[6:19AM, 6/7/2019] Abue Saleh Al~Quyraemey: COMPILED BY
Abubakar Saleh Quyraemey Ne Mutumin ku
Admin @Top Hausa Novels
What@PP No: 08138873799
@Facebook Group Qurami Hausa Novel Group
For more novels contact me


[5:16AM, 6/12/2019] Abue Saleh Al~Quyraemey: *_Typing📲_*



    *_Haske writer's asso...._*💡



     
     *_♦RAINA KAMA......♦_*
              _{Kaga gayya}_
               

     

             *_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻

____________________________

     *_Dolene page d'in farko yazama sadaukarwa agareki MAMAN JUNIOR😭, ALLAH ya gafarta miki, ya raya abinda kika bari, ALLAH ya k'addara bazakiga k'arshen wannan littafiba. (Masoyan Raina kama kusaka wannan baiwa a addu'arku, ta rasu cikin azumi, kusanma k'arshe, member ce a group d'in raina kama, ALLAY ya yafe mata🙏🏻😭._*

 
   _INA fata kunyi salla lafiya gaba d'ayanku, ALLAH ya kar6i ibadunmu. Ya yafe mana, yasa kar6a66iyar ibada mukayi🙏🏻😭._
       Sai dai banci naman salla ba sosai, gashi banida d'inkin dallah🤦🏻‍♀🤥.

______________________________


~Book 2~ 👉🏻1⃣

 
   .............Tunda mukayi maganar nan dashi banyi k'asa a gyuwa ba wajen dagewa da addu'oi wa mahaifinsa, ina buk'atar ruwan zam-zam, dan haka yau nashirya fad'a masa ya nemomin. tunda safe ya fice, dan haka bamuga juna ba.
      Yauma dai haka Na tashi banida wata isashshiyar lafiya, Na tak'ark'ara nayi gyaran d'akin har zuwa falo, sannan Na had'a ruwa mai zafi nayi wanka dashi.
      Ina cikin shiri najiyo sallamar Samha a k'ofar falon, rigar dana fara sakawa Na k'arasa, sannan nace ta shigo.
        “humm Aunty gimbiya kina kallon kanki a mirror kuwa?”.
     Cikeda mamaki Na kalleta sannan Na kalli jikina, nace, “kamarya?”.
       Zama tayi a sofa tana 'yar dariya, sannan tace, “wlhy kinyi k'iba, sati uku kacal da zuwanmu India kin koma wata madam”.
      Nad'an fiddo idanu waje, sannan Na harareta, “lallai Samha nagode da zagi to”.
       “tab wlhy babu wani zagi gaskiya Na fad'a, halan Uncle Sam bai ta6a fad'a mi ki ba........”
     Ta k'arasa Maganarta da d'ai-d'ai saboda shigowarasa d'akin da sallama ciki-ciki.
        Suna had'a idanu ya watsa mata harara, hakan ya tabbatar mana da yaji maganar tata, da sauri tamik'e ta fita, Nikuma najawo gyalena na yafa sannan Na kallesa.
       Saman sofar ya zauna ya dafe kai, kallo d'aya zaka masa ka karanci damuwar dake shimfid'e bisa fuskarsa.
        “yalla6ai lafiya kuwa?”. ‘nafad'a cikin tausayawa’.
      Shiru bai amsaniba, banyi zuciyaba nataka a hankali zuwa gabansa, durk'usawa nayi a gaban nasa, a d'arare nasa hannu Na najanye nasa dayay tagumi dashi.
     Ya d'ago idanunsa da sukai jaa yana kallona. kasa jurar kallon cikin idonsa nayi, Na janye nawa gefe, cikin dakiyar zuciya nakuma fad'in “bakada lafiya yalla6ai?”.
      Yanda nayi maganar a marairaice saiyaji yakamata ya fad'amin, kodan nuna damuwar danayi akansa......
       Ganin yamin shiru nikuma saina yink'ura natashi ina fad'in “kayi hak'uri idan nashiga hurumin daba nawab......”
       Bankai k'arshen maganarba naji tattausan tafin hannunsa cikin nawa.
     Rintse idanuna nayi, saboda wani yarrr da tsigar jikina tayi, shima agaresa saiya lumshe idanu kawai. najuyo danufin zare hannun kawai ya fisgoni na fad'a saman kujerar, rabin jikinna duk yana a jikinsa, yayinda sauran rabin nake a kan kujera.
     Bansan nawani lumshe idanuba saboda daddad'an k'amshin turarensa d'aya ratsa hancina zuwa magudanar jinina. shikuma ya sauk'e 6oyayyiyar ajiyar zuciya.
      Ya karkato da fuskarsa inda tawa take a gefen kafad'arsa har inajin saukar numfashinsa saman face d'ina, mayun idanun nan nasa suka kuma shiga cikin nawa, na janye da sauri, sannan nafara k'ok'arin cire kannawa daga kafad'arsa.
   Hannunsa na dama da nake jiki ya sak'alo ta bayana, ya maida kai na ya kwantar a kafad'ar tasa, cikin muryarnan tasa mai kama da anmasa tilas yace, “jikin Abie ne ya motsa, Ashe tun jiya basuyi barciba gaba d'aya, da safennan Akash yakirani yake sanarmin, nakasa kallon halin da mahaifina yake ciki Munaaya! Abie na yana cikin mawuyacin hali..” ‘yak'are maganar cikin zirarowar kwallar data cika masa idanu tunda yafara maganar’.
       Wani matsanancin tausayinsa ne ya ratsani, duk jarumtar Galadima kaga yana kuka ai kasan lamari ya 6aci gaskiya, nima hawayen suka fara gudun fanfalak'e a kumatuna, tashi nayi zaune sosai, cikin wata jarumtar da bansan inada itaba nasaka hannu Na kamo hannunsa cikin nawa. Sai kawai naga ya zame sosai ya kwantar da Kansa bisa cinyata, tareda hard'e hannayensa  a k'irji. duk da kujerar tama tsawonsa kad'an, dan ma Love's chair ce.
        Kansa nafara shafawa a hankali, hawaye na zirara daga idona har yanzun.
       Shikam idanunsa a lumshe suke.
     Cikin tausasa harshe da tsantsar Nuna kulawa da tausayawa nace, “Yalla6ai kayi hak'uri, Abie d'inmu yana buk'ar addu'armu ne fiye da kukanmu, sannan itace jarabawarsa, wad'anda suka aikata masa hakan summa kansune, domin ALLAH bazai barsuba. idan ka amince akwai wasu addu'oi Dana Sani, Nina kakanmu ne yabama innarmu kafin yarasu, shine ta koya mana, mizai hana ka samo mana zam-zam muma mu farayima Abie su, Ubangiji gafurun rahimunne, babu abinda ya gagaresa, kuma shine yace mu rok'esa zai amsa mana”.
         Tunda nafara maganar bai bud'e idonsa ba, nikuma ban fasa shafa masa kaiba. Saida nakai k'arshen zancen sannan ya bud'e lumsassun idanunsa dasuka koma launin jaa a kaina. yamotsa baki kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru.
    Nima shirun nayi ban sake yink'urin yin magana ba, nadai cigaba da shafa kan nasa a hankali. ba akai 3minutes ba barci ya d'aukesa, sai numfashinsa danaji yakoma sauka a hankali.
    Ajiyar zuciya na sauke kawai, na tsurama fuskarsa ido, yaune ranar farko dana ta6a nutsuwa namasa kallon tsaff, sosai yake kamanni da dukkan iyayensa, Abie da Momma, amma yafi tsananin kama da Momma gsky, duniyar tunani nafad'a batare dana fargaba, tausayin Galadima da families nashi yana cukurkud'ar ruhina, insha ALLAH nayi alk'awarin bada gudun mawa a duniyarsu har zuwa lokacin da aurenmu zai k'are.
       kaina na jingina da jikin kujera, nima sai barcin ya kwasheni, dama bajin dad'in jikina nakeyiba.


********

         Bayan anma Abie allurar datake temaka masa yin barci mai nauyi idan jikinsa yamotsa irin haka su Momma suka sami nutsuwa, dan yayi barci.
     Sai alokacin hankalin Momma yadawo kan Neman Galadima, tabbas taga yafita hankali a tashe lokacin da Abie ke fidda numfashi a wahale, amma hankalinta bai koma kan  Galadiman ba.
       Aunty Mimi ta kalla tace, “Mimi ina d'an uwanki?”.
     Itama aunty Mimi sai yanzu hankalinta yadawo ta farga babu Galadima d'in, hankalinta a tashe tace, “Momma inagafa ya fita, bara na duba”.
    Bata jira cewar Momma ba tafito daga d'akin da sauri. ganin babu Galadima a wajen hankalinta yak'ara tashi, fitowa tayi harabar asibitin tana tambayar securitys d'in wajen.
    d'aya ya sanar mata ya fita a rikice gaskiya, dan suma sun nemi su taimaka masa amma baima tanka musuba.
   Innalillahi tashiga ambata. Bata koma wajen Momma ba tashiga mota tanufo gidan.
     Ta iske Samha a falo kwance, ko sauraren sannun datake mata batayiba tace, “k ina Uncle d'inku?”.
     Samha tace, “yana sama Mummy”.
     Da sassarfa ta haye step's d'in, itadai Samha da mamaki taringa binta da kallo.
       Ko knocking bata tsaya musuba ta turo k'ofar ta shigo.
      Ajiyar zuciya ta sauke dan ganin Galadima kwance, kansa bisa cinyar Munaya, hannunta d'aya na bisa Kansa, yayinda shikuma yarik'o d'ayan hannun munaya ya had'e da nasa ya d'ora kan kirjinsa, suduka barci ya kwashesu a haka. cikin sand'a ta juya ta fita taja musu k'ofar tana share hawaye dayima ALLAH godiya d'aya bama d'an uwanta mace tagari wadda take kulawa dashi. inda dane kafin yayi aure shima sai ciwonsa yatashi saboda damuwar dazai saka Kansa akan motsawar jikin Abie, amma gashi yanzun yasamu mai kwantar masa da hankali, suma kuma nasu ya kwanta suji da Abie kawai.
      Momma ta kira ta fad'amawa dan hankalinta itama ya kwanta.
     Momma harda hawayen farinciki, tana godema ALLAH.
     Aunty Mimi bata zaunaba suka koma asibitin itada Samha da tace zata bita, itama sai yanzu takejin jikin Abie ya motsa.


*************

     A k'alla munyi barcin 47minute's, Galadima ne yafara farkawa, ya bud'e idanunsa a hankali, hannuna dake rik'e a nasa yafara kallo, kafin yad'ago ido zuwa kaina, yamin kallo kusan na 2minutes sannan yad'an motsa da nufin gyara kwanciya, saina bud'e idona, ido muka had'a, kowa yay saurin janyewa cikin basarwa, hannuna dake kansa na cire, sannan nazame Wanda yarik'e d'in, dan wata matsananciyar kunya ce kuma takamani.
    Shima sai ya tashi zaune sosai, a hankali yacemin “thanks”.
      Daba kusa dashi nakeba ma bazanjiba. Bance komaiba, shima bai sake cewa komaiba yamik'e tsaye. takalmansa kawai yacire ya d'auki jallabiya a wardrobe d'insa yashige bayi.
      A hankali na sauke ajiyar zuciya, tareda janye idona daga k'ofar bayin, komai banceba nakuma zamewa saman kujerar na kwanta.

       Ya d'auki adadin wasu mintuna masu tsawo kafin yafito sanye da jallabiya ruwan toka, da alama wanka yayi, kallona yayi batareda yayi magana ba ya nunamin agogon dake ajiye a drowan gefen gadon alamar time d'in salla yayi.
     Kaina kawai na girgiza na mik'e, zuciya ta na mamakin hali irinna Galadima.
       Shikam turare kawai ya d'auka ya fesa yafice salla.



★★★  ((★))(())((★))  ★★★

               A gidanmu kam hankalin mamansu yaa hameed da Zarah a tashe yake, dan babu Sa'eed babu labarinsa, kira Zarah tamasa yafi 50 amma yak'i d'agawa, ta tura massages babu reply, bata aikin komai sai kuka, ga ciki.
        Abbanmu kuma jin sanadin sawowar tata gida yace bazai kira Alhaji halliru ba har sai Zarah tafad'i ainahin gaskiya, danshi bai yarda ba itace ta d'auki kud'inba..
     Innarmu dai dasuke zagi suna kallonta mak'iyarsu batakai komaiba itace tashiga lalla6a Abba damasa magiya.
    Itama da farko buris yay da ita, saida yaga tanace sannan yace, “wai kekam Ai'sha miyasa kika damu kankine? kinbi kin damu da lamarin wad'anda basu damu dakeba, na tabbatar da Munaya ko Munubiya ke cikin wannan halin su murna zasuyi a gidannan”.
    Murmushi innarmu tayi, cikin kwantar da murya tace, “Alhaji ai daga Zarah harsu munubiya duk d'ayane a wajena, domin kaine mahaifin Zarah, dukkan abinda kuma yakasance naka ina kaunarsa fiye da zatonka, a duba lamarin yarinyar kodan abinda ke gabanta, ba'a son mace mai ciki da shiga tashin hankali, muyima tufk'ar hanci tun munada sauran dama, basai Abu yayi tsamariba kuma muce zamu nemo mafita, hannunka baya ru6ewa ka yanke kayar alhaji, dan ALLAH kayi hak'uri kaji”.
         Jawota yayi jikinsa ya rungume yanamai saka mata albarka da aminta da buk'atarta na kiran senator halluru da safe insha ALLAH.
      Innarmu tamasa godiya itama.


**********

       “Babyna wai mike faruwane haka?”.
      Da gyar Munubiya ta d'ago ido daga kwancen datake a kujera ta kalli yaa Marwan dake mata tambayar.
    Ta shagwa6e fuska tace, “wlhy Yaya jikinne babu dad'i, kamar jiya sai kwankwatsa kasusuwane keyi”.
    Zama yay kusada ita, yad'ago kanta ya jinginata a jikinsa yana ta6a wuyanta, “please ki yarda muje asibiti adubaki mana?”.
       “a'a dan ALLAH Yaya, wlhy banason zuwa, kabari muga kwana biyu idan bai dainaba saimuje d'in”.
        “Amma kuma k'ya zauna da ciwo, ki daure dai, kinga ko abinci kin kasa mana fa”.
       “babu damuwa Yaya, yanzu zan tashi na d'ora, dan zazza6inma ya sauka ALLAH”.
      “Ana dai so aima Yaya wayo kawai”.
     Murmushi tayi tana tashi daga jikinsa,, takama hannunsa ta sumbata sannan tatashi tafice daga falon.
       Binta kawai yay da kallo yana murmushi, yana k'aunar matarsa kuma 'Yar uwarsa, gaba d'aya Munubiya ta canjashi, dukda bawai miskilancinsa yabariba, itace kawai yanzu baya iyama miskilancin nasa, komai a d'auren da fuskarsa take da zarar ya tunkaro gida zakiga yafara sakin murmushi, balle yay tozali da fuskar tauraruwar nan tashi mai haske da kawalwalniya a zuciyarsa.
     Mik'ewa yayi yabi bayanta zuwa kitchen d'in danya taimaka mata da aikin, dan yau d'in weekend ne baije aikiba. dan yayi resume tun last week.



((★))*((★))*((★))*((★))


            Tunda na idar da sallar nazame a wajen na kwanta, bawai barcin nakeba, jikinane kawai da baya min dad'i, jinake kamar ana kwankwatsamin kashin jiki, sallamarsa tasakani d'ago ido na kallesa, sannan na amsa ciki-ciki nima.
        Frigate ya bud'e ya d'auki ruwa yakoma saman sofar ya zauna, murfin kawai ya 6alle ya hau kwankwad'a, saida ya shanyeshi tas sannan ya ajiye goran yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. nikam na k'ura masa idanu nakasa janyewa. saida yad'ago muka had'a idanu sannan nayi saurin yin k'asa da nawa.
      Shi bai janyeba yana kallona yace, “tashi muje hospital d'in, daga nan saimu samo zam-zam d'in”.
     Tunkan yakai k'arshen maganarma na mik'e tsaye, hijjab kawai nasaka nad'an gyara fuskata, shikuma ya d'auki kaya yashiga bayi ya canjo sannan muka fice.
      Jin gidan shiru yasashi d'aukar waya yakira sashen bayin gidan, babu dad'ewa saiga d'aya acikinsu tazo.
    Zubewa tayi tana gaishemu, ya d'aga mata hannu yayinda nikuma na amsa. yace, “ina Samha?”.
        “Ranka ya dad'e sunfita suda mummy”.
       Yasan aunty Mimi take nufi, dan haka bai sake cewa uffan ba yafice abinsa. sai nice nace tatashi taje, sannan nabiyoshi abaya.
     Sai da yasakama k'ofar security sannan muka nufi wajen motarsa, bayin dake zaune a harabar gidan maza sukazo da sauri suna gaishemu, hannu kawai suma ya d'aga musu muka shiga motar, suka bud'e mana gate d'in muka fice.
      Tunda muka fita babu Wanda yay magana tsakanin ni da shi, yana aikin tuk'insa da sauraren redio daya kunna a motar, nikam ina lafe a kujera ciwo ya isheni, dan bana fahimtar yaren dasukeyi a redio d'in, tunda ba English baneba gaskiya.

       Mun Isa wani babban shagon Islamic camix, komai zaka iya samunsa daya shafi maganin muslinci.
          Abinda ya kaimu muka shigayi, yad'ebo zam-zam dayawa, sannan ya kalleni yana fad'in “saikuma mi?”?
     Shiru nayi ina nazari. Dame yakamata muk'ara?, zuwa can nad'an hau duddubawa ina karanta sunayen magungunan ajikin kwalin, duk maganin danaga zai iya shafar jinnu ko sihiri, saida na d'akkoshi, (a tunanina idan mun dawo gidan zan d'auki hotunansu na turama Munubiya ta bincikamin yanda yadace ayi amfani dasu.
       Duk abinda nake yana a tsaye yana kallona, saida na kammala sannan nasanar masa na gama.
     Mun k'arasa wajen biyan kud'i, bayan yabiya yaran shagon d'aya ya d'aukar mana zuwa mota.

     Daga nan asibitin muka nufa, mun tarar har lokacin Abie yana barci, sai gaisawa nukayi da momma da aunty Mimi, duk sunji dad'in yanda sukaga Galadima cikin nutsuwarsa. Zama yay kusada Abie yana mai tsurama masa idanu da masa addu'oi samun lafiya a zuciya, da kuma kudirar binne Wanda ya cutar masa da mahaifi da ransa idan ya kamashi a hannu.
       Momma tayi farinciki da yanayin Galadima d'in cikin k'oshin lafiyarsa, dan da a dane da yanzu shima yana gadon asibitin, amma Alhmdllh yanzu gashi normal.
       Mukam ni da Samha muna gefe zaune muma, ba hira mukeba, kowa yayi shirune yana tunanin duniya.
     Sauban ma yana dawowa daga school shida Khaleel nan suka taho.
    Bamu bar asibitinba sai dare, harda Momma muka wuce, dan yau suna buk'atar Abie ya kwana tare da ma'aikatansu.

          Koda muka shigo Galadima sama ya wuce abinsa, ganin haka Momma tace natashi na naje nima na kwanta na huta hakanan.
     A kunyace na mik'e domin cika umarninta.
     Na iske yana cire kaya, dan haka nakoma da baya zuwa falo, saida na kintaci yagama sannan na shigo, na iskeshi yashiga wanka, nima natu6e nawa na d'aura zani nasaka hijjab tareda d'aukar kayan barcina ina jiran fitowarsa.
          Bai dad'eba sosai kuwa yafito, sanye yake da bathtub fara tas, ban yarda na kalleshi ba natashi nashige nima.
      Mai makon yayi shirin barci saiya kwanta a bakin gadon a haka, k'afafunsa na k'asa, ya tsurama rufin d'akin idanu alamar yatafi duniyar tunani.
        Nikam ruwa mai zafi na had'a nashiga koda zanji dad'in jikina, na dad'e acikin ruwan kwance, jinakema kamar karna fito. shikansa yafara tunanin lafiya kuwa?, lokaci-lokaci yakan kalli k'ofar bayin, Amma babuni babu dalilina.
      Yana shirin zuwa yamin knocking sai gani nafito kuma, janye idonsa yayi daga saitin k'ofar cikeda basarwa.
   Ni bammasan yanayiba, dama nayi shirin barcina tun aciki, saina d'auki zani na d'ora a saman kayan nasaka hijjab nayi sallar shafa'i da wutiri, bayan na idar nad'akko roban zam-zam d'in d'aya na zauna nafara karatu Qur'an acikin ruwan zam-zam d'in. a hankali nake karatun cikin nutsuwa, dukda barcin dakecin idona.
        Har cikin 6argonsa da jini yakejin sautin karatuna, ya lumshe idanu yanamaijin kamar mu kwana a haka inayi. mik'ewa yayi shima yayo alwala yazo yay shafa'i da witiri yay joining d'ina muka cigaba da karatun a tare.
   Bamu kwanta ba saida mukayi sallar asubahi. (da yake sai zuwa 1 zasu bari ashiga wajen Abie, yau kuma babu aiki).




____((()))((*((()))*))((()))____

           
            Yauma dai haka innarmu tadagema abbanmu saida yakira Senator Halluru agabanta, dan Zarah tana kwance babuma lafiya, ga mamansu Yaa Hameed ita kanta kallo d'aya xaka mata kagane abirkice take.
    Innarmu duksai suka bata tausayi, matan gidanmu kuwa abin magana yasamu, sai gulma da dariyar gatsatsa, ita kanta Momy Hadiza ta hannun damar mamansu yaa Hameed d'in dad'i takeji, tanadai nuna damuwarta agaban mamansu Yaa hameed d'inne.
        Bayan Abba sun gaisa da Senator halluri sukad'anyi barkwancinsu na abokai sannan yasakko xancen Zarah.
     Hankalin Senator halluru yatashi, danshi koda wasana baisan Zarah bata nanba, yadai lura kullum Sa'eed saiyaje gida yaci abinci, shi duk zatonsa Zaran bata iya girkine saboda ciki.
      Hak'uri yashiga bama Abbanmu yace wlhy shi baima saniba, amma insha ALLAH zai bincika, zuwa dare sa'eed d'in zaizo ya d'auki matarsa.
      Dahaka sukai sallana da Abba kowa nakuma bama d'an uwansa hak'uri akan lamarin.
    Innarmu bata buk'atar jin k'arin bayani dantaji komai, takumaji dad'i sosai.



()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()


           Jikin Abie dai kam yayi tsanani a tsakaninnan, yau kwana biyar kenan lamarin sai addu'a, dan baisanma Wanda yake a kansa ba, mai martaba Sarki Abdul'fatah ma yazo shida inno matarsa, (wannan ne karon farko dana gansu ido da ido), mutanen kirki masu d'aukar kowa nasu, duk da d'ar-d'ar danai tayi haka sukaita jana ajikinsu. yanda Galadima yake zubama inno da papi shagwa6a sai abin yaso bani dariya, amma dai sun birgeni, mu a gidanmu wazaima innaro wannan ta6arar bata k'arema uwarsa tanadiba, ba kamarma mu 'yan d'akinmu.
       hakama sarki jalalludden shida uwargidansa sunzo da mama Fulani.
     Ranar momma har tausayi tabani, kai mama Fulani batada kirki wlhy, idan kunga yanda take shinfid'a mulki a asibitin nan. Hummm🤦🏻‍♀.
     Galadima ne kawai maganinta, tamasa magana ya dage ya ya6a mata bak'a shikuma.
      Ba gidan suka saukaba, a hotel suka sauka, dan haka yau mun iskesu a asibitin sun rigamu zuwa.
        Tunda muka shigo mama Fulani ta zubamin ido, Galadima ya gaida mai martaba da matarsa yakoma kusada Abie ya zaina.
     Nima k'asa na durk'usa na gaidasu su dukansu har Momma da aunty Mimi.
        Momma ta nunamin kusada ita alamar nazo na zauna kusada. banyi musuba naje na zauna, dan kallon k'urillar da Mama Fulani kemin duk sai na takura.
       Tad'an ta6e baki sannan ta gyara zama idonta na kaina, tace “toke amarya halan saikin tashi haihuwa zaki koma mana? daga zuwa dubiya kuna Neman share wata 1 a india”.
     Gaba nane yafad'i, dan nafahimci dani take, saina rasa amsar dazan bata.. 
     'Yan d'akin kam kowa ido ya zuba ma mama Fulani har Galadima.
     Aunty Mimi ce tace, “Ranki yadad'e Kodai kina Kishine haka? Amarya ta kwance Miki fada wajen mai gidanki?”.
        Ajiyar zuciya Momma ta sauke a hankali, taji dad'in yanda aunty Mimi ta mayar da maganar wasa, ko nad'an batason abinda zai munana Munaya ko muzantata, dan bataso yarinyar taji kamar ita dabance a cikinsu.........
       Wani munafukin murmushi mama Fulani tayi, ta kalli Galadima da zuciyarsa tafara hasala akan tsohuwar, kamar daga sama sukaji tace, “cikin namu wata nawane Galadima?”............✍🏼



E me🙆🏻 mama Fulani mai gani har hanji🤦🏻‍♀.






*_ALLAH ya gafarta na iyayrnmu😭🙏🏻_*
[5:16AM, 6/12/2019] Abue Saleh Al~Quyraemey: *_Typing📲_*



    *_Haske writer's asso...._*💡



     
     *_♦RAINA KAMA......♦_*
              _{Kaga gayya}_



             *_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻



  ~Book 2~ 👉🏻2⃣


..............Shiru Galadima ya mata,  da ace babu Momma daya ya6a mata maganar da har tabar India tana mata zafi kuwa. amma duk da haka maganar ta daki zuciyarsa, bai saniba ko zancen tsohuwarnan gaskiyane.
     Momma da Aunty Mimi da matar sarki kuwa kallona duk sukayi, nayi k'asa da kaina gabana Na luguden duka, saboda zancen tsohuwarnan yana son tsoratani.
        Shigowar Sarki Abdul'fatah (papi) da inno matarsa da mai martaba Sarki Jalaluddeen ce ta tak'aita zancen. dan daganan kowa yasaki maganar, saidai munata juyata a zukata ni da Galadima, yayinda aunty Mimi da Momma ke fatan ALLAH yasa hakane.



_____________________________


         Misalin 8:pm saiga Sa'eed yazo gidanmu, a time d'in gwaggon Haleematu da mamansu yaa Hameed suna ta hayaniyar fad'a, wai mamansu yaa Hameed ce takama gwaggon Haleematu tana kallon Zarah dake alwala a fanfo tana dariya.
    Shinefa mamansu yaa Hameed tace gwaggon Haleematu taci kanta tasha bak'in ruwa, karta lashe mata jika tun yana a ciki.
     Wannan kalma ta mamansu yaa Hameed itace tajawo fad'a, Dan gwaggon Haleematu tace mamansu yaa Hameed tace mata mayya bazata yardaba. Fad'a sosai sukeyi suna cin zarafin juna da gori, dama kowa kishi Na cinta a zuciya.
      Matan gidanmu duk sunyo waje anrasa masu dakatar dasu sai innarmu dake cewa suyi hak'uri Dan ALLAH, darene fa.
    Amma Sam sunk'i saurarenta.
      Innaro dataji hayaniyar tundaga gidanta yasata d'akko fayafi tafito, kamar anjehota haka tashigo gidan.
     Sa'eed da Sulaiman suna awaje a mota, duk badak'alar da akeyi daga cikin gidanmu suna jiyowa, har shigar innaro kuwa suna kallo. Dayake su Abbanmu suna masallaci.
      Innaro tanata magana sunk'i saurarenta, saiyi sukema kamar zasu fara danbe.
       Mamansu yaa Hameed Na k'ok'arin kwalama gwaggon Haleematu ludayin miya dake hannunta innaro takawo jiki zata kare sai a goshinta, jikake kwarrrr!.
     Tako dafe goshi tafasa k'ara..   
     Hakan kuma yay dai-dai da shigowar su Abba gidan, su duka ukun, tunkan sushigo sukejiyo hayaniyar dama, dukansu rai a 6ace suka shigo. Dan iskancin matan nasu ya ishesu hakanan, idonsu yarufe ko ganin motar su Sa'eed basuyiba.
        Ran Abba yakuma 6aci, Dan ganin duk matansa ne ma masu hayaniyar, ga abinda sukaima mahaifiyarsa akan idonsa. batareda yabi ba'asiba yace duk sufice su bar masa gida.
      Ananne kowa yay tsitt, yadaka musu tsawa yana fad'in wlhy idan basu fitaba zaisa a fiddasu, ko d'akunansu bai yarda wata takomaba kuma.
        Dole sai 'ya'yansu suka d'akko musu hijjabai suna kuka da bama Abban hak'uri.
     Amma yak'i sauraren kowa, daddy da baba k'arami kuwa babu Wanda yay yunk'urin hanashi.
    Innarmu tamatsa kusadashi tana rok'onsa karyayi haka, yazauna ya sauraresu tukunna, Hararar daya zuba matace yasata jada baya tai 6am da bakinta.
        Innaro kuwa maman safara'u ce takamata ta zaunar, goshi harya fara kumbura🙆🏻.



                           
                     (((+)))***(((+)))***(((+)))


      Kafin mu baro asibitin nama manta da maganar mama Fulani, saboda murnar bud'e ido da Abie yayi ta d'aukema kowa hankali kuma, gaskiya ina tausayin bawan ALLAHn nan sosai.
     yauma bamuyi k'asa a guywa ba wajen cigaba da addu'oin damukeyi cikin zam-zam ni da Galadima, somuke muyi na 1week sannan afara bashi.


      Washe gari Alhmdllh jikin Abie yayi k'yau sosai, Dan inka gaidashi yakan maka murmushin sa Na dattako, hakan ya sanya su papi sukayi shirin tafiya da yamma.
      Ni da Galadima da Sauban muka musu rakkiya, sainaji tamkar nabisu. Harda 'yar kwallata kuwa. Inno tanata tsokanata, Dan tsohuwar tashiga raina sosai.
        Tunda muka d'akko hanyar dawowa asibitin nakife kaina a cinya inata hawaye, sauban ne kawai ke tsokanata, amma Galadima tamkarma baya cikin motar. hakan saiya k'ara tunzura zuciyata, nakuma k'ara k'arfin kukan nawa.

     Sauban yasamu guri yay parking, da hannu Galadima yamasa alamar yaje.
     Fita yay yana k'uk'uni da k'umshe dariya, wai “su boss za'ayi lallashi shine aka koroni”. Saida yay nisa da motar sannan yasami damar dariyar, har yashiga wajensu Momma.
     Daga Momma har Aunty Mimi kalli
onsa sukeyi,, aunty Mimi tace, “Auta lafiyarka kuwa?”.
     Saida ya zauna sannan yashiga kora musu bayani, dariya kawai sukayi, sunsan Sauban babu sauk'i wajen taso mutum agaba.

         Tunda Sauban ya fita sai Galadima ya gyara zamansa kawai ya zubamin ido, mutum ne shi dabaya son shiga hak'in wani, ko kad'an baiso ace wane yana cikin damuwa ta dalilinsa......
      Wayarsa aka kira, ya kalli wayar kafin yakai hannu ya d'auka, salamar da akayi daga can ya amsa suka gaisa.
        Jin ya ambaci Nuren nagane da Wanda suka ta6a yin waya kwanakine, nad'an tsagaita da kukan ina sauraren mizasu tattauna. Galadima naji yace,
        “miya farune kakeson nazo Nigeria haka da gaggawa Nuren”.
       “no babu wani damuwa, driver da yarinyar nanfa suna hannu, so yakamata ka shigo muyi abinda yadace ko?”.
       “ok babu damuwa, insha ALLAH zuwa Wednesday idan jikin Abie ya kuma lafawa zan shigo”.
        “O right, ALLAH ya k'ara masa lafiya, a gaishesu”.
     “zasuji insha ALLAH, bye”.
      Wayar ya ajiye a tsakkiyarmu ya maida hankalinsa kaina.
   
     Cikin wani salo yace, “Munaaya!”.
        Wani Yarr naji a jikina, karo na biyu kenan danaji sunana a bakinsa, sainaji sunan nawa ya canja kamar ba shiba, danya iya sarrafa sunan a harshensa..... ganin ban d'agoba yakuma kiran sunan.
    Kasa jurewa nayi nad'ago idona na kallesa, ganin ya tsareni da idanu saina janye nawa. yad'an lumshe nasa ya bud'e a kaina ya furzar da huci “kina ganin haka abokai yakamata su kasance? ni friend nakine, miyasa bazaki iya fad'amin damuwarki ba? kiyi hak'uri nasan kina buk'atar zuwa gida, last week naso maidaki Nigeria, amma sai jikin Abie Daya motsa ya dakatar dani”.
       Tausayi yabani, nad'ago na kallesa, mutumne shi mai sauk'in kai, saidai idan baka fahimceshi ba zaka sameshi a amurd'e, domin yanada wahalar sha'ani, hawayen dasuka ziraromin na goge, muryata na rasa nace, “kayi hak'uri ina kewar su Munubiya ne, insha ALLAH bazan sake yin kukanba amma”.
       Murmushi yaymin yana jinjina kai, yad'an shafa girarsa zuwa kai sannan yace, “kinada tsiwa, amma wani time d'in kinada kirki”.
      Bansan lokaci da dariya tazominba, nad'an dara sannan nace kaima ai hakan kake, kanada tsauri kanada sauk'i”.
    Yawani k'ank'ance idanu cikin wani salon kallon yace, “really?”.
      Gira d'aya na d'aga masa nima nace, “yaah”.
     Murmushi mai k'ayatarwa yayi yakwashi wayoyinsa yabud'e motar yafita batare data sake cewa komaiba.
    Ganin haka nima saina fito fuskata washe da murmushi, kamar banice nagama kukan shagwa6a ba😉.
           Tunda muka shigo aunty Mimi da Momma suka zubo mana ido, Sauban kam dariyar shak'iyanci yafara k'asa-k'asa.
    Momma tace, “ina kuka mak'ale haka?”.
       Murmushi yayi yana zama kujerar dake kusada Abie yace, “ba ko ina Momma”..
         Momma tayi 'yar dariya tace, “shikenan tunda ba'aso muji”.
    Sauban da Aunty Mimi ma dariya sukayi, nikam kunya tasani k'asa da kaina inad'an murmushi.



__((*))__((*))__((*))__((*))__

               Abba dai bai yarda su maman yaa Hameed su kwana a gidanba, a daren kowacce tanufi gidansu, yayinda baba k'arami ya d'auki innaro zuwa asibiti.
        Su Sa'eed kam zare jiki sukai suka koma gida, zukatansu tab da mamakin wannan lamari.

     A ranar zarah sai sashenmu ta kwana a  tsohon d'akinmu ni da munubiya, saboda Aminu ya sanar mata yaga Sa'eed da mijin Siyama a k'ofar gidanmu.
       Gaba d'aya saitaji yau tanajin haushin mamansu, dan daba ta tanka dariyar da gwaggon Haleematu tamata ba ai dabasuyi rigima har Abba ya korasu gidaba, dayanzu gidanta zata kwana jikin mijinta itama, wane irin abin kunyane wannan kai kana gida uwarka na gidansu itama🤦🏻‍♀.



     %%%%%%%%%%%%%%%


     Dawowarmu kenan ni da Sauban da Samha daga zagaya gari, nagaji ovar, jikina sai ciwo yakemin, dama Yaya lafiyar giwa, saman sofa na zube Ina sauk'i numfashin wahala, wani zazza6ima nakejin yana neman rufeni, harna rufe idanu naji wayata na wringing, lalubowa nayi na duba mai kirana, nasan dai duk Wanda zai kirani to daga Nigeria ne, dan su Samha duk suna gida, Galadima kam bai ta6a kirana a wayaba, banmayi tunanin yanada number ba duk da shine ya sayi layin.
   Sunan munubiya dana gani yasani fad'ad'a murmushina, saida nabari ya katse sannan na kirata.
          Bugu biyu ta d'aga, jin muryarta can k'asa sai hankalina ya tashi, nashiga tambayarta ko lafiya.
       “sweetheart wlhy banajin dad'i, ko school nakai sati banjeba, ya kuke?”.
      “ayya sorry sweetheart, mike damunki?”.
     “wlhy zazza6i, kema naji muryarki wata iri ai?”.
       “nima lafiyar sai a slow wlhy, ina yaa marwan?”.
      “tofa, ciwo a time d'aya mu duka? ALLAH yabamu lafiya to, yaa marwan yafita gaida su mama, ya jikin Abie da Galadima?”.
        “everything Alhmdllh dear, jikin Abie ma yanata sauk'i, sun fara masa amfani da addu'oin, amma naji kamar doctors d'inshi suna complain wai abar shafa masa abinda ake shafa masa”.
      “karku wani sauraresu, Ku cigaba kawai, ALLAH yasa muji alkairi”.
       “insha ALLAH dear, dama haka Galadima yace shima”.
       “ALLAH ubangiji yabashi lafiya, bara na barki ki huta, a gaida minsu”.
      “ok sweetheart bye”.

        Ina ajiye wayar na mik'e, bayi nashiga nahad'a ruwa mai zafi nagasa jikina kozanji dad'i, haka nake kusan yini wanka da ruwan zafi, wai ko zan dainajin ciwon jiki, amma a banza, danayi wanka bana wuce mintuna talatin ciwon yake dawowa sabo.
     Wani ash d'in wando da Riga na jawo na saka, kayan basuda nauyi sosai, wandon kad'an yawuce guywata, rigar kam hannunta iya kafad'a ya tsaya, kamardai vest d'in maza take, saidai daga gaba tanada banbanci data maza. nasan Galadima bazai dawo gidan yanzuba saboda koya tashi aiki saiya biya ta asibiti kafin yazo gida, yanzu kuma akayi isha'i nasan sai zuwa irin 11, shiyyasa nayi tunanin sakasu ko zan ragema kaina nauyin jikin. komawa nayi saman sofa data zama gadona na kwanta, amma sai naji dukna takura, najujjuya naji babu dad'i kwanciyar, tsaki nayi namik'e nakoma saman gadon na kwanta, insha ALLAH kafin maishi yadawo dai natashi😏.
     Banfi 5minutes ba da kwanciya barci ya d'aukeni.


*****
          Kansa daya fara matsa masa da ciwone yasashi tattara kayansa yabaro office, Dan yau sunyi overwork ne, suna shirin fidda laptop sabon k'ira, saida yashiga office d'in vijeey da Alexander yamusu sallama sannan yanufo gida, ko asibiti bai biyaba, Dan har wani jiri-jiri yake gani a idonsa, yasan barcin dabasa samun yine ya haddasa masa ciwon kan, bama kamarshi, Dan gara ni idan yafita nakan kwanta nayi barcin.
     Da k'yar ALLAH yabashi Damar isowa gidan. Ko rufe motar baiyiba sai a cikin bayin ne wani yataso yarufe, a falo ya wuce Samha na barci itama, tunda muka shigo ta zube a wajen, tun yana taka steps d'in yafara cire bottom d'in Indian suit d'in dake jikinsa white color, burinsa yana shiga d'akin yagansa a gado kawai.
     Ganina baje a gadon yasashi yin turus yana kallona, yay saurin kauda idonsa gefe saboda kayan jikina sun kamani sosai, sun mugun fito da surar jikina d'as, gashi sun bala'in min k'yau, yau da ace matar dayake soce babu abinda zai hanashi yabawa harma yabata tukuycin wannan kwalliyar, tsigar jikinsa sai tashi takeyi, gashin jikinsa duk ya mimmik'e, rigarma yakasa k'arasa cireta, ya dafe kansa yanajan guntun tsaki, miya kawo yarinyarnan gadonsa?. Yayi maganar cikin zuciyarsa.
    Jin jiri na neman zubdashi a k'asa yay saurin zama bakin gadon, samu yay ya lalla6a ya ida cire kayan, duk da yafi buk'atar kwanciyar haka ya daure yad'an watso ruwa, sannan yafito yasha magani, koma shafa'i da wutiri baiyiba, a nufinsa sai zuwa anjima zai farka yayi.

      Abin dariya, saiya jawo dogayen filullukan gadon yajerasu a tsakkiyar gadon sannan ya kwanta can k'arshe, shima babu dad'ewa barcin yay gaba dashi. (Wlhy kafad'o babu ruwana fad'ama fans zanyi Galadima ya tik'o k'asa ehe😏🤨🤣🤣)
    Can cikin barci Galadima yafara juye-juye, yasaba shi kad'ai yake kwana abinsa, jin fillos a gabansa yasa hannu ya d'aukesu yayta wurgawa k'asa cikin barci, sannan yay juyi zuwa tsakkiyar gadon.
       Munaya kam tasaba da kwanciyar mutum biyu. dan haka ko juyin zatayi bata barin inda take kwance, duk da ma batasan da Galadima a gadon ba, tunda batasan ya shigoba.
     Barci yay barci saiga su yalla6ai Galadima masu jera fillos a jikin munaya😂, d'umin jikinta yasashi kuma nanik'e mata, saboda zazza6in daya rufeta, kasancewar yanajin sanyi-sanyi sai jikinta yamasa dad'i.
      Itama saita kuma lafe masa a jiki saboda jin sanyi-sanyi da k'amshin turarensa kuma, sunbi sun k'adandane juna kaikace ana shirin rabasune, kowa yana amfanuwa da yanayin jikin d'an uwansa.


Humm, bara na lek'o su innaro 'yan Nigeria suma🤗, mai tuk'ulluma a goshi ba🤭🤫, ni nama godema mamansu yaa Hameed🤣 dama k'afar suka karya😝.



_____________________________

        Anbama innaro magani a wani camix suka dawo gida, gidanta aka kaita, innarmu tad'an dafa ruwa tazauna kusada ita tasaka k'aramin towel danta gasa mata goshin koza'a samu yarage tukullumar dayayi.
     Innaro ta 6ata fusaka zatama innarmu tijara.
     Baba k'arami yay saurin tareta da fad'in “haba inna, Dan ALLAH kibari tamiki, naga wad'anda suka miki abunma ko kallo baki ishesuba balle su nuna damuwarsu akai, wai shin minene laifin Ai'sha agarekine?”.
      Abbanmu da daddy suna zaune basuce uffanba sudai. Harara innaro tazuba ma baba k'arami kawai amma batace komaiba, itakuma innarmu ta saka towel aruwan tafara gasa mata.
     Tanama innarmu masifa dai har akad'an gasa mata, aikam saigashi wajen yad'an saki, baba k'arami yamik'a mata kofin tea d'in da maman fauziyya ta had'a.
     Kar6a tayi tana yatsine Baki, amma saigashi ta shanye tas, aka bata magani shima tasha ta kwanta.
     Basu bar gidanba saida tasamu barci, da innarmu tace zata kwana annan, sanin halin innaro Abba yace a'a tatashi suje gida tunda ga habiba d'iyar gwaggo safiyya dabata komaba.
      Badan innarmu tasoba tahak'ura, Dan aganinta innaro itama uwace agareta, kodan hallacin da mijinta yama iyayensu da darajar abbanmu, amma takula ran Abba a 6ace yake, kad'an yake jira a ta6ashi ya fashe, shiyyasa bataja zancen yay tsawoba ma.
     
      Koda suka shiga gida kowa sashensa yayi, innarmu harta kwanta saiga Abba yashigo d'akinta, abinda bayayi kenan, yakan shiga sashen matansa amma baya kwana, saidai mace tabishi nasa d'akin.
     Tana yunk'urin tashi zaune zata tambayesa lafiya? ya d'aga mata hannu kawai ya hawo gadon tareda janta a jikinsa suka kwanta.
    Bai bata damar maganaba Dan haka tayi shiru kawai kamar mai barci.
        Kamar yanda Abba bai isashen barciba hakama innarmu batayiba, Zarah ma kwana tayi kuka akan rashin shigowarsu Sa'eed.
         Hakama mamansu yaa Hameed da Gwaggon Haleematu basu rintsaba dasukaje gida.

      Kwana biyu da faruwar lamarin Abba yak'i cewa komai, yakuma k'i sauraren wayar da ake masa daga gidan matan nasa.
       Innaro harta fara samun sauk'i itama.
       Sa'eed kam dadynsa ya taso k'eyarsa washe gari gidanmu, an tattauna akan maganar, yafad'i dukkan abinda zarah ke masa, wani ta amsa laifinta wani kuma ta musa ba ita tayiba, sai wani cikin iyayenmu ya harareta take shiru.
      Nandai aka musu fad'a bayan itaba dad d'insa yace tafad'i abinda yake mata, saboda kar ahanata komawa saitace ita baya mata komai, wannan yasa aka musu fad'a da nasiha kawai akace yad'auki matarsa su tafi.
     Dad'i tamkar zai kar zarah kuwa, saitaji zuciyarta wasai, bata tareda damuwar komai, (kota manta uwarta bata gidansu itama a dalilinta kuma🤕?).

     Washe garin rana ta uku tunda safe saiga mamansu yaa Hameed tareda yayanta ya maidota, (dayake babanta ya tsufa sosai, komai nasu yanzu sai yayan nata, ko kud'inma dashi suke tak'ama yanzun, duk da mahaifinsu ya tara musu).
       Abba dai k'in saurarensa yayi, saida yaje ya kama k'afa da baba mai kanwa aminin marigayi mal. faruku, daddyne yamasu jagora zuwa gidan innaro dake kwance tana jiyyar goshi, damma kullum sai innarmu ta gasa mata safe da yamma, duk da masifar innaro da take sha batayin zuciyar ko nuna gazawa.

        Ansha fama akan Abba kafin ya sauraresu, danma akwai baba mai kanwa ne a zancen, amma ya tabbatar musu da Cewar shifa yagaji da iskancin dasuke masa a gida, tun zamanin k'uruciya har girma yafara kamasu sun k'asa canjawa, yabama kowaccensu damar k'arshe inhar suka kuma Tayar masa da rikici agida kowacce zata nemi hanyar gidansune, kuma tatafi kenan har abada, Dan bazai duba 'ya'yan dake tsakaninsuba ma.
       Tunda ga ranar mamansu yaa Hameed tadawo gidan, Gwaggon Haleematu kam bata dawoba, itada iyayenta sunce sai Abba yazo da Kansa koya turo anbasu hak'uri.
      Shikuma ya rantse saidai tayita zama inhar saiyaje bikonta.

       Gidanmu dai kam kwana biyu tsit kakeji, Dan baba k'arami da daddy ma summa matansu kashedi da sharad'in barin gidan gaduk wacce tasake fad'a da wata, wannan dalilin yasaka gidan yin lafiya, 'yan anguwa da makwafta sukaji kasiririt.

    Innaro ma ta warke abinta, saidai kam sun k'ulla da mamansu yaa Hameed, Dan yanzu ko 'ya'yanta basuda farinjini wajen innaro, ko Naziru autansu yamata Abu saita makeshi (ho innaronmu ta mutunci🤣😝).



***************



     Zazza6i dai yahana Munubiya sakat, yaa marwan yagaji da lalla6ata ga ciwo na cinta, yau dai yakwasheta zuwa asibiti tana kukan batason zuwa, amma yak'i saurarenta.
      Haka dai sukaje, bayan yankar kati dabin layi suka sami ganin doctor, gwajin farko doctor yabasu albishir d'in samun rabo na wata d'aya kacal (yaa marwan sharpshooter🤭, Munubiya dai inaga tuntu6e akayi🤫🤣).
         Wayyo zokuga murna wajen ogan miskilanci, babu kunya yakira Abbansa ya sanar masa, shima murna yaytayi ata cikin waya, kafin kace mi zance yabaje dangi, har innarmu labari yakai kunnenta.
      Harda kukan dad'i tayi, ikon ALLAH kenan, ita saida ta jera shekara 20 tana kuka da shan gori kafin ta samesu, amma ga Munubiya wata 1 da sati d'aya da aure har ALLAH ya kawo rabo. Saura munaya, k'ila itama d'indai an samu, tunda shekaran jiya dasukai waya take mata complain batajin dad'i. haka innarmu taita murnarta a d'aki ita kad'ai, babu Wanda ta sanarmawa tabarma cikinta, a cewarta idan yafita ko Munubiya tazo gidan sagani.

       Abin nema yasamu fa, yaa marwan tamkar zai maida Munubiya ciki, kokuma ya maido cikin nata jikinsa yarage mata wahalar laulayi haka yakeji, Dan tana d'an shan wahala gaskiya. ko girki yanzu bata iyayi balle gyaran gida.
      Hakanne yasaka mama rabi'a cewa yadawo da Munubiya wajenta harta samu sauk'i.
      Saiya fara fushi da rok'on tabarta Dan ALLAH shima zai kula da ita ai, abasu Ayusher ko feena takoma wajensu saita taimakawa Munubiya da aikin gidan.
     Mama Rabi'a tace a'a, Ayusher itake taimaka mata itama, feena kuwa ba cikakkiyar lafiyace da itaba, ba kowanne aiki take iya yiba ko agida (kunsan masu sikila dai🤦🏻‍♀, ubangiji ALLAH yabama dukkan masu irin wannan ciwo lafiya, ALLAH yasa yazamema rayuwarku kaffara kuda iyayenku da kullum suma hankulansu ba a kwance sukeba😢, duk mai wannan ciwon ina tsananin tausayinsa wlhy😭).
        Babu Wanda yaa marwan ya iya, dole ya tattaro kayansa shida Munubiya suka dawo gidan kawai, ai ko su Ayusher sunci dariya, danma fadeel bayanan, saidai a waya suka bashi labari.
     Munubiya tacigaba dasamu kulawa wajen mama Rabi'a, bata aikin komai saidai amata, sai idan boss nason rage nauyi ya janyeta d'akinsa da wayo ya kashe arna😉😎.
    Mama Rabi'a duk tana kula da su, amma saitayi kamar batasan bikin dasukeyiba, Dan taga idon yaa marwan a tsakar goshi yake😂😜.



    🤥kai jama'a mu koma India.🛫⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀



....................................................
______________________________
....................................................



        Zafin jikinane yafara masa yawa, dan yafara shiga sosai jikinsa, cikin barci ya laluba danson jin minene mai zafi ya rungume haka? jin kamar mutum yasashi k'ok'arin bud'e idonsa dasukai masa nauyi  saboda barci, dishi-dishi yafara ganin fuskar munaya, hardai yasamu nasarar bud'e idon gaba d'aya a kanta🤫.................✍🏼








_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🤚🏻✋🏻_

[7:28PM, 6/13/2019] Abue Saleh Al~Quyraemey: *_Typing📲_*



    *_Haske writer's asso...._*💡



     
     *_♦RAINA KAMA......♦_*
              _{Kaga gayya}_



             *_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻



  ~Book 2~ 👉🏻3⃣


............Shiru kawai yayi yana kallon fuskarta ta cikin d'an hasken mai kalar jaa, sai fuskar tabada wata kala data k'ara mata k'yau. yaune ranar farko dazaice yamata kallon k'urilla irin haka, yadad'e yana kallonta kafin ya janye idanunsa dake cike da barci. hannu ya mik'a ya kunna ainahin fitilar, haske ya gauraye d'akin, cikin dabara yafara yunk'urin janye jikinsa, amma tak'i yarda, saima farkawa datayi, tabud'e idanunta dasukai nauyin barci a hankali, kad'an take kallon face nashi, ta lumshe idon tasake bud'ewa.
       “wannan d'aurin goronfa?”. ‘galadima yay maganar a hankali cikin muryar barci, yanabin hannun munaya da ta zagaye cikinsa da kallo’.
      Sosai Munaya ta waro idonta yanzun, ganinta a jikinsa kwance, gashi tawani dabaibayesa saita sakeshi da sauri tana matsawa baya da waige-waigen inda take kwance. gabanta ne ya fad'i, dan ita harga ALLAH tama mance ta hau masa gado, tayi saurin rik'e kanta dake sara mata tana tashi zaune.
      Shima saiya tashi yana binta da kallo, a mugun sanyin murya yace “bakida lafiya ne?”.
       Hawaye suka wanke mata fuska, muryarta na rawa tace “kaina kamar zai tsage”.
      Saida yaja 1minute kafin yad'an matso kad'an, yatsunsa biyu ya d'ora gefen wuyanta, saiyaji jikin zau da zafi, ya janye ya d'aura zuwa gefen kanta, jijiyar wajen sai motsi takeyi d'ass d'ass d'ass d'ass, alamaun kan namata ciwo sosai. hannun ya janye tareda sakkowa daga gadon gaba d'aya.
          Ya zagayo 6ari da take, hannu yasa ya zame nata hannun data tallafe kanta dashi, ta tad'ago idanunta dake cike da barci, sunyi d'anja sun k'ara girma, idonsa a kanta, Dan haka ta janye nata ta maida k'asa tana cigaba da hawayenta.
     Kad'an yad'an furzo iskar bakinsa, kafin a hankali yace “mike miki ciwo bayan kan?”.
      Saida takuma matso wasu hawayen sannan tace, “duk jikina”.
     “kin fad'ine?”.
  Kanta kawai ta iya girgiza masa, ya cigaba da tsura mata idanu batare da yace komaiba, ganin tana hawaye duk sai yaji babu dad'i, koba komai itad'in Friend nashice ai, kamar yanda yafad'a tun farko. yad'an sauke ajiyar zuciya mai sauti kafin ya mik'e, bayi yashiga, mintuna kad'an yafito, tana a inda ya barta dafe da kanta, yace “taso kid'an watsa ruwa, ko jikin zai huce”.
       d'agowa tayi ta kallesa, sai taga ya tsatstsareta da mayun idanun nan nasa, tayi saurin janye nata, amma takasa tashi. matsowa yayi kusada ita, ya mik'a mata hannunsa, alamar takama ta tashi, ta d'ago ta kallesa ya d'aga mata kansa yana mai lumshe idanunsa alamun tabbatarwa.
      Hannunta ta saka a cikin nasa, ya had'e waje guda sannan ya taimaka mata ta tashi tsaye, kallo d'aya yamata ya kauda kai, dukda kayan nata masu kaurine saida yaji wani Abu daban, dansu fidda surarta sosai. Har wajen wankan yakaita, sannan yafito batare da ya ce uffanba. da kallo tabi bayansa, a ranta tana mamakin sauk'in kai irin nasa, ada kallon mutum mai girman kai take masa, amma tunda suka fara rayuwa a tare saita fara fahimtar ba haka baneba, kawai dai shi mutumne dabai cika hayaniya da surutu ba, shiyyasa inbaka gama saninsaba saika dunga masa kallon mai girman kai.
      Koda ya fito saiya had'a mata tea, shi dama baya rabo dasu a d'akinsa, magani ya d'akko shima ya ajiye, yakoma bakin gadon ya zauna yana tsumayen fitowarta.
    Kusan mituna 10 tagama watsama jikinta ruwan, lallai naji dad'i sosai, saidai kuma bazan iya maida kayan dana cireba, inajin kunyarsa, kuma jinsu nake sun d'auki zafi, towel naja Na d'aura, saidai bashida girma, bazan iya fita a haka dashiba Galadima yana d'akin, kad'an nabud'e k'ofar Na lek'oda kaina, yad'an juyama k'ofar bathroom d'in baya kad'an, a hankali cikin muryata mai nuna alamun banida lafiya nace “please yalla6ai ka taimakeni da hijjab”.
       Waiwayowa yayi ya kalleni, alamun baijiba sosai, Na turo baki kad'an sannan nace “please yalla6ai hijjab”.
    Baice komaiba ya mik'e, inda nake ajiye hijjab d'in yaje ya d'ako, yazo inda nake ya d'oramin akan hannuna dana mik'o, kallon ido cikin ido mukaima juna, kowa ya janye cikeda basarwa.
       
     Bayan nasaka hijjab d'in nafito kamar wata muna fuka, sai k'asa nakeyi da idanu nakasa kallonsa, shima idonsa a lumshe ya jingina da fuskar gadon, wucewa nayi wajen akwatina Na d'akko wasu kayan barcin, bayi nakoma Na saka, saina yafo k'aramin Vail Na cire hijjab d'in.
    Yabud'e idanu kad'an a kaina, batare da yayi magana ba ya nunamin mug d'in daya had'a tea a ciki. nad'an yatsine fuska da marairaice murya tamkar xanyi kuka, “ALLAH yalla6ai banajin yunwa”.
    Shiru yay kamar bazai tankaba, saida yaja kusan 2minutes sannan yatashi zaune sosai,  batare da yayi magana ba ya d'auki mug d'in da drug's d'in ya taso inda nake zaune a kan sofa, saman k'aramin table d'in gaban kujerar ya zauna yana fuskantata, d'an gaf d'in daya bari tsakanina dashi bai wuce tafin hannuba, Dan har inajin saukar numfashinsa, baya nad'anja kad'an Na jingina da jikin kujerar, amma hakan bai hana kusanci sosai tsakanina da shiba. babu magana babu komai naji dirar cup a bakina, d'ago ido nayi tamkar zan fasa kuka, danni wlhy banajin shan shayinan, yamin hararar data saka 'yan cikina harmutsawa, babu shiri nabud'e baki na kar6a, ya had'e girar sama da k'asa, baibar ko k'aramar k'ofar dazan kawo masa wargiba, haka naita kar6a ina hawaye, saida yaga Na shanye tas sannan ya barni yana hararata, nidai yau babu k'arfin mayarwa, yabani maganin, shikam babu musu Na kar6a nasha. ganin yanda naketa hawaye saiya zubamin ido kawai yana kallon ikon ALLAH, nikam banida niyyar daina kukan nawa, kuma nima bansan dalilin kukanba, kawai dai jinake hawayen Na tahowa.
    Ya zuba tagumi abunsa yana kallona kamar yasamu television. kallon dayake min saiya k'ara tunzurani, nafara kuka mai sauti harda shashsheka.
     Tagumin yacire yana wani k'asaitaccen murmushi, ya mik'e tseye yakoma kan gadon, filolin dasuke k'asa ya d'auka ya jera a tsakkiyar gadon kamar d'azun. nidai duk ina kallonsa, saida ya lullu6ama k'afafunsa bargo zuwa cikinsa sannan yace, “taso ki kwanta sarkin arhan hawaye”.
      Harara Na zuba masa batare da Na shiryaba, sai kawai ya ta6e bakinsa yay kwanciyarsa ya barni, tareda kashe fitilar ya maida ta barci.
      Kusan mintuna 4 Na zame Na kwanta a kujerar, amma sainaji duk babu dad'i, saboda maganin bai fara tasirin da jikina zai bar ciwonba, tashi nayi nakuma zama, kusan 5munutes sannan natashi sad'af-sad'af tamkar munafuka na haye gadon. Ni duk tunanina yayi barci. Ashe duk abinda nake yanajina da kallona. murmushi yayi kawai yana lumshe idonsa, a ransa yana jinjina irin rashin wayona.

      Ajiyar zuciya Na sauke a hankali, sannan naja bargon dayake babbane Na lullu6a, mintuna kad'an nafara zufa, alamar zazza6in ya sauka. Bargon na janye don insha isaka, bansan sanda barci ya saceni ba.
     Juyowa yayi ya kalleni, yaga ina sauke numfashi a hankali alamar nasamu barci, k'aramar ajiyar zuciya ya sauke kafin yasake addu'a shima ya gyara kwanciyar sa.


★★★★★★★


             Yau gidanmu sun tashi cikin tashin hankali, Abbah yay Accident yayin dawowa gida daga wajen aikinsa, innarmu Na kwance ciwon kai dukya isheta, tunda ta  tashi da safe dashi ta tashi, gasu Aryaan sun isheta da ihun fad'ansu, sai mugun wasa sukeyi suna guje-guje a falon, amma takasa d'aga kai ta tsawatar musu.
      Zuciyarta cike da kewar su Munubiya, inda suna nan da yanzu suke bata taimako, koyaya tace batajin dad'i zasu rud'e, amma gashi yau ko wanke-wanke tama rasa mai matashi, sai Zainab maman fauziyya tasaka tayi mata, amma 6angarenta ko shara bai samuba yau, kuma tun d'azun tafara jin mamansu yaa hameed tana k'ananun magana akan tak'i fitowa ta aza musu girki, maimakon sunga shiru su lek'o suji ko lafiya? A'a su babu ruwansu, kawai a dafa abasu suci da 'ya'yansu...
    Wayarta dake ring ta katse mata tunani, ta kalli su Aiyaan dake danbe Aryaan Na kuka saboda dukansa da Aiyaan yayi a baki. “wani cikinku ya d'akkomin wayata saman freight”.
        Cikin kuka Aryaan yace “Innarmu kingafa ya dokarmin baki”.
      “kukuka Sani, nidai nace wani ya d'akkon waya acikinku, idan kuma kuka bari Na tashi sai jikinku yagaya muku”.
       Aryaan ya d'akko mata wayar ya kawo mata, lokacin harta tsinke, ganin Abbanmu ne yasata bin kiran, bugu biyu aka d'aga, ko gaisuwa bai bari sunyiba, yace mai wayarne yayi Accident, yanzu haka suna general hospital.
       “innalillahi wa'inna'illaihirraji'un” innarmu tafad'a tana mik'ewa zumbur, ga wata zufa Na karyo mata, batasan tayo waje tana kwalama matan gidan kiraba.
      Kowacce tafito jiki Na 6ari, azatonsu wata acikinmu aka sako, musamman ma ni dasuke kiran aurena auren d'ori d'afini.
        tana hawaye ta sanar musu da abinda yafaru. Nanfa gidan ya rikice, yara suka garzaya suka sanarma innaro.
     Ko takalmi babu haka tanufo gidanmu tana shar6ar majinar kuka da kiran tashiga uku, Awwalu zai mutu ya barta. wannan kwakwazon natane ya ankarar da jama'ar anguwarmu.

        A rikice baba k'arami da Dady suka nufi asibitin, Dan matan gidanmu sun kira suma sun sanar musu abinda ke faruwa.
     Kafin wani lokaci jama'ar gidanmu sun gama cika asibitin, sai koke-koke sukeyi suna son ganin Abba, amma an hanasu, Dan bak'aramin buguwa yayiba.


______________________________

     Alhmdllh natashi jikina da sauk'i, Dan kuwa babu zazza6in da ciwon jikin, hakama ciwon kan babu, bai tadani ba saida yadawo massalaci, lokacin har gari yafara haske ma.
     Na idar da salla ina zaune ina addu'a yafito daga bathroom, da alama wanka yayo, Dan sanye yake da bathrobe sky blue, yana rik'e da k'aramin towel a hannu yana goge ruwan fuskarsa.
    Kallo d'aya namasa Na d'auke kaina, shikoma bai kalleni ba ya wuce gaban mirror ya zauna, saida yafara shafa mai sannan Na tsinkayo muryarsa yana fad'in “ya jikin naki?”.
        Yanda yay maganar a cinkushe yasakani d'agowa Na kallesa, ganin hidimarsa kawai yakeyi saina d'auke kaina, nace “da sauk'i”.
     Bai sake magana ba, harya kammala yabar gaban mirror d'in, wajen wardrobe yakoma, nidai kaina Na  k'asa bansan hidimar dayakeba.
      Koda ya d'auki kayan saiya koma bayi ya saka tamkar yanda ya saba, ya fito ya iskeni ina gyaran gadon, ta gefen ido Na kallesa, yayi k'yau cikin wani bak'in lallausan yadi, Wanda akaima ado da jan style, nakula yanason kayan al'adarsa, dukda baitashi ya girma cikin k'abilar tasaba, sock's ya d'akko da bak'ak'en takalma sau ciki ya zauna saman sofa, yana sakawa yana magana, “uhm Zanyi wata 'yar tafiya Na kwana 2 kacal, mikike da buk'ata?”.
       Tsayawa nayi daga gyaran gadon danake, Na d'ago ina kallonsa kawai, jin nayi shiru kuma yanajin alamun ana kallonsa ya d'ago shima. Ido muka had'a saina janye nawa.
      “kallon fa?”. ‘yafad'a yana k'ok'arin saka d'ayan takalmin’.
       Cikin la6e baki nace “yoni yalla6ai mizan kalla anan?”.
       Banza yamin, saida yagama saka takalminsa sannan yamik'e tsaye yana fad'in “hakanefa, Ashe babu abin kallo anan”.
       Nima shiru namasa ban tankaba, ya saka laptop d'insa dawasu 'yan abubuwa a k'aramar briefcase d'insa, ya zuge zip d'in yana fad'in “ki shirya muje kiga likita kafin Na wuce”.
        Da sauri nace “a'a kaje abinka, Indai nice Na warke”.
     Idanu ya tsuramin alamun tuhuma, nikuma nak'i kallonsa, ya girgiza kansa kawai sannan ya ajiye min kud'i akan gadon, “ni Na tafi, a yafi juna”.
        'Dagowa nayi ina kallonsa da mamakin kalmarsa ta k'arshe, bansan sanda bakina ya su6uce nace “ALLAH ya tsare hanya, ya dawo dakai la fi ya”. ‘na k'are maganar da d'aid'aya’.
      Cak ya tsaya abakin k'ofar, saboda yanda addu'ar tawa tazo masa a bazata, dan bai tunanin hakan daga gareniba, yajuyo a hankali tamkar maison gaskata abinda yaji, kallona yayi muka had'a ido, amamakina saiya sakarmin wani tsadajjen murmushi,  irin Wanda zan iya rantsuwa ban ta6a gani daga garesaba. Baice komaiba yajuya yafice da sauri.
     Yabar zuciyata da luguden dabansan dalilinsa ba. Wata ajiyar zuciya Na sauke, tare da zama jagwaf a bakin gadon na dafe kaina da mamakin murmushin da Galadima yamin.

           
         Bai dad'eba sosai a hospital yamusu sallama yafito, dama tun a daren jiya ya sanar musu zaiyi tafiya, ga jirgi kuma ya kusa tashi. yafito sunata binsa da addu'oin dawowa lafiya, yayinda shikuma yake amsawa cikeda murmushi. Saida yafara xuwa sukayi magana da doctors d'in dake kula da Abie, yaji babu wata Matsala sannan yafito.
     Dama Khumar ne ya kawoshi, Dan haka yanzu ma shine yatafi kaisa airport d'in. Zaman da baifi 30minutes ba jirginsu yataso zuwa 9ja.
      Zaune yake kusa da window, yayinda wata matashiyar budurwa ke gefensa, tunda tazo da nufin zama yawani kuma had'e fuska, a d'age ma ya amsa mata sallamar data masa,  yasaka belt tareda bud'e Newspaper yahau karatu.
      Budurwar sai satar kallonsa takeyi, tanason masa magana amma bataga fuska ba. Sai da akazo tambayar misuke buk'ata?, yace Coffee.
     Itama da sauri tace Coffee d'in. juyowa yayi ya kalleta, ta sakar masa wani tsadajjen murmushi.
    Janye idonsa yayi yanajan tsaki a zuciyarsa. duk yanda taso yamata magana ko sau d'ayane Galadima yak'i yayi, ya had'e gabas da yamma abinsa. Haka kawai sai tunanin tahowarsu da Munaya ya fad'o masa a rai, yatuna yanda tadinga wani dakewa irin itafa ta saba da hawan jirgi. jaridar yasaka ya rufe fuskarsa yana murmushi da jinjina jan aji irinnan yarinyar, ita bata yarda aga marenarta ba. ya tuna diramarsu ta daren jiya, wani murmushin yakuma saki...... haka abubuwa da yawa sukaita dawo masa akan Matar tasa ta auren Contract. wani abun nata abin dariya, wani Na mamaki, ita bata yardaba adole big girl Ce.
       Koda suka sauka baiko kalli inda yarinyar nan takeba, da sauri tabi bayansa tana fad'in “haba yayana babu sallama? Ai kodan darajar makwaftaka mayi sallama”.
     Yana sauka daga step d'in k'arshe Na jirgin ya juyo ya kalleta, aransa yace yarinya sai nacin jaraba. Ta kuma fad'in “kozaka bani Number ka muke zuminci”.
     Yanzu kam wata uwar harara ya zuba mata kafin yay gaba abinsa. tsaye tayi tana binsa da kallo, jitake kamar ta tsala ihu, harma tafara tunanin ko shid'in kurmane?. cikin matuk'ar mamaki ta hango wasu masu kaya iri d'aya sunyo wajensa, daka gansu kaga jama'ar masarauta. da k'yar ta had'e yawun bakinta, kenan shid'in jinin sarautane?. Batada mai bata wannan amsar, Dan haka taci gaba dabin motocin Galadima da kallo har suka fice abinsu.
       Driver d'in da yazo d'aukarta yak'araso inda take, gaisheta yafarayi kafin ya k'ar6i handbag d'in hannunta. amota take tambayarsa koya San wanene Wanda masu kaya iri d'aya sukazo d'auka?.
      Yace, “ma'am Galadima Sameer kenan, d'an tsohon Sarki, kusan 1month kenan da aurensa ai”.
       Hararsa tayi cikin daka tsawa tace “ina ruwana dawani aurensa, bashi Na tambayeka ba. Punishment d'inka Na fad'amin abinda ban tambayeka ba shine ka nemomin number sa”.
       “ALLAH ya huci zuciyarki Ma'am”.
     Banza tamasa, yayinda shikuma zufa keta karyo masa dukda AC n dake motar, tunaninsa a ina shikuma zai Samo number babban mutum irin Galadima Sameer shikam? yasan idan bai samo d'inba yashiga uku, dan yarinyar nan ba mutunci gareta ba.



     *********************

        Tun bayan tafiyar Galadima saina zama wata sukuku, abin mamaki saigani da kewar Galadima wai, gaba d'aya yinin sai nayishi wani babu dad'i, ga gabana yanata yawan fad'uwa, jinake kamar wani al'amari yana shirin faruwa da rayuwata.
     Sauban ma sarkin tsokana kasa shiru yayi saida yay magana.
         Bayan ya dawo school sai muka tafi asibiti, tunda Na gaida Abie da Momma da Aunty Mimi saina koma gefe nayi shiru abina, ciwon jikine kawai ke nuk'urk'usata, dan ga6o6ina masifar ciwo sukemin, narasa wannan dalili? zazza6inma banaji yanzun, ga yawan fad'uwar gaban dana yini inayi, sai kasa kunne nake naji ko Galadima zai kira wani a 'yan uwansa yace ya sauka lafiya, dan zuciyata tafi karkata da fargaba a kansa.
      Shirun da Sauban yaga nayi shine ya kalleni yana dariya k'asa-k'asa. “Aunty gimbiyarmu har kin fara kewar Hubbin naki halan?”.
     Idanu nad'an waro ina kallonsa, ganin su Momma Na dariya saina 6oye face d'ina cikin veil d'ina ina fad'in “kai yaa Sauban ALLAH a'a”.
       Dariya suka kuma sanyamin, Abie nata murmushi shidai, Momma tace, “A'a Mrs Galadima kifad'a gaskiya dai?”.
       Kunya takuma lullu6eni, saina k'udundune kaina gaba d'ayama a gyalen saboda. ina k'aunar wannan family sosai a raina, saboda nima suna nunamin tsantsar k'auna, ko yau nabar cikinsu auren contract d'inmu yak'are bazan manta da alkairinsuba a gareni.
      Haka nagama shirin barci Na kwanta a gadonsa ina shak'ar k'amshin turarensa danakejin dad'insa fiye da da. nadad'e ina juye-juye banyi barciba saboda damuwace cinkushe da raina, ga zazza6i mai zafi ya rufeni, bansan ina Galadima yajeba balle nayi tunanin samun number na kirashi, Na gwada number shi ta nan India tak'i wucewa, dama a wayar Samha Na d'auki number bama ta saniba, yau babu mai kulawa dani, sainaji wata kewar innarmu da Munubiyata sun dawomin sabo fil a zuciya. Sai da dare yakusa rabawa kafin barci mai nauyi ya d'aukeni.



_____   .★.  _____  .★.  _____


         Har yamma ba'abari kowa yaga Abba ba, 'yan gidanmu sunci kuka harsun gode ALLAH, Su Munubiya da dukkan yaran gidanmu Na ma'auri tuni labari ya iso musu, kuma duk sun tattara a asibitin suma.
       Doctor d'in dayake kan Abbanmu ne yafito yana basu hak'uri akan suje gida hakanan, dan gaskiya baza'a bari suga Abba ba a yau.
       Sabon kukane yatashi, musamman ga innaro, idan ka kalleta dolene tabaka tausayi wlhy, yau babu jarabarnan da rashin mutunci, kuka take da fad'in Auwalu karya tafi ya barta..........
     Sambatunta yakuma raunana zukatan mutane da yawa a wajen.
      Munubiya tayi yunk'urin kirana amma network yahana, da Yaa marwan yakula da hakan kuma ya hanata, yace karta sake ta sanarmin yanzu. Wannan dalilin yahana a sanar min d'in.
        Kowa zuciya babu dad'i suka tattara suka tattafi gida, dady da baba k'arami, yaa hameed yaa shafi'u da ya Naseer aka bari a asibitin zasu kwana.
     Ranar duk Wanda yasan gidanmu yasan babu lafiya, Dan gidan yayi tsitt, kowa tashi ta isheshi a zuciya, barcima k'alilanne daga cikinsu suka yisa.



___________________________



        Sosai hadimansa sukayi farincikin ganinsa, kamar yanda shima yay farin cikin ganin Nasu, sud'in mutanene masu muhimmanci a rayuwarsa, sunzama wasu 6angare na duniyarsa.
        Kwance yake a bayan motar idonsa a lumshe, ya saki guntun murmushi saboda tinano yanda zata k'are masa a wajen Momma, koda wasa bai sanar mata Nigeria zai zoba, yayi hakane kuma dan kartayi yunk'urin dakatar dashi ma. jin alamar motar ta tsaya ya bud'e lumsassun idanunsa tareda furzo k'aramar iska, duk da isowar dare yayi hakan baisa sauran hadimansa sun kwanta ba, ya iskesu zazzune a k'ofar sashensa suna jiran isowarsa.
        Dogarin daya bud'e masa k'ofar yafara k'ok'arin d'aukar briefcase d'insa domin shigar masa.
    Shima ziro k'afarsa d'aya yayi ta inda aka bud'e masan, ya zuk'i iskar masarautarsa tareda fesota tabaki yana lumshe idanunsa, ko ina kwanyar yake da hasken lantarki tamkar rana, duk lokacin daya zo cikin masarautarsa, mahaifarsa, yakan tsinci kansa cikin tunano abubuwa masu d'aci da rad'ad'i a zuciyarsa, yakanji inama ace shid'in ba kowa baneba, inama ace shid'in talakane fitik mai tarin kwanciyar hankali, da za'ace yaza6i rayuwar dazaiyi, da zai za6ama kansa zama talakane, dan babu Wanda yakai talaka kwanciyar hankali inhar yanada k'yak'yk'yawar zuciya da wadatar zuci, amma babu komai a cikin dukiya da mulki sai damuwa darashin kwanciyar hankali, kai kenan kullum cikin rashin nutsuwa, idan kayi wasama ibadar da ubangiji ya halicceka dominta bazakayiba, ya had'iye wani Abu mai d'acin gaske a mak'oshinsa. sannan yashiga k'ak'aro murmushin dole ga sauran hadimansa dake gida basuje tarbarsaba. daka kallesu kasan suna cikin tsantsar farincikin ganinsa, dan sunyi kewarsa, shima hakance agaresa. bayan sun gama gaggaisawa ya tambayesu lafiyarsu sannan yashige ciki.
      Ko ina k'al yake tamkar yanda yake buk'atar ganinsa, (hadimansa nada k'ok'arin tsaftace sashensa koda baya k'asar).
    Zama yay bisa kujera yana fad'in “ya ALLAH! Alhmdllh”.
         Dogarin daya shigo masa da jakka yakuma masa sannu da zuwa sannan yafice.
    Yakai mintuna 5 a wajen zaune, sai k'ullawa da kwancewa kawai yakeyi, ga gajiyar zaman jirgi na nuk'urk'usarsa data rashin isashen barci dabasa samu shida Munaya. da k'yar dai yamik'e zuwa bedroom d'in, komai need sai k'amshin mayen turarensa da air fresheners mai sanyin dad'i ke tashi, ya ajiye jikkarsa a kan gadon sannan yafara zame kayansa danya samu ya watsa ruwa.

      Ya d'an jima a bayin sannan ya fito d'aure da towel, yana tsane fuskarsa zuwa kai dawani. wardrobe yabud'e ya d'akko boxes kawai yasaka, sannan ya saka jallabiya, sallolin da suka riskesa a hanya ya rama, yana idarwa yacire jallabiyar, matsawa yay jikin mirror ya fesa turare kad'an ya hau gadonsa da yay missing. harya kwanta yatashi zaune, briefcase d'in dayazo da ita ya bud'e, ya Ciro wayoyinsa tareda layinkansa na Nigeria duk ya saka, sannan ya ijiye wayoyin, insha ALLAH zuwa lokacin da zai tashi yana fata komai ya dai-daita.
       Addu'ar barci yayi ya gyara kwanciya, amma sai barci yace bai gadaba, tunanin ahalinsa daya baro wata k'asa ya dabaibaye zuciyarsa, wata kewarsu ke tsikarar zuciyarsa, yanzu yasan Abie yayi barci, hakama Momma watak'il ta kwanta, dan macece mai yawan k'iyamull laili, duk da a asibiti takan kwana hakan baya hanata kusanta kanta ga mahaliccinta, Aunty Mimi da Samha ma yasan sunyu barci, Sauban ne dai dakamar wahala ace ya kwanta, ya juya kwanciyar sa yana murmushi, zuciyarsa tace “to matar contract fa?”. ya d'age kafad'a da ta6e bakinsa kad'an, saikuma yasaki k'aramar dariya, daren jiyane kawai ya fad'o masa a rai, yau kuma koyaya ta yini ta kwana? (danba time d'inmu d'aya da India ba), a fili yace, “ALLAH yasa yau dai babu zazza6in, my Friend kin cika taurin kai, dakin yarda nakaiki asibiti zanfi samun nutsuwa, oh god🤦🏼‍♂”. ‘ya k'are maganar da dafe kai’.
         Shima yajima baiyi barciba, sai can dare yaja da nisa sannan ya saceshi.


          Da asubahi da k'yar ya iya tashi, alwala yay yafita massalaci, bayan an idar da salla yafito suka had'u da Sarki da jama'a keta zubewa suna kwasar gaisuwa.
     Sarki yayi mamakin ganinsa, dan har saida fuskarsa ta nuna hakan, murmushi kawai Galadima yayi yana rissinar da kansa k'asa.
     Sarki baice masa komaiba yanufi sashensa, sai Galadima yabi bayansa, dogarai kuma suka take musu baya, bayan sun gaida Galadima d'in.

       A hamshak'in falon mai martaba na farko suka yada zango, Sarki na zaune bisa kujera mai zaman mutum biyu, Galadima na k'asa kusada k'afafunsa. Kukun Sarki ne suka shigo shida jakadiyya bayan sunyi sallama.. 
      K'aramin tire suka ajiye dake d'auke da butar shayi, sai mug da wani k'aramin bowl mai k'yau anzuba sukari, sai jug k'arami shima an zuba tataccen lemon tsami, saikuma Zuma shima a k'aramin bowl.
       Kuku da jakadiyya suka zube gaban mai martaba suna kwasar gaisuwa, sannan suka gaida Galadima shima da masa barka da zuwa.
        Cikeda kulawa ya masa musu, har kuku ya durk'usa zai had'ama mai martaba shayin Galadima ya dakatar dashi, tareda masa nuni dayaje abinsa.
    Kuku ya rissinar da kai alamar girmamawa sannan suka fice shida jakadiyya suka basu waje.
         Galadima ya had'ama Mai martaba shayi da ruwan lemon tsami kamar yanda yasan yana sha a kowacce Safiya, (ada mahaifinsa yasani da wannan al'adar, dan awajensa Sarki jalaludden ya koya). cikeda girmamawa ya mik'ama mai martaba mug d'in, kar6a yayi yana masa murmushi, sannan yace “kaifa?”.
       Girgiza kai Galadima yayi, yace “a'a Abba, wannan sai ku”.
     Mai martaba yay murmushinsu na manya sannan yace “Saukar yaushe Sameer?”.
       Galadima yad'an shafa wuyansa, cikin tsantseni yace, “da daddare Abbah, wani business ne ya kawoni, inaga insha ALLAH zamu bud'e company anan Nigeria saboda muma matasanmu su Mora daga guminmu”.
       Murmushi mai martaba yayi, ya kur6i shayinsa sannan yace “tunani mai k'yau yarona, ALLAH yasaka hannu a lamarin. ya jikin d'an uwana dasu auntyna Zeenah?”.
        “jikin Abie Alhmdllh Abba, dan bayan tahowarku sauk'i yakuma samuwa gaskiya, Momma kam suma lafiyarsu lau”.
       “to Masha ALLAH, tareda iyalin naka kazo kenan?”.
       “a'a Abba, ni kad'ai nazo, saina kammala abinda nazoyi itama idan zan dawo zamu dawo tare”.
      “to ALLAH ya tabbatar”.
      “Amin Abba, bara naje nad'an kimtsa mu gaisa da jama'a, dan zan d'an fita”.
        “ok, ALLAH yayi Albarka”.
     “amin Abba, a huta lafiya”.
     Hannu kawai mai martaba ya d'aga masa, Galadima kuma yafita.

      Babu inda ya Shiga, ya koma sashensa domin yayi shiri. saida ya had'a coffee da kansa kamar yanda ya saba idan yazo k'asar, ya zauna yasha danba abincin kowa yakeci a masarautarba, ko Ummu hasheem bayacin abincinta kota kawo, duk da kuma kulawa datake nuna masa fiye da kowa a gidan, gimbiya zulfah uwargidan sarkima tanada k'ok'arin aika masa abincin inhar yazo, amma ko kallon kulolin ma bayayi, saidai bayinsa su cinye.

        Yafito wanka yana tsane jikinsa wayarsa tayi k'ara alamar shigowar sak'o, wayar ya d'auka danya duba ko company ne, dan yana fatan ace komai ya daidaita ne, yanason kiran su Momma yaji Yaya jikin mahaifinsa.
     Ganin number ce sai abin yabashi mamaki, bud'e sak'on yayi kawai azatonsa ko Nuren ne.

      _Gargad'i!! tabbas sirikinka ya tsira a wanan karon, amma ka tabbatar masa next time bazamu barsaba, saimun raba ruhinsa da gangar jikinsa!!!!.................._✍🏼












*_ALLAH ya gafartama mahaifanmu😭🤚🏻✋🏻_*
[7:28PM, 6/13/2019] Abue Saleh Al~Quyraemey: *_Typing📲_*



    *_Haske writer's asso...._*💡



     
     *_♦RAINA KAMA......♦_*
              _{Kaga gayya}_



             *_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻



  ~Book 2~ 👉🏻4⃣


.............Cikeda tsantsar mamaki Galadima ya jujjuya wayar a hannunsa, kai kace itace zata fassara masa ma'anar sak'on, kuma komawa yay yana karanta sak'on a karo na biyu, a fili yace, *“SURIKI! SURIKI!.* to nikam wanenen sirikina?”.
      A take zuciyarsa tabashi amsa da *Baban matarka ta contract*. wata fad'uwar gabace ta samesa lokaci guda, wadda ALLAH ya tak'aita bata buga da bugun zuciyarsa ba, cikin tsitstsinkewar tunani dana zuciya yashiga bitar message d'in kamar mai haddar karatu, idan ya fahimci sak'onan dai akwai mummunan al'amari daya faru akan mahaifin munaya kenan? “ya salam”. ‘ya furta a fili, cikin dafe kansa yakuma fad'in “to adalilin mi wani abu zai samesa kuma yazam kamar yashafeni?”. gabansa yakuma fad'uwa, mutuwar Alhaji Abdussalam Abba mahaifinsu Samha ta dawo masa a rai, (mijin aunty Mimi). dafe kansa dake shirin sara masa yayi, to mizai kawo Abban munaya cikin case d'insa kuma? Sam bazai yuwuba ma, koma dai by mistake wani yaturo masa sak'on ne?. “mtoww! K'ilama hakane”. ‘yay maganar a fili yanajan guntun tsaki, tareda jefa wayar kan gado yacigaba da shirinsa.
            Shiri yake amma yakasa fidda abin a ransa, koyayi k'ok'arin ture tunanin gefe sai yakasa, dukda zuciyarsa tak'i yarda ta gaskata sak'on nasane. shiri ya kammala cikin Ash color d'in shadda gizna dakakkiya, tamasa k'yau ainun, komai nasa saiya saka Ash, Takalminsa helf cover, agogo da hula duk ash, ya kwashi phones nashi a hannu, ya fesa turare da gyara zaman hularsa sannan ya ciro wayarsa d'aya a aljihu, dan yakasa daurewa, number yaa marwan ya lalubo ya kirasa.

        A time d'in yaa marwan nata lallashin Munubiya tasha shayi sutafi asibitin amma tak'i, ta gardame akan ta k'oshi itadai su tafi kawai, mama Rabi'a dasu Ayusher sunyi lallashi amma tak'i yin shiru tasha, sai kuka take, hakan yasaka feena zuwa d'akin yaa marwan takirasa, shine yaketa lalla6ata amma tak'i kar6a, sai kawai ya had'e fuska ya koma mata ainahin marwan da bai d'aukar raini, cikin daka tsawa da hargagi yamik'a mata shayin, jiki na rawa takar6a tafara sha, tayi nisa dashan tafara amai kuma, mama Rabi'a tarik'eta, sukuma suka shiga mata sannu, yaa marwan na dafe da kansa cikin damuwa kiran Galadima ya shigo masa, kamar bazai d'aukaba saikuma yaciro wayar a aljihu ya diba.
     Mamakine ya kamashi dayaga sunan Galadima ta Nigeria, (ko sunzo k'asarne?), da hanzari ya d'auka tana gab da katsewa.
     Yanda Galadima yaji muryar yaa marwan yayinda yake amsa masa sallama sai hankalinsa ya tashi, ko gaisuwar kirki basuyiba Galadima ya hau masa tambaya akan Abba.
     Yaa marwan yace “gaskiyane ranka ya dad'e, jiya misalin 12pm Abba yayi accident, sunyi taho mu gama da wata thriller, yanzu hakama yana general hospital”.
        Zufar dake tsatstsafowa a fuskarsa yasa handkerchief ya share, muryarsa na rawa yace, “Marwan da gaske?”.
        Kula yaa marwan yayi Galadima kamar ba a hayyacinsa yakeba, shima muryarsa na rawa yace, “da gaskene ranka ya dad'e”.

       “hasbinallahu wani'imal'wakil” Galadima yafara maimaitawa akan la66ansa, ya sauke wayar a hankali zuciyarsa na wani irin suya, yama rasa wane kalar tunani yakamata ace yayi? Yaya zai fassara wannan lamarin? Kenan akwai wani Abu dabai saniba, kodai Abban munaya yanada wata masaniya akan lamarinsa, kokuma bai saniba yafad'a tarko, tabbas yakamata ma akan kansa yay wannan tunanin kodan abinda yayta faruwa tsakaninsa da Munaya, cikin k'araji yace “MUFTAHU!! kasan komai, dolenema kasan komai muftahu!!!, tabbas duk da kasancewarka d'an uwana, jinina, saina binneka da ranka a tsakkiyar masarautarnan inhar mahaifin matata ya rasa ransa wlhy, wannan ALWASHI NANE!!.
      ya k'are maganar yana buga table glass dake gabansa da masifar k'arfi, aiko ya tarwatse a wajen, kwalba ta yanka masa hannu. baibi takan ciwon dayaji ba yamik'e a harzuk'e ya d'auki wayar ya fice.

       A yanda yafito sai hankali hadimansa ya tashi, ga hannunsa yana d'igar da mini kad'an-kad'an, kuma suna gaisheshi yak'i amsama kowa gaisuwarsa, ko hannun daya saba d'aga musu inbaya buk'atar maganar yau basu samuba, da kansa yabud'e motar yashiga, hakan yasaka sarkin Mora Shiga da hanzari shima shida sauran dogaran dakan bisa in zai fita.
      Ko takan zuwa fada yay gaisuwa baibiba, suna fita daga masarautar kiran Nuren yashigo wayarsa.
     Yana d'agawa yace, “kajiramu a plaza”. ‘abinda yace kenan kawai ya Yanke wayar'.
      Nuren yabi wayar da kallo, inhar kunnensa yajiye masa dai-dai to ran Galadima a matsanancin 6ace yake, to mi aka masa? kokuma shida mutuniyar tasane mama Fulani? Nuren ya girgiza kai kawai yana murmushi, mama Fulani da Galadima sai addu'a kawai, dan tamkar suna ganin hanjin junane.
         Tafiyar mintuna 30 takawosu plaza, amma basu shigoba, dan haka Nuren yana hangosu yataso yafito.
     Matashin Saurayine shima, mai kama da Galadima sosai, dan wandama bai saniba saiya d'auka tagwayene, abubuwa kad'anne suka banbantasu, dan a shekaruma zasu iya zuwa d'aya, shima Nuren dagani yana cikin Hutu sosai, gashi d'an gaye ajin farko cikin nutsatstsun matasa masu ji da kai.
       Da sauri dogari d'aya yafito ya rissina yana gaisheshi, hannu ya d'aga masa cikin sarauta (hakan ya tabbatar min shima jinin sarautar ne) dogarin yabud'e masa inda Galadima yake ya shiga.
      Kallo d'aya yayma Galadima ya tabbatar akwai Matsala, hannu yabashi sukayi musabaha, cikin tsantsar kulawa yace, “brother mike faruwa ne?”.
       Galadima ya kalli Nuren da idanunsa da suka koma jajaye, cikin matsanancin d'acin zuciya yace, “bansan alak'ar data sashi cikin tawa ba”.
        Nuren yace, “waye?”.
    Kauda idonsa Galadima yayi daga kallon Nuren, ya maida ga window yana kallon mutane daketa harkokinsu, wani murmushin takaici yayi, sanan yafurta *“SIRIKI!”*
     Nuren yazaro idanunsa waje, a zabure yace, “yanzu haka yana ina?”.
      “general hospital ”.
     Nuren yay hanzarin fad'ama sarkin mota “muje general hospital na garinnan”.
     “to ranka ya dad'e”. ‘sarkin mota yafad'a a ladabce.

      Hannun Galadima dake d'igar jini har yanzu Nuren ya kamo, ya kalli Galadima da alamar tambayar miya damesa? amma shi galadiman sai yamak'i kallonsa, Nuren ya girgiza kai kawai Dan yasan hakan dayayi bazai fad'aba ne, handkerchief d'insa ya Ciro ya d'aure hannun Na Galadima Dan jinin a samu ya tsaya daga zubar, dukya d'an 6ata seat d'in mortar kad'an, da yake a nan ya ajiye hannun daga gefe. ran Nuren a 6ace yace “brother dolene muyi bincike akan Surukinka, dan duk ta yanda zamu fassara a yanzu, zukatanmu bazasu d'aukaba. zamu iya zargin akwaima hannunsa a ciki, zamu iya zargin sunnemi wani Abu daga garesa yak'i basu had'in kai, zamu iya zargin abubuwa da dama”.
    Iska Galadima ya furzar daga bakinsa, yasaka hannu ya tura hularsa baya, kansa ya jingina da kujerar tareda lumshe idanu. zuciyarsa tana tunani yaushene zai kawo k'arshen mak'iyan mahaifinsa? Sai yaushene za'ayi walk'iya yagansu? yana buk'atar sanin dalilinsu Na za6ar maida masa mahaifi haka, miyayi musu?.
    Wannan tambayoyin yakema kansa kullu yaumin ta kowacce rana.
     Hannunsa Nuren yakamo yad'an matsa, Galadima yabud'e idonsa dasuka fara komawa kalar jaa. “brother a wannan karon bana buk'atar 6acin ranka, dan duk sanda ranka ya6aci baka iya Controlling d'in fushinka, fushinka Na saka aikinmu tafiyar wahainiya, lokaci yayi dazaka saba da irin wad'annan abubuwan fa, karinga saka nutsuwa a zuciyarka aduk lokacin da irin haka tafaru, kamarfa yanda takawa (papi) yake fad'a mana ne a kullum, sufa sunayin wad'annan abubuwanne dan kawai su fusata ka, a haukansu zasu iya samun nasara a kankan saboda ciwon da ALLAH ya jarabceka dashi, waynote kaikuma ka karya wannan kwarin guywar tasu OK?”.
     Ajiyar zuciya Galadima ya sauke, shima ya dafa hannun Nuren d'in yana lumshe idanu, a hankali yace “Okey it's better”.
      Daga nan motar ta d'auki shiru, ahaka suka isa asibitin.

     Zuwa lokacin jama'ar gidanmu sun kuma cika asibitin, harsu Munubiya duk sunzo suma.
     Tunda motocin Galadima uku suka shigo asibitin kallo ya koma Kansu, kowa son ganin mai fitowa yakeyi.
    Dogaraine suka fara fitowa, kafin abud'ema su Galadima.
       'Yan gidanmu sun fahimci daga masarautane, amma babu Wanda yay tunanin ganin Galadima d'in.
     Tunda yafito kwarjininsa da cikar haibarsa ta kasancewarsa jinin sarauta ta cika idanun jama'ar wajen, dogarensa sun tsare ko ina babu mai damar ra6arsa, Nuren na gefen hannun damarsa.
     Wayyo, nanfa ido yaymasa caa, baya son kallo ko kad'an, amma yaya zaiyi, tunda jama'a sunga abin kallon.🤦🏻‍♀
      Tunkan ya k'araso su yaa Hameed suka mik'e suka nufoshi. Munubiya kam bayansa kawai take lek'awa, azatonta harda 'Yar uwarta. amma ganin babu alamar mace ma acikinsu sai jikinta yay sanyi.
         Hannu Galadima ya d'agama dogaransa alamar su dakata, baya suka ja, yayinda shikuma yamik'ama yaa Shafi'u daya fara k'arasowa hannu, sun gaisa da yayuna cikin girmama juna, kafin sumasa jagora zuwa ciki inda Abba yake.
      Dayake su Munubiya suna daga gefene, shiyyasa basu gaisa da Galadima ba, sai k'amshin turarensa daya cika hancinansu.
     Dukda halin da ake ciki, saida 'yan gidanmu sukaji Hassada, kowa jitake inama mijin 'yartane🤕🥴.

       Humm doctor daya hana kowa ganin Abba saigashi jikinsa Na rawa ya tarbi Galadima, daddy da baba k'arami sunje gida suyo wanka, bayan dawowar su yaa Naseer sai sukuma suka tafi.
         Doctor yama Galadima jagora har d'akin da Abba yake kwance. “Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un” kawa Galadima ke iya fad'a a la66ansa, maganar gaskiya jikin Abba babu k'yawun gani, yaa Shafi'u ma mai ragguwar zuciya kasa daurewa yayi yafice da sauri yana hawaye, yaa Hameed kam runshe ido yayi zuciyarsa Na suya kamar zata fad'o k'asa.
       Galadima ya dafe bango tareda rik'e kansa dayaji ya sara masa, halin da Abba yake ciki exactly dana Alhaji Abdus'salam Abba.
        Da sauri Nuren yaruk'o hannunsa, a hankali yake fad'in “Control yourself please”.
        Doctor yajawo kujera biyu yabama Galadima da Nuren dansu zauna.
    Ina kasa zaman sukayi, dole suka fito. Galadima yabuk'aci ganin doctor d'in.

        'Yan gidanmu kuwa fitowar yaa Shafi'u yana share hawaye yasaka zukatansu kuma tashi, caa sukayo kansa da tambayar lafiya.
    Kasa magana yayi, ahaka su Dady suka samesu, sukansu jiki a sanyaye suka k'araso wajen, kardai ace d'an uwansu yatafi ya barsune. muryoyinsu har rawa sukeyi wajen tambayar lafiya?.
     Sai alokacin yaa shafi'u yasamu bakin maganar cemusu bafa rasuwa yayiba, jikinnasane sai babu dad'in kallo.
     Baba k'arami yace, “sun bari kun gansane?”.
     “Eh baba, Galadima ne mijin Munaya yazo”.
     Dady da baba k'arami ciki suka shiga, sukabar 'yan gidanmu dake kuka abin gwanin tausayi.

    Doctor bai 6oyema Galadima komaiba, yafad'a masa gaskiya jikin Abban yayi tsanani, dan yaji raunuka Na tashin hankali, ga karaya a jikinsa takai hud'u.
    Galadima ya cije lips d'insa, kafin yace, “ina police d'in  dasuka kawoshi nan?”.
      “ai wlhy yalla6ai basu kwana ba, tun jiya around 11pm suka tafi abinsu, kuma har yau basu dawoba”.
      Amatuk'ar fusace Galadima yace “Why!!?”.
      Doctor yagama rikicewa, jiki Na rawa yace “ban saniba wlhy ranka ya dad'e”.
     Harara Galadima ya watsa masa, yace “saboda kaima bakasan aikinka ba?  wai......”.
      Nuren yay sarin fad'i “Cool down Sameer!”.
      “haba Nuren, kajifa wani zancen banza, saboda jami'an tsaron k'asarnan basu san aikinsuba, su kawo mutum cikin irin wannan mawuyacin halin amma bazasu dakata suji wani issues akansaba su tafi, bazama su iya zama zuwa washe gariba ko za'a iya buk'atarsu”.
        “sorry ranka ya dad'e”. ‘cewar doctor a tsorace’.
         Dady da baba k'arami dake tsaye abakin k'ofa tun d'azun suka k'arasa shigowa, sune suka kwantarma Galadima hankali da nuna masa yayi hak'uri. A girmame ya risina ya gaidasu da tambayar mai jiki.
     Suka amsa masa da Alhmdllh.

       Cikin mintuna 30 Galadima yasa aka canjama Abba d'aki Na musamman, sannan aka kawo police 5 suka zagaye d'akin.
       Hakan yama familyna dad'i sosai, dansu baba k'arami tun a daren jiya sukaga wasu sunata zagaye-zagaye a k'ofar d'akin da Abban ke kwance, ba k'aramin tsoro abin yabasuba, amma basuda mai taimakonsu, sai addu'a dasukai tayi da Neman tsarin ALLAH akan mutanen. Amma gashi yanzu ALLAH ya kawo musu Galadima.
         Galadima yasaka doctor yayi shirye-shirye daduk tattara bayanan Abba.
   
    Da k'yar Nuren ya lalla6a Galadima ya amince aka masa treatment d'in hannunsa shima, sai da Dady yasa baki ma, amma da ya dage akan abarsa shifa baya masa ciwo, saigashi hardasu d'inki akayi masa a wajen.
      Daga nan suka fito daga office d'in doctor d'in, sunason zuwa inda Accident d'in yafarune.
      Harsun kusa fita Galadima yatuna, ya buk'aci abashi wayar Abba idan babu damuwa.
       Baba k'arami yace, “ai bama azo da wayarsa asibitin ba gaskiya, maybe ma tana can inda abun yafarune”.
       Galadima ya jinjina kai kawai suka tafi.
     Su innarmu sunji dad'in abinda Galadima yayi, innaro sai kwararo masa addu'oi takeyi tana kuka.



            ____(((★)))____


        Zuwa yanzu hankalina yakai k'ololuwar tashi, saboda mafarkin Abba na danayi da daddare, abin mamaki a barcin safema dana koma hakance ta faru, nakuma mafarkin Abba yana cikin mawuyacin hali, a firgice na farka jikina sharkaf da zufa, wayata na lalubo nashiga neman wayar Abbana, amma Switch up, nakira Innarmu network yahanata wucewa, hakama Munubiya, hankalina fa ya tashi, haka naitabin Number's d'in 'yan gidanmu ina kira. Amma daga Wanda zaik'i amsamin sai wadda zan kira switch up, saikuma marasa tafiya. kuka nazauna rerawa babu mai lallashina.
      A wannan halin Samha tashigo ta sameni, itama hankalinta tashi yayi, takira Momma a waya ta sanar mata gani inata kuka.
      Babu shiri Momma tabaro jakadiya da aunty Mimi a hospital tanufo gida, dan itama a cikin damuwa take, na rashinjin Galadima. dan bai sanar da ita ina zaijeba, itakuma bata kawo yana Nigeria bane, tunda bai ta6a tafiya bai sanar mataba, tazata tafiyar kota shafi company d'insu ne.
     Ta iso ta iske Samha nata lallashina, jikinta a sanyaye tazo bakin gadon ta zauna, hannuna ta kamo ta jawoni jikinta, batayi maganaba tashiga shafa kaina da bubbuga bayana, munkai kusan 10minutes a haka, harna bar kukan sai ajiyar zuciya kawai.
      A tausashe tace, “kiyi hak'uri kinji Munaya, ni kaina hankalina a tashe yake da rashin kiran, dan baita6a hakaba”. (ALLAH Sarki momma ita ta zata saboda rashin kiran Galadima ne, shima rashin jinsa na damuna kam, amma yanzu na Abba ya danne komai).
     Samha tace, “Momma amma an gwada Number sa ta Nigeria?”.
       “Samha banyi tunanin can yajeba, amma bara na gwada na gani”.
      Wayarta ta d'auka ta kira number Galadima ta Nigeria, a mamakinta kuwa saita shiga, cikeda al'ajabi taciro wayar a kunnenta takuma kallon number d'in, tabbas itace dai da gaske. Harta katse bai d'aukaba, takuma kira a karo na biyu.

    Lokacin Galadima suna mota zasuje inda Accident d'in Abba yafaru. ganin momma saida gabansa ya fad'i, harta tsinke yakasa d'auka, sai da aka kuma kira Nuren ya d'aga yasaka masa a kunne. muryarsa a sanyaye yay sallama, daga can Momma tace, “lallai Muh'd, yanzu nan dan zakaje Nigeria shine ka 6oyemin? kabi ka tada mana hankali muda matarka, maimakon ma ka sauka kakiramu hankalinmu ya kwanta”.
      Runtse idanunsa yayi, muryarsa a sark'e yace, “ki gafarceni Momma, wlhy banason ki hanani zuwanne, nazo kuma na iske wani tashin hankali, shiyyasa ban kirakuba”.
      Mik'ewa Momma tayi tafice daga d'akin, ni da Samha muka bita da kallo, tace “innalillahi.. miya farune Muh'd? ”.
         Zuciyarsa na suya ya zayyane mata komai daya faru, dukta rikice, “kodai wani yafad'ama Munaya Muh'd?”.
       “banajin hakan gaskiya Momma, dan mutanen gidansu basuda Nutsuwar ma sanar da ita, amma miya faru?”.
        “hankalinta gaskiya a tashe yake, dan ina asibiti Samha takirani tana sanarmin Munaya nata kuka, babu shiri nabaro asibitin nazo gida, da k'yar na lallasheta, ni na zatama ko rashin kiran dabaka yi baneba”.
        “to maybe rashin kiran nawane gaskiya. Amma batasan komaiba, Momma kuma banason tasani harsai yafara samun sauk'i kin...........”
      Da sauri Momma ta katseshi “bazai yuwuba Muh'd, dolene anema mata ticket ta taho ko itada Sauban ne, mahaifi yawuce gaban wasa, ko kai baka sanar da itaba dolene wani a cikin 'yan uwanta ya sanar mata, bakuma zata ta6a samun kwanciyar hankaliba, mukuma saita mana wani kallo daban na 6oye matan da mukayi”.
       “to shikenan Momma, Sauban yaje ya bincika ko'akwai jirgin dazaizo Nigeria, saiya nema musu tickets, yanzu muna kan hanyar zuwa inda Accident d'in yafaru, idan na koma gida zan kiraki”.
      “to shikenan saina jika”.

      Momma ta kwantarmin da hankali sosai, sannan takoma asibiti da alk'awarin indai gida nakeso zatasa Sauban ya nema min ticket natafi, amma bata fito ta nunamin ainahin abinda ya faru zanje gidanba.
     Dukda inason tafiya gida sainaji kamar akwai abinda ake 6oyemin, saboda wannan tafiya ta gaggawa, sai dai ban tambaya ba nabarma zuciyata kawai.
    Sauban kuma yashiga mana shirin tafiya.



______________________________


       Tunda Galadima ya ajiye wayar babu Wanda yayi magana a cikinsu, daga Nuren har Galadima kowa damuwar ganin halin da Abba ke ciki tanacin zuciyarsa.
      Su Dady ma suna mota kowa shiru, tausayin d'an uwansu da addu'ar samun lafiyarsa kawai kowa keyi.
      Police d'in dasuka musu jagora inda Accident d'in yafaru ne suka samu hanya da k'yar, dan motar Abba da thriller d'in data hau kan motar Abban sun tsare rabin hanyar, hakanne ya haddasa go slow sosai, Galadima kam yakasa koda motsi, saima tsirama motar idanu da yayi tacikin glass d'in motar zuciyarsa Na matuk'ar suya.
        Saida Nuren ya taimaka masa sannan yafito.
     glasses d'insa yad'auka yasaka, Wanda ya 6oye jajayen idanunsa.
      thriller d'in data hau kan motar Abbanmu Na gefe itama a kife take, duk Wanda yaga motar ta abbanmu zaiyi zaton mai motar bazai rayuba, saboda fita hayyacinta da tayi.
       Jingina da mota kawai Galadima yayi ya hard'e hannayensa a k'irji ya zuba musu idanu.
      Nuren kam yanacan jikin motar sosai tare da police d'in dasu Dady ana laluben wayar Abba acikin motar.
     Harsun fidda rai da samunta ma, da k'yar aka sami wayar, amma tayi rutsu-rutsu, ga jini dukya bushe a jikinta, cikin Leda aka Sanya, Nuren ya kar6a yabama sarkin mota.
    Sund'an k'ara bincikawa kozasu samu wasu muhimman abubuwa, takardune kawai sai abinda ba'a rasaba.
    Nuren ya kalli police d'in yana fad'in “amma kamarma wasu sun d'ebi wasu abubuwa a motarnan?”.
       “zata iya yuwuwa ranka ya dad'e, Kasan mutane da anyi accident maimakon taimako dasuke bayarwa sai wasu su 6ige da sace-sace kuma”.
    Nuren ya jinjina kai kawai, danshi ba mutane yake zargiba.
        Yafi zargin wad'anda sukaso kashe abbanne kawai.
    Dady da baba k'armi da suke gefe kam harda kwallan su, Dan kallon motarma kawai ya ishi bawa shiga tsantsar tashin hankali.
   Sund'an jima a wajen kafin su tafi, Galadima dai yayi d'if, ko magana yakasayi.
   Su baba k'arami asibiti suka wuce, sukuma birnin gayu plaza.
     Tunda suka shigo ma'aikatan wajen suka zube suna kwasar gaisuwa, Nuren ne kawai ke iya amsa musu, galadima kam hannu kawai yake d'agawa. Kai tsaye Office d'insa Na plaza d'in ya shiga, saima yazo k'asar sau nawa bai shiga Office d'inba kwata-kwata.
     Ya zauna tareda zame hular Kansa da glasses d'in, sannan ya jingina kansa da kujera yana mai lumshe idanu.
    Nuren ma zama yayi kawai ya zuba masa ido, kusan minti 2 da zamansu Manager d'in plaza yashigo, gaisuwa yakumayi ga uban gidan nasa cikin girmamawa, Galadima ya d'aga masa hannu batare da ya bud'e idonsa ba. hakan yakuma tabbatarma manager babu lafiya kenan.

      Kirane yashigo a wayar Galadima, yad'an bud'e ido kad'an ya kalli phone d'in, Harun ne, tun d'azun yake faman kiransa amma bai d'agaba, yasan labarin zuwansa k'asar yazo musune.
    Yanzunma bai d'aga ba, ya share, saima kwanciya daya kuma gyarawa a jikin kujerar, da hannu Nuren yayma Manager nuni da yaje.
    Manager ya gyad'a kai sannan yafice yana mamakin miya ta6a yalla6ai hakane?.

     Idon Galadima a rufe yace, “Nuren wane layine akan wayarnan?”.
         Wayar Abba da sarkin mota ya goge fes, duk babu jinin yanzu Nuren ya d'auka ya bud'e, Mtn ne da glo aciki. ya kalli Galadima sannan yace, “glo and mtn ne”.
      Galadima ya bud'e idanunsa akan wayar shima, ya d'an yamutsa fuska sannan yace, “dolene muje office d'insu kenan, dan zanso sanin dawa yake mu'amulla, k'ilama zamu iya samun wani abidance”.
         “o right, hakan yayi, amma waynote mu fara zuwa kaci abinci kasha maganinka, dan bazai yuwu muyita yawo bakaci komaiba, ni gamma ni nayi breakfast a hotel kafin na fito, kaiko nasan bakaci komaiba, gashi har time d'in lunch yayi”.
         “karka damu, banajin wani yunwa ni kam, muje dai muyi salla muje”.. 
       “ina, bazai yuwuba, bara nasa amana oder a wancan restaurant d'in naga suma sun iya abinci”.
    Galadima bai sake cewa komaiba, Nuren ya d'auki waya yakira cikin ma'aikatan plaza d'in, saiga Saleem, dan Nuren yasan Galadima ya yarda da Saleem sosai, bayan ya gaishesu Nuren yabashi kud'in.
      Amma sai Saleem yak'i amsa, ya fita kawai.
    Kusan 30minutes saigashi da yaran restaurant d'in su uku, kowanne d'auke da babban tire, shiya dunga kar6a yana shigarwa office d'in.

     Da k'yar Galadima yad'anci abincin, danma tuwone, yanason tuwo sosai, maganin Nuren ya 6alla yabashi yasha, sannan suka nufi massallaci dan gabatar da sallar azhur.



'*****'*********'*******'*******'

        Sauban ya sama musu tickets d'in tahowa Nigeria, Momma bata bari Munaya ta d'ebo wasu kayaba, tunda tanada kayanta anan, d'an abinda ba'a rasaba kawai ta d'akko, sunje asibiti sukaima Abie sallama sannan khumar yakawosu airport shida Samha da Khaleel dasuka musu rakkiya.
      Sunyi zama nakusan 1hour sannan jirginsu yasamu tasowa......................✍🏼












*_ALLAH ya gafartama mahaifanmu😭🤚🏻✋🏻_*

[10:54PM, 6/18/2019] Abue Saleh Al~Quyraemey: *_Typing📲_*



    *_Haske writer's asso...._*💡



     
     *_♦RAINA KAMA......♦_*
              _{Kaga gayya}_



             *_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻



  ~Book 2~ 👉🏻6⃣


............Har ya fita ya dawo, laptop da wasu takardu ya d'auka a falonsa ya fita, zai zauna a falonta saikuma wata dabara ta fad'o masa, bedroom d'inta ya nufa yana wani ciccijewa (kaida zaka karoro, miye na fuska to yalla6ai?🤔😂).
       Munaya Na tsaye tana ninke hijjab d'in data rama sallolin dasuka risketa a hanya sai kawai shigowarsa tagani da sallama ciki-ciki. k'ok'arin warware hijjabin tafarayi tana masifa ita kad'ai a zuciya, haka kawai aita shigoma mutum d'aki babu izini, wannan wane irin rayuwane.
    Shikam Galadima kallo d'aya yamata ya d'auke kansa, Dan daga ita sai zani d'aurin k'irji. Laptop d'in hannunsa da takardu ya ajiye a bakin gadon, sannan shima ya zauna, batare da ya kuma kalllon Munaya ba yace, “kinajin yunwa ne?”.
        Ba yunwar takeji ba, amma dan Neman magana kawai tace “eh”.
    Kallonta ya sakeyi, bata yarda sun had'a idoba, yace “Saidai kisha fresh milk kuwa, dan bani da abinci”.
     Manyan idanunta ta waro masa waje, kamar wadda akace tasha wuta, cikin dafe k'irji tace “yalla6ai fresh milk?”.
     Da mamaki ya kalleta, danshi bai fahimci ma'anar razanar tataba, yace, “uhmmm”....
       “Na yafe wlhy”.
Tafad'a da saurinta.
     “To mine nawani birkicewa haka? fresh milk d'in wani abune dashi?”.
      “Humm”. Munaya tafad'a tana ta6e baki, tace “yalla6ai nikam idan kaga nasha fresh milk d'in data fito daga d'akinka saidai idan bana a hayyacina”.
     Da tsantsar mamakin furucinta yake kallonta, da yake basuda nisa saiya mik'a hannu ya rik'o nata, zatayi magana ya fizgota ta zauna kusadashi, kad'an ya rage ta hau masa laptop, amma yay saurin janyewa da d'ayan hannunsa.
     “wash hannuna”. Munaya tafad'a tana matse baki.
        Banza yamata, yakuma matsa hannun da mugunta. tasaki k'aramar k'ara tana fad'awa gefen kafad'arsa.
       Ya d'an kalleta ya janye yana ta6e baki “ban fahimci zancenki daga nesa ba, maimaitamin”.. 
         Cikin tunzuro masa baki tace, “yoni babu abinda nake nufi fa, nidai bazan sha fresh milk d'in data fito daga d'akinka ba wlhy. haka kawai aje asakama mutum abinda zai halakashi”. ‘k'asa-k'asa ta k'arasa maganar, amma yajita sarai’.
       Shifa saima yanzu yagane inda zancenta ya nufa, wani miskilin murmushi yasaki yana danne dariyarsa datake shirin kufcewa, amma dukda haka saida taji sautin fitar murmushin nasa.
     Munaya dake satar kallonsa idonta harya cika da kwalla, a zuciyarta tace mugu d'an masa, dole fa kamin dariya.
      Saida yayi dariyarsa a zuciya ya gama ya kalleta, itakuma saiwani mar-mar takeyi da idanu wai zatayi kuka.
     Murmushi ya kumayi, sannan yace, “wannan bakin dakike tunzuromin ko, hummm.....”. ‘yak'are maganar da cije lips nashi’.
       Yunk'urawa tayi zata mik'e, tace, “yalla6ai ni wlhy barci nakeji fa”.
       Dawo da ita yayi ta fad'o jikinsa shima yana fad'in “nikuma gadinki zanyi ko? yalla6iya!”.
         Tace “wayyo innarmu kice ya fitarmin a d'aki please”.
        “ko waya zan baki ki kiratane”. ‘yay maganar cikin d'age gira d'aya’.
      Munaya tai saurin janye idanunta daga Kansa ga k'amshin turarensa ya gallabeta, barci takeji, amma takula mugunnan soyake ya hanata ma.
     Kamar zatayi kuka tace, “yalla6ai wai mikazo nemane please? Wlhy barci na keson yi?”.
        Shiru yamata, saida ya mula dan kansa sannan yace “jikina fa”. ‘yay maganar yana kallon k'ugunta’.
      Da sauri Munaya ta sauka daga jikinsa tana k'unk'uni da tura baki.
     Medical glasses d'insa ya d'auka ya saka, tareda cigaba da aikinsa a laptop, a zuciyarsa yana fad'in yarinyarnan akwai ruwan tsiwa, amma duk randa Na kama bakin tsiwarcan sai yamin bayani dalla-dalla kuwa.

    Ganin ya shareni ya cigaba da sabgarsa a System, nima sai ban kuma bi ta kansa ba Na d'auki kayan barcina nashiga bayi domin Na sanya. Sai dai zuciyata cike take da fargabar miya kawoshi d'akina?. haka na fito kamar wata munafuka ina lallak'ewa jikin bango.
      Duk yana kallona ta gefen idanu, amma yay kamar baima San dani a d'akinba.
         Sai zuwa can ya d'ago yana kallona, yana wasa da pen d'in hannunsa kan la66ansa, “idan bak'yajin barci zokimin wani d'an aiki nan”.
      Saida gabana ya fad'i, a raina nace aikin mi kuma?, a fili saina aro jarumta na yafama kaina, Dan nakula tsoron daya fara gani a idona ne yake neman fara rainani da samin fargaba (🤣ho munayan shagali).
     Takowa nayi inda yake, ina niyar zama bakin gadon sai ya nunamin tsakiyar gadon, shima laptop d'in ya tura sosai kan gadon ya haye tsakkiya yana gyara zamansa. kuma had'e fuska nayi ina wani dojewa na hau nima na zauna, cigaba yayi da danna laptop d'in, kusan mintuna 3 ya jehomin tambaya.
    “shin kinsan minene aikin Abba?”.
       Da mamaki na kallesa, nace “wai Abbana kake magana?”.
     “uhmm”. ‘yafad'a batare da ya d'agoba’.
      Shiru nayi alamar tunani, harya d'ago ya kalleni bance komaiba, maida kansa yayi ga laptop d'in yacigaba da aikinsa, zuwa can nace, “ma'aikacin gwamnati ne kawai tawani fanin kuma aikinsa yanada Nasaba da jarida”.
     Tunda nafara magana ya tsuramin idanu, bakina kawai yake kallo yana taune lips nashi, saida nakai aya sannan yace, “jarida?”.
    Nace, “eh, wani abune ya faru?”.
     Kansa ya girgizamin, “innalillahi” yashiga maimaitawa a zuciyarsa, baya fatan zarginsa yazama gaskiya, cikin dakiya yakuma cemin “kokin san abokansa? ina nufin cikin manyan mutane haka?”.
       “eh to, akwai senator halluru garba, sai kuma wani anacemasa Alhaji Mamman k'afur, last year yafito takarar shugaban k'asa......”
    Caraf ya kama hannuna, “kina nufin Alhaji Mamman k'afur abokin Abban kune?”.
     Ni tsoroma yabani, yanda yay maganar cikin rawar jiki, na jinjina masa kaina a hankali.
     Gani nai ya taune lips nashi da masifar k'arfi, ya kaima iska naushi. da sauri na matsa baya Dan karya nausheni, ganin kamar na tsorata sai yay murmushi, cikin k'asaitacciyar muryar nan tasa yace “my Friend! Yanzu ne zamu fara aiki tare da gaske ni da ke”.
       “kamar ya yalla6ai? wane irin aiki kuma?”.
      Murmushin takaici yayi, ya kalleni ido cikin ido, kasa jurewa nayi nai k'asa da nawa. shima lumshe nasa yayi yana fad'in “zaki gani”. daga haka ya janye laptop d'in gefe ya zame ya kwanta.
    Binsa nayi da kallo tamkar wata sokuwa, gaba d'aya ya kulle magudanar tunanina da wadda ke kaima kwakwalwata sakonni.
      Medical glasses d'in idonsa ya cire ya ajiye, sai kuma ya juyo gareni, hannunsa d'aya ya mik'amin yanamin alamar nazo gareshi.
    Idanu na d'an zaro, sai kuma na nok'e kafad'a alamar nak'i din.
     Wani murmushin da bako yaushe yakeyinsaba ya sakarmin, ya juyamin baya yay kwanciyarsa. bai sake juyowa gareniba har kusan 6minutes. nagaji da kallonsa da nazarin murmushinsa da tambayoyinsa na janye idanuna, waishi guy d'innan mike damunsa ne? gaba d'aya ya canjamin daga saukarmu zuwa yanzun, dubana nakai ga agogon d'akin. 3:27am, “ya salam” na fad'a a hankali, muna Neman kwana a zaune. can k'arshen gadon na koma na kwanta, zuciyata cike da tsoron ALLAH yasa bawani Abu ya shiryaminba, babu dad'ewa barci 6arawo ya saceni.

    Numfashina dake sauka a hankali yasaka Galadima gane nayi barci, juyowa yay yana kallona, yayinda zuciyarsa keta cud'a amsoshin dana basa yanzun, tabbas mahaifin yarinyarnan akwai abinda yasani, kwarai da gaske zaiyi amfani da ita wajen gano ko wanene mahaifinta?, minene alak'arsa da case d'ina?, sannan minene alak'ar Muftahu da ita?, Dan tabbas akwai manufar sako yarinyar acikin wannan tak'addamar, kuma Muftahu dashi aka shirya komai. yasaki wani murmushin mugunta tareda nuna kansa, a fili yace _MAK'IYAN MAHAIFINA SAINA ZAME MUKU_ *RAINA KAMA  KAGA GAYYA* tabbas lokaci yayi dazakuga wannan *Gayyar*.



Tofa masu karatu, ana zaton wuta a mak'era🤔, mikuna yasako Abban munaya a rikicin masarauta? Kodai ba masarautar kawai bace  keda alhakin ciwon tsohon Sarki Saifudden Abubakar🤔?, shin tsakanin Galadima da Munaya & munubiya, innarsu Munaya. Wanene RAINA KAMA...... d'in🤗?.

      Kumuje zuwa kudai my Guy's😁, duk nisan jifa👆🏻, k'asa zai fad'o👇🏻🤗


★___________________________★


     Bayan shigewar su Galadima Muftahu ya fito daga mota shima yana murmushin dashi kad'aine yasan fassararsa, jiyay kawai handkerchief ya rufe masa fuska, yay saurin cirewa yana waige-waige dan dunba wanene ya jeho masa, wayam babu alamar mutum a wajen, bai gama dube-duben ba yay luuu zai fad'i, saigashi a hannun mutum, idanunsa sunriga sunyi nauyi, dishi-dishi yake kallon Wanda ya tareshi d'in, dama gashi ya rufe rabin fuskarsa ba'a gani, wasu samarine su biyu sukazo suka kama Muftahu tareda wancan suka danna a mota, tun yanajinsu sama-sama har idonsa da jinsa suka rufe baki d'aya.


    🙆🏻tofa suwaye?.


★__________★_________★


          Tun kusan around 8pm Nuren yake k'ofar wajen, a dukkan bayanan daya samu daga majiya mai k'arfi yarinyar Minister ta shigo gari yau, kuma zatazo shan ice-cream wajen, wayarsa ya d'auka yay wasu 'yan danne-danne, murmushi yayi ya maida wayar ya ajiye tareda dasama k'ofar wajen idanu, dolene kafin tashiga ciki zai saceta, dan bincikrnsa ya nuna masa cctv camera d'aya ce a cikin wajen kawai, a waje babu, dan haka bama ya buk'atar ta Shiga, murmushi yayi saboda ganin motar da driver d'inta yamasa kwatancen zasuzo aciki, saida driver n yaga motar Nuren sannan yazo kusada ita yay parking, bud'e murfin gefen mai zaman banza Nuren yayi, hakan kuma yay dai-dai da fitowar zankad'ed'iyar budurwa daga motar datai parking kusada ta Nuren d'in, murfin ne ya daki gefen hannunta kad'an.
     A fusace ta kalli motar Nuren, shikuma yay mata murmushi, wani haushine ya kamata, banda rainin wayo ya bigeta amma yamata murmushi saboda wulak'anci, yau saitaga wanene ubansa a garinnan?. da k'arfi tabuga saman motar tana lek'a kanta ciki, “kai wawa bakaga abinda kayi bane?”.
     Maimakon ya bata amsa saiya jefa mata handkerchief d'insa saman fuskarta, janyewa tayi da sauri zatayi magana kanta ya sara mata, da lalube ta dafa kujerar motar ta shiga ta zauna, sai faman lumshe idanu takeyi. murmushi Nuren yayi, ya taimaka mata ta ida shigowa Sannan ya rufe motar, komai akan idon driver n ta ya faru, bashida damar hanawa, dan Nuren yasashi a tsaka mai wuyane. Agaban idonsa Nuren yaja motarsa yabar wajen yana murmushin samun nasarar tafiyar plan d'insa yanda ya tsara. a wannan daren yanufi gidan Galadima dake can bayan gari inda aka ta6a kai Munaya.


    😱humm yau 'yar kidnapping akeyi kawai😂🤪.


------------(((★)))--------------



         Galadima yariga Munaya farkawa, dama bawani isashshen barci yayiba, tunani da damuwa suka taru suka hana idonsa rintsawa sai gabannin Asuba. Ana kiran sallar farko kuma yana farkawa, tashi yay zaune dafe da kansa, kusan mintuna biyu ya juya yana kallon munaya data juyo tana fuskantar inda yake yanzun, da gani kasan barcin bamai dad'i takeyiba, dan sai yamutse fuska takeyi a cikin barci. matsawa yayi kad'an ya d'ora yatsunsa biyu gefen fuskarta, sai yaji zafi jikinta, ya janye yana mamakin wai mike damun yarinyar nan kwana biyu haka? dolene yau yasata taga doctor idan sunje ganin Abba. gabansa yad'an fad'i daya tuna har yanzu itafa batasan komai ba, shi baima San ta yadda zai sanar mata abbanta yana cikin mawuyacin hali ba, ya dafe kansa yana ambatar sunayen ALLAH kozaiji sassauci a ransa. Da k'yar ya samu ya mik'e domin yin rakata ainul'fijir kafin akira assalatu.

      Bayan ya idar ya tadani, da k'yar na iya tashi dafe da kai, dan barcin bai isheniba, muryarsa da alamun shima rashin isashshen barcin yace, “time d'in salla yayi”.
     Idona dake bud'ewa da lumshewa Na kad'a masa alamar amsawa, yay saurin janye nasa saboda wata fad'uwar gaba da tsirgawar wani Abu dayaji lokaci guda tun daga Kansa zuwa yatsan k'afarsa, bai sake magana ba yafice. nikuma nakoma Na sake kwanciyata.

     'Dakinsa ya shiga ya tada Sauban dansu tafi massalaci.
       Babu dad'ewa Sauban ya kammala alwala yafito ya iskeshi a falo yana jiransa, harara ya antayama Sauban, shikuma ya kauda kai gefe yana had'iye dariya (yo daga  taimako saiya zama laifi?).

        Sarki yayi mamakin ganin Sauban, dan yaron bawani zuwa k'asar yakeba saida dalili mai k'arfi, bayan yagama k'ar6ar gaisuwa wajen jama'arsa Galadima da Sauban sukabishi zuwa sashensa.
      Kasa 6oye mamakinsa yayi, ya kamo hannun Sauban d'in dake d'ayan 6arinsa zaune kamar yanda Galadima yake, “yarona ne yau ak'asarsa ba biki ba ba bikin salla ba?”.
        Dariya Sauban yayi, yace “Abba nazo gaidakune kawai”.
    Sarki ya Murmusa yana kallon Galadima, “Galadima kodai akwai abinda ke faruwane kuke 6oyemin?”.
       Galadima ya d'ago kansa cikin damuwa yace “babu abinda muke 6oyewa ranka ya dad'e. Mahaifin Munaaya ne yay Accident shine suka taho da Sauban d'in”.
         “mu bamuda muhimmancin da zamu Sani kenan ko?”.
       “ALLAH ya huci zuciyarka ba haka nake nufiba, bayan barina wajenka jiya nima aka sanarmin, lokacin dana shigo kuma dare yayi”.
       Ajiyar zuciya mai martaba ya sauke, yace “ALLAH yabashi lafiya, zuwa anjima sai su waziri suje dubashi ai, tana ina ne ita d'iyar tawa?”.
       “tana nan cikin masarauta”.
    Jin jina kai kawai Sarki yay bai kuma cewa komaiba, sai zuwa can yacigaba dayima Sauban tanbaya akan jikin Abie, shikuma yana bashi amsa. Galadima dai Na jinsu bai saka bakiba.


*************

        Saida gari yafara haske ALLAH yabani ikon tashi, dan zazza6in kuma ya sauka, yanzu kuma haka yakemin, da dare yayi zan fara zazza6i, lokacin da gari zai waye saikiji ya sauka. Sai dai ciwon jiki.
    Saida nayi wanka da ruwa mai zafi sannan nayo alwala, sallar asubahi data kwacemin nayi, Na jawo handbag d'ina danazo da ita Na d'akko wayata, sim card d'ina Na 9ja Na d'akko shima Na saka akan wayar, massage suka turomin Na adadin awannin da suka bani sim card d'in zai d'auka kafin ya cigaba da aiki. ganin haka saina ajiye wayar natashi domin gyara d'akin, ina cikin kakka6e gado idona yakai bisa wayar Galadima. dad'ine ya kamani, koba komai nakira wani d'an gidanmu Na sanar dasu nazo 9ja.
       Wayar Na d'auka Na saka number Abbana, dan yanzu nafi kwad'aituwa dajin muryarsa fiye da kowa, kodan mafarkai marasa dad'i danakeyi a kansa, Mtn d'insa nafara kira amma a kashe, saina kira glo d'in, shima switch up, ban kawo komai a rainaba na maida kiran kan innarmu, bugu biyu aka d'aga, wani dad'ine ya kamani, cikeda d'oki nace “innarmu I miss you”.
      Aiyaan daya d'aga wayar yay dariya, aunty ba inna baceba. Nine, Nima Na iya waya yanzun”.
    Dukda naji dad'in jin muryar d'an uwana, hakan bai hana zuciyata shiga fargaba ba, nace “Aiyaan Kaine? ina innarmu d'in?”.
       “Tana wanka ne zamuje asibiti wajen Abba”.
    Da sauri Na dafe k'irji, nace “Asibiti kuma? miya sami Abban?”.
        “Lah Aunty baki saniba? Ai accident yayi fa, kuma innarmu nata kuka, hakama innaro dasu daddy”.
       “Aiyaan!!...” nafad'a da k'arfi, kafin nace wani Abu naji an rik'emin hannu ta bayana an zare wayar daga kunnena.
        Kuma rikicewa nayi, Na juyo da hanzari, cikin kuka naketa fad'in “abbana! Abba da gaske Aiyaan yake yi? Yalla6ai da gaske Abbana yayi accident?”.
       Wani tausayina yaji ya tsargashi, ya dafa kafad'una, cikin sigar lallashi yace “cool down mana my friend”.
      “to ka fad'amin da gaskene Abbana yayi accident d'in?”.
     Rasa mizaice min yayi, sai bin fusakata da idanu yakeyi, ya cije lips nashi yana fad'in “inhar kinason na kaiki ki gansa toki nutsu”.
     Share hawayena nayi da sauri nace, “to na nutsu muje”.
      Yaja hancina, a hankali ya furta, “good girl”. Sai ya juya kuma ya fita.
     Binsa nayi da kallo hawaye na zuba a kumatuna, kenan da gaske Aiyaan yakeyi Abba yayi Accident d'in, “hasbinallahu wa'ni'imal wakil”. Na dafe kaina tareda zama a bakin gadon nacigaba da raira kukana.

    Shikam yana fita ya dunk'ule hannunsa yana cije lips, yama akayi yabar wayarsa harta d'auka tayi kira dashi, ko kad'an baiso hakaba. Baiso tajiba kai tsaye.

      Saida naci kukana na gode ALLAH sannan natashi na hau shiryawa, atamfa na saka zani da riga, bawata kwalliya nayi ba, na shafa fauda kawai da lips gloss, turarema kad'an na shafa. ina cikin Neman mayafi ya shigo, kamshin turarensa yasani juyowa na kallesa, sanye yake cikin oxblood d'in shadda, hularsa takalmi agogo duk black, link d'in hannun rigarsa yake sakawa, sai alk'yabba pink da ratsin milk a hannunsa.
    d'auke kaina nayi naci gaba da neman gyalena a cikin kayan lefena.
    Baimin magana ba ya tako har inda nake, hannu yasaka a kafad'una ya d'agoni, fuskarsa babu walwala ko kad'an, idonsa akan fuskata, kusancin damukai da juna sosai yasaka numfashinsa ke sauka akan fuskar tawa, janye idona nayi na maida kan design d'in gaban rigarsa, yayinda shikuma ya warware alk'yabbar hannunsa mai k'yau ya sakamin, d'agowa nai muka k'ara had'a idanu, ya jinjina min kansa kawai.
     Jinai tamkar in fasa ihu, banason saka alk'yabba d'in nan nidai, dan nauyi sukemin, garama wannan batada nauyi gaskiya, dan tamkar riga After dress take, saidai suffar alk'yabba aka mata, kuma tanada kaurin dabaza'a ga jikin mutumba.
    Hannunsa yakuma d'orawa akan kafad'una ya d'ago hular alk'yabbar dake kwance a baya ya sakamin, ni kaina koba'a fad'aba nasan nayi k'yau, yanzunma baice uffanba ya juya ya fita yana nunamin agogon hannunsa alamar time yana tafiya.
        Handbag d'ita na d'auka da wayata nabi bayansa, dauriya kawai nakeyi na hana kuka tasirin zubowa.
      A falo na iskeshi shida Sauban dake zaune a kujera shima cikin manyan kaya, dayake ba sakawa yakeba sainaga ya canjamin, ya kalleni cikin halinsa na tsokana yana fad'in “kaga sarauniya gagara badau ta gobe, takawarki lafiya 6auna mai tafiyar k'asaita.......”.
     Harar da Galadima ya zuba masa ce ta sakashi gimtse bakinsa yana had'iye dariya.
    Nidai banma tankaba, dan yau zuciyata babu dad'i.
     Galadima ne yay gaba mukabi bayansa, tunda muka fito hadimansa suke zubewa gaishemu, Sauban kawai ke amsa musu, shikam Galadima saidai d'aga hannu, Niko ko kallonsuma banayi. Hakan yasa suka fahimci har yanzu akwai matsala kenan, dansu bama Susan munzo nida Sauban ba.
   
      Muna k'ok'arin shiga mota Harun ya iso wajen, gaidashi Sauban yayi, nima na gaidashi, ganin ni da Galadima kowa fuska a tamke sai abin yabashi mamaki, hannun Galadima ya kama suka koma gefe.
    Nikuma da Sauban muka shiga mota.

    “Sameer babu fad'a miya kawo gaba?”.
       Murmushi Galadima yayi, ya cije lips nashi kad'an yana kallon Harun, “bazaka ganeba Harun, na iske abinda ya dagula lissafinane kawai, naga kiranka jiya, amma ina cikin rud'ani a time d'in shiyyasa ban d'agaba”.
     “rud'ani? mike faruwa ne?”.
     “mahaifin munaya ne yay Accident, a time d'in ina hospital wajensa”.
     “ya salam, ya jikin nasa to?”.
    “Alhmdllh, zamuje canne bayan mun gaida jama'ar gidan”.
         “ok bara na k'arasa abinda zanyi kafin Ku fito saimuje”.
     Kai kawai Galadima ya jinjina masa.

      Bud'e masa gefena akayi ya shigo, yad'an kalleni, kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru.
      Sashen mama Fulani muka fara Isa, amma sai aka sanar mana tasha maganin mura ta kwanta, daga nan muka nufi sashen matan Sarki, inda yafi ko ina k'awa da ado a gidan kenan.
      Mun sami tarba ta musamman ga Uwar gidansa, nidai matarnan tana k'aunata na lura, kuma tafi sakarma Galadima fiye da kowa a Matan sarki, tanada kirki sosai, haka taita jan Sauban a jikinta, nakula suma sunfi sakewa da ita.
      Sosai ta nuna damuwarta akan Accident d'in mahaifina da Galadima ya sanar mata, taita jinjina maganar tana lallashina da jerama Abba addu'ar tashi cikin k'oshin lafiya.
        Tasa aka kawo mana break fast wai saimun karya anan, Sauban ne kawai yaci, amma Galadima cewa yay ya k'oshi, nima nace bazan iya ciba. dan burina kawai naga mahaifina, gaisuwarma duk akan k'aya nake.
     Shima Sauban d'in bai wani ci abun kirkiba yace ya k'oshi, mun fito muka shiga sauran sassan, amma ba ko inaba.


    Sauban da harun sun tafi a mota d'aya, nikuma ni da Galadima. Sai motar dogaran Galadima guda biyu, sai kuma kuyangi hud'u da Uwargidan sarki gimbiya Zulfah tahad'oni dasu, wai kafin mu dawo nima a turamin bayina da zasu ke kula dani, ni dai da to kawai na amsa, Galadima kam baima ce uffanba.
     Babu mai magana a cikinmu daga ni harshi, sai saukar ajiyar zuciyata da share kwalla time to time danakeyi.



............................................


         Innarmu na fitowa daga bayi Aiyaan ya sanar mata na kira, da mamaki tace masa kodai Munubiya ce?”.
      “wlhy Innarmu aunty Munaya ce, kuma batasan Abba bashida lafiya ba”.
     “ka sanar mata ne?”. tafad'a a rikice.
     “eh innarmu na sanar mata, kumafa naji tana kuka”.
      “innalillahi Aiyaan wayace ka sanar mata? da wace Number ta kira?”. Tayi maganar tamkar zata make Aiyaan.
    Runtse idanu yayi yana k'ank'ame jiki saboda tsoro. innarmu dukta rikice, tasan su Munaya da shiga Rud'ani akan Abu, yanzu haka tana cikin damuwar Munubiya itama, dan jikinta yakuma janga6ewa, ga laulayi ga wannan damuwar Abban.
    K'ok'arin kiran Number tashigayi danta kwantarmin da hankaki amma sai tak'i shiga.
    Har suka gama shirin asibiti wayar bata shigaba.
    Koda suna mota taita gwadawa.
     
    A asibitin suka had'u da mama Rabi'a suma sunje, ganin innarmu a cikin damuwa yasata k'ok'arin fara kwantarma 'Yar uwarta da hankali.
     Innarmu ta sanar mata kato6arar da Aiyaan yayi.
      “to Yaya ko su Munaya sunzo k'asarne?”.
     Anya kuwa Rabi'a, naga jiya mijinta na nan amma baiyi maganar zata zoba”.
      “ito da wannan dan wanann, amma ai bama fidda raiba”.
     “hakane”. cewar innarmu.

       Babu dad'ewa da zuwansu saiga gwaggon Haleematu da matan k'annen ta sunzo duba Abba, (dayake har yau bata dawoba ita). k'in gaisawa tayi da innarmu da mamansu yaa hameed, innarmu bata damuba, amma mamansu yaa hameed saida taja tsuka, babu dai Wanda ya tanka. Sukuma suka shiga suka ga Abban, dayake yau ana barin na jikinsa zuwa su duba shi.
      Koda suka fito harda kuka takeyi, matan k'aninta suka tafi amma ita saita zauna, kaf 'yan gidanmu babu Wanda yace mata danmi, kowama tasa ta isheshi aransa.


★★★★★

      Tunda motocinmj suka shigo harabar asibitin sai kallo ya koma sama, 'yan gidanmu dakeda yak'in Galadima ne kowa tsumayen fitowarsa yakeyi, sauran jama'a kuma da 'yan dubiya son ganin wad'anda zasu fito sukeyi.
     Sai da aka bud'e mana sannan muka fito, suma su Harun duk sun fito.
      Su yaa Hameed suka taho garemu sunama Galadima sannu da zuwa, cikeda kulawa yake amsa musu.
    Kowannensu  fuskarsa ta nuna farin cikin ganina, yayinda nikuma naketa faman zirar da hawaye.
     Cikin d'okin ganina Fauziyya tazo ta kama hannuna itada Safara'u, saina rungumesu na fashe da kuka, kukana ya karyar musu da zuciya suma suka fara, sauran 'yan uwanama duk suka taso gareni, dama duk sun zo, ni kad'aice wadda nake nesa.
      Saida baba k'arami yamana magana sannan suka sakeni, na matsa ina sharar kwalla na gaida iyayena, Munubiya ce kawai ban ganiba, ina share hawaye na tambayi tana ina?.
       Aunty khalisat tace “sunje ganin doctor itada yaa marwan, dan batajin dad'i itama”.
     Kaina kawai na jinjina, na k'arasa gabansu innarmu na durk'usa ina gaishesu, duk sun amsamin cikeda kulawa, da tambayata ya hanya?, nace “Alhmdllh”.
        Matan gidanmu kowacce kallona take da mamakin canjawata a cikin wata 1 kacal. Na katse musu tunani da tambayar d'akin da Abba yake.
        Aunty Ramlah ce taja hannuna muka shiga corridor d'in dazai sadamu da d'akin da Galadima yasa aka canjama Abba.
     A ciki na iske Galadima da Harun da Sauban, sai doctor da yaa Shafi'u yaa Hameed.
    Takun takalmanmu yasakasu juyowa suka kallemu, na zare hannuna daga na aunty ramlah ina toshe baki saboda kukan dake Neman kufcenin, taka wa nayi gaban gadon da Abba yake, na durk'ushe ina sakin kuka mai tsuma rai da zuciyar mai saurarona, tare da kife kaina jikin gadon.
       Kukana babu zuciyar Wanda bai karya ba, Galadima ya tako a hankali inda nake, hannayensa biyu ya saka ya kamoni na mik'e tsaye, fad'awa nayi saman k'irjinsa na kuma sakin wani sabon kukan.
     Bashida za6in daya wuce kar6ata, dan haka shima saiya saka hannayensa ya zagaye bayana dasu, ya d'ora ha6arsa saman kaina yana lumshe idanu da cije lips. kad'an-kad'an yake buga bayana alamar lallashi.
      d'ai-d'ai su yaa Hameed suka zare jikinsu suka fice daga d'akin, aka barmu mu kad'ai sai Aunty Ramlah da muka birgeta, itama ganin sun fita saita fice taja mana k'ofar.

      Munkai tsawon lokaci ahaka, saida na tsagaita da kukan sannan Galadima ya d'ago kaina daga jikinsa, hannunsa yasa yana gogemin hawayen fuskata, amma ya gaza cewa komai. sai girgiza min kai kawai yakeyi.
      Ajiyar zuciya kawai nake saukewa a jere, da hannu ya nunamin hanyar fita.
     Banyi musuba nabud'e k'ofar muka fito, ina gaba yana bina a baya. tafiya nake a hankali saboda juwar dake Neman fara hajijiya dani, burina kawai nakai inda 'yan gidanmu suke zaune akan kujeru nima na samu na zauna.
      Muna gab da k'arasawa wajen na dafe kaina, sai nayi baya luuuuuu.
       Da sauri Galadima dake bayanta ya tareta ta fad'o jikinsa, gaba d'aya 'yan gidanmu da mutanen wajen suka mik'e tsaye cikin ambaton sunan ALLAH.
       sosai Galadima ya tallafota jikinsa, yayinda wasu Nurses biyu suka iso da gudu domin kar6ar Munayar.
     Amma saiya hanasu yana daka musu tsawa da ambatar su kira Doctor.
     Basu ba kowama a wajen saida tsawarsa ta rikitashi....................✍🏼



     *_Comments d'inku shike k'aramin k'arfin guywar rububutun nan wlhy, amma da tuni na ajiye saina samu lafiya🤦🏻‍♀, amma yanda kuke k'ok'arin Comments sai bana iya barinku banyiba😃, ina godiya kwarai da gaske, I love you all🥰🥰🥰🥰🥰🤝🏻👍🏻❤_*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[10:55PM, 6/18/2019] Abue Saleh Al~Quyraemey: *_Typing📲_*



    *_Haske writer's asso...._*💡



     
     *_♦RAINA KAMA......♦_*
              _{Kaga gayya}_



             *_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻



  ~Book 2~ 👉🏻7⃣


................Gaba d'aya ya rikice ya rikita Nurses d'in da jama'ar wajen, cak ya d'auki Munaya, gadonma da aka kawo masa domin d'orata ko kallonsa bai yiba. Wani d'aki suka nuna masa ya shiga da ita.
        Da sassarfa doctor dazai duba munayar ya iso, dan dogaran Galadima tasoshi gaba sukaje sukayo.
      Kai tsaye Galadima yace baya buk'atar namiji mace yakeso ta duba masa matarsa.
     Hak'uri doctor d'in ya bashi,  sannan yakira wata likita mace mai suna doctor Farida.
    Isowarta yasaka Galadima da yay bake-bake a k'ofar bata hanya ta shiga.
    Duk yanda taso yabata waje tayi aikinta yak'i, gashi duk yabi yagama rikitata da tsawarsa.
      Doctor d'in da Galadima ya hana ya duba Munaya ne ya matsa kusada su harun yana fad'in “dan ALLAH sir Ku lalla6a yalla6ai ya fito danta samu damar aikinta, wlhy dukya rikitata”.
      Murmushi Nuren da isowarsa kenan asibitin aka masa bayani shima yayi, suma su harun duk murmushi sukayi.
    Nuren ya kalli baba k'arami yana murmushi, “Abbanmu inharfa bakai kamasa magana ba bawai zai fito baneba”.
       Shikansa baba k'arami murmushin yakeyi, koba komai hankalinsu Yakuma kwanciya da zaman 'yarsu inda suke tunanin anfi k'arfinta.
      Bayan doctor yabi zuwa d'akin, Galadima dake zaune, kan Munaya na bisa cinyarsa sai murza tafin hannunta yakeyi wai kozata farfad'o, yayinda doctor Farida ke k'ok'arin lik'a mata oxygen ita kuma”.
       Shima baba k'arami da k'yar ya lalla6ashi ya fito.

     Tsawon lokaci doctor Farida tana ciki bata fitoba. Galadima dukya damu, danma ankawo masa kujera ya zauna, amma sai jan tsuka yakeyi time to time.
     Hankalin 'yan gidansu Munaya ma duk a tashe yake, jiran fitowar doctor Farida kawai akeyi dan aji mike damun munayar.
    Innarsu Munaya kam gefe ta koma tana sharar kwalla, itakam batasan yazata misalta wannan tsakaniba, miji da 'ya'ya duk babu lafiya, Munubiya ma fa sunacan ana k'ara mata ruwa.
      Fitowar doctor Farida yasaka kowa mik'ewa anason jin bayani, Galadima dai yana daga zaune ya zuba mata idanu shima. Doctor Farida tace su kwantar da hankalinsu ta farfad'o, amma tamata allurar barci, yanzu tanason ayo gwajin jinin Munayar data d'iba.
     Galadima ya lumshe ido yana ambatar “Alhmdllh” akan la66ansa.
         Sauban ne ya kar6a suka tafi shida Sarkin mota lab d'in.
      Dr Farida ta kalli Galadima tana murmushi, “ranka ya dad'e zaka iya Shiga ka ganta yanzun”.
        Nuren ya kalli Galadima ya jinjina masa kai alamar yaje.
    Saida yaja wasu seconds sannan yamik'e cikin takun nan nasa na k'asaita da izza, duk idon jama'ar wajen akansa yake, yana birge kowa.
      d'akin ya tura ya shiga, ya taka har gaban gadon da Munaya ke kwance, idanu ya tsura mata, tayi wani fayau da ita, ya jawo kujerar dake wajan ya zauna, har yanzu idonsa na kanta, cikin cije lips da lumshe idanu ya d'ora hannunsa bisa sumar kanta da d'ankwalinta ya zame ta fito, saikuma yasaka d'ayan hannunsa ya shafi kumatunta, a kan la66ansa ya furta “sorry my friend, ALLAH yana tare da masu hak'uri kinji”.
     Daga haka bai sake cewa komaiba,  ya janye hannunsa daga kanta ya mik'e ya fito.
     A k'ofar d'akin ya iske Doctor Farida tsaye, kallonta yayi cikin maganarnar tasa mai kama da an masa tilas yace “zata iya kaiwa wane lokaci bata farkaba?”.
       “Ranka ya dad'e inaga daganan zuwa kamar awa d'aya”.
     Kansa ya jinjina mata, bai sake magana ba yanufi d'akin da Abba ke kwance. ya Tatar da doctor d'in dake kula da Abban a d'akin.
    Da sauri doctor yabashi kujera ya zauna, k'afa d'aya kan d'aya ya d'ora ya Ciro waya a aljihu yana danne-danne. batare da ya kalli doctor ba yace, “kunyi gyaran karayar?”.
      Doctor yace, “eh ranka ya dad'e duk an gyara, saidai na hak'ark'arinsa yaso kawo matsala, amma Alhmdllh komai ya dai-daita”.
       “humyim, maganar bayanan danace a tattara minfa?”.
      “shima komai ready ranka ya dad'e ”.
      “o right, insha ALLAH zuwa jibi nakeson mu tafi, amma wai har yanzu bai ta6a farfad'owa bane?”.
       “ai ba'a sume yakeba, allurar damuke masace kawai takesakasa yawan barci”.
       d'ago ido Galadima yayi yana kallon doctor d'in, yace “amma danme ake masa?”.
         “ itace ke taimaka masa wajen rage masa rad'ad'in ciwukan, dan maganar gaskiya yana cikin matsanancin ciwo”.
     Cije lips Galadima yayi kawai, yace “ALLAH ya bashi lafiya”.
        “amin ya rabbi”. ‘cewar doctor.

     Daga haka suka fito shida doctor d'in.
      Inda Harun yake Galadima ya nufa, “brother yau ba zakaje aikiba kenan?”.
      Kallon agogon hannunsa Harun yayi, sannan ya kalli Galadima, “ka rikitamu ne ranka ya dad'e shiyyasa ban kula time ya tafi hakaba”.
       Murmushi kawai Galadima yayi amma baice komaiba.
     Harun yay musu sallama ya fita da nufin zuwa anjima idan yatashi aiki zai dawo.
    Su yaa Hameed sukai masa godiya da fatan alkairi sannan yatafi.
   Daddy ya kalli su yaa Hameed d'in yace ai kuma da tafiyar kukayi, karku makara wajen aiki”.
        A ladabce suka amsa masa da to, suna shirin barin wajenne saiga motocin su waziri  sun shigo, dole su yaa hameed suka dakata.
     Waziri ne da matawalle, sai Garkuwa da baraya, sai kuma wasu manya-manyan 'yan majisar Sarki. dogarai duksun kasa sun tsare, wasuma zato suke sarkinne yazo da kansa.
        Su daddy ne suka musu iso har d'akin da Abba yake kwance, sosoi suka nuna tausayawarsu gareshi, sunja doguwar addu'ar samun lafiya da fatan alkairi ga Abba. Sannan suka Isar da sak'on Sarki.
     Sun d'an jima a d'akin suka fito da nufin tafiya, a dai-dai time d'inne kuma doctor Farida ta iso gaban Galadima cikeda sassarfa. Bakinta a washe tamkar gonar auduga. Wani dogari Na k'ok'arin dakatar da ita Galadima ya d'aga masa hannu alamar ya barta tazo.
      Cikin girmamawa doctor Farida tace “wannan asibiti da dukkan jama'ar cikinsa suna taya masarautar gagara badau murnar samun k'aruwa daga jikin gimbiya Munaya, insha ALLAH nanda watanni 7 dawasu satittika zata zama uwa, ma'ana tana d'auke da cikin wata 1 da sati uku”.
       Atare dogarai suka d'auki kabbara,  Galadima dake tsaye baki bud'e cikin tsantsar mamaki ya kafe  doctor Farida da idanu, sai kawai yashiga zame agogon hannunsa mai masifar tsada da k'yau ya mik'ama doctor Farida.
     Sauban yazo ya rungumesa, hakama matawalle.
     'Yan gidansu Munaya sai suka koma 'yan kallo kawai, amma bakin kowa yakasa rufuwa.
    Doctor Farida ta kalli Galadima cikin mamaki da al'ajabi, “ranka ya dad'e ni Na cancanci wannan agogon mai d'unbin tsada kuwa?”.
       Wani murmushin Daba a cika gani Galadima yayiba ya saki, ya gyara tsayuwarsa yana fad'in “idan duk abinda na mallaka a duniya kike buk'ata zan baki shi, saboda wannan shine albishir Na farko da aka ta6amin Na farinciki a rayuwata, kifad'i dukkan abinda kike buk'ata inhar baifi k'arfina ba kafin nabar asibitinnan za'a kawo miki shi”.
      Kanta ta shiga girgizawa, kafin ta d'aga agogon ga mutane su gani.
     Mamaki ya cika kashe matan gidansu Munaya hassada da al'ajabi ya cika zukatansu, tunma ba'a haifi cikinba Galadima yake wannan rawar kan inaga an haifoshi?, Kansu bai kuma kwanceba saida sukaji waziri da baraya Na sanarda tasu k'yautar ga doctor Farida, hakama matawalle da Nuren.
    Doctor Farida fa ta rikice, itakam yau taga farar rana, (🙄idan ta ALLAH ake niya kamata abama wad'annan k'yaututtuka ma😏).

     Nuren da matawalle suka hau rabon kud'i a asibitin, tamkar basu San ciwonsu ba.
    Waziri kam d'akin da Munaya take kwance aka musu rakkiya, sun mata addu'a kafin su fito, kowa bakinsa a washe, wasukam ta cikin Na ciki kawai😳🤭.

     Kafin kace mi labari yagama zagaye asibitin, gidan Sarki kam kafin su waziri su Isa labarin cikin Munaya yaje.
   
     hakama Sauban ya kira su Momma ya guntsa musu, Momma saida tayi sujudar shukur.
      Abie bakinsa yakasa rufuwa, kamar daga sama sukaji yace “ALLAH ya inganta”.
      Dukda a hankali yayi maganar hakan bai hanasu ganin motsawar la66ansa ba, Khaleel dake kusa dashi yace “Lah Abie yayi magana Momma!!”.
      ba momma ba hatta da jakadiya sakin kwanon hannunta tayi ta waigo tana kallon Abie. Aunty Mimi ta tura laptop d'in gabanta tafad'o, hakama Samha wuntsilowa tayi daga kujerar datake zaune tayo inda gadon Abie yake.
     Gaba d'aya suka rufu akan abie, kowa yanason sanin gaskiyar batun Khaleel, murmushi Abie yamusu yana jinjina kai alamar gaskiyane, sannan a hankali yakuma furta “da gaske Khaleel yake”.
       Ai yau babu kunya Momma ta rungume Abie a gabansu aunty Mimi ta fashe da kuka mai ban tausayi.
      Aunty Mimi ta had'a momma da Abie d'in ta rungume itama.
      Jikin Samha har 6ari yakeyi takira Number Galadima ta Nigeria.
    Ya rako su waziri da zasu tafi kiran Samha ya shigo, bai d'auka ba, itakuma bata gaji da kira ba.
    Saida su waziri suka wuce sannan yaciro wayar a aljihunsa cikeda haushin wanene mai nacinnan. yana dubawa yaga Samha Ce.
      Murmushi yayi kawai sannan ya kirata da kansa, bugu d'aya Samha ta d'aga, kuka kawai ta fashe masa da shi, zuciyar Galadima tashiga tsitstsinkewa. tsawa ya daka mata yana tambayar lafiya?.
      Share hawayenta tayi, murya Na rawa tace, “Uncle Sam wlhy Abie yayi magana, yanzun nan da Uncle Sauban ya kira yace aunty gimbiya nada ciki sai Abie yace ALLAH ya inganta”..
       Galadima ya ciro wayar a kunnensa ya kuma kallon number, tunaninsa wasune kawai keson masa yawo da hankali, ganin dai da gaske number Samha d'in ce saiya maida a kunnen, cikin sanyi murya ya kira ainahin sunan Samha, “Zeenah! banason wasan banza kema kin sani”.
     “wlhy Uncle ba wasa nakeba, ga Momma ma kaji awajenta”.
   Kafin yace wani Abu yaji muryar Momma namasa sallama, yanayin muryarta yasakashi lumshe idanunsa. Momma tace, “Muh'd! Yau ranace dabazamu manta da itaba a tarihinmu, k'yautar abinda kud'i baya saya, ALLAH kuma yabama takawa damar magana, narasa yanda zan musalta farin cikina Muh'd”.
      Wasu hawayene suka gangaro a kumatun Galadima, ga murmushi yak'i barin fuskarsa, cikin nutsatstsiyar muryarsa yace “Momma ko yanzu Ubangiji ya d'auki raina yagama min komai, Momma mizanyi duniya tasan ina cikin tsantsar farincikin da tunda nazo duniya ban ta6a riska ba?”.
    Dariya momma tayi, tace “godiyar ALLAH ta wadatar da komai Muh'd, lallai yarona zai zama baba”.
    Galadima yayi dariya yana goge hawayen fuskarsa, “Momma bama Abie wayarnan”.
        Cikin tsokana tace, “nawa zaka biya? kasan mu yanzu komai Na kud'ine”.
    Sosai yasaka dariya, har jerarrun hak'oransa Na bayyana. Dogaransa duk sun saki baki suna kallonsa, duk da bajin maganar da yake sukeba, tunda suke da shi basu ta6a ganin yana dariya makamanciyar wannan ba, Sauban kan ai hotuna yaketa masa bai saniba.
        “shikenan Momma, inhar baki had'ani da Abie ba kema kuwa d'iyarki bazata dawo India ba ashe?”.
      “a'a miyay zafi? indai takawa ne gashi”.
        Nanma dariyar Galadima yayi, Abie da tun d'azu yaketa murmushi shima saboda a Hans free momma tasaka wayar duk sunaji, a hankali yace Daddyn Unborn!”.
     Galadima baiji mi Abie ya fad'a ba, amma tabbas yana jiyo alamun motsi, da sauri yace, “Momma video call please ”.

     Mota ya bud'e ya shiga, Sauban ma ya k'araso dan kuma taya d'an uwansa murnar k'aruwar daya samu. tunda aka bayyana maganar cikin Galadima bai samu Kansa ba, balle su ke6e.
     Motar yashigo shima, ganin video call Galadima ya had'a dasu Momma saiya matso kusada shi sosai yana d'aga musu hannu.
    Momma tace, “ho autana ina ka shige wai?”.
      “momma ina zaki ganni nazama Abban Unborn”.
     Dariya sosai suka sanya, Galadima ya rankwashi kansa.
      Wayar aka saka kusada Abie sosai, a hankali yace, “lallai wad'annan iyaye akwai zumud'i dai”.
      Basuji miya fad'aba. Amma sungane ta hanyar motsin la66ansa. cikin zaro ido Sauban yace “Abie!!”. Sai kawai ya rungume Galadima ya fashe da kukan farin ciki.

   
    Humm masu karatu, nabama kowa damar k'iyasta wannan farin cikin a zuciyarsa shima😁😉.



    ★*★★*★*★★*★*★★*★

            A lokacin da Galadima suke can suna waya dasu Momma Munaya ta farka, doctor Farida ta cire mata k'arin ruwan danya k'are.
      Ta kalli doctor Farida tace “doctor Abbana fa? karki cemin dai Abbana ya mutu Dan ALLAH?”.
     Hannunta doctor Farida ta rik'o, fuskarta d'auke da murmushi tace, “gimbiyarmu Abbanki nanan da ransa, insha ALLAH kuma zai tashi, kedai kici gaba da masa addu'a kinji”.
     Kai Munaya ta jinjina mata, sannan tace, “to zanyi fitsari”.
     Doctor Farida ta amsa da to, da kanta ta taimakama Munaya tashiga bayi, fitowa tayi tabata waje, saida ta gama sannan ta kuma taimaka mata ta fito.
       “doctor 'yan gidanmu fa?”.
     Murmushi Dr Farida tayi, cikin tsokana tace, “Gimbiya Galadima yakamata ki fara tambaya ai”.
    Murmushi Kawai Munaya tayi, amma batace komaiba, Dr Farida tace “to bara Na musu magana”.

     Babu dad'ewa saiga 'yan gidanmu nata shigowa, yanda kowanne fuskarsa ke a washe sai suka bani mamaki, nakasa hak'uri nace, “Abba ne ya tashi? kuke farin ciki haka?”.
        “shima insha ALLAH zai tashi 'Yar albarka”. Cewar innaro tana dariya.
     Ni duk sun kuma d'auremin kai da addu'ar da sukeyi suna fad'in ALLAH ya inganta.
     Mamansu Fauziyya tace minakeso akawo min naci.
       Nace, “banajin yunwa mama, ni sonake ma Na kuma ganin Abba”.. 
       “karki damu, Abba yana barci ne, kedai kisamu kici abinci babynmu yak'ara k'ato kafin ki haifo mana”.
       Ban fahimci maganar ta Fiddausi ba, Dan naga awajen akwai masu ciki da yawa, aunty Ramlah, aunty Khaleesat, aunty  Hauwa'u, Siyama, Zarah, aunty Raihana duk cikinsu ya tsufa, haihuwa yau ko gobe.
     Na kalli innarmu dake tsaye batace komaiba, murmushi namata, itama saita mayarmin, nace, “wai har yanzu Munuhiya ba a cire mata ruwanba?”.
     Mama Rabi'a tabani amsa da cewar “an cire, barci takeyi”.
      Cikin marairaicewar murya nace “ALLAH sarki Sweetheart d'ina, ALLAH yabaki lafiya”.
   Duk suka amsa da amin.
     Doctor Farida tashigo tana sanar musu ga Galadima nan zai shigo.
      'Yar rige-rigen fita iyayena suka farayi, kowa yana jin nauyin suruki ya shigo ya iskeshi, ni dariyama suka bani, nayi murmushi ina komawa Na kwanta.
     Saida suka fita kaf sannan nafara jiyo takun takalminsa.
     Idanu Na lumshe kamar mai barci.
      Tunda ya shigo idonsa Na kaina, yacigaba da takowa gaban gadon, duk tunaninsa barcin gaske nakeyi, maimakon ya zauna saiya dafa gadon ya rankwafo kaina, da sauri da sauri zuciyata tafara bugu saboda kusantoni da ya keyi, fuskarsa daf da tawa tamkar zai had'e bakinmu, mikuma ya tuna saiya janye ya maida saitin goshina ya manna min kisses guda biyu a goshi da saman hanci.
      Cikeda mamaki Na waro manyan idanuna, kallon ido cikin ido mukaima juna, ya d'aga min gira d'aya.
     Saurin kauda idanuna nayi gefe.
      Shikuma yaja kujera ya zauna dab da fuskata yana murmushi.
      Munja wasu seconds sannan yasaka hannunsa bisa kumatuna ya juyo da face d'ina inda yake, kin bud'e idona nayi Na kallesa, bai damuba yace “yalla6iya dama haka kike da saurin cafke Abu?”.
       Babu shiri Na waro idanuna kansa, nace “yalla6ai mina cafke?”.
        Idanunsa ya d'an jujjuya alamar tunani, saikuma ya kalleni, har yanzu hannunsa Na tallafe da fuskata, yace “uhuumm mima kika cafke? Na manta ma”. Ya k'are maganar da d'age kafad'a yana ta6e baki.
      d'an hararsa nayi ina tura baki, mutuminnan ya iya rainin wayo.
      Yanzunma murmushin yamin, saikuma ya d'ora hannunsa saman shafaffen cikina mai kama da babu ko kayan ciki balle kayi tunanin akwai mutum.
      Da sauri Na rik'e hannunsa ina fad'in “ yalla6ai lafiya kuwa?”.
      Cikin basarwa yace “itace ta kawo haka, bakimin murna ba”.
      Nace, “Murna kuma? tami?”.
      Cikin d'age gira d'aya yace “Muhammad Sameer Saifudden yazam pah-pah”.
      d'auremin kai maganarsa tayi, Na yunk'ura a hankali zan tashi, mik'ewa yayi ya taimakamin Na zauna yana fad'in “yi da kula karkima jama'ar gari 6arna, dan akwai sarkinsu anan”.
     Waige-waige Na farayi, nidai banga kowa ba bayan mu biyun dake zaune, saina d'auka da kansa yake, na d'an ta6e bakina kawai.
      Shima saiya ta6e bakin yana komawa ya zauna. kusan mintuna biyu duk mukai shiru.
      Zuwa can nace, “nikam dai na dawo normal, kace musu su sallameni kawai”.
        Batare daya d'agoba yace “nafi buk'atar hakan, mi kikeso Sameer yamiki k'yauta da shi?”.
        “k'yauta kuma? akanmi?”.
        “Abie ya fara magana”.
      Babu shiri na wuntsilo daga gadon ina fad'in da gaske?”.
      Da sauri Galadima ya ruk'oni, jikinsa har rawa yakeyi, jina nai kawai bisa cinyarsa.
     “yalla6ai!”. nafad'a cikin zaro idanu, sai kuma na hau waige-waigen kar wanifa ya ganmu.
       Daf yamatso da fuskarsa kusada tawa, numfashin junanmu na sauka bisa fuskokinmu, na marairaice fuska tamkar zanyi kuka, yanda yasaka idonsa cikin nawa tsigar jikina dukta mimmik'e, jikina har tsuma yakeyi, amma tsabar muguntarsa yak'i ya janye, yakuma hanani damar da zan janye nawa.
       A hankali tamkar mai rad'a, yace “ki kula, domin abin cikin kwan yafi kwan dad'i my friend ”. ‘ ya k'are maganar da d'age min gira sama’.
      Lumshe idanuna nayi kozan sami sassaucin daina ganin abinda ke yawo a idanun Galadima.
        hakan yabashi damar d'ora bakinsa akan nawa, shima ya lumshe nasa idanun.
      Babu shiri na bud'e nawa saboda tsorata, ni Munaya mike damun wannan bawa yau? duk yanda naso kwatar kaina hakan ya gagara, dole na sallama yayi iya yinsa sannan ya sakeni.
       Zumbur na mik'e daga jikinsa ina sharar kwallar takaici, shima saiya mik'e yana karkad'amin d'anyatsa, ya matso daf dani a hankali ya furta “k'yautar farko kenan”.
      juyawa yay yafita yana murmushi da gyara zaman hular kansa.
    Na bishi da kallo ina maimaita zancensa na k'arshe, “k'yautar farko? Kamar ya k'yautar farko? mi yake nufi to?”. ban kai ga samo amsarba doctor Farida ta shigo tana murmushi. “ginbiyarmu yalla6ai yace abaki sallama kuje gida ki huta gaba d'aya”.
       Saboda Banason tafiyar, sai nace doctor jikina bai gama sakiba, ki Ce masa sai dare zaku sallameni kawai”.
       'Yar dariya tayi, ta nunamin Galadima dake bakin k'ofa tsaye ya hard'e hannaye a k'irji.
      Baki na tunzuro gaba saboda borin kunya.
     Shikuma ya janye idanunsa yana ta6e baki.

     Doctor Farida ta bamu sallama, na d'auki alk'yabbata na saka, tareda d'aukar handbag d'ita, sai wani ciccin Magani nakeyi, shi da nakeyi danshi yawani share tamkar bai gane da shi nakeyi ba.
        Jinai ya sak'alo hannunsa cikin nawa, na kalleshi da sauri, saiya kannemin ido d'aya.
      Ja nayi na tsaya, shima saiya tsaya, ga mutane duk sun zubo mana idanu, kuma har 'yan gidanmu. tamkar zan fasa ihu nace, “yalla6ai ni dai wlhy ka sakeni, kai bakajin kunyar su innarmu ma?”.
        Yace “kai ALLAH dai ya shiryeka Sameer, yalla6iya Sameer najin kunyar su Innarmu fa, sai dai kuma yana gudun amasa gangancin abin cikin kwan ne”.
      Kallonsa nayi,  “ wai minene wannan abin cikin kwan daka ishi mutane da fad'a”.
       Ya d'an d'ora hannunsa saman bakinsa alamar mamaki, “yamzu nan bakisan abin cikin kwan ba friend? Lallai news ya wuce dake, ina tayaki jaje kam”.
       Kuma kullemin kai yayi a duhu.
    Ita dai doctor Farida dake bayanmu sai kuma birgeta muke da bata dariyar salon namu.
    Mutane kam dake kallonmu tunaninsu koda doctor Farida muke magana, Dan bazaka ta6a d'auka Galadima ya iya zaro magana hakaba. nikaina mamakin dama yana magana mai tsayi irin haka nakeyi, narasa miya d'abbak'a wannan farin cikin nasa na yau?, duk da bawai yanata dariya baneba, fuskarsa nanan yanda take babu walwala, sai dai yau akwai sakewa tattare dashi, kuma yakan yawaita murmushi bakamar ko yausheba.
      Nidai nace, “dan ALLAH yalla6ai kayi hak'uri, wlhy bazan iya zuwa gabansu baba k'arami ahakaba”.
     Baice komaiba ya saki hannuna, amma munci gaba da tafiya kafad'a da kafad'a dashi.
      Wata kuyanga cikin kuyangin da uwargidan Sarki ta had'omu tai saurin tasowa ta kar6i bag d'in hannuna, ban musaba na mik'a mata, mutane sai gaishini sukeyi, nidai kunyama ta isheni, Dan wasu sun girmemin.
     Mun Isa gaban 'yan gidanmu, kowa ya taso yana k'ara min sannu da jiki, nidai sai ce musu make na samu sauk'i.
     d'akin da Abba yake muka shiga, hawaye suka cikamin idanu, Galadima ya ruk'o min hannu, kallonsa nayi saiya girgiza min kai alamar kar nayi.
    Bance komaiba na janye idanuna, sannan na k'arasa gaban gadon nafara tofa masa addu'oi, shima Galadima ya matso ya tayani, daganan fitowa mukayi, Galadima yakuma gargad'ar police d'in akan su kula sosai, inhar wata matsala ta biyo baya to suyi kuka da Kansu.
    Cikin girmamawa suka amsa masa da insha ALLAH hakan bazata faruba ma.

     Ni dai ina wajen 'yan gidanmu, jinake kamar karna tafi wlhy, amma innaro tace kartaji karta gani, nabi mijina naje gida na huta, suma sauran 'yan uwana duk gida zasu tafi hakanan, tunda dai iya k'ok'ari galadima tsaye yake akan komai na abban, dukkan kulawa yasaka ana bashi gwargwadon iko.
      Nidai sai tunzura baki nake su Fiddausi namin dariya.

     Muna haka Galadima ya k'araso wajen, cikin girmamawa yace yakamata suma 'yan gidanmu suje gida hakanan su huta, insha ALLAH Abba zai samu kulawa tamkar suna nan.
     Godiya suka shiga yimasa, innaro nata kwararamasa addu'oin gamawa da rayuwa lafiya, da samun afuwa shima ga mahaifinsa, ta k'are maganar da f'adin “ALLAH ya kawo mana kishiyata ko angona duniya lafiya”.
     K'asaitaccen murmushi Galadima yayi, a kan la66ansa ya amsa da ammin Granny ”.
     
    Daga nan wajen Munubiya muka nufa, suma 'yan gidanmu suka shiga dansu k'ara ganin Abba su tafi.
      Munubiya na kwance tana barci har yanzu ana k'ara mata ruwa, rungumeta nayi ina hawaye, yayinda Galadima da yaa Marwan suke gaisawa cikin mutunta juna, inajinsu sunama juna Congrat, amma ban fahimci na mineneba.
    Nace “yaa marwan wai mike damun sweetheart ne haka ta rame?”.
      Dariya yaa marwan yayi, yace “babynku ne”.
      “lah yaa marwan kana nufin tanada cikine?”.
     Kansa ya jinjina min.
    Cikeda murna na kuma rungume munubiya ina fad'in “ashe na kusa zama mummy”.
     Galadima ya kauda kai gefe yana murmushi kawai, shina yaa marwan sai k'aramar dariya yakeyi.

       Da k'yar dai na hak'ura na baro asibitin nan badan nasoba, suma 'yan gidanmu duk sun wuce gida.


*****************

       A mota sai zun6ire-zun6iren baki nakeyi, saboda haushin banso rabuwa da 'yan uwana ba yanzu, Galadima ya wani shareni.
    shikam dukya gajine, bai cika wahalar zirga-zirga irin hakaba, gashi dama bawani isashshen barci yasamuba jiya.
       Batare dana kalleshi ba nace “wai ina yaa Sauban ne?”.
       Bai d'ago daga latsa wayar dayakeyiba ya bani amsa da “suna tare da Nuren”.
    Da sauri na kalleshi danjin ya ambaci sunan Wanda nake son Sanin wanene shi?, cikin kwantar da murya nace “yalla6ai wai wanene Nuren? ”.
       Tambayar tabashi mamaki, amma saiya share ya d'ago muka had'a ido, kowa ya janye cikin basarwa. bai bani amsarba har muka shiga cikin masarautar...................✍🏼



   Kuyi manage da wannan sister's🤗.






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻

*_Typing📲_*



    *_Haske writer's asso...._*💡



     
     *_♦RAINA KAMA......♦_*
              _{Kaga gayya}_



             *_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻



  ~Book 2~ 👉🏻8⃣


.........Tunda aka bud'e mana muka fito hadimansa sukayo caa akan mu, kowanne k'ok'arin nuna farincikin sa yake ga Galadima.
    Casuke ALLAH dai ya infanta mana, ranki ya dad'e ALLAH ya saukeki lafiya.
     Cikin tsantsar farinciki yake amsa musu, murmushi yak'i barin fuskarsa.
    Nikam zuciyata Ce ta shiga tsitstsinkewa, idan har Na fahimci inda zancensu ya nufa cikine dani kokuma wani keda cikin? Galadima Na kalla, amma saiyamin wani miskilin murmushi yana kauda idonsa, alk'yabbar jikinace kawai taima mutane katanga da ganin zufar data gama jik'emin jiki.
    Tun a falon farko Na dakatar da kuyangin da damuke tare, handbag d'ita Na kar6a nace suje nagode. cikeda girmamawa suka amsamin suka fita suna min addu'ar k'ara samun lafiya. suna fita na juyo ga Galadima, amma tuni ya shige d'akinsa. handbag d'in Na dungurar saman kujera nabi bayansa, hankalina bazai ta6a kwanciya ba sainaji gaskiyar lamarinnan.
      Na iske babu kowa a falonsa, Dan haka nashiga bedroom d'insa, ranar farko kenan dazan fara shiga bedroom d'in. babu kowa nanma, sai motsin ruwa dana jiyo a bathroom.
    Waige-waige nafarayi ina k'arema d'akin kallo, komai ya birgeni a d'akin, sai k'amshin mayen turarensa da ya mannema d'akin. karaf idona ya sauka ga takarda kusada kayan daya cire, mik'ewa nayi Na d'akkota, Na dawo Na zauna. cikin nutsuwata nafara karantawa, nai mugun waro idanu ina fad'in “wlhy impossible, abindama bazai ta6a yuwuwaba kenan” sai kuma Na fashe da kuka.
     Dai-dai lokacin Galadima ya fito daga bathroom, sanye yake da rigar wanka fara, ahankali ya ringa takowa idonsa a kaina, sai dai fuskarsa a d'aure take tamkar bashine cikin walwala ba a asibiti.
     Bai k'araso inda nakeba ya tsaya a tsakkiyar d'akin ya cigaba da goge ruwan kansa zuwa fuska hankalinsa kwance. a harzuk'e nayo Kansa ina cigaba da kukana, naja birki a gabansa, da d'anyatsa Na nuna masa takardar, har yanzu kuma kukan nakeyi, nace “wannan cikin a jikin wa ake nufin yake?”.
     d'auke fuskarsa yayi daga kallona yana wani lumshe idanu, batare daya bani amsa ba ya taka zuwa wajen mirror, cikeda izza yace “sunanwa kika gani a jikin takardar?”.
    Da sauri Na ruk'o bathtub d'in jikinsa, cak ya tsaya, murmushin gefen baki yayi, saikuma ya kuma d'aure fuska sannan ya juyo yana fuskanta ta, inda Na rik'e ya kalla yana fad'in “kona kwance miki igiyar ne?”.
       Sakin rigar nai da sauri ina share kwalla, cike da tsiwa nace “aini ba 'Yar iska bace ba”.
     Shikuma cikin gatse yace, “amma kikayi ciki?”.
      Hannu na aza akaina nakuma fashewa da kuka, “wlhy koma mi za'ayi sai dai ayi bazan haifi wannan cikinba, aiba haka mukayi da kaiba, kawai daga auren Contract sai aganni da ciki? ka tabbatar saina zubar dashi yau d'innan, dan bazanje gidan miji da agola ba, ba kuma zan haifi d'ana Na bari gidan wani ba matar uba ta kashemin”.
       Da k'yar ya iya danne dariyar dake k'ok'arin kufce masa, yay saurin cafko hannuna saboda zaburar danayi xan fita.
     “k yi ahankali karkimin asarar abin cikin kwan fa”.
    Wani bak'in cikine ya turnuk'omin, Na harzuk'o masa da masifa amma saiya wani tsare gida, dolena Na had'iye maganar nacigaba da kukana.
     Shikuma ya watsa mini harara yana jan tagwayen tsaki, sannan yaja da baya yakoma bakin gadonsa ya zauna.
      Durk'ushewa nayi saman carpet d'in gaban gadon Na fashe da kuka mai tsuma rai ina rok'onsa. “dan girman ALLAH ka kaini a zubda cikinnan, kafa tuna da Girman alk'awari, a auren yarjejeniyarmu babu wannan, aikin had'in guywa ka nemeni muyi, kaifa ka tabbatarmin da zaka kasance mai cika alk'awari aranda Na kwana biyu a masarautarnan, miyasa yanzu zaka kasa cikawa? kacemin a matsayin kuskure abinda yafaru ranar ya faru, dukda zuciyata Na cike da bak'in cikin faruwar tasa haka Na hak'ura Na danne Na yarda dakai, ka taimakeni mu rabu cikin salama batareda d'ayanmu ya cutuba, karka k'ask'antar da rayuwata saboda kana ganina mace kuma talaka wadda take k'ark'ashin mulkinka, kamin adalci Dan girman ALLAH Muhammad Sameer”.
   
     Tunda munaya  tafara magana Galadima ya tsaya daga k'ok'arin fara shafa man da yakeyi, idanunsa ya tsura mata, dukkan maganarta ta shigesa, dukda yana k'aunar cikin dake jikinta shima baiso gudan jininsa yazo ta wannan hanyar da babu soyayya tsakaninsa da mahaifiyar d'ansa ba, sai dai wayonsa ko dabararsa bazai ta6a canja k'addararsu ba shi da ita. da k'arfi ya cije lips nashi tamkar zai hudasu da hak'ori.
      Ya mik'e tsaye yana mai fidda huci mai zafi, takawa yay zuwa jikin window n d'akin, ya zuge labilan yana kallon waje, bayi keta kaikawonsu hankali kwance, dukda kasancewar rana ta take. ya maida labilan ya rufe Yakoma takowa tsakkiyar d'akin yana fad'in “tabbas ni Muhammad Sameer mai cika alk'awarine, kuma dukkan alk'awarin Dana d'auka miki ina k'ok'arin cikasu, sai dai nayi kuskure d'aya a cikin AUREN YARJEJENIYA, Na manta da babbar rahamar da ubangiji yake shinfid'awa ga dukkan wasu ma'aurata dazasu iya killace Kansu a matsugunni d'aya, Na manta da ko babu aure tsakanin  mace da namiji inhar zasu kasance waje d'aya shaid'an yakan iya zama Na ukunsu ya sakasu aikata sa6o, balle mu da Muke ganin akwai igiyar aure a tsakaninmu, gaskiya kika fad'a, munyi yarjejeniyar aure domin gano mak'iyanmu bata zama Abu d'aya ba, amma kuma sai bamu d'auki matakan dazamu nisanta kawunanmu ba, daga ni har ke bamu Isa hana ubangiji ikonsa ba akanmu, tabbas ALLAH shidane bada gangan Na kusancekiba a wancan lokacin, sannan bansan ciki ya shiga jikinki ba, to mizaisa kizo ki titsiyeni kina min bore akan zubda shi. Bara kiji Na tabbatar miki yarinya, koda ace ta hanyar aikata zina Na Samar da wannan cikin inason abuna, kuma baza a zubarmin ba, ballantana sadaki Na biya d'unbin mutane suka shaida ke matata ce, mu uku kad'ai mukasan da wani Auren Contract. Dan haka kima nutsu idan zaki nutsu, kamar yanda kikace Duk abinda za'ayi saikin zubar da ciki ko? to Nima duk abinda zai faru saidai ya faru, babu ubanda ya Isa yasaka a zubar da cikinnan, sai dai idan Wanda yabani ne ya kar6a banida ikon hana wannan, idan kin gadama kici gaba da duk abinda kikeso har k'udirin zubda cikin, ni kuma Muhammad Sameer ina mai miki rantsuwa da ALLAH saina nuna miki ainahin color d'ina”. ‘ya k'are maganar da buga yatsunsa biyu suka bada sautin d'ass! d'ass!! A saitin fuskarta’.
           Fita munaya tayi da gudu daga bathroom d'in tana kuka, ahaka ta isa bedroom d'inta ta fad'a saman gado.
      Shi kuma tana fita yaja wani wawan tsaki ya fad'a kan gado yana dafe kansa dake sara masa. ga wata yunwa dake cinsa, shi saima yanzu ya tuna ko breakfast basuyiba suka fita, tsaki kawai yaja yana jawo wayarsa. number Nuren ya kira, bugu biyu ya d'aga yana tsokanarsa da fad'in “ho angon k'arni”. Galadima ya danne 6acin ransa, dan baya buk'atar kowa yasan wannan matsalar data kunne kai tsakaninsa da Munaya, muryarsa a sake yace “kun gama ne?”.
      “eh mun kammala, saidai kuma baka fad'i dawa-dawa za'ama visa ba cikin 'yan gidan nasu?”.
    Ya cije lips nashi yana gyara kwanciya, “tokai dawa yaka mata kake ganin zasu tafi?”.
     “eh, indai tanine gaskiya yakamata ace cikin k'annensa d'aya yaje, sai kuma  mummynsu gimbiyarmu itama, tunda kaga itace first wife nashi”.
     “Okay hakan yayi, zuwa dare sai muje gidan muji yanda zasuyi, nasan kai dai bazaka shigo nanba, please kabama Sauban Abinci ya shigo mana dashi, dan ko breakfast My mata batayi ba”.
      “kai brother amma wannan sakacine ai, gashi ba ita kad'aiba?”.
       “wlhy Na mantane, saboda kaga ai yanayin da take tun barinmu gidan, inaga zanma inno magana a bamu mai abinci kawai”.
     “hakan zaifi kam, bara Na bashi ya taho yanzu kawai, amma zuwa anjima fa saika fito mun had'u”.
     “okay babu damuwa”.

      Yana yanke wayar kiran papi Na shigowa, fuskarsa d'auke da murmushi yay picking. cike da girmamawa yace “ran papinmu ya dad'e tare da k'yak'yk'yawan aminci”.
      “tunda kamin laifi fa ai dole ka faramin da dad'in baki”.
     Murmushi Galadima yayi har sarki Abdul'fatah na jiyo sautinsa, yace “a gafarceni ranka ya dad'e. ina fatan kuna cikin k'oshin lafiya kaida inno da dukkan ahalin masarautarka?”.
     “Alhmdllh Muhammadu. sai kuma wasu k'yawawan albishir suka riskemu a wannan rana. to ALLAH ya inganta, ya sauketa lafiya, shi kuma mahaifinka ALLAH yaci gaba da d'orar da lafiyarsa”.
       “Amin ya rabbi ranka ya dad'e ”.
     “Muhammad mikuma ya faru da sirikinka haka mara dad'in ji?”.
       “humm, ranka ya dad'e bansan miya sakoshi cikiba shi kuma?”.
        Murmushi mai sauti papi yayi, ya gyara zamansa akan kilisarsa, cikin nuna kulawa yace, “akwai abinda bamu saniba ne kawai, amma a fiddashi daga k'asar kafin  mu fara wani yunk'uri”.
      Kamar Galadima na gabansa yashiga jinjina kansa, “to insha ALLAH zuwa gobe da daddare idan ALLAH ya kaimu zasu wuce".
     “hakan yayi, aci gaba da hak'uri dai kaji Muhammad, hak'uri jarine, jarabawa kuma tsanice ta zuwa wajen nasara, ALLAH yayi muku albarka”.
        “amin ranka ya dad'e, nagode sosai”.
       “yaushe zaku shigo?”.
       Murmushi Galadima yayi, hakan yana nufin kakansa nason ganinsa kenan, a ladabce yace “dasun tafi insha ALLAH ”.
         “ALLAH ya kawoku lafiya”.

      Tunda suka katse wayar saiyayta sauke ajiyar zuciya, koba komai ya sami nutsuwa akan wayar dasukai da papi. tashi yay ya k'arasa shafa man, sannan yasaka kayan da bazasu takurashi ba.
      Falonsa ya fito, abinda ake nunawa a tv ya d'auki hankalinsa sosai, ana cigiyar d'iyar Minister Ce, wai an nemeta an rasa tun a daren jiya. Akan la66ansa ya furta “Nuren!” Sai kuma yayi murmushi kawai ya kwanta saman doguwar kujera.
       A haka Sauban ya shigo ya sameshi da sallama, sai bayi buyu dake binsa a baya d'auke da ledoji.
         Galadima ya bud'e idanunsa yana kallonsu amma bai tashiba, bayan bayin sun ajiye suka zube sunama Galadima barka da hutawa, murmushi kawai ya musu ya d'aga musu hannu.
    Sauban yabasu izinin tafiya.
      Zama Sauban yayi a kujerar dake kallon Galadima, “kai yau ina cikin nishad'i wlhy yaa Sam...”
     Kallonsa Galadima yayi yana d'an murmushi, amma baice komaiba.
       Sauban yace “yaa Sam... Aunty gimbiya fa?”..   
        Galadima yace “barci takeyi”.
          “tofa Unborn babynmu yazo da sabon salo kenan”.
      Hararsa Galadima yayi, ya mik'e yana dariya ya shige bedroom.
      Galadima ya girgiza kai kawai yana tashi zaune. ledojin ya duba dan ganin mi suka sayo?.
        Abinda yasan zata iya ci ya d'auka ya fita.
       Saida ya d'anyi jimm a k'ofar d'akin sannan ya shiga da sallama, har yanzu tana a kwance tana kuka, lips d'insa ya d'an cija sannan ya ajiye abin hannunsa saman table d'in dake gaban gadon, idanu ya tsura ma bayanta nawasu 'yan seconds, ko alk'yabbar bata cireba, zama yayi a bakin gadon kusada ita, amma ya juya mata baya.
      Tun daga shigowarsa har zamansa tana jinsa, amma ko motsi batayiba, kusan mintuna 3 suna zaune a haka, ganin batada niyyar tashi ko kulashi ya sakashi juyawa yana kallonta, gyaran murya yayi sannan yace, “tashi kici abinci”.
     Shiru tayi ta shareshi, ko motsima bata yiba.
    Tsawa ya daka mata, babu shiri ta tashi zaune, jikinta sai rawa yakeyi, tunba yanzuba munaya akwai tsoron tsawa, bata barin saita kwana amma batason amata tsawa. Shi kansa yayi mamakin tsoratar tata, ya watsa mata harara yana kwafa, sai kuma yaja tsaki, alk'yabbar yacire mata, sai hawaye take zirarwa, bai kuma cemata uffanba ya bud'e abincin ya ajiye a gabanta, kafeta kawai yayi da idanu, hakan saiya tasirantar da tsoronsa a zuciyarta, dan haka tafara cin abincin, tanayi dai hawaye na zurara, cikin nata bamai tsurfa baneba, komai ci take hankali kwance, sai dai laulayi na ciwo.
        Dolenta ta saki jiki taci abincin, danya kafeta da idanu ga fuska cid'in-cid'in, duk jarumtarka dolene kaji shakkarsa.
      Kallo d'aga tamasa ta janye idonta, shi kuma ya harareta yana fad'in “kin k'oshi ne?”.
     Kanta ta jinjina masa tana matso kwalla. baice komaiba ya sauke sauran abincin k'asa, sannan yace “sauka kije kiyi wanka”.
       Baki ta bud'e zatayi magana ya dalla mata harara. sauka tayi tana k'unk'uni akan la66a. yana kallon motsin la66an nata, sai dai bayajin mi take fad'a.
     
     Yau kam Alhmdllh taji dad'in jikinta, ko k'arin ruwan da aka saka matane yasakata jin kwarin oho, ruwa mai d'an d'umi ta tara tayi wankan, tanayi tana hawaye, itafa ko mi zaiyi ba masifaba bazata bar cikinnan ba, babu yanda za'ayi ta reni ciki ta haifeshi sannan yazo daga baya ya saketa, bazata d'auki wannan rainin hankalinba, su maza a kullum d'aukar mace suke mai k'arancin tunani, kowane yayin rashin mutuncinsu suka kwaso saiya k'are akan mata, wlhy akan cikinnan tata d'aga masa hankali kenan harsai ya amince an zubar dashi sannan, kuma ana zubarwa zata k'ara gaba, mahaifinsa kam kobasa tare insha ALLAH zata cigaba da masa addu'oi ana aika masa.
         
     Jin shiru tak'i fitowa ya sakashi mik'ewa, bai wani kwankwasa ba ya bud'e k'ofar bathroom d'in kawai, danshi zatonsa ba wankan takeba ta tsaya kukane.
       A birkice munaya ta kalli k'ofar, ganin Galadima tsaye yana kallonta ta fasa k'ara, yay hanzarin ida shiga bayin ya rufe bakinta da tafin hannunsa dankar ta tara masa jama'a.
      Juyawa tayi ta ruk'unk'umesa, tare da saka hannayenta ta zagaye bayansa ta manne k'irjinta da nasa, ita duk bata son yaga jikinta ne😂😝.
         Shima fuskantar hakan da yayi ya sakashi sakin murmushi, saiya saka hannunsa biyu ya zagaye bayanta ya manneta sosai a jikin nasa.
   Shiru sukayi nawasu seconds, tana sauke ajiyar zuciya shima yana saukewa, saboda yanason ganin yanda zatayi saiya fara k'ok'arin janye jikinsa itama zai janye ta.
    K'ank'ameshi tayi ta fashe da kuka, jiyay tamkar ya kwashe da dariya, amma saiya daure, cikin dakiya yace, “malama sakeni mana? konaci bashinki ne wai?”.
       Cikin dasashshiyar muryarta datasha kuka tace, “to kabani zanina da hijjab na saka”.
        “to kin k'udunduneni ta ina zan iya baki wani zani? sakeni saina baki”.
       Kafad'a ta nok'e alamar tak'i.
       Murmushi Galadima yayi, ya shafa bayanta cikin murya k'asa-k'asa yace, “idan an hanani ganin can ai gashi ina kallon nan”.
     Da sauri tayi wata wulk'itawa ta koma bayansa ta 6uya.
       Kansa ya dafe yana fad'in “yau Sameer kaga ta kanka, ranar farin cikinka sai saka maka ciwon kai da zafin kai akeyi, wai ke yalla6iya mikike 6oyemin daban saniba ne?”.
      Baki ta murgud'a masa tana fari da idanu, dayake ba ganinta yakeba baisan hidimar datakeyi ba.
    K'ok'arin juyo da ita ya farayi amma tabi ta kanannad'e shi, rasa yanda zai mata yayi. yakula yarinyarnan 'Yar daruce kawai. zaninta ya jawo ya mik'a mata, saida ta tabbatar ta d'aura sannan ta sakeshi, yana juyowa ta juya masa baya ita kuma.
       Baice komaiba ya ta6e baki ya fice daga bathroom d'in.
        Harar bayansa tayi ta na fad'in “ALLAH ya isana”.


Nace Humm.😏

        Fita yay daga d'akin gaba d'aya, tunda dai yasamu taci abincin, harya kai k'ofarsa ya tuna batasha maganinta ba, dawowa yayi da baya.
     Ita kuma motsin fitarsa dataji yabata kwarin guywar fitowa.
    Shigowarsa tasata kwakumar hijjab ta saka, bakinsa ya ta6e ya wuce wajen handbag d'inta batare daya kalleta ba.
       Magungunan ya fido, ya zauna bakin gadon, “kizo kisha magani”. ya fad'a cikin k'asaitarsa.
     6ata fuska tayi, tace “babu amfanin tattalin abinda za'a zubar ai”.
      Lips d'insa ya cije, sai kuma ya ajiye drugs d'in yana kallonta, mik'ewa yayi ya taka inda take, a bayanta ya tsaya, fisgota yayi ta fad'o saman k'irjinsa, saida ta rumtse ido dan zafin dataji, ya matso da fuskarsa daf da tata, a wani yanayin data kasa fassarawa yace “adadin nawa kike buk'atar na biyaki danki barsa?”.
     Rik'esa nayi da k'yau gudun karna fad'i, na janye idona dake cike da kwalla  daga cikin nasa, “Bana buk'atar ko sisinka yalla6ai, cikinne kawai bana buk'ata, kuma bazan raineshi ba balle nakai ga haifeshi”.
       Wani murmushi mugunta yayi, sanan ya sakeni tamkar zai hankad'ani, mikuma ya tuna oho masa, saiya kuma damk'e hannuna, muryarsa a kausashe yace “wlhy idan kinga baki haifi cikin nanba to sai dai idan wanine a cikinmu numfashinsa yabar gangar jikinsa, sai kuma idan ubangiji ya kaddara Shiba mai Shak'ar iskar duniya bane, dan bani da hakk'in kowa, ubangiji kuma bazai barki ki shiga nawa ba”.
     yana gama fad'ar haka ya saki hannuna yafice daga d'akin baki d'aya.

       Yariga yasan zai fuskanci abindama yafi haka daga munaya, shiyyasa bai zafafama zuciyarsa akan wannan rikicin nata ba, shi babbanma burinsa yanzu Abbanta yabar k'asar nan, danya samu damar gudanar da aikinsa yanda ya kama ta.
       Da wannan tunanin ya dawo d'akinsa, ya iske Sauban kwance wai zaiyi barci, hararsa yayi yana fad'in “ kama tashi, time d'in zuhur yayi.

      Yana fita na raka bayansa da harara ina murgid'a baki, “oho dai, koma mizaka fad'a ka fad'a, nima ai bani tare da hak'k'in kowan, ALLAH kuma bazai baka damar danne nawaba, sokake nazama shashar mace ko? munyi auren contract batare da sanin iyayena ko naka ba, kazo kamin ciki na haifa maka ka sakeni na koma gidanmu, katashi da riba biyu kenan, nikuma babu ko d'aya sai bak'incikin danakema iyayena tanadi da kaina, Galadima ko a matanma ai _AKWAI BANBANCI?_ wlhy.


 
    gaskiyane Munaya, rik'e darajarki shine 'yancinki😄👍🏻.


*******

        Bayan sun fito massalaci sukejin labarin wai an rasa inda Muftahu yake, a safiyar yau aka samu motarsa a bud'e, sai kuma agogonsa da takalminsa d'aya a k'asa alamar da k'arfin tsiya aka saceshi.
    Hakan yasaka aka kama dogaran dake tsaron k'ofa ta uku, dan anga alamun tanan aka fita dashi.
   Dukda Galadima najin haushinsa saida hankalinsa ya tashi, dan haka suna shigowa ya d'au waya ya kira Nuren.
    Nuren na d'aga wayar Galadima yace, “Nuren Muftahu, kaine ko?”.
       “Muftahu kuma? nine naimi?”.
     “A daren jiya an rasa Wanda ya bar masarauta dashi”.
     “humm brother, dukda muna ganin Muftahu cikin masu mana zagon k'asa banta6a tunanin saina d'aukeshi zan gane hakaba, wlhy bani bane”.
     “ya salam”. ‘galadima ya fad'a cikin dafe kai da cije lips, wayar ya yanke ya Shiga safa da marwa, yarasa wazai hararo.
     Yana cikin wannan halin saiga harun shima a rikice, kowa yasan su ukunnan abokan junane, kuma akwai shak'uwa tsakaninsu, matawalle ne dama bai cika shiga cikinsu ba, saboda mama Fulani Na hanashi tun yana yaro, a cewarta shine d'an Sarki mai mulki, kuma shine mai jiran gado, darajarsa datasu Galadima ba dai-dai takeba, wannan hud'ubar ce tamasa tasiri sosai, amma yanason 'yan uwansa har zuciyarsa.
       “galadima shin kaji kuwa mike faruwa a masarautarnan?”.
     Cikin damuwa Galadima yace, “Harun su waye da wannan aikin?”.
       “kowa abinda yake tambaya kenan Sameer, Muftahu bashida wani abokin fad'a”.
       Hankalin Galadima kuma tashi yayi, shi duk damuwarsa karda a cutar da Muftahu ta dalilinsa, tunda ya kula duk wani makusancinsu shine abin harin mak'iyansa. shifa baima yarda ba Nuren bane da wannan aikin, dan yasan halinsa sarai, dolene kuwa yafita wajensa yanzunnan.
     Harun yace bara yaje, suna son akai report gidan radio da television.
     Jin jina kai Galadima kawai yayi, shima ya shige ciki danya shirya.
   

       Tun safe an sanarda jami'an tsaro 6atan Muftahu n, kuma suna a kan aikinsu.



★★★


    Yunwar da yakeji tasashi bayan yayi shiri ya samu fresh milk yasha kawai, sannan yafito, d'akin Munaya ya lek'a, saiya isketa baje a gado tana shak'ar barci, baiyi yunk'urin tashinta ba yafito.
      Har dogaransa sun taso yace suyi zamansu su huta, zai fita shida Sauban, cikin damuwa sarkin mota yace, “kayi hak'uri ranka ya dad'e, koda nine kawai mu fita, Mai martaba ya sanar yau a fada kar'a sake barin wani d'an gidannan yafita wani waje shi kad'ai”.
     Kallonsa Galadima yayi, kamar zaiyi magana saikuma yafasa ya bud'e mortar da kansa ya shiga, batare da ya jira an bud'e masa ba.
        Da hannu sarkin mota yayma sauran dogaran nuni da su biyosu a baya idan sun tafi.

      A wani waje suka had'u da Nuren, Nuren ya fito daga motarsa yadawo inda Galadima yake, sai sarkin mota yafita yabasu waje kawai.
       Galadima yace “please idan kaine ka sakeshi”.
    Da mamaki Nuren yace, “wai Muftahu n dai? am telling you banida alak'a da d'aukarsa. yarinyar Minister ce kawai a hannuna”.
        “innalillahi, wlhy Nuren inajin tsoro, karsuje su cutar dashi”.
       “Sameer! nifa ina zargin kawai ya had'a baki da wasune suka kamashi dan yayi wasa da hankalinmu”.
       Idanu Galadima ya tsurama Nuren tamkar yana hango gaskiyar maganarsa, ya saki wani guntun murmushi, sannan ya gyara zamansa yana fad'in “well, koma minene dai zai fito ai”.

       Nuren yace “ni kaga dama kabar zancen wani Muftahu n banza can, way note mu wuce gidan sirikanka kozamu samu wasu evidence daga canma akan Accident d'innan”.
       Agogon hannunsa ya kalla, sannan ya kalli Nuren d'in alamar suje.

     Anan Nuren yabar motarsa suka tafi ata Galadima, saida suka fara tafiya Galadima ya lura da mototin dogaransa a bayansu.
    d'an murmushi yayi yana kallon Sarkin mota, yace “sarkin mota an karya min doka kenan?”.
      Sarkin mota daya fahimci Galadima yagane dogarai Na binsu sai yayi 'yar dariya, yace “ka gafarceni ranka ya dad'e, bazai yuwu mu barka ka fita kai kad'aiba ai, dan fitarka babu kowa tafi ta kowa had'ari a masarautarnan, mai martaba ma nasan saboda kaine ya saka dokar ai”.
       Galadima baice komaiba sai murmushi dayayi, Nuren ma murmushin yayi, sannan yace “amma kamar bayan motar dogaranka akwai wata bak'ar mota Na bin tasu?”.
       Galadima ya juya shima, tabbas anabin motar dogaran a baya, “sarkin mota su wucemu, karsu tsaya”.
     “To ranka ya dad'e”.
      Bayan sarkin mota ya sanar musu suka wuce su Galadima, motarma ta wuce, da kallo Nuren da Galadima suka bita, Nuren yay hanzarin d'aukar motar hoto a wayarsa. “humm da alama suna zaton kana d'aya daga cikin motocin canne”.
     Murmushi Galadima yayi, a k'asaitarsa yace, “kokuma suna son wasa da hankalinmu ba”.
     Da mamaki Nuren yace “kamar ya?”.
        Murmusawa Galadima ya kuma yi, ya kwantar da kansa jikin seat yana lumshe idanu, “Nuriddeen! Sameer ya wuce tunanin dukkan mai tunani, kai tsaye ba'a gane manufar zuciya, kwanji ko dama basu ke nuna k'arfin ikon mai ikoba, nazarin komai daki-daki da iya sarrafa duniya a yanda tazo shike nuna k'arfin gwarzan taka, mazantaka ba'a shaidata a fuskar namiji, duk lokacinda kai gamo da nama, kud'i, mata bisa hanya, karkayi rawarkan d'auka ko murnar ALLAH ne ya baka, zata iya yuwuwa tarko aka d'ana maka, shi k'yawu had'arine, 6oyeshi kuma nagartace, maiyi baya fad'an zaiyi, sai dai aga aikinsa a k'asa, tasowar iskar hadari bashi ke nufin ruwan zai zuba ba, watak'il sunan wannan iskar gyara kayanka. Dalili da dalilai basa ta6a saka zuciyar Wanda yake nema ta raunana, time d'in da zan nunama mak'iyan mahaifina d'an zaki ya girma yayi, sun durk'usar da shi a k'asa batareda tunaninsu yabasu ya haifi Raina kama ba, Su cigaba da raina aikin Muhammad Sameer daga k'arshe kuma saisuga gayya, tafiyar hawainiya bashike nufin gazawar kuzarinta bane, lokuta da dama hanzari kan katse igiyar cikar buri, a sannu kowa zai fahimci wanene *_RAINA KAMA....._*👎🏻
       
     Ba Nuren ba hatta da sarkin mota maganganun Galadima ya shigeshi, tabbas mutane dayawa sunama Galadima kallon mutum mai yawan sakaci da rashin ho66asa, koshi yana d'aya daga ciki, amma wannan zantukan nasa sai suka sakasu a rud'ani, kenan akwai abinda sud'in basu saniba...........
     Dole tunaninsu ya katse saboda isowarsu gidansu Munaya.

      Fita sarkin mota yayi yanema musu iso, babu dad'ewa saiga baba k'arami ya fito, sarkin mota ya bud'ema Galadima, yayinda Nuren ya bud'e da kansa, zuciyarsa sai jujjuya hannunka mai sandar Galadima yakeyi.
         Dukda baba k'arami yayi mamakin zuwan Galadima haka ya danne, yaymusu k'ar6a ta girma, sannan suka shiga cikin gidan.
     Gidan tsitt tamkar babu mutane, saikace ba gidannan bane mai kama Dana 'yan dambe😂, (yo kowa Na tsoron a korashi gidansu🤣😝).
        A falon daddy aka musu masauki, dan danan aka cika musu gaba da kayayyaki, baba k'arami ya fita domin basu damar cin wani Abu.
    Babu abinda suka ta6a, dukda kuma Galadima ma yunwa yakeji, a haka daddy da baba k'arami suka dawo.
        Daddy yace “anya kuwa wannan d'an namu yana d'aukar gidannan matsayin nasu?”.
      Murmushi Galadima da Nuren sukayi, Galadima yace “sosaima daddy”.
       Baba k'arami yace “ta INA zamu amince da haka kuwa, bayan inada tabbacin ko ruwan gidannan Baka ta6a sha ba”.
    Kunya Ce ta kama Galadima, sai kuma yaga bai k'yautaba, ya rissinar da kai yana fad'in “amin afuwa zan gyara”.
      Mik'ewa baba k'arami da daddy suka kumayi, “to mun bada dama ta biyu”. cewar Dady yana dariya.
      Bayan fitarsu Nuren ya bud'e kulolin shima yana dariyar, danbun shinkafane daya samu nutsuwa ta musamman, sai k'amshi mai dad'i yakeyi, daga Galadima har nuren saida kwad'ayin cin abincin yazo musu.
      Kallon Galadima Nuren yayi yana d'aga gira, Galadima yay murmusa tareda fad'in “kadaiji kunya”.
      “kaima jinta zakayi yanzu, dan nasan ci zakayi”.

     Yau dai kam Galadima yaci abincin gidansu Munaya, kuma gashi girkin innarsu, babu kunya sukaita zuba Santi shida Nuren sunama juna dariya, Galadima harda su6utar baki yana fad'in “amma my mata muguwace, bata ta6amin irin wannan ba”.🙀
      Mi Nuren zaiyi inba dariya ba🤣, su Galadima anji dad'i har kwalwar kai Baki ya bud'e😂😝.

     Saida suka mammala tsaf sannan su baba k'arami suka dawo, sunji dad'i dasuka iske sunci.
     Daga nan sukayi gaisuwa, su baba k'arami suka d'ora da godiyar d'awainiyar Abba da Galadima ya d'auke musu.
     Murmushi kawai Galadima yayi.
     Nuren ya gyara zama, a ladabce yamusu bayanin son fidda Abba da Galadima kesonyi, dan likitoci sunce ana buk'atar kulawa saboda karayar hak'ark'arinsa data k'ugu, “to yanzu haka dai angama setting d'in komai gameda tafiyarsa, har asibitin daza'a kaisa, visa d'insa da komai, sai dai anason tafiya da mutum biyu a cikinsu, mi kuka gani akan Wanda za'aje da shid'in?”.
      Daddy da baba k'arami suka kalli juna, summa rasa wane irin farin ciki zasu nuna dan Galadima yasan sunji dad'i? sunta jero masa k'yawawan addu'oi, kafin daddy yace “ai kawai sai atafi da jafaru da Ai'sha, dan bai kamata mutafi mu duka ba gida babu kowa, dukda akwai su Anas, gakuma su Hameed zasuke zagayowa, amma hakan yafi dai.
        Duk sun gamsu da hakan, dan haka suka buk'aci passport d'in baba k'arami da inna, ita inna babu, sai sunje an mata, amma baba k'arami an samu.
     Sun bari akan zuwa anjima za'azo akai inna tayo.
      Daga nan Galadima ya buk'aci number da aka kira aka sanar musu da accident d'in Abba.
       Daddy yace Ai'sha aka kira, saidai akawo wayar tata. Kiranta yay yace tabama cikin su Aryaan ya kawo wayarta.
      Babu dad'ewa saiga Aryaan d'in da ita, yanda yaron ya gaishesu saida abin ya birge Galadima, ya yarda yaran gidan akwai tarbiyya babu laifi kam.
       Galadima yace, “amma Dady ko numbers nawa Abba ke amfani dasu?”.
      baba k'arami ya bashi amsa da cewar “uku ne”.
       Nuren yace “kozamu samesu dukansu?”.
    Dukda baba k'arami da daddy sunshiga mamaki, dansu zukatansu basu kawo musu akwai wani Abu a k'asa ba, sun d'auka kawai Abba yayi Accident ne dai.
       Baba k'arami yabasu Numbers d'in duka.
      Bawani bincike Galadima yayi a wayar innarsu Munaya ba, wani Abu kawai ya saka (Wanda Nima ban saniba😱) yabama Dady wayar yana fad'in “zata bar wayar anan dan a can bazatayi aikiba, kuma gashi muna buk'atar wayar, dan haka daddy saika rik'e a hannunka tunda kai kana gida”.
      Dady ya amsa da to, duk su Galadima sun kuma sakasu a duhu.
     Sallama sukai musu suna fito domin tafiya.
     Harsun Shiga mota saiga Aiyaan da gud'u d'auke da wata Leda.
     Sarkin mota ya tareshi yana fad'in yaro miya farune?”.
       “Auntynmu za'a kaimawa inji innarmu”.
     Galadima yayma sarkin mota nuni da yabar Aiyaan d'in ya k'araso.
        Bud'e murfin Galadima yayi, Aiyaan ya k'arso, Galadima ya kamo hannun Aiyaan yana murmushi, “my friend ya akayi?”.
    'Uncle innarmu ce tace akaima Auntynmu dan ALLAH”.
     murmushi Galadima yakumayi, sannan ya kar6i ledan yana fad'in “ita kad'ai banda ni?”.
     Aiyaan yad'an zaro ido waje, sai kuma yace “to bara naje Na fad'am innarmu kaima ta baka naka”.
     Da sauri Galadima ya kamo hannunsa dan yana neman tsillawa da gudune, “kaga dakata, idan naje saimu raba wannan da ita, yanzu dai ka fad'ama innarmu ta shiryaka gobe zan aiko a d'aukeka kazo ka zauna damu tunda kuna hutu ”.
        Cikin murna Aiyaan yace, “wajen auntymu?”.
     Galadima ya jinjina masa kai.
     “to amma kuma Aryaan fa?”.
     Cikin mamaki Galadima yace, “wanene Aryaan d'in?”.
     “lah baka San mu 2wins bane ba?”.
     “da gaske?”.
   “ALLAH kuwa”.
         “to shikenan, kacema innarmu ta shiryaku Ku duka biyun zakujema Aunty hutu”.
     Cikeda murna Aiyaan ya shek'a da gudu gida danya kai labari.
     Galadima yay murmushi yana rufe k'ofar motar, Nuren ma murmushi yakeyi, a fili yace, “yara sunyi wlhy”.
     Galadima ya kalleshi, cikin d'age gira sama yace, “kayi aure”.
     Sosai Nuren yay dariya.


******
     A inda suka d'auki Nuren anan suka ajiyeshi, su kuma suka koma masarauta, sun iske tuni dogaran sun dawo abinsu.
     d'akinsa ya Shiga, ya iske Sauban nata barcinsa.
    Bai tadashiba, yadawo falo ya zauna.


_____________________________


     Da daddare Galadima Na falonsa zaune yana aiki a system akayi knocking d'in k'ofa, izinin shigowa ya bada, sarkin mota ya shigo hannunsa d'auke da leda.
    Galadima dake aikinsa bai d'agoba,  a haka ya amsa gaisuwar sarkin mota.
     Sarkin mota yace “ranka ya dad'e kayi mantuwane a mota ”.
     d'agowa Galadima yayi ya kallesa, ganin ledar da Aiyaan ya kawo yatuna masa sak'on munaya, nuni yama sarkin mota daya ajiye.
     Sarkin mota ya ajiye yana masa saida safe.
   Nanma bai tankaba, kansa kawai ya jinjina masa.
       Bayan fitar sarkin mota ya mik'e d'auke da laptop d'insa da ledar, dama tunda ya shigo baima lek'a ta ba, dan Sauban yace yakai mata abinci, kuma tun d'azu suna tare suna hira. Hakan yasa yagane shine ta raina kenan. wannan haushin ya hanashi Neman inda take.
     
        A bakin gado ya isketa zaune tagama waya da Munubiya, k'in d'agowa tayi ta kallesa, tadai amsa masa sallama.
    Shima bai kula taba ya zauna bakin gadon d'an nesa da ita.
      Shiru kowa yayi suka share juna, haushi ya turnuk'e Galadima, lokaci yayi dazai daina d'agama yarinyar nan k'afa, yakamata su goga raini shi da ita. ta gefen ido ya saci kallonta, sai wani cika da batsewa takeyi, ya cije lips nashi.
     “k baki iya gaisuwa bane?”.
     Saida takuma tura bakin sannan tace “ina yini” tana mik'ewa da nufin bar masa d'akin, tana k'unk'uni
    Bai amsata, sai mik'ewa da yayi shima, matsawa tashiga yi baya yana binta, fuskarsa a matuk'ar d'aure, da jikin bango ta manne, shikuma ya mata runfa, hannunsa d'aya a dogare da bangon yayinda yasaka d'aya ya rik'o hannunta ya matsa da k'arfi, zatai magana ya jawota tafad'o jikinsa, ya manne bakinsa kan nata, duk yanda taso kwatar kanta hakan ya gagara, dan ya kama hannuwanta biyu ya murd'esu ta baya yanda ta kasa koda motsi. A haka ya  wulk'itata takoma saman gadon, shima yabi bayanta.
      Ya d'ora hannunsa kan bakinta dan karta ishesa da tsiwa, idonsa ya saka cikin nata ya hanata kata6us, cikin tsare gida yace “dolene yau Na kora miki warning na musamman danki ringa banbance inda zakiyi tsiwa”.
    Bai bata damar dazata fad'i nata ba yashiga aikata yanda yakeso da ita🤥🙆🏻.................✍🏼



   Kutttt Galadima auren Contract nefa😱😂, ba ruwana kaida masoyan Munaya aradu🤣⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀🤧.


i miss you wujiga-wujiga my sweet fans😂😜😜😜🥳.









*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭

*_Typing📲_*



    *_Haske writer's asso...._*💡



     
     *_♦RAINA KAMA......♦_*
              _{Kaga gayya}_



             *_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻



  ~Book 2~ 👉🏻9⃣


.................Salon nasa yasani bashi ragama, dan Galadima yazo min da sabon salo mai tafiya da gudun jini dana zuciya.
    Duk da kasancewata farin shiga, hakan bai hanani gane Galadima Na daban bane, kamar yanda kuka sanshi mutum mai izza da k'asaita, hakan bai canja ba ta wannan fanin, komansa a nurse da izzar k'asaita yake gudanar dashi. ban tashi farga nayi kuskure ba saida labari yafara nisan zango, anzo wajenda tsorosa yafara tasiri a gareni, Sai dai kuma nayi sakacin da Galadima yazama kurman dutsen dabaya ji baya gani. Sai lokacin hawaye suka fara ambaliya ga fuskata, hannayena na k'ok'arin d'agawa domin rok'o, sai dai ya hanani wannan damar gaba d'aya..........


   🤥🙆🏻kai babu ruwana, iya nan nagani nima🤫 aradu aunty Magajiya da aunty Ni'ima zasuci k'aniyata ne idan na k'arasa fad'a😱🤭⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀.

 
      Tabbas na gurzu, dan yau na banbance tsakanin aya da tsakkuwa, banbancin baya cikin hayyacinsa da yau d'inma kad'anne, dukda babu yanda za'ayi daren farko yayi dai-dai da kowacce rana ta bayansa.
      Duk ajiyar zuciyar danake saukewa yana jina, amma yay luf a gefena, hakan ne Yakuma tunzurani, a zalinceka akasa lallashinka saboda jin kai, wlhy kasaitar bawannan tayi masa yawa, duk randa yazama sarki kam fadawa sunga takansu, dan magana dai idan sarki na uku a fada toshi bazaiyi ko guda d'aya ba😏.
      Galadima daduk yake sauraren kukan nata da ajiyar zuciya ya juyo kad'an yana fuskantarta, hannu yasaka ya tallafo fuskarta ta matso dai-dai da tasa, jinai kawai ana huramin iska saman ido, tsaf na fahimmci iskar bakinsa yake huramin, amma saina dake nak'i bud'e idona.
    Muryarsa can k'asan mak'oshi ya furta “my friend are you okay?”.
     Banza na masa, nakuma k'i bud'e odon, lallai mutuminnan yacika d'an latsin rainin wayo number 1, yanzunan Galadima har yanada bakin yimin wannan banzar tambayar?, idona a rufe har yanzu na bud'e baki cikin salon tsiwa zan maka masa bak'ar magana, amma saiya d'ora yatsansa saman bakina yana fad'in “shiiii!🤫” da bakinsa, shirun kuwa nayi kamar an rufemin bakin Dan Nina Na tuna illar yin tsiwar.(😝😂)
    Ya matso dani jikinsa ya rungume, hannunsa na buga gadon bayana k'ad'an-k'ad'an, ya d'ora bakinsa saitin kunnena, “yanzu kin gane banbancin Sameer da Munaya right?, idan kuma har yanzu baki fahimta ba to bakinki ya cigaba d'amin tsiwa OK?, nikuma bazan gaji da punishment nashi ba sala-sala yalla6iya💋”. ‘ya k'are maganar da sumbatar cikin kunnena’.
      Babu shiri na k'ank'amesa dan har cikin kwalwar kaina naji sumbar nan.
     Kad'an ya buga bayana sannan ya janyeni daga jikinsa ya sauka daga saman gadon.
      “hasbinallahu wani'imal wakil” na iya maimaitawa kawai, na k'ank'ame pillows d'in gabana ina rintse idanu da cije lips (copy copy😝).

         Kusan mintuna 15 duk nazata yama fitane, sai kawai jinai an d'aukeni. a razane na bud'e idanuna, kallon ido cikin ido mukaima juna, da matuk'ar Sauri na maida nawa na lumshe.
       Wani muskilin murmushi Galadima yayi yana cije lips.
        Ba shiri na bud'e ido, saboda jina cikin ruwan zafi, yunk'urawa nayi zan mik'e cikin 6ata fuska ya maidani ya zaunar yana fad'in “za6i ya rage naki, zama kiyi da kanki, kokuma ni nayi miki..”
      Banma bari yakai k'arsheba na koma na zauna ina kare k'urjina.
       Kafad'a ya d'age sama yana ta6e baki da fad'in “hummm”.
      Fita yay daga bathroom d'in ya rufe mata K'ofar.
   
       Na kai tsawon lokaci a bayin ina Gasa jikina, dan nasan idanma banyiba kaina nama mugunta, saida naji ko ina ya saki sannan nayi wankan tsarki ina hawaye, bansan yanda zan fassara wannan muguntar ta Galadima ba kuma, wannan karon kuma tsautsayin zaice kokuwa ba yin Kansa bane?.
    Haka dai na kammala na d'aura towel d'ina, a zuciyata ina addu'ar ALLAH dai yasa ya fita, dan towel d'in guntune, bai gama rufe cinyoyina bama baki d'aya.
     Da sand'a na fito, yauma inajin zafi kad'an-kad'an, amma ba kamar na ranar ba. ganin baya d'akin saina ida rufe k'ofar na tako cikin d'akin sosai.
       Ina neman kaya a wardrobe ina share hawaye, indai rashin tsiwar dayake fad'ace na daina masa, dan bazan zauna ya illatani a banza ba, wannan k'addararren cikinma daya hanamin gangar jiki hutawa da ciwuka ya isheni, basai na cigaba da 6alloma kaina wata muguntar tasa ba.
      wata 'yar riga mai d'an nauyi-nauyi na samo, na cirota dan sanyi nakeji, juyowar da zanyi saina gansa zaune bakin gado yana danna laptop, hannunsa d'aya rik'e da glass cup yana shan fresh milk hankali kwance.
       Saida nad'anja baya, nakuma bud'e rigar ina kare jikina.
    Duk abinda takeyi yana kallonta ta gefen ido, amma yawani share kamar baima San da itaba.
      Da bin bango da sand'a na koma bayin, ta gaba kuma ina karewa da rigar.
   Saida ta shige ya d'ago kai yana kallon k'ofar bayin, saikuma ya girgiza kai yana murmushin gefen baki. cigaba yayi da aikinsa a nutse.
     Barci nakeji, ga zazza6i yafara rufeni, hakan yasa ina gama saka rigar na fito, naci serious kawai sannan na fito.
    d'ago idanu yayi muka had'a ido, da sauri nad'an rankwafa inajan rigar barcin k'asa wai danta rufemin cinya zuwa kwauri.
     Baki ya ta6e yana wani janye ido cikeda basarwa. Irin shi baiga abin kallo d'in nanba.
    Ni kuma na dalla masa Harara ina k'ok'arin hayewa gadon.
      “ji mana”. ‘yafad'a cikin izza’.
    Banza na masa zan haye gadon.
    Yace “iyim, bakije daddarawa ba kenan yarinya, saina sake kaiki yanzunnan....”.
      Kafin ya rufe baki nama iso gabansa na tsaya.
    d'agowa yayi yana kallona yana kur6ar fresh milk nashi, ya d'agamin gira d'aya.
     Baki na turo masa ina share hawaye.
     Ya kamo hannuna ya zaunar kusa da shi, “nikam yalla6iya karki haifomin abin cikin kwan da halin kuka, bana son ragwan taka, 'yata ko macece jaruma za'ayi, irin wadda labarinta zai zaga lungu da sak'o na duniya”.
    Harara na balla masa, yay saurin rik'e cup d'in hannunsa dayake zuba frash milk a ciki, “eh me, malama karkisa hantar cikina fitowa, irin wannan harara haka”.
      Kad'an yarage banyi dariya ba, da gaskiyar Momma, halin Galadima d'aya da Sauban, tsantsar harmutsine da sanya damuwa a rai ya lullu6e halinsa na barkwanci, hakan kuma yanada nasaba da rashin samun mai jansa a jiki yana d'auke masa kewa da rage masa rad'ad'in damuwarsa. Momma hankalinta nakan jiyyar Abie, Aunty mimi kuma rainon Sauban, mom kuma tayi aure lokacin dayake buk'atar makusanci, s.......
    Firgigit nayi saboda hancina da yaja, na kalleshi ina tura baki.
     “maida wuk'ar yalla6iya, abin bana fusata bane, wace duniyar kika tafi hakane da nisa inata magana?”.
      Marairaice fuska nayi ina shirin fara kuka, “please ka barni na kwanta barci nakeji”.
       Kofin hannunsa ya mik'amin, na waro idanu ina girgiza masa hannu alamar a'a”.
    Shima saiya waro nasa idanun yana fad'in “why?”.
      “kawai ni bazan sha bane, aje a zubamin wani abu”.
      “hakane kuma”. ‘ya fad'am yana kamoni ya jawoni jikinsa’.
     Saman cinyarsa na zauna, da hanzari nafara k'ok'arin mik'ewa. shima saiya kama hannayena ya maidasu baya yanda bazan iya kata6us ba, madarar ya d'auka ya guntsa da yawa a bakinsa.
      Waro idanu nayi ganin ya nufo bakina gadan-gadan, duk yanda naso kauda fuskata ya gagara, na datse hakwarana da sauri, shi kuma saya toshemin hanci, hakan yasa ni bud'e baki dole, dan ina buk'atar shak'ar numfashi. Tas ya juyemin fresh milk d'in abakina, sannan ya kuma rufe hancina saida na shanyeta sannan ya janye bakin, ni dashi duk muka hau sauke numfashi, kuka na sanya masa, amma hakan bai hanashi kuma guntsar madarba ya kuma juyemin a baki na, haka yayta min, ya kuma k'ara rabin kofi kuma, saida yaga ta kwalin ta k'are sannan ya sakarmin hannu na tashi zaune.
    Bansan kawai na fara kaima k'urjinsa k'ananun dukaba, ina fad'in wlhy sai ALLAH ya sakamin, kai bama zan yarda ba fa, saboda k'azanta kaita had'a yawunka da fresh milk kana d'uramin, ni bazan yardaba”.
       Shagala kawai yayi yana kallona, yakasa kare kanshi balle yunk'urin hanani, saida nayi mai isata sannan na fad'a k'irjin nasa ina raira kuka.
     Lumshe idanunsa yayi yasaka hannayemsa ya zagayeni sosai yana kuma sakani jikinsa sosai. Nima sainayi luf Ina shak'ar k'amshinsa da yariga ya mannema fatarsa.
     Munja wasu times a haka, ni ina kuka shi kuma idonsa a lumshe yana shafa kaina da saurarena.
    Jiyay kawai jikinta ya saki, alamar barci ya d'auketa, sai ajiyar zuciya da take ta saukewa, bud'e idonsa yayi, sannan yakai bakinsa a hankali ya sumbaci sumar kanta dake tare da danshin ruwa har yanzu. zafin zazza6inta dake ratsa 6argon jikinsa ya sakashi fidda huci yana kuma sumbatar kanta.
    Dr Farida ta sanar masa babu abinda zai hanata wannan zazza6in, koda tasha magani ya sauka saiya dawo, sai idan cikin yayi kwarine maybe ta daina ma gaba d'aya, amma mai juna biyu ba'a rabata da k'ananun ciwo makamantan haka. jiyay ya kuma k'aunar Momma d'insa a ransa, a hankali ya furta I love you my Momma”.
       Tashi yay d'auke da Munaya a hannu, ya kwantar da ita sannan yaja bargo ya lullu6a mata. tare da sunkuya wa ya sumbaci goshinta ya shafa cikinta da hannunsa sannan ya mik'e ya koma inda yake.
    Ya cigaba da aikin dayake a laptop Wanda ban fahimci komaiba a ciki, tsawon lokacin yana aikin, saida ya fara hamma sannan ya kashe. bayi ya shiga ya d'auro alwala, ya gabatar da nafila kafin yay shafa'i da wutiri yaja doguwar addu'a da kirari wa Ubangijin talikai, harda hawayensa sannan ya mik'e.
    Ya kuma daidaita hasken fitilar d'akin sannan ya hau gadon shima ya kwanta, yay musu addu'a ya shafe cikin munaya (😂Galadima saboda tsaro ba tsoroba ko🥺).
        a zatona zai rungumeta, sai naga ya gyara kwanciyarsa kawai a gefenta yaja bargo shima.
    Galadima asuba ta gari, (ni dai rungume nawa mijin zanyi aradu🤫🙈⛹🏻‍♀).
   
          Ga bannin asubahi zazza6in munaya ya sauka, hakanne ya sakata samun dad'in barci sosai, ta kuma kanainaye Galadima, wanda shi da kansa ya mirgino har inda take cikin barci ya rungumeta, dukda zafin zazza6inta nata ratsa nashi jikin yakasa barinta. ahaka kiran sallar farko ya riski kunnuwansu.
       Kusan a tare suka farka, ganinsu manne da juna yasaka kowa barin jikin d'an uwansa da sauri, munaya dai kunya ta sakata juya baya, amma boss ko a kwalar rigarsa, saima tashi da yayi yana wani ciccin Magani ya shiga toilet.
     Alwala ya yo, baiyi mata magana ba ya fice abinsa.
    Munaya ta raka bayansa da harara tana fad'in Girman kai dai rawanin tsiya wlhy. tashi tayi itama ta shiga bayin, amma sa6anin shi ita harda wankan gasa jiki (lallai kinji basawa Munaya🤭, wannan gasa jiki dabaya k'arewa haka🤥😂).
         Fitowa tayi tanata kumbura fuska, ni dai na lalla6a na shige bayinta danna dandalo arzik'i😝 lol (koya kukace fans🤷🏻‍♀😂?).


****************************

     Ban sake jin d'uriyarsa ba sai around 9:30am.
           Tashina a barci kenan na rarrafa zuwa bayi da k'yar nayo wanka, dan banajin dad'in jikina gaba d'aya, danan ya saki sai nan ya kama ciwo.
      Motsin mutum naji a bayana dan haka na waiga, Galadima ne cikin Farin wando da t-shirt itam fara tas, ya d'aure k'ungunsa da Navy blue d'in belt, sannan ya kawo jacket navy blue itama ya saka, babu takalma a k'afarsa, sai dai k'afar fes tamkar ba'a takata a k'asa, sai agogon azurfa mai k'yau d'aure a tsintsiyar hannunsa.
     hummm dan k'yau kam dai yayishi, sai dai ni bawai ya birgeni bane😏 (ho Munaya banda zuk'i ta malli dai🤥🤣😝🙆🏻).
        Janye idona nayi na maida kan gyaran gashina da nakeyi.
      Shima baice uffanba ya wuce wajen frigate, fresh milk ya d'akko yatako gaban mirror inda nake zaune.  a saman mirror ya ajiye kwalin madarar ya jingina bayansa shima, idonsa a kan gashina danake gyarawa. ya d'au madarar ya zuba a cup d'in daya d'akko tare da mik'omin.
     “ni ba ita zan shaba”. na fad'a ba tare da na kalleshi ba.
      “mikenan?”. shima yafad'a cikeda k'asaita.
      Yanzunma ban kalleshi ba nace “tea”.
      Kofin ya dire saman mirror yana tattare hannun rigarsa, “salon ki k'onamin idon abin cikin kwan kenan, to za6i ya rage naki, sha da arzik'i ko kuma d'ura”.
     Babu shiri na d'auki kofin na kwankwad'e, dama iyayine inajin yunwar.
     Kofin na mik'a masa ina 6ata fuska tamkar zan fasa ihu.
      Ya d'agamin gira yana fad'in “taimakon kai my friend”.
      Gefe nayi da fuskata ina fad'in “kai duk salon mugunta ka sani ai”.
         “martabar gudan jinina nake karewa”. yay maganar yana k'ok'arin ficewa.
     Baki na na ta6e ina harar bayansa, su gudan jini anji jiki kuwa.
    Ganin zai fice nai saurin cewa “nifa inason zuwa kitso, kuma zan koma school”.. 
          Tsayawa yay cak daga yunk'urin fitar da yakeyi, Batare daya juyoba yace “babu wannan tsarin a masarautar gagara badau”.
    Yana gama fad'a ya ida ficewarsa.
    Tamkar zan fasa kuka nayi jifa da cumb d'in hannu na ina fad'in “ina ruwana dawani tsarinku ni, makaranta ta nakeson komawa ehe”.
     Yana jiyota amma ko'a jikinsa yaci gaba da k'ok'arin fitarsa hankali kwance.



★★★★★★★★★


Tunda Aryaan ya shigo da gudu inna ta tareshi tana fad'in “kai lafiya? minene na gudu?”.
      “innarmu wlhy Uncle ne yace ki shirya mana kayanmu ni da Aiyaan zai aiko gobe a kaimu wajen Auntynmu”.
     Inna tayi d'an murmushi kawai, dan ita bata d'auki maganarma serious ba.
   Su dai su Aiyaan sunata murnarsu, sun tafi d'aki sun hau had'a kaya.
     Babu dad'ewa da yin haka saiga daddy ya shigo da sallama, inna ta amsa masa tana gyara zama, shima zama yay kujerar dake kusada k'ofa, ganin haka inna ta fahimci da magana yazo, dan haka ta maida dukkan hankalinta Kansa.
     Bayani yamata dalla-dalla akan zancen da su Galadima sukazo dashi, ya d'ora da fad'in “saiki shirya dan zamuje ai miki passport”.
        Inna tace, “amma dadynsu nake ganin ai da kud'in kukaje kamar zaifi”.
      Murmushi Dady yayi, yace “Ai'sha nasan miyasa kikeso zamewa, to ai kaf cikin matan yayan kece ya cancanta kije koda ace bawai Galadima ne ya biyaba, maganar ciwo Muke bawai jin dad'i ko gutsiri tsomar wasu ba, ki shirya dan zai turo wanda zamuje immigration office d'in”. daga haka ya tashi ya fice.
      Shiru kawai inna tayi, itadai inda ta itace da antafi da ko innaro, dan tasan wannan tafiyar dukda ta ciwoce sai ta janyo 6acin rai a gidan.
 
      Aiko tamkar inna tasani, dan ana fad'ama innaro tace “bata amince ba, ita ta haifi auwalu kuma da ita za'aje tayi jiyyar yaronta, bazata bama kowacce mace acikinsu wannan ragamarba.
     Shiru baba k'arami da daddy sukayi, taci masifarta ta gama tayi shiru.
     Baba k'arami yace, “amma dai inna kinsan jinyar Yaya sai da matarsa a kusa, kekuma k'arfinki ya k'are ya za'a d'ora miki d'awainiyar da matansa ne keda hakki a kai?”.. 
      “yo d'awainiya ba tare da kai za'a tafiba? Kai basai kamasa ba. ni dai fa ban amince Ai'sha tajeba, dan wlhy bazan ta6a son Ai'sha ba komi zata zama, tunda dai ta silar jikokinane balle amin ilimi. k'ilama itace ta jefeshi dan taga ta kama k'asa 'yarta Na auren d'an Sarki, t........”.
    “innaaaa! haba mana, dan ALLAH karma ki bari maganar nan ta fita, waishin minene laifin Ai'sha a gareki? duk cikin matanmu banga wadda take girmamaki da d'aukarki matsayin uwaba irinta, inna ya kamata wannan k'iyayyar ta koma soyayya hakanan, a baya kince dan basuda asali, kin dawo kince juya ce bata haihuwa, gashi kuma yanzu har ALLAH zai fidda jikoki daga tsatsonta, to miye kuma matsalar?”.
       “toko zaka shak'eni Na fad'a makane Hameesu?”.
      “a'a inna, ALLAH yabaki hak'uri”.
      “kaidai ka Sani, ni yanzu bara Na tashi Na shirya Ku kaini inama kace, imagesa nema ko uwarmi oho”.
    Daga Dady har baba k'arami babu Wanda ya tanka mata, tana shigewa baba k'arami ya mik'e yana cema dady “yaya ka jireta, bara naje mutafi da maman 'yan biyun, kota fito kace naje shiryawa ne”.
     Kai Dady ya kad'a masa yana murmushi, baba k'arami ya fita da hanzari.

     Bayan wasu mintuna saiga innaro an fito ana warware gyale za'a yafa, “yauwa jafaru muje Na shirya”.
    Habiba dake kitchen tana girki duk diramar da ake tana saurare ta tuntsure da dariya, lallai tsohuwarnan akwai daru, mama Na hanya ai, itace maganinki (gwaggo Safiyya mamarsu).
      Kallonta Dady yay yana murmushi, yace “to inna mu jira jafar d'in yaje shiryawa”.
     “ato shikenan bara kafin ya dawo nad'anci abinci, k! Habiba zubomin idan abincin nan ya tsotse, gara Na fita cikina da d'an nauyi”.
     Habiba ta had'iye dariyarta sannan tace “innaro bai tsotseba, amma nanda kamar dai minti 5”.
        “babu damuwa ai, nasan jafaru ma bai dawoba harnaci, kinsan shi da dak'undar shiri, ya tsufa amma kullum kallon kansa yake sa'ar Abdul-hameedu”.
     Dariya Dady ya had'iye da k'yar, yasa handkerchief yana toshe baki dan karta fito.


★★★★★★★★

      Tsaf na kammala shiryawa sannan Na kimtsa d'akin, ni dukfa a nufina nayi shirin asibitine.
     Fitowa nayi dan naga ko yana falone, wayam babu kowa, sai sallama da nakeji a bakin k'ofar, amasawa nayi na bada izinin shigowa saboda naji muryar matane.
      Su 10 ciff suka shigo, k'asa suka zube suna gaisheni, Na amsa musu da 'yar sakewa, “lafiya dai?”.
     “lafiya lau ranki ya dad'e, mune zamu kasance hadimanki, masu miki dukkan hidima.
    Nifa wlhy banason wasu bayi, amma dolene Na barsu tunda wad'ancanma Galadima ne yace su tafi, yanzu kuma baya wajen, ni kuma banida ikon korarsu tinda bansan kan abinba.
     Amsa musu nayi da “to” sannan nawuce Na zauna a kujera.
     Tasowa sukai suka biyoni, a tsanake suka dinga fad'amin sunansu da aiyukan da zasuyi.
     Wad'anda naga bazan iya yarda suyiba Na canja musu aiki. Sallamarsu nayi, Ina k'ok'arin tashi Na shige ciki saiga Sauban ya shigo, duk zubewa sukayi suna kwasar gaisuwa a gareshi, ya amsa musu yana wani yatsine face, sai kuma ya basu izinin tafiya, fita sukayi harabar sashenmu.
     Na kalleshi ina murmushi, “ashe kaima dai sarautar Na jininka yaa Sauban? Wanda bai saniba saiya d'auka duk bazaka iya wani Abu daya shafi sarautaba”.
      Dariya yayi yana zama, “aunty gimbiyar mu kenan, wannan ai sai mijinki”.
    Nima murmushi nayi kawai.
      Ya mik'omin kayan hannunsa yana fad'in “ga break fast d'inki”.. 
        “wayyo yaa Sauban, nikam dai nagaji da ciye-ciyennan ma, zuwa zanyi Na fara abinci da kaina”.
      “wlhy dakin taimakemu Aunty gimbiya, mijinki shiya saba da cin abincin waje shiyyasa bai damu ba, ya kamata kafin Na wuce gobe naci girkinki”.
       “kamarya gobe? Kana nufin zaka koma kenan?”.
      “tab da gudu kuwa, aini bazan iya zaman k'asarnanba Na tsawon lokaci, tarema zamu wuce da Abba ai, harma da innarmu, yaa Sam bai sanar dakeba kenan?”.
    Baki bud'e Na girgiza masa kai alamar a'a.
     Sauban yay murmushi, “kinsan halin Galadiman namu ai, soyake yamiki surprise maybe, yanzu hakane yaje cuku-cukun visa d'insu ne. waito miyasa bazamu koma tare da kubane?”.
     Murmushin yak'e nayi, nace, “maybe akwai ayyukan dabai gamaba shiyyasa”.
       “inaga hakanne kam, ni bara naje, yace Na iskeshi birnin gayu, ga mahfuz can Na jirana”.
      “ok sai kun dawo” Na iya cewa, danni daga 'yan matan masarautar har samari ba kowa Na saniba, tunda time d'in daya kamata nad'an San mutane sai muka tafi India. ni bama nason Na saba da kowa, ni da ba zama ya kawoni ba.
      Maganar fita da Abba da Galadima yakeyi sai yayta cin zuciyata, kimar Galadima da darajarsa saita cika zuciyata, inason mahaifana, kuma dukkan Wanda zai nuna musu kulawa bazan manta da shiba, harda 'Yar kwallata Na share, Na tashi Na koma bedroom ba tare da nayi break fast d'inba ma.


*****************************

     Innaro dai tun ana jiran dawowar baba k'arami harta fara gyangyad'i, habiba data kammala abincin ta d'ebo ta kawo mata, nuni Dady yay mata akan ta koma.
    Habiba ta koma da baya ba tare da ta k'araso falonba.
    Tun tana gyangyad'i harta 6ingire a kujerar barci mai nauyi ya d'auketa (ho innaronmu ta mutunci🤸🏻‍♀😜).

     Baba k'arami da innarsu munaya kam tuni sunyi ficewarsu, dayake Abu Na kud'i dandanan aka gama cuku-cukun komai, Nuren ne tsaye, saida komai ya daidaita suka samu visa d'insu a hannu sannan suka fito.
     Har gida ya maidosu ya koma suna jera masa godiya da addu'a shi da Galadima.

     Innaro daga gyangyad'in jiran abinci ya tsotse aka zarce da barci mai nauyi, shima Dady lalla6awa yay ya fito dan asibiti zaije.
    Tafiyarsa babu dad'ewa saiga gwaggo Safiyya ta iso da yaranta biyu.
     Hayaniyar su Dahiru ita ta tada innaro, ta mik'e zumbur tana fad'in “yauwa Jafaru kadawo mu tafi ko? Habiba bar abincin kawai idan muka dawo naci.
        Mi Dahiru da Naja'atu zasu ba dariya ba, suka shiga shek'ama innaro dariyar shak'iyanci. Wai kota kwanta da yunwa ne.
     Zaginsu ta hau yi ta d'auki filon kujera tana dukansu.
   Sai da gwaggo Safiyya ta musu magana sannan suka nutsu, “inna ina zakuje da Jafaru ne?”.
      Gyara zama innaro tayi tashiga bama gwaggo Safiyya labari.
     Murmushi kawai gwaggo Safiyya tayi, danta gane wayo suka mata suka gudu kawai, itama sai tace “to inna ki cigaba da jiransu, k'ila dan sunga kina barcine suka jira ki tashi sannan Ku tafi.
     Da wannan gwaggo Safiyya ta rufe bakin innaro ta zauna jiran su dady.


    Aiki🤣🤣😝.



**********


        Galadima daya fita kai tsaye asibiti ya nufa, su yaa hameed kawai ya iske can, dan dady ya hana matan gidan zuwa sai anjima, doctors Na complain akan suna cika wajen da yawa.
    Cikin mutunta juna Galadima ya gaisa dasu yaa sabi'u sannan yashiga yaga daddy.
     Yau kam Alhmdllh dan ba barci yakeba, kumbirin fuskarsa kuma yad'an sa6e kad'an, saidai baya iya magana sai dai yayta bin mutane da idanu.
    Dukda bazai iya amsawa ba haka Galadima ya risinna ya gaidashi, tare da masa fatan samun lafiya sannan ya fita office d'in doctor.
    Bayan sun gaisa doctor ya bama Galadima file d'in bayanan Abba dasuka tattara.
    Kar6a Galadima yayi ya duba, dukda bawai ya fahimci bayanan bane, ( kusan dai rubutun doctors sai su). Suka d'an tattauna akan cigaban da aka samu sannan Galadima ya fito.
     Ya iske daddy ya iso, suka gaisa sannan yamasa dukkan bayanan da doctor yamasa shima. Dady ma yaji dad'in cigaban da aka samu.
    Galadima yay musu sallama ya fito.

   Guntun tsaki yaja saboda yanda jama'a suka wani zuba masa idanu tamkar sunga magiji, da sauri wani dogari ya bud'e masa motar ya shiga, sannan suma suka shiga.
     Daga asibiti Galadima yace su wuce birnin gayu plaza.
    Cike da girmamawa sarkin mita ya amsa da to.
     Maida kansa yayi jikin seat ya kwanta tareda lumshe idanu ya fad'a duniyar tunani................✍🏼



   Barkanku da juma'a💋💋💋🤝🏻.



Musha weekend lafiya sisters⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀😄.





*_ALLAH ka gafartama iyayen mu_*🙏🏻😭


*_Typing📲_*



    *_Haske writer's asso...._*💡



     
     *_♦RAINA KAMA......♦_*
              _{Kaga gayya}_



             *_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻

_________________________
            _Duk marubucin daya kafa alk'alaminsa bisa takarda tabbas yagama tanadar yanda labarinsa zai kasance ne, amma sai wasu wabubuwan mamaki kaga sun gaza k'arewa a social Media, ban saniba ko samunmu available ne yakesa a kullum kuke mana kallon marasa aikinyi?, ni dai nasan time d'in dana shirya labarin RAINA KAMA ban zauna tebirin shawara da kowaba a online, inkuwa hakane tayaya wasu har suke tunanin nafara sauka akan layin labarin?, to magana d'aya zanyi a wannan ga6ar, ban gina labarin Raina kama akan kwanciyar aure bane, dan haka masu maganar  munaya bata da aiki saima Galadima rashin kunya saisu jira saina kai k'arshen labarin kafin su k'alubalanceni, abin dariya, (wai aikina kenan daga nasa munaya ta murgud'a baki sai ta harari Galadima da masa k'unk'uni) tunda aikina kenan babu lallai wajen 6ata lokaci karantawa, haka Na tsara labarina tun farko kuma haka zanyi, duk wanda yaga bai masaba zai fara iya rubuta nashi shima kawai. wannan abun da kukema writer's yana 6ata mana rai, bai kamata ku dinga k'alubalantar writer's ba, bayan su suke da masaniyar yanda suka shirya labaransu, idanma zakuyi saiku ringa tanadar lokaci har zuwa bayan mun kammala, hakan zaifi tasiri fiyeda katsalandan a tsakkiyar labaran mu, akoda yaushe kuzama masu kula kafin Ku k'alubalanci mutum🤷🏻‍♀._
     *Ba akan kaina kawai nayi wannan bayaninba, harda sauran writers da yawa da akema makamancin hakan koma fiye da nawa.🙅🏻*

_____________________________


  ~Book 2~ 👉🏻1⃣0⃣➖1⃣1⃣


         
  ...................Koda motocin suka tsaya sarkin mota ya bud'e masa k'ofa yakai tsawon lokaci baiko motsaba, saboda tsantsar tunani da zuciyarsa ta lula, aduk sanda zuciya take cikin matsanancin matsi gangar jiki ma gazawar karfin ikon jini dana 6argo sukan mata k'aranci, shi kansa yasan yanada buk'atar mataimaki a kan wannan lamarin, amma k'arancin rik'on amana Na d'an Adam ne yake yawan gargad'arsa da taka masa birki, ba kowane zai fahimci ma'anar nok'ewar tasaba, sai mutum daya tsinci kansa a makamancin halin da yake ciki.........
        “Ranka ya dad'e mun iso”. Sarkin mota yasake fad'a cikin taraddadi da taka tsantsan.
      A hankali Galadima ya bud'e idanunsa da suka koma launin jaa saboda damuwa a kan sarkin mota, batareda yace uffanba ya ziro k'afarsa k'asa yana cije lips da had'iye wani kududun damuwa a mak'oshi.

    Tunda ya fito ma'aikatan wajen suketa masa sannu da zuwa, dan tunda ya shigo k'asar sai yanzu ne zai shiga cikin plaza d'in.
    Hannu kawai yake iya d'aga musu, amma bakinsa yay masa nauyi, kallo d'aya kuma zaka masa ka nazarci damuwa da buk'atar hutun dake tartare da kuzarinsa.
      A cikin plaza d'in ma bata sauyaba, d'aga hannu agaresu shine yazama linzamin amsa gaisuwar dasuke masa.
    Da hannu yayma d'aya daga dogaransa nuni da amso masa key.
     Da sauri dogarin ya amsa yana mai nufar sashen da zai kaishi office d'in Saleem mai kula da CCTV camera's.
    Sai dai kafinma yakai ga k'arasawar suka had'u da saleem, Wanda tun shigowar motocin Galadima ya gansa.
     Keys d'in ya damk'ama dogarin, sannan ya k'araso domin mik'a gaisuwa ga ogansa na wajen aiki kuma magajin garinsa.
    Shima d'in dai hannu Galadima ya d'aga masa, hakan kuma ya saka Saleem fahimtar akwai damuwa kenan.
            Koda aka bud'e ya shiga saiyayma dogaransa nuni da suje kawai, sannan ya maida idanunsa ya lumshe tareda kwanciya jikin kujerar yana lilawa a hankali.
     Shi kansa baisan tsawon lokacin daya d'auka a hakanba, amma tabbas yasan yashiga kudin nazari mai zurfin gaske. Knocking d'in k'ofar da akayi yasakashi bud'ar baki da k'yar ya bada izin a shigo.
    Nuren daya shigo ya maida k'ofar ya kulle, kafin ya ida takowa cikin office d'in, idonsa nakan d'an uwannasa.
    Zama yay a d'aya daga kujerun dake fuskantar Galadima,  “brother what happen?”.
      “Northing”. Galadima ya fad'a batare da ya bud'e idonsa ba.
    Shiru kawai Nuren yayi shima, ya d'akko laptop a briefcase d'in daya shigo da ita, kunnawa yay, kusan mintuna biyu ya d'ago ya kalli Galadima, sai kuma ya maida kansa ga laptop d'in. “Sameer nasan kaga cigiyar da akeyi takowacce kafar yad'a labarai ta k'asarnan akan d'iyar minister, sannan jami'an tsaro tsaye suke akan binciken inda take. yakamata musan abinyi kafin lokaci ya k'ure mana”.
     Guntun murmushi Galadima yayi, batareda ya bud'e idanunsa ba yace “Nuren indai har babu wata waya datake aiki inda kakai yarinyarnan, kuma ka cire sim card d'in phone nata a lokacin daka d'auketa, to babu wata hanya dawani jami'in tsaro zai ganota, dama hanya d'ayace da kuskure zai basu damar bibiyarta, na d'aya lokacin daka d'auketa yazam wayarta na aiki, tabbas zasubi ta wannan hanyar su gano har iya inda ka kashe wayar, hanya ta biyu itace ka kashe wayarta baka cire sim card d'in ta ba daga phone nata, koda wayar a kashe take zasu bibiyeta ta hanyar 📡 su ganota” ya tashi zaune sosai yana bud'e idanunsa akan Nuren, “wannan hanyoyin biyu kawai ke garesu saikuma idan da camera tare da ita, idan duk babu wannan basuda wata hanya, ka kwantar da hankalinka my brother, komaina da tsarinsa right?”.
       Murmushi Nuren yayi, kafin ya salute d'in Galadima yana fad'in “I thrust to you my dear broth”.
       Shima galadima salute d'in Nuren d'in yayi yana murmushi.
    Komawa yay ya sake kwanciya jikin kujerar, “yanzu inaga time d'in turama minister Massage yayi?”.
     Cikin zaro idanu Nuren yace “baka kallon hakan a matsayin ganganci kuwa?”.
     Baki Galadima yad'an ta6e yana crossing k'afarsa, cikeda izzarsa yace “sai idan nabama wani damar hakan ai”.
      Nuren baice komaiba, dan yagama sanin hatsabibancin Galadima wajen iya sarrafa Computer, dan haka ya bar wannan zancen ya d'akko wani. “yauwa to maganar Malam Saminu fa? Kasan yana hannunmu fa har yanzu?”.
      “wannan barsa saiya kuma magantuwa, dan da alama yasan wani Abu, saidai akwai abinda ya sakashi za6ar 6oyewa. ni yanzu damuwar 6atan Muftahu yafi damuna, nasaka camera's jikin mutane 10 danake iya zargi a masarauta amma banga alamun da hannun koda mutum d'aya ba, hakan ya tabbatar min da gaske Muftahu na bibiyar lamarina, sai dai bansan dalilinsa ba, ko kuma waye sakashi?”.
         Nuren ya jinjina kansa, “brother aini da Harun dama mun dad'e da zargin Muftahu, Kaine kawai kake masa kallon mutumin kirki daman”.
     Lips kawai Galadima ya cije, amma baice uffanba, Nuren yaci gaba da 'yan danne dannensa a laptop d'in, zuwa wasu mintuna batareda ya d'agoba yace, “maganar Sirikinka fa?”.
     Shiru Galadima ya masa, saida ya mula dan kansa sannan ya murmusa tareda maida idonsa ya lumshe, “a daren jiya nagama da wannan matsalar, sim card d'insa 3, akwai Contact 300 da 38, mtn yanada mutum 172, ya fara saka credit a layin shekaru 15 kenan, ranar 3/6/2005, glo 107, ya fara amfani dashi shekaru 8 kenan, wad'annan sune Sim card d'insa da yake mu'amulla da kowa a ciki, kuma anfi saninsa da su, akwai 6oyayyen layinsa Na mtn shima, yafara aiki dashi shekaru 13 kenan, kuma mutane 59 ne kawai acikinsa, sannan ba kowane yasan layinba, dan dukkan family nashi basu San da zamansa ba,  ita kanta mahaifiyar su Munaya batasan anyi saving number a phone nata ba, suma da suka kirata basusan da number a wayarta ba, dan baita6a kiranta da shiba, akwai matakan tsaro dake tattare da Layin, hakanne ya tabbatar min da akwai abinda yake 6oyewa a Sim card d'in, dan sai time to time yake amfani da shi, kiran matarsa da sukayi da layin wannan shine kuskuren farko da suka tafka da Sameer ya samu hanyar musu takun sauro. zan fara aiki akan layin na shigesu ta hanyar da basu zataba”.
      Jinjina kai kawai Nuren yakeyi dan mamaki, Galadima da banne, kamar yanda basirarsa take daban, ya sauke ajiyar zuciya yana kama hannun Galadima da idonsa ke a lumshe har yanzun, cikin karsashi yace “lallai kai RAINA KAMA ne Sameer”.
      Murmushi kawai Galadima yayi, amma baice uffanba.

      Knocking akayi, Nuren ya kalli k'ofar yana bada izinin a shigo, Sauban ya shigo da sallama, su duka idonsu a kansa, Nuren yace “lafiya kuwa?”.
     Zama Sauban yayi yana sauke Numfashi da k'yar, cikin magana d'ai-d'ai da alamar a birkice yake yace, “wlhy Yaya binmu aka ringayi da wata bak'ar Jeep, da k'yar mukasha wlhy, ni dai yau zanbar k'asarnan gaskiya”. Sauban ya fad'a tamkar zaiyi kuka’.
       Gani kawai sukai Galadima yana dariya, saida yayi mai isarsa sannan ya tsagaita.
     Nuren da Sauban suka tsaya kawai suna kallonsa.
     Tashi yayi tsaye yana takawa cikin izzar k'asaita, ya dafa bango yana lek'en waje ta window d'in office d'in, yakai wasu adadin lokuta a wajen, sai kuma ya juyo yana kallon Nuren d'in da Sauban da suma suka zuba masa idanu.
      “my dear brother! daka tsaya sun kamaka ai, tabbas da wannan shine kuskuren da zasuyi Wanda bazasu ta6a mantawa da waye Muhammad Sameer Saifudden ba a tarihin rayuwarsu. Waya gaya maka kana yawo cikin 9ja ne batareda idon Sameer ba a kanka?”.
     Sauban ya sauke ajiyar zuciya yana share gumin daya jik'a fuskarsa, “wlhy yaa Sam daka fad'amin da bazan tsorata ba”.
     Daga Galadima har Nuren dariya suka kwashe da shi, Nuren ya dafa kafad'ar Sauban yana fad'in “matsoracin banza”.
      “uhm-uhm yaa Nuren bazaka ganeba wlhy, tsoro halak ne fa”.. 
      Galadima dai baice komaiba ya koma ya zauna yana murmushi.



★)))*(((★)))*(((★)))*(((★)))*(((★


        Ganin har anyi sallar Magriba babu baba k'arami balle Dady ya saka Innaro d'aukar gyale ta fito, lokacin gwaggo Safiyya tana salla, shiyyasa batasan innaro ta fitaba, habiba da Naja'atu dake tsakar gida suna tattare kaya saboda hadari na farkon damina dayake nuna alamar zai zubda ruwa. suka kalli juna, Naja'atu tace “yaya habiba tsohuwarnan fa bata da dama wlhy”.
     Dariya habiba tayi, “ai kad'anma kika gani Naja'atu, yanzu dai zataje ta tadama baiwar ALLAH hankali”.
      “to ALLAH ya k'yauta”. ‘cewar Naja'atu tana rik'e ha6a’.

      Lokacin da Innaro ta shigo gidan d'akin Innarsu Munaya ta nufa kai tsaye, sai dai ta iskeshi rufe, kwala kiran sunanta ta shigayi cikin masifa, “Ai'sha!! Ai'sha!! Nasan kina jina, wlhy ki fito kafin yau d'innan igiyar aurenki ta tsinke”.
        Mamansu yaa Hameed da gwaggon Haleematu ne suka fito, mamansu yaa hameed tace “aiko tafita fa inna, dan gab da magribar nan naga Fadeel ya shigo sun fita, bansan mike faruwa ba dai”.
      “yaza'ayi kusan mike faruwa tunda anyi k'ulle-k'ullen munafunci, lallai jafaru, wai yau da kaine za'a muzantani hannun mak'iyana, to nikuma naga ta yanda Ai'sha zataje wata k'asa jiyyar Auwalu da raina”........ haka taita zuba banbamin masifa matan gida na saurarenta, daga daddy har baba k'arami suna gidan amma sukak'i fitowa. Jarabar Innaro ta saka kowa na gidan fahimtar mi ake ciki, nanfa hassada da bak'in ciki suka kume zukatansu, dukda kuwa sunsan tafiyar bata dad'i baceba, maman fauziyyace kawai hakan yamata dad'i, koba komai inna ta huta da cin zarafin Innaro koyayane.

       Sai da Gwaggo Safiyya ta shigo tama Innaro magana sannan ta tafi gida, su matan gidanma sai yanzu suka San da zuwa gwaggo Safiyya d'in.
     Amma sunso ace innarsu munaya na gida Innaro tayi wannan rashin mutuncin.

   
    Hummm😕.



****************************


        Bayan fitowar su Galadima daga birnin gayu, sun wuce gidane, Nuren kuma yakoma hotel d'in daya sauka.
         Galadima kawai ne ya shiga sashensu, amma Sauban 6angaren mai martaba ya nufa neman yarima Mahfuz.
     
     Munaya na zaune a falon farko tareda sabbin kuyanginta guda uku, (dan bata amince su shiga falonta ba, saita gama tantance su sannan) ba wani hira sukeyiba, d'ayace a cikinsu ke sak'a shine abin ya birge Munaya take kallo, tana kwance cikin doguwar kujera ne, yayinda su kuma su ke zaune a k'asan lallausan carpet d'in falon.
      Dogarai biyune suka fara shigowa hannunsu d'auke da ledoji, sai kuma mai gayya mai aiki Galadima.
     Da sauri bayin suka mik'e tsaye, saida ya ida shigowa sannan suka d'urk'ushe a k'asa suna kwasar gaisuwa.
    A la66ansa ya amsa yana d'aga musu hannu, yayinda idanunsa ke kan munaya da itama ke satar kallonsa
       Duk d'insu kowa janyewa yayi, yayinda bayin da dogaran suka fice bayan sunkai ledojin falon Galadima.
     Baice da ita uffanba yafara takawa zai shige, tamkar mai tsoron fad'a tace, “sannu da zuwa”.
    Ysayawa yayi cak, sannan ya juyo da kansa tamkar mai ciwon wuya ya kalleta, bata yarda sun kuma had'a idoba takuma fad'in “nagode sosai”.
     “for what?”. ‘ya fad'a cikin isa’.
      Shiru munaya tayi, ta kasa cewa komai.
    Shima bai sake cewa komai ba ya taka ya shige abinsa.
      Harara munaya ta raka bayansa da shi, sai kuma ta sauke numfashi tana tashi itama, bedroom d'inta ta koma, a saman sofa ta zauna tana dafe kai, sosai take buk'atar zuwa sake duba mahaifinta, amma ta kula Galadima bashida niyyar cemata taje, kai itako wannan wane irin abune haka? shi dama gidan Sarautar haka yake bakada 'yancin kanka?, komai saida k'a'ida. tun d'azu kuma take kiran number inna bata d'agaba, tadai kira baba k'arami da daddy sun gaisa ta tambayi jikin Abba, shine ma har suke kuma sanar mata k'ok'arin da galadiman keyi. tabbas hakan da yayi yasata jin farin ciki, koba komai tasan shi adaline, ko anan gaba ragamar shugabanci ta riskesa zaiyima na k'asa da shi adalci.


       Galadima daya shiga tun a falo yafara k'ok'arin cire navy blue d'in jacket d'insa, ya wullata saman kujera, sassauta belt d'in yayi shima amma bai cireba, ya zauna cikin tsantsar nuna gajiya yana furzo iskar bakinsa, remote ya d'auka ya kunna tv, tamkar ya saita lokaci saiga hoton d'iyar minister mai amsa sunan Farhat ana nunawa, an saka 2.5 millions ga dukkan wanda ya kawota koya bada bayanan sirri akan wanda yasan wani Abu akan 6atanta.
    Wani mugun tsaki Galadima yaja a zuciyarsa yana fad'in wawaye, saiku k'ara yakai 100millions ba 2 ba, idan ubanta ya shirya kawo kansa gareni nima a shirye nake nabashi shashashar 'yarsa mai zubin ta6arya, ya kashe TV d'in kawai ya mik'e ya shige ciki.
    Ko ina fes da shi, yasan baida Matsala da Sauban a 6angaren tsafta dama. kayan jikinsa ya ida cirewa ya shiga wanka.
     Bayan ya fito samu yay yad'an kwanta, dan ya samu Hutu kona 2hours ne, dan yanzu akayi sallar zuhur. aiko kwanciyarsa babu dad'ewa barci yay gaba dashi.

     Munaya ta jawo wayarta da nufin kuma kiran inna, amma sai taga Ashe credit d'inta yama k'are, kanta ta dafe dan haushi, zuwa can tamik'e domin bin shawarar zuciyarta. turare ta kuma fesama jikinta ta d'auki gyale ta yafa.
         Ta d'an dad'e a k'ofar d'akin tana tunanin idan kuma ta shiga hasashenta bai zama gaskiyaba  ya kenan?, wata zuciya tace kije abinki k'ilama wanka yake.
    Da sand'a na ida shiga tamkar wata 6arauniya, sai kuma na tuna ai yanada CCTV camera, nutsuwa nayi na daidaita kaina, na koma normal saboda tsaro. Ganin babu abinda naje nema d'in a falo saina zarce bedroom ina wani ciccijewa.
    Mamaki ya kamani ganinsa kwance a kan gado yana shak'ar barci hankali kwance, hakan yamin dad'i kam.
     Saida nabi ko'ina na bedroom d'in da kallo, ganin babu alamar akwai camera a nan saina ida shiga, wayoyinsa biyu na ajiye gefen filon dayake kwance, rabin hannun damarsa ma nakan d'aya ya d'ora cikin barci halan?.
       Dole saina hau saman gadon, dan haka na tsaya tunanin yanda zanyi, banida wata mafita dan haka nahau a hankali, kai kace wata hawainiya ce.
      Cikin rintse ido da cije la66a nakai hannu zan d'auki wayar d'aya.
     Caraf aka rik'emin hannu, babu Shiri na bud'e idona zuciyata nawani tsitstsinkewa.
     Fisgoni yayi na fad'o jikinsa, zafin danaji ya sakani sakin k'aramar k'ara.
          Ya matseni a jikinsa batare da ya kula miya aikata ba. nikam jikina sai rawa yakeyi, tsorona karya d'auka ko cutar da shi zanyi ma........ maganarsa cikin yanayin barci ta Sani kallonsa.
     Kad'an ya bud'e idonsa dake jajir, alamar da gaske barci yakeyi, muryarsa a sark'e irinta barci yace, “sata kika koma?”.
     Baki na tunzuro ina marmar da idanu da suka cika da kwalla, nace “ALLAH ya kiyaye, arafa zanyi”.
      Kuma matseni yayi har saida na rik'e hannunsa,, yace “wannan ba aro bane sata ce yalla6iya, dan haka dolene ki kar6i punishment”.
     Jin ya ambaci punishment saina kuma rikicewa, nahau k'yarma ina rantse-rantae da matso kwallan idona.
     Bai wani saurareni ba ya hau sumbatar wuyana, tureshi nafarayi amma saina gaza, dan haka na koma mintsini, shima a banza man kare😩.
       Dukna d'auka wasa yakeyi kawai farfaganda Ce danna tsorata, amma saina tsinci ya fara sakin layi, iya yina da rok'o, yakushi, mintsini, ban samu ku6uta ba, saima salonsa yafara tasiri a kaina, nima nai luf harda k'ok'arin maida murtani. saida naji zai kama wata tashar nai azamar tsaidashi ta hanyar fad'in “please yalla6ai camera”.


       Maganinki ai baby😝, su Galadima akwai bak'in wayo dai🤥😂, idan ta gaskiya za'abi ni banga abin punishment anan ba🤣, dama yadawo 'Yar matsalarsa dai tsautsayi ya kawo mai karanbani dason banza ta fad'a tarko😜🥳😆.

**********★********



     Koda inna ta dawo saita had'ama su Aryaan kayansu, da nufin su koma wajen mamansu yaa hameed harta dawo.
     Amma suka tibire akan bazasu jeba, su Uncle yace zaizo ya kaisu wajen Auntynsu.
    Tun inna na lallashinsu harta kai ga mammakesu suka fara kuka, daga nan sukai barcin dole.
    Bata fasa had'a kayanba, tagama tsaf ta d'auki akwatin zuwa d'akin mamansu yaa hameed.
    Su Bintu kawai ta iske a falo suna kallo, Aminu ne yace “innar 'yan 2 ina zaki da daddare?”.
    Murmushi inna tamasa tana fad'in “kayansu Aryaan ne Aminu........”
    Bata gama rufe bakiba mamansu yaa hameed ta fito. ganin innarsu munubiya da kaya saita had'e fuska. Inna bata damuba tace “ga kayansu Aiyaan, saisu dawo nan da zama kafin na dawo”.
    “to”. Kawai mamansu yaa hameed tace tana kauda kai gefe.
   Ran inna ya sosu, amma sai batace komai ba ta ajiye ta fice jiki a sanyaye.
    Da murnar Haneeff ya tashi zai d'au jakar yakai d'akinsu, amma sai Maman ta watsa masa harara. babu shiri ya koma ya zauna. Jakkar dai sai anan ta kwana, bata d'auka ba, bata bar 'ya'yanta sun d'auka ba saboda bak'incikin inna zataje jiyyar Abba ba itaba.


   ALLAH ya k'yauta😡.




****************************

     Dakatawa yay daga abinda yakeyi, ya bud'e idanu a hankali akan fuskata, murya k'asa-k'asa ya furta “camera?”.
      Kaina na d'aga masa batareda na bud'e idoba.
    Bai kuma cewa komai ba ya koma ya kwanta yana furzar da huci mai zafi daga bakinsa, sai kuma ya cije lips yana gyara kwanciya da sake rungumeni kawai.
    Idona na bud'e a tsorace, azatona zai cigaba ne, sainaga ba haka bane.
    A cikin kunnene ya furta “barci please”.
    Kallonsa nayi ta gefen ido sai naga idonsa a rufe, nima banida za6in daya wuce na rufe nawan, dan haka na lumshe kawai.

       Ni sai barcin ya d'aukeni, amma shi ya k'auracema idonsa, mamakin furicina ya dami zuciyarsa, dama yadad'e yana zargin akwai camera a d'akin nan nasa, sai dai bawai ya tabbatar bane, kuma bai ta6a yunk'urin dubawa ba. da wad'annan tunanin ya cinye lokacin barcinsa har aka kwala kiran sallar la'asar.
    Bud'e idanunsa yayi akan fuskata, yad'an tsuramin ido nawasu time's, sai yaga barcin yamin k'yau, kauda idonsa yayi cikeda basarwa, saikuma ya janyeni daga jikinsa yana yunk'urin tashi, hakanne ya sakani farkawar nima, na tashi da hanzarina ina gyara rigata, sai kuma na sauka na fice batareda nako waiwayoshi ba.
    Bina yay da kallo harna fice sannan ya janye yana ta6e baki.


       Ban kuma jin labarin Galadima ba har dare yayi, nafito wanka ina shirin barci ya shigo, yau dai babu laptop d'in kaddara, dagashi sai phone guda d'aya ma, yana sanye da kayan barci kalar gwaiduwar kwai masu duhu.
      Zama yay a kujerar dake cikin d'akin, yayinda ni kuma na k'arasa saka hijjab d'in dana jawo, babu walwala ko alamar wasa kwata-kwata a face nashi, dan haka nima saina kama kaina.
       cikin k'asaitarsa yace  “muyi magana mana”.
     Kallonsa na d'anyi, saikuma na amsa da “ina jinka”.
    d'ago ido yay muka kalli juna, da ido yay min nuni da bakin gadon.
   Ban musaba nazo na zauna, amma sai nayi k'asa da kaina ina wasa da zoben hannuna.
      Maida kallonsa yayi ga zoben danake jujjuyawa, kusan mintuna 4 harna d'auka ya ma fasa maganar, na d'ago na kalleshi.
       Ya kauda kai gefe yana fad'in, “waya fad'a miki da CCTV camera a d'akina?”.
       Nima ban kalleshi ba na bashi amsa a tak'aice, “bakai ka saka kayarka ba danni?”.
    Da mamaki ya kalleni, sai kuma ya kausasa muryarsa, “Munaayaa seriously nake miki magana!”.
       nad'an razana, amma saina dake, nace “kana nufin bakasan da itaba?”.
     “idan nasan da ita mizai sani aikata wani Abu na sirrina  a d'akin”.
     da mamaki na kalleshi domin tabbatarwa, tsantsar gaskiya na hanga a idonsa, dan haka na danna yatsun hannuna da k'arfi suka bada sautin “k'asss!, k'asan zuciyata na tunanin minene sirrin nasa?”.
      Idonsa a kaina ko k'yaftawa bayayi, nima na d'ago mukaima juna kallon ido cikin ido, dukda tsorata danai da hango masifa cikinsu ban janyeba, nafara fad'in “tabbas naga camera a falonka, tana nan saitin hotonku kaidasu momma, inda flower d'in nan take, hakanne yasani zargin kai ka saka kayarka saboda tsaro”.
      “hummm”. kawai yafad'a yana janye idanunsa, sai kuma ya taso ya dawo inda nake zaune, ganinai kawai ya rungumoni jikinsa, na waro idanu dan mamaki, shikuma ya lumshe nasa tareda sumbatar goshina a hankali, shigar sumbarce tasakani lumshe nawa idanun nima tareda k'ank'ameshi.
      Cikin kunnena ya furta “i'm proud of you my friend”.
      Da sauri na waro idanu ina kallonsa, saiya d'agamin gira d'aya yana wani miskilin murmushi, sannan ya tadani zaune shima ya tashi ya fita.
       Baki da idanu da hanci duk na saki ina binsa da kallo, a k'asan raina ina tambayar mike damun guy d'innan ne wai?.
      Banida mai bani amsa, dan haka na mik'e na cire hijjab d'in nai kwanciyata.

       d'akinsa ya koma ya d'akko wani Abu kamar k'aramar ball🎱 ya ajiye saman table d'in gaban gadon, sannan ya manna wani dogon Abu a jikin 'Yar ball d'in, ya d'akko laptop d'insa ya kunna. shiru na kusan mintuna uku ya k'urama abinnan ido, zuwa can yafara wata k'aramar k'ara d'i! d'i! d'i!, sai kuma k'aramar danja ajikin abinda ya manna d'in shima tana kawo haske  jaa da d'aukewa.
     Murmushin takaici kawai yayi, a zuciyarsa yanama ALLAH godiya dabai ta6a kusantar Munaya a d'akin nanba. dan tabbas ga CCTV camera ya gani a d'akin, an sakatane can ta saman wardrobe, yanda ko alama hankalinsa bazai kaiba, baiyi yunk'urin cirewa ba, ya d'auki kayan aikinsa ya koma parlour, dan yaga itakuma tanan a ina take?. yanama shigowa tun'a k'ofar tsakanin bedroom da falon ya gani, baima k'arasaba ya koma ciki, kashe laptop d'in yayi ya d'auke k'aramar ball d'in ya 6oye.
   Duk wannan hidimar da Galadima keyi Sauban na kwance bisa gadonsa yayi d'ai-d'ai yana kwasar barci.
      Gyara masa bargo yayi saboda tasowar hadarin farkon damina da iska tafara kad'awa sanyi ya busa. daga nan ya kashe masa fitila ya fita zuwa d'akin Munaya.

      Ita harma tayi barci, tana k'ank'ame da fillo saboda sanyin hadarin dake busawa, gadon ya hau tareda warware bargon ya lullu6a musu. dai-dai iska ta taso mai azabar k'arfi, a rikice Munaya ta juyo ta k'ank'amesa saboda tsorata.
      Rik'eta yay sosai yana fad'in “uchh! Karki karyani”.
     Babu shiri munaya ta bud'e idonta, tana k'ank'ame da shi tace, “wai miyasa bazaka ke kwana naka d'akinba ne?”.
     “k miyasa time d'in da kikaje India kika gajemin d'akina?”.
      Shiru tamasa bata amsaba, amma yanajin alamar murgud'a bakinta akan k'irjinsa.
        “punishment ya tabbata agareki yalla6iya”.
     Da sauri nace “wlhy a'a, inba hakaba zaka koma saman sofa ne, ai kaima haka kamin a d'akinka”.
      “uyim Madan tsiwa, to ai nima dankar ki murk'ushemin abin cikin kwan cikin barci yasani kwantawa anan?”.
    Zan bashi amsa aka kwad'a wata tsawa data sakamu ruk'unk'ume juna babu shiri, sai kuma ruwa ya 6alle.
    Da wannan damar Galadima yay amfani wajen canja salon kwanciyar tamu, tun ina nuna banaso har salonsa ya sakani sakin layi, (😆anya munaya wannan cikin naki bashine tarkon da Galadima ya d'ana miki ba?😜).
     

           Da asuba tashi nayi inata zum6ure-zum6ure, baice dani uffanba yashiga toilet ya tsarkake jikinsa. Bayan yafito nima na shiga.
    Baki ya ta6e yana wani d'age gira d'aya tamkar ina kallonsa ya fice.

      Saida nasha kukana sannan nayi wankan tsarki, narasa mike sakani biyema Galadima? insha ALLAH zan d'auki mataki (🤣idan babu abin cikin kwan ba😂, nasan inhar yana nan babansa zaita samun bonus😜).


Bayan na idar da sallar ban koma barciba, saina gyara d'akin nayi wanka,  shirin fitarma na  sake yi yau, dan baba k'arami yacemin k'arfe goma na safe zuwa 11 zasu tafi.
    Kammalatawa kenan ya shigo, ko kad'an banji alamar shigowarsa ba, saida na gama fesa turare ina k'ok'arin ajiyewa na hango kamar mutum tsaye a bayana.
    Da sauri nayi azamar juyowa, dayake yana gab dani kad'an ya rage na fad'a masa a jiki, na dai samu nad'anyi baya na jingina da mirror ina tura baki.
       Ko motsi baiyiba shikam, bai kuma janye idonsa daga kallona da yakeba.
     Haushi ya kamani, nima nabi jikin nawa da kallo kozanga abin da yake kallon, ganin babu wani Abu daya faru na d'ago na kuma kallonsa, “wai yalla6ai mi kake kallone haka?”.
      d'an yatsansa d'aya yasaka yad'an shafi girarsa yana gyara tsayuwa,  “abin cikin kwan mana”. ‘ya fad'a cikin basarwa’.
     “ta gefensa na ra6a zan wuce ina fad'in “ai lokaci kad'an ya rage maka ka bar ganin nasa”.
    Da sauri ya rik'o hannuna, na juyo muka kalli juna, mayun idanunsa ya saka cikin nawa, “kina zaton idan nabar ganinsa kema za'a cigaba da ganinki?”.
      Guntun murmushi nayi ina janye idona daga cikin nasa, nace “kana zaton kasheni zakayi nima?”.
      “cire maganar ma zato”.
     Kallonsa na kuma yi, cikin yanayin da shi kansa bai ta6a zaton ina dashiba nace “saika fara shiri”.
    Shima a dake yace “dama a shirye nake kullum”.
    Na murmusa ina k'ok'arin cire hannuna daga cikin nasa, amma ya hanani damar hakan, kallonsa na kuma yi nace “ko har lokacin yayi ne?”.
       Fisgoni yayi na koma da baya, ya mannani jikin mirror d'in tare da maida hannuna baya ya rik'e, ya matseni da jikinsa, fuskarsa gab da tawa tamkar zai had'a bakinmu, yayinda idonsa ke cikin nawa, wani miskilin murmushin gefen baki yayi, yasaka yatsansa yana zagaya janbakin dake kan la66ana a hankali, cikin muryarnan tasa mai kama da an masa dole ya fara magana cikin karsashi “ko Ubangiji yakanyi hukuncine ga bawan daya bijirema umarninsa, koda ace zubarda wannan cikin kikayi dolene saikin kuma d'aukar wani, zubar da shi na dai-dai da haihuwar yara goma anan gidan kafin na aikaki inda shima ya tafi” ya matsa la66ana da k'arfi, wani zafi ya ratsani saiga hawaye a kumatuna, murmushi yayi, yasaki la66an ya dangwali hawayen a d'an yatsansa, nunamin yay yana fad'in “lallai momcyn abin cikin kwan kin cancanta 100%, amma bayan abin cikin kwanfa akwai k'annensa, please bar kuka my dear friend”. ‘ya k'are maganar da sumbatar la66ana sannan ya sakeni yaja baya.
        Koda ya sakeni sainayi murmushi kawai, sannan na juya ina fuskantar mirror, foda na d'auka na gyara fuskata, na sake saka jambaki kad'an kamar yanda na saka d'azun.
     Tsayawa yay cikeda mamakin abin da nayi na ko inkula yana kallona, mi wannan yarinyar take shiryawa ne haka?.....
    Kafin ya samu amsa Na juyo gareshi, fuskata d'auke da murmushi na ra6a zan wuce sa, bina kawai yay da kallo, naje gaban wardrobe na bud'e, alk'yabba na d'akko na sanya, sannan na d'auki handbag ina kallonsa har yanzu fuskata d'auke da murmushi.
       Gira ya d'agamin shima yana wani k'asaitaccen murmushi, ya juya ya fita batareda yakuma magana ba.
     Yana fita na sauke ajiyar zuciya ina dafe k'irji, wlhy ni kad'ai nasan dukan da zuciyata takeyi, kad'an yarage ya ranfo a tsorace nake, kalamansa ne suka shiga dawomin cikin zuciyata, mi wannan yake nufine wai..........?
     “Shin bazaki bane?”.
   Muryarsa ta daki dodon kunnena, da sauri na gyara yanayina na d'ago muka had'a ido, Ashe yana bakin k'ofar bai tafiba.
    Bance komai ba na biyo bayansa.
    A falon farko na iske kuyangina suna gaidashi, hannu kawai ya d'aga musu ya fice abinsa.
    Tsayawa nayi muka gaisa, d'aya a cikinsu ta yunk'urin k'ar6ar handbag d'ina.

    Na iske harya shiga mota, nima aka bud'emin na shiga, handbag d'ina ta mik'omin tana fad'in “ranki ya dad'e ana buk'atar rakkiyarmu ne?”.
    Murmushi namata, na juya na kalli Galadima danjin mizaice, kansa ya girgiza alamar a'a.
     Juyawa nima nayi na girgiza mata kai, tamana addu'a tana rufe k'ofar.
    Tunda muka tafi babu wanda yace uffan, yanata latsa wayarsa.
    Airport muka nufa kai tsaye.
    Bayan motocin sun tsaya sarkin mota na yunk'urin fita yace “2 minutes ”.
        Sarikin mota yace “to ranka ya dad'e”.
   Ni ban fahimci mi suke nufiba, naga dai sarkin mota ya fita mukuma ba'a bud'e mana ba, sai kawai nakai hannu zan bud'e.
     Hannuna ya rik'o, na juyo ina kallonsa, har Yanzu idonsa nakan waya,, ajiye wayar yayi ya juyo yana fuskantata, ina yunk'urin tambayar lafiya naji la66ana cikin bakinsa.
     Ya salam, na fad'a a zuciyata, saida ya shanye janbakin la66ana tas sannan ya sakeni. yanda kukasan gunki haka na koma masa, ya buga yatsunsa biyu saitin fuskata suna bada k'arar d'as d'as yace “gargad'i, first and last dazanganshi abakinki yayin fita”.
     Harya fita ban iya motsawa ba, saida aka bud'e murfin 6angaren danake sannan na iya sauke numfashi, na kasa fahimtar damuwar guy d'innan kwata-kwata. fita nayi nima, yana tsaye yana jiran fitowata. a tare muka jera muna tafiya, yayinda dogaransa ke take mana baya. ya wani miskile fuska tamkar bashine yagama ta6argaza ba a mota yanzun.
    Mutane sai kallonmu suke, masu gulma nayi masu nunamu nayi, ni dai duk sainaji wani iri, shima tsaki yayi danya tsani kallo.
     A mamaki na duk sai naga 'yan gidanmu ma a wajen, gaggaisawa muka shigayi, muka rik'e hannun juna nida munubiya muka k'arasa inda innarmu take, gaisheta nayi, nace “su Aiyaan fa?”.
      “suna gida zasu zauna da mamanku mana”.
    “kai innarmu, ya zaki barsu wajen muguwarnan, bama gara Maman fauziyya ba komu suzo wajenmu”.
    Murmushi kawai innarmu tayi, tace, “ashe bazaki canjaba Munaya?”.
      6ata fuska nayi, ina fad'in “kai inna, duk canjawarnan danayi”.
     Murmushi sukayi itada Munubiya. akuma dai-dai time d'in Ambulance ta shigo airport d'in, sai mota biyu a bayanta sai motar police guda d'aya.
    Gaba d'ayanmu hankalinmu saiya koma can, Galadima ya k'arasa wajen Ambulance d'in, yayinda sauran motocin biyu Sauban da Nuren baba k'arami Dady ya Shafi'u da yaa Naseer yaa hameed suka fito.

     Zuwansu baifi da mintuna 15 ba aka fara kiran sunan wad'anda zasu tashi a jirgin.
    Sai kuma ma'aikatan wajen mutum uku suka iso wajen Ambulance d'in aka fara k'ok'arin fidda Abba. Hankalin jama'a da yawa ya tashi a airport d'in nan saboda tausayin Abba, mukam kuka ma wasunmu sukeyi ai, muna kallo aka gungura gadon da aka d'oroshi har zuwa ga jirgin.
    Suma su innarmu suka shiga itada baba k'arami da Sauban.
    Rungume juna mukayi nida munubiya muma muna kuka.
    Galadima bai fito cikin jirginba saida yaga komai ya dai-daita. yana fitowa babu dad'ewa jirgin ya d'aga zuwa sararin samaniya, yayinda mukuma muke binsu da addu'oin fatan alkairi da samun sauk'i.................✍🏼




    🤥kutt harda na gobe nayi🙄⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀.







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


*_typing📲_*


 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*


           *_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
                  _(Kaga gayya)_



              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



   ~Book 2~ 👉🏻1⃣2⃣


...............Maman Fauziyya tamatso ta kama hannunmu ni da Munubiya tana lallashinmu, da fad'a mana mu bisa da addu'a, insha ALLAHU da k'afarsa zai dawo.

    Ganin mun fara shirin tafiya na taka inda Galadima yake tsaye da Nuren suna magana, tun d'anzun ina lura dashi ya kafeni da idanu, yanzunma suna maganar amma idonsa na kaina na k'araso garesu.
     Nuren daketa fara'a yace, “gimbiyarmu barka da hantsi”.
    Murmushi nayi sannan na gaisheshi, ya amsa yana tambayata yaya jikina?.
   Nace “Alhmdllh na  warke ai”.
      “to ALLAH ya k'ara afuwa gimbiya”. ‘yafad'a yana matsawa gefe domin bamu waje.
     Galadima dake kallona hannunsa duk biyu cikin wandon sky blue d'in shaddarsa da tsawon rigar iyakarsa rabin cinyarsa, yace, “Lafiya?”.
      Dakewa nima nayi, cike da jan ajina nace “k'alau. Dan ALLAH zanbi Munubiya please yalla6ai”.
       Janye idanunsa yayi daga kaina yana fad'in “awane farashi?”.
       “kamarya farashi? ciniki mukeyi?”.
    Hannunsa d'aya ya fiddo daga aljihu ya shafa sajensa zuwa gemu, cikin kafeni da idanu yace “kusan haka, kinsan rayuwar bani gishiri in baka manda akeyi yanzun”.
       Cikin son tura masa haushi nace “Ai ni bana gane Hausa cikin hausa”.
      “really? lallai kin fad'o kuwa, kuma saiki ce ke bahaushiyace?”.
        Baki na tunzura masa saboda haushin rainin wayon da yake min, gasu Munubiya kuma shirin tafiya sukeyi.
       “Kinsan wannan bakin kika bari na kamashi a airport d'innan....., hummm”.
      Idanuna na waro, “mi kake tunanin zakayi kenan?”.
      “kuma turowa saina nuna miki”. ‘yafad'a yana matsowa’.. 
       Baya na matsa da sauri zuciyata na harbawa, anya kan Galadima d'aya kuwa?.
     Kwafa yayi yana kallon agogon hannunsa yana k'ok'arin zaro waya daga aljihun gaban rigar datake ring.
    Nikuma na hararesa a zuciyata ina fad'in mara kunya ai nasan zaka iya. A fili kuma nace “please yalla6ai nidai badan halina ba”.
     Bai bani amsaba, sai sallamar danaji yayi wayarsa akan kunne.
     Jinai kawai yace, “Harun kana inane?”.
       Bansan wace amsa ya bashiba, naji yana fad'in “ok idan ka tashi saimu had'u”. daga haka ya yanke wayar sannan ya kalleni.
     “uhm mikike cewa?”
      Haushi tamkar zai karni nace “please mana autan Momma”.
     Murmushi yayi yana cije lips, “wlhy yarinyarnan kin gama rainani, ninema Autan?”.
       “lah nama manta ashe kaifa na tsakkiyar momma ne, karma Yaa Sauban ya jini”.
       “kinsan ALLAH na damk'eki a airport d'innan saikin fad'amin dawa kike”.
         Dariya nayi ina d'aga masa yatsu biyu, “karka damu yalla6ai zanyo maka tsarabar sweet and biscuit yeah”.
     Da sauri yay yunk'urin damk'o hannuna ganin zan gudu. yana rik'owa mukaji ance “hallo”. A bayanmu.
       Batareda ya saki hannuna ba duk muka waiga ni da shi.
     Matashiyar budurwa fara k'al, kuma k'yak'yk'yawa masha ALLAH.
     Dan danan ya tsuke fuska, tamkar ba shine yagama murmushiba yanzun.
    Nima bansan murmushi ya gushema tawa fuskarba, baiyi magana ba, sai nice nace “lafiya kuwa?”. yanda nayi maganar cikin rainin hankali yasaka yarinyar rik'e ha6a tana ta6e baki tana fad'in “ke kuma fa?”.
          Kamar zanyi magana saikuma Na shareta kawai, galadima Na kalla fuskata a cunkushe alamar fushi, d'ayan hannunsa ya d'agamin yana ta6e fuska alamar shifa babu ruwansa.
     Na tura baki tareda juyawa zan bar wajen.
      Hannuna dake cikin nasa ya kuma damk'ewa da k'yau, hakan yasani dawowa baya tamkar zan fad'a jikinsa, amma nayi jarumtar tirjewa kodan jama'ar gidanmu.
    Dama ajikin wasu motoci muke, sai kawai ya fisgi hannuna muka shige tsakkiyarsu ya mannani jikin mota shikuma yamin rumfa. ban ankaraba naji bawan ALLAHnnan ya ha.......🤥.
     Jikina kawai rawa yakamayi saboda tsoro, wlhy ban ta6a tunanin da gaske yake zai iya hukunta bakin nawa a airport d'inba.
     Ita kanta budurwarnan idanu ta zaro waje cikin wangale baki.
      Nuren dashi kad'ai yake saitin dazai iya ganinmu saikuma wasu tsirarun mutane dake nesa damu, wad'anda ba lallaine ma su fahimci abinda akeba, kaucewa kawai yay daga wajen yana tuntsura dariya.
     'Yan gidanmu sunga lokacin da Galadima yaja hannuna muka shige tsakkiyar motocin, amma basa hangomu. tsabar gulma irinta mamansu Yaa Hameed da Momy da Maman Safara'u sai suna shiga k'ok'arin son ganin mi mukeyi a wajen?😱 su duk tunaninsu wata maganar banza nama budurwarnan yake shukamin rashin mutunci Dan duk agaban idonsu tazo wajen har rik'omin hannu da yayi, dukda basa jin mi Muke fad'a Dan muna nesa dasune.
     Yaa Sabi'u dabasu lura da abinda ke faruwa ba suka Shiga musu maganar INA zasuje? suzo su ajiyesu gida sufa wajen aiki zasuje.
    Ina basu saurareshiba saida sukazo saitin dazasu iya ganinmu.
      A tare suka zaro idanu, Baki da hanci, duk sun shiga mamakin ganin Galadima Na kissing d'ina, ai babu shirin suka koma baya zukatansu Na tukuk'i da jifanmu da kalmar 'yan iska fitsararru.

    (🤣Yo wayace kuje gani? kazantar dabaka ganiba sunanta tsafta😏😜).

     
    Yana Sakina kunya tasakani fad'awa k'irjinsa Na 6oye fuskata, hannayensa yasaka ya zagaye bayana yana dallama yarinyarnan wata muguwar harara data saka hanjin cikinta kad'awa, babu shirin tabar wajen tana mak'yark'yata da tunanin Galadima ko dai kurmane da gaske.

      Driver d'inta dake kallon komai tun d'azun ya tuntsure da dariya yana fad'in ALLAH ya k'ara, bana fad'a miki Shiba Na wasan yara bane ba, banda jaraba kinbi kin nanik'ema bawan ALLAH daga had'uwa a jirgi, kinbi kin addabi rayuwata saina nemo miki number sa, aini nama godema ALLAH da kuma sake had'uwa ya kuma nuna miki ainahin halinsa, saida Na fad'a miki baima dad'e dayin aureba, ke gadararriya kikace aurensa bai damekiba........
    Yanda ta daka masa tsawa yasakashi firgita ya russuna yana Neman afuwarta.
      Cikeda masifa tace “tada mota mukoma gida”.
      “Amma ma'am kin manta jirginku yakusa tashi?”. A tsorace yayi maganar.
          Harara ta Dalla masa tace “Ubanka ne ya viyamin kud'in jirgin”.
       Wasu yawu masu rad'ad'i driver ya had'iye yana girgiza mata kai, ya bud'e motar ta Shiga sannan ya rufe shima ya zagaya mazauninsa suka koma Inda suka fito😜.

   
   Nasan dai kun fahimci yarinyarnan Ce da suka zauna waje d'aya a jirgi itada Galadima randa zaizo😆🥳.

     Ganin tabar wajen Galadima yay murmushi sannan yafara k'ok'arin d'agoni daga k'irjinsa, ban yarda mun had'a idoba na  bar wajen.
       “Saikin dawo” ya fad'a a hankali.
    Kasa daurewa nayi saida Na waigo Dan tabbatar da shine yay maganar kokuwa dai wanine?. Ido muka had'a ya janye nasa cikeda basarwa yana la6e baki.
        Nima harara Na watsa masa ina barin wajen.
      Tunda Na taho Maman safara'u da mamansu Yaa hameed da Momy suka zubamin ido.
    Nikuma fahimtar kallon k'urillar da sukemin saina canja salon tafiya da kuma had'e fuska na nufi zuwa wajen gungun yaran gidanmu masu aure dasuke hira.
    Suma duk kallona sukayi, namusu murmushi ina fad'in “lallai munada cin ragunan suna kwannan nan ashe”.
     Dariya duk sukayi, Fiddausi tace “yariman namu shikuma da kwad'ayin naman suna yazo?”.
     Harara Na zuba mata ina kai mata bugu ta waske itama tana dariya, yayinda su Munubiya ke tayata.
     Mun gaggaisa tareda tambayar lafiyar juna, muka d'an ta6a hira kad'an da alk'awarin duk zanje mu gaisa, suma sukace zasuzo tunda ba yanzu zan koma ba. daga nan mukai shirin tafiya, Siyama da Zarah anata mana iyayi su masu motar hawa, (dayake kowacce a motarta tazo).
    Ni dai ni da Munubiya Yaa Marwan ya d'aukemu muka tafi.


____________________________

       Tunda nabar wajen Nuren yazo ya tasa Galadima da tsiya, wai dama haka yake ashe?, rashin kunyar tasa har agaban surukai?.
       Banza Galadima yamasa yay shigewarsa mota yabarsa yana iskancinsa.
     Anan suka tafi suka barsa dayake da mota yazo shima.
 
       Galadima na barin airport gidanmu ya nufa shima.
     A lokacin 'yan gidanmu suma sun Isa gida, sunata k'ananun magana akan abinda Galadima da munaya sukayi, dan saida suka bama sauran labari, nanfa suka kacame da zancen harda k'arin k'arya akai wai ba kiss kawai sukaiba ('yan gidansu munaya annamimatu🙆🏻😂).
      Itadai Maman Fauziyya batace k'alaba, saima dariya da zancen ke bata, Dady kuma bai dawo gidanba, daga nan wajen aiki ya wuce, yaran gidan ma kowa gidanta ta koma basu biyo nanba. Innaro da gwaggo Safiyya kam gida suka shige ana saukesu, dan haka basuji komaiba.

        Galadima bai shiga gidan ba, saiya nemi iso gidan Innaro, Habiba ta fito tamasa jagora.
     Innaro na falo tana cika da batsewa gwaggo Safiyya na lalla6ata akan ta kwantar da hankalinta.
       Koda Galadima ya shigo innaro sai antaya masa harara takeyi, yana kula da ita ta gefen ido, ya murmusa yana zama saman kujera, cikeda tsokana yace “Sweet Granny Yaya dai?”.
       Harara innaro ta zuba masa sosai, tana fad'in mikuma kazo min nan?”.
     Galadima ya murmusa yana maida hankalinsa ga gwaggo Safiyya, gaisheta yayi ta amsa masa cike da kulawa, sannan ta d'ora da godiya da kwarara masa addu'ar fatan alkairi.
   Yaji dad'i sosai, ya amsa cikin fara'a, sannan yace, “Granny ina furar tsufa?”.
      “ai bazaka shata ba ”.
    Nanma murmushin Galadima yayi yana mamakin wannan rikitacciyar tsohuwa. Yace “tunda bazan shaba Ashe kema kuwa bak'yaje India ba”.
     Zabura innaro tayi, ta maida hankalinta ga Galadima tana fad'in “da gaske kake ko shak'iyancine?”.
      Mi su Naja'atu zasuyi inba dariya ba, Galadima ma handkerchief ya saka ya rufe bakinsa kawai. Gwaggo Safiyya kanta saida ta dara.
     Galadima ya gyara zamansa yana fad'in “karki damu Granny ninmu, insha ALLAH tare dake zamu tafi idan zamu koma”.
      Dad'i ya kama innaro ta shiga sakama Galadima albarka.
     Shidai murmushi kawai yakeyi. saida yaga sun nutsu sannan yace yazo tafiya dasu Aiyaan ne, babu musu innaro ta mik'e da kanta zuwa gidan danta kawo masa su.
    Bayan fitarta gwaggo Safiyya tabama Galadima hak'uri akan darun innaro.
    “karki damu gwaggo, ai dama kowa yasan idan sunkai irin wannan age d'in saida lalla6awa, ALLAH dai yaja mana ransu”.
     Amin gwaggo Safiyya tafad'a cikin jin dad'i.
      Tunda 'yan gidansu Munaya sukaji wai Galadima ne da kansa yazo tafiya dasu Aryaan sai zukatansu suka kuma tunzura, kowa tana ganin hakan salon munafurcine, Maman Fauziyya ta kawoma innaro su, dama suna d'akinta, dan mamansu yaa hameed suna dawowa ta d'auki jakkarsu Aiyaan ta kaimata, wai sai dai su zauna wajenta ita d'akinta babu fili.
     Maman Fauziyya batace komai ba ta kar6i su Aiyaan tana jinjina bak'in hali irinnan jama'ar gidan.
   Amma kuma yanzu sai gasu sune dajin haushi.
    Ita dai innaro ko'a kanta ta jawo hannunsu Zainab ta d'akko jakkar kayansu suka taho.
       Koda sukazo ma sai Galadima yace abar kayan nasu su kad'ai yake buk'ata. ya ajiyema Gwaggo Safiyya da innaro alkairi ya fito rik'e da hannun su Aiyaan daketa murna.
    Innaro har wajen mota ta rakosu, bata komaba saida taga tafiyarsu. tana komawa gida tahau had'a kayan tafiya, wai gara ta had'a ta huta, duk randa Galadima yazo sai tafiya kawai.
    Ita dai gwaggo Safiyya dariya kawai tayi, dan maganar Galadima gaskiyace, lamarin innaro yana buk'atar uziri, ta tsufa sosai, kawai dai ALLAH yabata lafiyane, dan da wuya kaga innaro na kukan wani waje namata ciwo irin na tsufa. (masifarta kam dai kunsan ance abinda kayi a k'uruciya shi kake maimaitawa lokacin tsufa, ALLAH ka azurtamu da k'yak'yk'yawar k'uruciya to🤦🏻‍♀).



★★★★)(★)(★★★★


        A k'ofar sabon  matsakaicin gidan motocin biyu suka tsaya, cikin wad'anda suke a motar baya d'aya ya fito ya bud'e motar farko, hamshak'iyar macece mai ji da mulki da kud'i ta fito, kallo d'aya zaka mata ka tabbatar tagama samun duniya, cikin tsantsar tink'aho da homa take zuk'ar iska tareda taku d'ai-d'ai irin na manyan mata.
      Cikin sauri aka bud'e mata k'ofar gidan ta shiga guard d'inta na take mata baya.
       A tsakkiyar tsakar gidan taja tunga, sai hura hanci takeyi tana harare-harare.
    d'aya a cikin guards nata yace, “ ma'am nan shine d'akin da yake”.
     Batace uffanba taci gaba da takawa d'ai-dai har zuwa k'ofar d'akin, hannu ta d'aga musu alamar su dakata. Dukkansu baya sukaja domin cika umarninta.

     Zaune yake a kujera an d'ad'd'aureshi, kallo d'aya zaka masa ka tabbatar a galabaice yake.
   Shigowarta baisa ya d'aga kai ba balle ya motsa, yasan dai bazai wuce k'artan dasuka kawosa wajen baneba. sai dai jin k'amshin turaren mace yabashi mamaki, hakanne ya sakashi d'ago idanu domin tabbatar da yaren hancinsa.
       Bakinsa na rawa yace, “Wacece ke?”.
   
     Bata bashi amsaba, saima kujera data ja irin wadda yake kai ta dinning ta zauna, k'afa d'aya ta d'ora akan d'aya tana wani cika da batsewa. “yaro baka isa sanin ni wacece ba, Sai dai cigaba da 6atamin aiki zai sakaka sanina”.
    Murmushi Muftahu yayi, ya d'ago idanunsa yana mata kallon rainin wayo, “Saninki dama aikin banzane a gareni, aikin ki kuma da kike ik'irarin ina 6atawa duk da ban sanshi ba, kisa a ranki yanzu ne na fara 6atawa, saiki shirya nunamin ke d'in wacece?”.
       “hahaha, yaro baisan wutaba saiya taka”.
      “Humm, wuta bata san yaroba saisu k'ulla”.
      “karan farauta yaushe uban gidan naka yafara koya maka irin izzarsa haka?”.
       “Kinsan zama da mad'aukin kanwa aishi ke kawo farin kai”.
      “lallai zan had'a da kanwar da mad'aukin nata duk na koyar dasu darasi. Shi kansa Sameer d'in baikai darajar karen gidana ba balle kai yaronsa”.
       Murmushi Muftahu yayi, “ Uhmm sai yanzu na fahimta, sai dai zan tunatar dake abinda kika manta, Wanda kikeyi danshi baima San da zamanki ba, kinga ashe ihu kikeyi bayan hari..........”.
           “hhhhhhhh! Abin dariya, inbai fahimta ba ai zai fahimta lokacinda sak'on sunana da gawarka suka isa a gareshi, yanda ban haifi magajin masarautar gagara badauba, zeenah bata isa haihuwar magajinta ba wlhy”.
      Idanu Muftahu ya tsura mata, sai yanzu yafara hango kamannin d'aya daga matan tsohon Sarki Abie da suka bar masarauta bayan shekaru biyu da fara jinyarsa, bashida wayau a time d'in, Dan dagasu har Galadima bazasu wuce 7-7 year's ba, saida suntaso sunji labarin bijirewar matan a lokacin da za'a tafi da Abie India, dama shekaru biyun da suka zauna basu ta6a saka hannu a jiyarsa ba, sai Momma keta fama...........
      Marin da aka zuba masane ya sakashi dawowa daga dogon tunanin daya tafi....
       “tunanin mi kakeyi Karen farauta?”.
     Jajayen idanunsa ya zuba mata, sai kuma ya kwashe da dariya, saida yayi mai isarsa sannan ya dakata tareda tsuke fuska, “ina tunano mummunan fuskarkine, in banda abinki miye na kishi da abinda kika bari da kanki? nasan dai Momma ba itace ta hanaki haihuwa ba ai, inason kisan ni ban isa kare Galadima ba dama, amma kulum cikin kariyar Wanda ya haliccesa yake, a tunaninki 6ata sunansa da kikayine ke nufin bazai mulki masarauta mai d'unbin tarihi da girmaba? kinyi kuskure babba wlhy, Dan kinsaka kanki a ramin damisa. duk ranarda Galadima ya gane kece kika saka amasa 6atanci a jarida wlhy saikinyi nadamar rayuwarki..........
      Bayan Hannu tasaka ta bugi bakinsa, gefe yay da kansa yana murmushi, ga jini na zuba a gefen bakin, dayake hannunsa a d'ure suke.
    Tace, “kafin ni nayi nadamar kai ne da shi zakuyi, Dan yanda kake a tarkona shima yanacan a cikinsa, wawa kawai, kai aboki mai gaskiya ko? zan shayar dakai mamaki, domin saikaga gawar Sameer a gabanka kwance kafin kaima kabishi baya”.
      Dawo da kallonsa yayi gareta yana murmushi, “miyasa kika tsorata tunban k'arasaba, Galadima maruci ne, kuma kainuwane, gashi dakalin majina, kina hawansa zamewa zakiyi wlhy, ina tausaya miki yayinda tunaninsa ya waiwayo kanki, Dan yanzu aikin manyanki ne a gabansa ba nakiba, d'ana masa tarkonki kuwa tamakar kin tado damisane daga barci, hakan kuma fitinace babba a gareki da shi kansa Karen farautar taki Harun, tirrr da zuciyarki, ni kaina danasan ma kece bazan 6ata lokacina wajen bibiyar ki ta hanyar Harun ba, amma banyi bak'in cikiba, ko babu komai na ribantu da abubuwa masu yawa, domin ta silar hakan na had'a auren sunna, gashi harda ribar ciki, magajin Galadima Sameer kenan.......
     A fusace ta d'aga kofin glass zata kwala masa.
    Yace, “relax relax mana giwar mata, ai bangama fad'aba OK?” ba kince zaki kawomin gawar Galadima ba sannan, to miye kuma na fusata haka da wuri?, ni ina kuma tabbatar miki indai Galadima ne zaizo, daga lokacinda yasan ina nan tabbas zai zo, banza karyar farautar wasu, na tabbata k'arya kikeyi ba aikin kanki kikeba kema, sakaki akayi, lallai ke farashinki ya fad'i k'asa, matar sarki mai fad'a aji irin Sarki Saifudden Ce ta k'are ahaka? Abin kaico abin jaje, tirrr”.
          Dariya ta kwashe da shi tana tafa hannaye, saikuma ta matsa gabda Muftahu tana magana cikin kunnensa “lallai bayan Sameer akwai magajin sa a gagara badau ashe?”.
     “oh sai yanzu kika fahimta ashe?”.
       “karen Sameer zaka mutu kaida uban gidan ka, saina saka wannan zuciyar tasa ta buga wannan shine k'udirina”.
            “hhhhhhh abin dariya, kudirin wasu dai, danke naki bamai muhimmanci baneba, tunda kuka kasa saka zuciyar Sameer bugawa a lokacin da k'uruciya da rashin sanin kansa ke damunsa, miyasa kuke tunanin zata buga a lokacin da yagama tanadar makaman yak'insa, ranar shiga filin daga kawai yake jira, nagaji da tattaunawa dake please”.
        “kaima kace wani Abu yaro, Dan haka mu zuba, kwana uku kawai zakaga gawar Sameer a gabanka!!!!!”.
     Bata jira yabata amsaba ta fice daga d'akin, tareda jan k'ofa da k'arfi.
    Idanunsa kawai ya rintse. Baya tsoron makircinta, amma yana tsoron na Harun, dan Galadima ya rigada ya yarda da Harun 100%, bazai ta6a kawo zai cutar da Shiba. Waige-waige yashiga yi, yasan babu wani abunda Galadima zai iya bibiya tare dashi.
    Da sauri ya girgiza hannunsa saboda tunowa da agogo, jin agogon tare dashi ya sakashi lumshe ido yana ambatar Alhamllh. Matsala d'ayace baya ganin agogon, saboda hannunsa yana a baya ne. Amma dukda haka zai gwada idan za'a dace.



___________________________


      Yau na kasance cikin farin ciki, saboda gani tsakkiyar 'yan uwana, dukda ma zazza6ine mai zafi ke nuk'urk'usata, amma kewarsu ta hanani gajiyawa, mun bud'e babin fira a tsakkiyar falon mama Rabi'a, duk abinda akayi bana nan shine ake labarta min, yayinda Nima nake basu labarin India da nuna musu hotuna.
    Haka mu kai wannan yini cikin farin ciki da annashuwar kasancewa da junanmu, musamman ma ni da 'Yar uwar tagwaicina da k'addarar aure ta tilasta mana nisantar juna, ji muke tamkar mun shekara ba'a tareba. Kowannenmu k'ok'arin ganin farin cikin d'an uwansa yakeyi.


_____________


      Tunda Galadima yabaro gida dasu Aryaan saiya wuce wajen wani hutawa dasu, ya yawata dasu sunata farinciki, yayinda shi kuma yake biyema shirmensu dan d'auke musu kewar mahaifiyarsu, yana son yara, shiyyasa ko yaushe Khaleel d'in aunty Mimi zakigansa manne dashi, sa'annin Khaleel dasu Aiyaan kuwa zai iya zuwa d'aya.
    Cikin lokacin k'ank'ani suka saki jikinsu dashi.
    Daga nan plaza ya nufa, haka kawai zuciyarsa keta tsikara masa zancen 6atan Muftahu, dukda k'ok'arin wofantar da lamarin da lamarin da ya keyi.
     Waya ya d'auka ya shige danne-danne, alamu sun nuna masa wayar Muftahu na cikin masarauta, kenan bai d'auki wayarba, yad'an murmusa kawai yana cije lips, yayinda idonsa ke kansu Aiyaan da Saleem yazo d'auka suje wajensa danya huta.
     Bye suka masa, shima ya d'aga musu hannu yana murmushi.
    Suna ficewa ya sauke ajiyar zuciya tare da mik'ewa tsaye. zagayen office d'in ya farayi hannunsa goye a baya, a wannan karon bazai ta6a k'yale Muftahu ba, dolene yayi wani Abu akansa, dama yana d'aga masa k'afane domin son ganin gudun ruwansa kawai, yanzu kuma lokacin yayi dazai San mi yake k'ullawa...........✍🏼




*_Duk Wanda yaga ban amsa massage nashiba yamin afuwa, cakwakiyar network tasani clearing charts d'ina batareda na dubaba, tun around 3:47pm nayi posting amma yak'i tahowa._*


Dan haka ina gayyata kowa gobe a court, zamu shiga shari'a ni da  network ne🙄.

Wad'anda suka ga basa ganin posting d'ina gaba d'aya a satinnan duk aikin network ne🙄.






*_ALLAH ya gafartama iyayenmhiyayenmu😭🙏🏻_*

*_typing📲_*


 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*


           *_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
                  _(Kaga gayya)_



              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



   ~Book 2~ 👉🏻1⃣3⃣


...............Muna tsaka da hira saiga Aunty salamah tazo, daga ni har Munubiya da Ayusher rungumeta mukayi.
    Cikin tsokana ta ture Munubiya da Ayusher tana fad'in “ku matsamin, kullum Ku ina ganinku, kewar gambo nakeyi”.
     Gwalo na shiga yi musu, mama Rabi'a da Feena namana dariya.
    Bayan mun zauna Aunty Salamah ta shiga yaba canjawar danayi tanamin shak'iyanci, nanfa su Munubiya ma suka samu abinyi, sosai suka tasoni gaba sai mama Rabi'a ke kareni.
    Can muna tsaka da hira takamo hannuna tana fad'in “zo nabaki wani sirri nan autana”.
      Mik'ewa mukayi inamasu Ayusher gwalo, yayinda suma suka tubure basu yardaba sai an bada sirrin dasu. da k'yar muka samu muka shige d'aki muka kulle.
      A bakin gado muka zauna Aunty slamah ta sauke ajiyar zuciya tana kamo hannuna cikin nata, serious nima na zama na maida hankalina gareta.
   Tace, “Munaya! Aiki yatafi yanda ya kamata, saidaifa labarin ya canja daga yanda kike zato, Muftahu ba munafuki baneba”.
       A matuk'ar razane naja baya ina ture hannunta daga cikin nawa, “Aunty kinsan mi kike fad'a kuwa? Anya yaranki Muftahu suka kama?”.
     Hannuna ta kamo tana murmushi, kinga zauna, shiyyasa na saka aka d'auki komai dan kema ki gani da idonki”.
    Zaman nayi kuwa, ita kuma tayi 'yan latse-latsenta a iPad d'inta ta mik'omin. kar6a nayi cikeda fargaba, da kaina nayi playing d'in video n, tun daga fitowar Aunty salmah daga mota har shiganta cikin gidan zuwa shigarta d'akin, tsayarwa nayi na kalli Aunty ina dariya, “kai Auntynmu kinfa iya Acting wlhy, wanifa saiya d'auka da gaske irin mugayen hamshak'an matan nanne”.
        Dariya Aunty Salamah tayi, “wlhy koni dai nayi mamakin dakewata, bakiga sai wani hura hanci nakeba, sukuma su Ameer saikace guards d'in irin manyan mutanan nan”.
     Dariya mukayi, sannan nakuma playing na cigaba da kallo.
     Shigar Aunty Salamah d'akin da tattaunawarsu da Muftahu. gaba d'aya jikina yayi sanyi, zuciyata sai wani tsitstsinkewa takeyi, idona cike da kwalla nace, “anya gaskiya Muftahu yake fad'a Aunty Salamah?, wlhy da gaske fa shine ya saka mana desire tablets, inhar bada wata manufaba miyasa yay haka?, kumafa ni banta6a ganin wani alamar rashin gaskiya ba ajikin Harun”.
      Murmushi Aunty Salamah ta yi, ta dafa kafad'ata tana fad'in, “Munaya mugu bashida kama, Ai Muftahu baisan nid'in ba matar sarkin bace ta gaske, mizaisa ya za6i 6oyemin? yanda yanuna akan k'yamar matar sarkin tabbas akwai mai mugun hali a cikin su da gaske, kinga ai kince bakiga fuskar wanda kika kama yana wayarnanba a bayan window d'inki randa kuka iso”.
     “Eh hakane, ban ganiba, maganganun kawai naji”.
     “to kin gani, kifa tuna kuma firar da kika ta6aji Galadima nayi a asibiti shida aunty Mimi. wad'annan alamomin sun nuna akwai wata a cikin matan Sarki dakeda hannu a ciki, maganar Harun kuma idanu zamu saka masa tamkar yanda mukaima Muftahu, dan ayanzu idan mun saki Muftahu zakiga sun cigaba da takun sak'ar datafi ta da zafi, dan nariga da nasaka rud'ani a zuciyar Muftahu cewar zamu kashe galadima, tabbas ta wannan hanyar Harun zaizo hannunmu. Maganar Galadima kuma har yanzu karki fara kwantar masa da kai, dan kwantar da kanki zai d'arsa masa rashin aiminci a kanki, ke dai kinsan halin mijinki ai yanzu, kinkuma fi kowa sanin yanda yakamata ki cigaba da tafiya da shi”.
     Insha ALLAH Aunty zan cigaba da k'ok'ari nakuma gode da gudunmawarki akanmu, sai dai akwai matsala, dan na lura agogon hannun Muftahu kamar akwai wani sirri a cikinsa, dolene a daren yau a fitar da Muftahu daga gidanan, zanma sarkin mota bayanin yanda zai taimakeku a maidashi masarauta kamar yanda yaymana aikin d'akkoshi, shima Galadima zansa ido akansa saboda tsuntsune shi nai azabar wayo”.
       “Hakan yayi Munaya, ALLAH ya cigaba da bamu nasara, insha ALLAH zamu gano komai, ALLAH dai yabama Abba lafiya, yasa mu fahimci komai cikin sauk'i, akan Galadima kuma kici gaba da k'ok'arin da kikeyi Fiyeda da, dan dolene saimun samu had'in kansa kafin musan komai, ALLAH ya ku6tar damu baki d'aya, dan kina dai ganin yanda suka maida Abba”.
        Hawayen da suka ziraromin a kumatu na share, cikin Murmushin k'arfin hali nace, “insha ALLAH Aunty Salamah, domin raina da farin cikina fansane akan mahaifina, kuma zuwa yanzu Auren Contract bai damuna, sai dai bazan 6oye mikiba aunty Salamah wannan cikin shine damuwata a yanzu, inaji ina gain zan haifishi na barsa inda yafi k'arfina, bansan wace rayuwa zaiyiba a wannan gidan da kowa zuciyarsa takeda k'arancin imani, Aunty Salamah gidan sarauta tsantsar matsalace kawai, bazaki fahimci hakaba saikin tsinci kanki a ciki, Aunty dan ALLAH ki amince na zuba da cikinnan”.
       “munaya waishin miyasa bakida hankaline? to idan baki saniba wannan cikin shine zai zamemiki tsanin mallakar cimma nasara, kuma ta hanyarsane kawai zamu samu had'inkan Galadima domin fidda Abba daga wannan matsalan da Ku kanku ahalinsa, kina tsammanin koda Abba mutuwa yay masu farautar rayuwarsa zasu barku Ku6utane? Dolene saisun samu abinda suke nema koda ace dukkan gidanku zai k'are, bak'ya tunanin aurenku yana cikin abinda yakuma hasala zukatansu, a zatonsu Abbanki yasamu damar had'a kan mijinkine, ya ina jinjinama fik'irarki ke da munubiya kuma zaki 6ata shirin, karma ki bari 'Yar uwarki taji maganar zubda cikinnan, wlhy zaku samu Matsala ne babu ruwana”.
      Munaya ta share hawayenta, “shikenan Aunty Salamah nabar maganar insha ALLAH. Amma a yaran nan masu mana aiki bak'ya tsoron wani yaci amanarmu?”.
      “komai zai iya faruwa, domin amana tayi k'aranci a rayuwa, tunda yau gashi Harun yafito cikin masu cin dunduniyar Galadima, amma ki kwantar da hankalinki, su duka ukunnan da kike gani amintattunane, kuma Saleem ya saka mana idanu sosai a kansu”.
      “to Alhmdllh aunty, ALLAH kamana jagora”.
     “amin dai, saikima Munubiya dukkan bayanin da mukayi, ki bata itama ta gani, zuwa gobe zan aiko Bilkisu ta kar6a min, kuma ki fad'a mata yakamata ta koma gidan ta, dan gaskiya aiki bazai cigaba da yuwuwaba tana gidannan, saboda kinga ba ita kad'ai baceba, yanzu haka randa zaku zo da zamu kama Muftahu wlhy nasha wahala wajen nemanta naji kokin iso? dan ta tabbatar min inhar kin iso k'asarnan saitaji a jikinta, amma naita kiranta batayi picking ba, ashe wai wayar na hannun Feena”.
      murmushi nayi nace, “sorry sweet auntynmu, insha ALLAH zata koma gobe”.
     “shikenan, bara na wuce to”.
     “to Aunty ngd sosai, ALLAH ya bada ladan zuminci, ammafa gaskiya kinci zalin muftahu da yawa”.
      Dariya tayi sosai, “kibari kawai, nima wlhy ina marinsa tausayinsa Na ratsani, insha ALLAH zan nemi yafiyarsa zuwa nan gaba, ALLAH yasa ya yafemin dai”.
      “hhhh zai yafe miki aunty ai duk cikin aikine”.

      Mun rakota har tsakar gida, su Munubiya na tsokanarmu wai nad'an sammusu sirrin suma.
    Daga ni har aunty Salamah dariya mukayi kawai.
       Bayan dawowarmu na turama Munubiya massage akan taje tagani itama.
    Sai da taja wasu times sannan tamik'e tana fad'in bara tad'an watsa ruwa. duk muka amsa da to saita fito.



**************************



     Su Abba sun isa lafiya, anzo da motar Ambulance d'in asibiti aka d'auki Abba, yayinda Sauban da baba k'arami da inna khumar yazo d'aukarsu su kuma.
     Inna da baba k'arami sai baza ido suke suna kallon gari.
    Gida suka wuce kai tsaye, yayinda aka wuce da Abba hospital shikuma.
     Sun iske jakadiya a gidan, dandanan aka shirya musu abinci, itadai inna sai jinjina k'yawun wannan gida take, yanzu anan gidan jininta ta rayu?. shi kansa baba k'arami ya yaba, Yakuma k'ara tabbatar da manyan k'asarmu Na hutawarsu.



**************************

       Babu yanda Muftahu baiyiba dan ya sarrafa agogon hannunsa amma hakan ya gagara, Dan bak'aramin d'auri ya shaba.
   Kusan gab da magriba Wanda ke kawo masa abinci ya shigo, ajiye kular abincin yayi sannan ya matsa kusada muftahu zai kwanceshi, cikin murya k'asa-k'asa kamar mai rad'a yace “yalla6ai inhar zaka biyani wlhy zan ku6tar dakai”.
    Kallonsa Muftahu yayi sosai nawasu mintuna, “ka tabbatar?”.
     “wlhy Oga da gaske nakeyi, Dan wannan matar da kake gani bata wasa bace, duk abinda ta fad'a zata iya aikatashi wlhy”.
      Murmushi Muftahu yayi, yace, “nawa kake buk'atar Na baka?”.
       “tab aini Oga dubu 100 ma ta wadatar”.
      Muftahu yakuma Murmusawa, “zan baka 200”.
     Da sauri yaron yaja baya cikin razana, “oga dubu 200 fa? Yo ai sai a d'auka nafara yankan kaine”.
     Sosai abin yabama Muftahu dariya, Dan haka ya dara, yo dubu 200 a wajensa ai bata wuce ta siyen agogo ko takalma ba, amma shine shi yake ganin 200k a matsayin wasu kud'in da har za'a iya d'auka yayi yankan kai.
     Kallonsa yayi yana murmushi, “karka damu to, amaimakon nabaka kud'in a hannu a zargeka mizai hana Na bud'e maka wata Sana'a da zakabar wannan aikin da kakeyi yanzu”.
      “to ai Oga karkaje kasa a kamani wataran, nikuma inhar zan samu Sana'a to zan nutsu”.
      “haba abokina, ya zakamin rana nikuma Na maka dare, karka damu kaidai ka aminta dani kawai”.
     “to Na amince,  yau sai k'arfe 11 zan kawo maka abincin dare, a time d'in sauran sun fita club, insha ALLAH nikuma zan dawo baya nace Na manta da abincinka, daga nan saina ku6tar dakai, sukuma na sanar dasu Na dawo ban gankaba”.
     “shikenan babu damuwa, idan zaka dawo kazo da account number, dana koma zan maka transfer insha ALLAH”.
       “to Oga Na gode sosai”. Ya fad'a cike da d'oki.
     Murmushi kawai Muftahu yayi.
      “yauwa Oga bara Na kwanceka kaci abincin to”.
       Girgiza kai Muftahu yayi, yace, “a'a ka barsa kawai, banajin ci, in kanaso d'auka kaci kawai”..
       “amma Oga ai.......”.
      Kai Muftahu ya girgiza masa alamar karyace komai.
     Shiru yaron yayi ya d'auki kular ya fice kawai, Muftahu kuma ya bishi da kallo.




**************************


     Har akayi isha'i Galadima yana birnin gayu, saida aka kira sallar magriba ne yafita zuwa massalacin dake plaza d'in yay salla tare da ma'aikatan wajen masu salla, daga nan ya gaggaisa da makwaftan wajen dakan zo masallacin yin salla suma, bai fitoba saida akayi sallar isha'i. daga nan yacema saleem yaje dasu Aryaan su za6i dukkan abinda sukeso ya mik'a mass ATM d'insa, shikuma ya kuma shiga office ya kulle kansa ya d'ora tunaninsa daga inda ya tsaya.
       Ya dad'e yana zagaye office d'in, yayinda zuciyarsa ke k'ulawa da kwancewa, agogon hannunsa ya kalla, ganin time yayi nisa yasashi furzar da huci, kayansa ya tattaro ya fito, dogaransa duk suka mik'e, suna gaisheshi, amsawa ya shigayi tamkar baya so.
       d'aya aciki yace, “zamu tafine ranka ya dad'e?”.
    Kansa ya jinjina masa alamar eh, sannan yace “ama saleem magana”.
     Da sauri suka amsa da to.
        Ficewa yayi, sauran dogaran sukabi bayansa. Mota aka bud'e masa ya shiga, za'a rufe murfin ya hana, idonsa akan k'ofar plaza d'in harsu Aiyaan suka fito tare da saleem, dogarai biyu d'auke da manyan ledoji.
     Suna hangoshi suka k'arasa da gudu, murmushi yayi ya d'aukesu d'ai-d'ai da kansa ya saka a motar, sannan aka rufe musu k'ofar.
    Sudai dogaransa sai mamakin yanda yake sakema su Aryaan sukeyi.
       Har sun fara tafiya ya fad'ama  sarkin mota suje zasu taho da Munaya.
     A ladabce sarkin mota ya amsa da to.

   
         *****************

       Muna tsaka da hirarmu aka kira wayata, sharewa nayi tamkar bazan amsaba, Munubiya ta harareni, ramawa nayi nima sannan Na d'aga.
      Ciki-ciki nayi sallama, ya amsa daga can, mamaki ya kamani danjin muryar Galadima, katseni yayi da fad'in “ki fito”. Bai jira cewata ba ya yanke wayar.
     Kamar zanyi kuka haka naji, Yaa Marwan ya fito daga d'aki yana saka rigarsa, kallona yayi yana fad'in “k ba jiranki akeba ne?”.
      Sai da Na kumbura baki sannan Na mik'e. shikuma ya fice.
    Da taimakon feena Na had'a komaina, har abubuwan da mama Rabi'a ta bani, sannan suka rakoni.  Mun iske Yaa marwan tsaye jikin motan ya dafa k'ofar suna magana da Galadima dake ciki bai fitoba.
       Dogari d'aya ya zagaya ya bud'emin, ido muka had'a da Galadima Na janye da sauri, shima janyewa yay ya maida hankalinsa ga Yaa marwan dake masa magana.
      Mamaki ya kamani ganin su Aiyaan, suma cikeda d'oki suka fad'amin a jiki suna dariya da fad'in “Auntynmu!”.
     Juyowa Galadima yay yana kallonmu, shima Yaa marwan yay dariya kawai, sannan ya rufe mana murfin yanama Galadima sai da safe.
       Su Aryaan sun kacame da bani labari, yayinda nikuma naketa musu dariya da biye musu, mamaki ya kama Galadima, bai ta6a tunanin ina magana hakaba, ya lafe jikin seat yana kallonmu cikeda birgewa.
    Nikam nama manta ko gaisheshi banyiba, saida yay gyaran murya sannan Na d'ago Na kallesa, murmushi namasa ina fad'in “yalla6ai barka da dare”.
      Shima wani miskilin murmushi ya min yana d'agamin hannu batareda yayi magana ba.
     Aiyaan yay saurin fad'a “auntynmu bafa yalla6ai sunansa ba, sunansa Uncle”.
    Kamar zan harari yaron sai kuma nad'an murmusa ina kallon Galadima dake kallonmu shima. janye idona nayi daga gareshi Na cema Aryaan to naji zanke fad'a.

         Har muka kai gida basu barmu mun hutaba, sai surutu suke da bani labarin abinda yafaru a gida bana nan, danaji zasu kauce hanya kuma sainai saurin waskewa.
     


 ★★*★*★★*★*★★


            Sarkin mota yana ajiye su munaya ya duba gefen seat d'in data zauna, takarda ya gani ya d'auka, dan sanda zasu shige tamasa wata inkiya da hannu.
     Dubawa yay yaga mita rubuta. Sallama yayma sauran 'yan uwansa sallama akan zai shiga gida.
    Daga nan ba gidan ya shigaba, saiyay dabarar da yabar masarautar gaba d'aya.
         Sun had'u da Saleem a inda suka shirya, saleem Ya bama sarkin mota handkerchief d'in da zasu shak'ama Muftahu.
     Sarkin mota ma yaje ya bama Ameer ne, daga nan ya dawo k'ofar fada amma k'aramar k'ofa tacan baya inda keda k'arancin tsaro.
      Agaban idonsa su Ameer suka sauke Muftahu a mashin yana cikin yanayin barci saboda abinda suka shak'a masa, saida ya tabbatar sunbar  wajen sannan shima ya koma ciki.


        Yau dai kam ni kad'ai Na kwanta a d'akina, Galadima ko lek'e bai lek'oba, yana can tare da su Aiyaan a d'akinsa.
    Nima kawai saina kira Momma mukasha hirarmu, tana bani labarin yanda jikin Abie yaketa k'yau a tsakaninnan, dukda kar yanzu maganar bata fita amma yakanyi bamai tsawoba, naji dad'i sosai, na masa addau'a mai tsawo tareda fatan alkairi, daga nan muka cigaba da tattaunawa akan maganar Abbana, da zancen su innarmu dasuka k'i yarda su zauna a gidan, innarmu ta dage bazata zaunaba tunda muma anan muke, saida Momma ta saka baki da mata bayanin da zata gamsu sannan ta amince zata zauna. Nasha dariya, dan dama nasan za'ayi hakan, innarmu kawai kunya da kawaici.
     Daga nan har muka dawo kan ta Muftahu, dayake tasan komai a kai, da taimakonta nima nake samun k'arfin gwuywa.
    Itama tasha mamakin jin Harun a lamarin, ta dad'e tana jinjina maganar nan. ta bama Samha muka d'ora da hira, saida naga time yaja ga zazza6in fama ya rufeni, sallama mukayi nai addu'a Na kwanta.
    Masu iya magana since sabo tirken wawa, saina kasa barcin, naji kawai ina kewar Galadima.

    Shima kansa yanacan sai juye-juye yakeyi, yakasa barci, bayan sun gama hirarsu dasu Aryaan yay musu shirin barci da kansa suka kwanta, aiki yad'an ta6a yana Neman dabaru akan binciko Muftahu, baiwani dad'eba ya kwanta shima, amma saiya kasa barci, juye-juye yaytayi agadon, ganindai da gaske ya kasa barcinne saiya mik'e yana jan guntun tsaki, kwanciya ya gyarama su Aryaan ya lullu6esu da bargo sannan ya fito da nufin wai zai duba munaya 🤣😜.

        Jin shigowarsa yasani k'ara lafewa tamkar nayi barci, ya kunna fitilar d'akin yana kallona, yaja wani dogon lokaci sannan ya kashe ya tako zuwa gadon, “nasan idonki biyu ai, dama kin tashi kinbar wani kumshe-kumshe”.
    Shiru nayi nakumak'i motsawa.
       Kwanciya yayi a gefena, yaja bargon shima ya lullu6a, tareda juyamin baya, yace “miya hanaki barcine?”.
        “farkawa nayi”. Na fad'a batareda ba kalleshi ba.
    Murmushi yayi yana fad'inn “ Hummm”.
     Daga nan duk mukayi shiru nawani lokaci, kamar an matse bakina nace “yalla6ai na tambayeka please? ”.
     Yace, “Uhmm”.
  Juyowa nayi ina fuskantar bayansa, a nutse nace, “wai dan ALLAH ina sauran matan Abie yanzu?”.
     Da sauri naga ya juyo gareni, ni harma tsoro ya kamani nai baya da sauri, nazata makeni zaiyi, amma sainaji ba hakaba, yace “Munaya mi kika sani a kaina ne?”.
     “yalla6ai kamarya mina sani a kanka? daga tambaya?”.
      Yace, “Humm yana matsowa gareni, zan matsa ya rik'o hannuna................✍🏼



Kuyi manage da wannan please🤦🏻‍♀








*_ALLAH ya gafartama mahaifanmu😭🙏🏻_*

*_typing📲_*


 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*


           *_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
                  _(Kaga gayya)_



              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



   ~Book 2~ 👉🏻1⃣4⃣


................Yanda ya rik'e hannun yasani fad'in “please yalla6ai akwai zafi fa”.
        Sassauta rik'on yayi, ya sauke ajiyar zuciya, muryarshi a sanyaye yace, “Miyasa kikeson 6oyemin abinda kika Sani? shin bak'ya tausayinane? kullum cikin aiki kwakwalwa ta take, aikin Neman kud'in da zan taimaki kaina da ahalina, aiki akan mak'iyana,  ya kike tunani a kaina? yanzu haka ji nake tamkar kwalwar kaina zata tarwatse saboda damuwa da abubuwan da suka sakata matuk'ar nauyi, ta6a kiji yanda zuciyata takoma bugawa a slowly”. ya kamo hannuna ya d'ora a k'irjinsa, saitin zuciyarsa. da gaskiyarsa kad'an-kad'an zuciyarsa ke aiki, ba kamar kowanne bugun zuciya dake tafiya normal ba. Sai naji tausayinsa ya kamani, cikin sanyin murya nima nace,
         “yalla6ai kayi hak'uri da abinda zan fad'a maka, inhar ka kawoni gidanka ne domin muyi aiki tare a matsayin Friend bai kamata ace ka gaza yarda daniba akan sirrinka. kasan minene yake saka kwalwarka da zuciyarka wannan nauyin kuwa?”.
     Kansa ya girgiza mini.
     Na gyara kwanciyata ina kallon p.o.p, “Matsalarka d'ayace baka yarda da kowa ba sai kanka, mu cire Momma da papi, dansu aiyukansu sunkai amusu uzuri, Momma hankalinta akan jiyya yake, dan haka kana k'ara mata damuwa, papi kuma babbane shawara da dabarun manya kawai kake buk'ata daga garesa. Sai kuma Muftahu da Harun nakula suma kakan d'an saki jiki dasu akan wasu abubuwan, to amma fa.........”.
    Saitayi shiru bata k'arasaba.
     Ya matso jikinta sosai, tare da d'ora hannunsa saman cikinta, murya k'asa-k'asa yace, “Harun da Muftahu amma fa mi? Please ki k'arasa mana”.
    Kad'an Na juyo nad'an kallesa, Na d'ora hannuna nima akan nasa daya d'ora akan cikina. Janye fuskata nayi Na koma kallon p.o.p d'in. “kayi hak'uri da abinda nake fad'a, badan ina zarginsu bane zan fad'a d'in, dama zancene Harun da Muftahu kuma kamar bai kamata 100% susan komaiba, dan za'a iya sayensu ko tursasasu suci dunduniyarka. domin koba komai har yanzu bakada tabbas d'in cewar babu hannun wasu a cikin masarautar nan. amma kayi hak'uri idan na shiga hurumin daba nawaba”.
     Shiru yay baice komaiba tsawon lokaci, har nayi zaton nayi laifi ko yayi barci, a sanyaye nakuma fad'in “please & please kamin afuwa yalla6ai”.
        “is okay”. ‘kawai ya fad'a yana kuma sakani a jikinsa, tareda d'ora ha6arsa saman kaina.
      Babu Wanda yasake magana a tsakaninmu, kowa yay shiru yana k'ullawa da kwancewa, har dai barci yafara fisgata.
     “Kina ganin su Aiyaan bazasuyi kuka ba idan suka farka sukaga su kad'aine?”.
     Naji maganarsa cikin kunnena.
       “a'a” na fad'a ina girgiza masa kai, “ko'a gida sukad'ai suke kwana dama”.
       “okay”.
Saikuma muka kuma yin shiru, har barci yakuma fara d'aukata yakuma fad'in “kozaki sha Magani ne?”. ‘yay maganar yana ta6a gefen wuyana’.
     Kaina Na girgiza masa batareda nace uffanba. shima bai sake cewa komaiba..

        Yanda numfashina ke sauka a hankali sai ya fahimci nayi barci, shiko gaba d'aya yakasa nasa barcin, tunanin wani Abu daya ta6a faruwa a baya ya fad'o masa, dukda shi ba yayi imani da hakan baneba.
               👇🏻
     *_Wata ranar juma'a a India, sai suka tashi da matsananciyar damuwar motsawar ciwon Abie, a time d'in ma sun zata rai zaiyi halinsa, hankalin Galadima ya tashi har ciwonsa shima yakai ga motsawa, amma yak'i yarda doctors su dubashi, yace abarsa kawai gara ya mutu ya huta, hankalinsu momma ya tashi, amma Galadima yak'i sauraren kowa, daga k'arshema saiya sulale daga asibitin ya fice abinsa, haka yayta tafiya rik'e da k'irjinsa saboda azabar ciwon da zuciyarsa ke masa, mutane sai kallonsa sukeyi, shiko baimasan sunayiba, yayi tafiya mai nisan gaske batareda yasaniba. k'arfinsa da kuzarinsa sukai gazawar da bazai iya cigaba da tafiyanba, shine yazube a wajen ya fad'i._*
      *_bai tashi farkawa ba sai awani d'aki mai kama dana bunu, ya yunk'ura zai mik'e amma saiya kasa, wani tsoho ba indiye, a cikin indiyawan ma irin masu k'yawunnan sosai, ya dafa kafad'arsa, cikin harshensu yace ma Galadima “koma ka kwanta d'an saurayi, bakada lafiyane”. Galadima yace “kayi hak'uri baba gida zanje nasamu sauk'i, zamana annan bak'aramin tashin hankali bane ga ahalina”. tsohon yay murmushinsu Na manya, yace “zakaje gida d'ana, ni da kainama zan kaika, amma lallai kai acikin al'amuranka akwai abubuwan ban mamaki da al'ajabi, gakuma tsantsar rud'ani, saidai komai yanada lokacinsa, kuma lokaci zai tabbatar maka hakan, albishir d'aya zanmaka, nanda wasu shekaru dabasu Gaza 7 ba mai taimakonka zatazo, kwarai zatazo gareka, ba lallaine ka fahimci abinda nake fad'aba ko yarda dani, Dan Na lura kaid'in musulmine, kuma bad'an wannan k'asarba, amma wannan mai taimakon naka itace zata zama fitilar haska maka hanya kakai ga cinmma burinka, domin taurarinta da naka sunada matuk'ar k'arfi, harma suna gogayya da juna, zaku zama sh........”. Saikuma yayi shiru yana murmushi, ya shafa kan Galadima yana fad'in “tarin Albarka sucigaba da baibaye rayuwarka data zuri'arka”._*
      *_daga wannan maganar sai barci mai nauyi ya kwashe Galadima, koda ya farka saiya gansa a asibiti tareda su Momma, yata tambayarsu INA tsohon yake sukace su basu San wani tsohoba, wasu samarine su biyu suka kawoshi asibitin, wai sungansa yafad'i a gefen hanya, zancen tsohon yata damun Galadima a time d'in har yayta bincike kozai gansa amma ko alamun mai kamarsa bai ta6a ganiba, daga hakama saiya cire abin a ransa yacigaba da harkokinsa._*

       Ajiyar zuciya ya sauke, tareda kuma rungume Munaya, a kan la66ansa ya furta “ALLAH kaine mafi sani”. daga haka yay shiru tareda lumshe idanunsa, barcine yayta fusgarsa harya samu nasarar sacesa.
     Can gabannin asuba yay wani mafarkin daya sakashi farkawa a firgice, har itama Munaya ta farka tana tambayarsa lafiya?.
   Kansa ya dafe, da hannu yaymin nuni na bashi ruwa.
    Sauka nayi daga gadon dan zazzza6inna ya fara hucewa nima, freight na bud'e na d'akko masa ruwa, na had'o da Kofi, zama nayi kusa dashi a gefen gadon na tsiyaya ruwan a Kofi na mik'a masa. kar6a yayi ya shanye, ya mik'o min kofin, zan kar6a ya girgiza min kai tare da min nuni da in k'ara masa.
    Kuma tsiyaya masa nayi, yakai rabi ya d'aga min hannu alamar ya Isa, bayan yakuma shanyewa ya mik'a min kofin yana fad'in “Thanks”.
       Kar6ar kofin nayi, ba tareda na tashiba nace “Yalla6ai lafiya kuwa”.. 
       “Mafarki”. ‘yafad'a yana komawa ya kwanta’.
    Idanu kawai Na zuba masa, kusan 4minutes ya juyo da kansa ya kalleni, “kizo ki kwanta mana”.
      K'aramar ajiyar zuciya kawai Na sauke Na mik'e, Na d'ora ruwan da Kofi a dirowan gefen gadon na koma inda nake na kwanta.
    Ganin ya sauya hannun da yay mafarkin kuma yana addu'a sai ban sake cewa komaiba, na kwanta shiru ina sak'e-sak'e a raina mafarkin mi yayi to? da har yasakashi firgita irin haka?. banida mai bani amsa dan haka nayi shiru.
      Saiya zamto da asuba na rigashi tashi, harma saida nayi alwala sannan na tadashi, da k'yar ya iya tashi yana dafe kai, binsa nayi da kallo kawai harya shige toilet.
     Lokacin daya fito na fara salla, dan haka saiya fice kawai. A mamakinsa saiya iske Aiyaan da Aryaan sun tashi suna alwala, hakan ya Burgesa sosai. Sai kawai ya kama hannunsu suka tafi massalaci.
    Bayan an idar da salla bai yarda sun had'u da Sarki ba, ya gudo. Sai dai abinda bai saniba shi Sarki ya gansa, dan yau ya makara salla shima.


      Wajen Around 9am nagama gyaran d'aki nayi wanka, saina d'an fito falon domin duba dubawa, natarar sabbin kuyangina suma komai sun gyarashi k'al, harma da mana break fast, banyi yunk'urin bud'ewa ba ma balle tunanin son ci, dukda kuwa natashi da yunwa, to amma Momma ta gargad'eni sosai akan cin abinci wani a masarautar, dan haka na fito daga kitchen d'in kawai.
      Tunkan na shigo nake jiyo maganarsu Aryaan, zaune na iske Galadima su Aiyaan na kusa dashi suna bashi labari, anmusu wanka tsaf, sunsha sabbin kaya iri d'aya.
        Har yanzu Galadima bayada walwala, na zauna ina gaisheshi, batareda yabar latsa wayarba ya amsa min, su Aiyaan suka dawo kusa dani suna gaisheni, kumatunsu naja ina murmushi, “oh my guys kunsha k'yau, waya muku wanka haka?”.. 
       Atare suka amsa min da fad'in “Uncle ne, kuma ya saka mana tirare yanda kuke mana”.
     Murmushi nayi, na saci kallon Galadima da yay biris damu kamar baya d'akin, alhalin sanda na shigo na iske suna hira shidasu 'yan 2.
     Sallamar da wata baiwa keta kwad'awa na amsa, sannan na mik'e na fita dannaji minene?  A k'ofar falona na isketa, nace, “miya farune?”.
       Duk'ewa tayi ta gaisheni, sannan ta mik'omin ledojin hannunta tana  sanarmin Sarkin motane yace “na kawo wannan ranki ya dad'e”.
      Kar6a nayi, na koma ciki.
     Ajiye ledojin nayi a gabansa, “gashi wai inji sarkin mota”.
     Idanunsa ya d'ago ya kalleni, yace, “breakfast d'inku ne”.
    Tashi yay ya fita yana fad'in na shirya zaije ya dawo mu shiga cikin gida gaida mutane.
    Na amsa masa da to.



___________________


       Tun a daren jiya wasu bayi sukaga Muftahu, dan haka suka shiga ihu, dandanan sauran bayin dake kusa da wajan suka firfito, manyan bayin cikinsu ne suka kai maganar  cikin gida, shine akasakasu d'aukar Muftahu su shiga dashi.
      Lamarin yabama kowa mamaki, babu wani mummunan rauni a jikinsa, inbanda d'an  jini dake gefen bakinsa, saidai sun sami kwanciyar hankali ganin yana numfashi.
    Maganar dawowar Muftahu bata baje masarautar ba sai washe gari.
    Bayan Galadima ya fito daga sashensa zaije fada yaji anata k'ananun magana akan dawowar Muftahu, saidai kuma miskilancinsa bai barsa ya tambayi kowaba ya nufi Fada.
     Ya isa mai martaba baikai ga isowa ba, dan haka suka gaisa da 'yan majilissar Sarki dake fadar, sannan ya nemi mazauninsa dake gefen Sarki Na dama ya zauna.
    Zamansa baifi da mintuna 10 ba Mai martaba ya iso, gaba d'aya suka mik'e tsaye, dogaran Sarki sunata kirari da fad'in gyara kintsi da k'yau, duksun baza riguna ba'a gani mai martaba, basu bar kowa ya gansa ba har saida ya zauna a kujerarsa.
     Baya suka mammatsa mai martaba ya bayyana, atare su Galadima suka rissinar dakai alamun girmamawa, sannan kowa yafito tsakkiyar fada ya mik'a gaisuwarsa ga Sarki, yayinda fadawa ke faman amsawa, tsakanin Sarki dasu kuwa shine d'aga hannu.
      Mai martaba yayi mamakin ganin Galadima yau azaman fada, bawai baya zaman bane, sai dai yakan dad'e bai zaunaba, an masa uzurine kasancewar ansan ba zaune yake dindin dinba, kuma idan yazo akwai harkokinsa Na kasuwanci da yakeyi, sai dai dolene yakan shigo yayi gaisuwa.
     Bayan fada ta nutsu aka fara fadanci.
    K'a idane fadar gagara badau takanyi fadancine a sati sau hud'u kawai, litinin ba'a zaman fada, domin ranace da ake tunawa da abinda ya faru ga tsohon Sarki mahaifin Galadima, talata, laraba, alhamis, asabar, sune ranakun da ake fadanci, ranar juma'a ma ba'ayi saboda muhimmancin ranar ga al'ummar musulmi. A wad'annan ranakun akanyi zamanne daga 10am zuwa 12:30pm, da an tafi sallar zuhur ba'a dawowa, idan kaga anwuce wannan time d'in a fada to tabbas akwai abinda ya farune.
    A wannan zaman fadancine maganar dawowar Muftahu ta fito, sun tattauna akai harda shirin kuma d'aukar matakai Na tsaro a masarautar.
   
   Bayan anyi sallar zuhur ne Sarki ya shige gida, sauran fadawa ma kowa ya kama gabansa, Galadima bai shiga gidaba saiya nufi sashen su Muftahu domin dubashi.
     Bayan an masa iso ya shiga, ya iske mahaifiyar Muftahu da 'yan uwansa zagaye dashi, har yanzu kuma yana cikin yanayin barci.
     Ya jajanta musu, Yakuma kwantarma da mamansu Muftahu hankali, kusan mintunsa talatin ya fito ya koma sashensa.
      Ya iske su Aiyaan kawai a falon Munaya suna kallo, suka taso da gudunsu suka rungumesa, fuskarsa cikeda fara'a ya tarbesu, ya tambayesu ina Auntynsu?.
      A tare suka bashi amsa, “Uncle tana d'aki ta kwanta kuma tace karmu tadata, inba hakaba jiki magayi”.
     Murmushi yayi yaja kumatunsu, “kuce zatayi zana kenan idan aka tada ita?”.
    Nanma atare suka amsa da “eh Uncle, kasanfa Aunty Munaya tacika fad'a, gidanmu tsoron masifarta akeyi, amma ita Aunty Munubiya babu ruwanta”.
     Galadima yace, “da gaske?”.
     “ALLAH kuwa Uncle, idanfa mukayi rashinji ita ke zanemu ba innarmu ba, kuma dukanta da zafi, gashi taita hararmu da katun-k'atun idanunta nan”.
       Sosai abin yabama galadima dariya, dan haka ya dara sosai abinsa yana fad'in, “kubari tajiku to, idan ta zaneku babu ruwana nidai, kunga bara naje naga kota tashi, karfa Ku shigo, dan zata iya zaneku”.
      Sukace “ai bazamu shigoba Uncle”.
      Yace, “good boys”.

    Da sallama ya shigo, amma saiya isketa baje a gado tana shak'ar barcinta, yad'an murmusa kafin ya k'arasa ya zauna a bakin gadon saitin fuskarta, yatsunsa biyu yasaka a gefen wuyanta dan yasan da wahala wannan barcin ya kasance na lafiya, aikam jikinta ringim yake da zazza6i, tausayinta ya kamashi, lallai uwa dabance acikin al'umma, Ashe haka sukeshan wala, tundaga d'aukar cikinma zuwa rainonsa, akoma rainon yaro, daganan tarbiyarsa, lallai masu raina mata ko kallonsu masu k'arancin tunani sune masu k'arancin tunanin ai, ya d'an lumshe idanunsa yana cije lips, ganin ta dunk'ule a waje d'aya saiya ja bargo ya lullu6a mata, harya mik'e ya koma ya zauna, risinowa yay kanta a hankali ya mannama goshinta kiss, sannan yamik'e ya fice.
       Koda ya dawo saiya wuce d'akinsa, yabar su Aiyaan suna kallonsu.
     Kayan jikinsa ya cire ya kwanta shima, dan yana buk'atar hutawa kona 2hours ne, kwanciyarsa kuwa babu dad'ewa barci ya saceshi.

     Kiran sallar la'asarne ya tashesu kusan lokaci d'aya, Galadima yatashi da k'yar, a mamakinsa sai yaga Aiyaan da Aryaan kwance a gefensa suma suna barci, murmushi kawai yayi yasako, saida ya watsa ruwa sannan yay shirin tafiya massalaci cikin k'ananun kaya.
     Harzai fita saiya dawo yashiga wajen Munaya. tana tsaye gaban wardrobe tana neman kaya, da alama wanka tayi, dan daga ita sai towel.
      Banji sallamarsa ba, saboda shi idan zaiyi magana bayason bud'e baki, ganin batajishiba saiyayi gyaran murya, a tsorace na waigoshi, ganin shine nai saurin saka kayan dana d'akko ina kare k'irjinna da tura baki, bakinsa ya d'an ta6e, sai kuma ya shiga takowa inda nake, duk takun da yayi sai gabanna ya fad'i, na waiga kozan samu nabar wajen ko abinda zan suturta jikinta sosai, amma sainaga babu a kusa, kuma ina jikin wardrobe d'inne sosai ai. ban gama yanke shawara ba ya k'araso daf da ni, kuma matsawa nayi na matse jikinna sosai a drowa d'in, shikuma yawani had'e gabas da yamma, wannan ne yakuma sakamin tsoronsa a raina, na zata kowata tsiyarce ta kawoshi.
     Hannu yasaka ya d'ago da ha6arta muka kalli juna, ya tsareni da idanu yanda nakasa janye nawa cikin nashin, munkai kusan 2minutes a haka, kafin yakumamatsoni sosai, ya kai fuskarsa gab da tawa tamkar zai had'e bakinmu, dan haka saina lumshe idanu, murmushi yayi ya hura mata iska akan idanun, ta rumtse idon sosai, ya d'an ja baya yana ta6e baki, kafin yasaka hannu ya cire nata dataketa faman kare k'irji da kayanta, still ya kuma matsawar saitin kunnenta yana fad'in “wane darene jemage bai ganiba yalla6iya”. ‘ya k'are maganar da shafa kirjina ya fice abinsa.
      Kad'an yarage namasa ihu wlhy, aiko yana fita na durk'ushe a wajen ina sauke numfashi,  sometimes nakan rasa yazan fassara Galadima da ayyukansa.
    Da k'yar Na iya tashi nayi sallar nakoma kan gado Na kwanta.

     Galadima kam daya fita dariya ce taita cinsa, ya kula Munaya akwai tsoro, kuma haryanzu a tsorace take dashi, cikinnan ne kawai kanci galaba akanta yake samunta cikin sauk'i, ya girgiza kansa kawai yana murmushi.
     Bayan ya dawo massalaci d'akin nata ya dawo, dan yanason suje su gaida jama'ar gidan, maybe gobe suje masarautar papi ma.
        A kwance ya iskeni, nak'i kallonsa, jingina yay da mirror yana fad'in “yaya jikin naki?”.
         Ban kalleshinba nace, “da sauk'i”.
        “ALLAH ya k'ara sauki, idan zaki iya tashi ki shirya muje cikin gida, kafin waccan tsohuwar tafarama mutane surutu”.
        “to” nafad'a ina mik'ewa, Na sakko a gadon, harna nufi wardrobe zan d'auki alk'yabba saina tsaya, batareda Na kalleshi ba nace, “toka fita Na shirya”.
       Hard'e hannayensa yayi a k'irji yana fad'in “ashe bazaki shirya d'inba, dan bazanje ko inaba”.
        “karkaje d'in, ai akwai bayi” nayi maganar a zuciyata.
    Kayan Na d'auka na shiga toilet, shikuma ya ta6e baki.

     Babu dad'ewa na fito tsaf, nayi k'yau, nazo ta gefensa na d'auki turare nasaka kad'an sannan na kallesa nace, “na shirya”.
       Baice komaiba ya nunamin hanya, gaba nayi yana bina a baya muka fice.
     Kasancewar tazarar dake d'an tsakaninmu da sassan nasu muka shiga mota, dan banajin dad'in jikinna, bama zan iya tafiyarba.
    6angaren Abba hayatudden muka fara zuwa, daga nan sai sashen matan mai martaba, soyayyar da uwargidansa ke nunamin yasani k'ara k'aunarta, sai addu'a take zabgamin akan ALLAH ya saukeni lafiya. Galadima kad'ai ke amsawa, amma ni saidai a zuciya kawai. daga nan muka d'an shishshiga wasu sassa, 6angaren mama fulani shine k'arshen zuwanmu.
      Kunsan dai mutuniyar taku akan mulki, tana kishingid'e kuyanginta nata bauta, mai matsa kafa daban mai firfita daban, ga masu bata labarai, tufa takeci cikeda k'asaita da izza.
      Amintacciyar baiwarta data mana iso tana gaba muna biye, mama Fulani ta d'agama kuyanginta hannu alamar subata waje.
    Rige-rigen ficewa suka, yayinda mukuma muka k'arasa gareta, idonta a kammu ko k'yaftawa batayi, nidai tsarin ALLAH na nema daga sharrinta, ina dalili   wannan kallon k'urilla haka?.
        Galadima yace, “barka da yammaci”. nima saurin fad'a nayi.
     A yatsine ta amsa mana, ta d'ora da fad'in “Saraki kayi wuyar gani?”.
     Galadima ya murmusa yana kallona, “Ranki ya dad'e kinsan mai amarya ai yafi dubu wahalar gani dama”.
     “Humm” kawai tace batareda ta amsaba.
     Sai zuwa can tace “nafa manta, ina tayaku murnar samun k'aruwa”.
      “mun gode ranki ya dad'e, amma taki murnar itace tazo a latti, gashi kuma idonkine yafara hango abin cikin kwan tun a india”.
       Mama Fulani ta tsatstsare Galadima da idanu, shikuma yay salute nata yana murmushi.
      Jitai kamar zata makesa dan haushi.
      Ya lura da haushin da taji, dan haka ya kama hannuna muka mik'e tsaye yana fad'in, “bara mukoma inda muka fito ranki ya dad'e, a huta lafiya”.
    Bai jira amsartaba mukayi fitowarmu.
       Da kallo kawai ta bimu, takasa koda motsawa, tarasa miyyasa yau Galadima da matarsa suka mata wani mugun kwarjini? batada mai bata amsar tambayar tata...


      Yini guda yau Galadima a gida yayishi, baije ko inaba, sai da daddare Nuren yazo sukayi magana, daga nan yace ya nema mana tickets d'in zuwa masarautarsu.
 
    Washe gari muka tashi da shirin tafiya masarautar su papi, mukad'ai muka tafi, babu kuyangi babu dogarai, dagani sai shi dasu Aiyaan, sai Nuren..................✍🏼








*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu_*😭🙏🏻

*_typing📲_*


 💡 *_HASKE WRITERS.    ASSO....._*


           *_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
                  _(Kaga gayya)_



              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



   ~Book 2~ 👉🏻1⃣5⃣


...................Abin yabani mamaki ganin yanda akazo tarbarmu, yo saikace wani Sarki, hakan yakuma tabbatarmin da Galadima d'an gatane a wannan masarautar.
        A masarautar ma gungun mutane muka iske wai masu tarbarmu, ni dukma sai kunya ta kamani wlhy, musamman da Mom ta rungumeni tana fad'in “ga maman twins d'inmu ga Maman twins d'inmu”.
    Galadima dai murmushi yayi, Nuren kam dariya ya kemin.
    Lallai naga tsantsar soyayya a wannan masarauta, sai nan nan ake dani kamar wata sarauniya, duk wani Motsina Inno tace minakeso? hakama mom.
     Aiyaan da Aryaan kam ai suna tare da Galadima, duk inda yasaka k'afa suna biye.
    Nikam dai a kwana biyun da mukayi babu abinda zance da wad'annan bayin ALLAH sai godiya, naga karamci naga hallaci sosai, hakama k'annena.

     Sosai Galadima yasamu tattaunawa da papi a tsakaninnan, sunyi maganganu masu muhimmancin gaske. Musamman akan ciwon Abie da cikin jikin Munaya, harma da Abbanta. sosai kuma Galadima yakuma samun haske akan lamuran.
   Kwannamu biyu muka dawo cikeda kewarsu, tare da tarin alkairi ga wad'annan mutane masu tsayawa a rai.
     Mun dawo da kwana 1 yaran gidanmu na ma'auri suka kawomin ziyara.
     Aunty khaleesa, aunty Hauwa'u, aunty Ramlah, aunty Raheenat, matansu ya hameed, Fiddausi, Siyama, Zarah, Safara'u, Fauziyya, Haleematu,Munubiya, Ayusher, Feena. Wayyo dad'i wlhy saika d'auka biki akeyi, rasa inda zansaka kaina nayi saboda dad'i, shi kansa Galadima ya fahimci ina tare da tsantsar farinciki, nima dagewa nayi namusu hidima iya hidima, dan hardani aka shiga kitchen.
    Sukam duksun rikice da mamaki, dama haka gidan sarautar yake, dan saidama Galadima yaje da kansa ya shigo dasu. Su Aiyaan anata murna anga 'yan gida.
     Ranar dai anan suka yini zir, dazasu tafi Galadima yay muzu alkairi mai yawa tareda godiya ta musamman. Sunji dad'i sosai kuma sunyi farinciki, sunata masa godiya nima ina tayasu.
    Da zasu tafi jinai tamkar na rik'esu, aiko harda 'yan kwallana, sauk'inama kawai su Aryaan tare dani.

     Kowaccensu tatafi da labarin data gumtsawa uwarta a bayan fage, dansu Zarah dai sun Shiga taitayinsu, sun gane ruwa ba sa'an kwando bane, nanfa hassada da bak'inciki tamkar ta babbake zukatansu, mamansu Yaa hameed hardama Abba ALLAH ya Isa tana sharar kwalla, wai yasan da gidan sarautar amma ya yarda Zarah ta auri d'an sanata, ga aunty khaleesa nanma kullum cikin matsala da miji, dan kishiyarta akwai kissa.


     *_ALLAH yarabamu da ciwon hassada fans_*😏


         Sati d'aya da zuwansu muka koma India, saboda Company suna Neman Galadima da gaggawa. harda innaro iya bala'i muka tafi🤣.
       A jirgi taita kudundune fuska a gyale wai batason ganin tashin jirgi, duk tsare gidan Galadima saida yayi dariya, Aryaan da Aryaan kam sukaita tsokanarta. Yau babu masifarnan dan bata kulasuba, saima Galadima ne ya hanasu. nikam banza na musu dan tawama ta isheni nikam. Jikina sai ciwo yakeyi, ga cikina na mun ciwo shima kad'an-kad'an.
       Khumar da Sauban da Samha sukazo d'aukarmu, muka rungume juna da samha muna farinciki.
      Daga nan muka wuce gida, yaukam munashan k'auyancin innaro, ni harma tabani haushi, komai tagani saita tambaya, Kodai su Aiyaan basa abinda takeyi.
      Mun iske jakadiyane kawai sai bayi, Su Momma da innarmu suna asibiti, Mudai sama muka haye ni da shi, 'yan biyu kuwa suna wajen Samha ta kasa ta tsare, innaro kuma aka barta da jakadiya.
      Ko ina tsaf yasha gyara tamkar mai d'akin na nan, Muna shiga kwanciya nayi bisa kujera, naja bargon saman gadon na lullu6e, kallona yayi da mamaki “k lafiyarki kuwa?”.
      “zazza6i”. kawai nace masa na k'udundune har kaina.
      Zama kawai yayi ya zubamin idanu cike da tausayi, ganin zaman bazai masaba yatashi ya shiga toilet, saida ya gama dukkan uzirinsa sannan nima ya had'amin ruwan wanka, tadani yayi, na tashi da k'yar tamkar zan masa kuka.
         Yace, “tashi kije kiyi wanka kozakiji dad'i”.
       Baki na tura masa gaba.
         “idan bazaki iyaba tashi muje na miki”. ‘yay maganar cike da basarwa’.
     Harara na zuba masa sannan na mik'e na nufi bayin. shikuma ya ta6e baki yana wani mikilin Murmushi.
        Abincima sai nan ya saka aka kawomin, dan nakasa sauka.
            Innaro sai catake wai nacika langyare, dan naga yana shagwa6anine shiyyasa nake ta6ara, ai badaga kaina aka fara cikiba.
     Galadima dai murmushi kawai yayi danshi lamarin innaro abin dariya ya d'aukesa, tana buk'atar uzuri.
      Bayan nasamu naci abinci daya bani nasha magani, harzan kwanta a sofa yace na koma saman gadon, kamar zanyi magana saina fasa, na tashi kawai na koma.
     
       Yana kammala duk abinda ya dace yafice asibiti domin duba Abie da Abba.
      Yaji dad'in yanda yaga canji sosai a jikin nasu su duka, dan raunuka da yawa sun warke a jikin Abba, da bakinshi ma ya amsa masa gaisuwa yana masa godiya, inna da baba k'arami sunata saka masa albarka. maganar da abie ya fara kuwa rungumesa yayi yana kuka Abie nayi, hakama su Momma, a hankali Abie yace “ina d'iyata Muh'd”.
      Murmushi Galadima yayi, yace, “zuwa anjima zaka ganta Abie, yanzu na barta tana barci zazza6i ya rufeta”.
       Momma da Aunty Mimi sukace “ALLAH dai ya sauketa lafiya to”.
     Babu kunya Galadima ya amsa da amin.
    Aunty Mimi dake kusan dashi ta doki gefen hannunsa, “kai mara kunya, shine zaka amsa”.
       Hannu ya saka ya rufe bakinsa yana fad'in “ni jikan Abdul'fatah da Abubakar”.
      Dak'uwa Momma tamasa tana kai masa duka, ya matsa da sauri yana dariya.
    Abie ma murmushi yakeyi, lallai yau yakuma ganin canji tare da d'ansa sanyin idaniyarsa, sukam yaushe rabon da suga irin wannan nutsuwar tare dashi haka, lallai dolene su godema ALLAH da shigowar Munaya cikin rayuwarsa, basu da wani abinda zasu iya biyanta har abadan, saidai suyita mata fatan alkairi da k'yautata rayuwarta.
      Saida na tashi sannan muka tafi asibitin muma, wajen su momma muka fara zuwa, Momma da aunty Mimi sukazo suka rungumeni tamkar zasu had'iyeni dan dad'i, nikam duk kunyarsu ta gallabeni, sai 6oye fuska nakeyi, koda zan gaida Abie ban yarda na kalleshiba.
    Sauban da Samha sai dariya sukemin.
       Duk bak'in halin innaro saida tayi kuka ganin halinda Abie yake ciki, taita kwarara masa addu'a kuwa.
    Su momma sunji dad'i, kuma sunata girmamata.
      Samha sai dama-dama takeyi dasu Aiyaan, motsi kad'an tace, “ALLAH yasa Aunty gimbiya muma ta Haifa mana irinku”. Su Momma sunata amsa mata da amin. Nidai kaina na k'asa saboda kunya, ina lura da Galadima kuwa duk sanda tafad'a saiya murmusa kuma bakinsa ya motsa alamar yana amsawa da amin.
         Sosai naji dad'in ganin jikin Abbanmu shima, dan har magana mukayi, jikinsa yayi k'yau sosai, karayunne ma kawai suka rage nakula, amma k'ananun ciwukan duksun warke, to wajene dayake samun kulawa ta musamman. Munaya harda rungume inna, itako ta tureta tana hararta, su Aiyaan kam duk sun d'are bisa cinyarta suna d'okin ganinta da kewarta. Itama tayi kewarsu over, tsakanin uwa da d'a kenan (iyaye mata ga naku fa🥰🥰🥰❤👍🏻).
     
     Haka muka dawo gida ina farinciki, koba komai nasamu nutsuwa mai yawa a yau d'innan, aiko ban yarda mun kwantaba saida nayi nafilfili domin mik'a godiya ta ga ubangijin sammai sannan na kwanta.
      Galadima kuwa muna shigowa d'akin sirrinsa ya shiga yanata aiki.




___________________________


       Hankalin Minister ya kai k'ololuwar tashi shida families nasa akan 6atan 'yarsa, farhat, duk wata hanya daya kamata subi sunbita amma babu koda labarin Wanda ya ganta, tun lamarin nabasu mamaki harya koma basu tsoro, ga wani text massage da akama minister d'in d'in kwana 10 daya wuce.

      _Idan kana buk'atar 'yarka kana iya mik'a wuya._

       Wannan massage ya tsaya masa a rai, har police sun kar6a amma sun gaza gane komai gameda massage d'in ko wannada ya turo shi.
     Mahaifiyar Farhat harda kwanciya asibiti, dan ita kad'aice mace a gidan, dan haka suke masifar son yarinyar da mata gata, dudu shekarunta 16 ne kawai, tana wata private boarding school ne a abuja. a binciken da Galadima yakeyine ya gano hakan, kuma yayta bibiyar yarinyar har saida yasamu nasarar saka Nuren ya kwamuso masa ita.



___________________________


     Tunda muka dawo India bani da lafiya, kullum innaro cikin min gorin ni ragguwace take, bana wani kulata dan tawa ta isheni, koma uwarmi zata fad'a ta shekara fad'i, bazan yarda mu Raba hali a gidan surukai naba, nakan bar lamarinta a wasan jika da kaka agabansu, amma ni nasan badan hakan takeyimin ba, ita kanta innarmu bata kulata ko kad'an, idan tanayi shiru take mata ma.
     Kulawa kam bazanyi butulciba ina samu wajen Galadima dasu Momma, musamman ma jakadiya da Aunty Mimi. Saukina ma cikin bamai tsurfa baneba, komai inaci hankali kwance, kuma ban ta6a amaiba ko wani zubda yawu, saidai zazza6i da ciwon jiki.
     Yaudai dole Akash yazo har gida ya sakamin k'arin ruwa, kozan sami sasaauci.
     Yini guda yau a gida Galadima yayisa, duk wani motsina akan idonsane.


**************************


        *_5 months ago_*🙆🏻🙄😆


          A kwana atashi babu wahala wajen ubangiji, rayuwa ta shud'a, kwanaki nata sauri, a wanni da mintuna kam ai ba'a cewa komai, abubuwa masu yawan gaske sun faru a watanni biyar d'innan, ciki harda warkewar Abbanmu sarai, tamkarma baiyiba, saidai k'afarsa da yakan d'an tizgid'a saboda matsala data samu, shima saika k'uramasa I done zaka fahimci hakan.
       Innaro dai dasu Aiyaan tuni suka koma saboda makaranta, sai dai duk Hutu Galadima yakansa azo dasu Aiyaan d'in, hakama Munubiya da yaa marwan sunzo sun mana sati biyu sukaga jikin Abba da Abie.
      A wattani biyar d'inna Galadima yaje Nigeria kusan sau hud'u, dukda bai ta6a fad'amin wani abuba ina samun bayanai ga Saleem da sarkin Mota. har yanzu kuma Farhan d'iyar minister tana hannunsa, hakama Malam Saminu driver Alhaji Balala.
         Yaran gidanmu masu cikkuna duksun haihu, su Siyama an zama iyaye, naji haushin rashin halartar taron suna ko d'aya, dan dana fad'ama Galadima inason zuwa banza yamin, naci kukana kuwa na hak'ura, sai turomin abubuwan da akayi sukaitayi ina gani.

      Cikina ya fito kwarai da gaske, dan yanzu yana cikin wattani 7 da wasi kwanaki, yamin d'as yakuma sakani k'iba, duk kamannina sun canja, kumatuna sunyi manya, dukdai wanda ya ganni zaisan na canja, hakama Munubiya, idan ta turomin hotonta nata dariya kenan.
      Tsakanina da Galadima kuwa har yanzu muna a yanda kowa ya sammu, canji d'aya zance ansamu shine nuna yawan tausayinsa akan cikin jikina, dan dukkan wani motsina cikin nuna damuwarsa yake. Idan yana wajen aiki kam yakan kirani sau uku sau hud'u dan yaji lafiyata kawai.
     A 6angaren iyayensa da danginsa kam banida abin fad'a sai godiyar ALLAH, dan tamkar a kainane aka fara ciki haka suke nunamin kulawa.
     Hakan nama Innarmu da Abba dad'i, hankalinsu na kuma kwanciya sosai akan aurenmu. baba k'arami yakanyi wata d'aya ya tafi Dady kuma yazo, haka suka dingayi har ALLAH yabama Abba lafiya.
         Jikin Abie ma said dai muyitama ALLAH godiya, dan bayan magana an kuma samun cigaba 6angaren motsa hannunsa, yanzu kuma maganarsa takan d'an fito yanda akeji, saidai duk wannan cigaban da ake samu babu Wanda yasan dashi, har mai martaba k'aninsa, kaf masarautar gagara badau da dukkan wani makusanci bai San komaiba a kai, dan papi yahana fidda maganar, ko zuwa akai dubashi yakan komane tamkar yanda ya saba kamar da, daga mama Fulani har mai martaba sunzo kusan sau uku dubashi, hakama Muftahu da Harun, 'ya'yan Sarki ma dama suna k'ok'arinzuwa lokaci-lokaci suma. Hakama Hayatuddin Autan mama Fulani. amma babu Wanda aka bama damar sanin wani sirri akan jikin Abie d'in. dagamu sai mu kawai muka Sani.
     Dukda fama danake da kaina haka na dage muka cigaba da addu'oin nan, zuwan innarmu ma yakuma sakamu ho66asa saboda taimakon da take bamu, sannan muka raba addu'oin ga wasu musulmai malamai dake nan suma suka cigaba da tayamu, aka cigaba da bama Abie yanasha da wanka, doctors d'in sunyi surutunsu harsun gaji sun barmu, dan munk'i fasa masa amfani dasu, tunda muna ganin haske a lamarin sosai.

    A wata ranar talatar da su Abba suke shirin tafiya k'arshen satinne ina zaune a falo ni kad'ai, dan Galadima ya fita aiki tun safe, zafine ya isheni na dawo falon na k'ure AC, dan Galadima ya saka ma na bedroom d'in key saboda k'urewa da nakeyi, gashi inata fama da mura, shi kansa abin cikina ance tana Neman shafarsa. nikam bana iya hak'uri da Abu mai sanyi konasha ko AC.
      Sosai na baje ina kwasar dad'ina, sai faman lumshe idanu nake a cikin kujera, gama wayarmu kenan da Munubiya itama tana bani labarin halin son Abu mai sanyin datake a ciki, kullum Yaa marwan fad'a shida mama Rabi'a amma bata d'aga k'afa, data faki ido saita sha, Ayusher da dole ta dawo gidan tayata wasu abubuwan saita gani ta sanarma Yaa marwan, shikuma yay ta jarabar masifa, amma hakan bazai hana gobe tagani ta shaba........
       Jinai kawai iskar dake ratsani ta daina shigata, na bud'e ido sai naga Galadima tsaye jikin k'arfen bene daya shigo ta falon ya hard'e hannayensa a k'irji ya zubamin ido ransa a 6ace, hannunsa rik'e da remote d'in ACn.
       Tsorone ya kama ni, na tashi zaune ina wani marmar da idanu, da hura kumatu danaketa yi, takowa yayi inda nake, idonsa tamkar zai fad'o dan hararata “k kin rainani ko? bazan hanaki Abu sau d'aya ki daina ba, ki duba muran dake damunki tun cikinnan nada wata 3, shin ke bazaki tausayama kanki baneba?”.
     Shiru nayi bance masa Uffanba, sai faman kumbura baki dai nake yi.
      “kinsan ALLAH idan baki maida wannan bakinba na kamashi saiyayi jini”.
       Da Sauri na maida bakina, dan ban manta muguntar da yaminba kwana biyu daya wuce, ba k'aramin morata yakeba yanzu, saboda ALLAH yabani ciki mai sakani yawan buk'ata, sai komai ya lafa nayita masa kuka, shikam ya shareni saboda shegen miskilanci da k'asaita, idan na ishesa yace zai makeni, aibashi yace na kawo kaina ba, dan haka nabar cika masa kunne da ihu, anjima ma nazo yi zaiyi tunda ba fyad'e yaminba ninake kawo kaina.
      Sometimes nakanji haushin furucinnan nasa, nakuma yi alk'awarin nisantarsa, amma bana iyawa, kona d'auki alwashin saina karya, da yazo yara6u jikina nake mik'a wuya, mugun tunda ya gano lagona saiya dunga bina ta wannan hanyar, duk sanda yaji buk'atata yasan yanda zaiyi ya ra6u da jikina harta kai ga wani abinda nikuma zan mik'a wuya batareda na saniba, saidaga baya nake gane kuskurena.
      Ganin namasa banza nak'i tankawa saiya shige bedroom yana tsaki, komawa nayi na kwanta ina share hawaye. ga zafi ya fara addabata.

        Kusan mintuna 19 sannan ya fito, ya canja kayansa zuwa k'ananu, da Alama wanka ma yayi, k'in kallon inda yake nayi harya samu kujera ya zauna, remote ya d'auka ya kunna TV.
     Haka mukaita zama tamkar wasu kurame, kusan 30minutes, kiran da Nuren yamasane yasakashi d'agawa, bansan miyake fad'a masaba naga dai ya mik'e ya shiga d'akin sirrinsa.
     Na dad'e ina kallon k'ofar, zuwa can nima na yanke shawarar binsa kawai.
      Doguwar rigace yellow a jikina, batada hannu, sannan bata kaimin k'asa ba, kad'an ta wuce guywata👗, banason kaya masu nauyi saboda jin zafi, sai silifas d'in k'afata jaa mai taushi. cikinan ya kaimin ko ina, jinake kamar na jawo haihuwar na juyeshi na huta.
        Ciki-ciki nayi sallama, bai jiniba, hankalinsa nakan Computers d'in d'akin dayake k'ok'arin dai-daitawa, duksun kawo wuta, har k'aton glass d'in dake jikin bango guda na d'akin, ban ta6a d'aukar shima Computer baceba sai yau, dukna d'auka saboda ado aka sakashi a wajen.
     Sallamar na k'ara yi, ya juyo yana kallona, idonsa na cikin medical glasses mai haske, dan har kwayoyin idanunsa ina hangowa.
      Kamar zai shareni saikuma ya amsa mini, juyawa yayi yacigaba da abinda yakeyi, mikuma yagani saiya juyo, ya jawo kujera ya gyaramin, yay min alamar da ido na zauna.
    Babu musu na zauna, ya d'auki remote ya rage gudun AC d'in d'akin, sannan ya juya ga abinda yakeyi.
       
      Yanda yake sarrafa Computers d'in saiya tafi da imanina, kai guy d'innan yasan Computer over.
       Bansan lokacinda bakina ya su6uce nace, “yalla6ai ALLAH ya baka”.
         Juyowa yayi yana kallona da mamakin furucina, ya saka pen d'in hannunsa a baki yana wasa da shi, kafin ya shiga takowa gareni, k'asa nayi da idanuna nabar kallonsa, yaja kujera ya zauna kusa dani, idonsa a kan cikina, ban Ankara ba naji hannun nasa a saman cikin, idanu Na d'ago Na kallesa, ya d'agamin gira d'aya yana fad'in “ALLAH ya bani k'yautar magaji?”.
        Murmusawa nayi ina girgiza masa kai, “niba haka nake nufiba fa”.
        “mikike nufi to?”. ‘yay maganar yana janye hannunsa daga cikin nawa’.
      Fuska nad'an ya mutse, cikin salon yanga nace, “ina nufin ALLAH yabaka nasibin sarrafa Computer's ”.
      Yanda nayi maganar cikin salo saiya sakashi murmusawa yana ta6e baki, “toni miye namin yanga yalla6iya? saikace kina tare da masoyinki?”.
      Haushi ya kamani Na dalla masa harara.
     Bai kulaniba ya mik'e yana fad'in, “masu cikifa saida uzuri”.
       Harna yunk'ura zan mik'e yace, “oh haushi kikaji? to sorry zauna kiga wani abu”.
     Komawa nayi Na zauna INA k'unk'uni.
        Hotunane da yawa ya nunomin daga cikin Computer, ya danna hoton farko ya fito sosai. Batareda ya kalleni ba yace,
      “wannan sunansa *Kabiru Ibrahim*, nasanshi shekaru kusan 9 da suka shige a dalilin neman bayanan sirrina tacikin Computer, nabashi dama yashiga sosai saboda a time d'in yaci k'arfina, inada yak'inin wanine yabashi wani yanki sirri daga abinda nake da shi, ganin ya zuk'i bayanai 90 a cikin 100, saina tura masa goman gaba d'aya, saida ya zamana 99 duk sun shige ga Computers d'insa sannan Na nuna masa banbancina da shi, Na lalata abinda yake da shi da Wanda ya samu agareni, tundaga wannan ranar kuma nafara bibiyar rayuwarsa. Abin mamaki saina gano yanada Ubangida, shine wannan, *Timothy yoha*, dukkan abinda ya aikata agareni Umarnin uban gidansane Timothy, Na maida akalar tunanina ga Timo, saina iske shima aiki yakema wani, ba kowa bane face tsohon shugaban k'asarmu *Labaran Ahmad kachia*. shine wannan, nasan kuma k'ila kisansa dukda dai lokacin dayayi shugabanci bana tunanin an haifeki ma gaskiya, ta silar *Former p... Labaran Ahmad Kachia* nasamu wani kundin bayanai akan tsantsar abotar dake tsakaninsu su a k'alla 15, babu maijin sirrinsu  saboda Kansu a matuk'ar had'e yake, ALLAH yayima 4 daga cikinsu rasuwa shekarun baya kad'an, saisu 11 suka rage”.
      Ya kumayin wasu 'yan danne-danne nidai duk ina kallonsa da mamaki, hotunan mutane 15 suka bayyana, sai dai an lik'e fuskar mutum 4 alamun wad'anda suka mutu kenan.
     Gaban frigate d'in d'akin yaje ya had'a Coffee a mug, sannan ya tako zuwa gareni ya mik'amin, kaina Na girgiza masa alamar a'a, ya d'aga kafad'a sannan ya juya zuwaga Computers d'insa.
      “wannan mutane hud'un sune jiga-jigan wannan abota, d'aya ya rasu a cikinsu saura uku, *Josaya Bamma* shine mataimakin *Alhaji Lawan tanderu*, bayan mutuwar tanderu shugabancin wannan abota ya dawo hannunsa, dukkan wani shigi da fici na man fetur dake faruwa a Nigeria josaya Bamma yasanta, dan sune masu yinsa, yanda ake fita da mai a k'asar da yanda suka mallaki rijiyoyin mai ba bisa k'a ida ba, gwamnati kuma batada damar magana domin sune masu fad'a aji, sune tsoffin shugabanni da suka San dukkan sirrin k'asar, sai *Bana baba gana*, dukkan wasu magunguna dake shiga Nigeria saida saka hannunsu, akwai wad'anda batareda k'a idaba suke kaita shi da *Alhaji balala* da *William Solomon*, domin manyan likitocine masana sosai, *Hajia A'i Barnawa*, babbar d'iya ga tsohon soja *Garba mai dala sokoto*, tashiga wannan group d'in sanadin k'awarta *Victoria*, dukkan wani cin zarafi mata ko cin dunduniya suke saka ido, kullum suna ik'irarin sune masu Kare hak'in mata a zahiri, amma a bad'ini ba aikin da sukeba kenan, suna aikin gyara aljihunansu ne. wannan shine *Mansur Habibu Abu*, wannan kuma *Abdul-Naseer Nafi'u*, da *Miracle Asun*, wad'annan dukkansu manyan 'yan kasuwa ne, amma a bayyane, amma a 6oye su sukasan tsiyatakun dasuke shiryawa a k'ark'ashin k'asa *Sagir sulaiman Sulaiman* minister mai mulki a yanzu, sai wannan da wannan duk sun mutu banida matsala a yanzu tsakanina dasu, Munaya inason sanin alak'arsu da Mahaifina, wad'annan mutanen, domin sune mahaifina yay zama dasu ana gobe wannan ciwon zai sameshi, a daren ranar kuma Abie yashiga wajen mama Fulani domin gaisheta, jakadiya data masa rakkiya ta tabbatarmin da lallai yafito ransa a 6ace daga wajenta. Sannan a wannan ranar matarsa ta uku ce ta kawana a turakarsa, alhalin kuma kwannan matarsa ta biyuce, amma saboda kud'in data bama jakadiya da dad'in bakinta saita kaita turakar Abie a wannan daren, takuma sanarma matarsa ta biyu cewa takawa bashida lafiya yana fama da mura. kwana biyu kuma kafin faruwar dukkan wad'annan abubuwan Abie yayi zama Na musamman da Hakimansa saboda kama Wazirinsa da yayi Dacin amanar Masarauta wajen d'aukar sirrin cikinta ya bama wasu bak'in turawa da ba'asan dalilinsu na yin hakanba, a bincikena d'aya a cikin turawan ya Mutu, amma d'ayan yana nan da ransa. Abie ya kwanta jiyya da sati biyu aka kashe babban malaminsa, limamin masallacin sarki maikuma bama Abie shawara akan addini. dukkan wad'annan dana ambata miki sunayensu a kwai hotunansu anan d'akin, akwai abokin mahaifinki da kika fad'amin, shine Alhaji Mamman k'afur Wannan babban yaron Alhaji Lawan tanderu ne, dan wannan group sunema suka tsaya masa ya fito takarar shugaban k'asa, babbar matarsa k'anwar matar tanderu ce, wadda a gidan tanderun ta taso tun tana k'arama. Senetor halluru garba abokin Alhaji Mamman k'afur Ne sosai, akwai wani 6oyayyen sirrin dake tsakaninsu kuma, sai dai ban saniba ko Abbanki yasan wani Abu a ciki. Idan nace zan cigaba damiki bayanin sirrikan dake cikin d'akinnan kanki bazai iya d'auka ba Munaya, amma nabaki damar kimin kowace tambaya ni kuma zan baki amsarta batareda shamakiba”.
           Ajiyar zuciya Na sauke, Dan tabbasa kaina bazai iya d'aukar wannan bayanan nashiba inhar suka wuce zurfin haka, Na yink'ura zan mik'e, saiya matso ya taimaka min da kansa, zaman silifas d'ina Na gyara a k'afata, sannan Na taka ga wasu hotuna, hotona na nuna masa dana muftahu, yad'an murmusa yana ta6e baki, kafin ya ajiye cofin hannunsa ya hard'e hannayensa a k'irji, “Ba manufar wannan hoton ke d'inba, dan haka manta da wannan kawai, sai nan gaba watak'il zaki iya sanin wani abu”.
     Zanyi magana ya girgizamin kansa, alamar karnace komai.
      Idona na janye daga garesa kawai, na maida kan hoton Muftahu tareda nunashi da yatsa.
    Takowa yay har inda nake, ya kama hoton yana kallo tamkar yau ya fara saninsa, “Muftahu d'an uwa nane, kuma abokina, sai dai bakomai ne nake sakin jiki da Shiba, domin lokacin muna yara mutumne shi mai yawan k'arya, hakanne yasaka ko yaushe muke fad'a, babu abinda na tsana ga hallayar d'an Adam irin k'arya dacin amana, wannan halayyar tasa saita gaza barin zuciyata har girmanmu, kullum kallonsa nake bai canjaba, wannan yasakani fin yarda da harun fiye dashi, saikuma yake gwadamin wasu halaye na rashin gaskiya a lokuta da dama, ban k'ara tsinkewa da lamarinsa ba sai a time d'in da abinnan yafaru tsakanina da ke a birnin gayu, Muftahu shine Wanda yakawomin shawarar mizai hana na aureki ko ta wannan hanyar zansan wani Abu, da farko na d'ana masa tarkone, na yarda da auranki na shekara d'aya, yanda yacigaba da rawar jiki sai lamarinsa yacigaba da tsoratani, randa ya saka mana pill's a fresh milk daga ranar na yarda 100% shi maicin dunduniya tane, kuma akwai wani 6oyayyan al'amarin da yake son cimma buri, wannan yasakani kauda idanu a kansa, nabashi dukkan dama, dukda kullum Harun kan nusar dani illar hakan, amma na share komai tamkar bana gani, sai dai wannan zuwan danayi maganar da kika ta6amin a wani dare ya sakani cikin dogon nazari, daga time d'in kuma na saka idanuna akan Muftahu da Harun, zuwannan da nayi na k'arshe Nigeria, naga wani abin mamaki da ban al'ajabi. akwai wani d'aurin Aure da mai martaba yace mu wakilcesa ni da Hakeem (Wambai) amma sai Harun da Muftahu sukace zasumin rakiya, ba rakkiyarce ta sani Ankara a kansuba, yanayinsu ya nusar dani kowanne akwai manufarsa, ban kulaba mukaje muka halacci d'aurin auren, anatashi Hakeem yace shi zai wuce, Dan yanada wajen zuwa, banbi ta kansaba Dan bana d'aukar raini, karramawar da aka shirya yima mai martaba sai ta juye kaina, aka karramamu sosai, ni bammaci abincinba, sai Harun da Muftahu ne sukaci, suna tsaka da cin abincin sai aka kira Harun, bai d'aga wayar a gabanmu ba ya tashi ya fice, ko alama ban kawo komai a rainaba, muka cigaba da hira ni da Muftahu, abinda na lura da shi rabin hankalin Muftahu akan Harun yake, dan yanayinshi ya nuna, zuwa can sai shima ya mik'e ya fice, yacemin yana zuwa, fitarsa babu dad'ewa d'ayar wayar Harun tayi ring, ni mutumne dabai damu da shiga abinda babu ruwansa ba, amma a ranar saina tsinci kaina da duba wayar, bansan Number d'inba, amma nasan fuskar wadda take jikin hoton da Number ta bayyana, ba kowa bace face d'aya daga cikin matan Abie na”.
      “Matan Abie kuma?”.
      “kwarai kuwa, wannan shine abinda na gani, Wanda ya zaunamin a rai, koda Harun ya dawo yaga wayarsa kusa dani sainaga kamar baiji dad'iba, na bashi ina fad'in hajia ta kiraka, kinga kuwa yanda yanemi zubewa? humm saida Muftahu ya taimaka masa, dana tambayesa se cewa yayi wai tunkan mu taho dama kansa na ciwo, nasan ba haka baneba amma na sharesa. tunda muka taho na lura ana kallon kallo tsakanina Muftahu da Harun, kuma duk sanda hakan tafaru, Muftahu kanyi wani murmushi mai tattare da ma'anoni masu yawa, Wanda har yanzu nakasa fasarasu”.

       Huci na fidda daga bakina, na koma Inda na taso na kuma zama, shima saiya tako zuwa inda nake, ya durk'usa a gabana tare da d'ora hannayensa bisa Gwiwoyina, idanu na d'ago a hankali na sakasu cikin nashi, k'ok'arin janyewa na farayi, saboda wasu abubuwa danake hangowa cikin idanunsa. Amma saiya hanani wannan damar, yay wani sassanyan murmushi yana fad'in.............🤫✍🏼




     Barkanmu da dawowa sister's😄🤝🏻🥰🥰🥰.








*_ALLAH k'a gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*




Download Raina Kama Littafi Na Biyu