa ya soma hawaye.

Qareeba na ganin ya goge ido tayi baya tana sake cewa Dahiru yayi a hankali ya kunna motar suka yi gaba. Itama juyawa tayi tana adduar Man dinta ya isa gida lafiya.

Har suka tsaya a danja dariya suke yi. Attahir sai ya kalli Dahiru yace "My Man" sai su sake kwashewa da dariya.

"Man da gaske fa idan ka auri  Woman babu zancen auren zumunci tsakanin 'ya'yanmu. Wai ji ko kadan bata ma fahimci ita ce abar dariyar ba"

"Ai baka ga komai ba. Ni da na zauna a gidan nasha kallo wani abin shiru ake yi kawai"

Har suka isa gidansu Mawadda suna dariyar Anti Qareeba.
******

Yanayin da Dahiru ya amsata da ajiye waya ya tsaya mata a rai. Jiki a sanyaye ta fita falon da take sauke shi ta sami Marwanu a kwance kan kujera yana bacci yazo hutu. Tashinsa tayi tace ya kwashe kwanukan abincin da ya soma tarawa daga zuwansa.

"Bako zaki yi ne Yayata ta kaina?" Ya tambaya yana daga gira.

"Jere zamu yiwa amaryarka dai" ta bashi amsa fuskarta ba walwala.

Tattare kayan yayi harda fesa wani turare da take hadawa na daki. Yana fita ya tambayi Ade me aka yiwa Mawadda tace itama tun jiya ta kula yanayinta ya sauya. Yaya tace sun sawa 'yarta ido a barta ta sarara.

Ba dadewa Dahiru ya sake kiranta yace sun iso. Har yanzu yana jin ba dadi saboda maganarta ta dazu kuma taji hakan a muryarsa. Ji tayi kamar tasa kuka da tayi tunanin me zaiyi kuma idan ta tabbatar masa da ya dena zuwa da sunan ganinta gabadaya.

Marwanu ne shigo dasu yana ta murnar ganin Dahiru. Sai da ya fita Mawadda ta shigo ta zauna a inda ta saba , bakin kofa.

Attahir ta gaisar ta dauke kai kamar bata ga Dahiru ba. Shima wayarsa ya shiga dannawa yaki kallonta.

Attahir yayi gyaran murya kamar suna jira duka su biyun suka kalle shi hakan yayi sanadin haduwar idanunsu. Mawadda ce ta soma kawar da kai gabanta yana faduwa. Ta rasa gane wane irin so take yiwa wannan Dahirun daga sake haduwarsu. Shima a nasa bangaren neman fushin ma yayi ya rasa amma sai ya basar ya kawar da kai.

Attahir ya gyara zama yana dariya "Fushin masoya da dadin kallo bari na dauka a waya ko na sami abin kallo da nishadi"

Murmushi Mawadda tayi "ayi haka Dan uwanmu? Ka tambayar min shi dai ko nayi masa laifi ne daga wasa"

Dahiru ya tabo "ka fada min me 'yar uwarmu tayi maka daga wasa ka shigo kana wani hade rai"

"Ta fada maka wurin wa taje zance har take iya fada min nida tace na tsaya iya yayanta kawai"

Juyowa yayi ya maimaita tambayar tace  cikin  murya mai rauni tana shirin kuka "ni wasa nake masa kace yayi hakuri bana so mu rabu haka"

Wata irin juyowa Dahiru yayi ya kalleta kafin ya sake cewa Attahir "kaji zancen rabuwa ma take min."

Attahir tashi yayi ganin abin ya soma zama na gaske "ni nayi nan idan kun gama sai ka kirani"

Matsawa tayi ciki ya fita ya barsu su kadai. Daga ita har Dahirun an rasa me cewa komai. Kusan minti uku kafin ya kawo karshen shirun nasu

"Duba wayarki nayi miki text"

Sai da ta harare shi ta duba wayar.

*Bazan iya rabuwa dake ba akan me zaki rinka zancen rabuwa?shi kuma wanda kika je wurin nashi yayi miki ganin karshe gara ki sani tun yanzu ina da kishi*

Sai da ta karance sakon tsaf sannan ta dago kai  "an sami matsala fa, ni ban iya karatu ba"

Sake rubutu yayi yace "duba yanzu na tabbatar zaki iya karantawa"

Wayar ta sake kallo ta saki baki.

*nima ina sonki*

Bakinta yake ta kallo tana cije lebenta tana wani kyakkyawan murmushi tayi rubutu sannan tayi masa alama da ya duba tasa wayar.

*yaushe nace ina sonka?*

Ajiye wayarsa yayi kusa da ta Attahir da ya bari a kan kujerar sannan yace
 "amsar abinda kike boyewa a zuciyarki na baki"

"Kace in fara turare a gidan nan na hadu da mai gani har hanji" tayi maganar cikin dariya.

"Ni tawa maitar tafi karfin turare idan na kama sai na...na dai yi shiru ki karasa a zuciyarki"

Kunya taji sai kuma tace "Allah Yayanmu ka iya rigima daga wasa duk ka tayar min da hankali."

"Kin tabbata har zancen rabuwar ma wasa ne?" Yace yana kafeta da ido.

Kokarin fahimtar dashi ta soma yi matsalolin da zasu iya tasowa daga dangi wanda bata so a maimaita irin na da.

Gabadaya maganganun bata masa rai suke yi don baya jin zai sake hakuri yadda yayi a baya. Sai da ya bari ta gama bayaninta kamar tayi kuka don ba karamin dauriya take yi ba yace

"Kiyi ki gama zille-zillen a daukoki a kawo min gidana"

Attahir ne ya tuna da wayarsa ya koma zai dauko.

Yadda Mawadda take a zaune kusan kan kafarta daya a takure Dahiru yace ta gyara zamanta mana bata gaji bane a haka. Tashi taso yi don itama ta gaji din kafar tayi tsami shi kuma Attahir ya taho bai ma kula ba ya kusa bugeta tunda a bakin kofa take. Motsin da taji yasa tayi baya ta zauna daram ba shiri.

Dahiru na ganin haka ya taso da zafin nama saboda ta kusa buguwa da kofa. Yadda ya taso ya bala'in bata tsoro dama gashi yamma tayi gari ya soma dubu. A lokacin babu abinda yake yawo a kanta sai BB balle da taga Attahir duka su biyun kasa gane kowa tayi sai mugun faduwar gaba ta sa ihu a razane har cikin gidan babu wanda bai ji ba.

Marwanu ne a gaba Baba ma ya taso yana sauri duk da yanayin jikinsa. Attahir dai gefe yaja yayin da Dahiru yayi yunkurin taimaka mata ta tashi don kwanciya tayi gabadaya ta cure jikinta wuri guda tana kuka.

"Don Allah ka rufa min asiri kar ka sake" take cewa da rokon kada yayi mata fyade.

Dahiru ja yayi baya zuciyarsa na kuna sai hawaye yake wanda bai ma san yana yi ba don tashin hankali.

Baba na zuwa ya zauna a gefenta yasa hannunsa mai lafiya ya rike hannunta daya sosai "bude idonki Mawadda nine"

Kuka take har yanzu tana surutai yasa Marwanu ya dago masa ita shi kanshi tasa muryar rawa take "ki kalleni Baba ne Mawadda"

Da kyar Dahiru yace "Wallahi babu abinda nayi mata. Faduwa tayi shine nayi niyar taimaka mata ta tashi"

Su Yaya suna son zuwa Inna ta hana tace su bari a shigo da ita tunda akwai baki a wurin.

Magana ta rarrashi Mal Fatihu ya cigaba sai a hankali ta bude idanun  da ta runtse "Baba BB ne ya biyoni ko?"

"Bashi bane Dahiru ne kin ganshi can tsaye kin tada masa hankali" ya nuna mata inda Dahiru yake tsaye yana mai takaicin rashin damar taimakonta da tsinewa wannan BB din ko waye shi.

Attahir kuwa abin ba karamin tausayi ya bashi ba. Da taimakon Marwanu Mawadda ta tashi ya rike mata hannu kamar yarinya suka koma cikin gidan tana ta waigen Dahiru. Shima din ita yake kallo yana kara so da tausayinta.

Baba yace su zauna yana murmushinsa na manya yace "kada ka damu nan da 'yan kwanaki zata warware. Wannan yana daga cikin abubuwan da mukayi ta fama dasu a garin nan. Idan ka kula bata taba wuce bakin kofa duk inda yake da maza. Ko ni mahaifinta dakina indai ina ciki wallahi iyakarta kofa sai nayi kamar bangane ba"

"Amma Baba babu wani taimako da zamu iya yi mata ko asibiti?"

"Duk munyi Dahiru al'amarin ne sai a hankali zai wuce kila. Ban sani ba ko ta fada maka nace ku hakura da juna."

Da sauri Dahiru ya kalli Baba shi kuma ya cigaba da cewa "ina jinka tamkar dan cikina domin samun namiji irinka sai an tona. Kaso Mawadda lokacin da duniya ta juya mata baya na tabbatar bazata taba samun kamarka ba. Amma yau ka ganewa idanunka kadan daga tabon da yaron nan ya bar mata."

Runtse ido Dahiru yayi kawai don bakinciki.

 "Har kullum ka dauki gidan nan gidanku amma na soke zancen aure don samun maslaha a rayuwar ku biyun"

Gabansa Dahiru yazo ya durkusa cikin yanayi mai ban tausayi
"Baba idan akan su Baffa ne tun sati biyu da suka wuce suka so zuwa sai ciwon sugan Inna ya tashi. Zasu zo gidan nan kuyi magana don Allah Baba kayi hakuri ko yaya take zan iya zama da ita"

Mal Fatihu yaji tausayinsa amma yana hango ko anyi auren to da wuya su sami rayuwa irin ta sauran ma'aurata. Idan hakane kuwa bai yiwa Dahiru adalci ba don yasan yau da gobe sai Allah.
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰17

*Batul Mamman*💖



BB ne akan ruwan cikin Qareeba ya matse mata hannuwa babu sutura a jikinsa kamar a dakinsa. Da zafin nama Dahiru ya fizgo shi ya kai masa naushi. Qareeba na ganin ya dagata ta mirgina gefe tana wani irin kuka. Minti guda da sun kara basu shigo ba da BB ya kafa mata tarihin fyade itama. Yaci mutumcinta karshe tamkar wani dabba. Kayanta da hannu ya tsarge su bayan ya gama dukanta. Dahiru ko kallonta baiyi ba ya haye kan BB dukansa yake iya karfinsa.

A daidai wannan lokacin babu abinda yake hangowa sai Mawaddansa da ta taba riskar kanta cikin yanayi irin wannan. Hakan ya kara masa kaimi ya jibgi BB iya karfinsa don ko motsin kirki ya gagare shi.

Kukan Qareeba ya dawowa da Dahiru hayyacinsa yaji tana kiran Mummy. Juyawa yayi Dr. Tani tamkar gawa a kwance. Sai da ya karawa BB duka a ciki da kafarsa sannan ya tsallake shi ya koma kanta. Dagata yayi amma duk da haka ya runtse idanunsa daga kallon Qareeba yace

"Zaki iya saukowa?"

"Eh"

"Ki rufe jikinki ki sauko muje asibiti ina jin suma tayi."

Wani zumbulelen hijab na sallar Dr Tani ta zura ta biyo bayanshi tana tafiya da kyar ga jini yana diga a kasa. Ashe glass ne ya soketa daga jug din da ta fada a kai wahala tasa bata sani ba.

Da gudu gudu Dahiru ya fita yana kwalawa maigadi kira. Shima a guje ya taho ganin Dr Tani a kafadar Dahiru yana son bude bayan motarsa ya sakata amma hannunsa sai rawa yake yi.

Maigadi ya bude masa yana tambayar me yake faruwa sai ga Qareeba ta taho fuska ta soma kumbura lebe da hanci duk jini. Gaban motar Dahiru ya bude mata ta zauna sannan ya kalli Maigadin.

"Akwai mutum a dakin Hajiya sannan ka kira maigidan nan..."
Lekawa yayi ta taga yace da Qareeba "zaki iya gane asibitin Hajiya?"

Ta amsa masa yace da maigadin ya fadawa maigidan ya samesu a can sannan ya shiga ya tada mota.

Qareeba sai kuka take yi tana kiran Dr Tani wadda har yanzu bata motsi. Dahiru ko danja baya tsayawa saboda tashin hankali balle da ya ga Qareeba ta rike kirji tana tari jini na fita. Da taimakon Allah ya isa asibitin. Ya fita ya kira wani da ya ga kamar likita ne yace masa Dr Tani da 'yarta ya kawo. Ana jin sunanta mutane suka yo kansa aka dauko su.

Tambayarsa ake me ya faru duk ya gigice tsabar tashin hankali.  Yafi so Dr Auwal yazo sai ya fara fada masa. Kusan minti shabiyar yana kai kawo a korido din dakunan da aka shigar dasu kafin wata likita mace ta fito ya tambayeta yaya ake ciki.

"Qareeba taji ciwuka a jikinta amma munyi nasarar cire gilasan da suka farfasa mata jiki. Sai kuma buguwa da su fashewar baki wanda zata sami saukinsu a hankali. Babbar matsalar dai bata wuce cikinta da aka taka...mtsw ko waye wannan dabba ta fishi hankali."

Cike da damuwa yace "yanzu dai zata tashi ko kuwa?"

Kallon ido cikin ido tayi masa "zata tashi amma yanzu haka theatre zamu shiga da ita"

"Ki ka ce kuma da sauki?"

"Akwai internal bleeding a cikinta tana bukatar surgery yanzun nan"

Tafiya tayi ta barshi nan a tsaye cikin rudani. Zai shiga dakin da Qareeban take likitan dake tare da Dr Tani ya fito. Yace ta farfado amma jininta yayi mugun hawa. Suna wurin Dr Auwal da su Najib suka karaso. Dukkansu Dahiru suke kallo suna tambayarsa me ya faru.

Dakin da Dr Tani take ya nuna musu su ka shiga duka. Tashi tayi tana kukan ina Qareeba aka ce ta kwanta aiki za'ayi mata yanzu. Hankalinta ya sake tashi ta fara wani abu kamar mai farfadiya dole nurse tace su fita aka sake taruwa a kanta.

A wajen dakin Dahiru ya sanar dasu abinda ya gani. Dr Auwal yayi baya saura kadan ya fadi yana salati Safwan ya rike shi. Faisal ne yace basu ga ta zama ba ya kira Maigadi akan ya rufe gidan zasu zo da 'yan sanda ya fada masa ai mutumin ya gudu. Yaso tare shi yayi kansa da mota dole ya bashi hanya.

"Zancen da nake maka yallabai ya balle kofar gate din" ya karasa da tambayar ya masu jiki.

Kowa cikin damuwa yake likitoci biyu da nurses suna ta shige da fice a tsakanin dakunan har aka fiddo Qareeba wadda fuskarta ta gama hadewa don kumburi zuwa dakin theatre. Zama suka yi jigum har aka fito da ita bayan awa daya.

Ranar sun ga tashin hankali mara misaltuwa. Dr Tani sai allurar bacci aka yi mata saboda jininta yaki sauka kuma ta sawa kanta damuwa da rashin ganin Qareeba. Awa uku Dahiru yayi a asibitin sai da ya fuskanci kamar komai ya daidaita ya fito da alkawarin zai koma washegari.
*****

Bakin motarsa yaje amma jikinsa sai rawa yake yi da kyar ya shiga ya bar asibitin.

Tuki ya rinka yi sai ganin kansa yayi a layin su Mawadda. Ita kadai yake bukatar gani a lokacin a yadda hoton BB da Qareeba suka zauna a kansa. Tunda yake bai taba ganin masifa irin wannan ba. Karin tausayin Mawadda ne ya mamaye zuciyarsa da babu wanda ya kai mata dauki kamar Qareeba har aka rabata da mutumcinta.


Takwas na dare ta dan gota ya kirata. Tana dauka muryarsa gabadaya ta canja yace "don Allah ki fito ina waje"

Tashi tayi zaune ba shiri saboda yanayin da ta ji muryarsa kuma ya katse kiran. Kwakwalwarta ce ta shiga tunanin ko lafiya ta dai saka hijab ta sanar da Yaya yazo ta fita.

A zatonta yana kofar gidan sai ta hango motarsa a inda yake ajiyewa karkashin wata bishiyar darbejiya a kunne. Tasan ba haka suka saba ba ciki yake shigowa amma dai bari taje ta gani.

Kansa ta gani ya kwantar akan sitiyari saboda ya sauke glass din tayi sallama. Yana dago kai gabanta ya fadi. Tashin hankali da damuwa ne karara a tattare dashi.

Kallonta yayi yace "ki koma ciki dare yayi."

"Bangane in koma ciki ba daga fitowa ta" tace tana kara matsowa jikin motar.

"Tafiya zanyi kinga dare yayi. Dama ganinki kawai nake son yi"

Giya ta ga ya saka zai tafi ta zagaya daya bangaren da sauri tayi sa'a a bude motar take kawai ta shige.

Bata san irin dauriyar da yake yi ba a wannan lokacin. Yadda jikinsa yake babu kwari haka zuciyarsa tayi rauni sosai. A sanyaye yace
"Meye hakan?"

Ta riga ta san akwai matsala har ta soma kwalla tace "kai zan tambaya, ka fada min ko ma mene ne don Allah"

Jikinsa ta kula rawa yake yi ya hade hannuwansa a kokarinsa na boye mata. Tsoro ne kawai ya sake kamata ta soma kuka.

"Yayanmu kana ganin ban cancanci sanin damuwarka bane?"

Ba niyarsa yasata kuka ba. Hasali ma zuwa yayi don a tunaninsa ganinta ne kadai a wannan lokacin zai kwantar masa da hankali. Sai dai abin ba haka yazo ba. Ji yayi ya tsani kansa a baya da ya kasa gama tanadin aurensu har aka tura ta aikatau.

Runtse idanu yayi  "ki koma ciki kada wani ya ganki a motar nan Baba bazai ji dadi ba"

"Wallahi bazan fita ba sai ka fada min ko kazo mu shiga ciki" tace tana hade rai.

Ya dago kai ya kalleta ta sake daure fuska.

"Naji fito muje".

Sai da ya fita sannan itama ta fito suka shiga ciki gabanta yana ta faduwa bata san me zai ce mata ba.

Sun zauna akan kujeru suna fuskantar juna duk ta kosa taji me zai ce.

"Ki yi hakuri da rayuwarki ta baya Mawadda, kiyi hakuri da talauci yasaki fita neman halak, kiyi hakuri da yadda talauci yasa aka danne miki hakkinki a kotu. Mawaddatan wa Rahma! Kiyi hakuri ni Dahiru banyi komai domin taimaka miki ba a wancan lokacin. Idan mutumin nan yana da rai ina fata Allah Ya hadani dashi ko sau daya ne...." muryarsa ce ta karye alamun yana boye kuka.

Maganganunsa da yanayinsa suka sake daga mata hankali. Yana magana tana hawaye zuciyarta tana tuna mata da kuncin da take ta kokarin mantawa. A tsorace tace "ka fasa aurena ko?"

Girgiza kai yayi "nan da kwana tara zaki zama mallakina in sha Allahu"

"Ka tayar min da hankali ka fada min abinda yake damunka mana. Me ya kawo wadannan maganganu?"

Da ace an daura aurensa da ita babu abinda zai hana shi rungumeta a wannan lokacin. Abinda yake zuciyarsa ya fada mata "Rarrashi nazo nema a wurinki Mawadda. Naso ace kin zama matata zaki iya rungumeni ki kwantar min da hankali. Ki rikeni kice komai mai wucewa ne. I need you a matsayin mata ba budurwa ba saboda a yau zuciyata ta hadu da mummunan tabo. Sai yau na gama fahimtarki da rayuwar da kika yi kina jinyar jikinki da zuciyarki"

Gabadaya ta tsinke da lamarinsa ya kara dagula mata lissafi. Tashi tayi zata fita yace ina zata je.

"Baba zan kira, na gaji da wannan juya maganar taka ka ki fahimtar dani yadda zan gane." Durkusawa tayi a kasa hawaye wani na bin wani a kumatunta "zan rarrasheka amma sai na san mene ne matsalar"

Bashi da zabi da ya wuce sanar da ita abin da ya sami Qareeba saboda baya so ta koma cikin gida kowa ya gane tayi kuka. Sai dai kafin ya gama labarin Mawadda tayi kuka har ta godewa Allah. Shima dauriya ce da rashin son nuna gazawarsa a gabanta tasa ya rike nasa hawayen.

"Ban taba ganin dabbanci irin wannan ba. Ba kasarmu ba duniya gabadaya tayi sake wurin karuwar fyade yanzu ya wuce kan 'yan mata harda yara kanana. Ke da ki ka taba fuskantar wannan abin zaki fini fahimtar halin da Anti Qareeba take ciki."

Kanta kawai take iya kadawa ta kasa cewa komai.

"Bakincikina ba akanta kawai ya tsaya ba. Ina tausayin duk wata mace babba ko karama, budurwa ko me aure da marasa imani cikinmu suke tozartawa ta hanyar yi musu fyade. Ina takaici idan na tuna ranar da hakan ta sameki karshenta bacci nake yi ko cin abinci. I was not there for you Mawadda ba haka naso ba."

"Ba laifinka bane"

Kallonta yayi fuska ta jike da hawaye "ni da nazo ki rarrasheni shine zaki barni da rarrashinki. Ki tashi ki zauna naji dadi ina da ke da zan fadawa damuwata. Kaina da zuciyata duka suka kulle na kasa tunani dazu"

Sun cigaba da hira akan wannan mummunar ta'asa da ta addabi al'ummar kasarmu. Taji tausayin Qareeba sosai balle da taji itama tasha duka kusan irin nata.

"Uhmm Yayanmu ita yayi mata dinne ko dukan ne kawai?"

"Bani da tabbas sai gobe idan naje zanji. Kinga da an daura aurenmu tare zamu je"

"Yanzu ma zanyi mata addu'ar samun lafiya domin wannan tabon da wuya yake warkewa duka zahiri da badini. Ka ga har yanzu ina da tabon belt a jikina guda daya yaki bacewa" tace a hankali.

Dahiru ya dubeta soyayyarta na kara samun gurbi a zuciyarsa.
"Ki tuna min ranar da aka kawo min ke wannan tabon zan fara nema a jikinki nayi kissing"

Tashi Mawadda tayi cikin matsananciyar kunya ta diririce tana neman hanyar fita tace  "na shigesu"

Dahiru shima ya tashi "ba ke kadai ba nima na shiga." Ya fada yana dukan bakinsa harda yi wa bakin fada.

Ya rigata kaiwa bakin kofa "kinga ni nayi nan ki tabbata kin manta wannan maganar kinji ko."

Da hannu biyu kamar tana korarsa ta rinka nuna masa kofa "jeka ni dai sai da safe"

Takalmansa ya zura ya juyo yana mata murmushi "nace ba...."

Shan kunu tayi kada ya kawo wasa sai dai kana ganinta kasan  dauriya tayi don ba karamar kunya take ji ba ganinsa ma da take a wurin "kace me?"

"Zan iya kiranki kafin na kwanta?"

"Na yafe Yayanmu don Allah ka tafi"

Gira daya ya daga yana murmushi "kin tabbata?"

"Eh, eh na tabbata"

"Da gaske zaki iya bacci batare da nace miki sai da safe ba Mawadda?"

Tunda suke bata taba jin tana so ya tafi irin na yau ba. Kuma sai wani jan zance yake yana kara sakata jin kunya.

"Wayyo Yayanmu kaje duka na yafe."

Dariya yayi ya tafi ta sauke ajiyar zuciya tana rike kirjinta da yake bugawa da karfi.

Ta taho zata fita kawai ya sake dawowa ciki idanunsa karaf cikin nata tayi kasa da kanta da sauri.

"Kina sona Mawadda?" Ya fada da wata irin murya a tausashe.

"Wai baza ka tafi ba?"

"Sai kin bani amsa ko na dawo ciki mu zauna naga daren da sauransa"

"Ka fa san amsar"

"Ban taba ji kin fada bane shiyasa yanzu naji ina kokonto"

Idanu ta ware tana ganin me zai sa shi wannan tunanin. So take ya tafi kuma saboda har yanzu maganarsa ta dazu tana mata yawo a kanta
"Ina yi"

Sake matsowa yayi ta ja baya "kina me?"

Cije lebe tayi ya lumshe idanunsa. Baya so tana wannan abin a yanzu dai da suke da katanga tsakaninsu.

Sai da taja numfashi sannan tace "Yayanmu Dahiru ina sonka amma don Allah ka tafi kafin nasa maka ihu"

"Nima ina sonki Mawaddatan wa Rahma, sai da safe"

Sake fita yayi tayi murmushi tana juyi "oh Allah Ka bani Yayanmu Dahiru"

Bata san ta ina ya sake bullowa ba sai ganinsa tayi a bakin kofar yace "Amin Ya Rabbi"

Ihu kawai tasa masa kunyar tayi mata yawa "Ahhhhh"

Yana jin haka ya fice da sauri yana dariya. Toshe bakinta tayi tana fatan babu wanda yaji daga ciki.

*****

A can asibiti an yiwa Qareeba aiki lafiya. Dr Tani kam basu da zabin da ya wuce sedating dinta wato aka sata baccin dole saboda suna so lokacin da zata farka ta ga Qareeba ma ta tashi. Me yiwu wa hakan zai taimaka wurin daidaituwar jinin nata.

Daki daya aka ajiye su zuwa wayewar gari. Dr Auwal sai shabiyun dare ya koma gida. Falon da abin ya afku wanda a waya ya sanar da Maigadi a fadawa maiaikinsu kada ta taba komai da sunan gyara yaje hankalinsa ya tashi haka ya hau sama yana ganin jinin 'yarsa a kasa. Daki gabadaya ya hargitse musamman da yake a nan Dahiru ya yiwa BB duka. Kansa yaji ya soma ciwo ya bar wurin.

Su Najib, matansu da Dr Auwal da sassafe suka koma asibitin. Sun sami Dr Tani tana ta bada order ayi kaza a dauko mata kaza tana tsaye akan Qareeba. Likitocin da nurses sai rokonta suke yi akan ta koma nata gadon ta kwanta zasu kula da Qareeba amma ta ki. Sai ma fada da take yiwa kowa.

"In koma in kwanta ku karasa min yarinya?"

Maigidanta da ta gani ne ta sa kuka murya a shake tace "Daddy ka ga Qareeba taki farkawa tun jiya"

Tausayi ta bashi matuka yasan yadda take bala'in son Qareeba duk cikin 'ya'yanta.
"Zo muje wani dakin ki basu wuri su yi aikinsu. Za ta tashi in sha Allah"

Sai da yayi da gaske ta biyo shi zuwa wani dakin sauran suka tsatstsaya a waje suna jiran bayani game da halin da take ciki. An dade ana bincike har ta fara wata irin jijjiga akan gadon. Can dai aka sake yi mata scanning abin mamaki wani dan karamin gilas ne cikin wanda su ka suke ta ya shige jikinta ya taba kodarta daya. Dole sai an sake yi mata wani aikin. Su Safwan da girmansu su ka rinka kuka yayin da wata nurse take musu bayanin hakan yana  faruwa sosai. Aji ciwo da glass ko karfe idan ya karye a jiki yawo yake yi. Zai iya bin duk inda yaso idan anyi rashin sa'a ya taba mahimman sassa ya jiwa mutum mugun rauni.

 Dr Tani dagewa tayi ita zata yi aikin tana ta kuka kamar ranta zai fita. Wani azababben ciwon kai ne ya bugeta lokaci guda sai jiri ta fadi a kasa. Gado aka mayar da ita mai yin aikin ya tafi da Qareeba yayin da wasu suka tsaya a kanta.

Iyalan gidan Dr Auwal sun ga abin da basu taba gani ba a wannan rana. Anyi aiki lafiya kafin azahar an fito da ita.

Suna tsaye a kanta ta bude idonta mai lafiyar a hankali tare da motsa hannunta da yake cikin na Dr Tani.

Tana hawaye ta sake riketa tace "Qareeba kalle ni nan, kin gane ni? Mummynki ce"

Baki da ido daya sun suntume da kyar ta iya motsa shi tace "Mummy"

Mahaifinta da 'yan uwa ta rinka bi da ido daya bayan daya tana hawaye. Ina suke lokacin da take ta kiransu da neman agaji. Hannu ta daga ta yafito Dr Auwal ya duka daidai bakinta da kyar tace "Babawo"

Idanunsa sunyi ja sosai yace "na sani Qareeban Daddy bazan barshi ba. Warkewarki kawai nake da bukata"

Dr Tani na kuka tace ina wayarta. Maigidanta ya miko mata tace da su Safwan duk su fita zata yi waya. Kallon juna suka shiga yi kafin su bi umarninta.

Suna fita ta kira Haj Mara. Ringing biyu kamar tana jira ta dauka a lokacin kuma babban wan Dr Tani ya shigo dakin bata da damar katse kiran tunda ya shiga kuma a zuciye take.

Haj Mara kusan kwana tayi tana kiranta dama harda Qareeba babu wanda ya dauka.

"Haba Tani, haba don Allah. Kun daga min hankali ina ta nemanki tun jiya inji ina Babawo yake daga cewa...."

Daga murya Dr Tani tayi irin yadda wani bai taba ji ba cike da masifa tace "dakata min Marakisiyya. Babawon banza, ashe dan naki dan akuya ne dabba mara hankali... "

Gabanta ne ya fadi ba dai yaje ya tafka wata ta'asar ba. Sai kuma bacin rai don bazata taba yin shiru ana zagar mata da ba.

"Tani kinsan da wa ki ke magana kuwa?"

Cikin fada tace "Wacece ke banda macuciya azzaluma. Ni zaki ha'inta ki turo min wannan mahaukacin ya auri Qareeba.  To ki saurareni na rantse miki sai naga bayanki da na Babawo"

"Wai meye haka? Me yayi miki?"

"Ashe iskancin nasa na karya ne tunda bai dawo gida ya fada miki ba. Muna asibiti daga jiya zuwa yau anyiwa Qareeba surgery har biyu kinji daya. Yayi mata dukan da ko a film ban taba ganin an yiwa mutum irinsa ba kinji biyu. Ba don tsarewa ta Allah ba sauran kiris ya yi mata fyade kinji uku. Ki tsananta addu'a yarinyata ta shi idan ba haka ba ban ga kudin da kuke dashi da zai hana na rufe danki ba. Idan kin manta 2010 ni ban manta ba. Amma ki sani ta inda aka hau ta nan za'a sauko"

Kashe wayar tayi batare da ta bata damar amsawa ba. Hannu ta dora a ka ta saka kuka. Karo na biyu ana fada mata wannan kalma. Rannan Yasmin ta fada yau Dr Tani. Abu daya ya tsaya mata a rai....Mawadda!

Dr Auwal ne ya kalli matarsa saboda gabadaya ya kasa fahimtar inda ta dosa.

"Me ya faru a 2010 Tani?"

Alh Munzali wan Dr Tani yayi dariya "ashe 'yan boko ma suna boyewa juna sirri"

"Yaya don Allah ka bar maganar nan" kadai ta iya cewa duk da tasan ranar wanka ba'a boyon cibi.

"Fadawa mijinki ba hurumi na bane Tani nazo dubaku ne duk da kin yanke alaka damu saboda sawa ranki da ki ka yi bama kaunarki bama kaunar zuri'arki. Duk wani abu da muke yi miki muna yi ne don gyara son 'ya'ya ya rufe miki ido kin kasa fahimta"

Kujera ta samu ta zauna tana kuka Alh Munzali ya kalli Qareeba yace  "Allah Ya baki lafiya Ya saka miki. Fyade ba karshen rayuwa bane zaki cigaba da harkokinki kamar kowa"

Dr Tani ta katse shi "Yaya Munzali baiyi raping dinta ba"

Irin dariyar kin ma raina min hankali yayi kafin yace mata "ko duk jikina kunne ne bazan yarda. Nasan dama dole kiyi kokarin boyewa amma ki sani rufewar ba gata bane. Zan wuce amma zamu dawo anjima tunda na tabbatar da labarin ba jita jita bane"

Bin bayansa ta yi tana ta cewa ba'a yiwa Qareeba fyade ba yayi tafiyarsa ya kyaleta. Da ta koma tsareta Dr Auwal yayi tana kuka take bashi labarin komai tun daga zuwan Mawadda asibitin har yadda suka yi da Haj Mara da shigarsu kotu.
Qareeba tana ji tayi ta kuka saboda ita mahaifiyarta ta bada shaidar zur ta batawa wata rayuwa. Batun Alh Munzali kuma alkalin da ya yi shari'ar Justice Dawud ashe kanin abokinsa ne bata sani ba. Ta manta wani lokaci da rashin haihuwa ya damesu Alh Munzali ne yayi sanadiyar hadata da matarsa har aka dace. Ranar da taje kotun bada shaida bata gane shi ba. Shine ya tuna ta har yake fadawa dan uwansa ya ga likitan nan yau a kotunsu wanda Alh Munzalin yaji labarin a wurinsa. Baiyi kasa a gwiwa ba har gida yaje ya sameta saboda ya bincika ya gane shine wanda aka ce zai auri Qareeba a lokacin. Dr Tani ta shafawa idonta toka tace karya ne kuma ta kula dukkansu 'yan uwan nata basa son yaranta su cigaba. Yayi bakinciki sosai a lokacin yace mata taje da sannu duniya zata bayyana mata halin yaron domin yayi bincike a kansa ya kuma tabbatar bashi da tarbiyya. Gashi kuwa ta gani zahiri.

Dr Auwal ransa yayi matukar baci "shine kika boye min abu mai girma irin wannan saboda kina son 'yarki tayi aure? To gashi nan kin bada shaida an sake shi yazo ya lalata miki taki 'yar. Auren da ki ka so tayi kuma bai yiwu ba."

Hakuri ta shiga bashi yana rike da hannun Qareeba yaki kallonta " Kuma bai sami nasarar yi mata fyaden ba mu ka je dakin"

"Da gaskiyar Alh Munzali tunda asibitinki ne nan nayi imanin zaki yi duk yadda zaki iya ki rufe maganar "

"Daddy zan gyara al'amarin nan wallahi ko zan rasa aikina sai na kulle Marakisiyya da danta. Amma ku yarda Allah bai bashi dama akanta ba"

Tana ta magana bai sake ce mata komai ba har 'yan uwansu 'yan ganin kwaf su ka fara taruwa zance ya bazu kamar gobara an yiwa Qareeba fyade.
*****

BB da ya bar gidansu Qareeba wani abokin shashancinsa ya nema yazo ya dauke shi saboda ya kasa tuki. Hanci jini baki jini jikinsa ya bugu sosai Dahiru ya tara masa gajiya.

Kashe wayarsa yayi don yasan Haj Mara zata kira. Shi kuwa burinsa ya cika wannan wawiyar Qareeban yanzu ko giya iyayenta ke sha dole su sarara masa. Takaicinsa daya da bai samu ya karasa ba sai kuma tunanin waye wannan mutumin da yazo har ya dake shi haka. Ko bacci ya kasa yi saboda rashin sanin mutumin da sunansa. Ya sawa ransa don sun fado masa a bazata ne amma ranar da zai sake haduwa dashi sai ya nuna masa shi BB ba'a ja dashi.
******

'Yan uwan Mawadda su Rafia duk suna gidan yau ana ta tsare tsaren biki. Jinsu take yi wai ita ce zata yi aure abin kamar almara. Gani tayi har azahar ta wuce yau Dahiru bai kirata ba ta tashi ta barsu a tsakar gida taje ta kira shi.

Yana zaune a falon Baba Prof ana masa gyaran targade. Hannunsa na dama garin dukan BB ya sami targade bai sani ba sai cikin dare wurin babban yatsansa ya kumbura ya soma damunsa da ciwo. Abu harda su zazzabi karfe takwas ya kira Attahir shine ya taho dashi gidan. A hanya kafin su zo yake bashi labarin abinda ya faru.

"Ina ma tare muke wallahi bayan munyi masa duka mu dandake matsiyaci. Irinsu fa kamata yayi a mayar dasu huhulahu ta yadda ko sun ga mace nan gaba iyakar su da ita ido"

"Gara da baka gani ba Bro, da abin na kwana a raina ya dameni matuka. Da shi da wanda ya yiwa Mawadda jiya na tsine musu yafi a kirga."

Ana gyara hannun yana gumin wahala ta kira har sau biyu. Attahir ne ya dauki wayar a kira na uku yace mata ana masa gyara zai kira idan an gama.

Tunda taji haka hankalinta ya kasa kwanciya ko hirar ta kasa da yayyenta. Bayan minti goma ta sake kira Attahir ya kuma dauka.

" 'Yar uwarmu an gama amma kinsan mutumin nawa rago ne kuka yake yi shiyasa na karbe wayar"

Dahiru ya tashi yana cewa ya bashi ya hana. Yadda yaji ta damu sosai yace ta kwantar da hankalinta zai kawo mata shi yanzu.

"Baka tausayina zaka ce na fita yanzu" Dahiru yace yana karbe wayarsa.

"Naji kamar tana kuka ne" ya zolaye shi.

"Waye ma yace ka daukar min waya?"

Sai da ya huta yaci abinci sannan suka tafi da Attahir din. Da ya kirata yace suna waje cewa tayi su shigo ciki.

Shi kadai ta samu a zaune ta tambaye shi ina Attahir tana kallon hannun.

"Na kora shi waje"

"Yaya hannun?" Tace da damuwa.

"Ni fushi nake tun safe baki neme ni ba"

"Yayanmu kaine fa jiyan nan..."

Yayi murmushi "me nayi jiyan?"

"Babu komai"

"Ashe dai kina sona Attahir yace kinyi kuka da ya fada miki"

"Ba wani nan kaine yace kayi kukan. Naso in gani sai na tara bokiti"

"Kinci bashi yarinya. Bari na tashi zazzabi nake ji. Hankali ya kwanta kin ganni ko" yace da dariya.

Ita ma tace "Kai naka bai kwanta ba da ka ganni?"

"Sosai kuwa Mawaddatan wa Rahma. Saura kwana 8 kina tayani kirge kuwa?"

Dariya tayi suka mike tare tana masa Allah Ya kara sauki.

Ya karkace kai yana kallonta "kina jindadinki"

"Me kuma nayi?"

"Nine mara lafiya, ni na kawo miki kaina ki dubani sannan ko rakiya babu."

Murmushi tayi masa "Allah Ya baka hakuri muje"

Tare suka fito waje suna yiwa juna murmushi Attahir yana hira da tasa masoyiyar Nawal ya hango su sun burge shi.

Daga bayan motar babban yaron Garwashi ne Danmani ya saitasu ya dauke su hoto a kofar gidan. Dariyar mugunta yayi shi kadai. Garwashi kwatancen karya ya yiwa BB duk da sun gano ainihin gidan harda batun aurenta da za'ayi. Batare da bata lokaci ba BB ya turo musu kudin wanda suka raba su bakwai. Shine Danmani ya zagaye shi kadai ya dauko hoton duk da baisan waye Dahiru a gareta ba. Burinsa ya dauketa a kofar gidansu dama. Wayarsa ya tura a aljihu ya nufi titi yana fito zai je ya saidawa BB a farashi mai tsada.
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰16

*Batul Mamman*💖



Baba ya kalli Attahir da tausayin Dahiru ya tsinka masa zuciya "samari yaya sunanka?"

Amsa masa yayi jiki a sanyaye. Baba yace ya tafi da Dahiru gida don ya sami nutsuwa shima ciki zai koma ya duba Mawadda.

Sai da ya fita Attahir ya kwashe wayoyinsu ya dago Dahiru. Ko kofa basu kai ba aka soma kiran sallar Magrib. Marwanu ne ya fito cikin sauri yace Baba yace su jira shi zai fito suje masallaci kafin su tafi.

A ciki dakin su Inna aka kwantar da Mawadda. Kuka take yi sosai mai cin rai su Yaya suna rarrashinta amma ta kasa shiru. Rabonta da irin wannan firgicin anfi shekara. Tun wata rana da tana cikin adaidaita sahu suka tsaya a danja. Gefe da gefe maza ne akan babura sun matsi adaidaitan. Abinka da 'yan tasha suka fara yi mata zantukan banza bata san lokacin da ta fara ihu ba. Abu ya kaita da suma ranar ne ta fara haduwa da Dr Imran.

Yau kuwa kukan bakincikin nakasa ta da BB yayi take yi. Wannan abu ya kara tabbatar mata aure bai kamaceta ba domin da wahala matuka ta iya rayuwa da miji. Bata jin akwai wata soyayya da zata sa namiji ya iya hakuri da matar da bazata iya kebewa dashi ba batare da tsoro da fargabar kada ya tabata ba.

Ade tun tana rarrashinta itama har ta soma fada karshe ta fashe da kuka. Tashi tayi ta fita daga dakin ta barsu da Yaya. Zuciyarta bata iya jurewa kukan Mawadda don tasan yarinyar ta ga rayuwa.
Kuma a haka ma don tana da dauriya ne.

Bayan sun dawo hakuri Baba ya sake basu Dahiru ko uffan bai iya cewa har suka tafi. Gani yayi Attahir ya dauke hanya alamun gidan Baba Prof zasu koma yace ya kaishi gida baya jindadi.

Idonsa akan titi yace "nasan baka jindadin shiyasa bazan bari ka kwana kai kadai ba yau."

"Attahir please" yace da kyar.

"Sai dai kayi hakuri idan ba haka ba zan sanar da Baba halin da ake ciki.Kuma ka manta motarka na can?"

Taga ya koma kallo bai kara magana ba sai tunane-tunane. Suna zuwa dakin Attahir din ya wuce ya kwanta. Shima sai ya rabu dashi don yasan yana cikin damuwa.

Sai bayan isha ya matsa masa suci abinci yace ya koshi.

"Sannu baban soyayya abin kuma harda hora kai da yunwa? Dadin abin gidansu Anti Qareeba babu nisa..."

Saurin kallonsa Dahiru yayi shi kuma yayi dariya sannan yace "na rantse ko kaci ta dadin rai ko kuma naje gidansu na kirawota. Nasan zata zo kaga sai a nunawa su Haj Mama"

Tsaki Dahiru yaja sannan ya dauki cokali kamar shine ya bata masa rai ya rinka tura abincin da kyar.

Can dare bacci ya gaza daukarsa. Tunaninsa bai wuce wane hali Mawadda take ciki ba. Da abin ya isheshi alwala ya dauro ya soma nafila da addu'o'i a nan kan abin sallah bacci ya dauke shi.

*****

Wayarsa ce take kara alamun kira ya bude idanu da kyar. Karfe goma da rabi ya gani ya tashi yana dafe kansa dake matsanancin ciwo. Da kyar yayi sallar asuba ma saboda ciwon kan. Bilya ne ya kira shi Baffa da Inna sun zo suna gidansa. Amma Baffa yace bazai kwana a Kano ba saboda haka yayi sauri ya zo ya kaisu gidan Mal Fatihu.

Da sauri ya mike yayi sa'a ba ranar aiki bace.  Attahir ne ya shigo ya ganshi yana saka kaya cikin sauri.

"Sai ina koma Baban soyayya? Yaya kan naka"

Dube dube yake da sauri sauri "Attahir ina mukullin mota ta? Jiya sai da nace ka kaini gida gashi su Baffa sunzo ina nan"

Kafadunsa Attahir din ya rike "dakata mana, ni bansan ka da wannan garajen ba. Me yake faruwa?"

Daurewa yayi duk da yana ganin lokaci na kara tafiya ya fada masa wayar Bilya. Murna sosai ya tayashi don ya kula ba karamin so yake yiwa Mawadda ba. Abu ne kuma na gida shiyasa da Dahirun ya nemi ya raka shi yace ba yau ba. Har ya fita ya dawo ya mika masa hannu suka yi musabaha.

Rike da hannun nasa Dahiru yace "nagode kuma kayi hakuri ina ta masifa"

"Its called love babu damuwa. Abu daya ne dai idan ka kwaso mana Anti Qareeba ..."

Fita yayi yana dariya ya tafi gidansa domin ya shirya. Fatansa dai iyayen nasu su taimaka su amince wannan karon kada wani abu ya sake rabasu.
******

Garwashi da yaransa sunyi nasarar zuwa garin Tariwa inda da naira dari biyu suka sami wani mai bakin reza ya kwashe komai da ya sani game dasu Mawadda ya fada musu. Gidan ne kawai bai sani ba a Kano amma yasan na Maigari ne.

******

Mawadda tana kwance a daki Ade ta shiga ta sameta. Tashi tayi da sauri don tasan Ade ta hanata wannan kwanciyar da tunani. Kamar ta sani kuwa Ade tace

"Me na fada miki dazu da na shigo?"

"Kiyi hakuri na tashi yanzu" ta amsa tana gyara katifar da ta kasance tasu ita da Rafi'a a da.

"Dazu me yasa da aka turo tambayar gyaran jiki ki ka sallami yaron wai baki da lafiya? Zaki fara wasa da sana'arki ne saboda damuwa ko me."

Yadda tayi maganar da  fushi yasa Mawadda yin kasa da kanta. Bata da wani kuzarin aikin kanta cushe yake da tunanin rayuwarta.

Sakaya kofar Ade tayi kada ace tasa 'yar fari a daki ta sassauta murya
"Ki kara hakuri yadda ki ka saba kinji ko? Ni kaina abin nan ba karamin damuna yake ba amma yaya muka iya da abinda ya gagaremu." Hawaye ne ya taho mata tayi saurin sa gefen dankwalinta sai dai Mawadda ta riga ta gani. Hankalinta yayi matukar tashi kuwa.

"Ade wallahi na dena. Me zan dafa idan kin tafi?" Tace tana bude kofar dakin.

Yau ake kai lefen 'yar Barira kanwar Yaya shiyasa ta fita da wuri. Itama Ade yanzu zata karasa shiryawa su tafi dasu Iya. Mawadda kadai zata rage saboda Baba.

Fara'ar dole ta kirkiro domin kwantarwa mahaifiyarta hankali ta tafi kitchen. Tana fita Ade ta zauna taci kukanta don tasan babu wani abu da zasu iya yi domin kawowa 'yarsu farincikin da kaddara ta shiga tsakaninta dashi.
******

Shabiyu Dahiru ya isa gidan Bilya. Baffa ya gama fadan ya bata musu lokaci yayi ta aikin bada hakuri.

Inna ta kalle shi a ranta ta yaba da yadda 'ya'yanta suka koma. Burinta yanzu akansa ya kare shima ya ajiye iyali kamar 'yan uwansa.

Hansa'u ana ta firirita Dahiru yazo. Abinci ta kawo masa dayake yunwa yake ji yau bai gwaleta ba yaci.

Furaira tace "kana yawo da yunwa har tsakar rana haka ance kayi aure ka zauna shiririta."

"Kai Yaya Furaira kin matsawa Yayanmu Dahiru" cewar Hansa'u tana satar kallonsa.

Inna ta gane ina zancen ya dosa don Furaira ta jima tana maganar a hada Hansa'u da Dahiru aure. Sauya hirar tayi saboda kada su fara rigimar da suka saba.

"Ince ko ka sanar da su Mal Fatihu zamu zo?"

Dafe kai yayi tace ya hanzarta kiran Mawadda ta fada kafin Baffa ya fito daga dakin da suke tattaunawa da Bilya.

Jin an ambaci Mawadda yasa Furaira hade rai "Inna gidansu Mawadda zaku je kuma? Yanzu biye masa zaku yi ya auri yarinyar da ta gama lalata rayuwartaa titi? Idan ma Hansa'u ce bakwa so ba dole amma bai kamata ku barshi ya dauko wadda zata gurbata mana dangi ba"

"Tashi ki bar wurin nan kafin na saba miki" Bilya ya daka mata tsawa yana shiga falon. Ranta a bace ta mike Hansa'u na mara mata baya suka fita.

Inna tace ya rinka hakuri tunda yasan halinta. Dahiru kuma ya fita waje ya kira Mawadda. Wayar tana ringing gabansa yana faduwa kada taki dauka.

Su Ade sun gama shiryawa suna jiran Adaidaita sahu da Marwanu yaje samowa a bakin titi ita kuma tana gyaran salad taji wayar.

Ganin sunan mai kiran ya sanya zuciyarta tsananta bugu. Muryarta ma gabadaya chanjawa tayi kamar wadda tayi gudu tayi masa sallama.

Lumshe idanu yayi yana jin daddadar muryarta tana gaishe shi.

"Yayanmu ko baka ji ne?" Ta fada tana jijjaga wayar.

Ajiyar zuciyarsa taji sannan yace "ina jinki, kin tashi lafiya?"

"Lafiya kalau" tace duk ta kidime da jin muryarsa.

"Zamu zo dasu Inna nan da...ina ganin bazai kai awa ba. Baba yana nan ko?"

"Eh zan sanar dashi"

Kashe wayar tayi ta tashi. Yanzu me zata fadawa Baban. Tana tsoron kada ace ita tace ya kawosu tunda bata san yadda suka kare jiya ba. Ade taje ta fadawa ta hau salati

"Mu da zamu fita? Tsaya na sanar da babanku"

Basu jima ba suka fito tare da kansa ya fadawa su Inna. Mawadda kitchen ta koma Ade tace ta kara abincin. Tana aiki tana ji suna tattaunawa akan amsar da Baba zai bayar idan Mal Isiyaku ya tado da zancen Dahiru. Iya kadai ce tabi mai adaidaita sahun aka bar Ade da Inna.

Biyu saura suka karaso. Mawadda ta sake gyara gida ko'ina yaji turaren wuta. Falonsu na soro a gyare sai kuma dakin Ade inda Inna zata zauna shima da tsakar gidan fes. Hatta abinci, kunun aya da ruwan sanyi duka ta ajiye musu.

Marwanu ne ya yiwa Inna jagora zuwa cikin gidan yayin da Baffa, Bilya da Dahiru suka tsaya a falon tare da Baba.

Tamkar wani abu bai taba hadasu ba Baba ya taso ya tarbe su cikin mutumci da karamci. Haka Innar Fatihu da Ade suka yiwa Inna suma a ciki.

Da Mawadda ta fito gaisheta janyota tayi jikinta kwalla na taruwa a idanunta.

"Allah Sarki 'yata, na rasa me zan ce dake. Kiyi hakuri kinji 'yannan"

Innar Fatihu tace "Haba Indo do Allah banda dawo da hannun agogo baya. Yadda lokaci ya shude haka komai ya wuce. Ziyarar da kuka kawo mana tafi komai a wurinmu"

Ade ta tursasawa Inna cin abinci tace ciwon suga ke damunta bata dade da samun sauki ba shiyasa take tsoron shinkafa.

Wata karamar jaka Ade ta dauko ta ciro kudi ta bawa Mawadda.
"Yi maza ki bawa Marwanu ya siyo cous-cous a bakin titi. Idan baya nan ki hanzarta kije"

"Kai Sa'ade kamar baki ki barshi ba yunwa nake ji ba"

Mawadda tuni ta saka hijabinta mai hannu wanda ya sauko zuwa gwiwarta tayi waje. Tana jin Inna na cewa ai fa dole ne taci.

Kiran Marwanu tayi a waya yace ya tafi gidan Anti Barira. Takalmi ta dauko wasu masu tudu kadan ta saka ta fita. Dahiru yana cikin falon soron kuma inda yake zauna yana fuskantar kofa ya ganta ta wuce da sauri kada su hangota. Tashi yayi yace yana zuwa ya biyo bayanta.

Tana fita daga gidan ya fito shima.

"Ina zaki je?"

Cak ta tsaya har ya iso gefenta ya tsaya.

"Uhmm, uhmm cous-cous zan siyo"

Ya dan bata fuska "da kanki?"

"Marwanu baya nan"

"Tsaya a nan na siyo miki"

"Ka koma ciki zanyi sauri ba nisa sosai"

Yadda ya kalleta yasa ta mika masa kudin. Ko kallonsu baiyi ba ya wuceta ya shige mota ya ja. Tafiyar da tasan da ita ce a kafa zata kai har yanzu bata isa titin ba shi da yaje a mota sai gashi ya dawo cikin 'yan mintuna.

Mamaki ya bata ganin ya dauko katan guda ta bude baki tana kallonsa har ya iso bakin kofar gidan inda take tsaye.

Murmushi yayi ganin tana ta kallon ikon Allah ita da zata siyo kwali daya shi ya dauko katan

"Rufe bakin mana Kanwarmu"

Kamar tayi masa kuka tace "Yayanmu me zance idan na shiga da wannan?"

"Aikena ki ka yi shiyasa baki dade ba mana"

Turo baki tayi "kasan ba haka nake nufi ba"

Jingina bayansa yayi da bango a gefenta sannan ya juya kansa bangaren da take. Shashantar da zancen yayi don ba hirar katan din cous-cous yake so suyi ba.

"Wane irin so nake yi miki ne? Komai naki ina so harda wannan tura bakin"

Daburcewa tayi ta shiga tura katan iya karfinta saboda kunyar da taji. A nan waje ta barshi yana mata dariya ta tura shi kitchen ta dafa rabin kwali daya ta kaiwa Inna.

A falo su Baba suna hirar yaushe gamo inda Baffa ya roke shi da ya yafe masa abinda ya faru a Tariwa.

"Fitar maganar nan daga gidana ne sai na kasa zama aboki nagari nima na biyewa sauran jama'a"

"Kada muyi haka da kai mana Mal.Isiyaku. Kaddara ai ba'a guje mata. Ni dai don Allah mu bar zancen nan. Zumunci yafi komai gashi kazo har gidana me zance banda godiya?"

Bilya taya Baffa bada hakuri yayi Baba yace shi dai a bar tada tsohon zance baya so.

Baffa yace da Bilya "ina kaninka ne?"

Shima dayake yaga fitar Mawadda dazu sai yayi murmushi kawai "ina jin iska ya fita sha"

Sun cigaba da hirarsu Mawadda kuma ta koma daki. Zamanta ke da wuya Dahiru ya kira. Kai ta girgiza kafin ta dauka.

"Ki fito muyi hira"

Kamar yana gabanta ta zaro idanu "Da wa? Rufa min asiri"

"So nake naji yaya kika kwana jiya?"

Zancen jiyan take ta gudu don bata son tunawa ma.

"Lafiya kalau"

"Kizo na ganki na tabbatar"

"Ba yanzu ka ganni ba?"

"Aikena fa kika yi daga fitowata"

Yana ji tana dariya kasa-kasa.

"Ina mota ni kadai bana son hirar manya. Ke da nake son taki hirar kuma kina ja min aji. Bari kawai na kira Anti Qareeba" yace a kalar tausayi.

Dariya yaji ta sake yi ya shiga bata labarin haduwarsu ta gidan mai jiya. Mawadda sai da ta koma rufe bakinta kada a jiyo ta. Yayin da shi kuma yaji ransa ya sake gabadaya babu sauran damuwa tunda ya sakata farinciki.
*****

Sai da suka yi la'asar suka fara haramar tafiya saboda a ranar zasu koma Tariwa. Bilya ne ya fara fita Baffa ya danyi gyaran murya Baba ya kalle shi.

"Mal Fatihu game da yaran nan..."

Baba yace "munyi magana da Dahiru jiya nace ya hakura mu cigaba da zumuncinmu"

Fuskar Baffa ta nuna rashin jindadi "nasan bamu kyauta ba kuma bazan gaji da baka hakuri ba. Amma rashin amincewarka yanzu tamkar baka mayar da komai ya wuce din bane kamar yadda ka fada min"

Dariya yayi
"Kada ka daureni Mal Isiyaku. Ai shi ya gani da idanunsa yarinyar nan har yanzu fa bata gama dawowa daidai ba. Abu kadan yake zaburar da ita ta firgita. Karin nauyi kawai zamu bashi idan aka aura masa ita"

"Sauki na Allah ne. Ni dai zuwan yau na zumunci ne amma zamu dawo ayi magana ta gemu da gemu" yace yana dariya.

Baba ya rasa amsar da zai bashi yace bari ya kirawota ta gaishe shi sai ta yiwa Inna magana ta fito.

Cike da ladabi tazo ta gaishe shi sannan su Ade suka rako Inna yayin da ta koma ciki.
*****

Kwanakin da suka gabata Dahiru ya yisu cikin neman amincewar Mawadda a bangaren su Baffa shima sau biyu yana kiran Baba akan zancen. Iyayensa biyu da zaiyi shawara dasu duka suna gidan ya tara matansa a gabansu yace ga yadda suka yi da Mal Isiyaku.

"Anya baka ganin wannan wata dama ce Allah Ya bamu domin samarwa Mawadda farinciki?" Cewar Innarsa.

Iya tace "kuma ina tsammanin mun daukaki abin nan da girma sosai muma mun bada gudunmawa wurin dakushe mata tunanin aure. Mace take gama yawon bariki ma tayi aure balle wadda aka yiwa fin karfi? Mutanen nan ba mune muke binsu ba kazalika babu abinda basu sani ba su da dansu suka kawo kansu saboda haka ni dai tawa shawarar shine a basu dama"

Har kasan zuciyar Ade godiya take ga Allah da Iyanta ta kawo wannan shawara. Tana son Mawadda tayi aure kuma bata ga wanda ya dace da ita ba sama da Dahiru.

Yaya ma dari bisa dari ta goyi bayan shawarar Iya
 "mu gwada Malam kada nan gaba muzo muna dana sani. Yarinyar nan tayi kokari kuma tana kan yi wurin nuna maka komai ya wuce kuma ta amince da hukuncinka gareta. Sai dai wallahi tana da rauni sosai. Sai dare yayi kaji tana kuka ita kadai gari ya waye ta shiga aiki kamar babu komai a ranta."

Ade Baba ya kalla yana jiran jin ta bakinta sai tayi murmushi kawai sannan tace duk shawarar da aka tsayar tayi mata.
*****

Mal Isiyaku ya nemi 'yan uwansa akan maganar tunda dole dasu za'a nemi aure babu wanda ya goyi bayansa. Daga me cewa tun farkon karuwanci tayi sai masu cewa yanzu ma da jikinta take ciyar da iyayenta. Rigingimu dai daban daban Inna har ta soma tunanin ko su fada masa ya hakura kawai. Don abin yafi zafi daga bangaren 'yan uwan da suka so ya auri 'ya'yansu bayan sun fara masa kallon Alhaji.

*****

"Alhaji kasa baki mana" Haj Mara tace cikin bacin rai. Gani take ita kadai ce ta damu da rayuwar danta. Yanzu ma maganar zuwa Kano tayi masa yace ba inda zashi.

Kallon BB yayi wanda yake tsaye a gefen dinning table yaki ma yazo gabansu.

"Babawo wannan karon na goyi bayan mamanka. Ka shirya ranar Juma'a kaje ku gaisa mu kuma zamuyi abinda ya dace game da sa rana da sauran shirye shirye"

Kankance idanu yayi "Alhaji zanyi aure fa ku dena damuwa. Akwai information da nake jira akan yarinyar ku zan fara sanarwa idan magana ta kankama"

"Babawo wallahi zanci mutumcinka akan maganar Qareeba. Kai wane irin yaro ne mara jin magana? Dole ne sai yadda kake so za'ayi?" Ta taso tayi kansa kamar ta mare shi sai ta kasa. Yanzu fa makotansu ma kowa zancen BB yake ana cewa yaje turai ya zama dan iska. Kitson kansa yafi komai kona mata rai.

"Wai da marina zakiyi. Hahahahhh abin dariya"

Hanyar dakinsa yayi ta dafe kirjinta da hannu daya ta rike kujera.

Alh Sule ya taso yazo gabanta "Marakisiyya duk wanda yace gyara kayanka ba yana nufin sauke mu raba bane. Ni da dana kika koya masa yaki jin maganata wai bana sonsa. Ki duba ki gani yadda yake neman haddasa miki ciwon zuciya. Yarinyar nan da ya taba nema ki fada min garinsu idan da rabo sai mu nema masa ita ko zai kintsu"

"Allah Ya kiyaye wallahi. Ni na hada zuri'a da masu aiki makiyana su sami abin fada. Idan wadancan 'ya'yan so dinne ai bazaka taba fadin haka ba." Cike da takaici ta buga tsaki ta bar wurin.

Alh Sule ya dade a tsaye shima nasa ran a bace. Haj Mara ta lalata Babawo da soyayyar da take ikirari ta kai shi matakin da addu'a kawai ta rage masa.

*****

Dahiru duk ya matsu yaji amsawar Baba saboda ya ma dena zuwa gidan yana jiran amincewarsa. Da ya sake tuntubar Baffa da zancen ce masa yayi dole su bi a sannu domin ko waye zaiji tsoron saurin sake amincewa a koma 'yar gidan jiya.

Ana haka ne bayan duka su Inna sun amince Baba da kansa ya kira Baffa ya sanar dashi cewa ya baiwa Dahiru Mawadda. Baffa yayi murna sosai da godiya yace in Allah Ya yarda babu zancen bata lokaci da wuri zasu zo a daidaita magana. Suna gamawa ya kira Dahiru ya sanar dashi.

Mawadda bata san me ake ciki ba tana fama da gyaran wata mai jego tayi arbain za ta koma gidan mijinta. Aikin nasu har magariba don na kwana uku suka yi washegari zata koma. Almajiri ne ya shigo daga soron Mawadda tana ce masa ya dakata daga waje za'a karbi kwanonsa.

Yace mata "Ba bara nazo ba sallama ake da wata wai Mawadda"

Iya ta sa dariya dan karami dashi ya iya rashin kunya. Kodayake ba laifinsa bane. Iyaye sun sake shi da malamin da aka bawa amanarsa.

"Jeka kace waye yake sallama da ita" inji Yaya.

"Yaya ko wanka banyi ba ki ko waye ya tafi kawai bari na gyara tsakar gidan"

Yaro ya koma waje abinsa ya tsaya gaban Dahiru kerere.

"To tace ko waye ya tafi bata yi wanka ba kuma zata gyara tsakar gida"

Rike baki yayi yana kallon yaron shima. Ya kira wayarta yafi sau goma bata dauka ba lokacin tana aiki. Shi kuma murnar bashi ita da akayi tasa bazai iya hakuri ba. Sunfi sati uku basu hadu ba.

"Koma kace mata Dahiru ne" ya sake tura yaron ba don yaso ba.

Yaro ya koma ya isar da sako. Mamaki tayi don rabonsa da gidan tun zuwansu da su Baffa. Inna ce tace tayi sauri taje su gaisa karshenta ya sami labarin bashi ita da akayi ne.

Tsintsiyar hannunta ce ta fadi ta tsaya tana kallon Inna.

Yaya tayi murmushi ko ba'a fada ba banda mamaki akwai farinciki bayyane a fuskarta "jeki ki kimtsa da sauri kin bar shi a waje"

Daki ta shiga ta dauko wayarta. Missed calls rututu biyu daga amarya Rafi'a sauran kuwa duka na Dahiru ne. Allah ne Ya kawo Saifullahi shima yazo gida aka sa shi shiga da Dahiru ciki ya zauna jiranta.

Cikin minti ashiri tayi wanka da shiryawa duk cikin sauri. A kunyace ta wuce su Ade taje ta same shi.

Maimakon ta ga gajiyawa da fushin zaman jira a tattare dashi da ta shiga sai ta ga yana ta mata murmushi.

Langabe kai tayi "Yayanmu kayi hakuri aiki nake wayar tana daki"

Shima ya langabe nashi "kinji nayi korafi?"

"A'a"

"To zauna mu gaisa matata Mawaddatan wa Rahma"

Ja da baya tayi tana sunne kai.

"Kunya?"

Ta gyada kai a karo na farko kuma tana zama a kujerar da tafi kusa da kofa. Yaji dadi sosai da yaga wannan chanji a tare da ita.

Gani yayi tana ta boye fuska cikin mayafi shima ya cire hularsa ya dora akan fuskarsa yace "nima fa kunyar nan nake ji"

"Sai kace mace?"

"Ba mace bane amma na macen ne." Ya bata amsa yana kallonta.

Ya sake cewa "ko ba haka bane? An bani ke an baki ni"

Murmushin nan ne dai a fuskarta mai shiga ransa tace "Ni fa yanzun nan na sani"

"Are you happy?"

"Kai Yayanmu...." ji tayi kamar ta tashi ta gudu.

"Allah sai kin amsa min"

Duk yadda taso zillewa kin yarda yayi dole ta amsa masa ta hanyar daga kanta.

"Na fiki farinciki amma bazaki san haka ba sai nan gaba kadan. Kinga ma dai ki fara shiri bikin nan ba zai dade ba"

"Da sauri haka?"

Yayi dariya "nima irin abin nan zaki min ince ba kya doki? Duk kukan da ki ka gama yi da rashin bacci an fada miki ban sani bane zaki wayance"

Kallonsa tayi da mamaki sosai tace da karamar murya "Yayanmu ka fara bani tsoro fa. Waye ya fada maka?"

Dahiru ya rinka dariya "assha Mawadda ashe ba zan sha wuyar yi miki wayo ba"

Cije lebenta tayi tana cewa sai ta rama abin da ya kula sararta ne shi kuma yake matukar bashi sha'awa game da ita. Dena kallonta yayi ba shiri.

"Alkawarinmu yana nan har yanzu?"

"Wanne? Ni ban san wani alkawari ba"

"Ni na sani ai kuma dakin nan ma shaida ne. Da bakinki ki ka ce idan na sami mata zaki yi mata gyaran jiki kyauta. To don Allah ina so ki fara da wuri kiyi irin wanda baki taba yiwa kowa ba"

Cewa tayi bata yarda ba wannan wayo ne yace shi kuma sai ta cika alkawarin. Haka suka yi ta hira cikin nishadi da farinciki.

Cikin lokaci kankani sun sake shakuwa ga wata soyayya da suke yiwa juna mai karfi. Anzo neman aure wanda harda Baba Prof a ciki. Dama tun kafin su zo ya sanar da  Baffa gara a hada lokaci daya da na Attahir. Baffa yace bai sani ba ko zasu amince tunda baifi wata biyu ba ya rage.

Sunyi sa'a Baba yace shima baya son a ja lokacin saboda haka sun amince.

Dahiru ya dage shiri komai tare da Attahir suke yi. Wata rana ya dawo daga wurin aiki Baba Prof ya kira shi. Yana zuwa ya tarar da Attahir. Nan ya zube musu mukullai biyu yace suje wani gida ne a rijiyar zaki sama da kasa iri daya sababbi. Kowa ya gwada inda mukullinka ya bude nan ne naka. Gudunmawarsa kenan ya biya musu kudin haya na shekara.

Rasa bakin magana Dahiru yayi tamkar yasa kuka haka yake ji. Me zaice da wadannan bayin Allah? Shiyasa shima ya dauki nauyin wani yaro dan garinsu yanzu yana aji hudu a Dawakin kudu. Ya ga amfanin kyauyayawa sosai ji inda rayuwa ta maida shi matsayin da bai taba zato ba.

Sunje gidan banda wani daki kamar na maigadi sai borehole da wurin parking na kusan motoci hudu sannan gidan. Dahiru ne a sama Attahir a kasa.

A gidan Mal Fatihu ma shiri suke yi sosai. Ade tayi tarin kudi da sa ran Allah zai kawowa Mawadda mijin aure. To gashi lokaci yayi. Itama Mawadda nata kudin sana'ar da take ta tari ta fitar. Baba ya kawo abinda yake dashi Yaya ma tayi rawar gani. Kawunnai da Gwaggoni babu wanda aka bari a baya. Yayyenta su Bilki kowa da tata bajintar. Ashe kowa jiran lokaci yake Mawadda ta sami miji gashi kuwa an samu. Kudin suka dunkule aka saya mata gado mai kyau da kujeru. Duk da gidan dakuna biyu ne da falo karamin dakin kafet da kayan turaren wuta za'a saka.
*****

Su Dr Tani suma shirye shirye suke yi baji ba gani. Sun kashe kudi ba kadan ba wurin kayan dakin Qareeba. Biki tsiransu sati biyu dana Dahiru.

Qareeba ce kadai a gida BB ya kirata yace zai zo suyi sallama kafin ya wuce Kaduna. Har yanzu idan an bata zabi Dahiru take so amma ba yadda ta iya dole ta karbi BB tunda tana son auren.

"To My Man sai ka iso" tace ta tashi ta shirya.

Da yazo shigarsa ta kamala yayi yasa manyan kaya harda hula. Kamar bashi ba don tun kafin zuwan farko yayi aski. Wani munafukin murmushi yake dauke dashi a fuskarsa sakamakon gidansu Mawadda da Garwashi yace masa ya samo. Yau dinnan zai yakice Qareeba ya huta itama kuma Haj Mara dolenta ta barshi ya auri wadda yake so ko ya debo abin kunya.

Falon saukar baki suka zauna yana ji mai aikinsu tace zata je kitso Qareeba tace sai ta dawo ya wani murmusa dama ta samu. Hira ya rinka janta dashi can yace

"My dear muje ki nuna min dakinki mana"

Qareeba ta yi masa wani irin kallo kafin tace "dakina fa kace Man"

Tasowa yayi ya dawo kujerar da take mai cin mutum daya ya zauna akan hannun ya sakalo hannunsa akan kafadarta. A hankali ya sauko da kansa yana shakar kamshin turarenta ta tashi da sauri ta chanja kujera.

Gabanta yazo ya durkusa ya kama mata hannuwa "kinsan ina sonki ko?"

Hadiyar yawu tayi da kyar tsoro ya fara kamata "uhmm"

"Kuma nasan kin matsu ayi aurenmu " yace da murmushi.

Itama murmushin ta kakalo "eh mana amma please koma ka zauna ka dena tabani an kusa a daura"

"Auren da kike so na kawo miki kyauta Qareeba. Muje ki nuna min dakinki ni kuma na nuna miki soyayya irin wadda ta dace dake"

Zuwa yanzu banda tsoro harda bacin rai. Ta yarda bazata karyata ba tana son aure amma ita ba mutuniyar banza bace.

"Man bana son irin wannan wasan idan ma kana min kallon wadda bata da kamun kai ne to ka dena don ban taba zubar da mutumcina ba"

Tafi yayi ya tashi tsaye "da kyau ashe dai dolancin naki wuri yake samu"

Maganarsa tayi mata zafi ta tashi zata bar wurin kawai ya kamo wuyanta yana kokarin sumbatarta ta karfin tsiya. Ture shi tayi tana cewa ita ba 'yar iska bace.

Wani wawan mari ya kai mata a take bakinta ya fashe "nine dan iskan kenan. Yarinya kinyi gaskiya kuma yau zan nuna miki waye BB"

Qareeba na jin haka ta fara ja da baya ya biyota. Kuka ta saka tana kiran Mummy. BB ya samu ya fizgota tana kokarin gudu ta fada kan centre table jug da kofunan suka fashe wasu suka suketa.

Jinin da take zubarwa bai sa BB ya kyaleta ba ya dagata akan kafadarsa ya hau sama. Dakin farko na Dr Tani ya shiga ya jefata akan gado. Hankalinta yayi mugun tashi tana kuka wiwi ta durkusa a gabansa ganin yana cire kaya.

"Kayi hakuri Babawo kada ka cutar dani. Indai aurene na hakura kuma wallahi zan rufa maka asiri ka tafi"

"Hahhhh shegs Qareeba ashe kinsan suna na. Naji kina Man- Man nace bari dai in nuna miki man dinnan yau"

"Na tuba kayi hakuri don Allah" tace tana hada hannuwa.

Belt dinsa ya zare ya shiga zuba mata banda ciwukan da taji a kasa. Tayi kuka har hawaye ya kafe mata sannan yayi kanta.

*****

BB bai dade da zuwa ba Dahiru yazo. Haka kawai yace bari ya kawo musu katin aurensa. Yana wurin Dr Tani ta dawo itama.

Ganinsa da tayi ta wani tabe baki. Bai damu ba ya gaisheta tare da mika mata katin bikin.

Budewa tayi ta karanta sannan ta mika masa abinsa "naga kamu da walima kawai zata yi amaryar taka ni kuma saboda yanayin aikina dinner kawai nake iya zuwa."

Sarai ya gane magana take son fada masa yayi dariya kawai ya jefa su mota ya bude zai shiga ta dawo.

"Kaga motar wanda zai auri Qareeba itama saura 3 weeks. Dan jira na kirawo shi ku gaisa ko"

"Allah Sarki Anti Qareeba ashe lokaci yayi bana zata tashi. Kai na tayaku murna  zan jira shi sai ya fito"

Ran Dr Tani yayi baki da maganarsa ta shige fuu yayi dariya kawai.

Falon baki taje ta tarar da kaya baja baja a kasa ga dishi dishin jini. Sama tayi cikin sauri tana kiran Qareeba taji motsi daga dakinta da kukan Qareeban amma kofa a rufe. A guje ta fito ta kirawo Dahiru.

Shi tsoro ma ta bashi amma ya kula ba lafiya don da takalmi daya ta fito ma. Binta yayi da sauri tayi sama tana kiransa da ya taimaka. Suna jiyo kukan Qareeba yayin da BB yake dukanta.

Dahiru baiyi wata wata ba ya kaiwa kofar wani irin duka sai ta bude.

Abinda suka gani ne yasa Dr Tani sumewa shi kuwa Dahiru yayi kan BB kamar zaki ya ga nama.
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰18

*Batul Mamman*💖



Haj Mara duniya tayi zafi ta rasa ina BB ya shiga. Ta kira wayarsa har ta gaji.

Bata sanshi da wasu abokai ba yanzu balle ta neme su. 'Ya'yanta mata ta fadawa halin da ake ciki kowacce ta zuke saboda sun gama gajiya da halinsa.

Ta san Dr Tani akan 'ya'yanta da kowa ma fada take balle an taba Qareeba.
*****

Kano kuma Dr Auwal ya debo 'yan sanda ya shigar da kara. Cikin gidansa suka shiga aka dauki hotuna da za'a gabatar shaida. Komai a ilimance don yasan me yake yi shiyasa ko tsinke bai yarda an taba ba. Bayan sauraron bayanan maigadi suka ce suna son ganin wanda ya kaisu asibitin wato Dahiru.

Basu jima da fita ba Dr Auwal ya kira Alh Sule. Yana ofishinsa dake Lagos. Yayi zaton magana zasu yi da ta shafi auren 'ya'yansu sai yaji sabanin haka. Fada Dr Auwal yake yi cikin kunar rai.

"Alh Sule ina Babawo yake?"

"Dakata Dacta meya faru ko gaisawa bamu yi ba"

"Gaisuwa? Gaisuwa ai a gidan mutumci ake yinta. Saboda ku nuna hali an fada muku abinda yaron nan yayi amma daga kai har iyalinka babu wanda yazo yau kwana uku. Wallahi duk inda Babawo yake ku fito dashi domin na riga na hada da 'yan sanda sai munyi shari'a da ku"

Kan Alh Sule ne ya daure ya dai ce masa yayi hakuri sannan ya katse kiran ya nemi Haj Mara.

Tana dauka yace mata "me yake faruwa da Babawo yanzu Dr Auwal ya kirani"

Kuka tasa masa "Na shiga ukuna Alhaji Babawo fyade ya yiwa 'yarsu na rasa yadda zanyi bansan inda yake ba shi kansa"

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Marakisiyya kin kasheni" ya harzuka matuka ya fita da kansa ya kira drebansa. Ko gida bai koma ba ya wuce airport. Jiran awa biyu yayi kafin ya sami jirgi zuwa Kaduna.

Kai kawo Haj Mara take yi ya shigo rai a bace.

Tasowa tayi tana ganinsa "Alhaji."

"Marakisiyya kinga abinda nake gudu ko? Banda lalacewa yarinyar da zai aura nan da 'yan kwanaki ace yayi mata fyade. Wannan wane irin bala'i ne."

"Alhaji ba ta wannan nake ba yanzu shi kanshi bansan inda yake ba. Na kira wayarsa kullum a kashe."

Cikin takaici ya rike kafadunta yana jijjigata "ina tsammanin Babawo mahaukaci ne kuma a jikinki ya tsotso haukan. Ya za'ayi ina fada miki yayiwa yarinya fyade kice ba"a ganshi ba shi allura ne? 'Yar mutane tana gadon asibiti kin kasa fada min gashi har iyayenta sun shigar da kara"

"Kara??? Na bani na lalace Babawo wace irin rayuwa ka zabarwa kanka" tace tana zama dabas akan kujera.

Alh Sule yace "irin wadda ki ka zabar masa mana. Da ace kin bari mun gyara waccan barakar da abubuwa sunyi mana sauki tunda da bakinsa yace yana son yarinyar zai gyara barnar da yayi"

Hararar Alh Sule tayi rai a bace "kai babu dama ayi zancen Babawo sai ka sako wannan yarinyar. Mawadda, Mawadda dai kamar autar mata. Ana maganar 'yar mutane kana kiran 'yar aiki kazama 'yar kauye"

Hade bakinsa da ya saki yayi cikin mamaki "wato Qareeba 'yar mutane tunda iyayenta suna da kudi. Waccan yarinya Mawadda kuma ba mutum bace saboda 'yar aiki ce? Gaskiya kina da matsala da ke da duk masu yiwa 'yan aiki kallon bayi. Bawa ma Marakisiyya akwai hakki tsakaninsa da ubangida ballantana wadda tazo neman halak da guminta"

"Maganar yarinyar nan ta riga ta wuce da wanne zanji kuma? Yaro ya bata ga kuma wata a asibiti ka tsaya kana dauko min wani zance mara tushe. Har yau bana nadamar kashe maganar Mawadda domin tayi tsararo rayuwar dana ta gurbace saboda ita"

"Da kyau matar Alh Sule Chanji" yace yana tafa hannuwa "sai dai ina son tuna miki dukiya da duk wani abu da kike tunkaho dashi nawa ne ba na uban kowa ba"

Juyowa tayi jiki a sanyaye "Alhaji zagina ka ke yi ko gori?"

"Duk wanda ki ka dauka a ciki daidai ne. Kinga Malama na baki minti shabiyar ki shirya Kano zamu tafi yanzu"

******

Bayan sallama sai da aka bashi izinin shiga sannan Dahiru ya bude kofar dakin da aka nuna masa an mayar da Qareeba.

Tana kwance Dr Tani na bata tea gefe kuma yayunta ne. Najib ya matso kusa dashi fuskarsa dauke da murmushi "Dahiru bamu da bakin gode maka. Allah Ya saka da alkhairi"

Hannu ya mika masa Dahiru ya dago nasa da yake nannade da bandeji babu halin gaisawa.

Faisal da Safwan ma duka sunyi masa godiya Dr Tani ta tambaye shi me ya sami hannun cike da kulawa. Banda 'ya'yan cikinta duk duniya babu wanda ta taba jin ya kwanta mata tamkar ita ta haife shi kamar Dahiru.

Murmushi yayi "Targade ne amma an gyara. Zazzabi ne ya rikeni ban sami dawowa ba. Yaya jikin naku?"

Sakin fuska tayi "da sauki Dahiru"

Ya mayar da kallonsa ga Qareeba da ta kafe shi da idanunta daya da rabi "Anti Qareeba ya naki jikin?"

"Da sauki. Dahiru ba don kai ba da rayuwata ta zo karshe...."

Faisal yace "shhh Sis ki dena irin wannan magana"

Kuka ta soma yi har lokacin Dahiru take kallo "you are my hero Dahiru bazan taba mantawa da kai ba. Tun da na farfado nake neman me zance idan kazo na godiya na rasa"

Murmushi Dahiru yayi ya kalleta da tausayawa "gashi kin kirani Dahiru har sau biyu, ina ganin babu sauran godiya a tsakaninmu"

"Kuskure ne Ahirin my hero nake nufi" ta sake cewa itama tana dariya.

Gabadaya dakin suka sa dariya Dr Tani tana ta jan shi da hira anyi sabon da kuma wannan karon har ranta take nufi don Dahiru yayi mata abin da dole ne ma ta kaunace shi.

Zuwan Dr Auwal hirar ta chanja zuwa karar da ya shigar da kuma neman BB da 'yan sanda suke yi. Dahiru yayi alkawarin tsaya musu shaida a duk lokacin da aka neme shi.

Yadda ya dauki zafi sosai akan lamarin ya sanya Dr Tani tunanin ko dai da gaske yana son Qareeba din ne. Idan kuwa hasashenta gaskiya ne ta kuduri niyar Dahiru ko matansa uku zata bashi 'yarta. Ashe hakan take a wurin itama Qareeban. Soyayyar da bata taba sanin ana yi ba mai zafi ita ce ta kamata akan Dahiru. Kallo daban take yi masa yanzu. Kuma kamar Dr Tani ta ta'allaka taimakon da jin zafinsa da soyayya wanda shi kuma duk yana yi ne idan ya tuna Mawadda ta taba shiga wannan halin kuma tsaninsu ta karshe da zata taimaka musu taci amanarsu a kotu. Bashi da wannan burin, tunda Allah Ya dawo masa da ita har ana kirgen kwanakin aurensu dole ne ya nuna godiyarsa ta hanyar taimakon masu bukata.

*******

Yana barin asibitin Alh Sule da Haj Mara suka iso. An nuna musu dakin suka tafi jiki a sanyaye.

Haj Mara ce a gaba ta tura kofar Dr Tani ta hayayyako mata cikin bacin rai "Marakisiyya kada ki shigo dakin nan don baki da abinda zaki fada min"

Alh Sule ya biyo bayanta ya nufi Dr Auwal ya mika masa hannu yaki mika nasa sai ma kallon banza da yake binsu dashi. Jikin Alh Sule ya sake mutuwa, da mutumcinsa da komai da guda daya ya zame masa wake daya bata gari. Bai daddara ba yace "Dacta don Allah..."

"Kalli 'yata Alh Sule. Dubi yadda Qareeba ta koma a dalilin danka"

Daga shi har Haj Mara sun tsorata da ganin Qareeba. Jikinta ya sha bandeji fuska kuwa sai kayi mata farin sani zaka ganeta saboda kumburi.

Gaban Haj Mara ya fadi har wani jiri ta soma ji saboda yadda ganin Qareeba ya tuna mata da maiaikin da ta tsani jin sunanta da labari a kanta.

Matsawa tayi jikin gadon "sannu Qareeba"

"ALLAH YA ISA ANTI MARA"

Kowa sai da ya kalli Qareeba yadda ta daga murya ta sake cewa "bazan taba yafe miki kuma ina addua duk wata masifa ta duniya ta fadawa Babawo"

Turus ta tsaya tana bin mutanen dakin da kallo "Tani kina jin Qareeba za ta yi min rashin kunya"

"Rashin kunya ta wuce wannan dan akuyan da yazo ya kaita har gadon mahaifiyarta zaiyi mata fyade? Idan baki fita daga dakin nan ba zaki ga rashin mutumci irin wanda baki taba tsammani ba"

Ja da baya tayi wai yau ita Haj Mara wadda maza da mata suke tsoro itace matar da ta rainawa wayo a baya take fadawa magana haka.

Alh Sule zai yi magana Dr Auwal yace dashi "kaga ka dauki matarka ku tafi kawai zamu hadu a kotu idan an kamo shi."

"Ba don wayarka ba ko da wasa bansan abinda yake faruwa ba Dacta kayi hakuri muyi magana"

"Babu fa abinda zaku ce da zai sa mu janye karar nan"

Haj Mara tace "Allah ko? To bari kaji in fada maka idan baku janye ba Dr Tani sai ta rasa wannan aikin da asibitin saboda shaidar karya da tayi a kotu."

Tsananin bakinciki ya kama Alh Sule "yanzu ina kokarin shawo kan matsalar kina kawo wani zancen banza daban"

Ido a soye tace "Yo me ya rage min Alhaji? Ka tsaneni ka tsani dana. Gara tun wuri na fada mata idan tana son ganin bayana ne sai dai mu ga bayan juna."

Dr Tani ta tako gabanta kamar me neman wani abu sai ji suka yi ta taske Haj Mara da mari dakin gabadaya ya dauka. Dago kai tayi a kufale Dr Tani ta sake kara mata a dayan kumatun

 "Marakisiyya ni dake shege ka fasa. Da kika ganni nan ko zanyi bara na rantse da Allah sai naga karshen dan mahaukacin yaron nan naki. Kudi ne dai kike takama dashi ko? Kin dade da sanin daga gidan da na fito nafi karfin tunkaho da dukiyar gaibu dukiyar miji. Idan kin cika ki tareni gaba da gaba in kudi ne zai bada nasara a kotu kin sani na fiki, idan kuma shaidu ne to dama a tafin hannuna kike."

Tsananin mamaki da gigitar mari yasa ta rike kumatun duka biyu "ni ki ka mara?"

Dr Auwal ya dubi Alh Sule "ka fitar da matarka daga asibitin nan haka Alhaji"

Matsawa yayi daga kusa da ita kamar wata abar kyama "Ina ganin lokaci ne yayi da zanyi abinda ya dace game da ita. Marakisiyya kin tuna lokacin da na fada miki akwai ranar da zaki girbe duk tsiyar da kika shuka? "

A matukar tsorace tace "Alhaji kada ka sakeni don Allah"

"Alfarma daya zanyi miki mu koma Kaduna tare ki kwashe kayanki zama dake bashi da wani amfani sai tarin bakinciki"

Kallonsa ta jima tana yi kafin ta hade rai sosai "a gaban makiyana ka wulakanta ni me zai sa na bika, sakina nawa kayi min?"

"Babu sauran zama tsakaninmu"

Su Safwan da suke gefe suka yi zuru zuru suna kallonsu. Dr Tani ta tabe baki ta koma ta zauna sai Dr Auwal ne ya iya cewa yayi hakuri su tafi tare.

Shima harara ta buga masa ta fice kamar zata tada kura. Alh Sule ya kwantar da kai duk da yadda yake ji ya cigaba da basu hakuri "idan rufe Babawo ne zai kawo karshen fitinarsa Dacta zan baka dukkan goyon baya. Dana ne kuma wallahi ina son sa amma bazan zuba masa ido ya cigaba da lalata 'ya'yan mutane ba."

Fita yayi bai tarar da Haj Mara ba ta sami tasi ta tafi tasha. Mota daya tayi shata sai da ta zauna ta shiga kuka sosai. Dreban yana ta tambayarta ko lafiya bata tanka masa ba ya gaji ya rabu da ita.

Har gida ya kaita ta ciro kudinsa ta bashi ta shige maigadi yace ina Alhaji harara ta bashi amsa. Kayanta taje ta hada wanda zata iya hadawa a lokacin ta duka karkashin gado ta dauko kit dinta. Komai mai mahimmanci kama daga kudade, gwal da takardu suna ciki.

Daukar mutumci tayi masa saboda tasan yana da nauyi sai taji abu sakayau. Zuciyarta ta harba ta dire shi akan gado hannu na rawa ta bude. Kasa ta fadi wanwar saboda tashin hankali. Fanko haka ta same shi ko kura babu.

"BABAWO!!!!"
******

Biki ya gabato inda Haj Mama da Baba Prof suka nuna bajinta sosai. Su wannan ne bikinsu na karshe saboda Attahir ne auta. Shima kuma Dahiru shine karshen aure a nasu gidan kannensa biyu sun riga shi. Saboda karamci da dattako ko a jikin katin Mother's Eve an rubuta sunayen angwaye biyu, Attahir da Dahiru. Wannan abu yasa masa kara son mutanen da jin nauyinsu. Yadda baya gajiya da yi musu godiya da addu'a haka ma su Inna da Baffa. Su kuwa sai dai su ce da na kowa ne baka san wanda zai ji kanka ba nan gaba.

Kowane ango an bashi katunan da zai kaiwa dangin amaryarsa saboda wurin taro sai da kati ne. Babbar 'yar Baba Prof ita ta dinka musu kayan da zasu saka iri daya. Karshe Dahiru har hawaye yayi yana ta addu'ar kada Allah Ya bashi ikon cutar dasu ko daidai da kwayar zarra. Ya san yadda zamani ya canja yanzu sai ka taimaki mutum ya zame maka alakakai. Ka nufe shi da kyakkyawar zuciya idan ya sami sukuni kaine mutum na farko da zai bakantawa musamman idan naka karfin ya kare. Wani ko labarinsa ma bazaka kara ji ba likkafa taci gaba. Saboda irin wannan hidima da ake yi musu Inna da Baffa suka ce ko bayan ransu idan Dahiru ya butulcewa wannan iyali basu yafe masa ba.

Sannan fa suma ba'a barsu a baya ba. Buhun wake uku, kwandunan tumatir da tattasai da albasa wanda kila har a gama bikin ba sai sun nema ba haka suka kawo musu. Ga su gero da kabewa tuli guda. Lallai kyautatawa abar so ce kuma babban tsani na samuwar farinciki ga mai yi. Babbar bukata ka nufi Allah da kyakkyawar zuciya babu gori ga wanda aka kyautatawa kuma babu saka tsammanin za'a ramawa kura aniyarta.

Zuwa yanzu Mawadda da Nawal sun kulla zumunci da juna duk da basu taba haduwa ba amma suna waya har hotunan juna sun gani. Su ma kowacce nata dangin suna ta shiri ne domin fita kunya.

Anje anyi jeren Mawadda kayanta babu karanta babu karya. Duk wani abu da ya kamata iyaye su yiwa 'yarsu mace nata iyayen sun kamanta. Idan ka duba 'yan uwanta dole kace Mawadda ta wuce zarra domin kuwa ita kusan da biyu ake mata komai. Wanda ya auri 'yarka da duniya take gudu saboda laifin da bai zama nata ba ya cancanci godiya. A wurinsu kuwa godiya idan ta wuce ja wa 'yarsu kunne akan ladabi da biyayya to fa sai fita kunyar juna su nunawa duniya bata wulakanta ba ko da aka juya mata baya Allah Ya tsare bayinSa.

Katin daurin aure bugun farko sunan wani masallaci a nan unguwar tasu aka saka. Sai kuma abin dadi abin mamaki kanin Mal Fatihu yazo gidan tare da wasu dattawa su uku da Maigari ya wakilta akan ya bada umarnin aje fadarsa a tsakiyar garin Tariwa a daurawa Mawadda da Dahiru aure. Suna fadin sakon Baba yasa kuka.

Guda cikin 'yan aiken yace "Mal Fatihu nayi zaton zaka yi farinciki da wannan abu"

Hankici yasa yana goge ido yana murmushi "Mal Uba burina ne ya cika. Ban damu da auren Rafi'a da nayi a nan ba. Amma kaga Mawadda, saboda Mawadda kowa ya tsanemu har ana ikirarin cinnawa gidana wuta. Saboda ita aka yi mana iyaka da mahaifarmu mu duka. Yau gashi saboda ita zamu koma. Kullum kukanta idan ta tuna da gida shine ta janyo an rabamu da 'yan uwanmu tana ganin ita ce silar komai."

Wani mai suna Muntari yace "ka godewa Allah kuma ka yafe mana. Maigari yace shine zai yiwa amarya walicci idan ka amince domin dinke barakar da aka samu a baya"

Shi kuwa Mal.Fatihu idan ba yasha giyar wake ba me zai cewa Maigarinsu. Mutumin da ya ceci rayuwarsu kuma ya basu muhalli harda yafe kudin haya na wata shida. Abinci yasa aka dafa musu aka karramasu karshe sannan yace a sanarwa Maigari ya bashi wuka da nama. Alfarma daya yake nema akwai dan uwan Dahiru wato Attahir da za'a fara daura nasa auren a ranar. Suna son a kara kamar awa hudu ko zuwa azahar ne ayi na Mawadda saboda kowa ya sami halarta.

Baki na tafiya ya sanar da iyalinsa. Kowa kuka musamman Innarsa wadda ta tuno rabonta da garin tunda ta fita takabar Malam mahaifinsa.

Daki Mawadda ta shige tayi sujjadar godiya ga Allah Madaukakin Sarki. Wayar Dahiru ta kira cike da zumudi ta fada masa.

"Zan ajiye miki tukwici babba saboda na fiki farinciki. Burina dama na nunawa 'yan garinmu ina son Mawadda duk runtsi duk wuya"

"Nima ina son Dahiru duk runtsi duk wuya"

Wayar ya kankame kamar ita ce a gabansa "maimaita don Allah"

Tana murmushi tace "Me zan maimaita?"

"Mawadda manaaaa pleaseeee" yace yana jan kowane harafi a kasalance

Mawadda sai da taji bugun zuciyarta ya karu ta daure tace "Yayanmu mata ne ke shagwaba fa a iya sanina. Amma kai naga alama Inna tasha fama."

"Gara ma ki shirya tarihi yazo min ance kyuya ce dani da son jiki."

"Kada ka damu bazan rinka saka ka aiki ba kasha zamanka da son jikinka"

"Assha, ba kya ganewa. Son jiki fa irin wanda zanyi ta makale miki dinnan. Duk inda ki ka zauna ina kwance a jikinki"

Bata san Dahiru ya kware a iya bata kunya ba sai yanzu. Ta dan cije lebe tana tunani sannan tace
"Ban ma san me kake cewa ba. Kasan nakan kurmance lokaci zuwa lokaci sai abinda kunnen ya ga dama yake ji....hello, hello, Yayanmu bana ji ka sake kira"

Yana dariya yace "idan ki ka ajiye wayar nan zamu yi fada Mawadda. Ki saurareni kawai ki tsinci na tsinta ki bani amsa"

Turo baki tayi da nata salon shagwabar
 "me yasa ma na kira ka ne?"

"Soyayya mana. Ina yi miki kallon wata saliha ashe ashe" yace yana tsokanarta.

"Ashe me? Yanzu ni ba saliha bace?"

"Ban ce ba. Amma fada min gaskiya me kika fi so game dani uhmm?"

Tsuke bakinta tayi tana tunanin rayuwarta dashi tun a Tariwa har yanzu.

"Yayanmu babu abinda bana so game da kai. Kayi abinda babu wanda yayi min irinsa a duniya banda iyaye da 'yan uwa. Matsayinka naka ne kai kadai. Allah Ya bani ikon zama da kai da amana"

Yaji dadin kalamanta sosai. Jan hanci tayi ya gane kuka take yi "kefa kin iya bata abu. Muna hirarmu mai dadi zaki soma kuka."

Kukan ta cigaba tace "na dade ina son fada maka hakan ne ban samu dama ba sai yau"

"Baki sani ba ai Mawadda, irin wannan jira akeyi sai an kai amarya ya rage mu biyu sai ki fada kina kuka ni kuma na sami damar daukanki na rungume"

"Kurmanci, kurmanci ya sauko Yayanmu bana ji bana ji" tace tana jin wata irin kunyarsa ta katse wayar tana jiyo dariyarsa.

Sumbatar wayar tasa yayi yace "saura kwana hudu."
******

BB ya kalli wayar da yayi jifa da ita rai a bace ya tashi yaje inda ta fadi ta tarwatse ya rinka dukanta da kwaftatareren boot dinsa irin na 'yan kwayar Amurka.

Ya dago kai ya kalli Danmani wanda jikinsa ya soma bari. Duk takadarancinsu basu taba ganin hodar iblis ba balle su sha. Amma wannan gidan samari ne da 'yan mata 'ya'yan masu kudi kuma musulmai suke ta busa hayaki suna shanta.

Idanun BB a birkice ya danko wuyansa yana wani shafa masa gefen fuska a hankali idanunsa na rufewa don kansu.

"Ya kaga Mawaddata da kaje? Tayi min kyau kamar na lasheta a hoton kawai. Amma wannan arnen mutumin me yake yi tare da ita? Ko dama kasan harda shi nake nema?"

Danmani ya girgiza kai "ban sani ba yallabai amma tunda kana nemansa sai na binciko maka ko yaya suke"

BB ya sake shi jikinsa babu kwari kwaya ta fara dibansa "haka ne sannan ka binciko min wane kafirin ne zai aure min mata. Kaga hotonta ya kamata nayi ta kallo yanzu amma tunda ka hado ta da wani kasa na fasa wayar"

"Tuba nake yanzu zan sake zuwa na samu wasu"

BB yayi dariya ya mika masa wayar da yake amfani da ita bayan ya canja sim.
"Ka ciko min wannan da hotunanta masu kyau kaji. Mawadda zata kasheni da kyaunta...hakurina ya soma karewa I NEED HER" ya kare cikin karaji.
******

Karfe takwas ta wuce ana kiran sallar Isha Mawadda da Bushra 'yar yayarta Hasiya mai kimanin shekaru goma sha biyu suka sauka daga adaidaita sahu daga bakin titi. Dreban da suka tsadance tun a gidan Anti Zahra wadda ita ke yi mata gyaran jiki ya amince zai shiga dasu har ciki. Amma yana ganin wasu mata da yawa yace su sauka ya fasa. Dama gashi ana ta mata waya cewa dare yayi. Yau aka gama gyaran jikin da jan lalle. Da safe kafin lokacin kamu za'ayi mata baki.

Fita suka yi suna hirar da Bushra ce take ta surutunta Mawadda tana dariya.

Daga nesa Danmani ya hangota saboda akwai haske duk da babu wuta gidaje da dama sun kunna inji. Layin babu mutane sosai an shiga masallaci.

Sauri yayi ya iso gabansu yace "Mawadda dan dakata mana"

Gaba na faduwa suka tsaya ita da Bushra. Gefensa suka yi niyar rabewa su wuce ya nuna musu wukar dake makale a gefen wandonsa.

"Ki tsaya kawai ba wata tsiyar zan miki ba, Oga hotunanki kawai yake so"

"Oga? Hoto?? Kana da hankali kuwa???" ta daure tace tana kankame hannun Bushra.

Janyo Bushran yayi ya manna mata wukar a gefen ciki. Mawadda ta rasa yadda zata yi sai kuka da roko.

"Kinga idan kika daga murya har mutane suka taru bazan bar yarinyar nan ba sai na burma mata wukar nan Yasin. Ungo ni ki kashe selfie kamar kala goma ki bani kafin a idar da sallah"

Wannan wace sabuwar masifar ce kuma tace tana hawaye. Jikinta ko'ina yana rawa haka ta karba ta fara dauka. Shake Bushra yayi yace ta saki fuska ta dena kuka.

Bushra taji wuya tace "Anti kiyi murmushi"

Mawadda na kuka tace "To don Allah kada kayi mata komai."

Ita kanta bata san nawa ta dauka ba sai dai zuciyarta tamkar ta fito ta baki don bakinciki da tsoro. Numfashinta har neman daukewa yake. Rayuwar Bushra take dubawa kawai da take hannun wannan mahaukacin.

Sallama yaji liman yayi ya fizge wayar ya hankada Bushra kan ta suka fadi tare. Sai da Bushra ce kadai ta tashi Mawadda kokawa take da numfashi. Duhu ya mamaye idanunta  zuciyarta kamar an daddaure.

Bushra na ganin yadda take sandarewa ta soma kuka tana cewa ta tashi wayarta dake cikin purse ta soma kara Dahiru ya kira.

Bushra na dauka ko suna bata gani ba cikin kuka tace "kuzo Anti ta mutu"

A wurin ta yar da wayar maza suka taru a kansu ana cewa me ya sameta.

Kusan dakika talatin Dahiru yana rike da wayar kwakwalwarsa ta toshe ya kasa gane me yaji yanzu.


[31/01 9:36 am] Batuul Mamman: *GUMIN HALAK...*💰19

*Batul Mamman*💖



Cikin kankanin lokaci jama'a sun fara taruwa. Marwanu da Saifullahi sun fito daga masallacin suka hango taron mutane suka je. Mawadda da Bushra suka gani nan da nan suka daukota suka yi gida ana ta jajanta musu. Danmani yana cikin masu jajen don bai bar wurin ba har aka tafi da ita.

A tsakar gida aka shimfideta Yaya ta rinka shafa mata ruwa a fuska. Ade tayi gefe tana matsar kwalla. Bushra tana kuka ta fada musu gamon da suka yi a kasan layi kowa sai al'ajabin wannan abu yake yi. Da kuka mai cin rai Mawadda ta bude ido  ana ta bata baki amma kamar suna zuga ta ne. Mutum baka san shi ba baka taba ganinsa ba kawai ya tsareka yace ka dauki hotunan kanka a wayarsa. Wannan abu da ban mamaki yake. Su Marwanu harda Baba waje suka yi da iya kwatancen da Bushra tayi na mutumin suna nemansa.

Shigowar mota layin a guje yasa kowa kallonta. A gaban gidan Dahiru yayi parking ya fito da sauri ko kashe motar baiyi ba saboda yadda ya ga su Baba da maza da yawa ana ta kai kawo a wurin.

Gwiwoyinsa ne suka yi sanyi duk taku daya tamkar yana yi a iska sai bin mutane yake da kallo.

Baba ya nunawa Marwanu shi "riko min Dahiru kamar bai san me yake yi ba"

Hannunsa yaji an kamo zuwa gaban Baba ga wasu dattijai makota suna masa jaje yaji wani yace Allah Yasa ayi nasarar kama shi dai.

Hantar cikinsa ta kada yaji ina ma ya bude ido ya ga mafarki yake yi jiki na tsuma yace  "Baba..."

Katse shi Mal Fatihu yayi "Mu shiga ciki ta farfado kafin fitowarmu. Dama nasan ko waye bazai zauna a kama shi ba. Allah Ya kare mana ita daga sharrin ko ma su waye"

Kan Dahiru sai ya sake daurewa saboda rashin gane me Baba yake nufi. Danmani da yake tare da mutane kuma ya ga zuwan Dahiru mutumin da BB yace yana nema babu shakka ko dar a ransa ya matsa kusa da Saifullahi.

"Wannan shine mahaifinta?" Ya nuna Baba. Saifullahi ya amsa masa. Sai ya kuma cewa  "Ku uku kuma 'yan uwanta kenan"

"Mu biyu dai, wannan shine zai aureta"

Marwanu ya janyo hannun dan uwansa yana karewa Danmani kallo "kai kuma waye?"

" Dan agaji ne, muna can bayan layi ne aka ce anyi hatsaniya a nan nazo gani" yana fadin haka yana ja baya basuyi aune ba ya bar wurin ta cikin jama'a da cincirindon almajirai da suka taru.

Baba ne a gaba ya sanar da iyalinsa tare suke da Dahiru. Kowa ta shiga suturta kanta sannan suka shiga idanunsa da suka kankance suka yi ja suna neman Mawadda. Hamdala yayi ga Allah da ya sameta da ranta bai san wane hali zai shiga ba da ta tabbata ta sake barinshi a karo na biyu.

Da kyar ya tattaro kalaman gaisuwa ga su Ade.

"Waye ya fada maka ne ko zuwa kayi kawai?"

Iya ce tayi tambayar ya amsa mata da cewa waya ya kira.

Bushra ta rufe baki "Laaaaaahhh ashe kaine, lokacin tsoro naji na zata ta mutu"

Hasiya mahaifiyarta ta daka mata duka "ce masa kika yi ta mutu don rashin hankali"

"Wallahi Mama baki ga fa yadda ta rinka rike kirji ba sai kuma ta dena motsi" tace cikin kuka.

Baba ya numfasa "To mu godewa Allah abin yazo da sauki. Ke Bushra bai ji miki ciwo da wukar ba ita ma iyakarta hoto. Allah Ya cigaba da karemu baki daya"

Iya ce ta taba Yaya ta nuna mata su Mawadda. Nata idanun a kasa suna digar hawaye yayin da Dahiru ya kura mata idanu kawai.

Yaya tayi dan tari "Mawadda kije ku gaisa da Dahiru sai kiyi masa bayanin abinda ya faru sosai. Mungode kaji Dahiru ayi ta addua da neman tsari"

Sallama yayi musu ya tashi ya tafi inda su ka saba zama falon soro. Kamar wadda kwai ya fashewa itama haka tabi bayansa.

Tana shiga ko zama bata yi ba ya tsareta da idanunsa "what happened my love?"

Kyabe baki yaga tayi zata soma wani kukan ya shiga girgiza kansa a hankali a hankali yace "babu wata kalmar tausasa zuciya da zanyi amfani da ita wadda ba'a fada miki ba kafin na zo, ki daure ki fada min abinda aka yi miki kinji."

Ta gyada kai sannan su ka zauna "ina jin ki"

Tun daga bayyanar Danmani a gabansu har zuwa farfadowarta  ta fada masa. Fuskarta duk ta kumbura saboda kuka.

Dahiru kuwa ko yawu ya kasa hadiya saboda wani daci da yaji ya taso masa har wuya. Bakinciki, bacin rai da damuwa babu wanda bai rufar masa ba. Tashi yayi ya koma bakin tagar falon wadda ta bulle wajen gidan ya tsaya. Ya rasa ma ta ina zai fara. Wane irin dan iska ne zai tare mace yasa ta daukar kanta a hoto. Me yasa kowane mara kirkin idan ya kwaso shararsa akanta yake ajiyewa.

Kukanta yaji ya tsananta ya juyo ya dawo gabanta ya tsuguna "me ki ke so nayi miki kiji sauki a ranki? Ko menene ki fada min nasan bazaki nemi abinda Dahiru bashi dashi ba."

Sai da wasu hawayen suka zubo ta iya bashi amsa.
"Ka dubi girman Allah ka fada min gaskiya Yayanmu. Ina yin wani abu ne da yayi kama da gayyatar maza masu mugun hali gareni? Ina bayyana tsiraici a inda ya kamata na boye ne?? Yanayina ko maganata sunyi kama da na mata marasa kamun kai??? Meyasa sai ni kawai suke bi????" ta kuma fashewa da kuka.

Ba karamin karyar masa da zuciya tayi ba tamkar ya tayata kukan.

"Babu ko daya sai dai ke din baki fi karfin Allah Ya gwada imaninki ba. Kin manta yana daga cikin abinda Allah Yake mana nuni dashi wato kada muyi tunanin don munce munyi imani shikenan mun tsira daga komai na rashin jindadi. Dole ne mu fuskanci kalubalen rayuwa sai dai na wani ya fi na wani. Allah Yace bazai dora mana abinda yafi karfin imaninmu ba. Ki sawa ranki komai ya wuce."

Murya a dashe tace "Yayanmu tsoro nake ji. Tun farkon maganar auren nan sai naji gabana yana yawan faduwa."

Gyara zamansa yayi daga tsugunawar saboda gajiya da ya soma ya zauna sosai a gabanta amma ya bar tazara tsakaninsu domin ya san iyakarsa. Domin ya kwantar mata da hankali yayi murmushi.

"Nima ina jin haka sai dai na alakanta shi da sabuwar rayuwar da zamu fuskanta daban da wadda muka saba. Kinsan fa aure ba karamin abu bane. Hatta sunanki sai ya chanja"

"Daga aure sai chanja suna? Ni dai ban taba ji ba"

Kallonta yayi tana tuttura baki yayi dariya kadan "Yanzu sunanki Mawadda kawai, amma muna aure zaki ji an koma cewa Matar Dahiru, Mawaddan Dahiru idan wata tara da kwana tara ya cika kuma ki koma Maman wane ko wance"

Bata san lokacin da ta soma dariya ba tana rurrufe fuska.

Yaji dadin ganin ta saki ranta ya sami damar cigaba da tsokanarta kuwa "sai yanzu na tuna ma, ko irin hirar nan ta sunan 'ya'yanmu na fari bamu taba yi ba."

"Ni dai kada ayi wannan hirar ko na koma gida yanzun nan" tace tana masa murmushi.

Alamun sakawa baki zip yayi "To Qulqulatul qurabati na bari"

Wannan suna da taji yasa ta rinka dariya harda guntun hawaye tana yi tana rufe baki.

"Allah Sarki Anti Qareeba Yayanmu kaima kasa mata rai fa"

Yasha kunu "ta sawa kanta dai, kinsan fa daga baya ko muryarta naji sai gabana ya fadi saboda kawai nasan akwai abinda tazo dashi na takura min"

"Idan....idan"

Karkace kai yayi yana kallonta "idan me?"

Maimakon ta fada sai ta tsuke bakinta. Kunya take ji tace masa idan ta tare tana son zuwa duba Qareeba.

"Bari na tafi tunda kin kasa fada"

"Zaka kaini na dubata idan...."

Ya karasa mata "idan kin tare kin zama matar Dahiru? In sha Allahu ko an sallameta zamu je"

Dahiru bai bar gidan ba sai wuraren goma da rabi. Shima don kada a ciki a ga rashin hankalinsa ne amma ko kadan bai gaji da zaman ba yana ta sako hirar da zata dauke mata tunani.

Da ya tashi wayarsa ya dauko "please kada ki zauna tunani idan na tafi bacci kawai."

"Yes sir" tace tana masa salute irin na sojoji.

Da haka suka yi sallama cike da farinciki sun manta da wani mai daukar hoto.

******

A bangaren Danmani kuwa gidan da BB yake ya wuce kai tsaye. Wayarsa da ya bashi ya dauki hotunan kasa budeta yayi tun a hanya. Dayake aljihunsa da nauyi waya ya fara saya kafin yaje unguwarsu Mawadda. Yanzu da ya kai masa sai ya bashi wayarsa yace ya tura.

BB kamar yayi hauka da ya ganta. Tayi kyau ta canja gabadaya fatarta sai sheki take yi. Idan ya aureta ya more ya ayyana a ransa yana cewa Danmani da fatan bai taba koda yatsanta ba don yarinya ce mai daraja.

"Wane ni yallabai, sai dai na bincika wannan mutumin shine zai aureta asabar dinnan"

Wata irin dariya BB ya rinka yi sannan ya dawo ya tafa da abokinsa "ko kasan komai ya koma more interesting da wannan bayanin. Sai yayi danasanin dukan da yayi min."
******

Sannu sannu bata hana zuwa inji Bahaushe sai dai a dade ba'aje ba.
Yau alhamis aka tashi da kamun Mawadda. Iyaye da 'yan uwa da ita kanta amaryar farincikinsu bazai misaltu ba. Filin wata makaranta suka kama da ake yawan biki zasuyi taronsu a ciki. An gyara wurin sosai ya kayatar.

Amarya ta hade cikin wani purple din lace da pink din ashoke. Lokacin da zasu tafi wurin kamun Ade har kuka tayi. Ta dade da cire rai zata ga auren tilon 'yarta mace ashe inda rai da rabo. Dahirun da take matukar so da 'yarta Allah Ya sake dawo musu dashi lokacin da basuyi zato ba.

Dayake kamun shine babban taro daga bangarensu sun kashe masa kudi don ya tafi daidai da zamani suma. Komai nasu cikin burgewa daidai ruwa daidai tsaki. Haj Mama ita ce ta fesawa Mawadda turaren kamu na al'ada ta rugumeta a jikinta aka yi musu hoto. Ganin Mawaddan na sunne kai tace mata ita dai surukar zamani ce matar danta ta zama 'yarta gara ta ajiye wannan kunyar sun zama daya.

******

Ana can ana taro Dahiru da Attahir da wasu abokansu suna gidan da Dahirun yake zama don nan suka dawo saboda baki. Itama Nawal ranar suke nasu kamun.

Hira ake yi da barkwanci irin na angwaye Attahir ya sako zancen kai amaren da za'ayi ranar asabar.

Da fari an tsara akan kowacce za'a fara kaita gidan iyayen nata mijin. Sai dai saboda nisa da ma kawaici na mutan kauye Inna tace Dahiru ai dan su Hajiya Mama ne saboda haka a kaita gidan Baba Prof kamar yadda za'a kai Nawal. Daga nan sai kowanne ango ya dauki amaryarsa. Murna wurin angwayen ba'a cewa komai su tsari yayi musu daidai.

"Dahiru ka shirya tsere fa zamuyi aga wanda zai fara zuwa gida da matarsa"

"Baka isa ka sani yin gudu da Mawadda akan titi ba ranar shigarta motarmu ta farko. Idan kasan tafiyar kwai to ita zanyi"

Ihu abokai suka sa shi kuwa ya fuske. Attahir yace "kai dai kana da matsala na rana dayan ma bazamu yi ba. To ba tsere ba mu tafi a mota daya"

"Inaaaa bukulun hirar soyayya zaka yi min ta ganka taki sakewa dani. Malam kowa yaji da kansa kawai. Ni da kake gani idan na hau saman nan sai nayi sati baka sani a ido ba"

Nan fa aka sami nayi suka rinka tsokanarsa karshe dai yace abu daya ya amince ayi. Shine zai dauko Nawal zuwa gidan Baba Prof shi kuma Attahir ya dauko masa Mawadda.

*****

Alh Sule yayi tambayar har ya gaji ya zubawa Haj Mara idanu.

Tamkar wata zararriya haka ta koma tun ranar da ya saketa a Kano. Ya dawo gidan da baiyi tsammanin samunta a cikinsa ba ya ganta a birkice. A zatonsa zafin saki ne kawai yake damunta shiyasa ya fita harkarta gabadaya. Tunda ya saketa duk wasu tarkacensa yake hadawa zai mayar da komai Abuja inda Yasmin take.

Yau ya dawo gida cikin dare ya sameta a falo zaune da daurin kirji sai dankwali da ta yafa a kanta. Dauke kansa ya yi daga gareta yasan wani salon jan magana take. Shi kuwa jira yake ciniki ya fada ya sayar da gidan. Dole ta tashi lokacin ko bata so.


Shan gabansa tayi ta mika masa wayarta ya kalli yarinyar da take jiki ya dago cikin rashin fahimta
 "wace ce wannan din?"

"Mawadda ce Alhaji" tace tana kuka "Babawo sai da ya nemo yarinyar nan shine ya turo min sako wai mu fara shirin tarbar amarya. Ko dai yana da tabin hankali ne ban sani ba?"

Fasa wucewa yayi ya koma ya zauna yana fuskantarta.
"Marakisiyya idan kina kaunar Babawo irin son da musulunci yake so ki yiwa danki to ki fada min inda yake idan kin sani na dauko shi."

Sai yanzu ta dan saki rai "za ka yi masa visa ko China ne ka tura shi sai na bishi tunda nima yanzu babu auren."

"Babu inda zaije sai ya amshi laifinsa na yiwa 'yar mutane fyade. Idan case din Mawadda kun rufe shi ai na Qareeba babu yadda zakiyi"

Tashi tayi a tsorace "Alhaji yaron nan jininka ne meyasa baka kaunarsa? Idan muka tafi nayi maka alkawarin ko Nigeria ya dena zuwa. Ta yaya zan rayu idan aka rufe shi?"

Gani yayi zata bata masa lokaci ya tashi abinsa "tunda kina da kudi sai ku tashi sama idan kun ga dama. Soyayya daya ta rage min tsakanina dashi itace addua, bayan haka bazan kashe kaina akansa ba."

Wayarta ya fizge ya tafi da ita. Sai san yadda yayi ya tura masa sako da ita ya janyo shi gida.

Haj Mara ta dade a tsaye tana tunanin mafitar da take jira guda daya. Ita ba kudi ba sannan babu Babawo. Sai dai ta sani duk abinda Alh Sule zaiyi musu danta yana da gadonsa.

Wanka Alh Sule yayi ya fito wayar Haj Mara tana ringing. Da sauri ya dauka yayi zaton Babawo ne yaji muryar agent dinsa da suke harkar gidaje da filaye. Mutumin bai jira anyi magana ba yake sanar da cewa ta duba wayarta ko alert ya shigo ciniki ya fada sun sayi gidan a miliyan tara da rabi saboda cinikin a kurarren lokaci yazo.

Alh Sule ya kasa shiru "Badau nine Alh Sule bata kusa. Wane gidan kake nufi ne"

Yayi dariya "Ah ranka ya dade barka da dare. Gidanka na anguwan dosa da tace ka bada umarnin a sayar zaka hada ka sayi wani babba na bayansa."

Kasa ya sauka da sauri bata nan ya koma dakinta tana zaune tayi tagumi. Yana shigowa ta tashi ya yi niyar marinta ma ya fasa don takaici.

"Ashe barauniya ce ke ban sani ba sai yau. Waye ya baki izinin sayar min da gida?"

Ta ware masa idanunta babu alamun nadama "wanda yace danka ya yashe ni ya kwashe min kadarori. Wannan gidan kuma da na sayar idan ka mutu a cire a gadon Babawo ince ko shikenan"

"Shikenan kuwa Marakisiyya. Zanje na kwanta sai da safe"

Kallonsa tayi da mamaki "au shikenan kawai zaka ce?"

"Banda abinki tsawaita magana da mahaukaciya baki ganin bata lokaci ne?"

Baki bude ya fice ya barta tana cizon yatsa.

******

Ranar juma'a da yamma akayi taron Mother's eve da Haj Mama ta shirya. Taro ne na gogaggun 'yan boko amma matar nan ko kadan bata nuna kyama ko kaskanci ga dangin Dahiru ba.

Kayansu yayar Attahir ce ta basu iri daya su biyun. Shiyasa suna karba suka sayawa amaren nasu material iri daya da ya dace da nasu kayan. Dinki ma awo kawai suka nema don so suke yadda zasu saka komai iri daya matansu ma haka. Hatta jaka da takalmi da su dankunne iri daya suka saya musu.

Karfe hudu da rabi a kofar gidansu Nawal tayi musu. Baya ta shiga kawarta zata biyota Attahir yace mazaunin daya amaryar ne su a hadu a venue.

Shi da Dahiru suna ta hira kunya ta hanata magana har suka isa Tunga daukar Mawadda.

Tayi kyau ba kadan ba Rafia ta rakota har mota gabadaya fuskarta a rufe da mayafin kamar yadda aka shigo da Nawal.

Sun fara tafiya motar shiru a hankali ta bude  fuskarta kadan ta tabo Nawal.

" 'yar uwa bamu gaisa ba"

Itama ta bude nata ta mikowa Mawadda hannu "cikina ke kadawa Sis"

Kasa-kasa Mawadda tace "ke nima haka fa kunya da tsoro nake ji. Amma kinyi kyau sosai" ta kare da murmushi.

Nawal tace "kema haka, a waya nayi ta miki surutu yau kema kunyarki nake ji"

Dariya suka yi a hankali suka sake rike hannun juna.

"Ehem, ehem.....ya kake gani idan muka wuce gidan dasu tun a yau? Sai su kwana a kasa mu kuma mu hau saman. Gobe ana daura aure kowa ya tafi gidansa" cewar Dahiru yana kyaftawa Attahir ido.

Ya amsa masa da cewa "shawara tayi fa dadina da kai kenan saurin fahimta kamar ka shiga zuciyata"

Idanun Mawadda da Nawal suka kwalalo kowacce ta rikice.

Attahir ya kara da cewa "ina jin yunwa mu fara biyawa ayi cefane sai mu wuce yau girkin amare zamu ci."

Tafawa suka yi shi da Dahiru.
"Idan an nemesu sai muce mun tafi honeymoon"

"Me??" Su Mawadda suka ce a tare.

Kusan tare Dahiru da Attahir suka waigo suna kallon bayan suna musu dariya.

"Ashe duk kuna da baki. Kun shigo kun ki kula mu kuna hirarku ku kadai"

Mawadda tayi murmushi "haushi kuka ji kenan"

Nawal tace "mu suke so mu fara lallabasu muna amare"

Attahir ya amsa maganar Mawadda "Ina batun jin haushi bayan hirar taku bata wuce mallakar miji"

"Fada musu dai su san mun san komai" Dahiru ya taya shi

Nawal ta hada ido da Attahir da yake tuki ta madubi tace "wasu matan dai banda mu"

Dahiru yace "ke dai 'yar uwarmu Nawal abar kaza cikin gashinta"

"Da ka bari na figeta dai mu ga masu shan kunya" inji Attahir.

Har suka isa wurin event din suna zolayar juna suka fito kana ganinsu kowanne ya dace da amaryarsa soyayyarsu ga juna bata boyuwa.

Ba karamin kyau suka yi ba komai nasu mazan da mata irin daya sai daukar ido. Kowacce amarya 'yan uwanta sun zo haka aka yi taro cikin mutumci aka watse da farinciki.

Washegari karfe goma na safe aka daura auren Attahir AbdulHadi da amaryarsa Nawal Ahmad akan sadaki naira dubu hamsin. Ko zama basuyi ba aka dunguma zuwa garin Tariwa.

Wani masallaci da Mal.Fatihu bai san dashi ba kafin ya bar garin babba nan aka taru. Duk yadda yaso ya daure sai da yayi kukan farinciki.

Maigari Muhammadu shine ya tsaya waliyin amarya yayin da ko ba'a fada ba Prof Abdulhadi shine waliyin ango. Bayan addu'o'i dimbin jama'a masoya da 'yan ganin kwaf suka shaida daurin auren DAHIRU ISHAK da MAWADDA FATIHU akan sadaki naira dubu dari lakadan wanda Baba Prof ya zaro daga aljihunsa batare da yabi ta kan kudin da Bilya yake kokarin mika masa ba dubu hamsin.

Dahiru hularsa ya janyo ya rufe fuska saboda da gaske kuka yake son yi. Lallai a duniya idan ka sami mai sonka domin Allah Kada ka yar dashi domin kauna ta fisabilillah ba kasafai ake samu ba.

Shi kuwa Prof Abdulhadi jama'ar da ya gani da zantukan da ya ji a waje ana cewa yarinyar nan ce da aka koresu. Yasan labarinta wurin Dahiru daga baya yaji yana sha'awar kara mata kima a idanun mutanen.

Maza dai basu wani dade ba saboda kada su makara yau za'a kai amare. Su Inna kuwa ana can ana taro gida da makota an cika makil abin sai son barka.
*****

Motoci hudu BB ya samo shi da abokansa 'yan duniya suka tafi gidansu Mawadda tare da Danmani. Motar da tafi kyau wadda a cikinta wani abokinsa ke tukawa yana gefe ita suke sa ran daukota a ciki. Sun gama shewarsu da iface-iface a gida wai yau BB yake ango.

Cikin jerin motocin daukar amarya suka shige abinsu suna jiran fitowarta bayan gama tsare-tsaren yadda zasuyi ko da lamari ya kwabe.

Ana idar da magariba akace su fito. Kuka Mawadda take yi kamar idanunta zasu fito tana manne da jikin su Iya an kasa bambareta. Kowa haka yayi kafin ya bar gida da kyar sai da Ade ta dake ta soma fada aka fito da ita. Atampa ce a jikinta riga da zani tayi matukar kyau sai katon mayafi an lullubeta ko fuska ba'a gani.

Suna fitowa guda cikin abokan BB yayi saurin zuwa inda Yaya da matar kanin Ade suka sakota a tsakiya yace ga motar daukar amaryar can. Waige suka fara suna neman Gwaggonin Dahiru uku da suke cikin gidan. Wadda ta fara fitowa ta kalli yaron tace kaine Attahiru yace a'a  bai sami zuwa ba, ba don yasan waye Attahir din ba. Matar tayi dariya tace suje su shiga tunda akwai namiji a gaban tayi musu kadan motar. Ta cigaba da cewa dama ta fada da wuya su iya zuwa daukan amaren juna ana hada hadar biki. Motocin duka a layi suke harda ainihin na wasu abokan angon da ma Danlami a cikin motar Bilya shiyasa basu kawo komai ba ta tsakiyar suka je suka shiga wadda aka bude musu.

Zamansu ke da wuya Attahir ya shigo layin ta baya ya ajiye motarsa daidai kofar gidan yadda ba sai amarya tayi doguwar tafiya ba.

Su BB kuwa bukata na biya dama yawancin motocin duk an gama shiga kawai suka tada motoci suka shiga cin taya suna tada kura. Kan kace kwabo sun fice daga layin a guje.

Kowa yayi zaton sun fara gaba ne nan fa akayi ta shiga mota ana tafiya. Attahir yana tsayawa ya tura a yi masa magana da daya daga cikin iyayen Dahiru. Anyi sa'a ta dazu ce kanwar Mal Isiyaku.

"Kaine Attahirun?"

"Eh Gwaggo, Dahiru ya fada miki a motata zamu tafi da amaryar ko?"

Tayi shiru sai kuma tace "ya fada amma yanzu wani abokinku yace wata lalura ta hanaka zuwa kace yazo ya dauketa. Ko minti biyar basuyi da tafiya ba"

Me kenan yace a ransa yana tunanin waye wannan. Bai bata lokaci ba ya kira Dahiru ya dauka yana dariya "sarkin zumudi gata nan sun fito da ita yanzu zamu taho. Ka dauko min tawa?"

Gaban Attahir ya fadi ya tabbata Dahiru bai  turo kowa ba kenan ya daure yace "yanzu na iso"

Cike da murna Dahiru yace "nagode Dan uwanmu Attahiru angon Nawal"

Kashe wayar yayi jikinsa gabadaya yaji yayi matukar sanyi. Mota ya koma yace bari ya dan kara lokaci ya tabbatar kada ya tayar musu hankali a banza.
******

Sunyi tafiya mai dan nisa dreban da yake jan su Mawadda ya kira daya daga cikin na bayansu wanda suke tare yace sunyi faci ya kira sauran su jira su.

Su Yaya a tunaninsu duk 'yan daukar amaryar tare suke. Nan kuwa plan ne. Motoci hudun nasu duk suka tsaya. Sauran idan sun tsaya sai suce suyi gaba. Sai da ya rage su kadai kowane dreba banda nasu Mawadda suka fadawa matan da suka debo wai kwatancen kuskure akayi musu ba amaryarsu suka dauko ba. Su unguwar Diga zasu ce jen gaban zawaciki sai suka zaci tunga aka ce. Mata rai a bace balle da suka nuna bazasu mayar dasu ba. Haka suka sassauka suna ta mita su kuwa suka yi gaba. Yaya ce ta kula babu motocin suna ta tafiya an bar mata. Saboda su biyun sun fito don a cire taya dreban yace amarya tayi zamanta a ciki.

"Ya haka abokanku suke bar mana 'ya'ya a titi?" Tace tana lekawa gaban motar inda ta kula mutumin ciki ko kala bai ce ba.

Dago kai yayi ya kalleta yayi wani murmushin mugunta "ku ma sai ku nemi mota ku kara gaba. Kai Bobo zo mu ware"

Cikin Mawadda ne yayi wani mahaukacin kara saboda komai dadewar lokaci tasan bazata taba manta muryar BB ba. Ta mika hannu ta bude kofa Bobo dreba ya danna lock yayin da su Yaya suka soma ihu suna kallo ya figi mota suka yi gaba.

Innalillahi Yaya take ta maimaitawa jikinta tamkar mazari ta shiga firgicin sake ganin wannan yaro da ya tarwatsa musu rayuwa. Sauran matan suka nufosu jin tana kuka tace an sace amarya.

******

Attahir kasa zama yayi  ganin motocin sun gama tafiya. Wata yarinya ya tura ciki yace yana son magana da Ade don ya tabbatar tana gida.

Jin ance Attahir ta taso da sauri ta same shi a bakin kofa rike da hula. Baya son firgitasu da abinda babu tabbas sai dai hankalinsa yaki kwanciya. Duk abokansu da zai tambaya game da daukar Mawadda kowa yace ba motarsa ta shiga ba.

"Attahir yaya akayi, naji ance kaine mai daukar amarya.

Kai ya dukar yace "Ade wallahi bani bane na dauketa. Nazo ance sun tafi "

Maganarsa bata gama shigarta ba suka ji kukan Bilki tana kiran Ade. Ita dama babu ita a 'yan kai amarya saboda faduwar da tayi ga jikin kiba tana ta dingisa kafa.

Ade ta ruga ciki a guje Attahir ma baiyi wata wata ba yabi bayanta.

Kuka take sosai tana fadawa Ade dasu Iya wayar da ta gama da Yaya.

"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN"

Suka ce a tare sai ga Ade ta fasa ihu tana kuka iya karfinta. Ba karamin so take yiwa Mawadda ba sai dai kara da kunyar 'yar fari yasa take boyewa. Amma tun da akayi mata fyade ta ajiye abubuwa da dama ta jawo 'yarta jikinta.

Innar Fatihu tace ba kuka zata yi ba a kirawo Baba. Cikin dan lokaci ya shigo dama yana masallaci suna hira da abokan arziki.

Gida fa ya rude gabadaya sai koke-koke. Attahir ya rasa inda zai sa kansa. Baba ne yayi ta maza yace su wuce ya kaishi can gidan nasu inda za'a kai Mawadda. Gara su tabbatar basu je ba kafin a tayar da hankalin kowa.

Ade najin haka ta tashi "wallahi nima sai naje"

Inna da Iya ma suka ce zasu. Attahir yace duk su fito. Bilki aka bari da kalilan cikin 'yan biki sai yaransu.

******

An shige da amarya Nawal ciki Dahiru ya janye motarsa gefe yana duban hanya. Ya sani nan da 'yan mintuna Attahir zai shigo masa da Mawadda. Murmushi ne ya kufce masa shi kadai yana hango anjima shi da Mawaddatan wa Rahma.

Zance har ya fara isowa nan yana mota yana tsarawa Mawadda text bai sani ba. Gilmawar motar Attahir ya gani ta shigo fargajiyar gidan a guje. Fitowa yayi a ransa yana cewa sai yaja masa kunne tunda yayi gudu da ita.

Tsayawa yayi gabansa yana wani irin matsanancin bugu saboda ganin Baba, Ade, Iya da Inna sun fito daga motar Attahir din.

Ya soma takowa zuwa garesu ya ga Yaya da wasu mata biyu sun shigo a adaidaita sahun da Attahir ya yiwa kwatancen gidan ta wayarta.

Haj Mama ya gani ta fito da dankwali a hannu bai san me suke cewa ba ya ga ta riko Ade wadda ta sake zube musu a kasa tana kuka Yaya tana rungume da ita suna yi tare.

"Babu lafiya" ya furta cikin wata irin murya mai ban tausayi da taba zuciya a lokaci guda yana runtse idanuwansa.
[31/01 9:36 am] Batuul Mamman: *GUMIN HALAK...*💰20

*Batul Mamman*💖



Dahiru ya fara tafiya zuwa garesu kawai yaji zuciyarsa bata da karfin daukar ko ma menene ya faru. Juyawa yayi abinsa ya shige mota ya tayar zai fita daga gidan.

Attahir ne ya fara hango shi ya shiga kiran wayarsa yaki dauka. Hannunsa har rawa yake ya kira maigadinsu yace yayi maza ya rufe gate da sauri. Maigadi ya cika umarni daidai isowar Dahiru bakin gate din yana ce masa ya bude masa. Sai dai yana magana zaka gane muryarsa bata tsayawa ma rawa take yi ya karaya sosai.

A guje Attahir ya iso gareshi "fito mu koma ciki Dahiru"

"Ku kyaleni don Allah, ku barni na tafi Attahir bani da lafiya" ya dago kai suka hada ido kawai sai ga hawaye yana zirarowa daga idanunsa.

Ba karamin tausayi ya bashi bawa Attahir ba yasa hannu ya bude motar ya janyo shi yana nuna masa su Ade "ka duba halin da mahaifiyarta take ciki Dahiru they need you now more than ever."

Daurewa yayi kafin zuciyarsa ta buga yace "me ya sameta?"

"Mu shiga ciki zaka ji komai" ya fada yana jan hannunsa.

Wani katon falo suka shige dukkaninsu. Dahiru iyakarsa kofa yana jin kamar ya fita kada yaji.

Baba Prof da Baba sune manya a maza sai su Iya da kuma iyaye mata.

Yaya ce ta fada musu yadda abin ya kasance daga fitowarsu kawo amarya.

Naushi Dahiru ya kaiwa bango da hannunsa mai targaden da bai gama warkewa ba jikinsa yana tsuma kamar wadda zashi filin daga. Zuciyarsa ce take zafi kamar zata tarwatsa kirjinsa ta fito. A karo na biyu wannan matsiyacin ya sake shiga tsakaninsa da Mawadda. Fita daga gidan zaiyi ya nemo ta duk inda take. Idonsa idon mutumin nan baya jin zai iya barin shi da rai.

Baba yaji yace "Dahiru ina zaka je?"

Murya a dake yace "neman Mawadda"

Baba Prof da kansa yaje ya dawo dashi ciki ya zaunar dashi a gabansa.

"Wannan al'amari ba karami bane amma duk da haka kada muyi garaje. Idan ka fita kasan ta ina zaka fara nemanta? Hukuma zamu sanar sannan mu dage da addu'a Allah Ya tsare mana ita"

Zaman me zaiyi har sai 'yan sanda sun iso. Sake tashi yayi kawai cikin zafin nama "Baba banki taku ba amma suyi nasu nima nayi nawa. Wallahi bazan iya zama ina jiran sai ranar da 'yan sanda su ka ganta ba. Idan yana tunanin yaci galaba akaina ya dauketa ni rayuwarsa zan karar sai dai nima a kasheni"

"Ka dawo ka zauna Dahiru mu bi komai a sannu" Innar Fatihu tace tana hawaye.

Ade da Yaya ya sake kallo yadda suka fita hayyacinsu kawai ya fita daga falon ransa yana kuna. Yana ji ana kiransa ko waige baiyi ba. Ya kusa mota Attahir ya cimmasa a guje.

"Bude mota Dahiru Ade is unconcious" yace yana juyawa da gudu.

"La haula wala quwwata ila billah" ya rike kansa da yake zugi ya bude motar da sauri.

Saifullahi da Marwanu ne suka riko Ade bata san inda kanta yake ba. Gidan ya kaure da koke-koken mata. Danlami da yake gidan ake wannan hatsaniya tuni ya kira iyayensu sun kamo hanya a daren.

A bayan motarsa aka sakata. Baba Prof yace Attahir ya tuka kada a kuskura abar Dahiru yaja mota.

Dahiru yana gaba Ade, Yaya da Marwanu a baya. Sai motoci biyu na bayansu wadanda su Baba suke binsu a baya. Asibitin Dr Tani yace su je banda rashin nisa sosai yana ganin ita zata fi fahimtar halin da Ade take ciki tunda har yanzu a cikinsa take ita ma.

******

Dr Tani tana tsaye a reception din asibitin tare da kusan duka ma'aikatanta harda masu shara da goge-goge. Ranta a bace yake ta dora hannunta akan kafadar Qareeba da take zaune akan wheelchair tana ta sharbar kuka.

"Kiyi shiru haka nan Qareeba ki nuna min waye a cikinsu yayi maganar?"

Qareeba kuka ya ci karfinta ta kasa kallon mutanen gabadaya. Dr Tani ta daga yatsa tana nuna su daya bayan daya daga likitoci zuwa kananan ma'aikata.

"Gabadayanku babu wanda bazan iya kora ba kun san haka ba tun yau ba. Yarinyar nan a gabanku aka kawota kowa ya sani duka ne kadai aka yi mata wanda ya janyo mata surgery har biyu. A wane dalili ne zaku rinka yawo da magana kaf clinic dinnan kowa cewa yake yi raping dinta aka yi"

Wani nurse ne da Qareeba ta taba yiwa haukanta a gaban maman budurwarsa tazo asibitin ta jefa shi cikin muguwar kunya ya kekashe idanu yace "Doctor sai dai fa ayi hakuri kowa ya sani case din rape ne ake ta wani rufa-rufa. Nasan dani ake saboda Qareeba taji lokacin da nake bada labari"

Wasu cikinsu harda dariya suna yi kasa-kasa ran Dr Tani in yayi dubu ya baci. Likitoci biyu da suka duba Qareeba lokacin ta kalla mace da namiji da shi ma nurse din tace.

"You are fired! Ni zaku ci wa amana ku batawa yarinyata suna ta rasa miji"

Mamaki ya kamasu domin ko kadan su likitocin basu su ka fitar da zancen ba. Namijin ya cire whitecoat dinsa ya bugata da kasa.

"Asibitin ma da kike yin kudi da guminmu amma kin kasa biyanmu halak dinmu yadda ya kamata? Meye bama yi domin cigabansa amma albashinmu bai taka kara ya karya ba. Mtswwww" ya juya a fusace.

Cikin kankanin lokaci wurin ya kaure da surutu. Da gangan ma saboda samun dama da yawansu suka yi ta cewa anyi fyaden kuma magana yanzu suka fara. Kusan mutum hudu ta kora daga aiki harda kukanta ta gurgura Qareeba dakinta.

Asibitin ko ina maganganu ke tashi hatta dakunan patients. Gashi ta kori likitoci biyun da suke on call a lokacin shiyasa komai ita ake kira.

Su Dahiru sun iso asibitin dukkansu suka shiga reception suna kiran azo a taimakawa Ade. Dr Tani kai ya dau chaji kamar zata zare gashi yau mutane da dama ake ta kawowa.

Da gudu gudu ta sauko ance mata emergency idonta ya sauka akan Dahiru. Sakin fuska tayi kamar ba ita ba.

"Dana daga ina haka ba yau ake kawo amarya ba? Ko ka biyo ganin Qareeba ne"

Ade ya nuna mata batare da ya amsa ba "ki duba mamana faduwa tayi har yanzu bata farfado ba"

Matsowa tayi da sauri ta nuna daki aka kaita aka kwantar. Ta duka kanta tana tambayar me ya sameta Iya ta rike mata hannu tana kare mata kallo "DaftaTani?"

Dr Tani ta gyada kai ta dago ta kalli Iya kamar ta san fuskar nan.

Bata yi aune ba taji an shako wuyanta ta baya. Tana juyawa Yaya ta watsa mata yatsu biyar ta rike kumatu a gigice. Baba bai ce komai ba haka Inna domin sun ganeta suma.

Dakin yayi tsit suna mamakin wannan abu. Dahiru Yaya ta kalla idanu rufe da bacin rai
"mu bar asibitin nan tun kafin Sa'ade ta farfafo ta sake sumewa saboda bakinciki"

Cikin tsananin mamaki yace "Yaya kun santa ne?"

Baba ne ya nunata "Dahiru wannan matar ita ce ta bada shaidar karya a kotu aka saki yaron nan gashi yau a karo na biyu ya sace Mawadda a ranar aurenta"

Dr Tani tayi mugun kaduwa. Iyayen Mawadda ne yarinyar da ta canja duka evidence dinsu na asibiti karshe aka kori karar BB.

Hayaniya ta tayar da Ade abin mamaki Dr Tani ta gani a kusa da gadon. Da sauri ta tashi tana zubar hawaye ta gama jin me suke cewa tace
"Karasani ki ka zo yi yadda ki ka watsa mana rayuwa shekarun baya? Ku kaini gida gara na mutu da ta tabani"

Bacin ran Dahiru bazai misaltu ba. Idanunsa tamkar gauta sun kara kankancewa. Wani mugun kallo yake yiwa Dr Tani wanda ya karasa razana ta soma ja da baya don a ganinta wannan kallon nasa kadai ya fassara mata zai iya karar da numfashinta a duniya batare da yayi nadama ba.

"Dahiru ka tuna zaman da muka yi a baya kayi hakuri ban san kuna da alaka ba. Ka gani yadda nima yazo ya yiwa 'yar uwarka Qareeba"

Fuska babu alamun annuri yace "kina nufin mutumin da na hana ya yiwa 'yarki fyade shine wanda ya yiwa matata a shekarun baya?"

Ta zaro ido "matarka kuma?"

"Mawadda nake nufi ko kin manta sunanta yadda kika manta cutar da kika yi mata da iyayenta?"

Jikinta yayi mugun sanyi ta gyada kai. Dahiru kamar ya zare haka yake ji a wannan lokacin. Kusan kowa a dakin tsoron yanayinsa yake ji.

"Ban taba nadamar taimako ba musamman idan musulmi na yiwa. Amma a yau Dr Tani nayi, naji a raina ina ma ban je gidanki ba a wannan ranar yadda ya dandanawa Mawadda bakinciki inama ya yiwa taki 'yar kiji yadda su Ade suka ji. Kina babbar makiyata ace nayi zaman aiki a gidanki...Ya Allah" wasu zafafan hawaye ya goge.

Attahir ya yunkura ya riko hannunsa ya kwace da karfi ya daga zai mareta.

Tsawar Baba Prof ce ta dakatar dashi "DAHIRU!!! Bamuyi maka wannan tarbiyar ba kada ka yarda ka daki matar wani"

Sauke hannunsa yayi zuciya na tafasa ya sake matsawa daf da ita har lokacin ta kasa magana sai faduwar gaba.

"A yau na auri Mawadda kuma a yau BB din da ya kusa yiwa taki 'yar fyade ya saceta bayan abinda yayi mata 8 years ago. Kiyi addu'a Tani, ki tsananta addu'a domin ni Dahiru Ishak nayi miki alkawari idan ya kuskura ya sake maimaita kusantar iyalina wallahi babu wanda ya isa ya hanani mayar da tsinannan asibitin nan naki toka kinji na fada miki. Sai na kona shi da duk wanda ya rage a cikinsa" ya kare maganar da kada yatsunsa biyu a gaban fuskarta suka yi kara.

Durkushewa tayi a kasa ta hada hannuwanta biyu "don...."

Attahir ya yatsina fuska ya kada mata yatsa "kada ki bata bakinki babu wanda zai yafe miki. If I were you zan sallami duk wanda yake asibitin nan don na san dan uwana baya magana biyu."

Tare suka fice da Dahiru iyayensu suna kallonsu sun kasa yi musu magana. A jikin bango Dahiru ya ga Qareeba tana wani irin kuka saboda sai a yau komai ya warware mata. Mummynta tayi karya ne kawai don tayi aure. Ko kallo bata ishe shi ba ya wuce ga wani bala'in zugi da hannun damansa yake yi saboda targadensa da ya fama.

*****

BB da abokansa suna ta sheke ayarsu sun yi biris da Mawadda da take bugun kofar iyaka karfinta kamar zata ballata. Kuka take yi haikan tana hadashi da Allah ya duba darajar aure ya saketa ta tafi.

Tafi awa daya tana bugu tun tana roko har ta koma fada da nasihar yaji tsoron Allah.

Gajiya tayi ta koma bakin taga ta leka. Karfe ne ta waje ko ta sauke glass din babu damar fita. Bata ma san wace unguwa bace saboda a hanya rudewa tayi tana ta buge bugen kofa da magiya bata kallon ina suke bi. Ta dai kula wurin akwai karancin gidaje sai filaye da kango.

Iyayenta da Dahiru take tunani tana kara kuka. Ta san duk inda suke hankalinsu ba a kwance yake ba. Gashi tun a hanya su ka karbe mata jaka. Da suka iso ya zagaya zai daukota tace ya barta zata shiga da kanta. Banda tsoronsa da ya gama mamayeta tana kyamar ya tabata da kazantarsa tana matar Dahiru.

Kofar taji ana tabawa bugun zuciyarta ya karu.

BB ne ya shigo yasha wanka harda gyaran fuska ga shadda da hula yana ta kamshi. Ledar hannunsa yaje gabanta ya ajiye ta matsa baya da sauri ta sake mannewa da bango.

Murmushin gefen baki yayi mata "wai duk amarya sai ta yi pretending tana tsoron miji ne? Ni fa na sani kuna so tsabar gulma ce kawai ace muku nagari"

Bata ce masa komai ba ya dauko ledar ya bude kaza ce a ciki tana tiriri da kamshi.

"Ga fa abin arziki kazar amarci matso mu ci tun da zafinta"

"Ko maita nake yi bazan ci abin hannunka ba ko da yunwa zata kasheni"

Ya kada kafada "suit yourself" ya fara ci kamar shine mayen.

Bayan ya gama ya dauko juice a cikin fridge dake dakin ya tsiyaya a kofi ya haye gado yana sha.

Ran Mawadda ya soma baci ta yarda BB mahaukacin gaske ne da taji yace "amaryata yau fa daren farko me ki ka tanadar min?"

Neman makami take yi ido rufe bata samu ba yana kallonta ta gama dube dubenta ta gaji ta dawo tsakiyar dakin ta durkusa gwiwoyi a kasa "don Allah ka taimaka ka barni na tafi gida. Me nayi maka haka da zafi ka kasa hakura har kake bibiyata?"

Dariya yayi yana buga kafa "ashe zaki saduda my baby. Sonki nake yi amma saboda kwarewa wurin cin amana ki ka auri wani ba ni ba. Ga sadakinki nan ki dauka a waccan drawer din domin nima na aureki daga yau. Ki kwantar da hankalinki mu zauna lafiya"

"Baka da hankali ne?" Tace cikin daga murya.

"Kin tafi dashi kin barni da dakon sonki a raina. Mawadda ki karbeni a matsayin miji zan rike ki da gaskiya"

Me kuma zata ce masa tunda alamu sun nuna bashi da hankali ko kadan.

Tashi yayi ya fita bai dade ba sai gashi da kayan bacci.
"Daga ni sai ke muka rage amaryata kowa ya tafi yau an bar mana gidan kiyi wanka don yau ranarmu ce."

Bata yi masa musu ba ta karbi kayan ta shige bandakin. Rufe kofar tayi da mukulli ta zame a kasa ta rizgar kuka. Burinta ta bude ido ta ga Dahiru a gabanta. Tana nan zaune sama da rabin awa taji BB ya soma bugawa yana cewa ta bude.

Da farko kamar lallami ya fara sai gashi ya rikide yana zaginta ta uwa ta uba yana cewa hakurinsa ya kare.

Rasa wurin buya tayi ta gama tsorata tana jin numfashinta kamar zai dauke. Robar watsa ruwa ta dauko ta tsaya daga gefen kofar yana budewa ta rafka masa a kansa iya karfinta ta fita a guje tayi sa'a dakin a bude yake.

Kofar gidan an garkame ta kasa budewa ya biyo bayanta yana kiranta. Kitchen ta hango ta shiga babu kayan kirki a ciki da sauri ta rinka jan drawers tayi sa'ar dauko wuka.

BB ya shigo daga bakin kofa ya tsaya "kinsan bani da kyau Mawadda. Ki ajiye wannan haukan mu zauna lafiya kafin na tuna miki da waye BB."

Wukar ta saita a wuyanta har yanzu tana kuka amma kokari take ta dake zuciyarta domin idan tsoro yayi galaba ta suma shikenan zai sami yadda yake so "da ka tabani BB gara na kashe kaina"

A karo na farko da yaji tsoro kenan. Duk wahalar da yasha meye ribarsa idan ta mutu.

Ja yayi da baya "ajiye wukar kizo muyi magana. Ga wayarki nan" ya fito da wayar daga aljihunsa sannan yace "kizo ki kira ko ma wa zaki kira don baki isa na kaiki gida ba"

Jiki na rawa ta yar da wukar sannan ta taho bakin kofar ta mika hannu "bani"

Cafkota yayi yana kokarin hadata da jikinsa ta suka soma kokawa yana shirin fara yi mata muguntarsa ta duka ta dage ta kai masa wani naushin hauka a kasan mararsa sai gashi ya saketa ba shiri yana kurma ihu kamar mahaukaci. Wayarta ta dauke ta koma dakin ta rufe tana numfarfashi.
*****

Su Baffa sun iso daga Tariwa gidan Mal.Fatihu ya cika da 'yan jaje kamar ba dare ba. Dahiru da Attahir suna kofar gidan a mota bayan sun gama magana da 'yan sandan da suka zo.

Hannunsa da ya soma kumbura Attahir ya kalla "don Allah ka amince muje a gyara hannun nan kaga har ya fara kumburi"

"Ka barshi baya min ciwo"

"To idan ba'a gyara ba  me zaka dauki 'Yar uwarmu idan ta dawo? Kada kace min da kafarta zata hau saman nan kana biye da ita"

Murmushi Dahiru yayi "nagode Attahir"

"Da me?"

"Komai ma, amma ka tafi wurin Nawal don Allah"

Daure fuska Attahir yayi "iyakar amintar tamu kenan Dahiru? Kana cikin wannan yanayin in shiga dakin amarya inyi me?"

Marwanu ne ya kwankwansa gilas din motar yace su shigo ciki akwai baki.

Da su ka shiga Dr Tani ce tare da mijinta da Qareeba da bata iya tafiya sosai sai an riketa. Ko zama Dahiru baiyi ba ya fita abinsa. Tana kuka ta shiga basu hakuri har take nuna musu Qareeba da labarin abin da BB yayi mata.

"Kinsan ance komai nisan jifa kasa zai fado. A da baki damu da halin da wannan iyali zasu shiga ba da abinda kika yi musu. Sai dai gashi tun a duniya kina ganin sakayya" cewar Baffa

Dr Auwal ya tayata basu hakuri da basu taimako wurin neman 'yarsu domin su ma neman BB din suke.
******

Loba boy ya sami wani gefe ya tsaya ya kira Garwashi.

"Oga hasashenka fa ya zama true"

Garwashi ya ture yarinyar da ke kusa dashi a wani club a Kaduna ya matsa gefe.

"Ina sauraronka me Danmani yake yi?"

Kwanaki biyu da suka wuce kafin Garwashi ya koma Kaduna ya ga Danmani da sabuwar waya. Yana tambayarsa sai cewa yayi cikin kudin da suka raba ya siyo. Garwashi ya karba yana gani shi kuma Danmani shaf ya manta da hotunan Mawadda da ya daukowa BB. Batare da nuna fushi ba yayi saurin rufe folder din hotunan ya cigaba da dube dube amma zuciyarsa ta bashi babban yaron nasa ya ha'incesu ne shiyasa da duka suka yi shirin komawa Kaduna yace yana da uzuri sai Garwashi ya rabu dashi amma ya bar Loba boy yana binsa a boye.

Shi Loba boy ya jima yana harin mukamin Danmani yana son zama na hannun dama sai yanzu dama tazo.

Garwashi ya gama jin bayaninsa na satar amarya ya kutuntuma ashar "kai baka wurin nace zamu yi mata solidarity saboda 'yar uwa ce 'yar Kano ce?"

Loba boy an sami yadda ake so zai ture gwamnatin Danmani yace "Oga alakar tafi haka ma. Sai da abin ya faru na gane ashe dangin matar kawuna ce"

"Bana son shafta Loba boy. Ita da suke Bebeji kai kuma Dawakin kudu?"

"Oga ashe baka sani ba Bebejin daga jikin Dawakin kudu aka yanketa lokacin mulkin sojoji"

Garwashi rai ya baci kuwa jin haka yace "kace dai wannan rigimarmu ce ta famili  lallai Danmani don wulakanci abin kuma harda tabo gida"

Loba boy ya cigaba da ingiza shi yace kada yayi komai gobe da sassafe zasu taho Kano.
******

Sun cika alkawari kuwa domin karfe goma da rabi ma a garin Kano tayi musu. Zama suka yi kamar wasu 'yan sanda suka gama tsara yadda zasu  sulala Danmani kamar tafasasshen nama.

******

Yadda Mawadda bata runtsa ba haka su Dahiru suka kwana tare da iyayenta. Gari na wayewa suka koma ofishin 'yan sanda aka sanar dasu ana bincike sosai su cigaba da addu'a.

Hannun Dahiru ya kumbura Baba da kansa ya nemi mai gyara aka matsa matsa ya shigo ciki lokacin ya matsawa Attahir shima ya tafi gidan Baba Prof ganin Nawal.

An gama gyaran Attahir ya dawo yaci karo dasu Garwashi a kofar gidan. Wai saboda kada ace musu 'yan daba shine duka su biyar suka sako manyan kaya burum burum kamar wasu barayi.

Hannu Garwashi ya mikawa Attahir suka gaisa yace sun kawo taimako ne suna bukatar izinin ganin iyayen amaryar da aka sace ko babanta.

Attahir ya hade rai "kun zo damfara dai to ayi gaba mun yafe"

Garwashi ya rage murya yace sun zo da bayani ne akan BB. Janyo shi Attahir yayi suka yi ciki sauran na biye dasu.

Baffa yace "wadannan fa?"

Garwashi yace yana so a rage jama'a ko su sami wuri da zasuyi magana babu takurawa domin aikinsu na bukatar sirri. Ba don sun yarda ba sai don ganin Dahiru ya tada hankalinsa yace a sauraresu suka tashi suka koma dan falon nan. Wuri ya cunkushe Attahir yace ko zasu koma gidansu ne tunda Garwashi yace baya son hayaniya a bakin aikinsa. Mamaki suke yi amma ga dukkan alamu dai bai yi kama da irin malaman bogin nan ba. Rankayawa suka yi gidan Baba Prof aka zubawa su Garwashi idanu.

Dariya yayi ya soma musu bayanin kansu da haduwarsu da BB da kuma sa hannun Danmani da suke zargi.

"Zamu taimaka saboda munyi alkawarin solidarity ga 'yar uwa. Kuma ashe ma dangin matar kawun wannan ce ta wajen kakarta mace ko? " ya nuna Loba boy.

Inna da Iya suka kalli juna. Iya tace "ko kece naga kamar yana da billenku?"

Innar Fatihu ta rufe billenta da sauri "meye haka ne TaRasulu?"

Baba Prof yace sun basu dama amma idan suka ga ranin wayo su shirya zasu damka su wurin 'yan sanda ne.

Garwashi ya dubi wani yaronsa ya ce masa fara.

Yaron ya bukaci shiru banda ko da tari ne sannan ya kunna wayarsa ya bude recorder ya karkace kai sai gashi ya fara muryar Nasiru Salisu Zango

_"a yau ne kuma majiyar inda ranka take dauke da labari mai cike da al'ajabi inda iftila'i ya afkawa wata amarya. Amaryar dai wadda danginta suka bukaci a sakaya sunanta wasu bata gari ne suka  yi sama da fadi da ita kamar allura an nemeta an rasa a cikin zugar kai amarya. Yanzu haka iyayenta da sabon ango suna cikin gagari suna rokon duk wanda yake da wani bayani da zai taimaka wurin ganota ya nemesu ta wannan lambar waya da zan bayar. Angon harda alkawarin kyauta mai tsoka ga wanda ya sada shi da amaryarsa. Ga dai yadda mukayi da angon"_

Matashin da baifi shekaru ashirin da shida ba ya sake karkata ya kyabe fuska kamar mai kuka sai ha murya ta fito a raunane

_Don Allah ko waye ya dauketa kada ku cutar min da mata. idan kudi kuke so zan bada miliyan daya da rabi ga duk wanda ya taimaka ko yaya ne_

Daga nan ya sake komawa muryar Zango _"to Allah shi kyauta amma ga dukkan alamu lokaci yayi da za'a fara daukar rijistar masu zuwa daukar amarya."_

Kusan kowa sakin baki yayi bayan yaron ya gama Garwashi ya kira Danmani yasa wayar a speaker. Dahiru da Baba suka matso kusa yayi musu alama da suyi shiru.

"Oga ya kana lafiya?"

"Kai Danmani kana Kano abu irin wannan ya faru baka fada mana ba sai wani ne cikin abokai na yace yasan ina da network ya turo min rakodin din"

Danmani ya dan tsorata "ban gane ba Oga"

Garwashi ya rage murya "kaga yanzu nake ji an sace wata amarya jiya angon yayi alkawarin miliyan daya da rabi. To nafi son muyi aikin nan mu biyu a kyale su Loba boy yadda kake ta bani shawara"

Tashi Danmani yayi jiki na bari bayan Garwashi ya kunna recording din da ya manna da wayarsa ya gama ji. Yace masa "ance Kano ta rude mutumina kowa na son nemota, ni kaina sammako nayo na shigo gari kazo mu hau aiki"

Danmani mayen kudi wanda shine babban lagonsa yace "Oga ina jin fa mutumin nan BB ne ya sace matar da ya tura mu aiki a kanta. Haka kawai hankalina bai kwanta dashi ba bayan ya bamu kudin nan har gidan da yake nabi bayansa rannan. To amma daga baya na share. Kana ina ne mu hadu sai mu nemi angon. Sai dai banji lambar wayar ba"

Garwashi yayi murmushin saurin kama Danmani "bari naje gidansu mu tabbatar sai na sameka a cikin gari mu wuce"

Babu wani dogon tunani Danmani ya amince. Shi akan kudi dama kansa toshewa yake. Dahiru ne ya bawa kowa mamaki da yazo ya rungume Garwashi yana masa godiya tun ba'a ganta ba. Jiran minti shabiyar suka yi bayan anyi notifying 'yan sanda amma basu sanar dasu su waye Garwashi ba domin sunyi musu halacci.

Danmani doki ya hana shi sakat ya kira Garwashi yace su hadu  a hanya. 'Yan sanda suka yi basaja akayi akayi Dahiru ya zauna ba'a sani ba ko suna da makamai ya dage sai yaje.
*****

BB yayi kwanan izaya don ya daku fiye da tunaninsa. Gumi yake ta yarfewa a nan falon ya kwana a yashe. Mawadda tana daki tana kuka bayan tayi sallah. Wayarta ta kalla ta sake fashewa da wani kukan. Ashe fanko ce ya cire batir din.

Da kyar ya tashi ya rarrafa ya dauko wayarsa ya kira Bobo yace yazo ya kaishi asibiti. Sannan ya koma kofar dakin yana bugawa yace idan bata bude ba har ya bude da kansa zai bata mamaki.

Jikinta yana rawa tana tsoron kada ya bude ya sake maimaita abinda yayi mata ta danne kofar tana kuka. Wannan mutum ya zame mata masifa.

A waje kuma Garwashi da Danmani ne suka sauka daga babur din da Danmanin yazo dashi a kofar gidan. Daga bayansu batare da saninsa ba su Dahiru ne da 'yan sanda.

"Oga ko zaka bani lambar mijin nata na kira sai su taho. Jikina yana bani ita ce amaryar kuma tana gidan nan" Danmani yace cike da zumudi.

"Nima jikina ya bani dan ubanka" Garwashi ya shake masa wuya nan da nan su Dahiru suka fito.

'Yan sanda suka zagaye su Garwashi ya nuna Danmani "wannan ne dan daban da nake fada muku da hannunsa aka saceta yace tana gidan nan"

Danmani ya zaro idanu "Oga nine fa, karya yake shine shugabanmu"

Dahiru yayi murmushi ya ce da Inspector din "wannan dan agaji ne da ya taimaka mana"

Wani sergent ne ya ingiza Danmani cikin motarsu aka saka mai ankwa sai rantsuwa yake tare suke da Garwashi.

Gate din suka buga wani buzu ya bude a zatonsa abokan BB ne don ya san wane irin mutane yake yiwa gadi. Bude baki yayi zaiyi ihu Attahir ya toshe shi sannan shima 'yan sanda suka tura shi waje suka shiga.

Bugun farko a kofar BB yana daga kwance ya baje yana shan iska saboda azaba yace kofar a bude take.

Kamar daga sama ya ga 'yan sanda da su Dahiru sun shigo. Su Baba ma ashe sun biyo bayansu sai gasu ya tashi da sauri babu wurin gudu.

Kansa Dahiru yayi hannusa ya hana shi dukansa yadda yaso. BB yasan yau dai karyarsa ta kare bashi da sauran mafaka ya soma dariya "ka biyomu ne ka sami sudin da na rage maka? Jeka tana ciki jiya ta shayar dani soyayyar ban mamaki"

Wani kukan kura Dahiru yayi da hannunsa na hagu ya doki bakin BB sai ga hakora uku a take sun zubo. Ya kuma danne shi a kasa yana duka Attahir yana taya shi.

Inspector zai hana Garwashi yace "Yallabai ka auna ka gani idan matarka ce"

Su Dahiru sun yi masa mugun duka don ma 'yan sandan suna hana su tare da su Baba da Baffa.

Ligi-ligi aka daga shi baki na jini yace "wallahi nima sai an bi min hakkina"

Inspector din ya kalli abokan aikinsa "ku cikinku waye ya ga wanda ya cirewa mutumin nan hakora?"

Girgiza kai suka yi kowa yace bai kula ba. Garwashi yace shi ya gani tuntube yayi ya fadi.

Mawadda tana cikin daki a takure don bata jiyo su saboda gidan kato ne taji ana buga kofar dakin.

A tsorace tace "wallahi idan ka shigo zan kasheka nima na kashe kaina"

Dahiru yayi ajiyar zuciya ya dora hannu a jikin kofar ya jingina  "Mawaddatan wa Rahma"

Ji tayi kamar tana mafarki ta taho jikin kofar da gudu itama ta jingina "Yayanmu?"

"Matarmu!"

Wani kuka ta soma amma na farinciki ta bude kofar da saurinta.

Dahiru yana tsaye ta bude suka hada ido. Zukatansu ke bugawa da soyayyar da suke yiwa juna. Gani take yi kamar mafarki take Dahiru yazo cetonta.

A hankali ta tako gabansa tasa hannu ta shafa fuskarsa don kawai ta tabbatar ba gizo yake mata ba. Lumshe ido yayi yau ranar farko da hannun Mawadda ya taba jikinsa ya kama hannun ya sumbaci tsakiyarsa.

Rufe ido tayi wasu hawayen masu dumi suka gangaro tace "kaine?"

"Nine?"

"Ka tabbata ba mafarki nake ba?" Ta sake tambayarsa yana matsowa gabanta.

Ba tare da ya dauke idanu daga kanta ba yace "Mijin Mawadda ne a gaban Matar Dahiru"

Jikinta na rawa ta rasa da yadda zata kwatanta farincikinta Dahiru ya janyo hannunta "come here"

Yace yana rungumeta tsam a jikinsa. Kusan a tare suke sauke numfashi yana kara matseta a jikinsa. Samun kanta tayi da jin kunyarsa balle da ya dago habarta da yatsunsa biyu ya kusanto da kansa kasa yana kokarin hada lebensa da nata.

"To ya isa wallahi baka isa ba kuma" Attahir yace ya wani kanne ido daya yana kallonsu da daya idon.

Dahiru ya sake riko Mawadda ta barin hannunsa mai lafiya ta sa hannayenta ta rufe fuska ya harare shi "sa ido kowa yana falo meye na biyoni har nan"

"Gani nayi zaka wuceni. A ka'ida ni aka fara daurawa aure amma ko dan kiss dinnan na hakura dashi ina maka *_SOLIDARITY_* shine kai kuma zaka min solo. 'Yar uwarmu welcome back kinji muje daga waje wurin su Baba"
[31/01 9:36 am] Batuul Mamman: *GUMIN HALAK...*💰21

*Batul Mamman*💖



Sai da suka kusa kofar gidan Dahiru ya saki hannunta ba don yaso ba. Wurin Baba tayi a guje ta fad jikinsa tana kuka. Abinka da mutan karkara ga rashin sabo sai yayi ta sunne kai cikin kunyar su Baffa. Ita kuwa kuka take bilhaqqi. Ganin haka Baffa yace su shiga mota su koma gida domin ta sami nutsuwa.

BB suka ga an fito dashi yana tafiya da kyar ga fuska ta dame babu kyan gani. Da farko tsoro ya fara ji da aka tura shi cikin motar 'yan sandan. Sai daga baya da ya tuno mahaifiyarsa zata yi komai domin fito dashi yayi wani munafukin murmushi. Baya jin duk kudin da mutanen suke dashi sun kai mahaifinsa. Kudin mahaifinsa kuwa Hajiyarsa sai yadda tayi dashi.

Gabadaya suka dunguma zuwa gidan Baba Prof tunda kowa yana can. Daga waje aka tarbesu tsabar farinciki sun kasa jira a shigo da ita ciki. Yayyenta su Bilki da kanne su Saifullahi duka suna gidan ana kukan murna. Rafi'a ce kawai tun da akace an ganta Yaya tace ta tafi gida tayi girki mai rai da lafiya. Maman Nawal ma da Babanta ba'a barsu a baya ba.

Ba ko kunya Mawadda ta makale Ade bayan ta gama rungumar su Yaya da 'yan uwanta. Bata taba tunanin zata tsira daga sharrin BB da wuri haka ba. Bayan an zazzauna an sake jajantawa juna su Yaya suka ce gara su wuce gida da ita a samu tayi wanka taci abinci.

Haj Mama ta bata rai "Amarya fa tazo kenan sai dai ku yi hakuri zata kawo muku ziyara idan taji dama-dama nan da kamar sati guda. Nan za tayi wankan da cin abincin ko 'yata?" Ta kare da murmushi tana rike da hannun Mawadda.

Sunkuyar da kai tayi tana mai jin kunyarta. Dahiru na jin haka ya tashi yayi waje Attahir ya biyo bayanshi.

"Kaima fa ya kamata muje muyi wankan nan muci abinci"

Sai da ya harare shi yace "baka ji ba wai a nan zata zauna har sati, kila kai ba ka da matsala za'a baka matarka ku tafi"

Dariya Attahir ta rinka masa ya kuwa kara bashi haushi.

"Da nasan hakane dazu da na kyaleka kun dan..."

Kansa ya ga Dahiru yayi ya nuna masa hannunsa "yau fa kaine za ka ji jiki don ni kam hannu biyu gareni"

Dama sun saba da wasan bin juna tun farkon zuwan Dahiru gidan ya fahimci Attahir yana da tsokana. Kofa Dahirun ya nuna masa.

"Ko dai kaje ka fito min da matata ko kuma naje na janyota kuma ince kaine ka fada min ance nazo na janyota"

"Da gaske kake ko wasa"

"Ana wasa da angon da aka hana amaryarsa ne?"

Attahir ya kada kai "a'a"

"To ka taimakeni idan ba haka ba muje gidan a kasa wurinku zan kwana kasan mara lafiya sai da jinya" yace yana dariyar mugunta.

Attahir ya san ko bai kwana ba Dahiru zai iya zuwa ya zauna don kawai ya takura shi. Bata fuska yayi yace "na shiga uku inji mata. Yanzu me zan ce musu?"

"Oho ina nan" yace yana juyar da kansa gefe shima yana dariya.

A falo kuma bayan Haj Mama tace Mawadda zata kwana a gidan Baba Prof kallonta yayi ya dubi su Baffa "kunji halin mata wai a barta sati daya, mijin nata kuma fa? Mafi dacewa su dauki matansu su wuce gida Allah Ya bada zaman lafiya"

"Banda abinsu ma me ya rage kuma" inji Baffa.

Innar su Dahiru ta nuna itama tafi son a barta taje gida "yarinya duk wahalar da tasha ku barta taje taji dumin iyaye a kaita daga baya

Wata karamar muhawara suke neman yi 'ya'yansu suka tashi suka basu wuri.

Baba da kansa da ya kula zancen yaki karewa kowa na kawo dalilinsa yace ya amince ta bi mijinta babu damuwa.

Baba Prof yayi murmushi "Yauwa Mal Fatihu ka gama magana bari a kirawo su dai muyi musu nasihar da bata samu ba jiya su wuce"

Hamdala Attahir ya rinka yi da yaji an chanja shawarar ya kirawo Dahiru da Nawal dama Mawadda tana wurin.

Baffa da Baba duk wanda aka ce yayi magana sai yace ya barwa Baba Prof wannan huruminsa ne domin gabadayansu ya  mayar dasu tamkar 'yan uwansa har da Baba da bai dade da sani ba.

Godiya ya fara yi ga Allah SWT da Ya dawo musu da Mawadda lafiya sannan yayi musu nasiha akan zaman lafiya da juna da biyayya ga mazajensu. Matan ya kalla kowacce kai a kasa suna hawaye saboda nasihar tasa ta kashe musu jiki.
"Hadin kanku shine hadin kan mazajenku. Ku sani ku ba kishiyoyi bane sannan samun mazajenku ba daya ba saboda haka kada muji kada mu gani wai rigima ta tashi saboda kinga wance da zani naki mijin bai saya miki ba. Zama irin haka idan kuka tsarkake zukatanku yafi komai dadi ku zamewa juna 'yan uwa. Amma idan aka tsiro da kyashi da hassada wadda sukan bullo a rayuwar zaman tare to baza'a je ko ina ba gayyar zata watse. Allah Ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyiba. Kuma Allah Ya hada mana kawunanku"

Falo ya kaure da "AMIN"

Mawadda da Nawal suka kare kukansu suka yo waje tare da 'yan uwansu.

Attahir ya karbi mukullin motar Dahiru yace zai tuka su duka saboda hannunsa washegari zai dawo daukar tasa.

Nawal ta zaga zata shiga baya Attahir yace ta dawo gaba "mutumin nan hararata fa zaiyi ta yi yace na hanashi zama kusa da matarsa. Ki dawo gaba kawai"

Murmushi suka yi ita da Mawadda suka shige bayan yana ta magiya. Dahiru ya shiga gaba yana masa dariya "so kake ta biye maka ta zauna ka jefamu a rami ko?"

Suna tafe suna taba hira a tsakaninsu mazan don Mawadda da Nawal kowacce ta fada duniyar tunani da fargabar sabuwar rayuwar da zasu tunkara a yau.

Yaya ce ta kira Dahiru da wayar Saifullahi tace Marwanu zai kai musu abinci daga gidan Rafi'a kada su saka matansu girki. Godiya yayi mata ta sake tambayarsa yaya 'yarta babu matsala ko.

Murmushi yayi yace babu ko ya bata ne sai taji kunya tace a'a. Ba'a dade ba sai Ade ma ta kira itama dai so take taji yaya Mawadda take ya maimaita mata yadda suka yi da Yaya a kunyace ta ajiye wayar da yace zai bata itama.

Murmushi yayi yadda suke son 'yar tasu ya burge shi da irin zaman amanar dake tsakaninsu kamar ba kishiyoyi ba.

Layin gidan nasu kusan duka sababbin gidaje ne harda titi har kofar gidan. Dakin maigadi dai babu kowa Dahiru ne ya bude Attahir ya shigo. Wurin ajiye mota zai ci motoci hudu ma ga borehole da katon tanki a jikin katanga daga karshen gidan.

Gidan nasu tun daga waje yayi kyau. Kofa ce daga can karshe a kasa ta karfe wadda ta nan bene ne kawai zuwa saman inda su Dahiru zasu zauna.

Suna fitowa kowacce ciki ya duri ruwa sai rabewa suke a gefe. Attahir yace " 'yar uwarmu Allah Ya bamu alkhairi bari mu shiga ciki"

Kanta a kasa tace "to mungode Allah Ya saka da alkhairi"

Nawal ta kalleta kamar tayi kuka ganin yadda mijin nata yake ta rawar kai duk ta firgice. To itama Mawaddan dauriya ce kawai ta kalleta tayi murmushin dole.

Dahiru ya kama hannun Attahir "Dan uwa Allah Ya saka da alkhairi"

"Ka ji ka da wani zance sai da safe kaji"

"Sauran sallolin yau an yafe maka jam'i ne?" Dahiru ya amsa yana tsokanarsa sannan kowa yayi gaba matarsa tana biye dashi.

*****

Da sallama ta shiga gidan wani hadadden kamshin turaren wuta ya ziyarci hancinta. Duka turarukanta hatta humra da kanta ta hada saboda yanzu ta gama kwarewa. Kullum jikinta cikin sassanyan kamshi yake yau da gobe sana'arta ta janyo hakan balle kuma tana amaryarta guda.

Katon falon nasu suka shiga wanda aka kawata da kayan alatu na zamani. Daga gefen inda kofar kitchen take harda dinning table da kitchen cabinet. Kalle kallen dai ba yau ba ta samu wuri akan kujerar mutum daya ta zauna a takure.

Kujerar gefenta Dahiru ya zauna ya mika hannu ya riko hannunta daya. Jikinta taji yayi sanyi fiye da yadda taji dazu da suka hadu ko don lokacin tana tattare da fargaba ne.

"Mawaddatan wa Rahma yau gaki a gidan Dahiru a matsayin matarsa. Babban burina ya cika ina fata zamu zauna lafiya mu rike juna tsakani da Allah"

Kanta a kasa tace "In sha Allah."

Irin kararrawar nan mai sallama ce ta doka sallama a falon. Daga wajen kofar hawa saman Dahiru ya saka saboda kada a buga basu ji ba idan kofar saman a rufe take. Mike yayi yace mata yana zuwa. Fita ta ga yayi bai dade ba ya dawo rike da kwandon abinci.

"Marwanu ne ya kawo"

Hannunsa na dama ta kalla har yanzu da kumburi ga dukkan alamu yana masa ciwo ta tashi ta karbi kwandon ta ajiye a kan dinning table.

Har lokacin yana tsaye "bari na nemo plates to tunda kin karasa min wannan ladan"

"A'a barshi zan duba" tace tana dan waige. Plates ne masu kyau da cokula, kofuna da jugs a cikin kitchen cabinet din da yake manne a bango daga bayan table din komai a jere yadda ya kamata. Budewa tayi ta dauko plates biyu, da sauran kayan bukata ta ajiye.

Gani tayi ya ja kujera daya ya zauna tace "in zuba maka?"

Ya tsareta da ido ganin jikinta ya soma rawa amma tana ta kokarin boye masa "ki zuba mana dai"

"Na'am?" Tace a sanyaye tana mai fargabar kada ta fara wannan abin don tunda ya tsayaba wurin table din taji zuciyarta ta tsinke.

"Kinji me nace ko yau ma kurumtar ce ta tashi?"

Cije lebenta tayi tana karfafawa kanta gwiwar kada ta tsorata yaji babu dadi shi kuma ya kawar da kansa yana mai tuna maganar da Inna tayi masa jiya bayan daurin aure. Ita ma kuma Yaya ce ta fara yi mata bayanin yanayin da Mawadda kan shiga idan ta kebe da namiji na tsoro da firgici.

_"Dahiru kai ba bako bane game da sanin wacece Mawadda. 'Yar shawara zan baka ka sani cewa soyayya daban sha'awa daban. Duk son da take yi maka kasan kaddarar da ta afka mata a baya har yanzu tana iya tasiri a kanta. Idan kana son samun nutsuwa da kwanciyar hankali a gidanka ka fara neman kusanci da yarda daga matarka kafin ka bijiro mata da wani abu daban. Ina fata ka fahimceni. Idan kaje mata lokaci guda tana iya alakanta hakan da wannan lamari na baya ku zo kuna samun sabani"_

Wannan sune kalaman Inna gareshi kafin ya baro Tariwa. Ya gamsu da su dari bisa dari ya kuma san cewa hakan shine zai sanya shakuwa a tsakaninsu.

A plate daya ta zuba musu abincin dayan kuma ta zuba soyayyan naman kaza.

Kallonta yayi ya sake kallon abincin "kin tabbata zai ishemu? Ina jin yunwa sosai"

Bata ce komai ba ta kara musu. Tana gamawa ya sake hada komai a cikin kwandon "bari na kaiwa su Attahir"

Jin haka tayi murmushi saboda tayi wannan tunanin sai dai kuma tsoron kada ya zama kaiwar akwai takura.

Inda ya barta ya dawo ya sameta. Kujera yaja ya zauna sannan yace ta zauna ganin ta tana tsaye har lokacin.

"Matarmu kinsan me nake so dake?"

Ta girgiza kai a hankali  tana jin alamun hawaye mara dalili.

"Don Allahi ki cire komai a ranki ki saki jikinki. Ban aureki domin na takura ki ba duk da nasan cewa da wahala idan kowacce amarya ba haka take yi ba. Amma kinga mu special case ne."

Yadda yake daga gira yasa ta murmushi tace "kamar yaya?"

"Kinga dai ke da rana tsaka kika tare, gashi ango ya shigo ko kullin kazar al'ada babu. Sannan kin shigo gidanki babu irin kwalliyar nan ko inji kamshiki tun daga kasa"

Kallon kayanta tayi mayafin duk ya yamutse shi kuma ya nuna mata fuskarta a jikin wayarsa ta kode idanu zuru-zuru. Ita kanta ta bawa kanta dariya wai amarya kenan.

Turbune fuska tayi cikin shagwaba "ai kasan me ya janyo hakan"

"Na sani shiyasa nace miki komai namu daban ne. Saboda haka nake so daga yau har ranar da tayi miki ki dauke ni a matsayin yayanki, kaninki ko abokinki. Duk wanda kike so ki zaba. Ni kuma zan jira ki zuwa lokacin da kanki zaki dawo dani miji."

Sunkuyar da kai tayi ya ga hawaye ya diga akan tafin hannunta.

"Kina so muyi fada ne?"

"A'a"

"Na soke kuka a gidan nan daga yau. Idan kika kuskura na kamaki kina kuka zaki sha mamakin abinda zanyi"

Goge hawayen tayi ya taso ya dagota tsaye sannan ya rabata da jikinsa ya daga waya "hoton tarihi zanyi mana"

Hannu biyu tasa ta rufe fuskarta "naki wayon wallahi bazanyi kyau ba"

"Zakiyi mana" yace yana ta daukarsu tana kaucewa har ya sami wanda duka su biyun suke dariya.

Zama suka yi cin abincin ya dauki cokali da hannun hagu yana satar kallonta "ni gashi hannun daman yana ciwo, hagun kuma ban wani iya amfani dashi sosai ba"

Sam bata kawo me yake son yi ba tace "daurewa zakayi Yayanmu nasan kana jin yunwa"

Marairaicewa yayi "sosai ma amma kinsan Annabi SAW yayi hani da cin abinci da hannun hagu"

Ajiye cokalin da ta rike tayi ta dago kai "lalura ta kori komai Yayanmu"

"Haka ne amma kinsan lalura shine idan babu yadda zakayi gabadaya. Ni kuma a misali kinga ina tare dake"

Dariya ta shiga yi ta gano me yake nufi "daga zuwana gidan nan ko awa daya banyi ba zaka bani aiki?"

"Wane ni? Wai dama ina tunanin ko a matsayin yayata ki dauki kanki sai ki daure ki bani. Kinsan idan nace kanwata kanne akwai tsiwa kila ki rinka bani ba yadda nake so ba. Amma yayye mata akwai kirki"

Da fargaba Mawadda ta shigo gidan amma yanzu Dahiru yasa ta soma sakewa batare da ta ankara ba.

Roko da magiya harda cewa zai fasa cin abincin yayi a dole ta amince zata bashi. Lomar farko sai da ta rufe ido saura kiris ta tura masa a hanci ya riko hannun. A haka dai aka ci abincin sai da ya koshi ya tashi sannan ta iya ci don ko loma daya ta kasa yi a gabansa.

******

Motsinsa take ta ji a kitchen da ya shiga bayan ya gama cin abincin. Bai fito ba har sai da ta gama sai gashi yana wani sunkuyar da kai.

"Uhmm ruwan zafi ne babu na wanka amma na kunna miki heater. Ni kuma sai na dora a kitchen saboda kada na makara sallah"

"To" ta amsa masa tana dukar da kai.

Sai da yayi murmushi sannan yace "baki fahimceni ba, ruwan yayi zafi amma kinsan saboda hannuna bazan iya saukewa na kai toilet ba"

Ji tayi kamar ta shige kasa saboda kunya maganar take bata. Dahiru kuma yasan idan yana mata haka bazai bata damar tsawaita tunani akan abubuwan da suka faru ba balle ta shiga damuwa.

Ya sake kallonta yana shagwabe fuska "in dauko bokitin ki juye min?"

Kafin ya motsa ta tafi hanyar dakunan. Na farkon ta shiga ta ga babu toilet ciki amma tasan ta ga wani a falo. Sai ta bude dayan dakin. Yana da girma yayi matukar kyau da kayan da aka jera mata. Kamar yadda ta zata akwai bandaki a ciki ta shiga ta dauko bokitin a ranta tana ta tunanin wai haka ake yiwa amare ko kuwa dai ita ce daban. Ita fa duk labaran da take ji ranar da aka kai amarya tamkar sarauniya take komawa don mulki. To ita me yasa Dahiru yake yi mata haka? Babu amsa tunda bazata iya tambayarsa ba.

Ruwan ta juye ta kai masa ta ajiye yace mata za ta iya jira na heatar bandakin yayi zafi saboda akwai wuta. Kuma wai yana gama fada sai ya fara sosa kai.

"Akwai wani abin ne naga kin tsaya ni kuma kunyarki nake ji bazan iya cire kaya na shiga..."

Rasa ma me zata ce masa tayi tsabar mamaki. Saboda Allah me tayi ko tace da zaisa ya fadi wannan magana har wani sunne kai yake yi. Kuma shi ya tsayar da ita da bayanin ta jira ruwan zafi. Kwafa tayi ta fita tana auno me zata yi masa ta rama.

Sai da ya ga fitarta ya kwashe da dariyar yadda ta kwalalo idanu da yace yana jin kunyarta. Ko babu komai tunda suka shigo gidan bai yi mata wani abu da zai bata tsoro ba sai ma tsokanarta da yake yi.
******

Tamkar Dr Tani ta zuba ruwa a kasa ta sha lokacin da Dr Auwal ya gama waya da DPO din station din da suka kai karar BB yace sunyi magana da abokan aikinsu yanzu haka BB yana Bompai station.

Babu bata lokaci ta dannawa Haj Mara call tana jin ina ma za ta iya ganin yanayin da zata shiga idan taji wannan labari.

Haj Mara tana tare da wani Agent wanda ta bawa passport dinta da na BB akan zaiyi kokarin nemo musu visa China. Duk tsiya tasan akwai kudi a hannun Babawo ga dukiyarta da ya kwashe. Lallaba shi zata yi su hada komai nasu su bar kasar. Da wane idon za ta kalli 'yan uwanta idan ta koma gida. Sannan abin takaici yaranta mata wai jiya suka taru suka zo yi mata nasiha akan ta bawa Alh Sule hakuri akan laifukan da tayi masa kuma ta fadi ina BB yake a dawo dashi. Kaca-kaca tayi musu dukkansu tace basa kaunarta.

Yau dai gashi ta bada miliyan uku cikin kudin gidan Alh Sule da ta sayar wai kudin visa da ticket.

Da murmushi ta dauki wayar Dr Tani "yau kuma an tuna dani ne ko batan kai kika yi?"

"Haj Marakisiyya kenan gaisheki na bugu yi" tace cikin gatse.

Ta san da biyu ta ce hakan ta tabe baki "Ko ma dai meye sai a dena bibiyata haka. Ni da dana shirin bar muku kasar muke yi sai ku karata ke da 'yarki. Don Allah kafin mu dawo ki aurawa Qareeba mijin kece raini"

"Adana damuwarki akan annobar danki ba Qareeba ba. Na bugu ne albarkacin amintar mu ta baya in fara fada miki BB yana hannun 'yan sanda an kama shi ya sace amarya Mawadda Fatihu ina fata baki manta ta ba."

Cikin Haj Mara ya bada wani sauti ta soma cewa karya ne barazana ce kawai Dr Tani ta bugo tayi mata. Har da karin cewa Babawo a gida ta baro shi yana bacci saboda kawai ta tabbatar.

Dr Tani dariya tayi sosai " su Mara ashe kema ki kan taba kazzibu, kodayake na tuna kin kware a wannan fannin. Mu dai munyi matukar sa'a case din za'a mika shi ga wata Alkali da ta tsani masu fyade sosai bata musu sassauci. Sai ku fara shiri irin naku na masu kudi"

Sakato Haj Mara tayi da waya a hannu kafin ta kira Alh Sule ta soma kuka ta fada masa.

"Allah Yasa sanadin shiriyarsa ne" ya bata amsa.

"Zaman gidan yarin?"

"Kinga ki rufawa kanki asiri ki bari a hukunta shi kafin lokaci ya kure. Ke bakya tsoron idan ya laluba ya rasa wadda zai saukewa rashin mutumcinsa kan wa zai dawo?"

A tsorace tace "kan wa zai dawo?"

"Nima ban sani ba" ya bata amsa a dakile sannan ya kira Dr Auwal.

Ya sanar dashi iya abinda suka ji yayi masa godiya da alkawarin a ranar zai taho Kanon. Haj Mara ma gida taje ta shirya ta kira dreba yace Alhaji yace kada ya sake janta a mota. Ta kira ta gama masifarta dole ta hakura don yaki amincewa. Wani yaro ta kira dan 'yar uwarta da kyar ya amince zai tukata zuwa Kano ta biya shi.

******

Daga masallaci bayan su Dahiru sunyi sallar la'asar Attahir ya kula da yadda yake yarfe hannu.

"Ka sake fama hannun nan ko?"

Kallon babban yatsansa yayi babu alamun sacewa ga ciwo.

"Ina jin bai gyaru bane"

"Kana sakaci dashi dai. Ko muje a sake duba maka?"

Ba don yaso ba Attahir ya matsa masa sai an sake dubawa kada ciwon ya koma wani abin daban.

"Bari na fadawa Mawadda babu waya a hannunta"

Yayi dariya "Nima ba tafiya zanyi ba banje na fadawa amaryata ba. Kasan mu ne da amarci, mai hannu daya sai dai jinya"
******

Mawadda bata jin ta taba yin wanka taji dadin jikinta kamar yau. Ta jima tana sake ruwa sai da taji mai zafin ya fara karewa ta hakura ta fito.

Ta gama shafa mai da feshe feshen turare tayi kwalliya da kayan da aka jere akan madubin ta laluba dakunan kaf babu akwatunan kayanta sai na Dahiru. Salati ta shiga yi ga dukkan alamu bayan dauketa da akayi jiya kayanta da aka ce sai za'a kaita zasu tafi dasu an mayar gida.

Ta kalli wadanda ta cire ita kanta kyamarsu take yi duk wahalar nan dasu tayi harda zama a kasan bandakin gidan da aka kaita jiya. Ga lokacin la'asar na neman wucewa har hudu rabi tayi. Da kunya ta tambayi Nawal kuma babu wayar kiran gida.

Bata da wani zabi dole taje gaban akwatunan Dahiru ta shiga daga kaya tana kallon kofa kada ya shigo sannan kayan kansu kunyarsu take ji. Wata shirt ta samu yellow da rubutun baki a tsakiya tayi sauri ta zura tana kamshinsa. Ji tayi kamar shine da kansa a jikinta tayi murmushi sannan ta cigaba da bincike. Wani wando ta samu ash kamar na sanyi a gaggauce ta saka saboda ta ji kamar motsin kofa.

A bayan kofar dakin ta labe gabanta sai faduwa yake. Yana daga labulen ya ga akwatunansa a bude duka bayan kuma ko wanda ya dauki kayan da yasa yasan ya rufe shi.

Shiga cikin dakin yayi bai ganta ba kuma kofar toilet bata rufe sosai ba yasan bata ciki. Ta mudubi ya hangota tsaye sanye da kayansa da suka yi mata burum-burum abin dariya amma kuma tayi masa kyau. Shagala yayi da kallonta har suka hada ido ta mudubin.

Ya shafa kansa da hannu daya sannan ya bita bayan kofar ya matseta babu wurin fita. Mutsu-mutsu ta soma yi tana son barin wurin saboda irin tsayuwar da suka yi motsi kadan zai kara ta fada kirjinsa.

Dukawa yayi daidai kunnenta har tana jin sautin numfashinsa tayi mutuwar tsaye yace "shhhhh kada su kama mu"

"Su wa?" Ta fada a tsorace

"Ke da na gani a bakin kofa ai ke zan tambaya"

Takaici ne ya kamata kamar tayi kuka ta tura kofar da kafarta ta kuwa koma ta kulle da kanta.

"Ya zaki tona mana asiri" yace yana waigawa kamar me neman wani abu.

"Yayanmu ni fa saboda kai na buya."

"Au, tuba nake Matarmu koma ban ganki ba" ya sake jawo kofar yadda ya ganta tana tsaye tana cika tana batsewa jin ya fara cewa "Mawadda, kina ina?"

Turo kofar ta sake yi harda guntun hawayenta ta soma shagwabar da bata san daga ina ta zo ba tana cije lebe "ni wallahi ba haka ake yi ba"

Juya fuska yayi kamar wanda ya shiga tashin hankali "ba haka ake me ba?"

Ta turo baki tana harararsa "bayan ba haka ake yiwa amare ba. Ni sai wasu abubuwa kake yi min kamar ba amarya ba"

"To Mawadda fada min yaya ake yiwa amaren nima nayi miki kinji" ya kashe mata ido.

Kunya taji ta dauko mayafinta ta yafa "ni sallah zanyi"

"Babu damuwa idan na dawo sai ki fada min yadda ake yi."

"Fita za ka sake yi?"  A tsorace tayi maganar ya dago mata hannunsa mai targaden da ya gagara warkewa.

"Gyara na uku zani kuma wallahi akwai zafi. Amma bazanyi kuka ba kada Attahir ya baki labari. Daga can zamu biya mu taho miki da kayanki kada ki buda min nawa"

Ya kare da tsokana saboda yadda ya ga tana kallon hannun da tausayawa.

Hararsa ta fara yi sai kuma tayi masa addua ya fita.

Har akayi magrib basu dawo ba ta gama leken ko ina a gidan ta rasa abinyi ga wuta ba'a jona tv ba. Amarya da take tarewa da jamaa ko da daddare yadda lokacin bazai dameta ba ita ta shiga gidanta da rana tsaka gagal. Allah Ya isa ta makawa BB tana jiran ranar shiga kotu.
*****

Gyaran yau yafi na kullum ba karamar wuya Dahiru ya sha ba mutumin yayi ta masa fadan sakaci. Kasa magana yayi a mota da suka je daukan kayan Mawadda wanda har su Saifullahi sun gama loda su a tasi ko fita daga motar bai iya yi ba suka dawo dasu tasu.

Da yake tun a hanyar zuwa wurin gyaran Attahir yace masa yakamata su tsaya siyan nama kada su jewa amarensu haka shiyasa a hanyarsu ta dawowa yace su tsaya duk da Attahir din yaso su hakura.

Ba su suka koma gida ba sai takwas da rabi har anyi isha. Akwatunan Mawadda har bakin kofa Attahir ya hau masa da biyu sauran Dahiru yace sai da safe.

Tana jiyo su suka yi sallama ta tashi daga kwanciyar da tayi akan doguwar kujera ta zauna tana gyara mayafi.

Yana shigowa ta ga hannun nasa an daure da farin kyalle. Sannu ta rinka yi masa akwatunan ma ita ta ja kayanta daki.

A zaune ta dawo ta same shi yayi shiru azabar hannu ta ishe shi.

"Yayanmu ko zaka yi wanka sai ka kwanta"

Ledar naman ya mika mata yana magana da kyar saboda wani irin ciwon kai da zazzabi da suka rufar masa "bani ruwa na siyo pain reliever idan nasha sai nayi wankan"

Da sauri taje ta dauko ruwa da aka jere mata su da lemuka a kasan kitchen kafin ta samar musu wurin zama.

Yana sha ya shiga daki bai dade ba ya kirata.

"Yanzu dai nine kanin kece yayar"

"Me aka yi?"

Ya nuna kayansa "riga kawai zaki cire min "

Tace "kawai ne ma"

"Ki tausaya min bazan iya da hannun nan ba ina tsoron famawa"

Wannan daren amarcin nata dai bazata taba manta dashi ba ta ayyana a ranta. A hankali tace
"Ba ka jin kunyata to?"

Ya langabe kai "ji kai, shiyasa nace kizo a yayata.  kawai don kada na fama a sake gyaran ne. Yau fa na kusa kuka don ciwo"

Runtse ido tayi ta matso kusa dashi tana cewa zata tambayi Attahir kila yayi kukan.

Kasan rigar ta kama zata fara dagawa yace "wash kiyi min a hankali"

"A hankalin fa nake yi"

"Ni dai ki bude idonki sai ni na rufe nawa. Allah idan kika fama min kuka zanyi"

Bude ido tayi suka sauka cikin nasa suka yi dariya tare. Haka akayi ya rufe nasa idon "kuma saura ki kalleni"

Mawadda ta cije leben da ya kurawa ido ta soma mitar shi da ake taimakawa shine da sharudda "haka ma zaka ce,  me zan kalla ma"

Sai da ya bari ta cire masa rigar tana ta kawar da kai daga shi sai vest da dogon wando sannan yace "ki ka ce babu abin kalla a jikina ko"

"To ai kai din ne"

Gabanta ta ga yana kara matsowa ta fara ja da baya yana biye da ita  har bakin gado saura kadan ta fada.

"Ko zaki karasa ladanki a matsayin Yayata tunda babu abin ganin"

A tsorace take jiki har yana rawa tace "rufa min asiri akwai abin kallo a jikinka"

Saurin matsawa baya yayi harda rufe fuska da hannu "wayyo Matarmu kinsa ni jin kunya. Nifa nufina ko zaki iya tara min ruwan wankan"

Kifta idanu ta shiga yi ba kakkautawa sannan ta yi hanyar toilet din da sauri "kaine baka fada yadda zan gane ba"

"Ah....da me kike zato ina nufi? Huhhhhhh ba dai...ba dai...." ya sanya hannunsa ya wani kare jiki kamar an bude kwaila tana wanka.

"Na shiga uku Yayanmu!" Tace tamkar ta fasa ihu "Me yasa kake min haka ne? Ni ba haka nake nufi ba"

Abin da ta saba wato cizon lebe idan tana tunani ta soma yayi murmushi "yanzu ma banyi miki irin yadda ake yiwa amare ba kenan"

Ta gyada kai bakin nan tana juya shi ita kadai tasan me take cewa.

Bata san yadda aka yi ba sai ganinsa tayi a gabanta hannunsa mai lafiya ya zagaye ta bayanta ya matso da ita daf da jikinsa.

"Kinga farkon abinda ake yiwa amare idan sun tare"

Bata ankara ba taji ya hade bakinsu wuri daya dukkansu bugun zuciyoyinsu ya karu a lokaci guda.

******

"Mummy yanzu yau ta tare matar tasa?" Qareeba ta tambayi Dr Tani.

"Allah Ya takaita mata wahala daga shegen yaron nan an samu an ganta da wuri. Har gidan nasa zamu je dake don ina so in roketa ta yafe min itama"

Qareeba ta sa hannu ta share hawaye "yanzu ni Mummy a ta biyu zanje gidan kenan? Ina ta burin nima kamar ke na zauna ni kadai da miji"

Wani wawan duka Dr Tani ta kai mata a baya ta manta bata gama warkewa ba "Dahirun zaki aura don baki da hankali?"

Ta chuno baki "to ba son sa nake ba"

Takaici ya kama Dr Tani tace "yanzu ke Qareeba bayan duk wahalar nan ko warkewa baki gama ba idan aka ce miki ga namiji sai kije koda da aure yazo?"

Ta gyara kwanciya "me zai hana?"

Jinjina kai Dr Tani tayi "anya kan nan naki kalau kuwa?"

Cikin yanayin ko in kula tace "ina laifina don ina son raya sunnah Mummy? Ba don kin wulakanta dan gidan Antin gadon kaya ba tun ina secondary da yake sona kila da yanzu ina da 'ya kamar shekara shabiyu ai"

Tagumi Dr Tani tayi tana kallonta kawai babu amsar bayarwa.
[31/01 9:36 am] Batuul Mamman: *GUMIN HALAK...*💰22

*Batul Mamman*💖



Har Dahiru ya saketa ya shige toilet yin wanka Mawadda tana tsaye ya barta da kaduwa. A hankali ta dora hannu akan bakinta daga bayanta kawai taji muryar Dahiru.

Kansa ya leko ta kofar da ya dan bude "na dawo ne kina jirana?"

Da sauri ta fice daga dakin kamar zata fadi.

Shima nasa bakin ya tsaya kallo a madubin toilet yana jin kamar ya koma gareta.

"Wai ba da zazzabi ka dawo bane" ya tambayi kansa sai kuma yayi murmushi "Dama na jin baki ne ga dukkan alamu"

Wankansa yayi ya shirya cikin kayan bacci. Falo ya fito Mawadda ko kallonsa bata yi ba ta shige dakin ta rufe kofa. Dariya ta bashi ya zauna yana jona wayoyin tv.

Itama wanka tayi har yanzu tana fama da kunya. Da ta shirya daki ya kaure da kamshin turarukan su ta nemi zani ta daura akan rigar baccinta da hijab ta sami wuri ta zauna.

Shirun da yaji ne ya biyo baya ya sameta a zaune. Zaro idanu ta fara tana ganinsa.

"Kina da mara lafiya kin dawo daki ko abinci baki bashi ba"

Mikewa tayi ta sha kunu "muje amma a yayarka"

Tana rufe baki ya matso ya rungumeta. Dama tunda ya shigo kamshin turarenta ya hargitsa masa lissafi.

Ture shi tayi "yayarka fa nace"

Ya sake riketa yana dariya "kanne ne ba'a hugging fa, amma yayye ana ganinsu ake makale musu musamman idan suna kula da kannensu"

Ta fuskanci jindadin tsokanarta yake ta sake ture shi zata gudu.

"Wash...wash hannuna"

Dawowa tayi da sauri "mu gani."

Runtse ido yayi ta yi tana masa sannu. Naman da ya kawo da juice ta zuba yanzu ma a baki ta bashi yana yi yana makale hannu. Wani lokacin sai taji kamar ba na gaske bane sai kuma ta tuna duk saboda ita yake ta fama hannun sai ta hakura.

Sun gama komai anzo kwanciya suka tsaya a gaban gadon. Ta kalle shi ta kalli gadon.

"Tare zamu kwanta ne?"

"Nayi zaton har yanzu yayata ce. Babu matsala ana haka dama mace da kani gado daya"

"Inji wa? Ni dai gaskiya..." ta turo baki.

"Assha ba sai kinyi kuka ba. Zan kwanta a kasan ko na koma falo na takure akan kujera. Hannu na nake ji dama mai gyaran yau har fada yayi min"

Pillow ya dauka ya marairaice mata "kina ganin bazan fama ba idan na kwanta a wuri mara laushi?"

Sai da tayi ajiyar zuciya tace ya kwanta ita zata koma falon yace tana fita zai bita shine namiji idan da mai hakura da gadon shine. Irin dogon pillon nan ta ajiye a tsakiyar gadon saboda a gajiye take idonta har ya soma yaji. Ta nuna masa bari daya

"Ka kwanta a can kuma kada ka wuce pillon nan"

"You are the best Yayarmu Mawadda. Sai da safe. Ki kashe fitilar bana son haske"

Kwanciyarsa yayi a barin da ta nuna masa ta lalubi makunnin fitilar ta kashe. Zata rama ne bari dai yaji saukin hannun nasa tace a ranta.

A darare ta kwanta ta takure jikinta ko hijabin bata cire ba sai zanin kawai ta kwance. Yau ita ce kwance gado daya da Dahiru a matsayin mijinta. Godiya ta yiwa Allah da Ya cika mata burin da ta fitar da tsammani daga tabbatuwarsa. Ba jimawa bacci ya fara fizgarta har Dahiru yaji sauyin yanayin saukar numfashinta.

Wani dadi ne ya kama shi ya matso ya dauke pillon ya cilla shi kasa "anyi kanekane tsakanin mata da miji"

 A hankali don kada ya tasheta ya matsa kusa da ita ya lullubesu. Rungumota yayi dama baccin nata babu sakin jiki a take ta farka zuciyarta ta tsananta bugu. Yaji ta fara motsi tana neman kwacewa daga rikon da yayi mata.

"Assha don Allah kada ki koreni tsoro nake ji" yace da karamar murya.

"Tsoron me" ta fada itama a hankali.

"Dodo"

"Zan daure"

"Da me?"

"Mu kwanta a haka Yaya da kaninta matsoraci"

Zai sake magana ta dora hannunta akan bakinsa "bacci nake ji ka dena magana"

Murmushi yayi ransa fari kal kamar an zuba madara. Allah Yayi shi Dahiru zai auri Mawadda. A nata bangaren kuwa shiru tayi kawai zuciyarta kamar ta fito amma tana so ta danne don ta faranta masa. Gajiya da rashin baccin da yake kansu yasa basu dade cikin tunanin da suke yi ba bacci ya kwashe su duka.

*****

Bacci dadi sai da hasken rana ya fara shigowa dakin suka tashi. Mawadda ce ta fara farkawa ta gansu sun cure wuri daya ga hijabinta a gefen gadon ko yaushe ta cire bata sani ba. Matsawa tayi daga jikinsa da sauri. Hannun ciwon ta kalla, wannan hannu ya ga ta kansa ko yaushe zai sami sukunin warkewa.

Bandaki ta shige ta dauro alwala ta fito tazo tana dukan gefen gadon. Da kyar ya bude ido yana ganin haske ya ware su sosai ya tashi "Subhanallahi wane irin bacci nayi haka?"

"Na gajiya"

Ya kula tayi alwala yace ta jira shi suyi tare. Bayan sun idar ya duba wayarsa ko Attahir ya kira shi tunda sunyi akan wanda ya fara tashi ya tashi dan uwansa suje masallaci tare. Bai ga missed call ko daya ba yaji dadi ya sami abin tsokanarsa.

Bayan azkar a wurin Mawadda ta sake bingirewa ya saka mata pillow shima ya janyo wani ya kwanta. Bacci suka sha sosai sai shadaya wayarsa ta tashesu. Sunan Baffa ya gani ya gyara murya tare da yin sallama suka gaisa.

"Dahiru kayi hakuri zan fito da kai kana fama da wannan hannun. Ana nemanmu a ofishin 'yan sanda wai mahaifiyar yaron ce tazo"

Zama yayi sosai yana kallon Mawadda ransa ya soma baci. Ya tsani komai da zai sa ya tuna da BB to amma fa dole wannan karon a yiwa tufkar hanci ta yadda za'a kawo karshen abin once and for all.

Da sauri-sauri ya shirya motsinsa ya tashi Mawadda. Kunya taji ace tana bacci har wannan lokacin Dahiru ya tashi yayi wanka.

Hijabinta ta gyarawa zama "Yayanmu ina kwana".

"Lafiya kalau, na tasheki ko?"

"Yakamata na tashi dama, yaya hannun?"

"Da sauki. Kinga koma kiyi kwanciyarki kada ki tashi sai azahar. Baffa ke nemana zamu je police station akan case din BB"

Dukar da kanta tayi jikinta yayi sanyi lakwas da jin sunan mutumin da ya zame mata dodo. Dahiru ya saki fuska yazo gabanta ya tsaya ya dago da kanta da hannunsa. Rufe ido kawai tayi ya ga hawaye yana zuba. Matseta yayi kam a jikinsa ta fashe masa da kuka mai ban tausayi. Kyaleta yayi tayi kukan har don kanta ta dena ta koma ajiyar zuciya.

"Mawadda" ya kira sunanta daga kasan makoshi har taji tsigar jikinta ta tashi.

"Uhmm"

"I love you so much abinda nake so ki sakawa ranki kenan a kodayaushe"

Kankame shi tayi ta cusa kanta cikin kirjinsa. Ita ta sani har abada bata da hanyar sakawa Dahiru. Yayi mata halaccin da addu'a da fatan alkhairi a kullum sune kadai abinda zata iya yi masa.

Dariya yayi yana son hada ido da ita "ko dai yau Mr and Mrs muka tashi ne? Kinga ina dawowa sai na cigaba da nuna miki yadda ake yiwa amarya"

Matsawa tayi da sauri tana murmushi a kunyace ta canja zancen "baka ci komai ba zaka fita"

Ya shafa cikinsa "zaki iya hada min coffee kafin na karasa?"

Ta gyada kai ta fita shi kuma ya kira Attahir yana tambayarsa mukullin motarsa.

"Fita zaka yi ne?"

Nan ya fada masa wayarsa da Baffa. Attahir ya nuna rashin jindadinsa da bai neme shi ba akan su je tare.

" Ba don kai na rabu da kai ba. Idan na yiwa Nawal haka ban kyauta ba. Ka zauna ka kula da ita don Allah."

Attahir yayi dariyar shakiyanci "me kake nufi?"

"Ka fini sani. Zancen gaskiya bai kamata muyi ta shiga hakkinta ba. Idan akwai matsala zan nemeka amma yanzu kayi min wannan alfarmar kayi zamanka"

Attahir ya kalli inda Nawal ke kwance tana bacci fuska a kumbure an sha kuka. Shima yasan idan ya fita bai kyauta ba gaskiya. Mukullin ya je ya ajiye a seat din gaba na motar ya koma wurinta aikin lallashi.

Dahiru ya sha coffee sai bread kadan saboda kiran da Baffa ya sake yi masa. Mawadda ya jaddadawa tayi bacci zai taho musu da cefane saboda babu kayan miya idan zai dawo.

"Nasan zanyi missing dinki so zan kiraki duk rabin awa"

"A wace wayar?" Tayi murmushi.

"Ohhh to sai kin sake hutawa zamu je a sayi sabuwa. Da kanki zaki zaba"

Tana tsaye a bakin kofar ya soma sauka benen ta daga masa hannu. Sai da yaje kofar kasa ya dawo da sauri ya sumbaceta a kumatu ya sake sauka.

*******

"Nace ko nawa kuke so ku fada a fito min da yarona na ganshi" Haj Mara kenan tana ta kumfar baka a cikin police station din.

Wata murdaddiyar police ce ta fito ta daka mata tsawa "kina hauka ne zaki cika mana wuri da ihu kamar kasuwa? Kai Corporal idan ta sake bude baki ku rufe min ita"

Haj Mara shiru tayi sai da matar ta gama magana ta tafi ta sassauta murya "ku taimaka don Allah"

Wani Sergent yaji tausayinta "Hajiya case din fyade da satar mutum ne akansa ba'a bari a gansu sai anje kotu"

Duk ta fita hayyacinta saboda damuwa ta nuna jakarta "kai ni wurin DPO a kashe maganar nan zan biya."

Tsaki yayi ya bar wurin suka kyaleta tana ta babatu. Sai bayan kusan awa guda Dr Auwal, Dr Tani da Alh  Sule suka shigo tare.

Ganinsa da tayi da makiyanta ya harzuka ta matuka. Dr Tani ta washe baki kai kace gonar auduga saboda jindadin ganinta a wannan yanayin.

"Haj Mara ashe rai kan ga rai? Kwana biyu. Me kike yi a nan?"

Dr Auwal ya bita da kallo wai don ta dena ta dauke kai kamar bata gani ba ta cigaba da magana.

"Yaron da yaso kassara min 'ya ne aka kamo yaje ya sace amarya ranar da zata tare don karfin hali."

Haj Mara ta cika kamar ta fashe ta kalli Alh Sule shekeke "ka biyosu ne domin a ga yadda za'a hukunta danka ko me?"

"Marakisiyya ki ajiye makaman yakinki mu ceto yaron nan."

"In ceto abuna daga hannun makiya dai. Alhaji kotu fa za'a je da dan cikinka."

Irin alamun kwancewar kai Dr Tani take yi da hannunta tana kallon Haj Mara, wato bata da hankali.

Shigowar Dahiru da Baffa da Baba ya mayar da hankulansu bakin kofa. Duk hassadar mutum dole ya yabi Dahiru saboda ganin farko zaka gane ya wuce raini. Ba wai ta fanin kudi ba don su Haj Mara sun kere shi nesa ba kusa ba. Kwarjini gareshi da cikar zati ga kyau ga kuma iya ado na mazan da suke ji da kansu a wannan zamani.

Da sauri Dr Tani ta matsa kusa dasu "Dahiru dana na kaina  ina kwana"

Ya dan dakata ya kalleta ya tabbatar kunnensa ba karya ya jiyo masa ba. Dr Tani ce take gaishe shi yau da kanta.

"Lafiya kalau, yaya mai jiki?" Yace yana karbar hannun da Dr Auwal ya miko masa.

Wani dadi Dr Tani take ji kawai ace tasan Dahiru. Bayan an gama gaisawa ta nunawa Haj Mara shi "ga fa dana Dahiru angon da Babawonki ya sacewa mata. Kin tuna Mawadda Fatihu ai, ita ce amaryar"

Yawu ta hadiya da kyar tana kallonsu. Ta gane Mal Fatihu sai dai sabanin sanin da tayi masa da jikinsa da suturarsa sun nuna duniya bata wulakanta shi ba.

Ofishin DPO aka kira su domin karin bayani.

"Wannan case din babu zancen sulhu domin ita Dr tace sai an bi mata hakkinta. Haka nan iyayen amaryar Mawadda da mijinta sun ce su ma babu maganar sulhu saboda haka mun tattara komai za'a mika kotu"

"Wane irin kotu officer? A kashe maganar nan kowa ya huta" inji Haj Mara tana daga murya.

"Hajiya gaki ga mutanen da aka yiwa laifi"

"A yadda kuka ce ba. In ba tsoro ba ina ita amaryar da aka yi masa sharrin ya sata kamar wata jaka ko allura?"

Cikin fushi Baba yace "sharri fa kika ce? Kin manta ni ne? Kin manta 'yata da danki ya lalatawa rayuwa...."

Dahiru ya kankance ido yana kallonta "Baba ka barni da ita kafi karfin bata amsa. Mawadda da kike nema tana gida bazaki ganta ba sai ranar da za'a fara sharia."

A fusace ta mike tsaye "aikin banza kai, an fada muku zan yarda da wannan kullalliyar ne? Tani kinji dadi ki zuba ruwa a kasa kisha. Kinje kin samo mutane kun biyasu kudi ace shine mijinta saboda kin sha alwashin ganin bayana don yaki auren dolowar 'yarki"

DPO ya soma cewa suyi shiru amma ina kowacce ta kule. Haj Mara ta tafi kowa zakalkalewa har tana cewa

" *wane mahaukacin ne zai auri yarinyar da aka taba yiwa fyade har ya daki kirji ya nuna kansa idan ba biyansa aka yi ba*"

Shiru ofishin yayi sai da ta fadi maganar ta gane abinda tayi sai kawai tasa kuka.

DPO kuwa dama ransa ya baci da hayaniyar da tayi don har ya kira azo a kulle su.

"Wannan abu yayi kyau ga shaidu sun ji da kanki kin amince anyi mata fyade kamar yadda iyayenta suka sanar damu tun farko. A kotu sai kiyiwa alkali bayani sosai."

Kuka ta saka "wannan duk sharrin Tani ne yallabai. Kuyi hakuri a taimaka min in ga dana"

Baffa yace "yaro taimaka ka fito mata dashi ko don a tabbatar dan nata ne ba wani kuka kama ake yi musu sharri ba"

Basu jima ba kuwa sergent ya ingizo keyarsa aka shigo dashi da ankwa a hannu.

"Na bani na lalace BABAWO!"

Kansa tayi a gigice ta rungume shi. Tafiya yake baya iya hade kafafu wuri ya kumbura. Fuskarsa kuwa fitar hakora uku ba wasa ba. Tayi suntum kuma yayi rashin sa'a cell daya aka hadasu da Danmami. Bakincikin an kama shi ya yiwa BB dukan kawo wuka cikin dare saboda ya janyo masa za'a sake kaishi kurkuku. Ya taba zaman wata uku baiji dadi ba ko kadan.

"Wallahi nima sai na shigar da kara. Inji ubanwa yace idan ana tuhumar mutum ayi masa jinajina?"

Babu wanda ya kulata BB da ido daya yake hawaye don dayan ya hade don kumburi shima. So yake ya tambayeta ko an sake shi ne a yau amma babu dama. Ya kalli Alh Sule wanda shima zuciyarsa ta tausaya dan nasa sosai ya kawar da kai.

Alh Sule a raunane yace "Babawo Allah Ya fissheka alkhairi Yasa wannan abu ya zama izna ga 'yan baya."
Muryarsa ta soma rawa ya fice yana jin babu dadi.

Haj Mara tana kallo aka kada keyar gudan jininta tana kuka kamar ranta zai fita shima yana yi. Su Dahiru ko gezau suka fita bayan DPO yace kowa ya nemi lauya za'a sanar dasu lokacin shiga kotu.

******

Baba suka fara ajiyewa sannan ya wuce ya kai Baffa gidan Bilya inda daga nan zasu wuce Tariwa a yau.

"Baffa ko hutawa baku yi ba"

"Wane hutu kuma banda abinka. Gara mu kuma kaima ka samu natsuwa kafin kwanakin da aka ce za'ayi zaman farko su cika. Ga waya nan ku rinka sanar damu yadda abin ya kasance"

Tare suka shiga gidan. Inna ma ta gama shiri ta nunawa Dahiru abinci tace ya dauka Furaira ce ta dafa musu shi da amarya. Zaiyi godiya ya ga uwar hararar da take watsa masa daga ita har kanwarta Hansa'u. Ya tabbatar dole Inna tayi mata ta zuba abincin.

Bata san halinsa bane har take tunanin zaici wannan abincin da aka bawa matarsa ba da zuciya daya ba. Ai kuwa tana ganin Inna ta koma daki dauko jaka taja tsaki.

"Wahalalle tunda ka fara soyayya da yarinyar nan matsalar yau daban ta gobe daban amma ka like kamar wanda aka bawa ruwan asiri."

Amsa ya tattaro zai yaba mata sai ya tuna daraja da kimar Bilya ya fasa "Abincin nan idan na tafi dashi karashenta sai dai a bawa almajiri don tayi girki ma"

Furaira ta sha kunu "ita wa?"

Kai ya sunkuyar wai shi kunya "ita din"

Hansa'u ta rike haba sai kuma ta soma tafa hannuwa "matar taka ce bazaka iya fadan sunanta ba?"

Irin murmushin nan mai ban haushi yayi musu duk su biyun "so kuke Inna taji? Duk abuna da kunya in fadi sunanta a gaban iyaye. Kunsan Babyna nake kiranta"

Babu wadda ta tanka masa suka wuce ciki a fusace. Dariyar Danlami ya ji a bayansa.

"Yayanmu Dahiru ka matsawa matan nan wallahi"

"Baka san takaicin da nake na yadda take yiwa Yayanmu Bilya ba. Shi kuma sai yayi shiru baya iya nuna bacin ransa ma"

"Dama dai yayi aure" Danlami yace yana daukar jakar Innarsu.

Idanun Dahiru ne suka kara girma saboda wata idea da ta fado masa. Shi kadai yake ayyanawa a ransa lokaci yayi da Anti Qareeba zata hadu da Man.

Suna bakin mota da Inna yake tambayarta game da rashin zuwan Ummiyo.

"Kaima kasan dalili dai"

"In sha Allahu har tsakar dakinta zan kai Mawadda komai ya wuce"

******

Sahad ya wuce ya siyo kayan da yake tunanin suna bukata. Sauran ko nan da sati sai ya fita da Mawadda su saya ko tayi masa list. Daga nan ya tsaya ya sayi kayan miya da nama. Dariya abin ya bashi wai cefane.

Mawadda tana zaune a falo tayi kwalliya cikin wani material mai santsi anyi mata gown me siririn hannu. Irin daurin nan na murde jelar dankwali ta gaba a zagaya dashi daga bari daya tayi. Tayi matukar kyau kamar a sace. Gidan kuwa tun daga kofar hawa saman yake zuba kamshi.

Dahiru na tsayuwa da mota ya fita da sauri yana burin saka matarsa a ido. Da sauri ya hau saman yana bude kofa ya ganta tana fitowa daga daki.

Tamkar numfashinsa zai tsaya tsabar kyaun da tayi masa. A tare suka sakarwa juna murmushi ta ware mayafin da ta dauko da niyar idan ya dawo ta yafa saboda haka kawai taji kuma nauyin zama da rigar.

"Kada ki yafa ki bata min kwalliya mana" yace yana ware mata hannuwansa ta taho gare shi.

Dage gira tayi tana dariya "Yanzu a Gwaggo nake sai ka karaso mu gaisa ka sami wuri ka zauna"

Dariya yayi harda hamdala sannan ya nufota gadan-gadan. Bayan kujera ta koma da sauri ya biyota tana  gudu tsakanin kujeru.

"Yayanmu ba kyau wayo Gwaggo nace fa"

Yana bayan kujera ita kuma ta zagayo gaban yace "haba Gwaggo don Allah ki tsaya duk na gaji"

"To ita Gwaggo ana rungumeta ne?" Ta turo baki.

"In kinji runguma daya kenan. Tsakaninmu da Gwaggonni rungume-rungume ne. Haka ake yi idan an gansu har kwanciya ake yi a jikinsu"

"To waye ba'a rungumewa?"

Ya dan kalli sama "amare saboda kowa ya sansu da kunya"

"Wayo kake son yi min to ban yarda ba"

Kai ta ga ya dukar "na hakura bari na koma akwai kaya a motar da ban dauko ba"

Da jan kafa ya soma tafiya har ya kusa kofa ta bishi da sauri ta kamo hannunsa. Wani abu suka ji duka su biyun ya juyo yana kallonta.

Daurewa tayi tace "rabin minti a matar Dahiru"

Wani irin kallo yayi mata mai tattare da soyayya da kauna.

"Kin tabbata?"

"Ko in fasa?"

"Maganar farko Sarki yake karba."

Hannun nata da ta rikeshi da shi ya janyo ta fada jikinsa. Wata kyakkyawar runguma yayi mata suna jin bugun zukatan juna.

Muryarta a sanyaye tace "rabin minti ya cika"

"Me ki kace?"

"Ra...."

Hadiye kalmar tayi lokacin da ya hade bakinsa da nata. Sun dauki lokaci a cikin yanayin da su kansu basu san yadda zasu fassara shi ba.

Ya dago kai yana neman idanunta ta rufe su.

"Kunya?"

Ta gyada kai tana kara hannunwanta akan fuskarta.

"Nima haka" yace yana rufe tashi fuskar.

Sosai taji kunyarsa ta juya bayanta ya tsaya yana kallonta daga sama har kasa yana dada godewa Allah da Ya bashi ita.

Sauka yayi ya dauko ledoji biyu da hannu daya. Tana gani tazo ta karba sai ta koma bakin benen idan ya dauko sai ta karba har suka gama hawowa dasu.

Daukar komai tayi tana kaishi inda ya dace shi kuma ya tafi yayi wanka. Yadda take aikin tana tunanin Dahiru haka yake shiryawa yana tunaninta da jin kewarta ta dame shi kamar wadda bata gidan.

Kananun kaya ya saka ya fito bata falo amma ga abinci akan dinning table.

Kitchen ya shiga tana gaban sink tana wanke nama.

"A ina muka sami abinci?"

"Wani yaro ne yace inji Haj Mama"

"Allah Ya saka musu da alkhairi."

"Amin"

Shiru taji na dan lokaci kafin ta juyo taji shi a tsaye a bayanta.

Wani iri taji zata motsa ya sauko da fuskarsa daidai kunnenta yana mata magana kamar mai rada "apron zan saka miki kada ki bata kayanki"

Zura mata yayi ta saman sannan ya janyota jikinsa ya daure mata igiyar a kugunta.

Dena komai tayi saboda yadda take ji a lokacin ya dora kansa a kafadarta tare da zagaye hannuwansa a cikinta "cigaba da aikin Matar Dahiru"

Da kyar tace "uhmmm na koma Yaya"

"Da wuri haka ba notice"

"Eh ni dai na koma" tasan idan suka cigaba da zama a haka da wuya ta iya karasa aikin. Soyayyarsa na ranta da kuma fargabar da take kasan zuciyarta.

"A bani rabin minti please"

Wuyanta taji yana sumbata ko ta ina sannan ya daure ya rabu da ita ba don yaso ba.

"Yaya in tayaki?"

"Jeka kaci abinci" ta kakaro maganar da kyar.

"Mawadda ina son ki!"

"Wallahi nima ina sonka Yayanmu" ta fada tana kallonsa.

Kallon juna suka tsaya yi kafin ta nuna masa kofa da yatsanta.

"Ko baki ce ba tafiya zanyi ko don tseratar da kaina daga soyewa"

"Me zai soyaka ana zaune kalau?"

"Ke mana da idanunki masu hanani sukuni"

Kofar ta sake nuna masa ya fice yana dariya ita kuma ta cigaba da aikinta cikin tunanin mijinta abin son ta Dahiru.
[31/01 9:36 am] Batuul Mamman: *GUMIN HALAK...*💰24

*Batul Mamman*💖




Annurin fuskarta ne ya bace bat kamar anyi ruwa an dauke ta hade rai "me kace?"

Dahiru an sami abinda ake so ya wani kashingida akan kujera ya basar "cewa nayi zamu je neman auren Anti Qareeba"

Wani abu taji ya tokare mata a wuya ta tashi ta shige daki ta barshi a wurin. Shafa kansa yayi wanda gashinsa irin na Fulani da suka gada wurin mahaifinsu har ya fara taruwa ya ce "Allah nagode Maka Mawaddata tana sona"

Kusan minti uku tana daki tana kuka. Aure ko wata bai cika ba Dahiru yake fada mata zaije neman aure. Don karfin hali harda cewa taje wurin Nawal wato ma dare zasu raba. Yanzu haka Attahir zaiyi mata duk irin girmamawar da take masa. Shi kuma Bilya karshenta matarsa ce ta fada masa tayi mata ba daidai ba da suka zo shine zaice ayi mata kishiya. Allah Sarki rayuwarta daga wannan sai wannan. Amma tayi alkawarin daurewa bazata taba bijirewa Dahiru ba. Wani matsanancin tausayin kanta ne ya kara kamata ta kifa kai akan filo tana kuka haikan kamar yau za'a kawo mata amaryar.

Dahiru ya taso yana rangaji abinsa don shi idan ya ga alamun kishinsa a idanun Mawadda wani kara sonta yake ji. Kukanta ya jiyo kafin ya bude kofar yaji gabansa ya fadi. Da sauri ya tura kofar ya ganta kwance a tsakiyar gadon tayi rub da ciki sai sautin kuka ke tashi.

Gadon ya hau yayi kokarin juyata ta makale jiki.
"Subhanallahi Mawadda me ya sameki?"

Shiru tayi tana mamakin rainin wayo na maza. Yanzun nan ya juyar mata da duniyar farincikinta shine kuma yake tambayar me ya faru.

"Don Allah fada min. Baki da lafiya ne?"

Nan ma babu amsa. Duk yadda zaiyi taki shiru sai da kyar ne ma ya samu tace masa ya rabu da ita ya tafi wurin wadda yake so. Sai lokacin ya harbo jirginta ya danne dariyarsa ya gyara zama daga gefenta ya bude baki sai jiyo shi tayi kamar yana kuka.

Da farko ta zaci wasa ne ta kyale shi sai daga baya taji ya bude murya yana neman cika mata kunne. Jiki na rawa ta tashi ta ma manta da nata kukan "menene?"

Kara sauti yayi ta saka hannu akan bakinsa da sauri ta toshe ga nata hawayen na zuba cikin muryar kuka tace "Yayanmu me ya sameka kuma?"

Ya kwabe kyakkyawar fuskarsa ma'abociyar saje wanda ya hade duka gefen fuskarsa.

"Ba ke bace kike kuka kuma na tambayeki kinki yi min magana"

Harara ta dalla masa idanun  nan kamar su fado ya daure iyakar dauriya kada yayi mata dariya.

"Kishiya fa kace zaka yi min ba dole nayi kuka ba" ta fada tana turo baki.

Sake bude baki yayi harda daga murya ta dora hannu a ka tana salati "so kake a jiyo mu ne?"

"Gara wasu daga waje su zo su rarrashemu duka mu biyun tunda ni baki son nawa"

Hawayenta ta goge da sauri ta tattaro wani murmushin dole ta yaba a fuskarta "na dena don Allah kaima kayi shiru idan aka shigo ai kunya zaka bani"

"Saboda kada kiji kunya kike son nayi shiru....Allah Sarki Dahiru bawan Allah" matso kwalla yake ta son yi abu ta gagara yana ta kikkifta idanu.

"Ba haka bane, ai kai dinne kukan naka har yafi nawa"

Yatsanta karami ya kama ya murda da nasa yana murmyshi "na dena amma kiyi min alkawarin kin dena zama kina kuka ke kadai."

"Nayi" tace ba don ta so ba.

"Ranar da ki ka karya idan na kamaki hukuncinki shine nima kukan zan tayaki in bude murya banda su Attahir makotan hagu da dama duk sai sunji sun shigo"

Ta zaro idanu "kace Allah"

Ya matso kusa da ita "ko a gwada ne?"

Girgiza kai tayi da sauri "rufa min asiri"

Janyota yayi jikinsa suka kwanta ya rungumeta "kukan me kike yi to daga tambayata ina zani?"

Sai da taja hanci ita a dole abar tausayi tace "aure kace min zaka nema na Anti Qareeba anjima"

"Don nace zani neman aurenta ba ina nufin nemawa kaina ba. Solidarity zanyi mata na hadata da Yayanmu Bilya"

Dariya ce ta kwacewa Mawadda farincikinta bai buya ta tashi ta zauna ta goge hawayenta tas "Yayanmu ka rinka bayani dalla-dalla ko don gaba. Kaine baka yi yadda zan fahimta ba amma yanzu komai ya wuce kamar iska"

Hannunta ya riko ta fada kansa gabadayanta fuskokinsu na kallon juna "don Allah kema kina jin yadda nake ji akanki? Sonki nake sosai"

Bayan hannunta tasa ta shafi gefen fuskarsa  "nima haka"

Ya sake narke mata a jiki "Kema me?"

"Abinda kace mana"

Noke kafada yayi yana kara matseta "ni gaskiya a'a ki fada yadda na fada"

Kallonsa tayi yadda ya koma mata shagwababbe tun bayan aurensu. Duk wani ture turen baki ya iya ya sata yin abu ko babu niyya.

Wani abun idan yayi har mamaki take wai Dahirunta ne tun na da can ko kuwa. Komai yayi burgeta yake yi shiyasa idan ya fita sai taji kamar bata da lafiya. Wani dan tunani tayi ta tashi zaune da sauri tana ture shi.

"Me kuma nayi yanzu?"

Bata rai tayi "wallahi ba haka ake yi ba Yayanmu"

"Har yanzu ban fara yi miki yadda ake yiwa amaren bane?" Ya fada yana kamota.

"Ni ka kyaleni bana so"

Muryarsa da take matukar so mai tayar mata da tsigar jiki ya sake ragewa yana turmurmusata "Uhm uhmm ni ina so"

Hawaye ne ya digo mata dama ta iya saurin kuka "ya zaka rinka yi min hakane?"

Ganin abin nata na gaske ne ya dena wasan ya zama serious "what is wrong?"

"A iya sanina mata ne suke shagwaba amma tunda nazo gidan nan kullum kaine kake yi duk ka tare komai. To ni me zanyi don Allah" ta fada tana ware hannuwanta tayi kicin kicin da fuska.

Sai da yayi dariya mai isarsa har ta kule ta fara kai masa duka yana karewa yana cigaba da dariyar yace "idan nayi ki rarrasheni"

"Haka akeyi dama?"

"A gidan Dahiru da Mawadda ba" ya riko hannayenta da take kokarin dukansa dasu.

Kwafa tayi tace "har fa huduba aka yi min akan na rinka maka"

Cikin tausayawa yace "Allah sarki kice a baki wata satar amsar wannan dai na riga bari ma ki gani"

Zillewa ta soma yi ya kankameta suka kwanta yana dariya tana masa kukan shagwaba.

"Iyyeee ashe kin iya, kara sautin muji"

Rasa yadda zatayi dashi tayi duk abinda tayi sai ya mayar na tsokana. Wayarta ce ta soma ringing ya miko mata. Sunan Nawal ta gani amma muryar Attahir.

Muryarsa ta nuna yana cikin damuwa yace "Mawadda ina Dahiru?"

Kansa a cinyarta sai shige mata yake ta kasa magana da kyar tace "gashi nan"

Ajiyar zuciya yayi "bashi please"

Wayar ta dora masa akan kunne ya hada da hannunta ya rike. Attahir yace  "dadinta dai nima ina da tawa matar amma Allah sai na rama. Kace karfe biyar zamu fita amma gashi shida saura kwata ina ta waya baka dauka"

Sai lokacin ya tuna wayarsa na falo. Attahir yana ta mita ya rinka dariya yana bashi hakuri. Idan yana tare da Mawadda baya sanin lokaci ya ja sosai.

Kafin ya ajiye wayar Attahir yace "kuma sai na fadawa Yaya Bilya me ka tsaya yi"

Kashewa Mawadda ido yayi ta kawar da kai tana murmushi yace "me nayi"

"Abinda zuciyarka ta raya maka" ya amsa da shakiyanci.

Jikin Mawadda ya sake makalewa ya sassauta "kai Attahir har kasa naji kunya"

Attahir ya hau salati "shikenan Dahiru ya lalace"

"Muka lalace dai"

Mawadda ta juyo da sauri ya dora hannu akan bakinsa yana duka  sannan ya cewa Attahir ya bashi minti goma yana zuwa.

Kaya ta dauko masa yadi mara nauyi sky blue da hula mai fari da blue itama. Yana shiryawa yace mata shi dai baya son fitar ko yace musu sai gobe.

"Idan ka fasa ma bazan zauna a gidan ba saboda munyi fada"

Turare take fesa masa suke maganar ya karbi kwalbar ya ajiye "duk kin tayar da kwantacciyar soyayya zaki koreni. Haka zan tafi kina yi min gizo"

Kunya ce ta kamata ta rufe ido ya juyata tana kallon madubin.

A daidai kunnenta yace "bude ido ki tayani ganin matata"

Kanta ta kalla ta ba kanta dariya. Dahiru na bayanta yayi kyau sosai ita kuwa kayan jikinta duk sun gama yamutsewa saboda yadda ya tumurmusata akan gadon. Gashin kanta ya fita daga cikin ribbon din shima ya baje ko ina.

"Ji yadda ka mayar dani kamar sabon kamu"

"Sababbin kamu dai....amma na kin gane" ya kashe ido yana rike da hannunta suka je falo.

"Kije kasa bana son ki zauna kiyi ta tunani na kewata na damunki"

"Wai ni yaushe ka zama haka ne?"

"Tun lokacin da na fara ganinki. Sani ne bakiyi ba. Hmm bari naje kada mu tsinci Attahir a bakin kofa"

Bakin kofar kasa ta raka shi zai fita ta riko hannunsa "i will miss you"

"I know"

Ya saka idonsa cikin nata ta runtse nata da sauri. Hannu yasa a bayan kanta ya matso da ita ya shiga kissing dinta kamar wanda za'a kwace masa ita. Horn Attahir yayi da karfi ta ture shi ba shiri ya fita.

Yasha tsiya a mota tun yana ramawa har ya kama bakinsa ya tsuke don duk bakin da yayi yanzu still Attahir ya dama shi ya shanye.

******

*Kwana biyu da suka wuce*


Kamar ta durkusa a gaban mutanen biyu don magiya da roko.  Fito da kudin da bata san adadinsu tayi ba.

"Bobo ga wannan ka bashi kuma na rantse idan ya fito min da Babawo a yau zan kara masa"

Bobo aminin BB wanda a gidansa aka ajiye Mawadda lokacin da suka sato ta. Mahaifinsa babba ne a gwamnati ya taso cikin gata da sangarta kamar BB din. A halin yanzu iyayensa ko keyarsa basa son gani saboda abubuwan kunya da ya jawo musu a unguwa da gari. Shiyasa ya karasa kangarewa duk abinda yasan zaiyi karshe ya komawa iyayensa baya bata lokaci wurin aiwatarwa kawai don ya bakanta musu. Uwa uba BB baisan zafin kudi ba yana sakar masa sosai.

Haj Mara da taimakon kofur Pascal wanda ta jika da kudi ta sami damar ganin BB shine ya bata numbar Bobo yace ta neme shi su fitar dashi.

Sunyi iya yinsu sun rasa hanyar kubutar dashi suka rasa mafitar da ta wuce hada baki da Kofur Pascal.

Kudaden hannunsa ya shafa yaji da nauyi ko da bai kirga ba.

"Hajiya kada ki damu. Nayi miki alkawarin zaki dauki yaronki ku tafi"

Wani abu da ya jima akan kirjinta taji ya sauka. Mutumin da ta bawa miliyan uku domin yayi musu visa ya bace a doron kasa don kuwa ta neme shi ta rasa. Kudaden hannunta sunyi mugun kasa amma bazata karaya ba. Idan Babawo ya fito sai su koma wani garin da zama. Zata ja masa kunne akan mata ko ta sami wata yar masu karamin karfin ta aura masa kowa ya huta.

Sun gama tsarin komai don Bobo master planner ne. Ko satar Mawadda shi ya kawo idea din yadda za'ayi. Wannan karon ma ya baje basirarsa ta kulle kulle kamar wata mace.

*4:07pm Police Station*


Kofur Pascal yana ganin abokan aikinsa  mutum uku da suke teburin karbar korafi na farko da an shigo station din sun bingere da bacci ya kira Bobo yace ya shirya idan komai ya tafi daidai yanzu BB zai fito domin kamar yadda ya fada musu an shiga meeting akan case din wasu barayi. Sa'arsu daya cell din BB shine na farko ana shiga kuma an raba shi da Danmani saboda dukan da yake masa ko da an hukunta shi. Bude shi yayi ya fito sai wari yake ga ciwukan jikinsa jini ya bushe ya dankare. Da sauri sauri suka fito saboda yana kallo security dinsu ya zaga bandaki saboda murdawar ciki a dalilin abinda ya saka masa a fura.

Suna fitowa inda wadancan ke bacci guda cikinsu ashe baccin baiyi nisa ba amma bashi da kuzarin daga koda yatsa sai dai ya ga fitar BB da Pascal wanda ya kawo musu youghurt mai sanyi da aka sakawa maganin bacci.

A guje Bobo ya fizgi mota suka bar wurin shi kuma Pascal  ya koma ya kwanta cikinsu kafin su DPO su fito daga meeting.

Ruwa da abinci wanda Haj Mara ta bada domin yaci kafin su iso inda zaa dauketa su wuce Kaduna ta tattare abinda zata iya su nausa kudu Bobo ya bashi. Kamar tsohon maye haka ya ringa gabzar abincin nan ko taunawa babu. Sai da yaji cikinsa kamar zai fashe yayi wata muguwar gyatsa.

Idanu a kekashe bayan Bobo ya gama yi masa bayanin komai yace "bazan bar garin nan ba sai na lahanta munafukin nan da ya aure min mata. Ko baccin kirki bana iyawa saboda tunanin suna can suna cin amanata"

Dariyar mugunta Bobo yayi "nasan zaka bukaci hakan BB shiyasa rannan nazo station din na bi bayansa bayan Pascal da ya fito da kai ya tabbatar min shine mijinta. To cut the story kit nasan gidansu"

"Muje gidan Bobo"

"What? Yanzun nan? Haba ka bari kaje wurin Hajiyarka idan an natsa kwana biyu ka dawo muje a gabansa wallahi ayi mata aiki"

"Idan banje yau ba bacin rai sai ya kasheni kafin  'yan sanda. Muje da wannan kazamin jikin a gaban idonsa ka daure min shi ya ga yadda ake nunawa mace soyayya"

Tafawa suka yi Bobo ya karkata mota sai unguwar Rijiyar zaki. Suna zuwa gidan Attahir da Dahiru suna fita. Gilashin motar Dahiru saboda tint ne sai suka yi zaton Mawadda tana baya suka shiga binsu har gate din gidan Dr Auwal. Ciki suka shiga da motar su BB suka jira a waje don yau sai ya wulalanta Mawadda da mijinta zaiji dadi. Haj Mara tana ta bugo wayar Bobo amma BB yace kada ya dauka bata plan zata yi.

*******

Da rawar jiki Dr Tani ta fito bakin nan har kunne tana ta murmushi.

"Menene haka 'ya'yana zaku tsaya daga waje. Ku shigo nan gidanku ne ku ba baki bane"

Murmushi suka yi a tare suka bi bayanta. Bayan sun gaisa ta tashi da kanta kawo musu abin sha sai bare-bare take bata son abinda zata batawa Dahiru yanzu ko kadan kuwa. Yaron yana burgeta inama nata ne ko mijin 'yarta.
Tana kawo musu ta tafi kiran Qareeba wai tazo sun zo dubata ne.

Itama da sauri ta tashi Dr Tani tace "yi hankali cikinki bai gama warkewa ba"

"To Mummy zabar mim kayan da zan saka"

Murmushin Dr Tani ya fadada ta dauko mata wani hadadden material ta saka. Fuska tasha kwalliya tana zuba kamshi suka fito tare.

"AHIRIIIINNN" tace tana saukowa baki bude.

"Anti Qareebaaaa" shima ya fada yadda tayi suna dariya shi da Attahir wanda sai lokacin ta kula dashi.

"Attashir ashe tare kuke"

"Eh wallahi Antinmu yaya karfin jiki?"

Sun gama gaisawa a mutumce suna dan taba hira Bilya ya kira yace ya iso dama cewa yayi zaizo da motarsa saboda yana da uzuri daga nan.

Attahir ya fita shigo dashi. Dahiru kuma yace da Dr Tani yana son magana da ita.

Qareeba na zumbura baki ta tashi ta basu wuri.

Hankalinta a dan tashe tace "lafiya dai ko?

"Akan Anti Qareeba ne"

"Dahiru zaka aureta ne?"

"A'a" yace da sauri.

Jikinta a sanyaye tace to me ya faru.

"Hajiya duk abubuwan rashin jindadin da suka faru tsakaninmu basu sa na dena tausayin Anti Qareeba ba. Ni da ke da mutane da dama kowa yasan tana son tayi aure"

Kwalla ce ta ciko a idanun Dr Tani "wallahi Dahiru ko waye yanzu yazo nemanta idan yana da sana'a zan bashi ko don kallon da ake yi mata na wadda aka yiwa fyade. Yar uwarka bata jin kunyar fada min tana son auren nan kaga idan bata yi ba sai mu sami matsala"

"Ko da dan uwana ne kuma makanike?"

Yawu ta hadiya ta kalli idanun Dahiru wanda suka matukar tsorata ta ranar da yace zai kona mata asibiti.

Bakinta yana rawa a hankali tace "makanike?"

Ya dage gira yana jiran ya gani ko zata fadi magana mara dadi su tattara su bar gidan. Duk halin shirmen Qareeba yana ganinta da wani dan mutumci tun bayan abinda BB yayi mata kuma ba don tozarci yake son hadata da dan uwan da bashi da kamarsa ba. Don ko me ya zama yau Bilya ne mafari.

"Eh makanike mai mace daya da 'ya'ya biyar. Yana da kirki fiye da zatonki kuma mutum ne mai tsananin hakuri....and yes yana da garejin kansa yanzu da mota ba yaron kowa bane"

Ga tsananin mamakinsa hawaye ne suke saukowa hadaddiya kuma rikakkiyar 'yar boko Dr Tani.

"Ko a cikin 'ya'ya Dahiru ka fita daban. Nagode kuma in sha Allahu zan baku mamaki a kotu. A shirye nake na rasa komai don ganin bayan Haj Mara da BB. Allah Yasa tayi masa yayan naka"

Murmushi Dahiru yayi wanda ya karawa fuskarsa kwarjini da kyau.
"Kada ki damu da wannan in sha Allah"

Tare suka koma falon lokacin Attahir ya shigo da Bilya. Kana ganinsa ka ga jinin Dahiru saboda kama da suke yi. Dukkansu suna da tsayi musamman Bilya da Danlami da suka rankwafa kadan. Shiga yayi ta kamala yayi kyau kallo daya zaka gane mutum ne mai sanyin hali.

Tunda suka shigo Qareeba ta kasa dauke ido daga kansa don sai da Dr Tani ta zauna a gefenta ta dan daki gefen kafarta tayi firgigit ta dago.

Sun gaisa da Dr Tani a take ya kwanta mata. To ita wane sauran zabe zata zauna bayan duka isharar da tayi ta gani a kwanakin nan.

Dahiru ne ya fara mikewa "Hajiya zamu je wurin Baba Prof mu dawo sai mu wuce gida"

Qareeba ta dago da sauri "dukkanku Ahirin?"

"Yayanmu Bilya zai jiramu a nan ba jimawa zamuyi ba"

Tayi wani fari da ido "no take your time fa sai na zauna dashi kada a barshi shi daya"

Bilya yana jin haka ya daga ya kalli Dahiru. Anya zai iya da wannan tunda yazo dama ta kafe shi da idanu.

Cikin sanyinsa da ya janyo masa raini a wurin Furera yace  "ko dai na biku ne"

Qareeba taji kamar ya mareta daga zuwa sai tafiya "don Allah ka tsaya mu sake gaisawa sai na raka ka gidan. Ba nisa daga nan"

Attahir ya kunshe baki yayi waje Dahiru ya biyo bayansa "ba fa nason iskanci matar Yayana zata zama."

Attahir ya fashe da dariya "solidarity sak dan uwa ai nima yayana ne. Muje mu basu wuri. Amma wallahi kamar tsoronta yake yi. Allah Sarki Yayanmu Bilya"

******

Shiru falon daga Qareeba har Bilya an rasa wanda zai fara magana. Shi bai san ta ina zai fara ba ita kuma nan ta kame ne kada tayi abinda ta saba ake cewa bata da kan gado. Gajiya tayi ta danyi gyaran murya.

"Ehemmmm"

Bilya ya zubo ruwa da sauri ya miko mata "sannu karbi ki sha"

Fari take tana juya idanu kafin ta karba ta dan kurba kadan.

Bilya ya kalli yadda tayi da idanu ya zuba hannuwansa a aljihun riga "me ya sami idanun ko zaki shiga ciki ki wanke?"

Kasa hakuri tayi cikin muryarta ta sangarta tace "wai kai baka taba zuwa wurin mace bane?"

Sai da ya koma ya zauna ya amsa mata "ni da nake da aure da 'ya'ya ma"

"Duk abuna nasan wurina Ahirin ya kawoka ko ba haka ba"

Bilya a ransa yace toohh wannan gaba gadi take sannan ya gyada kai.

"Ina ganin sun fita na gane. Shine kazo babu wani tambayoyi irin wanda ake yiwa mace farkon zuwa kayi shiru abinka."

Murmushi yayi saboda yadda take tuttura baki da gani an saba yi mata yadda take so amma kuma tsoronta yake ji don yadda take magana yasan kila ana jinsu kada azo ace ya yi mata wani abu.

"Yi hakuri gani nayi kamar kinfi karfina shiyasa nayi shiru"

Sunkuyar da kai tayi tana jin kamar kwalla muryarta tana rawa tace "kai dai ka fadi gaskiya ko kaima banyi maka bane? Its ok an saba haka bazan ji haushi ba"

Jikinsa ne yayi mugun sanyi ta bashi tausayi. Mace har mace bai hango wata makusa ba amma Allah bai nufeta da aure ba. Aure babu ruwansa da arziki ko kyau. Idan lokaci yayi ne kawai sai anyi.

"Qareeba ni talaka ne, makanike mai mata da yara kuma dan kauye wanda karatunsa ya tsaya a JSS 3. Ina zan kaiki?"

"Inda ake kai mata"

Hannu biyu tasa ta rufe bakinta bayan maganar ta subutu ta fito ta shige kunnuwansa suka hada ido. Mayafinta da yake a kafada ta dauko ta rufe fuska karo na farko a rayuwarta da taji kunyar wani da namiji.

Wani murmushin ya sake yi "indai zaki iya aurena a haka to wannan talakan yayi alkawarin kaiki inda ake kai matan...dakin aure ne a killace su a basu kulawa"

Tashin hankali mamakin kansa ne ya kama shi. Daga ina yake zaro wadannan zantuka shi kuwa. Qareeba tsabar kunya balle da yace zai aureta ta shiga tattaba wuya ta tabbatar kalau take ba zazzabi bane yasa ta kasa magana.

Yana lura da ita yace "baki da lafiya ne?"

"Ina jin dai ba kalau ba. Kaga na kasa dago kai na kalleka abin mamaki" tace da gaske cikin mamakin.

"Bayan kin gama yi min kirikiri da ido meye baki gama gani ba" ya zolayeta.

Ta sake rufe fuska "ban taba jin haka ba tunda nake akan kowa"

"Me kike ji Qareeba?" Bilya ya sami kansa da tambayarta. Sosai yake jindadin magana da ita.

"Farinciki"

Karamar dariya yayi ta dago da kai "don Allah kada ka samin rai kaima naji shiru. Nasan Ahirin ya fada maka komai a kaina amma wallahi ba'ayi raping dina ba"

Bilya ji yayi ko gobe akace yazo a daura musu aure zai yarda saboda yadda Qareeba ta shiga zuciyarsa musamman saboda tausayi.

"Ki bari nayi zuwa uku sai mu tabbatar da zamu iya zama da juna. Sai dai matsala daya wallahi Dahiru baya son sunan nan Ahirin"

Bude mayafin tayi ta sa dariya "ai wallahi sai dai yayi hakuri sunansa kenan a wurina"

******

Dahiru da Attahir a kafa suka fita tunda ba nisa bane titi kawai zasu tsallaka suyi tafiyar kasa da minti biyar.

Fitowarsu a idon BB da Bobo ya tabbatar Mawadda bata bayansu yace "Bobo dawo nan da sauri"

Chanjin seat suka yi ya tada mota da sauri ya bata wuta. Attahir ya haye dan tudun gefen titi inda zai sada shi da gidansu shi kuma Dahiru yana daga bayansa. Daga kafarsa ke da wuya basu san daga ina ba sai ganinsa suka yi yayi sama saboda wani mugun bugu da BB yayi masa ya dawo ya daki kan bonnet dinta ya fadi kasa ko motsi kwakkwara baya yi.

Attahir mutuwar tsaye yayi har maigadin gidan Dr Auwal da wasu maza suka taho suna kokarin daga Dahiru. Jikinsa gabadaya ji yake kamar an sara masa guduma. Bai tashi gane me yake yi ba sai da suka yi ido da ido da BB Sule Chanji yayin da ya fizgi motar a guje kamar zai tashi sama.
[31/01 9:36 am] Batuul Mamman: *GUMIN HALAK...*💰23

*Batul Mamman*💖


Kwanaki shadaya da auren su Dahiru wanda yayi daidai da kwana goma da tarewar Mawadda. A dan tsukin lokacin nan shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu. Duk abinda Dahiru zaiyi domin ya cire mata tsoro kuma ta saki jiki dashi yana yi. Shiyasa bata da wata damuwa sai ta kokarin kyautata masa.

Zamansu gwanin sha'awa kana ganinsu kaga masoyan da suka yi nisa cikin soyayyar juna. Tsakaninsu dasu Attahir ma sai son barka. Matan suna matukar kokari su hada kai domin jindadin mazansu. Nawal bata da matsala. Yadda ta rungumi Mawadda babu kyama ko nuna ta fita domin ita a yanzu bautar kasa zata fara sabanin Mawadda da Adult education tayi.

Yau da sassafe matan suka tashi saboda aikin da yake gabansu. Gidan Baba Prof zasu je daga can kuma kowanne zai tafi da matarsa gidan iyayenta. Washegari kuma Dahiru da Mawadda su tafi Tariwa su kwana biyu.

Mawadda ta gama tuwon shinkafa da miyar agushi tun daga falo kamshin miyar sai yasa yawu tsinkewa. A kasa kuma Nawal ta kusa gama suyar samosa da doughnut da zasu hada su kai musu.

Shadaya da rabi ta gama komai harda breakfast ta gyara gida ta koma daki domin tashin Dahiru sannan tayi wanka. Filon da take sawa tsakaninsu dogo shi ta gani a kasa shi kuma yana amsa waya.

Wardrobe ta bude inda ta jera musu kayansu ta tsaya tana karewa kayanta kallo.

Bayan Dahiru ya gama wayar taji yace "Matar Dahiru yau ba gaisuwa?"

"Ina zuwa gaisheka na ga ka jefar min da dan amana a kasa"

Dariya ya soma yi yayi rub da ciki ya rike fuskarsa da hannuwansa.
"Kin jawo masa yau zan jefa shi ta taga ma. Haka kawai kullum yana tsakiyar mata da miji shi ko tsoron daukan alhaki baya yi ma"

Sai da tayi dariya tace "babu wani hakki, tunda hannunka ya warke ko zaka koma kasa? Idan ka sauka da kaina zan jefar da filon"

"Haka ma zaki ce? Kwana kike makale da shi fa ga bawan Allah a gefe" ya nuna kansa yana bata rai.

"Laushi ne dashi baka ji ba kamar auduga"

Dauko shi tayi daga kasan ta mika masa wai ya taba yaji laushin. Yana karba ya cilla shi wurin kofa.

"Indai laushi kike nema to kisha kuruminki na fishi. Yau don Allah in meye gurbinsa kinji"

"Kai bread ne?"

Tana fada ya taso yayi kanta tana dariya zata gudu ya janyota kan gadon ya danneta "nine bread din?"

Dariya take sosai "wasa nake yi Yayanmu"

"Sai fa kin dauki bread dinnan yau" yace yana sakar mata nauyinsa.

Nishi ta soma "wayyo Babana mijin Mawadda zai ballani, tsokanar da kake min zan rama amma na fasa kayi min rai tuba nake"

Kadan ya dagata amma yadda bazata iya tashi ba.

"Waye ni?"

"Mijin Mawadda mana"

"Ba kaninki ba ko yayanki ba?"

Sake sakin nauyinsa yayi tace "inaa da kenan, yanzu ka hada duka harda aboki da miji"

"To me zaki bani?" Ya kuma danneta.

"Me kake so? Wayyo kirjina Yayanmu nauyi gareka fa"

Dagata yayi suka tsaya ya nuna filon "kishiyan can nawa zaki dauke yau daya dai a barni na kwanta kusa da amaryata"

"Washhh, naji kuma dole na amince kafin ka rabani biyu"

Hancinta yaja yana tsokanarta reshe ya juye da mujiya. Tazo tsokanarsa abin ya koma kanta. Fada masa tayi ta gama girki da komai gara suyi wanka kada su Attahir su jirasu.

Wata atampa ta nuna masa a kayanta ya girgiza kai ta cigaba da nunawa yana cewa basuyi ba. Sai da ta nuna wani lace mara nauyi ruwan toka da digon ja yace shi zata saka.

Fita yayi ya bata wuri ta shiga wanka shi kuma ya kira lauyansu suna tattaunawa akan case din. Ya sanar dashi yadda suka yi da su Qareeba ta fada masa duka wani abu da ya bukata. Dr Tani da Maigadinsu zasu bada shaida tare dashi kansa Dahirun.

"Yanzu statement din matarka nake bukata duk da na samu wasu bayanai a police station din"

"Idan babu damuwa sai mu hadu ranar litinin in sha Allahu sai kayi mata tambayoyin. Mungode sosai"

"Aikina ne Dahiru. Allah Ya bamu nasara"
******

Daya saura gidajen biyu sun gama shiri. Dahiru da Attahir suna tsaye jikin motocinsu suna hira da tsokanar juna. Kusan minti biyar babu wanda matarsa ta fito.

"Wato da gaske dai idan za'a fita da mata sai anyi jira"  cewar Dahiru

"Ga alama ka gani kamar sun hada baki. Shikenan muma mun girma. Yadda manya suke mitar jiran matansu yau abin yazo kanmu"

Dahiru ya soma dariya "sai yanzu ka girma ashe?"

"Ana shafa Fatiha nace to girma salamu alaikum"

Tafawa suka yi suna yiwa juna shakiyanci aka turo karamar kofar gate din da suke bari a sakaye.

Hayaniyar yara suka fara ji kafin Furere ta sako kafa tana cewa su shigo. Su biyar ne yaran harda ita da Hansa'u mutum bakwai.

Dahiru na ganinta ya hade girar sama da kasa. Dazu da safe lokacin da Mawadda take aiki a kitchen wayarta ce ta tashe shi ta sanar dashi zasu zo yini ita da yara. Tun a lokacin ya fada mata fita zasu yi kuma dama har gidan zasu je  domin a basu girmansu na yayyensa. Tana jin haka ta tambayeshi yaushe zasu tafi yace suna yin azahar. Wato shine ta tare shi don kawai ta bata masa rai.

Har suka shigo ya kasa sakin fuska sai da Attahir ya tabo shi "meye haka ne Dahiru?"

Saurin gyara fuskarsa yayi "babu komai zamu dan bata muku lokaci matar Yayanmu Bilya ce"

"Na gane ta"

"Dan bani minti goma su gaisa da Mawadda sai mu tafi"

"Haba Dahiru don Allah kuyi zamanku gobe ko wata ranar sai kuje."

Karasowa suka yi Hansa'u tana tafiya kamar ta karye saboda kwarkwasa.

"Ango kasha kamshi kace gara da muka zo yau din tunda fitar bata yiwu ba"

Attahir ne ya masa kallon yayi shiru ya daure yace tazo su hau saman.

Yana bude kofar Mawadda tana yafa mayafi ta rike kunnuwanta "sorry"

Kallon mutanen da suke shigowa tare dashi tayi ta saki fuska duk da bata sansu ba ta ajiye mayafin a hannun kujera.

"Baki muka yi haka? Sannunku da zuwa"

Wurin kofar taje da fara'arta tana cewa su shigo su zauna.

Hansa'u ta tsura mata idanu kamar ta cinyeta har sai da ta tsargu.
"Ba baki bane. Matar yayansa ce da 'yaranta ni kuma kanwarta ce"

Murmushi Mawadda tayi "Allah Sarki ku zazzauna mana bari na kawo muku lemo yau akwai rana"

Anti Furere ta hakimce akan kujera "Allah Yasa da sanyi dai"

Mawadda bata tanka ba ta wuce kitchen. Hansa'u da Anti Furera suka bita da na mujiya. Riga da zani ne a jikinta na lace da gani yana da tsada. Rigar tayi mata kyau sosai ta fiddo da surarta wadda take tafiya da Dahiru duk sanda ya kalleta. BB kansa wannan jikin ne ya fara kwadaita masa ita. Bata fiye tsayi ba don bata cikin layin dogaye ma amma surar jiki da kyaun fuskarta suna daukar hankalin mutane da dama.

Tana tafiya Dahiru yace "Anti ba na fada miki zamu zo ba?"

"Dahiru korata zakayi daga gidanka? Ikon Allah sai kallo. Yau kayi arziki kayi aure dole ka wulakantani"

Kallo ya bita dashi na takaici bai iya bata amsa ba ga yara a wurin. Mawadda ta fito musu da lemuka masu sanyi da ruwa. Sai cake da snacks din da Nawal ta miko mata. Itama tuwon da tayi haka ta dibar musu ta bata idan sun dawo babu mai yin girki.

Zama tayi ta sake gaishe da Anti Furera ta dauko kofuna zata tsiyaya musu lemon.

"Da kin bari kowa ya dauki roba daya zasu iya shanyewa"

Tayi murmushi "to shikenan"

Hansa'u ta dauki remote ta kunna TV ta shiga canja tashoshi. Rai a bace Dahiru ya tashi ya koma daki. Duk wannan.abin yasan ana yi ne kawai don yayi magana. Rigarsa ya cire yayi jifa da ita daga shi sai dogon wando da singeleti ya kwanta ya soma kiran Mawadda.

Tana zaune a kasan kafet suna ta hayaniya su da yaran babu mai kula ta taji yace "Babyna"

Yadda suka tsura mata ido da mamaki itama shi din ne ya kamata.

Hansa'u jiki yayi mugun sanyi kamar tayi kuka dama tana ganin Mawadda ta raina kwalliyar da tayi.

Anti Furere ta soma fada "wane irin abu ne wannan nazo da yara za'a bata musu tarbiya."

Da sanyin jiki ta tashi ta tafi. A kwance yake ya daga hannu yana mata alamar ta taho ta bata rai "Yayanmu so kake ka bani kunya?"

Sai da ya taso ya rike hannunta ta zauna akan gadon sannan ya kwanta ya dora kansa a cinyarta abin yazo mata wani iri.

Dago kai yayi yana kallon fuskarta "kiyi hakuri to. Anti Fureran ce sai da haka."

"Saboda me?"

"Kiyi dai hakuri nasan zasuyi ya yin abubuwa don kiji haushi. Da biyu ne Hansa'u taso na aura"

Kallon idanunta yayi da suka nuna zallar kishi ya kuwa kankameta sosai ta hanyar zagaye kugunta ya cusa kansa wurin cikinta.

"Kada ki damu ke kadai nake so Mawaddatan wa Rahma. Na fada miki ne don kada ranki ya baci ko me zasu yi"

 A hankali tace "to sakeni na koma kafin nayi laifin barinsu su kadai"

"Uhmm uhmm" yace yana kara matseta "ni mu zauna a haka"

"Don Allah"

"Kiss me"

Jikinta taji ya soma rawa tsabar kaduwa da kunya ta shiga ture shi "ba zaki tashi ba fa sai kinyi yadda nake so"

Cije lebenta tayi ya janyo kanta daidai fuskarsa ya shafa leben "wannan abin yana burgeni sosai" ya karashe da kissing dinta.

Kamar daga kofar dakin suka ji ana cewa "Kawu Dahiru Umma tana kiranka"

Firgigit suka tashi daga shi har Mawaddan yace "kin gani ko"

"Ba laifinsu bane kaine ka janyoni"

Doguwar riga yasa suka fita tare.

"Don munzo gidanka shine zaka mana wulakanci Dahiru?"

Mawadda ta nufi dinning table inda ta ajiye abincin da ta shiryawa su Haj Mama bisa umarnin mijinta.

"Yi hakuri Antinmu kirana akayi ta wayarsa ni tawa ta lalace. In kawo muku abincin nan kasa ko na barshi a nan?"

"Sauko dashi muna kallo muna ci"

Haka ta kai musu ta hado da plates suka ci suka sha ba godi bare nagode. Sai ma da suka gama Hansa'u tace wai zuciyarta tana tashi kifin miyar yana neman dawo mata. Mawadda tana yi mata sannu taje ta kawo mata cingam.

Zama tayi cikinsu tana hira da yara tunda su tasu suke daban.

Labulenta Furere ta nuna "laaa Hansa'u kinga irin labulen nan da muka gani a kofar wambai mutumin yace akwai kyau a ido sai rashin kwaliti shiyasa suke arha"

"Aikuwa shine. Tun dazu nake masa kallon sani"

Maganar ta yiwa Mawadda zafi sai share. Sunyi dabdalarsu a gidan har akayi magariba. Bayan ta sake yi musu girki sunci abinci tana wanke-wanke Hansau ta sake cewa tana jin tashin zuciya. Daga kitchen din ta fada mata inda zata duba a falon ta sake daukar cingam.

Anti Furera ta tashi tayi hanyar kitchen din "Ke kuwa da anyi magana sai ki ce aci cingam kamar wata tsohuwar karuwa"

Ko motsi Mawadda ta kasa don bakinciki itama Hansa'un da akayi dominta fuskarta ta sauya alamun rashin jindadi.

Ganin haka nata jikin yayi sanyi ta tura babban danta har dakin su tace ya kira Dahiru yazo ya kaisu gida. Duk da baiji dadin shigar yaron ba don a kalla shekarunsa kusan sha daya amma yaji dadin zasu tafi. Jeans da shirt ya saka ya fito.

Kowa ya mike  burin kunya Anti Furera har kitchen ta shiga "amarya mu zamu tafi babu rakiya"

"Hannu zan dauraye gani nan"

Ta rakasu har kofar kasa da irin tarkacen gidan amare kayan zaki da na kwalliya da ta bawa yaran. Ta yiwa Dahiru adawo lafiya ta koma. Tana rufe kofar saman hawayen da ta rike tun da aka jefeta da wannan kalma suka soma zuba ba kakkautawa.

Da jan kafa ta koma ta gyare gidan tsaf tana aiki tana sharar hawaye. A ganinta fyaden da aka taba yi mata shine dalilin da yasa har Anti Furere ta iya danganta ta da wannan kalma.

Idanunta sun kumbura da ta fito daga wanka ko abinci bata iya ci ba ta saka rigar bacci mai kyau tayi kwanciyarta.

Tunanin rayuwa da yadda abubuwa suka kasance mata take yi har dawowar Dahiru.

Rufa tayi har ka don kada ya ga hawayenta sai ya zaci bacci tayi ya shiga wanka. Da ya fito har lokacin bata bude kanta ba ya zauna a gefenta ya dan ja bargon "wannan irin rufa iska na shiga kuwa?"
Rike quilt din tayi yana ja tana ja "dama idonki biyu kina jina?"

Shiru ba amsa ya zagaya bayanta ya bude bargon.

"Ka fita ka shirya" tace tana kara rikewa.

Budeta yayi da karfi "naki." Sai kuma ya bude baki hankalinsa a tashe "...Mawadda me ya sameki? "

"Bacci nake ji sosai kawai"

Ya bata rai "wane irin bacci? Kukan me ki ke yi?"

Gabanta ne ya fadi don kuwa bazata taba fada masa ba. Tun da can surutu ba dabi'arta bane bare yanzu da iyaye suka ja mata kunne akan kai kara musamman ma ta dangin miji.

"Na fada maka bacci ne"

Ya daga murya "Me tayi miki?"

"Wa?"

"Anti Furaira. Dama tun da zasu tafi na kula baki da walwala sai na zaci gajiya ce."

Kwantar da kanta ta sake yi akan filo "nace babu komai ko karya kake so nayi maka?"

"Mawadda ba wasa nake yi ba. Ko ki fada ko na koma gidan na tambayeta da kaina, kinsan kuma zan iya"

Tashi ta ga zaiyi ta riko hannunsa da sauri. Tasan abinda ya sakata kuka zai bata masa rai shiyasa da ya zauna sai ta fada masa abinda suka ce game da labulen falon. Sai da ta gama ya riko fuskarta a cikin tafukan hannunsa.

"Shagwaba ko Matar Dahiru. Da nine ke sai nace na gidanta na fada miki a bakin rimi aka kada masa kararrawa. Amma bari idan munje gidan sai ki rama"

Murmushi tayi ganin sakayawar tayi rana.

"Hankalina ya tashi sosai nayi zaton abin yafi haka. Shima idan munje baki rama ba zan rama miki da kaina"

Kwantar da kanta yayi a kirjinsa yana shafa gashinta. Tunawa yayi da ya ajiye su a gida Hansa'u ta biyo shi bakin mota tana cewa yayi hakuri yasan halin yayarta. Ya tabbatar abin da suka fada yafi haka kuma shine dalilin da yasata kuka ya kuma sa Hansa'u bashi hakuri. Bazai turasata ta fada ba amma zai rama ita kanta Fureran ranar da komai zai tabbata yana so tasan shine yayi  hadin wannan auren don ta tuna me ta yiwa matarsa.

"Kinyi bacci ne?"

Dago kai tayi a hankali dama kunya ta hanata tun dazu ko shiryawa baiyi ba yazo ya zauna.

Ya dage gira "Shine kika wani kwanta min a jiki kamar kin sami bread"

Kunya taji zata janye jikinta ya sake riketa yana fada mata kalamai masu sanyaya zuciya cikin nutsuwa ya fara nuna mata dadaddiyar soyayyar da ya jima yana dakonta.
******

Dahiru ne ya fara tashi da asuba. Mawadda tana kwance a jikinsa tana baccin wahala. Godiya yayi ga Allah da ya bashi ita domin baya nadama ko kadan da irin son da yake mata. Duk wata kulawa da soyayya da ango zai bawa amaryarsa ya bawa Mawadda. Jin nauyinsa da girmansa ne ya karu a wurinta shi kuma ya sami damar tsokanarta son rai.

Tafiyarsu Tariwa ce tasha ruwa don yace yanzu ya fara angwanci babu inda zai je ta gama nacinta ta hakura ta koma tana zumbura baki. Sai akayi sa'a Baffa ma ya kira yace su hakura da zuwan yafi son tazo bayan an gama case dinnan ta dawo garinsu da martabarta.

Suna zaune a falo ya hanata sakat duk inda ta motsa yana nan tace "yau babu inda zamu je kenan?"

"Haba Matar Dahiru a taimaka min mana. Saura kwana uku na koma aiki kuma dan lokacin nawa sai kin cinye shi a yawo?"

Har ta fitar da rai yana dawowa gida daga sallar la'asar yace ta shirya su fita.

Tunga ya kaita murna ta isheta kafin ya tsayar da motar ta kama kofa zata fita.

"Tsaya mana"

Ta dakata tana ta murmushi zata ga iyayenta  kamar ta shekara basu hadu ba.

"Ba dadewa zamuyi ba saboda zamuje siyan wayarki."

"Yayanmu nagode" tace tana murmushi

"Rike godiyarki sai mun koma gida a gidan ma a daki, a dakin ma kuma..."

Hannu tasa ta toshe kunnenta ta fita tana dariya. Tare suka shiga gidan zo ku ga murna wurin su Yaya. Ade kam baki yaki rufuwa. Yau ga Mawadda tayi aure tayi fes da ita. Duniya bata ga dan kwarai kamar Dahiru ba. Bata fata Mawadda ta bata masa rai daidai da wuni daya. Sun sha hira Dahiru yana tare da Baba suna maganar shiga kotu.

Da zasu tafi Yaya har kofar gida ta rakota. Sai da Mawadda ta tare lafiya  a gidanta ta sami nutsuwa sosai a ranta don duk shekarun nan tana baiwa kanta laifi a matsayinta na uwa gareta. Tana tsoron zargin mutane akan cewa nata 'ya'yan babu wadda ta taba fuskantar matsala makamanciyar wannan sai 'yar kishiya.

Kamar yadda yayi alkawari ita ya baiwa damar zabar waya. Ba wani sanin mai kyau tayi ba ta nemi ya tayata zabe. Waya mai kyau da tsada ya saya mata sannan suka wuce gida. Aka bude sabon shafin soyayya.
******

Barr Jibril Jibril (JJ) shine lauyan da zai karesu. Kafin Dahiru ya neme shi sai da yayi bincike sosai aka tabbatar masa da cewa yana da gaskiya da amana.

Suna zaune a ofishinsa su uku washegari yana yiwa Mawadda tambayoyi bayan ta bashi labarin komai tun daga farko. Tana yi tana kuka Dahiru ya rike hannunta ya matse "ina tare dake a kowacce gaba Mawadda, duk abinda kika san zai taimaka mana ki fada boyewar bazata amfanemu ba kuma ita ce take cutar da victims irinki"

Kai ta gyada tana kallonsa. Sun burge JJ sosai yace "anya na taba ganin masoya irinku?"

"Babu" Dahiru ya amsa masa yana murmushi "Wannan Dahirun da Mawaddansa su kadai ne"

Dariya suka yi su biyun kafin JJ yace "Mawadda asibitin da aka kaiki a Bebeji muna bukatar likitan idan zai yiwu yazo a matsayin shaida. Yaya sunansa?"

Nan fa daya ita bata san sunansa ba, kamanninsa ma ta wuya ta tuna. JJ yace babu damuwa tunda sun san a wane wata ne da shekarar zai taimaka musu wurin gano shi da sauki.

"Sai kuma 'yan sandan da suka zo suka sa hannu aka karbeki. Mal Dahiru idan mun gano su kuma munyi sa'a akwai hotunan da suka dauka akwai yiwuwar muyi amfani dasu a kotu domin samun biyan bukata"

Mawadda tayi saurin kallon Dahiru cikin tashin hankali. Idan bata manta ba harda su baya da cinyoyi inda shatin belt din BB ya fito duka an dauka. Sauran kuwa fuska ce da wuya.

Barr JJ ya kula da yanayinta "sai ta kure zamu nuna idan mun sami karancin shaidu masu gamsarwa. Fatanmu Allah Yasa su ma suna nan"

Dahiru yace babu damuwa wannan case din ba da wasa suka fara shi ba saboda haka zasu bada goyon baya yadda ya kamata.

Ta cigaba da amsa tambayoyi ta bada numbar Dr Imran a nan take Dahiru ya kira shi ta bayyana masa matsayinsa da dalilin kiran. Baya gari akayi auren shiyasa baiji labarin saceta ba. Shima dai ya amince duk bayanan da zasu tabbatar da gaskiyarta da magudin waccan shari'a zai tattara kafin a neme shi.

Mutane na karshe sune su Garwashi. Dahiru ya fada masa halin da ake ciki yace zasu zo solidarity wajibi. Abin yayi masa dadi yace idan babu damuwa yana son ganinsu washegari zai fada musu inda zasu hadu tare da barrister domin daukar nasu bayanan.

A hanya yana tuki da hannu daya dayan kuma ya rike hannun Mawadda yake fada mata yana so ta yiwa su Garwashi abinci gobe.

"Amma fa ba a gida zamu hadu ba. Ina tunanin me ya kamata nayi musu ne domin gyara rayuwarsu. Ba don su ba da bansan a wane hali muke yanzu ba."

"Yayanmu mutane da yawa sun kuntata mana a rayuwa kuma da yawa sun kyautata mana. Idan na tuna hakan sai in kara jin imani a zuciyata. Komai na Allah yana tafiya bisa tsari ne"

Gabansa yake kallo yana yi mata magana "Shiyasa karbar kaddara ga mumini yake cikin shika shikan imani. Kinga yau mun wayi gari ma'aurata sabanin wadanda da munyi aure shekara takwas da suka wuce bazamu zama haka ba. Munyi kuka mun kuma yi hakurin rashin juna cikin talauci da rashin ilimi. Yanzu kuma mun zama mallakin juna cikin rufin asiri da ilimin"

Kallonsa take cikin so da yarda "Allah Ya saka maka da dukkan alkhairi Mijin Mawadda. Babu inda zanje in kasa fadin ina sonka saboda kai abin so ne. Kaine babban arzikina a wannan duniyar. Allah Ya bani kai a aljannah"

Ya dauki lokaci maganganunta suna masa yawo a kansa ya rasa amsar da zai bata saboda tsabar farinciki.

"Allah Ya kaimu gida lafiya in baki tukwicin wannan addua"

"Ni dai na yafe bacci ma nake ji" ta kakalo hamma.

Ya rike haba "Oh yarinyar nan me kike tunanin ina nufi?"

Tuni ta dago tsokanarta zaiyi tace "ba tausar da kace zaka yi min da safe kake nufi ba? Kai me ka zata ina nufi?"

Dariya yasa "shikenan duk mu wayance kowa eya rike nasa a zuci"
******

Dahiru da Attahir suka je wurin Barr JJ a wajen office dinsa sai ga su Garwashi da mukarrabansa su Loba boy. Sunci abinci harda santi wanda aka zuba musu a pack yace sako ne daga Mawadda.

"Ayya da bata wahalar da kanta ba. Yo meye amfanin famili ne banda abinka? Mu fa yanzu mun zama surukanka tunda akwai alaka ta jini tsakanin kakaninta da matar Kawun Loba boy"

Attahir ya soma dariya "hakane dan uwa kuma gashi dole mu rinka yiwa juba solidarity"

Garwashi ya mika masa hannu suka tafa "ashe kaima duk famili dinne Allah Wallahi....to dai yanzu ya ake ciki kada fa muje daga bada shaida a rufta damu gidan maza ko kuwa gayis?"

Dahiru ya kalli JJ cike da damuwa ba zai so aikin alkhairinsu ya juye a kamasu a matsayin 'yan daba ba.

"A lokacin ba ku bashi wani information da zai cutar da ita ba. Sannan baa tuhumar ku da komai so ina ganin babu matsala in sha Allah"

******

Da yamma Dahiru ya fadawa Mawadda zasu fita da Bilya da Attahir.

"Zaki je wurin Nawal ko zaki kwanta idan na dawo muyi hira"

"Wurin Nawal zani idan ka dawo muyi bacci dai"

Dariya yayi yana cewa sai ya dawo din a zabi daya sannan yace "Gidansu Anti Qareeba zamuje neman aure"
[31/01 9:36 am] Batuul Mamman: *GUMIN HALAK...*💰25

*Batul Mamman*💖



Da gudu Attahir yabi motar batare da yasan ina zata ko me yake yi ba. Ko kadan bai cimmata ba ya sake dawo a guje wurin da Dahiru yake ya samu maigadinsu Qareeba ya dora kansa a cinyarsa yana ce masa ya dauko motarsu a tafi asibiti. To yace kawai ya tafi gidan tsabar rudewa ya ma manta gidan nasa iyayen yafi kusa.

Gate a rufe ya shiga bugu baji ba gani. Dr Tani tana sama dakin mijinta don tuni ta sallama nata dakin inda aka kusa gamawa da Qareeba ta jiyo bugun. Tasowa tayi tana mitar waye da gajen hakuri kuma ina maigadinsu.

Mai aikinsu mace ce tazo ta zare sakatar da basu san ta yaya akayi ta dawo ta rufe da kanta ba ya banko kofar ya shiga.

"Bude min gate, bude min da sauri" yace yana kokarin zura mukullin gidansa ya bude motar.

Dr Tani har ta fito lokacin ta ganshi duk a daburce. Dama Haj Mama takance Attahir bai iya shiga tashin hankali ba tamkar mace idan ya rude kasa tunanin kirki yake. To a yanzu Attahir babu abinda yake hange sai Dahiru yana ganin kamar ya mutu ne.

A tsorace tace "Attahir me ya faru haka?"

"Dahiru ne. BB ne yazo ya buge Dahiru da mota zan kaishi asibiti" ya amsa yana laluben aljihunsa babu mukullin motar da ya manta suna wurin Dahiru.

Bilya ne yace "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" fitowarsu kenan shi da Qareeba  su ma sunji bugun da takun Dr Tani cikin sauri.

Duka su hudun tare suka fita. Motar Bilya tana waje yayi saurin budeta. Baba Prof da Haj Mama sun fito tana kuka maigadinsu ne ya fada musu. Dunguma suka yi sai asibiti hankalin kowa a tashe.

Emergency akayi da Dahiru domin samun taimakon gaggawa. Ana cewa hatsari ne likitoci suka fara cewa a nemo 'yan sanda. Ana cewa 'yan sanda Bilya yace a nemi wayar Dahiru a kira DPO din bompai su ji ya akayi haka ta faru sannan su zo domin a karbe shi. An dauko wayar ta kwankwatse aka saka sim din a wayar Attahir yana sawa kuwa wayar wani inspector ta shigo.

"Mal.Dahiru ina ka shiga muna ta nemanka. Babawo ya gudu yanzu haka nemansa muke ido rufe..."

Wata tsawa Attahir yayi rai a bace "Dahiru yana kwance yanzu haka muna asibiti BB ya bige shi da mota saboda sakacinku"

Inspector ya zaro idanu ya mikawa DPO. Yana karba ya tambayi asibitin da kansa da wasu suka tafi yayin da suka baza nema BB lungu da sako.

Kafin su iso Baba Prof yana zaune ya mike da sauri "Mawadda, Attahir su Mawadda suna gida?"

Hankulansu sai lokacin suka kara tashi ya amsa a gigice yana tunanin Nawal da Mawadda su kadai a gidan.

"Suna gida Baba bari na tafi"

Bilya yace ya dakata "daga nan zuwa unguwarku da tafiya Attahir abinda yafi shine su fito daga gidan. Danlami ne a kusa bari na fada masa amma dole su fito yanzu yanzu babu bata lokaci"

Jikin Haj Mama da Dr Tani yayi mugun sanyi domin kuwa tun dazu ya kamata suyi wannan tunanin. Yanzu da wuya idan su BB basu je ba indai sun san gidan.

Qareeba harda kuka ganin Ahirin a wannan yanayin ga kuma matarsa ana tunanin zai je gidansu.

Attahir ya dage sai ya tafi Baba Prof yace ya fara kira masa Nawal ya bashi wayar zaiyi mata magana. Kuskure kalilan zasu yi komai ya ruguje BB ya sake samun dama a karo na biyu.

Shi dai Attahir ji yake kamar ya tashi sama haka ya kira Nawal shi kuma Bilya ya fadawa Danlami ya gaggauta zuwa gidansu Dahiru ya taho dasu.

******

Nawal zata shiga wanka kenan wurin karfe takwas na dare taji wayar ta dauka da murmushi ganin sunan mijinta. Muryarsa ce ta bata tsoro yace ta rike waya Baba zaiyi mata magana.

Cike da nutsuwa da kokarin danne tashin hankali saboda sanin halin mata yace "kuna tare da Mawadda?"

Gabanta yayi mugun bugu tace masa ta tafi gida yanzun nan.

"To ki saurareni da kyau Nawal rayuwarki da ta Mawadda tana ga Allah tana gareki"

Fitsari ne kawai bata saki ba bayan Baba Prof ya gama fada mata yadda zata yi da halin da ake ciki.

Kayan da ta cire ta saka da sauri ta dauko mukullin motar Attahir da gudu har tana tuntube ta hau sama.

Mawadda tana hada fruitsalad ta ganta ta shigo babu sallama ta tashi tana neman gudu kafin taji me yake faruwa.

"Nawal ke da waye?"

"Dauko mayafi Mawadda yi sauri"

"Lafiya?"

Daurewa take kada ta tsorata amma abu yaci tura "BB ya gudo daga police station"

Wata irin kadawa cikinta yayi har ya kulle taji gumi yana kwararo mata. Hannu na rawa ta rarumi wayarta tuni har ta soma hawaye "Yayanmu zan kira Nawal yaya zanyi?"

Sai kuka tana ta kokarin kira Nawal ta karbe wayar ta dauko hijabin da ta ajiye a falon bayan ta dawo daga kasa ta dora mata.

"Tuki yake yi hankalinsa a tashe yake shine Yaya Attahir yace gara mu fita kada mu zauna a gidan"

A gurguje suka sauko suna zuwa bakin mota Mawadda ta koma sama da gudu ba jimawa sai gata da tabarya da muciya tayi musu riko na musamman.

Gate taje budewa Nawal da ta iya mota tun a gida ta tayar da ta Attahir ta juyata yadda zasu iya fita. Batare da bata lokaci ba suka shiga ko rufe gidan basu yi ba suka fice daga layin.

Suna hanya Danlami ya kira suka sanar dashi inda suke yace su hadu a Health Matters wani sabon asibitin kudi.

A gigice tace "wurin wa zamu je?"

"Mu hadu a can din dai kada ku tsaya ko ina"

Kashe wayar yayi ta shiga rusa kuka jikinta yana bata wani abu ya sami Dahirunta. Ta tabbata ba tuki ba ko me yake yi bazai taba kin nemanta ba idan yaji BB ya fito. Ta rasa me yake faruwa sai addu'o'i take janyowa.

Layi biyar su BB suka shiga suna neman gidan Dahiru amma kamar wandanda aka shafewa kwakwalwa sun kasa tuna wanne ne gidan har fada ya kaure musu. Bobo yana layi na uku BB yana cewa dazu da suka zo layi na hudu ne. A wannan yanayin su Nawal suka wucesu batare da sun gane su ba.

Daga karshe sun gane gidan a layi na biyu amma ganin gate din irin wanda ake ja gefe a bude suka san cewa tabbas babu kowa a ciki. Duk da haka sun shiga ga sun ga shatin yadda Nawal taci taya wurin ribas. Duka BB ya kaiwa gate din da hannunsa wani mugun bakinciki yana cin ransa. Yaso kwarai ya sami Mawadda da sai yayi mata rashin mutumci fiye da wanda yayi mata a shekarun baya. Wulakanta ta yayi niyar yi saboda tana zaman aure da mutumin da ya zubar masa da hakora har uku.

Bobo ya dafa kafadarsa "BB kazo mu tafi kasan dole 'yan sanda zasu biyo ka"

"Bazan iya hakura da yarinyar nan ba fa. I must have her kafin na haukace da sonta" yace yana furzar da iska.

Bobo yayi murmushin gefen baki. Wai soyayya BB yake kira. Wannan abu yafi dacewa da hauka zalla amma yadda ya kula ransa ya kai kololuwar baci gara yayi shiru.

Chanjin wurin zama suka yi ya dauko kwalaben giya biyu daga karkashin kujerar ya bawa BB wai ya sha yaji sanyi a ransa. Ba bata lokaci kuwa ya kafa kai duka kwalba biyun ya shanye kafin su isa gidan wani kawun Haj Mara inda ta koma a dole saboda kudin hotel yana ruguza musu guzuri. Kawun nata ma dai a bisa dole saboda girman zumunci ya bata masauki ba don yaso ba.

*******

Suna shiga asibitin Attahir da Danlami da yazo a babur din abokinsa suna bakin gate. Ko kashe motar bata yi ba suka fito Nawal tayi wurin Attahir da gudu Mawadda kuwa ciki tayi saboda ganin adaidaita sahu ya ajiye iyayenta a ciki.

Su Yaya sunyi zaton ta san Dahiru ne a kwance suka fara tausarta akan hakuri. Wani irin kuka ta saka ta wuce ciki idanunta rufe da hawaye masu dumi.

Kofar dakin da ta hango Bilya da 'yan sanda wurin biyar ta nufa sai ga Qareeba da basu taba haduwa ba ta taho ta rungumeta cikin muryar rarrashi da tausasawa tace "Mawadda ki dena kuka zai tashi in sha Allah"

Ita bata san wannan ce Anti Qareeba ba sai dai kawai ta tsinci kanta da kankameta saboda wani tukukin zuciya da ya debota tana jin kamar ta zube a wurin. Hawaye take yi babu kakkautawa babu mai cewa tayi shiru sai Qareeba da take bubbuga bayanta.

Kofar dakin aka bude idanuwa sama da goma suka yo kan likitan da nurse da suka fito. Sai tambayoyi akan yaya jikin nasa.

"Alhamdulillah munyi mamaki kuma mungode Allah domin Ya takaitawa Dahiru wahala. Ya sami gocewar kashi ne a kafa wannan likitan kashin..." ya nuna wanda ya fito a lokacin "shine ya gyara masa. Sai kuma buguwa nasan zaiyi kwanaki yana fama da ciwon jiki. Idan an cire wannan babu wata matsala in sha Allahu"

Ajiyar zuciya suke ta saukewa ana da mika godiya ga Allah sai kuma tsinuwa ga BB ta biyo baya. A kidime Mawadda ta kalli Attahir.

"Ba hatsari kuka yi bane?"

"BB ne ya buge shi da mota"

Sulalewa tayi kasa zuciyarta tana matsanancin bugu kamar ta faso kirjinta ga wata irin mutuwar jiki da ta saukar mata.

Muryarta tana rawa ta dago ta kalli Baba "Baba kaji saboda ni zai kashe Yayanmu" cure jikinta tayi a wuri daya ta saki kuka. Ta bawa kowa tausayi.

Nawal tazo ta rungumeta a wurin suna kukansu tare da Qareeba.

Baba Prof yace "to yanzu kuka zaku yi in sa a mayar daku gida ko zaku yi shiru mu shiga mu ga halin da yake ciki?"

Sharewa Mawadda hawaye Nawal tayi ta tayar da ita tsaye. Manyan suna gaba suka yi tururuwar shiga dakin.

Idanun Dahiru akan kofa yana nemanta. Ita kuwa daga karshe ta tsaya tana zubar hawaye da fargabar yadda zata ganshi.

Suna hada ido ya sakar mata wani lallausan murmushi a take taji hawayen nata har sunfi na da. Qareeba ta kama hannunta ta janyota gaban gadon tana yi mata radar da kowa yake ji.

"Kanwata ba'a haka. Mijinki yana kwance yanzu ya kamata ki nuna masa kulawa yadda ya kamata ba ki tsaya a baya kina rabe-rabe ba"

Tun daga Bilya har su Nawal babu wanda baiji kunya ba musamman Mawadda da aka fadawa. Danlami dariya ya rinka yi kasa-kasa. Manyan kuma sai suka dauke kai kamar basu ji ba. Dr Tani dai tamkar kasa ta dare ta shige haka taji. Daukar 'yarta zatayi su tafi kafin ta saida hali kowa ya gane wacece Qareeban Dr Tani.

Sun gaisa da Dahiru ana tambayarsa jikinsa yace da sauki. Mawadda ce kawai bata yi magana ba sai ruwan hawayen da yake daga masa hankali.

Bayan dan lokaci Baba yace zasu koma gida kada su rasa abin hawa.

"Haba Mal Fatihu yaushe zamu bari ku fita neman abin hawa" cewar Baba Prof.

"Hanyarmu ta baude ne bana son dora muku nauyi"

Baba Prof yace babu matsala Attahir ya daukesu a motarsa.

Bilya yace zai tafi dasu. Shi kuma Attahir ya tambaya ko ya kai Mawadda da Nawal gidan Baba Prof sai ya dawo ya kwana.

"Ji min wani abu. Mutum da matarsa kace zaka yi jinyarsa. Ka daukesu ku koma ita Mawadda ta dauko musu abubuwan bukata na kwana kai kuma sai mu wuce gida da Nawal kafin a kama dan iskan yaron nan"

Maimakon su tafi sai hira ta koma kan BB da bakin halinsa. Da zasu tafi Ade, Yaya da Baba aka ce su shiga motar Bilya Danlami su Baba Prof suka ce ya jira su tafi a motarsu sai a ajiye shi a hanya.

Duka suka fito sai 'yan sanda biyu sannan aka ce daya ya bi su Attahir tunda gidan zasu koma daukar kaya.

Qareeba tayi saurin biyo su Mawadda dama motar tasu tana kusa da ta Bilya. Dr Tani tace ina zata je ga tasu motar.

"Kanwata zan raka  dauko kaya kinga har yanzu bata da nutsuwa"

Janyota baya tayi da sauri basu san Bilya yana cikin motarsa ba ya gama waya da Baffa ya fada masa komai.

"Bana son wannan rawar kan Qareeba don Allah ki ja mutumcinki ki wuce mu tafi"

Ta bata rai "Mummy ba a yiwa dangin miji haka. Idan banyi kokari mun saba da ita tun yanzu ba ko anyi auren ba zata saki jiki dani ba."

Toshe mata baki Dr Tani tayi tana waige "shashasha anyi auren ne ko me? Maza ki cigaba da wannan bare-baren shima yace ya fasa. Dazu ko kunyar idon mutane kika hau sakin baki"

Turbune fuska sosai Qareeba tayi "yanzu Mummy meye laifina? Wallahi ina son Bilyamin to don ina son samarwa kaina wuri a zuciyarsa sai ya zama rawar kai? Su fa maza akan 'yan uwansu basa ji basa gani"

Wannan karon haba Dr Tani ta rike cike da mamakin Qareebar "you are just unbelievable Qareeba. Ni kike fadawa me ya kamata da dangin miji?"

"To Mummy kowa yasan tsakaninki da 'yan uwan Daddy fa. Ni kuma ina so su Ahirin su so ni kuma su so 'ya'yana"

Maganarta gaskiya ce shiyasa Dr Tani ta kasa cewa komai. Bilya da ya gama sauraronsu sai yaji ta sake burge shi yayi murmushi shi kadai.

Duka aka watse Attahir ya kai Mawadda ta dauko kaya da abinci suka dawo da ita. Zai sake shiga ciki bayan ya tayata diban kaya ya kai Nawal ta rike masa hannu. Ya fahimci dai nufinta a kyalesu shiyasa suka yi mata sai da safe suka wuce.
******

A hankali ta tura kofar dakin ta shiga. Dahiru yana kwance idanunsa a rufe kamar mai bacci. Kayan hannunta ta ajiye sauran duka Attahir ya shiga dasu. Ta koma gefen gadon ta tsaya tana kallon shi cike da so da tausayi.

Banda gocewar kashin gwiwar hannunsa ta kalla wanda take nade da bandeji saboda muguwar daujewa da wurin yayi. Ga kuma gefen idonsa na hagu da plasta shima yaji ciwo. A hankali ta tako zuwa bakin gadon ta kura masa ido tana zubar da hawaye.

Sautin kukanta a hankali yake shiga kunnuwansa yana taba masa zuciya. Bude idanunsa yayi ya sauke a kanta tana ganin ya tashi ta fada jikinsa ta kankame shi iya karfinta.

"Nayi zaton na rasa ka. Idan ka tafi ka barni nima mutuwa zanyi. Yayanmu ka yafe min a dalilina ka ke ta ganin bacin rai gashi yau harda lafiyarka an taba...."

Dago fuskarta yayi idanunta sun kankance saboda kuka "kada ki sake cewa a dalilinki ne domin duk abinda ya shafeki ya shafemu ne gabadaya"

Murmushi tayi ga hawaye na zuba "kai komai naka daban yake"

"Sosai kuwa. Shiyasa ma banyi korafi ba kinzo kin cika min kunne da kuka da surutu babu yaya jiki ko sannu"

Rungumarsa yaji ta sake yi tana dariya a hankali "ba sai nace yaya jiki ba saboda nima ina jin ciwon yadda kake jinsa"

"Mawaddana mai dadin baki. Idan anzo allura sai mu raba kenan"

"Ni na hakura ayi maka kai kadai saboda ka samu sauki da wuri"

Sai da ta sashi dariyar da baiyi niyya ba saboda jikinsa ya fara tsami ko ina ciwo yake masa. Sallah yace zaiyi ta dauko ruwa da bokiti ta taimaka masa yayi alwala a wurin sannan yayi sallolinsa akan gadon. Ita ma tayi isha ta bashi abinci. Kadan ya iya ci yace ya koshi. Fita tayi da sauran abincin wurin masu shara ta taho tare da nurse aka cire masa ruwan da ya kare aka sa wani. Har sandunan tafiya aka kawo masa ko da zai bukaci tashi.

Shirin bacci suka yi ta kula ya zurfafa a tunani wanda tasan bazai wuce na BB ba. Kashe fitilar dakin tayi ta dawo kusa dashi akan gadon "matsa min"

"Gadon mara lafiyan?"

Ta zauna tana riko hannunsa "baka ganeni bane? Matar patient ce tazo raba jinya da patient dinta"

Tasan yana cikin damuwa shiyasa take kokarin kwantar masa da hankali duk da itama nata hankalin ba a kwance yake ba.

"Ni dai gaskiya ki kwanta a waccan kujerar zata isheki."

"Yayanmu mana don Allah" tace tana bubbuga kafa a kasa.

Matsawa yayi yana murmushi. "shagwababbiya kawai"

"Zama da kai ne"

"Saura ki fama min kafata"

"Saura ka danneni garin juyi"

Kansa yana daga wurin kirjinta don ya bar mata filon ya zame jikinsa kasa kadan yace "yaushe kika koyi surutu ne?"

Fuskarsa ta dago tace "saka min kayi"

Muryarsa a shake yace "yaushe?"

"Ranar da ka fara wannan..." ta amsa masa tare da kissing dinsa.

Ba don rashin lafiyarsa ba da ta ga tukwicin wannan kulawa da yasan da biyu take masa kamar yadda shima yake yi mata idan tana da damuwa. A hankali bacci ya kwashesu tana rungume dashi.

Can cikin dare ta soma jin zafin jikinsa yana shirgarta. Tana bude ido ta shafa kansa da wuya sunyi zafi sosai. Kusan fadowa tayi daga kan gadon don sauri ta fita neman likita. Zazzabi yake mai zafi da azababben ciwon kai. Allurai da magunguna aka bashi tana gefe tana kuka har suka gama.

"Wannan fever da headache din are normal. Ya bugu sosai amma in sha Allah zuwa safiya zai fara jin saukin jikin"

Godiya tayi masa tana share hawaye. Zama tayi tana ta masa sannu tun yana amsawa da kyar har bacci ya daukeshi. Ita kanta sace ta yayi ba don taso ba tana rike da hannunsa.

******

A can gidan Kawun Haj Mara kuwa Bobo ne ya kirata a waya ya sanar da ita sun iso. Unguwar babu wuta amma an tada inji a gidan gashi dama yana da girma bari-bari ginin gargajiya inda wasu 'ya'yansa suke zaune da iyalansu. Dakatar dasu tayi a waje ta je ta sanar da kawun nata an sako BB saboda bincike ya nuna sharri aka yi masa. Ko kallonta baiyi ba yace tace su shigo sai ya kwana a dakin samarin gidan amma da safe yana so su tafi saboda shi baya son harkar 'yan sanda. Maganar ta bata mata rai amma bata da wata mafita da ta wuce kwana a gidansa shiyasa bata mayar masa da baka ba.

Tana fita ta ga BB a jikin Bobo yayi mankas ko tsayuwa baya iyawa. Kirji ta dafe a tsorace "kai Boiboi a buge yake ne?"

"Hajiya Bobo nake fa. Ya dan kurba ne ya wanke yawa. Yau yarinyar nan ta kwafsa mana amma ai jikin mijinta ya fada idan bai mutu ba kenan"

A fusace ta janyo BB har yana faduwa ta wanka masa mari tana hakin bacin rai "Babawo bazaka barni na huta ba ashe? Me kuka sake aikatawa kuma?"

Bobo da ya fara jin kansa a sama shima saboda ya sha rabin kwalba shine yayi mata bayani sannan ya shige motarsa yayi gaba. Mayafinta ta cire ta lullube BB tana kukan bakinciki. Maimakon dakin samarin inda akayi mata masauki ta wuce dashi saboda bata son kowa ya ganshi a wannan yanayin. Suna shiga ta kama kofa ta rufe harda saka sakata ta warbar dashi akan katifa ta koma gefe ta tsaya tana share hawaye.

Tafiya ta jiyo alamun ana tahowa hanyar dakin ta saki labule da sauri. A sannan kuma BB ya fara tari ta saka hannu ta rufe masa baki. Ai yana jin hannun ya mika nasa ya shafa yaji alamun mace kawai ya shiga kokawar danneta. Tun tana mutsu-mutsu a hankali har ta ga abin ba na hankali bane ya fara cire nasa kayan.

Duk da duhun dakin ta lalubi kumatunsa ta tsinka masa mari "kai don ubanka nice, Hajiyarka ce"

Yadda idanuwansa suka rufe haka kunnuwansa suka toshe. Mawadda yake tunani da yadda yaso kwarai yau ya sameta. Haj Mara bata yi aune ba ya soma tafkarta yana mari da duka yana mata fadan taci amanarsa tunda ta auri waninsa. Kayanta ya shiga yagawa a haukace.

Jikan kawun nata da aka aiko ya fada mata akwai abinci idan BB zai ci ya fita a guje ya tafi fadin hayaniyar da yake ji a dakin.

Kuka take kamar ranta zai fita saboda ba dukan wasa yake mata ba. Muryarta har ta shake saboda rokonsa kada ya keta haddin da yafi kowanne muni a gare shi. Da kyar ta lalubi fitilar da ta kashe ta kunna ta durkushe a kasa.

"Babawo ka dawo cikin hayyacinka don Allah nice Marakisiyya mahaifiyarka"

Kara bude idanuwansa yayi yaja tsaki "auuu ashe ma kece"

Suna haka taji muryar kawunta yana fada "Marakisiyya bude min kofar nan"

BB ya kalleta "a ina nake ne? Kada ki bude Hajiya 'yan sanda ne"

Bata saurare shi ba ta tashi zata bude ya damko hannunta ta saki ihu. Nan da nan samarin gidan suka yiwa kofar dukan maza sai gata tana lilo. Carko-carko akayi ana kallon kallon. Haj Mara dai rigarta kamar babu saboda BB tsargeta yayi sannan zanin duk ya tattare ya juye. Shi kuma gajeren wando ne kawai ya rage masa.

Salati aka dauka Kawunta ransa ya zo wuya "mutuniyar banza mutuniyar hofi ashe tsiyar da kuke shukawa kenan da dan naki shiyasa kowa ya juya muku baya. Allah wadaran wannan dabi'a kuma wallahi bazaku kwana min a gida ba"

Tana kuka kamar ranta zai fita ta hau yi masa bayanin cewa ba abinda yake zato bane. Tsawa ya daka mata har kokon ranta don dama mafadaci ne.

"Duk iskancin da yaron nan yake yi kina tarewa idan ba kuna naku a gefe bane ai yakamata ace kin tsawatar. Amma kinyi kunnen uwar shegu ke gaki wadda tafi kowa son da. Inace yanzu kin budewa kika yi saboda gudun tonon asiri. Nace ki kai shi dakin samari kin taho dashi naki tirrr da haihuwarki Mara"

Zaman dirshan tayi a kasa tana ji ana aibata ta kowa yaki sauraron bayaninta. Da BB yaga haka ya soma rashin kunya dama samarin a kagauce suke suka finciko shi suka hau duka ba ji ba gani karshe aka mika su ofishin Hisba.

******

A kan kujera Mawadda ta kwana ta dora kanta akan gadon daidai fuskarsa ga hawaye ya bushe mata. Dahiru ya bude ido yana ta kallonta. Goshinta ya sumbata ta bude ido da sauri tana tambayarsa jikinsa cikin kulawa.

"Mai jinya ta saki baki tana bacci har patient ya riga ta farkawa."

Murmushi tayi "bazanyi rigima da kai ba patient dina kai abin lallabawa ne"

Sallar asuba suka yi sannan ta jona musu ruwan wanka da heater din da ta sako a kayanta daga gida.

Jikinta babu kuzari sosai kamar ita ce mara lafiyar komai tana yi a sanyaye a dalilin fargabar yadda Baffa da Inna zasu dauki lamarin an kusa kashe musu da dominta. Yadda ta koma yasa shi jin babu dadi yace ta jawo kujera gaban gadon kusa  dashi ta zauna.

"Meye yake damunki kuma, duk kinyi wani iri. Ko wuyanki ne na kula kina ta rikonsa tunda kika farka. Kwanciyar bata yi miki dadi ba" ya dora hannu a wurin ya soma murza mata jijiyar wuyan cikin nutsuwa.

Tun tana nokewa saboda rashin jindadin wuyan da zafi har ta sake da ta fara jin yana warwarewa. Kallonta yake yi har ya gama ta jujjuya wuyan tana dan murmushi.

"Nagode Yayanmu"

Ya kawar da kai "ni dai wallahi ba haka ake yi ba"

Dariya ya bata tasan ita ce mai masa wannan korafin "me akayi ba daidai ba?"

"Nine mara lafiyan amma kece kike langabewa kin barni da aikin jinya. Gaskiya bazan yarda ba"

Dadi taji ta fara tsokanarsa yau ta rama yadda yake mata.

"Sai kaji idan da dadi"

Tura baki yayi "sai kin biyani jinyata"

Ruwan wankan ta je ta kashe saboda ya tafasa ta dawo kusa da gadon ta tsaya "ayya sai hakuri babu wani biya da zanyi. Ga tawul zan sirka maka ruwa ka fara wanka kada a shigo bamuyi wanka ba"

Kwanciya ta ga yana shirin yi tace "yaya haka"

Ya dago yatsunsa biyu "nace sai kin biyani jinyata sai ki zabi dayan biyu. Ko dai kiyi min wankan nan ko kuma ki goyani."

Idanu ta zaro saboda mamaki sai kuma ta koma dariya "amma shagwabar taka harda rigima a ciki. Yanzu da wane bayan zan goya ka?"

Hannunta ya janyo ta dawo gabansa yana zaune ya zuro kafafunsa a kasa ya dora hannu a bayanta "wannan"

A take taji kunya ta runtse ido "kayi masa girma"

"Wankan fa?"

"Rufa min asiri"

"Kunya kike ji?"

Ta lumshe ido ya sunkuyar da kansa "Nima ina ji amma saboda lalura na roka kika ki. Ai shikenan"

Murmushi tayi bata ankara ba taji a hankali ya zaunar da ita a gabansa tsakiyar kafafunsa ya zura hannuwansa ta cikinta tare da dora kai a tsakanin wuyanta da kafada.

"Gashi kin goyani saura zani" yace yana kara karfin rikon da yayi mata don kada ta tashi. Dankwalinta ya zamo ta kasan hijab din jikinta ya daura musu daga bayansa zuwa cikinta ta rasa inda zata yi.

Ba karamar kunya taji ba shi kuwa ya sake lafewa a bayan nata wai bacci zaiyi. Ta daure tace ya tashi kafin ruwan ya huce.

"Ki rufe kofar dakin muje kiyi min don Allah Mawaddana...kinji. Bani da lafiya fa" ya marairaice mata.

"In rufe kofa kuma? so kake idan anzo an buga shiru ace...ace..." ta kasa karasawa.

Kanta ya dungure "Allah Ya shiryeki wato har kin fassara. Jikina inda na bugu nake so ki gasa min fa kike wani tunanin. Bawan Allah mai kafa daya da rabi salihi ne ba ruwansa"

Kwafa tayi ta tashi ta rufe kofar dakin ta dawo ta cire hijabinta ta mika masa sandunansa. Fuskarta babu alamun wasa tace.

"Tashi muje nayi maka"

Ya kalleta ya kalli kansa sai ya dan ja baya "me? Wankan?"

Ta sake hade rai "ba shi kake so ba da gasa jiki? Tashi muyi sauri nima sai nayi. Idan anzo anji kofar a rufe su jiramu kowa yasan jinyar amare sai hakuri"

Kamar gaske ya zaro ido "a gabana zakiyi wankan kuma kiyi min?"

Tawul dinta da yake cikin akwatin da ta hado musu kaya karami ta dauko "akwai wani abu ne?"

"Bazaki ji kunyata ba?"

"Ko digo" tace tana ware masa idanunta masu kada masa zuciya.

Mikewa yayi yana wani shu'umin murmushi da karfinsa har sai da yayi kara ya manta da kafar. Sandunan ta bashi yana gaba tana binsa yace "da nasan da haka kullum ciwon karya zanyi miki. Amma yanzu ma nagode I love you soooo much" da dokinsa yake tafiya.

Tana daga baya ta amsa "I love you too"

Yana shiga ta janyo kofar ta rufe shi ta waje tana dariya "kayi wanka idan ka gama kayi min magana in shigo in daddanna maka jiki da ruwan zafi"

"This is cheating" yace yana dariyar shima.

"Yayanmu?"

"Na'am" yadda ya amsa shi a dole yana fushi.

"I love you kaji banda mita kasan babu kyau surutu a bandaki"

Bai san haka zata ce ba ya hau murmushi sannan yayi wankan. Bayan ya gama taje ta gasa masa jiki ya ji dadin hakan kuwa sosai.

Yana shiryawa itama tayi nata wankan. Kafin takwas duk sun shirya sai ma bacci da ya sake daukesu. Kofar da aka buga ce ana sallama ta tayar da Mawadda. Muryar Inna da taji a kofar dakin tsoro ya ziyarci zuciyarta ta bude da fargabar da wace irin fuska zasu kalleta.
[31/01 9:36 am] Batuul Mamman: *GUMIN HALAK...*💰26

*Batul Mamman*💖



Kana ganin Mawadda kasan ba karamin tsoro ne a ranta ba wanda Dahiru ya gano dalilinsa tun kafin ya tambayeta. Ga tsananin mamakinta Inna tana shigowa kallonta tayi cike da tausayi.

"Mawadda ya naga kin fada firgicin kwana guda har kinyi kashin wuya. Hakuri zaku yi da jarabawar rayuwa watarana zaku wayi gari kamar ba'ayi ba"

Sanyi ne ya ratsa zuciyarta ta rinka tasbihi ga Allah domin Ya sani ta kwana da tararrabin haduwa da su Innar sai gashi abin yazo ba yadda tayi tsammani ba.

Durkusawa tayi ta gaisheta kanta a kasa tana jin hawaye na barazanar sauko mata. Ita kanta Innar taji yadda muryarta take rawa ta kama hannuwanta ta tayar da ita.

"Ki sakawa zuciyarki hakuri domin sai kinyi hakan ne zaki iya kulawa da mijinki. Kuka ba naki bane tunda kin sani ko ba jima ko ba dade wannan tsinannen yaro sai ya hadu da fushin Allah idan bai tuba ba."

Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi "nagode Inna"

Inna ta mayar mata da murmushin ta karasa gaban gadon inda Dahiru yake zaune yana kallonsu. Farincikinsa a lokacin ya sassauta masa radadin bacin ran zuciyarsa da ma ciwukan jikinsa. Kafin yayi magana Baffa da Ummiyo suka shigo daga ciki Mawadda ta gaishe da Baffan shima ya jajanta mata tare da karfafa mata gwiwa cike da kulawa. Ummiyo ta kasa kallon Mawadda matsananciyar kunyar matar yayan nasu ta kamata. Rabonsu da haduwa tun kafin ta tafi aikatau Kaduna. Sanda ta dawo Tariwa bayan tsautsayin nan ya faru basu hadu ba har kuma maganar da ta fitar ta janyo aka hanata fita gabadaya.

Tunda Dahiru ya fadawa Mawadda yadda Ummiyo ta dauketa ta matsu su hadu. Yanzu da ta ga duk ta takura kanta sai ta saki fuska ta matsa ta riko hannunta. A dan firgice ta kalli Mawadda ita kuma tayi mata murmushi tana kallon Inna.

"Inna don Allah waye babba a shekaru ni da Ummiyo?"

Kallonta suka yi duk su biyun ita da Baffa suna dariya. Inna ta amsa mata "kece mana bare kuma yanzu girman naki ya karu"

Mawadda ta sake murmusawa "to sai ki gaisheni tunda kinji da kunnenki nice babba idan ba haka ba kuma duk inda muka hadu har kasa zan durkusa miki"

Ummiyo taja da baya da sauri sai ga hawaye "don Allah rufa min asiri abin sai yayi min yawa"

Hankalin Mawadda ya tashi ita da take kokarin ganin ta daidaita tsakaninsu "menene haka daga wasa"

Gefen mayafinta tasa tana goge hawaye "ki yafe min don Allah"

Dahiru da su Inna duka kallonsu suke yi. Shekara da shekaru Ummiyo tana fama da wannan damuwar saboda ta dorawa kanta laifin komai da ya biyo bayan rayuwar Mawadda. Shiyasa bata iya sakewa kamar da duk surutun ya tafi.

Har zuciya maganar ta daki Mawadda. Ta dade da yafe mata ko ince bata taba daukar abin a rai ba ko don albarkacin Dahiru tun a wancan lokacin. Idanun iyayensu ya sanya mata jin nauyi ta rungume Ummiyo ta barin jikinta "komai ya wuce Ummiyo don Allah kada a sake tada zancen nan."

Sai yanzu Ummiyo ta iya murmushi tun fitowarsu daga gida. Bilya ne ya daukosu a tasha don shi niyarsa yaje da kansa ko Danlami su daukosu sai wayar Baffa ya samu wai sun kusa shigowa gari. Shine yaje ya daukosu ko wanka baiyi ba. Yana kawosu ya koma gida batare da ya shigo ba.

Sai da Dahiru ya kula hankalin iyayen ya koma ga Ummiyo da Mawadda suna ta murmushin wannan shiryawa tasu.

"Wallahi Allah Innarmu ba haka ake yi ba" yace yana kankance ido fuskarsa na nuna alamun fushi yake.

Inna ta ware idanu tana masa kallon tambaya "me aka yi ba daidai ba?"

"Jiyan nan mota ta kwasheni ta wulwulani a sama sannan na fado na hadu da gaban mota da zafin kwalta" yana magana yana kwantatawa da hannu "amma shine kun shigo kawai kun biyewa waddan" ya nuna Mawadda da Ummiyo.

"Yanzu kai kishi kake da matarka da kanwarka? Wannan abin kunya da yawa yake" cewar Baffa.

Inna ta zauna a kusa dashi "da gaskiyarka Dahiru babu wani abin kunya. Ya ya jikin"

Saitin Mawadda ya kalla yana harararta "da sauki"

Baffa yace "abin naka harda jin baki."

"Ba fa kace min ya jikin ba har yanzu"

Duka dariya suka yi sai kuma hira ta barke tsakaninsu su uku a can gefe kuma Ummiyo da Mawadda ke yi tasu tana tambayarta game da 'ya'yanta.

Basu jima ba sai ga Attahir da Nawal da abinci. Rungume juna suka yi da Mawadda tana tambayarta mai jiki bayan ta gaisa da su Inna. Suna haka Marwanu ya iso shima da kayan abinci yace su Baba zasu taho anjima. Inna da Iya sunce sai sun biyosu ga kuma su Bilki duka sun baro gidajensu shine suka yanke shawarar sai kowa ya iso zasu taho tare.

Bai dade ba ya fita saboda dakin ya cika. A bakin kofa ya hadu da Danlami da matarsa suma da kayan abinci. Yana rike da kwandon abincin ita kuma ta goya Humaira. Tuni dakin ya kaure da hayaniya. Baffa ya fita daga waje ya bar Inna da 'ya'yanta.

Wata kumbular mota mai kyau ce tayi parking Qareeba ta fito. Tayi kyau sosai don kuwa taci kwalliya saboda tasan zasu hadu da Bilya. Idan bai zo ba ma jiransa zata yi. Tun asuba taso shiga kitchen Dr Tani ta korata daki wai zumudin yayi yawa. Bacci ya sake dauketa tana farkawa ta fada kitchen ta hada girki mai dadi domin farantawa kanin miji don ta sake samun shiga wurin yayansa. Ba yadda Dr Tani bata yi ba akan ta zauna sai shabiyu ta fito taki amincewa har kuka ta kusa yi.

A cikin kwando mai kyau ta jera komai wanda kwanukan Daddynsu ta debo batare da sanin Dr Tani ba. Har zata wuce ciki daga kasan bishiyar dake gefen inda ta ajiye mota a farfajiyar asibitin ta kula da wani dattijo ya kara karamar rediyo a kunnensa. Jini baya karya kallo daya tayi masa ta san matsayinsa.

Riga da skirt ne a jikinta ta kashe dauri mayafi a kafada. Gyara mayafin tayi ta janyo shi har ka a ranta tana cewa dole ta chanja wannan dabi'ar girma ya kusa hawa kanta.

Baffa bai kula ba hankalinsa yana ga labaran da yake ji sai ganin mace yayi a gabansa ta rufe rabin fuskarta.

"Baba ina wuni? Anzo lafiya? Yaya su Mama? Ya mai jiki kuma?"

Kallonta yayi tana ta jero tambayoyi ya amsa mata ba don ya santa ba "baiwar Allah wurin Dahiru kika zo?"

Murmushi tayi cike da kunya tace eh sannan ta tashi ta tafi. Ladabinta ya burgeshi ya bita da fatan alkhairi.

Daga waje ta fara jiyo surutu kofar a bude take ta kutsa kai da sallama tana mitar sun dami kaninta da surutu baza su barshi ya ji saukin jikinsa ba.

Idonta akan Mawadda tana zuba masa abincin da Nawal ta kawo. Dankali ne aka dafa sannan taka burgeshi ta kada da kwai da nama da kayan kamshi ta soya da kauri sai farfesun kaza.

Hannu ta daga ta dakatar da ita "ga nawa abincin nasan zaiji dadinsa faten tsaki ne harda yakuwa da ugu saboda yaji dadin bakinsa. Kuma kinga basai ya tauna ba"

Sam bata kula da Inna ba tayi zaton su kadai ne a matsayinta na matar Bilya to be ta isa tayi musu gyaran kuskure. Mawadda ta tsaya kallonta ta turo mata kwandon ta karbe plate din da ta gama zuba wancan abincin. Nawal ta hade fuska tsaf rai a bace tana kallon Attahir ya kawo dauki. Tasha wahalar girkin kuma ace bazai ci ba wanda akayi dominsa.

Dahiru da Danlami sai dariya suke yadda Nawal ta hade rai itama Qareeba ta sha kunu tana kallon Mawadda "bazaki zuba bane in zuba da kaina? Bawan Allah bai ci komai ba"

Yau dai ta karewa Anti Qareeba kallo kuma har ranta taji tana sonta. Nawal ta kalla "uhmm kinga Sis in ajiye wannan sai yaci da rana?"

Kusa da Inna Nawal ta koma "Inna don Allah ba nice na fara kawowa ba"

Ita Inna bata san wacece Qareeba ba itama Qareeban lokacin ta kula da ita ta zube a kasa a gabanta cike da kunya. Dakin ya kaure da dariyar yadda tayi harda Nawal mai fushi.

Ta gaisheta a mutumce Inna tana tambayar wace ce ita Dahiru yace Anti Qareeba. Dama Mawadda na gefenta ta kuma janyo hannunta sai da tayi kasa itama a hankali tace mata "kiyi mata bayani sosai"

Bata san Mawaddan ma kunyar Inna take sosai ba ta dago ta kasa cewa komai. Kyakkyawan mintsini ta kaiwa Mawadda a dantsen hannunta taji zafi ta hau susa ta kuma fahimci sakon "Inna idan Allah Ya yarda fa Yayarmu zata zama"

Qareeba ta saki yalwataccen murmushi Inna ta kalleta ta koma kallon yaran nata da alamun tambaya. Danlami yace "Yayanmu Bilya"

Kai wannan abu yayi mata dadi don fuskarta ta nuna sai ta wayance da cewa bari taje su wuce gidansu Mawadda da Baffa dakin ya cika. Attahir ya mikawa Danlami mukullin motarsa "ka kaisu"

Qareeba tace "yanzun nan nasha mai ina da full tank gara ya dauki tawa"

Inna tace sun gode babu damuwa zasu tafi a ta Attahir. Jikinta yayi sanyi ko batayi maraba da ita ba.

"Inna nima 'yarku ce don Allah ku dauki tawa"

Sai da Inna tayi da gaske ta yarda su tafi a ta Attahir ta bi bayan su Mawadda aka raka su har mota.

*****

Sun dawo dakin suna hira Mawadda ta zuba masa faten dakin kuwa sai kamshi don yaji kayan hadi. Da zafi sosai sai ta ajiye akan fridge ta sake dukawa zata dauko kofi Furera ta shigo tana faman yatsina. A wulakance ta yiwa Dahiru ya jiki harda karin cewa ya auri wahala.

"Ace tun kafin a shafa fatiha ka gagara kwanciyar hankali ina dalili. Yanzu har an fara harin rayuwarka"

Mawadda tayi shiru tana jin zafin maganganun da Furera ta cigaba da yi. Dakin duka tsit yayi kowa yasan da wa take dama. Dahiru baya son yi mata rashin kunya a gaban su Attahir da Ummiyo sai yace da Mawadda ta bashi ruwa ya fara sha.

Jiki a sanyaye ta zuba masa ta dago ta kusa buge bowl din faten Ummiyo tayi saurin daukewa tana cewa "hankali dai Yayarmu"

Furera na kyalla ido ta hango mene a cikin bowl din ta mika hannu ta karba babu kunya.

"Faten tsaki kayan marmari bari muji..." ta ciko cokali da naman da aka yanka kananu fal a ciki ta kai baki. Dadi ya ratsata ta lumshe idanu "Allah Ya tsaga rabona da haka zaku barshi ya bushe a zubar. Mara lafiya ko don gaba Mawadda abinci kadan ake zuba musu idan sun bukaci kari a kara daga baya."

Wannan zubar da mutumci nata ya kular dasu amma Qareeba nata ran yafi na kowa baci amma tana mata kallon mara kan gado ta sassauta murya tace "Ahirin wace wannan ne?"

Bai amsa ba Bilya ya shigo. Ba karamin kyau yayi da kayan jikinsa ba kufta da wanda na wani lallausan yadi baki sai hula. Ya tsaya a waje magana dasu Baffa da zasu tafi shiyasa bai shigo da wuri ba.

Furera tana shan faten tana ganinsa tace da Mawadda "shima ki zuba masa yana sonsa sosai. Ni bani da jimirin yi ne kawai"

Kallon kallo ake a dakin yadda ta shigo hannu na dukan cinya take nuna iko akan abinda ba nata ba. Da bacin ranta suka fito da Bilya don tun dare da ya fada mata yayi zaton zata yi girkin zuwa asibitin. Da zasu fito yaga babu komai a hannunta yayi magana tace tasan zaa kai daga gidan Baba Prof da gidan su Mawadda. Rai a bace yace duk fadin Kano shine yafi cancanta da  Dahiru yake da hakki akansa tunda shine babba. Duk wanda ya kai kara yayi musu. Sai tayi mirsisi abinta ta shige mota.

Qareeba tunda ta ganshi haukan matar da take tunanin 'yar uwarsu ce kawai ya dena damunta ta sunkuyar da kai bayan kowa ya gaishe shi itama ta gaishe shi.

Yaji dadin ganinta sosai kuma yadda yayi tunanin jin tsoron Furera ta sani sai abin baizo masa a haka ba.

Attahir da gayya yace "Anti Qareeba ki zuba masa mana"

Furera tana ta kalkale bowl din da cokali yana ta fitar da sautin kwal kwal ko a jikinta. Sai shine ma yace a koshe yake. Ai da kunya yazo dubiya dubiyar ma ta kaninsa ga matansu a wurin ya hau cin abinci duk da yadda ransa ya biya don da yunwa ya fito saboda bacin ran baa yiwa 'yan asibiti abinci ba. Hararar Furera yayi jin tace a kara mata "tashi mu tafi yanzun nan akace hayaniya tayi yawa a dakin zasu zo suce kowa ya tafi"

Dahiru ya kalle shi ya kalli Qareeba "Yayanmu baku gaisa da Anti Qareeba ba har zaku tafi."

Daga shi har ita sai murmushi yayin da Furera ta shiga bude kwanuka neman fate. Tashi yayi ya fita ta bi bayanshi tana nunawa Mawadda ta karbe food flask din kada Furera ta cinye.

Attahir ma yace gara su tafi an hana su Dahiru cin abinci. Sallama suka yi musu zasu dawo anjima suka fita ya rage dakin saura Ummiyo, Furera da Mawadda.

Sai da Mawadda ta jira Furera ta dibi mai isarta tace da Dahiru zai ci ya bata fuska. Ko don tabawar da tayi ta bata wurin jage jage saboda keta yace baya so. Na Nawal ta sake zuba masa ta wanko hannu ta dawo ta haye gadon daga gefen kafarsa da take a nade a mike ta takwanshe kafafunta yana jingine da filo a zaune ta soma bashi.

Furera tana kallonsu har ta gama zaman wanda dama da uku ma tayi ba da biyu ba don ta tanka ta samu ta fada mata magana.

"Iskanci da rana tsaka Mawadda meye haka? Mutum yana fama da lalura don bakin naci da jaraba a nan din ma sai..."

"Anti Furera abinci zan bashi ba wani abu zamuyi ba fa"

Ummiyo ta soma dariya gashi dai taji kunyar zaman da suka yi. Bude baki yayi da hannu take bashi idanunsa a kanta suna yiwa juna murmushi.

Furera sai ta kasa hadiyar abinda yake bakinta don takaici. Da yanzu fa Hansa'u ce take kula da Dahiru yake nuna mata soyayya irin haka. Itama shegiyar yarinyar wai ta kalli tsabar idonta tace mata ta hakura da Dahirun. Tsaki ta ja bazata iya kallon wannan rainin wayon na Mawadda ba. Ta kalli Ummiyo.

"Ke! Tashi mu fita wannan abin da suke yi gaba zai kara don idan bakiyi wasa ba cinyarsa zata hau a gabanki"

Mawadda ta rufe ido "kai Antinmu ai ba lafiya gare shi ba yanzu" ta mayar da kallonta gareshi tana wani fari da ido yana biye mata da tambayar ko itama ya bata a baki.

Saura kiris Furera ta fashe ta tashi ta fice Ummiyo ta bi bayanta tana dariya. Haba mata duk basa sonta saboda yadda take wahalar musu da dan uwa.

Can bayan fitar Bilya da Qareeba wurin motarta suka je.

"Bilyamin me yasa baka ci faten ba? Ni nayi da kaina"

Wani benci ne a jikin bango suka zauna da tazara a tsakaninsu kafin ya amsa mata "ashe kin iya girki"

"Kala-kala kuwa"

"To amma kina ganin za'a bawa wannan makaniken mace kamar ki Qareeba ya rinka cin daddadan girkinki?"

"Kana tunanin guje min ne?" Ta fada tana kallon idanunsa. Duk abinta kasa jurewa tayi ta kawar da kanta.

Gyaran murya yayi ya nemi ta saurare shi da kyau "Qareeba ban mallaki komai da zai bani damar aurenki ba. Kinga jiya muka hadu zan so mu bi komai a sannu saboda kada nan gaba abin yazo bai yiwu ba"

Zuciyar Qareeba ta karye. Tasan me yake hange amma tayi rantsuwa idan har ya amince mata to bata miji sai shi.

"In hakura kenan?" Tace idanu na ciccikowa da kwala.

"Zaki iya zama dani da matar nan da ta cinye abincin da kika dafawa Ahirin?" Ya bata amsa da dariya.

Rike baki tayi kafin ta kwashe da dariya.
"Matarka ce don Allah"

Yayi murmushi "uwargidanki ba"

Qareeba abin ya bata mamaki yadda Furera ta shigo ta iya cin abinci bata zo da komai ba harda yiwa mijinta tayi. A take taji ta rainata. Ta rinka dariya yau ta ga wadda ta fita.

Fitowar Furera da Ummiyo ya katse mata hanzari. A fusace ta matso inda suke.

"Ka bani kudin mota na tafi. Wai don rashin mutumci a gabana yarinyar nan Mawadda take bawa Dahiru abinci a baki...a baki fa kamar wani karamin yaro. Shi kuma sai wani lumshe idanu yake kamar wanda ya sha wani abu"

Iska Bilya ya furzar ransa yana kuna ya mike zai bata amsa Qareeba ta riga shi don haushi matar take bata sosai.

"Mawadda da Ahirin ba miji da mata bane"

Ummiyo tace "kuma masoyan asali ba"

Furera ta daure fuska.
"To waye mara mijin?"

Qareeba ta kalli Bilya "Bilyamin...."

Zaro idanu Furera tayi "Bil me kika ce? Kai wai ma wace ce ke ne? Me kuke yi a nan?"

"Wadda tayi faten da kika shanye " Bilya ya ce.

"Anti Qareeba sunanta" Ummiyo ta bata amsa a takaice.

"Auuuu ita ce wadda Dahiru yayi aiki a gidansu ko? Shine kima zo duba shi harda girki? Sannu da kokari. Su Mawadda an manta da asalin miji sai wani fiffika take ita ta auri mai kudi"

Qareeba ta kalli Bilya don ta tattaro bakar magana zata bata amsa amma tana tsoron kada yaji haushi. Sai gashi ya bata mamaki.

"Qareeba ga uwargidana Furera. Furera ga Qareeba amaryarki in sha Allahu"

Su biyun kallonsa suke yi ya dake abinsa yana binsu da ido shima. Qareeba ta tabbatar yau Allah Ya kawo mata nata mijin. Furera sai da ta nutsu maganar ta sauka a kwanyar kanta kawai sai ta tura hannunta a makogaro tana kakarin amai. Kanta suka yi Bilya yana cewa meye haka. Ta dago idanu jazir da bala'i.

"Ni zaku kashe don kana son yin aure? Shine aka barbade faten aka bani nasha. To Allah Ya isana. Kuma kayi auren idan ka isa."

Ummiyo ta matsa gefe "Anti Furera babu wanda yayi kiki tayi kika dauka fa"

"Aikin asirin kenan Ummiyo. Abu a ajiye babu mai ci sai ni ina zuwa naji kamar yana cewa daukeni Furera...daukeni"

Da gaske tana ta kakaro amai abu ya gagara. Bilya ya kira Danlami yace yayi sauri ya dawo da motar idan ya kai matarsa gida shima zai tafi ne.

Ciki suka koma suka barta don ita tace kafin ta fara kishi dole ta fito da faten tsakin nan wanda ya sami wuri a cikinta ko gezau yaki fitowa.
*******

Wayar gaggawa aka yiwa Alh Sule tun dare daga ofishin Hisba sai gashi asubar fari yana idar da sallah ya kamo hanyar Kano hankali a tashe. Da kwatance ya isa ofishin nasu da aka kwatanta masa.

Haj Mara ta fita hayyacinta saboda tsabar tashin hankali. Yana isowa bayan an fito dasu ya daga hannu ya sharara mata mari sai da ta ga wani haske nan ya gilma.

Duk zafin bai dameta ba kamar wata muguwar tsanarta da take gani a idanunsa. Zubewa tayi a kasa jiki na rawa ta rike masa babbar riga.

"Alhaji kada kace kaima ka yarda da zargin da ake yi min."

Zuciyarsa har kuna take "Marakisiyya kin cuceni kuma a yau na kara nadamar aurenki. Sai dai nasan kaddara ce ta rayuwata. Na fada na kuma fada yaron nan kina cutar shi ne amma kin ki ji. Karshe ma kin koya masa tsanata da kin jin maganata a matsayin makiyinsa. Yau gashi dan cikina ake zargi da neman mahaifiyarsa"

BB da jikinsa ya gama tsami ya dago kai da kyar "Alhaji na zata Mawaddata ce fa. Mutanen nan sharri suka kula mana."

Shima Alh Sule ya sani Haj Mara bazata taba yin abinda ake zargi ba. To amma tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa ke duka. Cike ciken takardu yayi tare da 'yan sandan da aka kira suka zo suka daukesu bayan ta aminta da bakinta biyan kudi tayi aka fito mata dashi.

Wunin ranar sur ayi nan office din dasu su gama bayani a koma yi wani wurin dasu. Sai da aka gama komai aka kwashesu sai police station. Wannan karon harda Bobo anyi nasarar kamawa inda suka tarar da kofur Pascal a cell din shima yaci uban duka. Haj Mara kuma tana bangaren mata.

Sai da komai ya kammala da yamma aka kira Dahiru aka sanar dashi an kama su BB kuma an matso da shigarsu kotu nan da sati daya. Godiya yayi musu yace Allah Ya nuna mana lokacin.
******

Kwanan Dahiru uku aka sallame shi. A cikin kwanakin nan ya san shi cikakken dan gata ne don sosai Mawadda take bashi duk wata kulawar da ta dace. Shagwabarsa yake mata son rai tana biye masa.

Qareeba kullum sai taje asibitin inda  ita da Bilya suka sake shakuwa kowa ya san da soyayyarsu mai ban mamaki.

Son juna suke yi da gaske ba wai don Dahiru yayi masa tayinta ba itama ba don ta dade da rashin aure ba. Cikin dan kankanin lokaci Bilya ya gama fahimtar wacece Qareeba. Mutane sun santa da dolanci da shagwaba ne kawai. Shi kuwa a yanzu ya santa a matsayin mutum wadda bata boye boye. Abinda tasan gaskiya ne to ko a gaban waye bata shakkar yinsa. Haka zalika shagwabar da dolancin shi burge shi suke yi sosai. A tata fahimtar kuma ta gane Bilya irin mutanen nan ne masu sadaukar da farincikinsu domin kyautatawa wasu. Yana da matukar kirki da saukin kai. Sai kuma to her advantage ta gane baya jindadin rayuwar aurensa. Bai fada ba amma a shekarunta da iya abinda ta gani game da Furera ta san cewa Bilya aure dai yana dashi amma soyayya irin ta ma'aurata ku nesanta da juna kuna begen juna bai sansu ba. Hirar soyayyar ma bai iyawa sosai sai kawai tayi amfani da wannan damar take nuna masa kulawa irin wadda bai saba gani ba. Hakan yasa nan da nan ta shige zuciyarsa. Balle yadda take yiwa 'yan uwansa.

Daren ranar da za'a sallami Dahiru ta kira Bilya. Yana zaune ya saka abinci a gabansa sai juyawa yake ya kasa kai ko loma daya saboda masifar Furera. Abincin ma Hansa'u ce tayi don ta dena girki babban dansa ya kawo masa.

"Ka dai ji kunya Yasin. Ka rasa wadda zaka nema sai matar da kaninka da kuka fito ciki daya ya gama wankewa rigar mama."

Bai iya fada ba wannan sai Dahiru. Shiyasa yaki kulata. Amma furucinta na karshe ya kona masa rai "idan dai ya taba wankewa to lallai Dahiru ya cika yaron kirki mai girmama na gaba. Tun a lokacin ashe yaji a jikinsa matar yayansa zata zama shiyasa yake wanke komai nata"

"Rigar mama fa nace ko baka ji da kyau bane"

A hankali saboda baya son daga murya yaransu suji yace "naji mana. Idan ta zo sai ni kuma na cigaba da wanke mata tunda 'yar hutu ce bata saba ba"

Haushi ya kamata saboda so take suyi fada kuma yaki biye mata. Sai ta chanja taku "wa ya sani ma ko sai da suka gama watsewarsu aka yi maka tayin kwantai"

Hannu ya daga zai mareta sai ya kasa. Yadda taga idanunsa sunyi ja ba karamin tsoro ya bata ba. Amma ganin ya sauke hannun ta shiga tafi harda guda.

"Ahayyeeee nanaye...wato saboda zaka yi aure kake shirin dukana. Ga fili ga maidoki wallahi ka tabani ka tabo masifa ka tabo bala'i. " ta nuna shi da yatsa tana cigaba da cewa "banda kai ma dai lusari ne mara zuciya me zai kaika yin auren jari auren kwadayi"

Bata gama rufe baki ba ya falla mata marin da yake ta kokarin danne fushinsa kada yayi.

"Furera bana son zama cikin mazan da suke tauye iyalansu don suna neman aure amma ki sani idan ki ka kaini bango ranki ne kadai zai baci. Qareeba zata shigo gidan nan ba da dadewa ba in sha Allahu. Bazan ce ki kwantar da hankali ku zauna lafiya ba. Idan tazo ki cigaba da nuna mata haukanki itama zata nuna miki nata. Kuma ina mai tabbatar miki ke karamar alhaki ce a wurin Qareebata"

"Qareebarka? To ni kuma ta waye?" Tace a fusace.

"Ohooo"

Fita yayi abinsa bayan yasha turare yayi kyau sai gidan Dr Tani. Yau Dr Auwal ne ya bukaci ganinsa inda ya tabbatar masa ya bashi ita bayan yayi masa 'yan tambayoyi.

Gida yace zai bashi kyauta inda zai sakata yace ayi hakuri zai kama haya kafin ya gama ginin da yake yi a Zawaciki. Bai nemi Qareeba don ta zama jarinsa ba. Ya tabbatar samunsa na yanzu da yardar Allah zai ishe shi ya rike mata biyu.

Wani sabon girma da kima ya kara a idon su Dr Tani suka ce idan an gama da case din BB ya turo domin basa son a dauki lokaci mai tsaho.

Bayan sun shiga ciki ta fito da murnarta.

"Bilyana Mummy ta fada min an baka ni"

"Shiru ya kamata kiyi ni zan fada miki da kaina"

Bakinta ta rufe tana dariya. Can kuma tace "gaskiya ka bani wuya sosai"

"Da nayi me?"

Da muryar shagwabarta tace "Tun yaushe ka sanni ashe kaine mijin amma sai yanzu ka fito"

Dariya ta bashi "ko in koma ne?"

"Wasa nake yi don Allah"

Kayan abinci ta jere masa kamar tasan da yunwa yazo. Yana ci tana masa hira mai cike da ban dariya.

******

Washegari karfe bakwai a gida ta yiwa Mawadda. Ta gyara gidanta da ya soma hada kura saboda shigowar sanyi ko ina sai kamshi. Lafiyayyen girki tayi sannan ta shiga bandaki ta soma gyara da turara jiki tamkar amarya.

Shiryawa tayi cikin kananun kaya bisa shawarar Nawal. Wando ne mai laushi a hannu amma a ido kamar jeans blue ya kama jikinta. Rigarta fara mai dogon hannu da duwatsu a tsakiya itama ta kama ta. Kunyar kayan taji don bata taba shiga irin wannan ba sai yau. Navy blue din mayafi siriri ta samu tayi yafa a kanta da yasha gyara.

Tana gaban mudubi wurin biyu da rabi taji shigowar mota ta hau murmushi ita kadai. Dama duka kayan kwanan nasu ta taho dasu tun safe abin sallah guda daya ta bar masa da zata taho. Bakin kofa tazo ta tsaya amma bata bude ba tana jiyo takunsa har ya iso suna magana da Attahir yana kara yi masa godiya. Kofar taji ya kama tayi saurin bude masa haka kawai gabanta yake bugawa kamar ta dade bata ganshi ba. Ga kunyar kayan jikinta.

Labule ta daga masa tana tsaye daga gefe ya kura mata ido kamar yau ya fara ganinta. Idanunsa na kanta har ya isa kan kujera ya zauna ya ajiye sandunansa a gefe.

"Taho taho kada ki sani suman zaune" yace yana miko mata hannu.

A kunyace ta karasa kusa dashi ta zauna ya janyota barin jikinsa ya rungume. Yana ji ta saka hannuwanta ta zagaye shi itama tana kara makalewa jikinsa.

Shakar kamshinta yake mai ratsa zuciyarsa "I miss you Matar Dahiru"

"Awa ta nawa da baroka a asibiti?"

"Kenan bakiyi kewata ba ko"

"Maida wukar Mijin Mawadda"

Ya dago habarta "to kinyi?"

"Fiye da zatonka" tayi masa murmushi.

Tashi yayi ya sakala hannu a kafadarta ta kaishi daki. Duk wani motsinta akan idonsa yana binta da kallo. Jikinta kadai ya isa ya ruda mutum.

"Zaki yi min wankan"

"Nifa bana son shagwaba ka warke. Tun ciwon na sabo banyi maka ba sai yau saboda rigima"

Langabe kansa yayi "ni ko?"

"Rigimarka tayi yawa Yayanmu. A asibiti...."

"Can ma don kada kisa a kama mu ne na hakura"

Ita kam gaskiya tana jin kunyar wannan abu amma ya ta iya. Sai wani nanikarta yake ya kwanta akan cinyarta yana mita.

"Kwalliyata zata baci kafin ka gama gani" tace a sanyaye saboda rashin mafita.

"Zanyi miki kuka irin wanda sai Attahir ya hawo a guje"

Tashi tayi ba shiri ta hada masa ruwan sannan tazo ta ja hannunsa tana kumburi don ba haka taso ba. Wani fitinannen  murmushin ya rinka yi mata tana shiga ya tura kofar da hannu. Da kayan jikinsu ya sakar musu shawa a ka suka jike. Kamar ta saka masa kuka

"Yayanmu!"

Zagayeta yayi da hannu yana dora kansa a kafadarta "kinga tsoron zamewa nake shiyasa na rikeki. Ai banyi laifi ba ko"

"Baka yi ba" tace don ta riga ta sallama tasan bata da wata mafita kuma. Da kanta ta matsa jikinsa tana hade bakinsu.
********

Kotu ta cika makil duk yawan fankoki zafi ake yi saboda jama'a. Dangin Mawadda, na Dahiru, Baba Prof, Dr Tani da kuma uwar gayya Haj Mara su ne daga gaba gaba.

Alkalin wannan karon mace ce wadda tayi fice a cikin Nigeria saboda rashin ramgwamenta akan duk wata shari'a da ta shafi fyade. Justice Raliya Habu kenan matar da kudi ko son zuciya har yanzu bai sa an taba kamata da laifin tauyewa wani hakki ba sai dai idan lauyoyin ne suka gaza. Gilashinta ta turi kan hanci ta bukaci lauyoyi su gabatar da kawunansu.

"Sunana Barrister Jibril Jibril nine lauyan masu kara"

"Barrister Wisdom Odili lauyan wadanda ake kara"

Justice Raliya ta basu damar fara gabatar da hujjoji da shaidu. Wannan karon shari'ar bata yi kama da zata bada wahala ba saboda yawan shaidu da suke a hannu. An shigo da BB ya rame ya kwanjale babu kyaun gani. Haj Mara tamkar wadda cutar tsotsewar jini ta kamata duk shekarunta sun fito karara babu kyaun gani.

Bisa aiki na kwarewa da JJ ya nuna yayi nasarar nemo likitan da ya duba Mawadda a asibitin Bebeji. Haka nan kuma ya samo Inspector Nalado wanda suka samo hotunan raunukanta tun na farko.

Dr Tani tazo ta fadi duk abinda tayi a wancan zaman shekarun baya sannan Qareeba da Dahiru suka bada shaida akan abinda ya sameta itama.

Zugar su Garwashi kaf sun nuna solidarity domin kuwa sun bada tasu shaidar har zuwa yadda suka taimaka aka gano Mawadda bayan sun saceta.

Barrister Wisdom dena yi musu tambayoyi yayi saboda babu amfanin yin hakan. Haka aka gabatar da Bobo shima ya tabbatar da kade Dahiru da suka yi wanda yazo da sanduna.

Jama'a cikin kotun sunyi tir da halin akuyanci irin na BB da uwarsa mai taya bera bari. Alkalin ta dage shari'ar zuwa kwana shida ranar da zasu dawo a yanke hukunci.

******

Yau kotun har tafi zaman farko cika saboda 'yan jarida har daga gwamnatin tarayya. Case ne babba da yake ciwa mutane tuwo a kwarya.

Bayan gama sauraron bayanai Justice Raliya Habu ta soma magana kamar haka.

"Duba da hujjoji da shaidun da lauyoyi suka gabatar wannan  kotu mai alfarma ta yanke hukunci kamar haka."

Shiru kotun tayi baka jin ko da tari an baza kunnuwa.

"Kotu ta karbe lasisin aikin Dr Tani daga yau bazata sake aiki a matsayin likita a kasar nan ba saboda tayi amfani da damarta wurin bada shaidar karya da cutar da mai gaskiya."

Dr Tani sunkuyar da kanta tayi dama ta dade da zaton hakan.

"Hussaini Joji wanda aka fi sani da Bobo kotu ta yanke masa hukuncim shekara biyu saboda taimakawa wurin sace matar aure, fitar da mai laifi daga hannun yan sanda da kuma bada gudunmawa ta yunkurin kisa"

Gigicewa Bobo yayi don bai taba shiga hannun hukuma ba duk tsiyarsa.

"Haj Marakisiyya kotu ta ci ki tarar naira miliyan biyu da zaki bawa Mawadda Fatihu saboda danne mata hakki, bacin suna da taimakawa wurin cutar da ita. Har ila yau zakiyi zaman gidan yari na wata shida saboda fitar da mai laifi daga hannun hukuma"

Kukan ma tuni ta dena saboda dacin zuciya da bacin rai. Ta rasa komai ta rasa kowa saboda Babawo.

"Babawo Sule Chanji. Duba da irin laifukanka wannan kotu ta yanke maka daurin shekara ashirin da biyar tare da horo mai tsanani"

Murna da farinciki a wurin su Mawadda baa cewa komai. Dahiru ji yayi kamar ya taso yaje ya rungumeta don kukan farinciki take yi.

Garwashi da yaransa Alkali tayi musu gargadi akan daba ta kuma basu shawarar su nemi sana'ar da zata rikesu bata fatan sake ganinsu a kotunta indai ba alkhairi bane ya kawosu.

BB yana ta hargagin sai ya kashe Dahiru ya auri Mawadda aka fitar dashi sannan aka sallami kotun bayan Alkali ta tashi.
[31/01 9:36 am] Batuul Mamman: *GUMIN HALAK...*💰27

*Batul Mamman*💖



Daga kotun gidan Mal Fatihu suka wuce gabadayansu. Dr Tani kafin su tafi da nata iyalin ta rike hannun Mawadda ta sake rokonta gafara. Babu bata lokaci tace ta yafe.

Garwashi yazo tare da yaransa. Loba boy dai yaji dadi an kulle Danmani shima ya sami rabon wata shida. Dahiru da Attahir suka jasu gefe suka basu sati daya kowa yayi shawarar me zaiyi amma kafin nan duk su koma gaban iyayensu su nemi gafararsu. Da farinciki suka tafi bayan Mawadda da kowa ya sake yi musu godiya.

Suna isa gidan abincin sadaka da aka dafa tun safe aka shigar fitarwa lodi lodi ana kaiwa asibitoci domin godiya ga Allah. Gidan ya cika da hayaniya tamkar ana biki. Dahiru ya turawa Mawadda text don yaji shiru ko nemansa bata yi.

_(yau fa akwai celebration kiyi ki gama mu tafi da wuri)_

Murmushi tayi Nawal ta zungureta.
"Ade na kallonki dai hajiyar soyayya"

Tana dagowa suka hada ido da Ade kuwa ta rufe ido tana dariya. Sai dare suka bar gidan bayan doguwar nasiha daga Baba da kuma karin godiya ga Dahiru.

A wannan rana da hankulansu suke a kwance Dahiru da Mawadda sunyi kwanan farinciki da dimbin soyayya. Basa ji basa ganin kowa sai junansu.

Bayan kwana biyu suka wuce Tariwa harda su Baba gabadaya. Gabanta har faduwa ya rinka yi akan hanya saboda yadda take ji. Yara da manya tun a hanya suka yiwa motocin dafifi aka rakasu har kofar gidan Maigari dattijon arziki irin albarka.

Shima fitowa yayi yana zaune jamaa sun zagaye shi ta kowane bangare yayi musu nasiha da jankunne akan rayuwa. Mawadda da take sanye da kaya na alfarma kana ganinta kasan ta wuce sa'a ya nuna musu tare da tunatar dasu babban abinda ya kamata a hadu a yiwa mutane irinta wato tsayawa juna da kuma tausasawa.

Ita da su Yaya sun sha kuka mata suka yi ta rumgumarsu ana murna. Satinsu guda a garin suna zaga 'yan uwa sannan suka koma gida.

*****

Sati uku kenan da gama shari'arsu BB aka kira Dahiru da Mawadda kotu domin karbar kudin tarar da aka yankewa Haj Mara.

Alh Sule suka gani ya bada cheque na miliyan biyar. Dahiru ya duba da kyau yace ba haka Alkali tace ba.

Nannauyan numfashi Alh Sule ya saukar "na sani kuma kudin da na kara ba fansar mutumcin Mawadda bane da dana ya tozarta. Na bata ne domin tun shekarun baya naso haduwa da ita Allah bai nufa ba. Allah Ya gani ban goyi bayan abinda akayi miki ba amma bansan inda zan same ki ba. Wannan kudin duka harda na Marakisiyya ne. Shine abu na karshe da zan iya yi mata don nasan ko wuka zaa saka mata yanzu bata da inda zata fitar da wannan kudin. Idan da hali ko don rage nauyi da hakki kuji tausayina don Allah ku yafewa Babawo. Nasan zaku ce wannan tsoho da son kai yake. Sai dai kaddara idan ta hadu da son zuciya rayuwar mutum sai ta lalace. Babawo bashi da sauran gata sai yafiyarku a gareshi"

Fuskar kamala da dattako ta Alh Sule Chanji ita ta sanya Dahiru ya dubi Mawadda.

"Idan har na isa...."

"Ka isa Yayanmu" ta katse shi "Na yafe masa Alhaji"

Bata kara cewa komai ba bayan wannan ta fita daga wurin ta nufi motarsu. Dahiru ne ya karasa komai yazo ya sameta jingine da motar tana tunani. A gefenta ya tsaya.

"Kinsan me na tuna?"

Ta juyo ta kalle shi "me?"

"Ranar da na fara sake ganinki. Wallahi da kika fito ba karamar dauriya da jarumta nayi wurin kin fitowa na rungumeki ba. You looked so sweet lokacin"

"Yanzu fa?" Ta tsare shi da ido.

"Mawadda ce Dahiru, Dahiru kuma Mawadda..."

Kallon fuskarsa tayi suka hada ido a hankali tace "I love you"

Bude mata kofa yayi ta zauna ya rufe sannan ya zagaya ya zauna shima. Hannunta ya kamo ya sarke yatsunsu yana kallon yadda nata suka yi kyau sun sha jan lalle.

"Ina rokon Allah Ya kara min sonki da kaunarki kuma Ya bani ikon kulawa dake har karshen rayuwarmu."

Kwalla ce ta cika mata ido yana gani hawayen ya soma diga duk ya rude.

"Na bata miki rai ne?"

Ta girgiza kai da sauri sannan ta kwantar da kanta a jikin kujera soyayyar Dahiru tana sake cika mata zuciya. Har tunani take yi me zata yi domin faranta zuciyarsa. Kallonsa tayi idanunta kamar tana shirin bacci.

"Ka kaini gida kada nayi abin kunya a gefen titi"

Jin haka ya ware idanunsa a kanta "abin kunya kuma?"

A kagauce ta kalle shi "mu tafi mana da gaske nake"

Tayar da motar yayi suna tafiya yana kallonta yana tsoron me zata yi. Suna zuwa gida ta fice ta barshi a tsaye da rikon baki.

Da saurinsa ya bita suka ci karo a bakin kofa ta cire mayafi da dankwali ga wani zanin a hannunta.

"Ina zuwa?"

Haki take yi saboda gudun da tayi na hawa saman ta durkusa a gabansa ta juya baya.

"Hau"

"Ina?"

"Goyaka zanyi Mijin Mawadda na kaika daki sai nayi abinda ba na kunya ba yanzu tunda mun dawo gida"

Sai da ya gama dariya ya ga ta sha kunu ita da gaske take.

"A wannan dan bayan? Na kagu dai naga abin kunyar nima na koya" ya dora hannunsa a tsakiya.

Murya na rawa tace "Na rasa me zanyi maka a duniya kasan cewa nagode da duka abubuwan da kake yi min."

Tayar da ita yayi ta soma kuka ya rungumeta.

"Abu daya zaki yi min"

Ta dago kai da sauri "me kake so?"

"Mu zamewa juna komai na rayuwa. Abokai, 'yan uwa, masoya da duk wani abu da kika san yana kara shakuwa. Banyi miki komai don kice kin gode ba. Allah ne Ya saka ki a nan" ya dora hannunta a saitin zuciyarsa.

Ga ido fal hawaye ta soma murmushi kuma kunyarsa tana saukar mata. Matseta yayi a jikinsa ya soma shagwabar da ta riga ta sallama masa "zaki goyani din muje ki nuna min abin da kika ce?"

Ta zille "a wane bayan?"

"Irin yadda muka yi a asibiti zaki yi min kinji Mawadda mana"

"Ya na iya tunda ka iya dadin baki"

Dakin suka shige suna yiwa juna dariya yana cewa sai tayi abinda ta fada tana cewa ta fasa.

*******

Abu kamar wasa bikin Qareeba da Bilya saura sati biyu. Dama wata uku aka saka gashi lokaci ya gabato. Dr Tani da mijinta harma da 'yan uwan Qareeba maza kowa ya nuna bajinta ajin farko. Sun kashe kudi sosai wurin kawata gidan da Bilya ya kama mata babu nisa da su Dahiru.

Bisa shawarar Nawal da amincewar Attahir tunda gida dai nasu ne su biyu Dahiru ya gyarawa Mawadda dakin da yake a matsayin na maigadi a gidan da dan karamin bandakinsa wurin ya koma bangaren gyaran jiki. Watanta guda da farawa yawancin costumers dinta na da da ma 'yan unguwar da suka fara ganeta suka soma zuwa kasuwa ta fara budewa.

Wanna satin ta rufe karbar kowa sai Anti Qareeba. Gyara take yi mata sosai su wuni suna hira harda Nawal. 

Yau da wuri suka fara saboda Dahiru yace zai zo su fita. Wayarta ce ta soma kara tayi zaton ya taho ne ta ga ashe Nawal ce.

" 'Yar uwa yau naji shiru ko zazzabin ne? Na ga Dan uwanmu bai fita ba shiyasa ban shigo ba"

Attahir ne da kansa ashe hankalinsa daga ji a tashe yake "asibiti zan kaita ta dora girki ne don Allah ko zaki karasa"

Mayafinta ta yafa tana yiwa Qareeba bayani. Zamanta kenan ko kaya bata cire ba ta bita suka yi sallama. Gabadaya babu kwari jikin Nawal din Attahir ya rikota ta kasa tsayuwa.

Mawadda tana mata sannu itama a rude Qareeba tace

"Allah Yasa dai baki sha wasu magungunan zazzabin ba da alama ciki ne."

Duk da hankalinsa a tashe yake bai hana murmushi bayyana a fuskar a Attahir ba.

"Da gaske?"

Nawal ta rufe ido tana jin kunya saboda dama tayi tunanin hakan. Kallonta yayi yana murmushi "da gaske akwai babyna a nan...."

"Ehem ehemmm" Qareeba tace tana kamo hannun Mawadda itama kunya ta kamata.

"Ina ne kitchen din naji kauri"

Shigewa suka yi Attahir yana ganin sun shige ya daga Nawal yana murna.

"Ka bari ayi confirming mana"

"Ni nayi. Dama na kula sai wani cikowa kike yi ashe ashe yarinyar nan ta girma"

Mawadda ta kalli Qareeba tana dariyar shakiyanci don suna jin su Attahir har suka fita "ni dai idan ina da ciki kada wanda yazo ranar farko"

"Saboda me?"

"Daga ni har Mijin Mawadda nasan zamu taba abin kunya a gaban mutane"

Dama tsokana ce take yi ai kuwa Qareeba ta hau dariya kamar me tana cewa ya kamata ko kuda ne ta zama ranar don ganin kwaf.

"Da kallon wata saliha nake miki fa"

Mawadda tayi dariya "Antinmu bari dai mu kaiki gidan Yaya Bilya zaki bamu labari"

Qareeba tace "Allah ko? Wayyo ni kinsa naji kamar na matso da bikin"

Tsokanar juna suka shiga yi har suka karasa girkin da gyara kitchen din sannan aka fara aiki.

Dinkuna na gani na fada Mawadda tayi a kayan da Dahiru ya saya mata na fitar biki.  Dasu ake komai don ma Nawal tana fama da laulayi mai wahala.

Ranar kamu wani tsadadden leshi ruwan madara da adon shudi Qareeba ta saka anyi mata dinkin buba. Zanin akan rigar ta daura sai ashoke blue da gold da takalmi da jaka suma gold.

Tayi kyau sosai ta fito a amaryarta. Murmushin farincikinta yaki buya saboda wannan ranar daban take a wurinta. Manyan kawayenta wanda kuma su kadai ne kawayen da suka dade tare Jameela da Fatima 'yan shagwaba irinta sune kan gaba wurin komai.

Zuwa yanzu sun zama tamkar 'yan uwa da su Ade shiyasa suka zo akayi komai tare dasu saboda yadda Dr Tani take shige musu duk don ta nuna nadamarta kuma ta samu 'yarta ta zauna lafiya.

Anyi bikin kwana hudu events kala kala an gama lafiya. Bayan an gama taron yini ango da kansa yazo daukar amarya bisa yarjewar mahaifinta don tun abinda ya sami Mawadda sun tsorata da kai amarya.

Dr Tani tana ta kuka ta kankame Qareeba ita kuwa ko gezau. Sai da ta sake rungumeta a kunne ta rada mata "to sarkin shirme ki dan matso kwalla mana"

"Kai Mummy kwalliyata sai ta baci ya ganni banyi kyau ba"

Dr Tani ta sake make murya "kinga kallonki ake yi. Ko dan yaya ne ki danyi kinji. Haka al'ada take"

Zumburo baki tayi sannan ta ja mayafi ta rufe fuskarta ta soma ihun kuka "yeeeeee"

Hakuri aka soma bata a ranta tace dama sun bar bata bakinsu yau ranar murna ce a gareta.

Bakin mota aka rakota Bilya ya kasa fitowa saboda kunyar jama'a. Bude mata yayi yana daga ciki ta shigo kamshin jikinta ya cika motar.

Kafin su bar layin ta soma kokarin bude fuska ya rike hannun. Wani abu yaji ya tsirga masa har kafa a tausashe yace

"Akwai mutane fa kada ki bude su gane min amaryata kafin na fara gani"

Zantukansa duka ta bayan kunne suke shigarta tunda ya rike mata hannu. Bakon yanayi na farinciki ne yazo gareta amma ga mamakinta sai da ta tuna BB a wannan lokacin. Kukan da taki yi a gida ne ya kwace mata sosai take yinsa yana dagawa Bilya hankali. Yayi zaton kukan rabuwa da gida ne yayi ta rarrashinta har suka isa gidan.

Hannu ya mika mata don ta fito sai taki kamawa saboda tsoron kada ta sake jin yanayin dazu. Bai kawo komai ba a ransa suna shiga gidan da yaji komai na morewa aka fara kiran isha. Masallaci ya fita ya barta a zaune. Sai da taji gidan shiru ta tashi tayi sallah.

Tana idarwa batare da ta tashi daga kan abin sallar ba ta dauki wayarta ta kira Mawadda.

Kwance take komawarsu gida kenan duk ta gaji ko kayan jikinta bata iya ragewa ba. Sunan Qareeba ta gani gabanta ya fadi.

"Antinmu lafiya dai ko?"

Kuka Qareeba take yi da gaske "Mawadda yaya zanyi? Ya kika yi ke? Wallahi BB ne yake fado min gabana sai faduwa yake kamar in koma gida"

A take fuskar Mawadda ta sauya itama ta soma kukan tana tausaya mata.

"Antinmu kiyi hakuri kuma ki sakawa ranki wannan masoyinki ne wanda ya aureki domin Allah ba don jikinki ba. Ki daure zuciyarki domin a duniya bamu da masoya sama da masu aurenmu duk da wasu sun rigasu ganin tsiraicinmu sun tozarta mu da wulakanta mana rayuwa"

Kukan Qareeba ya tsananta itama Mawadda haka.

"Ina son Bilyamin sosai Mawadda amma zuciyata ta karaya. Bazan taba yafewa BB ba ina fatan ko ina yake Allah Ya kara saka mana"

"Amin Antinmu Allah Ya kare sauran mata"

Kuka suke ta yi suna rarrashin juna sannan suka ajiye wayar.

Dahiru yana tsaye a jikin kofa yana jin yadda take kuka kuma ya fahimci da wa take wayar. Idanunsa ne suka yi ja yana kara jin tsanar BB a zuciyarsa. Shigowa dakin yayi Mawadda ta taso daga kan gadon da sauri ta rungume shi.

"Zan kai karar Anti Qareeba ta taba min mata"

"Ayi mata afuwa amarya ce"

Mayafinta ya soma warewa "Baki cire kayanki ba ko babu nauyi?"

Kwantar da kanta tayi a kirjinsa "jira nake yi ka dawo ka cire min na gaji"

Ya dage gira "in gasa miki jiki kuma tunda kin kwana biyu babu hutu"

Ta gyada kai tana sake shigewa jikinsa ya.

******
Qareeba ma ashe Bilya yaji duka wayar da tayi. Tausayinta da sonta ne ya sake shiga ransa. Yana matsowa gareta tana yin baya idanu kamar su fado don firgici. Binta yayi ta yi har suka isa jikin bango.

"Ya muka yi dake?"

"A ina?" Tace a tsorace.

"Kince bazaki taba bari abinda yaron nan yayi miki yayi tasiri a ranki ba. Me ya faru yau? Tsoron Bilyaminu kike yi?"

Ta girgiza kai hawaye yana digowa.

A nutse yake kallonta tayi masa kyau. Mayafinta ya cire a hankali yana yi mata magana.

"Ni masoyinki ne, ni mijinki ne, ni abokinki ne wanda bazai taba cutar dake ko son ganin hawayenki ba."

A hankali tace "kayi alkawari?"

Hannuwanta ya janyo ya rungumeta tsam a jikinsa sannan yace "nayi alkawari...amma akwai 'yan lokutan da zan dan sakaki kukan kadan"

"Kamar yaushe?" Tace da karamar murya.

Dan bakinta ya zana da yatsansa yana kallon fararen idanuwanta "kamar daren yau" sannan ya hade shi da nasa.

*******

Cikin Nawal yana da wata hudu Mawadda ta soma nata laulayin. Murna a wurin Dahiru baa cewa komai. Wannan karon ita take shagwaba son ranta yana biye mata.

Ranar da Qareeba tazo sun sha hira sosai suna karfafawa juna gwiwa akan kaddararsu. Amincinsu ya dore fiye da zato da tsammani.

Nawal ce ta fara sauka ta haifi da namji kyakkyawa dashi kato. Farat daya ya shige zuciyar Mawadda har ana tsokanarta ko mace zata haifa ne ayi 'yar gida.

 Attahir ya bawa Dahiru damar yiwa yaron huduba da suna Ahmad wato mahaifin Nawal. Wata hudu a tsakani Mawadda ma ta haifi nata kyakkyawan bafillacen da ya dauko mahaifinsa sak. Shima Attahir ne yayi masa huduba da sunan da Dahiru ya zaba wato Abdulhadi (Abdul).

Anyi taron suna inda 'yan uwa na kusa da nesa suka halarta.

Yaransu sun taso cikin kulawa daga iyaye biyu a bangare guda kuma Dahiru ya bawa Mawadda shawarar bude kungiya da suka sanyawa suna _GUMIN HALAK_. Wannan kungiya da kudin da Alh Sule ya bata suka kafata wadda zasu rinka kai taimako da agaji ga duk wani mai karamin karfi da iyayen gidansa suka tauye masa hakki bisa zalunci musamman mata 'yan aiki wadanda ake duka ko yiwa fyade.

Cikin dan kankanin lokaci kungiyar ta bunkasa inda aka sami likitoci, lauyoyi da manya sukayi hadin gwiwa dasu domin kwatowa mutane 'yancin da talauci ke sawa a danne musu. Mutanen da suke neman halali da guminsu aka tozartasu.

Ahmad na da shekara daya da wata hudu Abdul kuma shekara daya Qareeba ta haihu. Bakin Dr Tani kamar zai hade da keya Qareebanta ta haifi 'yan biyu mata kyawawa dasu. Dakin cike yake da mutane Bilya yana gefen matarsa don ido ya bude yanzu daga shi har ita soyayya suke gwadawa juna da gaske. Furera an zama yan kallo don ta buga ta hakura saboda Qareeba da gaske tayi mata fintinkau. Ko kadan Bilya baya wulakanta ta amma ta zubar da damarta tun da dadewa.

Wata mata ce mai wankin bandaki ta shigo wata nurse ta daka mata tsawa cewa tun yaushe ake kiranta ta wanke bandakin bata zo ba.

Jiki na rawa tace " kiyi hakuri mara lafiya gareni a gida"

"Idan bazaki iya aikin bane sai na fadawa yallabai a nemi wata"

Hakuri matar take ta bayarwa har su Yaya suka sa baki. Ade ce ta kura mata ido can dai tace "kamar Hajiya Sakina maman abbati"

Da sauri ta dago "nice ina kika sanni?"

Ade ta rike baki...lallai duniya rawar 'yan mata ta gaba ta koma baya. Sakina matar Alhaji ita ce a haka.

"Ade ce tsohuwar mai muku wanke-wanke"

Sakina sai kuka harda rungumeta "Ade kece haka? Ikon Allah"

Waje suka fita inda ta fada mata a satin da ta koreta mijinta yayi mata saki uku wai ta sace masa kudi. Ashe daya daga cikin masu aikin da take yiwa rashin mutumci ce ta dauke. Tun daga lokacin duniya ta juya mata yau gata tana wankin bandaki a asibiti. Naira dubu biyu Ade ta bata tana jinjina lamarin Ubangiji.

Iyaye sun tafi dakin ya rage su Dahiru da matansu. Qareeba ta kalli Attahir tace "kanina Attashir ungo"

Hassanar mai dan karen kuka ta mika masa sannan ta mikawa Dahiru Hussainar tana kallon Bilya "Bilyana kasan burina akan yaran nan"

"Sai kin fada Qareebata"

Dariya aka soma yi tace "suna gama ko da JS 3 ne kowacce ga baban mijinta nan. Na yiwa 'ya'yana Ahmad da Abdul kamu"

Bilya ya riko hannunta "in sha Allahu zasu yi mana biyayya mu hada zumunci"

Dahiru yace "mungode Anti Qareeba"

"Ni ke da godiya Ahirin. Ina haifar namiji sunansa Dahiru"

Attahir ya saba Hassana a kafada tana kuka duk da babu yunwa da gani zata yi rigima. Sai jijjiga ta yake yana 'yar rawa.

Dahiru dariya har da dukawa yana tuna lokacin da Attahir yake cewa bazai hada jini da dangin dolaye ba. Ana bashi yarinya ya cafe sai juyi yake kamar ya manta ba su kadai bane a wurin. Kukan ne yaki karewa ya ce da Mawadda ta sauke Ahmad yazo ya rarrashi matarsa.

Akan abin sallah ya zauna ya dorata a cinya daya Ahmad na daya cinyar yasa hannu a kanta sai gata tayi shiru. Nawal ta daukesu hoto a waya tana dariya.

Mawadda tace dauko Abdul ta hadawa Dahiru suka zauna suka yi selfie su hudu.

Suna can suna hotuna Bilya ya kamo hannun Qareeba ya sumbata.

"Nagode matata"

Suma kowa kallon nasa iyalin yake yana godiya ga Allah.

~~~~~~~~

   ALHAMDULILLAH

Ina mika godiyata ga Allah da Ya bani ikon rubuta wannan labari. Abinda na rubuta daidai Allah Yasa mu amfana dashi. Inda nayi kuskure kuma ina rokon Allah Ya yafe min.

~~~~~~
Godiya ta musamman ga 'yan uwana ahalin Fikra da kuma ku da bazan manta daku ba wato members na groups din *TASKAR FIKRA* hakika kunyi min *SOLIDARITY* shiyasa nake muku *SonSo*.

Kamar yadda kuka sani labarin *GUMIN HALAK* na sayarwa ne amma ina godiya ga duk wadanda suke bibiyar rubutuna ko a ina suke.

A karshe ina fatan Allah Ya sake hadamu da alkhairi a littafina na gaba _*KU DUBE MU*_.

Ina fatan zakuyi min solidarity ku saya domin shima na sayarwa ne in sha Allahu.

*Batul dinku ce mai Son So*


Download Gumin Halak Littafi Na Daya