[10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: *INA ZAN GANSHI*💖
          Rubutawa
                ©Xarah Bukar

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION {NWA}

xarahbukar.wordpress.com

                  1 - 5

   Banko k'ofar d'akin da k'arfin gaske ya firgita Hajjo dake k'ok'arin had'e tabarmin dake yashe gefe guda. Fuska murtuk'e ta sak'alo k'afa ciki d'akin tana gunguni. Cike da k'unin rai Mahaifiyarsu Hajjo ta zuba mata idanu.
"Batula baki iya Sallama ba?"
Haushi ne ya kuma turnuk'e ta da sunan Batula da Hajjo ta ambata, tafison akirata da Fatima Zarah ainihin sunanta.
"gaskia Hajjo ana shiga hakkina a matsiyacin gidan nan, saurayina yazo daga fita ta Baba ya izo k'eyata, da alamun kuma da d'an maik'on sa, oh ni Fati naga samu naga rashi" karashe maganar tayi cike da tashin hankali, hannuwan ta biyu bisa kanta.
    Tak'aici ne ya cika Hajjo, wana irin k'aramar kwak'walwa yarinyan nan keda shi, "Batula miyasa baki da hankali, talauci ba hauka bane, ki kuma iyawa bakin ki, matsiyacin gidan nan gidan uwarki da ubanki ne ba yadda kika iya"
    Shuru Batula  tayi zuciyar ta na tafasa, banda harara talautaccen dakin da take.
"Maza jeki rumfar babanku ki amso kayan miya kafin ya kasa na kasuwa" acewar Hajjo batare data kula da yanayin ta ba.
Ware idonu tayi, tayi tace "nikam bazani niba, ajira dawo wan su Hassan saisu karb'o"
"Dole kije dan bazan tsaya jira harsai sun dawo makaranta zan aza abinci ba, wuce ki karbo kafin na mazge ki" Hajjo ta fadi da niyyan kai mata dundu
Gunguni tahau yi bata da alamun tafiya saida Hajjo ta hada mata tsawa mai dauke da ashariya sannan ta fice ak'ufule bayan ta tsuri mayafin ta dake lank'aye bisa taga.
    Gaban karamin gidan nasu dako fenti babu ta iske wani yaro tsaye.
"Baba mai kayan miya na nan ? Yaro ya tambaye ta.
Idan akuya na magana to ta tanka bangajesa tayi ta wuce abunta cike da haushin yadda Baba ke zubar mata da aji, wai itace diyar mai kayan miya, dogon tsaki taja ta k'arasa can gaba da gidansu inda runfam Baba yake, bata kai ka zuwa rumfam ba ta mak'ale daga gefe inda baba bazai hango taba, amma tuni ya ganta ya dauke kai, Lawali ta kira yaron auguwan su ta aikesa amso kayan miyan.
   Sabo da halinta yasa Baba bai nuna yaganta ba, jinjina kai kadai yayi, albasa batayo halin ruwa ba. leda taf ya cikawa Lawali sannan ya damk'a mai.
    Hankalin ta gabadaya ya shagala da kallon wasu yara da Mamansu cikin wata arniyar jeep, sai kallonsu take ji take dama itace acikin motar da tafi ko wace ya mace morewa, sai dai kuma aka samu akasin Baba talakana ne saidai su k'are da tumatur da albasa.
"Butula gashi" taji yaro na fadi, harara takai ma sannan ta warce ledar tayi gaba, Hajjo na iza wuta a gindin murhu ta shigo ta dire ledar tayi cikin kusurwar daki.
     Girgiza kai Hajjo tayi, tunanin barkatai ke yawan mata a kwakwalwa, inda ba a gidan ta haifi Batula ba tana iya cewa an mata musanye, amma ba daman fadin haka kamarsu daya da Baba kamar an tsaga kara.


 ***
K'asak'asa suke zantawa da alamun wata muhimmaciyar magana sukeyi, nisawa Hajiya Fatima tayi tace "Safara ya kikeso nayi kinsan Rasheed wani irin murd'add'en mutum ne da baa iya tank'wara shi, tun rasuwar ubansa ya koma hawainiyar da babu kala"
Murmushin dabai kai zuci ba Hajiya safara ta mata sannan tace "yaron nan dai d'an kine ke kika haifeshi bashi ya haifeki ba sai kisan yadda zakiyi ya amincin da kudirin mu.."
Turo kofar tafkeken palon ne ya katse masu zance, sanye yake cikin black suit, haunna sa rike da karamin brief case, ciki ciki yayi sallama, basu amsa ba banda kallo da suke bisa da shi, maihaifiyar sa hajiya Fatima ce tayi karfin halin cewa my boy ka dawo.
"e" kawai ya amsa mata agajarce ya wuce hanyar dakinsa cike da haushin Hajiya Safara dake hakince kan babban kujerar palon, idan bai manta ba tun yana yaro yake ganinta saidai jininsu bai taba haduwa ba, ya rasa mai suke yawan zantawa tare da momyn sa akullm idan suka hadu, tsaki kawai yaja ya cusa kai ciki had'add'an dakinsa.
    Fitowa tayi daga kitchen, hannuta ruke da kwalin exotic ta karasa cikin palon cike da yauki da iyayi. "Mardiyyah mutumin ki fa ya dawo"
Acewar hajiya Safara,
"Dagaske " Mardiyya ta fadi tare da kwalalo ido tana kallon Momy dake mata murmushi, sai kuma ta kalli ogogon hannuta tun 4 tabaro office amma shi sai yanxu 8 ya dawo.
Tashi tayi da azama, zata bar palon, hajiya safara tace "kardai ki dade, dare yayi kar Abban ki yajimu shuru"
"Toh Umma" ta fadi  tayi rushing zuwa kitchen ta sanya ruwa a glass cup sannan ta nufi kofar dakinsa gabanta na dukan uku, tasan sarai xai iya korota shiyasa tayi dabarar kaimai ruwa, ahankali ta tura kofar dakin ta shiga.
    Tsaye yake yana kokari cire neck tie bayan ya ajiye coat din gefe, ganinta da yayi ya dakatar dashi yanai mata kallon kina bukatar wani abune, kaman tasan abunda yake aynawa, girgiza kai tayi tace "Mr Rasheed sai yanxu ka kawo, ga ruwa kasha" ta fadi at once hade da mikamai glass cup, bai karba ba balle ya tanka, closet ya nufa yadau towel yabar ta tsaye ya shiga bandaki, ya rasa wace irin mayyace Mardiyya, at work bai tsira ba sai taxo har office yimai shishigi ya dawo gida kuma ta biyosa, wace irin rayuwace wanan, most annoying part of her shine yadda take kura mai manyan idanuwan ta da mak'e muryarta tamkar wata sabuwar farar kura.
   Rashin tankata da yayi ko a kwalar rigarta, inda sabo ta saba, sukanyi shafe awa hudu biyar ko tari bai yiba, duk wannan ba matsalarta bane koda ace ma wuka zai dauka yana datse naman jikinta bata damu ba, tana sonshi kuma ganin  kyakyawan fuskar sa ya ishe ta farin cikin shekaru ashiri. Murmushi tayi ta kwank'wade ruwan tas sanna ta fito palo, hajiya safara na ganin empty glass cup din taji farin ciki ya ziyarceta, komai yafara kankama tsakanin yarta da Rasheed kenan tunda har ya iya amsan abu gareta. Duk aganinta shiya sha ruwan.
    Sallama sukayi da Momy, ta rakasu har bakin motar su sannan ta dawo cikin gida ta wuce dakinsa.
   Gefe gado yake zaune yana brushing lausassiyar kashin kansa bayan ya fito daga wanka, zama tayi kusa garesa heda da amsan brushern tahau tazarmai lufluf tana fadin,
 "my boy ya aikin ?
"fyn" ya amsa mata, fuska ba yabo ba fallasa.
"My boy ka girma, ga kudi ka tara ta ko ina, yanxu miya rage ?"
Anxo gurin, daure fuska Rasheed yayi tamau, tacigaba
" sa'anninka masu shekaru talatin da uku duk sunyi settling banda kai, ya kamata kayi aure"
Murya can kasa yace.
"am not ready, infact ban samu wace nakeso ba har yanxu"
"wannan ba excuse bane, kana da alot of yammata masu sonka, ga Mardiyya yarinyar kirki masu hannu da shuni, itace daidai dakai, naira na gugan naira"
Kai ya girgiza "bana son Mardiyya infact banason ya'ya masu kudin nan yawanshi basu da isheshen tarbiya, it better nasamo wata can cikin talakawan nan"
B'ata rai Momy tayi, inda akwai alumma data tsana bai wuce talaka ba, mikewa tayi tsaye tanai mai wani mugun kallo, cike da karaji tace "talauci badai a xuri'ata ba, na gwamma ce mutuwa ta akan naga ka auri dangin tsiya, ban haifi dana dan talaka suci arzikin saba, tunda ubana ya haifeni bansan miye talauci ba kayi na farko kayi na karshe koda wasa karka kuskura ka ambata kalmar talauci a gidan nan, Mardiyya kuma saika aureta" karashe maganar tayi cikin huci sanan tai wurgi da brushen ta fuce dakin afusace.
Murmushi mai sauti yayi,
ya lura dai dabiar Momy bazata gyarabu, hatred dinta towards talakawa bazai canxu ba, ya rasa miye tsakanin dinta da takala, same story dinta kenan tun yana karami shiyasa yake da burin aurar talaka dan ganin miye illarsu da Momy ke masu kara tsana. Wayarsa dake kusa dashi ya dauka yayi dailing numbern Daddy Malam, bugu daya ya dauka suka gaisa. Yace "Mr  Rasheed kwana biyu, fatan kana cikin k'oshin lapia
"Am good, Aikuwa suka min yawa a office, kayi ready din komai gobe xan zo na cigaba a inda na tsaya"
"Toh sir, Allah ya kaimu"?
"Amin ya amsa mai sanan ya katse call din ya shingid'e bisa gado hade da lumshe idanu.
     Safa da marwa Momy keyi adakinta, wana irin abun kunya my boy yake son jaza mata, ga Hajiya Safara duk ta daura mata zafi, wani zubin ma k'awarka ma tasan sirinka wani tashin hankali ne, dole ne ta tursasa Rasheed auran nan ko yanaso ko baya so.

Cute xarah👌
[10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI?*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com

               6 - 10

Tafiyar kusan minti goma  tayi kan babban titin Kawo dake cikin garin Kaduna. Hankalinta gabad'aya na bisa titin da babu alamun abun hawa na haya banda mayan motaci dake walk'yawa. Ajiyar zuciyar mai dauke da wahala ta sauk'e, rashin abu hawa a unguwar tasu ba k'aramin ci mata ruwa a k'warya yake ba, ina ma ace tana da motar kanta saidai kawai yan polytechnic su ganta da ride dinta koda ma ace comot make i enter (One door).
    Jakarta irin wace ake sak'alewa a hammata ta bude ta ciro dubu biyu da Baba ya bata na siyan handout, kallon su tayi tana jinjina rashin k'yaun da dattin kud'in dayasha satalif, mai shesu tayi cikin jakar akayi rashin sa'a iska yayi sama dayan canjunan.
    Da azama ta mike tahau tsintarsu, saidai kash, ashirin uku sun haura saman titi, tsabar rud'u bata ankara da SUV dake dannowa aguje ba tahau bin ashirin dinta dake tsilla tsilla a titin.
    Kiiii!!!! Kakeji, yaja mugun burki da ita kanta saida ta razana, jiki na rawa take kalan motar da tunda uwarta ta haihefa bata taba gamo da irin taba, ko inuwar mutum bata hange ciki kansancewar tinted glass dinta, kallan motar kawai take tana imaging kanta aciki. Kallo daya yakai mata ya dauke kai yaja motarsa yabi gefenta ya wuce, RMD data gani cikin plate number yasata wage idanu, tanajin labarin family din a fulanin talla, yau gashi tayi gamo da motar, inama ace taga mai tuka motar yau da tayi kwanan farin cikin haduwa da mai kudi, duban kayan jikinta tayi ta buga tsaki, ta tabbata ya fola mata, ba mamaki kodaddiyar arabian gown dun jikinta ya kwafsa mata, last week kadai ta siyeta a gwanjan kasuwar bacci ganin sabuwar ita yan makaranta ke yayi.
Cike da tausayin kanta ta ida tsince kudin sannan ta nufi k'aramar kasuwar dake gurin, tafi awa daya tana zagaye kasuwar kanan tasamu jakar swagger da ake yayi, cikin dubo biyun ta fidda duba daya ta siyeta, acewarta ta gaji da rike mak'ale mata.
    Bayan ta ida dakyar  tasamu achaba ya karasa da ita inda yan Marwa (keke Napep) ke tsayawa, aranta sai mita take tayi latti zuwa makaranta (sai kace wani ya aiketa kasuwan).
   "Ke tafiya ne" Ogan gurin ke tambayar te, amsa mai tayi da eh, yahau k'walla kiran Mamuda dake zaune can gafe yana gabtar rake.
"Kaida kake layi maiya kaika da zama can" acewar ogan cikin muryar sa nayan tasha.
"gani zuwa" Mamuda ya fadi hade da mik'ewa kyakyabe jikin sa, wata tsohowar yadi mai araha ke sanye jikinsa da wata jar hula bisa kansa, jikinsa dukun dukun da bakin mai tamkar wani mechanic, fari ne dago dasai mai ido ne zai gane akwai farin, kacakaca da yake yasa na kasa tantance kamannisa.
   Tamkar wani shashasha haka yake magana, cikin maganar sa ta e'ena yace "shi shi gaaa muje"
Tsulum Batula ta fad'a cikin marwan, ta k'agara tabar gurin.
Suna tafe tahau gyaran rolling din veil dinta dake nema warwaro, bayan ta gama kudin da suka zube tahau dirgawa dari uku da saba'in tagani, babu naira ashiri cikin, Allah ya isa taja, tana maganganu kasa kasa, yasata asara ya tafi yabarta.
    Duk abunda take yana kallonta ta circle side mirror,  daure fuska yayi tamau had'e da dauke kai ganin ta dauko jar hoda tana shafawa, suna hawa booms hodar ta subuce hannuta, tas kake ji dankarariyar jar hoda ta fashe mai hade da madubi, baima lura ba, lailayo ashar da tayi yasa shi tsayar da Marwan.
"Kan uban can, dan Marwa kamin babban asara"
Kallonta yayi sannan ya kalli inda idon ta yake, yace "ayi hakuri abisa rashin sani ne, banda ke wake shafe shafe a titi"
Harara ta kaima, "dayake titin na ubanka ne, ai dole kace haka, ina ruwanka kaine ke siyamin kayan shafan komi"
"Allah ya wuce zuciyar ki, cikin kudin da zaki biya ki cire murtala uku da goma ki siya sabuwa"
Wani k'askantaciyar kallo ta aika mai, "bura ubar murtala uku da goma, nayi maka kama da talaka mai shafa hodar hamsi, banxa matsiyaci, talaka kun dauka kowa irin kune" tsaki ta buga tana cigaba da banka mai harara.
Kallonta kawai yake yana maimaita abunda tace, shidai baiga banbanci sa da ita ba da take kirasa talaka harda zagin dan tsohonsa dabai san hawa ba balle sauka.
Shareta yayi ya kunna Marwan yaja, tsine tsine tahau yi bai tanka ba.
"Kad poly xaka ajiye ni" yaji ta fadi cike da karaji.
Suna isa ta sauka ta fiddo tsofin goma da ashiri, naira saba'in tabasa, bata jira cewar saba tayi gaba abunta.
Mamaki da tsoron Allah ne ya turnuk'esa, yahau juya saba'in din, akalla daga Kawo zuwa gurin daya ijiyeta Jaka biyar ce, danta raina masa wayo ta basa saba'in tsabar tsiya, mai take nufi kenan, kudin hodar ta cira komi. Kai ya girgiza ya karasa gaba inda yaga passenger.
    B'angaran Batul kuwa dama saba'in tayi niyya basa koda ace hoda bata fashe ba, tana isa hall har angana 8 to 10 lec, ta tsaya jira na 12 to 2. Jikin motar Minal yar ajin su ta jingine jikinta, duk wanda yaxo wucewa saiya tsamma nin motar tace, daga gefen motan taji murya Minal da kawarta Billy suna hira da dariya sam batasan sun kunno kai ba da alamu suma basu lura da ita ba, hirar wata magazine dake rike hannun Minal sukeyi.
"Amma fah RMD dinnan ya burgeni, duba fa kiga CEO ne a Mobile oil Nigeria(MON), one of the major petroleum product marketing companies amma ji yadda yake keeping low profile, ko picx dinsa baa gani, koda yake ance ma hardly 20 letter word ke fita daga bakin sa" acewar Billy
Murmushi Minal ta saki wanda babu tantama ta fola mai dukda sunansa kadai yaya appearing a magazin din, "Ina zan Ganshi, na jima ina neman sa, ni wlh ganinsa kadai ya wadatar ni."
Dan duka billy takai mata tana dariya, "ance komai nasa customised yake da sunansa, kila idan da rabo zakiga motocin sa ko wani abu nasa wataran.
Tsur Batul tayi tana sauraran su, tana tuna motar RMD data gani dazu, dabarace ta fado mata ta saki murmushi, yawaci yaran masu kudi nan basu fiya sanyi kawace da talaka ba saidai iri iri su, balle ma Minal da take daukar kanta diyar shugaba, maganin su kadai zatayi ta hanyar raina masu wayo, tun shigowar ta poly bata samu kawaye ba yawanci yan kuci ku bamu ke manne mata, ita kuwa ta wuce ajin su.
Wayar ta chaina kirar S7 da screen yagama tsagewa ta fiddo ta dasa a kunnuwanta, da ganin wayyar sai ki rantse original dince.
"Hello RMd nayi fushi tun d'azo kace zaka xo"
"Toh ba komai, ka gaishe min dasu mama sai naxo gida gaidata" katse wayan tayi tana kallon su ta gefe ido, sarai sun jita, imani ya hanasu magana banda saki baki da sukayi suna kallon ta.
Taku daya biyu tayi da niyan barin gurin, sukayi azama tarota, Minal tace "Fatima kin san shine ?
A yatseni ta dubeta, aranta tana fadin shegia ashe tasan suna na, a fili tace "wa kenan ?
"Rmd mana, naji kin kira sunansa ne"
"Ayyo wai cousin dina Rmd, kina neman sane ?
Kafin Minal tayi magana Billy ta janye ta gefe,
Tana magana kasa kasa, alamun bata gamsu da Batul ba, kayan jikinta ma ya isa ya nuna class din data fito.
Gyara murya Batul tayi tace "nasan bazaku yadda dani ba, amma kusani ni abun duniya bai dameni ba shiyasa nafison zama simple, dan kun ganni haka dat doesnt mean am poor" k'arashe maganar tayi dakai masu harara sannan tayi gaba.
Da azama Minal tayi saurin taro ta tanai bata hakuri, harga Allah ta gamsu da kalamanta tunda shi kanshi Rmd din ance kudi bai dame saba same goes to his cousin kenan. Dakyar jidda ta hakura bayan billy tasa baki, sai wani ja masu aji Batul take wai ita mai cousin, Minal dai sai kokarin chilling dinta up take, a lecture ma kuna da ita suka zauna bayan an gama suka wuce African dish cin abunci, nan ma sai yatseni take ko dogon surutu tak'iyi karsu k'ureta da tambaya, gabanta sai dauks uku uku yake karsu barta da biyan kudin abinci dan plate dinsu akwai tsada gashi ta cire kunya taci tayi nak, sa'ar ta Minal ta biya duka bill din sannan suka firo tafiya gida, ba yadda basuyi da ita su ijiyeta gida ba taki yadda acewar ta  library xata shiga karatu, sai da taga sunja sun tafi da mintuna talatin sannan ta hau Marwa ta wuce gida murna fal zuciyan ta tasamu b'agas, sai dai tunanin ta daya "Ina Zan Ganshi?"



   Nima xarah nace Ina xan Ganshi, kuma Readers ina zaku ganshi ?


   Ku biyoni muje Neman sa😂😂
[10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI?*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com

                11-15

Cikin takun ta mai daukan hankali ta karaso tafkek'en had'add'an office dinsa, office mai shegen kyau. s
Secretary dinsa Charles tayi kicibis ya fito rike da wasu doc a hannusa, da axama ya risina gaidata cikin harshen turanci.
Atakaice ta amsa.
 "Mr Rasheed yana ciki ?
Yace "Baya ciki"
Bata jira cewarsa ba ta cusa kai cikin office din, binta yayi da duba ciki da mamaki halin rashin zuciya irin nata, ako yaushe saita baro department dinta taxo ganinsa amma ko kallo  bata ishe shiba, ba kuma shi zai hana gobe ta dawo ba.
    Lumshe idanu tayi ta karasakan swivel chair dinsa ta zauna shakar hadaddiyar kamshi dake tashi daga bisa kuma ta shingid'e barawo bacci yayi awon gaba da ita.

Agajiye likis yake driving harya karaso katafera building mai dauke da tambarin Mon, parking yayi, kafin ya fito guard uku sanye da black suit suka bude mai murfi hade da mika mai gaisuwa, ciki ciki ya amsa, ya fito hade da dagatar dasu ganin suna kokarin take mai baya, tsayawa cak sukayi ya wuce cikin building din, maaikatan  ciki sai gaida sa suke cike da girmamawa bai tanka ba banda haryan office dinsa ya nufa cike mamakin abu daya da yake a kullum idan yaxo office, idan kai ba komai bane ko kallo baka ishe mutane ba, laila kuwa yaro da kudi abokin tafiya.
Da azama charles ya mike hade da risina, "Good afternoon sir"
Hannu kadai ya d'aga mai bai tanka ba ya wuce cikin office, ranshi ne ya kuma bacci ya karasa kan daya daga cikin sofa dake gefe  ya zauna hade da daukar Wayar yana latsawa jifa jifa kuma yakan dago ya kalli yadda take baccinta anutse, yarinya kyakyawa tana bata lokacin sa akanta shifa bazai aure taba amma ta kasa ganewa. Koda yake laifin hajiya safara ce da take bata hope game dashi.

Charles ne ya shigo rike da wasu takaddau, ganinta yasashi ware idanu, sam ya manta Mardiyya ta shigo, idan bai tashe taba saidai kuwa ta kwana gurin yasan sarai Mr Rasheed baxai tashe taba, nufa yayi saitin ta yahau bubuga desk din, firgigit ta walka tana kokarin adjusting mayafin ta dake kokarin yarfowa kasa, kunya ce gabadaya ta kama ta ganin sa zaune saidai da alamun baisan tana gurin ba, mikewa tayi da azama ta gaida shi, bai tanka ba tayi saurin takawa bakin kofar xata fice taji yace karna kara ganin thin legs dinki agurin nan"
"toh" ta amsa cikin rawar ciki ta fice.
Kimtsa gurin charles yayi sannan ya ajiyemai takardun ya fice.


 ***
Salati tayi hade da mik'a bayan ta farka daga baccin wahalan da tayi, k'iran sallah magrib ya tabbatar mata da tafi awanni uku tana bacci, duk da tasan bacci sakaliya zuwa magrib ba kyau hakan bai hanata shingidewa ba, wani mugun yunwa taji ya turnuke ta sai sannan ta tuna da tun abincin African dish dataji da rana bata lashi komai ba.
Fitowa tayi daga dakin ta iske hassan da husaini na alwala gindin rijiya, sai yusuf dan karaminsu dake zauna yana cin shinkafa da wake. Hajjo sai kokarin kankamta gurin murhu take.
Mik'a ta kumayi akaro na biyu, tace "Hajjo kin gama abincin kuwa, har wani jiri jiri nakeji tsabar yunwa"
"Dayake ga uwarki baiwa ko, dan ubanki kizo kice tunda ke na girkawa, yar kusun uwa" Hajjo ta fadi cike da bacci rai, bata ko kalle taba tadau lankar samirar tayi cikin daki.
Dariya Hassana ya fece dashi, aranshi yaji dadi yadda Hajjo tayi mata, "toh ayi dai mu gani ko sabulu xai daina kumfa, "
Harara Batul takai mai tasan sarai inda ya dosa, tsaki tayi tace "banza kawai, toh munyi da toka ma yayi kumfa, kuma wlh ka shiga taitayinka idan bakaso nayi kudi na manta ka kasan dai ni matar manya ce"
Dariya yayi "wazai kwashe ki badai ..
Katse mai xancen Hajjo tayi daga daki, tana fadin "baza ku wuce masallaci ba ko ?
"Zamu" husaini ya fadi hade da jan Hassan suka wuce, dan shi dama magana ce makiyinsa, idan kaga yayi doguwar magana toh da Baba ne.
Cize baki Batula tayi danba karamin shak'a tayi ba, akalla shekaru shida ne tsakanin ta da hassan amma ya mugun raina ta, yaro dan shekara sha biyu sai ki rantse dan arba'in ne yadda yake tsaro xance. kallon yusuf tayi da har yanxu ya kasa cinye yar lomar dake cikin kwanon, tace "Kai tashi amso min salad da tumatur gurin Baba"
Kafin yayi magana Hajjo ta fito, bazai jeba, "ajiye abinci ka wuce sallah" ba shiri ya karashe loman yayi waje.  Ganin ba mafita yasa batul yin alwalar tayi sallah sannan ta zauna tsakar gida jiran ace ga nata abinci amma taji shuru.
Sallaman baba ne ya sata mike wa tsaye, ta amsa. "baba sannu da zuwa" ta fadi hade da amshe kwandon dake hannusa.
"Yauwa fatima, har kin dawo, ya makarantar ?
"Alhamdulilah"
Tabarma ta dauko ta shimfida ya zauna hade da shi mata albarka, itama zaman tayi tana kara mai sannu, baiyi mamakin abunda takeyii ba dan kuwa ta saba tarairayar sa, idan kuma halin nata ya motsa ko gaisuwa dakyar takeyi balle ta nuna su suka haifeta.
 Fitowa da langar abincin Hajjo tayi, tamai sannu da zuwa sannan ta koma daki dauko furar dana dama mai, sannu baba" Batul ta kuma fadi akaro na biyar,
"Kinci abinci kuwa
Tace "a'a, dama kai nake jira Baba"
"Lailai kuwa kin cika yar baba, hada mata muci", ba shiri tahau zuba mai da yaji suka fara ci, Hajjo na fitowa tahau salati, dire furar tayi tahau Batul da dundun, "dan ubanki tashi nace, wannan abinci badake na dafaba, yar banxan yarinyar marar mutunci"
Murtuke wa batul tayi bata da alaman tashi,
Cikin sanyi muryarsa baba yace "waike Bareera ban hanaki zagin taba, baki san cewa wana bakin naki shine xai iya kaita ga halaka ba"
Hajjo kam ta kule "Malam ai dole nayi magana, yarinyan nan na ganina ina aiki ko sannu balle ta temakamin, nagama kuma dan batta kunya taxo ta baje tana ci".
"Ki dunga hakuri, Fatima ai yarinya ce komi tayi bai kamata ki hurar da ita da yunwa ba"
Toh" kawai hajjo tace ta koma daki ta zauna, tana jinsu suna hirar da dariya har sauran yaran suka shigo aka barke da hira.


 ***
Washe gari dakyar tasamu wata bakar doguwar riga ta sanya,yawanci yan atamfofin nata sun sha jiki, kunyar sasu take kar su Minal su raina ta, mayafi karamin ja ta dauko tayi rolling, fitowa tayi ta leka dakin Hajjjo ta iske tana sharar, tace "hajjo saina dawo"
Zuciyar hajjo fawas ta amsa mata da
Toh batula, Allah ya temaka, ki dawo dawuri dai"
"Amin" butula tace tana murmushi, shiyasa takeson Hajjo sam bata da riko kaman ba jiya ta kama d'addaurewa ba.

Zaure sukayi kicibis da Baba xai shigo ta gaidasa, yace da ita ta koma tasanya hijabi dan shigar ta tayau zam bata mai ba, ba musu ta sanyo hijab bayan ta saka mayafin cikim jaka, ta fito ta amshi kudin mota ta fice.
Bata sha wuyaba tasamu marwa ya kaita poly, da sauri ta wuce girl toilet ta cire hijab din tasaka mayafin sannan ta wuce zuwa hall, already su Minal sun kama mata sit, zama tayi tana wani shan kamshi ana gamawa suka fito da niyya wucewa gida kasancewar lec guda garesu.
Minal tace "Fatima yaushe zamu je gaida cousin dinki ?
Yatsine fuska tayi tace "very soon, baya gari ya raka mamansa Abuja checkup suna dawowa zamu je"
Allah ya kaimu" Minal ta fadi.
Billy tace "y not muje gidan ku"
Gaban ta ne ya fadi, aita gwamma ce su mata duka akan suje gidansu, mazewa tayi tace "okay muje, saidai Daddy baya gari yaje paris"
"Ba damuwa" acewar Billy.
motar Minal suka shige, billy abaya, Batul ta babbak'e agaba suka kama hanya, tunanin karya da zatayi kawai take, tafiya mai dan nisa sukayi har suka iso Kawo, billy tace" Minal shigar mu layin can na siyi salad da tumatur mai kyau"
"Ki bari akwai wani can gaba"
"Nidai muje can din, customer din mama ne, can take turamu siyo mata"
"Tonaji", lemcy tace hade dayin ribas, Batul jiki duk ya mutu,  Allah yaaa ba gurin Baba take nufiba, bata gama tsorata ba saida Billy ta nuna Baba dake nesa tana fadin karasa teburinsa....
[10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com

            16 to 20

Tashin hankali ne ya dabaibaye ta, tayi saurin shingid'e cikin kujerar hade da janyo mayafi ta rufe fuskarta.
"Bba ina wuni" suka gaida shi, ya amsa ciki da fara'a, dan kuwa ya taba ganin Billy. Salad da tumatir masu kyau ta siya ta bashi kudinsa, ba yadda batayi ba yabar canjin yak'iya yabata kudinta, sai sannan Minal ta tab'ota "bazaki siyi komai ba'. banxa tayi kaman bataji ba. Godiya suka ma Baba kanan suka bar gun, Baba yaso ya gane kaman itace sai kuma yayi saurin kawar da tunanin sanin cewa da hijab ta fita kuma ma ina Fatima ina yawo da manyan masu kudi haka.

Adan firgice ta yane mayafin fuskar ta, duban Minal tayi tace "kinsan mi ajiye ni nan,  na msnta ashe mama ta aikeni chemist"
"Haba dai muje to" acewar Minal.
Cikin nuna damuwa tace "ku bari kawai, next tym sai kuzo, yanxu muna xuwa gida zatace na tsaya shad'anci a hanya".
"Eyya to ba komai, zaki gane gida daga nan" Minal ta fadi hade dayin parking
"Eh, gobe mu hadu skul, tnx"
Da sauri ta fito daga motan gudun karsu tsayar ta, Billy tai mata bye hade da dawowa gaba, itadai har yanxu ba wani yadda tayi da Fatima ba.

Saida taga sunja gaba sannan ta sauke ajiyar xuciya, "yan durun uwa halan hauka nake na kaiku gidan mu, yadda kuke nema Rmd nima nemansa nake, dan kuwa dani ya dace, ina xan Ganshi ?" Ta fadi hade da waiga wa kaman yana kusa.
Marwa tagani ya nufota tayi sauri tarar sa, leko dakansa yayi da niyyan tambayan inda zata sukayi ido ihu, atare duk suka ja tsaki, inda tasan wanslan matsiyacin ne da bata tsayar dashi ba, amma ba yadda ta iya.
"Layin yan wanzan xaka kaini "
Bai saurare taba ya kunna marwan sa yayi gaba, ya gwammace ya k'ona mansa akan ya dauki fitsararar yarinyar nan, yana ji tana xurfa mai zagi bai tsaya ba yayi gaba abunsa. Dakya tasamu wani ya kaita gida sam ta mance da sauya hijab, tana sauka idon Baba akanta daga can nesa yana kallonta, mamaki sosai yayi ganinta da gyale kuma babu tantama itace yagani a mota yammatan nan, ransa ya bacci ba kad'an ba, haka ya shigo gidan da magrib, yaran na gaida sa ciki ciki ya amsa, ya kira hajjo sun dade suna wata mahimmaciyar magana daga bisani kuma ya fice, Butul kam ko ajikinta aganinta can maganar da suka sabayi sukeyi, tun ba yauwa ba zataga iyayen suna tattaunawa k'asak'asa wataran harda sharar kwalla sukeyi, itadai bata san masu ba. Kayan da zata sa gobe take gogewa da dutsan guga na gwarwashi tana gama ta hange su, ta dauko sauran fanta dinta da Minal ta siya mata ta sha rabi, hade da tande baki, arziki akwai dadi da yanxu dan jolly juice zata jika tasha. Yusuf ta kwallawa kira ta bawa sauran yasha.


 ***
Zaune suke a dinning suna breakfast, babu mai magana cikinsu tsabar yadda suke bawa table manners dinsa, shiya fara gamawa ya mike zuwa palo ya zauna yana latsar wayarsa, sanye yake da kananun kaya dasukayi matukar amsar sa, tana gamawa Altine mai aikinsu ta kira kwasar kayan gurin itama ta koma kusa garesa ta zauna. "My boy bazaka office ba, Mardiyya tacemin kwana biyu baka zuwa da wuri ?
Fuska murtuke yace "xanje" ba tare daya dago kallan taba.
"Easy my boy, da Mom dinka fa kake magana".
Shuru yayi kaman bazaiyi magana ba yace "i know, did i say sumthing bad"
"No, amma ai saika kalle ni ko ?
Dagowa yayi ya kalleta, sam bayason yin fara'a yanxu saita kawo mai xancen Mardiyya, bama wana ba so yake kawai yasan meke tsakaninta da Hajiya safara danya tabbata itace ke uxura mata.
Kwankwasa kofar palo ne ya katse masu hanzari, Altine taje ta bude hade da gaida mai shigowa.
Murmushi Rasheed ya saki ganin daddy malam, dan saurayi ne mai shekaru 26 daganin kayan jikinsa kasan ba wasu masu hali bane sai rufin asiri. Dogon tsaki momy taja bai damu ba ya duka kasa gaidata bata amsa sa, ya nufi Rasheed suka gaisa cike da fara'ar sannan ya zauna, it seems urgent magana zasuyi saidai Daddy malam yayi shuru ganin hararar da Mom ke aikama sa,
"Muje waje " abunda Rasheed ya fadi suka mike tsaye.
Ba karamin haushi Momy taji ba, idan bata manta ita ta kawo daddy malam amatsayin mai wanke mata mota da dadadewa, tama manta dashi abunda bata sani ba ashe suna tare da Boy dinta har ila yau, ba yadda bata raba suba, sunki rabuwa. Tsaki ta buga akaro na goma tana fadin "mi xaai da talaka".

Garden suka nufa suka zauna a sit for two, Daddy malam ya nisa yace "ya gajiya ?
Lumshe idanu rasheed yayi yace akwai "stressed fah, amma am enjoying it, kamin aikin dana saka ?
"eh nayi, komai it ready".
Sun dade suna tattaunawa daga bisani suka tashi, mukullin motarsa na aljihu suka shiga motar yaja yayi dropping Daddy malam sannan ya wuce office.

***
Cikin sauri tagama shirun ta tsaf na zuwa office, dukda tayi latti bai hanata tsantsarwa kwalliya ba, harta fita ta dawo dauka wani hadaddan farin hanky dake ajiye karkashin pilonta, dauka tayi tana kallon yadda akayi embroidery sunansa RMD cikin hanky din da golden thread, ya burgeta matika, bisa hancinta takai tana shakar kamshi mai dadi dake tashi sanan tasa cikin handbag dinta ta fito da sauri, dan kuwa ostrich take son tsayawa tsiya mai kodan burger da pizza ne.
Hajiya Safara ta iske palo sai Abba dake tsaye da alamu shima aiki xai wuce, gaidasu tayi aladabce hade da masu sallama kanan ta wuce.
Abba yace da hajiya safara, "kinga yarinyar nan wlh tafiki hankali, halina ta iyo"
Harara takai mai, tace "oho dai koma miye nina haifeta ba ita ta haifeni, marasa hankali saidai ka nema a adanginka"
Kwafa yayi hade da karkata hulansa, ya fice daga palon cike da haushin yadda matarsa bata girmamasa, kaman shi mai y'a 25years amma baa ganinsa da gemu, ko dayake ya kusa tufkar hanci, maganin Safara kadai xaiyi ya huta, kuma yasan ta inda xaibi ya huce haushi.


***

Tun 8am suke zaune hall jiran lecturer yaxo, shuru bai xoba har 9 yayi, class rep yayi announcing bazai samu daman zuwa ba, watse wa kowa yayi kafin 12 lecture, Suna zaune pavement Minal ta kawo shawara suje ostrich siyan snack kasancewar ba nisa da poly. Bayan sun isa Minal da billy suka fito daga motar banda Batul da ta rike kai bata da alamun fitowa, Minal tace "bazaki shiga ba"
"Kuje dai, headach ke damuna"
"Mi zaki ci"
Fari da ido tayi, dama abunda take jira kenan, rashi kudi yasata tayi respecting kanta ta zauna, murya can kasa tace koma ma, ki hada mun da coconut ice cream"
"No p" Minal tace taja hannu billy suka karasa ciki.

Zaman mintuna uku tayi cikin motar, Mardiyah ta fito daga bakery din rike da ledar ostrich, tun daga nesa Batul ta saki baki tana kallon ta, ba karamin burgeta matar tayi ba ga wani takunta na kasaita,  bata gama sakin bakin ba taga ta karaso jikin motar rav4 dake parke agefenta,
hannu tasa cikin jakarta ta ciro mukullun motar saidai bata lura da farin hanky daya fado dagw cikin jakar ba ta shiga motar taja, da azama Batul ta fito daga motar tadau ka kafin tayi taku daya zuwa uku dan mika mata tuni Mardiya taja motar da axama tayi gaba, Allah sarki  ko sauri mi take, Batul ta fada tanai karewa hanky din kallo wani kamshi mai dadi ke fita daga jikinsa, warware wa tayi taga embroidery din RmD jiki kaman marar gaskia tahau ware idanu, ji take tamkar amafarki, wata mata ce wannan tahau mamaki, ita kam gaba ta kaita gobara titi jos, komawa motar tayi da sauri ta zauna ganinsu su Minal sun fito.
"Sannu kinsha zama" Billy ta fadi.
Minal ta mika mata nata ledar, ba kunya ta amsa ko godiya babu. Suna isa makaranta refreshment centre suka nufa suka zaman ci, kadan kadai Batul ta tsakura taci tabar sauran da niyyan kaiwa gida yin bagu.


***
 Bata daddara ta nufo office dinsa rike da ledar ta, tura kofar yayi daidai da budewa xai fito, kawunan su sukaci karo, "auchh" ya fadi hade da matsawa baya yana mata kallon sama da kasa, tsabar rudu ko nata azaban bata jiba tahau mai sannu hade da kai hannunta gurin, "dan Allah kayi hakuri basan kana gurin ba"
Hannuta ya matsar gefe, fuska daure yace "Mardiyya ban hanaki shiko min office ba?
Amaraice tace "am sorry, dama breakfast na kawo ma" ledar ta mika mai.
Amsa yayi yace "thank you" ya fice daga office din.
Ajiyar zuciya ta sauke, ta rasa mai xatayi ya burge sa, duk gayun ta da kyan ta bai dadarasa ba, kallon jikinta ta tayi babu abun less than 100k ajikinta, sarkar wuyarta ma ta Gold ce but still abanza harara a duhu.
Ficewa tayi daga office din ta iske Charles zaune a desk dinsa yana cin abunda ke cikin ledar, takaici ne yakamata kaman tayi kuka, wato bazai ciba shine yabawa secretary dinsa, kwafa tayi ta wuce yana gaidata ma bata amsa ba.


Bayan sun gama lecture ba yadda su Minal basuyi da Batul su ajiye ta gida ba taki fir acewarta wani research xatai a library, basu kawo komai aransu ba suka wuce abunsu sannan itama ta fito waje neman abin hawa bayan kusan minti 20 da tafiyar su. Allah Allah take kadai taje gida tama su Hassan kwalelen ice cream.
Cikin sa'a kuwa tasamu Marwan daya ajiye wasu tayi azama shiga tun kafin ma tahau ciniki, tasan idan ta tsaya ciniki saita kai dare babu wanda ya dauke ta.
"Yammata drop ne ? Taji muryar sa tamkar saukar aradu a kunnuwanta, shi kansan baisan itace ta fado mai cikin Marwan ba.
Dogon tsakin dataja yasa shi kyallero fuskan ta ta mirrro, ba shiri kuwa ya tsayar da niyyar taryarwa, batare da yace uffan ba ya tsaya jiran saukar ta.
Ganin ice cream dinta xai narke kafin taje gida yasa ta sausata murya , "eh drop ne  muje ko nawane xan baka, kudi ba matsala bane"
Hmm" yayi yaja Marwan suka kaman hanya da niyyan yimata rashin mutunci indai bata mai biya mai tsoka ba.
Wayarta ce tayi ringing, Dubawa tayi taga Minal ce, guntin tsaki taja gashi wayarta saida speaker akeji, idan kuma tace xata dauka zataji iskar hanya. Tsinkewa call din yayi ta kuma ringing.
"dan Marwa dan tsaya xan amsa kira"
Baice komai bw yayi parking daga gefe, kallonta yayi ta mirriro sai wani yatsine take sannan tadau call din.
"Fatima kin wuce ne ? Minal ta fadi daga dayan bangaran.
Cike da iyayi tace "eh, kuna tafiya Daddy yaxo dauka ta, ina cikin Jeep dinsa yanxu"
"Eyya Daddy ya dawo kenan?
Rike baki Batul tayi shataf ta manta tace masu yana  paris, mazewa tayi tace "yau yadawo, daga Airport yaxo dauka na"
"Okay, ina gaida shi, sai mun hadu gobe"
Bye" ta katse wayar hade da sauke ajiyar zuciya, Mamuda kam ya gama tsorota da yarinya mai babban suna, karya kiri kiri ba kunya balle tsoro Allah, gashi kuma ko ajikinta, bai gama mamaki ba saida yake ta ciro farin hanky daga jakarta tana shakar kamshi jiki hade da zuba murmushi. Idanuwa kawai ya zuba mata.
"Malam karka cinye ni man, ja muje" ta fadi tana harara sa, sai sannan ya dawo hayyacin sa, yakama kan kekensa sukayi gaba.
  Baba ke tsaye baki titi da tulin tumatur da tarugu a kwando yafi mintuna 30 tsaye, akalla Marwa kusan bakwai sun wuce ba wanda ya kallesa yawanci dama basu fiya daukan masu kayan miyan ba acewarsu kar Marwan su yayi datti, hango Marwan da yayi yana tohowa yasashi adduaa Allah yasa ya daukesa.
"yammata saidai kiyi hakuri, ga wani tsoho can dole na daukesa" Mamuda ya fadi
"Bangane ba, drop fah na dauka kuma kudi xan baka ba kyauta ba.
"Nasani karki manta kudi naki ne, amma Marwan nawane, kina iya sauka kibin rabin kudina"
Tsaki taja, "matsiyaci dai baiji dadi rayuwa ba"
Bai tanka ba, ya tsaya daidai ina Baba ke tsaye, ya fito yana "sannu Baba" hade da daukar gwandan tarugu yasa kan sit kusa da ita, afusace ta fito daga Marwan tana fadin "waikai wane irin wawane, zaka batamin jiki da taruugu..." Makoshinta xancen ya makale, ganin Baba agefe yana kallonta, "baba ina wuni" ta fadi tana yak'e.
Ciki ya amsa fuska daure inda gayamai akai bazai yadda yar cikinsa ke zubar da kimar ta hakaba, Mamuda kam bai kawo komai aransaba atunaninsa kawai ta gaida Baba ne amatsayin girmama babba.
"Baba muje" ya fadi bayan ya saka dayan kwando, su biyu da Baba agaba, sai Batul abaya da ta rukub'e, tsoronta daya kar Baba ya mata fada gaban matsiyacin nan.
[10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

xarahbukar.wordpress.com

          26 - 30

K'ashe gari bataje makaranta ba, fuskarta gabad'aya kumbure tsabar kuka, tana jiyo Hajjo da k'annan ta a tsakar gida suna hira taki fitowa, ga uban yunwa da takeji tun abinci jiya bata latsawa bakinta komai ba har ila yau da sakaliya tayi. Wayarta dake kashe ta kunna ta kira wani saurayinta shehu da tuni ta dade da jefasa a k'wandon shara, matashi ne irin masu son aci duniya, Baban sa mai kudi ne sosai, yana son Batul saidai son jiki irin nasa yasa Batul bata son basa fuska, bugu daya ya dauka tamkar jira yake, kirarin daya saba mata yafara tuni ta dagatar dashi, tacemai lailai yaxo bayan magrib akwai muhimmaciyar magana da takeson yi dashi, sannan kuma wen coming yaxo mata kayan dadi, naam yayi da bukatun ta cike da jin dadin kota sauya shawara game dashi.
Kaste wayan tayi taja jiki zuwa  bangon dakin ta shingid'e.
     Baba ke zaune daga gefen teburin kayan miyansa yana alwala, Mamuda ya karaso da Marwan sa ya faka gefe ya fito suka kara gaisawa da Baba, bai jima da bari gurin ba. dayar butar dake cike da ruwa ya janyo yayi alwara sannan suka mike zuwa masallaci dake gaba dasu kadan.
    Sadaf ta fito daga dakin rike da siliwas dinta a hannu, Hajjo ke sallah tsarkar gidan, ta tako ahankali ta bayanta tayi  waje da azama, ajiyar zuciya ta sauke ganin babu kowa rumfar Baba, waigawa tayi ba alamun motar Shehu sai ganinsa tayi da kafarsa yana tunkaro ta hannusa rike da bakar leda.
"Miye haka zaka zomin da kafa, ina motar" ta fadi tana karasawa garesa.
Dariya yayi.
"Popcy na yanani daukan mota saboda reckless driving danakeyi, mashin ma naso zuwa dashi"
Harara takai mai, "Allah kiyaye kazo gurina da mashin, ai aji down kenan, yanzu dai miye a ledar ?
Daf da ita ya matso, yanai kai mata wani shu'umin kallo, yace "Tukun nadai, , nifa duk kin hargitsa min kwakwalla, wace magana zaki gayamin ?
Ja da baya tayi kadan tanai mai kallon bansan haka sannan tace "Shehu temako zakamin, gobe xan kawo frnds dina gidanku su kanga amatsayin wani cousin dina"
Kallon rashin fahimta yayi mata, waye cousin dinki, ya sunan shi
"I dont know, nasan dai Rmd ake cemai, i want you to act like him idan mukazo"
Galala yake kallon ta, baiyi mamaki abunda takeso yayi ba, dan kuwa yasan halinta sarai, farkon haduwan su ba yadda bata jifan shi da karya, daya gano gidansu ne yasata saduda ta koma real Batulan ta, yanxu kuma ba mamaki wata bomb take shirin ajiyewa.
"Okay ba matsala, saikun zo din, amma nikuma mai zan samu in return, kinsan dai gwamnati ta hana aikin banza" cikin zolaya ya fadi yana kai hannu zai rikota, batare da ya kai hannusa ba ta warce ledar zatayi gaba, saurin shawon gabanta yayi yana fadin "Batula babu kodan kiss" kiris yarage yakai mata kiss tayi saurin kawar da kanta gefe sukayi ido hudu da Baba da Mamuda dake tsaye suna kallonsu. Rai bace Baba nufeta yana cewa "mia kikeyi da yaron nan, ban hanaki haduwa dashi ba"
Jiki na rawa tace "dama assignment zaimin"
"karya kike" Baba yafadi yana kallon shehu da tuni yasha jinin jikinsa, "uban mi ya kawo nan ?
Shehu kam be boye komai ba ya zayyane wa Baba abunda ya kawo shi, salati baba ya saki, wana wace irin yarinyace, shi Rmb yake kowa, wayene,  ina kika sanshi ?
Tsuru  tayi tana kokarin boye ledar abayanta, warcewa baba yayi ya bude yaga bankararriya kazar yahuza, innalilahi kadai yake ambata ya mikawa shehu leda hade da korarsa, fashewa da kuka tayi ta ruga cikin gida, Mamuda kam kasa magana yayi, kila idan aka duba ransa yafi na Baba bacci, tir kawai yake da hali irin na Batula, wani irin tsanar ta ke sokanshi a zuciya.
 Kwafa Baba yayi yace "yarinyan nan ga karya da kwadayi, tsoro na daya karta fara sata da bin maza"
Nisawa Mamuda yayi yace, "ayi hakuri Baba, kuruciya ce zata gyara nan gaba"
"A'a dai mamuda, i dont tink fatima zata gyaru, aurar da ita xanyi gobe goban nan kafin tajaza min abun kunya,  Yekuwa xa'ayi a masallaci maiso na aura masa"
"Baba ayi haka kuwa, kasan fah Batula mai kudi tasa ran aura kar talaka irina ya ansan tayin"
Kur Baba yayi yana kallonsa sannan yace "Mamuda na baka ita, dan Allah karka ce a'a kaine daidai da ita ba wasu can maisu kudi datasa agaba ba"
Gaban Mamuda ne ya fadi, shikam mai xaiyi da yarinyar nan, shuru yayi baice uffan ba banda nauyin da kimar tsohon da yake gani.
"Nasan baka sonta, dan Allah ka amsheta amatsayin Sadaqa na baka ita" baba ya fadi cikin murya kaman xaiyi kuka.
Kasa cewa Uffan Mamuda yayi har suka taka zuwa inda rumfar baba, Marwan sa yanufa ya zauna zaija ya kalli baba da shima kallonsa yake, jiki sanyaye yace "sai da safe"
Baba yace "indai ka karbi sadaqa ta gobe xan ganka karfe biyu agurin nan da shirin daurin aure,  bai iya amsawa ba banda jan marwan da yayi ya wuce, jan marwan yake amma gabadaya hakalinsa ba ya jikinsa, xancesu da baba kemai yawo akai, jin awani wawa horn abayansa yasa shi dawowa hayyacinsa,  parking yayi gefen hanya hade da fiddo wayarsa, dannawa yayi ya  kira Daddy Malam, magana daya biyu sukayi sannan ya katse.
Bayan mituna goma da parking dinsa wata arniyar Jeep ta karaso gurin, da azama Daddy malam da wani suka fito daga ciki, gaida Mamuda sukayi, bai amsaba ya fito ya shiga cikin jeep din, dayan da suke tare yaja Marwan yayi gaba, Daddy Malam na gefe shike driving suka isa wani karamin gida mai shegen kyau.
Parking yayi suka fito atare, Daddy malam yace "Mamuda ne ko Rasheed" ya karasa maganar cikin zolaya.
Fuskar daure yace "Rasheed ne"
Dariya Dddy malam yayi, "daga gani nagane wanan Rasheed ne, irin daure fuska haka, watx wrong ?
Ajiya zuciya Rasheed ya sauke, baice komai ba suka karasa cikin palon, zama yayi kan kujera, Daddy malam ya shiga toilet ya dauko spirit da detol ya zauna gefensa, yace
 "tym to get back to real Rasheed Mohammad Deeni" ya fadi yana mika mai cotton wool.
Amsa yayi, ya cire kodaddiyar rigar dake jikinsa yahau goge ko ina na jikinsa dake shafe da bakin mai, har kafafusa saida ya kalkale, artificial mustache dake fuskar sa duk saida ya cire  sannan ya shiga toilet yayi wanka ya fito fas ainihun Mr Rasheed dinsa, red tshirt da blue jean ya sanya ya fito palon.
Bai boyewa Daddy malam komai game da Batul da sadaqan ta da baba ya bashi.
 Sosai Daddy malam ya bushe da dariya, yace "ka yadda kawai tunda tana sonka, kuma kai take burin aure"
Nisa wa Rasheed yayi,yacd "Rmd mai kudin takeso ba Mamuda talaka ba, nifah na mugun tsanar ta ba kadan, i cnt tolerate her, nayi disguise din kaina ne just to find true love ba wata gold digger can ba"
"Ni kuma i tink you should marry her, just to teach her a lesson, irin su they have to experience defeats kafin su shiga taitayin su" Acewar daddy Malam.
Rasheed yace "Hakane kuma, ka kawo point, i will personally deal with her to the extend idan taji mai sunan Rmd bazata tayi gigin cewa tasan shiba, matsala ta Mom ce, i dont tink she will accept"
"Karka damu, i have an idea," Daddy malam ya fada, matsawa kusa garesa yayi ya gayamani wasu magana dani kaina banji ba.
kai Rasheed ya kada yace "are you sure zata yadda?
Daddy Malam yace"Bata da matsala, i'll talk to her"
Sun jima suna tattauna nawa daga bisani kuma Rasheed ya mike ya wuce gida.


 Kuka Batul tayita tsugawa a tsakar gida har Baba ya shigo gidan, takalmin kafarsa ya cira yana fadin kina tashi ana ko saina mauje ki" huf ta mike ta shige daki.
Hajjo da saura yaran dake zauna suna cin abincin a faratin daya ko ajikin su, yi sukai ma tamkar bata wajan.
"Mallam sannu da zuwa" Hajjo ta fadi hade da mikewa tsaye, yauwa Baba ya amsa mata ya kirata suka shiga daki, xayyane mata komai yayi da hukuncin daya yanke, sosai taji dadi danta jima tana neman yadda zata raba hanya da Batula sai gashi yau an badata sadaqa asauwake, fatan ta daya kar Mamuda yaki amsa, kodama yaki amsa saidai anemo ko waye alaka mai ita.

****

Yau friday tun Karfe goma na safe Batul ta fito da shirin fita makaranta, dakin Hajjo ta leka "na tafi" ta fadi fuska daure ko gaisuwa babu.
Kallon banza Hajjo takai mata, tace "babu inda zaki, ki koma daki ki hada kayanyi, yau zaki barmin gida"
"Ina da test ne, kuma ai nan gidan mune"
Harara hajjo takai mata
"Ayyo ashe dai matsiyacin gidan nan nakune bansani ba, toh baki da gado a gidan nan tuni Babanku yayi sadaqa dake, anjima kadan mijin daya temaka ya kwashe ki zai dauke ki ku tafi"
Ware idanu batul tayi tanai mata kallon rashin fahimta,
" kina bace min daga nan ko saina sharareki da mari" Hajjo ta fada cikin karaji da zare ido.
Tsum tsum Batul tayi ta koma daki ta cire kayan jikinta, tujajjiyar tshirt na tun lokacin siyasar Baba buhari ta APC ta sanya jikinta da tsohon zani ta fito gindin rijiya ta zauna hade da tagumi, ba xancen da Hajjo tayi ke damun taba, asalima bata gane inda maganar ta dosa ba dan kuwa babu yadda xaai ace an mata aure bada sanin taba.
 yunwa sosai takeji baa mata tayin abinci ba, gashi Hassan da Husaini basa nan, yusuf dake daki tare da hajjo ba bari zatai ta aike saba, ganin yunwa xai halakata yasa tahau hada wutan gwarwashi dan dama koko.

Fitowar su lecture suka shiga mota zasu wuce gida, Minal tace "Allah yasa dai Fatima lapia, tun jiya batazo skull ba, ga wayarta kashe"
Kwafa billy tayi tace, "bana gayamiki ba, fatima makaryaciya ce, na tabbata ramin tane ya kure shiya hana ta zuwa".
"Billy kar kice haka, ki mata uxuri, am sure zuwa monday zatazo ta kaimu gidan Rmd"
Tsaki billy taja, "wlh ta raina miki yawo, nikam muje gurin Baba mai kayan miya na siyi Salad.
Haka dai kika ce" Minal ta fadi hade dajan motar suka nufi rumfar baba, baya gurin sai Hassan dake zaune yana jiremai, ganin su Minal sun tsaya yasa shi mikewa hade da gaidasu, amsawa sukayi, Billy ta siya salad na 300 masu kyau, harza su wuce Minal tace "kyakyawan yaro, billy baki ga kaman su da Fatima ba" karaf a kunna Hassan, kallosu yayi ya kara fadada fara'arsa.
Billy tace "aikuwa suna kama, amma bazaki hada ba, Fatima masu kudi ina ita ina hada iri da masu saida kayan miya".
Dariya sosai Hassan ya kece dashi, jikinsa kawai ya gayamai fatima yayarsa suke nufi, yace "aikuwa inada yaya Fatima, kamar mu daya da ita"
"Haba" suka fadi atare, ina take
"Ga gidan mu can, kuje tana ciki" nuna masu gidan yayi da yatsa.
Billy tace "bana gayamaki ba, yarinyar nan makaryaciya ce, muje mu gani"
"Kidaina saurin concluding muje dai" Minal ta fadi hade daja motan zuwa gaban gidan, sauka sukayi suka karasa gaban kofar gidan mai langalanga, babu ko sallama Billy tayi gaba ta afka cikin gidan.
      Fatima na zaune gidin rijiya tana kurban koko a kwanan silba, tana ganinsu ta firgita, atsorace take kallon yadda suke mata kallon mamaki.
Sabule dankwalin kanta tayi tace "Minal sannu ku, kuma kunzo yin kitson ne ?
Kai kawai suka girgiza alaman a'a, tacigaba "gidan mu nacan baya, kitso nazoyi agidan nan"
Hajjo dake kokarin kama ruwa abayi kasawa tayi jin karyar da yarta take k'wandarawa, fitowa tayi bayan tayi adduaa fita bayi, kallon su Minal tayi da suma kallan ta suke, sannan ta kalli Batul datai tsuro tsuro da ido, tace
"Ba shakka gidan kitso kike zo, saidai bansani ba ko uwarkice makitsiyar....
[10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com

*For the world, it's just another day, But for you today is the best day of the year!* *Happee Bufdæ Biebee Isa, Wullnp..... It your Day Have fun🎉*

              31 - 35

Shuru Batul tayi tana sosa gashin k'eyarta cike da kunya, ji take tamkar ta mike ta fad'a rijiyar dake fuskantar ta, kayan jikinta ma ya isa susan karya take ba gidan kitso tazo ba.
Murmushin dabai kai zuci ba Hajjo ta sakar masu sannan tace "yammata mungode da ziyara, saidai bamu dafa komai ba balle mu baku gashi yaune daurin auran kawar taku"
Cike da mamaki su ukun suka zaro idanu suna kallon Hajjo, hardai Batul da firgici ya bayyana fuskarta, atare Minal da Billy sukace "Auran gaske ?
Kallon baku da hankali Hajjo takai masu, ina aka tab'ayin auran karya koda yake sunan Batul na biyu karya dole su watso mata tambayar, bata amsa suba ta juya ta shige daki.
    kallon tir da hali Billy ta watsa mata, "amma dai kinji kunya fatima, haihuwar irinki asara ce, banza, makaryaciya".
Haushi ne ya turnuk'e Batul, cikin borin kunya ta mike suka hau cece kuce, kasa cewa Uffan Minal tayi banda mamakin hali irin na batul da take, sau da dama ana bada labarin masu halinta bata taba yadda ba yau sai gashi ya faru akanta. Dakyar Minal taja Billy suka fice daga gidan, Hajjo dake jinsu bata lek'o ba, saidai asarar haihuwa da Billy ta fadi yay mugun mata ciwo, ita haihuwa k'yautar Allah ce komin ya yaro yake bai kamata ka dangan tashi da asara ko tsiya ba saidai ka bishi da fatan shiriya idan ya kauce hanya, tanaji da Batula har ranta halinta kadai yasa batason tsakan mata fuska.
 Saida Batul ta tabbatar sunja mota sanna ta fad'a dakin hajjo, ba tambayar duniya daba tai mata akan gaskiar auren, banxa kadai Hajjo tai da ita tana mai cigaba da hajun gabanta.

Farar yadi wace ake kira da mamar ya sanya da hula buluwa, fuskar sa fayyus daka ganshi kasan baya cikin farin ciki, daure wa kawai yake, nan suka hadu da Baba a bakin massallaci, gaidasa yayi alabadce, Baba ya amsa, ganin yanayin sa baba yace "Mamuda karka damu, idan baka da kudin sadakin nizan biya maka"
Yaken dole ya saki yace "Baba ba matsla, akwai kudin".
"Madalla, Allah yayi ma Albarka"
Amin",ya amsa suka karasa ciki, bayan sun gabatar da Sallah aka dauran auran AbdulRasheed Muhammad Deeni da Fatima Muhammad Yero akan sadaki duba goma kacal.  
Bayan sun fito wani mugun sanyi jikin sa yayi, wani abun mamaki shine yadda Baba bai tambaye sa akasari suna daya bambamta ba, sai mai cema dayayi "Mamuda aure zaman hakuri ne, dan Allah banda niba kayi hakuri da yarinyan nan"
"Insha Allah" kadai ya iya furta mai, Babu wanda yace uffan cikinsu har suka karasa gida, ta bangaran Baba bai kawo komai aransa ba game da sunan, aganinsa Mamuda da ake kiransa dashi lakabine na gidansu.
 Tsaye yayi waje Baba ya shigo gidan, turus yayi ganin Batula tsaye bakin kofar dakin hajjo da kodadan kayan jikinta, atunanin sa batayi wanka ba.
"dauko kayanki muje" Baba ya fadi.
Turo baki tayi "babu inda zani.." bata rufe baki ba taji saukar wayan rediyon bayanta, "wuce dan ubanki ki dauko kayanki" Hajjo tace tana shirin kara lafta mata.
Kaman zatayi kuka tace "banyi wanki ba, duk sunyi datti"
"Haka kuwa zaki kwashe su, idan kinje can kya wanke abunki"
K'in motsawa Batul tayi, saida taga Hajjo dagaske take sannan ta ruga daki tana kuka, kayanta dake cikin  tsohuwar ghana must go  ta daukA ta fito, hannu Baba yasa ya karbe suka fice waje Hajjo na mata fatan zaman lafiya.
     Kuka sosai Batul take bata gama girgiza ba saida taga Baba ya jefa ganar cikin Napep ga kuma Mamuda agaba yana shirin ja, harara ta watsa ma cike da tsana, cikin muryar kuka tace "Baba babu mota ne ?
"Kedai shiga muje" baba ya fadi.
Rai bace ta shiga, sannan ya shiga ya zauna kusa da d
Ita.  Kuka take ba k'agauta, ba auran miji ne ke b'ata mata rai ba sai cikin keke da za'a kaita, wato ma mijin matsiyaci ne, uwa uba yadda tayi planing ma kanta big wedding shine Baba da Hajjo suka k'askantar da ita, irin su Dinner, mother's eve, fulani day event dayawa datasa buri sun wuce ta, honeymoon da ake fita waje duk bazata samu ba, Allah ya isa kawai take ma dan iskan daya amshi Sadaqan ta kuma tadau alwashin ko waye sai yayi dana sanin amsarta.

Tudun wada layin yan kosai ne unguwar da Rasheed yayi parking Marwan, nan take ta kara fashewa da kuka da ganin gidan, tasan su talakawa ne, gidansu da take rainawa yafi wanan fasali nesa ba kusa ba, karamin gidane wanda rabinsa da salansa mai tsatsa aka kewaye shi, unguwar ma gabadaya ba fasali irin ghetto area ne da gwamnati batasan da zamansa ba.

Nasiha sosai Baba yayi mata sannan suka fito ya taka mata zuwa bakin kofa, yace "ki shiga kakarsa na ciki" acewar Baba.
Jiki sanyaye ta cusa kai ciki tana waigowa kallon Baba,   ran Rasheed adakule yake amma saida ya dara, nikaina xarah saida na dara (hhhh), Marwan Baba ya koma rasheed yaja maida sa gida.

Tsohuwar tagani zaune tana carafke adan karamin tsakar gida dako mutum 5 ya masu kadan su tsaya cikin sa, dukuna biyu ne  kananu da bayi dake lungu tsakar gidan an kewaye shi da kwano, hannu Batul ta aza akai tana ihun ta shiga uku ta lalace, sai sannan tsohuwa mai Suna Inna kulu ta lura da ita, mikewa tsaye tayi tana guda "amarya ta iso yiririiii"  karasawa kusa Batul tayi zata rikota, da azam Batul tayi baya tanai mata wani mugun kallo, "karki kuskura ki tabani"
Galala Inna kulu tayi tana kallonta, "kaji ja'ira miye aciki danta tabaki, jikana fa kike aure"
Harara takai mata, "jikanki ko matsiyaci, jifa gidan da kuke kaman akurkin kaji"
Bata ankara ba sai gab taji abakinta, Inna kulu ta buga mata dutse, hannu takai gurin taga jinin, kafin tayi magana Inna ta cafke kunnata, "bamu da tsiya agidan nan, bamu ganta ba bamu santa ba kina jina ? Kara damke kunnan tayi.
"Eh naji" Batul ta fadi cikin kagara, sakin kunna tayi, bata jira komai ba ta fada dayan daga cikin dakunan tana kuka,  wayam dakin yake ko yar katifa babu sai tabarma a shumfud'e, ajiye Ghanar tayi bisa tabarmar ta kwanta tayi filo dashi, kuka kadai take daga bisani Bacci  yayi awan gaba da ita, bayan Magrib ta walka kasancewa hutun Sallah take, jiki mace ta mike ta leko tsakar gidan, Inna tagani zaune tana can carbi, tsaki taja tace "tsohuwa yunwa nake ji"
Banxa da ita Inna tayi saida ta kare hade da shafa addua sannan ta kalle tace, "ba abinci agidan, saidai  kici kanki".
Gyara tsayuwa Batul tayi, "Aikuwa saidai ku nemo, dan ban iya xaman yunwa ba, Hakkina ne jikanki ya ciyar ni" cike da tsiwa take magana.
Murmushin dabai kai zuci ba Inna kulu ta saki sannan tace "lailai kin tabbata matar Sadak'a, daga zuwa yau sai nema hakki, anya kina barinsa ya runtsa yau ?
Salamar sace ta hana Batul kai mata amsa, amsawa Inna tayi ya karaso ciki rike da bakar leda da kullin kaya.
 kallon sa Batul tayi tace "nagodewa Allah, nasan Baba bazai barni agidan nan ba, bara nadauko kayana" ta fada hade da komawa cikin dakin da saurinta.
Kallon juna sukayi da Inna alamun ina xancen ta ya daso.
Ghanar ta dauko ta fito tana fadin "akurkin nan ba gidan zamana bane"
Kallonta kawai yake bashi da niyya motsawa, tace "Mamuda muje mana kar dare yayi,"
Zama yayi jikin wata rashe dake guri, yace "Muje ina ?
"Gida mana" ta fadi tanai mai kallon banza, duk atunanin ta Baba ya aiko a maida ta gida.
Cikin ko in kula da yanayinta yace, "kin taba ganin inda amarya ta koma gidansu bayan an kaita ?
Takaici ne ya cika, so take kadai subar gidan kafin jikin Inna ya dawo.
Inna kam ta gama kulewa da ita, tace "miye kake boye mata, kaine Mijin nata ba kowa ba, idan bata shima albarka ba ai bata zage kaba, in banda kai ma waxai amshi Sadawar ta"
Ware idanu Batula tayi jin kalaman Inna, saidai ta kasa gasgata shin mafarki take ko gaske, yama zaai ta auri Mamuda, mai yake dashi, waye ubansan, murya Inna data ciyo tana fadin mijinki ne yasa ta zabura hade da wurgi da Ghanar, ihu take tana nema agashi dan kuwa mutuwar tace kadai xai fiye mata akan taga mumunar rana irin tayau, kuka take tana fadin "Allah ya sauwake na zauna dakai, banza matsiyaci, talaka, bakauye, kashe kaina xanyi akan na zauna dakai" sambatun take kaman sabuwar mahaukaciya, kallonta kawai suke, zuciya Rasheed kaman ta fito dan haushi, kalamanta ba karamin zafi sukai ma, inda da gaske zata kashe kanta dayafi kowa farin ciki.
Iya k'ulewa Inna takai, gaftareran wuka dake bisa tagar dakinta ta dauko, ta cilla daidai inda kafar Batul, atsorace taja baya dan kiris ya rage bata kwaye mata fata ba.
"dan uwarki dau wukar ki kashe kanki, shegiyar yarinya, kin dauka muma sonki muke, kina mutuwa bamu da asara, keko uwarki da ubanki basu da asara, yar banxa tantiriya, gwara ki mutu mu huta" Inna ta fada cikin daga murya da tsananin bacin rai.
Cikin karaji Batul tadau wukar kamar zata cakawa kanta, ganin ko ajikinsu yasata cefar da wukar, tabbas basu da asara idan ta kashe kanta balle ma wana hauka yakai ta kashe kanta tun burinta bai cika ba, danne zuciya kadai zatayi ta zauna kafin kwana biyu ta san inda dare yayi mata.
Tsaki taja tadau ghanar ta koma daki, mikewa yayi yama Inna ido sannan yabita zuwa dakin, jikin bango ta rakube tana sauke ajiyar xuciya, ko fitila babu dakin sai hasken farin wata daya gauraye ta waje, ganinsa da tayi yasa ta mike tsaya hade da kaimai kallon banxa, ledar ya mika mata "ga abinci kici"
Ba kunya ta amsa, ya fice.  zama tayi  bata lura da kullin kayansa daya ajiye ba, bude ledar tayi taga
Kosai biyar da guntun biredi, tsaki taja, aranta tanai karajin tsanar Mamuda, in banda tsiya ko yar kazar amarye bai iya siya ba (ni xarah nace idan ya baki kaza, ke kuma ki bashi miye ). yunwar da takeji yasata cusawa dan dole.

Hira da dariyar Inna da Rasheed keyi, tana jiyo dariyar su amma bata tantance mai suke fada ba, tashi tayi ta sakawa kofar sakata sanna ta koma tayi kwanciyar ta. Mikewa yayi ya kwakwaso yace ta bude, tayi banxa tayi dashi, saida yace ta miko mai hula cikin kayansa sannan ta lura dasu, dauka tayi ta bude kofar bata mika mai ba tayi cille dasu waje hade da rufo dakin da sakata.
Bai damu ba, dan kuwa da gangan ya ijiyesu, tsince su yayi yakai dayan Dakin da Inna take ya ajiye sannan yay mata sai da safe yabar gidan.





TeamMardiyyah ❤
[10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

             21 - 25

Daidai inda rumfar Baba ya tsaya duk suka sauko yahau agazamai sauk'e kwandon. Batul kuwa bata jira komai ba tayi gaba da azama.
"ke yazaki gudu baki bani kudi ba ? Mamuda ya fadi ayayinda yake kokarin dire kwando hannunsa, bata juyowa ba balle ta tanka banda saurin da takeyi, nisawa Baba yayi yace "ya'ta ce, zan biya gabadaya"
Sunne kai yayi, kunya Baba yaji ya lulub'esa, inda ya biyemata yaukam da girma ya fad'i, taimakon Baba yayi  da wanke tumatir sannan ya tayasa kaso, albarka sosai baba ya shimai, dukda ba wata doguwar hira sukayi ba amma tsohon ya kwanta mai arai, yana shirin tafiya Husaini ya k'araso gurin ya gaida sa aladabce, ciro dari takwas Baba yayi ya mikamai, fir yaki karba, ba yadda baba baiyi ba, ganin yaki karban halal dinsa yasa baba yace Husaini ya kaisa gida yaci abinci kanan ya wuce, dukda Mamuda baiso hakan ba amma wata xuciyar ta tursasa mai son xuwa gidan.
    Hassan tsaye gindin rijiyawa yana wanki, sai yusuf dake zaune daga gefe yana homework, Hajjo ta fita mak'ota barkan haihuwa,  Sallama sukayi Hassan ya amsa suka karaso ciki ya gaida shi, "Batula fito ki sawa bak'on Baba abinci" Husaini ya fada daidai tsetin dakin, kayan jikinta take ragewa tasanya wani kod'adda tshirt da zani, tana jinsa tayi banza banda kokarin bude ostrich ledan ta da take, sake maimatawa yayi sannan ta amsa mai, "Batula yafita daga bakinka kafin na fito na wanke ka da mari"
"Tofah, Manya na magana" Hassan ya fada yana dariya, harara Husaini yakaima,  ya kalli Mamuda yace kayi hakuri bara na zubo ma" tabarma ya shimfada mai sanan ya zubomai dambun hatsi da Hajjo tayi, murmushi Mamuda yayi hade damai godiya yahau cin abinci da tunda uwarsa ta haifesa bai taba gamo dashi ba, haka dai ya daure yana cusawa.

 Fitowa tayi daga dakin rike da ledar tana shewa, batama lura dashi ba tadau kujerar tsugunno ta zauna tsakaiyar gidan, "yehoo ku fito yau party zamu.." Ido hudu sukayi ta kasa ida maganar, sai kuma ta dauke kai kaman bata sanshi ba gudun kar yayi mata magana su Hassan su dauka ko saurayinta na.
"Party nami" Hassan ya tambaya.
Ta gefe ido ta kalli Mamuda sanna tace "kayan dadi sabon saurayi na ya tsiya min, idan kunaso na baku zakamin wanki, shi kuma husaini yamin guga, auta kuma ya gogemin takalmi" ta karashe maganar tana kallo yusuf da tuni yawu ya tsinke mai, atake Hassan ya yadda ta mika mai burger ya karba yana santi, yusuf kuma ice cream aka bashi banda husaini daya hada rai bayaso.
Hassan yace "wai waye saurayin nan naki, yana zuwa nan ?
Fari tayi da ido, "mai kudi ne ba lailai ne kasan shiba, kana jin labari wani Rmd, most influential family a garin nan"
Yace "gaskia bansan shiba, halan shi ne saurayin naki ?
"Eh fah shine, very soon xai turo gaiswa".
Wage baki Hassan yayi yana kallonta, yasanta sarai da karya amma wanan kam ya wuce tunaninsa, kwashewa yayi da dariya yace " uwaka karya, ubanka karya, Batula kinayi ina jin dadi kina bari ina jin haushi, ina mai kudi ina talaka irinki, dan Allah ki rage ta gobe"
Kowa gurin saida ya kwashe da dariyar abunda Hassan yace, Mamuda kam harda rike ciki yana darawa, yarinya ga kyau amma ba kyau halin, saidai yadda take karya in a classy way ke kara bashi dariya.
Akule ta mike tsaye, "banxaye sai kuyi tayi dai, yan bakin ciki" fuu ta wuce daki da kunin rai, tana jiyosu suna kara darawa.
Mikewa mamuda yayi yamasu sallama ya fice dan kuwa idan ya xauna yana iya amayo kayan cikinsa, gurin baba ya nufa yamai godiya samlnna ya wuce.


 ****
A firgice ta farka tana karewa dankareran palon kallo, hamdala tayi da Allah yasa mafarki tayi ba dagaske bane da yau hankalin ta tashi xaiyi idan 
My boy ya gano akwai boyayyan al'amari da take boye mai sama da shekaru talatin. Altine ta kwalla wa kira ta kawo mata fresh milk tasha ta shingide cikin kujerar tana kokarin kawar da rayuwar past dinta dake neman dawo mata sabon fill ababin rayuwarta na yanxu.
Sallama sa ce ta katse mata tunani, ta amsa cikin boye damuwar ta, karaso wa yayi kusa gareta, "Mom are you alright, naga your face is pale"
Murmushin dabai kai zuci ba ta sakar mai, "am, good, ya yau din ?
"Lapia kalau, i really enjoy it" ya fadi yana murmushi, itama murmusawa tayi cike dajin dadin ganinsa cikin farin ciki, bisa cinyarta ya ajiye kansa tasa hannu tana kwantar mai da lausasan gashin kansa, tace "Abdulrasheed yau kasani farin ciki, alway b happy kaji?
"I'll Mom" ya fadi yana kara fadada fara'arshi. Wayarsa ya laluba aljihu ya ciro yayi daillng no din Mardiyya, zaune take tsakiyar gadonta Tana tofa addu'ar bacci taga call dinsa, tsoro da mamakine ya kamata by diz tym ace ya kirata, jiki sanyaye ta dauka, tayi shuru.
Murya kasa kasa
Yace "Mardiyya hope dai ban tashe kiba ?
Dadi taji yadda ya kwantar da murya tace, "banyi bacci ba, ya daran ?
"Cool'
Shuru tayi tana juyo heart beat dinsa, nisawa yayi yace "mi kika dauka a office dina ?
Gabanta ne ya fadi itakam bata dau komai ba banda daya daga cikim hanky dinsa data zara amma kuma bata san inda ta ajiye ba, tace "ban dauki komai ba"
"Are you sure ?
Tsoron Allah ne ya shigeta, karya itace abunda bata iyaba, "am sorry Mr rasheed   na dauki hanky dinka without ur consent"
Ajiya zuciya ya sauke, "ina hanky din yake"
Cikin rawar murya kaman zatayi kuka tace "i lost it"
Abinda yake sonji kenan, katse call din yayi, aransa yana tunatin where on earth ita kuma wacan tasamu hanky dinsa, Mom ce ta katse mai tunani da cewa "my boy nasan kana santa, ka aureta i promise you won't regret it"
Kallon rashin fahimta ya daga kai yay mata, tace "dont be silly, who else idan ba Mardiyya ba"
Yake kawai yayi ya maida kansa, zuciyar na bijiromai abubuwa da dama.

****
Yau da wuri taje lec ta dawo kasancewar ruwa da akayi ta makawa yasanya yawanci lecturers basu zoba, tana ganinsa tare da Baba akaramin zauren gidan ta bata fuska, shishigin yafara isarta tun ranar daya sauke su akullum sai yaje teburin Baba hira, yanxu kam tamkar yaron baba haka ya zama duk wani aike da dauko kayan miya gurin tsari shi Baba ke aika, takai ma yanxu sun saba da Hajjo, har wani kwanan abincin daban take ajiye mai.
Baba sannu" ta fadi cikin hade rai, dama akulle ta dawo da haushi Billy yau data tsitsaye ta akan deceiving dinsu take, fada sosai sukayi saida Minal tasa bakin akan lailai gobe saita kaisu gidan su cousin dinta Rmd, karfin hali kawai tayi ta amsa masu da naam, ranta duk ajagule ta rasa mafita.

Kallon ta Baba yayi, yanayinta ya nuna ba lapia ba, yace "fatima mike damunki ?
Kuka ta fashe dashi "Baba nikam na gaji da talaunci nan, wai yaushe zakayi kudine, miyasa ma na fado cikin zuria ka" sosai tafashe da mugun kuka, kollanta Baba kadai yayi yana murmushi bayau mace tasaba cin zarafin saba, saidai kalaman fatima ba karamin fama mai ciwo daya dade da samun waraka azuciyar saba.
Ran mamuda kam ya gama bacci hannu ya daga da niyyan sharara mata mari, baba yarike hannusa "dukan mace bai kamace kama, karka kuskura" Acewar Baba.
Harara Batul ta kaimai ta ruga gida aguje, baba ya rike hannusa suka fice zuciyarsa na tafarfasa.

Gam Hajjo ta capke ta data shigo, dan kuwa duk abunda tace taji ta, kaman an aikota tahau Batul da dukam tsiya, banda ihu da kuka ba abunda take,
"Kafin ki kashe ubanki ni xam kashe ki" hajjo ke fadi cikin kunin rai tana mai kara kai mata naushi, saida tayi mata lillis sanan ta barta tana fadin "yar banxa yarinya, kasheki xanyi na huta da bakin cikin ki, nagode wa Allah daya azurtani da kannanki dayau kin kasheni abanza"
Kuka sosai Batul take, tana jawa bawan Allah mamuda Allah ya isa, aganinta tunda yaxo hajjo ke kirbanta, dan kuwa rannan abinci taki zubamai hajjo ta mata lilis yauma ba, wani mugun tsanan shi take ji aranta, ayyada zuciyarta ke tafasa inda zataga Rmd binshi kawai zatayi tabar masu gidan, dan kuwa shine kadai gatan ta yanxu.
"Oh ni fatima ina Xan Ganshi,.." Ta karasa magana cikin matsananci kuka, atunanin ta a zuciya ta fadi not knowing afili tafada, jim muryar Hajjo tayi akanta rike da ludayin miya, tana cewa , idan na fasa maki baki zaki ganshi da kyau"
Ba shiri ta mike da azama tayi cikin bayi da gudu tana kuka.
[10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com

              36 - 40

 K'ashe gari da k'arfinta ta tashi, fuskar ta dauke da murmushi dan kuwa tayi alwashin daina zubda tsad'addan hawayen ta kan matsiyacin nan, ranar kin dillanci kadai take jira.
Kayan jinkinta ta cire ta dauro zanin wanka ta fito tsakar gidan, bayin ta leka taga babu ruwan balle famfo sai bukitin k"arfe marar hannu dake ajiye, tsaki taja aranta tanai tir da talauci, kofar Inna kulu ta nufa ta tsaya, babu ko gaisuwa tace "Tsohuwa xanyi wanka".
Daka cikin k'uryar dakin Inna tace.
"nazo na mike ne ?
Mikewa tayi hade da sunkutan redionta ta fito tana kara maimaita abunda ta fadi.
Cike da tsiwa Batul ke kollanta, "ruwa zaki ban nayi wanka"
Yar tsugunno dake gurin Inna ta dasa mazaunin ta akai sannan tace "ayyo ainan babu ruwa, waje zaki je akwai burtsatsan unguwa saiki dibo"
Kallon rainin Batul takai mata, tayama xata fita waje diban ruwan kamar wata buduwar k'auye, agidama Hassan ke jamata ruwa a rijiya balle kuma nan daba zama taxo ba.
"Ba girma na bane, saidai jikanki ya fita ya debo min"
"Toh saiki jirasa yaxo" Inna ta fadi cikin ko ta kula da kallon da take mana.
"Ina ya fita da safan nan" Batul ta tambaya .
Banxa da ita Inna tayi, saima redio data kunna jin labaran karfe takwas. Tsayuwar mintinu ashiri Bayul tayi, Inna bata tanka taba, wanka kadai takeson yi danji dadin jikinta, ganin tsayuwar ba amfani yasan ta komai daki tasanya hijb ta fito, bokitin dake bayin ta dauka ta fice waje.
Sai yanxu ta karewa unguwar kallo, jama'an cikin ta ba abun kallo akara bane, gaba da gidansu kadan butsatsan yake, mutane kusan ashirin data ganin bisa layi yasata jan mugun tsaki, itakam bada ita zaai haukar nan ba, dole nema subarta ta diba dan ita ba kalar subace. Karasawa tayi tanai ma kowa kallon wulakanci, su dinma ita suke kallo, dire bokitinta kusa da wanda tagani yana diba, jira kaidai take ya cire tasanata, yana cirewa kuwa ta sanya, murmushi tayi ya kusa cika babu wanda ya tanka ta, saima kallon ta da kadai suke, kadan ya rage ya cika, wata yarinya dake can baya ta karaso tasa hannu tayi wurgi da bokitin ruwan ya kelaye gurin.
"Ke kin isa, wa kika fi gashin tsuliya anan dahar zaki raina mana wayo kizo ki ganmu alayi dan iskanci shine zakiyi babakere" yarinya mai suna Dija ke magana cikin karaji da zare idanu.
Murtukewa Batul tayi, ta nunata da yatsa, "ke bakauyiya, ki kiyaye ne, kinsa dawa kike magana kuwa "
"Nasani mana, da mutum nake bada dabba ba, layi kuwa sai kinbi tunda ba ubanki ya kafa famfam ba"  kallon sama da kasa Dija ke mata ayayinda take maganar.
Dariya yan gurin su kwashe dashi, daya dake gurin tace "kalle tafa damu da ita banga bammaci ba, sai felekan tsiya harda wani ansan dawa take magana, kaji ja'iri, mukam nan saidai kici na jaki"
Ruwan ne ya cinye Batul tayi tsit, tayi underestimating dinsu, batayi expecting zasuyi magana ba yadda tayi masu kallon yan primitive society, cike da kunya tadau bokitin ta koma baya ta tsaya, dariya kuwa basu fasa ba, ignoring kadai Batul tayi har layi yaxo kanta, bisa kai ta aza ta koma gida cike da tausayin kanta. Wanka ta shiga sharp shrp ta fito, sauri take tana da lecture by 10.
 Kwalliya sosai tayi cikin atamfa riga da skirt ta fito ta riske Inna hartai wanka tana zauna bisa tabarma tana shan shayi da buredi da fried kwai, mamaki karara tayi yaushe Inna ta debo ruwan waima yaushe ta kunna murhu aza ruwan zafi da soya kwai, gadai murhu babu alamun an taba, tsaye tayi kan Inna, "kudin mota, xan wuce makaranta"
Cikin fara'ar Inna ta kalleta tace "mijinki zaki tambaya bani ba, kuma ai kyaci abinci kafin ki fiti ko".
Kaman jiran take tace toh xan ci" wazai ga kwai da biredi ya kyale, dama yunwa takeji ba kadan.
"Gashi" inna ta fadi hade da mika mata bakar leda
Budewa tayi da azama, saidai abunda tagani yasata yamutse fuska, taliyar hausa ce danya da manja da kulli gishiri da yaji, "Tsohuwa miye wannan"
"Abincin ki mana, dare da rana, ga murhu can ki dafa asawake, ga langar samira xan ara miki tunda baki kawo tukunya daga gidan kuba"
Kuka ne ya rage Batul batai ba, daurewa kadai tayi ta ajiye ledar ba tare datace uffan ba, tunanin kawai take ta tashi ta gudu ne ko yaya, toh idan ta gudu taje ina, shi wanda take muradin so baima san da zaman taba, fuskar sama ba sani tayi ba, ance he is  rich & simple, amm toh ina zata ganshi, burinta daya taga tazama matar mai kudi ba matar matsiyaci ba.

 Zaman kusan awa biyu tayi  gurin Mamuda bai zoba, yunwa na nema illata ta, mikewa tayi tahau aza murhu, abunda bata taba yiba saidai Hajjo tayi, ba karamin wahala tasha ba sannan wutan ya kama, karamar bokiti datagani tadau ta debo ruwa ciki tahau kikirkiri din daura taliyar.
 Bayan ta sauke, ko tayi batama Inna ba tahau ci. Sai bayan Sallah azahar Rasheed ya shigo gidan, tana ganin sa tahau surfa masifan yaja mata bataje makaranta ba, gaisawa da Inna yayi kafin ya zaune yace mata "banda halin ciyar dake da biya miki na makaranta, hakuri xakiyi idan Allah ya hore nan gaba kyaje, rayuwa saida manaji, ina abinci na ?
Ya gama soka mata kibiya azuciya, daskerwa tayi tana sauraran sa sannan tace "duk inda kudi suke dole ka nemo su, uwarka ma tayi kadan ta hanani zuwa balle kai karan kadan miya, abinci kuma ban dafa dakai ba"
Kallonta kawai yake bai ce uffan ba, aransa fadi yake bakisan uwata ba dole kice haka, duk randa kika shigo hannuta zaki gane ruwan ba sa'a kwando bane.
Masifa sosai da fitsara tayi tamai, wata zuciyar nace mata toh idan kinje makarata kicewa su Billy mene, ai da kunya ma, kila ma sun gama yada ta aduniya, hakura kadai zatayi tayi da batun makaratta kafin tasan abunyi nan gaba.



****
Sati biyu zani bata canxa ba, halin Batul sai wanda ya karu, akullum Rasheed xaije gidan amma maganar arziki bata hadasu, iya kaci susha hira da Inna da dare ya koma gida, dadi sosai Batul takeji aganinta a kekensa yake kwana waje ita ta kame a daki, wanka da cin abinci duk bayayi agidan, atunaninta tsoronta ya hanasa sakat.
 Ta bangaran Inna kuwa ta rasa daga ina ake kawo mata abinci mai rai da lafiya, saida taga tanaci amma ita an barta da manja da yaji, ba abunda ya shafe ta, opportunity kadai take jira ta fece.

 Yau ya jima a gidan suna hira da Inna, sai kusan tara yamata sallama, rai bace yabar gida, yafara gajiya da cin mutunci Batula, sakinta zaiyi ya shafawa kansa lapia tunda ba sonta yake ba. Inyaso taje can ta karata da karyar ta, shidai Rmd ya mata nisa saidai ta nemi wani can daban.


Agajiye likis ya dawo gida bayan ya tsaftace jikinsa, Mom ya tarar tsaye tsakiyar palon tana kai komo, kafin yakai ga isa gareta ta tunkaro sa, cike damuwa tace "my boy daga ina kake by this tym
Agogon hannusa ya kalla, goma dayan mintinu amma ji yadda take interrogating dinsa kaman karamin yaro ,rabawa gefenta yayi ya zauna kan kujera,
"Ancemin kwanan biyu bakaje office ba, idan kasa wasa asset dinmu xai iya dropping" ta fada tana kai mazaunin ta dayan kujerar dake gefensa.
Takaici ne ya cikasa, matan biyun duk sun dauramai zafi, ya dawo gida bai tsira ba, Mom dinsa mai kudi amma sai shegen son kudi alway seeking for more, dayar can kuma talaka but desperate to be rich by all mean, kodayake baima san inda ta dosa ba, karyata kadai ya isheshi bugun zuciya.
Nisawa yayi yace " Mom gayamin make tsakanin ki da Hajiya safara"
Gabanta ne ya fadi, wace irin tambaye ce wannan, ta fadi aranta, afili tace "babu komai, kawata ce tun muna yammata, miyasa ka tambaya ?.
Kawar da tambayar yayi dacewa, "na yadda xan aure Mardiyya"
Dariya mai dauke da farin ciki tayi, "ka fara sonta kenan ?
Kai y girgiza, "a'a, xan bata chance ne, you once said kwarya tabi kwarya, shiyaaa nayi deciding auranta"
Dadin sosai Mom taji, atleast xata huta da threat din Hajiya safara, saidai wani hanzari ba gudu ba, zusa katsina ya kamata, amma da wana ido zata dubi kawu Habibu, kusan shekarau sama da ashiri ta yayesu a ababin rayuwar ta, saukin abun ma My boy yakan kai masu ziyara. Mikewa Rasheed yanai mata Sai da safe, bai jira cewarta ba yayi gaba, tuni ya gano ta lula duniyar tunanin dabai san ta miye ba.

Bayan kwana biyu ba inda yake zuwa sai office, da wuri yau ya shirya ya fice office, aiki sosai ya wuni yana yi, charles ne ya shigo yace Mardiyya keson ganinsa it urgent, izini ya mai data shigo, sanna ya fice.

Da sallama ta shigo, hannun ta rike da files, amsawa yayi yanai sakar mata murmushi, karfin gwiwa ta samu ta karasa ta  hade da mika mai, bai karba ba ya mata nuni da ta ajiye,
"Ki zauna mana" ya fada ganin tana shirin fita.
Akunyace ta zauna, yace "Momcy bata gaya maki good news ba ?.
Sunne kai tayi danta gane inda xancen ya dosa,
"Ya preparation"
Nisawa tayi, dakyar tace "babu wani shiri, am sure kaima you aint interested da wani grand Preparations".
Murmushi yayi yana cigaba da kallonta, duk lokacin nan yarasa miyasa bai gano good side of her ba sai yanxu, koda yake Batula ta sanya shi gano hakan, sau da dama akance yaran masu kudi basu da tarbiyya ashe ba duka aka taru aka zama daya ba, guntun tsaki yaja aranshi,  bai taba cin  karo da bad girl irin Batula ba, wani mugun tsanar ta yakeji aranshi.
"Marfiyya inason auran nan yaxama grand weedding, wanda kowa a duniya saiya san ni Rmd nayi aure".
Tsuru tayi tana kallonsa, ita mamaki ma yabata all of a sudden ya yadda da auranta kuma big wedding yakeso, kodayake itama hakan takeso, halinsa yasa ta kama kanta.
Hira sosai sukayi kaman masoyan asali, tun tana kame kanta harta saki jiki tana dariya.



          *Katsina*


Wedding Bells 💃💃💃💃💃💃💃💃💃
[10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com

              41 - 45


Katsina..

K'arfe sha biyu na rana direban Mom yayi horn gaban kataferan gate din gidan Kawu Habibu, bude  gate mai gadi yayi da azama kansancewar ubangidansa ya sheda mai zuwa su.
  Parking yayi ya fito ya bude mata kofar b'angaranta, cikin isa ta fito tanai karewa gidan saman kallo sannan ta taka zuwa  tangameman palon.
    Ajiyar zuciya kawu Habibu ya sauke, tun shigowarsu yake tsaye bakin window benan yanai kallonta, hali da bazai canza ba abunda kadai ya furta sannan ya juyo saukowa.
    Hajiya Suwaiba matar sa  ta fito daga kitchen, kicibis tayi da ita tanai ma palon mugun kallo, "hajiya Fati harkin karaso ashe, sannu da zuwa" Hajiya Suwaiba ta fada cik'e da fara'a.
Ayatsine tace "sauri nake kice wa Kawu na iso"
Gyaran murya kawu Habibu yayi yana saukowa.
Kunya ne ya kamata batayi tunanin zai jita ba, mazewa tayi tace "Kawu ashe kana kusa, ina wuni".
"Lapia lau Fatima",ya amsa  hade da zama kan kujera, itama zaman tayi, hajiya Suwaiba ta koma kitchen nema mata abun sha.
Gaisuwa sukayi mai tsawo kafin Mom ta gabatar da abun da ya kawo ta, Jinjina kai kawu yayi, yasan tabbas rana irin tayau zataxo, matar da bata daukesu abakin komai ba shine yau ta tako taxo dan danta xaiyi aure,  ashe dai komai nada ranarsa.
Nisawa yayi yace "naji dadi matika, Abdulrasheed zaiyi aure, naso ace na hadashi da diyata Hafsat saidai hakan bai yuyu ba".
"Gaskia ne" Mom ta fadi tana murmushi dabai kai zuci ba, yaushe ma zata yadda Hafsat ta auri Rasheed, mai kawu yake dashi ma, mutumin da rabin dunkiyar sama Ubanta ne basa, dan lecturing da yakeyi nawa yasamu, shima dai xance kawai yage, bazata yuyuba, Mardiyya ce daidai da Boy dinta.

Tattaunawa sukayi da kawu, sannan ta gayamai sun riga sun tsayar da rana sati daya kacal, farin ciki sosai Kawu yayi, yanaji da Rasheed tamkar dansa, halin uwarsa kadai yasa yake maintaining distance. Sun dade suna magana daga bisani Mom ta masu sallama ta kamo hanyar Kd.
Gidan Hajia Safara ta nufa, nanma sun dade suna tattauna yadda buki zata kasance, daga bisani ta mike zata wuce suka hadu da Abban Mardiyya ya shigo, gaisawa sukayi da Mom yana zolayarta ya shirye shirye, dariyar kawai tayi bata amsa baima ta wuce waje Hajiya safara ta rakata bakin motar ta. Murmushi Abban Mardiya ya saki aransa yana fadin "ku gama shirin bukin ku kafin nima nawa buki yaxo" darawa yayi ya karasa wuce warsa ciki.


***
Bikin ya kusanto gadan gadan, kwana biyu kadai ya rage, pre-wedding picture kusan ashirin suka dauka da differnt photographers, sunyi matukar kyau, matured style sukayi wanda bai sabawa addinin musulunci ba, Duk inda ka shiga xancen kadai ke ruruwa,  Iv din bukin da picx sai yawo suke a social media,  daga masu murna sai masu ihu ganinsa, wasu dan shishigi ma har watapp name dinsu Rmd suka maida.

Tun bayan datayi sallar azahar Batul take jin jikinta amace, gabadaya ta rasa make mata dadi, shi matsiyacin can kusan sati bata gansa ba, hajjo da Baba da yan kannanta ne suka fado mata arai tahau lalubar wayarta da tunga aka kawota bata bi takan shiba, dauka tayi taga yaki kunnuwa, tsaki taja sanin cewa rashin caji yahana ta kunnu, gashi kuma gidan ko wuta babu balle soket.
Fitowa tayi tadau bokiti tace, "Inna na fita dibo ruwa"
"Kar dai ki dade"Inna tafada  daga cikin daki.
Dire bokitin tayi ahankali bakin karga sannan ta fito tsakayir unguwar dubawa tayi ko zata samu masu cajin haya, wayam babu ko alamun su, wani gidan siminti tagani can gaba dasu da wutar lantarki awaje, da azama ta taka ta shiga gida, Kwakwasawa tayi, yarinya mai suna Hafsat Rano ta bude,
"ina wuni, dan Allah caji nakeso asamin, ga gidan mu can" Batul ta fada tana mata nuni da gidansu.
Shigo, amma maman mu ta fita" acewar Hafsat.
Godiya Batul tayi ta shiga ciki, yammata biyu zaune tagani kusa da socket suna cajin wayoyinsu suna chating, kaman munafuka ta gaidasu sanna ta sakala nata cajin, gefe guda taja ta zauna hade da tagumi.
      Dariya daya cikin yammatan mai suna Baby nurse tayi tana fadin "nashige su mistakely na tura pre wedding picx din Rmd da matarsa group, yaukam nasan dole xarah ta cireni".
Dayar mai suna Dija Waziri tace "maiya kaiki kinsan dai Xarah bata bari aturo abunda bai shafi littafi ba, turomin hoton Iv dinsu, zakije Dinner din ?.
Ihu murna Baby Nurse tayi tace "invited or no invited we must be there,".
shewa sukayi hade da tafawa, (ni xarah nace gayyar sode)

Sauraran su Batul take amma tarasa inda xancen su ya dosa, kalmar Rmd kadai hankalinta yafi karkata akai, kasa daurewa tayi ta kunna wayarta, gashi kuma bata watsapp balle su turo mata hoton, karfin hali tayi tace "sis dan Allah turonin picx din Rmd ta Bluetooth".
Kallon banza Baby nurse takai mata, abun mamaki wai ta bluetooth, har yanxu ana yayin sane ta fadi aranta.
Cikin rawar jiki Dija waziri ta kunna Bluetooth tahau tura mata, godiya sosai Batul tayi bata tsaya jiran wayar ta cika ba ta cire ta koma gida, dakinta ta shige da gudu batare data tsaya sauraran Inna dake magana ba.
Addua takeyi wayar na bisa kirjinta, so take ta kalli pic din amma tana tsoro karya zamana Rmd da take muradin samu bai hadu ba, dakyar dai tasamu courage ta kalli pic din, kur tayi tana kallon kyakyawan fuskar sa mai dauke da murmushi, saidai kuma kaman taso tasan fuskar wani guri, a iya tunanin ta bata gano ba, sanin ya mata nisa inama zata ganshi, wani irin sonshi da begansa ne ya mamaye zuciya ta, ware idanu tayi adaidai lokacin da suka sauka a fuska Mardiyya, tsaf tagane ta kwanaki sun hadu a ostrich bakery, last tym da taganta ba karamin burgeta tayi ba amma yau duk sai taji wani irin haushi da kishinta....dafe kai tayi tana fadin innalilahi wa inna'ilaihi rajun, Mamuda ka cuceni,, adalilinka wata ta maye gurbin wanda nake muradi arayuwata, Allah ya isa tsakanin dakai, na tsane ka, banza matsiyaci dan tasha" kuka sosai ne ya kufce mata, su baba da hajjo da tayi niyan kira fasawa tayi, wurga wayan tayi gefe cike dajin haushin su, koma miya faru sune suka caza mata.



******

Buki Budiri ya kankama💃, duk wata shagali na bukin hausa, turawa dana India gabadaya an kwatanta, duk fadin duniya zancen su ake, BBc, cnn, aljazeera, channels, nta tashoshi da dama ka kune hirar auran Rmd Da Mardiyyah ke wanzuwa, manyan mutane ,yayan sarakuna da gwamnoni duk sun hallara ranar daurin auren su.
   Karfe 3 na rana aka mika amaryan gidansu Rmd nan inda suke zama da Mom, Hajiya safara baki yaki ruhuwa sai murna take yarta tayi goshi, guraran 8pm aka fara shirin tafiya haddaddiyar Dinner da xaa ayi a fountain Mansion...ni xarah nace bara na leka Batula nasan za ayi african time kafin afara.


**
"Yaunxu Batula baza ki bar kukan nan ba, abu yakici yaki cinye wa tun shekaranjiya kina abu daya" Inna ta fada tana tsaye bakin kofar dakin.
 cikin shesheka tace "Inna dan Allah kice wa Mamudu ya dawo ya sakeni, bana sonshi, ki taimaka ya sakeni na auri wanda naso" karasa maganar tayi cikin kuka mai tsuma zuciya.
Ba karamin tausayin ta Inna taji ba, karasa shiga dakin tayi ta zauna gefen ta tana fadin "karki damu very soon xai sakeki,
"Dagaske Inna" ta fada in cool voice.
Kai kadai Inna ta taga mata alamu eh,  hankalinta na kan fuskar wayar Batul, hoton Rmd din ke kan screen saver ta wanda tuni tayi croping ta cire fuskar Mardiyya, "kaico yarinya kishe ke dawainiya dake," inna tace aranta
Lallashi sosai Inna tahau yi mata amma kamar zugata take kara sautin kukan ta take.
    Tamkar an tsigare ta mikewa tayi tana zara idanu sannan ta janyo ghana must go din ta, budewa tayi tadau yar dubu daya rak data mallaka arayuwarta sannan tadau jan gyale ta yafa bisa kodaddiyar goriyar atamfa dake jikinta, "Ina xaki adaran nan" Inna ta fadi tana kallonta.
Cikin saurin tace "bazan dade ba" ficewa tayi da azama ba tare da ta jira cewarta  ba.
Sauke numfashi Inna tayi ta mike tsaye tana kai komo adakin, yazamata dole tama Rasheed magana, lokaci yayi dazai fito ya nuna mata shine wanda takeso tun kafin ciwon zuciya ya kamata, yadda taga Batul na kuka  ta yadda cewa lailai tayi sanyi kuma ta saduda, dakinta ta nufa tahau lalubar wayarta dan kiran Rasheed.

Babban titin unguwar ta tako tanai sak'a da warwara a zuciyan ta, Iv data gani ya nuna mata a fountain Mansion xaai Dinner saidai kuma batasan gurin ba, amma kuma idan taje ya xatayi, nuna kanta garesa xatati ko miye ?, gigiza kai tayi hakan bazai yuyyba, zataje ne kawai taganshi ido da ido.
    Napep data tsada ba wanda ya dauke ta acewarsu gurin district area ne da napep ko achaba basa zuwa, dakyar dai tasamu  taxi sukayi ciniki ya kaitaa naira dari shida dan ba karamin nisa ne da inda ya dauke taba, can farkon hanya ya sauketa ta tafara takowa toward the gate,  Kasa karasawa tayi bakin gate din, sojijin kusan 20 ke tsaye bakin gate din, sai manyan motoci da suke artawa ciki a guje, daga gurin da take tana jiyo sautin wak'a dake dashi.
  Tsuru tsuru tayi, bugun gabanta na tsananta, shahada tayi ta nufa gate din, daya daga cikin soja ya dakatar da ita yana tamvayar ta Iv, ba'a bata ba tace dashi, tuni ya kuma daure fuska, dan kuwa babu mai shiga sai da Iv, dinner din is strictly on invitation.
"Oga dan Allah ka barni na shiga " ta fada amarairace. bai tanka taba saima kallon gefe sa da yake, Mom ke takowa cikin takun kasaita, sanye take cikin tsadaddiyar leshe kanta daure da gele wanda Oshewa beauty suka mata tieing, kallonta Batul tayi aranta tana adduaa Allah sa matar ta barta ta shiga.
Karasowa tayi.
"Julius make sure ku tsaya postion dinku, gasu nan isowa" ta fada tana kallon julius bata ma lura da Batul dake tsaye ba, juyawa tayi zata tafi sai kuma ta juyowa kallon Batul, dauke kai tayi da sauri ta kalli julius tace "miya kawo almajirai gurin nan ?
"Hajiya ayi hajuri, yanxu zata tafi"
Harara takaimai taja tsaki ta wuce.
"Yarinyar kibar gurin nan, kafin nasa a wulla ki titi"
"Dan Allah ka barni na shiga, it very urgent" kuka ta sanya tana magana.
D'ayan soja dake tsaye yace "yunwa take ji, bara atura kodan snack ne abata ta tafi"
Gefe Batul tayi ta tsaya tana sharar kwalla.

 Covony na mayan motoci guda ashirin sukayi, motar amarya da ango ne a tsakiya, suka karaso gaban gate din basu shiga ba, duk motocin suka tsaya, Zaune suke a motar babu mai magana tsakanin, jifa jifa ne Mardiyya ke kallonsa ta saki murmushi, shima murmushi yake sakar, gabadaya hankalin sa baya jikin sa, maganar su da Inna a waya kadai ke yawan mai a kai, ita so take ya nunawa Batul kansa, saidai bazai iyaba dan kuwa ba sonta yake kuma bai yadda ta saduda ba, nan gaba tana samu wani oppurtunity halin karyar ta xai dawo, asalima he is planing of sakinta idan Baba ya dawo daga tafiyar kauye da sukayi.
     Numfasawa yayi ya jingine kansa cikin seat hade da kawar da kansa gefe yana duban waje da hasken lantarki ya gwauraye, gabansa ne ya fadi ganinta can nesa tsaye tana zubda hawaye, idanuwan na kallon motarsa tasu da tasha decoration, motar kadai take gani banda mutane dake ciki kansancewar tinted glass dinta.
   Kallon ta kawai yake yana mamakin abunda ya kawota gurin nan, Inna tacemai ta fita amma baiyi tsammanin nan tazo ba, gashi yanxu sha daya na dare yayi baisan ma yadda zata koma gida ba dan babu abun haya gurin. Hannu yasa da niyya bude bangaransa xai fito tayi sauri daura hannunta daya sha lalle bisa nasa, kallonta yayi ta sakar mai murmushi, tace 'it time" murmushin dabai kai zuci ba yayi yace "okay'
Fara tafiya motocin sukayi suka shiga ciki.

Bangaran Batul kuwa kuka kawai take ba kagauta, snacks da soja ya kawo mata fir taki karbar, dakyar da sudin koshi tabar gurin bayan Julius ya sama mata lift a motar wata da zata koma gida.

Karshe haduwa Hall din ya hadu, Fadin haduwar Hall din kauyanci ne, jama'a masu hannu da shuni ke zaune gurin, daka ga couple din kasan suna cikin farin cikin, dukda cikin damuwa yadda xata koma gida yake bai hanashi sakin fuska ba.

Budirin kadai ake ana ciye ciye cikin jin dadi da annashuwa, can na hango members na *xarah Bukar novel 1, 2, & 3, Home of novel, Pherty novel, Musha karatu, Qurratul-Ayn Novel, Mom fatu Novel*, mamakin ina suka samo Iv nake, ban gama mamaki ba sai ganin su *Miss xoxo Ummee Agoss, Sadiya Jegal, Mom fatu, Queen Miemee, Rookie kazxx, Ramalurv, Hafsat Rano, Dija Waziri, Waliyyah* hakince nagansu suna kwasar loma, nima baa barni baya ba, ledar dake boye cikin jakata na fiddo na kwashi varieties of abincin dake gurin dan kaiwa kawayena su *Mrx Ay, Naja wali, Faty so, fati Imam, Aysha Gajo, Aisha Magasa*😋😋😋😋

Kusan 3am taro ya watse, kowa ya tattara yayi gida, couple ma suka koma gidansu.


*****
 Bayan kwana uku.
Mom ta wuce Abuja huta da gajiya, Zaman Rasheed da mardiyyah ba yabo ba fallasa, sosai Mardiyya ke kokarin faran tamai, ba laifi shima yakan kokarin faranta mata dukda bata gabansa, sunyi waya da Innaa  ya yanke shawara zuwa dauko Batul ya dawo da ita gidansa, dukda haushinta yakeji zai yi kokarin sanyata farin ciki dan ya lura her case is critical.
 Bayan Sallah Isha Mardiyyah ta taimaka mai yayi shurin sa tsaf cikin kananun kaya daya kara fiddo da azahirin kyau sa, har bakin mota ta rakasa ya fice daga gidan sannan ta koma cikin gida cike da shaukin sanshi.

 Kwalliyarta tayi cikin dogowar bakar abaya. Tsakar gidan ta fito rike da empty Ghanar ta tana kakkabewa, Inna dake zaune tayi dariya ganin tabar kukan da takeyi tun safe,  jira take Rasheed ya iso taga reaction dinta, gashi kuwa tayi kwalliya abunta tayi kyau, komawa daki Batul tayi tana maida kayanta cikin ghanar sannan ta zuge ta fito rike dashi,
Cike da tsiwa ta tsaya kan Inna "tsohuwa Allah kaddara saduwa, idan jikanki ya dawo ki tabbata ya sakeni, idan ms bai sakeni ba xan dawo dakaina na amshi takarda ta".
Mikewa Inna tayi da azama, tace "Batul ina zaki adaran nan ?
Yake da yafi kuka cuwo tayi, tace "Babu ruwanki, na riga na yake shawarar fita duniya dan cinma burin rayuwata, babu wanda ya isa ya hanani"
Kwantar da murya Inna tayi tace "tabbas ba wanda ya isa ya hanaki, amma dan Allah kiyi hakuri ki tsaya kona minti 20 ne, i promise you won't regret it".
"Sai kiyi ai" Batul ta fada tana hararar Inna, juyawa tayi zata fita, Inna tayi saurin rike Ghanar tanai rokonta karta fita, fir Batul taki hakura ganin Inna zata bata mata lokaci yasa ta saka mata Ghanar ta fice waje tanai tsinewa matsiyacin gidan. Da gudu Inna tabita waje amma ina Batul ta riga ta tsare, gudu kadai take batare data waiwayo ba, Hannu Inna ta aza akanta tana fadin "Batul kinwa kanki, opportunity daya rage maki kikai shuri dashi", haushin kanta sosai Inna tayi, da tasan mai hali bazai canxa ba da bata tsaya lallaba Rasheed ya bata chance ba. Komawa tayi gida ttadau waya ta kira Rasheed, driving yake kan titi, kadan ya rage ya karaso unguwar, daukar wayar yayi Inna ta shaida mai abunda ke faruwa cike da damuwa, kwantar mata da hankali yayi yace zasuyi magana idan ya karaso.

Gudu take harta karaso titi, batama ankara da kokarin tsallaka titin da take ba, sai ganin hasken mota tayi ya kusan to da gudu, cike da kidema tayi baya dan kauce mata amma tuni tayi latti motar sa dage dayan lane dince ta faso aguje, wani mugun burki yaja adaidai lokacin da ta kwalla ihu ta fadi kasa sumammiya.

Hankali tashe yayi parking ya fiso, Addua kadai yake Allah yasa bata ji ciwo wa, karasawa yayi gareta yana haska fuskatar, wazai ganni inba Batula ba, wani mugun tsaki yaja cike da tsanarta, ji yake kaman ya barta gurin yayi tafiyarsa saidai bazai iya ba kodan darajan mahaifin ta.

Daukata yayi yasata bayan mota sannan yaja komawa Gidansa da ita, yana parking farfajiyan Mardiyya ta fito da fara'arta,  bude motar yaya ya fito da ita kwance bisa hannunsa, da azama Mardiyyah ta nufesa hankali tashe, magana take bai saurare taba banda saurin da yake yaje ya direta, babbab daki mai shegen kyau  ya nufa da ita sannan ya kwantar da ita bisa lausassan gado.
"Sweetie wace wanan" Mardiyya ta fadi arude, dan kuwa ta fisa tsorota, atunanin ta macacciya ce.
"Accident tayi, ki kula da ita" ya fadi ya fice daga dakin, dakinsa ya nufa ya zauna cike da taikici sannan kuma ya kunna karamin Tv dake manna a bangon dakin, Tv ne mai dauke da connection footage na gidan gabadaya, part kusan goma na gidan ya nuna, yasa remote yayi zooming part din dakin da ya kwantar da Batul, jira yake kadai ta farka yaga reaction dinta.

 Toilet Mardiyya ta shiga ta dibo ruwa a bowl hade da hand towel sannan ta dawo kusa gareta tahau goge mata fuska inda ya kwarzane, bayan ta gama mikewa tayi ta sauka kasa kiran altine ta hada ruwan zafi a flask.

Bayan mintuna biyu Batul ta farka a gigice, tsorata tayi ganin ta a wagegen daki, zaburewa tayi ta mike tana karewa dakin kallo, ina ne nan kadai take tambaya aranta, tasan dai moto ya kusa bige ta ta fadi daganan kuma sai gata anan, "kodai wanda suka kusa kade tane suka kawo ta" ta fadi aranta.
Tsoro da mamaki ne ya kamata, da sauri ta fice daga dakin, bin tangameme stairs din tayi da kallo tana adduaa neman tsari, atunaninta gidan yankan kai aka kawo ta, dago da idanuwanta tayi taga hadaddudun frames mai dauke da picx din Rmd da Matarsa kusan shida anyi decor dasu ajikin bagon, rike baki tayi kam tamkar wace tayi niyyan ihu, jin motsin zaa hawo yasata rugawa dakin da gudu, kwanciyar tayi tana neman mafita, dan kuwa indai gidan Rmd Allah ya kawota bazata fita ba, mafita kawai take nema, can kuma dabara ta fado mata ta saki murmushi hade da runtse idanunta.

 Kallonta Rmd yake ta Tv, saidai baisan dalilin komawar ta cikin dakin da gudu ba.
 Murmushin gefen baki yasaki,  yasan definitely she is up to somtin, kashewa yayi ya fice zuwa dakin.
   
  Ahankali Mardiyya ta shigo dakin ta karasa kan gadon ta zauna, bude idanu Batul tayi tana lumshe su kaman wace yanxu ta farfado, mikewa tayi zaune tana kallon mardiyya da itama kallonta take.
"Wace ce ke ? Batul ta tambaya tanai mata kallon rashin sani.
Murnushi mardiyya tayi ta matso da ita tana fadin "ya jikin naki ".
Kallon rashin fahimta Batul tayi mata, "banda lafiya ne ?
"sweetie ya kawo ki dazu, wai kin samu accident"
Tsurewa Batul tayi tahau kuka karya, "accident when n how, i cnt remember anything".
Mardiyya sarkin tsoro, tashin hankaline ya bayyana karara a fuskarta, atunanin ko Batul tayi loosing memories dinta.
Rikota tayi tace "baiwar Allah ya sunanki
"Na manta" batul ta fada cikin muryan kuka.
Cike da tausayi Mardiya tace "plz try to remember wace ce ke, koda ma garin da kika fito ne, kiyi kokari ki tuna"
Shuru batul tayi kaman mai tunani can kuma tace "abu daya na iya tunawa
Mardiyya tace "Gayamin "
"Nasan dai ni yar sarki ce, it seems someone is plotting to kill me" karashe maganar tayi tana juya kanta as if she is trying to recall wasu abubuwan.
"Kill you " mardiyya ta fada in shock.
Yes" abunda na sani kenan, kuka sosai Batul ta fashe dashi hade da fadawa kafadar mardiya, lallashin ta Mardiyya tahau yi.
Duk drama da Batul take akan idonsa, basu lura daya shigo ba, gyarar murya yayi duk suka dago suna kallon sa, mikewa Mardiyya tayi ta karasa garesa, tana fadin "mutune abun tsoro, i wonder mai beautiful princess tayi suke son kasheta"  cike da tausayi tayi maganar.
Kasa magana yayi tsananin tsanar Batul da yakeji aransa, kallonta yake, aransa yana fadin "she will never change......
[10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 
 xarahbukar.wordpress.com

              46 - 50

Amarairece Mardiyya ke kallonsa, ko alamun tankawa bai yi ba, banda kallo Batul da yake fuska murtuke, murya kasa kasa tace "Sweetie bakace komai ba"
Ficewa yayi daga dakin batare dako kanzir ba, Batul dake kallonsa duk taji ba dadi, mugun kallo dayake mata yasa ta kasa sukuni, tsoronta daya kar ya gano karya ta shirga masu.

Daga inda Mardiyya ke tsaya tace "kar ki damo da looks dinsa, he is nyc magana kuma ba kasafai yake ba"
Girgiza kai tayi kaman zata tayi kuka, Mardiyya tacigaba, "ki kwantar da hankali, you're welcome to stay har ranar da xaki tuna masarautar ku"
Nagode",Batul ta fadi cike da tausayin kanta, deep down aranta murna take abun nema yasamo.

Mardiyya bata bar dakin ba saidai ta kira Altine ta kawo mata komai na bukata sannan tai mata sai da safe ta fice. Dadi sosai Batul taji  mikewa tayi tsaye tana tikar rawar murna.

Toilet ya shiga ya sakan wa kansan shawa, mafita kadai yake nema ya rasa, duk hanyar da yabi Batul ce zataci riba, idan ya fito ya bayyana mata kansa gaba takai ta, idan kuma ya sake ta still taci rabi wani guri zata je tacigaba a inda ta tsaya, shawara daya ya yake danci galabarta at her own game.

 Karfe takwas na safiya Batul ta farka daga bacci, agurguje ta shiga bayi ta dauro alwawa tayi Sallar asuba, aranta tana jinjina lausassan gado da Sanyi Ac dakin, da wayota bata taba missing sallah asuba sai yau, istigifari tayi ta koma gadon taci gaba da baccin ta, sai kusan goma ta tashi.

Shigowa dakin Altine tayi da nikiniki kayan ta ajiye cikin wardrode sannan ta gaidata tace mata kayan sawane Aunty ta aiko akawo mata.
"Okay" kadai Batul tace cikin nuna rashin damuwa akansu, bayan Altine ta fita mikewa tayi ta ciro kayan tana kallo, kayane yan kanti masu matukar kyau da tsada, tsalle tayi tana taka rawar "if" na mawaki Davido.

Wanka ta shiga da axama ta fito ta shirya cikin riga da skirt na kanti daya amshi jikinta sannan tayi zaman tsantsara kwaliya, bayan ta gama, fitowa tayi sukayi kicibis da Mardiyya zata shigowa, murmushi tayi tace
Princess kin tashi"
"Eh" Batul ta fada tana kallon yadda mardiyya tasha kyau, kamar mai zuwa buki, duk saita rena nata.
Hannunta Mardy ta riko tace muje muyi breakfast, tsum tsum tabita tanai karewa gidan kallon in a Stylish way gudun kar su gano bata saba ganin hadaddn gida haka ba.
Dinning suka nufa taja mata kujera ta zauna sanna tace "minti daya barin dauko Sweetie" da sauri ta haura sama.
Haushi ne ya kama Batul ganin yadda Mardiyya ke wani rawan kai da Rmd, banda feleki miye saikin dauko sa" ta fadi aranta, shataf ta manta da wani mijinta Mamuda sai yanxu ta tuna shi,  tsaki taja tanai kallon  abinci dake jire gurin, karaf idonta yakai kan roasted chiken dake gurin, wani mugun yawu ta hadiya, Jira kadai take suzo afara.

Tsaye ta iske sa yana button din shirt dinsa, temaka masa tayi sanna suka fito tare saukowa, kallo daya Batul tayi masu ta dauke kai, wani irin xafi zuciyar ta ke mata, bata rai tayi ta daura kafa daya kan daya, karasowa sukayi Dinning din ya janyewo Mardiyya kujera ta zaunna sannan ya zauna gefenta, kallon batul yayi bata da niyyan gaidasa saima daure fuska da tayi, murumshi ya saki dan bakaramin kyau tamai ba, yace
"Good morning Princess"
Kaman jira take, princess daya kirata dashi yay mata dadi, wato shima ya yadda kenan, murmushi ta saki tace "morning My prince"
Atare Marfldiyya dashi suka ware idanu suna kallanta,.
Murmushi ta saki irin ta yan duniyan nan tayi tace "kuna yana yi dashi, dou i cnt recall his face, shi yaka mata na aure, datx y am trying so hard na tuna shi, i love him alot am sure shima yana can yana nemana".
Ran mardiyya yadan sosu, kasa boye kishinta tayi, haushi taji yadda Batul tace prince dinta na kama da mijinta, hannunta Rasheed ya riko, cikim murya kasa kasa yace "we have to support her idan har munaso tayi regaining memories dinta, plz be strong and trust me"
Kai ta girgiza alamar ta yadda da xancen sa, tana son Rasheed shiyasa kome ya fada mata take naam dashi, farin cikinsa shine nata.

Basu tanka Batul ba, suka fara  cin abuncin bayan Mardiyya ta zubawa kowa a filet, sultan chips ne da roasted chicken sai tea hade a kowane cup, Satar kallom su Batul take tana ganin yadda sukecin abunci cike da yauki, jifa jifa kuma Rasheed ya saki Murmushi, ko tari babu maiyi cikin su tsananin yadda suke bawa table manners dinsa,

kasacin kazar Batul tayi saboda fork da table knife da taga suna ci dashi, gashi ba daman tasa hannu class dinta ya zube, daurewa tayi ta rike fork da wukan ahannu daya, kazar tayita cacakawa ta kasa dauka, mazewa kawai tayi ta ajiye fork din tadau tea din tana sha.
Duk a idon Rasheed, dariya ne kadai baiba ya dake, kadan kadai yaci a abinci ya mike tsaya ya karasa gurinta, "Princess har kin koshi ? Ya fadi yana murmushi
Yatsine fuska tayi tace "i dont eat much"
Fork din ya dauka yace "plz kici, baa zaman yunwa agidana" hannuta ya rike yasa mata fork din.

Wani irin yir Batul taji da hanusu suka game guri daya wani irin yanayi ta shiga da ita kanta bata gane ba, "tnx my Prince" ta fadi hade da kirkiro murmushin dole, gabanta sai faduwa yake, zuciyar na tuna mata tana da miji.

Barin Palon Rasheed yayi yahaura sama, Mardiyya ta mike ta maramai baya.
Tsulum Butal ta mike tahau kwashe duka kazar dake cikin filet dinsu tana fadin "waya ki dadi, ai dole ma naci kodan huce haushi kosai da bredi da Mamuda ya kawo min daran farko na" hadesu tayi cikin filet dinta tahau ci da hannu cikin sauri tana duban stairs kar su sauko su kamata.
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com
 
              51 - 55

 Dire mazauninta tayi kan dayan daga cikin d'ima d'iman kujeru dake parlour, Altine ta k'wallawa k'ira, daga can kitchen ta amsa ta karaso dagudu.
"Barka da rana Aunty Princess" Altine ta fadi hade da risinawa.
Murya ciki ciki ta amsa mata da "barka dai, akwai fruit ?
"Ranki shi dade akwai su"Altine ta fadi cikin rawar jiki, aganinta ba karamin matsayi tayi ba yar sarki na mata magana.
Yatsine fuska Batul tayi tace "kawo min, kafin ki wuce ki kunna min Tv"
Altine tace "angama" Tv din ta kunna sanna ta koma kitchen dauko mata fruit.

Murmushi Batul tayi ta k'urawa tangameman Tv idanu da kusan mintuna 10  da suka shude tayi tana kokarin kunnawa takasa, shiyasa ta kira Altine ta fake da fruit dan kawai ta kunna mata.
Atsaftace Altine ta kawo ta ajiye mata a side table din kujerar da take zaune kanan ta wuce tsabgogin gabanta.

Ahankali yake saukowa daga stairs, kunnesa nanuke da wayarsa yana answering call, sai ipad dinsa rike a hannu ,hada ido sukayi tayi saurin kawar da kanta adalilin wani yanayi data shiga, baiko bi takan taba ya karasa ficewa waje. Ajiyar zuciya ta sauke, tanai hamdallah da ya fice daga gidan.  Mikewa tayi ta leka window waje babu alamunsa sannan ta kira Altine ta dauko mata talkalmi heel dake cikin kayan da Mardiyya ta bata, sanya su tayi akafarta sannan ta fice haraban gidan dan karewa ko ina kallo.

Tafiya take dakyar cikin heel kasancewar bata saba ba, kallon ko ina take cike da sha'awa colourful folawowin dake shuke ta ko ina na gidan, can ta hango karamin stone waterfall na zubda ruwa da azama ta kara sauri takunta, ba karamin burge ta yayi ba, abunda bata taba gani ba. Ba ta ankar ba tayi missing steps, tim ta fadi kasa hade da sakin yar kara, kokarin mike tayi, taji muryar sa akanta.
"Fatan dai Princess bataji ciwo ba" ya fadi yanai mika mata hannu dan agaza mata.
Kallon hannusa tayi kaman zata mika mai nata sai kuma ta fasa, mikewa tayi tana kakkabe jikinta sannan dubesa,
"Banji ciwo ba My prince, mi kakeyi nan ? Ta fadi tanai smiling.
Gurin zaman mutum ya nuna mata, yace "zaune nake ina tunaninki"
Kallon rashin fahimta tamai, hannuta ya rike yajata gurin suka zauna sannan yace "Tun farkon haduwan miyasa kika boyemin ke princess ce ?
Ware idanu Batul tayi, bata fahimci inda xancensa ya dosa ba.
Hannuta biyu ya rike gam yana fuskantar ta.
"kalleni dakyau, i want you to remember my face, nasan kinyi loosing memory naki, but plz try hard to remember"
Shuru Batul tayi tana kallonsa, hannuta ya saki ya kunna ipad din yana fadin "let me show you sumtun, am sure zaki tuna"
Photo gallery ya shiga yahau nuna mata picx da sukayi tare, sanye suke da english outfit, ko wanne su sanye da handwarmer bisa kansu ga snow ta ko ina a background din hoton, iya tsurewa Batul takai, mamaki da tsoro ne suka kamata, yarinyar kan hoton itace ba kowa ba amma tasan dai ba ita bace din, murya sarke tace yaushe mukayi snaping picx dinnan kuma a ina ne"
Numfasa yayi yace "two year back a London, can muka hadu muka fara soyayya, unfortunately you left without saying goodbye sai dana kawoki gidan nan nagene ki, am sure ganina da kikai yasa kikace nayi kama da prince dinki, bakiyi karya ba dan kuwa am your prince"
Hauka ya rage Batul ba tayi ba, dan kuwa ya gama daureta ta, look alike dinta yake nufi badai itaba, tunda uwarta ta haifeta ko bakin border bata taba zuwa ba balle london.
      Ajiyar zuciya ta sauke.
"Na manta gaskia, saidai zuciyata batai karya ba ina ganinka nasan akwai connection tsakanin mu, ashe dai dagaske you are my prince".
"Yes my princess" ya fadi hade da janyo ta jikinsa.
"Jikina yasha gayamin zamu hadu smday, am so happy to meet you"
Ihu kadai yarage Batul tayi, tsam ya rungumeta ta kasa kwance kanta, igiyoyin auranta uku kadai ke yawan mata akai,
Sakinta yayi tayi azaman mikewa tsaye tana fadin "kaina na ciwo, i need some space" bata jira cewarsa ba ta bar gurin da saurinta.

 Murmushi yayi yanai bin bayanta da kallo harta shige cikin gidan.
   Cike da fargaba ta shiga parlour, sauri kadai take ta ganta dakinta, hannu data ji bisa kafarta yasata korma uban ihu, a tsorace ta waigo "Lapia kuwa "Mardiyya ta fadi tana kallonta, tun shigowar ta take mata magana amma hankalinta baya jikinta.
Cikin rawar Murya kaman zatayi kuka tace "bana jin dadi ne" rugawa sama tayi  da gudu ba tare data jira cewar Mardiyya ba.
Tausayinta Marfiyya taji, aganinta ko rashin memories dinta yasa ta zama traumatise.

Yunin ranar zuwa dare adaki Batul ta zauna, gabadaya jikinta yayi sanyi tsoro ma take su hadu da Rasheed kar yaxo mata da batun da ita kanta bata gane ba, saidai har yanxu mamakin picx din data gani take, babu tantama look alike dinta ce, amma toh ina take, ya sunanta, why did she left him without saying goodbye, duk tambayoyin nan a zuciyar ta take fadi, tunanin kadai take yadda zata gayamai ba ita bace, idan kuwa tace mai ba ita bace lailai kuwa zai gano memories dinta ya dawo daga nan kuma asirinta ya tono.
    Jin motsi an taba kofar dakin yasata azamam mikewa tsaye cike da fargaba, Altine ce ta shigo rike da Dinner ta ahannu, gaidata tayi ta ajiye bisa center table dake gurin sannan ta fice.
    Kadan ta iya tsakura taci, daga bisani kuma ta shiga toilet freshen up.

 Kwance take bisa kirjinsa tanai zubamai shagwaba, daure wa kawai yake yana biye mata, azahirin gaskia hankalinsa baya jikinsa, numfasawa yayi yanai shafan gashin kanta,
"Diyyah" ya kira sunanta da salon da bata taba ji garesa.
"Miyasa banga princess  during dinner ba" ya fadi.
Lumshe idanu tayi ta dago dubansa, tace
"I dont know, kaman bataji dadi datx y na bata space,  why do you care? Ta karasa maganar amarairace.
Matse ta yayi tsam jikinsa yace "am the cause, kinga dole nadamu"
You are right" ta fada tanai shafar sajansa.
Janye jikinsa yayi kadan.
"Ina zuwa" ya fadi tare da kokarin matsar da ita daga jikinsa.
Riko hannusa tayi.
"Sweetie ina zakaje ?
"Am thirsty, i need some water"
Zaune tayi da azama
"Let me get it" kokarin mikewa tayi.
Ya zaunar da ita, "dont worry, yi baccin ki, yanxu xan dawo".
Ba yadda ta iya ta koma ta kwanta, dan bazata iyamai musu ba, slight peck yakaimai ta a cheek sannan ya fice yabar dakin. Ajiyar uciyar ta sauke, tana bukatar Man dinta ta rasa ya zatayi, ba mamaki ma office dinsa na cikin gidan ya nufa ya fake da ruwa zai sha, gyara kwanciya tayi tanai lumshe idanu cike da so da shawa'arsa.

Ahankalin ya turo kofar dakin ya shigo,  shuru babu kowa banda sanyin Ac daya ratsa ko ina na dakin, motsi ruwan daya jiyo a toilet ya tabbatar mata tana wanka.
Sofa dake dakin ya nufa ya zauna jirar fitowar ta.
     Fitowa tayi daure da karamin pink towel, karasawa tayi gaban dressing mirror tanai karewa kanta kallo, duk da jikin ta asanyaye yake bai hanata iyayi da kwarkwasa a gurin ba, tsadadun mayukan dake gurin duk saida ta bude ko wanne ta shafa sabanin da Vaseline blueseal ne manta, turaruka kusan goma duk saida ta bude ta fefesa sannan ta sanyawa lips dinta red lipstick dake gurin,  tayi kyau matika dukda ba wata kyale kyale tama fuskar ba, kallon Madubin take tana admiring kanta.

Akan idonsa duk abunda take, gabadaya ya gama shagala da kamshinta dake shigar mai hanci, lumshe ido yayi ya mike ya karasa bayanta, yatsun sa yakai bisA wuyanta yanai yawo dasu. Batul kam tayi nisa, dream nation dinta ta lula, fuskar kadai ke kallon mirror amma ruhin baya tattare da ita.
   Motsin Hannu dataji kan boobs dinta yasata dawo wa hayyacinta, idu hudu sukayi ta mirror, ihu taso kwalla wa yayi caraf ya rufe mata baki da Hannusa, kokarin guduwa tayi ta kasa kasancewar matse ta gam dayayi jikinsa.
Cigaba yayi da mata yawan tsutsa da hanusa at the same time kuma yana fadin
"Kin tuna da wannan " ya fadi saitun kunna ta, numfashinsa gabadaya ya gaba firgita ta, kai ta girgiza alamu bata tuna ba.

Hannusa yakai kan towel din yanai kokarin cirewa yace"you used to enjoy it, idan ina miki hakan, how cms kin kasa recalling happy moment or your life"
Iya tsurewa Batul takai, wana irin iskanci ne wanna, ta fada azuciyar ta, daurewa kawai take, wani irin yanayin marar mistallatu ta shiga, sama sama Take ji numfashin ta.

Wani mugun karfi ne yazo mata tayi sauri warce jikinta daka nasa, cikin zafin nama ya janyo ta ta faso bisa jikinsa, kafin takai ga ihu yama tsukeken bakinta cafka, cikin salon mugunta yahau tsotsan lebbenta, tuni tara fita hayyacinta, saida yaga ta tsumu sannan ya turewa iya karfin sa yanai kai mata mugun kallo, jajir fuskan ta yayi tsabar azaba, kuka ta fashe dashi dan ba karamin tsorata tayi dashi ba.
Cikin wata kasalalliyar murya yace "did you enjoy it?.
Harara takai mai, banxa dan iskaa" bata karasa ba ya wanke fuskar ta da lafiyayyar mari da saida taga wuta ya wulka,
 Dan kara tasaki ahankali hade da dafe kunci ta da tunda uwarta ta haihefa babu namiji daya taba mata haka, kallonsa kawai take afirgice,  da gudu ta fada toilet tana tsuga kuka, ko amarfiki batayi tunanin Rmd dinta xai iya mugunta haka ba, asalima batazo gidan dan yana harassing dinta ba tazo ne kawai yasota amma shi yanai bata kallon yar iskan budurwar shi, kuka kawai take tana sumbatu sai yau taga ranar Mamuda da komin rashin Mutunci da takemai bai taba tanka taba, shine yau kalma biyu kacal sun caza mata mari.

Baibi bayanta ba banda Murmushi daya keyi, duk da a mugunta yayi kissing dinta he really enjoys it, ficewa yayi daga dakin ya koma dakinsa, tsaye yaga Mardiyya tanai kai komo a tsakiyan dakin, tana ganinsa ta karaso garesa, "Sweetie ka dade.." Ta fadi, bai amsa taba yakai bakinsa cikin nata, suka fara kissing juna passionately.


***
Bayan kwana Uku

Tun randa hakan ta faru Batul tahau wasan boya dashi, Duk wata hanya da zata tsada ta dashi bata bi, koda wasa bata zaman dakinta gudun karya shigo ya farmata, ako yaushe gurin Mardiyya take makalewa danta lura ko kallonta bayayi idan suna tare, shi dinma yayi busy, aiyuka sosai ke gabansa, wuni yake a office dinsa na gidan yana danne danne computers sa, ganin haka yasa Batul sakin jikinta da kare zagewa akan ita princess ce.
     Da yamma likis, zaune take dakin Mardiyya tanai karambani gyarawa kayan shafanta dake kan dressin mirror zama, Mardiyya na kan gado kwance tana latsar wayarta, jifa jifa kuma suma juna magana.
Roban ban kitso Batul ta daga tana fadin "Sister Mardy kinga wannan ya kare"
Dagowa Mardiyya tayi tace "tun jiya nace Altine ta wulla trash, ashe bata dauka ba"
Gefe Batul ta ajiye robon tace "ni gobe saloon nake son zuwa"
"Ba matsala, Allah ya kaimu goben sai muje"
Dadi sosai Batul taji, turowar kofar dakin ya katse mata hanzari, shigowa yayi rike da wasu takardu a hannusa, nan take jiki Batul yahau bari, matsawa jikin bango tayi ta lafe, ko kallonta bai ba ya karasa gurin Mardiyya da tuni ta mike zaune.
"Diyyah, ga wannnan kije office kimin compiling dinsu cikin data base na marketing department" ya fadi yana mika mata papers din
Karba tayi tana fadin "right away" mikewa tsaye tayi da azama tana cewa batul "princess ina zuwa, duty calls" sannan ta fice ya mara mata baya.

Ajiyar zuciya na relief ta sauke, gadon ta karasa da niyya zama taji ya banko kofar ya shigo, atsorace ta daskarewa agurin, karasowa gabanta yayi yanai mata shuumin kallon sanna yakai hannusa bisa fuskarta, "princess baki iya gaisuwa ba ?
Daburcewa tayi, tahau fadin "ina kwana my Prince" baki na rawa ta karashe maganar.
"Ina kwana by this time" ya fadi hade da janyota jikinsa, kame jikinta tayi tsam dan bataso irin kallon dayake mata.
"Princess" ya kira sunanta cikin wata kasalalliyar murya daya kashe mata jiki, kallonsa tayi tanai kokarin jan baya, yayi saurin tarota, boobs dinta dake neman fasowa daga cikin yar karamar riganta yake kalla, da sauri tayi azaman sa hannu ta tokare, cire hannun yayi yace "bakya so na kalli abuna".
Gutun tsaki taja cikin kaguwa da kallon dayake mata,
"Ni kike ma tsaki ? Ya tambayeta
Banza tayi dashi hade da dauke kai, matse ta gam yayi yahau kissing ko ina na fuska ta, kokarin karkato da kanta yayi dan kissing lips dinta, fir taki yadda dan ba karamin haushi yake bata ba, murmushi mugunta ya saki yakaima boobs dinta wani irin raruma data saki karamar ihu, bata ankara ba sai ganin tayi yana latsar boobs din hade da kokarin cire mata riga.
Hannusa tayi saurin rikewa, "Dan Allah kayi hakuri, banaso"
Bai kulata ba saima kara cigaba da abunda yake, kuka ta fashe, "Dn Allah kabari, akwai aure akaina"
Sakin ta yayi yanai mata mugun kallo, sanna ya shako wuyanta, "yaushe kikai aure, wa kika aura?
Cike da karaji da zare idanuwan sa da suka sauya launi zuwa ja yake maganar.
Akideme Batul ke kallonsa ba tare da kwakwaran motsi ba, ita kanta batasan ya ankai tace akwai aure akanta ba.
Baki na rawa tace "bansani ba, nadai san ina da aure, dan Allah kabari"
Fuska daure yace "Ni zaki rainawa wayo, gayamin wa kika aure, waye mijin"
Shuru tayi banda matsar kwalla da take, shakar da yayi ma wuyarta ma ya isheta.
"Yau zaki san baa raina min wayo" fizgo ta yayi suka fada toilet dake dakin,, duk ta furgici tarasa uwar mai xai mata, bowl mai fadin dake cikin jacuzzi ya kunna ruwan sanyi ciki sannan ya kashe bayan ya cika.
Kallonta yayi yace "yau dolene ki gayamin waye mijinki" wuyarta ya damko gashin kanta ya zubo dan tuni hular kanta ya fice, kallo yalwan gashi yayi ya dauke kai, tuni Batul ta rikice atunaninta wanka xai mata sai kuma taga ya tsugunar da ita hade da tura kanta cikin ruwar, ihu ta saki bayan ya ciro kanta daka cikin ruwan
"Waye mijinki" ya fadi fuska ba annuri.
Iya galabaita Batul takai, ga ruwan bai dan banxa sanyi, tsabar mugunta sai kanta yayi sakanni yake fidda ta.
"Nakasa numfashi, dan Allah karka kashe ni"  ta fada, numfashi sama sama, ido jajir.
Tambayar ta ya kuma yi, tayi shuru ba amsa kara danna kanta yayi cikin ruwan sannan ya fiddo ta.
Kuka sosai ta fashe dashi "kayi hakuri, nakasa tuna waye mijin"
Murmushin mugunta ya saki, ya kuma danna fuska ta ciki, kusan sai hudu yayi bata da niyya gayamai waye mijinta, cikin fusata ya ture ta, tsantsin ruwan dake gurin ya kwasheta ta fadi kasa, atake bakinta ya fashe, jini yahau zulala, ko kallonta bai yiba yayi hanyar ficewa sai kuma ya  dawo ya damki wiyanta,
"na baki nan da 24 hours idan baki gayamin waye mijinki ba, abunda yafi wannan zan miki" take yatsu kafarta yayi ya fice afusace.
"Innalilahi wa inna'laihi rajun" kadai Batul ke ambata, cike muryar kuka mai tsuma zuciya, agabadaya jikin ta radadi yake mata, kanta wani irin azababban ciwo yake mata, kuka kadai take tana dana sanin kawo kanta gidan Rmd dayake barazanar kasheta, da yanxu tana gidan Mamuda bawan Allah hankalinta kwace ba tare da yayi gigin taba lafiyar jikinta ba, sai yanxu ta tabbarta kauyanta shine birninta, talaucinta shine kwaciyar hankalin ta, ina amfanin an wadata ta da komai amma
 ba kwashiyar hankali.
24 hours daya bata kadai ya kara firgita ta, mikewa tayi tsaye dakyar tana fadin "gidannan ba gidan zamana bane, mundin na kara kwana daya saidai afita da gawata" fitowa tayi daga dakin tayi hanyar stairs ba tare data leka ko dakinta ba, gudu gudu sauri sauri ta fice waje ba tare da kowa ya ganta ba, tsakanin cikin gidan da gate ba karamin nisa ne dashi ba haka ta taka ta karasa, securities hudu sanye da uniform tagani, harda mata biyu cikin su, ko kallonsu batai ba tahau kokarin bude gate din, kallota sukayi sukace
"Baa fita saida izinin Oga
"Ni ba yar gidan nan bace, ku bani guri"  tafadi tana harara su.
Damko hannuta mata biyun sukayi suna fadin "oga yace karmu bari ki fita"
Hankali batul atashe tahau masu magiyan su barta, ko kallonta basui ba suka cicibeta zuwa cikin gidan, direct inda suka hango Rmd tsaye suka kaita, wani wawam mari ya tsakar mata afuska, yace "My princess baa fita a gidan nan sai da izinina" .
"Ba fita xanyi" ta fadi, fuska jajir ko ganin haske batayi sosai tsabar azaba.
Cema security din yayi su kaita up stairs inda dakinta yake, sannan ya kalleta yace "23 hours 30 minute remaining...."
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com

              56 - 60

Zazzab'i mai zafin gaske ta kwana dashi ba tare da runtsawar kirki ba, har kusan 11 tana lullub'e cikin bargo bata sauko breakfast ba.

Turo kofar dakin Mardiyya tayi hade da sallamA, can ta hango ta dunk'ule karshen gado tana freezing, karasawa bakin gado tayi da axama ta yane bargon.
"Princess baki da lafiya".
 Hannu takai bisa jikinta, zafi rau taji tayi azaman cire hannun.
 kuka Batul ta fashe dashi ta riko hannuta, "Sister Mardy dan Allah ki temakeni nabar gidan"
"Haba princes keda bakya cikin hankalinki taya zaki ce haka, kiyi haukari har memories dinki ya dawo nayi alkawarin maida ki masarautar ki dakaina"
Kuka sosai Ta kuma fashewa dashii, tayi dana sanin ce masu tayi loosing memories gashi tana son barin gidan sunki yadda, lallashi da ban baki Mardiyya tahau bata, dakyar tabar kuka bayan Mardiyya ta ce mata zata kaita asibiti, dadi taji aranta tafara tunanin yadda zata tsere daga can.

Zaune yake parlour yana sipping coffe dake rike hannusa cikin mug, Tv dake kunne yake kallan labaran duniya. Cikin takun sauri mai dauke da tashin hankali ta sauko, dayan daga cikin kujerar ta nufa lalubar mukullin motar ta data cilla gurin.
"sweetie princess bata jin dadi, zan kaita asibiti" ta fadi tanai cigaba da laluban ta, ganin mukulli tayi ta juyo tana fadin,
"barin dauko ta" taku daya biyu tayi da niyyan haurawa saman taji ya kira sunan ta, tsayawa tayi tanai kallonsa, bai kalleta taba, fuskar sa na bisa Tv yace "babu asibitin da zakuje"
"Sweetie dan Allah ka bari muje, she needs a Doctor"
"Diyyah" ya kira sunanta a tsawace, kallonta yayi fuska daure.
"naje baza kuba, koma ki zauna"

Tuni Mardiyya ta tsorata, ya rikide mata ainihin Mr Rasheed din data sani, "Adalilin Mene (Ummi Jay) zai mata tsawa" ta fadi axuciyanta, jiki ba laka ta taka kujerar dayake zaune ta zauna gefe dashi adan rukube.

Wayarsa ya fiddo ya kira Doctor Ramalurv sukayi magana sannan ya katse.

Shuru ne ya ratsa sakanin su, kowa da abunda yake sakawa a zuciyarsa, bayan minti sha biyar Doctor Ramalurv ta karaso gidan, gaisawa sukayi ya mike  rakata dakin Batul.

 Kwance take tanai jiran shigowar Mardiyya, ganinsa ya banko kofar dakin yasa  ta razane
"Shigo Dr" yace da Ramalurv da take biye dashi abaya.
Saurin rufe idanu tayi kaman mai bAcci amma tuni yasan ba baccin take ba, taba jikinta da aune aune Doctor tayi sannan tA rubuta mata magungunan bukata ta mika mai takarda, tana fadin "Mura ya haddasa mata zazzabi, for now dole ta kiyaye amfani da ruwan sanyi"
"Okay" ya fadi hade da godiya, bai karbi takarda ba yace ta baiya mardiyya dake kasa taje ta siyo, sallama sukayi ta sauka kasa.

 Mardiyya bata kawo komai aranta ba ta amshi takardar ta fice zuwa pharmacy da azama.

Jin alamun shuru yasa Batul bude idanu, karaf sukayi ido hudu dashi, tsaye yake yana kallon ta hannuwansa biyu bisa kirjinsa yayi folding.
Murya can kasa yace "princess ya jikin ki ?
Karashe magana yayi hade da zama kan gadon, fuskokin su na fuskantar juna. Janye jikinta tayi gefe tana kara lullubewa, ba karamin shayinsa take yi ba, sai kace bashi yajaza mata zazzabin ba.
"Da sauki" ta amsa mai cikin murya kaman zatayi kuka.
Hannu yasa ya cire bargon, yarage daka ita sai karamin nitie dake jikinta, saurin takurewa tayi gurin guda hade da kawar dakai gefe, tsoron ta daya karya dawo mata da batun tambayarsa, adiriganta awanni sha hudu suka rage ta bashi amsa, saidai har yanxu batasan abunda zata fadi maiba.
"Tashi kiyi wanka" yace ita
Raurau tayi da idanu "Sanyi nake ji"
Cikin zafin nama ya mike hade da sunkutar  ta zuwa toilet, kuka ta fashe dashi tanai rokansa, atunanin ta abunda yay mata jiya zai sake, dire ta yayi, yahada warm toilet cikin jacuzzi.
Kallanta yayi yace
"Baza ki shiga ba saina turaka ciki"
"Zan shiga" ta fadi hade da rabawa ta gabansa, taba ruwan tayi taji da dumi sannan ta kalle sa "dan Allah ka fita"
Harara yakai mata "kina gamawa make sure kizo down stairs breakfast"
Kai da girgiza alaman eh, ya juya ya fice daga dakin.

Yunin ranar yar gata ta zama daga shi har Mardiyya lallbata suke, duk abu da takeso shi sukeyi, kokarin kame kanta kadai take gudu kar gata yayi yawa tafara wuce gona da iri, atleast Rasheed ya kyaleta bai kuma mata batun komai, opportunity kadai take nema ta fice tabar gidan saidai ta lura babu daman hakan saboda tight security na gidan, babban tashin hankali shine idan ta koma gida mai zata ce da Mamuda da Inna, dan kuwa karyarta takare, asalima karya ce ta sanya ta cikin ukubar da take ciki ayanxu.

Washe gari, guraran biyu na ranar taga anata dafe dafe da gyaran ko ina na gidan,
Mardiyya sai up and down take tana aikace aikace sai kusan 5 taga sun kammala.
   Mamaki kecin ta, tarasa wanda zata tambaya what the occasion is all about, tana daga parlour ta k'wallawa Altine, da azama tazo hade da dukawa kasa.
"Altine yimin tausa" ta fadi.
"Toh ranki shi dade" Altine ta fada tana washe baki, tausar tahau yi mata cikin kwarewa da hazaka.
Tambayar ta takeso yi amma ta kasa, dakyar dai tasamu courage din tambayar ta ko bakine zasu zo.
Kara washe Baki Altine tayi tace "Momy ce xata dawo, mahaifiyar mai gidan"
Ware idanu Batul tayi, gabanta na dukan Uku uku, fatan ta daya Allah yasa matar mai saukin kaice, indai ta biyo danta a mugunta lailai kuwa kashin ta ya bushe.



     To be Continued.........
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com

              61 - 62


K'arfe shida motar Mom ta diran agidan, ajiyar zuciya mai dauke da relief ta sauke tana shakar sanyayyiyar iskar dake bazama a farfajiyan gidan. Cikin takun takama ta k'arasa takawa bakin kofar parlour gidan cike da mamakin Altine batazo tarbar taba
    Turo kofar palon tayi ta kusa ciki kai batare da tayi sallama ba.
"Altine" ta kira sunanta ganin ta duk'e tanai ma Batul tausa, duk atunanin Mom mardiyya ke kwance gurin, ganin Mardiyya na sauko wa daga stairs fuska dauke da fara'ar yasa ta karasa shiga cikin palon.
"Sannu da zuwa Mom" Mardiyya ta fadi
Yauwa" Mom ta amsa cikin k'aguwa da ganin waye hakinci kan kujerar palon gidanta.
"Bak'uwa mukayi" Ta fadi tanai kallon Batul dake kokarin mikewa zauna tana sosa idanu, dan tuni bacci ya kwashe ta jin surutu yasata farkawa.
    Ido hudu sukayi tayi azaman mikewa tsaye adan firgice.
 "Ina wuni, sannu da zuwa" ta fada murya sarke, gabanta na faduwa sakamakon gane Mom da tayi wace ce ta k'irata da almajira a fountain Mansion.
Kallon wulakanci Mom ke mata, aranta tanai fadin "wanne ne karo na uku da take ganin yarinyar nan, amma miya kawo ta gidan nan"
Afili tace "wace ke, daga ina, gurin wa kika zo" atare ta jeho mata tambayoyin, fuska ba annuri.
Caraf Mardiyya ta amshe dacewa " tayi loosing memories dinta,  abu daya mukasani game da ita shine she is a princess"
Murmushin dabai kai zuci ba ba Mom tayi, tace "Princess my foot, dayake baku da hankali wannan tayi kaman da princess, she looks more like a Gold digger"
Shuru Batul tayi kaman ruwa ya cinyeta, fisgo ta Mom tayi da karfin gaske ta rike ta kam, cikin karaji da zare idanu tace
"Nawa kikeso nabaki ki fita daga rayuwar mu, kinsan dai nasanki, duk wani cunning moves dinki bazai yi aiki akai naba"
Fashewa da kuka Batul tayi dan ba karamin riko tayi mata ba, ita ba kudi takeso ba asalima idan zaa bude mata gate fecewa zatayi, saidai mamaki take yadda Mom ta ganeta so easily, dan ko ranar dinner ba wani kallon k'urilla tayi mata ba.                       Matsowa Mardiyya tayi ta cire hannun ta daga mugun riko datai mata, tace "plz Mom kiyi hakuri ki barta, bata da isheshen lapia, ina kika santa ?
Nisawa Mom tayi.
"bansanta ba, all i know is saita bar gidan nan yanxu" ta fadi hade da kara riko hannuta, janta tayi bakin kofar palon hade da hankada ta waje ta fada jikinsa dayake kokarin shigowa.
"Mom"ya kira sunanta cike da baccun rai, yasan zaa rina yasa yaketa sauri danya iso gidan unfortunately traffic jam ya tsayar shi.
"For goodness sake Mom mai tayi miki daga zuwanki? Ya fadi yanai rike da ita suka shigo ciki, kuka sosai Batul take, taga samu taga rashin da tuni ta ware.
    Dogon surutune bazata iya ba, balle akan matsiyaciyar yarinyar nan, abu daya tasani shine bazata bari ta zauna mata gida ba, kallonsu tayi tana girgiza kai, aranta tana fadin bazai yuyuba, almajira da danta over her dead body" batace uffan ba ta wuce dakinta dake nan kasan, hand bag dinta ta dire tadau wayarta ta kira Hajiya Safara, sun jima suna magana sannan ta katse cike da tsananin baci rai.

"Hope bata ji miki ciwo ba" ya fadi yana k'arewa jikinta kallo, kai ta daka mai bata bar kukan ba, yace "kiyi shuru banaso kuka, very soon zaki bar gidannan kinji"
"Okay" ta fada araunane.
Nufasa Mardiyya tayi tace
"Sweetie kodai na kaita gidan Umma ta zauna"..
Kallan baki da hankali yayi mata, yadda ya tsani Hajiya Safara ko makiyinsa bazai kai gidan ba, balle ma Batul, dukda ba sonta yake ba taci albarkacin mahaifinta.
"babu inda zata" ya fada atakaice, janta yayi suka haura sama, Mardiyya ta bisu da kallo zuciyar ta na zayyano mata abubuwa iri iri.
     Da dare kowa daban yaci abunci adakinsa, daka ga su hudun kasan basa cikin walwala, kowa da abunda yake sakawa aransa.

Da safe Mom ce tafara zama dinning yin breakfast sannan Mardiyya da Rasheed suka sauko, gaida ta sukayi ta amsa da fara'arta tamkar ba abunda ya faru, "My Boy kayi resuming work ?
"Not yet" ya fada fuska ba yabo ba fallasa.
"Allah kaimu" .
"Amin" ya amsa agajarce. Serving dinsa Mardiyya tayi suka fara ci atsanake. Altine ta karaso rike da plate ta dibi abincin xata wuce, Mom ta dakatar da ita da cewa "ke, ina zakije da abincin nan?"
Altine tace "Aunty princess xan kaiwa"?
Takaici ne ya cikata, kalmar princess da suke ambata yana mugun kona mata rai, "ajiye ki wuce aikinki" ta fadi.
Ajiyewa altine tayi tabar gurin.
    Mikewa yayi hade da daukan abincinsa yabar gurin batare daya kallesu ba yahaura sama.
Tsaki Mom taja hade da dangwarar da spoon din hannuta, kallon Mardiyya tayi da itama kallonta take, tace "ban taba ganin shasha kamar kiba, da wayewar ki da komai kalli yadda mijinki ke tashi zaune kam shegia yarinyar can amma ko aji kinki"
Galala Mardiya tayi tana kollanta tace "ni banga wani abu acikiba, shi yayi causing accident dinta so kinga dole ya damu da ita"
Harara takai mata, "jiya daya ke rungume da ita duk damuwar ce komi ?
Shuru Mardiyya tayi tana gasgata xancen.
Mom tacigaba, "dole musa hannu tare musan yadda tabar gidan nan"
Ware idanu tayi.
 "Mi yayi zafi haka, plz mom ki bari tayi regaining memories dinta, nidai ba hannuna ciki, dama keda Umma kun saba kulle kullen ku nidai bada niba".
Gwab'e mata baki Mom tayi tamike tana cewa "wawiyar yarinya"
Turo baki Mardiyya tayi tanai gunguni, itadai bata ga wani abu tattare da princess ba da akeson barin ta gidan, asalima tausayi take bata.

 Tsaye take tsakiyar dakin tanai kaiwa da komowa jikinta sanye da yar figiyar rigar bacci, sak'a da warwara na abunda zata fada mai take, shawara daya ta yanke na fadi mai gaskiyar wace ce ita, idan har ta fadi hakan kadai xaisa yabarta tabar gidan asauwake.
    Turo kofar dakin ne yasata ta dan firgita, shigowa yayi fuska murtuke.
Jiki na rawa ta tadau zani ta daura tana fadin "ina kwana".
Bai amsa ba ya mika mana plate din hannusa,
"bana jin yunwa" ta fadi araunane bata da niyyan amsa, mugun kallo ya kai mata ba shiri ta amsa hade da matsawa lungun gado ta zauna..
Zama yayi kan Sofan dakin hade da shigidewa, fuskarsa na kallon sama.

Kasa cin abinci tayi tanai jujjuya spoon din hannuta, so take ta gayamai amma tana tsoro, dakyar tasamu courage ta mike tadau mayafi ta karasa gabansa ta zauna.
"Dan Allah kayi hakuri ka barni na tafi "
Yana jinta bai tanka ba saima runtse ido da yayi kaman mai bacci.
Taci gaba, "niba yar kowa bace agarin nan, asalima karya nayi dana ce ni jinin sarauta ce".
Ko motsi Rasheed bai yiba banda kasa kunne dayayi yana sauraranta.
Bata boye komai na rayuwarta taba ta kwashe ta fadi mai sannan ta hada da cewa "ina son mijina dan Allah ka barni na tafi na nemin gafarsa" Karasa magana tayi cikin shesheka, shuru ne ya ratsa sakanin su na mintina biyar sannan ya bude ido yanai mata kallon mamaki.
"Princess yaushe kika iso nan, kukan mi kike, kiin gama cin abinci ? Ya fadi murya kasa kasa kaman wanda ya farka daga bacci.

Gabanta ne ya fadi, badai baiji abunda tace ba, murya sarkake tace, "ban gama bama"
Mugun kallon yakai mata, cikin tsawa yace "zaki tashi anan ko saina mare ki"
Tsum ta mike, tanason tambayarsa ko yaji amma tana tsoro ganin yadda ya daure fuska.

Mikewa yayi ya fice daga dakin tanai binsan da kallon bakin ciki da takaici, ajiye plate din tayi gefe tana rusa kuka.

Office dinsa na cikin gidan ya nufa ya zaune hade dafe kansa, maganar zuci yake. what next, tunda tayi confessing, shidai ba sonta yake ba balle ya cigaba da zama da ita. K'wafa yayi yana yana neman mafita,  chance daya zai bata tayi proving kanta, idan har batayi ba he has no choice daya wuce ya rabu da ita for good.
   Kusan awa hudu ya kwashe gurin yana sake sake, daga can palon kasa yafara jiyo hayaniya kamar ya share sai kuma yafasa sakamakon muryar Mom daya jiyo tana tsine tsine.

Fitowa yayi da azama ya iske yan sanda kusan goma tsaye a Parlour Mom na yi masu bayani cikin daga murya, Mardiyya na tsaye gefe tana sauraran ta.
"Make faruwa ne" ya fadi yana kallon Mom,
"Sata akamin acikin gidannan"
Kallon ta yake ya kasa gasgata xancen, miyasa tunda baai sata ba sai yanxu daga zuwanta.
"Miye aka dauka"
"Sabon Gold earring dana zo dashi is missing" cikin huci ta karashe maganar, kallon yan sanda tayi tace "kuyi searching ko ina na gidan including the rooms"
"Toh hajiya" suka fadi atare hade da fara dube dube.
Murya kasa kasa yace "Mom miyasa baki gayamin an miki sata ba zakiyi alerting police"
Harara takai mai,
"Nayi laifi saika dakeni"
Matsawa tayi can gefe batare data tsaya saurarasan ba, Mardiyya ce ta matso garesa tace "cikin mudai ba barawo, i tink ko Mom tayi misplacing earring din wani gurin".
Shuru kawai yayi baice komai ba, yasan drama ne kawai Mom take babu wani Gold dinta da aka sace.

"Muje sama, kuyi checking duka dakunan" Mum ta fadi tanai masu jagoran hawan saman, da azama yabi bayansu yana fadin "mom dan Allah ki bari, i will get you a new one"
Banza tayi dashi suka karasa hawa, direct dakin da Batul take suka fantsama ciki, ran Rasheed ya baci matuka, dadin abun ma bata dakin tana toilet tana wanka, bakin kofar toilet din yaja tsaya gudun karta fito su ganta.

"Lungu lungun da sako ku tabbata kun duba, cox i dont trust her" Mom ke magana ayayinda yan sanda sai biincike da bude bude suke, itadai Mardiyya kallon su take cike da haushi, dan kuwa bazata bari ama dakinta iskancin nan ma.

Daga pilo daya daga cikin yan sanda yayi saiga dankareriyar earing na gold shumfide gurin , dauka yayi yana fadin "hajiya wanan ne?
Kwarai kuwa shine" ta fada hade da dafe kirjin cike da mamaki"
Ta kuma cewa "Dpo tana wanka, ku shiga bandaki ku kamata karta gudu"
Mamaki ne yakama Rasheed, wanan wana irin abune Mom dinsa keyi haka, yasan Batul da karya badai sata ba, idan ma sata tayi how com ta sace one earring, wata zuciyar tacemai it can be possible mayb siyawar xatayi tayi kudin data ta jima tana mafarki zama mai kudi. saurin kawar da tunanin yayi yana girgiza kai.
"Mom dan Allah kiyi hakuri, nasan bakison zaman princess agidan nan, insha Allah yanxu zatabar miki gida".
Mugun kallon ta jefasa dashi.
 " idan na barta taci bulus kenan, bai xai yuyuba dole hukuma su yanke mata hukuncin daya dace da ita koda ma ace yanke hannuwan ta xa suyi"
Dafe kai yayi cike da tashin hankali, yace "xan yanke mata hukunci da kaima, dan Allah Mom ki sallami yan sandan nan" kamar xaiyi kuka ya karashe maganar.
Tausayi yabata saidai kuma bazata iya hakuri so called princess ta zauna mata a gida ba, kallon police tayi ta sallamesu hade da ce masu zata bukace if needed. Fita sukayi ta mara masu baya hade da hararar Mardiyya dake tsaye tsuru tsuru.

 Zuciya daya ta fito tana kakkabe ruwan gashin ganta, jikinta daure da towel, ganinsa datayi bakin kofar yasata azama komawa ciki, da sauri yasa hannu ya riko gashin kanta hade da finciko ta waje, ware idanu tayi tanai kokorin kwace kanta, Mardiyya dake tsaye ta shigemai gaba, "sweetie plz calm down, trust me nasan ba ita ta dauka ba"
Ido jajir ya kalleta, turera gefe yayi yana fadin "stay out of this."
Jan Batul yayi suka fice daga dakin ayayinda take mai magiyan ya saketa.
Ran Mardiyya ya sosu, ina xai kaita ahakan daba kaya jikinta, binsa tayi abaya, kafin takai ga karasa wa dakinsa tuni ya shige da Batul ya banko kofar da karfin gaske.
     Gabanta na dukan uku uku ta makale jikin kofar hade da dasa kunne tana sauraran abunda zai wakana.

Wurgi yayi da ita kan gado har kanta yana buguwa, zaburewa tayi ta mike zaune, atunanin ta ko fade zai mata yasata kara susucewa
"Dan Allah kayi hakuri" ta fadi cikin murya kuka.
Iya kuluwa yakai, koma miye Mom dinsa tayi mata itace sila,
Fuska ba annuri yazaro belt dake cikin closet. Zama yayi  bisa kujera dake dakin yan fuskan tar ta.
 "Zonan" yace da ita.
Mikewa tayi tsaya cikin rawar jiki ta nufesa.
Kawar dakai gefe yayi yace "On our kneels"
Astorace tayi axaman ijiye gwiwowin ta kasa tana kara basa hakuri.
Daga belt din sama yayi hade da mikar da ita sannan ya kalleta.
"Miyasa kika sacewa Mom Gold earring dinta"
Tsuru tayi dan bata fahimci inda xancen sa ya dosa ba. "wana Gold" ta fadi cikin shesheka.
Tashin yayi yakai mata bugu daya, tuni ta bankare hade da kwalla uban ihu.       Rutse Idanu Mardiyya tayi, bazata jure abunda kunnanta ke saurara ba, bugun dataji yay mata tamkar ajikinta taji sa, barin gurin tayi cike da tsananin tashin hankali ta sauka zuwa dakin Mom.

Zare mata idanu yayi yace "ki gayamin gaskia, nasan ke kika sace ?
Kuka sosai take tana fadin bata dau komai ba, rufe idanu yayi ya dinga dukan ta iya son ransa sannan ya kuma tambayanta "ke kika dauko, Yes or no ?
Hawaye kadai take iya zubdawa, tuni karfin ihun ta yakare, ta lura idan ba cewa tayi itace ta dauka ba bazai kale taba
"Yes nina dauka" ta fadi cikin hopless murya.
Cikin rashin damuwa da yanayin yace "Good, abunda nakeson ji kenan"
Saida ya kara bugunta sau uku sannan yayi cille da belt ya shiga toilet.

Ko kwakwara motsi ta kasa, zubar kwalla kadai take tana kallon farin fatar  jikinta daya sha tabon laftar daya yi mata, "duk adalili mene" ta tambayin kanta, bakin halinta na rashin wadatar zuci, biyyayyar iyaye, kwadayi da neman duniya ya janyo mata, Sata da bata taba yiba yau an k'alamata tasha duka abanxa, sai yau ta kara gasgata xance bature dayace All that glitters is not Gold, shedan yakaita ya barota, kaso abu ya zama shairin ka, kuka sosai take tasan ukubar ta bai kare ba idan Baba da Hajjo suka san abunda ta aikatawa kanta. Amma mijinta Mamuda fah mai zatace dashi, abun kunya nema ace da auranta tazo gidan wani namiji da zama, duk a zuci take fadin hakan.

 Tsaye yayi gaban mirror dake toilet din, idonsa jajir yanai zubda hawaye mai cike da bacin rai, ji yake tamkar ya cire hannusa yayar tsabar yadda yake jin haushin bugun da yay mata akan laifin da bata aikataba.
 Hannusa yakai ya bugi madubin da karfin gaske ya tarwatse, jini sosai yafara malalowa daga hannusa, dafe hannu yayi jikin bango yana kuka cike da wani yanayin marar fasara, tunanin kadai yake ya zaiyi tabar gidan, dabarace ta fado masa ya dauki karamin hand towel dake gurin ya lullube hanusa dake tsiyaya da jini ya fice daga bandakin, nan tsugunne ya ganta inda ya barta baice kala ba ya fice daga dakin.

Banko kofar dakin Mardiyya tayi ta k'usa kai ciki, Mom na zaune tana karatun Newpapers taganta tsaye fuska ba annuri.
"Mom kije tsoron Allah, bakya tunanin ki mutu da alhakin princess akanki, am 100 percent sure ke kikayi plotting komai"
Mikewa Mom tayi tsaye ta nufo, "ni kike gayawa magana kamar wata saarki"
Mari Mom ta kwashe ta dashi kafin takai ga bata amsa.
Kuka ta fashe dashi hade da dafe kuncin ta.
"Zaki ci ubanki ne" Mom ta fadi hade da daukan waya ta kira Hajiya Safara, magana sukayi sannan ta mikawa Mardiyya wayan.
"Hello, Umma" ta fadi cikin shesheka.
Ashariya Hajiya Safara tahau lailayo mata cikin masifa tace "Mardiyya ki shiga taitayinki, am trying to secure your future kina can kina hauka, idan nazo gidan nan zaki ci ubanki ne, yar banxa yarinya marar wayo.
"Umma nifa bance komai ba, nidai injustice ne banaso, makirci da kuke plotting da Mom bazai amfane ni da komai ba saidai ya kashe min aure" duk cikin kuka take fadin hakan, bata jira cewar Umma ba ta mikawa Mom wayar, amsa tayi cikin zafin nama ta dasa a kunne suka cigaba da magana sannan ta katse.

Mugun kallo tama mardiyya tace "Rasheed da nane, koda kin gayamai nice nayi plotting komai, bazai yadda dake ba cox he loves me alot more than yadda kike tunanin, tun muna mu biyu ki lallaba bakin ki kiyi shuru, yarinyar nan da kike siding she is a big treat to our lives, am warning you stay away from her"

Karaf a kunna Rasheed dayake kokarin shigowa dakin, fasa shiga yayi, yabi hanyar fita waje da azama cike da mamaki kalaman Mom, ina tasan Batul da har take ikirarin treat, kawar da xancen yayi dan ba wannan ne ya damesa ba, Batul kadai yakeso tabar gidan tun kafin Mom ta illata ta.     
Ma'ajiyar motoci ya nufa yashiga mota yaja, bakin gate ya karaso yace da security subarta ta fice idan ta fito sanna yaja yabar gidan, tuki yake yana kara jajjadawa kansa last chance kadai ya rage ma Batul, idan har tayi loosing  he has no choice other than to leave her.

Kuka sosai Mardiyya takeyi, fitowa tayi daga dakin ta haura sama zuwa dakin. Zama tayi hade da tagumi tana tunanin wana abu mamanta da maman mijinke ke aikatawa, koma miye tasan babu alheri cikinsa.

Dakyar ta iya mikewa, dafe bango tayi ta karasa dakin ta, zani da hijabi kadai ta dauka ta sanya jikinta, barin gidan kawai zatayi koda ace ta fence ne, ahankali tasamu ta sauka taci saa ba kowa palon tayi saurin rugawa waje, tun kafin takai ga isa bakin gate din taga an wangale mata, atunanin ta wata motace zata shigo, ba tare da bata lokaci ba tayi sauri ruguwa ta fice daga gidan.
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com

              63 - 68

Cab ta gani pake gurin da azama ta fada tanai fadin mai unguwar da zai kaita, bai tsaya ciniki da ita ba, yaja motar, da isar su, fitowa tayi, cikin sheshek'a ta tambayesa nawa kudi, "oga ya biya" ya fada had'e dajan motar yayi gaba.
Mamaki da faduwar gaba ne suka diran mata.
"kodai Rmd yaga fitar tane" ta fadi a zuciyar ta.
   Kallon kofar gidan tayi tana tunanin makomarta, wani sabon kuka ne ya kufce mata dakyar ta iya samu courage din tura kofar langalangar ta k'usa kai ciki gidan hade da sallama.
     Zaune yake a tsakar gida bisa tabarma, kunnen sa nad'e da radio yana sauraro, jikinsa sanye da koriyar yadi da bakar hula bisa kansa, sauraran radio yake cikin nishadi da annashuwa.
Ciki ciki ya amsa, ba tare daya dago kansa dake kollan k'asa ba.
Arakub'e ta karaso gabansa hade da tsugunna wa, dukar dakai kasa tayi, kasa kallon sa tayi tsabar kunya shi dataji ya diran mata, ko adama ba wani k'are mai kallo take ba tsanin yadda take k'insa, yanxu data fara sonshi kunyar abunda tayi ya hanata ta dagowa.
K'ara sautin kukan tayi tace
"Sannu da zuwa"
Dago dakai yayi ya dube ta sannan yace
"Nina dace da miki sannu da zuwa, ya duniyar fatan dai kin samo abunda kikeso ko dayake amsa takardar ki ya dawo dake"
Kai ta girgiza hade da riko hannunsa.
"Mamuda dan Allah kayi hakuri ka yafemin"
Dan k'ara ya saki kadan tsabar azaban yadda ta matse mai tafin hannunsa.
Saurin sakin hannu tayi sakamakon jinin da taga yana diga, cike da kid'ima ta ciro hijab dinta tahau kulle gurin dake yanke. Bruises din jikinta ya kalla yana kara jin haushi kansa, hannu yakai gurin yana fadin "Batula miya same ki haka ?
Tsigarr jikinta ne ya tashi, ga wani uban radadi da gurin kemata.
"faduwa nayi" ta fadi cikin matsananci kuka, mikewa tayi da axama ta fada cikin dakinta, kuka sosai take tana tunanin yadda xata fadimai gaskia, saidai tsoro take karya rabu da ita.
    Jinjina kai yayi yasan zaa rina, shi kuma yadau alwashin idan bata fadi mai gaskia halin data shiga ba bazai cigaba da kasancewa tare da ita ba.
    Mikewa yayi hade da cire hijab din dake kulle hannusa ya fice daga gidan  zuwa pharmacy dan samun cikekken treatment.

Sallamar Almajiri ce ta katse mata kukan da take, hijab dake ghanarta ta ciro ta sanya sannan ta fito, mika mata ledar kayan miya da danyar shikafa yayi yana cewa maigidan ya aiko sa, amsa tayi sannan ta roki almajirin ya dibo mata ruwa a burtsatse, ba musu ya dauki bokitai dake gurin ya fice waje.
    Tun shigowarta bata lura da dakin Inna dake datse da k'wad'o ba sai yanxu da hankalinta yakai gurin, jiki mace ta nufi Bakin murhu aza wuta.

Har bayan sallah isha bai dawo ba, dan abinci data ajiye mai cikin samira tuni tayi sanyi, kara aza wuta tayi ta dumama sannan ta zauna bakin kofar dakinta jiran dawo warsa cikin tagumi.


Mikewa Mardiyya tayi dakyar ta karasa gaban drawer, janyowa tayi ta ciro magunguna kusan kala hudu sannan ta balle ko wanne tasha ta kora da ruwa dake rike hannuta a glass cup. Jiri sosai takeji, ta jima bata jita jikin yanayin ba, tsabar kuka da tayi ke barazanar janyo mata zazzabi, Shuru har dare bata ji motsin Saba atunaninta ko yana office, dakin Batul tuni ta duba bata cikin, kayanta data gani yasa tayi tsammanin ko ta shiga toilet gasa jiki dan tuni ta leka dakinsa babu kowa.
    Dakin Batul ta nufa, wayam ba labarinta, toilet ta leka babu ita balle alamun danshin ruwa, cike da tashin hankali ta nufi dakinsa nan ma ba alamun bil'adama ciki, tura kofar toilet tayi ta shuga, saidai jinin da broken mirror data gani yasata girgiza, azaman tsaftace gurin tayi cike da mamaki abunda ya faru, fatan ta daya kar ya zamana Rasheed ya jima princess ciwo agarin bugunta.
    Fitowa tayi ta leka office baya ciki, daki ta koma tadau wayarta tahau kiran sa no response.
    Saukowa kasa tayi ta nufi dakin Mom dake kwance kan gado tana kallon tashar Aljazeera a Tv, ganin Mardiyya ta fado dakin yasata daure fuska.
"Mom banga princess ba kuma Rasheed baya gida" akideme take maganar.
Tsaki Mom taja, tuni taga ficewa Batul da gudu ta window dakinta.
"Ta koma gidan Ubanta" ta fadi.
Ware idanu Mardiyya tayi tace "mom badai kin kore taba, kinsan dai Rasheed bazai ji dadi ba"
K'wafa Mom tayi
Tace "Mardiyya ki shiga taitayin ki, kinsa dai auran nan naki nice nayi insisting, Rasheed ba sonki yake ba".
Anzo gun, b'ata rai Mardiyya tayi, yau ita Mom kema gori, batace uffan ba ta juyawa zata bar dakin.
"Rasheed ba karamin yaro bane, he has the right to sleep duk inda yakeso dan bai dawo ba dat doesnt me ki hana kanki bacci" Mom ta fadi cikin kota kula da yanayin ta.
Karasa ficewa Mardiyya tayi cike da kunin rai, dakinta ta nufa ta kwanta cike da tunanin yadda rayuwarta zata kasance gaba.

 Karfe sha daya Rasheed ya dawo gidan da Batul take, leka dakin yayi yaganta makure can karshen bango tana bacci, tabarmar dake jingine yadau ya warwareta hade da shimfuda ta, kwanciya yayi kai yana tunanin bazai iya kwana agidan ba, asalima ya dawo yaga lafiyar tane.

Motsin dataji yasata farkawa, mikewa tayi ta fito rike da samirar abincin, gidan duhu ko haske babu banda haske farin wata daya gauraye gurin, karasa tayi inda yake kwance, ta durkusa aladabce, cikin sanyin Murya tace "ga abinci"
"Na koshi" yafada ataikace.
"Dan Allah kaci"
Banxa yayi da ita bai tanka ma, idan yayi magana mai tsawo tana iya dago muryar sa.
Ajiye abincin tayi gefe, ta kwanta kan tabarmar dan nesa dashi suna fuskantar juna. shuru sukayi na dan sakwanni kowa da abunda yake sakawa aranshi.
Ajiyar zuciya ya sauke yace
"Batula ina kikaje ranar da kika bar gidan nan ?
Gabanta ne ya fadi, tace
"Ranar dana fita wani mutum ne ya kadeni da mota yakaini gidan sa da matarsa mai kirki, shine nayi masu karyar ni yar sarki ce na manta komai, barina sukayi na zauna a gidan shine kuma yau na dawo, Nasan nayi kuskure dan Allah ka yafemin" cikin muryar kuka ta karase maganar.
"Cigaba" ya fadi.
Shuru Batula tayi tana tunanin gayamai abubuwan daya faru tsakaninta da RMD, tsoro takeji sosai, mudin yasani tasan rubuwa xaiyi da ita, bazata fadimai ba amma tayi alkawarin gayamai nan gaba idan ya fara sonta.
Cikin shesheka tace "Shikenan abunda ya faru"
"Kin tabbata abunda ya faru kenan, babu ragi babu kari ?
Kuka sosai ta kufce dashi tace "eh na tabbata".
Numfasawa yayi yace "gobe zamu je inda xan yanke maki hukunci"
"Dan Allah kaiyi hakuri ka yanke min ko wana hukunci amma karka rabu dani, i cnt leave without you" sosai take kuka.
Hannu yakai bisa fukarta yace "ki kwantar da hankalin ki"
Tsayar da kukan tayi, tana feelling hannusa dake bisa fuskarta.
"Good nyt" ya fadi hade da cire hannusa.
Lumshe ido tayi tana mai jin dadin kasan cewa tare dashi.

****
Washe gari data farka tuni ya rigata tashi ya fice masallaci sallah asubah, Murmushi tayi data jima bata yiba, kama ruwa tayi sannan tayi alwala ta shige dakin gabatar da Sallah.
     Karfe bakwai shuru bai dawo ba, tashi tayi ta kyalyale gidan fes sannan ta dubama shinkafar ta sanya asamira ta ajiye jiran dawowarsa.
    Sai kusan sha daya saura ya dawo, tana daga dakin ta jiyo dirar mota agaban gidan, gabanta ne yafadi atunanita RMD ya biyota, hijab ta dauka ta sanya, fitowan ta tsakar gidan yayi da daidai shigowar sa, bata kallesa ba tasan shine sakamakon kyakyawan kafarsa data kalla,
Risina wa tayi tace "ina kwana
Bai amsa ba ya riko hannuta zuwa waje, ganin dankareriYAR  jeep parke agurin yasata firgita, saurin tirjewa tayi tana fadin
"Mamuda ina zaka kaini"
Bude bayan motan yayi ya turata ciki ya rufe sannan yashiga gaban mazaunin banxa ya zauna.
     Gabanta ne ya fadin Ganin wani daban ke tuka motar, tsoronta daya kar ya zamana gidan RmD zasu nufa.
"Gidan zamuje ?" Daddy malam ya fadi yana kokarin tayar da motan..
"Eh, hurry up inason zuwa office" Rasheed ya fadi cikin muryar sa na ainihi.
Ware idanu Batul tayi jin Mamuda na batun office, bama wannan ba Muryar sa sounds familiar, tsananta bugun gabanta yayi har suka karasa madaidaicin gidan Rmd na ainihi wanda babu mai zama ciki sai shi idan ya tashi b'adda kama.

Parking Daddy malam yayi a farfajiyan Gidan, sauka Rasheed yayi ya bude side dinta, ta fito yayi gaba ta mara mai baya cike da tashin hankali da tunani kala kala.

Parlour ya bude ya shiga, ta shigo ta rakube gefe, zama yayi bisa kujera yanai kallon yadda tayi tsuru tsuru.
"Zonan ki zauna" yace mata yanai mata nuni da kujerar dake fuskantar sa.
Karasa tayi ta zauna fuska duke.
Yace "Dago ki kalle ni"
Ahankali ta tago tana kallan sa,
"kin gane ni ?
Daga kai tayi alamar eh sannan tace "mamuda ne mai keke Napep"
Murmushi yayi dan kuwa ta basa dariya.
Mustache din fuskarsa ya cire ya kuma tambayanta kota ganesa, kura mai idanu tayi yaso yayi kama da Rmd amma tasan bashi bane.
"Baki gane niba bako princess ?"
Jin kalamansa tayi tamkar saukar aradu, mikewa tayi cike da tashin hankali tana kallon sa.
Daure fuska yayi yace "to show how stupid you are kin kasa tantance mutum daya with two different identity"
Kai ta girgiza, it cant ba possible, tayama xaace mutum daya ne, sai yau takarewa Mamuda kallo bammanci su da Rmd mi haske ne da muryarsa daya canxa.

Daddy Malam ne ya shigon Parlour, kallonsa yayi hade da mikewa tsaye yace
"Make sure bata gudu ba, she is really good at it" shigewa daki yayi ya nufi toilet.
Kuka Batul ta fashe dashi zuciyar ta na azalzalanta da bashi bane, plan ne kawai ake son rena mata wayo, amma Mamudan ta ba Rmd bane.

Bayan 30 min ya fito sanye da Grey suit, kyakyawar fatarsa sai kyalle take, yayi kyau matika, binsa tayi da idanu har ya zauna.
Cikin kuka tace "i dont believe you, nasan Mamuda is somewhere around, dan Allah ka fito dashi
Cikin ko in kula da yamayinta yace
"I dont own you any explanation, na baki chance jiya still baki gayamin gaskia ba, it seems you will never stop been a liar, ajininki yake"
Kallonsa take tana gasgata  lailai shine, amma miyasa xaiyi playing dinta haka, tasan both mamuda da Rmd tana sonsu miyasa shi ya boye mata kanshi, lailai ramin karya kurarre ne, all this while da mutum guda take zauna tana sharo mai karya akan wanda batama sani ba, duk azuciyan ta take fadin haka.
    Takadda ya ciro daga aljihunsa yana fadin "burinki Mamadu ya sake ki, gashi yau ya cika maki" mika mata takarda yayi taki amsa saima sautin kuka data kara, cilla mata yayi bisa fuska tasa hannu ta bude. Saki daya taga yayi mata, wani irin ihu ta kurma tanai rokonsa,
Mugun kallo yakai mata yace "tashi ki fita na sallameki", rokonsa sosai tayi akan ya janye sakin, tsawa ya daga mata ba shiri ta mike tsaya cike da kidema, hanyar kofar tayi taji yana fadin "kina iya kwana a gidan for today, gobe saiki tattara ki koma gidanku saboda suma iyayenki goben zasu dawo daga kauye, saiki saurarun jiran hukuncin su"

Bata iya tanka saba ta cusa kai tayi waje, tashin hankali mai tsananin ke tattare da ita, idan har Baba yayi hakuri ya barta tasan Hajjo ba zata barta da rai ba, kuka sosai take wani irin mugun son Rmd da Mamuda ke fuzgarta lokaci guda, ita kanta ta kasa tantance wata fiso acikin su.

Kallonsa Daddy Malam yayi cike da tausayin Batul yace "she loves you alot, kayi hakuri ka maida ta, "
Mikewa Rasheed yayi cikin rashin damuwa yace "am late for work" bai jira cewar Daddy ba ya tsuri mukulin mota dake ajiye ya fice daga parlour.
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com

              69 - 70


Tsananin ranar daya k'walla garin bai hana ta ganin duhu da jin sanyi ba,
Tafe take tana lailayi sakamakon jirin dake neman d'ibar ta tsabar yunwa da radad'in da zuciyan ta yake, kuka take ba k'agauta, horn din motar dataji bayanta yasa ta daskarewa tsaye batare data waigo ba.
     Tuk'owa gaban ta yayi hade da wining glass kasa, hada idanu sukayi yanai kallon yadda idanuwanta sukaisauya launi zuwa ja, kawar da kai yayi ya ciro d'ari biyar daga wallet  dinsa, cikin rashin damuwa da yanayinta ya cilla mata kudin afuska yabai wa motar wuta yayi gaba.
     Yak'en da yafi kuka ciwo tayi hade da sa hannu tadau kudin da tuni ya fad'i k'asa, jinjina kai tayi, tana xancen zuci, ko mi yay mata bataga laifin sa ba ita ta jama kanta, asalima sonshi ba raguwa yayi a xuciyan taba idan ma ya dawo gareta hannu bibbiyu xata amshe sa, saidai ayadda taga fuskar sa she doesn't tink xai k'ara waiwayanta, kuka sosai take tana consoling kanta, tasan Mamuda nada kirki da kyakyawan zuciya  baxai share taba, he will definitely come for her.
    Hope sosai tayi ta bawa kanta, taxi ta samu ya dawo da ita gidan sanna ta biyasa da dari biyar din.
     Marwa tagani tsaye gaban gidan, yana zuba yan tarkace a gidan baya, da azama ta shige gidan sanin cewan tarkacan Inna ne.
   Tsaye taga Inna bakin kofa tana kokarin datsewa da k'wado, dan ihu mai tattare da tashin hankali tayi tana fadin
"Inna karki tafi ki barni"
Sai sannan Inna ta ankara da ita, sosai Batul ta bata tausayin sakamakon fita hayayyacinta da taga tayi.
"Batula kin dawo ashe" Inna ta fadi hade da zare mukillin k'wadon.
Karasawa gabanta Batul tayi ta tsugunna, cikin kuka tace "inna dan Allah ki zauna dani, bansan ina xan nufa ba, Mamuda ya sakeni ko kuma ince RMd ya sakeni dan nasan kinsan komai"
Dagota Inna tayi tanai kallonta.
"Batula laifin kini ai, kwanaki ba yadda ban rokeki karki tafi ba kikayi kunnan uwar shegu kika kara gaba, inda ace kin tsaya da Rasheed bai sake kiba, aranar yaso bayyana maki kansan amma ke kika tafi nuna mai kanki"
Sosai take kukan tace, "nasan na tafka babban kuskure, amma Inna ai bai kamata ya sakeni ba kodan son dana kemai"
Goge mata hawayan Inna tayi.
"Kidaina kuka, Allah yasa sakin yafi alheri, yanxu
Ki dau kayanki ki koma gidan ku"
Kai ta girgiza, "Inna tsoro nakeji bazan iya komawa gida ba, ki temaka ki zauna dani kafin wasu kwanaki saina koma gida inyaso muje tare ki tayani bawa Baba da Hajjo hakuri"
Ajiyar zuciya Inna ta sauke tace "kinga ni baa garin nan nake ba, Jikana ne abokin rasheed shiya kawoni nazauna dake na dan wasu lokuta, yanxu kuwa gida xan koma Zaria na cigaba da sana'ata shiyasa kika ga na dawo daukan sauran tarkace na"
Kyankyame Inna tayi tana rokonta, "dan Allah kije dani Zaria, ko talla ce xan miki, Inna ki temaka.." Karashe maganar tayi cikin matsananci kuka.
Ba karamin tausayinta Inna taji ba, tace mata ta dauko kayanta su tafi, cikin rawar jiki Batul ta fada daki ta warb'o ghanar ta fito sukayi waje, Marwan suka shiga yajasu zuwa tashar kawo suka shiga motar Zaria.



        *Kauyen Marke*

Jigawa state.

 Zaune Hajjo take a tsakar gidan su mai zagaye da kara masu kauri, Rike take da rariya tana tankadar garin masara. Shigowa baba yayi yanai wa su Hassan nuni da inda zasu ajiye buhun albasar dake lafce bisa bayansu, ajiyewa sukai hade da sauke numfashi.
Zama Baba yayi bisa tabarma dake shimfud'e, Hajjo tamai sannu hade da mikewa bakin randa dibo mai ruwa.
"Noma akwai dadi, kaman karmu koma Kaduna" Hussaini ya fadi yana zama kan tabarmar.
Hassan dake tsaye yace "nikam na matsu mu koma naga Batula"
Guntun tsaki Hussaini yayi.
"Batula ta manta mu, tunda tayi aure bata kira kosau daya ba, gashi ita layinta baa samu, na tabbata arziki tayi ta yashe mu"
Kwafa baba yayi yace "banason gulma, ku tashi ku bani waje".
Tsum suka mike suka fice,   takaici ne yakama Hussaini, ya dade da lura duk cikinsu Baba yafi son Batul, sau da dama tayi laifi baya hukuntata saiko Hajjo ta mata duka amma su abu kadan yahau masu fada, shiyasa sam Jinin su bai hadu da itaba dan kuwa bayason raini dukda ita din yayar shice.

Ruwan Hajjo ta mikamai ta zauna tanai kara mai sannu.
"Ka sanar da Mamuda batun fasa tafiyar ? Acewar Hajjo.
Wayar aljihunsa ya ciro yana fadin "zuwa gobe dai xan kirasa yanxu wayar ba caji".
Numfasawa Hajjo tayi tace, "na yaba da hankalin yaron sosai, saidai halin Batul nake tsoro, Allah yasa tana kyautatamai"
"Karki damu, Insha Allahu lafiya suke".
"Allah yasa" ta fadi,
Hira su cigaba dayi cikin kwanciyar hankali.

****
Kaduna.

Aiki sosai yayi a office, bayan yayi sallah isha ya nufi hanyar gida.
    Cikin shirin atampa riga da skirt tayi, fitowa tayi daga dakinta da niyya sauka kasa taji tashin zuciya, da azama ta ruga toilet, wani mugun amai yaxo mata tahau kwararawa, dogon numfashi ta sauke bayan tagama ta wanke baki ta fito, bakin mirror ta nufa ta kara shafa powder sannan ta sauko kasa.
    Mom ta iske zaune parlour tana shan fruit,
Kallon ta tayi sannan ta zauna tace
"Mom yaushe kika dawo " ta fadi  in state of confusion tana kura mata idanu.
Guntun tsaki Mom taja bata tanka taba, zama Mardiyya tayi tana tunanin tambayar danai mata can kuma tace
"Mom har yanxu fa princess bata dawo ba
 Takaici ne yakama ta, magana xatayi ya shigo palon hade da sallama, jacket suit dinsa rike a hannu.
Mardiyya ce ta amsa fuska dauke da fara'ara tanai mai sannu da zuwa, mikewa tayi zuwa kitchen dauko mai abun sha.
Zama yayi kan doguwar kujerar da mom ke zaune, gaidata ta yayi ta amsa ciki ciki.
"Ina fatan bakaje bibiyar matsiyaciyar yarinyan nan ba" ta fada tana kallonsa.
Amsar ruwan da mardiyya ta mike mai yayi ta koma ta zauna.
Kai ya girgiza yana kallon Mom yace "nasan bakya kaunar ta, pls Mom kibar kiranta da matsiyaciya, she was once your daughter inlaw but not any more"
Tashin hankali ne ya durar mata, cike da kidima tace "Bangane ba, inlaw as how.
Maida da dubansa yayi bisa Tv dake kunne yace "ex wife ditace"
Zabure wa Mom tay tsaye, cikin rawar jiki ta kwashe sa da gigitancen mari da saida Mardiyya ta kwalla ihu tsabar firgita.
 "Abdulrasheed ni zaka rainawa hankali, da izimin ubanwa ka aureta.." Cikin huci mom tayi magana.
Ransa ya bacci matika, saidai bazai tsaya yi mata bayanin sanadin auran ba, dukda ba son Batul yake ba bazai fadi masu halinta da dalilin zuwanta gidan nan ba.
 murya mai dauke da bacin rai yace "it doesnt matter tunda nariga na saketa" mikewa yayi yahaura sama ba tare daya tsaya jiran abunda zata ceba.

Rai bace Mom ta zauna tana huci, yaushen hakan ta faru bata da matsaniya, lailai kuwa Rasheed yayi betraying soyayyar da takemai, kallon Mardiyya tayi dako ajikinta saima remote dake hannuta tana canxa channel.
"Waike wace irin dabbace, kinaji ya maki kishiya bada saninki ba amma ko ajikin ki" Mom tafadi cikin tsananin baccin rai.
Ajiye remote din tayi ta dubeta sanan tace "Mom mi kikeso nayi, ihu da hauka dan kawai ya auri princess, d first time dana gansu tare nagane he truly loves her, shiyasa ban taba interfering da duk care da yake nuna mata ba"
Harara Mom takai mata tace "sai yau nagane bakya son d'ana kin aureshi ne dan kudin sa"
Murmushi Mardiyya tayi.
"Ko daya wlh, as far a good wife kuma maison mijinta dole nayi supporting abunda yakeso, koda ace zai dawo da princess i"ll support him.
Haushi da takaici ne suka cikata, miketa tayi hade da wurga mata pilo dake gurin tabar palon afusace.
     Cikin rashin damuwa Mardiyya ta mike ta nufi kitchen, fridge ta bude ta dauko ice dake leda ta fito ta haura sama.
     Ahankali ta tura kofar dakin ta shiga, zaune yake kan gado kansa dafe bisa hannusa, zama tayi kusa garesa hade da janye hannusa, dagowa yayi duban ta da idanuwan sa da suka sauya launi.
"Sweetie kayi hakuri" ta fadi tanai dumama mai gurin marin da ice, shuru kadai yayi ya kwanto da kansa bisa kafadarta haunta daya na shafar mai baya.

***
Washe gari daya tashi hankalinsa gabadaya yayi gurin Batul, ko breakfast bai ba ya wuce gidan, wayam yagani bata gidan kuma babu jakar kayanta.
    Hankali tashe ya fito yana tunanin ko su Baba sun iso ne ta koma can gidan da sassafe, da axama ya fada motan ya nufi gidan Baba nan ba basu dawo ba.
Wayarsa ya fiddo yayi dailing no din Baba, buga daya ya dauko.
Aladabce ya gaidasa.
Baba ya amsa da fara'a
Shuru yayi yama rasa mai xaice, katse shuru Baba yayi da cewa "Mamuda kaji mu shuru ko, dawowar bata yuyuba sai nan da sati uku saboda aikin noma daya rikeni"
"Allah ya kaimu Baba" ya fadi cikin kokarin boye damuwarsa.
"Ya matar taka ? Baba ya tambaya.
"Kalau take" ya amsa agajarce.
Sun jima suna waya da Baba daga bisani sukayi sallama.
Iya kidima Rasheed yakai, tsoransa daya kar ace ta gudu wani gidan, number Daddy malam yahau trying, kusan sau biyu bizy, ana ukun ne yadauka.
Rasheed yace "wai dawa kake wayane kusan rabin awa"
Dariya yayi yace "inna ce fah, kasan jiya ta koma Zaria"
Guntun tsaki yaja.
"Miyasa Inna ta koma da kanta, naso ace nina maida ta Zaria dakai na".
"Kunfi kusa, saika kirata kamata ya hanya"
"Tukun nadai, nazo gidan banga Batul ba
Dariya daddy malam yayi yace , "why do you care, ta tafi gidan su kenan".
Bata rai Rasheed yayi yace "bata gidansu, so nake ka bincika min unguwan masu kudi ko Allah zaisa aganta sannan har kad poly ka je ka bincika min"
Dariya sosai Dady yake babbakawa, "toh kadai yace mai"
Rasheed ya katse wayan, can gidan da take ya koma ya zauna na kusan awanni biyar babu alamun ta.


Bayan kwana Uku

*Zaria*

Abinci dake gabanta ta matsar gefe tana sharar kwalla, rashin nemanta ba karamin ci mata zuciya yake ba, all her tot xai dawo gareta, amma shuru ko inuwarsa bata gani ba, kuka sosai ta fashe dashi, rashin zuwan sa kadai ya nuna mata both Rmd da Mamudan basu da good heart kuma ba santa suke ba, itace kadai take wahalar da kanta, share kwalla tayi ta mike tana alwashin yakace sonshi aranta, tunda har baixo ba he is dead to her, gwara kawai ta cireshi aranta dan samun nutsuwa.
Dakin Inna ta shiga ta sanyo Hijan ta fito gaban gidan inda Inna ke tuyar wainar, ga mutane da dama zagaye da ita suna jiran abasu.
      "Inna kawo" ta fadi tana amshen ludayin hannuta,
Murmushi Inna ta sakar mata ganin yadda tayi maganar ba tare da kuka ba, tunda suka iso zaria bata da aiki saina kuka, asalima yauce rana ta farko data fito temakawa Inna, sabanin da saidai ta zauna gidin pampo tana kuka.
    Sakar mata Inna tayi ta mike zuwa cikin gidan dauko miyar wainar, zuciya daya Batula ta dage da juya waina a tanda, tuni masu miko kudi suka fara tana zuba masu, wani matashi ne ya karaso gurin yana fadin "jikar mai waina sako min na dari" ba masu ta amsa mai hade da zuba mai.
Murmushi Inna tayi, tana daga gefe tana zuba miyar, mamaki sosai tayi da Batula bataji haushin sunan da yaron ya kirata dashi ba, sabanin ada saidai ta bisa da ashariyar an zubar mata da aji.

Babu inda Rasheed da Daddy Malam basu nufa ba babu labarinta, sosai hankalinsa ya tashi, duk wayar da sukayi da Inna bata taba cemai Batul na tare da ita ba, shima bai mata xancen ba yasan ba yadda xaai Batul taje gidilanta.
     Sosai ya wahala ya gangara komawa gida.

Handbag dinta dake ajiye kan gado Mardiyya ta dauka, sanye take cikin doguwar abaya ta yane kanta da babban mayafi, gurin takalma ta nufa da niyya sanya heel sai kuma ta fasa sakamakon dan kumbura da kafafunta sukayi, flat tadau tasa, ta sauko ahankali tayi waje gurin motarta, shiga tayi taja ta fice daga gidan, motar Abbanta taga yayo kwanar unguwar, mamaki sosai tayi saida bazata iya komawa gidan ba sakamakon appointment da take dashi da Doctor a asibiti.

 Jiki ba lak'a motarsa ta danno cikin gidan, parking yayi ya fito ya iske Motar Abba parke daga gefe, baiyi mamaki ba atunaninsa Mardiyya yazo gani.
    Cusa kai yayi cikin palon, harxai haura sama ya jiyo muryar Mom da Abban Mardiyya daga can Guess Parlour.
     Kaman xai wuce ya fasa, mamaki ne yakamasa, yasan Hajiya safara da Mom basu rabuwa da kuskus, yau kuma miya kawo mijinta gidan, karasawa yayi bakin kofar ya tsaya sauraran su.
"Alhaji nasha gayama ka rabu dani danba auranka xanyi ba, yama zaai ace na aurin mijin aminiyata bazai yuyuba" acewar Mom.
Nisawa yayi yace " amintakar ku ba hujja bace, gidanta daban naki daban"
Murmushin dabai kai xuci ba ta saki, ta lura dai yana son ballo mata ruwa.
"Bafa xan aure kaba" tafadi.
Magiya da rokonta yahau yi, Mom kuwa ta k'ule dashi, dan kuwa bai kai matsayin da zata aure saba, tafi karfin sa.
"Kai Alhaji ka bar batun auran nan, akwai igiyoyin aure akaina, kasa kuma baa aure kan aure".
Kallon rashin fahimta yayi mata yace "kina da aurene, yaushe kika sake aure, bayan mutuwan Baba Rasheed" atare ya jero mata tambayan.
Guntun tsaki taja cikin kagara da batun sa tace, "akwai Auran Baban rasheed a akaina
Ware idanu yayi
"Bangane ba, a aljanna ko a duniya, nasan mamaci baya dawo wa"
Afusace Mom ta mike tsaye
"Waikai baka da fahimta ne, nace ma auran Babban rasheed na rataye wiyana kuma yana nan da ransa bai mutu ba" cikin karaji ta karashe maganar.
"What" Abban Mardiyya da Rasheed suka fadi atare cikin zare idanu.
Karasa shigowa parlour Rasheed yayi yana kallon Mom da tuni tasha jinin jikinta.
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com

*Special greetings to IZG* *fans, thanks much for the* *love & Support, ILYSM*❤                 
*TeamDiyyah*❤


                  71


Daskarewa Rasheed yayi, tashin hankali da firgici shimfid'e bisa fuskar sa.
   Shi kansa Alhaji Bello ware idanu yayi yana sauraran karin bayani, kallan wulakanci tamai sannan tace
"Alhaji ka fita idanu na, kaga adalilin nacin ka na furta abunda ba hakan bane, tunda kaki ganewa gwada nama b'aro b'aro, bana sonka dan Allah ka shafamin lapia".
Hular kansa yahau gyarawa yana fadin "Allah ya baki hakuri, kinga tafiya ta" ficewa yayi daga palon batare daya jira cewarta ba.
     Ajiyar zuciya ta sauke ta maida dubanta ga Rasheed da itama kallonta yake
"My boy dont mind my words, haushi yaban yasa na furta hakan, babu wani aure akaina"
Cikin rashin gamsuwa da maganar yace "kince my Dad is alive"
Kwantar da Murya tayi tace "bakaji nace kawai fada nayi ba, believe me your Dad is dead".
Baice uffan ba ya fice parlour ba tare daya gamsu da abunda tace ba. Tunda har ta furtan hakan akwai kamshin gaskia ciki, idan ma koran Abba mardiyya take sonyi ai akwai oda strategies da zatayi using ba wannan ba.
      Main palon ya k'arasa ya zauna yana tunanin wazai tuntuba da batun yadda mutuwar Babansa ta kasance, kawu Habibu ne ya fadomai arai, tabbas shi d'aya zai iya fayyace mai ko Babansa nada rai koya mutu, duk azuci yake xancan, dafe kai yayi, gabadaya duniyar tamai zafi, bai gama nutsuwa da b'atan Batul ba ga wata gagaruma Mom ta janyo mai.
     Mikewa yayi da zama ya haura sama zuwa dakinsa. Freshen up ya shiga toilet yayi ya fito, ya shirya cikin kananun kaya, ya sauko kasa ya fice haraban gidan, motarsa yafada yaja zuwa home of hospitality (katsina).
     Cikin sa'a ya iske kawu habibu gida bai fita ba, gaisawa sosai sukayi daganan ya zayyano mai xancen dayaji Mom ta fada.
Jinjina kai kawu Habibu yayi yace.
 "Tabbas abunda ta fadi ta fade sane kawai dan wata manufarta, amma kam Baban ka ya dade da rasuwa, tunshi kuma bata sake aure ba"
D'aurewa kan Rasheed yayi da kalaman kawu, yakasa aminta da abunda suke fadi, shidai yasan akwai wata boyayyen al"amari dan jikinsa na fadi mai babansa na raye tunda Mom ta furta.
Nisawa yayi yace "kawu miye sanadin  mutuwar sa, kunyi mai jana'iza ?
Girgiza kai yayi, yace
"Bana nan sanda ya rasu, ina Ghana karatu lokacin, bayan na dawo Maman ka kece min ya jima da rasuwa, nayi kuka rashin sa ba kadan ba, tsohonka akwai halin kirki da daddako"
"Allah yaji kanshi" Rasheed ya fadi asanyaye, saidai ayyada ya lura da xancen Kawu bai da matsaniya akan mutuwar Baba, same story da Mom tabasa shine wanda yasani, ba yadda ya iya dole ya nunawa kawu ya yadda da xancensa dan bazai iya mai masu ba.
Sun dade suna hira daga bisani yamai sallama ya kamo hanyar dawo wa Kaduna.


                *Zaria*

8.26pm

Iya karfinta ta sanya tana wanke shinkafa wainar gobe, daga can gefe Inna ke zaune tana yankar alaiyaho.
"Ilimi akwai dadi, Inna nima dai xan shiga islamiyyar daran nan" Batul ta fada tana sauraran karatu dalibai dake tashin daga can islamiyar dake gaba dasu.
Inna tace "Islamiyar akwai karantarwa, babu wasa sam, yaro kadai xan tura ya karbo maki form ki ciki gobe ki fara zuwa'
Cikin jin dadi tace "nagode sosai Inna".
Yaro ya shigo hade da sallama, amsawa sukayi yace "Nafi'u mai shayi ke sallama da jikar mai waina, yana waje"
"Kai yaro koma kace bata fitowa" Inna ta fadi tanai zarowa yaro ido, tasan xaa rina sunga yar kyakyawa zasu fara damunta da k'wado sallama.
Dakatar da Yaro Batul tayi tace "kace mai gani nan"
Toh" yaro ya amsa ya fice.
Kallon Inna tayi tashe, "inna kiyi hakuri naje, kinsan shi  dan adam komin yadda yake ba abun wulakantawa bane, wannan abu ya faru akaina, banaso tarihi ya kuma maimaita kansa.
Dariya Inna tayi, tace "gaskia ne, kije amma karki dade".
Hijabin ta dake lankaye kan igiyar shanya tadau tasa ta fice wajan gidan.
      Tsaye ta iske shi, hannusa rike da bakar leda, jkinsa sanye da kodaddiyar tshirt da wando daga ganin wankan kure adaka yayi.
"Ina wuni" ta fadi hade da sunne kai kasa, tasan dama saiya biyota, dazu dataje teburansa siyan biredi sai wani kirki yake mata.
"Lapia kalau yammata" ya amsa.
"Sunana fatima" tace
Yace kiyi hakuri nakira ki da yammata, gaki da babban suna"
Murmushi tayi tace "ba komai, ya kasuwa ?
"Alhamdulilah" ya amsa mata.
Shuru ne ya biyo baya, sai can kuma yace "fatima tunda naganki naji sonki araina, dan Allah ki bani dama na nuna maki tawa salon soyyayar.
Murmushin dayafi kuka ciwo tayi, tuni ta cire so aranta, shi kuma gashi yaxo da kokan baransa, dago dakai tayi ta dubesa, Nafiu ba laifii dukda ba sonshi take ba tana iya aurensa, yana da kirki hankalinta zaifi kwanciya dashi.
Nisawa tayi tace "nagode sosai da Soyayyar ka, Allah yasa hakan yafi alheri".
Dadi sosai yaji ya mika mata ledar hannusa, kin amsa tayi, yace "ki karba, biredi ce na taho maki dashi"
"A'a wlh ka barshi, so kake na cinye ma jarinka"
Dariya yayi, ba yadda baiba ta karba taki amsa, hira kadan suka dan tab'a, tamai sallama ta koma gida, tuni Inna ta shige daki, zama tayi tsakar gidan tanai tunanin Baba da hajjon ta, kiransu take sonyi saidai wayar ma batasan a wace duniya ta yarba tsabar rawan jikin zuwa nema Rmd, ba mamaki ranar datai gudun nan Inna ta biyota wayar tafadi daga hannuta.


 *****
Washe gari cikin mayuwaci Hali Rasheed ya kasance, duk ya susuce, bini bini ya koma gidan can ko zaiga Batul amma wayam, ta bangaran Mom kuwa bai kuma tunkararta da zancen ba.
     Agajiye likis ya dawo gidan, dakinsa ya nufa ya iske Mardiyya na kokarin shimfuda bedsheet, saurin rikonsa tayi ganin yana kokarin faduwa.
"Sweetie are you alright" ta fadi tana kokarin zaunar dashi kam sofa,
"Am not" ya fadi cikin murya kaman xai kuka.
Zama sukayi atare tace "plz ka gayamin matsalar ka na taimake ka, i hate seeing you like this"
Ajiyar zuciya ya sauke yanai lumshe ido, murya kasa kasa yace "Diyya ki gayamin gaskia meke tsakanin Abbanki da Mom".
Gabanta ne ya fadi, jin tambayar bambarakwai, "babu komai" ta fadi.
Gyara zama yayi ya xayyane mata komai dayaji suna fadi.
Mamaki sosai ya kamata wai abbanta da Mom so disgusting ma, yaushe ma Ummanta zata yadda hakan ta faru.
"Amm sweetie kana ganin akwai kamshin gaskia babanka is alive"
Yace "Am sure he is alive, babu dai wanda xai gayamin gaskia"
Ajiyar zuciya ta sauke tace "i have an idea".
Kallonta yayi.
Gabanta na faduwa, tana tsoron fadi mai easy way dazai gano gaskia, saidai ayyanda yake bazata iya jure ganin sa cikin bakin ciki ba dole ta fadi dabarar dake ranta, amma tasan hakan na iya barazanar da auranta.
Tace "sweetie kaje ka samu Umma, ita kadai ce tasan duk wata sirrin Mom, am sure zata gayama gaskia, idan har tace ma your Dad is dead you have to believe her, itace kadai hope dinmu yanxu"
Murmshi yayi hade da riko hannuta yace "Diyyah you are smart saidai Hajiya Safara is smarter than you, kema kinsan ko sama da kasa zata hade she wont say a word"
"I know she wont say a word, shiyasa zan fadima weak point dinta"
Mikewa yayi kadan daga shigidan da yayi yana kallon ta.
tace "hajiya safara nada matukar kishi marar mitsaltuwa, abu daya zaka gayamata she will blow out all abunda kakeson sani"
Bakinta takai kunnan sa tamai rada danima banji ba.
Yace "are you sure it will work ?
Tace "trust me"
Mikewa yayi tsaye yana fadin "i'll be back" ficewa yayi da axama.
Numfasawa tayi, tana fadin "Allah yasa ban ballo wa kaina ruwa ba".


Bai zarce ko ina ba sai gidan Hajiya Safara dake unguwar Rimi, horn yayi mai gate ya bude, karasawa ciki yayi yay parking motar.      
      Tunda daga window palon Hajiya Safara ta kyallarosa, Biebee dee mai aikinta ta kwallawa kira, da azama Biebee ta karaso hade da risina, "sirikina ya iso, maza dauko kayan sha da motsa baki ki kawo".
"Toh Hajiya" Biebee ta fadi hade da juyawa zuwa kitchen, sosai take tsoron Hajiya shiyasa komai take kaffakaffa.

Knocking yayi ta karasa ta bude mai kofar, fuskar ta dauke da fara'a
"Auta momy yau kaine da kanka" ta fadi tanai washe baki.
 Gaida ta yayi fuska ba yabo ba fallasa sannan suka karasa kujera hade da zama.
"Ya mardiyya, hope dai tana lapia"
Kalau take, urgent magana ya kawoni" ya fadi atakaice.
Cikin hankalta da nutsuwa ta kasa kunne saura ransa.
"Umma ki gayamin gaskiA nasan kinsan komai, dagaske Babana na raye ?..
Dariya sosai ta fashe dashi tace "waya gayama shirman nan, toh idan ma mafarki kake ka farka, ubanka na karkashin kasa.
Murmushi yayi ya kalleta yace "rumour naji agari, nima ban yadda ba".
"Karma ka yadda, karya ce babban". Acewar Umma.
Hira kadan suka taba cike da wasa da dariya daga bisani ya mike xai wuce, taka mai tayi zuwa bakin kofar ya juyo yana fadin "Umma Allah ya sanya alheri fah".
Kallon rashin fahimta tamai
Yacigaba "Abban yaje can gidanmu sun dade suna hira da Mom, ashe soyyaya suke, kwanannan ma zasuyi aure" cike da farin ciki ya karasa xancen, bai jira cewar taba yayi gurin motar sa.
Daskakera Hajiya Safara tayi kaman kankara tsabar kidima da tashin hankali, jikinta har wani rawa ya dauka, hango Mom kadai take amatsayin kishiya, dafe kai tayi tsananin yadda kanta ke tsarawa, ita Fatima zatama zamba cikin aminci, sai yanxu tagane kallon da mijinta ke mata idan taxo gidan, bazai yuyuba, fatima kinyi kadan baki isa ba, duk azuciya take maganar.
     Cikin zafin nama ta karasa da sauri inda Rasheed ke tsaya yana kokarin bude motar.
"Yana nan da ransa bai mutu ba" ta fadi cikin huci.
Fasa bude motar yayi yana kallonta, hannuta ya riko yace "Umma yana ina, plz ki gayamin"
Cike da baccin rai take magana.
 "yana garin Kaduna, saidai bansan a ina yake ba, kaine kasan inda yake"...
Kallon rashin fahimta yayi mata.
Tace "yarinyar da Mom ta tarar a gida she is your sister, babanta shine mahaifinka"...
Rasheed kam ya gama rudewa, wace yarinyar take nufi badai Altine mai aikin suba.
Tacigaba "ranar daka fadi mata fatima ex wife dinka ce she was very devastated, fatan ta daya Allah yasa auratayya bai shiga tsakanin kuba"..
Iya gigita Rasheed yakai yama kasa gane wace Fatima take nufi,
Haunnsa ta rike gam tana fadin "yarinyar nan princess kanwar kace ta jini"
Wani mugun kara ya kwalla wanda gabadaya gidan saida ya amsa, cikin rawar jiki ya saki hannuta ya fada motar yaja ta afusace.
     Dogon tsaki Hajiya Safara taja aranta tace "no i messes with my husband" afusace ta juya tayi cikin parlour, garara raf sukayi da Biebee dake rike da jug da ruwa, wani wawan mari Hajiya safara ta kai mata sannan ta wuce daki. Jikin rawar jiki biebee ta durkusa tsince glass daya fashe.

Gudu yake shararawa harya karaso gidan, ko parking motar bai iyayi dakyau ba, ya fito cike da kidema ya shiga gidan, Mardiyya ya iske zaune Palo, ko kallanta baiba ya fada dakin Mom agigice, kwance take kan gado ganin yadda ya faddo cikin dakin yasata razana hade da mike tsaye.
     Durkusowa yayi gabanta, cikin muryar kuka da tuni ya sarke sa yace "Mom y, miyasa kika min karya babana ya mutu, wosrt part of it princess kanwatace, kinsani baki gayamin"
Wani mugun mari ta kwashe shi dashi, tace "ni nake maka karya, a gidan ubanwa ka jiyo labarin nan".
Bai damu da mari ba, yace "hajiya safara ta gayamin, kuma nasan datx the truth".
Gabanta ne yafadi jin ya ambaci Safara, lailai kuwa itace babu wanda yasan da hakan sai ita, amma kinci amanata safara, mu zuba nidake, duk azuci take magana.
Karyarta ta kare dole ta fadi mai gaskia ayita ta kare, dagosa tayi kan gadon sannan ta zauna gefen sa suna fuskanta juna.
"My boy kayi hakuri, i did all that to protect you, your father was cruel, he never appreciate us"
Kuka ta fashe dashi, hannuta ya riko "mom cigaba sai miya faru ?
Tsayar da kukan tayi tace "rabuwa yayi damu adalilin matar daya auro, Mahaifiyar so called princess, My boy d first day dana ganta yasa nayi kokarin tabar gidan cox banason past dinmu yazo yana hunting dinmu, plz stay away from her"
Kuka sosai ya fashe dashi yan hango fuskar Baba wai shine mahaifinsa, saidai halinsa da Mom ta fadi he isnt buying it a bit, babban tashin hankalinsa bai wuce na cewa Batul kanwar shice ba, bai taba jin sonta ba sai yanxu da yaji wai kanwar shice, wani irin sister love game da ita ke ratsa mai gangar jiki da zuciya.
Yace "Mom ki temake ni, Princess is missing, duk fadin kaduna na bincika ban ganta ba" ya fadi yana kuka, ido jajir.
Lallashi sa tahau yi tanai kara basa hakuri.
Karasa shigowa Mardiyya tayi da tuni tana tsaye bakin kofar, kuka take ta nufosa,
Mugun tsawa Mom ta daga mata hade da mikewa tsaye
"You have overstayed your welcome, pack your tinx ki barmin gidana"
Ko kallanta mardiyya batai ba tacigaba da takowa gurinsa, kafin ta kara taku daya tuni Mom tayi taku biyu uku takai mata gigitaccen marin da yayi baraxanar sanya jinin gabobin jikinta daskarewa.
Ihu ta saki tsabar raradi,  kallon Rasheed tayi da bai san abunda ke faruwa ba, kuka kawai yake yana kiran sunan princess.....
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com

*IZG*

      *Kwadayin abin duniya* *Kwara ta wahala inta samu kudi shi won't know d value of it and she wil use dat to humiliate  d poor, gwara shi should be greatful to wat Allah destiny for ha, en she* *wil live happier without mach more money*
*Hankali kwance Aren't d poor one succeeding  en living peace ful in live* *without being wealthy enough?*

*Baga baban batul da maman ta ba da kannar taba,hankalinsu ba a kwance take ba? Basu ci ba su sha basu sutura?wake takura ma rayuwarsu?*

*Unlike Hajiya safara ,hajjo, RMD, Diyya duk ga harzikin amma ba kwanciyan hankali tareda su,kullun daga wannan sai wannan, Meh arzikin tayi masu?*
*Yasa ma masu kwanciyan hankali kodai tashin hankali  da hawan jini?*

*Hmmmm wani lokaci arziki ma wata bala'i ne wlhy Allah ya bamu wacce zata zama alkhairi gare mu da tsari kuma mai albarka*

                   💕 _*Ummiee Khaleel*_💕


*Nyc one Ummiee, after reading this intelligent write up i was like this girl really understand what am trying to initiate, it was so* *educative & remarkable.*
       *Thanks so much dear, i hope odas zasu fahimci* *sakon da muke son isarwa.*
   *All that Glitters is not Gold....*



                   72


Gabad'aya baya cikin hayyacinsa, jin ihu mardiyya akaro na biyu yasa shi dawo wa hayyacin sa, bakin kofa ya ganta Mom na kokarin turata waje.
"Sai kin bar gidan nan tunda bana ubanki bane" Mom ke fadi cikin daga murya.

Mikewa yayi ya karasa gurin.
"Mom plz calm down, xata bar gidan yanxu nan"
Kallon mardiyya yayi da har yanxu bata bar kuka ba, yace "bakiji abunda tace ba, wuce ki hada kayanki"
Kasa cewa uffan Mardiyya tayi saima kara sautin kuka da tayi ta bar gurin da azama, mara mata baya yayi ya fice daga dakin.
     Dogon Ajiyar zuciya Mom ta sauke ta koma gado ta zaune hade da dafe kanta tsabar takaici, Hajiya Safara idan kinsan wata baki san wata ba, nayi danasani gaya miki sirri na, saidai akwai certain things da baki sani ba.
    K'wafa tayi,  yazama dole tadau mataki akan Batul, dan bazata yadda danta ya kara auro bata, just jini daya da tace suke duk yabi ya rikici, she wonders ya zayi idan yagano ba kanwarsa ta jini bace, duk azuci take magana. Tunanin ranar data fara ganin Batul ta shiga yii...

Tuna Baya (Flashback)
Shekaru Shida da suka wuce.

Daidai round about ta kasuwar checheniya ta cikin jahar Kaduna ta hango sa daga can gefen titi suna loda kwandan kayan miyan cikin keken Napep, Gabanta na ya fadi, madubin fuskata dake nane bisa idanuwan ta cire cike da mamakin kara ganin sa, kusan shekaru ashirin da bakwai rabon ta da sashi a idanu sai yau tun bayan rubuwa da tayi dashi a katsina.
     Saidai ganin data mai ya tsofe ba kamar da ba, keken taga ya shiga matuk'in yaja su suka tafi.
   Saurin tada motar ta tayi zuciyar ta na azalzalarta ta bishi taga ina zai nufa, can cikin unguwar kawo taga keke ya nufa, tsayawa yayi daidai wani gidan bulo da babu sementi, daga cen nesa tayi parking tana kyallarosa.
     Kyakyawan Yarinyar yar kimanin shekaru sha biyu taga ta fito gidan, jikin sanye da kayan makaranta na islamiya, gaida sa tayi ya fiddo naira ashirin ya bata sannan ta wuce, sai kuma maza biyu masu kama taga sun fito, suma sanye da kayan makarantar, gaidasa sukayi suka wuce.

Duk akan idonta, karaso wa Satin Motar ta yarinyar tayi natai karewa motar kallo, baa ganin wanda ke ciki kasancewar ta tinted, nan Mom ta samu daman kare mata kallo sakamakon hannu datasa tana taba motar cike da sha'awar ta,
"Batula munyi latti fah" Hassan ya fadi yana juyowa baya dan tuni sun yi gaba"
Guntun tsaki taja tace "oh ni fatima, yaron nan bazai daina kirana batula ba" ruguwa tayi tanai ihu su jirata.
Maida dubanta Mom tayi zuwa gurinsa saidai tuni ya shige gida, mai keken ma baya gurin, dogon tsaki taja hade da buga steering, taso ace ta samu details akanshi, reverse tayi kokarin yi taga wani dattijo ya shiga gidan ya fito cikin sakanni kalilan rike da kwandan albasa, ganinsa tayi ya karasa wani teburi hade da ajiye albasan akai
   Saurin jan motar tayi garesa, sannan tayi wining glass.
"Sannu" ta fadi
Washe baki abokin Baba mai suna Lamido yayi, tambayarsa tayi nawa kwando albarsa, yace da ita dubu da dariya biyar, dubu biyu ta fiddo tabasa hade da barmai cancin, godiya sosai yayi.
Tace "naga wani da kayan miya ya shiga can gidan, waye shi ?
Dariya lamido yayi "muhammadu ne shine mai teburin ai, nazo ne kafin ya karaso"
Murmushi dabai kai zuci ba Mom tayi tace, "ayyo, naga yaran sun fito daga gidan yanxu, halan yayan sane"
Lamido yace "su yan biyu ba, hassan da hussaini yaran sane"
K'wafa Mom tayi, aranta tana fadin wato shi aure yayi ita tana can igiyoyin akanta, afili tace "naga wata yarinya tare dasu, wace ita.
"Yar'sa ce ta fari"
Gabanta ne ya fadi.
Yacigaba "bayan mutuwar danuwan sa ya auri uwar yarinyar wato ikilima, kinga kuwa shine ubanta kuma amatsayin yarsa ta fari".
Bata cira cewar saba taja motar afusace tabar gurin, wani mugun tsanar sa da yaran taji azuciyar ta, ba mamaki Ikilima matar kaninsa Ahmadu ya aura, sunyi zaman gida daya dasu a kauyan kafin hausa, kuma zaman baiyi dadi ba, dan alokacin basa shiri da Ahmadu ko kadan dan baya daukan raini daga baya ne ma tafara girmama shi Amma toh yaushe rasu, ta tambayi kanta... Rai bace ta koma gida ba tare data fadiwo kowa xancen ba.

Saidai abunda bata sani ba bayan Baba yaxo lamido bai boye mai komai ba ya fadi mai yadda sukayi hade da kwatanta mai Mom, tsaf baba ya gane itace, cikin rashin damuwa ya cigaba da tsafgogin sa.

Dogon Tsaki Mom taja bayan ta dawo daga doguwar tunanin data lulA, mikewa tsaye tayi tana kai komo a tsakiya dakin, zacen zuci take.
"Dole na nemo Batul duk inda ta shiga a fadin duniyar nan kafin My boy ya ganta, i have to deal with her kafin nakai ga ubanta, amma ta ina zan samu phone number dinta balle nasa a binciko min ita"
Tunanin mafita tahau yi, can dabara nemo wayar Rasheed ya fado mata tasan bazai rasa nambar taba, cikin azama ta fice palon da niyan hawa sama ta hango wayoyinza jefe kan kujera, dauka tayi da zama, babu lock ko code tayi azaman shiga contact bincike, tsaf ta duba babu contact mai suna Batul, fatima ko princess, tsaki taja dabarar shiga maajiyar hotuna ta fado mata, cikin saa kuwa tana shiga taga pic dinta kwance kan kujerar parlour tana bacci da alamun ma batasan ya dauka ba, daukar wayar tayi ta shiga daki ta tura hoton wayarta sannan ta dawo parlour ta ajiye mai tasa wayar. Dakin ta koma cike da muguyan manufa aranta.

Gabadaya kayanta Mardiyya ta kwashe tasanya akwati, kuka kawai take ta caza ma kanta saidai still bata blaming mijinta, atleast she is happy tunda ya gano baban sa is alive da kuma sister daya jima yana fatan ace yana dashi.
   Bude kofar dakin tayi sukayi kicibis zai shigo.
"Muje yace da ita, hade da karban dayan daka cikin trolley da take rike dashi.
Kallonsa take kamar zatayi kuka ganin dayan hannusa ruke da nasa akwati.
"Sweetie ka bari kawai na tafi, kayi hakuri ka zauna da mom she really needs you".
Kai ya girgiza,
"Diyyah muje kawai, it high time mubar mata gidanta, for 33 year nake tsugunne da ita, this time kuma i need some space" ya fadi hade da sauko wa, binsa tayi a abaya har suka sauko, wayoyinsa dake parlour yadauka, suka fice daga Parlour.
    Ma'ajiyar mota suka nufa, ya bude butt ya sanya kayan suka shiga mota yabar gidan.
     Tuki yake yana trying numban Baba da dayan hannusa, saidai not reachable kadai yakeji, kusan sau wajan goma abun daya suke maimaita mai, tsaki yayi hade da wulla wayarvbaya, yasan Mom bazata mai Karya ba sai dai yadda tace Baba ne ya rabu dasu bai yadda koda k'wayan zarra ba, definitely saiko itace ta rabu dashi dan yana talaka, ayadda yaji labarin Mom tana karama yar gata ce sosai kuma babanta mai bala'in kudin ne, it doesn't make sense ace shi yayi abandoning dinsu, for wat reason, buga steering yayi cikin tsanin bacin rai, rashin sanin inda Batul take ba karamin konamai zuciya yake ba, ita kadai yakeson gani koya ji sanyin a zuciyar sa, yasan itama bazata rasa sanin wani abu game da auran baba da Mom ba.
      Haka dai suka karaso
maidaidecin gidansa mai dauke da daki biyu da palo, parking sukayi ya sauko cero masu kayansu, dakyar Mardiyya ta samu ta fito daga motar, taku daya biyu tayi, taji tana neman faduwa, sauri taro ta yayi dan kuwa kiris ya rage bata je kasa.
"Are u alright" ya fadin yanai kallonta, itama kallonsa take saida ta kasa furta koda kalma daya.
"Muje ciki" yace da ita, kasa takawa tayi yayi saurin cicibarta suka shiga ciki, dakin ya shiga ya direta kan gado yanai mata sannu.
"Diyyah kodai muje asibiti"
Kai ta girgiza kafin yayi wata maganar tuni ta rufe idanu, bacci yayi gaba da ita
Shafe gefen fuskarta yayi yana jiyo numfashin ta dake fita ahankali, cike da tausayinta ya janyo comforta dake gurin ya lullube ta, yasan kukan data yi yasa tazama exhausted.

Shuru dataji yasa Mom fitowa parlon, haurawa sama tayi ta leka Dakin Mardiyya, babu ita balle kayanta, murmushin jin dadi tayi ta karasa dakin Rasheed, wayam ta gani babu kayansa sai wata takarta data gani da rubutu, an ijeye kan gado.
    Dauka tayi ta bude, tahau karanta abunda ke ciki.
"Am sorry Mom, banda zabi daya wuce nabi matata mubar miki gidanki, burina daya na nemo duk inda princess take although she is my sister i won't stop loving her, dukda da diyar kishiyar ki ce, i hope wataran zaki sanyawa zuciyar ki so da kaunar ta. Love you Mom"
Squeezing takardar tayi hade da wurgi dashi tana huci, wayarta dake hannuta ta duba hade da dialling wata number, bugu daya aka dauka
Tace "Roze kaga picture dana ma sending ?
Cikin muryarsa ta yan daba yace "Nagani, na miye ne ?
"Roze yarinyar nake so ku nemo ku kawo min ita dead or alive"
Dariya yayi yace "angama hajiya, yanxu xan tura yara parade duk inda take zasu ganta.
"Make sure duk wata kauye da birni na kaduna ku bincika, Yarona is desperately searching for her, make sure ku kawo min ita kafin ya ganta".
"Ba matsala Hajiya, muna da branch ko wana gari, duk inda take zamu ganta.
Katse wayan Mom tayi tana huci, afili tace "saura ke Safara, i have unfinished business dake" afusace tabar dakin.
    Mayafi kadai da car key ta dauka ta fice waje, motarta ta shiga taja zuwa gidan Hajiya safara cikin fusata.  
     As usual, daga window Hajiya safara taga dirar motar Mom, fito tayi da azama zuwa farfajiyan gidan sukayi kicibis.
"Munafuka maciya amana, kwadayayya, duk hallacin danai miki haka zaki sakamin " mom ke fadi cikin daga murya.
Harara hajiya safara takai mata, tace "karuwan banza kin dauka bansan bibiyar mijina kike ba, idan ni mai kwadayi ce ke kuma karuwa ce"
Hannu Mom tasa ta wanke ta da mari,
"Kika mareni" Hajiya safara ta fadi kin shock.
Kokuwa ce ta barke tsakanin su, da gudu Biebee dee dake labe bakin kofa ta fito tanai rabasu, dakyar tasamu ta janye Hajiya safara da tuni tafara jigata.
Cikin huci mom tace "zaki ci ubanki, saina nuna miki ni ba tsarar ki bace" juyawa tayi ta koma motarta.

Zagi sosai Hajiya safara take lailayo mata, dakyar Biebee taja ta suka koma parlour cike da mamaki aminan juna yau sune da zage zage da bankadawa juna asiri, jinjina kai tayi, azuci tace "aminantaka akwai dadi, saidai duk yadda kake da mutum ba ko wana sirrin ka zaka fadi mai ba, koba jima koba dade akwai shaidan yana iya shiga tsakanin ku, daganan kuwa fallasan asirin ya biyo baya, love all but trust no one" (ni xarah nace maganarki dutse.)

Fitowa Mom tayi tare da parking gefen titi, tunanin kadai take yadda zata rama betrayal da aminiyarta tai mata, sai yanxu takejin haushi fadi mata komai nata alhalin ita bata taba gayamata komai game da ita ba, dogon tsaki taja tana karason tuno wani abu da zatai using against her, abu daya ta dade tana son sani game da Hajiya Safara shine "source of her income (asalin dukiyar ta)" asali Alhaji Bello talakane, Mardiyya nada shekaru biyar aduniya hajiya safara ta koma Ghana gaisuwar rasuwar Babanta, bayan wata shida ta dawo amatsyin mai kudi, abu daya tace masu wai gadon Ubanta ne, kadarorin daya bari ta siyar ta dawo Nigeria.
K'wafa Mom tayi tana kara fadin "babanki talakane, asalima talauci ya kawo ki nigeria har muka hadu a skull din da kika shigo amatsayin yan alfarma, i know you're hiding something, amma miye ne ?
Ajiyar zuciyar ta sauke ta kunna motar ta karasa gida.

****

Bayan kwana biu.

Rasheed da Daddy Malam basu bar neman Batul ba, sune har Abuja zuwa nemanta, aganinsu can garin Manya ne kila can ta nufa, ba hope haka suka dawo kaduna.
    Ta bangaran Mutanan Mom su Roze suma basu fasa baza idanu ba, akullum saita ninka masu kudi da zata masu idan har suka gano ta, sosai suka fantama yin aikin su.


           *Zaria*

Juya wainar take cikin hankali da kwarewa, masu siya sai siya suke, wani yaro ne ya miko kudi.
"Gashi inji Nafiu wai kisamai ta hamsin"
Toh" Batul ta fadi hade da amsan kudi tana murmushi.
"Shiga cikin gida ka dauko min kwano" tace da yaron.
Kwanon ya dauko ya bata, ta zubamai harda miya tare da karamai da nama.
"Gashi ka kai, kace ina gaida sai, karya manta da dare idan na dawo islamiyya zamu hadu" ta fadi tare da mikama yaron kwano, amsa yayi da toh sannan ya wuce.
"Mu kenan bazaa a samana a kwano ba sai leda" wata yarinya dage gurin ke magana.
Dariya kawai Batul tayi tasan zolayar ta take.

"Ke jikan mai waina sako min ta dari" wani matashi dan Tasha ke fadin haka cikin daga murya.
Daure fuska tayi, koda wasa taga iri irin su b'ata rai take, "kawo kudi" ta fadi.
Hannu yasa aljihu yana kokarin ciro kudin tare da kare mata kallo, fasa ciro kudin yayi, ya ciro wayarsa kirar Techno yana kallon hoton ta dage cikin wayar, kusan minti biyu yayi yana compare and contrast din fuskar ta dana hoton, babu tantama yagano ita dince, fasa siya yayi yabar gurin, lungun ya samu ya kira ogansu na gurin ya shaida mai yaganta, nan take suka ajiye plan din cafketa da dare.


           Kaduna

Cikin sauri ya fito daga dakin, kitchen ya nufa inda yaji motsi Mardiyya.
"Diyyah na fita" yace da ita.
"Sweetie ina kuma, dazu kawai fa kadawo"
"Kin manta we are still searching for princess"
Kallon rashin fahimta tamai
"Wace princess?
Gira sa ya daga yanai kallonta, yace "Sister inlaw dinki"
Still bata gane ba, ganin zata b'ata mai lokaci yasa yabar gurin.
Dafe kai tayi tace "Allah ya bayyanaki Princess"
Rasheed dake labe bakin kofa yana jinta, recently haka take behaving so confused anjima kuma ta koma normal, bai kawo komai aransa ba ya fice ya shiga mota yabar gida.

Daddy malam ya kira awaya suka hadu a hanya ya daukesa suka bazama da shiga unguwanni neman ta, daddy malam kam ya fara gajiya da abu daya babu hope, shawarar zuwan gidan redio da talabijan y kawo, ba masu Rasheed ya yadda dan shima ya dade da tunanin haka.
       Juya kan motar yayi zuwa hanyar da zata sadasu da gidan labarai.
     Wayar Daddy ce tayi rurri, dubawa yayi yaga Inna, cike da fara'a ya dauka suka gaisa,
Tace "wato ka manta ni ko?
"Haba kakus zanxo kwanan nan, aiki ne yamin yawa" ya fadi.
"Wana aiki ni xaisa kaki xuwa" Inna ta fadi atakaice.
Yace "Batula ce ta b'ata, shine fa muke yawon nemanta haryau babu labarinta"
Salati Inna ta saki, tace "Batula ai muna tare, ta jima a Zaria"
Cike da mamaki yace "batula na gidan ki"
Wani mugun burki Rasheed yaja tamkar yaji maganar da suke, karbe wayar yayi yace "Inna gani nan zuwa" katsewa yayi hade da saurin yin reverse.
"Nidai sauki ne na koma gida, nabar Maman Aryan ita daya" Daddy malam ya fada yana dariya.
Tsayar da motan yayi ba tare daya kallesa ba.
Daddy yace "ka bari gobe sai muje, yanxu fa Magrib tayi"
Harara ya kai ma "kaidai sauka kawai".
Sauka yayi yana Dariya.
Rasheed yaja motar, massallacin hanya ya tsaya yayi Sallah sannan ya buga motar to zaria, cikin mintina ashirin da biyar har ya iso, a gurguce ya fito ya shiga gidan.
     Inna na zaune tsakar gida tana jan jarbi ya shigo, zama yayi jiran ta sallame sannan ya gaida ta, cike da faraa ta amsa mai.
"Inna ina Batul take ?
Dariya tayi.
Daure fuska yayi atunaninsa wasa take mai
"Bata nan, taje islamiya, sai tara zasu tashi".
Ware idanu yayi, wai batula a islamiya, mikewa yayi yanai tambayarta ina islamiyar take, nan ta kwatantamai na bisa bakin titi.
Da azama ya fice, bakin gate din islamiyar ya tsaya cike da farin cikin xai ganta, agogon hannusa ya duba just 20 minti ya rage su tashi.

 karamar kofa dake bayan Islamiyar suke tsaye daga can nesa.
"Ka tabbata tanan take biyowa idan suka tashi"
"Eh, ta nan ne, yafi kusa da gida da take azama"
Matsawa gefe su hudun sukayi jiran ta fito su chapke ta.
     
Cikin sa'a Batul ta fito daga karamar kofar, tafe take hankalin kwance tanai kara tilawar karatun da Malama Sophie ta koyar su, takun data ji abayanta yasata waiwayawa da sauri, wayam tagani babu kowa, gabanta ne yahau dukan uku uku, cikin sauri takara daga kafafunta tanai waiwayan bayan, kamar daga sama taga gardi biyu tsaye a gabanta, kafin ta juya tuni biyu su tsaya daga baya sun zagaye ta.


Murmushi Rasheed yake baki yaki rufuwa, yan mata da samari sai fitiwa suke daga gate din, ware ido kadai yake yana jiran fitowar little Sister dinshi.....
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com

                   73


Shuru babu alamunta, har dalibai suka k'arasa fitowa, Mai gadin gurin ne ya mike hade da kokarin kullo gate din.
Yace "dan dakata, karka kulle kanwata bata fito ba"
Karasa kulle gate din yayi hade da datseta ta k'wado, sannan ya kallesa yace.
"Lokacin rufewa yayi, saidai ka duba karamar kofar baya"
Nagode" yace da dashi yayi azaman zagawa baya.
Dalle mata idanu Roze yayi yana kallon fuskarta, kallon hoton wayarsa yayi yace da sauran ita dince, ku dauke ta kusa ta cikin mota.
Tsoro ne ya dabaibayeta, kallon su take bata gane ko wanne cikin su ba sakamakon mask dake sanye fuskar su, kuka ne ya kufce mata tahau rokonsu, ko sauraranta basu yi ba sukayo kanta, ihu ta kwalla, dabarar tsugunnawa tayi ta kwaso kasa ta watsa masu fuskar. A 360 ta arta aguje, cikin tsananin fusata suka bita da gudu suna goge idanuwa da shikadai ke bayyane cikin mask din.
      Ihun ta daya karad'e dodon kunnansa yasanya shi saurin barin gurin da tuni ya iso yana jiran ganinta, cike da tashin hankali yahau zubawa hanyar ido, daga nesa ya gano katti na gudun famfalaki, motarsa ya fada da azama ya fuzgeta afusace.
Gudu sosai take. Tsabar kid'ima wuce layin gidan Inna tayi ta fada makarantar UBE dake fuskan tar ta, ajin farko ta fada ta karasa can karshe ta boye karkashin desk, dagowa tayi ahankali tana lek'e ta window, tsaye tagansu daka can nisa suna leka ajujuwan dake gefe, aji biyu kadai ke tsakani kafin su karaso inda take. Sosai hankalinta ya tashi tanai sharar kwalla, ziro kofofinta tayi ahankali ta window ta fito kasancewar babu glass, tuntube taci da dutsen dake gurin ta kwalla ihun daya janyo attention dinsu gurun, da axama suka fada ajin tare da baza idanuwa.
     Cike da radadi da azaba ta falla da gudu, bata ankara ba taji hannu ya rikota, ihu xatayi yayi saurin sa hannu ya toshe mata baki, janta yayi suka lafe cikin bishiryar dake gurin, runtse idanu tayi tuni ta sadakar sun kamata, saidai kamshi prince dinta dake bugar mata hanci yasata faduwar gaba.
Hannu yakai bisa fuskar ta yanai share mata kwalla, cikin sanyin muryar sa ya kira sunanta da princess, kin bude danu tayi banda rawa da jikinta yake, atunanin ta bashi bane, zuciyar ta keson yaudarar ta.
"Princess baxaki bude ido ki kalli prince dinki ba"
Bude idon tayi ahankali ta daura sa bisa fuskarsa, kuka ta fashe dashi ta fada jikinsa tana fadin "i know you hate me but plz ka temakeni kar mutanan nan su kamani, plz save me" kuka sosai take tana maganar.
Baice komai ba, yasan inda xancen ta ya dosa, rikota yayi suka karasa motarsa yabude yasanya ta ciki sannan ya shiga yaja.
    "Oh shit" Roze ya fadi adaidai lokacin da suka karaso yaja motar, kallan yaran yayi yace operation continues tomorrow, jiki sanyaye da haushi rashin kamata suka bar gurin.
     Kuka kadai take a motar har suka karasa gidan Inna, kafin ya daidaita parking tuni ta sauko ta ruga cikin gidan, daki ta nufa hade da rufo dakin ta ciki.
      Mikewa Inna tayi daga inda take zaune a tsakar gidan.
"batula lapia kuwa" Inna ta fadi cike da tashin hankali, ganin rasheed ya fado adan kidime yasa ta kallesa tanai tambayar sa make faruwa, bai iya amsa taba ya karasa bakin kofar yanai bugama Batul kofa hade magiyan ta bude. Banxa tayi dashi tanai cigaba da kukanta.
      Yaro ne ya shigo yace Nafiu mai shayi na sallama da Batula, daga Shi har Inna kasa tanka yaron sukai, Batul dake jinsa ta bude kofar ta fito, bata ko kallesa ba ta raba gefensa tayi waje, Sauri binta yayi ya tsaya bakin kofar ganin ta tsaye gefe kusa da wani saurayi.
    Gaidasa tayi cikin kokari boye yanayinta, cike da farin ciki ya amsa, yahau ta da hira da ba fahimta take ba, banda eh da a'a dakadai take cemai, gabadaya hankalinta baya tattare da ita
Yace "fatima yaushe zamu je ki gaisa da iyayena, na jima ina basu labarin ki"
Yaken daya fi kuka ciwo tayi tace "duk randa ka shirya sai muje"
Dariya yayi.
"Toh amarya yata, Allah ya kaimu, nizan wuce sai da safe.
"Haba dai, tun yanxu" ta fadi ita kanta ta kosa da hirar, saidai ganin Rasheed tsaye gurin yasa batason ya tafi.
Tsayar da Nafiu tayi na kusan awa daya sannan sukayi sallama ta shigo gida.
     Riko ta yayi da sauri ta fuzge zata shige daki, Inna ta kira sunanta, dole ta tsaya bazata iya share taba.
"Zonan ki zauna" Inna ta fadi hade da mata nuni da tabarma, jiki sanyaye ta zauna kanta na kallon gefe daban.
Zama yayi kusa da ita, "plz princess ki saurareni.
Dogon tsaki taja tare da dubansa tace "kaga malam idan ma kazo ne kamaida ni gidan ka you're mistaken, cox bazan bika ba, i'd rather die akan na kasance dakai, saboda na tsanake"
Murmushi yayi da jin kalamanta, mikewa tayi afusce tana fadin "ga mahaukaciya na magana dole kayi dariya" rikota yayi yace dawo ki zauna.
Zama tayi tanai buga mai harara.
      Yace "nazo ne amatsayin yayanki na jini ba mijin kiba, plz princess ki gayamin gaskia matan Baba nawa ?
Kallon rainin wayo tayi tace " Allah ya sauwake ka zama yayana, mugu kawai, kuma babu ruwanka dako matan Baba nawa"
"Dan Allah ki gayamin badan hali naba" ya fadi amairace.
Kallonsa tayi taga lailai ba wasa tattare dashi, saidai tambayar tai mata bambarakwai.
Tace "matan Baba daya, itace Maihaifiyata Hajjo"
Hannuta ya riko, kaman zaiyi kuka yace "princess ke kanwata ce ta jini, baban mu daya dake"
Kallon rashin fahimta tamai, gabadaya yasata duhu.
Yacigaba "apart from Hajjo wace mace ce kika sani arayuwar Baba ?
Shuru tayi tanai tunani tasan dai babu ko wace mace daga Hajjo sai ita, can dai ta tuna da wani abu tace "akwai mace daya mai sunana, saidai bansanta, Baban bai taba xancen taba, abakin Hajjo nima nasanta, idan nayi laifin takance halin ku daya da mai sunanki, wataran na tambayi Baba wace ce mai sunana, cewa kadai yayi baya fatan nasanta".
Kur yayi mata da ido, yace "Ci gaba"
"Shikenan abunda nasani"
"Plz princess try to remember wani abu
Bata rai tayi hade da dauke kai, tace "ni ba princess bace kadai na kirana da hakan".
Juyo da fuskar ta yayi yace "to mi you're a princess, sunan Momcy gareki kinsan bazan iya fadin sunan kiba".
Gabanta ne ya fadi adalilin kamshi gaskia data fara ganowa cikin xancen sa, sau da dama takan ga kamarsu da Baba saidai bata taba kawo komai aranta ba, kallon sa take tana son tuno wani abu, azubure ta mike tana fadin "OmG".
mikewa yayi hade da riko ta, tuni jikinta yahau rawa.
Cikin muryar kuka tace "you're right, kai yayana ne, what am not sure shine ba Mom ta haifeka ba, i tink Hajjo ta haifeka"
Sabon rudani ya shiga, yasan dai Mom ce uwarsa, yace "miyasa kika ce haka
"Hajjo once told me bani ce yarta ta fari ba, tacemin akwai yayana saidai ya b'ata baa gansa ba" ta fadi cikin kuka, rungumota yayi yanai lallashin ta, abunda dama yake son sanin wato su sibling ne, it doesnt matter ko wace ta haifesa, abu daya yasani shine Mom ce amatsayin mahaifiyar sa.
Kuka sosai take cike da tashin hankalin ya haramta gareta, sai yanxu tagane ashe tun asalin soyyayar jini ce ta hadasu take ta shirme da haukan son shi.
"Princess" taji tlya kira sunanta cikin wata kasalalliyar voice.
Kasa amsa mai tayi, tajanye jikinta gefe, kusa da Inna ta zauna hade da daura kai kan cinyarta tanai kara sautin kukan.
Tausayin su sosai Inna taji, ita kanta sharar kwalla take, matsowo yayi daf da ita yace "Baba suna kauye, gobe ki shirya sai muje can, ai kinsan garin ko ?
Girziza kai tayi alamun a'a bata san garin ba, asalima ma ko sunan kauyan bata sani ba, Jigawa state dai tasan kauyan yake, tun bayan da tana karama suka bar garin bata kara zuwa ba, alokacin ganin take idan taje kauyen yar kauye zata zama, su Hajjo da hassan ke zuwa ita kuma ta zauna gida tare ba baba dasu Hussaini, sai wataran kuma Baba yaje shi daya.
Baiyi Mamaki da rashin sanin kauyan taba, yasan xaa rini balle alokacin kanta na hayaki ba yanxu data saduda ba.
"Gobe zamu koma gida kinji?
Mak'e kafada tayi "nikam bazan bika gidan matar nan ba"
Yasan Mom dinsa take nufi, saidai bazai barta a zaria ba, yace "kiyi hakuri muje, banason  barayin nan na dazu su cafke ki"
Tsoro sosai taji dan tuni ta manta dasu, tace "gidan Baba xaka kaini"
"Ba kowa agidan, sabon gidan  Mardiyya xan kaiki ki zauna"
Fir taki yadda, saida Inna tasa Baki bayan ya zayyane mata abunda ya faru dazu Sanna ta amince zata bishi.

**

Washe gari dakyar Batul ta yadda suka shiga mota, kukan rabuwa da Inna take sosai, lallashi sosai suka hau bata da sharadin zaina kawota ganin Inna.
     Sun kama hanya titi tace ya tsaya, ba masu ya tsaya ta fito daga motan, daga can nesa da teburan sa ta tsaya tare da tura yaro ya kira mata shi, Ganinta yayi tsaye yayi azaman ajiye biredin dake hannusa ya nufota, sallama tamai hade da bashi hakurin tafiyar tazo a tsaitsaye, sosai Nafiu yaji ba dadi haka dai sukai sallama bayan ya bata numbar wayarsa akan cewan zata kirasa.
    Duk akan idonsa, saidai ya tausaya mata da karewa Nafiu kallo, koshi da yake a Mamuda yafi sa kimtsi da wadata, dawowa motar tayi ta zauna hade da dauke kai gefe.
Yace "kinyi sabon Prince ashe ?
Kallan sa tayi hade da daure fuska "Naf'iu mijina na, the only prince da nake dashi kaine, my brother my prince"
Dariya yayi yace to miye na daurewa prince fuska.
"Ai dole na harrare ka, idan na tuna dukan da kamin i feel like slapping you"
"Bismilla" yafadi hade matso mata da fuska.
Hararar sa tayi.
 "kasan dai bazan iya ba, amma zan gayawa Babana duk muguntan da kamin"
Kumatunta yaja yace.
"zaki sha wani dukan kenan"
Ture baki tayi tace "nifa ba ruwana dakai, kadaina min magana"
Toh princess you wish is my command" ya fadi.
Shuru duk sukayi kowa da abunda yake tsakawa game da haramtar Junan su, tsaki suka ja atare hade da kallon juna.
 "miye" suka fadi atare.
"Bansani ba" Batul ta fadi adan tsiwace, kallon side mirrro tayi kaman xatayi kuka, ba karamin tausayawa kanta take ba, wani irin so da kaunar sa ke shigar ta, saidai kokarin yakacesa take a zuciyanta.
       Haka suka karaso gidan ya fito hade da zagayawa gurinta.
"Fito" yace da ita ganin bata da alamu saukowa.
"Nifa bazan fito ba, kamanta agidan nan ka wulakantani ko tausayina baka jiba ka sakeni, nayi alkawrin bazan kara taka kafata cikin sa ba".
"Koh" ya fadi hade da kashe mata idanuwa.
Dauke kai tayi.
Cikin azama yasa hannu ya cicibota yana fadin "tunda bazaki takama daukar ki xanyi"
Ihu tayi
"Dan Allah ka sauke ni, wasa nake"
Bai kula taba ya direta apalo, Mardiyya ce ta fito daga daki fuskar ta dauke da fara'a tana fadin "Sweetie sannu da zuwa"
Yauwa" ya amsa mata.
Kallon Batul tayi tace "welcom back sister inlaw"
Dariya Batul tayi, wai ita inlaw, gaida ta tayi cikin girmamawa hade da jajan yaushe rabo, dakinta taja ta suka shiga suna hira.
Tuni dama yafita dauko mata kayanta, shigowo dasu yayi ya shigar mata dashi dakin.


 ****
Kwance take tana tunanin yadda rayuwarta ta kasance, su Baba kadai take son gani, ga Nafiu ya isheta zai turo abunda bai sani ba tuni aure ya fice mata arai.
    Jin kaman Mardiyya na amai a toilet yasata mikewa hade da karasawa bakin kofar, "Sister Mardy lapia kuwa ?
Ido jajir ta kalli fuskar ta ta madubi, dakyar tace "babu komai, ki duba wardrobe dina daga gefe ki mikomin wani magani a kwali"
Okay" Batul ta fadi hade da dauko mata maganin, mika mata tayi ta kofar data bude ta miko hannu ta amsa.
   Komawa gadon Batul tayi ta zauna ba tare data kawo komai aranta ba, "bari dai na leko yayana" ta fadi aranta, mikewa tayi ta nufa dakinsa hade da kwankwasawa, izini yayi mata ta shigo, zaune yake kan gado yana danna laptop din gabansa, jikinsa sanye da rigar bacci wando da riga mai kauri.
"Prince kunyi wayar da Baba ? Ta fadi hade da zama gefensa suna fuskartar juna.
Matsar da laptop din yayi gefe hade da dubanta, yace "kazamar, kowa na shirin bacci da sanya nitie, amma ke amtafa ce jikin ki"..
"Ina ruwanka toh, nidai gayamin koka kirasa"
"Layin Baba baya shiga"
Bata rai tayi, cikin turo baki tace
"Ni wlh na matsu nabar gidan nan"
Daga girasa yayi sama yace "kin daina sona huh ?
Dariya tayi
"Dama ai banasonka, yauwa kama tunamin, bani wayarka na kira saurayina"
"Mai shayin?
"Eh shi, kuma haka nake son abuna ehee" karasa maganar tayi cikin juya idanu.
Wayar ya mika mata, tuni ta rike numbar sa, sawa tayi hade da dailling, bugu daya ya dauka, nan suka fara hira  cikin raha da annashuwa.
Kallonta yake kaman yayi hauka tsabar tsananin kishinta dayake ji, saidai dole ya kama kan sa danta haramta gareshi, jan laptop dinsa yayi yacigaba da harkar gabansa.
    Mardiyya ce ta shigo dakin, jikinta sanye da nitie, ganin su zauna kan gadon yasata zauna gaban dressing mirror hade da dauka comb dake gurin tana tazar gashin kanta da batayi niyya ba.
      Gama wayar tayi ta ajiye gefe tana fadin "Nafiu akwai kirki, My prince yaushe zaka kaini Zaria naje gaida Mamansa"
Bata rai yayi, bai dago ba yace "ba rana".
"Kama isa" ta fadin hade kaimai mitsini a hannu.
Daure fuska yayi ya kalleta, "kika mitsini " karashe maganar yayi hade da kawar da laptop din gefe,
Murguda baki tayi
"Eh din, ko zaka dakeni ne"
"Ba duka ba zagi" ya fadi hade da janyota, jakwulkuli yahau yi mata tana dariya tana fadin "dan Allah ka bari, Sister Mardy kinga shiko"
Murmushi Mardy tayi tana kallon su ta mirror, inama ace ita yake ma wasa haka da taji dadi.
Dakyar Batul ta mike tana dariya, tana fadin "Allah kuwa gobe saina rama"
Saurin sa hannu yayi zai rikota tuni ta fice daga dakin tanai ma Mardiyya Good nyt.
    Dariya sosai yake, Mardiyya ta mike tahau gadon ta kwanta, "good nite" tace dashi.
"Nyt dear" ya fadi hade da tsayar da dariyan ya cigaba da danna dannan sa.
   Yaken dayafi kuka ciwo tayi, hade da jan bargo ta rufe jikinta, tunani take, bawai sex dinne ya dame taba, asalima bata da karfin tab'uka komai, i dont care habit dayake nuna mata ke mugun sanyaya mata jiki, farkon auran yanai kokarin kulata amma yanxu duk ya wani birkice mata.



***


Sosai ran Mom ya bacci da rashin kamota dasu Roze basuyi ba, masifa sosai take zazzaga masu sunai bata hakuri, katse wayan tayi tanai kai komo adakin, ta tabbata My boy dinta ne ya dauke ta a motar, Amma ina ya kaita, tambayar da tama kanta, har gidan Baba ta tura basa nan sun tafi kauye, dole tadau mataki kafin Baban ya dawo.
      Dabarar kirar Mardiyya ce ta fado mata, yarinyar tsokuwa ce, tasan tana iya gayamata ko suna tare da princess, wayar ta danna tahau dialling numbar ta.
     Kowa ya tashi banda Batul dake kwance tana bacci, karar wayar Mardiyya dake kusa da itane ta farkar da ita, daukar wayar tayi taga number ce ba suna, ajiye wayar tayi ta cigaba da baccin ta, kusan sau biyar wayar na ruri, cike da haushi tace bari tacewa mai kira bata kusa, dauka tayi hade da dasawa akuune.
"Hello, mai wayar bata kusa" ta fadi tanai hamma.
Daga can bangarean Mom tace "wake magana".
Zuciya daya batul tace "fatima ce kanwar mijinta, xan gayamata kun bugo"
Sosai Mom taji dadin haka, faduwa tazo daidai da zama, tace "Batul ce ?
Ware idanu Batul tayi sakamakon dago muryar mom da tayi.
Baki na rawa tace "itace" mugun tsoron Mom take.
"Yar banxa yarinya, ki bude kunnen ki dakyau ki saurari abunda xance"..
Cike da kidema Batul ta tashi zaune.
Mom tacigaba "naso rabaki da d'ana hakan bai yuyyba, dayake ke mayya ce koh ?
Girgiza kai kawai Batul tayi, tuni hawaye yafara wanke mata fuska.
"Na baki nan da kwana biyar kiyi convincing Rasheed ya daura miki aure dakoma waye, idan ma baki da mashishini xan turo mai gyaramin mota na ya kwashe ki"
Kuka sosai Batul ta fashe dashi, cikin rawar murya tace "Mom dan Allah kiyi hakuri, baxan iya aure yanxu ba"
Daga murya Mom tayi cikin kuluwa tace "wato kina jiran Ubanki ya dawo ya fada miki akwai aure tsakanin ku ko, to baki isa ba, aure kuma dole ya daure miki in 5 day if not, har can kauyen da ubanki da uwarki Ikilima suke zan tura amasu yanga rago, harma da kannanki hassan da Hussaini, Make sure kuma Rasheed karya san abunda na fadi maki" katse wayan Mom tayi..
Gabanta ne ya fadi tsoro, da firgici suka dabaibaye mata zuciya, cilli tayi da wayan ayayinda kukan ta ya tsanan ta yankan rago kadai take maimaitawa azuciyar ta, sai kuma inda Mom ke fadin akwai aure tsakanin su.
 shin dama akwai aure tsakanin su ? Amma miyasa Mom zata mai karyan Ubansa ubanane, kodai kanin baba ne Ubansa, duk azuciya take fadin hakan cikin tsananin gigita da tashin hankali.
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com


  *Wannan Shafin nakune TeamBatul, bukin budiri on point* 🤸‍♂🤸‍♂🤸‍♂
                 

                  74

Kuka take sosai cikin tsananin tashin hankalin da bata tab'a fuskanta arayuwarta ba. Turo kofar dakin yayi yana fadin, "Princess baza ki fito breakfast.." Makale wa kalaman sa sukayi a mak'o shinsa ba tare daya ida ba sakamakon ganin dayay mata.
    Sauri goge hawayan fuskanta ta hau yi amma tuni yagani, kasa daurewa tayi da boye damuwar ta karasawa gabansa tayi hade da fadawa jikinsa tanai kuka mai tsuma zuciya.
Cike da tashin hankali ya rike to suka zauna kan gadon,
"Princess mike damunki, waya tab'amin ke" ya fada yanai kokari dago da fuskarta dake boye cikin kirjinsa.
Kuka take tana tuna kashedin da Mom tayi mata, mudin idan tafadi ma Rasheed bazata barta lafiya ba, saurin tsayar da kuka tayi, ahankali ta dago da fuskarta suna fuskantar juna.
Baki na rawa tace "tsoro nake ji"
"Tsoron miye ? Ya fada yana kawar da gashin kanta dake neman tsone mata idanu.
Sabon kuka ta fashe dashi tana fadin,
"Mutanan nan su nake gani a mafarki zasu kamani"
Hannu yakai bayanta yana lallashin ta "Plz dont cry, its just a dream, babu wanda zai kamaki"
Kai kawai ta daga mai, lalashin ta sosai yahau yi saida yaga tabar kuka sannan ya lallabata ta shiga wanka, Parlour ya koma ya cigaba da cin breakfast dinsa akan dinning, tuni Mardiyya ta kammala cin nata abinci, zaune take kan kujerar apalo tana kallon Tv.
    Cikin bakar abaya Batul ta fito, bata karasa Dinning ba ta zauna kan kujera hade da gaida Mardiyya.
"princess baza ki ci abinci ba" Mardiyya ta fadi ganin bata da niyya tashi.
Yaken dole Batul tayi, aranta tana fadin ashe da ex kishiyata nake zaune ban sani ba, afili tace "zanci, xuwa anjima"
Kafin mardiyya takai ga bata amsa ya mike daga ina yake zaune yana fadin "Diyyah dauko min abincin ta" karaso yayi ya zauna kusa da Batul.
Abincin Mardiyya ta dauko a plate ta mikemai hade da mango juice cikin glass cup.
"Tnx dear" ya fadi hade da amsa.
     Kallon Batul yayi da tuni tafara yamutse fuska, diba yayi a spoon akai bakinta, dauke kai tayi alamun bazata ciba.
"Zan dauko Bulala fah "ya fadi hade da daure fuska.
Tsoron duka taji, ba shiri ta jiyo yanai feeding dinta tanai zuba mai shagwaba, dakyar tasamu ta iya cin rabi tace ta koshi, juice din yabata tasha sanna ta langwab'o jikinsa.
"Prince yaushe zamu je zaria" ta fadi kaman zatai kuka.
Cheeks dinta yadan ja cikin salon wasa yace "kin fiya son yawo, gobe if am less bizy sai muje"
Kare shigewa jikinsa tayi hade dayin Lamo batare data ce uffan ba, runtse idanu tayi tana sak'a da warwaran yadda zatai convincing dinsa.
      Shuru dayaji yasa ya dubi Mardiyya da gabadaya hankalinta na kan Tv, yace "Diyya dauko min Car key dina adaki"
Ba musu ta mike ta shiga dakin ta dauko.
Mikewa yayi ahankali hade da kwantar da Batul kan kujerar, amsa key din yayi yace da ita ya tafi office sannan ya fice.
   Plate dake gurin ta dauka ta nufi Kitchen ajiyewa, mikewa zaune Batul tayi hade da dafe kanta, duniyar gaban daya tai mata zafi ji take tamkar ta shige karkarshi kasa, jiki sanyaye ta mike tsaye ta fada dakinsa, wani irin sanyayyar kamshi da sanyi ne suka bigi hancinta, kwanciya tayi kan gadon cike da tausayin kanta.
     Fitowa Mardiyya tayi daga kitchen ganin Batul bata palon yasa tayi tunanin ko ta shiga dakinta, zuciya daya ta shiga dakinsa da niyya kwanciya ganin Batul kwance kan gado yasa tayi azama juyowa ba tare data karasa shiga ba, Dakinta ta nufa ta zauna kan gado hade da daukar wayarta, dialing nambar Hajiya Safara tayi, ringing daya, biyu ta dauka daga can bangaran.
"Hello, Umma ina Kwana" ta fadi cikin yanayin ba yabo ba fallasa.
"Lafiya lau Mardy, ya kuke, fatan dai shegia matar nan bata tsangwame kiba ? Acewar Hajiya Safara
Takaici ne ya kama Mardiyya tace "plz Umma ki bar fadin haka, kinsan dai maman mijina ce kuma she deserve some respect"
Tsaki Hajiya safara taja.
"Toh uwar son Miji, sai kiyi ai, ya jikin naki ?
"Da sauki, nasha magani"
"Idan kin shirya zuwa Asbiti kimin magana sai muje" acewar Umma.
"Toh Umma" Mardiyya ta fadi, hira kadan suka dan tab'a sannan ta katse.
     Ajiyar zuciya ta sauke tana xancen zuci, "am sorry Umma, wannan karan na sab'a maganar ki, kusan shekara daya ina zuwa asibiti ba tare da saninki" tunani tahau yi hawaye na d'isa bisa fuskarta.


Bai wuce office ba ya nufa gidan Mom, Shingide ya isketa bisa kujera apalo tana shan fruit, Altine na daga gefe tanai mata tausa, gaida ta yayi aladabce.
Bata amsa gaisuwa ba tace "ina fatan dai ka dawo ne da zama".
Murmushi yayi hade da zama, yace "Mom yanxu abunda kikayi kin kyauta"
Gabanta ne ya fadi, tayi yunkuri gyara Zama, atunaninta Batul ta fadi mai threat dinta.
Yacigaba "tunda kika tura thugs su kamota, ta fita hayyacinta da mugayan mafarkai"
Ware idanu tayi tanai mai masa kallon rashin fahimta, dukda ta gano inda xancensa ya dosa.
"Mom dont give me that look, nasan kinsan komai, kece kika turo kattin nan"
Daure fuska tayi tace
"Of course nina tura, nayi hakan ne danna baka ita as surprise, naga ka jima kana nemanta baka ganta ba, idan baka godemin ba ai bazaka zageni ba"
Nisawa yayi yace "thanks Mom, ai bansan you were trying to help me find her ba".
Murmushin dabai kai zuci ba Mom tayi tace "Never mind, nayi hakanne kawai amatsayin she is a daughter to me, kuma kanwarka ta jini, she deserve more from me"
Sosai Rasheed yaji dadi da kulawan Mom, godiya sosai yayi mata, sun jima suna hira daga bisa ya fice zuwa office.

Yunin ranar haka Batul ta kasance jiki sanyaye, bayan ya dawo ko hirar kirki batai dashi ba ta lallaba ta kwanta bayan sallar isha'i, tuni Bacci yayi awo gaba da ita.

***
Washe gari, Da fara'ar Batul ta tashi, karfe sha daya na rana ta shirya da temakon Mardiyya cikin atampa riga da skirt, farin ciki sosai take zataje Zaria gurin inlaws dinta.
     Palo ta fito ta iske shi kwance kan kujera, jikinsa sanye da gajerar wando da singlet, wayarsa rike a hannusa yana latsawa, babu alamun shirin zuwa Zaria tattare dashi.
Murtuke fuska tayi ta tsaya gabansa.
"Na shirya fah".
"Sannu da shiri" ya fadi yana cigaba da danna wayar ba tare daya dube taba.
Cize labban ta tayi, idan bata lallaba saba shareta xaiyi, gashi kuma kwana hudu ya rage mata, yazama dole taje ta lallaba Nafiu ya temaka ya aureta.
      Tsugunnawa tayi gabansa, hade da kashe murya tace "My prince dan Allah tashi muje" karashe maganar tayi hade da kai hannuta bisa soft hair din kansa tana shafarmai dasu baya.
Ajiye wayar yayi yana dubanta, ba karamin kyau tayi masa ba, murmushin dabaiyi niyya ba ta subuce masa.
"Plz" ta fadi cikin kasalalliyar Murya.
Bata rai yayi yace "nagaji bazan iya tashi ba"
Mikewa tayi da azama hade da riko hannusa dan ya mike tsaye, "plz yayana tashi muje" kaman zatayi kuka ta karashe maganar.
Mikewa yayi yana fadin
"Kin fiya naci"
"Eh din",ta fadi hade da jansa zuwa daki, toilet ta turasa tana fadin "yi wanka, bara na fiddo ma kayan da zaka sa"
Closet dinsa ta nufa ta fiddo mai kananu kaya jean da short sleeve tshirt, rikosu tayi tana shakar kamshin su, ajiyewa zatayi kan gado Mardiyya ta shigo rike da kaskon tiraran wuta.
"Na miye kayan nan" ta fadi tana kallon Batul, fuskar ta dauke da fara'ar.
Ida ajiye kayan tayi tana fadin "Kayan da prince zai sane, shine na fiddo mai"
Dariya Mardiyya tayi hade da ajiye kaskon, kayan ta dauka tana fadin "Sweetie bayasa irin kayan nan, by this time" karasawa tayi closet din hade da maida kayan ta ciro wasu traditional outfit marar nauyi, ajiyemai kayan tayi kan gado hade da kallon Batul da tuni jikinta yayi sanyi, tace
"Thanks sister inlaw, kije parlour ki jira shi, karki damu xanyi making sure bai bata maki lokaci ba"
Kai kadai Batul ta daga, bata iya cewa uffan ba ta fito palo ta zauna kaman zatayi kuka cike da tsananin kishin dake kokarin fasa mata zuciya.
     Kara gyara dakin Mardiyya tahau yi, fitowa yayi daure da towel yanai goge jiki, karasawa yayi inda yaga kayan a ajiye, Murmushi yayi, aranshi yana jin dadin yadda tasan taste dinsa,
    Duk akan Idon Mardiyya, tasan sarai ya dauka Batul ce ta fiddo mai kayan, batace komai ba, taci gaba da adjusting pilo acikin case dinsa.
      Shiryawa yayi tsaf cikin kayan, fita Palo xaiyi Mardiyya tayi saurin bin bayasan tana fadin "Sweetie kayi kyau sosai"..
Murmushi yake cikin jin dadi yace "Thank dear"
    Kallo daya tayi masu ta tashi tabar palo, ta fita gurin Motar ta tsaya, wani irin haushi take ji na ba gaira ba
 dalili.
Har bakin Motar Mardiyya ta rakosa tanai masu Allah ya kiyaye hanya.
Yaken dole Batul tayi tace "Sister Mardy saimun dawo" hade da fadawa cikin motar.
Amsata Mardiyya tayi fuskarta dauke da Murmushi, saida taga sunja sannan ta koma cikin gidan.

 Tuki yake cikin hankalta da kwarewa harya iso Zaria, babu mai magana da junansu, kallonta yayi yaga yadda ta daure fuska, kumatun duk sun kumburo, kiris ya rage ta fashe da kuka, Dariya sosai tabashi, dakewa yayi yace "Princess kinfi kyau when you smile"
Bata kallesa tace
"Babu ruwanka dani"
Dariyar daya kasa barin aransa yahau yi, yace "yayanki kike cewa babu ruwank dashi ?
Ya gama kuleta ba kadan ba, ita tana kokarin boye sonshi aranta, amma shi kallon kanwa ta jini yake mata, bata iya basa amsa ba tace "gidan inlaws dina zaka ajiye ni, daga kwanar gidan Inna sai tasu"
Daure fuska yayi
"Wato kinma san gidan har zuwa kike kenan ?
Kaman zatayi kuka ta dubesa tace "ban taba zuwa ba, Nafiu ya min kwatancen gidan"
       Baice uffan ba har suka shigo layin, da hannu tamai nuni da gidan, parking yayi kafin ya karasa gurin, kallon gini yake wanda kiris ya rage ya rushe tsabar tsufan sa.
     Maido da dubansa yayi gareta ganin bata da shirin sauka asalima k'asa idanuwanta ke kallo tana zubda hawaye.
"Miye kuma na kuka" ya fadi cikin rashin damuwa da yanayinta.
Kasa magana tayi banda kukan daya sarke ta, sosai takeyi harda shesheka, bai kuma cewa uffan ba banda kafeta da ido dayayi tanai kukan ta.
   Dakatar da kukan tayi tahau kokarin bude motar zata fita taji ya riko hannuta, wani irin yanayin taji ta shiga marar mitsaltuwa, juyo da fuskanta tayi suna duban juna cike da so da kauna.
    Handkerchief ya cusa mata a hannu yana fadin "ki sharar hawayanki, banaso inlaws dinki su ganki haka"
Janye hannuta tayi tace "thank you"
Yace "In 30 minute xan dawo daukar ki"
Bata iya basa amsa ba ta fice daga motan. Afusace yaja motar yabar gurin, bin kurar daya had"a tayi da kallo.
     Bakin kofar gidan ta tsaya hade da sallama cikin sanyayyar Murya, daga ciki aka amsa hade da mata iso.
      Wata dattijuwa tagani tsaye tana surfen gero a turmi, daga gefe kuma yar budurwa ke tankade da reraya.
    Risinawa tayi tana fadin "Ina wunin ku"
Dattijuwa mai suna Goggo tace "lapia yammata, dadddawa da kuka zaki siya?.
Kafin tayi magana yarinya mai suna Naja'atu tamike tsaye tana fadin "Goggo bara na leka waje ko budurwar Ya Nafiu ta iso" da azama ta rugu waje.
    Bata rai Goggo tayi ganin Batul bata da niyya magana, kuma da alamun yar masu kudi ce, ita kuma batason harka dasu dan bata daukan raini, balle ayadda suke marasa hannu da shuni.
"Lafiya kika tsayamin akan" Goggo ta fada cikin kakkausar murya.
Tuni Batul tasha jinin jikinta, tace "Fatima ce, Budurwar Nafiu"
Ware idanu Goggo tayi tana kallonta, fatima da take expecting iri iren suce ba wannan ba, Sallamar Nafiu ce ta katse mata hanzari.
Karasa shigowa yayi, fuskar sa dauke da fara'ar yana fadin "Fatima kin iso ashe, na fita siyo kankana ne"
Gaidasa tayi aladabce, tabarma yayi saurin shimfuda mata yace da ita ta zaune, zama tayi cikin dardar ganin har yanxu Goggo bata saki fuska ba, saima dauke kai da tayi tana cigaba da dakan ta.
    "Goggo ga Fatima fah ?
"Naganta" ta fadi atakaice
Baiji dadi da yadda ta ansa ba, tanason fatima yanxu data ganta kuma ta sauya yanayi.
     Hira yahau jan Batul dashi, amsa shi kawai take, jikinta asanyaye, tunanin yadda zatai aure agidan take ganin yadda Goggo ta daure mata fuska.
      kankanar Naja'atu ta wanko ta dire wa Batul, godiya tayi sosai, Naja ta mike zuwa aikinta suka cigaba da hirar su.




Gidan Inna Rasheed ya nufa, sun jima suna hira daga bisani ta shiga daki ta fiddo wata takarda
   Zama tayi tana fadin "tun ranar data bani takardar na karanta abunda ke cikinta ya sanyani matukar mamaki da abunda take fadimin"
Dariya Rasheed yayi yace "ranar bata cikin hayyacinta, kallo daya tama abunda ke rubuce ta dauke kai, banyi tsammanin ta karanta ba"
Warware takarda Inna tayi tana karanto abunda ke rubuce kamar haka "Ni Mamuda na bawa Matata wata d'aya ta koma gidan ta zauna har tayi hankali" dariya sosai Inna tayi tana karantawa, tace "tsabar kidima yasa wata dayan data gani yasa tayi tsammanin Saki daya kayi mata"
Yace "ban sake taba, saidai ayadda tayi tunanin na mata sakin naji dadin hakan, sosai hakan ya temakamin cikin plans dina"
Nisawa Inna tayi "yanxu ya zaka fadi mata akwai auranta akanka kuma kai ba yayanta bane"
Ajiyar zuciya ya sauke yace "datx d problem, bazata ji dadi ba idan tasan ba Baba ne mahaifinta ba, shiyasa nake lallaba ta as my sister har Baba ya dawo ya sanar da ita da bakinsa"
     "Ka kawo shawara mai kyau, saidai Mamanka fa, anya zata barta kuwa, kasan dai idan akwai abunda ta tsana bai wuce babanka da zuri'a saba"
Nisawa yayi yace "ayanxu dai bata san cewa nasan komai ba, dole na bitta ayadda ta dauke ni, dadin abun am one step ahead of her".
Jinjina kai Inna tayi tace "Mamanka tayi nisa Allah ya shirye ta"
"Amin" yafadi, mikamai takardar Inna tayi ta nufi gindin murhu tana iza huta.

Murmushi Rasheed yayi hade da shingidewa kan tabarmar dayake zaune, jinjina kai yayi yana mamaki halin Mom dinsa dana Batul two different womem from different world amma halin su daya, at first strategy din Batul yayi using har ya gyara mata zama ta shiryu, ga Mom dinsa data zauna tana fadi mai karya da gaskia, very cunning, haka take shiyasa shima yayi using style dinta ba tare data sani ba, baya Manta ranar data dawo daga Abuja, da dare ya sauko palon kasa sha coffee, yaji maganganu na fitowa daga dakinta, adan tsoroce ya karasa bakin kofar dakin da kusan rabinta bude yake, lekawa yayi yaganta tanai kai komo adakin tanai surutai kaman tab'ab'iya, kasa kunne yayi saidai bai dago inda xancenta ya dosa ba, kalamai kalilan yaji tana fadin "dole yarinyar tabar gidan nan tun kafin My boy yagano cousin dinsa ce" karaf yaji ta rufo kofar dakin da karfin gaske, barin gurin yayi batare daya dago inda xancen ta ya daso ba, washegari dayaga she was desperate ta kori Batul agidan ya sashi sensing akwai wata boyayye, begama gagasta xancenta ba saida yaga ta k'ala mata sata duk dan tabar gidan, baiyi niyyan duka Batul ba amma saboda Mom kawai ya dageta sanna ya bata chance din barin gidan.
     Ranar daya bata takardar nan duk part of his plan ne dan ta koma Gidan Inna da zama just to protect her from Mom, unfortunately she was confused tayi tunanin ko sakinta yayi.
     He wasn't stupid dazai barta ta kwana awannan gidan datx y turo Inna kwasan wasu takarce yasan definitely bazata zauna ba bin Inna zatayi.
Bayan ya koma gida ya fadi ma Mom Batul matarsa ce, yadda tayi overreacting yasa shi zuwa gurin Abban Mardiyya hade da rokonsa ya auri Mom dinsa akan ta rasa mashishini, dakyar ya amince mai, ranar daya zo kuwa yaji abunda ya dade yana son sanin daga bakinta.
     Saidai inda tace Batul kanwarsace ya gigita shi, bai zame ko ina ba sai gurin Baba Lamido dayake ganinsa tare da Baba, gurinsa yaji labarin Batul ba yar cikinsa bace.
    Tun ranar daya fadi ma Mom princess is missing ya lura akwai motar dake binsa duk inda ya nufa, shiyasa ya tsiro da aikin nemanta akullum tamkar baisan inda take ba, abunda bai saniba shine yadda Mom tagano Batul na Zaria saidai baiyi mamaki ba yasan hali mom, idan tasawa abu ido sai taga bayansa.

Abincin da Inna ta ajiyemai agaban sa ne ya dawo dashi daga tunanin daya lula,
"Inna harkin gama kenan".
Dariya tayi tace kusan awa daya fa baka hayyacinka.
Ware ido yayi, yace "nabar matata damai shayin"
Dariya Inna tayi, yahau cin abincin, sharp sharp yagama yay mata sallama hade da barin gidan.


Wajen gidan Batul da Naf'iu suka fito jiran dawowar sa, hira suke Nafiu na bata hakurin yanayin Goggo, "akwai ta da wadatar zuci, shiyasa akullum bata tunani  kai kanta inda Allah bai kaita ba, laifina take ganin akan ban samo daidai dani ba"
Kwantar da Murya Batul tayi tace "karka damu Nafiu, ka kwantarwa Goggo Hankali, nida kai duk daya muke, saidai wata alfarma nakeso kamin"
Kallon nutsuwa yabita dashi
Tace "Nafiu aure nakeso muyi nan da kwana hudu".
Gabansane yafadi, yasan dawuya Goggo da Baffan sa su yadda yayi aure in four dayx.
Tacigaba "Nafiu ka temakeni ka aureni, karka damu da shirin komai, adai dauran auran kawai"
Sosai yaji ba dadi, saidai bazai iya kin auranta ba dan yana sonta sosai, balle ga dama yasamu bazai so ta kufce mai ba.
Nisawa yayi "insha Allah Fatima karki damu, na amince xan aureki"
Dadi taji sosai aranta dukda wata gab'a a zuciyar ta nai mata radadi, "nagode sosai Nafiu, Goggo kuma nasan zata soni"
Farin ciki shima yake, hira kadan suka taba Rasheed ya iso daukan ta, ganin yadda take washewa Nafiu baki yasa shi daure fuska, gaidashi Nafiu yayi bai amsaba yaja motar afusace.

Murnan dayafi bakin ciki ciwo take a motar, dadin ta daya Mom bazata kashe mata iyayenta ba, kallon Rasheed tayi daya daure fuska.
"Yaya prince ka tayani murna, yau ina cikin farin cikin"
Bai tanka ba banda gudu dayake.
Cikin rashin damuwa da yanayun sa tace "nan da kwana Hudu zamuyi aure da Nafiu, kuma kaine zaka dauramin auran" .
Wani wawa burki yaja da saida kanta ya buge da glass din window.
Huci kadai yake batare daya kalle taba ya kuma tada motar.
Kallonsa tayi kaman zatayi kuka, ba lailai ne ya yadda ya daura mata aure ba, saidai bata da wani zabi daya wuce ta daure ta rokesa.
Shuru tayi bata kara magana ba har suka iso gida, fitowa yayi ba tare daya jirata ba, da sauri ta fito hade da riko hannusa, "plz yaya ka dauramin aure, nayi magana da Nafiu xai turo gobe ayi maganar"
Bai tanka taba har suka shigo palon tanai mai magiya.
     Mikewa Mardiyya tayi daga kujerar da take zaune tanai masu sannu da zuwa, bai iya tankawa ba banda tsayawa dayayi tsakiyar palon cikin tsananin baccin rai.
Hannun Mardiyya Batul ta riko tana fadin "Sister inlaw plz ki tayani rokonsa ya amince ya dauramin aure in four dayx"
Ware ido Mardiyya tayi cike da mamaki, saidai zuciyanta na fadin ta rokesa koba laifi zata huta da yadda Batul ke mannewa mijinta.
Kallon Rasheed tayi tace
"Sweetie if dax her wish, y not kayi mata granting, tunda tace aure takeso it better ka aurar ta b4 its too late"
Yaken da yafi kuka ciwo yayi, kusan minti biyar yadauka yana nazari sannan ya dubi Batul yace "na amince".
Ihun murna sosai tayi ta fada jikinsa,
   Ran Mardiyya ya sosu, sosai take jin kishin Batul aranta dukda ma kanwar sace, b'ata rai tayi zata wuce daki taji ya riko Hannuta
"Am so happy My prince" Batul ta fadi hade da janye jikinta, idanuwan tane suka sauka kan hannusa dake rike dana Mardiyya, sosai taji ba dadi saurin dauke fara'arta tayi hade da juyawa ta shige daki.
     Kallon Mardiyya yayi yana murmushi, "bazaki kawo wa Sweetie ruwa yasha ba"
Saurin sakin fuskarta tayi, cox she cnt afford to lose murmushin dayake mata, "right away my sweetie" ta fadi hade da janye hannuta, kitchen ta nufa da azama yanai bi dakin da Batul ta shiga da kallo.




   Am sorry Rasheed, this time around Mom is one step ahead of you.
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com
                 

                  75


kufcewa da kuka Batul tayi had'e da fad'awa kan gado, tunani barkatai ke yawo a kwakwalwar kanta, so take ta fad'imai akwai aure tsakanin su amma bazata iya ba, dole tayi sacrificing love dinta for her parent safety...
      Kusan mintinu talatin ta kwashe tana zubda hawaye, turo kofar dakin ne yasata azaman mikewa tsaye tamkar marar gaskia, hannuta takai bisa fuskarta tanai kokarin goge hawayan hade da kirkiro murmushin dole, karasa nufota yayi, fuskarsa dauke da fara'ar yace "Amarya da kanta take kuka"
Girgiza kai tayi tana ja da baya sakamakon matsowan dayayi daf da ita suna shakar numfashin juna.
Hannunsa yakai bisa hab'arta hade da tallafo fuskarta sunai duban juna.
"Miyasa kike son yin aure in four dayx"
Kawar dakai tayi tana fadin "ina son Nafiu, bazan iya rayuwa ba tare dashi.." Kasa karasa kalamanta tayi sakamako murde mata baki da yayi yana fadin
"Gayamin gaskia"
"Dagaske nake" ta fadi kaman zatayi kuka, hannu takai tana matsa bakinta daya murd'e.
     Kallon idanuwanta yayi tuni ya gano ba hakan bane band tsoro da fargaba dake kwance jikinsu, karanceta yayi tsaf ya gano akwai abunda take boyewa mai. Baice mata uffan ba ya juyawa ya fice daga dakin
       Dakinsa ya nufa yanai kai komo, azuci yake fadin it doesnt make sense tace tana son yin aure in just 4dayxx, tabbas akwai wata boyeyye akasa amma ya kasa figuring out, kodai Mom ke threatening dinta ? Sauri kawar da tambayan yayi, yana fadin it cnt be. Sosai kanshi yayi zafi dabarar kirar Nafiu yayi da tuni numbarsa na wayan, bugu daya Nafiu ya dauka, atunaninsa Batul ce yasashi   washe baki, jin muryar yayanta yasa shi nutsuwa hade da saurara kalaman da yake fadi akan yayi hakuri ya rabu da Batul matar aurece ita kanta batasan dakwai aure kanta ba.
   Jiki sanyaye Nafiu yahau basa hakuri akan bai taba sanin matan aure ceba kuma yayi akawarin bazai kara kiranta ba dan tuni Gogonsa ta taka mai birki tsakanin su.
       Sosai RmD yaji dadi da fahimtar sa, katse wayan yayi hade da hamdala, saidai yasan Batul bazata fasa nemo wani ya aure taba ayyadda yaga she is desperate taga tayi aure cikin kwanaki hudu, kaman wasa ya gwada trying Numbar Baba, yaji tayi ringing, farin ciki marar mitsaltuwa ce ta mamaye mai zuciya, sau kusan hudu yana ruri baa dagawa, ana biyar ne Baba dake aikace aikace agona ya adaga hade da sallama.
Gaisuwa sosai sukayi, nan take cikin girmama Rasheed yahau mai bayanin abunda ke faruwa in Brief.
Cikin nuna rashin damuwa Baba yace karya damu gobe zaibar abunda yake su dawo kaduna, maganar tafi karfin waya, sun jima suna tattaunawa daga bisani sukayi sallama.
Ajiyar zuciya ya sauke cike da mamakin rashin damuwa da Baba yayi, atunaninsa xai nuna farin ciki bayyanar dansa sai yaga sabanin hakan tamkar dama yasan shi amatsayin dansa.

***

Zaune suke su ukun a parlour, kowa wanne su da abunda yake tsakawa aranshi ba tare da sunce uffan ga junan suba.
      Mikewa Batul tayi daga ce nesa da take zaune dashi ta karaso inda yake hade da daukar wayarsa sa,   baice da ita uffan ba ta koma mazauninta hade da dialing no din Nafiu, akashe ta jita kusan sai goma tana trying.
    Guntun tsaki taja hade da dubansa da gabadaya hankalinsa na kan Tv.
"Yayana nambar Nafiu bata shiga, kuma munyi dashi zasu xo yau"
Bai kalleta ba yace "nasani ai, suna hanya"
Ware idanu tayi cike da murna tace "kunyi magana dashi ne"
Kallo daya yayi mata yadauke kai, aranshi yana fadin "she's really an actress".
Shurub da yayi bai tanka ba yasa ta tunanin ko dagaske suna hanya.
Murmushi Mardiyya tayi daga inda take zaune tana latsar wayarta, kallon Batul tayi tace "Sister inlaw yakamata muje shopping, afara shirye shiryen bukin".
Yatsine Fuska Batul tayi
"Sister Mardyy banason wani shiri, iya kaci ashafa fatiha ya mik'a ni, aurena na farko aka akamin balle kuma ma na biyu" karashe xancen tayi cikin zolaya.
Dariya ne yakusa kufce mai amma ya daje yace "Diyya ta kowa good idea, ki tashi sai kuje tare yin shopping din"
Fir Batul taki yadda, saida taga yayi mata jan ido sannan ta amince suka fita shopping din bayan ya baiwa Mardiyya credit card su siya abunda suke so, shopping din kayayyaki masu tsada sukayi da temakon Mardiyya, saidai ita ko zobe bata siyawa kanta ba haka suka dawo gida.


****
Matashin saurayi da Mom ta tura unguwar su Baba sa idon dawowar sune tsaye a farfajiyan gidanta yanai jiran fitowan, cikin takun isa ta nufosa, yan dubu dubu rike a hannuta.
Gaidata yayi bata amsa ba tace "ya ake ciki ?
"Sun iso jiya da daddare" ya fadi hade da risinawa.
"Ka tabbata".
Yace eh.
Kudin hannunta ta mike mai ya amsa hade da godiya, ya juya ya fishi.
Ciza labba tayi tanai neman mafita, batayi expecting dawowar suba tun kafin Batul tayi aure, kwafa tayi tana tunanin abunyi, dole nate gidan naci masu mutunci kafin My boy su rigata zuwa, muddin ya iske Baba akwai amatsala.
    Kwalla Altine kira tayi hade da fadin ta dauko mata mayafi da mukullin motar ta. Da azama altine ta dauko ta fito ta bata, saurin fadawa Mota Mom tayi taja tabar gidan..

Tun jiya da Batul taji shuru, babu alamun zuwan Nafiu da yan'uwa sa ya sanya ta tashin hankali, nambarsa da take trying abu daya yake fadi mata, switch off, iya kidima takai gabadaya ta rasa mafita kwana biyu kadai yarage a sharadun Mom, cikin sauri tagama shirinta cikin atampa zasu fita da Rmd, saidai batasan inda zasu ba fatan ta daya Allah yasa zaria zasu, cikin sauri ta fito palo, tuni yana waje cikin mota, sallama tama Mardiyya ta fito da azama ta shiga motar hade da sauke ajiyan zuciya.
"Miye haka" ya fadi yanai hararanta cikin sigar wasa.
Nisawa tayi tace "ba komai, muje plz, kar dare yayi"
Dariya yayi aranshi sai kace tasan inda zasu nufa.
Hanyar gidansu taga ya nufa, gabantane ya fadi, bata gama tsorata ba taga sun shigo unguwar..
Cike da kidema tace "ina zumuje, su Baba sun dawo ne ? Duk tare ta jeho mai maganar.
Cikin rashin damuwa da yanayin ta yace "tunda kinki fadimin dalilin sonyi aure ai dolen ki fadawa Baba..
Hannusa dake kan steering ta riko tana fadin "prince dan Allah karka kaini gurin Baba, kayi hakuri bayan nayi auran sai naje" karashe maganar tayi kaman zatayi kuka.
Murmushi yayi bai tanka taba, magiya da rokonsa tahau yi, bai kula taba har yayi parking gaban gida.
Bude bangaransa yayi ya fito hade da zagayawa gurinta ya bude motar.
"Fito'
Kin motsawa tayi banda bakin ta dake rokansa, janyota yayi ta fito ya rufe motar sannan yaja hannuta suka shiga cikin gidan.
     Cikin kamala da farin ciki baba da Hajjo suka tarbesu, tattauwa sosai sukayi game da abunda ke faruwa,  dakyar Batul ta fadi ma Baba yadda sukayi da Mom, sosai ran Baba ya baci, nan ya fayyace masu lailai ba siblings suke ba saida be fadi masu dalilin rabuwar sa da Mom ba dukda Rasheed yaso ace ya fadi, kukan dadi da bakin jiki Batul take, sosai tayi dana sanin rashin daa da take nunawa Iyayan musamma ma dataji baba ba mahaifinta bane, hakuri sosai da gafara ta rokesu.
     Su hassan ma baa barsu abaya ba sunji ddin kasancewa da yayansu da yayarsu, yunin ranar agidan suka wuni, duk aikin gidan kin bari tayi Hajjo tayi da kanta ta kammale komai.
      Zuwa yamma suka fara shirin komawa gida, karar dirar mota a gaban gidan yasa hankalinsu ya koma bakin kofar, garaf suka ji an rufe motar, karaso shigowa tayi cikin gidan cike da kyankyamin da kallon gidan a wulakance, ganin Family reunion dake faruwa tsakar gidan yasa ta jan dogon tsaki, kallon banxa tahau yiwa ko wannasu sannan tahau su zagi
Rikota Rasheed yayi yanai rokonta ta dena, fir taki denawa saima ashariya data dinga lailayo Baba da Hajji, basu iya tanka taba banda ido da suka xuba mata, inda sabo sun saba da halinta tun shekaran baya da suka shude.
    Tuni jikin Batul yadau rawa tsabar tsoro, nunota Mom tayi da yatsa tana fadin "ke kuma matsiyaciyyy..."
Wanke ta da Mari Baba yayi kafin takai ga karashe kalamanta.
Cikin tsananin bacin rai Baba yace "rashin mutuncin ki ya tsaya akanmu karki kuskura ki koma kan ya'yana"
Dafe Kuncinta tayi cike da mamakin marin dayay mata, a iya zaman da tayi dashi da irin cin mutunci da take mai be taba mayar mata da martani ba saiyau, yau din ma akan Angolan yarsa.
"Muje na rakaki Mota" Rasheed ya fadi hade da janyo ta suka fito waje, kasa magana tayi banda hannuta dake dafe kan kuncin ta.
Shiga motar tayi yace "mom ki bawa Baba hakuri ku dawo normal, har yanxu fah akwai auran sa akanki"
Bata iya cewa uffan ba taja Motar afusace tabar gurin ciken da tsananin baccin rai da bata taba fuskanta arayuwar taba.
    Dafe kai yayi aranshi yanai mata fatan shiriya, Gidan ya koma yabai wa Baba hakuri sannan sukayi sallama, dakyar dai Batul ta bisa, ba karamin tsorata tayi ba da yanayin Mom ba.

 Tuki yake jifa jifa yakan kalli yadda take takure, yasan hakan baida nasaba da Mom dinsa.
Murmushi yayi yace.
"Princess weds mai shayi"
Dariya da batai niyya yiba ne ya kufce mata
Tace "Nafiu nada kirki, amma fah prince ka raina min wayo ba kadan ba, wai dama baka sake niba ?
Dariya yayi hade da bude side box din motar ya ciro takardar yabata.
Budewa tayi ta karanta, dariya tayi tace "i was so stupid & tense, ka shammace ni kuma saina rama" ta fadi hade da kaimai duka cikin salon wasa.
Damko hannuta yayi tahau basa hakuri, wasa sosai sukayi tayi amotar har suka iso gida, nan ma shagwaba tayi ta zuba mai ita bazata shiga gidan ba saida yace Gidan Mom zai mai data sannan tayi azaman fitowa hade dabin bayansa da gudu, palo suka shiga suna dariya atare.
       Welcome Mardiyya tayi masu, fuskarta dauke da fara'ar tace
"Sweetie watx d good new, naga both of you are rejoicing"
Daki Batul ta gudu cike da kunya, hannu Mardiyya ya riko suka zauna kan kujera, murna kadai take tana jiran ya fadi farin cikinsa dan ta tayasa murna.
Murmusawa yayi hade da shafar fuskanta yace "you look gorgeous"
Thanks sweetie" ta fadi cikin kaguwa da yafadi mata.
Yace "the good news is nida princess ba siblings bane, dou na jima da sanin hakan".
Kallonsa take murmushi dake fuskar ta na raguwa.
Nan ya zayyane mata akwai aure tsakanin su, dama tun asali ba sakinta yayi ba.
Shuru tayi tana sauraran sa, tuni annurin fuskanta ya dauke, kiris ya rage ta fashe da kuka, daurewa tayi ta rungumesa tana fadin "am happy for you"
"Tnx Diyyah, tnx so much for your support, am always proud of you" yafadi hade matse ta jikinsan.
Kasa daurewa tayi hawayan dake makale ya zubo bisa kuncinta, gyaran Murya tayi hade da janye jikinta, bata bari yaga fuskar taba tace Sweetie bari na hada ma ruwa kayi freshen up" dakinsa ta nufa, ya shingide kan kujerar hade da lumshe idanu.
       Kunya duk ta ishi batul, kasa fitowa cin Abincin dare tayi saida taga sun kammala ba kowa a palo sanan ta fita taci, kwance yake yana jiran shigowar princess dinsa unfortunately Mardiyya ta shigo sanye da nities hade da kwanciya kan gadon batare data kalle saba
"Diyyah princess tayi bacci ne" ya fadi murya kasakasa.
Banxa tayi dashi tamkar bata ji saba, haka dai suka kwantar hade da bawa juna baya, ko wanne su da abunda yake sakawa aransa.


 ***
Da safe kitchen suka hadu su biyu suna aikin breakfast, ko wanan su fuska ba yabo ba fallasa, babu mai yiwa juna magana tun bayan gaisuwa da sukayi.
    Kammala komai sukayi suka jera a dinning sannan kowace tayi wanka tayi shirinta, dakinsa Mardiyya ta nufa ta iske har yayi shirinsa jikin suit.
"Sweetie breakfast is ready" ta fadi hade da kai hannu tanai gyaramai neck tie dinsa.
Cheeks dinta ya laguda hade da riko hannuta suka fito, dining suka nufa yaja mata kujera ta zauna, yace "someone is missing, ina zuwa"
Bai jira cewar taba ya nufi dakinta, kwalliya ya iske Batul tanai yi bakin mirror, da ganinsa tayi sauri labewa jikin labule.
Dariya yayi yace "yaushe princess tafara kunya prince dinta"
Kaman zatayi kuka tace "my prince dan Allah ka fita"
Karasowa yayi hade da janye labulan, tafin hannuta tasa ta rufe fuskarta
Sunkutar ta yayi kaman Baby, ihu take cikin salon shagwaba tanai rokonsa ya sauketa, bai kula taba suka fita, a Dining ya direta hade da ja mata kujera ta zauna.
    Dauke kai mardiyya tayi kamar bata gansu ba tahau serving kowa a plate.
  Fara ci sukayi, saidai rabin hankalinsu nakan juna, cike da nutsuwa Mardiyya kecin abincinta, kaiwa hannuta yayi daidai da kaiwa hannu Batul kan tumbler mai dauke da coconut juice, janye hannusu sukayi atare ba tare da kowannan su yadau ka ba.
   Murmushi Rmd yayi hade dakai hannusa kan Tumbler din, dauka yayi ya zuba acikin glass cup dake gaban Batul sanan ya ajiye.
"Thanks my prince" ta fadi cikin salon dani kaina bansanta dashi ba.
     Iya bacin rai da Kuluwa Mardiyya takai, wato shine bazai zuba mata ba, matsar da abincin tayi gefe hade da mikewa tsaye, barin gurun tayi ta koma dakinta, gado ta fada cikin matsananci kuka.

Cikin rashin damuwa da barin ta gurin suka cigaba da kallon love dinsu, kammalawa yayi yace "princess am off to work, kicewa Sister dinki na wuce" mikewa yayi cikin sauri dan tuni yayi latti.
    Mikewa tayi kaman zatayi kuka tace "my prince xaka tafi ka barni"
"Oh princess, plz dont cry" hugging dinta yayi yanai lallashinta, tare suka fita saida taka ya shiga motar yaja sanan ta dawo tsaftace kan dining din.


Yunin ranar Mardiyya daki ta wuni tanai kuka, koda Batul ta isketa hakan, karya kadai tayi tace kanta na ciwo, ganin ba mafita yasata fita haraban gidan ta zauna kan sit din zama dan shakatawa da shan iska.

Daga cikin office ya kira charles, da azama yazo hade da risina
Yace
"Akwai wasu document na oil export a office din  Mardiyya dauko min".
"Yes sir" charles ya fadi, harzai fita.
 Yace "dont worry, bara naje dakaina, it been long dana leka marketing department".
Mikewa yayi ya fice daga office din, direct building din ya nufa, maaikata da dama sai gaidasa suke, shiga office dinta yayi, komai tsaf tsaf, zama yayi kan swivel chair din yanai duba tumilin document dake gurin, dakyar yasamu yagani , mikewa yayi zai fita ya hango wasu takardu zube karkashin desk din.
   Guntun tsaki yaja aranshi yana fadin baya son carelessness, tsugunnawa yayi ya kwashi takardu hade dakai dubansa kan abinda ke rubuce, sunan Doctor Amjad yagani, gabansane ya fadi, dan kuwa yasan Doctor din, karasa karanta abunda ke cikin takardar yayi cike da tashin hankali.
    Ajiye Document din yayi ya fito rike da takardu, bai koma office ba ya shiga motarsa yaja.

Kallon flowers din dake shuke gurin take cike da sha'awa, ga wata sanyayyar iska dake bugar jikinta, ajiyar zuciya tayi hade da jingine kanta tanai lumshe idanu, agogon Hannunta ta duba taga tara na dare ta kusa, mikewa tayi hade dayin salati, ganin motarsa ta shigo gidan yasa tayi azaman komawa ta zauna, fasa shiga cikin gidan tayi dan basu space.
    Parking yayi ya fito daga motar, hangota da yayi can zaune yasa ya nufeta.
Ganin gurinta yake nufowa yasa ta mike tsaye tana kallon sa.
     Takardar Hannusa ya mika mata, ido jajir yace "Diyyah miyasa kika boyemin".
Cikin rashin damuwa ta amshi takardar ta duba sanan tace "miyasa xan gayama, awana dalili, you never cared about me, you always take me for granted, you never appreciate me" kuka sosai ne ya kufce mata.
    Hannuta ya riko, kaman xaiyi kuka yace "Diyyah you deserved some justice, duk laifin Hajiya safara ne, plz permit me to have her arrested, i promise to stand with you until justice is served"
Kuka sosai take tace "Abdulrasheed i dont care about any justice, the only justice i deserve is for you to love me, datx d only tin i want"
"Oh Diyyah stop it, banason Kuka, you know i love you alot" hugging dinta yayi yanai lallashinta.
Tace "i dont believe you"
"Of course i do"
Janye jikinta tayi tana kallonsa da itama kallanta yake tace "if you really love me, then prove it.."
Dafe kanshi yayi
  Rab'awa gefensa tayi zata wuce ya janyota ta fada jikin sa, lips dinsa yakai kan nata yafara aika mata sabon salon kisses da duk jinin jikinta saida yasan yau Rmd dinta is on duty.


Sanye take cikin pink transparent short nyt gown,  kayan alatu da kankana duk sun bayyana fresh dasu cikin nitie din, dakinsa take kwance akunya ce jiran shigowar sa bayan dirar motar sa dataji, jin shuru bai shigo ba yasa ta mike tsaye hade da yane labulan dakin ta leka waje, abunda tagani yasata saurin tsakin labulen cike da tashin hankali da kidema, wani irin passionate kiss taga suna aikawa juna, jikinta ne yahau rawa tuni tafara kuka, saurin bude dakin tayi ta fice ta koma dakinsu, sexy nyt gown din jikinta ta cire hade da maida wata nitie riga da wando, fadawa gadon tayi tana kuka aranta tanai tunanin Rmd baya sonta, kuka sosai take tana tuna last tym da yayi kissing dinta so Unromantic....
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com
                 

*Wannan shafin Naku ne Dija Waziri, Hafsat Rano, Ummi Khaleel, Mrx, tanx so Much for the love & Support, ILYSM* ❤❤❤❤❤
      *TeamDiyyah*

*Wawu*🤸‍♂
              


                76

Jin motsin za'a shigo d'akin yasa ta azaman dauk'e kukan da take tare da runtse ido, shigowa yayi batare daya kalleta ba ya karasa wardrobe inda Kayan Mardiyya suke ya ciro rigar bacinta sannan ya fice.
      Sabon kuka ta b'arke dashi bayan fitarsa, bargon dake guri ta janyo hade da rufe fuskarta cike da tausayinta kanta, so da kaunar sa kadai ke rura mata zuciya, ganin ba Mafita yasa ta d'aurawa zuciyanta dangana hade da gyaran kwanciya, daga bisani kuma bacci barawo yayi awon gaban da ita.
    Washe gari koda ta fito palo bata iske kowa ba, da alamun ma basu tashi bacci ba, sosai ranta ya sosu, kitchen ta nufa ta hada masu Breakfast sannan ta jera bisa Dinning, zama tayi palon jiran su, shiru ba alamun su har kusan sha daya, ganin yunwa na nema illatata yasa ta zuba nata taci, bayan ta kammala Tv ta kunna tana kallo amma rabin hankalinta na bakin Kofar.
     Bayan yan mintinu kalilan taji motsi tab'a kofar, saurin kawar dakai tayi gabanta na dukan uku uku, fitowa yayi hannusa rike da ipad yana dannanwa, jikinsa sanye da gajerar wando da armless riga, zama yayi ba tare daya lura da ita ba.
    Dubansa tayi, cikin murya kaman zatayi kuka tace "Morning my prince".
Bai dago ya kalleta ba, yace "Morning"
Tuni ta mike da niyya karasawa garesa, ganin yanayin daya amsa mata yasa jikinta sanyi, komawa tayi ta zauna hade da tagumi, shuru bai tanka taba balle ya kalle ta, ajiyar zuciya ta sauke tace
"My Prince baza kayi breakfast ba ?
Murmushi yayi, still bai dago fuskar saba yace "zanci mikomin nan?
Cike da jin dadin yadda ya murmusa ta mike da azama hade da zubo mai a plate sannan ta karasa garesa, zama tayi gefen shi tare da mikamai, amsa yayi yanaci rabin hankalinsa nakan ipad dinsa, kammalawa yayi tadau plate din takai kitchen sanan ta dawo ta zauna kusa dashi tare da daura kanta bisa kafadar shi.
"Prince kaina na ciwo" ta fadi adan shagwabe tanai kokarin shigewa jikinsa.
Guntun tsaki yaja hade da janye jikinsa, kallonta yayi fuska daure yace "miye haka, baki ganin am bixy with my office work ba, kadan ya rage hannunki bai gogemin abunda nake yiba"
Cikin rashin damuwa da yanayinsa ta kuma kai kanta jikinsa tana fadin "nacema kaina na ciwo"
Tureta yayi hade da mikewa afusace,
"I said stop it, idan kanki ke ciwo ga wanan" hannu yasa cikin aljihu hade da ciro dari biyar ya mika mata
"Ki fita waje akwai pharmacy saiki siya magani"
Sakin bakin tayi tanai kallonsa cike da mamakin abunda yake cewa, yaken dole tayi tamike tana fadin
"Allah ya baka hakuri" kujerar nesa dashi ta koma ta zauna ba tare data amshi kudin ba
  Cike da haushinta ya koma ya zauna, sunfi minti 20 babu mai tanka kowa, ajiye ipad din yayi kan kujera ya nufa dakinsa, da azama Batul ta mike ta karasa gurin hade da duba ipad din, puzzle game tagani da alamun kuma game din yake shine ya raina mata wayo da aikin office, kaman zatayi kuka ta koma mazauninta, tunanin iri iri tahau yi game da sauyin halayansa, ansa daya zuciyarta taba ta shine baya sonta.
    Hankali Kwance take baccin ta batare da wata damuwa ba, karasa shigowa dakin yayi hade da durkusawa saitin kunnanta, iska ya hura mata sannan yace
"Diyya wake up baccin nan ya isa haka"
Ko motsi batai ba banda baccin ta da take, zama yayi gefenta hade da dakai hannusa yanai shafar gashin kanta cikin tsananin so da kaunarta, kusan awa daya yayi zaune yana begenta sanan ta bude idonu, murmushi ta sarkar mai ya mayar mata martani.
   Temaka mata yayi ta mike tare da kaita Toilet tayi brush sanan ya rikota zuwa palo yanai mata mitan saitaci abinci kafin tayi wanka.
Murya shagwaba take fadin "Sweetie banda appetite, i cnt eat"
"You must eat" ya fadi yanai kokarin ja mata, zaunar da ita yayi hade da fara feeding dinta.
      Daskarewa Batul tayi a inda take zaune, hawaye ke ambaliya a fuskar ta ganin Mardiyya sanye da shirt dinsa a jikinta, abun daya yafi b'ata mata rai yadda suka nuna basu san da ita agurin ba sai wani mannewa juna suke, sosai take jin kishi azuciyar ta, baxata iya enduring ba ta mike ta shiga daki.
    Dakyar ya samu Mardiyya taci rabin abincin, mikewa tayi taji mugun tashin zuciya da azama ta rugu guest toilet dake palon tanai kwarara amai, cike da kidema ya nufota, saurin sa hannu tayi tanai dakatar dashi.
"Sweetie dont come close, it so disgusting" ta fadi cikin wahalalliyar murya.
  Bai kula taba ya karasa hade da temaka mata.
Dogon ajiyar zuciya ta sauke hade dakai hannuta kan fuskarta da take jin kaikayi.
"Sauro ko ? Ya fadi yanai kallon gurin.
Kai ta girgiza, riko ta yayi ya rakata dakinsa tayi wanka sannan ya dauko mata kayanta adaki tasanya, duk akan Ido Batul sai dai babu wanda yacewa juna uffan harya fice.

Yunin ranar dai yar Kallo Batul ta zama tsoro take tamai magana ya gwaleta, tanai jiyo dariyar su apalo cike da annushuwa, kasa jurewa tayi tadau pilo ta rufawa kunnuwanta.
     Da dare, wanka tayi ta sanya riga bacci riga da wando, zama tayi bakin mirrow tanai kallon kanta cike da tausayi, shigowa dakin Mardiyya tayi hade da Sallama, amsawa tayi fuska ba yabo ba fallasa, duk yadda take jin kishin Mardiyya bazata iya share taba sakamakon hallarci datai mata, alheri dankone bai zubewa kasa banza.
   Mikewa tayi tana fadin  "Sister Mardy kin shigo" karasawa gado tayi zata kwanta, Madiyya tayi saurin dakatar da ita da cewa "bacci nakeji, kwanciya xanyi, Sweetie na jiranki kije ki tayashi hira"
Galala Batul tayi tanai kallonta, aranta tace kingama dashi dole ki mikomin saura, afili tace "nima bacci nakeji" hannuta tasa tana kakabe gadon.
Dariya Mardiyya Tayi tace "you are joking, kinsan dai ba yadda zaai kishiyoyi su kwana guri daya, shi kuma mijin dawa xai kwana"
Takaici ne ya kama Batul danta lura sodai take taje gurun prince alhalin kuma ba damuwa yayi da ita ba, hamman karya ta kirkiro tana fadin "Sister y not ki kwana can, ni saina kwanta nan"
Harara takai mata cikin sigar wasa tace "naki wayon, yau kece da prince charming dinki, idan kinaso har gobe ma, jibi sai kiyi hand over".
Ganin dagaske Mardiyya take yasa ta amice zataje akan gobe bazata koma ba.
"As you wish" Mardiyya ta fadi tanai dariya.
   Jiki sanyaye tadau hijab tasaka, tsoron zuwa take karya korota, kallonta Mardiyya tayi hade da daga gira tace "princess kina bukatan escort"
Kunya Batul taji, tayi azaman bude kofar ta fita.

Ahankali ta bude kofar tashiga, zaune ta iske shi kan sofa yanai dannan lapton dinsa, bata iya cewa uffan ba ta karasa can karshe gadon hade da kwanciya ba tare data cire hijab dinta ba, sosai ta takure kanta guri guda idanuwanta na kansa tanai kallon kyakyawar fuskar shi, sosai take bukatar sa ajikinta saidai haka bazai yuyuba ayadda taklga fuskarsa tamau ko annuri babu.
     2 hours yayi yana danna dannansa daga bisani kuma ya mike ya kashe wuta, hawa gadon yayi ya kwanta can gefe da ita hade da bata baya, idanuwan ta kulle saidai ba bacci take ba, budesu tayi taga uban tazarar dake tsakanin su, babban takaicin ta shine yadda ya juya mata baya uwa baisan da halittar ta gurin ba, kukane ya kufce mata tayi saurin rufe bakinta da Hannu hade da juya mai baya, kuka sosai take ba kagauta, tunani take wace irin kiyayaya Rmd ke mata....
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com


  *Wannan Shafin naku ne Miss xoxo, Aunty Maijidda, Sady Jegal, Mom Fatu, Dota Waliyya,  khadija Tsafe, Baby Nurse, Bady Social Sophie, Ummu A'sad, Momikky, Bilikisu Baraya, thanks so much for the love & Support, Princess na tare daku*
                 *ILYSM*❤❤

  *TeamBatul🤸‍♂*
                 

                  77

 Bata runtsa ba har asubah, tanai jinsa ya tashi ya shiga toilet, alwala ya dauro ya fito ya fice masallaci bayan ya zurawa jikinsa dogowar jallabiya, ajiyar zuciya ta sauke mai dauke da shesheka, wani irin azababban ciwon kai ke damunta, dakyar ta iya mikewa ta shiha bayi alwala sannan ta fito tayi sallah, jirin sosai ke dibanta, adaddafe ta iya karasawa gadon ta kwanta, bacci barawo ya saceta.
     Saida gari yayi haske Rmd ya dawo gida, zama yayi parlour hade da Kunna Tv. Wayarsace tayi ruri, dubawa yayi yaga Mom ce da azama ya dauka hade da gaidata aladabce, sun jima suna magana daga bisani yace mata karta damu zaizo gidanta suyi magana, sallama yayi mata sannan ya katse.
     Zaman awa kusan hudu yayi gurin babu alamun tashin daya daga cikin su, mikewa yayi ya nufa Dakin Mardiyya, zaune ya iske tanai kokarin sakalawa kunnanta dankune, jikinta sanye da English wears na riga da skirt, gaisawa sukayi cikin so da kauna juna sanya suka fito palo, earring din ya amsa ya sakala mata.
Tace "Sweetie am so sorry, ban hada maku breakfast ba" mikewa tayi zata nufi kitchen yayi saurin rikota hade da zaunar da ita.
Murmushi tayi sunai fuskantar juna yace "don't worry, princess xatayi, kinsan i cnt allow you stay away from me"
Murmushi tayi bata ce uffan ba, mikewa yayi ya shiga dakinsa, guntun tsaki yaja ganin yadda take sharar bacci tamkar matacciya, pillow ya dauka hade da wurga mata.
   Atsorace ta farka hade da zuburewa zaune tanai sosa idanu.
Daure fuska yayi yace "tashi kije ki hada mana breakfast"
Dauke kai tayi gefe tace "banice da girki ba Sister Mardy ce".
Kollan mamaki ya bita dashi, if he could remember tunda taxo gidan Diyya ke kirki, jiya kadai ne yaga ta taimaka mata.
"Daga yau kice in charge of kitchen ko ba ranar girkin kiba, Understand ?
Bata iya bashi amsa ba, ficewa yayi ya koma palon.
    K'wafa tayi, aranta tanai fadin ta daina kuka daga yau, ko miye xai mata she is ready for him, mikewa tayi ta fice daga dakin, kwance taga Mardiyya yanai mata tausa suna dariya cikin anushuwa, kallo daya tai masu ta dauke kai, daki ta shiga tayo wanka sharp sharp sannan ta nufi kitchen hada breakfast, bayan ta gama nasu ta kai kan dinning, tayi respecting kanta ta zauna a kitchen taci nata.



 ***

Gidan Mom ya nufa, magiya sosai take mai akan ya tayata baiwa Baba Hakuri da neman gafararsa, tayi nadama ba kadan ba, duk cikin kuka take fadi mai hakan.
Kallon ta da sauraranta yake saudai bai yadda da sudden repentance dinta ba.
Yace "Mom koda ace Baba ya yafe miki, hukuncin Ubangiji na jiranki, you left your marriage for years ba tare da wata hujja ba, kinsan hakki aure ba wasa bane shi Vaba da kika raina aljannar ki na karkashin tafin kafarsa, all those years miyasa baki saduda"
Kuka sosai ta fashe  "my boy nasan na tafka babbban kuskure plz help me talk to him"
Nisawa yayi yace.
"I cnt, if you really seek his forgiveness, its better you talk to him, besides ni ba sanin abunda ya hadaku nayi ba, keda kika sani i tink should try clean your dirt"
Hannusa ta riko tace "it all my fault, if you can't talk to him, allow me ta talk to his daughter"
"Oh Mom stop it, plz dont involved princess a problems dinki"
Girgiza kai tayi tace "okay, i'll talk to him, but not now nafison saiya huce, nasan he is very angry with me"
Murmushi yayi, dama abunda yakeson tagane kenan, sun jima suna hira daga bisani kuma yabar gidan.



Life goes On, zamantakewar gidan bai canxa ba, tuni Batul tayi catching head one side, tsakanin ta da Rmd sai gaisuwa, ranar kwananta adakin sa ba abunda ya canxa, kowa zaman you're on your own suke ma juna su, ba abunda yafi kona mata zuciya kaman yadda yake zuwa dauka Mardiyya ranar girkinta, dakan shi zai shigo dakin daukaera tamkar wata sabuwar amarya, tayi ta zuba mai shagwaba yanai biyeta.
     Saidai zamansu da Mardiyya ba yabo ba fallasa, sosai take girmamata da darajata, ko da wasa bata taba mata kallon baccin rai ko haushin abunda takeyi ba, iya kaci ta bita da murmushin dayafi kuka ciwo.
    Sati Biyu kenan zani bai canxa dauri ba, jira kadai Batul take taga ranar dazai waiwaye ta, ta nunamai ita ba kanwar lasa bace.
  Bangaran Mom kuwa ta kasa samun courage din zuwa gurin Baba, kullum cikin saka da warwara take.

***

Kamar Kullum shigowa dakinsu yayi, sanye yake da nite gown riga da wando.
Zaune ya iske Mardiyya gaban dressing mirrow Batul tanai mata oiling gashin kanta, ganinsa yasa tayi azaman ajiye comb dake hannuta, juyawa tayi ta shiga Toilet kafin su daura mata hawan jini.
     Bayan Mardiyya ya karaso yanai shafar gashin kanta hade da kallonta ta mirrow.
"Alway late, yauma saida kika bari nazo daukan ki ko?
Ya fadi yanai murmusa.
Kallon mamaki tamai daga cikin mirro tace "Sweetie where are we going by these time".
"My room" ya fadi murya kasa kasa.
Juyowa tayi tanai kallonsa sannan tace "let sleep here"
Dariya yayi yace
"Idan muka kwana nan, wacen yarinyar fa, ina zata kwana"
Ware idanu Mardiyya tayi tace "na manta shataf, ashe Altine ke kwana anan"
Kallonta yayi aranshi yana tausayinta, she is totally confused, dagota yayi hade da rikota suka fita daga dakin tanai fadin "Altine nada kirki sosai, dazu har ruwa taban nasha"
"Eh hakane" ya fadi, karasa shiga dakinsa sukayi ya rufo kofar.
       Fitowa Batul tayi daga toilet cike da mamakin maganganu Mardiyya data jiyo, "kodai Sister Mardy bata da lapia ne" ta fadin aranta, kwana biyun nan ta lura kaman akwai abunda ke damunta saidai ta kasa  ganowa, zama tayi kan gado hade da sauke ajiyar zuciya, fayus take jin zuciyanta, wani haushi da kishin Mardiyya duk sai taji babu shi aranta, hannu ta daga tanai godewa Allah daya cireta mata kishinta, Mardiyya is too good ace ta sanyata a zuciya, addua sosai Batul tahau yi akan Allah ya basu zaman lafiya.

Kan sofan dakin ya zaunar da ita sunai fuskanta juna, shuru sukai nadan sakwanni sannan tace
"Sweetie inaso muje muga Doctor Amjad Gobe"
Ajiyar zuciya ya sauke ganin she is back to her senses, yace "Diyyah karki damu, mutuwa ta Allah ce bata Doctor ba, just because yace tun last week yakamata ki shiga final stage dinki that doesn't mean you will die, gashi mun shigo second week you are still kicking, plz don't loose hope"
Murmushi tayi hade da kwanto wa jikinsa, cikin sanyin murya tace "Sweetie"
Murya kasa kasa yace "You should be laying down"
Tace "no, it better we sit and be staring at each other"
Tausayin tane ya cika mai zuciya, yace " i was wrong to deny you the satisfaction of love"
 Nisawa tayi tace " i know I'm supposed to be cruel or vicious but i cnt because my heart is full of your love, Am I angry at what you did to me? Yeah,
and I've been living in agony for what you did, marrying princess without telling me, it really hurt"
Hawaye ne ya zubomai yayi saurin sharewa, matse ta yayi jikinsa yace "Am sorry"
Tace "Apology accepted, I wish i knew you were such a romantic guy, I would have played so hard to get you 10 years back"
"Let not speak of regret, the past isnt a story to tell"
Murmushi tayi, tanai kokari  sauke numfashin ta dake kokarin dauke wa, cikin wahalalliyar murya tace "you showed me your whole life, and i understood it, i know that princess will alway be around to stand by you"
Yace "Why you telling me this"
Lumshe idanu tayi tace "because I won't be
Around any more to tell you"
 Kuka ne ya kufce mai, yayi sauri dauke kai
Hannu takai fuskar sa
Tana fadin  " Hey, hey. Look at me. It's going to be okay, i don't like it when you cry" juyo da fuskar sa tayi suna fuskan ta juna.
     Saurin janye jikinta tayi sakamakon mugun tari daya tsarke ta, cike da kidema yahau yi mata sannu, amai ne yazo mata tayi saurin rugawa toilet, binta yayi yanai mata sannu, wani irin bakin aman jini take kwararawa cike da tsananin tashin hankali, ruwa ya diba hade da gyara mata jiki sanna suka fito, zaunar da ita yayi kan sofa hade da dauko mata maganinta dake side drawer, balla yayi hade da daukan bottle water dake gurin.
"Diyya plz take it".
Kawar da fuska tayi
Ya kuma fadin "plz Diyya ki sha, it will ease the pain & dull the symptoms"
Dakyar ta yadda ta sha, zama yayi kusa da ita, ta kwanto kanta bisa cinyar sa hade da kwanciya tanai numfashi dakyar.
     Hannu yakai yana shafar fuskarta har bacci ya dauke ta, shingide kansa yayi jikin gadon hade da runtse idanu.
      Bayan some mintuna bacci ya kwashe sa, kirar sallah asuba ne ya farkar dashi, jin alamun kaman tanai magana yasa yace "Diyyah kin tashi".
Bata iya tanka saba, ta gyara kwanciyar ta, mikewa yayi ya shiga alwala sanana ya fice masallaci, bai jima ba yadawo, kusa gareta ya karasa hade da kwanciya,  shuru yaji ba alamun numfashi tattare da ita, mikewa yayi azabure yanai kiran sunanta.
       Tab'ata yayi yaji alamun babu rai tattare da ita (Kulli nafsin za'ikatul mauti) mikewa yayi cike da kidima bakinsa na furta salati, kasa komai yayi banda hawaye da yake zubdawa, zani yadau ya rufe mata sannan yadau wayarsa ya kira Numbar Hajiya Safara..
    Carbi take ja taji rurin wayarsa, ganin lambar sace yasata faduwan gaba dauka tayi .
Yace "cox of your unknow selfish motive, your daughter is dead, believe me kuma Justice must me serve....." Katse wayar yayi.
   Tuni Hajiya safara ta kwalla ihu hade da cilli da wayar, Abba mardiyya dake shigowa dakin ne yahau tambayar ta lafiya.
Kuka take tana fadin "Mardiyya ta rasu...
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

 xarahbukar.wordpress.com
                 
    *This whole Book is Dedicated to My one & only Cutest Miss Xoxo*
                 

*Last Page*

       _Allahumma Innaka Afuwwan Tuhibbul-afwa Fa"afuana_


           78 - 80




Ba k'aramin girgiza Alhaji Bello yayi ba, cikin tsananin tashin hankali yake tambayar ba'isin mutuwarta, a iya saninsa kalau diyarsa take, farat daya baza'a cemai ta mutu ba.
    Kwantar masa da hankali Hajiya Safara tahau yi tanai karar tunasar dashi Ajali idan yayi kira dole aje koda ciwo ko babu, addua kadai ya daje da mamaci ba kururuwa da neman kauce hanya ba.
   Sosai jikinsa yayi sanyi dangana ya sanyawa zuciyar sa.
Ba tare da bata lokaci ba jamaa har sun hallara, sutura da jana'izar ta akayi sannan aka mik'a ta makwancin sa, (kulli nafsin za'ikatul maut, Allah yaji kan musulmai). Jama'a da dama na nesa da kusa duk sunzo ta'aziya da ban hakuri, kowa yaban ta yake sanin ta macen k'warai.
      Bangaran Batul kuwa tafi kowa girgiza da mutuwar sister dinta, tsabar tsoro da firgici kasa zama tayi agidan, tuni ta koma gidansu cikin tsananin tashin hankali, dakyar Baba ya barta ta zauna bayan ya kira Rmd ya sheida mata zuwanta.

Takardu masu dinbin waya Hajiyar Safara ta fiddo daga tsohuwar ma'ajiya, kitchen ta nufa ta baiwa biebee taje bayan gida ta konasu, bata konasu ba tahau karanta abunda ke ciki, fasa konawa tayi ta ajiye su, ganin Alhaji Bello zai fita tayi azama kaimai takardu, karba yayi yahau karanche su cike da tashin hankali, wayar sa ya fiddo ya kira Rmd, sun jima sunai magana daga bisani suka ijiye inda zasu hadu.

Gidan Baba ya nufe ya dauki Batul da tuni tagama Sadudu da rayuwar duniyar, mutuwar mardiyya ba karamin kara mata tsoron Allah yayi azuciyan taba, taso rama Abunda Rmd yay mata saidai bazata iya ba, sai yanxu ma tagano duk abunda yayi hakan ne kadai zaisa mu daman kasancewa da Mardiyya, inda ace bai kula Mardiyya yaba harta mutu, ita kanta she wont forgive herself, guilty conscious kadai ya isheta, tana son Rmd, dole ta tallafe sa balle ma yanxu da yake cikin kunci da tashin hankali.
   
Tuki yake amma daka ganshi kasan yana cike da damuwa, sosai Batul take tausayinsa, ganin hanyar gidan Mom suka nufa yasata tsorota, rokonsa tahauyi karya kaita gidan, parking yayi yahau bata baki da kwantar mata da hankali, dakyar dai ta hakura bayan ya shaida mata Mom dinsa ta shiryu, koda suka isa gidan faram faram Mom ta amshe su, ganin Batul taki sakin jiki yasata ta neman gafarar ta, sai sannan Batul ta iya sakin jiki, Mom sai lailaya ta take tamkar kwai.

Da yamma Rmd ya shirya suka hadu da Alhaji Bello awani Guest in, takardun Ya mika mai hade da tambayarsa ko yasan da faruwar makamanci haka..
Gigirza kai Rmd yayi cike da kidema ganin takardar mai dauke da shedar siyar da kidney din Mardiyya shekaru ashirin da suka wuce, numfasawa yayi yace  "Alhaji yaushe akayi hakan, kuma miye hujjar ku na siyar da kidney dinta a black market"
Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke yace "ni kaina bansan da faruwar hakan ba, signature dai ya nuna Hajiya safara ta siyar da kidney dinta batare da sani naba, shiyasa nazo tambayar ka ko kasan wani abu game da hakan ?
Sosai ran Rmd ya baci, yace "banda masaniyan akan komai sai kwanakin baya dana ga takardun treatment dinta, direct gurin Doctor Ajmad na nufa, nan yake fada min Mardiyya nada chronic kidney disease (renal failure) due to improper treatment, the only kidney da take dashi bata taba zuwa ayi mata haemodialysis ba (dialysis to remove waste product from the blood), by the tym da tayi realizing it was too late, left untreated for so long yayi causing mutuwar ta"
Jinjina kai Alhaji yayi kaman yayi kuka yace "bata taba gayamin ba, am sure kuma Safara tasa komai"
"Tabbas tasan komai, cox Mardiyya tafadi min tare suke zuwa asbiti duk wani test result dinta karba take bata bari koda wasa Mardiyya tagani, ciwon yay mata tsananin yasa ta koma ganin Doctor amjad secretly"
"Amma kai hw coms bakasan bata da lapia ba, baka gani weird symptom game da ita" acewar Alhaji Bello.
"Ina gani, saidai symptoms din are not specific to renal failure, they can occur in other disease, kaman ni at first nadauka she was pregnant, amma dana lura da she is always confused yasa nafara tunanin ko tana da mental dis order"
Nisawa Alhaji yayi yace "dole naje Ghana gobe na bincike komai, i just cant belive Safara ta siyar da kidney din only dauta dita, for wat reason, anawa ta siyar, abunda kadai nakeson sani"
Sun jima suna magana, daga bisani Rmd ya yanke shawara suje Ghanan tare, kasancewar sunan wanda ya siyi kidney din na jikin takardar.
     Washegari kuwa hakan akayi, suka dira a ghana batare da wata wahala ba suka samu gidan hamshakin mai kudi Alhaji Tafida charno, tarba mai kyau yayi masu, nan suka fadi mai abunda ke tafe dasu, sosai yayi mamaki dan kuwa ya jima yana neman Hajiya Safara, tun ranar daya biyata 25 million tayi donating ma yarsa Kidney din mardiyya bai kara ganinta ba, asalima tun kafin agamawa Mardiyya treatment ta dauke ta suka gudu, bai kuma jin labarin taba, nan ya kwashe komai ya fadi masu,
  Kuka sosai alhaji da rmd keyi cike da tausayi, haka suka dawo nigeria, cike da baccin rai Alhaji bello ya saki Hajiya safara bayan ya hadata da hukuma, nan take kuma ya yanke hukuncin auren yar aikinta Biebee dee.

Kuka sosai Mom tayi da taji labarin abunda ya faru, sai yanxu ta tabbatar Safara makira ce ta karshe da tsananin son abun duniya, nan tahau bawa Rmd labarin ta da Baba. Tun asali ba sonshi take ba Babanta ya hadasu aure sakamakon yadda ta rena mutune da kin sanin darajan dan adam shiyasa babanta ya aura mata shi ko zatai hankali, rashin mutumci iri iri tayi ta shukamai bai taba damuwa har ta haifi rasheed, yana shekaru biyar a duniya babanta ya rasu yabarwa Baba rabin dukiyar sa sauran kuma yabaiwa kawu Habibu, kadan daya rage Babanta ya bata duk dan ta iya zaman duniya tasan kuma ba kudi ne komai ba, rana d'aya Hajiya Safara tazo ta zugeta tsaf akan lailai karta yadda, alokacin kuwa Bataji maganan kowa saita hajiya Safara, ba kunya ta amshe dukiyar daga hannu Baba sannan ta rubu dashi ta komo zaman kaduna duk dan abun duniya..
     
Kuka sosai Mom tayi, haka suka shirya duk sun ukun sukazo tayata baiwa Baba hakuri, cikin rashin damuwa ya nuna shi daman bai taba riketa azuciya ba, kuma dama yayi alkawarin sakinta duk ranar data sududa, nan take ya rubuta mata saki daya, kuka sosai tayi cikin rashin dadin abunda yayi, batai kasa a gwiwa ba, ta kwaso duka takardun dukiyar Babanta ta bashi tunda dama nashine, fir yaki karba, ya godewa Allah daya bashi rufin asirin saida kayan miya.
   Bai karba ba ganin ta nace yasa ya karba ya mikawa Rmd hade da cemai ya basa kyauta halak malak, kin karba yayi saida yaga lailai ran Baba ya baci sanan ya amsa.


Life Goes on, kwanaki, watanni sun ja harma da shekaru.....

Mom an sadudu kullum cikin neman gafarar Ubangiji, da rokonsa Baba ya maida ta dakin ta.
   Baba kam kasuwa ta bunkasa, shago babba ya bude na siyar da buhun kayan miya, koda wasa arzikin dansa bai tsone mai idano ba, kokari kadai yake ya samu na kanshi, dukda Rmd yaso yabar sanar fir yaki bari.
      Rmd da Batul soyayya sai wanda ya karu, tuni suka koma zaman Abuj, zama cikin tsananin kwanciyar hankali da so da kaunar juna. tsaya fadin soyayyar su  bata lokacine (Ramadan by the corner), zama mai dadi suke har Allah yasa ta samu ciki ta haifi yarta kyakyawa, taci sunan Mardiyya, sunai kiranta da BabynDiyyah.





       *Alhamdulilah*
Godiya ta tabbata ga Allah daya bani ikon kammala littafin nan, kura kuran dake ciki Allah ya yafe mata.


      Gaisuwa musammam ga yayar Mu *Aunty Maijidda Musa*Allah yasa ki gama da duniya lafiya.


 My Die hard Fan *Hafsat Sani Maihula* Allah ya barmu tare.

     *Na Sadaukar da Littafin nan ga Kawata, Diyata, Yar'uwata Nana Hafsat Xoxo, Allah ya barmu tare, You are such a Darling, ILYSM❤❤❤❤*


My people i no forget Una...
    Baby Nurse & her crew....🤸‍♂🤸‍♂🤸‍♂🤸‍♂🤸‍♂🤸‍♂

   *Happy Sallah In Advance to all my fan*😍😍😍


Download Ina Zan Ganshi Littafi Na Daya Complete HausaNovel