RANA D'AYA!
#RD
Love... King Miemiebee👄✨
RANA DAYA Chapter 35
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
Tareda Naja'atu Lawal Rijau Niger State
@Whatapp 08083232323 or 09060202323
PAGE 35
"Ka san Amal kuma ka yarda da ita? Lmao" wani kalan
dariyan rainin hankali ya saki "So kake kace ka fini sanin halin
matata ko mey Maza?"
"I dunno but I guess yes saboda komin yaya nasan Amal
bazata ta6a aikata wannan aika-aika ba."
"Mak'aryaci ne ni kenan? K'arya nakeyi maka? Is that it?"
"Ba haka nake nufi ba Triple A amma da hankalinta kam
Amal bazata ta6a aikata hakan ba, it's either she's possessed
or something baka tunanin hakan?"
"You mean you deny ba ita tayi wannan rubutu ba?"
"Ba wai nace ba ita tayi bane it's crystal clear rubutun tane
amma waya sani ko wani mental illness ne yake damunta
wanda idan ya tashi yake sanyata yin abubuwan nan daka irgo
saboda a gaskiya bana tsammanin kan Amal ya waye d'inda
har zatayi wannan abubuwa. Triple A kayi tunani mana kai fa
da kanka kake yabawa da irin kyawun halatayyar ta."
"Mental illness? Gani kake kaman tana da ta6in hankali? Just
so you know har asibitin mahaukata na kaita aka kuma duba
ta and you know what likitan yace ba abinda yake damunta
idan kuma tunanin aljanu kake nan ma na kaita gun Malami
anyi mata ruk'iya shima yace bata tattare da komai lafiyarta
k'alau so stop giving me lame excuses."
"Wow! But what's really wrong? Ka sameta kayi mata
magana? Kayi confronting nata? Maybe akwai wani 6oyayyan
al'amari."
"Mey zance mata? Besides kasan ni ba d'abi'ata bane yima
mutum magana idan yamun laifi idan shi hankalinsa be basa
hakan ba ya nemi tuba ba sede a cigaba da zama hakan."
"Kana nufin tunda abubuwan nan suka soma faruwa baka
ta6a yiwa Amal magana ba?" Ya tambayesa da mamaki
gaskiya ne mey hali baya canzawa ko shi yana iya tuna
lokacinda suka kusan shafe term d'aya (k'imanin watanni uku)
a makaranta shi da Afzal lokacinda suke boarding house basu
magana a sanadin wasu maganganun da abokansu suka je
suka shiryawa Afzal cewan Sultan ne ya fad'a. Shiko Afzal ba
bincike ba komai kawai ya hau kan magana ya zauna akai.
Kyat kawai Sultan yaga Afzal ya dai na yimai magana da k'yar
suka zo suka daidaita tsakaninsu. Tun daga wannan rana ya
karanci halin Afzal ko meye mutum yayi masa bayi ta6a
tinkarar mutumin da maganar sede yayita kallon meshi da
abun har zuwa lokacin da mutumin zey gano yayi kuskure ya
nemi tuba. Bayan nan Afzal ya kasance d'aya daga cikin jerin
mutanen da basu tsananta bincike game da duk wani abinda
aka fad'a musu wanda hakan yake babban hatsari. Su komai
aka same su aka fad'a musu d'auka suke su zauna akai ba
bincike ba komai wanda sam hakan be dace ba musamman
ma ga magidanci kamansa mey mata biyu. Tabbas yasan a
banza Afzal yake hukunta Amal baiwar Allan da bata ma san
mey tayi ba yanzu. Ashe dalilin da yasa ta zube tayi duhu
kenan bak'in ciki ne da tashin hankali ba stress na makaranta
kaman yadda tace ba. Allah sarki.
"Maza that's so unfair hukuncin nan da ka yanke yayi wa
Amal tsauri dayawa kuma wallahi bazan 6oye maka ba ba
haka ake ajiye gida ba, ba haka ake handling mata biyu ba.
Afzal da dayanzu ba d'aya bane, yaci ace ka zubar da
mumunan d'abi'ar nan naka na kallon mutum da laifi ka fara
tunkararsa da laifin da yayi maka kaji mey zece, kuma be dace
a matsayinka na mey mata biyu ace dan uwar gidan ka ta
fad'a maka abu kawai ka hau ka zauna akai ba kamata yayi ka
tsananta bincike ka zaunar da Amal kuyi magana kaji nata
6angaren labarin itama na tabbata akwai ababen da Nazeefah
takeyi mata wanda bata jin dad'insu amma ta za6i ta had'iye
wa kanta dan karta had'a kanku haba maza! Wallahi sam baka
kyauta wa Amal ba."
"Naji nasan bana tsananta bincike kuma bana confronting
mutum idan ya mun laifi amma wallahi akan Amal na fara yin
hakan bayan da Nazeefah ta irga mun komai nayi mata
magana."
"And mey tace?"
"K'aryata komi tayi abinda ya fi bani haushi kenan, tayaya
Nazeefah zata na sanin abubuwan da suke gudana a cikin
gidan nan idan ba wai kirarta ake ana sanar da ita ba? Ai
abinda zaka duba kenan."
"Wow! Ko ze iya yiwuwa hakan ne?"
"Hakan kaman ya?"
"Akan ba ita bace bata aikata abinda kake tuhumarta dashi
d'in ba."
"Are you kidding me? Ka zauna kayi tunani Sultan ko tsinke
na saya mata a gidan nan se naji labarin a bakin Nazeefah
how on earth Nazeefah zata san abinda ke gudana acikin
gidan nan idan ba wai kirarta ake ana fad'a mata ba? Ko so
kake kace tana da CCTV ne?"
"No bawai haka nake nufi ba."
"Then tell me, tell me how exactly would Nazeefah know of
everything da nakeyi wa Amal?"
"You have a point amma still da kayi mata uzuri sanin kanka
ne Amal yarinya ce, halan yarinta ke damunta ka sameta kayi
mata magana kaja mata kunne I'm sure zata saurareka ta
kuma daina."
"Yarinta ko rashin tunani? Wallahi da gan-gan takeyin komai,
and you seem to be forgetting her actual age, Amal is 21
years old Sultan she's nomore a child."
"Naji nan Amal bata kyauta ba tayi laifi, amma batun shigo da
course mates nata maza cikin gidan nan fa? Ka ga hakan da
idonka ne?"
"A'a amma ai 'yar aikinta ne ta fad'a mun."
'"Yar aikinta?" Yayi questioning nasa unbelievably '"Yar aikinta
fa kace maza?"
"Yes ba ita take gida ba kullum ai tana sane da shigowa da
fitan kowa."
"Amma Maza ka bani kunya, ban ta6a sanin kana da
k'arancin tunani haka ba se yau ashe baka fasa halinka ba har
yanzu wai tayaya ma zaka fara amincewa da abinda baka ji ba
bale ka gani? Wallahi zato zunubi ne."
"Ce maka akayi zato nakeyi? Clearly 'yar aikinta tace sau
biyu take ganin Amal na shigo da course mates nata har
ragowan snacks da drink data basu ma na dawo gida na tarar
ranan what else do you expect me to believe?"
"Ka tambayi me gadinka ne? Ka tsaya kayi wa ita Amal d'in
magana kaji labarin daga bakinta? You have to listen to both
sides before taking a decision Afzal dole ne ka zubar da
wannan halin naka kafin lokaci ya k'ure kazo kana nadama,
tabbas duk wanda baya tsananta bincike yana tattare da
babban hatsari bana son kazo kayi nadama daga k'arshe."
"Kana tunanin Safiyya zatayi ma Amal sharri ne? Meye ribarta
idan tayi hakan?"
"Kai kuma kana tunanin Amal zatayi maka k'arya ne da tace
maka ita bata shigo da na miji gidan nan ba? Wai taya ma
zaka fara amincewa da maganan mey aikinka akan na matarka
ne Afzal? A ina aka ta6a yin hakan?"
"A gaskiya ka bani kunya maza yadda kana ganin gaskiya
kake takewa."
"Ma tukun a ina ka tsinci wannan paper?"
"Cikin kayakina."
"Lmao cikin kayakinka? Wallahi ka bani kunya Afzal, it's so
unfortunate that you're my friend. Har kana tunanin Amal zata
rubuta wannan abu takuma sake ajiye maka shi acikin
wardrobe inda ze fi sauk'in ka gani? A tunani na sede ta 6oye
ba ta ajiye a inda zaka gani ba. Wallahi Allah this's a trap."
"Har wani marasa aikin ne ze zauna yayi wannan aiki? Kuma
har ya iya yayi irin rubutunta sak?"
"The world isn't a safe place and there are toxic people
everywhere so zan baka shawara ka zauna ka bi diddigin
lamarin nan idan ma da hali ka zaunar da Amal d'in da
Nazeefar da mey aikin nata da mey gadin naku duk gabad'aya
kayi musu tambayoyi ka kuma saurari both parties am very
sure zaka sha mamaki da sakamakon da zaka samu" yana
kaiwa nan ya mik'e "wannan kuma" yayi nuni da takardan
hannunsan.
"Duk da cewa rubutun Amal ne karara ajiki hakan baisa na
yarda itace ta zauna ta rubuta ba kuma koda ma ita d'ince zan
iya cewa tana da daman yin hakan tunda gashi a fili kake
nuna mata rashin k'auna da adalci ta hanyan yanke hukunci ba
tare da ka saurareta ba zan iya cewa abubuwan da kakeyi
mata su suka tunzira ta har ta zauna tayo wannan rubutu, kai
baka san the more kake k'untata mata the more kake sa take
tunanin masoyinta Abdul take kuma kewon sa ba? Ko ka
manta yadda kukayi auren nan ne Afzal? Yarinyar nan fa ba
wani sonka take ba, lami lafiya suke soyayyansu da saurayinta
suna building dreams nasu ka shiga tsakanin su haka dan ta
ceto ranka ta sadaukar da farin cikinta da abin alfaharin
zuciyarta. Kana ganin ta cancanci wannan walak'ancin da
kakeyi mata? The earlier the better Triple A it's time for you to
make things right idan kuma har bakayi ba toh ni zanyi da
kaina" yana kaiwa nan ya ajiye takardan ya fice.
Mugun d'aurewa kan Afzal yayi gabad'aya ya rasa meke
masa dad'i what if duk abubuwan da suka faru set up ne
kaman yadda Sultan ya fad'an amma ai kuma wannan rubutu
is real ko a mafarki aka nuna masa rubutun nan yasan na
Amal ne. Amma kuma idan har ita ta rubuta ai baza ta ajiye a
open place inda ze gani ba sede ta nemi wani 6oyayyan wajen
ta ajiye, ya Allah what's really happening? Yini yayi gabad'aya
ranan yana tunani ya kasa samun sukuni wajajen tara
hak'urinsa ya k'are. Maybe is about time ya tunkari Amal suyita
ta k'are.
D'akin ta ya nufa inda ya tsince ta zaune bakin gado tana
karatu da mamaki ta tsaya tana kallonsa ba tare da tace
komai ba. Takawa cikin d'akin yayi ya k'wace handout natan
kafin tace zatayi magana yaja hannunta ya mik'ar da ita ya
shiga janta waje.
"Yaya what're you doing? Ka sakeni let me go" ko sauraranta
beyi ba seda ya kaita tsakan d'akin nasu. Wardrobe ya nufa ya
zaro takardan har anan kallonsa Amal take yayinda zuciyanta
yake bugun d'ari-d'ari dan yadda ta tsure a tunaninta
gabad'aya dukanta yake shirin yi. Takardan ya bud'e a idonta
"rubutun waye wannan?" ya tambayeta?
"Rubutu na" ta amsa a takaice.
Sa mata yayi acikin hannu "here read it" d'agawa tayi ta shiga
karantawa layi uku ta karance ta shiga kad'a kanta yayinda
idanunta suka ciko dam da hawaye amma Allah ya isa
tsakaninta da Safiyya da Nazeefah. Tun a asibiti ta gano
Nazeefah ba sonta take har cikin zuci ba, tun anan ta gano
Nazeefah ba da zuciya d'aya ta d'auketa ba. Tun anan ta gano
Nazeefah is behind everything that has been happening to her
barin ma yadda ta dage ta rink'a nunawa Ummi cewa lallai-
lallai ita ce ta sa zuciyan Afzal ya buga. Ta sani ba wanda zeyi
mata wannan d'anyen aikin se su, Maamah batayi k'arya ba da
tace suna aiki tare idan ba haka ba tayaya Nazeefah zata san
takai Afzal asibiti idan ba wai kirarta Safiyya tayi ta sanar da
ita ba.
"Wallahi Yaya bani na rubuta ba" ta sanar da shi cike da
tashin hankali.
"Ba ke kika rubuta ba?"
"Yaya wallahi bani bace wallahi bani na rubuta ba" rantsuwa
ta shiga yi yayinda hawaye ya fara tsiyaya daga idonta.
"Can you even listen to yourself Amal? Aljani kike son kice ya
rubuta ko mey? Ko kin k'aryata wannan ba rubutun ki bane?"
"Yaya you have to believe me wallahi bani ce na rubuta ba
bazan ta6a yin abu haka ba" ta sanar da shi cikin tsan-tsan
kuka ransa ne ya gama 6aci gabad'aya besan a lokacinda ya
damk'ota ya shiga jijik'ata ba "Why do you have to keep on
lying to my face Amal? Why!?" Ya tsawata mata kakkarwa take
sosai yayinda hawaye ya shanye mata murya "I love you Amal,
I love you morethan anything in this world amma da abinda
zaki sak'a mun kenan? Duk kalan halaccin da nayi miki a
rayuwa you think I deserve this from you? Har ni zakice jikinki
kawai nakeso ba zuciyarki ba? Ni Amal? In ba da mukayi aure
ba ko hannunki na ta6a sha'awan rik'ewa ne?"
"Ya- Yaya please believe me" ta ce dashi muryanta na
d'aukewa "Wallahi bani na rubut-"
"Damn it Amal!" Ya katse ta. "You're such a horrible liar, idan
ba ke ba toh waye? Waye yake da irin sigar rubutunki bayan
kanki? Answer me!" Ya sake daka mata wani tsawan da
gabad'aya yasa jikinta rawa fiye da na da. Ita tsoronta ma kar
gabanta ya cigaba da fad'i abu ya samu d'an cikin nata ne
tunda de bawai cikin babba bane abu kad'an yana iya zubar
dashi.
"Wallahi bani bace-"
"When will you stop lying to my face? When Amal?" tureta
yayi kad'an ya rage bata sha k'asa ba "Stop lying to me
already just admit it, confess all your crimes a shirye nake in
yafe miki mu fara sabon rayuwa all over again Amal just admit
it."
Cikin tsananin kuka tace, "I have nothing to admit Yaya
saboda bani bace wallahi ba ni na rubuta wannan abu ba."
"You're still not telling me the truth."
"You have to believe me wallahi ba k'arya nake yi maka ba-"
"You're lying! Just admit it, admit it already."
"Yaya I have nothing to admit ya, taya kake tsammanin zan
amince da laifin da bani na aikata ba? Wallahi bani bace
wallahi bani na zauna na rubuta wannan abu ba, kana
tsammanin har zan rubuta mumunan abu haka kuma se in
ajiye a inda nasan idonka ze kai?"
"Fvck it!" Yayi growling yayinda yake wani irin nishi kaman
zaki. "Amma rubutun waye ne?"
"Yay-"
"Just fvcking answer me!" Ya katseta cike da rashin hak'uri.
"Rubutu na ne amm-"
"Shhh!" Ya katse ta "Abinda nakeso inji kenan" hannu ya mik'a
ya amshe paper'n "You've really hurt me Amal, you've hurt me
so badly, kin karya zuciyan da take mutuwar sonki kin yasar,
bazan ta6a mancewa da wannan abu da kikayi mun ba I might
forgive you someday amma bazan ta6a mancewa dashi ba."
Cikin sautin kuka ta kira sunansa "Yaya-"
"Just get out" ya sanar da ita a hankali.
"Yaya dan Allah ka saur-"
"I said get out!" Ya daka mata tsawa a raunane ta tsaya tana
kallonsa sannan ta shiga takawa a sanyaye ta bar mai d'akin.
Tana isa d'akinta ta baje akan gado ta shiga raira kuka. Kuka
take wane zata cire ranta har seda ta fara jin k'warnafi. Bayi ta
fad'a ta shiga kwararo amai kaman ba gobe seda ta harar da
duk wani abunda yake cikinta sannan ta lalla6a ta fito. Yanzu
ta tabbata da abinda Maamah ta jima tana fad'a mata. For all
these while Safiyya amanarta ta rink'a ci ita ta ringa zuba
mata gishiri da borkono a girki, ita ta rink'a kwasan abinda
Afzal ya keyi mata tana kaiwa Nazeefah, ita ce ta fad'a masa
tana kawo maza gida, ita ta kira Nazeefah ta sanar da ita suna
asibiti bayan da ta ajiye masa wannan takarda ya karanta.
Wow!
Meyasa ta kasa gane gaskiya tun farko? Meyasa bata gane
Safiyya ce behind everything ba? Tabbas ta tafka sokanci
gaskia ne da Maamah tace mata yadda ka d'auki nutum da
zuciya d'aya yanzu shi ba haka ya d'aukeka ba. Ko da wasa
bata ta6a kawowa a ranta cewan Safiyya zatayi mata abinda
tayi ba. Bature beyi k'arya ba da yace "Trust No One" tabbas
da tun farko bata ajiyeta kusa da zuciyarta ba da tun kafin abu
ya ta6ar6are haka zata gano gaskiya. Tsakaninta da Nazeefah
kuma sede tace Allah, Allah kad'ai ze sak'a mata yabi mata
hak'k'inta. Chan ta mik'e taje ta samu Safiyya a d'akinta.
"Sannu Aunty ya jikin naki?"
"Safiyya a iya zama na dake ban ta6a cutar dake ba, ban
ta6a tokararki ba, ban ta6a tauye miki hak'k'in kiba a matsayin
k'anwa ta ta jini na d'aukeki da zuciya d'aya shiyasa har yanzu
na kasa gane dalilin da zaisa kiyi mun abinda kikayi mun." Cike
da d'aurewan k'wak'walwa Safiyya ta tsaya kallon Amal
yayinda cikinta ya d'au ruwa lokaci guda bade Amal ta ganota
ba? Yau kashinta ya bushe ta shiga uku ta lalace.
"Mey na miki da kika za6i ki k'untata mun acikin gida na ki
hana ni sakat? Mey na miki da kika za6i ki shiga tsakani na da
mijina kisa har ya fara zargina akan ina ci masa amana? Mey
na ta6a yi miki Safiyya? Amma ba komai ki kira uwar d'akinki
ki sanar da ita cewan ta kwantar da hankalinta saboda burinta
na rabani da Ya Afzal ya cika koda Yaya be sakeni ba ni zan
tattara kayakina in bar gidan nan tunda kun riga kun juyar
mishi da kai kunsa yana mun kallon munafuka, mak'aryaciya,
annanimiya wace bata da aiki sena gulma. Ba gidan kukeso
ba? Zan tattara kayakina in bar muku ita" bata jira jin mey
Safiyya zata ce ba ta juya ta fice. Bayi Safiyya ta shiga a guje
ta juye fitsarin da ya matseta a lokaci d'aya sannan ta fito ta
d'au wayarta dan kiran Nazeefah se kakkarwa take yayinda
jikinta yayi la'asar da irin kalamun da Amal ta fad'a mata sede
sam layin Nazeefah yak'i shiga.
****
Babban akwatinta ta janyo daga d'akin da ta tarasu aciki ta
nufi d'akinsu da Afzal sallama tayi sannan ta shiga ko kallan
Afzal dake mik'e akan gado batayi ba ta zarce direct wajen
wardrobe, da mamaki ya mik'e zaune yana kallonta sede bece
da ita ko uffan ba. Kayakinta yaga ta shiga tattarewa na
matuk'a ta basa mamaki shin mey take shirin yi? Tafiya? Tafiya
zatayi ba tare da ya bata takarda ba? Ido ya cigaba da zuba
mata yana ganin iya gudun ruwanta. Kayakinta ta cigaba da
tattarewa tana had'awa tana gamawa da fannin kayakin ta
zarce gaban mirror ta d'ibi mayukan shafawanta da turare da
makamancin haka sannan taja akwatin ta fice har anan Afzal
beyi mata magana ba. Handouts nata da littafafai da sauran
muhimman abubuwan da zata buk'ata ta tarasu cikin wani
akwati daban shima.
Na sosai Afzal ya kasa kunne yana jiran jin k'aran engine na
mota inda ze tabbatar da tafiya Amal zatayi kokuwa kawai ta
tare kayakinta ne ta k'aura izuwa d'akin da ta koma gabad'aya.
Washegari da sassafe ko karyawa Amal batayi ba taja
akwatinta ta fice. Ko da driver yace ze kaita inda zata hanasa
tayi napep ta tsara a waje bayan d'an takawan da tayi ta wuce
gida. Har bakin k'ofa ya sauk'eta sannan ta sauk'e kayakinta ta
sallamesa ta k'arisa ciki.
Papi ta tarar a tsakar gida yana zaune yayinda suke hira da
Mami dake kitchen tana shirya musu abun karin kumallo.
"Baby!" Ya kirata da mamaki yana bin jakukkunan hannunta da
kallo "Ya haka? Meya faru?" Ya jero mata tambayoyi. Ba shiri
Mami dake kitchen ta sauk'e tukunyarta ta fito tana kallon
abin al'ajabi. Ba k'aramin tsinkewa zuciyanta yayi ba ganin
Amal da akwati haka, Allah de yasa ba abinda take zargi bane.
Da sauri sukayi kanta suna tambayarta meya faru. Sede wane
'yi kuka' suka ce mata dan yadda ta rushe da wani irin
masifaffen kuka, a rikice Mami ta jata jiki ta shiga hugging
nata tana bubbuga bayanta yayinda Papi yaja akwatunan nata
suka k'arisa ciki. Dan kukan da takeyi Papi ya rok'i Mami da
tabar ta da tambayoyin haka ta bari se idan ta huta tukuna.
Dan haka suka fita daga d'akin suka barta, kukan ta cigaba
dayi har izuwa lokacin da wani wahalallen bacci ya d'auketa.
****
Wajajen tara da rabi Afzal ya tashi daga bacci bayan yayi
wanka ya sanya shirt da shorts ya fito inda ya tarar da Safiyya
na goge-goge. Cikinsu duka ba wanda yasan da tafiyan Amal
banda mey gadi da driver. A cewan Safiyya har Amal ta irga
wa Afzal halin da ake ciki ne don haka tayi surrender ta tsaya
chak gu d'aya tana jiran sauk'an mari a fuska kawai setaji ya
tambayeta "Ba gaisuwa ne?"
"Yi hak'uri ina kwana Uncle wallahi hankalina ya tafi wani gun
ne" Ta gaishesa "Lafiya" ya amsa "Kiyi mun frying chips da
two eggs."
"Toh barin kammala aikin nan" instead ya wuce d'akinsa se
yayi tunanin lek'a na Amal inda ya tarar da d'akin empty, shiga
yayi ya zauna yana jiran fitowarta dan a tunaninsa gabad'aya
ta shiga bayi yin wanka ne sam be kawo a ransa wai har Amal
ta tafi ba. A cewansa tunda bata tafi jiya ba that means ba yaji
zatayi ba kawai ta tattare kayakinta ne ta dawo dasu nan
gabad'aya. Sede da ya duba gaban dressing mirror ya tarar
dashi empty ko vaseline babu. Tirk'ashi! Ba shiri ya mik'e yayi
knocking bisa k'ofan bayin, jin shiru seya bud'e ya lek'a ciki
inda ya tarar da bayin empty a guje ya fito yana tambayar
Safiyya ko ina Amal taje sede kaman yadda baida masaniya
itama hakan ne. Waje ya fita yana tambayan mey gadi ko yaga
fitan Amal.
"Tabbas naga fitanta Ranka shi dad'e nima na bud'e mata
k'ofar."
"Ina taje? Ita kad'anta ta fita ko kuwa da akwati?"
"Akwati har biyu."
"Damn it! Meyasa baka hanata fitan ba kokuwa ka kirani ka
gaya mun? Shin baka san aikinka bane? Mstww!" ciki ya dawo
ya d'aga wayansa har ya danna kan contact na Amal don
kiranta se kuma ya fasa yayi sauri ya katse wato shi be yi
zuciya ya ce ya saketa ba be kuma ce ta tafi gida ba itace
take da zuciyan yin hakan? Ita gata tana da gun zuwa wato, da
kyau ta kyauta taje duk inda zata je.
*****
Wajajen goma da rabi Amal ta tashi inda ta fara duban
wayanta saidai da mamaki taga ko message Afzal be tura
mata ba bale ya kirata, lallai yau ta gane waye Afzal. Wannan
walak'anci da mey yayi kama? Ace yana kallonta tana shirya
kayakinta amma ko yayi mata magana bale yayi tunanin
hanata. Yanzu kuma da ya tashi yaga bata gidan meya kamata
yayi? Lallai yau tasan inda ya ajiyeta, yau tasan matsayinta a
zuciyansa, yau ta tabbata Yaya baya sonta.
Masa me kyau Papi ya aika aka siyo mata ta karya da shi
tasha magunanta alai sannan Mami ta shigo suka gaisa.
"Bakida lafiya ne?" Mami ta tambayeta tana bin magunan
dake gabanta da kallo.
"Eh Mami ban ji dad'i sosai ba kwana biyu."
"Allah sarki, Allah sawwak'e."
"Ameen."
"Ya baki ci masan ba sosai duka fa naki ne mu tun d'azun
muka karya."
"A'a Mami na k'oshi na d'an ci ai anjima ma ina da test."
"Kai haba?"
"Wallahi around 1 haka."
"Toh Allah ya bada sa'a Papinki na buk'atan ganinki."
Hijabinta ta sanya ta mik'e a sanyaye tabi bayan Mami bayan
sun k'arisa d'akin nasa suka nemi waje suka zauna daga
angles na d'akin. Gaisuwa suka fara yi bayan nan Papi yake
tambayarta meke faruwa.
"Papi komai ma ya faru, ba abinda be faru ba ni kawai kar ku
sake turani gidan Yaya dan Allah" seta rushe da kuka.
"Subhanallahi ya isa haka kinji? Ba wanda yace ze sake mai
daki gidansa fad'a mun meya faru."
"Nazeefah ba kishiyar arziki bace after all, yadda na d'auketa
da zuciya d'aya ba hakan ta d'aukeni ba, ashe duk shiri ne
bawai har cikin zuciyarta bane tana so na, son munafurci take
yi mun...." nan ta kwashe labarin duk yadda akayi tun daga kan
lokacin da Safiyya ta fara zuba mata gishiri da borkono a girki
zuwa kan lokacin da Afzal ya fara shasshareta zuwa kan
lokacinda tayi masa magana yace tana kire-kiren waya tana
baza sirrin gidanta a waje, zuwa kan lokacin da Safiyya tace ta
fara kawo maza gida har izuwa na takardan da suka sa wa
Afzal cikin kaya bata 6oye masu komai ba illa labarin cikin da
take d'auke da shi.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" kawai Papi yake ta nanatawa
da mamaki bayyane karara a fuskansa itakam Mami se tafe
hannu kawai takeyi dan mamaki ko salatin ma ta kasa ambata.
"Kikace a idon shi kika tattare kayakin ki beyi miki magana
ba?" Mami ta tambaya.
"Wallahi a idonshi Mami" ta amsa tana share hawayenta.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" ta sa salati.
"Har yanzu kuma be kira ki ba?" Papi ya tambaya.
"Be kirani ba."
"Kuma nima be kirani ba ko ya kiraki Jameela?"
"Sam" ta amsa tana kad'a kai.
"Tabbas Afzal zeyi nadama, ashe har za a fad'a mishi
magana akanki ya hau ya zauna akai ba tare da ya tsananta
bincike ba? Ashe har zega ayan tambaya akan tarbiyyan dana
baki a gidan nan Baby? Har ke yake tsammanin zaki ci masa
amana sabida 'yar aikinki ta ce hakan? Baze tsaya ya
tambayeki yayi bincike ba?"
"Wallahi Afzal butulu ne" cewan Mami "Ko a mafarki aka ce
mun zeyi haka wa Baby bazan yarda ba, wannan sigan
walak'anci da mey yayi kama? Ai ko a bishiya ya 6alloki be
kamata yayi miki haka ba ni fa ba abinda ya fi ci mun rai
kaman da ya koraki daga d'akinsa. Wannan wani irin gori ne?"
Ta tambaya cike da tsiwa.
"Ya isa haka Jameela ki kwantar da hankalinki uwata ta shi
kije ki huta ai ba makaranta yau ko?"
"Akwai ina da test."
"Kinyi karatu?"
"Eh jiya nayi yanzu ma zan d'an ta6a kafin lokaci yayi."
"Toh uwata Allah bada sa'a kinji? Ina son ki kwantar da
hankalinki ki cire Afzal daga zuciyarki. Nasani abinda yayi miki
da zafi amma hak'uri ya zama dole mamana, dan shi baza ki
bari ki cutar da kanki ba, in shaa Allahu shi yake tattare da
asara ba ke ba gashi ai da kika cigaba da hak'uri kina kai
kukanki wa Allah, Allah ya bayyano miki da komai kuma batun
cewa za mu miyar dake gidansa k'arya ne, baki komawa har
se idan ke kika ce hakan bazan mayar masa dake ba koda
yazo yin bikon ki Baby zan nuna masa cewa ba wanda ya kai
ya walak'anta mun ke muddin ina raye so ki kwantar da
hankalinki kinji? Ki cigaba da karatu Allah yayi miki albarka."
"Ameen Papi nagode."
"Tashi Mamana" da haka ta mik'e ta fice zuwa d'akinta ta
cigaba da karatu. "Amma Afzal be kyauta ba wallahi" cewan
Mami bayan ficewan Amal.
"Dama na sani wataran se ya gorantawa Baby shiyasa ban
goyi bayan ka sanar dashi asalinta ba tun farko."
"A gaskiya nima Afzal ya bani kunya yadda ba bincike ba
komai ya yanke hukunci."
"Ai walak'anci ne ba komai ba wallahi kuma kasan meya fi
6atan rai? Yadda tana tattare kayakinta a gabansa amma ko
k'ala be ce ba irin bata da gata bata da gun zuwa d'innan
kokuwa duk inda taje zata sake dawowa da k'afarta."
"Ya isa Jameela ki kwantar da hankalinki in shaa Allahu ba
shi ba Baby."
"Ahtoh dan wannan rashin mutunci ne a fili saboda bata da
uba yake ganin ze iya walak'anta ta toh wallahi yayi k'arya
Baby nada gatanta."
"Ki sauk'ar da muryanki kar Baby ta jiki dan Allah magana ya
riga ya k'are muddin ba Baby ce tace zata koma gidan sa ba
toh ba shi ba ita cin fuskan ya isa haka."
***Sha biyu nayi ta shiga shiri sallama tayi wa Mami sannan ta
fice, tana gama test nata sukayi sallama da Maamah. Dama
yawancin ana samun napep na jiddari (unguwansu) acikin
makaranta se yau kuma Allah yayi babu dan haka ta taka har
wajen gate ta shiga nema. Tazo tsallake titi kawai kaman
daga sama wani mota mey d'ankaren gudu ya d'auketa ya
wuce ko kewayowa beyi ba. Nan mutane suka duk'ufa sukayi
kan Amal da tuni ta sume a wajen yayinda kanta yake bulbulan
jini. Mota aka shiga nema wanda zeyi gaggawan kaita asibiti
ana cikin haka sega wani babban motan daya fito daga cikin
makarantar ya faka a dai-dai inda abun ya faru. Daga ciki
babban mutum da ake ja yace da driver'n sa "Iliya sauk'a kaje
ka taimaka musu mu kai yarinyar asibiti." Nan da nan aka
d'auki sumemmiyar jikin Amal aka sata cikin motan inda suka
wuce TH.
****
K'ofan ta rufe ta fad'a bayi a guje sannan ta d'aga wayan.
"Hello Aunty?"
"Safiyya mission complete yau burina ya cika, na fidda Amal
daga gidan Ya Afzal maganan da nake miki yanzu har
mutanen nawa sun bigeta in shaa Allah se cikin ya zube."
"Aunty meyasa kika sa aka bigeta? Kin fidda ta daga gidan
nan bey isheki ba har sai kinsa an bugeta? Seda na ce miki ya
isa haka amma kika k'i ji wallahi abunda mukayi wa Aunty yayi
yawa ni nayi nadaman fara aikin nan da ke."
"Mey kike cewa Safiyya? Bayan burin mu ya cika kike
wannan banzan maganar? Kin manta da mak'udan kud'ad'en
da na miki alk'awari ne?"
"Ban fad'a miki bane amma Aunty ta riga ta gane mu, ta gane
muna aiki tare, kap abinda muka aikata ta irga mun jiya kafin
tabar gidan nan."
"Sai mey? Ba ta riga ta bar gidan ba?"
"Aunty duk da haka da bakisa an bigeta ba wallahi Aunty bata
cancanci abubuwan da mukayi mata ba."
"Kiji ni Safiyya wallahi idan kika kuskura kika 6ata mun aiki
na sena tabbata na lahira ya fiki jin dad'i hello Safiyya?
Safiyya? Hello?" Tuni Safiyya ta katse wayan. Tun tafiyan Amal
yau ta kasa samun sukuni, sosai kalamun Amal suka ta6a ta
suka sa duk ta tsani kanta. Bud'e k'ofan da tace bari tayi taga
Afzal tsaye bakin k'ofan bayin yana wani irin nishi wane zaki
ga yadda idanunsa suka kad'a sukayi ja zir, wai shin har
yaushe ya shigo bata ji sa ba? Innalillahi ashe batayi locking
k'ofar ba duk dan sauri ta d'auki call d'in Nazeefah kafin ya
tsinke. Kafin ta hankara kawai taji ya fincikota da hannunta
seda ya fiddo ta daga bayin.
Tsulewa tayi ta shiga yin kakkarwa yayinda idanunta suka
ciko dam da hawaye.
"Da wa kike waya?" Ya tambayeta cikin wani irin salon da ya
mugun sanyata jin fitsari. Kai zalla take iya kad'awa "Nace da
wa kike waya?!" Ya daka mata wani irin tsawan da tuni ya sa ta
shiga sake fitsarin da take ji tsabaragen tsoro.
"Uncle dan Allah kay-"
"Shut up you fool! nace da wa kike waya?" hannu ya mik'a ya
fisge wayan nata tare da shiga call logs last numban da tayi
waya da shi yayi dialing bada dad'ewa ba Nazeefah ta d'aga
"Hello Safiyya? Hello Safiyya?" Wani irin rawa jikin Afzal ya
fara lokacin da yaji sautin muryan Nazeefah acikin wayan.
Kashe wayan yayi daga sama kawai Safiyya taji sauk'an mari a
fuskanta tass! wani irin rikicaccen ihu tasa yayinda ta soma
ganin stars suna bin kanta. Be bari tayi overcoming zafin
marin ba ya k'ara mata d'aya kumatunta duka ta rik'e tana
kuka.
"Abinda ta turoki gidan nan kiyi kenan ko? Ki shiga tsakani
na da Amal is that it?"
"Uncle dan Alla-"
"Shut it!" Ya daka mata tsawa "wa kuka tura a kad'e?" Kai
zalla take kad'a masa yayinda ta gama tsurewa "Nace wa kuka
tura a kad'e?" Nan ma shiru "You fool I'm talking you" fincikota
yayi had'e da kai mata wani marin again a rikice tace, "Aunty
wallahi Aunty a ka kad'e ni bani bace."
"What?" Yayi exclaiming cike da k'in yarda. "Kun sa a bige
Amal? Bakuda hankali ne?" Turata yayi har jikin bango sannan
ya shak'ure mata wuya take idanun Safiyya suka kad'a yayinda
ta shiga yin tari kad'an ya rage Afzal be kasheta ba sannan ya
saketa nan ta sauk'a k'asa tana wani irin tari.
"A ina kuka sa aka bigeta?" Shiru tayi se kuka kawai take
wani ball yayi da ita da k'afa "Nace a ina kuka sa aka bigeta?"
Cikin tsananin kuka tace "Wallahi ban sani ba tunda Aunty
tace zata sa a bigeta nace kar tayi amma tak'i jina" wani ball
d'in ya sakeyi da ita "K'arya kikeyi nace k'arya kikeyi a ina kuka
sa aka bigeta?"
"Uncle wallahi ba k'arya nakeyi ba tace de daga makaranta
za a bi Aunty amma wallahi ban san a dai-dai ina bane dan
Allah ka yarda dani."
"Wallahi tallahi kin de ji rantsuwa ba kaffara ko? Muddin wani
abun ya samu Amal ki sani da hannu na zan kasheki" yana
kaiwa nan ya fice daga d'akin makulli yasa ta waje sannan ya
k'arisa d'akinsa ya d'au key'n motansa ya fice be tsaya ko ina
ba se gidan Nazeefah. Tana zaune akan dining tana cin abinci
kawai taga shigowan Afzal kaman diran yesu.
"Ya Rouhi?" Ta kira sunansa had'e da mik'ewa dan yi mai
sannu da zuwa. Peck ta mishi placing a gefen kumatu "Ya
Rouhi mey ka shigo yi? Ba se gobe zaka shigo ba?" Ko amsata
ya kasa yi yayinda zuciyarsa ke raya masa kawai ya had'a
kanta da jikin bango ya shak'ure mata wuya se idan ta daina
numfashi tukun ya saketa danne zuciyan nasa yayi sannan
daga gefe yayi dialing lambarta ta wayan Safiyya.
"Excuse me" tace da shi tare da nufan dining dan d'aukan
kiran, ba k'aranin har6wa zuciyanta yayi ba ganin Safiyya ke
kira shin wai meke damun yarinyar nan ne haka? Rejecting call
d'in tayi take nan Afzal ya sake buga mata har rawa jikinta
yake ta kuma rejecting juyawan da zatayi taga Afzal gab a
bayanta.
"Muje ka watsa ruwa ko? Bari in sirka maka ruwan." Kafin
tace zata taka k'afa Afzal ya rik'o hannunta "Who's calling?" ya
tambayeta.
"Ermm.. ermm Airtel ne Wallahi kasan su da kiran mutum
anyhow." Wayan Safiyya ya d'aga ya sake dialing lambar nata
nan ya shiga ruri kafin tace zata katse yasa hannu ya hanata
"Ba Safiyya ke kira ba? Ki d'aga mana." Kakkarwa ta shiga yi a
wajen bata san lokacinda ta sake wayarta a k'asa ba da ta
hango wayan Safiyya rik'e a hannunsa. B'ari bakinta yake
yayinda cikinta ya d'ura ruwa.
"Ya Rou-" wani irin zafaffan mari me rikitarwa ya zabga mata,
wani irin rikicaccen ihu tasa bata hankara ba ya sake kai mata
wani abinku da farin fata take fuskan nata yayi ja yatsun Afzal
biyar suka bayyana akai.
"Ya Afzal dan Allah kayi hak'uri" ta furta cikin wahala da
tashin hankali har wani kurma-kurma ta fara jin kanta tsan-tsan
zafin marin.
"I can't believe your guts Nazeefah, how could you? For all
these while ashe wasa kike mun da hankali? Wace irin
munafuka ce ke? Ma tukun mey Amal ta tare miki? Tell me
mey Amal ta tare miki da kika za6i ki k'untata mata kisa in
tsaneta ki shiga tsakanin mu haka? Baki tsaya anan ba har
seda kika sa aka kad'eta? Are you forreal? So kike ta mutu?"
"Ya Afza-" wani marin ya sake kai mata dan yadda ko
muryanta baya son saurara. Ihu Nazeefah tasa seda Hindu
dake bacci ta fito daga d'aki a kid'ime ganin Afzal ne da kansa
ta ja k'ofanta ta sa key.
"Mey ta tare miki nace?!" Hannunta ya damk'o yana yi mata
wani irin rik'o tuni k'asusuwanta suka shiga yin k'ara "Ya Afzal
dan Allah kayi hak'uri kar ka karya mun hannu."
"Answer me then mey Amal ta tare miki?"
"Zan fad'a maka zan fad'a maka amma dan Allah ka sakeni
wayyo Allah na" sassauta rik'on nasa yayi. "Speak up! Idan kika
bari na sake tambayanki wallahi na lahira seya fiki jin dad'i,
mey Amal ta tare miki nace?"
RANA DAYA Chapter 36
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
Tareda Naja'atu Lawal Rijau Niger State
@Whatapp 08083232323 or 09060202323
PAGE 36
Cikin tsananin kuka da azaba tace, "Mene Amal bata tare
mun ba Ya Afzal? Komi ma Amal ta tare mun, tamkar katanga
haka Amal ta shiga tsakani na da samun soyayyarka, yadda
kake sonta ba haka kake sona ba, yadda kake jin zaka iya
sadaukar da rayuwanka mata ba haka kake ji da ni ba, komi
Amal komi Amal, ko shopping muka fita seka tambayi ina na
Amal, wayanka duk hotunan Amal ne aciki, girki nasani Amal
ta fini iyawa, tafi ni iya tarerayarka, ta fini iya nuna maka
soyayya, ta fini kyau ta fini fasali, ta fini ilimin boko da na
islamiya gabad'aya komi da nake tunani Amal ta fini da shi.
Gashi da shigowanta gidan nan dududu bata fi wata uku ba
amma har ta d'au cikinka ni shekarana uku da watanni na kasa
yin hakan-"
"Amal na da ciki?" Ya katseta cike da k'in yarda.
Kuka take sosai ta gyad'a mai kai "Amal na d'auke da cikinka
Ya Afzal bazan iya ba, ta ko ina Amal ta fini taya kake
tsammanin zan iya yin kishi da ita. Ya Afzal I love you dan
Allah karka ga laifi na wallahi son da nake yi maka ne ya janyo
komai, akanka zan iya sa ayi ma mutum kallon me ta6in
hankali ko ciwon aljanu, akan ka zan iya yin duk wani irin
mak'ircin da kake tsammani, akan ka zan iya sa mutum ya
zargi matarsa akan ka zan iya sa a bige mutum dan a
illatamun shi, I love you Ya Afzal, akan soyayyarka kuma zan
iya yin komai-" zuciya ne ya d'ibesa ya sake gaura mata wani
marin, na hud'u kenan k'asa ta sauk'a yayinda ta shiga raira
kuka.
"Kinsan Amal nada ciki kika sa aka kwa6eta saboda ki kashe
ta ki kashe abinda ke cikinta Nazeefah?" Har yanzu ya kasa
amincewa da hakan. "So it's all been you these while, duk
kalan mak'iricin da kika shuk'a har kika fitar da Amal daga
d'akinta be isheki ba no har sai kin sa a kwa6eta? Ashe
haukan naki har ya kai stage d'in da zaki iya yin kisan kai?
D'ana kikeson ki kashe? Kuma a haka kike cewa kina so na?
You're insane Nazeefah, ki sani na tsaneki, na tsani duk wani
mey k'aunar ki, I hate you Nazeefah."
"Ya Afzal dan Allah kar kace haka, Ya Afzal bazan iya
rayuwa ba kai ba, a shirye nake da in hallaka duk wanin da
yake da shirin shiga tsakani na da kai Ya Af-" zuciya ne ya
d'ibesa ya shiga yin ball da ita a wajen. Belt nasa ya zare ya
shiga zaneta ta duk inda zanan ya sauk'a dama gashi vest ne
kad'ai a jikinta da wandon rigan bacci iya guiwarta.
D'an banzan duka Afzal yayi mata sekace ya samu ganga ko
jaki, dukan da tunda baabarta ta haife ta ba a ta6a yi mata
irinsa ba seda yaga ta fara yin amai a wajen sannan ya barta
se huci yake.
"Ki bud'e kunnuwan k'ashin nan naki ki saurareni da kyau
Wallahi tallahi kin deji rantsuwa ba kaffara ko? Idan abun ya
samu lafiyan Amal mey hanani kasheki a gidan nan se Allah
Nazeefah, da hannu na zan kasheki nace a dai-dai ina kika sa
aka bigeta?" Nazeefah ba bakin magana banda kuka ba abinda
take iyayi ga yadda jikin nata ya tashi nan take, belt d'in ya
sake zabga mata "Ba magana nakeyi maki ba?"
"Ya Afzal dan Allah kayi hak'uri na tuba."
"Aww bazaki amsa ni ba?" Bata hankara ba ya sake zabga
mata belt d'in Nazeefah se ihu take tana kuka tana neman
agaji amma ba wanda ze iya taimaka mata, ba mai gadi Hindu
kuwa uwar tsoro tuni ta rufe kanta a d'aki se hasbnullahu wa
ni'imal wakeel take ta nanatawa. "Answer me! A ina kika sa
aka kad'eta?"
"Wallahi a dai-dai bakin makaranta ne dan Allah kayi hak'uri
na tuba Ya Afzal."
"No Nazeefah you're never sorry and I swear to you, na miki
imani da Allahn da raina yake hannunsa you must pay for this,
you must pay for everything you've put Amal go through I
don't care if it costs you your life, sekin biya abinda kikayi wa
Amal" yana kaiwa nan ya wuce kitchen ya kulle k'ofan da key
ya zare sannan ya wuce d'akinsu ya tattara spare keys na
gidan ya sanya a aljihunsa ya dawo ya d'aga wayanta ya fice
ya kulle k'ofar ta waje yadda bata isa ta kira kowa ba bale tayi
tunanin guduwa. A 360 yabar gidan nata ya wuce chan bakin
unimaid ya shiga tambayan mutanen dake kusa batun hatsarin
da akayi d'azu ina aka kai yarinyar dayawa suka ce basu sani
ba da k'yar ya samu wani mai shagon da yace yana da
tabbacin TH suka wuce tunda shine asibitin dake kusa da nan
d'in. Be 6ata lokaci ba ya wuce TH d'in inda ya zarce
emergency ward ya shiga neman d'akin da Amal take ciki.
******
"Se anje an siyo jini ba jini a blood bank and the patient is
losing so much blood" cewan likitan dake aiki akan Amal ma
wata nurse. "Kuje ku nemo jinin yanzu type O- (negative)" a
guje ta fito inda suka ci karo da mutumin da ya kawo Amal da
driver'nsa.
"Ya nurse? Ya jikin patient d'in?" Yayi saurin tambayarta.
"I'm sorry sir amma patient d'in ta rasa jini sosai wanda dole
se anyi mata transfusion se gashi anje blood bank kuma babu
type nata."
"Wace blood group ce?"
"O-" ta sanar da shi.
"O-?"
"Yes Sir."
"Idan ban manta ba nima blood group O ne."
"Sir O+ daban O- shima daban O+ ze iya receiving daga O+
kaman shi da kuma O- amma O- dole se O- kaga kuwa yanzu
idan kai O+ ne bazeyi ka bawa patient d'in jini ba."
"I'm sure O- nake nima."
"Sir you have to be certain."
"Amma kun tabbata inda zakuje neman akwai blood group
natan?"
"Gaskiya bamu da tabbacin hakan sir se munje mu duba
tukuna."
"Toh ai duk 6ata lokaci ne wannan ina kuma ace anje chan
d'in babu blood group natan? Ai mun koma baya."
"Hakane kuma Sir."
"And mey ze faru idan ba ayi mata transfusion d'in da wuri
ba?"
"Based on tests da muka gudanar sakamako ya nuna tana
d'auke da juna biyu toh muddin ba ayi supplying nata da jinin
akan lokaci ba eventually zata iya rasa ranta da kuma abinda
ke cikin nata."
"Muje ku gwada jinin nawa in irin nata ne se ku d'iba, bags
nawa kuke buk'ata?"
"D'aya da rabi Sir."
"Let's go muje ku d'ibi nawa kusa mata da wuri kafin lokaci
ya k'ure."
"Sir are you sure?"
"Let's go we don't have time" haka kawai wannan Alhj yaji
wani irin strong connection tsakaninsa da Amal duk da cewan
bey santa ba, amma jinta yake a kusa da zuciyarsa. Nan da
nan akayi d'akin d'iban jini da shi amma da fari aka gwada
blood type nasa inda yayi matching dana Amal, bayan nan aka
kuma wani gwajin don tabbatar da cewa jinin nasa baya
d'auke da wani cutan zamani. Anan aka zuge leda d'aya da
rabi kamar yadda nurse d'in ta fad'a sannan akayi masa
recommending magunan k'ara jini da zena sha dan ya maido
masa da jinin nasa.
Godiya sosai mutanen asibitin suka tayi masa. Nan da nan
akayi infusing wa Amal aka bata taimakaon gaggawa da ikon
Allah kuma aka samu aka ceto cikin nata ba tare da wani abin
ya samesa ba.
Har anan su Mami basu da labari saboda ko waya Amal bata
fito dashi ba bale a lalumo layin wayansu aciki, saboda
acewarta test kawai zatayi ta dawo gida se bata damu ta fito
da wayan ba.
Har anan wannan Alhaji da ya ba wa Amal jinin jikinsa be tafi
ba ya na nan yana jiran farfad'owanta. Tana farfad'owa nurses
sukayi masa magana nan ya k'arisa cikin d'akin inda ya tarar
da ita kwance akan gado da bandeji nad'e a kanta da k'afarta,
da kuma wani a hannunta wanda aka nad'e mata shi tun daga
wuya dan support da alama shima hannun ta samu matsala
ne. Sosai ya tausaya mata barin ma da yaji tana da ciki.
"Ga wannan shine mutumin da ya baki jinin jikinsa har leda
d'aya da rabin da aka sa miki kyauta se kiyi masa godiya"
nurse d'in tace da Amal. A hankali Amal ta shiga juyo da kanta
har ta kai akan wannan mutumi. Mutuwan tsaye mutumin yayi
lokacinda k'wayoyin idanunsu suka had'e. Ita kanta Amal seda
taji wani iri a jikinta, tabbas bata mance fuska amma seji take
a jikinta kaman ta ta6a had'uwa da wannan mutumi amma
kuma ta rasa a ina. Shi ma on the other side kallon Amal yake
na sosai ba tare da ya koda kyafta ido ba, ji yayi kaman sun
ta6a had'uwa a wani gun amma duk yadda yayi ya kasa tuna a
ina, da ya cigaba da kallon cikin idonta kuwa se gani yake
kaman kansa yake kalla aciki there's something about her
eyes that reminds him so much of himself, he sees himself in
her. Wani irin mumunan tsinkewa gabansa yayi yayinda
rayuwansa na da ya fara taho masa.
"Nagode sosai Allah sak'a da alkhairi Baba" tace da shi kai
yayi saurin kad'awa had'e da sakar da murmushin dole "Ba
komai 'yata sannu Allah sawwak'e."
"Ameen" ta amsa da murya chan ciki-ciki.
"Ya sunanki?"
"Amal Abdallah" ta sanar da shi haka kawai yaji gabansa na
fad'i jin sunan mahaifinta.
"Mahaifiyar ki fah?"
"Jameelah Muhammad" ido ya rufe na k'ank'anin lokaci yana
k'ok'arin composing kansa. Baze ta6a mancewa da wannan
suna ba, ko a ina yaji sunan nan yasan sunan Jameensa ce
amma kuma ai ba ita kad'ai bace Jameelah Muhammad a
duniya ba, ze iya yuwuwa wata Jameelah Muhammad d'in ce.
Amma idan kuma itan ce fah? Can it be? Noo da sauri ya
kad'a kansa yana d'auke wannan mumunan tunani it can't be
possible it can never be.
Murmushi ya sakar wa Amal "Ko zaki bada lamban mahaifinki
a kirasa?" Da biyu ya tambayeta hakan don jin mey zata ce
idan har tace 'eh' ta basa that means ba shida alak'a da ita
idan kuwa har tace ba na mahafinta se na mahaifiyarta that
means zarginsa akanta ya tabbata kawai se yaji tace "Eh."
Wani irin ajiyan zuciya ya sauk'e had'e da yima Allah godiya
tunda har tana da mahaifi toh ba abinda yake zargi bane
barka. Nan da nan ya zaro wayansa daga aljihu Amal ta irga
masa lamban Papi wanda ya kira take bayan sun gaisa ya
sanar dashi abinda ke tafe da shi inda Papi yace yanzu haka
ma suna hanyan zuwa asibitin ne mijinta ya riga ya kira ya
sanar da su.
"Iyayenki suna hanyan tahowa sunce mijinki har ya kira ya
sanar da su" yace da Amal. A lokaci guda zuciyan Amal ya
buga to the mention of Afzal's name. Idan su Mami sunayi wa
Allah kar su k'ariso nan da shi, bata k'aunan sake sanya sa a
idanunta har k'arshen rayuwarta, baza ta ta6a mancewa da
abinda yayi mata a rayuwa ba "Toh Amal barin je inyi settling
bills naki in amso miki magunanki ko?"
"Baba da ka bari ai kayi mey wuyan wannan ko iyaye na
zasuyi handling dan Allah kar ka damu."
"Ba komai 'yata kede Allah baki lafiya"
"Ameen nagode Allah sak'a da mafificin alkhairi." da haka ya
samu ya fice inda ya tura driver'nsa ya biya komai aka amso
magunan sannan aka mik'awa nurse ta kaiwa Amal.
"Nurse?" Amal ta kirata.
"Na'am kina buk'atan wani abu ne?"
"How about my baby? Cikin na nan ko ya zube?"
"Cikin ki na nan baiwar Allah, an samu an tsayar da bleeding
d'in tun kamin ya isa cikin mahaifarki ya 6ata cikin." Wani
hamdala Amal ta sake "Thank you, k'afa na da hannu fa?
Targad'e ne ko kariya?"
"Targad'e ne duka biyu" Tasan zato zunubi ne amma tana da
tabbacin Nazeefah is behind everything, na sosai ta duba
kwalta kafin ta tsallake har yashe ne bata ga wannan mota
mey uban gudu ba idan ba wai dama fakonta motan yake ba.
Tana sake zargin Nazeefah ce behind this saboda duk yadda
akayi taji batun tana da ciki ne daga bakin Safiyya shine take
son rabata da abinda ke cikinta, k'arshe kuma idan har ba a
bakin Nazeefah ko Safiyya ba ba yadda za'ayi Afzal yasan tayi
hatsari.
"Don't mention" nurse d'in tace da ita tana me tsamota daga
duniyan tunanin data wula "iyayenki sun sake yin waya anyi
musu kwatancan d'akinki yanzun zasu shigo" kai zallah Amal
ta gyad'a mata sannan ta maida kallonta ga jinin da ke kan
shigewa jikinta ta canula. Mamakin halin alkhairi irin na
mutumin nan kawai take, yadda be santa ba, be san wani nata
ba, be san daga ina ta fito ba amma har ya d'ibi jinin jikinsa
leda d'aya da abu ya bata gaskiya ne na Allah basu ta6a
k'arewa toh Allah ya sak'a masa da mafificin alkhairi.
****
Dab su Papi sun zo shiga k'ofan ward nasu Amal suka tarar
da Afzal tsaye bakin k'ofan da tashin hankali bayyane karara a
fuskansa yana ganinsu ya nufe su "Papi-"
"Dakata Afzal" Papi ya tsayar da shi ta hanyan d'aga
hannunsa "Bana buk'atan jin komai daga bakinka, ka kira mu
ka sanar damu abinda ya samu Baby mungode Allah saka da
alkhairi kana iya tafiya dan babu wata alak'a kuma tsakaninka
da Amal yanzu."
"Papi dan Allah kar kayi mun haka dan Allah kar ka rabani da
Amal I beg of you please."
"Miss" Papi ya kira wata nurse. "Dan Allah ku janye bawan
Allah nan daga nan."
"Bawan Allah ba tun d'azu aka sallameka ba? Baka da
appointment da kowa anan bazeyi ka shiga ba nan restricted
area ne dan Allah kayi hak'uri ka tafi, yes Sir how can I help
you?" Ta kewayo tana tambayan Papi bayan da ta gama da
Afzal.
Nan Papi yayi mata bayanin komai lamban wayansa ta amsa
ta zuba cikin computer'n dake gabanta yana gama scanning ya
nuna wayan da sukayi last da phone desk. "Bismillah kuzo in
shiga daku."
"Mami? Mami please don't don't do this please" Afzal yace
da Mami lokacin da tazo shigewa ciki "Please karku hana ni
ganin Amal" ko kallonsa Mami batayi ba bale tasan yanayi ciki
akayi dasu akayi directing nasu zuwa d'akin da Amal take
yayinda aka bar Afzal tsaye a waje.
Kuka wane d'an yaro Afzal ya shiga yi a wajen, yau ina ze sa
kansa idan su Papi suka raba sa da Amal? Ya suke son ya rayu
idan ba Amal a ganga da shi? Taya suke son ya fara neman
tuba idan ko kallonta bazasu barsa yayi ba? Yau ina ze jefa
kansa? Tabbas ya tafka babban sokanci na k'in saurara mata
da yayi lokacin da take son yi masa bayani, tabbas ya tafka
babban laifi na amincewa da maganan Safiyya akan na Amal
da ta kasance matarsa, ta ina ze fara bata hak'uri? Ta ina ze
fara nuna mata how deeply sorry he is and how badly he's
regretted everything he's done to her? Tabbas ya tafka babban
kuskure a rayuwansa na amincewa da duk maganan da aka
fad'a masa ba tare da ya gudanar bincike akai ba. Tabbas duk
mey irin hali irin nasa yana tattare asara, masifa da kuma
nadama.
***
Tunda Alhajin yaji isowan iyayen Amal ya 6oye kawai se
basa jikin sa yake Jameensa ze gani. Ba k'aramin tsinkewa
zuciyansa yayi ba lokacin da yaga ana shiga da Mami da Papi
cikin d'akin Amal.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" kawai yake ta furtawa
yayinda jikinsa yayi la'asar. Shekaru ashirin da biyu da suka
wuce kawai yake tunawa, yau ina zai sa kansa idan gaskiya ta
fito? Shikenan mutunci da girman da 'yan unguwa suke basa
ze rushe, shikenan reputation na family'nsa ze rushe. Shin da
wani idon ze sake kallon Hajiya Surayya? (Mummy'n su
Nazeefah) meke shirin faruwa da shi? Shin yanzu Amal 'yarsa
ce? Shin ciki ya shiga jikin Jamee bayan abinda ya faru a
tsakaninsu? Wannan ne dalilin da yasa suka baro garin Askira?
Duk da cewan blood group nasu da yazo d'aya ma babbar
shaida ce akan cewa Amal 'yarsa hakan baisa ya amince ba.
He needs to carry out a DNA test. Test d'in da ze tabbatar
masa da cewan Amal jininsa ce ko kuwa a'a.
"Alhj yanzu PA'nka ya kirani batun meeting da kake da shi da
deputy governor" Driver'nsa ya sanar da shi.
"Ohh haka zamu tafi ko?" Ya amsa yana k'ok'arin composing
kansa.
"Eh Alhj" daga haka suka kama hanya suka fice har anan
Afzal na zaune bakin k'ofan akan wani benchi inda ya had'a
kai da guiwa. Seda Alhj'n nan ya wuce Afzal ya d'ago kansa
bisa ji da yayi an bud'e k'ofar a cewansa ma Papi ne yazo
shiga da shi sede yaga ficewan mutum, zama ya cigaba da yi
a wajen yak'i tafiya
****
"Sannu Baby" cewan Mami.
"Ya kikeji? Ya jikin naki?" Papi ya tambayeta.
Kai ta gyad'a musu a hankali "Da sauk'i" ta amsa.
"Ya Nurse meya sameta?"
Ta samu internal bleeding sannan tayi losing blood sosai
bisa ga fashewan da kanta yayi bayan nan kuma ta samu
targad'e a k'afarta da hannu amma ba abinda ya samu lafiyan
abinda ke cikinta." Da mamaki both Papi da Mami suka juyo
suna kallon Amal da alaman tambaya bayyane karara a
fuskokinsu.
"Ciki?" Mami ta tambayeta "Baby kina da ciki?" Shiru tayi bata
amsa ta ba.
"Meyasa baki sanar damu ba Baby?" Papi ya tambaya nan ma
shiru tayi "Kiyi magana kinji Mama na? Kar kiji komi."
"Papi, Mami kuyi hak'uri kar ku d'au na 6oye maku wannan
al'amari saboda wani dalili ne k'wak'k'wara nayi hakan ne
sabida gudun da nake kar kuce zaku miyar dani gidan Yaya
saboda wannan lallura."
"Sam baza muyi miki haka ba Baby shin baki yarda dani bane
dana ce miki se idan ke kika ce kina so zaki koma gidan Afzal
zaki koma? Ki sani nida mahaifiyarki bazamu tilasta ki akan
abinda bakiya so ba, sanin kanmu ne nan duka Afzal be
kyauta miki ba so ki kwantar da hankalinki kinji? Allah ya
inganta kuma."
"Ameen Papi thank you."
"Wata nawa ne?"
"Sati uku ne kacal Mami" ta sanar da ita.
"Allah inganta Mamana sannu Allah sawwak'e."
"Shin har ya aka bigeki Baby? Baki kalli hanya bane kafin ki
tsallake kwaltan?" Mami ta tambayeta.
"Mami na kalla kinsan shi tsautsayi baya wuce ranan sa" haka
kawai taji ta rufa wa Nazeefah asiri saboda tasan halin Papi
muddin yaji Nazeefah na da hannu acikin wannan al'amari abu
baze zo yayi kyau ba saboda ba Afzal kad'ai ba har su Ummi
da Abba da ze shafa ita kuma abu da tashin hankali ne bata
so. Tun da de Allah ya raba ta da su yanzu sede tace Allah
miyar masu da anniyarsu.
"Ermm Nurse" Papi yayi ma nurse d'in magana.
"Yes sir?"
"Nace shin meyasa baku kai ta regular ward ba? Gani nayi
nan VIP ne."
"Tabbas nan VIP ward ne."
"Toh ai kud'in zeyi yawa kuma kin dega ba k'arfi muke da shi
ba."
"Kar ka damu da wannan sabida bawan Allahn da ya kawo
'yarka asibitin nan ya riga ya biya kud'in d'akinta har na sati
sannan ya saye mata magunan da duk likita ya rubuta."
"Subhanallah! Wannan wani mutumi ne haka?"
"Bayan nan jinin nan da kake gani ma na jikinsa aka janye aka
sawa 'yarku leda har d'aya da rabi."
"Blood type nasu yaso d'aya?"
"Tabbas duk O- suke."
"Alhamdulillah Alhamdulillah amma dan Allah waye mutumin
nan? Nasan godiya kad'ai baze biya abinda yayi mana ba
amma dole ne inyi masa godiya."
"Shigowanku ya tafi kuma bey ajiye mana wani identification
card nasa ba yana biya ya tafi."
"Allah sarki Allah sak'a masa da alkhairi ya biya sa da gidan
Al-jannah."
"Ameen" duka suka amsa "Tabbas na Allah basu k'arewa"
fad'in Mami. "Amma Baby kinga mutumin ke?"
"Eh Mami har nan ya shigo nima na basa lamban Papi."
"Allah sarki baki san sa ba?
"Gaskiya ban san sa ba amma se gani nake kaman mun ta6a
had'uwa da shi."
"Allah sarki Allah ya biya sa, zaki ji yunwa ai yanzu ko Baby?"
Ta tamabayeta.
"A'a Mami."
"Kaman ya a'a Baby? Kin manta zaki sha magani ne bayan
nan kuma kinsan dole seda cin abinci yanzu in ba haka ba
abun cikinki baze samu lafiya da k'wari ba ko dan shi seki
hak'ura kina cin abinci."
"Bari inje da kaina cikin restaurant anan in sai miki abincin"
fad'in Papi.
"Toh Papi nagode."
"Allah ya baki lafiya shine babba uwata." A bakin k'ofan ward
d'in ya sake had'uwa da Afzal da har yanzu yak'i tafiya.
Wucesa Papi yayi niyyan yi amma Afzal ya dakatar da shi ta
hanyan shan gabansa cikin hawaye yace, "Papi dan Allah kayi
hak'uri nasan nayi kuskure, nasan ban kyauta maku ba, na sani
na ci amanar rik'on amanar da na d'au alk'awarin zanyi amma
wallahi sharrin shaid'an ne Papi kafi kowa sanin yadda nake
son Amal dan Allah kar ku rabani da ita I beg your pardon."
"Kana son Amal? Meyasa bakayi tunanin hakan ba kafin ka ci
mata mutunci ka walak'anta ta haka? Ka sani Afzal Amal tafi
k'arfin a walak'anta ta, Amal tafi k'arfin kace zakaci mata
mutunci" ransa ne ya mugun 6aci ya shiga d'aga murya se
tunawa yayi a asibiti suke "Kaga a asibiti muke bazan so in
d'aga murya in shiga hak'k'in wasu ba so tun wuri kafin ka
6ata mun rai ka fice anan."
"Papi dan Allah kayi hak'uri, Papi I'm not asking for too much
nasani abunda nayi muku will take much time to heal all I'm
asking is ku barni inga Amal, dan Allah kar ku hanani ganinta
please Papi."
"Baza ka ganta ba Afzal, ganin Amal ne nace baza kayi ba
maza ka kama hanya kabar nan tun kafin insa a koreka."
"Bazan gaji da baka hak'uri ba Papi kuma koda kasheni za'ayi
bazan fasa zuwa duban Amal ina baku hak'uri ba har se idan
Allah ya huci zuciyanku" Papi be sake cewa da shi komai ba
ya fice haka nan har Papi yaje ya siyo abincin wa Amal ya
dawo Afzal be tafi ba. Se chan wajajen k'arfu hud'u da rabi ya
mik'e yaje yayi alwala yayi sallah ganin ba mahalicci se Allah
kuma ko min yaya ba barinsa su Papi zasuyi yaga Amal ba
kawai ya d'ibi kansa ya fice. Police station ya wuce inda ya
tattaro 'yan sanda sannan yayi gida dasu inda aka d'au Safiyya
aka sata a mota se kuka take tana had'a Afzal da Allah amma
ina idan shima ze sha wuya toh se ya tabbata ita da uwar
d'akinta sun d'ana wuyan da ze sha. Daga gidan Amal suka
wuce na Nazeefah inda ya tarar da ita zaune akan carpet na
parlour ta had'a taguni tana ganinsa ta mik'e tsaye yayinda
jikinta ya hau 6ari. Kallonta yayi sau d'aya ya kawar da kansa
dan yadda yayi mata jina-jina da jiki ko ina a jikinta ya
kumbura yayi pink dan azaba ga shatin belt kaca-kaca.
Takawa yayi yaje ya sameta cikin rud'ani tace, "Dan Allah Ya
Afzal kayi hak'uri na tuba dan Allah kar ka sake ta6ani."
"I'm so sorry Nazeefah, I'm terribly sorry" ya bata hak'uri cike
da d'aurewan kai tace, "Ya Afzal ni ya kamata in baka hak'uri
please forgive me."
"A rayuwa ba abinda na tsana kaman inga na miji yana dukan
mance, musamman ma inga magidanci yana dukan matarsa,
tun da nake ban ta6a sha'awan d'aga hannu in mari 'ya mace
ba bale har in d'au abun zana in zaneta hasali duk mijin da
naga yana dukan matarsa tsanansa nake sega yau kinsa na
aikata abunda nafi tsana a rayuwata Nazeefah. It pains me
alot ace yau na d'aga hannu na mari matata ban tsaya anan
kad'ai ba har seda na zaneta ta tayar maga da jiki haka" yayi
maganan had'e da d'aga hannunta yana shafa kan shatin belt
d'in a hankali cike da tausayi "Kinsa na tsani kaina yau Nazee
I so much hate myself for hurting you like I did amma kuma
babban abinda kikayi yau shine na sanya ni tsanarki. I hate
you right now Nazeefah, I hate the fact that I'm married to
you, looking at you disgusts me right now. Na so ki Nazeefah,
na so ki har cikin zuciyata son da bana tsammanin wani d'a na
miji ze iya yi maki irinsa, akwai gur6in da ke kad'ai kika
mamaye shi acikin zuciyata, gur6in da ko Amal bata isa tace
zata mamaye sa ba amma se mey? Se keda kanki kika 6ata
rawarki da tsalle kika sa na tsaneki tsanan da bana jin zan iya
sassauta shi. Zaman ki a gidan nan ya k'are Nazeefah yadda
kika rabani da Amal kema dole ne in rabu dake idan har zanyi
ma Amal adalci, yadda kika fiddata daga gidan nan be kamata
ace ke kin cigaba da zama ba."
"Ya Afzal dan Allah kar kace haka I beg of you dan Allah kar
ka sakeni idan ka rabu dani ban san ina zansa kaina ba bazan
iya rayuwa ba kai ba, Ya Afzal I love you, I love you so very
much" ta sanar da shi cikin kuka.
"Nima bazan iya rayuwa bake ba Nazeefah, batin duk abinda
kikayi mun, batin yadda nakejin na tsaneki yanzu know that I
still love you, kin riga kin zame ga6a a jikina Nazeefah amma
bazan iya cigaba da zama dake a cikin gidan nan ba looking at
you everyday remembering what you did to my innocent Amal,
I can't Nazeefah."
"Ya Afzal dan Allah kayi hak'uri I'm terribly sorry wallahi na
tuba dan Allah ka yafe mun."
"No Nazeefah, you're never sorry, you're never sorry na sani
tuban muzuru kikayi ba dan wai kinyi nadaman abinda kika
aikata ba, hungo" yayi maganan had'e da janyo hijabinta dake
kan couch "Amsa kisa" ba gardama ta amsa tasa "Na taho da
'yan sanda sunzo su d'aukeki."
'"Yan sanda?!" Ta nanata yayin da gabanta yayi wani irin
mumunan tsinkewa '"Yan sanda fa kace Ya Afzal? Dan Allah ka
rufa mun asiri Ya Afzal dan Allah kar kayi mun haka" jikinsa ta
fad'a had'e da zagaye hannayenta a bayansa tana kukan
tsuma zuciya "Ya Afzal dan Allah kar ka bari su tafi dani bazan
iya kwanan cell ba Ya Afzal I beg of you please don't do this
idan tuban Amal kakeso in nema na amince zanyi hakan
amma dan Allah kar ka bari 'yan sanda su tafi dani" shi kansa
seda idanunsa suka cika da hawaye dan yadda ta rik'esa gam
take kuka take kuma had'asa da Allah. Na sosai ta basa
tausayi shima har cikin ransa beso hakan ba amma hakan ne
kad'ai hanyan da ze iya sak'awa wa Amal abubuwan da
Nazeefah sukayi mata. Hannu ya sa na k'arfi da yaji ya raba ta
daga jikinsa "Securities!" Ya kira su Nazeefah bata tashi
rikicewa ba seda taga matan polisawa suna dosan inda take
wani irin rikicaccen ihu tasa had'e da fashwwa cikin wani irin
kuka mey tsuma zuciya "Ya Afzal dan Allah kar ka bari su tafi
dani Ya Afzal I'm deeply sorry please don't let them take me
wayyo Allah Mummy na dan Allah kizo ki taimakeni Ya Afzal
please don't let them take me wayyo Allah na."
"Take her away" yace da polisawan hawaye na tsiyaya daga
idanunsa hannu yasa ya share da wuri. Ihu da bori Nazeefah ta
cigaba da yi bata kuma fasa kiran sunansa ba tana da had'a
sa da Allah sede he's mind is already made up, ko juyawa ya
kalleta beyi ba se hawaye yake ta zubarwa shima kaman ba na
miji ba haka yana ji yana gani aka janyeta waje aka sata mota
d'aya da Safiyya sukayi police station.
Ga shi nan yau ba Nazeefah ba Amal daga kansa se kansa
sauk'a yayi a wajen ya zauna kan kujera sannan ya shiga yin
kuka tsakaninsa da Allah, kukan da ya rasa akan wa yake yi,
akan Nazeefah ne ko akan Amal ne. Daga k'arshe ya gane
kuka akan dukansu biyu yake. Kuka yake akan zafin rabuwa da
Amal da kuma abinda yayi wa Nazeefah a matsayinta na
matarsa. Be ta6a tsammanin Allah ze k'addaro masa da ranan
da zeyi wa matarsa jina-jina kaman yadda yayi ma Nazeefah
ba har yanzu zafin hakan yakeji, sannan kuma har ya sake
turata kwana a cell tabbas yau rana ne da baze ta6a mancewa
da shi ba a rayuwansa.
Yunwa yake ji amma baya jin ze iya sanya komi a bakinsa
tuna Amal nasa na kwance a asibiti rai a hannun Allah, ruwan
zafi kad'ai ya iya sha ya watsa ruwa sannan ya kwanta. Da ya
rufe idonsa se ya tuna da abinda mey shagon d'azu ya fad'a
masa akan cewa kan Amal ne ya fashe acikin jini aka d'auketa
aka sanyata cikin motan da ya yi agaji. Wayansa ya d'auko ya
lalimo lamban Amal sannan ya shiga kiranta.
***
Tana rigingine jikin gadonta Mami na bata abinci wayanta
ya shiga ruri a hankali take juya kanta ta kai kan wayan gani
tayi Habib Albi🌹💍🔐 na flashing akan screen d'in da
hotonsa wanda tayi saving contact d'in da shi. Silencing
wayan tayi ta bar shi ya cigaba da ruri, be dad'e ba Afzal ya
shiga kira again kafin tayi silencing Mami ta tambayeta "Wa ke
kira? Afzal ne?"" Kai zalla ta gyad'a.
"Amma baida kunya shin mey ze kira ya fad'a miki?" Wayan
na tsinkewa Afzal ya shiga kira again kashe wayan Amal tayi
gabad'aya yanzu. "Kin san kuwa d'azu yana nan? Tun kafin mu
shigo yake nan amma nurses suka hanasa shiga saboda
restricted area ne nan d'in, haka har seda Papinki yaje d'ibo
mana kayakin mu sannan ya tafi."
"Mami dan Allah kibar yi mun maganansa I'm not
interested."
"Shikenan Baby yi hak'uri yi sauri ki cinye mu kwanta ki huta."
Wajajen goma da rabi ta d'au wayanta ta kunna da sak'on
Afzal ta fara cin karo ko bud'ewa batayi ba ta goge baza ta
ta6a mancewa da kalan walak'ancin da yayi mata ba, in shaa
Allahu ba abinda ze sake had'ata da shi idan ta samu sauk'i
zatayi ma Papi magana a amso mata takardanta dan muddin
Nazeefah na cikin gidan chan bazata ta6a komawa ba.
*****
GIDAN ALHJ ABDALLAH.
"Khaleefah d'auko mun glasses d'ina a d'aki" fad'in Daddy
lokacinda suke zaune duka a kan dining suna shirin karyawa.
Mik'ewa yayi ya wuce d'akinsa ya d'auko masa sannan ya
dawo yana zama wayan Mummy dake kan dispenser.
"My phone Khaleefah" ta sanar da shi kaman wanda zeyi
kuka ya mik'e a rayuwa ba abinda ya tsana kaman aike. "Wa
ke kira?" Ta tambaya.
"Number ne" ya amsa yana mik'a mata, swiping tayi ta d'aga
"Halo Mummy?"
"Nazeefah?"
"Na'am Mummy."
"Ina kika ajiye wayanki? Tun jiya ina trying numban ki
switched off."
"Mummy dan Allah ki taimaka mun."
"Meya faru?"
"Mummy a cell na kwana."
"A cell! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" chak Daddy dake
karanta newspaper ya tsaya haka Khaleefah ma dake shan
tea.
"A cell? Meya faru? Ina Afzal?"
"Mummy shi ya kawo ni."
"Innalillahi mey ke faruwa me kikayi?"
"Mummy dan Allah kizo police station na Damboa road
muke."
"Toh gamu zuwa" tana sauk'e wayan Daddy yayi saurin
tambayarta "Ya meke faruwa?"
"Nazeefah ce wai Afzal ya kaita police station a chan ma ta
kwana."
"Police station?" Daddy Yayi exclaiming "Dalili?"
"Nima bata fad'a mun ba kawai cewa tayi muje mu sameta
achan Damboa road take." Breakfast da basuyi ba kenan duk
suka mik'e suka duk'ufa cikin mota se police station.
Suna isa akayi dasu 6angaren da su Nazeefah suke kuka
tasa lokacin da ta gansu haka Mummy ma. "Nazeefah meya
faru? Meyasa Afzal ya kawo ki nan? Mey kikayi masa."
"Mummy dan Allah kuyi hak'uri Mummy I'm so sorry."
"Meya faru Nazeefah?" Daddy ya tambaya.
"Ya Nazeefah?" Khaleefah da har yanzu ya kasa amincewa
da abinda idanunsa ke gane masa kirata.
"Daddy laifi nayi masa, laifin da ni kaina ina jin kunyan sanar
daku please help me out Daddy dan Allah kar ka barni in sake
kwana acikin nan." Waya Daddy ya zaro ya kira Afzal bada
dad'ewa ba ya d'aga.
"Ka taho inda ka kawo Nazeefah yanzun ina jiranka." Bacci
yakeyi lokacin da Daddy ya kirasa yana sauk'e wayan ya koma
baccinsa seda ya k'ara baccin kusan minti talatin sannan ya
mik'e ya d'aga wayan nasa sak'o ya tura wa Amal ya miyar da
wayan ya zarce bayi yayi wanka ya fito ya karya da corn flakes
ya koma d'aki ya shirya tsaf sannan ya fito. Isansa police
station d'in ya tarar da su Abba da Ummi har su Daddy sun
kira su. Saidai ko alamun tashin hankali babu tattare da Afzal
dalili kuwa yasan shine da gaskiya. Binsu yayi duka da
gaisuwa sannan yasa aka fito da Nazeefah daga cikin cell d'in
jikin Mummy ta fad'a tana kuka sosai yayinda Safiyya ta la6e
a lungu tana kuka itama. Breakfast da ya siyo musu ya mik'a
aka basu nan da nan suka karya a wajen sannan Abba ya
tambayeshi meya faru.
"Baki fad'a musu abinda kikayi bane?" Ya tambayi Nazeefah
da jikinta keta k'yarma har yanzu. "Magana nake miki
Nazeefah confess your crime, crimes if possible" sede ta kasa
magana gyaran murya yayi "Tunda bazaki fad'a ba ni zanyi
hakan. Mutane tayi hiring tasa aka kad'e Amal yanzu haka
Amal na kwance a gadon asibiti rai a hanun Allah duk wai a
sunan kishi."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" salati kawai kukeji yake tashi
a wajen. "Nazeefah?" Mummy ta kewayo tana kallonta "Da
hankalinki? Yaushe kika fara kisan kai?"
"Mummy dan Allah kiyi hak'uri wallahi sharrin shaid'an ne."
"Sharrin shaid'an? Sharrin shaid'an?" Mari me kyau Mummy
ta zabga mata cike da 6acin rai, wannan wani irin haihuwa ne?
Taya zaka haifi d'a amma d'a ya gagareka? Ashe duk kalan
nasihar da takeyi wa Nazeefah a wajen take ajiye mata abinta?
take Ummi ta shiga tsakaninsu tana bata hak'uri.
"Tarbiyyan da na baki kenan? Da abinda zaki sak'a mun
kenan nida Daddy'ki? Wannan wace irin rayuwa ce?" Tuni ta
shiga yin kuka yayinda Ummi ta cigaba da bata hak'uri.
"Afzal kayi hak'uri" cewan Daddy "Dan Allah kayi hak'uri."
"Hak'uri nayi Daddy amma Nazeefah must pay for what she
did" har a nan Abba bece komi ba yana bayan d'ansa d'ari-
bisa-d'ari saboda akan gaskiyansa yake.
Wayan Nazeefah Afzal ya zaro daga aljihunsa ya kunna
"Gashi da hannunki zaki kira mutanen da kika sa suka bige
Amal kice musu suzo su sameki dai-dai bakin junction d'innan
justice must be served for Amal." Amsa Khaleefah yayi ya
mik'a mata nan ta lalumo lamban d'aya daga cikinsu tayi
kaman yadda Afzal ya umarceta se kakkarwa take. Har anan
mamakin ta Mummy take, sam ba irin tarbiyyan data bata ba
kenan, kunya take ace ita ta tsuguna ta haifi gagararriyar 'ya
kaman Nazeefah idan a d'an shekarunta zata iya sa a bige
mutum gaba mey zatayi kenan?
Yaran suna isowa bakin junction d'in sukayi mata waya nan
Afzal ya d'au 'yan sanda uku a motansa suka fice tare da ita
Nazeefar a gaban mota suna isa wajen ya umarceta da ta
sauk'a tayi musu magana achan aka kamasu aka k'ariso dasu
cikin police station d'in. Mummy se kuka take Ummi da
Khaleefah suna bata hak'uri.
"Officers ku hukunta mun su hukuncin dake dai-dai da
attempt nayin kisan kai" Afzal yace da polisawan yana nuni da
yaran da Nazeefah tayi hiring samari guda biyu. "Wad'an nan
biyu kuma" yayi nuni da Nazeefah da Safiyya "Ka miyar dasu
cikin cell ka kulle mun su I'll speak with my lawyer in shaa
Allah justice must he served for Amal nan gaba ko akan mey
bazasu sake yin ganganci ta6a lafiyar wani ba bama Amal
kad'ai ba."
Yana kaiwa nan ya juya ya fice kiransa Daddy yake amma ko
ya juya bale ya sauraresa motansa ya shiga ya basa wuta.
Kaf wajen ba wanda kansa ya mugun d'aure yake kuma cikin
tsananin tashin hankali kaman Daddy da yaji Afzal ya ambaci
sunan Amal a matsayin wanda Nazeefah tasa aka kad'e. Shin
wata Amal ce wannan? Amal da ya tsince ta a bakin
makaranta jiya ya kai asibiti ne? Shin Amal Abdallah ce
kishiyar Nazeefah Abdallah 'yarsa? yau wani irin k'addara ne
wannan? Wani irin fallasa ne yake shirin afkuwa masa? Wani
irin badak'ala ne wannan? Ta inda Allah ze kamasa alhak'in
Jamee da ya d'auka kenan? Fatansa d'aya ne Allah yasa Amal
Abdallah ta asibiti ba 'yarsa bace idan kuwa har hakan ya
tabbata 'yarsa ce nasa ya k'are that mean 'ya'yansa biyu suna
auran miji d'aya kenan. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.
RANA DAYA Chapter 37
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
Tareda Naja'atu Lawal Rijau Niger State
@Whatapp 08083232323 or 09060202323
PAGE 37
"Ina securities?" Daddy ya tambaya "Nawa ne kud'in bailing
nata?"
"Ranka shi dad'e ai baze yiwu kayi bailing nata ba saboda
'yarka is accused of an imprisonable offense wanda hukuma
take tsoron saketa gudun kar ta sake tafka wannan laifi dan
haka kotu ya nemi a ajiyeta under close supervision idan har
ba wai wanda yayi filing case akantan bane ya buk'aci a
saketa that is idan yaja baya da case d'in" d'aya daga cikin
securities d'in yayi masa bayani.
"Alhj Amin dan Allah kayi wa Afzal magana yayi hak'uri duk
nan mun san Nazeefah bata kyauta ba amma yayi hak'uri yaja
baya da filing case d'innan hannun mutum baya ri6ewa ya
yasar komin munin halin Nazeefah bazan so ta k'are a gidan
yari ba kuma tabbas idan Afzal ya kai k'aranta kotu tunda tana
da laifi chan zasu kaita, ni bazanyi fighting against Afzal ba
saboda shike kan gaskiya. Amma dan Allah ba dan ni ko ita
ba kayi wa Afzal magana yayi hak'uri, kai kad'ai keda ikon
hanasa aikata hakan please." Hannu Abba ya dafe a
kafad'ansa "Karka damu Alhj Abdallah zanyi masa magana in
shaa Allahu za a sake Nazeefah."
"Nagode nagode sosai."
"Toh bari mu wuce Hjy Mariam mu tafi ko?" nan sukayi
sallama suka fice. Har anan kuka Mummy keyi.
"Yanzu mey riban wannan abin kunyan da kikayi mana kika
kuma yi wa kanki Nazeefah? Ki gaya mun mey riban hakan?
Kiga yadda Daddy'nki ke rok'an Abban Afzal kaman mey
maula yanzu hakan ya miki kyau?"
"Mummy dan Allah kiyi hak'uri, Daddy I'm sorry" ta amsa
cikin sautin kuka.
"Wace wacan?" Mummy ta tambayeta tana nuni da Safiyya.
'"Yar aikin Amal ce."
"Mey tayi ita kuma?"
"Mummy please forgive me."
"Ki bud'e bakinki kiyi magana ana tambayanki!" Daddy ya
tsawata mata.
"Daddy dan Allah kayi hak'uri wallahi sharrin shaid'an ne."
"Am asking you for the last time idan har baki amsa
tambayan da Mummy'nki tayi miki ba wallahi tallahi kin deji
rantsuwa ba kaffara ko? Zame hannu na zanyi acikin wannan
al'amari Afzal yayi duk abinda yaga dama da ke tunda ke
kince bakida hankali."
"Daddy wannan itace 'yar aikin Amal Safiyya wacce nayi
amfani da ita na fidda Amal daga d'akinta."
"Kika fidda Amal daga d'akinta?" Mummy ta tambaya da
d'umbun mamaki. "Kina nufin kinsa Afzal ya saki Amal?"
"Be saketa ba yaji tayi."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Nazeefah! Is this how evil
you've become? A iya shekarunki kike wannan mak'irci? har
kinsan ki raba aure ki shiga tsakanin miji da mata? Wallahi ba
tarbiyyan dana baki ba kenan Allah ma shaidana ne" ta k'are
maganan tana neman fara sabon kuka. "Duk kalan wa'azi da
nasihan da nake yi miki ashe shiga kunneki kawai yake ta
dama yana fita ta hagu ashe a wajen kike ajiye mun magana
na, wallahi ba abun in ja miki Allah ya isa ba."
"A'a Hjy Surayya kiyi hak'uri duk bey kai ga haka ba" Daddy
yace da ita yayin da Khaleefah ya cigaba da bata hak'uri yana
shafa bayanta a hankali. Shi kansa mamakin halin 'yar uwarsa
yake.
"Mey da mey kika rink'a sanya yarinyar nan yi haka har kika
sa Amal tayi yaji iyyeh?" Tisata Mummy tayi a gaba seda ta
irga dukkan abubuwan da ta aikata "Wallahi Alhj idan har baka
bari an hukunta taba an yanka mata watanni ko shekaru a
gidan yari ba uba kage ga 'yar nan ba, ni da kaina zan kira
Afzal in k'arfafa masa guiwa in shaa Allah sekin biya abinda
kikayi wa baiwar Allahn nan, har kisa mijinta ya zargeta?
Zargui fa Nazeefah! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."
"Mummy dan Allah kar kiyi mun haka Daddy na tuba dan
Allah karka saurari Mummy."
"Kin bani kunya Nazeefah, na d'au kinyi hankali dagaske har
nake alfahari da hakan ashe halin nan naki na nan har yanzu,
yaudara na da Mummynki kawai kikayi kika nuna mana kin
shiryu, wallahi ban ta6a tsammanin hakan daga gareki amma
bazan biye miki ba, Hajiya Surayya kiyi hak'uri hanun mutum
baya ri6ewa ya yasar komin mey Nazeefah tayi har yanzu a
matsayin 'yarmu take hakan baze ta6a canzuwa ba. Kuma ko
kema fad'a kawai kike baza kiso ace an kai 'yarki gidan yari ba
hak'uri ya zama dole dama acikin 'ya'yanka dole akwai wanda
ze gagareka saidai mu a matsayin mu na iyaye muyi hak'uri
mu cigaba da yi musu fatan shiriya."
"Hakane Alhj" ta amsa tana kewayowa kan Safiyya "Ke kuma
Safiyya kike ko wa kinga abinda kwad'ayi ya janyo miki ai ko?
Shin a ina ma kika samota tun farko?" Ta tambayi Nazeefah.
'"Yar mey aikin Su Rumaysa ce k'awata wallahi tun farko ita ta
fara bani shawaran nan."
"Ke kuma dake dabbace Allah beyi miki hankali ba kika biye
mata ko? Ai kinga ni da idonki kinga yadda ta kaiki ta baroki."
"Mummy dan Allah kiyi hak'uri wallahi na tuba."
"Tashi mu tafi Khaleefah."
"Mummy please don't go Mummy I'm sorry Daddy dan Allah
ka bata hak'uri." Ko sauraronta Mummy batayi ba ta fice "Alhj
muna jiranka." Juyowa yayi ya kalli Nazeefah ba shida bakin yi
mata horo saboda abun kunyan da ta aikata kad'an ne a ganga
da nasa, tausayi ta basa sanin duk abinda takeyi shi ya janyo
komai, ko dan alhak'in Jameela daya d'auka yaci ace Allah ya
basa gagararriyar 'ya kaman Nazeefah.
"Nazeefah kiyi hak'uri in shaa Allahu zan nemi Afzal inyi
masa magana bazaki sake kwana cikin nan ba."
"Daddy kaima tafiya zaka yi? Dan Allah kar ku tafi ku barni."
"Mummy'nki na jira na a waje se anjima idan na dawo" kuka
take sosai tana kiran sunansa amma haka ba waiwaya ya fice
shima, nan aka sake miyar dasu cell ita da Safiyya, ba abinda
take nadama kaman fara bin shawaran Rumaysa da tayi. Gashi
yanzu tana chan tana morar rayuwarta a k'ark'ashin AC ita
tana nan tana shan wuya. Tabbas duk duniya bakada abokiyar
shawarar da ta fi mahaifiyarka, itace kad'ai zata baka
shawarar da bazata cutar da kai ba amma idan ka biye wa
k'awaye musamman na banza irin su Rumaysa da Suwy da ta
so sata aikata shirka toh tabbas kana tattare da k'alubale. Yau
ta gane bin shawaran k'awa bala'i ne musamman irin nasu
Rumaysa. Tayi nadama, tayi nadama matuk'a.
Mummy ta kasa hak'ura suna isa gida takira maman
Rumaysa bayan da suka gaisa take irga mata halin da
Rumaysa ta jefa Nazeefah aciki. Atafir maman Rumaysa tace
ita sharri ake yi wa 'yarta, 'yarta baza ta ta6a aikata haka ba.
Itama Rumaysan munafukar kanta bayan da Mamanta ta kirata
tayi mata maganar bushe ido tayi tace ita bata ma san da
wannan zance ba iyaka abinda ta sani Nazeefah tace ta nemo
mata yaran aiki guda biyu d'aya nata d'aya na kishiyarta.
***
Afzal kam yana fita daga police station d'in ya kama hanyan
TH dan duban lafiyar Amal tasa, saidai kaman jiya yau ma
nurse dake bakin k'ofan ta hanasa shiga. Ba irin rok'an duniyan
da beyi mata ba amma ta hanasa shiga acewarta bashida
appointment da kowa. Ana cikin haka sega Mami ta fito be
6ata lokaci ba yaje ya tareta. "Mami ina kwana?" Kaman
wacce bazata amsa ba tace "Lafiya wani abu ne?"
"Mami ya jikin Amal?"
"Da sauk'i idan abinda ya kawo ka kenan kana iya kama
hanyanka ka koma."
"Mami dan Allah kar kiyi mun haka, Mami nasan ban kyauta
muku ba amma kuyi hak'uri ku bani wani daman, d'an Adam
ajizi ne kuma na gane kuskure na please forgive me."
"Ka 6ace ka bani waje Afzal, duk kalan walak'anci da rashin
mutuncin da kayi wa Baby har kana da bakin cewa a sake
baka wani daman? Saboda ka kuma walak'anta ta? Toh
wallahi kayi k'arya Afzal dan kuwa Baby tafi k'arfin a
walak'anta ta shiyasa nake son tun kafin raina ya 6aci ka fice
anan kar insa securities su ja mun kai waje" tana kaiwa nan ta
bi gefensa ta fice. Kad'an ya rage Afzal beyi kuka ba a wajen,
gu ya nema ya zauna ya had'a tagumi haka har Mami tazo ta
wuce sa da bak'ar leda a hannunta da alama breakfast ta siyo
musu anan restaurant bata yi mai magana ba, ko kallon kirki
bata k'are mai ba. Mik'ewa yayi ya fice inda ya wuce gidan
madara ya siyo kayan tea da dama wanda a hanyan sa na
dawowa Abba ya kirasa, connecting wayan nasa da car
Bluetooth yayi sannan ya d'aga.
"Halo Abba?"
"Na'am Prince kana ina ine?"
"Na d'an fita cikin gari ne Abba."
"Ko zaka iya biyawa tanan? Ina son muyi magana."
"Toh Abba ba matsala."
"Ya jikin Amal? Wani asibiti take kaga ya kamata nida
Umminka muje mu dubata ai." Gabansa yaji ya fad'i yasan
komin jimawa da dad'ewa gaskiya ze fito su Abba zasu gane
Amal tayi masa yaji, daga nan kuma ya san nasa ya k'are har
hango kalan masifa da fushin da Abba zeyi masa yake idan ya
gano cewan Amal tayi masa yaji bisa ga rashin kyautatawan
da yake yi mata.
"Prince?"
"Eh a TH aka rik'eta" ya amsa cikin sauri.
"Toh in ka taho se ka kaini da Umminka muje mu dubata ko?"
"Eh Abba sena shigo."
"Yauwa Allah ma albarka."
"Ameen Abba" sannan ya katse wayan. Ajiyar zuciya ya
sauk'e sannan ya k'arisa asibitin nurse d'in dake gadin bakin
ward d'in still yaje ya sameta.
"Bawan Allah wai baka gajiya ne? An fad'a maka bakada
appointment da kowa baze yi ka shiga ba."
"Nurse na sani, na sani kuma bawai na dawo dan hakan
bane" ledan daya ciko da gongonin madara da milo da kwalin
sugar da su biscuit da cookies irin masu tsadan nan da kuma
sauran kayan tea ya d'ago ya ajiye akan table natan.
"So nake in biya bills na drugs nata da kuma na d'akinta na
kwana bakwai I'm sure kafin nan an sallameta."
"Karka damu da hakan, bawan Allahn daya kawota asibiti jiya
ya riga ya d'auke nauyin komai."
"Ko waye shi?"
"Ya 6oye identity nashi."
"Allah sarki Allah sak'a mishi, ga wannan toh ina son ki kai
mata amma nasan idan kikace in jini ne bazata amince ta
kar6a ba."
"Inji wa zan ce toh?"
"Kice mata inji mutumin da ya kawota asibitin jiya."
"Toh zan sa akai mata kar ka damu."
"Kice ina gaisheta dan Allah."
"Karka damu amma ince inji wa?"
"Kije inji Habib Albinta."
"Habib Albi? Toh zan fad'a."
"Thank you and one more favor please."
"Don't you think you're asking for too much?" Ta tambayesa
had'e da zuba mai ido.
"Dan Allah ai nace."
"Ma tukun mey had'inka da patient d'innan? Kai mijinta ne?"
"Yes."
"Then meyasa iyayenta suke korinka haka?"
"Matsala muka samu har tayi yaji ta koma gida shiyasa nake
son ki taimaka mun dan Allah, I really love my wife, I love her
soo much."
"Fad'i abinda kakeso."
"I want to know ko abu ya samu lafiyan cikin dake jikinta
bayan hatsarin jiyan."
"Toh ni bani muka mata aiki ba jiya 'yar uwata ce sukayi
mata kaga ko bazan sani ba."
"Please call her and ask I really want to know ko babyna na
nan har yanzu." Shiru tayi bata ce komai ba tana
contemplating. Hannu Afzal ya sa a aljihunsa ya ciro wallet
nasa tare da irga dubu biyu ya ajiye mata. "Ki sa kati da
wannan but please ki kira 'yar uwar taki ki tambaya mun ita."
Ba makawa ta d'au wayanta ta yi kaman yadda ya buk'ata.
"So?" Eager Afzal ya tambayeta bayan data sauk'e wayan.
"Your baby is still safe, tace ba abinda ya samu lafiyan cikin."
"Alhamdulillah" wani kalan ajiyan zuciya Afzal ya sauk'e.
"Alhamdulillah! Thank you so much I really appreciate."
"Lallai da alama kana ji da wanan d'an naka, d'an fari ne ko?"
"In shaa Allah" ya amsa ta yana murmushi yayin da ya kasa
6oye farin cikinsa.
"Ayyah Allah ya sauk'eta lafiya toh."
"Ameen thank you bari zan koma anjima zan dawo."
"Toh seka dawo."
"Please make sure kin isar mata da sak'o na."
"Kar ka damu" da haka sukayi sallama yana ficewa ya bi ta
gida inda Abba ke tsammaninsa.
"Ka hau kujera ka zauna mana sekace wani bak'o" Abba yace
dashi.
"A'a Abba kar ka damu nan d'inma yayi mun."
"Batun Nazeefah ne dama, hukuncin da ka yanke yayi dai-dai
Prince kuma nida Umminka muna bayanka d'ari-bisa-d'ari" ya
sanar dashi yayinda Ummi dake gefensa take gyad'a kai cike
da goyin baya.
"Thank you Abba."
"Tabbas duk wanda ya zalunci wani shima be kamata a barsa
haka ba sai dai Allah ma muna yi masa laifi kuma idan muka
nemi tuba yana yafe mana shine nikeson kai ma ka duba kayi
mata hak'uri, Nazeefah matarka ce har yanzu Prince, nasan
abinda tayi da zafi amma kayi hak'uri."
"Abba kasan evil acts da yarinyar nan ta rink'a yi kuwa? Inda
ka sani baza ka ce a tausaya mata, ban so in irga abubuwan
da tayi mun bane saboda darajan iyayenta amma abinda
Nazeefah tayi mun ta kuma yi wa Amal yaci ace na rubuta
mata takardan ta yanzu haka."
"Subhanallahi me tayi haka?" Kwashe komi yayi ya fad'a
musu abu d'ayan da ya 6oye shine yajin da Amal tayi da kuma
cikinsa da take d'auke da shi.
"Nazeefan de?!" Ummi tayi exclaiming.
"Ita fa Ummi."
"Subhanallahi yarinyar da nake cewa tayi hankali ta rungumi
k'addararta? Toh inde haka ne head na Amal da aka d'auke
ma ranan bikin dinner ku ita ce."
"Sosai ma kuwa Ummi kika barni har rushe cake d'in da
yarinyar chan tayi ita ta turata."
"Kai amma yarinyan nan akwai ta da sharri, ace a iya
shekarunta haka take wannan mak'irci? Allah sarki Amal
baiwar Allah ya jikin nata?"
"Alhamdulillah da sauk'i."
"Bataji ciwo bade sosai ko?"
"Toh Alhamdulillah de" be isa yace eh gashi ba saboda shi
kansa be san iya ciwon nata ba banda fashewan kai da
mutumin shago ya fad'a masa.
"Gaskiya Nazeefah bata kyauta ba kuma koda nine a position
naka abinda zanyi kenan amma Prince kayi hak'uri ko dan
iyayenta kayi mata hak'uri kar ka kai maganan nan kotu
dukanta da kayi da kuma sata kwanan cell da kayi ma kad'ai
ya ishi ya sata nadama kayi hak'uri kaja baya da maganan dan
Allah."
"Abba-"
"Dan Allah nace Prince wallahi rok'ana Abbanta yake dukda
shima bawai ya ji dad'in abinda ta aikata ba amma sedon
'yarsa ce kasan hannun mutum baya ri6ewa ya yasar, yaso ko
anyi releasing nata se iyayenta su d'auke ta su tafi da ita chan
gidansu kai kuma idan kaji ka huce zaka iya dawo da ita
d'akinta se kayi bikonta."
"Toh shikenan Abba amma dan Allah ka bari ta sake kwanan
cell d'in yau yaso gobe se na sa a saketa abinda tayi wa Amal
zafi yake mun."
"Ko ya kace Prince nide kawai kar akai maganan nan kotu."
"Toh Abba in shaa Allahu."
"Nagode Allah ya cigaba da yima albaraka."
"Ameen" shi da Ummi suka amsa.
"Toh Hjy Mariam kije ki shirya Prince ya kaimu muje mu
duba Amal, seki d'iba mata fruit juices d'innan biyar ko shida
haka da carton na ruwa d'aya, duk dey yadda kika ga ya dace."
"Toh Alhj" nan ta mik'e bayanta Afzal yabi izuwa sashinta
yayinda yake tunanin ta ina ze fara sanar da ita cewan Amal
tayi masa yaji. Shi kad'ai ya zauna a parlourn yayinda ta shige
d'akinta dan canza kaya sede har ta fito ta zauna gefensa be
sani ba tsan-tsan yadda yayi nisa a tunani.
"Prince?" Ta ambaci sunansa had'e da tapping nasa akan
cinya a firgice ya d'ago kai yana kallonta "Lafiya? Tunanin mey
kake haka?"
"Urhmm.. Babu."
"Yau kuma? Gaya mun menene? Tunanin Nazeefah kake?"
"Ummi no."
"Yaya ne toh? Feel free to talk to me kaji?"
"Ummi it's Amal."
"Innalillahi!" Haka kawai taji gabanta ya tsinke. "What about
her? Bade wani abun bane ya sameta dai ko?"
"Ummi dan Allah kar kiga laifi na wallahi zafin so da kishin da
nakeyi mata ne ya janyo komai, sanin kanki ne ina son Amal,
son da ni kaina wataran har tsoro yake bani."
"Tabbas ina sane da hakan Prince, meya faru? Tell me
already."
"Ummi Amal tabar gida."
"Tabar gida kaman ya?"
"Tayi mun yaji kwana biyu kenan yau."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kana nufin Amal bata gidan ka
ma da Nazeefah ta tura aka kad'e ta?" Kai zalla ya gyad'a.
"Meya faru ta tafi? Akan abubuwan da Nazeefah keyi mata
ne?"
"Kusan hakan."
"Prince ka bud'e baki kayi mun magana mana mey kake
cewa?"
"Ummi ni ne, ni janyo komai tun da Nazeefah ta fara kawo
mun k'aran Amal ban ta6a d'aukan mataki akai ba haka nan na
cigaba da kallonta da shi har ya zammana ko magana ba ma
yi, ana cikin haka kuma Safiyya tace mun wai Amal ta fara
shigo da maza cikin gidan-"
"Kai kuma ka amince?" Tayi saurin katsesa.
"Ummi wallahi kishinta da nake ne ya jan-" mari me rai ta kai
masa a k'eyarsa "Amma ban ta6a sanin kai soko bane Prince
se yau" rai ya had'e yana susa k'eyan nasa bisa ga zafin marin.
"Har za'a ce Amal tana kawo maka maza cikin gida kuma ka
amince ba tare da kayo bincike ba? Ai bama abin bincike anan
daga ji an san sharri ne da k'azafi."
"Ummi ni wallahi ba zarginta nake ba."
"Toh mey kakeyi? Ai de idan ance mutum na kawo maza gida
kwana dasu yake kenan."
"Wallahi ni ba haka nake nufi ba, I know Amal nasan baza ta
ta6a cin amanata ba."
"Toh da aka fad'a maka se kayi mey seka sameta kace mata
kana zarginta?"
"Ni kawai ce mata nayi ban yafe ba idan ta sake shigo min da
maza gida."
"Wallahi kai ka sayi yin yajin Amal da hannun ka lallai ashe
baka fasa halin nan naka na amincewa da duk abinda aka
fad'a maka ba, yaushe zakayi wayo Afzal? Ace kaman ka
amma ba bincike ba komai da an gaya maka abu ka d'auka ka
zauna akai?"
"Ummi I'm sorry."
"Kai ka sani ai yanzu kam, bakin da ya sa Amal tayi yaji shi
zeje ya dawo da ita d'akinta."
"Ummi please don't talk like that please help me get Amal
back wallahi I can't do without her."
"Kaje ka samu iyayenta?"
"Jiya muna tare a asibitin amma ko sauraro na ba su son yi
bale in samu daman basu hak'uri, duk fushi suke dani ko ganin
Amal sun hanani d'azu ma naje amma fushi suke dani har
yanzu."
"Ai daidanka kenan nan gaba ko d'an akuya ka gani cikin
gidanka akace maka na Amal ne zakayi bincike ka ji bakinta
kafin ka amince."
"Ummi please don't do this."
"Toh ya kake son inyi? Kai shikenan kullum bakada aikin da
yafi ka ringa tafka shirme ka barni da Abbanka da bada hak'uri
da neman alfarma?"
"Ummi I'm sorry wallahi bazan iya rayuwa ba Amal ba."
"Zaka koya kar ka damu ina Abbanka in sanar dashi wannan
rashin hankalin da ka tafka" kafin ta mik'e ya zaunar da ita.
"A'a Ummi please karki fad'a masa kibari se idan mun dawo
na koma gida, kema kika mun surutu wallahi na Abba bazeyi
kyau ba."
"Ashe kasan kayi ba dai-dai ba kenan har Amal ce za ace
maka tana kawo maza gida ka yarda? 'Yar da har yau ban
ta6a ganin k'wayan idonta ba tsan-tsan kunya."
"I'm sorry."
"Ai ita zaka bawa hak'uri ba ni ba."
"Kema zan baki dan Allah karki sanar da Abba."
"D'agani ni kam mutum ga shekaru ga hankali amma bayi aiki
dasu nan gaba zakayi wayo ai." Hannunta ya sake kankamewa
"Please don't tell Abba Ummi dan Allah" ya sanar da ita
tamkar zeyi kuka.
"Kuka zakayi mun ne?" Kai yayi saurin kad'awa "A'a."
"Aikin banza kawai duk nabi na 6ataka ka zama wani abun
daban."
"Ita Amal d'in fah? Ka samu kunyi magana da ita tun
tafiyarta?"
"Nata kiranta jiya amma bata returning calls d'ina tana
matuk'ar fushi dani please help me out Ummi" hararansa tayi
ba tare da ta sake cewa komai ba.
****
Haka har suka isa asibitin bata sanar da Abba ba. Tunda su
Mami ba son ganinsa sukeyi ba ko k'udurin shiga ciki Afzal
beyi ba gudun kar a garin hakan magana ya fito Abba ya gano
gaskiya ya kuraresa, yafi son se idan har ya sauk'e su ya koma
gida tukun Ummi ta sanar da shi komin yaya dey yasan ba
kiransa Abba zeyi musamman yace ze mai masifa ba.
"Ermm Abba wayana ba credit ko zaka kira Papi kace mishi
mun iso?" Ya k'irk'iro k'arya sanin ko ya kira Papi ba lallai ne
ya d'aga ba.
Ba gardama Abba ya kira Papi ya sanar dashi isowansu.
"Toh gani fitowa."
"Ya wai?" Ummi ta tambaya.
"Yace yana fitowa." Jin haka se Afzal ya shafe aljihunsa
"Omi'god!" yayi exclaiming da gan-gan.
"Ya lafiya?" Abba yayi saurin tambaya.
"Nayi mantuwa a mota ina zuwa Ummi d'an rik'e wannan
please" yayi maganan yana mik'a mata ledan soft drinks da
suka d'ibo wa Amal had'e da tura mata carton na ruwan
gefenta. Sarai ta gane kan plan nasa, so yake ya gudu gudun
kar asirinsa ya tonu. "Ummi" ya kirata a hankali through gritted
teeth yadda Abba baze ji ba, yana mey mata ido kai ta kad'a
sannan tasa hannu ta amsa da sauri ya bar wajen kafin Papi ya
fito.
Har su Ummi suka mik'a gaisuwansu Afzal be dawo ba se
chan daya hangosu daga nesa sannan ya k'arisa lokacin har
Papi ya rakasu ya koma ciki.
"Kai kuma daga d'auko abu se ka k'i dawowa?" Abba yace da
shi.
"Ermm" yayi maganan yana susa gefen kansa "Mun had'u da
wani abokina na ne matarsa ta haihu shine naje nayi mata
barka." Ita de Ummi banda ido ba abinda take bin Afzal da shi.
Tun yana yaro haka nan yake da d'an banzan halin nan ba
yadda batayi da shi ba amma ya kasa canzawa, mutum zeyi
masa lefi baze samesa ya fad'a masa ba se aukin zurfin ciki
bayan nan gashi duk maganan da aka fad'a masa ba bincike
ba komai yake amincewa gashi ai yanzu inda banzan d'abi'ar
tasa ta kaisa a banza ze rasa mafi son halittar rayuwarsa.
"Allah sarki Allah raya abinda aka haifa."
"Ameen mu tafi ko?"
"Ba zaka je ka duba matar taka ba yaso mu jira ka? ko
kuwa?"
"Zan dawo anjima Abba bazan so in ajiye ku waiting ba ai."
"Toh shikenan mu tafi" nan suka koma gida.
***
"Ya na d'au ai zaka koma?" Abba ya tambayi Afzal dake
k'ok'arin sauk'owa daga mota. "Zan ci abinci ne tukuna."
"Toh ni na wuce site d'ina zan shirya ma ina da meeting"
daga nan Afzal ya bi bayan Ummi suka zarce site nata.
"Nifa banida abincin da zan baka" tace da shi bayan da suka
shiga ciki.
"Badan hakan nake nan ba Ummi I just wanted to ask you ya
jikin Amal."
"Da sauk'i" ta amsa shi sama-sama.
"A ina taji ciwon?"
"Kanta ne ya fashe ta gefe sekuma targad'e da ta samu a
hannu da k'afa." Har cikin ransa yaji wa Amal yayinda yake
sake tsanan Nazeefah ji yayi kaman kar ya ja baya da kai
zancen kotu sa'an ta d'aya Abba ya sa baki da kuwa seta ga
abin mamaki. "Allah sarki I wish I could see her."
"Toh kana iya komawa gida tun da na sanar da kai abinda
kake buk'atan ji."
"Ummi kema fushi kike da ni?" Ya tambayeta a maraice.
"Taya bazan yi fushi ba da kai Prince akan wannan rashin
hankali da tausayi daka tafka?"
"Ummi I'm so sorry Amal na fushi da ni, Papi da Mami suna
fushi dani ke ma kina fushi dani a ina kikeson insa kaina? Dan
Allah kiyi hak'uri." Se kuma ya bata tausayi.
"Shikenan mey kakeso kaci?"
"Ni bana jin yunwa abu d'aya nakeso ki daina fushi dani dan
Allah."
"Shikenan na daina Allah ya bawa Amal lafiya."
"Ameen" ya amsa tare da rungumarta she's the only one he
has left ba Amal ba Nazeefah yanzu. A hankali ta zagaye
hannayenta a bayansa tana bubbugasa "Zan yima Abbanka
magana in shaa Allahu Amal zata dawo a gareka amma da
sharad'i" ta sanar da shi had'e da janyesa daga jikinta.
"Muddin muka samu muka dawo da Amal a gareka ka sake
ka kuskura ka ci zarafinta zanyi fushi da kai sosai Prince
fushin da komin yaya bazan sake sauk'owa ba."
"Ummi na amince in shaa Allahu bazan sake zaluntar Amal
ba, wannan d'in ma sharrin shaid'an ne amma daga yanzu nayi
hankali bazan kuma sake ba."
"Yauwa."
"Ummi?" Ya kirata.
"Wani abune?"
"Ummi Amal is pregnant."
"Iyyeh? Kace mene?" Ta tambayesa had'e da zaro ido.
"Amal is pregnant jikanki na hanya."
"Prince wasa kake kokuwa?" Ta tambayesa yayinda ta kasa
6oye farin cikinta. "Kasan fa ba a wasa da irin maganan nan."
"I'm serious."
"Masha Allahu, Alhamdulillah Alhamdulillahi ashe de akwai
rabo nima watarana zanga jika na kai amma nayi farin ciki,
wayyo Amal baiwar Allah. Yarinyar nan ta ko ina tayi ne Prince
ga kunya, ga nutsuwa, ga hankali da ladabi, bugu da k'ari kuma
gashi yanzu tana d'auke da jika na, wata nawa ne?"
"Nima ban sani ba a bakin Nazeefah nakeji ashe dalilin da
tasa a kad'e Amal kenan dan ta samu ta raba Amal da abinda
ke cikinta."
"Oh! Wallahi ko a mafarki ban ta6a sanin Nazeefah bata da
hankali haka ba se yanzu. Yanzu saboda Amal ta rigata
d'aukan cikinka shine har zata sa a bige baiwar Allah?"
"Wallahi Ummi shiyasa ban so Abba ya amince wa Daddy ba,
na so ya barni in kai k'ara kotu saboda a hukunta mun ita."
"Kayi mata hak'urin kawai Prince ai ko a haka ma ta horu.
Allah ma kansa yace yana tare da masu hak'uri da yafiya,
kuma kaga wala Allah ma idan ka yafe mata kai ma Amal da
iyayenta su yafe maka."
"Haken kam Ummi toh bari zan koma gida in d'an huta."
"Bazaka jira kaci abinci ba kace?"
"No need Ummi thank you."
"Toh Allah kare."
Gidan Amal ya koma ya mik'e akan gado se tunanin ta yake
ya kasa daina yin hakan chan ya d'ago wayansa ya shiga
kiranta missed calls kusan 5 yayi mata amma ba wanda Amal
tayi returning aciki, da ya gaji kawai seya tura mata sak'o daga
k'arsge kaman jiya yau ma ko karancewa batayi ba ta goge.
"Sannu ko?" Mami tace mata.
"Sannu da hidima Mami sakillahu bil jannah."
"Ameen wannan k'awarki Maamah na sonki wallahi, Allah
yabar zumunci."
"Gaskiya sede ince Alhamdulillah."
"Kawai de Allah ya sanya rabo ne tsakaninki da Afzal in ba
haka ba da Abdul d'inki kika aura na tabbata wancan baze
walak'antaki yadda Afzal yayi ba."
"Hakane Mami ko nima saida nayi tunanin hakan, idan da Ya
Abdul ne na tabbata ze min uzuri amma Yaya baya wa mutum
uzuri kuma ace kamata har ze amince zan shigo masa da
maza gida?"
"Kede barsa shike tattare da asara da alama ma be fad'awa
iyayensa kinyi yaji ba shi kansa kunyan abinda ya aikata yake."
"Tunda Allah ya fitar dani kam ai sede inyi masa godiya, Yaya
baya sake samuna bale har ya walak'anta ni yadda yayi a
baya."
"Kina nufin kun rabu kenan?"
"Toh Mami a dalilin mey zan koma masa tunda zargi ya
shiga tsakanin mu, ai ko Allah ma ya haramta zaman da zargi
ya shiga."
"Hakane kam Baby amma-"
"Mami please bana k'aunan maganan da ya shafi Yaya."
"Toh shikenan, nace kayan tea d'in chan fa? Daga gun wa?"
"Oh wannan? Wata Nurse ce ta shigo min dasu d'azu wai inji
mutumin daya biya min kud'in asibitin ne."
"Allah sarki wannan bawan Allah dagaske yake a neman
aljanah idan da haka duk masu kud'i suke ai da talaka yaji
dad'i Baby."
"Sosai ma kuwa wallahi Mami Allah sak'a mishi da alkhairi
dey kawai."
"Ameen kina jin yunwa ko?"
"A'a d'azu na sha tea."
"Tea abinci ne Baby? Yanzu fa bake kad'ai bace dole kina cin
abinci sosai dan lafiyan abinda ke cikinki."
"Toh Mami."
"Gashi kuma baze yi ana siyo miki abinci ba kullum kinsan
halin da muke ciki dey amma bari yanzun inje gida in dafa
miki duk abinda kikeso akwai nama akwai komi mey kikeso?"
"Banida matsala da hakan Mami dama Papi ne yayi insisting
ni kwad'ayin kuka da brabisko ma nike, tun da nayi aure ban
sake ciki ba Yaya baya so se bana yi."
"Allah sarki bari inje in hura wuta toh muyi miki alwala tun
yanzu tunda azahar d'in ya kusa ko?"
"Gaskiya kam kika tafi ba wanda ze tayani." Bayan Mami ta
taimaka mata tayi alwala tayi mata sallama ta fice.
Daddy na tasowa daga sallan Azahar yayo TH don duban
Amal so yake ya samu koda tsillin gashin kanta ne da za a iya
gudanar da DNA test da shi don ya samu ya gano 'yarsa take
koko a'a. Cikin sa'a kuwa daya isa asibitin ba Mami ba Papi,
k'ofan ward d'in aka bud'e masa sannan ya shiga inda yasa
driver'nsa yi mai gadi daga waje. Sallama yayi amma shiru ba
amsa kasancewar Amal na sallah shi ko se yayi tunanin ko
bacci take tunda nurse d'in tace masa ba kowa akanta. A
hankali ya bud'e k'ofan ya tarar da ita tana sallah a zaune.
Tsayuwa yayi daga bakin k'ofan yana jiranta yayin da yake
tunanin ta ina ze fara samun tsillin gashin kanta chan seya
hango comb a gefen gadon nata wanda Mami ta taje mata
gashinta da shi ta kuma manta bata yasar a bola ba. Wani
hamdala ya sauk'e sannan a hankali ya k'arisa ciki ya d'au
comb d'in had'e da zare gashin ya cusa a aljihu. Lokacin da
yake ajiye comb d'in Amal take sallame sallar.
"Baba sannu da zuwa" tace da shi lokacin da idonsu ya
had'u tana mey mamakin ko mey yakeyi a kusa da gadonta
haka gano kaman tana suspecting nasa ne se ya wayence ya
zaro envelope na kud'i a aljihunsa ya ajiye a gefen gadon
"Dama nace bari in duba ki a hanzarce kafin in wuce sekuma
na tarar kina sallah shine nace bari in ajiye miki kawai tunda
ba abu bane mey yawa."
"Allah sarki Baba baka gajiya damun d'awainiya haka? Naga
kayaki da dama d'azu nagode Allah saka da alkhairi" dukda
cewan bey fahimci wani kayakin take nufi ba se kawai ya
amsa "Ameen 'yata ba komai Allah k'ara sauk'i ina fatan jikin
naki da sauk'i?"
"Alhamdulillah Baba ina samun kulawa sosai."
"Toh madallah barin koma ina da gun zuwa."
"Allah sarki nagode sosai Allah ya saka da alkhairi gashi kazo
yau ma iyayena basu nan suna ta son suyi maka godiya."
"Ba komai kice musu kar su damu, toh na wuce se na sake
zagayowa." Nan yayi mata sallama ya fito. A gurguje suka bar
asibitin gudun kar su had'u da Mami ko Papi. Wani private
clinic suka nufa inda ya sanya gashin kan Amal acikin wata
farar leda sannan shima ya tsinke kad'an daga cikin na
gemunsa ya sanya a leda daban ya mik'a wa driver'nsa tare da
yi masa kwatancan likitan da yake son ya kai masa.
"Har ka kai masa?"
"Eh Alhj yace results ze fito nan da kwana uku."
"Toh madallah se mu wuce office ko? Ina da appointment da
wasu."
***
Da yamma Daddy ya dawo gida sede har anan beji labarin
an sako Nazeefah ba wayan Afzal ya kira inda yaji switched
off dama da gan-gan Afzal ya kashe wayan nasa sanin Daddy
ze nemesa da misalin k'arfe shida sabon layi ya kira Mummy
tana d'agawa taji muryan Nazeefah.
"Mummy dan Allah ku taimaka mun Mummy bana son in
sake kwana anan dan Allah kuyi hak'uri."
"Ba daga mu bane Nazeefah Daddy'nki yayi wa Abban Afzal
magana shima yace zeyi wa Afzal d'in magana amma shiru har
yanzu an kira Afzal d'in ma layinsa a kashe."
"Innalillahi dan Allah ku kira Abbansa please help me out
Mummy."
"Naji Nazeefah ki k'ara hak'uri" anan ta katse wayan.
"Alhj ko zaka kira Alhj Amin d'inne kaji daga bakinsa?"
"Kar yaga kaman mun tak'ura masa Hjy Surayya."
"Amma ai ze iya yiwuwa ya mance beyi ma Afzal maganan
ba."
"Da wuya mu jira de zuwa gobe."
"Yanzu a cell d'in Nazeefah zata sake kwana kenan?"
"Toh ya muka iya Hjy Surayya?"
"Wallahi Nazeefah ta cuci kanta duk mey hali irin nata yana
tattare da asara."
***
Rok'an alfarma Nazeefah ta sakeyi gun securities d'in akan a
sake ara mata waya ta kira Afzal sede wayan nasa a kashe,
private numbernsa ta kira nan ya shiga a karo na biyu ya d'aga.
"Halo?" Ya soma da cewa.
"Ya Afzal" ta kira sunansa.
"Nazeefah?" Take ya gano muryarta.
"Ya Afzal I'm sorr-" katse wayan yayi nan take ta sake kira
haka yana gani yak'i d'agawa daga k'arshe ma kashe wayan
yayi gabad'aya. Kwana Nazeefah tayi tana kuka ranan yayinda
take nadaman biyewa Rumaysa da tayi. Washegari Afzal yayi
resuming office, wajajen k'arfe tara Daddy ya sake gwada
layin Afzal se gashi ya shiga, sede har ya tsinke Afzal be d'aga
ba instead seya tura masa sak'o akan cewa wai yana meeting
ne idan ya fito ze biya police station d'in ayi releasing Amal.
Da misalin k'arfe sha biyu da rabi Afzal ya wuce TH dan
duban Amal sede yau ma nurse d'in tak'i barinsa ya shiga,
rok'anta yatayi kaman ba gobe har seda ya samu ya shawo
kanta.
"Naji zan yi maka hanya ka shiga amma daga yau se yau."
"Thank you so much I couldn't ask for more ita kad'ai ce
aciki?"
"Eh d'azun mahaifiyarta ta fice."
"Papi fah?"
"Shi tun safe yazo ya lek'a su ya koma dama shi ba a nan
yake kwana ba."
"Okay."
"Muje in kai ka" bayanta yabi ta kaisa d'akin Amal. "Seka yi
sauri" kai ya gyad'a mata yayinda ta juya ta fice. A hankali ya
bud'e k'ofan yana lek'an ciki, akan gado ya tarar da Amal tana
kwance, ciki ya k'arisa ya maida k'ofan inda ya tabbatar da
bacci takeyi. Kujera yaja ya zauna a gefenta yayinda hawaye
ya ciko masa a ido he can't believe yau kwana uku kenan be
sanya ta a ido ba. Hannunta ya d'aga ya sa acikin nasa yana
murzawa a hankali "I'm so sorry Amal, I'm terribly sorry" ya
shiga bata hak'uri har anan baccinta take ba makawa. Strands
na gashin da ya fad'o mata akan fuska ya shiga miyar dasu
cikin hulan dake kanta sannan ya soma shafa fuskan nata a
hankali yayinda gobaran sonta da tausayi yake ruruwa acikin
zuciyarsa. A hankali ya sauk'e hannunsa akan cikinta yana
feeling presence na baby'nsa. Gani yake kaman a mafarki, wai
Amal na d'auke da cikinsa, oh he can't ask for more.
Ya kai kusan minti goma zaune akanta yana kallonta da
hannunsa manne akan cikinta har anan. Cikin bacci Amal ta
d'an motsa hannunta dake kan gado ta d'aga dan ajiyewa
akan cikinta inda ya sauk'a akan hannun Afzal. Gagam ta rik'e
hannunsa yayin da ta cigaba da baccinta minti biyar a gaba
Afzal yayi tunanin komawa gudun kar Mami ko Papi suzo su
iskesa. Hannun nasa ya shiga janyewa amma ya kasa dan
yadda Amal ta k'ank'amesa. Gashi baya son ya tayar da ita, ya
zeyi? Hannun nasa ya cigaba da k'ok'arin cirewa amma ya
kasa wanda daga k'arshe seda Amal d'in ta farka. A hankali
take bud'e idanunta har ta sauk'e su akansa ba k'aramin
razana tayi ba ganinsa da tayi akanta. Kad'an ya rage bata sa
ihu ba, shin har ya akayi ya shigo ciki? Ta d'au nan restricted
area ne se idan an san da zuwan mutum ake barinsa ya shiga
how comes toh?
"Amal" ya kira sunanta a hankali cikin wani irin salo hannun
nasa ta sake da wuri ta shiga kalle-kalle cikin d'akin tana
neman Mami.
"My adorable Kitten" yake sake kiranta lokacin da ta kawar da
kanta gabad'aya daga kallonsa. "Amal please turn around and
look at me" saidai kaman ba da ita yake ba.
"Amal I'm terribly sorry, please forgive me for doubting on
your faithfulness, I've realized the truth nagane Nazeefah da
Safiyya ne ke bayan komai dan Allah kiyi hak'uri maganan da
nake miki yanzu haka na mik'a su ga hukuma a hukunta
munsu, I can never forgive them for what they did to you, yau
kwanansu biyu kenan a cell." Mamaki sosai kalamunsa suka
sanyata, akanta har ya kaisu police station? Sede tayi shiru
bata ce dashi komai ba.
"Amal I felt horrible when I found out Nazeefah ce tasa aka
kad'eki however I'm grateful for the fact that you still chose to
be alive and didn't leave me all by myself. Bazan iya rayuwa
ba ke ba Amal, kinfi kowa sanin hakan, you're my necessity
and everything I need to complete my life please don't leave
me" hannunsa ya d'au ya ajiye akan cikinta hakan ne kawai
yake tunanin ze sata yin magana ai kuwa ba shiri ta cire "Don't
you ever touch me Yaya" ta sanar da shi ba tare da ta juyo ta
kallesa ba.
"Thank you for speaking to me Kitten, at least yau zan iya
bacci tunda na saurari muryanki thank you so much" nan ma
shiru tayi masa "Baby why didn't you tell me? Meyasa baki
fad'a mun kina da ciki ba?" Mamakin yadda akayi ya gano
tana da ciki take, waya sani ko nurses d'in ya tambaya suka
sanar da shi.
"Kitten gani kike kaman in kin fad'a mun zanyi denying
baby'n ince ba nawa bane? Amal I've never and will never
accuse you of cheating on me, I know who you're nasan
bazaki ta6a cin amanata ba kuma koda nace miki ban yafe ba
idan kika sake shigo mun da maza cikin gida bawai ina nufin
wani abu bane course mates naki nake nufi kuma Wallahi ni
ban san shirin yaji kikeyi ba da na baki hak'uri na hanaki,
senayi tunanin ko so kike ki tare zuwa d'ayan d'akin gabad'aya
ban san lokacinda kika tafi ba se washegari dana lek'a d'akinki
naga bakiya nan."
So take ta ce masa meyasa be kirata ba toh bayan da yaga
bata nan d'in se taga kuma ba amfani tunda ba komawa
agaresa zatayi ba.
"I got so mad shiyasa ban kiraki naji daga gareki ba amma
bawai hakan na nufin bana sonki bane ko kuwa nayi hakan dan
in nuna isa ko dan in walak'antaki ba, Amal sanin kanki ne
bazan ta6a yi miki haka ba, I love and respect you alot please
come back to me abinda ya faru ya riga ya faru nasan ni mey
laifi ne, nasan nayi kuskure, na san ban kyauta miki ba na k'in
miki uzuri da nayi da kuma k'in baki dama kiyi bayanin kanki
Wallahi duk sharrin Nazeefah ne, she manipulated me please
forgive me Amal Yaya is so sorry."
RANA DAYA Chapter 38
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
Tareda Naja'atu Lawal Rijau Niger State
@Whatapp 08083232323 or 09060202323
PAGE 38
"Amal why aren't you saying anything?" Ya tambayeta a
maraice bayan dogon shirun da tayi, shirunta a garesa ba
k'aramin tashin hankali bane but he really can't force it ya
zama masa dole ya hak'ura ya bata space da take buk'ata har
izuwa lokacin da za ta huce.
Tabbas mutum ya guji fushin mey hak'uri koda wasa be
ta6a tsammanin Amal zatayi masa fushi haka ba saidai bai ga
laifinta ba ko d'aya saboda shi ya turata har bango, idan da
wata ce da tun ranan da ya korata daga d'akinsu zatayi mai
fushi amma dukda hakan bata fasa yi masa ladabi ba, he's
sure with time she'll come by.
Envelope da ya tanadar mata ya zare daga aljihunsa ya ajiye
mata a kan gadon daga gefenta sannan ya mik'e "I have to go
now, Allah k'ara miki lafiya I can't wait to see you back on
your feet I love you so much my adorable Kitten" badan yana
so ba ya mik'e ya fice juyawanda Amal zatayi hawaye ya
tsiyaya daga d'ayan idonta. Tabbas har yanzu tana son Yaya
amma idan ta tuna da abinda yayi mata se taji gabad'aya ya
fita mata a rai, she never wished for things to turn out bad
between them two like this, amma ya ta iya? She can't change
the past only can she make the future better. Gyara
kwanciyanta da tace zatayi taji k'aran paper, a hankali ta miyar
da idonta wajen nan taga envelope da ya ajiye mata da
hannunta d'aya ta d'aga ta zazzage inda ta tarar da kud'i da
dama aciki, sabin dubu d'ai-d'ai. Da hannunta d'aya ta irga
taga dubu ashirin ne sannan ta miyar ta ajiye a gefe.
***
Koda Afzal ya shiga cikin mota ya kasa kunna engine d'in, be
hankara ba kawai yaji hawaye na tsiyaya masa daga ido yau
ina ze sa kansa? Ya ze rayu idan ba Amal a kusa da shi? Gani
yake idan har bata dawo a garesa ba ze mutu saboda
zuciyarsa bazata iya jure rashinta a kusa da shi ba da k'yar ya
iya kunna motan ya koma office. Hud'u nayi ya tashi.
Gabad'aya ya mance da labarin Hindu se yanzu ta fad'o masa
a rai, gidan Nazeefah ya biya inda ya sameta kwance a
d'akinta tana bacci, tashinta yayi sannan ya kira driver'n Amal
da ya kaita gida bayan sallamarta da yayi. Tana isa gida
Ummansu ta rungumeta tana kuka tun jiya take kuka har zuwa
d'azu da taje ta duba Safiyya. Dama tun farko ita bata goyi
bayan kawosu birni ba dan gudun sharri irin wannan.
Se k'arfe shida Afzal ya wuce police station d'in yayi magana
akayi releasing nasu Nazeefah. Da gudu ta fito ta fad'a jikinsa
tana kuka "Ya Afzal dan Allah kayi hak'uri ka yafe mun na tuba
bazan sake ba" hannunsa yasa ya janyeta "Don't misinterprete
my intention, ba wai don ina so nasa akayi setting naki free ba
Nazeefah se don Abba ne ya buk'aci hakan, idan da ta ni ne
da se kotu ta yanke miki hukuncin da yake dai-dai da laifin da
kika aikata sannan zanji dad'i because I want you to change,
canji na tsakani da Allah bana muzurun da nake da tabbacin
kikayi ba. Bazan 6oye miki ba Nazeefah, da abinda kikayi
kinsa na tsaneki kaman yadda Amal ta tsaneni yanzu, ko
k'aunan gani na Amal bata so a haka kike cewa kina sona? A
tunani na idan kana son mutum har abinda yake so zaka so,
kin san ina son Amal but you still went ahead and hurt her I'm
still mad at you Nazeefah I might forgive you someday amma
bazan ta6a mancewa da abinda kikayi wa Amal d'ita ba let's
go home." Driver'n Amal ya kira yazo ya d'auki Safiyya itama
kud'in sallamarta yabata sannan ya buk'aceta da idan ta isa
gida ta tattare ina-inata tabar masa gida yayinda shi da
Nazeefah suka koma nasu gidan suma.
Babban akwatinta ya d'auko mata "Here start packing your
clothes ki bar min gida bana k'aunan ganinki anan Nazeefah as
long as kika cigaba da zama anan zakina sani tunawa da
munanan abubuwan da kika rink'ayi wa Amal d'ita wanda
hakan ze sa in sake tsanar kine kawai so its better ki koma
gida gun su Mummy." Kuka take sosai ta k'arisa inda yake
tsaye had'e da sauk'a k'asa akan guiwarta "Ya Afzal dan Allah
karka mun haka, dan Allah don't send me home I'm terribly
sorry please forgive me wallahi na tuba bazan k'ara ba dan
Allah kar ka sakeni Ya Afzal bazan iya rayuwa ba kai ba please
don't divorce me" ta k'arisa cikin tsananin kuka. Hannu yasa ya
d'agata "Bazan sake kiba Nazeefah saboda despite everything
I still love you and I cherish the moments we spent together, I
just need some space and alone time anytime I'm ready zan
dawo dake but you really have to go now." Rungumesa tayi
tana kukan cire rai "Please don't send me away Ya Afzal I
can't live without you dan Allah kayi hak'uri ka yafemun please
don't send me home I'm so sorry" kuka ta cigaba dayi ajikinsa
na sosai ta basa tausayi shima bawai dan yana so ze korata
gida ba dan kawai bayida wani option ne saboda zamanta
acikin gidan nan kawai sake sanyasa tsananta zeyi shi kuma
baya son hakan saboda idan ya tsani abu ya tsanesa kenan no
turbing back, so it's better ta tafi gida kawai. A hankali ya
sauk'e hannayensa a bayanta hugging her back sun d'au
tsawon lokaci a haka sannan ya janyeta na k'arfi dan yadda ta
kankamesa kuka take sosai tana kad'a masa kai "Please don't
do this Ya Afzal please don't."
"I'm so sorry Nazeefah I'm really sorry I wish there's
something I could do you have the next one hour to pack your
belongings zan sa driver'n Amal yayi dropping naki a gida"
yana kaiwa nan ya juya. Ihu Nazeefah ta k'urma tana kuka tana
kiran sunansa amma ko waiwayawa beyi ba ya fice rushewa
tayi a wajen tana kukan tsuma zuciya yau ina zata sa kanta?
Ya zatayi da ranta? Ya zatayi da masifaffen son Afzal dake
cikin zuciyarta? Bazata iya rayuwa ba shi ba, da ta rasa sa
gara ta rasa rayuwarta gabad'aya, soyayyan sa ya riga ya zame
mata jinin jiki, idan ba shi baza ta iya rayuwa ba. Tafi minti
goma a wajen tana kuka sannan da k'yar ta iya lalla6awa ta
k'arisa wajen wardrobe nata yayin da ta shiga tattare kayakin
nata, tana yi tana kuka haka har ta samu ta gama tattare
kayakin nata ta ja akwatin ta rufe sannan ta fito da akwatin
parlour ganin ba Afzal a gurin se ta k'arisa waje nan ma bata
gansa ba ashe acikin motansa ya 6oye yana kallonta daga
mirror. Waya yayi wa driver'n Amal nan ya k'ariso ya ja mata
akwatin nata cikin mota se kewaye take tana nemansa amma
ko alamansa babu ga kuma motansa na nan a fake, haka ba
don tana so ba ta k'arisa motan ta shiga har driver ya kaita
gida tana aikin kuka. Ba k'aramin hamdala su Mummy sukayi
ba ganinta ta dawo gida, text Daddy ya turawa Afzal yana yi
masa godiya, kwana ranan Nazeefah tayi musu tana kuka,
kukan zafin rabuwa da Afzal shima Afzal har hawaye seda ya
zubar bayan tafiyan ta, yana sonta amma baze iya cigaba da
zama da ita muddin Amal bata dawo a garesa ba toh baze iya
dawo da Nazeefah ba, wannan haka take.
****
GIDAN ALHJ AMIN
Seda Ummi ta jira Abba ya gama cin abincinsa sannan tayi
gyaran murya. "Alhj?" Ta kira sa.
"Yes My dear?" ya amsa had'e da d'ago kai yana kallonta.
"Dama wata magana nake son yi maka amma sena ga jiya
kaman a gaje ka dawo yau kuma throughout baka yini a gida
ba."
"I'm sorry schedule d'ina ne kwana biyun nan is so tight se a
hankali."
"Ba komai dear Allah taimaka ya k'ara arziki da bud'i."
"Ameen Hjy Mairama ta so what is it you wanted to
discuss?"
"Batun Prince ne dama."
"What about him?"
"Amal tayi masa yaji" bata tsaya yin corner-corner ba ta
sanar da shi gaskiya kai tsaye.
"What?!"
"Amal tayi masa yaji yau kwana hud'u kenan."
"Kina nufin har mukaje muka gaisheta dama ba a gidansa
take ba?"
"I'm sorry but yes."
"Kuma kin sani?"
"Dear I'm sorry."
"Meyasa baki fad'a mun ba?"
"Alhj ina gudun fushin da zakayi masa ne already matsaloli
sunyi masa yawa kaga idan kaima ka k'ara da naka abun zeyi
masa yawa."
"Wow! Meya faru har tayi masa yajin? Batun abinda Nazeefah
tayi ne?" K'arya taso yi masa tace eh amma tuna idan aka je
yin sulhu gaskiya na iya fitowa taji kunya se kawai ta fasa ta
irga masa gaskiyan al'amarin.
"Afzal d'in?" Ya tambaya da mamaki shi kam da ba a bakin
Ummi yake jin labarin ba se yace sharri akeyi wa d'ansa.
"Unfortunately abinda ya faru kenan amma yayi nadama
yanzu wallahi Alhj dan kad'an ya rage beyi kuka ba da yake
ban labari kayi hak'uri kayi masa uzuri sharrin shaid'an."
"Nadama? Bega komi ba tukuna kuma ki daina kawo zancen
sharrin shaid'an wannan ganganci ne da rashin mutunci da
kuma rashin tunani da rashin aiki da hankali a fili har 'yar
yarinyar nan ne zeyi zarginta? Mey ta sani?"
"Alhj yace shifa ba zarginta yake ba."
"Maganan banza amma ai abinda ya nuna mata kenan kuma
abinda zata fad'awa iyayenta kenan."
"Alhj kayi hak'uri tabbas Prince yayi kuskure amma baza mu
iya canza hakan ba kayi hak'uri a had'a kai ayi masa bikon
yarinyar nan yaso yayi hakan da kansa amma abun ya gagara
ko ganin Amal iyayenta sun hanasa yi wallahi yaron nan na
cikin tsaka mey wuya ace cikin matansa biyu ba ko d'aya a
wajensa."
"Ai daidansa kenan ko nine bazan barsa ya shiga yaga min
'ya ba tunda ya walak'anta ta haka, iyayen Amal sunyi mun
dai-dai ko a babu yanzu ze san matsayinta, ma wannan wani
irin rashin hankali ne? Wallahi wasu abubuwan in ance min
Prince ya aikata se inga kaman sharri ake yi mishi ban ta6a
sanin sa da wannan banzan hali da rashin wayo ba."
"Alhj kayi hak'uri ze gyara."
"Kibar 6ata miyan bakinki kina bani hak'uri Hjy Mariam ba
dani za'ayi abin kunyan nan ba in kinga na taka k'afa gidansu
yarinyar nan toh takardan sakinta na kai mata dan nasan koba
jimawa da dad'ewa iyayenta zasu nemi a kai musu takardan
'yarsu bayan nan ba abinda ze kaini gidansu, rashin hankalin
Afzal ya isheni haka."
"Alhj dan Allah kar kace haka kafi kowa sanin ciwon Afzal,
kafi kowa sanin raunin zuciyarsa da kuma abinda rashin
yarinyar nan a kusa dashi ze haifar, ina fatan baka mance da
abinda likitansa yace ba."
"Ai idan ma mutuwa yayi shi ya siya mutuwan nasa da kansa
kawai dan yarinya na da hak'uri shikenan seya walak'anta ta?
A idonsa yarinya ta tattare kayakinta amma dan gadara yak'i
koda yi mata magana bale yayi tunanin hanata? A ina aka
ta6ayin haka? Saboda yana ganin gidansa yafi gidan iyeyenta
gata ko mey? Sannan kuma dan rashin kunya da rainin wayo
yace wai bey d'au shirin yaji take ba? Kinga I've had a stressful
day I'm very tired in kina da niyyan kwanciya bismillah in kuwa
a'a ni seda safe."
"Alhj please kar kayi haka wallahi mune da asara idan muka
rasa Afzal kaman yadda Daddy'n Nazeefah yace hannun
mutum baya ri6ewa ya yasar toh muma fa hakane komin yaya
baza mu k'i Afzal ba kuma kaima fad'a kawai kake wallahi
baka gansa kwance akan gadona asibiti bane fighting for his
life" ko amsata beyi ba ya k'arisa d'aki abinsa ba tare da ya
kewaya ba. Ita kanta bawai taji dad'in abinda Afzal yayi bane
kokuwa tana goye masa baya kawai gudun halin da yake iya
fad'awa ne idan ba a dawo masa da Amal a garesa ba sanin
raunin zuciyarsa. Bazata gaji da basa hak'uri ba tasan
zuciyansa yana da saurin fushi amma kuma hak'uri kad'an aka
basa ze sauk'o.
***. ****. *****. *****
Kaman yadda likita ya d'au alk'awari bayan kwana uku ya
tanadar da results na Daddy. Da yammacin ranan yaje ya
amsa da kansa ko da driver be nema ya rakasa ba. Ba
k'aramin tsinkewa gabansa yayi ba bayan da ya karance
results d'in yaga komi positive yake nunawa, ma'ana Amal
'yarsa ce kad'an ya rage beci tuntu6e ba dan yadda ya razana
se hailala yake yana maimaita innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
Yanzu Amal 'yarsa ce? Ashe ciki ya shiga jikin Jameensa
bayan abinda ya faru a tsakaninsu, yau ina zesa kansa? Ta ina
ze fara sanar da mutane wannan badak'ala? Wai wannan a
duniya ma kenan Allah yake neman tozarta sa haka ina kuma
ace a lahira? Wannan wace irin k'addara ce taya yaransa biyu
zasu auri miji d'aya? Shin haka Allah yake kama duk wanda ya
d'au alhak'in wani? Shin haka duk wanda ya aikata aikin banza
yake fara ganin sakamako tun anan duniya ba ma se anje
lahira ba? Shin ashe komin yaya mutum yaso 6oye laifi ko
zunubi ta inda baya tsammani Allah ze tozarta sa a idon
jama'a? Yau yana cikin wani yanayi ta ina ze fara sanar da
Amal shine mahaifinta? Ta ina ze fara sanar da Hjy Surayyarsa
yana da shegiya a waje? Ta ina ze fara sanar da Nazeefah
Amal 'yar uwarta ce? Da wani ido yaransa zasu sake kallonsa?
Da wani ido amininsa da kuma manyan abokansa zasu sake
kallonsa harma da 'yan unguwa da masu aiki a k'ark'ashinsa?
Shikenan k'wan da ya jima yana gudun fashewansa ya tsage
yanzu k'iris ya rage kuma ya fashe ya zube. Kansa ne ya
mugun d'aurewa gabad'aya ya rasa mey ke masa dad'i. Allah
ne de kawai ya kaisa gida ranan saboda yadda ba hankali a
jikinsa yake tuk'i tunda ya isa gida ya rufe kansa a d'aki yayi
k'aryan migraine ne ke damunsa baya son a tak'ura mishi,
tunanin ta inda ze fara 6ullowa al'amarin nan yake amma ya
kasa tabbas acikin yaransa biyu dole se d'aya ta zama
bazawara dan bazeyi Afzal ya cigaba da zaman aure da
dukansu biyu ba tunda jini d'aya suke. Annabi beyi k'arya ba da
yace idan kayi me kyau me kyau ze bika idan kuwa kayi na
banza na banzan ne ze bika tabbas yaga hakan yanzu. Yanzu
da ace aikin alkhairi yayi a baya sede 'ya'yansa suci riban
hakan, amma daya shuk'a tsiya ba shi kad'ai ba harta yaransa
seda hakan ya shafa.
****
Nazeefah bata fasa turawa Afzal sak'o tana neman tubansa
ba safe ba dare tun tana kiransa baya d'agawa har ta hak'ura
ta daina yau kwanan ta biyu kenan gabad'aya ta fita daga
kamanninta dama ba k'iba bane da ita akan raman nata ta
sake ramewa ba aikinta se kuka da tunani kullum, gashi ko
makaranta ta shiga bin ta da kallo ake Rumaysa duk ta bazata
a gari mijinta ya kaita cell sekace ba ita ta d'aurata akan
gur6arcacciyar hanyar ba.
***
Afzal na zaune a office amma hankalinsa gabad'aya akan
Amal tasa yake kullum haka yake yini da tunaninta ya kuma
tashi da shi gashi tun ranan be sake sanyata a ido ba, koya
kirata bata d'agawa sak'o ma ya tura mata bata replying nasa,
whatsapp messages ma ko reading batayi he can't explain
how much he's missing her. So yake ya sake ganinta kafin a
sallameta daga asibitin dan yaji daga bakin nurse d'in cewa
yau za a sallameta jira yake lokacin lunch yayi yaje ya dubata
wanda kafin nan ya d'au wayansa ya kira Ummi jin shiru tun
ranan da sukayi magana har yau bata sake nemansa ba. Seda
wayan ya kusa tsinkewa ta d'aga bayan sun gaisa yake
tambayarta ko sunyi magana da Abba, bata 6oye masa komai
ba ta fad'a masa yadda sukayi da Abba yadda ya nuna komin
yaya shi bazesa hannu cikin wannan al'amari ba na sosai
zuciyan Afzal ya karye.
"Halo Afzal are you still on the line?"
"Yes Ummi" ya amsa cikin wani irin salo ko daga jin muryarsa
Ummi tasan zuciyarsa ta mace.
"Don't lose hope Afzal ka cigaba da addu'a nima bazan fasa
bawa Abbanka hak'uri ba in shaa Allahu ze sauk'i aje ayi maka
bikon Amal kaji? Amal zata dawo a agreka da izinin Allah."
"Ta yaya Ummi? Ko jiya naje na samu Papi amm he's not
willing to talk to me in the case of Amal it's worse ko magana
bata yimun Ummi I'm slowly dying I can't do without her."
"Ka kwantar da hankalinka Afzal."
"Ta ina hankalin nawa ze kwanta Ummi ina shirin rasa Amal?
I'm definitely going to die."
"Subhanallahi wai bazaka bar magana haka ba? Bazaka mutu
ma kuma in shaa Allah Amal zata dawo a gareka kar ka gaji
da bata da iyayenta hak'uri nima zan taimaka maka zan samu
Mami inyi mata magana."
"Thank you Ummi, I know I can always count on you thank
you so much Allah sak'a miki."
"Ameen ka kwantar da hankalinka kaji?" Kai ya gyad'a tamkar
tana gabansa "Se mun sake waya zan kuma cigaba da bawa
Abban ka hak'uri nasan ze sauk'o even though ba yanzu ba
amma definitely he'll."
"Thank you so much Ummi" da haka sukayi sallama. Azahar
nayi bayan ya idar da sallah yaci abinci ya wuce TH sede yana
isa ya tarar da sad news na cewa an riga an sallami su Amal
har sun koma gida, tamkar yayi kuka haka yaji dama yaso yayi
wa driver'nta magana yazo ya d'aukesu ya kaisu gida, a
cewansa gabad'aya se yamma zasu tafi ashe ba haka neba.
Be gaji ba washegari da yamma bayan ya taso daga office ko
gida be je ba ya zarce gidan su Amal sallama yayi Mami ta
amsa sannan yasa kai ya shiga ya nemi gu ya tsuguna.
"Bismillah hau kan tabarman mana ka zauna" Papi yace da shi.
"A'a Papi nan ma yayi nagode. Ina yini?"
Gaishesu yayi duka cike da ladabi da biyayya inda suka amsa
ba yabo ba fallasa har hakan yaso d'aurewa Afzal kai a
tunaninsa gabad'aya zasu koresa yau idan ya shigo sekuma ya
tarar da sa6anin hakan.
"Papi ya jikin Amal?" Ya tambaya afterwards.
"Da sauk'i Alhamdulillah."
"Jiya naje asibiti na tarar har an sallameku kun dawo gida
dama driver naso turawa ya dawo daku gida."
"Ayyah karka damu mungode."
"Papi bazan gaji da baku hak'uri ba dan Allah kuyi hak'uri ku
dawo mun da Amal, nasan nayi kuskure amma kuyi hak'uri ba
yadda banyi da Abba ba ya sa baki ya tayani baku hak'uri
amma yak'i saboda shi kansa fushi yake dani akan abinda nayi
wa Amal, dan Allah kuyi hak'uri wallahi sharrin shaid'an ne."
"Tabbas d'an Adam ajizi ne amma a gaskiya bazan 6oye
maka ba Afzal abinda kayi wa Baby ya ci mun tuwo a kwanu.
Ban ta6a tsammanin hakan daga gareka ba Baba na, atunani
na ko a bayan raina zaka kula min da Baby ka rik'e min ita
amana se gashi tun a ido na ka soma walak'anta ta kodan
gani kake bata da uba bata da gata?"
"Wallahi Papi ba haka bane, sanin kanmu ne nan duka Amal
tafi k'arfin a walak'anta ta kuyi hak'uri wallahi sharrin shaid'an
ne."
"Tafi k'arfin a walak'anta ta amma harda korinta daga
d'akinta Afzal? Saboda ko tsinke bata kai gidan ba?" Mami da
tayi shiru tun d'azu ta tsoma baki.
"Mami Wallahi ba don haka bane sharrin shaid'an ne amma
in shaa Allahu hakan baze sake faruwa ba."
"Tabbas saboda Amal baza ta sake komawa gidanka ba,
haka tace kuma ina biye da ita d'ari bisa d'ari."
"Mami dan Allah kar kiyi magana haka Mami keda ya kamata
ki tayani shawo kanta kuma kike cewa haka? Mami kin fi
kowa sanin yadda nake son Amal kin fi kowa sanin yadda
rashin ta a kusa dani yake babban hatsari da tashin hankali a
gareni dan Allah kar kiyi mun haka."
"Ina sane da hakan Afzal, shiyasa kai na ya d'aure na rasa
gane dalilin daya sa kayi mata abinda kayi ko dan gani kake
bata halacacciyar hanya aka sameta ba dan haka bata da
wani k'ima da daraja? Kake ganin kaman alfarma kake mata
saboda ka aureta hakane Afzal?? A jinka idan da anyi shawara
da ita zata so ta kasance hakan ne? Ko a jinka ni d'in inda
nasan sharrin dake jira na a yinin ranan zanje in sami
azzalumin mutumin daya cuceni d'in ne?" Ta k'are maganan
idonta na cikowa da hawaye, dama rana mey irin ta yau take
gudu shiyasa bata goyi bayan Papi ya sanar da Afzal asalin
Amal ba tun farko, ai ga irinta nan yanzu tun ba ayi nisa ba ya
soma walak'anta ta.
"Subhanallahi Mami dan Allah kar kice haka, Mami please
don't ever talk like that ni wallahi in ba da kika d'auko
maganan ba ma yanzu gabad'aya na manta da ita wallahi ban
ta6a goranta wa Amal akan asalinta ba idan k'arya nake muku
ku kira ta ku tambayeta wallahi bazan ta6a yin haka ba please
forgive me if you felt that way I'm terribly sorry."
"Ya isa Jameelah yi hak'uri ki koma ciki ni da Afzal zamuyi
magana karki d'aga muryanki Baby ta jiyoki yi hak'uri ki koma
ciki" batayi musu ba ta mik'e ta shige d'aki inda Papi da Afzal
suka cigaba da tattaunawa.
"Shin meya faru Afzal? Naji 6angaren labarin daga gun Amal
kaima zan so inji naka 6angaren."
"Papi kunfi kowa sanin yadda nake son Amal, wallahi sharrin
abokiyar zamanta ne, ita tayi manipulating mind d'ina ta shiga
tsakani na da Amal, Papi komi na saiwa Amal harta tsinke
idan na koma gun 'yar uwar nata senaji a bakinta taya zan san
wai ta had'a baki ne da 'yar aikin Amal tana kai mata rahoton
duk abunda ke gudana a cikin gidan namu?" bayanin komai
dalla-dalla yayi wa Papi.
"Tanan kam kayi gaskiya ko ni ne zan fi yarda da Nazeefah
akan ita Baby saboda wannan shaida k'wwak'k'wara amma
batun shigo da maza cikin gidanka fah? Ka ko san Allah ya
haramta auren da zargi ya shiga? Ashe har Allah ze kawo
ranan da zaka yi kokonton tarbiyyan dana bawa Amal?"
"Wallahi Papi ni ban ta6a zargin Amal ba, itace bata fahimce
ni ba dan ko da 'yar aikinta ta gaya mun cewa sau biyu tana
shigo da maza cikin gidan tunani na gabad'aya akan course
mates nata ya k'are ba wai kwartaye ba, wallahi sam ni hankali
na be kai ga chan ba saboda nasan da wata irin mata nake
zaune. Kuma ko da na tashi yi mata magana ce mata nayi kar
ta sake shigo mun da coursemates nata cikin gida ba wani
abun ba, itace tayi mun mumunar fahimta dan haka nake sake
baku hak'uri, kuyi hak'uri."
"Na fahimce ka, amma batun kana ganinta take had'a
kayakinta baka hanata ba baka kuma yi mata magana ba ba fa
shin hakane?"
"Wallahi Papi ban zata wai shirin yaji takeyi ba, dama tunda
muka soma samun matsala na turata d'ayan d'akin kowani
safiya takan shigo d'akin namu ta shirya toh ko da naga tana
shirya kayakin nata senayi tsammanin ko zata tare chan
gabad'aya ne washegari kawai na tashi na tarar bata gidan
wallahi ban san lokacinda ta tafi ba."
"Idan har haka ne meyasa baka nemeta ba bayan faruwan
hakan? Da ace a ranan kazo bikonta ka deji rantsuwa ko?
Wallahil azeem komin ya girman kuskuren da aikata yake
zansa maka Amal a mota ka koma da ita gida saboda ka nuna
tanada muhimmanci kenan amma bakayi hakan ba Afzal, ni
kake tunanin zan kiraka ince maka naga Amal ta taho gida
lafiya?" Kai ya kad'a a hankali cike da nadama "Abinda ya
6ata mun rai kenan, banzan da kayi da ita kak'i ka neme ta
kak'i ka neme ni ko mahaifiyarta, anan ka nuna baka damu da
ita ba, anan ka nuna ita ba kowa bace kasan komin jimawa da
dad'ewa zamu sata a mota mu miyar maka da ita mu baka
hak'uri tunda de gidanka yafi gidan iyayenta gata ko ba haka
ba?"
"Subhanallahi dan Allah Papi kayi hak'uri wallahi ni ba hakan
a zuciya na nasan nayi kuskure kamata yayi in kira Amal idan
banyi hakan ba kuma in kiraka ko Mami, amma d'an Adam
ajizi ne kuyi hak'uri ku gafirceni in shaa Allah hakan baze sake
faruwa ba wallahi fushinku a gareni babban tashin hankali ne
especially in the case of Mami bana son ku d'au bana son
Amal wallahi ina sonta, I really do love her kuma se inda k'arfi
na yak'are zan cigaba da baku hak'uri har se Allah ya huci
zuk'atan ku."
"Ni ba fushi da kai nake ba Afzal nayi maka hakan ne dan ka
gane kuskurenka ka kuma san k'ima da darajar Baby bayan
nan kuma don in tabbatar da kalan soyayyar da kakeyi mata
kuma na tabbatar da hakan yanzu don idan da wani ne da tuni
yayi zuciya kodan irin abinda nida Maminta muka rink'ayi
maka a asibiti amma haka baka fasa zuwa ba kullum dukda
tokarin da muke maka. Hakan ya nuna mun dagaske ne komi
ya faru bisa kuskure ne amma kana son Baby kuma ina
alfahari da hakan sosai Afzal tabbas se mey sonka ne ze so
wani naka akan Baby kuma na tabbatar da cewa kai masoyin
mu ne na hak'ik'a."
"Godiya nake Papi, ba k'aramin farin ciki kalamunka suka
sanyani ba kuma hak'urin nan shi zan cigaba da baka da Mami
kuyi hak'uri duk sharrin shaid'an ne."
"Shikenan Babana ya wuce Allah yasa mu dace."
"Ameen Papi godiya nake, Allah saka da alkhairi."
"Ameen."
"Shin yanzu zan iya dawo da Amal d'akinta? Dan Allah kar
kace a'a Papi, alk'awari na d'auka bazan sake k'untata mata
ko yi mata ba dai-dai ba bi iznillahi."
"Na yarda da kai Afzal amma nima ba daga ni bane, bazan
iya tilasta wa Baby akan cewa lallai-lallai se ta koma maka ba
iyaka inyi k'ok'ari in shawo maka kanta."
"A hakan ma godiya nake Papi, Allah sak'a da alkhairi yabar
zumunci."
"Ameen ba komai ana tare ai."
"Kuma dan Allah ka sake bawa Mami hak'uri ni wallahi sam
ba hakan a raina."
"Karka damu."
"A kuma gaishe mun Amal da jiki nasan koba don tana bacci
ba bazata amince ta fito mu gaisa ba."
"Zan gaisheta in shaa Allah."
"Godiya nake barin koma yamma nayi" hannu ya zira a aljihu
ya zaro envelope daya tanadar da 20k aciki ya mik'awa Papi
akan a sai wa Amal abinda take buk'ata sede sam Papi yak'i
amsa daga k'arshe ajiyewa kawai yayi ya mar sallama ya fice.
Mik'ewa Papi yayi ya d'au kud'in dan kai wa Amal a d'aki
dukda cewan yasan bacci takeyi. Bud'e k'ofan da yayi ya tarar
da ita tsaye dai-dai wajen ta jik'e jak'ab da hawaye. Salati yasa
ba shiri bade taji dukkan abubuwan da suka tattauna akai ba?
Bade taji labarin asalinta ba?
"Baby?" Ya kirata cikin mucacciyar murya, d'ago kan da tayi
zata kallesa kawai ta zame k'asa a sume.
"Baby?" Kumatun ta ya shiga tapping amma ba response.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Jameelah! Jameelah! D'au
waya ki kira Afzal beyi nisa ba Baby ta sume."
Da gudu Mami ta fito ta fad'a d'akin Amal inda tasa ihu had'e
da k'arasawa da salati "Abba meya faru? Na shiga uku!"
"Ki d'au waya ki kira Afzal" da hanzari ta d'auko wayanta ta
sanar da Afzal halin da ake ciki akan ya juyo, yana isowa ya
d'au Amal ya kaita mota inda Papi ya zauna a gidan gaba
Mami kuma a baya tana rik'e da Amal. Emergency ward akayi
da Amal lokacin da suka isa asibitin.
Cikinsu duka uku ba wanda ya iya ya zauna se safa da
marwah sukeyi a waiting room d'in, Mami se kuka. "Abba
meya sameta?" Ta tambayi Papi.
"Ban sani ba Jameelah tsoro na d'aya Allah yasa bata jiyo
abinda muka tauna akai ba, ina zaton taji komai saboda tsaye
a bakin k'ofan d'akinta na tarar da ita tana kuka lokacin da na
bud'e k'ofar."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mami tasa salati "Yau na
shiga uku Abba ya zanyi dan Allah? Mey zancewa Baby
yanzu? Shikenan abinda nake gudu ya faru."
"Ya isa haka Jameela ki kwantar da hankalinki in shaa Allahu
Baby zatayi miki kyakkyawan fahimta."
Bada dad'ewa ba likitocin da suka duba Amal suka fito nan
su Papi suka duk'ufa suna tambayansu ya jikin nata.
"In shaa Allahu ba wani abu serious bane kawai a bisa fad'in
da tayin ne ta kusan fama ciwon nata amma Alhamdulillah
achan Allah ya tsayar babu internal bleeding ba komai, ta ma
riga ta farfad'o kuna iya shiga ganinta." Hamdala dukansu uku
suka sauk'e a wajen sannan suka duk'ufa cikin d'akin, Amal na
ganinsu ta shiga zubar da hawaye.
Hak'uri Papi ya shiga bata Mami kam banda hawayen da take
zubarwa ta kasa yin komai.
"Kukan ya isa haka Mamana ko ta halal aka sameki ko kuwa
ta haram kaf nan bamu damu da hakan ba saboda ba abinda
ya isa ya canza matsayin ki a idanun mu da kuma yadda muke
sonki a zuk'atan mu Baby, kece Amal nan da muka sani muke
kuma so har yanzu."
"No Papi" ta amsasa tana kad'a kai "Bakuwa sona idan da har
kuna sona da bazaku min k'aryan asali na ba har na tsawon
shekara ashirin da d'aya, I can't believe you and Mami could
do this to me."
"Baby dan Allah kar kiyi haka sanin kanki ne ni da Maminki ba
wanda muke so sama dake."
"That's not true Papi how could you do this to me? Har ku
sanar da Yaya asalina amma ni ku hanani sanin gaskiya? No
one deserves to know the truth above of me no one Papi" ta
sanar da shi had'e da rushewa da wani kukan.
"Baby dan Allah kiyi hak'uri" Mami tasa baki "Wallahi ni da
Papinki mun so sanar dake gaskiya lokacin aurenki amma
Afzal ya hana saboda baya son hakan ya jefa ki cikin wani
hali."
Mamaki sosai kalamun Mami suka sanya Amal, har Afzal ne
yace kar a sanar da ita gaskiya kuma akan wannan dalili?
Wow! She's speechless ita kanta tasan batada masoyi sama
da shi bayan su Mami shiyasa har yau ta ke mamakin kanta na
kasa yafe masa kuskuren da yayi mata. Kai ta d'ago a hankali
ta sauk'e idanunta akansa murmushi ya sakar mata kafin tayi
sauri ta kawar da kanta.
"Meya faru Mami? For all my life you made me believed
inada Abba akan cewa mutuwa ce tayi mana yankan k'auna
ashe ba haka bane, ko a mafarki aka cemun keda Papi zaku yi
mun k'arya haka bazan ta6a yarda ba, why do you have to lie
to me Papi? Why Mami?" Kuka take sosai duk ta basu tausayi
a wajen.
"Baby kiyi hak'uri" Papi yace da ita "Bawai mun 6oye miki
gaskiya bane don son kai kokuwa makamancin haka munyi
hakan ne saboda muna sonki."
"Papi ba haka so yake ba, idan da har kuna so na bazaku
ta6a 6oye mun wannan muhimmiyar maganar ba."
"Ya isa kukan haka Mamana ya isa dan Allah karki k'ara wani
ciwon ma kanki." Kewayowa tayi kan Mami. "What happened
Mami? Meya faru? Na tabbata bazaki cuceni haka kawai ba
seda k'wak'k'warar dalili, na tabbata koma waye ne mahaifin
nawa shi ya cuceki."
"Tabbas 'yata, sanin kanki ne ba wanda nake so sama da ke
a fad'in duniyan nan kuma idan da har Allah na shawara da
bawa kafin ya k'addaro masa da k'addara da na hana afkuwan
wannan mumunar k'addara, kin fi kowa sanin bazan ta6a
sha'awar kawo ki duniyan nan ba uba ba Baby ko dan nayi
miki tsari daga tokarin 'yan unguwa da kuma yara 'yan uwanki.
Sai dai kaman yadda Allah ya fad'a a Qur'ani _fa inna ma'al
usri yusrah_ kowani wuya da musiba na tattare da sauk'i.
Acikin ikonsa da sassauci se ya kawo mun sauk'i ta hanyan
bani uba mey tausayi kaman Papinki, ubanda ze iya sadaukar
da rayuwansa dan farin cikin 'yarsa, uban da yayi playing role
na mahaifinki a rashin asalin mahaifinki Baby, ba abinda zance
da Papinki sede Allah ya sak'a masa da mafificin alkhairi ya
basa gidan Aljannah. Tabbas k'addarata mumunar k'addara ce
wanda bazan yi fatan irinsa wa mutum ba koda kuwa mutumin
ya kasance mak'iyi na" ta tsaya ta numfasa nan Afzal ya mik'e
"I'm sorry let me excuse you" yace dasu duka.
"A'a Afzal" Mami tayi saurin tsayar da shi "Ka riga ka zamo
na gida tamkar d'an cikina kuma nakeji da kai, kaman yadda
Baby zata ji wannan labari kai ma zanso ka zauna kaji komai"
ta buk'acesa sede du da hakan Afzal beji ya cigaba da zama a
d'akin ba gani yake kaman ya musu invading privacy.
"Karka ji komai Baba na ka zauna" Papi ya jaddada masa
lokacinda k'wayan idonsu ya had'e numfasa yayi sannan ya
dawo ya zauna inda Mami ta fara daga inda ta tsaya...
RANA DAYA Chapter 39
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
Tareda Naja'atu Lawal Rijau Niger State
@Whatapp 08083232323 or 09060202323
_Labari na ya fara ne lokacinda na had'u da Abdallah wanda
ake kira da Khaleefah, lokacin ina matakin form 5 (ss2) da
karatu a Government Girls College dake garin Askira inda
muke da zama a da kafin muka dawo nan. Umma
(mahaifiyata) ta kasance mey buri akaina kasancewar ni kad'ai
Allah ya azurta ta da, tunda ta haifeni har ta koma ga
mahaliccinta ko 6atan wata bata sake ba. A dalilin haka ta
d'au burin duniya ta sauk'e akai na, na cewa se mey kud'i ko
d'an wane zan aura. Lokacin da samari suka fara lek'o kai
suna nemana se Umma ta hanani kula kowanne daga cikinsu
acewarta se mey kud'i. Duk yadda Abba yaso ya ganar da ita
cewan shi fa miji na gari ake nema ba se mey d'ankaren kud'i
kaman yadda take buri ba hakan ya gagara, acewarta taya 'yar
shuwa kaman ni zan fara auren d'an talaka. Dan inyi ladabi a
gareta se na hak'ura ban kula kowa duk wanda yazo guna da
sunan zance se in ce masa ni an riga anyi mun miji ana cikin
haka ne na had'u da Khaleefah watarana a hanyana na
dawowa daga Islamiyya. Acikin duk manema na ba wanda ya
ta6amun ya kuma burgeni ya kwanta mun a rai kaman
Khaleefah, duk yadda naso sharesa lokacin da ya fara mun
magana hakan ya gagara kawai na tsinci kaina ina mishi
fara'a, har gida ya rakani ranan na basa lamba na a karo na
farko da ya tambaya. Khaleefah saurayi ne kyakkyawa san
kowa k'in wanda ya rasa, lokacin da muka had'u yana matakin
part 2 ne a karatu a wata jami'a a chan k'asar waje inda ya
samu scholarship. Khaleefah ba d'an babban gida bane amma
saurayi ne mey zafin nema saboda tun a lokacin yana d'an
sana'a haka, kafin ya koma makaranta soyayya me k'arfi ya
shiga tsakanin mu amma ban ta6a nunawa Umma ba sanin
bazata ta6a amincewa dashi ba. Ko da yazo ya koma
makaranta hakan bey hana mu cigaba da gudanar da soyayyar
mu ba, ze kirani mu wuni muna waya nima ranan da nasamu
kud'i kuma nakan sa kati in kirasa muyi hira. Ana cikin haka ne
d'an Alhj Iro Chairman na Askira ranan da suka zo makarantar
mu kawo ziyara ya ganni yace yana sona ni kuwa ban basa
fuska ba nace masa ina da wanda nakeso dukda haka be
saurareni ba seda yazo har gida ya samu Abba ya sanar da shi
k'udirinsa akaina da kuma abinda na fad'a masa na cewa ina
da tsayayye. Umma naji ta hau ni da surutu akan bata yarda in
kula kowa ba se Faisal d'an Alhj Iro. Niko a lokacin ba wanda
na tsana kamansa, daren ranan na kira Khaleefah na irga mai
halin da ake ciki inda ya rok'eni da in kwantar da hankalina
idan ya dawo next hutu zeyi ma Abbansa magana ya turo
magabatansa. Na sosai na tsaya da addu'a dan kar Faisal yayi
gaggawan turo magabatansa cikin ikon Allah se har wani
hutun ya sake zagayowa Faisal be turo ba. Lokacin ina matakin
ss3 da karatu har mun soma rubuta WAEC._
_RANA D'AYA ina cikin waya da Khaleefah Umma ta jiyoni,
fisge wayan tayi ta jawoni tsakar gida tun daga d'aki sannan ta
shiga duka na tana huci._
_"Ban ce ba ruwanki da wani d'a na miji a gidan nan ba se
Faisal?"_
_"Umma dan Allah kiyi hak'uri" na shiga bata hak'uri cikin
tsananin kuka._
_"Rufa mun baki maras kunya kawai ce miki akayi ban san
mey nake bane da nace se Faisal zaki aura? Ana neman miki
sauk'i da jin dad'i anan gaba kina shashashanci."_
_"Umma dan Allah kiyi hak'uri wallahi bana son Ya Faisal ni
Ya Khaleefah nakeso."_
_Zazzafan mari ta sauk'e mun a fuska. "Ina fad'a kina fad'a?
Mey za'ayi da talaka da talauci idan ba Allah ya d'aura ma
mutum ba? In ba rashin wayo irin naki ba ma taya a matsayin
ki na 'yar shuwa zaki hau auran talaka? Kin ci sa'a har d'an
chairman yace yana sonki amma kike sokancin nan? Naira na
kiranki kina cewa baki so? Jakar ina ce ke? Wallahi idan har
kinga kin auri Khaleefah yake kowa toh a bayan raina ne. Ma
tukun waye shi? D'an gidan waye ne?"_
_"Umma kiyi hak'uri."_
_"Tambaya nake miki waye shi nace?"_
_"D'an gidan Malam Ilu ne."_
_"Wani Malam Ilu? Na bakin titi?"_
_"Eh shi."_
_Wallahi ban ta6a sanin bakida wayau ba se yau, ashe rashin
wayon naki ya kai matakin da har zakiyi sha'awan aure a
wancan matsiyacin gidan."_
_"Amma Umma ai nagari ake nema ko musuluni bece se mai
kud'in bala'i ba bale ma fa yana karatu bazamu rasa na rufin
asiri ba."_
_"Uwarki da karatun da kuma rufin asirin nace, chin kwalin
degree d'in zakiyi kokuwa, kuma ni zaki gaya ma musulunci?
Toh naji musulunci bece se me kud'i ba amma ai al'adar ki
bata amince ki auri talaka ba."_
_"Umma amma-"_
_"Dakata idan kuma kina ganin ya akayi na auri Abbanki kike
bayan bayida komai kisani Abban ki d'an uwa na ne, auran
had'i akayi mana kuma nima muddin zaki amince ki auri wani
nawa koda baida kud'i zan amince miki amma muddin bare
zaki aura toh wallahi se mey na hannu kiji ki sani."_
_"Umma bana son Ya Faisal dan haka bazan aureshi ba" na
sanar da ita cikin 6acin rai. Amsana ba k'aramin tunzirata yayi
ba, kafin in hankara kawai naji ta rufe ni da d'an banzan duka
ana cikin haka ne Abba ya dawo daga kasuwa ya kar6eni.
"Haba Awatif! Meyayi zafi haka zakisa yarinya a gaba kina
dukanta kaman ganga? Meya faru?"_
_"Yo ba gara gangan ba dama an san ba mutum neba bale
yayi wayo, kuma ba ruwanka Malam wannan tsakani na da
'yata ne ehe! Bana son shisshigi."_
_"Shisshigi fa kikace? Ni da 'yata kice shisshigi?"_
_"Eh shisshigi ne mana kana na miji ina ruwanka da harkan
daya shafemu." Abba be sake kulata ba ya juyo a gareni
"Yayata ta kaina yi hak'uri" ya shiga bani hak'uri "Mey ya faru?"
Bayanin komai na mishi Umma na tsaye tana hararata cike da
takaici._
_"Haba Awatif! A ina akace se mey kud'i za'a aura? Tunda
yarinyan nan tana son yaron nan kuma yana da shirin turo
magabatansa me zey hana muyi mata abinda takeso?"_
_"Aww biye mata zakayi kai ma? Toh wallahi kunyi k'arya
dukanku 'yar nan bazata auri matsiyaci ba se Faisal mu zuba
daku mu gani" tana kaiwa nan ta janye hijabin ta daga kan
igiya ta fice. Kuka na cigaba da yi a wajen Abba yana ban
hak'uri._
_"Abba dan Allah ka bawa Umma hak'uri Abba bana son Ya
Faisal bana sonsa."_
_"Yi hak'uri Jameelah zanyi mata magana in shaa Allahu zata
sauk'o kinji? Kukan ya isa haka."_
_Haka nan Umma ta k'wace mun waya ta hanani waya da
Khaleefah ko fita ta hanani in ba Islamiya ko boko ba kullum
ina rufe kup a gida gashi duk yadda Abba ya so fahimtar da ita
gaskiya hakan ya gagara saboda Umma ta kasance mace mey
zafi ko Abba wani sa'in tana fin k'arfinsa daga k'arshe Abba
yace sede in hak'ura inyi yadda takeso saboda yayi-yayi ya
ganar da ita gaskiya amma tak'i fahimta niko nak'i amincewa
da hakan, ranan paper'n mu na k'arshe bayan mun gama naje
na samu Khaleefah na sanar da shi cewa Faisal ya kusa turo
magabatansa da yayi ma iyayensa magana su riga sa turowa
idan har akayi haka toh dole Umma ta yarda amma sai dai
shima koda ya kai maganan gida iyayensa suka k'i amince mai
acewansu ya bari seya gama makaranta tukun. Na sosai na
shiga wani irin yanayi bani da wata sana'ar data fiye na kuka
acikin gida. Ba waya gashi ko fita Umma bata bari na inyi
kusan sati biyu kenan banji daga Khaleefah ba rana d'aya
kwatsam kawai mukaji ana sallama, amsawan da Umma tayi
sega Khaleefah. Da fari da bata gane waye shi ba ta kar6esa
da fara'a ta k'arisa dashi ciki bayan ya zauna yayi mata
bayanin kansa ya fayyace mata k'udurinsa akaina Umma ta ci
mai mutunci tayi mai koran akuya a idona ta kuma nuna masa
ni Faisal zan aura. Ranan na kasa bacci dole washegari da
yamma na saci idonta naje duban Khaleefah. Wannan yini
shine mafi munin yini a rayuwa na, ban ta6a tsammanin
Khaleefah ze iya mun abinda ya mun ba, ashe abinda Umma
tayi masa ya mugun ci masa rai dan haka yayi tunanin
k'untata mata ta hanyan 6ata mun rayuwa, yana ganin idan ya
cuceni kaman ya cuceta ne, a tunaninsa Umma na sona d'inda
har idan abu ya shafeni zata shiga damuwa saidai ba haka
bane. A yinin ranan ne Khaleefah ya mun fyad'e ba irin rok'o da
hak'urin da ban basa ba amma haka seda ya aikata abinda
yayi niyya ba ko d'igon imani tattare da shi had'e da taimakon
abokansa k'waya biyu. Bayan faruwan abun ban sake sanin
inda nake ba se bayan kwana biyu dana farka na tsinci kaina a
gadon asibiti. Abba na fara tararwa nan take na shiga zubda
hawaye yana bani hak'uri shigowan Umma ta shiga zagina na
tana kira na da 'yar iska. Duk yadda Abba da likita suka so
ganar da ita fiyad'e akayi mun tak'i amince tana ganin gaskiya
amma ta take. Ba irin sunan da bata kirani da shi ba harda ja
min Allah ya isa. Har aka sallameni daga asibitin kuma bata
sake koda lek'oni ba, Abba ne ya zauna akaina har aka
sallameni. Ranan da muka dawo gida Abba ya shirya zuwa
tinkarar iyayen Khaleefah akan abinda d'ansu ya mun dan
k'watan mun hak'k'i amma haka mahaifin Khaleefah ya bushe
ido yace sam shi d'ansa be aikata wannan mumunan abu ba
sharri kawai ake son yi masa. Shima Khaleefah koda aka
kaimu gaban mey unguwa rantsuwa ya ringa yi shi ba abinda
ya ta6a had'amu ko sani na ma beyi ba haka muna ji muna
gani aka tauye mana hak'k'i. Faisal kuwa tun da yaji wannan
magana ya d'auke k'afa daga gidan mu hakan yasa Umma ta
sake tsanata, dama chan nasan ba sona yake har zuci ba,
kyau da jiki na kawai yake bi. Bayan wata biyu da faruwan
abun ne kwatsam rana d'aya na tashi da zazza6i da amai. Ko
kallon kirki Umma batayi mun ba, ina cikin aiki a kitchen da
rana kawai amai yabi kaina na fito na shiga kwararowa a
tsakar gida ana cikin haka Umma ta dawo gida daga unguwa,
salati ta shiga yi tana tafe hannu amma ko agaji bata taimaka
mun da ba seda na gama na kishingid'a jikin bango sannan ta
tako ta shiga dubata._
_"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ciki! Wayyo jama'a!
Shikenan tayi cikin shege" ihu ta shiga yi tana kururuwa seda
ta tara mana jama'a a gidan kafin ace mey magana ya zagaye
gari akan cewa 'yar Malam Muhammad tayi ciki alokacin kuwa
har Khaleefah ya koma makaranta, koda nazo na samu waya
na kirasa layin nasa bai shiga ba shakka ya canza. Tun daga
ranan da aka tabbata ina da ciki Umma ta sauya mun a gidan
tokari na safe daban na yamma daban tamkar ba 'yar da ta
tsuguna ta haifa ba haka ta tsaneni take kuma gaba dani. Sau
dayawa nakan zauna in sha kuka ina kokonton anya kuwa
Umma ce asalin mahaifiyata? Se daga baya Abba yake sanar
dani dalilin daya sa ta tsane ni. Tun farko bata so ayi mun
takwaran Baaba Jameela ba yar Abba wacce jininsu sam be
had'u ba, sam babu jituwa a tsakaninsu tun ma kafin ta auri
Abba, bayan auran nasu kuma se abun ya sake lalacewa
tamkar annabi da kafiri haka suke ji da juna, toh tunda aka
samun sunan Baaba Jameela Umma ta tsaneni. Shima Abba
bawai yaso yasa sunan bane sedon mahaifiyarsa da dama
akayi niyan yi mata takwaran tace ta yafe ayiwa Baaba
Jameela kasancewar tunda tayi auri sama da shekara ashirin
ko 6atan wata bata ta6a ba, dalilin da yasa aka sa min
sunanta kenan._
_Ba yadda banyi da Abba ba da ya barni in zubar da cikin
amma yak'i acewansa yin hakan haramun ne bayan nan kuma
nima ina iya rasa raina ta dalilin hakan. Ko fita ban isa inyi ba
haka ina ji ina gani na daina zuwa islamiyya bayan nayi nisa
sosai a karatun, shima Abba kaman wasa duk inda yaje se an
ringa binsa da kallo ana nuna sa da yatsa, harta kasuwa gun
aikinsa. Umma ce kad'ai ke fita freely ta dawo gida bawani
fargaba ko tashin hankali saboda ko zagi na ake seta tsaya ta
sa baki ayi da ita. K'arshe de haka zaman garin Askira ya
gagaremu amma Umma ko a bakin zaninta hasali itama ke
yad'a wa mutane nayi cikin shege. Alokacin da Abba ya gir6e
gonansa lokacin cikina na wata hud'u ya kawo shawaran
mubar garin Askira idan ba haka ba ko nazo na haife cikin
nawa ba bar min d'an za'ayi ba shi kuma abinda yake gudu
kenan, baya son laifin Khaleefah ya shafeki Baby._
_Koda Abba ya sanar da Umma cewa zamu bar Askira ita
tace ba inda zata tunda ba ita ta turani inyi abun kunya ba.
Ganin Abba dagaske yake ko ba ita shi zeyi tafiyarsa yasa ta
amince ta biyo mu. Gidan mu da komai da muka mallaka Abba
ya siyar muka dawo nan Maiduguri bada sanin kowa ba dan
ko Umma ma Abba be sanar da ita inda zamu ba kawai ganin
kanta tayi anan cikin garin Maiduguri. Mun dawo bada
dad'ewa Umma ta kamu da ciwon nono wato breast cancer,
ina da shekara sha tara na haifeki Baby, bamu ta6a neman abu
gun Abbanki mun rasa ba, komi yi mana yake, damuwa na tun
kafin in furta yake yaye mun. Tamkar 'yar cikinsa haka ya
d'aukeki yake kula da ke. Kina da shekara biyu mutuwa yayi
halinsa ya tafi da Umma sede har ta mutu bata ta6a rik'eki a
hannu ba. Tsanan duniya gabad'aya ta d'au ta aza mana ni da
ke ko kallon arziki ban ta6a ganin tayi miki ba, batun
Khaleefah kuwa har yau ban sake ji daga garesa ba. Sau
dayawa manyan 'yan kasuwa masu aure harma da samari su
kan nuna suna son su aureni amma tun kan abinda Khaleefah
ya mun naji na tsani na miji a rayuwata shiyasa kika ga har
yau ban sake yin aure ba, dan kuma gudun kar wataran yaran
dana haifa su nuna miki banbancin 'yan uba, bana son abunda
ze ta6a farin cikinki Baby, bana so"_ ta k'are cikin tsananin
kuka.
Kuka sosai Amal take itama, Afzal ma na sosai jikinsa yayi
sanyi yana mamakin rashin imani irin na Umma marigayiya da
kuma wannan Khaleefah mahaifin Amal.
"Baby kiyi hak'uri na 6oye miki wannan sirri da nida Papinki
mukayi dan Allah kiyi hak'uri."
"Kibar bani hak'uri Mami, ni ya kamata inyi hakan na rashin
fahimtar ku da banyi ba keda Papi please forgive me." A
hankali Mami ta rungumeta yayinda suka cigaba da kuka
shima Afzal seda k'walla ya ciki masa a ido dan tausayi. Be
dad'e ba aka sallamesu Afzal ya dawo da su gida chan dare
da Mami tashigo kawo wa Amal abinci Amal ta tsayar da ita.
"Mami alfarma nake nema."
"Fad'i ko mey kikeso Baby."
"Mami ku raba aure na da Yaya."
"Subhanallahi meya faru Baby? Wani abun ya sake miki ne?"
"Mami sanin kanku ne kun cuci yaya tun farko da kuka san
asali na be kamata ku had'a mu aure ba."
"Baby wani irin magana kuma kike? Ya kike magana sekace
mun zalunce shi? An fa fad'a mishi gaskiya kuma a hakan
yace yana sonki Abbanshi ma na wajen."
"Kina nufin Abba ma yasan asalina?" Kai Mami ta gyad'a
mata a hankali.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" ta furta cike da tashin
hankali yayin da hawaye ya shiga ciko mata a ido. "Bayan su
se suwa kuka sake sanar dasu asalina?"
"Wallahi babu Baby daga su shikenan."
"Nide na fad'a muki kuyi ma Yaya magana kawai ya bani
takarda na bazan iya cigaba da zama da shi ba, zaluncin ya
isa haka."
"Baby dan Allah kibar magana haka, ya kike magana sekace
laifinki ne kika kasance haka? Karfa ki manta wannan
k'addararki ce haka Allah yaso ya ganki kuma ba wai yayi
hakan dan baya sonki bane se don ya gwada k'arfin imanin ki."
"Na sani Mami shiyasa nake son Yaya ya sauwak'e mun,
Yaya be kamanci shegiya kaman ni a matsayin matarsa ba-"
"Baby dan Allah kibar magana haka ki daina kwatanta kanki
da wannan mumunar kalma" Mami tayi saurin katse ta yayinda
ta saki murmushin takaici "Akwai k'arya ne acikin hakan
Mami? Ko ba shegiyar bace ni?" A hankali Mami ta jata jikinta
"Dan Allah ki bar fad'in haka, Baby tunda muna sonki mijin ki
na sonki mey kuma kike nema? Wannan abu ya riga ya faru ba
abinda zamu iyayi mu canza ko a tunaninki ni d'in dad'i nakeji
na cewa bakida uba? Wallahi Baby na fiki takaici da zafin
hakan shiyasa ni da Papinki muka d'au burin baki tarbiyya da
ilimin boko da na islamiyya duka dan ki banbanta daga sauran
'yan matan da suka tsinci kansu acikin hali irin naki masu yawo
akan layi suna barikanci saboda ganin da suke ba ta hanya
madaidaiciya aka same su ba, Baby idan ba wai fad'a akayi ba
bawanda ze miki kallon shegiya dan Allah ki daina fad'in haka"
cikin kuka ta d'ago kanta daga jikin Mami tana share
hawayenta "Godiya nake da ilimi da tarbiyyan da kuka bani
Mami amma ban cancani miji kaman Yaya ba da yake da asali
da mutunci da ma komai ba bayan ni inada akasin hakan, dan
Allah ku mishi magana ku kuma basa hak'uri na zaman da
mukayi tare."
"Baby cikinsa da kike d'auke da shi fa? Ya zakiyi da shi? So
kike ki haifi d'an shima ba uba?"
"Sam Mami amma k'addara tariga fata cikin nan kuma zan
raineshi, yadda Papi ya tayaki rainon cikina na tabbata ze
tayani rainon wannan har zuwa lokacinda zan haifa in mayar
masa da d'ansa."
"Kekuma fa Baby? Haka kikeson ki k'arisa rayuwarki cikin
k'unci da takaici ba miji kaman ni?"
"Ya fiye akan in zauna da wanda nake ganin kaman ina
cutansa ne Mami, wallahi gani nake Allah ma baze yafe mun
ba."
"Subhanallahi bayan shi yace kar a fad'a miki gaskiyan
al'amarin ko bayan da yaji komai? Da ace mune muka 6oye
mai gaskiya da seya zama yadda kike fad'an amma fa da
saninsa da kuma amincewansa kafin aka d'aura muku aure."
"It still doesn't matter Mami, Yaya deserves someone much
better than me, he's way out of my league bazan iya cigaba da
zaluntarsa ba." Duk yadda Mami taso fahimtar da Amal
gaskiya hakan ya gagara ita sam hankalinta yak'i d'aukan
maganar ita kawai Afzal ya sallameta, game da soyayyar da
takeyi masa kuwa zata rok'i Alah ya cire mata shi daga
zuciyarta du da cewan tasan hakan ba k'aramin abu bane. Da
k'yar Mami tasamu kukan nata ya lafa ta sata taci abinci ta
sha magunanta sannan tayi mata sallama ta janye k'ofar taje
ta samu Papi take irga mai yadda su kayi da ita. Na matuk'a
Papi ya tausaya wa Amal dama ranan da ya jina yana gudu
kenan, ranan da zata gano gaskiya ta tsani kanta.
Tana mik'e akan gado tana kukan zuci wayanta dake kanta
ya shiga ruri dubawan da za tayi taga Afzal ke kiranta ba shiri
ta 6arke da kuka. Tunda take a rayuwarta bata ta6a tsanar
kanta da kuma k'yamar kanta ba kaman yanzu, gabad'aya ji
tayi batada mutunci bata da daraja, bata jin zata sake iya sa
Afzal ko Abbansa a ido waya sani ma ko sun sanar da Ummi
hala itama Ummin ta sanar da Nazeefah. Amma ko idan da
har Nazeefah tasan asalinta ta tabbata da ta yi mata gori da
shi. Shin meyasa Afzal be bari an fad'a mata gaskiya ba? Ai
idan da ta san gaskiyan al'amarin tun fari da bazata soma
auren sa ba ma. Haka tana gani wayan ya tsinke bata d'aga ba
har a karo na biyu ma k'arshe kawai seya tura mata sak'o.
Sa6anin yadda ta saba goge sak'onninsa anytime ya tura mata
yau se tayi tunanin ta bud'e inda ta fara karancewa kaman
haka;
_My Adorable Kitten please don't let what you found out
earlier ruin you, you're still the beautiful, charming, elegant,
intelligent, clever, and amazing Amal that I know, my wife and
mother to my unborn kids. I love you regardless have a
peaceful night rest, I'm missing you and our little one down
here. Xx_ 😘
Tana gama karancewa ta shiga wani sabon kukan haka ta
kwana tana yi se kusan Asuba bacci mey nauyi ya d'auketa.
Wajajen goma ta tashi bayan tayi wanka Mami ta kawo mata
breakafst nata taci sannan Papi yayi sallama cikin d'akin nata.
Zama yayi ya mata nasiha sosai amma inaaa Amal ta riga tayi
making up mind nata ita sam bazata komawa Afzal ba. Daga
k'arshe Afzal d'in Papi ya kira ya sanar da shi halin da ake ciki
yana tashi daga office ya biya gidan nasu. Ba yadda Papi beyi
da Amal ba da ta fito daga d'akinta Afzal yazo wajenta amma
tak'i ta rufe kanta a d'aki se kuka take. Na sosai zuciyan Afzal
yake k'una gabad'aya ya rasa ina zesa kansa. Kwana uku ya
jera yana zuwa duban Amal amma ko yaje baya samun su
had'u gashi koya kirata bata d'agawa, messages nasa ma bata
replying tamkar sabon mahaukaci haka Afzal ya koma. Su Papi
ma sunyi mata magana har sun gaji amma tace sam bazata
cigaba da zama da Afzal ba tana cutansa, acewarta zalunci
ne ace yadda yake d'an halak ita ko ga ta inda aka sameta
ace sunyi aure. Tun sha biyu ya baro office yau yaje ya samu
Ummi a gida kallo d'aya tayi masa ta gano yana cikin matsala.
"Meya faru kuma Prince? Amal d'ince har yanzu bata sauk'o
ba?"
"Ummi things just got worse."
"Subhanallahi kamar ya?"
"Ummi kiyi hak'uri na 6oye miki wannan sirri da nayi nasani
ko ba dad'ewa da jimawa gaskiya ze fito shiyasa nake son
sanar dake yanzu."
"Speak up already meya faru?"
"Ummi gab lokacin da na kusan auren Amal iyayenta suka
bayyana mun da Abba wani 6oyayyan al'amari wanda na
buk'aci Abba da kar ya sanar dake bawai dan ban yarda dake
bane se don ina gudun kar hakan ya canza miki ra'ayi akan
Amal."
"Ina jinka."
"Ummi Amal batada asali."
"Asali kaman ya kenan?"
"Amal ba ta halatacciyar hanya aka same ta ba."
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un kana nufin Amal shegiya ce?"
"I'm sorry but yes."
"Kuma ka aureta Afzal? Baka da hankali ne?"
"Ummi ki tsaya ki saurareni mana bawai abinda kike
tsammani bane, k'addarar fyad'e ne ya fad'o akan
mahaifiyarta."
"Haka suka ce maka? Kuma ka yarda?"
"Yes Ummi saboda ba k'arya sukeyi ba idan da har k'arya ne
da bazamu ta6a jin sirrin nan daga bakinsu ba amma fa Papi
da kansa ya sanar da ni da Abba."
"Toh ai wayo suka maku saboda sun san ba a iya 6oye abin
kunya ne."
"Ummi kibar cewa haka, just calm down and listen to me ita
kanta Amal bata ta6a sanin gaskiyan ba se last week."
"Ita Amal d'in?"
"Yes nida Abba suka fara fad'awa akan daga nan se su sanar
da ita amma na buk'aci da a cigaba da 6oye mata gaskiyan
saboda nasan halinta muddin har ta gano gaskiya toh zata iya
k'in amincewa ta aureni gashi yanzu ta gaano gaskiya tace ita
sena sauwak'e mata tana cewa she don't deserve to be with
me I deserve someone better."
"Ita Amal d'in? Ya akayi ta gane gaskiyan yanzu?"
"Shine ai nake kaiki, ranan da naje gidansu muke sulhu ne
taji komai" labarin duk yadda sukayi ya kwashe ya bata, Ummi
can't help but to remain shocked. Tausayin Amal ne ya
kamata na matuk'a.
"Toh yanzu ya kenan? Zaku rabun?"
"Kema kinsan bazan iya rabuwa da Amal ba Ummi."
"Toh ya zakayi Afzal tunda iyayenta ma sunyi su ganar da ita
sun gagara."
"Even stil Ummi I'll continue to try my best."
"Ko kana so inyi mata magana?"
"Nooo bana son tasan kin sani."
"Toh Allah baka ikon shawo kanta wallahi tabani tausayi
matuk'a yarinya ga haddan Al~Qur'ani."
"Ummi bakiga yadda take kuka ba ranan da gaskiyan ya fito."
"Allah sarki Amal 'yar nan jarabawanta a duniya dayawa suke
Allah de bata ikon cinyesu."
"Ameen Ummi."
"Ya batun Nazeefah fah? D'azu Mummy'nta ta kirani muka
gaisa when do you plan on bringing her back?"
"Ummi muddin Amal bata dawo mun ba bazan iya dawo da
Nazeefah ba."
"Zata dawo in shaa Allah Prince zan tayaka da addu'a."
"Thank you Ummi barin wuce gida in huta idan Abba ya dawo
ki gaishesa."
"Bazaka jira lunch ba sauran kad'an fa."
"I'm not hungry Ummi thank you." Rakasa tayi har gun mota
sannan ta dawo ciki.
Afzal be fasa zuwa duban Amal ba a rana na shida ne da
yaje ya tarar da Mami kad'ai itama tana shirin fita, tana gama
cin abinci ta basa hak'uri kan zata shiga nan mak'ota yin barka
akan ya jira Papi shi ma ya kusa dawowa.
"Ayya ba komai Mami sekin dawo zan jirasa."
"Yauwa toh barin wuce." Bayan ta fice ya mik'e had'e da zaro
wayansa daga aljihu sannan ya taka har izuwa bakin k'ofan
d'akin Amal dai-dai gun ya tsaya ya shiga buga layin nata sede
yana ji daga ciki yana ringing amma bata d'agawa.
A hankali ya gwada bud'e k'ofan sa6anin kullum ya tarar da
k'ofar a bud'e da mamaki ya bud'e mik'e akan katifarta tana
bacci ya tarar da ita a tunaninsa gabad'aya tana ganin call
d'inne kawai tak'i d'agawa ashe bacci take even though yasan
koda idonta biyu ma ba d'agawa zatayi ba. Cikin d'akin ya
k'arisa ya tsuguna a gefenta. A hankali ya aza hannunsa akan
cikinta yana shafawa a hankula.
"Kitten?" Ya kirata da k'aramin murya. "Kitten wake up it's me
Afzal" ya sanar da ita kaman a mafarki take jin sautin
muryansa, a hankali ta shiga bud'e idonta har ta sauk'esu
akansa ba k'aramin razana tayi ba ganinsa da tayi akanta
kad'an ya rage bata sa ihu ba.
"Shhhhh it's just me calm down" ya buk'aceta. Kanta ta
kawar ba tare da tace da shi komai ba.
"Amal?" Ya kirata nan ma bata juya ba a hankali ya kewayo
da fuskarta. "Babe please come back to me, dan Allah kiyi
hak'uri mu koma gida I terribly miss you." Shiru ta mai ba tare
da tace komai ba hakan yasa ya cigaba.
"Amal fushi kike dani har yanzu da bazaki mun magana ba?
Please forgive me I'm sorry, I'm terribly sorry."
"Why did you do it?" Ta soma da tambayarsa tare da
kewayowa.
"Did what Sweetheart?" Yayi saurin tambayarta.
"Mesa ka hana su Mami sanar dani gaskiya Yaya? Meyasa ka
aureni bayan kasan yin hakan kaman ka zalunci kanka ne,
sanin kanka ne iri na da bamuda asali bamu cancanc-" da
sauri ya katseta ta hanyan aza hannunsa kan dry lips nata.
"Please not a word Amal, I married you because ba laifinki
bane da kika kasance haka, I married you because I love you
Amal, I don't care koba ta halatacciyar hanya aka sameki ba
and above all I married you because it's been destined you're
going to be my wife and the mother to my kids Amal saboda
akwai rabo a tsakaninmu" ya k'arashe maganan had'e da aza
hannunsa akan cikinta. "Please come back home with me
Baby please don't say no." By now kuka take sosai "I can't
Yaya, I really can't" ta sanar dashi cikin tsananin kuka had'e da
kawar da kanta.
"So dagaske ne da Papi yace kince in baki takardanki?" Ya
tambayeta cike da k'in yarda. Kai zalla ta gyad'a masa.
"Lily ya kikeson in rayu in ba ke? Taya kike tsammanin zan
iya rayuwa idan ba ke a kusa dani please don't punish me like
this, by Allah my heart can't take it dan Allah kar kiyi mun haka
taya kike tsammanin zan iya rubuta miki takardan saki wallahi
koda wuk'a a wuya na bazan iya ba yaushe ne zaki gane cewa
kece rayuwa na Amal idan kuma ba ke bazan iya rayuwa ba?
When will you realize that?" A hankali ta shiga juyo da kanta
tana mey mamakin kalan tashin hankalin daya bayyana a
fuskansa tausayinsa kawai taji ya kamata har yanzu ta rasa
gane soyayya ne ko kuma wani ciwon yake damun Afzal ace
yasan asalinta amma be k'yamace taba bayan ita da kanta
k'yamar kanta take.
"I'm sorry Yaya I'm terribly sorry" ta basa hak'uri hawaye na
tsiyaya daga idanunta.
"I don't want you to be Amal just come back to me please ko
ba dan ni ba dan wannan" ya fad'a yana sake mayar da
hannunsa kan cikinta. Hannunsa tabi ta aza nata akai "Yaya
you don't deserve me at all, you deserve someone better."
"Dan Allah kibar cewa haka, I deserve no one other than you
Amal please come back." Shiru tayi bata sake ce dashi komai
ba.
"Kinji? Dan Allah kiyi hak'uri kibar cewa in sawwak'e miki."
Kai ta gyad'a mar a hankali. "Kin yarda zaki dawo?" Ya
tambayeta eagerly nan ma kai zalla ta gyad'a mishi. Wani irin
farin ciki Afzal ya tsinci kansa a ciki, hannunta ya d'aga had'e
da placing soft kiss akai "Thank you Amal, thank you so
much."
"Yaya meyasa kake so na haka?"
"Kitten ni kaina ban sani ba all I know is my love for yu knew
no bounds a jinin jikina yake."
"Yaya shin baka k'yamata ne?"
"Subhanallahi Amal wace irin magana kike haka? Dan Allah
kar ki sake cewa haka kinji?" Kai ta gyad'a mishi a hankali
"Thank you" mik'awa yayi a hankali yayi kissing kumatunta "In
shirya miki kayakin ki mu koma gida yanzu?"
"A'a Yaya" tayi saurin cewa.
"But Kitten why? Baki hak'ura ba har yanzu?"
"Ba haka bane, I was never mad at you I was just angry."
"Toh yaya ne?"
"Yaya ai ni nace zan dawo kar ka damu nafi son in had'a
kayakin nawa da kaina."
"Toh ai bazaki iya ba hannunki da ciwo har yanzu."
"Mami will help me kar ka damu."
"Har yaushe kenan?"
"Yaya don't you trust me?"
"I do Amal morethan I do trust myself I just can't wait to see
you back home." Murmushi kad'an ta sakar masa "You should
go, Papi ya kusa dawowa kar ya tarar da kai anan."
"Sure" ya amsa yana duban agogon dake d'aure a tsintsiyar
hannun sa. "Kafin nan baki fad'a mun how many months is my
baby ba Kitten" Wani kunya taji ya rufeta take ta kawar da
kanta wanda hakan ya sanya sa murmushi "Kunya na kikeji
Kitten?" Shiru tayi bata ce komai ba "Tell me kinji? In soma
counting."
"Yaya da saura fah."
"Toh how many months ne?"
"D'aya ne fa kacal" ta sanar da shi cike da kunya.
"Wow! In conclusion saura mana 8 months kenan we have a
long way to go don't we?"
"Yaya ka tafi kar Papi yazo ya tarar da kai please."
"Kori na kike haka Kitten?"
"Yaya please."
"Ba kiss ba komai kike son in tafi Kitten? Do you know how
terribly I miss your sugary lips?" Bata kai ga juya mai baya ba
ya rik'o hannunta "I can't wait to have you back Kitten" ya
sanar da ita kafin ya matso kusa da kunnenta "Sena biya
bashin duka kwanakin nan da muka d'auka bamu tare" kunya
ne ya rufeta gabad'aya kawai ta matse idonta. Murmushi ya
sakar sannan yayi pecking nata a kumatu "I'll call you later I
love you" yana kaiwa nan ya ajiye mata envelope daya tanadar
mata sannan ya mik'e ya fice ko jiran dawowan Papi beyi ba
ya koma gida cike da farin ciki.
Chan misalin k'arfe tara ya kira ta seda ya kusan tsinkewa ta
d'aga.
"Alhamdulillah I can't remember when last kika d'au wayana
Kitten thank you for picking up."
"You're welcome Yaya."
"So how're you and my baby?"
"Duka lafiya shine ka ajiye min kud'i d'azu Yaya?"
"Take care of yourself Kitten I love you."
"Thank you" ta amsa tana murmushi.
"Yaushe zaki dawo toh?"
"Zan dawo karka damu."
"Toh shikenan zanga ko zan iya cigaba da jirarki nayi kewarki
Kitten, there's no one to run to after coming back from home,
no one to bath with or sleep together with ni kad'ai na na rage
pity me and do come back soon please."
"Nazeefah fa?" Kawai ta tsinci kanta yana tambayarsa.
"Bata nan."
"Tana ina?"
"Na ce ta tafi gida Kitten muddin baki dawo ba bazan iya
dawo da ita." Mamaki tasha na sosai amma tayi shiru akanta
ya tura Nazeefah gida? Wow!
"Kitten are you there?"
"Uhmm" tayi mumbling.
"Kiyi ki dawo kinji? I miss you so much."
"Toh mun gaisa I'm sleepy ina son in kwanta."
"I can't ask for more Kitten, kwanta kinji? Sleep like a baby I
love you."
"You too seda safe" bata jira jin me zece ba ta kashe wayar.
Murmushin dake d'auke akan fuskan Afzal ya kasa gushewa
he can't wait to have his Amal back. Be kai ga ajiye wayansa
ba sak'on gaisuwan Nazeefah ya shigo na goodnight bayan ya
karance yayi replying nata da _Thank you I love you too_ 😘
💕
****
A kullum jira Afzal yake Amal tace masa ta shirya yazo ya
d'auketa sede shiru ko yayi mata maganan kuma setace tana
kan shiri ne gabad'aya ya k'osa ta dawo bayan kwana hud'u da
yamma yana zaune a parlour yana kallon sports sega call nata
yana shigowa hannu na 6ari ya d'aga baze iya tuna yaushe
Amal ta d'au waya ta kirasa ba.
"Halo Kitten?"
"Yaya kana gida ne?"
"Yes Kitten."
"Zaka iya zuwa ka d'aukeni ko se gobe?"
"Gobe kuma? I'm on my way right now." Wurgi da wayan yayi
ya mik'e ya sa sabin kaya red buttoned sleeves shirt me adon
bak'i da black trouser sanin yadda Amal ke son red color.
Combing gashin kansa yayi sannan yayi wanka da turare ya
fad'a bayi ya wanke bakinsa da mouthwash ya fito ya d'au key
ya fice. Nan da nan ya isa gidansu Amal yana k'arisawa ciki ya
tarar da su zaune a tsakar gida Amal tayi wanka tsaf abinta ba
bandeji ko d'aya d'aure a jikinta se yanzu ya gane dalilin da
yasa tayita jan dawowa a garesa ashe so take se ciwonta ya
warke. Masha Allah.
Sanye take da pitch hijab mey hula wanda ya mugun mata
kyau bayan sun gaisa duka Papi ya yi musu nasiha sosai
itama Mami ta d'aura nata akai da kansa ya janye akwatin
nata yakai mota ya kuma bud'e mata k'ofar bayan ta shiga ya
rufe. Har yanzu da k'ingishi take tafiya a sanadin accident d'in,
hannunta ma ba iya aiki take da shi sosai ba kawai de da
sauk'i ne. Sallama yayi dasu Papi sannan ya tada motan suka
fice se gida. D'agata yayi chak a sama ya kaita har ciki
yayinda yasa mey gadi ya shigo da akwatin nata.
Mamakin yadda ko ina yake tsaf Amal take bayan nan ga
k'amshin turaren wuta.
"Kai ka kunna turare?"
"Kin tuna lokacinda na tambayeki yadda kikeyi?" Ya
tambayeta da murmushi.
Kai ta gyad'a tana mayar masa da murmushin "I'm
impressed."
"Let's go in ki rage kayan jikinki" bata kai ga mik'ewa ba
daga kan kujerar daya ajiyetan ya dakatar da ita. "Let me."
"Yaya kar ka damu I can manage."
"No My lady allow me assist you."
"Toh Yaya ai likitan ma kansa cewa yayi ina k'ok'ari ina taka
k'afar idan ka cigaba da d'agani ai tsami k'afar zatayi."
"Naji amma ki bari na yau" bata sake mai musu ba ya k'arisa
ya d'agata suna kai corridor'n d'akin nasu tace "Ka manta
chan ne d'akina?" Ta tambayesa da gan-gan tana mai nuni da
d'akin data koma bayan daya korata daga d'akin nasu.
"Kitten da gan-gan kike ko? Ai sede ni in bar miki d'akin ba
ke kibar min ba, it was so wrong of me to send you out of
your own room forgive me okay?"
"It's okay Yaya" ta amsa tana mar murmushi, murmushin ya
miyar mata sannan suka k'arisa ciki ya dawo ya ja akwatinta
bayan ya sauk'e ta akan gado. Da kansa ya shirya mata
kayakin acikin wardrobe nata. Ya so su fita cin abinci bayan
sallan Isha amma ganin hakan ze bata wuya funda ga yadda
take taka k'afara har yanzu se kawai yayi deciding ya musu
girkin da kansa. Kulleta yayi a d'aki be bud'e ba seda ya gama
komai yayi arranging dining sannan ya d'auketa a hannunsa
zuwa dining d'in yana bud'e flask d'in Amal taja wani numfashi
"Hummm it smells so good."
"Wait until it is served" ya amsa cike da jin dad'i. Da kansa
yayi serving nata spaghetti d'in, da fari yaso suci a plate d'aya
amma tuna condition nata se be sake sha'awan d'agata ba
dan kar ya bata wahala. Na sosai Amal taci abincin harda
neman k'ari wanda hakan ya mugun yima Afzal dad'i. Wani
sabon soyayyarta yaji yana shigansa, tamkar k'wai kuma haka
yake jinta baya sake k'aunan abinda ze had'asu har wanda
zesa ta sake yimai yaji. Shi kad'ai yasan kalan tashin hankalin
da ya shiga a rashinta. Bayan sun gama yatattare wajen dukda
cewan taso yi amma ya hanata bayan ya dawo ya zauna kusa
da ita inda ta kira sunansa a hankali.
"Nazeefah fah yaushe zaka dawo da ita?"
"Soon" ya amsa.
"Ina Safiyya?"
"Na sallameta har gida nan Mahaifiyarta tazo ta bada hak'uri
tace ta riga ta mayar da ita k'auye dama tun farko bataso
kawo su nan d'inba."
"Allah sarki, Safiyya was innocent Nazeefah ce tayi
manipulating mind nata ta kirani yayi sau uku tana bani hak'uri
akan in yafe mata."
"Dukda haka be kamata tayi miki abinda tayi ba Kitten kodan
yadda kike kyautata mata kayakinki nawa kika bata?"
"Yanzu kam ai ya wuce."
"Nazeefah fa? Ta kiraki?"
"Tace mun mey? Ba abinda ya sake had'amu."
"Kitten I'm sorry nasan abinda Nazeefah ta miki da zafi kuma
nasan bata kyauta ba but I would appreciate it if you'll find it
in your heart to forgive her ni da kaina zan sa ta kiraki ta bata
hak'uri."
"No need Yaya godiya nake da Allah ya tozarta mana ita ka
gane halinta bale ta sake tunanin cutar dani kawai ka barta."
"But Kitten zan so ace you two are getting along ba abinda
zefi min hakan farin ciki dan Allah kiyi hak'uri."
"Yaya it's really okay" ta fad'a had'e da rik'e hannunsa. "In har
Nazeefah ta gane kuranta ta kuma nemi tubana nikam me yafe
mata ne kodan kai ma."
"Thank you so much Amal Allah yayi miki albarka."
"Ameen" ta amsa da murmushi.
"Muje mu kwanta ki huta kinsan yanzu da da ba d'aya bane
you'll be needing alot of rest now kafin nan kuma sena kar6i
hak'k'i na ko bazaki bani ba?"
"Yaya" ta ambata tare dukar da kanta cike da kunya.
"Sarauniyar masu kunya toh wasa nake miki besides you're
still sick I can wait until you get better" murmushi kad'ai ta iya
ta sakar masa "So let's go bath" chak ya d'agata se a bayi ya
direta inda ya fito ya d'auko musu towels nasu da kansa ya
rage mata kayan jikinta. Bayan lokacin kansu da suka samu a
bayin k'arshe ya tayata yin alwala dukda cewan tana iya yi da
kanta amma yayi insisting shi zeyi mata. Daga nan ya tayata ta
d'aure towel nata sannan suka fito tana rik'e a hannunsa.
Kayan baccin ma yak'i ya barta tasa, bayan ya sanya mata
yana cikin sa nasa ta mik'e a hankali ta nufi dressing mirror ta
zauna ta shiga warware gashinta da hannunta d'aya ganin
hakan ze bata wuya Afzal da ya gama sanya kayansa ya mik'a
hannu ya rik'eta "let me help you" warwarewa ya k'arisa yi ya
d'au comb ya shiga taje mata a hankali sannan ya shafa mata
mai ya kama mata shi sakwa-sakwa yadda zataji dad'in bacci.
"Thank you Habib Albi" ohhh how he misses her calling him
with the name, baze iya tuna rabonta da ta kirasa da sunan
ba. A hankula ya mik'ar da ita "Kikace?" Gano so yake ta sake
nanata sunan se tace;
"I said thank you" zalla.
"No ba haka kikace ba" yayi saurin kad'a kai had'e da zagaye
hannunsa a 'yar kunkuminta. "Yaya careful k'afana."
"Sorry so say the name again Baby."
"Wani suna?"
"Kitten mana!" Ya had'e rai.
"Ya Omri? Ya Amar? Ya Hayat? Mi Amor? Noorul qalb?
Noorul ein? Wanne d'aya?"
"Damn! My kitten is such a lover girl, all these sweet names
for me?"
"Yes Habib Albi so wanne kafi so? I'm giving you a new pet
name."
"Really why?"
"Saboda we're starting a new life all over again, wannan
karan ba fad'a ba komai se zallan soyayya da kulawa kawai."
"Masha Allahuu I'm so proud of you Kitten Allah cigaba da yi
miki albarka."
"Ameen Habib Albi so wanne kake so?"
"I think 'Ya Omri' sounds great."
"Then you garrit Ya Omri."
"How about I give you a new name too?"
"Really?"
"Yes Kitten."
"Toh ina sauraranka" shiru yayi na d'an lokaci yana nazari,
"How about Cherry? Peaches? Pearl? Flower? Rania? Snuggly?
Cupcake? Which one?"
"Cute names Ya Omri, Rania sounds arabic hakane?"
"Yes Kitten it means Queen, my Rania my Queen" yayi mata
bayani.
"Uhmm na d'au Malikati ne My queen."
"Rania is another form of it so wanne kikeso? Malikati ko
Rania?"
"Rania it's more fancy."
"Really?"
"Yes."
"Toh shikenan starting today you're My Rania."
"Thank you Ya Omri."
"All the time My Rania."
"So muje mu kwanta bacci nakeji." Kafin tace zata juya ya
sake kankameta yadda ko k'wak'k'waran motsi bazata iya ba
"Ya Omri lafiya."
"I want to kiss you so badly Rania."
"Ya Omri.." ta kuma furtawa tana k'ok'arin dukar da kanta,
yatsa yasa ya d'ago fuskan nata sannan ya shiga shafawa a
hankali "May I?" Ya tambayeta yana gangarowa kan lips nata.
Wani irin kunya taji ya rufeta kaman ta nitse a k'asa ba k'arya
aciki ita kanta she misses his tasty lips and minty breathe.
"Rania may I?" A hankali ta gyad'a masa kai "No Rania it
doesn't work like that answer me may I have a taste of this
lips?"
"Yaya mana" ta amsa a tak'ure tana kawar da k'wayan idonta
daga nasa. "May I?" Ya sake tambaya yana mata murmushi
"Yes Ya Omri you may kiss me" ta sanar dashi. Dad'i sosai yaji
ya shiga matso da fuskansa kusa da nata a nitse seda ya
had'e lips nasu, kissing nata ya shiga yi gently with tender
touches yayinda take replying nasa itama a hankali dictating
to him how much she missed him. Be bari numfashnta ya
d'auke ba yayi breaking kiss d'in, a hankali ta sauk'e goshinta
akan ha6arsa tana maida numfashi.
"I love you Rania" ya sanar da ita yana shafe kan sajen
fuskarta.
"I love you too Ya Omri" daga haka ya d'agata ya kaita d'aki
inda suka kwanta bayan ya kashe musu wuta.
"Goodnight Raina I love you" ya sanar da ita had'e da sanya
hannunsa k'ark'ashin rigarta yana shafa kan flat tummy'n ta.
"Goodnight Ya Omri I love you too" ta amsa tare da sauk'e
hannunta akan nasa.
RANA DAYA Chapter 40
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
Tareda Naja'atu Lawal Rijau Niger State
@Whatapp 08083232323 or 09060202323
_This chapter goes to Members of the prestigious group of Mukhtar Adam Nation thank you so much for the maximum
support and love guys, I love y'all fisabilillah 💕_
Da Asubah alarm na Afzal yayi ringing yana kashewa ya
tashi ya shirya bayan nan ya tayar da Amal sannan ya fice
masallaci, tana idar da sallan ta koma bacci ko jiransa ta kasa
sa6anin yadda ta saba. Murmushi kawai ya saki ya tu6e
jallabiyansa ya kwanta a gefenta sannan ya saita alarm nasa.
Shida na bugawa alarm d'in ya shiga ruri sa6anin yadda Amal
ta saba rigasa jin alarm d'in harma ta tashi ta kashe ta tayar da
shi se gashi yau se baccinta kawai take, lallai nauyin baccin
masu ciki daban yake. Mik'ewa yayi a hankali gudun kar ya
farkar da ita sannan ya gyara mata kwanciya ya shige bayi yayi
wanka, breakfast nasa ya had'a da kansa yaci ya shirya sannan
ya komo kan gadon ya mata placing gentle kiss a goshi ya
fice. Ba Amal ce ta tashi ba se chan wajajen k'arfe goma. A
razane ta farke had'e da duban lokaci a fankacecen agogon
dake manne a sentan gadon d'akin nasu.
"Subhanallahi!" Tayi exclaiming "Yaya you're going to be
late" ta furta cike da tashin hankali yayinda ta juya tana neman
Afzal kan gadon sede wayam ba kowa. Mik'ewa tayi ta lek'a
bayi nan ba shi wayanta ta d'au ta kirasa a karo na farko ya
d'aga "Good morning My Rania" ya gaisheta yana mey barin
duk wani abinda yakeyi focusing on the phonecall just.
"Morning Ya Omri where are you?"
"At work" ya amsa nan take.
"Kana nufin kana office?"
"Yes Rania."
"How? Yaushe ka tashi ka shirya? Baka sa alarm bane?"
"Kina bacci duk nayi hakan alarm kuma na kunna har ya
gama ringing baki ji ba."
"Omg! Ya Omri I'm sorry yanzu ka karya?"
"No harm done Rania I prepared breakfast myself."
"Next time ka tayar dani in tayaka shiri kaji?"
"No Rania, you're pregnant and still sick, kina buk'atan hutu
sosai so karki damu kinji? I can manage."
"Are you sure?"
"Yes Rania, yaushe kika tashi?"
"Yanzu ban san yaushe na soma bacci mey nauyi ba, daga
cewa barin kwanta kafin ka dawo daga Masjid kawai se bacci
ya d'aukeni ban kuma sake jin komai ba."
"Dama chan haka baccin masu ciki yake."
"Gaskiya bazamu shirya da baby'nka ba idan zena sani bacci
kaman gawa haka."
"Toh da mey zakiyi mishi?"
"Punishing nashi zanyi."
"Ta yaya kenan Rania?"
"By starving myself."
"So kike yunwa ya addabe min baby na?"
"Toh ba yana sani bacci ba."
"Yi hak'uri Rania beyi zafi haka ba, ga breakfast a kan dining
nasa driver ya saya miki je kici kinji?"
"O'o" ta amsa tana turo baki tamkar yana tsaye a gabanta.
"Yi hak'uri ko in dawo in baki?"
"Eh" ta amsa da gan-gan don jin mey zece.
"Toh shikenan I'm on way ki jirani."
"Lol Ya Omri yanzu dagaske office d'in zaka bari dan ka taho
ka bani abinci?"
"Anything for you Rania."
"Wasa nake maka yi zamanka kayi aiki, zanci da kaina bari
inyi wanka."
"Are you sure ba sena zo ba Rania?"
"Don't worry Ya Omri sekace wacce ba tada hannu."
"Alright I'm waiting for your dope pictures in kinyi wankan ayi
mun kwaliya na musamman a turo mun."
"Anything for my Omri I'll hang up."
"Take care I love you."
"I love you too" da haka ta katse wayan. Bayi ta fad'a tayi
brushing sannan ta fito ta karya bayan nan tayi wanka ta sanya
wata doguwar jallabiya mey d'ankaren kyau sannan ta zauna ta
tsara kwaliya ta taje sumarta da k'yar da hannunta d'aya ta
kwantar a bayanta ta shiga snapping pictures tanayi wa Afzal
sending ta Snapchat. Ko aiki ya kasa yi ranan se kallon
hotunan nata kawai yake. Da azahar bayan yaci abinci ya kira
Nazeefah a karo na farko ta d'aga. Bazata iya tuna when last
ya kirata ba, ko ta kira baya d'agawa ta sak'o kawai suke
gaisawa.
"Ya Rouhi?" Ta kirasa.
"Na'am Rabba'atul Bait" ya amsa.
"Ya Rouhi you callled!" Ta fad'a cike da k'in yarda.
"Yes Rabba'atul Bait ya kike?"
"Ya Rouhi I miss you, I miss you so much."
"I'm missing you too kina gida?"
"Yanzun na dawo daga lectures."
"Inzo?"
"Eh?"
"Nace inzo?"
"Ya Rouhi zaka zo gani na?"
"Yes Rabba'atul Bait baki yarda bane?"
"Ya Rouhi you're nomore mad at me?"
"Not anymore sweetheart so inzo?"
"Yes Ya Rouhi you're always welcomed."
"Alright I'm on my way" daga nan ya katse wayan. Kaman a
kyaftawan ido Nazeefah ta fad'a bayi ta watsa ruwa nan da
nan ta shirya cikin wani bak'in lace mey torches na pink. Na
sosai d'inkin da shi kanshi lace d'in ya amshi farar fatarta.
Light makeup tayi amma ta bala'in yin kyau kasancewar ta
kwana biyu batayi applying makeup ba. D'auri irin na Zahra
Buhari tayi ta cire gashinta ta k'asa sannan ta feffeshe jikinta
da turare inda ta shiga zaman jiransa, chan bada dad'ewa ba
Afzal yayi mata waya kan ya iso ta fito.
Mayafinta ta d'au ta yafa sannan ta fice daga gefen gidan
nasu yayi parking motansa, wani irin sanyi ne ya ziyarci
zuciyan Nazeefah na ganin Afzal kawai da tayi. Kishingid'a
yayi daga jikin motan nasa yana sanye da black suits, sky blue
shirt da red tie, ba k'aramin kyau yayi ba kaman a had'iyesa.
Bata san lokacinda tasa gudu ta nufesa ba, hannunsa ya bud'e
mata wide open inda ta fad'a jikinsa hugging him so tightly
sun dad'e a haka sannan a hankali ya janyeta sede kawai yaga
tana hawaye.
"Not the tears Rabba'atul Bait."
"Ya Rouhi I miss you so much" ta sanar dashi had'e da sake
fad'awa jikinsa tana hugging nasa be sake d'agata ba, tsam ya
rik'eta yana shafa bayanta ba k'arya shima yayi missing nata
na sosai. Da kanta ta d'ago daga jikin nasa tana share
hawayenta hannunta ya sauk'e had'e da zaro hanky daga
aljihunsa ya shiga share mata hawayen nata da kansa. "Cry
nomore Sweetheart" ya sanar da ita. Kai zalla ta iya gyad'a
masa.
"Kinga yadda kikayi kyau?"
"You too Ya Rouhi."
"Toh ya kike?"
"Ka shigo ciki dan Allah."
"No not today."
"But ba kowa a gida dukansu sunyi tafiya sun tafi Umarah ni
kad'ai ce se wata 'yar uwarmu kuma ta fita itama."
"Are you sure?"
"Yes Ya Rouhi please ka shigo." Hannunsa taja ta kaisa har
parlourn Daddy, da tayi yunk'urin kawo masa ruwa da abinci
kuwa seya hanata akan cewa yanzun ya baro restaurant. A
gefensa ya zaunar da ita yana kallonta tabbas yayi kewarta
shima, yana cikin binta da kallo idonsa yayi tozali da wani
shatin belt a hannunta wanda har yanzun ya k'i gushewa.
Sosai yaji zafin hakan, duk lokacinda ya tuna ya d'au abu ya
zaneta seyaji ba dad'i. Hannun nata ya d'aga a hankali yana
shafa wajen "Rabba'atul Bait I'm sorry, I'm sorry for bruising
you like this."
"Please don't be Ya Rouhi, you have no reason to be ni na
jawo komai wa kai na and I'm sorry please forgive me."
"I've forgiven you Rabba'atul Bait nazo ne don in jaddada
miki ina shirin dawo dake d'akinki, zaki dawo?"
"Ya Rouhi zaka mayar dani gida?" Ta tambayesa cike da k'in
yarda.
"Yes Rabba'atul Bait you're going back to your home."
"Ya Rouhi!" Ta ambata hawaye na ciko mata a ido yayinda ta
fad'a jikinsa tana kuka, zagaye hannunsa yayi a bayanta yana
calming nata "Ya Rouhi dan Allah kayi hak'uri na d'au alk'awari
bazan kuma abinda na aikata ba please forgive me" a hankali
ya d'agota yana share mata hawayen nata "Na fad'a miki I've
forgiven cry nomore."
"Thank you so much."
"Baki tambayi ya jikin Amal ba." Alokaci d'aya yaga yanayinta
ya sauya.
"Nazeefah na d'au kinyi nadaman abinda kika yi wa Amal
koba haka ba?"
"Ya Rouhi nayi."
"Then why this reaction? In har Amal tana da niyyan yafe miki
meyasa ke bazaki iya neman tubanta ba? Kinsan ko akwai
hak'k'inta akanki? Kuma muddin baki nemi tubanta ba ta yafe
miki Allah baze ta6a barin ki ba?"
"Ya Rouhi nayi nadaman abinda nayi mata, wallahi nayi."
"Then ki bata hak'uri I want you to call her and apologize."
Shiru tayi bata ce komai ba tana tunanin ta inda zata fara kiran
Amal ta bata hak'uri, wani irin k'ask'antarwa ne Afzal yake
shirin yi mata haka?
"Bazaki iya ba?" Ya tambayeta yana mey tsamo ta daga
tunanin da takeyi.
"Ya Rouhi ba haka bane" ta mai k'arya.
"Nazeefah yaushe ne zaki gane cewa Amal 'yar uwarki ce ba
abokiyar gabanki ba? Yadda kike ganin ina son ta kema fa
hakan nake sonki, in kuma kina ganin kaman nafi son ta ne
then you're right saboda Amal na mun abinda zuciya na keso.
Bata k'untata mun, bata sani surutu, kuma tana sonki saboda
tasan ina sonki. Ta sani idan taso wani nawa kaman ni taso
amma ke fah? You don't love her single bit. Why Nazeefah?
Do you even love me at all? I doubt so because if you really
do zaki so abinda nake so kema ki so Amal."
"Ya Rouhi dan Allah kar kace haka sanin kanka ne ina sonka,
I do love you above of everything."
"No Nazeefah, idan da har kina so na da zaki so Amal ki guji
aikata abinda ze 6ata mun rai but no, you keep on hurting
Amal which is technically like hurting me, ita kuma zuciya mey
kyautata mata take so ko baki san da haka ba?"
"Na sani" ta ambata kanta a duke.
"Good saboda haka nake son ki soma kyautata wa Amal, kin
fini sanin yadda Amal ta d'aukeki da zuciya d'aya, kinfi kowa
sanin cewa Amal bazata ta6a aikata kwatankwacin abinda
kikayi mata ba saboda tasan idan ta ta6aki kaman ta ta6a ni
ne why can't you do thesame? Yadda kike jin ni mijinki ne
itama fa haka takeji you both have equal rights on me, I love
you Nazeefah, I really do love you and bana son abinda ze
sake shiga tsakaninmu but idan kika cigaba da wannan halin
naki zakisa ki fita mun a rai kuma bana son hakan ya faru
because I don't want to hate you Nazeefah please change
your ways. Kece fa uwar gidana komin yaya matsayin ki daban
yake dana Amal a zuciya na da kuma ma a idon jama'a, be
kamata ace ke kike yin wannan rashin hankali ba kamata yayi
ace Amal ce keyi kina mata wa'azi, ke bakisan da wannan
abinda kikeyi ba Amal zata iya k'wace miki martabarki?"
"Ya Rouhi I'm sorry."
"Don't be Nazeefah, I just want you to change ki sauya
d'abi'un nan kiso 'yar uwarki muyi zaman lafiya dukan mu
please. Idan har kina sona zakiyi mun abinda nakeso."
"Naji Ya Rouhi in shaa Allah kuma zan canza, ko mey kakeso
I'll do it."
"Ki tuba ki bawa Amal hak'uri, that's all I want."
"Ya Rouhi sena bata hak'uri ne? Ai na tuba."
"Toh bakiya son in dawo dake gida?"
"Ina so."
"Then kiyi hak'uri ki sauk'e girman kan nan ki bata hak'uri I
kow it's not easy but do it for me okay?" Ya k'are had'e da
d'aga hannunta ya rik'e acikin nasa.
"Naji zan bata."
"And promise me bazaki sakeyin abinda zeyi hurting Amal ba,
promise me ko na mayar dake bazaki sake tada wa kowa
hankali a gidan ba, zaki bawa Amal dama kuyi zaman lafiya."
Hannunta ta aza akan nasa dake rik'e da d'ayan nata "I
promise Ya Rouhi in shaa Allahu bazaka sake jin kaina dana
Amal ba."
"Thank you Nazeefah thank you so much."
"Ni ce da godiya Ya Rouhi."
"So yaushe zaki kirata?"
"Bana son muyi magana ta waya nafison inje in sameta har
gida in nemi tubanta."
"Masha Allah."
"Yaushe zaka mayar dani gida toh?"
"Yaushe su Daddy zasu dawo?"
"Next week."
"Suna dawowa zan zo in d'aukeki Rabba'atul Bait kinsan be
kamata haka kawai in d'aukeki ba tare da sanin su ba."
"Hakane kam toh in yi mishi magana ta waya?"
"Still hakan beyi fasali ba kibari su dawo d'in ai nan da next
week kaman gobe ne."
"I know Ya Rouhi is just that I miss you."
"I miss you even more darling" ya rik'o fuskanta "And I can't
wait to have you back." Murmushi ta sakar masa sannan ya
mik'a a hankali yayi kissing lips nata na lokaci kad'an. "I
should get going."
"Tun yanzu Ya Rouhi?"
"I need to get back to work."
"Zaka gun Amal de."
"That is after I close from work."
"Toh tashi in raka ka" har gun motansa ta kaisa inda ya
d'auko wani pack k'arami daga cikin motan ya mik'a mata
"This is for you."
"For me?" Ta tambaya had'e da amsa.
"Open it" ya umarceta. Ba gardama ta bud'e wani Silver
bracelet ne me bala'in kyau ta tarar aciki "Ya Rouhi this's so
beautiful."
"Do you like it?"
"Alot, thank you so much Ya Rouhi."
"Alright ki koma ciki se mun sake waya." Da haka sukayi
sallama ya koma office.
****
_9:36pm_
"Gobe zamuje muyi first baby scan namu ba? Ko bazaki iya
zuwa ba?" Afzal dake kwance akan cinyan Amal a parlour ya
tambayeta. Hannunta dake cikin gashin kansa tana wasa dashi
ta cire "Mey ze hana Ya Omri? Allah kaimu."
"Ameen, d'azu naje gidan su Nazeefah."
"Oh how's she?"
"She's fine."
"Yaushe zaka maidota d'akinta?"
"Zuwa next week su Daddy sunyi tafiya so sai sun dawo "
"Allah kaimu:"
"Ameen" ya amsa had'e da d'ago kansa "I wish Nazeefah will
be like you Rania."
"Meyasa kace haka?"
"Inda zata rage zafin kishinta ta sauk'o kaman ki ai kinga da
mun samu zaman lafiya a gidan nan."
"Why?"
"Because bakida kishi Rania."
"Haka kake gani?" Ta tambayesa da murmushi kad'an.
"Yes Rania ban ta6a ganin kishinki ba."
"Saboda ina 6oye wa ne gudun sanyaka cikin damuwa kaman
yadda kake ciki yanzu."
"Kina nufin kema kina kishi anytime na ambaci sunan
Nazeefah?"
"Tabbas Ya Omri kawai dan ina 6oyewa ne ita kuma
Nazeefah bata iya 6oye kishinta shiyasa kake ganin haka. If
not ina matuk'an kishinka Ya Omri nakega fiye da yadda
Nazeefah ma keyi, ma tukun tayaya ne ba zanyi kishinka ba
bayan ina sonka?"
"Wow! So for all these while ranki na 6aci kema idan na kira
sunanta?" Kai ta gyad'a masa "Amma bawai hakan na nufin na
tsaneta bane saboda yadda nake jin inada iko da kai itama
haka ne, we're both your wives Ya Omri and we love you."
"Rania you're just different in a unique way, Allah sa
Nazeefah tayi koyi da halinki."
"Ameen" ta amsa tare da sakar da hamma.
"Baby na tana saki bacci ko?"
"Se kuma aka cemaka baby girl ce?"
"Toh mey ne da? Ai mace ce kyakkyawa kamar ki."
"A'a na miji ne, handsome kaman ka."
"Mu zuba mu gani."
"Eh mu zuba d'in, nida abu ke jikina kawani ce min na mace
ce? Na miji ne let that sink."
"Wow ni kuma da nayi ajiyan kikeson kice bansan mey na
ajiye ba?"
"Eh baka sani ba."
"Shikenan time will tell ba se munyi musu ba" cike da dabara
ya mik'ar da ita kan kujerar had'e da aza kansa dai-dai saitin
cikin nata kaman mey son sauraron abu "I wish I can listen to
its heartbeat Rania."
"Not only will you listen to its heartbeat Ya Omri, one day
zaka rik'e sa hannu" ta sanar dashi tana shafa kan nasa a
hankali.
"Allah nuna mana wannan rana."
"Ameen" ta amsa.
"I can't wait have a replica of you calling me Daddy Rania, I
really can't." Dad'i sosai taji ta sakar mar da murmushi "Thank
you so much Babe."
"Godiyan mey kuma kake mun Ya Omri?"
"For everything Rania, for trying to give me a family Allah ya
cigaba da miki albarka."
"Ameen Ya Omri everything for you yauwa d'azu ma Ummi ta
kirani."
"Ayyah ya take?"
"Lafiya k'alau ashe ka fad'a mata I'm pregnant."
"A tunaninki zan iya yin shiru ne? Bank'i a buga a newspaper
cewa kina da ciki ba Rania, you made me so proud and
happy" hira suka ta6a sannan chan sukaje suka kwanta.
***
Lafiya k'alau suka cigaba da zama abinsu ba tashin hankali
bale fad'a se zallan so da tsan-tsan k'auna amma kuma sey
me? Kwana biyu zazza6in safe da na yamman nan ke son
sake dawowa Amal, gabad'aya yabi yasata a gaba, kullum
cikin amai take abin tausayi harta zube. Kaman kar Afzal ya
fita office yau yakeji dan yadda jikin nata ya sake yin tsanani
shi ya d'au sun riga sun wuce nan yanzu ashe rashin lafiyan
mey tafiya ya dawo ne. Misalin k'arfe goma Maamah tazo
dubanta. Ga laulayi ga targad'e a hannu da k'afan da be gama
warkewa ba har yanzu.
"Sannu cikin nan na baki wuya Bestie."
"Thank you, anata lectures bani ko?"
"Gashi next week muna da tests har uku na Mallam Auwal
biyu da na Malama Binta."
"Na shiga uku Maamah ko notes bani dashi gashi Malam
Auwal baya bada handouts sede wani ikon Allahn kam in ba
haka ba nasan inada carry overs wannan semester."
"Karki damu na miki photocopying nawa notes d'in na
Malama Binta kuma gashi na sai miki" tayi maganan had'e da
zaro su daga jakarta tana ajiyewa akan side drawer.
"Maamah bansan ya zanyi in ba keba, thank you so much
Allah yabar zumunci."
"Ameen ba komai kede kawai ki samu time kiyi karatu in
fever'n ya sauk'a. Ya Ya Afzal?"
"Ya fita office da k'yar wai ze zauna ya kula dani."
"Ayya meyasa kika hanasa?"
"Toh ba amfani Maamah zuwa sha d'aya haka zazza6in ze
sauk'a."
"Ayyah ai ni na d'au kin rabu da zazza6in ashe da saura."
"Wallahi ko nima na d'au ya k'are kawai shekaran jiya ya fara
mun kaman wasa fa se amai, komi naci hararwa nake."
"Sannu wata nawa ne yanzu?"
"D'aya fa da sati uku."
"Allah sauwak'e toh in shaa Allah kina fita daga first trimester
naki shikenan."
"Ameen Maamah."
"Na gaya wa Ya Abdul fa."
"Mey d'in?" Amal ta tambayeta had'e da zaro ido.
"Batun kina da ciki mana."
"Innalillahi!" Ta dafe goshinta "Baki da hankali ne Maamah?"
"Toh mey? Ba abun farin ciki bane?"
"God help me wallahi baki had'u ba taya zaki fara sanar da Ya
Abdul ina da ciki dan Allah? Mstw se yace mey?"
"Ya taya ki murna of course yace in gaisheki."
"Mstw wallahi ke banza ce wani sa'in ya yake toh? Se yaushe
ze dawo?"
"Waya san masa ne kullum na tambayesa yace da saura da
alama ya samu wata achan ne take d'ebe masa kewanmu."
"Allaha yasa toh wallahi da sena fi kowa yi masa murna."
"Wallahi ko, ameen deh." Hira Maamah ta tayata da se
wajajen uku ta tafi sanin Afzal ya kusa dawowa. Saidai har
shida Afzal yau shiru dan haka Amal ta d'au waya ta kirasa
don jin ko lafiya, saidai da ya shiga seya katse yin hakan sau
biyu se tayi tunanin ko yana meeting ne bada dad'ewa ba
kuwa sega sak'onsa.
_Sorry for not informing you, I'm in a meeting be home in a
moment I love you._
Murmushi ta sakar ta furta "Allah dawo daki lafiya." Sannan ta
mayar da wayan ta ajiye.
Wajajen takwas Afzal ya dawo gida lokacin jikin Amal ya
sake tashi se kakkarwa take k'ark'ashin bargo. Jakansa kawai
ya ajiye ya nufi kanta yana shafa fuskanta a hankali "How're
you feeling Rania?"
"Sannu da dawowa" kad'ai ta iya fad'a masa.
"Kinci abinci?" Ya sake tambayarta inda ta kad'a masa kai.
"Rania why? Bakiji abinda Dr yace miki ba jiya?"
"Ya Omri ko naci hararwa zanyi yana tayar mun da zuciya."
"I'm sorry kinji? Ko black tea ne ki dage ki sha bari in had'a
miki."
"Please no bana so."
"Toh se mey? Bazeyi ki kwana akan yunwa ba Rania please."
"Koko nake so, idan nasha bana hararwa shi Mami ke bani
lokacin da nike gida."
"Kokon dana sani kunun kamu?" Ya tambayeta da mamaki
inda ta gyad'a masa kai.
"Toh Rania ina zan samu kamu? Ko da akwai ma ban iya
had'awa ba kuma kinga dare yayi ba inda zan iya samu bale in
siya miki."
"Don't worry zan sha ruwa kawai in kwanta gobe seka saya
mun."
"Rania don't you get it? Bazan iya barinki ki kwana akan
yunwa ba."
"I'm sorry" tace da shi idanunta na kakkafewa. Wayansa ya
zaro daga aljihunsa "Wa zaka kira?" Tayi saurin tambayarsa.
"Ummi to ask ko zata iya had'a miki se in amso tunda gida
ba nisa daga nan."
"Ya Omri ba seka sa Ummi aiki ba" saidai be saurareta ba ya
kira Ummin bayan ta d'aga sun gaisa yake tambayarta ko
akwai kamu a gida.
"Eh lafiya?"
"Ummi ban fad'a miki ba ko? Jikin Amal ya tashi."
"Subhanallahi bade laulayin ba?"
"Shi Wallahi gashi ko mey taci hararwa take se koko kad'ai
kuma babu a nan gida shi'e nake tunanin ko zakisa su Esther
su had'a mata yi hak'uri dan Allah."
"Kai kuma mey na wani bada hak'uri? Ai Amal 'yata ce bari in
had'a mata yanzun ni da kaina driver ya kawo muku."
"Ko nima zan iya zuwa in kar6o kawai a had'a mata d'in."
"No ka zauna ka kula da ita tunda ga driver."
"Alright thank you Ummi."
"Kayi mata sannu bari in yi sauri in had'a mata" nan da nan
ta wuce kitchen ta had'a kokon da kanta ta cika masu a wani
k'aton flask yadda har gobe Amal zata iya sha sannan ta had'a
musu da d'anye incase zata kad'a in ta samu k'arfin jiki. Zama
yayi akanta yana ta yi mata sannu ko kayan jikinsa ya kasa
cirewa kunun na isowa ya d'iba a cup yasa sugar kad'an yadda
baze tayar mata da zuciya ba ya koma d'akin sannan ya
kishingid'ar da ita jikin gadon ya shiga bata, na sosai yayi
mamakin yadda tasha kokon sosai gashi ko hararwa batayi ba
sa6anin duk wani abinda takai baki.
Ai ko idan haka ne ya zama dole ya koyi dama kokon dan
yana yi mata. Bayan ta shanye ya buk'aceta da ta watsa ruwa
zata fi jin dad'in jikinta amma tak'i, ba yadda beyi ba tak'i wai
yau Amal tasa me son wanka wane kifi ce ake had'a ta da
Allah tayi wanka take k'i? Tun jiya rabonta da yin wanka haka
k'arshe se da ya d'iba ruwan d'umi a bowl da tsumma ya
mammatse mata jikin nata da shi sannan ya samu ya sata tayi
bacci. Nan shima yaci abinci ya k'arisa aikin daya rage masa
daga office ya fad'a bayi ya watsa ruwa yana cikin fesa turare
wayansa ya shiga ruri dubawanda zeyi yaga Nazeefah ke kira
be 6ata lokaci ba ya d'aga inda suka gaisa.
"Su Daddy sun dawo ne?"
"A'a se next week kuma wai."
"Lafiya dai ko?"
"Lafiya kawai chan d'in ya musu dad'i ne."
"Ayyah se mun k'ara hak'uri sun dawo kenan ko Rabba'atul
Bait?"
"Ya Rouhi ni kawai kazo ka d'aukeni."
"Bazeyi ba Rabba'atul Bait ki k'ara hak'uri kinji? Allah dawo
dasu lafiya."
"Ameen ya jikin Amal?"
"Gashi nan Alhamdulillah deh."
"Allah sawwak'e toh."
"Ameen thank you."
"I miss you Ya Rouhi."
"I miss you even more darling it's late you should sleep by
now."
"Goodnight toh."
"Sleep like a baby" nan ya katse ya gama abinda yakeyi yaje
ya samu Amal suka kwanta. Duk yadda yaso kwantar da ita a
jikinsa ya kasa sabida yadda jikin nata ya d'au wani irin zafi,
sekace ba yanzu ya gama matse mata shi da ruwa ba.
Haka Amal ta cigaba da fama da zazza6in, da rana kad'ai
take samu tayi karatu, ranan da zasuyi test d'in Afzal da kansa
ya kai ta makarantar yayi magana da securities akayi cutting
line aka shiga da ita ta gudanar da E-test suka komo gida.
Haka duka sauran tests d'inma jiranta yake seta gama su taho
gida tare. Kokon nan kuma shi kad'ai take sha ba tare da ta
harar ba, da safe Afzal kafin ya fita office yake dama mata
yasa a flask yadda da ta tashi sede tasha. Acikin sati Amal ta
rame sosai tayi duhu sede jikin da sauk'i sosai yanzu zazza6in
ya tafi se k'warnafi ko turare inba na wuta ko khumrah ba
bataso, muddin tana d'aki Afzal be isa ya fesa turare ba se taji
amai. Gashi sam bata son wanka yanzu, kwana biyu yau tak'i
yin wanka matse mata jiki ma da Afzal yakeyi yau ta hanasa yi
wai bata so. Alwala idan tayi na Azahar da shi takeyin La'asar
wani sa'in har Maghrib. Shi de Afzal yanzu yake sake tabbatar
da zancen cewa ciki nasa wasu matan k'aramin hauka.
"Rania yi hak'uri kiyi wankan kinji? Ni da kaina ma zan miki
yi hak'uri." Ko tankasa batayi ba taja bargo ta rufe kanta,
sauk'e bargon yayi "Yi hak'uri kinji? Karfa zama da dottin nan
yayi miki illa."
"Wai wallahi inda kaine acikin halin nan ko alwala ma baza ka
iya yi ba ka barni kurum in wari nake maka kaje d'ayan d'akin
ka kwanta." Dariya sosai ta basa, mutumin da banda k'amshin
turaren wuta ba abinda ke tashi daga jikinsa ne wai ze ce yana
wari shi kawai gudun abinda zama da dattin ze iya haifar mata
yake ba don wai tana wari ba.
"Yi hak'uri Rania beyi zafi haka ba."
"Toh ka barni in kwanta."
"Toh shikenan seda safe Allah k'ara sauk'i."
"Ameen" ta amsa tana rufe idonta sauk'an lips nasa taji a
fuskanta "I love you."
"Ina da dotti ka manta ne?"
"I'll still kiss you Rania yi bacci kinji? Get well soon"
Murmushi ta sakar masa sannan a hankali bacci ya d'auketa.
***
Da kwana hud'u Nazeefah ta kira Afzal akan su Daddy sun
dawo, dad'i kenan he can't wait ya dawo da ita gida ta bawa
Amal hak'uri su fara shiri, it's what he's ever asked for. Yana
zaune a office yana aiki around 2:30 wayansa yayi beeping
alaman shigowan sak'o. Message yagani daga Amal from
snapchat da hanzari ya bud'e wayan ya bud'e, hotonta yagani
wanda yake da tabbacin yau ta d'auka. Tana sanye da wani
dogon rigan roba armless ba ko d'igon kwaliya amma tayi
bala'in kyau da gashinta kame a tsakiyan kanta jelan na lilo.
Be 6ata lokaci ba yayi replying nata;
_Triple A💦;_ Iyyeehh😍😍 yau baby na yabar min
Rania tayi wanka kenan._
Bada dad'ewa ba sega reply nata.
_His Rania👑; 🙈 na cika ka da wari two days ko?_
_Triple A💦; dama shuwa suna wari ne? Ai ban sani ba don
ni kullum na matso kusa dake k'amshin turaren wuta da
khumra nake ji._
_His Rania👑; 😩 Ya Omri you're so sweeet_
_Triple A💦; 😁💕 Ya jikin naki toh? Da sauk'i?_
_His Rania👑; Alhamdulillah bakace nayi kyau ba😩😩_
_Triple A💦; Haba 'yar shuwata kema ai kinsan kinyi kyau
😍😍, send me more._
_His Rania👑: O'o ai baka ce mun nayi kyau ba seda na
rok'a😕_
_Triple A💦; Rania please😩😩😭 Ya Omri is sorry._
Seda ta gama waina sa sannan ta d'au sabi ta tura masa inda
yata yaba kyanta, na sosai yaso posting hoton amma tuna
Nazeefah kan iya gani seya fasa, baya son abinda ze sake
had'a kansu.
Sa6anin kullum yana isa gida Amal ta taresa yau harda
hugging nasa.
"Yau turare na baya wari?" Ya tambayeta dan kuwa sede be
matso kusa da ita ba seta toshe hancinta wai turarensa wari
yake mata. Kai ta gyad'a tana masa murmsuhi "Welcome back
Ya Omri."
"Jiki da sauk'i kenan."
"Alhamdulillah."
"You look so takeaway Rania."
"Thank you Ya Omri."
"Toh ya baby na? Kin bata abinci?"
"Mun sha kokon daka had'a mana kafin ka fita office har sau
biyu."
"Mashaa Allahu, ya rage ko a k'ara had'a wani?"
"Ka bari seka huta besides na fara aiki mafa da hannun nawa
kaga" ta d'ago hannun nata mey targad'e tana juyawa a
idonsa. "Alhamdulillah, My Rania is such a strong woman
Allah k'ara miki lafiya Sweetheart."
"Ameen Ya Omri mu k'arisa ciki" rage kayan jikinsa yayi ya
ragar da shorts zallah sannan ya haura gado ya sameta inda
take mik'i da handout rik'e a hannunta tana karantawa. Tamkar
d'an yaro ya haye jikinta ya kwanta had'e da saita kansa dai-
dai saitin k'irjinta da suka ciko tim. "Ya Omri zafi suke min
kad'an gyara" tayi saurin sanar dashi.
"Ze daina Rania" yace da ita yana sake cusa kan nasa cikin
k'irjin nata "Bacci nakeji na gaji daga aiki" murmushi ta sakar
kad'an sannan ta zagaye hannunta a bayansa tana mey cigaba
da karantunta, daga haka har itama baccin yayi awon gaba da
ita. Da goshin Maghrib Afzal ya farka a hankali ya raba jikinsa
daga nata ya fad'a bayi yayi alwala sannan ya tada ita itama.
Bayan da ya dawo daga sallan Isha ya had'a mata kokonta
shi kuma ya had'a quarker oats yasha daga nan suka koma
d'aki sukayi wankan su tare kaman yadda suka saba. Sede tun
da suka kwanta Afzal keta tak'ura mata, itako tak'i barinsa
chimma abinda yake da niyya se wani shusshuresa take shiko
kaman maye ya kasa hak'ura.
"Ya Omri mana kana fa da office gobe."
"Rania yanzu duk hak'urin nan da nayi baki gani ba? I need
you today hak'uri na ya k'are."
"Ni banida lafiya" ta amsa tana tattare bargon a jikinta.
"Na sani ai Allah k'ara miki lafiyan amma yi hak'uri ki barni
kinji?"
"Ni gaskiya sena samu sauk'i."
"Haba My Rania yi hak'uri kinji? Kad'an kawai shikenan."
"Yimin wayo de" ta amsa tana cire hannunsa daya samu ya
sak'ala cikin rigarta.
"Yi hak'uri kad'an nace I promise a hankali zan yi miki"
rok'arta ya cigaba dayi har seda ya samu ya shawo kanta haka
har suka gamsar da junansu. Tana rik'e a hannunsa bacci yayi
gaba da ita. Shi kansa baze iya describing yadda yake son
Amal yake kuma jinta a ransa ba, all he knows is that bayida
irinta.
Kasancewar washegari Saturday ba aikin office se suka yini
a gida abinsu, da safe sukayi breakfast tare, yau bayan kokon
Amal har ta iya taci soyayyan k'wai da fries. Bayan breakfast ta
rok'i Afzal da ya kaita salon ta wanke kanta. Shirayawa sukayi
tsaf suka fice sede suka tarar da shagon a rufe, dawowansu
Afzal yace ze wanke mata da kansa.
"Ya Omri yaushe ka iya wanke kai?" Ta tambayesa da
mamaki.
"Da ke kike wanke min nawa?"
"Toh ai naka ba gashin kirki bane akai."
"Kede kam kizo mana kiga."
"A'a nikam gaskiya na yafe haka kurum ka jagwalgwala mun
kai?"
"Rania I'm serious ki tsaya kiga in be wanku da kyau ba sekiyi
complaining" wardrobe nata ya nufa ya d'auko mata vest da
shorts "hungo sanya su."
"Amshi mana Rania kinga fa La'asr ya kusa" amsan tayi ta
tu6e ta sanyasu ya jata bathroom d'in. Daga bakin tub d'in ya
ajiye mata kujera ta zauna akai ta mik'a kanta ciki inda gashin
nata ya sauk'a har k'asan tun d'in. Tsoro yawan gashin nata ya
basa shi kansa yama rasa daga ina ze fara wankewan,
maganin mey kaud'i kenan.
"Toh Ya Omri ka fara mana" tayi maganan had'e da tattare
gashin nata ta d'ago kai tana kallonsa yayin da yake tsaye a
kanta.
"Toh ki mayar da kan naki mana ai nasani" ya fad'a
confidently sannan ya zauna daga gefenta a bakin tub d'in.
Hand shower ya bud'e ya jik'a gashin nata da shi jak'ab
sannan ya tsiyaya shampoo akai ya shiga massaging kan a
hankali dan dad'i har wani bacci-bacci Amal ta soma ji a
gurin. Wanke mata gashin yayi mey kyau shi kansa be
tsamman ze iya ba bayan ya wanke ya d'aure mata head towel
suka fito ta zauna gaban mirror sannan ta kunce towel d'in
tana tsiyaye ruwan.
"Ya Omri zaka iya taimaka mun da jakan hand driers d'ina?"
Ta tambayesa politely.
"A ina?"
"A k'asan wardrobe d'ina." Wajen ya nufa ya d'auko ya mik'a
mata sannan ya cigaba da tsaye akanta yana ganin yadda take
busar da gashin, na d'an lokaci shima ya gane yadda akeyi.
Hannunta ya rik'e yana mey dakatar da ita. Da mamaki ta
d'ago kai tana kallonsa "Kawo inyi miki."
"Ya Omri ai kayi mey wuyan zan iya yin wannan da kaina
karka damu."
"No Rania kawo in miki" murmushi ta sakar masa sannan ya
amsa ya shiga busar mata da gashin yana tajewa kaman
yadda yaga tana yi har seda gashin ya bushe garau sannan ya
jawo mai ya shiga shafa mata bayan nan yayi combing mey
kyau sannan ya kama mata shi a tsakar kai sakwa-sakwa.
"Amazing Ya Omri you're just incredible."
"Yayi kyau?"
"Alot, thank you so much."
"Don't mention so you owe me big yanzu."
"Meyasa?"
"Nima wataran se kinyi mun aski." Dariya tasa na sosai "Ashe
kuwa zaka ga disappointment har nice zanyi maka aski? Ashe
wani ya kusa ya fara yawo da hula."
"Lool" dariyan yake shima '"Yar k'auye ko rik'e clipper ma
bata iya ba hala."
"Toh akwai na miji ne a gidan mu da har zan koyan?"
"Ni d'in akwai mace ce a gidan mu har na koyi wanke kan?"
"Ai wanke kai da sauk'i yake akan yin aski barin ma irin naku
na 'yan gayu da se an gyara saje, gaban kan ma a cire wani
shape, spare me please ni bazan iya ba."
Dariya sosai ta basa amma ya cize, "Toh shikenan zan je Uni
sex Salon (salon da maza ke zuwa mata ke zuwa) na Racheal
tayi mun askin tunda ita ta iya."
"Gun mace zaka je?" Ta kewayo tana tambayansa da mamaki
yayinda kishi ya bayyana karara a fuskanta.
"Toh ba kince ke baki iya ba."
"Toh ka je d'in zunubin ai ku biyu za a rubuta muku banda ni"
ta sanar da shi had'e da juya mai baki sannan ta cigaba da
harkan gabanta. Murmushin gefe ya saki nan da nan ya canza
kayan jikinsa yasa wani bak'in half jamfan da ya mugun
amsansa ya feffeshe jikinsa da turare ya zuba accessories
nasa sannan ya d'au jakan askinsa ganin fa dagske yake ze
fita Amal ta k'urma ihu kafin ya kai ga bakin k'ofan ta sa key ta
k'wace.
"Matar Afzal ki bani guri in wuce."
"Wallahi bazaka fita ba."
"Harda rantsuwa?"
"Eh wallahi bazaka fita ba."
"Toh ni da gida na?"
"Eh naji amma bazaka fita ba."
"Askin ke zakiyi mun ne?"
"Ai gashin kama be yi wani tsawo ba fitina ne kawai."
"Nide matsa min."
"Seka rantse gun na miji zakaje tukuna."
"Why?"
"Taya wata mace zata ta6amun kai? Wallahi Nazeefah kad'ai
na yarda ta ta6a ka."
"Really?" Ya tambayeta yana dariya.
"Sosai ma kuwa, bayan nan ga 'yan mata cike kullum a
shogon so kake su yi mun snatching d'inka?"
"Toh laifin waye? Ba ke kika ce baki iya ba."
"Toh zan koya" dariya sosai ta basa amma ya moze. "Ni
matsa min."
"Zan koya Allah zan koya amma kar kaje shagon Racheal dan
Allah."
"Yaushe zaki koyan toh?"
"Ya Omri ai kasan ba a dare d'aya zan iya koya ba but zan sa
kai."
"Promise?"
"I promise" ta amsa tana gyad'a kai dad'i sosai yaji ya jata
jikinsa had'e da zagaye hannayensa a 'yar kunkuminta "Ashe
kina sona haka dama?"
"Eh mana" ta amsa tana turo k'aramin bakinta. Bata hankara
ba kawai taji yayi owning lips nata a hankali yake turata har
suka fad'a kan gado ya shiga yi maya wasanni. Da k'yar ta iya
k'watan kanta "Ya Omri yanzu na wanke kaina Allah bazan iya
sake jure jik'asa ba."
"Karki damu zanyi miki drying."
"A'a Ya Omri da Allah kayi hak'uri ka bari" ko sauraranta beyi
ba ya tu6e vest d'in daga jikinta. "Ya Omri stop wallahi zanyi
maka ihu."
"Kiyi d'in se muga mey k'watan ki" haka ya cigaba da sarrafa
ta har seda ya kashe mata jiki lissss ya biya buk'atansa.
a_An hour later..._
Amal ce kwance jikin Afzal yana shafa dogon sumarta
yayinda wayansa dake kan side drawer ya shiga ruri. "D'an
mik'i mun wayana Rania" ba gardama ta juya ta d'ago "Wake
kira?" Ya tambayeta.
"Nazeefah" ta amsa had'e da mik'a masa, niyyan basa waje
tayi har ta janyo vest nata zata sa seya rik'e hannunta ya sake
kwantar da ita a jikinsa tare da zagaye hannunsa a bayanta
sannan yayi receiving call d'in.
"Halo Ya Rouhi?"
"Na'am Rabba'atul Bait ya kike?"
"Lafiya ya gida ya Amal?"
"Alhamdulillah lafiyanta."
"Jikin nata da sauk'i?"
"Eh Alhamdulillah."
"Su Daddy sun dawo d'azu."
"Oh haba?"
"Eh."
"Sun dawo lafiya?"
"Lafiya k'alau yaushe zaka zo ka d'aukeni Ya Rouhi?"
"Tunda yau suka dawo mu bari mana gobe? Su huta yau ko?"
"Ya Rouhi anya kuwa you miss me?"
"You know right I do Rabba'atul Bait ki shirya kayakin ki yau
kinji? First thing gobe zanzo in d'aukeki."
"Toh shikenan sekazo I love you."
"I love you too" yace sannan ya katse.
"Rania?" Ya kirata kai ta d'ago a hankali tana kallonsa. "I'm
sorry kinji?"
"Why? What for?"
"For everything I said to Nazeefah that made you felt
jealous."
"Karka damu Ya Omri, tunda nima kana fad'a mun daddad'un
kalamu haka dan mey zanji haushi sabida ka fad'awa 'yar
uwata? Wannan kishi dole ne amma bawai hakan na nufin naji
haushi bane, so karka damu kaji?" Dad'i sosai kalamunta suka
sanya sa ya sake rungumeta tsam ajikinsa "I love you soo
veryy much Rania."
"So gobe zaka je ka d'auko ta?"
"Yes in shaa Allah har gida tace zata zo ta baki hak'uri."
"Allah kaimu toh."
"Ameen."
"I'll miss you for the 2-2days da zaka na yi mata."
"I'll miss you terribly too Darling" ya sanar da ita had'e da
placing mata light kiss a goshi "Tashi muyi wanka toh muyi
sallah kinga ana neman hud'u se muje muci abinci ba?"
"Sure Ya Omri."
"Karde har kin mance?"
"Dame fah?"
"Seriously Rania?"
"Yi hak'uri ka tuna mun na d'an sha'afa ne."
"Wato kin ma manta yau zamu fita first baby shopping namu
ko?"
"Ya Omri beyi sauri ba?"
"Haka kullum kike cewa ai a hankali a hankali zamuna
ragewa please don't say no, I'm so excited."
"Alright toh."
"Kin yarda zamu je?"
"Anything for my Omri." Nan da nan sukayi wanka sukayi
sallah sannan suka shirya suka wuce shopping. Siyayya sukayi
sosai, Afzal na kwasan kayan baby girl Amal na yin na baby
boy se dariya masu shagon suke musu amma ko a jikinsu. Se
after 6 suka dawo gida da goshin maghriba.
****
GIDAN ALHJ ABDALLAH.
RANA DAYA Chapter 41
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
Tareda Naja'atu Lawal Rijau Niger State
@Whatapp 08083232323 or 09060202323
_Assalamu Alaikum readers, I would like to show my
deepest appreciation to each and every one of you that took a
minute or so out of their precious times and asked, prayed or
checked up on me. I really am grateful and feeling much
better Allah yabar zumunci ameen. 😘 Before proceeding on,
I would like to dedicate and give this chapter to SADNAS
marubuciyar •miemiebee a wanki garori• and her amiable
group members, thank you so much for the love and support
wannan chapter'n naku ne! Xoxo 😘❤️_
Cike da jin dad'i da rawan jiki ta d'auko akwatin ta ajiye kan
gado sannan ta shiga fiddo da kayakinta daga wardrobe tana
jerasu aciki, taci rabin aikin Mummy tayi knocking bisa k'ofan
d'akin. "Come in" ta amsa sannan ta bud'e ta shiga.
"Ya da shirya akwati haka ina zuwa?" Ta soma da tambaya.
"Mummy Ya Afzal yace gobe zezo ya mayar dani d'akina" ta
sanar da ita cike da jin dad'i.
"Kai haba!" Mummy ta tambayeta unbelievably tana mey
tayata murna.
"Wallahi ai tun last two weeks yaso mayar dani amman
bakwa nan yace in hak'ura sekun dawo."
"Allah sarki Afzal, toh Alhamdulillah yayi kyau sosai Allah
kaimu."
"Ameen Mummy" ta amsa delightedly.
"Kiga duk kalan rashin hankalin da kika tafka hakan be
hanasa yafe miki ba har yake shirin mayar dake d'akinki. Sekiyi
ma kanki fad'a Nazeefah ki kiyaye 6ata masa rai, kuyi zaman
lafiya da 'yar uwarki ba abinda hakan ze ragar miki."
"Hakane Mummy in shaa Allahu komai ya wuce har gida
zanje in samu Amal in bata hak'uri."
"Masha Allah, Allah baku zaman lafiya duka."
"Ameen Mummy."
"Toh kinata hanzari haka ko gobe bazaki had'a kayakin
bane?"
"Toh Mummy in kuma da safe zezo fah? Ai gara nayi na
gama yanzu tunda ba abinda nakeyi."
"Toh ki sauk'o muci abinci dinner is ready."
"A'a nikam zan sauk'o daga baya sena gama had'a kayakin
nawa tukuna."
"Toh barin sanar da Daddy'nku."
"Yauwa do please thank you" nan Mummy ta fice ta ja mata
k'ofar. Bayan sun gama cin abincin tayi gyaran murya, "Alhj?"
Ta kira Daddy.
"Na'am Hjy Surayya."
"Errm batun Nazeefah ne daman, Afzal yace gobe zezo ya
mayar da ita d'akinta." Dummm! Zuciyan Daddy ya buga ko
motsi ya kasa yi.
"Alhj lafiya?" Mummy data karanci yanayin da ya fad'a nan
take tayi saurin tambaya.
"Lafiya ba komai."
"Nace Afzal ze zo bikon Nazeefah gobe."
"Bazata koma masa ba" ya fad'a zalla. Da mamaki Mummy ta
tsaya kallonsa "Dalili Alhj?"
"Nace bazata koma ba zuwa zeyi ya bata takardanta
zamansu ya k'are."
Mummy ta kasa amincewa da abinda kunnuwanta ke jiye
mata da mamaki tace "Alhj ka ko san me kake fad'i? Har mun
samu yaron nan ze mayar da ita d'akinta kake cewa bazata
koma ba? Ko kai zaman 'yarnan a gidan nan haka na maka
dad'i ne? Ko so kake ka mayar da 'yar taka bazawara?"
"Nide na fad'a miki kije ki sameta kice mata ba inda zata"
yana kaiwa nan ya mik'e ya nufi d'akinsa. Kai Mummy ta
kewayo tana kallon Khaleefah da shima ya tsaya kallonta da
d'umbun mamaki d'auke a fuskokinsu. Daga bisani ta mik'e ta
je ta samu Nazeefah a d'aki, lokacin har ta gama had'a
kayakin nata tana cikin tattare jakukkunanta da takalma.
"Nazeefah wani abun ya had'aki da Daddy'nku ne?" Mummy
ta tambayeta bayan ta zauna bakin gado.
"A'a wani abu ne?"
"Gashi ina mishi maganan gobe Afzal zezo ya d'aukeki yana
cewa ba inda zaki."
"Ba inda zani kuma?" Nazeefah tayi exclaiming cike da k'in
yarda.
"Haka yace wai zamanki da Afzal ya k'are."
"Dalili? Ya Afzal yayi mishi wani abu ne?" Ta tambaya a rud'e.
"Anya kuwa? D'au waya ki kirasa muji" ba makawa ta janyo
wayanta ta shiga kiran Afzal sede yayi ta ruri har ya tsinke be
d'aga ba kasancewar ya riga ya kwanta. Three missed calls ta
masa be d'aga ba ta hak'ura.
"Mummy he ain't picking up."
"Kode yayi bacci ne?"
"Might be amma meyasa Daddy ze hana Ya Afzal mayar dani
d'akina?"
"Shine nima ban sani ba Nazeefah."
"Mummy dan Allah kiyi mishi magana Mummy bana son
abinda ze rabani da Ya Afzal please dan Allah Daddy ya rufa
mun asiri."
"Karki damu zanyi masa magana ki kwantar da hankalinki
nake ga sun d'an samu sa6ani ne."
"Please do Mummy."
"I'll je kici abinci kinga dare nayi."
"Ni bana jin yunwa."
"Toh kiyi sallah ki kwanta seda safe" da haka Mummy taja
mata k'ofar ta fice taje ta samu Daddy dake mik'e akan gado
ya zura wa ceiling ido. Sallama tayi amma ko amsawa beyi ba
don yadda hankalinsa sam baya jikinsa.
"Alhj?" Ta kirasa bayan ta zauna a gefensa nan ma shiru
k'arshe seda ta d'an ta6asa sannan ya dawo hankalinsa. "Alhj
dan Allah ka tashi muyi magana."
"Wace magana ce zamuyi? Na gaya miki 'yar nan bazata
koma gidan Afzal ba ko baki ji bane?"
"Naji Alhj amma-"
"Amma mey?" ya katseta a fusace "Ni da 'yata kike son nuna
mun iko akanta? Bazata koma ba bazata koma ba."
"Bawai haka bane Alhj a tunani na koda sa6ani kuka samu da
shi Afzal d'in be kamata ka hana sa miyar da yarinyar nan
d'akinta ba tunda tana sonsa yana sonta-"
"Surayya dan Allah nace kiyi min shiru" ya katseta cike da
rashin hak'uri "Idan kuma shirun ne bazaki iya ba ina iya bar
miki d'akin."
"Allah huci zuciyanka gobe zamuyi magana" Daddy be sake
ce mata komai ba. Abinda ya kama daga kan shi harma
Mummy da ita Nazeefar bawanda ya iya samun baccin kirki
ranan barin ma Daddy da yake ganin asirin sa ya kusa tonuwa
besan da wani idon ze sake kallon iyalansa ba.
****
Kiran Afzal ne ya tada Nazeefah daga bacci washegari ba
shiri ta d'aga wayan.
"Good morning Baby" ya fad'a a karo na farko.
"Ya Rouhi" ta kirasa cike da tashin hankali.
"Yes is everything okay?" Yayi saurin tambaya.
"Ya Rouhi wani abu ya had'aka da Daddy ne?"
"Nop why?"
"Ya Rouhi cewa yayi wai bazaka miyar dani d'akina ba."
"What?!" Yayi exclaiming had'e da dropping cup na tea da
yake sha.
"Ya Rouhi please do something I don't want to be separated
from you."
"Karki damu I'm on way now" daga haka ya katse wayan ya
fad'a d'aki ya d'au key'n motansa. "Rania?" yayi knocking bakin
k'ofan bayin.
"Yes Ya Omri?" Ta amsa daga ciki.
"Zan fita ina zuwa."
"Toh seka dawo" be 6ata lokaci ba ya fice.
****
Mik'ewa tayi ta fad'a bayi tayi brushing ta canza kayan jikinta
sannan ta sauk'o k'asa dan karyawa. Hayaniyan data jiyo ta
gun d'akin Daddy yasa ta k'arisa gurin inda ta tarar da Mummy
da Daddy se faman fad'a sukeyi.
"Haka kawai bazan zuba ido ka mayar min da 'ya bazawara
ba wallahi Afzal zezo kuma ze tafi da yarinyar nan" Mummy ta
fad'a cike da tsiwa kaman ba ita ba.
"Idan ke kike iko da Nazeefar se mu gani" Daddy ya mayar
mata.
"Daddy dan Allah kayi hak'uri" Nazeefah da idanunta suka
ciko tim da hawaye ta tsoma baki "Daddy dan Allah karka
rabani da Ya Afzal Daddy idan wani abun ya maka I'm sorry on
his behalf please don't separate us two."
"Kiyi hak'uri Nazeefah amma rabuwa da Afzal ya zama dole"
kuka ta shiga yi na hak'ik'a "Daddy dan Allah kar ka min haka
dan Allah kayi hak'uri I'm so sorry" har cikin zuciyansa Daddy
yaji ba dad'i ashe akan 'yarsa Allah ze rama wa Jameelah
abinda yayi mata, why not akanshi? Meyasa se akan 'yarsa?
Ashe anan Allah na nuna masa kamar yadda alheri yake
d'anko shima sharri haka ne muddin baka shuk'a me kyau ba
toh 'ya'yanka ma bazasu ga mey kyau ba.
"Ki barsa" Mummy tace da ita tana mey janta jiki "Afzal d'in
ai zezo se ya hanaki binsa muga" tana kaiwa nan taja
Nazeefah d'akinta ta shiga lalashinta amma inaa Nazeefah se
kuka. Ba'a dad'e ba sega Afzal ya taho yana isa ya kira
Nazeefah inda ta tura Khaleefah ya shigo da shi zuwa parlourn
Daddy sannan ya shiga daga ciki yayi ma Mummy magana.
Mayafi ta yafa ta fito da Nazeefah biye a bayanta. Bayan sun
gaisa take tambayarsa ko abu ya had'asa da Daddy.
"Wallahi ba komai Mummy kema kinsan bazan so abinda ze
shiga tsakani na da Daddy ba kodan Nazeefah."
"Hakane Afzal yanzu abinda nakeso da kai ka d'au Nazeefah
ku tafi karka sauraresa."
"Nace baze tafi da ita ba" suka jiyo muryan Daddy kaman
daga sama nan take duk suka kewayo suna kallonsa.
Har k'asa Afzal ya sauk'a ya gaishesa amma ko amsawa
beyi ba "Ka rubuta mata takardanta yanzun nan bazata bika ko
ina ba."
"Daddy ban fahimce ka ba."
"Sakin ta nake so kayi yanzun anan" ya jaddada masa.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya sa salati "Daddy idan wani
abun nayi maka kayi hak'uri amma karka rabani da Nazeefah
dan Allah."
"Baka ji me nace bane?"
"Daddy naji dan Allah kayi hak'uri."
"Ai ni na rok'eka da ka aureta daman tun farko yanzu kuma
ina rok'onka da ka sawwak'e mata zaman ku ya k'are."
"But Daddy I love Nazeefah, ina sonta bana kuma son in rabu
da ita."
"Zaman ku ya k'are nace Afzal ka sakar min 'ya."
"Wai Alhj meke damunka ne? Haka kawai kake shirin shiga
tsakanin yaran nan a ina aka ta6a yin hakan?"
"Hjy Surayya banyi magana dake ba saboda haka ba ruwanki."
"Niko nake da ruwa acikin zancen nan taya zaka sa na dole
miji ya rabu da matarsa?"
"Afzal ka rubutawa yarinyar nan takardanta nace" yace kaman
wanda beji abinda Mummy ta fad'a ba.
"Daddy dan Allah kayi hak'uri" Nazeefah ta rok'esa cikin tsan-
tsan kuka saidai ko kallonta beyi ba. "Idan kuma ranka ya 6aci
ne game da dawo dani gida da Ya Afzal yayi kayi hak'uri
amma bashida laifi, nice nayi mar laifi a matsayinsa na mey
mata biyu kuma dole ya kwatanta yin adalci tsakani na da 'yar
uwata. Tunda ni nasa Amal tayi yaji na raba ta da gidanta
nima dole a rabani da nawa. Amma ka duba yanzu da Amal ta
dawo ba gashi yana son ya miyar dani d'akina ba? Kuma seka
hana hakan Daddy? Please don't." Na sosai maganganun
Nazeefah suka shige jikin Daddy suna masu samun mazauni a
birnin zuciyansa. Ba shi kad'ai ba kowa seda kalamun nata
suka ta6a sa a gurin amma haka na dole Daddy yayi banza da
ita. "Afzal ba magana nake ma ba?"
"Daddy I'm terribly sorry idan mayar da Nazeefah gida da nayi
na kwanakin nan ne ya 6ata maka rai kamar yadda Nazeefah
ta fad'a. I had no option but please don't be mad, I'm sorry
and I do love Nazeefah."
"Ka rubuta mata takardanta nace-"
"Baze rubuta ba Alhj nace baze rubuta ba" Mummy da ranta
in yayi dubu be 6aci ba ta katse sa.
"Afzal baka jina ne?"
"Daddy ina ji" ya amsa na dole.
"Ka rubuta mata takardanta nace." Kuka Nazeefah ke sosai
tace, "Please don't do this Daddy, please."
"Me kake jira ne har yanzu Afzal?" Daddy yayi kaman be jita
ba "Biro ne ko takarda baka da ita? Khaleefah wuce d'akinka
ka d'auko mar."
"Daddy kayi hak'uri amma ka sani bazan iya rubutawa
Nazeefah takardan saki haka kawai ba please understand me."
"Daddy kayi hak'uri mana" Khaleefah da ya zuba musu ido
tun d'azun ya fad'a.
"Daddy please don't do this" Nazeefah ta kar6esa, "Please
don't Daddy, Afzal is sorry kayi hak'uri ka barni in tafi dashi."
"Nazeefah kiyi hak'uri amma gaba kad'an zaki gane am doing
this for your own good."
"Which good Daddy? Kana shirin raba ni da mijina wanda
yake sona nake kuma sonsa kake cewa you're doing this for
me? How? Mummy how is this going to be of help to me?" Ta
jiyo cikin tsananin kuka tana kallon Mummy data janyota jiki.
"Zaman ki da Afzal ya haramta Nazeefah bazeyi ki cigaba da
zama da shi ba dan haka ya zamanto dole ya sakeki ya
sauwak'e miki."
"Kaman ya zamansu ya haramta Alhj? Wani abun sukayi ne
da zakace zamansu ya haramta?" Mummy tayi saurin
tambayarsa "Dan na d'an wata ya korota gida kuma akan
gaskiyansa se kace zamansu ya haramta? A ina ne idan mace
tayi laifi akace miji baze hukunta ta ba? Tell me!" Tayi
demanding.
"Nide na fad'i nawa zamansu ya haramta don haka ya k'are,
Khaleefah yi maza ka d'auko mar paper da biro kar ka bari in
nanata kaina."
"Khaleefah zauna ba inda zaka" Mummy ta dakatar da
Khaleefah daya zabura.
"Daddy I'm sorry amma bazan iya rubutawa Nazeefah
takardanta ba" Afzal ya fad'a had'e da mik'ewa "I'll get going
ina zuwa amma."
"Afzal! Afzal!" Kiransa Daddy yake amma ko kewayowa beyi
ba. Gidansu ya wuce direct unfortunately Abba bayi nan yayi
tafiya Ummi kad'ai ya tarar. Irga mata halin da ake ciki yayi
inda ta sha mamaki na sosai.
"Toh yanzu ya zamuyi? Amma meya samu Alhj Abdallah
haka?"
"Wallahi Ummi I don't know and he seem so serious about
it."
"Subhanallahi meya buga masa kai toh? Kode koran
Nazeefah gida da kayi d'inne ya 6ata mar rai haka?"
"Amma ai ba koran walak'anci nayi mata ba Ummi besides
Nazeefah was at fault dole in hukunta ta kodan inyi ma Amal
adalci."
"Tabbas Prince kuma nima bawai nace kayi laifi bane am just
surprised gashi Abbanka baya nan."
"Se yaushe ze dawo?"
"Yau yace."
"Toh kafin nan kije ki samu Daddy kiyi mishi magana please."
"Ni kuma Prince?" Ta dafe k'irji.
"Eh Ummi I don't want to lose Nazeefah please go" ya fad'a
cikin tsananin tashin hankali.
"Prince ta ina zanje in fara yi wa Alhj Abdallah magana a
matsayinsa na sirki na? Ai beyi fasali ba kade bari Abban naka
ya dawo zuwa anjima."
"Ummi please" ya rok'eta abin tausayi.
"I'm sorry Prince but I can't" kafad'ansa ta dafe "Abbanka ze
dawo anjima I'll be the one to explain everything to him kayi
hak'uri kaji? I'm sorry" kai zalla ya iya gyad'a mata.
"Ka karya ko tukuna?"
"Na karya" ya amsa.
"Toh ka kwantar da hankalinka, muyi fatan Allah dawo da
Abbanka lafiya."
***
Wajajen sha biyu Amal da ta ji shiru daga Afzal ta d'au waya
ta kirasa lokacin har bacci ya fara d'aukansa zaune a kan
kujera a parlour, ba makawa ya d'aga inda ta soma da "Halo
Ya Omri?"
"Na'am Rania."
"Ina ka shige? Shiru tun d'azu."
"Rania akwai matsala" ya sanar da ita.
"Subhanallahi ina dey kana lafiya ba abinda ya same ka ko?"
"Not at all."
"Alhamdulillah" ta saki ajiyar zuciya "toh meya faru?"
"Rania sena dawo gida kawai I'm on my way."
"Toh Allah dawo da kai lafiya I love you."
"I love you too" ya amsa sannan ya katse. Duban agogo yayi
yaga pass 12 "Ummi!" Ya shiga kiranta chan sega ta tashigo.
"Lafiya? Naji kana kirana."
"Ummi se yaushe Abba ze shigo?"
"Zuwa anjima yace Prince bansan yaushe flight nasun ze
tashi ba."
"Ummi I don't want to lose Nazeefah please do somethibg."
"In shaa Allahu ba abinda ze faru kai de ka kwantar da
hankalinka kaji?"
"Zan wuce gida idan Abba ya shigo seki kirani."
"Toh shikenan Allah ya kare." Be kai ga tada engine na motar
sa ba sega Nazeefah na kiransa. Nan take ya amsa "Halo
Nazeefah?"
"Ya Afzal..." ta kirasa kawai seta rushe da kuka.
"Ohh dear!" Ya ambata had'e da murza temple nasa
"Rabba'atul Bait please kibar kukan haka ba shida amfani."
"Ya Rouhi tayaya ne bazan yi kuka ba bayan Daddy yana
shirin rabani da kai?"
"I'm not going to let that happen kinji? Abba is on his way
idan ya dawo zezo ya samu Daddy yayi mishi magana in shaa
Allahu ze sauk'o ya amince in dawo dake d'akinki okay?"
"But Ya Rouhi he seem so serious wallahi se rok'onshi muke
tayi amma ko sauraron mu beyi I'm scared."
"Don't be sweetheart in shaa Allahu mutuwa ce kad'ai zata
raba mu dan bazan ta6a aikata abinda Daddy ke cewa inyi ba
because I love you okay?"
"I love you too Ya Rouhi promise me komin yaya bazaka
rubuta mun takarda na ba."
"I promise darling" ya sanar da ita.
"Thank you Ya Rouhi."
"Yanzu share hawayenki kibar kukan haka toh sena shigo
anjima."
"Okay take care" daga nan ya katse ya sa key ya wuce gida
inda Amal ta taresa. Bayan ta kawo masa ruwa yasha take
tambayar sa meke faruwa nan ya labarta mata komai inda
itama tayi mamaki na sosai sannan ta shiga kwantar masa da
hankali.
***
Se wajajen hud'u jirginsu Abba ya sauk'a driver yaje ya
d'auko sa daga airport. Ruwa ya watsa sannan suka ci abinci
da Ummi inda take basa labarin halin da ake ciki. Kansa ne ya
mugun d'aure akan mey Alhj Abdallah zece a sakan masa 'ya?
Shin meya faru? Nan da nan ya kira Afzal a waya yake
tambayarsa kode wani abun ne ya had'asa da Daddy amma
Afzal ya nuna sam ba komai banda mayar da Nazeefah gida
da yayi akan laifin da ta aikata. Take a lokacin Abba yaje ya
samu Daddy saidai Daddy na kan bakansa har yanzu shi a
sakar mishi da 'ya ba yadda Abba beyi da shi ba, ba kalan
hak'urin da be basa ba amma ya dage ina shi a sakar mishi da
'ya kawai irrespective of abotakan dake tsakaninsu. Na
matuk'a ran Abba ya 6aci be ta6a tsammanin haka daga gun
amininsa ba, ai ko da ma ace laifi Afzal yayi masa be kamata
yayi haka ba.
"Na d'au zamuyi magana man-to-man mu fahimci juna da kai
Alhj Abdallah a matsayinka na amini na ashe ba haka bane."
"Kayi hak'uri Alhaji Amin ko ni ban so abubuwa su kasance
haka ba amma ya zama dole in raba auren yaran nan ne
badan son ra'ayi na ba nima."
"Sai don mey toh? Idan wani abun ne ka sanar dani mana kar
fa kamanta aminin ka ne ni."
"Ina sane da hakan Alhj Amin amma kayi hak'uri bazan iya
sanar da kai dalili na ba ni kawai asa Afzal ya sawak'e wa
'yata."
"Kaine mahaifin Nazeefah kuma se yadda kace za'ayi amma
a tunani na zaka sanar dani koma meye dalilin, in shaa Allahu
zanyi maka kyakkyawar fahimta."
"Kayi hak'uri Alhj Amin komin yaya naso sanar dakai bazan
iya ba shiyasa nake sake baka hak'uri kayi hak'uri."
"Shikenan tunda abinda kake so kenan Allah yasa hakan shi
yafi alkhairi."
"Ameen nagode da fahimta ta da kayi ina fatan hakan baze
6ata tsakanin mu ba?"
"In shaa Allahu ka gaishe da Madam." Har bakin gate Daddy
ya rakasa sannan ya koma ciki Abba ya k'arisa gida. Tun daga
bakin k'ofa Ummi ta soma tambayarsa yaya.
"Yace shi a sauwak'e wa 'yarsa" ya sanar da ita.
"Innalillahi! Toh Alhj ya zamuyi? Prince fa? Wallahi yana son
yarinyar nan ina gudun kar hakan ya jefa sa cikin wani halin."
"Toh mahaifinta yace ga abinda yake so mun isa muce a'a
ne?"
"Eh mana ai wannan bayi bane wallahi taya haka kawai ba
k'wak'k'waran dalili se don an kora 'yarsa gida akan laifin data
aikata ze shiga tsakanin masoya biyu yace se an rabasu,
rabawan ma wanda ba komawa?"
"Toh ya zamuyi Hjy Mariam?"
"Muko muke da abinyi wallahi mu kai k'ararsa kotu na
tabbata bazasu goye masa baya ba."
"Mey yayi zafi har da zuwa kotu Hjy Mariam? Shi prince d'in
bashida mata a gida ne? Kokuwa Nazeefar ce k'arshen
halittu?"
"Ko d'aya Alhj amma ai zaka duba halin da d'an nan ze iya
fad'awa cikine. Yaran nan yana son yarinyar nan haka kawai
kuma a rabasu wallahi babban hatsari ne ga rayuwansa harma
da ita d'in."
"Ina sane da dukkan hakan Hky Mariam kuma idan da akwai
wani hanyar da zanbi da na bi dan in dawo masa da matarsa
amma gar-da-gar Alhj Abdallah yace shi a sakan masa 'ya
baya son jin komai mey kikeso inyi? Zancen kai k'ara kotu
kuma ma be tashi ba idan dey mata ne Allah ya haliccesu
dayawa ko a gobe yakeso yakan k'ara wani auren."
"Hakane kam amma Alhj Abdallah bai kyauta ba ai ko dan
abotakan dake tsakaninku ma be kamata yayi haka ba."
"Zuwa gobe zan kira Afzal yazo anan ya rubuta mata
takardanta a kai musu mu rabu dasu lafiya."
"Oh! Duniya, toh shikenan Allah ya kaimu bari in k'arisa site
d'ina."
"Alright."
*****
"Ya Omri ka kwantar da hankalinka haka, everything is going
to be alright."
A raunane ya d'ago lumsassun idanunsa ya kafa mata.
"Rania I'm sorry" ya furta a hankali sam ba a son ransa bane
ya nuna tsan-tsan damuwa akan Nazeefah a gaban Amal haka
amma ba yanda ya iya ne abun ne yafi k'arfinsa.
"Why?" Ta tambayesa cike da rashin fahimta.
"For showing concern over Nazeefah like this nasan be
kamata in nuna tsan-tsan damuwa akanta a gabanki haka ba
but I just can't help it, kaman yadda nake sonki haka nake son
ta itama. Kuma kaman yadda bazan so abu ya shiga tsakanin
mu dake ba ba ita ma haka ne Rania. I can't afford to lose her,
I just can't" ya fad'a cikin raunannen murya.
Baza tayi k'arya ba da fari taji haushi da kuma kishin yadda
ya shiga matuk'an damuwa akan Nazeefah amma sanin yadda
zafin rabuwa da masoyi yake musamman ma na dole irin
wannan se taga ba laifinsa bane, ta tabbata idan da itane a
position na Nazeefah zeyi haka ko fiye da hakan ma, toh
kishin mey zatayi? Matsowa kusa dashi tayi sannan a hankali
ta kwantar da kansa a k'irjinta tana mey shafe gashin kan nasa
a hankali "Don't be sorry Ya Omri, na fahimci yanayin da kake
ciki and I'm here for you, feel free to cry in my arms I love you
so much." Hannayensa ya zagaye a 'yar kunkuminta yayinda
hawaye ya shiga tsiyaya daga idanunsa sun dad'e a haka har
seda wahalallen bacci ya d'aukesa. Cike da dabara ta kwantar
dashi kan gadon ta gyara mai kwanciya sannan tayi zamanta a
gefe tana mamakin dalilin da zaisa Daddy ya aikata abinda
yayi.
Chan wajajen Isha sega kiran Ummi da hanzari Amal ta mik'a
wa Afzal kiran inda ya d'aga. "Ummi?"
"Na'am Prince."
"Ummi ina kika jefa wayarki ina ta kira switched off?"
"Wallahi bak'i nayi d'azun suna ta game daga nan suka kashe
min wayar suka yasar a lungu se yanzu na samu."
"Ohh na d'au wani abu nema ya sameki ya Abba? Ya dawo?"
"Eh ya dawo" ta amsa a sanyaye.
"Yaje ya ma Daddy magana?"
"Eh ya mishi."
"And???"
"Prince-" se kuma tayi shiru.
"Please speak up Ummi" ya fad'a cikin tsananin fargaba.
"An yi mishi magana amma he's not willing to back out
Prince yace lalle-lalle se ka sakar masa da 'ya."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya saki salati "No Ummi."
"I'm truly sorry Prince amma abinda yace kenan gobe da
La'asr Abbanka na buk'atan presence naka. Seda safe ka
gaishe da Amal" tana kaiwa nan ta katse wayar. Ko sauk'e
wayar daga kunnensa Afzal ya kasa Amal ce ta tako daga
gaban dressing mirror ta amshe wayan had'e da mik'ar da shi
ta rungumesa tsam a jikinta tana basa hak'uri. Kaman d'an
yaro ya zage yana kuka a jikinta ba makawa. A dalilin mey
Daddy zeyi masa haka? No he can't stand by it, baze iya jure
rabuwa da Rabba'atul Bait tasa haka kawai ba sabida selfish
interest na mahaifinta. Tunda yana sonta tana sonsa toh in
shaa Allah ba abinda ya isa ya rabasu he don't care koda
maganan zata kai kotu. A shirye yake da yayi filing case akan
Daddy, ya tabbata kotu zata dawo masa da matarsa.
****
Washegari da safe suka shirya tsaf da Amal yayi dropping
nata a school. Wajajen sha d'aya Nazeefah ta kirasa bayan
sun gaisa ta buk'acesa da ya taho school a waje kaza yazo ya
sameta. Be 6ata lokaci ba ya fice be tsaya ko ina ba se inda
tace su had'un. Yana sauk'a daga motan ta ruga a guje taje
tayi hugging nasa tana kuka har na fitan hankali. Rungumarta
yayi tsam a jikinsa shima yayinda yake danne hawayen dake
k'ok'arin ku6uce mar. Sun dad'e a haka sannan a hankali ya
shiga raba jikinsa daga nata sede ina se sake matsesa
Nazeefah ke da k'yar ya samu ya d'agota ya shiga share mata
hawaye yana bata hak'uri yayinda take ta kad'a mar kai.
"It's okay calm down I'm here."
"It's not okay Ya Rouhi it's not" ta sanar dashi cikin tsananin
kuka.
"Look at me" ya buk'aceta "Look at me okay?" Cikin sanyi ta
d'ago jajayen idanunta ta kafa mai. "Nothing in this world will
ever seperate me from you except for death okay?"
"How Ya Rouhi? Tayaya? Abba ma ya mishi magana jiya yak'i
ya sauraresa se kai ne ze saurareka?"
"I know it's not possible just trust me."
"I really want to but I'm scared, tsoro nakeji Ya Rouhi."
"Kar fa ki manta nike da ikon rubuta takardan nan ko ba haka
ba?" Kai ta gyad'a yayinda ya cigaba "Idan ban rubuta ba kuma
Daddy be isa ya miki wani aure akan igiyan aure na ba ko ba
haka ba?" Nan ma kan ta kuma gyad'awa "Excellent ni kuma
ko da kasheni za'ayi sama da k'asa su had'u bazan rubuta
miki takardan nan ba Nazeefah I'll never do it."
"I know Ya Rouhi amma kuma ko da hakan Daddy baze ta6a
barina in koma a gareka ba ya gwammace in cigaba da zama
a gida da igiyan auranka akaina daya amince ka miyar dani
d'aki na."
"I'm coming to beg him again later today idan har be amince
ba zan kai k'ara kotu Rabba'atul Bait akan ki a shirye nake da
inyi breaking rules and even worse saboda bana son rabuwa
dake, da a rabani dake gara na rasa komi nawa dana malakka
I love you Nazeefah, I love you so very much." Kuka ne yaci
k'arfinta ba shiri ta fad'a jikinsa tana kuka shima ba don ya
danne hawayen ba da tuni ya jonata sunyi kukan tare. A
hankali ya rabata daga jikinsa ya rik'o 'yar fuskanta cikin
hannunsa yana mey share mata hawayen nata "Your home will
forever be here with me Darling" ya sanar da ita be hankara ba
yaji tayi owning lips nasa kissing him so dearly. Kasancewar
wajen ba mutane shima se be 6ata lokaci ba ya shiga
sumbatarta in a soft demanding way. Sun dad'e a haka
sannan yayi breaking kiss d'in daga bisani yayinda suka shiga
mayar da numfashi.
"Don't cry anymore okay?"
"Okay" ta amsa tana gyad'a kai fuskarta ya d'ago yadda take
kalon setin idanunsa "I won't rest har se idan na dawo dake
d'akinki Nazeefah you have my words."
"I trust you Ya Rouhi and I love you so dearly."
"I love you too Darling."
"Ka koma haka nan nima I have a class to attend."
"Alright se na shigo anjima da yamma okay?"
"Okay Allah kaimu."*******
_3:47pm_
Yana cikin tattare kayakinsa da shirin kulle office sega
wayansa ya shiga ruri dubawanda zeyi yaga Amal ke kira. Be
6ata lokaci ba ya d'aga "Hello Rania?"
"How're you Ya Omri?"
"Alhamdulillah what about you?"
"Lafiya k'alau."
"And my baby?"
"Itama lafiya."
"Yau kika galabaitar mun da ita ko?"
"Toh so kake inyi ta zaman gida ina tara wa kaina carrovers?"
"A'a Mummy'n Baby yi hak'uri kunci abinci?"
"Eh na dafa indomie."
"Akwai wani abinda kike buk'ata?"
"A'a I'm just missing you yaushe zaka dawo?"
"Abba requested to see me so daga chan zan wuce gida
okay?"
"Batun Nazeefah koh?"
"Yes."
"Everything will work out fine in shaa Allah."
"Thank you baby I love you."
"I love you too seka dawo."
"Sleep until then sena zo in tada ke." Da murmushi kwance
fal a fuskarta ta amsa "Toh shikenan take care" nan ta katse.
Be kai ga ajiye wayan nasa ba sega kiran Abba na shiga be
hankara ba ya d'aga inda suka gaisa.
"Ermm nace Umminka ta sanar da kai cewa ina buk'atan
ganinka ko?"
"Eh Abba I'm on my way."
"Alright Allah ya kare."
"Ameen" da haka ya katse ya gama tattare kayakin nasa ya
fice. Direct gida ya wuce inda ya samu Abba da Ummi zaune
a parlour suna jiransa. Ba tare da 6ata lokaci ba Abba ya
sanar da Afzal gaskiyan al'amarin inda yayi mar nasiha sosai
akan cewa ba komi mutum yake so yake samu a duniya ba
dole wataran se an k'ara da hak'uri amma ina Afzal tamkar
kurma haka ya zame a wajen maganganun Abba kawai suna
shiga ta kunnensa suna fita ta d'ayan ne shi bega abinda ze
rabasa da Nazeefah ba bayan mutuwa.
"Saboda haka ga takarda nan da biro ka rubuta mata
takardanta kuma saki ba d'aya ba, ba biyu ba yake nema saki
uku yake so."
"No Abba" ya sanar dashi ciki rud'ani "I can't do this."
"I know Afzal amma ya zame maka dole ba muke iko da
Nazeefah."
"Abba baka gane bane? Bazan iya rubutawa Nazeefah
takarda ba I can't."
"Prince kayi hak'uri" fad'in Ummi.
"No Ummi I can't zan je in samesa inyi masa magana in shaa
Allah ze sauk'o."
"Umminka bata sanar da kai cewa da kaina naje na samesa
bane? Alhj Abdallah ya riga yayi making up mind nasa ba
abinda zakayi da zaisa ya sauk'o."
"I'll still try my luck Abba idan kuma be hak'ura ba then I
have no choice dole in kai maganan nan kotu dan idan ba
mutuwa ba banga abinda ze rabani da matata ba."
"Nima haka nace mu kai k'aranshi kotu tunda de ba zaluntar
yarinyar nan kakeyi ba kotu zata tsaya maka ta dawo maka da
matarka."
"A'a Hjy Mariam seda na fad'a miki ki yasar da maganan nan
kink'i akan mey zamu kai maganan nan har kotu? Nazeefar
itace autar mata ko mey?"
"Ba itace k'arshen halitta ba Abba amma bazan iya rabuwa
da ita haka kawai saboda selfish interest na Daddy ba."
"Afzal kar ka manta Nazeefah 'yarsa ce kuma bamu keda iko
da ita ba."
"No Abba, Nazeefah matata ce kuma nafi Daddy iko da ita
shiyasa nake rok'onka da ka bani dama inje in samesa inyi
masa magana."
"Afzal wai kam mey kakeyi haka? Akan rashin mutuncin da
Alhj Abdallah yayi maka ya kuma yi wa mahaifinka ai yaci ace
ka fita daga harkansa da 'yartasa gabad'aya. Ka sani suke da
asara ba mu ba, idan aure kake so ka k'ara ko a yau ka kawo
mace gidan nan zan aura maka ita, infact ko uku kakeso ka
k'ara zanyi maka komai balle ma kai da kake da mace a gida?
Mene Nazeefah za tayi maka wanda Amal baza ta iya yi ma
ba? C'mon man up."
"Abba ba haka bane, baza ka ta6a ganewa ba Nazeefah and
Amal are two different people dan Allah ka bani dama inje in
sake basa hak'uri in shaa Allah he'll come around."
"Alhj kayi hak'uri ka barshi yaje d'in hala rabonsa ya ratse"
Ummi ta fad'a.
"Shikenan kaje amma ni ba ruwana na riga na fad'a maka
abinda ya kamata."
"Nagode" yace zalla had'e da mik'ewa "Ni zan koma duk
abinda akwai I'll let you know." Da haka ya fice dai-dai gaban
gidansu Nazeefah yayi parking ya k'arasa ciki.
"Ka kawo takardan nata ne?" Daddy ya tambayesa bayan
gaisuwan da sukayi.
"Daddy ba abinda ya kawo ni ba kenan dan bazan ta6a iya
rubutawa Nazeefah takarda ba haka kawai. Hak'uri nazo baka,
dan Allah kayi hak'uri."
"Shin mahaifinka be sanar dakai abinda nace masa bane?"
"He did Daddy amma bazan iya ba, wallahi ina son Nazeefah
kuma bana k'aunan rabuwa da ita idan wani laifin nayi kayi
hak'uri-"
"Dakata Afzal!" Daddy yayi saurin katsesa "Idan ba so kake
ranka ya 6aci ba ka bani takardan 'yata zaman aure ne nace
bazaku k'ara ba."
"Shikenan Afzal ka mik'e ka tafi zamuyi magana" Mummy
dake la6e tun d'azu jikin garu tace.
"Mummy dan Allah ki basa hak'uri wallahi bazan iya rabuwa
da Nazeefah ba."
"Na gane Afzal just go zamuyi magana." Ba dan yana so ba
ya mik'e ya fice. Acikin mota ya zauna ya shar6i kuka kaman
ba gobe.
Daddy da yaga dagaske Afzal yake baze iya rabuwa da
Nazeefah ba ya shiga nazari, yasani koda kotu ya kai k'ara da
k'yar su biye masa sabida bashida wata k'wak'k'warar dalili, da
ace Nazeefar ne bata son auren da rabasa bazeyi wuya ba
amma yasan komin yaya Nazeefah bazata ta6a amincewa ta
rabu da Afzal ba. Ya zeyi toh?
Chan bayan sallan Isha Mummy na zaune a d'akin Nazeefah
tana ta faman bata hak'uri Daddy yayi knocking bisa k'ofan ya
shiga.
"Ermm Hjy Surayya ki tattaro min passports naku."
"Passports? Kayi mey dasu?"
"Kede kam ki tattaro mun mana ina ruwanki?"
"So kake ka d'ibe mu kaje ka jibge mu a wani k'asan saboda
selfish intrest naka?"
"Ba abinda na tambaya ba kenan ki bani passports naku."
"Bazan bada ba."
"Nazeefah ina passports naku?"
"Daddy dan Allah kayi hak'uri Daddy meyayi zafi kake shirin
kaimu wani k'asan? A dalilin mey?"
"Saboda bana son abinda ze sake had'aki da Afzal."
"Daddy da igiyan auren Ya Afzal akaina kake son inyi tafiya
ba tare da izininsa ba?"
"Sau nawa zan fad'a miki Afzal ba mijinki bane? Zaman ku ya
haramta."
"Ya haramta kaman yaya wai? Idan wani abun ne ka fito fili
mana ka sanar damu Alhj meye amfanin wannan 6oye-6oyen
da kakeyi?" Mummy ta tambayesa.
"Ina jiran passports naku muddin Afzal baze sauwak'e wa
'yar nan ba toh barin k'asar nan ya zama dole."
"Daddy makaranta na fah? Khaleefah ma fa?" Nazeefah dake
kuka ta tambayesa sede ko ta kanta beyi ba ya ja k'ofan ya
fice. Fad'i tayi jikin Mummy tana kuka. "Wallahi wallahi kinji
ko? Ba inda zamu. Iyayin Daddy'n naku ya soma isa na Allah
kaimu gobe k'ara zan kai kotu akan mey dan na zuba masa
ido ze tsaya yana yin son ransa a cikin gidan nan? Ki kwantar
da hankalinki Allah kaimu goben.".****
Chan wajajen goma Nazeefah ta d'au waya ta kira Afzal,
ringing d'aya biyu ya d'aga.
"Hello Rabba'atul Bait?"
"Ya Rouhi please help me Ya Rouhi bana son in rasaka."
"Wani abu ya sake faruwa ne?"
"Ya Rouhi Daddy na shirin relocating namu out of Nigeria
gabad'aya."
"What?!"
"Wai muddin bazaka bani takarda na ba zamu bar k'asar,
d'azun yazo ya tattare passports namu Ya Rouhi please help
me out."
"Shhhh its okay don't cry ina Mummy?"
"Mummy tace zata kai k'aransa kotu."
"Ki kwantar da hankalinki kinji? Sena shigo gobe kibar kukan
haka."
"Please come."
"I'll, you should get some rest I love you."
"I love you too" ta amsa sannan ya katse. Safa da marwah ya
shiga yi a parloun yana nazari sannan chan yaje ya samu Amal
a d'aki suka kwanta.
Washegari bayan sallan Azahar Afzal ya taho gidansu
Nazeefah ba irin hak'urin da be bawa Daddy ba amma ina ko
sauraronsa Daddy baiyi ana cikin haka Mummy dake
sauraronsu tun d'azu ta sanya baki.
"Toh tunda de haka ne Afzal ni na baka dama kaje kayi filing
case a kotu se muga idan kotun zata basa goyin baya ya raba
wannan aure." Wani irin har6awa zuciyan Daddy yayi tabbas
idan ya bari maganan nan yakai kotu toh asirinsa ze toni
kenan. Ya zeyi?
"Ni kike shirin kaiwa kotu Hjy Surayya?"
"You give me no option Alhj. Idan wani abun ne kake 6oye
mana tell us we're your family zamuyi maka kyakkyawn
fahimta amma zancen canza mana gari be tashi ba."
Kai ya shiga girgizawa "No Hjy Surayya bazaku ta6a fahimta
taba, ba don ni ba dan Allah kuyi hak'uri a raba auren nan."
"Trust me Alhj zamu fahimceka just tell us" a hankali ta shiga
yi mai magana cike da kissa amma inaa Daddy ya kasa bud'e
baki yayi magana se kad'a kai kawai yake.
"Toh inde haka ne mu ma bazamu amince mu bika koma ina
ba kuma mayar da yarinyar nan d'akinta ba fashi."
"Afzal ka rubuta wa 'yar nan takardanta nace auren ku ya
haramta!"
"A dalilin mey ya haramtan?" Itama Mummy ta mayar masa
cike da tsiwa. Dai-dai lokacin Nazeefah da Khaleefah suke
sauk'owa daga sama. A bakin stairs d'in suka tsaya suna
sauraron iyayensu.
"Ya haramta nace kuyi wa Allah ku raba auren nan."
"Mey sukayi da zaka haramta musu aure? A dalilin mey?"
"Ya haramta Hjy Surayya ki yarda da ni."
"Na yarda da kai Alhj, just tell us ka gaya mana dalilin da
yasa ya haramtan, muddin kaine da gaskiya na maka
alk'awarin tayaka raba auren nan just tell us."
"Bazan iya ba ku gafirceni." Na matuk'a kan kowa ya d'aure
a wajen, ba wanda ya fahimci inda ya dosa gashi duk sun
k'osa suji dalilin da yasa yake cewa auren ya haramta.
"Alhj dan Allah kayi magana, ka fa sani rik'e maganan nan ba
shine mafita ba, we're your family komin yaya bazamu guje ka
ba just tell us."
"Ya haramta na fad'a muku ya kuke so inyi? Kar ku biye ma
Afzal. Tunda baze saki 'yar nan ba ku amince ku bini mu
tattara mu bar k'asar nan shine kwanciyan hankalin mu
gabad'aya."
"Tayaya Alhj? Mene wannan abu da kake k'in gaya mana?
Toh inde haka ne ina Nazeefah? Ku sauk'o mu bi Afzal mu bar
mai gidan idan tayi tsami maji."
"Hjy Surayya dan Allah karki tozartani a idon jama'a haka,
kar ku tafi ku barni ku kad'ai gareni."
"Fine seka sanar danu wannan magana da kake 6oyewa
kokuwa mu tafi."
"Ni koda zaku tafi ku amince a raba auren nan, na yarda ku
tafin amma a raba auren yarannan tukuna."
"Haka kawai ba gaira ba dalili kake son a shiga tsakanin
masoya biyu? Toh wallahi kayi k'arya Alhj."
"Sau nawa san gaya miki auren nan ya haramta?! Sau nawa!"
Ya daka mata tsawa.
"Sau nawa nima zan gaya maka muddin banji dalili ba bazan
yarda a raba auren nan ba?!" Itama ta mayar masa a tsawace.
"Ya haramta nace!"
"Mayar da aure ba fashi ku sauk'o mu tafi Nazeefah."
"Kar ku tafi ko ina, auran Afzal da Nazeefah ya haramta
saboda Amal da Nazeefah 'yan uwa ne!" Ya sanar dasu a
fusace ba tare da yasan yaushe ba.
RANA DAYA Chapter 42
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
Tareda Naja'atu Lawal Rijau Niger State
@Whatapp 08083232323 or 09060202323
PAGE 42
"What??" Mummy tayi exclaiming cike da k'in yarda yayinda
fuskokinsu duka ke d'auke da d'umbun mamaki barin ma Afzal
da Nazeefah da suke jin lamarin kaman raha.
"Ku gafirceni Hjy Surayya amma aure tsakanin Afzal da
Nazeefah ya haramta, dole ne ya sauwak'e mata saboda Amal
yar ta ce."
"Innalillahi wa inna ilai-" Mummy bata kai ga idda salatin ba
kawai suka ji k'aran fad'uwan abu a k'asa rigijib! Afzal kam
dan mamaki bakin yin salatin ma ya rasa.
Atake duk suka maida hankalinsu game da k'aran inda suka
ci karo da sumemmiyar jikin Nazeefah a k'asa. Kasancewar
Khaleefah ne a kusa da ita seya rigasu fara yin kanta yana mey
jijjigata amma ina ko motsi batayi ba shiri Afzal ya k'ariso ya
d'agata yayi waje da ita se cikin motansa inda Khaleefah da
Mummy suka zauna a baya da ita Daddy kuma a gaba. Nearby
clinic Afzal yayi rushing inda akayi emergency room da
Nazeefah. Tunda aka shiga da Nazeefah har Dr da nurses da
suka duba ta suka fito kap acikinsu Afzal ba wanda Allah ya
basa izinin sake yima Daddy wani tambaya as duk sun shiga
cikin rud'ani. Jugum suka zauna daga lungu daban-daban
kowa da abinda yake gudu masa a kai. Ita de Mummy har
yanzu ta kasa aminta da komai haka ma Khaleefah amma
banda Afzal da jikinsa ya soma basa tabbas Daddy ne
mahaifin Amal in reference to labarin Mami da yaji. Duk yadda
yaso k'aryata zancen Daddy ya kasa, yana da yak'inin cewa
Daddy ne mahaifin Amal. Shin wani irin cakwakiya ne wannan?
Taya za'ace yana auran wa da k'anwa? Innalillahi wa inna ilaihi
raji'un.
Da wani idon ze sake kallon Nazeefah ya kalli Amal? Shin
yanzu dukansu biyu sun haramta masa kenan ko ya? Yau ina
zaisa kansa idan ya wayi gari ba Amal ba Nazeefah? Wannan
wace irin k'addara ce? Ko a tatsuniya be ta6a jin inda abu
haka ya ta6a faruwa ba. Wayyo Allah shi. Ana cikin haka likitan
daya duba Nazeefah ya fito ya sanar dasu kan ta farfad'o suna
iya shiga ganinta. Mummy da Khaleefah suka soma shiga
sannan Afzal, daga k'arshe kuma Daddy da ya tsaya daga
bakin k'ofa tsabaragen kunyan da yake ji ko k'arisawa ciki ya
kasa. Jikin Mummy Nazeefah ta fad'a tana kukan tsuma zuciya
"Mummy please tell me it's a joke, Mummy it can't be Mummy
please."
"Shhh ya isa haka" itama Mummy'n bata san lokacinda ta
shiga zubda hawaye ba, ya rage Khaleefah kad'ai ke basu
hak'uri. Duk anan kallonsu kawai Afzal yake bako uffan, yayi
tsaye kaman gunki daga wani sashe. Daga bisani Mummy da
Nazeefah kenrik'e a hannunta ta kewayo kan Daddy.
"Alhj meke faruwa? Shin kama san kuwa abinda kake fad'i?"
Nauyayyen ajiyan zuciya ya sauk'e sannan ya k'ariso cikin
d'akin "Hjy Surayya ki gafirceni amma Amal kishiyar Nazeefah
'yata ce."
"Noo" Nazeefah ta shiga kad'a kai yayinda hawaye ke tsiyaya
daga idanunta "Please don't do this Daddy I beg of you."
"I'm very very sorry Nazeefah-"
"Daddy ta yaya?" Tayi saurin katsesa "Taya Amal ta zamo 'yar
uwata? How Daddy?" Ta tambayesa tana mey rushewa cikin
tsananin kuka.
"It's a long story Nazeefah, fatana Allah yasa kin fahimci
dalilin da yasa nake son ki rabu da Afzal ki kuma bani had'in
kai."
"No Daddy, bazan rabu da Ya Afzal ba idan ma akwai me
rabuwa da Ya Afzal toh Amal ce not me."
"Ya isa haka Nazeefah" Mummy ta dakatar da ita.
"No Mummy why will I be the one to pay for Daddy's
mistake? Balle ma ban yarda cewa Amal 'yar uwata bace.
Amal kishiyata ce she can never be my sister never!" Bori ta
shiga yi wanda da k'yar Mummy ta samu ta lafa da ita.
Hawaye na tsiyaya daga idanta ta d'ago kai tana kallon Daddy
da jikinsa ya gama mutuwa ga kukan da iyalansa sukeyi har
anan Afzal bece komai ba tsabagen state of shock da ya
shiga, gani yake kaman a mafarki komi yake faruwa.
"Taya Amal ta zame yar Nazeefah Alhj? Ta yaya? I need
answers."
"I'm terribly sorry Surayya."
"So kake kace mun kana da 'ya a waje?" Shiru yayi dan kunya
ko amsawa ya kasa ga yadda Khaleefah ya kafa masa ido. Da
irin wannan abin kunya da wani ido ze sake yima 'ya'yansa
horo yanzu?
"Magana nake maka Alhj!" Ta tambayesa a fusace "I need
answers we all need answers here!" Tayi demanding.
"Wallahi nima ban san da zaman Amal ba se lokacin da aka
kad'eta."
"Baka san da zaman Amal ba?" Mummy ta tambayesa
unbelievably. "Baka san da zaman Amal bafa kace? A ina aka
ta6ayin haka?"
"Wallahi ban san da zaman Amal ba se kwanan nan."
"Taya ya zakace kana da 'ya amma baka san da zamanta ba
Alhj? Until when zaka daina yi mun da 'ya'yana k'arya?"
"Wallahi ban san ciki ya shige jikin mahaifiyarta ba bayan
faruwan abun."
"Yanzu ko kunya baka ji kake k'arya a gaban sirinkinka da
'ya'yanka Alhj? Wannan abu da me yayi kama? Ashe kana da
'ya a waje na aureka ban sani ba? Kuma kak'i ka sanar dani
har yau? Ashe da ba don wannan cakwakiya ba haka zan
cigaba da zama da kai kana mun k'arya kana zolayata? Why
Alhj?"
"Surayya wallahi ba haka bane ni kaina recently na san cewa
Amal 'yata cr, na so in sanar dake kuma amma tsoro nake,
tsoron rana irin ta yau ki yarda dani Hjy Surayya."
"K'arya kakeyi wallahi k'arya kakeyi" ta fad'i tana kuka.
"Idan da nasan yaran nan 'yan uwa ne ajinki zan bari su auri
Afzal ne dukansu biyu Surayya? Please believe me."
"Shine kuma yanzu dan rashin adalci kake son 'yata ta biya
laifin da ka aikata? Toh kayi k'arya Alhj wallahi kayi k'arya."
"Hjy Surayya dan Allah kiyi hak'uri ki bani had'in kai a raba
auren nan."
"Wallahi Allah ya isa nida 'ya'yana Allah ya isan mana." Har
anan Afzal be ce komai ba. "Tashi Nazeefah tashi mu tafi."
Hak'uri Daddy ya shiga bata amma ko ta kansa batayi ba yana
yunk'urin ta6ata kuwa ta fisge jikinta "Koda wasa kar ka sake
yink'urin ta6ani mu tafi Khaleefah" har bakin k'ofa Daddy ya
bisu yana basu hak'uri amma ba wanda ya kewayo ya kallesa
acikinsu. Bayan sun fice ya juyo kan Afzal.
"Afzal da-"
"No Daddy" yayi saurin katse sa had'e da ficewa daga d'akin
yayi gun motansa be ratse ko ina ba se gida. Yana bud'e k'ofa
sega Amal ta taso yi masa sannu da zuwa hannunta ya ja ya
jefata jikinsa had'e da rungumeta tsam wane wani na shirin
k'watan masa ita. Wani irin rikicaccen kuka yasa wanda ya
mugun d'aurewa Amal kai.
"Subhanallahi Ya Omri why're you crying?" Se kuka kawai "Ya
Omri please stop" kokawan d'agosa daga jikinta ta shiga yi
amma ta kasa dan yadda ya damk'e ta. "Ya Omri cry nomore
I'm here" bayanshi ta shiga bubbugawa a hankali tana basa
hak'uri yayin da kukan nasa ya tsananta. Sun d'au tsawon
lokaci a haka sannan na k'arfi da yaji Amal ta samu ta janyesa
daga jikinsa yana mey k'ok'arin sake kankameta.
Kallo d'aya ta kaiwa idanunsa da suka kad'a sukayi ja nan
take itama idan nata ya cika da hawaye ba shiri ta shiga
tsiyayar da su tsan-tsan tausayi da k'auna. "Ya Omri what
happened? Meyasa kake kuka haka?" Janta yayi ya sake
rungumeta se chan ya saketa ya shiga share mata hawayenta
har anan tambayansa take meya faru.
Hannunta biyu ya d'ago ya had'a da nasa yana murzawa a
hankali yayinda ta k'ure masa ido tana shirin jin abinda ze
fad'a mata. Bayan nishin da ya fisga ya kira sunanta "Amal?"
Abinda ya jima beyi ba.
"Na'am Yaya?" ta amsa.
"Amal promise me."
"Promise you what Yaya?" Tayi saurin tambaya.
"Just promise me."
"I promise Yaya, everything for you."
"Thank you, thank you so much."
"Meya faru Yaya? Meyasa kake kuka haka? Batun Nazeefah
ne?"
"Ko kad'an Amal, this is about you." Na sosai kanta ya
d'aure "Ni kuma Yaya? meya faru?"
"Promise me again Amal, ki min alk'awari koda mey ya faru
bazaki ta6a tafiya ki barni ba."
"Subhanallahi shin meya faru Yaya? Meyasa kake magana
haka? Please talk to me."
"Just promise me Amal please."
"Yaya kafi kowa sani na bazan ta6a tafiya in barka ba
because I love you, I love you so much."
"Thank you Lily" nan ya jata jikinsa ya sake rungumeta. Na
matuk'a kanta ya sake d'aurewa shin meke faruwa? Hannu ta
zagaye a bayansa hugging him back. "Amal I've found your
biological father" ya sanar da ita a saitin kunnenta wani irin
mumunan fad'i gabanta yayi ba shiri ta janye jikinta daga nasa.
"Ka samu asalin mahaifina?" Ta tambayesa cike a k'in yarda.
Kai zalla ya gyad'a mata yana me rik'o hannayenta cikin nasa.
"How? When? Where? " Ta jero mai tambayoyi nan take.
Kafin ya amsa ta shiga k'aryatasa "No Yaya this can't be true,
har a ina ka sansa bale idan ka gansa ka ganesa? You're
mistaken Yaya koma waye ne mahaifin nawa nasan baya
raye."
"No Lily, not at all mahaifinki yana raye."
"How? Taya kasan yana raye? Ya ma akayi ka sansa? Yaya
please" kai take ta kad'awa cike da k'in yarda.
"Calm down Amal but that is not even the problem."
"Yaya what're you saying?" Seya bud'e baki ze sanar da ita
seya kasa.
"Yaya please speak up what problem? Meyake faruwa?"
"Ki kwantar da hankalinki bana son abu ya samu lafiyan
abinda ke cikinki."
"Yaya just tell me."
"Forget it, shikenan ma."
Hannunsa tayi saurin rik'owa kafin ya juya "Please tell me
Yaya what is going on?"
"Kiyi min alk'awari bazaki yi reacting ba, komin yaya bazaki
tada hankalinki ba za kuma kiyi wa bak'on lamarin nan
kyakkyawan fahimta."
"Yaya ka fad'amun mana."
"I have to know, bana son zuciyanki ya tsinke abu ya sameki
ko baby'nmu so promise me bazaki tada hankalinki ba."
"Okay I promise ka fad'a mun dan Allah" ta fad'a a k'ose.
"Amal you and Nazeefah are sisters" shiru kukeji a wajen ko
motsawa Amal ta kasayi bale magana, k'ok'ari take ta fahimci
inda ya dosa amma ta kasa. Daga bisani ta shiga kad'a kanta
"Ni da Nazeefah?" Ta tambayesa.
"Yes Amal, Nazeefah k'anwarki ce" sulalewa k'asa tayi wanda
da sauri Afzal ya tarota ya direta akan kujera yayinda idanunta
suke shirin kafewa. Ruwa ya nema ya shiga yayyafa mata
sede kaman sake kashe mata jiki yake tun yana iya ganin cikin
idanun nata har ta rufesu. Ba shiri ya yasar da glass cup d'in
inda yayi kaca-kaca a k'asa ya shiga bubbuga ta sede ina ko
motsawa batayi. Dafe hannunsa da yace zeyi jikin kujeran
kawai yaji abu kaman ruwa dubawanda zeyi ya tarar da jini
wani irin rikicaccen ihu ya saki. "Amal? Amal? Please wake up
Amal!" Se ihu yake yana kiran sunanta amma inaa ta riga ta
jima da sumewa. Ba shiri ya kicicci6eta a hannu bema damu
da jinin daze masa staining blue getzner'n dake jikinsa ba. A
bayan mota ya sata ya shiga gaba se TH inda akayi emergency
room da ita. Ko zama Afzal ya kasa gun se safa da marwah
yake yana kuka kaman k'aramin yaro kowa yazo wucewa seya
tsaya ya kallesa. Dan yadda ya rikice ko kiran Ummi ya sanar
da ita halin da ake ciki ya kasa chan wata nurse ta jasa wani
gu ya wanke hannunsa dake d'auke da jini har sannan ta
tayasa goge kayansa sede jinin ya riga ya kama amma duk da
hakan be damu ba. Bakin k'ofan nata ya koma ya tsaya yana
jiran fitowan likitocin chan bada dad'ewa ba sega k'ofan ya
bud'u. Ko daman yin magana be baiwa likitan ba ya shiga
kwararo masa da tambayoyi.
"Calm down calm down" Likitan ya shiga kwantar masa da
hankali sede is of no use saboda hankalinsa ya riga ya tashi.
"Please answer me how is my wife?"
"Your wife will be fine you don't have to worry nan da 'yan
mintuna kad'an zata farfad'o."
"And my baby?" Reaction daya gani a fuskan likitan kad'ai
yasa k'asusuwan guiwansa sakewa yayinda cikinsa ya d'au
ruwa. Ba shiri ya shiga kad'a kai "Please speak up Dr how's
the baby? Kun samu kun ceto cikin?"
"I'm very sorry Sir amma it was too late tun kafin ku iso nan
cikin ya lalace an de wanke cikin yanzu anyi duk wani abinda
ya kamata I'm very sorry zaka iya shiga ganinta." Motsi
wannan Afzal ya kasayi a wajen tun ficewan likitan da nurses
d'in se hawaye kawai yake zubarwa yayinda gobaran tsanan
Daddy yake ruruwa mai a zuciya. Ma shin meya kaisa sanar da
Amal cewa ita da Nazeefah sisters ne? Da ya san abinda yin
hakan ze haifar da be soma ba. Yanzu shikenan sunyi ban
kwana da baby'nsu kenan? Baby'n da har ya gama imaging
yadda kamanninta ze kasance d'aya da na Amal tasa? Baby'n
da ya gama picturing rayuwansu da ita? Innalillahi wa inna
ilaihi raji'un tabbas wannan rana a cike yake da masifa da
k'unci. Guiwa na rawa ya dafe handle na k'ofan ya bud'e ya
shiga ciki. Chak ya tsaya gun ya kasa k'arisawa tsan-tsan
tausayi kawai, ta ina ze fara sanar da Amal cewa cikin nata ya
lalace? Nooo baze iya ba. Jiki na rawa ya k'arisa ciki had'e da
jan kujera ya zauna a gefenta. Kakkarwa hannunsa ke ya d'ago
ya dafe nata da canular ke kai. "Amal I'm so sorry, I'm terribly
sorry please wake up karki tafi ki barni you promised to stay
by my side" kuka yake tamkar d'an yaro a gurin. Ba ma wai na
zubewan cikin ba sena tsoro da yake zamansu na iya k'arewa
shida Amal tunda dry gashi ita da Nazeefah 'yan uwa ne. Baze
iya rayuwa ba ita ba.
Kukan ya cigaba da yi ba fashi har seda Amal ta shiga bud'e
idanunta. Mik'awa yayi had'e da sumbatan goshinta "Thank
you for staying alive with me Rania" ya sanar da ita hannunsa
na acikin gashin kanta yana shafawa a hankali.
"Rania why aren't you saying anything?" Ya tambayeta bayan
dogon shirun da tayi hannunta kawai yaga ta kai akan cikinta a
hankali ya aza nasa akai shima.
"Is my baby still with me?" Ta tambayesa murya ciki-ciki.
Rasa na cewa yayi kawai ya shiga yi mata murmushi saidai
duk yadda yaso 6oye k'uncin da yake ciki ya kasa a hankali
hawaye ya shiga ciko masa a ido.
"Ya zube ko?" Ta sake tambayansa itama idan nata na mey
cikowa da hawaye. "Yaya please answer me idan zubewa yayi
just tell me" ta k'are hawayen na tsiyaya daga idanunta.
"Amal I'm so sorry please forgive me."
"Ya zube?" Ta kuma tambayansa kai zalla ya gyad'a mata
yayinda ta rushe da wani irin masifaffen kuka. Gadon ya haye
da wuri ya jata jikinsa ya shiga bata hak'uri amma se bori
takeyi da k'yar ya samu ya lafa da ita. Tana kwance a jikinsa
ta kira sunansa.
"Yes?" Ya amsa patiently.
"Meyasa se ita? Why not me?"
"Because you're more precious Rania, saboda Allah ya
tausaya mun yasan idan ya d'aukeki bazan iya rayuwa ba."
"Yaya na kasa amincewa da hakan, dan Allah ka gafirceni."
"Saboda mey Rania? Mey kikayi?"
"Na kasa rik'e amanan rik'on da ka bani Yaya I'm so sorry."
"Ko kad'an ba laifinki bane Rania idan har akwai wanda ze
nemi tuna toh nine, da ban sanar dake gaskiya ba da cikinki
be zube ba, da har yanzu baby tana tare damu."
"But for how long zaka ta 6oye mun gaskiya Yaya?"
"It doesn't matter now, ni kawai ki daina blaming kanki,
dama haka Allah ya qaddara baby bazata rayu damu ba, fatan
mu Allah yasa mey ceto ce."
"About what you said? Shin da gaske ne Nazeefah k'anwa
tace?"
"Amal that doesn't matter now lafiyarki ne a gaban mu
yanzu."
"No Yaya" ta d'ago kai a hankali tana kallonsa a raunane "It
does matter, is Nazeefah my half sister? Shin dagaske ne
Mahaifin mu d'aya ne da ita?"
"Amal I'm very sorry I never wished for things to turn out this
way."
"Just answer me."
"Yes Amal, keda Nazeefah 'yan uwa ne."
"Ta yaya? Taya ma hakan ze zamo gaskiya?" Nan ya kwashe
labarin duk yadda akayi ya bata Amal kam se kuka. Yanzu
ma'ana kenan mutumin da ya taimake ta lokacin da Nazeefah
tasa aka bigeta shine mahaifinta, mutumin da take ta fatan ina
ma ace mahaifinta shine asalin mahaifinta? Meyasa taji ta
tsanesa gabad'aya yanzu? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un taya
hakan ma ze zamo gaskiya? Tayaya ma ya gane ita 'yarsa ce?
Ashe de ba tsakani da Allah ya taimaka mata ya kuma kula da
ita ba lokacin, shin tayaya ma yasan ita 'yarsa ce? A iya labarin
da Mami tayi mata ta nuna mata cewa shi mahaifin nata
bema san an haifeta ba. How is this even possible?? She need
answers. Kuka take Afzal yana bata hak'uri.
"Yaya baka gane bane Daddy baze ta6a zama mahaifina ba,
baka fahimce sa bane."
"Please cut it out."
"No Yaya it can't be possible idan da Nazeefah k'anwa tace
da naji hakan a jikina please stop saying she's my sister
please."
"Amal saidai muyi hak'uri amma bazamu iya canza k'addarar
Allah ba."
"Ya zamo dole mu hak'ura da juna kenan Yaya."
"Saboda mey Lily?" Ya tambayeta a raunane.
"Bazeyi mu cigaba da zama ahaka ba Yaya, bazeyi muna jini
d'aya da Nazeefah mu cigaba da kasancewa matayenka ba,
zama damu ya haramta maka."
"No Amal please don't talk like that dan Allah kibar cewa
haka, I can't live without you kinfi kowa sanin hakan."
"I'm sorry Yaya amma gaskiya d'aya ce rabuwa ya zamo
dole."
"No please Amal, dan Allah kibar cewa haka, kefa kika ce our
love for each other is enough."
"Not in this case Yaya saboda we can't escape from the
truth."
"But you promised never to leave me."
"I'm sorry I'm breaking that promise now."
"Please don't Amal there has to be a way."
"What way Yaya?"
"I don't know, zamuyi tambaya akai in shaa Allahu zasu san
yadda zasuyi damu but please kibar cewa zaki tafi ki barni
bazan iya rayuwa ba ke ba Amal I really can't."
"I'm really sorry Yaya I'm so sorry."
"I dont want you to be Amal, I want you to stay please kiyi
mun alk'awari." Kai zalla ta iya gyad'a masa yayinda hawaye
ke bin k'uncinta. Ita abun ma ya taru ya mata yawa ga
miscarriage, gashi ita da k'anwarta suna auren miji d'aya.
Wannan wace irin k'addara ce?
"Kayi ma likitan da ya dubani magana I want to be
discharged."
"But Amal you're sick bakida k'arfi."
"Ina son in tafi gida."
"Wani gida d'aya? Har yanzu kina kan bakanki na tafiya?
Please don't leave me Amal please don't."
"Just take me home Yaya."
"Promise me bazaki gudu gida gunsu Mami ma?" Kai zalla ta
gyad'a masa amma abinda zuciyanta ke raya mata ba ta gudu
ta koma gunsu Mami bane so take ta gudu ta shiga wani
duniyan daban inda ba wanda yasan tarihinta. Cakwakiyan
dake cikin rayuwanta ya isheta, abin kunyan yayi yawa. Haka
Afzal yaje ya samu likita yace a sallamesu ba yadda likitan
beyi dashi ba akan yabari koda zuwa gobe idan Amal ta d'an
samu k'arfin jiki amma ina Amal tace ita sede yau za'a
sallameta hakan kuwa akayi daga k'arshe. Magungunan da aka
rubuta mata Afzal ya sai sannan suka koma gida inda Afzal ya
d'auketa ya kaita ciki, a kan gado ya kwantar da ita sannan ya
fad'a bayi yayi wanka ya sirka mata ruwan zafi bayan ya fito ya
taimaka mata tayi wankan itama sannan ya shirya ta tsaf ya
shirya kansa shima. Gabad'aya ya rasa nayi ga kukan da Amal
take tayi masa tun d'azu da k'yar ya samu ta hak'ura ta daina.
Wayansa ya d'aga ya kira Nazeefah amma layin a kashe yake
cewa, na Mummy yayi trying nan ma switched off dama yasan
za'ayi haka yasan Mummy zata kashe wayanta sannan tasa
Nazeefah ma ta kashe nata don kar Daddy ya samu ya same
su. Ummi ya kira next ya tambayeta ko tana gida inda ta
jaddada masa eh. Key'n motansa kawai yaja ya k'arisa kan
Amal da ke ta jan numfashi.
"Rania you're sick, enough already please kukan ya isa haka."
"Zaka fita ne?"
"Zanje gun Ummi zan dawo yanzun kinji? Akwai abinda kike
buk'ata?"
Kai ta kad'a masa yayinda ya janye mata bargo ya rufeta da
kyau, peck ya sauk'e mata akan goshi "Rest okay? I'll be right
back I love you" nan ma kai ta gyad'a masa sannan ya fice.
Bada dad'ewa ba Amal ta mik'e zaune, a sannu a sannu take
takawa ta d'auko akwatinta., bata da k'arfin ko sisi ta shiga
fiddo da kayakinta tana shiryasu cikin akwatin nata bayan ta
gama had'a kayakin nata ta sanya hijabi ta d'au wayanta ta
fito waje. Kaman Afzal yasan abinda take shirin yi yasa key ya
rufe k'ofan ta waje. Mey gadi na ganin ta fito yayi sauri ya je ya
sameta.
"Hjy lafiya?"
"Ka tayani jan akwatin waje dan Allah."
"Direba na gida ko in mishi magana ne?"
"A'a barshi kawai ka tayani kaja mun kayan nawa waje."
Amsan akwatin yayi sun kai dab bakin k'ofan suka iske a rufe
ta waje.
"Ya lafiya?" Amal da har jiri ya soma d'ibanta ta tambaya.
"Hjy kaman Alhj ya rufe k'ofan ta waje."
"Ya rufe k'ofa kaman ya? Bakada makulli ne?"
"Ya amsa kafin ya fita" ya amsa a takaice.
"Bakinku d'aya ko?"
"Wallahi Hjy ni Alhj be sanar dani komai ba face cewa da
yayi in basa makulli na."
"Ka bud'e min k'ofan nan."
"Hjy wallahi ba makulli a hannu na."
"Ka d'auko key ka bud'e mun k'ofan dan Allah ka bud'-" tana
cikin magana kawai ta sulale k'asa saboda jiri. "Hjy!" Mey gadi
ya sa ihu nan driver dake ciki ya fito mey ze gani jikin Amal
kwance a k'asa.
"Adamu meya faru? Mey kayi mata?"
"Wallahi ban yi mata komai ba dan Allah ka nemo waya ka
kira Alhj bai jima da fita ba." Nan da nan Driver ya shiga
neman Afzal a waya lokacin har Afzal ya isa gida an bud'e
masa gate sauran kawai ya shiga sega kiran Driver ba 6ata
lokaci ya d'aga "Alhj ka dawo gida akwai matsala, Hjy ta
sume." Ko amsa sa beyi ba yayi reverse, tuk'i yake kaman a
sama yake tafiya. Nan danan ya iso gida yayi parking bakin
k'ofa ya k'arisa ciki. Har anan su Adamu mey gadi basu ta6a
Amal ba gudun da suke kar yin hakan ya haifar da wani
matsala.
"Kan Amal ya k'arisa da sauri yana tapping fuskanta. Ashe ba
sumewa tayi ba jiri ne ya d'ibeta. Be 6ata lokaci ba ya
cicci6eta yayi d'aki da ita inda ya sauk'eta kan gado. Lamban
abokinsa ya kira da ya turo masa family doctor'nsa bayan nan
ya koma kan Amal.
"Lily meyasa bakiya jin magana ne? Seda na fad'a miki ba
inda zaki amma kika k'i ji? Ina kike so kije?"
"Yaya zaman mu ya haramta" kad'ai ta iya ce masa cikin
wahalallen murya.
"You're not the one to decide Amal, so kike ki kashe kanki
ne? Dan Allah karki sake yin haka stay here until you get
better."
"Just take me home Yaya."
"Amal this is your home please."
"No Yaya."
"Ya isa haka just keep quiet bakida lafiya in kika samu sauk'i
zamuyi magana." Zama ya cigaba da yi akanta har seda likitan
ya k'araso ya dubata inda ya d'aura mata ruwa yakuma
jaddada wa Afzal cewa kar ayi wasa da magunanta sannan
kuma tana cin abinci sosai bayan nan ya koyawa Afzal yadda
ze sake sa mata ruwa idan ledan da aka had'a d'in ya k'are.
Har waje Afzal ya rakasa ya sallamesa sannan ya taho ciki ya
koma kan Amal. Hannu ya aza akan goshinta yana shafa kan
gashin da ya sauk'o har kan wajen a hankali, "Yaya what of
Nazeefah? Ka sake ji daga gareta?"
"Rania please, ki bar zancen Nazeefah forget about
everything lafiyanki ne a gaban mu yanzu kinji?" Ba dan tana
so ba ta gyad'a mar kai.
"Nasan kina jin yunwa mey kikeso kici?"
"Bana jin yunwa Yaya I lost my baby."
"I know Rania and I'm sorry in shaa Allahu me ceto ne."
"Yaya I lost my baby" kawai ta rushe da kuka. Hak'uri ya
shiga bata amma takasa hak'ura, da k'yar ya samu ya shawo
kanta kukan nata ya lafa "Yaya baka tunanin cikin nan ya zube
ne saboda k'arshen zaman mu yazo? Acikin sauk'i zamu iya
rabuwa da juna tunda babu rabo a tsakanin mu yanzu, Allah na
sonmu ne shiyasa yasa cikin nan ya zube saboda guje mana
abin kunya da yake, dan Allah ka kaini gida."
"Rania har se zuwa yaushe ne zaki gane cewa kece ruhi na
idan bake kuma bazan iya rayuwa ba?"
"Yaya I'm sorry amma ba abinda zamu iyayi, k'addarace
rubucacciya dole mu rabu da juna."
"Ina son da kike ikirarin kina yi mun Amal? Ashe har Allah ze
kawo rananda zaki k'wad'aici rabuwa da ni? Ashe Allah ze
kawo rananda zaki tafi ki barni?"
"Yaya ba haka bane, kai kanka shaida ne game da irin
soyayyar da nakeyi maka but that still isn't enough, taya zan
cigaba da had'a miji d'aya da k'anwata? Shin akwai abu mafi
muni irin wannan? Yaya idan har Nazeefah k'anwata ce da
wani idon kake son in sake kallonta? Yaya wannan wani irin
abin kunya ne?"
"I'm aware of all that Amal kuma idan har da akwai wanda
zefi jin kunya acikin mu duka nan toh nine, ya Rabbi I married
two sisters and slept with both of them ni nafi kowa abun
kunya but I still don't care as long as you're willing to stay with
me."
"How Yaya? Wani 6angaren zaman mu ya haramta ne ka
kasa fahimta har yanzu? Baze yiwu ba ni kawai ka kaini gida."
"I don't care Amal!" Ya sanar da ita a tsawace ba tare da
yasani ba. A sanadin haka ta firgita se kuma be ji dad'i ba,
hannunta ya d'aga ya rik'e acikin nasa "Look I'm sorry but
please ki daina cewa auran mu ya haramta Amal I beg you
please." Hawaye na gangara daga idanta ta gyad'a masa kai
"In had'a miki kunun ki kisha?" Nan ma kan ta kuma gyad'a
masa "Kafin nan ka kira Mami ka sanar da ita banida lafiya."
"Is this what you really want Rania? Ko so kike idan ta taho ki
sanar da ita gaskiyan al'amarin dake faruwa saboda ta
d'aukeki ta tafi dake?"
"Yaya-" katseta yayi da wuri "Please Amal don't leave me,
abinda yake faruwa already ya riga ya mun yawa, I just found
out I'm marrying two sisters, after that kin samu miscarriage,
mun rasa future'n mu, I don't know ko addini na ze haramta
min ku duka ko ze bani za6i in d'auki d'aya, I'm so confused
akan hakan kuma kike son ki sake tafiya ki barni? Shin ya kike
son in rayu Amal? Dan Allah ba don ni ba koda bana nan kar ki
d'au waya ki kira Mami I beg of you."
Na matuk'a ya bata tausayi, tasani tashin hankalin da take
ciki kad'an ne a ganga da nasa amma saboda san zuciya se
su take abinda Allah yace suyi zaman haramun? Tana sonsa,
son da bata tunanin zata ta6a daina iya yi amma rabuwa ne
ya zama dole. Ba don tana so ba sedon yadda ya bata tausayi
ta gyad'a masa kai "I'm sorry."
"I dont want you to be Rania, kawai kiyi mun alk'awari bazaki
kira Mami ko Papi ba, idan lokacin yazo ni da kaina zan kirasu
in sanar dasu komai da kaina I just need time to sort out
things. Promise me okay?"
"I promise" ta amsa tana gyad'a masa kai. Peck ya sauk'e
mata a kumatu sannan ya fice nan da nan ya had'a kunun ya
kawo ya bata da kansa da ikon Allah kuma tasha sosai sannan
ya 6allo mata magunanta ta had'iye ya sake miyar da ita ya
kwantar da ita. Be bar wajen ba seda ya tabbata baccinta yayi
nisa. Duban agogo yayi yaga Maghrib har ya wuce nan da nan
ya idar ya shige mota ya fice gida bayan kunnen da ya ja wa
mey gadi cewa komin yaya kar ya bar Amal ta fita ga k'ofa ya
bar musu a bud'e saboda fita masallaci.
Sannu da zuwa Ummi dake ta jiransa tun d'azu tayi mai
sannan ya samu gu ya zauna a gefenta sede kallo d'aya tayi
masa ta fuskanci yana cikin damuwa ga fuskansa daya nuna
cewa yayi kuka.
"Prince lafiya?"
"Ummi Alhj Abdallah ba mutumin kirki bane."
"Ai dama sanda Abbanka ya fad'a maka ka sauwak'e wa
'yarsa kawai a rabu dasu lafiya kak'i ji, shin yanzun mey yayi
maka? 'Yan unguwa ya tara suka ma duka ko mey?"
"Idan da dukan nema ai da da sauk'i."
"Meyayi ma toh?"
"Ummi Nazeefah and Amal 'ya'yansa ne they're half sisters."
"What?"
"Alhj Abdallah ne mahaifin Amal, Matana 'yan uba ne Ummi
shine mahaifinsu duka."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un shin Afzal ka san mey kake
fad'i ma kuwa? 'Yan uwa fa kace?"
"Ummi dan Allah ki taimakeni Ummi bazan iya rayuwa ba
Amal ba."
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel kace mey? Amal 'yar Alhj
Abdallah ce? Yau na shiga uku na lalace Prince! Ya akayi
hakan ya faru? Ta ina Amal ta zama d'iyarsa?"
"Bana baki labarin Mami ba? Yadda akayi ta samu cikin
Amal?"
"Tabbas."
"Toh mahaifin Amal d'inne Alhj Abdallah shine yayi ma Mami
aika-aika ya gudu basu sake ji daga garesa ba."
"Yau wannan wace irin rayuwace? Wace irin mumunar
k'addara ce wannan? Innalillahi yanzu Alhj Abdallah yasan
yaran nan 'yan uwa ne amma be ta6a yin magana ba se
yanzu?"
"Cewa yayi shima recently yayi finding out gaskiya."
"K'arya yakeyi idan ba haka ba har ya akayi yasan Amal d'in
'yarsa ce." Labarin komi ya kwashe ya bata Ummi kam se
salati kawai take ta kasa yarda da komi da Afzal ya fad'a se
gani take kaman mafarki ne. Ta ina zasu fara 6ullo ma wannan
al'amari yanzu?
"Yanzu Amal ta sani?"
"Nayi kuskuren fad'a mata as a result ta samu miscarriage
Ummi mun rasa baby'n namu."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un wai shin meke faruwa ne yau?
Cikin Amal ya zube fa kace?"
"Ya zube Ummi yanzu haka tana kwance a gida likita yazo ya
dubata ya sa mata ruwa akan hakan kuma take cewa zata
koma gida, Ummi Amal na shirin tafiya ta barni ya zanyi da
raina ba d'a ba Amal ba Nazeefah haukacewa kukeson inyi
ne?" Ba shiri ya rushe da kuka. Hak'uri Ummi ta shiga basa
yayinda kanta yagama d'aukan zafi itama, ta rasa ta ina zata
fara 6ullo ma wagga al'amari ba abinda yafi k'ona mata rai
kaman lalacewar cikin nan na Amal, amma kam Alhj Abdallah
anyi mutumin banza. Ace duk zamanshin nan yana da 'ya a
waje?
"Ya isa haka Afzal crying is never a solution ka jira idan
Abbanka ya dawo musan nayi."
"I can't wait for that long Ummi, Amal bata da lafiya she
needs to be taken care of zan koma gida."
"Afzal kayi hak'uri amma dole Amal ta koma gida."
"Kema kin goyi bayan ta tafi kenan Ummi? Please don't ku
tausaya mun."
"Bawai ina nufin ta tafi har abada bane Afzal, ina nufin taje
gida na d'an lokacin nan ta samu kulawa mey kyau daga gun
Mami saboda kaima ba hankali a jikinka yanzu bale ka iya kula
da ita kai kanka kana neman kulawa."
"Ummi I can take care of her, zan kula da ita ni kawai kibar
zancen mayar da ita gida please."
"Toh Prince amma dey kasani koda bata koma yanzu ba zata
koma wataran ko?"
"Mey kike nufi Ummi?"
"Afzal har ka manta da cewa ya da k'anwa kake aura ne? A
ina aka ta6ayin hakan? A ganina kaman yadda Amal ta sanar
da kai hakan ne aure tsakaninka da dukansu ya haramta."
"No Ummi please there has to be a way, zamu nemi Malami
muyi tambaya in shaa Allahu ze san yadda zeyi damu."
"Prince don't get your hopes high."
""But Ummi I can't lose both of my wives ko za6i akace inyi
bazan iya ba bale kuma in rasasu duka. A tunani na idan suda
kansu suka amince zasu cigaba da zama as kishiyoyi
regardless they're siblings se mu cigaba da zaman mu tunda a
zamanin da ma ana had'a 'ya'yan Annabi Adam da Hauwa'u
aure."
"Ya kake magana haka Prince? Kai yanzu baka ji kunya ba da
gaskiya ya fito? An san ba laifinka bane amma ai da kunya
Prince, wa da k'anwa ne fa. Kar ka bari son zuciya ya rufe
maka ido ka aikata haramun, tun wani zamanin aka daina
had'a jini d'aya aure? Kuma a tunaninka su d'in zasu amince
au cigaba da zama tare ne yanzu bayan gaskiya ya fito?
Wallahi a'a zafin kishi ma baze bar su ba."
"Ummi ya zanyi toh? Wallahi muddin kuka bari aka rabani da
Amal toh nima kuyi shirin rasani because I can't do without
her."
"Nazeefah kuma fah?"
RANA DAYA Chapter 43
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
Tareda Naja'atu Lawal Rijau Niger State
@Whatapp 08083232323 or 09060202323
PAGE 43
"Ya Salaam! I don't know! I really don't know Ummi amma
bazan iya jure rashinsu duka ba because I love them both ko
za6i akace inyi bazan iya ba."
"Rabuwa da d'ayansu ko dukansu ya zama dole Prince kai
kanka ka sani."
"Bazan iya ba Ummi gara ni in mutu da in rasa d'aya daga
cikinsu."
Nauyayyen ajiyan zuciya ta sauk'e yayinda take tausaya wa
d'an nata tabbas yana cikin tsaka mey wuya "Yanzu ka kwantar
da hankalinka ka koma gida d'in kaje ka samu Amal tunda
bata jin dad'i gobe in shaa Allahu zan shigo."
"Allah kaimu" ya amsa.
"Yauwa nace su Mami fa ka sanar dasu?"
"Banyi ba tukuna but I'll."
"Ya kamata."
"Ummi tsoro nake kar suce zasu rabani da Amal."
"Baza suyi hakan ba in shaa Allah, kaide ka kwantar da
hankalinka ka kuma sa a ranka cewa komin meya faru shine
mafi alkhairi a gareka."
"Thank you Ummi bari in koma."
"Muje in raka ka."
"A'a ba amfani yi zaman ki" nan ya fice ya nufi motansa inda
ya zauna ciki yana tunani, gabad'aya ya rasa mey ke masa
dad'i. Wayansa ya zaro daga aljihu ya sake trying layin
Nazeefah luckily seya shiga sede yana soma ringing aka katse
cike da hanzari ya sake gwadawa wanda nan ma aka kuma
katsewa. Kansa ne ya d'aure yana cikin nazari sega sak'o nan
ta tura mai;
_I'm sorry I can't pick up your call, don't worry we're all fine._
Take yayi replying nata da;
_Alhamdulillah then, where are you at?_
Cikin minti d'aya reply nata ya iso
_Mummy ta kama mana d'aki a hotel zamuyi magana gobe
goodnight._
Ajiyan zuciya ya sauk'e atleast they're safe, ko bey tambaya
ba yasan Mummy ce ta hanata sanar dashi inda suke saboda
gudun kar Daddy yayi saurin ganosu. Oh Allah!
Key yasa ya kunna motan ya dawo gida. Har anan bacci
Amal ke, kayan jikinsa ya rage sannan ya duba ledan ruwan
nata yaga da ragowa, gadon ya haye ya sameta inda ya
kwanta a gefenta had'e da aza kanta a k'irjinsa wanda a
sanadin hakan ta farka.
"Shhh go back to sleep it's just me" ya sanar da ita yana
shafa bayanta a hakan har ta sake komawa baccin. Shi kam se
tuna abinda Ummi ta fad'a masa yake _Rabuwa da d'ayansu
ko dukansu ya zama dole Prince kai kanka ka sani._
Wajajen tara da rabi ya farka bayan yayi alwala yayi sallah ya
zarce kitchen ya kad'a wa Amal kununta sannan ya dawo ya
shiga tayar da ita. Taimaka mata yayi ta wanke bakinta sannan
ya bata kunun da kansa bayan nan ya 6allo mata magunanta
ta had'iye.
"Wa zaka kira?" Amal data k'ura masa ido ta tambaya ganin
ya d'ago wayansa.
"Ummi, tace in kin tashi in had'aku ta gaisheki da jiki" bata
sake cewa komai ba har se lokacinda Afzal ya had'asu suka
gaisa. "Mami fa yaushe zaka kira su?"
"Zan kira su Amal amma ba yanzu ba."
"Se yaushe Yaya?"
"Meyasa kika k'osa in kirasu Lily? Didn't we talked about
this?"
"Yaya I'm sorry I jus-"
"Ya isa please you're sick don't stress yourself. Zaki watsa
ruwa?" Kai ta kad'a masa zalla sannan ya mik'e ya ciro mata
kayan baccinta ya taimaka mata tasa. Bayan ta kwanta ya
d'aura mata sabon ledan drip d'in sannan suka kwanta.
Washegari kaman yadda Ummi tayi alk'awari tazo ta gidansu
da breakfast mey kyau da kuma kunun Amal da ta dama mata
cikin flask. Har cikin d'aki ta shigo suka gaisa da Amal sannan
suka dawo parlour ita da Afzal.
"Na sanar da Abbanka halin da ake ciki jiya."
"Meyace?"
"He was also shocked and disappointed at his friend mun
kuma samu mun tambayi Malamai har biyu mun kuma samu
amsa iri d'ai daga garesu."
"Mey suka ce Ummi? Zan iya ajiye su duka?"
"Kai ma kasan hakan ba mey yiwuwa bane Prince."
"Innalillahi! Then mey suka ce? In rabu dasu duka?"
"Sunce ya zamo dole ka d'au d'aya ka saki d'aya."
"What? So kuke in za6i d'aya daga cikin Amal da Nazeefah?"
"Yes Afzal."
"Ta yaya Ummi? Taya kukeson in d'au d'aya in saki d'aya?
Shin idan nayi hakan nayi adalc kenan?"
"Abinda yazo a shari'ance kenan, so sakan d'ayan su ya zamo
dole idan har zakayi abinda addininka yace."
"No Ummi there has to be another way. Bazan iya za6an
d'aya daga cikinsu ba I love them both yaushe ne zaku fahimci
hakan? Is like choosing between air and lungs I can't because
I need both to survive."
"Ya zama dole ka d'au d'aya acikinsu Afzal."
"No Ummi I can't!"
"Yes you have to, dubi nan" wayanta ta bud'e ta shiga kan
sak'on da malaman suka turo musu bayan tambayan da sukayi
inda ya shiga karancewa tun daga farko kaman haka;
arfrur
8442: Is it permissible to marry two sisters from one father at
the same time?
A man has 2 wives and from each wife he has 1 daughter. Is
it permitted for someone to marry the 2 daughters at one time
(who of course have the same father but different mothers)? I
am aware that it is not permitted to be married to 2 blood
sisters at the same time, but is the case mentioned above
slightly different?
Published Date: 2000-05-01
Praise be to Allaah.
It is not permissible to marry them at the same time, because
they are sisters, regardless of whether they share the same
father and mother, or they have only one parent in common,
because of the aayah (interpretation of the meaning):
“Forbidden to you (for marriage) are: … two sisters in wedlock
at the same time, except for what has already passed” [al-
Nisaa’ 4:23]
It was reported from Abu Hurayrah that the Messenger of
Allaah (peace and blessings of Allaah be upon him) forbade
marrying a woman then her paternal aunt, or a paternal aunt
then her brother’s daughter, a woman then her maternal aunt,
or a maternal aunt then her sister’s daughter, or an older
sister then the younger sister, or a younger sister then the
older sister.” (Narrated by al-Tirmidhi, no. 1045; Abu Dawood,
no. 1768. Al-Tirmidhi said, it is hasan saheeh).
Fayrooz al-Daylami said: I came to the Prophet (peace and
blessings of Allaah be upon him) and said: O Messenger of
Allaah, I have become Muslim and I am married to two
sisters. The Messenger of Allaah (peace and blessings of
Allaah be upon him) said: “Choose whichever of them you
want [i.e., and divorce the other].” (Narrated by al-Tirmidhi,
1048; Abu Dawood, 1915, et al.)
_A hausance_
[Shin ya halatta namiji ya auri mata biyu wadanda suka
kasance ubansu daya a lokaci daya?]
[Mutum ne ya kasance yana da mata biyu kuma daga
kowacce mace yana da d'ya guda d'aya da ita. Shin ya halatta
namiji ya auri yaran nan da suke uba d'aya a lokaci guda?
( wad'anda suka kasance ubansu guda amma kowacce da
mahaifiyarta)?
Bai halatta namiji ya auri mata guda biyu da suka kasance
yan'uwan juna ba maana yan'uwa na jini da ya kasance ubansu
guda]
[Sai dai idan case din da aka ambata yasha banban da wannan
ne?]
[Allah ne mafi sani]
[Ya haramta ga namiji ya auri mata biyu da suka kasance
yan'uwan juna na jini koda kuwa uwa kawai suka had'a ko uba
kawai suka had'a ko kuma uwarsu d'aya ubansu d'aya saboda
fad'ar Allah madaukakin sarki a cikin Al-Qur'ani mai girma.]
[An haramta maku (game da aure) ka auri mata biyu yan'uwan
juna na jini a lokaci guda, sai dai abinda ya riga ya wuce na
baya.
(Suratun Nisaa'ee 4:23)]
[An kar6o daga Abu Hurayrah daga manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi yace; an haramta ma
namiji ya auri mace Sannan ya auri gwaggonta ta dangin uba,
ko ya auri Gwaggon mace ta dangin uba sannan ya auri d'iyar
k'ani/wanta.]
[Ko ya auri mace Sannan ya auri k'anwar innarta ta dangin uwa
ko ya auri k'anwar inna sannan ya auri d'iyar K'anwa/yarta.]
[Ko ya auri Yaya Sannan ya dawo ya auri K'anwa.]
[(Al-Tirmidh N01045 da Abu Dawood N0 1678 ne suka
ruwaito shi. Al-Tirmidh yace hadith ne mai kyau ingantacce)]
[Fayrooz Al-Dalaylami yace" Nazo wajen manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi sai nace "ya manzon Allah
na musulunta amma kuma ina auren mata guda biyu yan'uwan
juna na jini ( a lokacin daya auresu yana kafiri ne baisan
hukuncin yin hakan ba) sai manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi yace; "ka za6i wadda tayi maka a
cikinsu sai ka saki dayar"]
[Abu Dawood N0 1915, Al-Tirmidth 1048 da sauransu suka
ruwaito shi.]
"Kaga anan tunda kaima a bisa rashin sani ka auri Nazeefah
tukun kazo ka auri Amal, se Malamai sukayi amfani da
wannan hadisi sukace kai ma zaka d'au d'aya ne ka saki d'aya
tunda ba ba tare da sani ba ka auresu ba, da ace da gan-gan
kayi hakan saboda son kai se ya zammana duka biyu sun
haramta maka. Amma tunda ba da sani bane se aka baka
za6i, kaga fa ba'a ce lalle se ka saki Amal ka zauna da
Nazeefah ba saboda Nazeefah ce uwar gida, kuma ba'a ce
lalle seka saki Nazeefah ka zauna da Amal ba saboda Amal ce
babba. Za6i suka baka kaman yadda Annabin Rahama ya bawa
wancan mutumin shima." Ummi ta sake yimar bayani.
Shiru yayi zaune a wajen yayinda zuciyansa yake yi masa
wani irin k'una, ina ma ace ba a ta6a k'addaro masa da rana
irin ta yau ba? Ina ma ace shi kam mutuwa kawai zeyi ya
zamanto ba seya za6i Amal ko Nazeefah yabar d'aya daga
cikinsu ba. Shin yanzu idan ya saki Amal yabar Nazeefah yayi
wa Amal adalci kenan? Kokuwa idan ya saki Nazeefah yabar
Amal yayi wa Nazeefah adalci? Wa ze d'auka wa kuma ze bari
a cikinsu?
"I can't do this Ummi dan Allah karku tilasta mun" ya sanar
da ita daga bisani.
"Kayi hak'uri Prince kowa yasan da zafi da ciwo amma dole
ne muyi amfani da abinda shari'a ya kawo mana saboda
gudun 6acin ran Ubangijin mu kuma kasani fa inna ma'al usri
yusrah, kowani musiba na tare da sauk'i. Take for instance
yanzu ace duka Amal da Nazeefan ne suka haramta maka ya
zakayi? Amma seka duba privilege da addininka yayi maka na
halatta maka d'aya acikinsu kayi godiya wa mahaliccinka."
"Hakane Ummi But wa zan d'auka wa zan bari?"
"This is not my decision to make Afzal, ka zauna kayi tunani
in shaa Allahu zaka samu amsa ga wannan tambaya, idan
kuwa hakan ya gagara se kayi istikhara, babu sharri acikin
za6in Allah duk wacce tafi kwanciya maka a rai itace za6in ka
seka ajiyeta ka sauwak'e wa d'ayar, ba wanda zeyi maka
mumunar fahimta. Batun iyayen Amal kuma ka tabbata ka
kirasu yau kokuwa kaje ka samesu ka sanar dasu halin da ake
ciki hak'k'insu ne su sani, Allah shige ma gaba."
"Ameen" ya amsa da k'yar bakinsa yana rawa.
"Ni bari in koma se anjima" bayan ficewanta Afzal da kowani
ga6a da sassan da suke jikinsa sun mutu sunyi lis ya mik'e a
kasalance, a corridor'n d'akinsu ya tarar da Amal tsaye wajen
se kuka take shark'af-shark'af. Wani irin tsinkewa gabansa yayi
bade taji duk abinda shida Ummi suka tattauna akai ba?
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
"Amal?" Ya kira sunanta da hanzari ta juya mai baya ta
k'arisa cikin d'akin bata kai ga rufe k'ofan ba ya hankad'e ya
fad'a ciki. "Amal please stop crying" ya buk'aceta cikin sanyin
murya yayinda yake k'ok'arin rik'o hannunta sede ta hanasa.
"Amal please enough ke baki san kukan nan rashin lafiya ze
k'ara miki ba?"
"One of us have to go Yaya" ta fad'a tana mey share abinda
yace mata.
"Amal-"
"Dole ka rabu da d'aya tsakani na da 'yar uwata koba haka
ba?"
"Am-"
"Just answer me Yaya na riga naji komai."
"Yes Amal amma dan Allah ki kwantar da hankalinki."
"Tayaya? Tayaya kake tsammanin zan iya kwantar da
hankalina Yaya bayan ina shirin rasa mijina mafi son komai a
rayuwata? Mijina wanda na d'au mutuwa ce kad'ai zata iya
raba mu? Mijina da na d'au shine mahaifin yaran da zan haifa?
Wanda farin cikin rayuwana ya dangana a jikinsa? Ta ina
hankali na yaga ta kwanciya Yaya? I'm about to lose you, I'm
about to lose the love of my life, my soul, my spirit, and my
everything!" Kawai ta fashe da wani irin kuka. Tsan-tsan
tausayi Afzal be san a lokacinda hawaye suka ciko masa a
ido ba, ashe itama Amal haka take sonsa kawai bata nunawa
ne? Ashe tana iya shiga damuwa idan har rabuwa ya shiga
tsakaninsu? Ya d'au shi kad'ai ze sha wuya a rashinta ashe
itama rayuwanta na iya fad'awa gwagwarmaya a rashinsa
wow!
"Amal please enough kibar kukan haka."
"Wa zaka d'auka acikinmu Yaya?"
"Amal please-"
"Just answer me Yaya" ta katsesa cike da tashin hankali "Just
answer me please."
"I don't know Amal saboda I can't choose, kaman yadda
bazan iya jure rasa ku duka ba haka ma bazan iya d'aukan
d'aya in bar d'aya ba. I love you both, I really do."
"But one of us has to go, baka ji abinda Ummi tace bane?"
"I know I just... I just don't know ni kawai kibar kukan nan."
"Bazan ta6a iya daina kuka akanka ba Yaya because I love
you, I love you so damn much shiyasa rabuwa da kai yake
min zafi, gani nake kaman idan na rasaka nima ina iya rasa
nawa ran" da sauri ya katseta "But Amal you're not going to
lose me bance Nazeefah zan d'auka in bar kiba."
"I don't know Yaya, ban sani ba ko Nazeefah zaka d'auka
akaina but I just want you to know that my everything revolves
around you, I don't think bayan kai zan iya kwad'aita wa
zuciyata son wani d'a na miji because my heart is with you
Yaya, I can never stop loving you" ta k'are tana kuka. A nitse
ya rik'o hannunta maras canular cikin nasa yana murzawa a
hankali "And I can never stop loving you too Amal I'm not
picking Nazeefah over you kema kin sani."
"But one of us has to go."
"Se kuma aka ce kece zaki tafi? Kin manta cewa zuciyana
baya bugawa se ya ji ki a kusa dashi? Kin manta cewa without
you I'm nothing? kin manta cewa ke kad'ai ce hasken da nake
buk'ata a rayuwa na da kuma Iskan da nake buk'ata dan in
rayu? Kin manta da duka hakan ne Amal?"
"Not for once did I forget any of these Yaya saidai a wannan
hali da muka tsinci kanmu yanzu nake ganin soyayyar mu ma
tayi kad'an ta ceto mu daga cikinsa."
"Meyasa kika ce haka Amal? I thought our love for one
another was enough."
"I'm sorry Yaya but it isn't."
"Amal it is because I'll never leave your side, I came into your
life to stay forever not just for some time because I love you, I
love you Amal morethan anything you could ever imagine."
"And I love you too Yaya, morethan life itself. Your love is
incomparable amma rabuwa ce ta zamo dole."
"Ba se mun rabu ba Amal dan Allah kibar cewa haka."
"Dole ne in fad'i haka Yaya, dole ne mu cire son zuciya muyi
abinda ya kamata."
"Mey kike nufi?"
"Ina nufin Nazeefah. Nazeefah k'anwatace Yaya kuma komin
yaya ina sonta komin mey tayi mun I'll always want the best
for her. Kai kanka kasan irin son da Nazeefah keyi maka, ka
kuma san cewa akan ka Nazeefah na iya yin komai, bazan so
ace a matsayina na 'yar uwarta kuma yarta ba na shiga
tsakaninta da masoyinta. I don't care ko ita bata feeling
thesame way I feel towards her, ban damu ko tana so na ko
bata sona ba, ban damu koda nice mak'iyar ta a duniyan nan
ba as long as she's my sister I'll love her and want only the
best for her, this is why I'm giving up on you for her."
"Amal kin kuwa san mey kike cewa?" Afzal da mamaki ya
rufesa ya tambaya.
"Yes Yaya, ina sonka amma hakan ba wai na nufin zan
cigaba da mallakanka bane, na yafe soyayyar ka wa k'anwata
na hak'ura ni ka sauwak'e mun ku kucigaba da zama tare,
seeing my sister happy is enough to make me happy."
"I can't Amal" ya amsata a raunane "Bazan iya rabuwa dake
ba, bazan iya ba."
"Zaka iya Yaya, ni kaina nasan how hard life will be for me
without you amma ba komai mukeso a duniya muke samu ba,
wani sa'in dole muyi making sacrifices koda kuwa akan
abunda muka fi so ne it is why I'm doing this. I love you but I
have to let you go."
"No Amal dan Allah kibar cewa haka, you're not leaving me
you're not."
"Yes I am Yaya, you have to let me go."
"No I can't I can't live without you."
"Idan baza ka iya rayuwa ba ni ba Nazeefah kuma fa? Mey
zakayi da ita?"
"I don't know Amal, but I can't afford to lose you."
"Kaman yadda kake jin bazaka iya rabuwa dani ba itama
Nazeefah haka take ji Yaya, haka take jin bazata iya rabuwa da
kai ba. Ka fini sanin yadda take sonka let's do this for her kar
mu bari sharrin laifin Daddy ya fad'a kanta."
"Ke kin amince ya fad'a a kanki kenan Amal? Keda Daddy
yafi cutarki da mahaifiarki?"
"Yes Yaya na hak'ura hakan ya fad'a akaina saboda
InnAllaha ma'as sabireen I'm sure Allah will listen to my silent
cries and see me through."
"But I can't Amal, bazan iya jure ganinki cikin bak'in ciki da
k'unci ba kullum. Kece aka sameki ta haramtacciyar hanya,
kece kika girma ba uba, kece kikayi girma cikin talauci bayan
kaman yadda Nazeefah tayi girma cikin kud'i da kulawa da jin
dad'i kema kin cancanci hakan amma haka akayi depriving
naki, bayan nan kece kikazo aure kina ji kina gani aka rabaki da
masoyinki na asali aka sanya ki aurena na dole dukda bakiya
so. For all your life you've never been happy-"
"But you made me happy Yaya" tayi saurin katse sa da
murmushin takaici d'auke a fuskanta "zan iya cewa ranakun
da na zauna da kai sune mafi farin ciki da murna a rayuwa na
gabad'aya, the happy moments I've spent with you have
erased every single bad day I've witnessed before and I'm
morethan thankful to God, I cannot ask more for more. You
gave me only the purest form of love, koda Papi ya sanar
dakai asalina baka k'i ni ba, baka k'iyamace ni ba infact sema
k'ara nuna mun so da kayi. You loved me as if your life
depended on it, ka bani kulawan da bayan Mami da Papi ba
wanda ya ta6a bani irinsa, your love was simply enough for
me Yaya so karka damu dani, I'm morethan satisfied."
Be iya ya sake cewa komai ba kawai tuna kalaman Nazeefah
yake da take cewa _No Daddy, bazan rabu da Ya Afzal ba idan
ma akwai me rabuwa da Ya Afzal toh Amal ce not me_ shi
kansa ya sani baza a ta6a had'a halatayyan Amal dana
Nazeefah ba, they're two different people. Idan akwai kalma
d'ayan da Nazeefah ta sani wanda Amal bata sani ba shine
'Son Kai' ko shi baze iya yin abinda Amal tayi ba yanzu. Janta
yayi jikinsa kawai ya rungumeta yayinda ta kuma rushewa da
wani kukan tsuma zuciya. Kukan ta cigaba da yi ajikinsa
yayinda ya rik'e ta tsam a jikinsa, seda tayi mey isarta sannan
ya d'agota ya shiga share mata hawayen nata inda ya jata
bakin gadon ya kwantar da ita had'e da sa mata sabon ledan
ruwan. "Rest okay?"
Kai zalla ta gyad'a masa be kai ga mik'ewa ba wayansa dake
aljihu ya shiga ruri dubawanda zeyi yaga Nazeefah, ba tare da
6ata lokaci ba ya d'aga "Nazeefah?"
"Na'am Ya Rouhi ina kwana?"
"Lafiya ya kike? Ya su Mummy?"
"We're all good."
"Wani hotel kuke? I need to see you."
"Deribe Hotels" ta sanar dashi.
"I'll come pick you up okay? Tell Mummy ni nace zan zo in
d'aukeki."
"I'll seka zo."
"Yauwa ba-bye." Nan ya katse tare da kewayowa kan Amal
data k'ura masa ido. "Zanje gida gun su Mami domin sanar
dasu halin da ake ciki okay? Daga nan inje in duba Nazeefah."
"Allah ya kare."
"Ameen I love you" ya sanar da ita had'e da sauk'e mata
peck a goshi sannan ya mik'e ya fice bayan ya ja wa mey gadi
kunne akan cewa komin yaya kada ya bar Amal ta fita. Daddy
yayi ma waya yace yaje ya samesa a gidan Nazeefah sannan
ya wuce Deribe hotels yaje ya d'auko Nazeefah inda suka nufi
gidansu Amal. Nazeefah da bata san ina yake kai su ba se
tambayan sa take ina ne nan, shi de iyaka ce mata yayi ze d'au
wasu mutane ne shikenan. Ciki ya shiga suka gaisa da su Papi
inda yake sanar dasu cewa Amal tayi 6ari bata da lafiya yazo
ya d'aukesu ne suje su dubata. Cikin k'ank'anin lokaci suka
shirya suka fito, sanin halin Nazeefah ba lallai ne ta yarda ta
koma baya haka kawai ba se yayi mata k'aryan cewa Papi d'an
uwansa ne Mami kuma matarsa ce don haka tayi hak'uri su
zauna da matar a baya se shi ya zauna a gaba. Batayi
gardama ba ta samu Mami suka zauna a baya bayan sun
gaisa.
Sude su Papi ko da suka ga Afzal ya d'au wani hanya daban
bana gidan Amal ba basuyi magana ba. Ahaka har suka isa
gidan Nazeefah suka k'arisa ciki. Fitowan da zasuyi daga
motan Nazeefah ta hangi Daddy dake zaune akan varenda
akan d'aya daga cikin kujerun da aka ajiyesu a wajen.
"Ya Rouhi meyasa ka kawo ni bayan kasan Daddy na nan?"
"Enough Nazeefah we're here to sort out things."
"Not when Daddy is around take me back to Mummy."
"Ya isa Nazeefah I know this is not easy on you amma kiyi
hak'uri magana kawai zamuyi shikenan."
"Ni bana so banida sauran abinda zance masa tunda ya
had'ani kishi da 'yar uwata."
"Nazeefah please" Afzal yayi mata ido wanda hakan yasa
tayi shiru.
Na sosai Mami da Papi suka shiga rud'ani domin a iya
saninsu de kaman yadda Afzal ya gabatar musu da Nazeefah
ce musu yayi ita matarsa ce toh mey take nufi da cewa
mahaifinta ya had'ata kishi da 'yar uwarta? Shin Afzal d'in
mata nawa ne garesa?
"Afzal lafiya dai ko?" Papi da ya kasa hak'ura ya tambaya
cike da rud'ani.
"Yi hak'uri Papi mu shiga daga ciki Mami, Nazeefah let's go
in." Har anan Papi da Mami basuga fuskan Daddy ba
kasancewar bayan sa ne ke fuskantansu itama Nazeefah dan
sanin da tayi masa yasa ta gane shine. Sun k'arisa corridorn
kenan Afzal yayi gyaran murya inda Daddy ya juyo idanunsa
wanda basu sauk'a a ko ina ba se akan na Papi da Mami.
Daga kan kujeran amma sanda yaci tuntu6e kad'an ya rage
kujeran be yasar dashi a k'asa ba yasamu ya tari kansa. A
rikice ya mik'e tsaye yayinda idanunsa dana Mami suke a
had'e har anan, ita kanta Mami dan mamaki ta kasa yin
magana haka Papi ma se k'ura wa juna ido kawai suke. Daga
bisani Daddy ya kira sunan Mami.
"Jamee?" Da mamaki Nazeefah ta tsaya kallonsa tana mey
tambayan kanta ta inda akayi Daddy yasan 'yan uwan Afzal
'yan uwan ma ba dangin kusa ba. Tun ganinsu da tayi
talakawa ta yanke hukuncin irin dangin nesa-nesa d'innan ne
su.
"Khaleefah?" Mami ta ambaci sunansa baki na rawa. Yau
shekaru nawa? Sama da ashirin, ashirin da biyu kenan. Ashe
dey Allah ze sake had'asu. Ashe de zata sake sanya mutumin
daya cuceta ya kuma 6ata mata rayuwa a ido. Nazeefah kam
kanta ya gama d'aurewa yanzu se raba ido take.
"Afzal meke faruwa anan? Waye mutumin nan? Meyasa
kuma ka kawo mu gidansa?" Papi ya kewayo yana kallon
Afzal.
"Mu shiga daga ciki dan Allah zan sanar da ku komai."
"Papi mu koma" cewan Mami had'e da juyawa. "Ba cikin da
zamu shiga."
Da hanzari Afzal ya sha gabanta "Please don't walk away
Mami, please kar ki tafi."
"Na d'au cewa kayi Baby tayi 6ari bata da lafiya" Ido
Nazeefah ta zaro waje cikin Amal ya zube? Shikenan bata da
wata tsoro yanzu, dama cikin nan shine tsoronta, kar don cikin
Afzal yace ze d'au Amal akanta. Amma yanzu da ya zube ta
tabbata idan ma za6i aka basa acikinsu biyu inhar ma basu
haramta masa ba kenan ta tabbata ita za a sanya sa na dole
ya d'auka tunda itace uwar gida.
"Yes Mami and ba k'arya nake muku ba I intend to take you
to her idan mun gama warware matsalar dake nan."
"Wace matsala kenan?" Papi ya tambaya.
"Papi wannan shine mahaifin Nazeefah matata."
"Mahaifin matarka?" Ya kuma tambaya.
"Eh Papi."
"Ka san mey kake fad'i kuwa Afzal?" Mami da ta kewayo ta
jefa mar tambayar "kasan kuwa wannan azzalimin mutumin
shine mahaifin Amal?"
"Eh Mami mahaifin Amal kuma mahaifin Nazeefah."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Papi yasa salati. "Jameela
yaran nan 'yan uwa ne" yace da Mami da tuni idanunta suka
ciko da hawaye.
Nazeefah kam se raba ido take yayinda abun ya tsaya mata a
wuya, yanzu Daddy ya rasa da wa zeyi barikanci ma seda irin
Mami?
"Mey nayi maka a rayuwa da ka za6i kayi ta k'untata mun
haka Khaleefah?" Tace da Daddy da har yanzu be kuma cewa
komai ba idonta na tsiyayar da hawaye. "Duk kalan zalunta ta
da kayi ka lalata mun rayuwa hakan beyi maka ba seda ka
dawo kan 'yata?" Anan kan Nazeefah ya sake shiga duhu aww
wai dama ba karuwar Daddy bace? Tarketa Daddy yayi ya
d'irka mata ciki? Oh Allah! Wannan abun kunya da mey yayi
kama ace a gaban mijinta ana tuhumar mahaifinta da aikata
zina. Ji tayi gabad'aya ya fita mata daga rai bata k'aunansa.
"Jamee-"
"Allah ya isa Khaleefah, Allah ya isa tsakani na da kai."
"Mami dan Allah kiyi hak'uri mu shiga ciki muyi magana"
Afzal yace.
"Wani magana zamuyi Afzal? Ya kama ya had'a 'yan uwan jini
kishi wani magana ne kuma za'a sake yi wanda yafi a
sauwak'ewa yaran duka? A tunani na da gan-gan yayi hakan
dan ya mayar mun da 'ya bazawara."
"Jameelah dan Allah kiyi hak'uri wallahi ban san cewa rabo
ya shiga tsakanin mu ba-"
"Dakata Khaleefah" Papi ya katsesa "Bamu buk'aci jin komai
daga bakinka ba, mu shiga Afzal muji abinda kake tafe dashi
muje Jameela." Ba don Mami na so ba ta bi bayan Papi suka
k'arisa ciki inda Afzal ya bayyana musu halin da ake ciki tun
daga kan lokacin da aka bige Amal zuwa lokacinda Daddy
yagano gaskiya dama komai, daga k'arshe kuma ya sanar
dasu tambayan da sukayi wa malamai da kuma amsan da
suka samu. Na sosai hankalin Nazeefah ya tashi, acewarta
baza a bawa Afzal za6i ba ita za'a sanyasa ya d'auk'a na dole
ashe ba haka abin yake ba. Ita kam ma bata yarda ba. Zata
nemi wani Malami tayi mar tambaya ta tabbata za a samu
sa6ani tsakanin amsan da Afzal ya samu. In ba haka ba ina
zata sa ranta idan Afzal ya za6i Amal akanta? Yau nata ya
k'are.
"Tabbas wannan abu da kunya yake da kuma zafi ace 'yan
uba suna auran miji d'aya. Anan Allah yana nuna mana cewa
komin yaya mutum yayi baze ta6a iya yi masa wayo ba kuma
muddin kad'au alhak'in mutum baka nemi yafiya ba toh tun a
duniya Allah ze fara kamaka ya nuna maka illan yin hakan.
Saidai ina son ka kwantar da hankalinka Afzal kasani wannan
k'addarar bata su Amal ce kad'ai ba no harda kai kaima. Ka
kuma sani kai kake da za6i tsakaninsu, kuma duk wacce ka
za6a bawanda ya isa ya tambayeka meyasa. In shaa Allahu
duk nan zamuyi maka kyakkyawar fahimta mu baka goyin
bayan da ya kamata Allah shige ma gaba" Papi yace.
"Ameen" Afzal ya amsa "Nagode Papi."
"Se yaushe kenan zamu sake ji daga gareka?" Mami ta
tambaya.
"Wannan ba abu neba mey sauk'i Mami, ba abu neba da zan
iya yinsa da kaina acikin k'ank'anin lokaci amma zan dey yi
k'ok'ari inga ban ja lokaci ba."
"Gaskiya ya kamata saboda kowa yasan inda ya tsaya, ba
yaran kad'ai ba harta mu manyan ma" Papi ya amsa.
"Tabbas Papi saidai ban san wa zan d'auka wa zan bari ba
acikinsu don gudun yima d'ayarsu rashin adalci, shiyasa na
yanke hukuncin yin istikhara duk za6in da Allah yayi mun shi
zan bi dafatan idan nayi hakan both parties bazasu ga kaman
anyi musu rashin adalci ba zasu kuma fahimceni."
"Ai zancen rashin adalci ma bai taso ba Babana, za6i naka
ne ba wanda ya kai ya tilasta maka."
"Nagode sosai Papi idan ba abinda zaku sake fad'a semu
wuce gida kuje ku duba Amal."
"Babu mu tafi" Mami ta amsa cike da hanzari.
"Papi dan Allah kayi hak'uri nasan abinda nayi muku is
unforgivable nasan banida right na baku hak'uri amma dan
Allah kuyi hak'uri ku saurareni wallahi tallahi ban san rabo ya
shiga tsakani na da Jameelah ba, ban ta6a sanin Amal 'yata
bace se lokacin da tayi hatsari. Meyasa zan so in had'a
'ya'yana biyu kishi? Dan Allah ku saurareni."
"Jameelah kina da abin cewa?" Papi ya juyo had'e da
tambayan Mami.
"A'a Abba mu tafi" ta amsa tamkar bataji abinda Daddy ya
fad'a ba. Nan suka mik'e duka "Ermm Ya Afzal can I have a
word with you? Papi ku d'an yi hak'uri dan Allah" fad'in
Nazeefah.
"Ba komai muna jiranku a waje." Hannun Afzal taja izuwa
d'akinsu sannan ta rufe k'ofan.
"Ya Rouhi za6a zakayi tsakani na da Amal kenan yanzu?" Ta
tambayesa a maraice.
"Nazeefah I have no other option inda ta nine da saidai in
cigaba da zama daku duka because I love you both."
"Nasan Amal zaka d'auka akaina I know."
"Please don't talk like that."
"Ka k'aryata hakan ne? Ka k'aryata cewa ba Amal zaka za6a
ka sauwak'e mun ba?"
"Nazeefah please-" yana yunk'urin ta6a hannunta ta ja da
baya. "For all my life, I've loved you Ya Rouhi, banida burin da
yafi inga na kasance tare da kai na sanya ka farin ciki. Duk
wani abinda nayi da abaya wanda ya 6ata maka rai kasani nayi
ne because I love you, saboda nafi son in mallakeka ni kad'ai.
Dukda auren biyayya mukayi I'll still choose you to be my
husband if I were to be given a second life. Lokacin da na fara
jin dad'in aurena kawai ka auro mun Amal out of the blue.
Amal da na tabbata kafi sonta acikin zuciyanka fiye dani
saboda ita za6in zuciyarka ce nikuwa za6in mahaifinka ne."
"Nazeefah-"
"Ba seka k'aryata komai ba Ya Rouhi hakan ne kuma nima na
sani. Kafi son Amal a kaina wai tayaya ma bazaka fi sonta ba
bayan she's fertile wataran zata haifa maka yaran da kata
mafarki kake so ni kuwa mey zan iya baka? Babu saboda ga
dukkan alamu juya ce ni."
"Nazeefah enough please ke kanki kinsan ba haka bane, ke
kanki kinsan ke ba juya bace."
"Then explain to me why shekarana sama da uku a gidanka
amma ko 6atan wata ban ta6ayi ba."
"Saboda kowa da lokacinsa ne Nazeefah" ya sanar da ita a
hankali yana mey d'ago hannayenta yana had'asu da nasa.
"Saboda Amal ta rigaki conceiving doesn't mean ke bazaki
ta6a iya d'aukan ciki ba. Ina kika mance da tarihin Annabi
Ibrahim da matarsa Saratu? Shin kin mance a tsufansu suka
haifi Annabi Isma'il? Haihuwa lokaci ne Nazeefah, saboda
Amal ta rigaki doesn't mean you're sterile. I believe in you
Nazeefah kuma ni koda ma bazaki iya haihuwa ba hakan baze
dameni ba ai dama ba jayayya mukayi kafin mukayi aure cewa
dole dole se kin haihu min ba."
"Then pick me over Amal, idan har kana nufin abubuwan da
ka fad'a ka d'aukeni ka saki Amal." Da mamaki Afzal ya tsaya
kallonta yayinda kalamun Amal suke dawo masa yadda ta cire
son kai ta nuna lallai lallai ita ta hak'ura ya d'au Nazeefah
akanta.
"Nazeefah shin bakiya tausaya wa 'yar uwarki ne ke?"
"Tausaya mata? Meyasa zan tausaya mata Ya Rouhi bayan
tana shirin sace mun mahaifi da miji?"
"Amal bata da niyyan hakan kema kin sani Nazeefah,
k'addara ce ta riga fata ba ita ta za6i mahaifinku ya zama
d'aya ba, ba ita ta za6i mijinta ya kasance d'aya dake a
matsayinki na 'yar uwarta ba, k'addara ce."
"Amal ba 'yar uwa ta bace Ya Rouhi duk wanda yake shirin
rabani da kai ba d'an uwana bane. I love you Ya Afzal, kuma
ba kai bana jin zan iya rayuwa. Nasani yadda nake sonka ba
haka kake sona ba but for once please choose me over Amal.
For once ka nuna min kana sona nima let me feel loved Ya
Rouhi. It has always been Amal, komai Amal komai Amal let it
be this time, let it be Nazeefah. Please choose me over her I
love you Ya Rouhi so much."
"Nazeefah I love you too, kema kin san hakan."
"Then choose me ka d'aukeni ka saki Amal."
"But I'm not the one to decide Nazeefah. By Allah ko wuk'a
aka sa min a wuya bazan iya za6an d'aya acikinki da Amal ba.
It's not as easy as it seems."
"I know it's Amal you're going to pick dukda hakan I want
you to know that I'll never stop loving you Ya Rouhi, koda ka
d'au Amal akaina hakan bazesa in daina sonka ba saidai in
tsani Amal na shiga tsakani na dai da tayi. I love you so much
Ya Rouhi" ta k'are idanunta na cikowa da hawaye. Janta yayi
jikinsa ya rungumeta tsam yayinda take k'ok'arin k'watan
kanta.
"Just let me go Ya Rouhi" ta fad'a tare da k'watan kanta
daga jikinsa, idanun nan sun kumburo sun kad'a sunyi ja
"Muddin ka za6i Amal a kaina bazan ta6a yafe maka ba Ya
Rouhi, I can never forgive you for causing me this so much
pain" tana kaiwa nan ta bud'e k'ofan ta fice yayinda Afzal yake
ta kiran sunanta. Daddy taje ta sama a parlour tace ya kaita
gun Mummy. Jiki na rawa ya mik'e suka fice dama so yake
yasan inda suke.
Afzal kam kansa ya gama d'aurewa, gabad'aya tausayin
Nazeefah yabi ya mamayesa shi kansa yasan bey kyauta mata
ba idan har ya saketa. Shi kamsa shaida ne gamey da irin son
da take nuna masa. Toh Amal fa? Ya zeyi da ita itama? Haka
nan ya fito sam babu walwala tattare da shi yaja su Papi suka
wuce gida inda suka duba Amal.
"Mami nida N-" tuna Afzal ya mata kashed'i se tayi shiru.
"Na riga na sani Baby, Afzal ya sanar damu komai" Mami ita
sanar da ita. "Allah na tare de ke kinji? Karki tada hankalinki
Allah k'ara lafiya."
"Ameen" so take ta ce mata ita zata bisu gida amma dan
ganin idon Afzal se tayi shiru, yana ficewa kuwa ta sanar dasu
tana son ta bi su.
"Kema kinsan hakan ba me yiwuwa bane Baby. Bamu keda
iko akanki ba, baze yiwu kina matarshi mu tafi dake haka
kawai ba tare da izininsa ba. Ki k'ara hak'uri nan da d'an lokaci
zamu san ajin da muke ciki." Lokaci kad'an su Mami suka
k'ara sannan Afzal ya mayar dasu gida. A hanyansa na
dawowa ya kira layin Nazeefah sede har ya tsinke bata d'aga
ba. Ba kuma wai bata kusa da wayan bane d'agawan ne baza
tayi ba.
****
Koda Daddy ya sauk'e ta bakin hotel nasun yak'i tafiya se
rok'an ta yake da ta kira Mummy yana son ya ganta yayi mata
magana. Itama dake a cike take shi, seta k'i gani take shine
silan komai. Da tun farko be tarke 'yar mutane yayi mata ciki
ba da duk hakan be faru ba. Ita se yanzu take sake gane dalilin
da yasa yayi mata auren wuri ashe tsoro yake kar yadda ya
lalata 'yar mutane shima a lalata masa ita. Se gashi da Allah
ya tashi kamasa ya kamasa ta inda baya tsammani. Haka nan
tak'i k'ira masa Mummy tayi shigewarta ciki. Mami kam koda
taji abinda ake ciki bata sa ran Afzal ze d'au Nazeefah akan
Amal ba sabida kaman yadda Nazeefah ta gaya haka d'in
yake, idan ba ikon Allah ba da wuya ya d'au za6in mahaifinsa
akan za6in zuciyarsa. Hak'uri tayita bawa Nazeefah yayinda
take sake tsanan Daddy na jefa mata rayuwan 'ya acikin
k'unci. Nazeefah yini tayi ranan tana kuka gashi ko Afzal ya
kira bata d'agawa.
Cikin dare Afzal ya tashi ya gudanar da raka'a biyu yana mey
neman kariya da haske daga Allah. Washegari ya cigaba da
kiran Nazeefah amma haka tana gani bazata d'aga ba. Har
hotel d'in yaje ya kira Mummy yana rok'anta da ta turo
Nazeefah yana son yi mata magana amma haka 'yar nan tak'i
fitowa. Ta 6angaren Daddy kuwa shima ya tak'ura wa Afzal da
kire-kire yana rok'ansa da ya basa address nasu Mami dan
yaje ya bada hak'uri amma Afzal yak'i akan cewa in bada
izinin Papi ba baze kaisa gidan ba.
Amal kuwa da ikon Allah take samun waraka, na sosai jikinta
ya warware. Tamkar bak'in juna haka Afzal da Amal suka
zame wa juna. Kamar yadda bata shiga harkansa shima haka
baya shiga nata, in ba wai abinda ya zama dole ba se su yini
basuyi ma juna magana ba. Deep down inside their hearts
kuwa ba k'aramin missing how open and free they're to each
other suke ba. Na kwana biyun nan acikin d'ayan d'akin yake
yini se bacci yake kawosa d'akin nasu.
Istikharan kwana uku yayi sannan ya iya ya amince da
sakamakon daya samu saidai ya kasa d'aukan mataki a kai
bale ya gudanar da abinda ya kamata. Rufe kansa yayi a d'aki
yinin ranan yayita kuka tamkar ba d'a na miji ba. Baze iya jure
rabuwa da ita, besan ya rayuwarsa zata kasance ba ita a kusa
da shi ba. Jin shiru Ummi da yayi mata alk'awarin a yau ze
sanar da ita sakamakon da ya samu ta d'au waya ta kirasa
domin ji daga garesa. Kaman wanda bade d'au wayan ba ya
d'aga a last ring d'in.
"Halo Prince?" Ta soma da cewa.
"Na'am Ummi?"
"Prince ya shiru? Tun d'azun nida Abbanka muke jiran kiranka
lafiya dai ko?"
"Lafiya ya jikin Amal?"
"Alhamdulillah da sauk'i."
"Ya naji muryanka k'asa-k'asa haka?"
"Babu."
"Bade kuka kake ba Afzal? Meya faru?"
"Ummi I can't do this" ya sanar da ita tsakaninsa da Allah.
"Wallahi bazan iya ba."
"Meya faru? Ka gama istikharan ne?
Hello Afzal?" Ta sake da cewa bayan shirun da yayi. "Afzal?"
"Na'am" ya amsa murya ciki-ciki.
"Ya sakamakon? Wace zaka d'auka? Wace tafi kwanciya
maka a rai?"
"Ummi I can't bazan iya sakanta ba she's been through alot
bana son yin hakan ya zame kaman na zalunce ta."
"Wacece? Amal ce?
"Ummi ina tausayawa rayuwar da zata fad'a bayan mun rabu
bazan iya rabuwa da ita ba."
"Ka sanar dani mana Afzal? Amal ce?"
RANA DAYA Chapter 44
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
Tareda Naja'atu Lawal Rijau Niger State
@Whatapp 08083232323 or 09060202323
PAGE 44
"Ummi no, ba ita bace."
"Then wacece, Nazeefah?"
"Eh Nazeefah, Nazeefah ce Ummi."
"Ni yanzu ka rud'a min kai, Nazeefah ce tafi kwanciya maka a
rai kokuwa ita zaka saka?"
"Ummi hankalina yafi kwanciya da Amal."
"Toh Alhamdulillah in shaa Allah hakan shi yafi alkhairi."
"Ummi Nazeefah kuma fah? Shikenan yanzu semu rabu?"
"Toh ya zamuyi Prince? Rabuwa da ita ya zamo dole se inde
zaka bijire wa za6in da Allah yayi maka ka saki Amal wanda
nima ba barinka zan ba tunda har Allah ya riga yayi ma za6i."
"I know Ummi kuma nima komin yaya bazan ta6a iya rabuwa
da Amal ba but Nazeefah kuma fa? Na tabbata baza ta ta6a
yafe mun ba, zan iya cewa soyayya na ne kad'ai ya bata wuya
a rayuwa. Lokacinda ta soma jin dad'in aurena kuma na kama
na k'ara aure nayi mata kishiya. Ban ta6a kyautata mata ba
Ummi and now da abunda zan sak'a mata kenan bayan duk
wannan wuya da ta sha? I need to treat her right one more
time please ki taimakeni Ummi."
"Hak'urin nan de shi zan cigaba da baka Prince, nasan da
wuya Nazeefah ta kar6i bak'on lamarin nan da hannu bibbiyu
kaman yadda ka fad'a amma as time progresses zata gano
cewa za6in Allah shine mafi alkhairi a gareku gabad'aya kuma
ba kullum bane muke samun abinda muke so. Don yanzu koda
ka bijirewa za6in da Allah yayi ma ka saki Amal kabar
Nazeefah, ba alkhairin da ze biyo bayan hakan se ma sharri. Se
ka ga ma rabon ya zame mata ajali, kuma zancen wai baka
ta6a kyautata wa Nazeefah ba kaima kasan k'arya ne. Duk
kulawan da ya kamata ace mace na samu daga gun mijinta
kayi mata kuma itama ta sani, so just calm down and do
what's right Allah na tare da kai."
"Thank you Ummi" da haka ya katse wayan yayinda kalamun
Nazeefah suke ta yi masa yawo akai. Ji yayi gabad'aya baze
iya sauwak'e mata ba. Dama seda ta fad'a mishi cewa tasan
Amal ze d'auka akanta saboda baya sonta se Amal se gashi
kuma Amal d'in ze d'auka yanzu. Sede ba don baya son ta
bane kaman yadda ta fad'a se don Amal ce za6in da Allah yayi
masa kaman yadda itama Yayi mata lokacin da zata aureshi.
Tsoronsa d'aya kar wannan za6i ya sake 6ata tsakanin wannan
'yan uwa. Dan kaman yadda Nazeefah ta sanar da shi ya
tabbata muddin idan taji Amal ya bari ya saketa seta tsani
Amal fiye da yadda ta tsaneta yanzu. Oh Allah shin ya zeyi
yanzu? Idan da ace ze iya rabuwa da dukansu biyu da yayi dan
hakan shi zefi wa kowa kwanciyan hankali. Gara duka su rasa
sa da ya d'au d'aya yabar d'aya amma yaya ya iya? Zuciyarsa
bazata iya jure masa rashinsu duka ba barin ma Amal tasa da
yake ganin idan har ya rasata baze iya sake samun mace mey
kyawun halatayya irin tata ba. She's just different.
Mik'ewa yayi a hankali yabar d'akin ya nufi nasu inda Amal ke
kwance a kan gado se tunani take. Har ya k'arisa kan gadon
bataji shigowansa ba. Seda ya kira sunanta tukuna.
"Rania?" Da mamaki cike da tsoro ta mik'e zaune tana
kallonsa. Bazata iya tuna when last ya kirata da wannan suna
ba, probably tun da ya gano cewa ita da Nazeefah 'yan uwa
ne. Ganin bata da niyyan amsasa seya mik'a mata hannunsa
da nufin ta sa nata a ciki. Bayan dogon nazarin da tayi daga
k'arshe seta mik'a hannunta ta sanya cikin nasa inda ya mik'ar
da ita tsaye akan k'afafunta. Na matuk'a kanta ya d'aure
yayinda zuciyarta ta shiga bugun tara-tara barin ma da Afzal
ya rungumeta a jikinsa.
Shikenan ya tabbata ita zata tafi. Se bata kawai jikinta yake
itace ze saka, tasani zamanta da shi ya k'are, ta sani Nazeefah
ce tafi kwanciya masa a rai, ta sani Nazeefah ce za6in da
Allah yayi mata. Tabbas tayi musu murna sedai kuma tayi
k'arya idan tace bata ji zafin hakan ba because she loves him.
No matter how hard she tried not to show how terrified she
felt takasa saboda yadda take jin zafin rabuwa da shi. Kawai ji
tayi hawaye na gangaro mata daga ido dai-dai wannan lokaci
Afzal ya d'agota daga jikinsa da k'yar dan yadda ta
kankamesa. Cike da mamaki ya tsaya kallon yadda take kuka
sannan daga bisani ya shiga share mata hawayen nata "Please
don't cry Rania."
"I should really start packing my clothes" ta sanar dashi tana
mey hana k'wayoyin idanunta had'uwa da nasa. "I'm really
happy for you two Yaya, Allah ya baku zaman lafiya mey
d'aurewa."
"Mey kike cewa haka Rania? Zaman lafiya tsakani na da
waye?"
"Da Nazeefah."
Murmushi ya saki kad'an "Meyasa kika ce haka? Why not
you?"
"Saboda bani ce za6in da Allah yayi maka ba Yaya. I know I'll
be the one to leave and even though nima hakan ne ze fiye
mun kwanciyan hankali I just can't deny the fact that I still
love you so very much and I'll miss you so damn much."
"But you don't have to miss me Rania because you're not
going anywhere, this is your home anan kuma zaki cigaba da
zama ba inda zaki."
"No ba sekayi hakan ba Yaya, zanje in samu Mami a gida,
chan d'in ze fiye mun kwanciyan hankali yaso ko haya ne se
kasa a nan d'in." Dariya sosai ta basa wanda ya kasa dannewa
yayinda ta tsaya kallonsa cike da mamaki da takaici. Mey yake
nufi da hakan?
"Rania listen to me, ba inda zakije nan ne gidanki kuma
d'akin mijinki okay?"
"D'akin mijina? Nazeefah kuma fa? Karka bijire wa za6in
Allah saboda son zuciya Yaya. Idan kuma tsoron abinda Papi
da Mami zasuce kake then ka kwantar da hankalinka kasani
duk zasuyi maka kyakkyawar fahimta kaman yadda nima nayi
maka. We all know you love me Yaya, please don't bother
yourself."
"Tsaya, kafin muyi aure mey kikayi? Kinyi Istikhara right?" Kai
ta gyad'a masa a hankali cike da rashin fahimta sannan ya
cigaba "Kuma bayan da kika gudanar se waye Allah ya za6a
miki?"
"Kai Yaya" ta amsa a takaice.
"Kina ganin it is possible ace ni kuma nayi Istikharan yanzu
se wata ta daban ta zame za6in da Allah zeyi mun bayan ke
kuma ni Ya za6a miki?"
"But Yaya-"
"Ki sani Rania ko sau dubu mutum yayi Istikhara za6in Allah
d'aya ne sedai idan shi yaso bijire wa hakan. Kaman yadda
kikayi naki istikharan Allah ya za6a maki ni, nima haka ya
za6a min ke yanzu. We two are meant to be Rania in shaa
Allahu mutuwa ce kad'ai zata shiga tsakani na dake. Rania I
love you so much kuma Allah kad'ai ne sheda game da irin
son da nake yi miki, shi kad'ai yasan idan bake bazan iya
rayuwa ba, shi kad'ai yasan muddin na rasaki bazan ta6a iya
samun kamilar mace mey kyawawan d'abi'u da halatayya irin
naki ba shiyasa ya za6an min ke ya sake bani daman da zan
soki in kuma kula dake har ila k'arshen rayuwa na. I can't do
without you Rania and I can't ask God for more da ya sake
bani daman kasancewa mijinki, forgive me for all the times
I've wronged you Rania, I'm terribly sorry please forgive me."
Kuka Amal ke sosai yayinda ta kasa amincewa da abubuwan
daya fad'a mata. Se gani take kaman a mafarki komai ke
faruwa tabbas itama bazata iya rayuwa idan ba shi ba. Gani
take kaman duk yadda yake jin yana sonta ita tafi sonsa, don
dai kawai ita bata nunawa ne. Daga k'arshe kuma bazata iya
yima Allah godiya ba da ya sake bata daman kasancewa
matarsa, sai dai kuma bazata iya duba irin rayuwan k'unci da
tashin hankalin da Nazeefah zata fad'a ba a rashin Afzal. Se
gani kawai take inda itace Afzal yace ze sauwak'e wa. Tasan
duk kalan rashin tawakkalinta tana bayan Nazeefah. Tasan
Nazeefah na iya yin k'aramin hauka akan wannan dalili, she
knows this is not going to be easy on her shiyasa take tausaya
mata sosai.
"Rania?" Ya kirata bayan shirun da tayi, jikinsa kawai ta fad'
yayinda ta shiga yin kuka na sosai. "Bakayi mun komai ba
Yaya don haka ka daina tambaya na yafiya I love you so very
much." Ba k'aramin dad'i kalamanta suka sanyasa ba, matseta
tsam ya sakeyi a jikinsa tamkar ana shirin k'watan masa ita
yayinda wani irin sonta yake sake shiga zuciyansa. Sun dad'e
a haka sannan daga bisani ya janyeta daga jikinsa sede har
anan hawaye Amal ke.
"Please don't cry Rania."
"I wish I could stop Ya Omri."
"But there's no need to."
"There's every need to cry Ya Omri."
"Saboda ban barki kin tafi gida kaman yadda kikeso ba kike
wannan kuka Rania? Saboda Allah ya za6an min ke? Ashe ba
haka kika so ba, I thought you said you love me" Kai ta gyad'a
mishi take tana murmushin takaici.
"Then meyasa kike kukan? A tunani na this is supposed to be
the most happiest moment for us both."
"Yes it is Yaya kuma hawayen nan da kake gani, hawayen
farin ciki ne gani nake kaman a mafarki komai ke faruwa, I
can't believe that we're still going to remain married to each
other after hope has been gone."
"I feel thesame way Rania, but tun farko tun kafin in gudanar
da Istikharan nan nasan komin yaya akayi ni dake bamu
rabuwa."
"Ko meyasa kace haka?" Tayi saurin tambayansa cike da
mamaki.
"Saboda Istikharan da kikayi kafin mukayi aure Rania, idan da
har ace akwai sharri a auran mu da Allah baze za6a miki ni
akan Abdul daya kasance masoyinki ba. Idan har na rabu dake
kinga kenan babu amfanin istikharan da kikayi. Ko ce miki
akayi shi istikhara temporal decision ne na d'an lokaci?
Hankali na ya tashi ne gabad'aya saboda Nazeefah. Ina
matuk'an tausayawa halin da zata shiga idan har ta gano cewa
I chose you over her, shiyasa nayi coming up da plan na cewa
zanyi Istikhara kinga idan har nayi ita da iyayenta bazasuyi
mun mumunar fahimta ba, zasuga za6in Allah nabi ba wai na
zuciya na ba. Sedai kuma yanzu bayan dana gudanar da hakan
nakega still Nazeefah bazata amince ta kar6i wannan bak'on
lamarin da hannu bibbiyu ba. Nasan komin tayaya bazata ta6a
fahimtar cewa Allah ne ya had'ani dake ba, bazata ta6a gane
cewa ba komi mutum yake so a duniyan nan yake samu ba,
gani take komai laifinki ne Rania and that is what hurts me the
more knowing who you really are. Bana son a sanadin hakan
ta sake tsanarki, ita gani take komai laifinki ne, ke kika janyo
bayan ba haka bane. I wish Nazeefah could see this kind and
selfless side of you. Har yau kalaman ki na yinin ranan da na
sanar dake cewa Nazefah k'anwarki ce suna kaina. Har yau na
kasa mancewa dasu kuma bazan ta6a mancewa da su ba.
Yadda kika cire son kai kikace kin yafe ni wa Nazeefah even
though kina so na bawai bakiya sona ba se don cewa da
Annabi yayi "La yu'minu ahadukum hatta yuhibbu li akhihi ma
yuhibbu li nafsihi" [imanin d'ayanku baya cika har seya so wa
d'an uwansa abinda ya so wa kansa] I get that you love me
but you're willing to let your sister have me and ba kowa keda
irin imanin nan naki ba Rania ko ni nan bazan iya aikata abinda
kikayi ba ranan saboda haka kuma naji respect naki ya k'aru a
idona yayinda sonki ya sake k'aruwa a zuciya na."
Murmushin jin dad'i ta sakar masa tana mey share
hawayenta "Ka sani ko da nace maka hawayen nan na jin dad'i
ne k'arya nayi because zuciyata tausayawa Nazeefah take, I
can't imagine the kind of hell she'll go through Yaya don haka
har nakejin kaman mu hak'ura da juna sedai kuma bazamu iya
yin jayayya da za6in Allah ba."
"Hakane Rania, let just pray for her in shaa Allah as time
progresses zata fahimci komai ta kuma nemi gafararki ayi
zaman lafiya gabad'aya."
"Da kuwa ba abinda zefi mun hakan farin ciki da jin dad'i
Yaya. Inspite of how Nazeefah disperses me wallahi I still love
her kuma zan cigaba da sonta ina yi mata uzuri har zuwa
lokacinda zata gane gaskiya."
"Allah yayi miki albarka Amal ya baki yaran da zasu kula dake
ranan da buk'atan hakan ya taso Rania, I'll forever love,
cherish and adore you."
"Ameen Ya Omri I love you too."
"Let's eat out ai zaki iya fita ko?"
"Why not? Bari in shirya."
***
Washegari...
Dai-dai gaban gidansu Nazeefah yayi parking sannan ya zaro
wayansa ya kira Daddy a karo na farko ya d'aga.
"Halo Afzal ka iso ne?"
"Eh Daddy."
"Toh bismillah mana ka shigo." Harga Allah beyi niyan shiga
ciki ba amma yaya ya iya? Gyara packing nasa yayi ya k'arisa
ciki inda ya samesa a parlour ya gaishesa. Bayan sun gaisa ya
zaro takardan daya ninke daga aljihunsa ya mik'awa Daddy
"Kaman yadda nayi muku alk'awari cewa zanyi Istikhara, duk
kuma wacce Allah ya za6ar mun ita zan d'au in sauwak'e wa
d'ayan. Toh game da sakamakon dana samu bayan na
gudanar da Istikharan na yanke wannan hukunci ba don son
kai ko son zuciya ko makamancin haka ba, da fatan kai da
iyalanka zakuyi mun kyakkyawar fahimta. Ga takarda nan na
sakin Nazeefah, dafatan ze isa gareta zaka kuma bata hak'uri
a madadi na ni zan wuce."
"Dakata Afzal kar kayi saurin tafiya. Kayi hak'uri ka bani
dama in baka hak'uri na jefaka da iyalinka cikin wannan
rud'ani da tashin hankali da nayi. Kuma ka sani wannan
hukunci daka yanke shine dai-dai koda ma ace bakayi
istikhara ba bazan bari ka saki Amal ba saboda abinda nayi
mata da mahaifiyarta kad'ai ya ishesu takaici da jarabawa.
Dole nima in gir6e abinda na shuk'a. Da fari na d'au zan iya yi
wa Allah wayo, na d'au idan har na aurar da Nazeefah
shikenan bani da wani tsoro kuma ashe ba haka abun yake ba,
ashe ita zina bashi ce idan har ka cita dole komin ta yaya ne
ka biya. Kuma muddin ba a kaina ze ramawa Jameela abinda
nayi mata ba dole se akan wanda nakeso. Dukda cewan Amal
da Nazeefah 'ya'yana ne amma kaman yadda zanfi jin zafin
sakin nan akan Nazeefah ba haka zanji ba idan da akan Amal
ne saboda babu shak'uwan nan na uba da 'ya a tsakani na da
ita. Allah ya za6an maka Amal ne saboda ya koya mun da
'yata darasi kuma saboda itama koda sau d'aya ne taji dad'in
rayuwa. Ka sani wannan hukunci da ka yanke dai-dai ne kuma
zanyi k'ok'ari in fahimtar da iyalai na, Allah ya baku zaman
lafiya mey d'aurewa da Amal ya albarkaci rayuwanku in shaa
Allah zan isar wa Nazeefah sak'onka."
"Nagode sosai Daddy."
"Ba komai, se kuma batun Jameela bazan gaji da rok'an
kanka ba da kayi mun kwatance injeni gidansu in nemi
tubarsu, idan ban samu sun yafe mun ba alhak'insu ya cigaba
da bi na kenan, ka tausaya mun da iyalai na please Afzal."
"In shaa Allah zanyi ma Papi magana karka damu."
"Toh nagode sena ji daga gareka."
"Ba komai ni zan wuce" ya fad'a had'e da mik'ewa "Ka
gaishe da Amal ina da niyyan shigowa inzo in dubata nima in
nemi tubarta amma ina son in d'an bata lokaci saboda nasan
yadda zata ji ta tsaneni yanzu."
"Zataji Daddy se anjima" yana kaiwa nan ya fice ya koma
office har a yau idan ya gwada kiran layin Nazeefah bata
d'agawa. Ba komai yasa yake son ya kirata ba se don so da
yake ya bata hak'uri, baya son taga kaman baya sonta ne, har
yau har gobe ze cigaba da sonta saboda akwai gur6in da ita
kad'ai ce ta mamaye a zuciyansa. Ita ce macen da ya fara sani
a rayuwansa, itace macen da ya fara sumbata itace macen da
ya fara sharing wani abu nashi da ita. Shin har ze iya mancewa
da ita a rayuwansa? He don't think so.
****
Daddy be samu ya kaiwa Nazeefah takardan nata a ranan
ba se a washegari. Bayan ya dawo daga sallan Azahar ya d'au
wayansa ya kira Mummy sedai kaman yadda ta saba ignoring
call nasa hakan ma tayi yau don haka ya tura mata sak'o.
_Hjy Surayya kiyi hak'uri ki d'au wayan nan muyi magana.
This is not about me it's about our daughter Nazeefah, thank
you._
Sak'on ya shiga bada dad'ewa ba Mummy ta karanta se
contemplating take ta kirasa taji lafiya ne ko ta bari. Chan
k'arshe de ta kira wanda ya d'aga a karo na farko. Bata basa
daman yin magana ba tace, "Meya samu Nazeefan?"
"Hjy Surayya wannan ba maganan waya bane gani nan
tahowa yanzu."
"Karka 6ata lokacinka bana nan na fita."
"We both know k'arya kikeyi zanzo yanzu please" bata sake
ce meshi komai ba ta katse wayan. Cikin mintuna da basu kai
ashirin da biyar ba sega shi nan ya iso. Waya yayi mata akan
ta fito nan da nan ta sanya hijabinta ta fice.
Ba yadda Daddy beyi ba da su k'arisa koda reception ne su
zauna suyi magana tak'i, tace ita idan har baze fad'i abinda
yake tafe dashi ba zata koma ciki. Toh suje cikin mota su
zauna nan ma tak'i. Yasan sam bey kyauta mata ba amma ba
wai yayi hakan dan ya raina ta bane ko makamancin hakan, shi
tsoron sanar da ita yake gudun kada ta gujesa kaman yadda
takeyi yanzu.
Hannu yasa a aljihunsa ya fito da takardan had'e da mik'a
mata.
"Mey wannan?" ta tambaya ba tare da nuna yunk'urin amsa
ba.
"Kedai bud'e ki gani." Kaman wacce bazata kar6a ba ta
amsa ta bud'e had'e da karancewa.
_A ranan Laraba, goma ga watan Juneru shekara dubu biyu
da goma sha takwas na saki matata Nazeefah, saki d'aya,
biyu, uku saboda haramta mana zama da shari'a tayi a
sanadin ta na kasancewa 'yar uwar matata Amal na jini._
Ajiyar zuciya Mummy ta sauk'e dama tasan za'ayi haka.
Dama tasan Nazeefah ce Afzal ze saka kawai bata so ta nuna
mata bane don kar ta tayar mata da hanaki amma tasan haka
za'ayi dama kodan ma Allah ya kama Daddy yasa shima yaji
zafin da mahaifiyar Amal taji sanda yayi mata fyad'e. Tasani
dole ne wannan k'addara ya fad'a akan Nazeefah saboda
itama Amal ta samu farin ciki koda sau d'aya ne a rayuwarta.
Idan harda ace wannan saki akan Amal ya fad'a da Daddy
baze ji zafi kaman yadda ace zeji yanzu da ya fad'a akan
Nazeefah. Ta hakan ne kawai Allah ze sanyasa gir6e abinda ya
shuk'a, ta hanyar mayar masa da 'ya bazawara kaman yadda
ya k'wace wa 'yar mutane budurci.
"Shikenan ka huta ai yanzu Alhj, amma kasani nida 'ya'yana
bazamu ta6a yafe maka wannan abun kunya daka aikata ba."
Be bari ta shiga takawa ba yayi sauri ya rik'e k'asan hijabinta
"Hjy Surayya bazan ma fara tambayan gafararki ba saboda
nasan abinda nayi miki da 'ya'yanki is unforgivable but atleast
give me a chance to apologize and tell you sorry. I'm gravely
sorry for hiding the truth away from you, wallahi bawai don
bana sonki bane kokuwa don bana mutuntaki yasa na 6oye
miki wannan al'amari, sonki da nakeyi ne ya rufe min ido,
bana son abinda ze shiga tsakani na dake Hjy Surayya, bana
son in rasa ki. Dan son zuciya irin nawa se naga idan har na
sanar dake gaskiya zaki gujeni kik'i aurena shiyasa na rik'e
komai wa kaina. I love you so much Hjy Surayya and I'll never
stop loving you, I'll wait. Zan jiraki koda kuwa zuwa k'arshen
rayuwana ne amma bazan gaji da baki hak'uri ba dan Allah kiyi
hak'uri ku dawo gida."
"Babu wani abinda zaka sake fad'amun da zaisa in canza
ra'ayina. Idan 'ya'yanka kake so kana iya shiga ciki yanzu ka
ebosu amma nikam takarda na nikeso. Kaman yadda ka shiga
tsakanin auren yaran nan kasa Afzal ya saki Nazeefah saki ba
d'aya ba, ba biyu ba har uku nima haka nake so ka rubuta mun
nawa. Idan har 'yata zata shiga k'uncin rayuwa ka tabbata kai
m seka shiga ninki ba ninkin nata don haka ka rubuta min
takarda na yanzun nan anan. Tunda rayuwan zawarci ka za6a
wa 'yarka tayi nima mahaifiyarta shi zanyi."
"Dan Allah kiyi hak'uri Hjy Surayya nasan nayi miki laifi, laifi
babba amma dan Allah kiyi hak'uri ki gafirceni. Idan kika tafi
kika barni ya kikeson in rayu?"
"Bakayi tunanin hakan ba kafin ka danne 'yar mutane kayi
mata fyad'e? Se kaje chan ku k'arasa da ita mahaifiyar Amal
d'in that is idan har zata iya yafe ma zaluntar ta da kayi."
"Kema kinsan bazan iya rayuwa da kowa ba bayan ke Hjy
Surayya, kinfi kowa sanin yadda nake sonki tun ba yau ba."
"Sam ba haka bane, I was a fool to believe you love me Alhj,
yaci ace tun a lokacin chan na gane kud'in mahaifina kawai
kake so ba ni ba. Wallahi Allah ne kad'ai ze sak'a mun. Duk
kalan halaccin danayi maka na sa mahaifina yayi maka duk
baka ga hakan ba you still chose to lie and cheat on me."
"Dan Allah kiyi hak'uri bazan ta6a gajiya da baki hak'uri ba
saboda nasan ban kyuata ba amma wallahi I love you Hjy
Surayya I really do."
"Shin anya ma kuwa labarin daka tsara min da iyayena na
cewa kai maraya ne gaskiya ne kuwa? Shin anya kuwa ba
k'arya ka shirya mana ba saboda ka samu kaci arzikin
mahaifina Alhj?"
Shiru Daddy yayi gun ya kasa cewa komai. Tabbas yayi mata
da mahaifinta daya kasance hanshak'in mai kud'i bahaushe
daga Kano k'arya lokacinda yazo aurenta. Saboda gudun da
yake kar a nemi iyayensa kowani d'an uwansa a garin hakan
asirinsa ya tonu na cewa yayi ma wata fyad'e a k'auye Mummy
ta fasa aurensa ko iyayenta su hanata. Tun bayan da abin ya
faru ya samu ya dawo makaranta be sake d'aga wayan
iyayensa ba, duk lokacinda yaga kiransu baya d'agawa har ta
tsinke saboda yasan akan mey zasuyi masa magana shi kuwa
bayida abin cewa. Daga k'arshe ma da yaga kiran ya soma
isansa se kawai ya sauya lamban wayansa gabad'aya, tun
daga nan be kuma sake ji daga garesu ba se...
"K'arya kayi mana ko? Why aren't you saying anything Alhj?"
"Hjy Surayya yes, yes nayi miki da Abba k'arya batun iyayena
amma wallahi ba don bana respecting naki bane se don tsoro
da nake kar a garin hakan gaskiya ya fito in rasaki."
"Wani gaskiya?" tayi saurin katsesa.
"Batun abinda ya faru tsakani na da mahaifiyar Amal."
"Wane irin mak'aryaci ne kai Alhj? Mey nayi maka a rayuwa
da ka za6i ka gina duk wani abinda mukayi accomplishing tare
akan k'arya?" Ta tambayesa hawaye na saurin ciko mata a ido.
"All I did was to love you Alhj I'm so disappointed in you na
tabbata da Abba yana raye a yau da shima baze ta6a yafe
maka ba."
"I'm truly sorry Hjy Surayya amma abinda ya faru ya riga ya
faru idan da zan iya mayar da lokaci baya da nayi dan in gyara
komai amma bazan iya ba please give me a second chance
idan kika tafi kika barni taya kikeson in rayu? Tabbas idan ba
ke su Nazeefah bazasu amince su dawo gida a gareni ba
please kiyi hak'uri."
"Bayan k'aryan nan se kuma wani k'arya ka sakeyi mun?"
"Hjy Surayya a shirye nake da in sanar dake duk wani abinda
kike buk'atan ki sani amma zaki galabaita tsaye a nan saboda
labarina nada tsawo kiyi hak'uri mu shiga mota kokuwa mu
k'arisa cikin reception." Bata ce da shi komai ba kawai ta
shiga takawa yayinda yake biye a bayanta, a VIP reception
suka zauna sannan Daddy yayi gyaran murya ya soma kaman
haka.
"A shekaran da na dawo hutun second year d'ina ne muka
had'u da mahaifiyar Amal wato Jameela wacce nake kira da
Jamee na. Jameela ta kasance itace mace ta farko da Allah
ya fara sanya min soyayyarta a zuciya na, so kuma na aure
bana lalata ba. We started off as friends amma cikin
k'ank'anin lokaci soyayya mey k'arfi ya shiga tsakaninmu.
Jameela was simply everything I could ever ask for, lokacin da
muka fara soyayya kwata-kwata shekarunta goma sha shida
ne, she was so beautiful, young and innocent. Tsaftacacciyar
soyayya muka gudanar nida ita as ko zance naje wajenta iyaka
muyi hira ba wani ta6e-ta6e bale makamancin hakan saboda
Jameela yarinya ce kamila wacce take san addininta sosai
take kuma k'ok'arin bin dokokin da ya kafa mata. Ahaka ne har
nazo na koma makaranta wanda bada dad'ewa ba Jameela
tayi mun waya cewa mahaifiyarta na shirin had'ata aure da
d'an chairman na garinmu idan har ban hanzarta turo
magabata na ba ana iya aura mata shi d'an chairman d'in.
Hankalina ne ya matuk'an tashi se Allah-Allah nake session
d'in ya k'are in dawo gida. Kasancewar a scholarship na samu
karatun seya zammana banida gatan dawowa gida kowani
hutu se shekara-shekara. Addu'a muka tsayar sosai nida
Jameela cikin ikon Allah kuwa se har wata shekarar ta zagayo
shi wannan yaro be turo ba. Na dawo bada dad'ewa ba na
samu mahaifina nayi mishi maganan Jameela akan ina son a
tura tambaya gidansu sede sam Abba yak'i amincewa akan
cewa da baki na ne zan ajiye mata idan nayi aure yanzu ina
karatu. Duk yadda naso fahimtar dashi cewa Jameela bata da
matsala da hakan besides ma ina d'an yin business,
makaranta kuma shekara d'aya ne ya rage sedai hakan ya
gagara Abba yak'i ya amince ya bani goyin baya. A sanadin
haka nida Jameela muka shiga tashin hankali sedai bamu cire
rai ba, muka mik'a komai ga ubangiji. Ban san ya akayi ba de
amma wataran mahaifiyar Jameela ta jiyota muna waya bayan
kuma ita ta riga tayi mata miji a sanadin haka tayi ma
Jameela duka tayi seizing wayarta sannan ta horeta da kada ta
sake kulani. Kwana biyu na daina ji daga gun Jameela ko na
kira layinta baya shiga gashi sun k'are makaranta lokacin bale
inje mu had'u a chan d'in. Rana d'aya kawai na jajirce na jeni
gidansu dan yadda shirun yayi yawa, dukda cewan ta haneni
da taka bakin k'ofan gidnasu saboda yadda ta nuna mun
mahaifiyarta bata sona. A farko da naje mahaifiyar ta kar6eni
da fara'a kasancewar bata gane waye niba a lokacin da nayi
mata bayanin kaina kawai ranta ya 6aci ta sauk'e duk wani
haushin da takeji a kaina tayi mun koran kare harda muciyan
tuwo ta bini waje. Hakan ba k'aramin 6ata mun rai yayi ba dan
dole na hak'ura da Jameelah saboda a rayuwa na washi
walak'anci na kuma d'au alwashin sena rama cin mutuncin
nan da tayi mun ko ta yaya ne. Rana d'aya ina zaune kawai
sega kiran Jameelah ban 6ata lokaci ba na d'aga inda take
sanar dani tana son mu had'u. Chan na kaita bayan gari da
siyasan cewa abu nake so in nuna mata, ina son Jameelah
amma abinda mahaifiyarta tayi mun ya tsaya mun a wuya ko
kallonta nayi se na tuna da abin. Haka kawai shaid'an ya soma
raya mun in d'au fansa akanta sedai kuma sonta da nake yana
rik'eni. Amma haka shaid'an ya rinjayi zuciyana ta hanyan raya
mun ai tunda mahaifiyarta tana sonta idan na ta6a lafiyarta
kaman na ta6a na mahaifiyar ne don haka idan na lalata mata
rayuwa abun seya fi wa mahaifiyar zafi. Ana cikin haka ne
sega abokai na guda biyu dana basu labarin abinda mahaifiyar
Amal tayi mun nan suka sake k'arfafamun guiwa suka bani
had'in kai nayi ma Jameela fyad'e ba tare da d'igon imani ba."
"Koda mahaifinta ya kai k'arana dana mahaifina gurin mey
unguwa k'aryata komai nayi na samu abokaina suka rufa mun
asiri shima Abba ya goya mun baya saboda baze ta6a kawowa
a ransa zan iya aikata abinda nayi ba. Acikin satin ko na gaba
na samu na koma makaranta ban sake ji daga garesu ba. A
karon chan ne na had'u dake Surayya, kika yi mun erasing duk
wani bad memory'n dana bari da a k'auyen Askira. Tunda na
sameki komai ya canza Surayya, soyayyar da kika nuna min ta
dabance. Banida komai, Baki sanni ba, baki san wani nawa ba
amma kika so ni kika kuma amince dani regardless. Ko a
mafarki ban ta6a tsammanin cewa wataran zan iya mallakan
'yar babbar gida kamar ki ba mey hankali da tausayi. Lokacin
da kika ce mun muyi aure ne nashiga tashin hankali badon
bana sonki ba se don banason hakan ya tono mun labarina
dana bari a garin Askira. Ban san da wani idon zan sake kallon
iyayena da na shafesu a doron k'asa saboda selfish interest
d'ina ba na kusan shekara. Rud'ani na matuk'a na shiga yayin
da na rasa ya zanyi gashi bana son in rasaki saboda da in rasa
ki gara na rasa komi nawa koda kuwa raina ne. Don haka nayi
miki da Abba k'aryan cewa ni maraya ne. A tunani na hakan ne
kad'ai zaisa Abba ya amince ya aura min ke Surayya. Ba
abinda Abba beyi mun ba bayan dana aureki, abinda ya kama
kayan da zansa, gidan da zamu zauna, motan da zan hau
harta sadakin ki shi ya biya mun, komai da na sani na mallaka
a lokacin na Abba ne. Harta aiki shi ya samo mun bayan da ya
biya mun kud'i na gama masters d'ina muka dawo gida nan
Nigeria idan ban manta ba kina da cikin Khaleefah."
"A lokacin da muka dawo ne bayan na tafi yin service d'ina
na koma k'auyen Askira dan d'auko su Abba in nemi tubansu
in basu hak'uri ake tabbatar min da cewa sunyi hatsari
shekaru biyu da suka wuce a hanyansu na zuwa k'auyen
Dambuwa. Shi Abba a take ya cika ita kuwa Umma tayi jinyan
wata shida sannan mutuwa yayi halinsa. I felt hopeless and
useless Surayya, iyayena sun mutu amma seda shekara biyu
nake sani. Ji nayi kaman in soka wuk'a wa kaina in mutu wani
irin d'a ne ni? Na sosai nayi nadaman abinda na aikata na d'au
alk'awarin yin sadak'atul jariya da sunayensu Allah ya kai musu
ladan kabari. Nasan rashin kyautatawan da nayi wa iyayena
yasa nima Allah ya jarabce ni da gagararriyar 'ya kaman
Nazeefah.l
"Daga gida na wuce gidansu Jameelah inda ake sanar dani
suma sun tashi sun k'aura sun bar garin gabad'aya. Ba wanda
ya sanar dani cewan rabo ya shiga tsakani na da ita bayan
faruwan abun shiyasa ban ta6a sanin Amal 'yata bace se
recently. Wallahi ba k'arya nake yi miki ba Surayya please
believe me, taya zan so in had'a 'ya'yan cikina kishi Surayya
bayan na san yin hakan haramun ne?"
"Yanzu ina ita mahaifiyar Amal d'in take Jameelah?"
Mummy data amince da duk wani abinda ya fad'a ta soma da
tambayansa.
"Tana cikin garin nan da zama amma bansan inda take ba,
rannan Afzal ya taho da ita da mahaifinta gidan Nazeefah inda
mukayi magana duka akan yadda za'a 6ullowa al'amarin nan
nasu."
"Baka san inda take ba kace?"
"Wallahi ban sani ba Hjy Surayya ai kinsan bazan miki k'arya
ba."
"Bawai ina k'aryata ka bane Alhj I just want to be certain,
tana da aure?"
"Wallahi banda masaniya akan hakan amma base on abinda
Amal ta ta6a fad'amun kaman mahaifiyar nata bata da aure."
"Ka aureta Alhj" ta sanar dashi. Da mamaki ya tsaya yana
kallonta yayinda ya kasa amincewa da abinda tace.
"Eh?" Ya tambaya.
"Nace idan har Jameelah bata da aure kuma bata niyyan yin
wani auran anan kusa ka aureta."
"Hjy Surayya kin ko san abinda kike cewa?"
"This's the only way zamu iya samu mu had'a kan yaran nan
Nazeefah da Amal mu gyara zuri'ar mu. Ka fini sanin halin
Nazeefah, yanzu da Afzal ya d'au Amal a kanta ba k'aramin
tsanar yarinyar nan zatayi ba dama already ta riga ta tsaneta."
"Toh mey auro Jameelah zeyi ya gyara wannan lamari Hjy
Surayya?"
"Tabbas auro Jameelah zaisa Nazeefah ta shiga hankalinta ta
nutsu ta sani cewa mu dasu mun riga mun zamo abu d'aya
yanzu ta kuma sani cewa shi kishiya na akan kowa ne idan har
da tanayin kwatance dani tagani toh yau nima gashi anyi mun
kishiya."
"Tabbas kinyi gaskiya Hjy Surayya amma bana son in had'a
soyayyarki da kowa ke kad'ai nakeso."
"Karka damu dani kuma ma ai nasan kana son Jameelar taka
har yau ko ba haka ba?"
"Amma ba kaman yadda nake sonki ba Hjy Surayya ni
tausayin Jameelah kawai nake yanzu."
"Karka damu ai ni nace ka aurota."
"Hjy Surayya nifa banga amfanin yin hakan ba. Ba sena auro
Jameelah ba."
"Ka aurota Alhj ni na baka dama karka damu."
"Surayya-" hannunta ta aza akan nasa cutting him off "Don't
worry nima ai zama ni d'aya tal d'innan ya isheni ka kawo mun
abokiyar zama tana tayani hira na tabbata kaman yadda Amal
bata da matsala itama mahaifiyar tata haka ne."
"Wannan ba sekin fad'a ba Hjy Surayya Jameelah sam
batada hayaniya."
"Toh kaga komi ya zo mana da sauk'i kenan, ka auro ta kaji?"
Hjy Surayya what can I say? You're the reason behind who I
am today and everything I've achieved, banida bakin yi miki
da Abba godiya. Allah saka da alkhairi ya cigaba da sanya miki
albarka a rayuwarki ya kuma ci gaba da kai rahama kabarin
Abba."
"Ameen Alhj tare da iyayenka kai ma."
"Kin hak'ura zaki biyoni gida?"
"Har sena amsa tukuna zaka tabbatar da hakan?"
"Gani nake kaman mafarki nake Hjy Surayya, Allah yabarn min
ke tabbas irinku acikin mata d'ad'd'aiku ne."
RANA DAYA Chapter 44
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
Tareda Naja'atu Lawal Rijau Niger State
@Whatapp 08083232323 or 09060202323
PAGE 44
"Ummi no, ba ita bace."
"Then wacece, Nazeefah?"
"Eh Nazeefah, Nazeefah ce Ummi."
"Ni yanzu ka rud'a min kai, Nazeefah ce tafi kwanciya maka a
rai kokuwa ita zaka saka?"
"Ummi hankalina yafi kwanciya da Amal."
"Toh Alhamdulillah in shaa Allah hakan shi yafi alkhairi."
"Ummi Nazeefah kuma fah? Shikenan yanzu semu rabu?"
"Toh ya zamuyi Prince? Rabuwa da ita ya zamo dole se inde
zaka bijire wa za6in da Allah yayi maka ka saki Amal wanda
nima ba barinka zan ba tunda har Allah ya riga yayi ma za6i."
"I know Ummi kuma nima komin yaya bazan ta6a iya rabuwa
da Amal ba but Nazeefah kuma fa? Na tabbata baza ta ta6a
yafe mun ba, zan iya cewa soyayya na ne kad'ai ya bata wuya
a rayuwa. Lokacinda ta soma jin dad'in aurena kuma na kama
na k'ara aure nayi mata kishiya. Ban ta6a kyautata mata ba
Ummi and now da abunda zan sak'a mata kenan bayan duk
wannan wuya da ta sha? I need to treat her right one more
time please ki taimakeni Ummi."
"Hak'urin nan de shi zan cigaba da baka Prince, nasan da
wuya Nazeefah ta kar6i bak'on lamarin nan da hannu bibbiyu
kaman yadda ka fad'a amma as time progresses zata gano
cewa za6in Allah shine mafi alkhairi a gareku gabad'aya kuma
ba kullum bane muke samun abinda muke so. Don yanzu koda
ka bijirewa za6in da Allah yayi ma ka saki Amal kabar
Nazeefah, ba alkhairin da ze biyo bayan hakan se ma sharri. Se
ka ga ma rabon ya zame mata ajali, kuma zancen wai baka
ta6a kyautata wa Nazeefah ba kaima kasan k'arya ne. Duk
kulawan da ya kamata ace mace na samu daga gun mijinta
kayi mata kuma itama ta sani, so just calm down and do
what's right Allah na tare da kai."
"Thank you Ummi" da haka ya katse wayan yayinda kalamun
Nazeefah suke ta yi masa yawo akai. Ji yayi gabad'aya baze
iya sauwak'e mata ba. Dama seda ta fad'a mishi cewa tasan
Amal ze d'auka akanta saboda baya sonta se Amal se gashi
kuma Amal d'in ze d'auka yanzu. Sede ba don baya son ta
bane kaman yadda ta fad'a se don Amal ce za6in da Allah yayi
masa kaman yadda itama Yayi mata lokacin da zata aureshi.
Tsoronsa d'aya kar wannan za6i ya sake 6ata tsakanin wannan
'yan uwa. Dan kaman yadda Nazeefah ta sanar da shi ya
tabbata muddin idan taji Amal ya bari ya saketa seta tsani
Amal fiye da yadda ta tsaneta yanzu. Oh Allah shin ya zeyi
yanzu? Idan da ace ze iya rabuwa da dukansu biyu da yayi dan
hakan shi zefi wa kowa kwanciyan hankali. Gara duka su rasa
sa da ya d'au d'aya yabar d'aya amma yaya ya iya? Zuciyarsa
bazata iya jure masa rashinsu duka ba barin ma Amal tasa da
yake ganin idan har ya rasata baze iya sake samun mace mey
kyawun halatayya irin tata ba. She's just different.
Mik'ewa yayi a hankali yabar d'akin ya nufi nasu inda Amal ke
kwance a kan gado se tunani take. Har ya k'arisa kan gadon
bataji shigowansa ba. Seda ya kira sunanta tukuna.
"Rania?" Da mamaki cike da tsoro ta mik'e zaune tana
kallonsa. Bazata iya tuna when last ya kirata da wannan suna
ba, probably tun da ya gano cewa ita da Nazeefah 'yan uwa
ne. Ganin bata da niyyan amsasa seya mik'a mata hannunsa
da nufin ta sa nata a ciki. Bayan dogon nazarin da tayi daga
k'arshe seta mik'a hannunta ta sanya cikin nasa inda ya mik'ar
da ita tsaye akan k'afafunta. Na matuk'a kanta ya d'aure
yayinda zuciyarta ta shiga bugun tara-tara barin ma da Afzal
ya rungumeta a jikinsa.
Shikenan ya tabbata ita zata tafi. Se bata kawai jikinta yake
itace ze saka, tasani zamanta da shi ya k'are, ta sani Nazeefah
ce tafi kwanciya masa a rai, ta sani Nazeefah ce za6in da
Allah yayi mata. Tabbas tayi musu murna sedai kuma tayi
k'arya idan tace bata ji zafin hakan ba because she loves him.
No matter how hard she tried not to show how terrified she
felt takasa saboda yadda take jin zafin rabuwa da shi. Kawai ji
tayi hawaye na gangaro mata daga ido dai-dai wannan lokaci
Afzal ya d'agota daga jikinsa da k'yar dan yadda ta
kankamesa. Cike da mamaki ya tsaya kallon yadda take kuka
sannan daga bisani ya shiga share mata hawayen nata "Please
don't cry Rania."
"I should really start packing my clothes" ta sanar dashi tana
mey hana k'wayoyin idanunta had'uwa da nasa. "I'm really
happy for you two Yaya, Allah ya baku zaman lafiya mey
d'aurewa."
"Mey kike cewa haka Rania? Zaman lafiya tsakani na da
waye?"
"Da Nazeefah."
Murmushi ya saki kad'an "Meyasa kika ce haka? Why not
you?"
"Saboda bani ce za6in da Allah yayi maka ba Yaya. I know I'll
be the one to leave and even though nima hakan ne ze fiye
mun kwanciyan hankali I just can't deny the fact that I still
love you so very much and I'll miss you so damn much."
"But you don't have to miss me Rania because you're not
going anywhere, this is your home anan kuma zaki cigaba da
zama ba inda zaki."
"No ba sekayi hakan ba Yaya, zanje in samu Mami a gida,
chan d'in ze fiye mun kwanciyan hankali yaso ko haya ne se
kasa a nan d'in." Dariya sosai ta basa wanda ya kasa dannewa
yayinda ta tsaya kallonsa cike da mamaki da takaici. Mey yake
nufi da hakan?
"Rania listen to me, ba inda zakije nan ne gidanki kuma
d'akin mijinki okay?"
"D'akin mijina? Nazeefah kuma fa? Karka bijire wa za6in
Allah saboda son zuciya Yaya. Idan kuma tsoron abinda Papi
da Mami zasuce kake then ka kwantar da hankalinka kasani
duk zasuyi maka kyakkyawar fahimta kaman yadda nima nayi
maka. We all know you love me Yaya, please don't bother
yourself."
"Tsaya, kafin muyi aure mey kikayi? Kinyi Istikhara right?" Kai
ta gyad'a masa a hankali cike da rashin fahimta sannan ya
cigaba "Kuma bayan da kika gudanar se waye Allah ya za6a
miki?"
"Kai Yaya" ta amsa a takaice.
"Kina ganin it is possible ace ni kuma nayi Istikharan yanzu
se wata ta daban ta zame za6in da Allah zeyi mun bayan ke
kuma ni Ya za6a miki?"
"But Yaya-"
"Ki sani Rania ko sau dubu mutum yayi Istikhara za6in Allah
d'aya ne sedai idan shi yaso bijire wa hakan. Kaman yadda
kikayi naki istikharan Allah ya za6a maki ni, nima haka ya
za6a min ke yanzu. We two are meant to be Rania in shaa
Allahu mutuwa ce kad'ai zata shiga tsakani na dake. Rania I
love you so much kuma Allah kad'ai ne sheda game da irin
son da nake yi miki, shi kad'ai yasan idan bake bazan iya
rayuwa ba, shi kad'ai yasan muddin na rasaki bazan ta6a iya
samun kamilar mace mey kyawawan d'abi'u da halatayya irin
naki ba shiyasa ya za6an min ke ya sake bani daman da zan
soki in kuma kula dake har ila k'arshen rayuwa na. I can't do
without you Rania and I can't ask God for more da ya sake
bani daman kasancewa mijinki, forgive me for all the times
I've wronged you Rania, I'm terribly sorry please forgive me."
Kuka Amal ke sosai yayinda ta kasa amincewa da abubuwan
daya fad'a mata. Se gani take kaman a mafarki komai ke
faruwa tabbas itama bazata iya rayuwa idan ba shi ba. Gani
take kaman duk yadda yake jin yana sonta ita tafi sonsa, don
dai kawai ita bata nunawa ne. Daga k'arshe kuma bazata iya
yima Allah godiya ba da ya sake bata daman kasancewa
matarsa, sai dai kuma bazata iya duba irin rayuwan k'unci da
tashin hankalin da Nazeefah zata fad'a ba a rashin Afzal. Se
gani kawai take inda itace Afzal yace ze sauwak'e wa. Tasan
duk kalan rashin tawakkalinta tana bayan Nazeefah. Tasan
Nazeefah na iya yin k'aramin hauka akan wannan dalili, she
knows this is not going to be easy on her shiyasa take tausaya
mata sosai.
"Rania?" Ya kirata bayan shirun da tayi, jikinsa kawai ta fad'
yayinda ta shiga yin kuka na sosai. "Bakayi mun komai ba
Yaya don haka ka daina tambaya na yafiya I love you so very
much." Ba k'aramin dad'i kalamanta suka sanyasa ba, matseta
tsam ya sakeyi a jikinsa tamkar ana shirin k'watan masa ita
yayinda wani irin sonta yake sake shiga zuciyansa. Sun dad'e
a haka sannan daga bisani ya janyeta daga jikinsa sede har
anan hawaye Amal ke.
"Please don't cry Rania."
"I wish I could stop Ya Omri."
"But there's no need to."
"There's every need to cry Ya Omri."
"Saboda ban barki kin tafi gida kaman yadda kikeso ba kike
wannan kuka Rania? Saboda Allah ya za6an min ke? Ashe ba
haka kika so ba, I thought you said you love me" Kai ta gyad'a
mishi take tana murmushin takaici.
"Then meyasa kike kukan? A tunani na this is supposed to be
the most happiest moment for us both."
"Yes it is Yaya kuma hawayen nan da kake gani, hawayen
farin ciki ne gani nake kaman a mafarki komai ke faruwa, I
can't believe that we're still going to remain married to each
other after hope has been gone."
"I feel thesame way Rania, but tun farko tun kafin in gudanar
da Istikharan nan nasan komin yaya akayi ni dake bamu
rabuwa."
"Ko meyasa kace haka?" Tayi saurin tambayansa cike da
mamaki.
"Saboda Istikharan da kikayi kafin mukayi aure Rania, idan da
har ace akwai sharri a auran mu da Allah baze za6a miki ni
akan Abdul daya kasance masoyinki ba. Idan har na rabu dake
kinga kenan babu amfanin istikharan da kikayi. Ko ce miki
akayi shi istikhara temporal decision ne na d'an lokaci?
Hankali na ya tashi ne gabad'aya saboda Nazeefah. Ina
matuk'an tausayawa halin da zata shiga idan har ta gano cewa
I chose you over her, shiyasa nayi coming up da plan na cewa
zanyi Istikhara kinga idan har nayi ita da iyayenta bazasuyi
mun mumunar fahimta ba, zasuga za6in Allah nabi ba wai na
zuciya na ba. Sedai kuma yanzu bayan dana gudanar da hakan
nakega still Nazeefah bazata amince ta kar6i wannan bak'on
lamarin da hannu bibbiyu ba. Nasan komin tayaya bazata ta6a
fahimtar cewa Allah ne ya had'ani dake ba, bazata ta6a gane
cewa ba komi mutum yake so a duniyan nan yake samu ba,
gani take komai laifinki ne Rania and that is what hurts me the
more knowing who you really are. Bana son a sanadin hakan
ta sake tsanarki, ita gani take komai laifinki ne, ke kika janyo
bayan ba haka bane. I wish Nazeefah could see this kind and
selfless side of you. Har yau kalaman ki na yinin ranan da na
sanar dake cewa Nazefah k'anwarki ce suna kaina. Har yau na
kasa mancewa dasu kuma bazan ta6a mancewa da su ba.
Yadda kika cire son kai kikace kin yafe ni wa Nazeefah even
though kina so na bawai bakiya sona ba se don cewa da
Annabi yayi "La yu'minu ahadukum hatta yuhibbu li akhihi ma
yuhibbu li nafsihi" [imanin d'ayanku baya cika har seya so wa
d'an uwansa abinda ya so wa kansa] I get that you love me
but you're willing to let your sister have me and ba kowa keda
irin imanin nan naki ba Rania ko ni nan bazan iya aikata abinda
kikayi ba ranan saboda haka kuma naji respect naki ya k'aru a
idona yayinda sonki ya sake k'aruwa a zuciya na."
Murmushin jin dad'i ta sakar masa tana mey share
hawayenta "Ka sani ko da nace maka hawayen nan na jin dad'i
ne k'arya nayi because zuciyata tausayawa Nazeefah take, I
can't imagine the kind of hell she'll go through Yaya don haka
har nakejin kaman mu hak'ura da juna sedai kuma bazamu iya
yin jayayya da za6in Allah ba."
"Hakane Rania, let just pray for her in shaa Allah as time
progresses zata fahimci komai ta kuma nemi gafararki ayi
zaman lafiya gabad'aya."
"Da kuwa ba abinda zefi mun hakan farin ciki da jin dad'i
Yaya. Inspite of how Nazeefah disperses me wallahi I still love
her kuma zan cigaba da sonta ina yi mata uzuri har zuwa
lokacinda zata gane gaskiya."
"Allah yayi miki albarka Amal ya baki yaran da zasu kula dake
ranan da buk'atan hakan ya taso Rania, I'll forever love,
cherish and adore you."
"Ameen Ya Omri I love you too."
"Let's eat out ai zaki iya fita ko?"
"Why not? Bari in shirya."
***
Washegari...
Dai-dai gaban gidansu Nazeefah yayi parking sannan ya zaro
wayansa ya kira Daddy a karo na farko ya d'aga.
"Halo Afzal ka iso ne?"
"Eh Daddy."
"Toh bismillah mana ka shigo." Harga Allah beyi niyan shiga
ciki ba amma yaya ya iya? Gyara packing nasa yayi ya k'arisa
ciki inda ya samesa a parlour ya gaishesa. Bayan sun gaisa ya
zaro takardan daya ninke daga aljihunsa ya mik'awa Daddy
"Kaman yadda nayi muku alk'awari cewa zanyi Istikhara, duk
kuma wacce Allah ya za6ar mun ita zan d'au in sauwak'e wa
d'ayan. Toh game da sakamakon dana samu bayan na
gudanar da Istikharan na yanke wannan hukunci ba don son
kai ko son zuciya ko makamancin haka ba, da fatan kai da
iyalanka zakuyi mun kyakkyawar fahimta. Ga takarda nan na
sakin Nazeefah, dafatan ze isa gareta zaka kuma bata hak'uri
a madadi na ni zan wuce."
"Dakata Afzal kar kayi saurin tafiya. Kayi hak'uri ka bani
dama in baka hak'uri na jefaka da iyalinka cikin wannan
rud'ani da tashin hankali da nayi. Kuma ka sani wannan
hukunci daka yanke shine dai-dai koda ma ace bakayi
istikhara ba bazan bari ka saki Amal ba saboda abinda nayi
mata da mahaifiyarta kad'ai ya ishesu takaici da jarabawa.
Dole nima in gir6e abinda na shuk'a. Da fari na d'au zan iya yi
wa Allah wayo, na d'au idan har na aurar da Nazeefah
shikenan bani da wani tsoro kuma ashe ba haka abun yake ba,
ashe ita zina bashi ce idan har ka cita dole komin ta yaya ne
ka biya. Kuma muddin ba a kaina ze ramawa Jameela abinda
nayi mata ba dole se akan wanda nakeso. Dukda cewan Amal
da Nazeefah 'ya'yana ne amma kaman yadda zanfi jin zafin
sakin nan akan Nazeefah ba haka zanji ba idan da akan Amal
ne saboda babu shak'uwan nan na uba da 'ya a tsakani na da
ita. Allah ya za6an maka Amal ne saboda ya koya mun da
'yata darasi kuma saboda itama koda sau d'aya ne taji dad'in
rayuwa. Ka sani wannan hukunci da ka yanke dai-dai ne kuma
zanyi k'ok'ari in fahimtar da iyalai na, Allah ya baku zaman
lafiya mey d'aurewa da Amal ya albarkaci rayuwanku in shaa
Allah zan isar wa Nazeefah sak'onka."
"Nagode sosai Daddy."
"Ba komai, se kuma batun Jameela bazan gaji da rok'an
kanka ba da kayi mun kwatance injeni gidansu in nemi
tubarsu, idan ban samu sun yafe mun ba alhak'insu ya cigaba
da bi na kenan, ka tausaya mun da iyalai na please Afzal."
"In shaa Allah zanyi ma Papi magana karka damu."
"Toh nagode sena ji daga gareka."
"Ba komai ni zan wuce" ya fad'a had'e da mik'ewa "Ka
gaishe da Amal ina da niyyan shigowa inzo in dubata nima in
nemi tubarta amma ina son in d'an bata lokaci saboda nasan
yadda zata ji ta tsaneni yanzu."
"Zataji Daddy se anjima" yana kaiwa nan ya fice ya koma
office har a yau idan ya gwada kiran layin Nazeefah bata
d'agawa. Ba komai yasa yake son ya kirata ba se don so da
yake ya bata hak'uri, baya son taga kaman baya sonta ne, har
yau har gobe ze cigaba da sonta saboda akwai gur6in da ita
kad'ai ce ta mamaye a zuciyansa. Ita ce macen da ya fara sani
a rayuwansa, itace macen da ya fara sumbata itace macen da
ya fara sharing wani abu nashi da ita. Shin har ze iya mancewa
da ita a rayuwansa? He don't think so.
****
Daddy be samu ya kaiwa Nazeefah takardan nata a ranan
ba se a washegari. Bayan ya dawo daga sallan Azahar ya d'au
wayansa ya kira Mummy sedai kaman yadda ta saba ignoring
call nasa hakan ma tayi yau don haka ya tura mata sak'o.
_Hjy Surayya kiyi hak'uri ki d'au wayan nan muyi magana.
This is not about me it's about our daughter Nazeefah, thank
you._
Sak'on ya shiga bada dad'ewa ba Mummy ta karanta se
contemplating take ta kirasa taji lafiya ne ko ta bari. Chan
k'arshe de ta kira wanda ya d'aga a karo na farko. Bata basa
daman yin magana ba tace, "Meya samu Nazeefan?"
"Hjy Surayya wannan ba maganan waya bane gani nan
tahowa yanzu."
"Karka 6ata lokacinka bana nan na fita."
"We both know k'arya kikeyi zanzo yanzu please" bata sake
ce meshi komai ba ta katse wayan. Cikin mintuna da basu kai
ashirin da biyar ba sega shi nan ya iso. Waya yayi mata akan
ta fito nan da nan ta sanya hijabinta ta fice.
Ba yadda Daddy beyi ba da su k'arisa koda reception ne su
zauna suyi magana tak'i, tace ita idan har baze fad'i abinda
yake tafe dashi ba zata koma ciki. Toh suje cikin mota su
zauna nan ma tak'i. Yasan sam bey kyauta mata ba amma ba
wai yayi hakan dan ya raina ta bane ko makamancin hakan, shi
tsoron sanar da ita yake gudun kada ta gujesa kaman yadda
takeyi yanzu.
Hannu yasa a aljihunsa ya fito da takardan had'e da mik'a
mata.
"Mey wannan?" ta tambaya ba tare da nuna yunk'urin amsa
ba.
"Kedai bud'e ki gani." Kaman wacce bazata kar6a ba ta
amsa ta bud'e had'e da karancewa.
_A ranan Laraba, goma ga watan Juneru shekara dubu biyu
da goma sha takwas na saki matata Nazeefah, saki d'aya,
biyu, uku saboda haramta mana zama da shari'a tayi a
sanadin ta na kasancewa 'yar uwar matata Amal na jini._
Ajiyar zuciya Mummy ta sauk'e dama tasan za'ayi haka.
Dama tasan Nazeefah ce Afzal ze saka kawai bata so ta nuna
mata bane don kar ta tayar mata da hanaki amma tasan haka
za'ayi dama kodan ma Allah ya kama Daddy yasa shima yaji
zafin da mahaifiyar Amal taji sanda yayi mata fyad'e. Tasani
dole ne wannan k'addara ya fad'a akan Nazeefah saboda
itama Amal ta samu farin ciki koda sau d'aya ne a rayuwarta.
Idan harda ace wannan saki akan Amal ya fad'a da Daddy
baze ji zafi kaman yadda ace zeji yanzu da ya fad'a akan
Nazeefah. Ta hakan ne kawai Allah ze sanyasa gir6e abinda ya
shuk'a, ta hanyar mayar masa da 'ya bazawara kaman yadda
ya k'wace wa 'yar mutane budurci.
"Shikenan ka huta ai yanzu Alhj, amma kasani nida 'ya'yana
bazamu ta6a yafe maka wannan abun kunya daka aikata ba."
Be bari ta shiga takawa ba yayi sauri ya rik'e k'asan hijabinta
"Hjy Surayya bazan ma fara tambayan gafararki ba saboda
nasan abinda nayi miki da 'ya'yanki is unforgivable but atleast
give me a chance to apologize and tell you sorry. I'm gravely
sorry for hiding the truth away from you, wallahi bawai don
bana sonki bane kokuwa don bana mutuntaki yasa na 6oye
miki wannan al'amari, sonki da nakeyi ne ya rufe min ido,
bana son abinda ze shiga tsakani na dake Hjy Surayya, bana
son in rasa ki. Dan son zuciya irin nawa se naga idan har na
sanar dake gaskiya zaki gujeni kik'i aurena shiyasa na rik'e
komai wa kaina. I love you so much Hjy Surayya and I'll never
stop loving you, I'll wait. Zan jiraki koda kuwa zuwa k'arshen
rayuwana ne amma bazan gaji da baki hak'uri ba dan Allah kiyi
hak'uri ku dawo gida."
"Babu wani abinda zaka sake fad'amun da zaisa in canza
ra'ayina. Idan 'ya'yanka kake so kana iya shiga ciki yanzu ka
ebosu amma nikam takarda na nikeso. Kaman yadda ka shiga
tsakanin auren yaran nan kasa Afzal ya saki Nazeefah saki ba
d'aya ba, ba biyu ba har uku nima haka nake so ka rubuta mun
nawa. Idan har 'yata zata shiga k'uncin rayuwa ka tabbata kai
m seka shiga ninki ba ninkin nata don haka ka rubuta min
takarda na yanzun nan anan. Tunda rayuwan zawarci ka za6a
wa 'yarka tayi nima mahaifiyarta shi zanyi."
"Dan Allah kiyi hak'uri Hjy Surayya nasan nayi miki laifi, laifi
babba amma dan Allah kiyi hak'uri ki gafirceni. Idan kika tafi
kika barni ya kikeson in rayu?"
"Bakayi tunanin hakan ba kafin ka danne 'yar mutane kayi
mata fyad'e? Se kaje chan ku k'arasa da ita mahaifiyar Amal
d'in that is idan har zata iya yafe ma zaluntar ta da kayi."
"Kema kinsan bazan iya rayuwa da kowa ba bayan ke Hjy
Surayya, kinfi kowa sanin yadda nake sonki tun ba yau ba."
"Sam ba haka bane, I was a fool to believe you love me Alhj,
yaci ace tun a lokacin chan na gane kud'in mahaifina kawai
kake so ba ni ba. Wallahi Allah ne kad'ai ze sak'a mun. Duk
kalan halaccin danayi maka na sa mahaifina yayi maka duk
baka ga hakan ba you still chose to lie and cheat on me."
"Dan Allah kiyi hak'uri bazan ta6a gajiya da baki hak'uri ba
saboda nasan ban kyuata ba amma wallahi I love you Hjy
Surayya I really do."
"Shin anya ma kuwa labarin daka tsara min da iyayena na
cewa kai maraya ne gaskiya ne kuwa? Shin anya kuwa ba
k'arya ka shirya mana ba saboda ka samu kaci arzikin
mahaifina Alhj?"
Shiru Daddy yayi gun ya kasa cewa komai. Tabbas yayi mata
da mahaifinta daya kasance hanshak'in mai kud'i bahaushe
daga Kano k'arya lokacinda yazo aurenta. Saboda gudun da
yake kar a nemi iyayensa kowani d'an uwansa a garin hakan
asirinsa ya tonu na cewa yayi ma wata fyad'e a k'auye Mummy
ta fasa aurensa ko iyayenta su hanata. Tun bayan da abin ya
faru ya samu ya dawo makaranta be sake d'aga wayan
iyayensa ba, duk lokacinda yaga kiransu baya d'agawa har ta
tsinke saboda yasan akan mey zasuyi masa magana shi kuwa
bayida abin cewa. Daga k'arshe ma da yaga kiran ya soma
isansa se kawai ya sauya lamban wayansa gabad'aya, tun
daga nan be kuma sake ji daga garesu ba se...
"K'arya kayi mana ko? Why aren't you saying anything Alhj?"
"Hjy Surayya yes, yes nayi miki da Abba k'arya batun iyayena
amma wallahi ba don bana respecting naki bane se don tsoro
da nake kar a garin hakan gaskiya ya fito in rasaki."
"Wani gaskiya?" tayi saurin katsesa.
"Batun abinda ya faru tsakani na da mahaifiyar Amal."
"Wane irin mak'aryaci ne kai Alhj? Mey nayi maka a rayuwa
da ka za6i ka gina duk wani abinda mukayi accomplishing tare
akan k'arya?" Ta tambayesa hawaye na saurin ciko mata a ido.
"All I did was to love you Alhj I'm so disappointed in you na
tabbata da Abba yana raye a yau da shima baze ta6a yafe
maka ba."
"I'm truly sorry Hjy Surayya amma abinda ya faru ya riga ya
faru idan da zan iya mayar da lokaci baya da nayi dan in gyara
komai amma bazan iya ba please give me a second chance
idan kika tafi kika barni taya kikeson in rayu? Tabbas idan ba
ke su Nazeefah bazasu amince su dawo gida a gareni ba
please kiyi hak'uri."
"Bayan k'aryan nan se kuma wani k'arya ka sakeyi mun?"
"Hjy Surayya a shirye nake da in sanar dake duk wani abinda
kike buk'atan ki sani amma zaki galabaita tsaye a nan saboda
labarina nada tsawo kiyi hak'uri mu shiga mota kokuwa mu
k'arisa cikin reception." Bata ce da shi komai ba kawai ta
shiga takawa yayinda yake biye a bayanta, a VIP reception
suka zauna sannan Daddy yayi gyaran murya ya soma kaman
haka.
"A shekaran da na dawo hutun second year d'ina ne muka
had'u da mahaifiyar Amal wato Jameela wacce nake kira da
Jamee na. Jameela ta kasance itace mace ta farko da Allah
ya fara sanya min soyayyarta a zuciya na, so kuma na aure
bana lalata ba. We started off as friends amma cikin
k'ank'anin lokaci soyayya mey k'arfi ya shiga tsakaninmu.
Jameela was simply everything I could ever ask for, lokacin da
muka fara soyayya kwata-kwata shekarunta goma sha shida
ne, she was so beautiful, young and innocent. Tsaftacacciyar
soyayya muka gudanar nida ita as ko zance naje wajenta iyaka
muyi hira ba wani ta6e-ta6e bale makamancin hakan saboda
Jameela yarinya ce kamila wacce take san addininta sosai
take kuma k'ok'arin bin dokokin da ya kafa mata. Ahaka ne har
nazo na koma makaranta wanda bada dad'ewa ba Jameela
tayi mun waya cewa mahaifiyarta na shirin had'ata aure da
d'an chairman na garinmu idan har ban hanzarta turo
magabata na ba ana iya aura mata shi d'an chairman d'in.
Hankalina ne ya matuk'an tashi se Allah-Allah nake session
d'in ya k'are in dawo gida. Kasancewar a scholarship na samu
karatun seya zammana banida gatan dawowa gida kowani
hutu se shekara-shekara. Addu'a muka tsayar sosai nida
Jameela cikin ikon Allah kuwa se har wata shekarar ta zagayo
shi wannan yaro be turo ba. Na dawo bada dad'ewa ba na
samu mahaifina nayi mishi maganan Jameela akan ina son a
tura tambaya gidansu sede sam Abba yak'i amincewa akan
cewa da baki na ne zan ajiye mata idan nayi aure yanzu ina
karatu. Duk yadda naso fahimtar dashi cewa Jameela bata da
matsala da hakan besides ma ina d'an yin business,
makaranta kuma shekara d'aya ne ya rage sedai hakan ya
gagara Abba yak'i ya amince ya bani goyin baya. A sanadin
haka nida Jameela muka shiga tashin hankali sedai bamu cire
rai ba, muka mik'a komai ga ubangiji. Ban san ya akayi ba de
amma wataran mahaifiyar Jameela ta jiyota muna waya bayan
kuma ita ta riga tayi mata miji a sanadin haka tayi ma
Jameela duka tayi seizing wayarta sannan ta horeta da kada ta
sake kulani. Kwana biyu na daina ji daga gun Jameela ko na
kira layinta baya shiga gashi sun k'are makaranta lokacin bale
inje mu had'u a chan d'in. Rana d'aya kawai na jajirce na jeni
gidansu dan yadda shirun yayi yawa, dukda cewan ta haneni
da taka bakin k'ofan gidnasu saboda yadda ta nuna mun
mahaifiyarta bata sona. A farko da naje mahaifiyar ta kar6eni
da fara'a kasancewar bata gane waye niba a lokacin da nayi
mata bayanin kaina kawai ranta ya 6aci ta sauk'e duk wani
haushin da takeji a kaina tayi mun koran kare harda muciyan
tuwo ta bini waje. Hakan ba k'aramin 6ata mun rai yayi ba dan
dole na hak'ura da Jameelah saboda a rayuwa na washi
walak'anci na kuma d'au alwashin sena rama cin mutuncin
nan da tayi mun ko ta yaya ne. Rana d'aya ina zaune kawai
sega kiran Jameelah ban 6ata lokaci ba na d'aga inda take
sanar dani tana son mu had'u. Chan na kaita bayan gari da
siyasan cewa abu nake so in nuna mata, ina son Jameelah
amma abinda mahaifiyarta tayi mun ya tsaya mun a wuya ko
kallonta nayi se na tuna da abin. Haka kawai shaid'an ya soma
raya mun in d'au fansa akanta sedai kuma sonta da nake yana
rik'eni. Amma haka shaid'an ya rinjayi zuciyana ta hanyan raya
mun ai tunda mahaifiyarta tana sonta idan na ta6a lafiyarta
kaman na ta6a na mahaifiyar ne don haka idan na lalata mata
rayuwa abun seya fi wa mahaifiyar zafi. Ana cikin haka ne
sega abokai na guda biyu dana basu labarin abinda mahaifiyar
Amal tayi mun nan suka sake k'arfafamun guiwa suka bani
had'in kai nayi ma Jameela fyad'e ba tare da d'igon imani ba."
"Koda mahaifinta ya kai k'arana dana mahaifina gurin mey
unguwa k'aryata komai nayi na samu abokaina suka rufa mun
asiri shima Abba ya goya mun baya saboda baze ta6a kawowa
a ransa zan iya aikata abinda nayi ba. Acikin satin ko na gaba
na samu na koma makaranta ban sake ji daga garesu ba. A
karon chan ne na had'u dake Surayya, kika yi mun erasing duk
wani bad memory'n dana bari da a k'auyen Askira. Tunda na
sameki komai ya canza Surayya, soyayyar da kika nuna min ta
dabance. Banida komai, Baki sanni ba, baki san wani nawa ba
amma kika so ni kika kuma amince dani regardless. Ko a
mafarki ban ta6a tsammanin cewa wataran zan iya mallakan
'yar babbar gida kamar ki ba mey hankali da tausayi. Lokacin
da kika ce mun muyi aure ne nashiga tashin hankali badon
bana sonki ba se don banason hakan ya tono mun labarina
dana bari a garin Askira. Ban san da wani idon zan sake kallon
iyayena da na shafesu a doron k'asa saboda selfish interest
d'ina ba na kusan shekara. Rud'ani na matuk'a na shiga yayin
da na rasa ya zanyi gashi bana son in rasaki saboda da in rasa
ki gara na rasa komi nawa koda kuwa raina ne. Don haka nayi
miki da Abba k'aryan cewa ni maraya ne. A tunani na hakan ne
kad'ai zaisa Abba ya amince ya aura min ke Surayya. Ba
abinda Abba beyi mun ba bayan dana aureki, abinda ya kama
kayan da zansa, gidan da zamu zauna, motan da zan hau
harta sadakin ki shi ya biya mun, komai da na sani na mallaka
a lokacin na Abba ne. Harta aiki shi ya samo mun bayan da ya
biya mun kud'i na gama masters d'ina muka dawo gida nan
Nigeria idan ban manta ba kina da cikin Khaleefah."
"A lokacin da muka dawo ne bayan na tafi yin service d'ina
na koma k'auyen Askira dan d'auko su Abba in nemi tubansu
in basu hak'uri ake tabbatar min da cewa sunyi hatsari
shekaru biyu da suka wuce a hanyansu na zuwa k'auyen
Dambuwa. Shi Abba a take ya cika ita kuwa Umma tayi jinyan
wata shida sannan mutuwa yayi halinsa. I felt hopeless and
useless Surayya, iyayena sun mutu amma seda shekara biyu
nake sani. Ji nayi kaman in soka wuk'a wa kaina in mutu wani
irin d'a ne ni? Na sosai nayi nadaman abinda na aikata na d'au
alk'awarin yin sadak'atul jariya da sunayensu Allah ya kai musu
ladan kabari. Nasan rashin kyautatawan da nayi wa iyayena
yasa nima Allah ya jarabce ni da gagararriyar 'ya kaman
Nazeefah.l
"Daga gida na wuce gidansu Jameelah inda ake sanar dani
suma sun tashi sun k'aura sun bar garin gabad'aya. Ba wanda
ya sanar dani cewan rabo ya shiga tsakani na da ita bayan
faruwan abun shiyasa ban ta6a sanin Amal 'yata bace se
recently. Wallahi ba k'arya nake yi miki ba Surayya please
believe me, taya zan so in had'a 'ya'yan cikina kishi Surayya
bayan na san yin hakan haramun ne?"
"Yanzu ina ita mahaifiyar Amal d'in take Jameelah?"
Mummy data amince da duk wani abinda ya fad'a ta soma da
tambayansa.
"Tana cikin garin nan da zama amma bansan inda take ba,
rannan Afzal ya taho da ita da mahaifinta gidan Nazeefah inda
mukayi magana duka akan yadda za'a 6ullowa al'amarin nan
nasu."
"Baka san inda take ba kace?"
"Wallahi ban sani ba Hjy Surayya ai kinsan bazan miki k'arya
ba."
"Bawai ina k'aryata ka bane Alhj I just want to be certain,
tana da aure?"
"Wallahi banda masaniya akan hakan amma base on abinda
Amal ta ta6a fad'amun kaman mahaifiyar nata bata da aure."
"Ka aureta Alhj" ta sanar dashi. Da mamaki ya tsaya yana
kallonta yayinda ya kasa amincewa da abinda tace.
"Eh?" Ya tambaya.
"Nace idan har Jameelah bata da aure kuma bata niyyan yin
wani auran anan kusa ka aureta."
"Hjy Surayya kin ko san abinda kike cewa?"
"This's the only way zamu iya samu mu had'a kan yaran nan
Nazeefah da Amal mu gyara zuri'ar mu. Ka fini sanin halin
Nazeefah, yanzu da Afzal ya d'au Amal a kanta ba k'aramin
tsanar yarinyar nan zatayi ba dama already ta riga ta tsaneta."
"Toh mey auro Jameelah zeyi ya gyara wannan lamari Hjy
Surayya?"
"Tabbas auro Jameelah zaisa Nazeefah ta shiga hankalinta ta
nutsu ta sani cewa mu dasu mun riga mun zamo abu d'aya
yanzu ta kuma sani cewa shi kishiya na akan kowa ne idan har
da tanayin kwatance dani tagani toh yau nima gashi anyi mun
kishiya."
"Tabbas kinyi gaskiya Hjy Surayya amma bana son in had'a
soyayyarki da kowa ke kad'ai nakeso."
"Karka damu dani kuma ma ai nasan kana son Jameelar taka
har yau ko ba haka ba?"
"Amma ba kaman yadda nake sonki ba Hjy Surayya ni
tausayin Jameelah kawai nake yanzu."
"Karka damu ai ni nace ka aurota."
"Hjy Surayya nifa banga amfanin yin hakan ba. Ba sena auro
Jameelah ba."
"Ka aurota Alhj ni na baka dama karka damu."
"Surayya-" hannunta ta aza akan nasa cutting him off "Don't
worry nima ai zama ni d'aya tal d'innan ya isheni ka kawo mun
abokiyar zama tana tayani hira na tabbata kaman yadda Amal
bata da matsala itama mahaifiyar tata haka ne."
"Wannan ba sekin fad'a ba Hjy Surayya Jameelah sam
batada hayaniya."
"Toh kaga komi ya zo mana da sauk'i kenan, ka auro ta kaji?"
Hjy Surayya what can I say? You're the reason behind who I
am today and everything I've achieved, banida bakin yi miki
da Abba godiya. Allah saka da alkhairi ya cigaba da sanya miki
albarka a rayuwarki ya kuma ci gaba da kai rahama kabarin
Abba."
"Ameen Alhj tare da iyayenka kai ma."
"Kin hak'ura zaki biyoni gida?"
"Har sena amsa tukuna zaka tabbatar da hakan?"
"Gani nake kaman mafarki nake Hjy Surayya, Allah yabar min
ke tabbas irinku acikin mata d'ad'd'aiku ne."
RANA DAYA Chapter 45
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
Tareda Naja'atu Lawal Rijau Niger State
@Whatapp 08083232323 or 09060202323
PAGE 45
"Ameen Alhj na."
"Mey hakan ke nufi kenan Hjy Surayya? Kin hak'ura kin yafe
mun kenan?"
"We all make mistakes Alhj amma ba dukan mu bane muke
gano kuskurenmu har ma mu nemi tuban wanda muka wa
laifi, shin meyasa bazan yafe maka ba tunda har kai ka gane
kuranka ka kuma nemi tuba? Na yafe maka Alhj Allah kuma ya
yafe mana gabaki d'aya" ta k'arashe tana murmushi. Daddy
baze iya kwatanta irin farin ciki da murnan da kalamun
Mummy suka sanyasa ba. Da murmushi kwance fal a fuskansa
ya mik'a hannunsa ya rik'o nata "Thank you so much Hjy
Surayya I can say my life has never been better until I met you,
Allah ya cigaba da miki albarka ya kuma barmu tare."
"Ameen Alhj you're welcome."
"Kinsan wani abu?"
"Seka fad'a."
"I love you" yana sanar da ita bata san lokacin da ta fashe da
dariya ba "Ji Alhj de, yaushe kuma muka fara wasan nan?"
"I'm serious Hjy Surayya saboda bana fad'a miki doesn't
mean I don't love you, I love you like the day I just met you
Hjy Surayya never forget that."
"Thank you Alhj."
"Thank you kad'ai? Ni bazaki cemin I love you in return ba?"
"Ka ga La'asar ya kusa gara ka tashi ka fice muyi niyya duka."
"Yau kuma? Toh sekin fad'a min zan bar nan."
"Lallai kuwa, nikam ka ga tafiya na" bata kai ga mik'ewa ba
ya dakatar da ita ta hanyan kama hannunta. "Alhj ka sakeni
mana!"
"Nak'i"
"Zan tara maka jama'a fah."
"Ni d'in Hjy Surayya? Ni d'in naki?"
"Toh ka sakeni."
"On one condition."
"Name it."
"Yaushe zaki dawo gida? Ina matuk'an kewarki."
"Kai da zaka k'aro amarya kode ka manta ne?"
"Amarya daban ke daban so yaushe zaki dawo keda 'yan'yan
namu?"
"Zamu dawo karka damu."
"Promise?" Kai zalla ta gyad'a mar sannan ya saketa "Toh se
anjima ki gaishe mun da Nazeefah da Khaleefah."
"I'll semun sake magana." Da haka ta fice ciki inda shi kuma
ya mik'e ya yi tafiyarsa.
D'akinta da Nazeefah ta wuce direct inda ta tarar da
Nazeefah mik'e kan gado kaman maciji ta zurfafa a cikin
tunani ko makaranta tak'i fita. "Tashi ki zauna muyi magana"
Mummy tace da ita bayan ta zauna a gefenta ta bakin gadon.
Ba gardama ta mik'e ta zaune.
"Ina son ki saurareni da kunnen masu hankali a matsayinki na
musulma me kar6an k'addara me kyau ko akasin sa." Tun
anan gaban Nazeefah ya fara bugun d'ari-d'ari dukda cewan
bata fahimci inda Mummy ta dosa ba.
"Ki sani cewa komai na faruwa ne bisa dalili fatan mu kawai
Allah ya sa hakan kawai shi ne mafi alkhairi a gareku
gabad'aya."
"Mummy ban fahimce kiba shin mey kike fad'i? Meya faru?"
"Ga wannan takardan ki ne Afzal ya kawo wa Daddy jiya
yana mey baki hak'uri kuma" ta fad'a had'e da mik'a mata. Jiki
na k'yarma Nazeefah ta mik'a hannu ta amsa had'e da
bud'ewa sannan ta karance hawaye kawai Mummy taga na
gangara daga idanunta ba makawa.
"Nazee-"
"Noooo!" Tasa wani irin d'ankaren ihu "Noo this can't be
happening, bani Ya Afzal yayi niyyan saka ba na tabbata
munafukan chan ce ta tilasta mai ya rabu dani wallahi bani
yayi niyyan saka ba Munmy."
"Nazeefah ya isa" Mummy ta fad'a tana k'ok'arin shawo
kanta saidai hakan sake tunzirata yayi. Zabura tayi tana kad'a
kai yayinda hawaye ke ambaliya a fuskarta "Mummy wallahi
bani Ya Afzal yayi niyyan saka ba ki yarda dani."
"Nazeefah please-"
"Tsaya kiga ina key'n mota na inje in samesa kiji bani bace
wannan takardan Amal ne ba nawa ba."
"Wani irin banzan magana kike Nazeefah? Bayan ga sunanki
nan boldly rubuce akai? Taya zakice ba naki bane na Amal
ne?"
"Wallahi Allah ba nawa bane ina key'n mota na yake?"
"Shin wai ina zakije?" Ta tambayeta. "Zan je in samesa
saboda bani yayi niyyan saka ba."
"Nazeefah there is no point kiyi hak'uri ki rungumi k'addarar ki
kowa yasan rabuwa da masoyi da zafi amma ba yadda kika
iya."
"Hak'uri? Hak'uri Mummy? Wallahi inde akan Ya Afzal ne
bazan ta6a hak'ura ba."
"Toh ya zakiyi? K'addara ta riga fata, the earlier kikayi
accepting gaskiya the better."
"How Mummy? So kike kice mun shikenan na rasa Ya Afzal a
rayuwa na kenan? So kike kice in nad'e hannu in bar Amal ta
sace mun miji ina ji ina gani?"
"Kema kinsan Amal baza ta ta6a yin hakan ba, Amal ba ita ta
sace miki miji ba Nazeefah, Allah ne ya k'addara rabuwan ku."
"No Mummy kinyi kuskure, idan ba mutuwa ba banga abinda
ze rabani da Y Afzal ba" mayafinta ta sanya ta janye key daga
gaban dresing mirror da niyan ficewa inda Mummy ta cafke
mata hannu.
"Bada yawu na zaki fita ba Nazeefah."
"Just let me go" tace da ita had'e da fisgan hannunta. Kaman
a kyaftawan ido Mummy ta isa bakin k'ofa ta kulle da key
had'e da zarewa ta rik'e a hannunta.
"Mummy ki matsa mun."
"Ba inda zakije Nazeefah saki ne ya riga ya auku ba abinda
kika isa kiyi da zeyi reversing case d'in sede hak'uri kawai, ki
d'au komi a matsayin k'addara ki yi tawasalli."
"Na gaya miki Mummy inde akan Ya Afzal ne bazan ta6a
hak'ura ba har se sakin nan ya koma kan Amal, bazan rasashi
ni kad'ai ba se inde mu biyu duka mu rasa sa so move out."
"Ina nan tsaye anan ba inda zaki." Dube-dube Nazeefah ta
shiga yi a d'akin chan ta hango wuk'a a kan bed side drawer
nan da nan taje ta d'auka ta saita dai-dai wuyan hannunta
(wrist) "Ko ki matsa ko in yanke kaina in mutu" Baki Mummy
ta hangame cike da mamaki da k'in yarda tana kallon
Nazeefah, batayi tsammanin rashin sanin addinin nata har
yakai matakin da za tayi tunanin d'aukan ranta da kanta ba.
"Nazeefah?" Ta kirata da d'umbun mamaki. "Da hankalinki?"
"Mummy banida wata amfani tunda na rasa Ya Afzal gara in
mutu in huta kowa ma ya mutu."
"Da hankalinki kike tunanin d'aukan ranki da kanki? Shin baki
san hukuncin hakan bane a addinance?"
"I don't care Mummy amma bazan iya rasa Ya Afzal ba I
can't because I love him, I love him so very much and Amal
stole him away from me, what else can I do?"
"Idan kika hak'ura komi mey wucewa ne Nazeefah wataran
se labari."
"No Mummy I can't move on, bazan ta6a iya son wani bayan
Ya Afzal ba, I can't do without him dan Allah ku bashi hak'uri
ya mayar dani d'akina."
"'Yar uwarki Amal kuma fah? Ya kikeson ayi da ita?"
"Ki daina kwatanta ta da 'yar uwata, idan da ta d'aukeni a
matsayin 'yar uwarta da bazata sace mun miji ba so ki matsa
ko kuma in yanke kaina."
"It doesn't have to be this way Nazeefah" Mummy ta sanar
da ita tana mey matsowa kusa da ita a hankali.
"Mummy stay away."
"Nazeefah dan Allah kiyi hak'uri karki yanke kanki" ko kallon
ta Nazeefah batayi ba ta sa wuk'an ta yanke hannunta wani irin
ihu Mummy ta k'urma had'e da k'arisawa kan Nazeefah da ta
shiga zamewa k'asa. Tarota Mummy tayi suka sauk'a k'asan
atare tana mey bubbuga fuskanta yayinda idanunta suka
cigaba da kakkafewa. "Nazeefah? Nazeefah? Innalillahi dan
Allah ki tashi Khaleefah!" Ba shiri ta saketa ta d'auko wayanta
had'e da kiran Daddy. A karo na farko ya d'aga, ko daman
magana bata basa ba tace, "Alhj ka juyo ka juyo da wuri
Nazeefah ta yanke kanta."
"What?!' I'm on my way" U-turn yasha nan take ya dawo ba
tare da 6ata lokaci ba akayi da Nazeefah nearest clinic inda
akayi emergency room da ita.
_53 minutes later_
Da wani irin gudu Afzal ya shiga haraban asibiti sannan ya
nemi waje yayi parking ya fito ya k'arisa ciki. Tsaye a inda
akayi mai kwatance ya same su da tashin hankali bayyane
karara a fuskokinsu.
"Afzal?" Daddy ya kirasa yana mey mamakin yadda akayi
yasan halin da suke ciki.
"Afzal waya sanar da kai muna nan?" Mummy ta tambaya.
"Mummy nine" Khaleefah ya amsa.
"How's she?" Afzal ya tambaya. Shiru ne ya d'auki wajen se
chan Mummy ta amsa "Muma jira muke likitocin su fito
tukuna."
15 minutes more sega emergency room d'in ya bud'u nan
duk suka duk'ufa sukayi wajen kowa da abinda yake tambaya.
Nan Dr'n ya musu bayanin komai yakuma tabbatae musu
cewa cut d'in beyi affecting Radial artery nata ba in less than
an hour zata farfad'o. Godiya suka masa sannan ya fice.
"Daddy, Mummy I'm so sorry I'm terribly sorry nasan duk laifi
na ne."
"Ko kad'an Afzal" Daddy yayi saurin katsesa "you're not to be
blamed for anything, idan har akwai mey laifi anan toh nine so
kabar damuwa."
"Mummy I'm sorry."
"Don't be Afzal mungode da kulawanka in shaa Allahu zan
sanar da Nazeefah zuwanka."
"Thank you Allah ya bata lafiya."
"Ameen mungode Khaleefah ka rakasa" cewan Mummy.
"No don't bother" Afzal yayi saurin amsawa sannan ya fice.
Gida ya wuce direct sede tun shigansa Amal ta karanci
yanayinsa wani iri. Bayan ta mar sannu da zuwa ta d'auko
masa ruwa ta zauna a gefensa. "Ya Omri lafiya?"
"Babu" ya amsa sama-sama.
"Kaman ya babu Ya Omri? Tell me kaji."
"Nagaji ne kawai barin je in watsa ruwa in huta" hannunsa
tayi saurin kamawa" kafin ya mik'e "Please tell me Ya Omri
nasan akwai abinda yake damunka."
"Rania I'm sorry."
"Why what for?"
"Rania it's Nazeefah tana kwance a asibiti yanzu haka as we
speak."
"Subhanallahi meya sameta?"
"Yanke kanta tayi."
"Nazeefan? Dalili?"
"Batun takardan ta, yanke kanta tayi in attempt to kill
herself."
"I want to go and see her Ya Omri."
"Rania-"
"Please" tayi saurin katsesa "Ya Omri ji nake kaman duk laifi
na ne, komin mey Nazeefah tayi laifi na ne."
"Kar kiyi magana haka Rania, in har akwai wanda za ayi
blaming anan mahaifinku ne and he's sorry mu taya Nazeefah
da addu'a kawai Allah yasa ta gane gaskiya da wuri."
"Ameen but I still want to go and see her please kar ka
hanani Ya Omri." Hannunta ya d'au ya rik'e a cikin nasa "Okay
zanyi wa Mummy magana se muje."
"Thank you."
"Don't mention so me kika girka mana? I'm hungry."
"Spaghetti ne kawai nima ban dad'e da dawowa daga school
ba."
"Oh! Muje toh."
****
Bayan Maghrib Afzal yayi wa Mummy waya inda ya tabbatar
da cewa ba a sallamesu ba har anan sannan yace mata suna
shigowa shi da Amal. Acikin k'ank'anin lokaci suka isa inda
Mummy ta taresu ta k'arisa ciki dasu. Nazeefah na ganin Amal
taji tsikan jikinta gabad'aya na tashi yayinda ta shiga yi mata
wani irin tsananin tsana.
"Mey wanann take mun a d'aki Mummy? Send her out send
her out!"
"Nazeef-"
"Bana k'aunan ganinta a kusa dani ku fitar mun da ita daga
d'aki" ta katse Mummy da hanzari.
"Nazeefah please" Afzal ya sa baki. "Kiyi hak'uri."
"Hak'uri Ya Afzal? Da abinda zaka sak'a mun kenan? Ashe for
all these while k'arya kake mun? I never expected this from
you, I thought you love me ashe ba haka bane, ka sani daga
kai har matar taka bazan ta6a yafe muku wannan abu da kuka
mun ba Mummy send them out."
"Nazeefah dan Allah kiyi hak'uri" Amal tace da ita.
"Ko da wasa karki kuskura ki sake kiran suna na Amal saboda
keba 'yar uwata ba ce. You ruined my life, first you stole my
father away from me and then now my husband, meyasa kike
nok'e-nok'e? Ki fito fili kice kina son ki zama ni kina son ki
sace nun rayuwa. Amal na tsaneki, na tsani duk wani mey
sonki, ba kuma abinda ze fi mun nishad'i da jin dad'i kaman
inga gawanki bana k'aunanki in har kina son kanki ki ficemun
daga d'aki you have absolutely no right to speak to me get
out." Hawaye Amal ta shiga yi yayinda Afzal ya janyeta jikinsa
"Ku fice mun daga d'aki bana k'aunan ganinku duka."
"Nazeefah meyasa bakida mutunci ne?" Mummy ta
tambayeta tana mey tsananin jin takaicin abinda Nazeefah ta
aikata.
"Shikenan Mummy zamu koma" fad'in Afzal "Nazeefah Allah
ya baki lafiya we mean you no harm" daga fad'in haka ya
sauk'o da ganinsa akan Amal "Let's go Amal." Badan Amal na
so ba ta amince ya jata waje se kallon Nazeefah take tana
kuka itako Nazeefah ko sake kallon 6angarensu batayi ba.
"Meyasa baku barni na mutu ba Mummy? I hate my life I
hate Amal."
"Nazeefah it pains me as a mother ace ni na tsuguna na
haifeki, Allah ma shaida ne ni ba tarbiyyan dana baki ba kenan,
bansan a ina kika d'auko wannan banzan hali ba dan bazan ce
na mahaifinku bane saboda koda wasa be ta6a gigin d'aukan
ransa da kansa ba. Kuma Amal da kike gani kika raina wataran
zaki nemata hannu bibbiyu ki rasata kuma ko kin k'i kin so 'yar
uwarki ce ba abinda zaki iyayi da ze canza hakan. Ki tashi ki ci
abinci yanzu za'a sallameki zamu koma gida."
"Wani gida?"
"Ban gane wani gida ba gida gida mana."
"Meya samu hotel da muke zaune aciki?"
"Zamu koma gida gun Daddy'nku nide na fad'a miki."
"No Mummy ni bazan koma gun Daddy ba, a dalilin mey?
Bayan duk bak'in ciki da k'uncin da nake ciki shine sanadi."
"So? He's still your father nothing can change that."
"Ni gaskiya bazan bi ku ba."
"Ni na fad'a miki" tana kaiwa nan ta fice had'e da rufo mata
k'ofan.
****
Tun da suka shiga mota har suka isa gida Amal take ta kuka.
"Amal it's okay with time in shaa Allah Nazeefah zata
fahimci komai kukan ya isa haka" Afzal yace da ita bayan sun
k'arasa ciki yana mey share mata hawayenta.
"Yaya I feel so responsible for everything Nazeefah is going
through, Nazeefah tana sonka har yau har gobe tana sonka
she can't ever stop loving you."
"And you too Lily, you love me don't you?"
"I do Yaya amma Nazeefah kuma fah? Yaya har ranta fa ta
so d'auka akan soyayyar ka."
"Amal you matter to me more than anyone morethan
Nazeefah kibar tada hankalinki kinji? I love only you"
rungumeta yayi a hankali itama ta zagaye hannayenta a
bayansa tana mey lumewa acikin rik'onsa yayinda kalamun
Nazeefah suke faman yi mata wasa a kai.
****
Washegari...
Dawowan Daddy daga gidansu Mami kenan amma sam babu
walwala tattare da shi. Yana shigowa Mummy da ta karanci
yanayin nasa tayi mai sannu da zuwa.
"Tak'i amincewa?" Ta tambayansa a hankali.
"Hjy Surayya ko bani dama in nemi tubansu sun hanani bale
in sanar dasu k'udurina, Jameelah tana matuk'ar fushi dani
haka ma mahaifinta. Ban san ya zanyi ba muddin tak'i yafe
mun, alhak'in ta ya cigaba da bina kenan idan da ma akaina
kad'ai ze tsaya da da sauk'i amma har ku baku tsira ba, bana
k'aunan sake ganin ku cikin k'unci Hjy Surayya bana son abinda
ze sake raba kanmu yadda na samu da k'yar Nazeefah ta
amince ta biyoki kuka dawo mun."
"Ka kwantar da hankalinka Alhj."
"Ta yaya Hjy Surayya? Ta ina hankalina yaga ta kwanciya
bayan rayuwan mu duka yana cikin gwagwarmaya."
"Ni da kaina zanje in samu Jameelah gobe muyi magana in
shaa Allahu zata yafe maka komai ta kuma amince da
k'udurinmu."
"Keda kanki?" Ya tambaya yana mey kasa 6oye mamakin da
ya sha.
"Baka yarda bane?"
"Hjy Surayya a ina aka ta6ayin haka? Dan Allah karki baiwa
kanki wahala-"
"Kabar zancen nan Alhj" tayi saurin katsesa "Ai mun wuce
haka yanzu try not to worry Allah kaimu goben."
"Ameen Hjy Surayya banida bakin yi maki godiya, Allah saka
ya biyaki da gidan Aljannah."
"Toh kuma godiyan mey kake? Muje kaci abinci."
"Ya jikin Nazeefah?"
"Da sauk'i tana kwance a d'aki tana bacci."
"Toh madallah".****
Tamkar mey ta6in hankali haka Nazeefah ta zame musu a
gidan ko abinci tak'i ci tun dawowansu daga asibiti jiya da
dare har izuwa yinin yau. Allah ma yaso ana sa mata ruwa.
Banda kuka ba aikinta a gidan, Mummy tayi mata nasiha tayi
mata fad'a amma ina tak'i ji haka zata kafa hotunan auransu
da Afzal tayita kalla ba fashi. Washegari kamar yadda Mummy
ta d'au alk'awari ita da Daddy suka jesu gidansu Mami inda ya
tsaya daga waje ita kima ta k'arasa ciki. Sallama tayi yayinda
take sa kai cikin gidan, Mami dake gida ita kad'ai ce ta amsa.
Kallo d'aya tayiwa Mummy ta tabbata mahaifiyar Nazeefah ce
saboda tsan-tsan kaman da sukeyi.
"Mahaifiyar Nazeefah?" Ta tambaya. murmushi Mummy ta
saka had'e da gyad'a mata kai. "Bismillah ki shigo" tabarma ta
shimfid'a musu inda suka zauna sannan suka gaisa.
"Bari in kawo miki ruwa."
"A'a 'yar uwa ba amfani."
"Toh lafiya dai ko?"
"Lafiya k'alau batun Abdallah nazo muyi magana."
"Kiyi hak'uri maman Nazeefah amma in har abinda ya kawo
ki kenan saidai ki koma."
"Nasani 'yar uwa nasan abinda Abdallah yayi miki da zafi da
ciwo amma abu ne ya riga ya faru ba abinda zamu iyayi da zai
canza hakan saidai muyi gyara. Kiyi hak'uri ki yafe masa, shi
yafiya ba kowa bane Allah yake basa iko da zuciyan yi amma
na tambayeki ne saboda nasan zaki yafe masa saboda ko ban
tambaya ba nasan a wajenki 'yarki Amal ta yo gadon
kyawawan d'abi'unta. Idan muka ce zamu biye ta zuciyoyin mu
toh wallahi ba abinda zamu tsinana wa kanmu na arziki. Ko
ban fad'a miki ba nasan kinsan irin tsanan da ke tsakanin
yaran mu Nazeefah da Amal. Duk yadda Amal ke son shirya
tsakaninta da 'yar uwarta hakan ya gagara kuma ba wanda ze
iya had'a mana kawunan yaran nan sama da ke."
"Ban fahimce kiba Maman Nazeefah ta yaya zanyi hakan?"
"Ki amince ki auri Abdallah."
"Iyyeh?" Mami ta zaro ido wuru-wuru waje. "Kikace?"
"Eh, ki amince ki auri mijina ta hakan ne kawai zamu iya
gyara zuri'ar mu mu had'a kawunan yaran nan dan Allah ki
amince."
"Kiyi hak'uri Maman Nazeefah amma bazan iya cika miki
wannan buri naki ba, bazan iya auran Khaleefah ba bazan iya
ba."
"Zaki iya 'yar uwa muddin kika yarda da hakan, dan Allah
karki bari tsanan dake tsakanin yaran nan yayi tsamari iche tun
yana d'anyensa ake iya tank'warasa, muddin ba'a sa musu a
jiki cewa mun zama abu d'aya ba yanzu toh wallahi gaba
tsanan da zasu tashi dashi a cikin zuciyoyinsu baze so yayi
kyau ba ki taimaka."
"Maman Nazeefah tunda nake ban ta6a jin inda uwar gida
tazo taya mai gidanta k'aro aure ba ko da kuwa a radio ne,
saboda haka ban san abinda ke cikin zuciyarki ba keda mijinki,
bansan mey kuke shirin yi mani ba amma koma menene kuyi
hak'uri ku janye ni daga cikin matsalarku tunda na samu auren
'yata be mutu ba Alhamdulillah koni na mutu a haka bazan
damu ba."
"Jameelah da zuciya d'aya nazo na sameki bada wata
manufa ba, Jameelah har yau har gobe nasan Abdallah yana
sonki, kema kin sani ba sena fad'a miki ba, ni kuma har ga
Allah har cikin zuciyata tun cemin da Abdallah yayi bakida
aure naji tausayinki ya shige min zuciya nasan ba komai ya
hanaki yin aure ba illa idan kika juya baya kika ga abinda
Adallah yayi miki, shi ya lalata miki rayuwa dan haka kuma shi
ya tantanci yayi making everything right don haka na basa
goyin baya na bashi shawaran ya auro ki. Kuma kinga ta hakan
ne kawai zamu iya had'a kawunan yaran mu. Zan barki kiyi
tunani anytime your mind is made up ga lamba na" ta fad'a
had'e da ajiye mata wani gajeren paper data rubuta
number'nta ajiki "Seki kirani, hope to hear from you soon ni
zan wuce."
"Toh bari in rakaki."
"Ba amfani 'yar uwa yi zamanki nagode da wannan lokaci da
kika bani se anjima." Tun fitan Mummy Mami ta shiga tunani,
gabaki d'aya kanta ya d'aure se bata jikinta yake trap su
Mummy suke shirin shirya mata in ba haka ba har a ina uwar
gida ta ta6a aran bakin mijinta dan nema masa mata?
Daddy kuwa a gida ya sauk'e Mummy ya wuce gidansu
Amal, yasani it's now or never. Bayan mey gadi ya bud'e mishi
gate ya k'arasa ya samu gu yayi parking sannan ya fito ya nufi
entrane door inda yake ta knocking amma ba response
kasancewar bacci da suke duka daga ciki. Ganin ba mahalicci
se Allah kawai seya kira wayan Afzal. Kaman a mafarki Afzal
ya soma jin ringing na wayansa dake ajiye akan side drawer'n
kansa kafin ya mik'a hannu ya d'aga har Amal itama ta farka.
Sorry go back to sleep" ya sanar da ita rik'e a hannunsa yana
mey sake daidaita kanta a k'irjinsa sannan ya d'au wayan inda
ya tarar da missed call na Daddy nan take ya kirasa back,
"Halo Daddy?
"Na'am Afzal gani a bakin k'ofan gidanku fa amma shiru ko
bakuwa nan ne?"
"Afuwan Bacci ne ya d'auke mu bari inyi ma mey gadi
magana ya bud'e maka."
"No already ina ciki ya riga ya bud'e mun ina bakin parlour
ne."
"Sorry bari ina fitowa yanzu" ya fad'a had'e da kashe wayan
sannan ya sauk'o da kallonsa akan Amal "Rania bari in fita
Daddy yazo yana waje." Kai zalla ta gyad'a masa sannan ta
koma gefe ta cigaba da kwanciyanta. Jallabiyansa ya sanya ya
fito ya bud'e wa Daddy yana mey sake basa hak'uri. Ruwa da
juice ya d'auko masa inda suka gaisa yake tambayansa ya jikin
Nazeefah.
"Da sauk'i Alhamdulillah."
"Toh Allah k'ara mata lafiya."
"Ameen yaya Amal kuma?"
"Lafiyanta itama."
"Ina sake baka hak'uri game da abinda Nazeefah tayi muku
ranan, ni kaina I'm having a hard time with her kuyi hak'uri kuyi
mata uzuri."
"Ba komai Daddy duka nan mun san what she's going
through is not easy fatan mu Allah kawo mata sauk'i."
"Ameen Afzal thank you."
"Ba komai Daddy."
"Yauwa dama batun Amal nazo ne Afzal, ina son muyi
magana da ita in kuma bata hak'uri gameda duk wani abinda
nayi mata, Afzal ka sani a addu'a I want to make everything
right I want to marry Amal's mother." Mamaki da dad'i ne ya
ziyarci zuciyan Afzal wanda ya kasa 6oyewa "Tabbas kayi
tunani Daddy, Allah sanya alkhairi acikin hakan ya biya maka
buk'atunka na alkhairi."
"Ameen Afzal zan iya yi ma Amal magana."
"Sure tana bacci bari in tayar da ita."
"No no in tana bacci ka barta kawai ko gobe ina iya
dawowa."
"A'a don't worry." D'akin nasu ya koma yaje ya samu Amal ya
shiga tada ita. "Rania?"
"Uhmmm?"
"Daddy yazo."
"Uhmm?"
"Yana son ya ganki kuyi magana." A hankali ta bud'e idanunta
"Yaya I don't want to face him ban san mey zance mishi ba."
"I know Rania, I know kiyi hak'uri kije kiji mey zai ce miki."
"Yaya-"
"Kar muyi haka dake kinji? Tashi hungo kayanki kisa" da
kanshi ya mik'ar da ita zaune ya sanya mata kayan da hijabi
suka fito suka zauna a kan two seater.
"Ina yini Daddy?" Ta durk'usa har k'asa ta gaishesa.
"A'a please Amal koma ki zauna Afzal ce mata ta zauna" duk
da haka Amal tak'i mik'ewa seda ya amsa tukuna. Gaisawa
sama-sama sukayi sannan ya fayyace mata dalilinsa na zuwa
dan ya nemi tubarta.
"Nasan na cuceki a rayuwa Amal, nasan nayi depriving naki
duk wani right da gatan da kika cancanta a rayuwarki, nasan
ban kyauta miki ba ban kuma kyauta wa mahaifiyarki ba amma
gani yau nazo neman tubanki" ya k'arasa had'e da sauk'a k'asa
akan guiwoyinsa. "Daddy please ka tashi" tayi saurin cewa
amma yak'i. "I'm dearly sorry Amal, kiyi hak'uri ki yafe mun I'm
here and ready to take full responsibility for everything ki bani
dama in cika aiki na a matsayina na mahaifinki, ki bani dama
in kula dake in soki a matsayina na mahaifinki da jini na ke
gudana a jikinki. Amal I'm so sorry" Afzal be ji tashin Amal ba
kawai ganinta yayi gaban Daddy tana k'ok'arin d'agosa "Don't
be Daddy komai ya riga ya wuce ka kuma sani ni na riga na
yafe maka komai da jimawa Allah ya yafe mana gabad'aya."
Rungumeta tsam yayi a jikinsa cike da farin ciki yayin da duk
suke zubda hawayen jin dad'i "Oh Amal thank you so much
Allah cigaba da yi miki albarka bansan da wani bakin zan yi
miki godiya ba." Itama a hankali ta zagaye hannunta a bayansa
"Ameen Daddy ka daina yimun godiya." Se murmushi Afzal
dake ganin komi kaman a mafarki yake faruwa, this's all he's
ever wanted, ranan da Allah ze bayyana musu mahaifin Amal
ya nemi tubanta su shirya se gashi Allah ya kawo musu ranan.
"Amal?"
"Na'am Daddy" ta amsa.
"Amal nasan kinsan yadda Mahaifiyarki ta tsaneni ko?" Shiru
tayi bata ce komai ba. "Amal I need your help, Mahaifiyarki
tak'i ta bani dama in bata hak'uri bale in nemi tubanta Amal a
shirye nake da in auri Mahaifiyar ki in har zata amince."
"Zaka auri Mami?" Ta tambayesa d'auke da d'unbun mamaki.
"In har zata amince, eh."
"Mummy kuma fa? Bana son abinda ya faru tsakani na da
Nazeefah ya faru dasu suma, in har Mummy bata goyi bayan
zancen nan ba babu amfani Daddy."
"Hasali Mummy'nku nema ta kawo shawaran nan Amal,
Mummy'nku batada matsala da hakan idan har keda
mahaifiyarki kun amince."
"Kayi wa Mami magana ne?"
"Naso amma tak'i bani dama d'azu nida Mummy'nku mukaje
tayi mata magana sede har yanzu bata shirya bamu had'in kai
ba please help me Amal nasan bani da daman tambayan
hakan daga gareki but Amal I love your mom, har yau har
gobe ina sonta kuma ina son in aureta." Na matuk'a Amal taji
dad'i ta juma tana mafarkin rananda Mami zata shiga d'akin
mijinta itama koda sau d'aya ne taji dad'i a rayuwanta. Inde
hakane kuwa se inda k'arfin ta ya k'are inshaa Allahu bazata
gaji ba seta shawo kan Mami waya sani ko da haka Nazeefah
zatayi accepting nata ta bata chance suyi working out
relationship nasu.
"Amal? Bazaki iya ba ko? Bakiya son mahaifiyarki ta kasance
tare dani ko? Look I'm terribly sorry wallahi nayi nadaman
abinda nayi muku please forgive me."
"Ko kad'an ba haka bane Daddy hasali nayi murna da farin
cikin wannan labari in shaa Allah kuma zan tayaka yima Mami
magana."
"Nagode sosai 'yata Allah miki albarka sak'a miki da
alkhairi."
"Ameen Daddy."
"Toh ni bari zan koma."
"Da wuri haka Daddy?" Fad'in Afzal "kabari mana muci
dinner."
"A'a karka damu."
"Please stay Daddy" Amal ta sanya baki.
"Tunda 'yata tasa baki na isa ince a'a? Se in jira d'in." Dad'i
sosai both Amal da Afzal suka ji haka Daddy ya yini musu
koda Mummy taji shiru ta kira ta tambayi dalili kuwa ce mata
yayi se zuwa dare ze shigo, zeci dinner a gidansu Amal. Kafin
su dawo daga masallaci Amal har ta gama tsara kan dining da
had'ad'd'un dishes ta bi gidan da turaren wuta. Nan tayi musu
magana suka k'ariso se yaba abincin nata Daddy yake Afzal na
ta jin dad'i ana yaba girkin matarsa. Hira suka sha kaman ba
gobe anan Daddy ya gano ababe da dama tattare da Amal,
he's in every way submissive to be a great Dad to Amal. Da
yazo tafiya kuwa har wajen motansa suka rakasa sannan Amal
tace a gaishe mata da Nazeefah.
Washegari...
Wajajen sha d'aya Amal ta dawo daga school bayan morning
lectures nata ya k'are. Tana dawowa ta kama shara bayan ta
gama ta aza tukunyan tuwo sannan ta d'au waya ta kira Mami
wacce ta d'aga a karo na farko.
"Halo Mami."
"Na'am Amal ya kike?"
"Ina yini Mami? Ya kike ya Papi?"
"Lafiya k'alau ya Afzal?"
"Yana office."
"Makaranta fah?"
"Alhamdulillah ban jima da dawowa bama kinsan mun kusa
fara exams."
"Aww haba? Se part 4 kuma ko?"
"Eh in shaa Allah."
"Toh Allah sanya alkhairi ya bada sa'a mamana."
"Ameen Mami."
"Ba wata matsala dai ko?"
"A'a ba komai."
"Toh madallah."
"Mami jiya Daddy yazo."
"Wani Daddy d'aya?"
"Daddy mahaifin Nazeefah."
"Kuma mahaifinki ba."
"Eh" ta amsa tana murmushi "jiya yazo muka yini se bayan
Isha ya tafi."
"Allah sarki."
"Yazo ya nemi tuba na."
"Kin yafe masa?"
"Eh Mami."
"Madallah toh yayi kyau."
"Mami kefa?"
"Baby-"
"Mami kiyi hak'uri komi ya riga ya wuce Daddy yace min yana
son ya aureki."
"Baby ke kanki kinsan baze yiwu in auri mahaifinki ba ko?"
"Dalili Mami? Hasn't it always been your advocate to get
married someday?"
"Yes Baby amma ba ga mahaifinki ba."
"Meyasa Mami? Didn't you loved him? Dan Allah kar kiyi ma
Daddy haka."
"Baby bazaki gane bane."
"Toh meneh Mami? Daddy yana sonki har yau har gobe kema
kin sani."
"Baby ba wannan bane matsalar."
"Toh meye ne?"
"Mahaifiyar Nazeefah."
"Mummy? Me tayi?"
"Baby bakiya ganin kaman wani muguntan suke shirin yi mun?
In ba haka ba a ina ne kika ta6a ganin inda uwar gida tazo
nema wa mai gidanta aure?"
"Gaskiya ba a ta6a yin hakan ba amma kuma I trust Mummy
na tabbata Mummy baza ta ta6a aikata abinda ze cutar dake
ba Mami."
"Wai meyasa kike biye wa Mahaifin naki ne haka?"
"Because he loves you Mami and he's sorry mey aciki idan
kin yafe masa kunyi reconciling? Duk mun san abinda Daddy
ya miki da ciwo da zafi amma yayi nadama Mami please kiyi
hak'uri ki yafe masa ki sauraresa."
"Baby-"
"Please Mami do this for me" rok'an kanta Amal ta rik'a yi
amma ina Mami fa sam babu a ranta ta auri Daddy. Suna
gama wayan Amal ta kira Papi ta irga masa komai mamaki
yasha yadda har abu haka ze faru amma Mami bata sanar da
shi ba. Chan dare bayan sun k'are cin abinci yayi gyaran murya
had'e da kiran sunanta.
"Na'am Abba wani abu ne?"
"Tun shekaran jiya kika ce Khaleefah be sake shigowa ba?"
Dum taji zuciyanta ya tsinke amma sam bata kawo a ranta har
Amal zata kirasa ta sanar da shi komai ba dan haka se tayi
masa k'arya "A'a wani abu ne?"
"Meyasa kike yi mun k'arya Jameela? Yaushe kika fara
haka?"
"Abba-"
"Ashe har matarsa ya turo da ta baki hak'uri amma kika k'i
sauraronsu?"
"Abba ba haka bane."
"Dakata tukuna, shi fa d'an Adam ajizi ne kuma dukan mu
nan ba wanda zece baya yi wa Allah sa6o amma kuma mey?
Da zaran muka tuba kuma muka nemi yafiyarsa yana yafe
mana ba wanda yace Khaleefah ya kyauta abinda yayi miki
amma tunda ya gane kuransa yana son ya dai-daita komai
meyasa bazaki basa had'in kai ba?"
"Abba ba haka bane."
"Jameelah har yanzu ke yarinya ce shekarunki dududu nawa
ne? Kin kai arba'in ne?"
"A'a Abba"
"Toh haka kikeson ki k'are rayuwarki ba aure? Bakiya son ki
bar yaran da zasu yi miki addu'a bayan kin rasu? Ko gani kike
Amal ita d'ai ta isheki? Kisani fa dan ba na nuna miki bawai
hakan na nufin ina jin dad'in zamanki a haka bane, kiyi wa
kanki fad'a ki dubi tuban mutumin nan ku rufa wa junanku
asiri." Shiru tayi batace ko k'ala ba "Ko baki ji ba?"
"Naji Abba."
"Toh tashi ki tafi."
"Toh seda safe." Ko bacci Mami ta kasa yi ranan se tuna
abunda Amal da Papi suka fad'a mata take gabad'aya ta rasa
mey take ciki ita har ga Allah bata k'aunan abinda ze sake
had'ata da Daddy saboda kasa mancewa da abinda yayi mata
da take. Duk sanda ta kallesa se ta tuna da wancan mumunar
ranan taji ta tsanesa. Amma ya ta iya yanzu tunda har Papi
yasa baki? Bayan nan kuma kaman yadda Mummy ta fad'a ko
ba dan tana so ba kamata yayi ta amince saboda su gyara
zuri'a su had'a kan yaransu. Daga k'arshe de kawai ta yanke
hukuncin yin Istikhara duk abinda Allah ya za6an mata shi zata
bi.
_One week later..._
Cikin satin nan da aka shiga su Amal da Nazeefah suka fara
exams har yau Mummy bata sake ji daga Mami ba shima Papi
be sake yi mata magana ba as ya zuba mata ido yaga iya
gudun ruwanta. Amal da Afzal suna zaune a parlour se faman
kallo yake a laptop nasa yasa earpiece a kunne ita kuwa se
karatu take kasancewar tana da paper k'arfe d'aya gobe.
Wayanta dake gefenta ne ya shiga ringing dubawanda zatayi
taga new number, without hesitation ta d'aga tare da yin shiru.
"Assalamu Alaikum" akayi sallama daga d'ayan 6angaren.
"Mummy?"
"Ashe 'yar tawa zata gane muryan uwarta."
"Mummy ina yini?"
"Lafiya k'alau ya kike ya gida ya Afzal kuma?"
"Alhamdulillah dukan mu lafiya."
"Ya exams toh?"
"Alhamdulillah Mummy ya Nazeefah? Jiya ma Khaleefah ya
kirani muka gaisa."
"Allah sarki ya Mami?"
"Lafiyarta k'alau."
"Kwana biyu shiru banji daga gareta ba nace ko zaki iya mun
texting number'nta."
"Sure Mummy bari in miki texting yanzu."
"Yauwa 'yata thank you Allah ya bada sa'an jarabawa."
"Ameen Mummy seda safe" nan tayi hanging take tayi mata
sending numban Mami, itama Mumny tana gani tayi replying
nata da 'Thanks.'
"Lafiya dai ko?" Afzal da ya zare kunnen earpiece nasa d'aya
ya tambaya.
"Lafiya kawai tana son su gaisa ne."
"Oh Rania I'm hungry."
"Toh Ya Omri baga kitchen ba."
"Aww ma ni zanyi girkin da kaina?"
"Toh Ya Omri karatu fa nakeyi" ta fad'a cike da shagwa6a.
"Ni o'o" ya fad'a harda doke kafad'a wanda hakan yasa Amal
dariya. "Toh mey kakeso kaci?"
"Na fasa chin abincin ma I just want to sleep."
"Tun yanzu?" Ta tambaya had'e da duban agogo "it's just 9
O'clock."
"Yes Rania na gaji kallon ma na fasa."
"Toh sekaje ka kwanta ai seda safe."
"Ni kad'ai?"
"Toh Ya Omri baka ga karatu nakeyi ba?"
"Nasani anan nake nufi" kafin ta karanci abinda yake shirin yi
kawai taji ya sauk'e kansa a k'irjinta ita ta rasa damuwansa, ga
gado amma yace shi se a jikinta ze kwanta adjusting kansa
yayi ya kwanta da kyau a jikinta "Toh goodnight" tace da shi.
"Goodnight Rania I love you."
"I love you too Ya Omri" ta amsa had'e da placing peck a
cikin gashin kansa. Handout nata ta d'auka ta cigaba da
karatunta haka har bacci ya d'auketa itama. Se chan wajajen
k'arfe biyu Afzal ya farka se jin numfashin mutum yake a kansa
shafawa da yayi ya gano Amal ce. Murmushi ya saki sannan ya
rik'e kanta ya janye nasa a hankali. Handout na hannunta ya
cire ya d'agata ya kaita d'aki suka kwanta.
Washegari Mummy da Daddy suka jesu gidansu Papi kaman
yadda Munmy ta sanar da ita cewan zasu shigo sede bata ce
da Daddy ba sam Mami batayi farin cikin zuwansu tare ba
amma ya ta iya? Sannu da zuwa tayi musu ta shimfid'a musu
tabarma sannan ta kira Papi inda duk suka gaisa.
"Toh ga Jameelah nan sama da sati kenan yau ina jiran ji
daga wajenta amma shiru se jiya da daddare bayan da Surayya
ta kira take fayyace mun cewa tayi Istikhara kwanaki hud'u da
suka wuce za6i kuma Allah yayi mata" se kuma yayi shiru.
"Muna jinka Abba" Daddy da ya kasa hak'uri ya tambaya.
"Khaleefah zan d'auki amanar 'yata in baka ba wai dan ka
cancanta ba se don yin hakan ne ya kamata kodan mu samu
mu had'a kawunan yaran nan. Kai ba yaro bane ka riga kasan
komai ba sena sake nanata maka ba seka taimaki kanka kayi
abinda ya dace wannan duka matanka ne ka kwatanta yin
adalci a tsakaninsu Allah ya baku zaman lafiya gabaki d'aya
batun yafiya kuma duka mun yafe maka Allah yafe mana
gabaki d'aya."
"Ameen Abba nagode sosai in shaa Alalhu zaka sameni mey
rik'on amana Jameelah nagode Allah sak'a da alkhairi."
"Ameen" duka suka amsa.
"Abba in ba matsala bana so a jinkirta auren."
"Toh Khaleefah gaskiya seka d'an bamu lokaci mu shirya."
"Wani shiri Abba? Ba shirin da zakuyi zan d'au nauyin komai
da komai ni kawai kar mu jinkirta."
"Toh madallah zamuyi magana duk abinda tace haka za'ayi."
"Toh nagode, nagode sosai zamu koma."
"Toh Surayya kekuma Allah ya sak'a miki da alkhairi ya baki
riban hak'uri tabbas irinku acikin mata d'ad'd'aiku ne Allah ya
baku zaman lafiya mai d'aurewa."
"Ameen Abba nagode" ta amsa.
"Toh zamu koma ga wannan" Daddy yayi maganan had'e da
zaro wani bak'in leda daga aljihunsa wanda yake d'auke da
kud'i.
"Na mey kuma? Kaga kar mu fara haka da kai."
"Abba dan Allah kar kayi rejecting mu tafi Hjy Surayya." Duk
yadda Papi beso kar6an kud'in ba seda ya kar6a saboda
yadda Daddy yayita insisting.
Da Maghrib bayan Daddy ya dawo daga masallaci Nazeefah
tayi sallama ta shiga d'akinsa inda ta tarar da Mummy aciki.
"Ya Nazeefah lafiya?"
"Daddy ina son bayan graduation namu inyi proceeding
masters program d'ina."
"Toh masha Allah anan Unimaid zakiyi?"
"A'a a UK."
"K'asar waje?" Mummy tayi sayrin tambaya.
"Eh Mummy."
"Ko meyasa?"
"Achan nafi so inyi yafi sauk'i."
"Toh shikenan se ayi making arrangements amma ai sekin
jira results naku sun fito."
"Zan tafi tun yanzu in results d'in ya fito seku amsa min a
tura mun achan, Nagode" tana kaiwa nan ta mik'e ta fice.
Bayanta Mummy ta biyo "Why the sudden decision Nazeefah?
I thought ke kikace bakiyason fita k'asar waje karatu?"
"I changed my mind Mummy."
"Saboda mey?"
"Babu."
"Saboda kiyi nesa da Amal yeah???"
"Mummy Amal ba matsala ta bace bani da damuwa da ita I'm
doing this for myself."
"Ke Nazeefah bakiya tunanin mutuwa ne? Rayuwan ma nawa
take da har kike neman gujewa 'yar uwarki haka?"
"Amal ba 'yar uwata bace stop referring to her as one."
"Da kin k'i da kin so Amal 'yar uwarki ce yanzu maganan da
muke da Daddy'nku ma shirin auro mahaifiyarta yake
Jameelah."
"What? Wa d'in?"
"Mahaifiyar Amal, Jameelah."
"Wannan wani irin abin kunya ne? Kuma kika amince?"
"Hasali ni na kawo masa shawaran ma saboda mun riga mun
zama abu d'aya yanzu."
"What? Mummy are you okay? Taya zaki amince Daddy ya
k'ara aure, auren ma wai mahaifiyar Amal of all people?
Wallahi baza ayi abun kunyan nan da ni ba."
"Ya kika iya? The earlier the better Nazeefah just accept it
mu da su mun zamo abu d'aya."
"No Mummy bazan ta6a accepting su Amal as one of my
own ba duk abinda kuke shirin yi count me out cause I'll never
welcome their kind into my family."
"Yayi miki kyau."
****
Acikin wata d'aya Daddy yagama had'a d'akin Mami, an sa
rana nan da sati uku. Da ikon Allah kuma su Amal suka k'are
exams nasu results yafito alhamdulillah duk sunyi passing. Ba
yadda Mummy batayi da Nazeefah ba da tabari se bayan
d'aurin auren tayi tafiyan nata amma tak'i. Ana saura sati
d'aurin aure tabar Nigeria.
****
"Rania lafiya?" Afzal daya kasa hak'ura dan jin meke faruwa
ya tambaya.
"Ya Omri" kawai seta rushe da kuka.
"Subhanllahi!" da sauri yayo kanta hugging her in his arms
yana bata hak'uri. "Ya Omri ta tafi" ta amsa at last.
"Ita wa?"
"Nazeefah" ta sanar dashi yana share mata hawayenta.
"Ta tafi ina?"
"UK tabar Nigeria tace bazata sake dawowa."
"What? Meyasa?"
"Ya Omri har yau Nazeefah takasa acepting d'ina da Mami
tun kafin ma taji Daddy ze auri Mami tace ita zata wuce Uk
tayi proceeding masters nata yanzu kuma dataji gaskiyan
al'amarin jiya bayan sunyi landing ta kira Mummy ta jaddada
mata cewa bazata sake dawowa ba."
"Shhh it's okay sooner ot later zata gano gaskiya in shaa
Allah kuma da k'afarta zata dawo."
"I really do hope so Ya Omri bana son Nazeefah tayi nesa da
gida the more she stays away from us the more lost she'll be."
"I know but don't lose hope okay? Nasan Nazeefah she'll
soon come around."
"Thank you Ya Omri."
"Anytime, still zamu fita d'in ko?"
"Yes."
"Alright toh."
***
Mami ce zaune a d'akinta ta baje zannuwa da dama a
gabanta tana za6an wanda zata kai d'inki. Tana cikin haka
sega wayanta dake gefenta ya shiga ruri dubawan da zatayi
taga Daddy ke kira. 'Yar murmushi ta saki sannan ta d'aga.
"Amarya bakiya laifi koda kin kashe d'an masu gida ne."
"Haka de kace" ta amsa tana murmusawa.
"Toh ya kike?"
"Lafiya k'alau ya 'yar uwata?"
"Lafiyanta k'alau yanzun tace tasan kanki yayi zafi k'ila ma
kina jin yunwa amma ba hankalinki."
"Ai kuwa wallahi ina ta sorting kayakin nawa."
"Toh mey kikeso ayi miki ordering wai?"
"Laaa kace mata kar ta damu zan dafa taliya in ci."
"A'a nikam kinga aikana tayi fad'a mun."
"Toh inde haka ne kace mata duk abinda ya sawwak'a."
"Toh shikenan ki gaishe min da Abba."
"Zeji se anjima."
"Yauwa" da haka sukayi sallama.
"Mey tace wai?" Mummy dake gefensa ta tambaya. "Cewa
tayi akai mata duk abinda ya sauwak'a."
"Toh se a sai mata fried rice and chicken ai ko ya kace? Ita
da Abba."
"Se abinda uwar gida tace."
"Kai Alhj bana son zolaya fa."
"Ai gaskiya ce."
"Nifa har yau fushi nake da kai."
"Afuwan in uwar gida na fushi dani a ina zan sa kaina?"
"Eh mana kak'i had'ani da 'yar uwata a gida d'aya."
"Ba wai nak'i bane Hjy Surayya."
"Kak'i ne mana tun yaushe nake binka ayi a had'a ginin nan
kak'i."
"Ai kinga har yau aikin ake kan yi in shaa Allahu ana
kammalawa zan dawo da ita nan chan d'in temporary ne."
"Promise?"
"I cross my heart."
"Toh Allah nuna mana ."
"Ameen Hjy Surayya nawa na kaina, bari in je in siyo ma 'yar
uwar taki abinci."
"Gaskiya kam kar mu bar amarya da yunwa."
"Toh a dawo lafiya."
***
Ranar Asabar aka d'aura auren Alhj Abdallah da Jameela
Muh'd akan sadaki dubu d'ari da sisin gwal arba'in. D'aurin
aure kawai akayi da yammacin ranan aka kai amarya d'akinta.
Se wani tattalinta Daddy yake, bayan sunci kajin amarcinsu
Daddy yasa su sukayi raka'a biyu dan yima Allah godiya.
RANA DAYA Chapter 46
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
Tareda Naja'atu Lawal Rijau Niger State
@Whatapp 08083232323 or 09060202323
Second 2 The Last
PAGE 46
Washegari...
Hayaniyan da Daddy ya jiyo a kitchen ne ya sanyasa fitowa
daga d'aki inda yake kwance. Mami ya tarar tsaye gun sink ko
mey takeyi oho.
"Jamee na mey kuma kike yi?" Ya tambayeta tsaye daga
bakin k'ofan.
"Oh Alhj!" Ta juyo a d'an razane "Har ka tashi ne?"
"K'aran kwanukanki suka tadani" ya sanar da ita.
"Ayya yi hak'uri inzo in mayar da kai baccin ne ko zaka koma
da kanka?"
"Ko d'aya tambaya nake mey kikeyi?"
"Oh! Doya nake ferewa Abba kasan bey karya ba."
"Inji wa? Ai da kin tambaya, tare aka siyo mana breakfast d'in
nasa mey gadi ya kai masa nasa se inde zaki site nasa ku
gaisa."
"Allah sarki nagode."
"Jimin matan nan fa godiyan mey kuma kike mun? Dan na
ciyar da Abban mu? Taho mu koma d'aki" ya k'are had'e da
mik'a mata hannunsa murmushi cike da kunya ta saki sannan
ta mayar da kayan aikin ta k'ariso ta mik'a hannunta ta sanya
acikin nasa, janta yayi izuwa d'akinsu had'e da zaunar da ita
kan gado. Cikin wardrobe nasu ya nufa ya d'auko wani
package sannan ya dawo ya zauna a gefenta.
"Hungo" ya mik'a mata.
"Mey wannan?" Tayi saurin tambaya.
"Kede bud'e ki ga" ba tare da yin gardama ba ta amsa ta
bud'e d'an kunne ta tarar aciki k'waya d'aya. "Ko na waye
wannan Alhj?"
"Bazaki iya tunawa ba?"
"A'a gaskiya" ta amsa tana kad'a kai amsa yayi daga
hannunta yace, "Kin tuna rana na uku dana fara d'auko ki daga
makaranta muna tsaye a k'ark'ashin makeken bishiyan chan
muna hira muna shan rakke chan kika ta6a kunnenki kikaji ba
d'an kunne? Muka ta nema amma muka rasa?"
Murmushi take sosai cike da mamakin yadda akayi har yau
Daddy be mance da wannan rana ba bayan ita da ba don ya
tuna mata yanzu ba ta riga ta mance da shi shaf. "Toh ai
bayan dana raka ki gida na dawo na cigaba da nema ashe ma
ba a wajen ya fad'i ba tun a bakin makarantar ku ya fad'i."
"Shine ka adana har yau Alhj?"
"Kamar yadda na adana soyayyarki a cikin zuciyata na
tsawon shekaru ashirin da biyu." Ya amsa nan take.
Mamaki ne ya mamaye Mami gabd'aya ta rasa na cewa chan
ta kira sunansa inda ya amsa a take "Alhj idan har kana so na
haka toh meyasa ka gujeni? Na fahimci kayi mun abinda kayi
ne saboda ka rama abinda Umma tayi maka amma meyasa ka
kujeni? Meyasa ka daina d'aukan wayana?"
"Duk da hakan ma be kamata inyi miki abinda nayi miki ba
Jamee amma a lokacin shaid'an ya riga ya rinjayeni I'm terribly
sorry."
"Komai ya riga ya wuce Alhj ka daina neman tuba na."
"Nagode Allah yayi miki albarka."
"Ameen Alhj baka amsa min tambayan danayi maka ba."
"Kinsan wani sa'in mutum baya sanin muhimmancin abinda
yake da shi se idan ya rasa, da fari nak'i in amince da cikin
Amal nawa ne saboda tsoro da nake kar in 6ata wa mahaifina
suna acikin gari, kowa ya sani mahaifina sanannen malami ne
ba k'aramin zubar masa da mutunci zanyi ba idan har na
amince da cikin cewa nawa ne. Tsoro ne yasa na gujeki
Jamee, na d'au bayan da nayi nesa daga gareki zan iya
mancewa dake, na d'au yin hakan ne ze fiye mun kwanciyan
hankali ashe sam ba haka bane. Tun bayan da nayi cutting off
conact dake da duk wani nawa rayuwata ta dame, acikin
k'unci nake kwanciya in tashi har seda Allah ya shigo mun da
Surayya cikin rayuwata, wacce ta yaye mun duk wani bak'in
ciki nawa take kuma bala'in tuna mun da ke ta kowani
6angare. Duk da hakan saide idan ban kwanta ba Jamee
senayi mafarkin ki, lokacin da na fara neman layinki kuma se
yayita cemun switched off."
"Ba shakka nakega lokacin da muka bar Askira ne Abba ya
buk'aceni da in yasar da sim card d'ina ze sai min sabo."
"Tabbas ma hakanne, saide duk da hakan ban kariya ba
kullum se na gwada layinki amma baya shiga, a wannan
lokacin ne na tabbata da cewa guje miki da nayi shine babban
kuskuren dana tafka a rayuwa na, a wannan lokacin na
tabbatar da cewa akwai gur6in da kika mamaye a zuciya na,
gur6in da se ke ne zaki iya cike mun shi. Lokacin da muka
dawo Nigeria na koma Askira don nemanki inda ake tabbatar
mun da cewa Allah yayi wa Abba da Umma rasuwa."
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un Allah ya jik'an su da rahama a
tunani na gabad'aya wanda ka kaini gunsu sune iyayenka."
"A'a wan Abba ne da matarsa."
"Allah sarki."
"Daga chan se na wuce gidanku inda ake cemin kun bar garin
Askira da dad'ewa kuma ba wanda yasan inda kuka dosa nayi
cigiyarku har na gaji amma rana baya ta6a wucewa ban yi
tunanin wani hali da yanayi kike ciki ba. Please forgive me
Jamee."
Hannunsa ta d'au ta had'a da nata tana murzawa a hankali
"Alhj komai ya riga ya wuce wannan d'an kunne kuma zan
cigaba da adana shi as a symbol of my love for you"
Murmushi ya sakar yana mey jin dad'in abinda ta fad'a sannan
ya janyo wayanshi "Bari in kira Hjy Surayya muji daga gareta."
"Gaskiya ya kamata." A karo na farko Mummy ta d'aga
wayan inda suka gaisa. "Kun jini shiru ban kawo muku
breakfast ba ko? Wallahi Khaleefah ne yamun tsiya na sa
Alarm a wayana kawai ya saci ido na ya d'auke wayan sena
makara."
"Barka, dama waya aikeki? Karki damu mun riga mun karya."
"Kai ina ruwanka? Idan na kawo se kar ka ci so ka fad'awa
'yar uwata kar tayi wahalan yin girkin rana I'll make it up to you
guys."
"A'a Hjy Surayya dan Allah karki sa kanki wahala."
"Nikam ka had'ani da 'yar uwata mu gaisa" yana murmushi ya
mik'awa Mami wayar "Assalamu Alaikum" ta soma da cewa.
"Amaryar mu" Mummy ta amsa.
"Kai 'yar uwa bazaki bar zolaya bade ya kike toh ya
Khaleefah?"
"Gashi se shiri yake ya kusan komawa school."
"Allar sarki Allah kiyaye ya bada sa'a."
"Ameen sena shigo anjima sauran kice zakiyi girki kuma."
"Oh 'yar uwa kar ki sakaltani dayawa fah."
"Ba ga Alhj ba yasan yadda zeyi dake ai."
"Kai 'yar uwa."
""Ahtoh barin bar ku haka se na shigo anjima."
"Toh muna godiya Allah kaimu."
"Yauwa se anjima."
Kaman yadda Mummy ta d'au alk'awari bayan sallan Azahar
ta shigo da abinci kala-kala se sauk'e kuloli kawai ake tayi
daga mota. Yini Mummy tayima Mami se kusan Maghrib da
Daddy ya kusa dawowa ta koma gidanta. Zaman lafiya maras
misaltuwa Mummy da Mami sukeyi sekace ba kishiyoyi ba
wane wasu 'yan uwan jini, dai-dai da rana d'aya Daddy be ta6a
jin kansu ba. Hasali har had'a kansu suke su biyu su waresa.
Bayan ya k'are wa Mami kwana bakwai na amarchi ya soma yi
musu kwana bibbiyu duka.
***
Haka kwanaki suka cigaba da shud'ewa yayinda zama yake
k'ara yima wad'annan abokan zama dad'i. Labarin Nazeefah
kuwa duk sanda ta bugi iska takan d'au waya ta kira Mummy
amma dai-dai da rana d'aya bata ta6an d'aukan waya ta kira
Daddy ba ko da shi ya kirata ma se ta ga dama take d'agawa.
9 months later...
Abubuwa da dama sun gudana, Amal hutu ya k'are sun koma
makaranta har sun k'are first semester suna second semester
yanzu. Maamah kuma an kai goron tambayan auranta, labarin
dawowan Ya Abdul kuwa shiru har yanzu ko su Mama sunyi
mishi magana se yace shi ba yanzu ba. Sultan ko har yau
labarin aure shiru ya tsaya rawan ido. Labarin k'awar Amal
Falmata kuwa tayi aure abunta tabar Maiduguri ta koma a
Azare take da zama inda mijin ke aiki. Har Azare su Amal suka
kaita suka dawo. Tun tafiyan Amal wane akan allura Afzal
yake zaune, minti-minti yake yi mata waya yaushe zata dawo.
Sam baya iya jure rashin ta a kusa da shi.
***
Amal ce zaune a d'akinsu da Afzal se faman karatu take
gefenta kuwa plate ne cike da kayan k'walama ba abinda babu
daga abinda ya kama kan tuwon madara, calanda, gullisuwa,
tsamiyan biri, ba abinda babu ta d'au wannan ta d'au wancan.
Haka kawai ta ke wani irin wawan kwad'ayi kwana biyu duk
abinda tagani setaji tana so. Ba da dad'ewa ba wayanta dake
ajiye a gefenta ya shiga ruri dubawanda tayi taga Afzal ke kira
k'aramar tsuka taja ta cigaba da yin abinda ke gabanta. Yana
tsinkewa ya shiga kira again nan ma tak'i d'agawa be dad'e ba
sega sak'on sa.
_Please pick up Rania I'm sorry._
Tana cikin shawaran ta d'aga ne kokuwa sega call nasa
again nan ma seda ya kusa tsinkewa ta d'aga had'e da yin
shiru.
''Baby yi hak'uri mana."
"Nifa ban ce kayi mun laifi ba."
"Toh meyasa in na kiraki bakiya d'agawa?"
"Karatu nake bana son distraction."
"Baby Ya Omrin na kine kuma yau distraction? Yi hak'uri kinji
Yaya is sorry."
"Shikenan ni kayi ta mun wasa da hankali kenan kullum, yau
kace gobe, jibi kace gata dan kawai kaga ina missing naka."
"Haba baby yi hak'uri wallahi sune suka k'i sakemu saura
mana trips biyu amma de yanzu."
"Toh nikam se yaushe zaka dawo?"
''Zuwa next week in shaa Allah.''
''Har next week Ya Omri?''
''I'm sorry.''
''Promise?''
''I promise Baby.''
''Toh Allah ya kaimu.''
''Ameen kin daina fushin?''
''Ba dole na ba."
"That's my Rania so ya kike? Should I FaceTime you?"
"Okay." Nan ya katse wayayn ya yi mata video call inda ta
d'auka suka cigaba da gaisawa. "Baby?"
"Na'am'' ta amsa.
''Mey kikeci haka ba ni?''
''Oh tuwon madara ne.''
''Da kuma mey? Mey wancan bak'in abun?'' Plate d'in ta d'aga
ta matso da shi kusa ''Tsamiyan biri ne.''
''Rania yaushe kika fara wannan ciye-ciye?''
''Ba ka nan ma ban tsira ba ko?''
''Toh ya Mami? Sun dawo?''
''A'a wai daga chan zasu wuce Dubai."
"Oh ayyah Papi fa? Yana nan k'alau?"
"Eh Mummy tana kula da shi."
"Allah sarki toh yayi kyau."
"Toh se anjima ko? Kaga karatu nake" tayi maganan tana
nuna masa handouts nata.
"Wait Rania d'an tsaya."
"Yaya wai yau kai kake hana ni karatu?"
"Not at all, Idona ne kokuma k'iba kika k'ara bayan tafiya na?"
"K'iba?" Ta nanata tana duban jikinta
"Eh mana kinga yadda kumatunki suka ciko."
"Kai Ya Omri ka fa san bana son inyi k'iba."
"Ai kuwa se kin fara slimming dan kin riga kin d'au hanya."
"Omg! Dan Allah dagaske kake na k'ara k'iba?"
"Kije ki duba mirror kiga" katse video call d'in tayi ta ruga gun
madubi tana matse kumatunta. Kuma fa hakanne da gaske ta
k'ara k'iba toh kode? Kai da k'yar tayi sauri ta kad'a kanta.
Koda tayi missing period nata last month bata damu ba cause
tunda ta samu miscarriage date nata ya rikice wani sa'in se
yayi wata biyu be zo ba atimes kuma sati biyu zuwa uku ya
dawowa. Amma kuma ai tabar shan planning pills nata there's
possibility cewa tana da ciki. Toh amma wani irin ciki ne
wannan ba laulayi ba komai? Ai wasu dama sunce cikin fari
ne yafi bada wuya na biyu da sauk'i yake zuwa. Ta shigesu
Allah taimaketa ba ciki take d'auke da shi ba in bahaka ba
zatayi bayani gun Afzal da yace su jira ta gama makaranta
tukuna su fara bearing children kasancewar yadda cikin farinta
ya mugun bata wuya. Da na sani ta shiga yi shin meyasa ma ta
daina shan pills natan ta kuma cire implant d'in? Har ga Allah
ba don rashin ji tayi hakan ba illa dan so da take ta azurta
Afzal da yara, so take yaga jininsa shima bayan hak'urin da
yayi na shekaru kusan biyar ba haihuwa. Bata son ta shiga
hak'k'insa dan wani personal interest nata. Ko ba a tambaya
ba tasan Afzal na son yara yadda kullum idan suka je gidan
wani abokinsa da suke mugun zumunci yake wasa da yaran
tamkar 'ya'yan cikinsa. Se kuma yanzu tsoro ya shigeta bayan
alamomin juna biyu sun bayyana a jikinta, ji tayi gabad'aya
dama bata cire implant d'in ba. Ita de zata jira zuwa nan da
jibi idan har period nata be zo ba zata asibiti a dubata.
Washegari bayan lectures nasu ya k'are suka wuce
restaurant dan chin abinci ita da Maamah sede Amal tak'i cin
komai bayan kuma tana jin yunwan.
"Wai toh mey zaki ci?" Maamah da abun ya isheta ta
tambaya.
"Ni wallahi ganda nake so."
"Gan mey?" Maamah ta tambaya unbelievably.
"Ganda wallahi."
"Ahh gaskia kin so nishad'i ganda? Da ranan nan kuma acikin
school?"
"Wallahi shi nak so Maamah ki taimakeni."
"Toh ya kikeson inyi Amal? Bawai ana siyar da ganda bane
anan sede ki bari idan an tashi se driver'nki ya tsaya a kasuwa
ya sai miki kije gida ki girka."
"Toh ai yanzu nake so bazan iya jira har anjima ba."
"Oh Amal! Ko mey sabon ciki sede hakan."
"Nikam da Allah."
"Kode cikin gareki?"
"Kaman ya ciki sekace bakisan ina planning ba?"
"Nasani ko kin cire."
"A'a kam bayan Yaya yace kar incire."
"K'arya kike."
"Dagaske fah"
Mak'aryaciya rantse muji! idan ma cikin ne da ke in Ya Afzal
ya gano zakiyi bayani."
"Maamah dan Allah ki taimakeni."
"Aww cikin ne dake dagaske?"
"Wallahi ban sani ba but ji nake kaman I'm pregnant jiya
muna FaceTime da Ya Afzal yace wai na k'ara k'iba."
"Ai gaskiyanshi kumatunki sun ciko."
"Na shiga uku!"
"Ya gane amma?"
"A'a hankalinsa be basa ba."
"Chab Allah ya taimakeki."
"Da Allah ki daina tsorata ni nasan yadda zan sanar dashi
idan har na tabbatar da komai."
"Gara miki kam dan kinfi ni sanin halin ogan naki kikayi wasa
se kunyi fad'a ma."
"Kai Maamah ki daina razana ni."
"Allah kuwa yadda seda ya ja miki kunne akan kar kije ki
cire."
"Nikam idan ba ganda zaki bani ba ki daina cika mun kunne."
"Ganda kam sede unborn ya hak'ura dan babu inda zaki
samu."
"Ni bance miki ciki ne gareni ba" tayi maganan had'e da
mik'ewa "Ina kuma zaki?" Maamah tayi saurin tambaya.
"Out of school zanje in nemi ganda."
"Lallai abu ya tabbata" Maamah tace cike da neman tsokana.
"Kanki akeji" Amal ta amsa had'e da galla mata harara
sannan ta fita. Nan da nan ta kira driver'nta yazo ya d'auketa,
haka suka shiga bin restaurant by restaurant suna tambayan
ko akwai ganda har seda suka samu.
Na sosai hankalin Amal ya tashi bayan da tayi carrying
pregnancy test a gida ya nuna mata positive sedai duk da
hakan bata amince ba se da taje asibiti akayi mata tests da
dama aka tabbatar mata da gaskiyan al'amarin cewa tana
d'auke da juna biyu. Tirk'ashi! Yanzu mey abun yi? Tasan se
sun haura sama idan Afzal ya gano gaskiya. Da fari tayi
tunanin kwata-kwata ma kada ta sanar dashi amma kuma
seta tuna idan har shi ya gano da kansa al'amarin zefi
damewa. Yanzu what's the way out??
Haka tana ji tana gani har Afzal ya dawo daga tafiya bata
yanke hukuncin ko ta sanar da shi kokuwa a'a ba. Gashi koda
ta gwada tambayan Falmata da Maamah shawara duk suka
sake tsoratar da ita.
"Rania k'iban nan naki lafiya kuwa?" Afzal dake mik'e akan
gado ya tambaya yana mey k'ure mata ido yayinda take zaune
akan kujera tana faman tsifan kanta. Zuciyanta taji ya buga,
miyau ta had'iye sannan ta saki murmushin dole.
"Kai Ya Omri dan Allah ka daina razana ni."
"Aikam da alama kinji dad'in tafiyan da nayi tunda har kika yi
wannan k'iba."
"Ni dama tayani wannan tsifa zakayi."
"In dawo daga tafiya kuma ki sani aiki Rania?"
"Toh kayi shiru ka kwanta."
"Zomu kwanta anjima in mun tashi se in tayaki."
"Karatu nake so inyi anjuma."
"Haba Baby na yi hak'uri mana."
"Nikam barni inyi tsifa."
"Toh zo kiji."
"Mey?"
"Kekam kizo mana."
"Meneh ka fad'e shi daga nan mana." Ba salon da Afzal bebi
ba amma haka Amal tak'i tasowa ta samesa gashi kuma baya
son ya fito fili ya tambayeta saboda sarai yasan ta gane
abinda yake nufi kawai bata son basa had'in kai ne. Mamaki
ya sha sosai saboda wannan ne karo na farko da ya ta6a
neman Amal tak'i basa had'in kai. Toh koma mey ne de Allah
ya sa lafiya.
Yau kwana uku kenan da dawowan Afzal amma Amal ta
kasa mustering courage ta sanar da shi cewa tana da ciki se
tayi kaman zata sanar da shi seta fasa.
"Rania kiyi sauri mana I'm gonna be late for work."
"Ermm ermm.." amma ta kasa yin magana se cin farcen
hannunta take "Yaya"
Anzo gurin Afzal ya furta a ransa dama duk lokacinda ta
kirasa da Yaya toh laifi tayi ko ne mey yanzu?
"Iyayen rashin ji mey kuma kikayi wannan karan?"
"Yaya" ta furta cike da shagwa6a.
"Rania speak up."
"Kaga har past 7 hurry kar kayi latti."
"Kin d'au na manta ne? Oya tell me what is it you want to tell
me."
"Dama so nake in ce maka I love you."
Wani kallo ya watsa mata "We are not done Rania zamuyi
magana idan na dawo." Kai zalla ta gyad'a mar tana turo
bakinta. Tun fitansa har dawowansa Amal ta kasa samun
sukuni.
****
Fitowan Afzal daga wanka kenan ya nufi wardrobe nasa dan
ciro kayan da zesa sede kap T shirts nasa Amal ta sanya tayi
masa datti da su. "Huh! God help me Rania ina kika kai mun
shirts d'ina?" Ya tambaya yana mey bud'e side na drawer'nta.
Kaman a kyaftawan ido Amal ta mik'e dan dakatar da shi
"Tsaya zan d'auko maka su da kaina kar ka d'aga chan" tayi
saurin sanar da shi sedai ina tuni ya kai hannunsa wajen,
paper ya ga wanda ya zaro waje. Hannu Amal ta mik'a zata
k'wace amma ya janye "Yaya ka ba ni." Ta fad'a tana k'ok'arin
yin tsalle amma ina ko kusa da hannunsa ta kasa kaiwa.
"Yaya please dan Allah kar ka bud'e." Gabad'aya ta tsure
tasan idan Afzal ya gani nata ya k'are.
"Mey aciki?"
"Babu ka bani please."
"Babu? Toh in babu bari in bud'e inga."
"A'a please Yaya ka bani" se k'ok'arin k'wata take amma ta
kasa.
"Dan Allah kar ka bud'e."
"Mey aciki toh?"
"Ermm ermmm script na test d'ina ne wanda na fad'i please
kar ka bud'e." Dariya yasa "D'an tsaya toh muga zeron da kika
ci d'in."
"Yaya ple-" tana cikin yin magana ya bud'e sega pregnancy
results na Amal da fari ma cewa yayi tun cikinta na fari ne
sedai kuma da ya duba yaga data d'in ko sati be kai ba.
"Amal?" Dum taji zuciyarta ta buga dama anytime ya kira ta
da asalin sunanta toh tana cikin big trouble nata ya k'are.
"Yaya-"
"Mey wannan?" Yayi saurin katse ta.
"Yaya-"
"Wait! Is this true?" Ya kuma katseta "Are you really
pregnant?"
"Yaya-"
"Just answer me Amal!" Ya fad'a a tsawace har seda ta
razana.
"Yaya yes amma kayi hak'uri I can explain."
"Explain what exactly Amal?!" Ya kuna daka mata wani
tsawan da ya mugun razana ta.
"Yaya dan Allah kayi hak'uri."
"Cire implant d'in kikayi?"
"Yaya-"
"I'm asking you for the last time Amal cirewa kikayi?"
"Eh" ta amsa k'asa-k'asa.
"Wow tun yaushe?"
"Yaya-"
"Amal answer me!"
"4 months back."
"Wow! Seriously? Ki ka kuma daina shan pills nakin?" nan kai
zallah ta gyad'a.
"Why? Mey na ce miki amma?"
"Kar in cire."
"Meyasa kikayi toh?"
"Yaya I'm sorry."
"Ba abun da na tambaya ba kenan meyasa kika cire?"
"Yaya I'm sorry gani nayi kaman ina d'aukan alhak'in ka ne
please don't be mad."
"Tayaya? Tayaya kike d'aukan alhak'i na? Ni na kawo
shawaran mu fara planning d'in kokuwa?"
"Yaya kaine I'm sorry."
"No answer me so kike kice kin fini sanin abinda nake so
kenan komey?"
"Yaya dan Allah kayi hak'uri."
"Ban san meyasa bakiya ta6a jin magana ba koda nayi miki,
seda na ja miki kunne nace miki this is my decision komin
yaya kar ki cire implant d'innan se idan kin gama school amma
kika k'i ji kika je kika cire saboda ni bansan abinda nakeyi ba
ko?"
"Wallahi Yaya ba haka bane I'm sorry."
"Then yayane meyasa kika cire?"
"Yaya-"
"I'm not done" ya katseta "Answer me nace kin fini sanin ya
kamata kenan ko mey? Kokuma ni da nace kar ki cire d'in
bansan abinda nakeyi ba? Wanne d'aya?"
"Yaya ko d'aya I'm sorry."
"I'm very upset with you Amal sanin kanki ne last year result
naki beyi kyau kaman yadda ya kamata ba, kinyi passing
amma duk series of D ne dalilin da yasa nace mu fara
planning d'innan kenan saboda ki samu kiyi concentrating a
karatunki ba tare da wani distraction ba."
"Amma wannan be bani wuya ba Yaya ko sau d'aya banyi
amai ba."
"I don't care Amal you're still not safe, and no matter what
dole cikin nan zeyi miki causing distraction daga karatunki,
abinda bana so kenan ni kuma I want you to focus on your
studies just. Ko nid'in a jinki bana son inga jini na ne nace mu
hak'ura se kin gama school? Na fiki damuwa Amal but haka
nayi hak'uri because thsit is what is best for you for us all" ya
k'arasa a tsawace.
"Yaya I'm sorry bazan sake ba."
"You're never sorry Amal bana ta6a gaya miki magana ki ji
sede kiyi abinda ranki yake so bans-" sautin kukan Amal ne ya
dakatar da shi, kuka ta shiga rera masa tsaye a wajen.
Sedai Afzal be shiga yi ma Amal masifa ba kawai se ta yanki
jiki ta fashe masa da kuka saboda tasan muddin ta fara kuka
Afzal yana yin shiru. "Yaya I'm sorry" tace tana ta matso 'yar
hawayenta. Kallo ya watsa mata kawai yabi gefenta ya fice
izuwa d'ayan d'akin inda ya kwanta. Kukanta tasha a wajen
seda ta gode wa Allah sannan ta mik'e ta je ta samesa a
d'ayan d'akin Allah ya taimaketa ma be sa key ba. Akan gado
ta tsincesa yana bacci, sid'ak-sid'ak ta taka taje tasamesa,
jikinsa ta shige ta kwanta akan hannunsa haka har itama
baccin ya d'auketa.
Chan dab da goshin maghrib Afzal ya tashi se ganin Amal
kawai yayi ajikinsa tana shar6an bacci. Ido ya k'ure mata
yadda take ta baccinta cikin kwanciyan hankali da jurwayen
hawaye a fuskanta. 'Yar murmushi ya saki tuna anytime ya fara
mata masifa se ta rushe masa da kuka sanin baya iya jure
kukanta. Ya rasa wani irin d'an banzan shagwa6a ne da ita
kodan chan a gidansu ba a saba mata da masifa bane kokuwa
da gan-gan takeyi ne oho shide amma shagawa6an nata na
burgesa duk lokacin da ta fara kawai se yaji ya huce. Hannu ya
aza akan cikin nata. "I'm sorry I got mad at you earlier, Rania
bana son a sanadi na GP'nki ya sake sauk'a, I only want the
best for you" tsugunawa yayi tare da pecking cikin nata. Daga
haka ya mik'e yaje ya kama ruwa yayi alwala bayan ya gama
shiri ya dawo ya tada Amal, yana tayar da ita ya fice ba tare
da yace da ita komai ba. Sallah tayi ta tofe add'u'o'inta sannan
ta zarce kitchen ta dafa macaroni da minced meat aciki ta
dawo ta shirya kan dinning. Tunda take girkin take tsammanin
shigowan Afzal amma shiru gashi ko da ta gwada trying
numbanshi taga wayar ma a gida ya barta. Haka se chan
kusan tara ya dawo Amal tayi jiran duniya har ta gaji. Yana
shigowa ta zabura, mayar da k'ofan yayi ba tare da nuna
ra'ayin yi mata magana ba so yake yaga ko zatayi masa.
"Yaya sannu da zuwa" tace tana susan kanta yayinda ta kafe
idanunta a k'asa.
"Sannu" ya amsa sama-sama sannan ya shiga takawa
gabansa tasha da wuri "Yaya I'm sorry dan Allah kayi hak'uri"
ta sanar da shi idanunta suna masu cikowa da hawaye.
"Ni ya kamata in baki hak'uri Rania I'm sorry kinji?" Cike da
d'unbun mamaki ta d'ago kai tana kallonsa "Eh?"
"I said I'm sorry for shouting at you earlier ki gafirceni."
"Yaya-" dan mamaki tama kasa cewa komai. "Yaya ka daina
fushi dani?"
"Meyasa zan yi fushi da maman unborn d'ina? Na fahimceki
Rania, and I appreciate your commitment to give me a family,
to give us a family. Just know that I'll always be here for you if
you needed me okay?" Hugging nasa kawai tayi tsabagen
yadda takejin dad'i. "I love you so much Ya Omri."
"I love you too babe" a hankali ya janyeta daga jikinsa. "How
many months is my baby?"
"Ko scanning banyi ba saboda tsoro da nake idan ka gano
gaskiya zaka mun fad'a hala ma ka daina mun magana."
"Be kamata in hau kanki da masifa ba d'azu Rania but I
couldn't help it bana son saboda ni ki sake komawa baya a
karatunki shiyasa nace mu fara planning I love you so much
my Amal."
"And I love you more Ya Omri a shirye nake da in rasa komi
nawa saboda farin cikin ka, I'm willing to sacrifice my life for
you Ya Omri. I've seen the way you so much love and adore
kids shiyasa nima nake so in yi maka fulfilling this one wish."
"And I appreciate that so much Baby, I can't believe I'm going
to be a Daddy in anytime soon, Allah ya inganta ya cigaba da
yi miki albarka."
"Ameen Ya Omri."
"So first thing gobe zamu je muyi scanning koba haka ba?"
"Duk abinda kace my King Allah ya kaimu."
"Ameen."
"Muje muci abinci tun d'azu na sauk'e ina jiranka."
"Har girki kikayi?"
"Eh mana ba kayi mun fushi ba."
"Yi hak'uri toh kinga ni bana son kina aikin wuya yanzu zan yi
ma Ummi magana ta turo mana mey aiki d'aya daga gida."
"A'a a'a nikam bana so bana so zan nayin komai nawa da kai
na."
"But Bab-"
"Trust me Ya Omri koda zaka d'auko mey aiki ma kabari ba
yanzu ba maybe idan nazo nayi nauyi amma yanzu kam da
k'arfi na bana so."
"What baby wishes she gets, fine se a bari se kinyi nauyi d'in
amma fa karki na aiki sosai bana son ki galabaita mun baby."
"Toh shikenan let's go and eat." Abincin su suka ci cikin
kwanciyan hankali sannan sukayi wanka abinsu tare suka
kwanta. Washegari kaman yadda Afzal ya fad'i suka wuce
asibiti sukayi scanning ashe ciki har na wata biyu da sati d'aya
ne tattare da Amal amma bata sani ba. Afzal dad'i kaman ze
kashe sa se buge-bugen waya yake yana sanar da mutane
Amal tasa is pregnant. Se tattalinta yake wane k'wai, idan ba
abu yafi k'arfinsa ba sam baya barin Amal tayi aiki se inde shi
yayi haka ta zama lalacacciya a gidan ko d'aga tsinke batayi
sede tayita ciye-ciye tace tana son wannan tace tan son
wancan. Wani irin d'an banzan kwad'ayi ta sake koyowa amma
Alhamdulillah ba amai ba jiri ba ciwo ba komai. Haka Afzal ya
cigaba da rainon cikin nata, kullum tare suke zuwa yin
scanning. Koda aiki yayi masa yawa ze buk'ace ta da ta jirasa
seya dawo. Cikin na da wata biyar sukayi first semester exams
nasu. Na sosai Afzal ya taimaka mata ta samu tayi passing
with excellent results. Seda cikin ya kai wata bakwai tukun ya
fara fitowa sosai acikin kaya, abinku da doguwar mace, tunda
cikin ya fara fitowa Amal ta auri zama da hijabi a gida 24/7
saboda tsokananta da Afzal yakeyi sede bata cire hijabin ba
seya nemi tsokananta. Har dan haka ma ta daina yin wanka
tare da shi. Cikin nada wata takwas ya fito yayi k'ato tim,
zama da k'yar tashi da k'yar kusan komai Afzal ne yakeyi
mata. Haka kawi zata wayi gari rana d'aya tayita kukan banza
in ya tambayeta dalili kuwa tace wai girman cikin ke bata
tsoro.
Bayan nan ga wani uban masifan da ta koya abu kad'an ta
hau surutu da masifa.
Da daddare wajajen goma Afzal na kwance yana bacci Amal
ko se kuka cikinta yake sanadin yunwan da takeji, baccin ma
ta kasa. Tun kafin su kwanta Afzal yake binta taci abinci
amma tak'i saboda haushinsa da takeji har yanzu na hanata
fita bikin sunan k'awarta da yayi. Shi kuwa dalilinsa wai saboda
EDD nata ya kusa ne, it is more safe idan tana zama a gida kar
labor yaje ya kamata acikin jama'a. Se harara take ta zuba
masa shiko se baccinsa yake hankali kwance. Mik'ewa tayi da
k'yar ta nufi kitchen ta bud'e fridge, jollof na shin kafa,
macaroni, d'anyen awara, soyayyan kifi ta tarar a cikin fridge
d'in sede duk ciki ba abinda ya gameta. Farin k'asa ta d'auko a
inda take 6oyewa ta shiga tsotsa saboda Afzal ya haneta da
sha tun lokacinda likitan ta tace musu abun baida kyau a jiki.
Seda ta sha har biyu sannan ta koma d'akin, lokacin har goma
da rabi yayi. Zama tayi daga bakin gadon tana tunanin ta
yadda zata fara tada shi.
"Yaya!" Ta ambaci sunansa. "Yaya ka tashi!" Cikin bacci ya
amsa. "Mey ne Baby?"
"Ni ka tashi" shareta yayi ya cigaba baccinsa.
"Yaya ka tashi mana!"
"Maman Baby na yi hak'uri mu kwanta kinga ina da office
gobe yi hak'uri."
"Toh ni yunwa nakeji."
"Yaya ka tashi!" Tasa ihu, ba shiri ya mik'e zaune.
"Dan Allah mey kikeso Baby?"
"Ni pepper soup nakeso."
"Toh ai akwai a fridge bari in miki micrwaving ko?"
"Ni ba na kaza nake so ba na kayan ciki wanda ba thyme
aciki nakeso."
"Baby fisabillahi a ina zan samu pepper soup na kayan ciki
cikin daren nan? K'arfe nawa ne?" Ya tambaya yana duban
agogo. "Baby sha d'aya fa ake nema, sha d'ayan dare."
"Toh laifi na ne? Ba baby'nka bace se kayi mata fad'a ba ni
ba."
"Ni ba fad'a nake miki ba yi hak'uri ki bawa baby hak'uri kice
mishi gobe da safe zanje in siyo mishi."
"Ni baby na ba na miji bane baby girl
ce ka daina canza mata jinsi."
"Toh naji yi hak'uri Maman baby girl ki bawa baby girl hak'uri."
"Ni wallahi shi muke so."
"God help me naji toh naji zanje in saya miki."
"Kuma in da thyme aciki bana so."
"Naji in shaa Allah ma babu." Nan da nan ya canza kayan
jikinsa ya d'au key. "Toh sena dawo."
"Allah ya kare I love you."
"Ameen maman baby girl I love you too." Cikin sa'a kuwa a
hotel na biyu da ya duba ya samu pepper soup d'in sede kuma
da thyme aciki haka seda ya biya extra kud'i aka samu aka
tankad'e masa romon aka yi getting rid of thyme d'in. Yana
isa gida ya d'iba mata a saucer ya d'au mata ruwa. Sam bataji
shigowansa ba kawai ji tayi karap an bud'e k'ofan. Kafin tace
zata 6oye farin k'asan da take shan har Afzal ya gani.
"Uhm uhm fito da shi na riga na gani fito da shi."
"Yaya" kame-kame ta shiga yi. "Oya mik'a mun."
"Yaya please"
"Rania give it to me."
Bata sake yin gardama ba ta mik'a masa.
"Ina sauran?"
"Babu wannanne na k'arshe."
"One... Two..." ya shiga counting inda ta dakatar da shi da
sauri. "Ka tsaya zan fad'a zan fad'a."
"Oya a ina kika 6oye?"
"Baby na" ta maraice fuska.
"Three... four..."
"Yana cikin second cupboard a kitchen."
"Kika sake saya se na kai k'aran ki gun Abba zance ko na
miki magana bakiya ji ga shi zauna kisha an samu pepper soup
d'in."
"Na fasa sha ni awara nakeso."
"Dan Allah kiyi hak'uri Rania bacci nakeji."
"Ba zaka kai k'ara na gun Abba ba? Ni bazan ci ba."
"Yi hak'uri wasa nake."
"Nide wallahi awara nake so in ba haka ba inyi ma kuka."
"Yi hak'uri Baby ta, ai bama haka dake kema kin sami, haba
maman baby girl yi hak'uri ki sha mu kwanta ko? Gobe da
kaina zan kaiki gidan k'awar naki kiga baby'n nata."
"Daga baya kenan bayan an gama komai mey zanje inyi? Ni
de awara nakeso."
"Wannan d'in fa? In zubar?"
"Ka sa a fridge amfaninsa ze taso wataran."
"God help me!"
"Ni de awara nake so." Haka dan dolensa ya juye pepper
soup d'in a fridge ya fito da d'anyen awaran daga fridge dama
already a yayyanke ne soyawa kawai za'ayi har ya shiga
soyawa ya tuna da gardaman Amal ze iya kai mata yanzu tace
ita mey k'wai ajiki takeso dan haka ya koma d'aki ya
tambayeta. Ai kuwa tace mey k'wai ajiki take so cikin mintuna
k'alilan ya gama soyawa ya kai mata nan ne ta zauna tacinye
tas shide Afzal tausaya mata yake tun cewa da likita tayi idan
ta fiye cin abinci sosai toh baby'n nata zeyi girma in akayi
wasa ma ta kasa haifa da kanta se anyi mata CS. Amma inaa
ita Amal ko a jikinta se aukin ci kaman gara. Dam tayi sannan
ta mik'e kan gado ta fara bacci. Se anan Afzal ya samu kansa
ya kwanta shima.
Haka yayi ta fama da Amal har zuwa lokacin da haihuwanta
yayi. Dama likita ta basu tsakanin 12th-15th on the 14th Amal
ta tashi da wani irin ciwon ciki mey tsanani, dama Mami tace
mata anytime taji cikinta na ciwo ko bayanta toh tayi mata
waya. Aikam Allah ya taimaketa ranan asabar labornta ya tashi
bata fita school ba saboda ba wani serious lectures sukeyi ba,
shima Afzal na a gida saboda ba aiki, tana zaune a d'aki ta
nad'e k'afa tana tsotsan tsamiyan biri tajiyo wani irin sharp
pain a mararta. Tuni tayi watsi da plate na tsamiyan birin ta
sauk'a k'asa, da cikin nata ya sake murd'awa ta sa wani
d'ankaren ihun da seda Afzal dake parlour ya shigo ba shiri,
kanta ya yo da wuri yana tambayarta ko lafiya.
"Yaya call Mami up I think I'm in labor."
"Labor?" Ya sake nanatawa a razane. "Sure!"
"Yaya kayi sauri wayyo Allah cikina zan mutu" nan da nan ya
kira Mami. Cikin mintuna k'asa da talatin ita da Mummy suka
iso kafin nan ba irin yak'ushi da masifan da Afzal be sha ba.
Amal se kuka da k'yar Afzal ya d'agata ya kaita mota Mummy
ta biyo su da maternity bag nata duka suka yi asibiti inda akayi
delivery room da Amal. Mutum d'aya aka buk'ata da ya shiga
cikin d'akin da Amal nan su Mummy sukace Afzal ya shiga
amma d'ankaren tsoro ne dashi atapir yace shi baze shiga ba
sede cikin d'ayansu ita da Mami d'aya ya shiga. Baze iya jure
ganin Amal tana kuka haka ba bayan ba abinda ze iya yi daze
tsayar da azaban da take ji ba. K'arshe de Mami ce ta shiga,
Amal se ihu take yi muryanta akeji ko ina a cikin asibitin Afzal
ko zama ya kasa se safa da marwa yake a haraban d'akin yana
mey rok'on Allah ya sauk'e masa matarsa lafiya. Bayan several
pushes Amal ta samu kanta, ta haifo zankaleliyar 'yarta. Ana
gama kimtsa su akayi ma Afzal magana.
"Congratulations matarka ta sauk'a lafiya ta samu 'yarta both
the mother and the baby are in good health zaka iya shiga
ganinta." Dr ya sanar dashi da Mummy.
Wani irin sanyi Afzal ya jiyo a jikinsa "Alhamdulillah
Alhamdulillah thank you so much Dr." Ita Mummy dan farin
ciki tama kasa magana.
"You're welcome" daga fad'in haka yabi gefensa ya fice nan
Afzal da Mummy suka k'arasa cikin d'akin. Wajen Amal tasa ya
soma nufa had'e da placing mata peck a goshi. "Sannu da
k'ok'ari my Rania, Allah yayi miki albarka sannu ko?"
"Ameen Ya Omri" ta amsa a galabaice tana mishi
murmushin dole.
"Ga chan 'yar tamu achan" Mami tayi masa nuni da crib da
aka sanya baby'n aciki. Nan da nan yaje ya d'aukota, baze iya
kwatanta irin farin cikin da ya ziyarci zuciyansa ba a lokacin da
ya rik'e baby'n nasa a hannu. Se kaman Amal kawai ya rik'e,
yarinyan ba abinda ya rabata da Amal wane kakinta Amal tayi.
Se masha Allah kawai Afzal yake ta furtwa har izuwa lokacin
da ya dawo ya zauna a gefen Amal. Addu'a yayi mata Mummy
ta mik'a masa zamzam da aka jik'a dabino aciki ya bata.
"Rania she looks just like you" ya sanar da ita had'e da mik'a
mata ita. Har kuka seda Amal tayi da ta rik'e yarinyar a hannu,
yau Allah ya amsa mata addu'arta dan azaban data sha a
labor room har cewa tayi ita mutuwa ma zatayi. Amshe baby'n
Mami tayi ta mata addu'a itama sannan ta mik'awa Mummy
itama tayi mata inda Afzal ya sake amsanta. "Gaskiya 'yar nan
ta d'ibo Amal dayawa" cewan Mummy.
"Nace miki kaman Amal kawai na rik'e a hannu ba abinda ya
rabasu" Mami tace.
"Alhamdulillah" Afzal ya sake mik'a godiyansa ga mahalicci.
Ya rasa wani kyauta zeyi wa Amal wanda zey sanyata farin ciki
kaman farin cikin da ta sanyasa a ciki yau. "Rania?"
"Na'am?" Ta amsa mik'a mata baby'n yayi "Wani suna zamu
sa mata?"
"Yaya nice zan bata suna? Ai kaine mahaifinta kai zakayi
deciding."
"Na baki wannan dama, ki sanya mata duk wani sunan da
kika ga ya dace." Shafe fuskan baby'n tayi a hankali had'e da
placing mata kiss a kan hanci "Ina son mu sanya mata
Nazeefah sunan k'anwata tilo." Gabad'aya wajen seda sukayi
mamakin wannan ra'ayi na Amal, barin ma Mummy. Ina ma
ace yadda Amal ke son Nazeefah haka itama Nazeefah take
son ta? Da kuwa ba abinda ze fiye wa Mummy farin ciki. Duk
sunyi murna matuk'a barin ma Mummy da har hawaye seda ta
zubar taso ace ta iya ta bawa 'yarta tarbiyya kaman yadda
Mami ta baiwa Amal, ta so ace Nazeefah tana da kyawun
halatayya irin na 'yar uwarta Amal. Amsan yarinyan Afzal yayi
ya mata hud'uba. "Welcome to the family Nazeefah, Allah ya
albarkaci rayuwanki."
"Masha Allah" fad'in Mami.
"Allah miki albarka Amal, Ya k'ara muku lafiya keda Nazeefar
mu."
Ameen duka suka amsa a gun.
RANA DAYA Chapter 47
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
Tareda Naja'atu Lawal Rijau Niger State
@Whatapp 08083232323 or 09060202323
End! End!! End!!!
PAGE 47
LAST AND FINAL CHAPTER DEDICATED
TO EVERY SINGLE READER ❤️
"Toh kai Afzal haka akeyi ne? Ka rik'e 'ya
tun d'azu ka hana mu kakanninta rik'e ta?"
Mami ta fad'a cike da wasa wanda hakan
ya sanya su duka dariya a wajen.
"Mami sai de fa kuyi hak'uri dan wallahi
duk yadda naso bayyana muku kalan farin
ciki da walwalan da nake ciki a yanzu ba
ganewa zaku yi ba, dan murna har gani
nake kaman mafarki nake, I can't believe
that this beautiful here is my daughter and
that Amal is her mother, Alhamdulillah
Allah abun godiya."
"Tabbas Allah abun godiya ne Afzal"
Mummy ta sanya baki.
"Thank you Amal, Allah miki albarka."
"Ameen Yaya" ta amsa da wahalallen
dariya, tana wasa da canular'n dake
hannunta.
"Toh shin za ayi wa Nazeefar tamu
alkunya ne ko da Nazeefan zamu na
kiranta? Naga ku iyayen zamani yanzu
haka kuke yayi." Mami ta kuma tambaya
inda Mummy ta gyad'a kai in agreement.
"Yaya?" Amal ta kira Afzal da ya kafa wa
'yar nasu ido ko kyaftawa ba ya yi. "Yaya?"
Ta sake kiransa se anan ne ya amsa
gabad'aya hankalinsa yayi nesa da shi.
"Na'am Rania?" Ya amsa yana d'ago kai.
"Baka ji Mami ba?"
"Sorry meney?"
"Za'ayi wa Nazeefah alkunya kokuwa?"
Murmushi mey alfarma ya saki sannan
yace, "Rania ni ai se abinda kikace."
"But Yaya I'm asking you now."
"A'a nikam se abinda kikace, don baze yi
ace bayan wannan gaggarumin kyauta da
kika mun in sake cewa ga abinda nake so
ba, this's your moment live in it, idan kina
son mu sanya wa Nazeefah alkunyan fine
se mu nemi mey dad'i mu sa mata in kuma
a'a we all good banida matsala." Kewayawa
Mummy tayi ta kalli Mami cike da jin
dad'in amsan da Afzal ya bada, inda itama
ta juyo tana kallonta suka sakar wa juna
murmushi. A gaskiya Allah ya amsa mata
addu'an da ta dad'e tanayi wa Amal tun
tana 'yar yarinya na cewa Allah ya bata
miji nagari wanda ze darajata ya kuma
kula da ita fisabilillah.
"Tuna mun wannan suna da kace yana
maka dad'i."
"Wanne d'aya?"
"Wannan da muka gani a cikin littafi
ranan."
"Wai NIHAL?"
"Yes shi why not muyi mata alkunya da
shi you once said you like the name."
"I really do but are you sure? In be miki
ba, ba semun sa ba."
"Of course Yaya duk wani abinda yake
maka dad'i nima yana mun ko Mami?" Ta
kewayo tana kallon Mami da murmushi
d'auke a fuskanta. Murmushin Mami ta
mayar mata had'e da amsawa "Eh Baby."
"Toh kaga se mu sanya mata shi ko?"
"Thank you so much Amal, Mami har yau
bansan da wani bakin zan yi miki godiya
ba na tarbiyyattar da Amal da kikayi kika
raineta har izuwa lokacin da na zo nayi
muku wayo na d'auke ta" dariya suka sa
sannan ya cigaba "Allah ya sak'a miki da
mafi alkhairi da ke da Papi gabad'aya."
Mami na murmushin jin dad'i ta amsa da
"Ameen. So kun yanke shawaran kenan
yanzu? Nihal zamu na kiran jikar tamu da
'yar uwata?"
"Yes Mami" yayi saurin amsawa.
"Toh Abban Nihal baka sanar damu
ma'anar sunan ba" fad'in Mummy.
"It means gratified; delighted; happy;
prosperous; and a blissful person just like
she truly is."
"Masha Allah gaskiya sunan yayi ma'ana
Allah d'ayyiba ya raya mana Nihal" ta
kuma cewa inda duk suka amsa da ameen.
Mami ta cigaba "Duk yadda zan so cigaba
da zama anan in kula da Nihal hakan baze
yiwu ba yau girki na ne ko tukunya kuma
ban aza ba, ni zan wuce Mummy seta bi ki
kin gane?"
"A'a baza ayi haka ba 'yar uwa" Mummy
tayi saurin katseta. "Jikar fari ce fah? Ku ku
tafi ni se in koma gida in yi ma Alhj girkin
karki damu."
"Wayyo 'yar uwa kin tabbata?"
"Kar kiji komai Allah ya raya mana Nihal."
"Ameen ya Rabbi kai nagode sosai
sakillahu bil jannah."
"Ameen wa iyyaki kuje idan na gama
girkin se na sa a turo muku naku had'e da
kayakin ki kema kokuma yanzu ina zuwa
in had'o miki kayakin se insa driver ya
kawo miki, wanne kika ga ze fi?"
"Kinga dad'in da muke gida d'aya yanzu
ko? In zaki iya had'a mun a yanzun nake ga
zefi ga key na site d'ina nagode sosai."
"Toh shikenan bari inyi sauri in had'o
miki" ta amsa had'e da kar6an key d'in.
"Ermm Mummy?" Afzal ya kirata.
"Na'am?" Ta amsa.
"Kiga ba sekin yi wani wahalan kawo
abinci ba already munyi waya da Ummi
tace zata kawo abincin so don't worry.
"Ji min d'a, ladan ma se mahaifiyarka ce
kake so ta samu wato ko?"
"Toh ai dukanku mummies d'ina ne
Mummy" ya amsa yana dariya.
"Toh shikenan breakfast de gobe ni zan
kawo ka fad'a mata na rigata."
"Toh ba matsala Mummy thank you."
"Yauwa barin wuce toh, mai jego sena
shigo gobe ko?"
"Toh Mummy thank you ki gaishe da
gida." Har waje Mami tayi mata rakiya
had'e da tuna mata kayakin da take so ta
tattaro mata sannan ta dawo ciki. In less
than an hour bayan kayan Mami sun iso
aka sallami su Amal suka komo gida bayan
tabbatarwa da likita yayi da ita da Nihal
suna cikin k'oshin lafiya. Wanka me kyau
Mami tayi ma Amal da kanta sannan ta
had'a mata tea mey kauri ta sha dan samun
ruwan nono. Afzal ko na zaune a parlour se
pictures yake tayi wa Nihal chan idan ta
fara kuka ya bata ruwan zamzam da suka
tanadar.
Bayan Amal ta gama shiri Mami ta kira
Afzal ya kawo Nihal dan a shayar da ita.
Mutumiyar ku kam ta cire mama ta shayar
da 'yarta ta kasa se tayi kaman zata sa mata
a baki seta fasa, kan Mami da Afzal ne ya
gama d'aurewa.
Chan Mami da ta kasa hak'ura ta tambayi
ko lafiya "Ya haka Baby?"
"Babu" ta amsa k'asa k'asa cike da
kid'imewa.
"Toh ki bata mana baki ji tana kuka
bane?"
"Zan bata."
"Toh mey kike jira? In taimaka miki ne?"
"A'a zan iya zan iya" ta amsa cike da
tsoro.
"Toh muna jiranki." Setayi kaman zata sa
mata a baki seta fasa. "Wallahi Baby zan
sa6a miki me ke damunki wai?"
"Mami wallahi zafi zeyi, baki ji yadda yayi
tsami ba, rik'e shi ma haka da nake zafi
yake mun" Baki Mami ta hangame tana
kallonta cike da d'umbun mamaki, Afzal da
ya san kayansa kam se kad'a kai kawai
yake. Ance aure na sa hankali toh ga har
Amal tasa ta haihu amma shagwa6a da
rashin hankalin nan nata na nan har yau,
Allah taimake shi.
"Dan zeyi zafi se baza ki shayar da 'yarki
ba? Ke d'in ba hak'ura nayi na shayar dake
ba kema?"
"Toh ai Mami ke kina da dauriya."
"Kinga bana son shashanci kiba 'yar nan
nono ta sha tunda ta shigo duniya fa banda
ruwa ba abinda aka sake bata."
"Ni wallahi zafi" ta sake cewa tana
zum6uro baki yayin da ta shiga cika
idanunta da k'walla.
"Ikon Allah toh wallahi inde haka zaki
cigaba se Ummi tazo kuyi jegon tare na
tabbata idan itace akanki zaki nutsu."
"Ya Omri ina ruwanta a sake bata."
"Ruwa?" Mami ta katseta kafin Afzal yayi
magana. "So kike cikin nata ya fashe? Kai
kuma Afzal kayi tsaye achan baza kayi
mata fad'a bane?" Ta kewayo tana kallon
Afzal dake rik'e da feeder'n Nihal a hannu.
"Zan yi mata Mami, Amal yi hak'uri ki
bata kinji?" Ya ce da ita a hankali yana mey
nufan inda take zaune.
"Aww ma hak'uri kake bata? Lalle kam
banga laifin Baby ba kai kake d'aure mata
gindi ko ka sata ta bawa yarinyan nan
mama tasha ko in kira Ummi tayi mun
maganinku duka" tana kaiwa nan ta fice
daga d'akin. Se kuka Nihal take Amal na
jijjigata, ta kuma bata maman ta sha ta kasa
wai ita zafi. A nitse ya k'arisa ya zauna
daga gefenta tare da dafe ta.
"Baby na?" Ya kirata, kai ta d'ago a
maraice da k'walla cike dam a idonta tana
kallonsa. Goshinta yayi pecking a hankali
sannan yace, "Yi hak'uri ki ba Nihal ta sha
kinji? Yi hak'uri."
"Ya Omri wallahi yayi tsami ta6awa kad'ai
nayi ma zafi yake mun" ta sanar da shi a
shagwa6ance.
"I know sweetheart but kinga Nihal na
kuka badan komai ba kuma se don yunwa
help her out okay? I trust you na san ki da
dauriya."
"Mu sake bata ruwa zuwa gobe se in
gwada breastfeeding nata nasan kafin nan
tsamin ya d'an ragu."
"Babe har zuwa gobe? Idan mukayi haka
munyi ma Princess adalci kenan? Yi hak'uri
kinji? I trust you I know you can do it"
lalashinta yatayi yet still Amal ta kasa sawa
Nihal mama a baki ita kuma da gajan
hak'uri ta k'i yin shiru. Lalla6ata ya tayi
har se da ya samu ta amince, rufe idonta
tayi gam sannan shi da kansa ya saita kan
Nihal ya ajiyeta, tana kama bakin Amal
tasa wani d'ankaren ihun da ya mugun
razana Nihal har da shi ma Afzal d'in. Sake
nonon tayi ta shiga kuka cike da tsoro
kaman ba gobe. Da hanzari Mami ta shigo
d'akin a kid'ime se gani tayi Amal na
hawaye, ita de ta na ganin shagwa6a yau, a
hankali Amal ta mayar da bakin Nihal kai
tashiga shayar da ita. Nihal bata yarda aka
cire maman daga bakinta ba har seda tayi
bacci.
Bada dad'ewa ba Ummi ta shigo da abinci,
se rawan jiki take ta kasa zama gu d'aya da
Nihal duk da cewan barci take, daga ta
d'auketa suyi nan se suyi chan. Ita wai
tunda take bata ta6a ganin fine baby ba
kaman Nihal ba.
*****
"Ka ga hoton yarinyar?" Mummy ta fad'a
had'e da mik'a wa Daddy wayanta across
the table inda ya amsa. "Kaiii masha Allah
Amal tayi k'ok'ari ita ta haifi wannan
k'atuwar baby'n da kanta."
"Wallahi ko Alhj da kanta, yarinyar
tubarkallah k'atuwa."
"Gaskiya Allah ya raya gobe in shaa
Allahu zamu je mu dubata. Sun sa mata
suna ko tukuna?"
"Eh sunsa Amal ce ma ta sa."
"Masha Allah ya sunan?"
"Nazeefah, tayi wa 'yar uwarta takwara
amma za ana kiranta da Nihal."
"Alhamdulillah Alhamdulillah Allah sarki
Amal, Allah ya cigaba da yi mata albarka
yasa 'yar uwarta tayi koyi da ita."
"Ameen Alhj wallahi addu'ata bata fin
haka kullum."
"Ya Nazeefar har yanzu tana kan bakanta
na cewa baza ta dawo ba?"
"Eh tun d'azu ma ina trying line nata
amma baya shiga."
"Toh Allah sa de lafiya."
"Amin."
"Jameelah zata kwana achan kenan ko?"
"Eh kasan dake girkinta ne setace ni in
taya Amal kwana amma ai kaga idan nayi
haka ban kyauta ba tunda de jikarta ce ta
farko shi ne nace suje ni zan kula da kai."
"Hakan yayi Hjy Surayya Uwar gida a
gidan Alhj Abdallah, Allah cigaba da yi miki
albarka."
"Kai Alhj ameen kayi ka gama muje ka
watsa ruwa ko baka fad'a ba na san ka
gaji."
"Wallahi kuwa kaman kin sani meeting
meeting baya k'arewa haka."
Yana gama cin abincin ta sirka masa
ruwan d'umi ya watsa suka kwanta.
Washegari da sassafe ta tashi ta shiga had'a
breakfast na nan gida da kuma wanda zata
kai wa su Amal. Tana cikin aikin ne
wayanta dake kan counter ya shiga ruri
hannunta ta d'auraye tayi drying a jikin
towel sannan tayi sauri ta d'aga duda
cewan new number ne ke kira.
"Assalamu Alaikum" ta soma da cewa.
"Wa'alaikumus salam" aka amsa daga
d'ayan 6angaren.
"Nazeefah?" Ta ambata had'e da sauk'e
wayan tana mey duban lamban da kyau.
"Nazeefah is that you?"
"Yes Mummy ina kwana."
"Wani layi nake ganin kaman Nigerian
number? Kin dawo Nigeria ne?"
"Eh Mummy ina Abuja yanzu haka, zuwa
anjima zan shigo in shaa Allah flight d'ina
by 2 ne."
"Toh Alhamdulillah Alhamdulillahi sannu
da dawowa Nazeefah sekin shigo."
"Ya Daddy?"
"Lafiyashi k'alau me kike so in dafa miki?"
"Anything will do Mummy."
"Don't you miss my Eghusi?"
"I really do Mummy amma bana son saki
aiki ne."
"Karki damu Allah kawo ku lafiya."
"Ameen Mummy se mun sake waya."
"Erm Naz-" sede har Nazeefah ta katse
wayan. Dama so take ta sanar da ita cewa
Amal ta haihu kuma tayi mata takwara but
then seta ga it'll even be better idan
Nazeefan ta shigo tukuna. She has a feeling
everything is going to work out yanzu
tunda yanzu ba tare da kowa ya mata fad'a
ba ta duba taga ya kamata ta dawo gida.
Ohh she can't wait ita da Amal su fara shiri.
Nan da nan ta kammala girkin ta kai musu
nasu dining, ta kai wa Papi da sauran masu
aiki nasu sannan tasa nasu Amal kuma a
flask ta shirya komi tsaf sannan ta shiga
bayi tayi wanka ta shirya. Har ta gama
karyawa Daddy na bacci seda tazo fita ne ta
tada shi "Alhj ni zan wuce yaso ko daga
baya seka shigo."
"Ina zakije da safen nan haka?" Ya
tambaya yana k'ok'arin bud'e idonshi.
"Gidan Amal zan kai musu breakfast."
"Ba munyi zamu fita tare ba? Ina Abba?"
"Ya na nan na kai mishi breakfast shima
yana kwance yaso anjima seku taho tare
naga baccin naka yayi nisa ne Alhj kaman
stress yayi maka yawa."
'"Yata ce fa ta haihu."
"Shiyasa ai zaka iya zuwa duk lokacin da
yayi maka, nasani 'yarka zatayi maka uzuri
now go back to sleep idan ka tashi breakfast
naka na jiranka akan dining ni na tafi."
"Toh ki gaishesu."
"Zasuji ba-bye." Acikin mintina k'alilan
driver ya sauk'eta gidansu Amal inda ya
shiga da baskets d'in ciki. Kasancewar ba
kowa zaune a parlourn seta wuce ciki, ta
inda ta jiyo hayaniya ta dosa had'e da yin
sallama bakin k'ofan kamin ta bud'e.
"Yanzu k'ara ruwan sanyi kikayi akan
wanda na sirka miki Baby?"
"Assalamu Alaikum" Mummy ta sake yin
sallama wanda se a nan sukayi noticing
presence nata suka kewayo bakin k'ofan.
"Ha'a 'yar uwa yaushe kika shigo?
Bismillah bismillah sannu da zuwa."
"Ya nake ta jin hayaniya haka?"
"Ina kwana Mummy?" Amal dake d'aure
da towel ta gaisheta tana mey k'ok'arin
sauk'a k'asa.
"A'a 'yata yi a hankali kinsan k'asan ki
ciwo ne ba sekin durk'usa ba hakan ma
yayi, ina kwana ya jiki?"
"Alhamdulillah da sauki'i ya daddy?"
"Lafiyanshi k'alau na barosa yana bacci
akan cewa anjima shi da Abba zasu shigo,
ya jikata?"
"Ayyah haka yace mun jiya Allah kawo su
lafiya."
"Ina Nihal tamu?"
"Tana gun Yaya a d'ayan d'akin."
"Har anyi mata wanka ne? Sannu da
k'ok'ari 'yar uwa."
"Sannu 'yar uwa ai da ma baza kizo ki
same mu haka ba sede kizo kiga kowa yayi
wanka tsaf amma wannan yarinyar" tayi
maganan tana nuna Amal da yatsa "Nakega
sede ke ko Ummi ne zaku tayata zaman
jegon dan ni kam ta raina ni bata ko shakka
na." Mummy na dariya ta tambayi meya
faru inda Mami ta shiga irga mata, "yanzu
haka ruwan dana sirka mata bayan nace
kar ta k'ara na sanyi akai ta kama ta k'ara."
"Toh Amal ai seda ruwa mey d'umi ake
wankan ko so kike jikin ki yayi tsami ya
rub'e shi ruwan zafin ai magani ne kar fa
ki manta jikin naki du ciwo ne yanzu."
"Mummy wallahi baki ji d'umin ruwan ba
har fa hayak'i yake."
"Rufa mun baki sangaltacciya kawai."
"A'a 'yar uwa ke kuwa ya zakiyi ma
maman Nihal haka? Kinga maman Nihal yi
hak'uri ki shiga bayin kiyi wanka bari in
sirka miki da kaina nawa baze kai na Mami
zafi ba." Haka da k'yar suka samu Amal
tayi wankan ta fito itama Mami ta shiga
suka karya sannan Amal taje amso Nihal
daga gun Afzal wa Mummy had'e da kai
masa breakfast nasa. Sallama tayi bakin
k'ofan bayan da ya amsa ta bud'e ta shiga.
Tsince akan gado ta samesa da gajeren
wando ajikinsa yayinda ya kwantar da
Nihal akan k'irjinsa tayi tsit sekace ba ita ta
fitinesu ta hanasu barci ba daren jiya.
"Toh kuma kinyi tsaye a wajen bazaki
k'araso bane ko inzo in kar6e ki?" Yace da
ita.
"Not at all Ya Omri I just can't believe my
eyes, like you two are the most cutest beings
I've ever seen."
"Look at you cute thing come in."
Murmushi ta sakar mishi sannan ta mayar
da k'ofan ta k'arisa ciki ta ajiye abincin kan
bed side drawer sannan ta zauna daga
gefensa. "Good morning Ya Omri" ta
gaishesa tare da kissing lips nashi a lokaci
guda.
"Morning my sunshine" ya amsa "You're
looking spectacular se kace ba ke kika
haihu ba jiya ba, such a strong girl."
"Kai Ya Omri" ta amsa tana murmushi.
"I'm damn serious kinyi kyau and above
all you smell sooo good."
"Thank you Love kai kam dan k'azanta ko
wankan ma bakayi ba anyways you're still
smelling good."
"Aww dan ina mana raino kike so ki
zageni?" Ya tambaya da d'aurarren fuska.
"Haba Sweetheart I was only kidding
jazakallah kaji? Ya Nihal? Tayi bacci?" A
hankali ya lek'a fuskan had'e da gyad'a
mata kai "Sekace ba ita ta cika mu da kuka
ba jiya."
"Toh baku yi mata abinda take so ba ai
dole."
"Kaman ya ba ayi mata abinda take so ba
Ya Omri? Ita wai kar in cire maman daga
bakinta, a ina aka ta6ayin haka?"
"Oho de se kiyi hak'uri after all dama nata
ne."
"Toh kawota in kaita wa Mummy she's so
eager to see her."
"Oh ayyah, ehemm before I forget, wai
Mami yaushe zat tafi?"
"Yaushe tazo ko yaushe zata tafi kake
tambaya?" Ta sa dariya.
"Babe wallahi jiya da k'yar nayi bacci I
miss your legs wrapped around me."
"Same here Ya Omri, I miss sleeping on
your broad chest amma ya muka iya? Se na
fita daga arba'in Mami zata tafi."
"What!! Wasa kike amma ko?"
"Ka zauna anan."
"Rania wallahi bazan iya ba gaskiya, if
only you have an idea how I suffered
yesterday alone."
"Toh Baby ya zamuyi?" Ta tambayesa tana
shafa gashin kansa a hankali "Kaman
yadda ban iya wankan baby ba kaima na
tabbata baka iya ba idan ba Mami wa ze
nayi wa Nihal?"
"Toh ba se ki koya ba, in fact ni zan ma
koya."
"Wa d'in wallahi baza ka iya ba."
"Toh ke ki koya mana Baby?"
"Ni wallahi tsoro nake gani nake kaman
zan karyata idan na rik'eta ba kaya a jiki."
"God help me is just that I miss you Rania."
"Me too Ya Omri" ta amsa had'e da
kwantar da kanta a gefen na Nihal a
k'irjinsa.
"She's so beautiful" ta furta tana wasa da
'yar hannunta.
"Just like you" ya amsa had'e da zagaye
hannunsa a bayanta. "Kinsan wani abu?"
"Tell me."
"Kinsan kin mun wayo ko?"
"Da nayi meh?"
"Da Nihal take kama dake ke kad'ai mana,
ina laifin ko ido nane ta d'an d'auka."
"Toh yi na ne Ya Omri? If it was my way ai
sede tayi kama da kai tunda de kafi ni
kyau."
"Inji waye na fiki? Besides I was only
joking, darling you're the most beautiful
being I've ever known amma de ina son
second child d'ina yayi kama dani kisan
yadda zakiyi."
"Wa ya fad'a maka ma zan sake haihuwa?
Daga Nihal se Nihal."
"Chab lalle ma! A dalilin mey?"
"Da nace ka shigo labour room ina k'i
kayi?" Tayi maganan tana k'ok'arin
mik'ewa.
"Sweetheart ba haka bane" yayi saurin
fad'a yana k'ok'arin dakatar da ita.
"Toh yaya ne? Ni ban ta6a jin inda mata ta
kira miji labor room yak'i shiga ba."
"Shine kikayi zuciya?"
"Toh bazan yi ba?"
"Baby ba haka bane I was so scared bana
son jin kukanki."
"But I needed you in there sweetheart."
"I'm sorry okay? Next time in shaa Allah
tare dani zaki shiga."
"Ba wani next time d'innan daga kan
Nihal na gama haihuwa na se inde zaka
auro wata."
"Ba watan da zan auro ked'in de zaki
haifo mun masu kama dani har goma."
"Sannu toh kad'au haihuwan wasa ne?"
Cike da dabara ya sake miyar da ita jikinsa
"Yi hak'uri baby na yi hak'uri kinji?"
"Naji toh."
"Then kiss me."
"Dalili?"
"Dama nasan ni kad'ai ke kewarki?"
"Kaga bani Nihal in tafi nasan Mummy har
ta gaji da jirana."
Mik'ewa yayi ya zauna "you must kiss me
first."
"Or else?"
"Or else bazan bada Nihal ba."
"lol ba se inje in fad'a musu ka hana ni
ba."
"Toh kije d'in" ganin ta mik'e dagaske yayi
sauri ya cafke hannunta wanda hakan ya
sata fad'i kan gadon. Nihal ya ajiye a gefe
yayi sauri ya haye kanta yana mata dariyan
mugunta.
"Yaya mey haka? Ka d'agani wallahi
banida lafiya." Wani killer'n murmushin
dake tafiyar mata da imani ya saki "Let
your dream boy kiss and take your sickness
away baby."
"Nikam ka d'agani Nihal dan Allah ki fara
kuka."
"Ai ita 'yar arziki ce ba kaman ki ba."
"Au nice 'yar tsiya?"
"Ni ban ce haka ba" ya amsa yana dariya.
"Wallahi Yaya nasan maganin ka, nikam
d'agani" bata hankara ba kawai taji
sauk'an lips nasa akan nata. Kissing nata ya
shiga yi a hankali yana mey tafiyar mata da
imani. A sannu a sannu yake kashe mata
duk wani sassa a jikinta, Amal bata san
lokacinda ta shiga mayar masa da martani
ba a garin haka har d'aurinta ya kunce.
Knock da suka jiyo daga bakin k'ofan ne ya
dawo dasu daga duniyan da suka fad'a a
rikice Amal ta ture Afzal daga kanta ta
mik'e zaune tana k'ok'arin mayar da d'an
kwalinta. "Baby??" Suka jiyo muryan
Mami.
"Ermm na'am Mami" ta amsa cike da
tashin hankali.
"Kar6o Nihal d'inne har yanzu?"
"Ermm ermm na bata nono ne."
"Ohh toh kiyi sauri Mummy na jiranki."
"Toh Mami gani nan zuwa." Juyowa tayi ta
danna wa Afzal dake ta faman kallonta
harara yana wani lasan le6ensa, daga
bisani kawai ta kai masa pillow fuska. "God
help me! Ni kuma mey nayi?" Ya tambaya
yana mata dariyan mugunta.
"Ma tambaya na kake ko? Fisabilillahi
wani irin abun kunya ne wannan Yaya?"
"Da nayi mey? Talking as if you didn't
enjoy it too."
"Aww ma haka zaka ce? Zaka gani" kafin
tace zata mik'e yayi sauri ya rik'eta
"Shikenan ke Rania abu kad'an zuciya."
"Ni sakeni in d'au 'yata mu tafi."
"'Yarki ko 'yar mu? Now that aside yi
hak'uri Yaya is sorry."
"Naji sakeni."
"Kiyi hak'uri mana toh I said I'm sorry."
"Nace naji."
"Toh smile" murmushi cike da tsangwama
ta sakar masa yayinda ya saketa ta d'au
Nihal dake kwance a gefe, har bakin k'ofan
yayi mata rakiya had'e placing gentle kiss a
kan goshinta "See you around, I love you."
"I love you too" ta sanar dashi sannan ta
k'arasa wajen su Mummy. Bada dad'ewa ba
Maamah, da sauran k'awayenta suka zo yi
mata barka. Da Azahar Ummi da Abba suka
kawo abinci inda Abba ya sawa Nihal
albarka, sun kusan tafiya Papi da Daddy
suka shigo suma. Wajajen 2:30 Nazeefah
tayi wa Mummy waya kan sun iso dai-dai
wannan lokaci Daddy suke shirin komawa
da Papi dan haka suka ke6e inda take sanar
da shi shigowan Nazeefah. Mamaki na sosai
Daddy ya sha take suka wuce airpot suka
d'aukota. Kuka sosai Nazeefah ta tsaya yi da
suka had'u se faman neman tubansu take
har suka isa gida. Bayan ta watsa ruwa ta
sauk'o ta sami Mummy inda tayi serving
nata abinci.
Abincin take ci amma gabad'aya babu
hankalinta a tattare da ita.
"Nazeefah lafiya?" Mummy da ta karance
ta na d'an lokaci ta tambaya.
"Ermm babu" ta k'irk'iro murmushin dole,
miyan yayi dad'i I've missed your
cookings."
"Thank you, fad'i tunanin mey kike?"
"Babu fa kawai naga gidan ne ya canza
site na waye wancan? Amaryar Daddy?"
"Eh na 'yar uwata ce mahaifiyar Amal
kuma amaryar Daddy'nku."
"Oh" ta amsa sama-sama sounding not
surprised. "Meyasa Daddy ya had'aku?
Kuma harda mahaifinta suka dawo?"
"Eh we're one big happy family down
here, kuma ni na kawo shawaran a had'a
mu."
"Happy?" Ta nanata cike da rainin
hankali.
"Nazeefah baki tambayi ya Amal 'yar
uwarki take ba?"
"Mey had'i na da ita? Please not this time
Mummy."
"Haba Nazeefah na d'au kin dawo saboda
kin gano kuranki ne kina son ki gyara
tafiyarki ko ba haka ba?"
"Wani kuskure Mummy? Mey na aikata?
I'm not back because of that so called Amal
I'm back because I've missed you and
unless kina so acikin sati in koma in da na
taho zaki daina mun maganan Amal bana
son jin maganan da ya shafeta."
"Uh well tunda kince haka dama ina son
sanar dake cewan ta haihu ne jiya ta samu
'yarta kuma tayi miki takwara." Chak ta
tsaya da hannunta da take k'ok'arin kai
loman tuwo. "What???" Ta tambaya out of
disbelief.
"You heard me right Amal ta haihu ta yi
miki takwara."
"Ni tayi wa takwara?" Ta kuma tambaya
had'e da sakar da wani dariyan rainin
hankali "You're always good at telling jokes
Mummy but not this time around."
"Yaushe na zama playmate naki da zan na
cracking jokes da ke Nazeefah? Amal ta
haihu kuma tayi miki takwaraamma ita da
Afzal sunyi deciing zasu na kiran 'yar da
Nihal."
"Mummy kinsan mey kike fad'i kuwa?"
"Tabbas na sani kinga" tayi maganan
had'e da d'ago wayanta kan pictures na
Nihal ta kai had'e da mik'a mata "here
swipe left ga yarinyar nan." Hannu na
k'yarma Nazeefah ta amshi wayan ta shiga
kalla da fari ma taso k'aryata komai
sekuma taga irin tsan-tsan kaman da
baby'n keyi da Amal nan ta sake tabbata da
cewa eh 'yarta ce amma kuma se tayi mata
takwara? Me ta ta6a yi mata mey kyau a
duniya da har zesa tayi mata takwara? Shin
Amal bata sane da irin k'iyayyar da tayi
mata ne? Shin bata san cewa bayan
shaid'an da fir'auna se ita tafi tsana fiye da
kowa a duniya ba? Wow! Bata hankara ba
kawai taji hawaye na tsiyaya daga d'ayan
idonta wanda tayi saurin sa hannu ta goge
had'e da mik'a wa Mummy wayanta
sannan ta mik'e.
"Ya haka lafiya?" Munmy tayi saurin
tambaya. Wanke hannunta tayi cikin bowl
ta goge da towel ta shiga tafiya ko amsa
Mummy batayi ba, tana kaiwa d'akinta ta
fad'a ciki ta nufi kan gado inda ta kwanta.
Kuka ta shiga yi kaman ba gobe tana mey
tsanar kanta na d'aukan tsana da k'iyayyan
duniya da tayi ta aza akan 'yar uwarta
wanda suka kasance jini d'aya da ita. Ji tayi
kaman ta kashe kanta dan irin munanan
ababen cutarwan da ta ringa yi wa Amal
baiwar Allah. Shin masu halayya irin na
Amal guda nawa suke a duniya irin tamu ta
yanzu? Ace duk irin sharratayyan da bita
dashi amma ita ta sak'a mata da alkhairi
haka har ta d'auki sunanta ta sanya wa
'yarta ta fari bayan ga mahaifiyarta dana
mijinta a raye? Subhanallah ita kanta baza
ta iya yafewa kanta abubuwan da tayi wa
Amal ba bale ta soma neman yafiyanta.
Gaskiya ne ta cuci kanta a rayuwa, da tun
farko ta gane cewa idan abu rabon mutum
ne ko ta yaya zai samu idan kuwa akasin
hakan ne toh ko ta yaya ya buga baze ta6a
samun abun ba koda ya samu ma abun
baze yi lasting mishi ba. Da tun farko ta
rungumi k'addaran cewa ita da Afzal are
not meant to be da batayi hurting one and
only sistee nata ba.
Tana cikin tsakiyan kuka Mummy ta bud'e
k'ofan ta shiga da hanzari ta shiga share
hawayenta.
"Nazeefah?" Mummy ta kirata had'e da
dafe kafad'arta.
"Kukan mey kike haka? Tashi ki zauna
muyi magana." Ba gardama ta mik'e zaune
cikin tsananin kuka tace, "Mummy I've
hurt Amal so much, ta ina zan fara bata
hak'uri? She really did not deserve
everything I put her go through Mummy
nayi nadaman abubuwan da nayi mata."
"Inde Amal ce na tabbata ta jima da yafe
miki komai Nazeefah tunda de har ta d'au
sunanki ta sanya wa 'yarta bayan ga
mahaifiyarta a raye, inspite of everything
Amal still loves you Nazeefah."
"Abinda yafi ci mun rai kenan Mummy,
meyasa zatayi mun takwara? Meyasa baza
ta tsane ni ba kaman yadda na nuna na
tsane ta? Meyasa bazata sak'a mun sharrin
da nayi mata da sharri ba? Why is she
making me feel like a bad guy?"
"She only did what's right to reunite you
guys."
"Mummy I feel like a total crap ji nake
kaman in kashe kaina Amal ta fini ta duk
inda nake tunani" ta fad'a tana kuka sosai.
"Kar kice haka Nazeefah, life is a
competition but we're not competitions
amongst ourselves, yadda kike ganin Amal
ta fiki da wani abun itama haka take ganin
kin fita ta wani fannin, you guys are sisters
Nazeefah you learn from each other okay?"
Fad'awa jikin Mummy tayi tana mey cigaba
da kuka yayinda Mummy ke lalashinta.
**** Washegari...
"Har kin shirya ne?" Mummy ta tambayi
Nazeefah dake sauk'owa daga kan stairs.
"Eh Mummy good morning."
"Morning breakfast naki na kan dining."
"Thank you Mummy ina Daddy?"
"Ya fita office just a while ago."
"Ohh kakan Amal fah?"
"Yana nan zaki je gaishesa ne?" Kai ta
gyad'a a hankali, dad'i sosai Mummy taji
"sunansa Papi ba Kakan Amal ba kinji?"
"Naji."
"Muje in raka ki toh."
***
Bayan sunyi sallama Papi ya tashi ya
bud'e musu k'ofa, a parlour suka zauna
inda Nazeefah ta sauk'a har k'asa ta
gaishesa. "Ina kwana Papi?" Na sosai Papi
yaji dad'i ya amsa da fara'a "Tashi
mamana, tashi ki zauna ya karatu? Ya k'are
ko da saura?"
"Ya k'are Papi sauran graduation ne
kawai."
"Toh madallah Allah sanya alkhairi."
"Ameen Amal tazo ta samu 'yarta kuma."
"Eh mun samu takwararki."
"Haka Mummy tace, toh Allah ya raya ya
d'ayyiba."
"Ameen ameen."
"Dama nace barin gaisheka kafin in wuce
chan gida in duba Amal kuma in baka
hak'uri game da duk wani rashin hankalin
da na tafka da a baya, please forgive me."
"Ba komai 'yata nagode Allah sak'a da
alkhairi ya miki albarka komai ya riga ya
wuce kinji?"
"Ameen Papi, thank you so much."
"Toh Abba bari mu koma" fad'in Mummy
har bakin k'ofa ya rakasu sannan ya dawo
ciki. Nazeefah na gama breakfast ta jira
Mummy ta shirya suka fice. Tun da suka isa
gidan gabanta ke fad'i shin idan sun had'u
da Afzal zatayi mishi magana ne ko kuwa?
"Mummy I can't do this" ta fad'a kafin su
shiga ciki.
"Sure you can Nazeefah karki ji komai
okay??" Kai zallah ta iya ta gyad'a sukayi
sallama suka shiga.
"Ha'a Mummy sannu da zuwa" cewan
Afzal dake zaune a parlour da Nihal rik'e a
hannunsa yana mey k'ok'arin tashi.
Mik'ewan da yace zeyi sukayi ido hud'u da
Nazeefah ba k'aramin fad'i gabansa yayi ba
for a second ya d'au ma ko hallucinating
nata yake.
"Nazeefah?" Ya ambata bayan tsawon
lokacin da suka d'auka suna kallon juna da
sauri ta kawar da kanta daga kallonsa
had'e da gaishesa "Ina yini Ya Afzal?"
"Nazeefah yaushe kika dawo? Bismillah ku
shigo" waje suka nema suka zauna ita da
Mummy yayinda ya cigaba da rik'e Nihal.
"Jiya-jiya ta shigo" Mummy ta amsa.
"Oh ayyah ya karatu? Ya k'are ko da
saura?"
"Ya k'are Amal ta sauk'a lafiya?"
"Lafiya k'alau Alhamdulillah an samu
takwararki" ya amsa had'e da mik'ewa dan
kai mata baby'n, a garin mik'a mata ita
hannunsa ya goga nata kad'an. Mutuwan
tsaye yayi waien yayinda itama tayi
freezing inda take zaune, ji tayi duk wani
rayuwan da sukayi da a baya suna dawo
mata, ta d'au by now tayi moving on, ta
d'au koda ta sake sanya sa acikin
k'wayoyin idanunta baza ta sake ji mishi
wani abu ba ashe ba haka bane, har yau
akwai ragowan soyayyarsa a cikin
zuciyarta.
"Masha Allah she's soo big" ta fad'a tana
k'ok'arin 6oye bak'on lamarin daya ziyarce
ta. "And soo beautiful ga shi kamanninsu
d'aya da Amal."
"Wane an raba kara" cewan Mummy.
Bayan Nazeefah ta d'an rik'eta ta mik'awa
Mummy sannan tayi gyaran murya. "Ya
Afzal nasan komi ya riga ya wuce amma
dan Allah ka yafe mun duk wani abinda
nayi maka da wanda na sani da wanda
bana sane da shi I'm really sorry."
"Nazeefah there's no need to, mun riga
mun zamo abu d'aya yanzu, Allah ya yafe
mana gabad'aya Amal will be so thrilled to
see you bari inyi mata magana." Knocking
yayi bayan an amsa ya shiga a gaban
dressing mirror ya sameta zaune tana taje
sumarta.
"Ya Omri?"
"Ina Mami?"
"Wanka" ta amsa.
"Come there's something you need to see."
"Menene? Meya faru?" Lokaci guda
hankalinta ya tashi a cewarta wani abu ne
ya samu Nihal.
"Kede kizo."
"Yaya please speak up menene ya faru?
Nihal ce?"
"Just come" cike da fargaba ta mik'e tabi
bayansa suna shiga parlour ya matsa gefe
wanda hakan ya bata daman sanya
Nazeefah a ido. Da fari ma k'in amincewa
tayi, ta d'au ko wasa idanunta suke yi
mata.
"Nazeefah?" Ta kira ta cike da k'in yarda.
"My sister" Nazeefah ta amsa idanunta
suna masu cikowa da hawaye.
"Nazeefah kece??" Itama ba shiri idanun
nata suka ciko da hawaye.
"Yes Amal ni ce" da gudu ta ruga taje tayi
hugging nata inda suka fashe da kuka
dukansu biyu. Mummy dake rik'e da Nihal
itama bata san lokacinda idonta ya cika da
k'walla ba.
"Amal I'm so sorry please forgive me." A
hankali Amal ta janyeta daga jikinta
sannan ta shiga share mata hawayen ta, "ki
daina neman tuba na Nazeefah, har cikin
raina na yafe miki komai duniya wa lahira
kukan ya isa haka." Sake rungumeta
Nazeefah tayi tana mey sake tsanar kanta
na duk wani cutarwan da tayi wa 'ya
uwarta.
"Amal ban san da wani bakin zan yi miki
godiya ba" cewan Nazeefah bayan sun
nemi waje sun zauna a gefen Mummy.
"Amal you named your first daughter after
me, duk kalan mugunta da bak'in halin da
na miki hakan be hanaki aikata abinda kika
fasa ba, da Mummy tace mun kin yi mun
takwara na kasa amincewa sabida kasa
gane wace irin mutum ce ke da nayi,
instead ki sak'a mun da sharri kaman
yadda nayita cutar da ke se kika gwammaci
ki sak'a mun da alkhairi, alkhairin da ba
kowa ne ze iya yin irinsa ba, Amal I hate
myself for ever hurting you please forgive
me."
"Nazeefah komi ya riga ya wuce and I
can't tell you how happy I am right now
that you're back with us, addu'ata kullum
bata fin Allah ya dawo mana dake cikin
k'oshin lafiya and here you're in good
health and shape Alhamdulillah."
"Amal thank you so much, thank you."
"Don't mention Nazeefah kuma dan Allah
kibar kukan haka ya isa."
"Allah ya raya mana Nihal gani nake
kaman mafarki har yanzu wai kin yi mun
takwara, 'yar uwata guda tayi mun takwra
it feels like a dream." Murmushi mey
k'ayatarwa Amal ta sakar wa Nazeefah "Ya
karatu ya k'are?"
"Eh saura graduation."
"Ayyah congratulations Allah sanya
alkhairi."
"Ameen, Naki fah?"
"Final year zan shiga nima."
"Masha Allah Allah sanya alkhairi ina
Mami?"
"Tana wanka nakega ta fito yanzu."
"Muje ki raka ni in gaisheta."
Da murmushi kwance a fuskanta ta mik'e
"Oya tashi muje toh." Afzal ya kasa daina
murmushi, all he's ever wanted is to see his
Amal happy and ya san ba abinda ze kai
mata shiryawa da Nazeefah dad'i se gashi
yau Allah ya shirya tsakaninsu, he can't ask
for more.
Har cikin d'aki gun Mami Amal ta kaita
inda suka gaisa sannan Nazeefah ta nemi
tubanta na duk wani abinda tayi wa Amal
wanda ta san yayi wa Mami zafi, a wajen
duk sukayi reconciling. Kusan Azahar
Mummy tace zata koma dan yin girki
Nazeefah kam tace sam bata tafiya, se hira
suke da Amal ta rik'e takwararta a hannu.
Chan da zatayi sallah ta mik'a ta wa Amal
dan yin alwala, tana cikin yin sallah ne
wayanta dake gefen Amal ya shiga ruri
lek'awa tayi dan ganin wake kira acewanta
ma ko Mummy ce se gani tayi Baby❤️💕🔐
na flashing akan screen d'in da hoton wani
kyakkyawan bawan Allah yana nan d'an
bak'i da shi attatched to it. Murmushi ta
sakar ta cigaba da rik'e Nihal har izuwa
lokacinda Nazeefar ta idar.
"Wa ya kira?" Ta soma da tambayanta.
"Baby" Amal ta amsa.
"Oh!" Ta furta tana sunkuyar da kai.
"Baza ki kira shi bane?"
"Ba matsala ko anjima zan kira shi."
"Wai kunya na kikeji ne? Kinga baza ki
shanya mun in law ba haka kawai, d'au
waya ki kira shi kice mishi sallah kike,
gashi" Mik'a mata wayan tayi sannan ta
cigaba da shayar da Nihal.
Kaman yadda Amal ta bui'aceta tayi ta kira
sa back inda ya d'aga a first ring.
"Halo Babe?"
"Belle how're you?"
"I'm fine Babe? Ya kake?"
"I also, just that I miss you." So take tace
she misses him too amma kunyan Amal
take ji "Ermm Babe kasan wani abu? I will
call you later okay? Se anjima" bata jira jin
me zece ba ta katse. "Iyyeee so tell me who
is the handsome looking dude?"
"Kai Amal kede kiyi focusing a abinda
kikeyi kafin kisa nono ya bi mun kan
takwarata."
"Baki amsani ba waye shi?"
"Wani ne."
"Your man?" Gira ta d'age mata as yes.
"Wow ina kuka had'u? A UK?" Nan ma
giran ta sake d'agewa.
"Awwn am so happy for you sister tell me
about him mana."
"Nak'i."
"Pleaseeeeee."
"Sa'anki d'aya saboda Nihal."
"Haha naji ina sauraronki."
"Sunan sa Ahmad A UK muka had'u naje
yin masters d'ina whereas shi kuma PHD.
He's a Nigerian, yana zama a abuja yana da
aure da yara biyu."
"Wow I'm really impressed in ba wai kin
fad'a ba mutum baze ta6a cewa yana da
aure ba."
"I know right ko ni da ya cemun yana da
aure ban yarda ba, ashe wai harda yara
biyu, ko da shike auren wuri yayi when he
was 22, he had his first son at 24 and his
second daughter at 27 he's now 34 years
old."
"Impressive Nazeefah I'm so happy for you
wallahi su Mummy sun sani?"
"Not yet ke na fara sanarda ina son se ya
gama karatunsa ya dawo se in yi
introducing nashi to the family."
"Hakan yayi Nazeefah wallahi nayi miki
murna sosai ya uwar gidan ta shi? Ya
had'aku ko tukuna?"
"Ya had'amu, ai be jima bama suka je
mishi hutu suka komo bari kiga pictures da
muka d'auka da ya fita damu outing ranan"
tayi maganan tana latsa wayanta "Here you
go" amsa Amal tayi ta shiga viewing tana
swiping "Goodness he's got such a beautiful
family wallahi, da ke da uwar gidan ban
san waye gaba a kyau ba gaskiya gata
itama very young."
"Yes she's 28 years old amma kika ganta
wane tana early twenties nata."
"Bata da wata matsala ko?"
"Sam wallahi yadda kika san kanki haka
take tamkar 'yar uwarta haka ta d'aukeni."
"Such is life Allah ya baku zaman lafiya
mey d'aurewa ya sunan yaran nasa?"
"Fawwas da Fauzah."
"Masha Allah I'm sooo happy for you sis."
"Thank you Maman takwara."
****
Ba Nazeefah ce tabar gidan ba se bayan
sallan isha. Haka kusan kullum tana gidan
Amal, kafin suna kuwa ta samu ta had'a
akwati mey set uku wa Amal biyu na baby
d'aya nata. Amal ta samu kyautuka sosai
sede ace masha Allah. Seda Mami tayi mata
arba'in sannan ta koma gida.
Nihal na da watanni uku Amal ta soma
shiga school so anytime zata fita school se ta
biya gida ta kai wa su Nazeefah raino.
Atimes kuma wa Ummi. Da Khaleefah ya
dawo hutu kuwa se su had'u suyita fad'a
akan Nihal cewa sam d'aya baze ta6a ta ba.
Yarinya san kowa k'in wanda ya tasa, ga
fara'a ga murmushi, gata very plumpy,
gashin kan nan tabarkallah. Haka nan
rayuwa ta cigaba da kasance musu cikin
kwanciyan hankali da so da k'auna. Na
sosai Afzal yake ji da Nihal sau dayawa
yakan riga Amal dawowa gida daga office
da ya tashi seya biya gidansu Mummy ya
amshi 'yarsa su dawo gida ya mata wanka
yayi rainonta kafin Rania'nsa ta dawo.
Amal could not ask for more, this is indeed
a dream she's living. A perfect daughter, a
perfect husband and a perfect family.
_7 months later..._
Ababe da dama sun gudana, da izinin
Allah su Amal sukayi graduating bata da
spill ko d'aya, ta d'ayan fannin ma
Nazeefah har taje UK ita da Mummy anyi
musu graduation nasu sun dawo. Shima
saurayin nata Ahmad ya gama PHD nasa ya
dawo gida har Nazeefah tayi introducing
nasa wa su Daddy. Maganan da ake yanzu
haka sa rana kad'ai ya rage. Kafin nan time
to time yakan zuwa Maiduguri ya duba
Nazeefah sannan ya koma, ko wani
zuwansa kuwa da tsaraban da yake
tanadarwa Nihal na musamman takwaran
wife to be nasa. Na sosai yake son Nazeefah
dan haka yake son duk wani nata tuni ya
nemi Afzal suka k'ulla abotaka abinsu.
Kullum sede be shigo gari ba se sun sa
Sultan da ya kasa yin aure har yau a gaba.
Maganan da ake yanzu haka Ahmad ya
had'a Sultan da wata cousin tasa, abu
kaman wasa wai Sultan ke soyayya. Na
sosai yarinyar ta masa bayan ya kwana
biyu haka yakan je Abuja ya duba ta. Afzal
da Amal kuma sede abinda ya k'ari,
soyayya suke zubawa kaman ba gobe
sekace jiya-jiya aka d'aura musu aure even
though suna d'an ta6a fad'ansu time to time
amma hakan baisa sun daina son juna ba
da kuma daina son farinta wa juna ba.
Yau ranan ta kama Asabar ranar da aka fi
sani da ranar d'aurin aure.
Amal ce zaune akan dining table da Nihal
dake da 10 months yanzu a gefenta tana
feeding nata custards, tana sha tanayi mata
wasa. Ba ruwanta ta sha nono ta sha
madara ta ta6a custards gata nan k'atuwa
gwanin sha'awa. "That's girl" Amal tayi
praising nata tana k'ok'arin sake kai mata
wani spoon d'in baki "shanye se mu tafi
unguwa ko? Muje dinner'n Aunty Maamah
da na Ya Abdool, ai zaki je?"
"Dada" ta amsa wane taji abinda aka ce
mata.
"Na Ya Abdool kikeso? Toh ai duka zamu
je ko kin mance a venue d'aya za'ayi?"
"Dada!"
"Yauwa Princess d'ina shanye toh se mu
tafi" Wayanta dake ruri ne tayi saurin
d'agawa ganin Nazeefah ke kira tare da
sawa a hands free.
"Mamman Nihal"
"Na'am sis yane?"
"Ina kwana ya kike?"
"Lafiya k'alau ya gida ya Ya Ahmad?"
"Yana nan d'an wahala yaushe ne ya tafi
ba last week ba?"
"Amal na dariya ta amsa "eh wani abu
ne?"
"Wai ze sake zuwa he's missing me."
"Shine zaki ce mishi d'an wahala?"
"Toh mey ne? Sekace baya son kansa dan
Allah, shi bai tunanin stress ne ai nakega
cewa Fareeda (matar Ahmad) zan kar ta
barsa yayi wannan tafiya."
"Ji min 'ya! Ke baki san cewa garin masoyi
baya nisa bane? Ko a tunaninki idan baya
sonki zena zuwa ganinki akai akai haka
ne?"
"Toh ai ni tausayinsa nake I don't want
him stressed out."
"Ke bar shi ya d'an d'ana kafin ya kaiki
gidansa, kinga fa da zaran kin shiga
gidansa se yadda yayi dake."
"lol toh uwar mugunta."
"Eh mana enjoy your time while it lasts,
kafin ya d'aukeki ya tafi dake."
"Ya tafi da wa? Ce miki akai zan bishi
Abuja?"
"Yo eh mana" ta amsa tana dariya.
"Lallai wallahi anan zan zauna kinsan ni
bana k'aunan zaman Abuja, gara nayi
zama na anan kusa da takwara ta."
"Lol toh zamu gani de."
"Ina takwara ta?"
"Gata nan ina feeding nata, Nihal ga
Aunty Nazeefah kice mata hello."
"Titi titi" ta soma cewa tana wasa wai Titi
ne Aunty Nazeefah.
"My baby how are you?"
"She's fine tana having breakfast."
"Oh ayyah yanzu tailorn ya kawo mana
gowns namu fa."
"Haba yayi kyau?"
"Wallahi sosai barin ma na Nihal sekinga
yadda d'inkin ya fita."
"Yaushe zaki shigo toh?"
"Yanzu idan nayi wanka na karya."
"Alright toh sekin shigo ki gaishe da kowa
da kowa."
"Zasuji ba bye." Ta kai ga ajiye wayan
kawai taci karo da 6arnan da Nihal tayi,
goran ruwanta ta kwantar se tsiyaya yake
tana kalla tana jin dad'i.
"Haba! Haba Princess shikenan ke ba a isa
a baki abinci ba se kin miyar da wajen
k'azanta?"
"Rania?" Afzal dake fitowa daga d'akinsu
ya kirata, yana sanye da babban riga sky
blue da ya sha aiki ya kuma mugun amsan
sa ba shakka d'aurin auren Maamah da
kuma na Ya Abdool zasa tunda se an d'aura
na Ya Abdool za ayi na Maamah a different
venue.
"Yes Ya Omri?" Ta amsa tana mey d'ago
kai don kallonsa. "Dayyumm" ta furta a
ranta dan wani irin kyan da yayi. "Kinga
sabon cuff links da na siya last tafiyan da
nayin nan? I'm running late" sede kaman
ba da ita yake ba dan yadda hankalinta
yayi nesa da ita. Nihal dake gefenta se
faman kiransa take da "Dada" tana
k'ok'arin mik'ewa daga kan kujerarta taje
ta wajensa. Cike da tak'ama yake takawa
har ya k'arisa dining aean, har anan binsa
da kallo Amal take.
"Rania?" Ya kirata had'e da shafe gefen
fuskanta wanda hakan ya sanya ta
murmushi. "Ya Omri you look you look..."
tama rasa abinda za tace.
"Handsome?" Ya d'age mata gira.
"Yes you look handsome, masha Allah"
tsugunawa yayi had'e da pecking nata
"Thanks Babe."
"Dada Dada!" Nihal ta cigaba da kiransa.
"My Princesss" ya mik'a hannu ze d'agata
"tukunah bari in d'auraye mata jiki kar ta
6ata maka kaya" murmushi ya sakar mata
sannan ya ja kujera ya zauna daga
gefeyana yiwa Nihal wasa har zuwa
lokacinda Amal ta goge mata jiki ya d'agata.
"So Kinga cuff links d'ina?"
"Wanda ka taho dasu last tafiyan ka?"
"Yep" ya amsa yana yiwa Nihal dake ta
faman dariya wasa.
"Muje yana cikin wardrobe naka."
"Na duba ban gani ba."
"Kai dama ka iya duba abu ne? Yana nan
a ciki muje."
"Ni d'in ko? Muje zakig" d'akin suka nufa,
Amal tayi gaba ta shiga neman pack d'min
bada dad'ewa ba se gashi ta fito da shi.
"Now tell me what is this?" Ta juyo had'e
da tambayeshi. Shiru yayi na d'an lokaci "A
ina kika samu? Bade a ciki ba."
"Da a ina? Here of course" tayi nuni da
cikin wardrobe d'in
"But I j-"
"Shhh literally Nihal is the only infant
baby here but technically there are two
babies tunda ko neman abu in ban sa
hannu ba baka iya samu, here kar6i inje
inyi wa Nihal wanka muma mu shirya."
Hannunta ya rik'e kafin ta fahimci abinda
yake shirin yi ya janyeta seda ta fad'a
jikinsa.
"Thank you for handling my crazy ass
Babe I love you very much" ya sanar da ita
looking deep into her eyes. It's been almost
5 years but anytime Afzal ya sanar da ita
cewa yana sonta se bugun zuciyanta ya
dad'u. There's no lying, she's immensely in
love with him.
"I love you much more my very own
handsome" ta mayar mishi, adjusting height
nasa yayi ready to kiss her, dai-dai lips nasa
yazo sauk'a akan nata Nihal ta tsinka mata
mari tas a kumatu
"Wayyo Allah Mami na!!" Amal ta sa ihu
Afzal be san sanda yasa dariya ba ganin
haka itama Nihal ta bi sa se dariya sukeyi
wa Amal.
"Nihal kika mareni? Kika mari Mamma?
Kai kuma Yaya maimakon ka mata fad'a se
ka tsaya kana dariya ko? Wallahi da zafi"
ta k'arashe tamkar zatayi kuka.
"Nihal tell Mamma sorry" itako se ta d'aga
hannu da niyyan k'arawa Amal wani
marin.
"Wallahi kika mareni ba ke ba shan nono
yau."
"A'a yi hak'uri beyi zafi haka ba Nihal and
Dada are sorry yi hak'uri kinji sweetheart."
"Ni kayi sauri kar ka makara Ya Abdool
yace nice ban shirya ka da wuri ba?"
"Ko da nayi latti ma ai zey mun uzuri ko?"
"Dalili?"
"Because I have such a gorgeous wife."
"Really?"
"Yes baby" da wayo ya sauk'e Nihal a kan
gado sannan ya zagaye hannayensa a 'yar
kunkuminta yana mey sunkuyar da ita ta
baya a hankali, "Now I really wanna kiss
y-" bata bari ya k'are maganan da yake ba
ta katsesa ta hanyan kissing lips nasa, a
sannu a sannu har suka kai jikin bango
suna manne da juna, chan Amal tayi
pulling out, "Yaya you really have to go n-"
shima nan be bata daman k'arisa abinda
tayi niyyan fad'i ba ya kuma crashing lips
nasa akan nata.
Warin da suka jiyo yana tashi ne ya dawo
dasu daga duniyan da suka fad'a. "Humm
Princess is that you?" Afzal ya kewayo yana
kallon Nihal data d'age d'uwawu a sama.
"Nihal sannu ko?" Fad'in Amal "Ya Omri
ka san mey za ayi yanzu? Bari in tayaka
cire babban rigan nan ka wanke wa
Princess taka pupu ko?"
"O my God Rania kiga it's almost getting to
10 ina hula na kar inyi latti."
"Now you're trying to run away huh?"
"Take care of yourself okay? I love you,
Nihal I love you too."
"Dada!!" Juyowa yayi ya sakar wa Amal
murmushi sannan ya nufi gaban mirror ya
sa cuff links nasa ya cakkwala hulan
Zannan nan ya kuma feffeshe jikinsa da
turare "See you around Babe." Murmushi
Amal ta tsaya yi wa kanta admiring how
gorgeous he is. "Be back safely, Allah kare
mun kai Yaya." Wajen Nihal ta nufa ta
d'agata sukayi bayi inda ta wanke ta da
kyau sannan tayi mata wanka daga nan
itama tayi nata. Tana cikin shafawa Nihal
oil a gashi Nazeefah ta shigo nan Nihal
tafara kiranta da "Titi Titi!" Nan da nan
Nazeefah ta amshi Nihal ta gama shiryata
itama Amal ta samu ta shiga shiri. Ana cikin
haka Maamah ta shiga kiranta a waya.
"Maamah zata kasheni gashi har pass 11
bamu tafi ba" ta furta tare da answering
call d'in.
"Haba Amal it's pass eleven already."
"Amarya a gidan Mansoor yi hak'uri
wallahi ankon dinner'n mu ne basu iso da
wuri ba kinga yanzu da mun tafi se kuma
bayan dinner mu dawo yi hak'uri we're on
our way."
"Toh se kunzo send my love to princess."
"I will bye se mun shigo." Nan da nan suka
gama shiri suka fita "Mamman Nihal
wallahi kinyi kyau tsaya in d'aukeku da
princess."
"Sis bakiga munyi latti bane kam?"
"Pleaseee mana Mamman Nihal bakiya
son in tura wa Ya Afzal ne? Mu d'an birkita
masa lisafi a gun d'aurin aure?" ta k'are
tana mata signal da gira.
"Alright pose d'aya kawai fa amma."
"Eh eh naji" nan ta ciro wayanta yayinda
Amal ta tsaya gyara pose nata dana Nihal
nan Nazeefah ta shiga d'aukansu bata tsaya
ba seda ta d'auki a k'alla ishirin "Yauwaaa
sauran selfie yanzu" da sauri tayi joining
nasu ta musu selfies. "Bari in nemi wanda
yayi kyau in tura wa Ya Afzal" tayi
maganan suna masu takawa gun mota inda
driver ke jiran su. Suna shiga driver yaja
mota.
"Yauwa kinga Ya Afzal yana ma online,
tsaya kiga yana bud'ewa ze kiraki." Cewan
Nazeefah se kuwa tana mishi sending pics
d'in yana bud'ewa in the next like one
minute wayan Amal ya shiga ruri tana
dubawa taga Afzal.
"Mena fad'a miki?" Nazeefah ta tambaya
tana dariya itama Amal d'in dariya take
sannan tayi swiping ta d'aga.
"Rania tell me I'm not dreaming how can
you be soooo beautiful?? Masha Allah I
have the most beeeyouteefull wife and
daughter" se blushing kawai Amal take ko
amsa sa ta kasa yi dan dad'i.
ALHAMDULILLAH Anan na kawo
k'arshen wannan littafi nawa mey taken
RANA D'AYA. Allah ya sa mu amfana da
darusan da suke ciki inda nayi kuskure
kuma Allah ya yafe mana gabad'aya.
Ameen.
Download Rana Daya Littafi Na Ɗaya Complete Hausa Novels
0 Comments
Thank you for this comment