TATTALIN SO 1**1
KANAL ALIYU Gwarzo jarumin soja
kenan, Alh yahuza shine mahaifinsa,
matansa biyu da 'ya'ya biyar. Hajiya
habiba itace uwar gida, da 'ya'yanta uku.
Aliyu shine babba, sai sani da sadiya, sai hajiya
talatu me 'ya'ya biyu, ni'ima da
hamza.
Dukkaninsu kansu a hade yake, da yake
sun samu tarbiya sam babu irin 'yan
ubancin nan bare nuna bambamci a
junansu. Alh safiyanu kanin alh yahuza ne,
uwarsu
daya ubansu daya, matarsa daya hajiya
saude, da 'ya'yan su uku, maza biyu faruk
da sadiq, sai karamarsu mace mai suna
zainab.
Babban gida ne kowane da bangarensa, gaba
dayansu akwai kyakyawar
dangantaka da son juna a tsakaninsu.
Mahaifiyarsu hajiya Babba, itama a gidan
take bagarenta daban.
Dattijuwar arziki ce mai addini da ibada,
gata da kokarin zumunci, du inda taji dan uwanta
wanda ko kaka dangantaka ta
hada su, saita jawo shi jikinta yaci
arzikinta dana 'ya'yanta. Hajiya kyaftin
kenan dattijuwar arziki, ko yaushe
jikokinta suna tare da ita tana hada
kawunansu, tana yi musu nasihohi da tattausar
murya, ta rinka yi musu tarihin
annabawa da abubuwan data san zasu
karu dasu, su kara samun fahimta koda a
makaranta ne.
Idan lokacin sallah yayi takan hada
samarin gidan su tafi masallacin gidan, ita kuma
da 'yan matan subi masallacin
daga gida.
ZAINAB itace karama a gidan, a lokacin
tana 'yar shekara shidda. Zainab yarinya
ce mai wayo da basira, ga dabara,
yarinya ce ma shiga rai, du wanda ya zauna da
ita sai yaji yarinyar ta shige
masa rai lokaci daya.
Gaba daya 'ya'yan gidan su takwas suna
gida banda yaya Aliyu, dashi yana
kaduna gidanshi, don ya gama
karatunshi tuni ya zama soja yana zaune a
gidanshi na kaduna.
Bayan sallar ishsha, hajiya kyaftin da
sadiya me shekara goma sha takwas, da
ni'ima mai shekara goma sha uku, sai
zainab 'yar shekara bakwai, suna idar da
sallar sukayi addu'a suka shafa. Zainab ta mike
ta duba fulas din abinci,
tasa babban faranti ta zuba musu
shinkafa da miyar kaji. Ta bude firij ta
debo musu lemukan kwalba guda hudu,
da pure water guda hudu, da coca-cola
guda hudu. Tace hajiya ga abinci idan mun cinye
saimu kara."
ni'ima tace ki kyalemu dai masu cin abinci
idan mun cinye idan mun cinye ma kara
amma banda ke me cakula ki dauke
hannu, da dai kayan zaki ne.
Zainab ta tabe baki, kin ganta ko aunty sadiya?
Sadiya tace, "ni'ima wai meyasa kike son
tsokanar zainab ne, kinsan ita kadan take
jira taki cin abincin ma."
sai anan hajiya tayi magana, tace, "haba
ita ta fara, aida na danneta nayi mata dura. Kuzo
muci abinci kada ya huce."
gaba daya sukayi bisimillah suka fara ci.
Yaya Aliyu ne ya tako cikin kasaita da isa,
yayi sallama ya shigo dakin, gaba daya
suka mike da murnan cewa, "ga yaya, ga
yaya. Hajiya ta rinka tafa hannu cikin murna
tana dariya, tace "babban mai gida yau
kuma saukar dare akayi mana?
Yace wallahi hajiya motarce ta bani
matsala a hanya." tace, ikon Allah, toh
Allah ya kiyaye gaba." daya bayan daya kannan
nasa suke gaishe shi.
Tuni zainab ta hada mishi abinci a
gabanshi dasu lemo da ruwa, yace sannu
autarmu." zainab ta koma waje daya ta
zauna.
Hajiya tace, a'a taho mana muci gaba da cin
abincin? Zainab ta shafa cikin tace,
"Allah yajiya na koshi."
ni'ima tace kin gani ko hajiya? Data fara
cin abincin nata wai ta koshi, shiyasa
kullum bata girma saboda bata son cin
abinci." sadiya tace zoki zauna na baki abaki."
zainab tace haba aunty dazu fa kina kallo
nasha youghot da biskit, nifa bana jin
yunwa."
yaya Aliyu ya daka mata tsawa, tashi kije
kuci, wato har yanzu kina nan dakin cin abincin
naki ko?
Ta mike jikinta na rawa, tazo tana cusa
abincin ba a son ranta ba, don tasan
halin yaya Aliyu, baya son wargi, yanzu
intayi wasa yakai mata duka. Don gaba
dayansu suna shakkar yaya Aliyu, don shi dama
bai fiya yawan magana ba, kuma
bashida sakin fuska koda wasa, shiya
yasa da ya shiga makarantan sojoji
mutane dayawa suka rinka ganin ya dace
da soja.
Suna gama cin abinci ta hada kwanukan ta
kwashe, daga nan ta kyalla
bangarensu da gudu ta fada dakin
mamanta, taje ta ta kwanta a bayanta
tana hakin gudu.
Maman nata tace lafiya gudun me kikeyi
haka? Tace "mama yau yaya ya kusa dukana
akan cin abinci."
maman tace, Allah shi kara, inama ya
dokekin."
tace mama saiki so ya daken da wannan
hannunsa mai zafin? Tace "kwarai kuwa, ba dole
naso ya dake ki ba tunda bakya
son cin abinci, kinfi so kullum kita zama a
haka ana tsokanarki dace mik 'yar tsanar
mama ko?
Zainab ta zumbura baki ta juya mata
baya, tace shikenan ma nayi fushi." maman tace
nima nayi fushi ba ruwana
dake."
zainab tayi saurin juyowa, tace nadaina
mama, ki daina fushi dani kinji? Maman
tace, toh na daina indai zaki rinka cin
abinci kinji? Tace toh naji mama zan rika ci.
**** *** *** *** ***
sadiya da ni'ima suma duk suka mike ko
wacce tayi bangarensu, hajiya ta dubi
Aliyu tace yanzu anya Aliyu bazaka yi
aure ba. Idanfa kayi aure zaka karawa kanka
daraja a gurinmu da wajen
kannenka. Kai ba abun farin ciki bane
kannenka su rinka faduwa suna tashi a
gidanka bane, don Allah ka daure kayi
aure.
TATTALIN SO 1**2
Yace, kai hajiya, kin matsanta min da
maganan auren nan, wai ke bakya
kishina ne?
Tace ni ai indai akan wannan ne banayi,
ka samo min abokiyar zama, idan kuma kai
bazaka iya ba ni na samo maka."
hajjaju kenan, za'a nemo in Allah ya
yarda. Tace dakai wani ne saika samo a
hadaka da 'yar uwarka sadiya, tunda
kaga ansa rana data yi candy za'ayi aure
insha Allahu." yace kai hajiya, kedai kina son
hada
sabgata da yaran nan so kike su rainani
ne?
Tace, "ai kaji sha'anin naka, sai son
girma kamar gyambo, yo meyesa baka
nemo tuni kayi ba? To bari kaji na fada maka, ko
ka nemo yarinyar da kake so ayi
auren kafin bikin sadiya, ko kuma ayi
auren lokaci daya da sadiya."
ya mike yana dariya, "hajaju kenan, kin
taba ji anyiwa namiji auren dole? Tace
za a fara shi kuwa daga kanka." hajiya dai da
gaske take lamarinta, don
ta matsu taga Aliyun yayi aure, tana so
ya kara samun daraja da mutunci a gun
iyayenshi, saboda Aliyu yaro ne nutsatse
mai hankali da nutsuwa, yana da biyayya.
Du abunda iyayensa suke so shi za yayi. Du da
karancin shekarunsa yanada halin
ya kamata, shiyasa ya zama abokin
shawarar iyayensa.
Karfe shidda na yamma direba ya kwaso
'yan makaranta tun safe. Da yake zainab
a firamare take, karfe daya ake tashinsu, to saita
shiga lesson na awa daya, karfe
biyu take fitowa sannan antashi su
sadiya da ni'ima da suke 'yan sakandare.
To sai suyi sallah direba ya kawo musu
abinci suci, sai kuma shiga islamiya data
ke duk a cikin makarantar. Karfe hudu zasu fito
sallar la'asar, suyi dan ciye-
ciyensu su kuma komawa aji, sai karfe
shidda za'a tashesu suyo gida.
Yau direba yana tsayawa zainab ta bude
ta fito tayi bangarensu, kicin ta nufa don
tasan mamanta tana kicin ita da 'yan aikinsu don
gudanar da girkin dare.
Hajiya saude ta tari 'yarta da murna tana
cewa, "sannu da zuwa auta." ta
rungumeta suna dariya ta cika uwar tata
ta nufi firiji tana cewa, wallahi mama
yunwa nake ji." ta bude firij tace kai mama ina
vanilla ice-cream dina?
Mama tace a'a zeey bana son rigima, ba
tun jiya kika gama shanye naki ba?
Tace "to mama bana sa ragowar dayan a
firij ba." tace to ai kuwa dashi sadik ya
tafi makaranta da safe. Zainab tanajin haka ta
yarda jaka ta hau
tsalle da ihu tana kuka, "wallahi saiya
biyata ice-cream. Faruk da sadik suka
shigo duk da goyon jakunan su, suma
nasu direban ya dauko su, don
makarantar matan daban ta mazan daban aka
sakasau.
Tace "wai ice-cream dinta tasa a firij
waye ya daukar mata a cikinku. Faruk
yace "mama ai sadik ne ya tafi dashi
makaranta."
sadik yace ai banaki bane ragowa ne na dauka da
zaki kama yiwa mutane kuka."
tace "to bani nasa shi a firij ba kaje ka
dauka min ba, wallahi sai biyani abuna."
taci gaba da kukanta tana tsalle. Aliyu
yana dakinsa ya ringa jiyo ihunta, ya
shigo da sauri yana cewa lafiya? Me akayi mata
mama? Tace rigimar data
saba ne kawai, ice-cream ne du sunsha
roba dai-dai, ragowar daya ne wai ta
dauka tasa a firij shikuma dan uwan
dayan abokin yin nata ya dauke ya tafi
makaranta dashi ya shanye, shiya kawo wannan
rikici nata." ya daka mata tsawa,
"tashi zaune." ta mike a razane tayi daki
da gudu. Dai-dai lokacin ni'ima take
shigowa take cewa "wallahi yaya ko
abinci bata ci a makaranta ba sai
youghot me sanyi ta rinka siya tana sha wuni
guda, yaya sadiya tai ta mata fada
ta kwace youghot din ta siyo mata meat
pie da yambos, saida taga zata daketa
sannan taci.
Aliyu yace a'a ba akai muku abinci bane?
Tace, "ankai mana mana, bata cin abinci sai
kayan zaki dana sanyi take sha."
ya kwada mata kira da karfi, "zainab kina
ina? Ta fito daga falon da sauri ta rabe a
waje daya. Yace maza ni'ima shiga kicin
ki zubo mata abinci ina zaune ta cinye
shi. Ni'ima ta zubo mata abinci ta dire a
gabanta, Aliyu ya daka mata tsawa dauki
ki cinyeshi. Taja filet din ta fara cin
abincin, tsoronsa take ji sosai, don tasan
baya wasa.
Yace ki cinye shi du idan kika rage ko kaka nida
kene. Ya juya ya fita, ya sami
direba a waje ya bashi dubu biyar, yace
yaje bakori ya siyo masa ice-cream da
youghot masu sanyi, da gashashiyar
kaza guda biyu." ya wuce dakinsa. Zainab
kuwa tana zaune tana kuka tana tura abincin,
saida ta cinye tas sannan ta
tashi tayi daki ta kuka, me aikinsu ta bita
tana rarrashinta, ta hada ruwa a baho, ta
cuda ta sannan ta kyaleata ta karasa
wankan da kanta ta dauro alwalar sallar
magariba, tana cikin shiryawa taji sallamar direba
da yake kaisu makaranta.
Mama ta amsa masa, ya shigo ya
durkusa yace, "gashi mama inji yaya
Aliyu, na zainab ne.
Maman ta karba tana budawa, tace "Aliyu
kenan, ai shine ma ja gaban sangartar da zainab,
don daman can shiya koya mata
irin wannan cimar bata damu da abinci
ba, gashi ta fara girma abu yana nema ya
zame mata jiki.
ta kwala mata kira, ta fito da sauri tana
cewa "mama me yayan ya kawomin. Ta tura ma
kayan, gashinan 'yar lelen yaya.
ta fito ta kama dubawa, robar yght guda
shida, ice-cream guda shida, gasassun
kaji guda biyu, ta dauki robar ice-cream
da nono dai-dai ta saka a firij, tace wlh
mama kada ki bari sukuma daukar min.
TATTALIN SO 1**3
MAMAN ta bata kaza daya da youghot guda uku,
ice-cream guda uku, gashi nan saii tafi gidan
hajiya ki hadu keda 'yan uwanki mata da mazan
tunda suna can kuci, wannan kuma in na nashiga
wajen su hajiya cin abinci maci acan."
zainab ta dauki ledar tayi bangaren wajen hajiya,
ta shiga da sallamarta, ni'ima ta tarota tana
dariya tare da cewa, "sai 'yar gidan daddy, me
kika samo mana.
Tace, "ai bazaki ciba tunda kika sa aka sani cinye
abinci." tace haba yi hakuri 'yar kanwata, kinsan
tsakaninmu bata baci."
sadiya ta karbo kayan tace, bawanin kunyi fada
da ita dani take shiri." gaba daya suka hadu suna
cin kazar da youghot din da ice-cream din. Ahaka
Aliyu ya shigo ya sami kujera can nesa dasu yana
duba jarida. Zainab tasa jummai mai aikinsu ta
dauko mata jakarta ta islamiya tana son yin
hadda, don gobe malaminsu yace su zo masa da
haddan Arrahaman izu bakwai.
Ta bude Qur'ani ta bawa hajiya, tace hajiya
rikemin nayi hadda, gobe malam yace muzo masa
da hadda, du wanda bai iya ba zai sha bulala.
Hajiya ta rike mata Qur'ani ta fara karanto
Arrraman cikin kwararen larabci irin wanda ake
koya musu a islamiyasu, da yake tana da zakin
murya, gashi ta iya fitar da kowane harafi, ta iya
rera karatun da kome kake yi in kaji saika tsaya
ka saurareta.
Aliyu ya lumshe ido yana mai jin dadin karatun
nata, a ransa kuwa fassara suran yake yi yana
fasalta mata 'yan aljannan da Allah ya yiwa
rahama. Tana kaiwa karshen suran tace
Alhamdulillah, na haddace a kaina."
hajiya tace "barakallahu fik, kin wuce dukan
malam." hajiya tace shiyasa nake sara miki
mutuniyata
shagwabarki bata damuna tunda akwai ki da
kwakwalwa mai kyau, du abunda aka gaya miki
kya dauke shi a kanki.
Sadik yace "iyayi dai da neman suna wai ita ace
mata mai ilimi."
zainab tace toh ilimi karyane? Ai ilimi shine kan
gaba a rayuwar dan Adam. Ilimi lallai ne mace ya
kasance tana kula dashi, ilimin addinin ta da
kuma ilimin rayuwa.
Misali, bari na baka misali da kowanne. Ilimin
addini don tasan yadda hukunce-hukunce sallah,
tsarki, jinin al'ada, jinin biki da dai sauransu.
Ilimin rayuwa kuwa, don kanta ya waye ya
kasance tasan abunda yake faruwa a duniya,
koda ta sauraron ko radiyo, kada ace mace bata
san sunan gwamnan garinsu ba, ko shugaban
kasa. Kinga akwai karancin wayewa a wajenki
kenan.
Ilimi wani abune da yake karawa mutum daraja,
Allah mai girma da daukaka yace "Allah ya shaida
lallai babu abun bautawa da gaskiya sai shi."
kuma mala'iku ma'abota ilimi sun shaida yana
tsayar da adalci mabuwayi mai hikima. Kaga
saboda muhimmacin ilimi a wannan aya, sai Allah
ya ga hada shaidarsa data mala'iku da kuma ta
masu ilimi.
Ashe du wanda ba malami ba, ba kuma mai
neman ilimi ba, toh bai cika cikakken mutum ba.
Haka kuma annabi ya fada acikin wani hadisi,
"duk wanda Allah yaso shi da Alkhairi, saiya
fahimtar dashi Addini." haka kuma yana cewa,
"neman ilimi farilla ne akan kowane musulmi
namiji ko mace.
Kuma Darajar farko idan ance ilimi shine ilimin
addinin musulunci,sai kuma ilimi na rayuwa,
kamar su ilimin likita, injiniya, siyasa, mu'amala
da dai sauransu.
Daraja da kimar 'ya mace tana karuwa
gwargwadon yadda ta kula da iliminta, kamar
kuma yanda darajar da kimarta take lalacewa a
wulakance sakamakon yanda taki yin ilimi."
mace ta gar itace wadda kunya bata hanata
neman ilimi, ilimi na addini kona rayuwa. Ka duba
ka gani, nana Aisha matar manzon Allah (S.A.W)
du da yarinya ce karama, domin har annabi ya
bar duniya shekarunta sha takwas ne, amma tayi
gwagwarmaya da maza wajen haddace hadisan
Annabi (S.A.W), domin itace ta hudu a cikin
mutane bakwai da suka fi kowa haddace hadisai
annabi acikin sahabbai.
Kaga wannan yana nuna kulawar mata da ilimi
kenan.
To kada kuma yi min zargin son gwaninta ne
yake sani yin karatu, a'a inason yin koyi da nana
Aisha ne, don nima inaso na zama mace ma
wadatatcen ilimi.
Hajiya tace Allahu akbar, Allah ya baki ikon yi.
'yan'uwan suka sa mata dariya, tare da cewa sai
auta.
Aliyu yarinyar yaji ta burgeshi, ta kara shiga
ransa sosai, yanda take da kyakyawar
kwakwalwa ya kamata abarta tayi ilimi mai zurfi
don ta zama wani abu gaba. Iliminta ya amfani
sauran al'umma.
Washe gari yaya Aliyu sammako yayi ya koma
kaduna bakin aikinsa. Cikin hukuncin ubangiji sai
ga mama da ciki, don ita harta fitar da ran sake
haihuwa, to ta ga zainab shekara bakwai harda
wata uku. Sannu a hankali hajiya tana matsawa
aliyu da maganar aure, shifa ya gaya mata bashi
da lokacin da zai tsaya duba matar da zai aura,
ita tace "to ta nemo masa, don ita tanada lokaci.
Du da akwai gidan makocinsu Alh haruna, 'yar
gidan mansura ita take mutuwar son Aliyu, du
sanda yazo tai ta shige da fice kenan a gidan, ayi
masa soye-soye na kayan dadi akawo masa,
amma baya kulawa saidai kannensa su cinye,
hajiya ta zuba tukuici.
Duk yanda mansura taso taja ra'ayinsa don ya
sota, ya rinka sauraranta bata isa ba, ko kallonta
ba yayi saboda miskili ne.
Ita kuwa hajiya taga tayi tayi dashi ya samo
matar da zai aura ya kasa, suka nema masa
auren mansura.
TATTALIN SO 1**4
SUKA nema masa auren mansura. Alh
haruna mahaifinta yaji dadi, inda yace a
hade sa ranar data yaya sadiya ayi biki
gaba daya."
da mansura taji wannan labarin kamar ta zuba
ruwa a kasa tasha don zumudi da
murna. Shikuwa yaya Aliyu ya hakura ne
ya yarda don bashi da yanda zaiyi, tunda
iyayensa da kakansa sunfi karfinsa.
Yaya sadiya sunyi candy a ranar suka yi
fatin candy, kawayenta da 'yan makarantar sun
shayin hotuna harda
bidiyo caset don dai tarihi. Sun kakkarbi
adireshin junansu da lambobin waya,
don dai su rinka tunawa da juna suna
sada zumunci a junansu.
Satinsu biyu da candy yaya sadiya ta fara rabon
katin bikinta. Inda itama mansura
ta ke raba nata katin bikin ga kawayenta
da 'yan uwa.
Haka yaya Aliyu anbawa sani ya kai
masa katunan can kaduna, yanata
rabawa abokan aikinsa da abokan arziki. Ranar
alhamis akayi kamun mansura,
ranar jumma'a akayi kamun yaya sadiya.
A ranar yaya Aliyu ya dira daga kaduna,
da wasu tawagar abokanan nasa da yayi
musu masauki a daya daga cikin gidajen
iyayensu. Washe gari ranar asabar akayi daurin
aure, gaba daya ankon galila shadda
suka matsa, da hadadden dinki yi mata
na aikin saa. Du ita suka sa, saida akaje
gidan su mansura aka dauro auren yaya
Aliyu, sannan aka daura auren yaya sadiya, daga
nan maroka suka shiga
busa da kade-kade, su Alh suka shiga
rabon kudi ana watsawa maroka kudi.
Haka abokanan yaya safiyanu mijin
sadiya, sukai ta watsawa maroka kudi.
Karfe hudu dai-dai aka shirya walima, kawayen
yaya sadiya da kawayen
mansura, abokanan yaya Aliyu da
abokanan yaya safiyanu, du sun ci
kwalliya ta kece raini, hadaddun 'yan
mata gogaggu, wannan ta wace wannan,
wannan tana wace waccan, sun sha ado da
kwalliya.
A harabar gidansu akayi da yake
farfajiyar katuwa ce, an kafa rumfuna
aciki an zuzzuba kujeru farare acikin
rumfar.
An ware gunda Aliyu da mansura, safiyanu da
sadiya zasu zauna.
Anyiwa wajen ado da fulawoyi da roba
balan-balan, an wadata wajen da amare
da angwaye, sunyi kyau kamar fulawa
aka dasa dan kyau.
Ni'ima 'yar shekara sha hudu ta fara zama
budurwa, domin makerin budurci
har ya fara kerata. Tayi kyau ta ratso
cikin tsakiyar filin gurin da lasfika take, ta
dauki lasfikar tace, "ansuturillah." ta fada
sau uku, jama'ar sai kowa sukayi shiru
suka zuba ido. Ni'ima ta kalli inda iyayenta suke
taga
daddyn zainab da Abbansu, shigarsu iri
daya. Haka iyayen su mata duka su ukun
shiga iri daya suka yi.
Ta kalli jama'a taga kowa yayi shiru ya
nutsu ya zuba mata ido. Saita ce "muyi salati ga
annabi." gaba
daya suka ce (s.a.w)." bayan an gama
karantawa tace, "ya shafi sha biyu, Allah
ya shafe du wata fitina da zata kunnowa
ma'auratan nan." gaba daya akace
ameen." bayan angama tace Ayatul kursiyu kafa
uku, Allah ka karemu ga mugun ji, mugun
gani, sharrin mutum dana Aljan, da
sharrin duk wani abunki.
Allah ya basu zaman lafiya, Allah ya basu
zuri'a dayyiba saliha, Allah yasa anyi wannan
aure a sa'a.
Ta cika da fatiha, ta daga hannunta tana
addu'a ana amsawa da Amin. "waman
yattikillah yaja'allahu makraja, wa
yarzurku min haisu lah ya tasiri, waman
tawakal alallahi fa huwa hasbun, innallaha baligul
amri kadija'Allahu li kulli
shai'in kadira. Amin.
Yayinda kowa ya shafa.
Tace to Alhmdllh, jama'a muna yi muku
barka da zuwa, mungode da hallartat
taronmu da kuka yi don ku taya mu murnar auren
'yan uwan mu.
Bari na kira muku autarmu dan tazo tayi
mana 'yar fadakarwa kadan kafin
malaman namu da zasu yi wa'azizzikan
su gama karasowa, tace "zainab zeey
daddy bismillah." zainab 'yar shekara takwas ta
taso cikin
nutsuwa tana murmushi daya karawa
fuskarta kyau, tana sanye da dan dan
datsetsen yelow les da yake ta walwali,
dambara-damran dutsuna ajiki kamar
madubi, tasa gwagwaro yelow, ta yafa dankwalin
les din. Tasa fashion azurfa
mai yalayen dutsuna wuya da kunne, da
zobensu, tasa warwaraye suma yaleye.
Yarinyar tayi kyau sosai, tsarin kwaliyarta
kamar wata babba. Shiga iri daya sukayi
da ni'ima komai da komai. Ni'ima ta mika mata
lasfikar suna yiwa
juna murmushi, yayinda masu hotuna
suke basu flasha, masu filet din dvd da
cd suke ta dauka, ni'ima ta koma wajen
zamanta, zainab cikin zakin muryarta
tace "Aslm 'yan uwa musulmi." gaba daya kuwa
suka amsa mata da "wslm.
"hakika ina taya 'yan uwana murna da
wannan rana ta aurensu, Allah ya basu
zaman lafiya dauwamamme, yaya sadiya
da aunty mansura, yanzu Allah ya kaiku
wani matsayi da rayuwarku zata canja ba kamar
sanda kuna gida ba. 1- abu na
farko da ake so 'ya mace ta gane ta
fahimceshi shine, hakkin mijinta akanta,
ta gane cewar miji shine shugabanta, ta
rinka jin hakan a ranta.
Saboda Allah ubangiji yace, maza masu tsayuwa
ne da shugabanci a kan mata,
kuma maza suna suke da fifiko wajen
girma da daraja akan mata."
wadanan dalilai su zasu mace ta dinga
jin cewa, namij fa shugabane, kuma ta
dinga jin haka a jikinta, kuma tasan yana da
hakki akanta, domin tasan bazata fita
ba saida izninsa, kuma duk inda zata je
saita san ransa bazai baci ba.
Manzon Allah (s.a.w) ya fada a cikin
hadisi ingantacce
TATTALIN SO 1**5
YA fada acikin hadisi ingantacce, saboda girman
hakkin miji akan matarsa, "da za'a umurci wani
yayi sujjada ga wani, dana umurci mace tayiwa
mijinta sujjda. Koda
miji zai bukaci amfani da matarsa, ita kuma tana
kan sirdin rakumi, to kada ta
hanashi.
A wata ruwayar ta bukhari, manzo Allah
(s.a.w) yace, "idan mij ya kirawo matarsa zuwa
ga shimfidarsa ita kuma taki har ya kwana yana
fushi da ita, to mala'iku zasuyi ta tsine mata har
sai an wayi gari,
bukhari ne ya ruwaito.
Idan mace ta gane hakkin miji akanta,
kuma tayi masa da'a akan abinda ba
sabon Allah bane, to hakan zai taimaka
kwarai wajen gyara zuciyarta. 2- abu na biyu
shine amana, anaso mace
ta zamo mai amana bata cikin abunda ya
shafi dukiyarsa, kuma bata ha'ince shiba
akan karan kanta.
Ha'intar miji wajen dukiyarsa daukan
wani abunsa batare da iznin sa ba. Ha'intar
miji aka karan kanta kuwa, shine
ta bada kanta ga wani namiji. Ko kuma
tayi kawance da mijin da banata ba. Du
matar kirki bazata yi haka ba.
Toh macen kirki itace wadda bata
ha'intar mijinta daga dukiyarsa ko kuma
akanta. Salihan mata masu da'a ne ga
mazajensu, masu tsare mutuncinsu ne
da dukiyoyin mazajensu, basa ha'intar
mazajensu alokacin da basa nan.
Manzon Allah (s.a.w) ya fada cewa babu
yanda za ayi mace ta dauki wani abu a
dakin mijinta ba tare da izninsa ba, to bai
halatta ba,
sai sahabbai suka tambayi annabi cewa "ko
abinci ne? Sai annabi yace "wannan shine mafi
daraja acikin dukiyoyin mu, ba a yarda mace ta
dauki abincin mijinta tayi kyauta dashi ba.
TATTALIN SO 1**6
BA AYARDA mace ta dauki abincin mijinta tayi
kyauta dashiba saidai in dafaffe ne in tayi, gudun
kada ya lalace, to sai a sadaukar dan gudun kada
ya zamo almubazaranci. Shima idan miji ya dawo
saiki sanar masa, ko gidanku zaki aika da abinci
saiki sanar masa, bare ki bawa wani can daban.
Wannan yana cikin cin amanar miji.
Manya mutane suka rinka mikewa suna yiwa
zainab kyautar kudi, saboda yanda yarinya
karama ta burgesu, Abba da daddy sai washe
baki suke yi don jin kokarin 'yar tasu da
kwazonta.
Mamanta kuwa tayi hamdala acikin ranta, tana
mai jin dadin baiwar da Allah yayi wa 'yarta tun
tana karama, kowane tebir mutum hudu ne a
zagaye dashi, akayi umurni da masu sabis su fara
rabon abinci, shinkafa ce fara da taliya itama
haka, sai soyayyun kaji da gasashen nama, sai
mitfy, samosa, sopringros, haka kowa za a tsira
katon filet a dire a gabansa, mata masu wa'azi
sun zo, wajen yayi shiru an nutsu ana cin abinci,
yayinda aketa kwararo wa'azi akan zaman aure
ga ma'aurata.
Washe gari akayi yini, ranar litinin akayi fati, a
ranar kuma aka kai amare dakunansu. Burin
mansura ya cika, yau ta auri gwarzon namiji
cikakke, wato Aliyu.
Tasan sarai Aliyu miskili ne bai fiya
wasa da dariya ba, shi hasalima magana wahala
take masa yi masa, don inzaka daka ta tashi sai
dai kuyi ta zaman kurame dashi.
Aliyu mutum ne mai tsafta, dan gayu ne mai son
kamshi, baya damuwa du tsadan turare zai saya
indai kamshin shi yana da dadi. Aliyu yana ji da
kansa, akwai iya jan aji, yana da tsananin iyayi
da gwalli kamar mace, ya fiya kasaita da son
girma kamar wani basarake.
Washe gari ranar talata gajiyar biki bata bar
ni'ima da zainab zuwa makaranta ba. Tun asuba
da aka tashe su suka yi sallah, suka sake
komawa gado suka nade cikin bargo suna bacci.
Karfe bakwai masu aikinsu sukayi ta tashinsu don
su shiry su tafi makaranta, amma du sunki tashi.
Dole sai rabuwa suka yi dasu.
Karfe goma dai-dai Aliyu ya shigo gidan don
gaishe da iyayensa. A farfajiyar gidansu mai gadi
da direbobi suna ta risinnawa suna gaisheshi.
Aliyu ya cewa malam idi direba, "ina 'yan
makaranta , i ce kodai basu makara bako?
Malam idi yace ai basu fito ba, yau ban kaisu
makaranta ba." a zuciye Aliyu ya shiga gidan,
kafa kawai yasa ya daki kofar ta bude garam.
Ni'ima da zainab suka tashi a firgice, suna
mitsike ido. Suna dago kai suka ganshi. Kafarshi
daya akan gadon, dayar tana kasa, fuskar nan
tayi kirtif da ita kamar bai taba dariya ba.
Zumbur suka mike suka diro kasa daga gadon,
suka durkusa can nesa dashi, suka kama cewa
"yaya ina kwana? Bai amsa musu gaisuwar ba,
sai tambaya daya jefo musu cewar "meya hanaku
zuwa makaranta? Gaba daya jikinsu ya hau bari
suna in'ina da kame-kame abunda zasu ce, ya
daka musu tsawa "ku tashi ku saka uniform
dinku, ina jiranku a falo." suka mike da sauri
kowacce ta nufi kwaba. Shikuma yayo falonsu
yana tsaye. Mintuna kadan suka fito sanye da
kayan makaranta da jakunkunansu a rataye, ya
sasu a gaba har farfajiyar gidansu, ya kwalawa
malam idi direba kira, ya taho jikinsa na rawa.
Yace "daga yau du ranar daka kara kin kaisu
makaranta abakacin aikinka."
malam idi ya rikice jikinsa yana bari, yace "kayi
hakuri yallabai, wallahi ba laifi na bane sune basu
fito ba." yace "daga yau idan kaga basu fito ba
kayi min waya kawai ka gaya min. Yace "to
yallbai." suka shiga motar direban ya jasu.
Shikuma Aliyu yayi cikin gida. Zainab tace,
"inbanda abun yaya, daga yin aure saika fito da
sassafe. "ni'ima tace, "ai gwandake bangarenku
ma na 'yan firamare ne, ni 'yar sakandare nasan
wallahi sai an dake ni, daya kyalemu gobe basa
muzo ba."
gidan Aliyu yana nan daga bayan gidansu ba
nisa. Amma tunda aka kai mansura basu je gidan
ba, saboda basu da wani lokaci sai dare, sukuma
ba fita suka yi da dare ba.
Yau alhamis ana tashi daga boko gida suka yo,
dan ba islamiya. Ni'ima da zainab tuni sun gama
shiri, anko sukayi na wani dandatsesen material
baki, ni'ima tana rike da hannun zainab suka tafi.
Suna zuwa gidan suka shiga, 'yan aikin gidan sai
sannu da zuwa suke yi musu. Suka karasa
babban falo inda matar gidan take, sukayi
sallama, saida akayi musu izni sannan suka
shiga. Mansura ta taresu da murna, a'a sai yau
zaku zo, nayi fushi." suka rike hannunta suna
cewa, "tuba muke aunty, kinsan kullum da
makaranta.
Tace, "to amma gaskiya yau anan zaku kwana."
suka ce wai kwana aunty? Ai baza a barmu ba a
gida." tace haba don Allah, ya ya zasu hanaku
kwana a gidan babban yaya." yayinda take
kwalawa mai aikinta kira talatuwa, "na'am ranki
ya dade, ta amsa da saurinta, ta durkusa a
gabanta, mansura tace "bakya ga munyi bai ne
baki kawo musu komai ba, nifa bana son
shashanci, kirinka kula da aikinki fa."
talatuwa tace kiyi hakuri aunty. Ta fita da sauri
ta shiga kicin ta hado musu lemuka da snacks
taje ta durkusa a gbansu ta ajiye. Zata mike
zainab ta bude jakarta ta dauko dari biyar ta
mika mata. Talatuwa tasa hannu biyu ta karba
tana godiya. Inna laraba tashigo ta durkusa a
gaban mansura tana tambayarta hajiya me za'a
girka?
TATTALIN SO 1**7
TA YAMUTSA fuska tana tsara mata
abunda zata girka. Harta mike ta
fara tafiya zainab tabita tasa mata
dari biyar a hannunta, tsohuwa
laraba tace, "auta me za a sayo miki?
Tace a'a ki rike baki nayi. Laraba ta
washe baki tana murna tana godewa
zainab.
Yaya Aliyu ya shigo, da sauri zainab
da ni'ima suka yi masa sannu da
zuwa tare da gaishe shi. Ya wuce
bangarensa. Mansura ta kwalawa
talatuwa kira, tazo da saurinta.
Mansura tace, "ki hadawa Aliyu
abinci kikai bangarensa."
zainab kanta data ke yarinya tayi
mamakin abun, bare ni'ima data fara
zama budura. Sun san haka bai
kamata ba, don ba haka ake yi a
gidan su ba.
Wata mata ce da goyon 'yarta ta fita
da hayyacinta kamar almajira, ta
durkusa tana gaida mansura.
Mansura ta hade rai tana ya musta,
da kyar ta amsa gaisuwan matar.
Ni'ima da zainab suka gaishe da
matar, zainab tace kwanto yarinyar,
bata da lafiya ne? Matar tace
"wallahi zazzabi ne da amai da kashi
na hakori." yayinda take kokarin
sakkota. Zainab ta mika hannu zata
karbeta, mansura tayi karaf tace "ke
zeey auta yarinyar ba lafiya kokarin
daukarta kike? Saita yo miki amai
ajiki." zeey tace to kije ki sai mata
magani ta sha mana.
Matar ta girgiza kai cikin yanayi na
tausayawa, tace, "aiba kudin ne,
magani har dari tara da hamsin,
banida kudin dazan sai mata, kudin
yayi yawa, ko dari da hamsin bani
da'ita bare har dari tara da hamsin."
zainab ta bude jakarsu ta zaro gudan
dubu daya ta mikawa matar, "ungo
kije kisai mata maganin." matar ta
karba bakinta yana rawa.
Mansura tace, "ke zeey kudin wa kika
samu kiketa rabarwa haka? Zainab
tace daddy ne ya bamu da zamu zo
ko zamu sai wani abun.
Mansura tace to shine kike rabar da
kudi baku sai komai ba." zainab tace
aunty ai muna da komai me zamu
saya? Ba gwanda mu bayarba."
matar nan dai tanata sawa zeey
albarka harta fice ta tafi.
Ni'ima ta fuzge jakar daga hannun
zainab, ta bude ta leke bakomai
aciki, ta harareta to kin rabar mana
da kudin, to yanzu dame zamu sai
ice-cream din? Ni shiyasa wallahi
bana so nabar kudin mu a hannunki,
du saiki rabarwa da mutane mu ki
barmu haka. Nidai kawai kirinka
bayar da iya naki, kada ki kuma
bayarmin da nawa kudin."
zainab tayi murmushi, tace "haba
yaya ni'ima, abunki ai nawa ne, zan
iya iko da komai naki, Allah ya bamu
rai da lafiya, muna da kudi a gida,
ko an bamu ma tarawa muke yi idan
bamuda abun siya. To ga masu
bukata saimu hanasu." ni'ima tace,
"to amma ai bakya bayar du ba, ai
kinsan zamu sai ice-cream."
zainab tace bakomai yaya ni'ima,
zaki ga Allah ya bamu wasu, don
ranan malaminmu yace, "anaso
mutum ya rinka ya waita sadaka,
saboda tana juyar da bala'i.
A zamanin annabi sulaiman (a.s)
akwai wani mutum a gidansa akwai
wata katuwar bishiya, tsutsuwa tayi
'ya'ya akai. Sai wata rana matar ta
gaya wa mijinta cewar, ya hau kan
bishiyar nan ya debo musu 'ya'yan
wannan tsutsunwar zasu ci suda
'ya'yansu.
Mutumin nan ya kwaso 'ya'yan, suka
gashe shi, shida matarsa da 'ya'yansa
suka cinye. Sai tsunsuwar nan takai
karar wannan mutumin gurin annabi
sulaiman (a.s), shikuma yasa aka
kirawo mutumin yayi musu tsakani
da wannan tsuntsuwar, mutumin
yayi alkawari bazai sake ba.
Ana haka sai wata rana matar nan ya
kuma gayawa mijinta ya hau bishiya
ya kuma debo musu 'ya'yan
tsunsuwa, mutumin yaki, yace
"annabi sulaiman ya hana shi ya sake
dibar mata 'ya'ya." sai matar tace
kana ganin annabi sulaiman zaiyi
maka wani abu danka kwashe 'ya'yan
tsunsuwa, alhalin shima me
shagaltuwane da mulkinsa? Matar
dai tai ta rudarsa har ya hau ya
debo.
Sai tsuntsuwar nan tasake kai kararsa
wajen annabi sulaiman, annabi
sulaiman yayi fushi, ya kirawo
shaidanu guda biyu, daya daga
gabas daya daga yamma. Yace sutafi
kan bishiyar nan su zauna, idan
mutumin nan ya sake zuwa wajen
'ya'yan tsunsuwar nan su rike
kafafuwansa su watsoshi kasa.
Shaidanu suka je kan bishiya suka
zauna. Shikuma mutumin ganin ya
debo wa'yancan ba ayi masa komai
ba, don haka sa wannan karon ma ya
sake komawa domin ya debo 'ya'yan.
Har ya taka kafarsa zai hau, sai yaji
almajiri yana bara a kofar gida, saiya
umurci matar nan data bawa
almajirin nan wani abu. Sai matar
nan tace bakomai awajenta.
Sai mutumin nan ya dawo ya samu
lomar abinci ya bawa almajirin nan,
sannan ya koma bishiya ya debo
'ya'yan tsuntsuwar nan, saita sake
dwowa ta gayawa annabi sulaiman,
sai yayi fushi mai tsanani, ya kirawo
shadanun guda biyu daya tura kan
bishiyar. Sai suka ce bamu saba maka
ba, muna kan bishiyar koda yaushe,
lokacin da mutumin zai hau kan
bishiyar sai wani almajiri yayi bara
ya koma ya bashi lomar abinci,
sannan ya dawo ya hau. Zamu kama
shi kenan sai ubangiji ya aiko da
mala'iku guda biyu, daya ya kamani
ta wuya ya jefar dani inda rana take
bullowa, daya yakama abokina ya
jefar dashi inda rana take faduwa.
To kinga dalilin sadakar da yayi ya
kubuta daga sharrin shaidanu. Aliyu
yana daga dakinshi yana jinsu, ya
sake jinjina hankalin autarsu, yasan
hakika akwai bawar da Allah yayiwa
autarsu na musamman.
Ya fito daga dakinshi.
TATTALIN SO 1**8
YA FITO daga dakinshi, yayi
gyaran murya, ya ciro dubu biyar a Aljihunsa ya
mikawa zainab, yace "zeey auta ga kudin ice-
cream." ta rissana ta karba tana godiya. Yaya
Aliyu ya wuce ya sake fita. Zainab tace yaya
ni'ima kinga abunda nake fadamiki ba, inka bayar
da kadan sai Allah ya baka mai yawa." ni'ima
tace nagani, amma bani su nan kada ki sake
bayar mana." ita kuwa mansura a zuciyarta cewa
takeyi, "wannan yarinyar da shegen iyayi take.
Wajen mangariba suka isa gida. Bangaren hajiya
suka nufa sukayi sallar mangariba, zainab ta
mike tayi bangarensu, saita tarar da mamanta
kwance tana juyi. Ta tafi da sauri ta rikota, tana
cewa menene mamana, meya sameki? Maman
tace banida lafiya zaina, marata da bayana ciwo
suke yi. Nan da nan sai zainab tasa kuka tana
cewa, "mama tashi muje asibiti kinji? Mama don
Allah tashi mu tafi asibiti ko kya samu lafiya.
Maman tace da kyar, saboda ta fara galabaita
"zainab asibiti babu abunda zasu iya yi min, Allah
ne kadai zai bani lafiya. Ki kirawomin hajiya da
umma da ummi, tayi cikin gida da sauri, du ta
gaya musu gaba daya suka taho, a lokacin Aliyu
yana gidan. Maman ta galabaita sosai, ko
hannunta bata dagawa. Umma tana ta hado
kayan haihuwar a dakin. Umma tana rike da
maman, hajiya tana mata tofi a ruwa a kofi,
zainab din taje ta rike maman tana jijjigata tana
kuka, tana cewa mama! Mama!! Ki bude idonki
kiga hajiyan fa na kirawo miki ita. Ki bude idonki
kifa tofi take miki, don Allah mama ki bude idonki
kiga umma da ummi., kefa kika ce nakira miki
su, don Allah ki tashi." ta kama jijjigata tana
gwale mata ido, tana cewa mama! Mama!!. Aliyu
yace "umma ku kamata mu tafi asibiti." a lokacin
Aliyu yaiwa abba da daddy waya, suka ce to
suma sun wuce asibitin." a can suka tarar dasu
Abban har sun riga zuwa, aka shigar da mama
dakin haihuwa, zainab sai kuka take yi, ta tafi ta
rungume daddynta tana kuka tana cewa daddy
kana ganin mama bata da lafiya sun shigar da ita
can, daddy kazo mu bita. Ya rungumota yana
rarrashinta, "kiyi hakuri zainab, ki kwantar da
hankalinki, mamanki haihuwa zatayi. Ko bakya so
tasamar miki kanwa? Tace ina somana daddy."
to kiy shiru ki daina kuka, mamanki haihuwa
zatayi kinji ko? Kita yi mata addu'a kinji? Tace
"to daddy zanyi mata. Abba yace, hajiya su koma
da zainab gida a ar umma da ummi a gurinta.
Abba ya taho da hajiya da zainab gida, zainab sai
kuka take yi, suna zuwa gida suna ni'ima da
sadik su ni'ima suka tare su da cewa ta haihu?
Hajiya tace musu a'a ta dai kusa. Du rarrashin da
hajiya take yiwa zainab ta kasa yin shiru, sai
kuka take yi. Su kuwa can asibiti sun kasa
samun nutsuwa, saboda jikin mama da yayi
tsanani. Wajen karfe uku na dare ta haifi 'yarta
mace, su umma da ummi suka ta hamdala suna
yiwa Allah godiya. Karfe bakwai na safe gaba
daya 'yan gidan sun hallara, ganin yanda jini ya
tsinkewa mama, hankalin kowa ya tashi. Daddy
mijinta yana rike da ita yana salati, yayinda
likitoci suketa iya bakin kokarinsu. Sunyi mata
allura jinin ya tsaya, du 'yan uwa sun zagaye ta,
harda sadiya amarya da mansura, su sadik da
ni'ima du suna wajen. Zainab kuwa hajiya ta
janye ta suna falon dakin da aka kwantar da
maman nata. Saboda kuka da zainab din take yi.
Ita kuma mama jikin nata yayi tsanani, sai wasiya
take bayarwa, sai cewa take cikin
dakushashshiyar murya, "ina zainab autata, ki
kirawo min zainab dina. Sadik ya fita da gudu
yana kuka ya kira zainab, ta taho da gudu ta rike
hannun maman nata ta jijjigawa, tana cewa "gani
mama, tashi gaya min abunda zaki gaya min, kinji
mamana? Ta kwantar da kanta akan ruwan cikin
maman nata tana kuka, maman data ke fitar da
nishi da kyar ta dora hannunta kan zainab din
tana shafawa, a hankali ta rinka motsa bakinta
tana karanto kalmar shahada 'yan uwa sunata
amsa mata, tana ta shakewa. Su sadiya da
ni'ima kuwa gaba daya sun rikice da kuka. Can
mama tayi shiru, hamza cikin firgita yace, "ta
mutu! Iyayen suka dauki salati ga daya da
hawaye, yayinda yaran suka cika daki gaba daya
da kururuwar kuka. Zainab kuwa tana yin baya
ba'a ankara ba ta sulale ta fadi kasa ba
numfashi. Aliyu ya sunkuce ta aguje ya shiga
office din likitan da ita. Likitan ya karbe ta da
sauri ya dorata kan gado yana kokarin ceto
rayuwrta. Aka tafi da mama gida akayi mata
sutura aka binneta, kowa yaji ciwon mutuwar
mama. Mama mutuniyar kirki me kawaici da
hakuri, daddyn zainab karfin hali kawai yake yi,
domin yasan yayi rashin da da wuya ya mayar
da'ita. Don rashin hajiya saude ba karamin gibi
rayuwarsa tayi ba. Anata amsar gaisuwa shikuwa
sai yayi jigudin yana tunani, ga 'ya'yanshi 'yan
mazan faruk da sadik suna manne da jikinsa,
yaran sun kasa manta mutuwar, sai dai kawai
kada suna sharar hawaye. Faruk shine sa'a
ni'ima mai shekara goma sha hudu, sadik kuma
shekararsa sha daya. Kwana daya da rasuwar
mama aka sallamo zainab suka taho, da yake
ummi ce a wajenta. Yarinyar tayi wata irin rama
sai kace wacce ta dade da ciwo
TATTALIN SO 1**9
YARINYAR tayi wata irin rama sai kace
wacce ta dade tana ciwo.
Wajen umma ta wuce ta karbi babyn da
mamanta mutu ta bari, ta rungume 'yar
tana wani irin kuka mai ban tausayi. Aliyu ya
shigo da abokanansa zasu yiwa su
umma gaisuwa, yana ganin halin da
zainab take ciki da jaririyar sai yaji
tausayinta ya dameshi, ya runtse ido
yana taya ta kukan zuci, don ba hawaye.
Yace "umma ya za kubar zainab da yarinya a
rungume a hannu alhalin jikinta
ba kwari, tama ci abinci kuwa? Umma
tace "wallahi tun dazu nake fama da ita
ta bayar da yarinyar taki, kaga abincinta
dana girka mata da kaina ma taki ci.
Ya mikawa zainab hannu, yace "bani 'yar. Zainab
ta mika masa babyn ya
rungumeta, yace mata dauki abincin kici."
ta jawo fulas din tana cin abinci tana
yamutsa fuska, don ba dadinsa take ji ba,
har wani daci yake yi mata a makogwaro.
Idonta kuwa ya kasa tsayar da hawaye. Ya
mikawa umma yarinyar. Umma tasa
zani ta goyata. A hannun umma jaririyar
take, ita taci gaba da kulawa da ita.
Saidai yarinyar ma madara take sha,
gado daya suke kwanciya da umma da
jaririyar da zainab. Ko yaushe zainab tana manne
da
jaririyar, ita tasa mata babyn mama, haka
aka cigaba da zaman makoki. Ranar
kwana shidda babyn mama taci sunan
maman, wato saude, itama a ranar ta
rasu, saboda wani zazzabi daya kamata. Zainab
tayi ihun kuka da tumami,
numfashinta ya rinka futa sama-sama,
muryarta ta dashe saboda kuka, ranar
sadakar bakwai hajiya iya mahaifiyar
mama ta nuna tana son zata tafi da
zainab wajenta, tunda itace karama kuma mace,
zata ci gaba da rikonta.
Daddy yace shi bashida magana sai
abunda yayansa ya zartar." hajiya iya
tasa aka kirawo mata Abban Aliyu, ta
nemi alfarmar abata rikon zainab, Abba
yace don Allah tayi hakuri, bazai so raba zainab
da 'yan uwantaba, saboda abun
zaiyi mata yawa, kuma shi gaskiya baya
son raba kan 'ya'yansa, kada taje tana
tasowa a ware.
Du iya kokarin hajiya iya don ta samu ya
bata zainab, yace shidai hakuri yake bata, ba zai
iya rabuwa da zainab ba.
Yana tausaya mata rashin uwa data yi.
Dole ne yasa ido a rayuwarta. Dole hajiya
iya tayi hakuri tabar musu 'yarsu.
Bayan sati uku da rasuwar mama, du
yara sun koma makaranta boko da islamiya.
Zainab kwance kan cinyar
umma, Aliyu ya shigo, yana ganin zainab
din ya daka mata tsawa, "ke meyasa baki
tafi makaranta ba? Ta kama in'ina ta
kasa cewa, "bakomai. Ya kama yi mata
fada, "me kike nufi? Haka zaki zauna baza kiyi
karatu ba sai sangarta, kina
ganin wannan shagwabar itace gata?
Wallhi du ranar makaranta nazo na
sameki baki je ba, sai jikinki ya gaya miki.
Tashi ki sako kayanki ki fito na kaiki." ta
mike da sauri ta shiga dakin umma. Aliyu ya kalli
mahaifiyarsa ya kwantar da
murya yana cewa, "haba umma, haba
umma, ya zaki daka ta tata ki kyaleta
bata je makarantaba? Umman tace
"wallahi tashi tayi da ciwon kai, ga
zazzabi a jikinta, shiyasa bta jeba. Wallahi ni
kuma bana son takura ta,
saboda tausayi take bani.
Yace "to umma in ance haka za ai ta
daka tajin tausayi nata ai sai a lalata
mata rayuwa, yanda yarinyar nan ta taso
da kwazo da basira da anbar wani abun ya tauyi
ilimin nata, shikenan an cutar da
ita.
Umma tace to shikenan ba za a kuma
ba."
zainab ta fito a shirye cikin uniform dinta,
umma ta miko mata fulas din data zuba mata
abinci, tace "um-um, umma ba zan
iya ci ba.
Umma tace anya zainab ayi haka, a ce
bazaki rinka cin abinci ba." Aliyu yace
kyaleta umma ta shige mu tafi.
Suna tafe ya tsaya ya sai mata ice- cream, ya
sauketa a makaranta, saida ya
rakata har ajinsu sannan ya fita ya tafi.
Kamfanin iyayensu ya wuce, yayi sallma
office din daddyn zainab, bayan yayi
masa iznin shigowa ya shiga, ya rissina
ya gaisheshi, ya jawo kujera ya zauna gaban
tebur din. Daddy ya hada shayi ya
fara sha.
Yace "daddy don Allah ka bani zainab na
riketa a wajena."
daddy yace, "aibakomai Aliyu, dani daku
daya, zainab kanwarka ce, kai kuma dana ne, kaje
ka tafi da ita, Allah ya baka ikon
iya rikonsu.
Aliyu yace, "yauwa daddy nagode, bari
naje office din Abba na sanar masa."
daddy yace, "to, saika fito.
Aliyu yayi sallma office din Abbansu, akayi masa
iznin ya shiga, ya samu waje
ya zauna, sannan ya rissina ya gaishe da
Abban nasu.
Yace, "daman nazo na gaya maka ne,
don Allah inaso kubani zainab na riketa a
wajena." Abban yace, "haba Aliyu, baka tausayin
zainab? Yarinya da ita tayi rashin uwa,
sannan yanzu kazo ka rabata da cikin
'yan uwanta ka kaita waje a ware, ita
kadai ai bazata ji dadin zama ba.
Aliyu ya kara rissinawa yace "Abba ba gani ba,
nima ai dan uwanta ne, kuma
sun saba da mansura." Abba yace nan
kakarta hajiya iya, ba yanda batayi dani
ba don na bata zainab nace tayi hakuri
ba zan iya rabata da 'yan uwanta ba. To
kuma sai suji nabawa nawa dan, alhalin matarka
yarinyace ko haihuwar fari bata
yiba.
Aliyu yace yi hakuri Abba ka bani zainab
din, insha Allahu zakuji dadin rikon
dazanyi mata, zamanta a gida yana tayar
mata da hankalin rashin ganin ba mamanta. Idan
kuwa bata gidan zata
samu kwanciyar hankali."
TATTALIN SO 1**10
ABBAN yace "toh shikenan Aliyu, Allah ya tayaka
riko." Aliyu yace amin Abba, nagode, Abban yace
to ka gayawa daddyn naku? Yace "eh, saida na
fara zuwa nayi shawara dashi tukunna."
yace, "to ai shikenan komai yayi dai-dai, Allah ya
tayaka riko." ya amsa da Amin. Ya yiwa
mahaifinsa godiya ya tashi ya nufi gidansu, ya
gayawa kakarsu.
Hajiya murna tayi takara karfafa masa gwiwa
daya rike 'yar uwarsa dakyau, ta hakane zumunci
zai kara karfi a tsakaninsu."
don ita hajiya mace ce mai zumunci, tana so taga
kan zuri'ar ta a hade, yayiwa hajiyar alheri, hajiya
tanata godiya dasa masa albarka, ya fice ya nufi
bangarensu. Ya tarar da umma da ummi a
babban falo suna hira.
Yace musu, "ku hadamin kayan zainab da
daddare zan zo na tafi da ita." gaba daya suka
hada baki cikin razana suka ce, "zaka tafi da ita
ina?
Gidana zata koma zan cigaba da rikonta.
Umma ta mike ta kama yi masa fada, " wato mu
ka raina irin rikon da muke yi mata, shine zaka ce
zaka dauketa saboda kafi mu sanin darajarta, ko
iko zaka nuna mana akanta?
Yayi murmushi yace "kuyi hakuri, umma ba haka
bane." iyakacin maganar kenan yayi musu shiru.
Sun riga sun san bai fiya yawan magana ba, sai
dai yayi atakaice. Inkin ji shi yana hira mai tsawo,
to da iyayensa ne maza.
Ya mike yana ce musu, "umma bari na karasa
gida." umma tace "saboda maganar tamu bata da
amsa ko? Yayi murmushi ya dire musu kudi a
gabansu, yace ummi kwasai goro." tace "to,
mungode, Allah yayi albarka."
yana fita umma ta kama baki, tace, "ki gane min
yaro, wai shi babba har ya fimu sanin abunda ya
dace. Ummi tayi dariya tace "Aliyu kenan
gadanga kusan yaki. Shifa zuwan da yayi yaga
dazu bata je makaranta ba, gani yake kamar
zamu kara sangartar da ita mu rika biyewa
shagwabarta."
Aliyu yana isa gidansa yayi fakin ya shiga, a falo
ya zauna yana karkade kafa. Mansura ta fito
daga daki, tace "sannu da zuwa Aliyu, ga break
dinka can, koda yake rana ma tayi kaine kayi fitar
safe."
yace "nayi break a office din daddy bana tare da
yunwa." yace kisa a share wancan dakin, zan
dawo da zainab gidan nan zata zauna acikin
dakin can.
Ta dafe kirji tace "haba Aliyu, ya zaka ce zaka
dawo da zainab? Ai zaka takurawa rayuwarta.
Don Allah ka kyaleta a gidanku, wannan
shagwababiyar yarinyar in zamu iya da ita anan?
Ya doka mata harara yace ba shawararki nazo
nema ba, idan zainab tazo kada ki barta ta zauna
ki koreta."
tace, "haba Aliyu kai ka fiya zafin zuciya, daga
'yar wannan maganan saika hau tari, ba nufi na
haka ba, ita da gidan wanta "ai ban isa na koreta
ba." yamata shiru bai sake ce mata komai ba
daman tasan ba zai sake magana ba, don ya fiya
miskilanci, baya son yawan magana.
*** ****
karfe shidda 'yan makaranta sun dawo, suna cin
abinci ba dadewa akayi mangariba, suna idar da
sallah hajiya ta rungumo zainab jikinta tana shafa
kanta, tace "zainab yanzu fa yayanki zai zo zai
tafi dake gidansa, zaki ci gaba da zama acan."
zainab tasa kuka tace, nidai hajiya bazan jeba
nace, yai tamin fada koma ya dokeni, hajiya tace
bazai dokeki ba, kuma fada ma ya daina yi miki.
Kije ki zauna kinji zainab? Ta make kafada, um-
um, ni ba zanje ba."
suna haka taji yo sallamarsa, da sauri ta tashi da
gudu tai cikin dakin hajiya. Aliyu ya shigo ya sake
gaida hajiya, hajiya tace masa "zainab dai tace
baza taje ba, ka ganta can harda kuka."
ya kwala mata kira ta fito a tsorace, tazo ta
durkusa a gabansa
yace "shine kika ce bazaki gidana ba? Ta girgiza
kai alamar cewa, a'a yace to meye nayin kukan?
Yi min shiru. Tasa hannunta ta toshe bakinta ta
hadiye kukan.
Yace ki goge hawayenki kije, kiyi wa Abba da
daddy sallama." tace to, ta goge fuskarta. Ta
shiga bangaren su umma ta tarar da Abba da
umma da ummi suna falo, Abba yace yaki 'yata
tazo ta zauna a jikinsa." yace menene naga
idonki alamar kinyi kuka? Tace bakomai, Abba
sallama nazo inyi muku zan koma gidan yaya."
Abban yace "zainab bana son abunda zai
takuraki, in bakya son zuwa ni zansa ya kyaleki
kiyi zamanki." tace a'a Abba zanje." yace to
shikenan zainab, Allah yayi miki Albarka, kici gaba
da maida kai da kokari a makaranta, tanan ne
zaku fi shiri da yayan naki kinji 'yata?
Tace "to Abba nagode." ta mike ta shiga wajen
daddynta, ta daura kanta akan cinyarsa tana
kuka. Yasa hannunsa yana shafa kanta yace "kiyi
hakuri zainab, nasan bakya son tafiya. Zainab ko
yaushe kina raina, dana ganki saikin tunamin da
mamanki. Zainab du ina tausaya mana ni dake
na rashin mamanki.
Kiyi hakuri zainab kiyi zamanki, nasan zai rikeki
da amana kamar ni. Kiyi masa biyayya shida
matarsa, banda rashin kunya kinji? Tace "to
daddy zan kiyaye." ya bude firij ya dauko rubutu a
roba ya bata, ungo shanye rubutunki maganin
tsari da kariya daga shaidanu." ta karba tayi
bisimilla ta shanye, ya karba yasa ruwa ya
dauraye mata, ta karba tasha, ragowar ya zuba a
hannunsa ya shafa mata a kanta da fuskarta.
Yaita mata nasiha mai shiga jiki, yace ta daina
kuka ta tashi taje su tafi." hajiya dasu ni'ima su
sadik har gindin mota suka rakota suna hawaye
tana hawaye.
TATTALIN SO 1**11
HAJIYA tana rungume da ita tana
rarrashinta suka bude mata gaban
mota ta shiga, ta dunkufar da kanta
akan gwiwoyinta tana ci gaba da
kukanta kasa-kasa, Aliyu ya sallame
su du yaraba musu kudi, yace su
koma gida, suna tunanin 'yar uwarsu
wai anrabata da gidansu kenan.
Ya kalleta au baki daina kukan ba?
Tayi saurin hadiye kukan nata, ta
goge idanuwanta. Tafiya kadan suka
isa gidansa, suka fito har daki ya
kaita, "nan shine dakinki, talatuwa
zata rinka taya ki kwana." dakin yayi
kyau, a yau dinan ya sayo mata
gadon silba da madubi, sai kwaba ta
jikin bango, sai labuye da jan kafet,
shikenan ba wani shirgi, sai toilet
aciki dake gefe, tace "to yaya." ya
fita ya nufi sashinsa, zainab itama ta
shiga dakin aunty mansura.
Zainab ta kwantar da hankalinta
tana zaune a gidan yayanta,
tsakaninta da abinci saita ga damar
ci, ko yaushe yayan nata yana cikin
siyo musu ice-cream, youghot su
biskit da cakulet, da yake abinci bai
dami zainab ba, ita hakan saya fiye
mata dadi.
Ita kuwa mansura ta fiya lalaci da
sangarta, bata wani iya girki ba,
shikuwa Aliyu dan gaye ne mai aji,
gashi da kyankyami, don haka bazai
iya cin abincin mai aiki ba.
Don haka inya zo garin ma saidai
yaje gida yaci abinci, don a gidansa
inna laraba ita take yin girki. Babbar
mace ce amma da kwarinta, don
bata wuce yin aure ba, sai 'yar
budurwa wato talatuwa, ita take yi
mata shara dasu goge-goge da
gyaran gado, inta yi baki ta kula
dasu. Don wata wauta ta mansura
dai-dai da mijin ma inya nason wani
abu sai dai ta kira talatuwa.
Don haka ma ko meye ya
gwammace yayi da kansa, abinci
kuwa saiya je gidansu sannan yaci. A
gidansu su umma har fada suke yi
masa, don me zai rinka baro girkin
matarsa baya son ci.
Sai dai yayi murmushi kawai yace
musu bakomai. Bama yanzu da
mansura take fama da laulayi. Da
safe yana zaune a falo da wando iya
gwiwa da farar shirt, yana lumshe
idanuwarsa kamar mai jin barci.
Mansura tana zaune kusa dashi tana
cin wainar kwai da dankalin turawa,
ta zuba shayi a kofi yana ta turiri,
gashi yayi kauri da hadin madara da
naskofi da dai sauransu.
Zainab ta fito sanye cikin shirin
makaranta, ta durkusa ta gaishe da
yayan nata da mansura. Ta mike a
gurguje take, dan takusa makara. Ta
dauki shanyin gaban auntyn nata
tadan kurba, tace "wai aunty wannan
kaurin ai yayi yawa, bakya tsoron ya
kulle miki ciki?
Mansura tayi dariya tace, laifin
babynku ne ba ruwana. Zainab tayi
dariya tace ai, "ai gwanda ki dinga ci
sosai don ki haifa mana katon baby
in rinka daukarsa da kyar." ta nufi
firij ta dauko ice-cream da youghot
da cake, tazo ta wuce su da sauri
saboda yayan nata, tace aunty natafi
makaranta." kafin tayi magana Aliyu
ya kirata "zainab."
tayi saurin juyowa tare da amsawa, a
sanyaye tace na'am yaya." zo nan. Ta
dawo ta durkusa a gabansa. Yace
haka zaki tafi makaranta baki karya
ba? Tace yaya zanci cake da ice-
cream da youghot a mota." yace
wato har yanzu kina nan dakin cin
abincin ki ko sai kayan kwadayi? Ke
wace iri ce ne? Da safe ma sai kin sha
sanyi bazaki ci abinda zai dumama
miki ciki ba?
Mansura tace wallahi haka nake
fama da ita, bata son cin abinci,
daga shan kayan zaki sai shan kayan
sanyi." yace ina break din nata?
Mansura ta kwalawa talatuwa kira,
tace mata ina break din zainab?
Talatuwa ta shiga dakin zainab da
sauri ta dauko break din data kai
mata, yanda ta ajiyeshi haka yake,
ko budawa bata yiba. Ta ajiye a
gaban zainab din.
Aliyu ya kalleta yace to maza ki
cinye shi yanzun nan." idonta yayi
rau-rau alamar sonyin kuka. Shikuwa
sai ya jingina da kujera ma ya
lumshe shanyayyun idanuwansa
kamar zaiyi barci. Ba yanda zata yi,
haka ta rinka tura dankalin nan da
kwai tana shan ruwan shayin.
Cikinta ya cika taji kokarin yin amai
take yi, tace a hankalin cikin sanyin
muryanta, "yaya ya dago kai yayi
mata wani kallo, bata iya fada masa
komai ba, ta sake sunkuyar da kanta,
ya sake lumshe idonsa.
Haka taci gaba da ci tana hawaye,
saida ta cinye du. Dakyar ta iya tashi
tsaye, tace yaya na cinye, na tafi? Ya
bude ido daya yayi mata alama da
hannu wai ta tafi. Ta fice inda direba
yake jiranta ta shiga ta tafi.
Mansura tace gaskiya Aliyu kana
matsawa yarinyar nan, da nice saika
bata min rai kace ina takurawa
kanwarka." ya bude ido daya yace
karki manta shekaranta goma sha
daya, yanzu ta shiga sakandari aji
daya, har yanzu ita yarinya ce, idan
bana matsamata taci abinci sai
yunwa ta kamata."
ta tabe baki tana gunguni, "in rashin
cin abinci ne ai a wurinka ta gado,
tunda kaima baka cin na gidanka."
ya kwanto akan cinyarta yace, kiyi
min da kanki mana, du rashin
dadinsa ai zanci. Amma zaki rinka sa
tsohuwar mutane wahalar girki,
sannan kisa wata yarinya daban itace
mai bani abinci, kallon yarinyar nan
kadai tayar min da zuciya yake."
ta zumburi baki bata ce komai ba, ya
shafa cikinta yana cewa, "i luv u
baby, yaushe zaka iso kaga
daddynka? Tace ai kuwa zai jima
baiga daddyn ba, sai nan da wata
biyar." ya gyada kanshi, Allah kawo
minshi lafiya."
tadan rankwafo kanshi tace, "Aliyu
dan Allah zaka danyi min tausa?
TATTALIN SO 1**12
ALIYU dan Allah zaka danyi
min tausa? Yace nikuma me zakiyi min? Tace
bakomai." yace to kyaleni bacci nake ji." ta ture
masa kansa akan kujera, tace to dagani naje na
kwanta." yau alhamis karfe biyu direba ya dauko
zainab daga makaranta, saboda yau basuda
islamiya, shiyasa basu kai shidda ba. Ta shigo
tana jan jakartata, ta zube a falo tace "wash!
Aunty sannu da gida, ya bybynmu? Mansura tace
gashi nan dai yana ta min zillo. Aunty ki bashi
abinci yaci yunwa yake ji, inya ci zai daina yi
miki zillo." ai naci abinci zeey, kin zata ni irinki
ce sai anyi min dura ina kuka? Zainab tayi saurin
mikewa, bari na tashi kada ya shigo ya ganni
anan ya kuma sani cinye abincin daya fi karfin
cikina." tayi dakinta suna dariya. Da mangariba
ni'ima tazo gidan, sukayi tsalle suka rungume
juna suna masu jin dadin ganin juna, kamar ba
dazu suka rabu a makaranta ba. Suka zauna a
falo suna dariya. Ni'ima tace auntyn mu ina wuni,
ya babyn namu? Lafiyarsa kalau gashi nan yana
jinki." ni'ima tace zainab kinsan gobe ne fatin
zara'u yusuf shidda na yamma, ya zamuyi wajen
tafiya, don yanda muke da zara'u dole ne mu
fasa fatin nan? Zainab tace, wallah yaya ni'ima
ina so in rakaki, to amma ya zamuyi da yaya,
dama ya tafine da sauki, to shi sai ranar littinin
da safe zaiyi sammakon tafiya kaduna kan bakin
aikinsa." ni'ima tace, "ai dolene ma kije zainab,
tare fa nayi mana ankon fatin, har gwagwaron,
har takalimin da not din iri daya ne. Kuma yanda
zara'u take sonki, ke wallahi kin fiya tsoro, ba sai
kice masa zaki zo gida ba sai muyi tafiyar mu ta
gida." mansura tace amma ni'ima anyi saurin
yiwa zara'u kawarki aure da wuri, shekararki sha
bakwai fa? Koda yake daga ganini zara'un nan ta
girmeki, Allah ne dai ya hada kaunarku." ni'ima
tace shekara biyu fa ta bani, yanzu da ita fa
zamuyi candy, wai mijin zai barta ta karasa a
gidansa." to saurin na meye? Inji mansura, saura
wata shidda fa kuyi candyn, da ya kyaleta ta
karasa ba shikenan ba." ni'ima tayi dariya tace
tsoro yake yi kada ayi masa kwace, tafiya samari
daya wa." talatuwa ta shigo tana jera musu
abinci, ni'ima ta bude jalof din taliya ce da
farfesun kifi. Ni'ima tace zubamin jalof din kadan
da farfesun." talatuwa ta zuba mata. Zainab
kuwa farfesun kawai ta diba, ta debo musu
fantar gwangwani a firij. Ni'ima tace, zainab wai
ke wace iri ce? Ban taba ganin makiyin abinci ba
sama dake, yanzu kuma inkinci wannan shikenan
saida safe ko? Tace "a haba yaya zai taho mana
da cake da icream. Ni'ima tayi tsaki tace,
shikenan abincin naki." tace don Allah aunty ki
rinka yi mata fada, shiyasa kullum gata nan
kamar a busheta ta fadi. Mansura tace ai tasan
karonsu da yayanku, saina shiga gaya masa
tukunna." talatuwa ta dawo da tangaram a rufe,
da gasasshiyar kaaza aciki da mansura tasa
agasa mata. Ni'ima tace kai aunty ni aida nasan
da wannan ai bazan ci farfesun ba, ba ruwanki
aunty, abinda kike so kici shi zaki ci. Muma dai
Allah ya aurar damu, ina daga kwance aita yimin
komai." mansura tayi dariya tace, ke kuma
abunda yake baki sha'awa kenan. Suka fara cin
kazar suna hirarsu, zainab ta fara cire hannunta
waita koshi, ni'ima da mansura kuwa har kashi
saida suka taune. Ni'ima ta kwalawa talatuwa
kira tazo, "gani. Kije ki gayawa direban gidan nan
gani nan fitowa zai kaini gida." talatuwa ta fita
da sauri. Ni'ima ta mike tana yafa mayafinta da
jaka, zainab ta rike hannunta tace, "don Allah
yaya ni'ima ki bari sai anjima kya tafi kinji? Tace
a'a zainab gwanda na tafi, kinsan yanzu yaya
yana kan hanyar dawowa gida, kada ya gane ni
nazo najaki ya hanaki zuwa goben." tace to
shikenan saina zo goben. Ta rakata har mota ta
tafi. Sannan ta dawo ciki ta wuce dakinta, alwala
tayi ta tayar da sallar ishsha. Aliyu ya shigo ya
wuce dakinsa, sai da ya watsa ruwa ya dan
shafa lotion a jikinsa, yasa kananan kaya, ya fito
falo yana kallon tashar zee-aflam, suna wani
tsohon film mai kyau. Mansura tana gefensa tana
cin tufa, zainab ta fito daga daki ta durkusa a
gabans, tace, yaya sannu da zuwa." ya amsa a
hankali. Taci gaba da tsugunnawa tana so ta
tambayeshi zuwa gida gobe ta rasa ta ina zata
fara. Ya kula da ita yasan akwai abunda take so
ta tambaye shi, don haka sai yaci gaba da
kallonsa ya dauke kansa daga bangaren tana
zaune tana zaune tana wasa da yatsun hannunta,
tace "yaya. Yace "uhm! Ba tare da ya kallo taba.
Saita yi shiru ta kasa cewa komai. Shikuwa yana
jingine da kujera ya lumshe ido yana kallo kamar
ma baisan da zamanta a wurin ba, ta sake cewa,
yaya don Allah gobe zanje gida. Yace me ake yi
a gidan? Tace bakomai. Yace to bazaki jeba." ta
sunkuyar da kanta sai hawaye kawai itada bata
da wahalar yin kuka. Mansura tace don Allah ka
kyaleta taje." yayi mata shiru kamar baiji abinda
tace ba. Mansura tace, ni tsiyata dakai kenan, sai
ayi ta ma magana kayi shiru kana jin mutane
kamar wani kurma. Ko motsi bayyi ba balle yasan
dashi take. Zainab ta mike a hankali zata wuce
daki, ya kirata "zainab." ta juyo da sauri tare da
amsawa na'am yace "don nace bazaki jeba shine
kike kuka?
TATTALIN SO 1**13 TA juyo da sauri tare da
amsawa na'am. Yace "don nace ba zaki gidan ba
kike kuka? Tayi saurin girgiza kai. Yace bakida
baki? Tace a'a ta koma ta durkusa a gabansa
tace, "yaya dama bikin kawar yaya ni'ima za'ayi,
shine zan rakata." yace "to me ya hanaki ki gaya
min gaskiya? Tace, "don Allah yaya kayi hakuri
ba zan sake ba." ya jinjina kai. Tace yaya naje
goben? Ya daga kai. Amma kada kiyi dare." tayi
murmushi, "yaya nagode, Allah ya saka da
Alheri." tamike ta shige dakinta tana murna. Da
safe a makaranta zainab take gaya wa ni'ima
yaya ya barta zata zo. Ni'ima tayi murna, tace
"to ki taho da wuri dai. Bayan sun tashi daga
makaranta, karfe biyar na yamma ni'ima ta bugo
wayar mansura tana neman zainab. Zainab din
tana karba ni'ima tace, "haba zeey, ki sauri kizo
man biyar fa tayi. Zainab tace, "nayi wanka na
gama kwalliya, yaya nake jira ya fita nasa kayana
na taho. Tace baya barki ba ki fito ki taho kawai
mu tafi. Tace mata, cewa fa yayi kada na dade,
to kinga gwanda yasan ban taho da wuri ba.
Tace eh to gaskiya hakane. Yauwa kingan shi
can ma ya fitarsa, yanzu direba zai kawoni.
Wajen fatin ya hadu, ango da amarya sunyi kyau
kamar fure, sai walwali suke suna sheki. Ni'ima
sai kaiwa da komowa take a matsayinta na
babbar kawa, du inda tayi kuwa zaki ga idanuwan
samari a kanta, saboda ni'ima ta zama budurwa
kyanta ya kara fitowa, ga gwalli ga iyayi. Su
masu sabis da aka dauka sunata kaiwa mutane
abinci dasu swan, lemon kwali dana gwangwani.
Jama'a suna cin abinci Ali jita ya saki kida, tuni
zakin kidansa yasa jama'a suka fara kada kai.
Amarya da ango suka shiga filin rawa, nan fa
kawaye da abokan ango 'yan uwan amarya da
'yan uwan ango, aka shiga filin rawa aka rinka
watsi da naira kamar ba a san zafin nema ba.
Hankalin zainab ya tashi ganin har takwas na
dare tayi, ta rinka damun ni'ima ta taho su tafi
gida. Ni'ima tayi tsaki, waike meye hakane? Ki
bari agama basa mu tafi ba. Zainab tace um-um
yaya ni'ima, kinsan halin yaya, kizo mu tafi,
ni'ima tace ke wallahi kin fiya matsala, saika ce
wata matar aure, kita faman jin wannan tsoron,
bafa abunda zaiyi miki. Tace um- um, nidai kizo
mu tafi bana son bacin ran yaya, wallahi du saina
ji na damu." dai- dai lokacin da Ali jita ya saki
cashiyar karshe ni'ima ta riko hannun zainab
suka fice suka shiga motarsu, direba ya kawo su
gida. Saida aka sauke zainab sannan ya wuce da
ni'ima gida. Yana zaune a falo yayi zaman nasa
na kasaita kamar wani basarake, ya lumshe ido
daga gani tunani yake yi, mansura tana kwance
da littafi tana karatu, zainab tayi sallama ta
shigo, mansura ta amsa sallamar tare da cewar
"kun dawo? Tace mun dawo aunty." tace yaya
sannu da gida." ya bude ido daya yace sai yanzu
kuka ga damar dawowa? Bance ku dawo da wuri
ba? Ta marairaice, "don Allah yaya kayi hakuri
bazan sake ba." ya daga kai "shikenan tashi kije.
Ta mike tana hamdala a ranta da abin yazo da
sauki. Ranar littini da asuba Aliyu ya nufi kaduna
bakin aikinsa, sai kuma ranar jumma'a da yamma
zai dawo. Kwanci tashi asarar mai rai, cikin
mansura ya shiga wata tara harda kwanaki, tana
zama dakyar tashi da bisimillah. Ranar jumma'a
da mangariba Aliyu ya iso, bai samu wata tarba
ba, sai dai mansura ta langwabe masa bata da
lafiya, sai kuka take yi masa. Shikoma du ya
wani rikice, don shi kukan yaro ma baya so bare
na babba. Ya kwasheta suka nufi asibiti, raki
take yi da ihu tana murkususu acikin motar.
Zainab kuwa sai hawaye take yi, tana cewa
aunty kidaina ihu salati zakiyi. Tun a motar Aliyu
yayi waya gidan su mansura da gidansu. Suna
isa asibiti aka shigar da mansura dakin haihuwa,
Aliyu yayi tagumi yana sauraron ikon Allah,
yayinda zainab ta dukufar da kanta acikin
gwiwarta tana kuka kasa-kasa. Tana tuna
lokacin
da suka kawo mamanta acikin irin wannan halin,
wanda haihuwarce sanadiyar mutuwarta, 'yan
gidan su mansura sun zo. Yart da kishiyar
babarta. Can saiga ummi tazo, zainab ta tafi ta
kankame ummi tana kuka, ummi ta rinka shafa
kanta tana rarrashinta. Wani ihu da suka ji
mansura tayi shine dai-dai da dan ya fado. Nurse
din ta garzayo da gudu tazo ta kwantsama musu
labarin haihuwa, tuni kowa ya washe baki ya
daga hannu sama yana yiwa Allah godiya. Sun
shiga dakin anata yiwa juna barka da yaba kyan
yaron. Aliyu ya rungumeshi a jikinsa yana maiyi
masa addu'a da fatan Allah ya raya shi. Washe
gari da safe ka sallamesu kasancewar mai jego
kalau da ita da babyn. Gidan ya cika da 'yan
barka 'yan uwan Aliyu dana mansura.
khamis Idris
TATTALIN SO 1**14
GIDAN ya cika da 'yan barka 'yan uwan
Aliyu da 'yan uwan mansura. Sadiya ta
taho tinkis-tinkis dana ta tsohon cikin,
ni'ima da zainab suka rungumota suna
murnar ganinta. Dakin mai jego sai kamshi yake.
Kowa yazo barka zainab ce
zata karbeshi da farin cikinta, ta dakko
masa jaririn. Ko yaushe yaro yana
rungume ajikinta, kamar kada ta bawa
kowa." ranar kwana hudu aka kawo
kayan barka a katuwar akwati, kayan jariri ne
tsala tsala masu kyau, da dan
jeans da shet na yara, takalma, safofi,
fidoji, saitin shawul da tawul, barguna
masu laushi.
Kaya ne masu kyau da tsari duk 'yan
waje. Sai karamin akwati kayan mai jego ne,
turmin super holllan biyu, leshi biyu,
shadda galila mai tsadar guda daya,
kowanne da mayafinsa, sai takalma da
jaka kala bibbiyu.
Ya bawa ni'ima da zainab da sadiya
super holland biyu su uku, ya karawa zainab da
galila anyi mata haddaden
dinki aikin sama mai tsalelen kyau.
Da mangariba Aliyu yana dakinsa,
mansura ta shiga da jaririn, Aliyu ya
karbeshi yana murmushi, sai shafashi
yake yana murmushi. A zuciyarsa kuwa godiya
yakewa ubangiji daya bashi
kyautar da duk duniya babu wanda ya isa
ya baka kyautar da sai Allah.
Mansura tace Aliyu nazone akan
maganan shirye-shiryen suna. Yace uhm!
Me da me zaku yiyyi? "inaso da yamma ayi
walima, da daddare
mu fita fati a daula hotel, sai bokitai da
manyan robobi da kalanda, du za'a
rarraba a wajen.
Yace za'ayi komai amma banda fati." ta
wani harzuko, haba don Allah don Annabi, wallahi
ka fiya yawa, ya zaka ce
ba za'ayi fati ba, alhali ni inaso na burge
saboda kawayena zamu kakko makadi
don kawata fatin, kuma zaka kawo min
matsala.
Yace albarka nake nemarwa 'ya'yan, bana so su
taso akan harkar shaidanci.
Ta mike ta kama masifa, kai dai kawai
kana so ka wulakantani a gaban kawaye
na, haka wai haihuwar fari dan kwaya
daya amma bazaka saki kudi ayi
bushasha ba, don kasan bakai kasha wahalar
haihuwan ba.
Ya daga mata hannu yace, ya isheni
haka fita ki bani waje." ta fito tana
kunkuni tare da bakaken maganganu. Ya
dafe kai don jin kansa yana sarawa,
mansura zata haddasa masa ciwon kai, shi baya
son hayaniya.
Ta dawo daki tana kunkuni da fadar
maganganunta. Saratu yayarta tace,
meye kuma?
Mansura tace kinji wai baza ayi fati da
kida ba. Saratu tace, ai wannan wulakanci ne, ya
mayar damu kananan mutane bayan ni
har na buga kati na fara rabawa?
Lawisa kawar mansura tace, kawai inba
zai bari mu tafi ta nan ba, ba saiki ce
masa zaki je kiyi sunan a can ba, inyaso da
daddare muyi tafiyarmu fatin, ai mun
riga munyi dai ai shikenan." saratu tace
ita wallahi jeki ce masa zaki tafi gida
zamuyi sunan acan.
Mansura tace wallahi yace na fice na
bashi waje, idan na koma nasan halin zuciyarsa,
sai ya iya marina.
Saratu tace tabdi ya mareki? Ai kuwa
wallahi daya mari aurensa.
Lawisa tace, tunda kuwa kika nuna kina
jin tsoronsa kinsha wulakanci iri iri.
Nan suka hadu sukaita aibata shi, suna fadar
maganganu son ransu. Zainab
kuwa ranta ya baci, kawai saita sa kuka.
Saratu da lawisa suka hau yi mata
masifa. Kinji yarinya da munafunci, dan
uwanki yayi ba dai-dai ba zaki hanamu
fadane munafuka? Kiyi kukan jini bana hawaye
ba." zainab ta mike tayi dakinta
tana kuka. Lawisa ta rike baki, tace ahaka
kike zaune da wannan yarinya mai
miskilancin tsiya, har wani kuka take don
anfadi laifinsa.
Mansura tace kuma wallahi baki ga yanda yake
takura mata ba, ni har
tausayi ma take ban, don inyana gari
bata da sakewa" saratu tace "ai wani irin
mutum ne, shiko fuska baya saki don
kada akawo masa raini." ranar suna dole
mansura ta hakura da maganar fati, akayi taron
suna da yamma akayi walima ta
burgewa da bajinta, mai jego sai shiga
take tana fita tasa wannan ta cire tasa
wancan ta cire.
Yaro yaci suna Ahmad, sadiya da ni'ima
da zainab, les din da Alh ya dinka musu suka
saka, da yamma a wajen walima
suka sa super ta wajen Aliyu. Can
jimawa zainab ta canjo da shaddar da
Aliyun ya dinka ma, sadiya tayi mata
daurin gwagwaro akanta, tayi kyau,
kamar ka saceta ka gudu. Sadiya da ni'ima sun
cancanja shiga,
suma dai shadda ce amma kalar ta kowa
daban. Sadiya ta rinka raba kalanda mai
hoton zainab tana dariya rungume da
jariri, kaandar tayi kyau
kowa ya karbi kalandar ya kalla saiya yaba da
ita.
Haka su saratu da lawisa su kaita raba
robobi da 'yan kananan bokitai. Da haka
taro ya tashi lfy, kowa yana san barka.
Kayan barka da atamfofi data samu, da
rigunan jarirai kamar wadda zata bude shago.
Ba ruwanta kibarta kawai take yi, taci mai
kyau tasha mai kyau, ta hau gado ta
mimmike ba ruwanta da harkar Ahmed,
yana wajen masu rainonshi su zasu hada
masa madara su bashi yasha, su bashi ruwa,
idan ya koshi su goya shi.
Shan nononsa sai lokaci lokaci, saidai
idan ta jiyo kukansa ta kirawo 'yan aikin
nata ta balbalesu da masifa, mai suke yi
masa yake kuka? Suyi ta faman rantse
rantse cewar, wallahi basu yi masa komaiba,
sannan zata karbeshi ta bashi
nono, tasa su goya shi suyi ta faman
jijjiga har sai yayi barci.
TATTALIN SO 1**15
TASA su goya shi suyi ta faman jijjiga shi
har sai yayi barci.
Sai dai fa du sanda zainab ta dawo daga
makaranta, tana yin sallah zata karbo
ahmad daga wajen masu rainonsa, taita yi masa
wasa tana tarairayarsa, tai
tayiwa mansura naci da magiya dole
saita karbe shi ta bashi nono ya sha ya
koshi.
Ahmad yayi wayo sosai, yayi mugun sabo
da zainab, don har yafi ganeta akan mamanshi
don zainab har ta iya yi masa
wanka, ta shirya shi cikin kaya masu
kyau, tasa mishi turare yaita kamshi. Har
mansura taita sha'awarshi, abinda ita
lalacinta da son jikinta bazai barta ta iya
ba. Du da zainab din ba wani lokacine da ita
ba, inta fita tun takwas na safe sai shidda
na yamma take dawowa, idan sun taso
data dawo gida inta ci abinci tayi sallah,
tayi wanka tasa kayanta, saita dakko
yaronta ahmad taita yi masa wasa tana
lallabashi, har lokacin bacci ta kaiwa
mansura shi ta bashi nono yasha ya
koshi ta taho dashi dakinta ta kwantar
dashi a gado, ta canja kayan barci tayi
musu addu'a taja bargo ta rufe su, ta
rungume ahmad a jikinta suyi barcinsu. Talatuwa
data ke tayaa kwana idan ya
farka cikin dare, ita zata dakko shi ta
bashi madara da ruwa, tasa shi shi
akafada ta jijjiga shi yayi gyatsa ya koma
baccin shi, saita shimfida shi a gaban
zainab ta rufe su. Itama ta koma baccinta du
sanda Aliyu yazo weekend, yana kula
da abinda yake faruwa da yaronshi da
yake kokarin zama marayan karfi da yaji.
Sun sha fada da mansura akan sakarwa
masu aikin dansa data keyi. Yasha korota
intaje kwana dakinshi, yace saita dakko mishi
dansa. Saita rabu dashi ta tafi
dakinta tayi kwanciyarta.
A hankali ya fuskanci tsananin son da
zainab take yiwa ahmad, ya gano zainab
ce take kwana da ahmad ba yan aiki ba,
sai ya samu nutsuwa a ransa, yayi wa Allah
godiya, don yasan zainab tafi
mansura tarbiya da sanin ya kamata,
yasan danshi zai taso da tarbiya matukar
yana tare da zeey autarsu.
Yau asabar, Aliyu yana gida, zainab babu
makarantar boko, wajen tara na safe tayi wa
ahmad wanka a bahon shi, Aliyu yana
kallonta yana yaba baiwar da Allah yayi
wa yarinyar, 'yar da har yanzu bata cika
shekara goma sha uku ba, amma tana da
nisan hankali da tunani wanda 'yar
shekara ashirin da biyar bata dashi, wato
mansura.
Ta gama yi masa wanka, ta nade shi a
tawul tana yimi shi wakar data ke yi masa
inyana rigima. Wayar falonce tayi kara,
zainab ta daga tace "hello yaya ni'ima."
daga can ni'ima tace yau ne fa yinin kawata
murja sule, kizo da wuri muje."
zainab tace don Allah yaya ni'ima kiyi
hakuri, ba zan samu damar zuwaba."
ni'iman tace saboda me?
Zainab tace, yaya ni'ima wallahi ban
tambayi yaya ba, kuma kinga yau nadan samu
hutu ba boko, ina so na wuni da
ahmadina, ba zan iya fita waje na barshi
ba.
Ni'ima tace kinfiya shirme zainab, ina
uwarsa ko zaki zama mai rainonta ne? Ita
ba unguwa take ficewa ta barshi ba, sai ke zaki
zauna ki rinka yi mata wahala
dashi? Tace "haba yaya ni'ima kada ki
manta ahmad dana ne gudan jinina ne,
don wallahi basu da maraba da abunda
zan haifa, tunda dan yaya nane. Ina
ruwana da halin uwarsa, tsarina daban nata
daban. Kiyi hakuri wata rana na
rakaki, kinji yaya ni'ima?
Tace to shikenan auta, ba komai ki
shafamin kan ahmad ki sumbace shi, kice
masa inji momynshi."
zainab tayi dariya tace, "to bar kiji ma nayi masa
kafin ki kashe wayar." ta
suabcin kumatun ahmad tace yarona
momynka tace nayi maka, tana kuma
gaisheka, inta dawo daga gidan biki zata
zo ganinka." ta ajiye wayar tana dariya.
Ta zauna ta gama gogewa Ahmad danshin
jikinsa, ta shafa masa manshi, ta
shafa mashi farar hoda, sannan ta daga
wuyarsa da hammatarsa ta zazzaga
masa, ta shafa masa kasan wuyansa da
hammatarsa, tasa masa kwalli, tasa mai
pampas, tasa masa farar ves, tasa masa safa da
dan takalminsa, ta shafa masa
turarensa. Shirin yaron yayi kyau, gashi
yana ta kamshi.
Ta dama mishi madararsa a fida daidai
cikinsa, tasa masa abaki ya kama zuka,
ya shanye tas, ta bashi dayan fidar mai ruwa a
ciki ya sha, ta dora shi a kafadarta
tana shafa bayanshi, yaron har yayi
gaytsa.
Ta dago shi tana yi masa wasa yana
dariya, daga bayanta taji ance " bani
yaron naki na taya ki raino." ta juyo da sauri tace
"lah! Yaya yanzu ka shigo?
Don ita kwakwata dazu bata ganshi ba,
don ita inta na tar da Ahmad bata
tunanin komai sai yanda zata kula da
yaronta. Ta durkusa ta mikawa Aliyu shi,
ta gaisar da Aliyun ta mike tayi dakinta itama ta
shiga wanka. Tana fitowa ta
goge jikinta da tawul, ta zauna gaban
madubi tana kalkale jiki.
Zainab tun tana karamarta 'yar iyayi ce
da son kwalliya, gata da son kamshi, da
kudinta ma sayan turaruka take yi bare yaya
Aliyu yana sai mata, hakama
Abbansu ko daddynsu suna bata.
Ta tsara kwalliyarta cikin wani fine les
mai fulawoyi, bashida nauyi, riga da siket
ne filet, ta kafa daurin dan kwalinta daya
kara fitowa da kyanta, ta fesa turaruka sai
kamshi take zubawa.
Ta fito falo har yanzu Aliyu yana zaune
yana lallaba Ahmad da yayi barci, tace
yaya yayi barci kawo shi naje na
shimfede shi. Ta dan marairaice masa
cikin shagwabarta tace.
TATTALIN SO 1**16
TA DAN marairaice masa cikin
shagwabarta, tace don Allah yaya
kabarni naje gida.
Yace meyasa kike so ki koyi karya ne, ba
inaji ni'ima tayo miki waya zakuje gidan biki
bane?
Tayi kasa da murya cikin shagwaba tace,
wallahi yaya ba gidan biki zanje ba, aina
gaya mata bazan jeba, tunda ban gaya
maka ba. Daman su hajiya zan kaiwa
Amadina su ganshi." ya gyada kanshi, "kuje
direba yana waje sai ya kai ku." tayi
murmushi, yauwa yaya nagode." ya
gyada kanshi ya jingina da kujera yana
ta kallonta, tana ta hada fidar Ahmad ta
ruwa data madara, da dan fulas dinshi na
ruwan zafi, ta debo masa kaya kala biyu da
pampas guda biyu ta zuba acikin jakar
goyonshi.
Wannan page ya dan samu matsala yayi
baki
kwanci tashi ba wuya, zainab ta zama
budurwa, tana da shekara goma sha bakwai,
yanzu tana aji shidda a
sakandare. Zainab kyanta ya kara fitowa,
tana da iyayi da kwainane, akwaita da
tsabta dason gayu, don du wata saita je
salon, bata gajiya da kunshin tafin
kafanta ko zanen fulawa ta lalle. Ta fiya sanyi
magana da marairaita; saiki
zata sangarta ce da shagwaba tayi mata
yawa. Idan tana magana mace ma
burgeta take yi bare namiji, akwaita da
iyayi da yauki da yanga.
Abinda yafi fisgar maza da hura wutan sonta a
ransu, inhar zata shiga waje
saita samu maza masu sonta. Amma
bata iya tsayawa ta sauraresu, domin
tana tsoron yayanta, tana gudun abunda
zai bata masa rai, bata so tayi masa laifi.
Don waya ma ya hanata rikewa, sai wata rana
data je gida Abba ya bata wata mai
kyau, amma ta rinka dari-dari da tsoron
gaya masa. Sai Ahmad ne ya dauka da
gudu ya kai masa yana gaya masa
Abbanshi ya bawa aunty maminshi waya.
Saida ya mata gargadi sosai akan in ta sake yaji
ta bawa wani saurayi numbar
wayarta sai ranta yayi mummunan baci,
don haka take kiyaye wa. Ni'ima anzama
babbar budurwa sosai, tana karatun
diploma har ansa mata ranar aure har ma
ankusa bikin. Aunty sadiya tanada 'ya'ya biyu,
hafiz da
sajida. Mansura kuwa tun daga Ahmad
bata sake haihuwa ba, tace dama saiya
shekara biyar, toh gashi yanzu ya
shekara biyar din. Zainab yarinya mai
hakuri, ga hankali da nutsuwa, tana da kwazo,
don tayi saukar qur'ani yanzu ta
juya hadda. Yau asabar tana tasowa a
daga islamiya ta ware kitson kanta tana
son zuwa salon, harta fara tunanin ta
yanda zata tambayi yayan nata fita, bata
son yayi mata fada. Zainab tayi murmushi tace
don Allah
aunty gayawa yaya zanje salon. Tace
"bazan je inda yake ba munyi fada." tace
haba aunty, don Allah kije ki lallabashi ki
bashi hakuri, ki tambayo min nidai na tafi.
Ta tabe baki tace hakuri? Hakuri fa kika ce? Don
ya kara wulakantani." zainab ta
kalleta cikin mamaki, Ahmad ya fito da
gudunshi da hijabin nata a hannunshi
yana cewa "aunty mami gashi mu tafi
kinji. Tace jeka gayawa Abbanka cewar
zanje salon. Dai-dai lokacin Aliyu ya shigo,
Ahmad yaje ya rike hannunshi
yana gaya mishi "Abba inji aunty mami
wai zamuje salon. Ya dago kai ya kalleta,
"saida kika dauki mayafin tafiya sannan
zakice a gayamin."
ta durkusa cikin marairaice warta, tace don Allah
yaya kayi hakuri, tun dazu nake
jiran fitowarka, ba mayafin tafiya
nadauka ba."
ya gyada kanshi kuje Allah kiyaye.
Tace yaya na gode. Ya bawa Ahmad
kudin salon din, suka tafi direba yakaisu. Suna
yin fakin a gaban shagon salon din,
suna fitowa daga kanta da zata yi karaf
idanuwanta suka hade dana wani dan
kyakyawan saurayi daya zuba mata ido,
tayi saurin kawar da kanta, taja hannun
Ahmad suka shiga ciki, a gurin suka wanke mata
kai suka gyara mata shi,
suka yanke mata farce, suka goge mata
kafa, du da karfa tata sumul take kamar
ta jarirai. Ta fito da youghot da biski ta
bawa Ahmad don kada yaji yunwa.
akayi mata kunshi kunshi sarka a hannu da kafa,
nan da nan ta canja ta kara yin
kyau kamar tauraruwa. Tana fitowa daga
wajen idanunsu suka sake haduwa, yayi
mata murmushi ta dauke kanta da sauri,
ya taso ya tari gabanta. Yace "don Allah
ki taimakamin ki saurareni ki gaya min inda
gidanku yake nazo na sameki a
gida."
ta mika masa katin yayanta, tayi saurin
shigewa motar direba yaja suka tafi.
Saurayin nan ya sumbaci katin data
bashi yana mai jin dadi da farin ciki haduwarsa
da wannan beb
din.
Suna tafe tana tunanin saurayin data
gani, gaskiya ya hadu, itace da tsayawa
yau harda bawa saurayi katin yayanta,
wyarta ce tes ya shigo, tayi mamakin waya turo
mata tes. To kodai ni'ima ce?
Ta bude tes din, bakuwar lambace bata
san mai lambar ba, ta fara karanta sakon
kamar haka.
"i 've been lucking 4 a chance to tell u my
message, i luv u." mamaki ya kamata bata
ankara ba ta
kuma jin shigowar wani sakon, ta bude ta
fara karantawa.
This secret has been in my heart enough
now i want to make it.
Ta bude dayar da suka shigo tare, i told you that
i want u to be my wife" a'a
wannan wane irin kalamomi ne masu
rikitar da zuciya, waye wannan? Ta sake
dubawa ta maimaita karantasu gaba
daya. Ba suna to waye wannan? Ita dai
tasan ba wanda suka hadu dazu bane, donshi
bata bashi lambar wayarta ba.
Kuma tasan ba wani namiji data bawa
lambar wayarta, to ko waye?
TATTALIN SO 1**17
Har suka karaso gida zuciyarta tana cike
da tunane-tunane, waye wannan?
Meyasa ya boye mata kanshi bai fadi
sunanshi ba?
Ahmad yayi barci, ta saboshi akafada ta kwantar
dashi kan kujera. Mansura ta
kalleta tace ammafa kinyi kyau, saide kin
dade." ta zauna tace "hum! Kedai ki bari
aunty, saurayi fa nayi a wajen, kuma
harna bashi katin gidan nan, ina tsoro
kuma kada yazo yaya yayi min fada. Mansura
tace a haba wane irin fada
kuma? Ai yanzu kin wuce wannan ajin.
Don ma keba wayayyi bace kanki a duhu
yake, amma yanda kike kyakyawar nan
gaki danyar budurwa shine dai-dai fara
wankar samari, toke sai rashin waye wa, kullum
kina like a gida, idan zaki fita ki
zurma hijabi saika ce gyatuma. Don Allah
ki waye.
Tace, to aunty wai ya kike so nayi ne,
wace iri ne ce wayewar?
Haka dai ta ringa ce mata tanasa matsatsun
dinki ita kuma zainab tace ba
haka Allah yace ba, ka waye akan
addininka shine wayewa, aunty sadiya ce
ta shigo da sallama da kanwar mijinta
yasira, a'a auntyn mu barka da zuwa.
Zainab taje ta rungumeta, tace yasira rabon goron
harda aunty kuke yi ne?
Tayi dariya tace to ya zanyi tace da ita
za'a kawowa zeey autarsu na fati.
Zainab tace fati yasira, anya zan dai zo
miki yini, yaya bazai barni naje miki fati
ba. Sadiya tace haba don Allah, ke bari zakiyi
yasan zakije? Kice masa gidana
zaki zo, ni'ima ma nan zata zo saimu tafi
tare, nayi muku ankon fati da
gwagwaronsa, harda takalmi set din
kayan."
zainab tasa ihu, "sai auntyn mu, kedai kina son
fito da 'yan kannenki.
A to inbanyi muku ba wa zanyi wa, ku
kenan fa kannen nawa mata, ai dole na
gyaraku.
Mansura tace, "ai wannan autar taku
saikin dage mata don taki wayewa, kullum kanta
a duhu yake.
Sadiya tana dariya tace ai laifin mijinki
ne, bakina kallo yke takura mana auta ba,
ki rinka hanashi kin barin ta da yake ta
sake.
Mansura ta kama baki tace rufamin asiri da
yayanku, idan nayi magana tawa ce
take yin zafi, ranar jumma'a wato ranar
fatin, mansura ta shigo dakin zainab
tace, "bazaki je ki fada masa maganar
fatin ba saiya fito? Tace don Allah aunty
gaya masa." tace kinsan in ni na gaya masa cewa
zaiyi inason koya miki yawo.
Ta mike bari naje, aunty kiyi min addu'a
Allah yasa ya barni." tace "to Amin."
yana shirin fita mansura ta kawo masa
jakarsa, zainab ta fito ta durkusa tace
"yayana. Bai kulata ba yace "uhm! Ya akayi?
Yaya dan Allah zanje gidan aunty
sadiya? Me akeyi a gidan?
Bikin kanwar mijinta ake yasira, shine
nake neman alfarma dan Allah yaya
kabarni naje. Ya daga kai kada ki dade. Tace to
yaya
nagode." yana fita ta tafi gidan sadiya,
direba ya kaita. A can ta tarar da ni'ima
suka rugume juna suna murna. Kinyi sa'a
'yar uwa ya barki."
kinganni dai, yayan namu ne sai a hankali. Amma
yau ba laifi fuskar tasa a
sake take. Hu! Aunty wannan material din
fa? Tana daga su tana yaba kyansu.
Tace Abban yasir ne ya kawomin su
tsaraba, amma naga sun zo akaya zan
sai muku. Yauwa auntyn mu kina burgemu fa.
Suka
gama tsra shirinsu na zuwa fati, wani
hadadden material ne da aka sake fito da
kyansa da wani dinki mai kyau.
Gaba daya su ukun sunyi kyau amma ba
kamar zeey da kamar don ita aka yoshi. Suna
bayan motar sadiya da mijinta suna
gaba. A gidan fatin suka bi bayan amarya
da ango suka rakata har mazauninta.
Yaron sa'adu bori yanata kida da waka
'yan mata sunata rawa daga baya aka
tsaya da kidan, babban kawar amarya tazo ta yi
addu'a tareda yiwa bakin da
suka zo barka da zuwa. Daga nan ango
da marya suka tashi suka ja zugar
kawaye da abokai suna biye da bayansu
har wajen masu sabis. Kowa shiyake
sabis din kansa. Zainab duk inda tyi idon mutane
ne akanta, ita kallon ya isheta,
don bata saba da irin wannan shiga ba,
ta saba kullum tana hijabi, to ita abunda
yafi damunta ma sha daya har tayi, tana
jin soron yaya fa.
Amma yaya sadiya da mijinta sunce har dakinta
zasu rakata su bawa yaya
hakuri.. Wata kawarta tazo taja
hannunta, dole saita yi rawa. A hankali
take juyawa, kusan maza hudu ne suka
rufa kanta suna mata liki.
Kamar daga sama yaya Aliyu ya diro wajen, saiji
tayi an damki hannunta. Ta
juyo a tsorace dan ta razana, ganin
yayanta ya hade rai kamar wanda bai
taba dariya, saita firgice ta tsorata. Ya
funciki hannunta yayi waje da ita, ya
bude mota ya turata ciki shima ya shiga. Ta
takure a tsorace take, saboda tasan
halin yayanta sarai, akwai zafin zuciya.
Aliyu ransa ya baci sosai ganin maza
suna yiwa zainab liki, ba dai sonta suke yi
ba? Wani abu ya soki kirjinsa, ya rinka
ganin bibbiyu a idonsa, yayin da motar ta fara
tangal-tangal kamar zata kifa.
Zainab ta fara salati ta baro kujerarta ta
rungume Aliyu tana ihu tana salati.
Tirkashi! Mu hadu a littafi na biyu,
waishin menene ya soki zuciyar Aliyu?
Download Tattalin So Littafi Na Ɗaya HausaNovel
0 Comments
Thank you for this comment