Compiled By Umar Dalha Funtua.
Coping By Aishat A Muha'd.

 Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
*​DIREBAN GIDANMU​*
       🍁🍁🍁


_​by​_
*_​​SaNaz deeyah​​👄_*

BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

_Godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki mai kowa mai komai daya bani ikon sake rubuta littafi a karo na 12,tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad(S.A.W)._

_Wagga labari dana zo maku dashi k'irk'irarren labari ne(fiction)ban rubuta shi dan cin zarafin wani ko wata ba,na rubutashi ne kawai dan na nishad'antar da duk wani masoyina_


_Littafin nan na sadaukar dashi gaba d'aya gareku._
_*MRS XERKS & SAFNAH LUV*_
_kunfi k'arfin komai a gurina kunyi a rayuwa,ko sadaukarwar da nayi maku na novel d'ina bai isa ace ya biyaku abinda kuka min a rayuwa ba,ya Allah ya had'a fuskokinmu da alkhairi kafin mubar duniya,Allah yasa ina da rabon ganinku a rayuwata_.

_SAFNAH kin b'uya tunda kika haifa mana baby muka daina jinki Allah ubangiji yasa dai lafiya🙏_




01

Yau ma kamar kullum suna zaune su biyar suna karyawa a dining area...

Janan ce ta kalli Abba tace "Abba ni kam dama ka barmu muna driving da kanmu wallahi zamu iya"

Kallonta yayi fuskarshi d'auke da murmushi yace "kiyi hak'uri Janan nafi son driver yana kaiku daga baya idan karatunku yayi nisa zan iya baku mota,ita fauziyya ma da take l2 bata yi magana ba sai ke da kike yin diploma"

"Amma Abba....."

"Kimin shiru Janan,na gama yanke hukunci driver na jiranku a waje Idan kun gama "
Tashi yayi ya haye upstairs ya barsu.

Ran Janan a b'ace ta kalli Mameey tace "dan Allah mameey ki saka baki a maganar nan Abba ya fahimce mu,we ar matured enough ba sai ana had'a mu da driver ba"

"Dalla rufa mana baki malama,ta ina kika zama matured?   a hakan?"

"Haba Yaya fahad nayi tunanin ma zaka lallab'a Abba"

"Baza'a lallab'a shi ba,sai k'arya kawai,kinfi son kina Murza kan mota kina nuna ke 'yar wani ce?to baki isa ba,Dan ma Abba baice zai had'a ki da security ba"

Wani d'an guntun hawaye ta goge tare da fad'in "shikenan"
Tashi tayi kawai ta fice.

Mameey ta bita da ido tare da fad'in "Allah rage miki wannan zafin ran Janan"
"Zan gyara tane ki barni da ita mameey" Fahad ya fad'a rai a b'ace

Fauziyya kam babu abinda ta iya cewa dan ranta ya b'aci sosai.

           ******

"Janan fito mu tafi"
Fauziyya tayi maganar tana tsaye daga bakin k'ofa.

Janan dake tsaye jikin mirrow ta gyara d'orin d'an kwalinta ta d'au jaka"

A farfajiyar gidan ta tsaya tana kallon securities d'in,can ta  hango direban tsaye jikin mota"

"Mts Ali direba ba,wallahi baka isa ba"

"Janan muyi hak'uri kawai"

"Aunty wallahi bana son naji kunya na muzanta a cikin friends"

"To ya ya muka iya?"

"Zanyi maganinsa"
Kawai tayi gaba.

Suna isa ya bud'e musu k'ofa,tsaki tayi tare da cewa "aikin banza kawai"

Ya San dashi take amma kawai ya shareta.

Sun fara tafiya a cikin mota kawai ta daka masa tsawa "dakata Malam"
Yayi saurin yin parking.

"Bani key"

Juyowa yayi ya kalleta cike da mamaki dan hatta Fauziyya sai da tayi mamakin maganar.

"Ka bani mana ka tsaya kana kallona kamar maye,wama ya sani ko mayen ne"

Mik'a mata yayi sannan ya bud'e motar ya fita,itama fitowar tayi tana masa kallon wulak'anci,"mtsw matsiyaci kawai"

Shiga tayi ta tada motar tare da watsa masa 'ura"

"Janan kar Abba yayi fad'a"
"Karki damu Yaya fauzah na d'auki duk fad'an da dai in wulak'anta"
"To Allah ya kyauta"
"Ameen"

Sai da ta fara dire fauziyya a skul sannan ta wuce tasu.

           ********

Yana tsaye jikin mainar gidansu idonshi gaba d'aya sun kad'a sunyi jajir,duk kanin jijiyar dake fuskarshi ta fito ta bayyana,ranshi gaba d'aya a b'ace yake.

Ummi ta goge hawayen idonta tace "Yaya idan babu dama kawai a hak'ura dan bana son rasa ka kamar yadda na rasa Aunty hafsa da baba"

Umma ta kalleta ta daka mata tsawa "ki rufa min baki Ummi,me kike nufi?mu barsu suci bulus,wallahi bazai tab'a yuwuwa ba dole Aliyu ya k'watar mana 'yancinmu,yanzu gashi nan karatunki ya tsaya tun daga aji hudu na sakandire bazai yuwu ba"

"yaya..."

"Yi shiru Ummi" ya katseta sannan ya cigaba da fad'in "zanyi iya bakin k'ok'arina dan ganin na karb'o mana 'yancinmu"

Kai ya saka ya fice daga gidan ranshi a b'ace.

       ************

Gidansu Zuhra ya wuce dan yasan nan ne kad'ai idan yaje hankalinsa zai kwanta dan ko babu komai Zuhra ta San darajar d'an Adam tana da girmama mutane.

_Zuhra fara ce kyakkyawa,tana da diri sosai doguwa ce amma ba can ba,tana da tarbiyya sannan akwaita da ilmin addini kuma mahaddaciyar qur'ani ce sai dai batayi karatun boko ba iya karta firamare skul_...

Aliyu na isa k'ofar gidan yasa aka kirawota.

Bata wani jima ba ta fito fuskarta d'auke da murmushi,ganin yanayinsa ne yasa itama ta daina murmushin ta k'araso inda yake
"Waya tab'a min angona?"

Kallonta kawai yake ba tare da wani sauyi ba.

"Pls ka fad'a min damuwarka"
"Kece damuwa ta"
Ya bata amsa tare da zama a dutsen da suka saba hira akai.

Zama tayi kusa dashi tare da fad'in "dan Allah ka fad'a min damuwarka wlh hankalina ya tashi"

"Zuhra na tsani Janan wlh bana ko k'aunar ganinta dama ba sonsu nake ba amma ta k'ara sa min tsanarta ji nake kamar na kasheta ita da mahaifinta da duk wani masoyinsu"

"Me?kisa fa angona"
Ta fad'a a razane tare da kallonsa,shima kallonta yake yana k'ara jin zafin a ransa.

"Wacece Janan?"

Tambayar da tayi masa ne ya sashi dawowa hayyacinsa dan bai ma San yayi wannan furucin ba.

Rasa amsar da zai bata yayi gashi ta kafa masa idanu tana jiran amsa.

"Kayi shiru"

"Wata yarinya ce tana neman raina min hankali,wai har yanzu su baffa basu gama yanke lokacin bikinmu ba?na gaji da ganinki a titi"

Cike da jin kunya tace "da amfanin gona ya fito za'ayi bikinmu kasan bikin 'yar fari sai da Babban shiri"

Murmushi yayi sannan yace "Allah ya kaimu lokacin"
"Ameen Angona"

Haka suka zauna suna ta hira tare da tsara rayuwarsu.

           ********

Tun da maigadi ya bud'e gate ta hango Abba da Ali a tsaye.

Gabanta ya fad'i ta kalli Fauziyya tace "Aunty Fauzah wancan munafukin ya kai k'ararmu wajen Abba"

"Hmm ni kam ba ruwana wlh ke kika karb'i key dama sai da nace karki karb'a "

"Karki wani damua na d'au laifin"

Suna yin parking ta suka fito dukkansu fuskarsu d'auke da rashin gaskiya.

Suna isa Janan tace "sannu da gida Abba"

Mari ya d'auketa dashi sannan yace "bani key"
 a tsawace

Mik'a masa key d'in tayi hannunta rik'e da kuncinta.

"Abba pls kayi hak'uri"

"Rufa min baki kema"
Ya sake kallon Janan yace "na soke miki driving ko kina so ko baki so Aliyu ne zai rik'a kaiki ko ina kuma ita Fauziyya zan bata mota ke kuma ke kad'ai zai rik'a kaiwa tunda baki da kunya,ke daga yau na mayar da Ali DIREBAN GIDANnan"

Kallonshi kawai take fuskarta d'auke da k'walla.

"Ku bar min gurin nan"

Da sauri fauziyya taja hannun janan suka shiga ciki.




_Alk'alamin Sadeey_✍
[9/29, 8:13 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁


_by_
*_SaNaz deeyah_*👄

```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


02

Suna shiga falo ta zube ta fara dirzar kuka.

Da sauri mameey ta taso ta rik'eta tana tambayar abinda ya faru.

Fauziyya ce tayi mata bayanin komai.

Janyo Janan tayi tana rarrashi tare da fad'in "ki daina musawa babanki Janan kin san shi baya da wasa kuma kaifi d'aya ne"

Ta d'ago idonta da suka gama rinewa tace "akan direba Abba zai mareni,ya zubar min mutumci a gabanshi"

"Ya isa haka kiyi hak'uri"

Ranar haka ta yini a bedrum d'inta tana kuka,ko abinci sai da aka tilasta mata sannan ta fito taci.

Bayan sallar isha'i Abba ya sa aka kirawota,nasiha yayi mata sosai akan babu kyau wulak'anta d'an Adam sannan kuma ya rarrasheta har zuciyarta tayi sanyi,fahad kuwa gaba d'aya lamarinta haushi yake bashi.



            ******

Haka ta hak'ura Ali ya cigaba da kaita makaranta amma kullum cikin zaginshi take tana nuna masa tsana k'arara.

A satin kuma aka sayowa Fauzah motarta sabuwa k'yal k'irar 'prado'.

Yau ma kamar kullum tana zaune a bayan mota tana latsa waya shi kuma yana driving a nutse.

'Dago kai tayi ta kalleshi tare da jan dogon tsaki "dalla malam kayi da jiki sai jan mota kake a k'asaice kamar ta tsohonka,Malam kar kasa na makara fa"

Da sauri yaja burki ya tsaya yana kallonta.
"Kallo na kake? To ko motar babanka ce kaifa direbana ne wall............"
Wuyanta ya shak'o Wanda ya hana ta k'arasa maganar.

"Karki k'ara ambatar mahaifina ki zaga" sakin wuyan yayi ta zaro idonta a tsorace cike da mamaki tace "ni ka shak'e?to wallahi a bakin aikinka"

"Zan miki abinda yafi shak'ewa idan har kika cigaba da zagin babana"

"Ni kam yau sai ka bar aiki a gidanmu tunda har kasan shak'a to tabbas zaka iya kisa"

"Na yarda zan bar aikin koda kuwa baki saka an koreni ba ni zan bar gidanku da kaina" ya fad'a yana goge hawaye.

Abin ya mutuk'ar bata mamaki ganin yana zubda hawaye _gaskiya yana son shi da yawa_ ta fad'a a zuciyarta.

Har suka je skul ba wanda ya sake yima wani magana tana son ta bashi hak'uri amma tana ganin kamar zai rainata ne.

Tana fitowa daga motar su Raihan suka k'araso,Lubna tayi saurin k'arasa jikin motar tace "sannu Aliyu ina yini"
"Lafiya lau ya karatu?" Ya amsa cikin sakin fuska.

"Karatu Alhamdulillah ya mantawa dani"

Da sauri Janan ta juya suka had'a ido tayi saurin janye k'wayar idonta daga kanshi.

"Ban manta dake ba saboda kina da matuk'ar mahimmanci a gurina"

"Nagode da wannan matsayi da ka bani"
"Nine da godiya"
"A'a ni dai Dana samu kyakykyawa handsome yayi appreciating d'ina"

"Lubna idan kin gama surutun ki samemu a hall"
Janan ta fad'a ranta a b'ace dan tana jin haushin yadda lubna ke kuranta Ali har tana fad'ar yana da kyau a gabanshi salon ya raina masu aji.

"Karku damu zan taho"
Lubna tayi maganar.

Ali kam sakin jiki yayi yana hira da lubna dan ya San Janan tana jin haushin hakan.


Suna zaune bayan Janan ta gama yiwa Raihan narrating duk abinda ya faru.

Murmushi Raihan tayi sannan tace "yana da kyau ki bashi hak'uri saboda kema bazaki so a zagi naki ba,ban San yaushe kika koyi wulak'anci ba Janan da ba haka kike ba"

"Wallahi yanzun ma ba haka nake ba,kawai dai na tsaneshi  saboda yayi min sanadin hanani driving"

"Ba dad'i amma kiyi hak'uri kuma ki bashi hak'uri tunda har kikaga yayi kuka tabbas baiji dad'i ba"

"Amma kuma bana son ya rainani"
"Bazai rainaki ba durk'usawa wada ba gajiyawa bane Janan"
"Shikenan nagode da shawararki insha Allah dayazo d'aukana zan bashi hak'uri"



Tun k'arfe biyu take tsaye tana jiranshi shiru babu alamun shi.

Waya ta d'aga zata kira kawai taji kiran Fahad ya shigo.
Da sauri ta d'aga tana fad'in "wai ina sakaran direban nan bayan nace masa k'arfe d'aya zan gama lecture gashi har biyu ta wuce"

Daga d'ayan b'angaren Fahad yace "marainin wayon naki bayanan saiki fad'an Inda kike zanzo na d'auke ki"

Gabanta yayi mummunan fad'uwa _ba dai da gaske ya ajje driving d'in ba_
"Kin min shiru ko bakiji ne"
 "Ina k'ofar library" ta fad'a a sanyaye.

"Ya dai lafiya?"
Lubna ta fad'an tana kallonta.

"Wai bayanan Yaya Fahad ne zaizo d'aukana"

"Oh my god,shikenan yau bazan ganshi ba,naso na sake ganin kyakykyawar fuskarshi gaskiya ban tab'a ganin kyakykyawan namiji kamar Aliyu ba,ina son shi matuk'a"

"What?so fa?"
"Eh"
"Wane so bayan akwai engaged a kanki da Besty ko kin manta?" Janan ta fad'a cikin b'acin rai

"Na sani"
"Kin daina son Bestyn?"
"Kamar ya bayan har an mana baiko"
"To su biyu zaki aura ne?"
"Ya kike min tambaya kamar 'yar jarida?"
"Dole na miki saboda kin bani mamaki wallahi"

Dariya tayi tace "kin San dai bazan tab'a auren direba ba barema direbanki,kawai ina son soyayya dashi ne saboda in fita kunyar friends dama ace yana da kud'i zan iya barin muktar na aureshi amma in rasa wazan aura sai direba"

"Amma kuma zakiyi soyayya dashi"

"Eh direba baya da wani value ai"

Cike da mamaki Janan ke kallonta dan batayi tunanin haka daga bakin lubna ba.

"Baya da value fa kika ce?shi ba mutum bane ko ba Allah ne ya hallicce shi ba?"

"Shi mutum ne amma talaka baya da daraja a waj............"

"Dakata lubna" Janan tayi saurin katseta.

"Na tsani a wulak'anta d'an Adam"

"Ai ba wulak'anta shi nayi ba,ina son shi amma bada aure ba"

"Kina son yaudarar zuciyarshi,lubna karki cutar da d'an Adam baki San lokacin da zai miki rana ba"

"Amma kuma ke kike wulak'anta shi?"

"Laifi yayi min amma ni ban tsaneshi ba kuma banji dad'in abinda kikai ba"

"Oho dai nikam sai anjima" da sauri ta bar gurin.

Tana tsaye tana tunani har Yaya fahad ya k'araso,da sauri taje ta bud'e gaban mota ta shiga dan ta San halinsa da fad'a.

Suna cikin tafiya ta kasa daurewa tace "Yaya kamar ma daga office kake?"
"Eh"
"Ina drivern yake"
"Oho ni dai kawai mameey tace in biyo in taho dake"

Bata ji dad'i ba dan har ta fara zargin kanta amma ba damar ta fad'a ma fahad.

Har suka isa gida yana ta surutu amma amsar da take bashi bata wuce um ko um um.

Suna zuwa gida ta shige bedrum ba tare da tayima kowa magana ba.

Tana kwance kan gado kusan minti talatin tana tunanin Ali meyasa ma tayi masa haka.

Tashi tayi zaune ta d'an ja tsoki tare da fad'in _akan me zan damu kaina?idan ya rasa aikin shi yayiwa Kansa_

Cire kayanta tayi ta shiga toilet ta watsa ruwa sannan ta shirya ta fito falo..

"Mameey Aunty Fauzah bata dawo ba?"

"Eh sai six"
"Okay bara naje gun Abba muyi hira"
Bata jira amsar mameey ba ta wuce side d'in daddy.

Sati guda babu Ali ba labarinsa dan kullum Fahad ko Fauzah ne ke kaita skul tana son tambayar ko lafiya amma ta kasa tunda babu Wanda yayi mata zancensa ko Fauzah da take tunanin zata fad'a mata wani abu game da rashin zuwansa.

Yau kam bayan sun fito daga lecture ta kalli Raihan tace "yau sati guda Ali baya zuwa tun ranar Dana fad'a miki na zageshi"

"To ke meya dameki?"

"Dole in damu Raihan,wallahi kusan kullum da abin nake kwana a raina"

"Son shi har yayi girma haka a zuciyarki"


Da sauri suka juya dan ganin mai maganar.






_Alk'alamin Sadeey_✍
[9/29, 8:13 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁


_by_
_*SaNaz deeyah*_👄


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


03

Lubna ce ta k'araso  fuskarta d'auke da murmushi tace "ai na dad'e da sanin cewa direbanki kike so hakan ne yasa kika daina min magana na tsawon sati tun lokacin da kikaji nace zanyi soyayya dashi,Besty ma yace zaizo yaji dalilin dayasa kika daina kulani"

Ran Janan ya b'aci sosai da har baza tayi mata magana ba amma jin zafin abin yasa tace "ke kika ja na daina miki magana domin talaka da mai kud'i matsayinsu d'aya a gurin Allah,Wanda yafi wani shine wanda yafi tsoron Allah"

"Hmmm to ai saiki aureshi tunda kina tausayinsa"

Duk kansu suka mik'e tsaye..
"Zan iya aurenshi tunda ba haramun bane"

"Kin ga sai a buga a jarida da gidan radio cewar ga wata ta auri direbanta"

'Daga hannu tayi zata mareta,Raihan tayi saurin rik'e hannunta.

"Ki sakeni in nuna mata kuskaranta meyasa zaki hanani Raihan?"
Tayi maganar tana zubda hawaye.

Nan da nan jama'a suka taru.

Lubna kuwa tayi ta fad'a tana cewa a barta taga me zatayi mata,dan Asara ta rasa wa zatayi soyayya dashi sai drivernta.

Kuka sosai Janan take yi,Raihan tayi saurin janyeta suka shiga cikin lecture hall d'in.

Tunda ta shiga kanta yake a k'asa tana kuka,su Khalid 'yan dprtmt d'insu suka zo suna tambaya amma Raihan tace su k'yaleta kawai dan kar abin ya sake damunta.

"Gaskiya lubna bata kyauta ba ai babu dad'i dizgi"
Zakiyya tayi maganar lokacin data dafa Janan.

"Ki k'yalesu kawai na San dole zasu shirya sun samu tsab'ani ne kawai"

Janan ta d'ago kai ta kallesu,fuskarta sharkaf da hawaye tace "a cikin taron jama'a tayi min haka,to zan aure shi zanyi soyayya dashi inga abinda wani zaice ko kuma naga abinda zatayi sai ta kaini gidan radio da hujja" hawaye ta goge ta d'auki jakarta ta fita.

Raihan na mata magana ta shareta kawai.

Napep ta tara abinda bata tab'ayi ba,kwatance tayi masa ya kai ta har k'ofar gida.

Tayi knocking maigadi ya bud'e ganin itace yasa shi saurin matsawa.

Tana shiga taga Ali zaune a kan bencin maigadi.

Ta d'an kalleshi fuskarta d'auke da hawaye,shima idonsa a kanta yake,kamar zata masa magana sai kuma kawai ta wuce ciki.

"Uhmm yarinyar nan akwai rigama"

"Da wulak'anci ba",Ali ya fad'a yana kallon inda ta wuce

" ai bata da wulak'anci akan yayarta"

"Allah ya shirya"
"Amin"
Maigadi ya amsa.

Tana shiga bata Tatar da kowa a falo ba,dan haka tayi saurin wucewa bedrum d'inta.

Wani sabon kukan tayi mai isarta sannan ta shiga toilet ta watsa ruwa..

Tana fitowa taje bakin mirror ta tsaya tana murza mai a jikinta ta kalli madubi taga yadda fuskarta ta d'an kumbura.
Mai ta murza a jikinta ta fesa turare sannan ta zura doguwar riga nylon ta fita.

'Dakin mameey ta wuce,tarar da ita tayi a kwance hannunta d'auke da waya da alama ta gama amsa kira ne.

Zama tayi kusa da mameey tayi shiru na tsawon lokaci sannan tace "mameey bakiga na dawo ba?"

Tashi tayi zaune ta kalleta tace "mamaki kika bani ai"

Murmushin k'arfin hali tayi sannan tace "mameey ina son in fara sanin yadda talakawa keji,saboda ban San inda rana zata fad'i ba"

"Amma kin San wannan ganganci ne ko?kin san halin babanki sai yayi fad'a"

"No mameey pls karki fad'a masa kinsan zaiyi fad'a"

"Oh kinsan da hakan amma kika dawo ba ki kira an d'aukeki ba?"

"Am srry Baran kuma ba"

"Ki kiyaye"

"Insha Allah mameey"
"Yawwa"
"Mameey ina Aunty Fauzah?"
"Tana skul"
"Okay Yaya yana office ba?"
"Kema ai kin Sani"

Hira suka cigaba dayi cikin raha da annashuwa.

Ranar dai haka ta yini duk abinda take sai ta tuno Ali direba har ta fara zargin kanta akan maganar lubna.

        *********

Tana jingine da fuskar gadon hira suke k'asa-k'asa.

Fauzah dai duk ta rasa mafita gaba d'aya gani take kamar abinda take shirin yi ba mai d'orewa bane.

"Gaskiya ina tsoron abinda nake shirin yi Zuby"

"Ban gane tsoro ba"
"Saboda duk abinda nake yi ina yinsa ne a b'oye wallahi duk ranar da aka gane na shiga uku,musamman Janan da ta samin ido zata Iya b'aro jirgina"

"Hmmm Fauzah kenan,Janan kike tsoro k'aramin alhaki,kefa macece karki bani kunya mana"

"Amma zuby karki manta *direban gidanmu* ne fa"


"Sai me a ciki,naga shima d'in d'an hannune da kinje masa da buk'atarki zai biya miki"

"Ta ina zan fara"
"Ki fara kamar irin kina son shi sai daga baya kina saka kayan da zasu ja hankalinsa kin gane ai"

Murmushin k'asaita tayi sannan tace "zan k'ok'arta"

      **********

Yau da wuri ta shirya dan bata so tayi latti.

A gurguje ta kammala break fast sannan ta samu mameey a d'aki tayi mata sallama.

"Kin fad'ama driver?"
"Eh tun jiya na ce masa ina da lecture k'arfe 8"
"To Allah ya tsare"
"Ameen mameey"

Da saurinta ta fita dan gani take kamar zai gudu.

Tana isa taga ya bud'e mata back seat duk sai taji ba dad'i duk da dama haka yake mata ko yaushe..

Sun fara tafiya tana son tayi magana amma zuciyarta na bugawa haka tayi shiru ta kafa masa ido yana driving abinshi.

Suna shiga gate a dai-dai central mosque tace ya tsaya

Parking yayi kamar yadda ta umarceshi,ta d'auki jakarta har ta fito sannan ta juyo tace "kayi hak'uri da duk abubuwan da nayi maka insha Allah bazan sake ba,zan kiraka idan mun gama lectures"

"Masoya yau kuma anan aka keb'e"

Da sauri suka juya suka kalli ko wacece dama ita Janan ta san itace.





_Alk'alamin Sadeey_
[9/29, 8:13 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


04

"Meye abin b'oye shi ai idan kana son abu kana nuna shi ga kowa ne"

Ran janan a b'ace tace "lubna meyasa kike min irin wannan?"

Murmushi tayi sannan tace "oh sorry na zo zan takura miki ko?ina ji ina gani kina neman yi min k'wacen Aliyu ai ba k'arya nayi ba kina sonshi"

A hargitse ta shak'o wuyanta tace "ina son shi sai me?"

"Sakarmin wuya ko in tara miki jama'a"

Ganin duk mutane sun tsaya suna kallonsu ya sa ta sake ta tare da fad'in "ba haramun bane soyayya dashi?to zanyi soyayya dashi kuma zan aure shi"

Tsaki taja tayi saurin wucewa ta bar gurin saboda kar tayi kuka gashi mutane sun fara ihu da hayaniya.

Saida ta tsaya a gurin da babu mutane sosai sannan tasha kukanta ta k'oshi sannan ta goge hawayenta ta nufi department d'insu.

Ranar bata yiwa kowa magana ba har suka kammala lectures, Raihan tayi-tayi ta fad'a mata abinda ke damunta amma tak'i fad'a,itama lubna bata yi mata magana ba bare su kaure da fad'a.

Babu wanda tayi wa magana a cikinsu haka ta kama hanya ta tafi.
A bakin main gate ta tsaya ta kirashi bai dad'e ba sai gashi yazo.

Kamar yadda ya saba haka ya fito da da sauri ya bud'e mata k'ofar baya.

Kallonshi kawai tayi  ta matsa ta bud'e murfin seat d'in gaba ta shiga ta zauna.

Yafi minti 1 a tsaye bai shigo ba ita kuma tayi banza ta k'yaleshi dan tasan mamaki yake.

Sai daya gama tsayuwarsa sannan ya shigo ya zauna.

"Dan Allah kiyi hak'uri ki koma baya"

Kallon tsiwa tayi masa tace "daga yanzu nan zan rik'a zama"

Hannunsa ya d'ora kan sitiyari ya saki ajiyar zuciya yace "nan ba hurumin ki bane,baki dace da nan ba,karki manta ni direbanki............."

"Shhhhhh" tayi saurin katse shi,tare da yin wannin sassanyan murmushi "Kai ba direba na bane,saboda ina son duniya ta sani ina sonka kuma zan aureka,kaga sai aji dad'in kaini gidan radio ace na auri direba na,ina son dan Allah ka amince dani bazan tab'a cutarka ba"

Cire key d'in motar yayi tare da mik'a mata.
"Me kake nufi da hakan?"
"Ina nufin ki karb'a ki ja motar zan wuce gida dan naga abinda kike buk'ata kenan"

"Kamar ya?Aliyu karka bani kunya pls"

"Dakata Janan,kada ki maida ni k'aramin yaro kada kiga dan ina direbanki ki nemi wulak'antani,dan Allah ki fita ki koma baya,bazan iya soyayya dake ba dan bakya tsarin matan da nake so"

Bata san lokacin da hawaye ya fara zuba a idonta ba.

"Aliyu tunda nake a rayuwata ban tab'a cewa ina son wani d'a namiji ba,hasalima idan akace ana sona bana amincewa so d'aya na tab'a soyayya kuma ta wahalar dani banyi tunanin zan sake ba amma hakan har ya zama laifi kana kallon tsabar idona kana wulak'anta ni"

"Ko zaki sake bada Aliyu ba,bana sonki kuma bazanyi soyayya dake ba ki daina ma wannan maganar ina ke ina direba,kin manta irin maganganun da kike fad'a a kaina ne"

"Wallahi baka isa ba ko kana so ko baka so dole kayi soyayya dani,gwanda ma kaso"

Da sauri ta bud'e murfin motar ta fita ta koma seat d'in baya ta kwanta tana  hawaye.

Shima baice komai ba,haka yaja motar cike da mamakinta ganin abin yake tamkar a mafarki.

Yana yin parking tayi saurin d'aukar jakarta ta fita.
Ya bita da kallo,cije leb'e yayi yana murmushi yace "kin d'ebo ruwan dazai k'ona ki".


Janan kuwa tana zuwa falo taci karo da mameey,k'arasawa tayi kan kujerar ta zauna ta rufe fuskarta da mayafi tana shashshek'ar kuka.

" Waya tab'oki ko keda Raihan d'in ne?"

Kai ta girgiza alamar a'a.

"To mene?kin shigo kina kuka ai sai ki saka in tsorata nayi tunanin ko wani abu ne ya faru"

Cigaba tayi da kukan kamar ana tunzura ta.
Mameey tayi banza ta k'yaleta saboda ta mata yin duniya tak'i fad'ar abinda ke damunta,daga k'arshe ma tashi tayi ta bar mata falon.


A b'angaren Ali kuma yana yin parking ya bawa maigadin key ya tafi.
Har ya isa gidansu yana tunanin abubuwan da suka fito daga bakin Janan yana jin maganar tamkar ba gaskiya ba.

A tsakar gida ya tarar da Ummi na wanki umma kuma tana gaban murhu tana fifita wuta.

"Yaya barka da zuwa"
"Yawwa Ummi sannu da aiki"
Gurin umma ya k'arasa ya durk'usa ya gaida ta ta amsa cike da fara'a.

Shiru yayi baice komai ba har saida tace "lafiya Aliyu?"
Kai ya sosa yayi murmushi sannan yace "babu komai umma"

"Karka b'oye min komai Aliyu ka fad'an gaskiya"

Labarin duk abinda ya faru tsakaninsa da Janan ya fad'a mata.

"Alhamdulillah ya Allah nagode maka daka karb'i addu'ata na dad'e ina jiran wannan rana"
Ta fad'a tana goge hawaye.

Ummi dake wanki ta k'araso gurin tace "Yaya yanzu ya za'ayi"
"Sai abinda umma tace"

'Dago kai tayi idonta yayi jajir tace "ka amince mata,ka cusa mata kanka yadda babu wani mahaluk'i da zai iya rabaku daga zarar ka aureta a sannan ne zamu fara d'aukar fansa,karkayi wasa Aliyu inaso ace cikin wata uku anyi bikinku"

Sai dayaji gabanshi ya fad'i dan duk duniya yafi tsanar Janan da babanta fiye da danginta kuma yanzu ace wai yayi soyayya da ita har da aure.
"Ko bazaka iya bin umarni na bane?"
Umma ta katseshi.
"A'a ina tunanin yadda Zuhra da iyayenta zasu kalleni"

"Karka damu zuhra itace matarka ta dindindin in har ina raye,ita waccan ai da mun karb'i hak'k'inmu zamu kad'ata"

A haka dai ta tsara masa komai duk wani abinda ya dace yayi.

          ***********

Tana kwance tana chatting Fauzah ta shigo.
Bata yi yunk'urin tashi ba bayan ta amsa mata sallama kawai ta cigaba da chatting d'inta.

"Ko na miki laifi ne naga baki fara'a nazo wajenki"

"Bakomai naga kema tunda aka baki mota kike shareni"

Murmushi tayi tare da fad'in  "wallahi ba haka bane kiyi hak'uri k'anwata"

Murmushi tayi tare da cewa "ya wuce"

"Zuwa nayi neman alfarma"

"Tame?"
Ta fad'a tare da ajje wayar.

"Drivern ki nake son ki aramin zai kaini gidan biki"

"To ke mezai hana kiyi driving da kanki?"

"Na gaji da driving sis"

"Wani na nema ke kina kin gaji"

"Ni dai ki aramin shi pls"

"Sai kace wani kaya kije kiyi masa magana mana"

"A'a nafi son ki masa magana da kanki saboda bani son ya raina ni"

"Nima haka"
Janan ta bata amsa.

"Aike drivern ki ne janan"

"Nifa na tsani guy d'in nan haushinsa nakeji wallahi dan saboda shi yau nak'i zuwa skul"

"Taimaka min ni dai pls"

Ranta bayaso haka ta tashi ta fita farfajiyar gidan.

A can kan bencin maigadi ta hangoshi shi kad'ai yana latsa wayarshi k'irar NOKIA X(RK) wadda tasha ado da kyaure(lol).

K'arasawa tayi bata ko yi sallama ba tace zaka kai Yaya Fauzah unguwa yanzu.

Tayi sauri ta juya zata tafi kawai taji yace "kinyi kyau"

Da sauri ta juyo dan ta tabbatar da ita d'in yake,tana juyowa suka had'a ido taga yana murmushi.

"Dama ke kyakkyawa ce kuma kwalliyar da kikayi ya sake fito da kyawunki ko sarauniyar kyau dole ta Sara miki,kyanta dake za'aje wannan unguwar saboda zanso ace har muje mu dawo ina kallon wannan kyakkyawar fuskar"

Jikinta gaba d'aya a sanye yake,ji take kamar a mafarki ne Aliyu yake fad'a mata haka.
  
Ta gabanta yazo zai wuce yace "kicewa yayarmu ina jiranta bara na d'akko motar"

Tafi seconds 30 a gurin kafin ta waiga sai take ganin kamar securities d'in gidan duk ita suke kallo,Murmushi ta d'anyi sannan ta ja k'afarta da tagama yin sanyi ta koma ciki,a tsaye ta tarar da Fauzah a falo.

"Lafiya naga kin dad'e kuma kin dawo a sanyaye"

 murmushi tayi  tace "Yace yana jiranki"
"Okay"
"Yaya Fauzah in shirya mu tafi tare?"
"Gaskiya sauri nake bazan Iya jiranki ba"
"Mayafi kawai zan d'auka"
"A'a ki bari maje wani lokacin gidansu zubaida zanje zamuyi wata magana ne"
"Amma da kika ce gidan biki"
"Na fasa gidansu zuby zani akwai maganar da zamuyi"
"Okay a dawo lafiya"

Fauziyya na barin gurin ta bi k'ofar da kallo.

_Ashe akwai ranar da zata zo inji ina son Aliyu?direba na ko dai asiri aka min?wannan wane irin sone na lokaci guda haka?_
Murmushi tayi tare da fad'in "lubna batayi k'arya ba.







_Alk'alamin Sadeey_✍
[9/29, 8:14 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
          🍁🍁🍁


*_by SaNaz deeyah_*👄


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```



05

A bangaren Fauziyya kuwa tunda ta fita ta sauya tafiya,sai wani irin taunar chewing gum take irin na tacaccun 'yan bariki.
Shi kanshi Ali yayi mamakin yanda take behaving a lokacin tamkar sabuwar kilaki.

Yayi sauri zai bud'e mata k'ofar baya ta dakatar dashi.
"Ban saka ka ba" ta furta tare da bud'e gaba ta zauna.

Shima zagayawa yayi ya zauna ba tare da yace komai ba.

Sun fara tafiya ne ya tambayeta ina zasu
"Park" ta bashi amsa
"Wanne"
"Duk wanda ya maka"
Maganar yaji ta wani iri dan haka kawai ya k'udiri niyyar zai ta tafiya koda zasu bar garin in har bata ce su tsaya ba.

Yanayin abubuwan da take yi ne yasa shi b'aro jirginta amma sai ya nuna baima damu ba.

Tana gani suna ta tafiya amma bata yi yink'urin tsayar dashi ba,daga tayi mik'a sai ta zame mayafinta daga jikinta kai duk wani abu da tasan zai ja ra'ayinsa haka ta rik'a yi har ya gaji yayi parking "naga mun tsaya?"
"Ina son ki fad'a min inda zan kaiki" ya furta ba tare daya kalleta ba.

Shiru tayi tsayin Rabin minti sannan tayi dariya tace "kayi kyau wallahi ka had'u"


Kallo ya bita dashi na _ban fahimci me kike nufi ba_
'Daga gira d'aya tayi ta sake fad'in "kayi min Aliyu tun ranar da aka kawoka gidanmu nake sonka"

"So kuma?" Ya fad'a a d'an razane.
"Eh so,kasan me?"
"Sai kin fad'a" kawai ya tsinci kanshi a mai bata amsa kai tsaye"
"Ina so muyi wani sirri amma ba yanzu ba ka bani number ka zan nemeka dan maganar bada rana zamuyi ta ba"

_ko dai Janan ta fad'a mata komai?_ ya tambayi zuciyarshi ba tare da ta bashi amsa ba.

"Yah kayi shiru" ta katse tunaninsa

"Yaushe zamuyi maganar?"

"Ka bani number ka sai na kiraka idan na saka time"

Babu musu ya bata numbershi,tayi masa umarni da su koma gida kawai.

          *******

Tana kwance akan gado tana juyi tunani kala-kala take a cikin zuciyarta...

_ki kalli kanki a mirrow zaki tabbatar da cewa ke d'in kyakkyawa ce ajin farko_

Maganar Salman ta fad'o mata lokacin daya fara furta mata kalmar so.

Da sauri ta tashi ta nufi jikin mirrow ta kalli fuskarta,wani murmushi ta saki na jindad'i sai take ganin kamar a lokacin ne yake fad'a mata.

_zan tafi bazan sake dawowa garinku ba dan bazan iya jurar ganinki a matsayin matar wani bani ba,k'addara ta raba mu dake,amma nasan bazan tab'a samun kamarki ba har k'arshen rayuwata_

Zubewa tayi a k'asa lokacin da ta tuno maganarsu ta k'arshe da Salman,tun a wannan lokacin bata sake jin labarinsa ba sai labarin rasuwarsa da Abbanta ya kawo mata.

"Allah yaji k'anka Salman ya yafe maka laifukanka" ta fad'a tana zubda hawaye,a dai-dai lokacin Mameey ta shigo.

"Oh dama kin shirya shine kika zauna direba na can na jiranki kin kirashi kusan awa d'aya ko kin fasa zuwa skul d'in?"

Bata bata amsa ba kawai ta cigaba da goge hawayenta.
"Janan"
"Na'am" ta amsa a sanyaye.
"Kukan me kike?"
Nan ma shiru tayi.

Kusa da ita ta k'arasa ta tallabo hab'arta
"Nace kukan me kike?"
"Bakomai"
"Oh dama anayin kukan dad'i?"
Tayi shiru
"Tambayarki nake"
"Mameey Salman na tuna"
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil,Janan meyesa bakya jin maganar iyayenki?wace nasihace mahaifinki baya miki ita akan Salman?idan kin tuno shi meyasa bazaki masa addu'a ba"

"Ina yi masa"
"To ba kuka yake so ba addu'arki yake buk'ata oyaa tashi ki saka gyalenki ki tafi skul"

Jikinta a sanyaye ta tashi ta zura hijab ta d'auki handbag d'inta.

Tana fita ta hango Aliyu tsaye jikin motar shi kam tun daya ga fitowarta yake murmushi.

Wani zugi taji kanta nayi ganin fuskar Aliyu take tamkar ta Salman.
A take ta zube a gurin a sume.

"Subhanallah" wasu daga cikin securities d'in gidan suka furta.

Da sauri d'aya daga cikinsu ya nufi cikin gidan dan sanarwa dasu mameey.

Aliyu ma a rud'e yazo gabanta ya tsaya a dai dai lokacin da mameey da Abba suka fito a tare.

"Me aka mata ne?"
"Fad'uwa kawai tayi bamu San dalili ba" Ali ya bashi amsa.

A kafad'a Abba ya sab'eta sukayi cikin gida.


_2hrs ago_

Fad'a sosai Abba yake yi ita kam tana jingine da fuskar gado tana kuka.

Fauzah da Fahad suna tsaye yayinda Mameey ke zaune gefen gadon.

Ganin Abba yak'i daina fad'an sai maimaita Abu d'aya yake yasa mameey cewa "fad'an nan fa bashi zai saka ta nutsu ba"

"Kamar ya kenan? Duk ba laifin ki bane,ina amfanin yarinya k'arama kamar Janan ace namiji ya shiga ranta haka,ki gaya min dalilin dayasa ta fara soyayya da Salman ba tare da iznina ba???"

"Me kake nufi da hakan?kana nufin kace Janan bata isa aure ba ko kuma bata isa soyayya bane?"

"She's just 18 me ta sani game da wannan?"

"Ko ka so ko karka so gaba d'aya yaranka sun isa aure"

"Ni kuma bazan tab'a aurar da 'ya'yana ba ba tare da sun gama karatu ba"

"Shi kuma Fahad da yake aiki fa?meyasa ka hanashi ya fito da yarinyar da yake so ka aurar dashi ba?"

"Hadiza mu bar wannan maganar na san lokacin daya dace ko wanne na aurar dashi"

"Nima ina da right d'in bawa 'ya'yana zab'i"

"Oh haka kika ce?"

"K'warai ma kuwa"

"Mu zuba mu gani"
Ya fad'a a fusace sannan ya fita ya bar d'akin,mameey tabi k'ofar da kallo ranta a b'ace.

Ranar haka kowa ya yini a gidan da b'acin rai.









_Sadeey_💫✍
[9/29, 8:14 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
   *DIREBAN GIDANMU*
        🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```



06

Sanye take cikin doguwar riga ta atamfa,tayi rolling ta d'an k'aramin veil,idanunta d'auke da farin glass  hannunta rik'e da wani d'an k'aramin novel.

A tak'aice tayi kyau matuk'a.
Tun daya hangota ransa ya b'aci,a zuciyarsa ya furta

_wannan kyawun naki nan bada dad'ewa ba zai zama muni sai nayi watsi da duk wani farin cikin zuri'arku_

smiling yayi itama ta mayar masa dan yanzu idan ta ganshi ji take tamkar an tsundumata a aljanna"

Tana k'arasawa gabansa ta saki murmushi wanda har ya bayyana hak'oranta.

"Barka da zuwa sarauniyar kyawawa"

Wani farin ciki ne ya mamaye zuciyarta ta bud'e baki zatayi magana taji muryar Fauzah a bayansu.

"Ku tsaya ku saukeni a skul"
Duk Kansu suka jiyo suka kalleta.

A hankali ta k'arasa jikinta sanye da wata fitted gown nylon wadda tabi jikinta.

Janan kawai kallonta take rai a b'ace.

Bata sake masu magana ba kawai ta bud'e  seat d'in gaba ta zauna.

Janan ta bud'e k'ofar baya ta shiga ta zauna.

Yana driving a nutse yayinda duk kanninsu suke latsa wayarsu.

"Kayi kyau sosai Aliyu" kamar daga sama sukaji maganar.

Duk kansu suka kalleta,ta maze tamkar bata ma San sunayi ba,ta sake fad'in "ko dan dama ai kai kyakkyawane"

Shiru yayi baice komai ba,Janan ji tayi zuciyarta na tafasa tamkar an watsa mata garwashi a ciki.

"Malam kayi sauri ka saukeni karna makara"
Shi kanshi yayi mamakin yadda ta masa magana a tsawace.

Nan ma bai tanka ba ya san ranta ne ya b'aci saboda furucin Fauzah.

Suna zuwa bakin gate tace ya tsaya.
A fusace ta sauka ranta a b'ace.

       ***********

Ya kirata yafi a k'irga batayi picking wayarshi ba,da ta gaji ma kawai ta kashe wayar.

"Waye haka ya dameki har kike kashe Waya?"

"Aliyu ne bayan ya b'atan rai kuma yake kirana komai zai ce min oho"

"Aliyu kuma,wanne kenan?"
"Wanne kika Sani?"

"Ni ban san kina da wani Aliyu ba bayan direbanki"

"To shi nake nufi"
"Ta fad'a tana kallon gefe da ban"

"Karfa maganar lubna ta zama gaskiya"
"Tama zama"
"Kamarya?"
"Kamar yadda nake soyayya dashi har muna shirin yin aure"
"Direbanki"
"Ya isa haka Raihan karki saka raina ya b'aci"
"Haba Janan wlh nayi tunanin duk wasa kike amma ina ke ina direba"

"Mu tsaya a nan dan wlh raina ya gama b'aci,na kawo Salman ance baya da asali shi kuma Aliyu ai kinsan asalinsa ko?"

Jakarta ta d'auka ta bar gurin,Raihan ta bita da kallon mamaki.


Tafiya take gaba d'aya ranta a b'ace ta nutsa sosai cikin makarantar inda take ma ba mutane sosai hanyar clinic ne,kawai taji ta gabza karo da mutum,wasu stars ta gani na azaba,ta d'ago dan ta bawa mutumin hak'uri kawai taji ruwan mari har uku kafin ma ta shaida ko waye.

Ta dad'e idonta rufe kafin ta bud'e shi ta dirar dashi kan kyakykyawan saurayin.

"Hannu ta d'aga zata rama taji an rik'e ta tare da hankad'ar da ita k'asa,dariya suka hau yi sauran samari uku"

Shi kuma ya d'urk'usa k'asa saitin fuskarta yace "Janan Hashim,yarinya mara kunya,duk rashin kunyarki baza kiyi dani ba ko kuwa baki tab'a sanin waye ni a cikin polytechnic?kije ki tambaya waye yarima"
Mik'ewa yayi tsaye yana murmushi yace "kije ki tambayi ko waye ni bani da wasa musamman da talaka kamarki"

Gaba d'aya sauran mazan suka saka dariya.
"Guys muje" sun fara tafiya tayi saurin cewa "idan ka isa kai namiji ne ka fad'a min cikakken sunanka"

Juyowa yayi yana dariya ya girgiza kai kawai ya wuce.

Tashi tayi tana kad'ai kayanta sai a lokacin taji wasu zafafan hawaye na fita a idanunta.

          **********

Tana kwance tana juyi gaba d'aya hankalinta a tashe yake,ga abinda ya faru a makaranta ga  rashin sanin tak'a mai-mai inda Aliyu ya tafi domin Mameey tace tunda ya fita kaita makaranta bai dawo ba,ta kira numbershi yafi sau ashirin bai d'aga ba tana tunanin ko ramuwa yayi,bata yi tunanin kiran Fauzah ba dan bata kawo suna tare ba.

Haka ta zauna cikin k'unci ga rashin sanin sunan wannan guy d'in wanda ya wulak'anta ta a skul.




A b'angaren Ali direba kuwa bayan ya dire Janan a skul ya juya zai yi hanyar skul d'in su Fauziyya tayi saurin dakatar dashi.
"A'a Aliyu Najman hotel zaka kaini"

Yayi saurin juyowa ya kalle ta,tayi saurin zuge jakarta ta fiddo sark'ok'in gwal dasu bangles tace zan Kaiwa wata mata kayan saidawa ne,tazo daga lagos so anan hotel d'in ta sauna"

Kai tsaye ya nufi wannan katafaren hotel d'in.

Bayan yayi parking ta kalleshi ta marairaice tace "please Aliyu ka rakani bani son a min kallon banza dan Allah ka rakani muje mu fito"

"Amma idan muka shiga tare ai shine za'a miki wannan kallon"

"A'a please ni dai tsoro nake saboda ban tab'a shiga hotel ba"

"Ba damuwa muje" ya kashe motar ya bita.

Kai tsaye yaga tana tafiya ba tare data kira wayar kowa ba koda matar da tace tazo gurinta.

Sun hau bene kusan hawa uku kafin su isa d'akin kasancewar hotel d'in babba ne.

Ganin ta fito da key daga Jakarta yasa abin yayi matuk'ar bashi mamaki.

"Kika ce gurin wata kika zo naga kina k'ok'arin bud'e d'akin da kanki
" taje ta dawo shine ta bada key a kaimin"

Murmushi kawai yayi dan ya san k'arya take.

Suna shiga d'akin kuwa ta rufe da key,cire mayafinta tayi sannan ta cire bands da d'ankunnenta ta baza gashinta ta fad'a kan gado"

Murmushi tayi ta kalleshi "na mallaka maka duk kanin kaina kayi yadda kaga dama dani"

"Subhanalla kin san kuwa me kike fad'a"

"K'warai ma kuwa domin son ka ya rufe min ido"

"Wannan ba so bane"
"Wannan kuwa shine so" ta fad'a tare ta tashi zaune.

"Kaji tausayina Aliyu nayi maka alk'awarin babu wanda zaiji sirrinnan zamu rik'a zuwa nan muna biyawa junanmu buk'ata batare da kowa ya sani ba"

"Bazan iya ba,bazan tab'a aikata zina ba"

"Nima ban tab'a ba sai yanzu nake son farawa saboda na kasa b'oye feelings d'ina"

"Tunda kin san haka ai sai kiyi aure gudun fad'awa halaka"

 "Abba bazai mana aure ba sai lokacin da ko wacce a cikinmu ta kammala masters ta fara aiki"

"Sai ki fad'a masa ke bazaki iya ba"

Duro wa tayi daga kan gadon ta k'araso gabansa ido cikin ido tace "kasan halin Abba yana da tsauri,Janan data fara soyayya haka ya rabasu yace shi ba zai bawa mai k'aramin k'arfi auren 'yar shi ba,sannan uwa uba baya da asali daga shi sai mamansa suke rayuwa a garin,tun lokacin daya rabamu ya hanamu kula kowa har sai mun gama masters sannan zai zab'a mana mijin daya dace damu"

"Baki da hujja,ki bud'e min k'ofa na fita"

"Aliyu pls"
"Ki bud'e nace" ya fad'a a tsawace"












_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:14 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
    *DIREBAN GIDANMU*
        🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


07

Tsayawa tayi tana masa kallon mamaki yadda har yau yake mata shouting dan ta buk'aci taimako daga gurinsa.

"Kin tsareni da ido baza ki bud'e ba saina kirawo Abba"

Dariya ta k'yal'k'yale da ita tana tafa hannu "ka kirawo Abba kaga yadda zan maka sharrin da sai kayi dana sanin zama direban gidanmu"

_Aliyu kayi a hankali ka kuji sharrin mace dan tana da had'ari sosai_

Maganar mahaifiyarshi ya tuna lokacin daya fara soyayyar k'arya da Janan.

"Aliyu da yanzu munyi abinda zamuyi mun tafi saboda kaga lokaci na tafiya har munci awa d'aya da wani abin anan"

_ban tab'a aikata zina ba bazan fara a kanki ba,da ace ni mazina cine da yau kinga k'ask'anci da daga yau baza ki k'ara sha'awar wani d'a namiji ba,yadda na tsaneku haka zanyi fata fata dake in barki cikin nadama._

"Kai nake jira"
Ta haye kan gadon ta kwanta tare da lumshe ido "wallahi ko zamu kwana anan bazan bud'e ba sai ka biya min buk'ata ta"

Zama yayi kan kujerar dake jikin mirrow yana kallon ikon Allah,abin yana matuk'ar bashi mamaki wai mace ce ke nemansa.

Sun shafe awoyi sama da 8 dan anan yayi sallahr Azhar da la'asar,yana gani itama tazo tayi.

"Aliyu na fara jin yunwa ya kamata muyi abinda ya kaw........." Mari ya d'auketa dashi wanda ya hanata k'arasa maganar.

"Ni ka Mara?"
"Ki bud'e min k'ofa"
"Wayyo Allah zai kashe ni" ta fad'a da k'arfi tare da kama rigarta ta yaga har zuwa k'irjinta"

Janyo waya tayi ta danna kira "Cikin kuka da kururuwa tace " kuzo Najman hotel zai kasheni dan Allah ku ceceni" d'if ta kashe wayar.

Baiyi wani yunk'uri ba dan mamaki ya sandarar dashi a tsaye.

"Zan nuna maka ni cikakkiyar makira ce"

Suna tsaye taji jiniya alamar su Abba sun iso,tayi saurin yace bedsheet d'in ta rufe jikinta ta wullah masa key d'in ta Shiga toilet ta rufe.

Kusan minti 20 basu zo d'akinta tasan k'ila ana duba each and every room tunda bata fad'i d'akin da take ba.

Kamar daga sama taji ana fad'in " 'yata kina d'akin nan?"

Da Sauri ta bud'e ta fito tana kuka ta rungume Abba tana matsanancin kuka.

"Naga motar Janan a waje ina Aliyu?waye ya kawoki nan dan ya keta miki haddi?"

"Abba Aliyu ne"
"Yana ina?" Ya fad'a ransa a b'ace.

"Yana ganin shigowarku ya gudu"

"Arrest him" ya fad'awa 'yan sandan da suke tsaye a gurin,da sauri suka fita.

Suka duba ko ina a cikin hotel da wajenshi basu ga Aliyu ba sai dai motar Janan.


_(Kun san ya akai Aliyu ya gudu)?_

Tana wurgo masa key lokacin data shiga toilet shi kuma ya bud'e k'ofa ya fita,kasancewar hotel d'in yana da steps ta ko wane side shiyasa ya rik'a bi yana b'uya daga securities d'in Abba da k'yar ya samu ya fita dan an baza 'yan sanda ko ina,amma bai samu damar d'aukar mota ba.


A gigice ya ya hau napep ya kaishi gidansu.

"Yaya lafiya?"
"Ina umma?"
Tana d'aki.

Da sauri ya wuce zuwa d'akin,zaune ya tarar da umma tana goge hawaye.
"Umma lafiya"
Kallonshi tayi yadda ta ganshi a birkice ta tsorata da hakan.

"Bakomai ina tunawa da mahaifinka da 'yar uwarka da suka rasu ta hanyar Muggayen  mutanennan"

"Umma ina cikin tashin hankali"
"Na me?"

Labarin duk abinda ya faru ya sanar da ita,tashin hankalin da ta shiga a lokacin ba na wasa ba.

"Akan wane dalili zaka bita ku shiga cikin hotel?kenan maganganun da nake fad'a maka duk sun tashi a banza?"

Kuka ta fara sosai,Ummi ta shigo ta rik'e ta "ka rugaza duk wani shirinmu Aliyu,ka cucemu"

Furucinta ba k'aramin d'agawa Aliyu hankali yayi ba.

"Umma karki ce haka ki gafarceni,nayi alk'awarin k'wato mana hak'k'inmu kota wane hali"

"Ta wane hali kenan?Auren yarinyar ne kad'ai mafita,kana tunanin wani mahaifine zai d'auki 'yarsa ya bawa fasik'i"

A gigice ya kalli umma yace "kina nufin kin yarda umma zan Iya aikata zina?ni d'anki ne na halak dan Allah ki daina jifana da wannan kalamai"

"Bance kai mazina ci bane amma kana tunanin akwai wanda zai yarda a cikinsu cewar baka aikata ba bayan kun shafe kusan awa takwas Ku biyu a d'akin?"

Kai ya dafe yana nadamar binta ciki da yayi,bai tab'a tunanin zata mai sharri haka ba.

"Yanzu meye mafita"

"Anjima zan je gidan saboda makullin motar janan ma yana hannuna"

"Inaso ka tafi yanzu Dan bana so ace an maimaita abinda ya faru a shekarun baya da suka wuce"

Jikinsa a sanyaye ya tashi ya fita.

Ummi na kuka ta bishi "Yaya bana son abinda ya faru damu ya sake faruwa dan Allah karka je"
Dafa kanta yayi yana murmushin k'arfin hali yace "karki damu zan dawo lafiya lau insha Allahu"

         ********
A bangaren su Fauziyya kuwa sai da Abba ya kaita asibiti aka tabbatar masa da lafiyarta k'alau sannan suka wuce gida,idanunta sun kad'a sunyi jajir kya kyace da gaske duk abinda ta fad'awa Abba gaskiya ne.

Mameey,Janan da Fahad duk suna falo hankalinsu a tashe suna jiran zuwan su Abba.

Aikuwa suna jin horn duk kansu suka fito.

Sunyi cirko-cirko Mameey ce ta k'arasa gurin Fauziyyar ta ruk'ota.

Falo suka koma duk suka zauna.
"Wai meya faru da fauziyya ne?"

Ajiyar zuciya yayi yace "Allah dai ya tak'aita amma daya lalata mata rayuwa"

"Waye wannan?"
Suka fad'a a tare.

"Wannan yaron Aliyu mana,ai na saka amin arresting nashi duk inda yake"

Tuni janan ta mik'e tsaye "wane Aliyu Abba?"

"Direban gidan nan mana,wai yaron nan ni zaici amana dubi duk abinda nake masa amma baya godiya,har ya yaga mata riga yana nemanta ta k'arfi sai shiga tayi ta kulle kanta a band'aki"

"Ai dama mutum ba abin yarda bane dan wa zaiyi tunanin Aliyu zaiyi haka" Mameey ta fad'a.

Janan kuwa ta sandare ta rasa me zata ce ma,kallon Fauzah kawai take.

"Abba kayi masa hukunci mai zafi" Fahad ya fad'a.

A hankali ta furta "bai aikata ba,bazan tab'a yadda ace Aliyu zaiyi haka ba"

Da gudu ta shiga d'akinta tana kuka.
"Meyasa haka?meke faruwa dani ne?"


"Ki jini da yarinyar nan"
"Bakaji me kace ba kaima,yarinya ai yarinyarce"
"A hakan kike cewa zasu iya zaman aure"
"Mu bar wannan maganar yanzu"
"A to"







_Sadeey S Adam_👄
[9/29, 8:13 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
    *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


_ohhni Safnah shiru babu ita babu labarinta,pls dan Allah ina cigiyar Safeenah writer d'in *Sunyi Sake* dan kaf numbers d'inta switched off Allah yasa dai lafiya Ameen🙏_



08

Tana zaune a d'aki tana ta kuka dan ta rasa mafita shikenan a karo na biyu ta rasa masoyi,ta san Abba bazai tab'a yarda ya bata shi ba tunda har haka ta faru kuma dama soyayyar a b'oye suke yinta dan ta san babu yadda za'ayi Abba ya aura mata direbanta cikin sauk'i.

Tana cikin yanayin nan taji muryar Abba yana fad'in "Arrest him" a tsawace.

Da sauri ta tashi ta fita falo,idanunta suka sauka akan Aliyu yana fad'in "Abba Ku tsaya ku fahimceni wallahi ita ta nemeni"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Janan ta fad'a tana kuka,da sauri ta k'arasa gabanshi "meyasa ta bugo waya tana neman taimako? kuma kace ita ta nemeka"

Kallonta yayi idonshi jajir yace "wallahi bani na nemeta ta ba ita tace na rakata hotel zata kaiwa wata mata kaya kuma tace bazata iya shiga ita kad........"
Abba ya wankeshi da mari "Rufamin baki" 

Janan ta juyo ta kalli Abba tace "bai aikata ba Abba"

"Janan baki da hankali ne?"

"Mameey da hankali na ku duba ku gani,akwai kissar wani malami da yake cewa duk macen da tace an mata fyad'e a duba a gani da takalmi ta shiga d'akin ko kuma babu,idan da takalminta ta shiga to tabbas ita ta kai kanta idan kuwa  babu takalmi to da k'arfi aka jata,sannan kuma tayaya Aliyu ya kai Yaya Fauzah hotel?idan ta k'arfi yayi mata babu yadda za'ayi su shiga saboda ma'aikatan ciki ai ba mahaukata bane,sannan meyasa tabi Aliyu bayan tana da motarta Aliyu baya da kud'in kama d'aki a katafaren hotel kamar Najman sannan rigar Yaya Fauzah ta gaba ta yage bata baya ba kinga kuwa duk zancenta k'arya ne koda ace Aliyu yana nemanta to tabbas ta amince ta kuma yarda sannan ita ta kama musu d'aki a wannan hotel"

"Abba k'arya take wallahi" Fauziyya ta fad'a tana kuka.

"Ki rufa min baki munafuka" fahad ya fad'a yana huci
"Abba tabbas akwai duba a maganar Janan"
"Kin cuceni Fauziyya ban yi miki wannan tarbiyyar ba" Mameey ta fad'a tana kuka

Abba da kanshi ya fara dukan Aliyu sannan ya bada umarni akaishi cell har sai ya nemeshi a kuma bashi abinci sau d'aya a rana sannan kar a yarda da belin.

"Abba"
"yi min shiru Janan".


Aliyu ya Ciro key daga aljihunsa ya mik'awa fahad "ga key d'in motarku"

Juyowa yayi ya kallesu d'aya bayan d'aya a lokacin ya k'ara k'udirar cewar sai ya shayar dasu ruwan bak'in ciki Wanda basu tab'a tsammani ba.

Suna fita dashi janan ta durk'ushe tana kuka.

"Na dawo kanki Fauziyya" a gigice ta d'ago kai ta kalleshi
"Ni kike neman zubda wa daraja da k'ima ko?"

Kai ta girgiza tana kuka "wallahi k'arya yake Abba,shine yace idan banje ba zai kasheni yaje ya wurga gawata inda baza'a tab'a gani na ba shiyasa na yarda na bishi" rufamin baki manufuka.

Fahad ya kalla yace "ka kulle min Fauziyya a d'aki kar ka yarda ko falo ta fito duk abinda take buk'ata a kai mata d'akin a k'wace system d'inta da wayarta har sai na gama bincike a Kansu"

Mameey dai kallonsu kawai take tana hawaye dan ta san duk abinda ya faru da 'ya'yanta laifin mahaifinsu ne.

        *********

Umma kuwa ganin har dare yayi Ali bai dawo ba ta San tabbas akwai Matsala.

Kallon Ummi tayi tace "ko dai zaki bi Aliyu ne?"

"Umma ki bari sai gobe saboda yanzu dare ne kuma kinsan muna da nisa sosai mu cikin k'auye su kuma cikin gari mota ma zatayi wuyar samu"

"To shikenan Allah yasa dai lafiyarsa lau duk da dai na san ba lafiya ba"

Haka ranar suka kwana cikin rashin kwanciyar hankali.

Washe gari tun sassafe Ummi ta dama masu koko suka sayo waina suka ci,sannan ta gyara ko ina a gidan,kusan k'arfe goma ta shirya Umma ta bata kud'in mota dan adaidaita yana da tsada ga wahalar samu daga k'auyen nasu zuwa cikin garin Kaduna.

"Umma ko dai bari zanyi sai zuwa anjima dan naga jikin naki babu dad'i sosai"

"Ciwon kai ne kawai kuma naji d'an dama-dama inason muji halin da Aliyu ke ciki tun jiya bai dawo ba"

"To umma Allah ya sawwak'e bara naje"

Sallamar da aka yi ya dakatar da Ummi daga shirin fitar da take.

Zuhra ce shigo kanta a k'asa tazo ta gaida umma,umma ta amsa cikin jindad'i.

"Umma dama jiya ne Aliyu yazo yace min dai yana cikin Matsala amma in tayashi addu'a zai je cikin gari ya dawo sannan yace idan ya dawo zaizo da dare naji kuma shiru bai zo ba,sai d'azu naji labari a gurin Nura wai har yanzu bai dawo gida ba,shima so yake yaje birnin"

"Wallahi kuwa muma bamu san dalilin rashin dawowar tashi ba tun da bai saba haka ba amma yanzu zan tafi cikin birnin in gani"

"Umma idan babu matsala zan bita" zuhra ta fad'a tana kallon umma.

"Kin tambaya a gida?"
"Nace masu nan na taho dan ganin ko lafiya nasan babu matsala idan na bita"
"Okay Allah ya kiyaye Ku"
"Ameen umma" suka fad'a tare.



Suna cikin mota Zuhra tace ma Ummi "to yanzu ina muka nufa"
"Gidan da yake aiki"
"Kin san gidan"
Farin sani ma"
"Toh ba damuwa"

Sun isa k'ofar gidan lafiya amma shiga cikin gidan ya faskara,Alh.Hashim commissioner of police ne shiga gidansa bazai zama abu mai sauk'i garesu ba,dan ma Ummi tayi dubara tace ma securities d'in wajen Janan suka zo.

Da farko abinda aka fara tambayarsu shine compliment card basu dashi.

Wani daga cikin securities d'in yace "kaji wannan mak'aryatan wai wajen Janan suka zo babu compliment card,babu Waya da zasu kirata suce sunzo wai kuma su k'awayenta ne"

"Hahahah amma dai basu da hankali ka dube su a hakan ne suke k'awayen janan?kai wannan zance ne"

Maigadin ya tausaya masu sosai amma baya da wani iko daya wuce bud'e gate da rufewa.

Sunga wulak'anci da k'ask'anci duk kansu ransu ya b'aci musamman dariya da cin mutuncin talauci da suke masu.

Sun fi awa biyu a zaune a bakin gate tun suna rok'onsu har suka gaji suka daina.

Sai wani security ne daya ga sun kafe sun k'i tafiya kawai ya d'aga Waya ya kirawo Janan yana dariya yana sanar mata ga wasu 'yan k'auye sunzo gurinta wai k'awayenta ne basu da ko waya kuma babu card a hannunsu

Daga d'ayan bangaren Janan tayi dariya tace "basu wayar na tambayesu"

Mik'a masu wayar yayi Ummi tayi saurin karb'a ta kara a kunne.

"Salamu alaikum"
"Wa alaikumussalam,yace min ke kawata ce amma ya akai bani da contact dake"

"Ni k'anwar Aliyu ce,ban san kowa ba a gidannan sai ke da yake yawan magana,dan Allah ki bamu dama mu ganki dan musan halin da d'an uwanmu ke ciki"

"Okay bama wanda ya baki wayar"
"Toh" ta fad'a tare da mik'a masa

"Hello hajiya"

"Ka shigo dasu cikin Babban falo"
"Okay"

Dariya yayi yace "to k'annen Ali direba Ku shigo"
"Oh dama k'annen Ali ne?hahah no wonder na gansu a haka" wani ya fad'a yana shek'a dariya.

Maigadi kuwa sai barka yake masu cike da tausaya wa dan ya san Ali mutumin kirki ne.


Janan kuwa da sauri ta sakko zuwa babban falo ta tarar da Mameey zaune tare da bak'inta

"Ina zuwa naga kin sakko da sauri"

Saida ta fara gaida bak'in sannan tace "wallahi mameey bak'i nayi yanzu Mudan zai shigo dasu"
"Okay"

Tana tsaye har suka shigo,Ummi sai kallon gidan take tana ganin yadda masu kud'i ke cikin aljannar duniya.

"Sannunku da zuwa" Janan ta fad'a tana murmushi.
Suka amsa sannan suka sunkuya suka gaida su Mameey.

"Ya sunan 'ya'yan nawa?" Mameey ta tambaya cikin bark'wanci,suma suka d'an saki rai suka fad'a mata.

Kallon Janan tayi tace ki kaisu falon bak'i ko naku ko kuma k'aramin falo"

"A'a bedroom d'ina zamu"
"Okay ba damuwa"

"Ku muje"
Tashi sukayi suka  bita.

Bayan sun shiga duk kansu zasu zauna a k'asa tayi saurin cewa a'a dan Allah karku zauna a k'asa ga sofa ga gado" ,Zuhra ce tayi murmushi suka zauna kan sofa.

Itama zama tayi kusa dasu tace "sannunku da zuwa" "yawwa" suka amsa

"Amma ni Ummi naji  yana yawan fad'a min a matsayin k'anwarsa"

Murmushi tayi tace "eh wannan Zuhra itace wadda zai aura"

Gabanta sai da yayi mummunar fad'uwa ji tayi kamar an caka mata mashi a lokacin da Ummi ke fad'a mata"

Ummi ta lura da hakan dama ta fad'a ne dan ta k'ular da ita.

"Bai tab'a baki labarina bane?" Zuhra ta tambaya.

Murmushin k'arfin hali tayi tace "yana fad'a min amma manta sunan nake" ta fad'a ne kawai dan kar Zuhra taji haushi.

"Ai na san dole yayi maganarta yadda yake k'aunarta"

"Uhmm bara na kowa maku ruwa na san kunsha hanya"

"A'a ki barshi mu dai kawai munzo muji ko lafiya Yaya Aliyu bai koma gida ba tun jiya"

"Karki damu bara dai na kawo maku ruwan"

Da Sauri ta tashi ta fita.

Ummi ta kalli Zuhra tace "ga yadda aka k'awata gida da kud'inmu"

"Kud'inku kuma?" Zuhra ta tambaya

"Eh mana kud'inmu mu talakawa mana ai har ke"

"Uhmm dama,amma Kin San me?"

"A'a sai kin fad'a"

"A yadda ake cewa masu kud'i na da wulak'anci sai naga sauk'in kanta sosai tana da mutunci da sakin fuska"

"Na munafurci ba" maganar zuciya tayi Wanda bata san ya fito fili ba sai ji tayi zuhra tace "kamar ya"

Sauri tayi ta canza maganar da fad'in "gashi sun saka yayana a matsala bamu san dalili ba"

"Insha Allah komai lafiya"

"Ni wallahi haushi nake ga d'akin nan wai duk girmansa na bacci ne kawai"

Murmushi Zuhra tayi tace "amma kamar ya tab'a cemin ya tsani wata janan"

"Wannan shegiyar Janan d'in 'yar Zaria ce taso raina masa hankali" ta maze

"Oh nayi tunanin wannan"

"A'a wannan ai tana da kirki ba karmar waccan ba"

Dariya zuhra tayi ba tare da ta fuskanci komai ba.


Janan kuwa tsaya wa tayi jikin step tayi kukan bak'in cikin wai Aliyu yana da wadda zai aura,sannan ta goge hawayenta,taje babban kitchen ta bada umarnin a kaiwa bak'inta abinci da fruit,sannan ta d'auki plate ta koma d'akin.







_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:14 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
       *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




_Wannan Shafin naku ne 'yan group d'ina *TASKAR SANAZ* bazan iya musalta farin cikina a gareku yadda kuke bani k'arfin gwiwa akan novels d'ina,nagode sosai ina alfahari daku Allahu ya barmu tare ya kuma bar zumunci_
*#ILYMTYE😍😘*



09

Fridge ta bud'e ta d'akko lemo da ruwa ta d'ora kan plate d'in sannan ta d'auki cups guda biyu ta nufo inda suke ta ajje
"Bismilla"

Ruwa suka zuba suka sha sannan Ummi ta sake tambayarta Aliyu a karo na biyu.

"Nafiso sai kun ci abinci kun huta yanzu za'a kawo maku"

"Dan Allah ki fad'a mana gaskiya ko dai ya mutu ne kike son b'oye mana?" Zuhra ta tambaya.

Ajiyar zuciya tayi ta kalleta tace "ki kwantar da hankalinki Aliyu yana raye nd am vry sure lafiyarsa k'alau"

"To idan hakane yana ina?" Ummi ta tambaya.

"Kinsan ai. .........." Knocking da ake na k'ofa yasa tayi shiru tare cewa "shigo"

'Yan aikinsu suka shigo hannunsu d'auke da tray na abinci da plates sai plate d'in fruit .

"Bismillah Ku ajje" tayi masu umarni,bayan sun ajje sun fita sannan ta juyo ta kallesu.

"Ai ya fad'a maku abinda ya faru jiya ko?"

"Eh amma wallahi yaya bashi da laifi bazai tab'a iya aikata zina ba"

"Hakane nima zan shaideshi akan hakan,amma matsala d'aya da suka zauna d'aki d'aya a hotel kuma da Abba yazo sai  ya gudu,shiyasa kowa ya shiga zulumi akan shiya jata ko ita taja shi"

"Amma kinsan idan mahaifinku ya zo a lokacin yaya baya da wani uzuri zai iya fuskantar ko wace matsala"

"Toh,yanzu dai Abba yasa an tafi dashi cell tun jiya itama yaya fauziyya ya saka an kulleta a d'aki sannan yace babu belin"

"Na shiga uku ni Ummi me zan cewa umma meyasa rayuwarmu ke tafiya a haka"

Zuhra ta ruk'o Ummi tana kuka, hakan ne yasa Janan taji hawaye ya sauka a fuskarta.

"Yanzu ko ganinsa bazamu iya yi ba?" Zuhra ta tambaya.

"Za muje daku Ku ganshi"

Da sauri Ummi ta tashi ta kalli Janan "dan Allah mu tafi yanzu ki taimaka mana"

Tausayi ta bata sosai dan haka ta tashi ta d'auki mayafi sannan ta d'auki jakarta ta kallesu "zamuje mufara yiwa Mameey sallama amma dan Allah Ku goge hawayenku Ku saki ranku karta gane wane abu bare ta hanamu zuwa"

Haka suka tashi jiki a sanyaye suka fita,Mameey still tana falo,Janan ta zauna kusa da ita tace "Mameey ina son kaisu gida gashi babu direba"

"Ina Mato?"
"Kin san mato ba yawan zama yake ba,Baita kuma ya fita da Abba"

"To ya za'ayi?"
"Mameey inyi driving d'in?"
"Ina tsoron fad'an mahaifinku Janan"
"Zan dawo kafin ya dawo insha Allah"
"Okay ki kiyaye janan karki ja mana fad'a"
"Insha Allahu"
"Kije d'akina ki d'akko masu laces guda biyu da turaruka,ki basu 10k"
"To Mameey"

"Mun gode Allah ya saka da alkhairi" Zuhra ta fad'a.

Ummi kuwa ba yabo ba fallasa.

Da sauri Janan ta shiga d'akin mameey ta d'akko komai kamar yadda ta fad'a.

Suka yiwa Mameey sallama suka tafi.

          *******

A k'ofar police station tayi parking suka shiga.

Lokacin da aka fito da Aliyu saida Janan tayi mugun firgita dan kana ganinshi kasan yasha duka.

Ummi kuwa kuka ta fara yayinda Zuhra ta dafe kai tana karanto addu'o'i.

"An zalinceka yaya Allah ya saka maka"

"Idris amma akan me za'a dake shi haka?"

"Umarnine daga wurin Commissioner"

"A wane dalili akan me?"
Shiru kawai sukai dan basu san me zasu ce mata ba.

"Cab wallahi zan wa abba magana amma akan me bayan bashine da laifi ba"

"Ummi" ya kira sunanta cikin dakiya.
Kallonshi tayi ba tare da ta amsa ba

"Ina fatan keda umma duk kuna lafiya"
"Eh yaya meyasa bazasu bamu belin ka ba?"

"Karki damu ko shekara nawa zanyi anan dole zan fita"

Basu wani dad'e suna magana ba suka tashi suka fita.

Har k'auyen su Janan ta kaisu, sai da suka fara sauke Zuhra a k'ofar gidansu sannan suka wuce.


Janan kamar bazata shiga gidansu Aliyu ba sai da Ummi ta rok'eta sannan suka shiga.

Umma na ganinsu ta mik'e tsaye
"Ummi ya ake ciki ina Aliyu yake?"

"Ki kwantar da hankalinki umma yanzu ma daga gurin shi muke, an kulleshi ne akan dai matsalar data faru jiya"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un wannan wane irin zalinci ne"

Janan ta k'araso kusa da ita tace "umma kiyi hakuri insha Allahu komai zai zama normal"

"Ummi wace wannan?"
"Ita ce Janan"
"Meyasa kika taho min da ita me zata min?"

Fad'uwar gaban Janan ta yawaita,idan har Mahaifiyar Aliyu bata k'aunarta taya rayuwarsu zata cigaba da tafiya da Aliyun.

"Fitar mana daga gida" ta sinkayi muryar umma na fad'ar haka.

Har k'asa ta durk'usa tana kuka tace "dan Allah kiyi hak'uri karkiyi sanadin rabani da Aliyu"

"Rabuwarki da Aliyu tazo tunda har bazaki iya kub'utar dashi daga wannan k'azafin ba"

"Zanyi iya bakin k'ok'arina nayi maki alk'awarin Aliyu zai dawo gida gobe insha Allahu"

"Idan kuma bai dawo ba fa"

Tayi rau rau da ido tace "zai dawo da iznin Allah"

"To ki sani idan har Aliyu bai dawo gida gobe ba, babu ke bashi, ban tsaneki ba ina miki haka ne dan ki gane irin yadda Aliyu ya d'aukeki a zuciyarshi"

"To umma nagode" jikinta a sanyaye tayi masu sallama ta tafi.

Ummi tayi tsaki ta kalli ledar hannunta "umma har da bamu lace da kud'i"

"Akan me?"

"Wai kyauta ce, umma kinga kuwa yadda aka k'awata gidan wani tangameme kamar aljannar duniya"

"Ki rabu dasu sakayya zata zo nan bada dad'ewa ba, ba tana son Aliyu ba in har naga ta saka an saki Aliyu a gobe tabbas zanyi amfani da wannan damar a d'aura masu aure nan da wata gudu"

"Wallahi ni duk haushinsu nake, ita kuwa Zuhra sai yabonta take"

"Itama dan bata san wace ita ba shiyasa take yabonta, yanzu wannan kayan ajjesu zamuyi har sai ranar data shigo hannunmu zamu bata tsiyarsu".


      **********

Tana shiga umma ta sanar mata dasu Raihan sun zo suna k'aramin falo.

Da sauri ta nufi d'akin cike da zumud'i.

"Ah harda wannan 'yar rainin hankalin akazo"

Lubna tayi dariya tace "darajar besty kika ci da bazan zo ba"

"Oh zuwanshi ne kenan ba naki ba?"

"Eh mana aini na rasa tsakaninku da besty ko dai snatching kike son yimin"

"Ah to waya san abu a duhu"
"Aikuwa baki isa ba"

"Kedai kawai ki kama k'afa dani koba haka ba Raihan"

"Hakane k'awas dan besty yana mugun yinki"

"To kinji fa"

"Ai baki isa ba"

"Naji, bara na kawo maku ruwa"

Dariya Raihan tayi tare da fad'in "kodai a rud'e kike?bakiga ruwa a gabanmu ba"

Dafe goshi tayi tace "wallahi kuwa ina cikin matsala Raihan"

Labarin komai ta basu da yadda sukayi da mahaifiyar Aliyu sai dai bata fad'a masu ga dalilin rufeshi ba ta dai ce yayiwa Abba laifi ne.

"Wallahi mugun mamaki kike bani Janan"

"Mamakin me?ai kece kika dasa min son Aliyu dan  haka duk abinda ya faru ko Alkhairi ko sharri to kece Sanadi"

"Ni kuma kiji zata min sharri Raihan"

"Gaskiya ce,  gani nake kamar anyi min asari, na rasa wane irin so nakewa Aliyu wallahi har ya zarta son da nayiwa Salman"

"Baki iya soyayya ba Janan sannan kina soyayya da wanda bai dace dake ba"

"Babu rashin dace a soyayya, kuma soyayya bata shawara kiga irin cin mutumcin da nakewa Aliyu amma a yanzu shi nakeso ya kasance  abokin rayuwata"

"Cab to babu yadda Allah bayayi mu dai fatanmu Allah ya zab'a miki mafi alkhairi"

"Ameen my Raihan na san Aliyu alkhairi ne a cikin rayuwata"

Kallonta kawai Raihan take ita kam kawai hakanan taji bata son tarayyarsu da Aliyu.

Lubna kuwa tsokanarta take akan taga kyakkyawa ta d'afe masa.

Sun shafe kusan awa biyu kafin su mata sallama su tafi.







_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:14 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```





10

Bayan sunyi sallar isha'i sun ci abinci Abba ya buk'aci ganinsu a babban falon gidan.

Janan ta k'udiri niyyar zata fad'a masa cewar ya saki Aliyu dan bashi da laifi koda zai kasheta zata tsaya da k'afafunta dan k'watar masa hak'k'insa.

Su hud'u ne a falo, Abba, Mameey, Fahad, Janan duk kansu sunyi shiru, Abba ne ya fara magana da fad'in "zan saka a saki yaron nan sannan na sallameshi bazai sake aiki a gidana ba, ita kuma Fauziyya zan mata horo mai tsanani dan sai tayi wata bata fita ko ina ba, idan ta fara samun carryover zata nutsu tasan mahaifinta cikakken d'an sanda ne kuma baya da wasa"

Janan ji tayi kamar an sakata a aljanna, cikin sauk'i za'a saki Aliyu,hamdala tayi a zuciyarta ko babu komai ta san umma bazata hanata Aliyu  ba.

Fahad kuwa yaji dad'in hukuncin Abba dan bai tab'a tunanin Fauziyya zata iya abinda tayi ba.

Mameey kuwa jikinta duk yayi la'asar, a haka tattaunawarsu ta k'are.

_Washe gari_

Kamar yadda Abba ya fad'a haka ya cika alk'awarinsa dama shi kam da wuya ya fad'i magana ya k'i aikatawa, sai dai baima yarda Aliyu yazo gidan ba daga can station yace ya tafi sannan baya son ya k'ara ganinsa a gidanshi, haka ya dawo masu da labarin ya sallami Aliyu kuma babban hukuncin da yayi masa shine rashin biyansa albashinsa na wannan watan.

Janan bata ji dad'i ba amma babu yadda ta iya da mahaifinta, ita dai dad'inta d'aya an sake shi.



A b'angaren Aliyu kuwa napep ya tara ya kaishi har k'ofar gidansu.

Yana yin sallama kuwa duk kansu suka tashi suka nufo shi, dama duk suna tsakar gida suna wanki.

"Aliyu haka ka canza?meyasa mutanen nan basu da imani?"

"Umma ai wannan ba bak'on abu bane a gurinmu kin san halinsu ai"

"Allah ya saka mana, Ummi maza d'ora masa ruwa yayi wanka"

"To umma".


Bayan yayi wanka yasha maganin ciwon jiki ya huta sannan umma ta bashi labarin zuwan Janan, haka ummi ma ta bashi labarin irin cin mutuncin da aka musu kafin su samu damar shiga gidan.

"Janan zan fara azabtarwa Umma, sai na gasa mata aya a hannunta, nafi tsanarta ita da mahaifinta domin ita ta fara nuna min tsana, kuma ta zagi mahaifina"

"Bana so ka tausayawa duk wani zuri'ar Alhaji Hashim, ina son duk runtsi ka samu damar da za'a d'aura aurenku da yarinyar nan a wata d'aya"

"Duk yadda kika ce haka za'ayi umma wannan damar ce zata bani damar auren zuhra ba tare dana sha wahala ba, Janan kuwa bayan na gama k'ask'antar da ita sannan inyi mata sakin wulak'anci"

"Tabbas bazamu raga musu ba yaya domin sunyi mana babbar illa".

          ********

_Bayan kwana 4_

Janan ce ta tura k'ofar cikin sallama ta shiga.

Hankalinsa na kan takardun da yake dubawa ko bayan amsa sallamarta da yayi kawai ya cigaba da duba abinda yake.

Kan sofa ta nufa ta zauna tare da fad'in " magana nazo muyi yaya"

"Indai akan wannan mara mutuncin ce karma ki soma"

"Yaya hannunka baya tab'a rub'ewa kace zaka yanke"

Kallonta yayi tare da fad'in "idan har hannun bai isheka da azaba ba, amma idan yana azabtar dakai ai tuni zaka yanke ka wantsar dashi"

"Wannan bai azabtar ba yaya hukuncin da Abba yayiwa yaya fauziyya yayi tsauri da yawa, friends d'inta sai kirana suke ana tayi masu lectures har da test yaya ka duba fa koni Abba ya hana na ganta dan Allah ka bashi hak'uri"

"Janan Abba ya yarda da fauziyya fiye da tsammaninki shiyasa ya bata har mota ke yana ganin kina da taurin kai da rawar kai shiyasa ya hanaki amma a k'arshe ki duba kiga abinda tayi, ai Abba ya san tabbas Aliyu bashi da laifi ya saka a hukuntashi ne kawai saboda ya kasa kiranshi a waya tun lokacin da sukaje hotel kinsan Abba da zafin rai"

"Hakane amma na san Abba da ka bashi hak'uri zai sakko"

"To zan k'ok'arta nagani"

"Yawwa yaya nagode, bara na barka ka cigaba da aikinka"

"Okay"

Cike da murna da jindad'i ta koma d'akinta ta kira number Aliyu.

Tayi ringing har ta katse bai d'aga ba sai da ta sake kira, shima har ta kusa katsewa sannan ya  d'aga.

Maganar da yayi ce ta bata mamaki yadda yana d'auka kai tsaye yace "ina wani uzurin ne zan kiraki idan na gama"

"Kada ka katse min Waya Aliyu na san baka da wani Uzuri da kake"

"Kenan nayi miki k'arya?"

"A'a ba haka nake nufi ba amma ya kamata ka zamo mai yafiya Aliyu,banyi maka laifi amma kana son ka dawo da komai kaina,kullum na kiraka sai kace min kana da Uzuri bayan ba haka bane"

Ajiyar zuciya yayi sannan yace "bai kamata mu cigaba da yaudarar kanmu ba muna wahalar da zuciyoyin mu domin nasan Abba bazai tab'a aura miki ni ba"

"Baka da tabbas akan hakan"

"Ni nake da tabbas saboda an fad'a min Abba bazai muku aure ba sai kun gama masters sannan shi zai zab'a muku mijin dayaga ya dace daku,ni kuma umma tace in fito da mata nan da wata d'aya ayi bikina dan ta gaji da ganina haka babu aure, Janan na san babu yadda za'ayi Abba ya aura miki ni,bayan abinda ya faru gashi kuma ni direba ne,muna son junanmu amma dole mu hak'ura da juna"

Wani guntun hawayene ya zubo a fuskarta,tafi seconds goma kafin tace "bazamu tab'a rabuwa ba da yardar Allah please a ina zamu had'u muyi maganar?"

"A skul d'inku" ya bata amsa kai tsaye.

"Okay idan na shiga skul gobe zan kiraka"

"Allah ya kaimu"

"Ameen" ta fad'a a sanyaye.

Shi kuwa cikin murna ya ajje wayar dan ya san hak'onsa ya kusa cimma ruwa.


'Dakin Fahad ta koma ta rok'eshi daya barta taga Fauziyya,da k'yar ya yarda ya bata key d'in d'akin sannan yace ta tabbatar ta dawo dashi.

Jikinta a sanyaye ta bud'e d'akin cikin sallama ta shiga.

Fauziyyar na kan sallaya bayanta jingine da gado.

Jiyowa tayi ta kalleta tayi murmushi "sai yau zakizo ganina ko?"

Yadda Janan taji muryar Fauziyya ta canza sai tayi matuk'ar bata tausayi.

Zama tayi kusa da ita tace "kinsan Abba yace kada a bari kowa yazo wurinki"

Kamo hannunta tayi ta rik'e wasu zafafan hawaye suka zubo a fuskarta "Janan na san Abba yana fushi dani,watak'ilma yanzu ya tsaneni ko kuma yana dana Sanin haihuwata"

Da sauri ta rufe mata baki tare da fad'in "haba dai ki daina fad'in haka kina nan a zuciyar Abba kamar yadda kike da" ta k'arasa maganar tana hawaye

"Hmmm Janan kenan na san halin Abba kuma na san tabbas yana fushi dani amma ki rok'ar min gafara gurin Mameey da Aliyu,ina ganin kamar gawata ce zata fita a d'akin nan"

"Ya salam!dan Allah ki daina furucin nan Yaya Fauzah komai fa zai wuce"

"Na sani Janan amma ina jin ciwon  abinda na aikata duk da Allah ya kub'utar dani Aliyu yana da hali mai kyau amma da wani ne na san da tuni mutuncina ya zube kuma duk laifin Abba ne da Sharrin k'awa,Janan k'awa tana da mugun had'ari"

"Wacece ta baki shawarar nan?"

"Zubaida ce,amma kin san da laifin Abba"

"Abba d'an boko ne addu'a kawai zamu cigaba dayi,ita kuma Zubaida wallahi sai ta gane kurenta wato shiyasa ta dameni da kira tana tambayar ina kike"

"Ni dai fata na kowa ya yafe min zan yi k'ok'arin gyara laifina"

"Allah ya yafe mana baki d'aya"

"Ameen,yanzu ina Aliyun?"

"Kinsan Abba ya koreshi ko albashin watan nan bai ba shi ba"

"Kanga matsalar ko Janan,amma ya kamata ace ya bashi hak'k'insa"

"Abba yana da zafi sai dai muce Allah ya sassauta masa zamuyi iya bakin k'ok'arin mu dan ganin mun fitar dake daga wannan k'angin"

"Janan kenan,ni wallahi bana son fita saboda kunyar had'a ido da Mameey"

"Mameey ta san baki da laifi duk aikin shaid'an ne wannan"

"Hmmm"

"Zan tafi kada a gane ina nan,idan na samu chance zan sake zuwa"

"Shikenan Janan nagode"

"To saida safe"
"Allah ya kaimu"
"Ameen"

Jan k'ofar tayi ta rufe,ta maidawa Fahad key d'in sannan ta tafi d'akinta da Zumud'in gobe tayi su had'u da Aliyu.






_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:14 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
       🍁🍁🍁


*_by SaNaz deeyah_*👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```



11

Batayi bacci da wuri ba hakan ne yasa ta makara sosai,dan sai kusan k'arfe 6:30am ta farka,ko sallar asuba batayi ba,da sauri ta fad'a bathroom ta d'ora alwallah ta fito ta gabatar da farilla.

Komawa ciki tayi tayi wanka ta fito ta fara shirin fita.

'Karfe tara ta fito k'aramin falo dan gabatar da break fast,sanye take cikin wani Swiss material  yellow da touch d'in red a jiki,ta yana d'an k'aramin veil(million stones), fuskarta d'auke makeup yauma ta saka fashion glass d'inta brown color,tayi kyau ainun.

Bata tarar da kowa a dinning area ba dan haka ita kad'ai ta zauna tayi breakfast sannan ta tashi ta nufi d'akin Mameey.

Da sallama ta shiga ta gaidata sannan tayi mata sallama,harta juya zata tafi Mameey tace "waye zai kaiki?"

"Baita! na fad'a masa tun jiya"
"Okay ki kula"
"Insha Allahu"

       *******

Suna zaune a plantation suna hira bayan sun fito daga lecture,Raihan ta kalleta tace "naga kina yawan duba time lafiya"

"Eh lafiya lau ina dubawa ne saboda Aliyu yace k'arfe sha biyu zaizo"

"Amma Janan me zai miki?"

Dariya tayi tana sake duba agogon hannunta tace "yanzu har an tambayi dalilin zuwan saurayi gurin budurwarsa"

"A'a amma ai inajin kinsan zamu shiga lecture na cost Accounting ko?kuma 12 d'inne sannan kinsan halin Mr Eze"

"Ki min attendance bazan samu damar shiga ba"

"Lallai yarinyar nan kin shirya rungumar  carryover kenan"

Kallonta tayi ta yatsina fuska tace "kawai dan banyi attending lecture guda 1 ba sai in samu carryover?"

"To naga kina neman yin wasa da karatunki Janan"

"Kinga Raihan ki rik'e wannan jawabin idan na dawo kin d'ora daga inda kika tsaya Aliyu ya kirani" da sauri ta tashi ta bar gurin.

"Ohni Raihan ya Allah ka magancewa Janan wannan mahaukaciyar soyayyar".

Janan kuwa tana barin gurin ta d'aga kiran " hello kana ina?"
"Inda kika ce mu had'u"
"Okay gani nan"

Cike da zumud'i ta nufi side d'in can wajen Faculty of engineering dan nan ne babu mutane sosai.

Tunda ta hangoshi take murmushi shi kuma gaba d'aya idanuwansa a kanta yana ta shiryo irin muguntar da zai shirya mata.

"Barka da zuwa"

"Yawwa sarauniya" ya fad'a yana murmushi.

Zama tayi kan kujerar dake facing d'insa ta kalleshi tace "kamar kana cikin damuwa"

"Eh damuwa mara misaltuwa kuwa"

"Subhanallah meya faru?"

"Gani nake kamar zan rasa ki Janan,kuma rasa ki tamkar rasa rayuwata ne" ya k'arasa maganar kamar zaiyi hawaye.

"Ka daina fad'ar haka Aliyu"

"Dole ne na fad'a saboda muna cikin had'ari sosai,muna da banbanci dake sosai gashi umma ta sakoni a gaba"

"Bamu da wani banbanci saboda dukkanmu mutane ne kuma munzo daga Adamu da hauwa'u"

"Janan kenan! Meyasa kike b'oye abubuwan da suka zama gaskiya,na tabbatar ba Wanda yake son tarayya ta dake har k'awayenki taya ya zamu samu damar zama abu d'aya"

Shiru tayi tana kallonsa kawai.

"Kinyi shiru?"
"Eh bani da abin cewa"
"Kamarya?"

"Aliyu ban san taya zan maka yadda zaka fahimta ba,ni a ganina indai har muna son junanmu ai babu ruwanmu da k'iyayyar mutane"

"Kin tabbatar?"

Kai ta d'aga alamar eh.
Murmushi yayi tare da cewa "indai har kin yarda da hakan inason ki fad'awa Abba cewar ni kike so kuma zan turo magabatana cikin satin nan,sannan ina son duk runtsi karki yarda a rabaki da masoyinki a karo na 2"

Mik'ewa yayi tsaye ya had'e hannayensa tare da fad'in "ina son a yau ki jajirce ki nunawa mahaifanki nine masoyinki wanda kika zab'a a matsayin mijin aure"

Gabanta yayi mummunar fad'uwa a zuciyarta take fad'in _taya zan furtawa Abba wannan kalmar?lallai na d'ebo dala ba gammo tabbas za'ayi wani d'an k'aramin yak'i a gidan nan_

"Idan kina son mutum karki ji kunyar bayyana soyayyarshi ga kowa" ta tsinkayi muryar Aliyu na fad'ar haka.

Shiru tayi dan ji take gaba d'aya tamkar babu jini a jikinta,Aliyu ya sake fad'in "zan tafi ina sauraren wayarki da daddare akan duk yadda kukayi da Abba"

Barin gurin yayi ba tare daya jira amsarta ba,tafi minti talatin tana zaune ta kasa ko motsawa sai da taji wayarta na ringing sannan ta duba,ganin Abba ne yasa ta firgita har ta mik'e tsaye.

Jikinta na tsuma ta d'aga kiran
"Kome kike ki dawo gida yanzun nan"

"Abb......." Bata ma k'arasa fad'a ba taji ya katse.

Hannu ta d'ora aka tare da fad'in "na shiga uku ba dai Aliyu yaje gida ya fad'a ba"

A sanyaye ta lalubo number baita tace yazo ya d'auketa,gashi a lokacin ana musu lecture gashi suna da wata ma 2-4 amma babu dama dole ta bi umarnin Abba"


Driver na yin parking tayi saurin fita ta doshi hanyar main parlor d'insu.

Tunda ta hango Abba a tsaye ya hard'e hannu a gefe ga Fahad da Mameey zaune kan kujera sunyi shiru ta san tabbas akwai matsala.

Jikinta a sanyaye ta k'arasa gabanshi ba tare da ta kalleshi ba tana neman ta tsugunna kawai taji ya sakar mata wawan mari.

Tsawon dak'ik'a goma tana rik'e da kuncinta ta d'an duk'a kamar mai shirin yin ruku'u.

'Dago kai tayi ta kalleshi cike da mamaki bata san dalilin marin ba.

"Ni zaki nuna wa aikina Janan?"

Shiru tayi bata ce komai ba,ya cigaba da fad'in "har ni zaki aiko Fahad ya ce min hukuncin da nayi wa Fauziyya yayi tsauri?kuma uban waya baki damar zuwa police station keda k'annen Aliyu"

Sai a lokacin sautin kukanta ya fito,ta d'ago kai ta kalleshi idonta a fek'e tace "Abba wannan dalilai biyun sune zasu Saka ka mareni"

"Ni kike fad'awa haka Janan?" Yayo kanta Mameey tayi saurin tasowa ta tare ta.

"Ki matsa yau in kawo k'arshen rawar kan Janan"

"Abba kayi hak'uri na fad'i hakane saboda ciki d'aya muka fito da Fauziyya,Aliyu kuwa shine ..........."

Sai kuma tayi shiru tana shashshek'ar kuka.

"Aliyu uban meye fad'amin"

"Ka gafarceni Abba,Aliyu shine wanda nake son na aura kuma cikin wata d'aya me zuwa"

Jikinta ya fara karkarwa tun kafin hukuncin da Abba zai mata yazo.

Code ya ciro ya fara tsula mata,kuka sosai take amma taurin kai ya saka tak'i tashi daga gurin(Juliet ko ince laila majnoon).

Cikin zafin rai ta rik'e wayar tace "ka barni haka Abba ka bari in kashe kaina da kaina.

Mamaki ya sashi ya tsaya ya daina dukan nata.

Cikin kuka ta cigaba da fad'in " Ka gafarceni Abba"

"Janan kin haukacene?" Mameey tayi tambayar a razane

A galabaice ta kalli Mameey tace "Mameey wallahi son gaskiya nake masa kada kusa ya rasa ransa kamar yadda Salman ya mutu a dalilina,zaku rasa ni idan har kuka hanani auren zab'ina a karo na biyu"

Fahad ya taso ya rik'eta yana jijjigata "Janan ki dawo hayyacinki"

"Fahad maza kirawo Family doctor" Abba ya fad'a.

Kallon Abba ta sake yi tace "karka zama sanadi Abba"

Kamar jira ake ta gama fad'a ta langwab'e kanta wanda suka kasa gano shin a raye take ko kuwa ta mutu.






_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:15 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
       🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



Dis page goes 2 Hawwy Garba(Ambaby),tnx 4 d luv n support,am glad 2 hav u as bst sista,a sista 4rm another mother❤words can never express how mch i luv u...i jst mean it.....tnx u 4 everything😍😍



12

_Bayan wasu mintuna_

Tana kwance akan gadonta tana baccin wahala,rabin jikinta a kan cinyar Mameey yake haka hannunta ma Mameey ta rik'eshi gam.

Abba na zaune a gefensu yana kallonta ransa duk a b'ace shi dai Allah ya jarabceshi da 'ya mai taurin kai.

Gyaran murya yayi ya kalli Mameey yace "wace irin yarinya ce Allah ya bani wadda take da taurin kai,Janan ta san bazan aurar da ita ba yanzu to akan me zata bi ta damu kanta?sannan Sanin kanta ne bata dace da irin mazan nan ba"

Cike da mamaki Mameey take kallonsa,ya cigaba da fad'in "ko zanyiwa Janan aure ai bazan tab'a aura mata wanda baya da albashin da zai rik'e kanshi bare iyalinsa ba"

"Kamarya?me kake nufi?Janan baiwace wadda Allah yayi maka dan ka gane illar abinda kake,ka kasa gane mutum bashi yake yiwa kansa arzik'i ba,dan haka a wannan karon zan jajirce a matsayina na Uwa dan ganin na aurawa Janan zab'inta tunda bashi da wani gurb'ataccen hali"

"Wallahi baki isa ba,ni nake da ikon zab'a musu mijin daya dace dasu,kuma bazan tab'a aurawa Janan wannan yaron Aliyu ba kamar yadda ban aura mata Salman ba"

"Idan har da ranmu kuwa kaine mad'aurin auren Janan da Aliyu bata da uba daya wuce kai sannan a wannan karon dole ka barta ta Auri Aliyu dan bazaka saka rayuwar 'ya'yana ta salwanta ba gashi kana so ka sabauta min Fauziyya duk ba kaine silar komai ba" ta k'arasa maganar cikin fad'a.

"Okay ai ga fili ga mai doki kisa in aura mata Aliyu mutumin da yayi yunk'urin lalata 'yar uwarta"

"In har da ranka zaka ga aurensu kuma kaine waliyinta,sannan ka daina alak'anta yaron nan da abinda bai aikata ba dan Fauziyya ta fad'i gaskiyar komai"

Haka Abba da Mameey sukayi Baran baran, Fahad daya dawo haka yayi ta bin kowa yana bashi hak'uri amma abin yaci tura.

Haka ya hak'ura ya zubawa sarautar Allah ido,gidansu daya kasance kullum cikin nishad'i yau gashi shiru tamkar anyi rasuwa.

          ***********

Yana ta aikin yiwa d'akinsa fenti da sauran 'yan gyare-gyare,Nura da Nazifi Wanda suka kasance aminansa suna aikin zagaye b'angaren nashi da jar k'asa.

Ummi ce ta k'araso gurin tace "Yaya kazo inji umma"

Hannu ya saka ya yarfe zuffar goshinsa sannan yace "kice ina zuwa"

Tafiya tayi,shima ya d'ebi ruwa ya wanke hannunsa sannan ya k'arasa gurin umma.

"Umma gani" yana fad'a yana k'ok'arin zama

"Sannu da aiki Aliyu"
"Yawwa umma"

Shiru ta d'anyi kafin tace "Aliyu kun gama magana da yarinyar?"

"Eh umma amma jiya na kirata dan jin yadda sukayi da mahaifinta naji wayarta a kashe na san k'ila ta samu matsala ne daga shi dan dama na san hakan zata faru"

"Kana ganin babu matsala?"
"Da yardar Allah umma"
"Toh Allah ya ida nufi"
"Ameen Umma,ina son a had'a komai kafin azo biki,inason na had'a mata lefe ma"

"Lefe kuma?"
Umma ta fad'a tana masa kallon Mara hankali.

"Ina son in had'a akwati guda in kai mata,a matsayin lefe ina son mahaifinta ya fara ganin b'acin rai tun kafin bikin,zan saka k'ananun atamfa guda hud'u,man shafawa 1 makilin da brush,sai reborn biyu hijabi da mayafi d'aya sai takalmin roba da sark'a da d'ankunne d'aya d'aya shikenan fa"

"To ba damuwa Allah taimaka" ta fad'a ba dan ranta yaso ba.

         *******

Tana zaune akan gadonta idonta na kallon silin yayinda hawaye ke bin kuncinta.

Mameey ce ta turo k'ofar ta shigo cikin sallama.
A hankali ta amsa mata sallamar idonta ya koma kan Mameey.

'Karasowa kusa da ita tayi ta dafa ta "Janan bazaki bar kukan nan ba,tun jiya kike abu d'aya"

Kamo hannun Mameey tayi ta rik'e,gwiwowinta a k'asa tana kuka take fad'in "Mameey ki taimakeni ban san ya zanyi ba wallahi Mameey tausayin talaka da yanda mutane ke wulak'anta su yasa na fara son Aliyu,ban tab'a tunanin zan so shi haka da yawa ba dan Allah ki tayani da addu'a Mameey ina ganin tamkar na haukace ne"

Rungumeta tayi tana rarrashinta tare da alk'awarin yau za'a bata damar tace wa Aliyu ya turo magabatanshi.

'Dago kai tayi ta kalleta tace "Mameey taya ya?Abba bazai tab'a yarda ba"

"Abba shima ai yana da manya ko?na sanarwa su Alhaji babba kuma yanzu haka ya kira shi yace yaje yana son ganinsa a wannan karon bazan bari rayuwarki ta shiga had'ari ba"

Hannu tasa tana goge mata hawayen tana fad'in "tashi muje falo"

Ita dai jikinta a sanyaye yake haka Mameey ta kama hannunta suka fita.

Suna zaune Mameey ta kunna tv suna kallo saboda ya d'ebe mata kewa ta saki jikinta.

_2hrs later_

Janan na kitchen tana had'a musu fruit salad taji k'arar motocin su Abba da alama ya dawo.

'Kirjinta sai buguwa yake dauriyace ta saka kawai ta cigaba da abinda take.

Kamar daga sama taji muryar Abba yana fad'in "ina Janan d'in".

Da sauri ta ajje wuk'ar hannunta ta koma falon a tsorace.

"Kin zab'i d'a namiji akan ni mahaifinki ko?kin zab'i aure akan karatunki ko?to ga Aliyu nan zan aura miki shi"

"A'a dakata Alh karka mata baki mana,idan har baka sanya alkhairi ba to kaja bakinka kayi shiru"

"Kin kaini k'ara gurin Alhaji babba kin sa ammin dole akan abinda banyi niyya ba to wallahi duk sai kun fuskanci hukunci daga gurina"

Da sauri ya haye sama shida guards nashi guda biyu.

Hawaye ne ya fara sauka daga fuskar Janan,ta kalli Mameey tace "Mameey kawai na hak'ura"

"A'a Janan ki k'yaleshi zai sakko"


Suna nan zaune a falon ya fito,da sauri Janan ta sauke kanta k'asa dan wani mugun tsoro ne ya ziyarceta.

Zama yayi kan kujerar dake gefenta,tayi saurin sulalewa k'asa ta zauna.

"Ki ce masa ya turo iyayenshi gobe,ke kuma ki shirya wani satin zan d'aura aurenki dashi kuma zaki bar min gida a ranar da aka d'aura aurenki,sannan na janye hannuna daga komai naki mijinki ne keda iko dake idan yaga dama ki cigaba da karatu idan baiga dama ba kanki,idan yaga dama ku zauna a daji ma ba gidan k'asa ba wannan ba damuwa ta bace abu d'aya zan sake nanata miki duk abinda ya biyo baya karki nemeni matuk'ar bazaki canza ra'ayi ba"

Da sauri ta d'ago kai ta kalleshi hawaye gaba d'aya ya wanke fuskarta.
Kafin tayi magana taji Mameey tayi saurin fad'in "sai kuma aka yi sa'a mamanta 'yar kasuwa ce kuma tana da arzik'i dai-dai gwargwado dan haka zan basu gidana dana gama ginawa su zauna,dama nayi shine ina son in bawa Fahad shi kyauta amma na barwa mijin Janan halak malak,ni dai fatana ka d'aura aurensu amma bance ka bada komai ba zan zamto Uwa da uba a gareta zan share mata hawayenta kuma duk abinda ya taso zan mata shi"

"Da kin kyauta" ya fad'a tare da tashi ya koma sama.

Janan ta matso ta rungume Mameey ta cigaba da kuka.

"Karki damu ki share hawayenki ki kira Aliyun ki fad'a masa ya turo iyayenshi gobe sannan ni zan bashi jari ya fara Sana'a mai kyau wacce zata rik'eku kuma zan bashi takardun gidan yayi signing na bashi ku zauna ku rayu a ciki,ko babu komai Aliyu ya ceci rayuwar fauziyya dan da yanzu ta shiga gurb'atacciyar rayuwa"

"Mameey Allah ya biyaki da gidan aljanna" ta fad'a tana goge hawaye.






_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:15 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU* 
        🍁🍁🍁



_by SaNaz deeyah_👄




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```



*_wannan shafin nakune kyauta Ummi,Asma'ul husna,Aunty Ramlat,Rabi'atu Adam,Zulaihat.......godia da soyayyarku ga ni da novels d'ina gaba d'aya ina yinku sosai_*



*_Mrs Xerks ban san da wani kalamin zan miki godia ba sai dai in k'ara godewa Allah daya bani mai sona da zuciya d'aya,fatana Allah ya barmu tare🙏_*



13

****
Cike da murna yazo ya sanarwa da Umma yadda sukayi da Janan.

Farin ciki ya rufe ta sosai har da goge k'wallah,lallai ta yarda Allah maji k'an bawa ne.

"Kaje k'auyen ka sanarwa su baffa idi da baffa mu'azu sai su shirya suje gobe a had'a harda sadakinta"

"To Umma"
"Yanzu zakaje fa kar lokaci ya k'ure naga kamar kana shirin fita wani wajen"

"Eh dama zanje gidan su Zuhra ance baffanta yana nemana,so daga can sai in wuce k'auyen su baba idin"

"A'a bana son ayi sanya ka dai fara zuwa k'auyen tunda su Malam Zakar muna tare idan ka dawo sai kaje"

"To umma"

Haka kuwa aka yi sai da yaje k'auyen ya sanar musu komai sannan ya bada dubu 11 a matsayin sadakinta dan baya da ko sisi.

Yana dawowa ya sauka a gidansu Zuhra,yaci sa'a kuwa Malam d'in yana zaure da samari biyu yana musu d'orin karatu.

Ya gaidashi ya samu gefe ya zauna,Malam ya bawa samarin umarnin su d'an bashi guri ya gana da shi Aliyun,tashi sukayi cikin girmamawa suka yiwa Malam sallama suka fita.

"Aliyu bismillah"
Tashi yayi ya dawo kusa da Malam.

"To dama magana ce nake ji jite-jite cewar wai zakayi aure cikin watan nan shine nakeson jin gaskiyar lamarin"

"Hakane Malam amma............"
"Ya isa haka" Malam ya tari numfashin sa tare da fad'in "karkace komai ai shi aure nufi ne na ubangiji fatana dai Allah ya tabbatar da alkhairi"

"Ameen Malam" ya fad'a jikinshi a sanyaye.

"Kajeka ba komai zan sake nemanka"

Babu k'warin gwiwa ya koma gida,Umma da ta ga yanayinsa ta tsorata sosai tunaninta ko wata matsalarce,sai  daya bata labari sannan hankalinta ya kwanta ta kuma tausasashi akan indai tana raye sai ya auri Zuhra.

Da dare haka ya shirya ya nufi gidan su Zuhran, koda ya aika tazo ma bata sauya a yadda ya saba ganinta ba da kuma yadda suka saba hirarsu hakan yasa hankalinshi ya kwanta sosai.

            *********

Tana kwance a kan gado tana ta juyi tunani babu wanda batayi ba,Raihan ce ta turo k'ofar ta shigo.

"Cab lallai yarinyar nan a kwance kike ma"

"Raihan"

"Dalla ki tashi meya hanaki shiga skul?wlh test zamuyi k'arfe 2 kinsan yanzu ma muka gama lecture barrister Sanusi yace mu yago paper mu rubuta test,na samu na miki amma kinsan ta statistics dole kizo kiyi dan kin fini iya calculation"

"Raihan anya kuwa zan iya nutsuwa inyi?"

"Saboda me?"
"Saboda ina cikin cakwakiya,ko kinsan wani satin bikina"

Mtsww "dalla malama bana son wasa"

"Wallahi dagaske nake"
Labarin yadda sukayi da Abba da Mameey ta fad'a mata sannan ta k'ara da cewa"a tsorace nake Raihan,gani na nake tamkar mahaukaciya,saboda Aliyu na rufe idona na kasa janyewa Abba fushi yake dani"

Raihan ta dafa ta tace "ki daure ki hak'ura tunda kinga Abba baya so Janan ni kaina wallahi bana son tarayyarki da Aliyu"

"Meyasa?" Ta fad'a cike da mamaki

"Wallahi kawai zuciyata bata kwanta dashi ba"

"Ina sonshi Raihan dan Allah kiso abinda nake so,wallahi bazan iya rabuwa da Aliyu ba ban san wane so nake masa ba amma a cikin jinina nake jin son Aliyu"

Ajiyar zuciya tayi tace "Allah ya tabbatar mana da alkhairi,ina Yaya Fauzah ne?"

Shiru ta d'anyi sannan tace "taje Abuja gidan kawu"

"Ah ah amma ai ba Hutu sukayi ba"

"Eh an turata research shine ta zauna a can amma tace min zata dawo upper week"

"Okay Allah ya kaimu,shirya mu tafi skul"

A gurguje ta shirya suka fita,sai da ta biya ta b'angaren Mameey tayi mata sallama sannan suka wuce driver ya kaisu.

Bayan sun fito daga test ne Raihan take bawa Lubna labari lokacin suna tafiya zasuje department suyi submitting wani file na Lubnan.

Dariya sosai Lubna keyi tana fad'in "ita fa wannan k'awar tawa so take ta rigani yin aure,ita a dole sai tayi gasa dani gashi ta k'wacemin kyakykyawan saurayina"


Janan ta d'an doketa a baya tace "to shikenan na fasa aurenshi kinga sai mu auri besty mu biyu"

"Cab wlh ban yarda ba kowacce ta rik'e nata" ta fad'a tana yarfa hannu fuskarta d'auke da annashuwa.

Ita dai Raihan sam bata so dan gani take Janan bata dace da Aliyu ba,tafi dacewa da gidan hutu yadda take haka kamar a hure ta,ta san bazata iya jurar wahala ba.

"Kunji wayata na ringing ban ma sani ba muna ta surutu"  Janan ta fad'a tana bud'e jaka zata lalubota,suna tafiyar wayar nata ringing ga jakar duk ta baza kayan make-up tana ta lalube sunzo dab da shiga kawai taji tayi karo da mutum,da sauri ta d'ago kai suka had'a ido.

_A karo na biyu kenan._
Ya fad'a a zuciyarsa sannan ya sake kallonta yace "ke! Baki da hankali ne?karo na biyu kenan kina bugeni"

"Dan Allah kayi hak'uri Yarima" Raihan ta fad'a.

Ya kalli Raihan yace "Kece bakinta?ita bara iya bada hak'uri bane"

"Amma duk d'aya ne kayi hak'uri mana" Lubna ta sake fad'a

"Wallahi sai ta bani hak'uri da kanta"

Kallonshi kawai Janan take cike da mamaki,shi d'an gidan uban waye da zata bashi hak'uri bayan a wancan karon hak'urin nata baiyi tasiri ba,ji tayi abin  daya faru ya dawo mata sabo.

"Bazan bada hak'uri ba,shi d'an gidan waye?wlh bai isa ba na bashi hak'uri idan yana tak'amar shi d'an wani ne nima haka,kawai bana son fitina shiyasa a wancan karon ma ban d'auki mataki a kansa ba"

Raihan tayi saurin rufe baki cike da tsoron abinda zai biyo baya.

Matsowa yayi dab da ita yace "kina son sani?"

Tsaki tayi ta matsa tare da bin gefenshi zata wuce ya fizgo hannunta ya dawo da ita "yau zaki san waye babana"

"A'uzubillah! Dalla Malam sakarni" ta fad'a cikin tsiwa

Dariya yayi ya sake fad'in "dole yau kisan babana" ya fizgeta yana tafiya su Raihan suna bashi hak'uri baibi takansu ba,ita kuwa sai fuzgewa take amma yak'i sakinta,abin mamaki duk mutanen dake gurin aka rasa wanda zai dakatar dashi.

Bayan motarshi ya bud'e ya watsata ya rufe sannan ya shiga yaja.

Raihan ta dafe kai tace "mun shiga uku lubna"

A rud'e lubna tace "bara na kirawo number Mameey na fad'a mata a sanarwa da Abba"

"A'a lubna hakan zai zama matsala kinsan dai su waye iyayensa shima,ki dai bari muga yadda Allah zaiyi,idan Mameey ta kirani ko ke sai muce bamu gama lecture bane,idan dare yayi muce mun san ta tafi gida amma bamusan inda ta tsaya ba,kar mu jawa kanmu da iyayenmu tashin hankali Janan k'awarmu ce amma kinsan matsayin ba d'aya bane"

"To Allah ya tsareta daga sharrinsa"

"Ameen"

A b'angaren su Janan kuwa sai k'ok'arin bud'e k'ofa take ta kasa,cikin zafin rai tace "ina zaka kaini?"
"Zan kaiki kiga waye ubana"
"Wallahi zan yi ihu in fasa glass in tara maka jama'a idan baka tsaya na fita ba"

Dariya sosai yayi harda buga sitiyari ya kalleta yace "kinga sai ince mahaukaciya na d'akko"

Ganin dai da gaske yake sai ta fara masa magiya tana rok'on ya k'yaleta,bai sake ce mata komai ba har suka isa wata unguwa haka wajen garine dan ba gidaje sosai,abin ya bata tsoro sosai lokacin da suka isa k'ofar wani katafaren gate,horn yayi akayi sauri aka bud'e gate d'in masu gadi biyun nan da suke bakin gate bata ga alamar wasu mutanen bayan su ba.

Akwai tazara sosai tsakanin gate d'in da manya-manyan ginin na gidan har part uku duka bene ne.

Fitowa yayi ya bud'e k'ofar tana shirin fitowa taji ya sake fizgota ya nufi d'aya daga cikin part d'in.

Remote ya danna k'ofar ta bud'e ya jata suka shiga k'ofar ta maida kanta ta rufu.

A katafaren falon wanda yayi matuk'ar bata tsoro ya hankad'ata k'asa,ya sunkuyo tare da rik'e hab'arta "kina son sanin waye ubana ko"

"Dan Allah karka cutar dani kaji tsoron Allah"

Murmushi yayi wanda har suka bayyana hak'oransa,tashi yayi tare da fad'in "yanzu kika san Allah?"

Jikin wani d'in glass drawer yaje ya bud'e ya d'akko Shisha,gabanta ya sake fad'uwa zuciyarta ta tsinke lokacin da taga ya janyo center table ya ajjeta akai yana zuk'a yana furzar da hayak'in.
"Ko zaki sha?" Ya fad'a yana turo mata.

Girgiza kai kawai take lokaci guda hawaye na zuba a idonta.

Sai daya sha ta ishesa sannan ya tashi ya kalleta yace "ki gama kukan ki goge hawayenki ki Shafa hoda ki gyara lipstick d'in kan lips d'inki sannan uban nawa yazo ki ganshi ko"

"Dan Allah kayi hak'uri karka ruguza rayuwata"

Dariya ya sake yi sannan ya d'auki jakarta ya fiddo wayarta ya danna Switch "ah kinga missed calls,bara na kashe kar a damemu" ya kashe wayar ya zura a pocket d'inshi.

Ganin yayi hanyar fita yasa ta rusa uban ihu,da sauri ya juyo yace "zaki lalata muryarki fa dan wallahi babu wanda yake jinki daga Allah sai ni,in zaki shekara kina kuka da ihu babu wanda zai sani idan ba ya shigo ba,dan haka ki sassauta ranki kar ubana yazo yaji muryarki a dashe,kid'an goga lipstick d'in dan babu alamar kin shafa duk kin goge shi da hawayenki" da sauri ya fita ta taso da gudu zata bishi k'ofar ta rufe.

Zubewa tayi a gurin ta cigaba da kukan da babu mai jinta.








_Sadeey S Adam_
[9/29, 8:15 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
       🍁🍁🍁




_*by SaNaz deeyah*_👄



_Ayshat A Muh'd wannan shafinki ne ke da masoyanki❣ ki d'au rabi ki raba musu sauran😊,Allah ya bar zumuncin dake tsakaninmu Ameen🙏_





14

Sai data gama kukanta har ta gaji sannan ta duba agogonta taga k'arfe 3:45pm,da sauri ta mik'e tsaye tana goge guntun hawayenta ga yunwa ga shi ko azzahar batayi ba.

Kallon k'ofofin falon tayi daban-daban ga wani k'aton dinning area a gefe sai bene side biyu.

_to waye babanshi da har zai mallaki wannan kud'in?shin waye shi?duk yadda akai shi d'an gidan shugaban k'asa ne,to amma ai na san 'ya'yan shugaban k'asa,to d'an waye???_
Gabanta ya yanke ya fad'i lokacin da wata zuciyar ke ce mata _masu garkuwa da mutane ne_

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un wayyo Mameey Ku cece ni" wani sabon kuka ta rushe dashi lokaci guda ta nufi k'ofar da zuciyarta ta raya mata.

Tana turawa taga wani falon ne amma bai kai wancan girma ba,kallon falon kawai take tana jinjina irin dukiyar da aka kashe wajen k'awata shi,wasu k'ofofin ta sake gani kai tsaye ta nufi wadda take facing d'inta.

Tana tura k'ofar ta tsaya cak zuciyarta cike da tsoro.

Yadda taga k'ayatuwar d'akin ko bedroom d'in Mameey daya fi ko wanne kyau a gidansu bai kaishi ba,baza ta iya fasalta kyawun d'akin ba.

A hankali take tafiya tana k'ara kallon d'akin k'ofofi biyu ta sake gani a ciki wanda ta tabbatar d'aya daga ciki toilet ne.

Tana tura ta side d'in dama taga d'an k'aramin d'akina ga  qur'ani guda uku a mazauninsu,sai sallaya guda d'aya mai matuk'ar kyau a shinfid'e kan lafiyayyan carpet daga gefe kuma d'an k'aramin fridge ne.

Janyo k'ofar tayi ta rufe sannan ta nufi ta left hand side d'inta,tana turawa taga toilet ne makeke shi Kansa abin kallo ya zame mata duk da tana cikin tashin hankali.

Alwallah tayi ta nufi wancan d'akin da taga sallaya ta shiga tayi sallah sannan ta janyo Qur'an ta fara karantawa tana kuka,can ta duba agogon hannunta taga k'arfe biyar har da minti sha tara "na shiga uku,na san su Mameey suna ta nemana,me bawan Allah nan yake nufi dani?ko dai da gaske kawoni yayi ya yanka kamar yadda zuciyata ke fad'a"

Tashi tayi ta koma falon ta zauna,idonta ya k'ank'ance fuskarta tayi jajir saboda kuka.

Har ta gaji da kukan ta daina kawai ta zubawa sarautar Allah ido.

Ganin duhu ya d'an farayi ta k'ara tsorata ta tashi tana d'an zagaye ga yunwa na neman halaka ta,kamar daga sama taga haske ya bayyana a gidan,nepa ce ko generator oho!.

'Dakin ta koma tayi sallar Magrib ta duba fridge d'in babu komai a ciki sai ruwa.

"Wayyo Mameey zan mutu" ta fad'a tare da sulalewa k'asa ta lumshe idonta kawai tana jiran Allah yayi ikonsa a kanta,gani tayi d'akin harya fara juya mata rabonda taci abinci tun jiya da rana.


         *********

Mameey na zaune akan kujera tana kad'a k'afa.

Kallon Fahad tayi tace "wai har yanzu bata d'auki wayar ba?"

"Ai a kashe ma wayar take tun d'azu"

"Wannan wane irin shashanci ne ta san zamu nemeta saboda yau akayi za'a zo ayi magana,gashi mutanen har suka tafi babu ita,ina Aliyu ya tafi?"

"Ya hak'ura ya tafi shima tun d'azu"

"Janan bata da kirki"

"Mameey ki barni da ita wlh sai na b'ata mata,gidan wa zataje ta kai dare haka gashi har magriba tayi"

Sallamar Raihan ce ta dakatar dasu,bayan ta gaidasu ta zauna tace "Mameey na kira number Janan tun d'azu bata shiga ba,shine nazo naga ko lafiya saboda tace zamuyi magana idan ta koma gida"

"To kinga tunda kuka fita bata dawo ba muma sai kira muke wayarta a kashe" Mameey tayi maganar

"Tun yaushe kuka rabu" muryarta na d'an rawa alamun rashin gaskiya ta d'an dake ta kalli Fahad tace "tun wajen 6:15pm da yake yau sai 6:00pm muka gama lectures "

"To Mameey maybe ta tsaya a wani gun tunda yanzu 6:30pm mu d'an jira mu gani"

"To amma meyasa ta kashe wayar bayan ta san za'a nemeta?" Fahad ya sake jefowa Raihan tambaya.

'Dak'ar ta lalubo kalmar "eh tace min Aliyu nata kiranta gashi muna lecture shine tace bara ta kashe idan mun fito sai ta kirashi to maybe ta manta bata kunna ba.

" kiji wani shashanci irin na Janan"
 "Mu dai jira mu gani".


           *********

Tana kwance taji alamun an bud'e k'ofa idonta a rufe take karanto addu'ar da duk tazo bakinta.

"ba dai bacci kikayi ba ga babana yazo" jin muryarshi ne yasa tayi saurin bud'e ido tare da mik'ewa zaune.

Manyan ledoji guda biyu a hannunsa ya dire mata "na san kina jin yunwa"

Wani sabon kukan ne yazo mata,ta had'e hannunta tana fad'in "kayi hak'uri dan Allah karka cutar dani ka maidani gidanmu na san ana ta nemana"

"Zan mayar dake amma sai kinci abinci sannan kinmin abinda ya kawoki"

"Karka cuceni dan Allah"

"Na miki kama da macuta?"

Bata bashi amsa ba kawai kallonshi take yana bud'e ledojin,takeaway ya fitar ya bud'eshi, lafiyayyan shinkafane da coslow a gefe,sai d'ayan ledar da wani  yogurt,lemuka,shawarma,pizza da kaji.

Kallonta yayi yace "bismillah"
Kai ta girgiza tace "na k'oshi"
"Baki son tafiya gida kenan?"

"Idan naci zaka kaini gidanmu?"

Har tausayi ta bashi amma bai nuna mata ba kawai dai ya amsa mata da "eh"

Gefe ya zauna yana kallonta tana ta cin abinci.

Ta d'an ci da yawa sannan tace masa ta k'oshi.

"Okay" ya fad'a yana  danna waya,gani tayi ya kara a kunne gabanta ya cigaba da fad'uwa,sai ji tayi yace "Hello Mom ga surukar taki ku gaisa"

Bai jira komai ba kawai ya manna mata wayar a kunne da sauri ta rik'e tanaji ana ta hello amma ta kasa magana,meyasa zai mata haka,kallonshi tayi taga ya had'e hannunsa alamar dan Allah tayi magana.

"Salamu alaikum" ta fad'a a sanyaye.

Daga d'ayan b'angaren taji wata daddad'ar murya tace "wa alaiki salam 'yata ya kike"
"Lafiya lau, ina yini ya gida?"
"Lafiya k'alau 'yata" shiru ne ya biyo baya sannan taji tace "yace min a poly kike ko?"
"Eh"
"Wane course kike karanta?"
"Business Administration"
"Okay ba course d'inku d'aya ba kenan?"
"Eh"
"To Allah ya taimaka,da fatan dai yana maida hankali dan nasan Yarima akwai rashin ji"
"Bayayi,yana karatu sosai" ta fad'a tana kallonsa.

"Ki kula dai 'yata banda shiririta banda biyewa abokan banza"
"Insha Allah"
"Madallah yaushe zaki kawo mana ziyara?"

Shiru ta d'anyi kafin tace "duk lokacin da kuke so"
"Ai mu ko yaushe ma muna son ganinki dan mun dad'e muna son ya fito da mata shida d'an uwansa sunk'i amma kimin alk'awarin da weekend zaki ziyarce mu next week"


Jikinta a sanyaye tace "insha Allahu"
"Mungode,af na manta baki fad'a min sunanki ba kuma shima bai fad'a min ba"

"Sunana Janan"
"Suna mai dad'i Allah ya inganta rayuwarki"
"Ameen" ta fad'a tare da saurin mik'a masa wayar.

"Hello Mom hankalinki na san ya kwanta yanzu"

Bata ji abinda tace ba sai maganarshi da taji ya sake fad'in "Mom ai a fili ma haka take"

"Mom insha Allahu" 

"Shima akwai lokaci da iznin Allah"

"To ba damuwa,bye bye" ya katse wayar,ita kam jikinta sai karkarwa yake.

"Saura babana" ya fad'a yana murmushi.

"Dan Allah kayi hak'uri ka rufamin asiri"
"Dama ai a rufe yake,kina nufin baki son ganinshi da sanin nasa"

"Dan Allah kayi hak'uri ka maida ni gidanmu"


"Amma da sharad'i?"

A tsorace ta kalleshi tace "sharad'i kuma wanne?"






*Ku biyo ni*✍









_Sadeey S Adam_
[9/29, 8:15 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
      🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```







15

Kallonta shima yake yana shafa fuska yace "ya naga jikinki na shaking tun kafin na fad'a miki"

Bata ce komai ba idonta yana gefe amma tsoronta k'ara dad'uwa yake.

"Idan na kaiki gida zaki gabatar dani gabansu mom da dad d'inki na gaidasu?"

A tsorace ta kalleshi,idonta duk ya firfito,ta marairaice tace "zan kaika gobe amma yanzu dare yayi za'a min fad'a"

"Okay ba damuwa kin dai yi alk'awari ko?"

Kai ta d'aga alamar eh
"Yawwa muje"


A mota suna tafiya ko wanne yayi shiru,ita tana tunanin k'aryar da zata yiwa su Mameey shi kuma yana tunanin yadda zasu k'arke da Mom.

"Kin san me?" Muryarsa ta daki dodon kunnenta,a tsorace tace "a'a" dan a matuk'ar tsorace take dashi.

"Zan fad'a miki dalilin daya saka na yiwa mahaifiyata k'arya dake dan karkiyi tunanin ko sonki nake u are not my type dan babu auren siririyar mace haka kamar ke,sirantarki tayi yawa tausayi ma kike bani dan ba zama ki iya zaman aure ba,zakiyi ragonta da yawa bazaki tab'a jurar ayyukan da matan aure ke sha ba"

"Na yiwa Mom k'aryane saboda hankalinta ya kwanta,dan tun lokacin da dad ya rasu take damunmu akan muyi aure amma aure baya gabanmu ma,kin san dalili?"

Bata bashi amsa ba,bama ta kallonshi,ya san tana jinshi murmushi yayi a zuciyarshi yace _kina da aji sosai_ a fili kuwa ya cigaba da fad'in
"Mu biyu ne a gurin iyayenmu duk kanmu maza ne, yayana Adnan sai ni yarima Jalal,na samo sunan yarima daga gurin kakana wato mahaifin Mom wanda ya kasance shine sarkin bauchi"

"Shine ya fara kirana da sunan kasancewata ina da k'asaita da isa da nuna izza tun ina k'arami,hakan ne yasa wasu mutanen suke kirana da saraki yayinda kakana Sarki Abdurrahman ke kirana da yarima"

"A lokacin zan iya cewa rabin rayuwata a bauchi nake yayinda iyayena suke zaune a Abuja,na samu tsangwama wajen 'ya'yan sarki dan gani suke duk cikin jikokinshi yafi sona,dan ko yana fada ina gefensa"

"Hakan ne yaja cece kace har abin yana son tab'a zumuncinmu dan haka Daddy yace a dawo dani Abuja kawai"

"Babana shine minista na kud'i a birnin tarayya ta Abuja C.B.N,muna da arzik'i sosai kuma mun samu gata fiya da tunaninki"

"Ni da Adnan dukanmu a U.S mukayi degree d'inmu bayan mun kammala muka dawo d'auke da kyakkyawan sakamako"

"Kwatsam bayan dawowarmu da wata uku sai daddy yace yayima Adnan mata d'iyar abokinsa mai suna bilkis"

"Kasancewarshi mutum ne mai hak'uri sai ya amince ba tare daya musawa daddy ba,ita kuma Mom tace bazai aureta ba saboda yarinyar  bata da tarbiyya"

"Fad'a ne ya kaure tsakanin Daddy da Mommy wanda har abin ya haddasa gaba tsakaninsu"

Ajiyar zuciyar da tayi ne yasa yayi saurin katse maganar ya kalleta "ya dai"
"Bakomai" ta bashi amsa,a zuciyarta tace _present abinda yake faruwa a gidanmu_.

Shi kuma ya cigaba da fad'in "Adnan dai ya cigaba da bawa Mom hak'uri akan insha Allah idan ya aureta zata canza hali,Mom tace sam bata yarda ba"

"Haka dai kin san namiji yafi k'arfi a fannin 'ya'ya Mommy dai bata so haka akayi auren Adnan da bilkis ya koma kano da zama saboda a can ya samu aiki a wani katafaren company na motoci dan yace shi yafi so ya gina kansa da kansa,ni kuma daddy ya sama min aiki anan C.B.N amma ko a lokacin bani da niyyar aure barni dai da wulak'anta duk macen da tace tana sona dan dama na gaya miki inada izza gashi bana jin magana,kuma dama ni da Adnan Allah bai d'ora mana biye-biyen 'yan mata ba"

"Shekarar Adnan da bilkis biyu da yin aure Allah ya basu haihuwa suka samu d'a namiji suka saka masa sunana Jalal suna kiransa da Prince"

"Shekarar yaron hud'u a duniya ya rasu sanadin rashin lafiyar da yayi tayi ba'a san dalili ba,sunje har turai amma abin ba sauk'i har dai Allah yayi ikonshi akan yaron,ni kaina sai dana sha kuka sosai kasancewar mun shak'u da shi sosai bare su iyayensa da suka haifeshi"

"Ko shekara d'aya prince baiyi da rasuwa ba itama bilkis ta fara rashin lafiya dsame irin wadda prince yayi,babu yadda ba'ayi ba akan suje asibiti tak'i,ta kuma k'i yarda doctor yazo gida ya duba ya,mamanta ta goya mata baya akan zasuyi magani a gida,shima mahaifinta ya zama tamkar mijin tace yace tunda sunce a barta a gidan to a barta"

"Watanta biyu tana jinya ta rame sosai tamkar k'warangwal,a cikin wata na uku tace ga garinku"

"Idan kinga yadda Adnan ya rame ya damu sai kin tausaya masa"

"Bayan 'yan watanni da rasuwarta daddy yace ya yanke shawarar bashi k'anwarta"

"Adnan ya hangi irin rayuwar da sukayi da Bilkis kusan kullum cikin fad'a suke zaman hak'uri yayi da ita,ga k'anwar tata ta fita bud'e ido da fitsara ga gantali kamar bilkis d'in dan haka yace wa daddy ya barshi a wannan karon ya zab'i zab'insa"

"Nan ma rigima ce ta sake kacamewa a gidanmu Mommy harda tattare kayanta tace wallahi indai ya auri hajar to sai ta bar gidan kuma sai dai ya canza uwa"

"Kwana biyu da faruwar abin muka tarar yayi wasik'a ya ajje akan shifa a wannan karon zai tafi nemo soyayyar gaskiya dan haka idan yayi musu laifi su yafe masa"

"Hankalin Mommy ya tashi sosai daddy kuwa yace duk wanda yasa akayi cigiyar Adnan bai yafe masa ba"

"Haka muka zauna cike da jimami,ni dai a cikin Abuja babu inda ban duba ba haka a kano ma na tattabayi abokansa cikin sigar da bazasu fahimci guduwa yayi ba,gidansa kuwa da naje a kulle da alama ya sallami maigadinsa ma"

"Kwatsam daddy yazo mana da labarin zai bawa hajar ni ma'ana zai had'a mu aure,na kuwa bud'e idona nace babu wanda zai min auren dole idan na shirya aure zanyi amma ni zan zab'o mata da kaina"


"Dagani har Mom abin mamaki yake bamu,mun rasa wace irin aminta ce tsakanin Daddy da Alh.Ibrahim baban su bilkis"

"Ganin dai ba yarda zanyi in auri hajar ba yasa ya hak'ura,banyi auren ba itama batayi ba,tsawon shekara uku sannan Adnan ya dawo,ganinsa ba k'aramin d'aga mana hankali yayi ba yadda muka ganshi ya rame ya d'anyi duhu ga gashi buzu-buzu ko ina a fuskarsa idan baka sanshi ba zaka gane shi ba"

"Mun tsorata sosai ganin yanayinsa amma kuma munyi murna da dawowarsa,daddy da kanshi yayi waya akazo aka aske masa gashin akai masa gyaran fuska"

"Kwananshi biyu da dawowa ya bamu labarin irin soyayyar da yayi da wata yarinya har suna shirin yin aure komai ya ruguje,da irin wulak'anci da k'alubalen daya fuskanta bayan tafiyarsa,babu wanda bai masa hawaye ba,a lokacin daddy yayi alk'awarin bazai sake yunk'urin yi masa auren dole ba ya yarda ya fito da duk wadda yake so saboda nima ya gaji da zamana a haka duk da lokacin shekarana 29 a duniya shi kuma yana da 33 amma bamu da jikin girman da za'ace mun kai haka"

"Adnan yace shi ya hak'ura da soyayya k'ila baya da farin jinin wannan"

"Haka farin ciki ya cigaba da wakana a gidanmu kamar ada kafin ayi auren Adnan"

"Watansa shidda da dawowa ya fara rashin lafiya yau ciwo gobe waraka,a k'arshe wani mugun gudawa ya rik'ayi ba tsayawa,da k'yar ya samu abin ya lafa"

"Wata rana bani mantawa muna zaune da yamma a main parlor da Mommy muna hira sai gashi ya shigo tamkar an hankad'o shi"

"Duk kanmu muka mik'e a tsorace dan a ranar ya koma kano da asuba sai gashi da yamma ya dawo ai dole mu tsorata"

"Takardu ya mik'a wa mommy yana kuka yana fad'in Mommy bilkis ta cuceni,tun Mom bata bud'e ba take fad'in lafiya meya faru"

"Ya goge hawaye da zuffa yana fad'in ashe HIV gareta shiyasa tak'i yarda muje asibiti lokacin da bata da lafiya kuma cutar ce ta kashe prince shiyasa bata tab'a yarda mukai prince asibiti tare sai dai taje da Mommynta,ko lokacin da za'a kaishi waje k'in yarda tayi muje tare sai Hajar na yiwa visa sukaje tare,sai yanzu ina bincike can k'asan kayanta cikin wata atamfa na gansu"

"Duk kanmu muka dafe kai muna salati,Mommy kuwa kuka take sosai tana fad'in dama sai da nace bana son auren nan saboda na san duk Kansu basu da tarbiyya"

"Zama mukayi zugum tamkar muna zaman makoki sai kusan k'arfe 11 daddy ya dawo yana ganinmu ya san da matsala"

"Mommy tana kuka tayi masa bayani tare da bashi takardun,shima salati yake tayi,a take ya kirawo family doctor d'insu aka masa test sannan doctor yace da safe zai dawo da result"

"Babu abinda Adnan yake sai kuka tamkar yaro ranar haka ya zama,sai k'ara fad'i yake wallahi ban tab'a mu'amala da wata mace bayan bilkis"

"Ranar kwana mukayi a zaune muna bawa Adnan hak'uri tare da bashi k'arfin gwiwa"

"Da safe da k'yar muka samu mukayi break fast dan Mommy ma saida daddy ya matsa mata,k'arfe 11 na safe doctor Hafiz ya dawo da sakamako ya nuna cewar shima Adnan yana d'auke da cutar tsawon shekarun nan,a take daddy ya suma,haka Mommy ma,shi kuwa babu abinda yake sai addu'a da hawaye yayinda nima nake hawayen"

"Da k'yar aka samu suka tashi,kwana uku da faruwar abin daddy ya rasu saboda tsananin damuwa zuciyarshi ta buga,dan gani yake kamar shine sila,dan koda ya sanar wa da mahaifin bilkis sai suka k'aryata mommynta har da zage zage wai sunwa matar dake cikin kabari sharri"

A dai-dai lokacin yazo k'ofar gidan.

Tsayawa tayi tak'i fita.
"Ya kika tsaya kije sai da safe" a lokacin ya lura fuskarta sharkaf da hawaye.

"Na san duk wanda yaji labarin Adnan dole ya tausaya masa,wai a hakan ma ba komai nake fad'a miki ba dan ban baki labarin wahalar daya sha lokacin daya bar gida yaje yayi soyayya da wata mara imani" ya fad'a shima yana goge hawaye.

"Ka k'arasa min labarin dan Allah"

"Ki bari sai da safe idan mun had'u a skul kinga yanzu 8 ta gota bana son a miki fad'a"

"Karka damu na san abinda zan ce masu"

"Kin tabbatar ba matsala?"
Kai ta d'aga masa.

Parking yayi a can gefe kar securities d'in su masa magana.


Ya cigaba da fad'in "Ran daddy ya b'aci sosai ganin ya yarda da abokin nasa amma ya ha'incesa,sukayi baran-baran aikuwa  tun a k'ofar gidansu bilkis d'in ya fad'i daga nan akayi asibiti dashi kwana biyu a asibiti ya rasu kuma har ya rasu yana fad'in Adnan ka yafe min nayi tunanin gata na maka ashe cutar da kai nayi,duk da Adnan yana fad'in ya yafe masa bai masa komai ba k'addara ce amma still baya awa biyu bai sake Neman yafiyar Adnan ba,kwananshi biyu a asibitin ya rasu"

"Karkiso kiga tashin hankalin da Mommy ta shiga tamkar itama bazata rayu ba,d'umbin mutanen da sukayi rakiyar gawar daddy kabari bazan ce ga adadinsu ba dan kinsan nace maki ministan kud'ine ga kuma d'imbin masoya saboda daddy mutum ne na mutane,ya samu shaida mai kyau haka akayi ta zuwa daga garuruwa daban daban harda turawa da sukayi aiki a Turkish suma sukazo ta'aziyyar daddy,har wata guda muna karb'ar ta'aziyya kuma har a lokacin Mommy ba lafiya,shi Adnan ma ya fara sakin jiki"

"Watan Mommy biyar sannan ta warware sosai a lokacin kuwa duk magana ta yad'u a Abuja cewar Adnan yana da HIV shiya gogawa matarsa ma da d'ansa har yayi ajalinsu,kiji sharri fa,kinsan muna da arzik'i dole baza muyi wahalar kwatance ba,abin mamaki sai ga abin a YouTube an d'ora wai shin zargin da akewa d'an gidan marigayi Alh.Abdullah ministan kud'i gaskiya ne?,wallahi da kaina na sa akaje aka kamo wanda ya bugo abin da wanda ya d'ora sannan naje har gidan tv n da aka fara yad'a abin na wulak'antasu na kuma ce suyi abinda ya ke gabansu"

"Da abin yayiwa Adnan yawa yacewa Mommy zaije k'aro karatu a lokacin tak'i yarda tace sai yayi aure yace tayaya zaiyi aure da cutar HIV a jikinsa nasiha sosai ta masa tace ai suna auren masu cutar suma kuma harsu samu zuri'a dan haka dole ya nemo ya aura,k'in yarda yayi yace shi gaskiya zai tafi karatu har sai maganganu sun lafa,itama ganin ya damu yasa tace masa ta yarda yaje"

"Tunda Adnan ya bar k'asar take ta damuna akan nima nayi aure ina ce mata zanyi insha Allah, cikin ikon Allah kuwa na nemi admission a skul d'inku saboda ina sha'awar samun kwalin diploma na kumayi sa'a na samu shine dalilin zuwana Kaduna dan ban tab'ayin sati a kaduna ba sai dana fara karatun nan naga mommy ta matsa shiyasa lokacin da kika min tsaurin ido na samu damar da zan kwantar mata da hankali dan ko baki je ba at least ta yarda ina da shirin aure amma a zahirin gaskiya bani da niyya dan na tsorata da halin da Adnan ya shiga mata biyu sun wahalar mana dashi d'aya zab'insa d'aya zab'in daddy shiyasa bana sha'awar aure ko kad'an kuma na tsani duk wata mace mai iyeyi shiyasa nake jin haushinki tun had'uwarmu ta farko dake naga kina da rawar kai"

Ajiyar zuciya Janan tayi tare da goge wani hawayen "Allah yajik'an daddy yayi masa rahma"
"Ameen"
"Yanzu kuma ina Adnan?"
"Adnan shekararsa biyu a span yace min baya jin dawowa anan kusa sannan ya sanar mana yana karb'ar magani a can kuma yana cikin k'oshin lafiya,dan wani lokacin ma video call muke,shiyasa hankalin Mommy ya d'an kwanta amma a Nigeria mu kad'ai muke waya dashi ni da Mom dan mun d'aukar masa alk'awarin babu wanda zamu bawa number shi"

"Allah sarki,Allah ya saka masa"

"Ameen janan"

"To ya bayanin iyayen Hajar da ita kanta?"

"Hmmm suna nan a Abuja amma babu abinda ke had'amu sai kallon banza idan mun had'u,ya kamata ki shiga gida Janan tara ta wuce"

"To sai da safe"
"Allah ya nuna mana" ya fad'a yana mik'o mata wayarta,jikinta a sanyaye ta karb'a ta fita.

A falo ta tarar dasu Mameey, jikinta duk yayi sanyi ta sugunna tace "na san na muku laifi kuyi hak'uri"

"Daga gidan ubanwa kike?" Fahad ya jefo mata tambayar

"Gidan su Raihan" ta fad'a kai tsaye.

Daddy ya kalli Mameey cikin mamaki sannan ya dawo da kallonsa kan Janan yace "yaushe kika zama karuwa Janan?"

A firgice ta d'ago kai ta kalleshi tace "Abba karuwa fa"

Mameey tace"Idan ba haka bane meyasa kikayi k'arya bayan yanzu Raihan ta bar gidan nan itama nemanki tazo tun kafin magrib baki dawo ba,yaushe kika zama mak'aryaciya Janan?"

Jikinta a sanyaye ta sadda kai dan bata da abin cewa.

"Ki fad'a min gidan ubanwa kika je?" Fahad ya sake tambayarta.

Shiru kawai tayi kanta a k'ansa.

Matsawa kusa da ita yayi ya d'auketa da mari.
"Gidan ubanwa kika je?"

Da hannu ya fara dukanta tana kuka amma bata bashi amsa ba.

"Fahad k'yaleta haka"

"Abba barni in hukuntata tun kafin ta b'atawa gidanmu suna"

"Ka k'yaleta ai ta kusa barin gidan mu huta" Abba ya fad'a.

Da sauri ta tashi ta ruga d'akinta tana kukan k'unci.







_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




16

Kulle d'akin tayi da key tasha kukanta ta k'oshi,sannan ta tashi ta nufi toilet tayi alwallah,har zata tada sallah ta tuna wayarta a kashe take,tayi saurin kunnawa da niyyar tana idarwa ta kirawo Aliyu.

Tana tada sallah kuwa wayar ta fara ringing, kafin ta idar an mata missed calls ya kai goma.

Bayan tayi addu'oi ta duba wayar taga duk missed calls d'in Aliyu ne,da sauri ta kirashi,har ta kusa katsewa sannan ya d'aga.

"Assalamu alaikum,Allah ya huci zuciyarka"

Ajiyar zuciya yayi sannan ya amsa sallamar yace "nayi tunanin ko laifi nayi"

"Bakayi laifi ba ni ce nayi maka laifi ina neman afuwa"

"Karki damu ai bakyayin laifi a gurina na yafewa matata" wani dad'ine ya mamaye zuciyarta sai taji har ta manta da abinda Fahad ya mata suka sha waya sosai har  yake sanar mata ranar asabar za'a kawo lefe kuma yana son ta rubuta I.v zai shigo skul gobe ya karb'a.

"A'a Aliyu karka damu Mameey ta d'auki nauyin komai"

"A'a abin yayi yawa,d'azu da mukazo ta bani mukullin gidan da zamu zauna can tudun wada yake,sannan ta karb'i account numberta tace zata turomin kud'in da zanyi business d'in da zan rik'e ki,Janan Mameey na sonki sosai kuma Mameey tayi min gata da ban san da kalamin da zan gode mata ba"

Wasu hawayene suka sauka a idonta  najin dad'i.
"Karka damu Aliyu ai yiwa kaine"

Haka suka gama hirarsu sukayi sallama cikin kewarshi ta kashe waya.

Labarin da Jalal ya bata ne ya dawo mata a rai.

Ta zauna ta zuba uban tagumi tana tunanin dama akwai azzaluman mata haka a duniya,tausayi ne ya rufeta gaskiya akwai babbar sakayya a lahira.

          ********

*12:30pm*

Kamar a mafarki taji ana ta knocking k'ofarta.

A hankali ta bud'e ido ta kalli agogo,hamma tayi tare da salati sannan ta sakko a hankali zuwa bakin k'ofar.

"Waye"
"Ni ce"
Jin muryar ne ya saka tayi saurin bud'e k'ofar ta kalleta.

Rungume juna suke cike da murna sai kuma fauziyya ta fara kuka.

Zama sukayi suna ta maganganu akan matsalar gidan nasu, anan Janan ta fad'a mata maganar aurensu da Aliyu.

Tayi mata murna sosai dan ji take dama itace dan matsalolin gidan ta fara gajiya dasu.

A haka suka tsara komai na game da shirin bikin.

"Zan fita skul karfe 2 fa"

"Ki shirya na rakaki saboda na dade ban fita ba,daga can sai mu wuce muyi shopping ko?"

"Okay ba damuwa bara na shiga wanka"

"Nima bara na shirya ko"

"Okay"

          **********

Fauziyya taji dad'in yadda taga Janan na mayar da hankali sosai a karatun ta,yadda take yawan  amsa tambaya a lecture hall.

Bayan sun fito Raihan tace "Janan mu zagaya da Yaya Fauzah taga skul d'in"

"To" ta amsa

"Ke ni baki bani labarin yarima ba naje har gida jiya fa baki dawo ba"

Hmmmm "ke dai bari kawai"

"Ban labarin yadda kukayi dashi jiya?"

Ganin bayan shi tayi daga can nesa a zaune kan kujera.
Jikinta kawai ya bata cewar shine.

Da sauri ta k'arasa ta barsu Fauzah da Raihan anan.

Tana isa taga shine kuwa "jalal"
Da sauri ya d'ago kai da alama yana cike da damuwa a lokacin.

"Ah ah Janan kin shigo kenan"

"Eh ya kake?"

"Lafiya lau"

Sai a lokacin su Fauzah suka k'araso cike da mamaki Raihan ke kallon Janan bakinta d'auke da tambayoyi da yawa,Fauzah na kallonsa a tsorace tace "Salman dama kana raye?"

"Salman kuma" Janan ta fad'a tana kallon Fauzah

"To waye?"

"Sunanshi Jalal"

"Wallahi yana kama da Salman sosai nayi tunanin shine ma"

Kallonshi Janan tayi sosai sai a lokacin taga yayi mata kama da Salman sai dai shi Salman ruwan tarwad'a ne (chocolate color) Jalal kuwa fari ne sol.

Hawaye ne suka sauka a idonta shima cikin mamaki yake fad'in "Waye Salman?"

Da gudu ta juya ta bar gurin,Fauzah nata kiranta amma tak'i ko juyowa,Raihan haka ta bita kamar mahaukaciya da taga gudun Janan ba mai k'arewa bane sai kawai ta dawo a rikice.

"Dan Allah mu bita a mota nifa ina ganin Janan ta fita a hayyacinta"

"Wlh banzo da motana ba kawomu akayi"

"Muje a mota na" Yarima ya fad'a cikin sauri suka wuce.

Parking space na gurin suka k'arasa da shida Fauziyya suka shiga gaba Raihan na baya.

A bakin main gate da suka tambayi securities d'in da wanda ke gurin akace an ganta ta hau napep a gigice anyi tunanin ma ko wani abu ya faru da ita.

"Mu tafi gidan" Fauzah ta fad'a a kid'ime.

Baita ta kalla tace "Janan ta dawo kuwa?"

"Eh"

"Okay a bud'e gate ina masu gadin?"da kanta ta danna horn suka bud'e ya shiga da gudu.

Fauzah da Raihan suka shiga ciki suna rige rige.

A Babban falo suka tarar da ita a kwance tamkar gawa,idonta a bud'e amma hawaye na zuba ta gefe,ba ta ko motsa idon dan ta tsayar dashi cak a kan cilin kanta na bisa cinyar Mameey.

"meya sameta ne?a waje ta fad'i sai zuwa aka yi aka shigo ta ita"

Fauzah ta zauna kusa da Mameey ta dafa Janan tace "Mameey daga naga wani mai kamar Salman shikenan ta rikice kuma already ta sanshi fa dan ita taje gurinshi"

Da sauri Janan ta tashi zaune idonta sharkaf da hawaye tace "wallahi shine, Salman d'ina ne"

"Janan kin haukace ne ko kin tab'a ganin wanda ya mutu ya dawo?" Mameey ta fad'a tana jijjiga ta.

"Mameey wannan fa sunanshi yarima" Raihan ta fad'a

"Waye shi?"

"A skul d'inmu yake tare muka zo dashi nan gidan ma yana waje"

"Wallahi Salman d'ina ne Allah ya dawo min dashi"

Da sauri take k'ok'arin fita,Mameey ta rik'eta.






*kuyi hak'uri masoyana wallahi kwana biyu ne na zama busy babu time d'in typing.Da masoya littafin _A dalilin so_ duk kuyi hak'uri,ku dai yi manage da wannan.*









_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:15 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
       *DIREBAN GIDANMU*
       🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




17

"Raihan ce masa ya shigo"

Da sauri ta fita.

"Mameey in har kina sona zaki yadda cewa wannan Salman d'ina ne ba k'arya nake ba" kuka ne ya sake kubce mata.

Fahad ne ya shigo da alama ma daga office yake.
Turus ya tsaya tare da fad'in "lafiya?ita kuma wannan me aka mata?"

"Wai wani ta gani kamar Salman shine ta dage wai shine" Fauziyya ta bashi amsa

Tsaki yayi a daidai lokacin Yarima suka shigo tare da Raihan.

Ita kanta Mameey da ta ganshi sai da ganshi tayi tunanin Salman d'in ne dan bata tab'a tsayawa ta kalleshi sosai ba bare ta gane wani banbanci tsakaninsu.

"Bismilla zauna"

Zama yayi kan kujera,itama Mameey ta zauna Janan kuwa k'in zama tayi Mameey ta rik'e hannunta sosai.

"Dan Allah ka daure ka fad'a mana gaskiya kaine Salman kuma kasanmu?" Mameey tayi masa tambayar.

Kallon Mameey yayi yana murmushi ya girgiza kai "yace wallahi ban tab'a amfani da wani suna bayan Yarima,Saraki,da kuma Jalal,gaskiya bani bane Salman saboda ban sanku ba sai yanzu"

"Karka yaudari kanka dan Allah ka fad'a musu kaine Salman"

Kallonta yake cike da mamaki.

"Janan wallahi zan miki dukan da zaki kasa tashi meyasa kika zamo matsalar gidannan ko dan kinga ana k'yaleki,idan Salman ne gidan ubanwa zaki kai Aliyu kuma?ko kina tunanin mu k'ananan mutane ne"

"Ka k'yaleta kawai,amma kina wannan abin kike tunanin zaki iya zaman aure?kina gidan Aliyu zaki rik'a gigicewa akan mutumin daya rasu har kina suma?kina tunanin idan mu mun d'auka mijinki zai d'auki wannan shashancin?"

Maganganu ta fara akan ita ko me za'ayi wannan Salman d'inta ne,sai da Aliyu ya bata mari sannan ta nutsu tayi shiru tana shashshek'ar kuka.

Jalal jin marin yayi tamkar a fuskarsa,Janan kuwa tana rik'e da kuncinta dan a yanzu kam kuncinta har ya saba da mari.

Da k'yar Mameey ta sulhunta abin,kuma suka yarda cewar kamannine kawai amma ba Salman bane har ita Janan d'in ta yarda saboda Salman da Jalal suna da babanci sosai sannan ta san Mahaifiyar Salman kuma ta san ta rasu tun kafin a rabasu da Salman sannan wadda Jalal ya nuna musu a waya bama sa kama sam da Maman salman kawai ta yarda kamannine suka kusan zuwa d'aya.

Mameey ta mata nasiha sosai akan ta sakawa zuciyarta salama.

A b'angaren su Jalal kuwa bayan sun tafi yake tambayar Raihan shin waye Salman d'in nan.

"Shine Saurayin da ta fara yin soyayya dashi, tana Ss3 lokacin,ban sanshi ba nima saboda a poly na had'u da Janan amma lubna itace childhood friend d'inta tare sukayi tun primary har secondary a yadda lubna ta bani labarin Salman tace duk wanda ya zauna dashi dole ya so shi mutum ne mai son jama'a da kuma karamci,daga shi sai mahaifiyarsa suke rayuwa a garinnan dan koda aka tambayi danginsa yace basu da kowa kawai daga shi sai ita,talaka ne sosai ko abinci wani lokacin wahala yake musu amma Janan babu wanda takeso bayan shi,bayan rasuwar mahaifiyarsa sai ya shirya auren Janan shi kuma Abba yace ba zai bawa d'iyarsa auren mutumin da baya da asali ba,gashi baya da ko sana'ar da zai rik'e masa 'ya,Janan tace ita tana sonshi a haka Abba fur yak'i yarda ya hana,haka sukayi baran baran da Salman,tun daga lokacin bata sake sakashi a idonta ba,tayi jinya kamar bazata rayu ba dan lokacin ta gama makaranta har ta samu admission a jami'a amma bata samu taje ba saboda ciwo, shine dalilin da yasa ta rasa gurbin karatu a Jami'a sai ta samu admission a poly kuma lokacin ne Abba yazo mata da labarin Salman yana lagos kuma ya rasu a can sakamokan fad'awa ruwa da yayi,wannan shine tak'aitaccen labarin Salman"

Ajiyar zuciya yayi yace "Allah sarki Allah yaji k'ansa da rahma"

"Ameen"

"Waye Aliyu kuma?"

Murmushi tayi tace "Aliyu shine wanda zata aura"

"d'an gidan waye?ko ince a ina yake?"

"Ba d'an gidan kowa bane,shima dai talaka ne kamar Salman amma shi yana da asali"

"A ina suka had'u?"
"Direban gidansu ne kafin su fara shirin aure"

"Direba kuma"
"Eh,a dalilin lubna ta aibanta shi shine ita kuma tace sai ta aureshi,shima still Abba bayaso amma Mameey tace sai ta aureshi saboda Janan d'in ta shiga damuwa"

"Lallai Janan tana da tausayi,wannan wane irin so ne"

"Nima na kasa gane shi,Janan idan tana soyayya gani take zata iya bada ranta saboda shi"

Jikinsa yayi sanyi a zuciyarsa yace _lallai mommy tayi rashin suruka tagari,ya zanyi in fitar da kaina daga k'aryar da nayi ma mommy?_

A fili kuwa ya sake murmushin k'arfin hali yace "yaushe ne zamu sha bikin Janan?"

"Next week ne"

"Sure?" Ya fad'a a d'an firgice.

"Wallahi next week ne bikin"

"Allah ya nuna mana" ya fad'a a sanyaye.

"Ameen" ta amsa tana murmushi dan ta gama gano loggarsa.


            ********

To! hausawa dai sunce _rana bata k'arya.....,sai dai uwar d'iya taji kunya_

A yaune dai aka d'aura auren Aliyu da Janan.

Ba sai na bada labarin irin occasions d'in da akayi ba kunsan dai d'iyar masu kud'i ce kuma 'yar gatan Mameey.

Gaskiya taga gata sosai a gurin Mameey,Fahad da Fauziyya.

Jalal ma ba'a barshi a baya ba dan ya kashe mak'udan kud'i sosai a wata dinner da yayi organizing,sai dai har aka k'are bikin yana ta tunanin me zai cewa Mommy game da Janan.

Ranar da za'a kaita furucin da Abba yayi ya tsaya mata a rai sosai.

"To na wullar da k'wallon mangoro na huta da k'uda,bazan miki baki ba,amma kinsan yawancin  talaka bai san halacci ba,to dai tunda kin zab'i haka gaki ga auren daga yanzu na zame hannuna daga kanki duk abinda yaje ya dawo karki nemeni kije can ki k'arata,kirki dawo min gida komai zai faru"

Wannan itace kalamin Abba na k'arshe daya yi mata kuma ya tsaya mata,dan hatta Mameey a lokacin sai da jikinta yayi sanyi,Fauziyya kuwa kuka ta rik'ayi.
           ****
Gidanta masha Allah yayi kyau sosai,plat building ne kuma safe content, bedrooms uku falo biyu,kitchen store sai kuma resting room inda aka Saka mata tuntu da show glass.

Tana zaune akan gado bayan kowa ya fita shi kuma Aliyu yaje rufo gidan,ta yaye mayafin fuskarta ta d'aga hannayenta sama tace "Allah na gode maka daka ciki min burina"

Tana nan zaune taji ya turo k'ofa,cike da murmushi ta d'ago kai,ganin ranshi a b'ace ne yasa ta mak'ale dariyarta a leb'e.

"Lafiya naga ranka a b'ace bayan yau ranar farin cikinmu ce"

Ya kalli akwatunan da aka kawota dasu kusan guda 15 yace "ki shirya kayan sawarki da abubuwan da zaki buk'ata a akwati biyu gobe zamuyi tafiya"

Da mamaki tace "tafiya kuma daga yin aurenmu yau?ko honey moon ne ai sai ka bari a d'anyi sati biyu saboda mutane zasu zazzo"

"Karki ce ban gaya miki ba,zuwa sha d'aya na safe zamu tafi ki shirya" juyawa yayi ya fita ta bishi da sauri,d'ayan d'akin ya shiga ya rufe.

Tun tana bugawa har ta gaji ta daina ta koma d'akin ta bud'e akwatunan tana zab'ar kayayyaki masu kyau dan tana tunanin honey moon zasuje kuma bata so a raina ta,sai data shirya kayan sawa akwati biyu sannan ta shirya kayan shafe shafe da turaruka a akwati d'aya,akwatuna uku ta cika dam da k'yar ta zuge.

Ta kwanta tana zulumin ko waye ya b'atawa Aliyu rai.



 _*Washe gari*_

K'arfe tara ta fito daga wanka ta zauna ta d'auki tsawon minti talatin tana makeup.

Ta shirya cikin wani tsadadden swiss lace Ash da touch d'in red.

Fitowa tayi falo ta bud'e fridge ta d'akko yoghurt ta zuba a glass cup tana sha.

_to ina Aliyu ya fita haka tun safe,wai me aka yi masa ne ko kajin nan a alibidi bamu ci ba  bamuyi nafilfili ba dan yiwa Allah godiya akan cikar burinmu,ko dai yana da damuwa ne?._

Ta furta a zuciyarta wanda babu mai bata amsa.

Wajen k'arfe goma ta d'anyi bak'i suma bata wani sansu ba 'yan unguwane kuma basu dad'e ba suka tafi.

Raihan da lubna ma sunzo dan sai kusan 12 bayan sunyi mata girki suka bar gidan,yara da mutane anata shishshigowa.

Sai kusan k'arfe uku ya dawo lokacin ma Akwai wata mata da tazo,a gurguje suka gaisa ya shige ciki.

"Bara na tafi tunda maigidan ya dawo"

"Da kin zauna muna hirarmu bama dad'ewa zaiyi ba yanzu zai fita"

"A'a na dawo wani lokacin tunda bamu da nisa gidana ne a opposite naki"

"To ba damuwa nagode nima insha Allah zan shigo"

Haka sukayi sallama ta tafi.

Da sauri Janan ta bishi ciki.

A tsaya ta ganshi yana zagaye a d'akin.

"Lafiya Aliyu?dan Allah ka fad'a min damuwarka"

Ransa a b'ace yace "ina kayanki da kika had'a?"

"Suna d'akin can" fita yayi,da sauri ta bishi.

"Naga akwati uku"

"Eh kayan nawa bazasu ci akwati biyu ba"

"Ba damuwa d'akko gyalenki"

Ta sauri ta bud'e closet d'in ta janyo red veil ta yafa,ta d'auki jaka ta saka takalmi.

Ya trolley biyu ita kuma taja d'ayar,har zasu fita daga falon tace "oh Akwai abinci fa da yawa kaima naka na kan dinning"

"Karki damu muje kawai"

Suna tafi taga wata mota golf duk taji jiki da alama ta haya ce.

"Malam habu a tayani saka kayan a baya"

Suka saka ta shiga ta zauna zuciyarta cike da wasiwasi,kawai sai ganinsu tayi a k'auyen su Aliyu kuma k'ofar gidansu.

Batace komai ba ganin ransa a b'ace yake.

Bayan an gama shiga da akwatunan ya kalleta yace "muje mana"

Ta shiga ciki da sallamarta.

"Ga d'akin nata can karka kawo mana tsiya nan" taji Umma dake tsaye a tsakar gida ta fad'a.

Cak Janan ta tsaya zuciyarta cike da mamaki.

"Kika tsaya kina kallonmu kamar mayya ko ba'ayi miki bayanin cewar ga d'akinki can ba" Ummi tayi naganar.

Kallonsu kawai Janan take tana ganin abin tamkar a mafarki.

Ta gabanta Aliyu ya dawo ya kalleta ido cikin ido "ke ba magana ake miki ba,ga d'akin ki nan anan zaki cigaba da rayuwa"

Sai a lokacin tace "ban gane ba bayan Mameey ta baka gida sannan ta baka jari taya zaka dawo dani nan kace in zauna bazan iya ba wallahi"

"Oh dama ta bani ne dan Ku dawo kuna goranta min?to bari kiji gida dai ita ta bani amma a halin yanzu bata da iko akanshi kuma kinaji kina gani za'a auri wata a kaita gidan ta cigaba da rayuwa a ciki ke kuma kina gidan nan babu abinda kika isa kiyi"

"Aliyu" ta fad'a da mamaki

"Eh Aliyu ba direban gidanku da kika wulak'anta lokacin yana k'ark'ashinku,ki k'arasa mana"

"Aliyu ko dai auren manufa kayi dani?"

Dariya yayi yana tafa hannu yace "karki shiga wasiwasi na aureki dan in rama sharrin da ubanki yayi min"

Jin yadda ya fad'i sunan mahaifinta gatse-gatse yasa ta harzuk'a cikin d'aga murya tace "kada ka nemi ka zagi Abba kuma  bazan zauna a wannan kangon gidan naku ba sai ka bani takarda ta in koma gida saboda ina da gata dama tsiyar ka auri talaka kenan saboda baku da halac....................." Mari ya wanke ta dashi wanda yayi sanadiyyar katse maganartata.












_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:16 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
       🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```



18

Tana zaune tana kuka tana k'arewa d'akin kallo, babu abinda ke cikin d'akin daga tabarma da bakko a gefe sai akwatunanta.

Har lokacin kuka take tana fad'in "na cuci kaine dana k'i bin shawararka Abba"

Jakarta ta janyo ta bud'e ta d'auki wayarta ta fara neman number Mameey,kawai ji tayi an fuzge wayar d'ago kai tayi kawai taga Umma ce.

Da sauri ta mik'e tsaye tana kallonta ido cikin ido.

"Ubanwa zaki kirawo da wayar?".

Shiru tayi bata ce komai ba,da mamakinta taji ta wanketa da mari.
" nace ubanwa zaki kirawo da wayar,munafuka kin tsareni da ido kina neman cinyeni"

Babu abinda Janan take sai kuka,wannan wace irin jarrabar rayuwace,tana tunanin tayi aure ta huta ashe ba haka bane.

Fita Umma tayi ta barta tana kuka tamkar yarinya.


Kusan magriba sai ga Aliyun ya shigo da wata katifa number 1, da kanshi ya ajjeta ya shinfid'a bedsheet ya ajje pillows sannan ya d'auki labulen k'ofa tare dana taga ya saka,sai a lokacin ta gane katifan tace extra da Mameey ta siyo bedsheet da labulayen tasan duk nata ne,ta tabbata anan zata zauna.

Sai daya gama tas yana shirin fita tayi saurin shan gabansa.

"Aliyu ban cancanci haka a gurinka ba ka tausaya min dan Allah, idan ma wani abu maihaifina yayi maka ka yafe masa karka manta Allah yana son mai yafiya"

Har ta gama maganar idonshi a kanta bai d'auke ba,kusan minti biyu sannan ya fara k'ok'arin bin gefenta ya wuce.

Tayi saurin sake tarar gabanshi,aikuwa ya saka hannu ya buge ta,fad'uwa tayi har k'asa cikin jin azaba da rad'ad'in ciwo,sunkuyawa yayi daidai saitinta ya d'an jona hannunsa akan hancinsa saboda idon ta a rufe yake.

"Oh ashe kina da numfashi,dan bana son ki mutu bakiga yadda zan k'ask'antar da mahaifinki ba"

Tashi yayi ya fice kawai,tana nan kwance kanta na sarawa tana d'an jin hayaniya sama-sama Umma na ta zaginta.

Tafi awa a kwance a gurin sai da taji an fara kiran sallar magrib sannan ta tashi jikinta na rawa alamar zazzab'i na son rufeta.

Tsakar gida ta fita da niyyar tayi alwallah,buta ta hango ajiye jikin randunan ruwa,ta nufi gurin ta d'auki guda d'aya tana shirin ta bud'e randar ta d'ebi ruwa caraf taji an rik'e hannunta.

'Dagowa tayi dan ganin ko waye.
"Bazaki d'iba ba tunda bake kike mana jigilar d'aibo ruwa ko siyan ruwa ba"

Mamaki take yadda Ummi take gaya mata magana kai tsaye,ta tuno lokacin da taje gidansu tana kuka an rufe mata d'an uwa a cell.

"Mamaki kike ko?to bari kiji wannan somun tab'i ne idan har kina raye sai kinga yadda ubanki zai rik'a bara a kasuwa yan.............." Mari Janan ta wanketa dashi cikin jin zafin cin mutumci da take neman yi mata.

A zafafe Ummi ta d'aga hannu zata rama Janan tayi saurin rik'e hannu ta wullar gefe tare da shak'o wuyanta ta matse ta jikin bango.

Wani ihun azaba da kururuwa Ummi tayi wanda ya saka Umma fitowa daga d'aki a guje.

"Ke kashe ta zakiyi?"

"Rai ba a hannuna yake ba amma ina mata gargad'ine"

Ummi sai k'ok'arin k'wace kanta take amma ta kasa,Umma sai dukan Janan take tana fuzgarta amma tak'i sakin Ummi har ta kai mak'ociyarsu ta lek'o ta katanga da yake bata da tsayi,ganin tak'i sakinta ne yasa mak'ociyar ta zari hijabi ta fito,Aliyu da Nura ta tarar kan taya suna shan rake ta fad'a masu abinda ke faruwa da sauri suka shigo gidan.

"Ke sakarta"

Jin muryar Aliyu ne ya saka ta tayi saurin sakin wuyan Ummi ta juyo zata masa magana kawai Umma ta fara kuka wai za'a kashe mata 'ya,aikuwa Aliyu ya harzuk'a ya fara dukan Janan ta ko ina,da k'yar Nura ya k'wace ta yana fad'in "ai sai ka kasheta wannan irin duka meyayi zafi Aliyu"

"Kai baka ga ba itama kisan take son yi"

Janan na tsugunne tana kuka,jikin mak'ociyar kuwa yayi sanyi dan batayi tunanin haka ba,daga kawo amarya yau.
Sumsum ta fice ta bar gidan.

Aliyu ya kalli Ummi yace "meya had'aku?"

Bata b'oye masa komai ba ta dad'i abinda ya faru.

"To ai ba k'arya kikayi da kanta sai taga hakan indai tana raye,yarinyar da aka gina da haram"

Kallon shi kawai take wai yau Aliyu ne ke fad'a mata bak'ak'en maganganu marasa dad'in ji.

Nura ne yace "haba Aliyu bai dace kana fad'ar haka ba kaifa musulmine kuma Janan matarka ce"

Umma tayi caraf ta amsa da "a'a ba matarshi bace saboda nina saka ya aure ta dan mu rama sharrin da ubanta ya mana,sannan yanaji yana gani Aliyu zai sakar masa ita saki uku kuwa"

Aliyun ma cewa yayi "me zanyi da wannan yarinyar kallarta kamar tsinke ai bata cikin jerin matan da zanso dan bana mata kallon mace ma,kai nifa a gidansu ma nafi tsanarta ita da mahaifinta"

Da sauri Nura ya jashi yana fad'in mu bar nan dan naga alama ranka a b'ace yake zaka iya fad'ar komai ma.

Kallonta ya sake yi yace "karki yarda ki tab'a musu ruwa idan kina buk'ata kije ki d'ebo naki na fad'a miki".

Ficewa su kayi suka bar gidan Umma da Ummi ma suka shige d'aki aka barta ita kad'ai a tsugunne.

Wani sabon kukanne ya sake kubce mata,sai da tayi mai isarta a gurin,tana gani suka fito suka d'ebi ruwa sukayi alwallah suka koma d'aki.

Ganin gari ya fara duhu ga sauro yana cizonta abinda bata saba ba kenan,ta tashi tana 'yan soshe soshen hannunta inda sauro ya cicciza.

'Daki ta shiga ta janyo jakarta,kud'in ciki ta fiddo duka dubu had'u ne dan sauran ta bada anyi mata depositing a banki.

Dubu d'aya ta d'auka ta mayar da sauran ta d'auki mayafinta ta fice.

Bata san inda shago yake ba wanda zata sayi ko pure water ne tayi alwallah.

Tafiya kawai take tana d'an waiwaye-waiwaye ta san tayi nisa da gidan amma babu alamun shago.

Wasu 'yan mata ta hango suna tafiya da sauri ta k'arasa gurinsu.

" sannunku"
"Yawwa sannu" suka fad'a suna kallonta.

"Dan Allah ina zan samu d'an shop d'in da zan sayi pure water"

Kallon juna sukayi,sukayi dariya,d'ayar tace "ai garin nan shago d'aya ne sai kuma masu saida abubuwa akan d'an tebur,kuma idan zaki karad'e k'auyen nan kaf bazaki samu pure water ba sai kinje can bakin titi gidan mai to anan zaki samu kuma dai yanzu kinga dare ne ga da d'an tazara tsakaninmu da titi"

"Hala ke bak'uwa ce?" d'ayar ta fad'a.

"Eh bak'uwa ce"

"To ke bazaki iya shan ruwan mu ba?,ai ruwanmu yana da kyau kuma kinga da kinsan hakane da kin taho da guzurin ruwanki"

'Dayar ta sake fad'in "to gidan da kika zo ba maza ne da baza'a karb'a a siyo miki ba"

Shiru tayi bata ce komai ba,tana tsoron tace musu alwallah take son yi   dan bata son tona asirin kanta.

"Naja nifa ban yarda da wannan ba"

"Kai lallai ku d'in nan me kuka tsaya yi anan?"
Budurwar da ta k'araso gurince ke fad'ar haka.

"Kinga wata ce wai tana neman inda ake sai da pure water kuma wai bak'uwa ce amma ace babu wanda zai karb'a a gidan da tazo ya siyo mata shine muke mamaki"

"Toooh" ta fad'a cike da mamaki ta haska fuskarta da touch light, ido Janan ta rufe saboda yadda hasken ya haskesu.

"Kai Janan" ta fad'a.
Ita kuwa jin an ambaci sunanta ya sata saurin bud'e ido.

Bata gane ko wace ba saboda ta kashe fitilar.

"Baki ganeni ba?"
"Eh" ta fad'a a sanyaye.

"Zuhra ce wadda muka zo gidanku ni da Ummi"

Ji tayi gabanta ya fad'i,dan ta tuno ko wacece.

"Kin Santa ne?"
'Yan matan suka tambaya.

"Eh na Santa mana itace matar Aliyu fa"

"Kut wallahi da na san itace da bazan tsaya bama"

"Haba Hassana meye hakan" Zuhra ta fad'a

Wadda ta kira da Hassana ta sake fad'in "Matar Aliyu fa kikace Aliyun daya ci amanarki ya auro wannan saboda 'yar masu kud'i ce"

Zuhra tace "Kiji ki sai kace bakya zuwa islamiyya shi fa aure nufine na Allah"

"Uhmm naga alama,Hassana dalla taho mu tafi" d'ayar ta fad'a, wucewa sukayi,Zuhra ta girgirza kai tace "Allah ya shiryeki Naja"

Kallon Janan tayi tace "meyasa shi Aliyu bai karb'a ya siyo miki ruwan ba,saboda dare yayi kuma da d'an nisa tsakanin mu da gidan mai duk da na san baza'a samu bama sai gobe in Allah ya kaimu"

Shiru ta d'anyi kafin tace "dan Allah idan ba damuwa ki taimaka min da ruwan alwallah ko magriba banyi ba"

Da mamaki Zuhra tace "subhanallah ba ruwa a gidan?"

"Eh" kawai tace.

Ran Zuhra ya b'aci dan ta san ko babu ruwa ai Aliyu zai fita ya nemo.

_Auren Manufa,lallai ashe abinda Ummi ta fad'a min gaskiya ne,Aliyu zai auri Janan saboda yayi ramuwar gayya,dama Aliyu zai iyayin haka?ni nayi tunanin da suka fad'an haka saboda zuciyata tayi sanyi ne ashe da gaske ne,ilmin Aliyu bai masa amfani ba,ita Janan meye laifinta?mace mai tausayi ga rashin k'yamar talaka._

Haka ta rik'a tunanin har suka isa gidansu.

Buta ta bata ta nuna mata band'aki, ta shiga tayi tsarki sannan ta fito tayi alwallah.

Bayan ta iddar da sallah tana addu'oi Zuhra taje ta zuba mata abinci ta kawo mata da ruwa a Kofi.

Tashi Janan tayi ta nad'e sallayar tace "bara na tafi kar Aliyu ya dawo ban koma ba,nagode"

"A'a kici abinci kafin ki tafi"

"Bana jin yunwa nagode"

"Hajiya kinga wai bazata ci abinci ba"
Zuhra ta fad'a da k'arfi.

Hajiya dake tsakar gida tace "A'a Jana kici abinci ai kuma kunayin irinsa a birni dambu ne,idan bakici ba sai muyi tunanin ko k'yank'yaninmu kike"

Murmushin jindad'i Janan tayi ta janyo abinci Zuhra na dariya tana fad'in "kinji hajiya wai Jana take ce miki"

Itama Janan d'in dariya take lokacin da taji hajiya na cewa "ina jinku kuna gulmata" sai taji ina ma ace Umma ce Hajiya Zuhra kuma Ummi,dan taji dad'in yadda basu nuna mata kishi ba.

Kad'an taci abincin ta tashi,Zuhra ta kira k'ananta Zainab da Isa,ta d'orawa isan jarkar ruwa ta ok tace ya bi Janan da ita,Zainab ta rakasu.

Tayi musu sallama tana godiya suka tafi.

A hanya ma sai hira suke kamar dama ta sansu,Zainab na fad'in "Aunty zanzo in rik'a tayaki aiki"

"Nima Aunty zan rik'a miki aike in za'a sayo miki abu"

Cike da farin ciki suka k'arasa gidan.

Tana yin sallama ta tarar da su duka ukun Zaune kan tabarma suna hira sun kunna fitilar k'wai.

"Yaya Ali ina yini,Umma ina yini"
Duk suka gaidasu

"Ah yau tsohuwa Abu ce a gidan da Isa"

"Eh"
"To sannunku" yadda taga suna binta da kallon yasa ta gama shan jinin jikinta.

A kewayansu ta kama da k'yar suka sauke ruwan.

Sukayi mata sallama suka tafi.

"Tab lallai yarinyar nan 'yar rainin hankali ce Yaya,to a ina ta san gidansu Zuhra" Ummi ta fad'a.

"Ka gani tana neman tozartamu bazaka d'auki mataki ba Aliyu" Umma ta fad'a.

Janan kuwa najin abinda suke fad'a hakan ne ya sata mak'alewa a bango jikinta sai rawa yake.

Shi kuwa a zafafe ya tashi ya nufi kewayen nasu.










_Sadeey S  Adam_✍
[9/29, 8:16 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
      🍁🍁🍁


*_by SaNaz deeyah_*👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


19

Tana ganin ya shigo ta runtse ido tana jirin me zai biyo baya.

Mari har sau biyu ya sauke mata a fuska sannan ya saka k'afa ya hankad'ata zuwa cikin d'akin sannan ya rufe k'ofar yayi mata duka tamkar ya samu jaka.

*02:30am*
Tana zaune jikin bango tana hawaye tare da soshe-soshe dan sauro ne birjik a d'akin ita kuma abinda bata saba bane,ga jikinta ciwo yake saboda dukan da tasha.

Gogan yana kwance kan katifar sai bacci yake abinsa da alama ya saba da cizon sauron ta fad'a a zuciyar.

Kallonshi kawai take tana mamakin yadda yake da mugunta haka,wai Aliyu mutumin da yake tamkar baya magana ashe gadar zare yayi mata.

Lokaci guda taji sabon zazzab'i na shirin sauka a jikinta ga masifaffan ciwon kai da take fama dashi.

Wasu hawaye na takaici ta sake gogewa tana fad'in ko me Abba yayi ma Aliyu bai kamata ya masu wannan sakayyar ba saboda farkon zuwanshi gidanmu Abba yana sonshi sosai.

Kwanciya tayi a k'asa kan tabarma inda ya umarceta da ta kwanta dan bazasu had'a makwanci ba,mayafinta ta janyo ta rufe jikinta duk da ba dad'in kwanciyar taji ba,amma a hakan bata san sanda bacci b'arawo ya sace ta ba.

*04:15am*

Kamar a mafarki yaji ana ta kyalkyala amai,yayi saurin bud'e ido ya haska tabarmarta yaga bata nan,hakan ne ya tabbatar mai da itace take amai.

Murmushi yayi ya juya kwanciyar a fili ya furta "yanzu kika fara zazzab'i dan a cikin abinda zan miki wannan somun tab'i ne sai naga kin fara aman jini sannan zan tabbatar da cewa na rama, lokacin ne zan fara murnar na cika burina"

Ganin tak'i daina aman ga dare ne gashi wata k'ila ma mak'ota na jinta.

Ya taso ransa a b'ace ya fito ya hasketa
"Oh a k'ofar d'aki kike min amai dan k'azanta?to wallahi ki tabbatar kin samu k'asa kin kwashe sannan ki saka ruwa a gurin banza k'azamar
 yarinya kawai"

Bata tanka masa ba yayi ta bala'i har ya gaji ya koma ciki.

Ita ko Janan da k'yar ta samu aman ya tsaya,a daddafe ta zuba ruwa ta wanke gurin da bibbiyu take ganin komai.

Shigowa d'akin tayi ta zube masa anan tana fad'in "Aliyu bani da lafiya dan Allah ka taimakeni da ko panadol ne"

Dariya yayi a fili irin ta marasa imanin nan yace " 'yar gidan mommy da daddy ai nayi tunanin zaki ce na kaiki asibiti ko na kirawo family doctor ashe kin sakko"

"To bari kiji anan k'auyen babu inda zaki samu wani panadol ki bari gari ya waye sai kije dawa ki sassak'o ki dafa kiyi turare ko ki jik'a ki sha,wannan shine maganinmu kuma babu bawanki da zai yo miki sannan ina kara jaddada miki duk sanda kika sake d'ibar k'afa kikaje gidansu Zuhra wallahi duka ne hukuncinki dan bazaki kashe min aure ba ki hanani auren adalal mace"

Batace masa komai ba ta kwanta tana ta karkarwa idonta a rufe tana hawaye ga jikinta yayi zafi zum.

Batayi bacci ba har sai da aka kira assalatu a kunnenta,da k'yar ta iyayin alwallah tayi sallah saboda sanyin da take ji.

        ************

Ji tayi ana dukanta da k'arfi,a hankali ta bud'e ido tare da yaye mayafin.

"Ki tashi ki dama koko gashi can an siyo gasara,Ummi ta tafi siyo k'osai"

A hankali ta mik'e zaune,akwai zazzab'i a jikinta amma ba kamar da dare ba.

Wani azababben ciwon kai take dan haka bata ma iya bud'esu sosai.

"Magana fa nake miki"

A hankali ta furta "ni ban iya ba na san koko amma ni bansan miye gasara ba"

"Kan uba! Ke ni kike fad'awa haka?"

Da Sauri ta Saka hannayenta a fuska dan karya mareta.

"Ki tashi ki fito yanzu-yanzu ki had'a wuta ki dama"

"Aliyu bana son in maku abinda zaizo bai ciwu ba ni ban Iya irin abincinku ba"

"Wallahi sai kin dama minti d'aya na baki yanzu-yanzu ki fito"

Ya fice ya barta.

Jakarta ta bud'e ta d'akko brush da maclean ta fita.

Ruwa ta zuba a budar ta zauna tana shirin farawa kawai taji an warce.

A tsorace ta d'ago kai ta kalleta.
"Umma lafiya?"

"Ni kike tambaya dan uwarki?"

Jin maganar tayi ta dira a k'irjinta,ga bata son hayaniya saboda bata da lafiya,shiru tayi ta sadda kai,Umma ta cigaba da fad'in "sannu d'iyar shugaban k'asa kowa yana wanke baki da gawayi ke kinayi da maclean ko"

_gawayi kuma?cab Allah ya sawwak'e min_ ta fad'a a zuciyarta.

"Oh ga 'yar iska tana magana kin shareta ko"

"Umma ina mamaki ne"

"Na uban me?"

"Ina ganinku ne tamkar aljanu dan bana ganin isowarku sai dai in ganku a gabana"

Wani wawan duka da takai mata a baya yasa ta bank'arewa tare da maida kanta ta had'e da gwiwa.

Fad'a umma tayi tayi tamkar ana tunzurata.

Aliyu na shigowa ta zayyana masa maganganun cin mutumci wai Janan ce ta fad'a mata,sai kuma ta hau kukan k'arya.

Ganin Janan d'in ta kifa kai bata d'ago ba yasa shi cewa "Janan me na fad'a miki?"

Ta d'ago kanta fuskarnan sharkaf da hawaye hancinta yayi jajir fatar idonta ma tayi jajir ta kumbura.

"Ina son nayi brush kafin na d'ora kuma ta k'wace min,haka wayata ma tun jiya bata dawo min da ita ba"

"Da wayar da wannan d'in duk kin rasasu ki d'auki gawayi ki daka ki wanke bakin kamar yadda kowa keyi" Umma ta fad'a.

Aliyu shima cewa yayi "kiyi yadda tace,idan kuma baza kiyi ba kanki,ni dai kije ki dama mana  koko dan yunwa nakeji kuma inason shiga Kaduna yin magana da ubanki dan shima ya dace ya fara fuskantar k'alubale daga yanzu"

A rud'e ta kalleshi,shi kuma ko a jikinsa ya wuce d'aki kawai.

Umma tayi dariya ta  fita tana fad'in "Allah yayi maka albarka d'ana"

Jikin Janan a sanyaye ta tashi ta nufi can tsakar gidan taje gefen murhunsu ta d'ebo gawayi ta koma ta d'auki dutse ta wankeshi sosai sannan ta daka,a tsantsance tayi brush da gawayi da yatsanta.

Tana gamawa ta shiga d'akin ta same shi a kwance.

"Aliyu nayi brush da gawayin" ta fad'a tana kallon shi.

"Wannan kuma ruwanki,ni dai kije kiyi abinda aka saki dan na fad'a miki fita zanyi"

Durk'usawa tayi a k'asa tace "Aliyu wallahi ban aureka da wata manufa ba,na aureka da zuciya d'aya kuma saboda son da nake maka meyasa bazaka soni kamar yadda nake sonka ba?"

Wata mahaukaciyar dariya ya shek'e da ita sannan ya kalleta yace "so kuma? Ban tab'a jin ina sonki ba,fansa kawai zan d'auka in kad'aki"

"To amma ni meye laifina da zaka rik'a azabtar dani haka?"

"Laifinki ke d'iyar maha'inci ce azzalumi,sannan kin girma an kuma ciyar dake da haram"

"To naji amma dan Allah zan so in san laifin da Abba yayi muku?"

"Ba damuwarki bane"

"To amma ai mahaifina ne"

Kallonta yake ba tare da yace komai ba.

Ta cigaba da fad'in "na yarda zan muku bauta duk abinda kuke so ko ban Iya ba zan iya in muku,duk abinda zakayi wa mahaifina ka dawo dashi kaina dan Allah karka cutar da mahaifina na yarda zan jure komai"

"Har mutuwa?"

"Eh zan iya bada rayuwata saboda soyayya"

"Son da nake maka kai da Abba"

"Hmmm gaskiyane"

"Hakane ai soyayya ba k'arya bace Aliyu,sannan ko wane mahaifi yana da daraja"

"Yayi kyau idan kin gama surutun sai ki tashi ki fita dan ni wallahi na tsaneki"

Tashi yayi ya fice ya barta anan.

Jikinta a sanyaye ta tashi ta fita.

Kallon Ummi tayi wadda tayi cirko-cirko a tsaye tace "ina garin kokon"

Kallonta tayi a yatsine tace "sai yanzu kikaga damar fitowa"

'Daki ta shiga ta d'akko ta mik'o mata tare da fad'in "ga karare da yayi can ki had'a wutar"

Kallon gasarar tayi ita a tunaninta ma kokon ne dan ta ganta fara tas.
_to ya akeyi ne?_ ta tambayi zuciyarta sannan ta wuce dan ta san bata da amsa.

Hayak'i sai tashi yake tana k'ara hura wutar da baki.

Idanunta sun yi jajir sai hawaye take.

Da k'yar ta samu ruwan ya tafasa,wata murar dole ce ta kamata saboda hayak'i.

'Daukan gasarar tayi ta zuba kan ruwan da yake tafasa.

Cigaba tayi da hura wutar tana jiran ya dahu.

Bayan ta gama ta juye a cikin kwanon da suka kawo mata sannan ta d'auka ta nufi d'akin Umma kanta nata zafi saboda ciwo.

Da sallama ta bud'e labilen sannan ta ajje a gaban Umma tace "gashinan na gama"

"Dama koko kusan awa guda,gaskiya yarinya da sauranki"

"Ummi d'akko Kofi in zubawa Aliyu idan yaga dama ya rage mata"

Mik'owa Umma tayi tana fad'in "Umma  yau rogo zata dafa mana da rana"

"In kin gama karyawa sai kije ki siyo bushsh........" Bata gama fad'a ba ta tsaya cak yadda taga kokon wani guda-guda gashi ya canza kala ma,a tak'aice ba wanda zai iya sha.

"Meye wannan?" Umma ta fad'a da k'arfi.

Duburburcewa Janan tayi ta rasa me zata ce ma.

"Tabb lallai ke d'in nan kin cika 'yar rainin wayo" Ummi ta fad'a.

"Maza ki kirawo min Aliyu a waje" Umma ta fad'a hannunta rik'e da murfin kwanon har lokacin bata rufe ba

Ummi ta tashi da sauri ta fita,ita kuwa Janan tun kafin ya shigo ta fara kuka dan ta san duka ne zata sha tamkar Jaka.








_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:16 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
    *DIREBAN GIDANMU*
      🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


_*🎶🎶Wannan taken na masoya ne👯🏻‍♂wannan shafin na masoya ne💃.🎶🎶*_
_Ban san yadda zan iya musalta jindad'i na gareku masoyana,wannan comments d'in naku yana matuk'ar ratsa zuciya ta,ta hakane nake samun more ideas,kuma kuna k'arfafan gwiwa ina yinku sosai masoyana makarantana wannan shafin naku ne kyauta🎁❤_.



20

Kafin yazo ta tashi tayi saurin shigewa d'aki.

Rufowa tayi ta saka sakata ta ciki.

'Kirjinta sai bugawa yake musamman lokacin da taji yana fad'in "Janan ki bud'e ko in b'alla k'ofar"

Zuciyarta nata wasi-wasin akan ta bud'e ko karta bud'e.

Daga k'arshe dai kawai ta bud'e tare da komawa gefe.

Yana shigowa ya shak'ota,da k'arfi ta k'waci kanta ta fito tsakar gidan,ya biyo ta yana ta duka.

Ganin yana neman kasheta ne ya saka tayi hanyar waje,zata fita yayi dai-dai da shigowar Zuhra gidan.

Da sauri ta tare ta tare da fad'in "Subhanallah"

Baima damu da ganin Zuhrar ba ya taho gadan-gadan,da sauri Zuhra ta shiga gabanta tare da tare wa da hannunta.

"Meye hakan?" Ya fad'a

"Kai zan tambaya meye hakan"

Iccen hannunsa ya yadda tare da hard'e hannunshi yana kallonta "shin wama yace kizo gidannan da sassafe haka?"

"Allah" ta fad'a tana masa kallon mamaki sannan ta cigaba da cewa "Allah ne ya saka na zo gidan nan yanzu dan ya nuna min irin yadda kake azabtar da matarka dan ya yanke min wahala"

"Kamar ya kenan?"

"Kamar yadda na fad'a dan bazan tab'a auren miji mai dukan matarsa ba,bari in tak'aita maka daga ranar da mijina ya kai hannunsa jikina to tabbas ya tsinka igiyar aurensa"

Ta juya ta kalli Janan taga yadda duk sauro yayi mata tamkar kuraje sunyi jajir,ga fuskarta da jikinta duk sahun duka.

"Wannan ai abin kunya ne,kuma ka jawa kanka zagi a k'auyennan,da a haka zata fita kai kuma kana binta da duka ko d'ankwali babu a kanta Aliyu ina ilminka?"
Wasu hawaye ne suka sauka a fuskarta ta saka hannu ta goge.

"Zo muje" taja hannun Janan zasu fita yayi saurin cewa.

"Idan kika fita wallahi sai kin fuskanci tsatstsauran hukunci"

Cak ta tsaya tana k'ok'arin janye hannunta daga na Zuhra.
Zuhra tayi-tayi Janan ta bita amma tace a'a kawai,ita tsoronta d'aya karya saketa dan son da take masa ta gwammace ta zauna a hakan.

Cikin b'acin rai Zuhra ta tafi,Janan ta juyo tare da ajje gwiwoyinta a k'asa
"Umma dan Allah kuyi hak'uri"

"Dalla yi mana shiru munafuka kawai"

"Yaya yanzu shikenan ta rabaku da Zuhra" a fusace ya juyo ya kalli Ummi Wanda kallon ya saka ta yin shiru dan yadda taga idonsa ya kad'a yayi jajir.

Bai sake yin magana ba kawai ya fice ya bar gidan.

        **********

A babban falon gidansu Janan yake zaune ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana jiran fitowar Abba.

Tare da Mameey suka sakko wanda yana ganin ran Aliyu ya b'ace ya kawo a ransa cewa lallai k'ila Janan ta masa laifi Wanda shi yace babu ruwanshi game da aurensu.

Zaunawa sukayi yana binsu da ido,ganin yak'i ko gaishesu ne yasa Mameey fad'in "na aika akai muku breakfast akace gidan a kulle"

"Ke kike tare da yunwa amma bani ba" yadda ya fad'i maganar ne ya saka ta saurin tashi daga kishingid'e ta kalleshi "Aliyu kasan kuwa dawa kake magana?"

" 'Kwarai kuwa Fatsima ce uwar Janan"

Abba ne ya tashi zai kifa masa mari ya rik'e hannunsa yace "dakata Hashim idan wannan hannun ya saba Marin Janan to ni nafi k'arfin ka mareni"

"Securities" Abba ya fad'a da k'arfi.

Aikuwa su wajen 5 suka shigo har lokacin Aliyu bai saki hannunsa ba.

"Ku kamashi Ku rufe min har sai na nemeshi"

Suna rik'eshi ya fara magana da k'arfi "Shekaru 8 nayi a prison dalilinka,ka kashe min mahaifina da k'anwata kuma matata sannan a wannan karon ma kana neman aikata haka,to wallahi ka tabbatar idan aka rufeni tamkar an rufe Janan a kabari ne,saboda na bada sallahun idan ban dawo ba a kasheta"

Jin hakane yasa Abba yace su sake shi sannan ya basu umarnin su fita.

Kallon Aliyu ya sake yi yace "waye kai?"

"Haidar abokin shahararren mai shigo da miyagun k'wayoyi Usman Attahir wanda a shekaru goma da suka wuce ka kamani ka saka a prison har tsawon shekara takwas dan haka yau nazo d'aukar fansa"

Shiru Abba yayi dan har yanzu ya kasa tuno ko wane ne.

"Lokacin da aka kawoni gurinku kuna meeting kasa aka fita dani kace a kulleni har sai ka nemeni tsahon shekaru takwas baka duba case d'in ba kuma kasan bani da laifi,sai wani bawan Allah ne yayi min hanya aka sake ni,ka cuci rayuwata ni da mahaifiyata da k'anwata da kuma Mahaifina da matata daka kashe,lokacin da na fito nan gidan shine gidanmu amma ina zuwa naga komai ya canza hatta mak'otanmu babu su duk an had'e har gidansu a gina maka tamfatsetsen gida, sanin da nayiwa unguwarnan a da bamu da yawa dan wajen garice sosai amma sai gashi ta dawo unguwa ta masu kud'i kuma cikin gari ,dukiyarmu da gadonmu gonakinmu da filayenmu duk suna gidan nan"

"Haka nayi ta garari tsawon wata biyar ina neman dangina,a sanadin wata yarinya zuhriyya na samu iyayena a can wani k'auye kusa da nan Kaduna,tun daga lokacin na shirya d'aukar fansa har na samu aiki a gidan nan kuma naga babu yadda za'ayi na d'au fansa ba tare da na auri zuri'arka ba,haka nayi ta addu'ar cimma nasara har Allah ya kawoni lokacin"

"Janan ta fara shan uk'uba domin kai bazan iya yi maka komai kai tsaye ba amma ka shirya amsar gayyata daga kotu dan daga nan can na nufa"

Ya juya zai fita Mameey ta fara kuka tana fad'in "Janan baiwar Allah ce karka cutar da ita"

"Nima bawan Allah ne amma an cutar dani"

"Kayi hak'uri Haidar" Abba ya fad'a a sanyaye.

"Ka rik'e hak'urinka zai maka amfani a kotu bana buk'atar jin wani abu"

Da sauri ya fice,Abba ya zube akan kujera yana fad'in "Allah ka sani banyi da niyya ba bani da shirin cutar kowa" hawaye ne ya sauka a fuskarsa Mameey tayi saurin cewa.

"Haba gwarzon namiji bai kamata ana ganin hawaye a fuskarka ba,duk kanmu musan baka cuceshi ba,hasalima bazaka ce ga kamanninshi ba in ba yanzu daya bayyana kanshi, shima idan zaiyi tunani ya san da ka cuceshi to zaka gane shi kuma ka hanashi aiki a gidanka bare auren 'yarka"

"Ni yanzu kawai Janan nake ji na san tana cikin wani hali gashi sun bar wancan gidan dana basu a tunanina"


"Karki dameni da maganar Janan babu ruwana da ita komai ya faru damu ita ce sila"

" Janan yarinya ce she's just 16 dole in damu da ita dan bata da wani wayo"

"Amma a hakan ai ta san tace tana son wani ko?"

"Ka daina wannan zancen soyayya ai daban ce"

"Nima ki daina min zancen Janan ki k'yaleni inji da lamarin yaron nan"

"Wai to da yake ik'irarin gidan nan nasu ne shin ba siya kayi ba?kuma ai kana da takardun filin"

"Babu nashi a ciki dan lokacin dana siyi filin mak'otansu shi gidansu babu kowa naga babu yadda zanyi in raba ginina kawai na saka aka had'a min dashi da niyyar idan masu gidan sun zo zan basu kud'in gidan ko nawa suke buk'ata,banma san gidansu Haidar bane, wallahi aiki ya shige min na manta shaf da case d'insa sai da aka yi shekara takwas sannan aka zo min da labarin har yanzu yana nan to a lokacin ne na rubuta aka sake shi dan ni ko kamannin shi ban sani ba a lokacin amma nace a bashi hak'uri kawai"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un,yallab'ai meyasa ka had'e da gidan da baka san ko na wane ba,yanzu dai kawai ka bashi hak'k'insa"

"Tabbas a lokacin ance min 'yan gidan sun tashi ba'asan ina suka shiga ba tun lokacin da 'yan sanda suka kawo musu farmaki suka kashe mutum d'aya suka tafi da mutum d'aya,ban tab'a kawowa a raina Haidar ne dan na manta da case d'inshi tun da dama kawo min akayi ina jin ko wani abu sukawa 'yan sanda ko rashin kunya shiyasa sukayi kisa,zan nemishi ya fad'i ko nawa yake buk'ata a matsayin kud'in gidan zan bashi,amma ni ban san labarin dukiyarshi da gonaki da filayen shi da yace suna hannuna ba"

"Allah ya rabamu da sharrin mugu yasa abin ya tsaya iya haka"

"Ameen" Abba ya fad'a.

Haka suka yini cikin damuwa,Mameey sai kiran Janan take amma wayarta a kashe.

Koda Fahad da Fauziyya suka dawo Mameey ta basu labari, Fahad yace k'arya yake kurin banzane babu abinda zai iya,Fauziyya kuwa tace zataje gobe ta gano lafiyar Janan tunda ta san k'auyen su Aliyun.


         *********

Tana zaune gaban Malam tana kuka, Aliyu na d'ayan gefen Malam ji yake zuciyarsa na k'ara zafi idan yana kukan.

Malam ya cigaba da fad'in "karka damu Aliyu duk kishi ne ke damun matan yanzu su a dole bazasu auri mai mata ba amma ai mune muke da iko dasu dan haka ka fara shirye-shirye wata na kamawa za'ayi aurenku da iznin Allah"

"Allah ya yarda Malam" Aliyu ya amsa cikin jindad'i.

"Tashi ki bamu guri" Malam ya fad'a

Jikinta a sanyaye ta fita dan bata da ikon musawa iyayenta kuma tana son Aliyu amma ta tsorata da lamarinsa.
***
Yana shiga gida ya tarar dasu Umma zaune a tsakar gida suna cin abinci.

Ya k'arasa ya zauna "Umma zan kai maganar kotu"

"Kotu kuma?"

"Eh dan nan ne kad'ai za'a k'watar mana hak'k'inmu,kuma mun gama magana da Malam yace wata mai kamawa za'ayi bikinmu da Zuhra dan ta kwashe abinda ya faru da safe ta fad'a masa tace kuma ta fasa aurena to bai yarda ba kuma yace dole ne aurena da ita da iznin Allah"

'Daga hannu Umma tayi tana godiya ga Allah tare da k'arfafa masa gwiwa akan ya kai kotu.

"Yaya waccan sakaran fa tana d'aki tun safe da ka fita ko abincin rana sai mu mukayi kuma bamu kai mata ba dan mu ba bayinta bane,tun d'azu take mana aman munafurci wai zazzab'i take"

"Ki rabu da ita duk zata ajje rawar kannan"

Karaf a kunnen mak'ociyarsu Asabe,ta tausayawa Janan sosai,tana jin Aliyu na fad'in ya fita ita kuwa tayi saurin d'ibar guntun taliyar data ajje in anjima yaranta suci,mayafi ta zura kawai tayi gidan dan ta bawa Janan.









_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:16 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
       🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


21

Da sallama ta shigo gidan ta gaida Umma sannan tace "Ni kuwa amarya na nan?"

Ummi ta kalleta tace "wace Amarya kuma"

"Amaryar gidan nan mana"

"Ai bamu da Amarya mu"

"To Janan nake nufi"

"Tana d'akinta" Ummin ta fad'a tana tab'e baki.

Asabe ta wuce zuwa d'akin Janan.

"Umma kiga wani tsegumi wurin Asabe?"

"To ke ina ruwanki"

"Uhmmm"

Asabe na shiga taga Janan d'in ta tattare guri d'aya sai nishi take,k'arasawa  tayi kan tabarmar ta zauna tare da d'ago Janan.

Bata abincin tayi idonta a rufe ta girgiza kai tare da fad'in "na k'oshi"

"A'a ki daure"

Da k'yar ta samu Janan d'in ta fara cin abincin,cokali uku tayi sai amai,Asabe ce ta bata ruwa ta kuskure bakinta sannan ta wanke gurin.

"Ki k'arasa cin abinci Janan"

"A'a na k'oshi kaina ciwo yake"

"Rashin cin abincin da kikayi tun safe shine ya jawo miki hakan,ki daure ki k'arasa ci,sai inje in d'akko miki magani na san in kika sha cikin k'ank'anin lokaci zaki samu sauk'i insha Allahu"

Haka Janan ta daure taci abincin ba dan yana mata dad'i ba sai dan yunwar da takeji kawai.

Asabe ta koma gidanta ta jik'owa Janan magani ta kawo mata,runtse ido kawai tayi tasha.

Aikuwa tana kwanciya bacci mai nauyi ya d'auketa,Asabe ta gyara mata komai sannan ta fita.

Tana farkawa taji wata muguwar kasala,ga uban zuffa duk ta had'e mata jiki,kallon agogon hannunta tayi taga biyar da rabi ma ta wuce.

Tashi tayi ta zuba ruwa a bokiti ta nufi band'aki tayi wanka,duk dai a tsantsance take rayuwar gidan da k'auyen ba irin tata ba.

Sai da ta dawo d'akin ta lura babu akwatunanta sai wani guda d'aya wanda bata san meya kawo shi ba kuma bata san na waye ba.

A hankali ta taka har gurin,ta janyo ta bud'e,atamfofi ta gani ta fara d'agasu duk kansu robber ne(lagona) d'inkakku guda 5 sai  Vaseline da kwalli da farar powder a gefe,sai kuma hijabai milk and black da wani takalmi irin na narkakkiyar robber wanda ake sayar dasu 500-800 shima black ne.

Abin ya matuk'ar bata mamaki dan tana d'aga kayan ta gansu tamkar an gwada ta.

"Nawa ne?hmm to ina lefen da Mameey tayi min?"

Murmushi kawai tayi lokacin data tabbatar Aliyu ne ya d'auke akwatunan ko shakka babu ta san shine.

Mai ta shafa sannan ta d'akko d'aya daga cikin atamfofin ta saka,riga da zani ne kina ganin d'inkin kin san a k'auyen aka yi shi.

Sai ta koma kamar irin wayayyiyar k'auyen nan.

Ita kanta data kalli kanta sai da tayi dariya tace "oh dubeni tamkar 'yar k'auye,lallai soyayya kenan Allah ka karkato da hankalin mijina gareni kasa ya soni fiye da yadda nake sonshi ya kuma yafewa Abba laifin da yace yayi masa.

Haka Janan ta cigaba da fuskantar matsaloli da ban da ban daga gurin su Aliyu amma tana jure komai duka da zagi har sun zame mata jiki,akwatunanta kuwa cewa yayi ya sayar da wasu sauran kuwa Zuhra zai kaiwa lefe.

Kullum babu ranar da bazai doketa ba saboda girki ita babu abinda ta iya a irin girkinsu in ba shinkafa da taliya ba su kam tsuro mata da abu suke Wanda Sam bata sansu ba,haka zatayi yak'i ciyuwa shi kuma ya jibgeta.

Yau ta kasance Monday satinta d'aya a gidan Aliyu bata ma san wainar da ake toyawa ba a gidansu.

Tashi tayi kawai da son taje skul yau,dan haka ta shirya da wuri ta tambayeshi yace
 "ban hanaki ba amma ko gwandala ta bazan baki ba kuma bance ki biya gidan kowa ba,daga makaranta ki dawo gida idan naji kin biya wani gurin ranki sai yayi mummunan b'aci"

"An gama" ta fad'a tana murmushi dan abubuwan sun zame mata jiki.

Har zata fita taji Umma tace "ina zaki je?"

Juyowa tayi ta kalleta tace "Zanje makaranta"

"Wa kike son ya miki girki?waye bawanki?"

"Zan dawo da wuri Umma"

"Babu inda zaki je"

"Umma k'yaleta taja munafurci ne ke damunta" suka juya duka suka kalli Aliyu.

"Oh kaine ka mara mata baya akan ta tafi"

"Umma ki barta kawai ai ta sani nace kartaje ko ina daga can ta dawo nan"

"Kaima ai bakayi karatu ba dan haka itama baza tayi ba"

Da k'yar Umma ta yarda Janan ta tafi,ita Janan ma har mamaki take da Aliyu ya barta.

      **********

Tun daga nesa lubna ta tsaya tana k'are mata kallo"

Tab'o Raihan tayi tace "kinga wata can tana tafiya kamar zata fad'i kuma wallahi kamar Janan"

Raihan ta tashi da sauri tace "wallahi itace" duk kansu suka k'arasa gurinta da sauri.

"Ke meye hakan?" Raihan ta tambayeta.

"Kamarya?"

"Naje gidanki sau biyu baki nan wayarki kuma bata shiga"

Murmushi tayi tace "ai mun canza gida mun koma can _kangire_"

"ina ne kuma haka?"

"Garin su Aliyu mana"

"Wannan d'an iskan?" Lubna ta fad'a tana tab'e baki.

"Mijina ne d'an iskan?"

"Haba lubna bai kamata kice haka ba" Raihan tayi maganar,tare da jan hannun Janan
"zo muje plantation akwai maganar da zamuyi"

Su ukun suka tafi,lubna da Janan suka zauna Raihan ta tsaya a tsaye ta hard'e hannu ta kalli Janan tace "duk wanda ya sanki a baya ya ganki yanzu yasan kina cikin wahala"

Zama tayi gefenta ta cigaba da fad'in "Janan kin ganki kuwa ?hijabin dake jikinki ma bai b'oye ramarki ba,kayan jikinki tamkar na masu furar bakin asibiti wanda wanki d'aya zaka musu su koma tsumma,takalmin k'afarki tamkar bathroom silifas d'inki haba Janan auren talaka hauka ne?at least ai ya kamata ki banbanta dasu ina uban kayan da Mameey ta had'a miki"

"Ya sai dasu saboda bashi da kud'i kuma nima ban hana ba kuma nina bashi da kaina"

"K'arya kike Janan ko ince k'ayar yake?akwai dalili dai dubi yadda kika zama fuskarki duk k'uraje da cizon sauro wanda da ba haka kike ba,ada fatarki smooth ce,sannan ga kuncinki nan sahun yatsu biyar bai b'ace ba,ko zaki b'oyewa kowa damuwarki bai kamata ki b'oye min ba saboda tare muka taso dake tun muna yara Janan"

Sai a lokacin yanayinta ya canza idonta duk ya cicciko ta kalli lubna tace "karku min tambayar titsiye dan Allah ni dai kawai ku tayani da addu'a Allah ya kawo min sassauci amma tabbas ina shan wahala kullum sai naci duka a gidan Aliyu"

"Mafita d'aya shine kice ya baki takardarki tun da babu dole"

"Haba lubna ki fad'i alkhairi ko kiyi shiru" Raihan ta fad'a.

"Ai gaskiya ce"

"Ina sonshi shiyasa nake jure duk wata wahala" ta fad'a lokacin da hawaye ya sauka a idonta.

"Kina da cikinsa ne?" Lubna ta sake tambaya.

"Babu abinda ya tab'a shiga tsakaninmu"

"To ni zanje in ci masa mutumci in kuma karb'ar miki takardar saki"

Mik'ewa tayi tsaye tace "karki soma lubna"

"Amma zaki iya cewa kinfi son Aliyu akan Abba?"

"Karki had'a iyaye da miji dan babu had'i"

"To in kuwa hakane kin iya banzar soyayya dan babu yadda za'ai ki cigaba da zama da Aliyu"

"Lubna kiyi shiru haka mana" Raihan ta fad'a a tsawace

"Dole in fad'a mata gaskiya"

"Shikenan"

Kallon Janan tayi tace "to Aliyu ya kai Abba kotu suna shari'a dan ranar laraba ma za'a cigaba da shari'ar"

"Me akan me?" Janan tana maganar tana kuka.

"Akan wata banzar hujjarsa,labarin yana da tsawo Janan sai mun zauna dan ko yaushe ina zuwa ina kuma jin shari'ar gaskiya Aliyu baya da mutumci"

Da sauri Janan ta juya,Raihan tayi saurin rik'ota.

"Ina zaki?"

"Gida" ta bata amsa sannan ta fuzge hannunta ta cigaba da tafiya da sauri.

Suka biyo ta a baya.

Ta inda Yarima yake zaune shi da friends d'insa ta wuce,da sauri ya tashi yasha gabanta.

"Amarya lafiya?yaushe kika shigo?me akayi miki?"
Hawayen fuskarta ta goge tana kallonsa tace "bakomai"

A lokacin su Raihan suka k'araso,ya tambayesu suka ce suma basu sani ba.

Yayi k'ok'arin binta Raihan tayi saurin wayencewa ta tsaya dashi ita kuwa Lubna ta bita.

Napep suka tara har k'ofar gidan.

Babu alamar security ko d'aya a gidan hakan ne ya tabbatar mata akwai matsala.

Tayi knocking maigadi ya fito,kallonta yayi sannan yace ''a'a Janan ce a gidan?"

"Eh ina su baita"

"Suna daga ciki" ya fad'a,taji dad'in hakan tana shiga kuwa ta gansu a farfajiyar gidan.

Da sauri kuwa baita ya taso yazo gurinta "Hajiya Janan sannu"
"Yawwa baita"
"Ciki zaki shiga?"
Tambayar ta bata mamaki ta kalleshi tace "da matsala ne?"

"Eh yace in dai kika zo karmu bari ki shigo"

"Cab wallahi dole in shiga inga halin da Abba yake ciki"

Da sauri ta wuce Lubna na biye da ita.

A falo taga 'yan gidan gaba d'aya.

"Karki sake ki k'araso nan''
Abba ya fad'a tare da mik'ewa tsaye.

Su Fauziyya da Mameey da Fahad ma duk suka mik'e.

" Abba karka yi min haka dan Allah kayi hak'uri"

"Idan baki bar min gida ba zan tsine miki Janan dama kina cikin fushina har yanzu"

Fauziyya ta taho da sauri gurinta Abba ya tsayar da ita cikin tsawa "idan kika je gurinta sai dai ki bita kema bazaki sake rab'ata ba"

Duk kansu kuka suke,idan ka d'auke Fahad da Abba suma dai kana ganinsu kasan suna cikin damuwa matuk'a.

"Bana k'aunar k'ara ganinki har k'arshen rayuwata Janan,kece sanadi kin take umarni na idan har na mutu to tabbas ke kika kasheni Janan domin ke kika yayo mana bala'in yaron nan baya ganin darajar ni mahaifinki ne ke kuma matarshi amma haka yake zagina nida mahaifiyarki ko kunya babu kin cuceni Janan"

Kukan ta ya fito fili ta fara fad'in "na shiga uku ni Janan Abba ka yafe min in har baka yafe min ba na san wuta zan shiga,Abba na cuci kaina na cuceku dan Allah kuyi hak'uri Mameey"


Duk tabi ta rud'e sosai,rik'e ta Lubna tayi itama tana basu hak'uri tana kuka.

Abba na k'ara cewa "babu yafiya tsakanina dake sai dai hisabi Janan,ki fita kawai bana son ganinki"

Da wannan kalaman suka fito daga gidan duk Kansu suna kuka har Lubna.

Gidansu Lubna suka nufa ta zauna tana ta bata hak'uri ita da ummansu amma kuka take k'ara yi.

Idonta yayi Jajir ta kalli Lubna tace "in har ni 'yar halak ce na bar auren Aliyu,na tsane shi bana son ko k'ara ganinshi Allah ya saka min zalunta ta da yayi,ko me Abba yayi wa. Aliyu bamu cancanci haka daga gareshi ba"

Hmmm "ba zuga ki nake ba Janan amma da kinji irin furucin da yayi wa Mameey a zama na k'arshe da saikin fi tsanarsa wallahi"

Ta goge hawayen idonta tace "ki fad'amin labarin Aliyu dan Allah ki fad'a min me Abba yayi masa?"

"Ki kad'ai kunnenki ki nutsu zan baki labarin Aliyu da kuma irin laifin da aka masa kamar yadda ya fad'a a kotu"

_*Shekarun baya da suka wuce....*_
_(Labarin Aliyu)_








*_Ku biyo ni kuji👂_*













_*Sadeey S Adam*_✍
[9/29, 8:17 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁




_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


_🎶Kin shiga raina kin samu guri kin zaunaaaa......zana rik'e ki hannu biyu alk'awari zan miki gata😄_🎶
*_Taken naki ne Ayshat A Muh'd(Aunty)_*



    💃💃 _...........🎶Soyayya ce,nayo dace ni nayo murna haushi ya gushe_🎶
_*in kana da masoya ka more💃in kana da masoya kafi k'arfin wulak'anci💃in kana da masoya ba k'unci💃Allah ka barni da masoyana ka k'ara min Adadin su ka inganta min rayuwarsu ka sa fara'a dawwamammiya a zukatan su Ameen ya rabbil alamin🙏*_





22

_Shekarun baya da suka wuce_
_*(LABARIN ALIYU)*_

Haifaffan garin nan ne cikin unguwarnan lokacin bata shigo gari ba dan k'auye ne sosai sai an fita daga Kaduna a lokacin kafin a had'e shi da garin Kaduna ya dawo cikin gari sosai,a lokacin sunan shi _bad'ko village_ kafin ya dawo G.R.A.

Aliyu tun tasowarsu Fulani ne usur kuma kyawawan Fulani kamar yadda kika gani.

Mahaifinsa shahararren manomi ne kuma makiyayi.

'Ya'yanshi biyu da Aliyu da Sabira wadda ake kiranta da Ummi, haka zalika matanshi biyu Umma Saude sai Gwaggo Zaliha wadda bata tab'a haihuwa a gidan ba.

Gidansu Aliyu Family house ne an kewayeshi da dannin kara sai dai ko wane gini a ciki ginin jar k'asa ne saiya kewaye abinsa still daga ciki.

'Kannen babansa,baba Isa da baba Tanimu ko wanne da matansa a ciki.
Shi baba Isa matanshi uku yayinda baba taminu yake da mace d'aya sai 'ya'yansu birjik.

Sai kuma d'an wansu baba halliru dashi yake zaune a can _Cinai_ shima d'ansa nan gidan yazo ya kafa nashi d'akin ya cigaba da noma anan.

Kinsan idan aka ce miki an had'a abu na yawa dole ayi gulma amma duk da haka suna da had'in kai wajen cima,domin abinci idan anyi kowa sai an kasa an bashi.

Hafsa d'iyace ga autansu baba Rabe(mahaifin Aliyu),tun tasowarta a gidan su Aliyu ta tashi ta ganta domin tun tana 'yar shekara uku iyayenta suka rasu sanadin cutar shanu data kama su a k'auyen da suke mai suna _dawo_ ita Hafsa lokacin an kawota gidansu Aliyu ta d'an zauna sai Allah yasa cutar bata ritsa da ita ba,haka baba Rabe ya cigaba da rik'onta ta, ta kuma zauna a d'akin Zaliha tunda itace bata tab'a haihuwa ba.

Zaliha kuwa ta d'auki son duniya ta d'orawa Hafsa haka tayi ta tara kud'i tana yiwa Hafsa gata.

Aliyu kuwa dama baba Rabe ya jajirce a kansa saboda lokacin suna shigowa cikin Kaduna a k'afa suzo makaranta sai yaran k'auyen suke gudun karatu saboda wahala sunfi maida hankalinsu ga noma da kuma kiwo wanda shine al'adar 'yan garin.

Ganin Aliyu baya wasa da karatu yasa baba ya rik'a tara kud'i yana biya masa,a haka har ya shiga aji uku na secondary Jss3 kenan,a lokacin kuma baba ya siya masa keke yake zuwa dashi har ya gama sannan aka canza masa da wani tsohon Babur.

A yadda ya bayyana yace yasha wahala sosai saboda shekara uku yana nema admission daya samu sai a bawa 'ya'yan masu kud'i,a shekarata hud'u ne ya nema shima ya damu dan yaci duk wata jarabawa da aka yi amma sai akace sai ya kawo dubu d'ari biyu sannan zai samu gurbin karatu a jami'ar.

Baba kuwa yace ya hak'ura kawai,shi kuma ya dage yace yana so sai baba yace to Indai haka ne sai dai ya nemo kud'i da kansa domin shi kud'in da yake tarawa nasu ne wanda zasu inganta rayuwarsu ko bayan ransa baya so su wulak'anta.

A haka ya shiga tunanin mafita,kuma lokacin ne aka saka bikinsu da Hafsa wanda dama suna son junansu.

Ganin ba yadda za'ai ya samu kud'in yasa yace ya hak'ura kawai ya koma gona ya cigaba da shuka da kuma taya baba kiwon shanuwansu.

Tun aurensu da Hafsa gidansu ya fara lalacewa domin gwaggo Zaliha Sam bata k'aunar auren Hafsa da Aliyu dan ita tafiso ta aurar da ita a birni yarinyar da ko primary batayi ba dan ko zo bata sani da turanci ba.

Kullum fad'a da tsegumi a gidan,goggo Zaliha bata da magana sai ta fad'in an asirce ta an hanata haihuwa d'iyar da take iko da ita an aurar da ita ga mutumin da ko gidan kansa baya dashi sai d'an kewaye a gidan ubansa tun abin baya damun Aliyu har yazo yana damunsa daga lokacin kuma ya fara Neman mafita.


Birnin ya shiga yaje gidan wani abokinsa da sukayi secondary school tare dan ya nema masa koda gadi ne a birni dan shi ya gaji da gori.

"Zaka samu abinda yafi gadi idan har ka daure" Usman ya fad'a lokacin da Aliyu yaje masa da k'orafi.

"Wane aiki kenan?" Aliyu ya tambaya.

"Aikine mara wahala amma kuma yana da had'ari sannan aikin bana ragwaye bane zaka iya?"

"Ka sakani a duhu Usman kamin bayani"

"Karka damu Haidar zanzo gobe muje in kaiwa oga kayan dana kawo, a cikin Abuja yake, sannan in had'a ka dashi kaima ka samu kasonka ai daga ranar abokina ka zama Alhaji dan zaka samu a k'alla dubu d'ari biyar idan har ka kawo kaya lafiya"

"Bazan iya sata ko yankan kai ba Usman na hak'ura kawai"

"Dalla Abokina karka damu magunguna ne zaka shigo dasu kawai,ai wallahi wannan tsohon mashin d'in ma babu kai babu shi"

"Kai fa baka da mutumci abin harda zagi da ai keke gareni yaushe nayi Babur d'inma"

"Mazaaa! ina gaya maka karka damu ba wata matsala"

A haka Aliyu ya dawo k'auyen cike da murna,yana tsara yadda zaiyi da kud'in idan ya samu.

Yana shiga gida ya tarar da malam zaune kan tabarma a k'asan darbejiya dake can k'arshen gidan.

Da sauri Aliyu ya k'arasa wajen yace "sannu da hutawa baba"

"Yawwa haidar dama dawowarka nake jira dan yaune nayi niyya fad'a maka wani sirri zo ka zauna"

Zama yayi kusa da baba,cikin rad'a baba yake fad'in "ka san ina da manyan gonaki guda hud'u Wanda duk Wanda ke shuka a gidan nan a ciki yake yi ko?"

"Eh" Aliyu ya amsa

"To inada manyan filaye guda uku Kasan su?"

"Na san guda d'aya dai"

"To zanje dakai in nuna maka sauran biyun,amma kafinnan ina son sanar da kai cewa takardun filayen dana gonakin dana gidan nan duk suna k'asan bishiyarnan nayi rami mai zurfi na saka a cikin tukunya dan karsu lalace,Aliyu na ajje muku ne domin zai muku amfani kaida k'anwarka bayan raina"

Jikin Aliyu yayi sanyi,a take sukaje baba ya nuna masa sauran filayen suka dawo.

Matarsa ya tarar kwance tana ta juyi,tsohon cikine da ita a lokacin.

Ganin bata jin dad'i sosai yasa ya kasa fita ko ina ya zauna suna ta hira yana kwantar mata da hankali dan tana mugun tsoron haihuwa ga wani lokacin cikin yana wahalar da ita.

Da dare bayan sallahr magariba suna zauna ta gama abinci kenan ta zubo sai ga laure 'yar gidan Malam Isa ta shigo kewayen "Yaya Haidar kazo kayi bak'o a mota"

Kallonta yayi yace "waye kuma haka har a mota?"

"Yace dai kai yake nema"

Tunda ta fara magana Hafsa ta tsaya kawai tana kallonta,ta shi yayi yana shirin fita tace "ah'ah ga abinci kuma na zubo mana"

"Ki fara ci kafin na dawo"
"A'a kaje ka dawo kawai" ta fad'a

Yana fita ya tarar da Usman tsaye jikin motarsa,bayan sun gaisa yace "lafiya kuwa na ganka a daren nan?"

Usman yace "wallahi wajen wani malami zanje nan bayan garinku kuma mota bazata shiga ba saboda gonaki ga kuma yashi,shine nazo neman alfarmar ka aramin Babur d'inka inyi sauri inje in dawo"

Aliyu bai kawo komai a ranshi ba ya shiga ya fito masa da babur d'in sannan ya bashi mukulli yace "Allah ya dawo da kai lafiya"

Shima Usman ya bashi mukullin motar yace "idan na dawo sai in karb'a"

"A'a ka rik'e a gurin ka"

"A'a ka ajje min"

Haka sukayi dashi ya tafi.

Aliyu ya dawo gida suka fara cin abinci da matarshi hankali kwance.

Tafiyar Usman batafi da minti 30 ba kawai sukaji ana  harbe harbe ga kuma jiniya ta motocin 'yan sanda.

Kafin su fito waje tuni 'yan sanda sun shigo gidan wasu kuma suna waje sun wa gidan k'awanya dan kar wani ya sid'ad'e ya gudu.

Salati su baba da baba Tanimu ke tayi kasancewar sunga bak'on abu dan sun san zuwan 'yan sanda ba alkhairi bane.

"Lafiya me muka yi muku?" Aliyu yake tambayarsu.

"Ina mukullin motar dake waje?" d'aya daga cikin 'yan sanda ya tambayeshi.

"Mai motar ya tafi da mukullinsa taya zai barshi anan?"

Mari ya kifa masa ya sake tambayar mukullin motar,shi kuma Aliyu a tunaninsa ko wani ne a k'auyen yaje yace an kawo masa mota ko kuma tunaninsa ana zargin motar sata ce shiyasa ya kafe yace babu mukullin a hannunsa.

'Dan sandan ya bawa sauran umarni da su shiga su duba ko ina,bayan an cajeshi babu mukullin a jikinsa.

Ba'a wani sha wuyar ganinsa ba dan ba b'oyeshi yayi ba.

"Wannan kuma na wace motarne?" d'an sandan ya d'aga mukullin yana tambaya yana kallon Aliyu.

"Yallab'ai wallahi ba nawa bane ajiya aka bani"

Fita sukayi suka bud'e motar,wasu manya-manyan kwalaye aka fito dasu guda uku sai bindiga 'yar k'arama.

Suna bud'e kwalin suka fara fiddo da cocaine d'in suna d'agawa,dukkanin mutane an taru sosai.

Juyowa yayi ya kalli Aliyu yace "muna zarginka da shigowa da hodar iblis"

"Hodar iblis kuma?"

"Eh miyagun k'wayoyi sannan meya kawo bindiga motarka?"

Ganin ana neman zura masa ankwane yasa yace "wallahi ba mota ta bace ta abokina ce,ya ari Babur d'ina Ku jira yanzu zai dawo"

Mari d'an sandan ya sake kifa masa yace "mu zaka rainawa hankali?taya mutumin da yake da mota zai karb'i Babur?meyasa ka karb'i motar baka san meke cikinta ba,shima nemasa muke kuma kaine abokin hark'allarsa"

"Allah ya isa tsakanina da kai da ka saka Hafsa ta aureka har da ciki,ashe mugun haline dakai,'yallab'ai Ku tafi dashi dan tun da ya rik'e bindiga wata rana muzai kashe ai halin uwarsa gareshi bak'ar zuciya ba" Gwaggo Zaliha ta fad'a,Aliyu na kallonta yana kuka yana fad'in "kin san halina gwaggo kinsan bazan aikata haka ba"

"Haba Haidar dama ai son zuciya b'acin ta kana da son zuciya fa"

Ganin za'a tafi dashi ne ya saka Umma da sauran 'yan gidan keta kuka.

Da sauri baba ya ruga ya rik'e su yana fad'in "d'ana kamili ne bazai tab'a aikata haka ba,na san wace irin tarbiyya na masa dan Allah Ku sake shi Ku kama Wanda ya muku laifi" wani hanb'ara da wani d'an sanda yayi masa ne ya sa ya fad'i k'asa abinka da tsohon mutum kuma ga wahalar k'auye jiki ba k'wari, Aliyu yana kallo amma ba damar ya tsaya dan janshi kawai ake yana kuka.

Duka 'yan gidan suka durk'usa aka d'ago baba ana ta kuka,a lokacin numfashinsa ne kad'ai zaka gani ka gane yana da rai.

Hafsa kuwa tashi tayi da sauri ta k'arsa gaban d'an sanda ta d'auki kara ta rad'a masa dan taji zafin yadda taga mijinta da baba basuji ba basu gani ba.

Shi kuwa yana juyowa a kufule ya mareta sannan yasa kulki ya daki cikinta.

Wani wawan k'ara da tayi ne yasa suka juyo kanta.

Jini ne shatata yake bin k'afarta babu abinda kowa ke fad'a sai "inna lillahi wa inna ilaihi raji'un"

Aikuwa Aliyu sai daya fuzgi kansa ya k'arasa gareta kallonshi kawai take bata cewa komai,sai da 'yan sandan suka d'aga shi sannan a hankali ta samu damar cewa "Haidar Allah ya saka mana,Haidar ka yafe min"

Aka tafi dashi aka maka a cell baiji ba bai gani ba.

Washe gari aka fito dashi da safe yaga an sakashi mota an nufi hanyar k'auyen nasu sai yayi tunanin ko Usman ya dawo ya fad'i gaskiya,suna zuwa yaga k'ofar gidan mak'il da mutane aikuwa ya fara hawaye dan ya san idan ba baba ne ya mutu ba to Hafsa ce.

Aikuwa ko gidan ba'a bari ya shiga ba,akan tabarma ya zauna baba Isa yazo yana ta bashi hak'uri ya sanar masa da Hafsa ta rasu.

Sai da yayi k'aramin hauka a gurin dan har gidan da ba'a barshi ba sai da ya shiga,baba ma babu  lafiya bai ma san wake kanshi ba,haka aka d'auki Aliyu aka maida cell tamkar zararre.

A ranar da yamma aka kaishi gurin commissioner Abba kenan shi kuma lokacin suna meeting sai yace a tafi dashi zai nemeshi idan ya gama bincike.

Shekaru takwas ya kwashe a prison sannan wani wanda yayi zaman shekara 10 dan yazo da shekara 2 aka kawo Aliyu to tare suke shi dama hukunci aka yanke mai na shekara goma to ranar da zai fita bayan yaji labarin Aliyu yace masa zai  je har wajen commissioner in Allah yasa ya samu ganinsa zai masa bayani.

Watan mutumin 4 da tafiya aka saki Aliyu,yana zuwa unguwarsu yaga ta zama gari sosai dan kuwa gashi duk a ciki muke kuma bamusan sunyi rayuwa anan ba dan babu alamun an tab'a ginin k'asa a nan,dan nan d'in ma sai da yasha wahala aka gane ta aka kawoshi,kuma yana zuwa ya tarar da gidanku shine gidannan nasu,yace sai da ya shekara biyu yana bara yana kwana a kango yana neman iyayenshi da 'yan uwanshi sannan ya samesu sanadin wata Zuhra.

Lokacin daya tambayi mamanshi ya akai suka dawo nan sai ta bashi labari ai tun bayan rasuwar Hafsa da kwana 5 Baba ma ya rasu,tun daga lokacin 'yan gidan kowa ya fara zamewa yana cewa shi bazai zauna dasu ba.

A haka kowa ya baje,hatta shanuwai da ragunan baba duk an sace babu su,to sai baba halliru yace su dawo kangire su zauna,tace shekarsu uku a kangire shima ya rasu,sai d'ansa habu daya mallaki gidan yace ya bar musu shi kyauta.

Tun daga lokacin yace sai ya d'auki fansa a gurin Abba,Usman da gwaggo Zaliha wadda ita bama asan inda take ba.


Ajiyar zuciya Janan tayi ta kalli Lubna da idanunta da suka gama rinewa tace "Lubna dani dake tare muka taso tare mukayi primary school tare iyayenmu sukayi deciding na dawowa unguwarnan shin kin tab'a jin ance Abba na da wani mummunan hali?meye laifin Abba?laifinsa shine ya barshi yayi shekara takwas a prison amma ai d'an adam ajizine"

"Yace wai Abba ne yasa akayi masa wannan cin mutumcin sannan dukiyarsu tana gidanku"

"Lubna taya Abba zai sa ayi masa wannan cin mutumcin?shi Abba ai baisan komai ba an kawo masa case kawai bama zaice ga Haidar d'in da akama laifi ba in ba yanzu ba"

"Shima haka Abba yace lokacin da mutumin yazo ya bashi labari kasa runtsawa yayi dan ya manta da case d'in,amma a lokacin ya fara bincike sosai ya gani gaskiya sannan yace a saki Aliyu a kuma bashi hak'uri sannan yasa a nemo Usman wanda har yanzu ba'a ganshi ba,kuma yace d'an sandan da aka ce ya daki matarsa ta mutu! Abba ya sallameshi daga aiki dan yazo kotun shima ya amsa laifinsa yace baima san ta mutu ba,Aliyu baiyi bincike ba shiyasa nake jin haushinsa duk da labarinsa abin tausayine"

"Wallahi Abba baya da laifi,bana tausayin Aliyu saboda ya wulak'anta min iyaye,sai yanzu nake dana sanin saninsa a rayuwata"

"Yanzu shine ake ta bincike a gidanku dan ba'asan inda bishiyar take ba an sare ta amma ranar Wednesday za'a cigaba da shari'a".

" to yanzu ya kike ganin shari'ar?wa ake bawa gaskiya?"

"Kowa Aliyu yake tausayi yana masa kuka dan Abba daya fad'i uzurinsa ma cewa sukayi k'aryane kawai inji lawyern Aliyu"

Kuka sosai Janan take tace " kimin Alfarma na zauna a gidanku zuwa ranar laraba dan Allah Lubna"

"Bazai tab'a yuwuwa mu zauna da masu bak'in hali a gidannan ba"

Dukkansu suka juya dan ganin ko waye ke maganar.










*Ku biyo SaNaz dan jin ko waye???📝*











_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:17 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
       *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




23

Daddy suka gani tsaye jikin k'ofa ransa a b'ace tamkar bai tab'ayin fara'a ba.

"Meya kawo ta gidannan?"

"Daddy Janan ce fa"

"Tun kafin kiyi wayo na san Janan dan haka ki tattara ta ta bar min gida yanzun nan sannan na datse alak'arki da ita kamar yadda na datse tawa data mahaifinta dan bazamu zauna da azzalumai ba"

"Daddy kayi hak'uri dan Allah,Abba yace ta bar masa gida kaima in ka koreta ina zataje?"

"Gidan uwaki" ya cilla mata dak'uwa ransa a b'ace ya cigaba da fad'in "ubanta ya koreta sai nine zan rik'e ta?tun kafin raina ya gama b'aci ki nuna mata hanya ta fita ta bar min gida"

Hawaye sharkaf a idon Janan haka ta tashi jikinta sai rawa yake ta rab'a ta jikin k'ofar ta wuce,da sauri Lubna ta saka mayafi zata bita daddy ya tsawatar mata yace ta zauna.

A falo Janan ta tarar da Umman Lubna a tsaye.
Kafad'arta ta dafa tace "Janan kiyi hak'uri kinji ki d'auki k'addara a duk yadda tazo miki Allah ya shige miki gaba"

Da k'yar ta iya cewa "ameen" ta wuce kawai.

Cikin kuka Lubna ke fad'in "Daddy tun tasowa ta nake tare da Janan baka tab'a rabamu ba sai yau rana d'aya zaka rabani da ita,daddy na san dani ce a halin da Janan ke ciki wallahi bazata tab'a min haka ba"

"Ki rufamin baki kafin in miki duka a gidan nan,ni bazaki fi k'arfina ba wallahi ni ba sakaran uba bane sakarai kawai" Jan k'ofar yayi ya fita ita kuma ta cigaba da kuka.

Napep ta tara ta shiga ya kaita har k'ofar gidan Aliyu,bata ga kowa a k'ofar gidan ba hakan ne ya bata damar fad'awa gidan Asabe.

A hankali tayi sallama dan kar su Umma su jita.
"Ah ah Amarya ce a gidan namu shigo bismilla"

Duk da tasha kuka ta k'oshi amma hakan bai hanata b'oye damuwarta ba wajen k'irk'iro murmushi,d'akin suka shiga bayan sun gaisa ta kawo mata ruwa.

Cikin jindad'i tace "nagode" Jakarta ta bud'e ta fiddo dubu biyu ta mik'a mata.

Karb'a tayi tana fad'in "me za'ayi dasu?"

"Kyauta ce na baki"

Baki bud'e Asabe tace "Jaka goma fa?ina zan kaisu? a'a wallahi sunyi yawa Amarya"

"Kin cancanci fiye da haka,wallahi naso ace ma siyayya na miki amma ban samu damar haka ba,kinga tun da aka kawoni nake ajje da dubu hud'u banyi komai dasu ba sai yau ne ma na kashe  500 nayi kud'in mota ki ajje kyayi wani abu dasu karki damu"

"To nagode Allah ya Saka da alkhairi,amma idan babu damuwa zan tambayeki dan Allah"

"Karki damu indai na san amsa zan fad'a miki"

"Kowa ya ganki ya san ke 'Yar manya ce dan Allah shin auren soyayya kukayi da Aliyu?"

"Tabbas auren soyayya mukayi"

Shiru tayi kafin tace "amma idan haka ne meyasa yake dukanki koda yaushe?sannan kowa a k'auyen nan yana son Aliyu tun sanda yazo garin nan saboda kirki,hak'uri da kawaici irin nasa amma akwai wata magana da naji d'azu wadda ta d'aure min kai"

Murmushi Janan tayi tace "karki damu bara na shiga gida dan ina dawowa nan nayo" tayi haka ne dan ta kawar da maganar.

Tashi tayi da sauri ta fito,Asabe ta biyota tana sake mata godiya.
            ***
Kwance ta ganshi kan katifa yana Waya,kallon daya bita dashi ne yasa tasha jinin jikinta.

Cire hijabin tayi tana k'ok'arin ajje jaka taji ya wullo mata wata tambaya "daga ina kike?"
Juyowa tayi ta kalleshi tace "kamarya?amma ai Kasan na tafi makaranta ko?"

"Sai kika biya gidan wa daga nan?"

"Ni babu inda na biya"

Cikin tsawa yace "kada ki yarda kiyi wasa da hankalina Janan"

Shiru tayi ba tare da tace komai ba,ganin yana neman ya rufeta da fad'a ne ta juya zata fita taji ya finciko ta.

Sai daya fara zabzabga mata mari sannan yayi ball da ita ta fad'i k'asa.
"Bance karki je gidanku ba?"

Kukan da ta fara ne yasa Umma da Ummi saurin shigowa kewayen dan bama su san ta dawo ba.

"Iyeee munafukar Ashe kin dawo?"

"Sai yanzu taga damar dawowa ba basarakiya"

"Umma gidansu taje dana ce karta biya ko ina"

"Ai ga irinta nan wayace ka barta taje makarantar ai sai da nace kar tayi tunda kaima bakayi ba"

"Wallahi bazata k'ara fita daga k'auyen nan ba sai ranar dana bata takardar sallama"

Umma tayi dariya tace "ai ranar tazo daga k'arshen satin nan ne in Allah ya kaimu,ai so nake a kasa ganeta amma har yanzu naga da sauranki,dalla tashi ki samo mana ruwa  kuma minti biyar na baki ki dawo"

Kuka kawai take zuciyarta cike da fargaba.

"Bazaki tashi ba sai na sake miki sabon duka?" Aliyu ya fad'a.

Da sauri ta tashi jikinta na b'ari ta d'auki gyalenta dake kan tabarmar ta yafa ta fita tsakar gidan.

Fanteka ta d'auka ta fita tana goge hawaye.

Zuciyarta kawai ta raya mata ta tafi rafi ta fad'a ta mutu kowa ma ya huta da takaicinta dan gani take ita ta jefa iyayenta da kanta a wannan ibtila'in.

Tafiya kawai take zuciyarta a cunkushe da damuwa.

Tsaye take bakin rafin babu kowa kasancewar rana tayi yawa,zama tayi a gefen rafin ta zuba k'afafun a cikin ruwan tana ta addu'o'in neman gafarar Allah kafin ta fad'a kawai taji an dafa kafad'arta.

A tsorace ta juyo ta kalleshi.

"Hey" ya fad'a lokacin da yake zare bak'in glass d'in dake fuskarsa.

"Sannu" ta fad'a a tsorace.

"Nazo wuce wa na hangoki a nan,pls ko zaki iya min wani taimako?"

"Na me?"

"Calm down ba cutar ki zanyi ba naga duk kin tsorata"

Bata ce komai ba illa tsoron kawai da yake bata.

"Mom d'ina ce babu lafiya so tana son fitowa tayi amai kafin ta fito har tayi a mota so shine nake so in babu damuwa kid'an taimaka min tun da naga ke macece"

"Babu damuwa" ta fad'a a sanyaye shi kuma ya bita da kallo yana mamakin yadda 'yan k'auye ke irin wannan wahalalliyar rayuwar dan ko dressing basu iya ba.
a zuciyarsa yake fad'a yayinda ya kafa mata ido tana d'ebo ruwa a fantekar.

"Muje ko" ta masa magana bayan ta d'ebo ruwan,gaba yayi tana binsa a baya a zuciyarta tace.

_abinda zan aikata haramun ne Allah yana sona da rahama shiyasa ya turo bawanshi ya hanani fad'awa ga halaka._

Yadda taga Maman nashi a galabaice ta tausaya mata dan haka bayan ta wanke mata jiki da inda ta b'ata da amai kawai ta d'auki gorar ruwan da ta gani a gefe ta kunce zaninta,guntun maganin da Asabe ta bata ne ta zuba a ciki ta jijjiga sannan tace "Idan kika sha wannan da yardar Allah zaki samu sauk'i"

Ta kafa mata gorar tana sha kawai taji anyi baya da ita.

Da sauri ya karb'i gorar ya d'aga hannu ya kifa mata mari.

"Daga cewa ki taimaka mana sai ki bata wannan k'azantar taku,Ku matsalarku 'yan k'auye Jahilci ya muku yawa babu wayewa ko kad'an a tare daku"

Kallonshi kawai take lokacin da wani hawayen ke k'ara tsiyaya a idanunta.

"Sai an zageku ku hau kuka sai kace Ku kukafi kowa hawaye,dalla matsa"
Ya fad'a yana kwantar da mamanshi sannan ya shiga motar ya jata da k'arfi.

Motar ta bi da ido wani sabbin hawayen na zuba a idonta.

Tafi taji daga bayanta a hankali ta juya hannunta rik'e da kuncinta.

"Shiyasa na biyoki dan inga me kike aikatawa nan ne gurin d'ibar ruwan ko?"

Girgiza kai tayi tana kuka tace "Aliyu wallahi taimakonsa yace nayi ma........" A d'ayan kuncin ya sake marinta sannan yasa k'afa ya tad'iyeta yana fad'in "ni zaki ha'inta?k'arya kike wallahi kuma ki dawo gidan zaki sameni"

Bai kula ba da halin da take ciki ya barta anan kwance gefen titi cikin jini.

          **********

A b'angaren wannan matar kuwa sai yamma lik'is ta bud'e idonta daga baccin data samu.

Kasala kawai taji amma ciwon k'irjin da bugun zuciyar da yake damunta babu ko kad'an.

Babban abinda yafi bata mamaki shine yadda suke ta kashe kud'i daga wannan asibitin zuwa wancan amma tamkar ana k'ara mata azabar ciwo ne,sai gashi lokaci guda duk wani ciwo da take ji babu shi.

Kallon d'an nata take da yake driving tace "Muhasin mu koma wannan k'auyen"

Sai da ya juyo ya kalleta sannan ya cigaba da driving yana fad'in "momma kece kike magana haka?"

"K'warai kuwa kuma yarinyar daka mara maganin data bani shine silar warkewa ta, dan haka mu koma ka nemi yafiyarta sannan mu mata godiya"

"Momma mun kusa katsina fa,taya zamu koma wannan k'auyen sannan mu dawo mu sake d'aukar hanyar yola bayan tafiyar da mukasha tun daga Abuja pls momma kiyi hak'uri" ya fad'a,dan shi a tunaninsa maganin da tasha a Abuja ne yayi tasiri dan sam bai yarda da maganin hausa ba.

"Muhasin ina magana kana musawa?kada kaima kace kabi hanyar da 'yan uwanka suka bi karkace kaima ka fara gajiya dani"

Parking yayi sannan ya juyo ya kalleta a tsanake yace "momma taya zan gaji dake bayan ke kika kawoni duniya,bana fatan kome na zama a rayuwa ace waini na gaji dake Allah kiyaye"

"To indai ba haka bane ina son mu koma ka bata hak'uri"

"Wallahi ko mun koma ba lallai mu ganta ba,a bakin ruwa na ganta fa taje d'iba kuma ban san ko sunanta ba ta ina zan ganta tunda babu gida a wajen?"

"Amma ai a k'auyen kusa da nan take ko?"

"Momma babu tabbas amma na san ko mun koma bazamu ganta ba"

"Indai kana bin umarni na to mu koma"

_wama ya sani ko maganin asiri ne ta bata,aini ko yanzu muka had'u da yarinyarnan in dai ba a gaban momma bane saina sake mata warning kawai zata halaka uwata da maganin k'auye yadda nake tsantsaninsu amma harta d'auki abu ta bawa uwata tasha._

"Magana nake maka Muhasin" ta katse masa tunanin.










_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:17 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
          🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


24

"Momma ina jinki"
"Oh shine kayi shiru?"
"A'a k'ok'arin juyawa nake"
"Cewa nayi mu tafi yolan amma fa zamu dawo neman yarinyar ka yarda?"
"Eh na yarda" ya fad'a cike da jindad'in bazasu koma ba.

          ********

A hankali ta bud'e idonta ta fara kallon d'akin,ta fara ware idonta tana k'arewa d'akin kallo.

Wani irin nauyi da ciwo taji kanta nayi,ta saka hannu ta dafe kan kawai taji bandage sai a lokacin ne hankalinta ya gama dawowa jikinta ta kuma tuna duk abinda ya faru.

Da sauri ta tashi zaune ta kalli drip d'in da bai gama zuba ba,yana d'isa a hankali.

_ina ne nan waye ya taimaki rayuwata?_ tayi tambayar a zuciyarta.

Shiru tana zaune a d'akin ita kad'ai ta jingina da fuskar gadon dan bama ta san wane yanayi bane safiya,rana ko dare,d'akin labuye sun rufe ko ina sai hasken fararen lights da suka haske d'akin.

Ta shafe kusan awa guda tana tunani kala-kala akan irin halin da ta tsinci kanta a yanzu.

Jin ana bud'e k'ofa ne ya saka ta k'urawa k'ofar ido,ana turo k'ofar ta kalli wanda ya shigo sai da tayi mugun zabura har ta kusa b'alle drip d'in da aka jona mata.

Murmushi kawai yayi sannan ya k'araso jikin gadon ya tsaya.

"Meya kawo ni nan?" Ta fad'a bakinta na rawa.

"Oh baki ma sani ba?" Ya bata amsa ba tare daya damu da irin tsoratar da tayi ba.

"Na shiga uku"

"Bazaki tab'a shiga uku ba indai ina raye Janan"

"Jalal ina Aliyu wallahi na san dukana zaiyi in har na koma yanzu"

"Duka kuma?" Yayi tambayar cike da mamaki.

Sai a lokacin ta san tayi katob'ara sai kuma tayi saurin cewa "zai min fad'a ne"

Murmushi ya sake yi tare da zama gefen gadon  "meyasa zaki b'oye min matsalarki?ko kina gani kamar bazan iya taimakarki ba?"

"Idan kika saka wannan a ranki baki min adalci ba"

Wani gumi daya tsatssafo mata a fuska tasa hannu ta goge,hakan ne yasa ya gane cewa lallai akwai abinda ke damunta take b'oyewa.

"Meke damunki Janan?"

Idanunta tuni ya fara fitar da hawaye "dan Allah ka mayar dani gidan miji na kar in samu matsala"

Ajiyar zuciya yayi ya  dafe kan shi da hannunsa yana kallon yadda take kuka tamkar yace zai yanka ta.

A sanyaye ya fara fad'in "ban tab'a tunanin cutar da wani a rayuwata ba bare ke Janan,amma yau ni ne kike buyewa damuwarki ni dama tun da naga yanayinki a skul na san akwai abinda ke damunki amma duk kanku kun b'oye min"

Hannu tasa tana goge hawaye tace "kar ka damu idan kayi addu'a ma ya wadatar amma kayi hak'uri damuwa ta tana da tarin yawa bazan iya fad'a maka ba"

"Shike nan Allah ya shige miki gaba a duk al'amuranki"

"Ameen" ta fad'a lokacin da wasu sabbin hawayen suke fita daga idonta.

Tashi yayi ya fita ya bar ta dan a tunanin sa ganinshi ne yake saka ta kuka.

Ya kwashi kusan awa d'aya yana tunanin wane irin miji Janan ta aura?wace irin wahalace ta mayar da ita haka duk sirantarta amma ta sake raguwa gashi duk ta canza kamar ba ita ba,ya rasa ta ina zai fara taimaka mata tunda bai san meke damunta ba.

Tashi yayi ya d'auki ledar da yayi mata takeaway ya kai mata,tana zauna tana kuka ko gajiya batayi a haka ya tarar da ita.

Ajjewa yayi a gabanta yace "ga abinci nan na san kina jin yunwa" da ido kawai ta bishi lokacin yana k'ok'arin fita.
"Nagode" yaji ta fad'a.
Ya d'an juyo yana murmushi yace "karki damu"

Sai da taci abinci sosai tasha yoghurt da ruwa sauran kayan kuwa bata tab'a ba.

Tayi lamo a kwance tana ta tunanin irin azabar da zata sha idan ta koma gidan Aliyu amma ta san dole ne ta koma saboda in ta zauna anan zata jawa Jalal matsala da zargi.

Jin an turo k'ofar ne yasa tayi saurin tashi zaune.

Shi da likita suka shigo ya kalli drip d'in yace "ai ya k'are har ya fara jan jininta.

Ita ma da sauri ta kalli gurin,likitan ya cire sannan ya duba ta.

Kallon Jalal yayi yace " jinin ya sauka"
"To Alhamdulillah"
"Yanzu sai dai a kula da ita tana shan magungunan akan lokacin"
"Insha Allah"

Sallama suka yi ya rakashi har mota ya tafi sannan ya dawo.

A tsaye ya ganta jikin k'ofar "lafiya?" ya tambayeta.

"Zan tafi gida"
"Gida?"
"Eh"
"A wannan daren gaskiya ki hak'ura da safe na maidaki,yanzu dare yayi sosai fa"
"A'a ni dai tafiya zanyi kawai ka barshi nagode"
"Okay Allah ya bamu alkhairi"
Jin haka ne ya saka ta saurin kallonshi tace "ka bud'e min k'ofa dan Allah"
"K'ofa a bud'e take sai dai masu gadi zance su bud'e miki daga waje"
Jikinta a sanyaye ta fita shi kuma ya bita da fad'in "ki gaida Aliyu"

Tun da ta fita a gate taji garin shiru babu kowa sai street light sai kukan karnuka da take jiyowa daga neighbors d'insa.

_a ina zan samu napep?ina da kud'i a gida idan ya kaini sai in bashi_. Ta fad'a a zuciyarta tana ta fargaba.

A haka har ta fita daga layin ta shiga wani.
A lokacin ta fara tunanin ko dai dare yayi sosai kamar yadda Jalal ya fad'a gashi babu agogonta a hannunta bata san ya akayi yayi missing ba,bare taga time.

A tunanin nan har ta isa babban titi,ta tsaya cak tana tunanin Allah yasa ta samu abin hawa.

Motocin dake wucewa akan titin jefi-jefi babu wanda ya kula da itama.

Ta d'ebi kusan minti talatin sannan wata mota tazo,har ta wuce sai kuma tayo baya,a hankali aka fara zuge glass d'in baya sannan aka kunna wutar motar.

Samari ne har su uku a bayan motar sai d'aya a gaba da kuma wanda ke driving d'in.

" 'yan mata ina zuwa?" Wani mugun fad'uwar gaba ta cigaba dayi jikinta na tsuma tace
"C....ci....cikin....gari"

'Daya ya kalli d'ayan sukayi murmushi "ki shigo sai mu rage miki hanya"

Girgiza kai tayi alamar a'a.

Bud'e k'ofar suka yi ita kuma ganin hakane yasa ta yanki layi ta shiga da gudu suka bita, ta bar layin har ta shiga wani suka rutsata.
Ganin sun finciko ta ne yasa ta k'walla k'ara,suka toshe bakinta suna janta taji an funciketa ta baya.

Suma da sauri suka saketa tare da rufe fuskarsu yanda baza'a gane su wane ba,hijabin jikinta kuwa sun yaga mata shi.

Ganin Jalal ne yasa tayi saurin rungumeshi tana kuka tace "ka taimakeni karsu lalata min mutuncina"

Shima rik'eta yayi sosai a jikinsa ganin sunyo kansa gadan-gadan suna fad'in "ka bamu ita ko mu fasa maka kai da bindiga"

Jin haka ne yasa Janan tayi saurin runtse idonta jikinta sai karkarwa yake.

Murmushi Jalal yayi ganin bindigar dake hannunsu ta wasa ce suke amfani da ita wajen tsorata mutane.

Hannu yasa ya zaro bindigarsa ya nuna musu yace "duk wadda ya cika d'an iska ya k'araso nan"

'Daya daga cikin su yayi dariya mai k'arfi  yace "mu zaka yiwa barazana da bindigar wasa?lallai yau sunanka matacce"

"Wayyo Allah Mameey ki taimakeni zan mutu"ta fad'a tana kuka tare da k'ara k'ank'ame Jalal tamkar zata shiga jikinsa.

 Jalal ya d'aga bindigar ya harbi sama dan su tabbatar ba bindigar wasa bace.

Wani k'ara da Janan ta saki bata sake motsawa ba.

Su kuwa tuni sun tsorata sun d'aga hannu suna fad'in "kayi mana rai yallab'ai"
"Oh ku 'yan iskan k'arya ne ashe,ku b'ace min da gani anan kafin in fasa kan naku kafin ku fasa nawa"

Da gudu suka bar gurin,ya kalleta yace "Janan tashi mu tafi sun tafi"
Jin tayi shiru ne yasa ya d'agota yaga tana neman fad'uwa.

Sai a lokacin ne taji wani abu ya tsarga jikinsa,da sauri ya karanto addu'ar neman tsari daga shad'an.

"Janan" ya kira sunanta yana sa hannunsa a hancinta dan ya tabbatar tana numfashi.

Ganin ta suma ne yasa ya d'ago ta a kafad'a ya nufi gida.

A kan gado ya direta har lokacin a sume take.

Da sauri ya nufi fridge ya d'ebo ruwa ya shafa mata a fuska.

Zubur ta mik'e tana neman gudu yayi saurin rik'e ta "Janan nine fa"

Kallonshi tayi jikinta na rawa tace "na shiga uku Jalal meke faruwa dani ne?ko dai nayiwa Allah laifi ban sani ba?"

"Ki nutsu Janan babu abinda kika ma Allah,kiyi ta istigfari kinji"

'Daga kai tayi alamar to ,ta cigaba da kuka.

"Shiyasa na hanaki tafiya kika k'i dama fa babu wanda zaki samu k'arfe 1 na dare"

Ita dai bata ce komai ba har ya gama surutansa ya tashi ya ja mata k'ofa.

Ranar bai runtsa ba dan tunanin abinda ya faru tsakaninsu kawai yake,wani sonta ne ya fara ratsa jikinsa tun da yake bai tab'a jin son wata 'ya mace ba sai a kanta.

Da sauri ya tashi yayi alwallah yana jero nafilfili tare da addu'oin kub'uta daga halaka.


_*Washe gari*_

Sai k'arfe goma yayi mata knocking sannan ya shiga,zaune ya ganta kan sallaya ta zuba uban tagumi idanunta sun kunbura sosai kana kallonta kasan bata runtsa ba.

"Kar dai ace bakiyi barci ba?"

"Ina kwana" ta fad'a a sanyaye dan ita kunyar abinda ya faru jiya take.

"Lafiya lau ya k'arfin jikin?"
"Alhamdulillah"

Ajje ledar hannunsa yayi akan gado yace "ga kaya nan ki shiga bathroom kiyi wanka sai ki saka in kin gama ina falo ki fito kiyi break na maidake gida"

"Nagode" ta sake fad'a sannan ya fita.

Bayan ta fito daga wanka ta bud'e ledar,mayuka ne masu tsada da turare a ciki sai doguwar riga blue black had'e da mayafi babba shima blue black ne.

 _Allah sarki Jalal,kamar ba kaine wanda na tsana ba amma yanzu babu mai kyautata min kamarka Allah ya saka maka da alkhairi._

Bayan ta gama shiryawa ta fita falon,a zaune ta ganshi yana waya yana dariya,yana ganinta yace "bara anjima zan kiraka" ya katse wayar yana kallonta.

"Ga abinci kan dinning table"
Jikinta a sanyaye taje ta zauna,ta fara ci kawai taji ya fita a ranta tunanin yadda shari'ar Abba da Aliyu zata kaya take.

"Na gama?" ta fad'a tana mik'ewa
"Kina nufin har kin k'oshi?"
"Eh bani jin yunwa"

Bai matsa mata ba key kawai ya d'auka ya fita ta bishi.

Ita ta rik'a nuna masa hanya har suka kai k'ofar gidan.
"Anan kike rayuwa Janan?" Ya fad'a cike da mamaki.

"Eh" ta bashi amsa a tak'aice,kallonta kawai yake cike da tausayinta.

Yara duk sun rufe motar suna kallo,tana shirin fita kawai ta hangi Aliyu da Nura a can bakin wani icce suma idonsu akan motar.

Gabanta yayi mummunan fad'uwa ta kalli Yarima Jalal tace "na shiga uku kaga Aliyu can, dan Allah ka taimaka muje kayi masa bayani"

Mamakinta kawai yake yanda yaga duk tabi ta rud'e "zamuje amma fa ki sani dole ki rage damuwa da tsoro saboda lafiyarki" kai kawai ta gyad'a suka fita tare.

Kafin ma su k'arasa inda Aliyu yake tuni su sun taho.

"Daga gidan ubanwa kike?" Yayi tambayar ransa a had'e,sai a lokacin Jalal ya k'ara tsinkewa da lamarin amma da yake miskiline sai yak'i cewa komai.

"Gidan ubanwa kika kwana" ya fad'a tare da tsinka mata mari.

Da sauri Jalal ya kallesa "akan me zaka daketa ko dan kana tak'ama kana aurenta kai baka da imani ne ko bakaga ciwo ne a goshinta ba"

"Dalla Malam dakata da matata nake ba da kai ba"

"Oh mata! dan kana tak'amar matanka ne shine zaka nemi ka zubda mata mutumci,Ku dama 'yan k'auye baku iya cin arzik'i ba"

Kallonshi Aliyu yayi yace "mutuncinta wanne ne bai zube ba tunda har zata iya zuwa ta kwana a gidanka,sannan cin arzik'i kuwa ita ce tayi dan ita tace tana sona bani ba"

Ya juya ya kalleta cikin tsawa yace "har ta kai ki kwana a gidan maza sannan k'ato ya kawoki"

Girgiza kai take tana kuka,ya matso daf da ita kamar zai mata magana ya k'ara wanka mata mari a karo na biyu.

Cikin zafin nama Jalal ya d'aga hannu ya mareshi.

Aikuwa yara sai ihu suke mutane duk an firfito waje.

Ya d'aga hannu zai rama Janan tayi saurin rik'ewa,ya fuzge har sai da ta kusa fad'uwa.

Ta kalli Jalal dake tsaye cak yak'i matsawa tace "kayi hak'uri Jalal na san ni na jawo maka dan Allah ka tafi ka tafi ka bar nan p.........."

Da k'arfi taji an fuzgeta ta juya taga Umma ce.

Bata saketa ba sai a tsakar gidan.

Juyowa tayi ta kalli Ummi tace d'akko min Razer.

"Dan Allah kiyi hak'uri Umma Ku barni haka dan girman Allah" Janan ta fad'a tana kuka.

"Yau saina yanka k'afar naga da wacce zaki sake fita yawon karuwanci"

A daidai lokacin Ummi ta mik'owa Umma Razer.

"Yanka min k'afarta sosai"

Kallonta tayi kawai taji bazata iya ba. "Umma ki mata hak'uri"

"Me?"
"Umma da tausayi fa gaskiya bazan iya ba"
"Wannan yarinya baki da hali,mik'o min Razer ki kuma kawo min gishiri"

Zare ido Ummi tayi tana mamakin yadda Umma ke shirya mugunta.

"Ba magana nake miki ba"

A firgice ta ruga ta d'akko gishirin ta kawo mata.

Idon Janan a rufe tana ta kicin kicin na k'wace kanta amma yadda Umma ta matseta yasa ta kasa.

Yadda taji an yanki k'afarta tun daga babban yatsa har zuwa gwiwarta,wani azababben zafi daya tsarga mata daga babban yatsan har zuwa k'wak'walwarta ne yasa ta zunduma uban ihu,cikin zafin nama Umma ta watsa mata gishirin wanda ya saka Janan k'ara runtuma ihu tamkar zautacciya.

Ummi tayi saurin runtse ido ganin yadda jini ke zuba a k'afar.

Nura da wasu mata guda biyu tare da Asabe har rege-regen shigowa gidan su ke dan ganin abinda ke faruwa.















_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:17 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
        🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


*_Wagga shafi naki ne kyauta Mom Haidar😍,ki daure ki karanta banso ki tafi strike shiyasa nasa dole Aliyu ya rangad'awa Janan saki uku🤪_*


25

*inna lillahi wa inna ilaihi raji'un* shine abinda ko wannensu ke fad'a.

Wata harara Umma ta zabga musu tare da fad'in "munafukan banza kawai salatin me kuke?"

Nura ne ya kalleta yace "meya faru da ita haka Umma?"

"Kai baka ga abinda tayi ba,da namiji ta dawo gidan nan fa"

Sum-Sum ya fice ya bar gidan dan yaga ran Umma ya b'aci sosai.

Asabe da Yabi suka durk'usa gabanta har lokacin kuka take a fili yanda take jin azabar ciwon na sake shigarta.

Ummi ba shiri ta shiga d'aki, tunda take bata tab'a tausayin Janan kamar yau ba.

" 'Dagata mu tafi da ita gidanmu sai dai kome Haidar zaiyi yayi"

"A'a mu kaita chemist" Asabe tayi maganar.

"Ina mukaga wani chemist a k'auyen nan muje kawai gidan Malam Ayuba ya bata magani"

Haka kuwa sukayi suka d'agata tana kuka ta kasa ajje ko k'afar,har a lokacin jini zuba yake a k'afarta haka suka isa har gidan malamin.

Sai daya shafa mata man alayyadi a k'afar sannan yayi mata addu'oi kuma ya bata maganin da zata rik'a shafawa a gurin.

Suna fitowa daga gidan malamin cikin kuka tace "dan Allah ku kaini gidanmu"

"Ai bamu san gidanku ba Janan" Asabe tayi maganar.

Cikin kuka tace "zan nuna muku dan Allah ku muje bakin titi mu samu abin hawa"
*
Tun a k'ofar gate d'in su Yabi suka rik'a mamakin yadda Janan ta auri Aliyu bayan ta fito daga wannan tafkeken gida.

A babban falo babu kowa dan haka tace suje k'aramin falon.

Suna shiga suka tarar da Mameey da Fauziyya ne kad'ai a zaune a falon.

Da gudu fauziyya ta k'araso ta rungumeta suka fara sabon kuka.

Mameey tashi tayi ta k'araso gabanta ta rik'eta tana kallon k'afarta da har ta kumbura tayi jajir.

Gaisawa sukayi da su Asabe sannan tace su zauna.

Janan na zaune kusa da Mameey tana kuka tana fad'a mata irin azabar da ake gana mata a gidan Aliyu.

Duk kansu kuka suke hatta Asabe sai da ta koka,'yan aiki suka kawo masu ruwa da lemo.

A lokacin Fauziyya take kuka tana fad'a mata irin shari'ar da ake gudanarwa sannan Abba yace kar a fad'awa kowa har ita.

Kuka sosai Janan take gani take k'ila laifi tayiwa Allah yake jarabtarta da hakan amma wannan tsanar da Abba yayi mata tayi yawa.

Kallon Mameey tayi taga itama hawaye take,da sauri ta saka hannu tana goge mata "Mameey kiyi hak'uri karki k'ara tsinka min zuciya dan Allah" ta fad'a tana hawaye.

"Meya kawo Janan gidana?" Suka ji muryar Abba.

Da sauri Janan ta mik'e tsaye sai kuma ta zauna saboda zafin k'afarta tama manta da ciwon.

"Bance bana son ganinki tare damu ba,na yanke alak'armu dake na sallamaki a matsayin 'yata dan haka ki bar gidan nan yanzu-yanzu"

"Yallab'ai baka da lafiya fa amma har ka jiyo muryar Janan ka fito"

"Saboda tayi min mummunan tabo shiyasa ko guri tazo sai naji jikina ba dad'i"

"Abba kayi hak'uri dan Allah, wallahi idan kana fad'in haka ji nake kamar ana sokamin wuk'a,Abba ka duba halin da nake ciki ka tausaya min"

Tari-tari yake yana fad'in "kina son kashe ni ko Janan?bana son ganinki ki daina zuwa wallahi idan na sake ganin k'afarki a gidan nan ban yafe miki ba,na haramta miki zuwa gidana"

Sunkuyawa yayi k'asa yana tari yana nunata da yatsa yana fad'in ta fita.

Kuka take tamkar zuciyarta zata tsinke haka ta bar gidan ita dasu Asabe da suka mata jagora.

         ***********

Yana zaune akan lafiyayyar kujerar ya zuba duka hannayensa ya rik'e hab'arsa.

Mommy sai fad'a take ta inda take shiga bata nan take fita ba,ya zuba ido kawai yana kallonta,ga tarin damuwa na damunsa ga fad'an Mommy ya rasa da wanne zaiji.

Maganar da tayi ne ya sashi saurin cire hannayen ya kalleta a d'an tsorace.

"Ko me zakayi saika kiramin Janan a Waya yau sai na k'ure k'aryarka,ka samu wata ka bata waya dan a tsarani ko?"

"Mommy wallahi ba k'arya nake miki ba?"

"Shiyasa nace ka kiramin ita a waya naji dalilin dayasa tace zata zo bata zo ba"

"Mommy bata k'asar an fita da ita waje bata da lafiya"

Hmmm "Jalal kenan ni zaka maida yarinya?to shima d'an uwan naka na bashi nan da wata d'aya ya dawo gida kuma ya samo mata acan inda yake karb'ar magani na gaji da ganinku a haka,ko so kuke sai na mutu banga jikokina ba"

Ajiyar zuciya yayi sannan yace "Mommy please kiyi hak'uri zaki ga jikokin ki harda 'ya'yansu insha Allah"

Hmmm "kamar da gaske"

"Dagaske nake Mommy ki kwantar da hankalinki"

"Okay ina dai jira ka kawo min Janan"

"Amma Mommy ya kamata a samo wata 'Yar aikin dan gani nake kamar aiki yayiwa inna Abu yawa" ya kawar da maganar

"Ai ina tayata da wasu abubuwa,to me za'a kawo bayan duk kun gujeni kai ka tafi Kaduna shi ya tafi waje,Asaben ce abokiyar hira kawai"

"Mun kusa dawowa fa"

"Allah yasa".

Ranar Mommy ta tsokano masa inda yake masa ciwo dan wuni yayi yana rik'e da agogon Janan yana tunanin ko yanzu a wane hali take?oho!.

         *********
A k'ofar gidan ta sake goge hawayen fuskarta ta kalli Asabe " bazan shiga ba kasheni zasuyi"

"Babu abinda zasu yi miki mu shiga in kaiki"

Girgiza kai tayi tana fad'in "wlh kashe ni suke son yi"

"To ko gidanmu zata?" Yabi tayi maganar.
"Haba Yabi taya zataje gidanki bayan da mijinta,haba kinsan k'auyennan yanzu sai abin ya zama surutu"

Da k'yar suka lallab'ata ta shiga gidan.

Gidan shiru kamar babu kowa haka d'akin ma da sukaje ba kowa.

Akan katifar suka kwantar da ita sannan suka zauna suna hira saboda su mantar da ita damuwarta.

Sai la'asar lik'is suka bar gidan dan abinci ma Fura Asabe ta siyo suka dama kuma har a lokacin Aliyu bai shigo gidan ba.

Haka in zatayi alwalla kamar zatayi kuka saboda zafin ciwon in ta saka masa ruwa.

Ranar haka ta sake kwana ba tare da ta runtsa ba,ga k'afar sam ta hanata bacci Aliyu kuwa bai kwana a gidan ba dan bata ganshi ba.

Da Asuba a daddafe tayi sallah sai a lokacin bacci mai nauyi ya d'auketa.

Maganganun da taji ne ya saka ta bud'e idonta.

Ganin Aliyu tayi tare da wasu maza guda uku wanda tayi imani cewa ma'aikata ne.

Da sauri ta tashi taja mayafinta ta rufe jikinta.
Abin har ya kai Aliyu ya shigo mata d'aki da maza saboda baya kishinta.

"Yawwa ta tashi ma" Aliyu ya fad'a yana kallonta.

Kanta na k'asa dan bata san dalilin zuwan nasu ba,ji tayi ance mik'a mata takardu tare da fad'in "gashi kiyi signing"

"Signing akan me?" Tayi maganar cikin sanyin murya tana kallon Aliyun.

"A'a naga kina kallona ko baza kiyi bane?"

"Ai ban san ko na mene ba"

"Daga kotu muke,zakiyi signing sannan ki rubata Account number da Account name d'inki"

Kallon mamaki kawai ta bisu dashi,hannunta na shaking ta karb'i takardar ta rubuta tayi signing.

"Dukiyata ta dawo hannu na"
Ya fad'a yana dariya yana kallon ta.

_kenan kud'in account d'inmu za'a bashi?,Dana san haka ne wallahi na wancan account d'in zan rubuta shine mai dubu 70 kacal a ciki._ tayi maganar a zuciyarta

Fita sukayi ta zauna kawai tana zulumi tana tunanin ko meya faru a kotu yau?,ita dai gabanta fad'uwa yake.

           ********

Suna fitowa daga kotu Abba ya zube.

Da sauri suka rufar masa duka suna kuka,da k'yar suka sakashi a mota zuwa asibiti.

Kai tsaye emergency aka nufa dashi dan ya fita hayyacinsa tamkar ya mutu.

Cikin ikon Allah likitoci suka samo kanshi.

*_6 hours later_*

Yana kwance akan gadon idonsa na kallon silin,Mameey na zaune gefen gadon yayinda Fahad da Fauziyya ke tsaye a jikin gadon.

Har lokacin suna cikin damuwa Fauziyya kuwa kuka kawai take.

Kallonsu yayi cikin k'arfin hali yace "karku damu akwai Allah kuma yana kallon duk abinda ke faruwa kuma ya sani ban zalunci kowa ba amma an zalunceni,duka gidana da nashi an had'a an bashi saboda kawai ba'a ga inda aka binne dukiyarsu ba sai ace komai bamu an basu, sannan an dakatar dani daga aiki ba tare da hak'k'ina ba duk irin ruk'on aikina amma ace wai ban san aikina ba"

Tari ne ya sark'e masa,Fahad ya rik'oshi yana fad'in "Abba dan Allah ka cire komai a ranka"

Ya kalleshi lokacin tarin ya lafa yace "Fahad bazan iya cirewa ba,kaima na ja maka matsala a gurin aikinka sun k'wace mana komai hatta kud'in dake account d'in mu sun karb'a duk wani kadararmu sun karb'e wannan wace irin shari'a ce?wane irin bahagon hukuncine,da kayan sawa kad'ai aka barmu Fahad" kuka sosai Abba yake suma suna kuka.

Turo k'ofar da aka yi ne yasa duka suka kalli wajen.

A fusace Fahad ya taso yana fad'in "me kazo kayi mana anan?"

Murmushi yayi yana fad'in "kwantar da hankalinka ba zama ya kawo ni ba"

Zai k'ara magana Abba yayi saurin d'aga masa hannu alamar yayi shiru.

Taku biyu Aliyu yayi ya k'arasa jikin gadon "sannu ko" yayi dariya 'yar kad'an sannan ya juya ya kalli Mameey.

"Kin gani ko haka Allah yake ikonsa,yau gani nine mai arzik'in,duk wani abinda kuke tak'ama dashi babu,kin san me?zuwa nayi na baku sadaka dan a samu a sayi magani kuma 'yarki zan mayar da ita k'ask'antacciyar baiwa a gidana"

" 'karya kake matsiyaci wallahi har yanzu bakayi arzik'in da zaka wulak'antamu ba" Fauziyya ta fad'a a fusace.

"Hahahahh keee! Har kin samu kanki kenan? 'Yar iska mai bin maza"

Hannu ta d'aga zata wankeshi da mari yayi saurin rik'ewa "kul! Karki kuskura ki fara" ya wurgar da hannunta gefe sannan ya juya ya sake kallon Mameey ya fiddo bandir na dubu ya wurga mata yace "ayi kud'in magani"

Wani damk'a da Fahad ya kai masa ne yaja kaurewar fad'a tsakaninsu,da sauri Mameey ta fara k'ok'arin rabasu  Aliyu ya kai mata duka a fuska ta dad'i,da gudu Fauziyya ta fita neman taimako,Abba ya tashi shima jiri ya d'ebeshi ya fad'i.

Da k'yar wasu likitoci suka shigo suka raba fad'an,Aka kama Mameey aka bata gado itama.

Abba kuwa aka Saka mashi oxygen saboda numfashinsa baya fita da kyau.

Aliyu na shigowa gida ya rufe Janan da duka,ta fito k'ofar gida da gudu ya biyota yana duka,mutane na rik'eshi yana fad'in a sakeshi ya illatata.

Mutanen gurin kuwa sukace a k'yaleshi ai matarsa ce,ita kuwa da gudu ta fad'a gidan Asabe,yana neman shigowa tayi saurin maida k'ofar ta rufe tare da zubewa k'asa.
Sai a lokacin taji zugi a k'afarta dan har ta manta da ciwon saboda wawan dukan da yayi mata,gannin jini a k'afarta ne yasa ta k'walla ihu a take ta sume a gurin,a haka Asabe tazo ta ganta.

        ******
Tana farfad'owa ta ganta a kwance kan gadon Asabe.

Asabe na mata fifita Zuhra na gefenta tayi tagumi.

"Inna Asabe kinga ta bud'e idanunta"

Kallon ta tayi tana hamdala,da sauri ta tashi ta kawo mata ruwa.

Bata ma karb'a ba illa kuka da take tayi dan ta gama tsinkewa da lamarin.

Ganin kukan yayi yawa ne yasa Zuhra ta fara magana rai a b'ace.
"Wai ke Janan hawayenki baya k'arewa ne?akan me zaki zauna Haidar yana neman kashe ki?"

Bata iya cewa komai ba sai kukanta daya k'aru.

Asabe tayi Ajiyar zuciya tace "ni wallahi na rasa rashin tausayi irin na mahaifiyarsa ita take zugashi"

"Wallahi na auri Aliyu ita bata isa ta saka ya dokeni na kasa ramawa a kanta ba,duk uwar mijin data kasa rik'e mutumci ta sai ka hau ka taka,ke Janan wallahi dole ki dokasu a kotu a raba aurenku ki huta"

Sai a lokacin ta fara magana tana fad'in "idan na kai Aliyu kotu ya sakeni ina zan koma?babana ya koreni in aka raba mana aure da Aliyu bani da inda zani"

"Baki da dangi ne?"

"Muna dasu amma kinsan dangi na yanzu ba wani zumunci ake ba babu wanda zai saurareni bamu had'uwa sai in har wata sabga ta had'a da kamar wuya yanzu in tunkaresu da matsala ta su karb'a"

"To gaskiya kije ayi miki tsakani dasu a kotu ina dalili,dubi yadda kika koma fa,wanda ya dad'e bai ganki ba bazai shaidaki ba".

         **********

Ganin yadda yake neman sark'ewa yasa Mameey ta tashi da sauri zata fita kiran likita.

Hijabinta ya rik'e yace " karki kira kowa"

"Meyasa?" Ta tambaya tana kuka.

"Saboda mutuwa zanyi" ya fad'a yana murmushi sannan ya saka hannu a aljihun wondonsa ya d'akko takarda ya mik'a mata.

"Ki bawa Janan wannan,ki fad'awa Fahad da Fauziyya na yafe musu suma su yafe min,sannan dan Allah karki raba kan 'ya'yana duk runtsi duk wahala ki zauna dasu ki k'ara musu darasi akan zaman duniya"

"Yallab'ai dan Allah ka daina fad'ar haka,ita mutuwa ko wanda yake lafiya k'alau tana d'auka"

"Baki san irin azabar da nake ji ba ni kad'ai na san yadda nake ji"

Ranar dai haka Abba ya rik'a shan azaba bai ma san wake kansa ba,k'arfe 11 na dare Allah yayi masa rasuwa.
_(wayyo Allah tashin hankali wanda ba'a sa masa rana,karkuso kuga yadda Mameey ta rik'a suma tamkar itama bazata rayu ba)._

Kafin safiya dubban mutane sun jin labarin mutuwar Alh Hashim,wasu suna Allah wadarai da hukuncin da aka masa a kotu wanda yayi sanadiyyar mutuwarsa wasu kuma suna cewa alhakin Aliyu ne.

A gidan mak'ocinsa aka yi masa sutura, wanda yake side d'insa, Alhaji Ibrahim  yana aiki a wani babban kamfanin saida motoci mutum ne mai karamci,side d'aya ya warewa su Mameey suka zauna zaman makoki tunda gidansu an k'wace musu.

Kwana biyu da rasuwar Abba Mameey tace su tafi su bar garin bata son zama duk da ana ta zuwa ta'aziyya ta dai fad'awa matan gidan ta wakiltasu su karb'i ta'aziyyar Abba.

Babu yadda Alh Ibrahim baiyi ba akan su zauna amma tace a'a duk da dai bata jindad'i kuma bama ta san ina zasu nufa ba.

Haka suka had'a duk kayansu na amfani suka tari taxi da sassafe suka tafi suna mai yiwa iyalan Alh Ibrahim godiya akan karamci da suka musu,sannan ta bawa haj kaltume uwar gidan takardar da Abba ya bada tace idan Janan tazo a bata a kuma bata hak'uri akan abinda ya faru.

Duk wannan abin da ake daga Janan har Aliyu babu wanda ya san wainar da ake toyawa dan a kwanaki biyun babu inda ya fita.

Janan kuwa dama daga d'aki sai band'aki saboda k'afarta ba lafiya bakuma ta jindad'i a kwanaki biyun nan.

Ranar da Aliyu ya fita ganin gidan yana son ya tsara yadda zasu zauna a ranar yaga mutane a k'ofar gidan mak'ocin Abba,koda ya tambaya sai aka ce masa Alh Hashim ne ya rasu yau kwana uku kenan kuma iyalansa sun bar garin.

Bai samu damar shiga gidan ba saboda yadda yaga mutane na masa gani-gani,babu shiri ya dawo k'auyen gaba d'aya jikinsa ya mutu duk da yana ganin hak'k'insu ya kashe Abba ya bi Hafsa da baba.

A tsakar gida ya tarar da Umma tana ta fito da kaya tana sakawa a bakko.

"Ya akai? ka kawo mai motar da zamu tafin?"

"Umma a bari sai gobe kinga yanzu yamma ta kusa"

"To a wane dalili kasan tafiyar ba yau ba kasa muke ta had'a kaya tun safe,to wallahi baka isa ba"

"Umma naga bama su kwashe komai ba,kayan d'aki da sauransu"

"Tunda kaga sun bari ai namu ne an hutar da kai siyan wasu"

Ganin ranta ya b'aci sosai yasa yace "to Ku shirya bayan sallar magriba zamu tafi"

"Allah ya kaimu" ta fad'a tana cigaba da had'a kayan.

Shi kuma ya wuce kewayensa.

A zaune ya tarar da ita tayi uban tagumi da duka hannunta biyu.

Tunda ya aureta bata tab'a bashi tausayi kamar yau ba,yana so ya fad'a mata rasuwar Abba amma ya kasa saboda da ciwo ace mahaifinta an kaishi har kuma kwana uku  bata ganshi ba bataji labarin rasuwarsa ba.
 _the same abinda ya faru dani_ ya fad'a a zuciyarsa.

"Ki shirya zamu bar garin nan mu koma Kaduna yau"

Gabanta yayi mummunan fad'uwa idonta ya ciko da hawaye tace "kana nufin gidanmu?ina su Abba suka koma?"

"Ba cewa nayi kimin tambaya ba umarni ne na baki" ya fad'a a dake,dan ji yake kamar yayi mata kuka.

Sauri yayi ya fita ya bar mata d'akin.

Ana yin sallah kuwa ya shigo yace su fito ,haka ta janyo trolley d'inta tana d'angasa k'afarta, fad'uwar gabanta ya tsananta.

A k'ofar gida ta had'u da Asabe "saura ki yada zumunci Amarya"

"Insha Allah zan rik'a ziyartarki bazan tab'a mantawa dake a rayuwata ba"

"Ki yawaita addu'a duk inda kike kuma a duk inda kika tsinci kanki karki manta addu'a"

"Insha Allah"

Wasu magunguna ta mik'o mata k'ulli biyu tace "wannan mai maik'on kina shafawa a ciwon,shi kuma na garin maganin na duk wani ciwo ne,ki kula da kanki,Allah ya kiyaye hanya ya kuma tsare ki"

"Ameen nagode sosai" ta fad'a ta d'aure maganin a zanenta

"Karki damu" Asabe ta fad'a cikin damuwa.

Duk abinda sukeyi Aliyu yana tsaye jikin motar yana kallon ta.

Su Umma da Ummi na fitowa tayi saurin zuwa ta shiga motar suka tafi.

A motar ma babu abinda Umma keyi sai habaici da zagin Janan tamkar wata sa'arta,ita kuwa tayi shiru tama rasa me yake mata dad'i.

Tun daga nesa ta hango canopy taji gabanta yayi mummunan fad'uwa duk da ba a k'ofar gidansu bane.

A zuciyarta tace _to ko mamansu bilkisu ta rasu ne dama ba cikakkiyar lafiyane da ita ba._

Suna tsayawa a k'ofar gate d'in gidan ta kasa fitowa,wai gidansu ne ya zama mallakin Aliyu,gani take tamkar a mafarki.

"To ki fito mana 'yar dad'i mota" Ummi tayi maganar tana yatsina fuska.

Jikinta a sanyaye ta fito tana k'ara kallon rumfunan da aka kafa a k'ofar gidan Alh Ibrahim.

Hasken lights d'in daya cika layin ne yasa Baita ya hangota, da sauri ya taso ya taho,lokacin ana sauke kayansu a mota.

Yana zuwa gabanta ya fashe da kuka.

Ita duk a tunaninta ko korar Abba daga gidan ne ya sakashi kuka dan haka tace "Baita pls ka bar kukan nan"

Cikin kuka yace "Janan wallahi ban san Abba ya rasu ba sai yau d'innan bamuyi adalci ba amma kuma ba laifinmu bane office aka ce dole sai mun koma"

Tunda ya fara maganar Janan ta saki baki tana kallonshi bata ma fahimtar me yake fad'a sosai.

Aliyu sadda kai k'asa kawai yayi yayinda Umma da Ummi ke mamaki.

"Wa.....wan...wane Abba?" Ta fad'a bakinta na karkarwa.

Jin haka ne ya sakashi yin shiru dan tunda yaji haka ya san bata san mutuwar ba.

Wuyan rigarsa ta shak'a tace "Abbana?wallahi k'arya kake yana raye bai mutu ba"

Dariya tayi irin ta zautattun nan sannan ta sake shi ta b'ata rai,sai kuma ta ruga da gudu ta fad'a gidan Alh Ibrahim d'in ta manta ma da ciwon k'afarta.














_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
        🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```



*_'Kawata Amarya Khadija,a gaskiya abinda kika zo min dashi yau bazan iya musulta farin cikin danaji ba,har na cire ran zan samu  saboda yadda nasha nema na rasa,ashe abin yana ranki har sai da kika samomin,zazzafar k'auna ce wannan,na yarda ke mai k'auna ta ce,fatana Allah ya saka miki da gidan aljanna ya biya miki dukkanin buk'atunki ya k'ara dank'on k'auna tsakaninki da maigidanki,ya k'ara dank'on zumunci tsakaninmu._*
```Nagode matuk'a```



26

A babban falon gidan ta tsaya tana zazzare ido tana kallon mutanen dake zaune.

A hankali ta fara ganin ko ina yana juya mata,cikin kuka ta furta "Mameey kina ina?ki fito ki fad'a min gaskiya Abba na san bai mutu ba" sai kuma ta rik'e gashinta ta sulale k'asa.

Salati aka hau yi,haj Mariya tayi saurin zuwa suka kamata aka yi d'akin bilkisu da ita.


*_Few minutes ago_*

Idanunta ta bud'e gaba d'aya tana kallon mutanen dake kanta.

Wani k'ara data k'walla sai daya gigitasu dukansu.

Ta mik'e tana neman ta ruga sukayi saurin rik'e ta,wani fizgewa da tayi Alh Ibrahim shi kad'ai ya iya rik'eta gam,aka kira likita yayi mata allurar bacci.

Idonta k'yar akan likitan har bacci ya d'auketa.

Kallon Alh Ibrahim yayi yace "tana neman rasa tunaninta fa ya kamata ana kwantar mata hankali"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,ya Allah ka bamu ikon ceto rayuwar yarinyar nan"

"Ameen" haj Mariya ta fad'a cikin damuwa.

Sallama sukayi da doctor ya rubuta wasu magungunan da zata samu relief sai kuma na ciwon k'afar tata,sannan yace zaizo washe gari ya cire mata bandajin goshin nata.

         *******

"Wai meke damunka Aliyu?naga duk kabi ka shiga damuwa akan waccan banzar yarinyar"

Ajiyar zuciya yayi yace "Umma wallahi ina mamakin rasuwar mahaifin Janan"

Mtsssw taja tsaki cikin b'acin rai tace "to ko shine Alh Rabe iya abinda zakayi kenan,mutumin daya kashe maka mahaifi da mata har ka ji tausayinsa,ai yanzu lokaci ne daya kamata ace muna farin ciki"

Shi dai bai ce komai ba illa kanshi kawai daya dafe "ina son dama kazo ka nunnuna mana abubuwan da bamu Sani ba,sannan kana sane da cewar wani satin za'a d'aura aurenku da Zuhra ko?"

Baice komai ba kawai tashi yayi yana fad'in "muje na nuna muku" ta lura dashi sarai akan damuwar daya sakama kanshi amma sai ta shareshi kawai.

         *******

Janan sai da tayi sati guda tana hauka-hauka sannan Allah ya bata sauk'in abin.

Yanzu ma tana zaune kamar ko yaushe tana ta kuka ,Bilkisu na gefenta tana bata hak'uri.

Haj Mariya ce tayi sallama ta shigo "Janan kukan ne har yanzu"

Zama tayi kusa da ita ta dafa kafad'arta tace "Janan Abbanki addu'a yake buk'ata ba kuka ba,ki Sani wannan kukan da kike yi kina saka masa rad'ad'i ne"

Cikin kuka tace "ina kukan takaicine,nabi son zuciya nayi abinda mahaifina baya so Ashe ajalinsa na janyo masa,ina dana sanin k'in bin maganarsa da nayi gashi har ya rasu bai bud'i baki yace Janan na yafe miki ba,sannan su Mameey sun tafi ban san ina suka shiga ba,taya bazan yi kuka ba,ku barni inyi dan Allah"

"Kiyi hak'uri Janan haka Allah ya k'addara"

"Ban san k'addarar mutuwar Abba da rashin su Mam.........." Da sauri Bilkisu ta rufe mata baki tana fad'in "kina addu'a Janan"

Jiki a sanyaye haj Mariya ta mik'a mata takardar tace "gashi inji Mameey tace Abba ne yace a baki"

Karb'ar takardar tayi ta kwanta ta cigaba da kuka,su kuma suka tashi suka fita dan ta samu damar karantawa a nutse.

Sai da tayi kuka sosai ta samu nutsuwa sannan ta ware takardar ta fara karantawa.

_Zuwa gareki 'Yata Jannah._
_Na san bazaki riski wannan takarda ba har sai na koma ga Allah, lokacin da zaki karanta na san zaki karantane kina mai zubda hawaye tare da nadamar k'untata min da kika yi na auren wanda ba zab'ina ba._

_Janan duk da na san bakya jin magana amma ban d'auki abinda kika yi a komai ba sai k'addara kuma babu yadda muka iya da hukuncin Allah._

_Janan ina mutuk'ar son ki ban tab'a jin sonki ya ragu a raina ba,ku uku Allah ya bani dan haka nafi son Ku fiye da komai a rayuwata,duk ranar da nayi muku wani abu kukaji haushi a ranar bana runtsawa saboda yadda nake jinku a raina yafi k'arfin wasa amma ina dannewa ne saboda in muku tarbiyya mai kyau bana son na sangartaku_.

_ko da kikaga ina korarki idan kinzo gida dan in hukuntaki akan laifin da kika yi ne,daga ke har Mameeyn naki na san baku tab'a hango abinda na hango muku ba,ba wai ina k'yamar talaka ba a'a ina gudun irin cin mutumci nasu da zarar ka mayar dasu inuwa,bance ko wane talaka haka yake ba,ban kuma ce daga yanzu Ku rik'a k'yamar talaka ba,a'a ina son kuyi bincike sosai akan duk abinda kuka saka a gaba._

_Sannan ina son sanar dake cewar Salman bai mutu ba,nace miki ya mutu ne saboda in fitar dake daga damuwar da kika shiga kuma in mantar dake shi,tabbas Salman mutumin kirki ne Janan, dan ko dana rabaku dashi bai tab'a min koda kuwa kallon banza ba har ya bar garinnan,na hanaki aurenshi ne saboda baya da asali Janan amma ki Sani Aliyu yayi min babbar illa,sannan ni ban san inda dukiyarshi take a gidana ba saboda ban san inda aka sare bishiyar da yake fad'a ba,gadonku yana hannunsa idan har ya cinye muku Allah bazai barshi ba,sannan ki k'ara sanar masa ina nan ina jiran ranar da zamu tsaya ni dashi a mana hisabi dan ban yafe masa ba._

_Ina son ki nemi gidan wani Malam Lado a cikin katsina yake a wata unguwar_  ```filin samji```  _yake kice masa yayi miki kwatancen gidan wani wanda ake kira da Alto sarkin gini a cikin garin Nijar ban san wane gari bane,in kikaje mutumin ko bai biyoki ba zai fad'a miki inda bishiyar da suka sare take don shine da yaransa sukayi aikin gidan duka,ban fad'awa kowa ba koda a kotu domin na san shari'ar ha'inci aka yi ban fad'awa kosu Fahad ba ke na zab'a na kuma fad'a miki kije ki farauto muku 'yancinku ki amso muku dukiyarku Janan kena wakilta dan haka tafiya ta kamaki da zarar kinga sak'on nan karki zauna_.

_daga k'arshe ina muku fatan Alkhairi a sauran rayuwarku,ina fatan zaku cigaba da rayuwa cikin jindad'i da amincin Allah, na yafe miki duniya da lahira nima ki yafe min 'yata._

Kuka har sark'e mata ya rik'a yi,tanayi ta magana tana fad'in "baka min komai ba Abba na yafe maka Abba"

Kasancewar gidan babbane suma basu jiyo kukanta har tayi ta gama ta kwanta lamo tanayin kukan zuci.

Shigowar Alh Ibrahim ce yasa ta d'ago kanta tana hawaye.

" 'yata kukan ya isa haka,mahaifinki kowa ya shaida shi mutumin kirki ne,har aka kaishi makwancinsa mutane suna kukan rashin adali,yana kwance cikin jindad'i amma ke kina d'aga masa hankali,kina son ya rik'a jin azaba da rad'ad'in kukan da kike masa"
Ta girgiza kai tana goge hawayen wani na k'ara zubowa.

"Abu d'aya zaki masa wanda zaiji dad'i ya kuma san ya haihu shine addu'a karkiyi wasa da yi masa addu'a kinji" ta d'aga kai alamar to.

Haka ya cigaba da mata nasiha cikin rarrashi.

          ********

Da sallama ta tura k'ofar d'akin ta shiga.
"Dama Umma tace kina nan kina kuka" Raihan ta fad'a lokacin da ta k'araso jikin gadon ta zauna.

Wasu sabbin hawaye ne suka fito daga fuskar Lubna ta saka hannu ta goge sannan ta fara magana.
"Dole duk ranar dana tuno Janan nayi kuma,ke! na san  Janan bazata tab'a gogewa a zuciyata ba"

"Hakane Lubna wallahi ni kaina ina jin Janan a cikin jinina lokacin guda na shak'u da ita yanzu haka Ummina fad'a take min akan meyasa ban kawota suka cigaba da zama a gidanmu tunda Akwai extra rooms"

Lubna na hawaye tace  "nifa saboda Janan daddy ya hanani fita ko ina dan kar inje gidansu,wallahi ina dana sanin barin Janan tayi soyayya da Aliyu,Ashe ba alkhairi bane shiyasa har mukayi fad'a da ita a kanshi,tunda yarinta muke tare da Janan tare mukayi primary, secondary skul sannan muna tare a high institution ma amma ace rana d'aya na barta ta barni,saboda Janan bata da lafiya nak'i cigaba da karatu har sai data warke muka fara poly tare amma ace yau an rabamu mahaifina ya mana tsakani da ita" kuka sosai take Raihan ta rumgumeta tana rarrashi.

Turo k'ofar da aka yi ne yasa Raihan ta juya tace "kinga Umma kukan take"

"Aini har na gaji da kukan Lubna ki rarrasheta dai ke k'ila taji maganarki"
Fita tayi taja musu k'ofar.

"Lubna dan Allah ki bar kukan nan"

"Dole inyi kuka Raihan,Abba ya rasu ban je musu gaisuwa ba gashi ance sun bar garin ya zanyi"

Hmmm "hak'uri mana Allah ya Sani ba da gangan mukayi ba,nima ban san rasuwar Abba ba sai jiya kuma yau ina zuwa na tarar wai Aliyu ne a gidan,dana fito na tambayi wani a waje sai yace sun bar garin kuma bai san inda suka koma ba"

"Kinji fa,gaskiya Aliyu azzalumine Raihan wallahi sai yanzu na k'ara dana sanin k'in fad'awa Jalal da mukayi na san da yayi wani taimako"

"Hakane gaskiya bamu kyauta ba,jiya ma munyi waya dashi ya tambayeni tana zuwa skul nace masa eh ni ban san ta ina zan fara masa bayani ba,amma yace min sai upper week zai shigo Kaduna"

"Idan ya shigo kawai mu sanar dashi dan k'aryar ba inda zata kaimu"

"Yawwa credentials d'in Janan komai da komai yana hannunki ko?"

"Eh"

"Ki bani in na shiga skul gobe zanje in mata deferring dan bana son ta rasa karatunta"

"Amma Raihan meyasa bazaki bari muga yadda Allah zaiyi ba ko zata dawo"

Hmmm "Lubna mun kusa fara exam yaushe kike tunanin zata iya covering bayan tana cikin damuwa koda ta dawo d'in ma kawai ki bani wannan itace hanya mafi sauk'i"

Tashi tayi a sanyaye ta d'akko mata ta bata,sukayi sallama ta tafi.

           ********

Yana kwance yana juyi akan makeken gadon Abba wanda a yanzu ya zama mallakinsa.

Hankalinsa gaba d'aya a tashe yake,yau satinsa biyu kenan bai saka Janan a idonsa ba,bai tab'a tunanin ta shiga ransa ba sai yanzu da bata gabanshi, da kuwa gani yake kawai ya tsaneta baya son ganinta amma yanzu babu abinda yake son gani sama da ita.

Yaje gidan Alh Ibrahim har sau biyu amma ko farfajiyar gidan maigadi ya hanashi shiga bare ya samu ganin Janan.

Shi unguwarma ta ishesa babu wanda yake mu'amala dashi kowa ya tsaneshi,ko a masallaci mutane basa musabaha dashi.

Kodan ansan shi ada *Direban* gidan ne shiyasa suke masa gani-gani.

_ni kuwa komai zai faru ba zan bar gidan gadonmu ba saboda anan na girma,in basuyi mu'amala dani ba wasu zasuyi._ ya fad'a a zuciyarsa.

Ummi ce ta turo k'ofar cikin sallama ta shigo ta zauna.

"Lafiya?" Ya fad'a yana kallon ta.

"Yaushe zan koma makaranta kuma Umma tace zaka koya mana mota tunda akwai motoci"

"Bazan koya miki ba yarinya tun kafin ki waye har kinsan k'arya" ya fad'a rai a b'ace.

Tashi tayi tana turje-turje ta fita.

Sai gata sun dawo da Umma.
"To mara kunya naji sak'onka"

Tashi yayi zaune yace "Umma wane k'aryar taje ta fad'a miki"

"Maganar koya mota dole ne a koya mata itama"

"Umma....."

"Rufamin baki kabi Umarnina kawai"

Knocking suka ji ana tayi dan haka duka sukayo waje dan sunsan babu wanda zai nemesu to waye haka?.

Yana bud'e k'ofar idonsa ya dira akan nata,gabanshi har fad'uwa yayi yadda yaga idanun nata kamar sun juye.

"Ohh kece kika dawo" Umma ta fad'a tana k'ok'arin fitowa.

Bata ma kalleta ba kawai tace "ba dawo wa nayi ba nazo karb'ar takardata ne"

"Ina nufin ka sake ni Aliyu" ta fad'a idanunta a cikin nasa.

"Kinzo a dai-dai gab'ar daya dace,dama saki ai ko baki nema ba zai miki shi dan haka na baka damar ka sake ta saki uku a take anan"

Ya kasa d'auke idonsa akan Janan sannan ya kasa magana.

"Ka saketa nace"

"Umma bazan iya ba,idan na saki Janan ina ganin babu adalci a lamarin"

"K'arya kake Aliyu" Janan ta fad'a tana nuna shi da yatsa tana k'ara fad'in "dole ka sake ni wallahi kai baka isa kayi min illa ba kuma in cigaba da zama da kai,har yaushe kasan adalci ai baka da adalci kai azzalumi ne" ta k'arasa maganar tana kuka.

Umma ta kalleshi cike da mamaki tace "ince ka saketa amma kana ce min bazaka iya ba"

"Kiyi hak'uri Umma bazan iya sakinta ba"

Sakin baki Ummi tayi tana mamakin yayan nata,Umma kuwa k'ara fad'i take wallahi sai ya saki Janan yana fad'in bazai iya ba.

Cikin matsanancin kuka tace "kayi shari'a da mahaifina kaci galaba to ka sani a wannan karon ni zanci galaba zamu tsaya gaban alk'ali da kai dole ne ka sake ni, ka jira sammaci daga kotu"

Da sauri ta juya ta tafi tana cigaba da kukan tare da k'udiri da yawa a kanta.






_Sadeey S Adam✍_
🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁


_*SaNaz deeyah*_👄




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


_*Zuwa ga readers naji k'orafe-k'orefenku game da Aliyu da Abba,ina son ku gane cewa a halin yanzu is hardly ayi shari'ar gaskiya,wani yana da gaskiya ake danne masa hak'k'i sannan shaidun Aliyu sun shaida mahaifinsa yana da d'unbin dukiya uwa uwa uba gonaki ,da filayensa wanda duk takardun sun salwanta a gidan tunda ba'a san inda suke ba wannan shine dalilin daya saka aka bawa Aliyu dukiyar Abba wanda k'ilama yafi Abba dukiya cox kunsan 'yan k'auye akwai hana kai a tara dukiya,ina son duk wanda ke karanta labarin ya karanta a nutse karku rikice please👏*_

_Godiya mai tarin yawa tare da fatan alkhairi gareku masoyana._


27

Tana fita Umma ta kalleshi tace "wallahi idan baka bita ka sake ta ba ban yafe maka ba,kawai muna zaman lafiya a nemi maidamu kotu"

Shiru kawai yayi baice komai ba.
"Zaka saketa ko saina tsine maka"

"Umma........"
"Ka saketa nace"

Jikinsa a sanyaye ya fita,a tsaye ya ganta jikin gate d'in tana goge hawaye.

Shima hawayen yaji suna k'ok'arin zubo masa yayi saurin dakewa yace "ba sai na wahalar dake ba wajen zuwa kotu, kije na sakeki saki d'aya"

Kallon shi tayi wasu hawayen na zuba a idonta tace "dama ka k'ara biyu dan na gama zama da kai Aliyu"

"Ni kuma ina saka ran zama dake anan gaba,ina sonki Janan"
Yana fad'a yayi saurin wucewa ciki tabi k'ofar da kallo,bayan aurensu bata tab'a jin ya furta mata kalmar so ba sai yau.

Kallon gidan Alh Ibrahim tayi tana hawaye dan bazata koma ba saboda sun hanata tafiya ko ina shiyasa ta yanke hukuncin tafiya ba tare da ta musu sallama ba.

Tana tafiya tana waiwayen unguwar dan ta san bazata tab'a komawa cikinta ba.

           **********

Hankici ya d'akko yana goge zufar goshinsa sannan ya juyo ya kalli Momma yace "wallahi momma babu alamun zamu ga yarinyar kinga duk kwatance da nema bazai kaimu ba,yau kwana biyu kenan muna garin nan babu alamun za'a ganta"

"Hakane Muhasin nima na fara fidda rai da ganinta amma zan cigaba da addu'ar Allah ya sadamu da ita da alkhairi dan duk ranar dana ganta tabbas na maka mata"

"Mata kuma Momma?"

"Eh mana"
"Wannan 'Yar k'auyen wallahi na tsaneta ni k'yank'yaninta nake"
.
"K'yank'yani kuma?"

"Wallahi Momma bana k'aunar 'yan k'auye"

"Baka k'aunata kenan?"

"Momma dan Allah ki daina fad'an haka"

"Dole na fad'a saboda kana fad'a min ka tsani wadda tayi silar samun lafiyata"

"Ni bance haka"

"To ka sani in har na ganta koda kayi aure zata kasance matarka itama"

Baice komai ba kawai ya nufi inda motarsu take ya shiga.

"Maganar da na maka ne yasa ka b'ata rai?"

Murmushin dole  yayi sannan yace "taya zanyi miki fushi Momma"

"Okay mu shiga cikin Kaduna ina son shiga central market inyi 'yar siyayya"

"Okay" ya fad'a tare da jan motar.

Suna cikin tafiya Momma tana tayi masa fad'an driving d'in da yake gudun yayi yawa,
Murmushi yayi yana fad'in "Momma ai nafi son mu koma yola yau"

"To ai sauri yana daga aikin shaid'an ko kana son muyi accident?"

"Kaiii haba Momma daina fad'a ma Allah y............"
'Kiiii.......ya taka burki tun daga nesan amma bai tsaya ba sai da yaje gabanta yayi sama da ita sannan ya dawo da ita yayi wurgi a tsakiyar titi,hakan ya faru ne da tafiyar da takeyi tun daga layinsu har zuwa bakin titi bata ma san me take ba tsabar tunani(pls mu tausasa zuciyarmu mu rage tunani akan titi musamman mu mata munfi kowa saka abu a rai).

Momma tayi saurin runtse ido tana salati shima salatin yayi tare da saurin bud'e motar ya fito.

Momma ma  da sauri ta fita lokacin Muhasin ya kutsa cikin mutanen,bai gane fuskarta saboda yadda jini ya wanke ta yayi mata hawaye.

Momma kuwa tana zuwa ta gane ta,da sauri ta sab'eta tayi mota shima da sauri ya shiga.

"Muhasin mu tafi asibiti kayi sauri"

"Momma ban san asibiti ko d'aya a garin nan ba" ya fad'a a gigice.

"Ka tambayi wani ya kwatanta maka" da sauri yayi gurin mutanen ya tambaya.

         ********

Suna tsaye a bakin emergency Momma ta kalli Muhasin tace "ina maka fad'an driving da gudu sai ga darasi ka gani,Allah ya tashi kafad'ar yarinyar nan"

"Ameen Momma"

"Munzo nemanta sai gashi Allah ya had'amu da ita a yanayin hatsari"

"Oh Momma wai itace?"

"Eh mana baka gane ta bane?"

"Eh" ya fad'a a sanyaye a dai-dai lokacin da likita ya fito.

"Ku kuka kawo patient d'in nan"

"Eh mune" Momma ta fad'a.

"Ku biyoni office zan muku bayani"

"Okay"

Suna zaune a office duk sun maida hankalinsu ga likitan.

Sai da yayi 'yan rubuce-rubuce sannan ya d'ago kai ya kalli Muhasin yace "Ta bugu sosai amma munyi nasarar tsaida jinin sai kuma cikin jikinta Alhamdulillah bai samu mats.................."

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" suka ji an fad'a a sanyaye.

Duk Kansu suka kalleta da mamakin yadda akai ta taso tazo.

Momma da sauri ta taso taje bakin k'ofar ta dafa ta tace "meyasa kika taso? baki da lafiya"

"Na shiga uku dan Allah ka fad'a min gaskiya taya za'ace ina da ciki wallahi ban tab'a sanin wani d'a namiji a rayuwata ba"

Shima likitan da sauri ya taso yazo gabanta yace "baki da lafiya taya kika taso?ina nurses d'in?"

Idanunta a jujjuye take kallonshi wasu zafafan hawaye suka sauka a fuskarta,a hankali ta sake fad'in "rayuwata ta gama lalacewa" a haka ta sulale zata fad'i Momma tayi saurin ruk'ota tare da jijjigata cike da fargaba.




_*Fans kuyi hak'uri da wannan,nayi shi d'an kad'an,kuma in brief gashi babu editing sai kunyi hak'uri da ganin errors, hakan ya samo nasaba ga wasunku da suka bini har PC akan inyi typing ko kad'anne amma yau banyi niyyar yi ba saboda ban samu lokaci ba sai dai bana son b'atawa masoyana rai shiyasa nayi d'an kad'an.*_
_#TARENE#_







_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
           🍁🍁🍁


*_by SaNaz deeyah_*👄


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




28

"Karki mana haka,dan Allah ki tashi"
Momma ta fara jijjagata tana hawaye.

Nurses ne suka shigo aka d'auketa aka mayar da ita gadon sai a lokacin ta dawo hayyacinta,ta bud'e idanunta wani mugun zugi take ji a k'afarta yayinda wasu hawaye ke k'ara fita a idanunta.

"Kina son k'afarki ya rub'e?" likitan ya fad'a lokacin da yazo dai-dai kanta ya tsaya.

Ba taka kalleshi sai dai hawayen dake idanunta basu daina zuba ba.

"Indai kina so k'afarki ya warke sai kin daina taka ta,ko bakisan kin samu karaya a k'afarki ga kuma ciwo,ki daina takata ki hak'ura har ki samu lafiya"

Idanunta ta lumshe saboda yadda ta fara ganin d'akin yana juya mata.

Momma ta zauna gefen gadon ta rik'e hannun Janan tana kallon fuskarta cike da tausayi.

Mtswww Muhasin yaja tsoki sannan yaja kujera ya zauna yana kallon Janan tamkar ya daketa,yana ta addu'ar karsu had'u amma sai da ta k'ara shigowa rayuwarsu.

_Na gode ma Allah daya kasance cikine da ita da yanzu an lik'an Jaraba auren 'yar k'auye ko wahala_ yayi maganar a zuciyarsa sai kuma ya mayar da kallonsa ga Momma wadda ta k'urama Janan ido tun lokacin data zauna.

"Momma yaushe zamu tafi yolan?"

'Dago idanu tayi ta kalleshi tace "sai munga abinda Allah yayi kaga ai bama tafi mu barta a wannan halin ba"

"Momma to ta fad'i k'auyen da take sai in kira iyayen nata idan yaso sai mu basu kud'in da zai isa su cigaba da jinyarta mu mu tafi"

"Saboda rashin Adalci?"

"A'a amma naga ko muna nan ko bamu nan zata samu lafiya,kinga na bar aiki kwana biyu kenan banje office ba"

"Muhasin!zaka iya tafiya ni ka barni anan,ai nasan hanyar Yola tun kafin na haifeku to zan taho idan ta warware" Momma ta fad'a rai a b'ace.

"Ku tafi kawai" sukaji ta fad'a.
"Nagode da kawoni asibiti da kukayi ku tafi kawai ni na san tawa ta k'are" duk maganar nan da take idanunta a rufe suke.

Shiru su kayi basu ce mata komai ba,Muhasin ko kallonta baya son yi saboda takaici.


_3 days later_

An d'an jingina mata pillow a jikin gadon tana zaune ta jingina bayanta dashi,duk ka idanunta a k'asa tana goge hawayen da basu daina fitowa ba.
Muhasin yana jikin bango ya hard'e hannunsa a k'irji yana kallonta yana mamakin yadda ko gajiya batayi da kuka,shi ya tsani yaga ana rarrashin mutum yana kuma k'ara cigaba da kuka.

"Dan Allah ki bar kukan nan ki tsaya ki fad'a min meke faruwa naga tun da na tambayi iyayenki kike kuka,abinda yasa na tambayeki  saboda yau muke son tafiya kuma ai bazamu barki ke d'aya ba shiyasa na tambaya saboda na san suna can hankalinsu a tashe tsawon kwana uku bakya nan,idan kuma cikin jikinki kike tsoron su sani ni zan musu bayani saboda babu wanda yake kaucewa rubutacciyar k'addararshi"

"Momma akwai sakaci fa,ni fa naga k'ok'arinki da kuka zauna asibiti jinya a tsohon kwana uku babu wata dangantaka"

"Muhasin idan ka sake magana sai na tsab'a maka"

'Daga kai Janan tayi ta sake kallonsa sannan tayi saurin kawar da kanta saboda gaba d'aya tsoronshi take,har yanzu idan ta tuno marin da yayi mata tana jin zafinsa.

Kallon Momma tayi tana goge hawaye tana d'an murmushi  tace "karki damu nagode sosai da taimakon lafiyata da kuka yi,karki damu zan cigaba da jinyar kaina"

"Kamarya kenan?"

Shiru tayi bata ce komai ba.
Momma ta rik'o hannunta tace "dan Allah ki fad'an labarinki 'yata kina nufin baki da kowa?"

Wasu hawayen suka zubo a fuskarta ta girgiza kai alamar a'a.

"Suna ina?"

Ai tana jin haka a b'arke da sabon kuka tana shashshek'a, muryarta na rawa tace "Mahaifina ya rasu,Mahaifiyata da yayye na kuma ban san ina suke ba tun bayan rasuwar mahaifina suka bar garin nan"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" Momma ta cigaba da nanatawa.

Rungume Janan d'in tayi tana ta rarrashi sai da ta d'auki fin minti talatin tana kuka sannan ta daina sai hawaye kawai daya cigaba da fita.

"Mene sunanki?

" Janan" ta fad'a murya a dashi.

"Jannat kenan?"
Ta d'aga kai alamar eh.

_wai Janan ashe 'yan k'auye ma sun yi wayewar da zasu saka sunan wayayyu._ ya sake furtawa a ransa ba tare daya damu da halin da take ciki ba.

"Ki fad'a min labarinki mana,dan abin yana d'aure min kai"

Idanunta a k'asa muryarta na cigaba da rawa tace "labarina yana da tsayi zaiyi wahala in iya baki shi a yanzu"

"To karki damu ki fad'amin gidan 'yan uwanki da kike zaune sai mu kirasu ko"

Girgiza kai tayi tace "bani da kowa saboda dangina na san babu wanda zai karb'eni saboda ko lokacin da babanmu yana da rai ba wani zumunci ake ba"

"To yanzu ya za'ai?"

"Shiyasa nace ku tafi ku barni kawai"

"Anan wai?"

"Eh" ta fad'a tana d'aga kai.

Muhasin yayi saurin cewa "Momma tun da tac......."
"Yi min shiru Muhasin" ta dakatar dashi.

"Dan k'aunarki da annabi Muhammad (S.A.W) ki fad'a min labarinki saboda sai naji labarinki sannan in san wane taimako zan miki"

Kallonta tayi sannan ta sake sadda kai "labarina yana da tsayi amma zan fad'a miki shi a gurguje"

"Ni haifaffiyar garinnan ce dan anan na tashi na ganni,tun lokacin dana taso nayi wayo nasan babana d'an sanda ne ya rik'e post-post da yawa kafin ya zama _commissioner of the office_.
Mu uku ya haifa yayuna biyu mace da namiji sai ni auta".

" mun taso cikin so da k'auna ga iyayenmu amma babanmu yana da tsatstsauran ra'ayi,dan shi a rayuwarshi baya da wani buri kamar yaga mun samu ingantacce ilmi shiyasa baya mana ko maganar mu tsaya kula samari"

"Ina Ss3 Allah ya had'ani da wani muka fara soyayya sanadin had'uwata dashi mun taso daga skul naji yana maganar mamanshi babu lafiya gashi baya da kud'i yana ta rok'an wani mai shago wanda kana gani kasan akwai alak'a tsakaninsu amma mutumin wulak'anta shi yake yana fad'in baya da sana'a taya zai biyashi idan ya bashi"

"Ganin haka yasa nayi saurin k'arasawa gurin nace masa bawon Allah nawa kake nema? Ya juyo a rud'e yace ban sani ba tana gida bani da ko kud'in kaita asibiti"

"Nayi saurin ce masa muje gidan,shi yayi gaba ina binsa a baya,inajin mai shagon yana cewa kaje ga masu kud'in banza"

"Ban ko juya na kalleshi ba,haka muka sha tafiya Wanda a lokacin naga nisan gidan saboda ban saba doguwar tafiya a k'afa ba,lokacin da mukaje k'ofar gidan har hawaye na zubda ganin wai dama akwai masu irin wannan rayuwa gidansu tamkar kango dan ya tsufa ya rub'e sosai amma cikin gidan a tsaftace a share yake tas,ganin mahaifiyar shi da wata tsohuwa ba k'aramin d'agamin hankali yayi ba yadda naga jini a bakinta ashe wai amman jini take saboda ciwon zuciya"

"Haka muka tafi asibiti da ita aka kwantar,ni na biya kud'in komai da yake bana barin Atm d'ina a gida kullum yana cikin jakana"

"Bayan an gama test har an sayo jini za'a k'ara sannan nace masa zan tafi gida kar a nemeni,sai a lokacin ya lura da uniform ne a jikina"

"Ke d'aliba ce a ina kika samu kud'i haka?"

"Kallon mamanshi nayi da take kwance kamar gawa nace,duk wata mahaifinmu na tura mana dubu talatin wataran hamsin"

"Baice komai ba yayi godiya ya rakani na hau napep na tafi,nasha fad'a sosai gurin Mamana saboda anje d'aukana ba'a ganni ba duk hankalinsu ya tashi gashi babana baya son hawa napep wai kar a sace mu"

"Dana shiga d'aki na bawa mamana labari itama ta tausaya musu sosai da yamma tare mukaje dubiya,a haka muka cigaba da jinyar Maman shi abinci ma daga gidanmu ake kawo musu,har Allah ya had'a jininmu sosai muka fara soyayya dashi ba tare dana hango k'alubalen da zan fuskanta daga mahaifina ba"

"Bani mantawa a ranar da mamanshi zata rasu da safe da yake asabar ne nina kai musu abinci break nida 'yan aikinmu,mun gaisa na d'an zauna da yake muna extra lesson sai na tashi zan tafi kawai ta rik'o hannuna tace min dan Allah ga amanar Salman na damk'a miki, shi maraya ne kuma shi kad'ai na mallaka,kimin alk'awarin zaki aure shi ko bayan raina karki gujeshi,cikin rauni na fara hawaye ina mata alk'awarin bani da wani miji da ya wuce shi,dana tafi ina dawowa da rana aka ce sun tafi saboda Allah ya mata rasuwa,a gigice na koma driver ya kaini har gidan wanda tun a waje na jaddada mutuwarta dana ga mutane a zazzaune kan tabarma wasu a tsaye lokacin ko kaita ba'ayi ba,aikuwa ina shiga na tsugunna gaban gawarta ina kuka ina mata addu'a,a ranar banma samu ganin Salman ba sai washe gari muka zo da 'yan gidanmu duka har babana"

"Haka aka shafe har arba'in sannan ya fara min maganar Aure saboda ya gaji da zama shi kad'ai shiru,gashi baya da sana'a sai dai in ya samu yayi a biyasa kud'i,nace masa ya jira sai mun gama jaraba lokacin mun fara neco"

"Ina gama exams banyi k'asa a gwiwa ba na fad'awa babanmu dan banyi tunanin abin zai zo min ba sauk'i ba,babanmu yasa na kirashi a nayi tunanin zai masa magana ne ya fara shirye-shirye sai gashi a gabana a gaban 'yan gidanmu yaci masa mutumci yace kuma bazai aurawa 'yarshi talaka ba kuma mara asali saboda dama daga shi sai mamanshi suke rayuwa a gidansu"

"Nasha kuka kamar raina zai fita,haka bayan kwana biyu yazo yace min zai bar garin nan saboda bazai iya zama yaga an bada ni ga waninsa"

"Tun daya tafi na fara rashin lafiya tamkar bazan rayu ba wani lokacin ma bana hayyacina,a haka akayi ta jinya ta har waje,bayan na fara samun lafiya babana yazo min da labarin Salman ya rasu a Lagos,nayi kuka sosai daga baya nayi tawakkali"

"Kuma tun daga lokacin in dai an zauna hira babanmu zaice nifa bazan aurar da 'ya'yana ba sai sunyi karatu sun kai har matsayin masters wani lokacin mamana takance ai shi Aure lokaci ne idan yazo babu tantama sai anyi"

"Na samu gurbin karatu a polytechnic lokacin yayata na jami'a L2,muna second semester baban mu ya kawo mana sabon driver wanda da da kanmu muke zuwa skul"

"A haka dai muke zuwa daga k'arshe ma ya zama driver na yayata aka siya mata mota shi kuma lokacin yayana already yana aikinsa"

"Kasancewar na tsani a wulak'anta talakka wannan shine mafarin fara soyayya da *Direban gidanmu* wanda shima banda mamana ta jajirce  da bazan aureshi ba,dan har akayi bikinmu babana yana fushi dani akan na auri talaka *direban gidanmu*"

"Mamana ce tayi komai wanda uba da uwa keyi,sannan ta bashi jari mai yawa wanda zai rik'emu dashi sannan ta bashi kyautar gidan da zamu zauna"

"Ranar da za'a kaini babana ya bud'i baki yace babu ni babu shi sannan kar in sake in zo masa gida duk abinda zai faru,tsabar so ya rufe min ido ban iya cewa komai ba"

"Washe garin ranar da aka kaini kuwa yace in had'a kayana zamuyi tafiya haka na had'a akwati uku muna tafiya na ganni kawai a wannan k'auyen cikin gidansu yace anan zan cigaba da rayuwa,nace gaskiya bazan iyaba aikuwa ya fara fad'a yana fad'in shi dama auren manufa yayi dani ya aureni saboda ya karb'o musu gadonsu a gurin babana sannan ya rama abinda yayi masa haka suka had'u da mamanshi da k'anwarsa su kayi ta zagin iyayena ina ji ina gani"

"Nasha kuka sosai na rik'a rok'ansa ya fad'a min abinda mahaifina yayi masa yak'i fad'an"

"Kullum sai sun jibgeni babu rana da bazai min duka ko mamansa ta min ba,haka zasu saka inje in d'ebo ruwa sannan suce in yi girki ni kuma ban iya irin girkinsu ba idan nayi baya ciyiwa haka zasu dakeni suce nayi musu asarar kud'i saboda ban san ciwon kudi ba,ni kudin haram babana yake ciyar dani,akwatinan dana zo dasu ya kwashe ya kawo min wani tare da kaya kala biyar yace wancan lefe zai dasu kuma gidan da nake tak'ama da cewa mamana ta bashi ina gani wata zata zauna,ranar daya sakeni zai wulak'antani da zarar ya karb'o gadonsa a gurin babana zaimin sakin wulak'anci,haka nake jure komai saboda son da nake masa"

"Ranar dana fara tsanarsa shine ranar da naje skul k'awata take bani labarin ya shigar da babana kotu ana shari'a ga wulakanci da zagin mamana da yake,a ranar naje gida babana daya ganni tamkar zai shid'e yace in fita kuma idan ya mutu nice sila"

"Ina kuka na fita na koma gidan su k'awar tawa to a lokacin ta bani labarin wai babana ya tab'a kulleshi shekara takwas saboda an kamashi da miyagun k'wayoyi wanda ba laifinsa bane abokinsa ne ya kawo masa shi kuma babana ya manta da case d'in har tsawon shekara takwas sannan aka zo aka fad'a masa yayi bincike sosai ya gane baya da laifi yasa a bashi hak'uri a sake shi dan yana jin kunyar had'uwa dashi,nayi niyyar zama a gidansu babanta ya koreni yace ya rabamu saboda bazai zauna da azzalumai ba,haka na fita ina kuka wanda bani da inda zan koma in ba wannan k'auyen ba,ina zuwa yayi min duka wai yace kar inje ko ina shine na biya gidanmu,mamanshi tazo tace in d'ebo ruwa in dafa abinci,koda na fita kawai nayi rafi da niyyar in kashe kaina kawai in huta,kwatsam sai Allah ya kawo ku wanda na d'auki wannan a matsayin Allah ya turo min ku ne saboda ya kub'utar dani saboda idan na kashe kaina tabbas na mutu kafura"

"Kuna tafiya kawai naji ana min tafi,ina juyawa na ganshi yace min dama abinda nake aikatawa kenan,kafin nayi masa bayani ya mareni tare da tureni na fad'i ban k'ara tsintar kaina ba sai a wani gida"

"Ashe wani skul friend d'ina ne yazo wucewa ya ganni cikin jini ya d'aukeni ya kaini gidansa"

"Ina farfad'owa na ganni da drip aikuwa likitanshi na ciremin nace gida zani saboda kar zargi ya shiga,bai hanani fita ba amma ina fita na dawo saboda 'yan iska da suka so b'ata min rayuwa Ashe dare ne sosai,ranar wallahi ban runtsa ba har safiya sannan ya kaini gida,tun a waje mijina ya fara dukana yana zagi wai abin har ya kai inyi iskanci saurayin ya kawo ni gida,hak'uri na rik'a bawa friend d'in nawa saboda na san na jaza masa wulak'anci cikin b'acin rai ya tafi"

"Ina shiga gidan mamansa ta d'akko Razer ta yanka min k'afa tun daga babban yatsa har gwiwa sannan ta watsa gishiri a gurin na kwalla ihu saboda ba k'aramar azaba naji ba"

 Momma ta runtse ido sannan ta bud'e tana hawaye lokacin da Jannan ta bud'e k'afar tana nuna musu gurin har ya kusa k'arasa warkewa ga karaya kuma a k'afar still.

Ta cigaba da fad'in "a ranar sai da mak'ociyar mu ta rakani har gida babana ya sake korana"

"Abinda yafi d'aga min hankali shine ana gama shari'ar da kwana biyu babana ya rasu saboda bak'in cikin abinda aka masa amma har yayi kwana uku su mamana da 'yan uwana sun bar garin sannan na sani shima lokacin munzo garin da niyyar mun dawo nan da zama,akwai wasu abubuwa da yawa wanda shi mijin nawa baiyi bincike ba sannan abin ya had'a da shari'a mara gaskiya bak'in cikin wannan abin ne yasa babana ya rasu,nayi alk'awarin bazan sake furta dalilan ba har sai na d'aukarwa mahaifina fansa,naje na karb'i takardar saki a hannunsa wanda bana fatan mu sake wani zama dashi amma kuma ace min wai ina da ciki,taya ya? Bamu yi zaman arzik'i dashi ba hasalima ko yatsana bai tab'a tab'awa ba in ba da niyyar duka ba ko mari,bamu tab'a had'a gurin kwana dashi ba ina na samu ciki? Wallahi tun da uwata ta haifeni ban tab'a aikata zina ba"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un Momma ta rik'a nanatawa tana kuka"

Muhasin shi yazo yana ta rarrashinta akan tayi hak'uri kar ciwonta ya tashi.

Kallon shi tayi lokaci guda idanunta sunyi jajir
"Muhasin ban tab'a ganin mutum kamar Janan ba,'ya'yan talakawan ma fa gudun 'yan uwansu suke sunfi son auren mai kud'i saboda su huta da yake yanzu ba soyayyar gaskiya ake sosai ba,labarinta tamkar shirin film ko littafi,wannan wane irin azzalumi ne"

Itama Janan d'in kuka take sosai,shi kansa Muhasin mamaki take bashi ta sadaukar da far in cikinta akan soyayya ashe dama 'yar hutu ce amma ta mayar da kanta tamkar wadda bata tab'a shiga class ba.

Sai tausayinta ya rufe shi a lokacin yayi nadamar marin da wulak'anci da yayi mata.

Ji yayi Momma ta sake fad'in "Muhasin duk cikin 'ya'yana kai ne kad'ai ke jin magana ta dan Allah kayi koyi da halin Janan,kirki,hak'uri,nutsuwa,tawakkali, da tausayi"

Baiyi magana ba sai kanshi kawai daya sauke k'asa.

Da rana Muhasin ya tafi yi musu takeaway Momma ta kalleta tace "Janan zan miki wasu tambayoyi"

Shiru bata ce komai ba sai da Momma tace "daga aurenki zuwa ranar da kika rabu da mijinki baki tab'a ji kin tashi kinga jikinki wani iri ba,ba sai na fad'a ba kin gane dai"

Shiru tayi na 'yan wasu lokutan sannan tace "Daren aurena na wayi gari a wani yanayi dan har wankan tsarki nayi amma ban kawo komai ba wallahi saboda Aliyu bai kwana a d'akin ba kuma ni ba maganin bacci nasha ba"

Murmushi Momma tayi tace "wannan cikin nashi ne"

Zabura Janan  tayi Momma tayi saurin ruk'ota.
"Ki kwantar da hankalinki"

"Na shiga uku" ta sake rushewa da kuka.

Momma tayi ta rarrashinta da k'yar tayi shiru.

Tana kwance tayi lamo Momma tace "Za muje gurin 'yan uwanki wanda suke shak'ik'ai a gurin mahaifinki idan sun karb'eki to idan basu karb'eki ba kuma ni zan rik'e ki,sannan zamuje gurin mijin naki a sanar dashi halin da kike ciki ba dan ya bada komai ba sai dan ya san akwai jininsa a tare dake ko dan wataran"

Hawaye kawai ke zuba a fuskarta bata fad'an komai.









_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
       *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


_*Fatima Muhammad Ali,sak'onki ya iso gareni da farko dai ina amsa gaisuwarki kuma nagode sosai nima ina sonki da yawa nagode da fatan alkhairi da kika min,kuma nima ina miki fatan alkhairi a duk inda kike😍*_

_'yan group na TASKAR SANAZ dana MRS OMAR da sauran groups dake bibiyar novel d'ina nagode sosai😘_



29

Muhasin haka ya koma yola ya d'ebowa Momma kayan sakawa,sannan ya siyowa Janan kaya ita ma.

Ya koma yola shi, sai dai duk k'arshen sati yana zuwa kaduna duba su yana mutuk'ar tausayin Janan d'in.

        ******

Hawayen daya kasa mak'alewa ne ya samu damar sauka a kuncinsa.

Kallon Raihan yayi ya girgiza kai sannan ya tashi yana neman tafiya tayi saurin cewa "dan Allah Jalal ka tsaya kaji"

"Me zan ji bayan abinda na gama ji yanzu"

"Amma ya kama ta ka saurare ni"

"Lokaci na k'ure min Raihan nafi so naje na kai cigiyar su a kafafan yad'a labarai tun kafin suyi nisa"

"Dan Allah kada ka Ka kai tunda ba b'ata sukayi ba"

"Ni a gurina sun b'ata ne"

"Bazasu ji dad'i ba ina ganin kamar tozarci ne"

Zama yayi yace "to ya kike so nayi?"

"Hak'uri da kuma addu'a"

"Amma meyasa kika min haka Raihan?meyasa tun abin yana d'anye baku fad'amin ba sai da bakin alk'alami ya bushe"

Shiru tayi kawai itama zuciyarta na k'una.

"Ina son Janan kuma na fara sonta had'uwata ta farko da ita,har Janan tayi Aure ban tab'a jin sonta ya ragu a zuciyata ba,na danne kawai saboda na san tayi min nisa,amma meyasa zaku k'i sanar dani halin da take ciki bayan kunsan ita d'in jinin jikina ce"

"So kuma?" Ta fad'a lokacin da ta kasa b'oye damuwarta.

"Eh so da kika sani"

Wani irin kishin Janan taji duk da bata kusa da ita.

_Allah ya k'ara nisantar da Janan yasa karta ji sha'awar dawowa Kaduna_ ta fad'a a zuciyarta yayinda ta rik'a jin haushin kanta da tayi mata differing.

"Ki min alk'awari Raihan" ta tsinkayi maganarsa kamar daga sama.

"Ina jin ka"

"Dan Allah ina son ki tayani addu'a Allah ya dawo min da Janan a cikin kwanakin nan"

"Insha Allah"

"Nagode! Yanzu zanje gidan su Lubna"

"Zan raka ka"

"A'a kiyi zamanki ba kince lecture zaku shiga ba"

Shiru tayi shi kuma yayi tafiyarsa.
*
Suna zaune a falon gidansu Lubna.

Ta sunkuyaar da kanta kawai tana kuka dan da taji maganar Janan sai tayi hawaye.

"Ki daina kukan ya isa haka"

'Dago kai tayi ta kalleshi tace "wallahi tun sanda na ganka da Janan na san kunyi mugun dacewa amma yadda Janan ta d'auki son Aliyu ta lik'awa zuciyarta shiyasa kawai na kasa furtawa,mun maka laifi amma kayi hak'uri"

"Bakomai fatana Allah ya dawo mana dasu lafiya"

"Ameen" ta amsa tana goge hawayen fuskarta.

          ********

_*Bayan wata guda*_

Suna tsaye jikin mota,Muhasin na gefe tare da doctor yana masa bayani akan magungunan da za'a saya.

Jikinta duk yayi sanyi saboda sam bata k'aunar k'ara had'uwa da Aliyu.

Momma ta gane hakan,dan haka ta janyo hannunta tace "karki damu Janan ki rik'a kwantar da hankalinki kinji"

Kai kawai ta d'aga,Muhasin ya dawo ya shiga motar suka tafi.

Sai da suka fara zuwa k'aton chemists suka siya magungunan sannan momma tace Janan tayi musu kwatancen gidan.

Har k'ofar gidan sukaje a bud'e ma k'ofar take dan haka suka kutsa kai suka shiga.

A k'ofar Babban falo sukayi knocking, sun d'an juma kafin a bud'e k'ofar.

Ummi ce ta fito tana kallon su a shek'e.

Kamar bazata matsa ba sai kuma kawai ta matsa tace "Ku shigo"

Bayan sun zazzauna ita kuma Ummi ta haye sama.

Sai jin muryar Umma sukayi tana fad'in "uban me ta dawo yi gidannan?"

Duk Kansu suka kalli gurin.
Tana gaba Aliyu da Ummi na biye da ita.

"Tashi ki fita matsiyaciya" ta fara fuzgar Janan.
Momma tayi saurin cewa "baiwar Allah dakata mana"

Juyowa tayi tana fad'in "ke kuma a suwa"

"Dakata iya haka kada ki yarda kici mutuncin uwata ba tare da kinsan matsayinmu ba"

Sai kuma tayi shiru,shi kuma ya kalli Aliyu ya cigaba da fad'in "dama munzo mu sanar da kai matarka na d'auke da cikinka ba wani abu muke buk'ata ba kawai ina son kasan akwai jininka ko nan gaba"

"Karya kuke wallahi, mu zakuyi wa d'anmu sharri"

Ta juya ta kalli Aliyu tace "ko gaskiya ne?"

Jikinsa a sanyaye ya girgiza kai.
"Naga kayi sanyi?" Umma ta k'ara tuhumarshi.

_idan ban k'aryata hakan ba tabbas komai zai iya faruwa._

Cikin d'aga murya yace "a gidan ubanwa zaki d'ebo cikin shege ki lik'a min"

Janan da tun lokacin da aka fara maganar ta sunkuyar da kanta tana kuka sai a lokacin ta d'agoshi ta kalli Aliyu
"Kaji tsoron Allah ka fad'i gaskiya karka shegantamin d'a Aliyu dan Allah ka fitar dani daga zargi"

"Dalla rufamin baki tanan kika b'ullo kuma?to wallahi ranki zaiyi mummunan b'aci idan har kika cigaba da kiran shegen cikinki a matsayin nawa danni ban tab'a had'a shimfid'a dake ba"

Muhasin ya kalleshi yace "ka yarda muje kotu kuyi li'ani?"

"Muyi mana wayake tsoro" ya mayar cikin b'acin rai.

Momma kuwa sai doka salati take tana hawaye.

Janan ta mik'e tsaye cikin kuka tace "ba sai anyi ba saboda bani da tabbas amma ni na san cikinka ne,amma ka sani ko wata rana kada ka nemi d'anka, ka k'addara baka da d'a dani"

"Dama ai babu,dalla ki fita bana son ganinki"

Da sauri ta wuce ta fita,Momma ta sake kallonsu kawai ta fashe da kuka tace "Allah ya saka miki Janan"

Muhasin kuwa kasa cewa komai yayi saboda yadda zuciyarsa ke tafasa komai zai Iya faruwa.

A farfajiyar gidan jiri ya d'auki Janan ta zube.






*_Masoya sai kun yi min hak'uri dan kwana biyun nan ina busy, kuyi manage da wannan_*












_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
       *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicates 2 Mrs Xerks & Safnah luv```

*_Kwana biyu kunjini shiru,wlh 'yata da cousin d'ina aka kwantar a asibiti_*
   _muna barar addu'arku_


_Wannan Shafin sadaukarwa ne gareku masoyana😍na san kun matsu nayi typing._



30

Da sauri Muhasin ya k'arasa ya d'agata yayi waje Momma na biye dashi.

Ganin idon Aliyu duk abinda ya faru, ji yayi kamar ya shak'e Muhasin saboda tsananin kishin Janan da yake.

           **********

Ta d'an goge guntun hawayenta bayan ta ji irin tarbar da iyalan Momma suka mata.

"Ba wai shawararku nake nema ba,na gabatar da ita ne a matsayin 'yata a gareku dan karku sakata a wani matsayi na daban daga yau matsayinku d'aya da ita a gidannan" Momma ta fad'a rai a b'ace.

"Wallahi ba'a isa a kawo mana wata haka kurum ace ta zama 'yar uwarmu" Zainab ta fad'a tare da tashi ta wuce ta bar falon.

Muktar ma tashi yayi yana gunguni ya bi bayan Zainab.

Momma cikin b'acin rai ta kalli Humaira tace "kema rashin kunyar zaki min?"

Itama Humaira ranta a b'ace take kallon Momma tana fad'in "taya zaki d'akko mutum kawai kice wai zata zauna a gidan nan"

"To gidanku ne ko gidana?"

Babban d'anta Umar yayi saurin cewa "gidanmu ne Momma saboda muke da gadon gidannan"

Baki kawai ta saki tana kallonsa cike da mamaki.

Haka rayuwar gidan Momma take duk kanin 'ya'yanta sun rainata Muhasin ne kad'ai ya fita zakka a cikinsu hakan ya samo asalina ga irin gatan da tayi musu fiya da misali.

Umar shine babba,yana da mata  da 'ya'ya biyu kuma a cikin gidan part d'insa yake.
Muhasin shine na biyu baiyi aure ba amma dai yana shirin yi,sai Muktar saurayi yana l3,Zainab tana l1 sai Humaira itace Auta tana Ss1.

Mahaifinsu ya dad'e da rasuwa tun Humaira na 'yar shekara 3 a duniya Momma itace gatansu babu abinda suke nema su rasa daga gareta tun mahaifinsu na da rai yakan ce mata wannan ba gata bane tana lalatasu ne kawai,amma sam bata yarda.

         ********

Momma na zaune a gefen gadon ta zuba uban tagumi,Janan na gefenta tana mamakin yadda akayi yaranta har suka rainata haka.

Zamewa tayi k'asa ta durk'ushe gaban Momma tace
"Ina neman alfarma a gareki"

 'Dago ido tayi ta kalleta tare da janyota tana fad'in "haba Janan taya zaki tsugunna har k'asa dan kina neman alfarma"

Hawayen daya so zubo mata ne tayi saurin mak'aleshi tace "bakomai! Dan Allah ina so ki barni in tafi saboda ki samu zaman lafiya keda yaranki"

"Karki damu Janan ko ki tafi ko karki tafi haka halinsu yake ba fasawa zasuyi ba"

"Amma........"
"Ya isa Janan pls karki damu kinji"

Haka Momma ta jata ta nuna mata d'akin da zata zauna.
'Daki ne daya tsaru da duk wani kaya na bedroom sai toilet a gefe.

Haka rayuwar Janan ta cigaba da tafiya a gidan,Sam bata jin dad'in zama da 'yan gidan idan ba Muhasin da Momma ba.

Haka ta daure ta cigaba da renon cikinta cikin k'unci da b'acin rai.

*_6 Months later_*

Tana zaune akan kujera tana danna remote tana neman canza tasha kawai taji an warce remote d'in.

Da sauri ta d'ago kai ta kalleta tace "lafiya?"

"Oh tambayata kikeyi ma,bak'ar munafuka kawai"

A hankali ta mik'e tsaye saboda cikin jikinta ya fara tsufa.

Kallon Zainab tayi tace "ya isheki haka dan na gaji da rashin mutumcin da kuke min"

"Da kin gaji da kin bar gidanmu saboda ba k'aunarki muke ba kuma ba k'aunar ganinki a gidanmu muke yi ba"

"To ai ba ku kuka kawoni gidan ba dan haka baku isa ku kureni ba babu yacce kuka iya dani"

"Oh keda kanki kike fad'ar haka?"

Da sauri ta juya ta kalli wanda yayi maganar.

Taku kad'an ya k'araso dashi gurinta,wani mari daya zabga mata yasa ta tsungunna har k'asa hannunta rik'e da kuncinta.

Umar ya ja hannunta ya d'agata yace "ki gaggauta barin gidan nan tunda bana ubanki bane ko dan kinga ban d'auki mataki akanki ba 'yar matsiyaci kawai"

Kallonshi tayi lokaci guda idanunta suka koma jajir,a gigice ta juya ta d'auki glass cup d'in dake kan center table ta fasa sannan ta nufo inda Umar yake gadan gadan zata caka masa.

Zainab ta d'ora hannu aka ta k'walla ihu,shi kansa Umar kawai d'ora hannu yayi aka ya runtse idanunsa.

"Janan!" Ya kira sunan a gigice,itama a gigice ta juya ta kalli Muhasin.

Da sauri ya k'arasa gurin ya rik'e kwalbar a hankali.
"Karki aikata kisan kai Janan"
Sakar masa tayi kawai ta durk'ushe a gurin ta rusa kuka.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,Abba kana k'ark'ashin k'asa ana zagar min kai,Abba koda baka nan bazan yarda sunanka ya wulak'anta ba"

Kuka take sosai a fili,duk kansu sai da jikinsu yayi sanyi musamman shi Umar duk sai yaji ya kunyata.

Muhasin ya durk'usa gabanta yana fad'in "dan Allah kiyi hak'uri Janan ya isa haka"

Girgiza kai take tana kallonsa tace "bansan me nayiwa Mameey ba da har zasu tafi su barni tsawon watannin nan a koda yaushe ina nemansu amma basu nemana,ko dai na tafka babban zunubi shiyasa Allah yake jarabtata da wannan abubuwan"

"Yau zan bar gidan nan zan bar muku gida in tafi can wani gurin in k'arasa rayuwata,zan dogara da Allah da kuma kaina,bazan k'ara zama k'ark'ashin inuwar wani ba bare har a zagar min Abbana,komai iyayena suka min bazan tab'a yarda su wulak'anta ba"

Jin haka yasa Muhasin ya d'aga waya ya kira Momma yace ta dawo gida ba lafiya.

Zainab da Umar kuwa sai sukaji tamkar maganar da Janan ta fad'a dasu take.

_yarinyar k'arama har ta san ta d'auki mataki akan dan an zagi iyayenta zagin ma ba wani na azo a gani ba,mu kuma da muke kallon idon Momma muci mata mutunci fa?matar da tayi d'awainiya damu tun muna ciki dole mu gyara halayenmu_ Umar ya fad'a a zuciyarshi.

Zainab ma a zuciyarta tace _Ashe haka soyayyar iyaye take?insha Allah daga yau na daina yima Momma rashin kunya._


 Suna nan a falon sunyi cirko-cirko a haka Momma tazo ta same su.

Zainab ta ruga gurinta ta rungumeta sai kuma ta fashe da kuka.

Jikin Momma gaba d'aya yayi sanyi,yaushe rabonda Zainab tayi hugging d'inta,tabbas ba lafiya ba.

Kallon Muhasin tayi tace masa "Ina Janan?"

Jikinsa a sanyaye yace "tana d'akinta"

Kallon Zainab tayi da har lokacin bata daina kuka ba tace "meya faru?lafiya?"

'Dago idanunta tayi da suke zubda hawaye tace "ki yafe min Momma na tuba bazan sake musu dake ba,bazan sake yin abinda bakyaso ba"

Kallon Umar da Muhasin tayi Wanda sun kasa zama ma.

Janyo hannun Zainab tayi suka k'arasa kan kujera suka zauna.

"Muhasin ka fad'a min meke faruwa?ka kirani a waya ina gurin aiki ka d'agamin hankali"

Umar ne yayi saurin durk'usawa k'asa yace "Momma ki yafe mana laifukan da muka miki,hak'ik'a yau abinda Janan tayi ya mutuk'ar d'aga mana hankali,ace babba dani na ajje yara amma bana daraja tawa mahaifiyar?idan yarana suka girma taya zasu daraja ni?"

Kallon mamaki kawai Momma take binsu dashi,shi kansa Muhasin mamaki yake.

"Shin mafarki nake ko gaskiya" Momma ta furta cikin raunanniyar murya.

"Momma ba mafarki kike ba,mune a zahiri muke neman yafiyarki" Zainab ta fad'a

Kallon Muhasin tayi tace "ka fad'a min gaskiya meke faruwa?"

Zama yayi a k'asa ya bata labarin duk abinda ya faru.

Da sauri ta tashi ta nufi d'akin Janan suka rufa mata baya.

Tana tura k'ofar ta hango Janan d'in kwance a tsakiyar gado ta saka hannayenta ta rufe fuska.

Har kan gadon Momma ta hau ta cire  hannun nata daga fuska.

A hankali ta bud'e idanunta hawaye har lokacin bai daina zuba a cikin su ba.

Da sauri ta tashi zaune bakinta na rawa tace "bana gani"

"Bakya gani kamar ya?" Momma tayi tambayar tana d'an jijjigata.

"Na shiga uku dan Allah ku taimakeni wallahi bana ganinku bana ganin komai sai duhu"

Muhasin yayi saurin hayowa kan gadon yace "kin ganmu fa ki k'ara kallonmu sosai"

Idonta a kan Momma yake saidai bata iya ganin komai.

"Shikenan bazan cika ma Abba burinsa ba bazan sake ganin Mameey da 'yan uwana ba,bazan ga Salman ba bazan ga abinda zan Haifa ba,ya Allah ka yafe min idan wani laifin nayi kake hukuntani da haka"

Wasa-wasa har farfajiyar gidan suka fito da ita amma bata gani.

Lokacin ma Humaira ta dawo daga skul abin ya bata mamaki ta kama hannun Janan har wajen rumfa tace "kin gane a inda muke"

Girgiza kai tayi alamar a'a.

A gurin ta sunkuya ta cigaba da hawaye Momma ta rungumeta tana kuka itama.

Dukkanin iyalan Momma hatta matar Umar da tafi kowa wulak'anta Janan sai da tayi mata hawaye lokacin da Momma na basu labarin rayuwarta.

_Asibiti_

Tana kwance a kan gadon asibiti idanunta nannad'e da bandage bama zasu gane bacci take ko idonta biyu ba.

Muktar ya goge hawayen idonsa yace "Momma bana son baiwar Allah nan ta mutu ban nemi gafarar ta ba,wallahi mun azabtar da ita sosai a cikin gidannan musamman idan kun tafi wajen aiki keda Muhasin, amma bata tab'a ko nunawa ba bare ta fad'a muku,hatta Yaya Umar haka zaisa taje gidanshi tayiwa matarsa duk wani aikin gida"

Humaira ta kalli Momma tace "Allah ya sani ta girmeni amma ni babu abinda yake had'ani da ita sai gori da hantara,wallahi har lemo na tab'a watsa mata lokacin da friends d'ina suka zo itama ta fito falo"

Zainab kuwa kanta a k'asa tana hawaye dan ta san ita nata yafi na kowa bama zata iya magana ba.

Momma tasa hannu ta goge hawayenta tare da kallon Janan cikin tsananin tausayinta.

Muhasin ya kalli inda Janan ke kwance yace "Wallahi Momma har yanzu abinda likita ya fad'a na kasa gaskata haka,wai dama da gaske kuka yana janyo makanta"

"Gaskiya ne yawan kuka yana sa makanta"

"Ya Allah ya bata lafiya ya raba ta da wannan azababben ciwo"

Duk kansu sukace "ameen".

            **********

Mommy ta kalli d'an nata cikin jindad'i tace "tunda har Allah yasa ka dawo gida bazaka sake komawa ka barni ba"

Yayi murmushi ya d'an shafa kansa yace "Mommy ga yarima a kusa dake"

"Shima da yaga ka gujeni sai ya gudu Kaduna"

Jalal yayi murmushi har sai da hak'oransa suka bayyana,ya kalli Adnan yace "ina fa zuwa duk k'arshen sati kuma nama kusa gama karatun"

"Kai yarima duk karatun da kayi bai isa ba?"

"Wlh a gurin aiki aka buk'aci mu kawo diploma certificate dole na tafi nayi"

"Eh hakane dole kayi tunda ance Ku kawo"

Mommy tayi dariya tace "oh ka dawo kenan shine zaka fara shigar masa ni bani da dangi ko"

"A'a Mommy mu mun isa muce haka"

"Kunyi yawa ma gashi tun yanzu har ka fara nuna min wariya"

Dariya yayi tare da fad'in afuwan Mommy"

"Nak'i yawon"

Dukkansu suka saka dariya cikin farin ciki da annashuwa.

"Ya bayanin aure Adnan?"
Mommy ta watso masa tambayar.

Kallon Jalal yayi suka had'a ido sannan ya dawo da kallon sa gurin Mommy.

Shiru yayi baice komai ba,itama ta kafeshi da idanu kawai.

"Kayi min shiru kana kallona,Jalal ya fito da mata kai muke jira sannan a saka rana gaba d'aya"

"Mommy ni kuma?"
"Eh mana ai na fad'a maka tun kana can"

"Mommy kiyi hak'uri ban shirya yin wani auren ba a halin yanzu babu macen da take burgeni bare har na aureta"

"Ni fa na saka maka doka Adnan" ta fad'a rai a b'ace

"Kiyi hak'uri kawai Mommy" yana neman barin gurin Jalal yayi saurin rik'eshi.

Ita kuwa ranta a b'ace ta tashi tayi side d'inta.

Jalal ya maido kallonshi ga Adnan yace "meyasa kayi haka Adnan?"

Murmushi yayi mai had'e da k'walla yace "bazan iya yi mata k'arya ba Yarima nafiso na fito fili na fad'i gaskiya dan bana son sake tsoma kaina a wata masifar"

"Adnan wannan ciwo da kake dashi bazai hanaka yin Aure ba ka rayu da matarka harma ku samu zuri'a"

"Wane Aure kenan?auren wadda take da cuta irin tawa bashine kwanciyar hankalina ba,nafiso na rayu da Mommy harna mutu a gabanta"

"Ka daina zancen mutuwa haba Adnan bafa kai kad'ai ne keda wannan larurar ba"

"Amma kaina na sani ko saboda bilkis ta zalunceni bazan sake aure ba,zan cigaba da bawa Mommy hak'uri akan hakan"

"Shikenan Allah yasa haka shine mafi alkhairi"

"Ameen nagode da fahimtata da kayi,ya sunan surukar tawa?"

"Raihan a poly take karatu"

"Okay amma dai idan ka aureta zaka bari ta cigaba da karatu ko?"

"Eh sosai ma kasan ni d'in d'an boko ne"

Dariya Adnan yayi tare da fad'in "yaushe aka saka bikin?"

"Su baffa sunje sun kai komai har lefe kai kawai ake jira Mommy tana son a had'a da naka"

"Oh kenan su can basu matsa ba"

"Eh baffa yace zai musu waya ya sanar dasu date d'in,naji dai Mommy tace bazai wuce 1 month ba tunda nace mata anan gida zan zauna dan har an gyara part d'ina da naka"

"Gidanka fa"

"Zan zuba 'yan haya kanaji Mommy na complain wai bamu son zama a gurinta"

"Hakan ma yayi Allah ya sanya alkhairi"

"Ameen bros"

"Tashi muje ka rakani rarrashin sweet Mom kaga tayi fushi dani"

Dukkansu suka saka dariya.








_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
        🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv ```



```Sadiya Mrs Xerks d'ita ni kad'ai😆.
kin zama tamkar 'yar uwa a gareni,u alwayx luv me nd nvr hurt me.```
_Kin zamo jinin jikina😍_


_wannan shafin nakine Zarah Darma,nagode da kulawarki a gareni😍_



31

Satinta guda bata ganin komai.

Har sai da aka yi mata aikin ido sannan aka d'orata kan magani.

Yau ma kamar kullum k'arfe 7:00am Zainab suka shigo ita da Humaira,Humaira na sanye da uniform d'inta dama sai tazo take wucewa skul.

Bayan sun gaida Momma suka zauna a gefen gadon Humaira ta kalli Janan tace "Aunty sannu ya jikin?"

Murmushi Janan tayi ta kalleta tace "da sauk'i"

"Momma naga kamar tana harararmu" Zainab tayi maganar.

Momma ta d'anyi murmushi sannan tace "Zainab idonta ne ya koma haka,harara garke(kallon ruduwa) idan tana kallon ki zakiyi tunanin gefe take kallo,idan tana kallon gefe kuma zakiyi tunanin ke take kallo ko kuma wani lokacin idan tana kallonki zakiyi tunanin harararki take"

"Momma shikenan idanunta ya koma haka?"

"Eh mana"

Kallonta Zainab tayi tace mata "sannu Janan Allah ya k'ara lafiya"

"Ameen Zee" ta amsa tana murmushi.

Sun dad'e suna hira har su Muhasin suka zo za'a mayarda Zainab gida itama ta shirya Humaira kuma a kaita skul.

Zasu fita kenan Janan tace "yawwa Humaira dan Allah ki sanmin takarda da biro mana"

"Okay" ta bud'e skul bag ta d'akko note buk da pen ta mik'a mata.

"Ki barshi a gurinki idan na dawo na karb'a.

" to nagode sosai "
Murmushi tayi tace "karki damu".

_5hrs later_

" Janan! Janan!! To ina ta fita kuma"

Bud'e toilet tayi taga babu kowa,ta fita har farfajiyar asibitin bata ganta ba sai tayi tunanin ko ta gaji da zaman guri d'aya shiyasa ta fita ta d'an zagaya.

Zama tayi ta cigaba da duba magangunan sannan ta sake gyara gadon.

Kusan awa d'aya da rabi Janan d'in bata dawo ba dan haka ta tashi da sauri ta sake fita tana dubawa.

K'walla ce ta taru a k'asan idanunta ta fara fad'in "Janan dan Allah karki gudu ki barmu,ina sonki Janan kin shiga ranmu da yawa"

Waya ta d'akko ta kira Muhasin ta sanar dashi duk abinda ke faruwa.

Cikin minti talatin ya iso asabitin
"Momma wai ya akai ta fita baki sani ba?"

"Wallahi naje karb'o sauran magunguna a pharmacy kafin in dawo naga babu kowa"

"Mu tambayi masu gadi ko sun ganta tunda asibitin ba wani girma ne dashi ba kuma gate d'in shiga shine na fit.............."
Bai k'arasa maganar ba ya hango 'yar takarda a gefen gadon ta d'ora biron da littafin a gefe.

Da sauri ya k'arasa ya d'auki takardar ya ware ta ya fara karantawa a fili.

_Momma da Yaya Muhasin nagode sosai da karamcin da kuka nuna min,Momma kiyi hak'uri zanyi kewarki da yawa amma babu yadda na iya zama bai kamani ba,zan tafi farautar hak'inmu sannan zan rik'e kaina iya wuya iya dad'i bazan k'ara zama inuwar da ba tawa ba,Yaya Muhasin ina maka fatan samun mace tagari a rayuwarka,ina fatan zaku kasance cikin yi min fatan alkhairi a koda yaushe nima zan cigaba da yi muku,dan Allah karku nemeni dan bazaku ganni ba tunda ba b'ata nayi ba,ina fatan Allah ya k'ara had'a fuskokinmu da alkhairi ameen._

"Shikenan! Ashe dama abinda zata rubuta kenan shiyasa ta karb'i paper a hannun Humaira" Momma ta fad'a lokacin da hawaye suka sauka a idonta.

"Allah sarki Janan Allah ya kare mana ke a duk inda kika shiga a fad'in duniyarnan"
Muhasin ya furta

Momma sunkuyawa tayi kan gado tana kuka na tausayin Janan "yarinya k'arama da batafi shekara 17 a duniya ba" ta furta tana hawaye.

"Momma nayi miki alk'awarin duk sanda Janan ta dawo kona ganta bata da wani miji kamar ni koda kuwa da matana a lokacin"

"Nagode Muhasin kaima kayi k'ok'ari ai,saboda sanadin Janan 'ya'yana sun shiryu ina son zama da Janan"

         *********
Janan ta sadda kanta tana hawaye lokacin da motarsu ta tashi daga Yola zuwa kano.

Kusan awa d'aya suna tafiya amma bata d'ago kai ba.

Matar dake gefenta ta dafa kafad'arta tace "baiwar Allah meyayi zafi haka tun d'azu kina kuka ko gajiya bakyayi ga da alamu tsohon ciki ne dake"

'Dago kai tayi ta kalli matar tace "karki damu da kukan da nake saboda mutane da dama irinki sun rarrasheni amma nak'i dainawa,hawaye ne ya jawo k'wayar idona ta canza daga lafiya zuwa akasinta,idona ya koma harara garke duk a sanadin kuka,kuka ya fiye min dad'i fiye da komai a rayuwa"

Ai kuwa wannan furucin nata yaja mata cece kuce a cikin mota kowa na fad'in albarkacin bakinsa.

Duk tana jinsu amma bata ce komai ba har sai da wani yayi maganar da tayi mata zafi sosai.
"Aikuwa ya kamata a kaiki gwajin k'wak'walwa domin mara hankali da tunanin ne kad'ai zaice kuka nada dad'i"

Bata ko kalli inda yake ba cikin muryar kuka tace "hakane bani da hankali saboda ko kaine aka yiwa abinda aka min zaka haukace,idan na haihu d'ana ya girma wa zan nuna masa a matsayin mahaifi?bayan ban tab'a aikata alfasha ba kuma da aure na samu cikin amma ina ji ina gani mahaifinsa yace ba d'anshi bane kawai saboda son zuciya da rud'in duniya,ka gaya min idan nayi kuskure da nace kuka yafiye min komai"

Nan ma hayaniya aka fara ana ta zaginsa,wasu na cewa insha Allahu zaiga sakayya wasu na cewa Allah yasa karya k'ara haihuwa a rayuwarsa kuma idan yazo neman d'ansa karta bashi.

Ita dai kukanta take bata k'ara saurarar kowa a cikin su ba.

Matar ta d'ago kanta ta d'ora kan cinyarta tana jijjiga ta.

Sun sha tafiya mai nisa har saida taga kamar baza suje kano ba saboda bata tab'a yin tafiya mai nisan haka a mota ba,ko yola da sukaje da Momma a motar gidane bataji wahala sosai ba,yanzu kuwa ga tsohon ciki.

Kusan k'arfe goma na dare suka sauka a kano.

Daga ita sai hijabin jikinta ta sauka ta d'an matsa daga gefe can.

Matar tazo ta tsaya kusa da ita tace "bara mijina yazo sai mu rage miki hanya ko"

Ta kalleta tana murmushin k'arfin hali tace "karki damu zan hau napep sauri nake"

"Dan Allah ki bani number ki muna gaisawa"

Ta sake yin murmushi tace "bani da waya"

"Toooo! Ai kuwa ina son muna gaisawa kawai naji ina tausayinki,dan Allah ki bani address d'inki tunda kince baki da waya"

"Eh to ki bani naki in Allah yayi da rabon zamu sake gaisawa sai na nemeki"

Da sauri ta bud'e jaka ta d'akko compliment card ta mik'a mata.

"Idan ba damuwa ki haskamin in gani"

Ba musu matar ta kunna torch light d'in wayarta ta haska card d'in.

"Okay na gani gashi"
"a'a to ki rik'e mana"
"A'a na rik'eshi a brain d'ina idan na karb'a zan iya yardawa"

"Dan Allah idan kin samu lokaci ki ziyarceni,sunana Hajara kefa?"

"Sunana Janan Baku da damuwa zan ziyarceki insha Allah"

"Nagode Janan"
"Nima nagode"

Napep ta tara ta hau tana d'aga mata hannu.

"Hajiya ina muka nifa?" Mai napep yayi tambayar.

"Tasha zaka kaini inda zan hau motar katsina"

"To ai dare yayi hajiya ki bari sai da safe saboda motar dare bata da dad'i ga mace musamman ke dana ganki da tsohon ciki"

"Okay ka kaini tashar sai in kwana a can saboda ina son zuwa katsina kafin fitowar rana"

"Hajiya ki fad'i dai unguwar da zan kaiki ki kwana tasha ai dandalin 'yan shaye-shayene akwai had'ari ko baki da 'yan'uwa anan?"

"Nan nace ka kaini Malam ba fa kyauta zaka kaini ba kudinka zan baka"

"Allah ya huci zuciyarki ban san abin zai b'ata miki rai ba"

Shiru tayi bata sake ce masa komai ba,ya kaita har tasha ta sinto kudi a gefen zaninta ta bashi.

Tana shiga kuwa da warin taba ta fara arba,wani amai ne ya taho mata tayi saurin toshe baki da hanci ta wuce.

Can baya inda ba mutane taje ta shimfid'a d'ankwalinta ta kwanta ta cigaba da kuka k'asa k'asa.

Kusan awarta biyu a gun taji ana fad'in "babaaa ga mutanenmu anan"

Da sauri ta tashi zaune tana kallon su duk sun tsaya mata a ka.

"Ke taso nan"

Bakinta na rawa tace "dan Allah kuyi hak'uri"

"Ai ke zamu bawa hak'uri dan baza muga kayanmu mu k'yale ba"

"Duk wanda ya tab'ata sai ya bak'unci lahira"

Duk suka juya suka kalleshi,ganin mutumin ne yasa suka fara k'ok'arin guduwa, ya nuna su da bindiga yace "Wanda kuma ya k'ara motsawa saina fasa k'wak'walwarsa"

Hannu suka d'aga suna fad'in "yallab'ai ayi hak'uri wannan fa yawa ne ko mun shiga cell zamu fito"
A haka sauran 'yan sandan suka kamasu  suka shigar dasu mota.

Shi kuma ya tsugunna a gabanta ya k'ura mata ido,tayi saurin sauke k'wayar idonta k'asa.

"Ai na fad'a miki nan gurin akwai had'ari kika k'i yarda"

'Dago idanunta tayi tana kallonshi tana tunanin waye shi yaushe ya fad'a mata hakan.

"Nine mai napep d'in daya kayo ki nan d'azu"

Ta d'an zare ido cike da tsoro mai had'e da mamaki.

Murmushi yayi yace "ni d'an sanda ne mai rik'e da muk'amin _dsp_ kullum da dare misalin k'arfe tara na kan zama d'an adaidaita saboda shine hanya mafi sauk'i da nake kama masu laifi.

"lokacin Dana kawo ki nan hankalina yak'i kwanciya musamman dana ganki da ciki,kai tsaye na nufi gida na sanarwa mamana sai tace in dawo inga halin da kike ciki idan har da taimako to in taimaka miki,a lokacin na tafi gida na nayi wanka na saka uniform sannan na kira yarana muka taho sai gashi na tarar dake a wannan hali"

Shiru tayi bata ce komai ba,ya sake fad'in "ki tashi muje gida ki kwanta da safe sai a kawo ki tasha"

Tayi saurin girgiza kai tace "a'a nagode ka barshi kawai"

"Umarnin mamana ne dan Allah karki musa wallahi mu ba macuta bane"

Da k'yar ya lallab'eta suka tafi gidan.

Suna shiga falo Maman nashi ta rufe littafin hannunta tana fad'in "da fatan dai komai lafiya Namijin"

Murmushi yayi yana fad'in "Alhamdulillah Mammy gata na kawo ta ta kwana anan Kausar sai ta kwana a d'akinki ko"

"Eh Yaya"

Da sauri 'yan matan suka taso suka rik'eta.

Jidda tace "sannunki ya sunanki?"

Bata amsa ba sai da ta gaida Mammy sannan ta zauna a k'asa.

"Ki tashi ki zauna kan kujera" laila ta fad'a.

Kausar tace "dan Allah ki zauna"

Sai da Mammy ta saka baki sannan ta zauna dan duk a d'arare take.

Kusan minti talatin suna hira amma ita bayan gaisuwa da gabatar da sunanta babu abinda ta sake cewa.

Ja'afar ne ya tashi ya k'arasa gaban Mammy ya durk'usa yace "Mammy zan wuce gida ki samin albarka"

Kanshi ta dafa tace "Allah ya albarkaci rayuwarka ya baka sa'a a duk inda kake ya kare min kai Namijin duniya"

"Ameen Mammyna nagode"

Ya tashi zai wuce sukayi masa sallama tare da fad'in ya gaida Aunty farha(matarshi).

Rayuwar tasu sai tayi matuk'ar burge Janan.

_*Washe gari*_

Ta gama shirinta tsaf suka bata kaya ta saka amma tak'i karb'a ta mayar da nata.

Mammy tace "da munsan bazaki karb'i wasu ba da an wanke miki"

"Babu komai hakan ma nagode"

"Da fatan zaki rik'e zamunci dan yanzu mun zama d'aya"

"Insha Allah"

"Idan kin haihu ki sanar damu wlh zamuzo har katsina"

"Da iznin Allah"

"Zan rubuta miki numbers d'inmu a paper tunda kince wayarki ta fad'i a mota kuma an kira a kashe" kausar tayi maganar

"Okay ba damuwa nagode"

Suka rubuta mata ta karb'a a lokacin ta haddace number Jidda dan itace babu wahala,da zumar tana fita ta yaga takardar kawai.

A falo suka tarar da Ja'afar a zaune ya hard'e k'afa ransa a b'ace.

"Lafiya kuwa?" Mammy ta tambayeshi.

"Mammy na gaji da halin farha daga bata labari shikenan ta d'aga hankalinta wallahi ko runtsawa bata barni nayi ba"

"Ka kai Janan tasha ka dawo sai muyi maganar"

Tashi yayi ya fita suka bishi.

Suna cikin tafiya tace masa "dan Allah kayi hak'uri ka daina kai matarka k'ara gurin iyayenka saboda zaka ja mata k'iyayya a gurinsu"

"Da kinsan irin laifukan da take min ina k'yaleta da baki ce haka ba,sai kace ba ita ta rik'a nace min ba har na aureta"

Murmushi tayi mai had'e da hawaye tace "wannan shine abinda kullum mijina yake fad'a wanda ban d'auka son da nake masa zai zama k'iyayya ba dan Allah ka sassauta ranka akan matarka"

Ganin hawaye a fuskarta yasa yace "shikenan na d'auki shawararki na daina insha Allahu"

Har tasha ya kaita ya biya kud'in mota sannan ya mik'o mata 5k yace tayi tsaraba tace a'a da k'yar sai da mutane suka saka baki ta karb'a tayi godiya"

Sai da har motarsu ta tashi sannan ya juya ya tafi.

Yana komawa gida ya tarar dasu a zaune sunyi zuru-zuru.

"Ya naganku wani iri" Ja'afar ya tambaya bayan ya zauna.

"Wallahi duk kewar baiwar Allah nan nake da alama akwai damuwa a tattare da ita dan kausar tace data tashi tsakar dare ma ta ganta a zaune tayi tagumi"

"Nima na fuskanci tana da damuwa Mammy amma kinga bazai yuwu mu tambayeta ba bayan taimakon gurin kwana muka mata amma wallahi a raina ta kwana"

"Yaya ka duba fa ka ganta 'yar k'arama da ciki anya kuwa ba cikin shege tayi ba shine ta gudu daga gidan iyayenta?" Laila tayi maganar.

"Gaskiya nima ina tunanin haka" Jidda ma ta fad'a.

"Tace min tana da miji amma tana shan wahala a gurinsa"

"Kai ban yarda ba,Namijin dan Allah kabi bayanta ka binciko mana ko wacece ita idan na mu taimaka ne saimu taimaka"

"Insha Allah zanyi bincike akanta dan nima ina tausayinta,Mammy jiyafa daga bawa Farha labari shikenan ta rik'a cimin mutumci wai son Janan d'in nake matar da take da ciki"

"To idan ma ka sota sai me ni wallahi yarinyar ta shiga raina ai tafi Farha"

"Wallahi tana da kirki da shiga rai" Laila tayi maganar.

"Ku dai tayani addu'a Allah yasa na nemota cikin sauk'i"

"Ameen" duk suka amsa.

            *******

Kwananta biyu a katsina cikin ```filin Samji```  tana neman gidan Malam lado amma kowa bai sani ba.

A rariya take kwana dan bata san kowa ba.

Kud'in gurinta kuwa duk ya k'are saboda zarya adaidaita ga abinci ga ruwa ga magani data siya.

A rana ta uku Allah ya bata ikon zuwa gidan,wani bawan Allah ya taimaka ya rakata har k'ofar gidan.

Gidane na jar k'asa da dannin kara amma kuma family house ne irin na k'auye dai da suke.

Cikin sallama ta shiga b'angaren farko da ta gani.

Bayan sun gaisa ne tace musu "dama ance min nan ne gidan Malam lado"

"Eh nan ne nine babban d'ansa, duk iyalansa anan suke"

"Yawwa Alhamdulillah dama gurinsa nazo"

Kallon juna sukayi da matar cike da mamaki ya kalleta  sannan yace "ai Malam ya rasu shekaru uku da suka wuce"

Jikinta a sanyaye tace "Allah sarki Allah yaji k'ansa ya masa rahama"

"Ameen dan son annabi" suka amsa

Ta d'anyi shiru sannan tace "dama nima mahaifina ne da zai rasu yace in nemi gidan Malam lado zai min kwatancen gidan wani alto sarkin gini wanda yake a k'asar Nijar"

"Allah sarki Allah ya gafarta masa"

"Ameen" ta amsa.

Shiru ne ya biyo baya,ganin basu sake magana ba yasa ta sake cewa "idan da wanda ya sanshi dan Allah a kwatanta min"

"Wallahi bamu sani ba da yake yana aiki da yawa da mutanen Nijar amma mu da yake munfi k'arfi a kasuwa ba harkar gini ba"

"Yanzu duk gidannan babu Wanda ya sanshi"

"Eh to muje in tambayi sauran"

Tare sukaje aka tambaya babu wanda ya gane shi hatta mak'ota da yake mu'amula dashi sunce kawai dai sunsan yana zuwa amma basu san inda yake ba tun bayan rasuwar Malam lado bai sake zuwa ba.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga uku ni Janan ya zanyi Abba kayi hak'uri kana ji wai babu wanda ya sanshi"

Zama tayi a k'asa tana rusa kuka tana fad'in ta shiga uku.

Hak'uri sukayi ta bata ta tashi kawai ta tafi dan bata son ganin gidan Malam lado ma.

Tafiya kawai take tana magana tamkar zautacciya.

"Anan zan k'arasa rayuwata to ina zanje duk inda naje ma ba karb'ata za'ai ba Mameey ta gujeni zama zanyi har Allah yayi ikonsa a kaina Aliyu kuwa na san yaci bulus kawai"

Tana tafiya tana ta zantuttuka a haka har ta fita daga unguwar ta fara shiga jeji gidajen unguwar ba yawa sai kango a can k'arshe.










_Sadeey S Adam✍_
🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```



_*Ummi kina burgeni,d way yadda  kike magana akan novel d'in nan na kanyi dariya ko ina cikin fushi😃Ummin Aliyu🤣tnx 4 d support*_



32

A dai dai kangon ta tsaya ta kalli ciki taga babu alamar datti.

Shiga tayi ta lek'a ko ina taga babu alamar 'yan shaye shaye na zuwa gurin.

'Dankwalinta ta cire ta zauna wasu hawayen na zuba a kuncinta.

_Ashe ma 70k d'in da nake tattali har ita sai da akaje banki aka karb'e,Allah ka saka min bazan tab'a yafe wannan zaluncin ba._


_Washe gari_

Bata farka ba sai da taji rana a tsakiyar kanta da yake kangon ba rufi.

Tashi tayi tana murza ido bacci har yanzu bai isheta ba ga uwar yunwa da takeji.

'Dan kwalinta ta d'ora sannan ta fito waje,unguwar tamkar babu mutane.

Zaninta ta kunce ta fiddo 2k d'in data rage mata ta fara tunanin me zata saya kafin wani lokacin.

Gari da suga ta tuno dan suna sha a gidan Aliyu duk da dole ce tasa take sha har yanzu bata saba ba.

Haka tayi ta tafiya a k'asa da k'yar ta samu wani guri ta sayi kofin roba da plate da cokali da buta da dai d'an tsince tsincen da zata buk'ata sai ta sayi gari rabin kwano da suga kwata.

Bayan ta dawo ta tsaya a wata borehole tayi pumping na ruwa a jerrycan(keg) ta tafi dashi.

Ta fara shan garin kawai taji anyi sallama a kangon
Gabanta yayi mummunar fad'uwa da k'yar ta iya amsa sallamar.

Farar dattijuwa ce,gashin girarta ma fari sol ne,fatarta duk ta yak'une saboda tsufa.

Kallonta Janan take har lokacin data samu guri ta zauna.

"Sannu baba"

"Yawwa 'yata sannu,ke kuwa meya kawoki kika zo kika zauna a kangonnan ga tsohon ciki?"

Murmushi tayi mai d'auke da hawaye tace "karki damu Iya nan ma ina jindad'in zama tunda a rufe yake"

"Ina rufuwa bayan sama a bud'e yake ga damuna tana shirin zuwa"

"Karki damu Iya"

"Yarinya ke kuwa meyasa kikayi cikin shege da k'uruciyarki?"

Jin haka ne yasa tayi saurin mik'ewa tsaye ta kalli tsohuwar tace "idan cin mutumci ya kawoki nan ki gaggauta fita,to waima ina ruwanki dani da har kike kiran cikina shege instead of ki tambayi ina mijina,bana son kowa ya sake shigo min rayuwa ki fita ki bani guri"

Tsohuwar ta tashi tana zare ido tana fad'in "ni kike fad'awa haka yarinya?"

"Na fad'a d'in idan har bakija girmanki ba tabbas zanbi ta kanshi in take"

"Shikenan kije zaki gani"

Cikin tsiwa Janan tace "Alkhairi zan gani insha Allahu"

Tsohuwar na fita ta zube ta fara kuka tana fad'in "ka cuceni Aliyu Allah kayi min sakayya".

Haka rayuwarta ta cigaba da tafiya a wannan kango take kwana,tun abinci baya gagararta har yazo yanayi.

Sai ta kwana ta yini bata ci ba,wani lokacin sai dai ta shiga daji ta ciro ganye taci saboda yunwa.

Ta zama k'azamar k'arfi da yaji dan a sati sau d'aya take wanka shima sai dare take d'ora hijabin jikinta tayi sannan idan da hali ta wanke kayanta kafin asuba sun bushe sai ta saka.

Idan har baka santa sosai ba bazaka tab'a gane ita bace.

Tayi bak'i ta rame idanunta sun sake yin zuru-zuru.

Wani lokacin idan ta rasa abinci har restaurant take zuwa wanda suka ci suka rage ayi wawa ita da almajirai.

Idan kuwa taga biredi an yarda lalatacce zata d'auka ta gyara taci.

Rayuwar Janan gaba d'aya ta zama abin tausayi.

Yauma kamar kullum tana zaune da yamma a kangon  lokacin anyi ruwa yayi mata dukan tsiya.

Tana zaune jikin ginin bayan an gama ruwan a fili ta furta " idan banyi mantuwa ba watan haihuwana ya kama,yanzu idan na haihu me zan sawa jaririna a jikinsa?bani da komai sai reza dana sayo gudun ta b'aci bansan tayaya ake yanke cibi ba kar in kashemu fa"

Wata zuciyartata tace _to ya zakiyi Janan mutuwarku itace jindad'in ki tunda kinga mak'otanki ma k'yamatarki suke harda wadda kikaje gidanta ta watsa miki kwata._

"Zan haihu a nan in mutu anan k'ila ma har sai gawarmu ta fara wari sannan a san mun mutu"

Ta cigaba da goge hawayen da kullum kuma ko yaushe sai ta zubar.

        *********

A firgice ya tashi tare da fad'in "inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" ya dafe kai.

Raihan dake jikin mirrow tana makeup tayi saurin ajje form d'in powder ta k'araso gabanshi ta zauna gefen gadon.
"Yarima lafiya"

Shiru kawai yayi yana kallonta,ganin hankalinsa a tashene yasa ta sake fad'ar
"Pls ka fad'a min meke damunka?"

"Mafarki nayi Janan na cikin mawuyacin hali,mafarkin ya mutuk'ar tsorata ni"

Wani abu taji yazo ya tokare mata mak'oshi,ranta a b'ace tace "amma kasan mafarki ba gaskiya bane ko?"

"Hakane amma dole inje inyi sadaka"

Da sauri ya tashi ya fice ta bishi da ido.

"Lallaima guy d'in nan ya rainamin hankali satinmu biyu da Aure har ya fara min zancen wata Janan to wlh dole in yiwa tubk'ar hanci"

Maganarsu da Lubna ce ta fad'o mata a ranar da aka d'aura aurenta da Jalal.

_Raihan idan Janan ta dawo taga kin auri Jalal bazata ji dad'i ba_

_kamarya?Janan ai tayi nisa bazata dawo ba._

_oh haka kike fata?_

_ni bance ba amma ai Janan bata tab'a cewa tana son Jalal ba saboda lokacin da suka fara mutumci dashi ai batayi Aure ba kuma maganar so bata shiga tsakaninsu ba har tayi Aure, ko ta fad'a miki tana son shi?_

_bata fad'a ba amma ai mun sani ko? kuma duk wanda yaga yadda Jalal suke da Janan ai yasan suna son junansu kawai dai sun kasa furtawa ne,sannan Jalal ya fito fili ya fad'a lokacin da Janan ta bar garinnan kin san kuwa bazai tab'a manta Janan ba kuma ba zai tab'a daina Sonta ba._

_matar mutum kabarinsa Allah yayi ni zan aureshi ba ita ba dan Allah bana son irin haka Lubna._

_Allah ya baku zaman lafiya ya huci zuciyarki._

_Ameen_

Ta ja tsoki lokacin data tuna maganar.

"Allah ka k'ara nisanta Janan da ganin Jalal,ba dan na tsaneta ba sai dan kishin da nake akan Yarima Jalal"


Tashi tayi ta fita main parlor ba tare data k'arasa kwalliyar ba.

A zaune ta tarar da Adnan da Mommy suna kallon ball.

"Barka da hutawa Yaya" ta fad'a lokacin data zauna a gefen Mommy tana fad'in "Mommy sannu da hutawa"

"Yawwa 'yata" Mommy ta fad'a cikin jindad'i yau gata ga matar muskilin d'anta Jalal,abinda ta dad'e tana mafarki,dan da gani take kamar Jalal baya da rabon Aure a duniya.

Cikin fara'a Adnan yace "Matar k'anina ya gidan?da fatan babu wata matsala ko?"

"Babu Yaya" ta fad'a cikin k'arfin hali.

Ranar kuwa da fad'a suka k'are da Jalal dan daya dawo tayi masa maganar kada ya sake kawo mata maganar wata Janan tunda itace matarsa ba Janan ba.

Shi kuma yace bazai daina ba,haka tayi zuciya ta bar masa d'akin ta koma falonta ta kwana instead of ta shiga wani bedroom d'in tunda ba d'aya bane amma saboda ta san zai damu shiyasa tayi haka.

Haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya gwanin sha'awa amma fa duk lokacin da yayi mata zancen Janan zasu kwasheta,wani lokacin ma idan yana son yin aiki dan karta takura masa sai ya fara maganar Janan.
Shi abin har mamaki take bashi wai Raihan bata son a ambaci Janan.

Adnan kuwa shima a cikin Abuja ya cigaba da aiki a wani babban kamfani.

        *********

Turo k'ofar yayi da k'arfi har saida ta tsorata ta saki kayan da take ninkewa.

"Lafiya Aliyu?" Ta fad'a tana kallon sa

"Ashe dama baki da mutumci Zuhra?"

"Ni ce bani da Mutumci Aliyu?shin ance maka ni karuwa ce ko an tab'a kamani da wani?"

"Ba'ace ba amma su Umma sunce miki cous cous da miya suke so kin tashi kin dafa jollof d'in macaroni"

Ajje zanin hannunta tayi tace "Aliyu gani nayi kafi son macaroni kuma kai nake Aure ba Umma ba,sannan kitchen ai a bud'e yake meyasa bazasu dafa abinda suke so ba ai ban hanasu ba"

" k'arya kike 'yar matsiyata wadda bata gaji arzik'i ba,kuma dole ki dafa abinda nake so a gidannan"

Fuska ta rufe ta fara kukan k'arya tana fad'in "na gaji da abinda mahaifiyarka take min Aliyu,kullum idan baka nan sai ta zageni wani lokacin harda mari wai tafi son ka zauna daga kai sai ita sai Ummi a gidannan,ni kawai ka sakeni tunda hakane"

A rud'e ya fara bata hak'uri Umma ta saki baki tana kallon su ta ma kasa cewa komai.

Juyowa yayi ya kalli Umma yace "Umma tunda abin hakane kuna dafa abinda kuke so itama tana dafa nata"

"Aliyu ni kake fad'awa haka?kasan kuwa irin rashin mutumcin da yarinyar nan take min?amma kana bin bayanta?"

"To Umma ya zanyi in ba haka ba?"

"Eh lallai ka kyauta zakazo har d'akina ka sameni"

Ta fita fuuuu.

Aliyu ya kalli Zuhra yace "kiyi hak'uri na miki fahimtar baibai"

"Karka damu mijina amma ka fad'a mata bai kamata tana shigo mana d'aki haka ba saboda zata iya tadda mu a wani halin a matsayinta na surukata ai bai dace ba"

"Hakane kiyi hak'uri,itama bara naje na bata hak'uri"

Bata ce komai ba kawai ta bishi da ido.

A zuciyarta tace _Alhaki kwikwiyo ne,ni ba Janan bace,kuma yadda kika raba Janan da Aliyu haka zan rabaki dashi,dan dole a canza muku gida ki barni da mijina in wala_.


         ********

Bud'e idonta tayi taji garin tsit babu ko motsi daya wuce na saurayen gurin,sai kuma taurari dake baje a sama da kuma hasken farin wata.

Ji tayi cikin nata yana k'ara murd'awa,tun tana salati har ta soma k'ara tana kuka.

Babu sarki sai Allah haka tayi ta murk'usu a gurin tanajin motsin cikinta yana yowa k'asa yana komawa.

Hannunta ta dafe da bango d'ayan ta rik'e cikin,sosai take kuka da salati,nishi babu abinda bata yi.

Kusan awa d'aya sannan taji ruwa na fitowa daga gun,ta kalla sosai amma bata gane mene ba.

"Mameey kina ina kizo dan Allah kizo ki taimakeni zan mutu,wayyo na shiga uku na lalace"

A galabaice take fad'in maganganu.

Kusan awa biyu tana ta shan azaba babu alamar haihuwa,tun tana magana har bakin ya daina magana sai maganar zuci kuma,hawayen idanunta sun daina zuba sam.

Ita kad'ai ta san tsananin azabar da take ji.

Can tayi wani yunk'uri ta k'walla uban ihu tayi wani bahagon nishi ai kuwa kukan jariri ya karad'e ko ina.

A galabaice take amma hakan bai hana ta d'auki reza ba tare da tasan ya ake yanke cibi ba kawai ta saita inda ya mata ta yanke.

Jaririn ya k'ara zunduma kuka,tayi sauri d'aukar ruwa a kofi ta tsiyaya a hannu ta fara bashi kenan taji ko ina na juya mata.

Wasu hawaye masu zafi suka sauka a kuncinta.

"Allah ka raya min koma mene na haifa Allah ka bashi ikon tausayi da jink'ai kasa ya k'ato min hak'k'in......."

Bata k'arasa ba ta fara kakari,tayi saurin rik'e k'irjinta,cikin seconds da basu wuce biyar ba har anyi angama.

Anan ta zube babu motsi mini faca-faca ko ina, jariri kuwa sai callara kuka yake cikin jini abin tausayi.







_✍Na ajje alk'alamina dan in huta saboda nima tausayin ya saka hannuna yin sanyi._







_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁


*_by SaNaz deeyah_*👄


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```



*_WASI'KA BU'DA'D'DIYA GAREKU MASOYANA MAKARANTANA._*
*_Gareku masoyana,ina son ku tsaya kuyi tunani akan Aliyu._*

*_Mahaifin Janan yayi abu cikin rashin sani._*
*_shima Aliyu yayi abu cikin rashin sani._*
*_Aliyu ya fara ramuwa ne ta kan Janan saboda sai abin yafi sosa zuciyar mahaifinta,sannan in baku manta ba Aliyu fa bai tab'a son Janan ba sai da mahaifinta ya rasu,in baku manta ba ya aureta ne saboda ya rama abinda aka masa._*
*_sannan duk wanda ya karanta novel d'ina HUZNUL HAYAT yasan Janan bata ga komai ba akan yadda Rabi'at taci wahalar rayuwa kuma ta mutu a wahala,wlh ni kaina akwai page d'in da idan nayi typing nazo yin editing sai nayi hawaye,kuma kirkirarren labari ne amma ina ganinsa tamkar gaske._*
*_ina son readers su gane cewa wahalar da Janan take sha akan abu biyu ne,na farko k'in jin maganar mahaifinta  wanda har yace ya zame hannunsa a kanta(wasu zasu d'auki wannan a k'aramin abu amma babban abu ne),kusan irin abinda ya faru da Sumayya ta littafin MENE AIBUNA,ina son readers su gane cewa su fa iyaye ko yaya sukayi furuci na b'acin rai akan 'ya'yansu wlh musiba ne har gwamma ka lallab'asu a hankali,na biyu kuma son zuciyarta ne yaja mata._*
*_Sannan ni har yanzu fa banga wahalar da Janan kesha ba😂karkuce SaNaz muguwa ce amma kunsan rayuwa babu yadda bata zuwarma mutum._*
*_saboda kar ayi gaba inji an fara SaNaz d'in nan.............🤣tun yanzu ya kama ta ko wacce tayi nazari kafin muje pages na gaba ace bana kyautawa._*



33

_Tafiya take a hankali cikin dajin cikin yanayi mai dad'i da take ji._
_Daji ne mai cike da fulawowi masu kyau da burgewa,farin gida ta hango kyakykyawan gaske,murmushi tayi cikin zumud'i ta k'arasa k'ofar gidan ta saka k'afarta zata shiga kawai taga mutum ya fito sanye da fararen kaya, ta kalleshi tace Abba dama Kaine a wannan babban gida?,murmushi yayi yace eh Jannat,Abba amma ni ina shan wahala kai gaka a cikin jindad'i,Jannat ki koma ki rik'e d'anki ki raineshi har ya girma amma karki yarda ki nuna masa Aliyu ne ubansa ki zauna dashi a matsayin wanda bashi da uba duk runtsi,koma Janan koma ga d'anki._

A firgice ta bud'e idonta,hadarin daya had'u sosai take kalla,ta juya k'wayar idonta ta kalli kangon.
_Abbana ina fatan kana kwance cikin kabarinka cikin jindad'i kamar yadda na gani a mafarkina,ya Allah ka sa haka ameen_ ta furta a zuciyarta.

Sai lokacin tunanin ya dawo mata a hankali ta tashi zaune ta kalli gabanta.

Jaririn na kwance idonsa a bud'e sai mamular leb'ensa yake yana numfashi sama-sama,jini kuwa wani har ya bushe wani kuma yana nan.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta furta lokacin da ta kai hannu ta d'auki jaririn nata.

"Bawan Allah" ta sake furtawa tana hawaye.

Mafarkin da tayi ne take sake tunawa tare da k'ank'ame jaririn data Haifa.

"Sannu yarinya" taji an fad'a.

Da sauri ta d'ago kai ta kalleta,wannan dattijuwarce dai gefenta 'yammata biyu d'aya na rik'e da bokiti da ruwan zafi da robar wanka d'ayar kuma na rik'e da ganyen carbi da  wani bokitin cike da ruwa shima.

Mamaki kawai take to taya ma akai ta san ta haihu da har tazo?.
Me ma ya sake kawota bayan sunyi Baran-baran.

"Karki damu zan miki abu dan Allah ne amma ba dan halinki ba"

Ita dai Janan binta kawai take da ido dan bata da ta cewa tana buk'atar taimako a halin yanzu.

Matar ce ta gyara ta ita da jaririn su kuma 'yammatan su suka gyara inda ta haihun.

Ta bata wasu kayan ta saka sannan ta wanke mata nata duk da dai sun k'od'e amma har yanzu da k'warinsu.

'Yan Matan ne suka dawo d'auke da kwanuka.

Tsohuwar ta amsa tace "to kuje zan taho"

Zama tayi ta saka Janan a gaba sai da taci tuwon nan.

Tuwon shinkafane da lafiyayyar miyar kuka taji kifi da man shanu da yajin daddawa.

Sai da ta cinye tas sannan ta kora da kunun kanwa mai zafin gaske wanda da k'yar take sha saboda zafi.

Shima tasha kusan rabin kwano saboda tsohuwar tace sai ta sha sannan zata samu ta shayar da jaririn.

Tana gamawa ta mik'o mata dabino guda d'aya da zam-zam "ki tauna dabinon ki bashi,sai ki d'isa masa ruwan zam-zam d'in"

Kamar yadda ta umarceta haka tayi,dattijuwar tayi murmushi tace "anjima kad'an ruwan mama zai kawo sai ki fara shayar da d'anki ni zan tafi"

Har ta juya ta fara tafiya Janan tayi saurin cewa "nagode Allah ya saka da alkhairi"

Da sauri dattijuwar ta dawo ta zauna tana dariya.
"Naji dad'i da kika fara godemin bani na gode miki ba,yau zan fad'a miki ko wacece ni"

Kallonta kawai Janan take ba tare da ta k'ara cewa komai ba.

Dattijuwar ta cigaba da fad'in "nan inda kike zaune gidana ne ni da iyalina anan muke zaune,babu mahaluk'in daya tab'a tunanin zama anan saboda da yawan maza sunsha zuwa nan da niyyar yin lalata zan sa a halaka min su saboda bani da tausayi,kin san meyasa bani dashi?"

Kai Janan ta girgiza alamar a'a.

"Saboda ina zaman-zamana a cikin gari gidana Babban gidane amma akazo aka min fin k'arfi aka rugaza min gida wasu 'ya'yan nawa sun mutu sanadin haka shiyasa na d'auki alk'awarin duk wanda ya zauna a kangon nan zan halaka shi,munyi tafiya ni da yarana kwatsam muna dawowa na ganki shiyasa nazo nayi miki magana ki tashi bai kamata ki zauna anan ba,abinda yasa na biki cikin lallama saboda naga kina da ciki amma ba dan haka ba saina halaka ki a take a gurin"

"Tun bayan tafiya ta nake neman hanyoyin da zan halaka ki amma saboda k'arfin addu'ar dake bakinki ko da yaushe,kullum dake muke kwana anan amma na kasa tab'uka komai a kanki,ta guri d'aya na samu nasara dana hana kowa ya taimakeki,na saka k'yamata tsakaninki da 'yan unguwarnan"

Gaban Janan yayi mummunar fad'uwa dan a lokacin idan da za'a tsagata baza'a samu jini a jikinta ba.

Addu'oi ta karanta a zuciyarta sannan ta dake tace "kina nufin ke ba mutum bace?"

"K'warai kuwa"

"Amma abinci da ruwan wanka da kayan dake jikina nida jariri na ya akai kika samu?"

"Na saka yarana sun je gidan wani babban mutum anan garin matarshi ma ta haihu yau ake suna shine aka d'akko wannan kayan na jikinki dana jikinsa,tuwo kuwa da kunu da ruwa a gidan wata maijego na d'ebo da kaina"

"Ya sunan mutumin?"

"Ba damuwarki bane kedai kiyi abinda ya dameki"

Cikin dakiya da zafin rai Janan ta nuna ta da yatsa tace "kada ki kuskura ki sake bibiyata,kuma yanzu zan cire kayan in ajje ki mayar inda kika d'akko banaso,sannan gidannan ba naki bane saboda mutum ne ya gina meyasa baza kuje can daji kuyi gininku ku zauna inda ba mutane ba, babu inda aka ce aljani ya rab'i mutum,dan haka bana son taimakonki akaina ko d'aya ki fita a rayuwata idan ba haka ba zan k'ona ki da ayar Allah"

Murmushi tayi tace "yarinya nayi miki ne saboda tausayi"

"Ba'ason taimako kada ki kuma"

Dariya ta b'ab'b'aka tace "kanki ake ji 'yar nan,zan tafi bazaki sake ganina ba dan naga jininmu baizo d'aya ba bazamu had'a hanya dake ba"

"Nafi k'arfinki addu'ata data iyayena tana tasiri a koda yaushe"

Da sauri Janan ta cirewa jaririn kaya,tayi sauri taja nata da aka shanya ta sab'i jaririn ta shiga can ciki ta cire ta maida nata.

Tana fitowa taga babu alamar tsohuwar nan.

Da k'arfi ta furta "ga kayannan na ajje dan bazamu saka kayan da ba mallakinmu ba"

Nad'e jaririn ta tayi a cikin d'ankwalinta ta rumgumeshi tana kuka.

Gaba d'aya a tsorace take dan haka ta tattara komai nata a viva ta tafi ta bar kangon tana tunanin Jarumta irin tata da har takewa aljana tsawa.

Wajen dandazon wasu almajirai ta nufa,dan gani take nan sai yafi mata dad'i.

A nan Allah ya had'a ta da wata mata Asabe wadda ta tausaya mata har tayi mata alk'awarin idan ta warware zata nema mata aiki a gidan da take aiki.

Kulum matar idan taje aiki sai ta ragowa Janan abinci da zata ci saboda shayar da d'anta.

A nan inda suke kwana kangone mai d'aki biyu  amma duk an musu rufin langa-langa haka dandazon almajiran nan ke kwana a cinkushe,Janan kuma ta dawo tsakar gida ta rufe jaririn ruf ta kwanta dan ita bata son zafin nan ga wari.

Sam bata fita ko ina dan ita a ganinta bara asara ce ga duk mutumin da bayada wata nakasa.

Ranar da d'anta ya cika kwana bakwai a duniya ta rungume yaron tana kuka tace "nayi maka hud'uba da sunan mahaifina Hashim sannan zan rik'a kiranka da Abba k'arami,dan Allah ina son kayo halin Abbana kaji"

"Haba Jannat ya zaki zo ki rungume yaro kina kuka"

Ta d'ago kai ta kalli matar tace "mama kukan da nake na tausayin yaron ne"

"Karki damu ai Allah yana ji kuma yana kallon halin da kuke ciki"

"Hakane"

"Zan tafi gurin aiki dan Allah ku kula da kanku kinji"

"Insha Allah".


          *******

Yau watan Janan biyar a gidan nan kuma Abba k'arami shima watansa biyar a duniya dan har ya fara zama,yaro fari kyakykyawa sak kamannin Janan ya d'ebo hatta rashin k'ibar.

Rayuwa ta fara canza mata,Mama asabe ta fara wulak'anta dayi mata gori.

Da yammacin ranar tana zaune a tsakar gidan tana shayar da Abba k'arami,tunanin data saba kawai take dan bata zama ba tayi ba,ji tayi kawai an watso mata kaya a jiki tayi saurin juyawa dan hatta Abba k'arami sai daya tsorata.

'Dago kai tayi ta kalleta bata ma yi magana ba Asabe tace "ga wanki nan zanje gidan aiki kafin in dawo ki wanke dan bazan rik'a ciyar dake a banza ba"

Fita tayi tana ta 'yan maganganu.

Janan kuwa tashi tayi ta goya d'anta dan ita ma yau fita zatayi neman aiki ta gaji da gori da wulak'anci ga kwana cikin dandazon almajirai.

A k'ofar wani babban store ta tsaya tana tunanin ko ta shiga taji in zata samu koda aikin zubar da datti ne.

Ta shiga cikin farfajiyar store d'in kai tsaye ta nufi inda k'ofar shiga take tana ta tunanin yadda rayuwarta take a baya in sunzo store.

Hawaye ya taho mata amma bai samu damar zubowa ba dan wanda ta gani yana k'ok'arin fitowa daga ciki shine yasa numfashinta ya fara neman d'aukewa.





_*Fans wane wannan?*_
_oyaa naji daga gareku?👂ko zaku canki abinda ke zuciyata._








_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
      🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safna luv```


_'Groups ina jindad'in comments d'inku.Nagode da yabo,da kuma k'aunar da kuke nuna min....much luv😍😘_




34

Kallon kallo suka tsaya yi dan shima mamaki yake da ya ganta a wannan yanayi.

Juyawa tayi da sauri da niyyar barin gurin yayi saurin cewa "Janan".

" ka santa ne?" Abbas ya tambayeshi.

"Janan d'ina ce fa"

Gabanta ya cigaba da fad'uwa tana tafiya zani na hard'e ta,yayi saurin shan gabanta.

"Janan ki tsaya"

Cikin dakiya ta kalleshi tace "wacece Janan?Malam ka bani guri in wuce"

"Karki raina min hankali Janan kina son kice bazan iya gane ki bane?"

Wasu zafafan hawaye suka fito daga idonta ta sake juyawa zata tafi ya rik'o hijabinta "karki min haka Janan na san kece"

Fuskarta sharkaf da hawaye tace "ba Janan bace dan Allah karka tara min mutane"

Ta fuzge hijabinta da sauri da sauri ta wuce ta cigaba da tafiya.

Shi kuma kawai yaji  zuciyarsa tayi rauni,ya sunkuya jikin motar dake kusa dashi yana hawaye an kai gab'ar da bazai iya rik'esu ba.

"Jalal kuka fa akan waccan k'azamar yarinyar?"

Ya d'ago kansa idanunnan sunyi jajir yace "waccan da kake gani ada bazaka nuna mata komai ba,kaidai kaji tsoron rayuwa kawai abokina"

"To ai naga kana mata magana tana wani zuk'ewa"

"Muyi sauri muje karta b'acewa ganina"

Yayi sauri ya tafi ya bud'e mota zai shiga Abbas yayi saurin cewa,mu had'u a gida kawai danni ban gama siyayya ba"

"Okay ga key"

"A'a zan kira sai a kawomin motana"

"No amshi kawai sai ka taho da kayan duka" yayi sauri saka masa a pocket sannan ya wuce Abbas kuma ya koma ciki.

Yana fita ya hangota a can gefe tana share hawaye.

Da sauri ya k'arasa gurin,tana ganinsa ta k'ara rikicewa tana neman hanyar da zata bi.

Hannunsa biyu ya had'e ya tsaya gabanta yace "dan Allah karki min haka Janan,babu irin neman da ban miki ba lokacin da naji labarinki raina ya b'aci saboda su Raihan basu fad'a min da wuri ba"

Kallonshi tayi har zatayi magana sai kuma ta fasa,gefenshi tabi ta wuce kawai taji ya rik'e hannunta cikin zafin rai ta d'aga d'ayan hannun ta saukeshi a fuskarsa.

"Janan" ya sake furtawa cike da mamaki.

Itama ta tsorata sosai da abinda ta aikata dan ta kasa kauda idon nata akan hannunta.

Ganin mutane sun fara taruwa suna tambayar ko lafiya ya saka ta sakin wani kukan a fili.

Kallon wani mutum tayi tana kuka tace "Malam kayi min tsakani dashi dan Allah tun d'azu yake bina yana cewa ya sanni ni ban san shi ba,kuma ni matar aurece taya zai rik'a bina? akan me?tun da nace ban sanshi ba meyasa bazai k'yakeni ba"

Ai kuwa aka yi kansa caaa ana ta fad'a masa maganganu amma ya kasa cewa komai  har lokacin hannunsa na kan kuncinsa.

Ita kanta sai take jin zafin yadda mutane suke aibunta Jalal.

Juyawa tayi da sauri ta tsallaka titi,shi kuma kawai yaji bazai iya bari ta kub'uce masa ba bayan dama nemanta yake.

Da sauri ya bar gurin da niyyar binta,ai kuwa yana hawa titin kafin ya tsallaka motar ta taho kansa ji kake k'iiii.
Mutane duka aka hau salati,jin haka ne yasa tayi saurin juyowa.

Ganin Jalal cikin jini ba k'aramin d'aga mata hankali yayi ba.

Da sauri ta dawo,yayi daidai da fitowar matashiyar budurwar da ta kad'aishi da kuma Abbas.

"Jalal na shiga uku dan Allah karka rasa ranka a dalilina"

Jin haka yasa mutane aka fara zaginta ana binta da muggayen kalamai musamman da aka ga yanayin talauci a tattare da ita.

Abbas kuwa jin abin da ya faru ne yasa ya figi hijabinta dan harya yaga mata amma sai da ya direta a gefen titin.
"Kada ki sake rab'arsa ke ba ajinsa bace sam amma a haka har kike wulak'antashi kina nuna baki sanshi ba"

Kuka sosai take tana ji tana gani aka saka Jalal a motar wannan matar aka tafi,Abbas ma ya shiga mota ya bi bayansu.

Ganin mutane sun dawo kanta ya saka ta saurin barin gurin dan wasu har sun fara dungure mata kai.

Da k'yar ta iya kai kanta gidan da suke zaune,dan ta zama tamkar mahaukaciya tana tafiya tana hawaye.

Tun a tsakar gida ta fara cin karo da b'acin rai.
"To tambad'ad'd'iya daga ina?kin san bazan ciyar dake ba  shiyasa kika tafi neman arzik'i da jikinki,to sai dai hakan in ba haka ba wazai d'auke ki aiki dubeki a k'azance haka"

Janan ta kalli mama Asabe sannan ta kalli kanta taga sam babu had'i tsakaninsu duk da tana cikin wahala bata barin kayanta kina yaronta da k'azanta.

Cikin b'acin rai tace "dan Allah ya isa haka,ina ganin girmanki tun da har ban ce zanci abincinki ba ai saiki k'yaleni ki barni inji da abinda yake damuna"

"An k'i a k'yaleki d'in,kuma daga yau ki daina ganin girman nawa kinji,kuma dole in fad'a miki duniyarnan cud'eni in cud'eka ce wanki da kika barmin nayi kayana abinci kuwa kin rasa"

Bata sake tanka mata ba,ta tsince goyon bayanta dan har yayi bacci ta kwantar dashi kan cinyarta  zuciyarta a cunkushe da damuwa.

Da yamma kuwa kasa jurewa tayi taje asibiti kusan guda biyar amma bata sameshi ba,haka ta dawo gida da tarin yunwa da gajiya a tartare da ita,bata da ko taro bare ta sayi abu taci haka ranar ta kwana da yunwa da tunani.

         *******

A hankali ya bud'e idonsa ya kalli matashiyar budurwar sannan ya kalli Abbas dake d'ayan gefen ya rik'o hannunsa yace "Abbas ina take?karkace min ka barta ta tafi ba tare da na san inda take ba"
 
Ran Abbas a b'ace yace "Haba Jalal wannan 'yar ficiciyar yarinyar wata k'azama da ita zaka wani damu,babu abinda zata nunawa matarka"

Hawaye suka biyo gefen fuskarshi ya sake furta "baki min adalci ba Janan meyasa zaki min haka?meyasa kika zab'i haka Janan?"

Tsaban b'acin rai Abbas yayi banza ya k'yaleshi.

Najwa ta matso kusa dashi tace "ka sassauta zuciyarka pls,likita yace karka fiya magana"

"Wace wannan?" Ya tambayi Abbas.

"Itace wadda ta kad'eka"

Ya had'e girarshi yace "oh itane tayi min tsakani da Janan,to me take kuma anan?"

"Haba Yarima Kaine fa ka kawo kanka taya zata muku tsakani,karfa k'azamar yarinyar nan ta haukata ka"

Kuka Najwa ta fara tana fad'in "ni ba da gangan na kad'e kaba dan Allah kayi mini kyakykyawan zato.

Dukkansu sai ta basu tausayi Abbas yayi ta rarrashinta.

A rannar mamanta da babanta suka zo suka dubashi.


Daga gidan su Abbas ake kawo masa abinci kuma Abbas shiya cigaba da kula dashi.


_*4 Days later*_

Suna zaune su biyu suna hira,Abbas ya kalleshi yace " Abokina ya kama ta a sanarwa da Mommy ko Adnan ko Raihan amma yaushe har aka sin ce d'orin nan har ka koma gida"

"Baza'a fad'a musu ba Abbas,saboda hankalinsu zai tashi kuma zasu ce a mayar dani asibitin can in cigaba da jinya ni kuma banason barin garin nan ba tare dana ga Janan ba"

"Allah ya sawwak'e"

"Amma ka duba ko ina kuwa?nifa ina tunanin in har ka karad'e garin nan zaka ganta,da ace ban samu gocewar k'ashi a k'afa ba da babu abinda zai hanani nemanta duk ciwon dake jikina"

"Najwa ta kirani a waya da safe" Abbas ya kawar da maganar Janan.

"Okay"

"Kasan me?"

"Sai ka fad'a"

"Ina tunanin yarinyar nan sonka take"

"Wa kenan?"

"Najwa mana ta damu da rashin lafiyarnan taka sosai,har fa a lecture hall ta kirani tana tambayana ya jikinka"

"Ai dole ta damu tun da ita ta kad'eni"

Abbas ya d'anyi tsoki yace "kai ana nuna maka hanya kana kaucewa"

"Hanyar ce batayi min ba abokina"

        *******

A gajiya ta juya ta fita daga emergency bayan ta k'asa samunshi a karo na ba adadi.

Ta fidda ran zata ga Jalal,ga kukan Abba k'arami har cikin ranta ta rasa meke damunsa,ga ita kanta ta galabaita dan tun safe take yawan nemanshi a asibiti yafi a k'irga bata samu ba,ga tafiyar k'asa ga tazara tsakani asibiti da asibiti.

Tana fitowa taga Abbas ya fito daga motarsa.

Ta manta sunanshi amma ta gane shi.

Da sauri ta k'arasa gurinsa ta d'an russuna tace "ina yini"

Kallon sama da k'asa yayi mata dan ya ganeta sarai amma sam yak'i nunawa.

"Dan Allah dama........." Bai bari ta k'arasa ba ya mik'a mata dubu d'aya "gashi karki tsaya kina min magiya"

Kallon kud'in tayi sannan ta kalleshi kawai taji hawaye dan a ganinta ya wulak'anta ta.

"Oh tun da kin raina shikenan" ya mayar da kud'in aljihunsa.

Jikinta a sanyaye tace "dama Jalal nake nema,nasha wahala tun safe nake nemansa naje asibiti yafi a k'irga ban sameshi ba"

"Wane Jalal?"

"Wanda na ganku ranar tare dan Allah ka taimaka min"

"Bazan taimaka ba,b'ace min da gani"

"Dan Allah"

"Wallahi zan miki d'an banzan duka a gurin nan nace miki ban san wani Jalal ba kin zo wata k'azama dake kina min magana"

Wuce wa yayi ya shige ciki ita kuwa a gurin ta tsaya tana kuka.

"Yarinya juya in fad'a miki inda yake"

A tsorace ta juya ta kalli dattijuwar tare da saurin matsawa nesa da ita jikinta na kyarma.








_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
       *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




35

"Meya dawo dake kuma?"
Ta fad'a a d'an tsorace.

"Wanda kike nema yana ciki,Amenity room3 cikin main male ward"

Ta bud'e baki zatayi magana taga babu matar.

Jikinta a sanyaye tace "kina son in yarda dake ne saboda in fara tunanin kin san komai,da Allah na dogara ba dake ba"

Jikinta ba k'wari ta cigaba da tafiya cikin asabitin.

Kusan mintinta biyu a tsaye a k'ofar d'akin kafin ta murd'a k'ofar ta shiga.

Yana kwance yana duba waya yaji an turo k'ofar.

Da sauri ya mik'e zaune ganinta a cikin d'akin ba k'aramin mamaki yaji ba.
Farin cikin dake zuciyarshi bazai musaltu ba.

"Janan"
"Jalal" ta kira sunanshi itama,a dai dai lokacin wasu zafafan hawaye suka sauka a kuncinta.

"Ki zauna ga kujera" a hankali ta k'arasa kan kujerar ta zauna tare da fad'in "ya jikinka?"

"Da sauk'i"
Kukan Abba k'arami ya saka ta mik'ewa ta fara jijjigashi.

Jalal kawai kallonta yake cike da tausayi.

Wai 'yar k'arama da ita amma tana wahala da yaro,wani ma sai yace ajiya aka bata.

Mamaki yake yadda gaba d'aya ta canza ta zama 'yar k'auye futuk,ya kalli takalmin k'afarta shima silifas ne green yasha d'inki da bak'in zare.

Wani hawayene ya sauka a fuskarsa ba tare daya shirya ba.

Sauke goyon tayi ta mayar kafad'a tana jijjigashi amma kamar k'ara cewa take yayi kuka.

Duk tabi ta rud'e gashi bata son ta shayar dashi a gaban Jalal kunya take ji,kuma ta san ma ba wani abu zai samu ba tunda itama ba k'oshi tayi ba.

Ganin ta rud'e ne yasa Jalal mik'a hannu ya d'auki yaron yana jijjigashi.

"Ke uban wa ya baki damar shigowa nan?"

Abbas ya fad'a,Najwa ma tsayawa tayi tana k'arewa Janan kallo cike da k'yank'yaninta.

"Zo ki fice" Abbas ya fad'a a tsawace yana nuna mata hanya.

Jikinta gaba d'aya rawa yake tama rasa me zatayi,Jalal kawai tsayawa yayi yana kallonsa cike da mamaki wai a gabansa yake ciwa Janan mutumci bayan ya fad'a masa matsayinta a gurin shi

"Rik'e shi Janan" Jalal d'in ya fad'a yana mik'a mata Abba k'arami da har lokacin yake callara kuka.

"Malama kiyi sauri ki fita ba b'ata lokaci nace ki tsaya yi ba kin damemu da kukan yaro"

Ta karb'i d'anta daga hannun Jalal tana zubda hawaye.

Baice komai ba ya sakko daga kan gadon yana d'angasa k'afa cike da jin zafin ciwo.

"Janan jirani mu tafi"

Juyowa tayi ta kalleshi tace "baka da lafiya Jalal ka zauna dan Allah karka damu dani ni yanzu rayuwata bata da wani amfani"

"Yanzu dan na koreta shine zaka bita Yarima?"

"Eh saboda ka gane muhimmancin ta a wurina"

"Jalal pls ka dawo ka zauna shikenan itama mun yarda ta zauna" Najwa ta fad'a

"Wallahi bazamu zauna ba,abinda kayiwa Janan kawai hannunka mai sanda ne,kana so kace Jalal na gaji da ciyar da kai da kuma biyan kud'in magani shine abinda yasa ka ciwa Janan mutumci"

"Subhanallah! Karka fassara ni baibai Jalal"

"Abbas wallahi bazan zauna ba,zan canza asibiti a cigaba da kula dani"

"Jalal pls kayi hak'uri" Najwa ta sake fad'a

Har zai yi magana sai kuma ya kalli Janan yace "Janan mu tafi"

Ganin Jalal da gaske yake yasa Abbas kiran daddynsa.

Yayi masa bayani daddy yace a bawa Jalal.

Hak'uri daddy ya bashi sannan ya koma ya zauna tare da karb'ar Abba k'arami.

Abbas ya kalli Najwa yace "muje waje mu bar masoya su shak'ata"
Ranshi a b'ace yayi maganar ya fita.

Najwa ta mik'e ta tsaya tana kallonsu itama ran nata ya b'aci ta bi bayan Abbas.

Tana fita Jalal yayi murmushi kawai sannan ya mayar da kallon shi ga Janan da har lokacin kanta a k'asa.

"Ya sunan babyn?" Kanta a k'asa tana murza yatsun hannunta tace "sunan Abba ne amma ina kiranshi da Abba k'arami"

"Ni kuma zan rik'a kiranshi da Prince"

Ta d'anyi murmushi.

"Wai da gaske ke kika haifi yaron nan Janan?"

Tambayar sai tazo mata a bazata gaba d'aya taji nauyin tambayar.

'Dago ido tayi ta kalli Abba k'arami sannan ta kalli Jalal ta d'aga kai kawai.

"Yaushe kika haifeshi?a ina?meyasa kuka bar Kaduna?ina su Mameey?taya ya idanunki suka juye haka?"

Ta d'anyi shiru na 'yan mintuna kafin tace "wannan tambayoyin sun min yawa wanne zan amsa?"

"Duka nake buk'atar amsar pls"

Ajiyar zuciya tayi tace "Na haifi yaron nan wata biyar da suka wuce a cikin garinnan,mun bar Kaduna saboda babu amfanin zama a garin da aka ci mana fuska,Mameey kuma ban san ina suke ba tun lokacin da Abba ya rasu suka bar Kaduna ni kuma ban san rasuwar Abba ba har sai ranar da yayi uku shiyasa ban san tafiyar su Mameey ba ban kuma san inda suke ba shekara d'aya da wata hudu kenan,idanuna kuma tsabar kukane yasa suka koma haka"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un,yanzu a gidanwa kike zaune a katsina?"

Kuka ta fara hakan ne yasa ya gane ba a gidan kowa take ba.

Abba k'arami kukan ya fara tsalawa Jalal duk yabi ya tud'e yana bawa Janan hak'uri yana kuma jijjiga Abba k'arami.

Sai da taci kuka ta k'oshi sannan ta mik'a hannu ta karb'i Abba k'aramin ta rufeshi da hijabi tana shayar dashi aikuwa d'if kakeji babu kukan yaron.

Kallonta kawai Jalal ya cigaba dayi yana ganin abin kamar a mafarki wai 'yar k'aramar Janan tana shayarwa,shi sam ya raina girmanta a tunaninsa ma bata isa Aure ba bare haihuwa.

Ganin ya kafeta da ido ne yasa tayi saurin cire Abba k'arami,aikuwa ya fara tsala mata kuka.

Jalal ya d'anyi gyaran murya yace "bai k'oshi ba idan kunyata kike bara na fita"

Har ya tashi,cikin kunya tace "a'a Jalal babu damuwa ba sai ka fita ba"

Tayi saurin maidashi cikin hijabin ta gyara zamanta.

"Meyasa kike jin kunyata yanzu?"

Shiru tayi batace komai ba.

"Dan Allah in tambayeki Janan?"

"Allah yasa na Sani" ta fad'a kanta a k'asa.

"Sanin kin sani ne yasa zan tambayeki,amma ki bani amsa tsakaninki da Allah"

"Ina jinka"

"Da kika haifi yaron nan waye ya d'auki d'awainiyyar yi masa ragon suna"

Hmmm "babu kowa hasalima ni kad'ai na haifeshi kuma nike tare dashi har zuwa wannan lokaci"

Da mamaki yace "ke kad'ai fa Janan tayaya zaki haihu ba d'an taimako?"

"Gashi kuwa na haihun kuma muna lafiya,sai dai shi da nake tunanin kamar bashi da lafiya"

"Janan wannan ganganci ne taya zaki haihu ba mataimaki" aikuwa yayi ta fad'ansa har ya gaji ya bari.
Sannan yayi alk'awarin yana warkewa zai sayi rago ya bada a yanka na suna sannan a rarrabawa mutane.

"Aliyu bai nemi d'anshi bane?"

Gabanta ya dad'i sai ta tuno mafarkin Abba da tayi,idanunta taf da hawaye tace "d'an nan nawa da kake gani bashi da uba,dan ban san waye mahaifinsa ba"

"Me kike nufi Janan?,Aliyu ne mijinki fa"
"Na samu cikin nan bayan rabuwata da Aliyu"

"Janan meyasa?" Ya fad'a yana zubda hawaye.
Itama kuka take tana fad'in "k'addarar rayuwa Jalal,ni kuma haka Allah ya tsara k'addarata a haka"

"Babu k'addara a cikin shege ban yarda da wannan k'addarar ba,dan Allah ki fita a d'akin nan ki fice bana son ganinki a gabana"

Cikin matsanancin kuka ta mik'e tsaya tana kallon shi.

"Fita ga hanya" ya nuna mata k'ofa.

Tana shashshek'ar kuka tana tafiya jikinta sai b'ari yake,har ta kai bakin k'ofa yace "kin cuceni kin cuci son da nake miki Janan"

Ta d'an tsaya kad'an sai kuma ta wuce da sauri tana kukan.

_2 Minutes later_

Abbas da Najwa suka shigo d'akin.

Najwa ce ta k'arasa gefen gadon tace "Sannu Allah yasa dai bata b'ata maka rai ba naga ta fita tana kuka"

Baima samu damar bata amsa ba gudun kar ya fad'i abinda ba daidaiba dan ransa a b'ace yake.

"Wai Jalal meya had'aku ne,tana fita fa ta fad'i k'asa,mutane duk an rurrufeta naje nace su k'yaleta iskanci ne"

Ai bai jira Abbas ya k'arasa maganar ba ya take k'afar ya fita da sauri..
Suma da sauri suka rufa masa baya.

Yana fita ya ganta zube a k'asa ana ta jijjigata tak'i tashi,Abba k'arami yana hannunta wata mata ta danne masa goshi gefen kunnenshi da  tsumma.

Baima tsaya tambayar meya sameta ba ya sab'eta key d'in motarsa na aljihu ya fito dashi ya bud'e ya saka Janan a bayan mota sannan ya dawo ya karb'i Abba k'arami wanda gaba d'aya fuskanshi a wanke take da jini.

Salati kawai yake tayi lokacin daya figi motarsa ya bar asibitin zuwa wani.

Da taimakon Nurses aka shigar da Janan da Abba k'arami cikin emergency.

Sai a lokacin yaji wani azabar zugi a k'afarshi tamkar an cire masa ita.

Zama yayi kan kujerar ya rik'e k'afa yana cije leb'e.
A nan ya fad'i ya suma daidai shigowar Abbas da Najwa cikin gurin.


       *********

"Kaiii na shiga uku wai shin Umma aurenki nake?ko dai zamu fara raba kwana ne tsakaninmu naga kina neman mayar dani kishiyarki kin hanani na sake a gidan mijina wai shin meke damun rayuwarki?"

"Umma kike cewa haka"
Ummi ta fada tare da taso wa gadan gadan kan Zuhra.

Umma tayi saurin cewa "barta Ummi karki yi fad'a"

"Ai da kin barta mun goga k'ashi dan ta tabbatar da ruwa ba sa'an gwando bane"

"Ai kin yi kad'an ke baki isa kice zakiyi wa Umma rashin kunya in kyaleki ba.

Tafa hannu tayi tana dariya sannan ta kama hab'a tace " oh Allah mai iko kaji masu Umma mu kuma da muka fad'o daga sama sai muyi kuka"

Shiru sukayi mata ta sake fad'in yau zaku bar gidannan sai inga nida Uwar taki wa yafi matsayi a gurin Aliyun"
A zafafe Ummi ta taso ta damk'i wuyan Zuhra,aikuwa Zuhra ta sakar mata mari har sau biyu a kumatu d'aya.

Ganin hakane yasa Umma ta taso suka had'u ita da Ummi suka fara dukan Zuhra harda waya,a haka Allah ya fad'o da Aliyu cikin gidan.

"Subhanallah,meke faruwa haka ya fad'a tare da zuwa ya fara fincike Umma yana bata hak'uri sannan yayiwa Ummi tsawa ta nutsu.

Wannan karon kuwa su biyun suka hau masa kuka,Zuhra da Umma"

Umma na fad'in wallahi saiya saki Zuhra,ita kuma Zuhra na fad'in sai ya canza mata gida bazata iya wannan abu ba,kullum baya gida suna cikin dukanta.

Hannunta yaja sukayi upstairs.
Umma ta tsaya galala tana kallon sa wato bama zai bata hak'uri ba kawai yaja matarsa suka wuce.

Ummi ta tab'e baki tace "Umma kin gani fa,da Janan ce hankalinmu a kwance,bata da wani tashin hankali ko fad'a amma ki duba ki gani Zuhra fa so take ta rabamu da yaya gaba d'aya"

"Ki barni da matsiyaciyar yarinyar nan wai har ta kai Aliyu yana tsallake magana ta ba shakka yarinyar nan asiri ta masa"

"Umma wallahi idan muka zauna kwad'o zai mana k'afa"

"To ya kike so nayi Ummi,da wanne zanji?"

Murgud'a baki tayi tace "ah muma muyi asirin to waye bai iya ba,daga k'auyen da ta fito muma fa daga nan muke"

"Amma ai bamu kai dad'ewarta ba saboda iyayenta anan suka girma haka ita ma"

"Umma gidan boka fa ba sai wanda ya san gari ba wanda bai san gari bama sai kiga yafi d'an gari sanin malamai"

"Ummi bazan yi asiri ba,kin san dai shirka ne ko,bana son aikata zunubi ina gudun shiga wuta"

"Umma zunubi kuwa ai mun gama aikata shi saboda ko iya goggo Zahila da Janan da iyayenta aka tsaya ai kin aikata babban zunubi,kuma wancan zuwan waye ya nuna miki gidan bokan sai wannan kawai saboda a dawo da hankalin Yaya Aliyu shine kike tsoron zunubi?"

" kaji shak'iyiyar yarinya?uban me na yiwa Zaliha bayan cutar da Zahila tayi min na sanadin mutuwar Malam,wallahi Ummi idan kika cigaba da wannan maganganu to lallai zamu raba hanya,bazan lamunta ba"

"Umma ni fa ba da wani abu na fad'a ba,na fad'a ne kawai dan muje mu karya asirin da waccan matsiyaciyar tayi wa Yaya,kuma idan komai ya daidai ta sai mu nemi yafiyar Allah ai shi gafurur rahim ne"(kuskuren da yawancin mutane keyi yanzu,wai kace zaka aikata aikin sab'o saboda kasan idan ka tuba Allah zai yafe maka saboda shi Allah mai gafara ne, 'yan uwa shin idan muka mutu muna aikata zunubin fa?wannan fa Babban ganganci ne da kuma hud'ubar shad'an,mu kiyaye)

"Eh hakane amma fa ina tsoro"

"Karki wani tsorata ai hadisi na hud'u cikin arba'una hadis yayi magana akan komai Umma"(wa iyazubillah Allah ka karemu daga fad'awa halaka)


" Shikenan ki bari sai na samo k'wararren malami wanda zai mana aiki kamar yankan wuk'a"

"Yawwa Umma".

        **********

Suna zaune ita da Nura a falo suna ta b'ab'b'aka dariya.

" amma Zuhra baki da dama,kamar bazaki iya aikatawa ba"

"Hmmm Nura kenan ai komai kamawa take"

"Kasan Allah ni ina yi mata ne saboda taji rad'ad'in irin muzgunawar da tayi wa Janan,saboda tun kafin na auri Aliyu nayi alk'awarin k'watowa Janan hak'k'inta in na Aure shi"

"Amma ai zaki barsu ko"

"Eh duk lokacin da naji ta furta alamun ta saduda abinda tayi wa Janan to zan k'yaleta in kuma fara mata biyayya,su fa a tunaninsu wai asiri na musu,cab Allah ya kiyasheni da yin asiri,babana Babban malamine na izala,Ahlul sunnah aikuwa kowa ya san babu kalar asiri a gidanmu sai tsantsan sanin qur'ani, hadisai,sira,tauhid,da sauran littattafai da yawa"

"Hakane kuwa babu wanda bai san Malam cikakken mai rik'o da sunnar manzo Allah (S.A.W) bane idonsu ne kawai ya rufe"

"Da kuma tsabagen son kud'i,barin ma wannan mai kama da figaggiyar kaza yanda kasan d'iyar gomna haka take ji da kanta duk zan saitasu ai"

"Kedai ki cigaba da addu'a dan wallahi gani nake Janan ma ba haka nan suka k'yaleshi ba shi kansa Aliyu"

"Hakane ne ai bana wasa da addu'a da nafilfili da kuma azumin litinin da Alhamis"

Shigowar Aliyu falon ne yasa sukayi shiru.

"Ya hak'uri Nura na barka   a zaune wallahi wai ina can ina yiwa Ummi fafutukar neman admission"

"Ai kuwa da ka dawo kaga bani nan dan har na gaji da zama"

"Ah haba dai"

Zuhra tayi masa sannu ta zuwa kawai ta wuce d'akinta.


       *******

"Ah har yanzu baka tafi gurin aikin ba?"

Yayi d'an tsaki na gajiya sannan ya kalli agogon hannunsa.
"Wallahi Momma ban tafi ba amma ina shirin tafiyar"

Hmmm tayi ajiyar zuciya sannan taja stool ta zauna gabanshi.

"Janan ko?"
Yayi sauri ya d'ago kai ya kalleta.

"Na san tunaninta ya hanaka zuwa office karka damu kayi mata addu'a kawai amma idan kace tunanin Janan zaka saka a ranka koda yaushe zaka zauna a b'acin rai gashi ka kusa Aure kaga inni na lamunta matarka bazata lamunta ba Muhasin na fika damuwa da rashin Janan amma kai kafini rashin hak'uri"

"Momma ba haka bane,Janan ta canza rayuwar gidannan gaba d'aya, fitar da ita a rai tabbas zaiyi wuya,wallahi har cikin zuciyata inason Janan Momma"

"Karka damu Muhasin Allah ya bayyana mana ita,kuma yasa tana cikin kwanciyar hankali a duk inda take"

"Ameen Momma,kusan wata tara kenan"

"Allah ya bayyanata"

"Ameen"











_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
     🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Safnah luv & Mrs Xerks```


_kuyi hak'uri fans_


36

A hankali ta bud'e idanunta tana k'arewa d'akin kallo.

Abubuwan da suka faru ne suka fara dawo mata tayi saurin tashi tana kiran "d'ana ina yarona?" kuka sosai take tana furta ina d'anta.

A rud'e nurses biyu suka shigo.
"Lafiya ya kike jin jikin naki?"

"Ina d'ana?" ta sake tambaya tana kuka.

'Daya daga cikin nurses d'in ta dafata tace "baiwar Allah ki kwantar da hankalinki d'anki yana cikin kulawa kinji"

"A'a Ku fad'amin inda yake inje in ganshi dan Allah"

Ganin ta rud'e ne yasa suka rakata har d'akin da  Abba k'arami yake.

A rud'e ta k'arasa jikin gadon tana k'ok'arin d'aukarta suka hanata.

"Baki ganin baya da lafiya?ki bari ya tashi sai ki d'aukeshi"

Kuka ta fara ganin fuskarshi da bandeshi,tana fad'in "karka mutu Abba k'arami dan Allah karka mutu ka barni kaine gatana ka tausaya min kaji"

Su kansu nurses d'in sai da suka tausaya mata.

Kujera taja ta zauna ta kifa kanta akan gadon ta cigaba da kukan da ta san bazata tab'a dainawa ba.

         ********

Yana jingine da filo hannunsa rik'e da kansa yana cije leb'e cikin jin zafin ciwon yace "doctor  yanzu ko da sanda bazan iya taka k'afata ba?"

Murmushi doctor yayi yace "kana cije leb'e amma kana tunanin tafiya a yanzu?"

"Indai zan iya takawa to zan tafi"

"Zuwa ina?ai in fad'a maka su Mommy suna kan hanya dan na fad'a mata komai" Abbas yayi maganar.

"Me?ka fad'awa Mommy dagaske?haba Abbas meyasa zaka min haka?"

"Saboda ina sonka kuma kasan bazan bari rayuwarka ta lalace akan wata banza ba,dubi yadda ka koma kayi wuju-wuju kusan kullum  ana abu d'aya"

"Wa'izubillah,Abbas kana daukar alhakin Janan me tayi maka?shin ka santa a baya ne ta maka laifine?akan me zaka rik'a muzantata?"

"Saboda kana da mata,na tabbatar idan Raihan taji bata tab'a jindad'i ba"

"To bari Raihan d'in tazo sai na tabbatar mata naga Janan kaji me zata ce"

Shiru yayi baice komai ba shima Jalal ya kwanta ya juya masa baya.

Da yamma su Mommy suka k'araso aikuwa ta rufe Jalal d'in da fad'a akan me yasa zai samu ciwo amma ya kasa fad'a mata.
Raihan kuwa har da kukan ta.

Adnan lallab'a shi ya rik'a yi yana masa sannu.

Sunso su mayar dashi can asibitin a Abuja amma yak'i yarda dole ta sa suka juya Raihan kuma ta zauna dan ta cigaba da kula dashi.

Bayan sallar Magrib Najwa tazo,ganin Raihan ne yasa tayi turus tana neman watso tambaya dan yadda taga Raihan na wani shishishigewa Jalal.
Abbas yayi saurin tarar numfashinta da fad'in "wannan matar Jalal ce sunan ta Raihan"

"Oh sannu" ta fad'a ranta a d'an b'ace

"Yawwa,wacece wannan Jalal?"
Tayi tambayar tare da kafeshi da idanu.

"Itace wadda ta kad'eni" ya fad'a kai tsaye
"Oh kece kika so rabani da farin cikin raina ko?" Ta fad'a tana murmushi

Ganin hakane yasa itama Najwa  tayi murmushin tace "a'a tsautsayi dai ko"

Zama tayi a kan kujera sai kuma hira ta b'arke tsakaninsu(mata ba wuyar sabo).

Jalal kuwa baya cewa komai shi tunanin sa d'aya taya zai bayyanawa Raihan Janan?
A zuciyarsa ya kud'urta cewar bazai bayyanata ga kowa ba har sai ya warke dan kar a samu matsala.

Haka Raihan ta cigaba da jinyar Jalal su Mommy kullum suna hanyar katsina.

Janan ma ta cigaba da jinyar d'anta ba tare da ta san wa yake d'aukar d'awainiyarsu ba,ta san komai ma'aikatan ke kawo mata hatta abinci,koda ta nemi ta sani ance mata wani bawon Allah amma sam bata tab'a kawowa a ranta Jalal ne.

Shi kam Jalal kullum tunanin sa da burinsa shine yaje yaga lafiyarsu amma babu dama k'afarsa tak'i sai dai yakan tura Abbas ya gano amma baya zuwa sai dai yayi shawagi ya dawo yace tace tana dubashi kuma jikin yaron da sauk'i.
Abu d'aya ne Abbas yayi daya k'i fad'awa Raihan Janan na nan kamar yadda Jalal ya haneshi.


*_2 weeks later_*

Tana tsaye doctor yana rubutu a takardar magani,kallon takardar kawai take yadda taga ya cika yana k'ok'arin juya baya tayi saurin cewa "doctor amma naga kamar ya samu lafiya sosai ma gashi har yana wasansa nayi tunanin za'a sallamemu"

"Za'a sallameku amma sai ya gama warwarewa,kije ki karb'o wannan magungunan ai kin san wurin ko?"

"Eh na sani" ta fad'a tare da fita da sauri dan batason ta barshi shi kad'ai.

Tana tsaye tana jiran layi kawai ta hango Raihan d'in tsaye ita da wata mata suna magana.

Cikin farin ciki ta tafi da sauri gurin.

Tunda Raihan d'in ta hangota ta tsaya tana kallonta cike da mamaki.

"Raihan dama ashe zan sake ganinki?"

"Lallai Janan ashe katsina kuka dawo" ta furta kamar batayi murna da ganin Janan d'in ba.

Sam Janan bataji dad'in yadda ta mata magana ba amma ta dake tace "eh! Meya kawoki asibitin nan?"

"Mijina ne babu lafiya,Janan share-share kike anan?"

Yadda tayi maganar yayi mutuk'ar b'atawa Janan rai ta kalleta rai babu dad'i tace "haba Raihan shara fa?"

"Ahh to ai gaskiya ne dan na san ko kwalin diploma baki rik'e ba,kuma na ganki kaca-kaca,kinga a gurguje Jalal ne mijina kuma jinyarsa nake anan sannan dan Allah bana so ki yarda ku had'u dan nemanki yake kuma da zarar ya ganki zaki iya dagula aurena"

Kasa motsawa Janan tayi dan abinda Raihan take fad'a tana jinshi tamkar saukar aradu a kanta.

"Kinga na bar Jalal shi kad'ai sai anjima"

Har ta juya ta fara tafiya Janan tayi saurin cewa "saboda Jalal d'in kike fad'a min maganganu son ranki Raihan?"

Juyowa tayi ta dawo daf da ita tace "eh saboda shine,kuma dalilinsa zan iya miki abinda yafi wannan"

Ta juya ta tafi,a jikin bangon Janan ta mak'ale tana kuka.
Sai da tayi mai isarta sannan ta share hawayenta taje ta karb'i magungunan ta tafi.

Tana ta sauri dan ta san tafi minti talatin da fitowa ga Abba k'arami shi kad'ai a d'akin.

Tana tura k'ofar taga Jalal rik'e da Abba k'arami.

Ganin Jalal ba k'aramin d'aga mata hankali yayi ba amma wanda ta gani zaune kan kujera shine ya sa har numfashinta ya fara k'ok'arin d'aukewa.

Shima ya tsorata da ganinta sosai amma ya daure kawai ya kafe ta da ido.

Idanunta duk sun firfito kasancewar tana harara garke ne yasa Jalal d'in yayi tunanin ganinsa ne yasa ta kid'ima.

Hannunta rik'e da k'irjinta bakinta yana k'ok'arin furta kalmar SALMAN amma ta kasa.

Jiri ne ya fara d'aukarta tana k'ok'arin fad'uwa kawai ta dafe bango ta zauna a k'asa dirshan.

Sai lokacin hawaye ya fara zuba a fuskarta tamkar an bud'e fanfo.

Jalal ya taso ya durk'usa gabanta yace "Janan dan Allah kiyi hak'uri da abinda nace wallahi b'acin rai ne,kin san irin neman da na miki bazan tab'a k'ink'i a rayuwata ba"

Runtse idanunta kawai tayi har lokacin hawaye na fita.

Adnan kuwa ya kasa motsa ko d'an yatsan shi daga inda yake zaune.

Jalal ya juyo ya kalleshi yace "Bro itace fa,wallahi dama na san hakan sai ta faru dan Allah ka bata hak'uri kasa baki kaima"

Cikin dauriya da jarumta ya taso yazo inda suke ya tsaya "kiyi hak'uri pls" abinda ya iya fad'a kenan ya kalli Jalal yace "bara naje mun bar Raihan ita kad'ai ka rarrasheta zan dawo.

Tana jin ya fita ta bud'e ido tace " Ku fita daga rayuwata dan Allah ku k'yaleni haka karku haukata ni"

"Bazan tab'a k'yaleki ba zan yarda ki sake rayuwar wahala ba ina tare dake har abada"

"Zan mutu Jalal k'irjina zafi yake" ta rik'e k'irjinta tana kakari kamar zata amayo zuciyarta.

Da sauri Jalal ya tashi yana d'angesa k'afa ya fita,a bakin k'ofa yaci karo da Adnan jingine da bango fuskarshi sharkaf da hawaye.

Cike da mamaki ya tsaya yana fad'in "kuka Adnan?"

A tsoroce Adnan ya d'ago ido ya kalleshi.





_*kuyi Manage pls,nayi alk'awarin insha Allahu gobe zan muku typing mai yawa*_











_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
       *DIREBAN GIDANMU*
        🍁🍁🍁





_*by SaNaz deeyah*_👄




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```





37

Murmushi yayi tare da matse leb'b'ansa sannan yace "Yarima ina mamaki da tausayin yarinyar nan wai wannan matsitsiyar yarinyar itace ta haifi yaron nan kuma take rayuwa a wahalce haka"

Ajiyar zuciya Jalal yayi sannan yace "wallahi bro ka ganta dai bata fi shekara 17-18 ba amma da kanta ta haihu babu d'an taimako"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" Adnan ya fad'a yana dafe goshinsa.

"Bara naje na kira doctor ka shiga bro kafin in dawo"

Girgiza kai yayi yace "a'a baka da lafiya ka koma bara naje na kira doctor"

Bai jira amsarsa ba kawai ya wuce.

A inda ya barsu nan ya dawo ya gansu ta kifa kanta tana ta kuka tamkar k'aramar yarinya 'yar shekara 3.

Fizge-fizge ta fara lokacin da doctor na k'ok'arin dubata amma ta k'i yarda ta tsaya.

Da k'arfi nurses suka rik'e ta,allurar bacci yayi mata dan itace mafi sauk'i saboda yadda take abubuwa a lokacin tamkar mahaukaciya.


"Ban san meke damun Janan ba wallahi bro idan ka ganta a baya bazaka ce ita bace,amma rayuwar Janan gaba d'aya ta canza,nayi alk'awarin zan zamo farin cikin rayuwarta zan dawo mata da duk wani farin ciki data rasa,wlh Adnan ina son Janan ina jin zabin yanayin nan nata"

Shiru Adnan yayi dan shi kansa ya san dauriya yake,ji yake kamar ana watsa masa garwashin wuta a jikinsa.
Da sauri ya mik'e ya fita kawai.

Motarshi ya shiga yaja da k'arfi ya bar cikin asibitin.

Sai daya fara fita daga gari sannan yayi parking a gefen titi.

"Inna lillahi wa inna ilaihi  raji'un" ya rik'a furtawa lokacin guda fuskarshi ta canza hawaye gaba d'aya ya b'ata masa fuska.

"Janan d'ina yau na gani kamar a mafarki,shekara kusan bakwai ban ganta ba sai yanzu,kuma a wannan hali,dama ashe Janan ce wadda Jalal ke bani labari,Janan d'ina ce Jalal yayi soyayya da ita,taya zan sanar dasu itace Janan d'ita bayan ban tab'a fad'a musu sunanta ba?"

Hawayen idonsa ya fara gogewa ya cigaba da fad'in "zanyi k'ok'arin nunawa Janan bani bane Salman d'inta nagode wa Allah daya saka Abba ya hanani auren Janan da yanzu na cuceta na saka mata cuta bata ji ba bata gani ba,na san wannan ma baiwace tunda har Allah yasa Jalal zai rik'e min ita,dole in bar abin nan a zuciya bazan bari kowa ya san itace Janan d'ina ba"

Zuciyarsa cike take da tambayoyi da yake son yi mata amma kuma babu dama saboda baya so ta yarda shi d'in ne,amma yana mamakin yadda Janan ta zama haka,gata kuma da d'a.

Sai da Jalal ya dameshi da kira sannan ya koma,yadda ya ga Raihan ta d'aga hankalinta tana fad'in maganganu  abin bai masa dad'i ba.

Kiransu yayi gefe yana tambayar meyasa zatayi haka.

Kuka ta fara tana fad'in "ita in har Janan ta dawo gidansu ta san Jalal gudunta zaiyi saboda ya fifita Janan fiye da komai"

"Karki manta ke fa matarshi ce,idan baki rufa masa asiri ba wazai rufa masa?sannan kin san bashi da lafiya amma kina neman d'aga masa hankali meyasa zaki haka Raihan?"

"Ni ban d'aga masa hankali ba amma tun d'azu ya tafi wajenta ya barni ni kad'ai sai da yaronta ya fara kuka zai kawo min"

"Ka rabu da ita Adnan wallahi saina d'aga mata hankali yadda ta d'aga min nawa" Jalal ya fad'a

"Kaji abinda yake fad'a fa Yaya" Raihan ta fad'a tana kuka.

"Jalal dan Allah karku d'aga hankulanku ni bana son Mommy taji komai har sai Janan ta warke kaga kaima an kusa sallamarka"

"Bro Janan fa k'awarta ce amma wai har ta kasa d'aukar d'anta saboda kishi"

"Eh a kanka zan iya yin komai"

Hannu Adnan ya mik'a ya karb'i Abba k'arami yana fad'in muje ka zauna ka huta.

Da k'yar ya sasanta tsakaninsu suka nufi d'akin da Janan take har lokacin bacci take,wucewa d'akin Jalal d'in sukayi Adnan na rumgume da Abba k'arami yana jin yaron har cikin ransa.

Da dare kuwa,yaron yana ta kuka Jalal da Adnan kowa karb'a yake yana jijjiga amma yak'i daina kuka,Adnan har fita yayi ya sayo madarar NAN amma da suka dama masa k'in karb'a yayi.
Raihan kuwa duk ta wani cune bata ko karb'eshi ba,har sai da wata nurse tace ita mace ce ta karb'eshi mana ai k'ila in yaji jikin mace ya daina kuka.

Ya yatsine ta karb'eshi tamkar zata karb'i kashi sannan ta k'ara da cewa "nifa na tsani kukan yaro wallahi"
Ran Jalal ya b'aci yayinda Adnan yaji haushinta da tsanarta dan ya san koda ya rasa Janan bazai yarda a wulak'anta ta ba.

"Kawoshi na fita kawai dashi" tayi saurin mik'a masa ya sab'a shi a kafad'a ya juya kenan ta  murd'a k'ofar ta shigo.

Sau d'aya ta kalleshi ta d'auke idonta kawai ta saka hannu ta karb'i yaron ta fita.

"Bro taya akai ta tashi?"

"Jini mana,watak'ila taji kukan yaron"

"Allah yasa bata ji maganar Raihan ba dan bazataji dad'i ba"

"Ina tunanin taji bara na bita"

Da sauri ya fita.

Yana tura k'ofar tayi saurin Jan hijabi ta rude jikinta dan ya shigo tana shayar da d'anta babu ko sallama.

"Amma baiwar Allah bai kamata kiyi haka ba,kin d'auki d'anki kawai kin fita"

Cike da mamaki ta kalleshi idonta taf da k'walla.

_wai Salman ne ya ke nuna baima santa ba_ ta fad'a a ranta lokacin hawaye suka sauka a kuncinta.

"Amma ko dan yadda Jalal ya damu dake bai dac............."

"Dakata Malam" ta tari numfashinsa,Muryarta na sark'ewa ta fara fad'in "d'ana ne ai ko?to ban nemi taimakonku ba karku kuskura ku sake min katsaladam"

Furucinta ya matuk'ar bashi mamaki
Ji yayi tamkar ya bayyana kansa a gareta amma sai ya dake yace "sai kace ba musulma ba har ayi miki abin alkhairi ki kasa karb'a?"

"Bana so a barni yadda aka ganni"

"Bazan iya ba Janan,na yarda duk hukuncin daya dace ki d'auka a kaina amma banda rabuwa dani"

Adnan ya juya ya kalli Jalal daya shigo,itama idon nata akan Jalal d'in yake.

Kujera yaja ya zauna ya cigaba da cewa "Janan ki tausayi min dan Allah wallahi ina sonki sosai ba zan iya rabuwa dake ba tunda har na samu damar ganinki bayan wahalar nemanki dana sha"

Kuka ya sake kufce mata sai da tayi mai isarta ta gama Adnan d'in yana tsaye ya kasa komai zuciyarsa tamkar zata fashe Jalal kuwa rarrashi kawai yake.

Raihan ce ta turo k'ofar ta shigo daga jikin bango ta lafe lokacin Janan tasa hannu tana goge hawayen idanunta.

"Jalal" ta kira sunanshi a sanyaye.

Bai bata amsa ba dan shima idonsa cike yake da hawaye.

"Nagode da taimakon da kayiwa rayuwata dan na san abinda kamin ba kowa ne zai iya yi min ba,amma na san ba zan iya zama daku ba,ku masu kud'i ni talaka almajira sannan ga yaron nan kai kanka ba sonshi kake ba"

"Ke ba talaka bace da gatanki Janan ba zan yarda kije ko ina ba k'afarki k'afata har Abuja,zan nuna wa Mommy ke domin ta dad'e tana son ganinki"

"A'a bazanje ba,babu inda zan bika Jalal"

"Janan karki min haka"

"Bazai yuwu ba inje gidanku in zauna"

"Kinfi so ki rik'a kwana a titi?"

"Eh saboda anan na rayu har na haifi yaron nan na san Allah yana tare dani"

"Bara na kira Mommy a waya" ya fito da wayar tayi saurin cewa
"Karka min rashin adalci karka sa inyi kaffara Jalal na riga na rantse bazan tab'a k'ara zama a inuwar da ba tawa ba"

"To shikenan zamu siya miki gida"

"Wallahi bazan zauna ba dan Allah ka k'yaleni Jalal" ta fad'a tana zubda hawaye.

"Ki mana alfarma kije gidanmu ki zauna koda a matsayin 'yar aiki ne ko dan rayuwar d'anki karya tashi a titi,na rok'i alfarmarki a karo na farko ki min wannan alfarmar Janan" Sai a lokacin Adnan yayi magana.

Kallonshi tayi lokaci guda taji zuciyarta na harbawa da k'arfi,abinda yake sake k'ona mata zuciya shine yadda Salman ya nuna halin ko in kula a kanta,yana nuna tamkar bai santa ba"

_Haushin Abba yasa Salman zai min haka?meyasa zai min haka bayan bani da laifi?dole in dauki shawararsa ko dan in inganta rayuwar Abba k'arami._

'Dago jajayen idonta tayi tana kallon Adnan sannan ta sauke su tana fad'in "na yarda inje gidanku a matsayin 'yar aiki amma da sharad'in bazaku tausaya min ba a matsayin Janan sai matsayin 'yar aiki ku rik'a kallona tamkar 'yar aikin sannan kada ku nuna kun sanni koda wasa bare har wani ya gane zanje ne a matsayin 'yar aiki saboda yarona sannan kada ku k'ara albashina yafi wanda ya dace a bawa mai aiki idan har kun yarda nima na yarda idan har kuka sab'a zaka nemeni ka rasa Jalal"

"Gaskiya ban yarda ba bazan iya jurewa ba" Jalal ya fad'a a raunane.

Adnan ya dako har inda yake ya dafa shi yana fad'in "karka damu Yarima in har zata zauna cikin mutane da sauk'i"

Haka Adnan yayi ta bashi baki har ya hak'ura suka fita neman takardar sallama a lokacin Raihan ta matso inda take cikin b'acin rai ta fara magana.....







*_Ku min afuwa fans_*👏


_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
       *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁



*_by SaNaz deeyah_*👄





```Dedicated to Mrs Xerks & Safnah luv```


_Wannan shafin na sadaukar dashi ga beebah luv_✍

38

"Janan naga alama kina neman ruguza aurena to wallahi baki isa ba,zan miki warning ne, a 'yar aiki zaki zo to a ita nake son kizo bani son ko da wasa ki nuna wa Mommy kece Janan bare har ta ji tausayinki,dan babu yadda zanyi ne da wallahi baza kije gidana ba to amma da kije gidan da yace zai siya miki gwara kije gidana don kar ayi min sakiyar da ba ruwa"

Kallonta tayi tana murmushin takaici tana girgiza kai tace "bana mamaki maganganunki a kaina saboda na san ba ko wane d'an adam ya san halacci ba,bana tantama idan lubna ce bazata min haka ba" ta k'arashe maganar tana hawaye

"Karki fad'a min magana Janan dan wallahi yanzu zan wulak'anta ki,lubnar da tuni ta mance da tarihin rayuwarki k'ila ma bazata ganeki ba idan ta ganki kucaka haka"

Za tayi magana aka turo k'ofar duk suka mai da hankalinsu gurin.

Adnan ne ya shigo ya zauna yana fad'in "mun amso takardar sallama ki shirya nan da 5minutes zamu tafi"

Gabanta yayi mummunan fad'uwa amma babu yadda zatayi haka ta d'auki tsumman Abba k'arami ta goyashi ta zauna gefen gadon ta rafka uban tagumi lokacin duk sun fita.

Sai bayan mintuna 20 sannan ya dawo  yace ta fito su tafi.

Hawaye zafafa suka sauka a kuncinta a fili ta furta "Abba ka yafe min na kasa cika burinka akan lokaci amma nayi alk'awari zan tara kudi in shiga k'asar nijar ko rayuwa ta zata k'are a can sai nayi abin da ya kaini"

Kallonta ya tsaya yi tana ta goge hawaye wani na sake zuba.

Yana so ya rarrasheta amma bazai iya ba baya so ta gane shine,bai san tuni ta gane ba.


A mota ta tarar da Jalal da Raihan,ran Jalal d'in a had'e yake idanunsa a lumshe,sai da ta shiga motar sannan ya juyo ya kalleta sai kuma ya d'auke kai.

Adnan ne yayi driving amma fa zuciyarshi a cunsheta take tunanin janan ya rufe ko wane b'angare na zuciyarshi,kusan sau uku yana neman karawa mota Allah ne ya kaisu lafiya amma da sai sun koma asibiti jinya koma wani ya rasa nashi ran.

Duk tsawon tafiyar nan da sukayi babu wanda yawa wani magana sai karatu kawai da Adnan yasa a motar.

A Kaduna ma da suka tsaya cin abinci Janan k'in fitowa tayi daga motar haka da Jalal yayo mata takeaway tak'i ci.

Karb'ar Abba k'arami yayi ya rik'a bashi fresh milk har yasha ya k'oshi sannan ya mik'a mata.
Hakan ba k'aramin zafi yayi wa Raihan ba,ta kuma k'udurta sai tayi abinda zai sa Janan ta gudu daga gidan da k'afarta.

Sai gaf da magriba suka isa gida.

Mommy ji tayi tamkar ta had'iye 'ya'yan nata saboda farin ciki,tana son ganin 'ya'yan nata a tare da ita.

Sai bayan sunyi sallar isha'i sannan suka had'u a babban falo.

"Adnan wacece wannan kuma?"

Ya d'an gyara murya sannan yace "Mommy 'yar aiki muka sama miki"

" 'yar aiki kuma?a wane dalili?" Mommy ta tambaya tana kallon Janan.

"Mommy tana cikin wahala ne shiyasa muka ga ya dace mu taimaka mata gashi kema kina neman taimako kuma aiki yama Asabe yawa"

"Saboda aiki yama Asabe yawa shiyasa ka d'akko min 'yar aiki mai d'anyan goyo?akan wane dalili?to bana so saboda nida Asabe muna yin komai"

Gaban Jalal ba k'aramin fad'uwa yayi ba,ya kalli Mommy zaiyi magana tayi saurin cewa "karka ce komai Jalal ku mayar da ita inda kuka d'akkota"

Janan kuwa tuni idonta ya fara zubda hawaye ganin abinda tafi k'arfi yau gashi yafi k'arfinta.

"Mommy kota tafi bata da kowa wallahi dan Allah ki taimaka"

Cikin fad'a tace "to wai aikin me?ga Asabe gani ga Raihan sai kun d'akko wata da ban kuma ba tare da iznina ba,bazata zauna ba bana son rigima Adnan"


"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" Jalal ya fad'a sannan ya tashi ya shige ciki dan hawaye ke nemen fitowa daga idanuwansa.

Jikin ta a sanyaye ta tashi ta goya Abba k'arami tana shashshek'a.

Sosai Mommy taji tausayinta tace "zo nan baiwar Allah"

Jikin ta a sanyaye ta k'arasa gabanta ta durk'usa k'asa.

"Ina mijinki?meya rabaki da mijinki ko iyayenki a k'arancin shekarunki kike yawo a titi?"

Gabanta ba k'aramin fad'uwa yayi ba,kukanta na neman fitowa fili amma ta damk'e.

Ganin bazata fad'a bane yasa Mommy ta sake cewa "zaki iya aikin gidannan?kingan shi dai babbane sosai"

"Zan iya komai ma dan Allah ki taimaka min bani da inda zanje wallahi in har kika koreni to bansan madafa ba"

Adnan ya sunkuyar da kai yana goge hawaye,Raihan kuwa sai tab'e tab'en baki take.

"Raihan kirawo min Asabe"

"To Mommy" ta fad'a sannan ta tashi ta fita.

Tare da Asaben suka dawo,ta kalleta tace "ki tafi da wannan yarinyar d'akinki ku zauna tare zata rik'a tayaki aiki"

"Bak'uwa muka samu kenan,sannu da zuwa"

Kai kawai Janan ta d'aga.

Juyawa tayi ta sake tambayar Adnan jikin Jalal da k'yar ya rik'a amsa mata.

Har zasu fita tayi saurin cewa "af baki fad'a min sunanki ba"

"Indo" kawai sunan yazo mata a baki kuma ta furtashi"

"Okay" Mommy tace.


Dan kar Mommy ta gane shiyasa shima Adnan yayi saurin tashi yayi sama.
Anan yaci karo da Jalal wanda yana lab'e duk yaji komai.

"Adnan wallahi bana son Janan ta wahala bana son na ganta a wahale"

Dafa kafad'arsa yayi yace "Jalal tunda tak'i yarda tazo a Janan ya zamuyi wannan itace hanya mafi sauk'i da zata dawo kusa da kai"

Ranar babu wanda ya runtsa a cikin su ukun,Adnan,Janan,Jalal.
Raihan kuwa ji tayi kamar ta kashe kanta saboda kishi,ta kuma d'aukarwa kanta alk'awarin bazata bar Janan ta huta ba sai ta ta wahalar da ita da aiki.

Adnan kuwa ji yake soyayyar Janan tamkar sabuwa,amma sai dai bakin alk'alami ya bushe.

Janan kam bayan ta  kwantar da Abba k'arami a katifar ta kwanta ta hau aikin tunani da kuka.

Babban abinda yake bata mamaki shine wai ashe dama Salman shine Adnan wanda Jalal ya bata labari,mutumin da har yau babu wanda ta tab'a yiwa soyayyar da tayi masa,amma yau ita ya nuna bai gane ba saboda kawai rayuwa ta juya mata baya,dama ashe zuwan da yayi Kaduna guduwa yayi daga gidansu,to meye alak'arsa da inna? tunda ko lokacin data mutu bata ga wasu masu kud'i sunzo ta'aziyya ba.
Da wannan tunanin ta kwana a ranta.

Har saida tayi sallar Asuba sannan ta samu bacci mai nauyi ya kwasheta dama Abba k'arami ba mai yawan kuka bane.

Kamar daga sama taji ana d'an bubbuga k'afarta ta bud'e ido a hankali sannan ta d'an murjesu da hannunta,tashi tayi zaune tana kallon Asabe.
"Ba harara ta zakiyi ba,ki tashi bakwai har tayi kije kid'an goge falon zanje in had'a break fast ni kuma"

Murmushi Janan tayi tace "wallahi ba harararki nake ba idona ne a juye haka"

Murmushi itama Asabe tayi sannan tace "k'warai kuwa ga alama"

Girgiza kai kawai Janan tayi dan ta san bata yarda ba.

Kallon Abba k'arami tayi wanda har a lokacin bacci yake.

"Zan iya barin shi anan?"

"Eh idan har kinsan bazai tashi ba"

"Bara kawai na goyashi"

Goyashi tayi ta shiga toilet ta d'auraye fuskarta sannan ta fito ta d'an tsane fuskarta suka tafi.

A farfajiyar gidan ma sun tarar maza masu aiki sunata share share da bawa flowers ruwa kai tsaye suka nufi part d'in gidan.

Hawaye duk sun taru a idon Janan dan rayuwar gidansu ta tuna da taga kowa na aikinsa.

Suna shiga babban falo suka tarar da Adnan kwance kan kujera idonshi a rufe.
Sai da gaban Janan ya fad'i sosai ta rik'a Allah-Allah su wuce ba tare daya farka ba.

Suna zuwa daf dashi kawai sukaji yace "Asabe kun fito"

Duk suka kalleshi kuma har lokacin idon nashi a rufe yake.

Durk'usawa tayi tace "eh yallab'ai ina kwana"

"Lafiya k'alau ya kuka wayi gari?"

"Lafiya k'alau" juyowa tayi ta kalli Janan tayi mata signing kan ta gaidashi,kamar baza tayi ba sai kuma tace "ina kwana" bud'e idonta nashi yayi ya saukar da k'wayarr idonshi akan tata,tayi saurin sauke idonta k'asa.

Murmushi yayi yace "ya baby?"
"K'alau" ta amsa a tak'aice.

"Amma yallab'ai Allah yasa dai lafiya na ganka a falo a wannan lokacin?"

"Eh lafiya k'alau"

Tashi tayi suka wuce sai da sukaje kitchen ta kalli Janan cikin b'acin rai tace "ke yarinya wallahi bazaki ja min tashin hankali da salalon tsiya ba,ki kalleni ki gani kin san dai nayi jika dake ko?har ni na durk'usa amma ke ki gaidashi a tsaye,dan ma su ba mutane bane masu fad'a to ki kiyaye ni"

Ruwa ta had'a mata a d'an k'aramin bucket amma sai fad'a take,ta mik'a mata ruwan da towel tace "kije ki goge goge idan kin gama kiyi mopping saura kiyi masa hauka kinsan yana falon dai".

Karb'a kawai tayi ba tare da tace komai ba ta wuce.

Tana zuwa falon ta dire bucket d'in, sai a lokacin hawaye suka samu damar zubowa daga idanuwanta.

Center table ta fara goge wa tana yi tana share hawayen idanunta.

Adnan tashi yayi zaune yana shirin tambayarta dalilin kukan kawai yaji ance "lafiya na ganka a falo yanzu?"

A d'an tsorace ya juya ya kalli Mommy yace "eh lafiya lau na fita ne dana dawo kawai nayi branching anan"

"Fita kuma da sassafen nan"

Shiru yayi Allah ya taimakeshi Janan ta k'atse mata tambayar da gaida ta da tayi.

Cikin sakin fuska ta amsa sannan ta kalleshi tace "muje ka koma d'aki ban son zamanka anan"

_ko Mommy ta fuskanci wani abu ne?_ ya tambayi zuciyarsa lokacin da ta fara tafiya.
Da sauri ya tashi kawai ya bi bayanta,sai daya juyo ya kalli Janan yaga har lokacin kuka take.


*_10:00am_*

Suna zaune su hud'u akan dinning Asabe da Janan na cigaba da jera musu kayan abinci.

Jalal kawai sunkuyar da kai k'asa yayi dan bazai iya jurar ganin Janan a wannan hali ba.

Tsam Adnan ya tashi yana shirin tafiya Mommy tace "ina kuma zaka"

"Mommy bana jindad'i kawai a kawo nawa d'aki"

"Ikon Allah" ta fad'a tana kallon bayansa dan har ya wuce.

Raihan tayi saurin kallon Janan tace "ke indo d'ebar masa komai da komai kikai masa"

"To" kawai tace ba tare data kalleta ba.

Jalal kuwa kallon Raihan kawai yake cike da mamakin yadda ta murje ido tana bawa Janan command.

A k'aton tire ta had'a komai bata san ina bane d'akin amma da bala'in Raihan sai da ta nuna mata, ita a dole sai ta bak'anta mata.

Ajje tire d'in tayi ta fara knocking, sai da taji yace ta shigo sannan ta d'auki tire d'in ta shiga.

Ganin itace yasa yayi saurin tashi zaune.

Bata ce komai ba kawai ta ajje kan d'an table d'in ta juya zata fita yayi saurin cewa "ya akai Janan d'ita ta canza lokaci d'aya ta zama tamkar mara gata?"

Cak ta tsaya,lokacin  da taji mugun bugun zuciya.

Kasa bada amsar da tayi ne yasa ya taso ya dawo gabanta.

"Ya naga kina hawaye Janan?amsa ya kama ta ki bani"

Hannu ta d'aga masa tare da fad'in "ka fitar da sunan Janan a bakinka ka d'aukeni a matsayin indo 'yar aiki ka daina kirana da Janan"

Tsayawa yayi yana kallonta kawai,ta cigaba da shashshek'ar kuka tana fad'in "ka cuce ni Salman ka cuci soyayyarmu ka gujeni lokacin da nake buk'atarka a kusa dani,sai da rayuwa ta dawo mara amfani sannan na ganka,meyasa kayi min haka?zuciyata bazata tab'a yafe maka ba"

"Janan"
"Ya isa haka ka barni in fita kawai kar mutanen gidannan su fuskanci wani abu"

Tana k'ok'arin fita yayi saurin tare k'ofa idonsa yayi jajir saboda tashin hankali "Janan dole yau in sanarwa kowa abinda ke tsakanina dake duk da na san bazan iya aurenki ba saboda cutar dake tattare dani amma zan yi k'ok'arin samo miki farin ciki ta hanyar had'aki da Jalal dan na san zai kasance mai sonki kuma jigo a gareki"


Idanuwanta gaba d'aya sun fito waje saboda tsananin tashi hankali.

Bata san lokacin dana dafe kanta ba ta zunduma salati tare da rugawa a guje,shima a kid'ime ya bita,steps bibbiyu ta rik'a had'awa tana zuwa falo ta zube sumammiya,Abba k'arami kuwa ya k'walla k'ara gami da kukan rud'ewa yadda ya bugu sosai.

Su Jalal dake kan dinning duk suka mik'e.......











_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
          🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated to Mrs Xerks & Safnah luv```



39

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda Mommy da Jalal ke ambata.

A kid'ime Adnan ya k'araso gurin,d'ago kai Jalal yayi yana masa kallon tuhuma,da sauri Mommy ta kunce mata goyon ta rungume Abba k'arami.

"Mommy ya za'ayi?mu kaita asibiti" Jalal ya fad'a a rud'e.

"A'a kirawo doctor kawai"


*_2 hours later_*

A hankali ta bud'e idanunta ta kalli silin kawai hawaye na zuba ta gefen idanunta.

Mommy ta dawo gabanta "Sannu kinji"

Kallonta kawai tayi sannan ta kalli  Abba k'arami dake hannunta yana ta wasa da hannunsa.

Hannu tasa ta dafe goshinta tare da lumshe idanunta.

"Adnan muje zanyi magana da kai"

Gabanshi ya fad'i sosai amma ya daure yace "babu damuwa mommy"

Suna fita Jalal yayi saurin dawowa gefenta "Janan me aka miki wanda har yasa ki gigicewa haka?"

Kafeshi da ido kawai tayi bata ce komai ba.

"Kiyi min magana dan Allah"

"Ba Janan bace" shine abinda ta fad'a tare da d'auke idonta daga kallonshi.

"Dole cikin biyu ki zab'i d'aya,ko mommy ta san wace ke ko kuma mu samar miki gida ki cigaba da zama a ciki"

"Zan zauna a matsayin 'yar aiki idan har ka canza wannan matsayin zaka nemeni ka rasa Jalal"

"Meyasa Janan" ya fad'a yana goge k'walla ita kuwa bata iya bashi amsa ba.


"Ka fad'a min matsayin yarinyar nan a gurin ka ma'ana wacece ita?"

Kallonta yayi a d'an tsorace yace "mommy ban gane me kike nufi ba?"

"Ka san me nake nufi Adnan tunda da hausa na tambayeka"

"Mommy ni dai kawai ta bani labarin rayuwarta shiyasa naji tausayinta na taimaka mata"

" 'Kila ma k'arya ta shimfid'a maka ka hau ka zauna,amma har kake cewa kana jin tausayinta to ba zai yuwu ba tana fad'uwa mana a gida da yaro dubi yaronnan abin tausayi yanzu idan ya tashi yaga uwarshi a haka ai mu kanmu bazamu ji dad'i ba"

"Mommy dan Allah ki barta anan ko dan yaron nan nata muji tausayinta pls"

"Idan kuma matsala ta faru ban san kowa nata ba me kake tunani?"

"Ba abinda zai faru da yardar Allah"

" to shikenan Allah ya shige mana gaba"

"Ameen mommy"


Adnan kuwa ya samu Jalal ya fad'a masa cewar sai sun d'an ja baya da Janan saboda Mommy ta fara fahimtar wani abu.

Haka Janan ta cigaba da gudanar da aikinta a gidan su Jalal dan har ta fara sabawa da wahala gashi sam basa shiri da Asabe,Asabe ta takura mata sosai musamman idan Abba k'arami na kuka duk da ba mai yawan kuka bane amma in yana yi Asabe ta rik'a masifa tamkar zata daki Janan.


Kullun Abba k'arami yana hannun Adnan saboda shine baya zuwa office yana ta neman transfer zuwa wani garin anan nigeria dan Mommy tace babu inda zai koma, Mommy kuwa ta kan d'aukeshi itama idan ta fito falo,gashi sun tsaftace shi sosai.

Ita dai Janan har a lokacin tana tattare da jin haushin abinda Adnan yayi mata dan gani take shine silar fad'awarta tarkon Aliyu.

Raihan kuwa kamar yadda ta kudurta haka ta rik'a wahalar da Janan bata bari ko kad'an ta huta,da zarar Jalal ya bar gida to lokacin wahalarta ya fara kenan tun da shi Adnan baya shiga b'angarensu

Wasa-wasa yau satin Janan uku a gidansu Jalal.

Raihan d'in ce zaune akan sofa  tana shan lemo tana latsa waya, Janan na zaune tana goge kayan Raihan d'in da ta wanke.

"Hello lubna"
Jin Raihan tace haka ne yasa Janan tayi saurin kallonta,itama kallonta tayi tace "Dalla malama ki cigaba da gugar munafuka kawai"

Ranta ba k'aramin b'aci yayi ba amma ta daure ta cije ta cigaba da gugar tana satar kallon Raihan.

"Ke Raihan wa kike zagi haka"

"Ke dai bari k'awata kin san 'yan aikin yanzu akwai gulma"

"Hmm Raihan kenan to ya gida ya kike?"

"Lafiya lau Lubna ya amarci kuna can Spain dai ko"

"Ke dai bari har na fara zuwa skul"

"Dan Allah fa,ni Jalal yace min sai na haihu"

"Haba?ba dai kin kusa haihuwa ba?"

"A'a fa kinji ki wane haihuwa bayan da muka had'u kin ganni sak'ayau"

"Ah to na sani ne, kusan wata 8 rabona dake fa tun bikina"

"Ke babu komai sai 'yan hanji"

Daga b'angaren Lubna kuwa dariya tayi tace "wallahi ni kuwa kin ganni nan wata uku kenan"

"Dan Allah fa"

"Wallahi kinga kuwa yadda besty ke ririta ni da k'yar yake bari na tafi skul"

"Amma na miki murna Lubna Allah ya saka mu a danshinku"

"Ameen,k'ila in kin tashi ki haifo mana twins ko triple"

"Rufamin asiri Lubna ina zan iya d'ayan ma ya isa"

Dariya tayi kawai.

"Amma in kin haihu zakizo ko?"

"Eh yace da nayi 2months da haihuwa zamuzo ganin gida"

"Woww Allah ya kaimu,amma zaki k'araso Abuja ko"

"Eh mana me zai hana"

"Sai kinzo har kinga Janan ma"

Janan tayi saurin kallonta,itama Lubna ta d'anyi shiru kafin tace.

"Janan d'ita dai?"

"Ita dai wadda kika sani amaryar Aliyu"

"Kina nufin Janan dama tana Abuja?"

"Eh yanzun dai tana Abuja tana aiki a gidana kinganta yanzu ma guga take min"

Da yake handsfree ta saka Janan d'in najin yadda Lubna ke jira salati.

"Yanzu Raihan kina so kice Janan ta zama ''yar aiki a gidanki duk yadda muke da ita"

"Yadda kike da ita dai,nifa zan iya komai akan Jalal wallahi ko uwarshi ce take neman rabamu to zanyi k'ok'arin rabata dashi kafin ta rabamu"

Maganar Lubna da alamun kuka take fad'in "shiyasa kuka zab'arwa Janan aiki a gidanki kuma Jalal yana kallo,Lubna kin san Janan bazata tab'a auren Jalal ba tun da taga kina aurenshi"

"Zuciya bata da k'ashi,kuma Jalal baya so amma haka  tace ita bata son kowa ya san itace zatayi aikin kawai dan ta samu gurin zama"

"Amma Raihan baki yi halacci ba"

"Wannan shine Babban halacci tun da bance Janan bazata zo gidana ba,da yaronta haka muka ganta cikin k'azanta muka d'akkota muka mayar da ita mutum"

"Dan Allah Raihan bawa Janan wayar muyi magana"

"Ki fad'a tana jinki"

"Janan! Janan!!"

Kuka kawai Janan take tana cigaba da gugar.

"Karki yarda k'azamin hawayenki ya d'iga a kayana" ta fad'a tana kallon Janan sannan tace "Lubna kinga bafa zatayi magana ba"

Cikin kuka Lubna tace "dan Allah Raihan zan aiko miki kud'i kiyiwa Janan visa ta taho Spain dan Allah kimin taimakon nan"

"Kin san dai Umma bata son tarayyarku da Janan ko"

"Yanzu a k'ark'ashin mijina nake kuma ni in har Besty zai auri Janan mu zauna mu biyu zan jidad'i wallahi"

"To gaskiya kinyi k'ok'ari, kinga ki samu wani yayi mata ni bazan iya ba"

Ta katse wayar kawai.

Lubna nata kira amma tak'i d'agawa.

"Janan ki goge hawayen nan ki cigaba da gugar karki k'ona min kaya"

Goge hawayen tayi duk da bai daina zuba ba ta cigaba da gugar kawai.

Ta kusa gamawa Mommy ta shigo da Abba k'arami a hannunta.

Cikin girmamawa Raihan ta mik'e tsaye "Mommy naga kamar fita zakiyi ko"

"Eh wallahi zan d'anje unguwane"

Da sauri Janan ta kashe socket ta tashi tana shirin karb'ar Abba k'arami,Mommy tace "barshi indo dashi zan tafi"

Raihan taji wani bak'in ciki sosai,Mommy ta kallesu tace sai na dawo.

"A dawo lafiya" suka fad'a.


         **********

Rayuwar Umma da Ummi abin tausayi dan yanzu komai ya koma hannun Zuhra basu da iko sai nata.

Aliyu kuwa gaba d'aya ya zama mijin tace dan sai abinda Zuhra tace akeyi a gidan

Ita bata bin boka amma mamanta tazo ta hura mata wuta akan sai taje,ganin bazata je bane yasa ita Maman tayi komai da kanta.
Zuhra kuwa gani take ai kawai isa da iya kissa ne yake jan Aliyu.

Yauma Umma da Ummin na zaune a falo suna tattatunawa akan matsalar gidan.

Zuhra ce ta fito zata wuce amma sai da ta jefa haibaici "tsab'ar k'wawa da maita irin ta kura ina ita ina cin rub'eb'b'en nama kuma guntu  maimakon abar sauran namun daji suma su warwasa".

" hmmm" kawai Ummi tace dan ta san bata isa tayi magana ba.

Umma ce ta fashe da kuka ta fara fad'in "Allah ya isa ban yafe ba kin mayar da d'ana bawon ki kin k'wace duk wani kadarorinshi kin maida su naki ke kike juya komai,mun tsamo ki daga rana mun maidaki inuwa amma kina neman tura mu rana"

Shewa tayi sannan ta tafa hannu tace "oh Allah sarki Janan ita kuma ko tace me?ita bayan an rabata da tukiyar ta sai da aka rabata da ahalinta,banga laifina ba dan wannan shi ake kira da sata ta saci sata"

"Zuhra wai kin manta mu ne kike mana irin wannan furucin?"

"Janan ce da Umma uwar Aliyu mana" Zuhra ta fad'a.


_Dare_
*_10:30pm_*

Yana jingine da jikin gado ya tallabo wuyansa da hannayensa duka.

Zuhra na tsaye jikin mirrow sai da ta gama feshe jikinta da turare sannan ta juyo ta kalleshi tana murmushi tace "yau ma tunanin kishiyar tawa kake ko"

" 'Dago kai yayi ya kalleta ita ma ta d'aga mai gira sannan ta dawo gabanshi ta zauna.

" Aliyu lokacin yayi da zaka fara neman Janan tun da kana k'aunarta"

Murmushi ya d'anyi sannan yace "bana k'aunar kowa sama dake Zuhriyya"

Itama murmushin tayi sannan tace "na san kana k'aunar Janan nima kuma ina k'aunar ta dawo garemu"

"Ki daina min zancen Janan kin san ba so nake ba ko?"

"To kayi hak'uri amma maganarta dole ce"

Juyawa yayi ya kwanta kawai,tayi murmushi tana kallon shi dan ta san yana son Janan d'in dan babu yadda zaiyi ne.







_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
       🍁🍁🍁




_*by SaNaz deeyah*_👄




```Dedicated to Mrs Xerks & Safnah luv```





40

Yau misalin k'arfe hud'u da rabi Mommy na zaune a falo ita da 'ya'yan nata da Raihan duk kansu sun mayar da hankalinsu akan wani program da ake gabatarwa a Arewa24, Janan ce ta shigo tana sab'e da Abba k'arami a kafad'arta.

Dukkansu su ukun hankalinsu ya koma kanta.

'Karasowa tayi gaban Mommy ta durk'usa tace "Asabe tace kina kirana"

"Eh dama coconut juice nake son a had'a mana,kin iya?"

"Eh na iya"

"Yawwa kije kitchen na ajje komai a fridge, kawo Abba na rik'e miki shi"

Murmushi tayi tace "nagode" sannan ta mik'a mata ta tashi.

Har ta d'anyi taku kamar biyar sai Mommy tayi saurin cewa "Yawwa Janan ki d'anyi da yawa saboda ku"

Tun kafin ta kai k'arshe Janan d'in ta tsaya cak tamkar wacce aka zarewa laka.

Jalal,Adnan da Raihan kuwa sunyi mugun d'imaucewa.

Mommy ta mik'e tsaye tana fad'in "ya naga kin kasa tafiya kina mamaki sunanki na gaskiya daya fito daga bakina?"

Jalal yayi saurin mik'ewa tsaye zaiyi magana mommy ta d'aga masa hannu "dakata Yarima ka zauna karka fad'i dan naga ka tsorata "

Adnan ne yayi saurin cewa "Mommy abin ne ya bamu mamaki kin kirata da sunan da ba nata ba,ita fa sunanta Aysha indo"

"Gaskiyane Adnan, saboda kai ka haifeni bani na haifeka ba dole ka nemi yi min wayo"

Kallon Jalal tayi wanda har lokacin ya kasa zama tace "ka saki jikinka Jalal yau dai ga Janan d'in da kake ta yi min k'arya da ita,kun d'auka duk abinda kuke bana lura,ni dama tun da tazo jikina ya bani,dan naso in gane muryarta amma na manta ina na san muryar"

Ta kalli bayan Janan wanda har lokacin ta kasa motsa ko d'an yatsan ta,murmushi tayi sannan ta taka har gaban Janan d'in ta kalleta taga yadda hawaye ya wanke mata fuska sai kawai itama taji hawayen.

"Meyasa kika bari rayuwarki ta koma haka bayan da gatanki?"

Shiru babu magana sai shashshek'ar kukanta "Janan kin san bazan tab'a cutar dake ba ko?kuma tun lokacin da Jalal ya kira muka gaisa naji kin shiga raina,bazan tab'a cutarki ba Janan meyasa kika min haka?yanzu ba dan wata k'awarki Lubna ba da haka rayuwarki zata k'are Janan"

"Lubna" Jalal ya fad'a cike da mamaki.

Mommy ta kalleshi tace "eh tun da kai ka zama mace kana da rauni,ka kasa fad'awa mahaifiyarka gaskiya to ita Lubnar da ta damu da damuwar Janan ai ta kira ta kuma sanar da ni komai"

Raihan sai a lokacin ta mik'e dan ta tsorata sosai da maganar Mommy.

Hannun Janan d'in Mommy taja sannan Janan ta motsa.

Janta tayi har cikin d'akinta ta zaunar da ita gefen gado.

Sai lokacin Abba k'arami ya fara kuka yana mik'a hannu alamar ta d'aukeshi.


Kallonshi kawai take dan jikin nata babu wani k'warin da zata iya karb'arsa.

Mommy ta mik'a mata shi tace "ki bashi yasha k'ila yunwa yakeji"

Karb'arshi tayi kawai ta rungume sai kuma ta fashe da kuka mai tsanani.

Jalal,Adnan,Raihan da sauri suka shigo d'akin.

Raihan d'in ce ta k'arasa gabanta tana fad'in "Janan kiyi hak'uri ki sassauta zuciyarki tun ranar da muka had'u nake son gyara rayuwarki amma kika ce ke a dole sai dai kizo gidannan a 'yar aiki"

Ko kallon ta bata yi ba sai da tasha kukanta ta k'oshi sannan ta fara goge hawayenta.

"Adnan ku fita zamuyi magana"

"Mommy duk abinda ya shafi Janan ya shafemu dan Allah ki barmu kawai"
Jalal ya fad'a ranshi a cunkushe.

Adnan kuwa hawaye yake hannunsa rik'e da hankici idanunsa sun koma tamkar gauta.

"Shikenan" Mommy ta fad'a sannan ta k'ara dafa Janan tace "ki fad'a min labarinki Janan"

Ta d'ago harara garken idanunta ta kalli Mommy ta d'anyi shiru sannan ta fara basu labarin rayuwarta.
Wani gurin sai ta tsaya tayi kuka sosai sannan ta cigaba.

Bata b'oye komai ba a tarihin rayuwarta tun ranar da ta fara soyayya da Aliyu har zuwa yanzu,amma ta b'oye musu cewar Abba k'arami d'an Aliyu ne.

Kawai sai gani sukayi Mommy ta rushe da kuka.

Ganin haka ne yasa Jalal ya koma gefenta ya rungumota shima yana hawaye.

Sai da tayi kuka sosai sannan ta goge hawayen ta ta shafa kan Abba k'arami ta mik'a hannu ta d'auke shi.

"Janan kina nufin wannan yaron aljanna ce tayi masa wankan farko a duniya"

"Nima ita tayi min wankan jego na farko a duniya ta kawo min kunu da abinci ta bani zam-zam da dabino"

"Ikon Allah kenan"

Kallon Jalal tayi tace "yanzu kai har ka biyewa Janan dan tace idan baka yarda tazo a 'yar aiki zata gudu,kai kuma Adnan kaima ka biye musu"

"Mommy wallahi gani nake kamar da gasken zata gudu shiyasa"

"To ai yanzu Lubna ta kirani ta fad'a min komai tun had'uwarku da Janan har rabuwarku kamar yadda Janan d'in ta fad'a yanzu,yarinyar tana kuka tana bani labari tace min bata k'asar tana Spain amma zatazo ta tafi da Janan d'in,nace mata ta bar Janan a hannuna babu abinda zai faru da yardar Allah"

"Mommy munyi kuskure kiyi hak'uri" Adnan ya fad'a.

"Shikenan ya wuce a kiyaye gaba,yanzu zamuje a siyawa Janan kayan sawa da komai amma kafin nan ina son Jalal ka saki Raihan yanzun nan zan kuma saka bikinka da Janan da zarar ta yaye d'anta"

Duk kansu sun kad'u da jin maganar.

Raihan ta durk'ushe k'asa cikin matsanancin kuka ta fara magana "mommy ki rufa min asiri dan Allah, wallahi idan kika rabani da Jalal kamar kin rabani da farin ciki ne"

Janan ta durk'usa a gaban Mommy itama cikin kuka tace "kiyi hak'uri dan Allah wannan hukuncin yayi tsauri,Raihan k'awata ce bazan so na auri mijinta ba sannan na janye batun aure a yanzu kam bani da wannan burin"

Rik'o hannun Janan Raihan tayi tace "hakane Janan kowa ya san muna son junanmu ni dake"

Mommy bata ce masu komai ba ta sake kallon Jalal tace "ka saki Raihan nace ko baka ji ne"

"Mommy kiyi hak'uri,ina son Raihan,kuma ina son Janan duk kansu zan iya zama dasu"

"Jalal ba iyawarka nake nema ba kawai so nake ka cika umarnina" ta fad'a ranta a b'ace.

"Mommy dan Allah kiyi hak'uri tun da yace duk yana sonsu kuma zai iya" Adnan ya fad'a

"Shikenan" ta fad'a sannan ta tashi.

Kawai sai suka ga ta janyo trolley ta bud'e closet tana d'ibar kaya tana zubawa.

"Mommy lafiya?"

"Zan bar maku gidan tun da bani da wani iko akanku"

Shima Jalal hawaye ya fara yana fad'in "Mommy ban san dalilinki ba kin sa ni a duhu Mommy"

"Amma bazan tab'a cutarka ba ko?jiya fa da kunnena naji wayarta da k'awarta,ita kanta Janan ai tayi hak'urin zama da Raihan kawai saboda Jalal ta rik'a wulak'anta ta kamar bata san darajar mutum ba"

Sai kuma ta hau kuka tana basu labarin duk abubuwan da taji,da irin aikin da Janan kewa Raihan bayan ta san k'awarta ce"
Sannan ta k'ara da fad'in "banyi wa Raihan lab'e ba dan ban tab'a yiwa wani ba amma kawai danaji tace ko uwarshi shiyasa na tsaya"

Raihan kuka sosai take tana bada hak'uri amma ina ran Jalal ya b'aci haka ya figeta har falo.
Mommy ta d'auki Abba k'arami ta bishi,, d'akin ya rage daga Janan a tsugunne tana kuka sai Adnan dake zaune gefen gado yana goge hawaye.
Tashi yayi ya durk'usa gabanta yace "Janan ki yafe min dan Allah wallahi akwai dalilin daya sa nak'i dawowa gareki"

'Daga hannu tayi ba tare da ta kalleshi ba,alamu tayi masa na yayi shiru kawai.

"Janan ki fuskance ni dan Allah"

"Babu wata fuskanta da zan maka, kayi min k'aryar suna da asali sannan ka gujeni,wallahi kaine silar duk wata masifa dana fad'a da ba ka gujeni ba da haka baza ta faru dani ba,ban tab'a yiwa wani namiji irin son dana yi maka ba"

"Na san nayi kuskure dana gujeki amma ki sani nayi haka ne dan in bi umarnin Abba da yace in bar garin saboda ki manta dani dan yace bai shirya aurar dake ba,kuma ko an tashi aurenki bazai bawa talaka mara asali ba,na dawo gidanmu da niyyar in kin kai lokacin da Abba zai bada aurenki zanje masa da nawa asalin,watana shidda da dawowa na gane ina d'auke da cuta mai karya garkuwar d'an adam shiyasa a lokacin na nemi number Abba na fad'a masa cewar bazan sake dawowa ba yace miki na mutu saboda bazan iya aurenki da cutar nan ba,na kuma godewa Allah daya sa ban Aure ki tun a lokacin ba dana cutar dake"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un,ina zan saka rayuwa ta Salman to meye alak'arka da Iya?" Tayi maganar tana hawaye.

"Iya ita na fara had'uwa da ita ta taimakeni dan zuwa na garin kaduna bani da gurin kwana ita ta jani a jikinta kuma ta sanar dani an kashe kowa nata ita 'yar gudun hijira ce,gidannan ma taimaka mata dashi akai,haka na za me mata d'a har lokacin data koma ga Allah"

"Wa iyazubillah" ta fad'a tana kuka sosai.

"Dan Allah ki rage kuka Janan so kike ki rasa idanunki ki daina gani"

"Wallahi gwanda na daina gani dana zauna ina ganin wannan masifun ji nake kamar na kashe kaina na huta"

"Janan na miki alk'awarin zan nemo miki su Mameey in har suna raye a duniya sannan zan nemo wanda sukayi ginin nan a kaf fad'in duniyar nan in har suna raye ko mutum d'aya in aka samu alhamdulillah"

"Nima na maka alk'awarin bani da wani miji kamarka"

Gaba d'aya ya zare idanunshi tare da fad'in "haba Janan ni ba azzalumi bane bazan iya aurenki da ciwo a jikina ba,kuma ko babu ciwo bazan iya aurenki ba saboda naga yadda Jalal ke sonki kamar ranshi bazai tab'a cutarki ba"

"Na san haka Jalal na sona amma ni kai nake so kuma kai zan Aura"

"Kamar yadda na rik'e alk'awarin ki nak'i fad'awa Mommy kece Janan nima kimin alk'awarin ba wanda zaki fad'awa kece wadda mukayi soyayya ki ajje wannan a tarihinki bazan tab'a aurenki ba har abada,,da Jalal kika fi dacewa"

Da sauri ya tashi zai fita cikin kuka tace "kai nake so zan zauna da kai a duk halin da kake ciki kuma zan zauna da kai ko wane ciwo ne a jikinka sai dai in guduna kake saboda yanzu bani da wani gata"

Cak ya tsaya sannan ya juyo ya kalleta "ko me kika zama a rayuwa bazan tab'a gudarki ba saboda kece macen dana fara gani naji inaso har cikin zuciyata"

"Dan Allah ka fad'a min kana so na kace kana sona Salman"

Sai daya d'anyi shiru sannan yace "ina sonki har gobe amma babu zancen Aure ga macen da k'anina ke so,uwa uba bazan aureki ba bayan ina d'auke da cutar HIV"


Kuka ne yaci k'arfinta har ta kasa mayar masa da amsa.

"Jalal na sonki yadda bakya zato kuma zai rik'eki fiye dani,ki manta da cewa mun tab'a soyayya ki d'auke ni a matsayin yayan mijin da zaki aura" yayi sauri ya fice.

Ta k'ara rusa kuka tana bubbuga kanta da hannayenta.










_Sadeey S Adam_✍

🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
        🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated to Mrs Xerks & Safnah luv```





_*Safeenah Safnah ina kika shiga ne?😭abin kamar wasa babu ke babu labarinki,ya Allah kasa kina cikin k'oshin lafiya a duk inda kike,Allah kasa ina da rabon k'ara jinki a rayuwata🙏*_




41

Yana fitowa falo ya tarar Raihan d'in janye da trolley idanunta duk sun kunbura saboda kuka.

Mommy ta kalleshi tace "ina Janan d'in"

"Itama kukan take" ya bata amsa murya a dashe.

"Bara naje gurin Janan, Jalal ka tabbatar Raihan ta bar gidannan yanzu"

Da sauri ta wuce ta haye sama.


_2days later_

Tana zaune a falo tana d'an wasa da Abba k'arami.

Har lokacin bata gama sakewa da gidan.

Jalal ne ya fito hannunsa dauke da wata k'atuwar tidy ya zo ya ajjeta gaban Abba k'arami.
"Prince ga abin wasa kanaso"

Hannu yasa yana dukan tidyn yana gwalan-gwalantunsa na yara.

"Meyasa kika zaune ke kad'ai?"

"Babu komai na gaji da zaman d'akin shiyasa na fito nan"

"Oh ko nazo mu fita yawo?"

Murmushi tayi tace "a'a"

Shiru ya d'an biyo baya sannan tace "yawwa Jalal dan Allah ina son magana da kai"

"Ina saurarenki"

"Jalal dan Allah ka dawo da Raihan ka bawa mommy hak'uri"

Hmmm "Janan kenan banyi niyyar sakin Raihan ba amma abinda mommy ta fad'a ya b'atan rai sannan ni a halin yanzu bani da burin auren ko wace mace bayan ke,zan rayu nida ke da prince da sauran 'ya'yan da zamu haifa amma ban da wata mace"

"Kana nufin ka mayar da Raihan bazawara haba Jalal"

"Ita ta mayar da kanta ki daina ganin laifina Janan"

Shiru tayi kawai bata sake cewa komai ba.
A zuciyarta tana fad'in _zan yi k'ok'arin kwantar da hankalinka Jalal ka dawo da Raihan,amma ni kam bazan iya auren wani ba bayan ina ganin Salman_


Shima ranshi ya b'aci shiyasa yayi shirun.

"Soyayya ake in koma ko kuma hira ake in k'araso"

Duk kansu suka dubi Adnan da yake maganar.

Jalal ne yace "hira ake bros"

"In shigo kenan" ya fad'a yana tahowa.

Wata harara Janan ta dalla masa duk da harara garke take amma still ya gane harararshi take.

Murmushi kawai yake dan shi lamarin nata har ya fara bashi dariya.

'Daukar Abba k'arami yayi ya cilla sama sannan ya cab'e shi,shi kuma sai dariya yake.

"Abbana akwai fara'a" ya fad'a lokacin da ya zauna.

Jalal ne yace "bros kaji wai rok'ona take in mayar da Raihan"

"Wace ce ma Raihan? Oh wai wannan yarinyar cab ai mun gama da babinta"

"To kinji ko,aimu duk abinda mommy bata so muma ba sonshi muke ba"

Bata basu amsa ba kawai dai ta cigaba da wasa da yatsun hannunta.

"Yawwa na saka a bincika mana wannan masu ginin wanda suka gina gidan commissioner saboda haka a ko yaushe zamu iya tafiya nijar ka zama cikin shiri" Adnan ya fad'a yana kallon Jalal.

Ita kuwa a zuciyarta ta cigaba da fad'in Allah yasa a samesu cikin sauk'i.

"Maganar su Mameey fa?" Jalal ya tambaya.

"Duk tare na bada cigiyan,jiya tun safe nake yawo har gidajen radio na Kaduna da gidan tv duk naje"

"Allah ya bayyana su"

"Ameen"

Da sauri Janan ta tashi ta fita dan ji tayi hawaye na k'ok'arin zubo mata.

           ********

A kwana a tashi yau  Janan shekararta d'aya da wasa hud'u a gidansu Jalal, Asabe ta sakko sosai take girmama Janan musamman da taga yadda 'yan gidan ke k'aunarta,ita kuwa Janan tana son Asabe ta kanje ta zauna suyi hira ma sosai,tuni ta yaye Abba k'arami tun yana wata sha shidda dan yanzu wata biyu da yaye shi magana kuwa sai kace d'an shekara uku bakinshi rau-rau musamman in yana tare da Jalal ko Adnan.

Yana cewa Adnan Abba yana cewa Jalal daddy kamar yadda suka koya masa.

Yau gidan yayi katari da manyan bak'ine Raihan da besty.

Raihan suna zaune a falon Mommy shi kuma Besty yana falon bak'i tare da Adnan dan lokacin Jalal yana gurin aiki Adnan kuma ya samu hutu ne.

Bayan sun gaisa da Mommy ne ta koma bedroom tana shirin  fita unguwa.

Raihan ta rik'o hannun Janan tace "ni fa mamaki nake wai wannan balaraben yaron ke kika haifa"

Murmushi Janan tayi tace "to mamakin nlme,ance muna kama haskene kawai nashi yayi yawa ni kuma nayi duhu kinga kuwa ai kowa ya gani ya san nawane ko ta kamannima"

"Hakane amma har yanzu mamaki nake,dan har yanzu baki da wani k'iba ko dogon tsayin da za'ace kin haifi yaron nan sai naga kamar bazaki iya haihuwa ba"

"To yanzu ai kinga na haihun ko ke da kuka tsafe kikayi k'iba kuka haifo Affan har ya kusa shekara bakizo ba ai sai ki fad'an sirrin ko"

Dariya tayi tace "wallahi kuwa na zama wata uwar mata ko?"

"Eh mana"

"nima ba son kibar nake ba amma dai bana son irin ramarki Janan"

Hmmm "dan ma baki ganni lokacin ina garari ba,wai a hakan na yi k'iba"

"Cab an kwashe k'ibar an bawa Abba k'arami"

Ta d'anyi 'yar dariya tace "ke dai bari"

"Kin san me?"

"Sai kin fad'a"

"Raihan fa tayi aure"

Ta d'an tsorata sannan tace "dan Allah a ina?"

"Wallahi a Zaria ai babansu cewa yayi bazai yarda ta masa zawarci a gida ba tana gama idda ya had'ata da abokinsa itace ta uku"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un"

"Meye na salati sai kace an miki rasuwa?"

Ta d'an goge hawaye tace "naso ta cigaba da rayuwa da Jalal saboda tana sonshi sosai"

"Ke dalla ai Jalal naki ne wallahi dan yana matuk'ar k'aunarki"

"Ni kuwa Salman nake so"

Lubna ta d'an zare ido tace "ke Janan,ada ba"

"Har gobe wallahi"

Hmmm "lallai Janan karki zama mai butulci,wallahi da ace babu Jalal kika sake had'uwa da Salman nima zan ce ki aure shi amma ni tun da kika ce min Salman d'an uwan Jalal ne hankalina ya tashi na san za'a rina,gaskiya karki zama mai butulci Janan"

"Babu zancen butulci amma ba zan iya auren Jalal ba saboda bana son shi ni ai dama ban tab'a cewa ina son Jalal ba"

"Janan"
"Lubna"
"Karki yiwa Jalal haka dan Allah, ya sadaukar da rayuwarshi saboda ke amma kice kina son yayansa ya kike tunanin zaiji?"

Ajiyar zuciya tayi sannan tace "ni bana tuna komai sai girman so,kuma Salman nake yiwa shi"

Haka dai sukayi ta musu duk yadda Lubna taso fahimtar da Janan amma ta kasa.

Da zasu tafi ma a bakin mota Lubna ta sake fad'in "ki zama mai adalci Janan kada kisa yayi biyu babu ba wan ba k'anin"

Bata ce komai ba haka tayi sallama suka tafi da alk'awarin zata zo Kaduna kafin su koma.

Mommy lokacin bata nan da suka zo ta fita unguwa nan gidan mak'otansu anyi haihuwa ta fita barka ita da Abba k'arami dan haka gidan ya rage saura su biyu Asabe ma na d'akinta.

Suna shiga falo Adnan ya fara sauri yana son shigewa aikuwa tace "oh har guduna ma kake"

Juyowa yayi sannan ya dawo baya sai dayazo daf da ita yace "karki zama mara halacci kamar yadda Lubna ta fad'a"

"Rashin halaccin me nayi?"

"Idan har kika guji Jalal"

Shiru tayi tana kallonsa kawai.

Shi kuma ya cigaba da fad'in "Jalal d'an uwana ne ciki d'aya muka fito dashi dole in so abinda yake so kuma idan har kika gujeshi kin zama butulu,shekara da shekaru bai tab'a furta so ga kowa ba amma ke daya furta miki kina neman gudunsa"

"Ni ban gujeshi ba kuma in har na k'i aurenka ban yiwa kaima adalci ba saboda kai nake so"

"Idan har kika k'i amincewa da Jalal tabbas keda shi za kuyi biyu babu, ki rasani ki rasashi shi kuma ya rasa ki gashi ya rasa Raihan"

"Kana k'ina ne kawai saboda yanzu na zama k'ask'antacciya ga kuma d'a,kana son ka rama abinda Abba ya maka tun da nima a yanzu talaka ce"

"Bance haka ba Janan amma kinsan........"

"Kayi shiru kawai na san baka sona saboda wannan dalilan"

"Ina sonki Janan ban tab'a jin ranar da babu sonki a zuciya ta ba amma ba zan tab'a aurenki bayan ina da wannan cutar wannan shine kad'ai halaccin da zan miki,idan na aure ki da HIV a jikina ban miki adalci ba"

"Kaine mutumin dana fara so a rayuwata dan haka nima wallahi saina Shafa ma kaina cutar HIV tunda a kanta kake guduna,idan mun zama d'aya sai ka aureni,amma na san duk wanda zan aura bayan kai gangar jikinsa zan aura ba shi b........."


Turo k'ofar da aka yi ne ya saka tayi saurin juyawa a kid'ime,shima Adnan ya tsorata ainun.








*_Fans wane ya shigo?JALAL ko MOMMY?_*
    












_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
        🍁🍁🍁




_*by SaNaz deeyah*_👄




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




_*Wannan shafin sadaukarwace ga duk wani masoyin littafin nan*_😘😍
_#TARENE#🤝❤_



42

Adnan rud'ewa yayi ya kasa cewa komai  dan yana ganin yanayin fuskar Jalal ya san tabbas yaji komai.

Dariya Jalal yayi wadda iyakarta leb'e sannan yace "kuyi hak'uri na muku katsaladan na shigo kuna magana na katse ku"

Yayi saurin wuce wa side d'insa duk suka bishi da ido.

Janan ta goge hawayen idanunta ta kalli Adnan tace "Jalal yana da damar da zai zab'i macen da duk yake so amma kai baka da dama, hakan ne yasa zan jajirce dan ganin na samo maka farin cikin rayuwa,ina son na ganka da d'anka na kanka Salman"

"Me?ke! Janan ko dai kin fara samun matsalar kwakwalwa?"

"Koma me zaka ce kace amma ka sani ba zan auri Jalal ba kai nake so Allah ya sani ban tab'a son wani kamarka ba"

"Karki saka raina ya b'aci a kanki bana son samun matsala dake Janan na san Mommy tana ta shirye-shiryen aurenku da Jalal,ki duba irin d'awainiyar da yayi miki amma kawai rana d'aya kice baki son shi"

"Bana son Jalal kai nake so idan har naga ana shirin aura min wani ba kai ba to tabbas zan bar muku gida"

"Ba sai kin bari ba Janan"
Kawai suka jiyo muryarsa.

'Daga ido tayi tana kallonsa Adnan kuma ya juya gareshi.

"Jalal ka fahimceni dan Allah karka saka zargi a zuciyarka" Adnan yayi maganar.

Murmushin karfin hali ya sake yi sannan yace "babu zargi a ciki sai gaskiya,idan har kaine Salman d'in da ake fad'i kuma itace wadda kaje kayi soyayya da ita a Kaduna to tabbas tana matuk'ar k'aunarka dan Raihan ta bani labari,bros kai take so bani ba dan haka zata auri zab'in zuciyarta ba zab'in wata zuciyar ba"


"Bata da wani zab'i da ya wuce kai Jalal" Adnan ya fad'a yana kallonsa.

Tun kafin Jalal d'in yayi magana tayi saurin cewa "ni ban tab'a cewa ina son Jalal ba kai nake so kawai kana guduna ne saboda bani da gata"

"To kaji ta fad'a da bakinta,bata sona kai take so nine nake son ta,nayi kuskuren sonta da nayi,dan Allah bros ka nuna mata ita d'in mai gata ce,ka aureta kawai"

"Abinda ba zai yuwu ba"

Kukanta ne ya fara fitowa fili dan haka tayi saurin to she baki da hannu ta wuce d'akinta da gudu.

Shima Jalal hawayen idon nashi ya goge yace "Adnan kaine zab'in zuciyarta"

"Ka daina fad'ar haka Yarima dan Allah, wai taya zan auri lafiyayyar mace bayan ina da ciwo"

"Tace zata sakawa kanta idan har baka saka mata ba ina tausayin Janan bana so ta cutu ka daure bros"

"Na san fad'a take kawai ka daina wannan furucin Jalal"

Hmmm "na san halin Janan wallahi zata iya aikatawa,karka damu na san yadda zan sanarwa Mommy"

"Karka kuskura ka fad'awa Mommy zancen nan,bazai yuwu in auri Janan ba"

"Saboda me bayan da kunnena naji kace kaima kana sonta,kana k'inta a yanzu saboda kawai ina sonta,to ni na bar maka bros"

"Yarima......."
"Dan Allah ka bar maganar nan Adnan"

Da sauri Jalal d'in ya wuce ya bar Adnan a tsaye shi kad'ai.

Kan kujera ya zube dan ji yayi k'afafunsa ba zasu d'aukeshi ba ga azabebben ciwon kan daya fara ji.


Janan kuwa tana zuwa d'akinta ta zube a gado tana kuka mai tsanani ita tana tausayin Jalal amma bazata iya auren shi ba bayan tana ganin Salman.


Ta b'angaren Jalal kuwa yana shiga d'akin nasa ya zauna kan sofa tare da dafe kai.

_ni da Adnan duk munyi Aure mun rabu da matanmu,cikin ikon Allah sai gashi mun fara son mace d'aya ni dashi,wannan k'addararmu ce._
   Ya fad'a a zuciyarsa tare da goge hawaye.

Wata zuciyarce take ce masa _kai baka sha wahalar da Adnan ya sha ba,saboda kai ka fito da wadda kake so shi kuma auren dole aka masa kuma aka aura masa macen da ta zama sanadin cutarsa._

Ajiyar zuciya yayi wasu hawayen suka sake sauka a fuskarsa.
A fili ya furta "sadaukarwa ba abu bane mai sauk'i amma dole ne in barwa Adnan Janan,duk da na san ba zan manta Janan ba bazan tab'a daina sonta ba amma zanyi k'ok'arin manta cewa nayi soyayya da Janan tunda bata sona bazan so b'acin ranta ba ina son farin cikin Janan da Adnan"

Haka yayi ta surutanshi shi kad'ai yana hawaye.

Kafin Mommy ta dawo tuni suka manta komai,duk da dai taso ta gane Jalal amma still ya nuna babu komai harma suka zauna suna hira a falo Janan kuwa tuni baccin wahala ya kwasheta.


_*Dare*_

Lokacin da Mommy da Asabe suka gama jera komai a dining Asabe take tambayar Mommy shiru tun d'azu bata ga Janan ba.

Mommy tayi murmushi tace "ai ta fito nace mata ta komai dan naga kamar bata jindad'i"

"Oh ni dai ince yau babu abokiyar hira tun bayan tafiyar bak'inta,Abba kuwa dama sai dai yazo ya isheni da surutu mara ma'ana ko kuma yace inyi masa tatsuniya"

"Abba sarkin son tatsuniya"

Haka suka cigaba da 'yar hira daga bisani Asabe tayi musu sallama ta nufi d'akinta lokacin  Jalal da Adnan sun fito.

Bayan sun zazzauna Mommy ta kalli Abba tace "je ka kira Ammi kaji"

Da gudu ya haya sama ya nufi d'akin Janan.

"Ammi! Ammi!! Ammi" ya shiga da gudu tana kwance kan gado ya fid'a  jikinta yace "Mommy tace kizo abinci"

Rungumoshi tayi tana goge hawaye tace "kai kaci abincin Abba?"

Girgiza kai yayi yana fad'in "Mommy tace kizo"

Kallonshi tayi ta shafa kansa sannan tace "kace wa Mommy na k'oshi kaji,sai ka zauna Mommy ta baka ka ci sannan ka dawo na maka tatsuniya ai kana so ko?"

'Daga kai yayi yana murna sannan ya ruga ya fita.

Wasu hawayen taji sun sauka a kuncinta a fili ta furta "ina kunyar had'a ido da Jalal"

Tana kwance tana hawaye taji maganar Mommy a kanta.

Da sauri ta tashi zaune tare da sauke k'wayar idonta k'asa.

"Dama na san Akwai abinda ke damunki"

Shiru tayi kawai ta cigaba da hawayen.


"Me suka yi miki?"
Girgiza kai tayi alamar ba komai.

Zama Mommy tayi sannan tace "Janan nifa tamkar mahaifiyace a gareki karki b'oye min damuwarki"

"Bani da lafiya ne"

"Meya sameki?"
"Zazzab'i"

Ta d'an tab'a jikinta taji kuwa da zafi.

"Sannu,amma shine zaki b'oye min,bara na kira doctor a waya yazo ya dubaki"

Tashi tayi ta fita ita kuma Janan ta kwanta sai kuma ta fashe da kuka.



*_Few minutes ago_*
Tana kwance an saka mata drip,Mommy na zaune gefenta sai Jalal dake tsaye ya jingina da bango,Abba k'arami na jikinta yayi bacci ma,Adnan kuwa dama tuni ya fita.

Bayan doctor ya gama rubuce-rubucensa ya mik'awa Mommy takardar yace "ga wannan takardar sauran maganin da za'a saya ne,sannan a daina barin ta tana yawan damuwa saboda jininta ya fara hawa"

"Insha Allahu mungode doctor"

"Okay babu damuwa"

Bayan tafiyar likita Mommy ta sab'i Abba k'arami tace "bara na kaishi na kwantar sannan nayi sallar isha'i ka zauna wajenta kafin in dawo"

"Okay ba damuwa Mommy"

Bayan fitar ta ne ya kalli Janan d'in yace "dan Allah ki cire damuwa a zuciyarki haba Janan"

"Jalal kenan tun ranar da Aliyu ya aureni har yau ban sake ganin farin ciki ba,ina son d'an uwanka amma na san kai da sauran mutane zaku kalli abin a matsayin butulci saboda kana sona kuma ka fito ka fad'a"

Ji yayi zuciyarshi ta harba,sai da ya karanto inna lillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarshi sannan yace "karki damu dani da Adnan duk d'aya ne kuma tunda shi kike so baki da wata matsala,Janan ko wani kike so wallahi zan tayaki so kawai saboda ina son farin cikinki bare d'an uwana Adnan, kuma na san irin son da kike masa tunda an bani labari"

"Adnan baya sona saboda kai da kuma cutar jikinshi,yana ganin kamar baiyi ma kanshi adalci ba idan har ya aureni ni kuma wlh ko wace irin cuta gareshi zan zauna dashi a haka,Jalal dan Allah ka tayani cika burin raina"

Wani irin tartsatsi yake ji a zuciyarsa amma ya daure ya sake cewa "in Allah ya yarda baki da wani miji daya wuce Adnan ki cire damuwa"

"Adnan har ya fara guduna fa"

"Ba gudunki yake ba shima baya jindad'in jikin nasa"

Shiru tayi na d'an wani lokaci kafin tace "Allah ya bashi lafiya"

"Lafiya ta k'alau karka d'auramin ciwo yarima"

Juyowa yayi ya kalleshi sannan ya k'araso ransa a b'ace yace "tabbas gudunki nake saboda na gaji da maganganunki marasa amfani,idan mafarki kike ki farka wannan Adnan ne ba Salman ba,kuma ni ba butulu bane bazan tab'a aurenki ba wallahi idan har kika bari Mommy taji maganar nan ranki zaiyi mummunan b'aci"

Kuka sosai ta fara ganin haka ne yasa Jalal ya fara fad'a yana fad'in kar yaja ciwon ya k'aru.

"Ya k'aru mana sai me,akan me zata rik'a kawo min shirme,idan kinsan wannan maganganun zaki rik'a min kada ki sake min magana a gidannan bani ba ke"

Da sauri ya fice ya bar d'akin,aikuwa ta rik'a kuka tana shashshek'a tamkar k'aramar yarinya.

Sai rarrashinta yake amma ko kad'an tak'i ta rage ko sautin kukan.

Ganin haka ne yasa yaje ya kira Mommy, koda ta tambayi ba'asi sai yace bai san dalilin kukan ba.

Da k'yar Mommy ta shawo kanta,sai wajen k'arfe d'aya ta samu bacci sannan suma suka bar d'akin.

Duk sautin kukan nata a kunnen Adnan yake sauka yana jin kamar ana watsa masa garwashi a k'irjinsa,wai Janan d'insa dayaso yin rayuwa ta din din din da ita,Janan d'in da ta so shi ba dan wani abu nasa ba,Janan d'in data yarda ta d'auki cutar HIV saboda shi amma yau ita yaje yana fad'awa magana.
"Anya na yiwa kaina da Janan Adalci kuwa?" Ya fad'a a fili.

Zuciyarshi ta bashi amsa da _wannan shine adalcin da zakawa Jalal,kuma shine halacci,hakan kad'ai ne zaisa Janan ta cire sonka a zuciyarta._

Haka zuciyarsa tayi ta yawo da hankalinsa,sai yaji kamar yaje ya bata hak'uri sai kuma yaji ina bazai yuwu ba.

A haka har ya daina jin sautin kukanta.

Hakan ne ya bashi damar tashi yayo alwallah ya fara jera nafiloli har zuwa Asuba.













_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
        🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄





```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```





_Sai kun rik'a min uzuri kwana biyunnan banjin dad'i ,yau inada lafiya gobe bani da ita,addu'arku ce jindad'i na nagode da masu min addu'a koda yaushe😍_


43

Kwananta uku a kwance amma idan yaje dubata ko kallonshi bata yi.

Duk da hakan bata masa dad'i amma yana ganin haka shine mafi a'ala.

Yau suna zaune su biyu a falo suna hira Jalal yace "Mommy dama ina son magana dake"

"Ina saurarenka"

"Mommy game da Janan ne"

"Meya faru da Janan d'in?"

"Mommy ashe itace wadda Adnan yayi soyayya da ita a Kaduna tsawon shekara uku,mahaifinta yak'i aura mata shi saboda baya da asali itace wadda yazo yana bamu labari"

Cikin mamaki Mommy tace "kai ya akai kasan wannan?"

"Tun lokacin da suka had'u sun gane juna amma suka b'oyewa kowa yanzu kuma tace ita idan bata aureshi ba ta hak'ura da aure a duniya"

"Amma Jalal kai kenan dama bata sonka ko me?,yau nake shirin in aika gombe fa,ina son saka bikinka da ita wata d'aya"

"Mommy tafi son Adnan domin shine ta fara so kuma rabasu akayi,shi Adnan d'in ne yace baya son kiji dan bazai aureta ba"

"To dama taya ya zai aureta bayan yana da ciwo a jikinsa,bazai yuwu ba"

"Mommy tace wallahi idan bai aureta ba zata gogama kanta cutar ni ina ganin da tayi haka gwanda ai auren tunda ta san yana da ciwon tace zata zauna dashi"

"Wannan babbar magana ce,kirawo min Adnan da Janan a waya"

"To Mommy"

'Daga waya yayi ya kirasu duka sukace gasunan zuwa.

Janan ce ta fara zuwa saboda ita tana gidan.

Ta taho hannunta rik'e dana Abba k'arami,ta samu guri gefe ta zauna shi kuma Abba k'arami ya nufi gurin Jalal ya d'aukeshi ya rungume.

"Oh yau gurin daddy ko ba gurin Mommy ba"

"Mommy zaki min tatsuniya" ya fad'a yana dariya.

"Nak'i bazanyi ba"

Ya d'aga kai ya kalli Jalal yace "daddy zaka min tatsuniya ko?"

"Eh mana zan maka wadda tafi ta Mommy dad'i"

Dira yayi yana ta tsalle-tsalle a haka har Adnan ya shigo.

Zama yayi ya tank'washe k'afa yana fad'in "Allah yasa dai lafiya"

Ita dai Janan har lokacin kanta yana k'asa.

Mommy ta gyara zama tace "naji wasu maganganu ne shiyasa na tara ku dan jin gaskiyar lamarin"

Duk kansu shiru sukayi.

Mommy ta kallesu tace "ya kukayi shiru,Janan, Adnan ku nake saurare"

"Mommy duk abinda kikaji hakane"
Labari ya bata na duk abubuwan da suka faru sannan ya k'ara da fad'in "Mommy itace ta kasa fuskanta"

Kallon Janan tayi tace " 'yata zo nan"

Sai a lokacin ta d'ago,idonta duk ya cicciko da hawaye.

Tashi tayi jikinta a sanyaye ta koma gefen Mommy ta zauna.
Dafata Mommy tayi sannan tace "Janan kiyi hak'uri,kinsan bazan zama uwar banza ba,kinada lafiya bazaki auri Adnan ba,karki cuci kanki kiyi yunk'urin daurawa kanki ciwon da Allah bai jarrabeki dashi ba shi kanshi Adnan da k'addarar ta hau kanshi ji yake da da hali da ya raba kanshi da ita,kina son Adnan amma Allah ya k'addara bazai kasance mijinki ba,wallahi ina da yak'inin duk abinda kike nema daga Adnan zaki samu daga Jalal domin duk 'ya'yana ne na san halinsu kiyi hak'uri ku d'auki k'addara"


Hawaye sosai yake zuba daga idon Janan shikenan da gaske an haramta mata auren Adnan.

Kallon Jalal tayi tace "bikinku sati biyu na mayar,sai ka fara shirye-shirye"

Adnan ji yayi zuciyarshi na harbawa da sauri saboda tsananin tausayin Janan dashi kanshi ya k'udurta a ransa ana yin bikin zai bar k'asar.

            *********

Yana tsaye jikin wardrobe d'inta ita kuma tana zaune gefen gado ta had'e ranta kanta na k'asa ta k'i d'ago shi.

Jalal yayi ajiyar zuciya ya sake cewa "amma ya kamata ki saurareni Janan  nazo tun d'azu ina magana tamkar da iska nake"

'Dago kanta tayi ta kalleshi tana hura hanci tana fad'in "bana son jin kalamanka mara dad'i Jalal,mene amfanin bani hak'uri bayan kai d'in za'a aura min"

Sai kuma ta fashe da kuka sannan ta cigaba da fad'in "Adnan nake so shine Salman d'ina bana sonka ban tab'a sonka ba kuma bazan tab'a sonka ba,ko da ka aureni gangar Jikina ka aura amma zuciyata na gurin Adnan"

"Janan ni kike fad'awa haka?baki jin ko kunyar idona"

Mik'ewa tayi tsaye tana fad'in "idan tsoho baiji kunyar hawa jaki ba to jaki bazaiji kunyar yada shi ba"

'Daga hannu yayi cikin zafin rai zai mare ta sai kuma ya tsaya.

"Ka mareni mana ai ga kumatun nawa,ba yau ka fara marina ba ai bazanji komai ba dan ka d'ora daga inda ka tsaya,kuma wannan shine banbancin Adnan da kai saboda shi mai tausayi da kare mutuncin 'ya mace ne"

Idanunsa tuni suka sauya kala suka koma launin ja.

"Ka cuceni saboda da ka barni da ban ga Adnan ba bare har ya tado min tsohuwar soyayya data kwanta a zuciyata, nayi dana sanin sanin ka a rayuwata ka cuceni Jalal"

Ya bud'e baki zaiyi magana aka turo k'ofar.

Dukkansu suka maida kallonsu ga k'ofar.
Abba k'arami ne ya shigo hannunsa rik'e da Balloon.

Gurin Jalal ya fara zuwa yanan fad'in "daddy me aka yi wa Ammi?"

Muryarsa a can k'asa yace "bata da lafiya Prince"

"Abbana zo nan" ta kira yaron.

Komawa yayi gurinta ta rungumeshi tana goge hawaye tana shafa kanshi tana fad'in "Abbana wannan ba daddynka bane Uncle ne kada ka sake kiranshi daddy saboda kai baka da uba"

"Janan......."

"Dakata Jalal dole in sanarwa d'ana matsayinka a gurinshi saboda idan ka haifi naka zai fara ganin banbanci duk da dai ba lallai in haihu da maci amana ba"

"Ya isheki haka Janan na gaji da jin munanan kalamanki"

Mtsww "idan baka son ji ka fita daga d'akina bana son ganinka"

Ta k'ara rungume Abba k'arami tana kuka.

Da sauri ya fita ya shiga mota ya bar gidan ma gaba d'aya.

           *********

Da sauri ya d'auki takardu zai fita ta tsayar dashi "Muhasin ka tsaya kayi min bayani wai dagaske ne ko kuwa  dai kana fad'a dan ka kwantar min da hankali?"

Ya juyo ya kalleta yace "Momma wallahi da gaske nake,da kunne na naji labarin abinda yasa ma na gane itace saboda ta bamu labarinta,kuma na kira shi mutumin ya tabbatar min da Janan tana gidansu a Abuja,har ya bani address d'in gidansu dan yayi tunanin ko nasan wani abu daga mutanen da ake nema"

Wasu siraran hawayene suka sauka a kuncinta na murna.
Cikin farin ciki ta goge hawayen tana fad'in "idan kuwa har hakane bamu ga ta zama ba,gobe da sassafe zamu tafi Abuja kayi mana booking na jirgi sai mu tafi tare da Humaira"

"Momma nima ina son zuwa naga Janan"

"Zainab mijinki ba lallai ya yarda ba shima Muhasin ba zuwa zaiyi ba saboda ba zai tafi ya bar matarshi ba daga yin Aure"

Kallonta yayi sannan yace "Momma ai nine jagoran tafiyar"

"Kwana hud'u da yin aurenka sannan kace zaka tafi Abuja"

"Momma komai kamawa take ina son zuwa,dan haka zan mana booking jirgi ni dake da Humaira"

"Yaya Muhasin dan Allah dani nima"

"Ki kira mijinki ki tambayeshi idan ya yarda to"

Ai a gabansu ta kira shi tayi masa bayani tace saboda yanzu za'ayi booking ma in ya barta aikuwa ya amsa mata yace ba matsala tun da da Momma ne.

Murna da farin cikin da suke ciki bazai musaltu ba.

Muktar na dawowa yace shima zaije,Momma tace sunyi yawa ya hak'ura sai wani jik'on.

          *********

An karramasu a gidansu Jalal sosai duk da basu san ko su waye ba,a falon bak'i aka saukesu.

Mommy ta fito sun gaisa sannan tace "sai dai ban shaidaku ba"

Momma tayi murmushi tace "ni ce marik'iyar Janan,dan tamkar 'ya take a gurina tun b'atanta shekara biyu da watanni bamu sake jin d'uriyarta ba sai yanzu"

Mommy ta d'anyi shiru sannan tace amma Janan bata tab'a sanar dani tana da wata uwar rik'o ba"

"Karki damu in dai ta ganmu zata gane mu"

"Okay bara na kira muku ita" tashi tayi ta fita.

Zainab ta kalli Momma tace "ko me Janan ta haifa?na san har ya girma"

"Koma meye ai zaki gani,uwar surutu" Muhasin yayi maganar.

Murmushi tayi Humaira ma tayi saurin cewa "ni kawai so nake naga yadda Janan ta koma"

 Murmushi Momma tayi tace "na san Janan na cikin kwanciyar hankali tunda gidan manya take zaune"

Suna zaune Mommy ta shigo Janan d'in na bayanta.

Tana ganin Momma ta ruga da gudu ta rungumeta tana fad'in "Momma dama kece,ashe zan sake ganinku a rayuwata" Sai kuma ta fashe da kuka.

Momma ma kuka ta fara yi,sukayi ta kuka a haka Jalal da Adnan suka shigo.

Zazzaunawa sukayi ta cigaba da goge hawaye sannan ta kalli Muhasin tace "Yaya Muhasin ina yini ya hanya?"

"Oh sai yanzu ma kika ganni ko?"

"Yi hak'uri Yaya"

Tashi tayi ta koma kusa da Zainab da Humaira tace "Humaira ya karatu?"

"Alhamdulillahi shine kika gudu ko?"

Murmushi tayi mai had'e da hawaye sannan tace "gashi yanzu na dawo"

"Mun nemo ki dai"

Murmushi duk sukayi.

Adnan yace "ko kaine wanda mukayi Waya?"

Muhasin yace "kwarai kuwa nine"

"Ina cikin ki Janan?" Gabanta ya fad'i ta fara Allah-Allah kar su ce cikin Aliyu ne dan su kad'ai suka san gaskiyar lamarin.

"Na haihu har ya kusa shekara biyu,bacci yake bara na d'akko shi"

"A'a ki barshi ai muna garinnan har gobe zamu ganshi idan ya tashi"

"A'a Momma na san ya tashi ma"

Tayi sauri ta hau sama.

Tana zuwa ta tarar dashi yana ta wasanshi.

Yana ganinta da gudu ya rungumeta.

'Daukarshi tayi ta shiga toilet ta sake yi masa brush sannan ta fito ta canza masa kaya ta fesheshi da turaruka suka nufi k'asa.

Dukkansu sunyi mamakin ganin wai wannan d'an Janan ne.

Ga yana da son mutane dan haka wannan ya d'aukeshi wannan ya d'auka duk suka rik'a santin kyawunsa duk da yana fuzgen kama da Janan d'in.


"Amma Janan bayan tafiyarki ina kika nufa,na rik'a nemanki Janan kullum na tunaki sai nayi kuka,da naga an shekara sai nayi tunanin kin had'u da su Mameey ne" Momma tayi maganar tana sake goge hawayen da suka zubo mata.

Labari ta basu tiryan-tiryan tun da ta fara Adnan ya kafeta da ido dan yanzu Janan har tsoro take bashi.

Momma,Zee,Humaira hawaye sosai suke musamman Momma fuskarta tayi Jajir.

Ganin Janan na kuka ne yasa Abba k'arami shima ya rud'e ya fara kuka.

Mommy ta karb'eshi tana fad'in "kun tsorata yarona"

Rarrashinsa ta hau yi yak'i dainawa sai da Jalal ya karb'eshi ya sab'a a kafad'a yana jijjigashi.

"Momma" Janan ta matso gabanta sannan ta sake cewa "Momma wannan fa shine Salman d'in da nake ta fad'a muku"

"Oh shine Salman"
"Eh"
"Allah sarki da rabon zaku sake had'uwa kenan"

Murmushi tayi.
"To Allah tabbatar da Alkhairi naji dad'i da kika ganshi ko dan alk'awarin Iya da kuka d'aukar mata"

Jalal ji yayi zuciyarshi na harbawa.
_Janan kenan sam bata tunawa dani bare har ta bawa wasu labarina,lallai na yarda bata sona._

Adnan kuwa duk wani nauyi yake ji rayuwarshi a Kaduna ta dawo tamkar sabuwa.

"Saura sati d'aya bikinta da k'aninsa Jalal"

"A'a to Salman d'in fa?"

Murmushi Mommy tayi tace "ai da yake Allah ya k'addara sai abu ya faru bayan rabuwar Janan da Salman sai kuma suka had'u da Jalal"

Anan Mommy ta basu labari sannan ta k'ara da cewa shine yace ai duk d'aya ne ya barwa k'anin nasa"

"Allah sarki,Allah ya zab'a maka mafi alkhairi"

"Ameen"

"Amma Janan zaki bimu ki kwana biyu ko?"

Murmushin k'arfin hali tayi dan ta tsani a had'a ta da Jalal ranta duk ya b'aci.

"Zata zo bayan biki insha Allahu dan ina mata shiri ne"

"Laaa zata min k'wacen 'ya,nima ai shirin zan mata" Momma ta fad'a tana dariya.

"To aini anan har na biya kud'i an fara" Mommy ma tayi maganar tana dariya.

"To shikenan sai a bamu d'an Amana mu tafi dashi yayi sati in zamu zo biki sai mu taho dashi"

"Wannan kuje an baku amma zaku sha damu akan tatsuniya"

"Indai tatsuniya ce yazo gidanta"

Duk sukayi dariya.

Su Momma a gidan suka kwana,Humaira da Zainab d'akin Mommy,Momma ta kwana a d'akin Janan amma sai da suka raba dare suna hira anan ne Janan ta fad'awa Momma dalilin hanata Adnan da aka yi ta kuma gaya mata k'udirinta.

"Abinda Mommy tayi shine daidai Janan,Jalal ya miki halacci duk da dai Adnan kike so to amma Jalal shi yafi cancanta da zama mijinki koda Salman lafiyarsa lau"


"Hawaye ta fara tana fad'in " Momma dan Allah ki tafi dani ki auran Yaya Muhasin wallahi bana k'aunar Jalal dan shi ya rabani da Adnan"

Rungumeta tayi tana fad'in "wallahi yana sonki tun da mukazo yake d'awainiya damu,Janan karki nemi saka wa kanki ciwon da Allah bai saka miki ba"

Cikin kuka ta sake fad'in "alk'awarin dana d'aukarwa Iya fa"

"Wanna kuma ai k'addara ce tasa bazaki aureshi ba,Jalal yana k'aunarki kiyi amfani da damarki sai nan gaba zaki gane cewa mun miki gata"

"Wallahi Momma Adnan ma yana sona kawai dan dai ciwon nasa"

"To kin gani ki d'auki k'addara kamar yadda ya d'auka"

Kuka tayi tayi Momma na rarrashinta.

*_Washe gari_*

Da sassafe su Zainab suka shigo aka kafa sabuwar hira.

Anan ne suka fad'a mata Zainab d'in tayi aure watanta shidda,Muhasin kuma kwana biyar tayi musu murna tace "saura Humaira da Muktar"

"Kai aini yarinya ce l1 fa nake" duk sukayi dariya.

Momma tace "dama aike yarinya ce tsahon k'afa kikayi,Muktar ma anyi baiko"

Sai Janan taji tana son ta bisu Yola,Momma tace tayi hak'uri sai bayan bikin.


Haka ta shirya kayan Abba k'arami tsaf,k'arfe sha biyu suka bi jirgi suka tafi.

Duk kewarsu ta rufeta ga rashin Abba k'arami taji kewar d'anta sosai.

Da yamma tana kwance akan gado tana tunanin maganganun da sukayi da Momma akan Auren Jalal.

Wasu hawaye ne suka sauka a fuskarta a fili ta furta "ku yafe min Mommy da Momma wallahi  Adnan nake so"

Da sauri ta tashi ta bud'e drawer jikin mirror ta d'akko razor ta bud'e ta kalleta tayi murmushi mai d'auke da hawaye "yau da darasinki zanyi amfani Umma,na san zafin razor a farko, ana biyu kuwa bazata min zafi ba"

Ta goge hawaye ta cije leb'enta tace "Jalal bana sonka kar kuma kasa in soka dan kawai ka taimakeni,kowa yana ganin kamar idan na gujeka nayi rashin halacci,to wai shin ina ruwan soyayya da halacci,kawai tana son wanda take so ne,dan haka tunda ank'i aura min zab'ina saboda ciwon jikinsa na san in muka zama d'aya zasu auran shi,yau zanwa tumk'ar hanci"

Da sauri ta fita tana goge hawaye.








*_Comments d'inku kawai zan saurara dan jin ra'ayoyinku readers._*
  










_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```





44

Kai tsaye d'akin Adnan ta nufa.

Tana tura k'ofar ta tarar dashi zaune akan sofa ya d'ora hab'arsa akan gwiwarsa.
Idanunsa akan plazma dake manne jikin bango amma a zahiri ba kallon yake ba.

Shigowarta yasa shi juyo kai ya kalleta.

Wasu zafafan hawaye ne suka sauka a fuskarta ta kalleshi tace "Adnan alk'awarin Iya dan Allah ka zamo mai halacci da adalci"

"Wannan ne iya adalcin da zan miki Janan,wannan shine zai nuna wa duniya cewa ina son ki kuma bana fatan cutar dake daga ke har Jalal,wallahi da kinsan irin son da Jalal yake miki da baki nuna masa k'iyayya ba"

Cikin kuka tace "kenan kai baka sona Adnan?"

"Ina son ki mana amma Jalal shi yafi cancanta da ke"

"Oh kenan idan da babu ciwo bazaka Aure ni ba saboda Jalal?duk irin son dana nuna maka?"

"Da babu ciwo a jikina babu abinda zai hanani aurenki Janan"

"Shikenan zan wa tufk'ar hanci yanzu"

Kafin yayi magana ta kai razor nan ta yankin hannunsa.

Yaji azabar zafi,amma a fusace ya rik'o hannunta dan karta aikata abinda take shirin aikatawa,aikuwa ta bank'are hannun cikin zafin nama ta yanke razor a cikinta.

Wanin azababben k'ara ta k'walla hakan bai hanashi d'aga hannu ya wanketa da mari ba.

Hawaye gaba d'aya ya wanke mata fuska hannunta rik'e da kuncinta wani jiri-jiri take ji.

Shima hannun nasa ya rik'e yana hawaye ya kasa tab'uka komai.
"Kin cuci rayuwarki Janan" ya fad'a a can k'asan mak'oshinsa.

A haka Jalal da Mommy suka shigo.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" Mommy ta fad'a tare rik'o Janan d'in da take k'ok'arin sumewa,jini gaba d'aya ya wanke mata gaban rigarta.

Jalal ya tsaya cak ya kasa motsawa wasu hawaye ne kawai ke fita daga idanunsa.

Mommy ta juyo a rikice tace Jalal muje asibiti.

Jikinsa a sanyaye ya juya zai fita tayi saurin cewa "Jalal bazan iya d'aukanta ba"

A sanyaye ya juyo ya d'auketa a sume kamar gawa ya fita.

Mommy ta kalli Adnan tace "tashi mu tafi ga yadda jini ke zuba a hannunka"

'Dago ido yayi ya kalleta yana hawaye yace "Mommy zan wanke da spirit ku kaita kawai"

"Haba Adnan idan kai baka san ciwon kanka ba ni na sani"

"Mommy kunyar had'a ido da Jalal nake"

"Adnan ka bar maganar nan ka tashi muje kawai,wai baka san ciwon kanka bane"

Jikinta a sanyaye ya  bita.

Har zata shiga baya Jalal yayi saurin cewa "Mommy dan Allah kiyi driving wallahi bani da wani k'arfin da zan iya yi"

Tausayinsa sosai taji ta karb'i key d'in maigadi ya bud'e gate d'in aikuwa a guje taja motar.

_*Asibiti*_

Suna zaune a office d'in likitan yana sake musu bayani.

Jalal kanshi a k'asa yake ya dafe goshinsa da hannu.

Adnan na tsaye rik'e da hannunsa da yasha bandage.

"Ya akai har hakan ta faru?"
Likita ya nemi k'arin bayani.

Adnan ne ya fara yi masa bayanin yadda abin ya faru,tunda ya fara magana Jalal d'in ya kafeshi da ido har ya gama.

Shi kanshi likitan salati yayi tare da girgiza kai.

"Doctor yanzu shikenan itama ta kamu da cutar?mun zo nan ne saboda kaine family doctor namu na san bazaka tab'a yi mana k'arya ba" Mommy tayi tambayar.

Gyara zama yayi yace "to yanzu dai duk test d'in da muka mata babu wanda ya nuna mana cewa tana da cutar a jikinta amma babu makawa ta kamu da ciwon tunda a lokacin ta yankeshi ta kuma yanki kanta,da ace razor tayi 15minutes sannan ta yanka kanta to babu wani abinda zai faru,sai dai bazamu tab'a tabbatarwa ba har sai nan da wata uku lokacin ne idan munyi test in dai ta kamu da ciwon zamu gani dan haka zamu d'orata akan magani kafin lokacin"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda Jalal yake ta nanatawa yana goge hawayen dake zuba a fuskarsa.

"Doctor ai magana ta k'are tunda har kayi bayani,sai dai kawai nan da wata uku mu dawo a d'orata akan magunguna na masu ciwon"
Mommy ta fad'a a sanyaye dan ita kanta dauriya take.

"Karki damu hajiya,zasuyi rayuwarsu kamar yadda kowa keyi tunda haka ta zab'a,amma fa sai dai bazata shayar da yaron ba sai dai da madara karki damu komai Jarabawa ce daga Allah"

"Na Janan sakaci ne da rashin jin magana" Jalal ya fad'a sannan ya tashi ya fita.

'Dakin da aka kwantar da Janan ya shiga.

Idanunta a rufe suke,bedsheet rufe da jikinta har zuwa wuyanta.

Jikin gadon yaje ya tsaya yace "ban tab'a tunanin tsanar da kike min ta kai haka ba Janan,har ki sakawa kanki cutar HIV saboda kawai karki aureni,ni dai na san son da nayi miki so ne na gaskiya na so ki tsakani da Allah da kuma zuciya d'aya,bana bak'in cikin auren Adnan da zakiyi amma ina bak'in cikin abu biyu ciwon da kika sakawa kanki da kuma rashin ki da nayi a rayuwa"

Ya d'an tsaya yana goge hawaye sannan yace "zan nisanta dake Janan saboda bana son in fara tsanarki kamar yadda kika tsaneni"

Juyawa yayi zai fita yaji tayi magana.
Da sauri ya juya ya kalleta.

Idanunta a rufe suke amma still hawaye na zuba.

"Jalal wallahi ban tsaneka ba,kawai bana sha'awar kasancewa matar wani in ba Adnan ba,shi nake so shina fara so a rayuwata,kayi hak'uri Jalal"

Fita kawai yayi da sauri ya bar d'akin.

Satinsu guda suna jinyar Janan, Adnan sam baya zuwa saboda haushinta kawai yake.

          ***********

"Lallai samu guri kenan,waye ya bawa wannan tsofaffin damar shigowa falona?"

'Dago kai Umma tayi ta kalleta tace "Zuhra kin san kuwa suwa ne wannan?"

"Koma su wane bai dameni ba kawai a fitar min daga falo bana son tarkace"

Cikin b'acin rai baba Isa ya tashi ya kalleta yace "idan ubanki ne zaki fad'a masa haka?"

"A'a dakata baba,ina ganin girmanka kada ka sake sako mahaifina"

Juyawa yayi ya kalli Umma wadda tayi tsumu-tsumu yace "wannan itace surukar taki dana sani ko kuwa musaya ne?"

"Itace wallahi ai yanzu ta gagari kowa a gidannan sam bata ganin girmana"

"Lallai kuwa dole muyiwa tumk'ar hanci,idan Aliyu ya dawo lallai kice ina nemansa" baba Idi da tunda ta fara rashin mutumcin ta baiyi magana ba sai lokacin.

"Ni fa ban sa daku ba ya kamata ku rufamin bakin nan naku da yayi dumu dumu da goro"

"Iyeee lallai na yarda Alhakin yarinyar nan ke binki Isa wuce mu tafi"

Ransa a b'ace suka wuce Zuhra ta bisu da fad'in "Umma ta gaida Assha"

"Lallai Baki da mutumci Zuhra kuma idan kikace dani zaki ja tabbas zaki zubda hawaye"


Dariya tayi ta tafa hannu tace "ahayye ayi mu gani mana idan sabulu zai daina kumfa,ai ga fili ga mai doki"

Wucewa tayi ta barta a tsaye.

Hawaye suka sauka a idon Umma a fili ta furta "lallai nayi sakaci dana har Aliyu ya saki Janan ashe dama Zuhra bata da mutumci"

'Daga hannu tayi tana fad'in "Allah ka kawo mana sassauci,ga dukiya sai k'ara hab'aka take amma babu kwanciyar hankali ina dalili"

         **********

Suna zaune su duka a bedroom d'in Janan,Mommy ta kalli Jalal da Adnan tace "dan Allah ina neman alfarma a gurinku"

Duk sunyi shiru basu ce komai ba ta cigaba da fad'in "koda wasa kada ku bayyana cewa Janan nada wannan cuta dan Allah saboda mutane da kuma yaronta mu rufawa kanmu asiri"

Ta kalli Janan tace "ko Asabe ban yarda kin fad'awa ba ki rufe sirrinki"

"Mommy insha Allahu babu wanda zai ji wannan maganar daga bakina" Jalal yayi maganar.

Adnan kuwa ya kasa cewa komai,tausayin d'an uwan nasa kawai yake.

Idon Janan a k'asa duk kunyarsu ta hanata kallonsu.

Bakinta na rawa tace "dan Allah Mommy kiyi min izni in koma Yola gurin Momma"

Kallonta ta sakeyi tace "Janan babu inda zaki je har sai bayan bikinki kamar yadda na fad'a,karkiji nauyina ni tamkar mahaifiya ce a gareki"

Kallon Jalal tayi tace "Mai martaba yana nemanku nayi masa bayanin da Adnan za'a had'asu tun jiya mukayi waya yace abar bikin nan da wata d'aya zai samu sauran 'yan uwa yayi musu biyani a fara shirye-shirye sannan yace yana son ganinku dan haka Ku shirya a wannan week d'in kuje"

"Insha Allah" Jalal ya amsa.


_3 weeks later_

Tana zaune a falo ita kad'ai ta zabga uban tagumi,rashin kulata da Jalal keyi abin na d'aga mata hankali,gashi ko magana tayi masa sama-sama yake amsawa.
 Adnan ya sakko daga steps fuskarsa d'auke da fara'a ya k'araso kusa da ita.

"Ya dai naga kin zabga tagumi?"

'Dagowa tayi ta kalleshi idanunta d'auke da hawaye.

"Kinji matsalarki fa wannan hawayen na mene ni na fito ina murna"


"kin san me?an samu wanda suka yi ginin nan shiyasa na fito kuma yanzu muka rabu da Jalal ya fito yace gurinki zaizo"

Tun kafin ya gama maganar ta mik'e tsaye tare da fad'in "da gaske ko wasa Adnan?"

"Wallahi dagaske nake"

 "Adnan suna ina yanzu"

" 'Daya daga cikinsu yana kano cikin wata unguwa Kuntau yayi min kwatancen gidan ma"

"Allah na godema" ta fad'a tana hawaye.

Da sauri suka nufi d'akin Mommy aka sanar mata.

A take Adnan ya sake kiranshi sukayi waya da Mommy tayi masa godiya sosai tace insha Allahu gobe Suna kan hanya.

Jalal ma daya dawo yaji labarin ba k'aramin farin ciki yayi ba.


_Washe gari_

Tun k'arfe takwas suka shirya suka nufi kano.

K'arfe 1 a kano ta musu,kasancewar Adnan yayi zaman kano unguwar bata musu wuyar samu ba.

Bayan sun huta ne mutumin mai suna Sule ya sake yi musu bayanin komai,ya sanar dasu cewa jibi ma ogan nasu zai zo dan baya nijar d'inma yana chadi amma da yaji labarin ne yace insha Allahu yana nan tafe.

"Babu damar muje kadunar yau?in har kai ka gane gurin da aka safe bishiyar" Jalal yayi maganar

Murmushi yayi yace "a'a ai shi ogan namu zanan gidan yana gurinsa da yadda ya zana tun kan a gina da kuma bayan an gina komai dai shi zai nuna saboda muma bamu muka sare ba  wasu aka kira mu gini kawai mukayi kuma shekarun da yasa ba lallai na gane gun ba"

"Ba damuwa Allah yasa mu dace" Mommy ta fad'a.

"Ameen"

Sai kusan la'asar sannan suka fito zasu tafi,ya fito shi da matarsa da 'ya'yansa suka rakasu har mota,Jalal nata musu godiya.

A daidai makaranta kuntau shagunan dake gefe nan taga Fahad zaune kan benci kamar a mafarki.

"Inna lillahi......" Ta fad'a a tsorace.

"Lafiya Janan?" Suka tambayeta

"Jalal dan Allah kayi parking"

"Meya faru?"

"Dan k'aunarka da annabi (SAW) ka tsaya"

Da sauri yayi parking d'in,ta fita da gudu suka fito suka biyota.

Bata kula da mazan dake tsaye da Wanda ke zaune a gurin ba da k'arfi tace "Yaya Fahad kai d'in ne dagaske?"

A dai dai lokacin su Mommy suka k'araso.

Kana ganin Fahad kasan yana cikin wahala da talauci.

Kallonta ya tsaya yi kamar bai santa ba.

Juyawa tayi ta kalli Mommy tace "Yayana ne fa" wasu hawayen suka sauka a idonta.

Mutane aka hau magana k'asa k'asa.

"Taya ban sanki ba zaki zo kina neman tara min mutane?"

Baki ta saki tana kallon sa.

"Kaine Fahad nima na shaidaka" Jalal ya fad'a yana kallonsa.

"Tabbas Fahad ne dan kamanninsa basu canza ba" Adnan ma ya fad'a.

Kallon Adnan da Jalal da Janan yake duk ya rud'e dan abin mamaki yake bashi.
_dama Salman bai mutu ba meya had'asu su suka tare?._  shine abinda zuciyarsa ke furtawa.

Janan ta sake fashewa da kuka tana fad'in "wane laifin nayi muku Yaya Fahad me nayi muku kuka tsaneni kuka gujeni"

"Dalla malama b'ace min da gani a ina kika sanni" ya fad'a ba dan ransa yaso ba,sai dan yana ganin ita ce silar shiga damuwarsu.

'Daga yatsa tayi ta nuna shi cikin karaji tace "Kaine na ratse kaine Yaya Fahad me nayi muku kuk........" Bata k'arasa ba ta zube k'asa sumammiya.

A gigice Jalal da Adnan suka sunkuya zasu rik'ota Fahad yayi saurin tallabota yana kuka yace "Janan ki tashi muna sonki dole ce yasa muka gujeki,dan Allah Janan ki tashi"

"Muje asibiti mana"
Adnan ya fad'a a rud'e.

"A'a gidanmu babu nisa muje can kawai mamanmu tana nan" ta sauri ya saka ta a kafad'a ya wuce suka bishi.









_Wai! Cab! ya Mameey zataji idan taga Janan?,dan ma a sume za'a kai mata ita._


_Ku biyoni dai cikin wannan littafi_📝











_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
       *DIREBAN GIDANMU*
          🍁🍁🍁




*_by SaNaz deeyah_*👄




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```






45

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un,Janan nake gani"

"Itace Mameey" ya fad'a lokacin daya shimfid'eta akan carpet d'in tsakar d'akin,ya shiga ciki da sauri ya d'akko fulo.

Mameey tsire Jalal da Adnan tayi da ido a d'an tsorace tace "dama baka mutu ba Salman?to ina kuka had'u da Jalal na kuma ganku da Janan ina kuka samo min Janan a sume?"

"Mameey a d'ebo musu ruwa tukunnan" Fahad ya fad'a.

"A'a mungode a k'oshe ma muke"

Jalal ya goge hawayensa daya ga yadda suke a wahale kamar basu ba.

Adnan kuwa zuciyarshi zafi take kukan zuci kawai yake.

A hankali Janan d'in ta bud'e idanunta ta dire su a fuskar Mameey aikuwa ta fashe da matsanancin kuka.

Mameey ta taso tazo kusa da ita ta zauna,da sauri Janan ta matsa gefe.

"Janan guduna kike?" Ta fad'a tana zubda hawaye.

"Mameey gudunki nake saboda baku k'auna ta kuma,kuka gujeni kuka sani a k'unci da matsananci hali kuka k'i waiwayata bare ku ga halin da nake ciki"

Da sauri Mameey ta k'ara matsawa kusa da ita ta rungumeta suka k'ara fashewa da kuka.

"Ban gujeki ba Janan taya zan gujeki wallahi bana k'aunar ganin Aliyu shiyasa na tafi"

"Amma Mameey aka rasa wanda zai sanar dani mutuwar mahaifina har sai da yayi kwana uku,shima ba dan nazo Kaduna ba da bazan sani ba"

"Janan muna cikin tashin hankali wa zai iya zuwa bak'in k'auyen nan?ina zamu je gidan mak'iyanmu gashi baki da waya,kiyi hak'uri Janan wallahi na tsani Aliyu"

"Mameey na fiki tsanar Aliyu saboda yayi min babbar illa ya cutar dani ya cutar da innocent Abba wallahi ban tab'a ganin azzalumin mutum kamar Aliyu ba"

'Daga kai tayi tana kallon d'akin wanda babu komai sai wannan carpet d'in dake shimfid'e a k'asa.

Idanunta sun k'ara jujjuyeta ta kalli Mameey tace "wai anan kuke rayuwa Mameey?"

"Eh anan muke tun bayan barinmu Kaduna da wata biyar muka dawo nan"

"A wata biyar d'in nan kuna ina?kafin ku dawo nan?"

"Muna Zaria,bamu da gidan zama tamkar almajirai haka duk inda muka samu muke kwana,Fahad yana zuwa yayi dako ko aikin k'arfi ya samo mana abinci,Janan takardar sallama aka bawa Fahad ko biyar ba'a barmu da ita ba,sai kud'i a hannun Fauziyya dubu biyu dashi muka fara amfani da suka k'are muka zauna a haka,Janan har a bakin juji mun kwana ruwa yayi mana duka,haka Fauziyya ta fara rashin lafiya tamkar bazata rayu ba"

Kuka sosai ta rushe dashi tana fad'in "Allah ka mana sakayya"

Mommy, Adnan da Jalal ba wanda baya hawaye a gurin.

"Kuma baku nemi 'yan uwa ba aka taimaka muka ta side d'inki ko Abba?"

"Fahad yafi sau a k'irga yana zuwa gidan bashar lokacin da Fauziyya ta fara rashin lafiya,sai suka ce muma lokacin da muke dashi bama nemansu dan haka babu abinda zasu iya mana,ko gurin kwana hanamu sukayi dana ga haka sai na hak'ura da zuwa gidan kowa,iyayenmu sun mutu dama sune dolen namu"

Kuka sosai Janan take tana cewa "babu wanda ya kai uncle bashar morar kud'in Abba amma yanzu saboda babu ranshi sun gujemu"

"Wallahi kuwa Janan,a haka naga Fauziyya na neman mace min na kaita asibiti bani da ko sisi,da k'yar aka samu d'ari a hannun Fahad aka siyo file,an bada gado amma babu kud'in biya,haka muka shafa kusan awa goma a opd muna rok'ar likita ya bamu gado ni da kaina zan fita neman kud'i amma suka k'i yarda"


"Ganin numfashinta nayin sama-sama ya saka ni zama a gurin ina kuka,sai a lokacin wani bawon Allah yazo ya biya dukkanin kud'ad'en"

"Watanmu guda muna jinyar Fauziyya ashe cutar ulcer ce ta kamata,wannan bawan Allah mai suna Sagir shi yayi ta d'awainiya damu har ta warke"

"Anan ya nemi ya san labarinmu,ganin irin gudunmawar daya bamu ne yasa ban b'oye masa labarinmu ba,yaji tausayinmu sosai kuma yayi alk'awarin taimaka mana"

"Ya sanar damu shi d'an kano ne,kuma sana'arsa itace wankin mota a wani car wash dake kano, yace da ace yana da kud'in da zai k'wato mana hak'k'i da yayi"

Haka ya biya mana kud'in mota har kano,ya kaimu har gidansu gurin iyayensa da 'yan uwansa sannan ya basu labarinmu suma sun tausaya mana sosai,satinmu d'aya a gidan yace ya kama mana haya saboda mufi sakewa,shine muka dawo nan da zama,ya samawa Fahad aiki a car wash d'in suna zuwa tare kuma tare suke biyan kud'in haya har yanzu"

"Tun kafin ya furta yana son fauziyya nayi mata sha'awar aurensa sai gashi hakan ya tabbata kuma iyayensa suka amince aka yi musu aure shekararsu biyu da yin Aure tana da d'iyarta mace takwararki ce watan yarinyar takwas a duniya"

Shashshek'ar kuka ta cigaba dayi tana kallon gidan.

Ta sake rungume Mameey ta cigaba da kuka.

"Janan a ina kika had'u da Salman shine abinda yafi bani mamaki"

"Mameey sunanshi Adnan fa,kuma dama a wasik'ar Abba ya fad'a min Salman yana raye,a katsina muka had'u kuma shine yayan Jalal dama lokacin nan shiyasa nace Jalal ne Salma ashe 'yan uwa ne"

"Allah sarki mu ai munyi tunanin ya rasu"

Girgiza kai kawai tayi alamar a'a.

"Janan meye labarinki bayan kinzo Kaduna kin tarar Abbanki ya rasu"

Sunkuyar da kai tayi ta sake fashewa da kuka.
Sai da ta shafe kusan minti talatin tana kuka,Mommy taji kamar tazo ta rarrasheta sai taga kuma ai ga Mameey bai dace taje ba.

Sai da taci kuka ta k'oshi sannan ta bada labarin komai,still ta sake b'oye cewar Abba k'arami d'an Aliyu ne,kawai tace zuwanta Katsina k'addara ta fad'a mata har ta haifi yaron kamar yadda ta sanarwa su Mommy,sannan tak'i fad'a mata wasu abubuwan musamman rayuwar gidan Mommy.

"Janan d'an shege fa" Mameey ta fad'a tana hawaye.

Har cikin zuciyarta tana jin zafin yadda ta sheganta yaronta amma babu yadda ta iya tana ganin kamar a gaske ne Abba yayi mata wannan furucin.

"Wannan wace irin k'addara ce" Mameey ta sake fad'a tana kuka.

Fahad dake gefe shima hawayen ne ke fita a idonsa.
"Ni ban lura da idanun Janan ba sai yanzu" ya fad'a yana goge hawaye.

"Haka Allah yaso,ya sunan yaron kuma yana ina?"

Ta goge hawaye tace "sunan Abba nasa,ina ce masa Abba k'arami,yana Yola gurin Momma a gidan dana zauna watanshi 20 yanzu"

"Zanso ganinshi,ina godema Allah daya dawo min dake lafiya"

Ta juya ta kalli Mommy dasu Jalal tayi musu godiya sosai.

"Ba dai k'wace min ita zakiyi ba" sai a lokacin Mommy ta sake yin magana itama tana goge hawayenta.

"Bazan k'wace miki Janan ba ai Janan ta zama taki"

"Dama har an saka bikinsu wata guda ita da Adnan d'in"

"Kuma shi zai aure ta ne bayan tana da yaro?kar dai ayi masa dole"


Wasu zafafan hawaye suka fito daga fuskar Jalal yana kallon Janan d'in kawai yana ganin abin da ta aikata kamar bazata yi ba.

"Babu abinda zance muku sai godiya,nagode sosai da abinda kuka min akan Janan"

"Karki damu ai Janan 'yata ce"

A lokacin suka yi magana yadda za'a tsara bikin da duk wasu shirye-shirye.

20k Mommy ta bawa Mameey da zasu tafi tace gashinan suyi duk wata siyayya ta kayan abinci,anan ta karb'i number Fahad saboda Mameey bata da waya.

Har sun shiga mota taga Janan d'in a tsaye bata da niyyar shiga.

"Janan shigo mana" Mommy ta fad'a.

Kallon Mameey tayi sannan tace "Mommy dan Allah ki barni anan"

"A'a Janan ai bazai yuwu ki zauna ba binsu zakiyi tunda tare kuka zo"

Mommy ce tayi tunanin ya kama ta a barta su zauna su hira da mamanta sosai.

Murmushi tayi tace "shikenan ki zauna amma dai zaki dawo kafin biki ko?"

Cikin jindad'i tace "eh"

"Sati d'aya ma ya isheta"
Mameey ta fad'a.

"To shikenan amma zamuyi kewarki ga babu Abba ma,sunce sai biki zasu zo"

Murmushi kawai tayi.

"To ya za'ai da kayan sawa kuma?"

Tayi saurin cewa "Zan karb'o na Yaya Fauzah kawai"

"In dai zai miki ai babu matsala ko kuma bara na baki kud'i sai ki sayi dogayen riguna kafin ki dawo tunda baki taho da kaya ba"

"A'a ki bar shi kawai mungode ai itama Fauziyya girmansu d'aya kayanta zasu shigeta"

"To mun gode Maman Janan sai munyi waya"

"Mune da godiya"

'Daga musu hannu tayi lokacin da motarsu ta tashi.

Da suka koma gida ma sabuwar hira ta sake b'arke musu tana ta sake basu labarib irin wahalar da tasha.

Fahad kuwa ya kira Fauziyya ya sanar mata tace tana nan tafe.

            *********

Da gudu fauziyya ta shigo gidan,tana shiga falo ta rungume Janan ta fashe da kuka.

Goyonta ta tsince Janan d'in ta karb'a, sabon kuka ya b'arke tsakaninsu.

"Sister! Aliyu ya cuce mu ya lalata duk wani burinmu"

"Yaya fauzah bana k'aunar ko sunansa a fad'a na tsaneshi wallahi Ashe da gaskiyar Abba daya hanani aurensa amma na kafe"

Labarin suka sake badawa da yadda Aliyu ya rik'a cin mutumcinsu a kotu itama tayi ta basu labarin gwagwarnayar da tasha.

Anan ta basu labarin cewa Abba k'arami d'an Aliyu ne amma ta haramta hakan ga kowa dan Aliyu ya shegantashi tun kafin ta haifeshi yace ba nashi bane sannan a mafarkinta ma Abba ya umarceta da karta sanar da cewa yaron Aliyu ne, hatta a gidansu Jalal babu wanda ya sani sai su Momma kawai.

"Amma kinyi k'ok'ari da har kika iya haihuwa kika yanke cibi,ina mamaki yadda har aljanna ta taimakeki amma kika kasa samun taimako daga gurin mutane,wallahi koni na baki goyon bayan kar wanda ya san d'anshi tunda baya so ko Abba k'arami idan ya girma karki fad'a masa sis" Fauzah tayi maganar

"Wallahi kuwa,suma fa nayi lokacin dana gama yanke cibi,ban tab'a tunanin haka haihuwa take ba sai ranar,gaskiya Allah ya saka miki da alkhairi Mameey"

"Ameen Janan! Amma ya aka yi kika dawo Abuja da kanki kikazo ko kawoki akai gidansu Salman?"

Labarin komai ta basu hatta rayuwarta a gidan da yadda suke bata kulawa da abinda Raihan ta mata da wanda Lubna ma ta mata.

"Dama Raihan Jalal ta aura?" Fauzah tayi tambayar.

"Eh shi ta aura amma yanzu sun rabu ma"

"Meyasa?"

"Mommy ce ta saka Jalal ya saketa saboda irin abubuwan da ta min da kuma wayar da taji,yanzu ma tayi Aure a zaria shine tace zata had'a ni da Jalal da har an saka bikinma da yanzu anyi"

"Allah sarki Lubna ashe haka take da kirki ina ganin kamar Raihan ta fita ashe Raihan muguwa ce"

Mameey ce tace "to ai Lubna tun suna yara suke tare kinga kuwa ai dole tafi Raihan,amma meya hana aurenki da Jalal dan naji Maman nasu tace bikinki da Salman nan da wata d'aya"

Shiru tayi na wasu lokutan sannan tace "saboda na goga wa kaina cutar HIV kuma Adnan d'ina yana da ita"

Duk a tsorace suka kalleta.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un Janan kin san abinda kike fad'a kuwa?" Mameey tayi tambayar a rikice.

Kuka ta fara tana basu labarin rayuwar Adnan d'in da irin wahalar daya sha ta k'ara da cewa "ina son shi Mameey ganin da gaske baza'a bani shi ba yasa nayi amfani da razor na gogawa kaina cutarsa"

Kuka Mameey ta fara tana fad'in "Ashe har yanzu baki da hankali Janan"

"Mameey kowa kallon haka yake min amma ni ina kallon girman so ne"

"Meyasa zakiyi haka sister?ni a ganina da Jalal da Salman duk d'aya ne tunda so iri d'aya suke miki"

"Yaya Fauzah ni kuma bana son Jalal na rasa ya zanyi in cusa son shi a raina indai har ina ganin Adnan babu wanda zansu kamarsa"

"Na yarda so guba ne"

"Tabbas so guba ne amma Jalal ya kasa gane hakan yanzu haka fushi yake dani"

Mameey ta kalleta ta girgiza kai tace "ko nima ji nake kamar na tashi na bar gurin ko kunya baki ji ba kika sakawa kanki ciwo kawai saboda kina son Salman,dole Jalal yayi tunanin kin tsaneshi ne kawai"


 "amma sis ai saiki hak'ura tunda yana sonki,wallahi tun satin bikinki ya gane bawan Allahn nan sonki yake"

"Nima ina son shi amma ba irin son da kuke tunani ba,Kenan abinda nayi kuskure ne?"

"Da butulci ba,bazaki gane illar abinda kikayi ba sai nan gaba,Janan meyasa kike da taurin kai meyasa bakida tunani cutar k'anjamau fa,mai karya garkuwar d'an Adam,dole wata rana kiyi dana sani musamman lokacin da cutar zata bayyana a jikinki kina ji kina gani ta kasheta" Mameey ta fad'a tana hawaye.

Rungume ta Janan tayi tana kuka tace "ance ana shan magani bata fitowa Mameey karki min baki wallahi kin tsorata ni"

"Ba baki nake miki ba amma tabbas kinyi kuskure uwa uba kin zalunci Jalal"

"Zalunci kuma?"

"K'warai kuwa saboda kin nuna k'iyayya ga mutumin daya nuna soyayya a gareki" sai a lokacin Fahad yayi magana tare da tashi ya fita.

"Kenan abinda nayi ba daidai bane,na shiga uku"

"Baki shiga ba wannan jarabawarki ce ki cigaba da addu'ar neman rahamar ubangiji kawai"

Haka sukayi ta tattaunawa har aka kira magriba.

Janan ce ta goya little Janan suka yi sallah.

Lokacin mijin Fauziyya yazo suka sha hira sosai,yaga Janan d'in da yake ta jin labarinta.

Sai k'arfe goma sannan ya d'auki fauziyya a lifan d'insa suka tafi.
Tace gobe da safe zaizo ya d'auki Janan d'in ya kaita ta taya ta hira.

Ranar Janan bata runtsa ba tunanin maganganun da suka yi kawai take,dan ma sunyi waya da Adnan shine kawai sassaucin da ta samu.

_Washe gari._

'Karfe 11 mijin Fauziyya yazo ya d'auki Janan ya kaita,tacewa Mameey zata dawo da anyi la'asar.

A Dorayi Fauzah take gidanta baya da wani girma,ciki da falo ne sai toilet da kitchen a tsakar gida sai wani extra room shima a gefe.

Labari take ta bata yadda rayuwarta ke gudana a gidan.

Duk da mijinta baya da wani k'arfi amma yana k'ok'arin kyautata mata,gashi 'yan uwansa duk suna sonta.

Janan taji dad'in haka sosai tayi musu addu'ar bud'i nagari.

"Kin san meye jindad'i na sis?"

"Sai kin fad'a"

"Wallahi jiya har mafarki nayi an tono ramin dukiyar su Aliyu su karb'i nasu su bamu namu,wallahi ba dan ba dan ba da babu wanda zaici gado sai mu saboda 'yan uwan Abba  basu k'aunarmu"

"Ke dai bari kawai ina ma Abba na nan a raye"

Hawaye Fauzah ta goge sannan tace "wallahi duk ranar da dukiyarmu ta dawo zan ci mutumcin Aliyu sai dai kawai Abba k'arami ya yafe amma baiyi sa'ar mahaifi ba"

"Ki daina had'asu Abba k'arami maraya ne babansa ya rasu tun yana ciki,koya girma haka zance masa"

Tare ta taya ta suka yi aikin komai.

Aikuwa ta hanata tafiya ranar a gidan ta kwana.

Tun azzahar take ta cewa "nifa anayin sallah la'asar zan tafi son ganin Mameey nake"

"Ke sis dan Allah ki bari sai gobe"

"A'a gobe ma cewa zakiyi sai gobe"

"Bazan ce ba"

"A'a muna gama aikinnan zan tafi"

'Karfe uku na rana Fahad ya shigo gidan.

Duk suka gaidashi yana daga tsaye yace "Janan ga Jalal yazo fa tun d'azu ya kawo miki kayanki saida ya huta Mameey tace na rakoshi nan ku gaisa"

Gabanta yayi mummunan fad'uwa.

Fauziyya tayi saurin cewa "Yaya ya shigo mana bara na bud'e d'akin can dama a gyare yake"

"Okay ni wuce wa zanyi gurin aiki daga nan"

Suna zaune a falon bayan ta gaidashi ta kasa fad'in komai.

Fauziyya ce ta shigo suka gaisa ta kawo masa abinci da ruwa.

"A k'oshe ma nake naci abincin Mameey"

"A'a dan Allah kaci wannan ma"

"To nagode"

Tashi tayi ta fita ta barsu.

Kallonta ya sake yi kanta na k'asa k'irjinta sai bugawa yake.

"Janan" ya kira sunanta a hankali.

Bakinta na karkarwa tana son cewa na'am amma ta kasa.

Shima bai damu ta amsa ba ya cigaba da cewa "jiya banyi bacci ba har sai da na tabbatar na samu transfer aikina zuwa Singapore, sannan da safe naje na karb'i takardar sheda sannan na taho kano,yanzu haka na fara neman visa dan bana son na k'ara koda sati d'aya a garinnan"

Da sauri ta d'ago kai ta kalleshi,ganin ita yake kallo yasa tayi saurin sadda kai.

"Zanyi nesa da ku saboda ganinki zai rik'a tuna min abubuwa da dama,bana son ruguza rayuwarki keda Adnan,kin sakawa kanki cuta saboda kina son shi ni kuma ina son duk abinda kuke so kuma na san shima yana sonki,zanyi k'ok'arin cireki a raina saboda kin zama matar yayana,alfarma d'aya nake nema a gurin ki shine idan kun haifi d'a namiji ku saka sunana zan rik'a ziyartar gida duk bayan shekara uku,idan Allah yasa na samu mata nima zanyi Aure a can ki gafarceni idan har na b'ata miki rai a iya zamanmu"

Hawaye gaba d'aya ya wanke mata fuska kalamansa sun k'ara raunana mata zuciya.

Hannu ya zira a aljihu ya fito mata da wrist watch d'in ta.

"Ga wannan" ya mik'a mata.

'Dago kai tayi ta k'urawa agogon ido.

"Tun ranar da kika samu ciwon nan nake ajiye dashi kullum ina ganin shi a matsayin soyayyarki amma yanzu dole in rabu dashi hakan zai tabbatar da cewa na rabu da soyayyarki"
Ajje mata yayi a gabanta.

Kukanta na neman fitowa fili tayi saurin toshe bakinta.

"A cikin trolleynki akwai wata Leda ki bud'e ki duba abinda ke ciki shine gift d'in biki dana baki,sai kuma k'aramar trolley siyayyar da nayiwa prince saboda na san zai dawo bana nan,nayi magana da wanda zai kawo furniture a sakawa Mameey na bashi number ki should incase"

Sai kuma ya mik'o mata ATM d'insa yace "gashi ATM d'ina ne bana amfani dashi sosai code d'in 2345 current ne karki manta zan rubuta miki, akwai 500k a ciki kuma zan rik'a turo kud'i each month kuma amfanin yau da kullum da kud'in,idan anyi biki ki bawa Mameey ko Fahad saboda kar zargi ya shiga tsakaninki da Adnan"

"Jalal...."

"Karki ce komai Janan kinfi k'arfin komai a gurina" ya ajje ATM d'in kusa da agogon.

"Na shiga uku" ta fad'a tana kuka.

"Yawwa nayi magana da Sule dan ta gidanshi na biya yace zai nemi Adnan da zarar ogansu yazo ki zama cikin shiri,Mommy da Asabe da Adnan duk sunce suna gaidaki"

Tashi yayi tare da fad'in "sai Allah ya k'addara saduwa"

Kukanta ya fito fili sosai ta fara rerawa,yana fita fauziyya ta shigo.

Da sauri Janan ta rik'ota.
"Naji komai sis amma pls muje kiyi masa sallama"

Da k'yar ta tashi suka fita lokacin yana k'ok'arin shiga mota Fauziyya tayi saurin cewa "to mungode sosai ka gaida gida"

"Nine da godiya" ya bawa Fauziyya amsa amma tamkar Janan yake bawa dan idonshi a kanta.

Itama ta kafe nata a kanshi tamkar tana harararshi dan dai kawai ya san a haka suke.

Fauziyya nata zungurarta kan tayi magana amma ta kasa cewa komai.

Yana jan motar ta runtse ido ta saki kuka.

"Haba sis kar mutane su tsaya kanki"

Bud'e idon tayi da niyyar tayi mata magana kawai taga matar tsaye inda Jalal ya bari.

"Kinyi sake" abinda ta fad'a kenan tana dariya.

Janan ta k'ura mata ido kamar baza tayi magana ba sai kuma tace "kina nufin ya tafi kenan?"

"K'wari kuwa ai kin cuci kanki da har kika bari cutar k'anjamau ta shige ki"

"Da gaske na kamu da ciwon?"

Fauziyya ce ta rik'ota dan tana tunanin kamar rikicewa ce ta saka ta surutai.

Fuzge hannunta tayi sannan ta matsa kusa da matar cikin kuka ta sake fad'in "ki fad'a min na kamu da ciwon?"

"Keda kika samarwa ciwon gurbi a jikinki har ni kike tambaya k'arin bayani"

"Ki taimaka ki hana Jalal tafiya ko ina dan Allah"

"Kada ki sake rok'ona,da kin san Allah amma kika iya yin butulci,zan k'ara ingiza Jalal ya tafi ya barki kici soyayya,kin cuci kanki kin yiwa kanki  babbar illa,butulu kawai keda ganin Jalal sai dai a lahira" b'at ta b'ace.

Janan d'in ta k'walla k'ara tare da zubewa k'asa.

_*1hour later*_

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda ta fara furtawa da ta bud'e ido.

Fauziyya dake gefenta tayi saurin d'agota tare da fad'in "sannu Janan,kin d'aga min hankali wallahi"

"Ya akai kika shigo dani" ta fad'a tana hawaye.

"Janan ai baki da wani nauyin da zan kasa d'agaki,ki sassauta ranki pls"

"Na cuci rayuwata na cuci Jalal"

"Ki fidda komai a ranki mana"

"Tayaya?na san Allah bazai yafe min irin abubuwan dana masa ,ki bani waya ta in kirashi in nemi gafararshi,tunda har aljan yace nayi butulci to nayi"

"Kina nufin aljanar nan tazo?"

"Eh tace ni butulu ce"

"Karki gaskata maganarsu sis"

"Ban gaskata ba dan dama ba k'unata take ba amma dan Allah ni dai ki bani waya na kira Jalal"

Mik'o mata wayar tayi cike da tausayinta.









_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
        🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




46

Ta kirashi kusan sau goma amma yak'i d'agawa.

Ta kasa nutsuwa dan haka ta ari wayar Fauzah ta kira still bai d'auka ba.

Kuka tayi-tayi dan shi kad'ai ne jindad'inta.

Ana kiran sallar magriba suka sauka a napep ita da Fauzah, Fauzah ta biya mai napep kud'in sannan suka shiga gida.

Mameey taga damuwa a fuskarsu amma ta kauda kai kawai tace "Ku d'auki buta kuyi alwallah"

Bayan sun idar Janan ta rab'e jikin Mameey tana kuka tana basu labarin abinda ya faru tsakaninsu da Jalal.

"Gaskiya ban tab'a ganin mutum mai mutumci kamar Jalal ba yanzu da zamu rabu ya bani 50k yace inja jari kafin wani lokacin da k'yar ma na karb'a" Fahad yayi maganar

Mameey tace "ga kuma uban kayan abinci daya kawo kuma sannan yanzu yace furniture"

"Haka yace" shine abinda Janan ta fad'a tana goge hawayen da basu daina zubowa ba"

"Na yarda banyi adalci ba Mameey na zama butulu" ta k'ara fashewa da kuka Mameey na ta rarrashinta.

"Janan kin riga kin yi kuskure sai dai ki gyara nan gaba, Allah yasa ki cinye jarabawarki"

"Ameen duk suka amsa.

Bata bud'e trolley ba sai da safe bayan tayi wanka.

Wani d'an box ne baifi tafin hannu ba,tana bud'ewa taga 'yar k'aramar ring,ta d'akko ta kalla sosai taga irin English ring d'innan ce.

Wasu zafafan hawaye suka sauka a fuskarta a take ta d'auka ta zura a hannunta.

Ta janyo trolley da yace na Abba k'arami ne ta bud'a taga kayan sawa ne sababbi da kayan wasa da kuma chocolate kala-kala.

" Allah sarki Jalal wallahi ban tab'a dana sanin abinda na aikata ba sai yanzu,ina neman yafiya a gareka Jalal".



Haka ta hak'ura ta cigaba da addu'a.

Kwana biyar da zuwan Jalal Adnan ma yazo,a ranar yake sanar da ita Jalal ya tafi kwananshi d'aya har lokacin ma bai isa Singapore d'in ba.

Zuciyarsa sosai ta rik'a bugawa tayi k'ok'ari sosai wajen b'oye damuwarta  da fad'in "amma meyasa Jalal ya tafi?"

"Ya cewa Mommy transfer aka yi masa amma tace dole ya rik'a ziyartarta akai-akai"

"Allah sarki to Allah ya taimaka"

"Ameen"

Sosai suka yi hira harta manta da wani babin Jalal.

Adnan ya sanar mata ranar asabar mutumin nan zaizo kano tayi murna sosai dan gani take burinta ya kusa cika.

Sai kuma da dare da tazo kwanciya bacci ta kasa tunanin Jalal ya hanata sakat.

Tashi tayi ta d'oro alwallah ta fara jera nafiloli na neman tsari daga shaid'an dake ta mata wasi-wasi.

Mameey ma tashi tayi ta d'oro alwallah itama ta fara yi kamar yadda ta saba,sai da suka yi sallar asuba sannan suka koma bacci.


            *******

Sai da ta d'aga trolleyn sosai sannan ta dara ta da k'asa a farfajiyar gidan.

"Oyaa abar min gidan miji"

"Mu kike wa haka Zuhra?"

"Nayi muku d'in,ai umarnine daga mijina"

Juyawa tayi tace bara na kira Jalal d'in.

"Umma wai mu Yaya zaisa a yiwa korar rashin mutumci?muma fa muna da gado "

Kuka baisa Umma tayi magana ba har Aliyu ya fito.

"Umma dan Allah ku tafi ku koma k'auye zan nemeku"

"Ni kake fad'awa haka Aliyu?"

"Umma ai kinji me nace dan Allah ku fice"

Muryarta har sark'ewa take saboda kuka.
"Zamu fita Aliyu amma ka sani ban yafe maka ba,na nema maka hanyar k'watar 'yancinmu amma kana neman tura ni a rana"

"Dan Allah kuje naji" ya sake fad'a.

"Babu inda zamu Umma saboda akwai gadonmu muma a gidan nan" Ummi ta fad'a rai a b'ace.

"To ki dawo ki gani idan ban kakkaryaki ba wawuya kawai"

"K'yalesu Ummi muje,indai malamai ne munsan inda zamu nemo su muma"

"Ni da Allah na dogara"

"Malamin soro ba,ki jira nan da la'asar kiga abinda zai sameki"

"Alkhairi zan gani da yardar Allah"

Basu d'auki trolleyn ba kawai suka fita.

"Umma to ina zamu?"

"Gidan Malam daga nan kuma shi da kanshi Aliyu zai dawo yana rok'ona mu komo"

"Ni wallahi bana son zuwa gidan boka gaskiya,wannan shirkace fa "

"Uban wa ya ce miki gidan boka zamu,gidan Malam muma zamu zata ga tagayyara.

Suna tsaye bakin titi suna neman napep d'in da zai kaisu tasha,wata mota Ash k'irar Accord tazo ta wuce  sai kuma tayo baya.

Mamallakin motar wanda a k'alla zaiyi shekara 45 a duniya ya zuge glass d'in motar.

" sannu hajiya,'yan mata ina zuwa haka?"

Had'e rai tayi sosai ganin haka ne yasa Umma tayi saurin cewa "zamu je k'auyen kangire ne"

"Ku shigo mana in ba damuwa sai na kaiku"

"A'a ka barshi mun gode" Ummi tayi saurin fad'a.

Umma ta dalla mata harara sannan ta kalle shi tace "Malam mun gode".

Da sauri taja hannun Ummi ," Umma kawai bamu san mutum ba sai mu shiga motarsa"
"Ki min shiru Ummi" b'ata rai tayi suka shiga bayan motar Ummi sai cizewa take ranta baya so suka shiga.

Suna shiga ya d'auki wata kwalbar turare ya fesa a bayan motar basu k'ara tsintar kansu ba sai a wani d'aki duk Kansu an d'auresu.


"Umma wayyo Allah na shiga uku ina ne nan?,Umma sai da nace karmu shiga kika yi mana dole"

Kuka kawai Umma take ta rasa abin cewa ma.

Kusan awarsu guda a gurin suna kuka babu k'ak'k'autawa.

'Katti uku ne suka shigo d'akin.

'Daya daga ciki ya daka musu tsawa tare da fad'in "dalla ku mana shiru idan zaku kwana dubu kuna kururuwa babu wanda zai jiku"

"Dan Allah ku rufa mana asiri ku mayar damu inda kuka d'akko mu" Ummi ta fad'a cikin matsanancin kuka.

"Ban d'akko ku ba dan na barku ku tafi salin alin" wanda ya d'akko sun ne ya shigo dagashi sai singlet da boxer.

Duk idanunsa ya firfito waje.

"Ke kika haife ta?"  Ya tambayi Umma.

"Eh 'yata ce"


"Amma mama kin iya haihuwa" ya fad'a yana lasar harshe tamkar wani maye.

"Karka cutar min da ita wallahi duk abinda kayiwa 'yar wani sai an wa 'ya'yanka"

Juyowa yayi ya kifawa Umma mari tare da fad'in "duk abinda zaki kada ki ambata alkaba'ir akan 'ya'yana"

Ya kalli k'attin yace "ku tube min ita inyi lalata da ita a gaban uwarta ta ga yanda ake isa da iko"

Ummi na kuka Umma nayi haka aka rabata da kayan jikinta Umma ta runtse ido sosai tun tana jin k'arar Ummi har ta daina.

Sai daya gama abinda zaiyi da ita sannan yace
"Zan tafi ina son kafin in dawo ko wanne yayi abinda yake so da ita"

A tak'aice sai da aka shafe kusan awa biyar cikin su hud'u babu wanda baiyi amfani da ita ba,ba kuma sau d'aya ba.

"Allah ya isa,Allah ya tona muku asiri ya wulak'anta ku tsinannu"

Shine abinda Umma ta fad'a cikin matsanancin kuka.

Wani k'aton k'arfe d'aya daga cikin su ya d'akko sannan yace "mu kike fad'a wa haka?" A k'afa ya doka mata k'arfen sannan ya sake d'agawa yayi mata fashin kwakwa aka,wani mahaukacin k'ara tayi ta zube anan cikin jini"

Da sauri suka fita dan sanarwa ogansu sun gama.

Ummi kwance cikin jini haka Umma ma.


"Ku sakasu a mota ku watsar dasu a bakin titi sannan a darennan a samo min wadda zan kwana da ita"

"Yallab'ai ina zamu zamu mace a darennan in ba karuwa ba?kuma kace kafi son nutsatstsu"

'Dago kai kawai yayi ya kalleshi.
A tsorace yace "sorry yallab'ai"

Da sauri suka shiga suka fito dasu ba tare da sun tsaya duba ko suna da rai ko sun mutu ba.

Har zasu fita gaba d'aya yace "Faisal ka dawo mu jirasu dan naga fuskarka na nuna alamun tsoro kamar yau ne ka fara"

"Abokina amma duk abinda muke babu wacce ta tab'a bani tausayi kamar yarinyar nan dubeta kamar gawa fa"

"Itama uwar tata da kuka buga gata kamar gawar"

"Bazaka fahimta ba Ayuba wallahi yarinyar mun wahalar da ita da alama yarince d'anya"

"To sai me? Ban tab'a jin dad'in mace ba kamar yarinyar nan dan dai idan nayi amfani da mace bana kuma yi sannan bana ajje mata a gidana da wallahi dadirona zata zama"

Shiru kawai Faisal d'in yayi ya tuno yadda take ihu da ranta lokacin da suka cin mata.

Kai ya dafe tare da sunkuyar dashi.


       **********

Likitan na tsaye jikin gadon da Ummi ke kwance har lokacin bleeding take,bedsheet d'in da aka rufeta a jik'e jigif.

Doctor ya juyo ya kalli d'aya daga cikin 'yan sanda uku da ke tsaye yace "Muna samun case sosai na fyad'e amma bamu tab'a samun irin wannan ba"

"Kamar ya kenan?" 'Dan sandan yayi tambayar.

Ajiyar zuciya doctor yayi sannan yace "ba mutum d'aya bane yayi amfani da ita sannan anyi amfani da ita kusan sau goma a lokaci d'aya"

Da sauri d'an sandan ya rufe ido tare da yin salati.

Doctor ya cigaba da fad'in "ya kama ta ku 'yan sanda kuyi hob'b'asa dan ganin an kauda yawan fyad'e a k'asar nan,dubi yarinyar nan tamkar gawa,har yanzu mun rasa yadda zamu tsayar da zubar jinin nata dole sai an had'a da aiki,itama waccan matar tana zan an kasa d'aura k'afar,k'ashin gurin yayi daga-daga, kanta kuma sai aske gashin aka yi sannan aka mata d'inki da alamu tazo ceton yarinyar ne su kuma suka amfani da wani abu mai k'arfi suka k'wad'a mata a k'afa da kanta,ya kama ta kuyi bincike sosai a kama wannan mutane marasa imani"


"Muna ta binciken akan hakan,saboda har yanzu an kasa samun kowa nasu,a bakin hanya wani bawon Allah ya gansu shine aka sanar damu,ga 'yan jarida na k'ok'arin d'aga mana hankali shiyasa muka zo nan dan bana son 'yan jarida su shigo cikin abinnan zasu k'ara b'ata mana suna wajen al'umma"

"Zamuyi k'ok'ari wajen ganin sun samu lafiya"

Hannu ya mik'a masa suka sakeyin musabaha sannan doctor ya fita.

Matsawa yayi jikin gadon ya sake kallonta ya girgiza kai sannan ya juya zai fita tayi saurin rik'o hannunsa.

Da sauri ya juyo ya kalleta.
Muryarta a sark'e tace "ka.....kkk..kace...Jan...Jannn.....Janan tat..ta yafe min"

"Janan?" Ya maimaita sunan.

Kai ta d'aga cikin jinjiki da hawaye tace eh.

"A ina kike?ina Janan d'in?su waye suka miki wannan abin"

"Kad......"
Kakarewa tayi idonta ya fara kakkafewa da k'yar ta iya yin salati daga nan bata kuma yin motsi ba ta rufe idonta hawaye suka zubo.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" ya furta lokacin daya tab'a tsintsiyar hannunta yaji ta daina aiki,yakai hannunsa jikin hancinta yaji babu numfashi.

"Kirawo doctor" ya fad'a da k'arfi.

"Okay sir"

Su duka suka fita suka dawo da doctor.

Sun rufe gurin sun gama duk wani gwaje-gwajensu sannan suka janye abin.

Ganin an rufeta ruf ne yasa ya tabbatar da ta rasu.

"Ya kamata a nemo 'yan uwanta su d'auki gawarta kuyi wani k'ok'arin"

Fita yayi ya bar shi tsaye yana zulumi.















_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
       *DIREBAN GIDANMU*
        🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄




```Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv```


*_Ke ta daban ce Miss Xerks_*



_Groups d'in da suke bibiyan novel d'ina nagode sosai._



```Na baki kyautan shafin nan Zahrah Mansur```



_Godiya ta musamman da fatan alkhairi ga_
*TASKAR SANAZ*
            &
*DIREBAN GIDANMU FANS*



47

Tunani ya rik'ayi wane gari ne kad da bai gane ba.

Yafi minti 50 a tsaye cak yana tunanin wane gari take son fad'a.

"Kad.....Kaduna" yana fad'a d'aya daga cikin yaransa ya shigo d'akin.

"Yallab'ai a gefen zanin waccan matar  aka samo wannan wayar"

Da sauri ya karb'a ya kunna.

Number farko ya fara d'auka a wayarshi sannan ya duba dialpad yaga duk dialed numbers d'in ciki sunan Aliyu ne.

Da sauri ya kira ya kara a kunne.

Ringing biyu tayi Aliyu ya d'aga.

Jin abinda ya faru ba k'aramin d'aga masa hankali yayi ba.

Babu shiri suka taho Kano dashi da baba Isa da baba Idi.

Awa guda da rabi ta kawosu kano asibitin doctor warshu dake 'yankaba saboda mahaukacin gudun da yayi bana wasa bane.

Ganin gawar Ummi da yanayin da Umma ke ciki unconscious ba k'aramin sake d'aga masa hankali yayi ba.

Kuka sosai yake kamar k'aramin yaro yake fad'in "ban san ya akai na koresu ba,ban san meyasa nace su bar gidan ba"

Jiri daya d'ebeshi anan ya zube,da k'yar shima aka samo kansa ya farfad'o.

Sai da 'yan sanda sukayi cike-cike akan case d'in sannan suka bada gawar Ummi aka kuma tafi da Umma dan su ba mazauna kano bane dole su tafi can su cigaba da jinyarta.

Anan ne 'yan jarida suka samu damar yin cincirindo akai.

Hatta Ja'afar bai tsira ba duk yadda yaso zamewa amma sai da suka samu damar cin masa.

Anan ne ya d'auki alk'awarin kamo duk wanda yake da ruwa da tsaki a wannan aika-aikar.

Yana shiga falon ya zube a k'asa.

"Namijin lafiya?"

Ajiyar zuciya yayi yace "Mammy case d'in yarinyar nan"

"Eh ina jinka an gano mutanen da sukayi aika aikar?"

"Ina fa,yarinyar ta rasu har 'yan uwanta sunzo sun d'auki gawar da waccan matar itama ashe mahaifiyarta ce,har suka tafi bata san inda kanta yake ba"

"Wa iyazubillah ya Allah ka tona asirin wannan shaid'anun mutane"

"Ameen Mamyna nima nayi alk'awarin kamo duk wanda keda hannu a wannan ta'asar,ina neman k'arin addu'a Mammy"

"Allah ya baka iko ya shigar maka gaba a duk wani al'amuranka Namijin duniya"

"Ameen Mammyna,kuma kinsan abinda ya tsaya min a rai,yarinyar kafin ta rasu tace min wai ince Janan ta yafe mata"

Janan kuma?"

"Haka tace"

"To ko Janan d'in da muke nema wannan yarinyar da ta kwana a nan?"

"Nima shine abinda ya tsaye min a rai"

"To amma ai ita wannan Janan d'in 'yar katsina ce su kuma wad'annan kace kaduna ne"

"Hakane kuma ba ita kad'ai bace mai sunan,ina ma zanga Janan d'in da take nufi in rok'ar mata gafara wallahi na tausaya mata sosai da k'yar ta iya fad'ar sunan"


"Wallahi ni kuma sai na tuno da Janan d'in da tazo nan inajin yanzu har d'anta ya girma kusan shekara uku fa kenan"

"Wallahi nima ita na tuno Mammy"

"Kuma tace zata neme mu amma shiru"

"K'ila ta manta damu ne gashi mu muna ta tunota"

"To Allah yasa tana cikin k'oshin lafiya a duk inda take"

"Ameen,Mammy ina yarannan naji gidan shiru"

"Sunje gidanka wai su taya Auntynsu hira tunda ka fita tun safe"

"Okay".




A b'angaren su Aliyu kafin suje gida tuni an fad'awa 'yan uwa da abokan arzik'i.

Dan haka cikin gidan da waje tuni ya cika da mutanen k'auye dana birni da yake yanzu ya zama mai kud'i ganin manyan motoci a gurin ba matsala bane.

Anyi mata wanka sannan aka yi sallah aka d'auke ta zuwa gidanta na gaskiya.

Har a lokacin Umma bata dawo hayyacinta.

Likitoci har hud'une a kanta a rana,sannan sunyi zarya a gidan daga safe zuwa dare har sau biyar duk dan ganin an samo kan Umma.

Likitan gargajiya ne yayi mata dorin k'afar ya sanar musu cewa nan da wata guda zai dawo a sin ce.

Zuhra kam hawaye yak'i tsayawa a idonta dan ko shakka batayi itace sila,duk da tana ganin alhakin Janan ne ya fara bibiyarsu,tunaninta d'aya ina zata ga Ummi bayan ta rasu,so take kawai ta rok'i gafararta duk da ta san ba wani abu ta aikata mata ba illa tsamgwamar da take kallon abin a matsayin ramawa Janan.

Idan ta zauna bata tunanin komai sai irin rayuwarsu a k'auye ita da Ummi k'awayene sosai kafin ta auri Aliyu,hakan ba k'aramin kuka yake saka ta ba.

Kwanan Ummi biyu da rasuwa Umma ta dawo hayyacinta.

Kuka sosai tasha kamar ranta zai fita da taji labarin Ummin ta rasu,Aliyu kuwa gafara yayi ta rok'arta,a ranar ta rantse yafi sau a k'irga kan cewa idan har ya cigaba da zama da Zuhra sai ta tsine masa,a haka ya lallab'ata yace tayi hak'uri ayi sadaka saboda mutane.

Shi kansa yana jin mutuwar Ummi har cikin ransa,yadda suka tashi da son juna,sannan tun suna fama da talauci yake mata alk'awarin inganta karatunta,sai gashi yana yin aure komai ya dagule,Ummi ta tambayeshi abubuwa da yawa yak'i yi mata bayan yana da halin yi d'in kuma Ummi nada hak'k'i a kansa,tana da burin yin karatu da kuma driving amma har ta mutu bai cika mata wannan burin ba,kullum tayi maganar ma ranta saiya b'aci.

_idan da Janan ce bazata aikata haka a gareni ba,Janan na da tausayi da tawakkali,lokaci yayi da zan nemi Janan da yarona in rungumi kayana dan na san ta haihu yanzu gashi har yanzu shi kad'ai ne d'ana gudan jini na._

Abinda ya ayyana kenan dan yayi imani Janan bazata saka ya aikata wa 'yan uwansa da sukayi wahala tare haka ba.

Kewar Janan yaji sosai tare da alk'awarin neman gafararta,sannan yayi alk'awarin zai faranta mata yadda bazata sake yin b'acin rai ko kad'an ba.

'Kudirin da yake ransa shine ana Shafa makoki zai fara neman matarsa da tilon d'ansa

Shi har yanzu ya kasa samo amsar abubuwan daya rik'a yiwa su Umma a wannan gidan.

Su Ja'afar sun zo sun k'ara tattambayar ta abubuwa game da mutanen da suka musu wannan abin ta kuma bada amsar iya abinda ta sani,sun masu ta'aziyyar Ummi sannan sun k'ara da cewa zasu rik'a zuwa akai-akai saboda bincike.


           ***********

Wayar hannunta ta zame ta fad'i k'asa "lafiya?"

"Ya Fahad ne ya kira ni" ta fad'a muryarta  a raunane.

"Meya faru ne?ko mutumin ne yace ba zai zo ba?"

Girgiza kai tayi alamar a'a.

Fauziyya tayi saurin cewa "To mene?kin d'aga mana hankali fa"

"Wai Ummi ce ta rasu yau uku yanzu yake jin labarin a radio anyi magana da Aliyu ma yace in yazo zai mana bayani"

"Wace Ummi?"

" 'kanwar Aliyu mana"

"To mu ina ruwanmu abinda ya kaimu shi zamuyi yau hatta azzulumin alk'alin daya yanke hukunci sai yaji kunya"

Kallonta Janan tayi tace "haba Yaya Fauzah mutuwa fa"

Cikin fad'a Fauziyya ta sake fad'in "mu da Abba ya rasu a cikinsu waya tausaya mana"

Kallon Mameey Janan tayi tace "Mameey ki saka baki a d'aga tafiyar nan zuwa wani satin"

"Shikenan Janan a barshi hakan"

"Mameey ki rabu da Janan wallahi na lura tausayinsu take kuma wannan tausayin yana nuna cewa har yanzu kina son wannan makirin Aliyun"

Kallonta kawai Janan tayi rai a b'ace dan batayi tunanin maganar zata fito daga bakin Fauzah ba.

Tashi tayi da sauri ta shige cikin d'akin ta fashe da kuka.

Mameey ta kalli Fauziyya tace "Janan ta fiki gaskiya,mu ai bai kamata mu nuna halin k'aranta ba,mutuwa da ban ce dan haka dole mu d'aga musu k'afa,ki kirawo Fahad ki ce ya sanar musu sai wani satin"

Wayarta ta d'aga ta kirashi ta fad'a masa sak'on Mameey yace dama tun d'azu ya sanar dashi cewar a d'aga saboda rasuwar.


Katse wayar tayi tace "Mameey kinji Janan can na kuka sai kace na zagi Abba ko ke"

"Ah to sai kije can ki  rarrasheta tunda dama ke kika tab'ota"

Tashi tayi da sauri ta shiga d'akin ta tarar da Janan d'in kwance tana kuka da haki.

"Sis kiyi hak'uri ni ban fad'a dan na b'ata miki ba"

"Amma meyasa kika fad'a?"

"Naga alamun haka ne"

Murmushi tayi mai had'e da hawaye sannan tace "kin san kukan me nake?"

Da mamaki Fauziyya tace "a'a sai kin fad'a"

Tashi tayi zaune tare da tank'washe k'afarta ta sake yin murmushi ta cije leb'e tace "ina kukan rashin Jalal da Adnan"

"Kamarya"

"Maganar da kikayi d'azu ita ta canza wa zuciyata shawara"

Shiru kawai Fauziyya tayi tana kallonta ita kuma ta cigaba da fad'in.

"Zan koma gidan Aliyu"

'Dan zabura Fauziyya tayi ta matsa gefe.

"Kina da hankali kuwa Janan?"

"Ai banyi kama da tab'ab'b'u ba ras nake"

"Ban yarda ba akwai matsala a k'wak'walwarki"

"Babu komai Yaya Fauzah ina son yin amfani da dama ta ne kafin in mutu,na yanke shawarar komawa gidan Aliyu in goga masa cutar dake jikina ba tare daya fargaba har sai lokaci ya k'ure ma'ana lokacin da cutar zata bayyana a jikinsa babu zancen shan magani,a lokacin zan sanarwa da d'ansa irin illar da yayiwa rayuwa ta daga nan zan daina shan maganin nima in mutu saboda na san lokacin na rasa Adnan"

'Daga hannu tayi ta wanke ta da mari a daidai lokacin Mameey ta shigo.

"Me nake gani Fauziyya?"

Tashi tayi da sauri ta rungume Mameey ta rusa kuka.

Janan ma sauke kanta tayi k'asa tana mamaki karo na farko Fauzah ta mareta.

"Meyasa Janan bata mutu ba ta dawo garemu?muna zaman lafiya Mameey Janan na neman tarwatsa d'an farin cikin da muka samu"

"Ki daina fad'ar haka Fauziyya"

"Mameey kinji mugayen kalaman da take fad'a kuwa?"

"Banji ba amma kema bai kamata kice haka"

"Zan tafi zanyi nisa daku bazan kuma dawowa ba tunda ba k'aunata kuke ba har fatan mutuwa kuke min"

Kuka sosai take.

Mameey ta rungumota tana kuka,fauziyya kuwa duk jikinta yayi sanyi ta rasa dalilin daya sa tayi furucin nan.

Alk'awari tayi zata bawa Janan d'in hak'uri idan ta huce dan ta san yanzu bazata saurareta ba.












_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
          🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Miss Xerks &  Safnah luv```



_~kowa ma ya san ke tawa ce,wollah ko bakiyi na ni ina yinki sosai my Aunty😘~_




*_Zuwa ga makaranta wannan littafin,naji k'orafe k'orafenku amma ina mai tabbatar muku cewa har na gama novel d'in nan bazanyi abinda bazai gamsar daku ba,karku duba dad'in novel d'in nan sosai kawai ku duba fad'akarwarsa,na tabbatar abubuwan da suke faruwa a yanzu akwaisu a littafin nan kuma in har akwai abinda ya zama akasin haka ko kuma kuna ganin babu fad'akarwa dan Allah ina son comments ya isa gareni kai tsaye babu wani b'oye-b'oye._*



48

Kanta na cikin gwiwarta har lokacin da Fahad ya gama basu labarin rasuwar Ummi abinda ya faru, amma Janan bata d'ago kai ba.

"Wannan fa meya sameta?"

"Ita da Fauziyya ne"

Kallon Fauziyya yayi yace "me kika ma autarmu mun samota da k'yar kina neman b'ata mata rai"

"Yaya nifa wasa nake mata,amma wallahi ka jawa autar nan kunne bata jin magana taurin kai ne da ita har yanzu"

"Ai a gurinki ta koya"

Ya dafa kan Janan yace "kiyi hak'uri Janan ki rabu da ita kinji"

Kai kawai ta gyad'a daidai lokacin wayarta ta fara ringing.

'Dan juyar da kai tayi sannan ta goge hawayen idonta ta d'aga wayar.

"Salamu alaikum"

Daga d'ayan b'angaren Momma ta amsa da "wa alaiki salam Janan ya kike ya gida?"

"Lafiya k'alau Momma ya su Zainab da Humaira"

"Zainab k'alau suke suna gaidaki,wato kinga mama shine kika guji Momma ko?"

Murmushi tayi tamkar Momma na gabanta tace "a'a ai zan koma insha Allahu"

"Ai tace da kanta zata zo ta d'auke ki jibi"

"To Momma"

"Kina wace unguwa a kano?"

"Kuntau ne daidai layin makaranta"

"Okay muna nan tafe yau d'in nan"

"Yau Momma, eh mana ai tun jiya muna Abuja yanzu mun taho kano ni da Muhasin"

"To Allah ya kawo ku lafiya"

"Ameen Janan ki gaida mamanki kafin mu k'araso"

"To"

Katse wayar tai batayi niyyar fad'awa su Mameey ba saboda yadda ranta ke a b'ace.

Amma da Mameey ta tambayeta kawai sai ta fad'a.

Babu shiri suka d'aura girki,Fahad ne ya fita ya sayo k'ank'ara Fauziyya ta had'a zob'o mai dad'i.

Duk abinnan da ake har lokacin bata saki ranta ba.

Duk da suna cikin aikin Fauziyya ta bata hak'uri tare da cewa haushi taji shiyasa tayi furucin.

Ita kuwa ta kudurta a ranta babu wanda zai hanata komawa gidan Aliyu ko dan ta hukuntashi akan abinda ya masu.

Kusan k'arfe hud'u su Momma suka k'araso.

Hankalinta sosai ya tashi ganin Abba k'arami a hannun Muhasin tamkar gawa.

Da sauri ta kai hannu zata karb'eshi suka had'a ido da Mameey ta fasa.

Iso aka masu bayan sun gaisa Momma ta kalli Janan wadda damuwarta ta fito k'arara.

"Kinga Abba ko?"

"Meya sameshi?" Ta fad'a da sanyi murya.

"Figar ruwa da ciwon hak'ark'ari wallahi banyi niyyar dawo dashi ba amma shekaranjiya ya d'aga mana hankali sosai ya rik'a mimmik'ewa daya dawo hayyacinsa ya fara kuka yana kiran Ammi da daddy shiyasa nace bari kawai mu kawoshi saboda gudun tsautsayi,muna shiga cikin Abuja ya mimmik'e mana ba shiri mukayi asibiti ina kiran Mommy kuma tace kina kawo shiyasa ban d'aga musu hankalina na k'i fad'a musu muna Abuja a asibiti muka kwana nasa suka sallamemu dan kiga d'anki"

Mameey ce ta karb'eshi.

Janan tayi k'arfin hali sosai ta danne hawayen dake k'ok'arin zubo mata.

"Mameey ai bamuga ta zama ba mu tashi mu kaishi asibiti bari na kira Sagir na sanar masa"

Da k'yar su Momma suka ci abinci sannan suka tafi Asibitin AKTH a motar dasu Momma sukazo da ita.

Kusan awa guda sannan aka gama processing aka basu gado a emergency kafin suyi scanning aga abinda ke damun nasa.

Sai a lokacin su Momma sukayi musu sallama da alk'awarin insha Allahu zasu dawo.

Suna zaune duk sunyi jigum lokaci-lokaci Janan na goge hawaye.

Fauziyya ta shafo kansa tace "Gaskiya mai sunan Abba ya girma Allah ya baka lafiya"

"Ameen dai,aini jira nake ya warke in masu tsiya daga shi har uwar tasa da ta zauna tanawa d'an fari kuka"

Mameey ta kalli Fahad tace "sai tak'i kuka kai ka mata nak'udar ko kai ka haifa mata, kai dai da ka zauna kak'i Aure ai ka ta ganin 'ya'yan k'annenka"

"Mameey abin harda gori"

"Eh in kaji haushi ka kawo min matar da zaka aura"

"Aikuwa tana nan tafe"

"Nima ina nan ina jiranta"

Ita dai Janan idonta yana kan d'anta dake kwance da uban oxygen a hanci ga drip a hannu.

'K'arfe shidda security ya shiga yana cewa dan Allah a fita lokaci yayi.

Janan ta kalli Mameey tace "su fa nan basa d'agin k'afa da lokaci yayi suke cewa a fita,kuma mutum d'aya ne ke jinya"

Mameey tace "To yanzu abinda za'ai ku tafi gida inya so sai na zauna dashi"

"A'a ni meye amfani na Mameey kawai zan zauna,Sai na sanar da Sagir baya da matsala yanzun ma aikine ya rik'eshi an bashi wanki da yawa shiyasa bai zo ba"

"Haba Fauziyya sai kace na zama uwar banza,da 'ya da mijinki ki taho jinya"

"To Mameey ai komai kamawa take,inda little Janan ce ba lafiya ai dole ya barni na zauna"

Janan tayi narai-narai da ido tace "Mameey dan Allah ku barni nayi jinyarshi"

Yadda tayi maganar Mameey taji tausayinta sosai, aikuwa tace to shikenan ta zauna.

Sai da suka suyo mata duk abinda take buk'ata sannan suka tafi..

Wajen k'arfe 8 wani nurse yazo ya bata takarda ta kai lab da safe za'a karb'o jini.

Hankalinta ya tashi sosai yanzu har k'arin jini za'a masa.

Kasa jurewa tayi ta tambayi nurse d'in meke damunsa.

"Bazamu gane ba har sai likitoci sunzo sun gani anyi scanning bana son fad'a miki abinda ba shikenan ba"

"To jinin siya zanyi ne ko d'auka za'ayi?"

"Eh duk wanda kuke so ai sai gobe za'a saka masa da safe to wannan takardar ta group d'insa ce in kije lab zasu ce ki saya ko ki kawo wanda za'a d'auka a jikinsa"

Jinjina kai tayi tana fad'in "Allah ya bashi lafiya"

"Ameen, yanzu ki kira mamansa ta zauna sai kije ki karb'o ke"

Ta d'anyi murmushi duk da a cikin damuwa take tace "ni ce mamanshi ai,kuma 'yan gidanmu sun tafi tun d'azu ban san ya za'ayi ba"

Kallonta ya sake yi yace "dagaske kece mamanshi"

"Nayi k'ank'anta ko"

"Gaskiya kam koni ban yarda ba sai yanzu na d'an ga kamannin naku,nayi tunanin k'aninki ne"

Murmushi ta sake yi kawai.

"Amma ya akai suka tafi da wuri haka har babansa"

"Babansa baya k'asar so sai mamanmu su kuma da 6 tayi akace lokaci yayi kawai sai suka tafi"

"Ai dama d'an tsayawa zasuyi a waje in an gama fita sai su dawo saboda irin haka,da ace babansa na nan da da dad'i"

"To yanzu ya zanyi?ko goyashi zanyi naje"

"Da oxygen taya zaki goyashi?jininsa dai yanzu 19% dole kayi k'ok'arin zuwa lab a san abinyi,bara kawai naje na kai miki"

"To nagode sosai Allah ya saka da alkhairi"

"Ameen".

Bayan ya dawo ya sanar da ita za'a zo a saka masa jinin da safe.

" oh siya akai?"

"Eh saboda ai babu lokaci tunda da safe ake buk'ata"

"To nawa ne kud'in?"

"Ki barshi kawai k'anwata na biya ga takardar,ai mamakinki ya sani biyan kud'in nan"

"Mamakin me?"

"Da kika ce yaronki ne wannan"

"Ba abin mamaki bane"

Haka yayi ta janta da hira har ya cire drip d'in ya jona wani yace da taga ya k'are ta fad'awa duk wani nurse da ta gani.

A daren ta kira Mommy ta sanar da ita,aikuwa tace suna nan tafe gobe.

_Washe gari_

'Karfe takwas Sagir ya kawo Fauziyya a lifan suka kawo mata breakfast.

Sun d'an tab'a hira kad'an sannan suka tafi kasancewar ba lokacin visiting bane kuma nurses da doctors sun fara round.

Bath wash ta masa sannan ta d'akko kayan da aka kawo nasa ta saka masa riga mara nauyi da pampers.

Likitoci hud'u ne tsaye suna ta magana akan yanayin ciwon nasa suna kuma duddubashi tare da yi mata tambayoyi.

Bayan sun yi rubutu a file d'in sun fita d'ayar ta dawo.

"Kamar na sanki ko"

Janan ta d'ago kai ta kalleta tana tunanin inda ta santa.

"Yes na san ki mana Janan ko?"

Kai ta d'aga alamar eh.

"Kin manta ni hala?"

"Gaskiya na kasa tuna inda na sanki"

"Mun shiga mota d'aya nida ke daga yola zuwa nan kano,Hajar ce wadda ta baki compliment card d'in ta"

"Oh eh hakane na gane ki"

"Kinma manta ni shiyasa baki nemeni ba"

"Kiyi hak'uri ba haka bane"

"To yane! Ba dai cikin jikin ki bane wannan har d'anmu ya girma"

"Shine fa"

"Masha Allah karki damu insha Allahu zai samu sauk'i,naji dad'in k'ara had'uwa dake"

Murmushi kawai tayi,sai kuma hira ta b'arke tsakaninsu har Janan ta d'an fara manta damuwarta.

Mameey da Fahad duk sun kira sun duba shi sannan suka ce da yamma zasuzo lokacin visiting amma Fauziyya da wuri zata zo saboda lunch.

Hajar ita ta raka ta tayi har scanning kasancewar Hajar likita ce bata sha wahala ba,sai da sukayi scanning har kala uku.

Sai da ta tabbatar anyi scanning d'in sannan suka koma ta tafi sai bayan kwana uku result zai fito.

Da zata tafi gidama tazo ta mata sallama tace da yamma zata dawo dubiya ta musamman.

Godiya sosai Janan ta mata ta tafi.


*************

Suna zaune ita da Mommy da Adnan sai Fauziyya da bata dad'e da zuwa ba.

"Ni fa rashin lafiyar nan ta bani mamaki lokacin d'aya fa"

"To ya za'ayi haka Allah yake lamarinsa"

"Mommy kawai zan mana visa mu tafi ko India ne sai yafi"

"Ka bari dai muga abinda Allah zaiyi"

"Mommy ki duba kiga Abba fa kamar baya da rai,wannan jinin na biyu kenan ake k'ara masa ni gaskiya gwanda aje can India tunda suna da k'wararrun likitoci"

"Adnan ka kwantar da hankalin ka mana kabi ka rud'e"

"Ai dole ne dubi itama Janan yadda ta koma a rana d'aya dole in damu da damuwarsu Mommy"

Kallon shi kawai Fauzah take tana jindad'in yadda suka damu da Janan.

Wani b'angare na zuciyarta yace _gaskiya Janan bata da hankali da har ta kasa gane masoyinta har tana ik'rarin zata komawa Aliyu,ita kuwa duk ranar da Janan ta koma gidan Aliyu tabbas zasu raba jaha da ita._

Salamar Hajar ce ta katse mata tunanin suma ta katse musu maganar da suke.

Duka su biyun suka mik'e tsaye Mommy da Adnan.

Itama Janan cike da mamaki ta bisu da kallo yadda taga Hajar ta tsaya cak ta kasa k'arasowa ya tabbatar mata akwai abinda ke faruwa.

"Meya kawo ki nan?" Adnan ya fad'a cikin b'acin rai.

Yatsina fuska tayi tace "kai zan tambaya dalilin zuwanka nan"

"Karki raina min hankali mana"

Janan ce tayi saurin tashi tace "Adnan itace wadda ta taimakamin fa,ta taimakeni har sau biyu a ray............"

"Dalla rufamin bakinki,ki rasa wa zai taimaka miki sai wannan matsiyaciyar mara kunya da tarbiyya"

Daga Janan har Fauzah sun tsorata da yadda ya had'e rai yana fad'a.

"Kada ka sake jifana da magana,akwai wanda ya kaika rashin tarbiyya,Alhamdulillai gidanmu babu gadon HIV naga mun........" Bata k'arasa ba ya sakar mana wawan mari har sau biyu.

Rik'e kumatu tayi zata sake magana ya shak'ota.

"Kin manta illar da yayarki tayi min,ta sakawa d'anta dani kaina muguwar cutar da ta kwaso a yawan banzanta,ke kanki da aka yi niyyar auramin ke guduwa nayi saboda ku d'in kowa ya san kunyi gadon iskanci"

"Wallahi sai na fanshe marin da kayi min a kotu"

Da k'yar aka rabasu tare da fad'a musu bai kamata suzo asibiti suyi fad'a ba inda ake jiyya,Mommy na kuka Janan na kuka.

Da sauri Hajar ta fita,Adnan ya kalli Janan har zaiyi magana kawai ya juya da sauri ya fita,tayi saurin bin bayanshi.

"Kada ki sake ki biyoni" tsawar da yayi mata ne ya saka ta saurin tsayawa a gurin tamkar an dasata.











_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
          🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv```






49

"ALIYU" ta furta cikin matsanancin kuka.

Jin sunan da ta ambata ne ya saka shi tsayawa cak tare da juyawa ya kalleta.

"Aliyu kike ambata a gabana?"

Sunkuyar da kanta tayi k'asa tana zubda hawaye,ya matso dab da ita ya tallabo hab'arta da yatsa d'aya "bayan janyo Hajar da kikayi shine kike ambatar Aliyu a gabana"

Janye kanta tayi sannan tace "Aliyu ya ruguza rayuwata,kai kana neman k'arasa ta da wanne zanji"

Har zaiyi magana sai kuma kawai ya fasa ya wuce da sauri ya fita,ita kuwa da sauri tabi bayanshi kamar wata jela.

Kan wasu kujeru ya zauna tayi saurin zuwa ta tsaya a gabanshi.

"Bakya kishina Janan,meyasa zaki rik'a ambarta sunan Aliyu?kina son na mutu da b'acin rai da damuwa?"

"Kaine fa,ko ka manta alk'awarin Iya?taya zan gujeka?taya zan kasa yin kishin abinda zuciyata take son ta rayu dashi,idan ka d'auke Mommy da Jalal nafi kowa sonka a duniya"

"Ina son kiyi proving,ki d'aukar min alk'awarin bazaki tab'a guduna ba nine mijinki na har abada"

Shiru ta d'anyi kusan minti 3 bata ce komai ba har ya fara zargin kodai bazata amince ba.

"Kana da buk'atar na dafa al Qur'ani?"

'Dago kai yayi ya kalleta wanda itama shi d'in take kallo.

"Bana buk'atar hakan amma ina buk'atar kiyi min alk'awarin zaki zauna dani har abada"

Idanunta cike da hawaye ta zauna gefensa tare da cewa "ni taka ce har abada Adnan,nayi alk'awarin da kai kad'ai zan rayu"

"Bana son k'ara ganinki tare da Hajar"

"Bazaka sake ganina da ita ba dama fa taimakana tayi shiyasa amma bazan so duk wanda zai wulak'anta min Salman d'ina ba"

Murmushi yayi yace "Salman d'in Iya dai"

Murmushin da tayi har saida suka bayyana hak'oranta "kasan me?"

"Sai kin fad'a"

"Sai naji dama Iya na raye taga aurenmu"

Kallonta yayi tayi saurin rufe fuskarta da hannu.

"Muga fuskar taki mana"

Da sauri ta tashi zata bar gurin yayi saurin rik'o hannunta tare da zaunar da ita inda ta tashi.
"Oh guduna zakiyi"

"Tunani nake Abba k'arami ya tashi kuma zai nemeni nasan"

"Eh hakane ashe yaronmu na kwance ba lafiya muka taho muna soyayya oyaaa tashi muje".

         **********

Washe gari tana zaune kan gadon Abba k'arami yana kan cinyarta lokacin an cire masa oxygen d'in.

Tunani kawai take ta hanyar da zata bak'antawa Aliyu ba tare da ta koma gidansa ba.

Ita kam a yanzu bata jin akwai wani wanda zata iya zaman Aure dashi idan ba Adnan ba uwa uba tana da cutar HIV ta san ta zama ta Adnan duk da taso ace ta koma ga Aliyu ko dan bak'anta masa amma kuma ta hak'ura dan Adnan ko sunansa baya son ji.

'Karar message daya shigo wayar ta ne ya sa ta dawowa daga duniyar tunanin da ta shiga.

'Daukar wayar tayi ta bud'e sak'on ta fara karantawa.

_Assalamu Alaikum!_
_Da fatan kina nan lafiya,ya jikin prince?Allah dai yasa da sauk'i,dan Allah ki kula min dashi sosai banason inji yana rashin lafiya idan ba haka ba zan zo in d'aukeshi dan nasan bakya wani kula dashi yadda ya kamata,Allah ya bashi ingantacciyar lafiya mai d'orewa ameen._

Duk da babu suna amma ta tabbatar Jalal ne saboda number da aka yi text d'in bata 9ja bace,duk jikinta yayi sanyi sosai.

Tana zaune tana sake karanta sak'on kawai taji sallama akanta.

'Dago kai tayi ta kalleta sai kuma ta had'e rai tare da juyar da kanta gefe.

"Janan kiyi hak'uri ban san alak'arki da Yaya Adnan ba amma yadda ya nemi fad'a min magana shiyasa nima na rama"

Ganin janan bata da niyyar bata amsa yasa ta k'araso zata d'auki file d'in Abba k'arami Janan tayi saurin rik'e hannunta.

"Karki tab'a" ta k'are had'e rai.

Ajiyar zuciya tayi tare da cewa "bani da masaniya akan ciwon da Yaya bilkis ke dashi wanda har ta d'orama Yaya Adnan,duk da bamu san me yayi ajalinta ita da d'anta ba a lokacinta amma inajin ance Yaya Adnan nada HIV na tabbatar Yaya bilkis ce ta shafa masa saboda na san tana tarayya da maza kala-kala dan haka samun AIDS a jikinta ba abin mamaki bane,nima ana min kallon haka amma wallahi ni ban tab'a yawon banza ba,na dai san nid'in kawai inada yawo ban san zaman gida"

Kallonta Janan tayi tace "to na buk'aci ki bani labarin ki ne?"

"Baki buk'ata ba amma ina son kawai ki nema min gafara wajen Yaya Adnan da Mommy amma bayan an sallameku,iyayena sun wulak'antasu amma wallahi daga baya duk munyi nadama" ta d'an goge hawayen idonta wanda yasa jikin Janan ya k'ara yin la'asar.

"Kiyi hak'uri akan abinda na miki"

"Karki damu Janan duk mun samu rashin fahimta ne"

Zama tayi tana sake bata labarin rayuwarsu hakane yasa Janan ta k'ara jin tausayin Adnan da son shi har cikin ranta.

A lokacin ta sanar mata cewar Adnan yace baya son ganinsu tare,tace aikuwa da taga lokacin zuwansu yayi zata bar gurin koda itace on call.


Washe gari kuwa suka je suka karb'o result,babu wani abu dake damunsa a cikin k'ashinsa ko kayan cikinsa zuwa brain d'insa sai ciwon convulsion (figar ruwa) kad'ai dake damunsa hakan ne yasa ta d'anji sanyi kad'an a ranta.

*_3 weeks later_*

Yau ne ranar da Janan suka dawo gida an sallami Abba k'arami,ya warke sosai sai dai ya rage surutu sai rigima daya tsira ta gaira ba dalili sai yayi ta mata kuka ina daddy,tun bata jin haushi har ta fara yi masa tsawa akan ya hau jirgi ya bashi can Singapore.

Ranar nan Mameey fad'a tayi ta mata akan yadda take yiwa Abba k'arami fad'a tamkar wani babba.

            *********

Yau ne suka dira a Kaduna a kuma kotun da aka yi shari'ar Aliyu da Abba.

Wani sabon kuka ne ya b'alle wa Fauziyya tana ganin kamar a lokacin ake shariar.

Mameey kanta dauriya kawai take amma hoton shari'ar take gani a idanunta.

Sagir,Mommy, Adnan,sai rarrashin Fauziyya suke yayinda take jin kamar cewa suke tayi kuka.

Lokacin da suka isa sai da sukayi jira na kusan awa biyu dan alk'alin a lokacin yana gudanar da wata shari'ar.

Bayan an gama ya buk'aci da su shigo,aka yi musu iso suka shiga.

Adnan ne yayi masa bayanin abinda suke tafe dashi.

Ya kalli Alto yace "Malam ka tabbata idan muka je zaka gane inda kuka sare bishiyar"

Alto ya russuna yace "k'warai ma kuwa dan bazan manta komai na daga kafin a fara gani har zuwa gama wa dan ban tab'a ganin mutum mai adalci da mutumci kamar Alhaji Hashim ba sannan ban tab'a aikin gida da yayi min dad'i kamar nasa ba Allah ya masa rahama" ya fad'a yana goge hawaye.

"Ameen" duk suka amsa.

"Shikenan zamu tafi dani daku da ma'aikata na,za'aje ka nuna gurin a tona amma fa da sharad'i"

"Wane sharad'i fa?" Adnan ya tambaya.

"Idan har bamu ga komai ba tabbas za'a hukuntaka hukunci mai tsauri"

Jikin Janan gaba d'aya ya mutu,ta kamo hannun Abba k'arami dake rik'e dana Adnan ta damk'e sosai tana karkawa.

"Na yarda" Alto ya fad'a.

"Idan kuma aka gani zamu barku da Allah domin kunyi sanadiyyar rasuwar mahaifinmu kun samu a k'unci kunyi shari'ar zalunci da son zuciya"

Duk suka juya suka kalli Fauziyya, wani security dake tsaye ya nufota alk'alin yayi saurin dakatar dashi sannan ya kalleta yace "ni kuma nayi alk'awarin idan ba'a ga kud'in nan ba sai kinyi zaman gidan yari na tsawon shekara guda,yanzu ma sa'a kawai kika ci ba ana shari'a kika yi min tsaurin idonnan ba".

        **********

Ja'afar yana zaune kan kujera,yayinda yaransa uku ke tsaye.

Daga upstairs d'in ya fara jiyo hayaniyarsu.

" fito wallahi kin bar auren Aliyu har abada 'yar matsiyata"

Trolley aka fara wurgowa tayo k'asa,kallon trolley yayi sannan ya maida hankalinsa saman.

Zuhra na gaba tana hawaye Umma na k'ara tunkud'ota Aliyu yana gefen Umma.

"Lafiya?" Shine abinda Ja'afar ya tambaya lokacin da suka k'araso falon.

"Ya saketa amma dan bak'in naci tak'i tafiya,wannan da kake gani 'yallab'ai ita ta tarwatsa rayuwar gidan nan"

"Kamar yadda kema kika tarwatsa rayuwar wasu" duk suka jiyo dan ganin wacece.

"Janan" Ja'afar,Aliyu,Zuhra duk suka furta lokaci guda.

"Janan ce, nazo d'aukar fansar mahaifina da kuka yi sanadiyyar mutuwarsa"

"Babu abinda kika isa kiyi munafuka"

"Kinci darajar ke babbace wallahi da sai na zageki"

"Janan kina da hankali kuwa?"
Kallon Ja'afar tayi har zatayi magana sai kuma ta fasa ta juya ta kalli k'ofa tace
"ku shigo".






_*Mu had'u a next page*_😉










_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
              🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄





```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```





50

Juyowa tayi sai lokacin ta kula da k'afar Mommy ninke da bandage amma dan bala'i haka ta fito da Zuhra duk da azabar da take ji.

Shigowar su Mameey ba k'aramin d'agawa Aliyu hankali yayi ba yadda ya gansu tare da 'yan sanda da alk'ali daya yanke shari'a.

Bayanin komai aka yiwa Aliyu sannan suka juya dukansu zuwa farfajiyar gidan.

Daga can tsakiya gefe ya nuna daidai rumfar da aka yi ta hutawa yace "Allah ya taimake ka nan ne inda aka sare wannan bishiya"

"Ka tabbata?"

"na tabbata yallab'ai"

Juyowa yayi ya kalli Fauziyya "karki manta idan har ba'a ga komai ba kinada shekara d'aya a prison shima sai shari'a ta hukuntashi"

"Ni kuma ina da kud'in da zan d'aukaka k'ara idan har aka sake zaluntar mu"

Duk suka juyo suka kalli Janan wanda a lokacinma hawaye take.

Ja'afar magana kawai yake son yi mata amma tsananin mamakin da take bashi ya hanashi cewa komai.

Kujera aka d'akko wa alk'alin ya zauna,yayinda duk su kuma suke tsaye.

"Janan dama zan sake ganinki a rayuwata"
Zuhra ta fad'a tare da rungumeta tana kuka.

Ja'afar ya samu k'arfin gwiwar kamo hannun Abba k'arami tare da rungumeshi.

Aliyu kallonta kawai yake ita da yaron dan ya tabbatar d'ansa ne a jinin jikinsa yake jin son yaron.

Suna tsaye aka kirawo masu hak'on rijiya dan su tona gurin.

Kusan minti talatin da fara abin Umma ta juyo ta kalli Zuhra dake tsaye a gefe "munafuka an sakeki shine kika tsaya ganin gulma" ta juya ta kalli Aliyu "ka kureta ta fice anan"

"Umma rabu da ita a gama wannan aikin tukunna"

Harara ta dallawa Janan lokacin da suka had'a ido.

Da sauri Janan ta tashi ta koma gefen Adnan ta ja kujera ta zauna.

Mommy na tare da Mameey a tsaye,Fauziyya ma suna zaune a gefe ita da mijinta da 'yarsu.

"Ba dai wannan shine babyn da kika haifo ba?" Ja'afar ya fad'a.

Murmushi tayi tace "shine,Ashe dama zamu sake had'uwa da kai d'an sanda mai basaja?"

Murmushi shima yayi yace "kece mai basaja ai,tunda kika tafi kika k'i dawowa kullum da munji sallama sai munyi tunanin kece"

"Allah sarki dan Allah kuyi min uzuri insha Allahu zanje in gaida Mammy"

"Allah yasa da gaske kike"

"Ameen"

_kenan dagaske itace Janan d'in da wannan yarinyar ta fad'a?to meye had'in Janan da wannan gida da kuma tonewar da za'ayi yanzu?tabbas zanso jin labarin chakwakiyar nan._


"Janan a ina kika san wannan kuma?"

"Shine wanda na kwana a gidansu lokacin da na taho daga Yola"

"Janan d'ita mai mutane"

Murmushi kawai tayi

Har kusan awa d'aya da wani abu  sannan aka ga akwatin,duk ya mak'ale da k'asa da k'yar suka fiddo shi.

Ajiyar zuciya Janan tayi dan gani take dukiyarsu ta dawo.

"Yallab'ai gashi mun fiddo"

'Daya daga cikin masu aikin ya fad'a yana goge zuffa.

Alk'alin da kansa ya taso ya tab'a akwatin yaga da kwad'o a jiki.

Kuka da Fauziyya ta fashe dashi ne yasa duk suka juya gareta.

Janan ta rungumeta sosai suka cigaba da kuka.

"Fauziyya kina babba bai kamace ki ba"

"Ina ma Abba na raye yaga wannan rana" Fauziyya ta fad'a tana cigaba da kuka.

"Ku b'alle akwatin" Alk'alin ya bada umarni.

Guduma suka saka suka dokeshi aikuwa ya bud'e.

Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana,wato da aka bud'e akwatin gara da k'wari duk sunyiwa takardun kaca-kaca sai b'urb'ushen wasu wasu kam babu ma,ga k'wari a ciki har lokacin.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda Aliyu ya fad'a tare da zubewa k'asa sumamme.

"Umma dake tsaye itama jiri ke d'aukarta tana fad'in " wallahi k'aryene bazamu yarda ba,k'arya suke sharri ne"

Rugawa tayi da gudu tayi waje da k'yar aka kamota.

Ganin tana hauka tuburan ga k'afar sai jini take hakan yasa aka k'ulleta tare da yi mata allurar bacci.

"Abba na cika maka burinka,da taimakon  Adnan da Jalal ya Allah kajik'an Abba ka sakawa wannan bayin naka da suka taimakamin,Abba meyasa ka mutu meyasa baka jira wannan rana ba nayi maka sanadi Abba ka yafe min"

"Janan kiyi hak'uri ki bar kukan haka" Mommy ta fad'a tare rungumeta

"Ku barni nayi kuka bazaku gane irin illar da suka min ba".

Anan ne Ja'afar yaji labarin komai ya tausaya musu k'warai.

Alk'alin yace za'a yanke shari'a da zarar sun samu sauk'i(Aliyu da Umma).

Fitowa sukayi zasu tafi Mommy tace Janan sai dai ta bita su tafi Abuja,har zata musa Mameey tace a'a taje.

Zuhra kuwa tausayin Aliyu ne yasa ta maida kayanta zata zauna har zuwa lokacin da zasu warware.

"Janan" Ja'afar ya fad'a cikin sanyin murya.

Ta d'ago idanunta da suka gama rine wa ta kalleshi.

"Dan Allah Janan ki yafewa Ummi dan lokacin da zata mutu sai da ta tabbatar ta rok'eni kan na rok'a mata yafiya gareki"

"Bazan yafe ba" abinda ta fad'a kenan tare da jingina da motar tana kuka.

"Karka damu zan lallab'ata zata yafe da iznin Allah" Adnan yayi maganar.

"Alk'awari na d'auka zan rok'ar mata"

"Nima zanyi iya k'ok'ari da kanta zata kira tace maka ta yafe"

Exchanging number sukayi sannan ya tafi.

Janan ta juyo ta sake kallon gidan ta tuno rayuwar da sukayi a baya ta k'ara fashewa da kuka tare da fad'in "So haka yake Ashe?ko dad'i ko k'unci".

Rarrashinta Mommy tayi sannan suka shiga mota suka tafi,Mameey kuma sukayi kano.

         ***********

Tsawon wata d'aya Mameey,Fahad da Adnan suna zarya game da dukiyar.

Basu bar Kaduna ba sai da suka tabbatar an karb'i komai na dukiyarsu.

ATM's d'insu ba'a tab'a kud'in kowa ba sai na Abba dashi Aliyun ke amfani,sai filayen Mameey da gidaje wanda Abba ya siya mata duk sun dawo hannunta.

An raba gadon Abba an bawa kowa nashi Janan nata tace Fahad ya cigaba da juyawa na Fauziyya kuma ta bawa mijinta dukiyar da suka samu ba ta wasa bace gami da filaye da ginanun gidaje duk da sun saukewa Abba nauyin bashishshikan da ake binsa suma still an kawo musu kud'ed'e da yawa da Abba ke bin mutane.

Aliyu kuwa lokacin ya tashi,Umma kuwa k'afa ta rub'e tuni aka mayar dasu kangire gidansu da suka baro,Zuhra ta tafi gidansu anyi anyi ta koma tak'i babansu yace a k'yaleta mamanta kuwa tun a lokacin ta fara dana sani Abinda tayi.

Fahad kuwa yace bazasu zauna a gidan ba sai an sake gyarashi dan haka suka koma can wani gidan Abba dake Malali.

Sannan Aliyu an bashi wata uku ya dawo da duk wani abu daya ci musu tunda babu wata dukiyarsu da aka gani.

A hakanma dan Adnan ya d'akko wani judge ne amma da wancan so yayi ya lank'wasa  abin.


_*2 weeks later*_

Fitowa tayi hannunta rik'e dana Abba k'arami.

Tun daga nesa ya k'ura mata ido bai d'auke ba har sai da tazo gabanshi tare da huta masa iska a kunne.

"Ke......"

Dariya tayi tare da cewa "sarkin tunani me ake tunawa kuma?"

"Abu biyu?"

"Da wanne da wanne?"

"Rayuwar da zamuyi idan munyi Aure sai na biyu kuma wallahi bana son tafiyar nan"

"Meyasa baka so?"

"Kawai bana son ganin Aliyu sai nake ganin kamar zakice zaki koma gare shi"

Ajiyar zuciya tayi tace "kai nawa ne nima taka ce, babu abinda zai rabamu da yardar Allah, yanzun ma zuwan dole ne ta kama inje d'in"

"Amma ai an gama komai me zakije kiyi musu kuma?"

"Akwai maganganu a bakina da yawa amma sai munje zakaji"

"Allah yasa alkhairi ne"

Murmushi kawai tayi ta shiga motar,shima zagaya wa yayi ya shiga ya tada motar suka tafi.

Suna tafiya suna hira har suka isa Kangire.

A bakin k'ofar gidan ta d'an tsaya wasu zafafan hawaye suka taru a idonta,abu biyu ta tuna Jalal da rayuwar k'auyen.

Da sallama suka shiga gidan Umma na kwance a tsakar gida k'afarnan a kumbure Aliyu na gefenta.

Ganin Janan da yayi ne yasa shi saurin tashi fuskarshi d'auke da hawaye yace "Janan dama zaki waiwayeni"

Adnan da ya gani a bayanta rik'e da Abba k'arami sai duk jikinshi yayi sanyi.

"Janan d'iyata,Janan kinga yadda Allah ya mayar damu ki yafe min Janan"

"Yafiya?Umma yafiya fa kika ce?" Ta fad'a cikin kuka.

"Lokacin giyar so na d'ibata ban damu da abinda kuke min ba amma babu irin rok'o da ban muku ba kan ku yafewa Abba duk da a lokacin ban san wani irin laifi ya muku ba amma kuka take,bak'in cikinku ne ya kashe Abba bazan tab'a yafe muku ba"

"Janan...."
"Dakata Aliyu dama ni abu biyu ne ya kawo ni gidannan"

Ta janyo Abba k'arami tace "ga d'anka ka sani na sani d'anka ne amma ka shegantashi tun kafin yazo duniya hakan ne yasa na cigaba da shegantashi dan babu wanda ya san kaine ubansa,bazan tab'a sanar dashi kaine mahaifinsa har sai ya girma yayi hankali in fad'a masa yadda kukayi amfani da son zuciya da irin sigar da kuka bi kuka tarwatsa farin cikina ta yadda zai k'ara tsanarka"

Ta cigaba da hawaye tana fad'in "abu na biyu shine ko ni kad'ai na rage na yafe maka sannan ka shiga aljanna wallahi bazan tab'a yafewa ba,kun cuceni kun zalunceni Allah ya isa tsakanina daku Allah ya mana sakayya"

Da sauri taja hannun Abba k'arami ta fita,yayi sauri zai bita Adnan ya rik'oshi.
"Karka bita yanzu"

"Dan uwa ka ceceni wallahi na san alhakinta ne ya fara binmu,Mamata ta gujeni,ga Umma kwance ance sai an yanke k'afarta bani da kud'in yin hakan ga kud'in da akace sai na biya duk 'yan uwanmu sun gujemu abinci ma da k'yar nake samu fatana ta bani d'ana ko ganin shi ne inyi sannan ta yafe min"

"Tabbas hausawa sunyi gaskiya da suka ce idan zaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere,Janan bazata yafe maka a k'ank'anin lokaci ba kadai ta yin addu'a"

Hannu yasa ya fiddo kud'i bai tsaya dubawa ba ya bashi sannan ya juya ya tafi Umma na kuka Aliyu nayi.

Yana fita yaga babu Janan,ya tsorata har yayi shirin shiga nemanta sai gata sun fito daga mak'ota.

"Wannan itace wadda ta rik'a dawainiya dani lokacin dana zauna a gidan can"

Gaisawa sukayi da Adnan shima da zasu tafi ya bata kud'i yace tayi cefane.


A hanya ne Adnan ya rage sautin wa'azi sannan ya d'an kalleta idonta na kan titi.

"Dama Abba d'an Aliyu ne"

Gabanta ya fad'i sai da ta d'an jima sannan tace "eh"

"Meyasa kuka b'oye mana?"

"Kayi hak'uri"

"Baki yarda damu ba"

"Wlh ko kad'an"

"To meye dalili?"

Labarin mafarkin Abba ta bashi.

Sai daya d'an murmusa sannan yace "mafarki ai ba gaskiya bane"

"Umm" kawai tace.

"Janan" ya kira sunan a can k'asan mak'oshinsa.

"Na'am" ta amsa a sanyaye.

"Janan ki zama mai yafiya sai kiga Allah ya kara bud'a miki"

Shiru tayi kamar bata jin me yake fad'a.

"Abinda aka yi miki ba'a kyauta ba amma ke ya kamata ki zama mai manta komai Allah ma muna masa laifi ya yafe mana,dan Allah ki yafe musu musamman Ummi da take k'asa kuma ki daina sheganta d'anki kinji"

Nan ma shiru tayi ta cigaba da yin game a wayarta Abba k'arami kuwa tuni yayi bacci.

"Magana nake miki fa Janan"

Kuka ta fashe dashi tamkar k'aramar yarinyar ganin haka ne yasa shi bata hak'uri.

Har suka isa gida bata daina kuka ba,nan ma Mommy ta shiga aikin rarrashinta.

Adnan kuwa hatta Jalal da baya k'asar sai da ya kira ya sanar masa cewa Abba k'arami na da uba,dariya yayi tayi yana cewa shi dama ya san halin Janan lallai a gaida Janan.

Kwanci dashi bikinsu sai matsowa kusa yake,kullum sai yayi mata maganar yafiya kuma sai tayi kukannan amma bai fasa ba dan yasan wata ran zata yafe kuma burinsa shine ta yafe d'in.

Da kanshi  ya kaita asibiti aka d'orata akan magungunan masu cutar HIV sannan aka fad'a mata ranakun da zata na zuwa lectures da kuma yadda zata bi k'a'idojin maganin.

Ana saura sati biyu biki Mameey ta rok'i Mommy alfarmar d'aukar Janan saboda suyi bikin acan ga danginta duk zasu zo.

Mommy kam bata musa ba amma tace sai dai abar Abba k'arami a gurinta.

Hakan kuwa aka yi Janan ta koma kaduna ta sake sabon shirye-shirye da Mameey ke mata tamkar auren fari.

            ********

Rana bata k'arya sai da uwar d'iya taji kunya,yau ne............





_*bikin Adnan da Janan dole a gwangwaje ku biyoni a shafi na gaba*_











_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
           🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




51

Anyi komai na shagalin biki tamkar na budurwa,Kamu,dinner, gala,da duk sauran occasions da ba'ayi ba lokacin bikinta da Aliyu sai da aka yi yanzu,duk da bata da wasu k'awaye a Kaduna amma 'ya'yan 'yan uwa da abokan Fauzah duk sun zo,Humaira da Zee kuma suna a gaba,Momma dama da ita aka fara biki Muhasin sai ranar d'aurin Aure zaizo,Mammy ma cewa tayi ranar d'aurin Aure zata zo Ja'afar zai kawota sai su Kausar Jidda da laila ne sukazo ,Raihan bata zo ba amma Lubna da ita aka yi komai dama tun wancan zuwan bata koma ba,Umman Lubna kuwa bata hanata komai ba dan itama tana zuwa ayi aiki anan ne take fad'awa Janan d'in cewa daddyn Lubna na tayasu murna da fatan alkhairi dan bazai samu zuwa ba yana jin nauyin iyalan Abba.

Haka Maman Raihan ma tazo amma bata fad'i dalilin rashin zuwan Raihan ba itama kuma Janan d'in bata tambaya ba.

Gidan dai cike yake da bak'i kala-kala.

Yau ma a gajiye ta dawo tana shiga d'aki ta cire kaya ta saka na bacci sannan ta zube kan gado tare da lumshe ido.

Lubna ta d'aleta "Lallai yarinyar nan me kike nufi?"

Ta d'an bud'e ido d'aya tace "ke wallahi bacci nake ji na gaji"

"Allah tashi zakiyi mu fita mu kama wani aikin gobe fa d'aurin aure"

Rufe idon nata tayi tace "babu inda zani wallahi a gajiye nake ga wayata nan Adnan ma ce masa nayi kada ya kira sai sun sauka saboda bacci yayi min yawa a ido idan ya kira ki tasheni"

"Cab kin raina min hankali fa wato ni zan jire miki kiran Adnan ba?"

"Haba kawata kinsan nifa Amarya ce sai da lallab'a"

"Lallai kam,sannu amarya ke d'in zan lallab'a?zaki bushe kuwa"

"Ni dai komai zaki ce baccina zanyi" ta juya mata baya.

Lubna tayi dariya ta fita kawai.

Kamar daga sama taji wayarta na ringing ta lalubo da hannu ta d'aga sannan ta kara a kunne.

"Har kun isa?"

"Itace sallamar?"

"Oh salamu alaikum da fatan kunje gida lafiya ya gajiyan dinner?"

Murmushi yayi tamkar tana gabansa yace "Alhamdulillah kinga yanzu muka sauka ko fita daga mota banyi ba nace sai na kira gimbiyata naji ya take"

Hamma tayi tare da yin mik'a sannan tace "wallahi har na fara bacci"

"Tun yanzu"

"Eh wallahi kasan tunda aka fara biki ban samu nayi baccin cikakken awa biyu fa"

"Meyasa?"

"Hayaniya mana ga kasan dai taro dole sai an gama ake samun nutsuwa"

"Hakane kam ai bayan biki a gaba zan sakaki ki rik'a yin bacci har sai na tabbatar kin huta kin rama baccin ki"

Dariya tayi cikin jindad'i tace "office d'in fa?"

"Ai hutu zan d'auka na wata uku inci amarcina dani dake babu mai takura mana in riritaki tamkar kwai"

Dariya ta sake yi tare da fad'in "wow kace na zama 'yar gatan Adnan"

"Sosaima"

"To yanzu kasan abinda za'ayi?"

"Sai kin fad'a"

"Kaje kayi wanka kaci abinci sannan ka kwanta kayi bacci dan ka huta kafa kashe wayarka kada ma Adam(amininsa) ya damar min kai da kira,ka kular min da kanka"

"Karki damu gimbiyata angama duk abinda kikace ai shi za'ayi"

"Yawwa na manta ban fad'i wani abu ba?"

"To ina jinki"

"Kayi mafarkina kaji,ina Sonka sosai" bata jira me zai ce ba ta katse wayar ta kasheta gaba d'aya saboda kunya taji, murmushin jindad'i tayi ta fara tunanin irin soyayyar da zata gina a gidan Adnan.

A haka har bacci ya kwasheta,k'arfe uku na dare alarm ya tasheta ta shiga toilet tayi alwallah ta fito ta kalli su Lubna dake ta bacci ta d'ala mata  duka zubur ta bud'e ido.

Dariya Janan tayi tace "a rage baccin asara a tashi ayi nafila"

"Dalla malama mene haka kin san Allah zan tashi su kausar da duk 'yan matannan in har baki barni ba"

"A'a suna baccinsu a takurasu shikenan dai kema koma".

Dariya kawai tayi ta juya kwanciyarta data baby.


         *********

Dubban mutane ne suka shaida Auren Janan da Adnan,Alh Ibrahim shine ya zamo waliyyinta.

Tana zaune ita da su kausar taji ana rangad'a gud'a.

Jinkinta yayi sanyi lokaci guda ta tsinci kanta a wani yanayi da bazata musalta shi ba.

Fauziyya da Bilkisu ne suka shigo d'akin suna rangad'a gud'a Janan tayi saurin rufe fuska.

" to Hajiyata an d'aura fa Salman ya zama na Janan" Fauziyya ta fad'a tana dariya.

Ita dai batace komai ba bayan farin cikin da ya mamaye ta.

Lubna ce ta shigo da gudu tare da zama gefenta tace "Umm auren masoya ya tabbata wallahi an d'aura yanzu Adnan d'in ya kirani suna wajen lunch na d'aurin yanzu zasu dawo ki shirya za'ayi pix fa.

Pictures kuwa anyi su kala-kala sai kusan k'arfe biyu 'yan d'aurin Aure suka fara shirin tafiya Abuja da yake tun 11am aka d'aura auren ita kuma Amarya da yamma za'a kaita da dare kuma za'ayi fitacciyar dinner ta friends kawai ba iyaye.

A waya Adnan ya kirata ya sanar da ita sun bar Kaduna yanzu amma da sun sauka zai kirata dan haka karta yi nisa da wayarta.

"Allah ya saukeka lafiya mijina ka kulamin da kanka"

"Ameen matata kema ki kulamin da kanki"

"Insha Allahu".


*_2hours later_*

Gida cike yake da mutane ana ta hada-hada.

Janan tana gidan su bilkisu ita da k'awayenta dan har ta sake yin wanka ta saka wani tsadaddan lace ga alkyabbarta a cikin closet d'in haj Mariya dan an fara shirye-shiryen tafiya kai Amarya,sai za'a kaita sannan za'a saka mata alkyabba.

Fauziyya ce ta shigo tare da jan hannunta tace "kizo inji Mameey"

Murmushi tayi tace "ya Fauzah ba dai har an kawo motoci ba?"

"A'a cewa dai tayi na kira ki"

"To"

"Lubna muje ki rakata"

"To Yaya Fauzah" har sun fito farfajiyar gidan Fauziyya na rik'e da hannun Janan wayarta ta fara ringing,d'agawa tayi ta kara a kunne tace "gashinan mun taho da Janan d'in fa?"

 Daga d'ayan b'angaren Mameey tayi magana ba dai suji me tace ba sai Fauziyya kawai tace "to shikenan"

Katse wayar tayi tace "wai muje falon  baffa(Alhaji Ibrahim) shine yake nemanki itama Mameey yanzu zata shigo.

" wai meya faru ne Yaya Fauzah nifa gabana fad'uwa yake "

"Babu abinda ya faru wa'azi dai kinsan dole a miki fad'uwar gaba kuwa dama ta zama dole ga kowace Amarya kafin a kaita"

A falon suka tarar da Baffa da wani abokinsa,Haj Mariya sai Momma da Yaya Musahin.

Suna yin sallama duk suka d'ago kai suka kallesu, gaidasu sukayi sannan suka zauna a gefe,Janan kanta a k'asa ta kasa had'a ido da kowa.

Fauziyya ta rik'e hannun sosai.

Momma ce ta tashi ta koma gabanta ta zauna "Janan kinci abinci?"

Kai ta d'aga alamar eh.

"Kin tabbatar kinci kin k'oshi ko zaki k'ara?" Haj Mariya ma ta jefo tata tambayar.

"Alhamdulillah" ta fad'a har lokacin kanta a k'asa.

"Janan d'ago ki kalleni" Alhaji Ibrahim yayi maganar.

"Na'am" kawai tace ta kasa d'ago kan.

"Kin tsinci kanki a jarabobi masu yawa na rayuwa kuma kin fawwalawa Allah hakane?"

"Hakane baffa" ta fad'a lokacin da taji bugun zuciyarta ya k'aru.

Ya d'an yi shiru sannan ya cigaba da fad'in "Janan ina son ki k'ara juriya ki zama jajartacciya mai tawakkali kinji"

"To"

"Duk abinda kikaga ya samu bawa muk'addarine daga ubangiji kuma kowa da tashi Jarabawar"

Nan kuma shiru tayi d'akin yayi tsit.

Alhaji Ibrahim yafi minti biyu kafin ya sake cewa "zaku shirya ku tafi Abuja dake da Mamanki damu,mijinki Allah ya k'addara musu sunyi accident a hanyarsu ta komawa yanzu haka suna asibiti acan Abuja"

Tun kafin ya k'arasa magana ta mik'e tsaye.

Da k'yar Momma ta zaunar da ita.

Kusan seconds goma bata ce komai ba babu hawaye a idonta.

Lokaci guda ta zunduma salati sannan ta rungume Momma "na shiga uku,na shiga uku meyasa rayuwa ke wahalar damu"

"Janan kiyi hak'uri ai da sauk'i jikin nashi"

"Momma na shiga uku wallahi na shiga uk......"  Daganan basu sake jin motsin ta ba.

"Janan! Janan!!" Sunanta suke kira suna jijjagata amma ina.

Fauzah da Lubna ma kukan kawai suke.


_30 Minutes later_

Tana bud'e ido taga Mameey rik'e da hannun ta.

Da sauri ta tashi ta sake fashewa da kuka "Mameey d'azu muka gama waya da zasu tafi fa wannan wace irin k'addarace ranar aurena"

Rungumeta Mameey tayi tana rarrashi.

"Na shiga uku"

"Baki shiga uku ba Janan Addu'a zaki masa ki tashi ku tafi kar dare yayi,an had'a miki kaya a trolley saboda ke zakiyi jinyar mijinki Allah ya bashi lafiya"

Wani sabon kuka ta fashe dashi.

Mameey ta kalli Fauziyya tace "ku tafi keda Lubna idan yaso sai ku dawo tare dasu Baffa ko?"

"To Mameey"

Mota biyu akayi,Momma, Fauzah, Lubna da Janan a d'aya.

Sai d'ayar kuma "Alhaji Ibrahim,Sagir Muhasin da Fahad.

Janan har suka isa tana kuka fuskarta tayi jajir idanunta ma haka sunyi jajir sun sake juyewa ga fatar idon ta kumbura.

A k'ofar asibitin aka jagorancesu har zuwa inda su Mommy suke dan har lokacin su kansu basu samu damar ganin shi ba,ga 'yan sanda a tsaitsaye.

Mommy idonta yayi jajir itama lokaci zuwa lokaci tana goge hawaye.

Abba k'arami yana ganin Janan ya ruga ya rungumeta yana fad'in " Ammi oyoyo".

Sun gaisa da Mommy ta janyo Janan tare da d'ora kanta a cinyar Janan d'in "kukan ya isa haka 'yata kiyi addu'a kinji"

"Ance sauran sun rasu?"

"Mommy ta kalli Momma tace "Motar da ta kara musu mutum biyu sun rasu motar su Adnan kam shi kad'ai ne ya rayu shima d'in baki ganshi ba" ta sake goge hawaye sannan tace "abindai sai godiya ga Allah sauran ukun ma har an tafi dasu gida za'ayi jana'iza,shi kansa Adnan d'in bai san inda kanshi yake ba har yanzu muma ba mu samu ganin shi ba tukun"

Adam dake tsaye yayi ajiyar zuciya yace "Allah kenan mota d'aya fa muka shiga a zuwa amma a dawowa yace bazai shiga motana ba saboda ina mahaukacin driving kawai dai Allah ya k'addara hakan zata faru dashi ne"

"Allah ya bashi lafiya"

"Ameen".







_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
           🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




51

Anyi komai na shagalin biki tamkar na budurwa,Kamu,dinner, gala,da duk sauran occasions da ba'ayi ba lokacin bikinta da Aliyu sai da aka yi yanzu,duk da bata da wasu k'awaye a Kaduna amma 'ya'yan 'yan uwa da abokan Fauzah duk sun zo,Humaira da Zee kuma suna a gaba,Momma dama da ita aka fara biki Muhasin sai ranar d'aurin Aure zaizo,Mammy ma cewa tayi ranar d'aurin Aure zata zo Ja'afar zai kawota sai su Kausar Jidda da laila ne sukazo ,Raihan bata zo ba amma Lubna da ita aka yi komai dama tun wancan zuwan bata koma ba,Umman Lubna kuwa bata hanata komai ba dan itama tana zuwa ayi aiki anan ne take fad'awa Janan d'in cewa daddyn Lubna na tayasu murna da fatan alkhairi dan bazai samu zuwa ba yana jin nauyin iyalan Abba.

Haka Maman Raihan ma tazo amma bata fad'i dalilin rashin zuwan Raihan ba itama kuma Janan d'in bata tambaya ba.

Gidan dai cike yake da bak'i kala-kala.

Yau ma a gajiye ta dawo tana shiga d'aki ta cire kaya ta saka na bacci sannan ta zube kan gado tare da lumshe ido.

Lubna ta d'aleta "Lallai yarinyar nan me kike nufi?"

Ta d'an bud'e ido d'aya tace "ke wallahi bacci nake ji na gaji"

"Allah tashi zakiyi mu fita mu kama wani aikin gobe fa d'aurin aure"

Rufe idon nata tayi tace "babu inda zani wallahi a gajiye nake ga wayata nan Adnan ma ce masa nayi kada ya kira sai sun sauka saboda bacci yayi min yawa a ido idan ya kira ki tasheni"

"Cab kin raina min hankali fa wato ni zan jire miki kiran Adnan ba?"

"Haba kawata kinsan nifa Amarya ce sai da lallab'a"

"Lallai kam,sannu amarya ke d'in zan lallab'a?zaki bushe kuwa"

"Ni dai komai zaki ce baccina zanyi" ta juya mata baya.

Lubna tayi dariya ta fita kawai.

Kamar daga sama taji wayarta na ringing ta lalubo da hannu ta d'aga sannan ta kara a kunne.

"Har kun isa?"

"Itace sallamar?"

"Oh salamu alaikum da fatan kunje gida lafiya ya gajiyan dinner?"

Murmushi yayi tamkar tana gabansa yace "Alhamdulillah kinga yanzu muka sauka ko fita daga mota banyi ba nace sai na kira gimbiyata naji ya take"

Hamma tayi tare da yin mik'a sannan tace "wallahi har na fara bacci"

"Tun yanzu"

"Eh wallahi kasan tunda aka fara biki ban samu nayi baccin cikakken awa biyu fa"

"Meyasa?"

"Hayaniya mana ga kasan dai taro dole sai an gama ake samun nutsuwa"

"Hakane kam ai bayan biki a gaba zan sakaki ki rik'a yin bacci har sai na tabbatar kin huta kin rama baccin ki"

Dariya tayi cikin jindad'i tace "office d'in fa?"

"Ai hutu zan d'auka na wata uku inci amarcina dani dake babu mai takura mana in riritaki tamkar kwai"

Dariya ta sake yi tare da fad'in "wow kace na zama 'yar gatan Adnan"

"Sosaima"

"To yanzu kasan abinda za'ayi?"

"Sai kin fad'a"

"Kaje kayi wanka kaci abinci sannan ka kwanta kayi bacci dan ka huta kafa kashe wayarka kada ma Adam(amininsa) ya damar min kai da kira,ka kular min da kanka"

"Karki damu gimbiyata angama duk abinda kikace ai shi za'ayi"

"Yawwa na manta ban fad'i wani abu ba?"

"To ina jinki"

"Kayi mafarkina kaji,ina Sonka sosai" bata jira me zai ce ba ta katse wayar ta kasheta gaba d'aya saboda kunya taji, murmushin jindad'i tayi ta fara tunanin irin soyayyar da zata gina a gidan Adnan.

A haka har bacci ya kwasheta,k'arfe uku na dare alarm ya tasheta ta shiga toilet tayi alwallah ta fito ta kalli su Lubna dake ta bacci ta d'ala mata  duka zubur ta bud'e ido.

Dariya Janan tayi tace "a rage baccin asara a tashi ayi nafila"

"Dalla malama mene haka kin san Allah zan tashi su kausar da duk 'yan matannan in har baki barni ba"

"A'a suna baccinsu a takurasu shikenan dai kema koma".

Dariya kawai tayi ta juya kwanciyarta data baby.


         *********

Dubban mutane ne suka shaida Auren Janan da Adnan,Alh Ibrahim shine ya zamo waliyyinta.

Tana zaune ita da su kausar taji ana rangad'a gud'a.

Jinkinta yayi sanyi lokaci guda ta tsinci kanta a wani yanayi da bazata musalta shi ba.

Fauziyya da Bilkisu ne suka shigo d'akin suna rangad'a gud'a Janan tayi saurin rufe fuska.

" to Hajiyata an d'aura fa Salman ya zama na Janan" Fauziyya ta fad'a tana dariya.

Ita dai batace komai ba bayan farin cikin da ya mamaye ta.

Lubna ce ta shigo da gudu tare da zama gefenta tace "Umm auren masoya ya tabbata wallahi an d'aura yanzu Adnan d'in ya kirani suna wajen lunch na d'aurin yanzu zasu dawo ki shirya za'ayi pix fa.

Pictures kuwa anyi su kala-kala sai kusan k'arfe biyu 'yan d'aurin Aure suka fara shirin tafiya Abuja da yake tun 11am aka d'aura auren ita kuma Amarya da yamma za'a kaita da dare kuma za'ayi fitacciyar dinner ta friends kawai ba iyaye.

A waya Adnan ya kirata ya sanar da ita sun bar Kaduna yanzu amma da sun sauka zai kirata dan haka karta yi nisa da wayarta.

"Allah ya saukeka lafiya mijina ka kulamin da kanka"

"Ameen matata kema ki kulamin da kanki"

"Insha Allahu".


*_2hours later_*

Gida cike yake da mutane ana ta hada-hada.

Janan tana gidan su bilkisu ita da k'awayenta dan har ta sake yin wanka ta saka wani tsadaddan lace ga alkyabbarta a cikin closet d'in haj Mariya dan an fara shirye-shiryen tafiya kai Amarya,sai za'a kaita sannan za'a saka mata alkyabba.

Fauziyya ce ta shigo tare da jan hannunta tace "kizo inji Mameey"

Murmushi tayi tace "ya Fauzah ba dai har an kawo motoci ba?"

"A'a cewa dai tayi na kira ki"

"To"

"Lubna muje ki rakata"

"To Yaya Fauzah" har sun fito farfajiyar gidan Fauziyya na rik'e da hannun Janan wayarta ta fara ringing,d'agawa tayi ta kara a kunne tace "gashinan mun taho da Janan d'in fa?"

 Daga d'ayan b'angaren Mameey tayi magana ba dai suji me tace ba sai Fauziyya kawai tace "to shikenan"

Katse wayar tayi tace "wai muje falon  baffa(Alhaji Ibrahim) shine yake nemanki itama Mameey yanzu zata shigo.

" wai meya faru ne Yaya Fauzah nifa gabana fad'uwa yake "

"Babu abinda ya faru wa'azi dai kinsan dole a miki fad'uwar gaba kuwa dama ta zama dole ga kowace Amarya kafin a kaita"

A falon suka tarar da Baffa da wani abokinsa,Haj Mariya sai Momma da Yaya Musahin.

Suna yin sallama duk suka d'ago kai suka kallesu, gaidasu sukayi sannan suka zauna a gefe,Janan kanta a k'asa ta kasa had'a ido da kowa.

Fauziyya ta rik'e hannun sosai.

Momma ce ta tashi ta koma gabanta ta zauna "Janan kinci abinci?"

Kai ta d'aga alamar eh.

"Kin tabbatar kinci kin k'oshi ko zaki k'ara?" Haj Mariya ma ta jefo tata tambayar.

"Alhamdulillah" ta fad'a har lokacin kanta a k'asa.

"Janan d'ago ki kalleni" Alhaji Ibrahim yayi maganar.

"Na'am" kawai tace ta kasa d'ago kan.

"Kin tsinci kanki a jarabobi masu yawa na rayuwa kuma kin fawwalawa Allah hakane?"

"Hakane baffa" ta fad'a lokacin da taji bugun zuciyarta ya k'aru.

Ya d'an yi shiru sannan ya cigaba da fad'in "Janan ina son ki k'ara juriya ki zama jajartacciya mai tawakkali kinji"

"To"

"Duk abinda kikaga ya samu bawa muk'addarine daga ubangiji kuma kowa da tashi Jarabawar"

Nan kuma shiru tayi d'akin yayi tsit.

Alhaji Ibrahim yafi minti biyu kafin ya sake cewa "zaku shirya ku tafi Abuja dake da Mamanki damu,mijinki Allah ya k'addara musu sunyi accident a hanyarsu ta komawa yanzu haka suna asibiti acan Abuja"

Tun kafin ya k'arasa magana ta mik'e tsaye.

Da k'yar Momma ta zaunar da ita.

Kusan seconds goma bata ce komai ba babu hawaye a idonta.

Lokaci guda ta zunduma salati sannan ta rungume Momma "na shiga uku,na shiga uku meyasa rayuwa ke wahalar damu"

"Janan kiyi hak'uri ai da sauk'i jikin nashi"

"Momma na shiga uku wallahi na shiga uk......"  Daganan basu sake jin motsin ta ba.

"Janan! Janan!!" Sunanta suke kira suna jijjagata amma ina.

Fauzah da Lubna ma kukan kawai suke.


_30 Minutes later_

Tana bud'e ido taga Mameey rik'e da hannun ta.

Da sauri ta tashi ta sake fashewa da kuka "Mameey d'azu muka gama waya da zasu tafi fa wannan wace irin k'addarace ranar aurena"

Rungumeta Mameey tayi tana rarrashi.

"Na shiga uku"

"Baki shiga uku ba Janan Addu'a zaki masa ki tashi ku tafi kar dare yayi,an had'a miki kaya a trolley saboda ke zakiyi jinyar mijinki Allah ya bashi lafiya"

Wani sabon kuka ta fashe dashi.

Mameey ta kalli Fauziyya tace "ku tafi keda Lubna idan yaso sai ku dawo tare dasu Baffa ko?"

"To Mameey"

Mota biyu akayi,Momma, Fauzah, Lubna da Janan a d'aya.

Sai d'ayar kuma "Alhaji Ibrahim,Sagir Muhasin da Fahad.

Janan har suka isa tana kuka fuskarta tayi jajir idanunta ma haka sunyi jajir sun sake juyewa ga fatar idon ta kumbura.

A k'ofar asibitin aka jagorancesu har zuwa inda su Mommy suke dan har lokacin su kansu basu samu damar ganin shi ba,ga 'yan sanda a tsaitsaye.

Mommy idonta yayi jajir itama lokaci zuwa lokaci tana goge hawaye.

Abba k'arami yana ganin Janan ya ruga ya rungumeta yana fad'in " Ammi oyoyo".

Sun gaisa da Mommy ta janyo Janan tare da d'ora kanta a cinyar Janan d'in "kukan ya isa haka 'yata kiyi addu'a kinji"

"Ance sauran sun rasu?"

"Mommy ta kalli Momma tace "Motar da ta kara musu mutum biyu sun rasu motar su Adnan kam shi kad'ai ne ya rayu shima d'in baki ganshi ba" ta sake goge hawaye sannan tace "abindai sai godiya ga Allah sauran ukun ma har an tafi dasu gida za'ayi jana'iza,shi kansa Adnan d'in bai san inda kanshi yake ba har yanzu muma ba mu samu ganin shi ba tukun"

Adam dake tsaye yayi ajiyar zuciya yace "Allah kenan mota d'aya fa muka shiga a zuwa amma a dawowa yace bazai shiga motana ba saboda ina mahaukacin driving kawai dai Allah ya k'addara hakan zata faru dashi ne"

"Allah ya bashi lafiya"

"Ameen".







_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
           🍁🍁🍁
        


_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


_Wannan shafin sadaukarwa ne gareki sister Ramlat,tnx 4 d luv & support😍._




52

Har su Mammy da Fauzah suka juya ba'a fito da Adnan ba.

Sun tafi ne da niyyar washe gari su dawo.

Sai gab da sallar isha'i sannan suka suma ganinsa.

Suma Janan tayi lokacin da ta ganshi dan ta tsorata ainun,guri kad'an ne a jikinshi ba bandeji da fulasta.

Kuka sosai take lokacin da ta tsinci kanta a kwance a gadon asibiti.

Tashi tayi da sauri ta koma d'akin Adnan d'in lokacin Mommy waya take Adam na rik'e da hannunsa.

"Sannu Janan" shine abinda ta fad'a bayan ta ajje wayar.

Janyota tayi jikinta tana rarrashi tare da cewa "ba kuka zakiyi ba addu'a zakiyi kinji".

Kai ta d'aga alamar to.

"Ga Jalal ma hankalinsa ya tashi sosai yace a satin nan zai samu yazo"

"Wlh kuwa Adam nima na ce masa yayi zamansa tunda koda yazo d'inma dubiya ce kawai amma yace a'a"

"Dole sai yazo d'in Mommy ai bazai iya hak'uri ba dan koni bazan ce karya zo ba"

"Allah ya kawo shi lafiya"

"Ameen"

Mommy babu yacce batayi ba akan Janan su tafi gida amma tace ita babu inda zataje ita zatayi jinyarshi.

Haka Mommy ta hak'ura suka tafi aka bar Janan d'in ita kad'ai.

Hannunsa ta rik'e sosai tana kuka.

Daga dare zuwa safiya nurses sunzo dubashi yafi a k'irga.

'K'arfe biyu ta tashi ta fara nafiloli na nemawa mijinta lafiya wajen ubangiji.

Da asuba kuwa yanayin sallah ta shiga toilet d'in tayi wanka saboda mutane zasu fara zuwa da gari yayi haske.

Mai kawai ta shafa a jikinta ta fesa turare,ko kwalli bata saka ba idanunma duk sun kumbura.

Material ta saka doguwar Riga mara nauyi sannan ta ajje gyakenta a gefe ta kalli inda Adnan yake kwance kamar gawa.

Komawa tayi ta kulle k'ofar d'akin da key sannan ta dawo tayi masa bed bath.

Ta gama sannan ta shafa masa turaruka ta zura masa kaya cikin dubara da k'ok'ari da jajircewa takeyin komai.

Tsura masa ido tayi bayan ta gama shiryashi,ta goge kwallar idonta tace "kaman ba kai ba Adnan lokaci guda kamaninka sun canza"

Ta zauna kan kujera tare da rik'o hannunsa tace "karka mutu dan Allah Adnan,ina buk'atarka a raye saboda mu cika burinmu na rayuwa ina son ka dan Allah ka tashi"

Sunkuyar da kai tayi ta cigaba da kuka a wannan kukan bacci ya d'auketa.

Ji tayi an d'an bubbugi kafad'arta,ta bud'e ido a hankali ta kalli nurse d'in.

"Bacci kika samu?"
Murmushi tayi tare da cewa "ban ma san ya d'aukeni ba"

"Kiyi hak'uri sister Addu'a zaki cigaba da yi kinji,duk da dai munji ance jiya aka d'aura auren ku lallai dole ki shiga tashin hankali amma dai addu'a itace magani"

Kai kawai ta d'aga.

"Ga wannan k'arfe takwas likita zaizo za'aje lab a k'arbo jini sannan za'ayi test da yamma"

"To" tace tare da karb'ar takardar.

Nurses d'in suna fita   suka fara gulmar yana da HIV a test d'in da aka yi sun gani.

'Dayar tace "kika sani ko itama tana dashi"

"K'ila kuwa gashi a haka kamar masu lafiya"

"To suna bin k'a'idoji kuma kinga ai musu kud'ine"

"Hakane kuma"

"Uhm kinga muyi abinda zai fishshemu"

Tafiya sukayi ba tare da sun sake magana ba.


'Karfe bakwai Mommy tazo itama kwantar mata da hankali ta cigaba da yi duk da cewar itama cikin damuwar take.

Su Mameey sunzo sun yi dubiya haka 'yan biki yawanci duk anzo an dubashi.

Cikin kwana biyu Janan ta sake zugewa ta rame tamkar ba ita ba,kasancewar yadda taga jikin Adnan na sake rud'ewa da an saka masa jini yake k'onewa hankalinsu ya kai k'ololuwar tashi.

Kwananshi hud'u a asibiti Jalal ya diro k'asar k'arfe 12 na dare.

Ko gida baije ba tun daga airport da direban gidansu yazo d'aukanshi yace su wuce asibiti.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda ya fad'a lokacin da yaga Adnan d'in.

Jin yadda ya rangad'a salati ba k'aramin d'aga wa Janan hankali yayi ba.
Aikuwa hawaye dama k'iris suke jira sai gasu shar a idanunta.

Juyowa yayi ya kalleta jikinshi a sanyaye yace "Janan ko kema baki da lafiyar ne?"

Kai ta girgiza alamar a'a.

"Gaskiya bazai yuwu a bar Adnan anan ba sai dai a tafi dashi can outside gurin k'wararrun likitoci"

Ita dai shiru tayi tana k'ara goge hawayen idonta.

Ya kai dubansa ga leb'ensa wanda yayi bak'i k'irin yace "Kamar ba kai ba Allah ya baka lafiya"

"Ameen" ta amsa a sanyaye

Juyawa yayi ya kai duba ga direban yace "Malam Hassan ka tafi gida kawai dan ni ina nan ka sanarwa Mommy haka da safe"

"Okay Allah ya k'ara masa lafiya kaikuma Allah ya huta gajiya"

"Ameen" ya amsa.

Yana gefen gado rik'e da hannun Adnan wanda a lokacin ma jini aka saka ita kuma Janan tana zaune kan kujera hannunta rik'e da al Qur'an tana karantawa.

'Karfe biyu ta shiga toilet ta d'oro alwallah ta dawo ta tada sallah,ganin haka ne yasa Jalal shima ya shiga yayi akwallah ya fito ya tada sallah.

Da Asuba kuwa yana fita masallaci tayi sauri ta shiga tayi wanka sannan ta saka kaya bata ma tsaya fesa turare da shafa mai ba kawai ta d'ebo ruwa tayiwa Adnan bed bath sannan ta shiryashi tana cikin shafa mai Jalal ya shigo.

"Ya mai jiki?"

"Da sauk'i ina kwana"

"Lafiya k'alau sannu da k'ok'ari Janan"

Murmushi kawai tayi.

"Bara naje gida nayi wanka sai na dawo"

"To ba damuwa".


         ***********

Yarinyar da suka yiwa fyad'e kwance take cikin jini tana jujjuya kai.

Faisal da yazo gareta ya durk'usa kusa da ita a hankali ta rik'o hannunsa bakinta na fidda jini da k'yar tace "mamana ni kad'ai take da ita dan Allah ku kaini gurin iyayena kar nayi mutuwar wulak'anci"


Wasu hawaye ne suka fito a idonsa sau biyu yanayin nadama meyasa bazai mik'a kansa gurin 'yan sanda ba.

"Ka kaini gurin Abbu dan Allah"

"Ya sunanki?"

"A...Amal"

Ganin tana mimmik'ewa yasa shi d'aukarta da sauri ya saka a mota ya shiga da ita cikin garin Abuja.

Yayi tunanin kiran ogan nasu sai yayi tunanin akwai matsala.

Dad'insa d'aya ba sosai suka fiya sato 'yan mata a Abuja suna lalatawa ba sundai fi yi a kano dan haka kai tsaye ya wuce private hospital d'in daya sani.

Da gudu ya shiga ya yi bayani aka fito da sauri aka d'auketa aka yi cikin da ita.

Yana k'ok'arin binsu ya hango Jalal tsaye yana waya da sauri ya k'arasa gurinshi yace "d'an uwa dan Allah kayi min taimako"

"Na me?"

Janyo hannunsa yayi suka zagaya sannan yayi masa bayanin irin abubuwan da aka yiwa yarinyar baisan kowa nata ba a hanya suka had'u da ogansa motarta ta lalace shine ogannasu yace bara ya rage mata hanya daga nan suka amfani da hoda suka gusar da tunaninta.

"Subhanallah to a wane unguwa take?"

"Ban sani ba tace min sunan ta Amal amma naji tana kiran Abbu maybe babanta ne,kada kace tsintarta kayi ka zamo d'an uwa a gareta in har Allah ya tashi kafad'unta zata sanar da kai komai ni yanzu kaduna zan tafi zan zartar da wani abu sannan in kai kaina ga 'yan sanda bana so a kamani yanzu ba tare dana isa Kaduna ba"

"Amma meyasa sai ni meyasa zaka ce saini taya ban san yarinyar ba........."


"Kayi hak'uri d'an uwa" da gudu Faisal ya shiga motarsa ya bar Jalal tsaye.

Yafi minti biyar kafin ya shiga ya tambaya inda take.

"Kaine ka kawota?"
 "Eh nine" ya fada a sanyaye.

"To gaskiya bazamu tab'a ta ba sai kayi reporting ma police"

"taya zaka ce inyi reporting ma police bayan kana gani yadda jini ke duba a jikinta"

Dafa kafad'arsa doctor yayi yace "tsarin ko wane asibiti a garinnan kenan case na fyad'e bama karb'a har sai an kira 'yan sanda saboda gudun kar abin ya zamar mana matsala"

Janan da ta fito zata je lab ta hangosa tsaye a gurin da sauri ta k'arasa ganin itace kar ta fad'i abinda zaisa a tuhumesa yayi saurin cewa "Kinga yadda Amal ta koma na rasa ya zanyi fyad'e aka mata kuma suna ik'rarin sai mun kirawo police sannan su tab'a ta"

Fuskarta d'auke da mamaki amma ganin yadda ya rikice ne yasa ta danna number Ja'afar ta kirashi tayi masa bayani dsame abinda ya faru da Ummi but wannan 'yar uwar Jalal ce ta santa ma(tayi masa k'aryar hakan).

Cewa yayi a bawa doctor waya,bayani yayi masa sosai tare da fad'in ayiwa yarinyar komai zasu k'araso cikin awa uku.

Ana shiga da ita suka had'a ido da Janan d'in wanda take masa kallon tuhuma.

Da sauri ta d'aga k'afa zata bar gurin ya rik'o hijabinta.

"Janan zan miki bayani"

Bincikewa tayi sannan ta wuce lab takai takardar ta dawo.

Ba kowa a d'akin kasancewar yau sadakar bakwai ta abokan Adnan da sukayi accident tare su Mommy suna can.

Kallon Adnan tayi ta zauna kusa da shi tana hawaye ta rik'o hannunsa tare da fad'in "dan Allah ka tashi kaji,ka tashi muyi rayuwarmu cikin aminci dan Allah Mijina"

Kanta ta d'ora a gadon tana kuka tunda aka kawoshi har yau bata tab'a ganin ya motsa koda fatar idonsa kwanansu bakwai kenan.

Tana nan zaune Jalal d'in ya shigo.

Ta d'ago idanunta ta kalleshi.

Zama yayi a gefe jikinshi a sanyaye.

"Ya jikin Adnan"

"Alhamdulillah" ta fad'a.

"Janan" ya kira sunanta da sassanyar murya.

Bata amsa ba kuma bata kalleshi ba.

Bai damu da hakan ba kawai ya fara bata labarin abinda ya faru tsakaninsu da Faisal.

Idonta cike da hawaye tace "kar kayi tunanin na zargeka a'a ko kad'an ba haka bane,kawai bana son ka shiga matsala ne"

"Kin damu dani kenan" yayi maganar a raunane.

'Dago kai tayi suka had'a ido tayi saurin sauke k'wayar idonta k'asa tace "dole in damu da kai saboda b'angare biyu kake,kana matsayin abokina wanda ya ceto rayuwata sannan kuma kai k'anin mijina ne kaga kuwa dole in damu da kai"

Shiru yayi ba tare da yace komai ba.

Su Mommy na zuwa yayi musu bayani tare suka je suka dubata yarinyar tamkar gawa.

Jinin Jalal aka d'iba aka saka mata kasancewar blood group d'insu d'aya.

Aikuwa gida ya tafi saboda jiri da ya rik'a d'ibarsa dan kwana biyu da d'aukar jininsa aka sawa Adnan yau gashi an sake d'auka.

        *********

A k'ofar gidan ya tsaya kusan minti biyu bai shiga ba,wanda ya rakosa tuni ya tafi amma ya kasa shiga.

Cikin dakiya yayi sallama ya shiga,Zuhra na bakin murhu tana hura wuta Umma na kwance kan tabarma har lokacin ba'a yanke k'afar ba sai zugin azaba take mata,rashin abincin ci yafi damunsu wani lokacin sai Nura ne ke taimaka musu kud'in da Adnan ya basu kuwa tuni suka k'are a magungunan da aka d'ora Umma akai dan Allah ya jarabto mata hawan jini tamkar bazata rayu ba,Zuhra kuwa tsabar son da takewa Aliyu da kuma tausaya masa ne ya saka ta dawo garesu wani lokacin Malam yana sawa a kawo musu abinci mamanta kuwa tace wlh babu ruwanta da ita natsawar bata dawo gida ba.

"Sannunki"

Zuhra ta d'ago kai cikin rashin gane ko shi waye tace "yawwa sannu"

"Ali yana nan kuwa?"

"Eh ya shiga bayi"
Tana rufe baki sai gashi ya fito.

Butar dake hannunsa ya saki sannan ya damk'o wuyan Faisal.

"Sai na kashe ka Ashe kana raye ka kawo min annoba ka gudu wallahi sai na kasheka"  duk wani k'arfinsa ya sake shi akan Faisal wanda ya kasa tab'uka komai.

Salati Zuhra keyi tare da fad'in ya sake shi dan Allah.

Ganin Aliyu na k'ok'arin yin kisan kai yasa ta fita da gudu ta kira mutane.

Da k'yar aka rabasu yana k'ara fad'in wallahi saiya kasheshi.

Da gudu Zuhra ta tafi gida ta sanarwa Malam abinda ke faruwa.

Tare suka taho ya jawosu dan sasanci.

Kuka sosai Aliyu yake yana bashi labarin abubuwan da Usman ya masa tun had'uwarsu har lokacin daya karb'i Babur d'insa ya gudu.

"Meyasa kai haka?kasan kuwa hak'k'in wanda aka kashe gaba d'aya ya rataya akanka saboda Kaine sanadi"

Shima Usman d'in kuka yake yana fad'in "tabbas nayi kuskure kuma bansan abin zai kai har haka ba,bayan sati d'aya da faruwar abin nazo garin naji abinda ya faru shiyasa nayi shawarar yin nesa da su tun kafin 'yan sanda su gano ni su kasheni,na yanke shawarar bazan sake dawowa ba na koma can lagos kusan shekara biyar sannan na dawo kano na cigaba da harkata"

Aliyu sai k'ok'arin kai masa duka yake Malam ya hana.

"Meya dawo da kai yanzu?" Malam ya sake tambayarshi.

"Nazo ne dan in nemi gafararsu saboda na tafka Babban kuskure kuma kullum da mafarkin abin nake rayuwa shiyasa na yanke hukunci in nemi gafarsu kafin in mik'a kaina ga hukuma,damu da oganmu ne muka hadu muka yiwa Ummi fyad'e"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" Umma ta fad'a tana k'ok'arin tashi amma ta kasa.

Zaginshi kawai take tare da yi musu Allah ya isa.

Cikin zafin rai Aliyu ya janyo kujera 'yar zaune yayiwa Usman fashin kwakwai.

Anan ya fad'i ya suma Umma ma tuni ta suma.

A gigice Zuhra ta fito da waya tayi wa Ja'afar text dama har yanzu yana tuntub'arsu akan case d'in.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda Malam ke nanatawa.

Dukkansu aka d'ebesu akayi asibitin cikin gari dasu.

_1 hour later_

Usman ya farka amma Umma har lokacin likitoci na kanta dan sunce dole ne a yanke k'afar.

"Kayi hak'uri Aliyu nayi amfani da son zuciya na cutar daku"

"Bazamu yafe ba meyasa ka tashi meyasa baka mutu ba" ya gigice a gurin yana neman kai masa naushi aka rirrik'e shi.

A b'angaren Umma kuwa itama bori take tana fad'in ya kashe min Ummi ta shine ashe"

"Umma kiyi hak'uri"

"Yaron nan ya cucemu ya rabamu da duk wani masoyanmu,Allah ya isa ban yafe ba"

Shak'uwa ta farayi a  gigice Zuhra ta kira likita,Umma ko minti biyu bata k'ara ba ta rasu.

Jin ance Umma ta rasu ne Aliyu ya janyo k'arfen da ake saka drip ya fara makawa Usman da k'yar aka fitar da shi a haukace,yana ganin gawar Umma kuwa ya fad'in ya suma a gurin.

Ja'afar kuwa da sukazo lokacin Usman baya cikin hayyacinsa dan haka suka ce likitoci su tabbatar ya rayu.

Kwanan Usman uku a asibiti sannan ya dawo hayyacinsa,bayanin komai yayiwa Ja'afar na inda suke dan haka cikin dabara sukaje da daddare lokacin sun kamo wata yarinya suna shirin lalatata 'yan sanda sukaje suka lalata komai suka kuma cafko su.

Kwana biyu case d'in na gurin 'yan sanda sannan suka mik'asu kotu.

Iyayen yara ganin anata d'aga shari'a ne yasa suka fara zanga-zanga.

A k'arshe aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar harbi da bindiga,watansu d'aya a prison suna aikin wahala anan ma sai da suka so suyi kisa Usman kuwa tuni ya tuba yana ta istigfari sannan aka kashesu duka.

Ranar da aka kashesu kuwa aka sanarwa da Aliyu cewar an kashe yasha kuka sosai babu Baffa,ba hafsatu,ba Umma ba Ummi duk sanadin Usman wani k'aramin hauka yaso yi da k'yar aka shawo kansa.

Kallon Zuhra yayi cikin kuka yace "duk abinda Janan tayi banga laifinta ba Abba na yarda baka da laifi dan da Usman ya dawo da an sakeni".

Haka dai yayi ta kuka yana fad'o abubuwan da suka faru.

Zuhra hak'uri ta rik'a bashi tana kwantar masa da hankali.

Ya rungumeta yana fad'in " ke kad'ai ce gatana a yanzu sai d'ana bayan ku bani da kowa su baba idi da baba isa ba su damu dani ba babu wani nawa da ya damu dani a yanzu"

Itama kukan take tana k'ara bashi hak'uri.

       ***********

"Janan dan Allah kizo kiyi min wani taimako"

'Dago kai tayi ta kallesa tace "na me?"

"Yarinyar sai kuka take na rasa ya zanyi na rarrasheta"

Kallon Adnan take da yake kwance kusan wata d'aya da sati biyu amma babu abinda ya canza numfashi kawai yake tabbatar da cewar yana raye.

"Muje" ta fad'a tare da tashi tabi bayansa.

Tun daga k'ofar d'akin suke jiwo shashshek'ar kukanta.

Suna isa Janan ta k'ara sa gefen gadon tace "haba baiwar Allah meyayi zafi haka?"

Kuka ta cigaba da yi ba tare da tace komai ba.

"Kiyi mana magana mana"
 Jalal ya fad'a.

"Ki fad'a mana dumuwarki kinji pls" janan ta sake yin magana.

"Na san na rasa masoyi sannan babu wanda zai k'ara yarda dani,na kasa fad'a muku waye iyayena saboda ina tsoron yadda zasu kalleni ga an kusa bikina har anyi baiko na san wanda zan aura ba zai amince ba"

"Karki damu babu wanda baisan k'addara ba"

"Wallahi ba zai aureni ba,dama baya sona yana ta wulak'antani yanzu yaji wannan abin daya sameni babu ta yadda za'ai ya aureni babu wani namiji da zai aureni a wannan yanayi shikenan na rasa masoyi meyasa ban mutu ba na rayu?idan har ban mutu aka sallameni wallahi saina kashe kaina" ta sake fashewa da kuka.


Karkice haka Amal na miki alk'awarin zan aureki in har wanda zaki aura yace ya fasa"

Kallon shi Janan tayi a d'an tsorace,shi kuma idanunsa suna kan Amal d'in.

"Ka daina fad'ar haka dan ka kwantar min hankali"

"Dagaske nake wlh"

Da sauri Janan ta juya ta bar d'akin.

Ya kalli k'ofar sannan ya zauna ya cigaba da kwantar mata da hankali.

_Anya Jalal bai samu matsalar kwakwalwa ba?Aure fa yarinyar da baima santa ba kuma yarinyar da aka illata,me ke samun Jalal?_

Rashin samun amsa ne yasa ta kwantar da kanta a kan gadon Adnan lokaci guda taji matsanancin sarawar kai.

Addu'a ta rik'ayi kafin bacci mai nauyi ya d'auketa a gun.











_Sadeey S. Adam✍_
🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
          🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```



53

"Yanzu ki samin number daddynki in sanar masa halin da kike ciki dan na san suna can hankalinsu a tashe"

Murmushi tayi sannan tace "ai Abbu idan ba gawa ta aka kai masa ba bazai nemeni ba Ummu ce zatayi ta tunanin ina na tafi ba dan Ummu zata shiga damuwa ba wallahi da bazan bayyana iyayena ba dan ina kunyar su ganni a haka"

"Ko da sun ganki babu abinda zai faru domin ai kowa yasan wannan k'addara ce"

"Banda iyayena domin ni sangartacciya ce ina iya barin gidanmu har na wata biyu ba tare da kowa ya damu da inda naje ba,a cewar Abbu ma ai ni 'yar hutu ce a barni inje in huta kawai,Mamana tana yin kuka dalilin rashin zamana a gida amma ina sanar da ita bazan tab'a d'ebo mata abin kunya ba shin idan taga haka me kake tunani?"
Ta fad'a tana goge hawayen daya zubo mata.

"Ina kike tafiya?mekika yi amma kin san abinda kike bai dace ba a matsayinki na 'ya mace"

Murmushi tayi mai d'auke da hawaye tace "kasan ina nake zuwa?"

Bai samu damar bata amsa ba ta cigaba da fad'in "ina zuwa k'auyika ina taimakar mutane marasa aikin yi da taimako na gyaran makarantun k'auye da suka lalace,wani lokacin na kan zauna dasu har gona nake binsu muyo itace,muci abinci tare,gaba d'aya rayuwata na karkata ta a can ina tausayawa rayuwar mutane marasa k'arfi wanda babana bai damu da hakan ba burinshi kawai mu zamo 'yan gata'yan hutu masu ilmi baya so sam ya taimakawa talaka hasalima in har aka zo maula ko neman taimako gidanmu ranar cikin b'acin rai yake yini,babana d'an kasuwa ne yana da arzik'i sosai amma arzik'insa bana talaka bane dan haka ni kuma sai na canza akalata da taimakon talakawa,duk tafiyar da nake a tunaninsa na tafi yawan shak'atawa ne bai damu da duk dad'ewar da zanyi ba in mun dad'e bamuyi waya ba na kance masa babu network sam a inda nake,Ummu kuwa ita kawai tayi tunanin yawon shashanci nake tafiya,wannan karon satina d'aya a k'auyen kawai naji ina son dawowa gida,har na shigo cikin Abuja Motana ta lalace sai ya nemi ya taimaka min ina shiga motansa ban k'ara tsintar kaina ba sai a wani d'aki ina ji ina gani su uku suka farr mini"

Runtse ido Jalal yayi jin tsigar jikinshi na tashi.

Cikin kuka ta cigaba da fad'in "a daren suka d'aukeni suka wullar a bakin titi,da Asuba d'aya daga cikin su ya dawo ban san dalili ba ni dai na ganeshi kuma na rok'eshi daya taimakeni"

Ajiyar zuciya Jalal yayi yace "komai yanzu ya k'are tunda an kashesu zasuje su girbi abinda suka shuka su kuma sauran Allah ya toni asirinsu"

"Ameen Yaya Jalal"

Duk sai yaji wani iri yau an kirashi da Yaya.

Kallonta yayi dududu bata wuce 22years ba.

_na dad'e banga jaruma gwarzuwar mace mai kamar maza ba kamar wagga d'iya,abubuwan da ta fad'a sun bani mamaki._

Wata zuciyar tace masa _Janan ma haka halinta yake uwa uba ta zab'i zama da direban gidansu fiya da daular mahaifinta,ta zab'i zama da talaka._

"Kin gama karatu?"
"A'a yanzu nakeyi ina cikin last year d'ina"

"Wane skul?"

"Base University ina karanta gynaecology"

"Kin kyauta ma mata Allah ya taimaka amma ki daure ki bani number daddy ko"

Karb'ar wayar tayi ta sa masa number  sannan ta bashi.

Sau biyu yana kiran wayar ba'ayi picking ba.
"Kayi masa text kace Amal ce ba lafiya shiyasa ka kira dan shi in bai san number ba baya picking"

"Okay"
 fara rubuta text d'in yayi kamar yadda ta fad'a.

"Amma a wane area kake?" Tayi masa tambayar tana murmushi.

"Ina Garki2 Sapale street"

"Okay ni kuma a Maitama nake"

Kafin yayi magana wayarsa ta fara ringing yana ganin number babanta yayi saurin d'agawa.

Waje ya fita yayi masa bayani sannan ya dawo.

"Me Abbu yace?" ta fad'a a d'an tsorace.

"Bai ce komai sai dai hankalinsa ya tashi sosai yanzu haka yace min yana airport yanzu ya sauka k'asar amma gashinan zuwa"

"Allah sarki Abbu yana k'aunata sosai amma matar gidanmu ta tsaneni"

Bai nemi ya sani ba dan ba huruminsa bane.

```Amal ba fara bace chocolate color ce da siririyar fuska mai d'auke da kyaun halitta uwa uba dimple daya k'ara fito da kyawunta tana da diri da kyaun sura sannan kallo d'aya zaka mata ka gane ita d'in 'yar hutu ce tana da kimanin shekaru 22 a duniya,ita kad'aice a gurin iyayenta mahaifinta yana matuk'ar k'aunarta kasancewa itace 'ya d'aya tilo a gurin second wife d'inshi itama daga nan bata sake haihuwa ba haka ma matarsa ta farko bata tab'a haihuwa ba sai 'ya'yan rik'o da ta d'akko su biyu mace da namiji suma sun addabi gidan da tsiwa dan sun girmi Amal d'in sosai,Namijin shine wanda aka mata baiko dashi sam baya Sonta amma ita tana mutuwar son shi saboda akwai addini da kamun kai rashin kunya ce dai yakanyiwa Maman Amal in har ta tab'a uwar rik'onsu.```


"Bara inje in dubo Janan ina tunanin ma Mommy sunzo"

"To amma dan Allah karka dad'e dan kar suzo baka nan,bazan iya tashi ba danaje na dubashi"

"Karki damu Allah ya baku lafiya"

"Ameen"

Yana shiga yaga ana shirin fita da Adnan Mommy da Janan sai kuka suke Abba k'arami ya tsura masu ido yana kallonsu ,Adam na gefen gadon Adnan.

"Doctor meke faruwa ne?"

"Zamuje ayi scanning kai kuma ka biyoni office"

Janan kukanta dake neman fitowa fili tayi saurin rufe baki ta fita da gudu.

Kan kujera ta zauna tare da saka kanta cikin gwiwa tana jan numfashi hawaye na k'ara zubowa a idonta.

Jalal kuwa bin doctor office d'in yayi Mommy da Adam suka wuce gurin scanning.

Yana fitowa daga office d'in yaga wucewar wani Babban mutum da securities d'insa wanda jikinsa ya bashi cewar mahaifin Amal ne.

Hango Janan da yayi a zaune kanta a kife ya sashi k'arasawa gurin.

Zama yayi gefenta tare da sakin ajiyar zuciya.

'Dago kanta tayi ta kalleshi idanunta sun k'ara juyewa sun kumbura tamkar tana hararar gefe.

"Meyasa baku fad'a min Adnan ya kamu da ciwon paralysis ba? meyasa kuka b'oye min Jalal ni fa matar shi ce"

"Kiyi hak'uri Janan bama son hankalinki ya tashi"

"Wa'iyazubillah na shiga uku ni Janan,me doctor yace?"

"Ya bamu shawarar a tafi dashi India ko Egypt suna da k'wararrun likitoci saboda tunda aka kawoshi nan munfi 5weeks amma babu wani sauyi,so yanzu na kira wani friend d'ina acan Egypt dan ayi booking kafin muje in Mommy tazo zan fad'a mata sai a fara processing na tafiya Visa ce babbar matsala amma tunda abune na ciwo insha Allahu bazamu sha wahala ba"

Bata ce komai ba sai hawaye da take ta faman gogewa yana k'ara zubowa.

"Bara ina zuwa" da sauri ya tashi yayi d'akin da aka kwantar da Amal.

Yana tura k'ofar ya hangota rungume da babanta tana ta kukan shagwab'a.

Jalal ya tsugunna har k'asa ya gaidashi shi kuma ya mik'a masa hannu.

Amal ta d'ago kai ta kalli Jalal tace "Abbu wannan shine ya taimaka min"

Godiya sosai yayi masa sannan ya mik'a masa compliment card yace ka sameni a office dan kana da babbar kyauta.

Murmushi Jalal yayi yace "karka damu nayi domin Allah bana buk'atar komai"

'Daga waya Abbu yayi ya kira Ummunta ya fad'a mata halin da ake ciki.

Aikuwa babu shiri sukazo lokacin Jalal baya cikin asibitin ya fita nemo masu Visa.

Da yamma ya dawo ya fara shiga yaga jikin Adnan yana nan dai kamar da.

'Kara kwantarwa dasu Mommy hankali yayi sannan ya nufi d'akin Amal ya dubota.

Yana tura k'ofar yaji guy d'in na fad'in "wallahi na rantse Abbu bazan auri Amal ba kaima kamar uba kake a gurina domin a gidanka na tashi kayi min adalci Abbu taya zan auri macen da har namiji ba d'aya ba yayi amfani da ita"

"Ni zan Aure ta" duk suka juyo suka kalleshi,Amal kuka kawai take.

Jalal ya k'arasa gaban Abbu yace "zan Aure ta domin Allah"

Haj Zinaru ta tashi tace "zaka iya aura mata shi tunda ta samu masoyi  amma Hafiz daya san ko ita wacece taya zai aureta duk wanda yasan halin Amal ai bazai so aurenta ba ni saboda ban tab'a haihuwa ba sai ace d'an rik'on ma za'a masa dole,zanga irin son da kakewa Amal d'in da har zaka aura mata wanda baka sani ba"

"Kimin shiru Zinaru kin nuna min ban isa daku ba ban isa da Hafiz ba shikenan zan aura mata duk wanda yazo gareta matsawar ta amince domin bana son rayuwar Amal ta lalace har yanzu yarinyar nan tana bleeding dan haka zan fitar da ita waje a mata aiki amma saina d'aura aurenta a satin nan"

Ummu dai bata ce komai ba hawaye kawai take.

"Amal kin yarda zaki Aure shi"

Kai ta d'aga alamar eh.

Kallon Hafiz yayi yace "dama na dad'e da sanin baka k'aunar Amal ni ne dai nayi tunanin ba wanda zata aura taji dad'i kamarka"

Ya kalli Jalal yace "kana da number ta ka turo waliyinka muyi magana a guest house d'ina gobe,jibi nake son a d'aura aurenta da kai sannan a shirya fita da ita saboda magani"

"Babu damuwa zan turo gobe da yardar Allah"

Tashi yayi ya fita zuwa d'akin Adnan ganinsu a zaune suna hira yasa hankalinsa ya d'an kwanta.

Zama yayi gefen gadon yace "lafiya ta samu tunda har kuke hira"

"Dole ai munga ya bud'e ido fa shiyasa hankalinmu ya d'an kwanta"

"Dagaske ya bud'e ido?"

"Wallahi ya bud'e amma dai baya cikin hayyacinsa"

"Amma naji dad'i"

Hirar ya zauna anayi dashi,a haka ya samu damar fad'awa Mommy yadda sukayi da Abbu.

"Jalal" ta kira sunanshi kanta a k'asa.

Gabanshi ba k'aramin fad'uwa yayi ba da k'yar ya amsa.

Ta d'ago kai tace "Ban san baka da hankali ba sai yanzu,kawai daga taimako sai a b'ige da Aure ko an fad'a maka aure wasa ne,idan gaskiya ne abin  ya turata ayi mata aikin tare da mahaifiyarta mana sai da kai dole"

"Mommy saboda yanayin halin da ta shiga"

"K'arya ne d'an uwanta wanda suka tashi tare ma ya k'ita sai kai,ban lamunta ba kuma ban amince ba"

"Amma...." tayi saurin tarar numfashinsa da "ka fitar min a ido Jalal ka fice ka bani guri"

Ranta a b'ace shima nasa a b'ace yayi saurin fita.

Da sauri Janan ta tashi ta bishi.

A jikin bango ta tarar dashi ya d'aga kanshi sama.

"Kana da saurin yarda wallahi"

'Dago kan yayi ya kalleta ba tare da yayi magana ba.

Uhmm "mu dai bamu amince ka auri wadda bamu san tushenta ba" d'aga hannu yayi zai mareta sai kuma ya tsaya,gaba d'aya idanunta sun fito waje kallonshi take cike da mamaki.

Da yatsa ya nuna ta yace "ina ruwanki,wallahi idan kika k'ara shiga sabgata sai ranki yayi mummunan b'aci ke har kin san wani tushe,ko sanin tushen ne yasa kika auri direban gidanku ke baki ma san ciwon kanki ba bare na wani,aurene babu fashi saina aureta ki bar Mommy tayi magana bake figaggiyar kaza cikon benci ba"

Har ya wuce zai tafi ya dawo ya sake cewa "sa'arki d'aya kina auren masoyina kuma yayana wallahi yau da saina sake sauke yatsuna a fuskarki kada ki sake shiga harkata na fad'a miki ba ruwanki dani"

"Bazan sake shiga ba da yardar Allah"

"In har kinada zuciyar ba" ya sake fad'a.

"Zan nuna maka ina da ita"

Kallon sama da k'asa yayi mata ya tab'e baki ya wuce.

Da ido ta bishi har sai daya b'ace sannan ta fashe da kuka.

Sai da ta share hawayenta sannan ta koma d'aki tare da alk'awarin ko magana bazata k'ara had'ata dashi ba,zata ja baya dashi.











_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
          🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv```



54

Ya kasa zama guri  d'aya ya zauna ya tashi duk abin duniya ya ishesa.

"Mommy meyasa zaki hanani yin abin alkhairi?"

Dafe kai yayi yana tunanin mafita.

Can yayi murmushi ya d'auki wayarsa yayi dialing number Saifuddeen ringing d'aya ya d'aga.

Gaisawa suka yi tare da jajen kwana biyu basu had'u ba.

Babu wani jinkira ya bashi labarin komai.

Daga d'ayan b'angaren Saifuddeen yayi murmushi yace "haba kai kuwa meye na d'aga hankalinka bayan akwai iyayen bogi kawai su za'a biya suje"

"Amma Saif kasan babu wanda baisan Mahaifina ba"

"Kuma babu wanda bai san ya rasu ba kawai ka sakasu a matsayin uncles d'in ka ne"

"To kana ganin har nawa za'a basu?"

"Bari yanzu zan fita idan na nemosu aka yi ciniki sai na kira ka ka tura ta account kaga goben sai muzo Abuja tare dan nima jiya na dawo Kaduna"

"Okay ba matsala nagode"

Katse wayar yayi ya zauna gefen gado tare da dafe kai a zuciyar sa yace _Amma nayiwa Mommy adalci kuwa?ta hanani yin abu nayi,ko dan na san Mommy nada fahimta idan komai ya lafa suka dawo da Amal daga can muma lokacin mun dawo daga Egypt na san Mommy baza tace komai ba dan tana da hak'uri._

_Janan fa shin ka mata adalci wulak'ancin da kai mata d'azu?_ wata zuciyar ta sake hangod'o masa question.

Ajiyar zuciya yayi a fili yace "gaskiya ban kyauta amma itama ai bai kamata tamin wannan furucin ba"

Wani irin ba dad'i yaji jikinsa a sanyaye ya tashi ya figi motarsa zuwa asibitin.

         **********

Kallonta tayi rai a b'ace tace "dalla malama in zaki saki ranki ki saki haba Najwa kefa ba yarinya bace,shikenan d'an abu k'ank'ani ya d'aga miki hankali"

Kallonta Najwa tayi tace "lallai Preety kece kike ganin abin kamar wasa amma banga laifinki ba tunda baki san zafin so ba"

Dariya sosai Saudat tayi tace "ina zansan zafin so tunda ban d'orawa kaina wahala ba,ni samarin ma wasi nake dasu in naga dama"

"Ke kika d'auki so a matsayin wahala saboda ke baki san so ba baki tab'a yin soyayya ba"

"Kina nufin duk tarin samarin da nake dasu ba sonsu nake ba kuma suma basa sona?"

"Ba haka nake nufi ba ina nufin har yanzu ke da samarin naki wasa kuke ko kuma yaudarar juna,so d'aya ne kuma Jalal nakewa nawa idan har bazaki taimaka min ba to ki daina rab'ata"

Dafata tayi tace "me yayi zagi haka,kiyi hak'uri k'awata kinsan wannan shine abinda ya kawo ni gidannan saboda Mommy tace ta kasa gane kanki kullum cikin damuwa kike kin daina ko fitowa falo kuma tasan baki da wata aminiya da ta wuce ni"

Uhmm "Saudat ina cikin mawuyacin hali wallahi so na neman haukata ni ina zanga Jalal,Jalal ya gujeni Saudat numbers d'insa sun daina shiga sau biyu ina zuwa gidan su Abbas baya nan na rasa mafita"

"Gidan su Abbas meye zakije gidan su Abbas kuma?"

"Abbas ne abokinsa dan ko lokacin da yazo garinnan a gidansu ya zauna zan tambaya da ya bani new number Jalal"

Saudat ta had'e gira tace "haba k'awata don me zakije gidansu ai sai a raina ki wallahi"

"Ni banga raini ba na kirashi ban samu ba kuma shi kad'ai nasan zai fad'an inda Jalal yake"

Uhm "kinyi nisa Najwa na san yadda kika damu dashi k'ila tuni ya manta dake ma watanshi nawa bai nemeki ba.

" ke kike gani haka amma na san Jalal bai mantani ba"

"Idan bai mantaki ba meyasa bai nemeki ba ai ya san hanyar katsina kuma yasan gidanku ko"

"Nima idan har baizo ba zanje Abuja nemansa"

"Lallai kin cika babbar mara hankali"

"A soyayya dama ai bani da hankali Indai akan Jalal ne"

"Yanzu dai me zan cewa Mommy ince Jalal ne ya hanaki sukuni?"

Da sauri ta rufe mata baki "ki rufan asiri kawai zan daure in saki raina amma zan fara shirye-shiryen zuwa Abuja"

"Cab wallahi bada ni ba gad'a a kabari kuma Allah in kikace haka zakiyi sai na fad'awa Mommy"

"Shikenan na fasa'yar bak'in ciki"

"Koma me zakice kice".

         *********

Kamar yadda Abbu ya tsara yau aka d'aura auren Jalal da Amal a Babban masallacin Jumma'a.

Ya kawo waliyyi da mutane biyar a matsayin 'yan uwa shaidu wanda duk hayarsu yayi akan dubu d'ari-d'ari.

Bayan an d'aura Aure ya tafi gidansu Amal d'in,anyi hotuna sosai itama ta sha shaddarta dark blue kamar tashi sunyi kyau sosai.

Duk da bata da lafiya amma ta daure ta fito anyi komai.

Sun keb'e yake sanar da ita bazai samu damar a tafi dashi U.S ba inda za'a mata magani saboda zasu tafi Egypt kai Adnan.

Abbu ta fad'awa suka masa fatan samun sauk'i na d'an uwanshi,sannan suka sanar dashi babu komai idan ya warke itama lokacin ta dawo sai ayi biki.

Sai bayan la'asar ya bar gidan su Amal yayi mata alk'awarin zai dawo da dare saboda friends d'in ta sunce suna  son ganinsa.


Tana zaune a d'akin ita kad'ai tayi tagumi yayi sallama ya shiga.

Ciki-ciki ta amsa sallamar.

" ya jikin Adnan d'in?ina Mommy? "

Banza tayi dashi kamar ma bata san dashi a d'akin ba.

"Magana fa nake miki kin yi min shiru Janan"

Nan ma bata ce komai ba,tsam ta tashi ta fita ta bar d'akin.

Zama yayi kan kujerar da ta tashi yana mamakin yadda tayi ignoring d'insa.

Mommy ce ta shigo tana masa kallon mamaki tace "ka fito kamar wani Ango"

Murmushi yayi yace "bikin wannan abokin nawa Saif da nake fad'a miki to yau aka yi d'aurin Aure"

"Shine kuma ko ka gayyacemu?"

"To ai naga babu lafiya nima dole ce tasa naje"

"Daddy....."  Abba k'arami ya fad'a tare da rungumeshi.

"Ya kake? Yanzu baka samun damar wasa ko tatsuniyar Mommy ko"

Kai ya d'aga alamar eh.

"Daddy ka sayo min chocolate"

"Ka jishi ko d'azu fa aka sayo masa ya shanyeta yanzu ma rigima yayi wai sai mun fita waje shine muka fita"

"Ai kuwa ga hak'oran sun fara yin bak'i alamun shan zak'i ai idan wannan suka fita wasu suka fito bazan yarda kana yawan shan zak'i ba kar hak'oranka su lalace"

"Daddy meya samu Ammi?" Abba k'arami ya sake tambaya.

"Yawwa Mommy wai me aka yi mata ne nima fa dana shiga k'in kulani tayi inata magana ni kad'ai"

"Wallahi nima na rasa gane kanta tun safe"

"Bara na fita na sameta"

"Yawwa maybe kai ta fad'a maka meke damunta.

A can bayan Amenity d'in ya hangota zaune tana kallon guri d'aya.

Yana zuwa ya tsaya gabanta tayi sauri ta tashi zata bar gurin yace " meye haka Janan?koma mena miki laifinki ne hankalina ya tashi kuma kinsan abinda zanyi ba haramun bane amma kika kicincine"

Tsoki taja ba tare data kalleshi ba bare ya samu damar ta bashi amsa.

"Tsoki kika min Janan"

A harzuk'e ta kalleshi tace "nayi tsokin meye na biyoni nan ina ruwanka da shiga sabgata kada ka kuma shiga ba ruwanka da lamurana ina zuciyar taka ko karen ya lasheta"

"Ban sani ba amma zaki iya zuwa ki tambaya"

"Wa zan tambaya?"

Tab'e baki yayi sannan yace "wanda kike kallo a matsayin kare"

Hannu ta d'aga zata mareshi sai kuma ta tsaya.
Nunashi da yatsa tayi tace "babu ruwanka dani,wallahi sa'arka d'aya ka girmeni kuma ina ganin girmanka amma da sai na sauke yatsuna a fuskarka"

Dariya sosai yayi yace "kin cini wasa fa,lallai yarinyar nan to da wane tsayi zaki mareni dubeki fa kamar sandar suluka,kinga malama ni dai ki daina had'e mun fuska bana so"

Mtsww "aikin banza" ta fad'a tare da wuce wa ciki.

Binta yayi da ido gace "ai dole ma in k'i zama da matata a gidan Mommy saboda kin koya zafin zuciya karki rik'a juye mana shi"

Da dare kamar yadda yayi alk'awari yaje gidansu Amal bayan yayi wanka ya saka k'ananun kaya, a babban falon bak'i aka musu masauk'i shida ita da friends nata da Saif daya rakoshi aka yi ta hira,friends d'in ta sukayi ta ce mata 'yar baiwa dan tayi dace da kamilin miji".

Kusan k'arfe goma ya ankare ya nufi asibiti.

Yana tura k'ofar idonshi yakai kan hotonsa da Amal na yau yana yawo kan screen d'in wayar Janan daga gani turo mata aka yi ko kuma an d'ora a social media ta gani.

'Dago kai tayi ta kalleshi sannan ta kashe hasken wayar ta kauda kai.

"Mommy tace idan kazo sun tafi saboda Abba  k'arami ya dameta su tafi"

Bakinsa ya kasa cewa komai zama yayi kusan minti uku sannan yace "ina son magana dake Janan"

Ko kallonshi batayi ba.

"Ko bazaki kalleni ba dan Allah ki saurareni"

Nan ma shirun tayi.

"Dan Allah kar Mommy taji zancen nayi au............" Tayi saurin tarar numfashinsa da fad'in "abu na 'yan uwa ni cikon benci ina ruwana,Jalal idan kaga dama ka Aure duk matan garinnan bai shafe ni ba"

"Kiyi hak'uri ko ranarma wlh raina ne a b'ace"

Banza tayi ta rabu dashi yayi ta rok'onta har ya tashi ya tafi bata sake cewa komai ba.

Bin k'ofar tayi da harara bayan ya fita tamkar tana kallonta.





_ba yawa dai😊😊_





_Sadeey S Adam✍_


Download Direban Gidan Mu Littafi Na Ɗaya Complete Hausa Novel